KRBBK: RDB3P001 Nana Haleema. #The Battle between love and marriage #Justice #Attack #Reward #Intense love. Baffa da sauri ya koma cikin gidan ya samu Saheer a zaune akan kujera ya dafe kansa cikin wani irin yanayi na damuwa da tashin hankali. Baffa ya yi turus, yadda ya ji Mmaa tana ƙwalla ihu ya yi tunanin suma ya yi, amma sai ya gansa a zaune ya dafe kansa da duka hannayensa. Ya ƙaraso lokacin da Mama take magana cikin faɗa tana cewa, "ƴar gwal ce? Tunda ta zaɓi kuɗi a kan halacci ba sai a ƙyale ta ba? Ita kaɗai ce mace a duniya da za ka kashe kanka saboda ita?. Daga hannun masu garkuwa da mutane ka fito, har yanzu jikinka bai yi daidai ba, in ka kashe kan ka kanka ka yiwa asara ba ita ba, ita ta yi aure a gidan masu kuɗi, ta bar ka a nan cikin tunanin banza da wofi. Ka manta da ita, domin ita matar aure ce a yanzu, ka raini lafiyar jikinka." A lokacin Baffa ya dafa kafadarsa, Saheer ya ɗago jajayen idanunsa ya kalli Baffa, sai ya riƙe hannun Baffa, muryarsa tana rawa sosai ya ce, "Baffa da gaske ta yi aure?." Baffa ya yi ajiyar zuciya cikin dubun tausayin Saheer ya riƙe hannunsa ya ce, "ta so mu je ciki." A hankali ya miƙe tsaye yana ji zuciyarsa tana bugawa kamar zata faɗo daga ƙirjinsa, jiri yana ɗaukarsa kamar zai kifa da kansa. Baffa ya riƙe hannunsa sannan ya juyo ya kalli su Mama ya ce, "kar wanda ya biyo bayan mu" ya faɗa yana kallonsu sannan ya ja hannunsa suka tafi ciki. Mama ta bi su da kallo sannan ta yi dariya ta ce, "ai na faɗa daman, indai ina da rai wallahi wallahi bazai auri wannan yarinyar mai buɗaɗɗen ido ba. Ko asalin yarinya ba mu sani ba mu haɗa jini da ita..? Sai dai in bana raye wallahi." Ita dai Adda bata ce komai ba, tausayin Saheer ya mamaye mata zuciya cikin tsananin tashin hankali. Hanan ce take biyewa Mama sannan suka shiga ciki. Baffa akan kujera ya zaunar dashi, ya ɗauko masa ruwa ya miƙa masa. Saheer ya karɓa ba tare da ya sha ba, ya bi Baffa da kallo har ya zauna a kusa da shi. Baffa ganin irin kallon da Saheer yake yi masa ya saka ya ce, "ka sha ruwan Saheer." Ya girgiza kai ya ce, "Bazan iya ba Baffa. Don Allah ka sanar da ni abinda yake faruwa, na kasa gasgata abinda na gani, na kasa yarda da abinda kunnuwana suka ji. Mafarki nake yi ko a zahiri ne ni na kasa ganewa, abu ɗaya nake so na tabbatar, da gaske Islaha ta auri wani ko wasa ake yi min?." Baffa ya sauke numfashi cikin tausayin ɗansa, ya san Saheer yana matuƙar ƙaunar Islaha, yana sonta so na zahiri kuma na gaskiya, yana yi mata so na aure, yana so ya ɗauke ta ya katange ta a cikin inuwarsa a matsayin matarsa. Ya so ta tun tana gidan marayu, son da yake yi mata ne ya saka shi ɗauko ta ya kawo ta gidansu, ya cigaba da ɗaukar ɗawainiyarta a matsayin Yayanta kuma mijinta na gobe. Bayan Saheer, in akwai mai son aurensa da Islaha to shine, zai iya cewa ya fi Saheer ɗin murna in ya auri Islaha, saboda ƙaunar da yake yi mata da yadda ya yaba da ɗabi'unta. Shiyasa ya so ya aura masa ita da wuri-wuri, dan bai ɗauki maganar Zulaiha a bakin komai ba, sai tatsuniya. Sai dai kash! Bazai taɓa bari auren ya kasance ba, bazai bar auren ya ba, dan faruwar auren ba ƙaramin masifa bace ga shi kansa da Islahan. Hukuncin da ya yanke shine yake ganin shine daidai, amma ya san ya yi breaking ɗinsu shi da ita, ya cutar da rayuwarsu shi da ita, dan dukkansu suna son juna kuma suna burin auren juna. Amma ya zai yi? Hakan shine ya zama zaɓi da mafita a gare su, hakan da ya yi shine yake ganin ya dace da Saheer da ita kanta Islahan. Tunda ya ke yi mata addu'a akan Allah ya zaɓa mata miji na gari, kuma Allah ya zaɓa mata Rehaan, sai yake ji a ransa Rehaan shine miji na gari a gare ta ba Saheer ba. Baffa cikin sanyin murya ya ce, "Saheer!." Saheer da ruwa ya taru a idanunsa, ya ɗago ya kalli Baffa yana jira ya ji me zai ce. Baffa ya bi sa da kallo tausayi sannan ya ce, "Da gaske ne." Saheer muryarsa tana cracking ya ce, "Da gaske ne me Baffa?." Baffa ya zuba masa ido cikin tsananin tausayinsa sannan ya ce, "Da gaske Islaha ta yi aure, tana hanyar zuwa gidan mijinta." Runtse ido ya yi jin maganar ta da ki zuciyarsa, ta ratsa jijiya da tsoka da ƙasususan jikinsa. Ƙwaawalwarsa ta harba da ƙarfi, ya ja numfashi da ƙarfi yana saukewa a wahalce yana jin zufa tana tsatstsafo masa daga ko ina na jikinsa. Har bayan rigarsa ya jiƙe saboda tashin hankali, goshinsa ya tsatstsafo da gumi yana ɗiga a gaban rigarsa. Baffa dai kallonsa yake yi cikin tsananin tausayinsa da jin nauyinsa. Allah ya sani ba haka ya yi niya ba, bai yi niyar cutar da ɗansa na cikinsa ba, amma ƙarshe aka kai shi shiyasa ya yi haka. Yana so ya samarwa da Islaha rayuwa mai inganci ne shiyasa ya amince, yana so ta gina kanta akan burukan da suke cikin ranta, ba ya so rayuwarta ta cigaba kasancewa cikin maraici da ƙasƙanci kamar yadda take ciki yanzu. "Baffa....." Sai ya kasa ƙarasawa yana kallon Baffa bakinsa yana rawa sosai amma ya kasa magana. Daƙyar ya ce, "Mafarki......" "Na ke yi......" "Ko?." Ya faɗa a rarrabe cikin yanayi mai wahalar fassarawa, wanda shi kaɗai ya san girgiɗin da zuciyarsa take yi, buri yake yi kunnensa ya ji Baffa ya ce mafarki ne ba gaskiya bane. Baffa ya ce, "Ba mafarki bane, da gaske ne Saheer." "Hasbunallahu wani'imal wakil!" Ya faɗa yana runtse idanunsa tare da jingina da kujera. Baffa ya sunkuyar da kansa ya kasa haɗa ido da gudan jinin nasa. Jin sautin kuka ya saka Baffa ya ɗago kansa ya kalli Saheer, ga mamakinsa kuka Saheer yake yi sosai, ya duƙa a gabansa ya ɗora kansa a jikin Baffa yana kuka da yake fita da sauti. Baffa sai ya ji kamar ya ta ya shi kukan, zuciyarsa ta karye ya ɗora hannunsa a kansa ya ce, "ka yi haƙuri Saheer, ban yanke mu ku wannan hukuncin dan na jefa ɗayan ku a cikin wannan yanayin ba. Itama yanayin da ta shiga kenan da a lokacin da sanar mata da maganar, ta shiga gigicewa fiye da tunanin ka. Ni kuma na yi haka ne saboda bana so rayuwar Islaha ta cigaba da zama jiya e yau, tana buƙatar cigaba. Kai ka san ina son auren ku da ita, tunda ka ga na aikata hakan ka san ina da hujja mai ƙarfi. Ban yi dan na raba ku ta ƙarfi da yaji ba, na yi ne dan hakan shine masalaha a gare ka da ita kanta. Wallahi in dai babar ka tana raye, baza ta taɓa bari auren nan ya yu ba." Saheer ba ya iya fahimtar abinda Baffa yake faɗa, abinda yake hange kawai Islaha ta yi aure tana kan hanyar zuwa gidan wani a matsayin matarsa, shi kaɗai yake yi masa amsa kuwa a kunnensa, ya kasa daina jin maganar a kunnensa tana ratsa jinin jikinsa. A lokacin Sadik ya shigo da sallama Baffa ya amsa ya ce, "ƙaraso Sadik, zo ka rarrashi ɗan uwanka akan laifin da na yi masa." Sadik ya tako a sukwane zuwa inda Saheeer yake cikin tausayi, dan ko shi ba Saheer ba, sai yanzu yake jin zafi da haushin auren da Islaha ta yi. Duk da shi ya san dalilin auren, amma ya kasa amfani da sanin nasa, yana jin zafin auren, yana kuma ta ya abokinsa kishi mai yawa. Ya riƙo Saheer ya miƙe zaune, Baffa ya bisa da kallo ganin yadda fuskarsa ta yi ja, idanunsa sun yi ja sosai kuma sun kumbura, ga shi daman ba shi da lafiya, har lokacin jikinsa bai dawo daidai daga azabar da ya sha a hannun masu garkuwa da mutane ba. Baffa ya ce, "Sadik ku je ɗaki ya huta, zamu yi magana. Yanzu ba ya fahimtar abinda nake faɗa masa." Sadik a sanyaye cikin raumi ya ce, "To Baffa. Saheer ta so mu je, magrib tana yi." Saheer kamar bai ji ba yana dai zaune ya rufe idonsa ya kasa motsi. Sadik ya ɗan yi gapping shoulder ɗinsa ya ce, "Tashi mu je." A lokacin ya buɗe idanunsa ya kalli Sadik, kamar zai yi magana sai ya rufe bakinsa, dan harshensa ya sarƙe bazai iya furta komai ba, miƙe daƙyar suka fita zuwa ɗakinsa. Baffa ya bi sa da kallo cikin tausayi, amma har lokacin ba ya danasanin aurar da Islaha a inda zata samu abinda zata gina rayuwarta yadda take so.      Saheer a gefen gadonsa ya zauna, sai kuma ya cire riga ya ajjiye a gefe yana jan numfashi daƙyar kamar mai cutar sarƙewar numfashi. Sadik ya zauna a gefensa yana kallon yadda ya rame, ga tabon dukan da ya ci a hannun masu garkuwa da mutane nan caɓa-caɓa a jikinsa, ga cizon ƙwarukan da bai san ya suke ba, har lokacin jikinsa da dauɗa bata gama fita ba. Ɗakin ya yi shiru babu mai magana a cikinsu, sai numfashin da Saheer yake saukewa a hankali kamar wanda ya yi gudu, zuciyarsa tana bugawa a guje, har yana jin sautinta a kunnesa. Sun jima a haka kafim Saheer ya yi breaking silence ɗin ya ce, "Kai ma ka san ta yi auren?." Sadik ya ɗan lumshe ido ya buɗe, ya ɗago ido ya kalle sa ya ce, "Ka bari ka samu lafiya sai mu yi maganar, za ka fahimta in sha Allah." "Kai ma ka san ta yi aure!?" Ya tambaya cikin tsawa yana kallonsa. Sadik ya kalle sa dan ya san ba ya cikin hayyacinsa, ta ɗaga masa kai ce, "Na sani, shiyasa....." Cikin ɗaga murya ya ce, "Shiyasa me! Shiyasa za ka ce min na bari za ka yi min bayani ko? To bayanin me zaka yi min, me ka ke so na sani wanda ban sani ba?." Sai kuma muryarsa ta yi ƙasa yana kallon idanun Sadik da jajayen idanunsa ya ce, "Aure fa ta yi, ba aiki ta tafi kamar wancan lokacin ba, ba sace ta aka yi ba, wani namijin ta aura har ta tafi gidansa zata tare. Kuma ka san da wannan maganar ka ɓoye min, Meyasa haka Sadik?." Sadik ya ce, "na faɗa maka zan yi maka bayani, amma na yanzu." Ya wara hannayensa ya ce, "bayanin me, me za ka faɗa min wanda ban gani ba? Ko za ka ce min auren ma haɗawa ta yi ba na gaskiya bane?." Sadik ya kasa magana ya yi shiru, Saheer ya girgiza cikin wani irin yanayi ya girgiza kai ya ce, "Islaha! Islaha!! Islaha!!!." Sai ya runtse ido ya kwanta da baya yana ji ina ma kawai ya suma ya huta, yadda yake jin azaba a ƙirjinsa so yake kawai ya suma, yadda zai daina fahimtar komai ko zai samu sassaucin raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa. Sadik cike da tausayinsa ya ce, "Islaha bata yi komai ba, bata cutar da kai ba, wallahi bata yaudare ka ba, komai ta yi shi ne saboda kai!." Saheer ya buɗe ido ya kalle sa, kamar ya ji me ya ce sai kuma idanunsa suka rufe ruf, daga nan ya daina jin abinda Sadik ɗin yake faɗa gabaɗaya. Islaha har suka yi nisa bata daina kallon gidan tana hawaye ba, ta sauke numfashi mai ƙarfi ta sunkuyar da kai hawaye na bin kuncinta. _i don't wanna go, but baby we both know, this is not our time, it's time to say goodbye, until we meet again, cause this is not the end, it will come a day, when we will find our way. Voilins playin and the angels crying when the stars align, then i will be there. No i don't care about them all, cause all I want is to be loved, And all I care about is you, you're stuck on me like a tattoo, no I don't care about the pain, I'll walk through fire and through rain just to get closer to you, you're stuck on me like a tattoo, I'm letting my hair down I'm takin' it cool You got my heart in your hand._ Waƙar tatto kenan da take tashi a motar kaɗan-kaɗan, ga wani sanyi da ƙhamshin turare da motar take yi mai tsayawa a rai. Islaha ta yi tana jin waƙar na shiga jikinta har tsigar jikinta tana tashi, sai take ji kamar dan ita da Hamma akayi verse, musamman inda aka ce this is not the end, sai take tabbatarwa da kanta wannan tafiyar ba itace ƙarshen rabuwar ta da Hamma, akwai wata haɗuwar a gaba. Ta rufe idanunta da suke ciwo saboda kuka ta ce, "this is not the end, zan dawo, wallahi zan dawo. Ni ƴar halak ce, duk in da naje zan dawo gare ka Hamma!" Ta faɗa tana curewa waje ɗaya zuciyarta tana yi mata zafin kewa da ƙauna da tunanin ta cutar da masoyinta... Safeera ta juyo ta kalle ta, ta ga idanunta a kulle ta ɗauke kai tana sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba. Jazy dai bai nuna komai ba, tafiya yake yi a hankali yana kallon gabansa babu wanda ya sake yiwa magana har suka je gidan. Safeera kallon gidan take yi kawai, ta girgiza kai dan bata da tabbacin inda aka zo, gidansu ne ko kuma gidan Islahan ne bata sani ba. Lokacin aka buɗe gate ya shiga da motar ciki, ta fara ganin mutane ƴan biki ana ta shiga da fita, kasancewar gidan babba ne baza ka ce ma biki ake yi ba, sai dai ka ga wata ta wuce wata ta sake wucewa. Har bakin apartment ɗin Mamy ya kai motar, dan ya san yadda al'adar fulani take wajan uwar miji ake fara kai amarya. Yana tsayar da motar ya kalli Islaha ta mirror ya ga fuskar ta a buɗe ta jinginar da kanta a jikin kujera, ya yi dariya a zuciyarsa yana mamakin wannan amarya mai buɗaɗɗiyar fuska, ko kukan ma ta daina. Ya buɗe motar ya fita bai ce komai ba Yana fita Safeera ta juyo ta ce, "Islaha meye haka? Don Allah ki kulle fuskar ki, hakan ba al'ada bane, Mama don Allah ki yi mata magana." A lokacin Atika ta ce, "Islaha ki rufe fuskar ki, kar ki saka a tafi da mu a baki." Kamar baza ta yi ba, sai kuma ta ja mayafin ta rufe fuskar ta har lokacin bata buɗe ido ba. Shi kuwa Jazy ganin gidan shiru a nan ya tabbatar da duk suna ciki ana event ɗin mother eve kamar yadda aka ce za a yi. Har zai shiga wajan Mamy ya ji ana kiran sa. Ya waiwayo ganin Mama sai ya saka ya tsaya cak, ta ƙaraso ta ce, "Amaryar ce?." Ya ɗaga kai ya ce, "Itace." "Kuma sai ka bar ta a mota? Buɗe ta fito mana." "Daman ina so na tabbatar in Mamy tana ciki ne." "Ai wajan Daada za a kai ta ba wajan Nadira ba, buɗe su fito." Bai ce komai ba ya buɗe motar ya ce, "bismillah." Safeera ta kalli Islaha da kamar bata ji me aka ce ba ta ce, "Islaha mu je." Ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba, Mama Atika ta fita Safeera ta ce, "Don Allah mu je." Kafin ta yi wani motsi Mama ta buɗe ɓangaren da Islaha take, cikin fara'a da sakin fuska ta ce, "Bismillah mana ɗiyata, ya za ki zauna a mota haka kamar ba gidan ku ba? Fito mu je ciki, ana ta zaman jiran zuwan ki." Islaha ta kalli Mama ta cikin mayafin da ta rufe fuska, ta ji Mama ta riƙo hannunta dole ta motsa ta fito daga motar ba dan tana so ba. Mama ta kalli Atika ta ce, "sannun ku da zuwa. Ku yi haƙuri, muna ta biki ne a ciki, shiyasa ba a yi mu ku tarba mai kyau ba." Mama Atika ta ji daɗin yadda Mma ta tarbesu da sakin fuska sai ta ce, "Babu komai, hakan ma mun gode." "A dai yi shiru kawai, amma ba haka muka so ba. Ina sauran mutanen kawo amaryar?." "Mu ke nan." Ta wara ido ta ce, "ku biyu? Amaryar Rehaan guda, ace mutum biyu ne suka yi rakiya?." Mama Atika ta ce, "Baffa ta ne ya ce ba ya son taron mutane.” Mama ta yi murmushi ta ce, "Allah sarki, Mu je." Har lokacin tana riƙe da hannun Islaha da ya ɗaukar ɗumi saboda tension. Daada tunda ta hango su ta kasa rufe baki saboda murna, har suka ƙarasa aka zaunar da Islaha a kusa da ita. Daada ta dafa kanta ta ce, "barka da shigowa dangina, barka da zuwa yarinyar albarka, sannun ku da hanya." Ta ɗago ta kalli su Safeera ta ce, "ku zauna mana, sannun ku da zuwa. Sadikka a kawo musu ruwa da abinci." Mama ta ɗaga kai ta fita. Safeera suka gaisa da Daada sannan ta ce, "Sallah zan yi." Daada ta sake jin daɗi ganin dangin Islaha sun fara da sallah daga zuwansu cikin gidan, cikin jin daɗi ta ce, "ga banɗaki nan." Safeera ta miƙe ta shiga ta yi alwala. Islaha a lokacin ta motsa kamar zata miƙe, Daada tana riƙe da ita ta ce, "ya dai ishlaya?." Islaha duk da bata cikin farin ciki sai da ta yi murmushi jin sunan da Daada ta faɗa, a hankali ta ce, "Zan yi sallah." Daada hakan ya sake yi mata daɗi, ta sake washe baki ƙaunar Islaha tana gudu a jininta ta ce, "to tashi mana, tashi ma za ki yi sallah. Ɗiyar albarka kenan, ranar da ta shigo gidan mijinta da sallah ta fara." Islaha ta miƙe ta shiga inda Safeera ta shiga domin yin alwala. Tana shiga Daada ta kalli Mama Atika ta ce, "Yarinyar ku ɗiyar albarka ce, ba dai tarbiyya ba." Ta yi murmushi ta ce, "ba yabon kai ba, amma Islaha ba daga nan ba kam." Daada ta sake jin daɗi, a lokacin Mama ta shigo da masu aiki aka zube musu kayan ciye ciye da na sha. Daada ta kalli Mama ta ce, "Ina Nadira take?." Mama ta ce, "suna wajan biki." Daada ta haɗe rai ta ce, "aje a tashi wajen bikin yanzu nan, sannan a sanarwa kowa ya hallara a wajan nan." Mama ta ce, "to." Ta faɗa tana fita dan cika umarnin Daada. Nana Haleema. RDB3P002 Nana Haleema. A lokacin Islaha ta fito daga yin alwala tana dafa bango saboda ciwon kai, ta tayar da sallah bata kalli kowa ba. Tana cikin sallah ta ji mutane suna ta shigowa, ta ja mayafi ta rufe fuskar ta dan Allah ya sani bata son ganin kowa, jiri take ji daƙyar ta iya sallar magrib a tsaye, magani take so ta sha ko zata ji daɗi, sannan ta kira Sadik ta ji ya Hamma yake. Ta ja sallar ta yi tsaho da gangan, taƙi idarwa tana sane dan bata so ayi mata wata magana ko kaɗan. Daƙyar ta idar, ta zauna bata juyo ba dan bata san adadin mutanen da suka shigo ba. Muryar Mama ta ji ta ce, "Amarya in kin idar duk ke ake jira." Gaban Islaha ya yanke ya faɗi, ta runtse ido ta sake jan mayafin ta rufe fuska sannan ta juyo a hankali. Mama ta ce, "Amarya tasowa za ki yi ki dawo kusa da Daada." Daada tana murmushi ta ce, "kema kin san ba iyawa zata yi ba, ki taimaka mata ta dawo nan ɗin." Mama ta ƙarasa wajan Islaha ta riƙo hannunta, ta miƙar da ita suka dawo tsakiyar falon Islaha ta zauna tana kallon mutane ta mayafinta, kowa ya zuba mata ido kuma dukkan su mata ne. A hankali ta zauna kowa na falon kallon ta yake yi, musamman Janan da Ikram da Nana da kuma Banisha da sauran ƴan uwansa mata. Daada ta ce, "Sadikka a buɗe mana taron da addu'a." Mama ta yi addu'a kamar yadda ta saka ta, sannan Daada ta ce, "za a yi buɗan kai, ina Nadira?." Mamy tana zaune bata ce komai ba, baza ka ce ma tana wajen ba, kallon Islaha kawai take yi tana ji ranta yana ɓaci sosai. Jin Daada ta neme ta sai ta ɗago a hankali fuskar ta babu walwala ta ce, "Gani nan." Mama ta kalli Mamy ta ce, "ki ƙaraso." Mamy ta miƙe ta ƙaraso ta zauna daf da Islaha. Daada ta kalli Mama Atika ta ce, "za mu siyi fuskar amarya." Mama Atika ta yi dariya ta ce, "ai ta ku ce yanzu." Daada ta ce, "daman yanzu ai ƴar gida ce." Daada ta juya ta ɗauko wata cover ta buɗe kowa ya ga ƙatuwar sarƙar gold mai nauyi da kauri sosai ta ce, "na siyi fuskar amarya da wannan." Mama ce kaɗai a cikin mutanen parlour ta ce, "Ma sha Allah! Amaryar Rehaan ta cancani haka" Bayan ita kowa ɗuf ya yi, babu wanda ya nuna jin daɗinsa a kan bajintar da Daada ta yi, sai masu aikin gidan da suke san barka suna guɗa. Mama Atika ta murmusa ta ce, "Amarya ta gode sosai." Mamy kamar baza ta yi magana ba, ganin irin kallon da Daada take yi mata ya saka ta ɗan motsa baki kamar zata yi magana ba dan ta san me sata ce ba, dan ita bata shiryawa wani buɗan kai ba, dan ta manta da wannan culture ɗin. Sai Sanah Yayarta da take wajan ta ce, "Mahaifiyar Rehaan, gata nan a zaune" ta faɗa tana nuna Mamy. Safeera da Mama Atika suka bita da kallo, fuskar ta gabaɗaya ba a sake take ba, ta haɗe rai kana kallon ta zaka fassara yadda ta ɗauki auren ba sai ta buɗe baki ba. Sanah cikin hausar ta da bata wani fita sosai ta ce, "ta siyi fuskar amarya da wannan" ta faɗa tana miƙewa a ƙarasa a hankali ta ajjiye basket ɗin kaba wanda aka yi masa ado mai kyau. Daada ta kalli Mama ta ce, "buɗe." Mama daman jira take ace ta buɗe dan ta ga abinda aka ɓoye a ciki, ta buɗe ta ɗauko rafar ƴan dubu dubu goma, sai awarwaron gold da zobe, da kuma english gold mai kyau, sai turare babba a cikin cover ɗinsa. Sai turaren wuta, da turaren ɗaki. Masu aikin gidan da suke wajan suka saki guɗa mai ƙarfi, ana ta san barka dan kyautar Mamy ta yi. Ita dai Mamy kallon Yayarta ta yi kawai, dan ta san aikinta ne, ita bata yi wani shirin komai ba, dan ta manta shaf da wannan abun nasu. Mama da take gefe ta ce, "Nima na siyi fuskar amarya da wannan." Ta faɗa tana ɗauko leda a bayanta aka cire luxury lace, kai da ka gansa ba sai ance mata ya haura million ba, kallo ɗaya zka yi masa ka san tsadarsa. Aka sake yin guɗa a falon cikin murna, Umma dai bata shiryawa komai ba, amma ganin kishiyar ta yi sai ta ce, "Akwai kyautar turaren wuta da na saka a yiwa amarya daga ƙasar larabawa basu ƙaraso ba, amma za a kawowa amarya a har ɗakinta." Amaryar Abba dai bata ce komai ba, dan ita bata yi niya ba. Daada ta kalli Mama Atika da ake ta ajjiye mata mata kaya a gabantq ta ce, "Yanzu za mu iya gamin fuskar amarya?." Ta yi murmushi ta ce, "a guje, an ba ku dama." Daada ta gyara zaman glasses ɗinta ta ce, "Ina Banisha?." Banisha ta taso Daada ta ce, "zo ki buɗe mana fuskarta, sannan ki zaɓa mata suna." Banisha ta zo kusa da Islaha da ko motsin kirki bata yi, tana zuwa ta fara leƙa mayafin suka haɗa ido da Islaha, ta yi murmushi itama dai Islahan ta yi murmushi dan ta gane fuskar ta. A hankali Banisha ta ce, "ya sunan ki?." Islaha a hanlali ta ce, "Islaha." Banisha ta ɗago ta buɗe fuskar sannan ta ce, "i chose Islam, as her new cultural name Daada ta harare ta ta ce, "dallah can iyayen iyayi, ku duk abinda aka haɗa da ƴan ɗakin ku sai kun yiwa mutane iyayin banza da wofi. In za ki yi hausa ki yi hausa, waye yake jin yaren da ki ka yi magana?. Kin ga na yi kama da ba'indiya?." Banisha ta turo baki ta ce, "na zaɓa mata suna, Islam." A take waje ya ruɗe da guɗa, Daada tana ta saka mata albarka. Islaha ta yi ƙasa da kai taƙi ɗagowa Mama ta ce, "tunda mun siyi fuska ya kamata a ɗago ko?." Islaha bata ɗago ba, sai sake sauke kanta ƙasa da ta yi tana wasa da abin hannun da Hammanta ya bata. Duk da ciwo kanta yake yi sosai, ta shanye ciwon saboda kar ta ɗago. Daada ta bita da kallo tana murmushi sannan ta ce, "Kunya take ji, kun san jinin fulani ba dai kunya ba." Mamy dai tana zaune bata ce komai ba, Daada ta fara yi mata nasihar zaman aure ita duk ba ji take yi ba. Sai da Daada ta gama sannan ta kalli Mamy ta ce, "baza ki ce komai ba?." Sai a lokacin Mamy ta buɗe baki kamar bata so ta ce, "Allah ya saka albarka." Duk mutanen ɗakin suka amsa da amin. Daada tana murmushi ta ce, "A rakata ɓangarenta ta huta" ta kalli su Safeera ta ce, "ga wannan na masu rakiya ne" ta faɗa tana basu ƙatuwar jaka cike da kaya da kuɗi. Su Mama Atika suka yi godiya suka miƙe dan raka Islaha ɓangaren ta. Kowa ya bita da kallo dan duk so suke su ga fuskar Islaha da ta ƙi ɗagowa. A hankali ta ɗan waigo suka haɗa ido da wata mata da take kusa da Mamy, ta janye idanunta sai suka haɗa ido da Mamy. Ta ɗauke kai da sauri dan ko ba a faɗa mata ba ta san itace mahaifiyarsa, yanayinta ya gwada hakan ba sai an yi maka dogon bayani. Ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ta shiga tunanin a ina ma ta san fuskar amma ta kasa tunawa. Ta ja mayafin ta sake rufe fuskar ta, a lokacin aka tashi dan rakata inda zata zauna, ita dai tana kusa da Safeera tana tafiya kamar bata so. Banisha ce ta buɗe ƙofar falon, suka shiga a hankali aka zaunar da ita a falon Rehaan na downstairs. Sanah Yayar Mamy ita ta zaunar da ita sannna ta ce, "amarya nan ne ɓangaren ki" ta faɗa cikin hausar ta da bata fita yadda ya kamata. Bata ce komai ba ita dai ta zauna ɗin kawai, idanunta yana kan hannunta tana kallon hannunta. Kowa ya fita daga apartment ɗin falon ya rage daga ita sai Safeera da Mama Atika. Safeera sai da kowa ya fita sannan ta ce, "Islaha kinga girman falon nan kuwa?." Islaha ta yi tsaki ta murguɗa baki bata ma buɗe fuska, sai kuma ta dafe kanta da hananyenta dan ciwo yake yi mata sosai. Tana ji su Mama Atika suna ta yabon kirki Daada da Mama, ita dai bata ce komai ba dan ta ƙi buɗe fuskarta, Allah kaɗai ya san me take ji, Allah kaɗai ya san me zuciyarta take yi. Har ɓangaren aka kawo musu abinci, a nan suka saki jiki suka ci suka sha. Islaha ta kalli Safeera sannan ta buɗe fuska ta ce, "bani wayata." Safeera ta bata wayar ta karɓa ta kira Sadik amma bai ɗauka ba, sai ta kira Hamma shima bai ɗauka ba, ta yi tsaki ta ajjiye wayar ta ce, "Zazzaɓi nake ji, kaina kamar zai rabe biyu." Mama Atika ta ce, "Ai dole, wanann kukan da ki ka sha ai dole ki yi ciwon kai. Sai kin yi bacci sannan za ki ji daɗi, dan fuskar ki ta kumbura sosai." Safeera ta ce, "Ni tsoro nake ji kar ta samu attack, kuka kamar an kunna fanfo?." Mama Atika ta ce, "Ita kaɗai ta san me take ji. Islaha ga kyautar ki, a ina za a ajjiye miki?." Islaha daƙyar ta ce, "ku je dasu, Safeera ta ajjiye a wajenta." Safeera ta buɗe ido ta ce, "wa, ni Safeera ni zan kai wannan dukiyar gidan mu? Haka kawai a shigo a yanka min wuya Ki ajjiye abin ki, ni wallahi bazan ɗauka ba" ta faɗa tana miƙewa a lokacin Banisha da Janan da Ikram suka dawo. Janan ba yabo babu fallasa ta ce, "Amarya mu je mu nuna miki bedroom ɗin ki." Islaha ta kalle su duk suka haɗa ido dan fuskar ta a buɗe take. Ganin babu wani mai sakakkiyar fuska a tare dasu sai ta sake kama kanta. Ikram wani irin abu ta ji ya tsaya mata rai, kishi ya taso mata ganin wai matar Rehaan ce a zaune a gabanta. Islaha ta ƙi miƙewa balle ta bi bayansu, yadda fuskarsu take a ɗaure in suka raina mata hankali tsaf zata mare su, zuciyarta a kusa take, baza ta juri raini daga wajen na ƙasa da ita ba. Safeera ganin yanayin ƙawar ta ta sai ta ce, "Bata jin daɗi, mu je ku nuna min." Suka wuce sama Safeera ta bi bayansu, basu jima ba suka sakko suka fita. Sai da suka fita sannan Safeera ta koma saman ta saka mata kayan da aka bata a ɗakin sanann ta sakko ta ce, "mu je na raka ki saman." Zata yi musuSafeera ta ce, "Dob Allah mu je." Islaha ta miƙe suka hau saman sannan ta ce, "ki daina wanann halin a gaban Mama, ita bata san komai ba." Islaha ta yi mata banza Safeera ta ce, "Kai amma ɓangaren nan ba dai kyau ba, kamar a aljanna." Islaha tsaki ta yi tana so ta nemi hanyar kushe apartment amma ta gaza, dan duk hassadar ta ƙarya take yi ta ce bai yi kyau ba. A haka suka shiga falon saman, suka fara haɗa ido ƙaton hotonsa yake jikin bango, Islaha ta kalli hoton ta ja tsaki sannan suka shiga ɗakin. Safeera ta ce, "gaskiya ke kam Allah ya taimake ki....." bata ƙarasa ba Islaha ta wani kalle ta, Safeera ta toshe baki tana dariya. Safeera ta ce, "ga kayan ki nan a nan, ga handbag ɗin ki, ga charge ki da kyautar ki. Nima na samu kuɗin siyan iphone 17, wannan kuɗin da aka bamu ai gaba ta kai ni wallahi." Islaha bata ce komai ba, ta zauna tana sake kiran wayar Sadik. Safeera ta ce, "Islaha wai me ki ke yi da waya?." "Hamma nake kira." "Ki bari sai gobe." "Yanzu nake so na san halin da yake ciki." "Shikenan, to mu zamu wuce." Islaha ta miƙe ta ce, “Mu je wajen Maman.” Tare suka sake sakkowa, ta rako su har bakin ƙofa, ganin zasu fita su barta sai ta sake fashewa da kuka. Safeera da ta fahimci kukan na meye sai ta rungumeta ta itama ta rungume ta suna kuka duka su biyun. Mama Atika ta ce, "Safeera ki daina kuka, in kina kuka baza ta daina ba, kina jin yadda jikinta ya yi zafi saboda zazzaɓi." Safeera ta raba kanta da ita ta ce, "Ki bar kuka Islaha, zamu yi waya." Islaha ta ce, "Don Allah ki dawo nan mu zauna." Safeera ta yi murmushi kawai, daƙyar dai suka rabu, aka nuna musu su a mota da kyautar da aka basu suka tafu aka bar Islaha. Mamy tana shiga apartment ɗinta ƙawarta ta riƙe hanmunta ta ce, "wai ba ki gane yarinyar nan ba?." Mamy ta ce, "Kamar na santa, amma daman ance ƴar jarida ce, maybe a aikinta na santa.” "Ba batun ƴar jarida ba. Ina yarinyar da ta yi mana rashin kunya asibiti, lokacin da ki ka bar  atm card ɗin ki a asibitin Rehaan?." Mamy ta buɗe ido ta ce, "tabbas itace, itace ta dinga yi miki rashin kunya ko?." "Kuma itace ɓarauniyar atm card ɗin ki." "aka ɗauko min as daughter inlaw?." "Wallahi an cutar dake, kar ki yarda da ita, ki saka shi ya warware auren nan kawai. In aka nuna wanann a matsayin sirikar ki kunya zamu ji sosai, ki san abinda za ki yi." Mamy daman haushi take ji a ranta, ga zuciyar ta babu daɗi gabaɗaya hakan ya saka ta ce, "bara Rehaan ya zo, bazan zauna da yarinya irin wannan matsayin sirikata ba....... Nana Haleema. RDB3P003 Nana Haleema. Jazy tunda ya saka a mayar da su Safeera gida ya tafi inda ya san Ray yana can. Kamar yadda ya yi tunani kam yana zaune yana amsa waya, Jazy ya yi tsaki dan in ya fara waya akan kasuwanci nan sai a kwashe awa biyu yana yin abu ɗaya. Jazy ya zauna yana sauke numfashi sai kuma ya ɗauki wayarsa yana kallon kyawawan hotunan matarsa. Ya yi murmushi yana pecking wayar kafin ya kira ta su yi waya kafin ya gama wahalalliyar wayar nan taasa. Har ta gama ringing bata ɗauka ba, ya ajjiye wayar yana yana kallon Rehaan, sai kuma ya yi tsaki a lokacin da Rehaan ya yanke wayar. Suna haɗa ido Jazy ya ce, "Ni fa gabaɗaya ba a kyauta min ba, kawai an ɗaga kai min mata sai gobe. Goben ma ance wai sai an yi ajo da buɗan kai, gaskiya ban ji daɗi ba." Rehaan ya taɓe baki baice komai ba Jazy ya kalle sa ya ce, "Abba ya ce yana kiran ka ba ya samu, nima na kira ka ta ƙi shiga, sai kuma yanzu da na zo na ga kana waya. Blocking ɗinmu ka yi ko?." Ya ɗora ƙafa kan ɗaya sannan ya harɗe hannunsa waje ɗaya ya ce, "bana son takura ne." "Har Abban takura maka zai yi kenan?." Bai ce komai ba dan bashi da wannan amsar Jazy ya ce, "na kai matar ka gidanta lafiya lau. Amma gaskiya tana son saurayin nan nata, shima kuma yana sonta....." Ya dakata yana kallon Rehaan sannan ya cigaba da magana ya ce,"haka kawai ka raba masoya, suna ƙaunar junansu ka farrraƙa musu soyayya, ka dinga jin tsoron Allah." Nan ma Rehaam bai tanka ba ya kalli wayarsa daidai lokacin da kiran Abba ya shigo amma shi Abba bazai san ta shiga ba. Bayan ta katse Abba ya kira Jazy, Jazy ya kalli Rehaan ya ce, "ka saka waya a dnd ga Abba yana kirana." Jazy ya saka wayar a speaker Abba ya ce, "Jafar kuna tare da Rehaan?." Jafar ya kalli Rehaan ya ɗan girgiza masa kai alamun kar ya ce suna tare, Jazy ya ce, "Ba ma tare Abba." "Ka nema sa duk ina yake ka ce yazo ya kwana a gida. Daada baza ta ɗagawa kowa ƙafa ba in bai shigo yau ba, tana ta faɗa dare ya yi an kawo masa amarya ba ya nan. Don Allah ka rarrashe shi ya zo gidan nan, bana son faɗan nan na Daada ko kaɗan." Jazy y ce, "to Abba, zan gwada in sha Allah." "Yauwa Jafar, Yadda ku ka yi dashi ka sanar dani da gaggawa." "In sha Allah." Daga haka suka yi sallama ya kashe wayar. Kafin Jazy ya yi magana Ray ya ce, "babu inda zani wallahi, ta yi faɗan ina ruwana?." Jazy ya ce, "Rehaan haka zaka daure, ba dan Daada za ka yi ba dan Abba za ka yi, mahaifiyarsa yake yiwa biyayya, ka taimaka ka ta ya shi yi mata biyayya." Rehaan ya ce, "tunda ka faɗa masa ba ma tare ka ƙyale kawai, bazan koma gida yau ba." Ya ɗan kalle sa ya ce, "ya kamata aje ka je, tunda har Abban yana so." Ya buɗe idanunaa akan Jazy yana zazzaro masa su ya ce, "Jazy bazani ba, kar ka faɗawa kowa ina nan!." Jafar ya cike da tsokana ya ce, "ban taɓa ganin angon da ba ya mararin amaryarsa ba sai kai, ni yanzu da aka ɗaga kai min tawa akace sai gobe ji nake kamar na yi hauka saboda baƙin ciki, so nake kawai goben ta yi na ganni tare da ita. Amma kai gata can a gidan ka kana wani shan ƙhamshi." Harararsa ya yi cike sa jin haushi da takaici, Jafar ya ƙyalƙyale da dariya yana miƙewa ya ce, "na wuce, abokaina suna can suna jirana, sai gobe" ya faɗa tana fita daga falon da sauri. Ray ya bisa da kallo sa kuma ya kwance gashin kansa ya zubo sa har fuskarsa, ya lumshe ido ya buɗe yana kallo kiran wayar Mamy yana zuwa itama bai buɗe ta daga dnd ba. Ya miƙa hannu ya ɗauki wayar, bayan kiran ya katse ya kira Mamy tana ɗauka a ya sanyaya murya ya ce, "Mamy." Mamy ta ce, "ina ka je, tun ɗazu nake neman ka ba ka nan? Haka za a yi dakai Rehaan, ana bikin Riyya guda amma ba ka zuwa wajan? A ganinka zata ji daɗi?." Ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "Bana son zaman gidan ne Mamy." "To meyasa ka saka wayarka a dnd?." "Bana so a dinga kirana ne shiyasa. Ina Riyya ɗin?." "tana tare da friends ɗinta, sai Banisha." Kafin ya yi magana ya ji Banisha ta ce, "Hamma." Ya ce, "kiddo." "Hamma an kawo amaryar ka, ni ce na buɗe fuskar ta, ka san wanne suna na saka mata?." Ya ɗan yi shuru bai ce komai ba Banisha ta ce, "na saka mata Islam, ya yi iri ɗaya da sunanta shiyasa na saka mata. Ka san me?." "Uhum uhum" ya furta can ƙarshen maƙogwaronsa. "she is very beautiful." "Hmmm" ya furta bai ce komai ba ya ji Mamy ta karɓi wayar ta ce, "yaushe za ka shigo nan ɗin?." "Sai gobe Mamy." "Okay ina jiran ka goben. Nima ai na san yarinyar da aka aura maka, sai yanzu da na ga fuskar ta na gane ta, yarinyar bata kirki." Haka kawai ya ji gabansa ya faɗi akan kalaman Mamy, bai san meyasa ya ji faɗuwar gaban ba, ya so ya share maganar amma sai ya kasa sharewa, ya gyara zama ya ce, "kin santa Mamy?." Mamy ta ce, "na santa, sai da na ga fuskar ta ɗazu na tabbatar na santa, gabaɗaya bana son ganinta." Ya ɗan yi shiru bai ce komai ba yana tunanin ita kowa ya yi mata shaidar rashin kirki, kuma kowa ba ya son ganinta saboda baƙin halinta?. Mamy ta katse shi ta ce, "sai ka zo ɗin." Daga haka ta kashe wayar. Ya bi wayar da kallo yana tuna kalman Mama jin wai ta santa har tana bada shaidan bata da kirki. Ya yi ajiyar yana jan tsaki, a bayyane ya ce, "ni kam a cuce ni" ya faɗa yana lumshe idanunsa, tunda har Mamynsa ta shaida rashin kirkinta ya tabbatar na gaske ne ba na wasa ba. Ya gyaɗa kai yana aiyana in wani rashin kirkin ta yiwa babarsa wallahi bazai ƙyale ta ba, zai ɗauki ko wanne irin abu a duniya amma ban da yiwa Mamy wani abun mara kyau. _No intimacy reletionship._ Abinda ya zo ransa kenan, ya yi tsaki mai tsaho ya miƙe ya ƙarasa gaban consoll ɗin da yake falon, ya saka hannu a aljihu yana kallon kansa yana tuna yadda suka yi da ita bit by bit. Ya lumshe ido yana shafa kansa, tunanin yadda zai iya rayuwa da ita a waje ɗaya ma kawai takaici yake ba shi balle in ya tuna matarsa. Ya harɗe hannunsa a ƙirji yana cigaba da kallon kansa, sai ya cize bakinsa kafin ya bar wajan ya shiga bedroom. Mamy tana tare da ƴan uwanta Yayar Sanah ta ce, "meyasa ba ki yi shirya tarbar inlaw ɗinki ba? Kin san yanayin culture ɗin gidan da ki ke ciki, yanzu da ban yi wannan tunanin na yi abinda ya kamata ba ya ki ke so a yi?." Mamy ta kalle ta ta ce, "Na manta ne gabaɗaya, ni na manta za a kawo wata matarsa balle na yi tunanin abinda zan bayar." Sanah ta ce, "ya aka yi ki manta? Ita ɗin matar Rehaan ce fa, za ki ji daɗi in aka kai Riyya Mummy ta ce ta manta da ita?." "Ita da Riyya ba ɗaya suke ba ai, itafa yarinyar nan ba son auren nan muke yi ba da ni dashi, kin san a yadda auren nan yazo, ya za a yi na yi tunanin wani culture? Ni kwata kwata yarinyar bata yi min ba.” "Na san bakya so shima ba ya so, amma ya kamata ki san yanzu dai matarsa ce, kuma ke ɗin inlaw ɗinta ce. Ya kamata wani abun ki dinga yin pretending ko dan mutanen gidan nan, ki duba kishiyar ki abinda ta bayar, yanzu da ta bayar ke ba ki bayar ba ya ki ke tunani?." Mamy ta ɗan sauke numfashi ta ce, "na yarda na yi laifi." Ta ce, "ya kamata ki dinga haƙuri, kin san ya mutanen gidan nan suke kallon ki, kina yin motsi kaɗan za a ce kin ce." Mamy ta yi shiru bata ce komai ba. A lokacin Abba ya kira ta a waya tana ɗauka ya ce, "Kun yi magana da Rehaan ne?." Kafin ta basa amsa ya ce, "ina ta kiransa wayar bata zuwa, na tambayi Jafar ya ce basa tare. In kin same shi ki ce nace ya zo gida duk dare, in ba haka ba ban san wanne irin fushi zan fuskanta daga Daada ba." Mamy Allah ya so bata ce masa sun yi waya ba, sai ta ce, "zan gwada kiransa in sha Allah, in na same sa zan faɗa masa." Daga haka Abba ya kashe wayar ta bi wayar sa kallo. Yayarta ta kalle ta ta ce, "ba yanzu ku ka gama waya da Rehaan ɗin ba?." Mamy ta ce, "yanzu ne, da alama Abbansa bai same sa ba." Bata ce komai ba itama bata ce ba, suka cigaba da hirar yadda komai zai kasance gobe in an kai Riyya gidanta. Abba kuwa yana kashe wayar wajan Daada ya koma yana shiga ya tarar da ita da Mama. Yana shiga Daada ta ce, "Rehaan ɗin ya taho?." Ya girgiza kai ya ce, "Ban same sa a waya ba wallahi, na kira Jafar shima ya ce basa tare, amma na ce duk dare ya faɗa nasa ina neman sa." Daada ta ta fara tafa hananye ta ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!…. Yaron nan so yake ya watsa min ƙasa a ido, so yake ya nuna min ban isa dashi ba. Tsakani da yarinya baƙuwa an kawo ta gidan nan, ƴan uwanta duk sun tafi an barta ita kaɗai ace bai zo ba? Me yake yi a inda da ya zauna? Sai ya nunawa duniya ban isa na saka shi ya yi ba ko?." Abba ya ce, "ki yi haƙuri, in sha Allah a gidan nan zai kwana." "Kaima ya raina ka balle ni, gwara ni ba haihuwarsa na yi ba ubansa na haifa, kai da ka haife sa ɗin ma ya nuna maka yanzu ya fi ƙarfinka, tunda yana da kuɗi kuma shi jinin indiayawa ne." Mama da take gefe ta ce, "gaskiya dai Rehaan bai kyauta ba, ko dan mutanen da suke gidan nan ya kamata ace ya zo ko iya yau ne. Bakin mutane ake gujewa, meye aibu dan yazo ya shiga inda matarsa take? Ba fa wani abun aka ce ya yi da ita, kwana dai a kwana a tashi meye aibu a ciki?." "In ma wani abun aka ce ya yi da ita ɗin ba matarsa bace, Aka san mata nawa yake yi dasu a ƙasar waje? Yadda mata suke yawo da ɗagaggun kayan nan meye ma bazai aikata ba?..." Sai kuma ta yi shiru tana girgiza kai ta ce, "kawai yana so ya nunawa duniya ban isa ba, yana so ya nunawa duniya da baƙin da suke cikin gidan nan, da fararen fatar ƴan uwan uwarsa ban isa dashi ba. In har bai zo gidan nan yau ba, ya nuna min kai ɗin ma ba ya daraja ka balle ka saka shi ya yi." Abba ya dafe kai cikin rashin jin daɗi ya ce, "zai zo ma in sha Allah, ki yi haƙuri." Daada ta ce, "kar ma yazo ɗin, ya zauna a inda ya ga dama, tunda daman uwarsa bata son auren ai bazai zo ba. Nan ta zauna sai cin magani take yi, saboda na zaɓawa ɗanta mata tana ganin ban isa ba. Ta kiyaye ni, na rantse da Allah sai na aurar da Banisha yanzu, na ga abinda ta isa ta yi." Abba ya ce, "Allah ya wuci zuciyar ki, ki yi haƙuri." Abba ya miƙe ya fita zuciyarsa babu daɗi yana sake kiran wayar Reahan amma har lokacin user busy take saka masa. Yana fita Mama ta ce, "Nadira bata san auren nan ko kaɗan, kuma na tabbatar ita baza ta saka samunsa a waya ba, itace zata ce kar ya zo." Daada ta ce, "ai ba sai kin faɗa ba, na san halin munafurcinta tsaf zata aikata wallahi." "ni ban ga aibun yarinyar nan ba, yarinya mai nutsuwa da girmama mutane. Ki duba yadda ta kasa haɗa ido da kowa a falon nan, tana magana kanta a ƙasa cikin mutunci da halin fulani. Wallahi in ka haɗa jini da wanda ba fulani na ma tashin hankali ne, gabaɗaya ta gurɓata mana yara sun koma kamar ba jininmu ba. Ko wacece yarinyar da take son aura masa ai baza ta kai Islahan ba, ga kyau ga ta jinin fulani." Daada ta ce, "ki ƙara da girmama na gaba, sanin darajar tsoho, ilimi, ibada da kuma wayewa. Ko wacece yarinyar da take son aura masa ai baza ta kai haɗa waɗannan abubuwan ba." Mama ta ce, "hmmm, ni fa na ji labarin Ikram take so ya aura." Daada ta wani kalle ta baki buɗe ta ce, "wacce Ikram ɗin?." Mama ta ce, "Ƙanwar Jafar." "Ƙanwar Jafar a gidan nan? Ke Saddiƙa ko dai Nadira tana shaye shaye ne?." Mama ta murmusa ta ce "ba wani shaye shaye, tsabar iskanci ne tana ganin kamar itace da gidan, tunda ɗanta shine lamba ɗaya a gidan." Daada ta ce, "Ɗanta dai shine lamba ɗarin gidan nan ba ɗaya ba, matuƙar ina da rai babu wanda zai zama lamba ɗaya sai ni. Wallaho bata isa ba, in dai ina raye wallahi bata isa ya auri ƙanwar Jafar ba. Ita ta isa? Dan an samu ma na amince da auren Juwairiyya da Jafar ɗin shine zata ɓullo da wannan wasan kwaikwayon? Lallai dole na yiwa tufkar hanci, Allah ya nuna mana gobe." Mams ta ce, "ya kamata kam, dan yadda ta ke ji da kanta ya kamata dinga nuna mata gaba da gabanta." Daada ta girgiza kai bata ce komai ba, dan Mama ta gama zugata, kuma ta zugu sosai. Mama ganin ta gama ɗora Daada sai ta yi murmushi, "Daada bara na koma ciki, ina da baƙi suma jirana." Daada ta ce, "Na gode Saddiƙa, ba a banza ki ka zama kece gaba a gidan nan ba. Allah ya yi albarka." Mama ta murmusa tana rusunawa ta ce, "Amin Daada, sai anjima." Mama tana fitowa ta harari ƙofar falon Daada ta ce, "Kaf ƴaƴana da suka yi aure, ba ki basu kwatankwancin abinda ki ka bawa wannan figaggiyar yarinyar ba. Sarƙar gold ki ka bata wacce kuɗinta zai kai miliyan talatin, ki ka haɗa da kuɗi da abubuwa. Ni nawa yaran da suka yi aurensu, da ƙaramar sarƙa ki ka haɗa matansu dashi, amma ita kalli irin kyautar da ki ka bata. Wallahi Allah bazan bar Rehaan ya zauna lafiya ba, ta jikin matar nan tasa zan san duk hanyar da zan bi na cimma burina. Babu ta yadda za ayi Rehaan ya fi ƴaƴana bayan su ne gaba dashi, biyayyar dole nake yi miki Daada, jira nake na gama da Rehaan na dawo kan ki, dan kema za ki iya hana ni rawar gavan hantsi." Kai tsaye ɓangaren Umma ta wuce ta same ta a ɗakin Salman tana bashi maganinsa. Ganin Mama sai ta fito ta ce, "Kin ga abinda uwar mijinki ta yi mana ko? Sarƙar da mu ke sakawa a wuyanmu ita ta ɗauka ta bawa yarinyar da ko awa biyar bata yi a gidan nan ba. Matar Rehaan, Oh Allah, ya zamu yi da yaron nan ne?." Mama ta ce, "Maza huɗu na aurar a gidan nan, amma bata taɓa basu kwatankwacin abinda ta bata ba." Umma ta ce, "kema ai na yi mamakin ki, harda ba da lace ɗin 2.7m kyauta ga yarinyar." "Ya zanyi, Abbanssu ne ya saka ni a gaba don Allah nima na yi, dole ce ta saka na yi ai ba don ina so ba." Umma ta haɗe rai ta ce, "Shi ya faɗa miki kema ki ba da kyautar?." "Shinw mana, ke bai faɗa miki ba?." "In da ya faɗa ai zan bayar." "Wataƙila ya manta ne, kin san ana ta hidimar biki abubuwan sai a hankali. Amma jira nake a gama bikin nan, Allah sai na yi maganin Rehaan." Umma ta ce, "haka ki ke faɗa ko yaushe, amma kin kasa yin komai." Mama ta yi dariyar nishaɗi ta ce, "kina wasa dani, amma in kina ganin bazan iya ba zan iya cewa ki zuba idanu." Umma gabaɗaya ranta ya ɓaci, jin abinda Abba  ya faɗawa Mama ita bai faɗa nata ba. Wato har kuɗi ma ya bata ta siya, ita ga banza mara amfani, ya ajjiye ta a gefe kamar ba matarsa ba. Mama ganin yanayin Umma ya canja sai ta ce, "sai mun haɗu gobe, bacci nake ji" ta faɗa tana yi mata wani irin kallon ba ki da wayo yarinya, sannan ta fita tana murmushin da ita kaɗai ta san ma'anarsa. Hajiya Mama ikon Allah😂🤣 Nana Haleema. RDB3P004 Nana Haleema. Islaha tunda su Safeera suka tafi ta koma ta zauna akan kujerar falon bata iya miƙewa ba. Kallon falon take yi babu sautin komai sai ac, ko sautin hayaniyar mutanen da ta gani a waje bata ji. Ta kasa ɗarawa daga falon, tana zaune ta yi tagumi tana tunanin Saheer. Ga ciwon kai, ga gajiya, ga tashin hankali, ga zazzaɓin da ya mamaye mata jikinta. Cikin rauni da sanyin ta jawo wayarta ta kira Sadik amma bai ɗauka ba, ta rufe ido ta rasa wa zata kira. Inda a dah ne sai ta kira Adda, amma yanzu Adda ta yi fushi da ita itama. Lokacin sallar i'sha ya yi, ta miƙe tana kallon ko ina kamar mai neman wani abun a cikin parlour. Falon babu wani tarkace mai yawa, sai stairs da yake gefe sannan sai ƙofa guda biyu. Ƙarfar farko ta buɗe ta ga kitchen ne mai matuƙar girma, bata tsaya ƙare masa kallo ta rufe ta ƙarasa ɗayan ta buɗe ta ga bathroom ne mai kyau. Ta shiga tana kallon sink ɗin ganin ita dai bata taɓa ganin sink irin sa ba, ta kalli tap ɗin amma ta rasa ina zata taɓa ruwa ya zo. Ta kama ƙugu tana kallon banɗakin ta rasa inda zata taɓa ta ruwa yazo balle ta yi alwala, sai ta furzar da iska cikin tunani, ta kalli mirror da yake saman sink ɗin tana kallon kanta. Ta yi tsaki ta sake kallon wajan amma ita bata ga inda zata ga ruwa ba. Ta kuma yin tsaki sannan ta fito, daman tana da alwala kawai tana son canjwa ne, a falon ta yi sallar i'sha, tana idarwa ta sake kiran Sadik amma har lokacin bai ɗauka ba. Ga kanta yana ciwo, ga zazzaɓin da yake jikinta, ga rashin ɗaukar waya da Sadik bai yi ba, ji take kamar ta ta tashi ta je gidan ta ga abinda yake faruwa, zaman waja ɗayq ya ishe ta gabaɗaya. Ta yi shiru ta dafe jijiyoyin kanta, sai ta ji wayar ta tana ringing alamum kira yana zuwa, ta ɗauka da hanzari ganin Sadik ɗin ne yake yi mata waya. Tana sakawa a kunne ta ce, "Hamma Sadik ka wahalar dani, ina ta kiran ka ba ka ɗauka, ka san dole zan damu in na kira ka baka ɗauka ba. Don Allah ka faɗa min ya Hamma ya ke, ya jikinsa?." Sadik cikin sanyin jiki ya ce, "Jikinsa da sauƙi, bacci yake yi yanzu." Ta yi ajiyar zuciya ta jin daɗin ance jin yana bacci sannan ta ce, "Ya yi fushi dani ko? Hamma Ya tsane ni ko?." "Bai tsane ki ba, amma yana jin ciwon abinda ki ka yi masa, gaskiya ya yi fushin da ba ki taɓa tunanin zai yi shi a kan ki ba." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Hamma Sadik ka san komai, ka san dalilin zuwana nan. Don Allah ka faɗa masa gaskiya, ka faɗa masa, ni ban san ya zan yi ba, na rasa inda zan saka raina na ji daɗi" ta faɗa tana fashewa kuka. Sadik ya ce, "ban faɗa masa ba, ina so ya nutsu sosai tukunna, in na faɗa masa yanzu ba bazai taɓa ganewa ba. So nake sai ya gama samun nutsuwa sai na faɗa masa, kin ga bai gama nutsuwa daga tashin hankalin da ya fito daga ciki ba.” Islsha bata iya magana na sai kukan da take yi mai sauti. Sadik ya ce, "ki yi haƙuri, ki daina kuka, ki kashe wayar ki kwanta." "Bazan iya bacci ba, ban san halin da Hamma yake ciki ba, ta ya zan iya kwanciya? Don Allah na kira ka video call ka shiga ɗakinsa ka haska min shi gansa?." Sadik ya ɗan yi shiru dan ba ya so ya faɗa mata suna asibiti, in kuma ta kira video call tabbas zata gane suna asibiti kuma zata sake ruɗewa, kuma shi ba haka yake so ba tunda yanzu a gidan wani ta ke, ko ta ya aka gina auren dai sunansa aure, bai kamata ya ɗaga mata hankali ba. "Islaha ki yi haƙuri, bazai yu na kira ki ba, saboda Mama tana tare dashi, kin san baza ta bari ba." Islaha ta ja numfashi mai ƙarfi ta ɗaga kai kamar yana gabanta ta ce, "To, amma don allah gobe da safe ka kira ni, ni ko ba gobe ba, ko ƙarfe nawa na dare ne in ka samu dama ka kira ni, don Allah." Sadik ya ce, "kar ki damu." Daga haka ta kashe wayar ta ɗora kanta a kan kujera tana cigaba sa zubar da hawaye. Ta jima a haka, kanta ya sake yin nauyi ko buɗe Ido bata son yi, yadda jijiyoyin kanta suke harbawa kamar zasu tsinke haka take ji. Tana a haka ta ji ƙarar door bell, ta ɗago ta kalli ƙofar tana da tabbacin da mutum a wajan yana danna door bell. Ta ɗan goge idanunta ta miƙe tana jiri, sai da ta ɗan nutsu sannan ta ƙarasa ta murɗa handle ɗin ta buɗe ƙofar. Haɗa ido suka yi da Daada da kuma wasu mata masu kama da masu aiki a tsaye a bayanta riƙe da manyan flaks. Islaha ta yi murmushin dole ganin Daada tana ta murmushi. Daada ta ce, "Ishlaya, kina zaune ke kaɗai ko? Ya na gan ki haka? Bakya jin daɗi ne?.” Islaha ta rufe ƙofar suka shiga ciki, sannan ta ce, “Kaina ne yake ciwo.” Daada ta ce, “Wayyo, bara a samo miki magani.” Ta kalli ɗaya daga cikin masu aikin ta ce, “samo mata maganin ciwon kai yanzun nan.” Ta amsa da girmamawa sannan ta fita. Islaha ta kalli abinda aka ajjiye mata, ta ga abinci ne a manya flaks da abin sha a ƙaton tray. Daada ta ce, "Na san ba ki ci abinci ba, ga abinci nan ki zauna ki ci." Bata ce komai ba ta sunkuyar da kanta ƙasa. Daada ta bita da kallo tana murmushi, a duniya bata taɓa jin ƙaunar yariya lokaci ɗaya ba kamar yadda take jin ƙaunar Islaha. Ta dafa kanta ta ce, "Mijin naki yana nan tafe, ki ci abinci ki sha magani sai ki hau sama ki yi baccin ki, za ki iya kwanciya ke kaɗai?." Islaha ta ɗaga kai alamun eh, ta yi murmuahi ta ce, "to ki ci abinci sai ki kwanta. Ki saki jikin ki, nan gidan ki ne, duk abinda ki ke so kawai ki faɗa min, in akwai abinda ba ki gane ba kawai ki sanar dani zan yi miki bayani." Islaha ta ce, "In sha Allah, na gode Daada." Daada ta shafa kanta ta ce, "Allah ya yi miki albarka." Islaha ta amsa da amin. A lokacin wacce ta tafi ɗauko magani ta dawo, ɗaya mai aikin ta buɗe mata ta shigo, ta miƙawa Islaha magani ta karɓa ta ce, “Na gode.” Daada ta miƙe zata tafi, Islaha itama ta miƙe ta raka Daada har baƙin ƙofa. Daada ta ce, "Koma ki zauna abin ki, ba sai kin fita ba." Ta buɗe ƙofar Daada ta fita masu aikinta suka tafi rakata. Daada tana fita Islaha ta yi tsaki mai cike da takaici ta mayar da ƙofar ta rufe, ta dawo tana kallon abincin bata iya buɗewa ba, ruwa kawai ta ɗauka ta sha maganin ta koma ta zauna a akan kujera tana lumshe idanunta. Saheer ya jima yana bacci, bai farka ba sai ƙarfe sha ɗaya na dare. Suna zaune a ɗakin gabaɗaya an ba shi abinci yana juya spoon ɗin ya kasa ci, ya yi shiru ya zubawa abincin ido, idanunsa da zuciyarsa sai hango masa abubuwa suke yi akan Islaha, shaiɗan sai hasko masa ita yake yi cikin wani irin yanayin da ya saka zuciyarsa bugawa da ƙarfi. Bai san ya yi cilli da plate ɗin hannunsa ba, abincin ya watse a ƙasa, ya dafe kansa da duka hannayensa yana jin zuciyarsa kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito saboda bugawar da take yi. Abubuwa sun yi masa yawa, ga tunanin Sudaisa da ya kasa barin zuciyarsa, yana tunanin a wanne hali take ciki, ga kuma tunanin Islaha da yake neman kai shi lahira. Mama ta riƙe hannunsa ta ce, "Saheer meye haka, kashe kanka ka ke so ka yi?." Sadik ya riƙe shi daga gefe ya ce, "Saheer sannu." Ya jingina da bango yana sauke ajiyar zuciya ƙirjinsa yana sama da ƙasa, cikin rauni ya ce, "Sadik Islaha tana gidan wani, ta yi aure har ta tare……” Sai ya dakata yana dukan ƙirjinsa kaɗan-kaɗan ya ce, “Zafi nake ji a ƙirjina, ji nake kamar na mutu saboda abinda nake ji. Meyasa Islaha zata yi min haka, meyasa ta zaɓi ta yi aure ta bar ni?" Ya ƙarasa faɗa cikin yanayin da shi kaɗai ya san me yake ji. Sadik ya kalli Mama da ta miƙe tsaye, kafin ya yi magana ta ce, "kai yanzu akanta ka ke ƙoƙarin kassara rayuwar ka? In ka mutu ta silar wannan abin kanka ka cuta, ita kuma tana can gidan AbdulAziz Yola tana rayuwar jin daɗi da walwala, kai kuma kana nan za ka kashe kanka a banza a wofi. Wallahi mamaki ka ke bani in kana tunanin wannan banzar yarinyar, yariyar da ta zaɓi kuɗi da abin duniya sama da kai da rayuwar ka, meye abin tunawa a cikin lamarinta gabaɗaya?.” "Assalamu alaikum" aka faɗa daga bakin ƙofa ana shigowa. Suka amsa suka juya ganin Aminiyar Mama Hajita Karima ce ta shigo. Ta ƙaraso ciki ta ce, "Sannu Saheer, Allah ya ƙara lafiya." Bai iya ko da ɗaga kai ba, Hajiya Karima ta kalli Mama ta ce, "ashe haka tsinanniyar yarinyar nan ta yi mana?…..” Mama ta girgiza kai ta ce, “Hmmm ni na rasa abinda faɗa Karima.” Hajiya Karima ta ce, “Ba ƙarya ba, hausawa daman sun ci tsintacciyar mage bata mage. Ni wallahi na yi tunanin a yadda Saheer yake a wajenta, da yadda ya yi ɗawainiya da ita, da yadda ya dinga nuna mata so, ko mahaukaci ya nuna mata ya ce ta aura na ɗauka zata aura ba tare da musu ba, saboda matsayin da yake da shi a wajanta." Mama ta harari Saheer ta ce, "Abin haushin ma kalle shi don Allah, wai ta silar ta ya ke kwance a nan, ko hutawa bai yi daga uƙubar da ya sha a wajen ƴan bindiga ba, ta sake jefa shi a wannan halin. Kalli yadda ya tarwatsa abinci da faranti saboda kawai ya tuna ta yi aure." Karima kalle sa sannan ta ce, "dole zai ji babu daɗi, ya tashi da son yarinyar nan, kuma ta yi masa abinda abinda bai taɓa zaton za ta yi masa ba, ko waye dole zuciyarsa ta karye, aure ta yi ta bar shi.” Hajiya Karima ta kalli Mama ta ce, "yanzu daga unguwar ku nake kafin na zo, na haɗu da Atika da munafukar ƙawarta Safeera, kin ga kayan da aka basu na kyautar kai amarya? Kin ga kuɗi da kayan abinci? Ina gani na ce ba a banza yarinyar nan ta guji Saheer ba wallahi, ta bar halacci ta zaɓi kuɗi." Mama ta kalli Saheer ta ce, "ka ji ko? Sai ka daina damun kan ka, ka daina saka damuwa a zuciyarka, daman ba ƙaunar ka take ba, kwantan ɓauna take yi maka, sai yanzu ta samu ta cika burinta. Da ita da mahaifinka sun haɗa kai sun aurar da ita a gidan kuɗi, kai kuma da yake baka da kuɗi sun cilla ka a bola.. Babban abin haushi da takicin ma mahaukaci ta aura ta bar ka." Sadik da yake jinsu sai ya ɗan fita, jim kaɗan ya dawo ya tsaya yana kallonsu ya ce, "Mama likita ya ce a ba shi lokaci ya huta, ba a son hayaniya." Jin haka duk sai suka yi shiru, sannan suka fita aka bar su su kaɗai, Saheer yana zaune ya jingina da jikin gadon. Bai san lokacin da hawaye ya fara ziraro masa ba, suka fara zuba wani yana bin wani kamar ba namiji ba, ya kasa dakatar dasu daga zubar da suke yi, ya bawa hawayen damar zuba yadda ya kamata, dan rashin zubar su matsala ce a gare shi. Babu abinda ya ke gani a idanunsa sai Islaha tana gidan wani namijin ba shi ba. Shi bai damu da kuɗin da suke ta zance ba, abinda idanunsa suke gano masa kawai Islahansa ta yi aure ta bar shi. Ya furzar da iska, ji yake gwara zaman wajan masu garkuwa da mutane akan raɗaɗi da ƙunan da yake addabar zuciyarsa. Nana Haleema. RDB3P005 Nana Haleema. A hankali ya ji an zauna a kusa dashi, ya kalli Sadik suka haɗa ido sai ya ɗauke kai, Sadik ya bi shi da kallon tausayi da rauni sannan ya ce, "Saheer!." Bai iya magana ba sai hawayen da ya goge yana ɗan girgiza kansa cikin rashin sanin abinda zai yi. Sadik ya ce, "don Allah ka dawo hankalin ka, ka daure ka nutsu sai mu yi magana. Likita ya ce jininka ya hau sosai, in ba ka nutsu ba ya ka ke so abin ya zama?.” Ya buɗe jajayen idanunsa ya kalli Sadik ya ce, "Aure ta yi fa Sadik, tana can gidan wani zata kwana tare dashi, a haka ka ke cewa na kwantar da hankalina?." "Saboda lafiyar ka nake faɗa maka, dole ka sassauta wannan damuwar saboda jinin ka da ya hau a samu ya yi ƙasa, kuma har yanzu akwai sauran wahala a tare da kai, baka gama warware daga wahalar da ka sha ba.” "Hmm! Ba ka san me nake ji bane Sadik, na kasa yarda Islaha zata yi min haka, na kasa yarda zata zaɓi kuɗi ta bar ni, na kasa yarda zata ci amanata har haka ba. Da abinda zata saka min dashi kenan, duk ƙaunar da na nuna mata, da zaman jiranta da na dinga yi, da wannan zata yi min sakayya? Mata nawa Mama ta bani naƙi aura saboda ita Sadik? Kai kanka har ƙanwar ka ka bani, amma naƙi na ce sai ita ɗin….” Ya ɗan daki kansa a hankali sannan ya ce, “Wai tana gidan AbdulAziz Yola tana aure, tana can matsayin matar wani ba ni ba.” Ya kalli Sadik suka haɗa ido sannan ya ce, "kuma ka ce min na kwantar da hankalina? Har abada hankalina bazai kwanta ba Sadik. Ka san ina son Islaha, bani da buri a duniya da ya wuce na mallake ta, itace kaɗaii abinda nake muradin mallaka a duniyata.” Sadik ya dafa shi ya ce, "Na sani, na san kana jin zafi da ƙuna a ranka da zuciyarka, na san babu wanda ya san me ka ke ji sai Allah. Amma ka yi haƙuri, ka daure ka kawar da damuwar komai zai wuce." "Komai zai wuce ko? Tana can gidan wani matsayin mata ka ce min komai zai wuce? Ta ya komai zai wuce?." Cikin tausayi Sadik ya ce, "ina so ka warware ka samu lafiya sai na faɗa maka yadda za ka fahimta. Abu ɗaya nake so ka sani, wallahi Islaha bata ci amnar ka ba, duk abinda ta aikata ta yi shine saboda kai." Wani irin kallo ya yiwa Sadik, ya buɗe idanunsa sosai yana kallonsa ya ce, "saboda ni, auren wani ta tare a gidansa shine ta yi saboda ni?." Sadik ya ce, "ka tsaya ka saurare ni ka ji dalilina kafin ka yanke min hikunci." "Har abada bazan taɓa sauraren kowa akan maganar nan ba, bazan taɓa amincewa Islaha ta bar ni saboda ni ba. Ban da rainin hankali, ta ya za ka ce ta bar ni saboda ni, hankali zai ɗauki wannan ne?." Sadik zai yi magana Saheer ya dakatar daahi ya ce, "Ka ga Sadik, in tare da kai aka haɗa kai za a ci kuɗin da wanda ta aura wannan ba damuwata bane, amma ka daina faɗa kin abinda zan ji haushin ka a cikin zuciyata. Kar ka sake yi min zancen ta, ko sunanta bana buƙatar na sake ji a kusa dani, na yanke duk wata alaƙa da take tsakanina da ita, ta je ta yi duk abinda ta ga dama, bazan sake sauraren ta ba." Sadik ya yi ajiyar zuciya dan ya san bazai fahimta a lokacin ba, amma zai saka ya fahimta wani lokacin in da rabon fahimtar, dan ba ya jin daɗin yadda yake zargin Islaha, bai so abin ya zo a haka ba, dan shi ya san sadaukar da kanta ta yi saboda shi, duk da ya san Saheer ɗin zai fahimta, naganganun su Mama yake tsoro. Sadik ya yi shiru yana kallonsa, sai kuma ya miƙe ya fita daga ɗakin jikinsa duk babu daɗi. Da Islaha da Saheer ɗin gabaɗaya tausayi suke ba shi, har ya fi jin tausayin Islaha akan Saheer, tunda ita aka jefa a cikin tsaka mai wuya. Ta sadaukar da farin cikinta da rayuwarta da duk wani burinta, ta kai kanta inda bata san abinda zata tarar ba, ta je can ta zauna a matsayin matar aure saboda shi. Babban abin takaici da tausayin shine wanda ta yi dominsa ya gaza fahimta, yana ganin kamar ta ci amanarsa. Amma zai san abinda zai dan ya gyara wannan matsalar, in bai gyara matslaar ba ba a yiwa Islaha adalci ba: Kiran sallar asuba ne ya farkar da Islaha daga baccin da ya ɗauke ta a kan kujera. , ta miƙe a firgice tana zare ido ganin haske a kanta, bata san ta yi bacci ba, ta dai san ta jima a haka a zaune tana saƙa da warwarewa. Kukan ɗawisu take ji kaɗan kaɗan, ta kalli window ta hangosa yana ta yawo a tsakanin falon zuwa baya. Ta lumshe ido ta buɗe, ta kalli wayarta ba tare da tunanin komai ba ta kira number Sadik. Har ta katse bai ɗauka ba, ta miƙe ta shiga banɗaki tana sake kallon sink dan bata san ya zata kunna tap ɗin ba. Ta ta dafe kanta jin har lokacin yana ciwo, ta fito ta ɗauki wayarta ta ɗauki hoton sink ɗin ta turawa chatgpt tana tambayarsa yadda ake amfani da shi. Cikin sakanni ya faɗa mata, tana kallon wajan ta ga inda zata taɓa. Bata ɓata lokaci ba ta yi alwala ta fito ta tayar da sallah a inda ta ke, bayan ta idar ta jingina da kujera tana tunanin masoyinta bata san a halin da ya ke ciki ba, a haka bacci ya sake ɗaukar ta bata san ta yi ba. Sautin kocking ne ya tashe ta, ta miƙe zaune tare da taɓa wayarta, gabanta ya faɗi ganin sha ɗaya na safe, ta zabura tana kallon wayar cikin mamakin gudun lokacin. Ta kalli ƙofar jin ana sake danna door bell, ta miƙe cikin bahagon yanayi ta ƙarasa ta buɗe. Tana buɗewa suka haɗa ido da Mama, Mama ta yi mata murmushi ta ce, "Amarya Islaha ko na ce Islam, na tashe ki ko?." Islaha ta ɗan murmusa kaɗan ta ce, "daman na tashi, sannu da zuwa." Mama ta ce, "yauwa amarya, ku shiga ku ajjiye mata" ta faɗa tana kallon na bayanta tana kallon matan da suke riƙe da breakfast. Suka shiga suka ajjiye. Islaha ta kalle su ta ce, "ku tafi da wannan ma, jiya aka kawo ban iya ci ba." Suka ɗauko wanda Daada ta kawo suka fita. Mama ta bita da kallo ganin kayan jiya ne a jikinta, har mayafin yana jikinta alamun dasu ta kwana. Islaha tana kallon Mama suka haɗa ido alamun daman kallon ta take yi. Mama ta murmusa ta ce, "Ba dai a nan ki ka kwanta ba?." Islaha ta ce, "ban san na yi baccin ba, sai asuba na farka." Mama ta ce, "Ai da kin sani sama ki ka tafi ya fi, nan sautin wannan kayan kiwon nasa ma ya tashe ki." Ɗan murmushi ta yi kaɗan amma bata ce komai ba. Mama ta ce, "zan koma, in kina buƙatar wani abu duk wanda ki ka haɗu da shi a ma'aikatan gidan ki ce a raka ki wajan Mama." Islaha ta ɗaga kai ta ce, "to Mama, An gode." Mama ta yi murmushi ta ce, "kar ki damu." Ta faɗa yana juyawa ta bar wajan. Islaha ta rufe ƙofar tana sauke numfashi ta ce, “tana da kirki sosai, babu ruwanta" ta faɗa tana kallon stairs ɗin da zai kai ta sama. Ta ɗauki wayar ta sannan ta fara hawa saman kamar mai jin tsoron taka ƙasa, ta buɗe ƙofar falon tana kallon falon kamar jiya bata gan shi ba, ko ina da duhu sosai, ko ina haskensa a kashe ya ke, ta ƙarasa ɗakin da suka shiga da Safeera. Ta kunna haske ta tsaya tana kallon ɗakin, sai kuma ta cire mayafin ta ajjiye ta shiga banɗakin. Banɗakin sai ya bata tsoro, dan bata taɓa ganin banɗaki mai girmansa ba, duk yadda ta kai ga ganin girman banɗakin Jeddah, wanda ta buɗe a yanzu ya fi sa girma. Bata tsaya tunani ba, ta gwada kunna shower ta tabbatar komai ya yi, sannan ta yi wanka da alwala. Garin buɗe-buɗe ta buɗe drawer ta ga brush da thoothpaste duk a ledar su, ta yi amfani dashi sannan ta fito. Kayan da Safeera ta zo mata dasu ta buɗe, ta ɗauki doguwar riga ta saka ta tsaya tana kallon uban kayan da aka bata jiya, ga wata sarƙar gold kamar ta yi magana da bakinta saboda girma. Ta ɗauki waya ta kira Sadik amma bai ɗauka ba, tana kiran Safeera ta ɗauka, Safeera ta ce, "Amaryar Rehaan, ya aka yi?." "Ban taɓa zagin ki bane, kar ki yi fatan na fara zagin ki yanzu." Safeers ta yi dariya jin ƙawar ta a fusace sai ta ce, "me ya yi zafi? Tuba nake ranki ya daɗe.” "Don Allah ki shiga gida ki duba min Hamma, na rasa ya zan yi, ki duba min shi kafin anjima na fito nazo na gansa" Da mamaki Safeera ta ce, "ki fito ina?." "Gidan mana." "Rufa mana asiri, kar ki fito don Allah.” "To na rasa ya zanyi, ina so na yi magana da Hamma, bazan iya zama Hamma yana fushi dani ba, yana ganin kamar na zaɓi kuɗi na bar sa. Bazan iya ba wallahi, dole na fito daga gidan nan, bazan iya cigaba da zama ban san halin da yake ciki ba." "Kwantar da hankalin ki, zan je na gano shi in sha Allah. In ki ka fito yanzu abin bai yi tsari ba, kuma za a fara yawo da ke ana cewa daga kawo ki jiya kin fito daga gidan, daman na ga kamar kakarsa da wannan maman ne kaɗai suke yi miki maraba a gidan." Islaha cikin rashin damuwa ta ce, "dukkansu basa gabana wallahi, abinda na ga dama shi zan yi, ko wanda ya ajjiye ni bai isa ya dakatar dani ba balle su, dan haka da su so ni, da kar su so ni duk bai damu islaha ba. Ke kin san daidai nake da kowa, ko babar ta sa ce fito na fito zan yi da ita, tunda ban ɗauke ta uwar miji ba.” Safeera ta sanyaya murya ta ce, "ban da dai babarsa, shi ɗin dai." "Ina faɗa miki ne ai ba wai dan zan yi ɗin ba, itama in ga zata kawo min abinda bazan ɗauka ba wallahi ta kanta zan bi na wuce. Ke Mama kaɗai na ke yiwa biyayyar dole, itama saboda Hamma nake ɗaga mata ƙafa." "Kwantar da hankalin ki Islaha, In dai Hamma ne yanzu zan je na duba miki shi. Ya za ki yi da aiki gobe?." "Zan zo." "Kamar ya?." "Kamar yadda ki ka ji. Kin ga, ni ba ta aiki nake yi ba, ki je ki duba min Hamma kafin na zo." Safeera ta ce, "sai na dawo" ta faɗa tana yanke wayar ita kuma ta miƙe jin tana son shan ruwa, kuma a ƙasa ta bar ruwan hakan ya saka. Tana ƙarasa sakkowa falon aka buɗe ƙofar ba tare da knocking ko an danna door bell ba, hakan ya saka gabanta ya faɗi ta tsaya cak a inda take tana kallon wajan har aka ƙarasa shigowa parlour. Da yake tana tsaye tana kallon wajen ana shigowa suka haɗa ido, gabanta ya faɗi, ta ɗan rufe ido ta buɗe tana sake kallon wajan........ Nana haleema. RDB3P06 Nana Haleema. Haɗa ido suka yi da ƙawar Mamy, bayanta kuma Mamy ɗin ce ta shigo tana amsa waya cikin ƙasarta ƙasarta. Islaha ta ɗan yi dumm dan ita bata san da wacce fuska zata karɓe su ba, bata san da me suka zo ba balle ta shirya musu, kuma duk ta gane fuskarsu, ta tuna yadda suka yi dasu a asibiti, da yadda komai ya faru, sannan tana lura da kallon da matar take yi mata, irin kallon raini da ƙasƙanci. Islaha ta ƙarasa tahowa falon cikin dakiya da son kawar da komai daga ranta, a lokacin Mamy ta sauke wayar ta ɗaga kai tana kallon Islaha. A daidai lokacin Islaha ta ƙaraso ta kalli Mamy suka haɗa ido, sai ta kawar da kai gefe ta rasa me zata ce musu, ta rasa da wacce kalma zata tarbe su tunda fuskarsu a ɗaure take, ta daure ta ce, “Sannu da zuwa, ina kwana.” Kafin Mamy ta yi magana ƙawar ta da suke kira sa Ammi ta ce, “in bata kwana ba za ki ganta ne? Ka ji min yarinya da karanbani? Kin manta rashin kunyar da ki ka yi mata a asibiti ko?.” Islaha bata ce komai ba, dan ba ita take kallo ba wani waje take kallo daban. Ammi ta ce, “Ki ka je ki ka yiwa kakar Rehaan asiri ki ka san yadda ki ka yi aka aura miki Rehaan har ki ka kwana a gidan nan, kina murna ke kin samu dami a kala ko? To ga ki ga gidan nan ai, sai mu gani in za ki samun ribar auren Rehaan ɗin. To in ba dan aikin asiri ba me Rehaan zai yi da le don Allah? Kalli Babar sa” ta faɗa tana nuna Mamy da take tsaye kawai bata ce komai ba. Ammi ta ce, “kamar ki latsata jini ya fito, saboda kyau da haske. Ki kalli ƙannensa, ke kin san ke ba sa’ar aurensa ba ce. Na rantse da Allah da ace na san ke za a aura masa, da sai na san yadda na yi na ɓarar da faruwar hakan kafin yau, ɓe Rehaan zai yi da ke saboda Allah? Ya zauna dake ya ce ya zauna da wa?.” “Matarsa!” islaha ta furta ba tare da ta sani, bata san ta faɗi maganar ba, kawai jin kalmar ta yi ta fito daga bakinta, yadda matar take jawabi tana wani zare idanu ne ya saka ta kasa riƙe magana, shiyasa ta ce mata haka dan ta ji me zata ce. Ammi ta ji shock na mamaki, ta buɗe baki kallon ta, sai ta kalli Mamy da take kallon Ammi ɗin ba Islaha, ta sake kallon Islaha ta ce, “rashin tarbiyyar ta ki za ki sake nuna min? Ni ki ke kallo ki ke cewa kece matar ɗana Rehaan? Ina matar tasa ta ke? A ina ki ka zama matarsa, ta suna ko ta rubutu?……” “Ki faɗa min wacce matar kirki ce za a kawo ta gidanta, miji yana wani wajen ko ina ta ke bai sani ba?……” Ta nuna Islaha da yatsanta ta ce, “ki kiyaye ni, in ki ka ce za ki min rashin kunya sai na saka an ɓatar da ke daga duniyar wallahi, ni ba sa’ar ki ba ce, ni matar former deputy gov of Adamawa state ce.” Sai a lokacin Mamy ta ce, “Ammi mu bar maganar nan haka.” Ammi ta juya tana kallom Mamy ta ce, “kina ji tana yi min rashin kunya? Wacece ita a garin nan da zan dinga faɗa ina faɗa kamar wata sa’arta? Wacece ita?.” Islaha ta sake zuwa wuya, ranta ya sake ɓaci daman a ɓace yake, ta buɗe baki zata sake yin magana sai ta fasa jin maganar Mamy. Mamy ta dafa Ammi ta ce, “ya isa haka, mu yi abinda ya kawo mu, kin san ina da baƙin da suke jirana.” Ammi ta yi ƙwafa tana hararar islaha sannan ta ce, “Daman so nake mu faɗa mata Rehaan ya fi ƙarfin ta, so na ke ta san sai dai ta zo a mai aikinsa ba dai matarsa ba, shiyasa na ce mu zo nan.” Mamy ta yi tsaki jin daman zuwan ba shi da mahimmaci ta takura mata akan su zo ta ce, “shine silar zuwan? Na yi tunanin wani abun ne ya saka ko ka ce na zo?.” “Warning nake so mu yi nata, kar ta saki jiki a gidan nan, dan gidan nan ba wajen zamanta bane. Sannan duk abinda ya samu Rehaan itace, kin san yaron nan ya tara maƙiya, tsaf za a haɗa baki da ita a cutar dashi.” Mamy ta ɗan kalli Islaha ta ga ta zubawa Ammi ido tana kallo, kamar zata yi magan sai ta fasa. A take wayar Mamy ta fara ƙara, tana ɗauka ta fita daga falon tana amsawa. Ita kanta Islaha da kallo ta bita, domin ba sai ance maka Mamy tana da kyau ba, ba sai ance maka mamy ta haɗa jini da india ba, kai kana gani ka san ita ɗin ƴar ƙasar waje ce. Ji ta yi an yi snapping fingers a kusa da fuskar ta, sai ta kalle Ammi ta ga tana harararta ta ce, “ba ki isa ba wallahi, yaranmu suna gida a zaune su basu zo wannan matsayin ba sai ke. Ba ki isa ki zo inda suka kasa zuwa ba, ba ki isa ya zama ke ce a nan su suna gida ba, sune suka dace da zama a nan bake ba, su ne suka dace da zama matar Rehaan ba ke ba. Ki rubuta ki ajjiye, sai na zama silar barin ki gidan nan, bana ƙaunar ganin ki ko kaɗan.” Islaha ta yi wani mayaudarin murmushi da ya tsaya iya fuskar ta, ta yi holding hannunta a ƙirji tana kallon ta ta ce, “ashe shiyasa ki ke ɗaga hankalin ki har ki ke wannan maganar, ashe na ki yaran ki ke so a ta ya a kawo su nan Allah bai yi ba. Ni ɗin da da ki ke ganin ban kai ba, sai gani a matsayin da na ki yaran basu zo ba, kuma babu wanda zai fitar dani sai Allah, ko yanzu na mutu, zan tashi da suna matar Rehaan.” Ammi ranta ya sake ɓaci ta kalle ta a fusace ta ce, “ni ki ke faɗawa wannan maganar banzar?.” Islaha ta ce, “na yi ƙoƙarin na girmama ki amma na gaza hakan, ban damu da wacece ke a gidan nan ba, ban damu da ke matar waye ba, kawai na so na tuna miki wani abu, akwai karin maganar da hausawa suke faɗa suna cewa in babban bai ji kunya hawa jaki ba, jaki bazai ji kunyar kayar dashi ba. Da kin riƙe kan ki mun gaisa lafiya da shikenan, amma kin kasa, sai da ki ka fito da abinda yake….” Maganar ta dakata saboda ganin Ammi ta ɗaga hannu zata mare ta, Islaha ta kauce gefe a daidai lokacin da Mamy ta dawo zata yiwa Ammi magana. Ammi ganin Mamy sai ta ce, “dukana za ki yi, rashin kunya da rashin ganin darajar manyan na ki har ya kai haka? Ni za ki ɗaga hannu ki kaiwa duka?.” Duk abinda ya faru bai taɓa ɓatawa Mamy rai ba sai a lokacin, sai ta ji ranta ya ɓaci, bata son ganin ana yiwa na gaba rashin kunya, lokaci ɗaya sai ta ji haushi Islaha a ranta. Tana so ta ga ana yiwa kowa biyayya, bata so ta ga ƙarami yana yiwa babba rashin kunya, yanzu sai ta fara jin haushin ko waye. Mamy ta ce, “me ki ke shirin yi? are you out of your mind?.” Ammi ta ce, “ƙyale ta ta dake ni, tunda bata da tarbiyya bata san darajar na gaba da ita ba. Mamy ta yi tsaki fuskar ta a haɗe ta ce, “let’s go please” ta faɗa tana fita Ammi ma ta bi bayanta. Islaha ta bisu da kallo bayan sun fita, ko kaɗan bata ji wani abu akan abinda ta yiwa Ammi ba, a ranta bata ji ta yi ba daidai ba, dan yadda take jin kanta Allah ko Mamyn ce ta yi mata sai ta mayar, ba son ɗanta take yi ba balle ta yi biyayyar dole. A nan ta yi sallae azahar, tana idawar ta sake jin ƙarar door bell, ta harari ƙofar a bayyane ta ce, “ni na gaji, barin gidan nan nake so na yi wallahi, Hamma nake so na je na gaji, bana son takura.” Maimakon ta miƙe sai ta gyara zama, ta kalli abincin da aka kawo mata ta harare sa ko buɗewa bata yi ba balle ta ci ko ta sha wani abun ba. Wani tsakin ta kuma yi jin an sake danna door bell, ta miƙe daƙyar ta buɗe lock ɗin. Mama ta sake gani a tsaye da housemaids ga a bayanta. Housemaids ɗin suka gaishe ta, bata iya amsawa ba ganin kamar bata cancanci amsawa ba tumda ita matar bogi ce, suka shiga suka ajjiye mata abincin. Sun juyo zasu fita Islaha ta ce, “ku tafi da wannan ma.” Cikin gimamawa suka amsa, suka ɗauka suka fita dashi. Islaha ta kalli Mama ta yi murmushi ta ce, “ina yini.” Mama ta yi murmushi tana dafata ta ce, “Islaha ba dai ba ki ci abincin ba?.” Islaha ta ɗan kalle ta ta ce, “bana jin yunwa.” “Ki kwana ki tashi kuma kice bakya jin yunwa? Ko akwai matsala ne?.” Ta girgiza kai alamun babu komai. Mama ta ƙarasa shigowa cikin parlour sannan ta mayar da ƙofar ta rufe ta ce, “ko rashin zuwa Rehaan ne ya saka ki ƙi cin abincin?.” _Ji wata magana, to kar ya zo mana, ya shekara bai zo ba in ya ga dama. Ina ruwana da zuwansa? Mtsww! Ni ba ku san ko ganinsa bana son yi ba, ba ku san zaman kuɗi kawai nake yi a gidan nan ba._ Ta faɗa a ranta tana jin haushin kalaman Mama, amma bayyane sai ta ɗauke kai bata ce komai ba. Mama ta ce, “kar ki damu, zai zo in sha Allah. Kin san ya raina kakarsa, ba wani ganin darajarta take yi ba, kuma Mamy tana goya masa baya, bata son laifin ɗanta, ko kaɗan bata son ta ga an ɓata masa rai. Sai kin yi haƙuri, amma za ki sha fama daNadira, dan baƙin hali ne da ita.” Sai a lokacin Islaha ta ɗaga ido ta kalli Mama, Mama ta ɗaga mata kai alamun tabbatarwa sannan ta ce, “Kar ki damu, ina bayan ki a ko yaushe a cikin gidan nan, duk abinda ki ke buƙata ki nemi ɗaya daga cikin masu aikin gidan ki ce a raka ki wajan Mama, sai mu yi magana.” Islaha ta yi murmushi dan haka kawai matar ta burge ta sosai, ta san darajar ɗan adam, kuma ta lura tana da kirki, kuma tana ƙaunar ta tsakani da Allah da zuciya ɗaya. Daga ita sai Daada ne kaɗai suke nuna mata ƙauna, duk da ba zama ta zo yi a gidan ba, amma ta ji daɗin yadda matar take nuna mata itama mutum ce. Islaha ta ce, “To Mama, na gode sosai.” Mama ta dafa kanta ta ce, “kar ki damu Islaha.” Ta yi murmushi bata ce komai ba. Mama ta ce, “Ki ci abinci, kar ki zauna da yunwa kin ji?.” Ta ɗaga kai alamun to. Wayar Mama da take hannunta ta yi ringing, tana dubawa ta ga Sameer ne, sai ta ɗauka ta saka a kunne ta ce, “Ina aparment ɗin Rehaan.” Daga haka ta yanke wayar ta kalli Islaha ta ce, “Zan Koma Islaha, Amma za ki fito in anjima ko?.” Islaha ta kalle ta alamun me zan yi in na fito, Mama ta ce, “Za a kai amarya Riyya, sannan a gidansu Jafar za a yi buɗar kai da ajo, ki fito in anjima sai mu je gabaɗaya.” Islaha ta ɗaga mata kai bata ce komai ba, dan gaskiya babu inda zata je… Nana Haleema. RDB3P07 Nana Haleema. Mama ta fara nufar ƙofar da niyar fita, Islaha ta bi bayanta a hankali da niyar rakata bakin ƙofar, dan tana yi mata kirki sosai, kuma husawa sun ce ka gaida mai gaishe ka. Tana buɗe ƙofar suka haɗa ido da saurayin da yake tsaye a jikin ƙofar, hannunsa riƙe da wata yarinya sanye da ƙananun kaya. Mama ta ce, “nan ka biyo ni?.” Sameer ya ce, “sauri nake yi ne Mama.” Mama ta kalli Islaha ta ce, “Ga Yayan Rehaan, sunansa Sameer.” Islaha ta ɗago ido suka sake haɗa ido ta ce, “ina yini.” Ya yi murmushi ya ce, “Islaha ko?.” Islaha ta sake kallon sa tana ɗaga kai alamun haka ne. Ya yi murmushi ya ce, “na san ki a social media, ina bibiyar programs ɗin ki sosai, all the best.” Ta sake yin murmushi kaɗan ta ce, “na gode.” “Mama Rehaan yana nan?.” Suka ji muryar Salman daga bayansu, a suka kalli wajan ganin Salman ne a tsaye yana kallonsu. Mama ta haɗe rai, ta kalle sa kallo irin na ƙyama ta ce, “ba ya nan, ka tafi.” “Ga wajansa nan a buɗe, ni dai sai na shiga.” Sameer ya ce, “kai mahaukacin banza, ba ya nan matarsa ce a ciki.” Salman ya kalli Islaha da take kallonsa ya ce, “ke ce matar sa?.” Bata amsa ba sai kallonsa kawai take yi, tana tuna kalamansu Mama da suke cewa mahaukaci zata aura. Mama ta ce, “Sameer ja shi ku je, kar ya ɓata min rai.” Sameer ya ce, “wuce mu je.” Tare suka tafi yana ta waiwayowa yana kallon wajen Rehaan. Mama ta ce, “Yana da taɓin hankali, ba shi da lafiya sai kin kula, kar ki dinga barin ƙofar ki a buɗe, kar ya shigo miki.” Islaha ta ɗaga kai ta ce, “To Mama.” Daga haka Mama ta tafi ita kuma ta koma. Tana shiga falon a bayyane ta ce, “Daman shine mahaukacin da su Mama suke faɗa? Su a tunanin su wannan na aura?……” Ta girgiza kai ta ce, “Da yake basa ƙaunata, na zo na auri mahaukaci salon kawai ya kashe ni, da yake bani da gata, marainiya baiwar Allah….” “Allah sarki, amma ya bani tausayi sosai.” Sai kuma ta tuna da Hamma, ta zabura ta ɗauki wayarta ta kira lambar Safeera amma shiru bata ɗauka ba, ta sake kiran Sadik bai ɗauka ba. Ta yi tsaki ta dafe kai dan gaskiya in aka kuma jimawa bata samu kowa a waya ba wallahi sai ta fita ta je wajan Saheer, sai dai duk abinda zai faru ya faru, ita kam ta gaji wallahi. Rehaan tunda ya saka waya a dnd bai yi ganganci ya cire ta ba, duk tarin kiran da Abba yake yi masa yana gani amma bazai iya kiransa ba, dan ya san maganar akan Islaha ne. A guest house ya yi baccinsa, baayan ya yi sallar asuba ya sake kwanciya bayan ya rufe ƙofa dan kar ma Jazy yazo ya dame sa. Ko kaɗan ba ya tunanin ya yi wani aure balle Islaha, hankalinsa a kwance yake baccinsa. Sai bayan sallar azahar ya tashi, yana zaune a gefen gado ya dafe kansa da hannayensa jin jijiyoyin kan suna harbawa, ya miƙe daƙyar ya shiga wanka ya fito ya shirya ya fito falo. Danna wayarsa ya yi da take gefe, ya ga tarin kiran da aka yi masa, ya ɗauke kai sai kuma ya ji ana knocking ƙofar. A haka ya miƙe ya buɗe ƙofar, chef ya shigo da tray a hannunsa ya ajjiye masa ya koma. Rehaan ya buɗe abincin ya ga american dishes ne, ya bi abincin da kallo kamar mai neman wani abun a ciki, kafin ya ɗauki ice matcha yana sha, sannan ya ci abinci. Wayarsa ya ɗauka ya kira chef ɗin ya dawo ya ɗauke kayan da ya yi amfani, shi kuma ya miƙe ƙafa akan center table ɗin yana duba waya yana ganin tarin kiran wayar da aka yi masa. Sai a lokacin ya cire wayar daga dnd, yana sake duba mutanen da suka kira shi da waɗanda suka yi masa messages, sai kuma ya buɗe mail ɗinsa nan ma ya yi karo da mails ɗin da dole ya buɗe. Ya gama karanta ya ajjiye wayar a gefe yana ganin kira na shigowa amma bai iya ɗauka ba. Jin an buɗe ƙofar ya saka ya ɗago kansa dan ya san daman sai Jazy ɗin, dan shine yake da spare key ɗin da zai buɗe ya shigo without knocking. Jazy ya ƙaraso da waya a kunnensa yana magana yana kallon Rehaan sannan ya ce, “Ga shi nan Abba.” Abba ya ce, “saka wayar a speaker..” Jazy ya yi yadda Abba ya ce, daga can ɓangaren Abba ya ce, “Rehaan.” Rehaan ya gyara zama ya ce, “Abba ina kwana.” Abba bai amsa gaisuwar ba ya ce, “Yanzu Rehaan baza ka ta ya ni yiwa mahaifiyata biyayya ba? Ashe daman za ka iya ƙin ɗaukar wayata, kamar ni ace ina kiranka kana kallo ka ƙi ɗauka? Kana cikin hankalin ka kuwa?.” Ray ya ɗan rufe ido amma bai ce komai ba, dan shi kansa ya san bai kyauta ba, amma babu yadda zai yi. Abba ya ce, “kana kallon kirana yana shigowa wayarka baza ka iya ɗauka ba? Ka ga messages ɗina duk ka yi banza saboda na yi maka dole akan abinda ba ka so ko?.” Ray cikin sanyin murya ya ce, “ka yi Abba, ba haka bane, na kwana bani da lafiya, yanzu haka ma kaina ciwo yake yi.” “Meyasa ba ka ɗauki wayar ka faɗa min haka ba? Da ka faɗa min zan takura ma ka da kira ne?. Kai ka san halin Daada, kasan yadda ta ɗaukaki auren nan, ka san yadda take son yarinyar nan, ka san yadda ta saka auren a ranta, dole in ba ka zo ba ranta zai ɓaci. Ta ya ina lallaɓata mu rabu lafiya kana neman ɓarar da albarkar da nake tattalinta? In kai ne Mamy ta ke yiwa ɗanka haka za ka ji daɗi ace yana misbehaving kamar yadda ka ke yi min? Ina alƙawarin da ka yi min akan auren nan Rehaan!?.” Kafin ya yi magana ya ce, “dan ka raina ni ko? Har ina kiran ka a waya ka ƙi ɗauka, da yake ba Nadira ba ce ba ko? Inda itace na tabbata baza ka taɓa ƙin ɗaukar kiranta ba, tunda ita itace ta haife ka ni kuma ka ajjiye ni?.” Ray jin Abba yana yi masa faɗa sosai sai ya yi sanyi ya ce, “ka yi haƙuri Abba, don Allah ka yi haƙuri.” “Haƙuri ya zama dole na yi Rehaan, tunda ka ɓatawa mahaifiyata rai nima ka ɓata min rai. Ko dan saboda idanun ƴan bikin da suke gidan ya kamata ace kazo ka kwana a gida, amarya guda aka kawo maka, amarya ce kamar ko wacce amarya, amma sai ka saka waya a dnd dan ka nunawa mutane kai ba sonta ka ke yi ba, ka nunawa mutane nima ɗin ban isa da kai ba, tunda ba Nadira ba ce dole ka ƙi ɗaukar kirana.” “Ka yi haƙuri Abba, ban yi dan ranka ya ɓaci ba.” Abba cikin ba da umarni ya ce, “Ka tabbatar da a gida ka yi sallar magrib, ban yarda ka je ajo ko buɗan kan Riyya ba, ka dawo gida ina nan ina jiran ka. Kar ka kawo min wani uzuri, wallahil azim bazan yarda da shi ba Rehaan.” Ray jin yadda Abba ya rantse ya ce, “in sha Allah, zan zo kamar yadda ka ce.” Daga haka Abba ya kashe wayar, Jazy ya saka wayar a aljihu yana kallonsa. Rehaan cikin wani irin yanayi ya ce, “wanne tsautsayi ne ya kai ni amincewa da auren nan oho, har an fara bani ciwon kai.” Jazy ya ce, “laifin ka ne, meye dan ka je gidan ka kwana a inda ka saba kwana? Akwai abinda zai cinye ka ne?.” Ray bai ce komai ba, sai kuma ya kalle Jazy suka haɗa ido ya sake ɗauke kansa daga kallonsa. Jazy ya ce, “haka kawai ka jawo an ce baza ka je wajan Ajo ba, daman haka ka ke so ai, sai ka je ka zauna da matar ka a ci amarci” ya faɗa yana dariyar shaƙiyanci yana ɗauko magani a aljihunsa. Jazy ya kalle sa ya ce, “Maleek da Ubaid sun koma Jeddah, sun so su haɗu da kai na ce bacci ka ke yi.” Bai san dalili ba, bai san meyasa ba, haka kawai ya ji gabansa ya faɗi ambatar sunan Ubaid da Jazy ya yi, ya lumshe ido yana tuna haɗuwarsu ta ƙarshe da Ubaid a ranar dinner Riyya, yana ta sake maimaita masa missing ɗin Islaha da ya yi, yana faɗa masa how sweet she was da sauran su. Ya ja tsaki, ya cize bakinsa bai ce komai ba. Sai kuma ya kalli Jazy ganin yana shan magani ya ce, “wannan fa?.” “Na masu aure ne.” “Meye shi?.” “Magani.” “Na meye?.” “Na gyaran aure.” “Like how?.” Jazy ya ce, “kai fa baka gane yare cikin yare ko? To na gyaran hanya ne.” Ray ya sake yin jim ya ce, “ban gane ba, yi min bayani.” Jazy ya yi ƴar dariya ya ce, “kai banza ne, ba ka gane magana sai an yi maka filla filla. Ina sha saboda ƙanwar ka Riyya, just for honeymoon.” Ray sai a lokacin ya ɗau haske ya fahimci inda Jazy ya dosa, sai kuwa ya haɗe rai ya miƙa hannunsa ya buge maganin daga hannun Jazy. Maganin ya faɗi ƙasa ya zube, Rehaan cikin ɓacin rai ya ce, “ba ka da hankali, kashe ta zaka yi?.” Jazy ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, “sabuwa mota ai sai sa lubraciation, ka taɓa ganin an hau sabuwar mota babu gyara?…..” Jazy ya kalli maganin ya ce, “Kawai ka zubar min da magani, ka san wahalar da na sha kafin na same sa?.” Ray ya sake ɗaure fuska alamun babu wasa ya ce, “ba wasa nake yi maka ba, ka daina wannan shirmen, in wani abu ya sanu Riyya sai na yi repoting ɗinka a court, Allah sai na nuna maka kuskuren ka. Ba ka da hankali ashe ban sani ba?.” Jazy ya yi dariya son ransa sannan ya ce, “Ka ga mai ƙanwa, kai ga big brother ko? Kaima ka sha ko za ka ga amfaninsa a wajan matarka.” Banza ya yi masa bai ce komai ba, Jazy ya cigaba da abinda yake yi. Ray ya sake kallonsa suka haɗa ido ya ce, “Jazy…” sai kuma ya fasa ya gyaɗa kai bai ce komai ba. “Malam meye? Matata ce fa, ina ruwan ka da shiga tsakanin mata da miji? Ban da saka ido ina Yayan mata zai dinga sakawa mijinta ido?.” Bai ce masa komai ba ya sauke numfashi yana girgiza kai, damtabbas sai ya nuna masa kuskurensa in ya cutar masa da ƙanwa, Allah sai y bashi mamaki. Jazy bai jima ba ya tafi saboda shirye shirye, shima Rehaan sai da ya yi sallar Magrib sannan ya shirya ya fito. Yana shiga gidan ya tarar duk matan gidan basa nan, gidan shiru duk an watse an tafi gidansu Jazy ana wani bikin a cam. Kai tsaye wajan Abba ya wuce, yana shiga ya same sa a zaune shi kaɗai yana danna waya. Ray ya ƙarasa ya zauna ya ce, “Abba ina yini.” Abba ya bi shi da kallo sannam ya ce, “Ka kyauta Rehaan, na gode da abinda ka yi min, ka nunawa mutanen gidan nan ban isa na saka ka ka yi ba, ka nunawa duniya ba ka son auren nan.” “Ka yi haƙuri.” “Dole ka ba ni haƙuri, tunda ka riga ka aikata.”Bai ce komai ba kansa dai yana ƙasa dan ya san ya ɓatawa Abba rai. Abba ya ce, “ka je ka taho da matar taka, ku same ni a ɓangaren Daada.” Ya ɗaga kai dan babu damar yi masa musu, yadda ran Abba ya ɓaci bazai musa masa akan abinda ya ce ba. Bai ce komai ba ya miƙe ya nufi ɓangarensa, yana tunanin yadda zai kira Islaha ya ce ta zo in ji Abba, da wannan tunanin ya shiga jikinsa babu daɗi. Nana Haleema. RDB3P08 Nana Haleema. Islaha tana zaune tana kuka wayarta tana kusa da ita ta saka a speaker tana jin duk abinda Safeera take faɗa mata akan halin da Hamma yake ciki. Safeera ta ce, "Don Allah ki bar wannan kukan, na faɗa miki ya samu lafiya har sun dawo gida." Cikin kuka ta ce, "Safeera in mutuwa Hamma ya yi ki faɗa min, ku daina ɓoye min don Allah." "Wallahi yana nan da rai, kuma ya samu lafiya sosai, ki daina kukan nan don Allah." Islaha ta ce, "yana jin haushina, yana gani kamar na ci amanarsa, yana gani kamar na zaɓi kuɗi na bar sa. Wallahi zuciyata cike take da danasanin auren nan, danasani nake yi sau babu adadi. Na gaji Safeera, kawai ina so a yi ta ta ƙare, kowa ya kama gabansa. Haba!Ina so na ga Hamma amma wannan ƙaddarreen auren ya ɗaure ni tamau a gidan nan, wanne irin halacci ne Hamma bai yi ba, wacce irin soyayya da ƙauna ce Hamma bai gwafa min ba? Kuma a ce da abinda zan saka masa kenan? Wallahi da ban cika ƴar halak ba......." ta dakata da maganar tana kuka. Sai kuma ta dakata da kukan ta ce, "Ko dai daman ni ba ƴar halak ɗin bace ba Safeeta?." A tausahe ta ce, "Haba Islaha! Ki daina wannan maganar don Allah, duk abinda ki ka aikata kin yi ne saboda shi, kin yi ne dan ki kuɓutar dashi daga hannun masu garkuwa da mutane. Ki nutsu don Allah, na tabbatar zai saurare ki komai ya dawo daidai." "Aure fa na yi Safira, wani daban na aura ba shi ba. Kar ki manta ranar da ya dawo gida ranar na taho gidan nan, ko gaisawar kirki ba mu yi ba. Ga wahalar da ya sha a hannun kidnappers, ga rashin lafiyar da ya yi, kuma yana dawowa gida ya tarar na yi aure zan tafi gidan wani ba shi ba. Wallahi ina tantama a kan asalina, ina tantama sosai." "Tantamar me ki ke yi?." "Ina ji a zuciyata anya ta hanyar aure aka same ni?." "A'uzubillahu! Wannan wanne irin ƙazamin tunani ki ke yi?." "Safeera gaskiya ce, duk ɗan halak bazai yi abinda na yiwa Hamma ba, shiyasa nake tantamar anya ni ƴar halak ce?. Ke kin san waye Hamma a wajena, kin san irin ɗawainiyar da ya yi dani a rayuwarsa ba sai na faɗa ba, ranar da dawo daga wajen kidnappers ranar na bar gidan. Abin ya yi yawa, ban kyauta masa ba wallahi.” Safeerw ta ce, "Ke ƴar halak ce, ki daina wannan banzan tunanin. Sadaukar da rayuwarki ki ka yi saboda shi, babu macen da zata iya ganganci da rayuwarta akan namiji kamar yadda ki ka yi. Kina son Saheer kowa ya sani, shiyasa ki ka yi duk abinda ki ka yi saboda ya samu kuɓuta ya dawo gare ki, kuma kin yi nasara ga shi ya dawo. Don Allah ki nutsu, ki bari a kwana biyu sai ki zo ku yi magana, zai fahimce ki yadda ya kamata." Islaha bata ce komai ba sai kuka take yi mai sauti, Safeera ta ce, "ki daina kuka don Allah, ki yi haƙuri komai zai wuce." Islaha bata daina kuka ba sai jan numfashi take yi, sai kuma ta lumshe ido ta ce, "ni zan yi cancelling contract ɗin nan, bazan iya zaman wata biyar a nan ba. Kwana ɗaya da na yi ji nake yi kamar a gidan yari nake, bazan iya zaman sati ɗaya ba balle na wata biyar, bazam iya ba Safeera." "Dole ki yi haƙuri ki zauna, zama ya kamaki Islaha, dole ki zauna ko bakya so." Katse kiran ta yi ta kifa kanta a kan kujera tana kuka sosai. Rehaan yana tsaye a falon bata san yana nan ba, duk abinda take faɗa yana jinta kuma yana kallon ta. Ya yi tsaki ya bita da kallo ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita, kukan da take yi ne ya saka har ya shigo ta san ya shigo ba, amma da zata ji motsinsa ko ya ya ya ke. Ya shafa kansa kaɗan, ya hau sama ba tare da ya faɗa mata saƙon Abba ba, bai jima ba ya sakko, footstep ɗinsa ya saka ta kalli wajan suka haɗa ido dashi. Bata ɗauke ido daga kallonsa ba, shi kuma ya janye idanunsa daga cikin nata yana sakkowa inda take a hankali. Islaha ta miƙe tsaye tana jira ya ƙaraso dan tana da case da shi, yana ƙarasowa zai gifta ta inda ta ke cikin murya mai sanyi da rauni ta ce, "Can we cancel the contract? Gaskiya bazan iya zama a gidan nan na sati ɗaya ba balle kuma wata biyarc Ina buƙatar barin gidan nan da gaggawa, ina da abubuwan da zan yi wanda bazan iya yinsu daga nan ba, kuma sun fi zaman yarjejeniyar nan mahimmaci a gare ni, allow me to go, na yi maka alƙawarin zan baya ka kuɗinka.” Shi dai kallon ta kawai yake yi ganin ta wani firgice, kana kallon ta ka san ta ci kuka ta gode Allah, ya yi nata shiru bai tanka ba dan ba shi da lokacin wannan wasan na ta. Ganin bai ce komai ba sai Islaha ta ce, "zan iya yin aiki a ƙarƙashinka har sai ka cire kuɗin da ka ke bina, amma mu kawo ƙarshen contract ɗin nan, sannan ka sake ni islamically." Wani kallon up and down yake yi mata jin tana raina masa hankali, sai ya kawar da kansa gefe ya sake kallon ta sannan ce, "let's go" ya faɗa yana wuce ta. Islaha bata motsa daga inda ta ke ba ta ce, "zuwa ina?." Ya waiwayo ya sake kallon ta idanunsa suna yawo akan fuskar ta, jin rainin hankalin tambayar da ta yi masa ya saka ya ce, "siyar da ke." Islaha ta buɗe idanunta waje tana kallonsa ta ce, "za ka iya ai, waye ya sani ko sana'ar ka ce?." Bai sake kallon ta ba dan ba shi da lokacinta ya ce, "let's." "Bazan fita ba sai an faɗa min inda za mu je, ka faɗa min ina za mu je sai na biyo ka, in ban ji dalili ba babu inda zan je." Ya girgiza kai bai ce komai ba, dan shima bazai faɗa ba sai dai a fasa zuwa wajan Abban gabaɗaya. Ya dawo da baya zai koma sama sai Abba ya kirasa a waya, yana ɗauka Abba ya ce, "kuna ina ne? Jiran ku muke yi fa." Ray ya kalle ta sannan ya ce, "Ta ce baza ta zo ba Abba." Islaha ta ɗan buɗe har tana dafa ƙirji jin sharrin da ya yi mata, sai ta dabarbace ta ce, "ni ban ce bazan je ba." Jin abinda ta ce sai ya yanke wayar yana yi mata kallon akace ba ki da kunya. Islaha ta harare shi ta ce, "kai na cewa bazan je ba sai ka faɗa min inda zaka kaini ba shi ba, ka daina yiwa mutane sharri kana faɗar abinda basu faɗa ba, kuma ko babu komai yanzu na san inda zamu je." Shi dai bai ce mata komai ba ya fita, ta bi shi da harara ta ɗauki mayafinta da aka kawo ta da shi jiya ta saka ta biyo bayansa bayan ta rufe ƙofar. Sai a lokacin ta ke kallon ɓangaren nasa, daban yake a cikin gidan, ga shi babba kamar gida mai zaman kansa, har gate ne da shi kamar ba a gidan ba, ga wajan ajjiye mota a ɓangaren kamar. Ɗawisu ta gani suna ta yawo, sai tattabaru da suke ta zagawa a wajan alamun a wajan ake kiwon su. Ta jikin gate ɗinsa ta ga wani apartment iri ɗaya da na kowa na gidan, dan ɓangrensa ne kawai ya fita daban kamar ba a gidan yake ba. A lokacin ta ga ya ƙarasa aata ƙofa ko waiwayonta ba ya yi, ta ɗaga ƙafa da sauri ta ƙarasa, yana buɗewa ya shiga ta bi bayansa da sallama a bakin ta. Tana shiga Daada ta tarbe ta da fara'a har tana tafi tana faɗin, "Ga Ishlaya, barka da zuwa. Ƙaraso nan ku zauna kusa dani." Islaha dai kanta yana ƙasa tana murmushi, dan Ishlaya ɗin nan yana bata dariya, ko bata yi niyar dariya ba indai zata ce Ishlaya sai ta yi dariya, ta ƙarasa inda Daada take ta zauna a ƙasa. Daada ta dafata ta ce, "Ishlaya ya na gan ki kamar kin yi kuka, lafiya?." Islaha ta girgiza kai ta ce, "Lafiya lau, Barka da dare." Daada bata amsa gaisuwar ba ta ce, "ban yarda ba, ko wannan mara kunyar ne ya yi miki wani abun?." Islaha ta girgiza kai alamun a'a amma murmushi take yi. Daada ta ce, "duk abinda yake damunki ki zo ki faɗa min, in akwai abinda ki ke so ina nan ina jiran ki, kar ki dinga takura kan ki, kin ji ko?." Islaha ta ɗaga kai alamun to nan ma bata ce komai ba. Daada ta ce, "ya zaman baƙunta?." "Alhamdu lillah." Islaha ta kalli Abba da yake yiwa Rehaan magana ta ce, "Ina yini." Abba ya kalle ta da murmushi ya ce, "Lafiya lau, Islaha ko?." Islaha ta amsa da eh dan babu yadda zata yi, da wani ne daban bazai yi gangancin yi mata wannan tambayar ba. Daada ta ce, "na kira ku nan ne dan na yi mu ku nasiha, kuma na ba da amanarta a hannun ka." Sai ta kalli Rehaan da ya ke danna wayarsa ta ce, "Kai ba danna waya na kira ka ka yi ba." Ray ya ɗago ya ɗan kalle ta sai ya ajjiye wayar ya haɗe hannayensa waje ɗaya. Daada ta ce, "Ga amanar mata nan na ba ka, in ka cutar da ita Allah bazai bar ka ba, in ka wulaƙanta ta ina so ka san babanka ka wulaƙanta, in ka yi mata wani abun da ya sosa ranta ina tabbatar maka da ga wanda ka yiwa nan a zaune. Ka riƙe ta hannu biyu, ku yi zaman lafiya daga nan har a tashi duniya, ka ji ko?." Kamar ba da shi take magana ba, sai da ta ɗan jima da magana maganar sannan ya ɗaga kai alamun ya ji. Daada ta kalli Islaha ta ce, "kar ki damu da yadda auren yazo, ki yi haƙuri ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce, kin ji?." Kamar yadda bai yi magana ba itama bata yi ba, ta yi murmushi kawai. Daada ta kalli Rehaan ta ce, "na san iyayenka sun dawo daga kai ƙanwar ka, ka shiga da ita ɗakin ko wacce su gaisa ka gabatar mata dasu." Bai ce komai ba ya dai kalli Daada kawai kafin ya ɗauke kai, ya rasa meyasa ko yaushe sai ta ƙirƙiri abinda ta san ba ya ƙauna. Daada ta kalli Abba ta ce, "Ba ka ce komai ba." Abba ya yi murmushi ya ce, "Allah ya ba da zaman lafiya, Allah ya ɗorar da zaman har abada." _Ba amin ba, zaman nan bazai taɓa ɗorewa ba in Allah ya yarda._ Islaha ta faɗa a ranta tana jin addu'ar ta yi mata nauyi sosai, shi kansa Rehaan abinda yace kenan, yana girgiza kai dan ba addu'ar da zai ce amin ba ce. Daada ce kaɗai ta amsa da amin tana fara'a, ta sake kallon Islaha ta ce, "an kai miki abinci?." Islaha ta ce, "Mama ta kai min da kanta. Daada ta washe baki cikin jin daɗi ta ce, "Saddiƙa ƴar albarka kenan, tana ta ɗawainiya da ke a gidan nan, na san daman in ba ita ba babu wanda zai kula da lamarin ki. Har gwara ma ta tsakiyar da ta ƙarshe za su kwatanta abin arzuƙi da daddatko irin na fulani, amma ta biyun ƙarshen nan daman ba halin fulani ne da ita ba, balle ta san kara da datattakun su." Babu wanda ya tanka mata a cikinsu, sai Rehaan da ransa ya ɓaci, ba ya son wannan baƙar maganar da take yawan faɗawa Mamy a a gaban ko waye, amma bai tanka mata ba ya share ta. Abba ya kalli Ray ya ce, " ku je wajansu, in kun dawo ka zo ina neman ka." A ciki Rehaan ya amsa da to ya miƙe tsaye ba tare da ya kalli Islaha ba. Daada ta ce, "ku je ku gaisa da mutanen nan gidan." "To Daada, a huta lafiya" ta faɗa tana miƙewa ta fita, shi tuni ma ya fita daga falon ta biyo bayansa tana harararsa. Daada ta bita da kallo tana murmushi har ta ɓace daga ganinta ta ce, "Ya ka ke ganin haɗin nan don Allah? Ba ka ga sun dace da juna ba?." Abba ya yi murmushi da son faranta mata rai ya ce, "sun dace kam, in zamansu ya fara daɗi da wuri zasu manta da yadda auren ya zo." Sai Abba ya sake faranta mata rai ta sake yin dariya ta ce, "ina ji a jikina hakan zai kasance, hakan ne ma zai faru in Allah ya yarda." Abba ya amsa kawai yana murmushi, tunda tana so dole ya biye mata, tunda abinda take so kenan haka zai biye mata ko da shi ba ya so. Dan Allah ya sani tunda Rehaan ba ya son auren shi kansa ba wani so ɗin yake yi ba, kawai dai yana biye mata ne, kuma sannan ya yaba da hankali da nutsuwar yarinyar. Burinsa ɗaya, kar a haɗa kai da ita a cutar da Rehaan, dan maƙiyansa ta ko ina zasu iya kawo masa farmaki.      Islaha bin bayansa take yi tana kallon gashinsa da ya sauka har wuyansa, duk da a ɗaure yake amma yana taɓa wuyansa, hannunsa riƙe da waya yana tafiya yana dubawa. Sai kuma ta ga ya tsaya yana duba wayar kafin ya cigaba da tafiya a hankali kamar ba shi da jini. Islaha bata san ta yi tsaki ba ta harari bayansa ta ce, "sai ɗan banzan iyayi kamar mace, kalle sa don Allah yana tafiya kamar wanda ba shi da jini. Abin takaici, na cuci kaina da na amince da wannan abin." Nana Haleema. RDB3P09 Nana Haleema. A lokacin Islaha ta ga yara ƙananu sun zo da gudu sun riƙe sa, su huɗu ne mata biyu. Sai ta ga ya mayar da wayar aljihu ya riƙe su duka yana maganar da bata jin me yake faɗa ba, yadda yake harkar gabansa kamar ya manta da ita, ya riƙe hannun yaran sun nufi ɓangaren Mama kai tsaye. Ɗaya daga cikin yaran ne ta juya ta kalli Islaha, sai ta yi murmushi ta ce, "Uncle she is your wife?." Islaha ta buɗe ido cikin mamakin ganin yarinya yar ƙarama har ta iya magana da ingilishi. Ray ya ɗan waiwayo ya kalli islaha, ya ɗauke kai kalli yarinyar ya ce, "who told you?." Yarinya ta ce, "Daada." Ya sauke numfashi bai ce komai ba suka cigaba da tafiya. Sai da zai ya yi pushing glass door ɗin falon Mama sannan ya kalle ta, ya ga tana tahowa kamar bata son ƙarasowa, ga wani kallo da take jifansa dashi kamar zata rufe sa da duka. A haka ta ƙaraso, ya yi pushing ƙofar suka shiga da sallama. Mama dawowar ta kenan daga event ko mayafi bata ajjiye ba. Ganin Rehaan da jikokin gidan ga kuma Islaha a baya sai ta saki fara'a ta ce, "amarya da ango ne da kansu? Ahh lallai ina da manya-manyan baƙi, sannun ku da zuwa." Islaha ta ƙarasa kusa da ita ta zauna Mama ta ce, "Islaha ya zaman baƙon waje?." Islaha ta yi murmushi kawai bata ce komai ba, Mama ta kalli Rehaan ta ce, "Yarinyar nan akwai tarbiyya ga kunya." Ya ɗauke kai kamar bai ji ba, ya cigaba da kallon yaran dan ba shi da lokacin kallon Islaha. Mama ta ce, "kamar yadda na faɗa miki, ni ake kira da Mama, ni ce babba a gidan nan. Ga shi kin zo ƴan uwan Rehaan ɗin duk suna wajan biki, balle ku gaisa." Islaha bata ce komai ba sai murmushi a zahiri, amma a baɗini takaici ne ya mamaye mata rai, dan zama waje ɗaya da Rehaan ma ɓacin rai ne. Rehaan ya miƙe ya ce, "zamu je wajan Umma." Mama ta ce, "ya kamata kam, sai kun fito." Bai amsa ba ya fita, Islaha ta bi bayansa tana ji kamar ta jawo sa ta dinga duka har sai ya daina numfashi saboda haushinsa da take ji. Mama ta bisu da harara ta ce, "shashashan banza, ai ba a banza na bari aka yi bikin nan ba, ina da ƙudurina a kan hakan. Yarinya sai iya bariki, bayan ta gama yawon banzan ta, ta san maza, maza sun santa, shine zata dinga wani sunkuyar da kai in ana magana? Mtsw Zan yi maganin ku wallahi, da kai da ita duk a hannuna ku ke."    Wajan Umma suka shiga, suka same ta a zaune ita da Salman yana cin abinci. Salman yana ganinsu ya miƙe tsaye, Rehaan ya yi murmushi ya ƙarasa kusa da shi ya ce, "Ina nawa abincin?." Salman ya miƙa masa nasa da ake ba shi, Rehaan ya yi murnushi ya zauna kusa da shi. Ya kalli Umma da ta wani haɗe rai ta kawar da kanta gefe, suka gaisa da Rehaan tana amsawa kamar an yi mata dole, sannan Islaha ma ta gaishe ta ta amsa a fizge. Salman ya nuna Islaha ya ce, "wace wannan?." Rehaan ya kalli Islaha suka haɗa ido, ya ɗauke kai ya kalli Salman kafin ya yi magana Salman ya ce, "ɗazu da na je ban ganka ba amma na ganta, in na je zan dinga ganinta? Ta yi kama da Dora ta cikin cartoon...." Ya faɗa da sigar da Rehaan zai gane wacce yake nufi. Rehaan ya ɗaga masa kai yana kallonsa, shi kuma ya ce, "Ni dai ina sonta." Rehaan ya yi murmushi cikin ko in kula da kalaman Salman ya ce, "kana sonta?." Salman ya ɗaga kai ya ce, "ina sonta."  Rehaan ya kalle ta ya ga ta zubawa Salman ido tana kallonsa, ya sake kallon Salma ya ce, "itama ta ce tana sonka, kuma za ka iya zuwa ko yaushe ku gaisa, daman ƴar uwarka ce, kai da ita babu banbanci...." ya ƙarasa faɗa a hankali yadda ita kaɗai zata ji, yana kallon ta dan da biyu ya faɗi maganar. Salman ya yi dariya yana juye abincin a jikinsa saboda dariya, Rehaan ya karɓi bowl ɗin yana ya saka spoon yana kwashe wacce ta zube a jikinsa. Salman da yake kallon Islaha ya riƙe hannun Rehaan ya ce, "zan zo wajan ta kullum......" Sai ya sake kallon Islaha ya ce, "da gaske kina sona?." Islaha ta kawar da kai gefe bata ce komai ba, tana jin haushin Rehaan jin a fakaice ya ce mata mahaukaciya. A lokacin Umma ta dawo wajan babu kunya ta kalle su ta ce, "To sai da safen ku, mun gode." Rehaan ya shafa kan Yayansa cikin tausayawa, ya miƙe Islaha ma ta miƙe ta yi hanyar da suka biyo bata sake kallon kowa ba. Salman ya miƙe zai bi bayanta Umma ta riƙosa ta ce, "ina za ka je?." Salman ya ce, "zan bita, ni a wajan ta zan kwana yau." Umma ta zare masa ido ta ce, "dallah zauna, wajan ubanwa za ka kwana?." Salman ya riƙe Rehaan kamar zai yi masa kuka ya ce, "ka tafi dani wajanta, ni a wajanta zan kwana." Umma ta ce, "sai na mare ka wallahi, dallah wuce ka bani waje, ko na kira kifayen Amir su cinye ka." Salman sai ya nufi ɗaki jin an kira abinda yake jin tsoro. Rehaan ya fita yana murmushi, zuciyarsa cike da tausayin Yayan nasa, jin ana tsorata shi da abinda yara ƙananu ne suke tsoron abun, Allah ya gani, yana son nemo masa lafiya amma babarsa ta hana. A tsaye ya samu Islaha ta haɗe rai, ya ɗan kalle ta ya ga ta sha mur tana kallon gefe ƙiris take kira ta fara masifa. Bai ce komai ba ya wuce ɓangaren amarya Abba, ganin ya tafi dole ta bi bayansa. A nan ma basu jima ba, sun gaisa sama-sama sannan ya fito suka tafi ɓangaren Mamy. Islaha suna shiga wajan Mamy gabanta ya faɗi, domin ita ba ita kaɗai bace, suna da yawa kuma duk irinta ne masu fararen fata, sai matar nan da suka samu saɓani da ita. Suna shiga Rehaan ya yi murmushi ya ce, "ba ku yi bacci ba?." Sanah itace take iya mayar da magana da hausa kaɗan-kaɗan ta ce, "yanzu muka dawo, ina mu ina bacci? Sannun ku da zuwa." Ya ɗaga kai alamun yauwa, Islaha tana daga tsaye ta kasa motsawa balle ta shigo. Sanah ta kalle ta ta ce, "shigo mana" ta faɗa cikin hausarta da bata wani fita sosai. Ammi ta yi caraf ta ce, "ta ya zata shigo, bayan rashin kunyar da ta yiwa uwar mijinta ɗazu? Har da ƙoƙarin marina." Islaha ta lumshe ido ta buɗe takaici yana mamaye mata zuciya, Allah ya sani zata iya yin aljanun ƙarya ta zane matar nan, bata son rashin jan mutumin da jan girma daga wajen wanda ya dace. Mamy ta kalli Islaha da take tsaye ta ɗauke kanta ta kalli Rehaan ta ce, "ka ci abinci?." Rehaan ya ce, "na ci." Sanah ganin Mamy ba ta Islaha take yi ba sai ta ce, "shigo mana Islaha, ko ba haka sunan yake ba?." Islaha ta yi murmushi tana jin daɗin yadda matar take yi mata, ta ƙarasa a hankali ta zauna a kan carpet. Ammi ta ce, "Rehaan yarinyar nan ɗazu ka ga abinda ta yi mana ni da mahaifiyar ka? Ni daman na santa, lokacin da ba ka da lafiya har ka kwanta a asibiti a nan muka haɗu, yarinyar nan ta tare mu ta dinga yi mana rashin kunya bayan ta ɗaukarwa Mamy atm card. Ban taɓa ganin yarinya mara tarbiyya da rashin sanin darajar na gaba kamar ta ba." Rehaan hankalinsa ba ya kanta, game ya ke taya yaran gidan da suka biyosa wajen Mamy, sai daga baya ya kalli Ammi bai ce komai ba ya kalli Islaha da ya ga tana kallon Ammi irij kallo na takaici. Sanah ta ce, "ya isa don Allah, ba abinda ya kawo ta kenan ba, zuwa ta yi mu gaisa." Mamy dai bata ce komai ba, kamar bata san dasu a wajan ba, waya ta ɗauka tana dannawa kamar babu wanda ya zo wajanta dan ya gaishe ta. Sanah ta ce, "a ina ki ke aiki?." Islaha ta ce, "Toron guiwa tv." "Ma sha Allah, Ashe tv presenter ce." Islaha ta yi murmushi bata ce komai ba, duk ta takura saboda yadda aka karɓe ta a wajan. Ba haushin tarbarsu take ji ba, wanzuwar Ammi a wajen shine takaicinta, ji take zata yi aljanun ƙarya ta karya ta wallahi. Ammi ta harari Islaha da ba ita take kallo ba ta ce, "Shashasha mara tarbiyya" ta sake faɗa a ƙufule cike da jin haushin sunan matar Rehaan da Islaha take amasa. A fusace Islaha ta ɗago suka haɗa ido, sai kuma ta fasa magana ta sauke kai ƙasa bata ce komai ba. Shiru ya ratsa falon sai yara da suke game suna ihu kaɗan kaɗan. Ganin Mamy ta ƙi magana sai Sanah ta ce, "Allah ya ba ku zaman lafiya, Rehaan ku je ku huta dare ya yi." Sai a lokacin Mamy ta ce, "Ita ta je, ina son magana da shi......." Ta kalli Rehaan ta ce, "Rehaan follow me" ta faɗa tana tashi ta shiga ciki dole ya bita bayanta shima. Suna shiga ɗaki ta kalle sa ta ce, "Rehaan bana son yarinyar nan ko kaɗan, bata yi min ba kwata-kwata, bana jinta a raina balle na karɓe ta a matsayin inlaw. Bata da kunya, bata girmama na gaba da ita, rashin kunya take yiwa waɗanda suka haife ta, kad ka saki jiki ka zauna da ita, ka dinga baya-baya kar ta cutar da kai." Rehaan sai ya ji babu daɗi a ransa, jikinsa ya yi sanyi sosai, haushin Islaha ya sake ninkuwa a ransa, ya ji ina ma bai taɓa sanin mai irin sunanta ba. Ya kalli Mamy ya ce, "To Mamy." Mamy ta ce, "Kuma ka shirya aure next month, ni Ikram nake so ka sake aure Rehaan." "Mamy mun gama maganar nan da ke, bazan iya aurenta ba. Amma zan yi aure nan kusa, amma ba Ikram ba." Mamy ta ce, "bana son ka ɗauko wacce zata cutar da kai." Ya riƙe hsnnunta ya ce, "zan kasance cikin ƙoshin lafiya ko yaushe." Ta shafa kansa ta ce, "Allah ya sa." Ya yi murmushi ya fito daga ɗakin, a nan ya tarar Islaha bata nan ya wuce ɓangaren Abba kamar yadda ya ce ya same shi. A zaune ya samu Abba kamar ɗazu, shima ya zauna Abba ya ce, "na kira ka dan na tuna maka alƙwarin da ka yi min akan auren nan, kana sane dai ko?." "ina sane Abba." Abba ya ce, "ka yi haƙuri ka riƙe auren, bana so a samu wata damuwa ka ji?." "In sha Allah babu abinda za a samu daga ɓangarena, zan yi komai saboda kai." "Haka nake so na ji, ka yi haƙuri ka kawar da kai kafin ka samu wacce ka ke ra'ayin aure." "To" ya amsa a taƙaice. Abba ya ce, "Tashi ka je, Allah ya yi maka albarka." "Amin Abba, sai da safe" ya faɗa tana miƙewa ya fita daga ɓangaren ya koma ɓangarensa. Yana shiga falon Islaha da take zaman jiran shigowarsa ta miƙe tsaye ta kalle shi ta ce, "ina so a yi cancelling contract ɗin nan, bazan iya zama a gidan nan a matsayin matar ka ba...." "Na gaji wallahi, iya kwana ɗaya da na yi a gidan ku na ji bazan iya zama, ina buƙatar komawa gida wajan Hamma, bazan iya zama a nan ba. Dan haka a soke shi, na yi alƙawarin zan biya ka kuɗin ka, kawai ka sake ni na kama gabana, in dai kuɗi ne zan san duk hanyar da zan bi na nemo su na ba ka abin ka, zaman gidan nan bai yi daidai da ra'ayina ba. Ni da Hamma za mu san duk hanyar da za mu nemi kuɗi mu ba ka, amma bazan iya zama a gidan nan gaskiya...." Rehaan ya tsaya cak jin maganarta a bayansa, ya waiwayo yana bin ta da kallon ba ki da hankali...... RDB3P10 Nana Haleema. Rehaan ya yi holding hannunsa a cheast ɗinsa yana kallonta jin tana maganar a soke yarjejeniya, bayan alƙawarin da ya sake yiwa Abba ko mintina goma ba a yi ba ta kawo masa shirme. Islaha ganin yana kallon ta sai ta ce, "zan yi ko wanne irin aiki ne a ƙarƙashinka, har sai ka fanshe kuɗin da ka bani, amma bazan iya zaman gidan nan a matsayin matar ka ba, ina buƙatar komawa wajen Hamma." Rehaan ya ɗan girgiza kai yana blushing sannan ya kawar da kansa daga kallonta, ya sake waiwayowa ya kalle ta ya ce, "A yi cancelling?." Islaha ta ɗaga kai alamun eh tana kallonsa, dan da gaske baza ta iya zama a cikin gidansu ba. Ya kalli ƙasa kamar mai neman wani abu kafin ya sake kallonta, ya saka hannu aljihu sannan ya ce, "So you have my account details, right?" Ta ɗago ta kalle shi jin abinda ya ce, Rehaan ya ɗaga gira sama ya haɗe fuska kamar ba shine yake murmushi ba. Islaha cike da damuwa ta ce, "bani da ita, kuma bani da kuɗin da zan biya ka a yanzu balle har na tura maka. Amma na yi maka alƙawari zan yi aiki a ƙarƙashin ka har sai na biya ka kuɗin ka, ko wanne irin aiki ne zan yi indai zan samu kuɗin da zan ba ka, ko da ba za a dinga bani salary ba na yarda, ni dai burina a soke yarjejeniyar nan na kama gabana." Rehaan ya ce, "Lokacin da ki ka yi signing kin ce kin taimaka min ne, meyasa ki ke neman a soke?." "Saboda Hamma, saboda shi na saka rayuwata a cikin ta ka, duk abinda na yi saboda shi nayi, ba dan shi ba da baza ka sake ganin fuskata ba har abada." Rehaan ya taɓe baki yana girgiza kansa cikin ko in kula da kalamanta ya ce, "Okay ki je ki faɗa masa ya biya ni kuɗin da na ba ki, once i receive my money, we can cancel the agreement. But if my money is not paid back, don't bring up canceling the contract again. Ya juya zai bar wajan sai kuma ya kalle ta ya ce, "fifty millions naira, not fiffty thousands" ya faɗa yana hawa sama yana ciro waya daga aljihu ba tare da ya kuma kallonta ba. Islaha ta yi shiru cike da damuwa, ta zauna tana tunanin Hamma yana wani waje ba shi da lafiya bata san halin da yake ciki ba, ta fashe da kuka mai taɓa zuciya, tana ji kamar haɗɗiye zuciya ta mutu saboda tunanin Hamma. Ta runtse ido cikin ƙunci da takaici, kamar ta dinga dukan kanta haka zuciya take raya mata, ta ɗauki waya ta kira Safeera. Safeera tana ɗauka ta fara yi mata masifa ta ce, "tun ɗazu nake jiran ki har yanzu ba ki ce min komai ba, kin koma wajan Hamman ko ba ki koma ba?." Safeera cike da gajiya da maganar ta ce, "wai sau nawa zan faɗa miki ne, na je yana bacci ya ki ke so na yi miki?." Sai ta tuna ashe sun yi magana ta faɗa mata ta je yana bacci, ita ta manta sun yi magana, damuwa da tunanin Hamma ya saka ta manta. Jikinta ya yi sanyi ta ce, "Safeera ban san ya zan yi ba, na rasa abinda yake damuna, ina so na ga Hamma, ina so na yiwa Hamma bayani, ina so Hamma ya san ban yaudare sa ba." Safeera ta ce, "don Allah ki nutsu, ni na san Hamman ya san ba ki yaudare sa ba, meyasa ki ke takura rayuwar ki haka?." Islaha ta sauke numfashi irin na wacce ta yi kuka bata ce komai ba. Safeera ta ce, "don Allah ki nutsu, wannan abinda ki ke yi ba shine mafita ba." "Ina a soke yarjejeniyar nan, ina so na dawo na kula da Hamma, ko ban koma gidansu da zama ba ni dai na bar gidan nan." "Kina da miliyan hamsin kenan?." "Bani da ita." "To ki bar batun za ki soke contract, ko da kina da kuɗin a hannunki dole sai kin zauna da shi tunda kin riga da kin amince akan za ki zauna dashi in ya ba ki kuɗi, kin yarda shima ya yarda, ki ka saka hannu shima ya saka. Ya ba ki kuɗi dan ki zauna da shi, ki ka karɓa dan ki karɓo Hamma kuma buƙatar ki ta biya. Saboda ke ki ka fi kowa son kai sai burin ki ya cika sai a soke contract ɗin? Ki zama wayayyiya wacce ta san shari'a mana Islaha." Ta lumshe ido ta ce, "bazan iya zama ba, ji nake zan iya mutuwa wallahi." Safeera cikin rarrashi ta ce, "baza ki mutu ba, kuma Hamma zai fahimce ki yadda ya kamata. Kawai ki nutsu, ki shirya tunkararsa kawai." Ta girgiza kai kamar Safeera tana kallon ta ta ce, "Kunyarsa nake ji." "Ki adana kunyar, ki ɗaura ɗammarar yi masa bayani yadda zai fahimta." Ta yi ajiyar zuciya kawai ta yanke wayar ta kwanta a kan kujera. Islaha yunwa take ji sosai, yunwa take ji tana yamutsa cikinta, dan rabonta da abinci tun tana gidansu Safeera. Tea kaɗai ta iya sha a gidan, bayan nan bata kuma cin komai ba. Ta kalli manyan flaks ɗin da suke ajjiye akan center table, ta miƙe daƙyar ta buɗe ɗaya ta ga kaji ne da dankalin turawa. Ta ɗauki mini plate ɗin ta zuba dankalin ta ci kaɗan, ta sha ruwa ta koma ta yi shiru a wajan. Knocking ƙofar ta ji ana yi, gabanta ya faɗi ta kalli agogo ta ga ƙarfe sha ɗaya na dare, ta sake kallon ƙofar sai kuma ta ji an buɗe ƙofar an shigo ta zubawa ƙofar ido. Banisha ce ta shigo ita da Janan da kuma Ikram, fuskarsu ɗauke da makeup da alama dawowarsu kenan daga gidan bikin Riyya. A tare suka yi sallama, ta amsa tana ɗago ido suka haɗa ido da Banisha. Banisha ta yi murmuahi ta ce, "Hiii Sis." Islaha ta ɗan murmusa ta gyaɗa kai ta ce, "Hello Banisha." Janan ta ce, "Hiii." Ta ɗan ɗaga kai bata ce komai ba tana kallon ta kawai. Ikram ta ce, "Hamma Rehaan yana nan?." Banisha ta ce, "Yana sama, ku zo mu je." Ta gabanta suka wuce suka hau sama bata sake kallonsu ba, dan gani ta yi suna da jin kai ga wani iyayin da suke ji da shi. Islaha tana daga falo tana jiyo dariyarsu daga sama, shi dai bata jin ko muryarsa, amma tana jin dariyarsu har suka sakko suna cewa, "good night bruh." Bata ɗaga ido ta kalle su ba har suka ƙaraso inda take, dukkansu fuskarsu ɗauke da nishaɗi. A tare suka haɗa ba ki suka ce, "good night." Ta buɗe ido ta kalle su ta ce, "Allah ya tashe mu lafiya." Daga haka suka fita tare da jan ƙofar, ita kuma ta miƙe ta ɗauki wayarta ta hau saman. Islaha a falo ta same sa ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana amsa video call, yana ta murmushi da alama da mutum mai mahimmaci yake magana. Daidai lokacin da ta shiga falon ta ji muryar mace cikin ingilishi ta ce, "ina ka bar matar ta ka take?." Rehaan ya ɗago ido ya kalli Islaha da take shigowa falon tana takawa kamar wacce aka yiwa dole sai ta shiga: Ya shafa kansa bai amsa ba ya ce, "yaushe za ki zo?." "Sai matar ka ta haihu." "Ashe baza ki zo ba." Ta yi dayar shaƙiyanci tana tafa hannu sai ya murmusa ya ce, "Bye. Ina da aiki." "Mr busy, Bye." Bai ce komai ba ya rufe laptop ɗin, ya ɗauki waya ya fara dannawa cikin nutsuwa. Islaha bata sake kallonsa ba ta wuce ɗakin da aka ajjiye ta, ta cire mayafinta ta shiga wanka. Bayan ta gama ta fito ta buɗe box ɗin kayanta ta ɗauko ƙaramar riga mara nauyi doguwa mai siririn hannu ta saka. Ta koma gefen gado ta zauna tana tuna abubuwa kala kala, tunanin Zainab ya danne na Hamma, sai ta firgita kamar wacce aka tsorata ta ɗauki waya zata kira Brr Suraj sai ta ga dare ya yi sosai, ta yi ajiyar zuciya tana ayyana ya zama dole gobe ta fita ta je inda ya kamata, dole gobe ta fita daga gidan nan dan samo mafita akan matsalolin da suka same ta. Rehaan kuwa yana zaune kiran wayar Jazy ya shigo, kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka, ya saka a speaker Jazy ya ce, "please Rehaan ka yiwa Riyya magana, sai kuka take yi kamar ba ni ba." Rehaan ya haɗe rai kamar yana ganinsa, sai kuma ya kashe wayar ya kira Jazy video call yana kallon Jazy sanye da pyjamas red colour wanda suka yi masa kyau sosai. Ray ya ce, "me ka yi mata?." Jazy ya harare sa ya ce, "me zan yi mata a wannnan lokacin? Dallah in za ka rarrashe ta ka rarrashe ta, ka daina yi min maganar banza." Riyya ta karɓi wayar tana kallon Rehaan, Ray ya tausasa murya ya ce, "Riyya What wrong?." "I'm just missing you." "Ba ga shi kina ganina ba, meyasa ki ke kuka? Ko na zo na tafi dake?." Ta ɗaga kai alamun eh, ya yi murmushi ya ce, "to ki daina kuka, zan zo mu tafi, shikenan?." Ta goge idonta tana murmushi tana bawa Jazy wayar. Jazy bai yi magana ba sai da ya fito daga ɗakin sannan ya kalli wayar ya ce, "Kai gidan ubanwa za ka zo ka ɗauke ta? Kana da hankali?." Ray ya yi dariya sosai sannan ya ce, "billah in na ga dama sai na zo har gidan na tafi da ita." Jazy ya ce, "kar ka fasa, don Allah ka zo in ka isa." Ray ya sake yin dariya mai sauti ya ce, "hmmm, kana wasa dani." Jazy ya ce, "ka je ka ji da matarka, mijin contract." Ray bai ce komai ba ya yanke wayar yana kallon room ɗin da Islaha ta shiga, a daidai lokacin Islaha ta buɗe ƙofar ta fito sanye da doguwar riga ta bacci, ta yafa mayafi a iya kanta, gashin ta ya sakko har ƙasa, sannan ta gaba ya fito sosai dan mayafin ya zame ta gaba. Tana fitowa suka haɗa ido, sai ta yi turus taja ta tsaya ta kasa gaba ta kasa baya. Charger ta ta bari a ƙasa, shine take so ta je ta ɗauko ta saka chajin wayar ta, bata san yana zaune da ba da bata yi gangancin fitowa babu mayafi ba. Nana Haleema. KRBBK: RDB3P11 Nana Haleema. Rehaan tunda suka haɗa ido ya ɗauke kansa, ya juyar da fuska kamar bai san da ita a wajan ba, nan kuwa yana kallonta ta gefen ido, so yake ya ga tsayuwar me ta ke yi a wajen. Islaha sai ta koma da baya ta ɗauko hijjab ta saka, dan bazata iya wuce shi da rigar jikinta ba, sai da ta saka hijjab sannan ta fito ta sauka downstairs bai ce komai ba itama bata ce ba. Yana jin takun saukar ta ya waiwayo yana kallon wajen, a lokacin ta dawo tana warware charger da take hannunta. Mamaki ta ba shi ganin har da wani saka hijjab, dan ya san ba a haka ta fito ba, har gashin kanta ya gani a bayyane lokacin da ta buɗe ƙofa, kenan komawa ta yi ta saka hijjab saboda yana zaune ko me take nufi? Dan ya san haka ƴan nigeria suke, da zarar sun ga namiji a waje sai su koma su saka mayafi dan su rufe jikinsu, kuma ya san addini ne ya ba da damar hakan, tunda Mamy ma tana yi. Haka kawai ya ji bazai iya yin shiru, dole sai ya yi magana ko da baza ta kula shi ba. Gab da zata wuce ta ji muryarsa ya ce, "wait a minute." Islaha ta ɗan juyo ta kalle sa suka sake haɗa ido, tana mamakin dalilinsa na tsayar da ita. Rehaan ya nuna ta da yatsansa ya ce, "meye na saka hijjab ɗin, Kin manta wacece ke?....Akwai abinda ya yi saura da za ki ɓoye?." Wani irin ƙunci ya sake mamaye mata zuciya, daman ga shi zuciyarta a wuya take, damuwa ta mamaye mata zuciya ta ko ina, ƙiris take jira ta samu abokin faɗa su yi kaca-kaca. Islaha ta girgiza ki cikin jin haushin kalamansa, ta cize baki ta kalle sa cikin dauriya ta ce, "babu sauran abinda zan ɓoye kam kamar yadda ka sani, kuma nasan ka tabbatar da babu sauran abin ɓoyewa, to babu ɗin." Ta nuna shi da yatsa tana buɗe idanunta ta ce, "amma ina so ka san akwai waɗanda basu cancanta su ga ragowar ba, ka san ko a mutanen da suka saba ganin ragowar ma matsayi ne, irin ku ba ku kai matsayin da idanunku zai ga ragowar ba, baza ku jure kallo ba, za ku iya makancewa. Ka kiyaye idanunka daga kallona, in ba haka ba zaka rasa idanun da ka ke gani dasu" tana gama faɗa masa haka ta bar wajan ta shiga cikin ɗakin ta rufe ƙofa. Rehaan ko kaɗan bai ji haushi ba, ya ɗan yi murmushi yana tuna wacece ita ɗin a Jeddah, yana tuna har ciki ta zubar kuma da idanunsa ya ganta. Ya yi tsaki kaɗan, ya tashi ya shiga ɗakinsa ya rufe ƙofa. Islaha tana shiga ta cire hijjab ɗin ta cillar ta ce, "lallai wannan mutumin da alama bai taki zaman lafiya ba, ni zai kalla ya dinga jifa da waɗannan kalaman munana?. Haka ɗazu ya faɗa min magana a falon waccan babar mahaukacin, wai ai ni mahaukacin ɗan uwana ne type ɗinmu ɗaya, Kenan nima mahaukaciya ce kenan?." Ta girgiza kai ta ce, "lallai zai ga salon hauka a cikin gidan nan, kafin na bar gidan nan sai na saka ya gangata ni mahaukaciya. Zan nuna masa ni ƴar iska ce lamba ɗaya, tunda kallon karuwa yake yi min bazan tsaya kare kaina ba, kawai zan nuna masa ita ɗince a aikace, sai na goge masa hadda wallahi." Ta ƙarasa ta saka chaji ta kwanta a kan makakeken gadon ta, ta ɗauki remote ta kunna ac ta lumshe ido tana ji kamar bata kyautawa rayuwar ta ba gabaɗaya, dan Ray bai dace da ita ba ko kaɗan. *Jeddah.* Kuɗi ne masu matuƙar yawa ne a hannunta tana lissafawa Aisha tana ta ya ta har suka lissafa kuɗin saudia masu yawa. Aisha ta yi dariya ta ce, "kin zama hajiya Labiba." Ta yi farr da ido cikin jin daɗi ta ce, "Ina komawa nigeria mota zan siya." Aisha ta dara ta ce, "yaushe za ki koma ɗin?." Labiba ta ce, "babu rana balle wata, yadda nake samun kuɗin nan me zai mayar dani gida?." Suka yi dariya tare sa tafawa cikin nishaɗi. Labiba ta ce, "Yanzu ina zamu nufa? Tunda kin ga ya ce zamu iya tafiya, zai yi tafiya kuma ƙasar zai bari. Ina zamu nufa yanzu daga nan?." Aisha ta ce, "kin shirya neman kuɗi Hajiya?." Labiba ta ce, "ki ninka shiri sau dubu, haka na shirya tsaf zan bazama neman arzuƙi." Aishs ta ce, "in dai kin shirya, ki shirya ɗaukar duk wani ganganci da za ki shiga. Ki tattara kayan ki mu wuce garin makka, acan zamu ci kasuwar kuɗi yadda muke so." Labiba ta buɗe ido ta ce, "Makka kuma, ba ance suna kama mutane ba?." Aisha ta ce, "a haka kowa yake zaune, in ba ki da visa ki o igama tabbas ana kama mutane a dawo dasu najeriya, amma mata nawa ne a can suna sana'ar su? Mu ma cikinsu zamu shige." Labiba ta ce, "ai ni ina da visa ko?." Ta harare ta ta ce, "visa wata uku suka buga miki, kuma yanzu kin zarce wata uku tuni. Visa ki ta jima da ƙarewa, dani dake duk ɗaya mu ke a nan." Labiba ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "Amma cewa aka yi visa shekara ɗaya aka yi mana." "Yaudarar ki aka yi, wallahi ta wata uku aka yi miki ba shekara ba. Da ne ki ke zaune zaman ƴanci a nan, yanzu za ki fara zaman ganganci, in ta yi ruwa rijiya, in bata yi ba masai." "kuma a haka zamu shjga makka?." Ta ce, "a haka zamu je, in kuma baza ki ba sai ki nemi abinda za ki biya wanda suka kawo ki." Labiba ta ce, "amma ance in visa ta ƙare, wanda aka kawo bai koma ba kamfani suke cin tara ko?." "Kamfanin na Maman ku ne?." "Aa, kawai dai...." "In ba za ki je ba Labiba ki sauka lafiya, Wallahi Jedda ba garin zama babu visa bane balle ki samu mafaka. Makka kuwa akwai inda zamu shiga, za ki manta a ƙasar ki ke saboda waɗanda za ki gani. In za ki je in anjima zamu hau mota, in baza ki ba ni kam zan wuce." Labiba ta ce, "dole na na je ai, Allah ya kaimu" ta amsa da amin suka fara haɗa kayan da zasu wuce garin makka. *Madina.* Umma ta rame, ta yi duhu saboda wajigata da mutanen gidan suke yi, ta fita daga hankalinta saboda rashin ishashen hutu da rashin bacci. Tana zaune a kan kujera tana gyangyaɗi, ta ji an kira ta da ƙarfi ta zabura ta miƙe tsaye tana goge idanunta. Zuwa yanzu tana fahimtar abubuwa sosai a kalmomin larabci, itama su yalla, mafi, la la la, na'am duk sun zauna a bakinta sosai. Irin su zo, zauna, tashi, duk da larabci take faɗa saboda da zama kuma tana chuɗanya dasu. Matae gidan ta ƙaraso ta nunawa Mama tulin  kayan wanki da akace ta wanke. Umma ta kalli kayan, bata zaɓi haka ta kwasa ta tafi ɗakin wankin ta zuba a washing machine tana yi gyangyaɗi. Jiri ya ɗauke ta bata san ta zube a wajan ba sai da ta jita a ƙasa a kan tiles. Ta dafe kanta, ta kwanta ta huta kafin wankin ya gama bacci ya ɗauke ta. Ruwan sanyin da aka watsa mata shine ya tashe ta, ta tashi a firgice a gigice tana jan nunfashi daƙyar ta zauna. Tana ji matar tana yi mata masifa amma ba fahimta take yi, ta gama ta fita Umma ta bi jikinta da kallo ganin yadda aka jiƙa ta sai kawai ta fashe da kuka. Ta haɗa kai da guiwa tana kuka sosai, ba komai take hange ba sai mijinta da yaranta da ta bari a gida ta taho tana bautar yaran wasu. Kanta ya yi nauyi, ga ciwo ga jirin da take ji. Ta miƙe tsaye ta cigaba da wankin tana ji zazzaɓi yana rufe ta. Kafin ta gama wankin zazzaɓi ya rufe ta ko buɗe ido bata yi, bata sake sanin inda kanta yake ba sai buɗe ido ta yi ta ganta a asibiti an saka msta ruwa. Tana buɗe ta ji babu ciwon kan, ya tafi gabaɗaya kanta ya daina yi mata nauyin. Ta kalli agogon asibitin ta ga ƙarfe bakwai na safe alamun ta jima tana bacci har gari ya waye. Ta mayar da ido ta rufe dan bacci ya kuma ɗauke ta, so take bacci ya sake ɗauke ta gwara ta fanshe baccin da ya tarar mata. Bata iya baccin ba ta miƙe, a lokacin wani likita ya shigo da sallama, kallo ɗaya ta yi masa ta san wannan ɗan ƙasar su ne dan ya yi kama dasu sosai. Ya ƙaraso ya ce, "Hausa?." Mama ta ji daɗi ya kamata ta ce, "Eh." Ya yi murmushi ya ce, "Sannu Mama, kin farka?." Umma ta miƙe ta ce, "na tashi." Ya yi murmushi ya auna bp ta ya kalle ta ya ve, "Mama ya aka yi bp ya hau haka? Bakya samun bacci ne?." Umma ta ɗaga kai ta ce, "bana samun bacci ko kaɗan." Ya ɗaga kai ya ce, "meyasa bakya yin baccin?." "Aiki nake yi." Ya ɗaga kai ya cigaba da abinda yake yi kafin ya ce, "waɗanda suka kawo ki suna ta zuwa kina bacci, in sun zo zance musukin tashi. Zuwa nan da azahar za a iya baki sallama ki koma gida. Amma ki gujewa rashin bacci da damuwa, in ba haka ba jininki zai dinga hawa ko yaushe." Umma ta ce, "Don Allah kar ka ce musu na tashi, ka bar ni na yi bacci yadda nake so, don Allah." Ya yo murmushi bai ce komai ba, dan ya fahinci aiki ta zo yi daga ƙasa nigeria, ya kashe ruwan ya fita ita kuma ta koma ta kwanta. Sai kuma ta tuna da sallah, ta miƙe ta shiga banɗaki ta yi alwala ta yi sallar da take kanta. Kamar yadda ya ce bayan ssllar azahar aka sallameta suka koma gida. Ta shiga ɗakinta a sanyaye ta zauna tana kallon maganin da aka bata. Ta yi tagumi tana tunani, ko haihuwa bata taɓa sakawa jininta ya hau ba, amma yau ga aikin wahala ya saka jininta ya hau har ta samu. Ta sauke numfashin nadama ta ce, "dole na nemi afuwar Baban Safeera, ya zama dole na nemi hanyar da zan koma gida, ya zama dole na bar gidan nan na koma nigeria." Ta tuna abubuwan da suka faru, ta buɗe jakar ta tana kallon ƴan kuɗin da tara wanda basu taka kara sun karya ba ta ce, "Ga shi dai na zo dan na tara kuɗi amma kuɗin basa taruwa, a magani ma kaɗai suke tafiya, ya zan yi?." Ta yi shiru babu mai bata amsa, amma ta yi ƙudurin ko me zata aikata yi zata yi indai zata bar ƙasar Jeddah ta koma ƙasar ta cikin ƴaƴanta da mijinta. "In sha Allah zai yafe min, in Allah ya yarda zai yafe min ya mayar dani ɗakina ko dan su Safeera. Da wannee ido zan kalli mutanen Katsina?." Sai kuma ta sake yin tagumi da hannu ta ce, "na tafka babban kuskure a rayuwata, na bar halak na taho ina aikin da babu lada, na bar sharar masallaci na zo nan ina yin ta coci." Umma ta kwanta ta rufe ido cikin tunani da neman mafitar da zata koma gida ta riƙe yaranta?. Washe gari.... Nana Haleema. RDB3P12 Nana Haleema. Islaha daƙyar ta iya yin bacci mai tsaho, tunda ta farka sallar asuba bata koma ba, tana idar ta miƙe ta shiga wanka, bayan ta shirya cikin abaya dan duk su Safeera ta zuba mata a cikin kayan da ta haɗa mata. Kayan ma gabaɗaya kala biyar ne sai undies na bacci, ta yi tsaki ta gama abinda zata yi ta zauna tana jiran bakwai na safe ta yi ta fita daga gidan. Gajiya ta yi da zaman ta miƙe ta ƙarasa windwow ta buɗe tana kallon kyawawan ɗawisun da suke yawo a compound ɗin apartment ɗin. Murmushi ta yi dan ɗawisu suna burge ta sosai, akwai kyau da ɗaukar ido ga kuma tsada. Kamar ance ta kalli gefen daga compound ɗin ta hango Rehaan a tsakiyarsu yana basu abinci, ga tattarbu a gefe suna ta cin abinci da ya zuba musu. Islaha ta taɓe baki tana hararasa kamar yana kallonta a bayyane ta ce, "Ni dai ban ga abinda mutumin nan zai yi ya burge ni ba wallahi, kalle shi don Allah, kamar wani na kirki har ciyar da dabbobi yake yi.” Sai kuma ta ga ya ɗauko roll ɗin chocolate ya buɗe yana zubarwa a ƙasa. Islaha ta gyara tsayuwa a bayyane ta ce, "me zai da wannan kuma?." Bata gama mammaki ba ta ga yana ɓarewa yana cillarwa a ƙasa, ta zuba ido tana jira ta ga abinda zai faru. Sai ta kuma ganin ya buɗe sweeted hollandia milk, itama ya zubar a ƙasa ya koma gefe ya tsaya ya harɗe hannu a ƙirji yana kallon wajen. Abin mamaki house flys ta gani sun hau kan alawar da holladia milk ɗin da ya zubar. Islaha ta buɗe ido cikin mamaki ta ce, "kenan house flys yake ciyarwa ko kuma dai iskanci ne? Su ma flys ɗin in aka ciyar dasu lada za a samu?.” Sai kuma ta ce, "Astagafirullah! Su ma halittar Allah ne. Amma dai wannan iyayi ne kawai, lallai sai ya nunawa mutane shi bature ne.” Islaha tana tsaye tana kallonsa shi kuma ya jima a wajan a tsaye, kafin ta ga ya bar wajem ya shigo cikin gidan. Tana tsaye tana kallo sai ga mai gyara wajan yazo yana gyarawa, lokaci ɗaya komai ya dawo tas kamar ba shi ya ɓata wajan ba. Islaha ta kulle window ɗin ta ce, "ɗan rainin sense." Ƙarfe bakwai tana yi ta ɗauki jakarta da wayarta ta fito falon, galon shiru babu kowa, ko haske babu balle ta ga wani a zaune, ta buɗe ƙofar ta sauka daga saman, ko abinci bata tsaya ci ba ta buɗe ƙofar ta fita. Gidan ma shiru kamaar ba monday ba, babu kowa sai masu aiki da suke ta kai kawo, ana ta hidima sa ɗore ɗoren abinci. Bata cewa kowa komai ba ta nufi gate da sassarfa ta fita daga gidan bata cewa kowa komai ba. Kai tsaye gidansu Safeera ta wuce, tana shiga gidan ta tarar da Safeera a tsaye ta juye ruwan wanka zata yi wanka. Ganin Islaha sai ta buɗe ido cikin mamaki ta ce, "ke meye haka?." Islaha bata ce komai ba kawai ta shiga ɗaki bata kula ta ba, Safeera ta bi bayanta da hanzari, ta same ta a tsaye tana kwance rolling ɗin kanta tana cewa, "Bani tea na sha, yunwa nake ji." Safeera bata ce komai ba, ta fita ta kawo mata iya tea dan ta san bata cin abinci da sassafe. Islaha ta zauna tana shan tea ɗin a hankali, har lumshe ido take yi saboda jin daɗin tea ɗin dan yunwa take. Safeera bata ce komai ba sai da ta gama ta ajjiye cup ɗin, sannan Safeera ta ce, "ke kuwa kamar wacce aka koro, da sassafe ki ka fito daga gidanki?." Ta ɗago ido ta kalle ta bata ce komai ba, Safeera ta ce, "lafiya na ga idanun ki sun kunbura haka Me ya faru?." “Meye ma bai faru ba? Ki yi wankan mu shiga gida wajan Hamma, abinda ya fito dani kenan." "Islaha na faɗa miki ki bari a kwana biyu, a yanzu babu lallai ya saurare ki." "Ni a yanzu zan yi magana da shi, ki shirya kawai." Safeera ta ce, "shikenan ai. Ga kayan ki nan, Mama ce ta tattaro komai na ki na cikin gidanta ta bayar aka kawo min, ina niyar na samu mai napep ya kai miki can, tunda yanzu kin zo sai ki wuce dasu." Islaha ta harare ta cikin jin haushi ta ce, "kamar wacce ta je zama a can? Haka kawai sai na kwashi kaya kamar yar cirani na tafi dasu can sai ka ce zama na je yi?. Ki ajjiye min a nan, in ina buƙatar  na dinga ɗauka a nan ɗin, na yi me da kayan nan a can?." Safeera bata ce mata komai ba ta shiga banɗaki. Har ta fito ta shirya babu wanda ya yi magana, tana gama shiryawa Islaha ta miƙe sai kuma ta dafe ƙirji ta ce, "gabana yana faɗuwa, ban san da wacce fuska zai karɓe ni ba." Safeera ta yi mata banza dan ta faɗa mata abinda ya kamata amma ai taƙi ji. Tare suka fito, Mama Atika ta bi Islaha da kallo cikin mamaki ta ce, "Kai kai kai! Amarya ce da kanta a gidan nan?." Islaha ta ji wani iri a ranta, wai amarya sai take jin sunan sam bai kamace ta ba. Cikin yaƙe ta ce, "Ina kwana Mama." "lafiya lau amarya, Daga aure shekaran jiya har kin fito?." Ta ɗan yi murmushi bata ce komai ba, dan ba ƙaunar zancen take yi ba. Mama ta ce, "Allah ya ba ku zaman lafiya, Aure irin wannan ba auren wasa bane ba, ki riƙe mijin ki hannu biyu, irin waɗnanan ba kowa ne yake samunsu ba sai wanda Allah ya zaɓa." Islaha ta yi murmushi ta ce, "Na gode Mama." Daga haka ta ja hannun Safeera suka fito daga gidan. Tunda suka hango ƙofar gidan su Saheer gabanta ya faɗi, Islaha ta tsaya ta ƙi gaba ta ƙi baya ta ce, "haka kawai gabana yake faɗuwa Safeera." Safeera cikin rashin damuwa ta ce, "ki daure mu je, babu abinda zai faru in sha Allah." Islaha ta gyaɗa kai suka ƙarasa ƙofar gidan tana tafiya kamar mara lafiya saboda fargaba. Suna tsayawa Baffa ya buɗe gate ɗin gidan ya fito, yana buɗewa suka haɗa ido da Islaha. Cike da mamaki da al'ajabi ya ce, "Islaha! Ke ce?." Islaha ta duƙa ƙasa ta ce, "Ni ce Baffa, Ina kwana." Baffa da mamaki ya ce, "Islaha da safe haka, ina fatan lafiya ko?." Ba tare da ta ɗago ba ta ce, "lafiya lau Baffa, wajan aiki zan je shine na biyo mu gaisa." "wajan aiki kuma Islaha? Daman basa bawa sabbabin aure hutu ne?." Islaha ta turo baki gaba ta ce, "Ni basu san ma nayi auren ba, bana so a sani wallahi." Baffa ya murmusa ya ce, "Amma yanayin gidan da ki ka shiga, da wanda yake amsa sunan mijinki, fitowar ki ke kaɗai akwai hatsari, Meyasa za ki fito yanzu ke kaɗai?." Ta yi shiru bata ce komai ba dan bata san me zata cewa Baffa ba, da dai wani ne ba Baffa ba da ta ba shi amsa daidai da shi. Baffa ya ce, "taso mu shiga ciki." Islaha ta miƙe ta bi bayan Baffa suka shiga cikin gidan har falon Baffa. Baffa ya zauna ya kalli Islaha da Safeera ya ee, "ku zauna mana." Duk suka zauna suna kallon Baffa, Baffa ya ce, "Safeera meyasa za ki bari ta fito a yau kuma da sassafe haka?." Safeera ta ce, "Wallahi Baffa babu yadda ban yi da ita ba, amma ta ce sai ta je wajan aiki, kafin  muje can sai ta biyo nan kun gaisa." Baffa ya girgiza kai ya ce, "babu laifi, tunda mijin nata ya barta ai shikenan. Ni fita zan yi, ku shiga ku gaisa da mutanen gidan daga nan sai ta wuce aikin. Amma ki cigaba da haƙuri, komai yana wucewa a hankali kamar bai faru ba." Suka amsa Baffa ya miƙe ya fita suma suka fito. Islaha suna fitowa ta tsaya a compound ɗin, ta kalli ƙofar ɗakin Hamma, ta kalli Safeera ta ce, "mu je na same shi." Safeera ta riƙo hannunta tana dakatar da ita ta ce, "Bai kamata ba." "Ban gane mai kamata ba, meye bai kamata ɗin ba?." "Shiga ɗakin Hamman kai tsaye shine bai kamata ba, yanzu ba dah bane, yanzu kina da aure." Islaha ta ɗora hannu a kanta cikin takaici da baƙin ciki ta ce, "Safeera wataran zan iya shaƙe miki wuya har sai na ga kin daina numfashi akan waɗannan banzayen kalaman naki, ke kin san ta yadda auren nan ya faru, kin san auren yarjejeniya ne a tsakanina da shi, kin san auren jiran lokaci ne, meyasa ki ke son maimaita min wannan maganar mara daɗin ji?." Safeera zata yi magana ta ɗaga mata hannu ta ce, "wallahi da dah da yanzu babu banbanci a wajena, ni ce dai Islahan Hamma ban canja ba. Auren da ya ke kaina na ɗan lokaci ne, da zarar ya ƙare komai ya ƙare zan kama gabana. Ki daina dakatar dani akan duk abinda na yi niya, ki bar ni na yi abinda naga ya dace da ni, na san abinda yake yi." "Gaskiya ce bakya so a faɗa miki, ni kuma sai na faɗa miki dan bazan bar ki kina saɓon Allah ba." "Saɓon Allah fa ki ka ce? Magana da Hamman ce saɓon Allah? Kin manta waye shi a gare ni?.” “magana da shi ba saɓon Allah ba ce, magana da shi ta fuskar da yake ranki shine saɓon Allah, gaskiya ce bakya so.” “Bana son gaskiyar ta ki, ki daina faɗa min bana son ji." Safeera ta yi murmushi kawai, kafin ta yi magana Islaha ta ɗauki hanyar ɗakin Saheer. A sanyaye take ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Saheer, Saheer yana daga ciki yana zaune a gefen gado ya saka bacci, saboda yanayin jikinsa gabaɗaya babu daɗi, babu abinda yake yi masa daɗi shiyasa ya tashi daga baccin yana yamutsa fuska. Jin ana buga ƙofar sai ya yi tunanin Sadik ne, ya miƙe daƙyar ya taso ya buɗe ƙofar yana cewa, "kamar ka san na kasa bacci, a samo allurar baccin nan...." Maganar ta tsaya cak ganin wacce suka haɗa ido. Saheer ya zuba mata ido kamar yadda ta zuba masa ido, ya rufe ido ya buɗe dan bai gasgata ita ɗin bace shiyasa ya tsaya yana kallonta. Safeera da ya gani a bayanta ya saka ya sake kallon Islaha, a daidai lokacin da hawaye ya sakko daga idanun Islaha muryarta tana cracking ta ce, "Hamma!." Saheer ya lumshe ido yana jan numfashi daƙyar saboda nauyin da ƙirjinsa ya yi masa, ya buɗe ido ya sake kallonta ya ga tana kuka sosai hawaye wani yana bin wani. Nana Haleema. RDB3P13 Nana Haleema. A hankali ya ja da baya zai rufe ƙofar ta yi hanzarin tarewa ta hana shi rufewa, ta girgiza masa kai ta ce, "Hamma ka tsaya ka saurare ni, kar ka yanke min hukunci cikin fushi. Ka tsaya ka ji abinda zan faɗa maka, na san na ɓata maka rai, na san ban kyauta ba, na san na karya maka zuciya, na san na saka ma ka ɗaci a zuciyar ka. Amma don girman Allah ka tsaya ka ji uzurina, na tabbatar za ka fahimce ni, don Allah Hamma ka dakata, kar ka riƙe ni a ranka." Kasa rufe ƙofar ya yi ya lumshe ido yana jin yadda take magana cikin kuka da rawar murya, ya buɗe ido bai kalle ta ba ya sake ƙoƙarin kulle ƙofar, ta buɗe ƙofar ta shiga ta tsaya tana kallonsa. Ta haɗe hannayenta guda biyu tana kuka ta ce, "na san na yi kuskure, na san na ɓata maka da na auri wanin ka, amma don Allah ka yi haƙuri, ka tsaya ka ji abinda zan faɗa maka dalilina, na san in ka ji za ka yi min uzuri." "Babu abinda za ki faɗa masa ya fahimta, babu abinda bakin ki zai furta da zai fahimce ki. Duk ɗawainiyar da ya yi miki ki ka zaɓi ki bar shi ki auri wani, ki ka tsallakesa ki ka je ki ka yi aure a gidan kuɗi, ki ka bar shi da kwnaciya a asibiti. Ko a mafarki ban yi tunanin haka daga gare ki ba, ke kin san kaf ƴan gidan basa tare dake, amma ni ina bayan ki, in kowa ba ya sonki ni ɗin nan ina sonki. Amma yadda ki ka ɗibi yaji ki ka zuba masa a idanu ya saka na ji kin fita daga raina.” “Mutumin da ya ɗauko ki daga rana ya dawo dake inuwa, ya ba ki ci da sha da wajan kwanciya, ya ɗauki kyautar zuciya ya ba ki, ko yaushe cikin wahala da ke yake yi, da ya buɗe ido sunan ki yake fara ambata, duk abinda ya samu sunanki ya ke fara kira kafin kowa, amma duk ba ki gani ba, ki ka munafurce shi ki ka auri wanin sa duk da tarin ƙaunar da yake miki. Wallahi Islaha kin bani mamaki, kin nuna mana ke ba ƴar halak bace, dan duk ɗan halak bazai aikata butulcin da ki ka yi ba, sai yanzu nake gasgata maganar Mama da take cewa ba a san a bolar da iyaye ki suka haifa suka yar dake ba!." A tare suka juya suka ga yadda Adda tana wuci tana magana, a bayan ta kuma Mama ce da kuma Hanan. Islaha ta girgiza kai tana kuka tana kallon Adda ta ce, "wallahi ban munafurci Hamma, wallahi ban zaɓi kuɗi na barsa ba, ku yarda dani, na yi komai saboda shi ba dan na munafurce shi ba…..”ta faɗa tana kuka sosai. Mama ta ce, "waye zai yarda dake ɗin? Kaf ahlin gidan nan babu wanda zai yarda dake sai Baffa da ku ka ƙulla munafurcin tare, sai kuma ƙawar ki da matar babbanta, tunda sun je an basu abin duniya sun dawo unguwa suna barbaɗawa. Suna faɗar suna zauna da kakar Rehaan yola a falo ɗaya, kamar waɗanda suka zauna da wata matar da ta shahara a duniyar sahabai. Kin zaɓi kuɗi akan halacci, dan haka kar na sake ganin ƙafar ki a cikin gidan nan, ki goge mu a ciki tarihin rayuwarki, ki goge mu a cikin duniyar ki, ki je can ki ƙarata babu abinda ya dame ki da halin da Saheer zai shiga.” “Ni daman na san baza ki taɓa aurensa ba, an bani labarin yadda larabawa suka buɗe miki ido da kuɗi a Jeddah, da yadda suka mayar dake kamar matarsu suna yin abinda suka ga dama dake. Ki je can ki cigaba da rayuwa, amma in na sake ganin ƙafar ki a gidan nan sai na saka an yi miki abinda ba ki taɓa tunani ba!." Islaha ta kasa magana sai kuka, ba kukan komai take yi ba sai kukan kalmar ta zaɓi kuɗin ta bar halacci da suke faɗa, in suka faɗi maganar sai ta ji kamar ana soka mata kibiya a ƙirjinta, ta ya zata zaɓi kuɗi akan Hamma?. Wanne irin babban kuskure ta tafka a rayuwarta haka? Meyasa ta amincewa zuciyarta ta kai ta ga danasani, meyasa abinda ta ke yiwa kallon ƙaramin abu yana neman zamar mata ƙadangaren bakin tulu? Meyasa ta amince da wannan auren wani ba Hamma ba tun farko?. Bata gama tunani ba, taji an ja hannunta da ƙarfi an fizgota daga cikin ɗakin. Ƙiris ya rage bata faɗi ba, ta juyo tana kallon Saheer da yake kallonta idanunsa sun yi ja sosai, ya kasa magana sai kallonta kawai yake yi, ga shi ya rame sosai. Islaha ta zube a ƙasa ta ce, "Hamma ka yarda ni Islaha zan zaɓi kuɗi akanka?." Mama zata yi magana Islaha ta dakatar da ita ta ce, "Mama don Allah, ki bar shi ya bani amsa da bakinsa, na san shi ya san wacece Islaha." Islaha ta kalli Saheer ta ce, "Hamma ka yarda da kalamansu? Ka yarda na zaɓi kuɗi na bar ka Hamma? Na san na yi kuskure da na auri wanin ka, amma zan dawo gare ka, in ban dawo gare ka ba ni ba ƴar halak ba ce!.” Mama ta ce, “ai ba sai kin maimaita ba, daman ke ba ƴar halak ba ce, kuma za ki tabbatarwa da kowa kalaman ki da kanki.” Shi dai ya zuba mata ido kawai bai ce komai ba, kuma in bai yarda da gaske ta zaɓi kuɗin akansa  ba da me zai yarda? Ga shi dai a gaban idanunsa ta yi aure a gidan da ya yi tambari a garin a kaf Adamawa. Ɗan gidan shine lamba ɗaya a cikin masu kuɗin garin, duk wanda ya ji wannan maganar dole ya amince da ta auri kuɗi ta bar shi. Yana jin zafin hakan a ransa, yana jin ciwo da kishi mai tsanani, yana ji kamar zuciyarsa zata buga, yana ji kamar zata faso ƙirjinsa ta faɗo, amma bai san ta yadda zai yi maganin abun ba. Hanan ta ce, "malama ki tashi ki bar mana gida, ki je can ki zauna a gidan da ki ka zaɓa. Ki bar Hamma a nan, ke ki je gidan masu kuɗin da ki ka zaɓa a matsayin gidan mijin ki. Kin cutar da Hamma, kin zaɓi kuɗi akan halacci!." Mama ta kalle shi ta ce, "Kai Saheer! Ka kalle ta ka faɗa mata kar ta sake zuwa wajan ka, ta je ta zauna da mijin da ta aura saboda kuɗi." Saheer ya kalli Islaha da take kallonsa tana kuka, ya ɗauka kai bai ce komai ba sai ya koma da baya ya shiga ɗaki ya rufe ƙofar. Babu wanda ya cewa Islaha komai, suka shige ciki suka barta a wajan ita da Safeera. Safeera itama kuka take yi sosai, dan yanayin yadda suka yiwa ƙawarta ta abin bai yi mata daɗi ba, musamman in ta tuna yadda aka yi auren, da ya yadda ta sadaukar da rayuwarta da farin cikinta a kansa, sai ta ga basu yi mata adalci ba ko kaɗan, har suna cewa ta zaɓi kuɗi akan halacci. Ko shi Saheer ɗin da ya ƙi magana bai yi mata adalci ba, tunda ya san halinta ya kamata ya saurare ta ko ya ya ne. Safeera ta goge idanunta ta dafa kafaɗar Islaha ta ce, "tashi mu je Islaha." Ta miƙe a hankali ta kalli Safeera ta ce, "Na faɗa miki daman ni ba ƴar halak ba ce, jikina yana bani a......" Safeera ta rufe mata baki ta ce, "kar ki ƙara faɗar haka, Allah ya san zuciyar ki, nima na san silar auren, Sadik ma ya san dalilin auren. Mu mun san rayuwarki ki ka sadaukar saboda Saheer, shima kuma zai amince da haka, amma na faɗa miki sai ya nutsu sosai." Islaha ta kwantar da kanta a kafaɗar Safeera ta ce, "Ko magana ya ƙi ya yi min, ya ƙi ya kalle ni, na yi dansani ta fi dubu Safeera. Kina ji suna cewa na zaɓi kuɗi na bar halacci……” Muryarta tana rawa tana muna kanta ta ce, “Wai…ni ce na zaɓi kuɗi akan halacci, Safeera wai ni ake cewa na zaɓi Rehaan na bar Hamma. Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Safeera wai na zaɓi kuɗi akan Hamma…” Safeera tana kuka ta ce, “dukkanmu mun san gaskiya, kar ki damu kan ki.” “ina ji kamar naita kuka har a tashi duniya." Safeera ta dinga bubbbuga bayanta cikin rarrashi ta ce, "ki yi haƙuri, ki daina kuka, Allah yana tare dake." Ta goge hawayenta bata ce komai ba, ta ɗauki handbag ɗinta da ta cillar, sai kuma ta dafe kanta saboda yadda ya sara mata. Ta ce, "Kaina yana ciwo, numfashina ba ya fita daidai" ta faɗa tana jan numfashi da ƙarfi. Safeera ta ce, "Sannu. Ina maganin da aka ba ki a Jeddah?." "Ya ƙare, inhaler kuma ban san inda take ba, na bar kwalayen a gidan nan, na san yanzu sun zubar." Safeers ta ce, "zan duba miki ko an saka a cikin kayanki, mu je ki sha magani sai ki koma gida." Ta girgiza kai ta ce, "wajan aiki zamu je, sannan ina so na je orpanage wajan Yafindo ko ta dawo." Safeera ta ce, "to mu je." "Islaha!." A tare suka kalli wajan da suka ji an kira sunanta, suka ga Sadik ne ya shigo; yana ƙarasowa inda suke taaye yana kallonsu. Ya bi su  da kallo ya ce, "Lafiya dai ko?." Safeera ta ce, "babu lafiya Sadik, tun ƙarfe bakwai da rabi tana unguwar nan, ta zo wajan Saheer amma ya gaza fahimtar ta." Sadik ya ce, "Islaha Saheer bazai fahimce ki yanzu ba, Saheer ba a nutse yake ba kwata-kwata, yana buƙatar lokaci kafin ya gane abinda za ki faɗa masa. Abu ɗaya yake kallo yanzu, kin ci amanarsa kin auri wani ba shi ba, kuma su Mama suma sake ɗora shi akan hakan. Dole sai kin sake haƙuri na wani lokaci. Ke kin san halinsa, na tabbatar zai fahimce ki da zarar ya nutsu yadda ya kamata." Safeera ta ce, "amma ko magana bai yi mata ba, at least ya kama ko sannu ya ce, ai ya fi kowa saninta, masu kuɗi nawa ta tsallake saboda shi?." "Ba goyan bayansa nake yi ba Safeera, amma ina so ki tuna aure ta yi, wani ta aura daban ta bar Saheer; kuma shi bai san dalilinta ba, kuma a ransa yana jin haushinta, ni da ke ne kaɗai mu ka san abinda yake faruwa shi bai sani ba. Ku ba shi dama ya huta tukunna, in ya huta zan yi masa bayanin komai daki-daki." Islaha ta ɗaga kai ta goge ido ta ce, "shikenan, babu damuwa..." ta faɗa tana fara tafiya, sai jiri ya ɗauke tata yi baya zata faɗi, kafin Safeera ta riƙe ta ta tsaya da kanta. Sadik ya ce, "ki yi a hankali, ki samu waje ki zauna." Ta zauna a inda ta saba zama a compound ɗin gidan, ta ja numfashi ta ce, "jiri nake ji kaɗan." Safeera ta ce, "sannu, ki huta sai mu je." Sai kuma ta miƙe tsaye ta ce, "Safeera mu je kawai" ta faɗa tana fita daga gidan da gaggawa. Sadik ya bi bayanta da kallo cikin tsananin tausayin Islaha, kafin ya shiga wajan Saheer da yake tsaye a gaban window yana kallon duk abinda yake faruwa. Sadik yana shiga Saheer ya ce, "Wanne abu ku ka shirya wanda ban san dashi ba? Akan me ku ke magana wanda ni ban san maganar ba?.... Nana Haleema. RDB3P14 Nana Haleema. Sadik ya kalle sa ganin ya kafe shi da idanu sannan ya ce, "ka zauna tukunna sai na faɗa maka abinda ya faru." Saheer ya ce, "ka faɗa min kawai, wanne abu ku ka shirya kai da ita da Safeera?." Sadik ya kalle sa na wani lokaci ya sauke numfashi ya ce, "Lokacin da ka ke hannun masu garkuwa da mutane, hankalin Islaha ya tashi sosai, in na ce maka ta fi kowa damuwa da halin da ka shiga kar ka musa. A wannan lokacin Baffa ya zo mata da maganar auren ɗan gidan AbdulAziz yola, ta ma kasa fahimtar maganar balle ta ɗauka. Tana ta ɓoye mana bata so mu sani, sai ranar da suka dinga dukan ka suka ce in ba a kawo kuɗi ba sai sun kashe ka, a lokacin ta ce kar a kashe ka zata nemo kuɗin." Saheer ya zuba masa ido yana jin abinda yake faɗa, ganin Sadik ya shiru ya ce, "ina jinka, sai me?." Sadik ya ce, "shine ta nemi wanda aka ce ana so a haɗa su auren, shima ya neme ta, ya ce zai aure ta saboda mahaifinsa yana son ya aure ta ba dan shi yana so ba, ita kuma ta ce zata aure sa in dai zai bata kuɗin da za a fanso ka. A kan wannan tsarin ake har yanzu, auren wata biyar ne a tsakaninsu. Saheer ya zuba masa ido yana kallonsa, sai kuma ga girgiza kai cike da mamakin raina masa hankali da Sadik yayi ya ce, "Kana so ka ce min shi wanda ta aura ɗin, shine ya bata miliyan hamsin kawai dan ta zauna dashi na wata biyar, ita kuma ta amince ta karɓa dan a sako ni, haka ne?." "Ya ka ke tambaya kamar ba ka yarda da abinda na faɗa maka ba?.” Saheer ya yi masa wani kallo ya ce, "kana tunanin zan yarda da wannan shirmen ne? Na lura kai da ita da Safeera bakin ku ɗaya, an sace ta, daga baya ta dawo kuma ta hana ayi bincike, ta tafi ƙasar waje ta dawo da kuɗin da ban san na meye, yanzu kuma ta ɗaura aure da wani, shima kuma ana faɗa min saboda ni ta yi hakan?." "Tafiyar ta Jeddah wannan bana goyan baya, sace ta ma ban san anyi ba. Amma wannan na sani, a ko ina zan bugi ƙirji na ce dani aka yi. Duk da nayi ƙoƙarin nuna mata illar hakan, ta nuna min ita a kanka babu abinda baza ta yi ba. Duk abinda ta yi saboda kai ta yi, zata zauna da wani a matsayin mijinta na wata biyar saboda ceton ranka da rayuwarka. Ko ka yarda, ko kar ka yarda, wannan maganar itace gaskiya, wallahi bata yi niyar cin amanarka ba, bata yi niyar wulaƙanta ka ko ta zaɓi kuɗi ta barka ba. Wannan shine zance na gaskiya, amma na san babu lallai ka amince." "Kaima ka san ba ka ɗauko layin da zan amince ba, ka san wannan maganar ta ka da wasan yara ta yi kama ba da maganar gaskiya ba, bazan amince da wannan tatsuniyar ba ba Sadik. Haka kawai saboda mahaifinsa sai ya bata miliyan hamsin? Waye shi a garin nan? Shine AbdulAziz Yolan ko kuma shine Rehaan Yolan?." Sai kuma ya ɗan tafi tunani kafin ya ce, "wait! Da farko ta ce mana Rehaan Yola ne ya sace ta har ta ɗauko masa kuɗi, daga baya ta tafi Jeddah ta ce a can ma ta haɗu dashi, yanzu kuma ta dawo ta yi aure a gidansu da sunan auren contaract." Ya dafe kai yana murmushi mai ciwo ya ce, "na jima ban ga ƴan wasan kwaikwayo kamar Islaha ba, na daɗe ban ga wacce ta ƙware a iya buga game kamar Islaha ba. Gabaɗaya ta mayar da ƙwaƙwalen mu empty, ta saka mun koma yaranta, sai saka mana igiya take tana jan mu inda ta ga dama." Sadik ya yi shiru dan shima sai yanzu tunaninsa ya kai inda na Saheer ya kai. Tabbas akwai ayar tambaya akan Islaha, meyasa Rehaan yola yake shigowa rayuwarta ta fuska mara daɗi?. Da fari ta ce shi ya sace ta, ta zo ta ce ai shi ta ɗaukowa kuɗi zata je Jeddah ta nemo kuɗin dan ta biya sa, sai kuma ta tafi aiki wata ƙasar, ta dawo tace musu a gidan Rehaan ta yi aikin a can Jeddah. Yanzu kuma batu ake na itace matarsa ce ta aure, duk da yadda abin ya faru da ta yadda suka yi auren, a addini da al'ada matarsa ce ta halak ba ta yarjejeniya ba, tunda ko a lokacin Rehaan ya bar duniya sai ta yi masa takaba ko da bata yi iddah ba. Tabbas akwai abinda Islaha ta shirya, shi kansa yanzu bai yi na'am da lamarinta ba, akwai lauje a cikin naɗi. Saheer ya katse masa tunani ya ce, "Haka kawai AbdulAziz Yola zai zo wajen Baffa ya ce shi Islaha yake so a aurawa ɗansa? To wanne ɗan nasa a ciki?." Sadik ya ce, "Wannan ita za ka tambaya bani ba." "Meyasa sai Islaha, duk matan da suke Yola da wajen Yola sai Islaha za a gani ace za a aura? Me yasa Baffa ya amince da auren, shima ya san wannan tatsuniyar ta ku?." "Baffa bai sani ba, amma shine ya ba da auren Islaha. Shima akwai manufarsa a akan hakan, dan ba dan shi ba da baza a yi auren ba." Saheer ya girgiza kai ya ce, "Shikenan, an kyauta min kuma na gode. Na yarda da batunsu Mama, Islaha mage ce mai kwanciyar ɗaukar rai, tabbas akwai abinda take burin cimmawa a cikin rayuwarta, da biyu take waɗananan abubuwan. Na gode da sakayyar da na samu daga wajenta, na gode da abinda ta yi min” ya faɗa yana barin wajen. Sadik ya bi shi da kallo har ya shige ɗaki, ya ɗan shiru yana tunani sannan ya fita shima zuciyarsa cike da tunanin wannan chakwakiyar ta Islaha. Islaha suna fita daga gidan ta tsaya a ƙofar gidan ta kawar da kai gefe. Safeerw ta ce, "idanunki sun yi ja, mu je gida ki wanke fuska." Ta girgiza kai ta ce, "ki ɗauko abinda za ki ɗauko daga gidan mu wuce kawai, bazan koma ba." Sanin halinta na taurin kai sai bata takura mata ba ta koma ba, ta koma ta ɗauko handbag ɗinta suka hau napep suka tafi wajan aiki. Tunda suka tafi babu wanda yake yiwa kowa magana, Islaha tana jikin window ta saka kanta waje tana shan iska idanunta a kulle. Har suka je bakin gate ɗin babu wanda ya ce kanzil, suna sauka Safeera ta biya kuɗin suka nufi ciki. Suna shiga suka haɗa ido da Ummi, ta bi su da kallo Islaha kam kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kai ta nufi ciki da hanzari. Da Chairman suka fara haɗuwa, ya saki murmushin jin daɗi ganin Islaha ya ce, "Barka da zuwa Islaha, da alama an sa ki masoyin na ki ko?." Islaha ta ƙaƙalo murmushi ta ce, "ina kwana." "lafiya lau. Ya dawo?." "Eh ya dawo." "Allah ya kiyaye gaba, ya kare mu daga sharrinsu." "Amin ya rabbi, na gode." Chairman ya ce, "da na san za ki zo ai da na kira ki tun safe kin yi mana labaran ƙarfe shida. Ko da yake, an canja timetable za ki iya zuwa board ki duba. Sannan akwai interview, akwai mutane uku da zamu yi invinting ɗinsu, kuma kin san aikin ki ne. Ki same ni a office in kin huta, akwai maganar da zamu tattauna." Ta ɗaga kai ta ce, "To." Chairman ya wuce itama ta wuce office cikin sanyin jiki da tunanin mafita. Tana shiga ta ajjiye jakar ta, ta dafe kai da duka hannayenta ta kunna fankar office ɗin. Sai kuma ta miƙe ta fita zuwa board ɗin da ya ce an canja timetable. A nan ta ga har an canja sunanta an sakata a wacce zata gabatar da labaran safe a satin, sannan akwai inverview da talkshow guda ɗaya. Ta lumshe ido ta buɗe ta riƙe ƙugu tana cigaba da sauke numfashi dan sarƙewa yake yi. "Hajiya islaha, amarya." Gabanta ya faɗi jin sunan amarya da aka kira ta da shi daga bayanta, ta haɗɗiye yawu ta juyo a hankali suka haɗa ido da wanda yake tsaye a bayanta. Nana Haleema. RDB3P15 Nana Haleema. Tana juyowa suka haɗa da Muslim, sai ta ƙirƙiro murmushi ta ce, "Alhaji Muslim, ango." Ya yi dariya ya ce, "da zan samu na zama angon mace kamar ki ai da na more. Ya ki ke, ya Saheer ɗin? Ina fatan yana cikin ƙoshin lafiya." Ta ɗaga kai ta ce, "Lafiya lau yake." "ma sha Allah, haka ake so daman. Jiya na je gidan ku akan maganar interview ɗin da ake so a gayyaci minister of depence amma aka ce min bakya nan, na kira ki sau babu adadi ba ki ɗauka ba kuma ba ki kira ni ba.” Ta kalle sa ta ce, "ba ka tambayi Safeera ba?." "ba mu yi magana ba." "Ina gidansu Safeera." Mulsim ya harare ta ya ce, "Ni ce min aka yi kin yi aure." Ta ɓoye tashin hankalin jin maganar auren a bakin Muslim ta ce, "Wanne irin aure, na gaske ko na wasa?." Ya yi dariya ya ce, "kin fini sani." Islaha murmusa ta ce, "To na ji kana wani batu ne kamar wata ƴar tsana. Yanzu tsakani da Allah sai na yi aure ba ku sani ba? Auren kamar wasan yara, ace har an yi an gama babu wanda ya sani a gidan nan?." Muslim ya ɗan taɓe baki ya ce, "kin san yanzu celebrities auren sirri suke yi, na sani ko kema shi ki ka yi." "Nima celebrity ɗin ce?." "Itace mana, waye bai sanki ba, Hajiya Islaha?." Ta sake murmusawa tana tattaro nutsuwa da dakiya amma bata ce komai ba. A lokacin Saleem ya zo wajan ya ce, "Islaha zamu je ɗaukar report, in kin fito daga wajan manager ina jiran ki." Ta ɗaga kai ta bar wajan ta nufi office ɗin manager. Muslim ya bita da kallo har ta ɓace sannan ya ce, "meyasa bata so a san ta yi aure? Bayan wanda ya faɗa min ina da tabbacin bazai yi min ƙarya ba? Meyasa ta yi irin wannnan auren na gaggawa haka?." Ya sake yin shiru yana nazari kafin ya ce, "ya zama dole na nemo abinda yake faruwa, in ma auren sirri ne ni zan buɗe sirrin." Islaha tana shiga wajan manager ta same sa a zaune, itama ta zauna sannan ya ce, "yauwa Islaha, a tsara iv da ya kamata a tura musu ta email, in saƙon bai yu ba sai mu je a kai musu. Ga list ɗin waɗanda nake so in da yuwa mu gansu a satin nan, ko ina suka ce mu je zamu je, dan muna da buƙatar mu tattauna dasu." Islaha ta karɓi list ɗin ta ce, "in sha Allah zan yi ƙoƙari." A lokacin aka ƙwanƙwasa ƙofar aka shigo, Safeera ta ƙaraso ta ce, "Chairman ga file ɗin." Ya karɓa yana dubawa. Daidai lokacin da aka hasko fuskar Rehaan Yola, ana labarin bikin ƙanwarsa da ya tara manyan mutane ciki harda shi da kansa. Islaha bata san ta yi tsaki ba, ta haɗe rai tana ɗauke kanta daga kan tv. _magana tana ta yaɗuwa akan Rehaan Yola ya yi auren sirri, da gaske hakan ta faru ko kuma ƙaryar mutane ce.?_ Abinda ɗan jaridan ya faɗa kenan, ta ja wani dogon tsakin da sai da Chairman ya ɗago ya kalle ta, ya kalli tv ya ce, "ba ki gayyato mana shi ba har yanzu, muna ta jira mu ganshi a tv mu Islaha, amma shiru." Islsha fuska a haɗe ta ce, "Har yanzu bamu yi magana da Mr Jafar ba, daman shine ya yi min alƙawari." "Ai ya kamata ku yi magana Islaha, bana so wata channel ɗin su riga mu gayyato shi har ya yi magana da yarensa, ina so mu zama mu ne na farko." Ta ɗaga kai ta ce, "In sha Allah zan yi iya ƙoƙarina wajan ganin na gayyato shi." Ya yi murmushin jin daɗi ya ce, "Na san za ki iya, za ku iya tafiya." Tare suka fito da Safeera da take ta gimtse dariya, tsabar son tsokana har office ta bita, Islaha tana saka id card a wuya, sannan ta ɗauki recoder da handbag ɗinta, ta ɗauki laptop ɗinta ta ƙi kallon Safeera dan ta san tsokana ce. Safeera ta ce, "Uhum, wai matar mutum ake cewa yaushe zata gayyato mijinta ayi hira dashi, Abin burgewa.” Islaha ta yi mata banza bata saurare ta ba, sai sake haɗe fuska da ta yi ko kallon inda take bata yi. "Ke Islaha, auren nan da alama bazai zama na sirri ba fa, ga shi har maganar ta fara fita." Islaha ta kalle ta ce, "Ni muslim ya tsare wai ance na yi aure, ina faɗa masa ƙarya ne yana cewa bai yarda ba. Ni dai na shiga uku, wannan dabara bata amfane ni da komai ba sai danasani, wanda na yi dan shi ɗin ma ko kallona ya ƙi yi. Kin san Allah, wallahi Hamma ya bani haushi, na yi danasanin zuwa inda yake, ban yi tunanin zai kasa buɗe baki ya yi min magana ba, ko da gaske abinda ake faɗa akan na bar shi saboda kuɗi na ɗauka akwai zumunci mai ƙarfi a tsakanina da shi." Safeera ta ce, "bai kyauta ba kam gaskiya, nima ban ji daɗin yadda ya yi shiru ba, ai ko sannu ya ce miki. Amma ta wani ɓangaren ba shi da laifi Islaha, yana sonki so mai tsanani, yana cikin raɗaɗi da ciwo, yana buƙatar hutu mai yawa." Ta ɗaga kai bata ce komai ba sai kuma ta ja tsaki ta ce, "Zan sake yiwa Mr Jafar magana akan hira da Rehaan, ko dan Chairman ya bar ni na sha iska.” "Rehaan gatsal, babu mai gida ko oga?." "Safeera zan iya shaƙe ki wataran." Safeera ta ƙyalƙyale da dariya ta ce, "Yi haƙuri matar oga, kuma amaryar Saheer, kai astagafirullah!" Ta faɗa tunawa da auren Islaha take haɗa ta da wani. "Meye na tuban, ƙarya ki ka faɗa?." "amma ba a daidai lokacin nan ya kamata na faɗa ba." "Ke ki ka sani." "Mu je na ta ke miki baya, na zama escord ɗin ki kafin nan gaba na gasken su fara take miki baya." Islaha ta harare ta. Safeera ta sake yin dariya suka fito dan tana jin daɗin tsokanarta. A tsaye suka samu Ummi ganin Islaha sai ta ɗan yi murmushi ta ce, "Islaha ya ki ke." Islaha ta bita da wani bad look tana frowning face ɗinta ta ce, "Lafiya." Daga haka suka wuce ta. Ummi ta ce, "akan me suke magana haka, matar wa ta zama, da gaske dai ta yi auren ko bata yi ba?." Babu mai bata amsa, hakan ya saka kai tsaye ta nufi wajan abokinta Muslim. Kiran wayar Abba ne ya tashi Rehaan daga bacci, ya miƙe yana kallon agogo ya ga ƙarfe sha ɗaya na rana, ya yi tsaki dan ya jima bai yi bacci ba daren jiya, ya jima yana hidimar aiki, yana buƙatar yin bacci mai nauyi da safe. Ya jawo wayar ya ɗauka ya saka a speaker Abba ya ce, "Rehaan kana gida?." Cikin muryar bacci ya ce, "Uhum Abba, ina kwana." "Lafiya lau. Ana ta knocking ƙofar shiru, Daada ta ba da abinci a kawo ba a buɗe ba." Cike da mamaki ya ce, "Abinci Abba? Daman ana kawo min abinci ne?." Abba ya ce, "matarka aka aikowa ai." Ya runtse ido cike da takaici da ɓacin rai, dan shi wallahi ya manta da ita a tare da shi, sai kawai ya yi shiru bai ce komai ba. Abba ya ce, "ku zo ku buɗe, ana tsaye ana jira." Rehaa ya bi wayar da kallo, ya yi tsaki ya kira number Banisha dan ta zo ta buɗe amma har ta katse bata ɗauka ba ya san bacci take yi.. Ya yi tsaki ya fi sau goma, ya sauka daga kan gadon a hankali, ya saka takalminsa ya fito daga ɗakin. Falon yana nan shiru babu kowa kamar yadda ya bar shi, ya kalli ƙofar ɗakinta dan shi bazai iya sauka ya karɓar mata abinci ba, in ba abincin Mamy ba babu abincin wanda yake ci sai na chef ɗinsa, bata isa tana bacci ya sauka ta karɓar mata abinci ya ajjiye ba. Slowly yake takawa yana nufar ƙofar ɗakinta, ya buɗe yana kallon ɗakin ganin komai a kashe yake alamun babu kowa. Ya ja numfashi ya jawo ƙofar ya rufe ya fito daga ɗakin yana kiran wayar Abba. Abba yana ɗauka ya ce, “Abba su koma da abincin kawai, na ga kamar bata nan." Cikin mamaki Abba ya ce, "ka ga kamar bata nan kamar ya? Kana so ka ce ta fita ba ka sani ba?." "Abba ai ba sai na sani ba, amma dai ni ban ganta ba." Yana jiyo salatin Daada daga waya, sai ya yi saurin katse kiran ya shiga ɗaki yana faɗin, "wannan tsohuwa tana takura min sosai, ta saka ni a gaba kamar itace ta haife ni, ina ruwana dan bata nan?" Ya faɗa tana shiga bathroom dan shikenan an katse masa bacci. Bayan ya fito ya tsaya a gaban mirror, ya ɗauki hair burner yana burning gashin sa da lafiyayyen scent mai daɗi. Burner ɗin bata fi girman brush ba, zaka jona ta a jikin socket, sannam ka zuba turaren da ka ke so a cikinta, ka ɗaure saman ta da comb, hayaƙin turaren yana shiga gashi kuma kana taje gashin. Bayan ya gama ya fara shafawa fuskarsa skin care, tun daga kan su oli cream babu abinda bai saka ba. Lokaci ɗaya fuskarsa ta fara fitar da kyau fiye da na baya. Ya miƙe ya ɗauki ƙananun kaya ya saka, ya ɗauki band ya ɗaure kansa a lokacin aka fara kiran wayar. Yana kallon wayar ya yi ya ga chef Yola, ya ɗauke kai bai ɗauka ba. Wani kiran ya sake shigowa ya ga cleaner nan ma ya ɗauke kansa. sai da ya gama tsaf, sannan ya kira chef da cleaner ɗin ya basu umarnin shigowa. Duk suna da access key ɗin da suke buɗe ƙofar, kowa ya fara aikinsa. Ba jimawa Chef ya kawo masa ice matcha dan ya san fav ɗinsa ne musamman da safe. Ai kam ya sha macha ɗin sosai, kafin ya miƙe ya sauka dan yana so ya shiga wajan Mamy. Yana fitowa Abba ya fara kiransa a waya ya ɗauka Abba ya ce, "Ka zo wajan Daada ina son ganinka yanzun nan." Ya zubawa wayar ido ganin Abba ya kashe wayar, ya fita daga inda yake ya nufi zuwa, ya nufi wajan Daada ransa a ɓace, dan ya san maganar bazata wuce ta yarinyar da ba shi yace a ɗaura masa aure da ita ba.... Nana Haleema. RDB3P16 Nana Haleema. Tunda ya shiga ya haɗe rai, ganin kowa yana zaune harda Mamy, bazai ba da fuskar da Daada zata faɗi wani abin da bai yi masa ba. Ya ƙarasa ya zauna a inda ya saba zama indai za a zauna a parlour Daada nan ne wajansa, kafin ya gaishe su Daada ta ce, "ina ƴar mutane ta tafi?." Ya yi shiru bai bata amsa ba kamar ba da shi take magana ba. Daada ta ce, "da kai nake magana fa, ina ƴar mutane ta tafi tun safe ba ka sani ba?." Nan ma ya share bai ce komai ba. Mama ta ce, "Rehaan da kai ake magana fa, ina islaha ta tafi?." Ya ɗago kansa yana kallon Daada ya ce, "Wace Islaha?." Daada ta yi masa daƙuwa ta ce, "uwarka Nadira, itace Ishlaya." Ya wani kalle ta kamar zai rama zagin da ta yi masa, sai kuma ya yi shiru. Daada ta ce, "kalle ni da kyau, in za ka rama sai ka rama tunda na ga tashin rashin kunya ka ke ji dashi." Abba da ya san yadda yake bi da Rehaan ɗin a tausashe ya ce, "Rehaan ina yarinyar ta tafi tun sassafe ba ka sani ba?." Ray ya kalli Abba ya ce, "Abba duk inda zata je sai na sani? Ina ruwana da inda zata je ko zata zauna? Yarinya ce ita da in ba a ganta ba za a yi tunanin wani abun ya same ta?. Kuma ni meye ya kawo ni a cikin maganar dan kawai ta fita?." "Saboda a waje ɗaya ku ke kwana, kuma matar ka ce ta aure” Daada ta bashi amsa tana harararsa.” Rehaan ya kalli Daada ya ce, "dan a waje ɗaya mu ke kwana ba hakan yana nufin duk inda zata je sai na sani ba, ba hakan yana nufin dan ta fita a dinga tambayata ina ta je ba. Tana da right ɗin zuwa duk inda ta ga dama, zan ɗaure ta ne ko kuma ita baiwa ce?…..” Daada zata yi magana ya riga ta ya ce, “Daada don Allah ki daina ɗaga min hankali akan abinda bai kamata ba, ko bacci ban samu na yi yadda ya kamata ba, kin saka an tashe ni." Daada ta ce, "rayuwar turawa za ka fara yi mana a gidan kenan, ka ga abinda uwarka ta ke yi shiyasa za ka ɗora matarka a kan hakan ko?.” Ya sake kallon ta Daada ta ce, "Eh mana, itama ai ba tambayar babanka take yi in zata fita ba, kai kuma ka tashi a wajenta ka ga yadda take tafiyar da rayuwar aurenta, sai ka ɗauka hakan abin arzuƙi ne shiyasa kaima ka ke ƙoƙarin ɗora matarka akan haka. To wallahi Allah bazan lamunci wannan iskancin ba, bazan ɗauki wannan rashin tarbiyyar a cikin jikokina ba, in ita ta yi daman ba jinin mu bace, amma kai jinin mu ne, matarka ma ta mu ce. Mu jinin fulani ne, babu wani jini da ya gurɓata mu balle a canja mana al'ada." "Itama Mamy babu wani jini da ya gurɓata ta, in ma ta gurɓace ɗin sai dai in jinin fulanin ne suka mayar da ita haka" ya bata amsa kai tsaye yana kallon ta. Abba ya buɗe baki cike da maamkinsa ya ce, "Rehaan...!" Rehaan ya ce, "Abba kar ka hana ni magana, ko yaushe kai ka ke cewa kar nace komai saboda mahaifiyarka ce, bayan ni tawa mahaifiyar take faɗawa duk abinda ta ga dama…..” Ya ɗan dakata kafin ya ɗora ya ce, “Uwa ba ta fi uwa ba Abba…… Shikenan dan ta kasance ba jinin fulani ba sai ta dinga takurawa rayuwarta? Meyasa bata ƙaunarta bata ƙaunar ƴaƴanta?. Maganar da ake yi daban, maganar da ta sako daban, me ya sako Mamy a cikin maganar nan? Dan wata ta fita kawai sai ya zama da laifin Mamy?. Ni na ce mata ina son wacce ta haɗa auren ne, ba kai ka saka na amince da auren har aka zo yanzu ba?." Kowa ya zuba amsa ido dan ya basu mamaki sosai, dan kowa ya san Rehaan yana da haƙuri, ba kowa ne zai jure cin kashin da Daada take yiwa babaraa a gaban idanunsa ba. Shi magana ba damunsa ta yi ba, in ba ya zama dole ba sai a haɗu a tashi bai ce komai ba. Tunda ya buɗe baki yana faɗawa Daada haka kowa ya dan ta ƙure sa, sai dai a ƙi faɗar gaskiya saboda baƙin ciki, Shiyasa ya fashe yake zazzage mata duk abinda yazo ransa. Mama ta ce, "Rehaan! Daada ka ke faɗawa haka." Ya jiyo ya kalli Mama ya ce, "Eh ita ɗin, nima uwata ta faɗawa ai. Yadda Abba yake jin zafin abinda na faɗa a yanzu, nima haka nake ji a duk lokacin da ta faɗawa Mamy magana, Yadda yake sonta haka nake son Mamy, maybe ba ya yiwa Daada son da nake yiwa Mamy. Komai ace Mamy, me ta tarewa mutanen gidan nan?.” Abba ya dafa kafaɗarsa ya ce, "Rehaan kar na sake jin bakin ka, ya isa." Rehaan ya sunkuyar da kai, sai kuma ya kalli Mamy da bata ce komai ba kuma baza ka fassara yanayinta akan fuskar ta ba. Sai gani suka yi Daada ta miƙe ta ƙaraso inda Rehaan yake ta zauna a ƙasa ta ce, "dake ni." Ya yi mata banza bai ma kalle ta ba. Ta sake cewa, "Sai ka dake ni za ka tabbatar min da kai ɗin ruwa biyu ne, ba jinin fulani ne kaɗai a jikin ka." Ya ɗauke kai daga kallon ta bai ce komai ba, dan Abba ya hana sa ne amma da ya tambaye ta su fulanin nan larabawa ne? A ganinsa babu wani tribe da ya kai su tunda a cikinsu annabi yake. Abba ya ce, "Daada ki yi haƙuri ki tashi." "Bazan tashi ba, sai Rehaan ya dake ni, in bai dake ni ba babu inda zan je." Abba ya ƙaraso ya kamata ya ce, "Don Allah ki yi haƙuri, ki tashi." Daada ta daki ƙasa ta ce, "Babu inda zan je, sai ya dake ni sannan zan miƙe daga wajan nan. Babu inda zan je daga nan, ya dake ni ya huce haushinsa. Sai ya dake ni sannan zan san shi jinin indiyawa ne.” Abba ya ce, "Rehaan bata haƙuri." Cikin fulatanci Abba ya yi magana, shima da yaren ya bata haƙuri kamar yadda Abba ya ce. Daada ta harare sa alamun daman haƙurin ta ke jira ta ce, "Kuma wallahi ka je ka nemo ƴar mutane, ka dawo da ita cikin gidan nan….” Sai kuma ta sake kallonsa ta ce, “Wai ya aka yi ma aka bari ta fita daga gidan nan? Akwai driver da ya tafi kaita ne?." Mama ta yi caraf ta ce, "ita kaɗai ta tafi Daada, Kuma a matsayin da take da shi a gidan nan fita kan titi ta hau abin hawa na haya ba matsayinta bane, yadda driver zai ja Rehaan a mota itama haka ya kamata ayi mata tunda aurenta yake yi. Haba, ko masu aikin gidan nan in za a yi aike zuwa kasuwa ko wani waje mota suke hawa, babu mai hawa napep in dai aiken gida ne. Balle ita, matarsa guda ace ta hau napep, wannan bai kamata ba kuma zubar da ƙima da sunan gidan nan ne.” Sai kuwa ta sake zuga Daada ta ce, "Ai da yake ya raina ni, ya raina abinda ya fito daga hannuna shiyasa yake wannan wulaƙancin. Gida kamar wannan, miji kamarsa ace matarsa ta hau abin hawa ta fita, meye ribar hakan?" Ta faɗa tana kallon Abba. Abba ya ce, "ba a kyauta ba kam, amma a yi masa uzurin rashin sanin ta fita ɗin, kin ga yanzu sai ya samar mata da wanda zai dinga kai ta duk inda zata je. Itama kuma fita a wannan yanayin bai kamata ace ta fita ba, ina zata je haka da safe tana amsa sunan amarya?." "Yana ɗaure mata fuska da harara ba dole ta fita ba? Wannan auren kawai sunansa auren je ka na yi ka." Rehaan ya ce, "Daman ai ke ki ka haɗa, akwai wanda ya ce miki yana so ne?" Ya faɗa yana kallon Daada. Daada ta ce, "kuma dole ka zauna da ita ba, ba ka isa ka rabu da ita ba indai ina da rai. Zama da Ishlaya daram, babu wanda ya isa ya ce ta bar gidan nan." Ya ɗauke kansa daga kallonta bai ce komai ba Daada ta ce, "kira wayarta mu ji tana ina." Ya yi mata banza kamar bai ji ba, Abba ya ce, "magana ake maka, ka kira ta aji tana ina." "Ita wa zan kira Abba?." "Ita matarka." "Da wayata kuma? Ka san ba kowa nake kira da wayata ba." Daada ta sake fusata ta ce, "shikenan! Ta tabbata ya raina ni ya raina ubansa, ubansa yana faɗa shima yana faɗa, Daman ance in mutum yana yana samun kuɗi sai ya raina kowa har iyayensa…..” “Rehaan baban naka ka ke faɗawa haka?." Shi bai ma kalle ta ba waya yake dannawa a nutse, dan ya daina ƙyaleta tana faɗa masa abinda ta ga dama. Abba jin abinda Daada ta faɗa sai ya girgiza kai ya ce, "ka kira ta Rehaan." A gajiye da maganar ya ce, "Abba ni..." sai kuma ya yi shiru ya yi kamar yana kiran waya, kafin ya kalle su bai ce komai ba ya kifa wayar a jikinsa yana kallon Mamy. Daada ta ce, "daga yau ban amince ta sake hawa napep ta fita ba, kuma duk inda zata je ka san ta tafi, ba rayuwar fararen fata zaka yi mana a gida ba, ka ji ko?." Ya kalle ta bai yi magana ba sai daga baya ya ce, "abinci da ake kaiwa apartment ɗina, a daina." Daada ta harare shi ta ce, "In aka ƙi fa uban ƴan iyayi? Ni ka ke bawa umarni ko baban ka?.” Sai bai tanka mata ba ya yi shiru kowa ya yi mamakin yadda take faɗa yana faɗa, duk da daman yana yi amma da alamaa yau ta kai shi ƙarshe. Bai ce komai ba kawai ya miƙe ya fita daga falon. Yana fita suka haɗu da Salman Rehaan ya yi murmushi ya ce, "Ka yi kyau." Salman ya ce, "wajan ta zani." "Ita wa?." "Wacce ka ce tana sona." Rehaan ya yi dariya dan yadda Salman ya yi maganar ya ba shi dariya sosai ya ce, "Bata nan, amma in anjima ka dawo sai ka ganta." "In aka yi kiran sallah na nawa?." "In aka yi kiran sallah na huɗu." Salman ya yi shiru yana irga sallah ta nawa ya rage ayi, sai kuma ya juya ya koma yana murna zai ga Islaha har ya je wajenta. Anya Rehaan ba ka yi ganganci ba?. Nana Haleema. RDB3P17 Nana Haleema. Rehaan wajan Mamy ya shiga ya kwanta a kan kujera ya lumshe idanunsa yana jin takaici a ransa akan abinda ake yi masa akan Islaha. Mamy ta shigo da sallama ya amsa ya ga ta ɗauki handbag ta ce, "Zan je guest house, daga nan zamu je airport zasu wuce india." Ya miƙe zaune ya ce, "da wuri haka? Na yi tunanin za a haɗa outing ayi shopping kuma a faɗa min zasu koma?." "Gaskiya baza su zauna ba, amma nima very soon zan je, sai mu je gabaɗaya." "Komai ya zama ready?." "Muna magana da Bilal, komai ya yi ready. Daga nan sai India in sha Allah." Ya ɗaga kai ya ce, "Allah ya kai su lafiya, ko in raka ki?." Mamy ta yi murmushi tana kallon sa ta ce, "in za ka je sai mu je, in za ka huta kuma ka huta kawai. Riyya ta kira ni tana ta kuka, wai she missed me." Ya yi murmushi tunawa da ƙanwartasa tana hannun Jazy da ya gama zubawa cikinsa magani, ya san Jazy ba ɗaga mata ƙafa zai yi ba, ga abubuwan da ya sha kama sa yana sha. Amma ya yi alƙawarin ba shi mamaki, in ya cutar masa da ƙanwa Allah sai ya hukunta shi. Mamy ta ce, "Rehaaan!." Rehaan ya kalli ta ce, "bana son yarinyar nan da aka haɗa ku ko kaɗan, tana zama silar ɓacin ranka, ni kuma duk abinda zai ɓata maka rai bana ƙaunarsa." Ya miƙe tsaye ya ce, "Mamy nima bana sonta, ta silarta ake mocking ɗin ki. Amma kar ki damu, zan kawo ƙarshen komai, ba za a ɗauki lokaci ba in sha Allah." "Maganar auren ka ta yaɗu fa, duk da ana ta kokwanto akan gaskiya ne ko ƙarya." Ya ɗaga kai ya ce, "na gani, nana so a sani ne saboda ba aure na yi ba, in na yi aure kowa zai sani." Ta shafa kansa ta ce, "Auren Rehaan kamata ya yi duniya ta sani ba ki ɗaya, ba iya nigeria ba." Ya murmusa ya ce, "za a yi bikin da ba a taɓa yin irinsa ba." Mamy ta yi dariya ta ce, "Allah ya kaimu. Ka kula da kyau, kar ka saki jiki da yarinyar nan, zata iya cutar dakai." Ya yi murmushi bai ce komai ba, Mamy ta ce, "na haɗa maka lunch, yana ciki a dinning. Ka tashi Banisha daga bacci sai ku ci tare, tana ta bacci ko breakfast bata yi ba." "Okay Mamy." "Sai na dawo" ta faɗa tana fita da sauri ya koma ya zauna yana lumshe idanunsa cikin ƙaunar Mamynsa..... Islaha basu gama aikin da zasu yi ba sai bayan sallar la'asar, duk ta gaji kuma ko abinci bata ci ba. Haka suka rabu da su Saleem ta wuce orphanage. Kamar ko yaushe da ta je kai tsaye wajan girki ta wuce dan Yafindo take so ta gani. Tana shiga suka haɗu da Baba Tabawa, Islaha da murmushi ta ce, "Baba ina yini." Ta yi murmushi itama ta ce, "Lafiya lau Islaha, kwana biyu kin ɓuya ba a ganin ki kwata-kwata." Islaha ta ce, "aiki ne ya yi min yawa, yanzu ma daga can nake. Yafindo ta dawo kuwa?." Baba ta ce, "ta dawo." Islaha ta ji daɗi ya mamaye mata zuciya ta ce, "Tana ina?." Kafin a bata amsa Yafindo ta shigo tana magana. Islaha ta ce, "Hajiya Yafindo ina yini." Da sauri ta kalli Islaha, gabanta ya yanke ya faɗi, ta ɗauke kai kafin ta ce, "Lafiya lau." Islaha ta ƙarasa inda take tsate ta ce, "Wajan ki nazo." Yafindo jikinta ya fara rawa ta girgiza kai ta ce, "aiki nake yi yanzu." Islaha ta bita da kallon mamaki ganin ta tsorata sosai, kafin ta ce, "Ai iya maganar baki ce, ba wani abun ba." "ni dai bazan saurare ki ba, dan Allah ki ƙyale ni na zauna lafiya." Islaha ta dinga karanyar yanayinta kafin ta ce, "Yi min magana zai hana ki zama lafiya ne?." Yafindo ta fara hawaye ta ce, "Dan Allah ki ƙyale ni, ki tafi kafin a ganki a wajena don Allah." Islaha ta girgiza kai ta ce, "Yi haƙuri ki daina kuka, zan tafi. Amma ki bani saƙon da..." bata gama ji ba ta cillar da ludayin hannunta ta fita da gaggawa. Baba ta kalli Islaha ta ce, "Nima na rasa me yake samunta, tunda ta dawo take a ɗarare gabaɗaya bata sakewa." Islaha ta ce, “Baba kina da waya?." "Ina da ita." "Don Allah bani lambar ki, zan dinga kira ina tambayar ki." Ba musu ta bata lamba ta yi saving Islaha ta fito daha kitchen ɗin tana tunani. Karo suka yi da mutum akan hanyar ta, Islaha ta kalli wacce suka yi karo suka haɗa ido, sai da gabanta ya faɗi ganin Hafsa ce. Islaha ta bita da kallo ganin yadda yarinya ta canja, ta yi haske ga wata kiɓa ta musamman da ta ƙara. Hafsa ta ɗauke kai kamar bata gane Islaha ba ta raɓa zata wuce. Ta riƙo hannunta ta dawo da ita baya ta ce, "In fuskar ki bata nuna kin sanni ba zuciyar ki ta nuna Hafsa. Irin rayuwar da aka ɗora ku kenan, a haka ake so a ga kun rayu? Kuna lalata rayuwarku su kuma kuna tara musu kuɗi, kun ɓata tarbiyar ku saboda abinda za ku tafi ku bari a duniya. Tunda haka ki ka zaɓa ya yi kyau, je ki" ta faɗa tana sakin hannunta sai Hafsan ta kasa motsawa. Fadwa ta ƙaraso wajan ta ce, "Hafsa me ki ke yi a nan? Zo mu wuce" ta faɗa tana jan hannun Hafsan da ƙarfi suka bar wajan. Ta office ɗin Mama ta zo wucewa, ta ga yadda yara suke shiga ciki sai kawai ta buɗe ƙofar itama ta shiga. Ganinta ya saka Mama ta miƙewa tsaye babu shiri, Islaha ta kawar da tashin hankalin fuskar ta tana kallon yaran ɗaya bayan ɗaya. Mama ta ce, "Islaha ke ce da yammar nan?." Islsha ta ɗaga kai ta ce, "Ni ce. Sannu ya aiki?." "Lafiya lau. Kwana biyu bakya shigowa." "Aiki ne yake yi min yawa. Waɗananan sababbin zuwa ne?." Mama ta kalli yaran ta ce, "wannan ne sabon zuwa? Da yawa duk kin san su." Ta ɗaga kai ta ce, "meeting ku ke yi kenan?." Mama ta ce, "a kan dai sana'arsu ne kawai." Ta ɗaga kai tana sake binsu da kallo kafin ta ce, "Shikenan, sai anjima" ta faɗa tana fita daga offife ɗin. Mama da gaggawa ta ce, "ku je, zan neme ku." Duk suka tashi suka fita. Ta ɗauki waya ta kira ana ɗauka ta ce, "Kaza ta dawo gidanta tana tone-tone. A harbe ta ko a yanka ta. Aikin nan da na ce a dakata da shi, a aiwatar da shi a yanzu. Kamar yadda ba faɗa, bana so kowa sani.” Ta faɗa tana yanke wayae tana bin bayan Islaha da kallo. Islaha tunda ta bar wajan take tunanin ya kamata ta ɗauko mataki kafin abin ya sake yin girma. Ta da ki hannunta tana dafe kai ta ce, "Hujja mai ƙarfi ce babu, Zainab ce hujjata ban san inda take ba, a ina zan ga Zainab? A ina zan nemo ta? Ina ta shiga?." "Dole na san abinda zan yi, ya zamar min dole na san abimda zan yi" ta faɗa tana shiga lambar zainab tana scrolling ɗin recording ɗin da ta taɓa tura mata lokacin da tana a Jeddah har recording ɗin ya fita. Baki buɗe Islaha take kallon wayar, wayar ta suɓuce a hannunta ta faɗi ƙasa. Audio ɗin ta ga babu shi a kan chat ɗinsu, an goge shi daga kan wayarta an goge shi daga chat ɗinta da Zainab. A bayyane ta ce, "innalillhi wa'inna ilaihir raji'un!" Ta faɗa tana sake ɗauko wayar ta cigaba da scrolling amma babu komai. "Waye ya goge, ina ya shiga, yaushe aka goge shi?!" Ta faɗa tana cigana da bincika wayar amma babu. Sai ta shiga lambar Hamma dan a lokacin tura masa, hannunta yana rawa take dubawa, ga maganar da ta yi masa akan audio ɗin amma babu audio ɗin. Kanta ya sara ta shiga lambar Barr shima an goge daga kan wayarta, ta shiga Safeera itama an goge. Bata san hawaye ya fara sakko mata ba ta runtse ido ta ce, "a ina aka goge? Yaushe aka goge min, waye ya goge?." Sai kuma ta share hawaye ta ce, "Su waye suke yi min haka, waye yake tare dani da fuska biyu?." "Ya zama dole na gano inda Zainab take, na gamo dalilin da ya saka Yafindo ta kasa yi min magana, sannan na gano munafukan da suke tare dani. Ni wayata babu security, kowa yana iya ɗauka ya yi amfani da ita. Amma waye ya san na turawa Hamma, Safeera da Barr a lokacui ɗaya da har ya bi lambobinsu ya goge?." Kanta ya kulle ta rasa abinda zata yi wanda zai kawo mata mafita, ta jingina da bango tana jan numfashi, a lokacin aka fara kiran sallar magrib, cikin ta ƙulle saboda yunwa mai tsanani, ta runtse ido ta fito ta hau napep ta nufi gidansu Safeera. Na ce waye ne yake fitar da sirrin Islaha? Mu je zuwa Nana Haleema. RDB3P18 Nana Haleema. Islaha da sallama ta shiga gidansu Safeera ta tarar dasu suna zaune a tsakar gida gabaɗayansu suna cin abinci. Duk suka amsa suna kallon ta Baba ya ce, "Wa nake gani kamar amarya Islaha?." Islaha ta shiga ciki ta ce, "Ni ce Baba. Ina yini." Baba ya ce, "Lafiya lau Islaha. Allah ya sanya alkhairi ya zaunar daku lafiya, Baffa ai ya faɗa min komai, na ce gwara hakan, Allah ya sa hakan alkhairi ne." Mama ce kaɗai ta amsa da amin, ta ɗora da faɗin, "Kai ba ka ga yadda iyalan gidan suke ƙaunarta ba, abin ya burge ni sosai." Islaha yaƙe kawai take yi wanda ya fi kuka ciwo, sannan kalli Safeera ta ce, "Sallah zan yi." A tare suka shiga ɗaki Islaha ta yi alwala ta tayar da sallar magrib bayan ta idar ta ce, "Yunwa nake ji Safeera." Safeera ta ce, "bara na kawo miki." Ta fita ta kawo mata abinci, ta ci kaɗan ta ajjiye, dan yunwar ta yi mata yawa har ta kasa cin abincin. Safeera ta ce, "na ganki wani iri, wani abu ya faru ne?." "Meye ma bai faru ba, neman chaja min kai ake yi, ana so a tarwatsa min ƙwaƙwalwata kawai." "Meya faru?." "In ka ga ɓarna kana so ka kai ƙara don a gyara wajan wa ake zuwa? Police, Dss, ko kotu kai tsaye?. Safeera ta ce, "bana ce ba gaskiya, amma zan tambayar miki na ji inda ake zuwa. Wani abu ne ya faru?." Islaha ta ce, "komai ma ya faru, na gaji da ajjiye maganar nan ta gidan da na tashi, lokacin da zan bayyanata ya yi, ko kashe ni za a yi sai a kashe ni. Ina so na san inda Zainab take, ina so na san waye a jikina yake ƙoƙarin kaini ƙasa." Safeera ta zauna a kusa da ita ta ce, "kamar ya a kai ki ƙasa, ban gane ba?." Islaha ta ce, "mu bar maganar nan kawai." Safeera ta ce, "Ai shikenan. Wai sai yanzu ki ka ci abinci tun tea ɗin nan na safe?." "Sai yanzu wallahi, shiyasa gabaɗaya cikina babu daɗi abincin ma na kasa cin mai yawa." "Ai dole. Ki daina yiwa kan ki haka, kar ki sake jawowa kan ki wata matsalar." Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, suna zaune har aka yi sallar i'sha suka yi sallah a ɗakin Islaha ta koma ta jingina da wardrobe ɗin Safeera kamar ba tafiya zata yi ba. "Ba yanzu za ki wuce ba?." Ba tare da ta kalle ta ba ta ce, "Ina?." "Gidanki mana." Ta ɗago ido ta kalle ta ta ce, "ina da gida ne?." Safeera ta gyara kalamanta ta ce, "gidan mijin contract." Ta yi ƙaramin tsaki ta kulle idanunta ta ja numfashi sai kuma ta buɗe ido ta ce, "ni bana son tunawa zan koma wallahi, bana son komawa gidan nan." "Haka za ki yi haƙuri ki koma, ke ki ka ce min so ki ke ya karya rule ɗaya dan ki samu mafaka. Ke kuma ga shi kina ta karya masa rule bakya tunanin shima zai samu mafaka a kanki?." Islaha ta kalle ta ta ce, "bana so komawa ne, wallahi ko ganinsa bana ƙaunar yi, bana son tunawa ina tare da shi balle har na je gidan." Safeera ta ce, "haƙuri za ki yi, ki tashi mu je na raka ki ki hau mota ki koma." Kamar bazata tashi ba ta yi mata shiru, sai daga baya dai ta jure ta miƙe suka fito, ta yiwa Mama sallama suka fito kan titi. Safeera ta ce, "meye ma sunan unguwar?." "kya tambayi kaza hanyar rafi? In za ki saka min wuƙa ki ce min ya sunan unguwar wallahi ban sani ba." Safeera ta yi dariya ta ce, "ni Safeera na ga ta kaina, wannan wacce irin amarya ce da bata san sunan unguwar da aka kai ta ba?." Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, tana ji Safeera tana tsokanar ta amma bata tanka ba. Safeera ta tare mata napep ta faɗa masa sunan unguwar ta shiga ta tafi ita kuma koma tana yi mata dariya.     A farkon estate ɗin akwai security barrier gate, irin ƙarfen nan da ake rufe hanyar, wanda sai an ɗaga maka shi sannan za ka wuce, kuma napep ba ya shiga wajan sai in kana ɗaya daga cikin ƴan estate ɗin, kuma gabaɗaya estate ɗin daga Abba sai yaransa, kuma duk sun girmi hawa napep. Mai napep ya ce, "Hajiya a nan babur yake tsayawa, ba ya ahiga ciki." Islaha bata ce komai ba ta sauka ta ba shi kuɗinsa ta fara takawa a hankali zuwa wajan. Yadda take tafiyar sai ka ɗauka bata da gaskiya, tana tafiya tana waiwayon bayanta, sannan a hankali take tafiyar kamar bata so. Bata yi zato ba ta ga security da ƙatuwar bindiga a tsaye a gabanta. Gabanta ya faɗi sosai, amma sai ta yi ƙoƙarin danne tsoron ta ta tsaya cak tana kallonsa, shima ya bita da kallo ya ce, "Hajiya cire facemask ɗin." Bata ƙi ba ta cire shi ya bita fuskar ta da kallo dan shi dai bai santa baya ce, "ina za ki je?." "Zan shiga gidan nan" ta faɗa tana nuna gidansu Rehaan su da hannunta. Ya kalli gidan sannan ya kalle ta ya ce, "wajan wa za ki je?." Islaha ta lumshe ido cike da takaici ta ce, "Daada." "Ta san da zuwan ki?." Ta ɗaga kai alamun eh. Ya ce, "mu bata sanar mana zata yi baƙuwa ba, ki kira ta a waya mu ji in da gaske ki ke." Ɗayan da suke tare daga gefe ya ce, "Ƙarya suke yi fa, sun ga an yi biki ana ta shiga da fita, shine yau ma suka dawo." Islaha ta juya ta kalle sa jin abinda ya ce, sai ta ɗauke kai bata ce komai ba dan bata san me zata ce musu ba, gwara ta yi shiru tunda da almajira ta yi musu kama. Wanda yake gabanta ya ce, "Ki kira ta mu ji in da gaske ki ke, gidan nan ba a yin baƙi masu zuwa a napep. Kuma kaf masu aikin na san su, babu ke a cikin su." "Ka ga na yi maka kama da mai aiki?" Ta faɗa tana kallon sa cike da takaici. Ya kalle ta ya ce, "Masu aikin gidan basu da kama, haka suke kamar ki." Ta yi tsaki a ƙufule ta ce, "in za ka bari na wuce ka bari, in baza ka bari ba na koma inda na fito. Ka tsare ni a hanya kana yi min tambaya kamar wacce zata shiga gidan tuba?." "Ke ni ki ke faɗawa haka?." "Na faɗa, don Allah ka saka bindigar hannunka ka harbe na mutu." Zai yi magana suka ji horn ɗin mota daga bayansu, yana ganin motar ya gane suka ɗaga masa ƙarfen dan ya wuce. Yana zuwa kusa da Islaha ya sauke glass ƙasa yana kallon ta ya ce, "Miss Islaha." Jin an kira sunanta sai ta kalli motar, ta ga Jafar ne a ciki ya yi kwalliya cikin manyan kaya, kansa ɗauke da hula ya yi kyau kana ganinsa ka ga ango. Kafin ta yi magana ya ce, "me ki ke yi a nan a tsaye?." Wanda suke magana dashi ya ce, "Oga ba mu santa ba, ta sauka daga napep zata shiga cikin, mun ce wajan wa zata je tace Daada, mun ce ta yi mata waya taƙi. Har tana yi min rashin kunya, wai na harbe ta." Ya murmusa dan ya san zata aikata ya ce, "Kar ku sake tare ta, ko sau nawa za ku ganta kar ku ce mata komai." "Okay Sir" suka amsa gabaɗayansu. Jazy ya kalli Islaha ya ce, "Zo mu ƙarasa." Kamar baza ta je ba sai kuma ta shiga motar Jazy ya ja motar suka shiga. Kasa cewa komai ta yi, dan a fusace take sosai zuciyar ta a sama take akan wukaƙancin da aka yi mata. Bata so ya yi magana ta sauke masa kwandon masifa shiyasa ta kama kanta. Jazy ya ce, "Miss Islaha me ya fito dake daga gidan nan ke kaɗai? Babu mota babu security? Ba ki san matsayin ki ya wuce haka ba?" Daidai lokacin da yake danna horn ama buɗe masa gate ɗin gidan. Islaha ta ce, "na je wajan aiki ne." "Aiki! A yau ɗin?." Ta yi shiru bata amsa ba ya ce, "kin manta ke amarya ce?." Ta kalle sa ta ga ba ita yake kallo ba glass ɗin gabansa yake kallo. Islaha ta yi ƙaramin tsaki cikin ko in kula ta ce, "amaran dai suna inda suke, ni kam wannan suna bai dace dani ba." Ciki yake shiga da motar har aparment ɗin Ray sannan ya kalle ta ya ce, "Ke kuwa sunan ya dace dake Miss, ko na ce Mrs Rehaan, yanzu Miss ba na ki bane." Bata ce komai ba ya ce, "Seriously fita ke kaɗai bai dace dake ba, yanzu ba dah bane, kina da buƙatar a killace ki. Ki duba abinda aka yi miki yanzu, in wani ya ji an yiwa matar Rehaan haka babban abin kunya ne.” "Bani da wannan buƙata Mr Jafar, ni ba ƴar gwamna ba, ba matar shugaban ƙasa ba, killace ni ɗin me za a yi? Wani na kashe da sai na fita da security saboda kar a ɗauki fansar kisan a kaina?. Wallahi bazan lamunci fita da wasu mutane ba, ban ce ina so ba, a bari duk ranar da ya ɗauko original wife sai a bata su dan su kula da lafiyar ta, ni kam bana so." Ya kashe motar sannan ya ce, "ke fake wife ce?." "Ni na fi fake wife zama fake." Ya yi dariya ya ce, "Islaha kenan, kina da drama" ya faɗa yana buɗe motar ya fita itama ta fita daga motar. Shine ya yi unlocking ƙofar, dan ita in za a kashe ta bata san me suke dannawa ba, ya buɗe falon suka shiga dogon corridor ɗin da yake falon kafin ka shiga. Ƙhamshi ya mamaye ko ina a falon, sai ƙhamshi yake yi kuma ko tass musamman tiles ɗin har fuskar ka kana gani. Basu same shi a falon ƙasan ba, Jazy ya hau saman tana bayansa. Suna shiga falon suka same sa yana danna waya ga laptop a gabansa yana video call, ga takardu a jibge a gabanda. Jazy aya ƙarasa falon ita kuma ta karya kwana inda ɗakinta yake. Jazy ya ce, "Mr Busy." Bai ko kalle sa ba ya cigaba da magana da english, ana faɗa masa yana jotting a wayarsa kafin ya gama a katse kiran. Ya ja numfashi ya ce, "zan je englaand in sha Allah." Sai kuma ya kalli Jazy suka haɗa ido ya ce, "sai kawai ka fito ka bar Riyya ita kaɗai?." Jazy ya ce, "Janan da su Ikram suna can." Ya ɗan yi murmushi ya ce, "ta ya zan iya auren ƙannena? Sune fa ƙawayen matar tawa." "Sai me?." "sai rashin class." "A wajan ka kenan. Bilal ne ya kira ni, yace yana ta neman ka baya samu. Akwai waɗanda suka kawo kaya mall, kayan sun yi yawan da dole sai da kai." Ray ya harare sa ya ce, "kai ko ni?." Shima ya rama hararar ya ce, "kai dai." Ray ya koma kalar tausayi ya ce, "Jazy ba ka tausayina, dame ka ke so na ji? Kaina ya kusa ya yi bindinga Allah." "Zama billionaire ai ba wasa ba, haka zaka cigaba da haƙuri. Matarka ce ma abin tausayi, yanayin yadda ka ke aikace-aikace nan ba ka da lokacin ta." Bai amsa ba Jazy ya ce, "ga asibiti ma ana neman ka." Ya yi masa shiru bai ce komai ba, sai kuma ya ɗauki ice matcha ɗinsa yana sha yana shafa kansa. "Ray barin Islaha ta fita ita kaɗai bai dace ba, kana taƙamar auren sirri ka yi amma ka san bana sirri bane, tunda jama'ar gidan nan kaf sun sani. Ɗazu ma a news an yi maganar auren nan naka, ana so a gasgata da gaske ne ko ƙarya. Barinta ita kaɗai ba daidai bane, yanzu na haɗu da ita a farkon estate ɗin nan an hanata shigowa, yanzu hakan siyawa kai mutunci ne? Matarka guda ace security sun hana ta wucewa?.” "Kai baza ku takura min akanta ba fa, ni na ce ta fita ita kaɗai ɗin? Meyasa bata nemi wani a gidan nan ya fita da ita ba?. Ya ku ke ɗora min laifin da ba nawa ba?." "kai ya kamata ka samar mata driver ɗaya da zai dinga kai ta inda zata je, matarka ce fa." "Point of correection! Ka kira ta da C wife, a haka nake kallonta ba mata ba” ya furta yana hararsa. Jazy ya ce, "Koma dai meye matarka sunanta, ban damu da wani C wife ba, tunda an bada sadaki an shaida sunanta matar ka. Ni zan yi magana da Shams, ya bani mutum ɗaya a ajjiye mata duk inda zata je su dinga comminicating a waya." Ray ya taɓe baki bai ce komai ba yana jinsa yana waya da Shams har ya ba shi number Lawal driver, ya kira ya ce yazo ya same sa. Sai da ya gama wayar sannan ya kalle shi ta ƙasan idanu ya ce, "amma in za ka yi aure na biyu da ita za ka yi ko?." Jazy ya kalle sa ya ce, "Eh mana, jira nake ka sake ta sai na ɗauka, ai ba haramci a ciki ko?." "I see, zaƙewar ka akanta ya yi yawa, kamar wata mai mahimmaci a gare ka. Amma ka sani sai dai ka rabu da Riyya, baza ka haɗa min ƙanwa da wannan gurɓatacciyar ragowar su Ubaid ɗin ba." Jazy ya ɗora ƙafa kan ɗaya ya ce, "wai ko kana kishinta ne?” Ya faɗa yana kallonsa dan yanayin yadda ya damu da maimaita magana ɗaya a kanta sai zuciyarsa take faɗa masa kishi ne… Nana Haleema. RDB3P19 Nana Haleema. Rehaan matcha ɗin da ya saka a bakinsa sai da ta dawo saboda yadda maganar ta dake shi, ya sarƙe yana tari kafin ya nutsu ya ce, "kishin wa? Ka taɓa ganin ana kishin irinsu ne daman?." Jazy ya ce, "Abin ne da mamaki, ba ka da magana sai maimaita yarinyar Ubaid ce, in ba kishi ka ke yi ba me ka ke yi? Wanda ake kishi ake yiwa irin abinda ka ke yi a kanta.” “Ba ka da hankali Jazy, yarinyar da har miscarrige ta yi na yi kishinta na ce ina kishin wa?.” “Sai ka yi ai Rehaan, matar ka ce yanzu, in ma ƴar iska ce kaima ka zama mijin ƴar iska." "Da na ga ranar da zan yi kishin wannan abin gwara na ga ranar mutuwata. Allah ba dan Abba ba, da yanzu bata cikin gidan nan. To na riga na yi masa alƙawari, da baza ta yi 48 hours a gidan nan ba. Bana son saɓa alƙawari shiyasa." Jazy ya murmusa ya ce, "ka daina badmouthing ɗinta, ba ka sanin a inda za ka amfana da wani a rayuwar ka." "To ban da ita. Ya isa, mu bar zancen nan kawai." Jazy ya yi shiru bai sake magana ba, amma a ransa yana fatan Allah ya kawo ranar da Ray zai yi danasani akan kalamansa. Dan shi ya yaba da Islaha sosai, yana yi masa fatan zama da ita, dan kowa ya san ba dan kuɗinsa ko ɗaukaka a auresa ba. Jazy ya miƙe ya ce, "kai ka sani kuma, ni zan tafi wajan matata." Ray bai ce masa komai ba ya cigaba da kaɗa ƙafarsa. A lokacin Islaha ta fito daga ɗaki ta kalli Jazy ta ce, "Mr Jafar zan iya tambayar ka?." "Ina jin ki Mrs Ray." Ta wani kalle sa ta ce, "Islaha sunana, ko ka ce miss ɗin, amma ka daina kirana da abinda ka ce, wallahi bana so." Ya murmusa ya ce, "ina jin ki Miss." "ina kana zargin wani abu mara kyau daga wani waje haka ina ake kai report?." "Kamar wanne abu kenan? Kin san komai stage by stage ne, ko wanne da side ɗinsa." "Kamar kana zargin cin zarafin mata, da safara dasu da sauran su dai.”" "Okay. National angency for the prohibition of trafficking in person (NAPTIP). Su ake kaiwa irin wannan report ɗin." "Suna da office a nan Yola?." Ya ɗan yi shiru yana tunani ya ce, "gaskiya babu. Ina tunanin Abuja, kano, lagos etc. Amma babu a nan, but za ki iya kiransu a daga inda ki ke. Abinda ake so make sure kina da evideance akan abinda za ki yi reporting." Ta ɗaga kai ta ce, "na gode." Bai ce komai ba ya wuce ta ya sauka. Sai kuma ta bi bayansa a last stair ta tsaya ta ce, "Mr Jafar." Ya kalle ta ta ce, "Alƙawarin da muka yi dakai a farkon haɗuwar mu, shi nake so ka cika min." "na me kenan?." "Interview da Rehaan Yola." Ya yi wata dariya yana kallon ta ya ce, "Miss Islaha, ai na fita daga wannan contarct ɗin, yanzu kin fi ni kusa da shi." Islaha ta haɗe rai ta ce, "Don Allah ka bar wasa, da gaske nake." "nima da gaske nake Miss, kawai ki zaɓi rana ki zo gida ki saka masa camera shikenan fa." "Please." Ya sake yin murmushi ya ce, "Shikenan Miss, zamu yi maganar da shi." "na gode. Amma don Allah kar ya san ni ce presenter sai ranar, bazan iya taking rubbish ɗinsa ba." Ya sake yin murmushi ya ɗaga mata kai ya fita ita kuma ta koma sama. Da ta koma ɗaki laptop ta ɗauko dan ta fara tura mails ɗin da Chairman ya bata. Tana shigar da report ɗinsu na ɗazu dan gobe za a gabatar da news ɗin. Ɗakin babu network yadda ya kamata, sai ta tuna bata gan shi a falo ba, ta saka hijjab ta dawo falon ta zauna tana aikinta. Har ya fito ya zauna bata sani ba, aiki kawai take yi sai kuma ta dakata ta ɗauki waya ta kira Saleem suka ɗan jima suna magana, kafin ta kashe ta cigaba da danne danne ta. Ta jima a haka kafin ta ɗan jingina da kujera tana jan numfashi na gajiya. "Im so tired." Islaha ta ji ya faɗa, da sauri ta kalle sa ta ga babu abinda yake yi amma wai ya gaji. Ta yi ƙaramin tsaki ta ce, "ragon maza kawai, wannan shine ya rako maza duniya, komai nasa irin na mata ne, ko ni na fi sa ƙarfi da kuzari" ta faɗa ƙasa ƙasa tana cigaba da aikinta. Wayarsa ta yi vibrating ya kalla ya ga Abba ne sai ya miƙe zaune sosai ya ɗaga, Abba ya ce, "Ta dawo?." A ciki ya ce, "Eh." "Kai da ita ku zo ina son ganin ku." Ya ɗaga kansa sanann ya ce, "To." Daga haka ya kashe wayar. Ya kalle ta ya ga ba shi take kallo ba ta mayar da hankali akan aikinta kawai. Ya yi tsaki ya rasa ta ina ma zai iya yi mata magana, dan shi ko kallon ta baya so balle ya yi mata magana. Ya sake kallon ta ya ce, "let's go." Ta kalle sa ta ƙasan ido suka haɗa ido, bata janye ido ba duk da yadda idanunsa yake rolling a kanta bai saka ta ɗauke ba. Ta mayar da kanta zuwa ga abinda take yi kamar bata ji ba. Ya bita da kallo ganin ta raina masa hankali ya ce, "Ba ki ji ba?." Islaha ta ɗago ta ce, "dani ka ke?." Saboda takaici da rainin hankalin da ta yi masa bai san lokacin da ya ce, "A'a, da kaina nake." Jin amsar da ya bata sai bata sake magana ba, ta cigaba da abinda take yi tunda ya ce da kansa yake. Ray ya zuba mata ido kawai yana kallon ta, babu wata macen da ta take latsa shi kamar ta, tunda ya ke a duniya babu macen da ta ke mayar da shi kamar wani banza sai ita. Ita kaɗai ce ta ke kallon idonsa ta faɗi duk abinda ya zo bakinta, ita kaɗai ce yana magana tana mayar masa, ya rasa me ta gani a cikinsa da ta yi saurin raina sa haka. Amma bazai yi mamaki ba, tunda ya san wacece ita, rashin kunya da raina maza a wajan irinsu ba komai bane, tunda ido ya buɗe ta saba da maza kala-kala. Jin shirun ya yi yawa bai ce komai ba sai ta kalle sa, ta ga ya harɗe hannu a ƙirji kawai yana kallon ta. Islaha ta ɓata rai ta ce, "wannan kallo ya fita daga musulunci, a dinga sassautawa, ni ba maharramarka ba ce." Ya buɗe ido kaɗan ya ce, "me zan kalla?." "Abinda ka ke kallo yanzu." "Na kalli me, abinda ya rage?." Ta ɗaga ido tana kallonsa sai ta ga ya miƙe tsaye kamar ba shi ya yi maganar ba. Ranta ya ɓaci sosai, dan tana jin haushi in ya ce mata ragowar nan, kalmar tana tsaya mata a rai sosai. Ta girgiza kai ta ce, "Ai ka san ragowar ma kala-kala ne, akwai ragowar da ta fi sabo daraja da ƙima, akwai ragowar da ta sabo tsada. Ko ban faɗa ba, ka san ni da nake ragowar na fi sababbi da yawa tsada. Shiyasa ka ke morewa lokacin ka da ƙaramar damar da ka samu ta kallona. Ban ga laifinka ba, ka kalla son ranka, lokaci kaɗan ya rage maka kallon ya gagari idanunka." Bai amsa mata ba ya share ta magana da ita ma sai ya ji kamar yana zubar da class ɗin da ya ke da shi ne, In ya tuna har zubar da ciki ta yi sai ya ji komai ya fice masa daga rai gabaɗaya. Bai ɗauki wayarsa ba ya yi hanyar sauka, sai ta ji tsoro ya shige ta, kuma daman ya ce tazo su je. Ta miƙe da hanzari ta bi bayansa ta samu yana dab da fita daga apartment ɗin. Islaha harare sa ta ce, "ji wata tafiya kamar ta mata, shi wannan gabaɗaya da mace ya yi kama, da zai saka kayan mata da ya saje damu, babu ƙarfi a tare dashi ko kaɗan." Yana fita ta bi bayansa a hankali har ya shiga ɓangaren Abba. Ta ja ta tsaya bata shiga ba Abba yana kallonta ta window ya kalli Rehaan ya ce, "ka ce ta shigo." Rehaan ya koma ya buɗe ƙofar sai ta ji muryar Abba ya ce, "shigo mana." Ta shiga a nutse tare da yin sallama. Abba ya amsa yana nuna mata wajan zama ita kuma ta zauna. Islaha ta ce, "Ina yini." "lafiya lau amarya, ya gida?." "Alhamdu lillah." "Ina ki ka je da safe?." "wajan aiki na je" ta faɗa a sanyaye. "Meyasa ba ki faɗa za ki je ba ki ka hau napep?." Ta yi shiru bata amsa ba dan bata san me zata ce ba. Abba ya ce, "Ko nan gaba kar ki sake, gidan nan ba a hawa napep, akwai direbobi da yawa da zasu kai ki duk inda ki ke so, kin ji ko?." Islaha ta ce, "To, in sha Allah bazan sake ba." "Yauwa haka nake so na ji." Abba ya kalli Rehaan ya ce, "Kai kuma laifin ka ne, ka san ai tana zuwa aiki, na faɗa maka maganar nan tun ba yau ba, gudun maganar Daada sai ka samu wanda zai dinga kai ta yana dawowa da ita. Yanzu ga shi nan ka tarawa kanka baki da magana a gidan nan." Ya kalli Abba ya ce, "Abba ni ban san da aikin ba, kuma ni na manta muna tare da ita." Abba ya harari Rehaan jin abinda yake faɗa a gabanta, a ganinsa kamar cin fuska ne ya faɗi haka a gabanta. Abba ya kalli Islaha da bata ɗago ba ya ce, "Jafar ya faɗa min ya nemi driver da zai dinga kai ki, gobe ƙarfe nawa za ki tafi?." "ƙarfe bakwai." "To in yazo zai jira ki, zai kai ki in kin gama ya je ya dawo da ke. Ko da wasa kar na sake ji kin fita kin hau napep, kin ji?." "In sha Allah, bazan sake ba." "Yauwa. Daman abinda ya saka na kira ku kenan, ku je sai da safe." Islaga ce ta fara miƙewa ta fita daga apartment ɗin, ta tsaya tana kallon gidan yara sai wasa su ke yi da kekuna kamar ba dare ba. Sai kuma ta nufi kowa inda aka ajjiye ta, tana hango ƙofar falon ta ga Salman a tsaye ya cake a wajan. Tana ƙarasawa wajan suka haɗa ido da ita, sai ya yi dariya ya ce, "na zo wajan ki." Sai da gabanta ya faɗi tunawa ance fa mahaukaci ne, kuma zai iya yi nata dukan tsiya ƙarshe ya karya ta kuma ya karya banza, amma sai ta daure ta ce, "Sannu da zuwa." Sai ta tsaya tana jiran Rehaan, dan ita bata san ya ake buɗe ƙofar ba dan ta ga lambobi ake sakawa, shi kuma thumb print ya ke sakawa. Salman kallon ta kawai yake yi, ita kuma tana daga gefe a tsorace dan bata san abinda zai yi mata ba. Allah Allah take ta hango Ray ya taho amma bata gano sa ba, ta ɗan matsa gefe kaɗan, tana sake kalle-kalle amma shiru babu alamunsa. "Sister." Da sauri ta juya ta ga Banisha a tsaye sai ta ce, “Banisha yi min unlocking ƙofar nan." Banisha ta yi dariya ta ce, "date of birth ɗina ne code ɗin." Ta faɗa tana buɗewa Islaha tana kallonta har ƙofar ta buɗe. Islaha tana shiga Salman ya bi bayanta Banisha ta ce, "Hamma Salman, Ray ɗin ba ya nan yana wajan Mamy." Ya nuna mata Islaha yana maƙale kafaɗa ya ce, "Ni wajanta na zo mu yi wasa." Kafin Islaha ta ce wani abu sai gashi ya ɗare kan kujera yana kallonta. Banisha ta ce, "Ka zo mu tafi, ko na kira maka Abba." Salman ya noƙe kafaɗa ya ce, "ni bazan je ba." Banisha ta ce, "sai na faɗawa Abba." Ta faɗa tana fita Islaha ji take kamar ta bi bayanta saboda tsoro. Islaha kallon sa take yi dan gaskiya Salman ya girma, ba sai na ce babba bane kowa ya kalle sa ya san ya girma sosai. Bata san ya kan ƴan gidan yake ba, amma tana da tabbacin ya girmewa Rehaan, ga shi da tsaho da kyau ma sha Allah, amma Allah ya haɗa shi da lalurar taɓim hankali. Salman kalle ta ya ce, "Mu yi wasa?." Ta ɗan yi murmushi bata ce komai ba, ita dai tana daga tsaye yadda yana kawo mata hari zata arce a guje. Buga ƙofar ake yi da ƙarfi kamar za a cire ta, Islaha daɗi ya mamaye mata zuciya, ta ƙarasa ta buɗe ƙofar suka haɗa ido da Umma. Umma ta jawo hannunta zuwa waje a fusace ta ce, "Wanne mugun abun ki ke yiwa ɗana da ki ka saka shi a ɗaki daga ke sai shi? Me ki ke yi masa a cikin gidansu kuma a ɓangaren mijin ki?" Ta faɗa da ƙarfi tana buɗe ido waje tana kallon Islaha da take kallonta........ Nana Haleema. RDB3P20 Nana Haleema. Islaha ta yi sak tana kallon Umma ta rasa abinda zata ce saboda mamakin kalamanta. Umma ta shiga falon ta jawo hannun Salman ta ce, "malam fito daga nan, me take yi maka da ta saka ka a ɗaki ta kulle ƙofa?." Salman kamar zai yi kuka ya ce, "Umma wasa muke yi." "Wasan me ku ke yi? Kana baligi tana baliga wasan meye a tsakani ku?." Zai yi magana ta ce, "Sai na tsinke ka da mari, wuce ka bani waje, in na sake ganinka a ɓangaren nan sai na fasa maka baki, tafi na ce!" Ta faɗa cikin tsawa tana nuna masa hanya. Salman ya noƙe kafaɗa ya ce, "ni dai a wajanta zan zauna, ni ina sonta, kuma Rehaan ya ce min itama tana sona." Da hanzari ta nufe sa zata dake shi, ya kwasa a guje ya bar wajan ko waiwaye ba ya yi. Umma ta kalli Islaha bayan ya bar wajen ta ce, "Babu abinda ya haɗa ki da Salman, kar na sake ganin ya shiga inda ki ke. Wasan meye tsakanin ki da shi? Ba dan Allah ya kawo ni ba Allah ne kaɗai ya san abinda za ki yi masa. Kar ki sake aikata hakan daga yau, in ba haka ba bazan raga miki ba wallahi." Mamy da Rehaan da Banisha da suka ƙaraso wajan, ganin Umma tana masifa sai Mamy ta ce, "Me ya faru?." Umma ta nuna Islaha ta ce, "Sirikar ki amayar Rehaan, ki faɗa mata kar ta sake saka min ɗa a ɗaki ta rufe ƙofa. Maharraminta ne ko kuma ɗan uwanta ne? Me take yi masa da zata rufe ƙofa da shi a parlour har yana cewa wai wasa suke yi" Banishs ta ce, "Lah Umma da kansa ya shiga, ni na ce masa ya fito amma ya ƙi fitowa, shine na koma na je na kira Hamma, ita Sis ɗin ma tsoronsa take ji." Umma ta harari Banisha ta ce, "Da yake ga dodo ko? Dole ta ji taoronsa." Ta lalli Rehaan cikin fusata ta ce, "Kar na sake ganin ta kulle ƙofa ɗana a ciki, in ba haka ba bazan ƙyale maganar ba wallahi." Islsha ta buɗe baki zata yi magana suka haɗa ido da Rehaan, bata san dalili ba sai ta ji bakinta ya ƙame ta kasa cewa komai. Rehaan ya yi shiru sannan ya kalli Umma ya ce, "Shine ya shiga ba ita ta kai shi ba, shi ya kamata ki dakatar da zuwa inda take." Umma ta bi shi da kallon up and down ta ce, "Lallai Rehaan, ta kwana biyu a gidan nan ka san daɗinta, kai ga mai mata har kana ka goyan bayanta ko? Ko da ya ke abokin ɗan iska shima ɗan iskan ne, daman a yawon biɗiɗi ake samu abokin biɗiɗi." Tana gama faɗar hakan ta bar wajan da sauri. Banisha ta ƙarasa ta riƙe Islaha ta ce, "Sis ai da kansa ya shiga ko?." Ta ɗaga mata kai kawai bata ce komai, Mamy ta juya ta koma ba tare da ta ce komai ba, Banisha ta bi bayanta. Kasancewar ƙofar falon a buɗe ta ke Iskaha ta shiga bata kalli Rehaan ba, shima ya shiga yana kulle ƙofar ya wuce zai hau sama. "Ba mu yi da kai a gidan ku zan dinga tolerating nonsense ba, ba mu yi da kai za a dinga faɗa min magana yadda aka ga dama ba. A cikin rules ɗina da kai, babu cin fuska ko cin mutunci a cikin gidan ku, meyasa a iya kwana biyu ƴan gidanku suka fara takura min?." Rehaan ya kalle ta kamar bazai yi magana ba, ya kalli dining area ya ga chef ya gama jera abinci da yawa a kan dining ɗin. Rehaan ɗan buɗe casrool ɗaya ya ɗauki cookies guda ɗaya yana juya shi a hannunsa. Ya waiwayo ya kalle ta ya ce, "sannan babu saka wani a ɗaki a kulle a rules ɗina da ke, in ma za ki yi meyasa baza ki samu mai hankali ya ta ya ki ba? Ba ki san iriinsu Salman da suke da mental issue basu da sirri ba?." Bai ƙarasa maganar ba ganin ta ɗago ido tana buɗesu a kansa tana kallonsa alamun mamakin maganarsa. Rehaan ya saka cookies ɗin a bakinsa ya tauna sannan ya ce, "Kowa sai ya ji abinda ki ka yi masa, make sure nan gaba ki samu complete mental, physical and social, in ba haka ba kowa sai ya san abinda ki ka yi. Bazan hana ki abinda ki ka saba yi ba, as your wish" ya faɗa yana kallon ta ido cikin ido. Wani irin ɗagawa ƙirjinta yake yi saboda ɓacin rai sa ɓacin maganarsu, ƙirjinta yana heaving, tana jin ɗaci yana mamaye bakinta, ta buɗe ido tana kallonsa jin irin munanann kalaman da yake jifanta dasu. Bata yi tunanin yana da doguwar magana haka ba, bata ɗauka zai iya tsayawa yana faɗa mata waɗandan kalaman muni ba. Ta lura ba ya ƙaunar zaman lafiya, ta lura kafin su rabu sai ta yi masa tambarin da zai yarda ita ɗin ƴar iska ce kamar yadda yake faɗa, ta lura sai ta haukace masa ta koma karuwar ƙarfi da ya ji sannan zai shiga hankalinsa. Bazata ƙare kanta akan kalamansa ba, baza ta dinga yi masa rantse-rantse a kan ita ba ƴar iska bace, tunda a haka yake kallonta bismillah, za ta nuna masa ita ƴar iskace a aikace ya gani. Yana gab da shiga parlour ta ce, "ai ban nemi shawara ka ba, ni zan yanke abinda na ga dama a rayuwata kuma na yi. Mai hankali ko mara hankali duk ni zan zaɓa, babu ruwanka da sirri ko rashinsa. Ni na faɗa maka ina neman sirri ne? Ko na taɓa faɗa maka ina neman a ɓoyewa duniya wacece ni?. Sirri sai ku, amma ni a bayyane nake yi duk abinda na ga dama, ban damu da abinda zai je ya faɗa ba, tunda na samu abinda nake nema fine....." Ta yi snaping fingers ɗinta ta ce, "kuma daman  ba ka isa ka hana ni abinda na saba yi ba, in baza ka iya gani ba ka rufe ido, in ba haka ba ka makance, amma yanzu na fara." A hankali yake hawa stairs yana jin duk abinda take faɗa, bai ko kalle ta ba ya shige abinsa. Islaha ta kama ƙugu ta ce, "Lallai gayen nan ya raina min hankali, kuma wallahi bazan ɗauki raini a gidan nan ba, babu wacce zan ragawa, in ba su ji kunyata ba nima bazan ji ta su ba." Sai kuma ta dafe kai cike da takaici, tunawa da akwai wani abu da ya kamata ace ta faɗa masa kuma bata faɗa ba, sai kuwa ta hau saman da sauri amma bata same shi a falo ba. Islaha ta yi ƙwafa a lokacin wayar ta ta yi ƙara alamun shigowar saƙo. Ta ɗago wayar daga hannunta tana dubawa, ganin Hammanta ne sai da gabanta ya faɗi, ta buɗe da gaggawa tana karantawa. _Ina jiran ki gobe a gida, ina so na ji bayanin komai daga bakin ki._ Islaha harari wayar a zahiri ta ce, "Sai yanzu za ka so ka ji, da ba raina min hankali ka ke yi ba?." Sai kuma ta fara yi masa typing tana faɗa masa bata son zuwa gidan in Mama tana nan. Ba jimawa ya dawo da amsa ya ce, _Mama bata nan gobe, ki zo._ Bata ba shi amsa ba sai ajiyar zuciya da ta yi, sai ta ji duk damuwarta tana yayewa a hankali. Ta yi murmushi tana tuna Hamma ya daina ganin laifinta, ɓacin ran da Rehaan ya saka ta a ciki yana gushewa daga zuciyarta da kaɗan-kaɗan. Sai kuma Zainab ta faɗo mata a rai ta sauke numfashi a bayyane ta ce, "A ina zan gano inda ki ke?."  Ta yi shiru dan babu mai bata amsa, ta juya ta shiga ɗaki. Da Islaha asuba ta fito falo, ta manta laptop ɗinta a falon kuma zata saka chaji kafin ta fita. Tana fitowa yana hayowa saman yana amsa waya, tun daga takunsa tasan shine, amma ta yi buris kamar bata ganshi ba, nan kuwa tana kallonsa ta gefen ido. Ya saka jallabiyya blue, gashin kansa a sake yana amsa waya kamar baya son magana. Ta sunkuya tana ɗaukar laptop ya zo wajen zai wuce, tana ɗagowa suka yi karo laptop ɗin ta faɗi ƙasa. Islaha ta kalle sa ya kalle ta, babu inda idanunsa ya kai a jikinta sai gashinta da yake sake ta sako shi ta gaba ya sauka har cikinta. Ya bi tsahon gashin nata da idanunsa da sauka har cikinta, kafin ya ɗauke kai ya sake juyowa yana kallon ta. Islaha ta ɗaga masa gira alamun kallon na meye, bai ce komai ba ya raɓa ta zai wuce. Islaha ta tare masa hanya ta ce, "ba ka ga abinda ka yar min bane? Ko ni ka ke so na sunkuya na ɗauka?." Daf da daf take yi masa magana, har ƙhamshin toothpast ɗin da ta yi brush yana ji a hancinsa. Ya ɗan lumshe ido ya buɗe a kanta, ya lura yarinyar tana da damuwa, in ya biye mata ciwon kai zata dinga saka masa. Bai ce komai ba ya koma ɗaya side ɗin ya wuce ta, ta bi shi da harara ta ce, "ɗan rainin hankali kawai, mai jikin mata" ta faɗa tana ɗaukar laptop ɗin tana faɗin, "Wallahi in ta lalace sai ka biya ni." Ganin babu abinda ta yi ya saka ta yi ƙwafa ta shiga ɗaki. Rehaan sai da ya shiga ɗakin sannan ya yi ajiyar zuciya, ya cire rigar jikinsa ya zauna a gefen gado ya ce, "Me ya kai ni haɗa hanya da yarinyar nan oho." Result ɗin da ta zubar da ciki ya tuna, sai ya lumshe ido ya buɗe yana girgiza kai ya ce, "a haka da kamar mutuniyar kirki, amma ta banza ce. " Ya yi tsaki ya miƙe ya ɗauki laptop dan yana da meeting na gaggawa. Islaha ƙarfe shida ta gama shiryawa ta sauka downstairs, tana sauka ta ji motsi a kitchen ɗin da bata taɓa shiga ba. Chef ne ya fito sanye da apron ya kalle ta ya ce, "Good morning madam." Ta bi shi da kallo sannan ta amsa, cikin ladabi ya ce, "the food is ready." Ta kalli dining ɗin ganin abinci ya fi kala goma a ajjiye, kamar table ɗin ƴan turkey da take yawan gani a drama, sai ga shi yau ta gani a zahiri, komai an yi decorating ɗinsa yadda ya kamata, ko ba ka yi niyar ci ba in ka kalla zai saka maka sha'awar cin abincin. Islaha sai ta tuna jiya ma da daddare haka ta ga an jera abinci, kuma ita dai bata ci bata san ya aka yi dashi ba. Islaha ta amsa ya koma kitchen ya cigaba da aikinsa. Ta ƙarasa wajen dining ɗin tana kallon abincin, wani abun ma bata san meye ba, kalolin abincin take gani kana gani ka san english breakfast ne ba irin nasu ba. A lokacin Chef ɗin ya dawo ya sake ajjiye wani abun, gashi yadda ya tsara table ɗin sai ya burge dole sai ya ka. Islaha ta nuna masa ɗaya daga cikin abincin ta ce, "What is the name of this food?." Chef ɗin ya kalla sannan ya ce, "Avocado toast." Islaha ta girgiza kai tana kallon abin green dashi, tana ayyana sai dai avocado ɗin daman. Bayan ya bar wajen ta haɗa tea kawai ta sha, dan bata iya cin abinci da safe tea ɗin ne zai zauna a cikinta. Bayan ta gama ta ɗauki handbag ɗinta ta fito daga falon tana kallon gate ɗin da zai kai ta harabar gidan. Nana Haleema. KRBBK: RDB3P21 Nana Haleema. Compound ɗin gidan babu kowa a wajan sai motsin abinda yake kiwo, ta fito a hankali tana kallon wajan. Tana fitowa ta ga an ƙaraso inda take tsaye, ya duƙa a gabanta cikin fulfulde ya ce, "Barka da safiya." Islaha ta kalli mutumin ganin ya girma, duk da ba tsoho bane amma yana da shekaru. Sai ta ji nauyin yadda ya duƙa mata ta ce, "barka dai." "Ni ne lawal, ni ne zan dinga kai ki duk inda za ki je." Islaha ta amsa, ya nuna mata motar tare da buɗe mata bayan motar. Islaha ta bi motar da ido, range rover ce baƙa mai kyau sai ƙyalli take yi kamar sabuwa. Islaha ta kalle shi ta ga yana riƙe da ƙofa yana jira ta shiga, ita duk sai ta ji kunya, amma haka ta shiga ɗin ya rufe motar ya shiga mazaunin driver suka tafi. Ac motar ta yi mata yawa, kuma daman ita bata son ac a mota, hakan ya saka ta ɗauki facemask ta saka ta faɗa inda zasu je. Gab da gate ɗin ta saka ya tsaya, dan bata so a shiga da motar a ga ta fito daga ciki. Yana tsayawa ya ce, "Ma'am yaushe zan dawo?." Islaha ya ɗan yi jim ta ce, "Bani numbar ka, zan yi maka waya." Jikinsa yana rawa ya bata lambarsa, ta saka a wayarta sannan ta fita daga motar ta shiga wajen aiki. Tana shiga ta gano Safeera ta fito da sassarfa tana nufo inda take, suna haɗuwa a hanya ta ce, "ke wannan zuƙeƙiyar motar fa?." "Munafuka, har kin gani?." "Tuni ma. Ya aka yi haka, shine ya ce baza ki zo ba sai an kawo ki?." "Shi a wa? Dallah can mu je" ta faɗa tana yin gaba, Safeera ta ce, "sai na zo jin labari, ki shiga studio ki fito." Bata cekomai ba ta wuce itama ta wuce. Ƙarfe sha biyu na rana Islaha ta tashi daga aiki, ta fito ta samu Safeera tana haɗa kayanta Islaha ta ce, "Safeera zan wuce." Safeera ta ce, "nima na ɗauki excuse, Mama ce bata nan ina so na zauna a gidan na yiwa Baffa girki." Islaha ta ce, "To mu tafi gabaɗaya, daman zan je wajan Hamma." Safeera ta ɗan dumm kafin ta ce, "Hamma kuma?." "Eh shi" ta faɗa tana duba wayarta jin ana yi mata waya. Ta ɗaga wayar daga can ɓangaren aka ce, "Islaha kina jina, Baba Tabawa ce." Islaha ta ce, "Baba Ina yini." "Lafiya lau. Daman faɗa miki zan yi jiya bayan ki bar nan, Hajiyan gidan nan tazo ta samu Yafindo, yau da sassafe ta yi min sallama ta tafi garinsu, kuma baza ta sake dawowa ba." Fargaba ta mamaye Islaha ta ce, "ta bar aikin?." "ta bari Islaha. Nayi-nayi ta faɗa min abinda ya faru amma taƙi." "To Baba ina ne garin nasu?." "A cikin garin zata zauna, babu nisa sosai." "Don Allah kin san gidan, za ki iya yi min kwatance?." Baba ta ce, "zan iya." Ta fara yiwa Islaha kwantance tana haddacewa kafin ta ce, "Na gode Baba, sai kin jini." Daga haka suka kashe wayar. Safeera ta ce, "me ya faru?." Ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "zo mu je." Tare suka fito, daga can nesa ta hango driver kamar inda tace masa ya tsaya. Ta ƙarasa suka shiga, Safeera ta faɗa masa inda zasu je. Yadda Baba Tabawa ta yi mata kwantace itama haka take yi masa, har suka zo ƙofar gidan da aka ce mata nan ne gidan. Safeera ta ce, "wai ina ne nan? Na faɗa miki girki zan yiwa Baba, ina mu ka zo nan?." Islaha bata amsa ba ta fita dole itama ta bi bayanta. Da sallama suka shiga gidan, Yafindo ta amsa ta ɗago suka haɗa ido. Ganin Islaha sai ta yar da tsintsiyar hannunta ta ce, "Islaha don Allah ki taimaka min ki tafi, ni bazan yi magana dake ba, ki tafi don girman Allah." Islaha ta ce, "Yafindo magana nazo mu yi, ki saurare...." Cikin faɗa da tsawa ta ce, "bazan saurare ki ba, don girman Allah ki fita Islaha, don Allah ki tafi. Kar ki saka ni a matsala, kar ki saka rayuwata a matsala. Ni Zainab bata bani komai ba, babu abinda ta bani." Islaha ta bita da kallo ta ce, "Ya aka yi ki ka san abinda ya kawo ni kenan Yafindo? Yadda muryar ki take rawa ya tabbatar min da akwai abinda ki ke so ki faɗa min. Meyasa baza ki sauke nauyi da aka ba ki ba?." "Islaha ki je don Allah, ki tafi kin ji. Kuma kar ki sake zuwa." Islaha ta ɗaga kai ta ce, "shikenan na tafi, kar ki damu. Amma ki sani, rayuwar matan da suke gidan da ki ka bari tana hannunki, in ta ɓaci alhakkin hakan yana kan ki. Duk yaron da yake gidan amana ce a gare ku, an ba ku kuma kuna wasa da ita. Tunda bakya son ganina na tafi, Safeera mu je." A sanyaye Safeera ta juya ta ta fita Islaha ta bi bayanta. Ko da suka shiga mota Safeera ce ta faɗi inda zasu je, Islaha tunda ta dafe kai bata ce komai ba har suka ƙaraso ƙofar gidan su Safeera. Islaha ta kalli Lawal ta ce, "ka je ka dawo, zan kira ka." Cikin girmamawa ya ce, "to ranki ya daɗe." Suka fita suka shiga gidansu Safeera, suka yi alwala tare da yin sallar azahar, Islaha ta jingina da gadon Safeera tana sauke numfashi a hankali. Safeera ta ce, "wai akan saƙon da Zainab ta bawa Yafindo ne?." Ta ɗaga kai ta ce, "Tunda ki ka ji haka, tabbas akwai lauje a cikin naɗi, sune suka hana ta magana dani, kuma wallahi bazan dakata ba." Safeera ta ce, "ki yi a hankali, ko dan saboda ita, kar a cutar da tsohuwar Allah." Islaha bata ce komai ba ta ɗaga kai kawai, sai kuma ta yamutsa fuska ta buɗe jaka ta ɗauko cincin a ƙaramar pack tana ci. Safeera ta saka hannu suna ci tare, kafin ta zame ta kwanta a wajen bacci ya ɗauke ta. Safeefa ma bacci take ji amma an kusa sallah bazata yi ba, sai ta tashi ta fita tana aiki. Bayan sallar la'asar Islaha ta ce, "Ina kayana Safeera?." "Gasu nan." "Zan ɗan ɗauki wasu" ta faɗa tana buɗewa tana ɗauka wanda zata yi amfani dasu. Ta ajjiye a gefe ta ce, "zan je wajan Hamma yanzu, ya ce yana so zamu yi magana." Safeera kai tsaye ta ce, "sai kin dawo." "Ki zo mu je don Allah." Safeera bata ce komai ba ta saka hijjab suka bar ƙannenta a gidan suka shiga gidan. A harabar gidan Islaha ta tsaya ta kira shi a waya ta ce, "Ga ni na zo." A lokacin aka yiwa Safeera waya ta duba ganin Baba ne yake yi mata waya sai ta ɗauka, tana kashewa ta ce, "Baba ya aiko daga kasuwa na ba da saƙo a kai masa, bara na je na bayar na dawo." Islaha ta ɗaga kai Safeera ta fita da sauri. Basu jima da wayar ba ya fito daga ɗakinsa yana nufo inda take tsaye, ya zuba mata ido yama kallo ganin fuskar ta babu walwala ko kaɗan. Saheer ya ce, "mu je Falon Mama, bata nan." Tare suka shiga suka zauna akan kujera daban daban, Islaha ta jingina da kujera bata ce komai ba. Saheer zuba mata ido na wani lokaci, ganin ita ba shi take kallo ba wani wajen take kallo daban. Ya ce, "Ba ki shirya magana dani bane?." Ta ɗago ido ta kalle sa ta ce, "sau nawa ina so nayi magana da kai kana share ni?." Ya ɗan girgiza kai ya ce, "kin san kishi kuwa?." Bata amsa ba sai kawar da kanta da ta yi bata amsa masa ba, dan bata da amsar tambayarsa. Saheer ya ce, "Ina jin ki. Ta sake kallonsa ta ce, "in na faɗa maka zaka iya cewa ƙarya nake yi, ni kuma bazan jure wannan kalmar ba." Ya zuba mata ido bai amsa ba, sai kuma ya ɗan ɗaga kai ya ce, "ina jin ki." Ta buɗe handbag ɗinta ta ɗauko takarda guda biyu ta ce, "auren contract ne, an bani kuɗin fansarka na bada kaina zan zauna a matsayin mata na wata biyar, yau an ci kwana uku, saura kwana ɗari da arba'in da bakwai. Ban sani ba ko baza ka yarda ba, Amma Allah ya san meye a zuciyata, na yi ne saboda kar su kashe ka" ta faɗa muryarta tana fara cracking. Ta yi ƙoƙarin daidaita kanta kar ta yi kuka ta ce, "Amma wai kaine ka ce min na zaɓi kuɗi akan halacci ko Hamma?." Saheer ya ce, "Islaha Allah ne kaɗai ya san abinda nake ji a raina, aure ki ka yi, ki ke zaune da wani namijin a mtsayin mijinki, ya ki ke so na yi?." "amma kai ka san babu wani mai kuɗi da isa ya ruɗe ni na aure sa na bar ka ko? Kasan babu wani wanda zai zo ya ɗauki hankalina saboda kuɗi. Wallahi babu shi a duniya, har yanzu ba a yi wanda kuɗinsa ko wani nasa zai yaudare nii ba, ka fi kowa sannin kuɗi basa ɗaukar hankalina kuma basa tayar min da hankali. In na ce ina so kawai ina so ne, ko da kuɗi ko babu na yarda zan zauna a inda Allah ya ajjiye ni." Saheer "Ina jin ki, ya saka hannu a takardar jarjejeniya sannan ya ba ki miliyan hamsin saboda ki zauna da shi? Waye shi a garin Yola?." Islaha ta kalle shi ta ce, "shima ba son auren yake yi ba kamar yadda bana so nima. Daga taimako abin ya zamar min alaƙaƙai, kakarsa na taimakawa na kaita gida, daga nan take cewa sai na auri jikinta. Da farko na yi tunanin wasa take yi ko kuma rikicin girma ne, ashe ni ce ban fahimta daidai ba. Shine suka zo da maganar wajan Baffa, ni kuma daman na san shi, ya nuna ba ya son auren har ya kawo zancen auren wata biyar, dan da ace bai kawo batun contract ba ko kaɗan ban ji a raina shi ya kamata na yi ba. A wannan lokacin aka turo video ka ana dukan ka, sai na kasa jurewa na je na amince da auren wata biyar amma da sharaɗin zai bani kuɗi. Kuma ya bani kuɗin, tunda ga si  har ka kuɓuta, ka ga dole na zauna da sji har lokaci ya ƙare." Saheer da yake kallon ta ya ce, "ba ki faɗa min waye shi ba." Ta ɗan sauke numfashi ta lumshe ido ta buɗe sannan ta ɗago ido ta kalle sa ta ce, "Rehaan yola." Saheer ya tsayar da idonsa ƙyam a kanta, ya buɗe su yana kallonta cikin tsananin mamaki da bugawar zuciya da firgici mai yawa....... Nana Haleema. RDB2P22 Nana Haleema. Ganin yadda ya zuba mata idanu sai ta ɗauke kai daga kallonsa, ta kawar da kai gefe ta yi shiru bata ce komai ba. Shiru ya ratsa tsakaninsu kafin ya tashi zaune sosai yana kallonta ya ce, "Ranar da aka sace ki, da ki ka dawo daga ba ya kin ce shine. Sannan da ki ka je Jeddah, nan ma da ki ka dawo kin ce kin haɗu dashi a can, yanzu kuma kin yi auren yarjejeniya da shi." Ya ja numfashi kafin ya lumshe ido ya ce, "Islaha!." Bata kalle shi ba ta ce, "Hamma!." Ya ce, "meyasa baza ki faɗa min gaskiya ba, meyasa baza ki faɗa min duk wannan abubuwan plan ɗin ki ne?. Anya garkuwa dani baya cikin plan ɗinku ke da Rehaan?." Islaha ta waiwayo ta kalle shi jin abinda yake faɗa, ta girgiza kai tana harararsa ta ce, "Hamma na gaji, na gaji da yi maka rantsuwa kana ƙaryata ni...." "Ina so ka san in ina da niyar auren Rehaan bazan ƙulla auren wata biyar da shi ba, zan aure sa ne kai tsaye kamar yadda iyayensa suka nema. Meyasa ba ka yarda dani ba, meyasa zuciyarka ta ke rawa a kaina ko yaushe?. Kawai dan na burge ka ko dan na ɓoye gaskiya sai na rantse akan ƙarya? Hamma bazan zubar da hawayena a kan ƙarya ba, bazan rantse akan ƙarya ba, bazan zo na zauna a gaban ka akan ƙarya ba. In kana ganin plan mu ka haɗa nida shi mu je a hakan ne kawai, Allah yana ji kuma yana gani." Saheer ya ce, "maganar ta ki ce bata yi making sense ba, ko waye a matsayina dole ya amince akwai wani abu a tsakanin ki da Rehaan. Rehaan yola da yake yiwa mutane wahalar gani, yaro matashi da sunansa ya yi tambari a ƙasar nan gabaɗaya, yaron da ake ƙididdigar ya fi ko wanne matashi kuɗi a ganin nan. Ba iya Yola ba, ana cewa a yanzu a nigeria yana daga cikin matasan da Allah ya yi musu baiwar kuɗi. Islaha ta ya ki ke so na yarda da wannan kitimurmurar?." "Ba ka yarda Rehaan Yolan bane?." "Ina shakku a kan hakan, me ya haɗa ki dashi da rayuwarki take katantanwa a cikin tasa?." Ta yi ajiyar ta miƙa masa takardun ta ce, "Ka duba, wataƙila in ka ga sunansa da signing ɗinsa  ka yarda shine." Bai musa ba ya karɓa, ya fara buɗe takardar Rehaan yana karanta rules ɗinsa bit by bit. Ya ninke ta Rehaan, ya buɗe ta Iskaha yana bi a hankali har ya gama, ya ajjiye mata ta kwashe ta saka a jaka. Ta sake kallonsa ta ce, "In ka amince dani daidai ne, in zuciyarka tana shakku a kaina wannan ma daidai ne Hamma. Abu ɗaya nake so ka sani, Rehaan shine ya shiga rayuwata bani na shiga ta sa ba, shine ya kwanto kura daga cikin kejinta ya sake ta a cikin jama'a. A yanzu ni matarsa ce, shaidu ɗaurin aure sun shaida kuma an ba da sadaki. Amma a wajena da wajensa ni matar yarjejeniya ce, da zarar lokaci ya ƙare kowa zai kama gabansa." "No intimacy, kuma ya yarda?." A sama ta ji tambayar tasa, ta ɗago suka haɗa Ido sai ta ɗauke kai daga kallonsa ta ce, "ka karanta da kanka ka gani, kuma ka ga inda ya saka hannu, da bai amince ba ka gani ba." Ya zuba mata ido bai ɗauke idanunsa ba yana kallon ta, sai ya gyaɗa kai ya ce, "Kuma ke kina ganin zai sake ki?." "Me zai hana? Da zarar contract ya ƙare zai sake ni na kama gabana. Shima ba ya son auren kamar yadda bana so. Kowa yana rayuwa da ɗan uwansa ne saboda babu yadda zamu yi, ni na zauna dashi saboda kai, shi yana zaune dani saboda kakarsa da mahaifinsa." Saheer ya sauke numfashi ya ce, "zuciyata tana faɗa min kamar auren nan bazai rabu, ina ganim kamar na rasa ki har abada. Ina ganin kamar kin tafi kenan, duk zaman jiran ki da na dinga yi kamar ya tashi a banza. Inda za ki dawo ɗin zan jira ki daga nan har shekara biyar ba wata biyar ba, amma dawowar ki ce na san baza ta taɓa yuwa ba. Babu yadda za a yi ki auri namiji kamar sa sannan ki bar shi ki dawo wajena ba." Islaha kin abinda yake faɗa sai ta ce, "Ka ɗauka na mutu kawai, amma matuƙar ina da rai auren nan zai ƙare kuma zan fito. Ni ta ka ce, wani daga waje bai isa ya zo ya ɗauke ni ba bayan tarin wahalar da ka sha dani. Zan iya jure ko wacce matsala indai a kan ka ne, kamar yadda na yi auren jarjejeniya saboda kai, zan iya ba da rayuwata saboda kai. Abinda yake bani matsala da kai, kana da ƙarancin yarda dani." Ya lumshe ido ya ce, "Ba rashin yarda bane, na kasa sarrafa kaina ne. Kawai na wayi gari ance kin yi aure, ya ki ke so na yi miki?." Ta sauke numfashi ta ce, "Nima na wayi gari ana kirana da matar aure ba dan na shiryawa hakan ba, sai dan saboda rayuwarka ta kuɓuta daga azaba da kuma uƙuba. Har yanzu ba ka dawo daidai ba, kowa ya ganka ya san akwai wahala a tare da kai, ta ya zan iya barin ka a can bayan na samu dama Hamma." Sai ta yi murmushi ta ce, "Wata biyar ne kawai, da zarar ya ƙare aurensa zai saula daga kaina. Babbar matsala kuma Mama ce, ta yi rantsuwa ta ce babu ni babu kai." Saheer ya ce, "Ba iya Mama ba, harda Baffa. Baffa zai yi wahalar sha'ani a wannan lokacin." Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, kanta yana ƙasa bata ɗago ta kalle shi ba. Saheer ya ɗaga kai ya ce, "Kar Mama ta dame ki, babu abinda Mama zata yi, zata janye kalamanta da zarar lokacin ya yi. Musmaman yanzu da zata daina ganin ki na wata biyar wasu abubuwan zasu ragu in sha Allah." "Allah ya sa, haka nake fata." "Kuma da gaske za ki iya barin auren Ray ki zo ki zauna dani?." Bata san ta yi siririn tsaki ta miƙe tsaye ba ta ce, "shi waye? Baka a kaf duniya babu wanda nake jin haushi kamar shi ba? Ba ka san duk duniya babu wanda nake jiran ƙiris da shi kamar sa ba?. Hmmm! Ban sake jin haushinsa yana ninkuwa a raina ba sai yanzu da nake ganinsa ko yaushe, ina jin kamar na soke idanuna da allura ko dan ya daina tozali da fuskarsa." Saheer a sanyaye ya ce, "Meyasa ki ka amince da auren nan, meyasa ba ki bari an kashe ni ba?." "Bazan iya hakan ba, bazan iya gani ina da dama a hannuna na bari wani abu ya same ka ba, shiyasa na amince ba dan zuciyata tana so ba Hamma. Amma babu yadda zan yi, hakan shine mafita a gare mu ba ki ɗaya. Ga shiyanzu ka dawo, har kana zaune muna magana da kai, da ba a kai kuɗin ba fa?." Ya gyaɗa kai yana lumshe ido ya ce, "bazan iya jiran wata biyar ba, ina ganin kamar shekara biyar ne." "nima ina wannan tunanin, irin raina min hankalin da yake yi sai nake ganin kamar bazan iya ba kai wa wata biyar tare das shi ba, amma in na tuna na karɓi kuɗi sai jikina ya yi sanyi." Saheer miƙe tsaye ya ce, "Zan jira ki daga nan zuwa ko yaushe, zan zauna zaman jiran ƙarewar contract ki dawo gare ni...." Ya ɗan dakata da magana sannan ya ce, "Islaha ki yi min alƙawarin baza ki canja maganar ki ba, ki yi min alƙawarin duk daren daɗewa za ki dawo gare ni ba tare da iddarsa akan ki ba!. In ki ka yi haka zan tabbatar da ina da mahimmaci a rayuwar ki, zan tabbatar da maganar su Mama ba gaskiya ba ce.” Islaha ta kalli cikin idon Hamma gabanta ya faɗi matuƙa, ta sunkuyar da kai bata ce komai ba sai kuma ta ɗago ta ce, "Na yi maka alƙawari zan dawo Hamma, yanzu ma ina zaune a can ne saboda kai, amma zan dawo gare ka in sha Allah. In Allah ya amince, in sha Allah  sai na zama matar ka, mu cigaba da addu'a." Saheer ya yi murmushin da tunda ya baro daji bai yi irinsa ba, itama ta yi murmushi tana sunkuyar da kanta zuciyar ta tana bugawa sosai ba tare da ta san dalili ba ya ce, "Islaha." Bata ɗago ba ta ce, "Na'am Hamma." "Ki yi haƙuri." "Babu komai, ai ya wuce." "Na gode, ban san soyayyar da ki ke yi min ta kai haka ba." Islaha ta yi murmushi ta ɗago zata yi magana, ya yi saurin tarar numfashin ta ya ce, "Na san kina sona Islaha, amma ban taɓa tunanin soyayyar ta kai ki sadaukar da kan ki saboda ni ba. Na gode, Allah ya sa muna da rabon zama ma'arauta." Islaha ta sake sunkuyar da kai bata ce komai ba ko Amin ɗin ta kasa faɗa, sai take jin bakinta da zuciyarta sun hanata amsa addu'ar. Buɗe ƙofar da aka yi ya saka suka juya suna kallon wandw ya buɗe ƙofar gabaɗayansu. Safeera ta bisu da kallo ganin ko wanne da murmushi a fuskarsa, da alama Islaha ta faɗa masa komai kuma ya yafw mata. Safeera ta ce, "Islaha ke nake jira fa, ki yi sauri." Islaha ta ce, "Hamma zan tafi, akwai aikin da yake gabana wanda nake so na kammala shi, sai mun yi magana a waya." "Wanne irin aiki ne?." Zata yi magana Safeera ta ce, "Islaha!." Islsha ta kalle sa ta ce, "zan faɗa maka, sai anjima" ta faɗa tana ɗaukar jakarta ta fita daga ɗakin suka tafi. Saheer bi Islaha da kallo yana tunani, zuciyarsa tana so ta gasgata Islaha amma wani ɓangaren ya hana shi hakan. Gani ya ke kamar ta riga ta yi masa nisa, gani yake ya rasa Islaha kenan har abada. Kalamanta sun ba shi ƙarfin guiwa, amma ta ya ya hakan zai kasance? Ya zai yi da Mama da ta yi rantsuwa akan bazai auri Islaha ba?. Ya ya ajiyar zuciya ya zauna a akan kujera ya dafe kansa yana lumshe ido cikin tunani kala-kala. Hankalinsa ya kwanta sosai da kalamanta, ya ji daɗi da ya ke da tabbacin har wata biyar ta ƙare babu abinda zai haɗa Islaha da Rehaan na auratayya, amma tunaninsa ta ya auren zai rabu, in ya rabu shi ya zai yi da Mama?. Islaha tunda suka koma gidansu Safeera take yi mata faɗa, cikin masifa da son nuna mata kuskure Safeera ta ce, "ina hankalin ki ya shiga Islaha, ina tunanin ki da ilimin ki ya tafi?. Kin manta wai kina da aure, kin manta ke matar aure ce, kin manta zama a waje ɗaya kina hira da namijin da ba muharramin ki ba haram ne balle kuma irin Saheer?. Maganar aure fa ku ke yi, da auren wani a kanki ki ke biye masa kuna zancen aure, meyasa akan Saheer idanunki suke rufewa har bakya gane daidai da ba daidai ba?." Islaha jin yadda take yi mata masifa ta ce, "ke ji mana, ba fa auren gaskiya mu ka yi dashi ba, auren bogi ne. Meye na tayar na jijiyoyin wuya akan auren da ko shi bai ɗauke sa da daraja da mahimmaci?." "Ke a wajan ki ne ya ke auren bogi, amma wajan Allah auren gaske ne. An tara mutane sun shaida, an ba da sadaki, an karɓi amanar ki a hannun waliyin ki, an tamƙa ki a hannun waliyinsa. Duk duniya haka ake ɗaura aure a duniyar musulmai, in ɗaurin aure bai yi kama da wannan ba to bana musulumci bane." "Auren yarjejeniya da yake tsakanin ki da shi wannan a tsakanin ku biyu yake, ban da a wajan wanda ya halicce ku. Aure sunan sa aure, indai an shaida an ba da sadaki magana ta ƙare. Wallahil azim duk dariyar nan da ki ke yiwa Saheer zunubi Allah yake rubuta miki, duk bibiyarsa da maganar nan da ki ke yi azaba ki ke jawowa kanki. Ke matar Rehaan ce ba matar Saheer ba, tsakaninki da Hamma gaisuwa ce, in maganar ta wuce haka kun keta iyakar halaccinku." Safeera ganin Islaha ta nutsu tana jin abinda take faɗa sai ta ce, "Kuma babu mai babban mai zunubi sai ke, domin ke ki ka biye masa har ki ka tsaya kina yi masa dariya. Ban san ina hankalin ki ya tafi ba, ban san me ya rufe miki ido ki ke so ki shiga wuta da ƙafar ki ba!." Islaha sai jikinta ya yi sanyi sosai, dan ta san duk kalaman Safeera gaskiya, kuma ta san ta yi kuskure babba. Ta kalli Safeera ta ce, "Wallahi Safeera shine ya saka nake ɗaukar auren nan a haka, Yayansa mahaukaci ya nuna ni ya ce wai ina sonsa, har yana faɗa min in zan....." sai ta yi shiru bata ƙarasa. "Shiyasa na ce miki wannan tsakanin ku ne, abu ɗaya nake so ki tuna, wallahi duk lokacin da ki ka sake kula Saheer da sunan soyayya ko maganar aure ke Allah zai kama ba Rehaan ba. Domin kin san kina da aure ki ke maganar aure da wani, sai Allah ya tsayar dake ya karɓawa Rehaan haƙƙinsa na wulaƙanta aurensa da ki ka yi, ban da azabar da Allah zai yi miki akan haka!." Islaha ta sauke numfashi cikin nadama da danasani ta ce, "shikenan na ji, na yi kuskure bazan sake ba in sha Allah." Safeera ta ce, "Ki tuba." Islaha ta ce, "Astagafirullah!." Safeera ta ce, "ya fi miki. Ki mayar da hankali akan abinda ya ke gabanki, in ba haka ba tarin zunubi ya saka ki ɗaiɗaicewa. Yiwa Saheer magana da fuskar soyayya kamar yadda ki ka saba kamar kin yi zina ne." "Ke Safeera! Zina fa?." "Eh, indai za ki dinga yi masa magana yana jin daɗin kalaman ki zina ce mana amma ta baki, Ko kina so ki ce min baki san akwai zinar baki ba?. Ƙawancen mu ya yi ƙarfi a islamiyya, lokacin da ki ka dawo gidansu Hamma. Ni na san wacece ke a islamiyya, amma yanzu na ga kamar kina daga cikin waɗanda Allah ya basu ilimi amma basa aiki da shi." Islaha cikin sanyin jiki da kunya ta ce, "Allah ya kiyaye mu, zan kiyaye in Allah ya yarda. " Sai kuma ta ɗago ta ce, "Ni wallahi ba akan aurenmu nake so Hamma ya daina fushi ba, kin san waye Hamma a gare ni, kin san shine dangina gabaɗaya. Na kasa jure fushinsa a kaina, na kasa jurewa in na tuna Hamma baya yi min magana, wannan shine ya ɗaga min hankali har sai da na ga ya sakko hankalina ya kwanta. Shine mai yi min faɗa, shine mai tsawatar min, shine mai kaini inuwa ya bani ruwa, duk da yan gidansu basa sona haka ya ce ya ji ya gani. Ta ya zan iya jure fushin wannan mutumi mai mahimmaci a gare ni?." Safeera ta ce, "kin ji nace miki wani abu a kansa ne? Cewa na yi iya gaisawa itace a tsakanin ku ba maganar aure ba, in za ku yi maganar aure ya jira Rehaan ya sake ki daga nan sai ku ɗora. Amma a yanzu saɓon Allah ku ke yi." Islaha ta ɗaga kai ta ce, "Na gode da tunatarwa Safeera. Daman daga ke sai shi ne masu nuna min kuskurena in na kauce hanya, wataƙila da ina da mahaifiya bazan aikata abinda nake yi ba yanzu...." Ta yi murmushi tana goge idanunta tana ɗaga kai ta ce, "Ke ƙawata ce kuma ƴar uwata, ba dan ku ko wuta zan faɗa babu mai dakatar da ni. Ta ya zan iya jure fushin Hamma?" ta faɗa hawaye yana sakko mata, ta sake sharewa ta ce,"Maraici!" Ta faɗa tana murmushi. Safeera ta bita da kallo bata ce komai ba ta fita daga ɗakin cike da tausayin Islaha da haushin Saheer a ranta, duk da Islaha ce mai laifi amma da ya nuna mata hakan kuskure ne da bata yi ba, kamar yadda ta faɗa shine mai faɗa mata gaskiya, shi take kallo a matsayin na gaba da ita har ya faɗa mata taji, kallon dangi gabaɗaya take yi masa, yana da mahimmaci sosai a wajenta, amma ta rasa meyasa akan auren nan idanunsa ya rufe, ya kasa tsawatar mata kamar yadda ya saba, ya kasa faɗa mata gaskiya kamar yadda ya saba, har yake so ya jefata a cikin halaka saboda son kai. Sai bayan sallar magrib sannan driver ya zo ya ɗauke ta suka wuce gidan. Nana Haleema. RDB3P23 Nana Haleema. A daidai apartment ɗin Mamy ya ajjiye motar, tana fitowa daga motar Banisha tana fitowa. Suka haɗa ido ta yi murmushi sai Islaha ma ta murmusa tana kallon ta. Banisha ta ƙaraso ta ce, "Sis Islaha ko na ce Sia Islam, ki zo mu je wajan Mamy." Babu yadda zata yi ta musa haka suka shiga wajan Mamy da sallama ,Mamy ta amsa tana kallonsu. Islaha bata kula da waye a kusa da Mamy ba, ta zauna a kan carpet ta ce, "Barka da dare Mamy." A ciki Mamy ta amsa sannan ta ce, "Daga ina?." Islaha bata fahimci tambayar ba sai ta ce, "na je wajan aiki." "i mean wacece ke?." Wani irin bugawa ƙirjin Islaaha ya yi, ta ɗago ta kalli Mamy suka haɗa ido, sai a lokacin ta lura da Rehaan a kwance akan kujerar ya ɗora kansa a kan ciyar Mamy yana danna waya. Banisha ta ce, "Mamy Sis Islaha ce fa." Ta kalli Banisha ta sake kallon Islaha ta ce, "ohh, sai na ga ta canja kamar ba ita ba, sannun ki." Guiwar Islaha ta yi sanyi, ta kasa motsi daga wajan saboda ƙasƙancin da aka gwada mata a wajan. Ta yi shiru ta kasa magana, tana jin hawaye yana taho mata tana mayar da shi dan bata so ya zubo. "Mamy na gaji sosai, bayana ciwo yake yi." Muryar Rehaan ta katse mata tunani, ta ɗaga ido ta kalle sa ta ga Mamy tana shafa kansa tana cewa, "Yau ka yi aiki ai, in dai za ka je asibiti haka ka ke dawowa a gajiye. Sannu, ko za a zo a yi maka massage?." Ya sake gyara kwanciya a jikunta ya ce, "No need" ya faɗa yana lumshe ido kamar bai san Islaha tana wajan ba. Takaicinsa ya saka ta yi ƙaramin tsaki bata sani ba, haushi yake bata matuƙa, bata so ta ga namiji yana shagwaɓa ko yana faman kiran ya gaji, wannan dalili yana ɗafa daga cikin abinda ya saka ko burge ta bazata taɓa ji ya yi a ranta ba, saboda gabaɗaya duk abinda take so shi akasinsa ne da shi. A hankali ta miƙe ta ce, "Sai anjima." Mamy ta amsa Islaha ta fita daga falon. Mamy ta ce, "Rehaan." "Mamy." "Anya yarinyar nan bata da wani shiri kuwa?." "na me?." "ni sai nake ganin kamar turo ta aka yi fa, wallahi ban yarda da ita ba kwata-kwata. Sannan bata yi min ba, saboda bata da kunya." Ya ɗan yi murmsuhi kawai bai ce komai ba, yana aiyana da kin san wacce ita da kin sake jin haushinta. Islaaha tana fita suka haɗu da Mama ta fito daga ɓangarenta da hijjab, ganin tana yi mata murmushi tun daga nesa sai Islaha ta dakata har Mama ta ƙaraso. Islaha ta gaishe ta amsa cikin sakin fuska ta ce, "Ɗazu na zo bakya nan, aka ce min kin tafi aiki. Kawai sai na kai channel ɗin ku, sai na ga ana haska ki kina labarai. Gaskiya kin iya aikin sosai, Allah ya taimaka." Ta yi murmushi ta ce, "Amin Mama." "Yanzu ina za ki je?." "Zan je na gaishe da Daada, daga nan sai na yi sallah." "Mu je wajan nata, nima can zan je. Kina iya cin abincin chef ɗin nan nasa kuwa?." "Ni ban taɓa ci ba." "Haka ki ke fita ba ki ci komai ba?." "Bana iya cin abinci da safe ne." "To na daren fa?." "Bana so, gwara na sha tea." Mama ta girgiza kai ta ce, "haka yaran nan ku ke, kowa baya son ya ajjiye kiɓa, Ai shikenan." Islaha ta murmusa tana jin ƙaunar Mama har cikin ranta, dan kaf gidan ita kaɗai ce mai sakar mata fuska sai Daada, har tana ji a ranta dama itace a matsayin Mamy, da ta ji daɗi ba a wulaƙanta ba. A haka suka shiga ɓangaren Daada da sallama.... Daada tana ganin Islaha ta fara murmushi ta ce, "maraba da Eslama ko na ce Ishlaya, dan wannan al'adar basu riƙe ta dakyau ba, mantawa suke da sunan buɗar kai, lokacin mu indai aka saka maka suna shikenan ya bika har mutuwa. Sannu da zuwa." Islaha ta ƙarasa suka gaisa, Daada dafata ta ce, "Ya aikin naki?." "alhamdu lillah." "wannan aikin wai ba a bada hutu ne in aka yi aure?." Ta ɗan yu murmushi ta ce, "Aikin ne da yawa, kuma a hannuna yake shiyasa." "Ɗazu ai na ga shirin naki, Allah ya dafa miki." Islaha ta amsa da amin kafin Daada ta ce, "ki je ki huta, kar na zaunar dake." Islaha bata musa ta yi mata sallama ta tafi. Daada ta bita da kallo tana murmushi ta ce, "Kaf sirikan gidan nan ban ga wacce zata shiga raina kamar yarinyar nan ba." Fuskar Mama sai ta canja, amma bata nuna ba ta yi yaƙe suka gaisa ta fita. Islaha sai a lokacin ta tuna da kayanta a motar, ta kira shi ta ce ya kawo mata, ba jimawa sai ga shi da kayan ta karɓa tana kallon ƙofar dan ita ta manta code ɗin ma wallahi. Ta tsaya tana danna code ɗin ta ji an riƙe hannunta, gabanta ya faɗi ta juyo dan ganin waye mai wannan aikin. Kafin ta gama banbance waye aka sake riƙe ɗaya hannun, ta kalle sa ta ga sai murmushi yake yi mata yana jan hannunta alamun su yi tsalle-tsalle. Lokaci ɗaya tsoronsa ya shiga ranta, ta kasa ƙwace hannunta daga riƙon da ya yi nata. Salman shi dai kallon ta yake yi, bai taɓa ganin abinda yake son zama tare da shi kamar Islaha ba, bai taɓa ganin wacce yake so ya dinga gani ko yaushe kamar islaha ba. Yana ta yi mata murmushi ya ce, "Za mu yi wasa, ki zo mu hau keke da mota da jirgin ƙasa." Islsha kamar ta kurma ihu saboda tsoro da tashin hankali, muryar tana rawa ta ce, "to ka sakar min hannu." Salman ya saki hannunta amma ya riƙe gefen hijjab ɗinta dan kar ta gudu. Ita dai a tsorace ta danna code ɗin aka yi sa a ta saka daidai, ƙofar ta buɗe tana shiga ya bi bayanta. Yana shiga ya ji muryar Umma tana ƙwala masa kira, sai kuwa ya ɓuya a bayanta ya ƙanƙame Islaha ta baya yana faɗin, "Ga Umma nan, ki ɓoye ni, ni a wajan ki zan zauna, ki ɓoye." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Na shiga uku" ta furta a bayyane jin yana ƙoƙarin yar da ita ta faɗi a ƙasa. Salman kwata-kwata bai san abinda yake yi ba, so yake ya ɓuya kar Umma ta zo ta tafi da ahi. Jikin Islaha ya hau rawa, ta tsorata sosai, hankalinta ya tashi, ta rasa ya zata yi masa, ta kasa ƙwace kanta kuma ta kasa motsin kirki sai yadda ya juya ta. "Salman kana ciki..." maganar Umma ta maƙale ganin ɗanta a bayan Islaha ya riƙe ta. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Me ki ke koya masa?" Ta faɗa da ƙarfi tana shigowa falon, ta dage ta ja shi da ƙarfi amma yaƙi sakin Islaha. Umma ta ce, "za ka cika ta ko sai na mare ka, baza ka sake ta ba?." "Ni dai Umma bazan bi ki ba, a wajan ta zan kwana, ni ki tafi" ya sake faɗa yana sake riƙe Islsha da take tsakiyarsu ta rasa ya zata yi. Ita dai wani namiji bai taɓa yi mata haka ba tunda tazo duniya, babu namijin da ya taɓa haɗa jikinsa da ita ya riƙe ta ƙam ƙam haka sai shi. Ko ya ta motsa sai jikinta ya gogi nasa, ta rasa ya zata yi. Umma ta kwaɗa masa mari mai zafi, ta finciko hannunsa ta ce, "ina magana kana faɗa min haka, yaushe ka raina ni haka ne?." Sai kawai ya fashe da kuka yana faɗin, "ni bazan bi ki ba, ni a wajanta zan zauna." Abba da ya dawo daga masallaci ya zo wucewa ya ji hayaniya daga ɓangaren baturen gidan, abin ya ba shi mamaki dan ko motsi baka ji daga ɓangaren Rehaan balle kuma hayaniya. Ganin ƙofar a buɗe ya saka ya shiga dan ya tabbatar ba lafiya ba. "Me yake faruwa?" Ya faɗa yana kallonsu. Salman ya ƙwace daga riƙon da Umma ta yi masa, ya ƙarasa wajan Abba yana kuka shaɓe-shaɓe kamar ƙaramin yaro ya ce, "Abba ni a wajanta nake so na kwana, Umma kullum sai ta zo ta tafi dani. Ni ina sonta, bana so na tafi." Abba cikin mamaki da tsoron kalaman Salman ya ce, "wa ka ke so Salman?." Ya nuna Islaha da take tsaye a wajan har lokacin ta kasa motsin kirki saboda tsoro da tashin hankali da ta ke ciki. Abba ya kalli Islaha sannan ya kalle shi ya ce, "Salman har ka san ka ce kan sonta?." Shi dai bai amsa ba sai kuka yake yi sosai, Abba ya girgiza kai ya ce, "shikenan daina kuka." Ya kalli Umma da take wuci kamar zakanya, kafin ya yi magana ta ce, "ka yi mata iyaka da ɗana, ban zan lamunci abinda take yi masa ba. Ya zata dinga saka min shi a ɗaki tana saka shi ya riƙe jikinta? Me Salman ya sani da zata dinga ƙoƙarin koya masa iskancin da da bai isa shi ba? In ba dan ta zo gidan nan ya aka yi Salman ya san ya ce ina sonta? Kai kanka yanzu da ya faɗa sai da ya ba ka mamaki da tsoro, saboda ka san bai taɓa faɗa ba sai da wannan annobar ta zo gidan nan. Zuwa na yi na same ta ta saka ya riƙe ta ta baya yana shafa jikinta." Islaha ta lumshe ido jin sharrin da aka ƙulla mata wanda bata isa fitar da kanta daga ciki ba, ta  kalli Umma da taƙe haƙiƙcewa tana faɗar ƙarya. Abba ya kalli Islaha ya ce, "Ya aka yi?." Islaha muryarta ta yi sanyi ta ce, "Wallahi bani na shigo da shi ba, kawai na ga ya shigo ne. Yana jin muyarta tana kiransa sai ya tashi ya riƙe ni wai na ɓoyesa, na so na ƙwace kaina amma na kasa" ta ƙarasa faɗa muryarta na cracking alamun zata yi kuka. Umma ta ce, "ƙarya ki ke wallahi, meyasa bai taɓa yiwa ko wacce mace haka sai ke? Kwanan ki uku a gidan nan amma kin fara ƙoƙarin lalata min yaro. Bai taɓa cewa yana son wata ba sai ke, bai taɓa yiwa ko wacce mace haka ba sai ke, in ba koya masa ba ya aka yi ya sani?." Abba ya ce, "ya isa haka, kar na sake jin bakin ki akan maganar nan." Umma ta ce, "wallahi bazai yu ba, dole a yi min iyaka da ita, baza ta gurɓata min tarbiyyar yarona ba." Abba ya riƙe hannun Salman ya ce, "mu je ka yi sallah." Salman ya ƙi tafiya ya ce, "ni a wajanta zan zauna." Abba ya ce, "zamu dawo, mu je. Kema fito..." ya faɗa yana kallon Umma. Sai a lokacin Abba ya lura da Rehaan a tsaye a jikin ƙofar ya haɗe rai, bai ce masa komai ba ya fita da Salman. Umma ta zo gifta Rehaan ta ce, "In baza ka iya tsare matarka ba ka sallamata ta je inda zata samu abinda take so, ta daina shafe min ɗana tana ƙoƙarin rage wani abun da shi." Haka kwaai ya ji maganar ta da ki zuciyarsa, ya haɗɗiye yawu, apple adam ɗinsa yana up and down, ya ƙarasa cikin falon ya same ta a zaune ta rufe fuska da hannunta tana kuka. Ya tsaya yana ƙare mata kallo, zuciyarsa tana wani irin tafasa cikin tsananin ɓacin rai da jin haushinta mai yawa. Yanzu yake danasanin yiwa Abba alƙawari akan aurenta, yanzu yake danasanin amincewa ya zauna da ita har na wata biyar. Tabbas ya cuci kansa, ya lalata backround ɗinsa ta ko ina. A hankali ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido, idanunta ya yi ja sosai fuskarta ta sake tsukewa ta koma kamar ta fuskar yara. Ganinsa a tsaye a kanta sai hawaye ya sake zubo mata, tana buƙatar wanda zai rarrashe ya bata gaskiya bata da kowa, muryarsa tana rawa ta ce, "Ni dai ka canja min gida, bazan iya zama a nan ba." Wani irin abu yake ji yana caccakar zuciyarsa, ƙirjinsa yana bugawa da ƙarfi, ransa ya ɓaci jijiyoyin kansa suna harbawa. Cikin wata irin murya ya ce, "kin san yanayin ki, saba da aikatawa ko yaushe meyasa ki ka saka no intimacy a rules ɗin ki?.... Nana Haleema. RDB3P24 Nana Haleema. Da hanzari ta ɗago kai tana kallonsa, gabanta ya faɗi tana jin kalamans suna sukar ta kamar allura har cikin zuciyarsa. Ta goge hawayen idanunta ta miƙe tsaye tana kallonsa ta ce, "me ka ke nufi?." Ya kalle ta ta gefen idanunsa ya ɗauke kai cikin hausarsa da ba ko yaushe ya cika yi ba ya ce, "kin ji ai, no need na maimaita miki." Islaha ta bi shi da kallo ta kasa magana sai ido da ta zuba masa dan bata san ma abinda zata ce ba. Inda zata samu yadda ta ke so da ta ce a jawo mata shi, ta dinga dukansa har sai ya daina numfashi. Rehaan ya kalle ta ya ce, "look! Ni ban hana ki abinda ki ke ra'ayi ba, amma ina so na tuna miki nan gidanmu ne kuma nan apartment ɗina ne. Bazan yarda ki dinga ɓata min suna ko yaushe ba, in za ki yi abinda ki ke so ki bar gidan nan, in kin gama ko meye sai ki dawo ba abinda ya dame ni ba ne. Sannan ki ƙyale Salman, na faɗa miki yana da mental issue bazai taɓa rufa miki asiri ba." Duk da ɓacin ran da ya danne mata ƙirji, takaici da haushinsa da suka tokare ta har take jin ta kasa numfashi yadda ya kamata, bai saka ta saurara masa ba ta ce, "ai na ji kana zancen na san ina so na saka bana so a rules ɗina, shine na ke so na na tuna maka…..kai dai!" ta faɗa tana nuna sa da yatsa irin up and down ɗin nan. Kafin ta cigaba ya harɗe hannunsa a ƙirji ya ce, "ni dai me? Kin ji na ce miki da ba ki rubuta ba akwai wani abu ne?." Sai ya yi murmushin takaici da baƙin ciki ya sake zuba masa ido, sai ya rasa me zai ce mata dan kamar zubar da class ne tsayawa yana faɗa tana faɗa. Sai ya ce, "i don’t have your time" ya faɗa yana hawa sama dan bai ga amfanin ya tsaya yana faɗa tana faɗa ba. Takaici ya saka ta yi kuka mai yawa, a nan ta zauna ta ci kukanta son ranta. Buɗe ƙofar ta ji anyi ta san kuma Banisha ce, dan itace mai shigowa falon kai tsaye. Banisha ta shogo ciki ta ce, "Sis Islaha me ya faru?." Islaha ta girgiza mata kai bata ce komai ba. Banisha ta ce, "Daada ta ce na kira ki" tana faɗa ta wucewa sama wajan Rehaan. Islaha ta ce, “Na shiga uku, ni fa bana so a ce na zo ɗin nan. Da me zan ji? Da sharrin da aka yi min ko da zaunar da ni a gaban mutane?. Na baro gidan Maman su Hamma ma ban huta ba, har gwara can a kan nan.” Sai ta miƙe zaune har suka sakko tare shi da ita, Banisha ta ce, "mu je." Ko hijjab ɗin jikinta bata cire ba haka ta miƙe ta bi bayansu a sanyaye. Bata kula da kowa a falon ba ta zauna dan kanta har ya fara ciwo saboda kukan da ta yi, ga shi ba wani abincin kirki take ci kwana biyu ba, har jiri take ji yana ɗaukar ta. Gabaɗaya bata lura da gabaɗaya matan gidan ne a zaune ba, ga Abba ga kuma Salman ɗin. Daada ta ce, "Ishlaya." Islaha ta ɗago ido a hankali ta kalli Daada. Daada ta ce, "Faɗa min me ya faru?." Islaha ta sunkuyar da kai muryarta a raunane ta ce, "bayan na bar nan na koma, sai na tuna na bar kaya a mota, shine na yiwa wanda ya kaini waya na ce ya kawo min. Yana kawo min sai ga shi ya zo wajan, kuma..." ta kasa ƙarasa tana dafe kanta cikin takaici. Umma ta yi caraf ta ce, "ƙarya ki ke yi, ke ki ka neme shi ki ka kai shi har cikin falon mijin ki, in ba ki neme shi ba ta ya zai zo?." Daada ta kalle ta ta ce, "ya isa, ba ke na tambaya ba ai ko?." Daada ta ce, "Ina jin ki Ishlaya." Islaha ta ce, "daƙyar ma na tuna lock ɗin da Banisha ta faɗa min, ina shiga ya bi bayana ya zauna. Sai ya ji muryarta tana nufo parlour, shine ya miƙe yana cewa na ɓoyesa kar ta tafi da shi. A haka ta shigo falon." Daada ta sauke numfashi ta ce, "Ishlaya ke kin ce haka aka yi, ita tace ba haka bane." Islaha ta ce, "Allah yana ganin duk abinda ya faru, bazan ɓoye gaskiya na faɗi ƙarya dan na burge wani ko dan na ɓoye laifina ba." Rehaan ya bita da kallo jin tana tauhidi ita lallai ga mai tsoron Allah. Tsakin da ya yi ya saka kowa ya kalle shi, sai kuma ya ɗaure fuska ganin ana kallonsa, gabaɗaya zaman ƙasar ya ishe shi wallahi, yana da ayyukan yi shiyasa yake so ya tarkata ya koma inda ya fito ko hankalinsa zai kwanta da wannan ƙananun maganar. Umma ta ce, "ni so nake yi a raba ta da ɗana, babu ita babu shi, kar na sake ganinsa a wajanta ko da wasa. Ai ba dole sai ta kula shi ba, kuma yayan mijinta ne ba ƙani ba, babu ruwanta da shi." Salman ya noƙe kafaɗa ya ce, "Abba ni dai ina sonta, don Allah ka ce Umma ta bar ni na zauna a wajanta, ni a wajanta nake so na zauna." Daada ta buɗe ido cikin mamakin kalamansa ta ce, "kana son wa? Kai Salmanu matar ƙaninka ce fa." Salman ya kalli Daada ya ce, "Ni dai ina sonta, kuma ya ce itama tana sona, ko Rehaan?." Ya faɗa yana kallon Rehaan, shima ya kalle sa amma bai ce komai ba yana jin zafi a zuciyarsa Daada ta ce, "dallah ka yi mana shiru, shashashan banza. Matar wani ka ke cewa kana so? Na faɗa maka matar ƙaninka Rehaan ce. Kuma mace in tana da aure ba a cewa ana sonta, ka ji?." Idonsa ya ciko da hawaye ya ce, "Ni dai ina sonta, kuma tunda kin ce matar Rehaan ce ba ɗan uwana ne zan iya cewa ina sonta. Ni dai ina sonta, kuma a wajanta zan kwana, ina sonta!" Ya faɗa da ƙarfi, sai kuma ya zabura ya yi kan Islaha da nufin ta ɓoye shi, babu shiri ta miƙe da hanzari ta yi bayan kujera gabanta yana faɗuwa. Kafin ya kai ga ƙarasa sai ya yi baya ya faɗi a ƙasa, duk suka yi kansa ana salati cikin tashin hankali. Umma ta kalli Daada ta ce, "wallahi bana son yarinyar nan, bana ƙaunar ganinta ko kaɗan. Tunda ta zo gidan nan Salman ya canja, tunda ta zo yake irin waɗnanan surutan da da bai saba dasu ba. Rabon da ya yi irin wannan faɗuwar har na manta, amma daga zuwanta zata dawo min da hannun agogo baya. Kawai dan an ga yana da matsalar kwakwalwa sai a dinga cutar dashi? Dan ita matar Rehaan ce kowa yana jin tsoronsa saboda kuɗin da yake da shi shiyasa baza a bata laifi ba ake ƙoƙarin ɗora masa?. Wallahi bazan amince da wannan abun ba, ko ita da Rehaan su bar gidan nan, ko kuma ni da shi mu tafi" ta ƙarasa faɗar haka tana zubar da hawaye tana jijjiga Salman amma ta san sai an yi masa allura zai farfaɗo. Abba ya kalli Rehaan ya ce, "A ɗauko allurarsa a yi masa." A fusace Umma ta ce, "bana so ya taɓa min ɗana, Janan ta zo ta yi masa, bana buƙatar ko shi ko babarsa wani ya saka hannunsa a jikina." Mama da take zaune ta ce, "Ina Janan ɗin ta ke, bara na kira ta da kaina” Ta faɗa tana tashi ta fita, jim kaɗan suka dawo da Janan da allura a hannunta, Janan ta yi masa a jijiya ta koma ta zauna. Falon ya yi shiru babu mai cewa komai, Islaha tana daga inda ta yi tsalle ta haura a tsaye cikin wani irin yanayi na tsoro da tausayin Salman. Daada ta ce, "Dawo ki zauna Ishlaya." Islaha ta dawo ta zauna tana sunkuyar da kanta. Daada ta ce, "Ke Salamatu! Kar na sake jin magana akan za a lalata miki ɗa, a gaban ki dai ga abinda ya faru, a kan idanun ki ga shi ya tashi a guje zai je wajanta." Umma ta ce, "In bata koya masa ba ai da bazai yi ba, itace ta ɗora shi a kan hakan shiyasa yake yi a gaban kowa." Cikin faɗa Abba yake kallon Umma ya ce, "har yaushe ta san Salman ɗin da zasu yi irin wannan sabon? Yau kwananta uku a gidan nan, yaushe ta san Salman da zasu yi wannan sabon?. Me yake damun ki ne Salamatu? Ana magana kina karkacewa dan kin raina mana hankali?. Tana da ilimi fa, ta san duk abinda take yi, ya za ki dinga ƙoƙarin tarwatsa mana kan gida a ko yaushe?. Ko yaushe ke ki ke kawo rabuwar kai a gidan nan da ƙananun maganganun ki, yanzu meye amfanin kalaman da ki ke yi akan matar ɗan ki?.” Umma ta ce, "shikenan sai a dake ni a hana ni kuka? A cuce ni ace bazan yi magana ba? Dan kawai an ga yana da matsala baza a yi amfani da maganarsa ba?." Mama ta ce, "Salamatu don Allah ki yi haƙuri, ba ga shi kin kawo maganar wajan Daada ba?." "Bakya jin abinda Daadan ta ke faɗa ba? A ko yaushe Rehaan shine a kan daidai, yanzu ga matarsa ma tazo, ana nuna mana itace dai matar Rehaan mu kuma mu ne banzaye. Ba a yi min adalci a gidan nan kwata-kwata, ana nuna min banbanci." Rehaan ya bita da kallo yana taɓe baki jin wai ana nuna mata bambanci, a ganinsa kaf cikin gidan Mamy ce ya kamata ta ce ba a yi mata adalci ba ita ba, amma wai itace take cewa ana nuna mata banbanci saboda rashin tsoron Allah. Mama cikin gajiya da maganar ta ce, "ki yi shiru don Allah." Daada ta ce, "ƙyaleta Saddiƙa, ƙyaleta ta gama yi min rashin kunyar. " Umma ta ɗauke kai bata ce komai ba. Daada ta ce, "haka kawai yarinya baƙuwa daga zuwanta za ki fara ɗora mata sharri? Shi ɗan naki da yake da matsalar ƙwaƙwalwa ba ki ɗora masa ba sai ita? Shi duk abinda aka ce zai aikata ai zai aikata ɗin ne, tunda ba hankali ne da shi ba. Ita kuwa daga zuwanta yau kwana uku har kin fara ɗaga mata hankali da sharrin ki na banza da wofi, wacce irin rayuwa ce wannan?." Umma ta yi shiru bata ce komai ba, amma a zuciyarta ji take yi da tana da dama sai ta fitar da Islaha daga cikin gidan ta ƙarfi. Abba ya ce, "daga yau kar na sake jin magana irin wannan a gidan nan. Salman kuma tunda abinda zuciyar ki take ba ki kenan ki hana sa zuwa wajan Rehaan, in ki ka yi haka ba shikenan ba?." Ita dai bata amsa ba, haushi take ji jin an ɗauki laifi gabaɗaya an ɗorawa ɗanta, bayan ga mai laifi nan a zaune. Haka taro ya watse kowa ya kama gabansa, masu farin ciki suna yi masu jin haushi suna yi. Islaha tana wajan Daada a zaune. Daada cikin rarrashi da kwantar mata da hankali ta ce, "kar ki damu Ishlaya, haka gidan nan yake, haka mijinki yake a gidan nan, ba kowa ne yake ƙaunarsa ba, kema kuma dole abin ya shafe ki tunda matarsa ce. Ki yi haƙuri, kar hakan ya dame ki kin ji?." Islaha ta ce, "In sha Allah." Daafa ta ce, "Janan da Banisha ku raka ta ɓangaren ta." A tare suka miƙe suna nufar apartment ɗin Rehaan babu mai yiwa wani magana a cikinsu. Nana Haleema. RDB3P25 Nana Haleema. Sai da suka shiga falon sannan Janan ta ce, "i’m sorry Sis, abubuwan gidan na mu ne sai a hankali." Islaha ta yi murmushi ta ce, "na gode." Janan ta miƙa mata hannu ta ce, "Dr Janan." Islaha itama ta ta bata hannu suka gaisa sannan ta ce, "Islaha." Janan ta murmusa ta ce, "ƴar jarida Islaha dai, amma mu da Islam zamu kira ki, In kina buƙatar wani abu za ki iya yi min magana." Islaha ta ce, "Na gode Janan." "Kar ki damu" ta faɗa suna fita ita da Banisha. Islaha bata bar abin ya dame ta ba ta yi alwala ta yi sallar i'sha, sannan ta kalli dining ta ga akwai abinci ajjiye ta zuba ta ci dan tana jin yunwa sosai. Bayan ta gama ta ɗauki kayanta da laptop ɗinta ta hau sama. In ta tuna abinda ya faru bata sanin tana hawaye, sai dai ta share ido ta yi ƙoƙarin kawar da tunanin dan ba shi da amfani a ta shiga wanka. Bata jima ba ta fito ɗaure da ƙaramin towel, ta ɗaura wani a kanta tana fitowa tana kwance na kanta gashinta ya sauka har ƙugunta. A daidai lokacin aka buɗe ƙofar, tana juyowa da niyar ganin waye suka haɗa ido da Rehaan da ya buɗe ƙofar a karo na farko. Islaha sai ta dirririce, karo na farko da wani namiji ya taɓa ganinta a haka, daga ita sai ƙaramin towel, ga shi kanta babu ɗankwali. Gabanta ya faɗi sosai, amma da ta tuna kallon ƴar iska yake mata sai ta ɓoye yanayinta, ta dake ta ɗauke kai daga kallonta amma fa zuciyarya bugawa take yi. Rehaan kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa, ya sake kallon ƙafafunta da take ɗage su sama kamar wacce take taka wuta, tun daga toes ɗinta yake kallo har laps ɗinta, sannan ya ɗauke kai kamar ba ya son magana ya ce, "Mamy tana jiran ki" yana faɗa ya kulle ƙofar ya koma. Islaha ta yi tsaki mai sauti ta ce, "aikin banza, ni na gaji da matsalar gidan nan wallahi, daga wannan sai wannan kamar gidan haya." Tana shiryawa tana mita a haka ta gama saka kaya ta sako hijjab ta fito ta samu Mamy a zaune a kan kujera shi kuma yana gefenta ya ɗora kansa a kafaɗar ta. "Shugaban masu shagwaɓa da son jiki, kalle shi don Allah, ƙato dashi ya dinga kwanciya a jikin babarsa" ta faɗa ƙasa ƙasa tana ƙarasowa ta zauna a kan carpet tana harararsa ta gefen ido.. Cikin sanyin murya Islaha ta ce, "Mamy ina yini." Mamy ta kalle ta ta ce, "Lafiya lau. Kina ji, a yanzu a matsayin inlaw ɗina ki ke, kina cikin part of my family, duk da a yanayin da auren ku yazo amma bazan canja sunan ki daga sirikata ba. Islaha ki dinga kiyaye duk wasu abubuwa da suka shafi gidan nan, ki dinga sanin abinda za ki yi saboda magana. Kowa a gidan nan jira yake a ce ɗan ɗakin Mamy ya yi wani abu, ana cewa za a haɗa meeting a zauna ana faɗar magana mara daɗi a kaina. Ki dinga kiyaye duk abinda zai jawo magana, bana son yawan abubuwan nan da suke faruwa tunda ki ka zo, kin ji?." Islaha jin yadda Mamy take yi mata magana a tausaahe sai ta ɗaga kai ta ce, "In sha Allah." Mamy ta ce, "na duba cctv, na ga clip ɗin abinda ya faru kafin ki shigo falon, na tabbatar ƙarya aka yi miki abinda aka faɗa ba gaskiya ba ne. Ki cigaba da kiyayewa, in ba haka ba wata ran abinda zasu ce kin yi abinda ya fi haka." Islaha sai ta ji hankalinta sai ya kwanta, ta yi murmushi har ta ɗago suka haɗa ido da Mamy sannan ta ce, "In sha Allah Mamy." Lokaci ɗaya gaban Mamy ya faɗi sosai, ta ɗan zuba mata ido na wani lokaci kafin ta janye idanunta ta ce, "Islaha sunan ki amma sun saka miki Islam, haka ne?." Ta ɗafa kai alamun eh, Mamy ta ce, "is okay, za ki iya tafiya" Islaha ta miƙe ta koma ciki tana waiwayon Rehaan da ya ke wani narkewa a jikinta tana jin takaici yana mamaye ta kamar ta zo ta rufe shi da duka. Mamy ta shafa kansa ta ce, "kamar tana da hankali." Ya ɗago ya kalli Mamy ya ce, "a hakan?." Mamy ta dungure masa kai ta ce, "meyasa baza ka nutsu ku zauna lafiya ba?." Ya zaro ido ya ce, "da wannan ɗin?." "Ita ɗin." "Rashin kunya ta yi miki fa." "Bani ta yiwa ba, kuma ko a lokacin laifin Ammi ne." Ya yi shiru bai ce komai ba sai daga baya ya ce, "zan koma engaland." Mamy ta miƙe ta ce, "ai an samu ka zauna ma, ina jin ba ka taɓa jimawa a ƙasar nan kamar yanzu ba, kullum kana yawo, amma nima zan je india." Ya yi murmushi ya ce, "Kun yi magana da Riyya?." Mamy ta yi murmushi ta ce, "mun yi ɗazu." Ya ɗaga kai bai ce komai ba, Mamy ta sauka daga saman. Islaha tunda ta koma take saƙa da warware akan lamarin Zainab, sai kai kawo take yi tana so ta samu wani abu guda ɗaya da zata riƙe matsyin makami amma ta kasa. Tana so ta samu hujja mai ƙarfi da kai kokenta ma'aikatar da Jazy ya faɗa mata, kamar yadda ya faɗa mata sai tana da hujja zasu karɓi report ɗin, ita kuma hujjar ta rasa. Ta yi ajiyar zuciyar rashin mafita, tana tuna abubuwan da suka faru tunda daga lokacin da aka goge hotunan Hafsa a wayarta, zuwa recording da komai da komai. Ta zauna ta yi tagumi ta rasa wanne irin tunani zata yi ta ji daɗi akan lamarin, tana buƙatar shawara, tana buƙatar ta yi magana da wanda zai fahimce ta har ya faɗa mata abinda ya kamata ta yi a wannan lokacin. Ta cire hijjab ɗin jikinta ta ajjiye, ta ja numfashi mai tsaho cikin tunani kala kala wanda bata da hanyar magance su a nan kusa. Sai kuma ta miƙe tsaye a bayyane ta ce, "Ya zama dole na koma wajan Yafindo, ya zama dole na je na same ta duk abinda zai faru sai dai ya faru. Zainab ce kaɗai hujjata kuma ta ɓace, saƙon da ta bayar kuma yana hannunta. In na samu saƙon da ta bawa Yafindo, wataƙila zai iya taimaka min na je inda Jafar ya ce min, wataƙila ƙarshen matsalar ta zo." Ta juya ta ɗauki wayarta tana duba mail ɗin da ta turawa mutanen da za su yi interview dasu, mutum ɗaya ya yi approving saura biyu. Haka kawai ta ji gabaɗaya bata jin bacci, ta zauna tana tunani akan gidansu Rehaan da matsalolinsu. Daga zuwanta zuwa yanzu ta fahimci babu haɗin kai a lamarin gidan ko kaɗan, kowa kansa ya sani. Sannan kamar Mamy ce ba sa so, shi kansa Rehaan ɗin ta fahimci ba kowa ne yake ƙaunarsa a cikin gidan ba. A bayyane ta ce, "Amma kuma Mama tana da kirki sosai, har ta so ta fi Mamy kirki. Ina ganin girmanta sosai, dan tana sona." Sai kuma ta yi tsaki ta ce, "Ina ruwana da tunanin akan gidan nan? Su kashe kansu mana, ina ruwana ni da ba zama nazo yi ba?" Sai ta watsar da tunanin ta cigaba da abinda yake gabanta. Haka take zaune ita kaɗai, ta saka tashi ta kwanta har ƙarfe ɗaya na dare sannan ta fara jin bacci. Ta miƙe tsaye ta shiga banɗaki ta yi alwalar kwanciya bacci, ta fito tana gyara kan gadon da niyar kwanciya. Kamar ance ta kalli window ta waiwaya tana kallon compound ɗin apartment ɗin Rehaan, ta gan shi a tsaye a kusa da mota, an buɗe masa bayan motar yana niyar shiga da alama fita zai yi. Islaha gabanta ya faɗi, tsoron barin ta ita kaɗai ya mamaye mata zuciyarta, ta dafe ƙirji ta ce, "Ina zai je ya barni ni kaɗai a wannan gidan? Sai wannan mahaukacin Yayan nasa ya zo an sake ƙulla min wani sharrin?." Ganin da gaske mota zai shiga kuma fita zai yi, bata san ta fizgi hijjab ta fita da gudu ba. Tana fitowa inda motar ta ke a daidai lokacin ya kulle mota ana niyar jan motar su fira. Isaha ta tsaya tana kallon motar sa ta glass, shima ganinta a tsaye sai ya ba shi mamaki, yana kallonta ta glass kamar yadda take kallonsa. Islaha ta miƙa hannunta yi knocking glass ɗin Rehaan sauke yana kallon ta. A karo na farko da Idanunsa suka yi mata kwarjini, kaifin idanunsa suka soki zuciyarta, lokaci ɗaya sai bakin ta ya yi nauyi sosai, ta sauke idanunta ƙasa tana turo baki ta ce, "ni gaskiya tsoro nake ji bazan iya zama ni kaɗai ba, zan bi ka duk inda zaka je." Rehaan ya bita da kallo bai ce komai ba, ganin bai yi magana ba kawai sai ta zagaya ta buɗe back seat ta shiga kusa dashi ta rufe ƙofar. Har a lokacin bai ce komai ba ya ɗauke kai yana kallon gabansa. Sai kuma ya ce, "Shams me ka ke jira ne?." Shams da mamakin ganin Islaha a kusa da Boss ɗinsa a zaune a back seat ya hana shi magana, jin muryar Rehaan sai ya ce, "Sorry Sir" ya faɗa yana kunna motar amma kallon Islaha yake yi. Dan wallahi bai manta da fuskar Islaha ba, har gobe in ya tuna dramar da suka yi da ita a lokacin da suka sace ta yana dariya sosai. Ganinta tare da mai gidansa a apartment ɗaya ya ba shi mamaki, amma bai ce komai ba ya ja suka fita        *** "Ranka ya daɗe motar Rehaan ta fio daga gida yanzun nan, kuma daga shi sai matarsa da Shams, babu security ko ɗaya, shi kaɗai ne." Daga can ɓangaren ya ce, "dakyau, ina zuwa." Yana kashewa ya kira waya ya ce, "Rehaan ya fita, a san abinda za a yi, kar ɗayansu ya dawo da rai. Dukka su biyun bani da buƙatarsu, a tabbatar da anga bayansu." Yana gama faɗar hakan ya kashe wayar, ya furzar da iska mai zafi ya ce, "Lokaci ya yi Rehaan, wallahi sai na bayanka, bazan taɓa bari ka rayu da rai da lafiya ba, sai na kashe ka. Matar ka da ta bi ka ku ka fita ka jawo mata, za a ɗauki gawa biyu. Mu je zuwa" ya faɗa yana lumshe ido cikin tsana da ƙiyayyar Rehaan wacce shi kansa bai san adadinta ba. Nana Haleema. RDB3P26 Nana Haleema Tunda suka tafi Islaha bata yi magana ba, tana jikin ƙofa ta jingina tana kallon window. Ac motar ta dame ta, da motar ta yi wani irin sanyi mai ratsa jiki, ga turarensa ya gama mamaye ko ina a cikin motar. Ta ɗan ja numfashi jin kamar numfashinta ya fara tokare ta, ta saka hijjab ɗinta ta toshe hancinta jin sanyin zai yi mata illa. Shi kam Rehaan kamar bai san da ita ba, waya yake amsawa tunda suka fara tafiya har suka tsaya bai daina magana a waya ba. Ta ɗan kalle sa ta ga sai yatsina yake yi kamar wanda ya yi doguwar tafita, ta ɗauke kai tana jan siririn tsaki tana ji kamar ta gaggaura masa mari saboda takaici. Kallon gidan da aka buɗe musu take yi, ta buɗe ido kawai tana kallo ganin girman gidan da yadda aka tsara shi ya burge ta. Harabar gidan kanta abin kallo ce, ga haske ko ina kamar ba ɗaya da wani abun na dare ba. Shams ya tsayar da motar, har lokacin Rehaan bai gama waya ba, sun yi minitina biyar da tsayawa sannan ya kashe wayar ya buɗe motar ya fita. Tana ganin ya fita itama ta fita, har lokacin bata lura Shams ne yake driving motar ba. Inda ya nufa take nufa yana gaba tana binsa a bayan, har suka shiga main parlor mai kyau da girma. Maimakon ta ga ya tsaya sai ta ga ya nufi stairs kai tsaye ya hau sama. Kamar ta bi sa sai kuma ta tsaya dan kar ta zaƙe da yawa, ta tsaya tana kallon falon. Rehaan yana shiga first parlour ɗin da yake upstairs ɗin ya jiyo kukan Riyya daga cikin bedroom. Rehaan ya kalli Jazy da yake zaune a kan kujera ya dafe kansa da hannu biyu, bai san Rehaan yana tsaye a kansa ba sai ji ya yi ya ce, "Jazy me ka yi mata haka da ta ke wannan kukan?." Jazy ya firgita jin maganar Rehaan a sama, dan bai dan ya zo ba kawai ya ji magana ne. Ganin Rehaan sai ya miƙe tsaye ya ce, "zo mu je don Allah, na rasa abinda ya kamata na yi mata, sai kuka take yi tun ɗazu, daƙyar na samu nunfashinta ya dawo daidai." Ray ya ƙi binsa ya daƙire ya ce, "ƙoƙarin kashe ta ka yi ne ko me? Me ya same ta haka?." Jazy ya ja hannunsa ya ce, "ka zo mu je ka gani." Rehana ya bi bayansa ya shiga ɗakin dan bai san me ya samu Riyya ɗin ba. Rehaan da hanzari ya ƙarasa inda Riyya take ganin tana kuka sosai, ya riƙo ta jikinsa ya ce, "Riyya me ya same....." bai ƙarasa maganar ba jin jikinta ya yi zafi sosai. Rehaan a rikice ya ce, "Oh my god! Wnnan fever daga ina kuma, me ya same ki Riyya?." Riyya jin muryar Rehaan sai ta buɗe ido daƙyar, ganin yadda idanunta suka yi ja suka kumbura sosai sai hankalinsa ya sake tashi, cikin faɗa ya kalli Jazy ya ce, "wai me ka yi mata haka, me yake damunta da za ka bar ta a gida baza ka kaita asibiti ba?......" Ya sake kallon Riyya ya ce, "Riyya me yake damun ki, ina ne yake yi miki ciwo?." Riyya ta riƙe hannun Rehaan cikin muryarta da ta dashe ta koma ta marasa lafiya ta ce, "ka tafi dani gida, bazan iya zama a nan ba, wajen Mamy zan koma." Rehaan ya sake kallon Jazy cikin masifa da son sanin abinda yake damun ƙanwarsa ya ce, "Jafaar me ka yi mata!." "We had our first night Ray!" Ya faɗa yana kallonsa sai kuma ya ɗora da cewa, "na rasa ya zan yi mata, gabaɗaya ta birkice tana ta kuka. Na san akwai ciwo, amma ya kamata ta daina kuka ko dan saboda ciwon kan da yake damunta. Kai kaɗai zan iya kira na faɗawa abinda ya faru, shiyasa na kira ka dan ka zo ka duba ta." Ray ya tsaya cak yana kallonsa cike da mamaki da tsoro ya ce, "You had your first night!" Ya maimaita yana kallonsa tare da sake riƙe Riyya a jikinsa dan har lokacin kuka take yi. Rehaan cikin ɓacin rai da ƙunar zuciya ce, “Just because you had your first night is that why you're causing her this pain? Ka ji yadda jikinta ya yi zafi kuwa? Are you out of your min Jafar!? Jazy shi ba wannan maganar yake so ba hakan ya saka ya ce, "ka taimaka mata ta daina wannan kukan please, in ka gama sai mu yi wannan maganar." Ray ya fara yiwa Jafar faɗan da Jazy ya jima bai ga irinsa ba, cikin faɗa ya ce, "kawai saboda first night sai ka yi mata wannan illar? Kwana nawa da auren na ku da baza ka iya bari ta huta ba?. Kwana biyu ne fa, har yanzu bata gama warware daga gajiyar biki ba, duk ba ka yi tunanin wannan ba, ba ka bari ta dawo daidai ba ka yi mata haka?......" Sai ya dafe kai cikin takaici ya ce, "Oh my god! Jazy kai ne kuwa?." Jazy bai biyewa Ray ba, dan in ya biye masa baza a dubata ba faɗa zasu yi, a tausashe ya ce, "ni dai ka fara dubata, don Allah." Ray ya sauke numfashi ya kalli Riyya da ta ke jikinsa a kwance har lokacin kuka take yi. Tausayinta ya mamaye masa zuciya, ya gyara mata gashin kanta yana taɓa forehead ɗinta cikin wani irin yanayi na tausayi da haushin Jazy. Sai kuma ya yi tsaki mai sauti, ya kwantar da ita ya miƙe ya fita daga ɗakin Jazy ya bi bayansa. Ganin yana niyar sauka downstairs da hanzari Jazy ya riƙo shi ya ce, "Ray meye haka?." Rehaan ya harare shi ya ce, "Ba ka dace da zama mijinta ba, ba ka tausayinta Jafar." "Na ji, na yarda da duk abinda zaka ce min, amma don Allah ka fara bata treatment ɗin da zata daina jin ciwon. Kana gani sai kuka take yi, ka saka ta daina kuka." Rehaan ya yi masa banza kallo ya ce, "Ka kira Mamy mana, aikinta ne ba nawa ba." Jazy ya waro ido waje ya ce, "Mamy fa! Ni wallahi bazan iya kiran Mamy ba. Don Allah ka dawo ka duba ta ba dan ni ba, saboda ita zaka yi ko zata daina wannan kukan." Cikin jin haushi ya ce, "Ka san zata yi kukan amma ba ka fasa ba." "Na yarda na yi laifi, mu je ka duba ta don Allah." Rehaan ya yi tsaki mai tsaho cikin jin haushin Jafar akan abinda ya yiwa ƙanwarsa sai kuma ya ɗauki waya ya kira Shams, ya tura masa abinda yake buƙata ayi masa sannan ya koma wajan Riyya. Ya kalli Jazy da yake tsaye a jikin ƙofa ya ce, "ba ka bata pain killer bane ka tsaya kana kallona?." Jazy ya ce, "wallahi ba mu da ko wanne magani a gidan nan, ko pcm babu." Rehaan ya sake fusata ya ce "Ba ka da hankali Jaafar, maganin ma ba ka san ka bata ba? Abu ɗaya kawai ka saka a ranka ko?." Jazy bai kula shi ba ya share ya yi shiru, dan ya san daman ya taɓo shi tunda ya taɓa masa Riyya. Ita kuma gata ƴar shagwaɓa, duk sun shagwaɓata, a haka ma dan ba Banisha ba ce, da sai kowa na duniya ya sani. Rehaan ya yi shiru yana tuna abinda ya kamata a yi mata wanda zai taimaka mata ta ji daɗin jikinta. Ya kalli Jazy yana harararsa ya ce, "Have you put her in warm water?." Jazy kamar ƙaramin yaro ya ɗaga kai alamun eh, Ray ya harare sa ya ce, "ba ka da baki ne ko ka zama kurma?.” Jazy da yake taimako yake nema sai ya ce, "eh mana."  Ya yi ƙwafa ya ce, "bani towel da ruwan sanyi, yadda za ka taimaka mata ayi reducing body temperature ɗinta ma ba ka sani ba. Ba ka cancanci a yi maka aure yanzu ba." Shi dai bai kula sa ba ya kawo masa, shi kuma ya jiƙa shi yana goge mata a jikinta. Babu jimawa Shams ya yi Rehaan waya ya ɗaga ya bada umarnin a shigo. Islaha tana zaune ta ga mace ta shigo sanye da uniform na asibiti, ta kalli Islaha ce, "Good day Madam, ina ne hanyar?." Islaha ta nuna mata dan ta san kiran daga sama ne tunda har ta ke tambaya. Nurse ɗin ta ce, "ban san hanyar ba, ko za a iya nuna min?." Islaha kamar ta ce ai itama bata sani ba, sai bata faɗa ba ta miƙe ta bi inda ya bi suka hau saman nurse ɗin tana bayanta. Falon farko babu kowa a cikinsa, Islaha rasa inda zata bi su je falo na biyun, kawai sai ga shi an buɗe ƙofar. Suka haɗa ido da Jazy amma da yake ba a hayyacinsa yake ba bai ma lura da ita ba, Nurse ɗin yake kallo ya ce, "shigo." Suka shiga gabaɗaya har Islaha, ita dai ta tsaya daga falo su kuma suka shiga ciki. Nurse ɗin tana shga ɗakin haɗa ido da Rehaan duk sai ta diririce ta ce, "good day Sir." Ya ɗaga mata kai bai amsa ba ya ce, "Zo ki dubata." Da hanzari ta ƙarasa kusa da Riyya ta ce, "me yake damunta?." "She had her first night." Nurse ɗin ta ƙarasa tana kallon Riyya da take kwance a jikin Ray Nurse ta fara tattare rigarta don ta dubata dan ta tabbatar da abinda ya kamata ta yi. Riyya ta riƙe sa sosai ta ce, "Da zafi sosai, ni bana so, ka ce ta bari." Ya shafa kanta cikin rarrashinta ya ce, "Calm down, is okay, relax" ya faɗa yana shafa kanta a hankali tana kuka. Nurse bayan ta gama aikinta ɗin ta ce, "babu wata matsala Sir, kawai an samu pain ne amma babu ciwo, za a yi mata injection saboda a rage ciwon." Rehaan bai ce komai ba, nurse ta haɗa allurar ta yiwa Riyya shi yana ta rarrashinta shi dai Jazy yana tsaye yana kallon su, ya zama kamar Rehaan ne mijin ba shi ba. Bayan ta gama yi mata allura ta ba da maganin da za a bata ta sha, Rehaan ya ɗagota daga jikinsa ya bata maganin ta sha sannan ta kwanta. Jazy ya ce, "nurse nima ina buƙatar injection." Ray ya wani kalle sa yana yi masa kallon baka da hankali ya ce, "wallahi ba za a yi maka ba." Jazy jin ya rantse sai ya gimtse dariyar da yake son yi. Rehaan ya kalli nurse ya ce, "can go." Cikin girmamawa sannan nurse ɗin ta fita Shams zai mayar da ita asibiti. Ita dai Islaha bata san me yake faruwa ba, tana zaune a falo jin kukan Riyya amma ko kaɗan bata yi wani hasashe akan hakan ba. Riyya a jikin Rehaan bacci ya ɗauke ta, sai da ya ga ta yi bacci sosai sannan ya kwantar da ita a hankali gudun kar ta tashi, ya shafa fuskar ta da ta yi ja ga shi ta kumbura. Ya ɗago yana hararar Jazy da bai ce komai ba, sai da ya kashe mata hasken ɗakin sannan ya jawo hannunsa Jazy suka fito parlour sannanya ce, "So ka ke ka kashe ta ko? So ka ke ka yi mata abinda zata mutu numfashinta ya ɗauke? Wannan shine first night ɗin, you can be gentle?." Jazy ya ce, "i try to be gentle, but i can't. Amma kai baza ka fahimta ba, ba ka zo stage ɗin ba shiyasa baza ka gane abinda zan faɗa maka ba. Kuma wallahi shagwaɓa ce kawai irin ta Riyya, ba ka ji nurse ta ce komai normal ba?." "In ba ka yi min shiru ba zan saka bakin ka ya yi jini Jafaar. Tana kwance bata da lafiya kana cewa shagwaɓa ce? Waye ya saka ta a ciwon in ba kai ba?....." Jazy ya yi masa banza bai ce komai ba yana dariya ƙasa-ƙasa. Rehaan ya ce, "Kawai saboda ba ka da hankali kuma ba ka da haƙuri ka yi mata haka, baza ka iya ƙyale ta for two weeks ba, zuwa lokacin duk wani stress da tension ya yi disappearing ba?." Jazy ya wani kalle sa ya ce, "Sati biyu fa, taɓ ni gani nake ma na yi ganganci da na bari ta kwana biyun." Ray kawai ya zuba masa ido yana kallonsa, sai kuma ya girgiza kai ya ce, "za ka jawo na ɗauke ta daga nan, kuma in na tafi da ita wallahi baza ta dawo ba sai bayan sati huɗu." Jazy ya yi dariya sosai ya ce, "ayi haƙuri Babban Yaya, incidence aka samu. Amma nima wallahi na wahala, bayana ciwo yake yi min." Rehaan ya yi tsaki bai ce komai ba dan ji yake kamar ya shaƙe sa wallahi. Jazy ya yi dariya Ray ya c, "tana kwance cikin ciwo saboda kai kai kuma kana dariya?....." Ya girgiza kai yana kallon Jazy ya ce, "Na yi gangancin ba ka auren Riyya, ba ka dace da zama mijinta ba Jafaar!." Jazy ya ce, "ka san dai ina son matata, kuma ba ka fi ni sonta ba, na fika jin ciwon yanayin da ta shiga ta dalilina. Amma ba wani abun bane ba, normal ne ga ko wacce mace da hakan take farawa, itama a hankali zata saba."  Jazy sai ya ga Ray ya fusata ya koma ɗakin yana ƙoƙarin ɗaukar Riyya, Jazy ya san tsaf zai Rehaan zai ɗauke masa mata, zai iya sakata a mota ya tafi da ita kuma bazai dawo masa da ita cikin sauƙi ba sai ya ba shi wahala. Jazy ya shiga da sauri ya hana shi ya ce, "yi haƙuri Rehaan, Allah bazan sake yi mata komai yanzu ba, kar ka tafi da ita ka taimaka min." "Na lura kashe ta ka ke so ka yi ko?." "I'm sorry big bruh, zan gyara. Zo mu ne falo kar mu tashe ta." Sai a lokacin Jazy ya lura da Islaha da take zaune a falon amma kamar bata ciki, waje ɗaya take kallo ba dan ta yin wani abun ba sai dan kunya da maganarsu take bata sosai, musamman Rehaan da yake haƙiƙicewa yana faɗa akan abinda aka yiwa Riyya. Har mamakin Ray take yi jin yadda yake magana cikin faɗa, bata ɗauka yana magana cikin faɗa haka ba kwata-kwata, sai ga shi yana yiwa mijin ƙanwarsa faɗa harda ƙoƙarin ɗauke ta. Nana Haleema. RDB3P27 Nana Halaeema. Jazy sai ya ɗan ji nauyin Islaha, ya shafa kansa dan bai san yaushe take a wajan ba, yana da tabbacin ta ji komai. Ya daure ya kawar da kunya ya ce, "Miss tare ku ke ashe?." Daƙyar Islaha ta ɗaga kanta tana kallonsa sai ta ɗauke kai haka kawai ta ji tana jin kunyarsa. Jazy ya juya yana kallon Ray yana nuna masa Islaha da ido. Shi kuma da ba a sirri da shi akan Islaha sai ya ce, "Ban gayyace ta ba, itace ta zo ta shiga motar taho nan. Bani na ce tazo ba, ka daina yi min wannan kallon." Jazy ya girgiza masa kai alamun meye haka, shi kuma ya yi tsaki ya zana a kan kujera yana tunanin Riyya. Islaha bata tanka masa ba, dan kunyar kalamansu take ji sosai, har Rehaan ɗin kunya yake bata balle kuma Jazy. Ray ya kalli Jazu ya ce, "dan ma ka raina ni, ka rasa wanda za ka kira a wannan yanayin sai ni?. Ka bar Mamy da ta ke O&G, ka bar Janan, bayan dukkan su healths workers ne." "Mtsww! Kai fa kana da ƙarancin hankali Ray, an faɗa maka kowa irin ka ne mara kunya? Kawai sai na yiwa Mamy waya na ce ta zo ga abinda ya faru? Ko sai na kira Janan na ce ta zo?." Bai bashi amsa ba ya yi masa banza, sai kuma ya tashi ya koma wajan Riyya ya taɓa jikinta ya ji zazsaɓii ya sauka har ta fara gumi. Ya kunna mata ac ya fito daga ɗakin bai ce komai ba kawai ya sauka Jazy ya bi bayansa. Islaha ta bi bayansu da kallo ta yi tsaki ta ce, "Ko kunya ba ya ji, shi lallai ga mai ƙanwa." Sai itama ta miƙe ta biyo bayansu, ta tarar da Rehaan har ya shiga mota yana sake yiwa Jazy warning akan Riyya. Islaha ta ƙarasa ta shiga motar ta zauna, tana ji yana sake yi masa warning ta waiwayo tana kallonsa cikin mamaki da harara, maimakon su haɗa ido da Rehaan sai suka haɗa ido da Jazy da yake tsaye suna magana ta window. Jazy ya ce, "Ka ga matar ka ma tana kallon ka, nasan tana tana mamakin wannan wanne irin Yaya ne." Ya waiwayo suka haɗa ido da Islaha, ta ɗauke kai shima bai kuma ta ba, ya ɗaga glass ɗin Shams ya shiga motar su tafi. Babu mai magana a cikinsu kowa harkar gabansa yake yi, tafiyar bata yi nisa ba ta ji ya kira Jazy yana tambayarsa ya jikinta. Islaha ta kalle shi ta harare shi bata ce komai ba. Bacci take ji sosai, dan lokaci har biyu na dare ta wuce, ta kwantar da kanta a jikin ƙofar motar ta lumshe ido ya bacci yana ɗaukarta a hankali. Hanyar da suka bi suka tarar an rufe, Shams ya tsaya a wajan, jin an tsaya ya saka Ray ya ce, "lafiya?." Shams ya ce, "Sir an kulle hanyar ne." Ray ya ce, "daman dare ya yi zasu iya kullewa, ka canja wata mana." "Sir hanyar bata da kyau." "Mu je kawai." Babu yadda zai yi haka suka koma da baya zuwa wata hanyar. Suna cikin tafiya a hankali kamar yadda Rehaan ba ya son gudu na wuce ƙa’ida, kawai sai suka ga saniya akan titin, Shams ya yi ƙoƙarin kauce mata amma ya kasa motar ta ƙwace suna tangal-tangal. A lokacin Islaha ta farka jin yadda motar take juyawa akan titi dan har ta matso daf da Ray bata ma sani ba. Ƙaton dutse motar ta daka da ƙarfi, Islaha ta yi gaba kamar zata faɗi, kanta ya daki kujera ta dawo da baya, ta riƙe hannun Ray gam ba tare da ta sani ba cikin firgici. Ray cikin firgici da tsoro ya ce, "Shams ya faru me haka?." Shams zai yi magana aka zagaye motar su gaba da baya. Ganin haka sai Shams ya ce, "Sir attack ne." Ray ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!." Shams ya ɗauko bindingar da take jikinsa yana kallonsu daga waje, dan yana cikin motar bai fita ba yana irga adadinsu dan ya san yadda zai yi dasu. Su kuma tayar motar suka harba, yadda baza su iya guduwa ba. Ta inda Islaha take zaune aka aiko da harbi guda ɗaya, sai bullet ɗin suka gani ya daki glass ɗin ya koma bai fasa glass ɗin ba saboda motar bullet prove ce. Rehaan bai san ya jawo Islaha ta dawo jikinsa gabaɗaya ba, dan da silent gun suke amfani, ba ka jin ƙara sai dai ka ga bullet. Shams yana niyar fita Rehaan ya ce, "kar ka fita, ka kira police kawai." Harbin motar suke yi yi ta ko ina, Islaha ta dafe kunnenta duk da ba sosai ake jin sautin ba, tana jikinsa a kwance ta cusa kanta a ƙirjinsa jikinta yana rawa saboda tashin hankali. Shima yana riƙe da ita, ya yi wrapping bayanta sun cure waje ɗaya saboda kar harbin ya same su. Mutanen da suke harbin suka nufo motar kai tsaye, suka saka ƙaton ƙarfe suka da ki glass ɗin ɓangaren da su Rehaan suke amma bai fashe ba, aka sake duka da ƙarfi ya tsage amma bai fashe ba. Shams cikin tashin hankali ya ce, "Sir ka bani dama na fita, zan iya maganinsu." "No, kar ka fita" ya sake faɗa har lokacin yana riƙe da Islaha sun koma tsakiya sun bar jikin window. Lokaci ɗaya hayaƙi ya cika motar gabaɗaya, numfashin Islaha ya fara hawa da sauka, ga tsoro ga hayaƙin da take ji yana mamaye ta lokaci ɗaya, ga zafin da motar ta yi ya mamaye ko ina. Su kuma waɗanda suka kawo harin suna su yi amfani da damar su su kashe Rehaah, kar su rasa shi a wannan lokacin, hakan ya saka suka fara zubawa motar fetur za su ƙona su. Hankalin Shams ya tashi ya ce, "Sir motar nan zata iya tashi ko yaushe, ta yi zafi sosai, kuma suna zuba mata fetur ya kamata mu fita!" Ya faɗa da ƙarfi dan Ray ɗin ya ji me ya ce. A lokacin suka sakawa motar wuta, ɓangare ɗaya ya fara ci su kuma suka gudu. Da hanzari Shams ya buɗe motar ya fito, ya buɗe buɗewa Rehaan ya jawo su da ƙarfi suka faɗo ƙasa shi da Islaha. Rehaan ya juya da ita a jikinsa, ta dawo sama ya koma ƙasa, ta dawo ƙasa ya koma sama har suka matsa daga kusa da motar suka koma gefe saboda wutar da take cin motar sosai. Shams ya zauna kusa daahi ya ce, "sir are you okay?." Rehaan iya cewa komai ba kallon motar yake yi yadda take ci da wuta, zuciyarsa tana bugawa yana ayyana da yanzu suna ciki suna ƙonewa. Sai a lokacin motar police ta zo wajen, da kuma motar da aka kawo wacce Rehaan shiga. Shams ya nunawa police inda masu laifin su ka yi, suka rufa musu baya dan binciko su waye. Rehaan ya ɗago Islaha da take kwance a ƙirjinsa ko motsi bai ji ta yi, yana ɗago kanta ya ga ta yi baya zata faɗi alamun bata nunfashi. Sai a lokacin tuna kamar tana da asthma, ya kwantar da ita a gefen titi, ya miƙe tsaye sannan ya ɗauke ta ya saka a bayan motar shima ya shiga bayan. Shams ya shiga suka tafi motar ƴan sanda tana biye dasu. Rehaan jijjiga Islaha yake yi gently amma bata motsa ba da alama numfashinta ya tsaya, ya cire mata hijjab ɗin jikinta, gashinta ya baje akan kujerar. Ganin da gaske bata numfashi sai kawai ya tsaya yana kallon fuskar ta yana tunanin ta yadda zai taimaka mata. Mouth to mouth recuscitation ne kawai ya dace da ita a wannan lokacin, tunda numfashinta ya tsaya, tana buƙatar a bata numfashi dan ya taimakawa na ta ya dawo. Tunanin yadda zai saka bakinsa a cikin nata yake yi, hakan ya saka shi ya zuba mata ido yana kallonta bai yi komai ba. Sai kuma ya tuna shi likita ne, taimako aikinsa ne, zai taimaka mata a matsayin mara lafiya ba C wife ba. Ba shi da zaɓi haka ya matsar da fuskarsa kusa da ta ta, ya ɗora bakinsa a kan nata, ya rufe hancinta da hannunsa, ya buɗe bakinta da lips ɗinsa ya bata numfashi mai ƙarfi. Ganin bata motsa ba ya saka shi cigaba da bata numfashi saboda taimakon gagagwa ake so ayi mata kafin su je asibiti. Bai farga ba ya tsinci kansa yana kissing lips a maimaikon recuscitation, ya riƙe tongue ɗinta da bakinsa, yana bata hot and soft kiss ba tare da ya san yana yi ba. Kamar an tuna masa da abinda yake yi, sai ya zabura ya janye bakinsa, yana tunanin ya aka yi ya yi wannan gangancin? Da farko numfashi ya fara bata kamar yadda ya yi niya, bai san me ya ɗauki hankalinsa ya zarce da kissing ɗinta ba. A daidai lokacin suka iso asibiti, aka shiga da Islaha a guje dan a bata taimakon da ya kamata. Rehaan yana kallon yadda aka shiga da ita ciki, ya jingina da kujera ya rufe ido, sai kuma ya kai hannunsa ya shafa lips ɗinsa har lokacin yana jin ɗumin bakinta a cikin nasa, kamar bai raba kansa da ita ba haka yake ji. Karo na farko da ya taɓa romantic kiss da wata mace a duniya kenan, duk da itama ba da niya ya yi hakan ba, amma dai ya yi. Cikin lokaci kaɗan Islaha ta farfaɗo, numfashinta ya dawo daidai ta buɗe ido. Tana buɗe ido yana shigowa ɗakin, ta zabura tana toshe kunnenta tana curewa waje ɗaya alamun ta tuna da abinda ya faru. Rehaan ya dinga binta da kallo, dan rigar jikinta doguwa ce mai hannun vest, sai dai tana da tsayi ta saukar mata har ƙasa. Ga gashin kanta yana zube a kan gadon, jikinta yana rawa alamun tana jin tsoro sosai. Ganin yanayinta sai ya saka aka yi mata allurar bacci, in ba haka ba tsoron zai iya cutar da ita. Yana zaune a ɗakin Shams ya shigo tarre da police guda biyu. Ɗaya daga cikin police ɗin ya ce, "mun rasa su, amma wajan akwai bank, timda kuma bank ne dole akwai cctv, gobe zamu je dan a nemo mana video abun." Ray ya rufe idanu ba tare da ya buɗe ba ya ce, "a yi abinda ya kamata, bana so ko mutum ɗaya daga cikinsu ya tsira." Suka amsa sannan suka yi sallama suka tafi. Shams ya ce, "Sir! Mr Jafar ya kira ni, ya ce yana kira ka bai samu ba shine yake tambaya ta ko mun koma gida lafiya, ni kuma faɗa masa abinda ya faru." Rehaan bai ce komai ba ya dafe kai da hannunsa dan kansa ciwo yake yi sosai. Ana haka sai ga Jazy ya buɗe ƙofar ya shigo ɗakin a gigice, ya ƙaraso kusa da Ray ya ce, "Ray lafiya ka ke, ko akwai binda ya same ka?." Ya ɗago yana kallonsa ya ce, "Am okay. Da wa ka bar Riyya ka fito a daren nan?." "Suna tare da housemaid." "Housemaid! Da su zaka bar Riyya ɗin Jazy? In wani abun ya same ta fa?." "Babu abinda zai same ta, yanzu zan koma. Hankalina ya tashi da na ji abinda ya faru, shiyasa na fito tunda bacci take yi." Jazy ya kalli Islaha da take kwance yana bacci ya ce, "me ya same ta?." Rehaan ya ɗaga ido kalle ta, haka kawai ya ji ransa ya ɓaci ganin yanayin da take ciki, dan surar jikinta a bayyane take ta cikin rigar jikinta, musamman daga ƙirjinta da rigar ta ɗame ta bi jikinta ta kwanta, ko ina ya fito rass ta vest ɗin. Ya cize bakinsa ya ɗauke kansa daga kallonta sannan ya ce, "ta samu attack ne, but she is fine." Jazy ya ce, "Thank god....." Sai kuma ya kalli Shams ya ce, "Shams an kama su?." "Ba a gansu ba wallahi." "Oh god! Su waye waɗananan haka?." "Bamu sani ba." Ray ya kalle saya ce, "ka koma wajan Riyya, nima zan tafi gida, i can't stay here" ya faɗa yana miƙewa tsaye cikin gajiya. Yana daga tsaye ya sake kallon Islaha da idanunta suke a rufe, sai ya ɗan matsa kusa da ita kamar mai tunani, yadda jikinta ya bayyana a rigar baccin jikinta gabaɗaya hakan bai yi masa daɗi ba, hakan ya saka shi ya miƙa hannu ya ja blanket yana rufe mata jikinta. Jazy da yake kallonsa bai ce komai akan hakan ba ya ce, "In ka tafi Ita kuma fa?." Ya waiwayo ya kalle shi ya ce, "akwai security zasu kula da ita ai." "Kawai ku tafi da ita, tunda attack ne, in ta farka zata dawo normal." Ya ɗan yi shiru alamun tunani yake yi, Jazy ya katse sa ya ce, "Shams sai ya ɗauke ta ya kaita har ɗaki ta yi baccin a gida, hakan ya fi akan zamanta a nan." Rehaan ya lumshe ido ya buɗe yana kallonta har lokacin bacci take yi, ya kalli Jazy ya ce, "wannan dalilin ne ya saka bana son yin aure, bana son saka rayuwar kowa a cikin risk. An yi min ba tare da ina so ba ma ga abinda ya faru, even C wife ɗin ma bata tsira ba." Jazy ya ce, "ko su waye an fi ƙarfinsu, shiyasa Allah bai ba su nasara ba. Amma kar ka barta ita kaɗai a nan, ku koma gida gabaɗaya ya fi kwanciyar hankali." Ganin bai ce komai ba sai Jazy ya fita ya kira nurses ya saka aka zo aka fara tura gadon da ta ke kai zuwa inda mota take, sai da suka tsaya sannan Jazy ya ce, "Shams sai ya ɗauke ta ya saka ta a cikin mota." Rehaan ya yi kamar bai ji ba ya yi masa banza, yana daga tsaye kamar bazai motsa ba, yana maimaita kalmar Shams ya ɗauke ta a ransa kamar mai wuridi yana kallon Jazy amma bai ce komai ba. Sai da ya ga dama sannan ya ƙarasa ya ɗauke ta da kansa ya saka ta a cikin motar. Jazy ya yi wani murmushi yana kallon sa amma bai ce komai ba. Rehaan ya kalli Jazy ya ce, "Kaima police za su raka ka gida." Jazy ya gyaɗa kai bai ce komai ba yana murmushi, dan ɗaukar Islahan nan da ya yi an burge shi, amma bazai faɗa masa a yanzu ba sai an kwana biyu. Islaha tana kwance a back seat, shi kuma ya shiga gaban motar suka tafi police suna binsu a baya...... Nana Haleema. RDB3P28 Nana Haleema. Har cikin gidan police suka raka shi har apartment ɗinsa. Rehaan ya sakko daga motar ya ƙarasa wajansu ya ce, "a bincike a gano waɗanda suke da hannu a attack ɗin nan, ko waye kar a bari su tsira." Police ɗaya ya ce, "In sha Allah za mu yi abinda ya kamata dan gano waɗanda suke da hannu a abinda ya faru, tunda akwai bank a kusa da inda abin ya faru abin ya zo da sauƙi." Rehaan ya ɗaga kai ya ce, "Ayi abinda ya kamata." "In sha Allah we will try our best." Rehaan ya ce, "thank you. Shams zai tura mu ku saƙo." Suka yi godiya sannan suka fita, shi kuma ya ƙarasa inda Shams yake a tsaye yana jiransa. Yana zuwa wajen ya kalli Shams ya ce, "you can go." Shams cikin girmamawa ya ce, "okay Sir. Amma ko na shiga da ita ciki?." Rehaan ya ɗago ido ya kalle shi, sai kuma ya ɗauke kansa bai ce komai ba. Shams ganin reaction ɗin Rehaan sai ya miƙa masa key ya ce, "Sorry Sir. A bar motar a nan ne?." Rehaan ya kalle sa ya ce, "babu wata motar a hannunka?." Ya ce, "babu." Rehaan ya ɗan furzar da iska cikin tunanin da ya addabe shi, dan gaskiya ba ya so ya ɗauko Islaha a gaban Shams, bai san meyasa ya ke jin haka ba, amma har cikin zuciyarsa yake jin ba ya so ya ɗauko ta a gaban Shams. Sai ya ɗan shafa kansa yana kallon motar, ya buɗe bayan motar yana kallon Islaha da take a kwance tana bacci. Haka kawai ya tsaya yana kallon ta, bazai ce ga dalilin tsayawa yana kallonta ba, shi dai ya san kawai ya tsaya yana kallonta ba tare da ya san me ya jawo kallon ba. Sai kuma ya ɗauke ido daga kanta, ya kalli Shams da yake tsaye yana jira ya fita da ita shi kuma ya hau motar ya tafi. Ya kalli agogon motar ya ga har ƙarfe uku na dare ta yi, ya sake waiwayowa yana kallon ta, kamar mai tsoron taɓata ya kai hannu ya tallafota ta ɗago daga kan kujerar, kanta ya yi baya gashinta ya sake zubewa a ƙasa, ya zubawa fuskarta ido yana kallon yadda bakin ta ya tsuke waje ɗaya, sai kuma ya ɗauke kai ya ɗago ƙafafunta ya ɗagota daga cikin motar ya riƙe laps ɗinta. Har zai fito da ita sai ya fasa, ya mayar da ita ya ajjiye, ya ɗauki hijjab ɗinta da ya cire mata, ya ɗora hijjab ɗin akan flat tummy ɗin, sannan ya ɗago ta ya fito da ita. Gashinta ya sauka sosai saboda tsahonsa da yadda kanta ya yi baya, sai tattare gashin ya riƙe a hannunsa, ya gyara kanta yadda ya kamata, ya ƙarasa wajen ƙofar ya saka thumb print na ƙofar ya shiga ya rufe. Shams ya bisa da kallon mamaki dan shi dai ya tabbatar wannan ƴar jarida Islaha ce da suka sace kwanaki, bai san me ya haɗata da shi har haka yake yi mata abu kamar matarsa. A bayyane ya ce, "to me islaha ta ke yi a gidan nan a kuma ɓangarensa? Kar dai maganar auren nan ta tabbata, kuma ita ya aura?." Sai kuma ya girgiza kai ya ce, "To kawai sai ya aure ta bayan kwanaki sace ta ya yi?." Shams ya riƙe baki ya ce, "uhum babu ruwana, amma dai na san daman ya yi aure, kawai bai faɗa min bane amma Mr Jafar ya faɗa min. Kai amma Islaha ƴar drama ce" ya faɗa yana dariya ya shiga mota ya bar gidan. A kan kujerar main falo ya ajjiye ta yana jan numfashi kamar wanda ya ɗauko giwa, bai yadda ya sake kallonta ba, dan gabaɗaya vest ɗin jikinta ta bayyanar da surar jikinta, ana ganin shatin komai na surarta a bayyane. Ya ɗauke kansa ya hau sama yana jin kansa yana sarawa saboda ciwon kai. Sai da ya yi wanka a daren, maimakon ya kwanta sai ya sha maganim ciwon kai ya tayar da sallah yana faɗawa Allah damuwarsa. Ya jima yana sallah, duk da baccin da yake fizgarsa bai dakata da yin sallar ba, yana ganin Jazy yana kirasa ya share bai ɗauka ba. Yana tsaka da addu'a ɗumin bakin Islaha ya dawo zuciyarsa da bakinsa, ya lumshe ido ya buɗe yana kallon wani wajan daban. Tunanin yadda bakinta ya kasance a cikin nasa ya so ya rinjayi addu'ar da ya ke yi, sai yi yi saurin kawar da tunanin, ya sake lumshe ido yana addu'a. Daƙyar ya iya zama har aka yi sallar asuba, a prayer room ɗin bacci ya ɗauke sa ba tare da ya sani ba. Gari yana wayewa labaran ƙarfe shida na safe da abinda aka fara kenan, hotunan motar sun baza duniya, da yadda aka yiwa motar kaca-kaca da bullet gashi kuma ta ƙone. Duk mutanen gidan a waya suka ga abinda yake faruwa, hankalin Mamy ya tashi matuƙa, tun ƙarfe bakwai na safe ta kasa komawa bacci, ta shiga wajan Rehaan ya fi sau babu adadi amma sai ta tarar bacci suke yi. Abba ma sai da ya kira Shams ya zo har gida, sannan Abba ya ce, "Me ya same su? Ina ku ka je a daren har haka ya faru?." Shams ya ce, "mun je gidan Sir Jafar ne." Abba ya ce, "shi da wa?." Shams ya ce, "shi da madam, a hanyar mu ta dawowa abin ya riske mu." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amma babu abinda ya samu Rehaan ko, meyasa baka sanar damu tun a dare ba?" Mamy ta faɗa hankali a tashe tana kallonsa. Ya ce, "shi ya ce kar na sanar da kowa, da safe za ku ji labari. Babu abinda ya same shi, ita ce dai ta ɗan samu ɗaukewar numfashi shine muka je asibiti." Abba ya ce, "Amma an kama su ko?." "Har yanzu ba a same su ba, ana kan aikin hakan." Mamy kamar zata yi kuka ta ce, "Me ya fitar da shi a daren nan? Me ya je yi gidan Jafar?." Shams ya ce, "Ban sani ba Mamy, amma da ya shiga ya ɗan jima kafin ya fito." Mamy ta fara kuka tana cewa, "Rehaan ba ya jin magana, na hana shi fita babu security amma ya ƙi ji. Tsakani da Allah ya fita da daddare a irin nan lokacin ba dole a yi ƙoƙarin kashe shi ba?." Shams ya ce, "nima na ce mu tafi da su ya ce no need." Abba ya ce, "Shikenan Shams. Amma daga yau in zai yi irin wannan fitar duk dare ka sanar dani ka ji?." Cikin girmamawa ya amsa sannan ya ce, "ƴan jarida suna son magana dani akan abinda ya faru, zan iya magana dasu?." Abba ya ce, "ka yi magana dasu ɗin, ka tabbatarwa da mutane yana cikin ƙoshin lafiya." Shams ya amsa sannan ya fita. Mamy da take ta kuka Abba ya ce, "Ki daina wanann kukan, ki yi haƙuri ya farka mu ji abinda ya faru." Mamy ta goge idanunta ta ce, "Me ya fitar da shi da dadare kuma shi kaɗai? Me zai je ya yi a gidan Jafar a cikin daren?. Yanzu da sun kashe min shi ba?." Abba ya murmusa ya ce, "basu kashe shi ba, kuma baza su kashe shi ba sai lokacinsa ya yi. Ki yi haƙuri." A lokacin Abba ya dinga amsa kiran wayar jajen abinda ya faru, labari babu inda bai zaga a duniya ba, waɗanda basa Nigeria abokan aikinsa duk sun gani ana ta nemansa a waya an kasa samu. _Rehaan yola yana cikin ƙoshin lafiya, bayan tattaunawa da muka yi da babban na hannun damansa Shams, ya tabbatar mana da yana cikin ƙoshin lafiya babu abinda ya same su. Sai dai har yanzu ba a yi nasarar cafke waɗanda suka kai masa harin ba, amma ƙoƙarin hakan._ Abinda yake ta yaɗuwa kenan bayan hira da Shams, hankalin abokan cinikinsa ya ɗan kwanta, dan kowa ya san shi da Shams, sai dai har lokacin an kasa samun Rehaan a waya. Islaha sai ƙarfe tara na safe ta buɗe ido, ta miƙe zaune a hankali tana tuna abubuwan da suka faru. Gabanta ya faɗi ta ware ido ta bi falon da kallo ta tabbatar a cikinsa take, ta kalli kanta ta ganta daga ita dai vest kanta ko ɗankwali babu. Ita dai ta san daga lokacin da aka fara harbin motar bata sake sanin abinda ya faru ba. Ta kalli agogo ta ga safiya tayi sosai, ta miƙe dan bata yi sallah ba ta hau saama, ta shiga ɗaki ta yi alwala ta yi sallah ta zauna tana tunanin duk abinda ya faru. Tana iya tuna lokacin da ya jawota ta yi ƙasa saboda harbi, ya riƙeta ita kuma ta kwantar da kanta a ƙirjinsa cikin tsoro. Daga lokacin bata san abinda ya faru ba, ta dai san a mota suke, kuma ta san da hijjab a jikinta, amma yanzu ta ganta a falo kuma babu hijjab. Ta sake kallon kanta dan ko bra bata saka ba, iya vest ɗin ce a jikinta sai hijjab, tunda ta yi shirin bacci ta ga zai fita, kuma bata saba kwanciya da bra ba. "Haka kawai sai ya cire min hijjab?" Ta faɗa cikin jin haushi, sai kuma ta yi tsaki ta miƙe ta shiga wanka har lokacin ƙirjinta bai daina bugawa ba saboda tsoron harbe-harben da aka dinga. Sai da ta fito ta shirya sannan ta kula da wayarta da take ajjiye wacce ta bari bata fita da ita ba. Ta ɗauki wayar ta ga tarin missed call da yawa, Saheer, Safeera, Saleem, Chairman da Baffa. Baffa ta fara kira, aka yi rashin sa'a bai ɗauka ba sai ta kira Saheer. Yana ɗauka ya ce, "Islaha kina lafiya, dake a cikin motar da aka kai harin?. " Islaha ta yi ajiyar zuciya, a lokacin ta tabbatar da maganar ta gama baza duniya. A sanyaye ta ce, "Eh dani a ciki, amma ina lafiya." Sai kuma ta ji muryarsa ta canja ba kamar yadda ya yi magana a farko cikin ruɗewa ba, ya ce, "tare ku ka fita kenan?." Islaha ta ce, "ina jin tsoro gidan ne, da zai fita shine kawai na bi shi, ashe rabon wannan abun ne." "Okay, tunda lafiya ki ke haka mu ke fata. Daman shi ance yana lafiya." Bata amsa ba ta yi shiru dan ita bata san me zata ce ba. Saheer ya ce, "za ki iya fitowa yau?." Islaha ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "zan iya, amma sai zuwa anjima." Bai ce komai ba ya yanke wayar ta bi wayar da kallo dan ta san kishi yake yi akan sun fita tare, ta yi shiru dan ita bata san me zata ce masa akan hakan ba, ta yi shiru tana tunanin abinda ya kamata. Chairman ta kira yana ɗauka ya ce, "Islaha lafiya yau ba ki shigo ba? Ga labarai masu kyau da ya kamata ace ke ki ka hau kai amma ban gan ki ba." Ba ta bashi amsar farko ba ta ce, "Ina kawana." "Lafiya lau." "na ɗan samu attack ne jiya, ban farka ba sai yanzu." "Ayya, Allah ya ƙara lafiya." Ta amsa da amin sannan suka yi sallama. Zata kira Safeera kenan sai ga kiranta ya shigo, itama tambatar farko akan harin ta bata labarin duk abinda ya faru. Safeera ta ce, "Allah ya yi da kwanan ku a gaba. Ana ta yaɗawa an kai masa hari, ashe har ke aka kai wa harin. Chairman yana ta neman ki kamar ke kaɗai ce presenter a gidan, sai da ya gaji sannan Saleem ya hau. Bai san tare aka kusa kashe ku ba." "Yanzu muka gama waya dashi." "Allah ya kiyaye gaba. In na tashi daga aiki zan zo, sai dai bana so na zo a hanani shigowa." "Ki zo kawai, baza a hana ki ba." Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar. Rehaan bai farka ba sai bayan sallar azahar, ya miƙe duk jikinsa yana yi masa ciwo saboda kwanciyar kan carpet, ya fito daga prayer room ɗin ya zauna a gefen gado yana shafa kansa. Wayarsa yake nema sai kuma ya tuna ta faɗi a motar kuma yana da tabbacin ta ƙone. Ya sauke numfashi rashin mafita, ya miƙe ya shiga wanka. Sai da ya shirya tsaf sannan ya fito, ya yi sallar azahar ya ɗan zauna yana tuna abubuwan da suka faru. Sai kuma ya miƙe ya fito falon a lokacin Mamy da Abba suka shigo. Mamy tana ganinsa ta nufe sa ta riƙe hannunsa ta ce, "Kana lafiya?." Ya ɗaga mata kai ya ce, "lafiya lau Mamy." Suka zauna a tare Abba ya ce, "Tun ɗazu nake jiran tashin ka amma shiru, Ina fatan babu abinda ya same ka?." Kamar ba ya son magana ya ɗaga kai ya ce, "Babu komai Abba, bacci ne kawai." "Ya aka yi hakan ya faru?." "Ban sani ba Abba, kawai mun ga an zagaye mu an fara harbi." "Me ya fitar da kai a wannan lokacin, bayan ka san yanayin da ake ciki?." Ya sauke nunfashi ya ce, "na je wajan Riyya ne." Abba ya ce, "kawai a cikin daren zuciyarka ta faɗa maka ka je wajanta? Ka rasa lokacin zuwa wajanta sai da daddare?." Ya yi shiru bai ce komai ba, dan bazai iya faɗawa Abba dalilin zuwan ba, yana jin kunya sosai. Abba ya ce, "dan ganganci, ƙarfe ɗaya na dare ka saka a ɗauko mota ka fita? Kuma dan shirme sai ka fita kai kaɗai babu masu kula da kai?. Yanzu in ba dan Allah ya saka motar bullet prove bace da ya kenan?." Kansa yana ƙasa bai ce komai ba yana jin faɗan da Abba yake yi. Abba ya ce, "Ka ga yadda motar ta ƙone?." Ya girgiza kai ya ce, "ban gani ba." "Ga labari nan ya cika duniya, har yanzu mutane basu da tabbacin kana lafiya." "wayata ta ƙone a motar, sai na nutsu." Abba ya ɗuako wayarsa ya nuna masa yadda motar ta yi, Rehaan ya dinga kallon motar kafin Abba ya ce, "kana ganin yadda aka ƙona motar, da da kai a ciki haka zasu ƙona ka saboda ganganci irin naka." Shi dai kallon motar yake yi, dan ta ƙone kam sosai. Abba ya ce, "Kar ka sake yin wannan gangancin, wannan Allah ya kiyaye, kar na sake ji ka fita da daddare, in fitar ta zama dole ka tafi da jami'an tsaro, ka ji?." Ray ya ɗaga kai cikin gamsuwa ya ce, "in sha Allah." "Na yi magana da su, ana ta binciken waɗanda suka yi wannan aikin, in Allah ya yarda bazasu sha ba. An ba ka guda a abin sha ka sha kuma sun tsira, wannan baza su tsira ba in Allah ya yarda. " Rehaan ya ɗaga kai bai ce komai ba, dan har lokacin ba ya jin daɗi. Abba ya ce, "ka ci abinci ka zo ku gaisa da mutanen gidan, kowa hankalinsa ya tashi." Ray ya ce, "In sha Allah." Abba ya ce, "ina matar ta ka, ance tare ku ka fita, ina fatan itama lafiya take?." Rehaan ya ce, "lafiya lau." "ta warware? An ce ta samu attack." "Eh, ta samu lafiya.” Abba ya ce, "Ma sha Allah, ina zuwa" ya faɗa yana tashi ya sauka downstairs Nana Haleema. RDB3P29 Nana Haleema. Mamy bata ce masa komai ba ta miƙe ta sauka, sai gata ta dawo da abinci a tray ta ajjiye a gabansa alamun ya ci. Daman yana jin yunwa, hakan ya saka ba ƙi ci ba ya sha tea sannan ya ci abincin kafin ya ajjiye alamun ya ƙoshi. Mamy ta kalle sa ta ce, "Me ya kai ka gidan Riyya a daren jiya?." Rehaan ya ɗago suka haɗa ido, sai ya sauke ido ƙasa bai ce komai ba. Mamy ta ce, "kai nake jira." Ya langwaɓar da kai ya ce, "Mamy don Allah a bar maganar nan." Mamy ta ce, "Allah ba za a barta ba, ka faɗa min meye fitar da kai zuwa gidan Jafar da daddare?." "Mamy kawai na je na ganta ne." "ban yarda ba, faɗa min dalilin." Ya kuma kallon ta ya ce, "Mamy please." Mamy ta haɗe rai ta ce, "Rehaan!." Sai ya lumshe ido ya buɗe, yana tunanin ta ya zai faɗawa Mamy wannan abin kunyar? Allah ya sani yana jin kunyar faɗa mata abinda ya faru, amma kuma babu yadda zai yi dole ya faɗa mata tunda bazai iya yi mata ƙarya ba. Ya rufe ido sannan ya ce, "Mamy ni ban san me zan ce miki ba." "Baza ka faɗa min ba kenan?." "Zan faɗa miki, kawai dai i'm shy." Sai ta yi shiru bata ce komai ba, ganin ta share shi sai ya daure ya ce, "Mamy they had thier.....first....night...." Ya ƙarass faɗa a rarrabe har yana rufe idonsa ya buɗe saboda kunya. Ya cigaba da magana ya ce, "Shine na je for treatment." Mamy bata nuna wani abu a fuskar ta ba ta ce, "meyasa ba a kai ka asibiti ba sai kai da kanka zaka je a daren?." Cikin shagwaɓa ya ce, "Don Allah Mamy a bar maganar nan tunda na faɗa miki." Mamy ta yi murmushi tana shafa kansa sannan ta ce, "When will you have your first night with your wife?." Rehaan ya runtse ido yana jin kunyar kalamanta ya ce, "Mamy!." "Ba wani Mamy, na ga kun fara shiri har fita ku ke yi tare." Rehaan ya ɗora hannunsa akan goshinsa ya ce, "Mamy please!." Ta sake yin murmushi tana cigaba da shafa kansa ta ce, "daman kana jin kunyata, i through ba ka jin kunya Rehaan." Shi dai bai ce komai ba sai murmushi da yake yi. Ta riƙe kunnensa ta ce, "Kar na sake ji ka fita da daddare kai kaɗai, ka ji?." Ya ɗaga kai ya ce, "In sha Allah." "How was Islaha?." Ya ce, "ban sani ba, tashina kenan kuka shigo." Mamy ta ce, "You didn't go check on her?." Ya ɗaga kai ya ce, "Maybe bacci take yi." Mamy ta miƙe tsaye ta ce, "in Jafar ya zo ka turo min shi." Rehaan da sauri ya ɗaga kai ya kalle ta sai ta haɗe rai tana kallonsa ta ce, "ba ka ji ba?." Rehaan ya ɗaga kai bai ce komai ba Mamy ta sauka. Mamy bata jima da sauka ba Jafar ya shigo da sallana ya ƙaraso ya ce, "Ya ka ke?." Ya gyara zama sannan ya ce, "i'm okay, ya Riyya?." Bai ce komai ba ya zauna sai ya kira Riyya video call ya ba shi. Rehaan ya karɓa yana kallonta ganin fuskar ta har lokacin bata dawo daidai ba, amma daga gani ka san ta ji sauƙi. Ya ce, "Riyya." Riyya ta ce, "Ray ina fatan kana lafiya, ina ta kiran ka bana samu." "Wayar ta ƙone a mota Riyya, amma ina lafiya. Kin ji sauƙi?." Sai ya bata kunya dan sai a lokacin ta ke jin kunyarsa sosai, ta sauke idanunta ƙasa ta ce, "i'm feeling well, but...." Sai ta yi shiru bata ce komai ba. Ray ya ce, "But what?." "I'm dizzy." "Kin ci abinci?." "Na ci." "Ki sha pcm ki kwanta ki sake yin bacci, za ki daina ji, sannan ki sha ruwa, kin ji?." Ta ɗaga masa kai sannan ta ce, "byee." Daga haka ta kashe wayar. Jazy ya ce, "Ya jikin Islaha, ina tunanin ta samu lafiya?." Rehaan ya ce, "ban sani ba." Jazy ya kalle sa ya ce, "ya kamata ace ka sani." Bai ce komai ba ya yi shiru. Jazy ya ce, "ya aka yi aka samu labarin ka fita daga gidan nan?." Ya kalle sa ya ce, "ban sani ba, tunda aka bani pioson a cikin gidan nan, sanin na fita bazai gagara a sani ba." Jazy ya ce, "yana da kyau a bincika sosai, dan ni a jikina yana bani akwai munafuki a gidan nan." Ray ya ce, "azo ayi min sim card swap, sannan ina buƙatar sabuwar waya ka saka a kawo min. Sim card ɗina na Uk ban san ya zan yi ba, dole sai na je can." Jazy ya ce, "Okay zan saka a kawo in na fita." Rehaan ya amsa da kansa bai ce komai ba. Sai kuma ya tuna da abinda Jazy ya yiwa Riyya, ya harare shi, shi kuma ya yi dariya dan ya san hararar ta meye. "Mamy tana nemanka." Ya wara ido ya ce, "wa take nema?." Rehaan bai amsa ba Jazy ya ce, "kar ka ce min ka faɗa mata abinda ya faru." Rehaan ya ce, "tana ta tambayar me ya fita dani, na ce a bar maganar amma ta ƙi, shine kawai na faɗa mata." Jazy ya ɗora hannunsa a kai ya ce, "Na shiga uku! Kenan ta sani?." Ya ɗaga masa gira alamun eh ta sani, sai kuma ya ce, "Ray ka kashe ni" ya faɗa yana dafe kansa bai ce komai ba. Ray ya murmusa ya ce, "Kasan kana jin kunyar ka aikata?." Bai ce masa komai ba ya yi shiru yana ji kamar Mamy ɗin tana wajan. Sautin buɗe ƙofa ya saka duka suka kalle ta, sai ta yi turus ganin suna kallonta ga shi bata saka mayafi ba. Fittrd gown ce a jikinta a cikin waɗanda ta ɗauko a wajen Safeera,ta yi mata kyau ta fitar da ko ina a jikinta. Kamar ta juya ta ɗauko mayafi sai kuma ya fasa ta ƙaraso ta ce, "Mr Jafar." Ya ce, "Miss ya jikin?." Ta ɗan girgiza kai ta ce, "Na ji sauƙi." "Allah ya ƙara lafiya." "Amin ya rabbi." Ta ɗan kalli Rehaan da yake kallonta, suna haɗa ido sai ya ɗauke idonsa ban san meyasa idanunsa suke kallonta a lokacin ba, musamman bakinta a da ya san ya ɗuminsu yake, da yadda laushi da tsantsinsu yake a cikin na sa. Islaha bata ce masa komai ba ta sauka ƙasa dan yunwa take ji. Jazy ya kalli Ray da ya wani basar kamar bai ganta ya ce, "a cikin kwana huɗu har yarinya ta fara fuskarta barazana ga rayuwarta, gaskiya zama matar mai kuɗi irinka ba abu ne mai sauƙi ba." Bai ce masa komai ba ya yi shiru Jazy ya ce, "meyasa ba ka ce mata ya jiki ba? A motar ka ta samu attack Rehaan, a kanka aka kusa kashe ta. Ya kamata ace ka ce mata ya jiki, ko babu komai zata ji daɗin ka kula da lafiyar ta." Ray ya yi masa banza bai amsa ba sai daga baya ya kalli Jazy ya ce, "da ta fito ka ji ta yi min magana ne?." "Ka damu da ta yi ma ka ne?." "Ta damu da na tambayi lafiyarta ne?" Ya ba shi amsa kai tsaye yana kallonsa. Jazy ya murmusa kawai kafin ya miƙe ya sauka ƙasa dan ya je wajen Mamy kamar yadda aka ce tana kiransa. A zaune ya same ta tana cin abinci a kan dining, bai ce mata komai ba ya fita. Bayan ta gama cin abinci sama ta dawo ta tarar da Rehaan a inda yake, ta tsaya tana kallonsa dan tana so ta yi masa warning akan kar ya sake tafiya da ita inda za a kashe ta. Ta gyara tsayuwa ta ce, "Da yake ka san za a kai maka attack, shiyasa ka bar ni na shiga motar ka, wato in aka kashe ni an kashe banza ko?." Rehaan a saman kansa ya ji maganar ta dan bai yi zaton tazo wajen ba. Ya ɗago ya kalle ta ga tana kallonsa, ya ɗauke kansa daga kallonta, dan suna haɗa ido sai ya tuna kissing ɗinta da ya yi a mota wanda ita bata san ya yi ba. Ya kasa mantawa da abinda ya yi, har lokacin yana ji kamar bakinta yana cikin nasa. Islaha bata san tunanin me yake yi ba ta ce, "Haka kawai sai ka saka na mutu da wannan ƙaddararren auren na ka a kaina? Dan ba ka ƙaunata sai ka bari na kai kaina inda za a kashe ni ko? Ni daman tunda na ga ka bari na shiga motarka ba tare da ka yi wani complain ba nasan da wata a ƙasa. Yanzu da na mutu fa?." Rehaan murmushi ya yi ba tare da ya waiwayo ba, dan haka kawai ta ba shi dariya jin wai da ta mutu fa, sai ka ce ba tare suke a cikin motar ba. Sai kuma ya ɗago ya kalle ta ya ce, "in kin mutu waye ya damu?." "Mutane da yawa zasu damu, su za su damu in na mutu. Su na ƙaunata, suna burin rayuwa na yi rayuwa a duniya kamar kowa, su ka yiwa asara kuma ka cuta. Kuma duk baƙin cikin ka sai na rayu a duniyar nan, sai na tsufa sannan zan mutu in sha Allah." Rehaan ya yi dogon numfashi bai ce mata komai ba, dan shi bai san abinda zai ce mata ba. Abinda yake tunani da ace ta san ya yi kissing ɗinta da babu zaman lafiya. Islaha ta ce, "Ni dai daga yau, in dai ka san za a zo kashe ka kar ka sake jawo ni ciki, ka je can su farfasa ƙwaƙwalarka da bullet bai damu Islaha ba, kai ba Yayana bane balle dan an kashe ka na damu. Duk ranar da za a sake kawo maka attack, ka bari na fita daga gidan nan salin alin, in ya so sai suzo su harbe ka." Rehaan da ya ga ji da surutunta sai ya miƙe tsaye yana kallonta, sai kuma ya shige ɗaki ya bar ta dan ba shi da lokacin biyewa shirmenta. Sai da ya shiga ɗakin sannan ya yi dariya, yana tuna abinda ta faɗa, wai ya bari ta fita daga gidan sai a kawo masa attack, kamar sai sun nemi izininsa kafin su zo. Jafar kuwa kai tsaye wajan Mamy ya nufa kamar yadda akace tana nemansa, haka kawai kunyar Mamy ta rufe sa daƙyar ya iya shiga apartment ɗin.A falo suka haɗu da Banisha ya yi murmushi ya bata hannu suka tafa sannan ya ce, "Ina Mamy?." "tana bedroom." "Okay Kiddo" ta faɗa yana nufar ɗakin Mamyn, yana jin kansa daban da kullum, yana jinsa kamar baƙo a wajen Mamyn. Jazy ya kawar da komai ya shiga da sallama ta amsa tana miƙewa zaune daga kwancen da take ta ce, "Yauwa Jafar, kamar ka san kai nake jira." Gabansa ya faɗi dan bai san maganar da Mamy zata yi masa ba, dan tsaf Mamy zata iya yi masa magana akan Riyya. Ya ƙarasa ya zauna ya ce, "Mamy good morning." "Morning my son, ya ka ke?." "Lafiya lau." Mamy ta ce, "daman tambayarka zan yi...." Sai kuma ta yi shiru, ta nutsu sosai sannan ta ce, "Wannan yarinyar da ta ke tare da Rehaan, a cikin kwana huɗun da ta yi a gidan nan abubuwa masu yawa suna ta faruwa. Daga kan Daada, Salman, yanzu kuma ga attack. Anya ba itace ta ba da masaniyar fitarsa a daren jiya ba?." Jazy ya yi ajiyar zuciya jin magana bata shafe shi ba, amma duk da haka ya kasa kallon Mamyn ya ce, "Meyasa ki ka ce haka Mamy?." Mamy ta ce, "Abin ne da mamaki, ya aka yi aka san zai fita har aka yi shiri mai kyau a kansa haka?." Jazy ya ce, "Mamy da ta san za a yi attacking ɗinsa da basa ta bi sa ba, da tana da hannu a abinda ya faru da baza ta yarda ta shiga motar ba. Tunda in ta shiga ta san itama mutuwa zata yi, kin ga kenan bata sani ba." Mamy cikin gamsuwa ta ce, "Haka ne kuma Jafar, amma ni na kasa yarda da hakan." Ya murmursa ya ce, "Mamy Islaha bata da matsala, na yi bincike a kanta in and out, babu abinda ban sani ba a kanta. Mamy yadda Rehaan baya son auren nan har ta fi sa ƙin auren, bata son Rehaan, haushinsa take ji sosai, ko haɗa ido dashi bata son yi. In kina neman wacce ta auri Rehaan ba dan kuɗinsa ba sai dan rashin mafita to itace." Mamy ta ce, "kamar ya kenan?." Jazy ya bawa Mamy labarin komai har auren wata biyar ɗin da suka yi sannan ya ce, "ta aure Rehaan saboda saurayinta, har yanzu akan hakan ta ke, in suka rabu zata je ta auri wanda take so. Ba dan tana son Rehaan ta aure shi ba, sai dan kuɗin fansar saurayinta da ya bata, shi kuma ya aure ta saboda ya yiwa Abba alƙawarin bazai ba shi matsala akan auren ba. Yadda ta ke ƙin auren nan nasu ko shi baya ƙinsa haka wallahi." Mamy cike da mamaki ta ce, "like seriously?." "Yess Mamy. Shiyasa na san baza a taɓa haɗa kai da ita a cutar da shi ba, dan bata shigo gidan nan saboda da shi ba sai dan saurayinta. Abu ɗaya na sani akan halinta, Islaha bata da kunya ko kaɗan." Mamy ta gyaɗa kai ta ce, "na san wannan, ni kaina na ga alamun bata da kunya, dan ta yiwa Ammi a gabana....." "Amma kuma bata rashin kunya akan rashin hujja Mamy, in ka ga ta yi rashin kunya an ɓata mata rai." Mamy ta ce, "Eh haka ne, dan ko lokacin da ta yiwa Ammi ɗin ma itace ta jawo. Amma ka san me Jafar? Sai nake jin na samu peace of mind a kanta, tunda har ba dan kuɗi ta aure sa ba, kuma kana da tabbacin baza a bata kuɗi dan ta cutar da shi ba." "Mamy ko Ikram ɗin da ki ke zancen za ki aura masa iya abinda zata yi akansa kenan." Mamy ta ce, "hakan ya yi min Jafar, sai nake ji na aminta da ita sosai, amma zan sake bata lokaci." Jazy ya ce, "wallahi Mamy baza ki samu wani abun mara kyau akan Islaha ba, bar ta dai da rashin kunya, amma baza ta taɓa cutar da Rehaan ba. Na yi bincike a kanta sosai, abinda bata san na sani ba ma na sani a kan rayuwarta." Mamy ta yi murmushi ta ce, "Na ji daɗin wannan labari." Ya yi murmushi ya ce, "ina fatan auren nan nasu ya ɗore." Mamy ta ce, "zan so hakan Jafar, burina ya ssmu macen da zata so shi tsakani da Allah, kuma na ga alama Islaha ce. Amma za mu gani Jafar, za ka iya tafiya, daman dalilin kiran kenan." Ya yi mata sallama ya miƙe Mamy bata tambaye sa Riyya ba, dan ta lura yana jin kunyarta sosai. Bayan ya fita ta yi shiru tana tunani, tabbas ya kamata ta gwada Islaha akan hakan....... Nana Haleema. RDB3P30 Nana Haleema. *Makkah.* Tunda suka shiga unguwar take kallon wajan cikin mamaki da al'jabi, yadda ta ga Aisha tana gaisawa da mutane da hausa baza ka ɗauka a ƙasar saudia ka ke ba. Uguwar gabaɗaya hausawa ne a wajen, ga unguwar a tsuke kamar irin layuka nan na cikin getho area. Kuma layin ba shi da space, gabaɗaya mutane sun cika wajen babu hanyar kirki sai ana tafiya ana bin layi. Ba dan ta san da gaske makkah suka shigo ba, da ta ce ƙarya Aisha ta yi mata wani wajen ta kai ta ba makkah ba. Kallon su take yi kawai ganin yadda suke sana'a hankalinsu a kwance. Wasu sun kwance kayan da suka ƙulle da babban abu kamar kayan gwanjo, wasu suna soya awara, wasu suna dama fura da nono, ga mai alala da mai tsire da duk wani abincin da bahaushe yake ci akwai shi a wajan. Labiba abin ya bata mamaki dan ba ta taɓa tunanin akwai irin wannan waje a cikin ƙasar saudia kuma a cikin garin makka ba. Ta dinga binsu da ido, maza da mata kowa yana harkokinsa. Kamar ƙiftwar ido sai ta ga kowa ya miƙe an kwasa a guje ana neman wajan ɓuya, Aisha ta damƙi hannunta suka yi cikin wani gida da gudu ana ture ta tana turewa. Gabaɗaya lokaci ɗaya wajen ya tsaye cak, kowa ya shiga wajan ɓuya saboda masu kame sun zo za su kama su. Duk kuɗin da suka tara a lokacin sun tafi sun bar shi saboda ceton kar a kama su a dawo dashi nigeria. Labiba bata san ya abin yake ba, shiyasa gabaɗaya take a ruɗe, yadda ta ga ana gudu maza da mata tsoro ya bata, ba dan Aisha ta riƙe hannunta ba da tsayawa zata yi. Sun fi su hamsin a gidan, kowa ya nemi waja ɓuya ya ɓoye. Labiba ta taɓa Aisha ta ce, "meye hakan?." Aisha ta ce, "shiii." Dole ta yi shiru tana kallon yadda kowa ya nutsu ko motsin kirki basa yi. Tana jiyo ihun wasu daga waje, suna ihu suna a taimaka musu amma babu wanda ya fita sai ma sake ɓuya da aka yi. Sun yi mintina asirin a haka, kafin su ji tashin mota alamun askar ɗin tafi, sai kuma lowa ya fito da gudu ya yi wajan sana'arsa ya ɗauke kuɗinsa. Labiba ta kalli Aisha ta ce, "Meye hakan yake nufi? Ban gane ba." Aisha ta ce, "jami'an tsaron ƙasar nan ne, sune suke kama mutane su mayar dasu nigeria, ba ki ji ihun wasu ba?." "Na ji." "An kama su, zuwa jibi za a kaisu ƙasar su." "Shine kowa yake guduwa haka?." "To ke za ki tsaya ne?." "Amma na ga kowa ya tashi ya bar kuɗinsa." "Ana ta ceto kai waye yake ta kuɗi? Tashi mu shiga ciki, ba mu shigo makka da ƙafar dama ba, muna zuwa mutanen sun fara kame." Wani tsukakken ɗaki suka shiga Labiba ta bi ɗakin da kallo ganin akwai wuta ga ac nan tana aiki, amma baza ka taɓa cewa a makka ka ke ba. Labiba ta ce, "kuma wai da gaske nan Makka ne? Ni na kasa yarda a makka muke, gani nake kamar a nigeria nake." Aisha ta kalle ta ta ce, "A makka ki ke." "Yaushe zan je na ga ka'aba?." "Ganin ka'aba ne ya kawo ki ko neman kuɗi? Ki kiyayi kan ki da shiga haram, wallahi in tsautsayi ya bi ta kanki sai dai ki buɗe ido ki gan ki a Yola. Ki tsaya ki nemi kuɗin ki, in yaso daga ba ya sai ayi abinda ya kamata." "Amma na zo har makka ace bazan ga ka'aba ba? Ni ko ban yi niyar umrah ba ina so na je na ga ka'aba." Aisha ta cire rigar jikinta ta ajjiye ta ce, "Hmmm! Na ki wasa ne, ba ki san ya makka take ba shiyasa" faɗa tana shiga wanka ta bar ta a wajan. Labiba ta nemi waje ta zauna har Aisha ta fito itama ta yi wanka ta canja kaya. Ba jimawa wata babbar mace ta shigo ta bi Labiba da kallo kafin ta kalli Aisha ta ce, "wannan fa?." Aisha ta ce, "itace wacce na faɗa miki zamu zo daga Jedda, sunanta Labiba, bafulatanar Adamawa." Matar ta kalle ta cikin hausarta da ta fara juyewa zuwa larabci ta ce, "sannun ki." Labiba ta ce, "Yauwa sannu." Ta kalli Aisha ta ce, "Amma kin san ɗakin nan a cike yake ko? A ina zata zauna?." "Sai ta zauna a nan ɗin, zuwa gobe za a nemi abinda zata fara siyarwa." Matar ta sake kallon Labiba ta ce, "Ya yi." Daga haka ta juya ta fita Aisha ma ta miƙe ta bi bayanta. Ita dai Labiba bata san bacci ya ɗauke ta a wajan ba saboda gajiyar zaman mota. Cikin bacci ya ji an matse ta, tana buɗe ido ta ga mutane harrr a kwance a ɗakin a matse. Ta ɗan gyara kwnaciyar ta, duk da akwai ac amma zafi take ji saboda yawan su. Ta saba da zama a ɗaki ɗaya a Jedda, ta saba da rayuwa a kan gado, ta juya inda take so a duk lokacin da ta ga dama. Ta ɗan gyara kwanciya tana tunanin sabuwar rayuwar da zata yi a waje irin wanann. Ko da asuba daƙyar ta samu wajen sallah da safe Aisha ta kawo mata kayan karyawa. Ta kalli Aisha ta ce, "a ina ki ka kwana jiya?." Aisha ta ce, "wani waje ne." Labiba ta ce, "Nima zan je, ɗakin nan babu daɗi anyi yawa a cikinsa." Aisha ta ce, "Inda naje na kwana kam mu biyu ne, ga ac da komai kamar dai a gidan Ubaid." Labiba ta ce, "gaskiya nima bin ki zan yi, bazan sake zama a nan ba, gabaɗaya ban yi bacci yadda ya kamata ba." Aisha bata ce mata komai ba, Labiba ta sha tea ɗin bayan an gama ta ce ta zo su shiga cikin gari. Sun ɗan jima suna yawo, Labiba ta tabbatar dai a makka take sannan suka dawo da siyayyar da suka yi. Da daddare Aisha ta shigo ɗakin ta ce, "za ki je inda na kwana ɗin?." Labiba ta miƙe tsaye ta ce, "zuwa kai, mu je." Aisha ta ce, "ba zuwan ba, kar mu je ki zo kina cemin ke kaza kaza." Labiba ta ce, "ni na isa, mu je don Allah, gabaɗaya ɗakin nan wari yake yi." Tare suka fito suka yi tafiya mai nisa, sannan suka shiga wani gida madaidaici mai kyau. Mata biyu suka tarar a zaune a falon, ɗaya tana ganin Aisha ta miƙa mata hannu ta ce, "My baby." Aisha ta miƙa mata hannu ta jawota ta zaunar da ita akan cinyarta. Aisha bata ɓata lokaci ba ta fara kissing matar cikin ƙwarewa da son nuna mata itama ta yi kewar ta. Labiba ta yi sak ta kasa motsawa ganin abinda yake faruwa, gabanta ya faɗi, tsoro ya mamaye mata zuciya dan bata yi zaton haka ba. Sun jima a haka suna kissing juna, sannan Aisha ta ɗago ta ce, "ga wata nan na kawo, tana son kwana a waje mai kyau." Ɗayar da take zaune babu abokin harka ta miƙawa Labiba hannu ta ce, "zo." Labiba ta kasa motsi sai kallonsu take yi Aisha ta ce, "Haba Labiba, kar ki ba da ni mana, ki ƙaraso ki zauna.." Labiba ta ƙarasa a hankali ta zauna a kusa da matar cikin fargaba da bugawar zuciya. Matar ta fara shafa hannun Labiba ta ce, "Ya sunank ki?." Labiba murya tana rawa ta ce, "Labiba." "daga ina ki ke?." "Nigeria, Yola." "Kina son zama mai ƴan a unguwar nan, kin son kwana a waje mai kyau?." Ta ɗaga kai alamun eh, matar ta ce, "ki zama tawa, ni kuma zan saka ki ki zama mai daɗi a cikin ƙasar nan." Labiba ta ce, "Ban gane ba." Matar ta shafa fuskar Labiba ta ce, "kina da kyau Labiba, kin gane me nake nufi ko na nuna miki abinda nufi?" Ta faɗa tana ɗaga rigar Labiba ta saka hannu. Labiba ta riƙe mata hannu ta ce, "bana ra'ayi." Matar ta zare hannubta ta ce, "Tashi ki je, babu dole." Labiba ta kalli su Aisha da sun fara fita daga hayyacinsu, duk sun fara watsar da sutturar jikinsu. Labiba ta miƙe zata fita, Aisha ta dakata da abinda take yi ta ce, "In ki ka tafi kar ki sake nemana, ki je ki yi rayuwar ki nima na yi tawa. Kuma gidan da na kai ki har ki ka kwana kar ki sake komawa ki je ki nemi wani ki je ki kwana. Sannan kar ki nuna kin sanni a ko ina, ki ɗauka ba ki taɓa sanin Aisha a rayuwar ki ba, tunda ina so na taimake ki ke bakya gani. Kuma kina fita tsaf za a iya cafke ki a a mayar dake gida." Matar da take neman Labiba ta ce, "Kuma ba kyauta za ki yi ba, zan biya ki kuɗi masu yawa, indai za ki yarda dani babu abinda zai gagare ki a cikin garin Makka." Aisha cikin wata irin murya mai nuna bata hankalinta ta ce, "Ki ka bi namiji ma balle ƴar uwarki mace? Kuma harkar nan ta fi wancan daɗi, dan ba ki taɓa yi bane shiyasa ki ke jin tsoro kina ganin abin kamar baƙo, amma da kin saba da wannan wani namiji bazai sake burge ki ba har abada." Ita dai Labiba kallonsu Aisha take yi ganin baƙon abu wanda bata taɓa zato zata gani a zahiri ba. Duk iskancinta sai ta ji tana ƙyamar abun taoro ya mamaye mata zuciya, ta zuba musu ido kawai tana kallon yadda suke sarrafa junansu kamar mace da namiji. Ganin ta shagala da kallonsu Aisha sai matar ta riƙota ta zaunar da ita ta fara yi mata abubuwan da zai saka ta fita daga hankalinta, cikin lokaci kaɗan ta yi nasara akan Labiba ta tsunduma a cikin harkar. Nigeria. Islaha tunda ta gama cin abinci tana zaune a faɗon ita kaɗai, ita ko tv bata taɓa karanbanin kunnawa ba, ga dai tv nan tana gani a bango, amma bata jin ƙarfin kunnawa balle har ta yi kallo. Ta zaune tana tunanin anya zata iya fita, tana so ta je wajan Hamma kamar yadda ya ce in ta samu dama yana so ya ganta amma bata jin ƙarfi a jikinta ko kaɗan. Ta ɗan zame a kan kujerar ta yi shiru tana tuna yadda aka dinga sakar musu harbi, da yanzu tana kabari a kwance, daga auren yarjejeniya ta mutu. "Astagafirullah!" Ta furta a bayyane jin gabanta yana faɗuwa haka kawai. Tana tunanin ko waye ya saka a kashe shi oho, ko me ya yi musu dai su suka sani. Door bell ake taɓawa, ta juya ta kalli ƙofar gabanta ya faɗi kar ta je Salman ne ta shiga uku. Sai ta miƙe tana ƙarasawa wajen ƙofar cikin tsoro dan ba ta son abinda zai sake haɗa ta da Salman balle a sake haɗa meeting a kanta. Tana dubawa saimta ga Daada ce da wasu mata guda biyu su riƙo hannunta, ta yi ajiyar zuciya sannan ta buɗe ƙofar. Daada ta yi murmushi tana kallonta, Islaha ma murmushin take yi cikin fulfulde ta ce, "Daada barka da zuwa." Daada da murmushi ta ce, "Barka dai Islama." Islaha ta riƙo hannunta suma tafiya a hankali har cikin falon, Daada ta zauna sannan Islaha ta zauna ta ce, "Barka da rana." "Barkan ki ƴar albarka, ya aka ji da fargaba?." "Alhamdu lillah." "Allah ya cigaba da kiyayewa." "amin ya rabbi." "An ce sai da ki ka kwanta asibiti, daman kina da ciwon ne?." Islaha ta ɗaga kai ta ce, "ina dashi." Daada ta ce, "Allah ya ye miki kin ji. Haka yake fama da maƙiya ta ko wanne ɓangare, kin san yadda ɗaukaka take, dole sai ka samu mai ƙoƙarin ganin bayanka. Har a cikin gudan nan an saka masa guba a lemo ya sha, an kwance masa burkin mota, an yi waye anyi waye. Abubuwa dai da yawa, kuma ba dan komai ba sai dan ɗaukaka da Allah ya basa. Shiyasa ake cewa ɗaukaka abar gudu, kuma abar nema." Islaha ta ɗaga kai ta ce, "Haka abin yake." Daada ta ce, "Yana ina?." "Yana sama." "Kira min shi." Islaha ta amsa ta miƙe ta hau saman Daada ta bita da kallo tana murmushin ƙaunarta. Da sallama a bakinta ta shiga falon amma bata same shi a falon ba, sai ta kalli ɗakin dan ta san yana ciki dan bata ga ya sakko ba kwata-kwata, ita kuma bata son shiga ɗakinsa ko da wasa. Nana Haleema. KRBBK: RDB3P31 Nana Haleema. Islaha ta harari ɗakin dan ita gaskiya bata son shiga ɗakinsa, so take har ta gama kwanakinta ta bar gidan bata shiga ta ga ya ɗakinsa yake ba, bata son shiga ɗakin sa ko kaɗan. Tunawa Daada tana jiran ta sai ta nufi ƙofar kamar mai jin tsoron wani abu, ta miƙa hannu ta ƙwanƙwasa ƙofar kamar wacce zata taɓa wuta ko wutar lantarki. Jin shiru ba a amsa ba sai kawai ta buɗe ƙofar ta shiga da siririyar sallama. Ƙhamshi da girman ɗakin ya ɗauki hankalinta, girmansa da tsaruwarsa da komai irin na film ɗin turawa, hakan ya saka ta tsaya cak tana kallon ɗakin har tana sake buɗe ido tana kallon yadda ya tsaru sosai. Ita fa Allah ya sani tana son lavish life, tana so ta ga babban bedroom kamar wannan ace mallakinta ne, tana so ta ga komai irin na ƴan gayu a tare da ita. Shiyasa kullum take yiwa Hamma addu'a, Allah ya ba shi kuɗin da zai wadata ta da duk abinda yake ra'ayi. Sanyi ne kawai yake tashi a ɗakin, sanyi mai ratsa ƙashi da ɓargo, ga ƙhamshin turarensa ya mamaye ko ina a cikin ɗakin, ya haɗe da sanyi yana ba da wani kalar ƙhamshi mai daɗi. Islaha ta gyara tsayuwa tana kallon wani babban falo a cikin bedroom ɗin, an saka masa wasu kujerun dasu ba gado ba, kuma ba kujeru ba. Motsin buɗe ƙofa ya saka ta juya da hanzari, kai tsaye suka haɗa ido da ahi ya fito daga wanka ɗaure da ƙaramin farin towel, ya naɗe gashin kansa a tsakiyar kansa, yana tafiya a hankali kamar mara jini. Islaha gabanta ya yi mugun faɗuwa, rana ta farko a rayuwarta da ta ga wani namiji a haka babu kaya, jikinta ya yi wani irin sanyi, kunyar duniya ta lulluɓe ta, ta kawar da kanta daga kallonsa da sauri, tana ji kamar ƙasa ta tsage a wajan ta shige kawai ta huta. Rehaan shima kallon mamaki yake yi mata, bai yi niyar fitowa ba sai ya shirya daga closet ɗinsa kamR yadda ya saba, hair burner ɗinsa ya manta a ɗakin shiyasa ya fito ya ɗauka sannan ya koma closet ɗinsa. Islaha ta kasa kallonsa saboda kunya da danasanin shigowa ɗakin sun gama mamaye mata zuciya, sai kawar da fuska take yi kamar munafuka, shi kuma ya tsaya cak yana kallonta dan bai san me ya kawo ta ɗakin ba. Cikin nutsuwa ya ƙaraso inda take, daga ɗan nesa da ita ya ce, "any problem?." Islaha bata amsa ba, so take ta buɗe baki tayi magana bata san me ya rufe mata baki ta kasa cewa komai ba. Shi kaɗai take hangowa a idanunta kawai, duk da kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kai amma har lokacin shi take gani a idanunra. Hasken da fatarsa take dashi, da gashin jikinsa, da yanayin jikinsa, da yadda ruwa yake bin fatar jikinsa kaɗai take iya tunawa a wannan lolacin, ta ruɗe ta rasa abinda ya kamata ta yi. Rehaan dai ya zuba mata ido yana jira ya ji me zata ce masa, dan ya san akwai dalilin da ya kawo ta ɗakin ba haka kawai ta zo ba. Islaha daƙyar ta ce, "Daada.." sai bata ƙarasa ba bakin ya ƙame saboda ruɗewa. Ya ɗan yi tsaki cike da jin haushi ya ce, "Yau ki ka saba ganin namiji a haka?...Ki faɗa min abinda ya kawo ki, ina da aikin ki" ya faɗa a hankali yana binta da kallo. Wani irin abu ya chaki zuciyarta, ta so ta daure ta ɗago ta kalli idanunsa amma sai ta kasa, tana so ta nuna masa ta saba ganin mazan a haka kamar yadda ya ce amma ta gaza aikata haka. Ji take ɗakin ya yi mata girma, kunya ta lalluɓe mata zuciya da idanunta. Duk da haka bata ƙyalesa ba, ba ta bari kunyarsa ta rinjaye ta ba, bata bari kunya ta yi tasiri ba, kunya bata kashe bakin tsiwa ba ta ce, "fiye da haka ma saba gani. Allah na tuba me na gani yanzu? Ai ban ga komai ba tunda ba namiji ne a gabana ba, kuma ba dan ban saba gani bane ya saka na ɗauke idanuna daga kan ka, kawai akwai waɗanda basu cancanci a gansu a hakan bane, shiyasa bazan iya kallon ka. Ba wai dan ban saba ba, sai dan ba ka kai matsayin da idanuna za su........." maganar ta maƙale ganin ya matso daf da ita yana kallonta fuskar ta. _Innalilllahi wa'inna ilaihir raji'un! Na shiga uku. Shi wai ba shi da kunya ne, bai san hakan bai dace bane, ni wallahi ƙarya nake yi, ko Hamma ban taɓa gani a haka ba. Na shiga uku ni Islaha._ Abinda take maimaitawa a ranta kenan, ta kasa ɗaga ido ta kalle sa har lokacin kuma bakinta yaƙi mutuwa. Rehaan ita yake kallo da ta sunkuyar da kanta, ita kuma tana ƙoƙarin ɓoye tsoronta amma ta kasa, bata so ta nuna masa ta tsorata saboda kar ya daina yi mata kallon ƴar iska. Ganinsa daf da ita ya saka ta matsa jikin bango ta ce, "Mr Rehaan....ka matsa don Allah." Rehaan ya yi ƙasa da idanunsa, yana kallon fuskarta calmly ya ce, "Ba ko wanne ido ne ya cancanta ya ga ko wanne jiki ba, kin ji?." Bata san ta ɗaga amsa kai alamun eh ba saboda duk ta ruɗe lokaci ɗaya. Ya yi murmushi yana ja da baya yana kallonta, rana ta farko da ya yi galaba a kan bakinta, har ya faɗi magana ta kasa mayar masa. Da hanzari ta nufi ƙofa zata fice, sai da ta riƙe handle ɗin ta tabbatar ta kusa fita sannan ta ce, "Kakarka tana ƙasa tana jiran ka" tana faɗa ta fita da hanzari. Ya yi tsaki ya ce, "Mara kunya" ya yi murmushi ya koma inda ya fito. Islaha ta jima a falon a tsaye tana sauke numfashi har da ɗora hannunta a ƙirji kamar wacce ta yi gudu, tunda take a duniya bata taɓa jin kunya irin ta lokacin ba, bata taɓa zaton zai faɗi magana ta kasa mayar masa ba sai a wannan lokacin. Tana dafe ƙirjinta tana ji a ranta kamar bata kyautawa kanta ba, ta ya zata kalli wani namijin daga shi sai towel?. Ta yi tsaki mai tsaho mai nuni da jin haushin abinda ta aikata, sai kuma ta tuna da Daada a ƙasa ta sauka da sauri. Tana zuwa ta ce, "Gashi nan." Daada ta amsa tana dafa ta cikin ƙaunarta. Basu jima sosai ba ya sakko, sanye cikin riga da wando na kamfanin Nike baƙaƙe waɗanda suka yi masa kyau sosai. Tun kafin ya ƙaraso ƙhamshinsa ya cika wajan, ita dai bata ɗaga ido ta kalle sa ba har ya ƙaraso ya zauna. Daada ta kalle sa ta ce, "Sannu Muhammad, ashe haka abu ya faru?." Ya ɗaga kai ya ce, "Barka da rana." "barkan ka, Allah ya kiyaye gaba." "Amin." "Ka cigaba da addu'a, ka cigaba da sadaka ka ji." "In sha Allah." "Allah ya ƙara kiyayewa." "Amin." "Iyayenka mata sun ahigo kuwa?." Ya girgiza kai ya ce, "Ban sani ba ko da ina bacci sun zo." Daada bata ce komai ba, ta miƙe tana kallon Islaha ta ce, "Ishlaya in kina son abinci ki dinga aikawa a karɓo miki, wannan abincinsa gabaɗaya na ƙasar waje ne, in kina son na gargajiya ki snaar dani." Islaha ta yi murmushi tana miƙewa tsaye. Daada ta ce, "Ke da ba ki da lafiya, yi zaman ki ba sai kin raka ni ba, akwai ƴan rakiyata a waje." Islaha sai da ta rakata har bakin ƙofa, sannan masu aikin suka riƙe ta suka tafi ita kuma ta rufe ƙofar ta dawo ta zauna. Yana inda ta bar shi bai motsa, sai ɗora ƙafa kan ɗaya da ya yi yana kaɗa ƙafa kamar basarake. Islaha ta saci kallonsa ta gefen ido, gashinsa ya sauka har wuyansa, tana kallon gashin tana aiyana ko ya irin gashin nan nasu yake, dan gashinsa gabaɗaya bai yi kama da na fulani ba, da irin na su Banisha ya yi kama, tana so ta ji gashin ya irin nasu yake mai laushi ne ko ya ya. Ƙofar aka buɗe aka shigo tare da sallama Banisha da Janan da Ikram suka shigo falon. A guje Banisha ta ƙaraso ta zauna a kusa dashi, ya yi murmushi ya riƙe hannunta ya ce, "Kiddo ya school." "lafiya lau, gobe zan yi presentation." Ya ja kunatunta ya ce, "all the best." Itama ta rama ta ce, "thank you." Ya kalli Janan da Ikram ya ce, "Na manta rabon da na gan ku, bakwa nemana." Suka yi dariya Ikram ta ƙarasa ta ba shi hannu suka gaisa sannan ta ce, "ka san mun yi busy, har yanzu ba mu huta da gajiyar biki ba." "Uhum i see" abinda ya faɗa kenan, ya bawa Janan hannu suka gaisa. Janan ta kalli Islaha ta ce, "Hii Sis Islaha." Islaha ta yi fara'a ta ce, "Hi Janan." "Ya jikin ki?." "na ji sauƙi." "Allah ya ƙara sauƙi." "Amin, na gode." "Let me introduce Ikram to you, Sister Hamma Jafar ce, inlaw ɗin Riyya." Ikram dai kallon Islaaha take yi har Islaha ta kalle ta suka haɗa ido, Ikram ta murmusa ta bata hannu suka gaisa. Janan ta ce, "Hamma Jafar ne ne ya kira ni ya ce na zo na faɗa maka, Bilal yana waje da masu sim swap ɗin." Ray ya gyara zama ya ce, "Okay su zo." Janan da Ikram suka fita. Babu jimawa suka dawo gabaɗaya da baƙin, Islsha tana zaune bata motsa ba tana kallon ikon Allah. Ganin kamfanin layin waya guda a gabanta, a take aka yi capturing ɗinsa aka yi masa sim swap cikin mintina ƙalilan. Bilal ya ba shi sabuwar waya a kwalinta, ya ajjiye a gefe bai ce komai ba Banisha sai surutu take yi masa. Sim swap ɗin gabaɗaya bai wuce mintina goma ba aka gama suka fita, ya rage daga shi sai su Ikram. Ikram sai satar kallon Islaha take yi da take ta ta danan waya kamar bata san dasu a wajen ba. Ƙare mata kallo take yi tun daga sama har ƙasa. tana so ta hango aibunta ko muninta amma ta gaza, kyau take gani mai ɗaukar ido da ɗaukar hankali, babu abin burgewa sai bakinta, da zananniyar gira da Allah ya bata. Islaha tana lura da kallon da Ikram take yi mata wanda bata san dalilinsa ba, ta basar kamar bata sani ba tana ta danan waya suna magana da Brr. Rehaan ya miƙe ya hau sama da wayar a hannunsa bai ce musu komai ba. Janan ta taɓa Islaha ta ce, "Sis bakya magana?." Islaha ta ɗago ido ta yi murmushi ta ce, "Ina yi mana." "Amma ki ka yi shiru?." Murmushi ta kuma yi kawai bata ce komai ba, basu jima a zaune ba duk suka fita daga falon. Islaha ta miƙe ta hau sama, bata same sa a falo ba ta wuce ɗaki ta rufe ƙofar.       *** Sai zagaye yake yi a cikin falon hankalinsa a tashe, ya kasa nutsuwa tunda ya ji an matsanta binciken akan waɗanda suka kai wa Rehaan hari, ba ya so sunansa ya fito, ba ya so a ce shine ya saka a kashe Rehaan. Ya kalli yaran da suka yi aikin ya ce, "Ba ku taɓa yin aiki daidai ba, ko yaushe sai kun ɓata komai. Yanzu da kun kashe shi da hakan ai bai faru ba." "Ranka ya daɗe motar bullet prove ce, babu harbin da ba mu yi mata ba amma bai same su ba." Cikin faɗa ya ce, "Amma kun san babu ta yadda za a yi ya hau motar da ba bullet prove ba ko? Meyasa ba mu fara ƙona motar ba tun farko?. Wancan kun ba shi guba ƴar kaɗan, wannan kuma kun kasa aikata komai." Suka yi shiru basu ce komai ba, ya nuna su da yatsa ya ce, "Na rantse da Allah in aka kama ɗaya daga cikin ku wani ya ambaci sunana kun san sauran, tunda ku ka yi aikin a bayan bank, kun sana akwai cctv a wajan, saboda shirme da rashin sanin makamar aiki. Yanzu ana kan bincike, na tabbatar za a ga fuskokin ku." "Ai duk mun rufe fuska." "ku ku ka sani kuma, ni dai ina sake maimaita mu ku babu ruwana a cikin maganar nan. In za ku tattar ku bar gaein ku yi, in komai ya lafa sai ku dawo." Zasu yi magana ya ce, "na gama sauraron ku, ku wuce ku bani waje, bazan sake yin aiki da ku ba." Basu ce komai ba suka miƙe suka fita. Ya saka ƙafa ya da ki kujera da ƙarfi, ya dafe kansa da yake sara masa saboda kishi da hassadar Rehaan ya ce, "Rehaan!." Sai kuma ya girgiza kai ya ce, "wallahi baza ka kasance da rai ba, sai na ga bayanka, sai na ga bayanka wallahi!" Ya faɗa da ƙarfi yana dukan kujera cikin tsananin fusata da baƙin ciki. "Ya zama dole na samo sabuwar hanyar ganin bayan Rehaan." Hannunsa yana rawa ya ɗauki waya ya saka a kunne ya ce, "ina son information akan yarinyar da aka aurawa Rehaan, ina son sanin wacece ita, aikinta da halayaenta duk ina son sani a yanzun nan" Daga ya yanke wayar yana ci kamar ya yi ta ihu saboda takaici......... Nana Haleema. RDB3P32 Nana Haleema Ikram tunda ta koma gida ta shiga ɗaki ta zauna a gefen gado ta yi tagumi tana tunanin masoyinta Rehaan da matarsa Islaha da ta kasa gano makusa a jikinta. Mummy tun wucewarta ɗaki ta kula da yanayinta, suna tare da Jafar a zaune har ta wuce bata ce musu komai ba, Jafar ya bita da kallo sannan ya ce, "ita kuma wannan lafiya?." Mummy ta ce, "Ikram bata ji Jafar, ita ta dage akan Rehaan ta ke so kuma shi za ta aura." Jafar ya yi murmushi ya ce, "To ai ya yi aure ko?." "Ina jin mantawa ta ke yi da yana da aure a yanzu." "Ya yi auren ma bata haƙura ba Mummy?." Mummy ta ce, "bata haƙura ba, dan yanzu ma daga gidan take." Jafar ya ce, "Zuwan ta gidan ba matsala bane Mummy, dalilin zuwan nata shine damuwa. Wallahi Rehaan bazai saurare ta ba, kin ji nace wallahi ko Mummy?." Mummy ta ce, "Na sani Jafar, Rehaan yana kallon ta kamar Riyya da Janan, bazai iya kallon ta a matsayin matar aure ba. Na yi mata bayani amma ta kasa yarda." Jafar ya ce, "Inda zai aure ta ɗin duk za mu so hakan, amma bazai aure ta ba Mummy. Ba wai dan bata dace shi ba, sai dan bazai iya kallonta a wannan matsayin ba. Ko a Jeddah sai da mu ka yi maganar ta da shi, ya sake maimaita min babu shi babu auren ƴar uwarsa har abada." Mummy ta ce, "na sani Jafar, ba sai ka maimaita min ba. A gaban idanun ku ita da Riyya suka girma, yadda yake yiwa Riyya haka yake yi mata, ni kaina na san bazai iya kallonta a matsayin matar aure ba." Kafin ya yi magana Mummy ta ce, "bara na kira maka ita, wataƙila kai in ka faɗa mata zata yarda, tunda ta san kai da Rehaan kamar hassan da usaini ne" Mummy ta miƙe ta hau sama dan ta kira masa Ikram. Babu jimawa suka dawo tare da Ikram da take tafiya kamar bata so saboda sanyin jiki. Jafar ya miƙa hannunsa ya riƙo hannunta ya zaunar da ita a kusa da shi, cikin sigar rarrashi ya ce, "Iky faɗa min meye?." Sai da gabanta ya faɗi dan Rehaan ne ya saka mata Iky, tunda ta girma ne bai cika faɗa ba, ya fi faɗar full name ɗinta.. ikram ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. "Talk mana, i'm here for you." Muryarta ta fara rawa ta ce, "Hamma Ray...." Jafar ya sake tausasa murya ya ce, "ki ke so?." Ta ɗaga ido ta kalle shi sai kuma ta ɗaga kai alamun eh, sai kawai ta saka kuka tana kwanciya a kafaɗarsa. Ya sauke numfashi mai nauyi ya dafa kafaɗarta yana bubbugawa a hankali, sannan ya ce, "ki daina kuka, ki yi shiru mu yi magana." Bata daina kukan ba, ya bata lokaci ta gama kukan sannan ya riƙe hannunta ya fuskance ta ya ce, "Ikram!." Ta ɗaga ido ta kalle sa ta ce, "Na'am." "Kina so na faɗa miki gskiya?." Ta ɗaga kai alamun eh. Ya ce, "Ki cigaba da addu'a, ki dage da faɗawa Allah damuwarki. Amma auren ki da Rehaan abu ne mai wahala." Ikram ta sake shagwaɓe fuska ta ce, "saboda ban dace dashi ba, bani da kyau ko Hamma Jafar?." Ya yi murmushi yana goge mata hawayen fuskar ta ya ce, "kina da kyau Iky." "to meyasa ka ce haka?." "Saboda Rehaan kallon ƙanwarsa yake yi miki, ba kallon macen da zai iya aura ba. Da ke da Riyya da Janan duk ɗaya yake kallon ku, da ke dasu Adda Anisa yayyensa mata, duk ɗaya yake kallonku, bazai iya keɓance ki daga cikinsu a matsayin matarsa ba." "Bazai iya sona ba?." "Rehaan yana sonki, kina daga cikin mutanen da yake so, amma so na ƴan uwa ba na aure ba." "Zan iya manage da hakan, tunda Mamy tana so ya aure ni." "ko Mamy tana so sai yana so, duk abinda Mamy ta ke so in Rehaan bai ba da goyan baya akansa ba ya lalace duk son da Mamy take yiwa abun, in kuma yana ƙin abu duk yadda Mamy take so itama zata daina so tunda ba ya so. Duk da tana son ya aure ki, amma in ya nuna ba ya so bazata yi masa dole ba." "Amma Daada ta yi masa dole ya auri Islaha take ko waye oho." Ya yi murmushi ya ce, "kema cewa ki ka yi ta yi masa dole, kin ga Mamy bazata yi masa dole ba. Kuma ke da bakya son kishiya, tunda ya yi aure ba sai ki watsar dashi ba?." Ta turo baki ta ce, "ai ba sonta yake yi ba." "Haka aka ce miki?." "Kowa ya san dole aka yi masa." "To yana son matarsa." "Allah ba ya sonta, yanzu da mu ka je gidan ko kallonta ba ya yi." "Na ji ba ya sonta, amma ke yana son na ki ne?." Ta yi shiru bata amsa ba. Ya ce, "ki bar wannan maganar Ikram, ki yi addu'a Allah ya ba ki wanda yake sonki ba wanda ki ke so ba, ki ajjiye batun Rehaan a gefe, in ki ka aure sa ma yadda ki ka ga ya yiwa Islaha har ki ke bada labari kema haka zai yi miki. Yanzu ki ke bani shaidar ba ya sonta saboda ba ya kallonta, kema in ba ya son ki bazai kalle ki ba. Ki bar tunanin aurensa a ranki, dan ko kin aure shi baza ki samu lokacinsa ba, Rehaan busy man ne, lokacin kansa cikakke ba shi da shi balle na ki. Ikram ki nutsu ki cire Rehaan daga ranki, kina wahalar da rayuwarki indai a kansa ne. Ki nutsu ki cigaba da addu'a kawai." Ikram ta ti ajiyar zuwa, ta san gaskiya yake faɗa mata amma ta kasa fahimtarsa yadda ya kamata. Ta kalle sa ta ce, "Amma kai ma a dah ka ce baza ka iya auren Riyya ko Janan ba, nima ka ga zai iya canja ra'ayi." Ya girgiza kai ya ce, "ba dai Rehaan ba, bazai canja ba wallahi, kin san nafi kowa sanin halinsa, ki yarda da abinda nake faɗa miki." Ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce, "Ni wajan Mamy zan koma" ta faɗa tana miƙwa ta hau sama ya bita da kallo. Mummy ta yi dariya ta ce, "Soyayyar da take yi masa ma bata da wani auki, ga shi nan har ka fara canjata." Jafar ta yi dariya ya ce, "Ba fa so bane ba Mummy, burge su kawai yake yi, suna so su auresa ko dan a nunawa ƙawaye ana auren Rehaan. Wannan gashin nasa ne yake ɗaukar hankalinsu, da yadda hotounansa suke yawo a social media, to sai kuma kyaunsa da yake sake ruɗa su." Mamy ta yi dariya ta ce, "da gaskiyar su Jafar, Rehaan ta ko ina Allah ya yi masa baiwa. Ga kyau, ga tarbiyya, ga kirki, ga zumunci, ga kuɗi. Allah ya cigaba da kiyaye shi a duk inda." "Amin Mummy. Dan yaron nan Rehaan da ki ke gani ya wuce tunanin ki, yana da madarar kuɗi a hannunsa wallahi, in na faɗa miki cewa za ki yi ƙarya nake yi." Muummy ta ce, "Kai kuma kana da sikarin kuɗi?." Ya yi dariya ya ce, "Mummy ki bar haɗa ni da Rehaan, shi na daban ne. Yana da sa'a, duk abinda ya taɓa da niyar kasuwanci sai ya samu riba. Yana da kwarjini sosai, mutum biyu ne kawai ba ya yiwa kwarjini a duniya." "Su waye?." "Daga ni sai miss." "Kai daman na san ka raina shi, duk da Yayanka ne amma baka girmama shi. To wacece miss?." Jafar ya sake yim dariya ya ce, "wata yarinya ce, in kinga yadda take yi masa sai abin ya ba ki mamaki, ta gama raina Rehaan sosai" ya faɗa yana miƙewa sannan ya ce, "Mummy na tafi, zan je gida." Mummy da murmushi ta ce, "a gaishe da Riyya, Yaush za ku koma ne?." "Next week in sha Allah." "Allah ya kaimu." "Amin, sai anjima." Mummy ta amsa ya fita yana ɗaukar waya ya kira Rehaan, dan zuwa lokacin ya san sim card ɗinsa ya zama ready. Islaha tun tana saka ran zata fita har ta cire dan gabaɗaya bata da ƙarfin zuwa ko ina, ta kira Safeera ta ce mata ta fasa zuwa. Haka ta yini a ɗaki ita kaɗai, sai dai ta danna wayar ta gaji ta kwanta. Washe gari friday da wuri ta tashi ta yi wanka ta shirya, ta buɗe window tana ganin yadda mutane suka cika a gidan ana karɓar sadakar abinci da kuɗi, ta bar wajen ta saka kaya gama shiryawa ta fito da niyar tafiya office. Bata same shi a falo ba kamar yadda ta yi zato, ta sauka ta fita suka wuce wajan aiki. Motar Lawal tana sauke ta suka haɗa ido da Ummi, Islaha ta ɗan yi tsaki ta ɗauke kai daga kallonta ta nufi ciki bata sake kalon ta ba. Daman ta san Safeera bata cika zuwa ranar friday ba, bata same ta ba ta wuce inda zata je. Ummi tana shiga ta nufi wajan Muslim ta rufe office ɗin sannan ta kalle shi ta ce, "Muslim ka ga abinda na gani." Ya waiwayo ya kalle ta ya ce, "me ya faru?." Ummi ta yi ƙwafa ta ce, "Islaha na gani a wata zundumemiyar range rover baƙa mai shegen kyau, kuma abinda ya bani mamaki tana baya a zaune, irin madam da driver ta ɗin nan." Muslim ya ce, "an zo wajan, tabbas zargina ya zama gaskiya, in Islaha ba ta yi aure ba to zaman dadiro take yi da wani. Gabaɗaya ta canja, ko gidansu aka je ba a cika samunta a can ba, abin yana ɗaure min kai." "Ba sai mu tambayi ƙawarta ba." "na yi tambayar duniya ta ƙi cewa komai, shima Saleem ɗin yaƙi ya ce komai. " Ummi ta riƙe baki ta ce, "Lamarin ya ɗaure min kai nima, ta ƙaro wani class. Ka ga girman motar da aka ajjiye ta kuwa?." Muslim ya ce, "ya zama dole mu san abinda zamu yi, da wannan damar zamu yi anfani wajen ganin ƙarshenta. Ko aure ta yi mu a wajan mu ba aure bane, zamu lalata mata suna mu zubar mata da mutunci a kafafen yaɗa labarai." Ummi ta ce, "Kar mu yi wannan gangancin, dan ba mu san waye a bayanta ba." "in ke baza ki yi ba ni zan yi, bazan zuba ido tauraruwarta tana cigaba da ɗaukaka ba. Wallahi sai na yi maganinta." "Ni sai nake gani me zai hana baza mu bi abin ta ƙasa ba, mu je wajan malamai a yi mana aiki a kanta." "Sai dai wannan ya biyo baya, amma wannan da na faɗa shi za a fara yi Ummi." Ummi ta ce, "Shikenan ayi hakan, in ba haka ba zata cigaba da wuce tunanin." Ya yi ƙwafa yana girgiza kansa cikin mugunta. Islaha bata jima a wajen aikin ba ta bar wajan, bata tsaya kiran driver ba ta hau napep zuwa gidansu Saheer. Sai da ta tsaya sannan ta kira Saheer yana ɗauka ya ce, "Islaha tun jiya nake jiran ki." Islaha ta ce, "gani nazo, ina fatan Mama bata nan." "Nima bana gida, amma gani nan ina hanya ki jira ni." Islaha ta yanke wayar ta cigaba da tsayuwa a wajan, ba jimawa Saheer ya ƙaraso da motar Sadik ya tsaya a gabanta, ya sauke glass ya kalle ta ya ce, "shigo." Islaha bata ce komai ba ta buɗe gaban motar ta shiga da sallama. Saheer ya amsa sallamar ya bita da kallon da ya yi mata yawa, har sai da ta ce, "Hamma ya dai?." Bai daina kallon ta ba ya ce, "Cikin kwana biyar na ga kin yi kyau abin ki, kamar kina gidana." Ta rufe ido ta buɗe cikin son kawar da maganar ta ce, "ina wani kyau a nan, kawai dan jiya ban fita bane shiyasa." "me ya hana ki fita jiyan?." "Kaina ne ya dinga ciwo, ka san na samu attack a shekaran jiya da abin ya faru." Saheer sai ya haɗe rai ya ce, "ni tambayar da nake so na yi miki, me ya kai ki fita dashi a mota daga ke sai shi?." "Hamma na faɗa maka komai fa, tsoro zama ni kaɗai nake ji shiyasa kawai na shiga muka tafi." "Islaha zama a gida ke kaɗai bai taɓa ba ki tsoro ba, meyasa yanzu ki ka fara jin tsoron zama ke kaɗai?." "Hamma dare ne a lokacin, ƙarfe ɗaya da wani abun na dare, ba dole na ji tsoro ba." Saheer ya girgiza kai ya ce, "Ni na fara jin tsoro, anya ban rasa ki ba?." Nana Haleema. RDB3P33 Nana Haleema. Islaha ta yi shiru taƙi ba shi amsa, dan bata cika son ya dinga kawo mata wannan maganar ba, tunda Safeera ta tunasar da ita take tsoron aikatawa, bata so Allah ya kamata da laifi mai girman wannan. Sai kuma ta kalle shi ta ga yana kallonta, gudun kar ya gasgata ya rasata ɗin kamar yadda su Mama suke faɗa sai ta ce, "Ba ka rasa ni ba Hamma, ina nan dawowa, ka bari lokacin ya yi kawai.” Ta dakata da maganar ta yi tsaki ta ce, "Ni ko babu kai me zai kai ni zama da wannan mutumin? Mtsww! Kayan takaici." Ya bita da kallon mamaki ganin bilhaƙƙi ta ke maganar ta, shi mamaki ta ke ba shi sosai, the most richies man in Adamawa amma ta dinga wani taɓe baki in tana maganarsa tana tsaki. Kuma magana ake yi akan ita matarsa ce, amma ita ko kaɗan bata nuna hakan yana yi mata daɗi, sai kushewa da take yi kullum. Saheer ya ce, "Yanzu ya jikin ki?." Ta kalle sa ta ce, "na ji sauƙi." "kin je aiki?." "daga can ma nake." "Daga nan sai ina?." "Zan shiga cikin jimeta." "Ki yi me?." "Wani aiki zan yi kaɗan." Bai tambaye ta wanne aiki bane ya ja bakinsa ya yi shiru, dan ya ga kwana biyu bata cika son faɗa masa abinda ya shafe ta ba. Jin ya yi shiru sai ta kalle shi ta ga ba ita yake kallo ba glass ɗin gaban motar yake kallo ta ce, "Hamma ba ka bani labarin zama a wajen masu garkuwa da mutane ba." Ya juyo ya kalle ta, kafin ya yi magana Sudaisa ce ta fara zuwa ransa sannan ya ce, "A ina nake ganin ki balle na ba ki labari?." "Yanzu ba ga ni ba, kuma ko a chat ai za ka iya faɗa min." "Hmmmm" abinda ya furta kenan bai ce komai ba. Islaha ta ce, "Har yanzu yanayin ka bai yi normal ba, kana nan da ramar da ka yi kuma hasken ka bai dawo gabaɗaya ba. Sannan ga ƙananun ƙurajen nan da suka ɓata maka hannu, har yanzu basu gama ɓacewa ba." Ya lumshe ido yana tuna Sudaisa zuciyarsa tana bugawa sosai, yana tunanin ko ta kuɓuta ko tana hannunsu bai sani ba. A bayyane sai ya ce, "Islaha kenan, dan ba ki san ya wajen yake ba." "To ka faɗa min." Ya yi shiru bai ce komai ba, ta ɗan kalle sa ta ga titi yake kallo ba ita ba ta ce, "Hamma." Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Islaha gani nake kamar kin tafi kenan.” Islaha ta ce, "ka daina kokwanto a kaina, ka daina kokwanto akan zan dawo ko bazan dawo ba, mu ajjiye maganar zuwa lokacin ka gani. Yadda na yi auren nan saboda rayuwarka, yadda na sadaukar da kaina saboda ranka, haka zan iya yin komai dan ganin na dawo cikin rayuwar ka. Auren watan biyar ne kawai, da ya ƙare shikenan kowa zai kama gabansa." "Ke ki ke ganin wata biyar a kawai, amma a gare ni mai yawa ne. "Me zai hana baza ka koma ƙasar Nijar ba, in kana zaune a can za ka fi ganin komai yana gudu fiye da zaman ka a nan." "Na tafi na bar ki a gidan wani, ni na zauna a can ko?." Islaha ta ji kamar ta yi tsaki saboda haushin da maganarsa ta bata, sai kuma ta tuna da waye shi a gare ta sai ta ce, "ba ka yarda dani ba?." Ya yi ɗan murmushi ya ce, "Na yarda da ke, amma shi ban yarda da shi ba." "Kar ya dame ka, ni ko magana ba ta haɗa ni shi sai ya zama dole." "Hmmm, ke ba ki san waye namiji akan mace bane, shiyasa ki ke faɗar haka. Lokaci ɗaya zai canja, ya juya sama ta dawo ƙasa, daga nan sai labari canja, na fara ji ana batun Islaha ta kusa haihuwa." Saboda haushin maganar sai da ta sarƙe tana tari ta dakata bata kalle shi ba. Ta ta ɗaga hannu sama ta ce, "Allah ya tsare ni, Allah ya kiyaye ni, mugun ji da mugun gani Allah ya kare....." a zuciyarta take addu’ar bata san ta fito waje ba. Ta kalle shi ta ga ita yake kallo ta ce, "Hamma ka daina yi min irin wannan maganar, irin wannan tunanin ya daina zuwa ranka. Na ce ka zuwa lokacin ya ƙare ka gani, ka jira ka ga abinda zai faru a wata biyar masu zuwa…” Ƙasa-ƙasa ta ce, “Waye wani Rehaan Yola da za ka dinga saka irin wanann banzan tunanin a ranka? Da na ga wannan ranar ba gwara na ga ranar mutuwa ta ba?. Mtsww!" Ta faɗa tana yin dogon tsaki mai nuni da takaicin da yake damun zuciyar ta. Saheer dai kallon ta yake yi yana mamakin wannan haƙiƙicewar da take yi, ya san gaskiyarta take faɗa har zuciyarta, amma ya kasa amincewa dan ya san namiji ba abin yarda bane akan mace. Saheer ya riƙe hannunta, a karo na farko da ta ji gabanta ya faɗi, ta zame hannunta daga cikin nasa, bai hanata ba sai kallonta da yake yo sannan ya ce, "ni dai don Allah ki dawo gare ni, ki riƙe min kanki, ki adana min kanki kar ki yi min wasa da kanki. Ke kin san ina da kishi ba sai na faɗa miki ba, bazan iya jure ganin wani namiji a matsayin mijiki na farko kafin ni ba, don Allah matar Hamma kar ki ba ni kunya." Islaha sai jikinta yi sanyi lokaci ɗaya, ba maganarsa ce ta saka take jin hakan ba, riƙe mata hannun da ya yi ya ne ya saka take ji zuciyarta tana bugawa, zuciyarta tana faɗa mata bata kyautawa auren da yake kanta ba. Amma ya zata yi? Bata so ta yi wani motsin da zai nunawa Hamma ta zaɓi Rehaan a kansa. Cikin sanyin jiki ta ce, "To Hamma.” Ya sauke numfashi ya ce, "Ni ko da wani abun zai haɗa ki da shi a nan gaba, indai za ki dawo gare ni ina son hakan, ke nake so ba jikin ba." Ta yi shiru bata ce komai ba, tana aiyana mai zai haɗa ta da Rehaan ana zaune lafiya?. Saheer sai ya yi nufin tsokanar ta ya ce, "Hmmm! In da a dah ne na yi irin wannan maganar da kina nan kin kulle fuska, amma yanzu...." Bai ƙarasa ba ta kawar da kanta gefe, sai ya yi murmushi ya ce, "Ina sonki." Haka kawai sai ta kasa amsa masa kamar ko yaushe, ta yi murmushin yaƙe bata ce komai ba dan ta san shi kansa Hamman ya san ba daidai yake yi ba, amma tana jin daɗi da ya kasance ya samu lafiya kuma ya daina jin haushinta. Saheer ya ce, "za ki je wajan Safeera ne ko kin je?." Ta ɗan yi jim sannan ta ce, "yanzu zan je." Bai ce komai ba ya kaita har ƙofar gidan ya ce, "sai mun yi waya." Ta amsa tana fita daga motar ya bita da kallo yana tunani kafin ya ja motar ya nufi gidansu Sadik. Saheer ajjiye motar ya shiga wajan Sadik, ya same shi a zaune yana ta lissafi, ya zauna Sadik ya ce, "Ya dai?." Ya kalle sa ya ce, "Kana ganin Islaha zata dawo gare ni kuwa?." Sadik ya taɓe baki ya ce, "it might be, tunda shima ba sonta yake yi ba, ita kuma ka san daman kuɗi basa gabanta, amma zama a cikin kuɗin zai iya canta ba." "Ni dai burina ta dawo ɗin, in ba haka ba ban san ya zan yi ba. Ina son islaha sosai, bazan iya jure rashinta ba." Sadik ya ajjiye abinda yake yi sannan ce, "kasan me, in ni ne kai wallahi bazan tsaya ina asarar lokacina akan zata dawo ko bazata dawo ba, zan yi amfani da damar da na samu." Saheer ya ce, "wacce irin dama?." Sadik ya ce, "kai fa ka san wanda take aure, ka san meye kuɗi a wajansa, da ita zan dinga amfani ina tara kuɗi na gina kaina, na gina rayuwata na samu abinda na samu na kama gabana. Ita ɗin banza, ai ba itace autar mata ta duniya ba, kuma ba cewa aka yi in ban aure ta ba bazan samu wata macen a duniya ba." Saheer ya ce, "ban gane ba." Sadik ya ce, "ka yi amfani da damar da ka samu, ka mayar da ita atm ka fanshe wahalar da ka yi mata, in ba haka ba kana kallon ruwa kwaɗo zai iya yi maka ƙafa ka faɗa ciki har wuta. Ka dinga yi mata waya ƴar miliyan ɗayan nan ta saka maka, ƴar miliyan biyar ɗin nan ga jefo maka ka chafe. Meye naira miliyan biyar a wajan matar Ray? Mutumin da duk juma'a sai ya ƙarar da miliyoyin kuɗi a wajen sadaka? Ai yanzu islaha ta wuce yin kyautar miliyan ɗaya wallahi." Saheer ya ce, "baka da hankali ai, ni ita nake so ba kuɗin ba." "Sai kai ta fama da wahala kuwa, dan babu yadda ban yi ka kawo ta yi aika tare ba ka ƙi, kai ga mai kishi. Yanzu ga shi nan ta auri wani, ta yi auren sunna ba ka isa ka hana mijinta yin abinda ya ga dama da ita ba. Ga zunubin hira da matar aure da ka ke kwasarwa kan ka, itama kana ɗora mata.” "hakan bazai faru ba, domin a cikin rules ɗinta ta haramta hakan." Sadik ya yi dariya ya ce, "rules ɗin nan ai gangan ne, in ka ji ana gangan to wannan yarjejeniyar ce. Shaidu sun shaida, an ba da sadaki, addini ya ba shi cikkakiyar dama akan matarsa." "Amma ai auren contract suka yi, dole kowa ya bi abinda ɗaya yake so." "Kai! Asalin auren contract na ƙasar turai ba a tara shaidu, babu waliyai, babu sadaki, shiyasa malaman mu suka haramta shi a musulunci. Amma su a nasu auren duk akwai, aure aka yi kamar yadda ake ɗaura ko wanne aure a musulunci, wannan yarjejeniya a tsakaninsu take ba a cikiin addini ko al'ada ba. Ko yanzu ya so babu abinda zai hana bai yi amfani matarsa ba, bata isa ta hana shi ba, kuma bata isa ta ce ya aikata haramci ba. Ka ajjiye batun Islaha, ka ware ka nemi wata ka cigaba da shirin aure, ita kuma Islaha ta zama atm machine ɗinka, ka dinga cire kuɗi duk sanda ka so." "Duk abinda ta aikata ta yi ne saboda ni Sadik." "Na san ta yi saboda kai Saheer, kuma na jinjina mata, ba ko wacce mace ce zata yi abinda ta yi ba. Wallahi Islaha tana sonka, tana ƙaunar rayuwarka shiyasa ta sadaukar da rayuwarta saboda kai." "Shiyasa nake ƙaunar ta, saboda soyyayar gaskiya take yi min." "Kaima soyayyar gaskiya ka ke yi mata, kuma na yarda tana sonka so na tsakani da Allah, amma kuɗi zai iya canjata ko yaushe." Saheer bai bashi amsa ba ya yi shiru, Sadik ɗin ma ya share sa, dan shi wallahi inda shine sai ya gina kansa da Islaha. Allah ne ya san manufar jaki da bai bashi ƙaho ba, wallahi da sai ya yi abinda ya ga dama da ita, sai ya tara kuɗi son ransa, taje ta cigaba da zaman aurenta sai me? Ai ba a kansa aka fara yin haka ba, ba a kansa mace ta saba yin aure ta bar saurayi ba.      Islaha tana daga soron gidansu Safeera ta yi nata waya tana ɗauka ta ce, "ke ina wajen gidanku, fito." Ba jimawa Safeers ta fito tana faɗin, "Yau kuma wani sabon salo ne, baza ki shigo ba?." "Wallahi nauyin Mama nake ji, kuma nasan juma'a ce Baba yana nan." "To meye, daga ina haka?." "Na je aiki, sai na biya mu ka gaisa da Hamma." "Kin kyauta. Ya jikin?." "Na ji sauƙi, ki ƙa zuwa." "ke ni bana son dizgi ne, kar nazo a hana ni shigowa shiyasa. "Nima ranar da na fara fitowa hanani suka yi, sai da Mr Jafar ya zo sannan mu ka shiga." Safeera ta ce, "balle ni karan kaɗa miya." Suka yi dariya tare da tafawa. Islaha ta ce, "zan koma wajan Yafindo yanzu, ko za ki raka ni?." "Gaskiya bazan je ba, sai kin dawo. Kuma ina ba ki shawara, ki daina saka rayuwarki a cikin hatsari." "Yanzu na fara, dan so nake na gama da wannan case ɗin, akwai wani binciken na musamman akan masu garkuwa da mutanen, Allah sai dai a tsire ni." Safeera ta ce, "Allah ya taimaka, sai ki ta yi ai." "Matsoraciya." "Tsoro halak ne." Suka tsaya suna hira har driver ya ƙaraso ya ɗauke ta suka tafi. Kamar wancan lokacin haka Yafindo ta yi mata, islaha babu yadda bata yi akan su yi magana ba amma ta ƙi. Islaha ta ce, "zan tafi kamar yadda ki ka ce, amma ki sani zan kuma dawowa, kuma duk abinda ya samu Zainab alhakkin hakan yana kan ki." Yafindo kuka take yi tana son faɗa mata gaskiya amma tsoro ya hanata, tana son ta ba ta amanar da Zainab ta bata amma baza ta iya magana ba. A haka islaha ta fito daga gidan cikin wani irin yanayi, ta matso kusa da motar tana tunani, daidai lokacin wani yana zaune a cikin mota yana kallonta tunda ta fito. Tana fitowa ya ce, "ta fito." Daga cikin wayar aka ce, "ka bi ta kanta da mota, ka tabbar ka taka ta ta daina numfashi, kuma tsohuwar za mu yi maganinta daga baya." Islaha babu zato da tsaammi ta ga mota ta yo kanta da gudun tsiya, kafin ta farga har motar ta iso inda ta ke, ta ɗora hannu a kanta cikin firgici ta ƙwalla ƙara. Nana Haleema. RDB3P34 Nana Haleema. Bata san ya aka yi ba kawai ta ji an cillar da ita gefe, bata gama dawowa hayyacinta ba har ta faɗi ƙasa a firgice. Bata gama nutsuwa ba, hangowa take yi mota ta taho da gudu zata take ta, gabaɗaya ta ruɗe ta fita daga hayyacinta, dan gani take har lokacin motar bata wuce ba. Lawal da ya yi hanzarin janye ta ya tsuguna a gabanta ya ce, "Hajiya kina lafiya?." Ta kasa ba shi amsa saboda tashi hankali, lawal sai ya ga kamar bata cikin hayyacinta, firgici ya fitar da ita daga ciki hankalinta lokaci ɗaya, numfashinta yana neman tsayawa lokaci ɗaya, firgici da tsoro da tashin hankali ya saka samu attack. Jan numfashi take da ƙarfi, tana ji kamar duniyar ta tsaya cak, dan bata jin iskar da zata wadaci numfashinta ko kaɗan. Lawal hankalinsa ya tashi matuƙa, ya gigice ya rasa abinda zai yi mata, ga numfashinta yana fizgewa kamar zata sume a wajen. Ya rasa yadda zai yi mata sai ya ce, "Madam lafiya? Kina jina?." Islaha bata jin abinda yake faɗa, numfashi take neman fitarwa, amma ta rasa inda zata samu. A lokacin wasu mata suka zo wucewa ta inda Islaha take zaune. Lawal da yake neman taimako ya miƙe tsaye yana kallonsu ya ce, "bayin Allah ku taimaka min don Allah, ban san wanne irin yanayi take ciki ba, ku taimaka min ko a mota na saka don Allah." Ɗaya ta ce, “Subahanallahi! Me ya same ta?.” “Haka kawai numfashinta yake neman tsaywa.” “Tana da asthma ne?." Lawal ya ce, "ban sani ba wallahi." Ɗaya ta ɗan bubbuga fuskar Islaha ta cr, "baiwar Allah kina jina?." Islaha bara ji su ba, dan idanunta sun fara lumshewa za su rufe. Ɗaya ta ce, "athmatic patince fa, ki ɗan rage mata rolling ɗin nan na kanta. Malam ɗan ba mu wani abu a yi mata firfita." Da hanzari ya buɗe mota ya ɗauko iv ya basu, aka dinga yiwa Islaha fifita suka rage roilling kanta. "Kwantar da hankalin ki, ki nutsu" ɗaya take faɗa a hankali cikin sigar kwantar da hankali. “Ina da Inhaler, ban sani ba ko zata iya amfani da ita, kar na je na bata a samu matsala.” Ɗayar ta ce, “bata kawai, zata taimaka mata.” Ta ɗauko a jakar ta ta matsawa Islaha a bakinta, suka cigaba da yi mata firfita. Sun ɗan jima a haka kafin Islaha ta fara dawowa hankalinta, ta buɗe ido a hankali tana kallonsa, cikin lokaci kaɗan ta dawo daidai. Wacce ta bata Inhaler ta ce, "Sannu baiwar Allah." Islaha ta ɗaga kai kawai bata ce komai ba. "Ina inher ɗin ki?." Bata iya bata amsa ba, sai lumshe ido da take yi kamar mai jin bacci. Shi dai Lawal hamdala kawai yake yi, ganin ta dawo daidai da bai san ya zai yi mata ba. Matan ne suka taimaka mata ta shiga mota, sai da ta ja numfashi sannan ta ce, "Na gode." Ɗaya ta ce, "babu komai, nima ina da irin ciwo. Amma ki dinga yawo da inlaher, in ba haka ba za a samu matsala." “In sha Allah, na gode.” “Babu komai” daga haka suka yi mata sallama suka tafi. Lawal ya shiga motar ya ce, "Sannu Madam." Islaha ta amsa masa da kanta bata ce komai ba Lawal ya kalli matan ta mirror, yana aiyana da suna tare da Rehaan da kakarsu ta yanke saƙa. Sai da ya ja motar sannan ta ce, "Ka rage ac don Allah." Da hanari ya rage yana tafiya a hankali kar a sake samun matsala. Lokacin da suka je gidan har bakin apartment ɗinsu ya ajjiye moyar, ya sakko ya buɗe mata ƙofar ta sakko yana ta yi mata sannu. Ta ɗaga kai ta ce, "Na ji sauƙi, na gode sosai." "Amma Hajiya ya kamata a sanar da mutanen gidan nan abinda ya faru, mai motar nan da gangan ya yi ƙoƙarin taka ki, kamar daman jira yake ki fito daga gidan, dan na lura kamar bayan mu suke bi." Islaha bata da lokacin yin tunani a wannan lokacin sai ta ce, "za a san abinda za a yi, na gode da taimakon da ka yi min, Allah ya saka da alkhairi" ta faɗa tana wucewa ciki. Ta so ta shiga wajan Mamy da Daada su gaisa amma baza ta iya ba, ta zauna a falon ta cire ɗankwalin kanta ta kwance gashinta ta dafe kai da duka hannunta. Ta jima a haka kafin ta miƙe ta hau saman ta kwanta a kan gado dan bata jin ƙarfi a jikinta ko kaɗam. A haka bacci ya ɗauke ta, sai la'asar ta farka ta tashi ta yi sallah ta yi wanka ta fito falon. Har lokacin babu alamun Rehaan yana nan, bata damu da yana nan ko baya nan ba ta sauka ta ɗan ci abinci kaɗan tana bin ko ina na falon da kallo. A bayyane ta ce, "Ba dole Hamma ya ce na yi kyau ba, tunda nazo gidan nan ko tsintsiya da sunan shara ban ɗauka ba, sai dai na zo na ga an gyara ko ina, balle kuma girki.” Sai da rana ta yi sanyi sosai sannan ta yafa mayafi akan ɗauraren gashinta ta fita zuwa wajan Mamy kamar yadda ta yi niya tun farko. Da sallama ta shiga cikin falon, sai da ta saka ƙafarta a falon sannan ta ɗago ido tana kallon mutanen ciki. Rehaan yana zaune akan kujerar da take farko cikin manyan kaya, farin mace lace da hula wacce ta dace da kayan jikinsa, kayan sun karɓi jikinsa sosai. Dawowarsa gidan kenan dan ba a gida ya samu juma'a ba, ya fita ɗaurin aure da reception da aka gayyace shi, yana zaune yana ta ya Banisha game a wayar ta. Sai Mamy da ta ke zaune a gefe tana amsa waya, sai Ikram da take zaune tana cin abinci a ƙaramin bowl. Mamy ta ajjiye wayar ta amsa sallamar tana kallonta ta ce, "Islaha shigo mana." Islaha ta ƙarasa tsakiyar falon da ƙhamshinsa ya cika ko ina. Kamar bai san ta shigo ba, ya mayar da hankalinsa wajan Banisha gabaɗaya. Islaha itama bata nuna ta gan shi ba, tafiya take yi da niyar ƙarasawa kusa da Mamy. Gab da zata gifta shi ta ji an ja mayafinta da ƙarfi ta bayanta, jan mayafin da aka yi sai ya taho da ribbon ɗin kanta, zafin jan mayafin da ya haɗo da gashinta ya saka ta yi ƙaramar ƙara a lokacin mayafin da ribbon ɗin suka zube a ƙasa, gashinta ya warware ya sauka a fuskar Rehaan gabaɗaya. Kafin su farga da wanda ya janye mata mayafin ya damƙi gashinta da ƙarfi ya ce, "Lahh wannan duka gashinki ne?." Islaha ta runtse ido jin zafin yana ratsa kanta da ƙwaƙwalwar, daman ga ciwon kan da take fama dashi, ga shi ana sake ja mata gashinta. Mamy cikin faɗa ta ce, "Salman meye haka?." Sai a lokacin ya sa ki gashin Islaha ya kalli Mamy ya ce, "Mamy ni wajanta nazo, tun ɗazu nake nemanta an ce bata nan, shine nake murna da na ganta." Kafin Mamy ta sake magana Salman ya nufo wajan Islaha kamar zai riƙe ta, babu shiri ta buga tsalle ta yi bayan Mamy a guje. "Meye haka ka ke yi!?" Rehaan ya faɗa cikin tsawa yana riƙe sa. Salman ya kalli Rehaan ya ce, "Ni wajanta na zo, kuma kaima ka ce ai tana sona ko?." Rehana ya yi tsaki ya ce, "Ka bar wannan shirmen" ya sake faɗa yana jan hannunsa ya zaunar dashi a kusa dashi. Islaha gabaɗaya ta tsorata da abinda ya faru, Mamy ta riƙo hannunta ta zaunar da ita a kusa da ita sanann ta ce, "Ikram bani ribbon da mayafin ta." Ikram kallon gashin Islaha kawai take yi, itma tana da gashi sosai amma ko rabin na Islaha bai yi ba, na Islaha baƙi ne sosai, ga yawa da tsaho. Ta ɗauke kaita miƙawa Mamy ribbon da mayafin, Mamy ta karɓa da kanta ta ɗaurewa Islaha gashinta, ta yafa mata mayafin a kanta ita dai satar kallon Salman take yi. Islaha tana zaune a kusa da Mamy bata ce komai ba, Rehaan shi kam kamar bai san da ita a wajan ba. Salman ya taɓa Rehaan hakan ya saka shi ya kalle sa ya ce, "Za ka bar min ita mu dinga wasa? Daada ta ce wai matar ka ce, kuma na san kai kana sona, za ka bani ita ko? Ni ina sonta kamar yadda nake son cartoon ta cikin tv." Reahan ya ɗan kalli Islaha da take kallon Salman, ya kalli Salman ya ce, "Ka je masallaci ka yi sallah?." Ya ɗaga kai ya ce, "tare muka yi da Abba." Sai ya yi shiru bai ce komai ce masa komai ba, dan bai san me zai ce masa ba. Salman ya sake cewa, "za ka bani?." "Zan bar maka ita, ba haka ka ke so ba?." Ya ɗaga kai da sauri yana dariyar farin ciki. Rehaan ya ce, "amma sai ka daina abinda ka ke, ka ji?." Ya ɗaga kai alamun to ya daina sannan ya ce, "To ta zo mu tafi wajan Umma ta zauna a can, ka ga cartoom ɗim ma a tv Umma na ke gani, itama sai na dinga ganinta a tv Umma ko?." Rehaan ya ce, "In na koma england shikenan na bar maka ita." Cikin zumuɗi ya ce, "yaushe za ka koma?." "Na kusa" ya faɗa cikin ƙoasawa da maganar yana ɗan lumshe idanunsa. Salman ya ce, "to zan je na faɗawa Umma, ta siya mata kayan wasa irin nawa ko?. " Ya ɗaga masa kai shi kuma ya miƙe ya fita da hanzari. Sai a lokacin Islaha ta yi ajiyar zuciya ta kalli Mamy da take kallon Rehaan. Mamy ta ce, "Ba hankali ne da shi ba, ka daina biye masa Rehaan." Ray bai ce komai ba sai waya da ya ɗauko yana dubawa. Islaha ta ce, "Mamy daman nazo na gaishe ki." Mamy ta yi murmushi ta ce, "Na gode Islaha. Ni bazan ce Islam ɗin an da Bansha ta saka miki ba, sunanki ya fi daɗi." Islaha ta yi murmushi bata ce komai ba, amma tana mamakin yadda Mamyn ta canja lokaci ɗaya, ta daina haɗe mata rai har take yi mata magana haka. Islaha ta miƙe ta ce, "Zan koma." Mamy ta ce, "to na gode.” Islaha ta nufi hanyar fita tana tafiya a hankali ta fita daga falon. Bayan Islaha ta fita Mamy ta taɓa Rehaan da ko hanyar da Islaha ta bi bai kalla ba ta ce, "kai lamarin Salman ba abin zuba masa ido bane ba, matar aure yake yiwa mata wannan shirmen?." Rehaan ya kalli Mamy cikin ko in kula ya ce, "ni me zan yi? Ɗan uwana ne." "dan ɗan uwanka ne matarsa ce? Kar abin ya yi nisa ya zarce tunanin mu fa, kar nan gaba ka zo kana danasani akan wannan alaƙar da ka haɗa.” Sai ya miƙe ya ce, "Mamy na gaji" ya faɗa yana fita daga apartment ɗin gabaɗaya. Mamy ta yi tsaki ta ce, "Rehaan yana da shirme wallahi, zan yiwa Jafar magana ya san yadda zai ɓullowa lamarin, wannan abun ba abinda za a yi shiru bane tunda Salman ba shi da hankali. Abin ya fara yin yawa, tunda har ya fara cire mata mayafi a gaban mutane" ta faɗa tana miƙewa ta shiga ciki. Ikram dai bata ce komai ba ta yi shiru, yanayin yadda Rehaan ya yi wa Islaha ya tabbatar mata da gaske ba ya sonta, dan in akwai so tabbas akwai kishi. Ita bata ga alamun kishi ko kaɗan a tare da shi ba, kamar bai san abinda ya faru ba, bayan matarsa aka cirewa mayafi. Sai ta tafi tunanin itama in ya aure ta ba ya sonta haka ne zai faru? Da wannan tunanin ta miƙe ta shiga ɗakin da Riyya ta bari. Islaha tana fita Mama ta hangota ta kira sunanta hakan ya saka ƙarasawa apartment ɗin Mama. Mama ta dafata ta ce, "Da ban gan ki baza ki shigo ba?." Islaha ta yi murmushi dan matar tana burge ta sosai ta ce, "Daman zan zo mu gaisa." "Ya na ji maganar ki haka, ba ki da lafiya?" Ta faɗa lokacin da suke shiga falon Mama. Islaha ta ce, "kaina ne yake ciwo." Cikin nuna kulawa ta ce, "Subahanallahi! Kin sha magani kuwa?." Islaha ta ɗaga kai alamun eh. Mama ta ce, "Allah ya ƙara sauƙi, ko a kawo miki abinci? Sinasir muka yi, na san za ki so ci, kin jima ba ki ci abincin gida ba. Kina tare da Rehaan baza ki ci abincin gida ba, sai na turawa." Islaha ta ce, "Na ƙoshi Mama." "Aa, sai kin ci Islaha" ta faɗa tana miƙewa da kanta ta shiga kitchen. Islaha ta murmusa cikin jin daɗi, ta fi jin ta zama comfortable in tana tare da Mama akan Mamy, ko dan Mama ta fi sakar mata fuska dai bata sani ba. Dan lura kamar Mamy tana da mulki kaɗan, Mama kuwa akwai kirki da sakin fuska. Tana wannan tunanin Mama ta dawo ta ajjiye mata abinci ta ce, "Gashi nan ki ci." Islaha ta kalli abincin, sinasir ɗin ya yi fari ƙal, gashi ya soyu sai ƙhamshi yake yi. Lokaci ɗaya ya shiga ranta, ta ji tana son ci dan da gaske ta kwana biyu bata ci abincin gida ba sai na ƙetare. Mama ta ce, "Babu uzuri fa, sai kin ci Islaha. Ga shi can na saka miki a flaks, sai ki tafi da shi ki sake ci in anjima." Islaha ta miƙe cikin jin daɗin kulawar Mama ta ce, "zan wanke hannuna." Mamy ta nuna mata sink ɗin dining area ta ce, "Bismillah." Islaha ta ƙarasa ta wanke hannu ta dawo ta fara ci tana jin kanta a takure. Mama bata ce mata komai ba tv kawai take kallo, sai ta canja channel ta kai channel ɗin su Islaha a lokacin ana maimaita shirin da Islaha ta gabatar a safiyar. Mama ta ce, "Gaskiya kina ƙoƙari, kin iya gabatarwa sosai.” Murmushi ta yi bata yi magana ba, a lokacin Janan ta shigo ta ce, "Ahh sis, ke ce a nan?." Islaha ta ce, "Ni ce Sis, sannu da zuwa." Ta ajjiye labcourt ɗinta ta ce, "Yauwa Sis, na dawo daga aiki na gaji." Mama ta ce, "Kawo mata ruwa." Janan ta kawo mata ruwa sannan ta ce, "Hamma Ray yana nan? Ina da case da shi." Islaha ta ɗaga kai ta ce, "Yana nan." Janan ta ce, "Sai anjima zan zo, zai koya min assigment. Yau na ga ya sha yawo, hotunansa sai yawo suke duniya, ana sake tabbatar da lafiyarsa lau babu abinda ya same sa." Ita dai bata ce komai ba dan kamar maganar bata shafe ta ba, sinasir ɗin ma ta ajjiye ba dan babu daɗi ba sai dan ta ƙoshi. Ta miƙe ta wanke hannunta ta dawo ta zauna ta ce, "Na ƙoshi Mama, na gode." Mama tana murmushi ta ce, "kar ki sa ke cemin kin gode, me aka yi da za ki gode?." “ Islaha ta miƙe ta ce, "Mama zan koma." Mama ta ce, "to Islaha, za a biyo ki da abincin. Janan kira min Shamsiyya ta bita da abinci, yana kitchen a pack." Ta amsa Islaha ta fita tana girmama ƙarfin kirkin Mama. Tana fita Mama ta bita da kallo tana murmushi a bayyane ta ce, "Yaro man kaza, Islaha kenan, ba ki san wacece Saddiƙa ba. Duk da na ga Nadira ta fara sakin jiki da ke, ni kuma ba haka nake so ba, zan yi maganin sakin jikin da ta fara yi dan bana so, bana so ki dinga kallon kowa a gidan nan sai ni kaɗai, ni kaɗai nake so ki dinga yiwa kallon mai kirki a kaf gidan nan. Da hakan zan yi amfani na gyarawa Rehaan zama, kema na gyara miki zama. Yanzu na barki ki huta na ɗan lokaci, da na waiwayo ki babu labari." Islaha sai da ta shiga falon sannan ta karɓi abincin ta hau dashi sama dan kar ma chef ɗinsa ya gani ya kwashe. Bata gansa a falo ba ta shige ɗaki ta zauna a kan gadon. Sai a lokacin motar da ta taho zata takata tazo ranta a bayyane ta ce, "nima na ga motar tun tsayuwar mu, to kenan bina ake yi?" Ta ɗan yi shiru ta ce, "to su waye suke bina? Me na yi musu da suka yi ƙoƙarin kashe ni?. To ya aka yi aka san zan je can, meyasa zasu yi ƙoƙarin taka ni da mota?." Ya ɗan daki kanta ta ce, "su waye haka? Meyasa za a yi ƙoƙarin kashe ni, ko dai an gano ni ce a tare da Rehaan a motar da aka yi ƙoƙarin kashe mu?." Sai kuma ta girgiza kai ta ce, "akan me dan kawai an gano ni ce za a kashe ni? Akwai wani abun a ƙasa, ni na san akwai abinda yake faruwa tabbas." Waya ta ɗauka da niyar faɗawa Saheer, ta kira sa bai ɗauka ba sai ta kira Brr. Yana ɗauka suka gaisa ta ba shi labarin abinda ya faru, ya ɗan yi murnushi sannan ya ce, "ba akan komai aka so kashe ki ba, sai akan case ɗin nan. Islaha maganar nan ba ƙarama bace, da bana ɗaukar ta da mahimmaci, amma yanzu na ɗauka. Tabbas kashe ki aka so yi, ni a ganina sun yi tunanin Yafindo ta ba ki saƙon da Zainab ta bata." Islaha ta ce, "innalillahi! Hamma Suraj kisa fa.” "ki fa Islaha, ko shakka bana yi ke aka so kashewa. Ina ne gidan da Yafindon ta ke? Ki yi min kwatance da hanzari dan itama rayuwarta tana cikin hatsari." Sai jikin Islaha ya fara rawa jin zata sake saka Yafindo a cikin hatsari, ta faɗa masa inda gidan yake ya ce, "zan je n duba da kaina, amma maganar ta tsaya iya ni dake, kar ki faɗawa kowa Islaha” bai tsaya ya ji me zata ce ba ya kashe wayar. Ta ajjiye wayar ta ce, "Kashe ni aka yi niyar yi kenan, dan ina ƙoƙarin yaƙi da zalumci shine za a kashe ni?." Ta rasa tunanin da zata yi, gabaɗaya hankalinta ya koma kan Yafindo da bata san abinda zai same ta ba. •••••• A yana zaune yake a babban falo yana danan waya, fuskarsa gabaɗaya babu walwala, tunda aka rasa damar kashe Rehaan a karo na biyu ransa yake a ɓace sosai. Maza guda biyu ne suka shigo suka zauna suna jira ya basu damar magana. Sai da ya ga dama sannan ya ce, "ina jin ku." Ɗaya ya ce, "Ranka ya daɗe mun samo komai akan matar Rehaan." Sai ya ajjiye wayar hannunsa jin an ambaci wanda ya fi tsana sama da kowa a duniya ya ce, "ina ji." "Sunanta Islaha, ƴar jarida ce a gidan tv toron guiwa. Auren da suka yi da Rehaan ba a son ranta aka yi shi ba, an tabbatar min da neman kuɗin fansar saurayinta shine ya kai ta ga auren Rehaan ba dan tana so ba. Kuma ko a yau ta haɗu da saurayinta kuma suna soyayya sosai, kuma tana da niyar kashe auren Rehaan ta fito ta dawo gare shi. A taƙaice ba zaman auren take niyar yi dashi ba, akwai wani abun da ta shirya. Dan tana son saurayinta sosai, shima kuma yana sonta." Ya ɗaga kai ɗayan ya ce, "Ina da shawara ranka ya daɗe." Ya ɗaga masa kai alamun ina ji ya ce, "A ganina saurayin ya kamata mu samo, mu ba shi kuɗi sosai, dan na tabbbatar yana tare da ciwon rasata a zuciyarsa, tunda yana ƙaunar ta. Tunda har yanzu tana sonsa kuma tana haɗuwa da shi, ta hanyarsa zamu iya samun damar ganin bayan Rehaan." Ya kalle sa ya ce, "kamar ya kenan?." "Tunda ita tana sonsa kuma tana jin maganarsa, in ya bata wani abun ya ce ta bawa Rehaan zata iya karɓa tunda tana sonsa kuma tana ganin kamar ta cutar da shi tunda ta auri waninsa. Ka ga sai mu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, mun yi nasara a akansa sannan mu ɗora mata laifi. In muka bi ta hanyarta baza mu yi nasara ba, kowa ya faɗa mana bata da saurin yarda da mutanen da bata sani bsa, da shi kaɗai ta yarda a duniya." Ya ƙyalƙyale da dariyar samun nasara ya ce, "shawarar ka ta yi, a ina za a gano saurayinta?." Suka yi dariya jin sun kawo shawara kuma an karɓa suka ce, "Wannan mai sauƙi ne, zuwa gobe za mu zo da shi." Ya tafa hannunsa ya ce, "Dakyau, ina jira na ga hakan, a tabbatar an yi komai yadda ya kamata, kar a yi kuskure.” “an gama ranka ya daɗe.” “Za ku ji alert, da kun ɓata min rai, amma yanzu kun faranta min ɗari bisa ɗari." Suka yi dariya suka miƙe suka fita, ya miƙe yana dariya, ya ƙarasa gaban window yana kallon waje ya ce, "….mu je zuwa....” Nana Haleema. RDB3P35 Nana Haleema. Labiba tun bayan faruwar komai ta tsangwami kanta, ta koma wani iri ko kaɗan bata so ayi mata magana, ta killace kanta, ko wajen Aisha bata zuwa ko yaushe tana waje ɗaya tana tunani. Tana ɗaki a zaune ta yi tagumi tana tuna abubuwan da suka faru, bata taɓa tunanin zata aikata abu mai muni da ƙazantar abinda ta yi ba, kuma babban abinda yake sake ɗaga mata hankali a cikin garin Makkah ta aikata wannan ƙaton saɓon. Ko ya ya ta so ta manta sai ta kasa, da ta motsa sai tunanin ya zo ranta. Da sallama Aysha ta shiga ta ajjiye mata abinci a gabanta sannan ta ce, "Wallahi Labiba kamar ba wayayyiya ba, ni na rasa meye abin damuwa a cikin abinda ki ka aikata, ke da ki ka bi Ubaid ma balle kuma mace ƴar uwarki?." Labiba ta kalli Aisha ta ce, "har gwara shi, gwara na cigaba da sauraren irinsu guda dubu akan abinda na yi, ni ban taɓa tunanin zan aikata neman mata a rayuwata ba." "Yanzu kuma kin aikata, a cikin garin nan da unguwar nan da kin aikata wannan abun ba komai bane, yawancin matan da ki ke gani suna fantamawa da kuɗi harkar nan suke yi, ɗaiɗaiku ne ba sa yi. Kuma ba daina bin mazan za ki yi ba, za ki cigaba da yin duk abinda ki ke so normal ne, in kina son larabawa kamar su Ubaid duk samu. Labiba tunda ki ka zo nan baza ki samu matsalar kuɗi ba, in dai za ki bayar za a ba ki. Kawai ki ɗaura belt, in macen ce ta zo ki karɓe ta hannu biyu, in namijin ne ya zo shima ki karɓe shi hannu biyu, in duka ne suka zo lokaci ɗaya ki haɗa." Labiba ta ɗago ta kalle ta ta ce, "Na haɗa fa?." "to sai me? Gajiya kawai za ki tarawa kan ki, da kin watsa ruwa kin yi bacci shikenan komai zai wuce. Sau nawa muna haɗa mata biyu lokaci ɗaya? Sau nawa muna haɗa maza biyu lokaci ɗaya?. " "Ban kai nan ba Aisha." "Za ki kai ne, ai tunda ki ka zo nan a hankali idanunki za su buɗe. Ni ma da haka nake faɗa, amma yanzu ga shi na waye, ko maza biyar ne zan iya dasu lokaci ɗaya. Burina kawai a bani, indai za a bani na cika jakata an wuce wajen." Labiba ta yi shiru bata ce komai ba Aisha ta ce, "Ki miƙe ki nemi kuɗi, ko a gidanku sai kana da kuɗi ake yi da kai." "Kuɗi na zo nema, amma gwara na fara sana'a kamar yadda kowa yake yi, akan na sake anincewa da wannan ƙazantar." "kina tsaka soyawa ko dafawa za a zo a tashe ki, in aka yi rashin sa'a aka cafke ki sai nigeria, abinda ki ka tara ya tashi a banza da wofi. Labiba ban da ke ban taɓa kawo wata gidan nan ba, amma ke saboda akwai amana na kawo ki  saboda a amfana." Labiba ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba. Aysha ta ce, "Ki ɗauki abinci ki ci, ki yi wanka ki zo ki raka ni kasuwa na yi siyayya. Ki saki jikinki, ba wani abu mai muni ki ka yi ba, neman kuɗi Mama ta turo ki, kuma ga shi kin samu. Ki duba account ɗinki, na mayar miki da kuɗin zuwa naira na saka miki. Waɗanan da suke hannun ki tunda suna da yawa za a iya mayar miki dasu naira ki saka a bank ɗin ki ko ki tura gida." Bata ce komai ba, Aysha ta fita tana ji suna larabcin da itama yanzu tana fahimta. Bayan fitar Aysha ta ɗauki wayar ta ta duba kuɗin  da Aisha ta ce ta canja zuwa naira, ta ga naira dubu ɗari uku ne. Ta yi ajiyar zuciya tana kallon kuɗin, dan bata barin kuɗi account ɗinta sai zata turawa Mama take canjawa ta tura mata. Cikin sanyin ta turawa Mama dubu ɗari biyu, ta bar dubu ɗari a ciki ko amfaninsu zai ta so. Ta kalli agogon wayar ta ga su ƙarfe tara na dare, nigeria kuma ƙarfe bakwai kenan. Saitabkira layin Mama, tana ɗauka ta ji Mama ta ce, "ƴar albarka gaba da baya, Allah ya tsare min ke, Allah ya ba ki nasara akan duk abinda ki ke yi. Yanzu na ga kuɗi sun faɗo, daman ɗazu nake zancen ki, nace baiwar Allah nan kwana biyu ban ga saƙo ba, ashe kina tafe." Labiba sai ta ji daɗi a ranta ta yi murmushi ta ce, "Amin Mama. Ina nan ta faffukar aiki dan na turo miki kuɗi." "Na san da haka Labiba, ki cigaba da dagewa in dai za ki samo mana kuɗi ko wanne aikin ne ki yi. Yanzu maganar da nake miki daga tafiyar ki zuwa yanzu kuɗin da ki ke aikowa har an kusa siyin babban fili, kin ga kuwa tafiya ai ta yi riba." Labiba ta yi murmushi ta ce, "Gaskiya ne Mama. Ina Hanan?." "Yanzu ta fita, amma nasan bazata jima ba zata dawo." "Baffa fa?." "Yana nan, kin san dai ba dai na ce miki komai a kansa ba." Ta yi dariya ta ce, "Gaskiya ne." "Kar ki dinga tunanin dawowa gida, ki yi zaman ki a nan sai kin zama hamshaƙiyar mai kuɗi sannan sai ki dawo. Cikin satin nan akwai waɗanda zamu aiko dasu in Allah ya yarda." Labiba ta ce, "To Mama, sai anjima." "Allah ya yi miki albarka." Ta amsa da amin ta kashe wayar. Aisha da take tsaye a kanta kafin Labiba ta yi magana ta ce, "Kina jin yadda take saka miki albarka, kuma ki ce ke za ki bar gidan nan, to ki je ina?." Labiba ta kalle ta ta ce, "Ni ban saba da harkar nan ba, shiyasa gabaɗaya na takura." Ta dafata ta ce, "Kar ki damu, za ki saba a hankali, nan gaba za ki fi amincewa da ita fiye da wanda ki ka yi a baya." Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Shikenan, Mu je." Aisha ta bata hannu hannu suka tafa ta ce, "ko ke fa yar gari, mu je." Labiba ta yi dariya sannan suka fita tare. **** Mama tana kashe wayar ta yi baƙi suka shigo da sallama, ta amsa tana bisu da kallo ganin ƴan mata ne guda biyu kuma bata san su ba. Suka gaisa sannan ta ce, "Ban gane ku ba." Ɗaya ta ce, "nan ne gidan woman leader ko?." Mama ta ce, "Gani a zaune ina kallon ki." Ɗaya ta ce, "Sunana Ikilima, wannan ƙawata ce sunanta Ma'arufa. Mun zo ne muna so a yi mana hanyar barin ƙasar nan, muna so mu je saudia aiki." Mama ta bi su da kallo ta ce, "To ai ba haka kawai ake tafiya aikin ba, ba haka kawai ake kwaso jiki ace ana so a tafi aiki ba ƴan mata. Ina iyayen ku?." Ɗaya ta ce, "Ba ma so su sani, muna so mu samu kuɗi ne kawai." Mama ta taɓe baki ta ce, "Yanzu aikin saudia ya zama na ƙa'ida, sai kina jin larabci ko turanci, sun daina karɓar waɗanda basa jin yarensu, saboda wahala ake sha wajen fahimtar maganar su. Kun iya?." Iklima ta ce, "Na iya turanci sosai, larabcin ma ina ji, amma ba sosai ba." Mama ta kalli ɗayar ta ce, "kefa?." "nima na iya, babu yaren da ba ma ji." Mama ta ɗaga kai tana binsu da kallo, daman ana neman ƴan matan da za a kai aiki, amma bata sani ba ko sun yi daidai da waɗanda ake nema ko ba su yi. Ita bata damu da amincewar iyayensu ba, indai su sun amince zance ya ƙare. Mama ta ce, "ku bani lambar waya, in na gama komai zan kira ku." Jikinsu har rawa yake suka bada lamba saboda suka yi mata godiya suka fita. Tana fita Baffa ya shigo ya kalle ta ya ce, "ki cigaba Zulaiha, wata rana za ki yi danasanin tura yaran mutane wata ƙasar aiki, za ki ɗanɗana irin abinda iyayensu suke ɗanɗanawa. Zulaiha wallahi za ki yi kuka da idanunki, a lokacin da kuka bazai yi miki amfanin komai ba, baza ki taɓa cin ribar haka ba." Mama ta haɗe rai tana kallon Baffa ta ce, "Ni fa ba karuwanci nake tura su ba aiki ne." Baffa ya yi murmushi kawai ya fita. Mama ta fara mita tana ta bala'i ita kaɗai har Hanan ta shigo ta same ta sai mita take yi, bata ce komai ba ta wuce, jim kaɗan ta dawo ta ce, "Mama kin san me?." Bata kalle ta ba ta ce, "Sai kin faɗa." "Kin ga ƙatuwar motar da ake yawo da Islaha kuwa?..." "Mtsww!" Ta yi tsaki bata ce komai ba. Hanan ta ce, "Ni na ji labari daga bakin masu aikin gidan, na ji ana cewa Rehaan yola aka aura mata." Mama ta kuma yin dogon tsaki ta ce, "Shine me? Ko shi Rehana ɗin ta aura sai me?." "Ta samu cigaba a rayuwarta fiye da yadda ki ke tunani." "Ta samu mana ina ruwana? Ni daman bance kar ta samu ba, ɗana ne bazata aura ba wallahi. Ta je ta auri ɗan ƙaruna ma ƙarewar kuɗi, ita ta ga zata iya. Ni fa ba dan kin yi zancen ta ba ni na manta da shafin rayuwarta." Hanan bata ce komai ba ta koma ciki. Washr gari. Saheer yana fitowa daga gida ya ga mota ta tsaya a kusa dashi, a tunaninsa Islaha ce a bayan motar amma sai ya ga maza biyu sun fito. Duk suka ba shi hannu suka gaisa, sannan ɗaya ya ce, "na san baka san mu ba." Saheer da ya ke kallonsu ya ce, "gaskiya ban san ku ba." Ɗaya ya yi murmushi ya ce, "In baza ka ba mu dama da mun shiga mota mun tattauna na mintina biyu." Saheer da yake yi musu kallon mamaki ya ce, "A kan me kenan?." "Akan wani abu mai mahimmaci, wanda zai sa ka ka ƙaru sosai." "Meye shi?." "Inda zaka shiga motar zaka ji. Ba sace ka zamu yi ba, magana ce kawai zamu yi da kai, in ka amince shikenan." Ya ɗan yi jim yana tunani, sai kuma ya shiga gaba ɗaya ya shiga baya ɗaya maxaunin driver. Saheer ya ce, "Ina jin ku." Wanda yake zaune a mazaunin driver ya kalli na bayan, shi kuma ga ɗauko jaka a gefensa ya buɗe, ya nunawa Saheer ya ce, "Miliyan biyu ce cash." Da mamaki ya ce, "ta meye?." Na gaban ya ce, "Mun zo ne akan Islaha, yarinyar da ta rabu da kai ta auri Rehaan Yola." Saheer ya nutsu sosai sannan ya ce, "Me ta yi?." Ya girgiza kai ya ce, "Wani aiki mu ke so saka ta ta yi mana akan Rehaan, aiki ne ba na cutarwa ba, sai na son sanin wasu abubuwa akan cinikaiyyarsa. Tunda ita tana tare da shi a matsayin matarsa, kai kuma kana tare da kai a matsayin wanda take so, har yanzu tana girmama ka kuma tana jin maganar ka, shiyasa mu ka zo gare ka akan maganar." Saheer dai kallonsu yake yi sannan ya ce, "Ban gane ba." "Kana ji, muna so za ka dinga saka Islaha ta dinga yi mana wasu abubuwa a game da Rehaan, ita zata yi ba kai ba, kai aikinka kawai ka dinga sakawa tana yi, cikin hikima da basira yadda baza ta fahimci aiki ka ke yi ba." Ya yi shiru ya zuba musu ido bai ce komai ba, na bayan ya ce, "in ka amince wannan kuɗin naka ne, aiki na farko in ya tabbata akwai naira miliyan biyar da za a ƙara maka, da alƙawarin duk aiki ɗaya naira miliyan biyar." Saheer ya ce, "wanne irin aiki ne wanann?." "Abokina ai na faɗa maka, ba sai na maimaita ba." Saheer ya girgiza kai yana kallonsu ya ce, "Shikenan maganar?." Kafinsu ce wani abu ya buɗe motar zai fita, amma kasancewar basu cire lock ɗin ba bata buɗe ba. Wanda yake kusa da shi ya ce, "kar ka yi wasa da damar ka, ba kowanne lokaci ake samun irin wannan damar ba a rayuwa, kuma ita zata yi aikin ba kai ba, aikin ka kawai bata umarni kana daga gida kuma kana samun kuɗi." "Bazan yi ba." "Za ka yi Saheer, ka je ka yi tunani. In ka shirya..." ya faɗa yana saka masa takarda a gaban aljihu sannan  ya ce, "ka kira ni, a shirye nake ko yaushe, kiran wayar ka ɗaya ya mallaka maka kuɗaɗen da aka nuna maka. Kar ka manta Saheer, naira miliyan biyu ce cash!." Saheer ya yi jim yana tunani, kafin ya fita daga motar ya koma gida dan ya fasa zuwa inda zai je. Nana Haleema. RDB3P36 Nana Haleema. Saheer yana shiga Sadik ya kira shi ya ce yana jiransa a mota, dole ya kuma fitowa ya ya shiga motar ya zauna yana dafe kansa. Sadik ya ce, "baza ka daina saka damuwar Islaha a ranka ba ko? Har yanzu ba ka gama samun lafiya ba." Saheer ya ce, "Ba a kan Islaha bane." "To me ye?." Saheeer ya ce, "Wani abu ne ya faru yanzu nan, shine ya ɗaure min kai." "Me ye?." "Wai ni aka zo aka samu za a biya kuɗi, ni kuma na dinga saka Islaha tana yiwa Rehaan Yola leƙen asiri akan ayyukansa. Harda two millions naira cash, in na yi aikin farko kuma akwai five, kai duk aikin da zan yi musu akwai five millions da za a bani." Sadik ya ce, "Tofa, sai ka ce me?." "Ni abinda ya bani mamaki, ta ya aka yi suka sanni da ita har haka? Ya aka yi suka san muna magana da ita har yanzu?." "Kai kana raina harkar masu kuɗi kenan, in suna son abu mintina kaɗan an yi an gama." "Na yarda kam yanzu. Dan har yadda auren ya faru sun sani, sun san har yanzu muna haɗuwa da ita." "Me ka ce mu su?." "Me zan ce kuwa, na ce ban amince ba." "Da aikin?." "Eh mana." Sadik ya ce, "Amma kai gaula ne wallahi, dama ta zo maka har inda ka ke ka ce baza ka yi ba? Ba fa wani abun mara kyau zaka yi ba, ɗan leƙen asiri za ka zama shima kuma ba a bayyane ba. Kana zaune a gida za a dinga ba ka naira miliyan biyar, kuma sai ka ce baza ka yi ba? In ba ka yi ba a ina za ka sake samun wannan damar?. Ai wallahi in ni ne kullum sai na saka ta yi min aiki, ka ga a kullum ina da miliyan biyar." Saheer ya ɗaga ido ya kalle shi ya ce, "in maganar ta fito na saka ta a matsala kenan ko?." "Ya za a yi maganar ta fito? Babu wanda zai san maganar nan kaima ka sani." "Ni bazan iya ba" "Ka huta. Amma ka yi tunani, tana can ta yi aurenta ta bar ka, kuma ga dama ka samu tana neman kubce maka. Da zaka ɗauki shawarata da na ce ka yi, ka ga ko babu komai za ka tara kuɗi ka wuce takaicin ka." Bai ce masa komai ba suka fara tafiya, zuciyarsa tana tunani akan abinda ya kamata ya yi akan lamarin da ya sako shi a gaba. ** Rehaan yana zaune a gaban Abba suna sallama zai tafi united kindom. Abba ya kalle shi a nutse ya ce, "Yanzu tafiyar ta tashi kenan?." Rehaan ya ɗaga kai ya ce, "eh Abba, na rasa sim card ɗina na can, dole sai na koma." Abba ya ce, "meyasa baza ka tafi da matarka ba?." Rehaan ya ɗan yi shiru kafin ya ce, "kafin ayi mata processing visa za a ɗauki lokaci, ni kuma sauri nake na je na dawo." "Rehaan kenan, ka manta kai haifaffen ƙasar ne? Ta ya ya visa shiga ƙasar da aka haife ka zata yiwa matar ka wahalar samu?. Kuma visar united kindom ai bata wahala, da kai Us ce sai ne sai na ce za a sha wahalar samu." Rehaan ya ɗan shafa kai alamun rashin gaskiya, sai kuma Abba ya ce, "sai dai kuma tana aiki, na san baza ta bar aikinta ta bika ba." Rehaan sai ya samu mafita, ya ce, "Saboda aikin nata ma shiyasa ban yi wannan tunanin ba." Abba ya ce, "Babu laifi Rehaan. Amma ka san irin zaman da za ka yi a can, kar ka je ka yi zauna ka ƙi dawowa kamar yadda ka saba, yanzu kana da wata a ƙarƙashinka, duk da ba sonta ka ke yi ba amma sunanta matarka." Rehaan cike da gajiya da maganar Islaha ya ɗaga kai dan shi Allah Allah yake ya bar wajan Abba, ya ce, "zan yi in sha Allah." Abba ya ce, "Shikenan, Allah ya kiyaye hanya." Ya amsa da amin, ya miƙe ya fita. Sai kuma ya shiga ya shiga wajan Daada bayan sun gaisa ya ce, "Zan koma Uk." Daada ta harare shi ta ce, "za ka koma U me?." Ya wani kalle ta yana hararar ta ƙasa-ƙasa ta ya ce, "Uk na ce." "burtaniya kenan ko?." "Eh." "Ka tafi ka bar amarya ka da wa?." Rehaan ya yi mata shiru bai amsa ba, Daada ta sake maimaitawa ta ce, "Da kai nake malam, ita amaryar taka a wajenwa za ka bar ta?." "Wajen ki" ya bata amsa yana kallon ta. Daada ta harare sa ta ce, "Kai bana ciki da wulaƙanci, ka ga wasa a cikin idona?" Ta faɗa har da cire glasses yadda zai ga idanunta dakyau. Rehaan ya ɗaga ido ya kalli idanun nata, sai ya ga bai ga komai ba sai ja da suka yi kamar wacce ta sha sigari. Bai san ya yi dariya ba, ya rufe bakinsa da hannunsa kafin ya cire ya ce, "Ban ga wasa ba, na ga dai ya yi jah kamar wacce ta yi smoking cigarettes." "Meye kuma moki sigiret?." Rehaan ya yi murmushi ya ce, "ga shi nan a kusa dake" ya faɗa yana nuna mata goron da yake ajjiye a gefenta. "Goro ne yake saka jan ido ban da iyayi da ƙarya irin na ka?. Jarumtar kenan, duk inda jaruma da jarumi suke haka za ka ga idanunsu jajaye masu ban tsoro. Ba irin na ka idanun ba, farare kamar na mai yaron ciki, babu wani gwarjini balle ban tsoro. Kai fa ta ko wanne ɓangare ba ka yi kama da jarumi ba, ni ɗin nan na fika zubin jarumai." Rehaan bai ce mata komai ba, dan ba ya so ya biye mata ta zaunar dashi. Daada ta ce, "Ka faɗa min, ka bar ta da wa? Amayar da bata fi sati ɗaya a gidan ka ba zaka tsallake ta ka bar ƙasar, kai ko ɗokin amarcin baka yi?." "Na bar miki ita." "Kai bana son iskanci, me ka ke nufi?." "Ai ba jimawa zan yi ba, sai anjima" ya faɗa yana fita da hanzari kar ta tara masa gajiya da ciwon kai. Yana jiyo ihunta daga bayansa bai koma ba, dan ya san ya gama da Abba, ko da ta kirasa da ya ce mata saboda aikinta an wuce wajan. A wajan Mamya ya jima sosai suna sallama cikin ƙauna da kewar juna, sai gab da zai tafi sannan ya fara shirin barin wajen Mamy. Rehaan ya miƙe tsaye ya ce, "Mamy zan tafi." Mamy ta ce, "Rehaan meyasa baza ka tafi da ita ba?." Ya juyo cike da gajiya da maganar ta ya ce, "kowa sai ya yi min maganar ta. Abba ya yi min maganarta, Daada ta yi, ga shi kema kin yi min. Na je da ita ta yi me a can? Mamy aiki ne yake kaini, ba hutawa nake zuwa yi ba. Kowa ita, me zan je da ita ta yi, me zata yi min?." Mamy bata ce komai ba dan ta san baya so, sai ta yi murmushi kawai, shi kuma ya yi hugging ɗinta ya ce, "sai na dawo." Ta shafa kansa ta ce, "Kar ka daɗe." "In sha Allah" daga haka ya fita ya shiga mota aka ja suka fita daga gidan. Islaha bata san abinda yake faruwa ba, gabaɗaya jikinta a sanyaye yake saboda akan abinda ya faru da ita jiya, ga maganar da suka yi da Barr, na neme shi dan ta san abinda ake ciki shiru bai ce mata komai ba. Kasancewar weekend ne bata yi shirin fita ba, tana ɗaki a kwance bata damu da ta ji motsinsa ba. Yunwa ce ta dame ta sosai, sai ta fito falon ta gan shi babu haske kamar ko yaushe. Ta sauka ƙasa ta ƙarasa dining table ta ga breakfast yana nan kamar ko yaushe, kuma da alamun an taɓa dan ga plate da mug nan a wajen, ga kuma ragowar da aka rage a ajjiye. Islaha ta harari plate ɗin ta ce, "yau ragon Mamy an tashi da wuri kenan" ta faɗa tana jan zuba abinda zata ci, ta ci yadda take so sannan ta koma sama. Tana shiga ɗaki kiran Barr yana shigowa wayar ta, da hanzari ta ɗauka ta ce, "Hamma tun jiya nake jiran ka shiru." Ya ce, "Islaha ina sane dake, ina tattara komai ne shiyasa." "Ya aka yi, ka je gidan?." "Na je." "Tana nan?." "Ban same ta ba, an tabbatar min da bayan fitar ki babu jimawa aka ga wasu sun shiga gidan, daga nan aka ga ta haɗo kayanta ta bar gidan." Islaha ta dafe ƙriji cikin tashin hankali ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amma ba su yi mata komai ba ko?." Ya ce, "Babu abinda su yi mata komai ba, kawai dai an ga ta haɗa kayanta ta bar gidan. Hakan alamu ne da an yi mata barazana a kan zuwan ki, shiyasa ta bar gidan." Ta dafe kai ta ce, "na shiga uku! Hamma na raba mata da muhallinta." Jin zata fara kuka sai Suraj ya ce, "Kar ki damu, aikin zai zo da sauƙi, yanzu nemo inda take zamu saka a gaba, daga nan sai mu san abinda zamu yi." "A ina zamu san inda take?." "Wannan ba matsala bane zan duba, dan ya zama dole sai mun nemo ta, itace mace ta ƙarshe da ta yi magana da Zainab, kuma Zainab itace kaɗai hujjarmu, dole mu nemo ta." Islaha tankasa cewa komai sai kuka da take yi. Daƙyar ya rarrashe ta ya kaehe wayar. Yana kashewa kiran Saheer ya shigo, tana ɗauka ta fashe masa da kuka mai sauti...... Hankalim Saheer ya tashi sosai ya ce, "Lafiya ki ke kuka, faɗa min me ya faru?." Cikin kuka ta ce, "Na shiga uku Hamma." "islaha meye?." Bata ce komai ba sai kuka da take yi, sai da ta gaji sannan ta ba shi labarin komai. Ta ɗora da cewa, "Yanzu ina za a ganta, in aka cutar da ita fa?. Na zama silar ɓacewar mutum biyu, ga Yafindo ga Zainab." Saheer ya ce, "Ki daina kuka, in Allah ya amince babu abinda zai same ta." Jin ta sassauta murya kukan ya ragu sai ya ce, "Na faɗa miki ki dinga bin komai a sannu bakya ji, yanzu da an kashe ki fa? Meyasa za ki je wajan ke kaɗai ba ki tafi da police ba? Da sun taka ki da mota kin mutu me gari ya waya?." "Hamma na damu ne, ina so na kawo ƙarshen....." "Nima na damu, damuwar ki damuwata ce. Ki tambayi Sadik, babu inda ba na zuwa a kan neman Zainab, babu information ɗin da ba na samu akan gidan saboda na taimaka miki ki yi nasara akana binda ki ka saka a gaba. Kin cika gaggawa, bakya bin komai a hankali, ke ko yaushe sai ki ce a take ki ke so ki yi abun. Ko yaushe abinda ki ke so shi za ki yi, bakya shawara da kowa sai dai kawai ki zartar." Jin yana ta yi mata faɗa sai ta yi shiru. Saheer ta ce, "ga shi nan har an fara harin ranki akan maganar, da sun taka ki da mota da ba ki cuce mu ba?." "To ka yi haƙuri." "ya zan yi miki in ban haƙura? Ai dole na haƙura." "To ka daina yi min faɗa, Allah na damu ne shiyasa ka ga ina waɗanan abubuwan. Ina so na kawo ƙarshen abun, bana so abun ya cigaba da gaba saboda yara masu tasowa. Lokaci yana ta tafiya, na kasa yin komai shiyasa na damu." Ya sauke numfashi ya sassauta murya ya ce, "Na sani, nima ina fatan hakan. Yanzu me Barr ya ce?." "ya ce ya zama dole a nemo ta, ita kaɗai ce hujjar mu take hannunta." "A ina za a ganta?." "Bamu sani ba." "shikenan, Allah ya sa a ganta ɗin. Da alama abinda yake hannunta babba ne, tunda ki ka ji ana maganar an neme ta an rasa." "Shine abinda nake nima." "Shikenan, Allah ya bamu sa a. Amma ki dinga yi a hankali, ki dinga bin komai a nutse, kin ji?." "In sha Allah." Saheer ya ce, "Zan kira ki in anjima" ya faɗa yana kashe wayar. Ta bi wayar da kallo tana lumshe ido, tana tunanin ina Yafindo ta tafi?........ RDB3P37 Nana Haleema. Har dare Islaha bata san Rehaan ba ya nan ba, tana ɗaki yin komai a sanyaye cikin tunanin abinda ya kamata ta yi akan matsalar da ta yi mata dabaibayi. Bayan sallar i'sha tana zaune a sama ta ji ana hayowa saman, sai ta zubawa ƙofar ido har ta ga Banisha ta shigo. Suna haɗa ido Banisha ta yi murmushi tana kallon Islaha ta ce, "Sannu Sis, Mamy tana neman ki." Islaha ta yi murmushi ta ce, "To mu je tare" ta faɗa tana gyara mayafin da ta yi sallah da shi suka fito tare. A zaune ta samu Mamy a falo ita da Ikram suna zaɓen kaya a waya. Sallamar ta ya saka suka ɗago suna kallonta duka su biyun, Islaha ta ƙarasa ta zauna sannan ta ce, "Mamy barka da dare." Mamy ta ce, "Barka dai Islaha. Ya ki ke?." "Lafiya lau." "Kin san Rehaan ya yi tafiya?." Islaha ta kalli Mamy suka haɗa ido, sai Mamy ta yi mata kwarjini sosai, hakan ya saka ta sunkuyar da kai ta ce, "ban sani ba." Mamy ta ce, "Ya koma Englaand, bazai dawo ba sai nan da two weeks. Ban sani ba ko chef ɗinsa yana zuwa?" Ta faɗa da sigar tambaya tana kallonta. Islaha ta ce, "Yana nan, ko yanzu ma an yi dinner." Mamy ta ce, "Good. Na yi tunanin babu abinci ne shiyasa na kira ki na faɗa miki, in kina son abinci sai ki faɗawa maids ɗina su dinga kawo miki, tunda akwai abinci a can shikenan." Islaha ta yi shiru tana so ta yi magana amma ta kasa, sai kuma ta buɗe baki daƙyar ta ce, "Mamy ni....." sai ta yi shiru ta kasa ƙarasawa. Mamy cikin kulawa ta ce, "Ina jin ki, faɗi abinda yake bakinki." "Bazan iya kwana ni kaɗai ba, tsoro nake ji." Mamy ta ce, "babu matsala, ki dawo nan sai ki zauna har sai ya dawo." Islaha sai ta ji daɗi a ranta ta ce, "To, na gode." Mamy ta ce, "za ki iya komawa, in kin gama abinda ki ke yi sai zo sai Kiddo ta nuna miki inda za ku zauna." Islaha ta amsa cikin jin daɗi kafin ta miƙe ta fita. Mamy ta kalli Ikram ta ce, "Kamar tana da hankali ko Ikram?." Ikram ta ɗan saukse numfashi ta ce, "Babu laifi." Mamy ta murmusa suka cigaba da duba kayan da suka yi order. Islaaha tana komawa apartment ɗin Ray ta ce, "Haka kawai a bar ni na kwana ni kaɗai a nan sai wannan mahaukacin ya zo ya ɗaga min hankali? A zo a sake yi min sharri a ce ni na kawo shi da yake ga shugabar ƴan iska. Gwara na je can ɗin na zauna, ni da ace ma Mamyn zata yarda da ko yana nan a can zan zauna, bana son haɗa inuwa ɗaya da shi. Allah na tuba zaman kwana nawa ne? Balle ma yanzu da zan daina ganinsa da wuri zan ga lokacin yana gudu. Kafin ya yi two weeks ya dawo, ni kuma na yi three weeks a gidan nan, lokaci yana ta raguwa. Allah ya raka taki gona" ta faɗa tana hawa sama, har wani daɗi ta ke ji a ranta in ta tuna ya bar garin, bata son haɗa ido da shi ko kaɗan. Harda hararar ɗakinsa sannan ta shiga ɗaki ta ɗauki abinda ta san zata ɗauka, ta kulle ƙofar ta fita dan ita zaman ne baza ta iya ita kaɗai ba, tsoron Salman take ji sosai. Da sallama ta shiga apartment ɗin Mamy Banisha ta amsa ta ce, "Sis sannu da zuwa, mu je na nuna miki ɗakin." Islaha ta yi murmushi ta riƙe hannunta kamar yadda ta miƙo mata hannu, suka shiga ciki dan Mamy bata parlor Ikram ce kaɗai a zaune. Banisha ta buɗe wata ƙofa suka ga dogon corridor wanda ya sha decor kayan adon parlour, sai ɗakunann a jere. Banisha ta buɗe mata ɗakin ta ce, "Shigo Sis, kina san nan ina ne?." Islsha ta ce, "sai kin faɗa." "Tsohon ɗakin Ray, har yanzu in ya so bacci a nan yake zuwa ya kwana, kin san yana son bacci a wajan Mamy." Islaha ta murmusa tana kallon Banisha, dan ta lura iyalan Mamy suna da magana, irin faɗi ba a tambaye ka ɗin nan bane, har ita kanta Mamyn tana da magana, Rehan ɗin ne dai sama-sama. Islaha ta ajjiye kayan hannunta tana kallon ɗakin, ɗaki ne babba mai kyau sosai, komai akwai a cikinsa kamar ana kwanciya a ciki. A lokacin Mamy ta zo wucewa, ta gan su a cikjn ɗakin ta ce, "Kiddo ku dawo falo a gyara ɗakin nan, akwai ƙura." Islaha ta kalli Mamy da take tsaye a bakin ƙofa, ta ga kanta babu ɗankwali har ta canja kaya zuwa kayan night wears. Islaha ta zuba mata ido tana kallon ta, in ka kalle ta baza ka ce itace ta haifi ƙaton saurayi kamar Rehaan ba, baza ka ce ta aurar da ƴa kamar Riyya ba, tana da kyaun jiki sosai, shekarunta ba su nuna a fuskarta ba. Islaha bata saba ganin haka a al'adarsu ta fulani ba, duk da ba wata shiga mara kyau Mamyn ta yi ba, doguwar riga ce ta bacci, sai gashinta da yake a buɗe ta naɗe ahi a tsakiyar kanta, sai hular sa take hannunta wacce zata saka. Kiddo da Islaha suka dawo falon, ita dai Islaha bata ga ƙurar da za a share ba, da ace akwai ƙura a ɗakin tana shufa zata jita a hancinta, ɗaki sai ƙhamshi yake yi a dinga zancen ƙura?. Suna fitowa falon Riyya da Jafar suka shigo, Ikram da Kiddo su ka yi tsalle suka suka rungume juna ita da Riyya suna murnar ganin juna. Riyya cikin farin ciki ta ce, "My Sisters" Suka ɗaga daga jikinta, Ikram ta ce, "Sis kin ga yadda ki ka yi kyau?." Murmushi ta yi ta ce, "Ina Mamy?." Mamy ta fito tana murmushi ta ce, "Gani nan Riyya." Riyya ta tafi da gudu ta yi hugging ɗinta, Mamy cikin murna ta riƙeta ta ce, "Amarya sannu da zuwa." Riyya ta ɗago ta ce, "Mamy na yi kewar ki." Msmy bata ce komai ba ta ja kumatunta ta kalli Jafar. Jafar ya murmusa ya ce, "Mamy ina yini." "Ya ka ke Jafar?." "Lafiya lau Mamy, Rehaan yana nan kuwa?." Mamy ta buɗe idananu ta ce, "Lah! Kai ma ba ka san ya gudu Uk ba kenan?." Jazy cikin mamaki ya ce, "bai faɗa min ba Mamy." Mamy ta yi dariya ta ce, "Ai yanzu haka ma bacci take yi, na tabbatar ya jima da shiga England." Jazy ya zauna ya ce, "Ya kyauta, tare fa nace za mu tafi, shine ya gudu." Mamy bata ce komai ba sai murmushi da ta yi. Jazy ya kalli Islaha suka haɗa ido, sai ta ce, "Ina yini, Mr Jafar." Jafar ya ce, "Hajiya Islaha, ya ki ke?." Islaha ta sake kallonsa jin ya saka mata hajiya a gaban sunanta, sannan tana mamakin yadda dukkansu suka saba da faɗar ya ki ke ko ya ka ke, har Mamy. Ta ce, "Lafiya lau." Mamy ta ce, "tana jin tsoron can, shiyasa na ce ta zo nan ta kwanta kafin ya dawo." Jazy ya ce, "hakan ya yi kyau." Mamy ta kalli Riyya tana nuna mata Islaha ta ce, "Riyya ga Islaha, sunan da suka mata kuma Islam, matar Yayanki." Riyya ta kalli Islaha sannan ta ce, "na san fuskar ta, amma na manta a ina." Jafar ya ce, "zaki santa, tana aiki a gidan tv." Riyya ta ce, "Sannu Sis, ya ki ke?." Islaha ta kalli wacce ake kira Riyya ɗin, sai ta tuna yadda Rehaan ya dinga yiwa Jafar masifa akan abinda ya yi mata. Ita yadda ya dinga masifa ta yi tunanin Riyya ɗin yarinya ce ƙarama, irin wacce bata wuce shekara sha bakwai ɗin nan ba, sai ta ga zata kai age mate ɗinta. Duk da bikinta ya yi trending a social media, amma da makeup a fuskarta bata gane ta ba sai yanzu da ta ganta babu kwalliya, tana ta girmama kyaun da iyalan Mamy suke da shi. Islaha ta ce, "Lafiya lau Sis" ta faɗa dan ta ga sun mayar da faɗar sis kamar ruwa a bakinsu. Shigowar Janan ya sake hargitsa wajan, suna ta ihun ganin juna kafin su shiga ɗakin Riyya gabaɗayansu. A lokacin aka gama gyaran ɗakin, Islaha ta shiga ɗakin dan zaman falon takura mata yake yi. Bayan ta shiga ɗaki Mamy ta kalli Jafar ta ce, "Tunda ka faɗa min wacece yarinyar nan sai nake jin sauƙin haushin auren da nake ji, sai na ke ji tana shiga raina sosai har na ke burin Rehaan ya karɓe ta a matsayin matarsa, dan na lura bata da hayaniya." Jazy ya ce, "Mamy islaha bata da damuwa ko kaɗan, kuma a kwanakin da zata yi a nan, zaki fahimci wacece ita, za ki iya sakawa ayi miki ɓoyayyen bincike a kanta, zaki fahimci abinda ta saka a gaba, wanda ko kaɗan babu Rehaan a ciki." Mamy ta ɗaga kai ta ce, "Zan yi hakan, kafin ya dawo ina so na tabbatar da wacece ita." Jazy ya ce, "Hakan ya yi kyau Mamy" daga haka ya miƙe ya fita. Su Riyya kuwa suna ɗaki sun saka Ikram a gaba akan soyayyar da take yiwa Rehaan, Riyya ta ce, "Ikram ya dai, har yanzu da batun Hamma Ray ɗin?." Ikram ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Riyya ban san ya zan yi ba, amma ina sonsa sosai, gashi kuma ya riga ya yi aure." Janan ta ce, "Ina ruwan mu da aurensa, in dai zai aure ki ba shikenna ba?." Riyya ta ce, "Kuma ba son auren nan yake yi ba, sannan matar ba type ɗinsa ba ce. Ƴaƴan gidan nan, da matan gidan nan, da sirikai gabaɗaya dukkansu farare ne tas, ita kaɗai ce mai irin wanann skin type ɗun, kin ga bata dace da shi ba." Ikram ta ce, "Amma tana da kyau, tana da kyaun da ni kaina na gani kuma na tabbatar. Ga wani gashi da take dashi, mai yawa da tsaho. Riyya duk gashin ki, kin ga dai kaf gidan nan kin fi kowa gashi ko? To ko ke baza ki nuna mata yawan gashi ba. Wani irin gashi ne da ita mai kyau, ga tsaho har baya." Riyya ta buɗe ido ta ce, "Da gaske?." "Wallahi, ni na gani a falon Mamy. Ta zo gaishe da Mamy Hamma Salman ya shigo ya ja mata mayafi har ribbon ɗinta ya faɗi. Kin ga yadda gashin ya buɗe har fuskar Hamma Ray ya sauka. Hmm! Ni na fara giving up, duk da na san ba sonta yake yi ba, amma tana da qualities ɗin da zai iya sonta nan gaba." Janan ta ce, "Ai Mamy a ɓangarenmu ta ke, zaki iya aurensa ko dan ita." Ikram ta ce, "Mamy ta fara sakkowa, da dai bata son auren, amma yanzu kamar ta yi accepting." Riyya ta ce, "Gaskiya Daada bata kyauta mana ba data ƙaƙaba masa wannna auren, yanzu da ke ya aura ba shikenan ba?." Ikram ta yi shiru kawai bata ce komai ba, suka cigaba da tattaunawa kafin su fito daga ɗakin. Nana Haleema. RDB3P38 Nana Haleema. Da suka fito ta ƙofar ɗakin da Islaha take suka zo wucewa, ta saka doguwar riga ta bacci wacce ta wuce guiwa da kaɗan, rigar tana da shape dan bata buɗewa, bin jiki take yi ta kwanta a ko ina. Ta saki gashinta har baya, tana tsaye ta juya baya bata san suna kallon ta ba. Ikram ta ce, "Kun gani ko, na faɗa muku daman ta haɗu." A lokacin Islaha ta juyo suka haɗa ido dasu, sai suka basar kamar ba kallonta suke yi na, Riyya ta shiga ɗakin ta ce, "Ma sha Allah, Sis kina da gashi mai kyau" ta faɗa tana taɓa gashin dan ya burge ta sosai. Islaha ta murmusa tana saka hula bata ce komai ba, ta zauna a gefen gado bata ce komai ba. Riyya ta ce, "Bara mu je wajan Mamy." Da kai ta amsa suka fita ta bisu da kallo ta sauke ajiyar zuciya kawai. Washe gari Islaha bata farka ba sai ƙarfe goma na safe, ta tashi ta yi wanka ta yi alwala ta yi sallar walha, ta ɗauki wayarta ta kira Barr Suraj bai ɗauka ba, ta ajjiye wayar kawai ta yi shiru. Apartment ɗin shiru, babu motsin kowa alamun bacci suke yi, sai ta miƙe dan tana so ta je apartment ɗin Ray ta ɗauko laptop ɗinta, ta saka hijjab akan doguwar rigar jikinta ta fito. Ko ina ƙhamshi yake yi, ta ƙarasa falo na biyu kafin ta fito main parlour ɗin. An gyara shi ya yi tas sai ƙhamhasi yake yi, ko ina haske babu alamun kowa bacci yake yi a ɓangaren. Motsi ta ji a bayanta sai ta juya sai ta ga Mamy ta fito daga kitchen, duk da sun gaisa da asuba sai da ta sake gaishe ta. Mamy ta amsa ta ce, "Har kin tashi?." Islaha ta ce, "Eh." Mamy ta ce, "Ga breakfast nan in kina so." Islaha ta ce, "To Maamy." Mamy ta kira mai aikinta ta ce, "Ki gyara min irish ɗin nan, kafin na fito a gama, bana so Dear ya ta shu ban gama breakfast ba." Islaha ta zaro ido jin wai Dear, ta kalli Mamy tana girgiza kai cike da mamakin sunan, dan dai ta san iyaye da an girma za a koma cewa abban wance. Mamy ta kalli Islaha ta ce, "in akwai abinda ki ke so ki ki faɗa musu sai a dafa miki." Islaha ta amsa Mamy ta juya ta shiga ciki. Islaha ta fita zuwa apartment ɗin tana fatan kar Allah ya haɗata da Salman, har zata wuce sai ta fasa ta nufi wajan Daada da niyar gaishe ta. Tana dhiga ta same ta tana shan tea a zaune akan kujera, tana ganinta ta sjjiye cup ɗin tana tafa hannu ta ce, "Ga islama, ga Ishlaya." Islaha ta yi murmushi ta ƙarasa har ƙasa ta gaishe ta, ta kalli Abba da wani babban mutum da yake zaune, ta gaishe su da girmama suka amsa. Abba ya nuna ta ya ce, "Itace matar Rehaan, na san baka santa ba." Yayan Abba ya ce, "Allah Sarki, kamar na san ki." Daada ta yi caraf ta ce, "ƴar jarida ce, ana haskota a ko ina." Ya ɗaga kai ya ce, "Tabbas a nan na santa kam, Allah ya taimaka." Daada ta ce, "ance min a wajan Nadira ki ka kwana ko?." Islaha ta ce, "eh Daada, ina jin tsoron can ne, shine ta ce na je na kwanta a wajenta." Daada ta riƙe baki ta ce, "Tunda nake da ƴar indian a gidan nan bata taɓa yin abinda ya burge ni kamar wannan ba, ashe su ma indiyawan sun san ya kamata, ba a yawon tsafi suka tsaya ba." Yayan Abba ya ce, "Haba Daada, ki bar wannan maganar mana." "Ƙarya na yi? Ai halinta ne. Farkon aurensu da ƙanin ka a ƙasar waje ta riƙe sa ya daina zuwa gaishe ni, sai da na miƙe tsaye da addu'a na ƙwato shi." "Daada ai kin ƙwato ɗin ko?." "Gashi a gabana kana gani." "Hakan ma mun gode Allah" ya faɗa yana miƙewa ya ce, "Daada zan koma, ya sunanki?" ya faɗa yana kallon Islaha. Maimakon Islaha ta amsa sai Daada ta ce, "Sunanta Islama." Abba ya yi dariya ya ce, "Sunan al'ada ne wannan, amma sunanta Islaha." Ya ɗaga kai ya ce, "Ma sha Allah, ya kamata a kawo ta ga ƴan uwa, na tabbatar bata san kowa ba." Daada ta ce, "kai da yake babansa ne sai ka faɗa masa ya amince, amma ni ai ya raina ni. Yanzu ba ya ganin darajata, ban isa na faɗawa Rehaan magana ta ji ba. Wacce ni, ni kaza?." Bai ce komai ba ya murmusa ya fita. Mata ne guda biyu suka shigo falon da sallma hannun ɗaya riƙe da yaro. Kana kallon fuskar ɗaya ba sai an ce maka jinin Umma ba ce, kamar su ta fito da Umma sosai, hannunta riƙe da hannun yaro guda ɗaya. Tun kafin su ta ƙaraso Daada ta ce, "Bana neman ku, ku koma." Mai kama da Umman ta ɗan ɓata rai ta ce, "Daga zuwa abin kirki." Sai kuma suka kalli Abba suka gaishe sa, ya amsa sannan ya ce, "Ya gidan da masu gidan?." "Suna lafiya lau, Wannan wacece?" Anisa ƴar Mama ta faɗa tana nuna Islaha. Daada ta harare ta ta ce, "Matar ɗan uwanki guda amma ba ki santa ba, kun raba kan ku da shi kamar ba jininku ba, kowa sai ɗan ɗakinsa yake zumunci da shi, kowa sai wanda babarsa ta haifa yake cewa shine ɗanuwansa. Duk son zumunci irin na Rehaan, kun saka ya ajjiye ku gefe kamar yadda ku ka ajjiye sa. Sai biki ya tashi, ka ga anyi anko ana hotuna kamar masu haɗin kai, nan kuwa kan ku a tarwatse yake. Sai ya yi aike da kuɗi kuma a amshe a saka a jaka a ƙara gaba. Duk abinda ku ka saka a ranku ku kuka sani, in Allah ya so ɗaukaka wani babu wanda ya isa ya hana, kuma da wahala a cikin dangi baka ga Allah ya ɗaga wani bar wani ba, ko da shine ɗan auta a dangin gabaɗaya. Shi Rehaan ta sa ƙaddarar sai ta zo akan ƴam uwa, musamman ku matan da ya fi sonku, amma ku ne ku ke watsa masa yaji a ido. Allah wadaran naka ya lalace." Duk sai suka haɗe rai cikin danasanin shigowa ɗakin Daada, Abba yana ji bai ce komai ba dan ya san gaskiya take faɗa, Rehaan ya ce masa in aka cire Janan da ƙananun yara ƴaƴan amaryarsa guda biyu, mantawa yake yi yana da ƴan uwa mata yaye da ƙanne. Duk yadda ya so su sake da shi sun ƙi, sun watsar da shi shiyasa shima ya jingina su a gefe, kowa ya yi rayuwarsa yadda yake so. Kuma da ba haka suke ba, daga baya ne suka canja gabaɗaya, kuma kowa babarta ce take zugata. "Ni fa Daada shiyasa bana son zuwa wajan ki wallahi. Kuma da ki ke zancen ba mu san matarsa ba ai ba a ɗauke ta an kai mana ita ba, tunda mu ne gaba da shi ba shine gaba damu. In da an kai mana ita har gida da mun santa har mun ƙulla zumunci." Daada ta yi tsaki bata ce komai ba, Islaha dai tana ji tana sake tabbatar da kan ƴam gidan a watse yake gabaɗaya babu haɗin kai. Amma a social media in suna biki in ka ga yadda suke shan anko su yi kyau sai ka ɗauka akwai zumunci mai ƙarfi a tsakaninsu, ita dai tana ta ɗaukar darasi a gidan, ta gama na haddace na gidansu Saheer ga sabo ta samu. Anisa da Sharifa suka fita daga falon Daada ba su sake kula ta ba. Bayan sun fita ta kalli Abna ta ce, "Laifin ka ne wallahi, kaine ba ka yi musu faɗa, kamar ba kai ka haife su ba, ko wacce tana iskancin da ta ga dama." Abba jin laifin zai dawo kansa sai ya miƙe ya yi mata sallama ya fita. Daada ta kalli Islaha, "Ishlaya kaf gidan nan babu mai son mijinki a cikin ƴam uwansa, daga Janan sai na wajan amaryar babansa, su kuma yara ne basu girma sosai ba. Sun ɗauki wani abu sun saka a ransu, tun yana bibiyarsu akan zumunci har ya gaji. Mutum ne mai son ƴan uwansa, yana da son ya kyautata musu sosai, duk sati akwai kuɗin da yake warewa na zuwa siyayya, duk da suna da aure bai daina basu ba, duk juma'a sai an ba da wannan kuɗi. Kuma duk ranar da ɗaya a cikinsu ta yi niyar barin ƙasar nan, waya kawai take yi masa, babu ko sisinta za je ta dawo. Yana so ya yiwa ƴan uwansa alkhairi su ji daɗi, yana so ya ji suna alfahari da kasancewarsa ɗan uwansu, yadda duniya take faɗar sunansa su kuma su yi alfahari da shi. Amma baƙin hali ya hanasu, kowa da abinda ya ƙudurce a ransa, kamar shine ya bawa kansa arzuƙin." Islaha tana jin Daada tana mamakin yadda ƴan gidan ba sa iya riƙe sirrinsu, komai faɗa suke a gabanta, basa tunanin ita baƙuwa ce a cikinsu. Islaha ta ce, "Allah ya kyauta." Daada ta ce, "Amin Ishlaya. Ke dai ki riƙe mijinki, ki zama masa inuwar da zai sha iska in ya kwaso rana." Islaha jin an fara yi mata wa'azi akan abinda baza ta iya ba sai ta miƙe ta ce, "Daada zan koma, sai anjima." Suka yi sallama ta nufi apartment ɗin har lokacin ko jikokin gidan babu kowa bacci yake yi.    Mama tana kallon fitowar Islaha ta window, tunda apartment ɗin Daada yana kusa da nata. Ta yi tsaki ta ce, "Shegiyar yarinya ƴar bariki, da iyayin tsiya da yauƙi kamar wata kuɓewa, ko waye ya aike ta ta je ta gaishe da Daadan oho. Na lura Nadira so take ta ɓata min gari, ta fara jan yarinyar nan a jikinta, billahillazi bazai yu ba, ba a banza na bari auren nan ya yu ba sai dan ƙudirina. Dole na san abinda ya kamata na yi, dole na yi abinda kowa zai farka daga dogon baccin da yake yi." "Mama." Kiran sunanta da ya saka ta ta juyo ta ta ga ƴarta ta biyu mai bin Zayyad ta ce, "Ke kuma lafiya ki ka fito da safiyar nan?." Anisa ta zauna tana haɗe tai ta ce, "in dai na zo gidan nan na je gaishe da Daada shine damuwata, mun shiga ni da Sharifa dan mu gashe ta, mu ka tarar da matar yaron nan Rehaan. A gabanta kin ji abinda take faɗa mana? Wai ba ma son Rehaan, kuma Allah ya ɗaukaka shi....." "Mama dama ana iya ɗauke ɗaukaka, da na ɗauki ɗaukakar nan na dawo da ita kan Hamma, ko Sameer ko Daady ko Amir. Haba, wannan baƙar magana har ina?." Mama ta gyɗa kai ta ce, "Shi ma ɗaukakar zata gushe Anisa, ɗaukakarsa zata gushe indai ina da rai." "Daman wannan itace wacce aka aura masa, ai na santa sosai. Babansu Khalifa yana son program ɗinta, Indai zata yi program ko ya yi missing a tv sai ya bibiya a youtube." "Shegiyar yarinya mai iyayin tsiya ba, itace matar da aka aura masa. Mai buɗaɗɗen ido, karuwa mai lasisi." "Karuwa kuma Mama!." "Ita fa, har aikatau ɗin ƙasar waje ta yi. Kuma gidan da ta ke zaune woman leader ake ceewa matar gidan, tantiriya ce lamba ɗaya." "Amma aka auro ta gidan nan?." "Ni na saka a yi hakan." "Akan me kenan?." "Akan Rehaan mana, da ita zan yi amfani na lalata rayuwarsa." Anisa ta ce, "ta wacce hanya kenan?." "Ta hanyar ta yarda dani, ni kuma zan bata abinda zata dinga ba shi kullum har ya bi jikinsa." Anisa ta ce, "amma kin san Mamy baza ta yarda ta amince da ke ba." Mama ta murmusa ta ce, "Ke dai mu je zuwa, Nadira ɗin banza da wofi, wallahi sai na ga bayan Rehaan. Ni ba kisan kai zan yi ba, amma wannan ɗaukakar sai ta gushe, sai an daina jin labarinsa, sai duniyar ta tsaya masa cak. Anisa in kina musu ku rubuta ki ajjiye!." Anisa ta yi murmushi t ce, "ni na san za ki iya Mama, ɗaukakar nan tasa da ƴaƴanki ta cancanta ba ahi ba. Yadda gidan nan yake a hannunki, Abba ma a hannunki, babarsa ta ke a hannuki, kishiyoyin su ke a hannunki, dukiyar mai gidan ta ke a hannun ƴaƴan li. Kamata ya yi ace sunan ɗakin ns ya yi tambarin da sunan da na Rehaan ya yi, ɗaukaka da ke ta dace ba da Rehaan ba." Mama ta yi dariya ta ce, "da zarar Rehaan ya yi ƙasa, to tabbas na ci gari." "Ki buɗe wuta Mama, dan kullum kasuwancinsa sake gaba suke yi, in ba mu farga ba sai dai mu buɗe ido mu ga mun zama ma su goge masa takalmi." Mama ta yi murmushi tana girgiza kai cikin mummunan ƙuduri ta ce, "a yi dai mu gani........ Nana Haleema RDB3P39 Nana Haleema. Saheer yana zaune a falon Mama yana cin abinci, gabaɗaya ba shi da walwala ko kaɗan, a hankali yake cin abincin kamar wanda aka yiwa dole, duk loma ɗaya da zai bakinsa Sudaisa yake ganowa a idanunsa, yana tunanin tana can suna bata abinci mara tsafta suna dukanta. Yana tunanin ko ya suka ƙare da black, ko ya suka ƙare da Arɗo bai sani ba. Wani lokacin sai ya ji kamar ya koma ya gano halin da take ciki. Baffa da yake zaune ya kalle sa ya ce, "Saheer yaushe za ka koma aiki?." Saheer ya kalli Baffa ya ce, "Na kusa in sha Allah, ina so a gama haɗa gidan can gabaɗaya, in ya so sai na koma." Mama ta yi caraf ta ce, "Abinda ba aure za ka yi ba, gidan me za ka takura kanka sai ka gama?. Ko ka kai kuɗin aure an saka rana ne?." Ya kalli Mama ya ce, "So nake na kammala gabaɗaya na huta kawai." Baffa ya ce, "ya kamata ka koma wajan sana'arka, ka cigaba da addu'a, Allah ya cigaba da kiyayewa." Ya amsa da amin ya ajjiye abincin ya fita. Haka kawai yake jin kewar Islaha a zuciyarsa, idanunsa ita suke so su gani, kunennsa suna so su ji muryarta, yana son ganinta matuƙa, kewarta ta dabaibaye masa zuciya da gangar jikinsa. Ya shiga ɗaki ya dafa bango yana ji zuciyarsa tana harbawa sosai, ya kasa cire son Islaha daga ransa, duk da ya san akwai auren wani a kanta, son da yake yi mata zunubi yake ɗaukarwa kanaa amma ya rasa yadda zai yi da zuciyarsa. Zuciyarsa itace take sarrafa shi ba shine yake sarrafata ba. Yana ji wayarsa tana ringing har ta katse bai ɗauka ba, aka kuma kira a lokacin ya ɗauka ba tare da ya duba ya ga waye mai kiran ba. Daga can ɓangaren aka ce, "Saheer ka shirya karɓar kuɗin ko ba ka shirya ba?." Ya ɗan yi jim yana tunanin su waye haka, kafin ya gama tunani aka kuma cewa, "Naira miliyan biyu taka ce, indai ka amince da abinda za ka yi mana." Saheer ya yi tsaki ya datse kiran, ta ya zai iya wannan abun mai kama da ganganci? Haka kawai ya jefa rayuwar Islaha cikin hatsari bata ji ba bata gani ba. Kuma in ya yi hakan kamar ya ci amanar ta ne, shi kuma bai shiryawa hakan ba. Sai kuma ya yi shiru yana tunani sai ya kira Sadik a waya yana ɗauka ya ce, "Sadik akwai kuɗi a hannunka? Akwai inda ba a gama saka kayan wuta a gidana ba, shi nake so na siyi na ƙarasa a huta. Bana son komawa Nijar ban gama abubuwan da suke gabana ba." Sadik da mamaki ya ce, "Gaggawar ta me ye?." "Ta aurena mana, ka manta nan da wasu kwanaki kaɗan Islaha zata dawo mu yi aure?." Sadik ya yi tsaki ya ce, "Wallahi ban taɓa sanin ba ka da hankali ba sai yau, kai wai har jiranta ka ke yi ta fito ka aure ta? Ko kishin abinda ka ke faɗa ji a ranka?." Saheer ya ce, "Kaine ba ka da hankali da ba ka san meye so ba, kuma meye abin kishin tunda ina sonta?." "Soyayya in dai irin wacce ka ke yiwa Islaha ce Allah ya yi wadaranta, dama nawa ka samu saboda ita ka ƙi karɓa?. Ko a yanzu akwai dama a hannun ka, amma kana ƙoƙarin saka ƙafa ka yi ball da ita." "Ka ga, in kana da kuɗi ka bani, in babu ka yi min shiru. Wata biyar kamar yau za ka ga ta zo, a ranar da auren ta ya mutu, a ranar nake so a ɗaura mana aure." "Ko? To kai za ka yi mata iddar kenan?." "Babu idda a zamanta da shi, ana idda ne don a tabbatar akwai ciki ko babu, to ita babu wannan labarin." Sadik ya sake yin tsaki cikin takaici ya ce, "Kai kana tunanin zata fito haka ba tare da anyi komai ba, kana zaton zama kawai suke yi a waje ɗaya ba tare da ya mori sadakinsa ba?. Ka tuna naira miliyan hamsin ya bata, a tunanin ka kuɗinsa a banza zasu tafi bai fanshe da wani abun ba?." Saheer ya ce, "Malam ya ishe ka haka, ka daina yi min wannan maganar." "Dole na yi maka, na lura kana neman ɓacewa daga hanya mai kyau, kana ƙoƙarin ɗora kanka a gurɓatacciyar hanya. Zan iya yi maka rantsuwa akan ko da Islaha zata fito baza ta fito kamar yadda ta shiga ba, in ma ta fito ɗin fa kenan. Gwara ka saki jikinka ka karɓi damar da ta zo maka, ka tara kuɗin gama gidan ka, in ta fito fine, in bata fito ba daman ka samu rabon ka." Saboda haushi Saheer kashe wayar ya yi ya dafe kansa, yana jin wutar kishi tana kunnuwa a zuciyarsa, shaiɗan sai hango masa Islaha yake yi cikin bahagon yanayi. Ya daki kanaa da ƙarfi, ya ɗauki waya yana kiranta amma bata ɗauka ba, ya yi tsaki yana ji kamar ya miƙe ya je gidan, da hanzari ya miƙe ya fita daga ɗakin cikin yanayi mai zafi. Islaha lokacin da ta shiga ɗaki laptop ɗinta ta ɗauko, har zata sakka downstairs sai ta kalli ƙofar ɗakinsa, ta tsaya tana kallon ƙofar a bayyane ta ce, "Sai na shiga ɗakin nan, na ga meye a ciki." Ta ajjiye laptop ɗin akan kujera ta shiga ɗakin, ta bi ɗakin da kallo dan komai a kashe yake ba ka ganin komai. Ta kalli gefenta ta ga switch, ta harari switch ɗin dan daƙyar ta iya amfani da shi da ta zo gidan, touching switch ne, wanda sai ka kula za ka gane yadda ake amfani da shi. Ta danna haske ya gauraye ko ina ta bi ɗakin da kallo. Ɗakin yana da wani irin kyau mai ɗaukar hankali, ga girma kamar zaka raba ball a cikinsa. Falon da yake cikin ɗaki ne yake burge ta, ta ƙarasa ta buɗe glass door ɗin ta bi falon da kallo ganin babu abinda babu a cikinsa kuma komai fari, ga wasu kujeru kamar gado kamar kujera. Ta tsaya tana kallon luxury parlour, kafin ta fito ta shiga prayer room da aka gidana shi a karkace, kai tsaye alƙibla ya ta kalla. Sai ta ji prayer room ɗin ya fi burge ta sama da falon, ga shi dai ba shi da girma, bai fi zaman mutum biyu ba. Ta kalli alkur'anin da yake ajjiye ta riƙe baki ta ce, "Ashe ya san karatun alkur'ani" ta fito tana kallon bed ɗinsa. Closet ɗinsa ta shiga tana kallo, ta ga kaya kamar wajan siyarwa, musamman suits da yallabiyya suna rataye a jikin anger, komai yana mahallinsa. Islaha ta wajan ta kalli bathroom ta ce, "Daga an fito daga wanka sai a shirya kenan. Allah ka yiwa Hamma arzuƙi ya yi min irin haka, har prayer room ɗin can ina so" ta faɗa tana ɗaukar hait burner ɗinsa. Tana kunnawa hayaƙi ya fara fita kaɗan kaɗan, ƙhamshi ya cika mata hanci, ta juyata a hannunta ganin samanta da comb, ta taɓe baki ta ce, "wai burner ta gashi ce kenan? Allah ya isa, ni da na ke mace ma ba na turara gashina, sai dai na saka hair spary na wuce wajan. Amma shi yana namiji kalli kayan gyaran gashi har ya fi nawa, kalli turaruka kamar ba a so. Allah ya yi mana arzuƙi mu samu abinda ya fi wannan, ba dan an gama gina gidan da zamu zauna Hamma ba, ai da na saka an yi min closet ɗin nan." Ita kaɗai take jawabinta ba da wani ba, ta kai hannu ta buɗe drawer, ta ga undies ne kawai a ciki a shirye kuma a ninke. Shorts ɗin gabaɗaya kamfanin Nike ne, haka takalmansa na ball, da slipper duk kamfanin Nike ne. Islaha ta taɓe baki ta ce, "Wannan dai sai dai in cleaner ɗinsa ne yake gyarawa, wancan ragon me zai iya? Komai ya gaji kamar ba namiji ba. Shi fa wannan da mace ya yi kama, bashi da wata kama da ta yi kama da ta maza, komai....."Maganar ta tsaya a lokacin da hotonsa ya gifta a idanunta ranar da ta gan shi babu riga. Ta runtse ido ta ce, "Astagafirullah! Allah ka sa na daina tunanin wannan mutumin." Bathroom ta buɗe tana kallo ta ce, "wow!." Ta shiga tana kallon ko ina a bathroom ba, ko body wash ɗinsa ma sun fi kala goma, ga perfumes, ga shampoos, towels, bathrobes da sauran haukan da bata san na meye ba. Ta gyaɗa kai ta ce, "Allah ka azurta ni, wallahi sai na yi irin banɗakin nan. Ni fa ina son luxury life, kawai Allah bai yi zan auri mai kuɗi bane, amma da anga gayu" ta faɗa tana kunna wani waje take iska ta fara fitowa alamun dryer ne. Bathtub yana waje ɗaya daban, mai cycle shape na mutane biyu, har da wani pillow a jikinsa guda biyu alamun an yi sa ne domin couples. Shower glass ma yana wani waje daban, ga latirine ɗin ma a wani waje daban, komai perfect kamar ka kwanta a ciki. Ta gama kallonta sannan ta fito tana kashe hasken ko ina tana raira waƙar sarkin waƙa tana cewa, "Allah ka ba mu kuɗi, amma wanda ya amsa kuɗi, amin." Ta gama kallon ta ta kashe hasken ta fito falo, ta ɗauki laptop ɗin ta sauka ta koma ɓangaren Mamy. Babu kowa a falon ta wuce ɗakin da aka ajjiye ta tana ta kunna laptop ɗin tana dannawa. Aiki take yi sosai, tana haɗa questions interview ɗin da zata yiwa guest ɗinta a gobe. Tana cikin aiki aka buɗe ƙofar aka shigo, ta ɗaga kai ta ga Banisha ta shigo da Laptop a hannunta tana cewa, "Bruh ga Sis Islaha" ta faɗa tana juya screen ɗin ta haska masa fuskar Islaha ita kuma ta kalli screen ɗin. Kai tsaye suka haɗa ido da shi yana zaune a sofa ya miƙe ƙafa, hannunsa riƙe cup yana shan tea. Kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kai, Banisha ta ajjiye mata laptop ɗin ta ce, "Ina zuwa" ta faɗa tana fita, ita kuma ta share shi bata kuma kallonsa ba balle ta ce wani abun. Shi kuwa kallonta ta yake yi yana mamakin ƙarfin hali irin na yarinyar, tunda suka fara zama bata taɓa ce masa good day ba, yanzu ma ga shi an haɗasu ta wani juyar da fuska tana aiki kamar bata ga kowa ba. In akace a duniya akwai macen da zata yi masa haka zai iya cewa ƙarya ne, amma ga wata da ya raina, yake yiwa kallon ƴar bariki ta mayar da shi kamar abin wasa. Islaha har ga Allah ta manta da laptop ɗin da Banisha ta bari a wajan, aikinta take yi hankali a kwance kafin ta duba wayarta. A bayyane ta ce, "ashe Hamma ya kira ni" ta faɗa tana kiransa. Shi dai Rehaan kallon ikon Allah yake yi, yana jinjina ƙarfin hali da zaƙewar ta, yana so ya ga adadin lokacin da za ta ɗauka tana raina masa hankali, shiyasa ya yi shiru yana kallon duk wani motsinta kamar tv. Saheer yana ɗauka ta ce, "Hamma ka kira ni bana kusa sai yanzu na ga kiran ka." Saheer ya ce, "Ina so na ganki Islaha, ya za a yi? Za ki zo ne ko na zo?." Islaha ta buɗe ido waje ta ce, "A'a kar ka zo, in an yi sallar la'asar zan fito, a ina zan ganka?." "Ki kira ni in kin fito ɗin, zan faɗa miki inda za ki je." "to Hamma. Ka siya min lays cheese." Saheer ya amsa mata ita kuma ta kashe wayar tana murmushi har ga Allah ta manta da wani Rehaan a gefenta. Kamar an ce ta juya ta kalli system ɗin, sai ta ga ya zuba mata idanu kawai yana kallonta. Islaha ta dafe ƙriji cikin firgici ta ce, "Innahu min sulaimanu, wa'innahu bismillahir rahmanir rahim!" Ta faɗa a tsorace irin wacce ta ga aljani, dan da gaske ganin fuskarsa tsoro ya bata. Maimakon ta yi masa magana sai ta ga babu amfanin yin maganar, ta sake ɗauke kanta dan wallahi in bai yi mata magana ba itama baza ta yi ba. A lokacin Banisha ta dawo ɗakin, Islaha ta kalle ta ta ce, "Banisha ana neman ki, ɗauke laptop ɗin ki aiki nake yi.” Banisha ta ɗauka ta fita. Ita kuma ta harari Banisha ta ce, "ni za ka nunawa jan aji? Kana kallona ina kallonka ka ƙi yi min magana kana zaman jira nace maka sannu? In aka zo ɓangaren class na dame ka na shanye wallahi" ta faɗa tana cigaba da abinda take yi. Rehaan kuwa ko ta kan Kiddo bai bi ba datse kiran, duk tarin rainin hankalin da Islaha take yi masa bai taɓa jin haushi ba kamar abinda ta yi masa yanzu. Ya miƙe zaune ransa yana suya saboda ɓacin rai, a matsayin da yake da shi har wata mace ce zata yi masa wannan shirmen dan ta samu dama daga gare sh?. Ya yi tsaki yana girgiza kai, haka kawai ya ji ransa ya ɓaci ba tare da ya yi zato ba, shi kansa ya san abinda ta yi masa bai kai ya ɓata masa rai haka ba, amma ya kasa dakatar da kansa daga ɓacin ran. Ya sauke ƙafafunsa ƙasa ya jawo wayarsa yana dubawa. Sai ya kira Jazy yana ɗauka kafin ya yi magana ya ce, "wanne driver ne yake fita da yarinyar nan?." Jazy ya ce, "wa kenan." "C wife." "oh Islaha?." "Ka ji ai." Jazy ya yi dariya ya ce, "meyasa ka ke so ka sani?." Rehaan ya ce, "Jazy ba wasa nake yi maka ba, ka faɗa min kawai." Jazy jin maganar Rehaan ɗin so serious abin ya bashi mamaki, bai tambaye shi dalili ba ya ce, "Lawal ne." Bai kuma cewa komai ba ya datse kiran ya tafi binciken neman number lawal a wayarsa. Ya duba ko ina amma na shi da lambarsa, hakan ya saka ya kira Shams. Shams yana ɗauka ya ce, "Good Sir." Ray bai amsa gaisuwar ba ya ce, "ka san Lawal dirver?." "Yes Sir." "Tura min details ɗinsa" kafin ya Shams ya yi kashe wayar yana jin haushinta yana sake ƙaruwa a ransa. A bayyane ya ce, "Allah ya kawo five months ɗin nan a rabu a huta" ya faɗa yana shafa kansa cikin yanayin da ya kasa fassara shi. Sai ya yi tsaki, yana tunawa duk bala'i dai ta cuce shi, dole ace ex wife ɗinsa ce. Alert ɗin shigowar saƙon Shams ya shigo wayarsa, ya duba ya ga Shams ɗin ne ya turo, yana ganin kiran Shams ya yi rejecting ya kira Lawal. Bata jima tana ringing ba ya ɗauka, cikin fulfilde Lawal ya yi sallama. Rehana shima cikin yaren ya amsa sallamar, bai tsaya sun gaisa ba ya ce, "Ka san dawa ka ke magana?." Lawal ya ce, "Ban sani ba." "Rehaan ne." Lawal ya dabarbarce ya ce, "Barka da safiya yallaɓai, ban san kai bane." "Wa ka ke ɗauka a mota in zata fita?." "Ranka ya daɗe madam ce." "ta kira ka ta ce maka zata fita?." "bata kira ni ba." "In ta kira ka kar ka je, ka ce mata na hana ka kaita ko ina. A yau ban yarda ka kai ta ko ina ba, ka ji?." "In sha Allah." "Sannan ka faɗawa gate mans, na ce kar a barta ta je ko ina." "An gama, ranka ya daɗe. Rehaan bai amsa ba ya datse kiran ya cillar da wayar yana shafa fuskarsa, yana jin ɓacin ran da ya jima bai ji irinsa ba. Nana Haleema. RDB3P40 Nana Haleema. Gabaɗaya zama waje ɗaya da ita ya fara fice masa da rai, just one week kaɗai har ta fara saka masa ciwon kai. A yadda Allah ya halicce shi sai ya yi kwana da kwanaki ba a ɓata masa rai ba, dan ba ya damuwa da damuwar kowa balle ta ɓata masa rai, amma tunda ta shiga rayuwarsa ko yaushe ransa a ɓace yake. Ba ya jure damuwa kuma ba ya jure rainin wayo. Ya yi ƙwafa yana girgiza kai cikin ƙunar rai, sai kuma ya fahimci abinda ya aikata, ya ɗan yi shiru ya ce, "Ina ruwana da ban bata kula ni ba?" Ya tambayi kansa cikin mamakin kansa. Ya yamutsa gashin kansa ya ce, "meyasa na ce kar a kai ta inda zata je? Ina ruwana da ita?" Ya faɗa yana ɗaukar waya zai kira Lawal sai kuma ya fasa, ya ajjiye wayar ya ɗora hannunsa duka biyun akan fuskarsa, ya kwanta a jikin kujerar yana tunanin abinda ya yi. Islaha sai bayan sallar azahar sannan ta kira Lawal dan ta faɗa masa zata fita. Lawal yana ɗauka ya gaishe ta, itama ta gaishe shi sannan ta ce, "In an idar da sallar la'asar in sha Allah zan fita." Lawal ya yi gyara murya ya ce, "Madam tun ɗazu yallaɓai ya kira ni, kuma ya bani umarnin kar na kai ki ko ina a yau." Islaha cikin mamaki ta ce, "waye yallaɓai?." "Mr Rehaan nake nufi." Islaha ta buɗe idanu waje ta ce, "shine ya ce maka kar ka kai ni?." Lawal ya ce, "haka ya ce min, ya ce min indai a yau ne kar na kai ki ko ina." Ta ɗan yi shiru tana tunani sai kuma ta ce, "na gode" ta faɗa tana kashe wayar. "Kai! me mutumin nan yake nufi dani? In ruwansa dani da zai kira Lawal ya ce kar ya kai ni inda zan je? Ya aka yi ya san zan fita?" Ta faɗa cikin mamaki tana riƙe da ƙugu. Sai kuma ta gyaɗa kai cike da tsiwa da neman magana, har sauri ta ke yi ta gama abinda zata yi ta fita saboda neman fitina. A dah sai bayan sallar la'asar zata fita, amma yanzu tunda aka yi haka a lokacin zata fita sai ta ga wanda zai hanata. Dan ya ce kar a kai ta a mota daman ba ita ta nema ba, amma bazai hanata fita da ƙafar da Allah ya yi mata ba. Ta saka hijjab ta ɗauki facemask ta saka ta ɗauki wayar ta fito. Falon shiru kamar ko yaushe babu motsinsu, ta san bacci suke yi dan sun mayar da baccin rana kamar ibada. Ta fitowa daga falon Mamy ta ga rana ta buɗe sosai dan lokacin ƙarfe uku na rana ta kusa. Amma da ya ke bala'i da neman rigima take ji dasu bata ji ranar ba ta nufi gate ɗin. Duk da ta rufe fuska amma ana gane wacece, ana ta gaishe ta akan hanyar ta, ita kam ba wani amsawa take ba dan bata son wannan gaisuwar. Tana zuwa gate bakin gate masu gadin da suke zaune sanye uniform duk suka miƙe tsaye cikin girmama ta. Babban cikinsu ya duƙa ya gaishe ta kafin ya ce, "Hajiya fita za ki yi?." Islaha cikin girmama shi ta ce, "Eh fita zan yi Baba." Shima cikin girmamawa ya ce, "Ki yi haƙuri, Yallaɓai Rehaan ya ba da saƙo ya ce a faɗa mana, yau kar mu bar ki ki fita." Islaha ji ta yi kamar ta yi ashar saboda takaici da baƙin ciki, ta kama ƙugu tana kallonsu cikin yanayin da ita kaɗai ta san me take ji. Wanda ta kira da Baba ya ce, "ki yi haƙuri, shine ya ba da umarnin hakan, kuma baza mu iya tsallake umarninsa ba." Wata irin masifa da bala'i islaha ta ji tana tasowa daga zuciyarta, ranta ya ɓaci, ta ji kamar ta rufe su da duka ta huta. Ta gyara tsayuwa ta ce, "ku kira shi ku faɗa masa, ni kuma na ce sai na fita, duk abinda ya ga dama ya saka a yi min." A firgice wanda yake yi mata magana ya ce, "ki yi haƙuri, amma baza mu bari ki bar wajan nan ba. Kuma ba mu isa mu kira shi ba, saƙo ya bayar a ba mu." "Kuma sai ku ba da saƙon, ku ce masa nima na ce sai na fita." Dukkansu mamakim kalamanta suke yi, na gefe suka fara fara ƙus-ƙus ana tattaunawa akan aurenta dashi, daman ga yan aikin gida da gulma. Baba ya ce, "Ki yi haƙuri." "In na zo fita za ku ɗauke ni ne?." "Mu mun isa? Amma ki yi haƙuri ki koma." Zata sake magana wayar hannaunta ta yi ƙara, kamar baza ta ɗauka ba sai ta ɗauka. Safeera ta ce, "Gani a bakin estate ɗin gidanki, tsoron mutanen nan nake ji, ki turo a shigo dani." Islaha ta yanke wayar tana wuci ko amsa bata bawa Safeera ba. Baba ya sake tausasa murya ya ce, "don Allah ki yi haƙuri, baza mu iya tsallake umarninsa ba." Ganin babba da shi yana bata haƙuri sai ta daure ta ce, "shikenan, akwai ƙawata Safeera, tana farkon estate ɗin nan, a je taho min da ita." Jikinsu yana rawa suka amsa, mutum biyu suka fita da sauri, ita kuma ta gefe ta tsaya tana ji kamar ta yi kuka saboda takaici. Ta so ta nunawa Rehaan bai isa ya ba da umarni akanta ba, ta so ta nuna masa ba shi da iko da ƙafafunta, da mota yake da iko. Babu jimawa Safeera ta shigo inda Islaha ta ke, ganin Islaha a tsaye sai ta bita da kallo ta ce, "ke kuma me ki ke yi a nan?." Islaha bata ce komai ba kawai ta juya ta koma, Safeera ta bi bayanta suka nufi cikin gidan. Babu a compound ɗin kowa kasancewar rana ce, sai masu aiki da suke ta aikinsu. Maimakon ta shiga wajan Mamy, kai tsaye ta nufi ɓangaren Rehaan. Safeera tana kallon yadda take typing ƙofar, ko magana ta kasa yi mata saboda ɓacin rai. Safeera tana shiga ta rufe ƙofar, ta waiwayo ta kalli Safeera ta ce, "Wai ni mutumin nan zai rainawa hankali, ni zai saka a wulaƙanta a cikin gidansu?." Safeera ta ce, "ni tunda na ga fuskar nan ta ki na san ba lafiya wallahi, na yi tunanin ko kina period ne, dan na ga lokacin na ki ya yi. Me ya faru?." Islaha ta cire hijjab ɗin ta cillar, ta dafe kanta yana zaga falon sannan ta ce, "Wai ni zai saka a hana fita daga gidan nan, ni zai saka masu gadi su tare su hanani fita dan ya raina min hankali." Safeera ta ce, "Akan me zai hana ki fita, wani abun ne ya faru?." "Wulaƙanci kawai, dan ya nuna musu ƙasƙantacciya ce a gidan shiyasa ya yi min haka. Ya kira driver da aka saka ya dinga kai ni unguwa ya ce masa kar ya kai ni ko ina, sannan ya kira masu gadi ya ce wai kar a barni na fita. Ki ji fa rainin hankali, wai ni za a hana fita. Hmmm! Na rantse da girman Allah, ba dan wanda ya ce na yi haƙuri ya yi sa'an Baffa ba, wallahi sai na fita in ya so su ɗauko ni su dawo dani!." Safeera ta ce, "baza ma ki yi hakan ba, amma meye dalilinsa na hana ki fita?." Ta wara hannayenta ta ce, "shi ya sani. Saata ya ci kin zo, wallahi da ko....?" Dai ta kasa ƙarasawa saboda takaici. Safeera cikin son kwantar mata da hankali ta ce, "Wataƙila yana da dalili." "Dalilin me yake da shi? Ba ya ƙasar nan fa." "Shi da ba ya nan ta ya aka yi ya san za ki fita, ko kin kira sa kin tambaye sa ne?." Islaha ta bita da banzan kallo ta ce, "a matsayinsa na wa zan kira shi na tambaya dan zan fita?." "Mijinki" ta bata amsa kai tsaye tana kallon ta. "Dallah malama ki gyara kalaman ki, contract Husband." Safeera ta harare ta ta ce, "ke dai ki ka sani. To ke ban da rigima me za ki fita ki yi da ranar nan? Nima sai da na fito na yi danasani saboda rana." "Hamma ne ya kira ni ya ce yana so mu haɗu, ni yanzu ban san me zan ce masa ba....." sai kuma ta yi ƙwafa ta ce, "Ke sai ma na fita, in ya ga dama ya saka a kashe ni. In ban fita daga gidan nan ba ya yi galaba a kaina, ni kuma ban shiryawa hakan ba." Safeera ta ce, "gwara hakan, ya yi min daidai da ya hanaki wallahi. Bakya jin magana, na rasa ina iliminki ya tafi, na rasa gane canja ki aka yi ko wani abun ne ya shiga kan ki dai ban sani ba, ko kuma daman addinin na ki a baki yake bai kai zuciya ba dai duk ban sani ba. Kina matar wani, igiyar aure uku cif a kan ki, amma ki dinga biyewa wani namiji har yana cewa zaku haɗu da shi waje? Kina manta haramcin da yake cikin hakan, saboda Saheer ya rufe miki ido." "Safeera ya kamata ki gane ba da wani nufi nake zuwa mu gaisa ba, ya kamata ki tuna waye Hamma a gare ni. Ina jinsa kamar jinina saboda kusancinmu, akan me dan na je wajansa zai zama laifi?." "Inda da zuciya ɗaya ki ke zuwa wajansa babu laifi, amma kina zuwa wajensa a matsayinsa na wanda ki ke so kuma wanda za ki aura. Wallahi ina guje miki fushin Allah, ana ta rubuta miki zunubi lodi lodi." Islaha ta ce, "A'a wallahi, tunda muka yi maganar nan na daina zuwa wajensa da wannan niyar, ina zuwa mu gaisa ne saboda shi ɗin ɗanuwana ne, ko maganar auren ya kawo min bana son amsawa." Safeera ta ce, "wataƙila a jikinsa ya ji za ki je wajan Saheer, shi kuma yana kare martabar aurensa shiyasa ya hana ki fita." Islaha ta buɗe idanu waje ta ce, "shi ɗin ne yake kare martabar aure? Shi ɗin da yake turo min ɗan uwansa mahaukaci har yana cewa nima ina son mahaukacin, wannan ne kare martabar auren?. Shi bai ma san meye martaba ba balle ya kare ta, wanda bai san martabar mace ba ta ya zai san martaba aure?. Kuma kawai dan zan fita sai ya ji a jikinsa saboda ni ɗin tasa ce?." "Tasa ce mana, matarsa ce ke fa." "Mtsw! In kina cewa matar nan sai na ji kamar na rufe ki da duka....In ba dan ke ɗin ba ce babu wanda ya isa ya dinga faɗa min maganar nan." Safeera ta yi dariya bata ce komai ba. Islaha ta ce, "Na fi tunanin a wayar da nake yi da Hamma ne ya ji, dan lokacin ƙanwarsa ta ajjiye min laptop ɗina suna video call, ni kuma aka kira ni, tabbas a nan ya san zan fita." Safeera ta yi dariya cike da tsokana ta ce, "gaisawa ku ka yi kenan?." "Na gaisa da wa? shi ɗin? Allah ya raba gatari da saran shuka. Yadda ta ajjiye haka tazo ta ɗauka, ko kallo bai ishe ni ba wallahi.." Safeera ta ce, "to ai ba burgewa ki ka yi ba ai, dan ko babu aure ya girme miki." Islaha ta yi tsaki ta zauna a akan kujera ta yi mata banza. Safeera ta zauna ta ce, "Ba ki kyauta ba dai, ko irin ka je lafiyan nan ya kamata ki ce masa. Ke ki ke kallon aurenku a matsayin na yarjejeniya, amma a wajan Allah ba haka abin yake ba. Kuma haɗuwar ki da Saheer ba daidai bane, in dai ki ka haɗu da shi wallahi sai an rubuta miki zunubi." Islaha bata ce mata komai ba, dan ta riga ta bata wannan amsar tun farko. Safeera dai ta kawar da zancen ta ce, "na kawo miki ziyara, ba ruwa balle abincin ƴan gayu." Islaha ta yi tsaki ta ce, "Ya ɓata min rai ne wallahi, kuma ni marata ciwo take yi." Safeera ta ce, "ko ba ki faɗa ba ai, fuskar ki ta nuna kina kan hanya." Ta miƙe ta ɗauko nata ruwa da lemo ta ajjiye mata. Safeera ta ce, "Abinci fa?." Ta kalle ta ta ce, "ke ni ba a nan nake kwana ba, a ɓangaren Babarsa nake kwana, tsoron nan nake ji. Na san wannan wahalallen chef ɗin nasa baya nan, kuma ni wallahi bazan iya girki ba, ban taɓa shiga kitchen ɗin nan ba balle na yi girki, in za ki iya bismillah. Safeera ta ce, "inye ka ga matar mai kuɗi, ki ce sai dai a dafa a baki, a ɗauke miki kuma a wanke? Shiyasa har ƙiba ki ka yi." Ta harare ta, Safeera ta yi dariya ta sha ruwan tana cigaba da janta hira, dan ta ga yanayinta yana canjawa alamun ta fara jin ciwon sosai. Sama-sama suka yi hira, ta lura har lokacin bata huce ba ga ciwo, a nan suka yi sallar la'asar. Bayan sun idar da sallah Islaha ta miƙe tana yamutsa fuska ta ce, "na fara jin ciwon nan sosai, ina da pcm a ɓangaren babarsa." Safeera ta ce, "ke kuwa ba Mama sai babarsa? Ke wacce iri ce ne?." Bata ce komai ba, Safeera ta ce, "mu je ki ɗauko." Bata musa ba, suka fita zuwa ɓangaren Mamy, suna shiga suka haɗa ido da Ammi da Mamy a zaune suna hira....... Nana Haleema. KRBBK: RDB3P41 Nana Haleema. Islaha ta ɗauke kai daga kallon Ammi suka ƙarasa cikin falon ta kalli Mamy ta ce, "Mamy ga ƙawata, sunanta Safeera." Mamy ta kalli Safeera da fara'a ta ce, "Sannu Safeera, ya ki ke?." Safeera ta gaishe da Mamy ta amsa tana ta murmushi, Ammi ta kalli Islaha ita kuma ɗauke kai bata ce. Mamy ta ce, "ku je ciki mana." Islaha ta riƙe hannun Safeera suka wuce Mamy da Ammi ba tare da sun kula ta ba. Suna wucewa Ammi ta kalli Mamy ta ce, "Ban gane ba, kin yi accepting yarinyar nan kenan?." Mamy kai tsaye ta ce, "Na ga bata da wani problems." Ammi ta buɗe idanu cikin mamaki ta ce, "wannan za ki cewa bata da matsala, kin manta abinda ta yi mana a asibiti, ko kin manta abinda ta yi min a gidan nan?. Har kin saki jiki da ita tana zama a apartment ɗin ki?." Mamy ta ce, "A asibiti kuskure aka samu, sannan na gidan nan ma duk kuskure ne." Ammi ta girgiza kai ta ce, "Kina bani mamaki, a haka ki ke cewa za ki kare Rehaan? Bayan ga wacce ta shigo da niyar ganin bayansa kin bar ta a zaune a ɓangaren ki? Gaskiya kin bani mamaki Nadira, ban yi tunanin za ki yi saurin yarda da ita akan Rehaan ba. Mamy ta yi shiru bata ce komai ba, dan ita har ranta a yanzu bata ga laifin Islaha ba, duk da har lokacin tana kan gwadata, amma bata ga wani kuskure a tare da ita ba, amma sai ta gama gwajin zata tabbatar da ita ɗin wacece. Ammi ta ce, "Me zai yi da yarinyar nan, kallle ta fa kaf in laws ɗin gidan nan farare ne, ko kunya bakya ji a ga wannan a matsayin sirikar ki?." Mamy cikin rashin damuwa ta ce, "Skin type ɗinta yana da kyau, ni sai nake ji kamar na cire nata na bata nawa. Kuma Rehaan irin skin type ɗinta yake so, ya jima yana faɗa min shi bazai auri farar mace ba, kin ga an yi eqaul." Ammi zata sake magana Mamy ta dakatar da ita ta ce, "Ina kan bincike a kanta, in na gama da kaina zan saka ya sallame ta." Ammi ta yi shiru bata ce komai ba, baƙin ciki kamar ya kai ta lahira, tana ji a ranta in ta bar Islaha kamar ta yi nasara a kanta, sai ta yi maganinta.     Islaha suna shiga ɗakin Safeera ta ce, "kai! Kuɗi suna inda suke, kalli wani haɗɗɗen falo da Mamy take zaune. Gaskiya Mamyn nan kyakykyawa ce, dole kishiyoyinta su dinga kishi da ita. Ki kalli gashi har baya kamar ba babba ba, ga maganarta kana ji ka san ba ƴar nan bace." Islaha ta ce, "Wannan wacce suke tare munafuka ce, bata ƙaunata." Safeera ta ce, "Na ga alama, sai hararar ki take yi. Amma itama Mamy ranar buɗan kanki ranta a ɓace yake, ya aka yi ta sakko haka?." Islaha ta ce, "da farko haka take yi min, in ta ganni ta haɗe rai ita a lallai na auri ɗanta, bata  san da shi da banza duk ɗaya suke a wajena ba, wallahi bai isa na auresa dan kyau ko kuɗi ba. Daga baya ne na ga tana ɗan sakar min fuska, har ta yi murmushi. Mai kirkin gidan nan fa Mama ce, uwar gidan Abban. Ita kaɗai ce mai sona, daga Daada sai ita. Amma kin ga Umman nan, kin ga ta ƙarshen da suke cewa Anty? Duk ƴan iska ne." Safeera ta ce, "Ke fa ba ki da hankali, ƴan iska fa ki ka ce? Sirikanki ne fa." Safeera ganin ta yi shiru tana dafe ciki sai ta ce, "Sannu, Ki sha maganin." Ta langwaɓar da kai ta ce, "Ki bani don Allah, yana cikin jakata." Safeera ta yi dariya ta ce, "Ke wato in kina period, kina so komai ayi miki." Ta ɗauko ta bata ta sha ta kwanta ta ce, "Ciwon ya fara damuna." "Sannu." Suka yi shiru kafin ta ce, "Ni zan wuce, ki kwanta ki huta, ba sai kin raka ni ba." Sai ta miƙe zaune ta ce, "Ba ki da hankali, ki zo har inda nake na kasa raka ki? Dan ma bani da kuɗi, ai da har kuɗin mota zan ba ki." Safeera cike da tsokana ta ce, "Matar Ray guda ace bata da kuɗi, abin kunya." Islaha jinta ta share dan ta san neman magana take yi, suka fito wajan Mamy. A ina suka bar Mamy suka tarar da ita a zaune Ammi ta tafi. Islaha ta ce, "Mamy zan rakata, zata tafi." Mamy ta ce, "Kiddo kira Ado ya zo ya mayar da ita, sannan ki ɗauko min kuɗi a drawer." Banisha ta tashi ta shiga ciki, Mamu ta kalli Safeera ta ce, "bara a mayar da ke gida." Safeera ta yi murmushi ta ce, "Na gode." Mamy bata amsa ba sai murmushi da ta yi. A lokacin Ikram ta fito daga ɗaki, Mamy ta kalle ta ta ce, "Ikram kira min Ado ya zo ya mayar da baƙuwar Islaha gida." Ikram ta kalli Safeera bata ce komai ba ta kira shi a waya. Mamy ta kalle su ta ga suna tsaye kamar baƙi ta ce, "ku zauna kafin ya ƙaraso." A tare suka zauna suna ji Ikram tana yi masa waya. Bayan ta gama kiran Ado ta kalli Mamy ta ce, "Na kira shi, ga shi nan." "Okay ya yi sauri." Ikram ta zauna ta kira Rehaan video call, kanta  babu ɗankwali sannan fuskarta ta yi kyau sosai, dan ta yi light makeup. Rehaan yana ɗauka ta fara yi masa shagwaɓa ta ce, "Hamma Ray ba ka nema na." Mamy ta kalli Ikram ta ce, "in kin gama bani shi, na manta ɗazu akwai abinda zan faɗa masa." Ikram ta cigaba da waya dashi tana zuba masa shagwaɓa tana magana kamar tana yi da mijinta, ita dai Safeera kallon ta take yi kawai, Islaha kuma ta kanta take y dan ciwon ya dame ta. Banisha ce ta dawo da rafar dubu dubu ta bawa Mamy, Mamy ta miƙawa Safeera tana murmushi ta ce, "Mun gode da ziyara." Safeera ta karɓa ta ce, "Na gode." Mamy ta yi murmushi ta ce, "mu ma mun gode, ke ce first guest ɗin Islaha." Islaha ta yi murmushi Mamy ma haka, a lokacin driver ya zo, Safeera ta yiwa Mamy sallama suka miƙe suka fita. Suna fita Safeera ta ce, "ke wannan mai waya da shi ɗin ma ƙanwarsa ce?." Ta girgiza kai ta ce, "ƙanwar Jafar ce, cousin ɗinsa ce. " "koda na ji, wannan shagwaɓa da take yi masa ba Yaya da ƙanwa bace." "Ke tsaf za su iya hakan ba, su cousins ma kamar ɗan uwan da suka fito ciki ɗaya yake, dan ya rungumeta ta a gaban ki ba komai bane a wajansa, a wajensu normal ne. Ta ko ina bai dace dani ba, in da ace mijina ne na gaske kullum sai mun yi faɗa akan rungume-rugumen nan na banza da wofi, dan bazan jure ba." "Au mijin wasa ne?." "Ban sani ba." Safeera ta yi dariya suna wannan hirar Safeera ta shiga mota suka tafi, Islaha kuma ta shiga part ɗin Rehaan dan tana buƙatar space bata jin daɗi. Ciwon ya dame ta, tana ta juyi akan gado ita kaɗai, tana kuka mai ƙarfi kamar yadda ta saba, tana so ta sha ruwa amma baza ta iya tashi ba, ta jima a wannan yanayin tana kuka babu mai taimaka mata, a hankali ciwon ya fara lafawa, yana raguwa kaɗan-kaɗan tana ajiyar zuciya. Sai da ta ji ciwon ya ragu sannan ta iya tashi ta gyara kanta ta dawo ta kwanta bacci ya ɗauke ta. Har bayan sallar i'sha bacci ta ke yi ita kaɗai a apartment ɗin Ray, sai daga baya ta farka tana jin  yanayinta ya canja gabaɗaya, zazzaɓi da ciwon kai da kasala sun rufar mata, ga yanayi da take kasancewa a ko wanne wata.  A haka ta miƙe ta sake yin wanka ta fito ta zauna ta yi shiru, yunwa ta ke ji amma bazata iya cin abincin ba, da dai zata samu a bata abincin a baki da ya fi yi mata daɗi. Knocking ƙofar aka yi sannan aka buɗe, Banisha ta shigo da sallama ta ce, "Sis ba ki fito ba, muna ta jiran ki." Kafin Islaha ta ba ta amsa sai Banisha ta bita da kallo sannan ta ce, "Ba ki da lafiya?" Ta faɗa tana ƙarasawa kusa da ita, ta taɓa wuyanta ta ji da zafi sosai. Banisha ta buɗe ido ta ce, "You are running temperature, bara na je na faɗawa Mamy, ko ta yi miki allura ko ta kira Janan." Islaha ta ce, "Banisha bani ruwa na sha." Banisha ta fita ta kawo mata ruwan, Islaha ta sha sannan ta ce, "zan ji sauƙi, ba sai kin kira ta ba." "Amma ba ki da lafiya, jikin ki ya yi zafi." Ta yi murmushi ta ce, "yanzu zan ji sauƙi, gani nan zan zo wajen Mamy." Banisha bata sake magana ba ta fita daga ɗakin. Islaha ta miƙe a hankali dan har lokacin tana jin ciwo, ta ɗauki hijjab ta saka ta fito daga ɗakin tana ji kamar zata faɗi saboda jiri. Tana shiga apartment ɗin Mamy ta ga Jafar da Riyya da Banisha a zaune, Banisha tana ganin Islaha ta ce, "Mamy bata da lafiya, jikinta ya yi zafi sosai, amma ta ce kar na faɗa miki." Mamy ta kalli Islaha cikin kulawa ta ce, "kar a faɗa kuma Islaha? Me ya same ki?." Islaha ta zauna a hankali sannan ta ce, "zazzaɓi ne." Mamy ta ce, "kuma sai ki ce kar a faɗa? Kin raina zazzaɓin ne?." Islaha bata ce komai ba ta yi shiru, Mamy ta ce, "Banisha ɗauko mata magani ta sha." Banisha ta kawo mata maganin tare da ruwa a glass cup, islaha ta karɓa ta sha duk da yunwa take yi.  Jafar ganin yanayinta ya canja sossi ya ce, "Sannu Islaha." Islaha ta ce, "Yauwa, Na gode." Riyya ta ce, "Allah ya ƙara lafiya." Islaha ta ce, "Amin, na gode" ta sake faɗa tana rufe idanunta a hankali. Islaha ta jingina da kujera ta lumshe idanunta, ta kasa zama waje ɗaya saboda ciwon mara, ta kasa samun nutsuwa. Mamy kallon Islaha yake yi, dan tunda ta shigo bata yarda iya zazzaɓi ne yake samunta ba, ganin yadda take frowning face ɗinta sai ta ce, "Ba iya fever ne yake damun ki ba Islaha." Islaha buɗe idanunta ta kalli Mamy ta ce, "da ciwon kai." Mamy ta ce, "Kin tabbatar?." Islaha ta ɗaga kai bata ce komai ba. Mamy bata sake yi magana ba, ta yi mata sannu tana yiwa Jafar da Riyya magana da suka zo yi mata sallama zasu ta fi honeymoon. Ta jima a zaune har ciwon ya ragu sosai, sai ta miƙe tsaye ta ce, "Mamy zan koma, akwai abinda zan ɗauko a can." Mamy cikin kulawa ta ce, "za ki iya?." Islaha ta ce, "zan iya." Mamy ta ce, "to sai kin dawo." Islaha ta fita daga falon tana tafiya a hankali. Nana Haleema. RDB3P42 Nana Haleema. Mamy suna ta hira da Jafar kafin ya miƙe ya fita, ya tafi ɓangaren Ray dan akwai abinda ya ce ya ɗauko masa a apartment. A main parlour suka haɗu da Islaha ya ce, "Sannu Miss." Islaha ta yi murnushi ta ce, "Yauwa Mr Jafar." "ya kamata ki faɗawa Mamy abinda yake damunki, sai ta ba ki magani." "Na samu sauƙi." Jafar ya ce, "Allah ya ƙara lafiya" ya faɗa yana hawa upstairs. Sai da ya sakko daga upstairs ɗin sannan ta ce, "Mr Jafar." Jazy ya kalle ta bai ce komai ba yana jira ya ji ƙarin bayani. Islaha ta ce, "za ka haɗu da Mr Rehaan?." Ya ɗaga mata kai ya ce, "zan je inda ya ke Miss, kina da saƙo ne?." Ta ɗaga kai alamun tana da shi tana miƙewa tsaye, duk da ciwon da take ji amma baza ta iya shiru ba, dole ta aika masa da saƙo ko dan ya kiyaye gaba, dan ya san ita ba irin matan da ba su san ƴancinsu bane. Islaha ce, "So nake ka faɗa masa, kar ya sake gangancin sakawa a hanani fita daga gidan nan. Ba haihuwata ya yi ba, kuma ba aurena yake yi ba balle ya ce yana da ikon hana ni zuwa inda na ga dama. Ina ruwansa dan zan fita zai kira Lawal ya ce kar ya kaini? Daman ni ban ce a bani driver da zai dinga fita dani ba, su suka haɗa meeting aka ce bazan dinga fita ni kaɗai ba dole sai da driver." "Ban ce sai an ɗauke ni a mota ba, a napep na saba fita, kuma a nan zan cigaba da fita. Bazan ji haushi dan ya ce kar a kaini a mota ba, daman motarsa ce ba tawa ba, kuma bani na ce ina so ba. Amma wallahi Allah, bai isa ya ce bazan fita daga gidan nan ba, ba baiwa ya siyo ya ajjiye ba, balle ace sai lokacin da ya ga zama zan fita. Ka faɗa masa, in ya sake saka masu gadi suka hanani fita daga gidan nan, wallahi sai na haura katanga...." Dariyar da Jafar ya yi ya hanata ƙarasa, ta lura tunda ta fara magana ya ke son yin dariya sai da ta zo gaɓa sannan ya yi. Jafar ya ce, "kuma za ki iya haura katangar Miss?." Ta haɗe rai ta ce, "Ba wasa nake yi ba Mr Jafar." "Oh sorry Miss, ina jin ki." "Ka faɗa masa a rules ɗina da ya saka hannu a kai babu hanani zuwa duk inda zan je, ko zan je wani waje na kwana dubu babu ruwansa. Kar ya sake karya min rule, babu ruwansa da duk abinda zan je, ba a ƙarƙashinsa nake ba balle ya hana ni. Kuma daman na faɗa masa, in aka karya min ɗaya daga cikin rules komai ya ƙare. Sa a ɗaya ya ci a ɗazu Safeera ta zo, sai kuma na fara rashin lafiya, wallahi da sai na fita." Jafar kallon ta kawai yake yi yana murmushi, dan shi mamaki ta ke ba shi sosai, in tana magana cikin faɗa da fusata kamar ba ita ba, sannan ya lura hanata fita ɗin da ya saka aka yi ya ɓata mata rai, kuma daman ranta a ɓace yake. Yadda ta raina Ray abin har tsoro yake ba shi, bata jin tsoronsa balle ya yi mata kwarjini, duk abinda ya zo bakinta faɗa masa take yi, bata jin nauyi kallon idanunsa ta faɗi magana son ranta. Babu wata mace a duniya da ta ke yiwa Ray abinda ta ga dama kamar ta. In yana waje mata masa iya buɗe baki balle su yi magana, in ya basu damar maganar ma basa iyawa saboda tsoro da kwarjini, amma ita kullum abin nata sake gaba yake yi. Jafar ya ce, "Shikenan, zan faɗa masa saƙonki Miss. Duk da in ki ka faɗa masa da kan ki sai ya fi fahimta, sai ya fi gane ya yi kuskurensa na sakawa a hanaki fita." "Wallahi da ace ina da number wayarsa da ɗazu sai na kira shi na faɗa masa, dan ya san ni ba irin macen da zai karyawa rule ya kwana lafiya ba ce." Jafar ya ce, "ko na ba ki number?." "bani da buƙatar magana da shi, bani da buƙatar ajjiye number sa a wayata, dan babu amfanin da zata yi min. Ni dai don Allah saƙona ya je inda nake so ya je." Ya ce, "kar ki damu, zan faɗa masa." Ta ce, "na gode." Bai ce komai ba sai murmushi da ya yi, dan shi dramar ta dariya take ba shi. Ya fita daga falon ita kuma koma ta zauna, sai ta ke jin sauƙin ɓacin ran, sai take ji komai yana raguwa kamar Rehaan ɗin ta faɗawa abinda yake ranta, sai ta ɗan ji sauƙin ƙunar ran da ta dame ta ɗazu. Islaha bata jima a zaune a falon Ray ba ta koma ɓangaren Mamy, ta shiga ɗakin da aka bata ta kwanta tana jin yunwa sosai. Sai kuma ta miƙe ta dawo parlour har lokacin su Mamy suna inda suke suna hira, abinci take son ci amma ta kasa cewa zata ci. Mamy kamar ta kula da abincin take son ci sai ta cs, "baza ki ci abinci ba?." Islaha sai ta ji daɗi a ranta ta ce, "Zan ci." Mamy ta ce, "ki ci ga shi nan akan dining, in kuma kina son wani abun sai ki saka a dafa miki." Islaha ta ce, "To." Mamy ta ce, "kar ki cuci kan ki, in akwai abinda ki ke so ki saka a dafa miki." Islaha ta yi murmushi ta ce, "zan ci wannan ɗin ma." Mamy ta ce, "Shikenan." Islaha ta miƙe ta ƙarasa ta zuba tea, sai irsh da ta ci kaɗan, ta koma bedroom ta yi wanka ta kwanta. Sai kuma ta tuna da sun yi da Hamma za su haɗu, ta miƙe ta jawo wayarta ta kira shi. Yana ɗauka bata jira ya yi magana ba ta ce, "Hamma don Allah ka yi haƙuri, na so na fito sai na fara ciwon ciki." Saheer da ya ke jinta ya yi shiru bai ce komai ba, jin bai ce komai ba sai ta ce, "Hamma." Ya ce, "Ya jikin na ki?." "Da sauƙi, har na kwanta." "Allah ya ƙara lafiya." "Amin Hamma." "Ki kwanta ki huta." "To, amma gobe in na dawo daga wajan aiki zan zo mu gaisa." Ya ce, "Allah ya kaimu." Har zai kashe wayar sai ta ce, "Hamma!." Ya ce, "Islaha." "Sai ji maganar ka kamar kana fushi." Saheer ya yi murmushi ya ce, "Ba fushi nake yi ba Islaha, na yi tunanin daman ba ki da lafiya, na san lokacin rashin lafiyar ta ki ya yi. Ki kwanta ki huta, Allah ya kaimu goben." Ta amsa da amin sannan ta kashe wayar ta kwanta a hankali. * A daren Barr yana tsaye a ƙofar wani gida ƙarami, ya yi sallama aka amsa ya shiga gidan, ya kunna hasken wayarsa ya haska gidan suka haɗa ido da Yafindo. Yafindo a firgice ta miƙe ta ce, "Suraj me ka zo yi nan?." Cikin sigar kwantar da hankali ya ce, "Kwantar da hankalin ki Yafindo, ni kaɗai na zo nan. Kar ki ɗaga hankalin ki, koma ki zauna." Yafindo ta zauna ta ce, "Don Allah ka tafi, ban shirya salwantar da rayuwar yarana ba. Ya aka yi ka san na dawo nan?." Suraj ya zauna a gefen ta ya ce, "na yi bincike na gano kina nan, shiyasa na zo. Ni ba Islaha ba ne, dan na tabbatar ba a hana ki magana dani ba, kuma babu wanda ya ganni lokacin da na zo nan." Yafindo ta grigiza kai ta ce, "Islaha tana ƙoƙarin ganin ta gyara abinda yake faruwa, amma da ta fara zata kasa, saboda wasu dalilai da suke tare da ita. Tana son ganin rayuwar yaran gidan ta fita daga hatsari, amma yadda mutanen nan suka ƙeƙashe zuciyarsu basu imanin da za su ƙyale ta ba." Barr ya ce, "Ranar da ta je gidan ki karo a na biyu ki ka ƙi yin magana da ita, har ƙoƙarin taka ta da mota aka yi, kai tsaye kashe ta suka so yi." Yafindo ta ce, "za su iya, yadda suka ɗauki lamarin nan za su iya kashe rai wallahi." Barr ya sauke nunfashi ya ce, "Yafindo ki faɗa min ya ku ka yi da Zainab kafin ta gudu, ina ta ce miki zata je, wanne saƙo ta ba ki ki bawa Islaha?." Yafindo ta yi shiru bata ce komai ba. Barr ya ce, "Yafindo yin shiru nan na ki ba mafita bane, muna zargin gidan nan da safarar mata, muna zarginsu da lalata rayuwar mata, mu na zargin suna ɗaukar marayu suna rabawa masu kuɗi su kuma suna ba su kuɗi.  So mu ke mu kai maganar inda za a daƙile wannan ɓarnar, kuma hakan bazai faru ba sai mun samu hujja, kuma a yanzu Zainab ce kaɗai hujjar mu. Duk hujjar da Islaha ta samu sai an tabbatar ta rasata, suna bibiyarta sosai, suna ɓatar da duk wata hujja da Islaha ta samu. Shiyasa na karɓi lamarin na zo nan ko ita bata sani ba, tunda ita suke bibiya bani ba, kin ga zan yi abinda ya kamata ba tare sa hankalinsu ya zo kain ba. Yafindo, ki taimaka ki faɗa min abinda Zainab ta ce miki, shirun ki bazai yi amfanin komai ba." Yafindo ta sauke numfashi ta ce, "sun ce indai na yi magana sai sun ga bayana, kuma sai sun kashe ƴar dana mallaka a duniya." "Kina da hujjar da za ki ƙi magana Yafindo, amma da Islaha su ka hana ki magana ba ni ba, kuma ni a yanzu babu wanda ya san nazo gare ki." Ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "zan faɗa ma ka Suraj, ko da zasu kashe ni ka kula da rayuwar ƙanwarka gata tana bacci" ta faɗa tana nuna masa ƴarta da take bacci. Suraj ya riƙe hannunta ya ce, "Babu abinda zai same ki in sha Allah, zan killace ki, ki zauna a ƙarƙashin inuwa ta in sha Allah. Bazan taɓa bari wani abun ya same ki ba, zan ba ki kariya ko da zan rasa raina." Yafindo ta ce, "Tabbas Zainab ta same ni kafin ta bar gidan, kuma mun yi magana da ita. Takardar ta bani tana nan" ta faɗa tana miƙewa ta shiga ɗaki, ba jimawa ta dawo ta miƙa masa. Har zai karɓa sai ta ɗauke takardar ta ce, "Amanar yaran suna hannunka a yanzu, kar a haɗa baki da kai a cutar da yaran nan. Ban sani ba ko a tsaginsu ka ke ko a tsagin Islaha, amma ga shi zan tamƙa amanar a hannunka, in ka ci amana Allah yana kallon ka." Duk da yadda ya ji maganar ta soki zuciyarsa amma bai nuna mata ba ya ce, "Baza a taɓa haɗa kai dani a cutar da marayu ba, nima maraya ne, zan so ƴan uwana marayu su girma cikin tarbiyyar da kyakykyawar rayuwa kamar yadda na tashi a ciki." Yafindo ta ba shi takardar ya karɓa sannan ta ce, "Mun yi magana da ita kamar yadda na faɗa ma ka. Da farko ta fita a gigice, daga baya ta dawo ta ba ni wannan." Suraj ya gyara zama ya tausasa muryarsa ya ce, "Me ta ce miki? Sannan ina ta tafi?." Yafindo ta yi ajiyar zuciya ta ɗago ta kalle shi, ta yi shiru ta kasa magana. Suraj ya ce, "bazan ci amanar yara ba, baza a haɗa kai da ni a lalata rayuwar yara marayu ba." Yafindo ta ɗaga kai cikin gamsuwa ta ce,.......... Nana Haleema. RDB3P43 Nana Haleema. Islaha tunda ta tashi wajen daga aiki ta kiran Barr amma bai ɗauka ba, bata jin daɗin jikinta saboda yanayin da take ciki. Ta yi ƙaramin tsaki, ta hau napep ta nufi inda suka yi da Saheer zasu haɗu.  Gab da ƙofar gidansu Saheer ta ga motar Sadik, ta sauka ta nufi motar ta buɗe kawai ta shiga tana jan numfashi dan jinta take a takure. Saheer ya kalle ta sai ya ga yi haske kuma ta yi kyau sosai, Islaha ta buɗe ido suka haɗa ido da shi, Saheer ya ce, "kwana a cikin ac, da ruwa mai roba ya karɓe ki, kin ƙara kyau Islaha. Allah ya bani kuɗin da zan sa ka mana ac a gidanmu." Islaha bata ba shi amsa ba, ta kawar da kanta sannan ta ce, "Hamma ina yini." Ya ce, "Ya jikin ki?." "Lafiya lau." "Yau sai na ganki a napep, ina driver na ki?." Islaha ta yi tsaki tana tunawa da rainin wayon da Rehaan ya yi mata ta ce, "ban neme sa ba." "Meyasa?." "raina min hankali aka yi akan motar, shiyasa ni kuma ce na daina hawa motar, sai na ga abinda aka isa ayi min a cikin gidan." Kafin ya tambaye ta ta abinda aka yi mata ta riga shi magana ta ce, "Baffa yana nan? Ina so na shiga mu gaisa." Ya ɗaga kai ya ce, "Yana nan" ya faɗa yana ɗauko leda a back seat ya miƙa ya ce, "Ga lays ɗin na ki nan." Islaha ta karɓa ta ce, "Na gode Hamma, ashe ba la ka manta ba." Ya yi murmushi kawai bai ce komai ba. Islaha ta ce, "ka ce kana so mu haɗu, kuma ka yi shiru." Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Ina Rehaan ɗin?." Islaha ta buɗe idanunta waje ta ce, "Yawo nake yi da shi a jaka?." Yadda ta yi maganar ya ba shi dariya, ya yi dariya ya ce, "Ina tambayar ki ne kawai." "To ai kaine Hamma, kamar wata wacce ta ke yawo da shi a jakar ta ka ce min ina Rehaan?. Ba ya ƙasar nan, an ce yana Engaland." Saheer ya girgiza kai bai ce komai ba. Islaha ta sake kallonsa ta ce, "Meyasa ka tambaye ni inda yake?." Ya ɗage kafaɗa ya ce, "kawai." Bata ce komai ba sai wayarta da take ƙara, ta ɗauko ta daga jaka ta duba ta ga abokiyar aikinta ce, ta ɗauka tana faɗa mata inda ta ajjiye abinda ta ke nema.  Bayan ta kashe ta kalle shi ganin har lokacin ita yake kallo, cikin gajiya da kallon ta ce, "Hamma na canja maka ne? Sai kallona ka ke yi." "Kin canja magana, ba ki ji nace kin ƙara kyau ba?." "Ina kyaun a nan?." "Ga shi nan na gani, skin ɗinki ta koma kamar zuma." Islaha ta yi murmushi dan ta kawar da maganar ta ce, "ya aikin gidanka, ana yi?." Ya ɗaga kai ya ce, "ana yi sosai ma, kuɗi ne babu a hannuna, kin ga ban koma aiki ba har yanzu. Tsoron hanyar nake ji wallahi, ni kaɗai na san wahalar da na sha a hannun mutanen nan." Islaha ta ce, "wai a daidai ina suka kama ka?." "A Bauchi ne. Kin san in zan je Nijar daga Adamawa hanya mafi tsaro da sauƙi, amma tafi nisa itace na hau motar Bauchi, daga Bauchi na shiga Kano, daga Kano na shiga Katsina, daga nan na hau hanyar Nijar. Na bi hanyar da ake tunanin tana da tsaron ma ban tsira ba." "Allah ya kiyaye gaba, in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba." "Allah ya sa. Akwai abinda nake tunawa a can, ina ji kamar na bar wani gurbi mai mahimmaci a rayuwata, wani lokacin sai na ji kamar na koma." Islaha da mamaki ta ce, "ban taɓa jin wanda ya baro dajin yake cewa yana ji a ransa kamar ya koma ba sai kai, meye abinda ka ke tunawa?." Ya waiwayo ya kalle ta yana ajiyarzuciya ya ce, "amana aka bani, kuma na taho na bar ta a can, amma akwai Allah." "Amanar me?." "Zan faɗa miki, ba yanzu ba." "To shikenan. Amma sai na ga meyasa baza ka cigaba da neman kuɗin ka a nan ba, ba sai ka canja wani wajen ba." Ya lumshe ido ya ce, "an fi samun alkhairi, kuma kin san ance mutum ya mayar da hankali akan ƙwarewarsa." Ta ɗaga kai tana kallon agogo jin ana kiran sallar la'asar. Ta ce, "har lokacin sallah ya yi, zan je mu gaisa da Baffa." Ya ɗaga mata kai ta fita daga motar. Ya bita da kallo yana bitar komai daki-daki a ransa, yana jin tsoro a zuciyarsa, yana ganin kamar ya rasa ta har abada, wani lokacin sai ya ga kamar Islaha ta fi ƙarfinsa gabaɗaya, amma alƙawarin da ta yi masa yana ba shi ƙarfin guiwa matuƙa. Islaha bata shiga gidan ba sai da ta tabbatar an idar da sallah, tana tsaye a harabar gidan ta harɗe hannu a ƙirji tana kallon gidan Baffa ya shigo suka haɗa ido, yana ganinta ya yi murmushi ya ce, "Islaha, ke ce tafe?." Islaha ta yi murmushi ta ce, "Ni ce Baffa." Baffa ya cs, "Sannun ki da zuwa, ya ba ki shiga ciki ba?." "Daman kai nake jira ka shigo." Baffa ya murmusa ta ce, "mu je to." Tare suka shiga har ɓangarensa ya zauna sannan ya ce, "Maraba da Islaha, jiya nake zancen ki a raina." Ta yi murmushi ta ce, "Ina yini Baffa." Ya amsa da fara'a ya ce, "Ina fatan komai lafiya." "Lafiya lau Baffa." "Ma sha Allah, Allah ya cigaba da shiga lamarin ki. Na ji daɗi da na ganki haka, na ji daɗi da ki ka karɓi ƙaddara ki ka saka a ranki Allah ne ya zaɓa miki mijin da ki ka aura, Allah ya yi miki albarka." "Amin Baffa." "Kamar kin san ina neman ki." Islaha ta ji gabanta ya faɗi duk da bata san akan me zai yi mata magana ba, amma sai ta ji kamar akan auren yarjejeniyar da ta yi ne. Baffa ya ce, "lokacin da aka ɗaura auren ki, akwai kuɗi masu yawa da aka tura min, akace mim kuɗi me irin wanda ake yiwa yarinya na hidimar aure. Kuɗin aure, lefe, da sauran hidimar da ba a yi miki a lokaci aurenki ba saboda ƙurewar lokaci. Kuɗi ne masu yawa Islaha, dan sai da aka kulle min banki da kuɗin suka shiga, ban jima da gama gyaran bank ɗin ba. Abinda ya saka ban yi miki magana ba saboda yadda ki ka bar gidan nan, da yadda Hamman ki ya dawo, shiyasa na jinkirta. Amma tunda kin nutsu, zan tura miki kuɗin ki." Islaha ta ce, "Baffa ka bar su a hannunka kawai, ni ba sai na karɓa ba." Ya yi murmushi ya ce, "A'a Islaha, bazan ajjiye a wajena ba, in na mutu ban ba ki ba fa? Faɗa min lambar akawun ɗin ki na saka miki kuɗin ki. Bazan ci abinda ba nawa ba, haƙƙinki ne, ke za ki ci kayan ki." "Amma Baffa ai ni na ce ka bari, ni wallahi ban san me zan yi da kuɗin ba." "Za ki sani in na ba ki, ba ni na sa ka miki." "Don Allah Baffa." "A'a Islaha, bana so muna ja in ja da ke, kawo kawai." Babu yadda ta iya haka ta ba da account details ɗin ta. Sai kuma ya ce, "rarraba su ma na yi a akawun mabanbanta saboda na tura miki lokaci ɗaya, Da na je banki akwai wanda muka yi magana da shi, ya ce in zan tura miki na faɗa masa, zai kwashe duka ya tura miki." Ita dai bata ce komai ba, kanta yana ƙasa tana ganin Baffa yana ta danna waya alamun kuɗin zai tura mata. Ya ɗan jima a haka kafin ya ce, "Ma sha Allah, na sauke nauyi. Kuɗin ki sun bar hannuna." Bata ji alert a lokacin ba amma ta san zasu shigo. Ta ɗago kanta ta ce, "To Baffa na gode, Allah ya saka da alkhairi." "Amin Islaha. Ki shiga ku gaisa da mutanen gidan." Bata yi masa musu ba ba ta miƙe ta fita daga falon a a daidai lokacin alert ɗin ga faɗo wayar ta. Ta kalli kuɗin ta notification sai ta buɗe ido, ta shiga bank application ɗin ta ga uban kuɗin da su ke ciki. Da hanzai ta shiga calculator a tunanin ko bata gane lissafin ba, ta rubuta kuɗin da ta gani, ta tabbatar da gaske kuɗin ta gani a cikin wayar ta. Islaha cikin firgici ta ce, "Na shiga uku! wannan kuɗin na yi me dasu?" Ta haɗa harda dafe ƙirji bayan ta zaro idanu. Da hanzari ta koma wajan Baffa, ta same sa a zaune inda ta bar sa ta ce, "Baffa kuɗin sun zo, ya zan yi da kuɗin nan? Wallahi ban san me zan yi daau ba. Kuma nima na san sai an yi frezzing account ɗina, bai taɓa ɗaukar kuɗi mai yawa haka ba. Baffa don Allah na dawo ma ka dasu ka ajjiye a hannunka." Baffa ya yi murmushi ya ce, "Haƙƙin ki ne, ki yi yadda ki ke so." Babu yadda ta isa haka ta fito tana sake kallon kuɗin ta shiga wajan Mama. A zaune ta same ta ita da Karima aminiyarta, suna ta waya da Labiba cikin nishaɗi ana saka mata albarka. Islaha ta shiga da sallama ta zauna daidai lokacin da Labiba ta ce, "Islaha ai yawonta ta gama yi a jedda, babu gidan balaraben da ba a santa ba, ba san adadin mazan da ta sani ba wallahi, ƙarshe har zubar da ciki ta yi." Mama ta kalli Islaha da take jin abinda Labiba ta cd sannan ta ce, "zata aikata, wannan yarinyar me baza ta iya ba?. Ke dai ki cigaba da kama kanki a duk inda ki ke. Allah ya yi miki albarka, Allah ya kare ki, ki cigaba da turo mana kuɗi muna harkokin gaban mu." "Amin Mama. Ai Makka ya fi Jedda daɗi, tunda nan da hausawa sosai, can kuwa babu." "ki yi zaman ki a nan, Allah ya kawo miji na gari ki yi auren ki." "Amin Mama, ina zuwa" ta faɗa tana kashe wayar ta. Islaha bata ce komai ba sai kallon Mama da ta ke yi tana murmushin da ita kaɗai ta san ma'anar kayanta, dan ita ta san abinda yake faruwa wanda su basu sani ba, ba ta ji haushi akan abinda Labiba ta ce ba, dan ita ta san dawar garin. Islaha ta ce, "Mama ina yini." Mama ta bita da harara ta ce, "Lafiya lau, sannun ki." Daga haka bata sake cewa komai ba ta miƙe ta fita. Karima ta ce, "Ka ga shegiya, wato ni bazata gaishe ni ba?." Mama ta yi dariya ta ce, "bar ƴar iska mu cigaba da abinda yake gaban mu. Yara biyu ne kuma ƴan mata, kuma zasu yi abinda ake so. Sai dai iyayensu basu sani ba." Karima ta ce, "wannan su ta shafa ba mu ba, mu kawai mu sanu kuɗi." "Gaskiya ne, tunda za su yi zan yi musu waya su zo mu san abinda za a yi." "Hakan ya kamata." Daga nan suka cigaba da tattaunawa akan abinda ya shafi aikinsu. Islaha ko gidansu Safeera bata shiga ba, Barr ya kira ta ya ce ga shi ya ƙaraso, ta ƙarasa ta shiga motarsa tana kallonsa. Suraj ya kalle ta ya ce, "Kin yi kiɓa abin ki Islaha." Islaha ta ce,  "Hamma ya aka yi, ka samu Yafindon kuwa?." Ya girgiza kai ya ce, "har yanzu ina kan bincike a kan hakan." Islaha ta ce, "Na shiga uku! Allah ka kare wannan mata, Allah ya kiyaye ta daga sharrin masu sharri." Ya amsa da amin sannan ya ce, "In Allah ya yarda babu abinda zai same ta." "Allah ya sa hakan. Ni wani abu nake so na yi." "Ina jin ki." "Bincike nake so na yi mai ƙarfi akan masu garkuwa da mutane, ina so na je inda ake kai mutane in kama su na ga abinda yake faruwa." Suraj buɗe ya ce, "ke Islaha! Wai me yake damun ki ne? Daga wannan sai wannan?." Islaha ta ce, "ina so na zama silar kawo ƙarshen abun." "Ke a wa? Dan kawai an sace saurayinki sai ki kawo ƙarshen kidnappers a Nigeria?." "Ba dan haka ba, kawai ina so." "To ki bari a gama da wannan case ɗin, sai ki yi abinda ki ke so." "Sai mu yi dai Hamma." Suraj ya buɗe baki ya ce, "Wa! ni? A'a, Islsha ke dai ki yi." Islaha yi shiru bata ce komai ba sannan ta ce, "Don Allah a cigaba da dubawa, a gano inda Yafindo ta ke, bana so wani abun ya same ta." Suraj ya ɗaga kai ya ce, "kar ki damu, in Allah ya yarda babu abinda zai same ta." "Allah ya sa hakan, na gode Hamma Suraj." "Kar ki damu Islaha." "Zan koma." "To sai kin ji ni" daga haka ta fita daga motar. Tana fita ya ɗauki wayarsa yana danne danne sannan ya ce, "na gama da case ɗin, komai yana hannuna, zan yi komai yadda ya kamata in sha Allah" ya faɗa yana jan motar ya bar unguwar. Nana Haleema. RDB3P44 Nana Haleema. Islaha haka ta koma gidansu Ray, ta shiga ɓangaren Mamy ta same su a zaune duna ta hira kamar ko yaushe. Mamy ganinta ta ce, "Islaha har kin dawo?." "Na dawo Mamy." "ki je ki huta." "To Mamy" ta faɗa tana wucewa ta shiga ɗakin ta rufe ƙofa. Babu irin tunanin da bata yi ba akan kuɗin da Baffa ya bata, tana tunanin ko ta ragewa Rehaan wani abun a wanda ta karɓa? Sai ta tuna tunda ba duka zata bawa Rehaan ba gwara kar ta bayar. Sai dai ko ta bawa Hamma ya ƙarasa aikin gabansa, da wannan tunanin ta yi bacci. Washe gari da wuri ta gama abinda zata yi ta tafi bank suka yi mata upgarading account ɗinta komai yana zama normal sannan ta fito, kai tsaye  ta turawa Baffa kuɗin sannan ta turawa Saheer masu yawa. Bata jima da tura masa kuɗin ba ya kira ta, tana ɗauka ya ce, "Islaha ke ki ka sa ka min kuɗi?." Ta ce, "ni ce." "A'a ba ke ba ce, ko dai an yi hacking account ɗin ki?." "Ni ce Hamma." "Islaha kin san nawa ne kuwa?." "Ten millions." "Kenan kin sani?." "Ina wajan aiki, in na fito za mu yi magana" ta faɗa tana kashe wayar. Saheer ya kalli Sadik da suke tare ya ce, "kenan ta san ta saka min kuɗin." Sadik ya ce, "ga shi ka ji ta faɗa." Saheer cikin mamaki ya ce, "A ina ta samu wannan kuɗin? Ba fa dubu goma ba, miliyan goma." "Kana bani mamaki Saheer, ka manta wanda ta ke aure ne?." Saheer ya yi tsaki ya ce, "Islaha bazata karɓi kuɗinsa ba, baza ta karɓi komai na sa ba balle har ta tura min, kuɗi meye ta saka min?." Sadik dai ya taɓe baki bai ce komai, shi kuwa so ya ke kawai su haɗu da Islaha su tattauna ya ji kuɗin waye sannan a ina ta samu. Sai yamma Islaha ta fito ita da Safeera ta ce, Safeera raka ni gidansu Hamma Sadik don Allah, zan yi magana da Hamma." Kafin ta Safeera musa ta katse ta ta ce, "wani abu ne mai mahimmaci zai kai ji wajensa, ba akan abinda ki ke tunani bane, nima na san abinda nake yi." Safeera sai ta yi shiru bata ce komai ba, suka hau napep suka tafi. Bata shiga gidan ba sai waya ta yi masa ta ce gata ta zo, yana fitowa kafin su gaisa ya ce, "kuɗin nan na me ye ki ka saka min, sannan a ina ki ka samu?." Islaha ta kalli Saheer sannan ta kalli Sadik, ta sake kallon Saheer sannan ta ce, "Hamma ko gaisawa?." "tambayar ki nake yi Islaha, a ina ki ka samu kuɗi irin wannan kuɗin da ki ka tura min? Sannan na meye ki ka saka min?." Islaha ta yi shiru sannan ta ce, "Jiya Baffa ya tura min su, ya ce min kuɗin da aka ba shi ne lokacin ɗaurin aurena, akace wai na yi hidimar aure da ake yi kafin ɗaurin aure, irinsu lefe da sauransu. Ni kuma shine na je bank aka yi min ugrading account ɗina, na tura maka na turawa Baffa. Sai Safeera da Hamma Sadik da zan turawa gobe, dan limit ɗin transfer ɗin ya ƙare." Saheer mamaki ya kusa kashe shi ya ce, "Miliyan goman ki ka bani Islaha?." "Eh mana, taka ce. Da na yi tunanin na biya Rehaan kuɗin da ya bani na fansar ka, sai kuma naga basu kai adadin da ya bani ba, na san bazai karɓa ba raina min hankali zai yi, gwara na ba ku." Saheer ya ce, "kin ce an ba ki dan ki yi hidimar biki wacce ba a yi miki, ni me zan yi dasu?." Ta ce, "Amma nawa ne ko? Ni kuma kyauta na bayar a cigaba da yi mana ginin gida kawai, so na ke da zarar kwanakin nan sun cika na san inda zan zauna, dan bana son sake zama a gidanku kamar wancam lokacin. Baffa ma kyauta na ba shi, kaima haka. Safeera da Hamma Sadik ma zan tura musu kyau, har Saleem da duk wanda mu ke mu'amalar mutunci da shi. Dan bana buƙatar ko sisi daga wajan Mr Rehaan, balle kuma na yi amfani da kuɗin da aka ba ni akan hidimar aurensa. Saheer ya ce, "Islaha..." Ta yi hanzarin katse shi ta ce, "Na san baza ka ji daɗi ba, zaka ga kamar na raina ka tunda har na yi maka kyauta da kuɗin kuɗinsa. Hamma ba haka ba ne, ban baka dan baka da ƙarfinsu ba, kuma ba kuɗinsa bane nawa ne. A al'ada ba laifi bane in an bani, tunda su Baffa da iyayensa basa san maganar yarjejeniya ba, kaga ba laifi ba ne dan an bani ni kuma na bayar. Don Allah kar ka ce baza ka karɓa ba, ka riƙe a cigaba da hidima da su. Jiya jiyan nan ka ce min babu kuɗi sosai a wajen, ka ga gasu an samu, ayi abinda ya kamata kafin Allah ya kai mu wata biyar." Ta faɗa tana duba wayar ta da take ringing ta ce, "Baffa ne yake yi min waya, sai na koma zan kirasa mu yi magana." Sadik ya yi caraf ya ce, "Hakan ma kin kyauta Islaha, mun gode sosai da ƙoƙarin ki. Gaskiya kina da halacci, kin son saka alkhairi da alkhairi." Sai ta ji daɗi a ranta har ta yi murmushi, "Ni ce da godiya Hamma. Sha biyu na dare in sha Allah, zan tura maka naka da kai da Bestie" ta faɗa tana ksllom Safeera da take kallonta ta kasa magana. Sadik ya ce, "mun gode, Allah ya saka da alkhairi." Islaha ta sake kallon Saheer ta ga ya kasa yi mata magana sai kallonta kawai da yake yi sai ta ce, "don Allah kar ka ce baka so Hamma, ka karɓa don girman Allah, kar ka yi wani tunani akan kuɗin, ka tuna nawa ne ni kuma na baka. Zan koma yanzu, zamu yi waya in anjima, bana jin daɗi, ina so na huta kaina ciwo yake yi." Saheer ya ɗaga kai kawai bai ce komai ba, ta ja hannun Safeera da bata ce komai ba suka fara tafiya. Suna barin wajan Sadik ya daki kafaɗar Saheer ya ce, "mutumina ka kama da wuta fa, miliyan goma daga sama? Lallai da ace auren nan na Islaha mai ɗorewa ne, da mun ji daɗi." Saheer ya kalle sa ya ce, "ni mayar mata da kuɗin nan zan yi, bazan iya cin ko sisi a kuɗin Rehaan ba." Sadik ya riƙe kunnensa ya ce, "ɗan maimaita, kamar ban ji daidai ba." Saheer ya yi tsaki ya ce, "bazan karɓa ba, bana so." Sadik ya ce, "ba kada hankali ai, Naira miliyan goma ce ba dubu goma bace, in ka mayar sai ka kusa ƙare rayuwarka ba ka same ta nan kusa ba." Saheer cikin kishi da ƙunar ya ce, "me zan yi da kuɗin mijin da ta ka aure a yanzu?." "Ka ci mana, ina ruwan ka da na mijinta ne? Ita kyauta ta baka, kuma ba roƙa ka yi ba." Saheer ya girgiza kai cikin wani irin yanayiya ce, "Ni bazan karɓi kuɗin nan ba, zan mayar mata da abinta, kamar yadda ka ce ba roƙa na yi ba, bana so." Sadik ya ce, "da ka cika babban ajawo, da ka ciki cikakken mara hankali wanda yake buƙatar a fara ba sa magani. Wallahi in ka mayar da kuɗin nan ta tabbata kai banza ne, soloɓiyo wanda babu abinda zai iya yiwa kansa. Kai yanzu sai ka mayar dan shirme? In ma shi ɗin ne ya ɗauko kuɗin ya ba ka ai ba laifi bane, ya kai ya baka kuɗin ne, ya kai ya kira ka ya baka tunda yana da matsayi mai girma wanda mu bamu da shi. Balle ita tace Hamma ga kuɗi an bani na baka, sannan ta ga zata bani kuma zata bawa ƙawar ta. Meye naka da za ka ce baza ka karɓa ba?." Saheer ya sauke numfashi ya ce, "kishi nake Sadik, bazan iya cin kuɗin aurenta ba." "ai ba wani abun bane, tunda iyayensa ba su san auren da yake tsakaninsu ba, dole a bata irin wannan kuɗin." Saheer ya sake kallon alert ɗin kuɗin, ya kalli Sadik ya ce, "Jikina ya yi sanyi, anya Islaha zata dawo gare ni, anya bata fi ƙarfina ba?." Sadik ya ce, "bata fi ƙarfin ka ba, tunda tana sonka zata dawo cikin rayuwarka nan gaba. Amma kafin wata biyar, ka tabbatar ka gina kanka, yadda in ta dawo rayuwarka baza ta yi kewar rayuwar da ta yi a wata biyar baya ba." Saheer ya yi shiru yana tunani zuciyarsa tama bugawa da ƙarfi. Shi kuwa Sadik murna yake yi, yana fatan Allah ya sa auren Islaha ya ɗore ko dan ta cigaba da tunawa dasu. Islaha suna fita Napep suka kuma hawa bata ce komai ba, Safeera ta kalle ta ta ce, "Bazan gaji da faɗa miki gaskiya ba, batun auren da ki ke yi da Hamma Saheer haramci ki ke aikatawa, kuma wallahi mala'iku zunubi suke rubuta miki, amma na ga kamar kin raina zunubin ne shiyasa. In za ki yi maganar auren ki da shi, ki jira a raba wannan auren da yake kan ki, in ya so sai ki fara." Islaha kamar jira take a taɓo ta ta fara masifa, "Ina ruwanki da ni? Kuɗin da na bashi Baffa ya bani su jiya, ki faɗa min me zan yi da waɗnanan kuɗin masu yawa? In ban bawa Hamma kuɗin ba me zan yi dasu, in ban baki na bawa Baffa da Sadik ba wa zan bawa? Me zan yi da kuɗin?." Safeera sai ta yi mata banza bata tanka ba, dan in ta biye mata faɗa zasu kaca kaca, a yanayin da take ciki ta san halinta, bata jurewa ƙaramar magana, da ka taɓo ta sai masifa. A haka ma bata daina mita ba, sai kuma ta fara hawaye tana murza ido. Sai da ta gama kukan sannan Safeera ta sauka ta riƙe ƙarfen napep ɗin tana kallonta ta ce, "Da ki ba wa Saheer wannan kuɗin, gwara ki je orphanage ki ɗauki nauyin yara ƴan uwanki. Ban ce Saheer bai cancanci a ba shi ba, amma da niyar da ki ka ba shi kuɗin, da amfanin da ki ka ce a yi dasu ne babu lada sai zunubi mai girma, da kin je gidan marayu kin bayar da kin samu ladan da Allah zai kawo miki mafita cikin wannan ruɗanin da ki ke ciki. Ina sake tuna miki, magana da Saheer ma haramci ne a gare ki, domin kuwa ke matar aure ce!. Sai anjima" ta faɗa tana barin wajan ta bar Islaha tana kallonta. Mai napep ya ce, "Hajiya ina muka nufa?." Ta ɗaga kai ta faɗa masa sunan estate ɗin suka tafi. Kamar yadda tayi jiya daga farkon estate ɗin ta sauka, ta ba shi kuɗinsa ta kalli security da suke kallonta, dan tunda Jazy ya yi musu magana basu sake hanata zuwa ko ina ba. Ta wuce ciki cikin ƙunar ran da bata san daga ina yake zuwar mata ba, gabaɗaya komai ba ya yi nata daɗi, komai ya tsaya mata tana buƙatar shawarar da zata kwantar mata da hankali, tana buƙatar rarrashin da zai saka zuciyar ta huta na wani lokaci. Bata da mai bata shawara balle ya rarrashe ta, sai dai ta yi kuka ta share hawayenta. Mai napep ya na hango ta har ta ɗan yi nisa, duk da ba ya gano gidan da ta shiga, dan daga farko zuwa ciki da ɗan nisa kaɗan. Ya kalli sigh board ɗin sa aka rubuta AbdulAziz Yola Estate, ya ɗauki waya yana danne-danne, kafin ya saka a kunne ya ce, "tabbas ta yi aure, sannan na sauke ta a estate ɗin gidan AbdukAziz Yola. Kuma da ta zo shiga babu security ɗaya da ya hanata, alamun sun santa ba yau ta saba zuwa ba. Sai dai kamar ba a son ranta ta yi auren ba, har yanzu tana shirin auren tsohon saurayinta in ta fito daga nan." Shiru ya yi alamun ana ba shi amsa, sannan ya ce, "Za a yi hakan, sai ka ji ni" ya faɗa yana kashe wayar yana sake kallon estate ɗin kafin ya juya kan machine ɗinsa ya fita..... Nana Haleema. RDB3P45 Nana Haleema. *Englaand.* Rehaan yana zaune a parlour yana shan ruwa, dawowarsa gidan kenan cikin gajiya ta tsata yake sosai, hutawa yake so ya yi dan ya gaji. Da ya gama shan ruwa ɗaki ya shiga ya yi wanka ya canja kaya sannan ya kwanta. Sallah ce kaɗai ta tashe sa, yana tashi ya duba wayarsa ya ga kiran waya da messages da yawa. Bai bi ta kai ba ya sake yin wanka, sannan ya yi sallah ya sakko ƙasa ya samu an yi masa girki, ya zauna ya ci ya ɗauko ipad yana duba abubuwan da ya kamata ya yi. Door bell aka danna sai ya kalli ƙofar yana tunanin waye zai zo masa yanzu, ya san shi bai yi da kowa zai zo ba, daman Alma yake tunani kuma itama tunda ya zo bai ganta ba. Sai ya yi tsaki dan shi ya tsani buɗe ƙofa a rayuwarsa, yadda yake a gajiyen nan ba yaso ya miƙe ko kaɗan, abincin ma da zai yu a baki za a bashi. Daƙyar ya miƙe ya buɗe, kafin ya gama tantance waye aka rungume shi Sai ya yi murmushi ya yi hugging ɗinta back ya ce, "Riyya, yaushe ki ka zo?." Ta ɗago daga jikinsa ta ce, "kwana biyu kenan." Ya ɗaga kai ya shafa fuskarta ya ce, "Welcome." Ya faɗa yana riƙe da hannunta suka shiga falon, Jazy ya ƙaraso ya rufe ƙofar sannan ya ce, "da yake ka ga Riyya ni na zama banza kenan ko? Kamar ba ka ganni ba." Ray bai kula sa ba Riyya yake kallo ya ce, "i hope kina lafiya, sai na ga kin rame, me ya kawo clavicle" ya faɗa yana taɓa clavicle ɗinta. Kafin ta yi magana ya sake cewa, "ba ya ba ki abinci ne ki ka rame?." Riyya ta yi dariya ta ce, "Ban fa rame ba, kaine ka ga haka, but am gaining weight, ƙiris na ƙarasa kiddo." Ray ya yi murmushi ya ce, "ba ya takura miki? Ba ya yi miki faɗa da shouting?." Riyya takalli Jazy da yake kallonsu yana murmuahi, ta kalli Rehana ta ce, "ba ya yi min komai." "Kar ki kare sa, ki faɗa min gaskiya." "Allah da gaske." "Good." Sai kuma ta kalli Jazy ya ce, "Meyasa ba ka kawo min ita ba sai yau? Meyasa bata zauna a gidan nan ba?." "Me zai kawo ni gidan nan? Ango ne ni, bana buƙatar wanda zai takura mana ni da matata. Hotel ya fi daɗin honeymoon, dan bana son takura na gida." Rehaan ya taɓe baki bai ce komai ba yana harararsa, ita kuma Riyya sai ta ji kunya ta rufe fuskarta. Ray ya kalle ta ya ce, "me ki ke so?." Riyya ta ɗago kai ta ce, "Babu komai" ta faɗa tana tashi ta shiga ciki ta bar su a falon. Jazy ya kalli Rehaan kafin ya yi magana Rehaan ya ce, "Ya batun mutanen nan kuwa, bayan na taho nan an samu feedback?." Jazy ya ce, "eh an samu, Cctv ta ɗauki fuskarsa, amma dukkansu sun rufe fuska, mutum ɗaya ne bai rufe ba, shi kuma an tabbatar mana da baya garin nan. Amma in dai ba lahira ya tafi ba Allah  sai an nemo sa." Rayya ce, "Thank you for that." "Alma ta zo?." "kai nima abin ya bani mamaki fa, ban yi tunanin zan yi kwanakin a gidan nan Alma bata zo ba." "Kuma ta san ka dawo?." "ni na san ta sani, sai dai in akwai abinda take shiryawa. Amma Alma ta san ina ƙasar nan, definitely." Jazy ya yi shiru bai ce komai ba, sai kuma ya tuna da saƙon Islaha ya ce, "Kai C wife ɗin ka ta bani saƙo na ba ka." Rehaan ya ɗago ya kalle sa alamun wanne saƙo ne, kafin ya yi magana da ya yi dariya son ransa sannan ya ce, "ta ce na ce maka she loves you." Rehaan ya harare shi dan ya san ba ƙarya yake yi, Jazy ya yi dariya ya ce, "Yadda ka ɗago ido kana jiran na faɗa maka saƙon ne ya bani mamaki, kamar daman jira ka ke acr ta bada saƙo. To bata ce tana sonka ba, kuma ka san baza ta ce ba. Wait! Kai meyasa ka saka aka hanata fita? Ina ruwanka da ina zata je za ka ce masu gadi kar su barta ta fita?." Ray ya ɗora ƙafarsa ɗaya akan table sannan ya ce, "Ra'ayin hakan na yi." "Amma ka san a cikin rules ɗinta da ka yi signing babu hanata fita ko? Ina ruwanka da duk inda zata je da za ka ce kar a kaita kuma kar a barta ta fita?." Ray sai ya yi masa banza bai kula sa ba, Jazy ya ce, "kai dai kana son tayar da rigima ne, in ba haka ba ina ruwanka da ita?. Ga shi nan ta ce na faɗa maka, wallahi duk ranar da ka sake karya mata rule ta gama zama da kai sai ka sake ta, kuma ta ce na faɗa maka, in ka sake hanawa ta fita ta gate, sai ta haura ta katanga ta gudu......." Ya dakata da maganar yana dariya sannan ya ce, "abinda ya bani dariya kenan, ta ce in ka hanata fita ta gate sai ta haura ta fita, ba ka isa ka hanata fita ba. Kai yarinyar nan ƴar drama ce, can you imagine tun daga ranar da ka hana Lawal ya fita da ita bata saka hawa motar ba? Shekaran jiya da jiya duk bata hau ba napep ta ke hawa ta fita. Lawal ya kira ni yana faɗa min, na ce to ya zanyi mata, ƙyale ta." "Mtsw! Bata da hankali fa, ni ban taɓa gani stupid girl kamar ta ba. Har na ƙagu wata biyar ɗin nan ya yi ta tarkata ta bar ni na huta, kamar a kan ƙaya nake haka nake ji wallahi, shiyasa zaman Nigeria ya fita daga raina." "Ka faɗi gaskiya Malam, daman haka ka ke, ba itace ta saka baka son zaman Nigeria ba, daman in ka zo nan ba ka son komawa. Amma da gaske ni ban ga amfanin hanata fita ba, ka san tana aiki kuma tana zuwa inda take so, in wani abu mai mahimmacin ne ya saka zata fita a lokacin fa?." Rehaan bai ce masa komai ba, Jazy sai ya yi nufin tsokana ya ce, "haka kawai bayan ka aure ta, ka rabata da masoyinta kuma sai ka hanata rayuwa da shi?." "Ni na ce kar yi rayuwa da shi ne, ina ruwana da shi, ko na san shi ne?." "Ba ka ce ba, amma auren ka ya ce." "Ba aure bane, na lokaci ne kawai. Ta je ta yi duk abinda ta ga dama bai dame ni ba, daman ta saba, Salman ma ba ƙyalesa ta yi ba." Jazy ya yi tsaki yana girgiza kai bai ce masa komai ba. Ray ganin kallon da Jazy yake yi masa sai ya ce, "kar ka yi tunanin na ce kar ta fita saboda wani abu ne, a ranar ma raina min hankali ta yi." "Tana da number ka ne da zata kira ka ta raina maka hankali?." "I was on video call with Kiddo, ban san ya aka yi na ganta apartment ɗin Mamy ba, ka san Kiddo bata ji, kawai sai ta kai mata system ɗin wai mu gaisa. Yarinyar nan tunda ta kalli screen sau ɗaya ta ɗauke kai ta cigaba da aiki da system ɗinta, i was on the video call for over five minutes, but she didn't say anything to me. Sai kuma aka yi mata waya, ta ɗauka tana cewa zan zo in anjima. Shiyasa na ce kar ya kai ta, kuma kar a bar ta ta fita." Jazy ya buɗe ido cikin mamaki ya ce, "Wow! Haushi ka ji kenan dan bata kula ka?." Ya wani kalle sa sannan ya ce, "Mamy ce?." "Ba Mamy bace, amma....." Ya dakatar da shi ya ce, "In ba Mamy ba, babu macen da zata ƙi kula ni na ji haushi." "Kai a ganin ka ba haushi bane, ni a wajena haushi ka ji shiyasa ka saka a ka hanata fita." Bai ce masa komai ba dan ba shi da amsar da zai basa, sai kuma ya ya tsaki ya ce, "Ni aure ma nake so na yi, na gaji da wannan wahalar." Jazy ta yi dariya ya ce, "Wa zaka aura to?." "Ban sani ba wallahi" ya faɗa yana rufe idanunsa a hankali. Jazy ya ce, "ka san an yi attacking C wife ɗin ka da mota?." Ray ya buɗe ido ya kalle sa ya ce, "A ina?." "Lawal ya ce min ya kai ta wani gida a cikin ƙauyen jimeta, tana fitowa aka yi kanta da mota za a taka ta, sai shi ne ya taimaka mata. Wannan firgici da tsoron da ta shiga sai da ya saka ta damu attack, daƙyar aka samu ta dawo daidai suka dawo gida. Abin tambayar a nan, waye ya yi attacking ɗinta, daga ɓangarenka ne ko daga wajanta?." Ray ya harare Jazy ya ce, "Bata da ko sisi waye zai yi ƙoƙarin kashe ta? A kashe ta ace an kashe waye?." Jazy jin da hausa Ray ya yi maganar sai ya yi dariya ya ce, "Matar Rehaan mana." "ka manta, uwar matar Rehaan." Jazy ya yi dariya sosai ya ce, "ashe ka iya zagi babu labari? Lallai Ray, baki yana ta buɗewa. Kuma babarta dai ta yi maka rana, ta haifa ka aura." "Yarinyar bata da hankali na faɗa maka, tsaf zata ɗauko abinda wani zai ce zai kashe ta. Ni kaina ba dan ina tsoron Allah ba ai da yanzu babu labarinta." Jazy ya ce, "In aka ce min akwai macen da zata raina ka kamar Islaha wallahi zan ce ƙarya ne, in aka ce min akwai macen da zata dinga faɗar maganar da ta ga dama a gaban idanunka zan ce ƙarya ne. Amma ga Miss Islaha ta goge min hadda, ta raina ka, raini na har abada. Tun kafin ta san waye kai take raina maka wayo, ko da ta sani ɗin ma bata daina ba." Ray ya ce, "Tabbacin yarinyar su Ubaid ce, in da kamar su Riyya take baza ta yi ba. Hmmmm! Yarinyar nan ni ta kalla ta ce min ta saba ganin maza da towel, ko babu towel ɗin normal ne." Jazy ya yi dariya son ransa dan shi da za a barsa da Islaha da ta zama maasa maganin damuwa. Ya ce, "Da ace ana saka mutum a pocket ko, Allah da ka ara min ita na saka ta a pocket, ta dinga bani nishaɗi ko yaushe." "Ba abin dariya bane ba fa." "To ko kaima ta ganka babu kayan ne? Ko daman shine silar rainin nan da ta yi maka?.." Ray ya harare shi ya ce, "Allah ya kiyaye, da na ga wannan rana gwara na saka bindiga na harbe kaina. Ni da ita sai dai kallo, na fi ƙarfin irinta goma balle ita ƙaramar alhaki." "Dama ta ce kai rago ne ai, maybe itama ba irin ka take so ba." "Wai rago! Hmmm" ya faɗa yana shafa fuskarsa yana murmushi, dan shima sai ya ji nishaɗi a ransa, bai sani ba yadda Jazy ya mayar da abin wasa ne ya kawo haka, ko kuma ita ɗin ce sila bai sani ba. Jazy ya ce, "amma itace daidai da kai wallahi, gwara ta daina raga maka kana faɗa mata maganar da ka ga dama son ranka. Kuma wallahi, indai aka cigaba da irin wannan yanayin, akwai lokacin da za ka yi danasanin kiranta da karuwa." Ray da mamaki ya kalle shi ya ce, "Wanne irin yanayi kenan?." Jazy ya murmusa ya ce, "mu je zuwa dai." Bai ce masa komai ba ya ɗauki waya yana dannawa shi kuma ya shiga inda Riyya ta shiga. Nigeria. Islaha tunda ta koma take bacci har bayan sallar magrib sannan ta tashi, ta yi wanka ta fito tana gyara kitson da Safeera ta yi mata. Ita ta riga ta saba, in tana period in ba a yi mata kalba ko kitso ba bata samun nustuwa, kuma guda biyu kacal ake yi mata irin na fulani. Ta gama saka riga Mamy ta yi knock sannan ta buɗe ta shigo. Islaha ta kalli Mamy da take shigowa ɗakin ta ce, "Sannu da zuwa Mamy." Mamy da take kallonta ta ce, "ba ki da lafiya ne?." "Lafiya lau Mamy." Mamy ta harɗe hannu a ƙirji sannan ta ce, "Islaha meyasa ki ka fita a napep? Ba an baki driver da zai dinga kai ki aiki ba?." Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, dan baza ta iya faɗawa Mamy hujjar ba, ko babu komai ta girme mata, kuma babu laifi tana yi mata kirki sosai. Mamy ganin ta yi shiru sai ta ce, "Kar ki sake fita a napep, bana son yawan magana a gidan nan, na faɗa miki you are part of my family, ƙiris ake jira aka failure daga apartment ɗin nan ya zama abin magana." Islaha ta ɗaga kai ta ce, "In sha Allah bazan sake ba." Mamy ta ce, "Good. Daada tana neman ki, in kin ci abinci sai ki je." Islaha ta ce, "To Mamy." Mamy har zata fita sai ta dawo ta ce, "wannan gashin ki?." Islaha ta kali gashinta da jelar kitson da aka yi mata, wanda ta sauka har laps ɗinta, ta kuma kallon Mamy ta ce, "Eh Mamy, nawa ne." Mamy ta yi murmushi ta ce, "Ma sha Allah! Ga wacce ta fi Riyya" ta faɗa tana shafa gashin nata sannan ta fita daga ɗakin. Islaha ta ce, "ikon Allah, kamar basu saba ganin gashi ba, ita kanta Mamyn gashin ta mai tsaho ne dashi, amma nawa burge su yake yi" ta faɗa tana tattarewa kitson ta saka hula ta ta yafa mayafi a kanta sannan ta fito falon. Bata samu kowa ba sai Banisha da sauran ƙannenta suna ta wasa. Ta ci abinci ta tafi wajan Daada kamar yadda Maamy ta ce. Bata jima a can ba ta fito, tana fitowa suka yi kiciɓus da Salman. Gabanta ya faɗi matuƙa, kafin ta yi magana ya yi mata dariya ya ce, "ki ke guduwa bana ganin ki, ni na daina kula ki" ya faɗa kamar yaro cikin shagwaɓa sosai. Sai ya bawa Islaha tausayi, ganin namiji babba kamar wannan rayuwarsa ta koma haka, gashi cikakken mutum, mutum mai kyau da suffar maza amma ƙwaƙwalwarsa irin ta yara ce. Sai ta ji tausayinsa ya shiga ranta  ta ce, "Ka yi haƙuri." Sai kuwa ya yi dariya ya ce, "Kin daina guduwa?." Ta ɗaga masa kai dan sai ta ji tsoron nasa yana barin zuciyarta. Salman ya riƙo hannunta ya fara janta ya ce, "zo mu je mu hau mota." Islaha ta turje ta ce, "A'a, ka cika ni." Janta ya sake yi da ƙarfi ya ce, "mota zamu hau." Yadda ya jawo ta da ƙarfu ƙiris ya rage bata faɗa jikinsa ba, ta yi gaba zata faɗi, kafin Allah ya bata iko ta ta tsaya. "Kai Salman! Me ka ke yi haka." Duk suka juya suna kallon wanda ya yi magana. Ameer ne ɗan Mama, Salman bala'in tsoronsa yake ji, kaf gidan babu wanda yake tsoro kamar Amir. Lokaci ɗaya ya nutsu, ya sunkuyar da kansa ƙasa. Amir ya ƙaraso ya ce, "sakar mata hannu." Bai musa ba ya saki hannunta, ya kalle sa ya ce, "Wuce ka tafi wajan Umma." Da sauri ya bar wajan yana gifta su ya fashe da kuka mai sauti kamar yaro ƙarami. Sai islaha sai ta ji babu daɗi, ita wallahi tausayi ya ke bata, babba da shi yana cikin wannan rayuwa ai abin a tausaya masa ne. Amir ya kalle ta ya ce, "Ki yi haƙuri, ina kallon duk abinda yake yi miki." Ta yi murmuahi ta ce, "babu komai." Ta wuce sa ta tafi wajan Mama dan ta gaishe ta. Ya bi ta da kallo ganin ta nufi wajan babarsa, sai ya bi bayanta dan shi ya ɗauka daga apartment ɗin Mamy ta ke. Yana shiga ya ga yadda Mama ta ke yi mata da dariya da fara'a. Mama ta kalle sa ta ce, "Wannan shine Amir, Yayan Sameer ne, na san kin san Sameer." Ta ɗaga kai alamun ta sani tana murmushi. Amir ya ce, "Mama ban santa ba." Mama ta ce, "ba ka nan lokacin bikin su Riyya shiyasa ba ka santa ba. Wannan ai itace wacce Daada ta aurawa ƙaninka Rehaan." Ya buɗe ido cikin mamaki ya ce, "wow! Ai ban sani ba, kawai naga Salman yana yi nata hauka yanzu, har yana riƙe mata hannu fa." Mama ta ce, "kai dai bari, yaron nan ya takura mata wallahi, kullum cikin bibiyarta yake yi." "Ku kuka bar shi da ba ku hukunta shi ba." Islaha sai ta miƙe ta ce, "Zan koma Mama." Mama ta ce, "Na gode." Daga haka Islaha ta fita daga falon. Amir ya ce, "ƴar jarida ce, na santa a social media, wannan Daada ta bashi?." Mama cikin son ji me zai ce ta ce, "tana da aibu ne?." Ya ɗan girzgiza kai ya ce, "ko ɗaya, kawai dai...." Sai ya yi shiru bai ce komai ba ya fita. Tana shiga wajan Mamy ta samu Ikram da Janan da Banisha da sauran yara a tsaye. Banisha ta ce, "Sis zamu je outing, ki zo mu tafi." Islaha murmushin da yake bayyanar da kyawawan haƙoranta ta ce, "Ina da aiki Banisha, zan je wani lokacin." Janan ta ce, "Sis ba jimawa za mu yi ba, za ki iya joning." "Na gode Janan, in sha Allah next time zan je." "Shikenan" janan ta faɗa suna fita ita kuma ta koma ciki. Tana shiga ɗaki ta kira Baffa a waya, Baffa yana ɗauka bai bata damar magana ba ya ce, "Ba ki kyauta min ba Islaha, sai da ki ka saka kuɗin nan?." Islaha ta ce, "Baffa kuɗin da yawa, kuma ni ba wani amfani zan yi dasu sosai ba, shiyasa na tura maka." "Amma ai na ce kar ki saka ko?." "Baffa ka wuce matsayin wannan kuɗin a gare ni, wallahi ko duniya na samu ni mai iya bar maka ce. Don Allah ka karɓa, ba dan wani abun na bayar ba sai dan kyautatawa. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi." Baffa da murmushin jin daɗi sannan ya ce, "Amin Islaha, na gode sosai, Allah ya yi miki albarka." "Amin Baffa." Daga haka suka kashe wayar ta kalli kanta a madubi. Ita kanta ta san ta canja, cikin kwana goma da ta yi a gidan jikinta ya canja ya yi kyau, ga wani glowing na musamman da fuskarta take yi. Ta koma gefen gado ta zauna, maganar Safeera tana faɗo mata a rai a ranta, tabbas ya kamata ta ba da kuɗin nan a orphanage, akwai abubuwan da ake buƙata da yawa a gidan wannan babu, kuma kuɗin gwamnati ba ko yaushe yake iske  gidan ba, rayuwar gidan marayu indai ba ta bace private ba yana da wahala, ko rashin suttura zaman kanaa yake yi. Ta sauke numfashi mai ƙarfi, ta kwanta da baya tana lumshe idanunta.      * Ummi zaune take a motar Muslim ya ce, "ta tabbata Islaha ta yi aure, kuma auren bata so a san ta yi, tunda kin ga ko a gidan tv ba a sani ba. Kuma bata son auren wanda ta aura, har yanzu  tana ƙudurin fitowa ta auri Saheer." Ummi ta ce, "meye na ɓoyewa dan ta yi aure? Wa ta aura?." "Ban san wanda ta aura ba, amma an tabbatar min da estate ɗin AbdulAziz Yola ta shiga, amma ba a tabbacin gidan da take, dan kin san shi da ƴaƴan sane a kewaye da estate ɗin." Ta ɗan yi shiru sannan ta ce, "me take yi a estate ɗin to?." "Ban sani ba, kuma an tabbatar min da yadda aka ga ta shiga ba baƙuwa bace, kai tsaye ta wuce babu wanda ya hanata shiga." Ummi cikin mamaki da ɗaure kai ta ce, "dole akwai wani abun, me zata yi a waɗannan manyan manyan gidajen?." Muslim ya ce, "yadda na gano ta yi auren shima mijin zan gano, sannan za mu yi maganinta a cikin kwanakim nan. Ki buɗe sabon gmail amma ba da sunanki ba, da wata number daban ba number ki ba, sai ki yi creating account a duk wani platform, ig, tiktok, facebook da ko ina." "Amfanin me hakan zai yi mana?." Ya kalle ta ya ce, "za ki gani, ki yi a yau, yadda kafin lokacin da za mu aiwatar da aikin mu zai  daina nuna new account." Ummi ta ce, "shikenan zan yi in sha Allah, sai na jika" ta faɗa tana fita daga motar, shi kuma ya ja motar ya tafi yana shirya yadda zasu biyowa Islaha....... Nana Haleema. RDB3P46 Nana Haleema. *Madina.* Umma ta shiga damuwa sosai, kwana biyu mafarkan yaranta take yi cikin yanayi na damuwa da kewar ta da suke yi, gabaɗaya ta tayar da hankalinta tana so ta koma gida. Ta rasa yadda zata yi, ga wahala, ga kewar yara, duk ta rame ta yi duhu kamar ba a ƙasar waje ta ke rayuwa ba. Ga rashin mutucin matar gidan kullum ta'azzara yake yi, sun mayar da dukanta ba komai ba, yarinya ƙarama sai ta mare ta kuma bata isa ta rama ba. A ranar bayan ta kammala aikin gidan, ta samu matar gidan a zaune ta hakimce tana kallon tv. Umma cikin yaren da ya fara zama a bakinta ta ce, "Ina so zan je na siyo magani." Kallon banza ta yi mata Umma kafin ta yi magana ta fice, dan wani lokaci bata ɗaukar raini ramawa ta ke yi. Tana fita ta shiga gidan da yake kallon gidana da take aiki, ta shiga har parlour gidan, tana shiga wata babbar mace wacce zata yi sa'ar Umman ta kalle ta ta ce, "Ahh sannu da zuwa." Umma ta ce, "matar gidan bata nan ne?." Matar ta ɗaga kai ta ce, "bata nan, ni kaɗai ce. Zauna mana" ta faɗa tana nuna mata waje sannan suka zauna. Umma ta ce, "in tazo ta ganni baza ta yi miki faɗa ba?." Ta yi dariya ta ce, "haba, ai ba a yi min faɗa a gidan nan, suna da kirki sosai. Kin ce kina so mu yi magana." Umma ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Lami ina cikin matsala, zamana a ƙasar nan nake so ya zo ƙarshe, na gaji." Wacce aka kira da Lami ta ɗan buɗe ido ta ce, "Kamar ya kenan, kin gama biyan kuɗin da aka kawo ki ne?." Umma ta girgiza kai ta ce,  "ban gama ba." "Amma ki ke son tafiya?." "Na gaji, wahala nake sha a gidan da nake, ban wuce duka a wajensu ba, ga wahala da tsawa. Kalli hannuna" ta faɗa tana nuna mata hannunta da fashe. Unma ta ce, "tsabar aiki ne wallahi. A rana sai na gyara kaji hamsin, ga wanki, girki, wankan yara. Na gaji da wannan azabat, gwara na koma gida na yiwa yarana na san su na yiwa." "Ai kuwa komawar ki gida bai ta shi ba, dole ki haƙura zuwa lokacin da za ki tara musu kuɗinsu, in kin biya su sai ki san hanyar da za ki bi ki koma." Umma ta ce, "bazan iya ba wallahi, na gaji Lami, zuciyata ta jima da komawa nigeria, gida nake so na koma cikim yarana." Lami ta ce, "kin san da yaran naki ki ka taho ai, ni ban ga abin ɗaga hankali a nan ba, Ba dai kina samun kuɗi ba?." Umma ta ce, "ina kuɗin? Har nawa nake samu da zan so na cigaba da wannan wahalar saboda shi. Har yanzu ban tara riyal dubu uku ba, kuɗin magani da ƙananun abubuwa a nan kuɗi suke ƙarewa. Kuma ni ko nawa nake samu na gwammace na haƙura na koma cikin ʼƴaƴana wallahi." "Ba kin san inda ki ka bar su ba?." Umma ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Basu san na taho ba, akan zuwa aikin nan sai da mijina ya sake ni, ƴan uwana suka daina nemana. Amma duk da haka na tsallake na taho aikatau ƙasar nan saboda roman bakan da ake yi min. Sai ga shi na ƙare a wahala da rainon yara da girki da wanke-wanke." Lami ta bita da kallon mamaki ta ce, "mijinki ya sake ki saboda tahowa nan, ki ka ɓata da kowa saboda nan, ki ka bar yaran ki a nigeria ba tare da kin san a hannun wanda ki ka barsu ba?." Umma ta ce, "abin takaicin ma duk mata ne, babbar har an kusa auren ta." Lami ta yi dariya ta ce, "ashe ba a banza ki ke shan wahala ba, sharar masallaci ce ba ki yi shiyasa yanzu ki ke share coci. Kin bar na ki yaran kin taho kina rainon wasu, kin bar mijinki kin zo nan mijin wata yana ƙoƙarin danne ki ya yi amfani da ke, kin bar aikin gidan ki kin taho nan kina aikin gidan wata da babu lada. Ga wahala, ga zagi, ga duka. Na sha jin case ɗin masu zuwa babu izinin iyayensu, da masu zubar da ciki saboda zuwa, amma ban taɓa jin wacce ta haɗa abu uku ba sai ke. Kin kashe auren ki, kin bar yaran ki, kin bar ƴan uwanki kin taho inda ba ki da kowa sai Allah.  To in ba ki sha wahala ba a tunanin ki daɗi za ki ji?." Umma ta goge hawayen da suka sakko mata ta ce, "nima na san sakkaya ce, wallahi babu abinda na rasa a gidan mijina, daidai gwargwado yana yi mana iya ƙarfinsa, amma neman kuɗi ya rufe min ido." "Son zuciya ya rufe miki ido, ga shi yanzu kina so ki koma gida babu hanyar komawa, dole haka za ki cigaba da zama." Umma ta ce, "wallahi bazan zauna ba, tafiya zan yi." "Ta ya za ki tafi? Visar ki ta ƙare, ke kin san risk ɗin da yake cikin zaman ki a ƙasar nan, kin san irin abinda za a yi miki in aka kama ki?. Izinin zama na wata uku aka ba ki, amma kin zo kin kai wata biyar a nan. Zaman da ki ke yi gabaɗaya ba a kan doka ki ke yinsa ba, kin shigo musu ƙasa kin zauna ba tare da ƙa'ida ba, kuma yanzu ba ki da visa, kuma ki zo ki ce zaki koma gida?." Umma ta ce, "Amma ai visa shekara ɗaya suka ce sun yi mana." "Na faɗa miki ƙarya suke yi miki, ta wata uku ce wallahi, kuma ta jima da ƙarewa. In suka kama ki kaf zasu cilla ki a gidan yari." "ni wallahi ban san haka abin yake ba, da bazan zo ba." Lami ta ce, "ai daman idanun ku rufewa yake yi a lokacin da ku ke son zuwa nan ɗin, bakwa hango matsala, bakwa bin tsarin da za ku zauna lafiya. Kin ga ni, ta kamfani na zo nan, hotona aka turowa ƙasar nan suka ce na yi musu, aka zo dani aka yi min gwaji da duk abinda ya kamata. Zamana a gidan nan ina da lasisi, ƙasar nan ta san dani, na zauna tsahon wata uku a nan kafin masu gidansu ce suna son cigaba da aiki dani. Yanzu ina sauran zama na shekara biyu, duk inda zan je babu ruwana da za a kama ni, dan ina da id card ɗin zai tabbatar da aiki nake yi. In shekara biyu suka ƙare, za a mayar dani kamfani in an samu waɗanda suka ce suna so a sake kai ni, in ba a samu ba a sallame ni na koma gida. Ku kuwa kun shigo da visa ta wata uku, kun zauna har na wannan lokacin kuna faman wahala. Ki gode Allah a Madina ki ke, wallahi da Makka ne da yanzu kin zama ɓera wajan gujewa askar." Umma ta ce, "gani a Madina, amma ban taɓa shiga masallacin Annabi ba." "daman ba nan ya kawo ki ba, aiki ki ka zo yi ba ziyara ba. Ni kuwa ina damar shiga masallaci na yi sallah, babu ɗar ɗar ɗin za a kama ni." "Ni dai ina so na koma." "Ki daina wannan maganar, ki yi fatan Allah ya cigaba da ɓoye ki har lokacin ki ya cika, in aka kama ki wallahi sai an mayar dake gida, sannan sai an yi miki thumbprint ɗin da sai kin kwana biyu baki shigo ƙasar nan ba. Ko shekara biyar ko goma, sai kin ɗauki wannan lokaci ba ki zo ba. Ko ɗanki shugaban ƙasa ya zama, kina ji kina gani baza ki zo ki sauke farali ba." Umma ta dafe ƙirji cikin firgici sai kuma ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "da zan samu na shiga masallacin Annabi kafin na tafi da na ji daɗi." "Kina nufin za ki je inda za a kama ki ɗin kenan?." "ban san abinda hali zai yi ba, amma gwara na shiga ɗin." Lami ta ce, "zan je sallar asuba masallacin, ki zo ƙarfe biyu na dare sai mu tafi." Umma cikin zumuɗi ta ce, "Zan zo in Allah ya yarda, ko matar can bata sani ba wallahi sai na fito. Na gaji, sai na je na ga masallacin nan in Allah ya yarda." Lami ta murmusa suka ɗan cigaba da hira sama-sama, kafin Umma ta koma gida. *** Islaha haka ta cigaba da zama a wajan Mamy, Mamy tana lura da duk wani motsinta, duk inda zata je tana sakawa ana yi mata binciken akan inda take zuwa da waɗanda take mu'amala dasu. Har kiran wayar da take yawan yi tana sakawa a bibiya, kuma an tabbatar mata da babu wani abu na rashin gaskiya a tare da ita. Har labarin Saheer da kowa Mamy ta sani, ta kuma tabbatar da maganar Jafar da ya ce auren contaract ne a tsakaninsu, kuma ta tabbatar ba son Rehaaan take yi ba, lokaci take jira ta ta kama gabanta. Hakan ya yiwa Mamy daɗi sosai, ta ji a ranta ta samu wacce ta ke burin Rehaan ya samu, wacce zata aure shi ba dan kuɗi ba, wacce zata zauna da shi ba dan yana da wani abun ba. Islaha ta yi daidai da ra'ayin Mamy, tana yi musu fatan ɗorewar aurensu har abada. Islaha ta ɗan saki jiki a wajan Mamy, Banisha ta zama yar ɗakinta kullum suna tare suna hira. Ikram ce sama-sama suke gaisawa, kuma ta fahimci son Rehaan take yi, kishi ta ke yi da ita shiyasa bata sakar mata fuska. Ita kuwa kallo ma bata ishe ta balle ta tanka. Janan ma suna shiri da ita, zata zo su yi hira kafin ta fita. Islaha ta yi mamakin ganin Mamy ta saki jiki da ita sosai, ta daina ɗaure mata fuska, in tana yi mata magana kamar tana magana da Banisha saboda kulawa, ko me ta gani a waya sai ta kira Islaha ta nuna mata dan ta ji ra'ayinta akan abun, sai hakan ya yiwa Islaha daɗi ta rage zaman kaɗaicin da take yi. Ranar tana zaune a ɗaki tana danna wayarta, ranar sai bayan azahar zata je aiki bata fita da safe ba, tana zaune cikin atamfa riga da siket suna hira da Saheer. Da sallama Mamy ta shiga ɗakin tana kallon Islaha, Islaha ta amsa tana kallon ta har ta ƙaraso. Mamy ta ce, "baza ki je aiki bane?." Islaha ta ce, "Zan je Mamy, sai an jima." Mamy ta ce, "Zo ki raka ni mu gaishe da Salman, kwana biyu jikinsa ya tashi, zo mu je sai ki samu lada." Islaha ta miƙe tsaye tana neman hijjab ɗinta dan ta saka ta raka Mamy dubiya. Mamy ta bita da kallo tana murmushi, dan Islaha ta yi daidai da ra'ayin Rehaan, dan ta fi kowa sanin irin type ɗin macen da Rehaan yake so, kuma Islaha ta cike duk wani abu a cikin abubuwan da yake lissafawa. Ita kanta ba san meyasa Allah ya ɗora mata ƙaunar Islaha lokaci ɗaya ba, duk da farkon zuwanta gidan haushinta take ji, saboda an bawa ɗanta ita ba ya so, amma yanzu bata jin hakan a ranta, tana girmama Islaha sosai. Islaha ta saka hijjab ta juyo suka haɗa ido da Mamy da take kallon ta tana murmushi. Mamy ta ta shafa fuskarya ta ce, "Mu je." Tana faɗa sai kuma wayarta ta fara ƙara alamun shigowar kira, kuma video call ne ya shigo. Mamy ta ɗaga ta ce, "Rehaan." Islaha da yake a kusa da Mamy take sai ta ji ya ce, "Mamy na gaji, na yi aiki sosai, bayana ciwo yake yi." Islaha bata san ta yi tsaki ba, ta kawar da kai tana maganganu a zuciyarta, gabaɗaya haushi yake bata, bata son wannan ɗabi'ar shagwaɓar da yake yi ki kaɗan, in aka cigaba da yin haka a gabanta wata ran zata iya rufe shi da dukan takaici. Mamy ta ce, "kaine ka ke takura kan ka Rehaan, ban meyasa ka ke haka ba." Islaha ta kalli Mamy jin yadda take yi masa magana kamar wani yaro ƙarami, ta taɓe baki bata kalli inda yake ba. Mamy ta ce, "Rehaan zan shiga duba Salman, in na dawo zan kira ka." Tana ji ya amsa sannan Many ta kashe wayar. Mamy kalli Islaha ta ce, "Ba ki taɓa cewa na ba ki Rehaan ku gaisa ba, ko kuna waya da shi?." Gaban Islaha ya faɗi sosai, rana ta farko da Mamy ta yi mata zancen Rehaan har ta nuna tuna mata ita wata ce a wajansa. Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, dan bata dan me zata ce mata ba gwara ta yi shiru. Mamy ta murmusa ta ce, "Mu je." Tare suka fito a jere kamar Yaya da ƙanwar ta, islaha sai take jinta wani iri, tana jin nauyin Mamy sosai a cikin ranta. Mamy kuwa ko a jikinta tafiya suke yi har ɓangaren Umma. Suka shiga da sallama aka amsa, Umma da Mama suna zaune ana ta fama da Salman akan ya sha magani amma yaƙi. Daman Rehaan ne kaɗai mai iya basa magani, bayan shi ko Amir ɗin da yake tsoro bai isa ba in dai akan magani ne. Umma cikin fusata ta ce, "wallahi sai ka sha maganin nan." Salman ya ƙi karɓa yana kawar da kai gefe suka haɗa ido da Islaha. Sai ya miƙe zaune ya kalli Umma ya ce, "Umma kin ganta tazo." Umma ganin Mamy da Islaha sai ta haɗe rai ta kawar da kai gefe. Islaha ta yi murmushi tana kallon Salman bata ce komai ba. Mamy a tausashe ta ce, "Salman ka sha maganin mana." Salman ya noƙe kafaɗa ya ce, "ni ita ce zata bani." Umma ta ce, "Wace zata ba ka?." Salman ya nuna Islaha da take tsaye a wajan. Umma cikin faɗa da fusata ta ce, "baza ka sha a hannuna ba sai itace zata baka dan ba ka da hankali? Bana ce ka daina yi mata magana ba?." Salman fara yi Umma kuka ya ce, "ni dai in bata bani magani bazan sha ba." Mama da ta fi kowa iya bariki sai ta karɓi maganin ta kalle shi ta ce, "Ita kake so ta baka?." Ya ɗaga kai alamun eh Mama ta ce, "goge idanunka." Salman ya goge ido, ita kuma ta miƙawa Islaha ta ce, "Islaha ba shi maganin." Islaha ta kalli Mama da take miƙo mata magani, sai ta kalli Mamy da ta ke kallon ta, ta miƙa hannu ta karɓi maganin, ta bashi a hannunsa ya karɓa ba tare da musu ba ya saka a bakin, Islaha ta ba shi ruwa ya sha da kansa. Umma ta bi shi da kallon takaici, bai taɓa shan magani cikin kwanciyar hankali haka ba, kullum cikin faɗa ake da shi in dai akan sha magani, amma yau shine ya karɓa da kansa ya sha. Mama ta yi murmushi ta ce, "Ba gashi ya sha ɗin ba." Mamy ta miƙe tsaye ta ce, "Allah ya ƙara sauƙi." Islaha ganin Mamy ta miƙe sai ta yi nufin barin wajan itama, Salman ya riƙo hijjab ɗinta ya ce, "kar ki tafi ki bar ni." Islaha ta kalle sa dan yanzu tausayi yake bata ba tsoro ba ta ce, "Zan dawo." Ya ce, "kin yi alƙawari?." Ta ɗaga kai alamun ta yi. Salman ya miƙa mata yatsansa ƙarami ya ce, "Mu ƙulla?." Ta ɗan yi murmushi ta kai nata kusa da nasa, bata bari hannunta ya taɓa nasa ba ta ce, "mun ƙulla." Salman ya yi murmushi mai fitar da kyaunsa ya ce, "Abba ya ce duk wanda aka ƙulla alƙawari bai yi ba Allah zai ƙona sa." Ta ɗaga kai ta ce, "zan cika in sha Allah." Sai a sannan ya sake ta ya koma ya kwanta yana murmushi. Islaha da Mamy suka fita, Umma ta miƙe ta shiga ɗaki Mama ta bi bayanta. Mama ta ce, "kamata ya yi ki yi murna mun samu wacce zata dinga ba sa magani ya sha." Umma ta ce, "shigowar yarinyar nan ba alkhairi bane a rayuwar Salman, tunda ta zo gidan nan ya san ya riƙe mace har ya ce yana sonta. Babban abinda ya bani tsoro, sai bayan shigowar ta gidan nan na tabbatar da Salman yana da lafiya kamar ko wanne namiji, a dah bana ganin abinda na gani a yanzu a tare. Hankali ya tashi, anya yarinyar nan ba neman Salman take yi ba? Daman an ce ta jima tana bin maza, ko an bata aikin da zata yi da irinsu salman ne? Dan ni wallahi na tsorota sosai, jikina yana bani kamar....." Mama ta katse ta ta ce, "Zata aikata indai wannan yarinyar ce, ba kunya ce da ita ba. Amma zamu tabbatar da hakan, ki cigaba da saka masa ido mu gan iya gudun ruwanta." Umma ta yi ajiyar zuciya ta ce, "zan cigaba in sha Allah. Ga shi yanzu na ga Nadira ta ja ta a jikinta, ba kamar farkon zuwanta gidan nan ba, yanzu ta riƙe ta hannu biyu alamun ta karɓe ta a matsayin matar Rehaan. Ni sai nake ganin kamar akwai wata manufa akan hakan." Mama ta ce, "nima na lura yanzu, yarinyar ta daina ɗari ɗari da Nadira, alamun an samu wani daidaito a tsakaninsu, amma ko meye zamu gani." Umma ta ɗaga kai Mama ta fita daga ɓangaren hankalinta a tashe, bata son alaƙar Mamy da Islaha, bata so a samu wani kusanci da ita ko kaɗan, bata so Islaha ta sake da Mamy ta saki jiki da hira har haka. Da ita kaɗai take so ta saki jiki, ita ta ke so ta ɗauka kamar uwar miji ba Mamy ba, amma ta ga alamar wankin hula zai kai ta dare, ya zama dole ta canja shiri, dan Mamy tana neman ɓarar mata da abinda ta jima tana yi. Islaha bayan sun koma Mamy ta kalli Islaha ta ce, "Ki dinga yin baya baya, akan Salman babu abinda babarsa bazata yi miki ba. Kina ganin sharrin da ta yi miki farkon zuwan ki gidan nan, zata sake yin wanda ya fi na farko indai akan Salman ne." Islaha ta ce, "In sha Allah, wallahi Mamy tausayi ya ke bani ne." "da tausayi Islaha, Salma ya girmi Rehaan, amma kalli yadda rayuwarsa ta koma. Da ace yana da lafiya kamar kowa da yanzu yana nan da matarsa da yaransa. Amma ikon Allah ba a taɓa samun wacce jininsu ya zo ɗaya kamar ki ba." "Allah sarki." Islaha ta kalli Mamy ta ce, "zan tafi aiki." Mamy ta ce, "To sai kin dawo." Islaha ta shiga ta ɗauko abinda zata ɗauko ta tafi. Da daddare tana dawowa tun kafin ta shiga ɗaki Mamy ta ce, "Salman zuwansa biyu parlour nan, ya ce baki cika alƙawari ba." Islaha ta dafe kai ta ce, "na manta." Mamy ta ce, "tunda kin yi alƙawari ki je ki cika ki dawo." Islaha ta ce, "To Mamy, bara ba je na dawo" ta faɗa tana fita ta tafi ɓangaren su Salma. Gab da zata shiga ya fito, sai ya juya zai koma alamun ya yi fushi da ita ta ce, "nazo na cika alƙawari." Salman ya juyo ya ce, "tun ɗazu nake jiran ki." Ta ce, "Na je aiki, sai yanzu na dawo." Sai ya yi dariya ya ce, "Umma tana ta faɗa ta ce wai kar na zo wajan ki, tana shiga wanka na gudo." Islaha ta yi murmushi ta ce, "to ka koma, zan je na dawo." "Ni zan bi ki." "Gidan uwarka za ka bita?" Umma ta faɗa tana jan hannunsa da ƙarfi ta turasa falon. Umma ta kalli Islaha tana nunta da yatsa ta ce, "Ki kiyaye ni, ɗana ya fi ƙarfin iskancin ki, zan iya sakawa a yi min maganin ki." Islaha bata ce komai ba ta juya ta koma, dan itama kawai tana daurewa ne dan yana bata tausayi. Washe gari ma bata dawo ba sai dare, kai tsaye ɓangaren Rehaan ta shiga ta yi wanka ta canja kaya zuwa ƙaramar riga ta bacci, ta saka haijjab da niyar tafiya wajan Mamy sai ta kalli ɗakin Rehaan ta gan shi a buɗe har tana jin magana daga ciki, sai ta ɗan zubawa ɗakin ido cike da mamaki, dan ita ta san kullum a rufe ɗakin ya ke. Ta ɗauke kai zata sauka daga saman sai ta ji ance, "Islaha." Islaha juyo suka haɗa ido da Abba, Islaha ta ce, "Na'am Abba, barka da dare." "Barkan ki, Shigo mana." Islaha sai abin ya bata mamaki, amma bata ce komai ba ta shiga ɗakin a hankali kanta a sunkuye. Tana shiga ɗakin ta ji babu sanyi ko kaɗan, temperature ɗakin ya yi normal babu sanyi kuma babu zafi. Islaha ta kalli kan gadon ta ga Mamy a zaune ga Rehaan a kwance a cinyarta, ta ɗaga rigarsa ta ɗora masa towel, goshinsa ma an saka ƙaramin towel sai sauke numfashi ya ke yi a hankali. Mamy ta kalle Islaha ta ce, "Kin dawo?." Islaha ta ce, "eh na dawo Mamy." Mamy ta shafa kan Rehaan da yake cinyarta ta ce, "Rehaan ne ya dawo, sai dai ba shi da lafiya" ta faɗa tana shafa gashin kansa. Saboda idanun Abba da Mamy ya saka ta ce, "Subahanallahi, me ya same sa?." Abba ya ce, "ciwon ciki ne, wannan ya zamar masa kamar sabo." "Allah ya ƙara lafiya." Suka amsa da amin. Abba ya kalli Mamy sai ya ce, "Nadira zo ki ji" ya faɗa yana fita daga ɗakin. Mamy ta kalli Rehana da ya ke kwance a jikinta, ta san in yana wannan ciwon cikin ba ya son motsi ko kaɗan, ko ya ya motsa sai ciwon ya dawo baya. Ba ta son motsawa saboda haka, ga shi ya saki jikinsa a jikinta sosai, in ta ce zata miƙa zata fama masa cikinsa. Amma babu yadda zata yi, haka ta zame shi daga jikinta, sai kuma ta kalli Islaha ta ce, "zo islsha." Islaha bata fahimci me Mamy take shirin sakawa ta yi ba, ta ƙarasa kusa Mamy. Mamy ta ce, "Cire Hijjab ɗin kar ya takura ki, ki zauna ya kwanta a jikinki kafin na dawo." Islaha ta bi Mamy da kallo tana maimaita ya kwanta a jikinta, ta ga Mamy tana niyar miƙewa alamun ita ta zo ta maye gurbinta ya kwanta akan cinyarta kenan. Mamy ganin ta tsaya bata ƙaraso ba sai Mamy ta ce, "ƙaraso mana, my dear yana jirana." Islaha ta ƙarasa a hankali tana magana ƙasa-ƙasa, Mamy ta miƙe a hankali hannunta yana riƙe da kan Rehaan kamar wani mai naƙuda, ta nunawa Islaha inda ta ta shi alamun ta zauna. Islaha ta zauna a inda Mamy ta tashi, Mamy ta kwanta da Rehaan akan cinyar Islaha, shi kuma ya zagaya da hannunsa ya riƙe bayanta, yana sake nutsa kansa a jikinta yana jan numfashi......... Nana Haleema. RDB3P47 Nana Haleema. Abba ya tsaya yana kallon Mamy har ta ƙarasa sakkowa downstairs sannan ta ce, "gani." Abba ya ce, "ki zo mu tafi ki kwanta, ki bar matarsa ta kula da shi." Mamy ta buɗe idanunta cikin mamaki ta ce, "Kamar ya ta kula da shi, me ta sani akan ciwon cikinsa da zata kula da shi?." Abba ya ce, "Nadira! Kula da Rehaan yanzu ba naki bane tunda yana da aure, ki bar matarsa ta kula da shi zuwa safiya." Mamy cikin damuwa ta ce, "ta ya zan bar sa da ita bayan ka san a yadda auren nan ya zo?." "Ko a ya auren ya zo sunanya matarsa ko?." Mamy ta yi shiru bata amsa ba Abba ya ce, "ba kin ce min kin amince da ita ba?." Mamy ta ce, "dan na amince da ita ba hakan yana nufin zan iya barinta da shi ba, in aka cutar da shi fa?.” Abba ya san Rehaan ne lagon Mamy, yasan bata da yarda akan ƴaƴanta musamman Rehaan da take jinsa kamar ranta, hakan ya saka ya tausasa murya dan ya san halin kayarsa indai akan ƴaƴanta ne, bata iya ɗaga ƙafa ko kawar da kai, sai ta nuna maka ɗanta ɗanta ne. Ya ce, "babu abinda zai same shi, addu'a za ki dinga yi masa, daga nan zuwa safiya zai samu lafiya in sha Allah." Mamy cikin damuwa ta ce, "Bata san ya ake yi masa in yana ciwon nan ba, kuma har yanzu bata saki jikinta da shi ba, ta ya zata iya kula da shi yadda ya kamata?." "Sai Ki faɗa mata yadda ake kula da shi ɗin, ni na san zata iya.” Mamy ta sauke nunfashi ta yi shiru cikin tunani, bata taɓa barin Rehaan da kowa ba in bashi da lafiya, ita take kwana a wajansa ta kula da shi, ta ba shi duk abinda yake buƙata. Ta ya zata iya barinsa tare da matar da ba su karɓi auren da yake tsakaninsu ba? Ta ya zata bar Islaha da shi bayan ta san Islaha ba sonsa take yi ba?. Ba dan bata yarda da Islaha ba, ko dan tana tuna tunanin zata cutar dashi ba ita kawai bazata iya ba. Abba ya katse mata tunani ya ce, "Ki je ki faɗa mata ki dawo, ina jiran ki." Mamy kamar zata yiwa Abba kuka ta ce, “Ka san ko da Jafar bana iya barinsa, kana ganin daidai ne na bar shi da ita?.” “Ta fi Jafar mahimmaci ai, ita matarsa ce, Jafar kuma ɗan uwansa ne. Babu abinda zai faru sai alkhairi, kasancewar ta a wajensa sai ya haifar da abinda ba mu yi tunani ba. Sai ki ga an samu maganin ciwonsa a tare da ita, sai ki ga silar zamanta a wajensa ya samu lafiyar da muka jima muna so ya samu. Ki yi fatan Allah ya sa zamansu waje ɗaya ya zama alkhairi.” Mamy ta yi ajiyar zuciya sannan ta juya ta koma saman jikinta a sanyaye, tana tunanin yadda zata bar Rehaan a hannun Islaha. Ta shiga ɗakin ta ga Islaha a zaune a inda ta bar ta, kamar wacce aka saka remote aka danna mata pause haka ta ƙame a zaune cikin wani irin yanayi. Mamy ta ƙarasa ta janye Rehaan daga jikinta, ta riƙe hannunta suka fito parlour sannan ta ce, “Islaha!." Islaha har lokacin jikinta a sanyaye yake saboda kwanciyar da ya yi a jikinta, daƙyar ta buɗe bakinta ta ce, “Na’am.” “Rehaan ba shi da lafiya, yana fama da ciwon cikin da an rasa maganinsa, babu abinda ba a yi akan ciwon nan ba amma babu cigaba, babu ƙasar da ba a kai shi ba amma amsa ɗaya ce ko yaushe, sai ace ba a ga komai a cikinsa ba.” Islaha cikin sanyin murya ta ce, "Allah ya ba shi lafiya." "Amin. Zan ɗora miki nauyin kula dashi, na yarda da ke hundrent percent, shiyasa na amince zan bar Rehaan a wajanki ki kula da shi daga nan zuwa safiya. Islaha ban taɓa bawa kowa ragamar kula da Rehaan ba, indai ba shi da lafiya ni ce a gefensa, sai na tabbatar ya samu lafiya sannan hankalina yake kwanciya. Ko Jafar da ki ke ganinsu tare ban taɓa bashi amanar kula da lafiyarsa ba, indai Rehaan yana gidan nan ni ce nake kwana tare dashi har sai na tabbatar ya samu lafiya.” Mamy ta riƙe hannun Islaha ta ce, "amma yau na bar shi a hannun ki, na bar Rehaan da lafiyarsa a hannunki. Islaha ki yi min alƙawarin za ki kula da shi kamar yadda za ki kula da lafiyar ki, ki yi min alƙawari za ki ba shi kulawar da ko ni ban taɓa ba shi irinta ba. Ciwon yana wahalar da shi sosai, har yanzu bai yi bacci ba, daƙyar bacci yake zuwa idanunsa in yana irin wannan ciwon. Ki kula da shi don Allah, kar ki bari wani abun ya same sa." Islaha sai kallon hannunta da Mamy ta riƙe take yi, tana jin wani irin abu yana shiga zuciyarta, jin ana ƙoƙarin sakata ta yi alƙawarin da ta san baza ta iya cikawa ba. Jikinta ya yi sanyi, tana jin maganar mahaifiya tana shiga zuciyarta, tana ji mahaifiya tana damƙa mata amanar ɗan da ta haifa dan ta kula mata da shi, ita kuma ta san baza ta iya ba. Mamy ta ce, “kin yi alƙawari za ki kula min da shi? Ba Rehaan ɗina bane a yanzu, na ki ne tunda kece matarsa.” Islaha ta kalli Mamy suka haɗa ido, sai ta ji nauyin haɗa ido da ita ta sauke ido ƙasa ta rasa me zata ce. Dan gaskiya baza ta iya kula da Rehaan ba, baza ta iya ba shi kulawar da Mamy ta ke so ta ba shi irinta ba, amma kuma bazata iya cewa Mamy a’a ba. Mamy ta ce, “kar ki kalli a yadda auren ku ya zo, ki kalli alƙawarin da nake so ki yi min, ki saka a ranki za ki yi komai saboda ni ba dan wani abu ba. Za ki yi min ko Islaha?.” Islaha ta yi ajiyar zuciya tana jin nauyi a kanta, Mamy ta ɗaure ta da jijiyoyin jikinta, tsakani da Allah ta ya zata yi alƙawarin kula da wanda bata so? Wanda bata so ɗin ma kuma Rehaan da ta fi jin haushinsa sama da kowa a duniya?. Sai ta ɗago ido suka haɗa ido da Mamy, sai ta sake sunkuyar da kai ta ɗaga kai alamun eh. Mamy ta yi murmushin jin daɗi ta ce, "Na gode Islaha, ki kula min da shi yadda ya kamata. In ya farka duk dare ki kira ni, kina da number ta?." Ta girgiza kai alamun a’a, Mamy ta zare wayar Islaha da ta ke hannunta, ta saka number ta ta kira ta katse sannan ta ce, "kar ki ce dare ya yi, duk dare indai ya farka ina jiran ki." Islaha ta ɗaga kai tana karɓar wayar ta da Mamy take miƙo mata. Mamy ta ce, "in ya farka yana shan tea, ki haɗa masa tea amma ba milk tea ba, black tea za ki ba sa with less sugar, sannan akwai towel a kan cikinsa, in kin koma ki shoga bathroom ki saka shi a ruwa mai sanyi sannan ki sake ɗorawa a kan cikinsa, if possible kina massaging cikinsa a hankali, kar ki yi da gaggawa, dan in ki ka taɓa cikinsa ko ya ya ne ciwon zai dawo baya." Islaha sai da ta ɗaga ido ta haɗa ido da Mamy jin wai ta dinga massaging cikinsa, wai ita ce zata yi massaging cikin Rehaan? Abin har mamaki yake bata. Mamy ta ce, "ya saba kwanciya a jikina in ba shi da lafiya, bata iya bacci indai ba a jikina ya kwanta ba, yau ki maye gurbina ya kwanta a jikin ki." Islaha gabanta ya faɗi matuƙa, amma bata ce komai ba tana tunanin yadda zata sauke alƙawari mai girma kamar wannan, dan ta san baza ta iya ba, kuma bazata yi ba. Mamy ta kuma riƙe hannunta ta ce, "kar ki manta, kin yi alƙawari." Islaha ta ɗaga kai ta ce, "zan cika in sha Allah." Mamy ta yi murmushin jin daɗi ta ce, "Na gode Islaha. Mu je na raka ki…” ta faɗa tana niyar shiga ɗakin, sai kuma ta kalli Islahan ta ce, “but take off your hijjab, zai takura ki, kuma ɗakin babu ac sosai, za ki ji zafi." Islaha ta buɗe idanunta waje jin wai ta cire hijjab sai ta ce, “ba sai na cire ba Mamy, i can manage it." "No you can’t, take it off." "Allah zan iya, ba sai na cire ba." Mamy ta ɗan yi jim kafin ta ce, "okay, mu je." Mamy ta riƙe hannunta suka shiga ɗakin, suka same shi kansa yana kan pillow yana kwance yana kallon sama. Mamy ta ɗauke towel ɗin da yake kan cikinsa, ta shiga bathroom ɗinsa dan ta ragewa Islaha aikin. Islaha ta kalli inda Mamy ta ɗauke towel ɗin, ta ga yadda numfashin yake tsayawa a cikinsa kamar baya sauka yadda ya kamata, ga cikin nasa flat kamar ba ya cin abinci, sai haske da kyakykawan gashin da yake kwance kaɗan-kaɗan. Idanunta suka ja ta daga kallon flat tummy zuwa ƙasa, ta kalli short ɗin jikinsa da ya fito ta ƙasan dogon wandon jikinsa, idanunta ya kai kan logon da yake jikin short ɗinsa na kamfanin Nike, dan iya logon ne kaɗai ya fito. Haka kawai ta zubawa logon idanu kamar bata taɓa ganin logon Nike a duniya ba, haka kawai logon ya ɗauki hankalinta kamar wani abu na musamman ne a tare da shi. (logo ne ya ɗauki hankalin ki Islaha kodai-kodai?🤣) A lokacin Mamy ta dawo da towel ɗin da ta ɗauke masa ta sake ɗora shi a kan cikinsa, ta dafa goshinsa tana shafa gashin kansa cikin kulawa da soyayya. Rehaan cikin wata irin murya wacce da bata zuwa cikinsa ya ce, "Mamy." Mamy ta ce, "Na’am Rehaan." Sai ya yi shiru bai ce komai ba, daman ta san maganar zata yi masa wahala, dan in yana fama da ciwon daƙyar yake magana. Mamy ta kalli Islaha da ta ƙame a tsaye kamar soja, ta yi mata nuni da ta matso, Islaha ta ƙarasa a hankali tana kallon yadda yake sauke numfashi a daƙyar, Mamy ta nuna mata inda zata zauna. Islaha gabanta faɗuwa yake yi, ta ji kamar zata kai kanta cikin wuta saboda tsoro da fargaba da bugawar zuciya, ita kanta baza ce ga dalilin tsoron ba, ta san dai tana jin zuciyarta tana bugawa sosai. Kamar mai tsoron wani abun haka ta hau kan gadon tana tattare hijjab ɗin jikinta. Mamy ta kuma yi mata alama da ta cire hijjab ɗin, Islaha ta shagwaɓe fuska dan ita gaskiya bazata iya cire hijjab ɗinta ba, iya rigar bacci ce a jikinta, kuma ko bra bata saka ba, ta ya zata iya cire hijjab ɗinta da rigar bacci a jikinta a ɗakin Rehaan?. Bata gama tunaninta ba ta ga Mamy da kanta ta ƙaraso ta fara zare mata hijjab ɗin, Islaha ta yi sak kamar tana turo baki tana ji kamar tsiraea Mamy zata yi mata. Babu yadda ta iya da Mamy, tana ji tana gani ta cire shi ta ajjiye, kunya ta lulluɓe islaha dan rigar bacci ne kaɗai a jikinta mai ƙaramin hannu, gabɗaya hannayenta a waje suke, ga rigar tana da wuya mai faɗi, gabaɗaya wuyanta a waje yake. Mamy ta koma wajan Rehaan cikin sanyin murya ta ce, “Rehaan ɗago ka kwanta” ta faɗa tana ɗago shi tana kwantar da kansa a cinyar Islaha. Islaha ta runtse ido tana jin kamar an soke ta da allura a lokacin da ya kwantar da kansa a jikinta, tana jin yadda gashinsa yake taɓa jikinta tana jin wani irin abu yana zaga jininta. Mamy bata ce komai ba ta kashe musu hasken ɗakin ta fita tana jan ƙofar. Islaha bata buɗe ido ba har Mamy ta fita, tana jin yadda ya riƙe jikinta zuciyarta tana cigaba da bugawa da ƙarfi. Ta buɗe idanunta tana kallonsa cikin ƙaramin hasken ɗakin, ta ga idanunsa a rufe su ke har lokacin, numfashinsa kuma a cikinsa yake tsayawa. Islaha ta yi ajiyar zuciya, ta ɗarare jikinta ko hannunta bata motsawa sosai, ta ƙi sakin jikinta dan ji take kamar tana cikin wuta, ta takure kanta a jikin gadon tana ji kamar ta zura da gudu. Motsi ta ji ya yi a jikinta, Islaha ta kalle shi ta ga ya juya yana miƙewa kamar zai tashi zaune, sai kuma ya mayar da kansa ƙirjinta, yana goga fuskarsa a fatar ƙirjinta yana sauke numfashi mai zafi. _Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Na shiga uku ni Islaha marainiyar Allah. Me hakan ya ke nufi wai?._ Abinda take faɗa kenan a zuciyarta, jin zafin numfashinta har tsakiyar fatar ƙirjinta, dan ya kifa kansa a ƙirjinta, gashin fuskarsa yana taɓa fatar ƙirjinta dan babu komai a jikinta sai rigar, kuma tana da faɗi daga sama sosai. Nana Haleema. RDB3P48 Nana Haleema. Rehaan juya kansa yake yi a ƙirjinta alamun yana jin ciwo, har lokacin numfashin yake saukewa kamar yadda ya saba yi indai zai canja kwanciya, ya kasa kwantar da kansa yadda yake so a ƙirjinta, in ya kwanta sai ya ji bai yi comfortable ba kamar yadda yake so, akwai abinda abinda yake hana kansa kwanciya yadda ya kamata, sai ya ji kamar akwai abinda ya tokare masa kansa. Islaha tana zaune kamar an dasa ta, ta kasa motsi tana jin yadda yake juya kansa a jikinta, yadda yake juya fuskarsa a ƙirjinta kamar da gangan yake goga mata gashin fuskarsa a ƙirjinta. Salati kawai take a ranta tana ji kamar tana aikata wani abu mara kyau, danasanin yiwa Mamy alƙawari ya mamaye mata zuciya, tana jin ina ma ta faɗa mata gaskiya ta ce mata baza ta iya ba kowa ya huta. A hankali ta ji ya daina numfashi mai ƙarfi kamar yadda yake yi da farko, ya kwantar da kansa a ƙirjinta, ya zagaya da hannunsa ya riƙe shoulders ɗinta yadda zai fi kwanciya yadda yake so. Bai riƙe ta sosai ba, hakan ya saka tana iya moving yadda take so. Gashin kansa take kallo dan fuskarsa gabaɗaya ya kifa a ƙirjinta, iya gashin kaɗai take kallo gabanta yana faɗuwa, ta tabbatar yana jin bugun zuciyarta a kunnensa, dan yadda take bugawa ko ita tana jin sautinta balle shi da kansa yake ƙirjinta. Kallon gashinsa kawai take yi, ta jima tana so ta taɓa gashin nan ta ji ya yake, irin nasu ne na fulani ko kuma nasu daban yake. Kamar mai jin tsoro haka ta kai hannunta zata ɗora akan gashin kansa sai kuma ta fasa, ta sake kai hannu ta kuma kasawa, sai a karo na uku ta ɗora hannunta a gashin kansa ta shafa dan ta ji banbanci da na su, sai ta ji sa kamar roba-roba bai yi laushin nasu ba. Ƙhmashin da gashinsa yake fitarwa ya mamaye mata hanci, ta cire hannunta daga gashin tana kallonsa. Sun jima a haka, ya jima a jikinta a kwance bata ji alamun ya yi bacci ba, dan ta san idanunsa biyu bata sani ko ya san itace a tare da shi ko bai sani ba. Bakinta ya rufe ruf, ta kasa ce masa komai balle ta ce ya ɗagata, tana jin yadda zafin da kansa ya yi yake ratsa ƙirjinta, tana jin yadda ya ɗora lips ɗinsa a ƙirjinta amma ta kasa cewa komai. Ta juya ta taɓa wayarta da ta ajjiye akan bedside drawer, ta ga awanta biyu kenan a haka, ita kanta ta gaji da zaman, so take ta kwanta amma babu damar hakan. A hankali ta ji yana sauke numfashi alamun ya samu bacci, jikinsa ya saki a jikinta ba kamar ɗazu ba. Ta yi ajiyar zuciya jin ya yi bacci, ta sake kallonsa a lokacin ya juyo da fuskarsa tana kallon gefe, duk da ba ganinsa take yi sosai ba amma ta ga yadda fuskarsa ta ɗan rame. Ta harare shi ta ce, “Sarkin masu rakin duniya gabaɗaya, da na ce sarautar iya ta Yola ce, to na ga ta fi ƙarfin Yola kaɗai sai dai ace duniya gabaɗaya" ta faɗa tana kallon fuskarsa. A hankali ta ke so ta zame ta gudu ba tare da ya tashi ba, dan babban abin kunya ne ya buɗe ido ya ganta a haka, girmanta zubewa zai yi a idanunsa. Tana motsawa ya motsa, ya sake riƙe ta ya cigaba da baccinsa. Ƙasa ƙasa ta ce, "Ikon Allah! An sangarta yaron nan da yawa, yanzu tsakani da Allah baccin ma sai ya riƙe babarsa yake yi? Ji yadda ya maƙale min kamar wata matarsa. Mtsw! Wannan matarsa zata yi kayan takaici, in irina ce bamu san lokacin da zamu gaggaura masa mari ba saboda takaici. Miji irin wannan sangartacce ko wahala, shi zai rarrashe ni ko ni zan rarrashesa? Ni zan yi shagwaɓa ko shi zai yi?” ta faɗa tana ɗan zamewa ta kwanta da baya amma bata yi flat ba dan yana jikinta, itama a haka bacci ya ɗauke ta bata sani ba. Sai asuba Rehaan ya buɗe ido, har lokacin yana kwance a jikinta, dan ta saki jikinta gabaɗaya tunda itama ta yi bacci. Ya ɗago kai a hankali yana cize baki saboda ciwon da yake ji a cikinsa, duk a zatonta Mamy ce, ya kalle ta da niyar gyara mata kwanciya sai ya ga sam bata yi kama da Mamy ba. Cikin ƙaramin hasken ɗakin yake kallonta yana so ya gano wacece wannan, gabaɗaya rigar jikinta ta tattare daga ƙasa ana ganin laps ɗinta, ya kalli samanta sai ya yi saurin ɗauke kansa, dan rigar ta same daga sama ana iya hango rabin ƙirjinta a waje, ya kalli fuskarta ya ga bacci take yi amma a takure, kanta yana gefe ga gashinta ya tarwatse a kan gadon. "C wife!.” Ta furta cike da mamakin abinda ya kawo ta ɗakinsa har kan gadon, har ya kwanta tare da ita. Ya ɗauke ido daga kallon ta, yana tuna yadda ya kwanta a jikinta kafin ya yi bacci. Ya sake kallota yana so ya gano abinda ya hanasa sakewa ya kwanta yadda yake so a ƙirjinta, shi daman ya ji banbanci sosai, ya saba jinsa comfort a jikin Mamy, amma a wannan lokacin sai ya ji wani yanayi daban. Ya ɗauke idanunsa daga kanta, dan kallon kawai ta yana sakawa ya ji wani iri a jikinsa, espacially daga ƙirjinta da yake a bayyane daga sama, ba ya so ya gani ko kaɗan. Ya zura ƙafarsa ya sauka daga kan gadon, ya miƙe daƙyar yana cize baki saboda yadda yake ji kamar ana ƙona cikinsa, ya ya shiga bathroom. A lokacin alarm ɗinta ya fara bugawa, ta buɗe ido  ta jawo wayar ta kashe. Sai ta firgita ta miƙe tunawa da inda ta kwana, ta kalli kanta ganin rigar jikinta gabaɗaya ta tattare, kuma in ban da pant babu abinda yake jikinta. Ta kalli ƙofar bathroom ɗin tana gano haske ta ƙasa alamun yana ciki, ta miƙe tsaye ta saka hijjab ɗinta ta fita daga ɗakin da hanzari.. Kamar wacce ta yi ƙaton laifi haka koma ɗakin jikinta ya yi sanyi sosai, ta yi alwala ta yi sallah tana zaune akan sallaya tana tuna yadda ya maƙalƙale mata a jiya. Gabaɗaya jikinta ƙhamshin turarensa yake yi, kamar ɗaukar turaren ta yi ta fesa a jikinta haka take jin ƙhamshin ya mamaye ta. A lokacin wayar ta fara vibrating kamar jira ake ta idar da sallah, sai ta kalli wayar ta ga new number ce sai ta share, a ganinta waye zai kira ta da asuba. Tana katsewa aka sake kira sai ta ɗauka ta ji ance, "Islaha Mamy ce." Islaha ta ce, "Mamy ina kwana." "Lafiya kau, Rehaan ya yi bacci kuwa?." "Ya yi bacci, yanzu haka ya ta shi yana sallah." "Ma sha Allah! Na ji daɗin wannan labarin sosai, kin haɗa masa tea ɗin?." Islaha ta ɗan harari wayar sannan ta ce, "sallah na yi, yanzu zan kai masa." Mamy ta ce, "Thank you Islaha, in da wani abun ki kira ni." Bata jira me zata ce ba ta kashe. "Ni fa dan kina yi min kirki kwana biyu ne ya saka na ce zan kula da ɗanki, amma gaskiya bana so a takura wallahi. Haba! Ya kwana yana maƙale min jiki kamar wata matarsa, kuma yanzu na haɗa masa tea?. Ni ba abinda ya kawo ni gidan nan kenan ba, ku nemi matar aure ta dinga yi masa ta samu lada, ni C wife ce” ta faɗa tana miƙewa ta fita daga ɗakin. Rana ta farko da ta shiga kitchen ɗin gidan, ta kunna switch a take haske ya gauraye ko ina. Ta ga babban kitchen ne iya ganin ka, mai kyau wanda da kayan alatu kala-kala. Ta ƙarasa tana kallon stove ɗin, sai kuma ta yi tsaki ganin kettel a gefe, ta zuba ruwa ta kunna ta tsaya tana jira ya yi. Tana tsaye tana tsaki saboda takaici, yana tafasa ta kashe ta ɗauki mug ta zuba, ta fara buɗe buɗe har ta jawo wata drawer da kana ja zata biyo ka kamaar spring. A nan ta ga kayan tea da yawa, ta ɗauki tea leave ta saka masa, ta saka sugar kaɗan kamar yadda Mamy ta ce, ta kashe hasken ta hau saman. Kai tsaye ɗakinsa ta shiga ta tarar ya kunna red light yana zaune a kan gadon ya dafe kansa da duka hannayensa. Yana jin an buɗe ƙofar sai ya yi tunanim Mamy ce cikin muryar marasa lafiya ya ce, "Mamy kaina yana ciwo, ina jin ciwon cikin har yanzu bai daina ba." Jin yadda ya yi maganar a sanyaye da shagawaɓa kamar ɗan shekara biyar sai ta yi siririn tsaki ta ce, "this boy is too lazy! Ko ni da nake fama da ciwon mara bana wannan rakin da yake yi” ta faɗa tana tsaki sannan ta ƙarasa ta tsaya nesa dashi tana harararsa. Sai da ta gama harararsa sannan ta ɗan matsa kusa da shi ta ce, "Ga tea,Mamy ta ce ka sha." A hankali ya ɗago kansa ya kalle ta suka haɗa ido, Islaha ta ga yadda fuskarsa ta rame lokaci ɗaya, idanunsa sun yi ja, kana ganinsa ka san da gaske ba shi da lafiya. Sai ta ji ya bata tausayi kaɗan ba mai yawa ba, ta miƙa masa tea ɗin ta ce, "Mamy ta ce ka sha tea." Cikin murya mai sanyi da ta ke nuni da yana cikin rashin lafiya ya ce, "tana ina?." "Bata nan." "Ki kira ta, ta zo ta bani tea ɗin" yana faɗa yana komawa da baya ya kwanta, rigar jikinsa ta ɗage cikinsa ya fito waje, har ana ganin navel ɗinsa a bayyane. Idanunta suka sake sauka akan logon short ɗinsa, amma yanzu fari ne saɓanin na daren jiya, ta yi tsaki tana ɗauke kanta. Bata san meyasa logon Nike ɗin nan yake burge ta ba, ba yau ta saba ganin kayan kamfaninsu ba, amma in ta gani a jikinsa sai ta ji yana burge ta sosai. Ta ɗauke ta rasa me zata ce masa, sai kuma ta kira Mamy a waya kamar yadda ya ce. Bugu ɗaya Mamy ta ɗauka kamar jiran kiran take yi, Islaha ta ce, "Mamy ya ce na kira ki ki ba sa tea ɗin ya sha.” Mamy ta ce, "Ki ba shi da kan ki Islaha.” Islaha ta yi shiru kawai bata ce komai ba tana jin maganar mamy kamar wasan yara, tana maimaita kamar ya ta basa tea da kanta ita bata gane ba, a baki zata basa ko ya ta kasa fahimta. Muryar Mamy ta katse mata tunani ta ce, "ki yi feeding ɗinsa, in ba shi da lafiya yana da rigima Islaha, ya fi son komai a yi masa, ki kula da shi, ki yi masa duk abinda yake so, Please" tana gama faɗar haka ta kashe wayar Islaha ta bi wayar da kallo cikin mamaki. Islaha ta ce, “tabɗi! Ashe sai dai kar ya sha, ya shekara dubu yana ciwon ciki bai dame ni ba, bazan iya wahala da ɗaukarwa kai zunubi ba. Shi ba ɗan uwana ba, ba mijina ba kawai na zauna ina ba shi tea a baki kamar wacce ya siyo ya ajjiye? Bazan yi iya wannan saɓon ba, ni bazan yi feeding dinsa ba wallahi, kwanciyar da ya yi a jikina ma Allah ya bi min...." Sai kuma ta tuna wani abu ta ce, "Astagafirullah! Allah ka yafe min abinda na ce. Amma tsakani da Allah bazan iya feeding wannan lazy ba, dama ace wani mutumin kirki ne sai na yi saboda Allah, amma bazan bazan iya aikin da babu lada ba, ga rashin mutuncin da yake yi min son ransa. Wai yana da rigima, ƙato kamar wannan ace yana da rigima kamar yaro ƙarami? Yau kam bazai sha tea ba indai ni zan ba shi” ta faɗa tana kawar da kai gefe, sai kuma ta sake kallonsa ta ji ya bata tausayi. Nana Haleema. RDB3P49 Nana Haleema. Islaha tana tsaye hannunta riƙe da mug bata motsa ba balle ta ƙarasa ta ba shi kamar yadda Mamy ta ce. Ta kawar da kai gefe daga, dan bata san me yake jan idanunta zuwa ga kallon logon short ɗinsa ba, bata san meyasa idanunta yake son kallon logon ba. Ƙirjinta sai bugawa yake yi cikin wani irin yanayi, ga tea a hannunta amma baza ta iya yin abinda Mamy ta ce ba. Gajiya ta yi da tsayuwar sai ta waiwayo ta ga yana yadda yake a kwance bai motsa ba, ta sake kawar da kanta ta kuma kallonsa ta ga yana yadda yake a kwance. Ta kalli tea ɗin hannunta sai ta lura har ya fara sanyi, ta sake kallon Rehaan sannan ta ce, "Ga tea in ji Mamy." Rehaan yana jinta dan maganarta har tsakiyar kansa ya ji ta shiga, ya yi shiru bai motsa ba dan ya ji daɗin kwanciyar sosai. Islaha ta zauna daga gefensa a ɗarare ta sake kallonsa, muryar ta a tausashe ta ce, "Ga tea." Ya buɗe idanunsa ya kalle ta suka haɗa ido, sai ta yi saurin ɗauke nata daga cikin nasa, dan yadda idanunsa suka koma kana gani ka san ba shi da lafiya. Rehaan ya miƙe zaune a hankali, Islaha sai ta ga ya ruɗe yana juya kansa alamun ya tsokano ciwon, a hankali kuma sai ya dawo daidai, ita dai kallonsa take yi tana mamakin wannan wanne irin ciwo ne, duk kuɗin da yake da shi ace an kasa maganinsa. Cikin muryarsa da bata fita sosai ta ji ya ce, "Ina Mamy?." Islaha ta ce, "Bata nan." Ya lumshe idanunsa ya ce, "call her, please." Jin ya haɗa da roƙo sai ta ɗauki wayar ta kira number Mamy. Mamy tana ɗauka Islaha ta ce, "Mamy ya ƙi sha ya ce na kira ki." Mamy bata ce komai ba da katse kiran, ɗakin ya yi shiru idanunsa a lumahe ita kuma tana zaune tana tunanin wannan ciwo. A lokaci aka yi knocking ƙofar daga baya aka buɗe aka shigo, Mamy ta shigo da sallama ta ƙaraso ta zauna a gefensa sai ya zama sun saka shi a tsakiya, Islaha tana dama, Mamy tana haggunsa. Mamy ta riƙe hannunsa ta ce, "Gani Rehaan, meye, ciwon ne har yanzu?" Ta faɗa cike da kulawa tana kallonsa. Rehaan ya kwantar da kansa a kafaɗarta ya ce, "Mamy bai daina ciwo ba." Mamy ta shafa kansa ta ce, "Sannu, zai daina a hankali. Me ka ke so? Ga tea an kawo maka tun ɗazu ba ka sha ba" ta faɗa tana miƙawa Islaha hannu alamun ta bata. Islaha dai kallonsa take yi tana taɓe baki, ganin yadda yake marairaicewa a jikin Mamy kamar wani yaro ƙarami, tana aiyana ko yaro ɗan shekara goma bazai abinda yake yi ba. Lokaci ɗaya ya sake bata haushi, ta yi siririn tsaki ta ce, "ina aka san namiji da raki? Sai a wajen Mr Rehaan" Mamy ta ɗago da kansa daga kafaɗarta tana basa tea ɗin a bakinsa ta ce, "har ya fara yin sanyi, karɓi ka sha." Rehaan ya girgiza kai alamun ba ya so. Mamy ta ce, "Sai ka sha Rehaan, cikin ka babu abinci, karɓi a ka sha." Rehaan ya ɗago kansa daga jikinta, ta saka masa mug ɗin a bakinsa ya ɗan sipping ya koma ya kwanta ba tare da ya yi swallowing tea ɗin ba. Sai daga baya yake swallowing yana jikin Mamy a kwance tana shafa kansa ta ce, "Sannu Rehaan." A haka ta sake ba shi ya sha har sau uku, sannan ya ce ya isa. Mamy ta ce, "zaka yi bacci?." Rehaan ya ɗaga mata kai alamun eh zai yi. Mamy ta waiwaya ta kalli Islaha da ta mayar dasu tv tana kallo, sannan ta sake kallonsa ta ce, "To ka kwanta ka yi baccin, ga Islaha nan, duk abinda ka ke so zata yi maka." Duk da ba shi da lafiya sai da ya ɗago kai ya kalli Mamy jin abinda ta ke faɗa wanda bai saba ji ba, Mamy ta ɗaga masa kai ta ce, "eh, zata yi maka duk abinda ka ke so. I trust her, shiyasa na bata ragamar kula da lafiyar ka a hannunta." Bai ce komai ba ya koma ya kwnata a jikinta. Islaha da take gefe tana jin abinda Mamy ta ce, ta girgiza kai ƙasa-ƙasa ta ce, "Ka ji Mamy da wata magana don Allah, wai ga Islaha nan, ni zan dinga kula da shi? In aka bar ni da shi yana yi min wannan rakin kafin a awa ɗaya ya fusata ni wallahi" Ta faɗa yadda Mamy baza ta ji ba Mamy ta ce, "ka kwanta, za ka ji daɗi." Sai kuma ta kalli Islaha ta ce, "Islaha ba ni ruwa a kofi." Islaha ta miƙe ta fita tana girmama wannan soyayya da kulawar da take tsakanin Mamy da Rehaan, dole mutanen gidan su dinga cewa Mamy bata da kunya, Rehaan shine ɗanta na fari amma ta ke yi masa haka, abinda fulani bazasu taɓa yi ba kenan. Kunya ce a tsakaninsu da ƴaƴansu na fari, wasu ko iya haɗa ido ba sa yi da su balle a dinga rarrashinsu haka. Ita kuwa hakan ya burge ta, sai ta ke ji ina ma itama tana da wacce zata yi mata haka, yadda take fama da cramp ɗin nan da zata dinga samu wannan gatan da ta ji daɗi. Tana wannan tunanin ta koma ta kaiwa Mamy cup ɗin ta karɓa ta ce, "thank you." Mamy ta yi masa tofi a ruwan ta ɗago kansa ta ba shi ya sha ruwan sannan ta ce, "Kwanta ka huta.." Bai ƙi ba ba ya kwanta, Mamy ta miƙe a lokacin aka kira wayarta da take hannunta. Sai ta miƙawa Islaha cup ɗin da ragowar ruwa a ciki ta ce, "ki ɗaga rigarsa sama, ki shafa masa ragowar ruwan a cikinsa, ina zuwa." Islaha ta ji gabanta ya faɗi sosai, ta tsaya tana kallon cup ɗin ba tare da ta karɓa ba, Mamy ta kalle ta suka haɗa ido sai ta karɓa Mamy ta fita tana amsa wayar. Islaha kalli ruwan hannunta, ta kalli Rehaan da yake kwance idanunsa a rufe, ta girgiza kai tana taɓe bakinta, dan gaskiya baza ta iya ba. Ta kuma kallonsa ta kalli hannunta tana gwadawa, tana gwada ta ɗaga rigarsa da hannunta, sannan ta shafa ruwa a skin ɗinsa. Ta sake girgiza kai ta ce, "taɓɗijam, bazan iya aikin nan ba gaskiya, da dai mijina ne na gaske sai na yi, amma bazan iya aikata aikin nan ba." A lokacin Mamy ta dawo ta kalli Islaha ta ga tana yadda ta bar ta, babu alamun ta tashi daga inda take zaune. Mamy ta ce, "ba ki iya ba?." Islaha ta turo baki tana sunkuyar da kanta ƙasa, Mamy ta yi murmushi ta riƙo hannunta suka fito parlour dan kar su dame shi da magana sannan ta ce, "ba za ki iya ba?." Da saurinta ta ɗaga kai alamun eh, Mamy ta ce, "meyasa?." Islaha ta kalli Mamy bata ce komai ba, Mamy ta ce, "ba mijinki bane?." Islaha ta kawar da kai bata ce komai ba, dan bata san wacce amsa zata bawa Mamy ba. Mamy sake yin murmushi ta ce, "mijinki ne, yin hakan ba laifi bane Islaha. Ki je ki yi abinda na ce ki dawo." Islaha ta shagwaɓe fuska tana kallon Mamy ta ce, "wallahi bazan iya ba." Mamy ta dafa kafaɗarta ta ce, "za ki iya, je ki." Islaha ta kalli ruwan hannunta bata ce komai ba, dan ita kanta ta san baza ta iya shafa masa ruwa a cikintsa ba, baza ta iya ɗaga rigarsa sama ta zuba ruwa a hannunta tana taɓa shi ba. Amma tana ganin girman Mamy, a cikin kwanakin ta yi mata abubuwan kirki sosai, kuma ko babu komai babbar mace ce wacce ta haife ta, zata iya yiwa duk wanda ta saka ta yiwa tunda neman lafiya ne. Matsalar da aka samu da ya zo akan Rehaan, da wani ne daban tsaf zata yi, amma Rehaan ɗin ne baza ta iya taɓa jikinsa ba. Ganin Mamy ta zuba mata ido sai ta nufi ɗakin kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki tana tunanin katoɓarar da zata tafka. A yadda ta bar shi a haka ya ke, yana kwance yana kallonsa sama. Ta hararesa sannan ta ce, "da mutumin kirki ne da akwai sauƙi, amma ba na kirki bane." Ta ƙarasa tana kallon fuskrsa ta ga idanunsa a rufe, gashin idanunsa sun sauka har akan fuskarsa, hancinsa ya sake yin tsaho, ga ƙaramin bakinsa a rufe. Ta ɗauke kai tana kallo ƙofar ɗakin da ta bari a buɗe, dan kar ta rufe a zo a same ta tana shafa masa ruwa a kan cikina ayi tunanin wani abun suke aikatawa da shi. Rigarsa ta ke kallo tana tunanin yadda zata ɗagata sama, ba dan kar Mamy ta gane ba ai akan rigar zata kwarara ruwan kawai a huta. Ta sake matsawa gab da shi, ta saka yatsu biyu ta riƙe rigar kamar yadda ake riƙe abin ƙyama ta tsaya a haka, ita bata ɗaga rigar ba kuma bata saki ba. _Ke Islaha ba wani abun bane ba, ba shi da lafiya taimaka masa za ki yi, ko babu komai za ki samu ladan taimakon mara lafiya. Ki shafa masa kawai._ Abinda zuciyarta take faɗa mata kenan, sai ta samu courage ta ɗan janye rigar kaɗan, kai tsaye idanunta suka faɗa kan logon Nike da yake jikin short ɗin jikinsa. Ta runtse ido ta ce, "Innalillahi! Na shiga uku, me yake kai idanuna wajan nan ne? Logon Nike ɗin ne ban sani ba koma meye?." Ta yi tsaki ta ɗaga rigar ta zuba ruwan a hannunta tana tunanin ta ina zata fara.Ganin tana ɓata lokaci sai hankali ta fara zuba ruwan a kan cikinsa, sannan ta kai hannunta zata taɓa ruwan da ta zuba, kamar mai jin tsoro ta tsayar da hannun a tsakiya, ita bata ɗora akan skin ɗinsa ba ita bata ɗauke ba. Ta runtse ido kamar wacce zata taɓa wuta a haka ta kai hannunta, sai ta yi saurin ɗaukewa kamar wacce wutar lantarki ta ja, ta yarfe hannu ta sake rufe idanu sannan ta shimfiɗa palm ɗinta a akan cikinsa. Wani irin shock ta ji ya ja ta a jikinta, ta daure bata ɗauke hannun ba ta ɗan shafa cikinsa a hankali. Santsi da laushin skin ɗinsa ya saka hannunta ya zame ya yi ƙasa sai jin hannunta ta yi akan nalve ɗinsa.Ta daure bata buɗe ido ba, ta yi ƙoƙarin daidaita hannunta yadda bazai sake zamewa ba, ta cigaba da shafe ruwan tana yi tana salati. Tana jin yadda cikinsa yake ɗagawa a hankali, ga zafi da cikin ya yi kamar mai zazzaɓi. A haka ta janye hannunta daga cikinsa, har lokacin bata buɗe idanunta ba, kuma yanayin da take ji har lokacin bai bar jikinta ba. Kafin ta ƙarasa janye hannunta ta ji an riƙe hannunta, hakan ya saka ta firgita ta buɗe idanunta tana kallon hannunta. Hannunsa ta gani riƙe da wrist ɗinta, ta wara idanu waje tana tunanin daman ba bacci yake yi ba kenan? Daman yana ji tana taɓa masa ciki bai hanata ba?. Ta kalli fuskarsa ta ga ya buɗe ido, ta ɗauke kanta saboda takaici, dan da ta san idanunsa biyu bazata aikata ba. Kamar mai raɗa ya ce, "Please don't stop, it makes me feel better" ya faɗa a hankali yana lumshe idanunsa kuma bai saki hannunta ba. Islaha ta ji abinda ya ce amma sai ta yi kamar bata ji ba, ya mayar da hannunta a kan cikinsa, stilt bai saki hannun ba. Ta bi hannunta da kallo ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta yi shiru, ta haɗe rai kamar yana kallonta. Sai sannan ya saki hannunta, kuma ta kasa ɗauke hannunta daga cikinsa, sai kallon hannun nata take yi kamar mai ganin wani abun a hannun. Mamy tana tsaye a bakin ƙofa tana kallon duk abinda yake faruwa, da yadda ta ɗaga rigar, da yadda ta ke shafa masa ruwan duk ta gani, tana daga tsaye tana kallonta bata sani ba. Duk tsaki da harararsa da ta ke yi tana gani. Ta yi murmushin jin daɗi, dan a ranta take jin Rehaan ya samu daidai shi, wacce bata aure sa dan kuɗinsa ko wani abu ba, ya auri wacce bata raga masa saboda yana da abin duniya, ya auri wacce bata san kara ko ɗaga ƙafa akan abinda ta saka a gaba ba. Tabbas Islaha ce daidai da Rehaan, bata aure shi da wani abu nasa ba, beside ta fi ko wacce mace raina shi a duniya. Mamy ganin Islaha ta zauna sai ta ƙarasa rufe ƙofar a hankali, ta juya ta sauka tana ji a ranta ta samu wacce zata maye gurbinta wajan kula da Rehaan. Nana Haleema. RDB3P50 Nana Haleema. Islaha kamar robbot haka ta zama, tunda ta ƙame haka bata motsa ba, ko hannunta bata motsawa, tunda ya mayar da hannunta kan cikinsa bata kuma motsi ba kuma bata janye hannunta ba kuma bata cigaba da shafa ruwan ba. Tunani take yi ta ya shafa masa ruwa a ciki ya zama yana jin daɗin hakan? Har ya kasa haƙuri ya riƙe hannunta ya cr kar ta daina?. Ita kaɗai take tunaninta ta ɗauke kai daga kallonsa. Sai daga baya ta kula ya yi bacci, numfashinsa ya yi daidai sannan ya saki jikinsa. Ta janye hannunta ta miƙe tsaye tana kallon yadda yake baccin a nutse. Goshinsa ta kalla sai ta ga kamar yana gumi, ta ɗauki remote ta ƙara ac ɗakin, sannan ta kashe sauran hasken da ya rage ta fita daga ɗakin. Da ta koma ɗaki itama bacci ta yi, ba wajan aiki zata ba je shiyasa bata yi ƙoƙarin tashi ba. Sai ƙarfe sha ɗaya na safe ta farka, bata fito ba sai da ta yi wanka ta canja kaya. Kayanta ta ke kallo ganin duk ta saka, daman kaɗan take ɗaukowa daga gidansu Safeera ta mayar dasu, ta mayar dasu ta ajjiye sannan ta fito parlour. Parlour shiru babu motsin kowa, komai na parlour a a kashe alamun bai tashi daga bacci ba kuma Mamy bata zo saman ba. Ta kalli ɗakinsa tana ji kamar ta je ta ga ya yake, dan ya bata tausayi, bata taɓa ganin ciwon ciki irinsa ba, sai kuma ta fasa ta juya zata sauka. Haɗuwa suka yi da Mamy tana tahowa upstairs ɗin ita kuma zata sauka, Islaha ta tsaya tana jira ta ƙaraso su gaisa. Mamy tana ƙarasowa kusa da ita ta yi murmushi tare da hugging ɗinta ta ce, "Good morning Islaha." Islaha ta yi murmushi ta ce, "Good morning Mamy." "Ya ki ka kwana?." "Lafiya lau." "ya jikinsa?." Islaha ta ce, "da sauƙi, bacci yake yi." Mamy ta gyaɗa kai ta ce, "let me check on him." Ta faɗa tana wucewa, sai kuma ta juyo ta kalli Islaha ce, "na san ba ki je kin duba shi ba kema, zo mu je tare" ta faɗa tana yin gaba, Islaha kamar zata yi kuka amma haka ta bi bayanta. Suna buɗe ƙofar ɗakin ya buɗe ido, Mamy ta kunna hasken ɗakin ta ce, "Good morning my love." Ya miƙe zaune yana yamutsa fuska saboda haske ya ce, "Morning Mamy." Ta ƙarasa ta zauna kusa a da shi ta ce, "Ya jikin?." "ya yi sauƙi." Ta riƙe fuskarsa ta ce, "Ya daina ciwon?." Ya ɗaga mata kai yana ajiyar zuciya. Mamy ta ce, "ka yi wanka, ka zo ka yi breakfast." "Okay." Ta yi pecking ɗinsa a goshi ta miƙe ta fita ta bar Islaha a ciki har da rufe ƙofar. Sautin rufe ƙofar ya saka Islaha ta juya tana kallon Mamy, a ranta tana ayyana wai me matar nan take nufi da ita ne da zata fita ta barsu su biyu harda rufe ƙofa?. Ta juya zata fita bata ce masa komai ba, kamar yadda shima bai ce ba, gab da zata ƙarasa ƙofar da zata kai ta parlour ta ji ya ce, "Thank you." Islaha ta tsaya cak jin maganarsa mai haɗe da godiya wacce bata yi tunani ba. Ta juyo suka haɗa ido, yadda ya rame lokaci ɗaya sai ya sake bata tausayi sosai, duk da ta san akwai rakinsa amma da alama ya ji jiki. Ta ɗage gira sama tana yi masa sani kallon up and down, dan ita tunda ta ga yana wannan langwaɓewar ta sake raina shi ta ce, "for what?." Bai san me ya ba shi dariya a kalamanta ba, ya yi murmushi yana kallonta sannan ya ce, "ask me" ya faɗa yana miƙewa tsaye yana yamutsa fuska ya ɗan ɗaga hannunsa yana stretching slowly. "Wayyo Allah!." Isɓaha furta ba tare da ta shirya ba, ganin idanunta sun sake janta inda suke fara janta jiya. Ita ta rasa meye a logon nan da take kallon, bata san meyasa idanunsa suke kallon logon ba. Jin abinda ta ce sai ya kalle ta ya ga idanunta a rufe, bai ce mata komai ba ya dama slippers ya shiga bathroom bai kuma kallonta ba. Islaha fitowa parlour ta tarar da Mamy a zaune, har ta haɗo masa breakfast daga ƙasa ta ajjiye. Mamy ta kalli Islaha ta ce, "zo ku yi breakfast." Islaha ta zauna a kusa da Mamy, da kanta take haɗa mata tea kafin ta kalle ta ta ce, "kina son milk?." "Ina so." "Okay my love" ta faɗa tana haɗa mata da kanta ta miƙa mata. Islaha ta ce, "thank you Mamy." Mamy ta zauna sannan ta ce, "enjoy your breakfast." Islaha ta fara shan tea ɗin, ta ɗauki two slices bread tana ci. Wani irin maiƙo ne da bread ɗin ga laushi da daɗi, daƙyar za ka iya cinye guda biyu saboda maiƙon da ya ke da shi. Daƙyar ta iya cinye ɗaya, sai ta haɗa da lamb pepper soup ta ci. Mamy ta ce, "ke kina shan madara, ga Rehaan ba ya son madara, in dai ya sha sai ta dawo, sai ya ce ƙarni take yi. Kuma zai sha a drink ko smoothie, amma bazai sha a tea ba.” Islaha ta yi murmushin da ya tsaya a kan laɓɓanta kawai, tana mamakin labarin da Mamy take bata, tana tunanin ko ina ruwanta oho. Sai da ta gama breakfast ɗin sannan Mamy ta ce, "Thank you Islaha." Islaha ta kalli Mamy tana ajjiye kofin hannunta tana murmushi bata ce komai ba. Mamy ta ce, "na gode da ki ka kula da Rehaan, in ba ke ba babu wanda zai kula da shi da zuciya ɗaya a cikin gidan nan, daga ke sai Dear, i mean Abbansu." Mamy ta ce, "akwai lokacin da ya yi irin wannan ciwon, na bar shi a hannun wani a gidan nan, wani yayansa Sameer na gidan nan, kafin gari ya waye an buɗe wayarsa an ɗauki document, an ɗauki kuɗi. At the end an ba shi abinda sai da ya kwana biyar yana ciwo bai san inda kansa yake ba. Amma ke da zuciya ɗaya na bar ki da shi, ga shi na same sa lafiya babu abinda ya same shi." Islsha ta yi murmushi kawai bata ce komai ba, dan ita bata san me zata cewa Mamy ba. Mamy ta dawo kusa da Islaha ta riƙe hannunta ta ce, "Islaha a kaf gidan nan, kar wani ya baki magani ya ce ki bawa Rehaan na ciwon ciki ko na wani abun ki karɓa ki ba shi, ko da an matsa sai kin karɓa, ki karɓa amma kar ki basa. In Daada ce ta ba ki ki karɓa da zuciya ɗaya, kar ta yi miki aike a kawo miki ki yo amfani da shi. Kaf gidan nan ba ƙaunarsa suke yi ba, masu sonsa kaɗan ne. Rehaan yana da son ƴan uwa, amma sun ware sa gefe saboda suna ganin shine ƙarami kuma ya fi su ɗaukaka. Ƙaramar hanya ake nema da za a cutar da shi, ƴar ƙaramar ƙofa ake nema a shigo a yi masa kisan gilla. Lokacin da muka taɓa haɗuwa da ke a asibiti, yana kwance an ba shi poison, har yanzu ba a san wanda ya bayar ba." Islaha jinta kawai take yi bata ce komai ba har ta je ƙarshe sannan ta ce, "In sha Allah Mamy." Mamy ta ce, "da farko ban karɓi auren ki ba saboda ba ya so, ni kuma duk abinda Rehaan yake so shi nake so. A zaman three weeks da na yi da ke sai na fahimci ki, sai na fahimci da Rehaan da babu shi duk ɗaya ne a wajan ki. Sai hakan ya yi min daɗi, saboda na san ba ki zo nan dan ki cuce shi ko dan kuɗinsa ba, dan na ga ke gabaɗaya ma haushi yake ba ki, ko?." Islaha ta zaro ido waje cikin jin nauyin Mamy ta rufe fuska da hannunta. Mamy ta yi dariya ta ce, "haka ne Islaha, haushinsa ki ke ji a yanzu, amma ina fatan nan gaba ki so shi." _Ba amin ba, har abada Mamy, ina da wanda na ke so, me zan yi da wannan ragon?._ Abinda ta faɗa a ranta kenan, amma a zahiri ba ta ce komai ba sai yaƙe da take yi. Mamy ta ce, "ki yi min alƙawarin za ki kula da shi kamar yadda nake kula da shi." Islaha ta buɗe fuska zuciyarta tana bugawa, bata son ɗaukar alƙawarin da bazata iya ba, dan gaskiya bazata iya kula da Rehaan ba. Kafin ta yi magana ya buɗe ƙofa ya fito, suka kalle shi yana sanye da jallabiyya black blue mai dogon hannu, gashinsa a ɗaure yana tahowa a hankali. Mamy ta miƙe ta riƙo hannunsa ya riƙe hannunta ya zauna a kusa da ita, ta ɗauki wani ruwa a kofi ta ce, "karɓi ka sha" ta faɗa tana ba shi glass cup ɗin. Bai ce komai ba ya karɓa ya sha, ruwan zamza ne da aka sauke masa alkur'ani, indai yana gida dashi yake fara breakfast sai dai in Mamy bata nan. Ta miƙa masa tea ta ce, "ka sha, za ka ji daɗi." Rehaan ya ajjiye tea ɗin da ya karɓa akan table, ya yi pecking goshinta sannan ya ce, "you are the best mother in the world, i love you so much Mamy." Mamy ta shafa kanta ta ce, "and you are the best son in the world, take your tea and enjoy, kafin ya yi sanyi." Ya wani shagwaɓe fuska yana kallon ta ya ce, "you can't say you love me?." Ta yi dariya tana jan hancinsa ta ce, "i love you." Ya yi murmushi ya kai tea ɗin bakinsa ya sha a hankali. Islaha kallonsu take yi cikin burgewa da ban sha'awa, bata san idanunta sun cika da hawaye ba sai da ta ji saukarsu a kan fuskar ta. Kewar mahaifiya ta ji tana tasowa a zuciyarta, sai ta ke gani ina ma tana da uwa da zata dinga kula da ita a duk lokacin da bata da lafiya, Ina ma tana da uwa irin Mamy da zata dinga rarrashinta har ta ba ta abinci a baki. Rashin uwa shine yake sakawa ta yi kuka mai ƙarfi a duk lokacin da take cikin wannan yanayi, bata da gatan da za a bata abinci a baki a rarrasheta kamar yadda Mamy take yiwa Rehaan. Babu wanda ya taɓa tsayawa akan nema mata maganin ciwon da take fama dashi a cikin ko wanne wata, duk da Hmma ya yi ƙoƙari akan hakan, sun je asibiti kala-kala amma bata daina ba. Amma ta san da mahaifiyarta tana nan da yanzu tana nema magani ko da ta san bazai yi amfaniba. Dafa kafaɗarta Mamy ta yi ta ce, "Islaha!..” “Me ya faru ki ke kuka?." Sai a lokacin ta farga kuka take yi, ta goge idanunta bata ce komai ba. Mamy cikin kulawa ta ce, "faɗa min, meye ya faru ki ke kuka?." Islaha ta goge ido ta ce, "ina tunawa da Mamana, ina so na tuna da fuskarta amma na kasa. Na rayu babu ita, ban san inda ta ke ba, tana da rai ko ta mutu ban sani ba. Iyayen gidan marayu kawai na sani, sai su Baffa da nake kallo a matsayin iyayena, amma ba mahaifa ba" ta faɗa hawaye yana sake sakkowa daga idanunta. Mamy ta yi hugging ɗinta tana shafa bayanta a hankali cike da tausayi da raunin da ya mamaye mata zuciya. Islaha jin ta samu gatan da wata mace ta rungumeta da fuskar rarrashi sai kawai ta fashe da kukan da yake damun ranta. Mamy tana shafa bayanta a hankali cikin wani irin yanayi, ƙirjinta yana bugawa da sauri, tana jin wani irin abu yana shiga jikinta a game da Islaha. Bata san meye, amma tana jinsa baƙo wanda bata taɓa ji ba. Soyayyar Islaha ta gama kamata lokaci ɗaya, ta gama shiga zuciyarta da jininta, yanzu kuma ga tausayinta da ya ke sake samun muhalli mai kyau a zuciyarta. Rehaan ma kallon ta yake yi, rana ta farko da zuciyarsa ta yi sanyi da rauni a kanta, ko lokacin da ta samu attack ta silarsa bai ji irin wanann yanayin ba. Sai ya tafi tunanin da shine babu Mamy wanne hali zai shiga? Wanne irin halin kewa zuciyarsa zata kasance a ciki?. Ya sake kallon Mamy, ya kalli Islaha da ta ɗago kanta tana share hawayenta. Ya ɗauke kai daga kanta jin zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi, ya ja numfashi mai tsaho, duk da ciwon da yake ji a cikinsa bai hana shi sauke numfashim da ƙarfi ba. Tabbas ya ji tausayinta sosai, lokaci ɗaya tausayin ya samu gurbi mai girma a zuciyarsa.... Nana Haleema. KRBBK: RDB3P51 Nana Haleema. Mamy ta gogewa Islaha hawayen da take yi sannan ta bata ruwa ta sha sannan ta ce, "Ki daina kuka, kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwarsa, ke maraici shine jarabawar ki." Mamy ta kuma cewa, "a da kin san iyayenki?." Islaha ta ɗaga kai ta ce, "Ban san mahaifina ba, amma na san fuskar Mamana, duk da ina gani kamar a mafarki na santa. Lokacin ya yi nisa da yawa, bazan iya tuna tsahon lokacin ba amma na santa, na san na yi rayuwa da ita. Bazan iya gane fukarta ba, amma ina iya hangen ta a idanuna, abu ɗaya na riƙe kawai, ina kiranta da Mama." Mama ta ce, "kina shekara nawa aka kai ki orphanage?." "Na taɓa sakawa an duba min file, ance min ina da shekara takwas na je gidan." "Akwai sunan wanda ya ki ki gidan?." "He is just wrote Islaha Muhammad Madibbo, ban sani ba ko sunan mahaifina haka, ko kuma shine kawai ya saka ban sani ba, shiyasa nake amfani da sunan Muhammad as my surnname." Mamy ta girgiza cikin taushin murya da son rarrashinta da kwantar mata da hankali ta ce, "ba ki san wanda ya kai ki ba?." "Hamma Saheer ne." "Meyasa ba ki taɓa tambayarsa a ina ya same ki har ya kai ki gidan ba?." Ta yi shiru bata ce komai ba, dan ta tambaye shi ba sau ɗaya ba amma sai ya ce mata zai faɗa mata sai sun yi aure, ita kuma bata matsa masa sosai ba, amma yanzu kam zata yi. Mamy ta shafa kanta ta ce, "is okay, Ki daina damuwa, in akwai rabo za ki ga iyayen ki wata rana." Bata ce komai ba sai ajiyar zuciya da ta yi. Rehaan yana jinsu bai ce komai ba, amma tabbas ya ji tausayinta mai yawa, ya ji ina ma zai iya da ya nemo mata mahaifiyata ko dan ta samu soyayyar da yake samu daga wajan Mamy. Kiran sallar ƙarfe ɗaya ya saka Islaha ta miƙe tsaye ta ce, "Mamy zan yi sallah sannan na wuce wajan aiki." Mamy ta ce, "okay my love, sai kin dawo." Bata ce komai ba ta wuce ko kallon Rehaan bata yi ba, babu sannu babu ya jiki ta shiga ɗaki. Mamy ta kalli Rehaan da ya ɗauke idanunsa daga kan Islaha yana stirring tea da har lokacin bai shanye ba. Mamy ta ce, "Rehaan!." Ya kalle ta ta ce, "Ina so a bincika min orphanage ɗin da ta girma, ina so a nemo asalin min iyayenta, ina so ta fita daga maraicin da take ciki." Ya gyaɗa kai amma ya kasa cewa komai, dan gabaɗaya tausayinta ya cika masa zuciya har ya kasa magana, tausayinta yake ji sosai, dan rashin iyaye ba ƙaramin abu bane. Ya kasa riƙe maganar a zuciyarsa, ya kalli Mamy ya ce, "Ta bani tausayi." Mamy ta ce, "nima haka Rehaan, shiyasa nake so a yi bincike mai kyau, if possible ka yi magana da Saheer ɗin ka ji a ina ya same ta har ya kai ta orphanage. Tunda sai da ta girma aka kai ta ba tana jaririya ba, tabbas akwai dalilin da ya saka aka kai ta can, kuma duk wanda ya kai ta ya san a inda ya same ta. In aka ji inda aka same ta za a iya samun wani abu har a ga iyayenta." Rehaan ya shafa goshinsa bai ce komai ba ya yi shiru ya fara shan tea ɗin da yake hannunsa. Mamy ta ce, “She looks very decent and modesty, i lover her as my daughter.” Rehaan yana ji bai ce komai ba, ya cigaba da shan tea ɗin yana tunanin ya kamata ya bincika ya nemowa Islaha iyayenta.     Islaha ko da ta je wajan aiki haka take yin komai a sanyaye, kewar iyayenta take ji sosai, haka kawai Allah ya saka mata kewarsu fiye da yadda ta saba ji. Bata da cikakkiyar walwala har ta fito, a haka suka haɗu da Barr akan case ɗinsu suka tattauna, sannan ta tafi gida wajan Saheer dan sun yi da shi zasu je gidansa da ake ginawa. Sai da ta je ƙofar gidansu sannan ta yi masa waya, ya fito ya saka ta ta shiga mota suka fara tafiya ba tare da ta san inda zasu je ba. Kallon ta yake yi cikin mamaki ganin fuskar ta babu walwala, kuma tun daga ina yini bata sake cewa komai ba. Hakan ya saka shi ya ce, "Islaha lafiya?." Ta kalle shi ta ce, "Hamma in tambaye ka?." "Ina jin ki." "Za ka faɗa min?." "Me zai hana naƙi faɗa miki?." Ta sauke nunfashi ta ce, "A hannunwa ka karɓe ni har ka kai ni orphanage?." Ya juyo ya kalle ta kafin ya ɗauke ya cigaba da tuƙa motar ya ce, "Meyasa ki ke tambaya?." "Ina so na sani ne." "na ce zan faɗa miki, sai ranar da ki ka zama matata." "Lokacin ya yi min nisa, ni dai ka faɗa min don Allah." Saheer ya sake kallon ta ganin tana tare da damuwa mai yawa, sai ya yi shiru bai ce komai ba, dan ya san abinda zai faɗa maya a damuwa zai sake jefa ta. Islaha ta ce, "Hamma ka faɗa min, ina jin kewar iyayena sosai..." ta ƙarasa faɗa tana fashewa da kuka. "Subahanallah!" Saheer ya faɗa yana tsayar motar dan bazai iya cigaba da tafiya tana kuka ba. Ya ce, "meye na kukan? Ba kin yi min alƙawarin baza ki sake kuka akan hakan ba? Kin ce min baza ki sake tayar da maganar nan ba har sai ranar da muka yi aure. Meyasa za ki dawo da maganar yanzu?." "Ina ganin yadda uwa take kula da ɗanta, tana hana idanunta bacci saboda shi. Ina ganin soyayyar mahaifiya ƙarara Hamma, ina ganin ƙauna da...." Sai ta kasa faɗa ta yi shiru tana kuka sosai. Saheer ya haɗe rai dan ko bata ce ba ya san Rehaan da babarsa take nufi, ya kawar da kai daga kallonta sannan ya bata tissue ya ce, "ki goge idanunki." Ta karɓa ta goge ta sake kallonsa ta ce, "ka faɗa min don Allah, ka taimaka ka sanar dani ko zan daina jin kewarsu da na ke ji a raina. Wallahi ban taɓa jin kewar mahaifiyata kamar yau ba, da na ga yadda uwa take sadaukar da komai nata saboda ɗanta, sai nake ji ina ma nima tawa uqar tana kusa dani, nima ta kula dani ta rarrashe ni har na yi kuka a jikinta. Ka taimake ni ka faɗa min Hamma, bazan jure sai wani lokaci ba, yanzu nake so." "Islaha na faɗa miki, nima bani ke aka yi aka ce na kai ki, ni kaina bazan iya tuna waye ba. Amma ina kan bincike akan hakan. Da can bana bincike akan hakan, amma yanzu ina yi saboda ke, in na gano komai zan faɗa miki." Ta girgiza kai tana kallonsa ta ce, "rana ta farko nake ji kamar ban yarda da abinda ka ce ba, rana ta farko da nake jin maganar kamar ƙarya ba gaskiya bace. Hamma ban yarda ba wallahi, ni na san ka san wanda ya baka ni ka kai ni gidan marayu ba, har cikin raina ina ji ban yarda da kai ba." Saheer ya bita da kallo ya ce, "Islaha ni ki ke cewa ba ki yarda da abinda na ce ba?." "Gaskiya ta kenan Hamma, dan ban yarda da wannan maganar ta ka ba wallahi." Ya zaro idanunsa ya ce, "Harda wallahi?. Ta yi shiru bata amsa ba, dan gwara ta faɗa masa gaskiya ko zai daina rufe mata. Saheer ya girgiza kai ya ce, "To ban san me zance miki ba tunda kin rantse ba ki yarda ba. Ni daman na kula da halayenki, tunda ki ka yi auren nan ki ka fara raina ni, ban sani ba ko dan kina da aure ne, ko dan kin fara sanin meye auren ban sani ba." Ta ɗago jajayen idanunta ta kalle shi ta ce, "me ka ke nufi?." "Kina ganin kin je level ɗin da ban je ba, kin auri mai kuɗi da suna a Yola, kina zaune a gida mai girma da kyau, dole ki dinga ƙaryata ni in na faɗa miki magana. Daman na ga kamar kin karɓi auren nan, dan ga kin zama very comfortable a kai, bakya yawan complain kamar farkon auren." Ta kalle sa da mamakinsa da ya mamaye mata zuciyarta, sai ta kawar da kai sannan ta kuma kallonsa ta ce, "na zama comfortable da auren Rehaan ka ke faɗa? Kana so ka ce na yi accepting hndrent percent?." "Abinda na gani a zahiri nake faɗa miki, kamar kin karɓi auren, ban san me ki ke aikatawa tare da shi ba." Islaha ta kulle idanunta tana jin ɗacin kalamansa, ta yi shiru tana ji in ba dan shi ɗin bane da yanzu ta nunawa ko waye ya yi kuskurensa, amma shi ɗin ma dole ta nuna masa ya yi kuskure ko dan ya kiyaye harshensa nan gaba. Ta ɗago a fusace ta ce, "ka ce auri mai kuɗin da da ya fi ko wanne a Yola, mai kyau, kuma ɗan babban gida da komai ma da ka ce. Hamma ina so ka sani, wallahi da ace kuɗinsa ne a gabana da ba ka isa ka ganni ba, dah kafin ka ganni sai ka cike form, an turo min form ɗin, na yi approving, sannan a yi ma ka iso ka zo zuwa inda nake, in ka samu damar ganin nawa kenan....." Kafin ya yi magana ta ɗora ta ce, "Wallahi da na karɓi aure Rehaan da yanzu na canja, da yanzu Islaha da ka sani a baya ba itace a zaune a motarka ba. Amma gani a motar ka a zaune, na fito kawai saboda na yi maka magana, amma ka ke faɗa min haka dan kawai na tambaye ka asalina?." Saheer manakin kalamnta sun gama kashe shi, bata taɓa faɗa masa magana haka ba, ko da wasa bata taɓa kuskuren faɗa masa maganar da ya ji zafinta a ransa ba sai a lokacin. Ya ce, "a dah bakya iya faɗa min irin wannan maganar, amma yanzu ni ki ke faaɗwa haka, Islaha in ban ce kin canja ba me zance?." A fusace ta ce, "na canja ɗin Hamma! Na auri mai kuɗi na canja, na canja, na canja, sai me!?…..” ta ƙasa da muryarta ta ce, “Me za ki yi min dan na canja? Laifi ne dan na canja daga Islahan Hamma na koma Islahan Rehaan?....." Saheer ya zuba mata idanu kawai yana kallonta ya kasa cewa komai ba. Ta ce, "Kuma da ka ke cewa ba ka san me nake yi a tare da shi ba, in na yi ɗin ina ruwanka Hamma? Babu ruwan ka a cikin duk abinda na yi da shi, tunda ka san shine mijina ba kai ba, zan iya yin duk abinda zuciyarka ta ke faɗa maka ina yi, ai ba laifi na aikata ba....sai ma lada da Allah zai ba ni." Sai kuma ta dafe kanta tana wani jan numfashi mai ƙarfi, tana ji kamar zata samu attack a lokacin saboda takaicin maganar Hamma. Ta cire hannunta daga kanta ta kalle shi shi ta ce, "Ka cigaba da kallona akan canjin da ka ga na yi, ka cigaba da kallona akan duk abinda ka ke kallona da shi, don Allah kar ka canja. In ka ga dama daga ka fara siyan kayan jariran, dan ƙanwar ka Islaha ta kusa haifo maka ƴaƴa da mijinta da take aure. Ka cigaba da kallona a yadda ka ke kallo, haka nake Hamma!" ta faɗa tana miƙewa daga inda ta ke zaune, ta miƙa hannunta sitiyarin motar ta danna lock ƙofar ta buɗe, ta fita ta bar masa motar hawaye yana zubowa daga idanunta. A gefen titi ta zauna ta dafe kanta da duka hananyenta, kuka take yi mai matuƙar sauti, zuciyarta zafi take yi mata, damuwar rashin iyayenta ya fi mata komai ƙona a zuciyarta, ga kalaman Hamma mai nuni da bai yarda da alƙawarin da ta yi masa ba, sai abin ya haɗar mata goma da ashirin. Saheer yana kallon ta har ta zauna, duk da kalaman da ta faɗa masa sun ba shi haushi ga kishin da ya mamaye masa zuciya, amma ya hakan bai saka ya iya tafiya ya bar ta a wajen ba. Ya fito daga motar ya ce, "ki tashi mu tafi." Islaha ta yi masa banza bata ce masa komai ba, ya riƙo hannunta ta fizge cikin tsananin fusata ta ce, "kar ka sake taɓa matar aure, ni matarsa ce ba matar ka ba, kar ka sake taɓa ni. In ka kuma taɓa ni sai na saka mijina ya kai ƙarar ka, kuma sai alƙali ya ɗaure ka wallahi.” Haushi ya sake mamaye masa zuciya, amma haka ya daure dan ba ya so ya barta akan titi ya ce, "na ji, mu je." "Wallahi bazan shiga ba Hamma, ka je kawai" ta faɗa tana fara tafiya ta ƙyalesa a tsaye a wajen. A kan idanunsa ta hau napep ta tafi, ya hau motar ya tafi zuciyarsa tana yi masa zafi cikin kishi da haushinta mai matuƙar yawa. Nana Haleema. RDB3P52 Nana Haleema. Islaha kai tsaye gidansu Safeera ta wuce, ta shiga ɗakin Safeera ta faɗa kan gado ta fashe da kuka mai sauti. Safeera bata ce mata komai ba, tana tsaye tana saka kaya har ta gama shiryawa, ta zauna a kusa da ita ta ce, "Islaha meye?." Bata iya bata amsa ba sai kuka take yi, Safeera ta yi shiru ta barta tana kuka son ranta. Sai da ta gama sannan ta miƙe zaune Safeera ta ce, "me ya same ki?." "Safeera ina kewar iyayena, ina so na san inda suke, ina so na gansu, na fito daga can gidan nazo na samu Hamma na tambayesa ya faɗa min amma yake raina min hankali, wallahi bai taɓa faɗar abinda na ji ban yarda da shi ba sai ɗazu. Hamma ya san komai a kaina, meyasa yake ɓoye min!" Ta faɗa da ƙarfi tana hawaye. "Relax! Ki daina kuka ki kwantar da hankalin ki, ya aka yi ki ka san ya san komai a kan ki?." "A hannunwa ya karɓe ni ya kai ni gidan, a ina waɗanda suka ba shi ni su ke?." "Meyasa bai faɗa miki ba, meyasa ba ki taɓa tambaya ba sai yanzu?." "Na jima ina tambayarsa, sai ya ce min sai mun yi aure zai faɗa min. Yau kaɗai na ji ina so na sani, na tambayesa amma ni yake kallo yana cewa na canja, har yana cewa wai bai san me nake aikatawa tare da Rehana ba. In na aikata abinda zuciyarsa take faɗa masa ɗin ina ruwansa, ba mijina bane!?." Safeera ta zaro ido jin abinda Islaha ta faɗa, tana girgiza kai tana aiyana lallai Hamma ɗan gold ya ɓata mata rai da yawa, tunda har tana cewa Rehaan ba mijinta bane. Safeera ta ji daɗi a ranta, dan wallahi bata jin daɗin biyewa Saheer da take yi tana ɗaukarwa kanta zunubi. Ta ce, "Lallai Hamma bai kyauta ba, shi meye na sako maganar Rehaan dan kin yi zancen iyayen ki?." "Oho masa, kuma na jima ina tambaya bai taɓa faɗa min, sai ya ce kaza in anjima ya ce kaza. Na gaji, na gaji da wannan rainin hankalin nan nasa, zuciyata tana faɗa min akwai wani abun a ƙasa." "Kamar me?." "Oho." Safeera ta ce, "kema ke ce bakya jin magana, meye na hawa motar Saheer ku fita ke da shi don Allah?." Islaha ta yi tsaki ta ce, "nima na yi danasani, da na san haka zai ɓata min rai da ban fara ba." Safeera ta yi murmushi tana girgiza kai ta ce, "ki yi haƙuri, in sha Allah iyayen ki suna nan suna neman ki, in sha Allah Allah zai haɗa fuskokin ku a duniya." Ta ɗaga kai ta ce, "Allah ya sa." Ta amsa da amin bata ce komai ba. Islaha cikin jin haushin kalaman Saheer ta ce, "Wai ni yake kallon yana cewa kuɗi sun canja ni, na rantse da Allah da ace kuɗi zasu canja ni ko kallonsa bazan yi ba. Ina ganin yadda ake wasa da kuɗi kamar ba nemansu ake yi ba, inda kuɗin suna gabana da yanzu na manta wani Hamma a duniya" ta faɗa tana miƙewa ta ƙarasa wajan kayanta tana buɗewa. Safeera dai bata ce mata komai ba, ta yi shiru tana duba wayarta dan hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba. Ta gama abinda zata yi ta dawo ta zauna, sai kuma ta kira Lawal ta ce ya zo su koma. Safeera ta ce, "gabaɗaya kin canja yau, ki nutsu don Allah." Ta ce, "Safeera ban taɓa jin ƙaunar rayuwa da mahifiayara kamar yau ba, kin ga yadda Mamy take nunawa Rehaan ƙauna, kin ga yadda take rikicewa akansa in ba shi da lafiya, kin ga inda ta ke riritasa tana ba shi kulawa kuwa?. Sun burge ni sosai, kallonsu ne ya saka min kewar tawa mahaifiyar. Yadda iyayenmu na fulani suke kunyar yaransu ita bata yi, kula da shi take yi da jikinta da zuciyarta kamar ta goya shi. Na yarda duk duniya babu kamar uwa, ya Allah ya haɗa ni da tawa in tana da rai." "Amin" Safeera ta amsa tana jin kewar Umma sosai, sai ta ce, "Rehaan ɗin ya dawo ne?." Ta ɗaga kai ta ce, "jiya na koma daga wajen aiki na gansa a kwance babu lafiya, wani ciwon ciki yake yi da ban taɓa ganin irinsa ba, har ciwon ya kai sai an jiƙa towel da ruwan sanyi an ɗora a cikinsa, magana ma daƙyar ya ke yi. Mtsw! Duk da dai yana da raki, shi fa wannan bai yi kama da maza ba wallahi, gabaɗayansa rago ne." Safeera ta yi dariya ta ce, "Bai yi kama da maza ba sai dake ya yi kama?." "Ai gabaɗayansa mace ne, bai yi kama da maza ba ko kaɗan, ba shi da wata alama da zata nuna shi ɗin namiji ne. Rago ne, ga raki, ga iyayi." Safeera ta yi dariya tana girgiza kai ta ce, "Ni dai ina roƙon Allah ya nuna min ranar da Rehaan zai banbance miki tsakanin mace da namiji." "Kamar ya?." "Kamar yadda ki ka ji, daga ranar da ki ka tabbatar shi namiji ne, daga rana za ki daina yi masa kallon mace ki koma yi masa kallon namijin gaske. Kuma duk jarumtar ka ciwon ciki ba abin wasa bane." Ta taɓe baki kawai bata ce komai ba, tana ji kamar ta bata labarin kwanciyar da ya yi jikinta, da shafa cikinsa da ta yi amma tana jin kamar kar ta faɗa. Sai ta share ɗin bata faɗa ba, dan ta san iskanci zata yi mata a kan hakan. "Amma dai kina ce masa ya jiki ko?." "Ni wallahi ban faɗa ba." "Ai kuwa ba ki kyauta ba, ko babu komai kuna tare, yana ba kici da sha da wajan kwana, kuma Mamy tana yi miki kirki sosai." Islaha ta ce, "to zan gani in zan iya. Ke rainin hankalinsa ne bana so, shiyasa bana shige masa, dan in ya ɗura min wani takaicin tsaf in na yi tsalle zan tsinkesa da mari." "Mijin naki?." "Ubana ne?." Safeera ta yi dariya bata ce komai dan ta san a fusace take. Islaha sai kuma ta tuna da abinda ya faru jiya, ta ja tsaki bata ce komai ba. Safeera ta yi dariya son ranta, dan ita bata fatan auren nan ya rabu, tana so ta ga idanun Islaha a lokacin da Rehaan zai nuna mata shi namiji ne ba mace ba. A lokacin Lawal ya zo Safeera ta raka ta har mota ta saka mata kayan da ta ɗauka sannan suka tafi. Rehaan yana zaune yana waya da Ubaid kamar ba ya son maganar, daƙyar yake amsa maganar alamun ta dole yake yi masa. Sai daga baya ya kashe wayar ya cillar da ita akan kujera ya ce, "wannan yarinyar ta cuci kanta, bana so Ubaid ya san ta a matsayin C wife ɗin." "Ray kai da wa ka ke magana kai kaɗai?" Jazy ya faɗa yana shigowa. Ray ya ɗaga ido ya kalle shi dan bai san ya dawo ƙasar ba ya ce, "kai kuma yaushe ka dawo?." "Da safe." Ray yana harararsa ta ƙasan idanu ya ce, "har honeymoon ɗin ya ƙare?." Jazy ya zauna yana dariya ya ce, "honeymoon ai ba ya ƙarewa, dole ce ta dawo dani, amma jibi zamu koma mu ɗora daga inda muka tsaya." Rehaan bai tanka ba Jazy ya ce, "Ya jiki?." "Alhamdu lillah." "Allah ya ye maka wannan wahalar, anya baza mu je a farke cikin ka a duba ba?." "inda hakan zai yu zan amince ko dan na rabu da wannan wahalar, amma kai ka san babu inda ban je akan ciwon nan ba." Jazy ya ɗaga kai ya ce, "ƙaddarar ka ce kam, duniya ce kaɗai bamu bari ba akan neman maganin ciwon nan ba, Allah ya ya ye maka." "Amin ya rabbi." "Ina Islaha?." Ya ɗaga ido ya kallesa yana wani tunani daban, lokacin da tana gidan suna tare da Mamy tausayinta yake ji, amma tunda suka yi magana da Ubaid gabaɗaya sai haushinta ya dawo masa sabo fil, ga shi dai ba zancenta suka yi da Ubaid ba, amma haka kawai yake jin haushinta. Rehaan a ƙufule ya ce, "tana jikina." Jazy ya yi dariyar tsokana ya ce, "sai dai kai ka zama a jikinta, amma ba dai ita ba." Bai ce masa komai ba ya share sa. A lokacin Riyya ta shigo ta ƙaraso kusa dashi ta yi masa side hug ta ce, "Hamma ya jikin?." Rehaan yana murmushi ya ce, "na ji sauƙi my love, ya ki ke?." "lafiya lau, Ka ji sauƙi?." Ya ɗaga mata kai yana kallonta da murmushi. Riyya ta ce, "amma ka rame." Bai ce komai ba ta ce, "ina sis Islaha take?." Ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce, "bata nan." Ta miƙe ta ce, "na kawo maka cocunot drink, yana wajan Mamy" ta faɗa tana miƙewa ta sauka daga saman. Ray ya kalli Jazy ya ga yana kallonsa ya buɗe ido ya ce, "meye?." Jazy ya ce, "ina da tambaya ne." "i'm all ears." "Kar ka yi deflecting maganar, ka fahimce ni a matsayin ka na likita ba Rehaan ba." Jazy daman ya san Rehaan bazai ce komai ba, sai ya ce, "What is causing Riyya feel pain during intimacy?" Wata irin ɗagowa ya yi yana kallonsa jin tambayar da ya yi masa ta rainin hankali, ya ajjiye wayar hannunsa yana kallon sa kamar tv bai ce komai ba. Jazy ya ce, "da gaske na ke ban sani ba, ina buƙatar na san me yake causing pain ɗin." Ya yi tsaki ya ce, "Go and ask a doctor." "You are a doctor." "Ka je ka tambayi Mamy, she's a gynecologist.." Jazy ya harare sa ya ce, "Mamy fa ka ce? Ni ka daina yi min irin maganar nan bana so, ta ya zan je na tambayi Mamy irin wannan maganar? Kai ɗin dai." "Wanda ka raina ko?." Ya yi dariya ya ce, "Ba raini bane, kawai kai ɗin kai ɗin ne." Zai yi magana kenan Islaha ta hayo saman cikin yanayin da ta baro gidansu Safeera, ganin Jazy a zaune sai ta yi murmushi ta ce, "Mr Jafar." Jafar ma ya yi murmushi "Miss Islaha, ya ki ke?." "lafiya ƙalau. Ya aiki?." "Alhamdu lillah. Ya mai jiki?." Ta ɗan kalli Rehaan da yake kallon Jafar sannan ta ce, "ga shi nan dai." Tunda ta shigo yake tuna zaman ts s Jedda, da yadda alaƙarsu da Ubaid ta ke, da cikin da ta zubar, da video Ubaid da koma suka dinga dawo masa daki-daki. Haushinta ya mamaye masa zuciya, ya bita da kallo har ta zo zata gifta shi sai ya ce, "ka tambaye ta, zata iya ba ka amasa." Kafin Jazy ya katse shi ya ce, "Can you tell us what causes pain during intimacy? Do you have any idea? I know you have experience with it." Cak ta dakata daga tafiyar da take yi tana ji kamar an soka mata kibiya, ta waiwayo ta kalle shi daidai lokacin da Jazy ya ce, "Rehaan!." Islaha ta zuba masa ido kawai tana kallo ta kasa cewa komai, ga ɓacin ran da take ciki ga abinda ya ce mata. Ta rasa abinda zata ce masa, ta buɗe ba ki zata ba shi amsa amma ta kasa, bata san hawaye ya sakko mata ba, kawai sai ta shiga ɗaki bata ce komai ba. Jazy ya ji haushin abinda Rehaan ya yiwa Islaha sosai, cikin fusata ya ce, "Haba Rehaan! Meye haka? Ya za ka dinga faɗa mata magana anyhow?." Rehaan bai ce komai ba dan shi kaɗai ya san me yake ji a ransa in ya tuna wacece ita. Jazy ya ce, "Ray ko da ace da gaske tana wannan ɗabi'ar bai kamata ka kalle ta ka ce mata haka ba. Wannan cin fuska ne, wulaƙanci ne, tozartawa ne, tunda rayuwarta ce ta sirri, bai kamata ka dinga faɗa a gaban kowa ba. Ka kalla ka gani, kuka take yi fa. Ina guje maka lokacin da za ka yi danasani akan kalamanka, ina guje maka ranar da zaka zubar da hawaye akan wannan furucin naka Rehaan. Zata tsane ka, za ka dinga bata haushi, zata ji…” Jazy ya yi shiru cikin takaici kamar shine Islaha. Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba, zuciyarsa tana bugawa sosai, yana jin wani abu mai ɗaci in in ya tuna waye Ubaid. Jazy ya ce, "Ban san yaushe ka koyo cin fuska ba, da ba haka ka ke ba wallahi. Ka tashi ka je ka rarrashe ta, dan ba ka kyauta ba wallahi." Rehana maimakon ya yi magana akan Islaha sai ya canja ya ce, "Tun yaushe ake samun matsalar?." "Wacce matsala?." "Wacce ka tambaye ni mana." Ya yi tsaki ya ce, "ka fara solving wannan matslar malam, ka je ka rarrashi matarka." Rehaan ya miƙe tsaye ya ce, "matsalar Riyya itace zata zo a farko Jazy. In pain ɗin ya fara tun last two weeks, it may be normal since she is a virgin and it might ease over time, amma in har yanzu tana jin zafin, it could be caused by a lack of vaginal lubrication. Amma tambayi Mamy, sai ta yi maka recommending abubuwan da zata dinga amfami dasu. Cikina ciwo yake yi min" ya faɗa yana shiga ɗaki ya bar sa a wajan. Jazy ya yi tsaki cike da takaicin abin Rehaan ya yiwa Islaha, gabaɗaya bai ji daɗi ba, shi kansa ya ji zafin kalaman Ray balle ita. Yana miƙewa tsaye Islaha ta fito tunawa ta bar kayanta da ta ɗauko a gidansu Islaha a ƙasa. Jazy ya kalle ta cikin tausayi ya ce, "Islaha." Ta kalle sa da jajayen idanunta ya ce, "i'm so sorry Islaha, na san...." Islaha ta dakatar da shi ta ce, "kar ka damu Mr Jafar, lokaci ne, saura kwanaki kaɗan komai ya ƙare, nan gaba in aka ce ya faɗa min bazai iya ba." "Duk da haka, ki yi haƙuri." Ta yi murmushin yaƙe bata ce komai ba. Jazy baboda ya ɗauke mata damuwa da takaicin Rehaan sai ya ce, "kin shirya interview ɗin nan kuwa?." Ta ɗaga masa kai ta ce, "ko yaushe a shirye nake." "To za a yi jibi in Allah ya kaimu, za ku je guest house ku same sa a yi a can. Mun yi gama magana da shi tun a englaand." Islaha ta ɗan ɗaga kai ta ce, "Shikenan Mr Jafar, Amma ina son addreess ɗin a rubuce, yadda zan kaiwa Chairman." "Zan tura miki ta email in sha Allah." "Na gode sosai, Amma ka kasance a wajan don Allah." "Miss ni a ranar zan bar ƙasar nan da daddare." "Ai da safe za mu yi in sha Allah, bazan iya tolereting waɗannan abubuwan nasa ba, bana so collogues ɗina su ga kamar akwai wani abu a tsakanin mu, in kana nan za ka iya hana wani abun." Ya ɗaga kai ya ce, "in sha Allah zan je." Ta yi murmushi ta ce, "na gode" daga haka ya sauka ya fita, ita kuma tana jin tsanar Rehaan na shiga zuciyarta, kuma ta yi alƙawarin sai ta mayar masa da amsa daidai shi........ Nana Haleema. RDB3P53 Nana Haleema. Saheer haka ya koma gidansu Sadik ransa a ɓace, ya samu Sadik da abokinsa Musaddik a zaune. Ya ajjiye key ɗin motar ya zauna ya dafe kansa. Sadik ya ce, "ya dai, har kun dawo daga gidan?." Ya girgiza kai ya ce, "ba mu je ba." Saheer ya ce, "kamar ya ba ku je ba, motar ce ta lalace?." Saheet ya ce, "babu ɗaya, fasawa mu ka yi kawai. Ka same ni a gida, na wuce" ya faɗa yana ta shi ya fita. Sadik ya biyo bayansa dan ya san ba lafiya ba, ya tsayar da shi ya ce, "Saheer me ye ya faru?." Saheer cike da jin haushi ya ce, "ni yarinyar nan zata dinga faɗawa magana son ranta? Ni zata kalla ta dinga faɗa min ai Rehaan mijinta ne in ma ta yi wani abun da shi sai me, shi yake aurenta ba ni ba?. Ina faɗa mata magana tana ƙaryata ni, ƙarshe ta fita daga motar, harda cewa wallahi baza ta dawo ba." Sadik ya buɗe ido cikin mamaki ya ce, "Wai islahan ce ta yi maka haka?." Shiru ya yi bai amsa ba saboda ɓacin ran da yake ji Sadik ya ce, "Ka yabi mutum in gaɓar yabonsa ta zo. Saheer na san halin Islaha, baza ta yi maka haka kai tsaye babu dalili ba. Ko dai kai ka fusata ta? Dan ka san halin kayarka, barkono ce." "Tambayata ta yi akan iyayenta, tana so ta san ya aka yi ta tsinci kanta a gidan marayu. Ni kuma ka san dalilina na ƙi faɗa mata, na ce mata sai mun yi aure zan faɗa mata, ta ce min ce ita yanzu take so. Shine dai na faɗa mata abinda zata fahimta, amma ta ce ita wallahi bata yarda ba, bata taɓa jin bata yarda da ni ba sai ɗazu." Sadik ya ce, "to kai ka faɗa mata gaskiya ka huta mana, tana da gaskiya fa, kowa zai so ya san iyayensa. Tunda ta san ba a gidan marayu aka haife ta ba, kuma ba tun tana jaririya aka kai ta ba, dole akwai iyayenta a waje." Saheer yi shiru bai ce komai ba, Sadik ya ce, "Kuma ana maganar gidan marayu me ya kawo batun auren ta da Rehaan?." Saheer bai ba shi amsa ba kawai ya yi tsaki ya fita, dan ya ji haushin Islaha sosai, in ya ce bata ɓata masa ba ya yi ƙarya. Shi take yiwa tsawa har yana faɗa tana faɗa, dan ta yi aure ta san meye aure yanzu ta raina shi. Haka yake ta mita shi kaɗai har ya je gida. Ya yi tunanin zai ga kiranta ko text ɗinta, amma babu ko ɗaya, ya yi ƙwafa yana jin zafin abinda ta yi masa a zuciyarsa. Islaha da ta sauka ƙasa sai kawai ta fita da niyar zuwa gaishe da Daada. Tana fitowa suka haɗu da Salman, ta yi masa murmushi dan yanzu ta daina jin tsoronsa kwata-kwata, tausayi ma yake bata sosai. Ta ce, "Hamma Salman ina zuwa?." Ya yi dariya yana kallon ta amma bai yi magana ba, wani lokacin ciwon nasa har magana tana ɗaukewa gabaɗaya. A lokacin Mama ta zo wajan ta kalli Islaha ta ce, "tunda na ga ban ganshi ba na san ya taho wajan ki, ga maganinsa, ba shi ya sha." Islaha bata ƙi ba ta karɓa, ta miƙa masa ya sha da kansa babu faɗa balle kuka. Mama ta ce, "Salman kenan, in ba dan ke ba babu wanda ya isa ya yi masa haka, a hakan ma Ummansa ni ta kawowa ta ce don Allah na basa shine ya gudu, kamar na san zan ganki na taho da shi a hannuna." Ta yi murmushi tana yabawa Mama ganin kowa nata ne a gidan. Mama ta ce, "ina za ki je?." "Zan gaishe da Daada." "To in kin fito ki zo akwai saƙon da zan ba ki." Islaha ga amsa Mama ta ce, "zo mu je Salman." Bai ƙi ba ya bi bayanta yana waiwayon Islaha. Kamar yadda ta ce bayan sun gaisa da Daada wajan Maman ta shiga ta zauna a falo, kafin mai aikin Mama ta ce Maman ta ce ta shiga ciki.. Islaha ta shiga cikin tana kallon ko ina tana ganin tsarin komai dan komai irin na Mamy ne, kayan ne suka banbanta amma tsarin gidan komai iri ɗaya. Islaha ta same ta a kan gado a zaune, tana shiga Mama ta nuna nata kusa da ita ta ce, "zauna mana." Islaha ta zauna sannan Mama ta ce, "Ya jikin Rehaan kuwa?." "Ya ji sauƙi." "wannan ciwon ciki yana takura masa, shiyasa da na shiga Bauchi na karɓo masa magani, ance maganin malamin yana da kyau sosai, ki dinga zuba masa a ruwa ko abinci ya dinga ci har sai ya shanye, In sha Allah za a samu waraka." Islaha ta karɓi maganin tana kallonsa a hannunta sannan ta ce, "In sha Allah." "Allah ya ba shi lafiya." "Amin." "Ga Rehaan ɗin irin Salman ne, ba ya son magani, amma na san ke kin san ta yadda za ki ba shi, ki tabbatar kin ba shi ya shanye duka, in Allah ya yarda za a samu sauƙi." Islaha ta ce, "Allah ya sa, an gode." Ta yi murmushi ta ce, "Kar ki damu, ai duk ƴaƴana ne." Islaha ta miƙe ta ce, "Bara na koma Mama, sai anjima." "sai anjima Islaha." Daga haka ta fita daga ɗakin, Mama ta bita da harara tare da jan tsaki ta ce, "za ki ci uabanki daga ke har shi, wallahi bazan zuba ido kullum yana cigaba yana barin ƴaƴana ba, sai na yi maganin ku daga ke har shi, mu zuba mu gani, sai na ba ku mamaki. "Mama!." Jin an kira ta ya saka ta juyo a fusacr ta ce, "Meye?." Sameer ya kalle ta ya ce, "Mama rancen kuɗi za ki bani, akwai kayan da zasu zo, kuma babu kuɗi a hannuna." Cike da jin haushi ta harare sa ta ce, "wai me ka ke yi da kuɗi ne cikin a kwanaki nan? Ka karɓi kuɗi a hannuna da sunan bashi har yanzu ba ka bani ba. Ina naka kuɗin? Kar ka ce min ka talauce, dan ni ban haifi ɗa dan ya zama talaka a ƙasan Rehaan ba wallahi, ban haifi ɗa da ya zama a ƙarƙashinsa ba. Ina kuɗinka suka je Sameer?." "Mama na kwashe na siyi kaya, shiyasa na zo ki bani aro na gama abinda zan yi." "bazan bayar ba Sameer, bana son wannan maganar." "In ba ki bani ba tabbas zan je wajan Rehaan ya bani, kuma shi na san kyauta zai ba ni ba aro ba." Cak ta dakata ta juyo ta kallesa ta ce, "dan baka da hankali taimako za ka je nema a wajansa?." Ya ce, "To ke na ce ki bani kin ƙi, shi kuwa kyauta in na nema a guje zai bani, nawa kuɗin da na nema ki ka hana ni a wajansa?." "Duk ranar da ka je ya ba ka bashi Allah ya isa ban yafe ba, tona min asiri ka ke so ka yi?.." "Mama na ce ki bani kin ƙi." Bata ce komai ba ta fita, shi kuwa yana sane ya sako Rehaan, dan ya san yanzu zai fusatata indai akan batun Rehaan ne, shi kuma haka yake so ta yi zuciya ta ba shi. Islaha kai tsaye ɓangaren Mamy ta shiga, ta same ta a zaune da photo card a hannunta tana kallo. Ganin Islaha sai ta yi murmushi ta ajjiye hoton ta ce, "Welcome daughter." Islaha sai ta ji wani iri a ranta, for the first time da ta kira ta da daughter. Lokaci na farko kenan a rayuwarta da wata mace ta ce mata daughter. Ta zauna kusa a da ita ta ce, "Ina yini Mamy." Mamy ta ce, "ya ki ke Daughter?." "Lafiya lau." Mamy ta ɗauki card ɗin ta cigaba da kallo amma murmushi take yi. Mamy ta kalli Islaha ta ce, "familyna ne, wannan itace Mamana, wannan shine babana, wannan itace Yayata Sana, wannan Yayana ne, wannan ƙanwata ce Sofia, wannan Fatima. Fatima itace last born ɗinmi, agemate ɗin Rehaan ce, in ki ka ganta sai ki yi tunanin girlfriend ɗinsa ce, dan itace mace ta farko da yake sakewa da ita a duniya. But Sofia...." Ta faɗa tana ɗora finger ɗinta akan fuskar Sofia. Ta sauke numfashi ta ce, "She has been missing for 20 years to above.” Islaha ta kalli wacce aka ce ta ɓatan ta ga kamarsu ɗaya da Mamy, dan a jere suke ita da ita sannan ta ce, "kuma ba a ganta ba?." Mamy ta ce, "babu inda ba a duba ba, amma ba a ganta ba. Kuma ba mu san mijin da ta aura ba balle a tambaya a san inda take." Islaha ta ce, "Allah Sarki! In tana da rai Allah ya bayyanata, in kuma babu rai Allah ya gafarta mata." Mamy ta ce, "amin Daughter. Ina ki ka je?." Islaha ta ce, "na je na gaishe da Daada." Mamy ta gyaɗa kai ta ce, "Kin kyauta." Islaha ta miƙe ta ce, "Mamy bara na koma, akwai aikin da zan yi yau." Mamy ta ce, "in akwai abinda ki ke so ki aiko a ba ki, in kuma kina so a dafa miki sai ki yi magana." Islaha ta ce, "to Mamy." Islaha ta fita daga falon Mamy ta bita da kallo tana murmushin ƙaunar ta da Allah ya saka mata. Islaha tana shiga parlour ta kalli maganin hannunta, sai ta tuna da maganar Mamy, ta sauke numfashi bata ce komai na ta hau saman a hankali. Tana hawa saman yana fitowa daga ɗaki ya shirya tsaf kamar ba shine ya yi ciwo ba, amma kallo ɗaya za ka yi masa ka san ya yi ciwo, dan ya rame kaɗan. Islaha ta bi sa da kallo tana tuna kalaman da ya faɗa mata da Jazy tana nan, ta yi ƙudurin daman sai ta rama, kuma ga lokacin ramuwar ya zo. Ta dafa hannun kujera ta riƙe ƙugu ta ce, "Ka samu abinda ka ke so ko a ƙara maka haske?." Rehaan bai ganta ba sai da ta yi magana sannan ya kalle ta, yana ɗauko wayarsa daga aljihu jin tana vibrating. Islaha ta harare shi tana harɗe hannunta a ƙirji cike da jin haushi ta ce, "ina so ka sani, ni na fi karfin na ba ka idea, sai dai in nuna practically...." Yadda ta faɗi maganar ita kanta sai da gabanta faɗi, sosai, ba shiri Rehaan ya dago ya kalle ta yana mamakin abinda ta ce yana maimaita practically a zuciyarsa yana kallonta. Ta so ta daure kar ta ɗauke idanunta daga kansa amma ta kasa saboda yadda yake kallonta idanunsa ko rawa basa yi, ta janye ido daga kansa dan ita kanta maganar kunya ta ke bata, amma tana so ta nuna masa ita tantiriya ce kamar yadda yake faɗa. Ya taɓe baki yana bin ta da kallon up and down, ya yi ƙasa da murya ya ce, "ohh really?" Ta juyo ta kalle shi ta ce, "yeah! Ai na fi Karfin na ba ka idea, sai dai na nuna practically, ka ga sai ka koya saboda gaba. Kai ma in....... Sai ta dakata ta yi snapping fingers dinta ta ce, "in ka ta shi aure, in kana da bukatar sanin akan abinda ba ka sani ba, za ka iya nemana in koya maka kaɗan daga cikin abinda nake da ƙwarewa a kai" ta faɗa tana niyar barin wajan dan ita ta gama magana. In less than two seconds ta ganshi a kusa da ita, ya riƙo hannunta hakan ya saka gabanta faɗuwa sosai tana kallonsa. Ta janye idanunta tana janye hannunta daga cikin nasa, tana so ta cire hannunta daga nasa amma ya ƙi ba ta damar hakan, ta jingina da bango kamar zata shiga cikin bangon shi kuma yana tsaye a gabanta. Rehaan ya zuba mata idanunsa da suka sake fitowa waje saboda ramar da ya yi, yana rolling ɗinsu a kan fuskarta. Cikin soft voice ya ce, "Are you sure you can teach me about intimacy?." Yadda ya matso daf da ita ya saka ƙhamshin turarensa ya mamaye mata hanci, ƙhamshin mai wani irin sanyi da ƙhamshin mai ratsa jiki da jini da jijiya, ga shi ya zo daf da ita, gashi tana jikin bango babu damar guduwa, ya yi mata kane-kane ya hanata motsi, gabaɗaya ta kasa nutsuwa duk ta ruɗe ta kasa ba shi amsa. Rehaan yana hango ruɗewa akan fuskarta, shi kuma yana so ya ƙure ta ne ya ga ƙarshen rashin kunyar da take taƙama da ita. Ta ɗago idanunta ta kalle sa ya ɗaga mata gira sama ya ce, "I would like you to be my teacher for that. Yaushe zan yi register Malamata, so you can start teaching me?." Islaha ta kasa magana tana tsaye kamar an yi mata wanka da ruwan sanyi, zuciyarta harbawa take yi a guje cikin tashin hankali da danasanin kalman da ta faɗa masa. Amma baza ta nuna masa tana cikin tsoro ba, sai ta aro jarumta, tsiwa tayi nasara akan tsoron da take ji ta ce, "Sai in na ga zan iya na ce maka ai, ba wai zan yi ɗin bane, ja jira layi ya zo kan ka, akwai maza a gabanka." "I want you to start teaching me now, my teacher." Ya faɗa yana sake riƙo hannunta, ya jawo ta jikinsa, ya riƙe waist ɗinta da hannu biyu, jikinsu ya haɗe waje ɗaya yana kallon yadda ta firgice, shi kuma ya saka a ransa sai ya ga ƙarshen rashin kunyar ta a lokacin Nana Haleema. RDB3P54 Nana Haleema. Fuskarsa yake matsawa da ita kusa da tata kamar zai yi kissing ɗinta, firgicinta ya ƙaru dan har lokacin bai saki ƙugunta ba. Ta kawar da kai zuciyarta tana bugawa ta ce, "Mr Rehaan ka ƙyale ni" ta faɗa tana saka hannunta duka biyun a kan nasa tana so ta ɓanɓare hannunsa daga jikinta amma ta kasa. Da zafin nama ya mayar da ita jikin bangon, ya riƙe hannayenta duka biyun ya yi pining a jikin bango har lokacin maganin yana hannunta, ya gyara tsayuwarsa yana kallon ta ya ce, "My intimacy teacher, yau za mu fara lesson?." Firgici, tsoro, tashin hankali, kunya, danasani, suka tararwa Islaha lokaci ɗaya, zuciyarta tana bugawa da gudu. Ga wani irin kallo da yake yi mata wanda bai saba yi mata irinsa ba, gabaɗaya sai ta sake dabarbarcewa, bakin tsiwar ya mutu. Ta rufe ido ƙirjinta yana bugawa ta ce, "Ni ka bar yi min haka" ta faɗa tana niyar ƙwace kanta amma ya hanata, ya sake matsawa kusa da ita, har lokacin bai cika hannayenta da ya yi pining ba ya ce, "you are my teacher, i am your student. Nawa za a biya ki ki fara koyar dani yanzu?." Islaha ta kasa cewa komai ta rufe ido ruf ta ƙi yarda su haɗa ido, ya zuba mata ido yana kallon yadda ta ruɗe lokaci ɗaya, sai ya sakko da hannunsa guda ɗaya ya shafa fuskarta ya ce, "My teacher kina jina?." Gabanta ya faɗi jin hannunsa a fuskar ta, kuma har lokacin bai saki hannayenta ba, kuma bai daina shafa mata fuska ba. "Mr Rehaan...." Ya yi shiru bai ce mata komai ba, ya matsar da fuskarsa daidai kamatunta ya yi pecking ɗin. Sai da ta firgita jin saukar bakinsa a kumatunta, ta buɗe ido da hanzari suka haɗa ido, sai ya yi murmushi ya ɗaga mata gira ɗaya. Ta yi saurin rufe ido gabanta yana faɗuwa, ya kalli yadda ƙirjinta yake heaving, tsaf zata rikice ta samu attack saboda tsoro, sai ya sassauta riƙo da ya yi mata, ita kuma ta ƙwace kanta da ƙarfi ta bar wajen, sai da ta riƙe handle ɗin ƙofa sannan ta waiwayo ta hararesa ta ce, "Ni maza nake koyarwa ba mata ba" ta faɗa tana shiga ɗakin da hanzari ta rufe ƙofa. Rehaan ya cize bakinsa ya girgiza kai yana murmushi, dan ya gama karantar farar kura ce, rashin kunya kawai take ji da ita amma damisar kwali ce, akuya lulluɓe da fatar kura. Ya kali ɗakinta yana tuna abinda ta ce masa, ya sake girgiza kai yana murmushi, ya shafa kansa yana tunanin ya kamata ya yi maganinta, ko dan ya saka bakin rashin kunyar ya mutu murus dan bazai ƙyale ta ba. Ya sake yin murmushin da bai san dalili ba, yana tuna idanunta da ya fito waje lokacin da ya yi kamar zai yi kissing ɗinta. Ya sha lips ɗinsa yana tuna kissing ɗinta da ya yi a mota, daga haka sauka daga saman yana amsa wayar da tun ɗazu ake kiransa. Islaha tana shiga ta kulle ƙofa tana raba ido, ta saka hannu tana taɓa wuyanta dan gumi take yi ga zazzaɓim da take ji yana son rufe ta. Ta dafe ƙirji cikin firgici ta ce, "na shiga uku, me ya ke nufi dani ne?." Sai ta ɗora hannunta a kanta ta ce, "Allah ya taimake ni, da mai zai yi min?." Sai kuma ta yi tsaki ta ce, "bai isa ya yi min komai ba ai, in ya yi kuskure akan hakan ya san sauran" ta faɗa tana buɗe drawer ta jefa maganin a ciki tana rufe drawer da ƙarfi. Ta shafa fuskarta tana jin ƙhamshinsa a hancinta, ta ɗan shinshina jikinta jin ƙhamshinsa take yi ta ce, "wai daga tsayuwa kusa dani har nima na fara ƙhamshin turaren, wannan wanne irin shegen turare ne?" Ta faɗa tana sake shinshina jikinta jin ƙhamshi Rehaan sosai kamar ta fesa. Ta yi tsaki ta ce, "ko daɗi babu." Ta sake yin tsaki ta ce, "shi kuma wancan ya ɓata min rai, duk wannan wulaƙancin da yake yi min ina haƙura dan shi nake ɗauka, amma ya wulaƙanta ni, babu komai zan rama" ta faɗa tana shiga bathroom tana tuna fuskar Rehaan da take kusa da ita. Washe gari da safe ta shirya tafiya aiki, ta fito falon bayan ta shirya tsaf, abin mamaki yana zaune a falon da laptop a gabansa, ga takardu da suke kusa da shi. Bata taɓa ganinsa da wuri haka a falo ba, amma yau ga shi a zaune yana aiki. Ta kalle sa ganin hankalinsa yana kan abinda yake yi bai san ma ta fito ba, ya dafe kai da hannunsa yana ɗan murza goshinsa kaɗan alamun tunani yake yi. Sai kuma ya yi tsaki ya cillar da pen ɗin hannunsa ya ce, "oh my god! Ta ya aka yi hakan ya faru?" Ya faɗa yana ɗaukar waya. Bata ce masa komai ba ta gifta ta inda yake, sai da ta wuce sannan ya ɗago ido ya kalle ta, bata ce masa komai ba ta sauka daga saman daman ba gaisawa suke yi ba. Shima bai damu ta ce ɗin ba, abubuwan da suke gabansa ya fi maganarta mahimmaci. Islaha kai wajan aiki ta wuce, wajan Safeera ta fara zuwa ta same ta a tsaye a wajen record room ɗin ita da Saleem. Ta ƙarasa tana murmushi ta ce, "masoyan asali, ku bakwa gajiya da soyayya ne?." Safeera ta ce, "Ya ranki ƴan mata?." Saleem ya ce, "Muna kan tattaunawa ne akan maganar kai lefe, kin san biki ya zo fa." Ta ɗan buɗe ido ta ce, "ni kuwa na sani, ba dan kai za ka aure ta ba da sai na ce na fika sani." Ya yi dariya itama haka, kafin ta kalli Safeera ta ce, "in kin gama zo mu je wajan Chairman." Safeera ta ce, "me zamu yi a wajansa?." "Ke dai ki gama mu je, za ki ji duk abinda za a yi, kuma in ki ka tsokane ni ke da Allah." Jin haka sai Safeera ta ce, "mu je kawai, sai na dawo" ta faɗa tana kallon Saleem suka wuce tare. Shi kaɗai suka samu a zaune ya gama cin abincin, Islaha ta gaishe sa ya amsa sannan ta ce, "Chairman ina da babban albishir." Ya ce, "ina jin ki Islaha." Ta yi murmushi ta ce, "Rehaan Yola dai ya yi accepting gayyatarmu, har an ba mu time da location ɗin da za mu yi interview." Chairan ya miƙe tsaye cikin murna ya ce, "da gaske ki ke?." Ta miƙa masa wayarta ya karɓa yana karanta mail ɗin da Jazy ya tura mata. Chairam ya ce, "oh my god, wai gobe kenan za a yi da yamma? Islaha gobe zamu yi hira da shi?." Ta ɗaga kai ta ce, "in sha Allah." "Kai amma na ji daɗi, na ji daɗin wannan labarin na ki. Islaha ban san me zan ce miki wanda zai nuna jin daɗina akan hakan ba. Rehaan Yola, a tashar mu, Ya Allah! Islaha you are the best wallahi." Ta yi murmushi ta ce, "Sai a san abinda ya kamata ayi, mu tabbatar komai ya zama ready kafin lokacin." "Dole ai, ai ko ba ki ce ba dole hakan ne ya faru. Za a haɗa team ɗin da za a je da su, nima dai gaskiya sai na je, dan ina so na gan shi ido da ido, kuma za a saka Saleem, da waɗanda suka kamata." Islaha ta ce, "a saka ƙawata" ta faɗa tana nuna Safeera. Ya kalli Safeera ya ce, "tunda kin ce za a saka ta." Ta yi dariya ta miƙe tsaye ta ce, "Na gode Chairman." Chairman cikim murna ya ce, "Islaha a ina ki ka samu damar magana da shi har ya amince haka?." Islaha ta ce, "Mr Jafar ne ya cika alƙawarin da ya ɗauka, bani na yi magana da shi ba." "Allah ya yi masa albarka, ya zama mutum mai alƙawari. Don Allah Islaha ki ninka basirar ki da iya maganar ki akan guest ɗin nan. Duk da bana jin ko ɗar a kan ki, amma don Allah ki sake ɗaura belt interview ɗin nan ta zama perfect. Rehaan Yola ba guest ɗin da za a yi wasa da shi bane." Ta ce, "shikenan Chairman, a tsara min tambayoyin da suka kamata." "Na ba ki dama ki tsara komai, abu ɗaya nake so ki saka a ciki, ki tambaye shi da gaske ne ya yi aure. Maganar tana ta yawo a gari, muna so ya tabbatar mana." Islaha tana ji Safeera tana jan hannunta alamun tsokana, ta share ta ta ce, "ai tambayar nan dole ta zo a farko farko, kowa yana da buƙatar ya san amsar ta." Chairamn ya ce, "kamar na jawo gobe haka nake ji, Allah ya kaimu" Ta yi dariya ta amsa da amin ta fita daga office ɗin. Sai da suka fita sannan Safeera ta ce, "Mata da miji za su yi interview, mata zata yi hira da mijinta, kuma zata tambaye sa da gaske ne ya aure ta. Kai i can't wait wallahi, ina so na ga yadda lamarin nan zai kasance wallahi." Islaha ta harare ta ta ce, "sai na fasa zuwa da ke." "Yi haƙuri boss, dan na ga alama nan gama ke za ki zama Chairman." Su ka yi dariya Islaha ta wuce itama ta shiga wajanta. Saheer ya damu sosai, sai yanzu yake ganin rashin kyautawa a kalaman da ya yi amfani dasu wajan yiwa Islaha magana. Ya yi tsaki ya fi sai hamsin, yana kallon number ta da ya kasa kira, sai daga baya ya danna ya kira ya kira ta, amma har ta gama ringing bata ɗauka ba. Ya ajjiye wayar dan ya san ta yi fushi, ya san halin kaayarsa sai ya sha wahala sannan zata sauko har ta saurare shi. Ya yi shiru yana tunani, lokaci ɗaya fuskar Sudaisa ta gifta masa a idanunsa. Da hanzari ya buɗe ido ya ce, "ko tana hannunsu, ko an karɓe ta ban sani ba. Allah ka kuɓutar da wannan yarinya, ka bata kariya daga cikin kariyarka, Allah ka kai mata ɗauki cikin gaggawa. Ba ita kaɗai ba, duk wanda ya maƙale a wajan waɗanann mutane Allah ka karɓo su." Sai jikinsa ya yi sanyi da ya tuna da Sudaisa, gabaɗaya sai ya ji damuwa ta mamaye masa zuciya fiye da damuwar Islaha. In ya tuna yadda take kuka tana kiransa da Hamma, da yadda aka ba shi amanar ta, sai ya ji kamar ya ci amanar Sudais. Amma kuma Allah yana gani, ya san babu yadda zai yi ne, wajen nan kowa ta kansa yake yi, babu mai tunawa da wani duk wanda ya samu dama guduwa yake yi. Tunda ya bar hannunsu kullum sai ya yi mata addu'a, in dai zai saka goshinsa a ƙasa zai faɗawa Allah ya bata kariya. A bayyane ya ce, "Allah ya kai mata ɗauki" ya faɗa yana jan numfashi a hankali. Sadik ya kira a waya yana ɗauka ya ce, "Ya zan yi ne, islaha ta ƙi ɗaukar wayata, ina son magaa da ita." "Ahto, ai na faɗa ma ka ba ka kyauta ba ka ke ganin kamar ba haka ba, sai ka sake kiranta." "Baza ta ɗauka ba, kaima ka san halinta. "Ka nemi Safeera, wataƙila zata taimaka." "Haka ne, na san tana wajan aiki yanzu, zan neme ta mu yi magana." "Ya dai kamata, dan ba a faɗa da mai kuɗi." Saheer ya yi tsaki ya kashe wayar ya jingina da bango _Anya ba dakon wahala nake yi ba? Soyayyar Islaha zata zama riba a gare ni ko wahala? Ta ya zan mallake ta bayan tana ƙarƙashin wanda ya fi ni sau babu adadi?. Anya bazan yi amfani da shawarar Sadik ba?._ A bayyane ya ce, "ina sonta, Allah ya sani ina ƙaunarta sosai." _Amma ƙaunar amfanin me zata yi maka tunda tana da aure? Furta kana sonta ma da ka ke yi babban zunubi ne. Gwara ka ajjiye son da ka ke yi mata, ka yi amfani da shawarar Sadik ka samu abinda ka samu. In sun rabu shikenan daman haka ka ke so, in basu rabu ba ka ga samu abinda ka samu, in ka zauna a haka wataƙila ka yi biyu babu, babu ita babu kuɗin._ Saheer ya da iska ya miƙe tsaye yana zaga ɗakin cikim tunani. Yana son Islaha sosai, yana fatan ta fito daga can ya aure ta kamar yadda aka tsara, amma sai yake gani kamar fitowarta ta da wahala, anya baxai ɗauki shawarar Sadik ba?. Sai kuma ya ɗan yi jim yana tunani, kafin ya kawar da tunanin ya ce, "bazan iya yi mata haka ba, zan iya jiranta daga nan zuwa ko wanne lokaci, zan jira ta fito ni kuma na aure ta. Da ita kaɗai nake so na rayu, ba kuɗi ba." Ya yi ajiyar zuciya ya fita daga ɗakin, dan in ya cigaba da zama bai san tunanin da zai yi ba.............. Nana Haleema. RDB3P55 Nana Haleema. Islaha sai bayan sallar magrib ta koma gidan, wajan Mamy ta fara shiga ta same su a zaune a kan dining table ita da Rehaan da Banisha. Duk ranar litinin da alhamis haka suke kasancewa, duk satin cikin azumi suke. Islaha ta girgiza kai tana tunani, tana sake tabbatarwa masu kuɗi suna yiwa talakawa wayo, ta ko wanne ɓangare mai kuɗi ya yi kane-kane ya mamaye komai. A fika kuɗi, a fika kyau, a fika gayu, ibadar ma a fika. Sun samu duniya, kuma suna gida lahirarsu da abinda suka samu a duniyar. _(Ƴan uwa mu dage da ibada, gidajen masu kuɗi sun yi mana wayo, Allah ya ba su duniya kuma suna neman lahira da abinda suka samu a duniyar. Da wahala ki ga gidan mai kuɗin da ba a azumin nafila, ga sallar dare, ga walha, ga sadaka, aje umra da hajj. Amma sai ka ji talaka yana alfahari yana cewa ni rabona da azumi tun ramadan, kuma bazan sake yi ba sai wani ramadan ɗin. Tun a zamanin Annabi Muhammad SAW akwai wani sahabi da ya ke cewa Annabi masu kuɗi sun tafi da lada. Annabi Muhammad S.A.W ya ce dukkan tasibihi sadaka, dukkan hailalaha sadaka ne, umarni da kyakykawan aiki sadaka, hani da mummuna sadaka ne, ɗauke abin cutarwa a hanya sadaka ne. Mu dage ƴan uwa, an fi mu a duniya, kar mu yarda lahirar mu a wuce mu. Allah ya sa mu dace.)_ Mamy ta kalli Islaha ta ce, "Shigo mana." Islaha ta ƙarasa ciki ta ce, "Sannu Mamy." Mamy tana murmushi ta ce, "ya aikin?." Islaha ta zauna sannan ta ce, "alhamdu lillah." Banisha ta ce, "Sis ki zo mu yi iftar." Islaha ta kalli Banisha kalle ta ta ce, "ban yi azumi ba." "Ai ba sai kin yi ba, ki zo ki ci." Zata musa ta ce bata ci Mamy ta ce, "Taho ki ci abinci." Babu yadda zata yi haka ta miƙe ta je ta zauna a kusa da Banish. Rehaan bai ce komai ba, white couscous ne a gabansa yana ci hankalinsa kwance, kamar bai san da wanzuwar ta a wajen ba. Islaha ta zuba abincin ta fara ci babu wanda yake magana a cikinsu. Kiran wayar Rehaan ya katse shirun parlour, zai ɗauka Mamy ta ɗauke wayar ta ce, "zaman ka a wajan nan sau nawa kana receiving calls? Ka ci abinci, ka yi maganar in anjima." Bai ce komai ba sai murumushi da ya yi ya cigaba da cin abincinsa. Islaha gabaɗaya ƙhamshin turarensa ya cika mata hanci, duk da ba cutar da ita yake yi amma yana hawar mata kai. Mamy ta kalli Islaha da bata cin abincin yadda ya kamata ta ce, "Daughter bakya cin abincin, ko ba ki da lafiya?." Islaha ta langwaɓar da kai ta ce, "na gaji ne kawai." Mamy ta ce, "Ayya ki gama ci sai ki je ki huta." Islaha ta ce, "To." Wayar ta da ta ajjiye a kusa da ita aka kira, ta kalli screen ɗin ta ga Hamma sai ta yi ƙaramin tsaki ta kashe ƙarar wayar. Banisha ta ɗauki wayar Islaha ta ce, "iphone 12 Sis?" Ta faɗa tana buɗe idanu irin wacce ta ga abin mamakin da ya ba ta tsoro. Banisha ta ce, "You're still using this old phone?." Islaha bata ce mata komai ba dan bata san me zata ce ba, ta dai yi murmushi kawai ba. Mamy ma bata ce komai ba, Islaha ta ɗauki wayar ta ce, "Mamy zan je in huta." Mamy ta ce, "Take care" ta yi murmushi ta ɗauki jakar ta ta fita. Mamy ta kalli Rehana da ya yi kamar bai san da zamanta ba har tashinta, nan kuwa yana kallonta yana tuna idanunta da suka fito waje da ya ritsa ta ta kasa yin komai, bakin rashin kunya ya mutu. Mamy ce, "Rehaan Islaha matarka ce, ba girman ta bane ace tana using ƙaramar waya kamar wannan." Ya kalli Mamy ya ce, "Mamy ni ban san wayarta ba, ban taɓa ganin wayar ba har yanzu." "Yanzu ka ji ai." "Okay Mamy, ki canja mata kawai, ni na gaji Mamy" ya faɗa yana tashi ya fita.    Islaha sai da ta yi wanka sannan ta yi sallar i'sha ta canja kaya ta zauna tana tsara tambayoyin da zasu yi guest ɗinsu gobe. Knocking ƙofar ɗakin aka yi ta kalli ƙofar sai ga Banisha ta shigo da sallama. Islaha ta yi murmushi ta ce, "Kiddo shigo mana." Banisha ta ƙarasa kusa da ita ta miƙa mata leda ta ce, "ga shi in ji Mamy." Islaha ta karɓa ta buɗe ta ɗauko kwalin iphone, ta kalli Banisha da har ta juya ta fita. Islaha ta buɗe kwalin ta ga iphone 17 orange colour, ta fito da wayar tana juyata a hannunta cikin mamaki ta ce, "maganar da Banisha ta yi akan wayata shine har an canja min wata? To me tawan ta yi?" Ta faɗa tana ɗaukar wayarta tana juyata a hannunta, sai kuma sake kallon sabuwar. Islaha ta rasa me zata yi, murna zata yi ko akasin haka?. Mamy tana da kirki sosai, haka Banisha tana da kirki kuma suna sonta shiyasa suke kyautata mata, amma ita bata so wata alaƙa mai ƙarfi ta dinga shiga tsakaninta da ƴan gidan, tunda ba zama tazo yi ba, lokaci take jira ta kama gabanta. Amma ta ga alama Mamy da gaske ta ke yi, da gaske ta karɓe ta hannu biyu a matsayin matar ɗanta ba kamar farko ba. Tana wannan tunanin sai ga Banisha ta dawo ta ce, "Kawo wayar ki na yi miki backup Sis, ba class ɗin ki bane a gan ki da Iphone 12, tun 2020 aka yi ta" ta faɗa tana ɗaukar wayar. Bata jira umarnin Islaha ba ta kunna 17 ɗin ta haɗa backcup da 12 ɗin, ita dai Islaha kallonta kawai take yi ganin yadda take operating wayar alamun an saba dannawa. Banisha ta ce, "bakya using wifi ɗin Ray?" Islaha dai bata cekomai ba tana kallon yadda Banisha take sarrafa waya. Yadda ta ce Wifi ɗin ma ya banbanta da yadda take faɗa, dan ita Wi fi take cewa, ita kuma Banisha Wayfay ta ce, kuma tana da tabbacin haka ne daidai tunda su turawa ne. Cikin lokaci kaɗan ta gama yi mata backup ta cire sim card ɗinta ta ɗora a kan sabuwar, ta goge komai na kan 12 ɗin ta ajjiye mata sannan ta ce, "Welcome to latest iphone my Sis." Islaha ta yi murmushi ta ce, "Thank you Bani." Banisha ta yi dariya ta miƙe ta fita, Islaha ta bi wayar da kallo ta ɗauka wayar kiran Hamma ya shigo a sabuwar, bata ɗauka ba ta saka wayar a chaji sannan ta saka hijjab ta fita. Ƙasa ta sauka ta nufi apartment Mamy da niyar ta yi mata godiya, bata same ta a falo ba ta bita har bedroom, ta same ta a tsaye tana shafe jikinta da turare, ga gahinta har baya ya sauka sai ƙyalli yake yi. Islaha ta ɗan yi baya jin ƙhamshin har tsakiyar kanta. Mamy da ta lura da zuwanta ta ce, "sorry daughter, ƙhamshin zai yi affecting ɗin ki ko?." Islaha ta yi murmushi ta ce, "Mamy an kai min waya, na gode Allah ya saka da alkhairi." Mamy ta dafata ta ce, "Amin. Amma bani na siya miki ba, Rehaan ne. Gobe friday, suna zuwa shopping duk ranar friday, ki dinga binsu kina siyan abinda ki ke so, in kuma baza ki je ba sai a ba ki kuɗin ki." Islaha ta ce, "To Mami, an gode." Mamy ta yi murmushi Islaha kuma ta koma apartment ɗin Ray tana ta murmushi tana jin daɗin yadda Mamy take yi mata kirki. Tana hawa upstairs ɗin ta same sa ya fito daga ɗaki, abinda bata taɓa gani ba shi ta gani, dan babu riga a jikinsa daga shi sai short. Kai tsaye idanunta ya sauka kan logon NIKE da yake rubuce a jikin small boxer da yake ta ciki, ƙaramin short shine mai logon Nike daga ciki, sai wani mai ɗan tsayi kaɗan daga sama. Ita bata san me logon nan ya yi mata ba, kuma logon bana takalmi ko na riga ne yake ɗaukar hankalinta ba, na small boxer ɗinsa ne yake ɗaukar hankalinta, gashi ta lura komai nasa na Nike ne kamar mai yi musu advert. Ta ɗan kalle shi ta ɗauke kai, tana mamakin halittarsa ce a haka ta ga muscles ɗinsa irin na mazaje ko kuma gym ne? Ita dai ta san ba shi da ƙarfin da zai iya gym, wataƙila Allah ne ya yi shi a haka. Ta yi tsaki ƙasa-ƙasa yadda ba zai ji ba ta ce, "mutum ya san yana tare da wacce ba muharramarsa ba ya dinga fitowa a haka, Allah ya kyauta." Ba ta yi tunanin ya ji ba sai ta ji ya ce, "Yau ta saba ganin maza a haka?." Islsha ta waiwayo ta kalle shi suka haɗa idanu, sai ta ɗauke kai tana nuna shi da hannunta ta ce, "au wai kai namiji ne?." Bai san ya buɗe idanunsa yana kallonta ba jin wata tambaya ta rainin hankali da ta yi masa, wai au kai namiji ne, to me ta ke ɗaukarsa?. Islaha ta taɓe baki ta ce, "Ni ban ga maza a nan ba, dan kai in ka saka kayan mata tsaf sajewa za ka yi dasu, daman ga gashi nan kana fama da shi. Don Allah ka daina saka kanka a jam'in maza, kana wulaƙanta mazan gaske. Dan banbancina da kai kaɗan ne, har na fika suffar jarumai wallahi" ta faɗa tana wani yamutsa fuska. Rehaan bita da kallo dan ta kulle masa baki bai san me zai ce mata ba, ita kuma ta wuce ta shige ɗaki bata sake kallonsa ba. Tana shiga ta ɗauki tsohuwar wayarta ta tana juyawa taba murmushi ta ce, "wannan ta Hajiya Safeeran Saleem ce in sha Allah." Ta faɗa tana buɗe inda aka ajjiye mata kayan buɗan kan tana kallo, komai yana nan har kuɗin da aka bata bata taɓa ko sisi ba. Ta ɗauki sarƙar gold ɗin tana kallo, sai kuma ta mayar ta ajjiye dan ba ta san me zata yi da su ba. Sai kuma ta ce, "ko na ɗauki kuɗin nan na haɗawa Safeera ta cika ta canja wayar ta siyi 14?." Sai kuma ta rufe bata ɗauka ba ta koma gefen gado ta zauna. Kamar a mafarki aka buɗe ƙofar, ta waiwayo ta kalli mai shigowa suka haɗa ido da Salman da ya shigo nan take gabanta ya faɗi. Ta miƙe tsaye tana kallonsa cikin firgici da tsoro, shi kuma ya shigo "Na zo mu yi wasa." Islaha ta yi yaƙe wanda ya fi kuka ciwo ta ce, "To sannu." Kafin ta yi magana ya ƙarasa ya zauna a gefen gadon yana taɓa lamp ɗin da take ajjiye a bedside drawer. Ganin ya zauna yana wasa da fitilar da ta ɗauki hankalinsa a guje ta fice daga ɗakin, kai tsaye ɗakin Rehana ta buɗe ta shiga. A lokacin Rehaan ya fito daga wanka ɗaure da towel a jikinsa, tana shiga suka haɗa ido ta yi tsaki ta juyar da fuska cikin nauyi da kunya ta ce, "please cover yourself." Rehaan ya bita da kallo yana mamakin zuwan ta ɗakinsa a firgice haka, sai ya zauna a stool da yake gaban mirror ya ce, "i was showering in my room, you did not even knock." Islaha har lokacin bata juyo ba ta juya masa baya, ba dan Salman da yake ɗakinta ba fita zata yi, dan wani abu mai nayi take ji ya lulluɓe ta, ƙirjinta har ɗagawa yake yi sama-sama, tana ji kamar ana zuba mata ruwan sanyi daga kanta zuwa ƙafafunta. Rehaan kallonta yake yi yana daga zaune, sai ya tuna da kalamanta da ta faɗa masa mintina kaɗan da suka gabata, ya miƙe ya matso kusa da ita ya tsaya bai ce komai ba. Islaha tsayuwarsa ta ji a kusa da ita, ta juyo bata yarda ta kalli jikinsa ba sai fuskarsa ta ke kallo, ta ɗan yi baya ganin kamar tsayuwar bata yi ba sannan ta ce, "Salman ne ya zo har ɗakin da nake, don Allah ka zo ka fita da shi, wallahi tsoro nake ji" ta faɗa tana cigaba da ja baya. Bai ce mata komai ba sai kallon ta da yake yi, ita kuma sai ta rufe idanunta dan bata son kallonsa a haka ta sake cewa, "yana cikin ɗaki, ka je ka yi masa magana." Bai yi magana ba sai da ya zo daf da ita sannan ya ce, "sauran lokacin da ya ke zuwa ni nake yi masa magana, ko yau ya fara zuwa?." Takaici ya saka ta yin tsaki ta juya zata nufi ƙofar da zata fita ya jawo hannunta da dawo baya. A fusace ta fizge hannunta tana kallon idanunsa ta ce, "ka daina ƙoƙarin cewa za ka taɓa ni, ka daina riƙe min hannu bana son wannan ɗabi'ar. In baza ka je ka yi masa magana ba zan je mu kwana tare, daman ai ba yau muka saba kwanan ba." Wani irin kallo yake yi mata wanda bata taɓa gani ba, tsakiyar idanunta yake kallo yana juya ƙwayar idananunsa a ciki. Kallon sai ya yi mata nauyi sosai, har ya saka jikinta ya yi sanyi, masifar da take yi ta gushe gabaɗaya. Ta sauke muryarta ƙasa ba kamar yadda ta yi magana a farko ba, tana ja da baya kaɗan-kaɗan ta ce, "ni dai zan je na yi magana da shi." Zata fita ya sake riƙo hannunta, ya sake dawo da ita baya yana kallon fuskar ta. Islaha jikinta ya yi sanyi sosai, tana jin soft and smoothie palm ɗinsa yana ratsa cikin jikinta. Kafin ta yi magana ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "i want to show you something." Ta ƙarfafa jikinta ta ƙwace kanta ta ce, "ni babu abinda zan gani, ka ƙyale ni don Allah." Islaha ta sake ja baya yana binta, Islaha ta girgiza masa kai ta ce, "Ni babu abinda zan gani, don Allah ka ƙyale ni, don Allah Mr Rehaan ka ƙyale." Ya ce, "ina so na banbance miki namiji da mace." Gabanta ya faɗi matuƙa, amma bata bari hakan ya yi tasiri ba ta harare sa ta ce, "ka jira mazan su zo sai su banbance, kai kam na faɗa maka banbancina da kai kaɗan ne, dan haka ba sai na ga komai ba dan ni da kai sammakal, ni ka ƙyale ni" ta faɗa tana niyar fita Rehaan ya finciko ta da ƙarfi ta dawo jikinsa gabaɗaya. Idanunta suka fito waje saboda taoro da firgicewa, gashi ko hijjab babu a jikinta iya rigar bacci ce kuma bata da tsaho ko kaɗan. Hannayenta suna jikinsa a zube a kan ƙirjinsa, saboda yadda ya jawo ta da ƙarfi bata san ta zuba hannunta a jikinsa ba. Ga shi jikinsa babu riga, hannunta ya sauka a kan ƙirjinsa da har lokacin ruwan jikinsa bai gama bushewa ba, ga gashin da yake kwance a ƙirjinsa hannunta yana taɓawa. Islaha ta ƙwace kanta ta yi baya cikin masifa ta ce, "ni ka daina yi min irin wannan abu, ka daina faɗa ni, hannunka ya daina zuwa jikina, bana so." Kallonta kawai yake yi bai cekomai ba, ta kawar da kai daga kallonsa ta ce, "Just beacuse we were under contract doesn't mean you can do whatever you want. Abin na ka ya fara yawa,ka dinga tunawa muna under rules ne, ka daina ƙoƙarin wuce gona da iri." Maimakon ya ƙyale ta, sai ya miƙa hannunsa da hanzari ya riƙo waist ɗinta ya jawota jikinsa ya haɗe ta da jikinsa hannunta ya sake sauka a ƙirjinsa. Islaha cikin firgici da wani irim yanayin da bata saba da shi ba ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Mr Rehaan ka bari don Allah, bana so!"ta faɗa cikin sanyin murya tana ji kamar ta yi kuka, tana jin wani abu yana shiga cikin jininta, ga shi ya haɗe jikinsa da nata ya riƙe ƙugunta ya matse ta a jikinsa. Rehaan ya kalli fuskar ta ya ga ta firgita sosai idanunta a rufe kamar zata yi kuka. Rehaan ɗage gira sama yana sake tamke fuskarsa, ya kai bakinsa daidai kunnenta hancinsa yana ɓata kunnenta, gashinsa ya sauka a gefen fuskar ta yana taɓa jikinta sannan ya ce, " i set the rule......" ya sake yin ƙasa da muryarsa sannan ya ce, "now." Nana Haleema. RDB3P56 Nana Haleema. Tashin hankali ya yiwa Islaha dirar mikiya, yadda ya yi maganar a daidai kunnenta ya saka ta ji wani irin yarrrrrr har gashin kanta sai da ya amsa, ta ji wani abu zirr a ko ina na jikinta, ƙofofin gashin jikinta suka buɗe suka firfito suka miƙe. Zuciyarta ta harba cikin wani irin yanayin da ya zamar mata baƙo a cikin duniyar ta, jikinta ya fara rawa saboda ta rasa inda zata saka ranta ta ji daɗi. Idanunta a rufe suke ruff, ta kasa motsi fuskar ta ta canja zuwa yanayin tsoro kamar zata fashe da kuka. Rehaan ƙhamshin turaren da ya ke wuyanta yake ji a hancinsa a hankali, ya kai hancinsa wuyanta ya shaƙi ƙhamshin har hancinsa yana taɓa wuyanta, ta firgita jin kamar ya tsira mata allura, fuskar ta sake canjawa zuwa wani irin yanayi. Bakinta yana rawa ta ce, "Mr Rehaan don Allah ka bari, wallahi bana so!" Ta faɗa kamar zata yi kuka har lokacin idanunta a rufe yake Rehaan ya yi murmushi yana bin fuskar ta da kallo, musamman bakinta da yake moving kaɗan-kaɗan, yana tuna yadda bakinta ya ke da laushi da santsi a lokacin da ya yi kissing ɗinta. Ya kai hannunsa kan lips ɗinta ya shafa yana kallon idanunta sannan ya ce, "Namiji da mace nake so ki banbance." Bata san ta rungume shi ba jin maganar a tsakiyar kanta, jikinta ya fara rawa ta kasa cewa komai ba kuma ta kasa guduwa. So ya ke ƙure rashin kunyar ta, so ya ke ya ga a cikin barikin a wanne stage ta tsaya, so ya ke ya ga rashin kunyar ta ta a wanne matakin ta tssya. Sai gashi tun ba a je ko ina ba ya ga bata yi nisa a harkar ba, barikin nata a baki yake, bai kai matakin da yake so ya ga ta kai ba, tunda ga shi abu kaɗan ya firgita ta. Rehaan ganin idanunta a rufe sai ya hura mata iskar bakinsa, ta buɗe ido a hankali ta kalli fuskarsa ya sake ɗaga rigarsa sama. Islaha ta yi hanzari zata gudu, kawai ta ji saukar bakinsa a wuyanta ya yi kissing. "Na shiga uku! Mr Rehaan...!" Ta faɗa zata fara kuka saboda tashin hankali. Bakinta kaɗai yake kallo, so yake ya yi kissing ɗinta amma ya kasa samun courage ɗin hakan, ganin ya gama firgitata sai ya sassauta riƙon da ya yi mata, ta ƙwace kanta ta ja baya, bata ce komai ba ta fita da gudu tana hakki. Rehaan ya yi tsaki yana murmushi duk a lokaci ɗaya ya ce, "shirme! Sai na koya mata hankali, ina so ta banbance namiji ne ni ko mace" ya yi murmushi yana shafa gashin kansa cikin sabon yanayi ya ce, "matsoraciya!" Ya faɗa yana koma closet ɗinsa Islaha a falon ta tsaya tana sauke numfashi tana ƙoƙarin daidaita nutsuwar ta ta dawo daidai. Sai da ta nutsu zuciyarta ta daina bugawa da ƙarfi, ta kalli ɗakinsa sai ta ga bai biyota ba. Ta kai hannu ta shafa wuyanta daidai inda ya yi kissing, ta runtse ido tana jin abun baƙo a gare ta. Ta girgiza kai cike da jin kunyar abinda ya yi mata, ta kalli hannunta tana tuna a kan fatar ƙirjinsa ta ɗora tafin hannunta, ta yi tsaki cike da takaici abinda ya farutsaki ta ce, "Wallahi sai na tuna masa, ya kamata ya san a matakin da mu ke kai nida shi." Bata san adadin lokacin da ta kwashe a wajen a zaune ba, jikinta ya gama mutuwa, sai ta nutsu sannan zata iya miƙewa tsaye. Tana zaune ta ga wucewarsa ya buɗe ɗakinta ya shiga ya samu Salman a zaune yana ta wasa da duk abinda ya gani. Ganinsa sai Salman ya miƙe ya ce, "Na zo wajan ta mu yi wasa." Rehaan ya haɗe masa rai ya ce, "not now, zo mu je wajan Daada" ya faɗa yana riƙo hannunsa. Salman ya turje ya ce, "ni dai a'a, a nan zan zauna." Rehaan ya bi shi da kallo yana tunanin waye ya buɗe masa ƙofar har ya shigo. Ya sake jan hannunsa ya ce, "yanzu zamu dawo." Bai ce komai ba suka sauka bai ko kalli Islaha ba, dan ya gama da ita tunda ya fahimci mara kunyar ƙarya ce. Islaha ta harare sa ta ce, "mai taɓa mata kawai." Saboda firgicin abinda ya yi mata ko barin wajan bata yi ba, har ya dawo ya sake wuce ta, ta sake hararaesa sannan ta shiga ɗakin tana dafe ƙirjinta dan har lokacin bugawa ya ke yi. Islaha tana shiga ta buɗe jakarta ta ɗauko contract agreement ɗinsu tana dubawa, ta girgiza kai ta ce, "ya fara wuce iyakarsa, ya zama dole na tuna masa a ina muke, bazan yarda ya sake kai hannunsa jikina ba, daman bamu tsara da hakan a zaman mu ba." Da wannan abun ta kwana a ranta, amma ko ya ta motsa jikinta sai ta dinga jin jikinta a haɗe da nasa, ga shi babu kaya a jikinsa, tana jin yadda hancinsa ya taɓa wuyanta, da yadda gashinsa ya dinga taɓa fatar jikinta, da yadda ya yi kissing wuyanta. Ta miƙe zaune tana tsaki kamar ta yi hauka saboda tunani, ta sake kwanciya ta runtse ido tana so ta kawar da tunanin amma ta kasa, a haka bacci ya kwashe ta. Washe gari friday, a zaman da ta yi a gidan ta ga suna hidima a duk ranar juma'a, sadaka ake yi babu kama hannun yato, na abinci na kuɗi da sauransu. Duk da sai yamma zasu yi interview, amma dole zata shiga wajen aiki da wuri a shirya abubuwan da ya kamata a shirya. Bayan ta gama shiryawa cikin black abaya cikin irin wanda Hamma yake kawo mata, har zata fita sai ta dawo ta ɗauki takardun contarct ɗin ta fita. Bata same shi a parlour ba dan ta ganshi ta window yana bawa dadbobinsa abinci, ta san ya kusa shigowa ita kuma so ta ke su haɗu. Downstairs ta koma tana kallon breakfast ɗin da aka haɗa, ta ƙarasa kan dining ɗin tana kallon madarar nido da take a babban gwangwani a ajjiye. Ita daman Allah ya yi ta da son madara, ko ba a tea ba in ta gani zata ɗauka ta sha. Ta ɗauki tea spoon ta buɗe madarar ta zuba a hannunta, ta rufe madarar sannan ta ɗora lips ɗinta a kan madarar tana sha, sai ta manne mata a bakinta gabaɗaya, ita kuma saka harshenta tana lashewa a hankali. A daidai lokacin Rehaan ya shigo parlour suka haɗa ido, ya dauke idanunsa ƙasa ya kalli bakinta ya ga duk madara ɓata ta har a mayafinta. Ya ɗauke kansa ya wuce ta ya hau sama, ita kuma madarar da ta ke bakinta ne ya saka bata yi magana ba, sai da ta gama ta karkaɗe jikinta, ta wanke hannunta da bakinta ssnnan ta bi bayansa. A falo ta same shi a tsaye yana ɗaukar wayarsa akan center table ta ce, "Mr Rehaan, ina so na tuna maka wani abu guda ɗaya...." Sai ta warware takardar contract ɗin da ya sama hannu ta nuna masa ta ce, "a ciki rules ɗina dana rubuta maka, na ce maka bana so wani abu ya haɗa ni da kai. Stop trying to create a bond between us, kar ka sake ƙoƙarin kai hannunka jikina, in ba haka ba ths contract will be cancelled!." Ya waiwayo ya kalle ta cikin mamakinta, ita kuma ta sake nuna masa takardar ta ce, "bana so ka sake ƙoƙarin taɓa ni, bana so hannunka ya sake zuwa jikina. Babu ruwanka dani, ka bar ni na ji da waɗanda suka saba taɓa ni a waje, amma kai ban da kai. Ka yi jiya kuma ya wuce, kar sake!." Shi wallahi mamaki take bashi, yarinya sai  magana ga rashin kunyar tsiya, ko kunyarsa bata ji take tsayawa a gabansa tana faɗa masa haka, har tana ba shi umarnin kar ya sake kamar wata Mamy. Ya ajjiye wayar ya harɗe hannu a ƙirjinsa yana kallonta, yana so ya tuna me ya faru jiyan da har zata so tana yi masa warning?. Ya ce, "Is that a command... or are you just trying to advise me?" "Umarni nake ba ka ba shawara ba! Ban yi signing akan takardar nan da sunan hannun ka zai zo jikina ba, kai kuma ka yi signing akan babu wata alaƙa makamanciyar ta jiya da zata haɗa ni da kai, meyasa tun kafin zaman ya yi nisa za ka fara ƙoƙarin karya min sharuɗa bayan ni ina ƙoƙarin kiyaye na ka?." "Mr Rehaan...kawai kar a sake, bana son abinda ka ke yi min, kuma bana buƙata, ka bari mu rabu lafiya don Allah" ta faɗa tana ninke paper da hannunta. Ta ku ɗaya biyu ta yi ya riƙo hannunta, dan in bai nuna mata bata isa ta ba shi umarni ba kwana zai yi yana tunanin maganar ta. Islaha ta rufe ido ba tare da ta juyo ba, ta buɗe idanunta a fusace ta juyo ta ce, "Mr Reh...." Maganar ta tsaya cak jin hannunsa a waist ɗinta, ta ɗaga ido tana kallonsa tana ta ga shima ita yake kallo, ta tafi tunanin me waist ɗinta ya yi masa ne da ya ke yi masa daɗin riƙewa? Abu kaɗan ya riƙe mata ƙugu?. Ta buɗe baki zata yi magana ya jawo waist ɗinta ya haɗa ta da jikinsa kamar yadda ya yi mata jiya, sai ta rufe bakin maganar, amma har lokacin bata daina kallonsa ba. Rehaan ya sakko da fuskarsa ƙasa yana kallon cikin idanunta da suka firfito waje saboda tsoro da mamaki ya ce, "answer me! Umarni ki ke ba ni ko shawara?" Ya faɗa fuskarsa tana daf da fuskar ta, dan ya yi ƙudurin in ta sake maimaita abinda ta faɗa wallahi sai ya nuna mata bata isa ta ba shi umarni ba, kuma sai ya bi takan rules ɗin nata ya tattaka sai ya ga abinda zata yi masa, ya gaji da ɗaukar shirmenta. Islaha mamakin canjawarsa da tsoro ya hanata magana, amma gudun kar ta yi masa shiru ya samu abin faɗa a kanta sai ta daure ta buɗe baki ta ce, "Ni dai....." Ya ɗora finger ɗinta akan lips ɗinta ya ce, "shiii!....." "Answer me, Is that a command... or just advice?." Islaha ta yi ɗuf ta kasa cewa komai, tana ƙoƙarin ƙwace kanta amma ta kasa, dan ya riƙe ta sosai ita kuma riƙon ne bata so. Ganin ta yi shiru sai ya ce, "kar ki sake ƙoƙarin bani umarni, in ba haka ba sai na yi breaking rules ɗin naki sai naga me za ki yi. Ba intimacy ki ke tsoro ba?." Zuciyarta bugawa take yi sosai, gashi a hankali yake yi mata maganar kamar mai yi mata raɗa a kunne, sai ta yi shiru ta kasa magana dan bata san me zai yi mata in ta yi magana ba. "If you ever give me an order again, I'll do exactly what you're afraid of, daga nan sai ki sakawa kan ki boom ki tarwatse." Ta buɗe baki zata yi magana ya kai bakinsa daf da mata kamar zai yi kissing, ta yi hanzarin ɗora hannunta a kan bakinta tana girgiza masa kai kamar zata yi masa kuka. Rehaan ba tare da ya matsar da fuskarsa daga kusa da ita ba ya ce, "in ki ka sake magana, sai na saka bakin rashin kunyar a nan...." Ya faɗa yana nuna bakinsa da yatsansa, sannan ya ce, "sai na yi hukunta shi yadda bazai sake yi min irin wannan maganar ba." "Bakya jin magana ko?." Islaha ta yi ɗuf idanunta suka ciko da hawaye kamar masa kuka, ya cigaba da kallon idanunta yana tuna yadda bakinta ya yi kaca-kaca da madara ɗazu, sai ya sake ta jin wani tunani na daban yana ɗarsuwa a ransa, bai taɓa jin yana sha'awar shan madara ba sai da ya ganta a bakinta, kuma ba wai ya ɗiba ya sha ba, ta bakin nata yake sha'awar shanyewa. "In ki ka sake sai na ba ki mamaki, kin ji?." Ta ɗaga masa kai da sauri, dan ita canjawar nan da ya yi cutar da ita yake yi, ta fi so su cigaba da faɗan da suka saba. Yana sakin ta ta sauka downstairs da gudu, sai da ta yi nisa da shi sannan ta ce, "Wallahi ba ka isa ka karya min rule na ƙyale ka ba, kuma na baka umarnin ka yi min abinda ka ga za ka iya. Har court sai mun je akan rules ɗina, gwara ma ka shiga hankalin ka" tana gama faɗa ta sauka da gudu. Rehaan ya yi murmushi kawai yana girgiza kai ya ce, "this girl....."sai bai ƙarasa faɗa ba ya cigaba da murmushi, ya shafa fuskarsa still murmushi yake yi ya shiga ɗaki. **** "Kin tabbatar kin ba da maganin nan? Kuma wanda ki ka bawa kina da tabbacin zai ba shi ya sha?." Mama ta ce, "ina da tabbacin hakan, dan yarinyar ta yarda dani sosai, baza ta kawo maganin cutarwa na bata." Malaam ya yi murmushi ya ce, "kar dai ayi wasa da maganin nan, daƙyar aka samo shi wallahi, ba a ƙasar nan ake samunsa ba, yana da tsada kuma yana da mahimmaci. In kin san baza ta iya ba ki saka ta dawo miki da shi ke ki ba shi da kanki, in maganin nan ya salwanta sake samun irinsa zai yi matuƙar wahala." "Ni na tabbatar zata ba shi, ta yarda dani sosai." "Ina yi miki albishir da indai ya sha magsnin nan na tsahon sati ɗaya, wallahi da shi da ɗan kishiyarki basu da banbanci, kansa zai kwance ya manta komai, hankalinsa zai gushe, jikinsa zai daina motsi na wani lokaci, zai zama mara amfani." Mama ta yi dariyar jin daɗi ta ce, "a duniyata bani da buƙatar wani ya cigaba in ba nawa yaran ba, bana so na ga wani a dangina ya ɗaukaka in dai ba ƴaƴana ba. Rehaan yana ci min tuwo a ƙwarya, gida da mutanen gidana a hannuna yake, amma shi na kasa sarrafa shi. Yanzu da ka faɗi haka sai na ji daɗi, sai nake ji a raina lokacin da kowa zai yi min biyayya ya zo." "Ba ki da matsala, indai ya sha maganin nan to an gama, za ki tabbatar da a cikin maganata babu ƙarya, zai zama sai dai a kwantar da shi a kuma tayar da shi, Rehaan zai zama labari." Mama ta yi shewar jin daɗi ta ce, "na gode ranka ya daɗe, zan yi maka gagarumin aike a cikin bank ɗinka, in kuwa abinda ka faɗa ya tabbata zan ba ka dama ka faɗi duk abinda ka ke so, ni kuma zan yi maka wallahi." Ya yi dariya ya ce, "in kin ga bai tabbata ba Rehaan bai sha maganin ba, in kuwa ya sha ina mai tabbatae miki da sai kin tambaye ni abinda nake so." Mama ta ce, "zan yi duk yadda zan yi ganin ya sha maganin nan ko ba ya ƙaunar Allah, da ni yake zance" ta faɗa tana miƙewa tsaye suka yi sallama bayan ta cika masa account da kuɗi masu yawa, ta fita ta tafi tana jin zuciyarta fess babu saura damuwa. Nana Haleema. RDB3P57 Nana Haleema. Islaha ko da ta je wajan aiki bata zauna ba, ana ta gwaje gwajen kayan da za a yi amfami dasu yadda baza su ba da kunya ba, hakan ya rage mata tunani akan abinda Rehaan ya yi mata Islaha ta bawa Chairman tambayoyin da zata yi ya duba, ya gyara na gyarawa ya bar na bari. Bayan ta bar wajansa tana zaune kan kujera tana sake duba abinda ya kamata, ta yi tsaki ta ajjiye pen ɗin hannunta ta dafe kanta tunawa da abinda ya faru tsakaninsu. Ta sauke numfashi ta ce, "Ya cuce ni, ya saka ni a tunani" ta faɗa tana lumshe idanunta. "In na tuna da shi zan yi interview duk sai raina ya ɓaci" ta faɗa tana kawar da kanta. Safeera da take tsaye tana kallonta ta shigo ta ce, "dan zaki yi interview da shi sai rai ya ɓaci?." Ta kalle ta ta ɗauke kai tace, "dan baki san abinda ya yi min bane shiyasa, ya gama raina ni wallahi." Safira ta yi dariya ta ce, "ko ke kin gama raina sa ba, mutum mai tarin matsayi kamar sa kin mayar dashi kamar wani ɗan wasan ki." Islaha ta ce, "daman ai ɗan wasana ne, tunda ya shigo cikin rayuwata. Amma abinda yake yi min ne bana jin daɗi, ban yi tunanin zai yi min hakan ba ko kaɗan." Safeera ta yi shiru bata tambaya ba tana murmushi, dan bata san me take magana a kai ba tunda mata da miji ne. Islaha jin bata tambaye  ba sai ta ce,"ƙoƙarin taɓa ni yake yi fa, a haka kamar bazai aikata ba." Safeera ta kalle ta ta ce, "To laifi ne hakan, ba sadakinsa yake taɓawa ba?." "Na san da hakan, amma ba haka muka yi da shi ba. Ni fa da babu contract a tsakanina dashi bazan dinga irin wannan maganar nan ba." "Tunda har kin yarda ke matarsa ce shikenan." "Mtsww! Ke ni ba wannan ba" ta faɗa tana buɗe jakarta ta ɗauko wayarta bata ta ce, "kina so?." Safeera ta ce, "ban gane ina so ba, ina so mana" ta faɗa tana karɓa tana duba wayar. Islaha ta ce, "jiya ne Mamy ta bayar da wannan aka kai min" ta faɗa tana nuna mata sabuwar. Safeera ta buɗe idanunta cikin ta ce, "17!" Ta faɗa tana karɓar wayar tana juyata. Safeera ce, "ashe ina da rabon taɓa iphone 17 nima?." Islaga ta harare ta ce, "sai ka ce wani in ki ka taɓa lada zaka samu. Ba dan kar ta ga an bani ban yi anfani da ita ba wallahi da bazan yi ba, da tawan zan cigaba da amfani ai ba zama ya kai ni gidan ba." Safeera ba jinta take yi ba santin waya kawai take yi, Islaha ta taɓe baki bata ce komai ba. Safeera ta ɗauki wacce ta bar mata ta ce, "na gode Bestie, Allah ya ƙara arzuƙi, ya bar ki da....." kafin ta kai ƙarshe ta katse ta ta ce, "Ya barni da Hamma, in ki ka faɗi sunan wani akasin Hamma Allah ya isa ban yafe ba." Safeera ta yi dariya ta ce, "Akan me zan ce Hamma, bayan da kina tare da Hamman baki canja min waya ba?." "oh! Kema lashe money ce kenan?." "Ki saka ni a wajan in hakan ki ka ɗauka, dan ga wanda ya zama silar da ki ka canja min waya, bazan ɗauki wanda bai zama sila ba." Islaha ta yi mata banza bata ce komai ba, Safeera ta ce, "Kin san kuɗin nan da ki ka bani Baba na turawa, na ce masa a haɗa a cigaba da shirye-shiryen biki." Islaha ta ce, "Baba ya kira ni yana ta yi min godiya, duk sai na ji kunya." "Ke dai bari, ai na ji daɗin kuɗin nan, Baba ma ya ji daɗinsu sosai. Daman wanda aka ba mu a gidan ranar da muka kai ki duk suna nan ina siyayyar biki hankalina a kwance. Ai ni wannan auren da alkhairi ya zo min, ba dole na dinga tsayuwar dare akan ya ɗore ba." Islaha ta haɗe rai ta ce, "Ya ishe ki Safeera." Safeera ta yi dariya ta ce, "Ke kowa yana son inda zai ji daɗi, daga shigar ki gidan Rehaan zuwa yanzu nawa na samu? Ranar da na je Mamy dubu ɗari ta bani na sha ice cream, dole na miƙe tsaye da roƙon Allah." Islaha ta yi mata banza bata sake tanka mata ba. A nan suka yi sallar azahar, bayan an idar aka cigaba da shirye-shirye dan ƙarfe huɗu da rabi aka yi za a fara hira. Bayan an idar da sallah aka hau mota aka tafi. Rehaan kamar yadda Jazy ya takura masa ana idar da sallar juma'a suka wuce guest house ba tare da ya san me zai yi a cikin gidan ba. Suna shiga cikin parlour ya ce, "wai me zan yi a gidan nan da ka takura sai na zo?." Jazy ya ce, "ai na faɗa maka, akwai channel ɗin da zasu yi interview da kai a nan, ka daina ƙoƙarin nuna min kamar ka manta." "mtsww! Ka raina min hankali, kawai akan interview ka saka na taho nan ko wajan Mamy ban je ba?." "ka ga! Kar ka kawo mana matsala don Allah, mun yi da kai kuma ka amince tun a Uk, dan haka ka je ka huta, saboda wannan shegen baccin na ka ya saka na ce sai bayan sallar la'asar." "Sai aka ce maka na shiryawa amsa tambaya?." "Kawai ka je." Rehaan bai ce masa komai ba ya shiga ciki. Lokacin da motarsu Islaha ta tsaya a ƙofar gidan duk fito daga motar suna kallon gidan da aka tsaya. Suna tsaye sai ɗaya daga cikin guard ɗinsa ya fito daga gidan ya ce, "ku shigo." Suka bi bayansa Islaha da Safeera sune a can ƙarshe gabaɗaya jilkinta a sanyaye yake. Safeera ta ce, "ki saki jikin ki mana, kar a fahimci akwai matsala a tsakaninku." Islaha ta ce, "Rainin hankali ne bana so, yanzu sai ya yi creating abinda zai ɓata min rai wallahi." Safeera ta ce, "ki daure, ki nuna kamar baki shi ba." Chairaman ya waiwayo ya kalli Isalaha ya ce, "ki ɗago ƙafa Islaha." Suka ƙarasa aka buɗe musu ƙaton falon da khamshi da ac yake tashi a cikinsa. Basu zauna ba, masu camera suka haɗawa aka ba da light da komai ya zama ready sannan aka zauna zaman jiransa. Yana ciki a zaune yana sanye da blue black ɗin suit yana meeting throw video call, ya ɗan jima a haka kafin ya rufe laptop ɗin. Yana rufe laptop ɗin Jazy ya ce, "suna jiran ka." Rehaan ya ɗaga kai bai ce komai ba, dan kawai iya cewa Jazy a'a ba ne; amma da bazai yi ba wallahi, to babu yadda za a yi Jazy ya nemi abu a wajensa ya kasa yi masa, shiyasa ya amince har aka zo yau. Rehaan Ya miƙe tsaye yana gyara zaman rigarsa, Jazy ya rigasa fitowa duk suka miƙe tsaye har Islaha. Jazy ya kalle su fuska ba yabo babu fallasa, suka gaisa da Chairman da Saleem da kuma camera mans. Sai ya kalli Islaha ta yi murmushi ta ce, "Good day Mr Jafar." "How are you" ya faɗa yana zama a kan kujera kamar bai saba da ita sosai ba. A lokacin Rehaan ya fito duk suka juya suka kallonsa yayin da shi ba su yake kallo ba wayarsa yake dannawa da alamun yana mayar da amsa. Sai kuma ya tsaya cak ya saka wayar a kunne tare da saka hannu a aljihu yana magana da turanci, mintina goma ya yi yana waya a tsaye, kafin ya kashe ya sake kiran wani ya canja yare zuwa hindi. "Mtsww! Sai ya ɓata mana lokaci" Islaha ta faɗa ƙasa-ƙasa tana kallon sa.  Safeera ta kalle ta ta ce, "Don Allah ki yi shiru." Ta ɗauke kai daga kallonsa a lokacin ya ɗago ido ya kalle su dukkansu, bai ga fuskar ta ba dan ta kawar da kai, ya ƙaraso cikin falon. Ya fara miƙawa Chairman hannu alamun su gaisa, jikinsa har rawa yake yi suka gaisa, ya bawa Saleem hannu suka gaisa, ya miƙawa Safeera hannu alamun su gaisa, sai ta kasa bashi hannunta saboda bata saba ba, kuma kamar ta ci amanar ƙawarta in ta gaisa da mijinta. Chairman ya ja mayafinta kaɗan alamun ta ba shi hannu mana, dole suka gaisa da Rehaan. Islaha sai ta ƙirƙiri gyaran mayafi dan kar ma ya bata hannu, ta yi nasara kuwa, ya tsallake ta ya samu waje ya zauna ya ɗora ƙafa kan ɗaya. Ya nuna musu wajen zama ya ce, "Have a seat." Sai sannan duk suka zauna Rehaan ya haɗe hannayensa waje ɗaya ya ce, "so what next? Who is the presenter?...." Ya kalli agogon hannunsa ya ce, "Kuna da mintina sha biyar." Chairman ya kalli Islaha da tunda Rehana ya shigo ta haɗe rai, bata ba shi hannu sun gaisa ba kuma bata gaishe ba. Chairman ya yi mata alamun ta miƙe ta gabatar da kanta. Sai ta yi ajiyar zuciya ta sauke numfashi ta miƙe tsaye ta ce, "ni ce. Sunana Islaha Muhammad Maddibo, daga toran giwa channel." Muryar ta ya ji har zuciyarsa, ya ɗaga ido yana kalllonta, dan yadda ya haddace muryar tsiwar nan ko a cikin mata dubu ya ji muryarta zai gane, ita kuma taƙi yarda su haɗa ido ta kawar da kanta. Rehaan ya kalli Jazy shima shi yake kallo, ya sake kallo Islaha sai ya yi shiru na wani lokaci. Gajiya ta yi da tsayuwa har ta juyo ta kalle sa, ta ga ba ita yake kallo ba, amma tana kallonsa suka haɗa ido ta ɗauke ido ta kawar gefe. Rehaan ya ce, "Okay, Can we start?." Islaha ta zauna aka kunna light da camera da sound yadda ya kamata. Chairman ya kalli Islaha ya ce, "Are you ready?." Ta ɗaga kai ta ce, "Yeah." "Okay 1,2,3 start." "Assalamu alaikum ma du kallo da sauraren wannan shiri na mu mai farin jini, shirin da yake ɗauko manya da ƙananun ƴan kasuwa da ma'aikata dan tattaunawa da su akan rayuwarsu, nasara da kuma ƙalubale." "A yau shirin na mu ya yi babban kamu, ya ɗauko babban kifi a cikin ruwa, ya shiga lungu da saƙo ya ɗauko ɗaya tamkar da dubu. Yadda ruwa yake wahala a cikin sahara haka baƙonmu yake da wahalar samu, shi dai wanda mutane suke mararin ji da gani, suke burin ganinsa a cikin wannan shirin na mu. Kafin na faɗa mu ku waye, zamu kalli tallah mu dawo, Kamar dai kullum ni ce ta ku, Islaha Muhammad Maddibo." Tunda ta fara magana yake kallon ta, yadda take maganar babu cracking, babu tsoro, tana yi tana smiling abin ya burgesa sosai, har yana tunanin ashe ba iya rashin kunya ta tsaya ba tana da skills. Amma da yake ita ce ba wata macen da zai yaba mata bace, sai ya taɓe baki amma bai daina kallon ta ba. "Na san kun ƙagu ku ji waye wannan baƙon na mu, nima na ƙagu na sanar da ku. Baƙon bamu ba kowa bane sai Alhaji, ko na ce Sir, ko na ce Mr Rehaan AbdulAziz Yola, wanda aka fi sani da Ray. shugaba, kuma mamallakin duk wata ma'aikata da ta fara da RAY." A lokacin ta juyo ta kalle sa ta ce, "Ranka ya daɗe barka da zuwa wannan shiri na mu mai albarka." Kamar bazai amsa ba sai kallonta da yake yi, ba komai yake tunawa ba sai yadda idanunta suka fito a ɗazu, da yadda take shan madara bakinta duk ya ɓaci da madarar. Maimakon ya amsa sai ya yi murmushi sai kuma ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Barka." Islaha ta ce, "Mutane da yawa suna cewa Mr Rehaan ba ya jin fulatanci balle yaren Hausa da ya tsallako ya shigo cikin garinmu na Yola, da gaske ne Mr Rehaan ba ya jin Fulfulde?." Ya yi shiru kamar ba zai amsa ba sai ya ce, "Ba da hausa ki ke magana ba, ya aka yi na gane me ki ka ce?" Ya bata amsa da fulfulde. Ta yi murmushi ta ce, "Kasancewar wannan shine karo na farko da ka fara hira da kai da harshen hausa, masu kallonmu zasu so su ji meyasa Mr Rehaan bai taɓa hira da yarensa ba?." "Lokaci ne bai yi ba." "Ɗaukakarka ta zo lokaci ɗaya, har ta kai ta kawo a cikin Yola in za a yi kwatance da matasa masu ɗaukaka da kai ake farawa. Mr Rehaan meye matakin nasarar ka a rayuwa?." "Iyayena and...." Ya dakata yana ɗauko bank cheque daga aljihun coat ɗinsa ya kalli Islaha ya ce, "Just tell me what you want from me, i promise i will give it to you, no matter how much it is." Islaha jin ya koma magana da english sai ta kalle shi, ba dan a gaban camera take ba sai ta faɗa masa me zata yi da kuɗinsa, amma sai ta ce, "Na zo nan saboda interview kawai Sir, ba dan a bani kuɗi ba." Ya yi murmushi ya ajjiye cheaque ɗin sannan ya ce, "The secret of my success is that, i never miss an opportunity, kamar dai ke." Islaha ta yi murmushi ta ce, "I'm sorry Sir, hausar za ka ɗan koma." Yadda take magana kawai yake kallo, kamar ba ita mara kunyar nan ta apartment ɗinsa ba, ta nutsu tana murmushi kamar ba ita ba. Islaha ta ce, "da yawan masu kuɗi in zasu kawo cigaba ƙasar nigeria suna farawa ne daga Abuja, Lagos da sauran garurun da suke kudancin nigeria da suka fi mu yawan kamfanoni. Babban asibitin da ka buɗe a cikin garin Yola, me ya ja hankalin ka har ka kawo babban asibitin da ake ƙiyasin ya fi ko wanne girma da tsari a nigeria cikin Yola?." "Yola garina ne, so bani da inda ya Yola." "Kasancewar ka ƙwararren likita a fannin tiyata, meyasa Mr Rehaan ba ya zama asibitin dan taimakawa ƙasarsa, bayan kowa ya san yana daga cikin likitocin da ake ji dasu a duniya?." "Bani da lokaci." "jama a da yawa suna yawan cewa ba ka yi kama da fulani ba, kuma gashi ka yi magana da fulfulde, za mu so mu a ina ka haɗa jini da fulani?." "Babana fulani ne." "Mama fa?." "hindi." Ta ɗan yi murmushi ta ce, "Ma sha Allah! India, Engaland, Nigeria, in aka baka zaɓi akace ka zaɓi ina za ka ɗauka?." Ya ɗan sauke numfashi ya ce, "Nigeria." "A ina ka fi jin daɗin rayuwa a cikin waɗanan ƙasashe?." "Englaand." "Muna ta jin magana tana ta yawo a ko ina, ana ta yaɗawa ana cewa Mr Rehaan ya yi auren sirri, da gaske ne akwai auren ko babu?." Nana Haleema. RDB3P58 Nana Haleema. Rehaan ya ɗan yi shiru yana kallonta, ita kuma ba shi ta ke kallo ba, ta ɗan ɗauke kanta tana addu'ar Allah ya sa kar ya tona musu asiri ya amsa ta shiga uku. Shi kuma kallonta yake yi ganin ta wani nutsu kamar ba itace mai bakin rashin kunya ba, kamar ba ita ya ritsa ta kasa magana ba.  Rehaan ya ɗaga kai ya ce, "kin ce auren sirri, kuma me ki ke so na ce miki?....." ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido. Ya ɗaga gira sama ya ce, "Sirri ne" ya faɗa yana kallonta.  Sai da ta yi ajiyar zuciya saboda jin daɗi sannan ta ce, "abinci fa? Biryani, Fura da nono ko kuma Burger, wanne ka fi so?." "non of the above." "muna jin labari akan Mr Rehaan yana shirin shiga siyasa, da gaske?." "No." "Akwai shirin shiga siyasar nan gaba?." "babu." "Kwanaki an kai maka hari, har aka dinga tunanin an cutar da kai. An samu labarin waɗanda suka kai harin?." Ya girgiza kai alamun a'a ya ce, "ana aiki akan hakan." "Kasancewar ka mutum na farko a Yola mai  ƙarancin shekaru da Allah ya bawa dukiya da baiwa mai yawa, wanne irin ƙalubale ka ke fuskanta akan hakan?." Rehaan ya ɗan yi shiru yana tunanin meye ƙalubale da hausa, ya san kalmar amma ta kwanta masa bai fahimci maganar ba. Ya ɗan kalle ta ya ce, "Ƙalubale...." Ya faɗa yana kallonta alamun me take nufi. Islaha ta yi masa kallon ka raina min hankali, amma da yake babu damar magana sai ta ce, "ina nufin challenges." "Mun yi maganar attack, and babu privacy." "Inda za ka zama shugaban ƙasar nigeria, wanne abu za ka fara gyarawa?." "Tsaro. Nigeria babu tsaro at all." "Me yake saurin ɓata maka rai?." "Mutum mai fuska biyu, a haka kamar mutumin kirki, amma ba haka bane." Islaha ta san da ita yake amma bata nuna ba ta ce, "Me ya ke saka ka farin ciki?." "My family." "Akwai wani shiri da Mr Rehaan yake yi wanda zai taimaki nigeria gabaɗaya?." "in sha Allah." "Allah ya taimaka ya ba da nasara." "amin." "Daga ƙarshe wacce shawara zaka bawa matasa ma su irin shekarun?." "Be smart, work hard, work smart. Kar ka raina duk abinda Allah bayar, a tsarkake zuciya." Zata sake magana ya rigata ya ce, "Ya sunan ki ka ce?." Ta wani kalle sa suka haɗa ido, ta san da gangan yake yi mata hakan dan bata da bakin ramawa tunda a gaban camera take, sai ta ce, "Islaha." Rehaan ya ce, "Kin san parrot?." "Na sani." "Meye sunan shi da hausa?." Ta kallingefenta sannan ta ce, "Ban san sunan da hausa ba" ta faɗa jin yana raina mata hankali. Rehaan ya ce, "ki ƙara parrot a gaban sunan ki." Ta yi murmushi mai sauti ta ce, "na gode Mr Rehaan." Islaha ta sake kallonsa ta ce, "mun gode da aka ba mu aron lokaci muka tattauna da kai a cikin wannan shiri na mu." Ya gyaɗa mata kai yana kallon fuskar ta ya ce, "can i ask you a question?." Islaha duk da gabanta ya faɗi, amma tunawa a gaban camera take sai ta ce, "Yes Sir." Ya ɗan yi jim kamar zai yi magana sai kuma ya ce, "is okay." "Mun gode da aka ba mu damar kasancewa da kai, haƙiƙa babbar nasara ce a gare mu da garin Yola gabaɗaya." Da ido ya bata amsa ta kalli camera ta yi sallama da masu saurare sannan aka kashe camera. Jazy ya yi clapping hannunsa ya ce, "weldone miss, kin yi ƙoƙari." Ta yi muemushi ta ce, "thank you Mr Jafar." Ta kalli Rehaan ta ce, "thank you Mr Rehaan." Bai ce komai ba ya miƙe tsaye Chairman ya ce, "mun gode ranka ya daɗe." Ya yi ya ce, "Your welcome, amma nan gaba ku canja presenter, wannan kamar bata san aikinta ba." Islaha ta wani kalle sa jin abinda ya ce, kowa ya kalle sa dan babu wanda bai yaba mata ba, Rehaan bai ce komai ba ya shiga ciki. Chairman ya ce, "Duk ƙoƙarin da Iskaha ta yi, ko akwai tambayar da ki ka yi bai ji daɗi ba?." Jafar ya yi dariya yana aiyana Chairman bai san dawar garin ba ya ce, "Ku manta kawai, ya faɗa ne kawai, amma Islaha ta yi ƙoƙari. Kar ku damu" ya faɗa yana shiga ciki. Sai a lokacin Chairman ya ji daɗi, ya ce, "islaha ke ta daban ce, Allah ya cigaba da ba ki kariya." Ta amsa Safeera ta yi hugging ɗinta dan hirar ta ƙayatar. A kunne ta raɗa mata ta ce, "ke gayen nan anya bai afka ba, wani irin kallo yake yi miki fa." Ta mintsine ta a ciki ta ce, "Allah ya kiyaye."suka yi dariya gabaɗaya aka fara tattara kaya. A lokacin Jazu ya fito ya kalli Islaha ya ce, "Miss, Rehaan yana magana da ke." Gabanta ya faɗi, dan bata so a san da wani abu a ƙasa tsakaninsu. Ta kawar da tsoron ta ce, "Dani kuma? Allah ya sa ba laifi na yi." "Kar ki damu" ya faɗa yana dariya ya fita daga falon. Ta kallu Chairman ta ce, "mai zai kira ni ya cemin?." Chairman jikinsa har rawa yake yi ya ce, "Jeki mana, ba ki san me zai ce ba." Ta nufi inda Jazy ya fito ta same sa a zaune ya cire court ɗin jikinsa ya ɗora ƙafa kan ɗaya. Ta tsaya tana kallonsa ta ce, "gani." Ya ɗago ya kalle ta amma bai ce komai ba, sai ta ce, "ance kana kira na, kuma na zo ka share ni." Ya san Jazy ne ya turo ta, shi kuma ya cewa Jazy ya tura musu kuɗin mota, sai ya ce bazai tura ba bara ya kira Islsha ta tura musu, shine ya turo ta. Ya ɗauki cheaque  ya ce, "It's just a small gift for your TV channel." Ta hararesa kafin ta miƙa hannu ta karɓa ta ce, "sun gode." Rehaan ya kalli idanunta  ya ce, "ke babu ke?." "Ai ban ce ina buƙata ba." "Su ma basu ce ba." "kai kaga zaka iya, ni ban ce a bani ba, bani da buƙatar ko sisin ka." Rehaan ya ɗaga gira yana kallonta ya ce, "Saboda ke matar Rehaan ce?." Islaha ta kalle shi da mamakin abinda ya ce, rana ta farko da ya kirata da matarsa tunda suka fara zama tare. Bata nuna masa ta yi mamaki ba ta ce, "Waye Rehaan ɗin?." Rehaan sai da ya yi murmushi sannan ya ce,"Your guest." "Ni ba matarsa ba ce, ni Contract wife ɗin Rehaan ce, lokaci na ke jira na kama gabana, bani da buƙatar komai nasa" ta faɗa kawai ta juya ta fita. Tana fitowa ta bawa Chairman ta ce, "ya ce gift ne."Chairman ya karɓa ya ga kuɗin ya zaro ido ya ce, "15 milions." "Ga shi nan ka gani, don Allah mu tafi na gaji wallahi" ta faɗa cike da gajiya. Suka fito gabaɗaya ana ta cecekuce akan kuɗin har aka shiga mota. Islaha a hanya ta sauka, dan sun yi da Barr zasu haɗu. Safeera aka sauke ta a gida gab da zata shiga gida Saheer ya ce, "Safeera." Ta kalle sa ta ce, "Hamma, ina yini." "Lafiya lau. Ina ta kiran ki ba ki ɗauka ba. "Wallahi ba ma nan, mun je interview dasu Islaha shiyasa." Saheer ya ce, "na yiwa ƙawarki laifi, ina ta neman sulhu ta ƙi bani dama." Safeera ta ce, "gaskiya dai Hamma Saheer ba ka kyauta ba, ta zo nan tana ta kuka, kuma ta bani labari. Ko me Islaha zata yi bata cancanci abinda ka ce mata ba, dan ka san ta yi auren nan saboda kai, tana zauna saboda kai, tana yin komai saboda kai. Har saɓon Allah take yi saboda kai." "saɓon Allah kuma Safeera?." "Eh mana Hamma. Magana da take zuwa tana yi ai saɓawa Allah ne da rashin ɗaukar aure da mahimmaci. Maganar da ta ke yi da kai rubuta mata zunubi ake yi, tunda kai ba muharraminta ba ne, kuma ba magana irin ta yaya da ƙanwa ku ke yi ba, kuna magana akan yaushe za a ku yi aure da sauransu. Ka ga kuwa babban laifi ne tunda da aure a kanta, babu ruwan Allah da auren da tayi, aure sunansa aure tunda an shaida an kuma ba da sadaki. Ina yawan yi mata faɗa akan hakan, amma sai ta nuna min kai ka fi kowa mahimmaci a wajanta, amma kuma kaine ka faɗa mata maganar da ta saka ta kuka. Gaskiya ta ji haushi, ta ta ce min bata taɓa jin haushinka kamar ranar ba." Saheer ya yi ajiyar zuciya ya ce, "kuskure aka samu, in Allah ya yarda baza a sake ba." "Me zai hana baza ka faɗa mata asalin waɗanda suka baka ita ka kai gidan marayu ba?." "Safeera inda zai yu zan faɗa mata, amma abin ne babu daɗin ji shiyasa bana so ta damu." "To ka samu abinda zaka faɗa mata, wanda ka san zata iya ɗauka kafin ku sake haɗuwa, dan tana kewar iyayenta sosai kuwa." "in sha Allah zan yi. Ki ta ya ni bata haƙuri, ko da ba mu haɗu ba ta ɗauki wayata na bata haƙuri. Kamar yadda ki ka ce zan dinga kiyayye haɗuwa da ita har lokacin da komai zai daidaita. Hankali ya gushe, na manta da haramcin da yake cikin hakan, ba ita kaɗai ake rubutawa zunubi ba har da ni, tunda na san tana da aure." "Hakan ya fi kam, Allah ya taimaka mana." "Amin Bestiyn bestie, na gode da ki ka fahimce ni. Sannan ina so ki ta ya ni da addu'a, in ina da rabon auren Islaha Allah ya tabbatar min, in babu Allah ya cire min ita daga raina, dan shan wahalar rayuwa babu ita." Safeer ta ce, "In sha Allah zan yi Hamma Saheer, Allah ya zaɓa mana abinda ya fi alkhairi, ya ɗora mu akan hanya madaidaiciya amin." Ya amsa da amin suka yi sallama ta shiga gida shima ya shiga cikin gida yana tunani kala kala........ Nana Haleema. RDB3P59 Nana Haleema. Islaha tana shiga gidan ko ɓangaren Mamy bata shiga ba Mama ta hangota ta window a tsaye tana yi mata alama da ta zo tana kira ta. Islaha ta nufi wajan Mama ta shiga da sallana, ta same ta a zaune a kan kujera ta ce, "Yanzu na hango dawowar ki ta window, yau kin daɗe." Islaha ta yi murmushi ta ce, "na yi interview ne shiyasa, ina yini Mama." Mama ta ce, "lafiya lau, ya aikin?." "alhamdu lillah." "Ma sha Allah. Na ce ya maganin nan kuwa, ya sha?." Islaha ta ɗan yi jim kafin ta ce, "Eh ya sha a tea, amma bai ma san ya sha ba gaskiya, dan bai san na saka masa ba." Mama ta saki fara'a cikin jin daɗi ta dafa Islaha ta ce, "Ai daman ba sai ya sani ba, na faɗa miki ba ya son magani, kina faɗa masa bazai sha ba. Yanzu ba ga shi ya sha ɗin ba?." Islaha ta ce, "ya sha kam." Mama ta ce, "daman abinda zan tambaye ki kenan, in yana ciwon cikin nan tausayi yake bawa kowa, shiyasa na kira ki na tambaye ki, tunda ya sha mun gode Allah." Islaha ta yi murmushi ta ce, "Bara na je Mama." Mama ta ce, "To in kina son abinci akwai a kitchen." Ta ce, "Na ƙoshi Mama." Mama ta bita da murmuahi har ta fita. Tana bi bayanta da harara ta ce, "shashasha, zaki yi kuka da idanunki wallahi, wannan murmushin da nake miki na ƙarya ne bana gaskiya bane, iyakacinsa fuskata bai zuciya ba." Islaha da ta je ɓangaren Mamy sai ta tarar dashi a rufe alamun bata nan, ta koma ta shiga na Ray ta hau sama tana jin jikinta a gajiya. Wanka ta fara yi sannan ta yi sallah ta sakko ƙasa ta tarar da an ajjiye abinci kamar ko yaushe. Ta zuba ta ci sai kuma ta shiga tunanin dalilin da ya saka Mama take son Rehaan ya sha maganin da ta bata. A bayyane ta ce, "Meyasa Mama take so ya sha maganin nan har haka? Tsayawa ta yi tana dakon dawowata, ina shigowa ta kira ni tana tambaya, anya maganin na tsakani da Allah ne?." Sai kuma ta taɓe baki ta ce, "Ni dai bazan ba shi ba, haka kawai wani abun bazai faru azo ace ai ni na yi." Wayar ta ta ɗauka ta kira Jafar dan ta yi masa godiya, bata jima tana ringing ba ya ɗauka yana ɗauka ta ce, "Mr jafar." Jafar ya ce, "Miss ƴar jarida, gaskiya na jinjina miki sosai, kina da ƙoƙari." Ta yi murmushi ta ce, "na gode. Na gode da ka cika alƙawarin ka, na ji daɗin hakan sosai." "Kar ki damu." "Na gode." "Welcome Miss" Daga haka ta kashe wayar ta. Haka kawai ta ji tana sha'awar kunna tv, tunda ta zo gidan bata taɓa kunna tv ba ko da wasa, sai dai ta kalla ta wuce hannunta bai taɓa kaiwa kan tv ba. Ga ɗauki remote ta kunna tana duba channels ɗin, ta ga gabaɗaya channels ɗin babu na hausawa, daga na ball sai na labarai, sai american films da sauransu. Ganin babu abinda ta saba kallo sai ta ajjiye remote ɗin ba tare da ta kashe tv ɗin ba. A lokacin aka buɗe ƙofar aka yi aka shigo, tun kafin ya ƙaraso ta ji ƙhamshinsa, ya rufe ƙofar ya shigo parlour. Ta san shine shiyasa bata ɗago kanta ba, ya wuce ya hau sama bai ce mata komai ba itama bata ce ba. Tana nan zaune ya sake sakkowa, ya canja kaya zuwa manyan kaya wanda bai cika sakawa ba, ya sake fita bai ce mata komai.  Tana ji an fita da mota ta san shi ya fita, dan bai rufe ƙofar sosai ta ɗame ba, ta harari hanyar da ya bi ta cigaba da kallonta tv ba tare da tana fahimta ba. Sai kuma ta cire hijnab ɗinta ta kwanta tana kallon americn film ɗin da ya fara ɗaukar hankalinta. Tana ganin kiran Hamma yana shigowa ta ƙi ɗauka, ta cigaba da kallonta kanta babu ɗankwali, a haka har bacci ya ɗauke ta wajan bata sani ba. Salman ne ya turo ƙofar falon ya shigo ganin ƙofar a buɗe, ganinta a kwance sai ya ƙaraso ya zauna a kan carpet yana kallon fuskarta. Gashinta ya zube a kan kujarar, sannan doguwar riga ce a jikimta mai ƙaramin hannu. Murmushi yake yana kallon ta, sautin tv ya saka ya kalli tv ya ga mace a kwance tana bacci kamar yadda Islaha take, sannan ga namiji a kusa da ita yana shafa gashinta. A hankali shima ya kai hannu ya taɓa gashinta sai ya yi dariya ya ce, "lah irin gashin Rehaan ne." Sai kuma ya sake taɓawa ya ce, "A'a irin na Mama ne." Ya girgiza kai ya ce, "Kai ba irin nata bane.... " Sai ya tafi tunani ya ce, "irin na Banisha ne, na gane" ya faɗa yana cigaba da riƙe gashinta daga ƙasa. Rehaan a hankali yake shigowa cikin falon, daidai lokacin da Salman ya ke leƙa fuskar Islaha, in kana shigowa sai ka ɗauka kissing ɗinta zai yi, amma shi fuskarta yake kallo dan ya ga bacci take ko idanunta biyu. Rehaan ya ji wani irin dumm a tsakiyar kansa, gabansa ya faɗi, ya ji wani irin yarrr kamar abu yana tafiya a cikin jininsa, kansa ya yi mugun nauyi, ya ji zuciyarsa kamar ana bugata da abu mai nauyi. Cikin wata irin murya mai amo wacce bai san yana da ita ba, ya yi hanzarin ƙarasowa parlour ya ce, "Hamma Salman!." Yadda ya kira sunan ya saka Salman yin ƙara dan ya firgita, ƙarar da Salman ya yi saka Islaha ta buɗe ido a firgice cike da tsoro. Salman ya waiwayo ya kalli Rehaan ya ce, "Rehaan ka tashe ta" ya faɗa cike da takaicin tashinta da Rehaan ya yi. Rehaan ya haɗe ransa yana ji kamar ana busa masa iskar wuci zafin yana ratsa jikinsa ya ce, "me ka ke yi a nan?." Salman kallonsa ya ke yi bai ce komai ba, Rehaan ya ce, "dare ya yi, ka tashi ka ka je ka kwanta?." Salman ya noƙe kafaɗa ya ce, "ni bazan tafi ba." Ran Rehaan ya sake ɓace ya rasa me zai ce masa. Salman ya nuna masa tv ya ce, "irin wannan wasan zan yi mata, tana bacci ba a tashe ta ba, kalli ka ga" ya faɗa yana nuna tv dan ya ga mace gana bacci ba a tashe ta ba. Amma a lokacin da ya nuna tv a daidai lokacin wacce take baccin suka fara undressing kayansu. Islaha ma ta kalli tv sai ta yi saurin ɗauke idanunta, ta dira daga kan kujerar ta baya, ta ja baya daga kusa da Salman. Salman ya zaro ido kamar ƙaramin yaro ya ce, "lah lah lah! Ka ga suna cire kayansu, babu ruwana sai na faɗawa Umma" ya faɗa yana sake kallon Rehaan. Rehaan ya yi tsaki mai tsaho ya kashe tv, ya kalli Salman cikin ɓacin ciki da takaici ya ce, "tashi ka je, ga Umma can tana neman ka." Salman ya noƙe kafaɗa ya ce, "ni bazan tafi ba, wajanta na zo ba wajanka ba." "Ka tashi ka je, gobe sai ka dawo yanzu dare ya yi." "Ni bazan tafi ba." "Salman ka fita!" Rehaan ya faɗa cikin tsawa yana nuna masa ƙofa alamun ya fita. Salman ya tsaya cak yana kallon Rehaan, lokaci ɗaya firgita jin Rehaan ya yi masa tsawa mai shiga zuciyarsa. Tunda ya san Rehaan bai taɓa yi masa tsawa, rashin faɗan da ba ya yi masa ne ya saka suke shiri har yake zama a wajansa, bai taɓa ɗaga masa murya ko ya ƙyare shi ba shiyasa yake son zuwa inda yake. Salman ya kalli Rehaan ya ga yadda ya haɗe rai, sai miƙe cikin sanyi ya fita, Rehaan ya ƙarasa ya rufe ƙofar ya rufe, ya canja mata lock ya dawo falon yana kallonta ransa a ɓace. "Living room wajen bacci ne? Meye amfanin ɗakinki da baza ki kwanta a can ba?." Islaha ita kanta tsawar da ya yiwa Salman ta firgirata, ga abinda Salman ya nuna ya ce shi zai yi mata har yana nunawa, gabaɗaya ta firgita tana tunanin ba dan Rehaan ya zo da me zai yi mata? Tana tunanin abinda ya yi mata tunda bacci ta yi bata san ya shigo ba. Karo na farko a zamanta a gidan ta sanyaya murya, cikin rauni da sanyin kiki ta ce, "ban san na yi bacci ba, na kunna tv ina kallo sai na yi bacci." "What's the use of your bedroom TV? Kin san tun lokacin da ya shigo ya ke a zaune a kusa dake? Kin san sau nawa ya taɓa ki?." Islaha ta girgiza kai ta ce, "ban sani ba, kuma ni ban san ya san ya aka yi ya buɗe ƙofar ba." "Jiya ki ka zo ɗakina ki ka ce ya shigo nazo na fita da shi, ya aka yi ya sake zuwa yau?." Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, tana jin yadda yake yi mata magana cikin faɗa amma ta kasa yin komai, ta kasa mayar masa kamar yadda ta saba, sai ma nutsuwa da tayi tana jin faɗansa har cikin ranta. Rehaan ya ce, "First and last, don't let me ever see you sleeping in the living room again,in kina son kallo ki je upstairs, Okay?." Bata san ta ɗaga masa kai alamun to ba, dan haka kawai faɗan yake shiga ranta. Rehaan ya yi tsaki ya hau sama, gabaɗaya haushin Salman yake ji a ransa dan ya fuskanci ya yi sake da yawa da ya bari yana zuwa inda Islaha take.. Rehaan yana undressing kayan jikinsa yana tsaki cikin takaicin da bai taɓa jin zuciyarsa a ciki ba, sai kuma ya ɗauki waya ya kira Jazy a cikin wanann yanayin yana ɗauka ya ce, Kun yi boarding ne?." Jazy ya ce, "sai anjima. Lafiya?." "ka faɗawa Abba ya yiwa Salman aure." "Wanne Salman?." "Na Umma." "Salman ɗin za a yiwa aure?." "Tunda har ya san ya ga romance a tv ya ce zai gwada ya kamata ko irinsa ce a aura masa." Jazy cikin mamaki ya ce, "meya faru ne na ji ka rai a ɓace?." "Salman ne ya ɓata min rai, kawai na dawo na same sa a zaune a yana kallon C wife tana bacci a living room, ga tv a kunne yana faɗa min irin abin ake yi a tv zai yi mata. Just imagine, da ban dawo ba fa?." Jazy ya yi ƴar dariya jin mutumin nasa a fusace akan C wife ya ce, "Tofa! Yaushe kenan?." "Yanzu abin ya faru, amma laifinta ne, bata da hankali ne, waye ya faɗa mata main parlor wajan bacci ne?." Jazy dariya ya ke so ya yi sosai, irin dariyar wacce take nuni da lokaci ya yi, amma ba ya so ya katsesa hakan ya saka ya ce, "Gaskiya ya kamata a kiyaye, kuma tun farko kai ka bawa Salman dama ne shiyasa yake zuwa wajenta." "Ni ban san haukan nasa ya kai haka ba, ban san raina zai ɓaci haka ba." "To yanzu ya za a yi Mr Rehaan?." "Ban sani ba Jazy, ina ji kamar na je na yi masa duka wallahi. Wani irin beating heart ɗina take yi, ban taɓa jin haka ba." "Ba shi da hankali fa, kar ka damu dashi." Rehaan ya yi tsaki kawai ya kashe wayar, haushi yake ji a zuciyarsa ba tare da ya san dalili ba, abinda ya damu zuciyarsa sosai, abinda yake tunawa kawai da bai zo parlor ba da mai zai yi mata?. Da wannan ɓacin ran ya yi wanka ya fito ya kwanta yana tunanin dole ma ya faɗawa Abba a yi masa aure a huta da wannan tashin hankalin. Ranar monday da safe ta shirya ta tafi wajan aiki, dan ranar ne za a saki interview ɗinsu da Rehaan. Ta je ta samu ana ta editing, bayan an gama aka yi posting a duk handle ɗinsu da social media, sannan aka saka a channel. Cikin lokaci kaɗan hirar ta zaga ko ina, kowa magana yake yi a kai saboda karo na farko kenan da aka ji Rehaan yana hausa da fulatanci. Hirar ta ɗauki hankali sosai, lokaci kaɗan ta dinga trending a inda ba a yi tunanin zata je ba. Islaha tana zaune a office dan bata jin daɗi ko kaɗan, period zata yi shiyasa take jin ta gabaɗaya ya canja. Safeera ta shigo ta ce, "ƙawata kin ga yadda ki ka zama cele?." Ta kalle ta ta ce, "bana jin daɗi Safeera." Safeera ta ce, "me ya same ki?." "Ciwon ciki nake yi." "Sannu, har lokacin ya dawo kenan?." "Eh, amma date ɗin ya canja, an rage kwana uku shiyasa." Safeera ta ce, "Sannu amma fa kin zama cele wallahi, kin ga followers da ki ka tara a ig da tiktok da facebook? Kin ga yadda ake maganar ki kuwa?. Ana ta cewa Mr Rehaan yana ta kallon ki, anya bai san ki ba, dan yanayin kallon da yake yi miki kamar ba a ranar ya fara ganin ki ba." Islaha ta lumshe ido ta ce, "Mutane an yi munafukai, su suka sani ni na gaji." Safeera ta ce, "Ki zo muje sai na raka ki gida." Kamar jira take ta miƙe tsaye, a lokacin Chairman ya buɗe ya shigo. Islaha ta daure ta saki fuska ta ce, "Chairaman da kan ka?." Ya ce, "islaha dole na zo da kaina wajan ki, kin cancani na zo har nan na same ki. Islaha kin kawo mana ɗaukaka cikin awannin da basu wuce uku ba, yanzu haka kamfani biyu ne suka kira ni yanzu zasu ba mu advert, ban da mabiya da muka sake tarawa. Ni daman na san hira da Mr Rehaan alkhairi ne a gare mu, ga shi cikin lokaci kaɗan alkhairi yana ta ɓollowa daga inda ba mu yi tuanni ba." Islaha ta yi murmushi ta ce, "Mun gode Allah chairman, nasarar gidan nan nasarar mu ce gabaɗaya." "Gaskiya ne Hajiya Islaha, Allah yasa kar wata babbar channel ɗin da gano ki ta ɗauke mana ke." Ta yi dariya ta ce, "ina nan, bakin rai bakin fama In sha Allah." "Allah ya sa." "Amin." "Sai dai ƴan comments section suna ta yi miki iskanci, ana yanke inda ya ce zai tambaye ki ɗin nan, ana cewa wai akwai wani abu tsakanin ku." Ta ɗan mursmusa ta ce, "na san hakan zai faru, kasan ƴan arewa ba ma mayar da hankali akan abinda mai mahimmaci." "Gaskiya ne. Yanzu kuɗin da ya baya ba mu, zan tura miki na ki da na sauran waɗanda aka je dasu." Kafin ta yi magana Ummi ta shigo office ɗin ta ce, "Chairman daman ranar friday da ku ka fita interview aka je aka yi da Mr Rehaan shine ko a faɗa mana, aka yi shiru aka je cikin sirri dan kar mu sani?." Chairman ya ce, "to sai aka yi ya ya, dukana ki ka zo ki yi kenan?." Ta girgiza kai ta ce, "Ba duka nazo na yi ba, kawai na faɗa ne. Dan gaskiya ba a yi mana adalci, a bayan bayan mu Islaha ta zo amma komai sai ace ita mu a ƙyale mu. Wallahi baza mu yarda ba, ai itama ma'aikaciya ce kamar mu." "Ba kamar ku ta ke ba, wallahi Islaha ta fi kowa a kaf gidan nan. Islaha har ni tafi, ta silar ta mun yi abinda da kaf Nigeria ba a taɓa yi ba. Sannan mun samu kyautar kuɗi, mun samu ɗaukaka cikin awanni kaɗan. Ko ina yanzu interview ɗinmu ake zance, ko ina zancen Islaha da Rehaan yake yi. Dan haka ta fi ki, ba ke kaɗai ba kowa ma ta fi shi." Ummi ta gyɗa kai tare da yin ƙwafa ta fita. Chairman ya kalle ta ya ce, "kar ki damu da irin waɗanan, ƴan baƙin ciki ne da hassada." Ta yi murmushin yaƙe dan Allah kaɗai ya san abinda take ji sannan ta ce, "Babu komai Chairman, zamu tafi ni da Safeera, ciwon ciki nake yi." "Allah ya ƙara lafiya. Ki huta na kwana biyu ba sai kin zo ba, Allah ya ba ki lafiya." Ta amsa da amin suka fita ita da Safeera. Ummi a fusace ta shiga wajan Muslim cikin baƙin ciki ta ce, " "iphone 17, manyan motoci, gidansu Mr Rehaan Yola, hira da shi, kallon da yake yi mata, tambayar da ya ce zai yi mata ya fasa. Ɗaukaka, da yadda sunanta yake ta yawo a iya yanzu nan. Ya aka yi haka? Meyasa hakan yake faruwa ne Muslim?." Muslim ya ce, "ni kaina abin ya ɗaure min kai, Islaha da iphone 17, a kawo ta a manyan motoci masu girma da tsada, ajjiyeta kuma a dawo a ɗauke sannan an ganta ta shiga gidansu Rehaam har masu gadi suna gaishe ta. Yau ta yi hira da shi yana kallonta, kallo irin na sanayya. Me hakan yake nufi?." Ummi ta ce, "dole a nemo wallahi, ni zuciyata tana faɗa min akwai alaƙar ɓoye a tsakaninsu." "To meye alaƙar ɓoyen?." "Bariki mana, akwai alaƙar da zata haɗasu in ba haka ba?. Kuma yanzu masu kuɗin nan me suka ɗauki bariki? Normal ne kawai." Ya ɗan yi shiru alamun tunani sannan ya ce, "amma baban saurayinta ya ce min ta yi aure." "Ka sani ko da haka aka yaudarar shi? Ka san dai babu yadda za a yi ace itace matar Rehaan." "Bariki a gidansu Rehaan ɗin kuma, ki tuna gidansu ta shiga ba gidansa ba." "Ka sani ko akwai abinda yake kai ta daga nan su haɗe? Ni wallahi zuciyata haka take faɗa min, daman ta saba iskanci ai." Muslim ya ɗaga kai cikin gamsuwa ya ce, "wallahi sai mun yi maganinta, a wannan karon baza mu ƙyale Islaha ba, sai mun yi mata abinda zata gwammace bata zo duniya ba."     Islaha a gidansu Safera ta sauka tana son ɗaukar wata riga a kayanta. Bayan ta ɗauka sun fito kenan Saheer ya tare su a soron gidan, ya kalli Islaha da ta haɗe rai ya ce, "Islaha ki yi haƙuri, na san na yi kuskure, amma ki yafe min." Sai kawai ta fashe da kukan da yake taso mata, ta ce, "babu wani na yi haƙuri, ka gama faɗa min magana kana cewa na zaɓi kuɗi a kanka kuma ka ce min na yi haƙui? Hamma ka je kawai." Ganin ta rikice lokaci ɗaya dsi hankalinsa ya tashi ya ce, "ki yi haƙuri, ki daina kuka." Safeera ta ce, "Hamma ka je kawai, bata jin daɗi ne daman, ka santa in babu lafiya rigima ce da ita, zamu yi magana ." Saheer ya fita dan babu yadda zai yi, Safeera ta riƙe Islaha suka koma mota, dole ta shiga motar dan ta rakata gidan dan lokacin magrib ya kusa. Suna ajjiye motar Safeera ta fito riƙe da Islaha suka shiga, daƙyar ta saka ta hau har sama dan ciwon ya fara damunta. Suna shiga falon sama ta zube a ƙasa ta ce, "bazan iya iya ba, zan mutu Safeera, zan mutu" ta faɗa tana kuka mai sauti kamar yadda ta saba. Safeera duk ta ruɗe ta ce, "yi haƙuri, sannu, a ina ki ka ajjiye maganin na ɗauko mi ki?." Bata iya magana ba sai juya kai take yi tana kuka mai sauti, marar ta azabar ciwo take yi mata gabaɗaya ta fita daha hankalinta. Rehaan yana cikim ɗaki ya ji kuka mai sauti daga falon, hakan ya saka shi ya fito yana kallonsu, Safeera ta riƙe ta tana yi mata magana, ita kuma tana kuka sosai. Rehaan ya ce, "Lafiya?." Safeera ta waiwaya ta kalle shi dan da harshen fulani ya yi maganar, itama sai ta yi amfani da yaren ta ce, "Bata da lafiya." Rehaan ya kalli Islaha da ta kwanta akan tiles tana kuka, ya sake kallon Safeera ya ce, "me yake damunta?." Safeera ta ce, "cramps ne." Ya ɗan yi jim kafin ya sake kallonta ganin da gaske kukan take yi. Safeera ta durƙusa a gabanta ta ce, "Islaha daure na raka ki ɗaki, ki tashi don Allah." Daƙyar ta iya miƙewa suka tafi ɗakin, sai da ta zuge mata zip ɗin rigarta ta cire mata, ta kwanta akan gadon ta rufe mata jiki da duvet, ta ɗauko magnin da yake ajjiye kan drawer ta bata ta sha, ta kunna mata ac ta ce, "sannu." Bata iya amsawa ba ta ɗaga mata kai kawai. Safeera ta dawo parlor ta ganshi a inda ta bar shi a tsaye kamar mai tunani. Cikin dauriya ta kalle shi dan kwarjini yake yi mata ta ce, "Sir yau tana jin ciwo fiye da ko yaushe, ko za a baya magani don Allah?." Rehaan ya ɗan ɗaga kai sannan ya ce, "tana ina?." "Tana cikin ɗaki." "Okay" ya faɗa yana komawa ɗakinsa. Safeera tana tsaye ya fito daga ɗakin ya buɗe ɗakinta ya shiga. Ɗakin babu haske ko kaɗan, ya ƙarasa inda ta ke kwance yana kallonta. Idanunta a kulle yake amma hawaye ne yake sakkowa daga idanunta, bai mata ce komai ba ya zauna daga gefenta dan ya lura serious ciwo take yi. Ya zuba mata ido yana kallonta, kafin ya miƙa hannunsa ya taɓa forehead ɗinta ya ji da zafi, ya taɓa wuyanta ya ji nan ya fi ko ina yin zafin. Water bag ce a hannunsa wacce ya ɗauko daga ɗaki, ya dinga juya bag ɗin a hannunsa yana kallonta, ya yi ajiyar zuciya yana tunanin yadda zai ɗora mata bag ɗin a ƙasan cikinta. A lokacin ya tuna da Safeera, ya miƙe ya fito da niyar ya sakata ta ɗora mata bag ɗin amma bata nan alamun ta tafi.  Ya koma da baya yana kallonta, kitson kanta guda biyun kawai yake kallo har ya ƙarasa ya zauna daga gefe. Kamar mai jin tsoro ya ɗan matsa inda ta ke, ya ɗauki water bag ɗin da ya zuba mata ruwan ɗumi, ya janye duvet ɗin da aka rufe mata jiki. Duk da babu haske ɗakin sai da ya mayar ya rufe mata jikinta ganin yanayin da take ciki daga ita sai baƙar bra, bai san babu riga a jikinta ba da bai fara buɗe ta ba, ya kulle ido ya buɗe yana sake kallon ta ya rasa me zai yi mata. Sai kuma ya ya sake mayar da hannunsa ya riƙe duvet ɗin, ba tare da ya janye shi ba ya saka hannunsa a ciki, ya kai water bag ɗin ƙasanta cikinta a hankali ya ɗora. Shi kansa sai da runtse ido, dan baya so ya aikata abinda yake niya, kar ta fassara shi da wata manufa. Bag ɗin bata hau kan inda ake so ta hau ba, dan a kan mara ake ɗorata, dole sai ya ɗan janye dogon wandon da yake jikinta sannan zai ɗorata a inda ake so. Kamar mai jin tsoro ya riƙe saman wandon, ya ɗan yi ƙasa da shi kaɗan, hannunsa ya shafi wajen gabansa ya faɗi lokaci ɗaya hannunsa ya fara rawa. Babu shiri ya ɗora mata bag ɗin a saman mararta, ya ɗora hannunsa akan bag ɗin ya ɗan danna kaɗan yadda ɗumin ruwan zai ratsa ta har ya saka jinin ya yi melting. A lokacin ta firgita ta riƙe hannunsa da yake akan bag ɗin, ta juyo tana kallonsa suka haɗa ido, sai ta yi nufin miƙewa ya riƙe kafaɗarta da ɗaya hannun ya mayar da ita ta kwanta. Ya kwanto kaɗan yana kallon fuskar ta ya ce, "ina taimaka miki ne, relax!." Sai ta koma ta kwanta a hankali, hannunsa yana kan water bug ɗin da ta ke jikinta, ga ahi jikinta babu riga, fatarsa hannunsa tana taɓa fatar cikinta. Ta yi shiru idanunta a rufe har lokacin hannunsa yana cikin bargon bai cire ba. Sai da ruwan da ya ɗora mata ya yi sanyi sannan ya ɗauko bag ya fito da ita ita ya ajjiye a gefe, ya sake taɓa goshinta ya ji zazzaɓin ya sauka har ta yi bacci. Ya kalli fuskar ta ya ga bacci take yi, kuma ga gumi a goshinta. Ya ɗora hannunsa a goshinta ya shafa gumin, sai ya ɗauki remote ya ƙara mata ac. Maimakon ya tashi ya tafi sai zauna ya zuba mata ido yana kallonta, ya kasa ya janye idanunsa daga kanta yana ji zuciyarsa tana bugawa sosai. Kanta yake kallo da aka yi mata kitson da yake ɗaukar hankalinsa, bai san ya kai hannunsa ya shafa kalbar kanta ba, abinda yake ɗaukar hankalinsa kenan indai zai gani a jikinta, tun a Jeddah take ɗaukar hankalinsa sai yau ya samu damar taɓawa. Allah ya taimaka baccin ta ya yi nisa bata san hidimar da yake yi mata ba, hakan alamu ne na ta ji daɗin abinda ya yi mata. Ya miƙe zai fita ya ji ta riƙe masa hannu, ya kalli hannunsa ya ga ta saka a ciki nata kuma bacci take yi. Ya yi murmushi yana kallon ta cikin wani irin yanayi, ya ɗan ranƙwafo ya janye hannunsa, ya shafa fuskar ta tare da pecking goshinta ba tare da ya yi nufin yi ba. Ya sake rufe mata jikinta, ya fita daga ɗakin yana waiwayonta....... Nana Haleema. RDB3P60 Nana Haleema. Yana fitowa daga ɗakin Mamy ta shigo falon ya kalle ta kafin ya yi magana ta ce, "Na haɗu da ƙawar Islaha ne tace min bata da lafiya, me yake damunta?." Ya ɗan yi shiru sannan ya ce, "Cramps." Mamy ta ce, "Ayya, na lura yana bata wahala da ba ka nan. Yanzu ya jikin nata? Ka bata magani?." Ya ɗaga kai ya ce, "ƙawarta ta bata magani, ta yi bacci." Mamy ta wuce shi ta shiga ɗakin ganin bacci take yi sai ta fito ta ce, "take care of her, ka yi mata duk abinda ya kamata, please." Ya lumshe ido dan a gajiye yake sosai, amma haka ya buɗe ido ya ce,”Okay Mamy." Mamy ta ce, "i saw your interview, za mu yi maganar gobe in sha Allah, Good night." Ya yi mata side hug sannan ya ce, "good night Mamy." Ta juya ta sauka ya rufe ido yana ajiyar zuciya, ya sake kallon ɗakin sai ya buɗe ƙofar ya ɗan leƙa ta yana hangota a kwance tana bacci. Shi in akace wani babu lafiya ba ya iya nutsuwa, ba ya so ya ji wanda suke tare ance ba shi da lafiya yanzu duk sai ya damu kansa. Ya shiga ɗakin yana kallon yadda take bacci peacefully, ya miƙa hannunsa ya taɓa wuyanta ya ji temperature ɗinta normal. A lokacin Islaha ta buɗe ido suka haɗa ido cikin ƙaramin hasken ɗakin, yanayin yadda idanunta suka koma irin na mai bacci ya saka Rehaan ya lumshe ido ya buɗe yana sake kallon idanunta da suka ɗauki hankalinsa, sai kuma ta mayar da idanunta ta rufe alamun a cikin bacci ta buɗesu. Ya ɗora hannunsa a kanta ya shafa gashinta da yake ɗaukar hankalinsa sosai, yana kallon fuskar ta yana tuna yadda suka yi da ita kafin su yi interview. Ya janye hannunsa daga kanta, ya fita daga ɗakin ya rufe mata ƙofa. Islaha sai cikin dare ta farka tana jin yunwa mai yawa, ta tashi zaune tana runtse ido har lokacin tana jin ciwon amma ba sosai ba. Ta miƙe tsaye ta shiga banɗaki ta yi wanka ta fito ta saka doguwar riga mara nayi ta kalli agogo ta ga ƙarfe uku da rabi na dare, ta buɗe ƙofar falon ta fito tana kallon falon. Falon shiru babu kowa, amma akwai blue light a kunne, ta ƙaraso tsakiyar falon tana tafiya a hankali dan har lokacin marar ta tana yi mata ciwo kaɗan kaɗan. Daidai lokacin Rehaan ya yi sallamar sallah ya juyo ya side ɗin da take tsaye. Ba su haɗa ido ba dan bata kula dashi ba, sai da ta juyo suka haɗa ido a lokacin har ya miƙe tsaye yana kallonta. Kallonta yake yi yana mamakin abinda ya fito da ita a daren, ga shi ko ɗankwali babu a kanta, rigar jikinta iyakacinta guiwa, kana kallon fuskarta kasan bata da lafiya. Islaha ganin yana kallonta sai ta yi nufin komawa ciki, dan bata so suna haɗuwa da ƙaramar riga a jikinta, bata jin daɗi in yana ganinta a haka. Cikin muryarsa mai ɗaukar hankali ya ce, "Are you okay?." Maimakon ta ƙarasa koma ɗakin kawai sai ta fara kuka, ta koma ɗaki da hanzari ta zauna a kan gado tana kuka. Rehaan ta dafe goshinsa ganin daga yi magana ta fara kuka, kamar kar ya bita dan bai sani ba ko maganarsa ce ta saka ta kuka, shi kuma ba ya son takura mata tunda bata da lafiya ba neman faɗa yake yi ba. Kasa haƙura ya yi haka ya bi bayanta ya shiga yana kallonta ganin kuka take yi da gaske ba wasa ba. Abin ya ba shi mamaki ya tsaya daga bayanta ya ce, "Are you okay?." Islaha cikin kuka ta ce, "Yunwa nake ji." Rehaan sai ya ji daɗi da ba wani abun ne yake damunta baya ce, "kawai dan kina jin yunwa sai ki yi kuka?." Bata ce masa komai ba kuma bata daina kuka ba, ya ce, "okay me ki ke so ki ci?." Ta lumshe ido tana jin yadda yake yi mata magana a hankali cikin kulawa da, ta ce, "Spicy Noodle." Ya bi bayanta da kallo dan bayanta kaɗai yake iya gani, shape ɗin jikunta ya biyo ta baya sosai, ya bayyana kamar an zana mata shi. Ya ɗan ɗauke idanunsa ya ce, "Okay dare ne yanzu, ki je ki dafa da kan ki" ya faɗa yana fita daga ɗakin. Islaha bata fito ba ta koma ta kwanta a hankali, gabaɗaya in tana period rasa nutuwarta take yi, ta dinga yin abubuwa kamar ƙaramar yarinya. Ta yi lamo a kan gadon, tana tunanin Hamma da yana nan da duk abinda ta ke so sai ya kawo mata a daren ya bata. A bayyane ta ce, "Allah ka kawo min mai bani." Rehaan da ya fita cigaba sallarsa ya yi, bayan ya idar da raka'a biyu ya kalli ɗakin ya ga bata fito ba, tunani yake yi ta ce yunwa take ji kuma tana zaune tana kuka, me ya hanata fitowa ta je ta nemi abincin?. Ya ɗauke kansa daga kallon ɗakin yana rolling idanunsa a waje ɗaya, tunanin abinda ya hanata zuwa ta yi girkin kawai ya ke yi, duk ya damu kansa akan rashin fitowar ta. Rehaan ya kasa daure sake miƙewa ya koma ɗakin, ya same ta a kwance ta yi shiru amma ta bar kukan. Bai ce mata komai ba ya koma da baya ya ɗauki waya ya kira chef ɗinsa, yana ɗauka ya ce, "kana ina?." Ya yi shiru alamun ana basa amsa kafin ya ce, "okay in zaka zo ka taho spicy noodles." Yana gama faɗa ya kashe wayar ya koma ya zauna a akan sallaya. Cikin mintina goma Chef ya kirasa, bai ɗauka ba sai ya miƙe tsaye ya sauka ya buɗe ƙofar parlour. Chef ya shigo ya ba shi pack ɗin hannunsa, bai cewa Chef ɗin komai ba ya hau saman ya shiga ɗakinta kai tsaye. Yana shiga ɗakin ya ƙara hasken ɗakin yadda bazai yi mata yawa ba, ta ɗago a hankali ta juyo ta kalle shi sai ya miƙa mata pack ɗin ta ce, "take it." Ta miƙa hannn ta karɓa ta buɗe ta ga abinda tace tana so ne, korean spicy noodles ce mai kyau sai ƙhamshi take yi, harda disposable fork a ciki yadda zata ci hankalinta a kwance. Islaha ta ɗago kanta ta kalle sa ta ga ita yake kallo sai ta ce, "Thank you" ta faɗa tana fara ci a hankali. Bai ce komai ba ya juya ya fita ya koma inda ya tashi ya cigaba da sallar yana jin daɗi ta samu abinda take so. Islaha kuwa yajin abincin ya yi mata sosai, ta dai ci kaɗan ta sha ruwan da Safeera ta bata magani ɗazu ta ajjiye sauran. Ta kwanta a kan gadon bayan ta kashe hasken, tana tunanin abubuwa kala-kala a haka bacci ya sake ɗauke ta. Washe gari bata shiryawa zuwa aiki ba, tunda ta yi wanka tana kwance tana juyi a kan gadon, yunwa take ji amma ƙiwar tashi take yi. Buɗe ƙofar da aka yi ya saka ta kalli ƙofar ta ga Mamy ce da Janan suka shigo. Sai ta miƙe zaune ta ce, "Mamy sannu da zuwa." Mamy ta ƙarasa ta dafa goshinta ta ce, "kin ji sauƙi?." Ta ce, "na ji sauƙi, Ina kwana Mamy?." Mamy ta yi murmushi ta ce, "kwana kuma daughter" sai ta kalli agogon da yake ɗaure a hannunta ta ce, "an idar da sallar azahar." Islaha ta yi murmushi dan ta ga gudun lokacin sosai. Janan ta ce, "Sis ya jikin?." Islaha ta yi murnushi ta ce, "Alhamdu lillah." "Daman kina fama da Dysmenorrhea ne?." Islaha ta ɗan ɗaga kai tana jin kunyar Mamy. Many ta ce, "ya ki ke jin ciwon? Yana yi miki tsanani sosai?." Islaha duk sai kunya ta rufe ta tana Allah wadai da wannan ciwo mai tona mata asiri. Sai daga baya Islaha ta ce, "yana yi sosai." Mamy ta ce, "har yanzu ma kina jin sa sosai?." Islaha ta girgiza kai ta ce, "bana ji sosai, in na sha magani yana raguwa kaɗan." Mamy ta yi shiru ta ce, "kwana nawa ciwon yake ɗauka kafin ki dawo normal?." Islaha ta ce, "kwana biyu." Janan ta ce, "kuma kina samun matsalar period ɗin wani lokacin?." Islaha ta ɗan ɗaga kai alamun eh. Janan ta ce, "Mamy i think it’s pelvic inflammatory disease." Mamy ta girgiza kai ta ce, "ba shi bane Janan, i’ts normal primary Dysmenorrhea as you said, canjawar hormonse yana kawo canjin lokacin, ba lallai sai pelvic ba." Mamy ta kalli Islaha ta ce, "kin yi breakfast?." Ta girgiza kai alamun bata yi ba, Mamy ta ce, "Janan je ki ki kawo mata breakfast please." Janan ta fita Mamy ta zuna a kusa da Islaha bata ce komai ba, ita kuma kunyar Mamy take ji. Suna zaune zaman shiru har Janan ta dawo da tray mai girma, ta ajjiye mata akan table ɗin da yake ɗakin ta ce, "ga shi nan sis." Islaha ta kalli Janan ta ce, "thank you sis." Janan ta ce, "welcome Miss Islaha. I saw ypur interview, gaskiya kin yi ƙoƙari sosai, yadda ki ke magana lamar baki san Ray ba, kin yi hira da shi normal kamar ba mijinki ba, har kina tambayarsa da gaske ne ya yi auren sirri.” Murmushi kawai ta yi ta taso ta zauna akan kujerar da kusa da table ɗin, Mamy ta haɗa mata tea ta bata a hannunta. ita duk nauyi take ji in Mamy tana yi mata wannan hidimar, sai ta ga babba da ita itace zata haɗa mata tea kuma ta bata?. Sai da ta sha tea sannan ta ci abinci, Mamy ta ce, "ki sha magani zai saka ki ji daɗi." Islaha ta ce, "To Mamy." Mamy ta ce, "na ga interview jiya, gaskiya kin yi ƙoƙari.” Ta yi murmushin jin daɗi ta ce, “Na gode Mamy.” “Kuma da gaske ana tambayar ya yi auren sirri?." Islsha ta ce, "sosai Mamy, Chairman ɗin mu da kansa ya saka wannan tambayar, dan ni ban tsara da ita ba." Mamy ta murmusa ta ce, "gabaɗaya duniya a kan hirar ta ke magana, sannan mutane sun ce basu yarda babu alaƙa tsakaninku ba, kuma ko da ina cikinsu bazan yarda ba." Janan ta ce, "kowa ma bazai yarda ba Mamy, yadda Ray yake yi mata magana ka san ba ranar ya fara magana da ita ba." Mamy ta ce, "ba ki ga kallon da yake yi nata ba? Irin kallon na san ki ɗin nan, like kamar ba a waje ɗaya muka kwana ba." Islaha ta yi dariya bata ce komai ba, amma ta ji daɗin zamansu Mamy a wajanta, hakan ya rage mata abubuwa da yawa. Mamy tana sakkowa ta fita sai ta ga Daada a tsaye Mamy ta ce, "Daada da kan ki?." Daada ta ce, "An ce min Islama bata da lafiya, shiyasa nazo na ganta, zata iya sakkowa?." Mamy ta riƙe Daada har falo ta zauna sannan ta ce, "ta ji sauƙi sosai." Daads ta ce, "ni ban iya hawa sama ba, a kira ta in zata iya sakkowa na ganta." Mamy ta ce, "Janan kira ta in zata iya zuwa." Janan ta koma, ba jimawa suka dawo tare da ita. Daada ta riƙe hannunta ta ce, "Ishlaya me yake damunki?." Islaha bata amsa tambayar nata ce, "Daada barka da rana." "Ya jikin ki?." "Da sauƙi." Daada ta kalli Mamy ta ce, "ku ne likitoci, me yake damunta?." Mamy ta ce, "Ciwon da ake yi ne yayin al'ada" ta faɗa tana kalkon Daada. Daada ta ce, "ciwon al'ada kuma? Me zai haɗata dashi ita da ta ke da aure?…..” A lolavin Rehaan yake shigowa parlor, Daada tana ganinsa ta ce, “Kai me zai haɗa mata ka da iriin wannan ciwon da ake dainawa bayan aure.” Rehaan bai tanka mata ba, Daada ta kalli Mamy ta ce, "in mace ta yi aure ba tana dainawa ba? Me hakan yake nufi da Ishlaya? Hakan yana nuna min ajjiye ƴar mutane ya yi tsahon wannan lokacin yana ɗirka mata shinkafa? An faɗa masa shinkafa ta zo ci gidan nan?. Ko an faɗa masa talabijin aka kawo masa da zai dinga kallonta ko yaushe? Matarsa ce fa.” Mamy ta tausasa murya ta ce, "Daada ba lallai sai an daina ciwon al'ada bayan anyi aure ba, wannan maganar duk ta manya ce, amma a lafiyance ba haka bane. Shi ciwon yana faruwa ne saboda mahaifa tana matsewa don fitar da jini (contraction) da kuma hormones (prostaglandins), ba dan rashin mu'amalar aure ba. Wasu matan suna iya lura da ciwon ya ragu bayan aure, amma ba hakan yana nufi kowa wacce mace ma in ta yi aure zai daina ba. Wasu bayan auren ba ya canjawa sai dai ma ya ƙaru fiye da yadda suka saba, duk da mu’amalar auren yana taimakawa wajan sakin wasu hormones (endorphins) ɗin, hakan shine yake rage muau zafin har su ga canji bayan aure.” “Amma hakan ba yana nuna yin aure ko yin mu’amalar aure shine magani ga masu fama da ciwon ba, wasu ciwon yana iya zama babban ciwo ne, shiyasa ake so in abun ya yi yawa aje asibiti a duba a gani.” “Wani Yana iya zama irinsu endometrioses, uterine fibroids, pelvic inflammatory disease. Irin wannan sai ayi ta fama, ba a san ciwo ne a jikin mace ba, a dinga tunanin me yake kawo shi, shiyasa zuwa asibiti yana da amfani akan irin wannan ciwon.” Mamy ta sake cewa, “Daada wannan ciwon da take fama da shi ba lallai ne in an yi aure sai an daina ba, wasu har su haihu ba sa dainawa.” Daada ta yi shiru sannan ta ce, "ni da aka ce min bata da lafiya ma wallahi na yi ciki gare ta, ashe babu cikin." Mamy ta ɗan murmusa kawai ta kalli Rehaan da ya zubawa Daada ido, shi Mamy ce ma ta basa mamaki da ta tsaya tana yiwa Daada bayanin da har abada bazata gane ba, hakan ya saka shi ya bar wajan ya hau sama bai ce komai ba. Daada ta dafa Islaha da kunyar duniya ta kashe ta, amma ta ƙaru sosai daga bayanin Mamy, dan ita kanta da ta yi tunanin da anyi aure ake dainawa, ashe abin ba haka bane. "Sannu, Allah ya baki lafiya." Ta amsa da amin a kunyace, tana jin kamar ta ta shi ta gudu saboda kunyar da take ji sosai. Daada ta ce, "koma saman ki kwanta ki huta, amma baza ki je aiki ba ko?." Ta ɗaga kai ta ce, "bazan je ba." "Jiya ai na ga hirar ki da Muhammad a talabijin, meyasa ba ki faɗawa dumiya ke matarsa bace?." Ta yi murmushi kawai amma bata ce komai ba, Daada ta ce, "ai da kin faɗa kowa ya sani, ko za a samu ƴan matan dangi su daina kawo masa hari." Murmushi ta sake yi amma ta kasa magana, Daada ta ce, "nan gaba ki faɗawa kowa kin ji?." Ta amsa da to, Daada ta fita ita da Janan da Mamy ita kuma ta koma saman. Tana shiga falon ta ji yana amsa waya ya ce, "ka ga mails ɗin da aka yi min kamar hauka? Dan na yi interview sau ɗaya sai dame ni?. Kar ka sake kawo min wani channel yanzu, a bari zuwa wani lokaci." Islaha tana jin yadda yake magana ta san Jazy ne, dan ta san dashi kaɗai yake irin wannan maganar. Islaha ta wuce ta shiga ɗaki ta ɗauki sabuwar wauyar nan ta ga saƙon Saheer ya shigo, ta buɗe ta ga ya ce, "ki bani lokaci Islaha, ina so na yi magana da ke, na san na yi kuskure, nima na yarda, ki bani dama don Allah." Sai ta ji zuciyarta ta yi sanyi a kansa ganin yadda yake roƙonta bayan ya wuce haka a wajanta. Kawai sai ta kira shi yana ɗauka ta ce, "Hamma ina yini." Saheer ya ce, "Kin bani wahala Islaha, kin yi fushi ni kuma bana so ki riƙe ni a ranki.” Kamar yana gabanta ta ce, "to ba kai ne ka jawo ba, ka dinga faɗa min magana." Jin zata fara yi masa kuka ya ce, "kina ji, kar ki yi kuka, yi haƙuri Islaha, na siyo miki lays da chocolates, ina so na gan ki na sake ba ki haƙuri, za ki iya fitowa yanzu?.” Yadda ya yi mata maganar cikin rarrashi sai tayi murmushi dan kwana biyu ta yi kewar masu rarrashinta, irin haka take so a dinga yi mata in tana cikin yanayin da take ciki. Islaha ta ce, "bazan iya fitowa ba, bani da lafiya." "Na san baki da lafiya, amma na san kin ji sauƙi, ko baza ki iya zuwa ba?." Ta yi shiru dan tana so ta je ko dan ta sake tambayarsa asalinta hakan ya saka ta ce, "Zan zo, a ina zan zo na same ka?." "Ki zo gida, sai na fito na same ki." "To, zan zo bayan la'asar in sha Allah." "Okay Islaha, ina jiran ki." "Lays ɗin nan na fi son tomato da salty." "To zan haɗa miki har spicy one ɗin." Islaha ta ce, "A’a, ni tomato ɗin nake so sai a haɗa da salty." Saheer ya ce, "To Islaha." Daga haka ta kashe wayar tana murmushin jin daɗin shiryawa da Hamma, dan shine jigonta. Bayan sallar la'asar Islaha ta kira Lawal ta fita daga gidan zuwa wajen Saheer, bayan ta sauka ta sallami Lawal sannan ta kira Saheer ta ce gata ta zo. Saheer ya fito ya kalle ta ganin fuskar ta ta ɗan kumbura kaɗan, da yake ya haddace komai nata kai tsaye ya fahimci a yanayin da take ciki, ba sai an yi masa bayani ba. Saheer ya yi murmushi ya ce, "Rabon da na ganki har na manta, sai dai a tv." Islaha ta ce, "kai Hamma, jiya fa ka ganni." “Jira ni na ɗauko motar Sadik sai mu yi magana saboda akwai rana." Bata ce komai ba ya ɗauko matar ta shiga suka fara tafiya sannan ya ce, "ki yi haƙuri, bazan sake faɗar abinda na faɗa miki ba har abada, ban san me ya shiga kaina na faɗa ba, amma bazan kuma ɓata miki rai ba.” Islaha ta yi murmushi ta ce, "shikenan ya wuce, amma na ji haushi.” Saheer ya ce, "ai na ba ki haƙuri ko?." Ta ce, "na haƙura, kuma ya wuce har abada. Amma ina so na san maganarmu ta farko wacce ta jawo har muka yi faɗan." Saheer ya ce, "Islaha na yi miki alƙawarin zan faɗa miki, amma sai kin ji sauƙi in sha Allah, yanzu ba a daidai ki ke ba, in kin dawo normal zan faɗa miki, na yi alƙawarin haka." Islaha bata ce komai ba dan daman ta san zai fahimci halin da take ciki. Ta juya ta kalli bayan motar, ta ga leda ta ɗauko ta buɗe tana cikin lays cheese ɗin ne kamar yadda ya ce. Saheer ya ce, “Safeera ta tuna min wani abu, kuma in sha Allah zamu kiyaye.” Ta yi masa shiru bata ce komai ba, bata tambaye sa me ta ce ba shima daga haka bai ce komai ba, ya fita ya bar ta a motar ya je inda zai je sannan ya dawo suka koma. Sai bayan sallar magrib sannan ya ajjiye ta a farkon estate ɗin gidansu Rehaan. Ya kalle ta ya ce, "sai da safe?” Ya faɗa da sigar tambaya yana kallonta. Islaha ta ce, "A gasihe min da Baffa da Mama." Ya gyaɗa kai ya ce, "zasu ji in sha Allah." Tana niyar fita ya ce, "Duniya gabaɗaya akan wannan ta ke magana, ana cewa yanayin yadda yake yi miki magana kamar akwai ɓoyayyiyar alaƙa a tsakaninku. Islaha! ni kaina yanayin da yake kallonki ya saka na ji a raina Rehaan yana son ki." Islaha ta ce, "Ɗan rainin hankali ne fa, ni fa abin kirki bai taɓa haɗa ni da shi ba….To sai jiya, na san ya....." sai gabanta ya faɗi ta kasa faɗa, tana tunawa da hannunsa har ƙasan cikinta ya je, kuma lokacin ko riga babu a jikinta. Sai ta canja maganar ta ce, "jiya ne kawai ya ɗan yi min abin kirki, ya bani magani da bani da lafiya, amma bayan nan ni ko gaisuwa bata haɗa mu." Saheer ya yi murmushi ya ce, "In kun gaisa ɗin ba laifi bane, tunda mijinki ne.” “Kaima ka yarda mijin nawa ne?.” “Ko bana tsoron Allah dole na yarda.” “Hmmm!” ta furta tana kawar da kanta tana tuna yadda hannunsa ya taɓa ƙasan cikinta, tana tuna yadda hannunsa ya jima a wajen yana matsa water bag ɗin a jikinta. Hakan da ta faɗa sai ya saka ya yi murmushi har cikin zuciyarsa ta bashi dariya ya ce, "Islaha ƴar daru, na tabbata ya san halin ki, ya san ke farar kura ce, ga tsoro ga ban tsoro.” Ta yi dariya ta ce, “Ni baƙar kura ce, bana tsorom kowa. Sai anjima Hamma" ta faɗa tana fita daga motar da ledar a hannunta. Islaha tana shiga parlour upstairs ta Rehaan a jikin window a tsaye yana kallon ƙofar gidan. Tana shigowa ya juyo ya kalle ta, daidai lokacin ta ɓare ledar cocholate tana sha. Ya zuba mata ido yana kallon yadda bakinta yake moving tana shan chocolate hankalinta kwance, tunda ta kalle shi sau ɗaya bata sake kallo ba ta ɗauke kanta. Rehaan ya kasa daure tambayar da ta ke yi masa amsa kuwa a kunnesa, ya cize bakinsa bai san san lokacin da ya ce, "waye wanda ya sauke ki a mota?." Islaha ta kalle shi ta ce, "me yasa ka tambaya?." Rehaan bai bata amsa ba ta ce, "Hamma Saheer, shikenan ka ji waye? To ka ƙyale ni don Allah, wallahi bana son tashin hakali" ta faɗa tana shiga ɗaki. Ya bita da kallo yana tunanin da bai san daga ya zo zuciyarsa ba, ya ɗan lumshe ido yana jin wani irin yanayin sa bai saba jinsa ba akan kowa. “Shiitt!” Ya furta yana shafa fuskarsa, yana ji wani abu yana shiga cikin zuciyarsa kamar shigar allura cikin jijiya. Gabaɗaya ya kasa gane yanayin da yake ciki a kwanakin nan, bai san meyasa lamarin yarinyar ya fara damunsa har haka ba, ko ina ruwansa da wanda ya sauke ta ɗin oho. Sai kuma ya yi tsaki kaɗan, ya shiga ɗaki bai sake bi ta kanta ba har aka kwana aka tashi. Bayan kwana biyu....... Nana Haleema. KRBBK: RDB3P61 Nana Haleema. Cikin kwana biyun Islaha ta zama cele, duk inda ta bi sai a dinga cewa ga wacce ta yi hira da Rehaan Yola har abin har ya fara bata haushi, in aka faɗa sai ta haɗe rai ta daina dariya, in da wani daban ne ba Rehaan ba sai ta yi fara’a, amma abokin faɗanta ne. Hirar ta sake jawo mata farin jini sosai, haka channle ɗinsu ta sake ɗaukaka, wanda bai san da ita ba yanzu ya sani. Islaha suna ta shirin bikin Safeera da ya ke tahowa, yayin da Saheer yana ta ginin gidan da zai saka Islaha in wata biyar ta yi. Islaha ta yi hankali, kuma raunin da take ganin ta yi masa ya fara warkewa, kuma da yake ba zuwa gidansu take yi ba kunnenta ba ya ji mata masu cewa ta zaɓi kuɗi akan halacci, daman maganar ce take ɗaga mata hankali. Zuwa lokacin sama-sama ta ke biye masa, ta ji nasihar Safeera sosai, shima kuma bai cika biye mata kamar farko ba, yana ƙoƙarin kiyaye dokokin Allah, ko maganar auren ce ta zo sai ta ce za su tattauna daga baya, suna jin tsoro ɗaukar haƙƙin aure. Islaha lokacin da ta tashi daga wajan aiki kai tsaye apartment ɗin Ray ta wuce, kwana biyu bata ganinsa kuma ta san tafiya ya yi, bata damu da sanin inda ya tafi ba, ta ji dai Mamy ta ce baya nan, bai yi mata sallama da zai tafi ba, itama bata yi masa ba. Tun kafin ta ƙarasa shiga main parlour ta cire mayafi da ɗankwalin kanta gashinta da yake a ɗaure ya bayyana, wanda ya sha gyara dan ta je gyaran kai, an gyara mata ya yi laushi sai ƙyalli yake yi. Tana hawa sama ta parlour suka haɗa ido, haka kawai gabanta ya faɗi sosai, sati biyu kenan bata gan shi ba sai a lokacin, kuma ko kusa bata yi tunabun ganinsa ba, duk da bata san ya tafi ba zai iya dawo bata sani ba, amma ganinsa ya saka mata faɗuwar gaba. Bata san dalilin da ya saka ta faɗuwar gaban ba, kawai ta san suna haɗa ido ta ji ƙirjinta ya buga da ƙarfi. Kallonsa take yi ganin ya canja mata sosai, ya ƙara yin haske, kuma ya gare gashin kansa sosai, ya rage tsahonsa, tsahon kaɗan ya bari ba kamar da ba, duk ya sakko amma bai yi tsahon wancan ba. Rehaan shima yana haɗa ido da ita sai da gabansa ya faɗi, kamar yadda bata san dalilin faɗuwar gaban ba shima bai san dalili ba, kawai dai ya ji zuciyarsa ta harba da gudu. Islaha ta ɗauke ido daga kansa, bata saba yi masa magana ba kwata-kwata, ta saba sai dai faɗa ya haɗa su sannan yake jin bakinta, amma sai ta ji tana so ta yi masa barka da zuwa. Ta buɗe baki zata yi magana unexpected ta ji ya ce, "How are you?." Abin ya bata mamaki, ta ɗago ta kalle sa ta ga ba ita yake kallo ba, wasu kaya da ya ajjiye yake ɗauka a kusa da shi. Sai kuma ya saka waya a kunne yana magana, kafin ta ba shi amsa ya shiga ɗaki. Islaha cikin mamaki ta ce, "Ikon Allah, yau kuma ni yake tambaya ya nake?." Ta bi ɗakinsa da kallo sai kuma ta ƙarasa nata ɗakin ta ajjiye jakar hannunta ta shiga wanka. Bayan ta fito ta shirya ta zauna tana aikin da yake gabanta. Sabuwar number ce ta shigo wayarta ta kalla sai ta ɗauka ta ji ance, "Islaha Mama ce, kina jina?." Islaha ta ce, "Mama barka da yamma." "yauwa barka. Na ce akan maganin nan da na ba ki kwanaki, Rehaan ya sha kuwa?." Islaha ta ce, "Oh wannan na ciwon cikin?." "Eh ya sha?." "ya sha amma sau biyu na basa gaskiya." "Haba Islaha, akan me za ki basa sau biyu? A sati fa na ce miki ya shanye sa." "to zan basa." "hakan ne ya kamata. Bana jin daɗin wannan ciwon nasa shiyasa na dage har aka samo maganin, ga shi ba a samunsa a kusa sai an yi nisa da garin nan, kar ki wasa dashi don Allah." Islaha bata ce komai ba ta kashe wayar ta bi wayar da kallo ta ce, "Ikon Allah, matar nan bata da gaskiya akan maganin wannan wallahi, haka kawai ta ɗaga hankalinta akan ban bashi magani ba? Kowa in ya ji yadda ta damu ya san akwai wani abun a ƙasa. Bara ki ga" ta faɗa tana miƙewa ta buɗe drawer ta ɗauki maganin, ta shiga banɗaki ta ƙarasa wajen a sink saka masa ruwa ya tafi, sannan ta wanke hannunta da sabulu ta fito ta cigaba da aikinta. Bata fito daga ɗaki ba sai bayan sallar magrib, ta fito ta ga Banisha a wajansa suna shan tea, Da Banisha suka gaisa ita kuma ta sauka ƙasa bata ce masa komai ba. Bata jima ba ta dawo da tea a hannunta, ta shiga ɗaki ta zauna ta cigaba da aikinta. Bayan ta shanye tea ɗin ta sake fitowa tana amsa waya hannunta riƙe da mug ɗin, tana cewa, "Bani da kati ne Safeera shiyasa ban kira ki ba, ina ta so na kira ki ashe katina ya ƙare." Ganin Jafar sai ta yi murmushi ta tsaya bata cigaba da tafiya ba kuma bata kashe wayar ba ta ce, "Shikenan ki yi haƙuri, zan tura miki yanzu" ta faɗa tana kashe wayar. Ta kalli Jazy ta ce, "Ina yini Mr Jafar.” Da murmushi ya c, "Miss Islaha, ya ki ke?." "lafiya lau." "Ya aiki? Ɗazu na ga interview ɗin ki, gaskiya ke good presenter ce." Ta yi murmushi ta ce, "Na gode. Ina Riyya?." "Riyya tana gidan Mummy.” Sai kuma ya kalli Rehaan ya ce, "anya ka taɓa kai ta gidan Mummy kuwa?." Bai ce komai ba itama bata ce ba ta sauka daga saman. Jazy sai bayan ta sauka sannan ya kalli Rehaan ya ce, "ba ka kyauta ba, a matsayin da ka ke da shi ace matar ka ce take cewa bata da katin waya? Wannan wanne irin mugun hali ne wanda ban san ka da shi? Ai ko zaman contarct ku ke yi ya kamata ace kana sauke responsibilities ɗinta, tunda sunanta matar ka. C’mon katin waya ace bata dashi? Haba Rehaan." Rehaan kalle sa cikin son kare kansw ya ce, "na sani ko an faɗa min?." "Riyya, Janan, Banisha, Ikram da su Nana sai sun faɗa maka ka ke saka musu kati? Duk sati ka ke saka musu katin waya koda na baya bai ƙare ba, har Riyya da ta yi aure ba ka daina ba, har alert remender ka saka a wayar ja saboda kar ka manta, meyasa baka saka ta a layinsu ba?.” Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba dan ya san gaskiya yake faɗa masa. Jazy ya ce, "ka saka mata katin Rehaan." Rehaan bai yi musu ba ya ɗauki wayarsa yana dannawa babu jimawa ya ajjiye wayar ya yi shiru bai ce komai. Jazy cike da tsokana ya ce, "Ashe kana da number ta?." Ray ya kalle sa ya ce, "ka san babu yadda zan zauna har zuwa yanzu da ita bani da details ɗinta, dole akwai, ko da bazai yi min amfani nan gaba. Kawai ban yi saving bane, amma na san inda number ya ke." "Allah ko? Sannu bature" ya faɗa yana yi masa wani kallo. A lokacin Islaha ta dawo idanunta suna kan waya, sai sake duba amount ɗin da aka saka mata katin take yi ganin kuɗin kamar ba daidai bane, so take ta banbabce dubu hamsin ce ko dubu biyar amma ta kasa gane katin nawa aka saka mata. Tsabar ta ruɗe bata san a falon ta tsaya ta kira Hamma ba, kuma ta saka a spekar ta ce, "Hamma ka saka min airtime ne yanzu?." Abin ka da sabuwar iphone 17 take muryar Saheer ta fito raɗau ya ce, "A’a, ban saka miki kati ba, wani abu ne?." "Ai kuwa wani ya yi kuskuren number ya saka min kati, dan ni dai in ba kai ba bani da wanda yake saka min kati. Kuma na kasa gane amount ɗin, kamar dubu biyar kamar kuma dubu hamsin." "Ayya maybe mistake aka yi, kuma babu number?." "Daga bank aka saka, amma ina zuwa" ta faɗa tana kashewa tare da tunanin wanda zai iya saka mata kati. Rehaan tunda ta fara waya ya wani nutsu yana jinta kamar mai ɗaukar karatu, ba muryar ta yake saurare na, muryar Saheer yake ji tana shiga ƙwaƙwalwarsa, yana jin wani iri a jikinsa kamar ya san mai irin muryar, ya kasa banbance sanayya ce ko wani yanayin dai bai sani ba. Sannan yadda ta ce ta san bata da mai saka mata kati sai shi sai ya ji maganar har ransa, ya dinga jin wani abu kamar ɓacin rai kamar haushin kansa. Jazy ganin ta ruɗe ya ce "Miss." Islaha ta ɗago ido ta kalle sa sai ya ce, "ki daina wahalar da kan ki, Rehaan ne ya saka miki airtime." Islaga mamaki ya saka buɗe ido ta ce, "ya saka min kati kuma, ni na ce masa ina so ne?." Jazy ya ce, "Nima ban sani ba, tambaye sa." Ai kuwa sai ta kalle sa ta ce, "Ni ban ce ina son airtime ba, zan iya siya da kuɗina ba sai an bani ba." Rehaan maimkon ya kalle ta sai ya kalli Jazy, kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru ya miƙe tsaye sannan ya ce, "in ka gama ka tura min, ina so na duba kafin na tura musu" bai jira amsarsa ba ya shiga ɗaki. Jazy ya kalle ta ita kuma ta ce, "ka faɗa masa ni bana buƙatar komai daga wajansa." "Ke kuwa ki ke buƙata Islaha, c’mon aritime ace ba ki dashi? Kina amsa sunan matar Rehaan ace ba ki dashi? Shine ya sa ka miki." Ta kalli wayarta sannan ta c, "shine kuma har fifty thosounds?." Ya yi murmushi ya ce, "duba dakyau ki gani, zero nawa ka ka gani?." islaha ta sake kallon amount ɗin sannan sai ta buɗe idanunra ta ce, "kamar dubu ɗari biyar ne fa." Jazy ya yi dariya ya miƙe ya ce, "good night Miss" ya faɗa tana sauka daga saman. Islaha ta jima tana kallon kuɗin, tana maimaita dubu ɗari biyar a zuciyarta, ta sake duba balance ɗin mtn ɗinta da dubu ɗari biyar, har da bonus ɗin data da aka bata saboda yawan kuɗin. Islaha cikin mamaki ta ce, "dubu ɗari biyar a katin waya kawai?.” “Ni ya zan yi da wanann kuɗin, wa nake da shi da zan kira shi da wannan uban katin wayar? Sai dai na rabar, na turawa Safeera da abokan arzuƙi, bazan turawa Hamma ba kar ya ga kamar na raina shi.” Ta sake kallon ɗakinsa, tana so ta je ta yi masa magana amma ta kasa. A lokacin ya fito daga ɗakin ya ƙarasa inda ya tashi ya ɗauki abinda zai ɗauka zai koma. Islaha ta kalle shi cikin murya kamar tana shagwaɓa ta ce, "ni ban ce ina son kati ba." Ya juyo ya kalle ta, ya rasa meyasa in ya kalle ta gabansa yake faɗuwa, kwana biyu da basa tare baya jin hakan, sai dai in ya tunata ya ji gabansa ya faɗi. Bai ce mata komai ba ya koma ɗaki dan bai san me zai ce mata ba. Islaha ta shiga ɗaki tana sake kallon kuɗin dan ita mamaki kuɗin yake bata, A haka ta kwamta ta yi bacci tana tunanin kuɗim. Washe gari ya zama date ɗin ya yi daidai da aurensu wata uku kenan, da farin ciki ta tashi, tana jin walwala saura kwana sittin ta rabu da ƙaya. Ko wanka bata yi ta sauka ƙasa, dan haka kawai take jin yunwa sosai. Bayan ta gama shan tea ɗin sai ta miƙe ta buɗe public bathroom ɗin da yake cikin main parlour ta shiga tana kallonsa. Komai akwai a ciki, hatta body wash sabbabi ne ba a taɓa buɗe su ba, ga soaps da komai sabo ba a taɓa amfani da shi ba. Ganin hakan sai ta shiga dan Chairman yana ta yi mata waya yana cewa ta zo akwai abimda zata yi a can. A ciki ta yi wankan tsaf, ta gama wankan ta ɗaura towel kenan ta kalli windown da take gefenta ta ga fuskar Salman yana kallonta. Gabanta ya yanke faɗi, suna haɗa ido da ita ya ɗaga mata hannu alamun hello, ta yi ihuu mai ƙarfi ta fito a guje daga banɗakin tana ihu kamar wacce wani abun ya biyo. Rehaan shigowar sa parlour kenan ya ji ihunta wanda ya saka ya daki zuciyarsa da ƙarfi, Ray ya ƙaraso ciki yana kallon ta ganin daga ita sai towel ƙarami, wanda bai wuce laps ɗinta ba, gabaɗaya brown laps ɗinta a bayyane suke, sannan ga ruwan da yake ɗiga daga jikinta alamun ko goge jikinta bata yi ba ta fito. Ray ya bita da kallo na musamman, yana bin laps ɗinta da kallo da skin colour ɗinsu ya fi na ko ina ɗaukar hankali. Daƙyar ya iya janye idanunsa ya kallibanɗakin da ya ke a buɗe, ya kalle ta ya ce, "Lafiya?." Islaha a ruɗe ta nuna masa window ta ce, “Salman na gani a tsaye yana kallona ina wanka." Wani irin dumm ya ji a zuciyarsa, duhu ya mamaye masa idanunsa, ƙwaƙwalwarsa ta harba kamar harbawar jijiyoyin da suke harbawa a yayin ciwon kai, ya je hutun taƙaitaccen lokaci dan zuciyarta ta girgiza sosai. "Sir what wrong?." Maganar chef ta dawo da shi hankalinsa, ya kalli bathroom ya sai kawai ya shiga, ya kalli window ɗin ya Salman a tsaye har hannu yake ɗaga masa. Ya juya da sassarfa ya fita daga falon, ya zaga baya inda window ɗin ta ke ya gan shi a tsaye ya ta ka bench ɗin masu gadi yana bathroom ɗin hankalinsa kwance. Wani irin abu ya ji a zuciyarsa, bai san lokacin da ya jawosa da ƙarfi ya diro daga kai, ba dan ya diro ba tsaf zai iya faɗuwa saboda yadda ya jawo shi da ƙarfi. Ray cikin faɗan da bai saba yiwa Salman ba ya ce, "meye haka Salman! Me ka aikata haka?" Ya faɗa a fusace yana kallonsa. Salman ya ce, "ina kallon ƙawata tana wanka, nima Umma tana kallona in ina wanka, shine nima nake kallonta.” Ya runtse idanunsa yana kamar ya gaggaura mari saboda ɗacin maganar da ya faɗa, sai kuma ya dafe goshi yana nuna sa da yatsa amma ya rasa me zai ce, bakinsa yana rawa ya kasa furta komai, yana ji ƙirjinsa yana bugawa da ƙarfi, zuciyarsa na harbawa. Shi ba abin ya ce masa mahaukaci ba daman shine, ba abin ya dake sa ba ya san ba hankali ne da shi ba. Salman ya jawo hannunsa ya ce, "zo ka ganta, tana da gashi mai tsaho irin na tv, har ta fi Mamy gashi." Faɗar hakan da ya yi ya fargar da Rehaan, ya fincike hannunsa cikin wani irin yanayi ya ce, "Ya isa Salman!.” Salman ya firgita jin maganar har tsakiyar kansa, ya tsaya cak yana kallon Rehaan da ya juye masa ya koma kamar wani zaki, fuskarsa ta canja gabaɗaya kamar ba shi ba. Ray ya ce, “Kar na sake ganin ka shigo apartment ɗin nan, kar na sake ganin kana kallon wani a banɗaki, ka jii!." Salman duk da ya tsorata ya ce, "ni ba kowa nake gani ba, ita nake gani kullum." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Rehaan ya furta cikin wani irin yanayin da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba, yana ji jiri yana ɗaukarsa kamar zai faɗi, ya dafa bango jin sabon yanayi zai yar da shi ya faɗi ƙasa. Ya kalli Salman yana nuna masa hanya ya ce, "fita!." Salman ya ce, "ni ba wajan ka nazo ba, wajanta nazo, Kuma..." cikin tsawa ya ce, "ka fita na ce!" Ya sake faɗa yana zazaaro masa ido waje. Salman sai ya ji tsoro ya shige shi, rana ta biyu kenan da Rehaan ya yi masa a duniya. Shi kuma ya juya ya koma ciki, amma bai same ta a wajan ba sai chef ɗinsa da ya gani a tsaye, takaici ya sake kama sa ya hau saman ya nufi ɗakinta kai tsaye, dan in bai yi mata warning ba ji yake kamar numfashinsa zai ɗauke. Ɗakin babu haske sosai sai blue light, Islaha tana zaune ɗaure da towel ɗin har lokacin bata dawo daidai ba, ta dafe kanta da duka hannuanta guda biyun, ta yi shiru tana jin nauyi da kasala a jikinta. In ta tuna bata san lokacin da yake tsaye a wajan ba sai ta ji ranta ya ɓaci, duk da a shower glass ta yi wankan amma ta tabbatar zai iya ganin jikinta tunda sai da ta fito ta ɗaura towel, kwata-kwata bata yi tunanin Rehaan zai biyo bayanta har ɗakin ba shiyasa ta zauna a haka. Buɗe ƙofar ɗakin ta ji an yi, gabanta ya faɗi sosai ta waiwayo tana kallonsa, tana jin nauyi da kunyar suna mamaye mata ko ina na jikinta. Rehaan ya kalle ta yana nuna ta da yatsa ya ce, "Are you out of your mind? Duk bathrooms ɗin da suke apartment ɗin nan, you could'nt find one to use except the public one in the main palour?. What kind of nonsense is this?." Islaha ta ɗago ta kalle sa jin yadda yake yi mata magana cikin kaushi da zafi, bata taɓa jin muryarsa a haka ba, bata taɓa ji ya yi magana mai ƙarfin wannan ba. Ko yaushe magana yake yi cikin steeze, yana yi yana basarwa. Amma yau ta ji akasin haka, har yana shouting. Bata motsa daga inda take ba, duk kunya ta gama mamaye mata idanunta, amma bata bari ya yi tasiri na ta ce, "don Allah ka bani waje in shirya, bana so kana shigowa inda nake anyhow. Ka san dai ni ba muharramar ka bace, zuwa inda nake without permission haram ne." Tsabar takaici bai san ya riƙo hannunta ya miƙar da ita tsaye ba. Bata yi zato ba zai yi hakan ba ko kaɗan, sai ta yi saurin riƙe towel ɗin jikinta jin zai kwance. Ya ce, "ba ki ji me na ce miki ba? Ina yi miki magana akan shirmen da ki ka yi kina yi min maganar na shigo ɗakin ki without permission?." Islaha ta bi sa da kallon mamaki, ita dai bata ga abin ɓacin rai haka daga wajansa ba, ita bata yi tunanin bazai ji haushi ba, ita ce zata ji haushi tunda jikinta aka gani ba nasa ba. Meye dan wani ya ganta tana wanka zai ɗaga hankalinsa haka, kamar ya ga matarsa ko wata ƴar uwarsa?. Ita kunya take ji ta rufe ta, daga ita sai ƙaramin towel a tsaye, ga kanta ko ɗankwali babu, ga towel ɗin ba shi da girma ko kaɗan kuma ya kusa kwancewa. Ta ɗan juya baya da nufin ta ɗauko hijjab ta ji ya finciko hannunta ya dawo da ita ta baya. Kafin ta ce wani abun, cikin muryar da take nuna yana cikin tsananin ɓacin ya ce, "dan kin saba yin hakan a wani wajan, shiyasa za ki yi a nan?." Bata yi niyar tanka masa ba, amma jin abinda ya ce sai ta kawar da duk abinda take ji, ta danne duk wata kunya da firgici ta ce, "tunda ka san na saba meye na zuwa ka same ni kana yi min shouting? Yau wani ya saba ganina ina wanka, ko ka manta har ta ya ni wankan maza suna yi?." Duk da babu haske sosai a ɗakin, tana iya ganin yadda fuskarsa ta canja kamar ba shi ba, ta yi jah sosai, kuma ransa a ɓace yake irin ɓacin ran da bata taɓa gani a tare da shi ba, fuskarsa ta nuna fushi sosai, sannan ta nuna yanayin da yake ciki. Ita wallahi mamaki yake bata, ko ina ruwansa dan an ganta tana wanka bata sani ba. Ta cire hannunsa da ya riƙe mata hannunta ta ce, "kar ka sake riƙe hannuna na faɗa maka, ka daina ƙoƙarin taɓa jikina, ka san a ƙarƙashim contract mu ke, taɓa ni baya cikin agender ta da kai. Ina ruwan ka dan ya ganni ina wanka? Kai ya gani kana wankan, ko matarka ya gani, ko ƙanwarka ya gani da za ka damu ka ɗaga hankalinka har haka?." "Na ga dai Islaha ya gani tana wanka ba kai ba ko, to meye na damuwa har ka zo kana ɗaga min murya kamar kana aurena?. Ai ba yau na saba ba, ka manta na saba zama da shi, ko ka manta kafin shi akwai maza da yawa da suka ganni a irin yanayin da ya ganni? Ko ka manta har ta ya ni wankan suke yi duk a cikin kuɗin da suka biya ni?.” "Mr Rehaan meye naka? Abu ne da na saba aikatawa kuma nake kan yi, wannan ba komai bane a wajena. In na ga dama zan kwance towel ɗin jikina in fita kan titi, rayuwata ce ba taka ba, jikina ne ba jikinka ko na matarka ba. Kaf mutanen duniya in na yi niya zan iya nuna musu jikina, kuma bai shafe ka ba, tunda ba aurena ka ke yi ba." “Ka bani waje don Allah, ka kuma daina yi min ihu. Babu ruwanka da duk abinda zan yi, rayuwata ce ai ba rayuwarka. Ka je waje don Allah!" Ta faɗa bata yarda sun haɗa ido ba, tana nuna masa ƙofar da zai fita daga ɗakin. Gabaɗaya ta kashe masa baki, ya kasa magana sai kallonta da yake yi ƙirjinsa yana ɗagawa saboda bugawar zuciya. Bai san abinda ya saka yake jin zuciyarsa tana zafi akan kalamanta ba, duk ya san dai gaskiya ta faɗa ta saba wanka da maza dan shi shaida ne akan hakan, amma bai san dalilinsa na jin haushin kalamanta ba. Islaha kuwa daƙyar take iya jurewa tana komawa mara kunya tantiriya a gabansa, tunda a haka yake kallonta bata so ta canja masa tunani, shine ya saka ta zama haka ta ƙarfi da yaji, bata so ta canjawa mutum tunanin da yake yi a kanta. Tunda ita ƴar iskace a idanunsa, aje a hakan. Maganar ta ce ta dawo da da shi daga duniyar tunani, ya tako ya zo kusa da ita daf da daf, yana kallon fuskarta ta ƙaramin hasken ɗakin, muryarsa very low ya ce, "mazan kan titi zasu iya ganin ki, haka ki ka ce ko?." Yadda ya yi maganar sai da gabanta ya faɗi, ga shi ya matso kusa da ita daf da daf, ga shi daga ita dai towel. Ta ɗan ja baya kaɗan sannan ta ce, "zasu iya, kowa ma zai iya, kuma babu ruwanka." "Kowa ma zai iya!" Ya furta yana cize bakinsa, cikin wani irin yanayin da bai taɓa jin irinsa ba. Ya ɗan girgiza kai yana kallonta, kafin ya sake yin ƙasa da muryarsa, cikin soft vioce ya ce, "tunda kowa zai iya ban ga amfanin rufe jikinki ba, I can also see you without a towel!" ya faɗa yana zagawa da hannunsa bayanta, ya saka hannunsa a inda ta ɗaure towel ɗin ta baya, ya ja shi da ƙarfi ya zare shi gabaɗaya. Nana Haleema. RDB3P62 Nana Haleema. Babu zato babu tsammani ta ji ya fizge towel ɗin jikinta, tsabar gigicewa da ruɗewa a wajan ta tsaya cak, kanta yana ƙara irin ƙuuuu kamar wacce ta buge a kanta bata dawo daidai ba, ganinta ya ɗauke, kunnenta ya toshe, komai na ta ya tsaya cak ta rasa a wacce duniya ta ke. Cikin sacanni sanyi a.c ya ratsa sassan jikinta, sai hankalinta dawo jikinta, ta gigice ta rasa inda zata saka kanta, ta yi ƙara mai ƙarfi, ta rasa inda zata saka kanta saboda tashin hankali. Ta jawo bedsheet a gigice ta kulle jikinta har tsakiyar kanta, kawai ta fashe da kuka mai sautin da ya dawo da Rehaan duniyar da ya tafi. Ray duk yadda ya so tsayar da idanunsa a iya fuskarta kasa ya yi, shi bai cire mata towel dan ya kalli jikinta ba ko kaɗan, ya yi ne dan ta ce kowa ma zai iya, shiyasa ya yi ba dan ya kalle ta ba sai dan ya ga yadda fuskar mara kunya zata koma. Amma sai ya kasa sarrafa kansa, sai ya kasa tsayar da idanunsa a iya fuskar ta, sai ya kasa sarrarafa ganinsa a iya fuskarta, bai san lokacin da idanunsa suka sauka daga kan fuskarta zuwa wani wajen ba, bai san me ya faru ba kawai ya tsinci kansa dumu dumu yana kallon ko ina na jikinta. Duk da ɗaki ba shi da wadataccen haske, amma hakan bai ɓoye bayyanar brown and shining skin ɗinta ba, babu inda bai gani a jikinta ba, babu abinda idanunsa ba su ganar masa ba, babu abinda bai haddace tsaf a cikin idanunsa ba. Duk ya so idanunsa su tsaya a kan fuskar ta kawai, ko dan ya ga yadda idanun mara kunya zai yi. Amma dai kash! Ya kasa yin hakan. Islaha da ta gama gigicewa jikinta karkarwa yake yi saboda tashin hankali, jinta take yi kamar ba a duniya take ba saboda tsabar tashin hankali da ruɗewa. Duk da ta rufe jikinta har kanta, ji take yi kamar har lokacin yana tsaye yana kallon jikinta da babu komai, ji take kamar ƙare mata kallo yake yi. Ta dafe kanta ta yi ƙara mai ƙarfi, tare da fashewa da kukan da yake zuciyarta. Ƙarar da ta yi ita ta sake fargar da Ray daga duniyar da ya afka, ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana kallon yadda ta cukwikuye bedsheet ɗin, ga shi yana shaking alamun jikinta rawa yake yi. Sai ya kasa motsawa, yana jan numfashi mai ƙarfi yana saukewa a hankali, apple adam ɗinsa yana up and down, tsigar jikinsa ta tashi, gashin jikinsa na ko ina ya fito ya miƙe, yana jin tsirgawar wani abu kamar wanda ya sha lemon tsami. Cikin wannan yanayin ya fara ja da baya, ya fara tafiya a hankali har lokacin yana kallon yadda take kuka a cikin bedsheet, ya shafa gashinsa tare da lumshe idanu yana hango abinda ya gani a jikinta musamman ƙirjinta da nan ya fi fitowa sosai, ya fi ko ina tsayawa cak a idanunsa wani abu yana fizgarsa da ƙarfi kamar zai kayar dashi. Da zafin nama ya juya ya fita daga ɗakin da sauri. Islaha ta jima tana kukan da bata san na meye ba, ta yi kuka mai yawa wanda bata san adadin lokacin da ta ɗauka ba. Kanta ya fara ciwo, ta fara jin numfashinta yana sarƙewa aalamun zata iya samun attack a ko yaushe. Ta buɗe kanta da ta rufe iya jikinta, fuskarta ta tasa saboda kuka ga kanta ya yi nauyi. In ta tuna babu komai a jikinta ta tsaya a gabansa bata sanin hawaye yana cigaba da zuba daga idanunta. Jikinta ya yi sanyi, zuciyarta bugawa take yi saboda tashin hankali, ta kwanta lamo tana tuna abinda ya faru. Kawai sai ta fara marin kanta, ta ko ina dukan kanta take yi ko zata wuce takaicin da yake zuciyarta. Tana ji wayarta tana ƙara amma ta kasa kallonta balle ta duba, zazzaɓi ya rufe ta lokaci ɗaya, ciwon kai ya sake saukar mata. _Rehaan fa, shine ya ganni babu kaya a jikina._ Abinda take maimaiwa kenan a zuciyarta, ga shi ta kasa tashi ta saka kayan ko zata ji sauƙin sanyin da take ji, ta jima a haka tana tunani, komai ya tsaya mata kamar ba a dumiya take ba. Daƙyar ta iya motsawa ta saka doguwar rigar ta ta bacci, ta koma ta kwanta tana ji kamar har lokacin yana tsaye yana kallon mata jiki.     Rehaan da ya fita daga ɗakin a parlour ya zauna ya yi shiru yana kallon waje ɗaya bai yi komai ba, a hankali yake sauke numfashin da ya tsaya masa a ƙirji yana haɗɗiye yawu, apple adam ɗinsa yana up and down, jijiyar kansa tana harbawa, har lokacin tsigar jikinsa bata daina tashi ba. Ya saka hannu ya hargitsa gashin kansa, ya jingina da kujera ya furzar da iska mai zafi. Da ya rufe ido ita ce ta ke zuwar masa a tsaye babu komai a jikinta, sai ya yi sauri ya buɗe yana ji zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi. Ya kalli ƙofar ɗakin da ya daina jin kukanta da ya ke jiyowa tunda ya fitowa. Ya yi ruf da ciki akan kujerar ya yi shiru, itace kawai take gilma masa a idanunsa da ƙwaƙwalwarsa, zuciyarsa tana harbawa na wuce ƙa'ida. Yanayin ya zamar masa baƙo, bazai ce ga asalin abinda yake damunsa ba, ya san dai yana jin kansa kamar ba shi ba. Ya jima a haka a kwance, kafin ya miƙe tsaye sai wayarsa ta fara ringing, da ya duba ya ga Jazy ne sai ya share bai ɗauka ba. Kamar zai ɗauki key ɗin mota sai kuma ya fasa dan yadda yake jin cikinsa bazai iya driving ba, ya shiga ɗaki ya wuce bathroom ya sakarwa kansa ruwan sanyi ba tare da ya cire kayan jikinsa, ya rufe idanunsa yana hango fuskar Islaha da surarta suna gilma masa a idanunsa. Ya jima a haka sosai a tsaye yana fitar numfashi a wahale, ya jima a tsaye ruwa yana dukan jikinsa, kafin ya fito daga shower glass ɗin, ya tsaya yana kallon kansa a madubi yana ji kamar ana canja shi gabaɗaya, sai ya ga kamar ba wancan Rehaan ɗin bane wani daban ne wannan. Daƙyar ya samu ya yi drying gashinsa, sannan ya fito closet ya canja kaya ya kira driver ya sauka ƙasa. Har zai gifta kitchen sai ya ji motsin chef a ciki, ya tsaya cak yana kallon kitchen ɗin amma ya kasa shiga. A lokacin Chef ɗin ya fito da tray a hannunsa zai ajjiye, ganin Rahaan sai ya tsaya cikin girmamawa ya ce, "Sir What do you want?." Ya zuba masa ido kawai bai ce komai ba, yana tuna shima ya ga Islaha da towel a jikinta. Ya runtse ido yana taune lips ɗinsa, ya buɗe ido ya kalle shi ya ce, "go back to England, sandra will replace you and continue the work here.” Abinda ya faɗa masa kenan ya fita daga falon yana jin haushin kowa a zuciyarsa. Guest house suka wuce da driver, yana shiga ya cillar da wayarsa a akan kujera, ko haske parlour bai kunna a falon ba ya zauna. Ya yi shiru yana kallon wani waje daban kamar mai karanta wani abu, duk inda ya waiwaya ita yake kallo, sai ya ga kamar tv aka saka aka kunna masa surarta yana gani. "Ya Salam! Ya Salam!!" Ya furta cikin wani irin yanayi yana hargitsa gashinsa, yana fitar da numfashi mai ƙarfi, yana ji dama yana da dama da ya goge abinda ya gani daga ƙwaƙwalwarsa. A lokacin Jazu ya shigo parlour, ganin Rehaan a zaune sai ya kunna haske sannan ya ce, "Kai kuma fa? Ina ta kiran ka ba ka ɗauka, daman ina so na tambaye ka ne." Rehaan ya ɗago ido ya kalli Jazy da yake ƙarasowa, Jazy ya ga yadda idanun Rehaan suka canja ga fuskarsa ta yi ja, ga wani irin yanayi da bai taɓa ganinsa akan fuskarsa ba, sai ya ji tsoro ya kama shi ya buɗe idanunsa ya ce, "ciwon cikin ne ya motsa? Na ganka wani iri.” Rehaan bai iya ba shi amsa ba ya lumshe idanunsa bai ce komai ba, dan bazai iya buɗe baki ya yi magana ba, in ya buɗe baki ya yi magana gani yake kamar Jazy bazai ji abinda zai faɗa ba saboda raunin da zuciyarsa ta yi. Jazy sai ya share sa bai ce komai ba, ya ɗauki file ɗin da yake gefensa yana dubawa. Ƙarar wayar Ray ya saka Jazy ya kalle shi, ya ga ya ɗauka kamar baya son magana ya ce, "Kiddo Please, i will call back" yana faɗa ya kashe wayar ya ajjiye. Jazy ya cika da mamaki mai matuƙar yawa, bai taɓa ganin yanayin da ya canja sa haka ba, har Kiddo zata kira sa a waya ya ce zai kira ta anjima, duk busy da yake cikin indai Mamy ko wani nasa zasu kirasa sai ya ɗauka, ko da meeting yake yi. Jazy bai ce masa komai ba dan yasan in ya tambaya shiru zai sake yi masa, gwara ya ƙyale sa in ya gaji ya san zai faɗa masa da kansa. "Salman...." Jin hakan sai Jazy ya kalle sa yana mamakin wannan wanne irin yanayi ne da ya canja masa muryarsa haka? Hakan ya saka Jazy ya tsaya cak da abinda yake yi, dan yana so ya ji musabbin wannan canjin da inda ya fito, dan shi dai tunda yake da Rehaan bai taɓa ganinsa haka ba. Jazy a nutse ya ce, "ciwonsa ne dai?." Ray miƙe zaune sosai ya haɗe yatsunsa waje ɗaya ya kalli Jazy, kamar zai yi magana sai ya sauke numfashi a hankali, ya rufe ido yana girgiza kai sannan ya ce, "I caught him….” Sai ya kasa ƙarasawa yana share fuskarsa da hannunsa, takaicin faɗar maganar yana mamaye masa ko ina na jikinsa. Ya giegiza kai ya rufe iso sannan ya ce, “i caught him peeping at that girl in the bathroom." Jazy ya buɗe idanu cikin mamaki ya ce, "which girl, Kiddoo?." Rehana ya yi masa wani irin banzan kallo kafin ya koma ya jingina da kujerar bai ce komai ba. Jazy ya ce, "Na ga Riyya bata nan, kuma na ji ka ce yarinya, shiyasa na yi tunanin Banisha ce." Ya yi tsaki yana cize lips ɗinsa yana girgiza sannan ya ce, "C wife." Jazy ya bisa da kallon mamaki ganin yadda ya canja gabaɗaya kawai dan an leƙa islaha a banɗaki. Jazy ya ce, "What! Islaha kuma? To garin ya ya hakan?." "I don't know Jazy!" Ya faɗa cikin wani irin yanayi yana jan numfashi mai ƙarfi. Sai kuma ya ɗago ya ce, "amma laifinta ne...." Ya sake dakatawa yana fizgo numfashi dan iya maganar sake ɓata masa rai yake yi. "Meyasa zata yi using public bathroom? Duk bathrooms ɗin da suke cikin apartment ɗina sun yi mata kaɗan ne……?…..” “Why sai sai guest bathroom Jazy…?” Ya ƙarasa faɗa a sanyaye kamar mai shirin yin kuka. Jazy ya yi murmushi yana karantar yanayin Rehaan ya ce, "Kuma shi window ɗinsa ta waje ya ke ko? Amma sai na ga kamar ya yi tsayin da Salman bazai gano ba." "Ya yi using bench ɗin da masu gadi suke zama." Jazy ya ce, "Subahanallahi! Har Salman ya san ya taka abu ya leƙa ta a bathroom? Kai Amma bai kyauta ba ko kaɗan, amma sai dai a bata haƙuri, saboda ba shi da hankali." Ya yi tsaki mai tsaho cikin takaici ya ce, "Dan bashi da hankali sai ya dinga binta har bathroom yana kallonta?." Jazy bai ce masa komai ba sai kallonsa yake yi yana mamakin wannan soyayya da ta yiwa Rehaan mugun kamu lokaci ɗaya haka. Ray yana girgiza kai ya ce, "dan ba shi da hankali sai akace masa ya dinga yiwa kowa hauka ba? Har ya dinga kallonta a bathroom?." Ya sake fizgar numfashi da ƙarfi sannan ya ce, “Daga yau, bazai sake shiga apartment ɗin nan ba, zan saka security a wajan. And.......god!" Ya kasa faɗar abinda zai ce jin zuciyarsa tana bugawa, ga wani irin ɓacin rai da yake ji a ƙasan zuciyarsa. Jazy dai kallonsa yake yi yana girgiza kai, ya yi murmushi yana mamakin Rehaan ganin ya faɗa da wuri har haka, shi ya ɗauka sai contract ɗin nasu ya ƙare ta bar gidan sannan zai damu, sai ga shi tun ba a je ko ina ba ya fara nuna soyayya mai ɗauke da zazzafan kishi. Jazy ya ce, "Allah Sarki! Amma ita ya kamata a bawa haƙuri." "bata da hankali fa, bata san abinda yake damunta ba. Na je na yi mata magana kuma wai ni take kallo tana cewa ai daman ta saba, ba yau aka fara ganinta haka ba." "ai gaskiya ta faɗa maka, ba rashin hankali bane, da gaske ba yau ta saba wanka da maza ba. Ba a haka ka ke kallonta ba?.” Baice komai ba ya ɗaga kansa sama yana kallon p.o.p, sai kuma ya sauke a hankali ya ce, "Zan samu Abba, ya kamata a san abinda za a yi akan Salman, bazan dinga tolerating wannan shirmen ba." Jazy bai san ya yi ƙaramar dariya ba, kamar ya tambayesa dalili sai ya share, dan ba ya so ya fargar da shi da wuri har sai ya tabbatar ya gama kamuwa ta ko ina, sannan sai ya ritsa shi ya tambayesa ya aka yi aka haihu a ragaya. Jazy ya ce, "ni ban ga abin damuwa a nan ba, tunda matar contract ce ba abin ɗaga hankali bane, kuma jikinta aka gani ba jikin ka, kuma Salman ba hankali ne da shi ba.” “Na ji ba shi da hankali, amma ya ganta ko?…” Jazy zai musa cikin tsawa ya ce, “Ya ganta ko Jazy..!.” “Ya ganta Rehaan, ka manta ka ce min suna kwana tare? Sai na ga normal ne.” Rehaan ya ja tsaki mai tsaho, ya buɗe baki zai yi magana amma sai ya kasa ya rufe idanunsa. Jazy ya girgiza kai cike da mugunta sannan ya ce, “ni ban ga abin damuwa a lamarin nan ba, amma tunda kana ganin hakan daidai ne fine. Lokacin na ku ma ai ya kusa ƙarewa, saura kwanaki kaɗan ku rabu kowa ma ya huta." Ya kalli Jazy kamar mai karanta wani abu akan fuskarsa, sai kuma ya ɗauke kai ya tashi ya hau sama. Jazy ya yi dariya mai isarsa sannan ya ce, "Islaha kin yi nasara, kin saka zuciyar Rehaan ta girgiza, kin saka ya tashi daga duniyar mara aure zuwa ta masu aure. Good job! Ina so a yi dramar nan da ni, ina so na ga yadda komai zai kasance, dan na san Islaha baza ta taɓa karɓar Rehaan ba, dan ba shi take so ba. Shi kuma Alhaji Rehaan ɗin Mamy bazai rabu da ita ba...." Ya girgiza kai yana dariy ya ce, "Wow! Akwai sabuwar drama a nan gaba, zamu kwashi hawayen Mamies boy, dan Islaha daidai dashi take" ya faɗa yana dariya sai kuma ya kira Riyya suna waya, yana jin nishaɗi yana ratsa zuciyarsa. Dan shi ba ya so auren nan ya rabu, ya fi so auren ya ɗore ko dan ya ga ya Rehaan zai yi da munanan kalaman da ya dinga faɗa mata. Nana Haleema. RDB3P63 Nana Haleema. Tun daga ƙasa Banisha take kiran Islaha amma bata amsa ba, harta shiga ɗakinta same ta a kwance jikinta yana rawa. Da sauri ta ƙarasa ta cire duvet ɗin da ta rufe kanta ta ce, "Sis lafiya?." Jin jikinta da zafi sosai, sai sauri ta koma ta faɗawa Mamy suka dawo tare. Mamy jin yadda jikinta ya yi zafi sosai sai ta tallafota ta kwantar da kanta a jikinta ta ce, "Islaha me yake damunki haka?." Islaha bata iya cewa komai ba sai hawaye kawai take yi takaici tana nuƙurƙusar zuciyarta, tana ji kamar ta ɗauki bindiga ta harbe kanta. Mamy ta kalli Banisha ta ce, "jeki ki samo min injection, na ji kanta yana ciwo sosai, ɗauko min." Kiddo da sauri ta koma babu jimawa ta dawo ta, ta haɗa mata allurar a sring. Throw vein Mamy ta yi mata tana shafa gashinta sannan ta ce, "sorry." Islaha ta yi shiru ta kwanta lamo a jikin Mamy tana jin zuciyarta tana bugawa, tana jin ina ma a jikin mahaifiyarta take a kwance haka, da ta yi kuka son ranta ko zata ji sauƙin abinda aka yi mata. A hankali zazzaɓin ya sauka ta fara gumi, Banisha ta ƙaro ac Mamy ta gyara mata kwanciya bacci ya ɗauke ta. Wayar Islaha ake ta kira, Banisha ta saka wayar a dnd saboda kar a tashe ta. Sai da suka tabbatar ta yi bacci sannan suka bar apartment ɗin. Sai bayan sallar azahar ta tashi, ta miƙe garau da ita bata jin ciwon kai da zazzaɓin, ta miƙe zaune tana jin bugun zuciya har lokacin. Screen ɗin wayarta ta taɓa ta ga lokacin sallah ya wuce, ta miƙe a sanyaye ya shiga banɗaki ta yi alwala ta tayar da sallah. Tana idarwa aka fara kiran sallar la'asar, ta sake yin sallah ta jingina da gado ta rufe ido abinda ya faru yana dawo mata a idanunta. "Wayyo Allah!" Ta faɗa tana rufe ido dan bata so ta tuna abinda ya faru ko kaɗan, ta zare hijjab ɗin jikinta cikin wani irin yanayi. Ta yi tsaki cike da takaici, ta dafe kai ta rasa tunanin da ya kamata ta yi. A hankali aka buɗe ƙofar aka shigo, bata kalli ƙofar ta ga waye ba dan ɗakin babu haske ko kaɗan, aka kunna hasken ɗakin sai ta juya ta ga Mamy ce riƙe da plate a hannunta. Ganin Mamy ce sai ta gyara zama ta ce, "Mamy." Mamy ta ƙaraso ta zauna ta ce, "Ya jikin ki?" Ta fafaɗa tana taɓa jikinta ta ji babu zafi ko kaɗan. Islaha ta ce, "na ji sauƙi Mamy, Ina yini." "Lafiya lau. Karɓi ki ci, zaki ji daɗi sosai." Islaha bata musu ta karɓi plate ɗin ta ci kaɗan sannan ta miƙe ta sha ruwa ta dawo ta zauna. Mamy cikin kulawa ta ce, "meye ya yi causing zazzaɓin nan daughter?." _Ɗanki ne ya kwance min towel Mamy._ Ta faɗa a zuciyarta tana jin haushin Rehaan mai matuƙar yawa, amma a bayyane sai ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce, "Stress ne kawai Mamy, shiyasa ban je aiki ba." Mamy ta dafa kanta tea ce, "Ayya sorry, In baki da lafiya ki dinga faɗawa Rehaan, zai dinga kula da ke, in ba ya nan ki faɗa min ko Janan. We are all health workrs, kin ji?." Ta ɗaga kai ta ce, "In sha Allah." "Allah ya ƙara lafiya. Daada tana neman ki, kwana biyu bata gan ki ba." "Zan je mu gaisa in anjima." "Yana da kyau" ta faɗa tana fita daga ɗakin. Islaha ta bi Mamy da kallo, Mamy tana burge ta sosai dan tana kula da ita sosai, tana nuna mata soyayyar irin wacce uwa take nunawa ƴarta, tana nuna mata ƙauna da soyayya a zahiri bata kallonta ta fuskar sirika ko kaɗan. Tana son Mamy, tana girmamata sosai, zata iya yin komai saboda ita saboda yadda take kula da lamarinta. Babu wata mace a duniya da ta taɓa kulawa da ita kamar yadda Mamy take yi mata, babu macen da take kallonta a matsayin ƴa sai Mamy kaɗai. Sai dai kuma bata son ɗanta ko kaɗan, bata ƙaunar Rehaan musamman wannan mummunan abun da ya aikata mata, sai yanzu take jin haushinsa, dah da take kukan bata sonsa ba komai take ji ba yanzu ne ta tabbatar bata ƙaunarsa ko kaɗan. Kamar wacce ta tuna wani abun sai ta jawo wayar ta cire ta daga dnd nan ta ga messages da kira babu adadi. Kiran Hamma, Chairman, Safeera da abokan aikinta. Chairman ta fara kira ta faɗa masa rashin lafiya ce ta hanata zuwa, daga nan ta ajjiye wayar ko Saheer ɗin bata kira ba. Miƙewa ta yi ta jawo drawer ta ɗauko takarda ta buɗe tana karantawa. A bayyane ta ce, "ai na ce masa in ya karya rule ɗaya daga ranar zamana ya ƙare, dole na je na same s...." Ta faɗa tana niyar fita sai kuma ta tsaya cak. A bayyane ta ce, "na je na ce masa meyasa ya cire min towel? Bayan ya gama ganar min jikina gabaɗaya, ko ina ya gani." Ta dafe kai cike da takaici, ta zauna tana ajjiye takardar zuciyarta tana suya saboda ɓacin rai da takaici. Rehaan bai shigo gidan ba sai bayan sallar i'sha, wajan Mamy ya shiga kai tsaye ya same ta a ɗaki a zaune tana amsa waya. Ya zauna a kusa da ita yana ɗora kansa a kafaɗarta ya yi luf yana jin bugun zuciyar, ta ɗora hannunta a kansa tana shafa gashinsa a hankali. Cikin harshen hindi take magana, hakan ya ba shi tabbacin da mutanen can india take waya. Idanusa ya lumshe bai ce komai ba, gabaɗaya yinin ranar ya yi sa a wani bahagon yanayi, bai san asalin abinda yake damunsa ba, abinda ya sani kawai ba ya jin daɗin jikinsa gabaɗaya, yana ji kamar an canja shi, ya zama kamar wanda bashi da jini a jikinsa gabaɗaya. Mamy ta kashe wayar ta kalle shi da kulawa ta ce, "Mr busy ina ka je yau?." Ya kalli Mamy yana miƙewa zaune ya ce, "Ina guest house." "Ka tafi can ka zauna, ka bar Islaha babu lafiya ko?." Nan take gabansa ya faɗi matuƙa, ya ɗago suka haɗa ido ta ce, "eh, ta yi fama da zazzaɓi sosai, Banisha ce ta shiga ta same ta a haka shine ta zo ta faɗa min, sai da na yi mata allura." Ya girgiza kai tana tuna yanayinta na ɗazu a idanunsa, ya runtse ido yana shafa fuskarsa sannan ya ce, "ban san bata da lafiya ba." Mamy ta riƙe fuskarsa tana kallonsa ta ce, "ba ka kula da lafiyar ta kenan ko?." Ya ɗan sauke ido ƙasa daga kallonta bai ce komai ba. Mamy ta ce, "na san halin ka Rehaan, ko housemaid ɗina ce bata da lafiya in ka ganta kana ganewa har ka bata magani, balle kuma matar ka!." _Matarka._ Ya maimaita a zuciyarsa jin yadda sunan ya shige sa sosai, har zuciyarsa ya ji shigar sunan da ƙarfi. Ya kalli Mamy amma ya kasa cewa komai, bakinsa ya ɗaure bai san me zai ce ba. Mamy ta yi murmushi tana kallonsa da kulawa ta ce, "me yake damun ka?." "Nima ban sani ba Mamy, ina jina kamar ba ni ba. Canjin babu daɗi, ina jin zuciyata tana bugawa.” "Sorry." Rehaan a hankali ya ce, "Zan yi tafiya Mamy." "Zuwa ina kuma, mr trip?." Ya yi murmushi ya ce, "Norway." "Allah ya kiyaye." Ya amsa da amin tare da yin shiru kafin Mamy ta ce, “ka je ka dubata." Ya ɗaga kai ya miƙe ya fita. Yana fita daga apartment ɗin Mamy ya hango ta daga can ƙarshen gidan ya hangota tana tahowa a hankali, ya tsaya yana kallon yadda take tafiya mai ɗaukar hankali, iska tana kaɗa hijjab ɗin jikinta, kanta a sunkuye tana tahowa daga ɓangaren Daada. Yadda ya ganta a ɗazu a haka yake ganin image ɗinta tana tahowa, ya runtse idanunsa ya ce, "hasbunahallah!!" Ya faɗa cikin wani mai wahalar fassarawa, bai jira ta ƙaraso ba ya shiga apartment ɗinsa, ya hau sama tun kafin ta ƙaraso. A falo ta same shi a zaune kamar bai san da zuwanta ba. Wata irin kunya da baƙin ciki suka mamaye mata zuciya, sai take ganin kamar a tsirara yake kallon ta. Idanunta suka ciko da hawayen baƙin ciki, babu namijin da ya taɓa ganinta a irin wannan yanayin sai shi, ko Salman ɗin ta san bai ga jikinta ba, lokacin da ta gan shi ta saka towel. Inda ace mijinta ne na gaske babu abinda zai dame ta, duk da zata ji kunya amma daga lokacin abin zai wuce. Amma Rehaan ne, mijinta na yarjejeniya. Tana so ta yi masa warning akan hakan amma ta kasa, bakin ta ya ɗaure ya yi nauyi sosai, kunya mai cike da takaici ta lulluɓe mata jiki gabaɗaya. Ta ɗauke ido daga kansa, tana ji kamar ta je ta rufe sa da duka ta ko wanne ɓangare, a hankali ta ɗaga ƙafa da niyar barin wajan. "Mamy ta ce ba ki da lafiya, i hope you are feeling well?." Abinda ya faɗa ya dakatar da ita daga barin wajan, ta kalle sa suka haɗa ido, ta yi saurin ɗauke kanta hawayen takaici yana sakko mata. Ta goge cikin sanyin murya ta ce, "abinda ka yi min Allah yana kallon ka, a zamana da kai bamu rubuta haka ba, bamu ce zaka yi min duk abinda ka ga dama ba...." Ta faɗa tana sake share hawayenta. Ta kuma kallonsa ta ce, "kana ta breaking conditions ɗinmu, ina ƙyale ka ne ba dan ka fi ƙarfina ba, sai dan ina so komai ya tafi cikin tsari. Na ga abin na ka is too much, zan ɗauki matakin da nake ganin ya dace da mu" ta faɗa tana shiga ɗaki ta bar sa yana kallon inda ta bari. _Abinda ka yi min Allah yana kallon ka._ Kalamanta suka sake dawowa cikin kunensa, ya sake kallon inda ta bari yana mamakin abinda ta ce. Ya buɗe baki ya ce, "Me ta ke nufi, ko ta manta ni mijinta ne?" Ya tambayi kansa yana kallon ƙofar ɗakin da ta shiga, sai kuma girgiza kai kawai ya lumshe ido kafin ya tashi ya shiga ɗaki. (Sai yanzu ka san kai mijinta ne kenan?😏).      ** Muslim ya kalli Ummi ya ce, "kin gani, a cikin daren nan zan aikata komai, so nake gobe duniya ta mamaye da magana akan Islaha." Ummi ta kalli abinda yake nuna mata ta ce, "Amma kana ganin iya wannan abun zai jawo mata baƙin jinin da mu ke da buƙata?." "A guje ma kuwa. Ƴan arewa ne fa, mu a ko yaushe mun fi mayar da hankali akan ya shafi rayuwar mutum akan rayuwar da mu ke ciki a najeriya. Ba mu damu da matsalolin da suke addabarmu ba, mun fi mayar da hankali akan matsalolin wasu. Ke kin san yadda irin waɗannan videon suke zaga duniya? Cikin minti ɗaya za ki ga yadda kowa zai gani, zaki likes da comments, zaki ga yadda bloggers za su dinga reposting. Ko mutum dubu aka ce an kashe a najeriya, baza su yi magana a kai kamar yadda zasu yi magana akan Islaha ba. Ki zuba idanu zaki ga abinda zan jawo mata a goben nan." "Shikenan Muslim, Allah ya kaimu." "Bani wayar ki, zuwa anjima zan aiko miki da ita, yanzu da ita zan yi amafani." Ta ɗaga kai ta ce, "Shikenan, gata nan." "Da sauri haka? Ba ki tambaye ni dalili ba kawai kin ce gata nan?." Ta yi dariya ta ce, "Haba Muslim! Ni indai akan karya Islaha ne ko kaina ka ce na ara maka zuwa gobe zan bayar, indai zan samu ahinda nake so ." Ya bita da kallon ƙasa ido ya ce, "Da gaske ki ke?." Ta ɗan yi dariya tana buɗe motar ta ce, "ina jiranka, ina so gobe duniya ta harsgite akan tsanar Islsɓaha, kowa ya fita daga sabgarta, ya zama ta koma kamar mujiya saboda baƙin jini." Ya gyara zamansa ya ce, "in na tabbatar da hakan meye tukuwici na?." Ta kalle sa ta ce, "duk abinda ka ke so, shi zan ba ka." "Har ke in na ce ina so, za ki bani?." "Ka tabbatar komai ya tafi daidai, sannan ka dawo mu yi magana." Ya yi dariya ya ce, "An gama Hajiyata." Ta fita daga motar shi kuma ya fara tsara abinda zai yi dan ganin bayan Islaha......... Nana Haleema. RDB3P64 Nana Haleema. Yadda Chairman ya takura mata da waya ya saka ta fita da wuri, ko abinci bata ci ba ta tafi wajan aiki. Lawal yana ajiiyeta ta shiga ciki kamar ko yaushe, tunda ta shiga ta ga ana kallonta ana magana ƙasa ƙasa, bata damu ba ta wuce ciki ta zauna a desex ɗinta bata cewa kowa komai ba. Sai kuma ta miƙe ta nufi wajan Chairman ta same shi baya nan, Program ɗinta ta gabatar sannan ta fito ta koma wajan zamanta ta zauna. A lokacin Safeera ta shigo, Islaha ta kalle ta ta ɗauke kai ta ce, "Tun ɗazu nake jiran zuwan ki, yaushe za a kawo lefen?." Safeera fuskar ta babu walwala ta ce, "Islaha!." Islaha ta kalle ta ta ce, "ya aka yi?." Safeera ta yi shiru sannan ta ce, "ba ki ga abinda yake faruwa a social media ba?." Islaha ta mayar da hankalinta kan Safeera ganin fuskar ta cikin damuwa harda alamun kuka sai ta ce, "ban gani ba, me ya faru?." Safeera ta sake jan numfashi ta ce, "ki duba za ki gani." Islsha ta jawo wayarta ta kunna data, notification suna ta zuwa bata tsaya dubawa ba ta shiga tiktok. Scrooling take yi bata ga komai ba, ta kalli Safeera ta ce, "ni ban ga komai ba, meye yak....." maganar ta maƙale da ta sake kallon wayar ganin abinda ya firgita mata tunani. Gabanta ya faɗi lokaci ɗaya, ta miƙe tsaye tana kallon abinda yake jikin wayar jikinta yana rawa. Sai kuma ta kalli Safeera ta ce, "Safeera meye wannan?." Safeera ta ce, "nima haka na gani, kuma kowa ya gani a cikin gidan nan, haka duniya ma ta gani." Hannunta yana rawa, muryarta tana rawa idanunta sun firfito waje ta ce, "Safeera meye haka? Kaina nake gani babu kayana a jikina fa, ni ce a kwance da wani fa! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Safeera me hakan yake nufi?." Safeera ta riƙeta ta ce, "Zauna." Ta fizge hannunta ta ce, "kamar ya na zauna! Safeera ki faɗa min meye wannan? Ki faɗa min ni ce da gaske?."      "In ke ce, in ma ke bace wannan ke ya dama ba mu ba, rayuwarki ki ka yaɗa a duniya ba rayuwar mu ba!." A tare suka kalli wanda ya shigo suka ga Chairman ne da Yayansa, wanda ya kasance mai gidan tv gabaɗaya. Mai gidan tv ya kalli Islaha ya ce, "Muna yabon ki a ko yaushe, ashe kema yar iska ce, bakya son cigabanmu, kuma bakya son cigaban gidan tv nan. Wacce irin ƙauna ce ba mu nuna miki ba? Wacce irin ɗaukaka ce ba ki samu a gidan nan ba?. Amma ashe cin amanarmu ki ke yi, kina ɗaukar sirrinmu da mu ke yi tare da ke kina kaiwa wasu gidajen da a ba ki kuɗi. Kin ba mu mamaki wallahi, ban yi tunanin haka daga wajanki ba." Cikin rashin fahinta da kiɗima da tashin hankali Islaha ta ce, "Me na yi?." "Bayan hotunan ki na iskancin da ki ke aikatawa sun fito duniya, kowa ya san wacece ke, wannan bai dame ni ba saboda rayuwar ki ce, ko me za ki aikata ke ya shafa bani ba. Abinda yake gabana cin amanar da ki ka yi mana, ina so ki san na samu labarin waɗanda ki ke kaiwa sirrin mu, duk abinda abu da ya faru ko zai faru ke ki ke zuwa ki faɗa musu. Duk ɗaukakar da fuskarki take da shi a duniya, duk son da ake yi miki a ƙarƙashin gidan nan ni bazan zauna da munafuka ba...." Chairman ya katse sa ya ce, "Yaya amma...." Ya dakatar da shi ya ce, "Wallahi sai ta bar aikin nan, ban ga amfanin zama da munafuki ba, da zama tare da munafuki gwara zama da ɓarawo. Da kanka ka ji saƙon da ta aika ta ke cewa burinta ta ga faɗuwar gidan nan, meye ribar zama da ita?. Ai ba ita kaɗai ce wacce ta iya aiki ba, suna nan da yawa a duniya." Ya kalli Islaha da ta ƙame ƙam ta kasa motsawa sai juya ido take yi ya ce, "daga yau babu ke babu aiki a nan, na sallame ki, ki je ki fara yiwa sauran gidajen talabijin ɗin da ki ke kaiwa sirrin mu aiki, ni kam bani da buƙatar ki a nan. Sannan abinda ki ka aikata kin cuci kan ki, duniya gabaɗaya akan ki kaɗai ta ke magana, ana yi miki tofin Allah ya tsine!" Yana gama faɗa ya futa daga office ɗin. Chairman ya kalli Islaha ya ce, "ki yi haƙuri, ina zuwa" ya faɗa yana ficewa da sauri. Islaha ta kalli Safeera cikin sanyin jiki ta ce, "Me na yi, Safeera me na aikata?." Safeera ta riƙe tana hawaye ta ce, "ki zo mu bar nan, zaman mu a nan ba shi da amfani." Wayar Islaha ce ta fara ƙara Safeera ta kalla ta ga Saheer ne, ta ɗauka ya ce, "Islaha me yake faruwa ne haka, waɗanne hotuna ne suke yawo a duniya?." Safeera ta ce, "Safeera ce Hamma." "Safeera ina Islaha take? Me ya faru?." "Wallahi ba musani ba, kawai mun wayi gari da waɗannan abubuwan. Yanzu mai gidan nan ya fita, yana ta faɗa wai tana kwashe sirrinsu ta kai gidan wata tv. Yanzu haka ya ce ta bar masa nan ya daina aiki da ita." "Subahanallahi! Safeera ina Islahan ta ke?." "Gata nan, bata cikin yanayin da zata iya magana shiyasa na ɗauka." "Kina ji, ku jira ni gani nan zan zo na ɗauke ku" ya faɗa yana yanke wayar. Safeera ta saka mata wayarta a jaka ta ɗauki handbag ɗin ta ce, "ki tashi mu tafi, zaman mu a nan ba shi da wani amfani." Islaha ta kasa cewa komai, ko hawayen ma ta kasa yi gabaɗaya. Safeera ta riƙe hannunta suka miƙe tsaye, suka fito compound ɗin gidan kowa yana kallon ta. Handbag ɗinta da take hannun Safeera ta saka hannu a ciki ta ɗauko wayarta, ta shiga media tana duba abubuwan da ake faɗa a kanta. Salati kawai take yi, ganin yadda hotunan tsaraicinta muraran suke yawo a duniya, ga kalamai masu muni da ake yi aka iyayenta, ana cewa daman cikin shege aka yi aka haife ta. Ƙafafunta suka fara rawa, ganin irin munanan kalaman da ake yi a kanta. Ta zube a wajan, ta cillar da wayar ta daki bango ta faɗi a ƙasa, sai a lokacin ta samu damar sakin kuka mai matuƙar ƙarfi. Safeera tana kuka ta bi bayanta suka durƙushe a tare ta riƙe ta ta ce, "Ki yi haƙuri Islaha, ki daina kuka, ki tashi mu tafi kowa kallon mu ya ke yi." Jikinta yana rawa saboda kuka, ta kasa magana sai kuka mai sauti da yake amsa kuwa a wajen, Safera ta riƙe ta sosai tana kuka itama, dan bata da abinda zata ce ba. Islaha kasa cewa komai, kuka take yi mai matuƙar ƙarfi tana ji zuciyarta tana bugawa da gudu. "Safeera da gaske ni ce a hotunan nan, da gaske cikin shege aka yi aka haife ni, da gaske ni ce ko?." Abinda take maimaitawa kenan tana kuka, Safeera tana ta ya ta kuka tana cewa, "ƙarya ne, ba ke bace, AI ne ya haɗa komai, don Allah ki daina kuka." Bata ce komai ba numfashinta da yake fizga da ƙarfi, ta kasa magana saboda tashin hankali. A lokacin Saheer da Sadik suka ƙaraso wajan, ganin yanayin da take ciki tana kuka cikin fiyar hayyaci ya saka hankalin Saheer ya tashi, ya tsuguna a gabanta ya ce, "Islaha ki daina kuka, ki yi haƙuri mu je." Jin maganarsa a kusa da ita sai ta zabura kamar mai taɓin hankali ta kalle sa ta ce, "Hamma ni ce ko? Kaima ka ga hotunan, da gaske ni ɗin ce?." Ya girgiza mata kai ya ce, "ki daina kuka ki zo mu tafi, taso" ya faɗa yana miƙewa tsaye. Safeera ta ɗago Islaha tana riƙe da ita ta kalli Saheer ta ce, "ga wayar ta can ta buga da ƙasa, ka riƙe mata." Ya ɗauki wayar ya riƙe, a lokacin ɗaya daga cikin ma'aikatan ya ƙaraso inda suke ya ce, "Gaskiya Islaha kin ɓata wayon ki, ban yi tunanin haka ki ke ba, ban taɓa zaton haka halin ki yake ba. A haka kamar mutuniyar kirki, ashe ke ɗin ma ƴar iska ce lamba ɗaya. Haba! Daman kwana biyu muna ta ganin canji a tare dake, ga iphone 17 a hannunki, ga mota daga wannan sai wannan, yau a sauke ki a fara, gobe a baƙa. Ashe da walakin goro a miya, ashe ban gishiri in ba ka manda ku je yi, tunda ga shi har hotunan ki sun fito." Hawaye ya ziraro daga idanunta, Saheer ya juya a fusace zai yi magana ta ce, "mu je hamma." Ya yi shiru suka shiga mota suka tafi.         "Mama! Mama!!." Sameer ya faɗa yana ƙwala maya kira da ƙarfi, dan ta ji a duk inda take. Mama ta fito daga banɗaki tace, "meye ka ke kirana haka kamar kana bina bashi?." Ya nuna mata wayar ya ce, "kalli ki ga, wannan ba yarinyar da take tare da Rehaan ba ce?." Mama ta karɓa tana dubawa sannamta wara ido ta ce, "itace mana, wannan Islaha ce. Mun shiga uku, yarinyar nan daman haka take?." Sameer ya ce, "gashi kuwa kin gani. Ɗaya daga cikin abokan iskancinta ne ya yi mata hotuna da video ya yaɗa a duniya. Kalli wannan, tare suke a kwnace fa" ya faɗa tana nuna mata wani. Mama ta kawar da kai ta ce, "ƙazantar ta yi muni, bazan iya gani ba." "Gaskiya bata da kunya, iskancin na ta mai lasisi ne. Dan kin san in dai video ko hotuna suka fara fita, tabbacin iskancin lamba ɗaya ne." Mama ta girgiza kai ta ce, "ai ni daman na san haka yarinyar take, an bani labarinta kaf tun kafin ta zo nan, har ƙasashen waje ake fita da ita a biyata. Ƙwanƙwararriyar ƴar iska ce fa, duk buɗewar idon Rehaan ta fisa wallahi." "Ta zubar mana da mutunci dai, duk da ba a san sirikar gidan nan bace, amma mu ai mun sani. Ko banza mun kalli banza, mun fara ganin babban sirrin Rehaan, dan gaskiya tana da gashi Mama" ya faɗa yana fita daga ɗakin. Mama ta yi hanzarin ɗaukar waya ta kira Abba, yana ɗauka ta ce, "ka fita ne?." Amsar da ya bata ya saka ta kashe wayar ta skaa hijjab ta fita. Tana shiga ɓangarensa ta fashe da kuka, Abba ya ɗago ya kalle ta cikin mamaki ya ce, "Saddiƙa lafiya?." Mama tana goge hawaye ta ce, "wani mummunan abu ne yake faruwa." "Wanne irin abu ne wannan da zai saka ki kuka a safiyar nan?." Mama ta goge hawayenta, ta yi shiru bata ce komai ba. Abba ya ce, "Ki faɗa min meye, kin bar cikin tunani da faɗuwar gaba." Mama ta basa wayarta ta ce, "kalli ka ga." Abba ya karɓa yana gani, sai ya kalle ta ya sake kallon wayar sanann ya ce, "wannan ba Islaha bace, matar Rehaan?." "Itace wallahi." "Subahanallah! Meye hakan, hotunanta da maza kala-kala nake gani fa?." "Ita ɗin ce wallahi. Yarinyar nan ashe haka take, sai yanzu nake jin asalin labarinta, har ƙasar waje ta je tana yawon iskanci. Na samu labarin har blue film an biyata ta yi, babu abinda bata aikata a duniya ba." Abba ya ajjiye wayar cikin faɗuwar gaba ya ce, "da gaske ita ɗin ce?." "Itace wallahi, an tabbatar min da zata iya aikata fiye da haka, yarinyar da ta ɗauki blue film meye baza ta yi ba!. Lokacin da ka karɓi auren ta baka yi bincike yadda ya kamata ba, dan wallahi bata dace da Rehaan ba kwata-kwata." Abba ya yi shiru sannan ya ce, "Ikon Allah! Anya itace kuwa? Kin san yanzu zamanin haɗa hotuna mu ke ciki.” “tunda ka ji na rantse ka yarda kawai, wallahi itace.” Wannan wanne irin zubarwa da kai mutunci ne?." "Da naka mutuncin ma, tunda sirikar gidan nan ce. Allah na gode maka da ba a san matar Rehaan bace, wannan taɓargazar ai sai ta saka Rehaan ya samu matsala da kasuwancinsa." Abba ya ɗan yi shiru yana nazarin abun cikin wani irin yanayi mara daɗi, sai kuma ya ɗauki waya ya kira Rehaan amma bai same shi ba. Abba ya ce, "in dai haka ne ban ga amfanin zama da ita ba, wanne irin tozarci da iskanci ne wannan? Hotunan tsaraici tare da wasu mazan a duniya, kuma a gidana?. Bazan ɗauka ba wallahi, bara na je na samu Daada, dole ta bar gidan nan tunda dmana ba a san da auren ba, kuma daman ba ƙaunar ta yake yi ba" ya faɗa tana miƙewa ya fita Mama ta bi bayansa tana murnar haƙarta ta cimma ruwa. Nana Haleema. RDB3P65 Nana Haleema.  Islaha tunda suka tafi ta ke kuka, kuka take yi mai taɓa zuciya duk sun yi shiru suna jinta. Saheer ya juyo ya kalle ta ya ce, "Islaha don girman Allah ki daina wannan kukan." Bata daina ba har zuka je gidansu Saheer. Da yake ba a nutse ta ke ba tare suka shiga har falon Baffa da ba ya nan. Saheer ya ɗauko mata ruwa ya miƙa mata ya ce, "ki sha ruwa." Kai take juyawa kawai amma bata iya magana, numfashinta ya fara sarƙe ta saboda takura kanta da ta yi. Sadik cikin sanyin jiki  ya ce, "waye ya fitar da asalin hotunann nan? Wanne account ne ya fara posting?." Safeera da ta ke riƙe da Islaha ta ce, "babu wanda ya sani, kawai an wayi gari sun baza duniya, tun ƙarfe huɗu na safe aka saka su har yanzu ba a daina ba." Sadik ya sake kallon hotunan sannan ya kalli Safeera ya ce, "wannan hotunan haɗawa aka yi, ba Islaha bace, amma kuma bai yi kama da AI ba ko kaɗan, ya yi kama da real hoto na haƙiƙa." Saheer ya miƙe ya ce, "duk wanda yake da hannu akan yi mata haka wallahi sai na yi ƙararsa a human right, sai an ƙwatar mata haƙƙinta."     "Haƙƙinta ɗin ubanka za a ƙwatar mata? Ka ga yarinya tsirara muraran ka ce wai za ka ƙwatar mata haƙƙinta?. Kai yanzu sai an faɗa maka ta cikin hoto nan Islaha ce? Ko kana so ka ce min  arhar jikin bata bai zo inda ka ke ba balle ka banbance itace ko ba ita bace haɗawa aka yi?." "Ni daman nasan ya san za a rina, ko ba a faɗa ba an san Islaha tantiryar ƴar iskar yarinya ce, kuma bana shakka cikin shege iyayenta suka yi suka haife ta, in ba shege ba babu mai aikata abinda ta aikata. Shi kansa auren da aka ce ta yi ban yarda da shi ba wallahi, tana can suna sheƙe ayarsu da sunan aure, amma waye zai ɗauki wannan ragowar ƙartin a matsayin matar aure? Sai dai zaman bariki!!" Mama ta faɗa tana shigowa tana kallon su. Saheer zai yi magana ta dakatar da shi ta ce, "na hana ka shiga sabgar yarinyar nan ka ƙi ji, ko da yake ba laifin ka bane, laifinta ne. Ita da ke da aure tana bibiyar ka dan ance tana kwana da wasu mazan ba abin ƙin yarda bane, kaima Allah ne ya kare ka da yanzu kana cikin lissafi, wataƙila da hotonka yana nan yana yawo. Ni Islaha ko me akace min ta aikata da gudu zan amince, tunda ni na san yar iska ce!." Islaha ta miƙe da gudu ta fita daga falon, Safeera ta rufa mata baya a guje suka fita. Saheer zai bita Mama ta ce, "kar ka sake ka fita, ka dawo ka zauna, su dai su je, amma kai ban aike ka ba." Ya kalli Mama ya ce, "Don Allah Mama..." Mama ta ce, "wallahi baza ka je ba, ka zauna a nan." Ya zauna kamar ya kurma ihu, abu ya haɗar masa goma da ashirin. Mama ta zauna ta ce, "aje can a ƙarata, ɗana dai wallahi ya fi ƙarfin ki." Islaha tana fita ta samu napep kawai ta shiga, Safeera daƙyar ta iya shiga itama ba tare da ta san inda zasu je ba. Kuka Islaha take yi sosai, cikin tashin hankali Safeera ta ce, "don Allah ki daina wannan kukan, ki nutsu mu gano daga ina matsalar take." Bata ce komai ba sai kuka, ta ɗago ta jingina da ƙarfin napep ɗin tana kuka. Mai napep ɗin ya kalle ta ta mirror, ya kalli wayarsa sannan ya ce, "wannan ai itace wacce take trending yau ko? Ɗazu na gama kallon video ta, gaskiya mun ga banza." Islaha ta nufi fita ta window machine ɗin yana tafiya, Safeera ta dakatar da ita cikin ɗaga murya ta ce, "ki nutsu Islaha, ki tsaya mu warware wannan matsalar, ki daina wannan abubuwan don Allah!!." Hanata motsi Safeera ta yi, ta riƙe hannunta da ƙarfi yadda baza ta motsa ba, sai juya kanta take yi wanda ya yi mata nauyi ga ciwo. A farkon estate ɗin napep ɗin ya tsaya, ta fita da sauri Safeera ta ba shi kuɗin ta bi bayanta. Babu wanda ya yi musu magana, ko takalmin babu a ƙafar Islaha ta shiga gidan a guje. Rehaan yana zaune a parlour ya ke ganin abinda ta faru, gabaɗaya sai ya rasa nutsuwarsa ya rasa abinda zai yi, ya rasa me zai yi dan komai ya tsaya masa cak kamar wanda aka tsayarwa da gudun jini. Sai daga baya ya ɗauki waya ya kira Jazy yana ɗauka ya ce, "me yake faruwa ne haka?." Jazy ya ce, "na ga hotuna da video Islaha yana ta yawo a duniya, Shi ka ke nufi?." Cikin kasala da damuwa ya ce, "Na faɗa maka yarinyar nan bata dace dani ba, ni na san halinta tun a Jeddah. Ka kalli abinda yake faruwa a yanzu." "Ina zuwa, yanzu zan kawowa Mamy saƙo, zan shigo" ya faɗa yana yanke wayar. Rehaan ya sake kallon video yana runtse idanunsa, wani irin abu yake ji a ƙirjinsa wanda dole sai da ya kife wayar tana tattauna lips ɗinsa. A lokacin Islaha ta faɗo kamar an cillo ta, kawai ta zube a corridor da yake a farko kafin ka shigo ta haɗa kai da guiwa tana kuka mai sauti da taɓa zuciya. Safeera ta shigo ta zauna a kusa da ita tana hawaye ta ce, "Islaha wannan kukan ba mafita zai bamu ba, ya kamata ki nutsu." "Safeera ni ce, jikina ne!...." Sai kuma ta dakata jikinta yana karkarwa ta ce, "Ni na san ni ce, ni na san jikina ne.....!" Ta ɗago tana kallon Safeera ta ce, "amma kin san ni ba ƴar iska bace ba ko? In kowa bai yarda dani ba ke za ki yarda Safeera...." Ta sake dakatawa da magana, tana jan numfashi ta ce, "Ki faɗawa duniya ni ba ƴar iska bace, ban san ya aka yi haka ya faru ba." Safeera tana kuka ta ce, "Ba ke bace, wallahi bake bace Islaha." "ki tashe ni daga baccin nan Safeera, ki saka na farka kafin na mutu a cikinsa." "Baza ki mutu ba Islaha, ki daina faɗa kin ji" ta faɗa tana kuka itama mai taɓa zuciya. Numfashin Islaha ya fara sarƙewa, saboda wajan babu a.c ga zafi ga shi tana kuka ga damuwa mai tsanani. Hankalin Safeera ya sake tashi ta ce, "Islaha ki nutsu don Allah, kar ki samu attack, ki dawo hankalinki, don Allah ki daina kuka." Islaha bata jin abinda Safeera take cewa, numfashin ya fara tafiya inda bata yi zato ba, saboda yanayin ya gigita ta sosai. Rehaan yana zaune yana kallonsu, yana ji yadda ta ke magana tana kuka, hakan shi ya zuba mata ido kawai yana yi kamar ana yi masa wanka da ruwa mai sanyi, tsigar jikinsa tana tashi, gabaɗaya jikinsa ya gauraye ya yi sanyi sosai. Ganin yadda take yi alamun zata samu attack bai san ya miƙe ya ƙaraso inda take zaune ba, sai da ya ƙarasa sai kuma ya rasa me zai ce, kawai sai ya tsaya tana kallonta zuciyarsa tana bugawa. Safeera ta kalle sa ta ce, "Mr Rehaan Islaha!....." Cikin kuka ta ce, "ka taimaka mata kar ta mutu" ta faɗa tana hawaye. Ambaton mutuwa da Safeera ta yi ya saka ƙirjinsa bugawa da ƙarfi, ya kalli Islaha ya ga abaya ce a jikinta kuma na ta naɗe kanta da mayafi, kamar mai jin tsoro ya tsunguna a kusa da ita yana kallon yadda numfashinta yake ƙoƙarin fizgewa daga jikinta. Yadda fuskarta ta koma yake kallo, yana ji zuciyarsa tana rawa sosai, ɗaci da zafi yana mamaye masa ko ina har kan harshensa. Ya haɗɗiye yawu apple adam ɗinsa yana up and down, ya miƙa hannunsa ya zare pin ɗin mayafinta ya warware sa ya buɗe. Rehaan ya kalli Safeera ya ce, "ina inhaler ɗinta?." Safeera tana kuka ta ce, "ba a san inda take ba." Rehaan ya sake kallon Islaha yana ganin yadda hawaye ya ke zarya akan fuskarta. Ya haɗɗiye abu mai ɗaci, yana jin zubar hawayenta a cikin zuciyarsa, yana ji jikinsa yana karkarwa saboda kukan da take yi, sai ya matsa kusa da ita sosai, ya miƙa hannunsa ya kwance gashin kanta. Ya kalli kalli ƙirjinta, ya ɓalle buttons biyu a gaban abayar jikinta. Ya waiwayo ya kalli Safeera da take hawayw ya ce, "kunna switch." Ta miƙe ta kunna ac, shi kuma ya zuba mata ido yana kallon ta, gashinta ya rufe mata fuska ya janye mata gashin fuskarta ta fito sosai. Ya kalli Safeera ya ce, "ki bata fresh air." Ya faɗa yana miƙewa ya koma parlour, ya ɗauko mata ruwa ya dawo ya tsuguna a kusa da ita, Safeera tana gefe tana yi mata firfita da mayafinta, shi kuma ya saka mata robar ruwan a bakinta. Ta haɗe haƙoranta taƙi ba da damar da zai saka mata ruwan, cikin raunin murya ya ce, "Take it!." Ta buɗe bakinta ya bata ruwan ta sha, ya rufe ya ajjiye yana kallonta bai motsa ba. A hankali ta nutsu, ta kwanta a ƙasa tana jan numfashi mai ƙarfi, hawaye yana cigaba da sauka daga idanunta har lokacin basu tsaya. Jazy yana tsaye yana kallon komai ba tare da sun san ya shigo ba, dan Islaha ta ba shi tausayi matuƙa, yana ji kamar shima ya yi mata kuka saboda tausayu. Sai kuma ta buɗe ido suka haɗa ido da Rehaan da ya kafa mata idanu yana kallonta ya kasa janye idanunsa daga kanta. Ganin sun haɗa ido sai ya sake ɗaukar ruwan miƙa mata alamun ta kuma sha, sai ta miƙe zaune tana riƙe kanta saboda ciwo. Ta karɓi ruwan ta sha, ta jingina da bango kanta yana sarawa sosai, zuciyarta tana bugawa, tana ji kamar ba a duniya take ba. Shiru ya ratsa wajen, babu mai magana a cikinsu sai numfashi da take yi a hankali a hankali. "Salama alaikum ina Ishlaya? Abinda zata yi mana kenan tsakani da Allah? Ina yabonta sallag sai na samu ta da kasa alwala?." Daada ta faɗa tana shigowa wajan, Mamy da Mama da Abba suna bayanta. Duk suka bita da kallo, kana ganinta ka san bata da lafiya kuma bata cikin hayyacinta. Daada ta ce, "me nake gani haka a duniya, ƴar nan dama fuska biyu ce dake?." Islaha ta runtse idanunta, hawaye ya sake sakkosa daga idanunta. Daada ta ce, "Duk soyayyar da na nuna miki ashe daman ke ba ta gari ba ce? Iskancin ki ya kai har a yi video da ke ana aikata alfasha? Ina kunyar fulanin da na gani a tare da ke har na yi ƙwaɗayin a auro ki?." Ta kalli Rehaan da har lokacin yana tsugune yana kallon Islaha, yana ji kamar zuciyarsa kalaman Daada suke shiga. Daada ta ce, "daman shi ba so yake yi ba, ƙwadayin tarbiyya ya saka na ɗauko ki, ashe ba ki samu tarbiyyar ba ko kaɗan, kallon kitse nake yiwa rogo, tarbiyyar ta ki a baki take bata kai zuciya ba. Bana son wanda bai girmama kansa ba, bana son wanda ya watsar da alkunya da ɗabi’un fulani. Dan haka ni bazan zauna da ke a matsayin matar jikana ba, bazan iya cigaba da zama dake ana zuba hotunanki tsiarara a duniya ba, ina ni ina ke Ishlaya? Kin fi ƙarfina. Gwara kawai a rabu lafiya, tunda daman ba so yake yi ba." Mama ta ce, "gwara haka, zubar da ƙimar gidan nan ne ace wannan tana cikinsa ko da a matsayin mai aiki ne balle kuma matar Rehaan. Gwara a yi ta ta ƙare, na ji daɗi da ya kasance babu wanda ya san da auren nan a waje, da mun shiga uku." Mamy da Abba dai basu ce komai ba sai Jazy ne ya ce, "Daada wannan hotunan haɗasu aka yi, ba ita bace." Daada ta juyo a fusace ta ce, "na saka ka a ciki ne? Uban ƴan iyayi, magana nake yi akan jikana da matarsa ba kai ba, ban saka ka a ciki ba. Kar na sake magana ka saka min baki, ban saka da kai ba balle na kwashe da kai. Auren nan dole a raba shi, bazai zauna da irin wannan matar a  cikin gidan nan ba." Daada ta kalli Abba ta ce, "Ashe da gaskiyar babar Salmanu, da take cewa zata lalata mata ɗa mu ke ganin ƙarya take yi, yanzu na yarda zata aikata." Sautin kukan Islaha ya saka kowa ya kalle ta, Islaha ta saka yatsunta ta toshe kunenta tana kuka jikinta yana karkarwa. Safeera itama kuka take yi ta ce, "ba halin Islaha bane, kuma wallahi ba ita bace." Daada zata kuma magana Rehana ya miƙe tsaye ya kalli Daada, fuskarsa ta canja cikin yanayin da ba su taɓa gani ba ya ce, "Daada ku je waje, don Allah!." Daada ta kalle shi tana harararsa ta ce, "bazan tafi ba, sai an warware auren nan." Ya lumshe ido yana jin sautin kukan Islaha yana ratsa jininsa, sai ya rikice ya rasa me zai yi ya ce, "Daada don Allah ki je, zan yi komai da kaina." Daada ta ce, "ai daman duk mai kishin kansa bazai zauna da wannan ba, kai ɗin ne nake tantama a kanka, dan na san ba dukkan ka ne fulani ba, tsaf zaka ce zaka zauna da ita tunda ku ƴan ƙasashen waje ba kunya gare ku ba.” "Daada ki je!" Ya faɗa cikin wata irin murya mara sauti amma ami amo yana runtse ido da ƙarfi, dan ji yake yi kamar ana zuba masa ruwan zafi. Daada ta dinga binsa da kallo ganin canjin da bata taɓa gani ba ta ce, "Ka tabbatar za ka yi ɗin?." Ya ɗaga mata kai, sannan ta kalli Abba da Mama ta ce, "mu je mu tattauna akan maganar nan..." ta waiwayo ta kalli Rehaan ta ce, "kai kuma ka kawo mana takardar sakinta yanzun nan." Daga haka suka fita Daada tana mita. Suna fita Rehaan ya kalli Mamy da take kallonsa, ta yi masa nuni da Islaha da idanunta, ya kalli abinda ta nuna ya sake kallonta, ta sake yi masa alamar da shi ya fahimta sannan ta fita. Islaha ta ɗago ido tana kallonsa kamar yadda yake kallonta, hawaye yana zuba daga idanunta, ko buɗe idanunta bata iya yi, saboda nauyin da kanta ya yi. Idanunta ya yi luu kamar zai rufe saboda kuka, muryarta ta dashe bata fita yadda ya kamata ta ce, "Kowa bai yarda dani ba, nima ban yarda da kaina ba, kuma bani da kowa a duniya, Allah kaɗai nake da shi." Rehaan yanayin da yake ciki ya ta'azzara, jikinsa ya fara rawa yana daga tsaye. Ya kasa jure ganin tana kuka cikin fitar hayyaci, ya kasa riƙe kansa kamar yadda ya saba, ya ƙarasa inda ta ke zaune ya tsuguna a kusa da ita ya riƙe kafaɗunta, yana kallon idanunta bai ce komai ba. Slowly ya jawo hannunta ya kwantar da ita a ƙirjinsa, ya sanya hannayensa duka biyun ya zagaya dasu bayanta, ya yi tapping bayanta da sigar rarrrashi, ya kai bakinsa kunnenta ya ce, "Waye ya ce ba ki da kowa? Ba gani nan ba..." "Stop crying, i'm here for you." Islaha ta saki jikinta a jikinsa sosai, ta lumshe ido tana jin sautin bugun zuciyarsa a kunnenta, ta yi luf tana hawaye tana jin yadda yake tapping bayanta cikin rarrashi da nuna tsantsar kulawa a gare ta. Nana Haleema. RDB3P66 Nana Haleema. Islaha a yanayin da ta ke ciki na ƙunar zuciya da nauyin kai, bata san ta kwantar da kanta a jikinsa tana kuka ba, ta riƙe shi sosai tama zubar da hawaye. Rehaan ko gajiyar durƙusawar da ya yi bata damunsa, yana riƙe da ita ya ɗora haɓarsa a gashin kanta ya rufe ido ya yi shiru cikin wani irin yanayi. Sun jima a haka kafin ya ja numfashi sannan ya ɗago kanta, ya ɗora hannunsa akan fuskarta yana goge mata hawayen fuskarta yana kallon jajayen idanunta, ya girgiza mata kai ya ce, "ina tare da ke, babu wanda zai wulaƙanta ki ya zauna lafiya. Ki daina kuka" ya faɗa yana shafa kumatunta. Ita da shi ne kaɗai suka ji me yake faɗa, yadda yake yin maganar ko Jazy da Safeera baza su ji ba, suna dai kallon bakinsa yana motsawa amma ba jin sauti. Ya shafa gashin kanta, ya sake goge mata hawayenta ita kuma ta sunkuyar da kanta. Ya miƙe tsaye ya kalli Jazy da yake kallonsa, ya ƙarasa inda yake ya ce, "Jazy!..." "A saka DSS su yi aiki a kan case ɗin nan, ina so a nemo min main account ɗin da aka fara posting pictures ɗin, sannan a rubuta min sunayen duk wani blog da ya yi reposting. A yau nake so a yi binciken ba gobe ba, a yau nake so na san su waye suke da hannu a case ɗin, a yau nake so komai ya ƙare, bana son ɓata lokaci!." Yadda Rehaan yake maganar cikin ba da umarni ya saka Jazy ya buɗe ido ya ce, "Okay Sir! Za mu yi duk yadda ka ce, zamu tabbatar sun san wacce suka taɓa." Yanayin da Jazy ya amsa ya saka Ray ya yi tsaki, ya ɗauki waya ya kira ɗaya daga cikin DSS ɗin da ya sani. Safeera ta koma kusa da Islaha tana rarrashinya, Jazy dai yana tsaye yana kallon ikon Allah ganin Mr Rehaan an faɗa tarkon love, shi kuma ya saka waya a kunne yana magana cikin ba da umarni, kuma a ranar yake so a kama su, ba ya son ɓata lokaci. Jazy ya murmusa kawai bai ce masa komai ba ya kalli Islaha ya ce, "Miss ki daina kukan nan, in sha Allah duk wanda ya ke da hannu a aikata wannan abun zai zo hannu, tunda har Ogan ki ya shiga maganar ki ɗauka an gama." Islaha ta kallesa da jajayen idanunta da suka yi nauyi ta ce, "da gaske ni ce a jikin hoton?." "Ki daina kuka, kin ga kin samu attack bai kamata ki dawo da maganar ba. Safeera ki je da ita sama ta huta." Tana niyar ɗagata Mamy ta shigo falon ta ƙarasa inda islaha ta ce, "Sannu Daughter..." sai kuma ta kalli Rehaan ta ce, "Rehaan!." Ya kalle ita ta ce, "ina so ka saka a yi bincike akan wanda ya yi posting hotuna da videos ɗin nan, ni na san ba Islaha ba ce, haɗawa aka yi." Islaha jin muryar Mamy sai ta sake fashewa da kuka ta ce, "Mamy da gaske ni ce ko?." Mamy ta shafa kanta ta ce, "in ma ke ɗin ce duk wanda ya yaɗa dole ya shiga hannu, muna da ikon yin shari'a da shi akan hakan, balle ba ke ba ce. Ki daina ɗaga hankalin ki, babu abinda zai same ki. Ina tare da ke, Rehaan yana tare da ke, Jafar da ƙawarki duk muna tare da ke. In kaf gidan nan zasu juya miki baya, mu zamu riƙe ki hannu biyu, babu wanda zai wulaƙanta ki ya zauna lafiya, kuma babu wanda zai saka Rehaan ya sake ki matuƙar ina da rai. Waɗanda suka haɗa kuma zasu yi danasani, sai sun san wacece ke, sai sun san kina da gata, sai sun san sun taɓo wacce ta fi ƙarfinsu wallahi." Mamy ta sake kallon Rehaan da yake tsaye ta ce, "Ka yi abinda ya kamata, Jazy please, don Allah kar ku bar kowa a cikin case ɗin, ina so su san wacece Islaha a cikin garin Yola. Jafar ko cikin mahaifiyarsu suka koma, ina so a fito dasu a nuna musu wacece Islaha!." Jazy ya ɗaga kai ya ce, "In sha Allah Mamy." Mamy ta riƙe hannun Islaha ta ce, "Mu je apartment ɗina ki huta." Islaha ta miƙe a hankali tana jin jiri yana ɗaukarta. Mamy ta kalli Rehaan ta ce, "a samo mata reliver inhaler." Bai ce komai ba suka fita daga falon. A lokacin aka yiwa Rehaan waya, ya ɗauka ya ba da umarnin a shigo dasu inda yake. Ya koma ya zauna fuskarsa kwata-kwata babu walwala, kana kallonsa zaka san ba a hayyancinsa yake ba, ya haɗe rai kuma damuwa ta bayyana ƙarara akan fuskarsa. Shi dai Jazy bai ce komai ba yana daga tsaye yana kallon Oga Rehaan. Shams ne ya shigo shi da wasu mutane guda biyu, suka ƙaraso suka gaishesa ya ja numfashi bai ce komai ba. Sai daga baya ya ce, "Case ɗin da yake trending a social media a yanzu, ina buƙutar a kawo ƙarshensa a daren nan." Ɗaya daga cikin Officers ɗin ya ce, "wanne daga ciki." Ya kalle sa amma bai ce komai ba. Ganin ya yi shiru sai Officer ya ce, "akan abubuwa biyu ne, akwai na wata yarinya Islaha da aka tashi dashi yau, sannan...." Rehaan ya dakatar da shi yana sake haɗe rai ya ce, "Akansa nake magana. Ina buƙatar na san main account ɗin da ya fara fitar da pictures ɗin, sannan ina so a bani list ɗin sunayen duk wani blog da suka yi reposting video. A yau nake so case ɗin nan ya zo ƙarshe, bana so a ɗauki lokaci." Officer zai yi magana Rehaan ya dakatar dashi ya ce, "kar ka ce min bazai yu ba, kawai a yi." Officer ya yi murmushi ya ce, "wannan ƙaramin aiki ne, in sha Allah zuwa anjima zan yi maka bayanin komai." Rehaan bai ce komai ba ya ɗaga masa kai suka fita daga falon. Jazy kanzil bai ce ba yana daga tsaye yana kallon Rehaan da mamakinsa, mutumin da yake ce mata mai bin maza meye nasa na ɗaga hankali akan abinda ya same ta? Yana so ya yi masa magana amma ba ya so ya saka ya farka da shi a yanzu, shiyasa ya yi masa banza ya gama bidirinsa daga baya sai ya faɗa masa kuma ya tsokane sa. Daada tunda ta koma ɓangarenta take ta sallallami tana mita akan abinda Islaha ta aikata, Mama tana gefe tana zugata ta ce, "Ai mun yi gaggawa Daada, wannan yarinyar sai yanzu nake jin asalin wacece ita. Tantiriyar ƴar iska ce, bata jin magana ko kaɗan, har ƙasashen waje ake fita da ita ana biyan ta. Ai daga kallon waɗanan hotunan kin san ta saba da bin maza, waɗannan video irin na turawa samari su bata kuɗi ne, kin san ƴan matan yanzu jikinsu ne jarinsu." Daada ta ce, "ikon Allah! Ashe daman akuya ce da fatar kura, a haka kamar mai hankali har ina alfahari da ita ashe ƴar iska ce, haka kawai muna zaune lafiya na ɗauko baragurbi na sakata a cikin ahlina. Bazai yu ba, kira min mijinki yanzu nan, dole a san abinda za a yi, in zan zauna da yarinyar da duniya ta gama ganin jikinta? Wannan ai babban abin kunya ne a wajan da Rehaan ɗin babansa. Ba zai yu ba, kira sa yanzun nan a san abinda ya kamata ayi." Mama ta kira Abba amma bai ɗauka ba ta ce, "Bai ɗauka ba Daada, amma na san zuwa anjima zai kira ni." "Ai gwara ya kira ɗin, bazan bar hakan ta cigaba da faruwa ba. In aka ga baragurbi cire sa ake yi, in ba haka ba sai ya lalata maka sauran. Ina ni ina cigaba da zama da yarinyar nan? Ai har abada." A lokacin Abba ya kira wayar Mama sai ta miƙawa Daada tana sakawa a kunne ta ce, "Maza ka zo ina neman ka, sannan a kira kowa da kowa ina buƙatar ganinsa yanzun nan." Tana faɗa ta kashe wayar Mama tana ta girgiza kai, dan wallahi baza ta bar Islsha ta sarara a cikin gidan ba. Mamy da Islaha tunda suka koma apartment tana zaune kusa da Islaha ta kwantar da kanta a kafaɗarta, Islaha ta yi shiru tana jin ciwo a zuciyarta, rarrashin da Mamy take yi mata yana sakawa ta ji daɗi, tana jin daɗin samun Mamy a gefenta, ta zamar mata jigo mai share mata hawaye, ta zamar mata bangon da ta rasa a shekarun da ta yi a duniya, yanzu ne ta samu bangon ya tsaya har ta jingina tana kuka. A lokacin Abba ya kira wayar Mamy, tana ɗauka ya sanar da ita umarnin Daada. Mamy ta kalli Islaha da ta yi lamoo a jikinta ta ce, "bata da lafiya, baza ta iya fitowa zuwa zaman meeting ba." "Ya zama dole ta zo Nadira, saboda ita za a zauna." "okay" ta furta tana kashe wayar. Ta ɗago Islaha daga jikinta tana shafa fuskarta da ta kumbura sosai saboda kuka ta ce, "zamu je wajan Daada wai tana neman kowa, kuma kin san a kan ki za a haɗa meeting ɗin. Kar ki damu, babu abinda zai faru, ni da Rehaan muna bayanki, babu wanda zai yi miki wani abun a gidan nan. Saka mayafin ki mu je." Mamy ta kalli Safeera ta ce, "ki jira mu a nan." Safeera ta ɗaga kai tare da yin tagumi, Mamy ta riƙe hannun Islaha suka nufi ɓangaren Daada, suka shiga suka tarar da kowa yana nan su kaɗai ake jira. Suna ƙarasa zama akan carpet Daada ta ce, "Ni ban san haka Ishlaya take ba, da ban ɗauko ta na saka a cikin ahlin mu ba, na yi tunanin yarinyar kirki ce, ta gari wacce zata haifi yara na gari, ashe ita ɗin ta wuce tunanina a fannin tantiranci. Gaskiya bazan iya zama da ita a gidan nan, yarinyar da duniya ta gama ganin tsarsicinta ai ba abar so bace, kuma wannan ba ɗabi'ar fulani ba ce, ni kuma duk abinda ya saɓawa al'adarmu bana sonsa. Dan haka..." sai ta dakata tana kalle-kalle sannan ta ce, "ina yake?." Sai a lokacin Rehana ya shigo falon jikinsa a sanyaye, tun kafin ya zauna ta ce, "Kai Rehaan! Ka saki yarinyar nan yanzun nan, tunda daman ba sonta ka ke yi ba, ka sake ta kawai ka huta da auren da na baka. Kuma daman duniya bata san ka yi aure ba, da ta ɓata maka suna." Rehaan kalli Daada ya ɗauke idanunsa, ya kalli Mamy ya ga tana riƙe da hannun Islaha, ya kalli Islahan da kanta yake a ƙasa, ko ba a faɗa masa ba yasan kuka take yi, ya kalli Abba da yake kallonsa ya yi shiru bai ce komai ba. Abba ya ce, "Ba ka ji abinda aka ce bane? Ka aikata kawai." Rehaan ya cize bakinsa sannan ya ce, "ina bincike akan case ɗin, a bani lokaci na gama komai sai ya biyo baya." "Binciken me za ka yi? Ga zahiri kowa yana gani, yarinya a kwance da wani namijin da ba kai ba?. Ni daman na faɗa muku tunda ta zo gidan nan Salman ya canja ake ganin kamar ƙarya nake yi, ni da kaina na faɗa muku na ga abinda ban taɓa gani ba a tare da shi sai da ta zo gidan nan. Ni ban san Salman yana da lafiya irin ta ko wanne ɗa namiji ba sai da ta zo gidan nan, daga nan ya san rungume mace har yace yana sonta. In ba ƴar bariki ba wacece zata yi haka? Ni na fara zargin anya....." "Umma please!" Rehaan ya katse ta jin zata fasa masa zuciya da banzayen kalamanta, ya waiwayo suka haɗa ido da idanunsa da suka canja sannan ya ce, "na ce a bani lokaci, bana son wata magana kuma." Daada ta ce, "anƙi a ba ka lokacin, na ga dai ni na haɗa auren ko? To yanzu na ce a raba bani da buƙatarsa ko kaɗan a cikin gidan, dan wallahi bazan zauna da wannan abin a gidan nan ba, ka ji na ce wallahi." Rehaan ya kalli Islaha da kukan ta ya fara fitowa fili, ya kalli Mamy da ta yi shiru bata ce komai ba, sai ya girgiza bai ce komai ba. Daada zata yi magana suka ga ya ƙarasa shigowa falon gabaɗaya, ya ƙarasa inda Islaha ta ke ya miƙa mata hannunsa yana kallonta alamun ta riƙe nasa. Islaha shadow ɗinsa ta gani a kanta a tsaye, ta ɗago jiƙaƙƙun idanunta ta kalle sa, ta ga ita yake kallo ga hannu ya miƙa mata yana jira ta ta saka nata a cikin nasa ya riƙe. Ta kalli hannun da ya miƙo mata tana kallonsa, fari tas dashi sai wani bracelet da yake zagaye a tsintsiyar hannunsa. A hankali ta ɗora hannunta akan nasa, ya damƙe nataa cikin nasa sannan ya miƙar da ita tsaye, jiri ya ɗan ɗauke ta ya riƙe kafaɗunta sannan ya kalli Daada ya ce, "na ce a bani lokaci, zan yi abinda na ga ya dace" ya faɗa yana jan hannunta suka fara tafiya. Sai ya ji Umma ta ce, "Wallahi sai ta bar gidan nan, bazai yu ta lalata min yaro ina kallo ba. Yarinyar da bata ji kunya buɗe jiki anyi mata video ba, ai lalata mutum irinsu Salman bazai mata wahala ba, sai ta bar gidan nan ai ba gidansu bane." "Amma ni kin yarda gidanmu ne?" Ya tambaya yana kallon Umma. Ta yi shiru bata amsa ba ya ce, "indai nan gidanmu ne itama gidansu ne. Babu inda zata je sai na gama abinda na ce ina yi!. Matata ce, ban yi niyar rabuwa da ita ba, kuma bazan yi ba." Ya faɗa yana kallon Umma da mamaki ya daskarar da ita a wajen, bai sake kallonta ba ya ja hannun Islaha suka fita. Daada ta fara tafa hannaye ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! AbdulAziz, haka ɗan naka jinin indiyawa ya zama? Ina magana da shi zai ja hannun wannan yarinyar su fita, ni yake kallo yana cewa bazai yi abinda na ce ba a bashi lokaci?." Abba ya ce, "ki yi haƙuri, zan yi magana da shi. Ina zuwa" ya faɗa yana miƙewa ya fita Mamy ma ta fita. Umma ta kalli Daada ta ce, "Kar ki amince ta cigaba da zama Daada, na rantse da girman Allah na ga abinda ban taɓa gani ba a wajan Salman sai da yarinyar nan ta zo. Salman bai san ya ce ina son mace ba sai ita, har rungumar ta fa yake yi, in ba wanda aka koya ba ta ya Salman da yake da matsala zai yi haka?." Daada ta ce, "bar ni da shi, ni na haɗa auren kuma sai na raba shi." Nana Haleema. RDB3P67 Nana Haleema. Rehaan daf da zasu shiga apartment ɗinsa ya saki hannunta ya shiga ciki, itama sanyaye ta shiga ta tsaya a jikin ƙofa tana sauke numfashi wahala da tension da ciwon kai. Bata taɓa jin kunya a rayuwarta kamar haka ba, bata taɓa jin ƙuncin zuciya kamar yadda take ji ba, ko lokacin da ta bar Hamma ta auri Rehaan bata ji abinda take ji a lokacin ba. Ta kalli Rehaan da ya ke hawa sama bai ce mata komai ba, ta samu waje ta zauna ta yi shiru tana tunanin meyasa bai sake ta ba kamar yadda Daada ta nema?. Islaha ta yi tagumi ta rasa abinda yake yi mata daɗi gabaɗaya. Na farko so ta ke ta tabbatar da jikinta ne ko kuma ba ita bace, ta kasa tsayawa ta yiwa videon kallon tsaf, tana so in ta kalla sai ta je ta kalli kanta a mirror ta ga ya jikinta ya ke, akwai banbanci da na wayar ko babu. Tunawa da Safeera tana wajan Mamy sai ta miƙe ta koma wajan Mamy, Mamy tana ganinta ta ce, "zo ki zauna."  Islaha ta kusa da ita Mamy ta ce, "Kar ki damu, Rehaan bazai sake ki ba babu abinda zai faru." Islaha ta kasa magana, ta sunkuyar da kanta ƙasa bata ce komai ba. Mamy ta ce, "Safeera ki haɗa mata tea ta sha, ko zata ji daɗi." Islaha cikin dashshiyar murya ta ce, "bazan iya sha ba." Mamy ta ce, "za ki iya, Safeera kawo mata." Safeer ta miƙe zuwa dining da ta ga komai akwai, ta zuba mata rabin kofi ta kawo mata. Mamy ce ta yi nata dole sai da ta sha ba dan tana so ta sha ɗin ba. Wayar ce take vibrating, duk da screen ɗin wayar ya ɗauke amma waya tana shigowa, kuma in ka san kanta zaka iya ɗaukar wayar har ka amsa. Screen ne dai ya ɗauke, tun buga ta da ƙasa da ta yi sai dai ka ji vibrating amma screen ya tashi aiki. Safeera ta ɗaga wayar Islaha ta ji muryar Baffa ya ce, "Islaha kina ina, ina so na ganki." Safeera ta ce, "Baffa Safeera ce." "Safeera ina Islahan?." "Gata nan Baffa, bata jin daɗi ne." "Ya Allah! Kuna ina?." "Muna gidan da take." "Ina so na ganta Safeera, wannan abubuwan da suka faru ina so na ganta ido da ido, na san bata jin daɗi sosai." Safeera ta kalli Islaha ta ce, "Gata Baffa, ku yi magana." Safeera bawa Islaha wayar ta saka a kunne ta ce, "Baffa." Baffa ya ce, "Islaha ya jikin na ki?." Maimakon ta bashi amsa sai ta fashe masa da kuka Baffa ya ce, "ki bar kuka Islaha." "Baffa ni ban san yaushe aka yi min video ba, wallahi ban san an yi ba." "Ki daina kuka, Hamman ki ya faɗa min an shigar da ƙara, za a nemo wanda ya yi wannan aika-aikar, ko waye sai an hukunta shi, sai ya girbi abinda ya shuka." Hawaye ya zubo mata ta goge ta ce, "kowa maganata yake yi, ana ta tsine min Baffa, kowa na duniya indai yana da wayar hannu ya ga tsiraina, kowa a fanko yake kallona Baffa, ana ta zagin iyayena. In sun mutu na san ana ta tashinsu a kabari ana cewa ga abinda ƴarsu ta yi. Zuciyata zafi take yi min." "Ki yi haƙuri Islaha, ki daina kuka Allah yana tare dake a ko yaushe. In ma an yi wannan abun da a tozarta ki Allah bazai bari ki tozarta ba, zai ba ki kariya in sha Allah." "Baffa ai na tozarta, an gama tozarta ni a duniya, an gama wulaƙanta ni, babu tozartar da ta kai wannan a duniya. Baffa ji nake kamar na kashe kaina na huta, so nake na daina numfashi ko zan ji daɗi Baffaaaa!" Ta ƙarasa faɗa tana jan sunansa cikin kuka. Baffa ya ce, "Islaha ki daina wannan maganar, kar na sake ji kin yi maganar za ki kashe kan ki, Allah zai kawo miki mafita in Allah ya amince." Saheer da yake kusa da Baffa ya ce, "Islaha ki nutsu, komai zai warware, ni na tabbatar ba ke bace." Ta ce, "Hamma ni ce, ni ce a jikin videon. Ni na san wannan jikina ne, ban san yaushe na aikata har aka yi min video ba. Shikenan an gama wulaƙanta ni Hamma, an cuce ni Hammaa!." "Ya isa haka, ki daina faɗar wannan kalaman babu daɗin ji. Ki nutsu, zuwa nan da gobe komai zai zo ƙarshe in sha Allah." Bata ce komai ba sai hawaye take yi, Baffa ya ce, "ina Safeera?." Sai ta miƙawa Safeera wayar ta saka a kunne ta ce, "gani Baffa." Baffa ya ce, "ki zauna da ita, kar ki bar inda take saboda tana cikin damuwar da jawo ta yiwa kanta illa. Zan faɗawa Baban naki, zan ce ni na ce ki kwana da ita saboda ita." Safeera ta ce, "To Baffa, zan kira Mama na faɗa mata." "Yauwa hakan yana da kyau, Allah ya yi mu ku albarka." "Amin Baffa." Daga haka suka kashe wayar. A lokacin Mamy ta fito ta ce, "Safeera ki kaita ɗaki ta huta." Safeera ta kalli Mamy cikin ƙauna da burgewa. dan yadda take faɗar Safeera ɗin burge ta yake yi sossi. Ta ce, "To Mamy." Ta kalli Islaha ta ce, "mu je." Ta miƙe suka shiga ciki. Islaha ta ce, "Safeera nuna min video nan don Allah." Safeera ta ce, "babu amfanin ganin Islaha, zai sake ɓata miki rai ne." "Ina so in gani, ki bani." "Bazan bayar ba, ki zauna." Islaha taƙi zama ta ce, "In kina ƙaunar Allah ki bani." "To meye abin gani a video?." Cikin murya mai rauni ta ce, "ina so in gani." Safeera ta sauke numfashi ta haska mata, ta karɓa tana kallo sai ta rufe bakinta da hannunta ta zauna tana juya ido akan wayar. Babu abinda ya banbanta da ta jikin video, komai irin nata sak da sak, ta girgiza kai ta ce, "Safeera ni ce, wallahi ni ce" ta faɗa hawaye yana sauka akan screen ɗin wayar. Ta ce, "komai irin nawa ne, yaushe na sha giya har aka yi video nan ban sani ba? Ni dai na san ban taɓa aikata zina ba balle na ce ko an yi min video a lokacin." Safeera ta ce, "Don Allah ki nutsu, ki daina wannan koke-koken, ciwo zai ƙara miki." "Dole in yi kuka, ni ce a ji ki Safeera, wallahi jikina ne. Yanzu shikenan kowa ya san ya jikina yake ko? Kowa ya daina ganina da suttura sai tsirara." Safeera ta ce, "don girman Allah ki daina wannan kukan, ki nutsu." Bata daina kuka ba sai hawaye da ya cigaba da ambaliyya, Safeera ta karɓi wayar ta ajjiye tana rarrashinta. Abba kuwa kai tsaye saman Rehaan ya hau ya same sa a zaune ya jingina da kujera ya rufe ido har ya shigo bai sani ba. Abba ya ce, "Rehaan." Ya buɗe ido yana kallon Abba. Abba ya ce, "Ya ka ke ganin za a yi da maganar nan?." Rehaan bai amsa ba Abba ya ce, "Yayana ya kira ni akan case ɗin nan, mutanen da suka san akwai alaƙa tsakanina da yarinyar nan sai kira na suke yi. Har Alhaji Rufa'i da na saka ya yi magana da mai riƙonta akan aurenku ya kira ni, yana faɗa min shi dai bai santa da irin wannan halayen ba ko kaɗan, bai sani ba ko ta canja. Nima ina tantama, ina jin kamar itace kamar kuma ba ita bace. Da kana da wannan halin da bazai ɓuya ba, irin binciken da na saka aka yi a kanta kafin aurenku babu halinta mara kyau da zai ɓuya." Abba ya ja numfashi ya ce, "Ko itace ko ba ita bace Allah ne ya sani. Amma Rehaan kana da ɗaukaka, duniya ta san fuskar ka, babban tozarci ne ace kana tare da ita a a matsayin matarka. Yadda na ba ka umarmin aurenta, ina sona baka umarnin sakin ta, tunda daman baka so kuma ba a san kana aurenta ba. Tunda aka fara yaɗa hotuna irin wannan, ko da ace ba ita bace ba mu san abinda za a yi nan gaba ba." Rehaan ya sunkuyar da kansa ƙasa bai ce komai ba, dan bai san me zai ce ba. Abba ya ce, "daman saboda ni ka ke zaune da ita, to kuma yanzu na ce maka ina so ka sake ta." Rehaan ya ja numfashi ya kalli Abban, kafin ya yi magana Abba ya ce, "ko dai ka fara sonta ne?." Ya girgiza kai ya ce, "A'a." "Meyasa baza ka sake ta." "Saboda ina da dalili Abba." "Meye shi da zai saka ka kasa sakin ta?." "Lokaci....lokaci nake so a bani Abba, Ina bincike akan maganar." "Meye naka na bincike tunda ba so ka ke yi ba? A ganina ka samu hanyar rabuwa da ita tunda daman ni na saka ka aure ta, kuma yanzu na ce a sake ta ba shikenan ba? Binciken me za a yi kuma?." Rehaan ya sauke numfashi yana jin ɗacin kalmar nan da suke faɗa sannan ya ce "Abba Mamy ta ce na yi bincike a kai bana son ƙin yi, a wancan lokacin na karɓi aurenta saboda ka ce na karɓa, wannan lokacin kuma zan yi bincike saboda Mamy ta ce in yi." "In ka yi ka tabbatar da ita ɗin ce fa?." "Baza ta sake yin sacan ɗaya da sunan matata ba, na yi maka alƙawarin sakinta a lokacin." Abba ya girgiza kai ya ce, "Bazan hana ka bin umarnin babar ka ba, dan a wancan lokacin ka yi min biyayya har ka ka zaune da ita a matsayin matar ka, a wannan lokacin kuma bazan hana ka yiwa babar ka biyayya ba. A yi binciken, nima zan so a ce ba ita bace ko dan zargin da duniya take yi mata." Ya ɗaga kai ya ce, "in sha Allah." Abba ya juya ya fita shi kuma ya lumshe idanunsa."    Sai dare Safeera da Islaha suka koma apartment ɗin Rehaan, zuwa lokacin taji sauƙin ciwon kan da yake damunta. A ɗakin babu mai cewa komai, Safeera bata ce mata komai ba ta shirya ta kwanta ita kuwa kaya ta canja kawai ta kwanta ta yi shiru tana tunani. Har safeera ta yi bacci ita ta kasa yi, ta tashi ta ɗauki wayar Safira ta sake kallon video tana kuka. Sai kuma ta tashi ta fita daga ɗakin, ta ƙarasa ƙofar ɗakin Rehaan tana tunanin ta shiga ko kar ta shiga, sai ta yanke hukuncin shiga kawai. Tana shiga ya ɗago ido ya kalle ta, yana zaune a gefen gado ya kasa bacci, shiyasa ya tashi ya kunna hasken ɗakin ya zauna yana tunani. Islaha ta shiga tsakiyar ɗakin tana kallonsa, sai kuma ta sunkuyar da kanta ta rasa me zata ce masa. Shima shiru ya yi bai ce mata komai ba yana kallonta, sai ta ɗago suka haɗa ido ta ce, "Ka kalli videon ko?." Bai bata amsa ba sai lumshe ido da ya yi ya buɗe akan fuskar ta da ta kumbura saboda kuka, ta sake sunkuyar da kai tana kallon ƙasa muryar ta tana rawa ta ce, "Kuma ka kalli jikina a ranar da na yi wanka a public bathroom, ka kalla ko?" Ta faɗa bata ɗago kanta ba tana kallon ƙafafunta. Rehaan ya ta so ya matso kusa da ita yana kallonta, bata ɗago kanta ba muryarta ta fara rawa sosai, ta buɗe baki zata yi magana amma ta kasa saboda kuka. Sai da ta tsayar da kukan tana jin ciwon kai ya dawo sabo a lokacin, muryar ta tana cracking ta ce, "Don Allah ka banbance min, da jikina da jikin ta cikin videon nan iri ɗaya ne? Na ruɗe, na kasa banbance kaina da.........." Sai ta kasa ƙarasawa ta durƙushe zata zube a ƙasa Rehaan ya taro ta ya riƙe duka hannayenta, ta ɗaga ido ta kalle shi ta ce, "Na kasa ganewa, kuma ina so na gane dan na fita daga halin da nake ciki. Ka taimaka ka faɗa min, don Allah!." Rehaan bai san ya yi hugging ɗinta ba da ya ji ta sake fashewa da kuka a ƙirjinsa, ya riƙe ta sosai a jikinsa yana runtse ido kukanta yana yin nutso a cikin jikinta. "Ni na kasa ganewa, ka faɗa min ka ji!" Ta sake faɗa tana jikinsa shi kuma ya kasa ce mata komai, kawai ji ya yi yana buƙatar rungumeta shiyasa ya yi, amma ba dan ya yi magana ba. Jin kukan nata ya yi yawa sai ya ce, "na faɗa miki, ina tare da ke. Calm down!." "I can't...." "Stop crying." "I can't..." ta kuma faɗa tana kuka a jikinsa ya lumshe ido yana sake hugging ɗinta. Ta jima a haka a jikinsa, kafin ta zare jikinta tana ja da baya yana kallonta, sai kuma ta buɗe ƙofar ta fita ta sauka ƙasa ta rasa inda zata saka ranta. Daga ƙarshe ta kwanta akaan carpet, ta rasa inda zata saka ranta ta ji daɗi. A haka bacci ɓarawo ya fara ɗaukar ta, sai ta ji kamar da mutum a kusa da ita a kwance, da farko ta share saboda ta san da Safeera suke kwance, amma tunawa a falo take sai ta buɗe ido a firgice tana so ta miƙe ta kunna switch amma ta kasa. Da ƙarfi aka jawo ta, sai kuma ya yi dariya ya ce, "Hooo ta ji tsoro, in gari ya bar duhu sai kin bani alawa na bata tsoro." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Ta furta tana so ta ƙwace hannunta daga riƙon da ya yi mata  amma ta kasa. A daidai lokacin aka kunna hasken falon gabaɗaya, lokacin ta yi nasarar ƙwace hNnunta ta koma gefe tana hakki, dan ƙiris ya rage tashin hankali ya saka ta samu attack. "Laa ila'ha illalahu, muhammadur rasulillah S.A.W!." Salatin da ta ji an yi ya saka ta buɗe ido a firgice tana kallon mutanen da suke tsaye suna kallon ta...... Nana Haleema. RDB3P68 Nana Haleema. Umma ta ƙarasa cikin zafin nama ta ja hannun Salman ta yi gefe da shi ta ce, "Na faɗa miki lalata min yaro ta ke yi, yanzu ba dan Allah ya kawo ni ba me zata yi masa?" Ta faɗa tana kallon Mama da ta ke tsaye daga bayanta. Umma ta juya ta chakumi wuyan Islaha ta miƙar da ita tsaye ta ce, "na rantse da girman Allah sai kin bar gidan nan, bazan zuba ido ki lalata min yaro ba, abin har ya kai ki dinga gayyatarsa nan? Na shiga uku! Tun yaushe ki ka saba gayyato shi nan ɗin?." Islaha dai bata ce komai ba, tana tsaye kawai dan ta ruɗe bata san abinda ya kamata ta ce ba. Mama ta ce, "na jima da dawowa daga rakiyar yarinyar nan ai, ki duba iskanci da ta yia waya, babu kunya babu tsoron Allah. Bayan hotuna da videon ta da suka gama yawo a duniya, bata haƙura ba sai da ta jawo yaro har ɗaki tana yi masa iskanci, abin kunya mijinta yana sama ita kuma tana ƙasa. Daman haka ki ke?." Umma ta ce, "wallahi sai na faɗawa Daada, dole yarinyar nan ta bar gidan nan, bazan iya zama da ita tana cutar dani ba." Salman da yake gefe yana ta taɓa wannan da wancan ya ce, "Umma tsorata ta nayi tana bacci." Umma saboda fusata bata san ta juya ta mare sa ba, ta nunasa da yatsa ta ce, "yi min shiru, in ka sake magana sai na fasa maka baki." Mama ta ce, "ya za ki dinga yi masa faɗa? Kin manta lalurar da yake da ita ne? Ga wacce ya kamata a yiwa faɗa nan a tsaye tana kallon ki." Umma ta sake riƙe rigar Islaha ta ce, "na rantse da Allah sai na koya miki hankali, sai na kore ki daga gidan nan wallahi tunda ba gidan ubanki bane." Rehaan yana tsaye a kan stairs yana kallon komai, ya harɗe hannu a ƙirji yana kallon duk abinda yake faruwa. Ya tashi zai yi sallah kenan ya ji hayaniya dole ya fito ya ga abinda yake faruwa. Takaici kamar ya kashe shi, duk abinda Islaha take yi bai taɓa jin haushi kamar ranar ba, bai san dalilin da ya saka ya ji ransa ya ɓaci ba, haushinta da takaicin wannan ɗabi'a'un nata sun tsaya masa a rai, bai ce komai yana tsaye yana kallonsu su kuma ba su kula da shi ba. Umma ta ce, "mu je wajan Daada, a daren nan sai ta bar gidan nan wallahi. Iskanci ya yi yawa, abin ya kai har tana gayyato shi ɗaki da daren nan? Kuma saboda rashin tsoron Allah mijinta yana sama ita tana ƙasa tana iskanci?. Bazai yu ba wallahi, dole a bar gidan ta je ta samu ƴan uwanta yan iska su cigaba daga inda suka tsaya." Mama ta yi caraf ta ce, "ni abinda yake ɗaure min kai, ya aka yi ya san lambobin falon nan in ba buɗe masa ta ke yi ba?." Mama ta sake fusata Umma, ta fusata sosai ta ce, "ko yarinyar nan ta bar gidan nan, ko kuma ni na bar shi, dole a yi ɗaya dan bazan zauna tana lalata min yaro ba." Islaha ta kasa cewa komai, bata da bakin da zata kare kanta shiyasa ta kama bakinta ta yi shiru kawai. Tana cikin damuwa mai yawa, bata da lokacin da zata buɗe baki ta yi magana akan abinda bazai amfane ta da komai ba. Mama zata yi magana Rehaan ta ga Rehaan, ya sanya hannunsa duka biyun a cikin pocket ɗin pyjamas ɗinsa fuskarsa a ɗaure, babu alamun wasa ko sassauci a tare da shi. Yana ƙarasowa ya kalle su ɗaya bayan ɗaya sannan ce, "Mama dare ya yi a bar maganar nan." Mama ta nuna islaha da ta zauna ta dafe kanta ta ce, "kamata muka yi dumu-dumu tana yiwa Salman fyaɗe, kuma ka ce a bar maganar?." Wani irin abu ya ji ya da ki zuciyarsa da ƙarfi, amma bai nuna ba sai ya daure ya ce, "dare ya yi yanzu, hayaniyar ku ta hanani bacci, ku je kawai." Umma ta kalle sa a fusace ta ce, "dole ka ce haka ai, dole ka ce mu je tunda ba ka da bakin da zaka kare ta. To wallahi da safe sai an yita ta ƙare, ko ta bar gidan nan ko ni na bar shi, dan ta gama zama a gidan nan, baza mu zauna da karuwa tana bin yaranmu tana lalatawa ba. Ta je ta yi a wani gidan, amma ban da nan wallahi." "Fine! Ku je" ya faɗa cikin gajiya da maganar. Hakan da ya faɗa sai ya sake fusata Umma da Mama, suka taso masa da faɗa kowa yana faɗar abinda yake bakinsa, shi dai yana tsaye ya yi shiru, dan sun bar kan Islaha sun dawo kansa suna yi masa faɗa kamar zasu da ke sa. A lokacin aka shigo falon duk suka juya suka ga Mamy ce ta shigo sanye da dogon hijjab a jikinta. Umma kamar jira take yi Mamy ta shigo ta nuna ta ce, "Ki faɗawa ɗan ki, dole karuwar matarsa ta bar gidan nan wallahi." Mamy cike da damuwa ta ce, "me ya faru? Ana jin maganar ku har apartement ɗina, dare ne fa." Mama ta nuna Islaha da bata ɗago kai ba ta ce, "wannan karuwar...! Ita mu k kama dumu-dumu  tana ƙoƙarin zugewa Salman zip ɗin wandonsa." "Hasbunallah! Ya Salam! Ya Salam!._ Rehaan ya faɗa a ransa jin kalmar Mama tana ƙoƙarin kayar dashi, in bai ambaci Allah ba zai iya kifawa a wajen, ya rufe idanunsa saboda yadda ya ji maganar tana juyawa masa kamar ana juyawa dashi a sama, bai sani ba ko kunya maganar ta ba shi, ko kuma meye bai gama fahimta ba. Mamy ta kalli Islaha sannan ta kalle su ta ce, "an samu misunderstanding ne, amma babu yadda za a yi Islaha ta aikata wannan abinda ku ke faɗa. Ni na yarda da ita, kuma na san baza ta taɓa aikata abinda ku ka ce ta yi ba." "Nazo na gani da idona ki ce ba haka ba? Na kamata tana ƙoƙarin danne min ɗana ki ce baza ta yi ba? Lallai Nadira kina da son zuciya, kina da son kai da nuna naki naki ne a ko yaushe. Kuma ina so ki sani, ko tayi ko ba tayi ba, tunda idona ya gani wallahi sai ta bar gidan nan, ai ba gidan ubanta bane." Rehaan ya kasa jure wannan cecekucen na su ya ce, "Umma don Allah na ce bar maganar nan." Ta juyo ta kalle ta ce, "baza a bari ba, sai an faɗa!" Ta faɗa cikin ɗaga murya tana kallonsa. "Me ya ke faruwa ne haka? Hayaniyar me nake ji daga ɓangaren nan kamar ba dare ba?." Duk suka juya suna kallon Abba da ya shigo shi da matarsa ta ƙarshe, Abba ƙaraso yana kallon kowa yana nazarin fuskokinsu sannan ya ce, "lafiya dai ko?." Sai kawai Umma ta fashe da kuka ta ce, "lokacin da na ce maka yarinyar nan tana so ta lalata Salman ba ka yarda ba, sai ake ganin kamar ƙarya nake yi mata, saboda ita matar ɗan gold ce bata laifi. To ka tambayi Saddiƙa, a gabanta komai ya faru, yau mun kama ta da idanunmu a cikin falon nan, ta kwanta a kansa tana ƙoƙarin cire masa kaya. Ni wallahi bazan cigaba da zama da yarinyar nan a gidan nan ba, dole ta bar gidan nan ko ni na bar shi!." Abba ya kalli Islaha da har lokacin fuskar ta take a rufe, ga gashinta ya sauka har ƙasa ya rufe fuskar gabaɗaya. Ya kalli Rehaan ya ce, "kai me ya faru ne?." Umma ta buɗe baki cikin mamaki ta ce, "shi zaka tambaya ya faɗa maka abinda ya faru? Ni bazan faɗa ka yarda ba ko?." Abba bai kulata ba ya sake kallon Rehaan ya ce, "baza ka yi magana ba?." "Abba ni ban san me ya faru ba, na ga dai kawai sun shigo suna ta faɗa. Ban san ya aka yi suka shigo parlour nan ba." Umma ta sake kallon ta ce, "na faɗa maka da idona na ganta, ita tasan na ganta. Wai meyasa baka yi min adalci a gidan nan ne, meyasa a komai sai ka nuna kafi son Rehaan a kan Salman? Dan Rehaan yana da kuɗi shikenan sai a dinga nuna mana banbanci a tsakaninsa da sauran yara? Ko dan Salman yana da lalura sai ya zama bashi da amfani? Wallahi ba ka yi mana adalci a gidan nan, ba kai yi mana abinda ya kamata" ta faɗa cikin kuka sosai. A lokacin Mama ta shigo riƙe da hannun Daada da ta je ta taso ta daga bacci dan ta san abinda yake faruwa. Daada ta nemi waje ta zauna ta ce, "Hayaniya ta cika gida, duk girman gidan nan ina jiyo amon muryarsu har ɗakina, Me ya faru?." Umma ta ƙarasa ta zube a gaban Daada tana kuka ta ce, "dan ɗana yana da taɓin hankali, dan an ga shi kaɗai na mallaka namiji a gidan nan, dan Allah ya ɗora masa lalura shikenan sai kowa ya juya mana baya? Ba a yi min adalci a gidan nan, ana nuna min ba shi da wani amfani tunda Allah ya jarabce shi da matsalar ƙwaƙwalwa. Ko yaushe Rehaan ne akan daidai a gidan, ba ya taɓa yin laifi, ko da ya yi laifin ana ninkewa a nuna kamar ba a gani ba, kawai dan yana da kuɗi?. Ya ake so na yi, da rashin lafiyarsa zan ji ko da rashin adalcin da ake yi min a gidan nan?." Daada ta ce, "ba ki faɗa min abinda na tambaya ba har yanzu." Umma ta ce, "ni da Saddiƙa, ido da ido muka kama yarinyar nan da Salman a ɗakin nan, fitila a kashe sannan tana kwance a samansa." Daada ta kalli Umma ta ce, "ke ki ji tsoron Allah Salamatu!." "Wallahi abinda muka gani kenan Daada, ba ƙarya mu ke yi ba" Mama ta tabbatarwa Daada tana kallonta. Daada ta kalli Islaha da take yadda take, ta kalli Salman da ya rakuɓe a gefe ɗaya yana kallon su, ta kalli Rehaan da har lokacin yana tsaye hannunsa yana cikin aljihu, ta kalli Mamy da ta jingina da bango bata ce komai ba. Daada ta ce, "bayan hotuna da video da ya ke yawo a duniya, abin har ya kai ta fara ƙoƙarin lalata mana Salman?." Umma cikin kuka ta ce, "na faɗi abinda ya faru maimakon Abba ya goya min baya sai yake kallon Rehaan yana tambayarsa me ya faru, kenan ni ga maƙaryaciya?. Da safe zan bar gidan nan, zan ɗauke sa mu bar gidan, zamu bar mata gidan tunda mijinta shine mai faɗa aji. Wallahi tunda ta zo gidan nan nake ganin canji, tunda ta zo gidan ann shikenan ya susuce. In ba nuna masa take yi ba ya za a yi ya sani, in ba buɗe masa ƙofar nan ta yi ba ya za a yi ya iya buɗewa?." Daada ta kalli Islaha ta ce, "amma wannan yarinya ba ki kyautawa kan ki ba, ban ji daɗin wannan abubuwan da suke faruwa ba, duk soyayyar da na nuna miki sakayyata kenan a gare ki?." Sai a lokacin Islaha ta fashe da kuka mai sauti, har lokacin bata buɗe fuska ba sai kukan da ya ke fitowa. Daada a tausahe take magana ta ce, "ni so nake a raba aure kawai, a yanke duk wata alaƙa da yake tsakaninmu kowa ya huta......" Ta ɗaga ido ta kalli Rehaan ta ce,"Kai! Ka saki yarinyar nan kowa ya huta, in Allah ya kaimu gobe sai ta tafi. Zamu iya zama da ita a gidan nan ba, mutuncinmu zubewa zai yi. Tunda bata jin kunyar Allah ta gayyato yayanka dan tana taƙamar ba shi da hankali, bata san Allah zai tona mata asiri ba, ai ko dan saboda idanunka sai ta ɗan saurara wani abun. Tunda abin haka ne, ka sake ta bana buƙatar ganinta a gidan nan ko kaɗan, laifina ne da na dage sai da aka auro ta, ban gama fahimtar wacece ita ba, a yanzu ina so ka sake ta." Rehaan ya ja numfashi mai tsaho ya sauke a hankali, yana jin yadda kukan Islaha yake ratsa ko ina na falon, sautinsa kaɗai ake ji dan kowa ya yi shiru tana jira ya ji me zai ce. Ya kalli Mamy da take kallonsa, sannan ya kalli Daada ya ce, "a bar maganar nan zuwa safiya." "Baza a bari ba! Saboda ba ka da kishin kanka?yarinya tana neman Yayanka da iskanci amma ka tsaya kana cewa bar maganar zuwa gobe? Matarka ce fa, aurenta ka ke yi tana neman wasu mazan da auren ka!" Umma ta faɗa da ƙarfi tana kallonsa. Ya kalli Umma ya ce, "kin ce matata ce, tunda kin san tawa ce babu ruwan ki da maganar kishi. Ina sake tabbatar miki da ita ɗince, ni nake da iko da ita ba wani ba, kuma bani da niyar sakinta a yanzu, kuma baza a saka ni na sake ta. Kawai ku bar maganar nan, kowa ya je ya kwanta!" Ya ƙarashe maganar cikin bada umarni. Umma ta ji kamar ta faɗa cikin wuta saboda takaici da baƙin ciki, ta kasa magana sai kallonsa take yi zuciyarta tana zafi. Mamaki yake bata tana tunanin daman ya iya rashin kunya haka? Dan ita tasan daga ina yini wata magana bata sake haɗa su. Mama ta ce, "ai kuwa dole ka sake ta, ko dan ƙimar gidan nan. In ka bar ta a gidan nan mutuncin Daada zubewa zai yi a idanun dangi, kaf dangin Abba alfahari ake da jikokin Daada babu ɓata gari, in ka bar wannan ka lalata mata suna." Daada ta amshe ta ce, "rabu da shi, bazan tashi daga wajen nan ba sai ya saki yarinyar nan, saki uku zai yi mata ba saki ɗaya ko biyu ba, so na ke in ta bar gidan nan ta bar shi kenan har abada." Abba ya kalle Rehaan shima ya kalli Abba kafin Abba ya ce, "Rehaan." Rehaan ya dakatar da Abba ya ce, "Abba kar ka ce komai don Allah, ka bani dama na yi abinda nake ganin ya dace dani, ko yaushe kaine ka ke saka, a wannan lokacin ka bari na yi komai da kaina. Bani da ra'ayin rabuwa da ita a yanzu, kuma bazan rabu da ita ba. Na ga dai duk kun damu da abinda aka ce ta yi saboda ni ko? Kuna ganim kamar ta ci amanata ne, kuna ganin bata dace ta zauna dani ba ko? To ni na amince zan cigaba da zama da ita a haka, bana buƙatar a sake maimaita min maganar nan, Ina son zama da ita, kuma bazan rabu da ita ba." Daada ta buɗe baki ta ce, "ta shanye shi, wallahi ta shanye mana shi. AbdulAziz kana kallo ko? In ba wanda aka shanye ba ace matarka ta aure tana yawon banza, tana neman Yayanka da mugun abu ka ce kana son zama da ita? Dole mu dage da addu'a." Rehaan shi Daada mamaki take bashi, kamar ba itace ta dage akan auren ba, ya kalli Islaha da take kuka shi kuma kukan ne baya so, ya sake yin tsaki ya ce, "mu je a hakan, ni dai ku je sai da safe, don Allah!" ya faɗa yana nuna musu hanya. Nana Haleema. RDB3P69 Nana Haleema. Saboda yadda suka kaure da hayaniya ba ya jin abinda suke faɗa, Daada tana yi, Mama tana yi, Umma tana yi kamar zasu cinye shi. Abba da Mamy da Anty ne kaɗai ba su ce komai ba. Ya kalli Islaha ya ga har lokacin tana yadda ta ke, ya ɗauke kai yana jin wani irin zafi a fatar jikinsa, ya yi ƙaramin tsaki ya ce, "Don Allah ku je, sai da safe" ya faɗa yana juyawa ya hau sama da sauri. Bai san ya suka ƙare ba ya ji shiru ɗuf babu motsin kowa a falon. Yana tsaye ya jingina da bango yana ajiyar zuciya sai wayar ta yi ƙara, ganin Mamy ce sai ya ɗauka abinda ta ce ya saka ya sakko ƙasan ya ganta a zaune kusa da Islaha ta kwantar da kanata a jikinta tana ta kuka. Mamy ta kalle sa bayan ya ƙaraso ta ce, "ban yarda ba Rehaan, wannan maganar shirya ta aka yi, ina so wannan ma ta shiga cikin maganarmu ta ɗazu, a warware komai Rehaan. A samo wanda yake buɗe ƙofar parlour nan, dan na ga kamar camerar bakin ƙofar ta daina aiki. Na tabbatar aiko Salman ake yi yana zuwa apartment ɗin nan, wani lokacin ba zuwan kansa bane aiko shi ake yi." Ta shafa fuskar Islaha tana goge mata hawaye ta ce, "Bana so na ga tana kuka, ina jin zafin kukanta a cikin zuciyata, ka yi min abinda zan daina ganin hawaye a idanunta Rehaan." Rehaan bai iya cewa komai ba, itama Mamy ganin yanayinsa bata yi tunanin zai yi magana ba, dan fuskarsa ta canja sosai ta nuna alamun ɓacin rai da damuwa. Sai ta miƙe ta fita ta bar Islaha a zaune tana jan nunfashi. Yana tsaye yana kallon ta, yana jin takaici da baƙin ciki suna zagaye ilahirin jikinsa, yana hango zubar da cikin da ta yi a Jeddah a idanunsa. Ga shi dai yana jin tausayinta sosai, amma bai taɓa jin haushinta kamar lokacin ba, bai taɓa jin yana danasanin haɗa ido da ita ba sai a lokacin, bai san meyasa abinda yake ji ya rinjayi tausayin ba, ya san dai zuciyarsa tana yi maza zafi da ƙuna amma bai san dalili ba. Har cikin zuciyarsa ya ke jin abinda ta aikata, yana daurewa ne bai nuna ba saboda mutanen gidan, amma in ya tuna yayansa ne, kuma ta buɗe masa ƙofa ya shigo sai ya ji takaici yana mamaye masa zuciya. Tambayar da yake yiwa kansa me ya sakko da ita? Dan ya san ƙawarta tana tare da ita, me ya sakko da ita ta bar ƙawarta a sama?. Islaha bata san yana tsaye ba ta ɗago a hankali tana buɗe idanunta da suka yi nata nauyi, ta kalli inda yake sai suka suka haɗa ido, ta sake rufewa ta buɗe ta miƙe zaune sosai tana kallonsa. A zuciyarsa yake ji yana faɗar maganar bai san ta fito fili ba ya ce, "Me ki ka aikata haka? Ki bari a gama da case ɗin ɗazu mana, ki bari saka wanda ki ka kai wajensa har ya yi miki ya goge video da ya yi miki, sannan a sauke shi da media kafin ki ki cigaba. Har cikin apartment ɗina, bakya jin kunyar Allah ki ka gayyato Salman har nan?. Oh shiyasa ki ka sakko nan, saboda ƙawarki tana sama ko? Meyasa baza ki jira a gama case ɗin da yake gaban ki ba?." Islaha ta ɗago iso ta sake kallonsa ta buɗe baki zata yi magana sai ta ji ta kasa, ta miƙe tsaye ta tsaya tana dafe kanta, dan bata san me zata ce ba gwara ta yi masa shiru. Ya ce, "Duk abinda zaki yi ki yi, amma ban da ɗan uwana, sai lokacin da ki ka zo gidan nan sannan ya zama haka, ki ɗauke ido daga kansa. In masu gadin gidan nan za ki nema wannan ra'ayinki ne, amma wani daga cikin gidan nan kar ki sake wannan kuskuren. Ki je can ki ƙarata da mazan da ki ka saba bi suna recording ɗin ki, amma a cikin gidan nan bazan yi tolerating wannan shirmen ba." Islaha duk da bata jin daɗi kwata-kwata, tana ji kamar zata sume a wajen amma hakan bai saka ta buɗe baki ta ce, "Mr Rehaan!." Ta ku uku ya yi ya ƙaraso daf da ita, ta buɗe idanunsa a cikin mata ya ɗora finger ɗinsa akan lips ɗinta ya ce, "shiiiiii!." Ya girgiza kai ya ce, "kar ki ƙara faɗar sunana, i saw anythings, i heard anythings, ba ki da abinda zaki faɗa min abinda na gani ko na ji." Ta zuba masa ido kawai tana kallonsa, ƙirjinta yana ɗagawa saboda numfashin da take yi. A kunnensa yake jin yadda numfashinta sauka, kana ji ka san bata da lafiyar numfashi, kuma tana fama da lalura a lokacin. Sai ya ja baya ya ce, "saboda Mamy, saboda ita kaɗai zan tsaya a goge pictures ɗin nan, in ba dan ita ba babu dalilin da zai saka na saka hannuna a case ɗin ki...." Ya kuma ja da baya yana tafiya ya ce, "saboda Mamy kawai!" ya faɗa yana juyawa zai hau sama, su ka haɗu da Safeera tana sakkowa. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai, ta ba shi hanya ya wuce ita kuma ta ƙaraso wajan Islaha. Islaha bata san ta ƙaraso ba sai da Safeera ta dafata ta ce, "Islaha meye kuma ya sake faruwa cikin daren nan? Kin ga yadda fuskar ki ta sake komawa? Me ye ya faru?." Islaha ta kalli Safeera ta ce, "zaki iya yi min wani taimako?." Safeera ta ce, "me zai hana, faɗa min ko meye ina jin ki." Islaha tana riƙe da kanta ta ce, "ina zuwa." Ta faɗa tana shiga kitchen, ba jimawa ta dawo ɗauke da sabuwar wuƙa sai ƙyalli take yi. Ta miƙawa Safeera ta ce, "Don Allah ki kashe ni, ki kashe ni na huta Safeera. Bana so na mutu kafira, da yanzu na jima da bugawa kaina wannan wuƙar kowa ya huta. Tunda bani da kowa, bani da mai saurarena, bani da wanda zai fahimce ni." Safeera da ta daskare a tsaye saboda mamaki ta ce, "Islaha kina cikin hankalin ki kuwa, me ki ke faɗa haka?." "Safeera ya zan yi, ni kaɗai na san abinda nake ji a zuciyata, so nake na mutu, gwara ki kashe kawai." Safeera ta ce, "dan ƙaddara ta same ki sai ki gaza karɓarta, dan Allah ya jarabce ki sai ki kasa cin jarabawar?. Abinda za ki sakawa wanda ya halicce ki da shi kenan, da irin waɗanann kalaman za ki karɓi ƙaddarar ki Islaha?. Musulma ce ke, kin yi imani da ƙaddara mai kyau da mara kyau, masu kyau sun zo miki sau babu adadi, kin karɓa kin gode kina farin ciki, kina alfahari da kasancewar ki a inuwar musulunci. Yanzu dan akasinta ta zo sau ɗaya tak sai ki juya baya? Zai ki rufe ido ki manta da Allah ne ya yi nufin hakan?." Islaha ta ajjiye wuƙar hannunta ta zauna akan kujera ta ce, "Safeera hotunan tsaraicina ne suka yawo a duniya, ga wani abinda da akace na sake yi, ance na gayyaro namiji har parlour nan, kuma bani da bakin kare kaina, dan kowa ya ganni. Safeera ina ji in ban mutu ba bazan samu sassauci ba." Ta zauna kusa da ita cikin rarrashi ta ce, "ki tuba ga Allah, ki nemi yafiya akan kalaman nan na ki yanzun nan." Muryarta tana cracking ta ce, "astagafirullah!." Safeera ta dafata ta ce, "Allah bazai taɓa bari ki wulaƙanta ba, zai shige miki gaba a duk lamarin da ki ka saka a gaba, zai ba ki kariya a lokacin da ki ke buƙatar kariyarsa, abu ɗaya kawai za ki yi, ki yarda da shine mai yi kuma shine mai yayewa, ki roƙesa zai amsa miki. Waɗanda suka yaɗa hotunan nan zai yi maganinsu, zai tona musu asiri a idannun duniya. Ki yi haƙuri, ki dinga maimaita innalillahi wa'in a ilaihir raji'un, ki dinga maimaita la'ilaha illahu azimul halim, la'ilaha illahu rabbil arsil azim, la'ilaha illahu rabbu samawati wal arabi wa rabbul arshil kareem, komai zai tafi yadda ki ke so." _(A duk lokacin da ɗayanmu ya shiga matsala, damuwa ko ya faɗa hannun ɓarayi ko mutane masu cutarwa, ya dinga maimaita wannan addu'ar bazai gushe ba sai Allah ya kawo masa mafita.)_ Islaha ta ce, "to Safeera, zan yi." Safeera ta dinga rarrashinta har ta daina kukan, ta ɗauke wuƙar ta mayar da ita mazauninta, kafin ta taimaka mata su koma saman, ta saka ta suka yi alwala ta tayar da sallah, Islaha ta yi sallar a zaune dan baza ta iya tsayuwa ba saboda ciwon kai. Rehaan tunda ya shiga ɗaki yana sauke ajiyar zuciya, a jikin mirror ya zauna idanunsa suna ƙasa yana furzar da iska mai zafi, tausayin Islaha ne yake mamaye masa zuciya, har ya fara jin haushin kansa akan abinda ya faɗa mata, yana ji kamar ya sauka ya rarrasheta har sai ta daina kuka. Ba dan cin fuska ko wulaƙanci ya faɗa mata ba, ya faɗa ne dan ya kore yanayin da yake addabar zuciyarsa, ya faɗa dan ya samu mafaka ya kushe ta ko zai daina jin abinda yake ji, amma bai daina ba sai ma hauhawa da yanayin yake yi. Sai kuma ya yi tsaki ya haɗɗiye yawu yana lumshe idanunsa ya ce, "Oh my god! Ya Allah me nake ji haka, meyasa raina ya ɓaci?." Sai kuma ya tuna da Mamy ya ce, "Saboda Mamy, saboda Mamy kaɗai nake yi, Itace ta saka ni, dole zan yi saboda ita" ya faɗa yana ɗaukar waya maimakon ya kira Dss ɗin da ya bawa aiki sai ya kira Jazy. Jazy yana zaune akan sallaya shi da Riyya sun idar da tahajjud ya ji wayarsa tana vibrating, ya jawo ya duba ya ce, "Ray kuma! A daren nan?" Ya faɗa tana ɗauka ya saka a speaker. Jazy ya ce, "Ray ya aka yi, wani abu ya faru ne?." Bai iya magana ba sai numfashi da yake saukewa a hankali. Jazy ya ce, "dare ne fa Ray, ka kira ni ka yi shiru." Cikin wata irin murya mai nuni da raunin zuciyarsa ya ce, "ka yi mgana da mutumin nan?." Da mamaki ya ce, "ikon Allah! Ka rasa lokacin tambayata wannan maganar sai yanzu? Ka jira gobe mana, ba da kai aka zauna dasu ba?." "Ina so case ɗin nan a kawo ƙarshensa a gobe, bana so a kai ya wuce gobe Jafaar." "Za a yi, ai ba wani case mai wahala bane, da an kama mai account ɗin shikenan. So calm down, za a yi komai in sha Allah." "Ina faɗa maka ina so a kawo ƙarshensa and you're telling me I should calm down, Jazy in ba a kawo ƙarahen case ɗin nan ba hankalina bazai kwanta ba." Jazy ya yi dariya kamar ya tambaye shi dalili sai kuma ya share ya ce, "Okay! Zamu yi magana" ya gaɗa yana kashe wayar ya ajjiye. Riyya ta ce, "Case ɗin Islaha?." Ya ɗaga mata kai ya ce, "shine, kuma ya rasa lokacin da zai kira ni sai yanzu." Ta murmusa ta ce, "amma ban taɓa jin voice ɗinsa cikin damuwa haka ba, ban taɓa jin yana magana cikin irin wanann yanayi ba sai yanzu." Ya yi dariya ya ce, "ke kuwa matarsa fa, aka samu wani ya haɗa AI video da fuskarta aka watsa a duniya, dole ya damu." "Is that means he loves her?." Ya kalle ta ya ce, "sai yana sonta zai damu?." "No, ban taɓa jin voice ɗinsa a haka ba, in ka ga ya shiga damuwa da damuwar wani to tabbas mutum ne mai mahimmaci a gare sa, kamar Mamy. Hakan yana nufin...." Sai bata ƙarasa ba tana kallon Jazy. Ya miƙe tsaye ya ce, "Yana nufin me?." "Ya karɓi aurenta a matsayin mata da miji, dan  na san da farko bai yi accepting ba." Ya yi dariya yana girgiza kai, shi kaɗai ya san irin kalaman da ya tanada waɗanda zai mayarwa da Rehaan a ranar da ya tabbatar yana son Islaha, shi kaɗai ya san irin abinda zai faɗa masa dan ya tuna masa baya har ya yi danasani akan furucin da ya dinga yi akan Islaha. Shi dai hasashensa ya nuna masa Rehaan ya faɗa tarkon ƙauna, kawai ba ya so ya fargar da shi sai ya yi nisa a cikin tafkin soyayyar, yadda yana faɗa masa zai amsa bazai musa masa ba. Ya kalli Riyya ya ce, "mu cigaba da sallah, ki bar yayan nan na ki kawai." Ta miƙe tana dariya suka cigaba da ibada...... Nana Haleema. RDB3P70 Nana Haleema. Islaha ta jima tana bacci, dan bata samu bacci ba sai bayan sallar asuba hakan ya saka ta yin dogon bacci har azahar. A firgice ta farka dan a cikin baccin ta tuna da abubuwan da suke faruwa, sai ta buɗe tana bin ɗakin da kallo, komai a kashe ya ke babu haske ko kaɗan, sai ƙarar ac da take tashi a hankali, ɗakin ya yi sanyi sosai. Waige-waige take yi tana neman wayarta amma bata gani ba, ta sauka daga kan gadon har lokacom kanta yana yi mata ciwo sosai ta shiga banɗaki. Bata jima sosai ba ta fito, a sanyaye take yin komai cikin mutuwar jiki da sanyin zuciya, ta canja kaya ta yi sallah. Buɗe ƙofar aka yi hakan ya saka ta ta kalli wanda ya shigo, duk da babu haske amma tana iya ganin mutum. Safeera ce da Mamy suka kunna hasken ɗakin, Mamy ta bi Islaha da kallo ganin yadda ta rame lokaci ɗaya, fuskarta ta canja ta nuna alamun damuwa mai yawa. Mamy ta ƙarasa ta zauna kusa da ita cikin damuwa ta ce, "Islaha are you okay?." Islaha ta ce, "Mamy Ina yini." Mamy ta ce, "ya jikin ki?." Ta ɗaga kai ta ce, "na ji sauƙi." Mamy ta ce, "taso mu je falo ki yi breakfast." Bata son yiwa Mamy musu saboda kulawar da take bata, hakan ya saka dole ta miƙe suka fita daga ɗakin Mamy tana riƙe da hannunta. Falon babu kowa sai ƙhamshi da yake yi mai daɗi, suka zauna Mamy ta yi serving ɗinta sannan ta miƙa mata ta ce, "ki sha tea sai ki ci abinci." Ta karɓa ta fara shan tea ɗin, sai kuma ta kalli Safeera ta ce, "Safeera ina wayata?." Safeera ta ce, "wayar ki tana nan, screen ɗinta ya lalace, ba a ganin komai sai fari." Mamy ta kalli Safeera ta ce, "meyasa baki faɗa min ba? Ai da sai a kawo mata wata…amma yanzu a ɗauko ta a ayi mata backup a computer, sai ta canja wata, tunda wannan ya lalace, kawo min kar a manta." Safeera ta dinga kallon Mamy jin wai ta lalace, dan kawai screen ya yi fari sai ace waya ta lalace? Ba screen ɗin kawai za a saka ta cigaba da aikinta ba? Ta gyaɗa kai tana aiyana masu kuɗi sun ji daɗinsu, ta koma ta ɗauko ta bawa Mamy Islaha dai bata ce komai ba. Sai da Islaha ta sha tea ɗin ta ɗan ci abincin, Mamy ta bata magani ta sha dan ta ji daɗin jikinta. Mamy ta riƙe hannunta cikin sigar kwantar da hankali ta ce, "Rehaan zai ji da komai, babu abinda zai same ki. Abinda ya faru a daren jiya kar ki saka shi a ranki duk plan ne." Islaha bata ce komai ba, sai kuka da take ji yana taho mata, ita ɗauka mafarki ta yi shiyasa take neman wayarta dan ta shiga ta ga da gaske akwai abinda ya faru ɗin, ashe gaskiya ne ba mafarki bane tunda ga shi Mamy ta faɗa. Mamy ta ɗago fuskar ta ta ce, "kar ki yi kuka, komai zai warware." Ta kwantar da kanta a kafaɗar Mamy tana hawaye, Mamy ta shafa kanta ta ce, "Ki daina kuka." Islaha bata ce komai ba ta yi shiru tana kwance a jikin Mamy. Mamy ta ce, "Ta so mu je apartment ɗina, akwai Baffa ki da Hammanki sun zo ganinki." Da sauri ta ɗago ta kalli Mamy, Mamy ta murmusa alamun da gaske ne abinda ta ji. Ta miƙe tsaye suka sauka tare su uku suka fita. Islaha bata bari ta kalli kowa ba, dan ta san kowa kallonta yake yi har suka shiga apartment ɗin. Suna shiga main parlour ta ga Baffa a zaune sai Saheer da ya kame a zaune fuskarsa babu walwala ko kaɗan. Islaha ta nufi inda Baffa yake ta zube a ƙasa ta ɗora kanta a guiwarsa tana kuka sosai, Baffa bai hanata ba, ya yi shiru yana jin kukanta har zuciyarsa. Ko Labiba da Hanan ne su ke kuka, baya jin kukansu har zuciyar kamar yadda yake jin na Islaaha. Sai da ta jima tana yi sannan ya ce, "ya isa Islaha, ki bar wannan kukan ni ba shi na zo ki yi min ba, na damu da ke, ina so na gan ki shiyasa na kasa haƙuri na nemi Safeera a waya har na zo gidan nan. Ki daina kuka, ki nutsu mu yi magana." Ta ɗago fuskar ta kaca-kaca da hawaye ta ce, "Baffa ban yi komai ba, ni ban san waye ya ɗauki video na ba, kuma abinda aka ce jiya na yi a gidan nan ban yi ba, ni ban san me ya faru ba” ta faɗa cikin ruɗewa ta manta da Baffa bai san abinda ya faru a gidan ba. Baffa yanɗaga mata kai ya ce, "na sani, ki nutsu mu yi magana, in kina kuka baza ki saurare ni ba." Ta goge hawaye sannan ya ce, "Allah ne ya rubuta miki wannan ƙaddarar, dole sai ta faru dake. Ki kwantar da hankalin ki, komai zai warware in sha Allah, ni na san ba ki aikata komai ba, duk wanda ya yi nufin cutar dake asirinsa zai tonu.” Ta ja numfashi ta ce, "Baffa kowa a banza yake kallona, kowa ba ya yi min kallon mutunci, kowa ya ga hotona jiya, ana ta tsine min Baffa." "Ki yi haƙuri, da gaskiya ta bayyana shikenan kowa zai zo yana ba ki haƙuri, duk wanda ya ga laifin ki a cikin rashin sani ne, ki daina kuka." Safeera ta ce, "ka yi maya faɗa Baffa, saboda wannan kukan har attack ya saka ta samu." "Subahanallahi! Ki yi haƙuri ki daina kuka, kin san kina da matsalar numfashi.” Islaha ta juya ido ta kalli Saheer da ya ke kallon ta ta ce, "Hamma ni ban yi komai ba." Kallon ta kawai yake yi bai ce mata komai ba, dan ko kaɗan bai so zuwa gidan ba Baffa ne ya yi masa dole sai ya rako sa, ya zo kuma sai ya ji ransa ya ɓaci gabaɗaya, bai san meyasa ya ji har ita kanta haushi take ba shi ba. Daƙyar ya buɗe baki ya ce, "Ki daina kuka, komai zai wuce, mun kai maganar human right, suna nan suna bincike." Mamy ta kalli Saheer dan tsaf ta san shine wanda take shirin aure in ta bar gidan, a binciken da ta saka aka yi mata har hotonsa ta gani. Ta ce, "kar ka damu, babu abinda human right zasu iya a kan case ɗin nan, wahala zasu dinga baka har sai ka gaji. Rehaan yana kan aikin case, an tabbatar min da har an gano mai account ɗin da aka fara fitar da nude ɗin, so a yau komai zai ƙare." Saheer ya yi shiru kawai yana kallon Mamy, yadda take magana ma abin kallo ne balle fuskar da kyaun da Allah ya yi mata. Ya sauke numfashi, dan ya zamar masa dole ya yi ƙoƙarin gano wani abu kafin Rehaan ya riga shi, ya zama dole ya zama silar farin cikin Islaha ba Rehaan ba. Amma ta ya zai bi? Wa zai samu da maganar a shige masa gaba a yi komai a gama kafin Rehaan ya riga shi?. Baffa ya dinga rarrashinta fa kalamai masu daɗi har ta nustu, kafin ya yi musu sallama suka fita ita kuma ta zauna a falon. Rehaan yana ɓangaren Abba, bai san da zuwansu Baffa ba, yana zaune yana jiran Abba har ya fito ya zauna yana kallonsa ya ce, "Rehaan yarinyar nan baki ya yi yawa a kanta, kana jin ahinda ake ta faɗa akan ɗan uwanka.” Rehaaan ya ce, "Abba duka zan yi bincike a kai, in na tabbatar abinda ya faru gaskiya ne zan yi abinda kace, amma a yanzu ka bari na cikawa Mamy alƙawarinta don Allah." Abba ya girgiza kai ya ce, "Rehaan ni ba ƙi nayi ba, amma ina so ka tuna ko da bata aikata ba yadda baki ya yi yawa a kanta rabuwa da ita shine mafita. An yi waje ka ce zaka yi bincike, na cikin gidan ma bincike zaka yi?.” Rehaan ya kalli Abba yana tuna lokacin da ya same shi ya faɗa masa ba ya son auren, amma ya dinga ba shi haƙuri yana yabonta, yana cewa zai yi alfahari da ita ya yi haƙuri, amma sai ga shi yau kuma shine ya ke kushe ta. Abba ya ce, "Daada ta matsa wuta akan yarinyar nan, itace tana sonta yanzu kuma ta ce bata so. Ka san Daada sa riƙo da al’ada, ta riƙe al’ada kamar yadda ta riƙe addini, duk abinda zai ɓata sunan Fulani bata ƙaunarsa. Dan haka ka yi gagggawa a san abinda za a yi." Zai yi magana ya ga ɗaya daga cikin masu aiki akan case ɗin nan yana kiransa, bai ɗauka ba ya kalli Abba ya ce, "Abba zan yi duk abinda ya kamata, yanzu ma akan case ɗin nake." Kafin Abba ya yi magana ya ce, "zan je Abba." Ya ɗaga masa kai ya fita yana ɗaukar wayar. Daga can ɓangaren aka ce, "Sir mun samu masu main account ɗin, yanzu haka suna hannunmu." Rehaan ya yi ajiyar zuciya ta jin daɗi yana lumshe ido kafin ya buɗe ya ce, "A kai su guest house." "Amma sir za mu barsu a office mu yi bincike." "Ina so a yi komai ina nan." "Okay Sir." Ya kashe wayar ya kira Shams a waya suka hau mota suka tafi gidan. A can ya same su gabaɗaya harda Jazy, yana shiga ya kallu wacce ta ke durƙushe a ƙasa tana kuka, ya kalli officer alamun ƙarin bayani. Ya ce, "Ummi Lamiɗo, itace ta yi creating account ɗin, amma ba da wayar ta aka yi posting ba, an yi posting da wata wayar ne." Ummi ta ɗago ido dan ta ga wanda ake yiwa bayani ta ga Rehaan a zaune yana kallon wanda yake yi masa magana. Cikin firgici "Mr Rehaan!." Officer ya kalle ta ya ce, "Ummi." Ta kalle shi ya ce, "dake da wa ku ka haɗa kai ku ka yi wannan aikin?." Ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "ni ban san komai a kai ba, abinda na sani kawai an buɗe account da wayata, bayan nan ban san komai ba." "Waye ya buɗe account ɗin?." "Muslim ne, abokin aikinmu gabaɗaya har Islaha." Officer ya ɗauki waya ya saka a kunne ya ba da umarnin kawo Muslim da ya ke hannu, daman ya tambayeta ne dan ta maimaita Rehaan ya ji. Babu jimawa aka shigo da shi aka duƙar da shi a wajan, Muslim ganin Rehaan sai da gabansa ya faɗi sosai ba kaɗan, duk da Rehaan ɗin ba shi yake kallo ba amma kwarjininsa ya cika wajan. Officer ya ce, "Muslim!.” Muslim ya kalle shi sannan ya ce, “meye dalilin ka na yaɗa hotunan nan?." Muslim ya kalle sa ya ce, "ni ban aikata komai ba, sharri ta yi min." Ummi ta ce, "ƙarya yake yi wallahi, shine ya yi komai, har ƙoƙarin zuba mata acid a fuska ya taɓa yi, ranar da aka taɓa sace ta, ya yi ƙoƙarin lalata mata fuska, wallahi shine." "Kema ba kin ce sai kin ga bayanta ba? Na ga case ɗin har yanzu yana gaban yan sanda. Ke ki ka ce sai kin kashe ta, kuma wannna hanyar ma hanyar kisa ce." Officer ya ce, "Muslim kar ka yi mana wasa da hankali, ka kalli wanda yake gabanka a zaune…” ya faɗa yana nuna masa Rehaan. Muslim ya sunkuyar da kai Officer ya ce, “ka faɗa mana gaskiya kawai, meye dalilinka na aikata haka?." Muslim ya yi shiru sannan ya ce, "saboda ta fi mu ɗaukaka ne kawai, mun kasance mune gaba kafin zuwanta, tunda ta zo kowa sunanta ake kira, mu aka manta da mu kamar ba da mu aka yi gwagwarmaya ba.” "A ina ka samu hotuna da videon da ka yaɗa?." "AI ne ya yi, ba hotunanta bane, Mun yi amfani da AI wajan haɗawa, mun ƙirƙira mun yi ne ba dan mun san ya jikinta yake ba, abu ɗaya mu ka sani a kan surar jikinta, tana da bracelet a hannunta sannan tana da dogon gashi. Fuskar ta kaɗai muka yi amfani da ita, amma bayan fuska komai ba nata bane.” "Ya aka yi ka san tana da dogon gashi?." Ya nuna Ummi ya ce, "itace ta ke gani in sun je sallah." "Kana nufin yanzu AI ne ya haɗa wannan video?." "Wallahi shine, mun samu wanda ya ƙware a fanni shine ya haɗa mana. Amma wallahi duk abinda mu ka ce ƙarya muke yi mata. Har Chairman ɗin mu muka samu aka haɗa ƙarya da gaskiya da muryar Islaha, mu kace tana kai sirrin gidan wani waje, duk ƙarya muke yi.” Officer ya ce, "ƙoƙarin zuba mata acid fa a wancan lokacin?." Muslim ya ce, "mun yi niyar lalata mata fuska ne, yadda mutane zasu daina marmarin son ganinta, bayan wannan babu komai." Officer ya kalli Rehaan ya ce, "that’s all Sir." Rehaan ya kalli Jazy da ba shi ya ke kallon ba su Muslim yake kallo, kafin Jazy ya ce, "Offier a yi musu video yanzu nan su faɗi laifinsu da bakinsu, sannan a kai su kotu ta yanke musu hukunci daidai da abinda suka aikata.” Ummi ta ce, "don Allah Mr Jafar, don girman Allah ka taimaka kar a kai ni kotu. Na amsa laifina dan a yafe min, wallahi bazan sake kallon Islaha ba balle na yi mata wani abun, ka yi haƙuri ka yafe mana don Allah." Babu wnada ya kula takamar da kurame take magana, Officer ya ce, "ke abin ya yi miki yawa ai Ummi, bayan wannan laifin, ga furucin sai kin ga bayanta…..” Ya kalli waɗanda suke tsaye ya cr, “Ku ɗauke su mu je" a take aka fita dasu suna ta magiya babu wanda ya sauraresu. Jazy ya ce, "good job Officer! Amma ina so a tabbatar an sun yi video, sannan duk wani blog da ya saka hoton ko video nan a tabbatar da an goge shi, ko da nan gaba in aka kuma ganin wani ya ɗora hoton kawai a kama shi." Officer ya ce, "an gama Mr jafar. Abin daɗin ma da ba ita ɗin ba ce computer ce, amma za a yi maganinsu, ko dan masu hali irin nasu." Suka yi sallama suka tafi aka bar Jazy da Rehaan da ya kasa magana. Jazy ya ce, "Mamy ta faɗa min abinda ya kuma faruwa a jiyan, mutanen gidan ku sun dage sai sun ga bayan yarinyar nan. Rayuwar ta abar tausayi ce gabaɗaya, bata cancanci wannan takurawar da baƙiin cikin da take ƙunsa a gidanku ba.” Rehaan ya ɗago ido ya kalle sa, bai ce masa komai ba ya miƙe ya shiga ciki. Nana Haleema. KRBBK: RDB3P71 Nana Haleema. Sunana Ummi, ni abokiyar aikin Islaha ce. Ni da abokin aikina Muslim, muka haɗa kai aka ƙirƙiri AI video da fuskar Islaha, mu ka yaɗa a duniya da sunan itace take fasiƙanci bayan ba ita ba ce, bata san ma mun yi ba. Wallahi ba Islaha bace, mu muka haɗa ba tare da ta sani ba. Mun yi ne saboda son zuciya, muna ganin ta fi mu ɗaukaka, kowa a wajan aikin mu ita yake so bamu ba. Har maganar sirrin gidan da muka ce tana fitarwa ta wajan aiki duk shirin mu ne, wallahi bata san komai ba. Mun yi ne dan mu tozarta ta. Abinda yake yawo a duniya kenan, kafin magrib labari ya cika ko ina, wasu suna tausayin Islaha, wasu kuma suna ganin kawai an yi ne dan a kare ta. Islaha Mamy ce ta saka ta ta yi bacci babu wanda ya tashe ta ya faɗa mata, sabuwar wayarta tana hannun Safeera, duk wanda ya kira itace take ɗauka ta ce bacci take yi. Sallah ce ta tashe ta, ta miƙe tayi alwala tayi sallah ta fito falon Mamy. Sai da ta zauna sannan Safeera ta nuna mata abinda yake faruwa, ta buɗe baki tana kallon Ummi da Muslim da suka yi wujiga wujiga alamun sun sha baƙar wahala, ta rufe baki da hannunta hawayen farin ciki yana zubo mata. Ta kalli Safeera tana dariya kuma tana hawaye ta ce, "da gaske bani bace haɗawa aka yi?." "Ba ke bace Islaha, haɗawa aka yi, kuma an goge su kaf, ko a tiktok babu." Islaha ta ce, “Ummi da Muslim ne zuka haɗa min wannan abun?." "Ga shi Allah ya tona musu asiri." Mamy da ta ke kallon ta murmusa ta ce, "ba kuka za ki yi ba, murna za ki yi." Ta kalli Mamy ta ce, "Mamy akan aikin jarida aka yi min wannan sharri? Akan aiki aka so a zuba min acid, akan aiki aka so kashe ni? Mamy me na tare musu?." "Mutane kenan ai, Allah ya kare ki daga sharrinsu." Islaha ta girgiza kai tana sake kallon videonsu tana mamakin wannan sharrin da suka yi mata. Safeera ta miƙa mata waya ta ce, "Ga Baffa." Ta karɓa suka gaisa da Baffa yana yi mata murna akan abinda ya faru. Islaha ta kira Saheer bai ɗauka ba sai bata sake kira ba ta ajjiye wayar. Islaha ta kalli Mamy cikin farin ciki ta ce, "Mamy ta ya aka yi aka gano su ne?." Mamy ta ce, "an yi nemo main account ɗin da suka buɗe, ita kuma da gmail ɗinta aka buɗe shi, ta haka aka gano su." "Kenan ana iya gano mutum ko da ya karya sim card ko ya goge account ɗin?." "Ga shi kin gani." "Amma muna da waɗanan kayan aikin a nigeria me ya hana a dinga bibiyar masu garkuwa da mutane a kama su? Tunda har aka iya kamo su Ummi da suka buɗe account a tiktok a cikin kwana ɗata, za a iya ganosu suma." Mamy ta yi murmushi ta ce, "kedai ki bar nigeria, wani abun in aka yi sai ki ga kamar plan ne." Islaha ta yi shiru tana jin daɗi ba hotunanta bane AI ne, amma ta jin tsoron sharrin da aka yi mata a cikin gidan. Daada tana can tana danasanin abinda ta yiwa Islaha akan hotunan, duk ta damu sosai tana jin babu daɗi a ranta, amma kuma batun Salman take maimaitawa.Bayan sallar i'sha Hajiya Daada ta haɗa meeting kamar yadda ta saba, aka kira kowa har Rehaan. Daada ta ce, "na ga waɗanda suka yi mata sharri, tunda an tabbatar ba ita ba ce wannan ya wuce. Amma na cikin gidan nan fa, ba ƙaramin abu bane ba fa." Umma ta ce, "ni dai ta bar gidan kawai, daman tana zaune da Rehaan, tana amsa sunan matarsa ba dole a rufe gaskiya a fito da ƙarya ba? Mu za a rainawa hankali ace AI ne? Mu za a mayar marasa wayo da ilimi ace wannan videon AI ne?. Hmmm, ni dai kawai a yi mana iyaka da ita, baza ta lalata min yaro ba wallahi." Daada ta ce, "Ina son Ishlaya, abinda na yi mata jiya ma duk ya dame ni. Amma akan Salman gwara a rabu da ita ɗin ya fi.” Rehaan ya ɗago ido ya kalli Daada sannan ya juya ya kalli Islaha da kanta ya ke a sunkuye. Daada ta ce, "bazai yu a ce yarinyar da aka kama dumu-dumu da ɗan uwanka kuma kake zaune da ita ba, dole a raba auren nan ko ba ka so." Rehaan ya ce, "Za a rabu ɗin, amma a bani lokaci, akwai abinda nace zan yi." Umma ta ce, "ba ka isa ba wallahi, dole ta bar gidan nan tunda ba gidan ubanta bane” Umma ta fara ɓata masa rai. Rehaan ya sake ɓaci jin ana zancen ubanta, shi bai ga dalilin zaginta a cikin maganar nan ba, ya ga alama Umma tana son zagin Islaha tunda jiya ma haka ta yi. Hakan ya sakaya haɗewa Umma rai ya kalle ta ya ce, "amma ni gidan ubana ne ko?.” "Gidan ubanka ne ba ubanta bane, dan haka dole ta bar gidan nan wallahi. Salman da ya ke babba an fara dashi ina ga yara mata ƙananu? Aka san abinda zata yi mu su? Ga jikokin gidan nan maza da mata, aka san abinda zata yi musu? Ai zama da ita ba shi da alkhairi ko kaɗan, dole ta bar cikin gidan nan." Kowa ya yi shiru bai ce komai ba Daada ta ce, "ni ban taɓa ganin rashin kishin kai irin wannan ba, ace an kama matar mutum da namiji kuma ɗan uwanka amma ka ce a bar maganar?." Ya yi ƙaramin tsaki ya miƙe tsaye ya ƙarasa inda Islaha take kamar yadda ya yi mata jiya, bai jira ya miƙa mata hannun ba ya riƙo hannunta ya miƙar da ita tsaye ya kalle su ya ce, "Matata ce ko? Tunda kun yarda matata a ƙyale ni na yi abinda na ce, ina kishi ko bana kishi duk babu ruwan ku, zata cigaba da zama a gidan nan kamar kowa." Cikin ɗaga murya Umma ta ce, "ba ka isa ba! Wallahi dole ta bar gidan nan." Rehaan bai kula Umma ba ya kalli da Daada ya ce, "ku kuka tsara ta zauna a nan ɗin tun farko, da kun yarda na zauna da ita a wani gidan da ba a yi haka ba, dan haka babu inda zata je wallahi. Tana da ikon zama a gidan nan kamar kowa, yadda Mamy zata ce nan gidan mijinta ne itama haka zata ce gidansu mijinta ne!. Wallahi baza ta tafi ba, kuma babu wanda zai saka ta bar gidan nan, na ce wallahi!” Ya sake maimaita yana kallon kowa da mamakinsa ya hana su magana Ya kalli Islaha da ta ke kallonsa cikin mamakin canje canjen da take gani daga halayensa, sai ya haɗe rai ya ce, "let’s go" ya faɗa yana jan hannunta suka fita. Mama ta ce, "Tabɗijam! Yaro ya lalace, an asiricesa, an kai shi wajen malamai sun yi masa wanka da ruwan magani. Yanzu Daada tana magana zai riƙe hannun natarsa su fita? Lallai Daada sai mun miƙe da addu'a." Umma ta ce, "babu wani asiri, iskanci ne dan ya ga babu wanda ya ke iya ɗaukar mataki a kansa, yana ganin komau in ya yi daidai ne, yana ganin ya fi kowa arzuƙi a gidan nan shiyasa ya ke wulaƙanci da ya ga dama. Ni dai bazan bari a cigaba da cutar min da yaro ba, zan tattara kayana mu bar gidan, tunda an nuna min itace matar Rehaan Yola, babu mai iya yi mata hukunci." Umma ta faɗa tama fita a fusace. Daada ta kasa magana saboda Rehaan ya kashe mata baki gabaɗaya, daman Abba ne mai dakatar dashi shima kuma ya yi shiru bai ce komai ba, Mamy ma tuni ta fice dan bata son ɓacin rai. Rehaan har falo suka shiga yana riƙe da hannunsa, sai da suka shiga sannan ya saki hannunta ya kalli fuskar ta suka haɗa ido ya juya zai hau sama. Islaha cikin taushin murya ta ce, "Mr Rehaan!." Ya tsaya cak ya waiwayon ya kalle ta suka sake haɗa ido, ta ɗauke kai ta ce, "Thank you so much." Ya zuba mata ido na wani lokaci kafin ya juya ya hau sama bai ce mata komai ba, amma a ransa yana maimaita kalamar Mr Rehaan ɗin nan, yana so wata ran ya ji ta ce Rehaan without mr nan da ta laƙabawa bakin ta amma bata taɓa faɗa ba, ko yaushe sai ta saka masa Mr a gaba kamar a office. * "Saheer!." Firgita ya yi ya kalli Sadik da ya zauna a kusa da shi ya ce, "ya na ganka cikin tunani bayan murna zaka yi waɗanda suka yiwa Islaha sharri suna hannu?." Ya kalle sa ya ce, "ba wai ban yi murna bane, kawai ban ji daɗi da ya zama ta silar Rehaan aka same su ba, na so ace ni na yi wannan aikin ba shi ba." "Laifi ne dan ya zama sila? Kai dai tunda an kama su ai komai ya ƙare ko?." "Ban so hakan ba, kawai na tsorata da lamarin Rehaan ɗin nan, jiya da mu ka je gidansu da Baffa gabana faɗuwa ya dinga yi, tunda nake ban taɓa shiga gida mai girmansa ba. Sannan yadda babarsa take yiwa Islaha tana nuna mata ƙauna abin ya burge ni, ta wani ɓangaren kuma bai yi min daɗi ba ko kaɗan. Ina ruwansa da tsaya akan lamarin nan? Sai na ga kamar wannan aikina ne ba nasa ba." Ya yi dariya ya ce, "gwara da ka ce kamar aikinka, kamar ɗin da ka saka a maganar ka ya tabbatar da kaima kana kokwanto akan maganar ka. Ya mutum da matarsa ka ce ba shi da hurumi akan wannan caese ɗin? Duk da a yadda auren nasu yake amma kaima da kanka ka san matarsa ce." Ya rufe ido ya buɗe ya ce, "don Allah ka daina faɗa, zuciyata bugawa take yi, tun ɗazu nake ganin kiranta ana na kasa ɗauka, har yanzu ba mu yi magana ba balle na ta ya ta murna akan hakan. Na fara jin tsoro wallahi, na fara tantama akan anya Islaha zata dawo gare ni?." Sadik ya daki kafaɗarsa ya ce, "tunanin da nake so ka yi tun farko kenan amma ka kasa ganewa. Saheer fitowar Islaha daga gidan nan abu ne mai matuƙar wahala, duk da na san zata yi iya bakin ƙoƙarinta dan ganin ta dawo saboda halaccin ka, amma ni a jikina ina jin bazata fito ba. Shiyasa tun farko na ce ka karɓi aikin nan, in ta dawo shikenan, in bata dawo ka samu abinda ka samu. Taurin kan ka ya saka ka kasa fahimtar abinda nake nufi." "Sadik ina son Islaha har gobe, ina kuma fatan ta fito na aure ta…..” "Nima ina yi maka wannan fatan, amma da kamar wahala. Daga jiya zuwa yau har an tabbatar da an kama waɗanda suka yi mata sharri, in da case ɗin a hannunka yake ana nan ana wahalae da kai ace ka je nan kaje can. Amma da yake shi wani ne a ƙasar ga shi har an zo ƙarshe, ko baka so dole ya burge islaha a wannan ɓangaren, duk rashin son da take yi masa dole ta gode masa indai ita ƴar halak ce.” Saheer ya sauke numfashi ya ce, "Na san da hakan. Sadik na san na san gaskiya, duk abinda ka ke faɗa na san gaskiya ne, kawai na kasa fahimta ne.” Ya taɓe baki ya ce, "in za ka nutsu ka kama kanka ka yi, in baza ka yiwa kanka faɗa ba za ka tashi da tutar babu, ba wan ba ƙanin. Ni dai ina faɗa maka ka samu damar da zaka tara, ka samu ka haɗa abinda zaka haɗa yadda ko bata dawo ba ka samu abinda ka samu." "Nayi ya da zuciyata?." "Ka cigaba da haƙuri, in so cuta ne haƙuri ma ai magani ne" ya faɗa yana miƙewa ya fita daga ɗakin ya bar Saheer da tunani kala kala a zuciyarsa.... Nana Haleema RDB3P72 Nana Haleema. Washe gari da safe Safeera ta shirya tsaf zata tafi, bata ga Islaha ba ta fito falon ta tarar babu kowa, tana nan tsaye sai ga Islahan ta shigo ta ce, "Islaha ni daga wajan aiki zan wuce, Chairman ya kira ni." Islaha ta ce, "don Allah ki zauna Safeera kar ki tafi." Safeera tabbuɗe ido ta ce, "in zauna na yi miki me? Na ga ai kin ji sauƙi ko?." "Ni dai ki zauna zuwa next week sai ki koma." "Lallai sannun ki. Chairman ya kira ni yana so ku yi nagana, yana ta bani haƙuri akan na ba ki haƙuri." Islaha ta dafe kanta ta zauna a akan kujerar parlour da babu haske ta ce, "ni na gama aikin nan Safeera, ko da basu zarge ni akan ina fitar musu da sirri ba na daina, balle an zarge ni akan abinda ban aikata ba. Haka kawai akan aiki za a nemi ganin bayana? Sai ka ce aikin shiga aljanna ko na samun rahama? Su je can su ƙarata, amma ni na daina aikin gabaɗaya." Safeera ta ce, "saboda su sai ki daina?." "Ai na ma daina Safeera, ki je kawai, in ya tambaya ki ce na daina aiki, amma don Allah ki dawo ta nan." Hasken falon aka kunna dukkansu suka kalli wajan, suka ganshi sanye da manyan kaya yana waya kamar ba ya son magana. Safeera ta juya zata tafi, dan gabaɗaya kwarjini yake yi mata sosai, har mamakin Islaha take yi in ta ga yadda take faɗa masa duk abinda ta ga dama, ita ko kallonsa bata iya yi saboda kwarjini. Zata sauka kenan Islaha ta ce, "don Allah ki dawo, kar ki tafi gida." Ta waiwayo ta ce, "Islaha na bar Mama da ƙannena su kaɗai, ina so na koma gida nima." Kamar zata yi mata kuka ta ce, "ni dai don Allah ki dawo in kin tashi daga wajan aikin, kar ki tafi." "Ki zo mu tafi aikin, sai in dawo." "Har abada, na gama aikin jarida." "Shine burin ki fa." "Na ajjiye." Safeera bata sake magana ba ta sauka tana dariya. Bata sake kuskuren sake kallon inda yake ba, har mamaki take yi in yana waya anya mutanen da ya ke magana dasu suna jin me yake faɗa? Magana yake yi kamar ba ya so, a ciki yake maganar yana yatsine fuska kamar ko yaushe. Rehaan ya yi ajiyar zuciya yana shafa kansa, ta ƙasan ido take kallonsa ya cigaba da danna wayarsa. Murmushi ta ga ya yi har haƙoransa suka bayyana, ya lumshe ido still yana kallon wayar bai ce komai ba. Sai kuma ya kalli fuskar wayar alamun video call ya ce, "kin raina ni?." Cikin english ta ji mace ta ce, "me ka ce? Ka san ban iya fulfulde ba balle hausa." Ya sake yin murmushi kafin ya canja harshe zuwa hindi suna hira yana ta murmushi kamar ba shi ba. _Budurwarsa ce mana, in ba ita ba wa zai dinga yiwa wannan murmushin?. Ko Mamy ba ya yiwa wannan fara'ar, amma yana yiwa wata yar india, shima da alama ya yi gadon babansa, ya ɗauko yar india. Amma bata yi sa'a ba, zata auri ragon maza. Duk da ya yi min kirki kuma ya taimake ni, amma bazan fasa faɗar halinsa._ Ita kaɗai take gulmarsa a zuciyarta, bata san me ya tsare mata ba take gulmarsa ba. Sai kuma ta ga ya kashe wayar ita dai bata ce masa komai ba shima kuma bai ce mata komai ba.A lokacin aka kira ta a waya ta saka a kunne ta ce, "Hamma Saleem ya aiki?." Saleem ya ce, "Lafiya lau Islaha, ba ki taho ba?." "Na gama aiki da ku ai, ni na ajjiye jarida gabaɗaya." "Meyasa?." "Haka kawai." "Haba Islaha, kamar ba ke ba? Don Allah kar ki taorata." Ta taɓe bakinta cikin ko in kula ta ce, "Saleem kenan, zamu yi magana zuwa gobe in sha Allah" daga haka ta yanke wayar a bayyane ta ce, "haka kawai akan aiki ana neman kashe ni, me zai saka na koma? Su je su yi duk abinda suke so, ni na daina." "Tsoro ki ka ji?." Da sauri ta juya ta kalle sa ta ga ita yake kallo da alamun shi ɗin ne ya yi magana ba wani ba, suka haɗa ido dan bata taɓa tunanin zai yi magana ba. Islaha cikin sanyi murya ta ce, "Eh tsoro nake ji, bazan iya zama a inda aka ƙoƙarin kashe ni ba, bayan kisa harda sharrin da bazan manta da shi ba. Har yanzu wasu basu yarda bani ce a videon nan ba, akan me zan kai kaina inda ake son kashe ni? Gwara na haƙura kawai." Ta ƙarasa tana sunkuyar da kanta ƙasa Ya zuba mata ido yana nazarinta sannan ya ce, "Kina son aikin?." Ta ɗago tana kallonsa, sai ta yi raurau da ido kamar zata yi kuka ta ce, "amma aikin ba ya sona, ina son aikin jarida saboda burina ne, amma aikin jarida ba ya sona. Gwara na haƙura na basu space tunda suna ganin nice nake tare musu ɗaukakarsu, sai su yi abinda suke so." Yadda take kallonsa idanunta ya ciko da hawaye ya saka shi ya lumshe ido ya buɗesu a kanta, ya gyara zama yana kallon ta ya ce, "ai su basa nan, beside yau za a kai su prison." "Bayansu akwai wasu, tunda aka samesu za a samu wasu masu irin ƙudurinsu a zuciya. Gwara na haƙura kawai, na yi fatan Allah ya zaɓa min abinda ya fi alkhairi a rayuwata." Ya yi shiru kamar bazai ce komai ba sai daga baya ya ce, "in tsoro ya saka ki ka ajjiye abinda ki ke so an yi nasara a kan ki, sun samu nasara tunda kin bar abinda suke so ki bari. Behind every success there are challenges, Every achievement comes with its own unique struggles, ke wannan ne ƙalubalen ki. Ba dani da ke aka yi attacking ɗina ba?." Islaha ɗago ido tana kallonsa ganin yadda ya zuba mata ido yana kallon ta kamar ba shi ba, ya ga ya wani nutsu yana magana kamar ba shine mai talakarta da faɗa ba. Sai ta ɗaga masa kai ta ce, "eh dani, but...." Ya dakatar da ita ya ce, "but what..? Ina da banbanci dake?." "Eh mana, kai daban ni daban." Ya yi murmushi ya ce, "every succes is succes. In ki ka bari aka yi nasara a kan ki kin faɗi" ya faɗa yana yi mata alama da thurm ɗinsa ya juyasa ya kalli ƙasa alamun rashin nasara. Ta kalle sa tana mamakin yadda yake yi mata maganar da zata ƙara masa ƙarfin guiwa, basu taɓa doguwar magana shi da ita irin haka ba, sai dai faɗa ya haɗa su. Rehaan ya ce, "ki cigaba da aikin ki as you can, in za ki bari ki bari saboda ra'ayin kan ki ba dan wasu ba. So don't let anythings make you afraid, har ki ce za ki daina aikin ki saboda su." Islaha ta yi shiru tana sauraren yadda yake yi mata magana cikin yanga da iyayi, ba a taɓa yi mata maganar da ta shiga zuciyarta lokaci ɗaya ba, bata taɓa jin bata son abu an yi mata magana ta ji tana so ba sai yanzu. Jin kalamansa take yi kamar ruwa ya ɗauka yana watsawa zuciyarta har ta wanke tas, tana tunanin wato shiyasa masu kuɗi suke samun nasara a rayuwarsu, ba sa barin ƙaramin abu ya tayar musu da hankali har su daina abinda yake gabansu saboda shi. Ta ɗago ta yi masa murmushi a karo na farko a zamansu, ta yi masa murmushin da ya kai zuciyarta ba iya fuskar ta ya tsaya ba. Ta ɗaga masa kai ta ce, "na gode." Bai ce mata komai ba ya ɗauke kansa amma shi kansa ya ji daɗin hirasu, basu taɓa zama sun yi magana haka ba sai dai faɗa ya haɗasu, amma yau sai ya ji abin daban a ransa. Kiran da ya shigo wayarta ya saka ta ɗauka ba tare da damuwa ba ta ce, "Hamma tun jiya nake kiran ka ba ka ɗauka, kana ina?." Saheer ya ce, "bana jin daɗi ne. Ya ki ke?." Islaha ta ce, "me ya same ka?." "Kar ki damu ba wani abun bane. Kina lafiya, ina fatan kin samu sauƙi ko?." Ta ɗaga kai kamar yana gabanta tana wasa da adon rigarta ta ce, "na ji sauƙi." "Komai ya wuce ko?." Ta ɗaga kai ta ce, "ya wuce Hamma. Ashe daman Ummi da Muslim ne? Daman ka jima kana cewa baka yarda da shi ba, ni kuma har ga Allah da zuciya ɗaya nake tare dasu." Saheer ya ce, "ke dai ki ga mutum kawai." "Haka ne kam, Yaushe za ka koma?." "Zuwa next week zan koma, bazan dawo ba sai kin dawo gida." Ta yi numfashi ta ce, "ni fa ko na bar nan bazan dawo gidan Mama ba, gwara na samu wani wajan na zauna." Saheer ya ce, "zamu san abinda zamu yi in lokacin ya yi, saura kwana nawa?." Islaha ta ce, "saura sati biyar lokacin ya cika, lokacin ne ba ya gudu, kamar ba kwana ake yi ana tashi ba. Gabaɗaya na gaji da zaman, so nake nauyin da yake kaina ya sauka na huta." Saheer ya ce, "uhum! Har wani nauyi ne a kan ki?." "Hamma aure fa, ai ka san ko ya ya ne aure dai sunansa aure. Nauyi ne a kaina mana, tunda Allah ne ya ɗora min." "Ya yi kyau. Sai ki sauke nauyin ai." Ta yi dariya ta ce, "ina nan ina sauke shi." Saheer ya ce, "shikenan zan je wajan Adda." "Sai ka dawo." Daga haka ta yanke wayar ta ɗora ta a ƙirjinta ta rufe idanunta, dan ita har ga Allah ta manta da Rehaan a wajan, wayarta take yi da zuciya ɗaya ta manta shaf yana wajan a zaune. Sai ta buɗe ido ta ce, "saura kwanaki kaɗan na bar gidan nan na huta da wannan tashin hankali, ni kaina na ƙosa lokacin nan ya yi, ko za a daina yi min sharrin ina kawo wani parlour nan" ta faɗa tana lumshe ido tare da kwanciya a jikin kujera. Rehaan yana jin duk hirar da take yi, har amsar da Saheer ya ke bata yana ji. Lokaci ɗaya ya ji zuciyarsa babu daɗi ko kaɗan, ya so ya tashi ya bar mata wajan, amma gudun kar ta yi tunanin wani abun ne sai ya zauna, amma ko kaɗan bai ji daɗin wannan wayar ba ko kusa, har zuciyarsa yake jin kalamanta ma su ɗaci. Ya sake kallon ta ya ga idanunta a rufe, ya ɗauke kai yana tunanin da gaske saura wata ɗaya, ya aka yi lokacin ya yi gudu haka bai sani ba?. Ya miƙe ya sauka, giftawarsa ta gani ta buɗe ta ga har ya sauka. Sai ta ɗan ji wani iri a zuciyarta kamar bata kyauta ba ta ce, "ashe fa yana nan nake waya da Hamma." Sai kuma ta ce, "to meye dan na yi wayar, ai ba wani abun nake faɗa ba gaisawa ce kawai."Da wannan tunanin ta share komai ta cigaba da harkokinta, ana ta yi mata waya ana yi mata murnar abinda ya faru tana jin daɗi. Bata yarda ta sauka ƙasa ba, kar ta haɗu da wani ɗan gidan a ɓata mata rai. Shi kuwa Rehaan kai tsaye gidan Riyya ya wuce, ya samu bata nan amma jazy yana nan, ya zauna ya rufe ido bai ce komai ba. Jazy ya share shi shima dan bazai kula shi ba ya san banza zai yi masa. Sai da ya gama zaman sannan ya ce, "a wanne date mu ka yi signing contract ni da c wife?. Jazy cike da mamaki ya ce, "ikon Allah! Lokacin ma ni zan riƙe ma ka?." "Jazy ka amsa min kawai." "Ban sani ba, ai ba ni na ke zaune da ita ba balle na riƙe." "Na ji tana saura one month fa." "It can be possible ai." Ya yi shiru sannan ya ce, "lokacin ya yi gudu sosai." "Ba ka so ya yi gudun ne?." "No, kawai dai..." sai kuma ya koma ya jingina da kujera bai ce komai ba. Jazy ya ɗan kall sa sannan ya ce, "so meye na damuwa dan lokacin ya zo, daman ba abinda ku ke jira kenan ba?." Ya kalle sa ya ɗafa kai ya ce, "yeah haka ne." "So take a chill pill, lokacin da ka ke jira ya kusa, ku rabu ka huta da wannan tashin hankalin itama ta huta, ba shikenan ba?." Wata irin bugawa zuciyarsa take yi, tana zafi-zafi kaɗan-kaɗan ba tare da ya san dalilin hakan ba, ya sake jingina da kujera ya ɗora ƙafa kan ɗaya ya sake rufe idanunsa. Murmushinta na ɗazu ya gifta masa a idanu, ya buɗe idonunsa ya sake rufewa, ranar da ya kwance mata towel ya gifta a idanunsa, da yadda dogon gashinta ya mamaye fatar jikinta. Da sauri ya buɗe ido, yana jin wani irin shock mai ƙarfi har brain ɗinsa. "Oh my god!" Ya furta ba tare da ya sani ba yana sauke numfashi a hankali. Jazy ya kalle sa ya yi dariya bai ce masa komai ba. Rehaan tunda ya yi shiru bai kuma magana ba, sautin bugun zuciyarss kawai yake ji, bai san abinda yake damunsa ba kawai ya san ba ya jin daɗi a jikinsa. Sai kuma ya kalli Jazu ya ce, "a kan waye ma ta yi signing?." Jazy ya kalle shi ya ce, "saurayinta Saheer. Yanzu haka suna shirye-shiryen aure, kana sakinta zai yi wuf da kayarsa, daman babu idda a kanta balle a ce sai an jira, kuna rabuwa a ranar zata faɗa gidan masoyinta." Ya shafa kansa bai ce komai ba yana girgiza ƙafa, jikinsa har wani rawa yake yi saboda sabon yanayin da yake mamaye masa jikinsa gabaɗaya, yana ƙoƙarin ɓoyewa ne saboda kar Jazy ya tambayesa dalili shi kuma bai san me zai ce ba. Jazy da yake kallonsa ta ƙasan ya ce, "Ai yaron nan yana matuƙar ƙaunar ta, kuma ya yi sa'a sosai, ya samu mai ƙaunarsa. Ta yi aure saboda shi, kuma zata fita saboda shi. Babban abinda ya saka nake taya shi murna shine a zaman auren da tayi babu abinda ya canja daga gare ta, yadda ta shiga haka zata fito, haka zai ɗauki kayyasa sabuwa dal." Ya runtse ido yana jin wani abu yana sukar ransa, ya buɗe idanunsa cikin son kawar da wancan yanayin da son kushe ta ya ce, "Ita wannan har wata sabuwa ce? Ka manta wacece ita?." Ya yi dariya ya ce, "kai a wajanka ta ke a haka, shi a wajansa sabuwa ce dal. Yadda ko wanne ango yake mararin amaryarsa, shima haka yake mararin matar da za ka saki." Ya yi tsaki kawai bai ce komai ba, ya sake kallon sa kamar zai yi magana sai ya share ya rufe ido. Jazy ya girgiza kai yana kallonsa yana dariya tare da godewa Allah, ko ba a faɗa ba ya san Rehaan ya faɗa tarkon love, Rehaan yana son Islaha, rabuwa da ita zai yi matuƙar wahala. Ita kuma har yanzu ba ya gabanta, Saheer ɗin ne a gabanta, dan shi ta auri shi. Ko ya wannan chakwakiya zata kasance?. Nana Haleema. RDB3P73 Nana Haleema. Islaha ta koma wajan aikinta kamar yadda Rehaan ya bata ƙarfin guiwa ta yi amfani da kalamansa ta cigaba da harkokinta tunda ba a san matarsa bace har lokacin. Su Ummi kuwa suna prison an yanke musu hukunci, daga gidan kuma a ɓangaren Salman bata kuma jin komai ba, hasalima Umma da Salman ɗin ba sa nan. Sai dai yanzu babu magana ita da Mama, har Daadan ta daina zuwa gaishe ta. Da yake shine mai faɗa a ji a gidan babu wansa ya sake tayar da maganar balle a ce ta bar gidan, kowa ya shiga hankalinsa. Gab da zata tashi daga aiki su gama gaisawa da Hamma a da ya koma Niger yana gab da dawowa, ta gama haɗa kayanta kenan aka shigo da wata mata cikin office ɗin. Islaha ta kalli matar ta ce, "sannu baiwar Allah." Matar ta ce, "Yauwa Islaha. Ya aikin?." "Alhamdu lillah! Ki zauna." Ta zauna sannan ta ce, "na san ba ki sanni ba. Sunana Hajara, ni ce mahaifiyar Ummi da aka kai gidan yari." Islaha ta ce, "Ayya, ban san ki ba." Hajara ta ce, "alfarma nazo nema a wajan ki, don Allah don girman Allah ki yi haƙuri a fito min da Ummi daga gidan yari, Ummi budurwa ce bata taɓa aure ba, zamanta a gidan yari zai lalata mata rayuwa gabaɗaya. Don Allah ki ji ƙaina, a matsayina na mahaifiyarta ki saka a fito min da ita." Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, matar ta fara yi mata kuka. Islaha sai ta ji hankalinta ya tashi ta ce, "Mama don Allah ki daina kuka." "Dole na yi kuka, zaman gidan yari ga mace bashi da daɗi. Na san ta yi kuskure, ta aikata babban laifin da ya kamata ace an kama ta, amma ki yi min wannan alfarmar dan matsayin annabi, ki saka a fito mun da ita. Na yi miki alƙawarin zan ɗauke ta ta koma zamfara can wajan dangina, baza ki sake ganinta ba har abada." "Mama bani na kulle ta ba, bani da ikon da zan saka a fito da ita." "Kina da shi, tunda case ɗin ki ne, don Allah taimaka min don Allah." Islaha ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Mama ban yi miki alƙawari ba, amma zan san abinda zan yi in sha Allah." "Ki taimaka min don Allah." "In sha Allah." Daga haka suka yi sallama ta fita duk ta kashewa Islaha jiki, ta ta fito Lawal ya ɗauke ta zuwa gidansu Safeera da aka kawo lefen aurenta. Rehaan yana zaune a gida aka kira shi a waya ya ɗauka aka ce, "Sir akwai matslaa, akwai matsalar tsaro. Kar a bar kowa ya fita, in an fita a dawo." Abinda aka faɗa kenan sai ya kashe wayar ya kira su Mamy ya tabbatar kowa yana gida, har janan sai da ya hana fita da su ikram. Can kuma sai Islaha ta zo ransa, ya kalli Jazy da yake kallonsa kafin Jazy ya ce, "C wife ɗinka ya kamata ka fara kira ba su Janan ko Riyya ba." Bai ce komai ba ya kira number Islaha amma ba a ɗauka ba, ya sake kira ba a ɗauka ba dole ya haƙura dan shi ba ya son a tara masa kira, shima kuma ba shi da lokacin tarawa wani kiran. Jazy ya ce, "ya kamata a san inda ta ke fa, tana cikin familyn nan a yanzu, ta fi kowa kusa da kai, ita za a fi saurin cutarwa fiye da kowa." Rehaan sai ya ji hankalinsa ya tashi sossi ya ce, "waye ya ke fita da ita?." Jazy ya ce, "Lawal ne, ka kira shi yanzu nan." "Bani da number, kira shi please." Jazy ya ɗauko waya yana yanga kamar bazai kira ba, yana danna wayar kamar ba ya so dan ya ƙular da Rehaan ya ga yanayinsa. Ray bai san ya karɓi wayar daga hannunsa ba ya ce, "Ana sauri ka tsaya kana yiwa mutane iyayi? Sai wani abun ya same ta?" Ya faɗa yan kiran Lawal. Yana ɗauka ya ce, "kana ina?." Lawal ya ce, "na kai hajiya gidansu ƙawarta, yansu haka tana ciki." "Ka kira ta da gaggawa ku dawo, bana son ɓata lokaci ku dawo yanzu." Tana gama faɗa ya cillawa Jazy wayar shi kuma ya chafe yana kallon Rehaan ɗin da hankalinsa yake a tashe sosai. Jazy ya ɗaga gira sama yana murmushi, sai ya miƙe ya fice bai ce komai ba. Islaha kuwa tana can wajan Safeera, tana ganin kiran Rehaan bata ɗauka ba, bata san lambar waye ba ta ga dai ana yi mata waya kuma bata ɗauka ba. Sai bayan sallar magrib sannan suka taho gida, tun daga farkon estate ɗin ta san akwai wani abu, dan an ƙara tsaro mai yawa kamar gidan shugaban ƙasa. Suna shiga kai tsaye ɓangarensu ta nufa ta hau sama sai ta tsaya cak ganinsa a tsaye yana kallonta kamar jiranta yake yi. Rabon da su haɗa ido da shi tun ranar da ya yi mata maganar aiki, daga nan ta daina ganinsa ko a wajan Mamy, Mamy ce take faɗa mata aiki ne ya yi masa yawa shiyasa ba ya zama a gida. Haɗa ido da shi ya saka jikinta ya yi sanyi sosai, a hankali ta ƙaraso inda ya ke kafin ta yi magana har ya ƙaraso daf da ita yana kallon idanunta, ya girgiza kansa ya ce, "so i called you, and you were not picking my call." Islaha ta ɗan yi jim ganin yadda ya ke yi magana kamar wani babanta, ita bata san ya kira ta ba, ita bata lamsarsa balle ta san ya kira ta. Tun taimakon da ya yi mata akan su Ummi basu sake faɗa ba, amma ganin kamar yana raina mata hankali ne sai ta kalle shi tana ɗage gira sama ta ce, "i did'nt feel like it." Ya ɗan zuba mata ido yana juya idanunsa akan fuskarta da idanunsa ya ce, "you did'nt feel like picking my call?." Ba tare da damuwa ba ta ce, "yes oh. I did'nt feel like picking your call." Rehaan girgiza kai yake yi cikin takaicin da bai taɓa jin irinsa ba, ya juyo yana kallonta irin kallon da ya ke jinsa har zuciyarsa, kafin ya miƙa hannunsa ya ɗora akan bangon da ta ke tsaye, yana kallon idanunta fuskarsa ta canja zuwa ɓacin rai. sai da ta tsorara sosai, dan yadda ya yi da hannunta ta ɗauka marinta zai yi idanunta ya fito waje tana kallonsa. "Now listen to me. When i call you....you pick up the phone." Yadda yake maganar bata san ta ɗaga kai alamun to ba, bata taɓa ganin ya fusata haka ba shiyasa ta ɗaga masa kai. Ya ce, "You undersatnd?." Ta ɗaga masa kai alamu eh, ya sake matsawa kusa da ita har ƙirjinsa yana taɓa nata ya ce, "and i'm not joking....." Islaha ta ce, "Okay. But......" ya ɗora hannunsa akan lips ɗinta ya ce, "shiii!" Ta yi shiru bata ce komai ba sai kallon fuskarsa da take yi, sai kuma ya ja baya ya sauka daga saman gabaɗaya. Ta bi bayansa da kallo ta ce, "Kamar wacce ya ɗaurewa baki na kasa magana. Tsakani da Allah ni na san ya kira ni ne, ko an faɗa masa ina da numbersa ne?" ta faɗa tana shiga ɗaki. Ta yi wanka ta yi sallah sannan ta fito cin abinci. Tana zaune a parlour ta ji tana sha'awar cin wainar gero, sai ta tuna ta ga ana soyawa a Bq ranar da ta taɓa zuwa wajen Daada, sai kawai ta fita wajan masu aiki da niyar karɓowa ta ci. Tana zuwa wajan ta ga hayaƙi ya yi yawa, dan da itace suke yin aikin saboda yawa abinda suke soyawa. Ta kore hayaƙin da hannunta masu aikin suna ta yi mata barka da zuwa. Islaha ta ce, "ina so zan ci...." Sai kuma ta sarƙe ta fara tari babu ƙaƙƙautawa. Duk suka yi inda take ana yi mata sannu tana tari, ga shi har lokacin tana cikin hayaƙin. A guje suka nufi wajan Mamy suka samu Mamy da Rehaan a zaune ransa a ɓace, sai Jazy da Riyya da Banisha. Mai aikin ta ce, "Mamy, Hajiyan yallaɓai Rehaan ce ta je wajanmu karɓar waina, gata can tana ta numfashi da tari." Mamy ta miƙe ta ce, "subahanallahi! She had attack Rehaan." Rehaan ya yarrr ya ji a jikinsa kamar jan wutar lantarki, bai san ya miƙe ya bi bayan Mamy da Jazy da Riyya da suka riga shi fita ba. In Rehaan ya ce ya shekara goma bai je wajan masu aikin ba bai yi ƙarya ba, dan babu abinda yake haɗa shi da Bq balle ya je. Yadda su ka samu Islaha ya tayarwa da Mamy hankali, ta duƙushe a wajan tana fitar da numfshi idanunta sun fito waje sosai, kafin Mamy ta yi yunƙurin taimaka mata Rehaan ya ɗauko ta cak ya baro wajan da ita, duk suka rufa masa baya har apartment ɗinsu. Suna shiga ya kwantar da ita akan kujera, ya cire mata hijjab da ɗankwalinta. Mamy ta kwance gashin kanta, aka kunna mata iska. Riyya ta ce, "Mamy bata da inhaler?." Ba a bata amsa ba, Rehaan tunda ya cire mata ɗankwalin kanta ya koma gefe ya tsaya yana kallon ta, yana kalllon yadda numfashinta yake sarƙewa har lokacin, yana ji kamar numfashin da take fitarwa daga jikinsa yake fita. Duk sun yi shiru suna kallonta, Mamy tana shafa bayanta cikin sigar kwantar da hankali, Banisha ta ɗauko ruwa aka bata aka cigaba da shafa bayanta, Mamy tana buɗe gashin kanta iska tana shiga yadda zata nutsu sosai. Sun jima a haka babu wanda yake magana, a hankali ta fara dawowa daidai, tana sauke numfashi a hankali cikin fitar hayyaci. Mamy ta kalli Rehaan ta ce, "A kawo mata inhaler, ya kamata ace ko yaushe tana tare da ita." Rehaan ya kalli Islaha da ta miƙe zaune tana gyara gashin kanta da ya rufe mata fuska, ya harɗe hannunsa a ƙirji yana binta da idanunsa ya ce, "meye ya kai ki Bq? Meyasa bakya son kiyaye lafiyar ki?." Mamy ta kalle shi da mamaki ta ce, "Rehaan meye haka? Bata da lafiya fa, ka daina ɗaga mata murya." "Mamy meyasa ta je wajan? Ta san tana da asthma mai zai kaita wajan da yake da smoke?......" Sai kuma ya kalli su Riyya ya ce, "Wai ba na hana amfani da firewood a gidan nan ba, ba nace a daina kunawa ba?." Mamy ta ce, "Ai tun lokacin Daada tace ba ka isa ba sai an yi, ita kasan bata son aiki da gas cooker." "Mamy dole a yi yanzu, baza a sake kunna shi a cikin gidan nan ba. A samo gas cooker da za a dinga amfani dashi, babu wanda zai sake kunna firewood a gidan nan." Banisha ta ce, "taɓ! Allah ya sa Daada ta yarda." Rehaan ya ce, "dole ta yarda! Dole ta yarda a daina amfani da shi indai tana cikin gidan nan......" ya faɗa yana nuna Islaha alamun a kanta yake magana. Ya ce, "daga yanzun nan a daina amfani da shi, a faɗa musu za a kawo gas cooker da za a dinga amfani da shi, kar wanda ya sake tara mana smoke a gidan nan......And you..." ya faɗa yana kallon Islaha da ta ke kallonsa ganin ya ɗaga hankalinsa. "Kar na sake ganin kin je Bq, duk abinda ki ke so akwai chef da zai yi miki, in kum irin na Bq ɗin ki ke ki kira Housemaid ɗin su nan ko wajen Mamy a yi miki, kin ji?." Islaha ta turo baki gaba tana kallonsa bata ce komai ba dan bata dawo daidai sosai ba, bata cika son yin magana ba. Mamy dai kallon ɗan nata kawai take yi ganin yadda ya ruɗe gabaɗaya, sai umarni yake rabawa kowa saboda soyayya. Sai ta yi murmushi ta ce, "Okay Sir! We will obey your command." Ya waiwayo ya kalli Mamy ya ce, "Mamy ba wasa nake yi ba." Ta sake murmushi ta ce, "na san ba wasa ka ke yi ba ai. Kawai gobe ka kai ta asibiti a bata inhaler, Riyya Banisha mu je ko" ta faɗa tana fita Banisha ta bi bayanta. Islaha suna fita ta kalle shi, duk da muryarta bata fita saboda numfashinta bai yi daidai ba, cikin wannan yanayi ta ce, "to wai meye na ɗaga hankalin ka dan na samu attack? Ni fa ban gane maka ba a kwanakin nan, halayenka sai canjwa suke yi, wanda ban san ka dasu ba suna ta bayyana. Sai shouting ka ke yi kamar Riyya ko Banisha ne suka samu attack, Islaha ce fa ba su ba, matar contract ɗin ka ce, meye naka damuwa dan na shiga smoke na samu attack?." Jazy sai da dariyarsa ta fito fili saboda yadda Islaha ta burge shi, haka yake so ta cigaba da ɗana masa tarko yana faɗawa, amma ya danne dariyar yana niyar fita daga apartment. Rehaan ya zuba mata ido yana kallonta na wani lokaci, ƙirjinsa yana bugawa da ƙarfi, ya rufe idanunsa ya buɗe a kanta ya ce, "because you are my wife!." Islaha ta kalle shi tana jin kalmar wife ɗin da ya faɗa har zuciyarta, ta dinga kallonsa da mamakin abinda ya ce kafin ta girgiza kai a hankali ta ce, "Ni ba matarka bace, matar contract ce, baka da guts ɗin da zaka ɗaga hankalinka dan na samu attack. Ya kamata ka tuna kwanaki kaɗan ya rage mana, in na tafi ganina sai ya yi maka wahala, Mr Rehaan" a hankali take yi masa maganar ba kamar yadda ta saba ba, amma maganar ratsa shi take yi. Sai ta kashe masa baki ya yi shiru yana kallon ta yana tunanin eh haka ne fa, meye nasa na ɗaga hankalinsa haka?. Ya juya ya kalli Jazy ya ga har ya fita, sai ya ya bi bayan Jazy da sassarfa, gab da zai fita daga apartment ɗin ya kira sunana. Jazy ya tsaya har ya ƙaraso sannan ya ce, "Jazy meyasa na damu? She is just my C wife" Jazy ya yi ƴar dariya ya ce, "dan tana C wife ai matar ka ce ko?." "Amma abin ya yi yawa Jazy" ya faɗa yana lumshe idanunsa ya buɗe. Jazy ya ce, "ka huta, sai mu yi magana gobe in Allah ya kaimu." "Yanzu na ke so." "Ka bari zuwa gobe, za ka fi fahimta." "Yanzu na ke so na ji Jazy! Meyasa na damu da ita haka? Meyasa na canja nake jin motsinta a jikina, da ba haka nake ji ba Jazy, ka faɗa min meyasa?." Jazy ya ce, "you are in love Rehaan, you are in love with Islaha!." Nana Haleema. RDB3P74 Nana Haleema. Ray ya zuba masa ido kawai yana kallonsa jin abinda yake faɗa kamar a mafarki, ya kasa janye idanunsa daga kallon Jazy dan ya kasa gasgatawa da gaske ne ko ƙarya. Jin maganar yake yi kamar a mafarki, ya kasa banbance kalaman Jazy na gaskiya ne ko na ƙarya ne. Jazy ya gyaɗa masa kai alamun taabbatarwa ya ce, "yes Rehaan, you are in love! Duk wannan abubuwan da ka ke yi kana yi ne saboda kana son Islaha. Wanda ake so shi ake jin iein wannan yanayin a kansa, in baka sonta baza ka ji irin abinda ka ke ji yanzu ba. Kana son Islaha Rehaan, kana yi mata so mai tsanani ba ɗan kaɗan ba." Ray ya shafa gashin kansa ya sauke numfashi yana kallon gefensa, sai kuma ya kalli Jazy ya ce, "Which kind of love?." Jazy zai yi magana ya dakatar da shi cikin wani irin yanayi mara daɗi ya ce, "ya ka ke min irin wannan maganar? Ka san wacece yarinyar nan Jazy, ta ya zan ka ce ina sonta? Aure contract ne a tsakanina da ita, lokaci mu ke jira komai ya ƙare. Wanne irin so zan yi mata haka? Dama haka ake jin son? A cikin raina ji nake kamar zai tarwatse. Haka son yake very cheap da zaka ce ina sonta? How comes?." Jazy ya murmusa yana kallon yadda ya ruɗe lokaci ɗaya ya ce, "Haka ka ke gani, amma ni na san ba iya contract bane Rehaan, akwai abu mai ƙarfi da ya ke tsakaninka da ita. Shine ya canja maka yanayi, shine ya saka ka ke jin duk abinda ka ke ji a yanzu." Ya girgiza kai cikin fitar hayyaci ya ce, "ba haka bane Jafar, ba abinda ka ke faɗa bane, ni ba wani love, babu shi a tsakanina da ita. Kar ka sake ɓata min rai akan wanda nake kai yanzu, ka bar maganar nan kafin kaina ya tarwatse...." Sai kuma ya kalli sama yana furzar da iska mai ƙarfi yana girgiza kai ya ce, "gwara ma auren ya ƙare na koma England da zama, ba zan sake dawowa nigeria ba." Jazy ya yi dariya ya ce, "well, we shall see." Ya faɗa yana ficewa ya ƙyale sa dan ya san daman bazai yi saurin karɓar maganar ba, sai ya fahimta da kansa sannan zai san gaskiya yake faɗa masa. Jazy yana shiga wajan Mamy ya kalli Riyya ya ce, "Mu tafi?" Ya faɗa da sigar tambaya yana kallon ta. Mamy ta ce, "Jaafar baza ku zauna a nan zuwa gobe ba? Kana ji ance akwai matsalar rashin tsaro." Ya yi murmushi ya ce, "Babu komai Mamy, zamu je lafiya." Mamy ta ɗaga kai ta ce, "Okay, kafin ku tafi ɗin zo ka ji" ta faɗa tana tashi ta shiga ciki ya bi bayanta. A tsaye ya same ta a parlour yana ƙarasawa ta kalle sa ta ce, "me ka fahimta daga yanayin Rehaan akan Islaha? Ba ka ga canji ba?." Jafar ya yi dariya ya ce, "Mamy ko ke na san kin ga canji a tare dashi, ba ke kaɗai ba duk wanda yake tare da shi ya san ya canja. Mamy Ray yana son Islaha shi kansa ya fahimta, kawai ya ƙi yarda yana sonta ne saboda abinda yake tsakaninsu, amma wallahi ya san yana sonta." Mamy ta yi murmushin jin daɗi ya ce, "na yi mamaki fa Jafar, yadda yake faɗa akan ta je inda ta samu attack ya bani mamaki shiyasa na tsaya ina kallonsa kamar tv. Ka san shi faɗa baya cikin halayensa, rabon da na ga yana irin wannan faɗan na manta, in na ce ban taɓa gani ya yi ba ban yi ƙarya ba. Amma ya za a yi da contract ɗin da yake tskaninsu kenan?." Jazy ya ce, "contract yana nan Mamy, dan ita Islaha babu Rehaan a gabanta, shirin fita take yi ta auri saurayinta. Shi ne dai Allah ya kama sa ya saka masa soyayyarta har ta mayar da shk haka." Mamy ta girgiza kai ta ce, "oh my God! Zan so na ga yadda wannan abu zai kasance, zan so na ga yadda za ayi da shi akan wannan maganar. Shi yana sonta ita kuma bata sonsa, ga shi kwanaki kaɗan ya rage su rabu." Jazy ya girgiza kai yana dariya ya ce, "Mamy kin san Rehaan ba ya bari ƙaaramar dama ta kubce masa, ko ya ya ƙaramar dama tazo masa yana amfani da ita koda bazai yi nasara ba. Rehaan bazai taɓa bari contaract ɗin nan ya ƙare ba, sai ya ƙirƙiri wani abun da Islaha bazata kubce masa ba, sai ya yi duk yadda zai yi ta zauna a gidan nan ko da bata sonsa." Mamy ta ce, "zan fi kowa son hakan, zan fi kowa farin ciki in ya kasance suna rayuwa a inuwa ɗaya matsayin ma'aurata. Rehaan ya samu macen da na ke buri ya samu, ya samu irin wacce na jima ina yi masa addu'a da fatan ya same ta. Islaha zata zauna dashi ba dan ya isa ba, ba dan tana sona ba, ba dan kuɗinsa ko kyau da wani abun ba, zata zauna da shi da ra'ayin kanta ba dan an yi mata dole ba. Islaha itace matar da na jima ina yi masa addu'a akan Allah ya ba shi. Ga shi Allah ya amsa ya ba shi ita ɗin, kuma tana ƙoƙarin kubce mana." Jazy ya ce, "sosai kam, Islaha ta haɗa duk abinda ki ka faɗa, babu macen da ta raina Rehaan kamar ta, baza ta zauna da shi saboda abubuwan da ki ka faɗa ba sai ta ra'ayi." "Kuma gata marainiya, ina yi mata fatan ta rayu a gidan nan ko dan ta samu gatan da bata samu a rayuwarta ba. Zan zamar mata uwa, Rehaan zai zamar mata uba kuma mijinta. Kai kuma ka zama Yayanta, Riyya da Banisha su zama ƴan uwanta. Duk wanda yake yi mata kallon mara gata daga lokacin zai yi danasani akan kalamansa, zai san gata da kansa in ya ganta sai ya girmamata. Ina son Islaha Jafar, haka kawai Allah ya ɗora min ƙaunarta a raina." Jafar ya ce, "Bata da damuwa ai, tana da kirki da hankali sosai." "Ku je ku tafi, dare yana yi." "Okay Mamy, sai da safe." "Allah ya kiyaye hanya." Ya amsa ya fita, Mamy ta zauna tana tunanin yadda wanann kwamacalar zata kasance. Ray ko da ya koma Islaha bata nan, ya tsaya cak yana kallon inda ta zauna yana tuna maganar Jazy da ya ce yana sonta, ya jingina da ƙofa yana ji zuciyarsa tana bugawa, har sai da ya ɗora hannunsa akan ƙirjinsa saboda yadda take ɗagawa. Ya jima a haka a tsaye, kafin ya yi tsaki ya hau sama. A lokacin ta fito daga ɗaki da hijjab a jikinta, tana so ta yi masa maganar mahaifiyar Ummi da ta je har office tana kuka, dan ita har ranta ta yafewa Ummi saboda mahaifiyarta, tana so ta ce in zai yu a fito da ita amma kuma tana jin haushinsa. Ya zuba mata ido yana kallonta yana so ya gasgata maganar Jazy, ita kuma ta janye idanunta daga kansa, kamar zata yi magana sai kawai ta fasa ta juya ta koma ɗakin. Rehaan ya bi ƙofar da ta rufe da kallo, kafin ya ja ƙafafunsa shiga ɗaki ya jingina da bamgo ya ce, "me nake ji akanta ne, meyasa na damu haka? Na manta wacece ita ne?." Ya hargitsa gashin kansa, ya samu waje ya zauna yana tunanin abinda ya kamata ya yi da zai daina jin wannan tashin hankalin. "Anya bazan kawo ƙarshen contarct ɗin nan na daina ganinta ba? In na daina ganinta maybe zan daina jin abinda nake ji a kanta." Ya kwanta da baya yana kallon sama, ya yi shiru yana tunani kala-kala wanda ya rasa mafita a cikin tunaninsa, ya juya ya yi ruf da ciki yana so ya gano abinda yake addabar zuciyarsa amma ya kasa. Gabaɗaya zaman ɗakin ya ishe shi, duk inda ya waiga ita yake gani a yanayi daban-daban, jin yana neman haukacewa sai ya miƙe ya ɗauki waya ya kira Shams ya ce ya zo su fita, a daren suka bar gidan dan gabaɗaya gidan ba ya yi masa daɗi ko kaɗan. Shi da ya bar gida dan ya daina tunaninta amma sai tunanin ya fi na gidan yawa, duk inda ya juya ita ya ke kallo, in ya rufe ido murmushinta yake gani, a kunnensa kuwa muryarta yake ji lokacin da ta yi masa godiya. Ya ɗauki pillow ya cillar cikin ɗaga murya ya ce, "Jazy why!....." Sai kuma ya yi sanyi ya ɗora hannayensa a kansa ya ce, "Meyasa ka ce ina sonta? Meyasa ka faɗa min, meyasa ba ka yi min shiru ba?..." Ya koma da baya ya kwanta yana rufe ido ya ce, "gashi na rasa nutsuwata, na rasa hankalina, na rasa tunanina, komai ya daina yi min daɗi. Jazy why...!" Ya sake faɗa kamar zai yi kuka, ya rasa inda zai saka ransa ya ji daɗi, duk inda yake zaune sai ya ji baya jin daɗi. Bacci ya ke so ya yi amma ya kasa, in ya rufe ido ita yake gani, ya buɗe ita yake gani, muryarta yake ji a kunnesa, zatinta yake gani a ƙwaƙwalwarsa, ƙhamshin turarenta yake ji a hancinsa, taste ɗin bakinta yake ji a cikin bakinsa, laushin fatar ta yake ji a tafukan hannunsa. Gabaɗaya ya haukace, ya fita daga hayyancin gabaɗaya, ta ko wanne ɓangare Islaha ta yi masa kane-kane ta hana shi sakat, ko bugun zuciyarsa da sunanta yake bugawa. Washe gari ko baccin safe na ƙa'ida bai yi ba, ya dinga kiran Jazy babu ƙaƙƙautawa. Shi ba mai son tarawa mutane kira bane, ko Mamy in ya kira sau ɗaya bata ɗauka ba baya sake kiranta, amma yau shine yake jerawa Jazy kiran da bai san adadi ba, har sai da ya Jazy ya zo gidan. Yana shigowa ya kalle shi ya ce, "Ray bashi ka ke bina ne ko ina da wata agender da kai da za ka takura min da waya? Ba ka san safiya bace, ina tare da matata gabaɗaya ka ɗaga min hankali sai da na fito. Me zan yi maka?." Rehaan ya kalli Jazy da idanunsa da suke lumshewa, cikin raunin zuciya da ya bayyana a tare da shi ya ce, "Meyasa za ka ce ina sonta? Jazy ka faɗa min na kasa nutsuwa, na baro gidan na dawo nan shima ban samu nutsuwa ba...." Sai ya yi shiru kafin ya ce, "Na kusa haukacewa Jazy, ban san me yake damuna ba, ko in na juya ita nake gani, maganarta nake ji, na rasa ya zan yi na daina ganinta." Jazy jin Rehaan ya yi rauni da yawa sai ya zauna a kusa da shi ya ce, "wannan shine love ɗin Ray, ka yarda kana son Islaha." "Ta ya zan yarda? Bayan ka san wacece yarinyar nan..." sai miƙe zaune sosai ya ce, "Yarinyar Ubaid ce, bayan nan bata daina duk abinda take yi ba, har Salman bata ƙyale ba." Jazy ya kalle sa ya ce, "kai da gaske ka yarda tana neman Salman? Mu ajjiye maganar Ubaid a gefe, amma a ranka ka yarda zata nemi Salman?." Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba, dan shi kansa ya san ƙarya ne, yana amfani da maganar ne dan ya sake kushe ta a zuciyarsa. Jazy ya ce, "kai ma kana faɗar tana neman Salman ne yi dan ka samu abinda zaka kore sonta daga ranka, amma kaima ka san plan kawai mutanen gidanku suke haɗa mata. Kai ka ce min yarinyar Ubaid ce, wacce take kula irin su Ubaid me zata yi da wani Salman?." Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba Jazy ya ce, "Rehaan ko da ace da gaske ta aikata abubuwan da ka ke tunanin ta yi, rayuwarta ta baya ta wuce, karuwai ma da suka amsa sunansu karuwai in suka tuba ana aurensu kuma a zauna lafiya. Tunda har kana sonta ka goge wannan tunanin, ka karɓe ta ku yi zaman aure kamar kowa. Kana sonta, ita kuma ka san ba dan wani abu naka take zaune da kai ba, ka ga an yi eqaual." Rehaan cikin sanyin murya ya ce, "Ta ya zata zauna dani Jazy? Bayan ka san abinda yake tsakanin mu da ita?. Sannan ka san tana da saurayi, that guy Saleem yake ko waye ban sani ba, a gabana tana yin waya dashi suna lissafin lokacin da zata bar gidanmu, lissafin ƙarewar kwanakin mu take yi kullum, ta ya zan zauna da ita? Ya zan yi Jazy?..." ya ƙarasa faɗa cikin tsananin rauni yana lumshe idanunsa. Nana Haleema. RDB3P75 Nana Haleema. Jazy da yake kallonsa ya girgiza kai yana aiyana baƙo ne a soyayya shiyasa ya rikice ya fita daga hankalinsa har haka ya ce, "Abinda na ke so na tambaye ka guda ɗaya ne, kuma ka faɗa min gaskiya, ban da kushewa ko faɗar Ubaid ko wani Salman...." Rehaan ya zuba masa ido yana jira ya ji me zai ce, Jafar ya ce, "Rehaan ka yarda kana son Islaha?." Ya sauke numfashi ya lumshe idanunsa ya buɗe akan Jazy, ya kawar da kai gefe yana girgiza kansa sannan ya ce, "ban sani ba Jazy." Jazy ya yi murmushi ya ce, "ka jira ka tabbatar, sai mu yi magana, ka ga in lokaci ya ƙare shikenan sai ka haƙura, kana ji kana gani zata auri saurayinta kai ta bar ka da rauni a zuciyar ta." "Ka bani solution." "Aa, sai ka fara tabbatar da abinda ka ke ji a kanta sannan sai na faɗa maka yadda za a yi." Ray ya yi shiru bai ce komai ba, ya rufe ido ya ɗaga kansa sama apple adam ɗinsa yana up and down. Jazy ya zuba masa ido kana kallonsa, kallo ɗaya zaka yi masa ka san tension ɗin soyayya ne ya fara walagigi da shi tun ba a je ko ina ba. Jazy ya ce, "ka san daga ranar da na fara noticing feeling ɗinka a kanta?." Bai yi wani motsi ba, sai dai ya buɗe idanunsa Jazy ya ce, "ranar da aka yi attacking ɗinku kai da ita a mota, har aka kai ta asibiti na ce ka bar Shams ya ɗauke ta amma ka ƙi, ka ɗauke ta da kan ka ka saka ta a mota, har kana rufe mata jikinta da blanket saboda night wears ne a jikinta. Ray daga ranar na saka maka question mark. Yadda ka dage ka ƙi sakin ta duk da abubuwan da aka ce tayi ya saka na sake yi maka alama, yadda ka tashi hankalinka akan ta samu attack jiya a nan na tabbatar da kana son Islaha, kuma baka so wani abu mara kyau ya same ta." A ƙagauce Ray ya ce, "Daman bana so wani abu ya same ta saboda a ƙarƙashina ta ke, ina so mu rabu lafiya ba tare da wani abun ya same ta ba." Jazy ya ce, "to kawai ka kawo ƙarshen zaman na ku mana, a ƙarar da contract ɗin a huta kawai." Ray ya sake lumshe ido ya buɗe ya ce, "abinda nake ƙoƙarin yi kenan, but......." Jazy ya katse shi ya ce, "But you can't ko?." Bai ba shi amsa ba sai kallonsa da yake yi rauni da bugawar zuciya. Jazy ya yi murmushi ya dafa kafaɗarsa cikin kwantar da hankali ya ce, "Rehaan!..." Ya kalle shi suka haɗa ido ya ce, "Wallahi you are in love, ko ka yarda, ko kar ka yarda, wallahil azim kana son Islaha." Rehaan ya ce, "Let assume ina sonta ɗin, ya zan yi da saurayinta da ta ke burin aure?." "In ni ne kai, a waɗanan kwanakin da suka rage mana wallahi sai na saka ta manta da wani Saheer da abinda ya shafe sa, zan yi ƙoƙarin ƙirƙirar alaƙa mai a tsakanina da ita, kafin mu rabu sai na samar mata da scar a zuciyarta wanda bazai taɓa gogewa ba har abada. Saheer ɗin banza, waye shi da zan tsaya ina tuna shi akan matata?. Ka fi shi komai, babu ta inda Saheer zai kamo ka, tazararka dashi bazata taɓa kwatantuwa ba. Ka daina kawo shi cikin tunaninka, Islaha itace abin tunani ba shi ba." Rehaan ya yi shiru bai ce komai baya jingina da kujera yana lumshe idanunsa. Jazy ya ce, "Kai ne mijinta ba shi ba, kai ka ke da ita a hannu ba Saheer ba. Ka nuna mata kai mijinta ne, shi kuma saurayinta ne na dah ba yanzu, kai ka ke da iko da Islaha ba shi ba. Hmmm! In ni ne kai ko? Bazan sake bata damar tunawa da wani Saheer ba, tuni zan goge mata hadda na saka ta manta da shi ya zama duk duniya babu wanda take tunawa sai ni." Rehaan yana jin kalaman Jazy yana shiga har cikin ransa, ya yi luff bai ce komai ba yana tunanin mafitar da ta dace daahi a halin da yake ciki, dan gaskiya bazai iya rabuwa da ita ba, ji yake in ya rabu da ita kamar zai rasa numfashinsa zai bar gangar jikinsa, ya zama dole a san abinda za a yi kafin ya rasa tunaninsa.    Islaha da ta tafi wajan aiki bayan ta tashi wajan Barr ta tafi, ta same sa a chamber ya fito ya same ta jingina da motarsa ya ce, "Hajiya Islaha." Ta kalle sa ta ce, "Hamma meyasa kwana biyu baka son ɗaukar wayata ne?." Ya yi murmushi ya ce, "kawai sai in ƙi ɗaukar wayar ki? Aiki ne ya yi min yawa." "Ban gane aiki ne ya yi maka yawa ba, ka san akwai case ɗin da na bari a hannunka, meyasa ka ke yi min wasa da hankali?." Ya ce, "in nan ina aiki akan hakan." "Kullum haka ka ke faɗa, ni kuma bana ganin improvement ɗin da ake samu, kullum jiya i yau ake abin nan. Ina Yafindo take? ka yi magana da ita ko baka yi ba, duk ba ka faɗa min abubuwan da suke faruwa. Ga Hafsa ta tura min da message akan tana son yin magana dani, na je kuma na kasa ganinta. Hamma Suraj in bamu dage ba rayuwar yara tana cikin hatsari." Suraj ya ce, "me ta ce miki a saƙon?." "Ka fara bani amsa, ka yi magana da Yafindo ko an samu Zainab?." "Ban yi magana da ita ba har yanzu, na je gidan da take an tabbatar min da ta tashi. Islaha ina iya bakin ƙoƙarina akan case ɗin nan, yadda ki ke ji ƴan uwanki ne nima haka nake jinsu a matsayin jinina, gabaɗaya tare muka tashi a gida ɗaya, ba ke kaɗai ki ke jinsu a ranki ba. Kuma wannan abu ne da sai an yi bincike mai ƙarfi, baza ku shigar da ƙara ba sai muna da hujja mai ƙarfi a hannunmu. Zainab ita ce kaɗai hujjar mu, ita ma ta ɓace mun daina gaminta. Islaha ta dafe kanta ta ce, "Yanzu ya za a yi?." "Ki bar komai a hannuna, zan yi komai yadda ya kamata." Ta ya yi tsaki ta ce, "Allah wadaran nigeria, kana gani ana aikata laifi amma baka da ikon yin wani abu a kai." Suraj da ya ke yi mata kallon ƙasan ido ya ce, "Kar ki damu, komai zai zo ƙarshe." Sallama ta yi masa ta wuce, ya bita da kallo yana ɗan murmushi ya koma inda ya fito yana saƙa da kwancewa. Islaha lokacin da ta koma gida tana shiga upstair parlour suka haɗu da Mamy, duk suka yiwa juna murmushi a tare Mamy ta ce, "daughther an dawo?." Islaha ta ce, "na dawo Mamy." Many ta ce, "jeki ki huta ki ci abinci, in kin gama ki same ni a ɗakin Rehaan." Islaha gabanta ya faɗi jin ta ce ta same ta a ɗakin Rehaan, amma bata nuna mata ba ta shiga ɗaki. Tana wanka tana tunanin abinda zata yi a ɗakin, ta fito ta yi sallah, bayan ta idar ta tsaya a gaban mirror tana dambe da gashin kanta akan sai ta tuke sa, tana yi tana hutawa a haka ta yi yadda ta saba, dan preiod ɗinta yana kan hanya. Da ta sauka ƙasa ma tea ta sha ta ci abinci, ta yi sallar i'sha sannan ta nufi ɗakin kamar yadda Mamy ta ce. A zaune ta samu Mamy shi kuma yana kwance akan cinyarta, gabanta ya faɗi sosai, dan kallo ɗaya ta yi musu ta san ba shi da lafiya. Mamy ta ce, "ƙaraso ki zauna." Islaha ta ƙarasa, kafin ta zauna Mamy ta miƙe ta bata wajan da take ta zauna ta ce, "Zauna." Islaha haɗɗiye yawun tashin hankali, dan yadda Mamy ta yi mata alamu ne na a kan cinyarta zai kwanta, amma haka ta zauna bata ce komai ba saboda girman Mamy ya wuce haka. Tana zama Rehaan ya mayar da kansa jikinta, ta rufe ido ta buɗe ta kasa cewa komai. Mamy ta ce, "take care of him Islaha, bashi da lafiya, jikinsa ya yi zafi sosai, ki taimaka masa ayi reducing temperature ɗinsa, in kina buƙatar wani abun ki kira ni. Good night" ta faɗa tana kashe hasken ɗakin ta fita. Islaha ta ɗauke ido daga kan ƙofa ta kalli gashin kansa da yake jikinta, tana tunanin shi kullum cikin rashin lafiya ya ke, kuma ace in ba zhi da lafiya a jikin mutum yake bacci kamar wani yaro ƙarami?. Ta sauke numfashi tana kallonsa, tana kallon yadda ya yi luf a jikinta ko motsin kirki ba ya yi a jikinta, yana kwance kamar bai san ita bace ba, bayan tana da tabbacin idanunsa biyu. Islaha cikin sanyin murya ta ce, "tunda dai Mamy bata nan don Allah ka ɗaga ni, ka san dai ba mu irin haka zai faru ba, kunyar Mamy nake ji shiyasa na shigo wallahi." Rehaan yana jinta dan tunda ta shigo zuciyarsa take bugawa, lokacin da kansa ya kwanta a jikinta ji ya yi kamar an kuma kunna gudun zuciyarsa ta cigaba da gudu kamar an ƙra mata speed, ya lumshe ido tare da yin shiru kamar bai san me ta ke faɗa ba, dan bashi da niyar tashi daga jikinta. A yadda ya ji daɗin kwanciyar bazai iya barin jikinta ba, hakan ya saka shi ya ƙara rungumeta. Islaha ba da niyar mugunta ba ta ɗan ture kansa daga jikinta ta ce, "Don Allah ka ɗaga ni." Sai ya bar jikinta ya koma gefe yana juya kansa, dan yadda ta taɓa kansa ba ƙaramin ciwo ta ƙara masa ba. Islaha ta ɗauke kai daga kallonsa, amma sai ta kasa jurewa ta sake kallonsa ganin da gaske fa ciwon yake ji sosai, sai hankalinta ya tashi ta matsa kusa da shi ta ce, "ciwon kan ne yake damun ka?." Bai ce mata komai ba so yake ciwon kan ya lafa sai ya iya kallonta. Jikinta ya yi sanyi sosai, tausayinsa ya kama zuciyarta, ta matsa kusa da shi ta ɗago kansa daga kan gadon a nan ta ji yadda kansa ya yi zafi sosai. Zuciyarta ta buga da ƙarfi, ta zube hannayenta akan goshinsa cikin tausayawa ta ce, "Sannu, ban san zaka ji zafi ba, da ban ture ka ba, ka yi haƙuri" ta faɗa a ruɗe dan ta ruɗe jin yadda kansa ya yi zafi sosai. Guiwarta tana zube akan katifar tana kusa da shi a duƙe, ta motsa da nufin sake zuwa inda yake sosai sai hijjab ɗinta ya harɗe ta, bata san lokacin da ta cire shi ta ajijiye ba, ta ƙaraso ta ɗago kansa daga kan katitar ta kwantar da shi a jikinta. Ta ɗora hannunta a kansa tana shafa gashin kansa cikin tausayin yadda kansa ya yi zafi sosai. Nana Haleema. RDB3P76 Nana Haleema. Rehaan duk da ba shi da lafiya amma yana jin duk abinda take yi masa, yana jin yadda ta riƙe kansa tana shafa gashin kansa. Ganin ya samu damar ta sai ya kwantar da kansa a ƙirjinta, ya zagaya da hannunsa ya rungume ta, ya cusa fuskarsa fatar tsakiyar ƙirjinta yana zuba mata nunfashi mai zafi ga zafin kansa yana ratsa fatarta. Luf ta yi gabanta yana faɗuwa matuƙa tana jin yadda ya riƙe bayanta sosai kamar za a ƙwace ta, ga kansa a kwance a ƙirjinta muraran ba akan vest ɗin ba. Ta yi shiru ta kasa motsi dan bata san me zata yi ba, shi kuma ya yi luf a ƙirjinta yana shaƙar night scent ɗinta da yake fitowa daga jikinta. Yana jin yadda ƙirjinta yake bugawa, shima a wannan yanayin yake, ya kasa tantance abinda yake ji a wannan lokacin, ya kasa banbance rashin lafiya ce ta kawo bugawar zuciyar ko Islaha ce bai sani ba. Yana cikin yanayin da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba, ko ina na jikinsa amsawa yake yi ba iya zuciyarsa ce take bugawa ba. A hankali ya buɗe idansa a tsakiyar ƙirjinta, yana so ya kalli brown skin ɗinta amma rashin hasken ɗakin ya hana shi hakan. Wani irin abu ne yake jansa zuwa gare ta, yadda yake jin zafin abun a jikinsa ko ciwon kan da yake damunsa ba ya jin zafinsa kamar abinda yake jansa. Ya juyar da fuskarsa zuwa gefe ɗaya yana goga fuskarsa a ƙirjinta, gashinsa mai laushi yana shafar fatarta. Islaha ta rutse ido jin yadda tsigar jikinta ta tashi, sai ta tsorata sosai ta fara ƙoƙarin zamewa ta gudu amma ya riƙe ta ya ƙi bata damar da zata kubce. Islaha ta kasa jure yanayin da take jin kanta a ciki ta ce, "Mr Rehaan!." Ray ya runtse ido da ƙarfi jin yadda muryarta ta da ki kunnuwansa, ya ɗan ɗago ido yana kallon yadda bakinta yake moving alamun magana take so ta yi amma ta kasa. Duk da ɗakin akwai duhu amma red lips ɗinta basu ɓuya ba, yana kallon yadda take motsasu a hankali alamun magana ta ke yi ƙasa-ƙasa. A lokacin ya tuna da ranar da ya yi kissing ɗinta a mota, ya tuna yadda teste ɗin bakinta yake a cikinsa nasa, ya tuna how sweet and soft it was, ya haɗɗiye yawu yana kallon yadda bakinta yake rawa a hankali. Duk da ya yi zama a cikin turawa, ya ga mata kala kala amma bai taɓa jin yana son kissing wata mace ba sai yanzu, bai san me yake jansa zuwa gare ta ba, bai san me yake ji ga me da bakinta ba, abinda ya sani yana tuna abinda ya ji a cikin mota kuma tana so ya maimaita. Bai damu da rashin lafiyarsa ba, ya ɗan ɗago daga ƙirjinta ya matsar da fuskarsa kusa da tata yana kallon idanunta a rufe bata san ma ya yi haka ba, tsabar ruɗewa bata san ya bar ƙirjinta ba. A hankali ta ji saukar hannunsa akan fuskarta, sai ta buɗe idanunta suka haɗa ido cikin ƙaramin hasken ɗakin. Lokaci ɗaya gabanta ya faɗi ganinsa daf da ita, sai ta tana ja baya jikinta ya fara rawa cikin yanayi na tsoro da fargaba.. Rehaan ya buɗe bakinsa kamar mai koyan magana ya ce, "za ki iya bani ruwa?." Da hanzari ta ɗaga masa kai ta ce, "Eh zan iya, let me go and get it to you" ta faɗa tana so ta gudu amma sai ya riƙo cikinta ya hanata guduwa. Islaha ta runtse ido tana jin huxin numfashinsa a kusa da fuskarta, ita kanta numfashinta ya garwaye ya yi zafi saboda halayen da Rehaan yake gwada mata wanda bata san da su a duniya ba. Rehaan a kusa da kunnenta ya ce, "can i....." Sai ya kasa ƙarasawa yana kallon idanunta da tsoro ya bayyana ƙarara, ya lumshe idanunsa saboda ciwon kai, amma da ya ke shauƙi ne yake ɗaukarsa sai ya sake buɗe su yana kallon cikin nata ya ce, "Kiss you?." Islaha ta zaro idanunta waje cikin tsoro da mamakin canjawarsa, tana girgiza masa kai alamun a'a. Rehaan ya riƙo fuskarta yana kallon idanunta ya ce, "please!" Bai jira umarninta ba ya ɗora lips ɗinsa a kan nata ba tare da ya fara kissing ɗinta ba, sai da numfashinta ya kusa ɗaukewa jin abinda bata taɓa tsammani daga wajensa ba, ya ɗora bakinsa a kan nata kuma bai yi mata komai ba sai kallon idanunta da yake yi. Islaha ta fara ƙoƙarin barin jikinsa, a nan ya samu damar riƙo waist ɗinta da yake masa daɗin riƙewa, ya buɗe bakinta da harshensa ya fara kissing ɗinta softly. Wata irin bugawa zuciyarta take yi da ƙarfi, ta kasa tsayawa waje ɗaya sai mutsu-mutsu take yi tana son ƙwatar kanta amma ta kasa. Tana jin yadda harshensa yake yawo a cikin bakinta yana haɗuwa da nata, tana jin yadda yake tsotasar lips ɗinta da nasa, tana jin yadda saliva ɗinsa yake shiga cikin bakinta yana haɗewa da nata tana haɗɗiyewa. Ga shi idanunsa a buɗe suke yana kallon nata, dole ya saka ta rufe ido tana so ta ƙwace kanta amma Rehaan ya hanata. Islaha ta gigice, ta ruɗe, ta ɗimauce, ta rasa inda zata saka ranta, jikinta ya fara rawa, tana so ta fizge kanta amma abin ya ci tura dan ya riƙe ta sosai. Cikin wannan ruɗewar ta ji hannunsa a sholders ɗinta, sannan ya saka hannunsa guda ɗaya a bayanta ya haɗe gaps ɗin da ya hana ƙirjinsu haɗewa waje ɗaya. Haɗuwar ƙirjinsu a waje ɗaya ya saka ta sake runtse idanunta, tana jin zuciyarta tana rawa sosai, shi kuma ya cigaba da kissing ɗinta bai dakata ba. Rehaan kuwa tunda bakinsa ya sauka a kan nata ya ɗauke wuta, duk da azabar da yake ji a kansa bai saka ya kasa tantance yanayin da ya shiga ba, lokaci ɗaya ya ji kamar ba a duniya yake ba, yana ji kamar a ƙoramar zuma ya saka bakinsa yana sha a hankali. Laushi da ƙhamshin bakinta ya sake gigita shi, ya fita daga duniyar da yake ciki ya shiga ta shauƙi, hakan ya saka ya sake riƙe ta ya hanata motsi, yana so ya samu abinda zai sanyaya masa maƙogwaronsa kamar yadda ya bushe. Islaha a ruɗe take sosai, jikinta rawa yake yi tana so ta samu damar da zata gudu amma ya hana hakan, babu abinda take ji sai sautin fitar numfashina kunnenta, tana jin hucin numfashinsa yana dukan fuskar ta, gabaɗaya yanayinta ya canja ta shiga baƙon yanayin da bata taɓa shigarsa a duniya ba. A cikin wannan ruɗewar ta ji ya zame bakinsa daga cikin nata ya mayar da bakinsa wuyanta yana kissing a hankali. Islaha bata san ta riƙe gashin kansa da ƙarfi ba, tana jin abinda bata taɓa ji ba a duniya, tana yim yadda yake kissing wuyanta kafin ya koma blowing kisses a ko ina na wuyanta zuwa fuskarta. Ganin in bata yi magana ba zata iya mutuwa, a lokacin ta samu bakin magana cikin wani irin yanayi ta ce, "Mr Rehaan don Allah…..!." Faɗar haka da ta yi sai ta sake mayar da bakinsa cikin nata yana cigaba da kissing ɗinta a nutse, salati kaɗai take yi a ranta, ga shi jikinta ya yi sanyi sosai, tana so ta samu damar da zata gudu amma ta kasa. Ya riƙe hannunta ya sarƙe fingers ɗinsu waje ɗaya, ya cigaba da abinda yake yi bai dakata ba. Tun tana son ƙwace kanta har jikinta ya yi sanyi sosai, ta saki jikinta a jikinsa amm duk da haka zuciyarta bata daina bugawa ba. Ta yi luf ta kasa wani motsi mai ƙarfi da zai saka ta gudu daga gare sw, tana jin duk abinda yake yi mata amma bata san me zata yi ba. Rehaan ganin jikinta ya yi sanyi ta saki jikinta sosao sai ya cigaba da kissing wuyanta. Ta buɗe bakinta muryarta tana cracking ta ce, ”Ka bari, bana so, don Allah ka ƙyale ni….” Maimakon ya dakata sai ta ji yana ƙoƙarin sauke hannun rigarta zuwa ƙasa, ta riƙe hannunsa tana girgiza kai ta ce, “Don Allah..!.” Bai cire hannunsa daga wajen ba ya sakko da kansa ƙasa ya cigaba da kissing ɗinta. Islaha kamar zata yi masa kuka ta ce, “Mr Rehaan ka bari don Allah..! Ka bari bana so..” ta faɗa zata fara yi masa kukan da bata san daga ina yake tahowa ba. Rehaan bai dakata ba, a hankali yake sauke hannun rigarta ba tare da ta lura ba har ya cire su gabaɗaya. Ya zama ya cire hannayen gabaɗaya, yana sauke rigar ƙasa shikenan. Ta runtse idanunta ta ce, “don Allah ka bari, numfashina yana tsayawa, bana jin iska, zan iya samun attack, ka bari ka ji…!.” A hankali ta ji ya dakata kamar yadda ta ce, a lokacin ta yi birgima ta dira daga kan gadon ta fita da hanzari ko waiwayensa bata sake yi ba. Yadda ta fita a guje bata tsaya ba sai da ta shiga ɗaki, zagaye take yi a ɗaki jikinta yana karkarwa kamar wacce aka ciro daga cikin ƙanƙara, ta kalli ƙofar ɗakin sai ta kuma ta zabura ta ƙarasa a guje ta sakawa ƙofar lock saboda kar ya shigo, ta jingina da ƙofar tana jin yadda zuciyarta take bugawa da sauri. Bakinta ta shafa tana jin kamar har yanzu bakinsa yana cikin mata, ta kai hannunta wuyanta ta shafa inda ya yi kissing dan har lokacin da danshin saliva ɗinsa a wajan. Ta runtse ido tana jan numfashi, tana ji zuciyarta tana bugawa a guje. Ta buɗe ido ta kalli rigarta ta ga gabaɗaya ya cire hannun rigar, kamar wacce ake yiwa video haka ta mayar da hannun a gigice tana ƙanƙame jikinta. Ta jima a haka tana samowa kanta nutsuwa, har lokacin abinda ya faru kaɗai take gani a idanunta, sautin numfashinsa da zafinsu kaɗai take ji a duk inda ta waiwaya, ta kasa wani tunani sai tunanin abinda ya yi mata. Bakinta yana rawa ta ce, "Na shiga uku! Me na aikata haka?Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Ta faɗa tana juya kai cikin wani irin yanayi da ta kasa fassara shi. Har lokacin ji take kamar kissing ɗinta yake yi, ga yadda take jin gashinsa a ƙirjinta, jikinta ya cigaba da rawa sosai, har hannunta rawa yake yi kamar wacce wutar lantarki ta ja saboda tashin hankalin da zuciyarta da jikinta suke a ciki. Ta kalli sama ta ce, "wayyo Allah!" ta faɗa tana buga kanta da jikin ƙofar, dan yanayin da take ciki zai iya sakata haukacewa. Har lokacin bata daina jin abu yana yawo a jikinta ba, har lokacin bata daina jin abu yana zaga jikinta ba, hakan ya saka ta kasa nutsuwa ko kaɗan. Sai kawai ta fashe da kukan da bata san dalilinsa ba tunda ta kasa sarrafa kanta, ba Saheer ko wani abun ne a ranta ba, sabon yanayi ne da bata taɓa ji ba shine ya saka ta kuka, ta rasa inda zata zauna ta nutsu, gabaɗaya ta ruɗe ta fita daga hayyacinta. A bayyane ta ce, “me yake niyar yi min? Sai da lokacin tafiyata ya zo zai fara ƙoƙarin yin wani abu dani?. Na shiga uku, dole na bar gidan nan, bazan sake kwana a cikinsa ba." Jikinta rawa yake yi duk ta ruɗe, karo na farko da hakan ya faru da ita a duniya, karo na farko da wani ya taɓa yi mata kiss balle romantic kiss irin wanda ya yi mata, shiyasa gabaɗaya ta susuce sai surutai take yi. Ta jima a wannan yanayin kafin ta zame ta kwanta a kan tiles, ƙhamshin turarensa jikinta yake yi gabaɗaya, har bakinta ƙhamshin bakinsa yake yi gabaɗaya hakan ya sake sakawa ta ruɗe. Ƙhamshin ya dame ta sosai, sai kawai ta miƙe ta shiga wanka ta wanke jikinta, amma duk da haka bata daina jin ƙhamshinsa a jikinta ba. Ta dawo ta kwanta amma ko ya ta rufe ido abin take tunawa, ta ɗauki pillow kan gadon ta watsar cikin fitar hayyaci ta ce, “Don Allah ka ƙyale ni na huta, ka bari na daina wannan tunanin….” Sai kuma ta sassauta murya ta kwanta lamoo akan gadon ta ce, “sai da komai ya zo ƙarshe, sai da lokacin tafiyata ya yi sannan zai dinga yi min haka…”ta girgiza kanta tana tunani sosai, ta lumshe idanunta tana tunanin ko ya ciwon kan nasa, ya daina ko yana yi masa ciwo bata sani ba.…. Nana Haleema. RDB3P77 Nana Haleema. Rehaan kuwa tunda ta fita ya koma gefe yana sauke numfashi a hankali kansa yana yi masa ciwo fiye da ɗazu, jijiyoyin kansa kamar zasu tsinke saboda yadda suke bugawa sa ƙarfi, ga wani irun sabon yanayi da bai taɓa jinsa a ciki ba yana yin nutso a jininsa, ya rasa inda zai saka ransa, abubuwan sun yi masa yaawa. Ga sabon yanayin da ya kawo masa ziyara, ga ciwom kai, ga shi Mamy bata nan. Haka ya dinga juyi akan gado yana addu'ar da ta zo bakinsa, a haka bacci ya ɗauke sa. Islaha haka ta kwana da mafarkin abinda ya faru a tsakaninsu, ko da da tashi ko wajan Mamy bata shiga ba gudun kar ta tambaye ta jikin Rehaan ta bar gidan. Shima da ya farka babu ciwon kan sai rashin ƙarfin jiki, ya shirya ya fito falo ya samu an ajjiye masa abinda zai ci. Ya san aikin Mamy ne, hakan ya saka ya sha tea yana kallo agogo ganin har azahar ta yi. Ya kalli gefensa a lokacin Bilal ya kira sa a waya, kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka Bilal ya ce, "Good evening Sir." Ya yi shiru bai amsa ba yana jira ya ji me Bilal ɗin zai ce, Bilal bai damu da shirun Rehaan ba ya ce, "Sir akwai taron da ka ce za ka je yau, ka ce na tuna maka in ranar ta yi, za a fara ƙarfe huɗu in sha Allah." Kashe wayar ya yi bai ce komai ba, ya jingina da kujera yana kallon ɗakin Islaha yana tunanin ko tana ciki ko bata nan oho. Ya shafa lips ɗinsa yana tuna yadda abin ya kasance jiya, yana jin zaƙin bakinta a cikin nasa, yana jin laushi da tsantsin bakinta kamar yadda ya ji jiya. Sai ya ji yana so hakan ta sake faruwa, ko dan ya tantamce zaƙin bakinta da ya ji daidai ne ko kuma dan ba shi da lafiya ne ya ji hakan. Sallah ce kaɗai ta tashe sa daga wajen, bayan ya idar ya sake kwanciya ko zai ji sauƙin ciwon kan. Sai ƙarfe uku ya tashi, da ya tashi ya ji sauƙin ciwon dan babu ciwon ko kaɗan. Sai ya yi wanka ya canja kaya zuwa ash ɗin shadda harda hula, ya ɗauko wayarsa ya fito parlour ya tarar da Mamy ta shigo. Ya yi murmushi ya ƙarasa ya yi hugging ɗinta ya ce, "Mamyna." Mamy ta shafa bayansa ta ce, "My son ya jikin?.” “na ji sauƙi sosai.” “Ya na ji zuciyarka tana bugawa haka, are you okay?." Ya girgiza kai yana jikinta bai ɗago ba ya ce, "I'm not okay Mamy, ban san me yake damuna ba." Ta shafa kansa ta ce, "Ayya sorry, Ka dinga addu'a a ranka ka ji?." Ya ɗaga mata kai yana sake rungume ta ko zai ji sauƙin bugun zuciyar da yake addabarsa, Mamy bata hana shi ba yana shafa kansa tana murmushi, sai da ya gashi sannan ya sake ta ta ce, "ciwon kan ya daina?." "Ya daina Mamy, yanzu ma fita zan yi na dawo." "Ina za ka je?." "Zan je wani taron ne, amma yanzu zan dawo." "Sai ka dawo, take care." Ya ɗaga mata kai ya sauka. Babban wajen taro ne mai girma, wanda yake cin mutane dubu ɗaya, an yi masa decor mai kyau da kujeru a ko ina. Manyan mutane ne a wajan. Tun daga kan gwamna da sarki da masu kuɗi da mulki, kowa da kujerar da aka tanadar masa a wajan, ƴaan jarida da masu hoto kowa yana aikinsa. Rehaan shi da Jafar suka shiga wajan, kujerun a jere, ɗaya an saka Alhaji Rehaan Yola, ɗaya an sa ka Alhaji Jafar Yola. A lokacin aka fara gabatar da taron, taro ne na karrama yara makafi da masu lalurar ji suka ƙirƙiri abubuwan masu amfani, abubuwan fasaha da al'umma zasu ƙaru da shi in an tallafawa yaran. Wani ya ƙera jirgi, wani mota, wata abinda zai taimakawa makafi, wani masu lalura ji, abinda dai ma sha Allah. Ana tsaka da taro Rehaan ya ɗago kansa ya hango Islaha a cikin ƴan jarida tana nunawa wani ɗan uwanta ɗan jarida wani abu a waya tana murmushi shima haka. Gabansa ya faɗi a karo na farko a rayuwarsa da ya ji irin faɗuwar gaban, ya runtse ido yana jin yana jin wani irin yaji yana mamaye masa ko ina na jikinsa, idanunsa har ruwa suka tara kamar wanda aka fesawa gas. Ya zuba mata ido yana kallonta, yayin da ita bata san yanayi ba, ta san dai da shi a wajan, amma bata ɗaga ido ta kalli inda ya ke ba, dan ko kaɗan bata son haɗa ido dashi shiyasa ta ƙi yarda ta kalli inda yake balle su haɗa ido. Yana can yana kallonta ana ta kiran sunansa akan ya fito ya yi magana akan yaran amma bai ji ba, Jafar ya kalli inda yake kallo ya ga Islaha ce da maza biyu a jere suna magana, sai ya ɗan taɓa sa ya waiwayo ya kalle sa ya ce, "ana jiran ka." Ya sake mayar da ido kanta, a lokacin suka haɗa ido da ita sai ta ɗauke kai tana jin gabanta yana faɗuwa ganin irin kallon da yake jifanta da shi wanda bata taɓa gani ba. Rehaan ya miƙe ya ƙarasa inda ake magana ya yi magana cikin fulfulde, sannan ya ɗauki nauyin yaran dukkansu, ya ɗauki nauyin karatunsu daga matakin primary har phd, in ƙasar za su bari su yi karatu ya ɗauƙi nauyi, komai nasu ya dawo hannunsa. Sannan ya saka a bincika lafiyarsu indai akwai wanda zai iya warkewa ya ɗauki nauyin biyan kuɗin. Sannan ya yi musu kyautar kuɗi masu nauyi, kyautar da ko gwamna da yake wajan bai yi abinda ya yi ba. Ana ta zuba masa video ana tafi, dan baƙon abu ne ka gan shi a taro, ba zuwa yake yi ba sai an ci sa a sosai, shiyasa ake ta yi masa hotuna da video. Bayan ya dawo ya zauna, Jazy ma ya je ya yi nasa ya dawo ya zauna ya kallr shi ya ga yana kallon ta, ita kuma a lokacin tana yiwa yaran tambaya suna bata amsa, ga camera ana yi mata video alamun recording ake yi. Jazy ya ce, "kana kishi ko?." Ya kalle sa ya ɗauke kai bai ce komai ba. Bayan taro ya tashi ana ta fita, ƴan jarida suka taho kansa amma aka hanasu zuwa, shine ya bada umarnin duk su ƙaraso inda yake zai amsa ko wacce tambaya, ai kuwa suka zagaye shi ana video ana miƙa masa speaker. Ray ya miƙe tsaye yana kallonsu ɗaya daga cikin ƴan jaridar ya ce, "Yallaɓai a dah ba a ganinka a irin waɗnanan tarukan, amma kwana biyu muna yawan ganin fuskar ka a ko ina, ko zamu iya sanin dalili?." Ya kalle shi ya ce, "na samu lokacin zuwa ne.” “Ka daina zaman Engalaad kenan?.” “ban daina ba.” Wani ma ya ce, "ka ɗauki nauyin yaran nan gabaɗayansu, ya ka ke jin abinda suka ƙirƙira a ran ka?." "ina alfahari dasu." "Me zaka ce akan baiwar da Allah ya yiwa yaran nan?." "Suna da baiwa ta musamman, in suka samu kulawa ƙasarmu zata samu manyan ƴan kimiya kamar su, zamu je inda ba mu yi tunanin zuwa ba saboda su." Islaha tana kallonsa yana magana ta ƙi ta motsa, bakinsa kaɗai take kallo tana tuna abinda ya faru jiya. Sai taɓe baki take yi ganin kamar ba shine ya gama taɓa mata jiki ba, yanzu gashi ya zo an zagaye shi yana jin kansa shi wani ne. Inda zata faɗawa mutane abinda ya yi mata jiya cewa za a yi ƙarya take yi, wani ma sai ya ɗauka bata da hankali dan bai yi kama da wanda zai aikata ba ko kaɗan. Chairman yana ta yi mata alama akan taje wajan Rehaan ta yi kamar bata gan shi ba, sai da suka haɗa ido sannan ta yi tsaki ta ƙarasa ta ɓuya a cikin mutane, sai voice ɗinta da speaker hannunta da ta miƙo inda yake ta ce, "Da gaske Mr Rehaan zai iya cika alƙawarin da ya ɗauka akan kula da yaran nan? Mun sha jin irin waɗannan alƙawarin daga bakunan mutane, alƙawarin na gaske ne ko irin wanda muka saba da shi ne?.” Duk da akwai hayaniya a wajen bai hana ya ji zaƙin muryarta har tsakiyar kansa ba, ya kalli inda ta ke tsaye, yana kallon hannunta da ya ɗan leƙo ta cikin mutane, sai ya yiwa mutanen wajen alama da su buɗa wajan, aka buɗa wajen Islaha tana tsaye tana kallon gefe har lokacin bata ɗauke hannunta da ta miƙa masa speaker ba. Ta juyo ta kalle shi, ya yi mata alama da ta zo da hannunsa. A take idon mutane ya dawo kanta, kowa ya zuba mata ido ana jira a ga zata je ɗin ko baza ta je ba. Saboda gudun abin magana sai yi ƙaramin tsaki ta ƙarasa zuwa wajan tana kallonsa. Rehaan kallonta yake yi yana jin nishaɗi mai yawa yana ratsa shi, in yana kallonta sai ya ji kamar babu wanda ya kai shi farin ciki a duniya. Sai da ta ƙaraso sannan ya kalli cikin idanunta ya ce, "Maimaita, me ki ka ce?." Ba tare da shakka ba Islaha ta ce, "Da gaske Mr Rehaan zai cika alƙawarin da ya ɗauka ko kuwa ya faɗa ne saboda idanun mutane?.” Ray ya kalli Jazy da yake wani smiling daga tsaye, ya kalle ta amma bai ce komai ba. Ɗaya daga cikin ƴan jaridar ya yi caraf ya ce, "ƴar jarida Islaha ce ta fara hira da kai da harshen hausa a kaf nigeria, kowa ya ga yadda hirar ta kasance da duk abinda ya faru. Mutane suna ta yaɗawa akan akwai ɓoyayyiyar alaƙa a tsakaninka da ita, zamu so mu ji daga bakin ka, da gaske akwai alaƙar ko babu?." Gabanta ya faɗi sosai amma bata nuna ba, ta kalle shi suka haɗa ido sai juyar da kanta gefe, dan wani irin kallo yake yi mata wanda yake yi mata nauyi, sai ta ji ta kasa jurewa sai ta ɗauke idonta daga kansa. Ita kuma in ta kalle shi daren jiya take taunawa, shiyasa bata yarda su haɗa ido, kuma bata damu da tambayar da aka yi masa ba, dan ta san ba faɗar alaƙarsu zai yi ba. Rehaan da yake kallonta ya yi murmushi ya ce, "yeah akwai alaƙa a tsakaninmu!." Islaha ta zaro idanu waje, da hanzari ta juyo suka haɗa ido, idanunta suka firfito waje tana girgiza masa kai alamun kar ya faɗa don Allah. Rehaan ya yi wani irin murmushi yana bin fuskarta da kallo, yana rolling idanunsa a fuskarta yana jin nishaɗi a zuciyarsa. Sai ya zura yatsunsa a cikin nata, ya sarƙe hannunsu waje ɗaya yana kallon fuskarta. Ta so ƙwace hannunta amma ta kasa, babban tashin hankalinta a gaban ƴan jarida ga shi ana ta ɗaukarsu hoto, kar ta yi wanj abin da zai jawo mata ɓatawar suna, ta haƙura da ƙwace hannunta ta kalli ƴan jaridar ta ce, "he is my...." "she is my wife.....” Ya dakata yana kallon idanunta sannan ya ce, “my secret wife" ya faɗa yana kallon idanunta da suka firfito waje, kafin ya duƙa ya yi picking ɗinta a kumatu. Islaha sai ta ɗan firgita lokacin da ta ji bakinsa a cheeck ɗinta, ta daskare a wajan idanunta suna waje ta zazzaro su saboda tashin hankali...... Nana Haleema. RDB3P78 Nana Haleema. Islaha kallon idanunsa take yi idanunta a waje saboda tsoro da tashin hankali, kwata-kwata bata taɓa zaton zai furta wannan maganar ba, ba taɓa tunanin zai amsa shine mijinta a gaban ƴan jarida ba. Ta zuba masa ido tana kallonsa cikin tashin hankali, sai da ya murza yatsunta sannan ta dawo hankalinta ta kalli yadda idanun mutane yake a kansu gabɗaya, sai ta ji kunya ta lulluɓe ta kamar ta nutse a wajan. "Yallaɓai tun yaushe hakan ya faru?." "Kenan da gaske itace matar sirrin da aka ce ka yi?." "Daman ita ce wacce ka aura?." "Meyasa da ta yi hira da kai bata faɗa ba?." Tambayoyin da ake ta yi masa kenan, shi kuma idanunsa yana kanta yana kallon yadda ta firgita da kalamansa, kafin ya juyo ya kalli ƴan jarida, sai ya kalli Jazy da ya yi clapping hannunsa alamun ya kyauta. Ya ɗauke kansa yana riƙe da hannunta bai saki ba, ya ja hannunta zasu tafi ya ji ta turje, ya kalle ta suka sake haɗa ido ya sunkuya ya kai bakinsa kusa da kunnen ta ya ce, "mu tafi, ko in ɗauke ki." Islaha ta sake kallonsa dan gani take kamar an canja shi, ba Mr Rehaan ɗin da ta sani ba, wani ne daban a gabanta ba wanda suka saba kafsa faɗa bane ba. In kuwa shine to ciwon kan da ya yi jiya ya taɓa masa ƙwaƙwalwa, ko kuma ya manta wacece ita shiyasa yake yi mata waɗannan abubuwan da bata taɓa zato ba. A ganinta inda ya san itace bazai yi ba, shiyasa ta saka a ranta bai fahimci ita bace. Jin ya ce zai ɗauke ta sai ta yi sanyi sosai, dan bata shiryawa faruwar hakan ba, ya barta ta ji da abinda ya faɗa a gaban mutane ba sai ya sake ƙara mata wani tension ɗin ba. Rehaan ya ja hannunta suka tafi, ita dai ta san an karɓi loudspeaker da take hannunta bata san waye ba. Har suka je wajan mota yana riƙe da hannunta, sai da suka je wajen motar sannan fizge hannunta zata fara yi masa masifa ya kalli fuskarta ya ce, "Calm down! Akwai securities a nan, ki bari mu koma gida." Wani irin wuci ɓacin rai take yi wanda Jazy ya lura da shi, ko ba a faɗa ba ya san Rehaan ya ɓallo ruwa mai kwarara daga sama, dan ya san bata yi tunanin zai faɗi alaƙarsu a wajan ba, ya san ko da wasa bata yi hasashen zai bayyanawa duniya uta matarsa bace. Shi kuma ya ji daɗi da ya faɗa ɗin, ko babu komai Poor Saheer zai san ta fi ƙarfinsa, zai daina hangenta har ya saka a ransa zata dawo. Matar da Rehaan ba matarsa bace, koda Rehaan ya rabu da Islaha a ganinsa ta fi ƙarfin Saheer. A haka suka shiga mota shi da ita aka ja motar suka tafi. Maimakom ta ga an wuce gida sai ta ga sun nufi ɗaya daga guest house ɗinsa, ta yi shiru ta daure bata ce komai ba, ga shi ya riƙe mata hannu ya hanata ƙwacewa, ta juya tana kallon window tana jira su sauka daga motar. Sai da zasu fito daga motar sannan ta fizge hannunta, ya sake riƙo hannunta yana yi mata magana da ido, kamar wacce ya yiwa asiri sai kawai ta dakata yana jan hannunta har suka shiga parlour. Suna shiga ta ƙwace hannunta cikin masifa ta ce, "meye naka na faɗawa duniya ni matarka ce, meye na yi hakan?.” Ya waiwayo yana kallonta yana cire hular kansa, Islaha ta ce, "Na ga a cikin rules ɗinka da ka rubuta min ka ce baka so duniya ta san ni matar ka ce, meyasa ka ke breaking rules ɗinka da kan ka?.” Islaha ta ɗora ta ce, "meye dalilinka na faɗa? Kawai dan ka wulaƙanta ni? Saboda ka nunawa duniya bani da wani mahimmaci shiyasa ka yi min haka? In faɗar zaka yi ka faɗawa abokanka a waya mana, amma meye na faɗa a gaban ƴan jarida? Kawai dan ka ɓata min rai ne ko?.” Rehaan bai ce komai ba dan shi farin ciki yake ji a zuciyarsa ba tare da ya san dalili ba, kallonta yake yi yana jin shauƙi da bugawar zuciya, dan yadda take yi masa faɗan ma kyau take yi ƙarawa, sai ya ji dama zata cigaba da faɗan shi kuma yana kallonta. Ita kuwa Islaha da gaske ta ji haushin abinda ya yi mata, dan ta san yanzu ta shiga uku a social media, inda bata yi tunanin videon zai je ba ma sai ya je. Daman ga abinda ya yi mata jiya yana ranta, ga wani ya sake maimaitawa. Ganin tana yi masa magana ya ƙi kulata sai ta sake fusata, ta kalle shi shi ta ce, "don Allah ka kira ƴan jarida ka faɗa musu ni ba matar ka bace wasa ka ke yi, wallahi bana so" ta faɗa idanunta yana cikowa da hawaye zata yi kuka. Rehaan da yake kallonta ta ya ce, "Kema ƴar jarida ce ko? Why not ki yi min video sai in faɗa?." Islaha ta ji kamar ta tsinka masa mari saboda  takaici, ta tsaya tana kallonsa dan da zata iya tsaf zata mangare sa ya zube a wajen. Kawai sai ta zube a wajan ta saka masa kuka, shi dai yana tsaye yana kallonta ya rasa me zai ce mata ganin da gaske take kukan, tun yana kallon ta har ya fara jin zafin kukanta a cikin ransa. Muryar ta tana rawa ta ce, "meyasa za ka yi min haka? Meyasa za ka cewa ƴan jarida ni matarka ce?. Ka san ni matar contract ce ba matar aure ba, lokaci kaɗan ne ya rage contract ɗin mu ya ƙare, meyasa zaka faɗa ka ce ni matar ka ce?. Tun meyasa baka taɓa faɗa ba sai yanzu? Kawai dan ka wulaƙanta ni, kawai saboda mutane su san ka aure ni bayan na bar gidanku?.” Kafin ya yi magana wayarta ta fara ƙara, ta kallah ga sunan Hamma a kan screen ɗin yana yawo, ta ɗago ta kalli Rehaan da yake kallonta ta ce, "Ni ba mu yi haka da kai ba, ba mu yi za ka dinga karya min rules ɗina ba. Amma yanzu sai breaking ka ke yi kana yi min duk abinda ka ga dama, sai da lokaci ya zo ƙarshe zaka dinga canjawa?" Ta faɗa tana kuka. Kukan da take yi ya ba shi mamaki sosai, kukan da take yi akan ya faɗawa ƴan jarida ita matarsa ce ya saka ya ji zuciyarsa cike da takaicin ɗora aurensu akan contract, ya saka shi yana jin ina ma bai amince da duk wasu rules ba an yi auren haka kamar ko wanne ai, da hakan ne ya kasance baza ta dinga yin kuka dan ya ce ita matarsa bace. Zuciyarsa tana faɗa masa akan Saheer ta ke wannan kukan, kishi yana mamaye masa zuciyarsa, abinda bai taɓa ji akanta ba yana mamaye masa zuciyarsa. Shi da yake mijinta bai yi kuka akan kalamanta ba sai ita ce zata yi kukan rashin dalili?. Ta rufe fuska da hannayenta tana kukan da bata san dalilinsa ba, tana ji wayarta tana ƙara ta kasa ɗauka dan tasan Saheer ne, kuma ta san akan video zai yi mata magana ita kuma bata so. Rehaan kallon ta kawai yake yi yana jin kishin Saheer a zuciyarsa, bai taɓa jin kishin abu kamar yadda yake jin kishin Saheer a lokacin ba, bai san haka kishin ya ke ba sai yanzu da take kuka saboda wani daban ba shi ba. Zafi yake ji a jikinsa kamar ana tasafa jininsa, zafin jinin yana zaga ko wacce jijiya ta jikinsa har cikin ƙwaƙwalwarsa. Ya kasa ce mata komai, ya yi shiru kawai yana kallon yadda take kuka. Da baya-baya ya shiga ciki ya barta a falo, ya tsaya ya jingina da bango yana jin zuciyarsa tana bugawa da gudu, ya dafe zuciyarsa da hannunsa na dama, yana jin yadda ƙirjinsa yake ɗagawa saboda bugun zuciya. Zafin kishin da yake ji ya saka shi ya cire rigar jikinsa ya ajjiye ya, ya cire dogon wandon ya zauna a gefen gado yana ji kamar ya yi kuka saboda takaici. Jazy ne yake kiransa a kira shi a waya ya ɗauka Jazy ya ce, "weldone! You shake the world, my guy. Ka ga yadda ku ke trending a duniya kuwa? Kuma ni wallahi ka burge ni, yanzu Saheer zai san Islaha ba matarsa ba ce." Cikin wata irin murya mai cike da rauni ya ce, "Like how? Kana ganin yadda take kuka kawai dan na ce ita matata ce? Tana parlour tana kuka saboda shi, tana kukan kar ya ga na ce matata ce." "Ka bata lokaci yanzu baza ta fahimta ba, amma nan gaba zata gane." Ray ya ce,"Jazy zuciyata bugawa ta ke yi." "Kishi ne, ba ka fara jin komai ba indai akan soyayya da kishi ne Rehaan." "ina ji kamar na yi kuka, Jazy jikina rawa yake yi." Jazy ya ce, "kishin kenan, yanzu ka fara son Islaha shiyasa za ka yi kishin da Saheer, kuma ya cancanci ka yi kishi da shi. Tun farko kai ka ba da matsala, da ka ɗora auren ku akan hanya mai tsafta da haka bai faru ba." Ray ya lumshe ido yana sauke numfashi ya ce, "na yi danasani, ina jin kamar na koma baya na yi erasing contract agreement. Ka bani shawara Jazy, zan rasa hankalina." "Rehaan ka yi abinda ya kamata kawai." "Kamar me?" Ya faɗa cike da gajiya da maganar. "Kana mijinta har sai na faɗa maka abinda ya kamata ka yi? Think." Rehaan ya yi shiru yana tunani, lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarsa ta harba ya hau kan layin da Jazy yake so ya hau, sai ya buɗe idanun waje cikin bugawar zuciya ya ce, "Jazy!." Ya katse shi ya ce, "ba lokacin jira bane yanzu, ba ka da cikkaken lokacin da zaka ce jira sai kun saba kafin wani abu ya haɗa ka da ita, ka yi amfani da duk damar da ta zo hannun ka, in ba haka Islaha bazata saka a ranta kai mijinta bane, zata cigaba da kallonka a matsayin mijin contract ba mijin aure ba. In kuma ka yi abinda nake faɗa maka abubuwan za su zo mana da sauƙi, ban san ka da losing oppurtunity ba Ray, kar ka fara daga yau, kar ka fara daga kan Islaha." "Kar ka bari tunanin conditions ya hanaka, duk abinda ka ke ji a kanta ka yi kawai, ka donga tunawa ita ɗin matarka ce, kana da iko da ita a ko yaushe. Ni premarital test nake tunani tunda ba ku yi, na san genotype ɗinka AA bani damuwa da shi, but Rhesus Factor and Hepatitis B & C shine abin jin….” Rehaan cikin rashin damuwa ya katse Jazy ya ce, “Ni ban damu da wani premarital test ba Jazy, ko wacce cuta ce a jikinta i can take it. Ni da ita na damu ba da wani test ba, bana so na rasata, in na rasata za ku iya rasa ni Jazy!” Ya faɗa cikin sanyin murya. Nana Haleema. RDB3P79 Nana Haleema. Jazy ya yi dariya jin baturen mutuminsa yana cewa shi bai damu da test ba, mutumin da yake da taka tsan-tsan akan lafiya, komai sai ya ce sai an yi gwaji. Akan Islaha ya fara ɗaukar housemaid ba tare da gwajin jini ba, ya saba sai an yi gwajin ciwon hanta da hiv wani lokacin harda gwajin TB. Amma yau Rehaan ne yake cewa shi bai damu da gwaji ba saboda soyayya. Jazy ya sake yin murmushi sannan ya ce, “Ahhh kamar lokacin da ta yi signing ta taho da takardar, na tuna ta yi test ɗin tabbas.” Rehaan a gajiye ya ce, “Jazy ni ba batun test nake yi maka ba, ina yi maka magana akan rayuwata. In ka bari ta tafi nima zan tafi.” Jazy kamar ya tsokane shi ya ce daman ai ba shi ya kawo ta ba balle ya hanata tafiya, amma a yanayin da yake ciki bazai iya tsokanarsa ba hakan ya saka ya ce, “Rehaan in ka bar wannan damar ta wuce ka baza ka sake samun wata ba, kawai ka yi amfani da ita a duk inda ta zo maka. Ni dai so nake ka tabbatar da maganata akanta, yadda zaka sake ninka wata uku nan gaba akan ragowar da suka rage maka. Koda rabuwa ta gifta dole sai ta jira ta yi maka iddah, kuma wannan ma lokacin ka ne. Balle bana fatan a rabu, kawai ka san abinda ya kamata ka yi kafin ka buɗe ido ka ga babu Islaha.” Ray ya yanke wayar ya kwanta a kan kujera ya dafe kansa yana juya maganganun Jazy a ransa. Tunani yake ta ina zai fara? Ta wacce hanya zai ɗauki layin da Jazy yake so ya ɗauka? Shi ba ya son saka ta a damuwa, ba ya son ya yi mata abinda bata so, ba ya so ta cigaba da kallonsa a a tsayin mai karya nata sharuɗa kamar yadda take faɗa ko yaushe. Yanzu ya zai yi? Shawarar Jazy zai ɗauka ko kuma zai cigaba da zuba mata ido har lokacin rabuwarsu ya yi?. Yana ta jin shigowar saƙo wayar, ya kalli notification ya ga messages ne ana ta ya sa murna da ake yi na auren da ya ce ya yi, ya danna power wayar ta ɗauke, ya yi shiru yana jin zuciyarsa tana bugawa a guje. Islaha tana zaune a parlour mararta tana ɗaurewa, ita kanta ta yi mamakin jin ciwon tana tunanin kamar lokacin bai yi ba, tana kukan Rehaan ya ce ita matarsa ce tana kukan ciwon mara. A lokacin aka sake kiran wayarta da ta ke kusa da ita, sai ta ɗauka ta saka a speaker kafin ta yi magana Saheer ya ce, "Islaha!." Hawaye ya ciwon mara ya zubo daga idanunta, ta runtse ido maimaikon ta ba shi amsa sai ta ce, "ni ban san dalilinsa na yin hakan ba, amma ba daga ni bane." Saheer bai yi niyar yi mata maganar ba, amma jin ta kawo maganar sai ya ce, "Islaha ya faɗawa duniya ke matarsa ce, sannan ya pecking ɗinki a gaban kowa, ya yi holding hannunki yana kallon cikin idanun ki. Ni ban ce ya yi laifi ba tunda ke matarsa ce, amma batun dawowar ki na haƙura kawai, dan na san baza ki taɓa dawowa gare ni ba." Islaha zuciyarta ta karye jin kalaman Saheer, tana tunanin shikenan zata tabbata ta zaɓi kuɗi akan halacci. Cikin gigicewa ta ce, "Kar ka sare, kar ka ji tsoro Hamma, na yi maka alƙawari zan dawo, bazan taɓa zama matar wani ba sai kai, kai ɗaya na shirya rayuwar aure da shi ba wani ba. Na aure sa saboda kai, kuma zan fito saboda kai, kuma na aure ka na zauna da kai." "Islaha tsoro nake ji, gwara kawai na haƙura mu cigaba da kasancewa a matsayin Yaya da ƙanwa. Yana da kuɗi da ikon da baza ki iya ja da shi ba." "kuɗinsa ɗin banza da wofi, ni kuɗinsa ba sa gabana, abinda yake gabana kawai na sani, kuma shi zan yi. Hamma kar ka yi tantama akan alƙawarin da na yi maka, wallahi sai na dawo gare ka a daidai lokacin da muka tsara hakan, zan aure ka a lokacin da da ka tsara auren. Abinda ya faru yau kar ya dame ka, in ma ya yi ne saboda wani dalili shi ya sani, ni dalilinsa ba ya gabana!." Ya yi shiru kawai bai ce komai ba, dan da gaske hankalinsa ya tashi sosai, ya kasa zaman Niger jirgi yake nema kawai ya dawo nigeria, dan tunda aka ɗauke su a hanya ya daina zuwa a mota sai jirgi, da ace ya samu jirgi a ranar zai dawo bazai cigaba da zama ba. Ya kalli video ya fi sau babu adadi, babu abinda yake sakawa ya ji babu daɗi zuciyarsa kamar pecking ɗinta da ya yi a kumatunta, faɗar matarsa ce bai dame sa ba saboda yasan gaskiya ya faɗa, yadda yake kallonta ya ɗaga masa hankali, dan kana ganin kallon ka san na soyayya ne zallah. (kai ma dai Hamma kana tare da wahala). Saheer ya sauke numfashi ya ce, "In ban yi haƙuri ba me zan yi? Haƙuri ya zamar min dole, amma...." Sai bai ce komai ba ya yi shiru. "Hamma alƙawarin Islaha ne, babu mijin zata zauna dashi a matsayin mijinta sai kai, in na bar ka ban yi halacci ba, ni kuma bana so na zama butulu a duniya, ka yarda dani Hamma." Bai ce komai ba ya yanke wayar, ta yi tsaki tana danasanin zuwa wajan taron. Facebook ta shiga ta ga yadda ake ta zuzuta maganar, ga mutane suna ta comments da Allahamumma bareek, ga masu cewa ta yi sa a suna yi, masu cewa basu dace ba suna faɗa, masu cewa sun dace suna faɗa. Islaha ta yi tsaki ta ce, "ku ne ƴan wahala da ku ke ganin zama da wannan sa a ce, ni a gare ni babbar rashin sa a ce. Meye abin so a tare dashi oho, haushin matan da suke haukacewa a kanaa nake yi.” Sai kuma ta kalli inda ya shiga ta ce, "ya zama dole na je mu yi ta ta ƙare, yana karya min rules, ko ya sake ni ko ya tsaya iya matsayinsa har kwanakin mu su ƙare" ta faɗa tana miƙewa ta shiga inda ta ga ya shiga. Rehaan yana daga tsaye yana kallon ta, duk abinda ta faɗa ita da Saheer ya ji, ya cize lips ɗinsa ya koma ganin ta taho a fusace irin jaruman india nan. A tsaye ta same sa ya juya baya yana sanye da baƙar bathrub wacce ta tsaya a iya guiwarsa. Tana shiga ta a ce, "Mr Rehaan na zo mu yi magana ta ƙarshe, don Allah mu kawo ƙarshen contract ɗin nan kowa ya huta." Ya juyo ya kalle ta, yana jin kishin Saheer yana mamaye masa zuciya, kishi ya hana shi yi mata magana ya ɗauke kai. Islaha ta ce, "ina magana ka yi min banza, kana ta breaking rules ɗina bayan ba haka muka yi da kai ba, mu ajjiye abinda ya faru jiya a gefe. Meye naka na faɗawa duniya ni matarka ce bayan ka ce baka son kowa ya sani? Kai ka ce min auren sirri mu ka yi, meyasa za ka faɗawa ƴan jarida da kanka?." "Saboda ba na sirrin bane." Ta shiga shock da kalamansa amma sai ta ce, "Dole ya zama na sirri, kamar yadda ka ɗora auren a kan haka dole ya cigaba da tafiya a haka. Ka ɓata min rai da abinda ka yi yanzu, ka ɓatawa......" Sai harshenta ya sarƙe ta kasa faɗar sunan Saheer, sai ta canja maganar ta ce, "ka ɓatawa waɗanda nake tare dasu rai." Rehaan da ya ji kamar ya yi ta dukan kansa har aai ya fitarwa da kansa jini, ya cize bakinsa cikin yanayin kishi ya ce, "Nawa za a biya shi ya yi farin ciki?." Ta sake kallon sa ta ce, "what! Kana tunanin akwai abinda za ka basa ya yi farin ciki da ya wuce ni? Ko kana tunanin ina zaune da kai a nan saboda kuɗi ne?." Sai kuma ta dafe kai ta ce, "ai baka da kuɗin da zai karɓa daga gare ka ba, ba ka da kuɗin da zaka iya siyana daga wajensa. Kuma inda ace na san kallon da ka ke yi min kenan, da duk abinda na yi maka wallahi sai ka biya ni, ina so mutum ya cigaba da kallona a yadda yake kallona, bana so na canjawa mutum fahimtarsa a kaina. Har jinyarka da Mamy ta dinga saka ni, da wacce ta wuce da ta jiya wallahi da sai ka biya." Rehaan ya yi murmushi yana mamakin ko yaushe ya ce mata tana zaune da shi dan kuɗinsa oho. Ya waiwayo yana kallon ta yana takawa zuwa inda take ita kuma tana yin baya kaɗan-kaɗan tana cewa, "ka daina bana so, ka dakata don Allah." A daidai lokacin suka zo kusa da gadon, ya saka hannu guda ɗaya ya turata ta faɗa kan gadon, ya kwance igiyar gaban rigar wankansa ya buɗe ta ba tare da ya cire ba, ya bi bayanta ya dafa hannayensa a kan gadon yana kallon idanunta. Islaha yadda ta faɗa kan gadon ya tsorata ta, ga shi ta ga yana kwance riga ya buɗe ta ya saka ta yi saurin rufe ido gabanta yana faɗuwa amma ka kasa magana. "Kina magana akan kissing ɗin ki da na yi jiya?....." ya faɗa yana ɗora yatsansa akan lips ɗinta yana zagayawa da shi. Ya sake sunkuyowa yana kallon bakinta kamar zai ɗora nasa akan nata sannan ya ce, "Fine! One million to whatever you want, is enough to buy you again?." Nana Haleema. RDB3P80 Nana Haleema. Islaha ta tsorata sosai musmaman da ta ji maganarsa daf da ita, kuma ga shi ya ɗora yatsansa akan bakinta. Ta wuntsila ta juya ta sauka daga kan gadon, cikin masifa da tsiwa ta ce, "You treat me like i'm just some toy, that you can wind up and toss aside. Na fi ƙarfin ka yi wasa da hankalina, kuma ka tsaya a inda ka ke tun farko, ka daina zuwa inda baka da hurumi a kai. Ka yi min jiya na yi shiru ban ce komai ba, ba dan ka yi nasara ba sai dan saboda wani dalili nawa shiyasa na share maganar ban ce maka komai ba..” Daga jiya ya zama na ƙarshe, kar hannunka ya sake zuwa jikina, ko da wasa kar ka sake kuskuren cewa zaka taɓa ni. Ni matar yarjejeniya ce, ina da hujjar da zan kai ka court akan taɓa min jiki, tunda ina da shaida ka saka hannu kuma ka amince baza ka taɓa ni ba. Ka dakata haka don Allah, ka jira lokacinmu ya ƙare kowa ya kama gabansa.” “In na tafi sai ka manta ya kalar fuskata take, ni daman ban riƙe kamaninka ba balle har na tuna. A zamana da kai babu wani abu mai amfani da zan dinga tunawa dashi lokacin da na bar gidan. Sai sharrin ƴan gidanku da sunayen da ka dinga kirana da shi, ni bani da lokacin tunawa da kai kaima ka daina, mu jira lokaci ya ƙare kowa ya watse” ta faɗa tana fita daga ɗaki. Ya yi murmushi yana shafa fuskarsa cikin nishaɗin da yake ji yana ratsa shi, in ya tuna ita matarsa ce ta aure farin ciki yake ji, iya hakan sai ya dinga kore masa tunanin Saheer da tsiyarsa. Ya sake yin ya ce, "C wife! you make me joy."    Islaha haka ta dinga hauka tana buge-buge a ɗaki ga ciwon mara da ya fara damunta, ga damuwar Rehaan da take nema ta saka maganar su Adda ta tabbbata a kanta. Gabaɗaya ta fita daga hayyacinta saboda takaicin da ta ɗorawa zuciyarta, tana ganin Safeera tana yi mata waya ta kasa ɗauka, haka ta gama haukanta ta kwanta a kan gado ta fashe da kuka saboda ciwon da ya fara damunta. Rehaan bai sake ganinta ba har dare ya yi, bai san a wanne ɗaki ta shiga ba dan ɗakunan gidan suna da da yawa. Yana so ya je dubata amma zuciyarsa tamna hana shi yin hakan, tun yana daurewa har ya kasa ya miƙe ya nufi ɗakin da ya ke kusa da wanda yake ciki amma bai ganta ba, ya rufe ya tafi wani nan ma bai ganta ba, ya sake duba wani nan ma bata nan. Sai ya ji gabansa ya faɗi, duk ya san bazata fita bai sani ba amma sai ya ji tsoro, da hanzari ya hau painthouse ya buɗe ɗakin, ga mamakinsa tana ciki a kwance a kan tiles tana kuka. Ya yi ajiyar zuciya yana girmama girman taurin kan Islaha, duk ɗakunan da suke gidan sai ta hau sama na uku sannan ta kwanta. Jin kukanta ya saka ya shiga da sauri ya duƙa a kusa da ita ya saka hannunsa ya ɗogota ya ji jikinta ya yi zafi sosai. Hankalinsa ya tashi sosai ya dafa kanta ya ji da zafi sosai cikin damuwa ta ce, "me ya same ki?." Islaha bata yi magana ba sai jan numfashi da take yi a hankali cikim ciwon mara, Rehaan ya rasa ya zai yi, ga shi bai san actual abinda yake damunta ba, ga shi farin shigar soyayya duk ya ruɗe. Hannunta ya gani a ƙasan cikinta, sai ya sake kallon fuskarta ya fahimci abinda yake damunta. Ya ɗagata cak ya kwantar da ita a kan gado, ya fara kalle-kalle a ɗakin dan ya san babu water bag, kuma kafin a kawo masa za a ɗauki lokaci. Gabaɗaya ya gigice saboda yadda ya ji jikinta ya yi zafi, ya shiga banɗaki ya kunna hot water, ya saka ƙaramin towel a ciki ruwan sannan ya dawo inda take. Ya zauna a kusa da ita yana kallonta, yana so ya yi undressing ɗinta ko zata ji daɗi amma ya kasa, ya rasa ta ina zai fara cire doguwar rigar jikinta. Ganin in bai taimaka mata ba babu mai taimaka mata, sai ya fara unziping doguwar rigar ta buɗe ta gaba, idanunsa ya sauka akan farar vest ɗin jikinta da dogon wando baƙi. Idanunsa yake buɗewa a kanta sosai, yana zagayawa da idanunsa akanta, yana bin lungu da saƙo na jikinta da kallo har sauke idanunsa a ƙirjinta, yana kallon yadda ƙirjinta yake ɗagawa  yana sauka a hankali. Rehaan ya yi saurin ɗauke idanunsa gabansa yana faɗuwa, ya sake kallonta sai ya ga ta juya kanta gefe ya miƙe tsaye ya koma bathroom ɗin ya ɗauko towel ɗin da ruwan zafi ya tsuma shi sosai, ɗaƙyar ya iya matse ruwan saboda zafi, yana yi yana yarfe hannu saboda ya yi zafi sosai. Ya ɗauko shi a hannunsa ya tako a hankali ya zauna a kusa da ita, ya kai hannunsa kamar mai jin tsoro yana ɗaga vest ɗin jikinta. "Ya salam!." Ya furta lokacin da idanunsa suka sauka a kan navel ɗinta, ya yi saurin ya ɗauke idanunsa daga kai yana jin gajiya ta tarar masa lokaci ɗaya, hakan ya saka ya fara sauke numfashi kamar wanda ya yi gudu. Rehaan ya sake ɗora hannunsa a saman dogon jeans ɗin jikinta, ya waiwayo yana kallon flat tummy ɗinta kafin ya ɗan zame shi daga sama. kaɗan.  A lokacin Islaha ta farga yana zame mata jeans ɗin jikinta ta zabura tana cewa, "Mr Rehaan ka daina yi min haka bana so!.” Yadda take maganar ya san tana cikin ciwo sosai, hakan ya ya ce, "taimaka miki nake yi, calm down" ya faɗa yana ɗora towel ɗin a saman mararta. Bata san ta ɗora hannunta a kan nasa ta riƙe da ƙarfi ba, ta rutse idanunta ta ce, "zafi!." Ya lumshe idanunsa yana jin sabon abu yana fizgarsa sosai, hakan ya saka shi ya yi pecking goshinta ya ce, "sorry." Har lokacin bata cika hannunsa ba ta lumshe idanunta, sai kuma ta fashe da kukan shagwaɓa ta ce, "ni gida nake so na tafi, bana son zama a nan. Ka daina taɓa ni, bana so kana yi min haka. Dan ka ga bani da lafiya ko? In lafiyata ƙalau bazan bari ta taɓa ni ba.” Rehaan ya ƙara matsawa kusa da ita, ya ɗago ta gabaɗaya ya yi mata masauki a jikinsa, still hannunsa yana dafe da towel ɗin jikinta saboda kar ya faɗi, ya tallafo ta saka hannunsa guda ɗaya ya riƙe bayanta, ya haɗata da jikinsa ita kuma ta kifa kanta a ƙirjinsa, ya zame hular kanta kyakykyawar kalbarta ta bayyana a idanunsa. Islaha bata daina kukan ba kanta yana kwance ƙirjinsa tana yi masa ƙaramin kuka na shagwaɓa, shi kuma hakan da take yi kwance masa nuts ɗin kansa take yi da wannan kukan nata, gata a jikinsa a kwance, ga hannunsa yana jikinta, daƙyar yake controlling kansa dan yanayin da yake ji ya fara girmar tunaninsa. Ya ɗora kansa a gashi kanta ya ja numfashi yana shaƙar ƙhamshin da yake fita daga kanta a hankali, a hankali yake shafa bayanta ya kai bakinsa kunneta yana hura mata iska a hankali ya ce, "sorry!." Bata daina kukan ba sai ƙara cigaba da ta yi, gashi kana ji ka san ba kukan gaskiya bane kawai na shagwaɓar da ta saba ne. Gabaɗaya ta ruɗa Mr Rehaan Yola, ya gigice mata yana jin kukanta har zuciyarsa, yadda kanta yake a kife a ƙirjinsa haka yake jin kukan yana ratsa fatar jikinsa yana shiga tsakiyar zuciyarsa, ga zafin da jikinta ya yi yana shiga nasa, ga kukan da take yi yana cigaba da ruɗa masa tunani. Rehaan ya kasa controlling feeling ɗin ya sake matse ta a jikinsa yana lumshe idanunsa, ya cire hannunsa da yake kan towel ɗin ya saka a cikin vest ɗin jikinta yana shafa flat tummy ɗinta a hankali. Islaha jin ɗumin hannunsa a fatar jikinta sai ta riƙe hannunsa ta ce, "ni ba mu yi haka d kai ba, ka bari bana so, don Allah ka ƙyale ni" ta faɗa amma kuma sake riƙe shi tana yi masa kuka. Ya ɗago yana kallon fuskarta da idanunta suke a rufe, ya zare hannunsa daga vest ɗin jikinta ya goge hawayen fuskar ta yana kallon bakinta wani abu yana jansa zuwa gare ta, ya ja numfashi daƙyar yana ji zuciyarsa kamar zata fito saboda bugawar da take yi. "Ka bani magani..." "cikina...!" Ta faɗa tana kwance a jikinsa. Faɗar hakan da ta yi ya saka shi ya rutse ido yana taune bakinsa, a bayyane ya ce, "Ya Salam!." Ya furzar da iska mai ƙarfi, ya saukar da fuskarsa ƙasa ya ɗora bakinsa a kan nata ya ɗan yi kissing kaɗan ya dakata, ya dinga bin fuskarta da kallo yana sake hango asalin kyaun da Allah ya yi mata. "Please, ka bari.." ta faɗa muryarta tana rawa, bakinta yana rawa kamar mai jin sanyi. Bai san ya fara kissing lips ɗinta ba sai da ya ji ta chakumi bayan rigarsa tana haɗawa da fatar bayansa ta baya ta riƙe da ƙarfi, hakan da ta yi shine ya faargar da shi yana kissing ɗinta. Kissing ɗinta yake yi softly, shi kansa bai san ya iya kiss ba, ya san dai yana gani a tv ko a ƙasashen waje, amma bai taɓa gwadawa ko da wasa. Nana Haleema. RDB3P81 Nana Haleema. Islaha shiru ta yi na wani lokaci ta rufe idanunta tana sauraren bugun zuciyarta, har lokacin bata cika rigarsa ba ta riƙe shi ƙam kamar mai jin tsoron wani abu zai kamata. Ta yi shiru tana jin yadda yake kissing ɗinta ita kuma ta riƙe hayan rigarsa. Shi kuma jin ta tsaya bata ƙoƙarin ƙwace kanta sai ya samu damar sake riƙo ta, ya cigaba da kissing ɗinta yana jin bakinta kamar zuma. Islaha ƙoƙarin zame kanta take yi, amma bata da ƙarfi kuma ya riƙe ta sosai yadda baza ta motsa dakyau ba, ga abinda take ji yana flowing daga jikinta wanda ko ba a faɗa ba ta san blood ne. Hannunsa ɗaya ya saka a rigarta ta baya yana shafa soft skin ɗinta mai ɗaukar hankalinsa har lokacin bai daina kissing ɗinta, tun daga wuyanta yake kai hannunsa yana shafawa har inda jeans ɗin jikinta ya tsaya, yana ji zafin jikinta yana raguwa, kuma ta tsaya ta daina ƙoƙarin ƙwace kanta. Rehaan sai ya zame kansa ba dan ya gaji ba, sai dan gudun kar ya tokare mata numfashi ga shi tana asthma, sai ya raba kansa da ita dan ta huta kafin ya ɗora, ya haɗe goshinsu waje ɗaya idanunsa a rufe yana ajiyar zuciya. Hannunsa ya dawo dashi inda ya ɗora towel ɗin, yana saka hannunsa sai ya taɓa fatar ta waksn a maimaikon towel ɗin. Jin hannunsa a wajen lokacin Islaha ta farga da abinda ya faru, ta dira daga kan gadon ta sauka ta shiga bathroom ta turo ƙofa tana fashewa da kuka. Rehaan sai a lokacin ya fahimci abinda ya aikata ya yi nisan haka, ya kalli inda ta tashi ya yi stain, ya kalli towel ɗin da ya faɗi ƙasa bai lura ba, ya kalli bathroom ɗin yana jiyo amon kukanta ya dafe kansa. Bai ce komai ba ya miƙe ya fita daga ɗakin, jin kaɗan ya dawo har lokacin tana banɗakin amma ba ya jin kukanta, ya ajjiye abinda ya shigo da shi ya ce, "ki fito." Islaha tana daga banɗakin ta ce, "Ni kar ka kuma taɓa ni, ka tafi." "Is Okay, na tafi" ya faɗa fita ya bar ɗakin ya koma ɗakin da yake yana kallon kansa a mirror. Gani yake kamar an canja shi gabaɗaya, ya susuce akan yarinyar da ya raina yake yi mata kallon bata kai wani mataki ba, yake yi mata kallon wacce ya aura dan ya ajjiyeta na tsahon wata biyar daga nan ya sallame, yake ganin ko mata sun ƙare babu abinda zai yi da ita. Ya shafa kansa yana tuna yanayinsu na lokacin da suka gabata, ya rutse ido ya ce, "oh my god! Me yake damuna haka? is that love?." Ya sake kallon kansa yana girgiza kai ya ce, "i'm in love with her......" "deeply!" Ya faɗa yana jan numfashi yana kallon kansa kamar mai son gano wani abu a jikinsa, dan shi kansa mamakin kansa yake yi gani yake kamar an canja shi, ba wancan Rehaan ɗin bane wani ne daban. Wani irin nishaɗi yake ji a ransa ya rasa inda zai saka kansa ya ji daɗi saboda nishaɗin zuciyarsa. "Rehaan, are you okay?" Ya faɗa yana ɗan dukansa kansa. Ya sake furzar da iska ya harɗe hannu a ƙirji yana cigaba da kallon kansa, ya sha ganin mata babu kaya ko kuma da bikini amma bai taɓa jin wani abu a jikinsa ba akan matan ba, har Jazy ya kan ce masa ba shi da lafiya saboda ko kaɗan bai taɓa jin zuciyarsa ta harba akan halittar ko wacce. Amma ita iya gashinta in ya gani yana sakawa ya yi losing control, balle kuma in ya navel ɗinta ya gani ya ji kamar wuta ta ja shi. Ya lumshe ido yana tuna ranar da ya cire mata towel, ya saka hannu biyu yana yamutsa gashin kansa ya ce, "Allah ka taimake ni! Wanne irin feeling ne wannan?." Ya sauke numfashi yana tunawa da yadda ya barta tana kuka ɗazu, sai ya ji yana so ya ga ko ta shirya ɗin, ko ta daina kukan da ta ke yi. Ya samu waje ya zauna yana jin kansa kamar ba shi ba, gabaɗaya zuciyarsa ta yi nauyi saboda soyayyar wacce bai taɓa tunanin zai so ta a duniyarsa ba.      Islaha kuwa tana ji ya fita ta fito ta ɗauki kayan da ya ajjiye mata ta koma ciki, bata ƙi gyara kanta ba ta gyara, duk da tana jin cikin ciwo har lokacin. Abin mamakin komai akwai a kayan, har panties roll guda ne, size by size. Bayan ta shirya ta kalli inda ta ɓata ta janye bedsheet ɗin ta shiga da shi bathroom ɗin, ta wanke iya wajen ta da ya yi stain bar shi a ciki, ta fito ta shimfiɗa duvet ta yi ruf da ciki ta ɗora kanta akan hannunta. Tana son shan tea amma bata san ya zata yi ba, tana tuna yadda ta riƙe shi ɗazu ta rutse ido tana ji kamar ta zane kanta. Bata san me yake shiga kanta ba take sakar masa jikinta har haka ba, da ya fara taɓa sai jikinta ya yi sanyi ta kasa yin wani motsi mai ƙarfi ta ƙwaci kanta, ko ta yi masa masifar da bazai kuma taɓa ta ba. Ta rasa dalilin da yake sanyaya mata jikinta. Tana ta juyi tana hawaye ita kaɗai, bata da mai taimaka mata ya bata pracetamol ta sha ba. Rehaan kamar ya san tana son shan tea ya sauka ya shiga kitchen yana kallo kettel, ya kunna ya jira ya tafasa ya zuba mata a mug, ya saka tea leave da sugar cubes guda biyu, Allah yasa in dai ya zo guest house komai na amfani aka kawowa a ajjiye, sai ya fito dining room ya saka mata madara ya ɗauki mug ɗin yana juya spoon a ciki. Sai kuma ya tsaya yana mamakin anya shine kuwa, dan rabon da ya dafa tea da kansa tun farkon zuwan sa Jeddah lokacin da ba shi da housemaid, tunda ta fara zuwa ya daina kuma bai sake yi ba har lokacin. Kafin lokacin ma ya manta rabon da ya shiga kitchen ya dafa wani abu da kansa, shi kwata-kwata baya son aiki. Duk ƙaunarsa da Mamy baya iya taya ta girki in tana yiwa Abba, baya iya tsayawa a kitchen ya dafa mata abinci dan ko kaɗan baya ƙaunar abinda zai wahalar da shi. Ya kalli mug ɗin yana tuna tea ya dafa, kuma ya haɗa a mug zai kaiwa wata macen da ba Mamy ba. Sai ya kawar da tunanin ya ƙarasa ɗakin ya tura ƙofar ya shiga da sallama a bakinsa. Yana shiga Islaha ta ɗago ta kalle sa, sai ta miƙe zaune cikin faɗa ta ce, "kar ka zo kusa dani, ni bana so ka dinga zuwa inda nake." Softly ya ce, "Relax! Tea na kawo miki, kina so?." Kamar yarinya ta ɗaga masa kai alamun eh, ya ƙarasa kusa da ita ya zauna sannan ya miƙa mata mug ɗin yana blushing ya ce, "enjoy." Islaha karɓa ta kai bakinta ta sha, sai ta runtse ido ta ce, "da zafi." Rehaan ya ce, "sorry don't cry!" ya faɗa ganin zata fara yi masa kukan da yake saurin kwance masa nuts ɗin jikinsa. Sai ya karɓi mug ɗin ya matso kusa da ita yana kallon fuskar ta ya ce, "can i..." sai ya yi shiru yana kallon yadda eyelashes ɗinta suka jiƙe da hawaye, ta ɗago ido ta kalle shi ya ce, "feed you?." Bai jira ta amsa ba ya kai mug ɗin bakinta, ta ɗan yi jim bata buɗe bakin ba tana tunanin wannan sabuwar ɗabi’ar ta MR Rehaan. Rehaan ya ce, “take it.” A lokacin ta buɗe baki ta ɗan yi sipping kaɗan shi kuma ya zubawa bakinta ido da ya jiƙe da milk tea ɗin, ya kalli wuyanta yana kallon yadda take haɗɗiye tea ɗin zuwa cikinta. Ganin ta ƙi kallonsa sai ya zuba mata ido yana kallonta, ko wanne motsi in ta yi sai jikinsa ya amsa, gabaɗaya kwance masa lissafi take yi, sai ya ga kamar da gangan take yi wasu abubuwan saboda shi. Ya kasa daina kallon fuskarta, wani abu yana yawo a jinin jikinsa ba tare da ya farga ba. A hankali ta buɗe ido suka haɗa ido, ta juya idanunta a cikin nasa tana shagwaɓe fuska ta ce, "kana tsallake iyakar ka, kai ka san dan bani da lafiya ne da bazan saurare ka ba, ka san da bazan ɗauki wannan abubuwan da ka ke yi min. Ka ji tsoron lokacin da zan daina jin ciwon nan, in na warware baza ka ji daɗi ba Mr Rehaan!." Ya kalli bakinta da yake maganar kamar na ƴar tsana, ya yi murmushi yana jin daɗin kalamanta na ƙarshe ya ce, "i'm just helping you Miss, duk abinda zan yi miki daga yanzu ki ɗauka taimako ne kawai, Okay?. "Meyasa ka ke taimaka min?." "Saboda kema kin taimaka min, kin tuna?." “Mamy ce ta saka ni, ba da son raina na taimaka maka ba. In dan ta ni ne ina ruwana da kai?.” Ya yi dariya mai ƙaramin sauti ya ce, “ni kuma ba Mamy ce ta saka ni ba, ni na saka kaina nake taimaka miki.“ Ta wani kalle shi ta ce, “Meyasa?.” Ya yi wani murmushin da ya saka gabanta ya faɗi sosai, ta ɗauke kanta ta juyar da fuskar ta gefe. Rehaan ya ce, “Na ji a raina in ban taimaka miki ba zan iya yin zazzaɓi.” Ta wani kalle sa cikin tsiwa ta ce, “a matsayina nawa a wajenka?.” Ya zuba mata idanu yana binta da kallon da ya kashe mata jikinta, ta ɗauke kanta daga kallonsa ta ce, “ni dai ka daina yi min abinda ka ke yi, in ba haka ba zaka ji sammaci daga kotu. Allah sai na kai maganar gaban alƙali, na ce kana karya min sharuɗan yarjejeniya.” “Me nake yi miki?.” “Ka fini sani.” “Laifi ne da miji ya taɓa matarsa?.” “ta aure ba, in matar aure ce babu laifi. Amma ni ba ta aure bace, matar yarjejeniya ce. Ka tuna sunan da ka ke faɗa min, C wife?. Kuma kai ba mijina bane, mijin contract ne.” Rehaan nishaɗi yake ji jin yana magana tana amsawa, duk da cikin tsiwa take yi masa magana kuma gargaɗi take yi amma daɗi yake ji sosai. Jin shiru bai ce komai ba sai ta ɗago kai tana kallonsa cikin harara, suna haɗa ido sai ta sauke ido ƙasa, shi kuma bai kuma magana ba ya sake kai mug ɗin bakinta ta kuma sha a hankali tana lumshe ido dan ya huce yana yi mata daɗin sha. A haka ya dinga bata har ta shanye tea ɗin tass, ya ɗauko pcm a aljihunsa ya kai bakinta ya ce, "pcm." Ta buɗe bakinta a hankali ya saka mata, ya bata ruwa ta sha. Ta yi shiru tana zaune tana wasa da hannunta, har lokacin tana jin ciwon amma yana raguwa kaɗan kaɗan, tana jin kanta kamar ba ita ba saboda canjin da ta ga Rehaan ya yi yana cutar da zuciyarta. Ita ba haka take so ba, so take kullum su cigaba da faɗa kamar yadda suka saba, bata son kirkin nan da yake yi mata ko kaɗan. Shi kuwa ya tallafi haɓarsa yana kallonta yana murmushi, ya yarda da gaske Allah ya saka masa soyayarta a zuciyarsa, ya yarda yana son Islaha so ba ɗan kaɗan ba, ya yarda da batun Jazy gaskiya ne ba ƙarya ba, soyayyarta ta yi masa mugun kamu ba tare da ya farga ba, sai da ta gama lalata masa jikinsa da zuciyarsa sannan ya ya fahimta. Ji yake ana buga zuciyarsa da ƙarfi, ji yake yana rasa nutusuwarsa in yana kallonta. Tana zaune bata motsa ba a haka ya ji ta kwanto jikinsa alamun ta yi bacci, ya kalli idanunta ya gansu a rufe ya yi murmushi yana jin kansa daban, yana ji kamar babu wanda ya kai shi nishaɗi a lokacin, ya saka hannunsa ya shafa gashinta. Sai da baccin nata ya yi nisa sannan ya ɗauke ta ya kwatar da ita a kan gadon, ya kunna mata ac ya kashe hasken ɗakin, ya duƙa ya yi pecking ɗinta a goshinta yana murmushi. Har zai fita zai ya ji bazai iya tafiya ya barta ita kaɗai ba, ya kwanta a kusa da ita yana dawo da ita jikinsa ya kwantar da ita a ƙirjinsa yana shafa kanta yana kallon kyakykyawar fuskar ta. Musamman bakinta da tana baccin ma turo shi gaba take yi, ya yi murmushi ya yi pecking bakinta cikin nishaɗi. Ya sauke numfashi yana ji kamar babu wani mutum da ya kai shi nishaɗi a wannan lokacin, sai murmushi yake yi shi kaɗai yana yi kamar su dawwama a haka. In ya tuna ita ɗin mallakinsa ce sai ya ji kamar an canja shi daga Rehaan ɗin Mamy zuwa na Islaha. Ya ɗaga rigar baccin da ta saka, ya saka hannunsa a ciki yana shafa bayanta idanunsa a lumshe cikin sabon yanayi mai wahalar fassarawa....... Rehaan dai ka zaƙe da yawa yasin🤭🤣 Nana Haleema