RAGAYAR DUTSE BOOK 2 Arewapen@nanahaleema11 #The Surgery #The working abroad #The kidnapping #The marriage. A hankali yake fitowa daga bedroom ɗin Mamy zuwa parlour, jikinsa a sanyaye yake sosai, gabaɗaya baya son zaman gidansu bai san meyasa ba. In ya dawo haka yake ƙarewa da sanyin jiki, bashi da kuzari ko kaɗan. Mamy da take zaune ta ce, "Rehaan ina zuwa?." Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Zan je in yi wanka, ina so na je na gaida Mummy." Mamy ta ɗaga kai jin ya ce Mummy ta san babar su Jafar yake nufi ta ce, "Okay, amma kar ka tafi kai kaɗai." Ya ɗaga kai bai ce komai ba ya fita daga apartment ɗin zuwa na sa. Yana fitowa suka haɗa ido da Mama ta rako baƙuwa daga ɓangarenta, ya ɗan ɗauke kansa yana tafiya a hankali ya wuce zuwa ɓangarensa. Ƙawar Mama ta bisa da kallo har ɓace ta ce, "kut! Haka ki ke fama? Ya fi ƙarfin ya gaishe ki kenan ko? Balle ni na saka ran zai ce min ina yini?." Mama ta girgiza kai ta ce, "shegen yaro ne, magana ma sai ya ga dama yake yi min balle gaisuwa. Kaf gidan nan babu tantiri kamarsa, sai ya yi sati biyu a ƙasar nan sai ya ga dama zai ce miki ina yini." "Kuma ki ka zauna, ki ka zuba masa ido ya raina ki har haka?. Ke ce fa uwar gida, ke ce babba a gidan nan fa." "Kema kin san bazan zauna ba, babu abinda ban yi ba amma wani lokacin kamar aikin ba ya ci, ina kan yi ɗin ma zan ce." "Kar ki yi sanya, ki maganin sa ta ƙarfi da yaji, kar ki bari nan gaba ya sake kallon ki ya ɗauke kai, raini ne mai girma. Da a gaban ƙawayen mu ya yi miki haka ai ya cuce mu, ya gama zubar miki da ajin ki wallahi." "Ki dakusar da ɗaukakar sa ta ƙarfi, a bazama wajen malamai su taimaka mana ya yi ƙasa. Bayan an dakushe shi, ki ɓata masa suna ta yadda bazai taɓa goguwa ba. In ba haka ba wallahi muna ji muna gani komai zai koma hannun ƴa india." "Bari kawai. Bazan taɓa ƙyale wani ya fi ƴaƴana ba, kema kin san bazan bar hakan ta kasance ba. Ban san ya aka yi na yi baccin da Rehaan ya kai wannan matakin ba, ban san ya aka yi hakan ta faru ba. Amma yanzu na farka, hana idona bacci nake yi na je neman taimako. duk dan saboda naga bayan ɗaukakar nan ta sa. Kuma na san zan gani, dan zan iya yin komai akan hakan." "Shegen yaro, ni kaina na tsane sa balle ke. Ki duba fa, ya wani kalle mu sheƙeƙe ya wuce." A lokacin Salman ne ya zo wucewa, ya ƙwacewa yara alewa, ya yi dagaje-dagaje da bakinsa kamar ba babba ba. Gashi kallon farko zaka yi masa ka san ya girma, yanayinsa da halittar da Allah ya basa ka san ta manya ce sosai. Ga gashin da yake fuskarsa, gashi fari tass kyakykawaZ Ya kalli Mama yana nuna mata alewar ya ce, "bazan baki ba." Ta ɗan taɓe baki ta ce, "jeka ka shanye kayan ka, na gode." Ya wuce ta da gudu ya shiga wajen Umma. Mama ta kalli ƙawarta suka ƙyalƙyale da dariya har suna tafawa. Ta ce, "wai wannan ba Salman bane, ɗan kishiyarki?." Mama ta ce, "shine mana." "Haka haukan nasa ya sake yin gaba? Kamar ya girmi Sameer ko?." "Ya girmi Baba ba ma Sameer ba, Sameer fa daga shi sai Rehaan." Matar ta ɗan yi dariya ta ce, "Ikon Allah, gashi nan ya zama kamar jikanki." "Haka ma da kyaun gani fa, wani lokacin abin tausayi." "Haka nake so na ga Rehaan, yana yawo yara suna binsa ana kiran mahaukaci." Mama ta yi dariya ta ce, "ke dai sai mun yi waya, akwai labari mai zafi" ta faɗa tana raka ta mota ta shiga ta tafi.      Rehaan yana kallon yadda Yayansa ya wuce a guje jikokin gidan suna binsa a guje ana kokawar ƙwatar alawa daga hannunsa. Ya sauke numfashi ya shiga ɓangarensa yana jin zuciyarsa babu daɗi akan hakan. Har ya shiga sai kuma ya dawo da baya ya shiga ɓangaren mahaifinsa da sallama. Umma ta amsa daga falon, ya ƙarasa tura ƙofar suka haɗa ido da ita. Rehaan ya ce, "Abba yana nan?." A daƙile ta ce, "yana wajan Daada." Bai ce ƙala ba ya juya ya nufi wajan Daada dan yana son ayi maganar Salman. A zaune ya samu Abba shida Baffa ƙaninsa a kusa da Daada, ya yi sallama suka amsa ya ƙarasa ya zauna. Ya kalli ƙanin Abba ya ce, "Baffa ina yini." Da murmushi ya ce, "lafiya lau Rehaan, ya jiki?." "Na ji sauƙi." "Allah ya ƙara lafiya." "Amin." Ya kalli Abba ya ce, "Abba wajan ka naje baka nan." Abba ya ce, "to lafiya?." Ya ɗan kalli Daada suka haɗa ido, ta harare sa ta ce, "ko na baka wuri ne?." Ya ɗauke kai daga kallon ta ya ce, "daman akan maganar Hamma Salman ne, naga yanayin sa ya sake lalacewa Abba, ba kamar wancen zuwan da na yi na gansa ba. Ban ji daɗin yadda na gan shi yanzu ba, shiyasa na zo dan na yi maka magana a kai. Akwai likitan da na sani zai yi masa aiki, in sha Allah za a dace akan hakan." Abba ya sauke nunfashi ya ce, "Rehaan ba yau aka saba yiwa Salman magani ba." Rehaan ya ce, "duk da haka Abba, ba a san inda za a dace ba. Kuma ai ba a taɓa yi masa aiki ba, in aka gwada sai a dace." Baffa ya ce, "gaskiya ne. Ba a san inda za a dace ba, magani lalube ne a cikin duhu." Daada ta ce, "Ni kaina lamarin yaron nan yana bani tausayi matuƙa, ya koma kamar yaro ɗan shekara biyar. Ya girmi Baba, ya girmi Sameer ya girmi Muhammad amma ya zama kamar jikokin gida. Abin akwai taɓa zuciya." Rehaan ya ce, "Daman zan je Jedda, zan saka ayi masa visa sai mu tafi dashi a duba sa." A lokacin Salman ya shigo a guje yara suna binsa zasu ƙwace chocolate ɗin hannunsa. Banisha ta shigo ta ce, "Hamma ka bani chocolate ɗina." Ya noƙe kafaɗa ya ce, "bazan baki ba, ai Abba ne ya siya min." Ta hararesa ta ce, "ba ka shanye ta ka ba, kawai ina tsaye ya ƙwace ta daga hannuna. Gaskiya ka bani." Ganin zata ƙwace sai ya gudu ta bisa zata ƙwace. Salman ya dawo kusa da Rehaan ya ce, "kaga Banisha zata ƙwace min ko?." Rehaan rauni ya mamaye masa zuciya, ya ɗan sauke nunfashi ya ce, "Kiddo meye haka?." Cikin shagwaɓa ta ce, "kawai na fito daga wajen Mamy ya ƙwace min. Ni ai bana kula shi, shine kawai ya ƙwace min." "ki je ɗakina ki ɗauki wata." Banisha ta harare sa, shi kuma ya yi mata gwalo yana riƙe hannun Rehaan. Salman ya miƙawa alawar bakin Reahaan ya ce, "ka sha." Rehaan ya girgiza kai ya ce, "na gode Hamma, bana sha." Ya sake miƙa masa ya ce, "kai kaɗai na bawa, in ba kai ba ko Daada bazan bata ba. Ka sha da daɗi" ya faɗa yana ɗora masa masa alawar a bakinsa. Rehaan ya riƙe hannunsa alamun baya so. Salman kamar zai yi kuka ya ce, "baza ka sha ba ko? Kaima ka ce ni ƙazami ne, kai ne kaɗai mai sona kaima baza ka sha ba?." Rehaan ya buɗe baki a hankali Salman ya saka masa alawar yana dariya. Shima Rehaan murmushi ya yi yana kallonsa cikin tausayi da ƙaunarsa. Ya kalli mutanen da suke kallonsu, kowa tausayin Salman ya bayyana akan fuskarsa, dan Daada kuka take yi, shi kansa Rehaan ɗin ji yake zuciyarsa ta karye kamar ya yi kuka. Abba ya sauke numfashi ya kalli Rehaan da yake kallonsa ya ce, "Rehaan yanzu ya ka ke so ayi?." "Kawai a bari mu tafi dashi Jedda, tunda ina can zan dinga kula dashi da kaina. In kuma Umma zata je sai ta je mu zauna tare dashi. In sha Allah zai dawo lafiya." A lokacin Umma ta shigo tana faɗin, "Daada sannun ku. Kai Salman kai nake nema, taso muje ka sha magani." Ya noƙe kafaɗa yana kwanciya a kafaɗar Rehaan alamun bazai je ba. Rehaan ya kalle sa ganin fuskarsa ta cika da gashi alamun ba a gyara masa ba, ya ce, "zamu je a gyara gashinka" ya faɗa yana shafa fuskarsa a hankali. Umma ta harari Rehaan ta ce, "ai da ba kai ka ke kai sa a yi masa ba ko? Uban ƴan iyayi. Kana can wata ƙasar kana rayuwa, sai yau zaka ce za a je a gyara masa gashi, haka aka ce maka ni bana kai shi?." A lokacin Mama ta shigo da sallama, ta samu labarin Umma dasu Rehaan suna ɓangaren Daada, hakan ya saka ta shigo dan bata san me zai faru a ciki ba. Abba ya ce, "ku ƙaraso ku zauna daman shawara ake nema, Rehaan ne yake da magana akan Salman." Rehaan dai kallon Salman yake da ya lalata kayansa da alawa, shi kansa ya ɓata masa kayan jikinsa. Sai kuma ya fara ja masa gashi, Rehaan duk da yana jin zafi, bai ce komai ba kuma bai hanasa ba. Abba ya ce, "Daman Rehaan ne yake so zai tafi da Salman Jedda a yi masa magani." Umma ta haɗe rai ta ce, "wanne irin magani? Bashi da lafiya ne?." Daada ta kalle ta cike da mamakita ce, "ke sai an ce miki bashi da lafiya ma?." "To na ga a haka yake rayuwa ko?." "asibiti ƙwaƙwalwa zai kai sa." Umma ta girgiza kai ta ce, "A'a, wallahi ɗana ba mahaukaci bane. Babu asibitin mahaukatan da za a kaisa." Abba ya ce, "asibitin ƙwaƙwalwa aka ce, ba mahaukaci aka ce masa ba." Umma ta ce, "a duk ɗaya ne, duk wanda aka ɗauka aka ce zai ga likitan ƙwaƙwalwa kasan mahaukaci ake ɗaukarsa. Ɗana ba mahaukaci bane, babu asibitin da zai je wallahi. Ban nema ba, na gode da niya, Allah ya ba da lada, amma bazai je ba." Baffa ya ce, "Haba ke kuwa, me ki ke cewa haka? Dan ance za a kai sa asibiti a duba ƙwaƙwalwarsa hakan yana nufin mahaukaci ne?." Daada da takaicin Umma ya mamaye mata zuciya ta ce, "to meye ma in ba mahaukacin ba? Ko ba a kira Salman kai tsaye da sunan mahaukaci ba, ace mai taɓin hankali. Duk wanda za yi abinda Salman yake yi ai mahaukaci ne lamba ɗaya." Umma ta ɗaure fuska tamau bata ce komai ba, tana ta girgiza kai tana hararar Daada. Abba ya ce, "Rehaan ya ce zai kai sa asibiti a dubasa, dan haka zasu tafi tare dashi. In za ki je sai ku tafi gabaɗaya." "Tsakani da Allah sau nawa ana kai shi asibitin, sau nawa ana kai shi a duba shi? Magana ɗaya ce, ko yaushe cewa ake babu komai a tare dashi. Ni gaskiya ban amince ba, babu inda zai je." Abba zai magana Daada ta katse shi ta ce, "kin hutar da shi, daman kuɗinsa ne ai ba kuɗin ki ko na mijin ki ba. Shi ya yi niya da ra'ayi, ya ga zai yi saboda zumunci, in ya yi ba kansa zai taimaka ba ɗanki da kanki zai taimaka. Tunda bakya so kin huta, sai ki je ki cigaba da saka shi a ɗaki kuna dambe in zai saka kaya. Wata ran azo a tarar ya karya miki hannu da ƙafa." Umma ta miƙe tsaye ta ce, "Allah zai bashi lafiya, Allah ne ya ɗora masa kuma zai yaye masa. Kuma ni ɗana ba mahaukaci bane ba wallahi, ɗa ne kamar kowa, ɗane kamar wanda kowa yake ɗa a gidan nan, lalura ce ta wani lokaci kuma zai wuce." "Yadda za a raba a bawa mai hankali haka za a raba a bashi kasonsa. Ban nemi kowa ya kai sa asibiti ba, a riƙe kuɗin na hutar da kowa, daman ban ce ina da buƙata ba. In niyar ya yi akwai mabuƙata da yawa a waje yaje ya yi musu, sunansa zai fi ɗaukaka akan ya yi min. Ta so mu je" ta faɗa tana ƙarasowa wajan Salman da yake kallon ta. Salman da yake kusa da Rehaan ya ce, "Umma tare da Rehaan zan zauna." Ta zare masa idamu ta ce, "dallah malam tashi ka wuce mu je, baza ka zauna dashi ɗin ba. Ƙanin uwar ka ne?." Salman yaƙi tashi, zata sake magana Abba ya ce, "Salamatu ki bar falon nan." Zata yi magana ya daka matsa tsawa ya ce, "ki fita nace ko!." Ta girgiza kai ta juya ta fita cikin fusata. Mama ta kalli Abba da Daada ta ce, "Sai haƙuri. Bata kyauta ba kam, ina laifin wanda ya ce zai taimaki naka?." Daada ta ce, "bar shashasha, ita ai komai akan kishi yake, neman lafiyar ma kishi take yi dashi. Mtsww! Zai a bar mata shi ta jiƙa a ruwa tasha, ita ta ga zata iya." Mama ta ce, "Allah ya kyauta" ta faɗa taa miƙewa ta fita bata sake magana ba. Abba ya kalli Rehaan da yake ta biyewa Salman da yake ta tsokanarsaya ce, "ka ji abinda babarsa ta ce, sai ka bar maganar kawai." Baffa ya ce, "akan me zai barta? Daman ai ba dan ita zai yi ba, dan Allah zai yi da darajar zumunci, ai bai kamata ya dakata ba." Daada ta ce, "tunda uwarsa bata so baza ta bari ba, ku ƙyale mata shi a yadda yake." Salman ya miƙe ya fita Rehan ya bisa da kallo kafin ya sauke ajiyar zuciya yana jin tausayinsa yana sake ninkuwa a zuciyarsa. Bai ce komai ba ya miƙe ya fita daga falon ya koma ɓangarensa.      Mama tana fita daga wajan Daada wajan Umma ta wuce, ta same ta tana cika tana batsewa, a zaune tana kaɗa ƙafa cikin ƙunci da takaicin abinda ya faru. Mama ta ce, "ki yi daidai, kin yi daidai da ki ka nunawa wancan ɗan jar fatan ke ki ke da iko da Salman ba shi ba, kin yi daidai da baki amince da kai sa asibiti ba. Ki ji wata magana, daman kallon mahaukaci yake yiwa Salman ɗin ko me?." Umma ta fusata ta ce, "Rehaan ya tsaya min a rai Mama, Rehaan yana neman ya tunzura ni na aikata abinda ban taɓa tunanin aikata masa ba. Na nemasa akan ya kai Salman asibiti ne?." "Dan ya nuna miki yana da kuɗi mana, ai ya nuna miki yana da kuɗin da ɗanki bashi dashi, tunda har zai iya kai shi Jedda a yi masa magani. Shine kawai." "kuɗinsa ɗin banza da wofi, kuɗinsa bazai taɓa ɗaga min hankali ba wallahi. Salman kuma babu asibitin da za a kai shi wallahi. Tun da ba a ce za a kai sa ba sai yanzu?. Wallahi Abba ne yake goyawa Rehaan baya, ki duba tsawar da ya yi min a gabansa." Mama ta ce, "Ke kin san Abba duk abinda Rehaan yake so shi yake so. Tunda kin murza kambu, kin nuna babu wanda ya isa da ɗanki sai ke kaɗai babu mai takura miki. Ya cika iyayi, shi lallai ga bature." Umma ta ce, "Sai ga Riyya ta kira ni a waya, wai Umma account details ɗinki ne ban gani ba, Hamma Rehaan ne ya bani kuɗi in saka miki" ta faɗa tana kwaikwayon muryar Riyya tana taɓe baki. Ta yi tsaki ta ce, "Su lallai sai sun zama lamba ɗaya a gidan nan." "Ni ta tura min, na ga kuɗi masu yawa sai na kira ta, shine ta ce wai na shopping ne in ji Rehaan. Ko godiya ban yi ba na kashe wayar." Umma ta yi tsaki ta ce, "Lokacin sa ne, ya yi gama, zai dawo tafin hannunmu wallahi." "Nan da lokaci kaɗan kuwa. Ke dai kar ki yarda da batun asibitin nan wallahi, ke aka aurowa Nadira ba ni ba, kina yarda aka fita dashi ta yi nasara a kan ki." "Ai wallahi ko Abba bazai saka na yarda ba, tunda na ce bana so a ƙyale ni, ni nake kula dashi ai ba wani ba." Mama ta ce, "gaskiya ne wannan, babu me zuwa inda yake sai ke ɗin. Bara na je na dawo" ta faɗa tana fita daga apartment ɗin ta bar Umma tana mita. Mama kuwa ta yi murmushi, ta ya zata bari a yiwa Salman magani? Ta ya zata bari Salman ya samu lafiya?. In ya samu lafiya an ƙaru kenan fa, zai shiga cikin masu riƙe da dukiyar mahaifinsu, ita kuma bata so ƴaƴanta kaɗai. Rehaan ko da ya gama shiryawa Shams da Mansur ya kira a waya, duk da shi kaɗai yake son fita amma Mamy ta ce kar ya fita shi kaɗai shiyasa ya kira su. Mota ya shiga suka tafi gidan Mummy kamar yadda ya ce mata zai je. Da sallama ya shiga falon, suka amsa suna kallonsa. Mummy cikin da farin ciki ta ce, "La la la Rehaan! Yau kai ne a gidan na mu? ." Ya yi murmushi yana ƙarasawa ciki. Ambatar Rehaan da aka yi, ya saka wata kyakykyawar budurwa mate ɗin Riyya yin tsalle ta fito daga kitchen, suna haɗa ido dashi ya sakar mata murmushi mai taushi, dan kallon Riyya yake yiwa Ikram ko yaushe, ta yi ihuuu ta nufesa a guje ta rungume shi tana murnar ganinsa. Ƙiris ya rage ta kayar dashi, yadda ta ɗafe jikinsa ya saka ya yi baya zai faɗi, sai da ya yi da gaske ya tsaya ya riƙe ta ya ce, "Ikram." Mumny ta ce, "Za ki yar dashi, kin san bashi da lafiya." Ikram ta sake shi ta riƙe hannunsa ta ce, "My favorite bro, ya jikinka?. Da na je asibiti baka yi min magana sosai ba, har na yi tafiya na je Abuja." Tare suke tafiya tana riƙe da hannunsa har suka zauna, ta zauna a kusa dashi tana ji kamar ta shige jikinsa saboda ƙauna. Ya bi fuskar ta da kallo yana ɗan lumshe ido ya ce, "Me ake yi a Abuja?." "Biki na je." Ya ja hancinta ya ce, "Sarkin biki." Mummy da take murmushi ta ce, "Sai kun gama gaisawa zamu gaisa?." Ya ɗan yi dariya kaɗan, a lokacin Daddy ya shigo ya ce, "Ahh Rehaan, daga samun lafiya sai yawo?." Ya yi murmushi suka gaisa har Daady. Daddy ya ce, "Ya jikin?." "Na ji sauƙi sosai." "Allah ya ƙara lafiya, ya kiyaye gaba." "Amin Daddy." A lokacin ƙannen Jafar suka shigo suka gaisa suka zauna Daddy kuma ya fita. Mummy ta ce, "gashi ka zo Jafar yana Uk." "Wajen Mummy nazo ba wajensa ba." Ta yi dariya ta ce, "Na gode sosai Rehaan. Ikram kawo masa abinci ya ci." Bai musa akan kar a kawo ba, daman bai ci komai a wajen Mamy ba, Mummy kuma kamar Mamy take a wajensa. Ikram ta miƙe ta ciko masa tray da kayan abinci ta kawo masa. Da kanta ta yi serving ɗinsa ta miƙa masa ya karɓa ya ce, "Thank you." Mummy ta ce, "Jafar ya ce min zaka tafi Jeddah." Ya ɗaga kai ya ce, "ina da contract, zan je in gama sai na dawo." "Allah ya taimaka Rehaan, Allah ya cigaba da kare ka." "Amin Mummy." "Riyya ta saka mana kuɗi ta ce na shopping ne, mun gode Rehaan, Allah ya albarkaci rayuwarka." "Amin" ya amsa softly yana shan ruwa. Sama sama suke hira da Mummy da Ikram, har ya gama ci, ya ɗan zauna kaɗan sai ya miƙe ya ce, "Mummy zan tafi." Mummy ta ce, "To Rehaan, a gaishe da Mamy." Ya amsa suka fita shi da Ikram suna hira. Har mota ta raka shi, tana riƙe da hannunsa ta ƙi saki kamar zai gudu. Ya ɗan kalle ta ya ce, "Ikram, ya school?." Ta yi murmushi ta ce, "Alhamdu lillah." "Allah ya taimaka. Ki koma gida, zan tafi." Cikin shagwaɓa ta ce, "Ni bana so ka tafi, zan zo mu tafi Jedda." Ya ɗan murmusa ya ce, "sai kin zo Ikram" ya faɗa yana sakin hannunta. Har zai shiga mota Ikram ta ce, "Hamma Ray." Ya juyo yana kallon ta kamar yadda take kallonsa, sai ƙifta idanu take yi tana kallonsa ta ce, "I love you." Ya yi murmushi yana ɗaga kai bai ce komai ba. Duk da ya saba da faɗar i love you ga ƙannensa da iyayen sa, but Ikram ya ga alamun ba irin love ɗin su Riyya take so ba, tana daban yake daga yanayin yadda take faɗa zaka san nata is different, shi kuma baya son causing wani abun shiyasa bai ce komai ba. Cikin shagwaɓa ta ce, "you can't say you love me too?." "i love you, shikenan?." Daɗi ya mamaye mata zuciya, ta ɗaga masa kai tana jin daɗi, sai ta ji babu wanda ya iya furta Ikram da kuma kalmar i love you. Rehaan ya shiga mota tana ɗaga masa hannu suka fita daga gidan. Ta yi ajiyar zuciya tana jin ƙhamshin turarensa yana mamaye ta kayan jikinta. Zama in ya yi a waje sai ka san ya zauna, balle ita da ta yi hugging ɗinsa. Ta yi murmushi tana shaƙar ƙhamshisa, tana jin ƙaunarsa tana sake shiga zuciyarta, ƙauna ba irin ta Yaya da ƙanwa ba, ƙauna ta masoya wanda suke burin aure... Da alama an samo zaɓin Mamy🤭🤣 Nana Haleema 09030398006. [6/15, 12:45 PM] KRBBK: RDB02P02 Arewapen@nanahaleema11 Tunda suka fizgeta suke tsula gudu akan titi, Islaha kawai jinta ta yi a cikin motar, bata san ta ya aka yi hakan ta kasance ba. Ta kalle su ganinsu su biyu ne kawai a ciki, sai mai tuƙa motar na uku, kana kallonsu ka san mutane ne ƙarfafa wanda suka yi kama da bouncers. Islaha ta buɗe baki zata yi magana ɗaya daga cikinsu ya ɗora hannunsa akan lips ɗinsa, ya buɗe idanu ya ce, "shii! Kar ki ce komai." Islaha bata ji kashedin da suka yi mata ba, duk da tana cikin tsoro haka ta daure ta ce, "kamar ya kar na ce komai? Ina za ku kaini, su waye ku?." Ɗaya ya kalle sa ya yi masa alama da kansa, kafin ta yi zato an saka mata baƙar hula, an kulle mata fuska. Islaha ta kurma ihuu tana fizge-fizge, duk da sun ɗaure mata iya hannu, amma sai fizge-fizge take yi ta ce, "su waye ku? Ina zaku kaini, me na yi muku ku ka ɗauko ni?." Suka yi shiru babu wanda yace mata komai a motar, dan van ɗin a kulle take, babu wanda zai ji abinda take faɗa. Ga glass ɗin baƙi, babu wanda zai hango ta duk haukan da zata yi. Islaaha ta fara dukan glass ɗin motar da hannunta tana faɗin, "A taimake ni, an sace ni! Wayyo Allah, ku taimaka min!" Ta faɗa tana ihuu sosai tana cigaba da dukan glass ɗin. Ɗaya daga cikinsu ya fusata, cikin tsawa ya ce, "ke! In ba ki yi mana shiru ba sai na dalla miki mari!." Islaha bata yi shiru ba sai ihu take yi kamar ba warning aka yi mata ba. Ɗayan ma ya kalle ta ya ce, "baza ki yi shiru ba?." Bata daina ba sai ma sake ƙara ƙarfin ihun da take yi. Wanda ya fara magana a farko  ya ce, "zan cilla ta window yarinyar nan wallahi." "A'a, kar ka yi haka. Yi haƙuri mu ƙarasa." Ya yi ƙaramin tsaki suka cigaba da tafiya tana fizge-fizge tana kuka. Ita dai ta ji an tsaya, sai sautin buɗe mota da ta ji, kafin ta ji an yi mata ɗaukar kaza. Wannan ya riƙe kafaɗarta ɗaya, ɗaya ma ya riƙe kafaɗarta ɗaya, ana tafiya da ita bata san inda zasu je ba, dan an rufe mata fuska. Ajjiye ta ta ji an yi, sannan suka kunce mata hannunta, kafin su cire mata abin suka rufe mata fuskar ta cire da kanta, a lokacin har sun fita sun kulle ƙofar. Islaha sai da ta ɗan jira, idanunta ya dawo daidai saboda duhu, ta bi inda suka ajjiye ta da kallo ƙirjinta yana bugawa da ƙarfi. Babban katafaren luxury parlor ne mai kyau da haske, duk inda ake neman haɗaɗɗen falo da kyau da girma yake ya kai. Ya haɗu sosai, ga sanyi da ƙhamshi da yake yi kamar gidan amarya. Islaha ganin wannan falo sai ta kuma firgita, ta nufi ƙofar a guje tana jijjiga ƙofar amma kamar babu kowa, ta ƙarasa wajan window ta janye lalube, ta buɗe glass ɗin window tana faɗin, "ku su waye? Ina ne nan ku ka kawo ni? Don Allah ku zo ku barni na tafi. Babana bashi da lafiya, yana asibiti, don Allah ku buɗe ni!." Tistt kamar babu kowa, dan ko mota ɗaya babu a ajjiye a wajan, kamar ba yanzu aka ajjiye ba. Ta sake buɗe murya ta ce, "Kuna ina!." Nan ma shiru babu motsin komai. Islaha ta dafe kai cikin rashin sanin abinda zata yi, ta sake kallon falon tana tunanin ina ne nan kuma? Ina aka kawo ta, waye ya ƙwamuso ta aka ajjiye ta a nan?. Kamar an tuna mata, sai ta fara duba aljihun jikinta, a nan ta jiyo wayarta tana nan. Hannu yana rawa ta ɗauko ta shiga kiran wayar Sadik amma network error. Ta saka wayar a flightmode ta cire, amma abinda service ɗin yake nuna mata no service. Islaha ta dafe kai ta zube a wajan ta rasa abinda zata yi, kuka take yi dan bata san abinda zata yi ba in ba kukan ba. Sai ta kuma zabura ta miƙe, ta sake komawa window tana ihuuu tana hawaye, amma babu wanda ta gani balle aji maganarta. Ta koma ta zauna ta rasa tunanim me zata yi, hankalinta ya tashi ta rasa abinda yake yi mata daɗi. Falon shiru babu motsin komai, sai sautin ac kaɗan, sai ƙhamshi da yake yi a hankali. Ta kalli agogo ta ga ƙarfe tara na dare, ta sake duba waya ta ga no service, ta cillar da wayar ta sake fashewa da kuka mai sauti. Kuka ta yi mai isar ta lokaci ɗaya kanta ya rike, ya yi mata nauyi, tana ji kamar zai cire saboda nauyin da take ji ya yi mata. Ta sake miƙewa ta koma wajan window, murya a dashe ta ce, "babu kowa ne! Don Allah ku buɗe min, Babana bashi da lafiya, ina so in je in gan shi, ku taimaka min!." Nan ma shiru babu alamun kowa, sai haske a compound ɗin gidan kamar hasken rana, da wata ƙaramar mage da take yawo a wajan. Takaici ya mamaye mata zuciya ta buga kanta a jikin bango tana kuka, tana ji kamar ta samu wuƙa ta dinga cakawa kanta har sai ta mutu, ga waya a hannunta amma ta zama babu amfani, gata a gidan da babu kowa amma bazata iya fita ba. A wajan ta zame ta kwanta tana kukan rashin mafita, sanyin falon ya fara yi mata yawa, ta cure a waje ɗaya ta haɗe kanta da guiwa tana kuka mai tsuma zuciya. Tun tana kukan cikin daɗin rai har ta gaza, ta koma sauke numfashi, tana sake curewa waje ɗaya saboda sanyin da yake ratsa ko ina na jikinta. Ta miƙe ta sake kallon window ta ga gidan shiru babu motsin kowa. Gabanta ya faɗi, ta tafi tunanin yanzu ita kaɗai ce a gidan mai uban girma?. Hawaye ya sakko mata, ta koma ta zauna ta rasa abinda yake yi ma daɗi. Bata san adadin lokacin da ta ɗauka a wajan ba, duk da sanyin da take ji haka take zaune a wajan, tsoro da tashin hankali ya cika mata zuciya, tunanin waɗanda suka sace ta ya hanata sukuni. Bata san lokacin da bacci ya ɗauke ta ba.             Washe gari. "Yauwa Hanan, don Allah turo min Islaha in kin shiga gida." Hanan ta kalli Sadik ta ce, "Islaha bata kwana a gidan nan ba." Ya kalle ta da mamaki ya ce, "kamar ya bata kwana a gidan ba?." Hanan ta ce, "eh, jiya kwata-kwata bata dawo gidan nan ba, ni na yi tunanin ma a asibiti ta kwana." Sadik ya zuba mata ido yana kallon ta, kafin ya janye idanunsa ya ce, "ni ban gane ba, kina nufin bata dawo gida ba gabaɗaya?." Hanan ta ce, "na faɗa maka na yi tunanin tana asibiti tare da Mama." Sadik ya ce, "wataƙila tana can ɗin, na kira wayar ta bata shiga kwata-kwata. Bara na je na duba." Zai kunna motar kenan sai ya ji Hannan ta ce, "to ai ga Maman ma." Ya dakata yana kallon Mama da ta sauka daga napep,  ya tsaya yana jira ta ƙaraso ya ji ko Islahan tana can. Mama tana zuwa wajen ta ce," Sadik ka ganni ko? Na dawo gida na ɗan kimtsa sai in koma, na bar Sa'ida a can. Ya batun kuɗin aikin, An samu kuwa?. Nima yanzu zan ɗan tattaro wani abun sai a haɗa dashi." Sadik ya ce, "ana kan haɗawa Mama. Islaha tana can ne?." Mama ta ce, "Islaha bata je ba, na yi tunanin tare za ku tafi da ita." Hanan ta ce, "ba a asibitin ta kwana ba?." Mama ta ce, "tun jiya da daddare da ta bar asibiti bata koma ba har na fito." Hanan ta ce, "to wallahi ba a gida ta kwana ba, dan kwata-kwata Islaha bata dawo gidan nan ba." Mama ta kalli Hanan ta ce, "to wajan ƙawarta fa? Wataƙila ai tana can ko?." Jin hakan sai Sadik ya ɗaga kai yana ajiyar zuciya ya ce, "eh gaskiya ne, bara na aika gidansu Safeeran." Mama bata ce komai ba ta shiga ciki shi kuma ya ƙarasa ƙofar gidansu Safeera Hanan ta bi bayan sa. Kafin Hanan ta ƙaraso Safeera ta fito, ganinsa sai ta yi murmushi ta ce, "Hamma Sadik barka da zuwa." Ya ce, "Barka dai Safeera. Ya gida?." "Lafiya lau, ya mai jiki?." "Da sauƙi. Ina ƙawar taki?." "Yanzu zan tambaye ka na ce tana ina, na ga ban gan ku tare ba." Sadik gabansa ya faɗi ya ce, "kina so ki ce ba tare ku ka kwana ba?." Safeera ta girgiza kai ta ce, "ni rabona da ita tun a wajan aiki, da ta tashi ta ce min ta wuce asibiti. Na kira wayar ta jiya wajan tara na dare amma wayar bata shiga ko kaɗan." Sadik ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!." Safeera ta firgita ta ce, "me ya faru? Ina Islahan take?." Hanan ta ce, "Islaha bata kwana a gida ba, hasalima ba a san inda take ba." Safeera ta zaro ido waje ta ce, "kamar ya ba a ganta ba, kamar ya ba a san inda take ba? Ku yi min bayani." Sadik ya ce, "abinda ki ka ji shine gaskiya, bamu san inda Islaha take ba. Dalilin zuwan mu nan mun yi tunanin kuna tare." "Innalillahi! To ina ta je? Ko tana orphanage?." Sadik ya kalle ta ya ce, "tana zuwa can ta kwana ne?." "Gaskiya tunda ta bar gidan bata taɓa kwana ba. Na shiga uku, ina Islaha ta tafi?. Bara na kira Zainab ƙanwarta ta gidan na ji ko suna tare" ta faɗa hannunta yana rawa ta kira Zainab ta saka a speaker. Daga can ɓangaren Zainab ta ɗauka ta ce, "Adda Safeera ina kwana?." Safeera cikin rashin nutsuwa ta ce, "lafiya. Zainab kuna tare da Islaha ne?." Zainab ta ce, "A'a, ina ta nemanta nima, ko a waya na kasa samunta." Safeera ta ce, "Na gode" ta faɗa tana kashe wayar. Safeera ta kalli Sadik ta ce, "ina Islaha take? A ina ta kwana?" Ta faɗa hawaye yana sakkowa akan fuskarta. Sadik ya ce, "kwantar da hankalin ki Safeera, zamu ganta in sha Allah." Safeera ta fashe da kuka ta ce, "Islaha bata kwana a wani wajen sai a Hamma Sadik, bata zuwa ko ina. A ina ta zauna haka, Ina ta je?." Ya yi ajiyar zuciya bai ce komai ba, dan abin ya ɗaure masa kai, ya rasa inda Islaha ta shiga, duk inda ake tunanin taje bata can. A lokacin Saleem ya ƙaraso wajan yana kallonsu. Ganin yanayin da suke ciki ya saka ya ya ce, "Sadik lafiya na gan ku haka?." Sadik ya ce, "Islaha ce ba a gani ba, tun dare jiya ba a sake samunta a waya ba. Kuma duk inda muke tunanin zata je ta kwana bata nan." Saleem ya zaro ido ya ce, "ban gane ba, wacce Islaha kenan?." Safeera ta ce, "Islahata, Islahata ce ba a gani ba. Ina ta shiga?" Ta faɗa cikin kuka mai tsanani tana kallonsa. Saleem ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ba a san inda take ba, kuma bata faɗawa wani zata je wani waje ba?." Sadik ya ce, "da zata je zata faɗa min, tunda yanzu ko yaushe muna tare." Kira ya shigo wayar Sadik, ya duba ya ga Saheer ne, ya kalle su ya ce, "Ga Saheer yana waya, na tabbata ya neme ta bai same ta bane shiyasa ya kira ni." Saheer ya ɗauka ya saka a speaker, Saheer ya ce, "Sadik kuna tare da Islaha ne? Tun jiya nake kiranta bata shiga kwata-kwata. In kuna kusa haɗa ni da ita don Allah." Sadik ya sauke numfashi ya ce, "Ba ma tare, amma in mun haɗu zan faɗa mata sai ta kira ka." "Yauwa kar ka manta don Allah. In ka je asibitin ka ɗauko min hoton Baffa ka turo min. Zuwa jibi zan dawo in sha Allah." Sadik ya ce, "to, ina zuwa" ya faɗa yana kashe wayar. Sadik ya kalle su ya ce, "tabbacin wani abun ne ya samu Islaha, dan da akwai inda zata je da zata faɗawa Saheer ko Safeera." Saleem ya riƙe haɓa cikin tashin hankali ya ce, "abu kamar wasa, Islahan ce ba a gani ba?." Safeera dai kuka take yi kamar ranta zai fita. Sadik ya ce, "ba tsayawa zmau yi a nan ba, mu je mu bincika ko zamu same ta a wani waje, in ta kama mu bada cigiya." Saleem ya ce, "gaskiya ne kam, mu je mu duba." Safeera ta ce, "nima zan je." Saleem ya ce, "ki koma gida, duk abinda ake ciki zan faɗa miki." "A'a, ina so in je, don Allah mu tafi tare." Suka nufi motar Sadik, Saleem ya bar tasa a wajan suka shiga suka tafi, Hanan ta shiga gida. Hanan ta shiga ta faɗawa Mama abinda yake faruwa. Mama ta ce, "ban gane ba a ga Islaha ba, ina ta je?." Hanan ta ce, "wallahi ba a sani ba. Duk inda ake tunanin zata je bata nan." "Ikon Allah, har gidan marayun bata can? Akwai yayyenta da suka yi aure fa, duk zata iya zuwa gidansu." "An kira iya wanda aka sani, amma bata nan." Mama ta ɗan yi shiru ta ce, "to ina yarinyar ta je? Gashi dai bata kwana a waje balle na ce harka ce ta yi kyau, duk tsiya da iskancin sai ta dawo. Gaskiya akwai alamar tambaya a lamarin nan, akwai abinda ya faru." Hanan ta ɗan yi shiru, duk da basa shiri da islaha amma ta ji babu daɗi akace ba a ganta ba.      Su Saleem asibitin suka je, suka ƙarasa wajan ma'aikata suka yi musu bayani abinda ya faru, suka nemi ganin cctv amma suka hana suka ce sai an zo da hukuma. Dole haka Sadik ya koma ya kai report wajan hukuma mafi kusa, aka basu ɗan sanda ɗaya suka taho sannan suka amince aka shiga camera room ɗin. Ɗaki ne babba, ɗaki ne mai ɗauke da tv guda biyar, ko wacce da inda take haskawa. Ɗakin kamar ɗakin camera turawa, komai ana gani a tv. Wanda yake aiki a wajan ya ce, "ina ku ke sm gani?." Sadik ya ce, "Jiya da daddare, misalin ƙarfe takwas na dare. Wajan asibitin nan mu ke so." Bai musa ba ya danna ya dawo da lokacin, suka fara ganin abinda yake faruwa. Sai ga fitowar Islaha daga asibitin ta miƙe hanya tana tafiya. Ɗan sandan ya ce, "camera ta gaba." Ya saka ta gaba inda ta ɗan tsaya cikin tsoro kafin ta cigaba da tafiya. Tana shiga wajan duhun ya kalle su ya ce, "daga iya nan cameras ɗin mu suka daina aiki." Sadik ya ce, "wayyo Allah, don Allah babu wata ma'aikata ko bank a nan kusa da zasu iya ɗaukar mana abinda faru?." Ya girgiza kai ya ce, "gaskiya babu. Asibitin nan ne kawai a wajen nan." Kowa ya yi shiru cikin tunani, basu da yadda suka iya dole suka fito daga ɗakin. Suna fitowa wayar Saleem ta yi ƙara, ya duba ya ga Muslim ne sai ya ɗauka. Muslim ya ce, "Saleem ba ka shigo bane? Chairman yana ta faɗa kai da Islaha ba ku zo ba." Saleem a raunane ya ce, "Muslim wallahi Islaha ce ba a gani ba, yanzu haka muna kan neman inda take." Muslim da mamaki ya ce, "kamar ya ba a ga islaha ba kamar wata tumatur? Ban gane ba." "Abinda ka ji shi na faɗa, an nemi Islaha an rasa." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!. A ina hakan ya faru?." "Ganin ta na ƙarshe a nan Nadira Hospital ne, ta fito ta hau kan hanya mara haske, daga nan ba a sake ganinta ba har yanzu." Mulsim ya cw, "subahanallahi! Wannan ai ba maganar da za a yi shiru ba ce. Bara a samu hotonta a yaɗa ko wani ya ganta." Saleem ya ce, "wannan shawara ce mai kyau, mu ma mun je wajan yan sanda mun yi report." Muslim ya katse wayar da hanzari shi kuma Saleem ya sauke ajiyar zuciya dan bai san me zai yi ba. Sadik ya ce, "yanzu meye abin yi?." "Cigiya zamu bayar kawai, baza mu yi sake ba, gwara mu bayar da wuri ko za a saamu wanda ya ganta." Sadik ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Allah ka nuna mana wannan baiwa ta ka, Allah ka bayyanata cikin aminci." Saleem ne kawai ya amsa, ita kam Safeera kuka take yi kamar ranta zai fita, hawayenta yaƙi tsayawa, da ta motsa sai hawaye sharr. A haka Adda Sa'id da ta gansu ta zo wajan, itama tana jin lamarin ta fashe da kuka cikin ruɗani da tashin hankalin da basu taɓa shiga irinsa ba. **** Muslim yana kashe wayarsa ya shiga office wajan Ummi, ya same tana bacci akan table, ya ɗan buga table ɗin ya ce, "ke tashi!." Ta ɗan buɗe ido ta ce, "me zan yi? Ina baccina ka tashe ni." "Dallah ki tashi ki ji." Ta miƙe zaune tana yamutsa fuska ta ce, "meye?." "Islaha aka nema aka rasa, tun jiya ake nemanta ba a same ta ba." Ummi baccin da yake kanta ya wartsake ta ce, "kamar ya ba a ganta ba?." "Wallahi ba a ganta ba, an nemi inda take a rasa." "Kana nufin masu garkuwa da mutane ne suka kamata?." "Waye ya sani? Yanzu Saleem yake tabbatar min da an neme ta a rasa, wayarta kuma bata shiga. Kuma bata taɓa aikata hakan ba." Ummi ta ji wani irin daɗi ya mamaye mata zuciya, ta kalle sa ta ce, "kuma ba aikin ka bane?." Ya girgizs kai ya ce, "ko ɗaya, ni ai na faɗa miki target ɗina. To a jiyan dai na aika, kuma wanda na tura a gabnasa aka ja islaha aka saka ta a van. Abinda ya saka ban faɗa ba na ɗauka ceton ta suka yi daga hannun mu, ashe suma da tasu manufar." Ummi ta kasa ɓoye murnarta ta ce, "kana nufin a gaban wanda ka tura ya watsa mata acid aka ɗauke ta?." "Wallahi kam. Ni tun jiyan na sani, so nake na ji ta inda maganar zata ɓullo." Ummi ta miƙe tsaye cikin tsananin murna tar tana taka rawa, ta rufe fuskarta da hannunta ta ce, "wayyo Allah! Daɗi zai kashe ni Muslim. Islaha ta tafi, ta tafi kenan in Allah ya yarda." Muslim ya ce, "dallah ki yi a hankali, yanzu ni ake jira zan faɗawa Chairman za a yaɗa hotonta ko wani ya ganta." "Baza a yi hakan ba, kar ka yaɗa hotunanta don Allah. Ka ƙyaleta ta je can ta ƙarashe rayuwarta a inda take. Bana fatan Islaha ta dawo garin nan balle ta dawo gidan nan, bana ƙaunar ta dawo, dan haka babu wani nemanta da zaka yi." Muslim ya ce, "hakan ya zama dole Ummi, in bamu yi ba za a zarge mu. Dole mu nuna bamu ji daɗin ɓacewarta ba, in ba haka ba za a ga kamar muna farin ciki da hakan ne." Ta dafe kai cikin takaici ta ce, "gaskiya ni ban so hakan ba wallahi, a barta ta je ta can ta ƙarata har Allah ya ɗauki ranta gabaɗaya mu huta da annabo." Muslim ya ce, "in so samu ne nima haka nake so, amma bazai yu ba dole hakan ya faru, dole mu nuna mun damu da ɓacewar ta." Ta harare sa ta ce, "ka je ka faɗa masa. In kuwa ta bayyana, baza mu rusa plan ɗin mu ba gaskiya." Ya gyaɗa kai ya ce, "watsa mata acid baza mu fasa ba, sai mun lalata fuskar nan, ina zuwa"ya miƙe ya fita zuwa office ɗin Chairman. Cikin lokaci kaɗan kowa ya san ba a ga Islaha ba, hankalin ma'aikata abokan aikinta ya tashi, dan Islaha ta kowa ce bata da matsala ko kaɗan. Bar ta da rashin kunya da tsiwa, shima sai ka shiga sabgar ta, in ba haka ba zaku zauna lafiya lau. Hankalin kowa ya tashi, aka tambayi kalar kayan da ta fita dasu, aka nemi Safeera ta bada hoton Islaha guda ɗaya, nan da nan aka yaɗa hotonta a kafafen yaɗa labarai. Da ka shiga duniyar yanar gizo hoton Islaha zaka fara gani, ana cigiyarta da daidai lokacin da ta ɓace. Da lambobin wayar da za a kira in an ganta... Nana Haleema 09030398006.✍🏻 [6/15, 3:57 PM] KRBBK: RDB02P3 Arewapen@nanahaleema11 Rehaan yana zaune ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa, waya ake yi masa amma bashi da lokacin kallon wayar balle ya ɗauka. Tunani ne kala-kala a ransa, ya rasa wanda zai kama ya yi nazari a kai. Mamy ce ta shigo falon nasa da sallama, hakan ya saka ya buɗe ido yana kallon ta har ta ƙaraso ta zauna a gefensa. Tana zama ya zame ya kwanta, ya kwantar da kansa a kan cinyarta yana lumshe idanunsa, ta ɗora hannunta a gashin kansa tana shaafawa a hanakali. A sanyaye ya ce, "Mamy wani abu yana damuna." Mamy ta ce, "meye shi?." Ya ɗago ya kalli idanunta  ya ce, "Mamy Salman..." sai kuma ya miƙe zaune ya ce, "jiya dashi na kwana a raina, ina so in tafi dashi Jedda a nema masa lafiya." Mamy ta sauke numfashi ta ce, "Abba ya faɗa min duk abinda ya faru, duk abinda ya faru a falon Daada ya sanar dani...." Ta riƙe hannunsa duka biyun ta ce, "bazan taɓa hanaka yiwa ƴan uwanka alkhairi ba, kome zaka yi musu ka yi, zumunci ka yiwa. Amma tunda uwarsa tace bata so sai ka ƙyale su ai babu dole ko?." Ya ɗan rausayar da kai ya ce, "Amma Mamy...." Ta dakatar dashi ta ce, "Allah ya ga zuciyar ka, Allah ya baka ladan niya. Yaushe zaka tafi Jedda?" Ta faɗa dan ta kawar da waccan maganar. Ya ɗan sauke numfashi ya ce, "na kusa." "Nima ina so na je gida amma mahaifin ka ya hana, kai ina so ka je. Na samu labarin an samu inda Sofia take." Ya ɗaga ido ya kalle ta ya ce, "Mamy har yanzu ba ku fitar da rai da samunta ba?." "Ta ya zamu fitar da rai? Har yanzu a jikina ina jin za a ga Sofia. Ka je gidanmu, ina so na san asalin abinda yake faruwa. Ya rausayar da kai ya ce, "Mamy ni bana son zuwa ƙasar nan taku fa." Ta harare sa cikin harshen hausa ta ce, "sai ka je, ɗan rainin hankali kawai. Ya yi dariya ya rungume ta ya ce, "Mamy har yanzu hausar ki bata zauna ba, kowa ya ji ya san koya ki ka yi ba da ita aka haife ki ba." "Kaima haka taka take, gwara ni akan ka." "Well, in na samu lokacin zan je." Ya kalli agogon hannunsa sannan  ya ce, "ina da baƙi a guest house, zan je can mu tattauna. Zan iya yin kwana biyu a can." "Kawai kana so ka gudu ne, ba wasu baƙi." "Allah ina da baƙi Mamy." Ta ɗaga kai ta ce, "shikenan. Ka ci abinci?." "Mun ci tare da Riyya." Ta shafa fuskarta tana pecking ɗinsa a kumatu ta ce, "Allah ya cigaba da baka nasara, Allah ya cigaba da kare ka daga sharrin duk mai sharri. Ya baka ɗaukaka da zuciyar taimakon wanda ya cuce ka." Shima ya yi pecking ɗinta ya ce, "Amin Mamy. Ki cigaba da yi min addu'a, daƙyar nake yi zaman ɗakin nan, sai na ji kamar ana bin bayana." Ta shafa kansa ta ce, "tsananin addu'ar ce ta kawo ka haka, kar ka damu. Kai mai nasara ne a ko yaushe. Shiyasa na so na saka maka sunan mai nasara, amma Kakar ka ta hana." Murmushi ya yi kaɗan, ya kwantar da kansa a ƙirjinta yana jin ƙaunarta tana sake shiga ransa. In ba wajen ta babu inda yake samun nutsuwa, daga ita sai Jazy, sai kuma Abba da yake yawan fahimtar sa. Amma Mamy daban take, ko ransa a ɓace yake da ya kwanta a jikinta sai ya manta, tunda shi bashi da riƙo, kana yi masa ya wuce. Ta shafa kansa ta ce, "aure zaka yi Rehaan, ya kamata ka rage wannan son jikin nan. Har yanzy baka girma da kwanciya a jikina ba. In kuwa ka yi aure sai ka kwanta a jikin matar ka." Ta ɗan yi murmushi ta ce, "matar ka zata sha wahala, kafin ta saba da wannan shagwaɓar ta ka, kamar wani last born." Ya sake narkewa a jikinta ya ce, "ni babu wani aure da zan yi." Ta yi dariya tana shafa bayansa ta ce, "tunda Kakar ka ta faɗa sai an yi, ka yi haƙuri kawai." Ya miƙe daga jikinta, hular da take bayan rigarsa ya ja ya rufe kansa ya ce, "zan tafi Mamy." Ta miƙe tsaye ta ce, "ka yi parking kayan ka ne?." "No need." "okay my billionaire, Allah ya raya min kai, na ga ƴaƴanka." Jin sunan da ta faɗa ya basa dariya, ya sake rungume ta sannan ya ɗauki wayarsa ya bar falon, ta bi sa da kallo tana jin alfahari a zuciyarta mai matuƙar yawa.       Islaha alarm ɗin wayarta ne ya tashe ta, ta miƙe a firgice tana sake jin sanyi yana sake dabaibaiye jikinta. Ta buɗe ido a hankali ta ganta a kwance a inda bata saba ganin kanta ba, a firgice ta miƙe tana jin sautin agogo, tik tik tik da yake aiki a falon. Ta ɗaga kai ta kalli agogon, ta ga ƙarfe uku da rabi na dare, ta sake kallon ƙofar falon tana tuna a inda take, sai ta zabura da hanzari ta nufi ƙofar tana jijjigawa amma ƙofar ko motsi bata yi. Ta koma wajan window ta buɗe tana kallo, gidan yana nan da hasken sa tar amma babu kowa a wajen. Hawaye suka sake gangaro mata, daman ga ciwon kan da ta kwanta dashi, ta dafe jijiyoyin kan ta zame a wajan tana kuka sosai. Bata san a in a inda take ba, bata san waye ya kawo ta ba, bata san a ina take ba. Ta numfashinta sai ta ji yana sarƙewa, ta ɗan ja sa da ƙarfi, ƙirjinta ya yi nauyi numfashin baya sauka yadda ya kamata. A hankali ta miƙe tsaye, ta ƙarasa wajan ac falon tana kallon a.c, sai ta bi wayar da kallo har ta ga inda switcg ɗin yake, ta kashe tana numfashi da  daƙyar. Ta sake zamewa a wajan tana kuka sosai, sai da ta gaji dan kanta sannan ta miƙe zuciyarta tana bata umarni ta miƙe ta yi alwala ta yi sallah kawai. Ta inda Allah ya taimake ta ta gama preiod, da ace tana kai ne da bata san halin da zata kasance a inda bata san ina ne ba. Wata ƙofa ta gani a falon, ta nufi wajan a sanyaye cike da tsoro ta murɗa handle ɗin ƙofar. Duhu ta gani babu haske ko kaɗan, ta ɗan taɓa gefe kawai ta ji ta kunna wutar wajan, ta bi wajan da kallo. Dogon corridor ne sai falo daga ciki, sai wasu ƙofofin da suke wajan a kulle. Ta taka a hankali ta buɗe ƙofar farko, ta yi karo da babban bedroom mai kyau da girma, ta kunna haskensa dan ta san baza'a rasa banɗaki a ciki ba. Ta ƙarasa ta buɗe bathroom tana kallonsa, bata tsaya ƙare masa kallo ba dan ba abinda yake gabanta ba kenan, ta shiga ta yi abinda zata yi ta fito ta dawo babban falon. Jin sanyin ya yi mata yawa sai ta ɗauki wayarta ta koma falon da ta baro, da application ɗin wayarta ta ga alƙibila sannan ta tayar da sallah. Sallah take yi tana kuka, bata san adadin sallolin da ta yi ba, ta dai san ta yi sallah da yawa tana faɗawa Allah damuwarta da neman ya fitar daga inda bata san waye ya kawo ta ba. A haka ta ji wayarta tana kiran sallar asuba, ta idar da sallar ta yi shiru ko zata ji kiran sallah amma ɗuf babu alamun kiran sallah a unguwar, ta miƙe ta tayar da sallah tana jin jiri yana ɗaukarta saboda ciwon kai da yunwa. Bayan ta idar ta jingina da kujera tana sauke numfashi cikin ciwon kai da yunwa.Tunaninta ya tsaya cak, tunaninta da hankalinta ya tsaya waje ɗaya ta rasa abinda ya kamata ace ta yi. Ta sake duba wayarta ta ga no service, ta sake fashewa da kukan takaici tana ji kamar ta samu wuƙa ta sokawa kanta ta mutu kowa ya huta. Bata san adadin lokacin da ta ɗauka a wajan ba, ta san tana jingine da kujera idanunta a tufe tana karanta azkhar. Ɗan taɓa ƙofar ta ji anyi, ta zabura ta fito tana fitowa ana kulle ƙofar main falon. Ta saki ƙara ta ƙarasa tana jan ƙofar amma an riga an kulle har an fita. Ta buɗe window tana cewa, "Don Allah ku buɗe ni, ban yi mu ku komai ba meyasa za ku kawo ni nan ku ajjiye kamar kayan wanki? Don Allah ku taimaka min ku buɗe min, Babana bashi da lafiya yana asibiti. Don Allah ku taimaka ku buɗe min!" Ta faɗa da ƙarfi tana kuka sosai. Tsit wajan kamar babu kowa, ta juyo tana kallon falon taga ƙaton tray a ajjiye, da mini tea flaks, sai kayan tea da plates a rufe. Sai slice bread mai girma ajjiye. Ta ɗora hannu a kai ta fashe da kuka, a. bayyane ta ce, "kenan ana sane dani, har abinci aka kawo min. Na shiga uku!" Ta faɗa cikin tsananin tashin hankali. Ta cire rolling ɗin kanta ta cillar da mayafin, ta zube guiwa a wajan tana kuka mai tsuma zuciya. Idanunta suka yi mata nauyi, ga yunwa ga ciwon kai ga taurin kai, dan baza ta ci abincin ba sai dai ta mutu ta yunwa. A fusace ta miƙe, ta yi fatali da tray ɗin ya faɗi a ƙasa komai na kai ya zube, kayan tea ɗin ne da suke gwangwani, sai flaks ɗin tea ɗin sune ba su yi komai ba, amma abinda yake cikin plate ɗin ta zubar. Cikin ihu ta ce, "bana ci, bana son cin komai. Ku bar ni yunwa ta kashe ni, bazan ci ba!" Ta faɗa tana hakki dan numfashinta ya ɗan riƙe, ga ciwon kai. Takaici ya saka ta rasa me zata yi, ta gaji da yin kukan, ji take kamar ta dinga dukan kanta har sai ta fitarwasa kanta jini. Ta koma ta yi lamo tana jin zuciyarta tana bugawa sosai, tana kwance a kan carpet tana jan numfashin da ya tsaya mata a ƙirji saboda yadda numfashin nata ya tsaya. Ta juya ta yi rigingine tana kallon sama idanunta a rufe cikin rashin sanin abinda zata yi, waye zai kuɓutar da ita daga halin da take ciki?. ****** Sadik tunda ya ga kiran wayar Saheer gabansa ya faɗi, ya kalli Saleem da suke zaune ya ce, "Saheer ne yake yi min waya, har bana so na ɗauka wallahi." Saleem ya ce, "ɗauki, rashin ɗaukar bashi da amfani." "Na tabbatar sanarwar neman Islaha ya gani, shiyasa yake waya" ya faɗa yana ɗaukar wayar ya saka a speaker. Cikin fusata Saheer ya ce, "Kai Sadik me nake gani haka? Wacce Islaha ce ba a gani ba?." Sadik ya yi shiru bai ce komai ba. Saheer ya ce, "ina magana ka yi min banza, wacce Islaha ce ba a gani ba?. Me ya kawo hoton Islaha duniya ana yaɗawa ana cewa ana nemanta?." Sadik ya ce, "Saheer gaskiya ne abinda ka gani, tun daren jiya ba a ga Islaha ba, kuma...." Cikin ɗaga murya da tashin hankali ya katse sa ya ce, "kuma me! Ka san da hakan shine ka yi min shiru baka faɗa min? Jiya me ka ce min, cewa ka yi bakwa tare ashe daman tun lokacin hakan ya faru ka ɓoye min?." "Bana so na tayar maka da hankali ne shiyasa ban faɗa maka ba." "Shirun da ka yi min yanzu kwantar min da hankali ya yi? Kamar Islaha ace tun jiya ba a ganta ba ka kasa faɗa min? Meye amfanina da bazan sani ba?." "Ka yi haƙuri." "Ina ta je? A ina aka sace ta?. Naga ana cewa ta fito daga asibiti, an duba cameras ɗin da yake wajan?." Sadik ya ce, "duk mun yi fa, amma babu wani labari wallahi. Iya fitowarta daga asibitin kawai mu ka gani." Saheer ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Sadik amanar da na bar maka kenan, ta ya za ka bar Islaha ta fito ita kaɗai cikin dare?." "Ka san ina ta cikun cikun neman kuɗin aikin Baffa, lokacin da ta je asibitin bana nan "Ya Subahanallahi! Yanzu ya ake ciki? Har yanzu babu wani wanda ya samu labarinta?." "Babu." Saheer ya ɗan yi shiru, muryarsa tana cracking cikin damuwa ya ce, "Anya ba ƴan kidnappers ne suka ɗauke ta ba?." Sadik jin rauni a muryar abokin nasa sai ya basa tausayi, ya tausasa murya ya ce, "bama fatan hakan in sha Allah. Kai ba ka da wani waje da ka ke tunanin zata iya zuwa?." "Babu Sadik, duk wajen wanda zata je na tabbatar yanzu kuna tare. Ya Allah! Ina Islaha ta ke? Allah ka sa duk inda take tana cikin amininci." "Amin." "Sadik ana sanyi a nan ko?." "Uhum ana yi." "Islaha bata son sanyi da iska mai ƙarfi, kasan tana da asthma. Yanzu in tana wani wajen da ciwon ta zai tashi fa, waye zai kula da ita har ya bata taimako?" Ya faɗa cikin rauni. Sadik ya ce, "in sha Allah tana waje na gari." "An sanar da ƴan sanda?." "Duk mun yi Saheer." "Shikenan, nima zuwa gobe zan taho nigeria." "Amma ka faɗa min akwai abinda zai riƙe ka a can, ka faɗa min mahimmacin aikin ko?." "Ta ya zan iya zama babu Islaha Sadik? Ta ya hankalina zai kwanta har na yi aiki ban san inda take ba?. Gwara na rasa komai na dawo mu nemo ta tare." "Dawowar ka ba ita zata bayyana Islaha ba, ka zauna ka cigaba da neman kuɗin aikin Baffa, ka dinga ta ya mu da addu'a, itace abinda take so faga gare ka." Saheer bai ce komai ba ya kashe wayar cikin ƙunar rai. Saleem ya girgiza kai yana jinjina ƙarfin son da Saheer yake yiwa Islaha ya ce, "gaskiya Saheer yana son Islaha, ban taɓa jin rauni a muryarsa haka ba." Sadik ya murmusa ya ce, "A dai wannan zamanin, ni dai na jima ban ga masoyi kamar Saheer ba, itama kuma na jima ban ga mace mai riƙo da halicci da soyayya kamar ta ba." Saleem ya ce, "Allah ya bayyana mana ita." "Amin ya rabbi." Kiran Saherr ne ya sake shigowa, Sadik ya ɗauka Saheer ya ce, "kuna tare da Safeera ne?." "Eh yanzu ta bar nan, muna tare har Saleem." "yauwa, akwai wata ma'aikaciyarsu Ummi, kwanakin baya ta yiwa Islaha barazanar sai ta ga bayanta. Ka tambayi Safeera a gabanta aka yi, aje a kamata ta fito da Islaha. A jikina nake jin itace ta ɗauke ta." Sadik ya ce, "anya zata aikata haka?." Cikin masifa ya ce, "in ba ita bace to waye? Ka je a kamata ta fito min da matata, in ba haka ba wallahi sai na saka an yi mata abinda bazata taɓa mantawa dashi ba. Ka tambayi Saleem da Safeera, su sun san case ɗin. Ranar da aka bata katin gayyatar Ray ranar abin ya faru." Saleem ya ce, "Saheer tabbas an yi haka, ta shigo wajan Safeera tana faɗa mata, nima kuma ina wajan." "Yauwa, kaima shaida ne. Don Allah aje a san abinda za a yi a kamata, ta faɗa mana inda ta kai Islaha, in ba haka ba mu tafi kotu." Saleem ya ce, "in sha Allah za a yi hakan yanzu kuwa." Saheer ya ce, "na gode" ya faɗa yana kashe wayar. Sadik ya ce, "Haba Saleem, ya za ka biye masa?." Saleem ya ce, "in abinka ya taɓa har a bakin allura nemansa za ka yi. Dole Ummi ta shigo ciki case ɗin nan saboda furucinta, dan haka ka tashi mu je kawai. Wannan babban case ne, kuma Ummi zata iya aikata komai dan ganin bayan Islaha." Sadik ya ce,  "a kan me?." "Saboda ta fita ɗaukaka a wajan aiki mana. Tashi mu je." Sadik ya miƙe ya ce, "Amma baza a karɓi shaidar Safeera ba, saboda ƙawar Islaha ce." "Ba za a rasa cctv ta ɗauka ba, mu je dai kawai." Aka kira Safeera dan a tafi police station a kai report akan Ummi. ******* Maman Orpanage tana zaune tana kallon abinda yake faruwa, tana ganin yadda duniya ta hargitse akan neman Islaha, ana ta reposting hotonta. Hotunanta sai yawo suke yi a duniya ana cigiyar inda take. Ta yi murmushi tana kaɗa kai ta ce, "aiki ya yi kyau" ta faɗa tana ɗagowa ta kalli wanda yake kallon ta. Ya yi murmushi ya ce, "duk abinda ki ka ce shi nake yi ranki ya daɗe." Ta yi dariya ta ce, "Aiki ya yi kyau sosai. Ka yi komai ta yadda babu wanda zai fahimta. Ka yi komai akan lokaci, a daidai lokacin da ake buƙatarsa. Zan ƙara maka naira dubu ɗari akan abinda mu ka yi za a baka." Ya yi dariyar nasara da jin daɗi ya ce, "Godiya nake uwar ɗakina, Allah ya ja da rai." Ta kalle sa a nutse ta ce, "bana so a samu matsala, yadda aka yi wannan babu matsala ina so aikin gaba ma ya zama mara matsala. A ɗauke wayar ta, a tabbatar an goge komai na kan wayar ta, ko da hotonta ne a goge ta yadda babu abinda zai dawo kai." "Sannan kar a barta ta dawo nan kusa, ayi nisa da zamaninta kamar shekara ɗaya zuwa biyu nan gaba. Ta cigaba da rayuwarta a nan, kar ku bari ta ga fuskar ku, ko ta ji wani abu daga gare ku. Tana da wayo, tana da kaifin basira, ƴar jarida ce, tsaf zata iya yin abin da baku yi tunani ba. Ku ɗauke wayarta gabaɗaya, kar ku barta da waya, in ba haka ba da gidan da ku kan ku zata iya yiwa video." Ya ɗaga kai ya ce, "an gama ranki ya daɗe." "Ba zancen an gama ba, Islaha ta wuce tunanaka, tana da wayo, tana da fikira tsaf zata yi abinda ba ku yi tunani ba." "Ai ranki ya daɗe tunda ta shiga hannu zancen ya ƙare wallahi." Ta girgiza kai ta ce, "haka nake so naji, haka nake so naji, dan na tabbatar da komai zai tafi yadda nake so. Zata iya tafiya, zaka ji alert." "an gama ranki ya daɗe, amma in aka samu akasi ko ta yi taurin kai za ki ji wani labarin da ba wannan ba." "Duk yadda ku ka yi, ku tabbatar kawai bata ganku ko ta ji sunana ba." "An gama" ya faɗa yana buɗe ƙofa ya fita. Ta sauke numfashi ta ce, "matsala ta ƙare!." ***** Ƴar sanda mace, da maza biyu ne suka nufi ma'aikatar su Islaha, ana zuwa aka nemi ganin Ummi aka nuna musu offfice ɗinsu. Aka yi knocking suka shiga akace ai tana office ɗin Chairman. Suka wuce can, ya basu izinin shiga, suka shiga suka gaisa. Officer ya ce, "Muna neman Ummi Mubarak ne." Ummi ta bi su da kallon mamaki ta ce, "gani." Ya kalle ta ya ce, "muna nemanki a office, za ki amsa wasu tambayoyi." Ummi gabanta ya faɗi, ta zaro ido waje ta ce, "me na yi kuma?." Macen ta ce, "an shigar da ƙarar ki, akan ana zargin da saka hannunki a ɓatan Islaha Muhammad Maddibo." Ummi ta buɗe ido waje ta ce, "wallahi ban san komai ba, ban san waye ya ɗauke ta ba." Ɗan sandan ya ce, "yanzu zamu je mu dawo, ba jimawa za ki yi ba, in har mun tabbatar da baki da laifi." Chairman ya miƙe ya ce, "Officer Ummi bata da laifi a kan hakan." Ya kalle sa ya ce, "duk wata magana zamu yi ta a can, a nan babu abinda zamu yarda dashi." Ummi ta ce, "na rantse da girman Allah bani da hannu a ciki, ku yarda dani." "gaskiyarki zata fitar dake, mu je." Ummi ta firgita matuƙa, ta ɗora hannu a akanta ta ce, "Wallahi Allah bani bace. Ban taɓa shiga police station ba, don Allah ku yi haƙuri." "Malama Ummi, ki amince mu tafi cikin salama da mutaunta juna, kar ki kawo mana hargitsi cikin lamarin nan." Muslim da yazo wajen ya ce, "shikenan Officer, ku bani dama na taho da ita a motata, ku yi min wannan alfarmar." Basu ƙi hakan ba suka wuce suka tafi, Ummi tana hawaye ƙirjinta yana bugawa da ƙarfi, zuciyarta tana barazanar tarwatsewa saboda tashin hankali da tsoro mai yawa Wai Islaha a hannunwa take ne? Abin ya ɗaure min kai fa🤔🤣🤣 1k on telegram 09030398006 Nana Haleema. [6/16, 9:59 AM] KRBBK: RDB02P04 Arewapen@nanahaleema11 Rehaan asibiti ya fara zuwa, tunda aka san ya shigo kowa ya shiga hankalinsa, aka mayar da hankali akan aiki sosai, dan kowa ya san halinsa, ba ya karɓar kuskure." Tare suke da mutane a bayansa, yana tafiya ana binsa a baya, aka buɗe masa office ya shiga yana kallon wajan secretary ɗinsa ya ga bata nan, ya juyo ya kalli Dr Abdul ya ce, "where is she?." Dr Abdul da girmamawa ya ce, "Sir kwana biyu bata zuwa gaskiya." Da ido ya yi masa alamun meye dalili, Dr Abdul ya ce, "ta yi aure, tana hutu." Bai ce komai ba, aka buɗe masa glass door ɗin office ɗinsa ya shiga yana bin ko ina da kallo. Babban Office ne mai kyau da ɗaukar hankali, komai na cikinsa baƙi da gold ne. Ga hotonsa babba a kafe a office ɗin, ga awards a ajjiye akan cabinet da aka yi ta dan su. Ga gadon duba marasa lafiya, ga kujeru masu kyau da aka tanada dan ganin mara lafiya. Komai na office ɗin perfect and luxury, babu tarkace komai decent irin na ƴan gayu. Rehaan ya nemi waje ya zauna yana kallon mutanen ɗaya bayan ɗaya. Sai kuma ya janye ido yana kallon wani waje daban ba tare da ya ce musu komai ba. Ƙaramin kuskure yake dubawa, so yake ya ga ƙaramin abu da zai yi magana a kai amma bai ga komai ba. Ya kalle su ya yi musu alamun su tafi, suka yi godiya suka tafi. Sallamar Dr Isma'il ya saka ya ɗago kai ya kalle shi yana amsawa. Dr ya ce, "Good Day Sir."  Rehaan kallonsa yake yi bai ce komai ba, Dr Isma'il ya ce, "Sir, we have a kidney transplant surgery, and a donor is available." Rehaan ya buɗe baki ya ce, "what next?." "We are waiting for your signature on this document, sir." Ya kalle sa ya ce, "haka nace maka nazo nan ne dan na yi aiki?." Dr ya ce, "sorry sir. But it's necessary." Ya ɗan taɓe baki ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana haɗe hannu waje ɗaya ya ce, "So, am I the only surgeon here who is going to perform this operation?." "No Sir! But it's only you." Ya ɗan sauke numfashi ya miƙa masa hannu ya bashi file ɗin. Jikinsw yana rawa ya bashi, Rehaan ya fara buɗe na donar ɗin ya ga kaf gwaje gwajen da aka yi masa is parfect, ya dinga bi bit by bit yana karantawa cike da ƙwarewa da son gano kuskure. Shi dai Dr addu'a yake Allah yasa bai yi wani kuskure a kan aikin, so yake kawai ya ga ya gama karantawa bai yi magana ba, ba ya so kuskure ya haɗa shi da Rehaan ko kaɗan. Rehaan ya rufe file ɗin donar ya buɗe na mara lafiya, ya dinga bi yana karantawa ya ga komai ya yi yadda ya kamata, babu kuskure har maganin da aka bashi ya yi daidai da ciwonsa. Ya girgiza kai yana miƙa masa file ɗin ya ce, "Good job." Ajiyar zuciya Dr ya yi tare da murmushi ya ce, "thank you Sir." Rehaan ya jingina ya ce, "Remind me on Sunday night, before monday, in ban samu dama ba sai ka yiwa Dr...." Bai ƙarasa ba sai Dr ya ce, "Dr Peter." Ya gyaɗa kai bai ce komai ba, ya yi masa alama da ya fita, ya yi godiya sannan ya fita. Message ne ya shigo wayarsa ya duba sai ya ja tsaki ya ɗauke kai ba tare da ya duba ba, ya dafe kai da hannayen sa duka biyun yana sauke numfashi a hankali. Remote ya ɗauka ya kunna tv, ya jingina da kujera yana ɗan juyawa a hankaki yana jira ta gama kamawa. Tana gama kamawa ta fara fitar da sauti, hakan ya ja hankalinsa ya ji ana cewa, "Ana cigiyar matashin ƴar jarida mai suna Islaha Muhammad madibbo, ta bar wajan aiki da yamma ta tafi asibitin Nadira hospital, ta fita daga asibitin Nadira hospital da yake babban titi. Ta ɓace a tsakanin karfe takwas na dare zuwa tara. Don Allah duk wanda ya ganta ga lambobin waya a tuntuɓi makusantnta." Rehaan ya kalli hoton Islaha da aka hasko, tana sanye cikin jalbab hijjab kalar fari tas, ta yi murmushi, tana zaune a office ta ɗora ƙafa kan ɗaya. Ɗauke kai ya yi daga kallon ta, ya sake kallon tv a lokacin an ɗauke ta an shiga wani labaran daban. Ya ɗan taɓe baki ya ce, "mara kunya" abinda ya furta kenan, ya miƙe ya ɗauki wayarsa ya fita daga office ɗin ba tare da ya kashe tv ba. Islaha ta fara daina gani saboda ciwon kai da yunwa, taurin kai ya saka ta yi watsi da abincin taƙi ci, ga yunwa tana ji amma ta yiwa kanta mugunta, ta ƙi ci sai juyi take yi akan carpet. A haka aka yi sallar azahar, daƙyar ta iya miƙewa ta yi alwala ta yi sallah a zaune, tana yi tana layi kamar ƴar maye saboda ciwon kai da gajiya. Bayan ta idar ta kalli abincin da ta zubar tun asuba, ba shiri ta rarrafa kamar yarinya, ta fara cin wanda ta zubar tana ci tana kuka. Hannunta har rawa yake yi saboda yunwa, ta ɗaga flaks ɗin tea ta zuba a kofin da bai fashe ba, ta zuba a bakinta. Ba shiri ta dawo dashi saboda zafi sai, ta kuma sha cikin gaggawa dan yunwa tana neman hallaka ta. Tana ci tana kuka tana tuna yanayin da Baffa yake ciki, zuciyarta sai bugawa take yi, jikinta yana rawa, tashin hankali ya yi mata yawa. Sai da ta ɗan ci ta koma tana jan numfashi, tana ji nutsuwarta tana dawowa a hankali, cikinta yana ƙullewa. A hankali ta ji ciwon kan yana raguwa sai kaɗan, shima dan kuka take yi shiyasa bai bar ta ba. Ta haɗa kai da guiwa ta cure waje ɗaya tana jan numfashi daƙyar, tana goge hawayen da suka ƙi tsayawa. Ƙirjinta ya yi nauyi, ga zafin da take ji in ta ja numfashi. A hankali ta ji an buɗe ƙofar falon an shigo, ta ɗago da sauri ta kalli ƙofar, ta ga wani mutum ƙato da baƙaƙen kaya hannunsa ɗauke da tray ɗin abinci. Islaha ta miƙe tana kallonsa, shi kuma ya haɗe rai ya ƙi kallonta, ya ajjiye mata yana kallon waɗanda ta fasa a wajan. Ganin ƙofa a buɗe sai Islaha ta tattare rigarta zata gudu, taku ɗaya ta yi ya cafko hannunta ya dawo da ita baya. Ta fara kokawa dashi tana neman guduwa cikin fitar hayyaci, tana kuka tana so ta fita daga falon amma ya hanata. Cikin dakakkiyar murya ya ce, "ke!." Bata san ta tsaya cak ba saboda tsawar har tsakiyar kanta, bata ƙaunar tsawa ko kaɗan, bata so a yi mata maganar da zata ji ta har tsakiyar kanta. Ya ɗora yatsansa akan bakinsa ya ce, "shiiii!." Maimakon ta yi shirun sai ta girgiza kai ta ce, "Su waye ku, me na yi muku ku ka kawo ni nan?." Bai ce mata komai ba ya juya zai fita, sai kuwa ta taka a hankali ta ɗauki flaks ɗin ɗazu ta bi bayansa ta buga masa a kansa, irin yadda take ganin ana yiwa mugaye a film. Maimakon ta ga ya zube a wajan irin yadda take zato, irin yadda take gani a film, sai ta ga ya dafe wajan ya juyo yana kallon ta irin kallon nan na boss. Ganin irin kallon da yake mata sai ta ji tsoro, duk da haka bata fasa jefa masa flaks ɗin ba, ya cafe ya ajjiye a gefe, ya saka hannunsa a bayansa ya ɗauko bindinga ya nuna mata. Islaha gabanta ya faɗi, tsoron ganin bingida muraran ba a film ba ya tsirga mata, amma sai ta duƙushe a wajan, ta zube guiwa biyu a ƙasa. Cikin muryarta da ta fara dashewa ta ce, "to kashe ni kawai, ka kashe ni na san bana duniyar, ya fi min wannan tashin hankalin da nake ciki. Don Allah ka kashe ni na rataya a wuyan ka, ka kashe ni haƙƙina ya rayata a wuyan ka. In baka kashe ni baka ƙaunar Allah, ka ɗauki raina ka binne ni a ɗakin nan ƙarewa kashewa." Shi wallahi sai ta ba shi dariya, bai taɓa ganin yarinya ƴar fitina kamar wannan ba, tana cikin wannan hali amma tana yi masa rashin kunya? Amma bai yi dariya ba, ya sake tamke fuska yana nunata da bindiga ya ce, "in ki ka sake yi min magana, sai na fasa miki kai." "To daman ai so nake ka fasa min kan, akan me zan yi shiru? Mutuwa nake so na yi, kawai ka kashe ni. In ka kashe ni ka haƙa rami ka binne ni a wajen nan ƙarewar sacewa." "Mutuwa ki ke so ko?." "Eh, ita nake so" ta faɗa tana kallon sa amma hawaye take yi. Ya girgiza kai yana jan bindigar ya ce, "sai ki faɗi kalmar ki ta ƙarshe kafin bullet ya fasa miki kai" ya faɗa yana nuna mata bindigar a goshinta. Sai ta fashe da kuka mai sauti, tana tuna yadda Hamma zai ji in ta mutu, tana tuna yadda Safeera zata ji in ta mutu, tana tuna su Zainab dasu Hafsa. Ta ja numfashi da ƙarfi ta ce, "La'ilaha illahu Muhammadu rasullah, SAW." "Kuma Allah ya isa ban yafe mu ku ba, zan tafi inda zak zo, kafin ku taho ayi mana hisabi" ta faɗa hawaye yana sakko, mata tana rufe idonta cikin wani irin yanayi. Ya yi dariya ya jinjina girman taurin kan yarinyar, kawai sai ya juya ya fita yana kulle ta. Duhu ta gani alamun an rufe ƙofa, ta ƙarasa buɗe ido, ta ga baya nan ta koma ta zauna tana kuka harda ihuuuu.          ******* "Ranka ya daɗe na rantse da Allah bani da hannu a ɓatan Islaha, wallahi ni ban ɗauke ta ba" Ummi ta faɗa cikin tashin hankali. Dpo ya kalli Safeera ya ce, "ki maimaita abinda ki ka faɗa." Safeera ta ce, "ni shaida ce, a kan idona Ummi ta cewa Islaha wallahi sai ta ga bayanta, har tana cewa ta rubuta ta ajjiye. A lokacin har ni da Saleem mu ke cewa Islaha wannan ba kalmar wasa bace, ya kamata hukuma ta shiga cikin maganar, dan baka san me za a aikata maka ba. Sai ta yi dariya ta ce babu abinda zata iya yi mata, barazana ce kawai. Akwai cctv, ta ɗauki komai." Saleem ya ce, "gaskiya ne anyi haka ranka ya daɗe, ni da kaina na yiwa Islaha faɗa akan ta saka hukuma a maganar nan." Ummi ta zaro ido t ce, "na rantse da Allah barazana ce kawai, wallahi Allah ni ban faɗa dan zan yi mata komai ba." Dpo ya kalle ta ya ce, "kin yarda kin faɗa kenan ko?." "Eh na faɗa, amma wallahi ba da wata manufa na faɗa ba. Tsabar kishi ne ya saka na faɗa." "Kin faɗa dan za ki aikata, ko kin faɗa dan barazana wannan duk bai tashi ba. Kin furta sai kin ga bayan Islaha, yau ba a yi sati biyu ba an nemi Islaha ta rasa. Ko kece ko bake bace ba kece, in kin ga kin bar case ɗin nan tabbaas anga Islaha, in ba a ganta ba, kotu zata yanke miki hukunci daidai da abinda ki ka aikata." Ummi ta ɗora hannu a kai ta ce, "Kotu kuma yallaɓai?." "Eh kotu, zamu cike muku FR mu tura ku kotu ranar monday in sha Allah. Kafin ranar zamu riƙe ki a nan." Ummi ta fashe da kuka ta ce, "na rantse da girman Allah bani da hannu a case ɗin nan ranka ya daɗe, wallahi ban aikata komai ba." Dpo ya ce, "babu mai fitar dake sai Allah. Ke da kan ki kin amsa kin furta sai kinga bayanta, dan haka kina cikin case ɗin nan tsamo-tsamo." Wani ɗan sanda ne ya shigo ya ƙame kafin ya ce, "Sir ga wani Muslim yazo tare da wata shaida akan ɓatan Islaha." Dpo ya ce, "su shigo." A lokacin mahaifin Ummi da yake zaunse ya ce, "Dpo ayi mana alfarma a bamu belinta, duk abinda ya faru da kaina zan kawo ta." Dpo kafin ya yi magana Muslim ya shigo shida mai napep ɗin da ya so zuba mata acid. Suka samu waje suka zauna Muslim ya ce, "Sunana Muslim, nima abokin aikin Islaha ne. Wannan bawan Allah ya zo gidan tv ya same ni ya ce ya ga lokacin da aka ɗauke Islaha." Dpo ya kalli mutumin ya ce, "Bawan Allah ya sunanka." Mutumin ya ce, "sunana Muddasir ranka ya daɗe." "Kana ina daidai inda abin ya faru?." "ina kan titin da abin ya faru a cikin adaidaita sahu. Da farko ni ta fara tsayarwa zata shiga, sai na faɗa mata kuɗi ta ce ya yi tsada baza ta iya biya ba. Ta nemi nayi ragi sai naƙi yi. Muna wannan maganar sai ga wata baƙar mota mai zubin motar asibiti, tun kafin su ƙaraso wajan suka buɗe ƙofar motar, suna zuwa inda take aka ja ta ciki da ƙarfin gaske. Kafin na fito daga napep ɗin sun yi nisa sosai saboda gudu suke yi." Ya girgiza kai ya ce, "Meye kalar motar ka ce?." "Baƙa ce, mai zubin motar asibiti." "Ka ga waɗanda suke a ciki?." "Ban gani ba, ban farga ba kawai naga an ja ta ciki sa ƙarfi." "Ka kula da lambar motar?." "Gaskiya ban kula ba ranka ya daɗe, saboda ruɗewar da nayi da lamarin, ban tsaya na kula ba." Ya girgiza kai ya ce, "amma me ya hanaka kai repost a ofishin ƴan sanda mafi kusa ba? Yadda abin ya faru a gaban ka ya kamata ka kai rahoto wajen hukuma. Meyasa baka yi ba?" Ya faɗa yana karantar yanayinsa. [6/16, 10 AM] KRBBK: RDB2P05 Nana Haleema Muddasir ya ɗan yi ajiyyar zuciya ya ce, "ban yi wannan tunanin ba gaskiya, ranka ya daɗe." Ya sauke numfashi ya ce, "hakan yana nufin da gaske sace Islaha aka yi..." ya ɗaga ido ya kalli Ummi da fuskarta ta yi gaje-gaje da hawaye ya ce, "Za ki iya faɗa mana waɗanda ki ka saka suka ɗauke ta, bana so maganar nan ta bar wajan nan, in ba haka ba za ki sha wahala." Ummi ta rushe da kuka ta ce, "wallahi bani bace, ban aikata komai ba wallahi." Sadik ya ce, "ai koda Islaha ta bayyana, wallahi matuƙar tana da hannu sai kotu ta raba mu. Sai an yi mata hukunci daidai da abinda ta aikata, baza mu bar maganar nan ta tafi a banza ba." Dpo ya ce, "kwantar da hankalin ka, a gaban hukuma ku ke, in sha Allah za a fitarwa da kowa haƙƙinsa." Ya kalli Mudassir ya ce, "kai jeka. Ka bada sunan ka da lambar wayar ka a kan kanta, in amfanin hakan ya taso za a neme ka." Ya amsa da to ya miƙe a nutse ya fita. Dpo ya kalli mahaifin Ummi ya ce, "kamar yadda na faɗa Alhaji, zamu riƙe Ummi a nan har sai ranar litinin mun aika maganar kotu." Mahaifin Ummi ya ce, "ayi haƙuri ranka ya daɗe a bamu belin ta, in sha Allah duk abinda ya faru da kaina zan kawo ta. Baza a samu matsala ba, zan san duk abinda za a yi." Dpo ya ɗaga kai ya ce, "Alhaji Ummi ta shiga cikin case ɗin nan gaba da baya, ta ko wanne ɓangare sai an nemo ta." "Na yi alƙawarin bazan bari ta gudu ba, zan tsaya wajan ganin case ɗin ya zo ƙarshe in sha Allah." Ajiyar zuciya Dpo ya yi, aka tsayar da magana aka ba da belin Ummi suka fito. Sadik suna fitowa ya kira Sheer ya da ya addabe sa da yawa, ya faɗa masa duk yadda aka yi har wanda ya zo ya bada shaida ya faɗa masa. Saheer ya ja tsaki ya ce, "akan me za a bada belita? Akan wanne dalili za a bada belin wacce ake zargi?." "Don Allah ka kwamtar da hankalin ka,ko da an ga Islaha na faɗa musu baza mu bar case ɗin nan ba, zamu tsaya wajan ganin an yi musu tsakani da Ummi." "Yanzu ya ake ciki?." "Babu komai a ƙasa, zamu jira mu gani zuwa wani lokaci, yanzu dai babu komai a ƙasa, amma in sha Allah zata bayyana." "Shi wanda ya ce ya ga lokacin da aka ja ta motar, waye shi?." "Mai napep ne kawai, sanarwa ya gani ya je ma'aikatarsu ya faɗa." "Ni fa ban yarda ba, akwai wani abun a ƙasa wallahi." "Kar ka damu, komai zai daidaita in sha Allah." Saheer ya ce, "ya batun aikin Baffa?." Sadik ya ce, "shima a nan ana ƙoƙari in Allah ya yarda, kar ka damu." Saheer ya ce, "Babana bashi da lafiya, an sace min matata amma ka dinga cewa in kwantar da hankalina. In ban ganni a nigeria ba hankalima bazai taɓa kwanciya ba wallahi. Haka kawai an kulle ƙasar nan, ji nake kamar na haura na gudu wallahi." "Sai haƙuri, zasu buɗe shigowa nan ɗin, matsala ce ta tsaro." Saheer ya yi tsaki ya kashe wayar cikin wani irin yanayi na bugawar zuciya da tashin hankali. ****** A hankali Mansur yake tuƙa motar da Rehaan yake ciki, cikin salon tafiyar kwantar da hankali, babu ta hayaniya da wuce ƙa'ida. Gab da zasu shiga gidan ya danna horn, mai gadi da yake yasan da zuwansu ya buɗe suka shiga da motar cikin gidan. A hankali Rehaan ya fito, mai gadin ya ƙaraso yana duƙawa ya ce, "barka da zuwa ranka ya daɗe." Ya ɗan kalle sa ya ce, "ya aiki?." "Alhamdu lillah. Ranka ya daɗe na ga saƙo, Allah ya saka da gidan aljanna." "Amin. Baƙi sun zo?." "eh ranka ya daɗe, suna ciki suna jiran ka." Bai ce komai ba ya wuce cikin gidan Shams yana bayansa yana takawa a nutse. Wani part ya buɗe ya shiga falon, mutanen da suke ciki ba su wuce biyar ba, suna ganin shogowarsa duk suka miƙe ya ƙarasa ya basu hannu duk suka gaisa, sannan ya zauna ya ce, "ku zauna." Ba musu suka zauna. Ya kalli Bilal ya ce, "ɓangaren ka kun yi magana da Jazy?." "Eh, mun yi magana dashi ya ce na sanar dakai bai san kan abun ba. Ga takardar da aka turo mana" ya faɗa yana miƙa masa, ya karɓa yana ɗan nazarinta kaɗan. Ya kalli wata baturiya ya ce, "and you." Itama ta faɗa masa abinda yake tafiya a ɓangarenta. Sun jima suna tattaunawa a akan abinda ya shafi kasuwancinsa. Sai da aka samu matsala da maganin matsalar sannan suka yi masa sallama suka fita daga falon. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana shafa kansa a lokacin aka yi kiran sallar i'sha. Ya miƙe ya fita waje suka haɗu da masu aikin gidan suka yi sallar i'sha, sananan ya koma ciki bayan ya kira babban yaronsa a ɓangaren tsaro. Ya amince da Shams ɗari bisa ɗari, ya kan bashi aikin sirri ba tare da kowa ya sani ba. Shams babban yaronsa ne, duk inda zai je suna tare dashi a mota, in dai kaga Shams kaga Rehaan. Ya kalle sa ya ce, "Shams where is she?." "Sir tana middle part." "Any update?." "Sir, She is so funny, and she is also stubborn. Abincin da aka bata for lunch taƙi ci, haka aka kai mata dinner shima yana nan bata ci ba. But Sir, it seems like she is not feeling well " Ya ɗago ya kalle sa yana binsa da wani irin kallon ƙasa ya ce, "ya aka yi ka san haka? Ka kai mata ziyara ne?." Shams ya girgiza ya ce, "A'a, na shiga kai mata abinci ne." "Babu wanda zai bata abincin....." Sai ya dakata da maganar yana kallonsa tare da ɗora ƙafa kan ɗaya ya ce, "sai kai?." "Ni kaɗai ka ce na dinga kula da ita, shiyasa nake shiga." Ya ɗan ɗaga kai kaɗan bai ce komai ba. Shams ya ce, "chef ya zo Sir." Bai ce komai ba ya yi masa alama da ya fita, ya fita shi kuma ya zubawa waje ɗaya ido yana kallo ba tare da ya san tunanin me yake yi ba. Ya jima a zaune yana tunannin da bai san dalilinsa ba, kawai ya zubawa waje ɗaya ido yana kallo, bazai ce ga abinda yake tunawa ba. A hankali ya miƙe kamar ba ya son tafiya ya nufi middle apartment ɗin slowly. Kamar mai jin tsoro haka ya yi unlocking ƙofar ya shiga, ya ji wani irin ɗumi a falom, falon ya ɗauki ɗumi sosai kamar babu ac a ciki. Da fasassun plates ya fara cin karo, a hankali ya kai idanunsa kan tray guda biyu na abinci har ya sauke idonsa a kanta, tana zaune ta cure waje ɗaya ta haɗa kai da guiwa tana jan numfashi a hankali. Mayar da ƙofar ya yi ya kulle, ya tsaya yana kallonta ba tare da ta san yana tsayen ba. Ƙarar kulle ƙofar ya saka ta san an shigo, ba tare da ta ɗago ba ta ce, "bana son cin komai, ku barni na mutu kawai." Jin yadda maganarta take fita sai ya yarda da maganar Shams da ya ce bata da lafiya, ko baka santa ba in ka ji voice ɗinta ka san bata jin daɗi, balle shi da yasan yadda maganar ta take kamar parrot. Bai ce komai ba, kuma bai motsa daga inda yake ba ita kuma bata ɗago ba dan bata san waye a tsaye ba. A hankali ƙhamshinsa ya fara zuwa inda take, ƙhamshin da ta shaƙa ya mamaye ta lokaci ɗaya, duk da hancinta ya ɗan rufe saboda sanyi amma hakan bai hana ƙhamshin ratsa hancinta ya shiga ba. Ta ɗan ɗago a hankali tana tunanin a ina ta taɓa jin ƙhamshin turaren nan, ta ɗago a hankali kai tsaye ta kalli inda yake, ta gan shi a tsaye yana ƙarewa falon kallo kamar mai neman wani abu. Yana juyowa suka haɗa ido, duk da nauyin da kanta ya yi mata haka ta miƙe zunbur tana binsa da kallo, shi kuma kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai daga kanta, ya cigaba da nazarin ko ina a falon, dan bai yarda da ita ba ko kaɗan. A hankali tako tazo gab dashi, ta buɗe ido sosai a kan fuskarsa tana ta tabbatarwa da kanta shi ɗin ne ko wani ne daban. Ta girgiza kai tana kallonsa, ta nuna sa da yatsa hannunta yana rawa, ta ɗan dafe kanta da yake ciwo ta ce, "kaine ka saka aka kawo ni nan ko kaima ɗaya daga cikin azzaluman da suka ajjiye ni a nan ne?." Rehaan kamar bai jo ba, kallon ta yake yi kamar yadda yake yi mata in sun haɗu. Ganin bai motsa ba sai ta dafe kai, tunawa da baya jin hausa, duk da bata taɓa ji ya yi magana ba, amma kana ganin sa ka san bai yi kama da wanda zai ji harshen hausa ba. Ta buɗe baki zata yi fulatanci sai ta kalle sa ta ga sam bai yi kama da fulani ba, kallo ɗaya zaka yi masa ka hango kamanni na ƴan ƙasashen waje a tare dashi. Ta ɗan rike kanta da yake juyawa, ta canja harshe zuwa turanci ta ce, "kaine ka saka a kawo ni nan?." Bai yi magana ba sai kallonta da yake yi, yana so ya ga ƙarshen rashin kunyar yarinyar. Ta sake kallon sa ta ce, "me nayi maka, Dan ka zuba min tea a jikina nayi magana? Ko dan ka fasa min waya na yi magana shine na cancanci wannan zaluncin?. Ban sanka ba, ban san sunanka ba, ban san waye kai ba. Dan ka yi min ba daidai ba na faɗa sai ya zama laifi?." Ta ja numfashi ta sauke, ta kalle sa ta ce, "kana ji? Ka bar ni na tafi naje na ƙarasa abinda yake gabana, in na kammala sai ka sake turawa a ɗauko ni, zuwa lokacin na nutsu, amma yanzu ba a nutse nake ba." _Wannan yarinyar bata da hankali._ Ya faɗa a mind ɗinsa yana kallonta bai ɗauke ido ba kuma bai ce komai ba. Islaha ta ja numfashi mai tsaho, ta zauna akan kujera saboda jirin da yake ɗaukarta tana sauke numfashi, dan ji take numfashinta yana sarƙewa, ga ciwon kai da ya saka mata jiri. Ta ce, "kana jina, ko kai kurma ne?." Kamar tana magana da rock haka Rehaan ya koma mata, yana tsaye cak bai motsa ba, babu inda yake motsawa a jikinsa ya ƙame a wajen kamar soja. Sai kuwa ta hargitse ta firgice, cikin bala'i da masifar da take ranta ta koma hausa ta ce, "Ina faɗa ka bar ni na tafi inda aka ɗauko ni ka zuba min ido kana kallona kamar ina magana da dutse, kawai dan na yi magana a kan haƙƙina sai ka saka a ɗauko maka ni kamar wata kayan miya?." "Ina da iyaye, suna buƙatata a kusa dasu, ina da mara lafiya da yake buƙatar kasancewata a kusa dashi. Me nayi ka ɗauko ni, Sata na yi maka ko fashi da makami? Ban yi maka komai ba ka kawo ni nan!." Ta sake jan numfashi ta ce, "Me ka ke nema dani da ka kawo ni nan? Meye ribar ka na ajjiye ni a nan kamar wata kayan wanki?." Sai kuma ta dafe kanta da yake harbawa, lokaci ɗaya ta daina masifar ta sanyaya murya ta ce, "ka barni in tafi, ina da mara lafiya, dashen ƙoda za a yi masa, ƴan gidanmu suna can suna nemana. Ka ƙyale ni, ni ban yi maka komai ba, laifi ka yi min, laifi ne dan na nuna hakan kenan? Laifi dan ka saɓa min na nuna maka?." Rehaan ya ɗan sunkuyar da kai ya ɗago ya kalle ta, ganin yadda take hawa da sauka abin ya tsorata shi. Yanzu tana masifa, yanzu ta canja ta sanyaya murya. Sai ya ga kamar tana da mental disorder. Bai saba da hayaniya ba, ita kuma ya ga yar hayaniya ce, hakan ya saka ya juya zai koma inda ya fito. Ta miƙe da sauri ta ƙaraso inda yake, ta tsaya a gabansa ta ce, "baka jina ne? Kai kurman banza, baka jin me nake faɗa ne?." Ya ɗan kalle ta ya watsar da ita, ya sake motsawa zai wuce ta. Islaha ta lumshe ido tana jin jiri yana ɗaukarta ta ce, "ina da mara lafiya, aikin ƙoda za a yi masa, ka bari in je a gama komai, in ya so sai ka saka a kawo ni....." Muryar ta tana sarƙewa ta ce, "A lokacin daidai nake dakai, daidai nake da duk wani rashin kirkin ka. Duk abinda ka ke ji dashi wallahi na fika, ƙarƙari ka kashe ni ko? To na shirya...." Ta ɗan lumshe ido cikin jirin da yake ɗaukar ta, hakan bai hana ta fasa magana ba, ta ce, "A yanzu kam bana cikin nutsuwata ko kaɗan!" Ya ɗan yi baya kaɗan bai kalle ta ba, sai yaga ta yi baya luuu zata kifa a ƙasa.... [6/17, 11:58 AM] KRBBK: RDB2P06 NanaHaleema. Rehaan daman ya yi expecting zata iya faɗuwa, yana kula da yadda take jiri daga tsaye, kuma yanayinta ya nuna zata iya collapsing. Ganin zata faɗi a ƙasa ya saka ya tako ya riƙo ta, ta faɗo jikinsa a sume. Ya kalli fuskar ta da idanunta suke a rufe, ya ɗauke kai daga kallon ta yana miƙar da ita tsaye a jikinsa. Gently ya riƙo ta ya kwantar a kan kujera, ya ɗan taɓa skin wuyanta ya ji zafi sosai. Ya ɗan shafa kansa kaɗan yana kallonta na wani lokaci, ya san stress da yunwa ne suka saka ta a haka, Shams yace bata cin abinci, kuma shima ya gani, ga kukan da take yi dole ta samu zazzaɓi. Sai kuma ya ja tsaki ya fita daga falon dan ya yi waya, dan ya saka an kashe duk service ɗin da yake wajan dole sai ya fita zai samu. Kamar ya kira asibiti ya ce a turo masa nurse sai ya fasa, ya yi order duk abinda zai taimaka mata a wayarsa, ba jimawa rider ya kawo, ya saka aka kawo masa inda yakr ya karɓa ya koma inda take. Ya ɗan kalle ta ya ɗauke kai, ya ɗan yi baya kaɗan ya ɗauko ruwa ya shafa mata a fuskar ta, ganin ta fara farfaɗowa sai ya ajjiye ruwan,  ya riƙe hannunta zai yi mata allurar da zata saukar da zazzaɓin. Da zata yi bacci, ta ci abinci, ta daina kuka da kansa zai sauka, to ya san ba zata daina ba, gwara ya yi mata kafin ta gama nutsuwa ta fara yi masa shirme. Throw the vein ya yi mata pcm ya haɗa mata da allurar bacci, ya miƙe yana kallon ta yana taɓe baki. Shi ba dan ta suma ya ɗauko ta ba, ya ɗauko ta saboda dalilinsa amma ba dan ta yi rashin lafiya, wannan dalilin shine ya saka ya tsaya ya taimaka mata, kar ta mutu a hannunsa. Ya ɗan ja tsaki yana kallonta, yana tuna abinda ta faɗa masa sai kawai ya fita daga falon bai ce komai ba. Wayar sa ya ɗauka ya shiga camera record ɗin gidan yana kallon yadda aka shiga da ita falon, tun lokacin da suka ajjiye ta da haukan da ta dinga yi. Da lokacin da ta tashi sallah, ta shiga ciki ta yi alwala ta fito ta yi sallah ta dawo. Yana ganin faɗan su da Shams da duk abinda ta ce, ya yi murmushi yana girmama girman taurin kai da rigima irin ta yarinyar. Ya sake dawo da inda take yiwa Shams Allah ya isa, ya sake yin murmushi yana shafa kansa ya girgiza kai ya ce, "Za ki ba da labarin waye Rehaan, daga wannan lokacin baza ki sake cewa waye ni ba. Babu inda zaki je sai na ga dama, kuma babu wanda zai san kina nan. If i like, zan bar ki ki shekara a nan, babu abinda aka isa ayi min" ya faɗa yana fita daga record ɗin, sai kiran Jazy ya shogo wayarsa. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka, Jazy ya ce, "Ray wacce yarinya ce a guest house?." Ray ya ɗan yi tsaki ya ce, "ni bani da pravicy ne? Komai sai ka sani?." Jafar ya ce, "ka bani amsa kawai, wacce yarinya ka sace?." "Bai shafe ka ba." "Ya shafe ni malam, ka faɗa min ko in kira Mamy na faɗa mata ka fara kawo mata gidan ka." Ya ɗan yi tsaki ya ce, "ina ruwanka da sanin wacece?." Jazy ya ce, "ya zama dole na sani, ina so na san yaushe ka samu gut ɗin kawo mata gidan ma? Yaushe ka samu courage na fara aikata wannan shirmen?. Infact me ka ɗauko ta ka yi da ita?." "Ciki, ko ban kai nayi bane?." Jazy ya yi dariya jin amsar da ya basa, duk da ya san Rehaan ba mutum ne mai dirty talks ba, tunda ya faɗa ya san yana da dalilin sa. Jazy ya ce, "ka kai ka yi ciki, kana da lafiyar da a rana zaka iya yiwa mata goma ciki. Dan ka kawo ta dan ka yi mata ciki tsaf zaka iya." Ray ya yi banza bai amsa ba, Jazy ya ce, "i'm not joking Ray. Wacece yarinyar da ka saka a ka ɗauko maka?." "Wata ce." "me zaka yi mata?." "ba ka ce na fara iskanci ba? Ciki zan yi mata." "Ray ba wasa nake yi ba, ka faɗa min." "Nima ba wasa nake yi ba." "Please." "Kana magana kamar wani Yayana, ka yi magana a tausashe mana, ka daina ɗaga min murya." "Okay my bad. Wacece?." "She is the girl from that hotel, she is the one I told you to find for me." Jazy ya ce, "Okay ina jin ka, itace wacce ka ke nema. Meye na ɗauko ta? Me zaka yi mata?." Rehaan ya ce, "I brought her here so she would know who I am. She always keeps asking who I am. I want her to know who Rehaan is." "is that all? Shikenan dalilin naka?." Ya yi masa banza bai amsa ba, Jazy ya ce, "wannan shine dalilin da zai saka ka ɗauko yarinya daga gaban iyayen ta? Ka san halin da iyayenta zasu shiga saboda raahinta?." "Ina ruwana da iyayenta? Ni abinda yake gabana kawai na sani. Ina so na tabbatar mata da ni waye, ina so ta san ina da ikon da zan yi mata duk abinda naga dama babu wanda ya isa ya hana ni." Ya ɗan dafe kai yana lumshe idanunsa ya ce, "Ina so ta san zan iya barinta over a year a nan babu abinda zai faru, ina so ta san in na kashe ta na kashe banza!....." ya ƙarasa faɗa cikin sanyi. Kafin Jazy ya ce wani abu Rehaan ya ce, "Yadda take a gidan nan, in na so a ciki zan yi nata kabarinta babu wanda zai san tana ciki. Who is she? Ta san waye ni? Ni take kallo tana faɗawa maganganu marasa daɗi, kuma sai na zuba mata ido ina kallonta?!" Ya faɗa cikin fusata, amma da yake muryar ƴan gayu ce dashi in ba sanin halinsa ka yi ba baza ka taɓa cewa faɗa yake yi ba. Jazy jin yadda yake faɗa ya san ransa ya ɓaci akan abinda yarinyar ta yi masa, kuma tunda har ya ɗauki mataki abin ya taɓa ransa sosai. Ya san shi mutum ne wanda zaka zage sa a gaban idonsa ma ya ɗauke kai kamar bai ji ba, bai cika mayar da ƙarami abu babba a wajansa ba. Yana da haƙuri da kawar da kai, duk abinda zaka yi masa sai ya ga dama zai ɗaga kai ya kalle ka, kawai baya so ka shiga rayuwarsa, yadda bai shiga taka ba, kaima ka ka shiga tasa. Tunda ya ji ya fusata har ya yi hukunci ya san ta taɓa masa rai, kuma ya yi mamaki sosai. Dan karo na farko kenan da wani abu ya taɓa haɗa sa da wata mace har ya yi mata irin wannan hukucin. Ray ba shi da saurin fushi ko kaɗan, yana da haƙuri, yana da kawaici, amma in ya yi fushin sai ka gwammace bai yi ba. Jazy ya ce, "kwantar da hankalin ka Ray, na san ta ɓata maka rai, amma meye na sakawa a ɗauko yarinya ƙarama don Allah?. Wannan ba girmanka bane, in sunan ka ya fita a kan wannan lamarin ka san abinda zai faru ko?." "So what? Babu wanda ya isa ya yi min wani abun, kaf danginta babu wanda zai iya ja dani. In na kashe ta na kashe banza, haka zan binne a nan, ta ko na bawa kare ya cinye namanta." "Amma haƙƙinta ai yana kanka, shi kuma akwai wanda zai rama mata ko?." Ray ya yi masa shiru bai tanka ba, dan ko me Jazy zai ce wallahi bazai bar Islaha ba sai ya ga damaX Jazy ya ce, "don Allah ka ƙyale ta tayi tafiyar ta. Wannan abun ba girman ka bane wallahi, ka ƙyale ta rashin sanin waye kai ne ya saka ta yi maka rashin kunya har ta ce waye kai, amma nan gaba ko kuɗi aka bata akace ta yi baza ta yi ba. Please, allow her to go." Ray ya yi tsaki ya ce, "So is that all you have to say to me? Should I hang up now?." Jazy ya ce, "calm down Mr Ray, don't do anything that will ruin your reputation, don't smeer yourself with black paint. Don Allah, ka ƙyale ta ko dan iyayenta, na tabbatar suna can gida suna nemanta. Ko Mamy in ta ji ka ɗauke yarinyar mutane kawai dan ka nuna mata who you are zata yi maka faɗa." Ray ya ɗan yi shiru kamar ya ji nasihar, sai ya kuma yin tsaki ya ce, "i don't have your time" yana faɗa ya kashe wayar ya cillar da ita gefe yana shafa fuskarsa da hannayensa, yana ji kamar a lokacin take yi masa rashin kunya, ya yi alwashin sai yarinyar ta san waye shi kamar yadda take tambaya. Babu wanda ya taɓa kallonsa ya ce masa waye kai, a ko ina girmama shi ake yi in yaje waje, kafin ya je sunansa ya riga shi zuwa. Amma sau biyu suna haɗuwa tana raina masa hankali, in ya ƙyaleta ma ai bai nuna mata capacity da yake dashi a Nigeria ba. Zai nuna mata yana da ikon da zai saka a ɓatar da ita gabaɗaya, kuma in ta ɓata ta ɓata kenan har abada, ko cigiyar ta baza a sake yi ba.       ****** Sadik yana komawa asibiti bayan sallar magrib Mama da Adda Sa'ida da Labiba suka fito daga reception zuwa waje. Adda ta ce, "Sadik ya labarin Islaha, an ganta ko an samu labarinta?." Ya ɗan yi shiru yana girgiza ka ya ce, "wallahi babu labari Adda. Kawai an samu wani ya faɗa yadda abin ya faru, ya tabbatar mana da ɗauke Islaha aka yi." Adda ta ce, "innalillahi! Aka ɗauke ta Sadik?." Ya ɗaga kai ya ce, "tabbas, a gaban asibitin nan kaɗan aka yi garkuwa da ita." Mama jikinta y yi sanyi matuƙa, ta kalle sa ta ce, "yanzu me ƴan sandan suka ce?." "Sun bamu tabbacin za a yi bincike, duk abinda yake akwai zamu ji. Yanzu muna jira mu ji ta inda za a ɓullo, in an yi waya an nemi kuɗin fansa to masu garkuwa da mutane ne, in ba ayi waya ba kuma wani ne ya ɗauke ta bisa dalilin kansa." Adda ta ce, "daman islaha ta tara maƙiya akan aikin jaridar nan da take yi, wataƙila ta tsayawa wani ko wata a rai." "tabbas kuwa, dan har an kama mace ɗaya, wata yarinya ce da ta yi iƙirarin sai ta ga bayanta." "Ka ji ko? Kai innallahi wa'inna ilaihir raji'un!. Saheer ya sani?." "Ya sani, mun yi dashi da gobe zai taho ma, to na ga gwamnatin ƙasar ta hana kowa fita saboda matsalar tsaron da ake samu, kin ga shima an rufe dashi sai lokacin da suka buɗe zai samu damar fitowa." Labiba ta ce, "Allah ya bayyana Islaha." Suka amsa da amin duk jikinsu ya yi sanyi, Mama da bata ƙaunarta ita kanta ta ji babu daɗi jin an yi garkuwa da ita, abin bai yi mata daɗi ba ko kaɗan. Adda ta ce, "ya batun kuɗin aikin Baffa? An dace?." "Wallahi ɓatan islaha ne ya ɗauke min hankali, amma in Allah ya amince za a dace, komai zai zo da sauƙi in sha Allah." Adda ta ce, "Allah ya sa. Nima zan turo maka wani abu da yake hannuna, sai a san abinda za a yi." Ya ɗaga kai kawai bai ce komai ba, dan jikimn a sanyaye yake akan ɓatan Islaha, ganin abin yake yi kamar wasa.          ****** Kyakykyawam mari ya sauke nata akan kuncinta, Ummi ta fasa ihu ta koma jikin mahaifiyarta tana kuka sosai. Mahaifinta ya ce, "shashasha mara hankali, tunda nake ban taɓa shiga police station ba sai yau. Ke kin san furuci akan sai kin ga bayan mutum? Kin san girman kuskuren da ki ka aikata kuwa?." Yayanta da yake tsaye ya ce, "wallahi akan wannan maganar sai ta yi zaman gidan yari." Abba ya sake fusata matuƙa ya kalle ta ya ce, "meya kai ki, waye ya aike ki furtawa wani sai kinga bayansa?." Ummi tana kuka a jikin babarta ta ce, "kuskure ne Abba, wallahi ni ban faɗa da niyar zan aikata ba." "Yanzu sai ki fito da yarinyar, sai ki faɗa mana uban da ki ka saka ya sace ta." Ta ɗago tana kuka ta ce, "wallahi Allah ni ban saka ayi mata komai ba, ban yi mata komai ba Abba. Tun daga lokacin ban sake tunawa na yi wata magana ba sai ɗazu." Abba ya ce, "ƙarya ki ke yi, tunda ki ka ce sai kin ga bayanta ke kika saka a sace ta, dan haka ki fito musu da yarinya." Ta fashe da kuka ta ce, "wallahi ban saka a sace ta ba!." Cikin faɗa Yayanta ya ce, "wannan ke kika sani, kotu bata san ba ke bace tunda kin furta. An samu shaida kuma kema kin amsa da bakin ki, iya wannan ya ishi kotu tura ki zaman gidan yari." Mamanta ta ce, "ke waye ya aike ki? Waye ya faɗa miki ana wasa da irin wannan maganar?." Ta share hawaye ta ce, "wallahi sai dai in wani ne ya yi amfani da kalamaina ya aikata, amma wallahi ni ban aikata komai ba." Abba ya girgiza kai ya ce, "wannan ke kika sani, abinda hukuma ta sani kin fi kowa hannu a ɓatan yarinyar nan, kuma koda ta bayyana case ɗin bazai mutu ba, ko ya ya wai abun ya same ta za a ce ke ce." Yayanta ya ce, "Abba in ta rasu fa? Ai tana mutuwa a hannunsu wallahi ita ta kashe ta, gidan yari zata tafi a ɗaure ta ɗaurin rai da rai." Ummi cikin kuka ta ce, "na shiga uku! Wallahi ban yi komai ba. Ni haushi take bani ne kawai, na riga ta fara aiki amma tazo ta mamaye komai, ba a saka mu yin komai sai ita. Mu da muka rigata zuwa ba a yi mana abinda ake yi mata, akan idanunmu ake ɗaukaka, ta koma kamar bamu rigata fara aiki ba." "Ranar ma katin gayyatar Mr Ray aka bata, kuma ni chairman ya yiwa alƙwarin zan yi hira da duk wani babban baƙo, amma sai bai bani ba ya bata. Shine na ji haushi na tare ta har na faɗi maganar, amma wallahi Allah ban saka ayi nata komai ba." Abba ya fusata ya ce, "rufe min baki ko na ɓalla ki, daman baƙin ciki ki ke yi nata kenan ko? Hassada ce take damun zuciyarki ko?." Yaya ya ce, "ga illarta nan ta fara gani yanzu, dan wallahi babu mai fitar dake a case ɗin nan sai Allah, ki yi addu'a dan daƙyar baki yi zaman gidan kaso ba. Kin ga sai ki ƙara hankali, nan gaba kar ki sake furtawa wani kalma makamanciyar wannan balle ki ce sai kin ga bayansa." Ita dai kuka take yi sosai ta ce, "Abba ka bani dama na gudu Lagos, don Allah." Yaya ya harare ta ya ce, "ai in kika kuskura ki ka gudu kin ƙarawa wutar fetur wallahi, dan duk inda ki ke sai an nemo ki kuma baza a sassuta miki ba. In kina wannan tunanin ma ki daina, shashasha mara hankali." Shi dai Abba bai ce komai ba ya bar wajen saboda ɓacin rai, Ummi ta cigaba da kukan rashin mafita, sai dai ta yi alwashin in har aka rufe ta to wallahi sai ta zama silar da za a kulle Muslim, sai dai ayi mutuwar kasko, a mutu har liman, baza a a rufe ta ita kaɗai ba wallahi. [6/17, 11:58 AM] KRBBK: RDB2P07 Nana Haleema Islaha bacci ta yi mai tsaho har asuba tana bacci, sai bayan an yi sallah sannan ta miƙe tana riƙe wuyanta da ya riƙe, sannan ga bayanta ya riƙe sosai saboda kwanciyar kan kujera. A hankali take sake kallon ɗakin tana tuna abinda ya faru, ita dai ta san ta tare masa hanya daga nan bazata iya tuna komai ba. Wani tunani ya ɗarsu a ranta, ta miƙe a firgice tana duba jikinta, tana tatttaɓa wuyanta da fuskar ta amma bata ji wani canji da zai nuna an yi wani abu da ita baz Ga kayan jikinta a yadda ta kwanta, alamun ba a taɓa su ba, babu alamun an buɗe wani ɓangare na jikinta. Sai lokacin ta yi ajiyar zuciya, hankalin ta ya ɗan kwanta, tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Tana dafe da kanta, ta duba wayar ta taga lokacin sallar asuba ya yi, ta miƙe a sanyaye ta nufi inda ta yi alwala jiya da niyar sake yi. Kayan jikinta duk sun dame ta, musamman undies ɗinta har wani zafi take ji a jikinta saboda yadda suka yi dauɗa, duk ta ƙyamaci kanta. A haka ta shiga banɗaki sai kawai ta haɗa da wanka, ta yi wanka ta cire undies ɗin ta fito dasu a hannunta, ta tsaya tana kallon kayan ta rasa me zata saka. Ta san dai bata da kayan sakawa, su ɗin ne kawai. Rashin mafita ya saka ta mayar jikinta amma bata mayar da undies ɗin ba, dan gaskiya baza ta iya mayar dasu jikinta ba, musamman pant ɗinta, yafi komai damunta. Ta jawo bedside drawer ta cilla undies ɗin a ciki, ta kalli undies ɗin da ta saka da niyar duk ranar da zata bar gidan zata ɗauke abinta. Ta kalli kanta tana tunanin anya ma kayan zasu yi sallah. Tunawa bata da mafita ya saka ta fito ta dawo inda aka ajjiye ta tayar da sallar asuba jikinta a snayaye. Ta ji daɗin jikinta, babu ciwon kai kuma zazzaɓin ya sauka gabaɗaya. Ta jingina da kujera tana lumshe ido tana tunanin halin da Baffa yake ciki, tana tunanin halin da masoyinta yake ciki. Ta san zuwa yanzu Hamma ya san an sace ta, ta san yana can cikin tashin hankali mai tsanani. Wayar ta ta ɗauka amma still no service, ta cillar da wayar a wajan tana sauke numfashi a hankai. Kallon abincin jiya ta yi, duk suna wajan babu abinda aka taɓa, kuma Allah ya sani yunwa take ji, ta daure ta ɗauke kai daga kallon abincin ta rufe ido, tana ji kamar ta dinga dukan kanta har sai ta daina jin takaicin da yake damun zuciyarta. A hankali ta ji an buɗe ƙofar, ta juyo tana kallon wanda ya shigo. Baturen Chef ne, ɗaure da apron a ƙugunsa sai wata maid a bayansa. Ta zuba musu ido tana kallo suka ɗauke abincin jiya, suka ajjiye mata sabo suka fita basu ce mata komai ba itama bata ce ba. Ta yi banza da abincin, ta rufe ido cikin rashin sanin abinda ya kamata ta yi. Har gari ya yi haske Islaha bata motsa ba, sai ma gyara zama da ta yi a wajan. Sai da ta ji zata kashe kanta sannan ta ƙaraso ta zuba tea ta sha, bata sake kallon komai na wajan ba ta kwanta a kan carpet hawaye yana zuba a idanunta. Rehaan kuwa da ya farka lokacin sallar asuba sai da ya dubata ta camera record ɗin wayar sa, bai ɗauko ta dan ta yi rashin lafiya ba, dole ya so ya ga ya take tunda ya san ta suma. Da ya duba ya ga yadda take bacci sai ya ja tsaki ya ajjiye wayar. Bayan an idar da sallar asuba bacci yayi mai aji, hakalinsa a kwance kamar bai ɗauke ƴar mutane ba, ya jima sosai yana bacci dan har rana ta fito bacci yake yi. Sai gab da sallar azahar ya tashi, ya shiga ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya, ya kwance gashinsa ya sauka har wuyansa. A lokacin ya ɗauki wayarsa daidai lokacin kiran Jazy yake shigowa. Ya yi tsaki ya share bai ɗauka ba, ya fito falon tare da sakkowa ƙasa cikin takun isa da ƙasaita. A kan kujerar dining ya zauna, babu abinda ba a ajjiye masa akan dining ba, komai yana ajjiye yana jiransa kamar banza. Kiran wayarsa da aka sake yi, ya zubawa wayar ido ganin Jazy yana yawo a kai,ya ɗan girgiza kai ya ɗauka Jazy ya ce, "na san daman zaka ƙi ɗaukar wayata, kuma bazan fasa faɗa maka gaskiya ba Ray, ajjiye yarinya a gidan ka babban hatsari ne wallahi." Bai kula shi ba, dan bashi da lokaci bashi amsa, dan bazai ɗauki maganar sa ba sai ya yi maganinta. Jazy yana ji yana wasa da cokali ya san abinci yake ci, dan ya san lokacin cin abincinsa ne, dan shi yafi damuwa da yin lunch akan breakfast ko dinner. Jazy ya ce, "malam kana ji ina magana fa." Nan ma ya yi masa banza bai ce komai ba. Jazy ya ce, "Wallahi zan haɗa ka da Mamy. Allah in na sake yin magana ka yi shiru sai na kira Mamy na faɗa mata, sai na ce mata ka saka an ɗauko maka mace kana abinda ka ga dama da ita, Allah sai na haɗa ƙarya da gasakiya na faɗa mata." "Daman ai kai maƙaryacin ne" ya furta a hankali yana cigaba da cin abincinsa. Jazy ya ce, "kai ka san ya ka ke a gidanku, maganar nan tana fita an samu dama, yanzu za a dinga yaɗawa ana cewa daman halin ka ne ka saba. Meye amfanin ajjiye yarinya budurwa don Allah? Kai ko tsoron ta mutu a hannun ka baka ji? Ko dan kana ji da kanka, kai ga matashin mai kuɗi ko ta mutu a gidan ka babu abinda za'a yi maka?." "Look Jay or Jazy. Faɗi matsalar ka." "ga matsalata nan ina faɗa maka, ka ƙyale yarinyar nan ta tafi." "In na ƙi fa?." "Zan faɗawa Mamy." "Wani ya riƙe maka hannu? Ka kira ta mana." "Dan bana son tayar mata da hankali ne kawai, amma wallahi da sai na faɗa mata. Kuma in ka ƙi jin maganata sai na faɗa mata." Ray ya yi shiru yana ɗaukar tissue ya goge bakinsa, ya ɗauki ruwa ya sha yana sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, "So ka shiga company ne? Ance an samu matsala, haka ne?." Jazt ya yi tsaki ya ce, "ina yi maka maganar ƴar mutane kama yi min maganar dukiya, kai akan dukiyar ka ka damu?." "ita na fito nema, Jafar." Jafar ya ce, "kai baza ka ji abinda ake faɗa maka ba ko?." "Kaima ka san da haka, meyasa ka ke wahalar da kan ka bayan ka san bazan ji ba? Ka bar ni nayi abinda nake so, ka daina dakatar dani dan ka san bazan dakatu ba. Meyasa ka damu ka ke ta magana a kai?." Jafar ya ce, "Rehaan wannan ba girman ka bane." "A wajena girma ne, zan ƙyaleta ne a lokacin da naga dama, duk abinda zaka ce bazai saka na bar ta ba, gwara ka yi shiru." "And ka san halina, ban ɗauko ta dan na yi wani abun da ita ba, amma inda ni ɗan iska ne tabbas sai na yi mata abinda nan gaba baza ta sake cewa wani shi waye ba, matsala ɗaya da aka samu bazan iya farawa daga kanta ba." "Rehaan ta san fuskar ka, in maganar nan ta fito babu daɗi fa." "Kai magana ta dama, ni bai dame ni ba." "Ni dai na faɗa maka wallahi zan faɗawa Mamy. Kuma ka faɗawa Alma kar ta sake zuwa gidan nan, ni ba irin ta bane, dukan tsiya zan yi mata wallahi." Ɗan murmushi ya yi, ya rasa meyasa da ya shigo nigeria yake mantawa da ita, amma in a can ne sai ya ji da gaske zai iya aurenta. Datse kiran ya yi ya miƙe ya fita cikin maids ɗinsa suka yi sallah sannan ya dawo. Kai tsaye inda ya ajjiye Islaha ya nufa, yana buɗe ƙofa ta juyo ta kalle sa ya mayar da ƙofar ya rufe. Gabanta ya yanke ya faɗi a karo na farko da suka haɗa ido, sai a lokacin take ƙare masa kallo, ganin wani irin kyau da kwarjinin da Allah ya basa, ga wani kwantaccen baƙin gashi a kwance a kansa kamar gashin mace. Islaha ta ɗauke kai daga kallonsa, ta sake kallonsa tana jin ƙirjinta yana bugawa dan ta tabbatar da baya jin hausa, yanayinsa bai yi kama da wanda zai ji yaren nigeria ba. Kafin ya yi magana softly ta ce, "Bawan Allah, ka fitar dani daga wajan nan, iyayena da ƴan uwana da kowa nawa suna can suna jirana. Ina da mara lafiyar da za a yiwa kidney transplat, in kana ganin ƙarya nake ka saka a bincika maka Nadira hospital and medical center, zaka tabbatar da gaske nake. Kome ka ke ji dashi a kaina don Allah ka ajjiye sa, ka bari na gama samarwa da Babana lafiya, in ya so ko meye ma sai ka yi." Rehaan yana jinta, duk da wata kalmar da turanci yana yi mata nauyin faɗa, amma yana ganin ƙoƙarinta yadda take magana da turanci cikin ƙwarewa haka. Yana mamakin yadda bata san fuskarsa ba, kuma har tana magana akan asibitinsa amma bata san shine a gabanta ba. Ya ɗan taɓe baki kaɗan yana kallon ta bai ce komai ba. Islaha jin ya shiru sai bata sake cewa komai ba, ta sunkuyar da kai ƙasa cikin rashin sanin abinda zata yi. Shi kuwa wayar ta yake gani, haka kawai zuciyarsa take faɗa masa akwai abinda take shiryawa, dan wayar a tsaye take a jikin kujera, an jinginar da ita kamar ana video. Ya yi taku ɗaya biyu, ya ɗauki wayar yana kallon screen ɗin. Islaha ta miƙe a firgice zata karɓi wayar amma ya riga ya ga video da take yi masa, ya saka wayar a aljihunsa. Sai kuwa ta fusata, cikin masifa ta ce, "wai meye haka ka ke yi? Ka saka an ɗauko ni ba tare da na yi maka komai ba, yanzu kuma ka ɗauke min wayata. Kaine ka siya min? Ko da ka fasa min ita ka gyara ne?. Me ka ke nema a wajena ne? Me ka ke so na yi maka ka bar ni na tafi? Na gaji, ni ba baiwa bace, na san baka yi kama da masu garkuwa da mutane ba, kawai ka sace ni ne saboda wani dalili naka. Me na yi maka?." Bai ce komai ba ya ɗan ja baya jin maganarta har tsakiyar kansa, yana jin yadda take masifa da yarenta ya yi kamar bai ji ba. Daman shi ya yi mamakin yadda take magana a hankali da ya shigo, ashe plan ta haɗa tana yi masa video dan ta samu evidence. Ta kalle sa ta kalli ƙofa, ganin yana gefe dai ta nufi ƙofae a guje amma ƙofa taƙi buɗewa, ta juyo ta kalle sa ta ce, "mugu, Allah ya isa tsakanina dakai, daga ganinka baka sallah, baka yi kama da musulmi ba ko kaɗan. Wallahi sai Allah ya saka min, kuma wallahi indai na fita sai na yaɗa maganar nan a ko ina, sai na nemo waye kai na faɗawa duniya halayenka!" Ta faɗa cikin yaren hausa dan ta san ba jin abinda take faɗa yake yi ba. Ya lumshe ido ya buɗe, kalmar waye kai ɗin nan tana tsaya masa a rai, yana mamakin daman har yanzu akwai sauran waɗanda basu sansa ba ko iskanci ne?. Sannan Allah ya isan da ta yi masa ya ji ta har ransa, ya girgiza kai zuciyarsa tana ɗarsa masa wani abu daban wanda bai yi niya ba, tana faɗa masa ya yi abinda tunaninsa bai zo kai ba, tana tunzura sa akan ya nuna mata waye ko dan saboda gaba. A hankali yake takawa zuwa inda take, idanunta suna gefe bata san yana zuwa inda take ba, sai da ya zo daf da ita ta farga. Ta buɗe ido tana kallonsa da mamaki, ta ga gap ɗin da ya rage tsakaninsu bashi da yawa, ko ya ta yi motsi jikinta zai iya taɓa nasa Islaha ta bi shi da kallo, sai kuma ta ɗan ja baya zata juya ta bar wajen ya riƙo hannunta.... [6/18, 10:04 AM] KRBBK: RDB2P08 Nana Haleema. Ƙare mata kallo yake yi ganin yadda ta zuba masa ido tana kallonsa, yana so ya ga ƙarshen ƙurewar ta a rashin kunya, ya ga ina zata iya zuwa. Sai kuma kallon idonsa ya yi mata nauyi, ta sauke ido ƙasa tana motsa baki fuskar ta cike da damuwa. Ya buɗe baki zai yi magana sai ya fasa, ya ɗan ja baya kaɗan zuciyarsa tana tunanin abinda ya kamata ya yi mata, wanda zata ji a jikinta da zuciyarta, wanda ko nan gaba akace ta saka maimaita abinda tayi baza ta iya ba. Ganin ya ɗan ja baya sai ta tuna ashe fa jikinta babu komai, daga ita sai doguwar riga, ta ɗan motsa kaɗan tana jin kanta wani iri dan gani take kamar ƙare mata kallo yake yi. Gani take kamar yana iya ganin jikinta, tunda yadin abaya yana da kwanciya a jiki sosai, ka saka undies ma ake ganin su balle baka saka ba. Ta ɗago iso ta kalle sa tana ɗan ɗarare jikinta, a sanyaye ta kalle sa ta ce, "Ka mayar dani gida don Allah, ban san me nayi maka ba, don girman Allah ka taimaka min ka mayar dani gida. Ina da mara lafiya a asibiti, ana buƙata ta a gida gidanmu. Duk wani abu da ka ke ji dashi a raina ka ajjiye sa, ka bari in babana ya samu lafiya sai ka ɗauko ni, a lokacin daidai nake da kai." Rehaan dai kallonta yake yi cikin mamaki, jin wai in babanta ya samu lafiya sai ya aika a ɗauko ta, a lokacin daidai take dashi. Yana jiniina girman taurin kanta, amma zai yi maganin ta nan kusa. Kuma ta ƙi cewa ya yi haƙuri, taurin kai da shegen iyayi irin nata ta ƙi basa haƙuri. Ya ɗan buɗe baki zai yi magana sai ya fasa, ya sake buɗe baki zai yi magana sai ya kuma fasawa a karo na biyu. Ganin da zai yi magana sai ya fasa sai Islaha ta ce, "ka yi magana, ka mayar dani gidan mu ni ban yi maka komai ba, ban yi maka sata ba, ban yi maka fashi da makami ba. Dan haka ka mayar dani inda ka ɗauko ni, in ba haka ba wallahi in na fita sai na yi reporting ɗinka a wajan ƴan sanda. Kar ka manta ni ƴar jarida ce, na rantse da Allah sai ya yaɗa maganar nan a ko ina. Kar ka ga ban san sunan ka ba, sai na san duk inda na nemo sunan kana yaɗa maganar ko ina. Daga ranar, baza ka sake marmarin ɗauke ƴar mutane ba." Da baya yake tafiya yana kallon ta, shi mamaki take ba sa wallahi, wai shi zata yi reporting a wajan hukuma. Ya ɗan taɓe baki ya kai hannunsa gashinsa ya shafa a hankali, ya ƙarasa ya shiga wata ƙofa ta bi bayansa da sauri, amma kafin ta je har ya fita daga wajan. Islaha ta jijjiga ƙofar amma taƙi buɗewa, ta koma ta zauna ta dafe kanta cikin yanayi mara daɗi. Rehaan koda ya koma tsayawa ya yi a falo cike da mamaki take basa, ta kasa cewa ya yi haƙuri akan abinda ta yi masa, har faɗa masa take yi ya bari babanta ya samu lafiya sannan sai ya sake ɗauko ta, a lokacin daidai take dashi. Ya yi murmushi, dan shi ya ga alama yarinyar kamar tana da mentel issue, dan in ba mai mentel issue ba babu mai aikata irin abinda take yi. Taruin kai take ji dashi, shi kuma ko me zai faru bazai ƙyale ta ba, sai ya tabbatar ta san waye shi, sai ta yi laushi yadda ya kamata. Waje ya samu ya zauna, ya jawo laptop ɗinsa dan yana da meeting da zai yi da mutanen London. Islaha haka ta zauna falom ta rasa me yake yi mata daɗi, ga jikinta duk babu daɗi saboda bata saba zama babu komai a jikinta ba. Ta ɗan sauke numfashi a lokacin aka buɗe ƙofar aka shigo mata da abinci, ana ajjiye abincin a inda suka saba ajjiye mata, ta kalli abincin ta kalli wanda yake shigowa ta ce, "Don Allah ina ogan ku?." Da mamaki yake kallon ta jin tana tambayar ogansu, kuma yau magana take cikin sanyi babu hayaniyar da ta saba ya ce, "waye?." "Wanda ya fita yanzu, wani fari haka" ta faɗa tana kallonsa. Ya bita da kallo yana mamaki, yana tunanin wa take tambaya, ba dai Mr Rehaan ba?. In shine mai zai kawo shi inda take? Shi fa bai gane kan Ogan nasa ba, mace ta farko da aka taɓa kawo masa gidan. Ko Chef namiji ne, house maids ɗinsa kaf maza ne, indai ba abokan kasuwancinsa ba, mata basa zuwa inda yake. Amma ga wata ƙaramar ƴar jarida, ya saka an ɗauko ta ya ajjiye har yana zuwa inda take. Tana faɗa kuma sai ya ji ƙhamshin turarensa, ya ɗan ɗaga kai yana mamaki, bai nuna mata ba. Ya ce, "ban gane wa ki ke nufi ba." "Mai gidan ku mana, wanda ya saka ku ka sato ni ku ka kawo ni nan." Shams ya ɗan yi murmushi kaɗan yana girgiza kai ya ce, "baki san sunansa ba?." "In na sani zan tambaya ne?" Ta tambaya a fusace tana kallonsa. Ya yi ƴar dariya ya ce, "ni ban san wa ki ke nufi ba." Ta lumshe ido kawai bata ce komai ba, har zai fita sai ta tuna Baffa, ta ga in bata kwantar da kai ba baza ta samu ta bar gidan ba, in bata yi laushi ba baza a bari ta koma su cigaba da fafutukar neman kuɗin aikin Baffa ba. Ta ɗan sanyaya murya, tana jin haushin sauke kai ƙasa da zata yi, ta ce, "Don Allah yana ina? Ka faɗa min inda yake naje na same shi, wallahi Allah ina da mara lafiya a asibiti, babana za a yiwa dashen ƙoda, ana buƙatata a wajen, ina da mahimmaci a wajen aikin. Ku bar ni na tafi, ban san me na yi muku ba." Ya dakata ya juyo ya kalle ta, dan shine ya yi bincike a kanta, kuma ya tabbatar da abinda ta faɗa gaskiya ne. Shams ya ce, "babu inda za ki iya zuwa daga gidan nan, kina wajan nan da aka ajjiye ki." "Na sani, nima ba guduwa zan yi ba, magana nake so na yi dashi, ka taimaka min na ganshi don Allah." Ya ɗan yi shiru yana kallon ta, sai kuma ya gyaɗa kai ya ce, "lokacin hutunsa ne yanzu, amma zuwa anjima na yi miki alƙawari da kaina zan same shi na faɗa masa, in ya amince zan zo na kai ki." Hawaye ya sakko mata ta ce, "na gode." Ya buɗe ƙofar ya fita, ta yi tagumi tana kallon ƙatuwar tv da take ajjiye. Shams bayan ya fita kiran wayar Jazy ya shigo wayarsa, yana ɗauka Jaafar ya ce, "yarinyar nan tana nan har yanzu?." Shams ya ce, "tana nan Sir." Jafar ya yi tsaki ya ce, "ba nace ku sallame ta ba?." "Ka faɗa Sir, amma bai bamu umarnin hakan ba, ka yi haƙuri." "Yana ina yanzu?." "Yana ciki yana hutawa." "Zan yi magana dashi, zuwa anjima ko bai baka umarni ba ka sake ta ta tafi gida, babu abinda zai faru." Shams ya gyaɗa kai ya ce, "To sir." Daga haka ya kashe wayar Shams ya bi wayar da kallo yana mamaki ya ce, "maganar wa zan ɗauka wa zan bari?" Ya faɗa yana zama cikin tunani. Bayan ya idar da sallar isha yana zaune a falo yana shan ice macha, Shams ya yi kocking ƙofar kamar bazai amsa ba, sai daga baya ya ce, "Yeah." Ya shigo da sallama, Rehaan ya amsa Shams ya ajjiye masa abinda ya aike shi ya kawo masa, ya koma daga gefe ya ce, "Sir." Ya ɗan juyo amma bai ce komai ba, alamun amsawa ce hakan. Shams ya ce, "yarinyar nan...." Ɗago kan da ya yi ya kalle shi sai Shams ya nutsu sosai, kar ya yi tunanin wani abu ya ce, "Ɗazu da na kai mata lunch, ta ce min tana so ta yi magana da kai." Ya ɗauke kai daga kallonsa ya cigaba da abinda yake yi kamar bazai yi magana ba, sai da aka yi minti biyu a haka sannan ya ce, "what next?." Shams ya ce, "as you said Sir." Ya ɗan kaɗa ƙafarsa da take ajjiye akan table ya ɗago ya kalle sa ya ce, "meyasa ka faɗawa Jazy maganar ta?." Gabansa ya faɗi matuƙa, ya ɗan sunkuyar da kai ya ce, "Sir...." Kafin ya basa amsa ya ce, "Sir what?." Shams ya yi shiru dan ya san baya so ka yi kuskure ka ce masa sorry. Rehaan ya gyaɗa kai ya ce, "meyasa ka faɗa masa?." "Saboda komai ina faɗa masa, kuma baka taɓa complain akai ba." Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba dan ya san gaskiya ya faɗa, ko kisan kai ya yi dole Jafar zai sani balle kuma ɗauko wata yarinya. Rehaan ya yi masa banza kamar bazai yi magana ba, sai daga baya ya ce, "ta zo." "Thank you sir" ya faɗa da hanzari yana fita kar ya sake kunno masa ruwa. Yana fita wayar Rehaan ta yi ƙara ya duba ya ga Mamy ce, ya gyara zama ganin video call ne ya ɗauka ya ce, "Mamy." Mamy tana kallonsa ta ce, "Rehaan me ka ke yi a nan ne?." "Aiki Mamy." "Aikin me? Me ka ke yi har yau baka gama ba? Kasan bana son zaman ka kai kaɗai a waje ko?." "Mamy har yanzu ban gama ba, yanzu m meeting nake yi." "bayan Jafaar ya faɗa min babu wani aiki da ka ke yi. Rehaan in ka san babu abinda ka ke yi ka dawo gida please." Rehaan ya ce, "ina aiki, ƙarya yake yi." Ta ɗan yi shiru ta ce, "Okay Allah ya taimaka. Amma gobe kazo gida, ka zo mu yi lunch, ina so na ganka." Rehaan ya gyaɗa kai ya ce, "Mamy gashi kina ganina, ai ba sai na zo ba" ya faɗa cikin shagwaɓa yana kallon ta. Dan baya son komawa gidansu, ya fi jin daɗin zama nesa da gida. Mamy ta yi murmushi ta ce, "Mamies Boy, ina so in yi hugging ɗinka Baby, ka dawo ka ji?." "In sha Allah." "Take care." Ya yi murmushi bai ce komai ba ta yanke wayar. Tana kashewa Jafar ya kira shi, ya bi kiran da kallo kamar bazai ɗauka ba, ya yi tsaki sannan ya ɗauka ya ce, "Sai me?." Jafar ya ce, "inyee lallai, hausa ta fara fita yadda ya kamata a harshen ka." Rehaan ya yi tsaki ya ce, "ina da abinda zan yi, ka faɗi damuwar ka ko na kashe wayata." Jafar ya ce, "baka ƙyale yarinyar nan ba ko? Wai meyasa ka ke da taurin kai ne?." "Wait! Wai sister ka ce?." "Not at all..." "So why are you bothering yourself about it?." "Saboda kai ne malam, meye na ajjiye mace a gidan ka for god sake?." "Na faɗa maka ina so ta san waye ni, har yanzu bata sanni ba, ina so ta sani. Duk lokacin da ta sani zan ƙyale ta, ni ban ɗauko ta dan cutarwa ba." Jafar ya ce, "wallahi zan faɗawa Mamy, ɗazu dai ban faɗa mata ba, amma in na tabbatar baka ƙyale ta ba wallahi sai na faɗa mata. Tunda baka jin magana, in ita ta yi maka magana zaka ji ai" yana gama faɗar hakan ya kashe wayar. Ya bi wayar da kallo yana taɓe baki ya ajjiye ta a gefe yana rufe ido. Tunda suka taho wajansa da Shams gabanta yake faɗuwa, girman gidan ma tsoro yake bata, bata tsaya tana kallo ba dan ba kallo ne a gabanta ba. A hankali take tafiya har suka ƙarasa babbar ƙofar, Shams ya nuna mata ya ce, "in ki ka shiga yana falo a zaune." Ta ɗaga kai ta ce, "na gode." Bai amsa ba ya juya ya fita, ita kuma ta ƙarasa wajan ƙofar a hankali. Ƙofar a buɗe take, ta tura a hankali sanyi da ƙhamshin turarensa da ya gauraye waje ɗaya ya daki hancinta, ta ɗan lumshe ido dan ƙhamshin ya yi mata daɗi, kuma sanyin bai yi yiwa yanayinta yawa ba. Slowly ta shiga da sallama, tana sake gyara mayafinta dan gani take kamar tsirara ake kallonta. Ya amsa sallamar a iya laɓɓansa dan bai bari ta ji ba, ta ƙaraso a hankali ta tsaya daga gefe tana ƙarewa falon kallo. Dakatawa ta yi daga kallon falon, ta kalle sa ganin ya canja shiga ba ta ɗazu bace, yanzu baƙar riga ce a jikinsa mai dogon hannu, sai baƙin jeans da baƙin slippers. Gashin kansa a sake, ya saka har wuyansa. Ta ɗauke kai daga kallonsa, ta ɗan sauke numfashi tana tattaro nutsuwar ta gudun kar ya raina ta, ta sauke numfashi tana kallonsa. Ta daure ta ce, "Ban san sunan ka ba, amma don Allah ka barni na tafi ina da abu mai mahimmaci wanda ban yi ba. Ban ga amfanin ɗauko ni ka ajjiye ni a nan ba, iyayena suna can suna ta nemana cikin tashin hankali. Ban san me nayi maka ba, ban san me na aikata maka ba, ka bar ni na tafi gaban iyayena. Babana bashi da lafiya, za a yi masa dashen ƙoda, ka bari na je a gama ya samu lafiya sai ka sake aikawa a ɗauko maka ni." A hankali take maganar babu rashin kunya ko tsiwa kamar yadda ta saba, shi kuma jira yake ya ji tace ya yi haƙuri, amma shegen taurin kai ya saka taƙi faɗa. Tana cewa yi haƙuri ko minti goma baza ta sake yi a gidan ba zai saka a mayar da ita, in kuma bata faɗa ba wallahi ta zo gidan kenan. Ya ɗago ya kalle ta ya ga kanta a sunkuye tana wasa da abin hannunta kamar wata mutuniyar kirki, ta wani nutsu kamar ba ita ba: A hankali ya buɗe baki kamar baya son magana  ya ce, "So......you can't say sorry for your mistake?." Anya Islaha zata ce sorry ɗin nan?🤣🤣🤣 Nana Haleema. [6/18, 10:05 AM] KRBBK: RDB2P09 Nana Haleema. Kamar a sama haka ta ji maganar, ta ɗago da sauri ta kalle sa sai ta ga kamar ba shine ya yi maganar ba, dan tunda ya sato ta bai taɓa yi mata magana ba sai yanzu. Da ta ji yadda ya furta maganar da english sai ta tabbatar da ba bahaushe bane, dan ko kaɗan turancin sa bai yi kama da irin na wanda ya koya ba, kana jin yadda english ɗin yake fita ka dan yaren sa ne, kuma british english yake yi. Ta ɗan kalle sa kallon up and down, da ta tabbatar baya jin hausa, sai ta taɓe baki ta ce, "Ji shi don Allah, wai jira yake na bashi haƙuri daman? To me na yi masa da zan basa haƙuri?" Ta faɗa ƙasa-ƙasa cike da mamaki ba tare da ta san ya ji ba. Rehaan ya ɗan ɗago ya kalle ta suka haɗa ido, ta ɗauke ido dan ba ji yake yi ba. Ta mayar da idanunta gefw ta ce, "ji shi yana kallona, kamar ji me nake faɗa. Ni dai bazan ba da haƙuri ba, sai dai ya kashe ni." Rehaan ya girgiza kansa yana mamakin wannan yarinya mai kama da aljanu, ya ɗauke kai bai ce komai ba. Ta ce, "Ni ban yi laifin da zan bada haƙuri ba, kaine ka yi min laifukan da zaka bani haƙuri ba ni ba. Ka zuba min tea a hotel, ka kalle ni ka share kamar baka sanni ba. Ka fasa min wayata a asibiti, amma ka share ko sannu baka ce min ba, yanzu kuma ka sato ni ka kawo ni nan, kuma duk jira ka ke na baka haƙuri?. Lallai sannu Malam bature...Ko zan iya sanin sunanka?" Ta faɗa tana kallonsa. Bai motsa ba baice mata komai ba, ta ɗan girgiza kai zata yi magana aka kira wayar sa. Ya kalli wayar sai ya ɗauke kai bai ɗauka ba ta cigaba da rining har ta katse. Islaha ta ce, "kai! Daman waya tana aiki a gidan nan? Kenan ni aka kashewa services?" Ta faɗa a hankali tana kallo wayarsa da waya ta kuma shigowa. Wayarta ta gani a ajjiye a akan table, ta kalle sa ta ga kamar ya manta da ita a wajen a zaune, harda lumshe idanunsa kamar mai jin bacci. Islaha ta ce, "bawan Allah baka ce komai ba, ka bar ni na tafi yanzu, duk abinda ka ke ji dashi a kaina daga baya sai mu tattauna." Bai kalle ta ba dan bazai sake yi mata magana ba, ko me zata ce ya gama da ita, shi dai bazai yi magana ba. Ya miƙe zaune sosai yana sauke ƙafa daga kan table ya ɗauki wayarsa yana dannawa. Hawaye ya sakko daga idon Islaha, ta tsani wulaƙanci a rayuwarta, musamman ta yi magana an jita kuma a share, yana daga cikin abinda yake tunzurata sosai, yanzu zata fusata ta birkice ta hau bala'i. Ta bi sa da kallo zuciyar ta tana tafasa sosai ta ce, "ka kashe ni mana kawai ka huta." Bai ko kalle ta ba ya cigaba da abinda yake yi, sai daga baya ya kalle ta, ya ga ta zuba masa ido, ƙiris take jira ta shaƙe shi saboda takaici. Bai ce komai ba ya miƙe ya hau sama ya bar mata wajan bai sake kallon inda take ba. Isaha ta bisa da kallo bata motsa daga inda take ba, yana ɓacewa ta ƙarasa ta ɗauki wayarta ta danna taga tana yadda take, ta kalli saman wayarta amma har lokacin no services. Abin ya bata mamaki, ganin shi gashi har waya tana shigowa wayarsa amma ita wayarta babu services. Inda ya tashi ta kalla, ta ga rafar dala ɗari ne guda biyu a ajjiye, ta ɗauke kai ta nemi waje ta zauna dan bazata fita ba, so take ayi ta ta ƙare kawai, in zai barta ta tafi ya barta, in bazai barta ba ya faɗa mata me yake nema da ita, Shi kuwa yana hawa sama Shams ya kira a waya, yana ɗauka ya ce, "Da gaske tana da mara lafiya?." Shams ya ce, "yes Sir. Wanda yake riƙon ta za a yiwa dashen ƙoda." "Meyasa baka faɗa min ba?." Shams ya yi shiru dan bai san me zai ce ba, lokacin da ya yi niyar faɗa masa shine ya dakatar dashi daga faɗar, amma a yanzu ya san halin ogan nasu bazai taɓa karɓar uzurinsa ba. Rehaan ya ce, "Is okay " daga haka ya kashe wayar ya zubawa madubi ido yana kallon kansa kamar mai son gano wani abun. So yake ya ajjiye ta tayi shekara ɗaya a gidan bata je ko ina ba, so yake ya nuna mata waye shi ta tabbatar yana da ikon da zai iya ɓatar da ita daga duniyar babu abinda aka isa ayi masa. So yake ya saka ta saduda, bakin tsiwar ya mutu, so yake ta zube tana bashi haƙuri tana roƙan ya haƙura ya fitar da ita daga gidan. Bai ɗauko ta don ya azabtar da ita ba, ko dan ya yi mata wani abun ba. Kawai iko yake so ya nuna mata, ta san waye shi. Ya sauke nunfashi yana kallon kansa, saboda mara lafiyar da aka ce dole zai yi haƙuri ya ƙyale ta, tunda har aka ce babanta ne, kuma yana da matsalar kidney ba abin wasa babe, babbar damuwa ce da ya kamata ya haƙura ya janye ƙudurinsa. Ya san daɗin iyaye, ya san ya ake ji in basu da lafiya. Ba dan ta isa ba, sai dan girma da darajar iyaye, in ba dan haka ba sai ta shekara a gidan ko compound baza ta fito ba, sai ya nuna mata iko da matsayin da yake dashi. Ya yi tsaki a bayyane ya ce, "amma bata bani haƙuri ba, sannan...." Sai ya yi shiru yana cigaba da kallon kansa kamar mai son gano wani abun a fuskarsa ko jikinsa. Ya furzar da iska a bayyane, ya lumshe ido ya buɗe, ya shafa gashin kansa yana ɗan girgiza kai ya ce, "is okay Rehaan, stop this drama please, allow her to go, saboda lafiyar babanta. Allow her Rehaan." Ya faɗa yana rarrashin kansa, dan so yake ya nuna mata shima babban mai taurin kai ne da kafiya, duk rashin jinta ya fita, ba ita kaɗai ta iya taurin kai ba, shima ya iya, ba ita ce mara kunya ba, shima ya iya. So yake kawai ta tabbatar ba kowa ake ɗagawa murya a kwana lafiya ba, shiyasa yake rarrashin kansa akan ya barta ta tafi, rashin lafiya tana gaba da ƙudurinsa. Bakin gado ya koma ya zauna, ya ɗauki wayarsa ya shiga camera falon da aka ajjiye ta yana ganin lokacin da suka yi magana da Shams da abinda take faɗa masa. Ya ajjiye wayar ya rufe ido yana fatan bacci ya ɗauke shi, amma da ya rufe ido sai ya tuna da ita, zuciyarsa tana faɗa masa yanzu in ya bari ta tafi ta yiwa banza kenan. Ya ja numfashi da ƙarfi, ya sake rufe ido ya rasa abinda ya kamata ya yi. Islaha kamar mayya ta ƙi barin falon, tana zaune akan kujera, daga ƙarshe ta zame ta zauna a ƙasa ta kwantar da kanta akan kujerar tana rufe ido cikin tunani kala kala da ya tokare mata zuciya. Ta yi alwashin babu inda zata je, a wajan zata zauna sai da in ya dawo ya saka a kashe ta, ta gaji da rainin hankalinsa. ****** "Yauwa Malam Sadik. Tun ɗazu nake neman ku. Na ga sanarwa an sace Islaha?" Dr Isma'il ya faɗa yana kallon Sadik cikin damuwa. Sadik ya ce, "Wallahi an sace ta, mun yi iya abinda zamu yi ba a ganta ba. An yi cigiya a inda aka san tana zuwa ba a same ta ba. Daga ƙarshe wani mai napep yazo ya ce a gabansa aka ɗauke ta." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Kuma an kai repost wajen ƴan sanda?." "An kai Dr. A gaban ƴan sandan ake faɗar an ga lokacin da aka sace ta. Ana ta bincike a kan hakan." "Allah ya bayyanata cikim aminci, Allah ya sa ba garkuwa aka yi da ita ba." "Amin ya Allah." Dr ya ce, "Akan maganar aikin mahaifin ku ne." Sadik gabansa ya faɗi, amma bai nuna ba ya ce, "Ina ji Dr." "ya kamata a haɗa kuɗin aikin nan a kawo, sai kuɗi yazo sannan zamu saka file ɗin ku a layin waɗanda za a yiwa aiki. Duk da na faɗawa wanda muke saka ran zai yi aikin, kuma ya amsa zai yi ɗin. Shine mai asibitin gabaɗaya, na faɗa masa zancen aikin ya ce na tuna masa ranar lahadi. Aikin mahaifin ku shine kaɗai dashen ƙoda da za a yi a ranar, dan haka dole ya kasance an shirya komai yadda ta kamata. Inda kuɗin a hannun ku aje a biya yanzu, in aka biya zasu tura file ɗin, in ya ga komai ya tafi yadda ya kamata sai ya fi mayar da hankali akan aikin." Sadik ya ja numfashi ya ce, "zuwa yaushe kenan?." "Gobe ko jibi, ya kasance an biya kuɗin. In aka biya kuɗin ma kafin ranar, in ya san da maganar za a iya yin aikin a wuce wajen." Sadik ya gyaɗa kai ya ce, "in sha Allah za mu san abinda ya kamata mu yi, za a haɗa kuɗin kafin lokacin." Dr ya ce, "Haka ya kamata ayi. In ka biya kuɗin ka faɗa min, duk da zasu tura min amma ka faɗa min ta yarda zan sanar da Dr ɗin." "Shikenan Dr, na gode" ya faɗa yana miƙewa ya fito jikinsa a sanyaye. Yana ƙarasowa reception ya ga su Mama suna jiran ya ƙaraso. Ya ƙarasa suke ya ce, "Akan maganar kuɗin aikin ne Adda, an ce ana so a biya kuɗin daga gobe zuwa jibi. Kuma ni wallahi tunda Islaha ta ɓace hankalina ya rabu biyu, har yanzu bazan ce ga abinda aka samu ba." Adda ta ce, "ai dole hankali ya rabu biyu, ga aiki ga kuma ɓatan Islaha. Yanzu ya zamu yi?." "Zan kira Saheer na faɗa masa, ka kawo kuɗin da ya tara a haɗa a ga abinda za a yi. Daman ni da Islaha muka ce zamu karɓi loan a bank, to bamu kai ga karɓar bashin ba aka neme ta aka rasa." Mama ta ce, "ba kace za a ba da jinginar gida ba?." "Wallahi Mama an rasa wanda zai karɓa ya bamu kuɗin. Abin ne sai a hankali, mutane babu yarda a lamarinsu. Amma zamu yi magana da mai gidan mu ni da Saheer, ko gidan ne ya karɓa ya bamu kuɗin, tunda har aka fara haka gwara ayi aikin a huta kawai." Adda ta ce, "Ta ya miliyoyin kuɗi zasu fito a wanann lokacin?." "Mu cigaba da addu'a Allah zai dafa mana." Mama ta ce, "Duk da haka Sadik, sai mun nema sannan Allah zai dafa mana. Baza mu zauna mu naɗe ƙafa mu ce Allah ya kawo mana wannan kuɗin ba, dole sai mun fita mu nema." Sadik ya yi ajiyar zuciya, sun kasa gane ruɗanin da yake ciki ya ce, "In Allah ya yarda za a san yadda za a yi, tunda muka shigo nan ai baza mu fita ba, iya kuɗin wankin ƙodar da ake yi masa ma zaman kansa yake yi, dole mu biya su kafin mu tafi." Suka yi shiru kowa yana tunani, ya bar wajen ya tafi wajen Saleeem da yake yi masa waya. Yana zuwa ya same shi a compound ɗin asibitin, ya ƙarasa ya ce, "Saleem ya ake ciki akan maganar Islaha?." Saleem ya ce, "Wallahi babu wani update, har yanzu shiru, babu wanda ya kira ni a waya yace an ga mai kama da ita balle ita. Zuciyata tana faɗa min anya ba yan garkuwa da mutane ne suka ɗauke ta ba?." "Wallahi tunanina kenan nima, bana so na gasgata ne. Ga Baffa, ana neman kuɗin aikinsa daga nan zuwa gobe. Daman Islahan ce mai taimakmin akan neman kuɗin, gashi ta ɓace bamu san inda take ba. Abin ya yi min yawa, na rasa wanne irin tunani zan yi. Mama ta kira ni, Adda ta kira ni, dangin Baffa su kira ni, Saheer ya kira ni, gabaɗaya na ruɗe." "Gaskiya ne, kana cikin ruɗani mai yawa. Allah dai ya bayyana mana Islaaha, ya ba da ikon samo kuɗin nan." "Amin. Amma tun farko mun san asibitin nan ya fi ƙarfin mu, ƙarfin zuciya da karanbani ne ya saka muka kai har yanzu a cikinsa." Saleem ya ce, "to ya za a yi? Haka Allah ya rubuta zai faru." Wayar Sadik ta fara ƙara, ya ɗauko wayar ta ga baƙuwar lamba ce, a yanayin da suke ciki na jiran waya ko yaushe baya ƙin ɗauka, ya ɗauka ya saka a speaker ya ce, "Hello." Daga cikin wayar aka ce, "Muna magana da Sadik, abokin Saheer, saurayin Islaha?." Gabansa ya faɗi sosai, ya kalli Saleem da yake sauraren wayar ya ce, "eh ni ne." "Islaha tana hannun mu, mu ne muka ɗauke ta." Gaban Sadik ya faɗi matuƙa, cikin wani irin yanayi ya haɗɗiye yawu ya kasa magana. Daga wayar aka ce, "Muna buƙatar kuɗin fansar ta naira miliyan ashirin, ko a bayar ko kuma mu kashe ta!." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Sadik ya faɗa cikin firgici yana saurare su. "Kai kawo ta su ji muryar ta, dan su tabbatar da ita ɗin ce a hannun mu." Sadik ya nutsu yana so ya ji maganar Islaha, sai kuwa ga muryar ta ta ce, "Sadik!." Gabansu ya faɗi sosai, tashin hankalin da bai taɓa ji ba yana ratsa shi, kafin su yi magana ya ce, "In an shirya kuɗin zamu faɗa muku yadda za a yi dashi. In ku ka saka hukuma a cikin maganar wallahi sai mun kashe ta!" Yana gama faɗa ya kashe wayar........ [6/19, 10:26 AM] KRBBK: RDB2P10 NanaHaleema. Sadik da Saleem baki a buɗe suka bi wayar da kallo dukkansu cikin ruɗani da tashin hankalin da basu taɓa shiga irinsa ba. Ko a mafarki basu taɓa tunanin za a yi musu irin wannan wayar ba, sai gashi ta faru a lokacin da suke tsaka da tashin hankali. Suka yi shiru na wani lokaci kafin Sadik ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Saleem kaji abinda suka ce fa." Saleem ya sauke numfashi mai nauyi ya ce, "na rasa abinda zance ne Sadik, abin ya ɗaure min kai. Muna jin irin wannan kalaman a wani waje, yau gashi yazo kan mu. Yanzu ya za a yi?." "Mu je mu samu Dpo mu faɗa masa, babu zancen kar mu saka hukuma a maganar, dole mu saka su saboda mafita mu ke nema." "Amma sun ce in aka saka ƴan sanda zasu kashe ta, bai kamata mu saka hukuma a ciki ba." "To Saleem muna da kuɗin da zamu basu ne? Da kuɗin fansar ta zamu ji ko da kuɗin aikin Baffa? Yanzu na faɗa maka halin da ake ciki akan aikin, gidana da nake ginawa, dana Saheer da yake yi zamu siyar a samu ayi abinda ya kamata akan lafiyar Baffa. Ban san taustsayin da ya kawo mu asibitin nan ba wallahi." Saleem ya ce, "to mu je mu samu Dpo, Allah yasa bai tashi ba, dan dare ya yi." Har Sadik ya ɗaga ƙafa zai fara tafiya ya ji wayar sa tana ƙara, yana dubawa ya ga Saheer ne, ya dafe kai ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Saheer ka yi haƙuri bazan iya ɗauka ba" ya faɗa yana kashe power wayar. Ya kalli Saleem ya ce, "Saheer indai akan Islaha ne baya fahimtar komai, ba ya ji baya gani. In ya samu mummunan labarin nan yau bazai iya bacci ba, jininsa zai iya hawa wallahi." Saleem ya ce, "mu daina ɓata lokaci, mu je mu samu Dpo." Bai musa ba suka fita aka shiga motar Saleem zuwa police station. A can suka same shi yana niyar tafiya gida, ganin su da yayanayinsu ya saka ya zauna, suka zauna Sadik ya ce, "Ranka ya daɗe an kira mu a waya ɗazu, yanzu haka mun tabbatar da garkuwa aka yi da Islaha, dan sun kira mu suna neman kuɗin fansa." Dpo ya gyaɗa kai ya ce, "mu ga lambar." Sadik ya ba shi lambar ya saka a wayarsa, sannan ya yi danne-danne ya saka a kunne ya ce, "Na turo maka wannan lamba, a bibiye ta yanzu nan" ya faɗa yana kashe wayar. Ya kalli Sadik ya ce, "ya ku ka yi dasu?." Saleem ya ce, "sun tabbatar mana da tana hannunsu, dan har maganar ta mun ji, sannan sun ce in mu ka saka ku a ciki sai sun kashe ta." Ya ɗaga kai ya ce, "na san zasu ce muku haka daman, zasu faɗa muku abinda zaku ji taoro lokaci ɗaya. Nawa suka nema?." Sadik ya ce, "miliyan ashirin." Cikin mamaki Dpo ya ce, "miliyan ashirin!?." Sadik ya ɗaga kai ya ce, "eh, miliyan ashirin. Sun ce zasu kira su faɗi inda za a kai kuɗin." "Sun taɓa kiranka ne kafin yau?." "Basu taɓa ba." "Kuma kai tsaye suka nemi miliyan ashirin?." "Haka ne." Ya ɗan yi shiru yana tunani kafin ya ce, "sun kira ka a yau kiran farko, kuma har sun faɗi kuɗin da suke so, naira miliyan ashirin bayan sun saka maka muryar Islaha. Sannan ya ce zai kira ya faɗi inda za a kai kuɗin, duk a yau..." ya faɗa cikin nazarin abun daki-daki. Sai ya ɗan daki table ya ce, "ƴan garkuwa da mutane basa taɓa neman kuɗi ƙasa da naira miliyan ɗari, kai tsaye suna iya cewa suna neman naira miliyan ɗari biyu ko ɗari huɗu. Kuma basa fara faɗar kuɗin kai tsaye a kiran farko, suna kira su tabbatar maka mutum yana hannunsu, sannan daga baya su kira su faɗi adadin kuɗi....." "Amma waɗannan kai tsaye sun neme naira miliyan ashiri kacal! A kiran farko, ba tare da ɓata lokaci ba." Ya ɗan kwanta akan kujera yana tunani kafin ya ce, "ba ƴan garkuwa da mutane ne suka ɗauke ta ba, tabbas an yi garkuwa da Islaha, amma ba garkuwa irin wacce aka saba ba a Nigeria ba. Wannan shirya ta aka yi, tsarawa aka yi kuma ba a yi tsarin yadda ya kamata ba." Sadik ya ce, "amma ranka ya daɗe sune da kansu suka kira ni." "Na sani Sadik, na faɗa maka an yi garkuwa da ita, amma ba ƴan garkuwa da mutane bane. Tsarawa aka yi, ana sane aka sace ta. In ka tuna ta yadda aka sace ta zaka tabbatar da wannan plan ne." Saleem cikin damuwa ya ce, "yanzu ranka ya daɗe me ake ciki?." "In sun kuma kira ku cigaba da magana dasu, da zarar sun kira ku ɗaya ya kira ni a waya a tura min lambar, ni kuma a lokacin zan bibiyi kiran dan na tabbatar da abinda nake zargi. Tabbas in ba yarinyar Ummi ce ta saka aka sace ta ba, akwai wasu a gefe da suka sace Islaha. Ko kuma wasu sun amfani sace ta ɗin da aka ce an yi, suka kira ku suna neman kuɗi. Tunda maganar sace ta ta yaɗu, tsaf wasu zasu yi amfani da wannan dama su cika aljihunsu." Sadik ya ce, "amma ranka ya daɗe naji muryar ta fa." Ya ɗan yi shiru ya ce, "kaima kamar ba ɗan zamani ba? Ake haɗa hotununan mutane su yi motsi balle kuma murya?. Ko da yake, koma meye zamu binciko shi. Yanzu ku je gida, a daren nan zan samo matsaya akan case ɗin nan." Saleem ya ce, "kuma har yanzu ba a samu wayar ta ta shiga ba?." "Wayar ta tana inda babu services, sannan an yi ƙoƙarin lalata duk wata hanya da zamu same ta. Wataƙila wayar bata tare da ita, garin a ɗauke ta wayar ta faɗi. In kuma wayar tana tare da ita ba ƙaramin expact ne ya ɗauke ta ba, dan sai mai ilimi da nazari ne zai yi ƙoƙarin kashe hanyoyin sadawar wayar ta." Sadik ya sauke numfashi a sanyaye ya ce, "shikenan ranka ya daɗe, sai mun ji ka." Suka gaisa daga nan suka fita suka shiga motaa. Saleem ya ce, "wato ban san haka ƴan sanda suke da saurin fahimta ba sai yau. Sadik wannan ɗan sanda kansa yana tafiya, kansa yana ja matuƙa, ya san aikinsa sosai. Sai da ya faɗa sannan nayi noticing, sace islaha bai yi kama da satar masu garkuwa da mutane ba, tabbas tsarawa aka yi, kuma Ummi nake zargi." Sadik ya ce, "wallahi nima na raina aikin ƴan sanda, saboda sai naga kamar ba wani abin kirki suke yi ba, ashe su ɗin mutane ne na musamman. Tabbas kuɗi ake so a karɓa a hannunmu, Islaha tana hannunsu amma ba wajan ƴan garkuwa da mutane ba, tabbas akwai abinda aka tsara kuma aka shirya ake son gabatar dashi." Saheer ya sake kiran wayar Sadik, Sadik ya dafe kansa bai ɗauka ba. Saleem ya yi dariya ya ce, "ka ɗauka mana, in baka ɗauka ba hankalin sa bazai kwanta ba." Ya lalle sa ya ce, "baka san Saheer ba ne, damuwar sa kaɗai yawa ce da ita, musamman in akace abu ya shafi Islaha ai ba zaman lafiya" ya faɗa yana ɗaukar wayar ya saka a speaker. Saheer ya ce, "Tun ɗazu ina yi maka waya ka ƙi ka ɗauka, ka san a yanayin da nake ciki zaka dinga share calls ɗina kamar wani yaron ka?." Sadik ya ce, "ina gaban dpo ne shiyasa ban ɗauka ba, ya aka yi?." "Kai zan tambaya, ya batun Islaha?." "Ka fara tambayar batun kuɗin aikin Baffa kafin ka tambaye ta ko?." "Baffa ko yau za a iya samun kuɗin aikinsa, ita kuwa fa? Malam ka faɗa min halin da ake ciki akan maganar matata. In ba dan ƙasar nan ta kulle dani ba ka isa na tsaya ina sauraren ka? Ai da yanzu na dawo ina nemanta da jikina da aljihuna. Har ma na dinga kiran ka ƙi ɗauka?." Sadik ya ɗan murmusa ya ce, "babu wani cigaba a maganar ta. Amma ɗazu wasu sun kira mu suna neman kuɗin fansa, kuma sun saka mana muryar Islaha mun ji. Sun ce mana suna buƙatar naira miliyan ashirin, in ba a bayar ba zasu kashe ta." Saheer cikin wani yanayi ya ce, "kafin a kashe ta, ni ka ke so ka kashe Sadik, meyasa baza ka aiko da mutane su harbe ni a nan kawai na huta ba?...." Ya cigaba da magana ya ce, "Yanzu ka san da irin wannan maganar ka yi min shiru? Ka san hakan ya faru ka ƙi ɗaukar wayata? A ina ka ke so na saka raina, ka san a yanayin da nake zaune a ƙasar nan kuwa?." Sadik bai ce komai ba ya yi masa shiru, Saheer ya yi shiru yana salati, muryarsa ta yi sanyi sosai kafin ya ce, "yanzu ya ake ciki?." Sadik jin muryar Saheer ɗin ta yi ƙasa kamar mai kuka sai ya ce, "kuka ka ke yi?." "Ban cancanci na yi kukan bane? Sadik mahaifina yana kwace babu lafiya, ga matata an sace ta, gashi ana batun kuɗin fansa alamun garkuwa aka yi da ita. Ni kuma ina nan wata ƙasa a kulle an hana shiga da fita, wallahi Sadik ji nake kamar zuciyata zata buga saboda tashin hankali, ni kaɗai na san irin abinda nake ji a raina. Baza ka taɓa hasashen yanayina ba tunda ba kai ne a cikinsa ba. Gani a raye amma na zama bani da amfani, gani da lafiya amma babu amfanin da zata yi min. Matata tana wani wajen da ban san ina ne ba, ni ina nan a kulle babu shiga babu fita." Ya sauke numfashi, cikin rauni ya ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!. Sadik a daji suke ajjiye mutane, Islaha tana da asthma, a wanne yanayi zata kasance? A cikin bishiya suke ajjiye su, ga iska, ga ƙura, ga sanyi, a wanne hali take ciki yanzu?." Sadik da Saleem suka kalli juna jin yadda yake magana cikin rauni, sai ya basu tausayi matuƙa, ko waye a yanayin da yake ciki dole ya shiga wani hali. Sadik ya tausasa murya ya ce, "ka yi haƙuri, ka cigaba da addu'a, in sha Allah komai zai wuce. Mun yi magana da dpo ya tabbatar mana da za a nemo mafita a cikin daren nan, dan shi bai amince ƴan garkuwa da mutane ne suka ɗauke ta ba, abin ya fi kama da plan aka haɗa mata." Saheer ya yi shiru kafin ya ce, "za a iya, ana jin haushinta sosai musamman akan case ɗin wasu yara da ta dinga yayatawa, ni kaina sai da na yi mata magana amma ta ce aikinta yake yi. Allah ka fito min da Islaha cikin ƙoshin lafiya." Suka amsa da amin Sadik ya ce, "duk abinda ake ciki zan faɗa maka" Daga haka suka kashe wayar dukkansu jikinsu a sanyaye yake. Saleem ya ce, "Allah ya bayyana Islaha cikin aminci, Allah ya sa Islaha tana hannu na gari." Sadik ya amsa da amin suka ja motar suka bar wajan. **** Zainab damuwa ta yi mata yawa, ta nemi Islaha sau babu adadi ta rasa, gashi akwai maganganu a bakin ta wanda take son sanar da ita, amma bata samu dama ba. Tana zaune ta yi shiru ita kaɗai aka turo tazo in ji Mama. Bata ce komai ta miƙe ta nufi office, ta tarar da Mama a zaune ita da wata baƙuwa. Zainab ta zauna ta ce, "Mama gani." Mama ta bita da kallo ta ce, "ke yanzu bakya yiwa kan ki faɗa Zainab? Bakya so rayuwar ki ta inganta kamar ta sauran mutanen gidan nan?." Zainab ta yi shiru bata ce komai ba, Mama ta sauke numfashi ta nuna mata wacce take zaune ta ce, "Za ki bita gidanta, za ku dawo nan da kwana biyu." Zainab ta ɗaga kai ta kalli yadda matar ta zuba mata ido, ta ɗauke kai ta kalli Mama ta ce, "Mama me zanyi a can har kwana biyu? Kitso za a yi mata?." Mama zata yi magana matar ta ɗaga mata hannu, ta miƙe tsaye ta ce, "kar ki damu, ku gama magana gabaɗaya sai komai ya biyo baya." Mama ta ɗaga mata kai ta ce, "shikenan sai mun yi waya." Matar ta fita Kama ta kalli Zainab ta ce, "ke ko sha'awar rayuwar Hafsa bakya yi? Hafsa an canja mata makaranta ta koma makarantar kuɗi, sana'ar ƙunshin da take yi yanzu tafi ƙarfinta. Wayar hannun Hafsa itace wayar da ake yayi yanzu, ke kuwa kina nan kina fama da wayar da ko dubu hamsin bata kai ba. Meyasa baza ki yiwa kanki faɗa ba?." Zainab ta ɗago kai ta ce, "Mama ni ban gane me ki ke nufi ba." "Da kin bita na kwana biyun zaki gane mai nake nufi, baza ki dawo gidan nan ba sai da manyan kuɗaɗe masu matuƙar yawa. Ni na rasa irin ki wallahi." A lokacin aka buɗe ƙofar aka shigo, ganin Fadwa ce sai Mama bata dakata da maganar ba ta kalli Zainab ta ce, "yanzu haka ki ke so a tsaya Zainab?." Zainab ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba. Fadwa ta ce, "Zainab jeki ɗaki." Zainab ta miƙe ta fita dan so ta ke ta bar wajan. Tana fita Mama ta daki table ta ce, "Yarinyar nan tana neman tarwatsa min tunani, tana neman neman yi min asarar da ban taɓa yin irinta ba. Ina zainab ta samo taurin kai ne?." Fadwa ta yi tsaki ta ce, "rainon Islaha ce fa, kin manta Hafsa da Zainab su ne ƙannen da tafi ji dasu a gidan nan?." Mama ta girgiza kai ta ce, "dole na samu nasara akan Zainab, ban ga dalilin da zai saka ta yi min asara ina ji ina gani ba." Fadwa ta ce, "Wallahi in ki ka zuba ido itama irin Islaha zata zama, muna ji muna gani komai zai dinga tsallake mu yana zuwa wajan wasu." Mama ta girgiza kai ta ce, "bata isa ba wallahi, in kin ga hakan ya faru to ki rubuta a zuciyar ki bani da rai, matuƙar ina da rai hakan bazai taɓa faruwa ba wallahi. Ko haukata Islaaha zan iya yi, indai zan yi nasara a kanta." Fadwa ta ce, "Daman na zo na faɗa miki zan je na dawo." Hannu kawai ta ɗaga mata dan Zainab ta chaja mata kao matuƙa. Tana fita aka kira wayar Mama, ta ɗauka ta saka a kunne ta ce, "meye kuma?." Daga can ɓangaren ya ce, "Hajiya naira duba ɗari biyu zaki ƙara mana, kuɗin hannunmu ya ƙare." Da mamaki ta ce, "kai dakata! Wai me kuke yi da kuɗi har haka?." "Ciyar da ita mu ke yi." "Islahan wacece da take cin wannan kuɗin a cikin kwana biyu kawai? Kawai akan abinci ta ake kashe waɗannan kuɗaɗen?." "Muna yi mata kiwo mai kyau ne shiyasa." "Bazan ba da wannan kuɗin ba, zan tura muku dubu hamsin, daga shi bazan sake ƙara muku komai ba wallahi." "Shikenan ki turo" ta yi tsaki ta ajjiye wayar ta ce, "Islaha har yanzu baki fita daga rayuwata ba, amma zan yi maganin ki. Zan sadaukar da komai dan ganin bayan ki" ta faɗa tana sauke numfashi cikin wani irin yanayi. Nana Haleema. [6/19, 10:27 AM] KRBBK: RDB2P11 Nana Haleema. A firgice ta buɗe ido ƙirjinta yana bugawa, yadda ta buɗe ido a firgice tana zare ido zai tabbatar da ba ƙaramin tsoro da firgici take ciki ba. Duk da ac da take falon amma zufa take yi, ƙirjinta sai sama da ƙasa yake yi saboda tsoro da tashin hankali. Ta dafe ƙirji tana kallon falon tana tuna abinda ta gani a cikin mafarkin ta. A hankali ta fara sauke ajiyar zuciya, tana tunawa ba gaskiya bane mafarki ta yi, ba a gaske ya faru ba mafarki ne. Taja numfashi mai ƙarfi tana lumshe idonta cikon wani yanayin faɗuwar gaba mara misaltuwa. Mafarki tayi wai Baffa ya mutu, sannna taga Hammanta cikin wani irin yanayi mara daɗi, duk ya birkice yana ta kuka yana kiran sunanta. Ita kuma ga wani abu ya yi mata katanga dashi, tana so ta fito amma ta kasa. Sai kawai ta fashe da kukan rashin mafita, ta cusa kanta a ƙafafunta tana kuka mai sauti. Ta san ko bata yi mafarki ba Hammanta yana cikin wani irin yanayi, ta san Hamma yana cikin yanayin da dole hankalin sa zai tashi saboda rashin ta. Duk wanda zai damu da ɓacewar ta a bayan Hamma yake, duk wanda zai ɗaga hankalinsa akan hakan a bayan Hamma yake.Tasan tabbas zai iya yin kukan rashinta, balle kuma basu san inda take ba balle a ɗauki matakin nemo inda take. Rauni ya sake mamaye mata zuciya, tana tuna yanayin da Hamma zai shiga, tana cigaba da kuka cikin baƙin ciki da ƙunar zuciya. Haushin baturen da bata san sunansa ba, suna sake mamaye mata zuciya. Sai da ta gaji ta ɗago a hankali tana cigaba da kallon falon, sai a lokacin ta kula ashe ba inda aka ajjiyeta take ba, a falon da tazo neman ya fitar da ita take a zaune akan carpert, a haka bacci ya ɗauke ta. Ta lumshe ido hawaye yana cigaba da zuba daga idanunta, ta kalli agogo taga dare ya yi sosai har asuba ta kusa. Ta fara kalle-kalle tana neman inda zata ga banɗaki ta yi alwala ta kai wa Allah kukan ta akan halin da take ciki. Ƙofa biyu kaɗai ta gani, sai stairs ɗin da taga ya hau a daren jiya, ta miƙe ta nufi ƙofa ɗaya ta buɗe a hankali taga bedroom ne mai girma sosai, ta taka kamar bata so ta shiga inda take tunanin banɗaki ne, ta shiga tayi alwala ta fito ta dawo inda take zaune. Kallon jikinta tayi ta ɗan tsaki, ji take kamar kayan jikinta baza su yi sallah ba, duk da basu yi dauɗa sosai ba amma sai take ji kamar basa su yi sallah ba. Tunawa da babu yadda zata yi sai ta tayar da sallah har lokacin asuba sallah take yi. Footstep take jiyowa a hankali, ta juya ta gansa yana sakkowa kunnensa maƙale da airpot, yana motsa bakinsa alamun magana yake yi. Hannayen sa duka biyun suna kansa yana tattare gashin kansa ya ɗaura band, sannan ya saka hular jallabiyar da take bayansa. Baƙar jallabiya ce a jikinsa mai dogon hannu, waccs ta yi masa kyau sosai ta haska fatar da take jikinsa. Tun kafin ya ƙaraso turarensa ya rigasa zuwa wajanta, ƙhamshinsa ya dabaibaiye falon cikin ƙaramin lokaci. Yana juyowa suka haɗa ido da ita, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi sosai, sai take so ta tuna inda ta taɓa ganin fuskarsa ko da sau ɗaya ne. Tunani take yi a ina ta taɓa ganinsa, kamar ba a hotel ta fara ganinsa, zuciyar ta tana faɗa mata ta san shi a wani waje, kawai bata san a inda ta ganshi ɗin bane, kuma gashi ta kasa tunawa. A lokacin taji ya ce, "Alright." Faɗar hakan da ya yi sai ta dawo hankalinta, ta kawar da tunanin inda ta san shi ta cigaba da kallonsa tana so ta ga ko zai yi mata magana. Bai kalle ta ba, ta taka a hankali ya nufi ƙofa ya buɗe ya saka thumb print ɗinsa, ƙofar ta bada sauti kaɗan samnan ta buɗe, ya fita daga falon bai sake kallon inda take ba balle ta saka ran zai yi mata magana. A sanyaye ta daina kallon sa, ta kalli gabas ta tayar da sallah tana hawaye, tana idaarwa ko addu'a bata yi ba ta ƙarasa wajan ƙofar tana ja ko zata buɗe amma bata buɗe ba. Ta ƙarasa wajan window amma ta kasa ɗaga labulen wajan dan ba normal labule bane da ta saba gani, ta koma ɗaya tagar nan ma ta kasa dan duk iri ɗaya ne bata san ta ake amfani dasu ba, bata taɓa ganin irinsu ba. Ta glass ɗin window take hangosa tsaye da yaransa, sai murmushi suke yi shi kuma bata ganin fuskar sa. Sai kuma taga ya juyo takowa zuwa falon, ta lumshe ido tana ji kamar da zuciyar ta yake tahowa, duk taku ɗaya da zai yi bugun zuciyar ta ƙaruwa yake yi, kamar wacce ta aikata masa laifi take jin tsoron zai kamata. A daidai lokacin ta ji an buɗe ƙofar an shigo, ta juyo tana kallo sa ganin ko kallon falon bai yi ba yana niyar wucewa sama. Da sauri ta ƙarasa inda yake, muryar ta tana rawa ta ce, "ban san sunan ka ba..." Sai ta kasa ƙarasawa saboda hawayen da take riƙewa suka sakko daga idanunta. Ta ja numfashi mai tsaho ta ce, "Babana yana asibiti........" tana faɗa ta fashe da kuka tana zubewa akan guiwar ta tana kuka sosai. Kamar an dakatar dashi ya tsaya bai hau saman ba, ya juyo ya ga yadda take kuka kamar wacce aka yiwa rasuwa a lokacin. Ko maganar ta bata fita yadda ya kamata, kuka take yi sosai tana haɗe hannunta waje ɗaya. Islaha ta ce, "Ban san me na yi maka ka kawo ni nan ba, ban san me na aikata ka saka aka kawo ni ba. Da nace bazan ba ka haƙuri ba, tunda ban yi maka laifin komai ba, kaine ka yi min laifi bani ce nayi ba. Amma na haƙura, saboda rayuwar Baffa zan sauke kai ƙasa, saboda rayuwar Baffa zan yi abinda ban taɓa yi ba. Baffa ya cancanci fiye sa haka a gare ni, ya cancani nayi komai saboda shi." Ta ja numfashi tana goge hawayenta ta ce, "ka yi haƙuri....." Ta faɗa tana lumshe ido hawaye yana cigaba da zuba a idonta. Hawayen baƙin ciki da takaicin sauke kai ƙasa da tayi, amma bata da mafita dole ta saka ta bashi haƙuri. Ɗan murmushi ya yi, ya ɗan girgiza kai ya ce, "finally." Islaha ta kalle sa ta ce, "Don Allah ka bar ni na tafi, ka ƙyale ni naje na cigaba da abinda yake gabana. Tunda na baka haƙuri, komai ya ƙare daga wajen nan." A lokacin ya juyo a hankali ya kalle ta, bai yi magana ba sai ɗaga kai da ya yi kawai, ya hau sama bai sake kallonta ba. "Mugu kawai, Allah ya isa tsakanina da kai, kar ka bari na tafi ɗin, in ka ga dama ka bari sai naman jikina ya koma ƙashi sai ka bawa karnuka. Saboda Baffa kaɗai na baka haƙuri, wallahi da baka isa na sauke kai ƙasa ba. Bana bada haƙuri akan haƙƙina, in ka ga na bada haƙuri nasan laifi. Zamu sake haɗuwa wani lokaci, a lokacin zaka tabbatar da bana sauke kai ƙasa wallahi." Rehaan yana jin ta, ya yi murmushi dan shi kallon mai taɓin hankali yake yi mata, yanzu zata yi maganar hankali in anjima ta yi maganar shirme. islaha tun tana kukan da ƙarfinta har ta gaji, ta koma sauke nunfashi idanunta biyu har gari yayi haske. Shiru gidan babu motsin kowa, ko ina tsitt kamar babu mutane a cikinsa. Motsi ta dinga ji, ta zubawa wajan ido sai ta ga an fito daga wata ƙofa an shigo inda take da sallama, ta kalli wanda ya shigo ganin Chef ne bature, ɗaure da apron a ƙugunsa, ya ƙaraso ya ajjiye mata tray bai ce komai ba ya koma ƙofar da take tunanin kitchen ne. Ta kalli abincin ta ga gabaɗaya english breakfast ne, sai wani munafukin kofin shayi kamar na yara. Ta yi tsaki ta ɗauke kai ta cigaba da zama har bacci ya ɗauke ta. Shi kam Rehaan tunda ya hau sama ya manta da wata Islaha, bai tashi daga bacci ba sai sha biyu na rana. Ya shiga ya yi wanka ya shirya zai fita, tunawa sun yi da Mamy zai je su yi lunch a gida. Tsaf ya shirya cikin ƙananun kaya, riga red colour, sai saka black ɗin jeans, ya kawo jacket black ya saka. Ya ɗauki comb ya gyara gashin kansa da gashin fuskarsa, ya zubawa kansa ido, har zai naɗe gashin sai ya fasa ya bar gashin sa ya sauka har wuyansa. Ya kawo face cap ya saka, yana gyara ta yana kallon kansa. A hankali yake sakkowa ƙhamshin turarensa ya mamaye ko ina. Islaha ta ɗago kai ta kalle sa dan tashin ta daga bacci kenan. Basu haɗa ido ba dan hankalinsa yana kan waya yana dannawa, sai da ya ƙaraso falon sannan ya ganta ya yi kamar bai ganta ba. Ya ɗan yi tsaki dan ya manta da ita, yaso yace su mayar da ita tun asuba sai ya yi bacci, daga nan bai sake tunawa da ita ba. Ganin ta zuba masa ido tana kallonsa sai ya kira kira Shams, ya ƙarasa ya buɗe ƙofar Shams ya shigo yana gaishe sa cikin girmamawa, da kai ya nuna masa ita yayi alamun a fita da ita. Shams ya ce, "Okay Sir." Rehaan ya fita Shams ya ƙarasa ya ɗauki tarkacen kayansa da suke ajjiye, waya ce guda ɗaya, zai laptop. Ita dai bata motsa ba har suka fita tana kallon su. A haka Shams ya dawo yana kallon ta da fara'a ya ce, "ƴar jarida kin yi free, mu je a mayar dake gida." Ta miƙe a zabure ta ce, "da gaske ka ke ko wasa?." "Da gaske nake, ƴar jarida Islaha." Ta gyaɗa kai cikin tabbatarwa ta ce, "Wallahi sai nayi repoting ɗinku a wajan ƴan sanda." Da mamaki yake kallon ta yana ɗan murmushi ya ce, "Lahh, lallai yarinyar nan kina tsaurin ido, shikenan sai kin dawo" ya faɗa yana dariya sosai, dan shi kam tana bashi dariya. Ya ce, "ina jiran ki" ya faɗa yana fita ya bar ta a falon dan ta ɗan kimtsa yadda ya kamata. Islaha duk ta ruɗe saboda murna, ta gyara hular kanta ta gyara zaman mayafin kanta, har zata wuce sai ta dawo da baya ganin rafar dalolin nan suna wajan har lokacin. _Islaha monday ta kusa, kuma lokacin aikin Baffa ne. Na tabbatar har yanzu Sadik bai samu kuɗin aikin Baffa ba, kuma in ba mu biya kuɗin nan ba daidai yake da mun rasa Baffa._ Magana take da zuciyarta tana kallon kuɗin gabanta yana faɗuwa matuƙa a karo na farko a rayuwar ta. _Ba fa sata zaki yi ba Islaha, kuɗin wahalar dake da yayi zaki ɗauka, ko banza kin fashe zaman da ya saka ki ka yi ba tare da kin yi masa laifin komai ba. Ki ɗauka kawai, ai bai san kin ɗauka ba, Allah ya san ba sata ki ka yi masa ba._ Da wannan shawarar zuciyar ta ta miƙa hannunta wajen kuɗin, hannun yana rawa ta ɗauki rafa ɗaya tana juya ta a hannunta. Bata taɓa riƙe dala ba balle rafar ta, sai dai ta ganta a waya ko a wani abun, amma bata san ya take a zahiri ba. Tsoro ya mamaye ta, ta mayar ta ajjiye tana tunanin abinda ya kamata ace ta yi. _Islaha in baki ɗauka ba a ina za ki sake samu wannan damar? Ki ara kawai, in yaso sai ki biya shi wani lokacin. Ba sata zaki yi ba, aro zaki yi kawai. Bashi ki ka ci, kuma gwamnati ma tana cin bashi, kema dan kin ɗauki bashinsa ai ba wani abun bane. Haka kawai ya kawo ki ya ajjiye ki a gidansa, da ya bar ki ai da yanzu kin nemo kuɗin. Dan haka ki ɗauka kawai, Allah ya san baki da mafita ne._ Da wannan tunanin ta sake saka hannu ta ɗauki guda ɗaya cikin wani irin yanayi na bugun zuciya.  Ta sake mayarwa ta ajjiye tana furzar da iska, ta dafe kai tana tuna yanayin da ta ga Baffa a mafarki, kuma ta san tashin hankalin ɓatanta bazai bari su nemi kuɗin aikin Baffa ba. Kuma ga kuɗi tana gani, in ta ɗauka ma ba sata ta yi ba, kuɗin wahalar da ita da ya yi ne. Islaha ta sake miƙa hannu ta sake ɗaukar kuɗin, tana kallonsu a hannunta jikinta da zuciyarta suna rawa. Ta ɗaga kai sama taga cctv tana ɗaukar ta, ta sake ajjiye kuɗin gabanta yana faɗuwa matuƙa, abin ka da baka saba gani ka ɗauka ba, duk ta ruɗe ta firgice. Sai ta kuma ɗauka kuɗin tana kallon camerar, ta nunawa camerar kuɗin ta ce, "Aron kuɗin nayi, ba satar maka kuɗi nayi ba, zan dawo dasu in na samu. Ni ba ɓarauniya ba ce, ban taɓa sata ba. Wannan ma aro nayi, zan dawo maka dasu duk daren daɗewa..... in ma ban dawo dasu ba, fansar wahalar da ka bani ce." Sai kuma dafe kai ta ce, "To kuma ai baya jin hausa" ta faɗa still tana kallon camerar. Shams ya leƙo ya katse mata tunani ta ce, "Yar jarida ke nake jira." Ta zubura tana neman inda zata boye kuɗin hannunta, shi kuma bai kawo komai ba dan ya san kaɗan daga cikin aikin Rahaan ya bata kyautar kuɗin. A sanyaye ta ɓoye kuɗin a rigarta tana takawa a hankali, sai kuma ta tsaya tana tunanin ta mayar da kuɗin, tana sake tunawa sata ce ba bashi ba, zuciyarta tana sake zugata akan ta tafi da kuɗin kawai ai kuɗin fansar sace ta da ya yi ne. A haka ta saka ƙafa ta fita daga falon. Ta ganshi a tsaye a jikin range rover baƙa, ya buɗe mata gaban motar shiga, ya zagaya ya shiga suka bar gidan gabanta yana faɗuwa sosai, ta waiwayo tana kallon gidan tunawa da ta bar undies ɗinta a ciki. _Hmm rashin mafita da neman mafita, ya kan ja mutum ya aikata abinda zai yi danasani. Kamar dai Islaha🥺_ Nana Haleema 09030398006. [6/19, 5:37 PM] KRBBK: RDB2P12 Nana Haleema. Tunda suka tafi take kallon hanyar, bata taɓa shiga mota irin wacce take ciki ba, ji take kamar ba tafiya suke yi ba saboda daɗin motar. Abin mamaki sai taji wayar jikinta tana ta ƙara alamun  shigowar saƙo. Tana dubawa taga services ɗin wayar ya dawo, abin ya bata mamaki, tana tunanin da gangan aka kashe mata services ɗin wayar kenan. Ta girgiza kai tana jinjina girman makircin mutumin, ta tabbata ba ƙaramin mutum bane tunda ya saka aka kashe mata services. Tana shiga camerar wayar sai taga ta daina nuna mata blank ta dawo aiki, ta riƙe haɓa cikin mamaki da ɗaure kaita ce, "kai!." Shamas ya juya ya kalle ta, ta girgiza kai tana kallon inda suke shiga suna fita, wani babban estate ne da dole ya rikita ka in baka san kansa ba, kusan gidajen duk iri ɗaya ne, layikan ma duk iri ɗaya. "Ina zan kai ki?." Ta wani kalle sa, irin kallon  ban sani ɗin nan ba ta ce, "inda ku ka ɗauko ni." Ya yi dariya ya ce, "Ƴar Jarida, kina bani dariya sosai." Ta girgiza kai ta cs, "na baka dariya a yanzu, da na koma gida kuma zan baka kuka, dan kaine mutum na farko da zan fara kai ƙara, in yaso sai kazo ka faɗi sunan ogan naku a kama shi shima." Ya yi dariya yana ta mamakin rashin sanin fuskar Ogansa da bata yi ba ya ce, "kina tunanin a ƙasar nan akwai hukumar da zata iya kama sa?." Cike da gadara ta ce, "Shi ba mutum bane?." "Mutum ne kamar kowa ƴar jarida, amma yana da ƙarfin ikon da bazai kamu ba a ƙasar nan ba." "Hmm, za a fara daga kaina kuwa, in ban zama silar kama shi ba kace ba sunana Islaha ba." Ya yi dariya bai ce komai ba, ƙarfin halinta da rashin tsoronta ya burge shi, sai yake ji ina ma ta shiga harkar tsaro, ta zama jami'a a hukumomin tsaro na nigeria. Islaha ta kalle sa ta ce, "Kai baka jin tsoron nayi maka hoto na nunawa ƴan sanda fuskar ka?." Ya ɗan kalle ta ya ce, "wanda ki ka yi min fa? Ko kina tunanin banga kin ɗauke ni a hoto ba?." Ta bisa da kallon mamakin ya aka yi ya gane, ya yi dariya ya ce, "ba zauna gari banza bane ba ni ƴar jarida, na wuce tunanin ki. Kar ki ga ba kallon ki nake yi ba, ina sane da duk abinda ki ke yi." Ba tace komai ba tayi masa banza, sai gani tayi ya tsayar motar a ƙofar gidansu. Ta kuma kallonsa ta ga ɗaure fuska kamar ba shine yake murmushi ba, ya nuna mata gidan ya ce, "ki shiga gida." Bata ce komai ta buɗe ta fita, sai da ta tabbatar ta fita daga motar, yadda ko sake kamata zai yi kafin ya fito ta shiga gida sannan ta ce, "ai daman zan shiga gidan, ba sai ka bani umarni ba. Kuma dukkan ku sai Allah ya saka min, kuma wallahi bazan bar maganar nan ta tafi a banza ba, ku jira na kammala abinda yake gabana ku ga abinda zan aikata. Sai na bawa ogan naka mamaki, sai na saka ya kwana a cell akan case ɗin nan. Mu zuba nu gani" tana gama faɗa ta bar wajan da sauri ta shiga gida. Shams ya bita da kallo yana dariya, ya girgiza kai ya ce, "Ko ina Oga ya samo wannan ƴar rigimar oho, yarinya kamar mai aljanu? Babu tsoro ko kaɗan a idanunta." Yaja motar ya bar unguwar da gudu. Islaha da sallama ta shiga falo, sai ta ɗauke kai ganin abinda yake faruwa a cikin falon. Hanan ce da wani saurayi, tana zaune akan cinyarsa yana bin ko ina na jikinta da kiss. Ganin Islaha babu zato sai ta zubara ta miƙe daga jikinsa, cikin borin kunya ta ce, "Islaha! Kin dwwo? Su waye suka sace ki?." Takaici bai bari Islaha ta bata amsa ba ta wuce ɗaki ta kulle kanta. Ta ƙarasa ciki a sanyaye, ta ajjiye kuɗin da ta ɓoye a rigar ta, ta shiga wanka a gaggauce. Ta fi minti talatin tana wanka sannan ta fito ta shirya ta yi sallar azahar. Kuɗin da ta ajjiye ta ɗauka da wayarta, sai ta kai su hancinta ta ji ƙhamshin turaren mutumin kawai suke yi, musamman wayar ta kamar shafa mata turaren ya yi. Ta yi tsaki tana hararar wayar, ta fita daga gidan da sauri. Tana fita ta hangi motar Saleem a ƙofar gidansu Safeera, da sassarfa ta ƙarasa ƙofar gidan, tana zuwa ta ga Saleem da Safeera a tsaye yana rarrashin Safeera tana ta kuka. Islaha ta ce, "Safeera!." Da hanzari Safeera ta juyo jin muryar Islaha, suna haɗa ido tayi murmushi ta ce, "Hamma Saleem rarrashi ka ke yi kenan, to na dawo ai." Safeera ta fito da sauri ta ce, "Islaha!" Tana faɗa ta rungume ta cikin tsananin kewa da farin ciki. Islaha ta yi murmushi ta ce, "na dawo, ki daina kuka." Safeera ta ɗago tana kallon Islaha ta ce, "Ina ki ka shiga? Su waye suka yi garkuwa dake? Ya aka yi suka sake ki ba a biya kuɗin fansar ba?." Ta kalli Saleem da yake kallon ta a rikice cikin mamaki ya kasa magana. Islaha ta ce, "kuɗin fansa kuma? Wanne irin kuɗin fansa?." Saleem ya ce, "Islaha an kira mu an nemi naira miliyan ashirin kuɗin fansar ki, ko mu bayar ko a kashe ki." Ta ɗan yi shiru tana nazafi kafin ta ce, "kuna ji, mu je asibiti wajan Baffa." Saleem ya ce, "wajan ƴan sanda ya kamata mu fara zuwa kafin mu je can." "A'a Hamma Saleem, mu fara zuwa asibitin akwai abinda zan yi a can da gaggawa, in mun gama daga can sai muje duk inda zamu." Safeera ta bita da kallon mamaki ta ce, "ni ban ga alamanun an yi garkuwa dake ba, gabaɗaya baki yi kama da wacce aka sace ba. Islaha daga ina ki ke?." "Duk za ku ji komai, muje kawai" ta faɗa tana shiga motar Saleem, shima ya shiga yaja suka tafi asibiti. A kan hanya ma bata ce komai ba har suka je asibitin, tana shiga wajansu Mama duk suka taso ana tambayar ta abinda ya faru. Bata basu amsa ba ta ce, "Lafiya lau nake Mama, ina Hamma Sadik?." A lokacin Sadik ya ƙaraso ya ce, "Islaha! Ke ce?." Ta ɗaga masa kai ta ce, "ni ce Hamma Sadik, ya batun kuɗin aikin Baffa?." "Mu fara da gama case ɗin nan naki, ya aka yi ki ka dawo? Waye ya sace ki?." "Na fi so mu gama da batun aikin Baffa, in yaso komai sai ya biyo baya, kazo muje" ta faɗa tana yin gaba ya bi bayanta da hanzari. Sai da suka bar wajan sannan ta kalle sa ta ce, "ina takardar biyan kuɗin aikin Baffa? An samu kuɗin?." Shi dai kallon ta kawai yake yi dan bata yi kama da wacce aka sace ba, duk da fuskarta a ta ɗan kumbura kuma ta ɗan rame, amma babu wahala a tare da ita ko kaɗan. Ya kamata wahala ta bayyana a kan fuskar ta ko ya ya ne, amma shi bai ga wata alama da zata nuna ta sha wahala ba. Ganin yaƙi magana sai ta ce, "Hamma Sadik kai nake jira." Ya ɗan sauke numfashi ya ce, "Naira miliyan biyar kawai aka samu, ita ce kawai a hannuna a halin yanzu." Islaha ta fito da kuɗin daga jakar ta nuna masa ta ce, "wannan zasu isa?." Gaban Sadik ya faɗi ganin rafar one hundrend dollors cikakkiya a hannunta. Ya bita da kallo cikin wani irin yanayi na firgici da mamaki ya ce, "Islaha!.....A ina kika samu kuɗin nan? Waye ya baki rafar dollors?." Ta dafe kanta dan bata so maganar ta yi tsaho ta ce, "ka amsa min kawai Hamma Sadik, waɗannan zasu isa?." "Akan me zan amsa miki bayan ban san a inda ki ka samu ba?....Islaha meye haka ne? Me nake shirin gani a tare dake? Kin fara bani tsoro, an nemi rasa, kwatsam kin dawo da waɗnanan kuɗin a hannun ki, me yake faruwa haka?." Islaha ta ɗan yi tsaki, ta buɗe datar wayarta messages suka fara shigowa kamar hauka, ta san daman za a samu haka, saboda ta jima bata buɗe data ba, kuma ga yanayin da ta shiga wanda kowa ya ji labari, ta san za a dinga tura mata da saƙo. Wayar ta fara hooking, amma a haka ta shiga google ta yi converting one hundrend dollor to naira. Bayan ta ga kuɗin dala ɗari, sai lissafa adadin kuɗin hannunta gabaɗaya, dala ɗari-ɗari sau ɗari, ta ga kuɗin hannunta miliyan sha bakwai ce da wani abun a lokacin. Ita kanta sai da gabanta ya faɗi, bata taɓa kawowa yawan kuɗin ya kai haka ba, bata yi tunanin kuɗin su kai miliyan goma ba balle sama da haka, tsoro ya mamaye mata zuciya, amma sai ta daure ta zare takardar hannunsa, ta tafi wajan payment bata kula shi ba. Shi dai ya kasa motsi yana kallon ta tana cike form, ƙarshe ta miƙa musu rafar dalar, suka karɓa tana yi musu magana suka bata takarda bayan an yi photocopy. Ta kusa dashi ta wuce da sauri, ta nufi inda suke ajjiye suka ta bata file ɗin Baffa ta saka a ciki payment bill ɗin a ciki. Wanda ya bata file ɗin ya ce, "donar ɗin yazo, yau a nan zai kwana." Ta ɗaga kai ta dawo wajan Sadik ta ce, "a kira Kawu, sun ce a nan zai kwana yau." Shi dai Sadik ya zuba mata ido ya kasa motsi sai kallon ta yake yi tana ta kai kawo daga nan zuwa nan kamar ba wacce aka sace ba. Ganin ya kasa magana sai ta tafi wajan Mama ta faɗa mata sannan ta dawo wajan Sadik ta ce, "Yauwa na gama, zamu iya zuwa inda zamu je yanzu" tana faɗa ta ƙarasa wajan Safeera da Saleem suka fita. Sadik ya biyo bayansu jiki a sanyaye, zuciyarsa tana faɗa masa abubuwa marasa kyau akan islaha, a haka suka shiga mota suka tafi wajan ƴan sanda dan a sanar dasu ta dawo. Babu wanda iya yi mata magana har suka je, suna zuwa wajan sa suka zauna. Dpo ya kalle ta ya ce, "Islaha barka da dawowa gida cikin aminci." Ta ɗaga kai ta ce, "yauwa barka." "Islaha zamu so mu ji waɗanda suka sace ki, hankalin mu ya rabu gida biyu saboda abubuwan da suka faru. Jiya mun amsa kiran da aka ce sai an bada naira miliyan ashirin za a bada fansar ki." Islaha ta sauke numfashi ta ce, "ni ba garkuwa aka yi dani ba, sace ni aka yi, amma ba masu garkuwa da mutane bane." "To kenan su waye suka kira mu waya?." "Wallahi ban sani ba, amma na tabbatar a inda nake, da inda aka ajjiye ni babu wanda zai yi waya ya ce a basa kuɗi." "A ina aka ajjiye ki? Waye ya sace ki kenan?." Ta ɗan yi shiru tana sauke numfashi cikin wani yanayi, ta lumshe ido ta buɗe ido tana tunawa da in fa ta faɗa zancen kuɗinsa zai fito, gashi ba a riga an yiwa Baffa aikin ba balle ta ce taci riba. Kuma kowa zai san ta ɗauko masa kuɗi, ita kuma ba haka take so ba. Ta kalle sa ta ce, "ni ban san sunansa ba, abinda na sani kawai ba ɗan ƙasar nan bane, dan ko kaɗan bai yi kama damu ba. Sannan yana da kyau sosai, sannan yana da dogon gashi, kamar balarabe ko ɗan india haka. An ajjiye ni a wani estate da bazan banbance ina ne ba, sannan an kashe services ɗin wayata, da aka fahimci ina video sai aka goge komai na wayar tawa, aka mayar da camerar waya ta blank, yadda bazan iya komai ba." "Kuma babu hannun abokiyar aikin ki Ummi a ɓatan ki?." Islaha ta girgiza kai ta ce, "Gaskiya bata da hannu ko kaɗan." Dpo ya ce, "Amma ta yi iƙararin sai taga bayanki, bakya tunanin ita ta sace ki?." Ta girgiza kai ta ce, "dan tace sai taga bayana ba hakan yana nufin zan yi mata sharri ko na ɗora mata laifi ba, gaskiya Ummi bata da hannu a sace ni ɗin da aka yi." Dpo ya ce, "Kuma gashi kin ƙi yi mana bayanyi yadda zamu gane waye ya sace ki. Meyasa bakya so mu sani? Bakya so a yi bincike a kai ne?." Islaha a gajiye ta ce, "kamar yadda na faɗa maka wallahi ban san sunsan ba, in na sani zan faɗa maka, kuma bazan rantse akan ƙarya ba, fuskarsa kawai na sani a idona." "Zaki iya yi mana bayanin fuskar sa mu tura a ɗauko forensic sketch artist su zana mana shi?." Ta ɗan yi shiru tana sauke numfashi, zuciyar ta tana tuna mata da kuɗinsa da yake hannunta, tabbas in yana da laifi itama tana da laifin aron kuɗinsa ba tare da ya sani ba. Da ace tana da kuɗin da zata bashi, da ta saka an zana shi ɗin kawai ko dan a kamo shi. Dan zata iya bada bayaninsa cikakke, tana hango fuskarsa yadda ya kamata a idanunta, ƙwaƙwalwarta ta riƙe fuskarsa sosai. Kuma tana da hoton Shams, in aka kamo Shams mai gidansa ya kamu. Babbar matsalar da zata hanata magana itace kuɗinsa. Ta ɗan yi shiru kaɗan ta ce, "Ranka ya daɗe...." Sai tayi shiru bata ƙarasa ba. Ya ce, "Ina jin ki, faɗi abinda yake bakin ki." Islaha ta ɗan lumshe ido kaɗan ta ce, "kawai a kulle case ɗin nan." Sadik da mamaki yake kallon ta ya ce, "kamar ya kulle case ɗin? Islaha sace ki aka yi fa." Dpo ta ɗaga masa hannu alamun ya ƙyale ta, ya kalle ta ya ce, "sun yi miki bazarana kenan, sun ce in muka ji labari sai sun kashe ki ko sun cutar dake, haka ne?." Islaha ta yi shiru bata amsa ba, bata so ta amsa ƙarya ta zama gaskiya a wajensu, dan ta san ƙarya take yi in ta amsa. Dpo ya ɗaga kai ya ce, "Sadik kuje da ita ta huta ta samu nutsuwa, in yaso sai a dawo mu tattauna." Islaha ta girgiza kai ta ce, "A nutse nake ranka ya daɗe, ina gane komai yadda ya kamata. Kawai tunda Allah ya bayyana ni a rufe case ɗin, bani da buƙatar a yi dogon bincike a kai. Ummi kuma bata da hannu a sace ni ɗin da aka yi, sannan waɗanda suka yi waya akan kuɗin fansa wasu ne daban a gefe, sun yi amfani da ɓatan da nayi suka kira waya suna neman kuɗin fansa, amma ni ba garkuwa aka yi dani ba" ta ƙarasa faɗa cikin sanyin murya tana kallonsu. Nana Haleema. [6/22, 9:41 AM] KRBBK: RDB2P13 Nana Haleema. Dpo kallon ta yake yi yana nazarin yanayinta daki-daki, ya girgiza kai ya ce, "Tunda har kin tabbatar ba Ummi bace, kuma kike da tabbacin ba waɗanda suka sace ki ne suka yi waya ba, hakan yana nufin kin san waɗanda suka sace ki." Ta ɗan dafe kai ta ce, "Officer na faɗa maka na sani, amma ban san sunansa ba." Dpo ya kalli Saleem da Sadik ya ce, "ku je da ita gida ta huta, zuwa jibi sai ku dawo mu cigaba da magana. Tana cikin ruɗani ne yanzu, wataƙila sun yi mata barazana." Zata musa ya dakatar da ita ya ce, "Ki je gida, kar ki ce komai, kawai ki je." Bata iya cewa komai ba suka tashi suka fito daga office ɗin suka koma mota. Safeera ta dafa Islaha ta ce, "ni ban gane miki ba Bestie, meyasa zaki ce a kulle case ɗin nan? Sannan su waye suka sace ki?." Sadik ya kalli Safeera ya ce, "Safeera ba wannan zaki tambaya ba, tunda har Islaha tace basu Ummi bane, sannan ta ce waɗanda suka yi waya suma ba su ne, kin ta tabbata ta san waɗanda suka ɗauke ta." "Kuma da ta tashi dawowa babu wahala a tare da ita, babu wata kama da zata nuna mana an sace ta. Kuma sai ta dawo da bandle ɗin hundred dollors, cikakkiyar rafa da ta kai miliyan sha bakwai. Ba rafar dubu ɗaya ba, rafar dala ɗari. Da nayi converting dollor to naira a wayata, a yadda dollor ta yi tsada a yanzu, naira miliyan goma sha bakwai da wani abun ne a hannunta. Tana dawowa kai tsaye ta biya kuɗin aikin Baffa......" ya ƙarasa faɗa yana kallon ta. Ya ce, "Islaha ta ya zamu amince da wannan abubuwan da mu ka gani a tare dake? Sace ki aka yi ko kuma tafiya ki ka yi?." Saleem ya buɗe ido cikin mamaki ya ce, "Rafar dala fa ka ce?." "Wallahi da gaske nake maka, yanzu maganar da nake yi ta biya kuɗin aikin baffa dasu." Sadik ya juyo ta kalle ta ya ce, "Islaha kar ki ce min saboda kuɗin aikin Baffa ki ka je kika sadaukar da kanki aka baki wannan kuɗin?." Da sauri ta ɗago ta kalle sa tana buɗe ido cikin firgici, ta dafe ƙirji ta ce, "Hamma Sadik! Zargin zina ka ke yi a kaina?." "Dole a zarge ki Islaha, bani kaɗai ba, ko Saheer in yaji wannna tatsuniyar taki dole wani abun ya ɗarsu a ranki. Haka kawai wanda ya sace ki zai ɗauki waɗanan kuɗi ya baki ba tare da ya ƙaru dake ba?." Ta goge hawayen da suka taru a idanunta ta ce, "Wallahi Allah ni ban aikata komai ba, abinda ku ke zargi ba haka bane. Mutumin nan ban san shi ba, ko sunansa ban sani ba, kuma ni ko hannuna bai riƙe ba." Saleem da ya cika da mamaki ya ce, "To wani ɓangare daga sassan jikinki ki ka siyar masa? Na tabbatar haka kawai namiji bazai ɗauki wannan kuɗi a baki ba." Ta dafe kai ta ce, "Ku yarda dani, wallahi sace ni yayi, sannan duk zargin ku a kaina ba haka bane. Rantsuwa nake yi muku da wallahi, ku yarda dani." Safeera a sanyaye ta ce, "Islaha ba ƙin yarda muka yi dake ba, mun ji ya sace ki, kina nufin bayan ya sace ki da ya tashi sakin ki sai ya baki kyautar kuɗin? Kuma ya aka yi ki ka bar hannunsa? Sannan waye shi?." "Na faɗa muku ban san sunansa ba." "Meyasa ki ka ce a rufe case ɗin?." Ta sauke numfashi ta kalli Safeera a sanyaye ta ce, "kema zargina ki ke yi?." Ta girgiza kai ta ce, "bana zarginki da fasiƙanci, amma zuciyata tana faɗa min kin san wani abu akan case ɗin nan. Meyasa zaki ce a kulle case ɗin? Ki bari hukuma tayi bincike a gano mai hannu a ciki mana." Islaha ta ce, "Wallahi Allah ban san komai akan case ɗin nan, kawai na buɗe ido na ganni a wani gida, daga nan aka dinga kawo min abinci kamar ina gida. Abinci ake bani mai rai da lafiya kamar na hotel, shiyasa baku ga wahala a tare dani ba. Ac nake kwana nake tashi, tsabar sanyi sai da numfashina ya fara riƙewa. Sai daga baya naga asalin wanda ya saka aka ɗauko ni." Sadik ya ce, "akan wanne dalili ya saka aka ɗauko ki?." "Saboda kawai nayi masa rashin kunya, yana so ya nuna min yana da ikon da zai iya ɗauke ni. Shine kawai." Sadik ya ja tsaki jin tana raina musu hankali, tana wata magana kamar a drama ko a tsatsuniya, ya kawar da kai dan tsaf zai iya zaginta, haushinta yake ji sosai, baya a dinga magana cikin rainin hankali. Saleem ya girgiza kai ya ce, "kawai dan kin yi masa rashin kunya sai ya sace ki?...." Ta sunkuyar da kai bata amsa ba, Saleem ya ce, "Hmm Islaha ba fa film muke kallo ba, ya kamata ki faɗa mana abinda ya faru, in kuma kina ganin sirrin ki ne ba sai mun san maganar ba sai mu cigaba da sabgar mu." Sadik ya ce, "shine kawai, kai tsaye ta ce mana bata buƙatar mu san komai, shikenan sai muyi shiru. Rayuwarta ce ai ba tamu ba, ita ta ga zata iya ai." Islaha ta yi shiru, bakin ta yayi nauyi ta kasa ce musu ɗauko masa kuɗin tayi, nauyin kalmar take ji sosai a zuciyar ta shiyasa ta kasa magana. Amma dan ta fitar da kanta daga zargi sai ta ce, "ni dai na faɗa muku wallahil azim ko hannuna bai riƙe ba, kuma ban siyar da ko wanne sassa na jikina ba. Wanda ya ɗauke ni kuma ban san sunansa ba, amma na san fuskarsa a yanzu. Kuma kuɗin nan aronsu na karɓo, kuma......" sai ta kasa ƙarasawa ta yi shiru tana kallon ƙasa. Sadik ya yi murmushin takaici yana binta da kallon kin raina mana hankali ya ce, "kar ki damu Islaha, tunda Allah ya bayyana ki abinda muke fata kenan daman. Ummi ta fita daga zargi, yanzu waɗanda suka yi waya suna neman kuɗin fansa za a nemo. Ko da yake, tunda kin ce a rufe case ɗin ai case close." Ta sauke numfashi a sanyaye ta ce, "Don Allah Hamma Sadik kar ka bari Hamma ya san labarin nan, don Allah kar ka ce masa ni na biya kuɗin aikin Baffa, ka ji?." Ya ɗaga kai ya ce, "akan me zan yi shiru, bayan ban san daga inda ki ka samo kuɗin ba?." "Wallahi ban yi abinda ku ke zargi ba." "Shikenan Islaha, bazan faɗa masa ba." Ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "na gode." Ta kalli Safeera da itama ita take kallo ta, ta mayar da ido ta rufe tana jin haushin kanta akan akan ɗauko kuɗin da tayi. Danasani ya cika mata zuciya, da bata ɗauko kuɗin ba da yanzu ta faɗawa hukuma kamanninsa an kamo shi. Sadik ya ce, "Na kira Saheer bana samunsa, ina jin ya taho ne." Ita dai ta yi shiru bata ce komai ba tana tuna yadda komai ya kasance a can gidan. Saleem ya ce, "na faɗawa Muslim ya yi update akan bayyanar ki, mutane sun damu da rashin ki sosai." Ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba, ta jinginar da kanta a jikin ƙofar motar tana tunani kala-kala. Bata san haka kuɗin da ta ɗauko suke da yawa ba, da ta san haka suke da matuƙar yawa da bata ɗauko ba. Yanzu wacce hanya zata bi ta samo masa kuɗinsa ta biyasa? Yanzu a ina zata samo kuɗin da zata biyasa? A ina zata gansa har ta basa kuɗinsa?. A ƙofar gida suka tsaya Saleem ya ce, "ki je ki huta." A sanyaye ta buɗe ƙofar ta fita ita da Safeera. A hankali aka buɗe gate ɗin gidan aka fito, tana kallon gate ɗin idonta ya faɗa cikin na Saheer, da dawowarsa kenan ya shiga ya ajjiye kayan hannunsa ya fito. Suna haɗa ido ta ji hawaye ya taru a idonta, gabanta ya faɗi tana tunanin da wacce kalma zata kare kanta a wajensa? Ta san bazai taɓa yarda a rufe case ɗin ba, dole sai an yi bincike ita kuma bata so. Saheer ya zuba mata ido yana kallonta cikin wani irin yanayi na kewa. A hankali ta taka ta ƙarasa inda yake ta ce, "Hamma!." Ya runtse idonsa cikin wani yanayi na rauni da sanyin zuciya, bai san lokacin da ya riƙo hannunta ya rungume ta tsam ba. Duk da tana cikin wani irin yanayi, amma hakan bai saka ta ji abin baƙo ba. Duk da son da Hamma yake yi mata bai taɓa rungume ta baa, sau ɗaya ya taɓa haɗa jikinsa da nata lokacin da ta samu attack, amma tana hayyacinta bai taɓa aikatawa ba. Sadik ne ya ƙaraso ganin ya riƙe ta gam yana lumshe ido yaƙi sakin ta, ya kalli inda suke yaga babu jama'a sosai, ya ƙarasa daidai kunnensa ya ce, "A kan hanya ka ke Malam, ka sake ta." Kasa sakinta ya yi, dan ji yake in ya sake ta kamar za a sake cewa ba a ganta ba. Ita ta fara ƙoƙarin raba kanta daga garesa, jin hakan sai ya sake ta ya riƙe hannunta suka shiga cikin gidan. Ya zaunar da ita a inda suka saba zama a harabar gidan yana binta da kallo. Sai ta sunkuyar da kai,  dan a yau idanun Hamman nata ba irin wanda zata tsaya kalla bane. "Matar Hamma, kina lafiya? Su waye suka ɗauke min ke!?" Ya faɗa cikin murya mai sanyi yana kallon ta. Ta ɗago ta kalle sa, a sanyaye ta ce, "Lafiya lau nake Hamma. Amma kai ma ka rame." "ta ya hankalina zai kwnata ina can an ce min ba a ganki ba? Ga Baffa babu lafiya, ga ki kema kin ɓace. Ai dole na rame." "Yanzu na dawo ai." "Waye ya ɗauke ki? Ina suka kai ki, basu yi miki komai ba?. Kin faɗawa ƴan sanda komai akai?." A sanyaye ta ce, "babu abinda suka yi min, kuma ni ban san wanda ya ɗauke ni ba Hamma." Ya ce, "Amma kin yi bayani yadda ya kamata a gaban ƴan sanda ko?" Sai ta juyo ya kalli Saleem da Sadik da Safeera da suke tsaye suna kallon su ya ce, "anje wajan hukuma? Sun ɗauki bayaninta yadda ya kamata?." Sadik ya ce, "anje, amma ta ce a rufe case ɗin." Da mamaki ya ce, "Kamar ya a rufe case ɗin?." "Haka ta ce." Ya kalle ta ya ce, "kamar ya a rufe case ɗin, meyasa za a rufe matar Hamma?." Ta sauke numfashi ta ce, "Saboda ni ban san shi ba, hasalima ba yaren mu bane ba fa, baya jin fulatanci kuma baya jin hausa. English ɗin da yake yi ma british ne, kana ji ka san ba ɗan ƙasar nan bane." Saheer ya ce, "saboda haka kawai sai a kashe case ɗin? Saboda kawai ba ɗan ƙasar nan bane sai a kashe case ɗin?. Mu mun isa mu je ƙasar su mu yi abinda ya yi, sai shine zai yi ya ci bulus?." Ta ɗan ɗaga kai ta ce, "kawai bana so ai ta wahala ne, domin baza a iya kama sa ba wallahi, babban mutum ne sosai. Kuma ni nafi so mu mayar da hankali akan rashin lafiyar Baffa shiyasa na ce haka." Saheer ya bita da kallo yana ɗaga kai ya ce, "saboda hakan kuma sai waɗanda suka sace ki a ƙyale su sun sace banza kenan? So ki ke a rufe case ɗin, shi kuma ajjiye ki ɗin da yayi ya yiwa banza ko?." Ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba dan tasan bazai fahimce ta ba. Ya kalli Sadik ya ce, "ku ji fa abinda take faɗa." Saleem ya ce, "haka ta faɗa a police station, ta ce bata buƙatar a yi bincike akan case ɗin." Ya bita da kallo tuhuma yana rolling idanunsa a kanta ya ce, "Islaha meyasa bakya so a bibiyi case ɗin, kin san shi ne?." Zata bashi amsa ya ɗaga mata hannu ya ce, "kar ki maimaita abinda ki ka faɗa min a farko, ki bani dalili mai ƙarfi wanda zai saka na amince." Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Saheer ya ce, "tunda baki da dalili ba za a rufe case ɗin nan ba Islaha, har Ummin baza ta fita ba. Domin zamu je ayi rubutu nida iyayenta, duk abinda ya same ki wallahi sai na ɗaure ta. Kuma dole ki basu bayani mai gamsarwa akan maganar nan, baza a ƙyale case ɗin ya tafi a banza ba wallahi, kin ji na rantse ko?." Ta ɗan girgiza kai cikin rashin mafita ta ce, "To Hamma." Sai a sannan ya kalli Sadik da Saleem ya ce, "ku yi haƙuri, ashe bamu gaisa ba" ya faɗa yana basu hannu. Suka gaisa suna dariya, Safeera ta ce, "ta ya zamu gaisa, ka ga Islaha ai dole ka manta damu." Ya yi murmushi ya ce, "Hankalina ne a tashe, sai da na baro ƙasar nan sannan na samu nutsuwa. Ina labarin waɗanda suka yi waya akan kuɗin fansar ta?." Sadik ya ce, "Amfani aka yi da ɓatanta aka kira dan a damfare mu, suma za a yi bincike a gano waɗanda suka yi wayar." Ya ɗaga kai ya ce, "babu wanda zai sha a cikim case ɗin nan wallahi, ko shi wanda ya ɗauke ta ɗin ne sai mun yi shari'a dashi indai ina da rai." "Hakan ne ya kamata daman" Saleem ya amsa yana kallon Islaha. Saheer ya ce, "Ya kuɗin aikin Baffa? An gama haɗawa ne Sadik?." Sadik ya ɗan kalli Islaha yaga ta zuba masa ido alamun kar ya faɗa, ya ɗauke kai daga kallon ta ya ce, "uhum an samu, har an biya ma. Sai dai mu yi fatan Allah ya sa a yi a sa'a." "Amin. Amma baka faɗa min an gama ba." "Ina gama biyan kuɗin islaha ta bayyana shiyasa na manta." Ya ɗaga kai, ya juyo yana kallon Islaha ganinta tsaf da ita kamar babu abinda ya faru da ita ya ce, "babu alamun wahala a tare dake, kin dai ɗan rame kaɗan, amma kwata-kwata baki yi kama da wacce aka sace ba." Ta sunkuyar da kai ta ce, "kaina ciwo yake yi min Hamma" ta faɗa dan ta kawar da waccan maganar. Ya bita da kallo cike da kulawa ya ce, "muje ki huta" ya faɗa yana miƙewa, ya riƙe hannunta suka shiga ciki. Sadik ya kalli Safeera ya ce, "ƙawar ki akwai abinda take ɓoyewa wanda bata so mu san dashi." Safeera ta girgiza kai ta ce, "nima na gani, zan je naji ko meye, dan na tabbatar zata faɗa min. Ina zuwa" ta faɗa tana bin bayansu da sauri...... Nana Haleema. [6/22, 9:42 AM] KRBBK: RDB2P014 Nana Haleema Rehaan yana zaune a falon Mamy yana danna wayarsa, magana yake akan sabuwar order da ya yi gabaɗaya ya yi busy har su Mamy suka zauna bai sani ba. Ƙaramin tsaki ya yi yana dafe kai, sai kuma ya kira waya ya saka a kunne ya fara magana cikin turanci. Ya fi mintina arba'in yana waya, sai ya sauke wayar ya yi ajiyar zuciya, sannan yaji Mamy ta ce, "Mr Busy." Ya hankali ya juyo suka haɗa ido, suna haɗa ido ya yi murmushi ya ɗan langwaɓar da kai cikin shagwaɓar da ya saba yi mata ya ce, "neman halak da wahala Mamy." Ikram da take zaune ta ce, "awwwn! Bruh ashe ka iya karin magana?." Ya ɗaga ido ya kalle ta suka haɗa ido, a lokacin ta ƙaraso ta basa hannu alamun su gaisa. Bai musa ba ya bata hannu suka gaisa, ya ɗan yi murmuahi ya ce, "Ikram, ya Mummy?." Ta zauna a gefensa tana kallonsa ta ce, "tana gaishe ka." Ya ɗan ɗaga kai yana kallon falon sannan ya ce, "Ina Riyya da Kiddo?." A guje Kiddo ta taho ta zauna kusa dashi tana riƙe hannunsa tana kallonsa ta ce, "My love." Ya shafa kanta ya ce, "My love bakya yi min waya." Cikin shagwaɓa ta ce, "na kira ka baka yi picking calls ɗin ba." Ya ɗan buɗe ido, sai ya ɗauki waya ya shiga recent calls ɗinsa, a nan ya yi karo da kiran ta har sau biyu. Ya ɗaga ido ya kalle ta, sai ta fara kukan shagwaɓa kamar bata girma ba ta ce, "kana gani ka ƙi ka ɗauka. Ka daina sona." Ya riƙo ta ya ce, "I'm sorry Kiddo, banga kiran ki ba, da zan yi pecking." Ta turo baki ta ce, "ni dai a'a." "Me ki ke so?." "Mu tafi Jeddah tare." "sai kin je Jeddah zaki haƙura?." "Eh." "Kiddo ni kaɗai ne a Jeddah, Jazy baya nan, in na tafi aiki da wa zaki zauna?." Sai ta ɗan yi jim kaɗan ta ce, "to yaushe zaka je danii?." Ya ja hancinta ya ce, "zan turo a zo a tafi dake." Ta ɗaga kai ya yi murmushi sannan ya ce, "Ina Riyya?." Banisha ta ce, "Tana school." "Janan fa?." "Tana wajan aiki." Ya gyaɗa kai bai ce komai ba, a lokacin Riyya ta dawo daga makaranta. Mamy ta miƙe ta ce, "tunda ga Riyya ta dawo muje muyi lunch gabaɗaya." Tare suka hau kan dining har Ikram aka fara cin abinci, rabin zaman nasa amsa waya yake yi, ko ka ji shigowar saƙo ya mayar da amsa ya cigaba da cin abincin. Mamy ta zuba masa wani abu ta miƙa masa, ya kalla yana kallonta ya ce, "meye wannan?." Mamy ta ce, "moimoi." "Moimoi!." Mamy ta ce, "in baka ci ka daina harararsa." Ya ɗan ture ya ce, "bana so Mamy. Kema sun koya miki cin wannan abun" ya faɗa yana cigaba da shan tea ɗinsa yana danna waya. Mamy ta ce, "Kai kuwa dole na koya ai, zaman da nayi a nan ban yi shi a inda aka haife ni ba." Ikram aka kira a waya, ta ɗaga waya tana magana kafin ta kashe ta ce, "Mamy zan je gida yanzu, zan dawo in anjima." Mamy  bita da kallo tana murmushi ta ce, "To Ikram, a gaishe da Mummy." "Zata ji. Byee Riyya, byee Hamma" ta faɗa tana ɗaga masa hannu ta fita. Mamy ta kalle sa a lokacin ya ce, "gobe zan yi tiyata Mamy, sannan a daren zan tafi Jeddah." Riyya ta ce, "Jeddah!" Ya kalle ta ya ɗaga kai alamun eh. Riyya ta ce, "Hamma why are you always traveling? We don't get enough time to spend with you. We really need you in our family. Daga Uk sai Jedda, kullum baka nan." Ya kalle ta ganin cikin yanayin damuwa take maganar, hakan ya tabbatar masa har zuciyar ta take yi ba wasa take yi ba. Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Riyya akan aiki, zan je wani asibiti for three months contract." Riyya ta yi fushi ta miƙe tsaye ta ce, "meyasa ko yaushe kana kan aiki? Meyasa baza ka tsaya a nan ba? meyasa lallai sai ka je can?." Ya riƙo hannunta ta zauna ya ce, "calm down Riyya, ba abin ɗaga hankali bane." Idonta ya ciko da ƙwalla ta ce, "Muna son ka dinga zama a kusa damu, muna so mu dinga hira da kai. Kai kaɗai ne Yayanmu, su Hamma Sameer yayansu su Janan ne, kaine namu. Don Allah ka dinga zama a kusa damu, ka ji?." Rehaan ya kalli fuskar ta cikin damuwa ya ce, "ko yaushe muna tare, kar ki damu." Riyya ta miƙe ta tafi ɗaki bata sake kula shi ba, ya bita da kallo cikin damuwa. Gabaɗaya ahlin Mamy babu wanda yake si yaga ɗaya yana fushi, sun fi so kowa ya kanace cikin farin ciki da walwala. Ba dan aiki ne zai kai shi Jeddah ba, tsaf zai iya fasa zuwa saboda fushin da Riyya ta yi, sun san darajar kansu, suna ƙaunar junansu, suna yiwa juna abinda ɗaya yake so. Mamy ta kalle shi ta ce, "su ma ƴan uwanka basa son zaman ƙasar wajen nan da ka ke yi, balle kuma ni mahaifiyar ka. Duk dani wani lokacin nafi son zaman ka a can ɗin, kafi zama lafiya kana sakewa fiye da zama a nan ɗin." Ya yi shiru bai ce komai ba, dan baza su fahimta ba. Ita Mamy ta san baya son zaman ƙasar gabaɗaya, takura yake yi kuma baya sakewa, shiyasa da aka kawo masa contract ɗin ma ya karɓa kawai, dan baya son abinda zai haɗa shi da zama a nigeria ko kaɗan. In haka akwai ne Abba baya bari ya zauna, amma in aiki yake yi bai cika takura masa akan ya dawo ba. Mamy ta sake kallonsa ta ce, "Banisha tana son zama tare da kai, kaga da kana da aure sai ku je tare ku dawo." Bai ce komai ba dan bai san amsar da zai faɗawa Mamy a wannan maganar ba. Kamar ta fi kowa sanin bashi da aure, kuma bai yi niyar yi a nan kusa ba. Mamy a tausashe ta ce, "meyasa baza ka yi aure ba?." Ya kalli Mamy cike da gajiya da maganar ya ce, "Aure Mamy! Na auri wa?." "Why Ikram?." Ya ɗan buɗe ido cikin mamaki ya ce, "ikram!." "eh ita. Tana sonka, kuma zaka iya aurenta, dan kaf cikin cousins ɗinka babu kamar gidansu Jafar. Suna sonka tsakani da Allah, ba dan wani abu da ka ke daahi ba. Kuma Ikram tana da kirki da hankali, zan yi farin cikin karɓarta as my daugher inlaw." Ya sake kallon Mamy yana girgiza kai ya ce, "i'm not interesting." Mamy ta dafa kafaɗarsa ta ce, "Why? Meye aibu dan ka auri Ikram?." "Mamy a matsayin Riyya nake kallon ta, bazan iya kallonta a matsayin matata ba. Infact duk wata cousin sistera ɗina bazan iya kallonsu a matsayin matan aure ba, ƴan uwa ne kawai. Yadda babu aure tsakanina da Riyya ko Banisha, suma babu. Bazan iya kallon cousin sister as my wife ba." Mamy ta girgiza ta ce, "Haka Jafar ma ya dinga cewa, amma yanzu saura few days bikinsa da Riyya. Zaka iya auren Ikram kaima, kamar yadda zai auri Riyya." Ya girgiza kai ya ce, "shi ya ga zai iya Mamy, amma ni bazan iya ba. Dan zai auri Riyya ba hakan yana nufin zan auri Ikram ba." "Amma ka san Ikram tana sonka ko?." "Na sani, nima ina sonta as my sister, soyayyar da nake yiwa Riyya nake yi mata, ba wacce zan aura ba." Mamy ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Zuwa yanzu ya kamata ace ka yi aure." Ya kalli Mamy ya ce, "ba kin ce zaki zaɓa min mata ba? Na baki dama kawai, ko wacece indai tayi miki nima tayi min, amma ban da cousins." Mamy ta girgiza kai tana ɗan murmushi ta ce, "Ga Ikram nan na faɗa maka, itace zaɓina." "Mamy ban dasu." "To ai gidan nan baza su yarda da zaɓina ba, kuma kakarka ta zaɓa maka matar aure." "Wannan matar tana da mental issue fa, babu wata mata da zan aura daga wajanta Mamy. Ko an aura min sai na warware" ya faɗa yana miƙewa tsaye. Mamy ta miƙe tana dariya ta ce, "Kai da Kakarka, wallahi babu ruwana, baza ka jawo a dinga ce min ni na zuga ka ba." Ya ɗan girgiza kai yana ɗaukar wayarsa ya ce, "matar aure indai ba daga wajan ki ba, bazan karɓa ba.....Zan kwanta Mamy." "Okay Baby. Kwana biyu baka yin azumi litinin da alhamis, meyasa?." Ya ɗan shafa kansa ya ce, "Zan yi, sai na je Jeddah." "Yauwa, bana so ka daina, shine garkuwar da yake kare ka." Ya ɗaga kai ya ce, "In sha Allah" ya faɗa yana fita daga apartment ɗin ta bida sa kallon ƙauna da soyayya. Gab da zai shiga apartment ɗinsa ya hango Salman yana tahowa inda yake, ya tsaya cak duk da wajan akwai rana amma haka ya tsaya yana kallonsa har ya ƙaraso. Yana ƙarasowa Salman ya ce, "Kai na ɗaukowa." Ya faɗa yana miƙa masa roba ta natural tamarind drink. Rehaan ya karɓa yana murmuahi ya ce, "na gode sosai." Shima murmushi ya yi yana kallonsa. Rehaan ya shiga ciki sai ya ga shima ya biyo bayansa. Bai hanasa ba ya bari ya ƙarasa shigowa sannan ya kulle ƙofar. Suna shiga falon aka fata ƙwanƙwasa ƙofar, Rehaan ya dawo da baya ya buɗe ƙofar ya ga Umma ce. Ya ɗan kalle ta a taƙaice ya ce, "ina yini." Umma ta harare sa tana tsaki ta ce, "Sai yau ka san ya na yini?..." ta kalli Salman ta ce, "Salman fito" ta faɗa tana shiga falon tana kallon Salman. Salman ya ƙi kallon ta ya ce, "a nan zan zauna." Ta yi tsaki ta shiga ciki ta riƙo hannunsa ta ce, "ina magana kana daɗa gyara zama, dallah ta so." Salman ya ƙi tasowa ya fizge hannunsa ya yi bayan Rehaan yana neman ya cece sa. Shi kuma ya rasa ya zai yi, sai ya kalli Umman a sanyaye ya ce, "Umma ki bar shi a nan ɗin." Umma ko kulasa bata yi ba sai da ta riƙo hannun ɗanta sannan ta ce, "na bar shi ka cigaba da yi masa kallon mahaukaci ko? Har ka samu damar cewa zaka kai shi asibiti, kai ga mai kuɗi ko...?" Ta ƙarasa faɗa tana hararar sa. Ta kalli Salman ta ce, "Mu je" ta faɗa tana jan hannunsa da ƙarfi suka fita daga falon.Ya yi ajiyar zuciya yana kallonsu har suka fita daga wajan gabaɗaya. Zai kulle ƙofar kenan ya ga kiran Abba yana zuwa wayarsa, ya ɗauka da sallaama, Abba ya amsa ya ce, "ka same ni a falo" daga haka ya kashe wayar. Rehaan ya ɗan yi jim, kafin ya mayar da wayar aljihu yana ji kamar ya yi kuka, dan bai san me Abba zai ce masa ba. Babu yadda ta iya haka ya fito daga falon ya nufi wajan Abba. A falo ya samu Abba da Mama a zaune, ya shiga da sallama suka amsa ya zauna, ya ɗan kalli Mama ya ce, "ina yini." Ta wani kalle sa kallon rainin wayo ta ce, "daman ina so na yi maka magana, wato nuna mana ka ke yi Nadira ce kaɗai babar ka, mu ba iyayenka bane. Kwanan ka nawa baka gidan nan, da ka dawo ba sai ka shiga wajan kowa ka gaishe ta ba? Sai yanzu da ka ganni da Abba shine zaka wani ce ina yini? Gaisuwar ma sai a kan hanya za a yi?." Shi dai ya yi shiru bai ce komai ba, sai Abba ne ya ce, "baka kyauta ba Rehaan." Ya yi ƙasa da kansa bai yi magana ba, dan bai san me zai ce ba. Abba ya ce, "akan maganar matar da Daada ta zaɓa maka ne, na nemi unguwarsu kuma na ji labari akan iyayenta. Abinda ya dakatar dani an ce min mahaifinta yana asibiti bashi da lafiya, shine maganar ta dakata, da yanzu sai dai ka ji an tsayar da lokacin auren." Rehaan ya kalli Abba cikin wani yanayi, Abba ya ɗaga masa kai ya ce, "Ka cigaba da shiri kawai, ku cigaba da shirye-shiryen auren ku kai da Jafar. In kana Jeddah zaka ji labarin an saka ranar aure, kar kace ban faɗa maka ba. Ka fara shirye-shirye dan tare zaku angwance da Jafar......" ya faɗa yana kallonsa kamar yadda shima yake kallon Abban. Another banger🔥😂😂😂 Nana Haleema. [6/23, 11:47 AM] KRBBK: RDB2P15 Nanahaleema. Rehaan ya ɗago yana kallon Abba jin abinda yake faɗa, ransa ya ɓaci sosai, yana ji a ransa ko me zai faru bazai taɓa auren zaɓin Daada ba sai dai ko meye ya faru. Rehaan ya kalli Abba ya ce, "Abba ban santa ba fa." Abba ya ɗaga kai ya ce, "Na san baka santa ba, amma kafin auren ai zaka santa." Rehaan ya ce, "Abba na faɗa maka bana ra'ayin auren nan, meyasa zaka biyewa Daada don Allah?." "Saboda uwata ce Rehaan, dole na biye mata nayi abinda take so." "Wanne irin aure ne wannan? Ban san yarinya ba, itama bata sanni ba, ace za a aura min ita?. Kuma kowa ana basa dama ya kawo wacce yake so amma ni meyasa za a yi min haka?." "Sai haƙuri, hakan za a yi Rehaan." Ya sauke numfashi bai ce komai ba zuciyarsa cike da jin haushi da takaici mai yawa. Mama cike da makirci ta ce, "gaskiya dai Abba a duba lamarin nan, a bashi dama kamar yadda ake bawa ko wannen su dama ya kawo wacce yake so." Rehaan ya kalle ta ya ce, "ki faɗa masa please, bana son auren nan, meyasa ake so dole sai an yi min?." Abba ya ce, "Rehaan gwara ka so auren nan, dan yin sa babu fashi, gwara ka daina ja kawai." Ya ɗan shafa kansa bai ce komai ba, Abba ya ce, "tashi ka je, na san lokacin yin baccin ka ne yanzu. Zamu ƙarasa maganar in ka farka." Ya gyaɗa kai ya miƙe ya fita yana ji kamar yaje ya shaƙe Daada ta mutu kowa ma ya huta, saboda haushinta ko gaishe ta bazai je ba ya yi shigewar sa apartment ɗinsa.        ****** Cikin lokaci kaɗan labarin ganin Islaha ya zaga ko ina, ana ta yi mata addu'ar barka da dawowa da fatan Allah ya kiyaye gaba. Ita kuwa tana gida, tunda Saheer ya rakata ɗaki take baccin gajiya da baccin da ya taru a idonta. Dan ko da Safeera basu yi magana ba, ganin tana jin bacci ya saka ta ƙyale ta. Sai bayan sallar magrib ta farka, ta yi wanka ta yi sallah ta fito falon babu kowa alamun duk basa nan. Tana gab da shiga kitchen Saheer ya shigo da sallama, ta amsa ya bita da kallo ganin kanta babu ɗankwali, gashinta ya sauka har baya, sannan gashin ya yi tudu daga sama, kamar wacce ta hargitsa shi da hannunta. "Da daren nan ki ke yawo haka?." Ta ɗan yi murmushi ta ce, "abinci nake so na ci, sai na kira ka mu je asibiti." Ya bita da kallo kafin ya tako inda take ya ce, "ki je ki saka ɗankwali sai kizo ga abinci na siyo miki." Ta ɗaga kai ta juya ya bi dogon gashinta da kallo, ta sauke numfashi, yana jin shauƙi in ya tuna nan da lokaci kaɗan ba gashinta kaɗai ba, ita kanta nan gaba mallakinsa ce. Ba jimawa ta dawo ta ɗaura ɗankwali ta zauna ya bata pack ɗin abinci, ta karɓa ta ga fried rice ce da chicken, an zuba mata sauce mai albasa sai ƙhamshi take yi. Ta ɗauki disposable spoon ta ɗebi ta fara ci. Yadda bakinta yake moving ɗaukar hankalinsa yake yi, bakinta yana daga cikin abinda yake ɗaukar hankalinsa akan fuskarta. Bata san yana kallon ta ba abinci take ci, sai daga baya ta ɗago suka haɗa ido. Sai yaji kamar ta watsa masa wuta, yadda ta ɗago ɗin ya saka ya ji sabuwar soyayyar ta a zuciyarsa. Islaha ta ce, "Hamma baza ka ci ba?." Ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "na ƙoshi, ke na siyawa." Ta kalle sa ta ce, "ya na ji voice ɗinka ya canja, meya faru?." Ya kalli idonta kafin ya yi murmushi bai ce komai ba. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya ya ce, "ya kika kasance a cikin kwanakin da ki ka ɓace? Wacce irin rayuwa ki ka yi?." Gabanta ya faɗi sosai, ta kalle sa a hankali bayan ta ɗauki ruwa a cikin ledar da ya kawo mata, ta sha sannan ta ce, "kullum sai na yi kuka." Ya ɗaga kai ya ce, "na san zaki yi Islaha.....Ana kiran sallah, zan je na yi sallah, in na dawo sai mu tafi ko?." Ta ɗaga kai ta ce, "to." Bai ce komai ba ya miƙe ya fita, itama bata jima tana cin abincin ba ta miƙe ta shiga ɗaki. Ta jima da gama shiryawa sannan ya yi mata waya ya ce ta zo su tafi, ta fita ta gan shi a mota a zaune ta shiga ta ce, "wannan motar fa Hamma? Na ga bata Hamma Sadik bace." Ya fara jan motar sannan ya ce, "daɗina dake baki da duhun kai, kina da tambaya akan abinda baki sani ba. Indai kika ga canji sai kin yi magana." Ta yi dariya kaɗan, shi kuma ya ce, "sabuwar da Sadik ya siya ce, da ni zan siya to saboda aikin Baffa ya saka nace masa na fasa. Yanzun ma ya ce na riƙe, ni kuma bana son bashi. Daman da ba a samu kuɗin aikin Baffa ba, da ita za a siyar. Daman niyata muyi aure da sabuwar mota, sabuwar amarya, sabon gida, sabuwar mota." Ta ɗan yi murmushi ta ce, "Gaskiya Hamma Sadik yana da kirki wallahi, ya ɗauki matsalar gidanmu kamar na gidansu. Haka sake son aboki na gari." "Na san kema zaki iya yiwa Safeera fiye da abinda ya yi ko?." "Wallahi zan iya." Ya murmusa bai ce komaai ba suka cigaba da tafi. Suna shiga asibitin yana ajjiye motar ta buɗe ta fito tana kallon asibitin da haske ya haskaka ko ina kamar dare ba. Zata shiga ciki kenan wata yarinya ta ƙaraso wajan a guje ta riƙe islaha ta ce, "Lah Mummy ga Islaha, da gaske an ganta ɗin." Islaha ta riƙe yarinya tana murmushi, ta kalli inda take magana da Mumny ɗin, ta ƙaraso ta miƙawa Islaha hannu suka gaisa ta ce, "Wallahi ke ce ɗin kam. Barka da fitowa, Allah ya kiyaye gaba." Islaha ta murmusa, ganin matar bata fi mate ɗinta ba ta ce, "Amin ya rabbi, na gode."  Ta kalli yarinyar ta ce, "ya sunan ki?." "Islam." Kafin ta yi magana babar yarinyar ta ce, "yarinyar fan ɗinki ce sosai, indai ke ki ka gabatar da shiri sai ta kalla har ta haddace roting ɗinki. Da ta samu labarin ɓatan ki kuka ta dinga yi, sai ɗazu da ta ga ance an ganki take ta murna." Islaha ta sake faɗaɗa murmushinta ta riƙe hannun Islam da bata fi six years ba, ta ce, "Allah Sarki Islam, ina sonki nima sosai, kina sona?." Ta ɗaga kai ta ce, "ina sonki Adda Islaha." Islaha ta kalli babar ta ce, "Ku bani number ki ina so mu cigaba da gaisawa da Islam, wata ran zan gayyace ki kizo mu yi show tare. Zaki zo?." Ta ɗaga kai da sauri babarta ta yi dariya ta ce, "daman ta ce kamar ki zata zama." Islaha ta ce, "Ma sha Allah! Ajin ki nawa?." Islam ta ce, "primary 1." Ta yi dariya tana shafa kanta ta ce, "Allah ya taimaka ƙawata." Suka karɓi number juna, Saheer yana tsaye yana kallonsu cikin murmushi. Bayan sun tafi suka nufi ciki tana ɗauko facemask  ɗinta da ta yi guzurinsa, saboda sanyin reception ɗin. Wajan su Mama suka wuce suka tarar da Kawu ya zo saboda aikin da za a yi gobe. Suna ɗakin da Kawu yake zaune ana yi masa bayanin yadda ya kamata ya dakatar da cin abinci ko shan ruwa saboda tiyatar. Dr Isma'il da yake tsaye akan Kawu yana faɗa masa yadda tsarin yake, ganin Islaha ya saka ya yi murmushi ya ce, "Miss Islaha barka da fitowa, na ji daɗin ganinki sosai, Allah ya kiyaye gaba." Ta yi murmushi ta ce, "Amin Dr, na gode sosai." "Ban san kin ɓace ba sai daga baya, ni daman ina ta yi miki kallon sani ashe a gidan tv da social media nake ganin ki." Ta ɗan yi murmushi tana kallon Saheer da ya yi haɗe rai, ta san kuma kishi yake yi dan tana magana dashi. Ta yi murmushi bata ce komai ba sai ta fara gaisawa da matar Kawu. Dr ya ce, "Gobe in Allah ya yarda za a yi aikin, a yi addu'a Allah ya sa a yi a sa a. Ina farin cikin sanar da ku mai asibitin nan gabaɗaya ne da kansa zai yi masa aikin, sai mutane masu sa'a ne suke samun wannan damar. Dan haka ku kwantar da hankalin ku, babu komai a aikin nan sai alkhairi." A tare suka amsa kafin Sadik ya ce, "Mun gode sosai Dr, Allah ya taimaka." "Amin ya rabbi, Allah ya ƙara lafiya. And miss Islaha..." ya faɗa yana kallon ta. Ta ɗan juyo ta kalle sa ya ce, "in kin gama zan iya ganin ki a office?." Ta kalle sa ta ce, "wani abun ne?." Ya ɗaga kai ya ce, "eh." Ta ɗan gyaɗa kai bata yarda ta kalli Saheer ba ta ce, "to in sha Allah." Ya yi murmushi ya fita har lokacin bata kalli Saheer ba. Adda da take tsaye tana shirin tafiya ta yi dariya ta ce, "Da alama likitan nan dai ya gani yana so, kuma bai san matar wani bace. Gashi nan ya haɗe rai kamar bazawarar saniya." Islaha ta yi dariya saɓanin Mama da Labiba da suka haɗe rai basu yi murmushi ba. A lokacin Hanan ta shigo, suna haɗa ido da Saheer sai ta ɗan ji tsoro, amma sai ta dake ta ƙaraso ya bita da kallo ya ce, "daga ina ki ke?." Ta ɗan kalli Mama sannan ta ce, "daga gidan su ƙawata, kuma Mama ma ta san zani." Mama ta yi karaf ta ce, "na sani Saheer, ta faɗa min kafin ta tafi." Ya yi shiru bai ce komai ba, dan bai ga amfanin yi musu faɗa ba tunda suna da goyan baya. Kafin ka ce wani abu Mama zata tare ka ta kare su, shiyasa suke yin abinda suka ga dama, damar hakan suka samu shiyasa. Adda ta kalli Saheer ta ce, "Saheer zo na ganka, daga nan ni zan wuce" ta faɗa tana fita ya bi bayanta. Islaha tana tsaye ta yi ajiyar zuciya, ta lumshe ido tana harɗe hannunta a ƙirji tana tuna abinda ya faru a hannun wanda bata san sunansa ba. Sai kuma ta sauke numfashi tana tuna kuɗinsa da ta ɗauka, gabanta ya faɗi tana ji kamar ta yi kuka in ta tuna sata ta yi masa. Dole ta san abinda zata yi ta biya sa kuɗin nan, ko meye zata aikata indai kuɗinsa zasu dawo ta biya sa. Ko aiki zata nema a ƙarƙashinsa ta yi indai har zata sauke nauyin da ta ɗorawa kanta. Ta sake yin ajiyar zuciya cikin tunani mai yawa haɗe da danasani mara amfani. Ji tayi an ɗan taɓa ta kaɗan, tana juyawa ta ga Saheer ne yana yi mata alama da tunanin me take yi. Ta ɗan girgiza alamun babu komai, ta fita daga ɗakin bata ce masa komai ba, dan tana buƙatar keɓe kanta ta yi tunani akan abinda ya shafe ta. Bata jima a zaune ba Saheer ya zo inda take, ya bita da kallon tuhuma ya ce, "Islaha!." Ta ɗaga kai ta kalle sa ya ce, "Tunanin me ki ke yi haka?." Ta ɗan girgiza kai ta ce, "Babu komai." Ya zauna a gefenta ya ce, "ban yarda dake ba. Kuma gobe bayan an yi aikin su Baffa zamu je wajan ƴan sanda akan case ɗin ki, ban amince a rufe case ɗin nan ba dole a yi bincike. Mun yi magana da officer, har Ummi da iyayenta zasu je." Ta ɗan kalle sa ta ce, "Hamma ni bana so...." Ya ɗaga mata hannu ya ce, "duk dalilin ki aka  rufe case ɗin nan bazan amince dashi ba, in ma tsorata ki suka yi akan kar ki faɗa bincike zai nuna hakan. Sannan waɗanda suka yi waya akan kuɗin fansa suma zasu ci ubansu, dan wallahi babu wanda zan ɗagawa ƙafa a cikinsu." "Hmma wanda ya kama ni fa kamar ya fi ƙarfin hukuma." Saheer ya zuba mata idanunsa yana kallon ta, kallo na tuhuma da son gano wani abu kafin ya ce, "kin san shi ma kenan?." Ta ɗan girgiza kai ta ce, "a'a, kawai yanayin inda aka ajjiye ni ne ya gwada hakan, kuma na faɗa maka ba ɗan ƙasar nan bane." "In ma aljani ne sai na yi shari'a dashi, ban ga wanda zai saka na rufe case ɗin nan ba." Islaha ta yi shiru, ta san halin Hamma indai a kanta ne baya ɗaga ƙafa ko kaɗan, ita ba wai bata so a yi bincike akan wanda ya kamata bane, bata so ayi binciken a binciko ta ɗauki kuɗinsa, babban abin kunya ne a gare ta in aka ji maƙudan kuɗin da ta ɗauko masa, shiyasa duk abinda zai faru bazata yarda a cigaba da case ɗin nan ba, zata san yadda zata lallaɓa Hamma a rufe shi. Kuɗinsa da ta ɗauko kuma duk inda zata nemo zata shiga ta nemo, ko meye zata aikata indai zata samu kuɗin, dan zuciyarta tana faɗa mata kawai ta shiga harkar film, in ta samu adadin kuɗin ta biya sa sai ta daina, dan dole ta nemo kuɗi ta biya sa ko ta wanne hali, bazata iya zama da bashi a kanta ba, dole ta saukewa kanta nauyi mai girma da ta ɗaukowa kanta. Ko a ina Islaha zata samu miliyan sha bakwai ta biya Reehaan?....... [6/23, 11:47 AM] KRBBK: RDB2P16 NanaHaleema. Jikinta har rawa yake yi saboda ɓacin rai da mamaki, ta miƙe tsaye tana sake kallon wayarta cikin mamaki da al'ajabi. Ta fita daga abinda take gani, ta kira wata lamba amma wayar a kashe, ta sake kira aka sake tabbatar da hakan. Ta fita ta kira ɗayan aka yi sa a ya ɗauka, yana ɗauka cikin faɗa da tashin hankali ta ce, "ban gane abinda yake faruwa ba, islaha nake gani ance ta bayyana. Waye ya saka ku sake ta?." Daga cikin wayar cikin ko in kula ya ce, "daman mu bamu kamata ba, amfani mu kayi da ɓatan da muka ji ta yi muka ɗan san na katin waya a hannun ki. Amma kafin mu kai ga aikatawa wasu suka riga mu. Mun yi amfani da hakan ne muka samu na kashewa, amma mu bamu ɗauke Islaha ba." Mama ta buɗe baki cike da mamaki da firgicin kalamansa ta ce, "ban gane ba, me ka ke nufi da abinda ka faɗa? Daman yaudara ta ku ke yi kenan?." "Ba yaudara ba ce aiki ne, daman ai sace ta ki ke so ayi kuma wasu suka riga mu, ba shikenan sun hutar damu ba?. Daman burin ki a ɗauke ta, kafin mu kai ga ɗauke ta ɗin wasu suka riga mu, ba shikenan duk mun huta ba?." Ta dafe kai cikin takaici da baƙin ciki ta ce, "yanzu duk kuɗin da na dinga tura muku daman baku ne ku ka sace yarinyar nan ba?. Ni zaku yaudara, ni zaku yiwa wulaƙanci da tozarci ko?." "Ai na faɗa miki gaskiya ban rufe ki ba, amfani muka yi da ɓatanta muka ce miki mun sace ta. Amma mu ko ganinta ma bamu yi ba. Ni ban ma santa ba wallahi, a tv kaɗai nake ganinta." "Tabɗijam! Ni zaku yaudara? Ni za ku saka na dinga tura mu ku kuɗi a banza ba tare da kun yi min aikin komai ba?. Kun san wacece ni, kun san me kunka ɗaukowa kan ku?." "Kawai ki yi haƙuri ki basar, kuɗi kam sun zo kenan. Ko sama da ƙasa zata haɗe baza mu dawo dasu ba wallahi, gwara ma ki rufawa kan ki asiri a bar maganar." "Wallahi baku isa ba, dole ku dawo min da kuɗina, tunda baku yi aikin da na saka ku ba. Baku isa ku ci min kuɗina a banza da wofi ba." "Batun dawowar kuɗin ki babu, sai dai a tara wani lokacin amma ba yanzu ba. Dan wallahi baza mu bada kuɗin nan ba, in kuma ki ka matsa akan sai mun bayar za a yi taɓare." "Wallahi sai kun bayar, in ba haka ba zan nuna muku bani da mutumci, nima ƴar tasha ce. Abu mai sauƙi ne a wajena na saka ƴan sanda su kama ku." Ya yi dariyar shaƙiyanci ya ce, "to ki saka a kamu mu ɗin mana, in aka kama mu sai muga damu dake su waye zasu fi shan wahala a wajen ƴan sanda, tsakanin mu dake wa za a tura gidan yari. Aikin sace yarinya ki ka saka mu, kin ga kece babbar mai laifi ba mu ba. Kuma ke kin san ba ki isa mu rufa miki asiri ba, sai kowa ya san aikin sace yarinya ki ka saka samu." Ta yi shiru ta rasa abinda zata ce, ta rasa abinda zata furta wanda zai yi daidai da abinda suka faɗa mata, dan sun ɗaure mata baki. Ya ce, "kawai ki basar a cigaba da harka, zamu cafke a wani lokacin. Amma wannan dai sun zo kenan, kawai ki bar zancen." Kafin ta yi magana ya kashe wayar, tabi wayar da kallo cikin wani irin yanayi na damuwa da tashin hankali. Ta ajjiye wayar ta kama ƙugu ta ce, "Dani suka baga wasa ba tare sa na sani ba? Meyasa ban nemi ganin Islaha ba tun farko? Yanzu gashi sun ci kuɗina a banza a wofi, ina nan na saki jiki tana hannun mu ashe haukan banza nake yi." Sai ta dafe kai cikin ƙunar rai, dan an kwance mata lissafi ya farko, an dawo da ita farko, sun warware mata tufkar da ta jima tana yi. Ganin wanda yake yi mata waya ya sakata dafe kanta gabanta yana faɗuwa, a bayyane ta ce, "me zan faɗa masa ne? Me zan ce masa?." Kiran ya katse bata ɗauka ba, wani ya sake shigowa, ta haƙura ta ɗauka kafin ta yi magana ya ce, "ya haka? Yarinyar nan nake gani fa, ya muka yi dake?. Sai da nace ki bar komai a hannuna ki ka ce zaki iya, gashi kin kasa yin komai." Cikin damuwa da sanyin murya ta ce, "Wallahi Allah yaudara ta yaran na suka yi, ashe basu ne suka ɗauke Islaha ba." "Waye ya ɗauke ta kenan?." "Wallahi ban sani ba, kawai amfani suka yi da sace ɗin da aka yi suka ce min sune suka sace ta. Suka dinga karɓar kuɗi a hannuna, suka dinga sakawa ina basu kuɗi ace ƙarya suke yi." "Amma ya aka yi hakan ta faru? Waye ya sace ta ɗin?." "Wallahi ban sani ba, hakan ya nuna min akwai wasu a ƙasa bayan mu."' "Yanzu meye abin yi?." "Zan san duk abinda zan yi in Allah ya yarda." "Ki tabbbatar kin yi abinda ya kamata, kin san halin yarinyar nan, in baza ki iya ba ki faɗa min ni nayi maganinta. Wallahi Allah in na ɗaura ɗammarar yaƙi da yarinyar nan bazata kwana da rai ba." "In sha Allah zan yi ƙoƙari ranka ya daɗe" bai ce komai ba ya kashe wayar. Ta cillar da wayar a kan kujera ta ce, "kai Islaha! Kina bani ciwon kai wallahi, ko wanne tsautsayi ne ya saka aka karɓe ki a gidan nan oho. Ya Allah ka kawo min mafita, ka fitar dani daga ruɗanin da nake ciki."        •••••• Da wuri suka je asibiti saboda aikin Baffa, suna tsaye aka shiga da Baffa da Kawu theater room, su kuma suna tsaye suna yi musu fatan fitowa lafiy. Islaha ta zauna akan kujera tare da yin shiru abubuwa da yawa suna nuƙurƙusar zuciyarta. Mafarkin da tayi a daren jiya ne yake dawowa cikin kanta, ta lumshe ido ta tallafe haɓa ta yi shiru tana tunani kala-kala. Saheer da Sadik duk suna lura da canjinta, suna kula da yadda take keɓe kanta ta yi shiru tayi tagumi. Ko ka je kana yi mata magana bata ji ba saboda tayi nisa a cikin tunani. Adda ta zauna kusa da ita ta ce, "Islaha lafiya dai ko?." Ta kalli Adda tana ƙaƙalo murmushi ta ce, "Lafiya lau Adda." "Amma ki ke tunani?." "Ina tuna a inda na kasance kwanakin da suka wuce." "Allah ya isan ki, Allah ya shiga tsakanin ki da waɗannan mutane." Ta amsa da amin ta yi shiru bata cewa komai. Tana ɗaga ido suka haɗa ido da Saheer, sai ta ɗauke kai ta miƙe a sanyaye ta bar wajan tana tafiya a hankali dan bata so ya takura mata da tambaya. Saheer ya kalli Sadik bayan ta ɓace daga wajen ya ce, "bata faɗa maka komai akan ɓatan nan nata ba? Ni zuciyata tana faɗa min akwai wani abun da ba daidai ba, kamar akwai abinda take ɓoye mana bata so mu san dashi." Sadik ya kalle sa yama ɗan taɓe baki ya ce, "kamar me ka ke gani?." Saheer ya kalli inda ta bi, ya kalli Sadik sannan ya ce, "meyasa bata so a cigaba da case ɗin nan? Meyasa ta ƙi bada wata alama da za a gane masu hannu a sace ta?. Na san halin Islaha, tana da wayo da saurin riƙe abu komai ƙanƙantarsa, amma ace ta kasa riƙe wani abu ko yaya ne da zai zamar mana shaida akansu?. Sannan meyasa jikinta yake a sanyaye kamar wacce aka yiwa wani abun?. Kana kallo tunda ta zauna take tunani, meye ya faru a can da bata so mu sani?." Sadik ya ce, "kai ma baka sani ba, ni ta ya zan sani Saheer? Wannan amsar ai tana wajan ka." Saheer ya yi shiru kafin ya ce, "akwai abinda yake ba daidai ba, akwai abinda take ɓoye mana bata so mu san dashi." Sadik bai ce komai ba, a ransa yana ayyana dan ma baka ga maƙudan kuɗin da ta dawo dasu bane, na tabbata da kaima zaka ɗarsa wani abun a ran ka. Tabbas yana zargin Islaha akan kuɗin nan, dan ya san bata da hanyar da zata samu dala ɗari balle rafar dala, ya yi shiru da maganar ne saboda ta roƙesa akan kar ya faɗa, amma da sai ta faɗa masa inda ta samu. Kuma roƙon nasa da ta yi akan kar ya faɗa ya sake saka masa zargi, dan gaskiya shi zargi yake ta bada kanta a bata wannan kuɗin. Amma kuma sai ya tuna wanne ɗan wahala ne zai bata wannan kuɗin dan ta bashi kanta? A lokaci ɗaya dai bazata samu ba, sai an ɗan saba. Islaha tana barin wajen elevator ta hau ta yi nisa da floor ɗin theater da suke, yana buɗewa ta fita ta tsaya ta jingina da bango cikin rashin sanin abinda ya kamata ta yi a lokacin. Kuɗin nan da ta ɗauko yana damunta sosai, ta yi danasani yafi cikin kwando, sai dai danasanin bata da amfani, tunda ta riga ta aikata. Danasani akan abinda ya riga ya wuce ɓata lokaci ne. Tana so ta yi focusing akan abinda zai faru a gaba,  amma ta rasa abinda ya kamata ace ta yi. Ta sauke numfashi tana cire facemask ɗinta, ta lumshe ido tana tuna hanyar da ya kamata ta bi wajan ganin ta samo kuɗin nan ta biya shi. Dan gaskiya sai ta biya, baza ta zauna da bashi a kanta ba, mutuwa ake yi ko yaushe, in ta mutu da wannan kuɗi ta cewa Allah me?. Bashi da yake hana kwanciyar kabari, haka kawai ta jawowa kanta bala'in lahira bayan wanda ta bari a duniya?. Bata san adadin lokacin da ta kwashe a haka ba, tana zaune ta jingina ta rufe ido ba tare da ta san tunanin me take yi ba. Maganar da taji a nesa da ita ya saka ta buɗe idanunta, ta ga likitoci a zagaye da wani farin mutum ya saka black ɗin suit ya juya baya yana magana. Yadda suka mayar da hankali suka ba sa attension ɗinsu zai baka tabbacin ba ƙaramin girmama sa suke yi, yadda suka nutsu kowa yana magana da girmamawa zaka san ba ƙaramin mutum bane. Islaha mamaki take yi ganin yadda duk suka nutsu, ta ɗan taɓe baki amma still kllon wajan take yi. A hankali ya juyo yana yiwa na gefen ta magana, a lokacin taga gefen fuskarsa sanye da blue ɗin facemask da farin glasses a fuskarsa, kafin ya waiwayo gabaɗaya kuma ya yi gaba sun binsa a baya kamar jela. Ta taɓe baki ta sake rufe idonta, sai kuma ta buɗe da sauri tana shaƙar ƙhamshin turaren da ya dabaibaye wajan da take. Cike mamaki ta ce, "kai! Wannan ai ƙhamshin turaren wancan baturen da ya sace ni ne." Sai kuma tayi sanyi ta ce, "babu lallai shine kuma ai" ta yi shiru ta gyara zaman ta dan bata san lokacin da zata bar wajen ba. Wayar ta yi ƙara, ta duba ta ga Hamma ne yake kira a karo na babu adadi, ta yi ajiyar zuciya ta ɗauka ta saka a kunneta. Inda take ta faɗa masa, ta kashe wayar ta yi shiru, bata so yazo ya tsare ta tambayoyin abinda yake damunta, kuma gashi baza ta iya ɓoye masa inda take ba shiyasa ta ɗauka. A kan idanunta ya ƙaraso inda take, ya zauna a gefenta ya ce, "an yi tiyata cikin nasara." Ta ɗan yi murmushi ta ce, "Allah ya basu lafiya." "Amin." Ta yi shiru bata ce komai ba shima bai sake magana ba, ta kalle shi suka haɗa ido alamun daman shi kallon ta yake yi. Ya ce, "meye a zuciyar ki ne? Ban yarda da wannan shiru shirun naki ba, duk wanda ya san halin ki in yaga yadda ki ka koma a yanzu ya san kina da damuwa. Meyasa ki ke keɓe kan ki cikin yanayi na damuwa har haka?." Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, ta sunkuyar da kai ta rasa amsar da zata bashi. Sai wasa take yi da hannunta, ta rasa abinda zata faɗa da zata kare kanta a wajensa. Saheer ya ce, "ina jin ki, faɗa min abinda yake damun ki. Kin san duk girman matsala, duk girman damuwa, zan taimaka miki mu yaƙe ta ni da ke. Dan haka faɗa min damuwar ki, kar ki ji komai, ki faɗa min ko meye zan fahimce ki. Wani abu suka yi miki da bakya so mu sani?." Islaha ta yi ajiyar zuciya, tana ji gwara kawai ta faɗa masa, gwara ta faɗa masa abinda ya faru ta huta da nauyin da zuciyarta take yi mata. In ta faɗa masa zata ji sauƙi, zata ji sassaucin abun da yake damunta. Amma kuma ya zai ɗauki maganar? A wanne ɓangare zai ajjiye ta? Zai ɗora ta akan ma'aunin fahimta ko zai kalle ta a akasin haka?. Ta ɗago suka haɗa ido, ta buɗe baki a sanyaye zata yi magana...... Nana Haleema. [6/23, 11:47 AM] KRBBK: RDB2P17 Nana Haleema. Islaha ta ɗauke kai daga kallon sa, ta ɗan sauke kai ƙasa a sanyaye ta ce, "Hamma babu komai fa" ta faɗa tana ɓoye masa dan bata san a yaya zai fahimci maganar ba. Ya yi shiru bai amsa ba yana kallon ta, jin shiru sai ta ɗago suka haɗa ido, ya ɗaga mata gira ya ce, "Ba dani ki ke ba ko?." "Da kai nake mana Hamma." A'a, da wani Hamman ki ke ba ni ba, dan kin san ni baza ki faɗa min wannan tatsuniyar ba ko?." Ta shagwaɓe fuska ta ce, "Allah babu komai, kawai ina tuna abinda ya faru a lokacin da bana nan ne." Ya zuba mata ido ya ce, "faɗa min me ya faru?." "Ina tuna a inda aka ajjiye ni, da baturen da ya sace ni, da yadda ya dinga..." sai ta yi shiru bata ƙarasa ba. Saheer ya ce, "ya dinga mene? Ina jin ki, ƙarasa." "Yadda ya dinga sakawa a kawo min abinci, shine abin yake ɗaure min kai. Na rasa dalilinsa na sace ni." "Iya abinda ya dinga yi miki kenan?." "Eh shikenan." Ya zuba mata ido yana kallo, dan shi zuciyarsa faɗa masa take yi ko dai sun yi raping ɗinta ne shiyasa take a sanyaye? Dan yawanci waɗanda aka sace da wahala su dawo ba a yi musu wani abu ba, sai waɗanda Allah ya kiyaye. Ya ce, "akwai abinda ki ke ɓoye min wanda bakya so na sani. Amma babu komai, tunda an fito daga tiyatar ki tashi mu tafi wajan ƴan sanda a cigaba da bincike." Ta kalle sa taga ya haɗe rai alamun babu wasa, ta buɗe baki zata yi magana, ya dakatar da ita ya ce, "kar ki ce min komai, ki tashi muje kawai, dan ba za a rufe maganar nan ba na faɗa miki." Bata iya musu da Hammanta, ta yi shiru tana turo baki gaba dan ita kam babu abinda zata ce wallahi, sai ranar da ta biyasa kuɗin da aro daga nan sai ta san abinda zata yi a akai. Saheer miƙe tsaye  yana kallon ta ya ce, "tashi muje." Ba yadda ta iya haka ta bi bayansa jikinta a sanyaye. Yana tsaye ya jingina da bango yana duba file ɗin hannunsa, ya ɗaga ido ya kalli tv da take nuna masa masu shige da fice a asibitin na ko ina. Ya ɗauke ido yana tuna wacce ya gani a zaune lokacin da suna magana tayi daidai da mara kunyar yarinyar nan da ya ɗauke, kamar wanda aka bawa umarni ya saka remote ya buɗe inda take zaune, ya zuba mata ido yana ya sake tabbatarwa da ita ɗin ce. Ya taɓe baki a bayyane ya ce, "shine mahaifinta" ya faɗa yana sake kallon file ɗin hannunsa, yana kuma karanta sunan Baffa a zahiri. Ya ɗaga kai ya sake kallon ta, a lokacin da Saheer ya zauna kusa da ita, ya ɗauke kai ya ajjiye file ɗin ya zauna a akan kujera a lokacin kiran Jazy ya shigo wayarsa. Kamar bazai ɗauka ba, sai kuma ya ɗauka ya saka a speaker ya ajjiye wayar a kusa dashi. Jazy ya ce, "kai wai me ka mayar dani ne? Ɗan aikin ka ko a ƙarƙashin ka nake aiki kana biyana albashi?. Dan ma ina taimaka maka ina yi maka abubuwa da baka san sai ka dinga raina min wayo, har ni na kira ka ƙi ɗauka sai yanzu da ka ga dama zaka amsa kirana?. Yaronka ne ni ko ɗan aikinka?." Rehaan ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "Jazy kana da matsala." Sai ya sake harzuƙa Jafar ya ce, "ni ne ma kai, in ina da matsala kai meye da kai?. Tun safe nake kiran ka a waya, yanzu na tabbatar azahar ta yi a inda ka ke, amma dan ka raina ni sai yanzu zaka ɗauka?." Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba, Jafar ya ce, "na samu labarin ka sallami yarinyar nan, wallahi ina gargaɗin ka akan kar ka sake ɗaukar wata yarinya ka kai gidan ka, in ba haka ba wallahi sai na faɗawa kowa na gidanku. Tunda kai naga har yanzu baka yi hankali ba, baka san ya kamata ba." Ya lumshe ido ya buɗe, ya ɗaga ido ya sake kallon screen ɗin daidai lokacin da Saheer ya miƙe tsaye yana riƙo hannunta. Ya jingina da kujera yana kallonsu kamar ya samu wani film a hankali ya ce, "kaine ka haife ni da ka ke yi faɗa min haka? Kar ka manta, na girme ka." "Ban haife ka ba, amma na isa da kai. In aure ka ke so daman kakar ka ta ce zata yi maka aure ai, wataƙila ma alamomin iskanci ta gani a tare da kai ya saka ta yanke wannan hukuncin a kanka. In ba ɗan iska ba, waye yake ajjiye mace a gidansa? Allah kaɗai ya san me ka yi mata. Banza kawai." Murmushi ya yi ya shafa fuskarsa yana kallon screen ɗin gabansa har lokacin da suka bar wajan, ya ɗan yi ajiyar zuciya ya ce, "Ka saka maids ɗin Al Hamra su gyara min apartment? Da safe zan shiga Jeddah." Jazy ya ja tsaki ya ce, "da yake ga ɗan aikinka ko? Ni zan saka maids su gyara maka apartment dan zaka je ko?. Kar ka je, don Allah ka zauna indai har sai na yi magana dasu." Rehaan ya ce, "kashe wayar sai na tura a gyara min, ka cika ni da maganar banza,  gabaɗaya baka da amfani." "Kai ka sani kuma. Sannan ka faɗawa budurwar ka, ta daina zuwa inda nake, wallahi zan saka a kamata. Ni ba ɗan iska bane, kai ka san ni ba irin ka bane." "Ni shine Jazy." "Har sai ka maimaita? Duk wanda ya kai mace gidansa har ta kwana biyu ai ɗan iska ne." Rehaan bai ce komai ba ya yanke wayar, yana ganin kiran Alma yana shigowa ta snapchat amma bai duba ba. Ya rasa meyasa Alma ta fi tasiri a wajansa in yana England, da zarar ya dawo Nigeria shikenan sai ya dinga mantawa da labarinta. In yana can sai yaji a ransa zai iya aurenta ya zauna da ita. Ya taɓe baki kafin ya ɗauki waya ya kira wanda zai kira, ya miƙe a hankali ya sauka ya fita daga asibitin gabaɗaya. Islaha kamar yadda Saheer ya ce wajan ƴan sandan suka nufa, da ita dashi da Sadik dashi. Tana zaune a bayan mota ta yi shiru, shi kuma shida Sadik suna gaba suna tafiya. Safeera ce ta kira ta a waya, ta ɗauka suka yi magana kafin ta ce, "Hamma Sadik zamu ɗauki Safeera a hanya." Ya amsa suka cigaba da tafiya har suka je inda take, ta shiga motar suka nufi police station ɗin gabanta yana tsannanta bugawa, dan bata san amsar da zata bayar wacce zata gamsar da Hamma ba. A can suka samu Ummi da danginta, aka zauna ana tattauanwa akan batun case ɗin sace ta. Islaha ta ce, "babu hannun Ummi a sace ɗin da aka yi." Dpo ya kalli Ummi ya ce, "Wannan case ɗin dai na yanzu, kin bar cikinsa. Amma kina cikin duk wanda zai iya afkuwa nan gaba, dan ko ciwon kai Islaha ta yi zamu nemo ki." Saherr ya ce, "ni ban gamsu da wannan maganar ba, ina so a yi mata tsakani da Islaha, ko ciwon kai Islaha tayi wallahi sai na ɗaure Ummi. Domin ta furta kalmar sai ta ga bayanta a gaban shaida, kuma ta amsa da bakinta ta ce ta san ta aikata." Dpo ya ce, "ba ina nufin rufe case ɗin Ummi ba, ina magana akan case ɗin sace Islaha babu hannunta a ciki. Tunda ga Islaha a zaune ta tabbatar mana da Ummi bata da hannu a ciki." Ya kalli mahaifin Ummu ya ce, "Alhaji wannan case ɗin babu ita a ciki, amma kamar yadda Saheer ya faɗa ko cuwon kai Islaha tayi da saka hannun Ummu a ciki. Domin kalmar da ta faɗa ba ƙaramar kalma bace, tun kwanaki na faɗa maka wannan kalmar zata iya sakawa a ɗaure ta a gidan yari, ita ake kira da baki shi ke yanka wuya." Mahaifinta ya ce, "na sani, na kuma san duk abinda ka faɗa gaskiya. Na gode da karamcin ka sosai." Dpo ya ce, "yanzu hukuma ta shiga tsakanin wannan kalma da Ummi ta faɗa, muna tsakiya akan kalaminta, dan haka ko yaushe in wani abu ya samu Islaha za a wayi gari Ummi tana wajan nan mun riƙe ta." Ummi tace, "wallahi bazan sake aikata komai ba, bazan yi mata komai ba." "Hajiya Ummi wannan daga baya ne, kin ɗaure kan ki da kalaman ki. A yanzu dai babu ke a case ɗin, amma nan gaba zaki iya shigowa. Alhaji zaku iya tafiya.." Godiya ya yi musu sannan suka yi sallama suka fita. Ya juyo ya kalli Islaha ya ce, "malama Islaha na dawo kanki. Ki bamu bayanai da abubuwan da za ki iya tunawa, wanda zasu bamu makama akan nemo waɗannan mugaye mutane." Ta ɗan sauke numfashi tana jin idon Hamma a kanta yana yawo, ta ɗago ta kalle sa a sanyaye ta ce, "bazan iya tuna komai ba, abu ɗaya na sani, shi ba bahaushe bane, kuma lokacin da aka ɗauke ni rufe min ido suka yi ban san ta inda muka bi ba." "Na faɗa miki indai za ki iya faɗa mana kammaninsa, zamu iya sakawa a zana mana shi." "Ko yaushe yana saka facemask bazan bambamce ba gaskiya" ta samu kanta da yin ƙarya dan ta ɓoye gaskiya. "Lambar mota, katin shaida, lambar gida babu abinda za ki iya tunawa?." Ta ɗaga kai alamun eh. Ya sauke numfashi ya kalli Saheer ya ce, "baza mu iya yin komai a case ɗin nan ba, indai bata faɗa mana wata makama ko hujja da zamu yi bincike a kai ba. A lokacin da motar ta ɗauke ta, cctv asibitin Rehaan Yola ta yanke, sannan mai napep ɗin da ya ce mana yaga lokacin da aka ɗauke ta, shima ya ce bai ga lambar mota ba, itama kuma sun rufe mata fuska bata ga inda aka ajjiye ta ba. Babu hoto ko wani abu da zai taimaka mana mu binciko abiinda muke son bincikowa." Islaha ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "mai napep! Kuna nufin yazo nan?." Dpo ya kalle ta ya ce, "kin gan shi ne?." Ta ɗaga kai ta ce, "lokacin da nake a tsorace akan hanyar, yazo zai wuce sai na tare shi, har muka yi ciniki zan shiga ya kai ni gida, sai zuciya ta bata amince dashi ba, domin ya saka facemask da baƙin glasses bana gane yanayinsa. Sai nace yaje na fasa hawa, sai naga ya fito ya biyo ni, nayi sauri na gudu, ya kamo ni yana buɗe wata kwalba da take a hannunsa, wacce ya riƙe ta da baƙin abu." "Ban san meye a cikin kwalbar ba, amma yana ƙoƙarin watsa min a fuskata. Yana gama buɗewa sai naji an jani da ƙarfi cikin mota, daga nan ban sake buɗe ido ba sai a wannan gida." Dpo ya zuba mata ido har ta gama ya ce, "shima mai napep ɗin ya yi nufin cutar dake kenan?." "Ƙwarai kuwa, duk da ban san meye a cikin kwalbar ba, amma tabbas abin cutarwa." Saheer cikin tashin hankali ya ce, "meye za a yi ƙoƙarin zuba mata? Meye a cikim kwalbar?." Dpo ya ce, "probably acid ne, hydrocloric acid!. Babu abinda za a yi ƙoƙarin zuba mata a fuska in ba shi ba." Ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ta dafe ƙirji tana buɗe cikin firgici ta ce, "Acid!." Sadik ya ce, "Sai a nemo Muslim ya nemo mana shi, daman tare suka zo." Ya ɗaga kai kafin ya ɗauki waya ya kira, ba jimawa wani ya shigo yana sara masa. Ya ce, "a je gidan tv toron giwa azo min da Muslim." Ya amsa ya fita. Dpo ya ce, "Mai keke napep, waɗanda suka sace ki, Ummi, waɗanda suka yi waya suna neman kuɗin fansa. Mutane huɗu suna cikin case ɗin nan, kuma ko wanne a cikin su abin zargi ne. Musamman mai keke napep, zuciyata bata amince dashi ba ko kaɗan. Su kuma waɗanda suka yi waya amfani suka yi da ɓacewar ki dan su samu kuɗi. Amma su waye suka ɗauke ki? Da zamu san su bincken zai zo mana da sauƙi" Ya faɗa yana zuba mata ido yana karantar yanayinta. Islaha ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, bata so ta yi wani motsi da zai saka ya zargi bata da gaskiya. Saheer ya ce, "Officer ni ina ganin ko sun tsorata ne shiyasa ta ƙi magana? Duk da na san Islaha bata da tsoro, amma yanayin abinda bata saba gani ba zai sakawa ta ji tsoron yin magana. Na santa da wayo, kuma tana riƙe abu komai ƙanƙantarsa, amma a wannan gaɓar tace bata riƙe komai ba." Officer ya ɗaga kai ya ce, "Islaha ke da ƙawar ki kuje ku jira mu daga waje." Ta miƙe a sanyaye ita da Safeera, har zata fita daga office ɗin sai ta juyo ta kalle su, a hankali da sanyin murya ta ce, "A nemo mai napep ya faɗi waɗanda suka saka ya zuba min acid, sannan a nemo waɗanda suka kira waya suna neman kuɗin fansa ta. Amma batun waɗanda suka sace ni don Allah a bar maganar, a rufe case ɗin, wallahi bana so a dinga tayar da maganar ko kaɗan. Ni aka sace, kuma nace bana so a yi bincike, kawai a bar maganar tunda na dawo lafiya" tana gama faɗa ta buɗe ta fita ita da Safeera. Safeera ta ƙarasa inda ta zauna, itama ta zauna ta ce, "Islaha meyesa ki ke so a rufe case ɗin nan? Kina ganin anyi ƙoƙarin zuba miki acid fa." Ta sauke numfashi zata yi magana sai ta fasa, ta riƙe hannun Safeera suka fita daga harabar station ɗin gabaɗaya, suka tsaya a jikin motar Sadik da take waje.  Islaha ta ɗan yi tsaki tana kalle-kalle ta ce, "ban gamsu da wajan nan ba, ki jira mu koma gida zan faɗa miki wani abu, amma..." Sai ta fasa faɗa ganin Hamma da Sadik sun fito, gabanta ya yanke ya faɗi ganin harara da banzan kallon da Hamma yake binta dashi. Ta san baya fushi da ita, kafin ya yi fushi da ita za a jima sosai, ko da itace babu gaskiya yana sharewa ya cigaba da rarrashin ta. Amma in ya yi fushin sai ta gwammaci duk kwanakin baya da yake sharewa ya yi fushin ta huta, dan in ya ɗaura ɗammarar fushi baya ji baya gani. Daga ganin yadda yake hararar ta ta san ransa a ɓace yake sosai, kuma sai dai ya yi haƙuri, dan baza ta faɗa masa ba gaskiya. Nana Haleema. [6/24, 11:32 AM] KRBBK: RDB2P18 Nana Haleema Tunda suka tafi babu wanda yake magana a cikinsu, ta san ran Hamma ya ɓaci sosai, shiyasa tayi shiru kawai bata ce komai ba, ta zubawa window ido ƙirjinta yana bugawa da ƙarfi saboda fargabar haɗuwa da Hamma. Bata san me zata ce masa ba, kuma tasan bazai yarda da dalilinta va Ƙarar da wayar ta ta tu ya saka ta kalli wayar, ganin sunan Zainab ne sai ta ɗauka, daga can ɓangaren Zainab ta ce, "Adda Islaha yaushe ki ka dawo? Shine baki neme ni ba, na damu da rashin ki, kullum sai na yi kuka." Ta yi murmushi ta ce, "ki yi haƙuri Zainab. Ya ki ke?." "Lafiya lau Adda. Allah ya tsare gaba ya cigaba da kiyaye ki." "Amin Zainab. Ina Hafsa?." "Adda ina son magana dake da gaggawa." Islaha ta ce, "kina ina yanzu?." "Ina gida, amma zan fito gobe sai mu haɗu." Islsha ta ce, "shikenan sai kin zo." Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar tana sauke numfashi mai nauyi. Sadik yana tsayar da motar Saheer ya fita daga ciki cikin ɓacin rai. Sadik ya kalli Islaha ya ce, "Islaha na kasa gane miki, sai abubuwa ki ke yi wanda bamu san shi dake ba. Yanzu da Saheer ya san labarin maƙudan kuɗin da na gani a wajan ki me zai yi zargi don Allah?." Ta sauke numfashi a sanyaye ta ce, "ka rufa wannan asirin don Allah, na faɗa maka ni ban aikata komai ba wallahi. Ban yi abinda ku ke zargi ba, ban yi abinda zuciyar ka take zato ba. Ka bar maganar tsakanin mu, da kaina zan faɗa masa in sha Allah" ta faɗa tana buɗe motar ta fita Safeera ma ta bi bayanta. Suna shiga gidan Saheer ya fito, kafin ta ƙarasa ciku shi ya ƙaraso, suka tsaya a compound ɗin gidan ya ce, "faɗa min dalilin ki na so a kulle case ɗin nan Islaha, faɗa min abinda ya saka kika ce a bar maganar, har ki ke cewa bakya so ki ji ana maganar case ɗin. Ina jinki." Yadda ya yi maganar sai da gabanta ya faɗi sosai, magana yake cikin fushi da ɓacin rai. Ba haka suka saba magana ba, sai ta ji hakan baƙo har ya haifar mata da faɗuwar gaba. Ta buɗe baki zata yi magana ya ce, "wallahi in baki bani hujja mai ƙarfi ba zan iya marin ki, In kin san baki da hujja ki yi min shiru kawai." Islaha ta buɗe baki cike da mamaki tana kallonsa, yau Hamma ne yake cewa zai mare ta? Lallai ta ɓata masa rai matuƙa. Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Ya gyaɗa kai yana kallon ta ya ce, "da haɗin bakin ki aka ɗauke ki kenan ko?." Ta girgiza kai ta ce, "a'a." "Faɗa min su waye." "Na faɗa maka wallahi ban san su ba." "Shikenan Islaha, ki yi yadda ki ke so" ya faɗa yana fita daga gidan a fusace. Ta zauna a wajan cikin damuwa mai yawa, Safeera ta ce, "tashi mu shiga ciki, lokacin sallah ya yi." Bata musa ba suka shiga ciki, gidan babu kowa suka shiga ɗakin Islaha suka yi sallah. Bayan sun idar safeera ta ce, "Nima kin neman jefa zuciya ta a cikin zargi, wanne kuɗi aka gani a hannun ki, sannan meyasa bakya so a yi bincike akan case ɗin nan?." Ta kalli Safeera ta ce, "Safeera wanda ya sace ni babban mutum ne, duk da ba yaren mu bane, amma kina ganinsa kin san yana da kuɗi sosai. Gidan da aka ajjiye ni ban taɓa ganin gida kamar sa ba, komai na gidan na daban ne da wanda ban saba gani. Ga masu tsaron sa a gidan da yawa, hakan ya tabbatar min da baza mu iya case dashi." Safeera ta yi dariya tana girgiza kai ta ce, "hakan da ki ka faɗa ya sake saka min zargin wani abu a zuciyata. Kin manta kece mai iƙirarin ko wa waye zaki iya shari'a dashi indai akan gaskiyar ki? Ko kin manta kece wacce kuɗi ko matsayi baya baki tsoro?." Islaha tayi ajiyar zuciya tana kallon ta ta ce, "Zan faɗa miki komai, amma don Allah kar ki faɗawa kowa." Safeera ta ce, "ina jin ki." "Kuɗi na ɗauko masa Safeera, kuɗi masu yawa na na ɗauko a gidan har rafar dala ɗari." Safeera ta ce, "kamar ya kin ɗauko masa kuɗi? Shi wa ki ka ɗaukarwa kuɗin?." "Shi wanda ban san shi ɗin ba mana. Na faɗa miki a inda na san shi, shine wanda ki ka tarar ina yiwa masifa a car park ɗin asibitin da Baffa yake a kwance, kafin haɗuwar mu a asibiti mun taɓa haɗuwa dashi a diamond hotel, lokacin da muka je ganin Mr Rehaan." "Ni fa ban gane me ki ke nufi ba" "Shi ɗin da nake faɗa miki, shine ya saka aka ɗauke ni." "dan kawai kun haɗu sau biyu saɓani ya shiga tsakanin ku sai ya ɗauke ki?." "Haka ne wallahi. Haƙuri yake so na basa ni kuma ba ƙi, dan ban ga laifin da na yi masa da zai bani haƙuri ba. A lokacin da yace a dawo dani gida sai naga kuɗin, kawai sai aikin Baffa yazo raina, na fara tunanin ko an samu kuɗin aikin ko ba a samu ba. Kuma sai na yi mafarki, aka nuna min rashin kuɗin aikin ya saka Baffa ya rasu....." Ta yi shiru tana ajiyar zuciya, ta rufe ido ta buɗe ta ce, "shine na ɗauko rafa ɗaya na biya kuɗin aikin Baffa. Amma wallahi ba da niyar sata na ɗauko masa kuɗi ba, ara nayi, kuma zan nemo kuɗin a duk inda zan nemo na biya sa in sha Allah." Safeera ta zuba mata ido cike da mamaki ta ce, "ki biya wa?." "Shi baturen mana." "A ina zaki gansa keda baki san sunansa ba?." Islsha ta yi shiru bata ce komai ba. Ganin kallon ban yarda dake ba da Safeera take yi mata, sai ta rikice ta ce, "Wallahil azim da gaske nake, iya abinda ya faru kenaan Safeera." Safeera sai a lokacin ta gamsu, dan ta san baza ta taɓa yi mata rantsuwa akan ƙarya ba. Safeera ta ce, "ke meye ya kai ki aikata sata? In akwai cctv a gidan ya gano ki fa? In ya saka aka yaɗa ki a duniya fa? Ko kuma ya saka kama ki da laifin sata, laifin waye?." "Wallahi Allah ba da niyar sata na ɗauka ba, da niyar aro ne, kuma ni ban san haka kuɗin suke da yawa ba, nayi tunanin basu kai yawan haka ba. Kuma sai da na ɗauko na dinga danasani." "Rafar dala ɗari ki ka ce, faɗa min a gidan da zaki samo kuɗin nan, kuɗin da sun kai miliyan goma? A ina za ki samo su?." "Miliyan sha bakwai ne Safeera." "Faɗa mina gidan da za ki samo waɗannan kuɗin Islaha." Islaha ta yi shiru bata ce komai ba tana tunanin mafita, dan ita kanta bata san a inda zata same su ba. Safeera ta ce, "tunda baki da hanyar su sata ki ka yi masa. Ke ko kina da hanyar da zaki biya shi wallahi sata ki ka aikata, ba wani rance, tunda ba shi ne ya baki da kansa ba, baki tambaye shi ba ki ka ɗauka. Kawai kin gani ya ajjiye, ke kuma ki ka ɗauka, kinga kenan satar masa kuɗi ki ka yi." "Kuma yadda ki ke faɗar bature ne zai iya sakawa a kama ki, wannan laifin zai shafe wanda ya yi miki, domin ke baki da hujjar shine ya sace ki, amma shi na san bazai rasa cctv da ta ɗauke ki a lokacin ba. Da yawan gidajen masu kuɗin nan akwai cctv a falon su, in hakan ta kasance wannd abin kunya ki ka ɗauko mana?." Gaban Islaha ya faɗi, ta shiga tuna lokacin da ta kalli camera ta yi magana, hakan yana nufin an ɗauke ta kenan. Islaha ta rikice, ta girgiza kai tana ɓoyewa Safeera gaskiyar akwai camera a falon ta ce, in sha Allah babu camera Safeera, in Allah ya yarda bai gani ba......" "Na shiga uku! Safeera a ina zan samu kuɗin nan na biya shi? Wallahi ko meye zan aikata indai zan biya shi kuɗin nan. In na mutu ban biya shi bashin nan ba ya kenan?." "Ni mamaki ma ki ke bani, ina jinjina ƙarfin halin ki wallahi. Ke da aka sace, har kina da damar ɗauko kuɗi? Yaushe ki ka koyi ki gani ki ɗauka Islaha?." "Ni dai tsoro nake ji." "Da ba ki yi wannan tunanin ba ki ka ɗauko masa kuɗin?." "Wallahi Baffa ne a raina, kuma na yi nadama wallahi." "Sata sunan ta sata, kin gani kin ɗauka sata ce ba rance ba. Faɗa min ta hanyar da zaki biya shi kuɗin sa." Islaha ta yi shiru, cikin sanyin jiki ta ce, "ina jin na canja wajan aiki kawai, zan nemi inda a kwanaki kaɗan zan haɗa masa kuɗinsa na nemi duk inda zan gan shi na mayar masa." "Ai indai ba turai za ki koma da aiki ba, babu inda zaki samu waɗannan kuɗin a kwanaki kaɗan. Ki faɗi abinda zai yu, ba wannan maganar ba." Ta ɗan yi shiru tana nazari, ta rufe ido ta buɗe kafin ta ce, "film zan shiga." Safeera ta harare ta cike da takaicin maganar ta, Islaha ta ce, "in na shiga film zan iya haɗa kuɗin na biya shi, daga nan sai na daina." Safeera ta bita da kallon up and down ta ce, "Islaha anya ƙalau ki ke?." "Lafiya ta lau wallahi." "To an faɗa miki ana shiga film ɗin ake samun kuɗi? Ko su ƴan film ɗin sai sun yi haƙuri da juriya sannan suke samun ribar abun, ba da an shiga ake tara kuɗi mai yawa ba, sai kin yi aiki da jikin ki sannan za ki samu." Islaha ta dafe kai ta rasa abinda yake yi mata daɗi, kawai ta fara hawaye ta ce, "Safeera ban san ya zan yi ba, ban san me zan yi na samu kuɗin nan na biya shi ba. Saboda wannan dalilin bana so a yi bincike akan case ɗin nan, saboda haka bana so a ɗaga maganar, dan na san dole maganar kuɗin nan ta fito. Da wanne ido zan kalli Hamma in ta bayyana na yi aron kuɗi masu yawan wannan? Da wanne ido za a cigaba da kallona a gidan nan?." Safeera ta riƙe hannunta ta ce, "dan kuskure kin yi kuskure babba Islaha, sai dai a kiyaye gaba a yi ƙoƙarin gyarawa. Kuma duk waɗanan hanyoyin da ki ke faɗa babu wacce zata baki kuɗi lokaci guda wallahi, dole sai kin yi a hankali, kin ƙara da haƙuri. Baki da wata mafitar da za ki samu wannan kuɗin indai ba sassan jikin ki zaki siyar ba. Ni a shawara ta, kawai ki neme shi ki ba shi haƙuri ya yafe miki, sannan ki bar case ɗin sace ki da ya yi ya wuce, shima ya rufe miki asirin satar da ki ka yi masa." "Ni fa ba sata na yi ba, aro na yi." "Wallahi sata ki ka yi, ki daina faɗar wannan maganar hajiya. Sata ce mai lasisi." "Ni ba sata nayi ba, bashi ne kuma kowa yana ci." "Sai ki yi ai, in zaki haƙura ki yarda kin sata ki haƙura, ki neme shi ki bashi haƙuri a wuce wajen. Kin ga jefi tsuntsun biyu da dutse ɗaya, kin biya kuɗin aikin Baffa, kuma kin sauke nauyin da yake kan ki." "Ni yanzu a ina zan ganshi?." "da ki ka ɗauko masa kuɗin har ki ke zancen biya, a ian zaki ganshi ki bashi?." Ta girgiza kai ta ce, "Safeera, ɗan rainin hankali fa, gaskiya ni bazan taɓa basa haƙuri ba." Safeera ta bita da kallon mamaki ta ce, "a wannan gaɓar tsiwa ko masifa babu abinda zata amfana miki danasani, gwara ki yiwa kan ki faɗa, ki nema shi ku sasanta akan hakan." "Bazan ba shi haƙuri ba, zan dai neme ko aiki ne nayi a ƙarƙashinsa." "In ya ƙi fa?." "Zan san hanyar da zan bi ganin na nemo kuɗin da zan biya shi, ko meye zan yi." Safeera ta ce, "ki daina cewa ko meye zaki yi fa islaha, in kina faɗar hakan wani zai ɗauka kamar zaki fara bin maza ne dan ki biya bashi." Ta ɗago jajayen idonta ta kalle ta, Safeera ta ce, "yes, gwara ki kwantar da hankalin ki ki daina wannan maganar, ki yi addu'a Allah ya warware wannan chakwakiyar.." "Amma nima a yanzu bana goyan bayan bincike akan case ɗin na, tunda lamarin ba daga inda muke tunani ya zo ba, ba daga wajan cutarwa ya zo ba, kinga da sauƙi. Ko ni bazan so a yiwa sunan ki tambari da Islaha ɓarauniyar dala ba." Islaha ta sake fashewa da kuka cikin takaici da ƙunar zuciya, danasani da raɗaɗi. Tabbas sai ta biya sa kuɗin sa, duk hanyar da zata bi zata bi dan ganin ta biya bashin nan, baza ta bar bashi akanta ba. Safeera ta yi dariya ta ce, "To meye na kukan? Ko kin ƙi, ko kin so, sunan ki Islaha ɓaraumiyar dala." Islaha ta sake fashewa da kukan takaici, Safeera ta yi dariya sosai ta ce, "Kar ki damu, komai zai wuce. Daman ance masu kuɗin nan da daloli suke yawo, yanzu an daina riƙe naira sai daloli." Islaha bata ce komai ba saboda takaici, tunanin ta ɗaya a ina zata samu kuɗinsa ta biya shi? Dan gaskiya baza ta bar bashi a kanta ba, dole ta sauke nauyin da ya hau kanta. Har dare suna tare da Safeera, a lokacin Mama da Labiba da Hanan suka dawo gida. Islaha da suke cikin ɗaki suka fito suka yi mata sannu da zuwa, Mama ta amsa tana faɗin, "Asibiti kamar na kafurai, wai ba a zama jinya ma'aikatan ne suke jinyar mara lafiya." Islaha da Safeera suka koma ɗaki basu tanka ba. Sai da suka shiga sannan Safeera ta ce, "Asibitin Mr Ray ɗin nan akwai abin mamaki, komai irin na turawa yake yi. Kin san asibitin turawa ne ba a ajjiye mai jinya, nurses ne suke jinyar marasa lafiya." Ita dai Islaha bata ce komai ba tana zaune ta yi shiru. Ba Mr Ray ne a gabanta ba, kuɗin wanda bata sani ba shine a gabanta. Safeera ta girgiza kai ta ce, "yaushe zaki dawo aiki?." A sanyaye ta ce, "Gobe in Allah ya yarda." "Na jira ki kenan?." "Eh, zan zo mu tafi." "Allah ya kaimu. Ni zan wuce." Islaha ta miƙe ta rako ta har bakin gate jikinta a sanyaye. Safeera zata yi magana Hamma ya shiga gidan, bai ce musu komai ba ya wuce ya shiga ciki. Islaha ta bi sa da kallo har ya wuce, sannan ta kalli Safeera ta ce, "fushi yake yi Safeera, ban san me zan faɗa masa ba." Safeera ta ce, "ki bashi haƙuri kawai." "Bazai haƙura cikin sauƙi ba wallahi, sai yaji dalilina, kuma kin san bazan faɗa ba." "Ki gwada." Ta sauke numfashi sannan ta ce, "ki gaida Umma." Safeera ta ɗaga kai ta fita daga gidan ita kuma ta koma ciki a sanyaye. Da ta koma abinci ta tarar suna ci, bata ce komai ba ta wuce ciki ta zauna ta zabga tagumi, ta rasa abinda yake yi mata daɗi. Har lokacin bata yarda sata tayi masa ba, ita aro ta ɗauka. Dole ta bisa kuɗinsa, dan ta san nauyin bashi akan mutane. Nana Haleema. [6/24, 11:32 AM] KRBBK: RDB2P19 Nana Haleema. Rehaan yana tsaye sun gama sallama da Abba ya shiga wajan Mamy, ya tsaya yana jiran fitowarta dan bazai shiga ɗaki ba, in ya shiga zama zai yi. A lokacin ta fito ta bi shi da kallo ta ce, "Baby sai Jeddah?." Ya ɗaga kai ya ce, "in sha Allah Mamy." Mamy ta yi murmuahi ta ce, "Allah ya kiyaye hanya." "Amin Mamy. Ina suke?." Kafin Mamy ta ba shi amsa ƙannensa suka fito, suka ƙaraso wajansa ya riƙe hannun Banisha ya ce, "i promise zan turo a ɗauke ki, ki zo ki yi one week ki dawo." Ta yi murmushi ta ce, "Okay, Safe trip my love." Ya yi pecking goshinta ya ce, "thank you my love." Ya kalli Riyya da ta sunkuyar da kai ya ce, "are you Okay?." Mamy ta ce, "wai tayi maka milk cincin ne, tana tsoron kar ta baka ka sake cin poison." Ya ɗan murmusa ya ce, "com'on Riyya, kawo min kawai." Ta juya a sanyaye ta kawo masa, ya buɗe ya ɗauki ɗaya ya ci sannan ya ce, "ki kai wa Shams ki ce ya saka min a cikin box." Ta karɓa ya ce, "thank you Riyya." "Zamu yi kewar ka." "Nima zan yi kewar ku." Ya ƙarasa ya rungume Mamy ya ce, "Mamy sai na dawo." Ta shafa kansa ta ce, "Allah ya kiyaye min kai Babyn Mamy, Allah ya baka nasara a duk inda ka ke." "Amin Mamy" ya faɗa yana raba kansa da ita ya fito zuwa inda motarsa take. A lokacin Mamy ta ce, "ka yiwa sauran iyayen ka sallama ne?." Ya ɗan yi shiru alamun bai yi ba, Mamy ta ce, "bai kamata ba, ka je ka yi musu sallama." Ya ɗaga kai ya riƙe hannun Banisha, Riyya tana bayansa suka nufi bangaren Mama. Ita da babban ɗanta suka same ta, sai Sameer da Janna da suke zaune. Ya shiga da sallama suka amsa, ya ƙarasa ya ce, "Mama zan tafi Jeddah." Ba yabo ba fallasa ta ce, "a dawo lafiya." Ya ɗaga kai ta kalli babban yayyansu ya ce, "Sai anjima Hamma." Ya kalle sa ya ce, "Allah ya kiyaye Rehaan." "Amin." Ya kalli Sameer da ya wani haɗe rai kamar bai san shi ba, sai bai ce masa komai ba ya kalli Janan da ta haɗe rai ta kawar da kai. Ya san fushi take yi dan bata san zai yi tafiya ba, ya ɗan saki fuska kaɗan ya ce, "Little Jan zan tafi?." Sai a lokacin ta kalle sa, kafin ta yi magana ya ce, "i'm sorry, zo mu je mota." Bata musa ba ta miƙe suka fita tare. Mama ta buga ƙwafa tana gyaɗa kai ta ce, "ayi dai mu gani." Ɓangaren Umma suka shiga suka tarar tana gyarawa Salman farcensa. Yana ganin Rehaan ya zabura zai gudu, ta buga masa tsawa ta ce, "koma ka zauna malam, uban ka ne shi da ka ke rawar jiki in ka gan shi?." Rehaan shi kansa sai da ya tsorata da tsawar da ta yi, bai ce komai ba ya yi mata sallama ya fita zuwa wajan amarya Abba.  Bai jima a wajan ta ba ya dawo ya shiga wajan Daada, Allah ya taimake sa ya samu bacci take yu. A bakin mota suka yi sallama da ƙannensa ya shiga mota suka nufi airport. Motarsa tana fita, wani da yake tsaye a estate ɗin gidan ya ɗauki waya ya ce, "Motar Rehaan ta fito, kun tabbatar an kwance burkin motar?." Ya yi shiru alamun ana basa amsa sannan ya ce, "Dakyau, bana so ransa ko lafiya sa ta tsira a wannan lokaci, a tabbatar da ya rasa ɗaya daga cikin waɗannan." Ya kashe wayar ya yi shiru yana kallon indai motar Rehaan ta bi. In ba mutuwa Rehaan ya yi hankalin sa bazai taɓa kwanciya ba.     Rehaan basu yi nisa ba ya ji an tsayar da motar, ya buɗe ido ya ce, "ya dai?." Shams da yake gaban motar ya ce, "Sir burkin naji yana rawa, shiyasa aka samu aka tsaya a nan.." "Kamar ya kenan?." "Bamu san ya aka yi hakan ya faru ba, amma yanzu zan yi waya a kawo mota." "Alright" ya faɗa a hankali yana lunshe idonsa. Ba jimawa aka kawo wata motar, suka canja mota suka wuce airport tsaye. Washe gari da safe Islaha da wuri ta shirya dan tana so taje wajan aiki, bayan ta shirya tana falo ta gama shan tea Saheer ya shigo da sallama. Islaha ta amsa sallamar tana kallonsa, sannan ta ce, "ina kwana Hamma." Saheer daƙyar ya ce, "Lafiya. Ina Mama?." "Bata fito ba." "In ta fito ki faɗa mata na tafi wajan Baffa." "To. Amma wajen aiki zan tafi, nima babu lallai mu haɗu." "Okay" ya furta yana ya fita. Haka ta gama abinda zata yi a sanyaye, ta fito tana kallon ƙofar gidan cikin tunani. Motar da suka shiga jiya ta gani, bata ƙarasa wajan motar ba, sai da ta kira Safeera take faɗa mata ita ta wuce. Horn ta ji yana yi mata, ta kalli wajan kafin ta ƙarasa a hankali dan ta san shine ta buɗe ta shiga suka tafi. Ta kalle sa taga ya haɗe rai kamar ba Hammanta mai yawan murmushi ba, ko kallon inda take ba yayi balle ta saka ran zai yi mata magana. "Kina fama da kanki ki ka saka wannan turaren mai ƙarfi, kin kyauta."  Ta kalle sa jin abinda ya ce sai ta yi shiru bata ce komai ba. Sai da suka tsaya Islaha ta kalle shi taga glass ɗin gabansa yake kallo alamun ta fita babu abinda zai ce mata. Islaha a sanyaye ta ce, "Hamma!." Ya yi mata banza kamar bai ji ba, cikin shagwaɓa ta ce, "Hamma ka yi haƙuri, ka daina fushi dani don Allah." Tsaki taji ya yi bai ce komai ba, ta sake kallonsa ta ce, "Hamma don Allah." Ya kalle ta ya ce, "bani da mahimmanci a rayuwarki ne kawai, dan haka ki fita ki bani waje." "ka yi haƙuri" ta faɗa hawaye yana sakko mata. Bata son fushin Hamma ko kaɗan, matuƙar ya yi fushi da ita to tabbas ta ɓata masa rai da yawa, baya iya fushi da ita sai abin ya ƙure sosai. Jin tana kuka sai ya sauke ajiyar zuciya, ya ɗan tausasa murya ya ce, "in baki faɗa min dalilin ki na son a kashe case ɗin nan ba bazan saurare ki ba, Islaha." Ta goge hawayenta bata ce komai ba, ya kalle ta ya ce, "za ki jefa min zargi a zuciyata, zan ga kamar da gagan ki ka gudu daman ba sace ki aka yi ba. Shaiɗan yana faɗa min abubuwa marasa kyau akan hakan, na ƙi bada damar da zan ɗarsa zargina a kan ki, amma in ki ka cigaba da ɓoye ɓoyen nan zan zarge ki Islaha!." "Wallahi Hamma ban san komai a kai ba, ban san shi ba balle na haɗa baki dashi ya sace ni, kuma ni ban aikata komai ba." "Nima ban ce kin aikata wani abu ba, amma in kika cigaba da ɓoye ɓoyen nan zuciyata zata amince kin yi, ko meye ya ɗarsu a raina zan amince kin aikata!." "Hamma!." "Islaha." "Hammana!." "Islahaaa!" Ya faɗa yana jan sunan yana kallonta. Ta girgiza kai tana langwaɓar da kai, cikin sanyi ta ce, "Hammana!." Ya zuba mata ido na wani lokaci kafin ya ce, "Matar Hamma." Ta lumshe ido hawaye yana cigaba da zuba daga idonta. Ta buɗe ido ta kalle shi ta ga shima ita yake kallo, ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ka bani dukkan yardar ka, wallahi bazan taɓa cin amanar ka ba." Ya taɓe baki yace, "kina san dawo a dawo bara bana kenan, indai baki faɗa min dalilin ki ba bazan karɓa. Zuciyata zata faɗa min akwai wani abu mara kyau da ki ke ɓoyewa." "Ina da dalili." "Am all ears." "Ka yi min alƙawari zaka saurare ni." "Ina jin ki." "Zan faɗa maka dalilina, amma ka bani kwana biyu don Allah." Ya zuba mata idanu yana kallonta cikin mamaki, da gaske zuciyarsa ta fara ɗarsa masa abubuwa marasa kyau, da ya yi tunanin raping ɗinta suka yi, amma yadda take ɓoyewa sai ya ga ba lamarin rape bane, abin ya girmi haka a tunaninsa. Saheer zai yi magana ta tare shi da sauri ta ce, "don Allah ka yi min wannan alfarmar." Ya ɗaga kai ya ce, "Allah ya kaimu. Jeki wajan aikinki." Ta ƙi fita, sai da ta tabbatar ya daina fushin sannan ta shiga. Tun daga gate take gaisawa da mutane har ciki, haka aka cika table ɗinta ana gaisawa tana murmushi tana amsa gaisuwa da addu'a. Bayan mutanen sun watse Safeera da Muslim suks ƙaraso wajan ta, Muslim ya ce, "Islaha ashe mai keken nan ƙoƙarin watsa miki acid ya yi?." Ta ɗaga kai alamun eh, Muslim ya ce, "amma bashi da kirki, nan yazo ya same ni fa ya ce yaga lokacin da aka sace ki, yana so ya ba da shaida ashe shima mugu ne." Safeera ta ce, "mugun gaske ma kam." "Kuma wallahi ya gudu, an nemesa an rasa." Ita dai bata ce komai ba sai kiran Zainab da ya shigo wayar ta, ta ɗauka take sanar da ita su haɗu a asibiti dan fita zata yi bata da aiki. Bata jima sosai ba suka fita ita da Safeera zuwa asibiti wajan Baffa. A can suka tarar da Umman Safeera ita da Mama suna tattaunawa akan abinda ya shafe su. Suka gaisa da Islaha daga nan suka wuce wajan Baffa dan ance sun farka. Da suka shiga Baffa idonsa biyu amma yana cikin raɗaɗi, dan a lokacin yankan yake yi masa ciwo sosai, kana ganinsa ka san yana cikin yanayi na zafi da ciwo. Dan haka basu jima a ciki ba, suka koma wajan Kawu suka tarar yana bacci. Kiran Safeera aka yi a waya ta tsaya tana amsawa, ita kuma ta koma wajan su Umma da Mama. Daga can gefe ta hangosu a tsaye Umma tana miƙawa Mama wata baƙar leda, sai ta matsa kusa dasu dan ta ji me za a ce, bata sani ba ko akan tafiyar Umma ne, tana so ta ji dan ta sanar da Safeera su yiwa tufkar hanci. Umma ta ce, "fasko ne kamar yadda ki ka ce, gashi nan nayi komai, visa za a buga min na tafi." Mama ta karɓa ta ce, "kin tabbatar zaki iya? Kar sai na yi asarar kuɗi an yi visa da ticket ki ce baza ki je ba." "Mai zai hana ni zuwa? Wallahi zuwa babu fashi sai dai in bani da rai." Mama ta saka a aljihun doguwar roga ta ce, "tunda akwai gidan aikin a ƙasa ko yaushe za a iya cewa ki fito. Visa ba wahala take yi yanzu ba, dan haka ki zama cikin shiri. Na karanta miki tsarin ko?." "Na haddace tsaf a kaina." "Kar a same ki da saɓa wani abun. Gidan aikin ki duk wata a kuɗin najeria naira rubu ɗari biyar za a baki. Ɗari uku ta kamfani ɗari biyu naki." "na amince da wannan." Mama ta girgiza kai ta ce, "tare zaku tafi da Labiba, yadda Babanta yake kwance a nan tsaf zata je ta samo mana abin arzuƙi. Itama ta yi komai, lokaci kawai ake jira." Umma ta ce, "godiya mu ke woman leader." "Ko kefa, yanzu ki ka fito a mace, da kun zauna namiji yana sarrafa ku bayan ba wata tsiyar ku ke samu ba a wajensa ba?. Ƙarshen cika bakin namiji fa saki ne, to sai meye dan ya sake ki? Mtsww! A kan ki aka fara saki ko a kan ki za a gama?." Mama hango ƙawarta na ƙarasowa, sai ta kalli Umma ta ce, "Jeki kawai Maimuna, za mu yi magana kawai." Umma ta fita a lokacin ta ƙaraso wajan. Tana zuwa ta ce, "komai ya kankama kenan ko?." Mama ta ce, "an sanu biyu, Labiba da babar Safeera." "Na taɓa ki da alkhairi, an kuma samun wani gidan a Jeddah. Albashinsa har ya fi na gidan da Labiba zata je wallahi. Dan a wata ɗaya miliyan ɗaya da rabi zasu bayar, ban da alkhairin yau da kullum." Mama ta zaro ido ta ce, "wayyo Allah, anya bani zan shirya mu tafi ba?." Ta girgiza kai ta ce, "yarinya suke nema, mai jin turanci, mara ƙiba, mai son aiki. In zai yu a samu  mai kyau, ƴar gayu dan basa son ƙazama." Mama cike da zumuɗi ta ce, "a ina zamu samu wacce zamu tura musu?." "Hanan baza ta je ba?." "Bana tunanin Hanan zata je, dan tana samu a nan sosai. Baza su tafi su biyu ba, saboda babansu." "Kin ga da ƴar rikon nan ta ki zata yarda itace daidai da abinda aka lissafa, yadda take da shegen iyayin nan da wuri zata yi saurin shiga." Mama ta taɓe baki ta ce, "kar ma ki ɓata min rai, mu koma ciki mu cigaba da magana." Islaha ganin suna tahowa tayi saurin komwa baya, ta yi shiru tana lisssafi a zuciyar ta. Miliyan ɗaya da rabi za a bayar duk wata, hakan yana nufin zata iya tara kuɗin wanda ta aro a ƙasa da shekara ɗaya. Ta yi ajiyar zuciya tana tunani, ta ɗan sauke numfashi cikin tunanin abinda ya kamata ta yi, dan gaskiya sai ta biya kuɗin nan hankalin ta zai kwanta. Ya kamata ta yi tunanin da ya kamata, indai zata samu kuɗi ta sauke nauyin bashi ko meye zata yi. Dafata ta ji anyi daga baya, ta juya a firgice tana kallon wanda yake tsaye a bayan ta..... [6/25, 11:14 AM] KRBBK: RDB2P20 Nana Haleema Tana juyawa suka haɗa ido da Zainab, Islaha ta ɗan sauke numfashi cikin tsoro ta ce, "kin bani tsoro Zainab." Zainab ta bita da kallo, kafin ta rungume ta cikin kewar ta ta ce, "na yi kewar rashin ki sosai Adda Islaha, na yi kewar ki." Islaha ta riƙe hannunta tana murmushi ta ce, "nima na yi kewar ki Zainab. Ya na ganki haka, akwai matsala ne?." Zainab ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "Adda Islaha Mama ce ta saka a sace ki, na ji da kunnena tana waya tana cewa a tabbatar an ɗauke ki." Islaha ta ja hannunta suka zauna a inda babu jama'a sosai, ta kalle ta cikin nutsuwa ta ce, "ban gane ba, yi min bayani yadda ya kamata." Zainab ta ce, "Ina nufin Mama ce ta saka a sace ki, saboda kina saka mata ido akan abubuwan da take aikatawa." Islaha ta yi shiru tana tunani cikin ruɗani, kenan mutanen da suka sako ta a gaba suna da yawa, tunda ga wata maganar ma ta sake ɓullowa daga inda bata yi tunani ba. Bata nunawa Zainab firgici akan haka ba sai ta ce, "faɗa min damuwar ki Zainab." Zainab ta sauke nunfashi ta ce, "Zaman gidan ya yi min zafi Adda, na gaji da zaman gidan wallahi. Abubuwan da ban yi zato ba suna ta faruwa, na kasa tsallake wasu abubuwan." "Me ya faru?." "Adda gabaɗaya kowa na gidan da kowa na gidan canjawa yake yi, ma'aikatan gidan Mama ta siye su, kowa a ƙarƙashin ta yake, shiyasa ba a taɓa jin ɓarnar da take cikinsa a bakin kowa ba. Da zarar maganar kuɗi ta shiga shikenan sai a canja.." "Akwai wata mata da ta takurawa Mama akan a kaini gidanta, kullum sai an takura min da maganar matar. Wai in na je za a canja min makaranta, za a yi kaza da kaza. Ni na gaji, da kin yi aure gidanki zan dawo da zama kawai, gabaɗaya zaman gidan ya fita daga raina." Islaha ta ɗan yi shiru sannan ta sauke numfashi ta ce, "in aka kai ki gidan me zaki yi a can?." "Nima ban sani ba, amma kamar ba abin arzuƙi zan aikata ba, dan matar kwata-kwata bata kwantan min a raina ba." Ta girgiza kai ta ce, "kina ji, ki kwantar da hankali ki, babu abinda zai same ki sai alkhairi. Ina tare dake a ko yaushe a ko ina. Ki nutsu ki ji abinda zan faɗa miki." Zainab ta ɗaga kai Islaha ta ce, "kar kuɗi ko wani abu ya ruɗe ki kamar Hafsa, ki cigaba da bijirewa, duk abinda za a ce miki kae ki yarda, ki nuna kw bakya ra'ayi. In aka takura ki amince ki je gidan, da zarar an tafi kai ki ki yi min waya ki faɗa min inda aka kai ki. Ni kuma a wannan lokacin zan haɗa hujja da nake son haɗawa akan su Mama da ma'aikatan gidan, in abin nan ya tabbata wallahi sai na yaɗa ta a ko ina, sai gwamnati ta san abinda take aikatawa da sunan riƙe marayu." Zainab ta share hawaye ta ce, "in na bisu babu matsala?." "Babu komai, Amma kafin ki tafin ki tabbatar kin sanar dani, yadda zan shirya komai na biyo sawun ki." "Zan yi duk abinda ki ka ce Adda." "Yauwa Zainab. Allah yana tare dake, bazai taɓa bari ki wulaƙanta ba in sha Allah." "Allah yasa." "Amin." "Adda kayana duk sun yi min kaɗan, bani da kayan sakawa sosai." Islaaha ta dafa ta, tasan yadda ake ƙarancin kaya a gidan marayu, ta san yadda kayan sakawa suke yankewa, ta san yadda yaran da basu kai matakin sana'a ba suke rasa kayan sakawa. Wani lokacin sai masu ziyara sun zo sun kawo kaya, a nan ne za a zaɓi wanda bashi da kayan sosai a bashi ya rage ko ya ƙara. Ita kanta ta shiga irin wannan yanayin, har ta kai ta kawo tana cire kaya ta wanke da daddare ta shanya,washe gari ta kuma mayarwa jikinta. _(Ƴan uwa ga wanda Allah ya bawa dama, in an haɗa kayan sakawa na bayarwa, a dinga tunawa da yaran da suka tashi a gidan marayu. Kayan yara ko na manya, na maza ko na mata, a dinga taimkawa ba a san inda za a dace ba. Allah ya sa mu dace amin.)_ Islaha ta ce, "Akwai kayan da zan baki, sannan akwai kuɗin da zan tura miki, ki shiga kasuwa ki siyi ƙananun atamfofi ki bayar a gidan a ɗinka miki. Ba su Kamila suna ɗinki ba?." "Suna yi Adda." "To ki bayar a ɗinka miki, nawa da zan baki ki basu su rage miki. Zan tambayi Safeera ma in tana dasu ta sake haɗo miki, indai ina da rai babu abinda zaki nema ki rasa Zainab." Ta yi murmushi ta ce, "Allah ya bar min ke Adda Islaha, Allah ya baki miji na gari, mai kuɗi wanda zai ɗauke ni na koma gidansa." Ta yi murmushi ta ce, "Amin Zeey. Ina auren Hamma zan ɗauko ki, kin gama zaman gidan nan in sha Allah." Zainab ta yi murmushi, suka cigaba da hirar gidan, har Zainab ta yi mata sallama ta tafi. Bayan tafiyar Zainab Islaha ta yi shiru tana tunani, abubuwa uku suna yi mata yawo a cikin kanta, abubuwa uku suna kai kawo a tsakiyar ƙwaƙwalƙwar ta. Zainab, Mama da ta da ta saka a sace ta, uwa uba kuɗin mutumin da ta ɗauko, dan ya fi komai ɗaga mata hankali a halin da ake ciki. Ta yi ajiyar zuciya cikin nauyin ƙirji, a lokacin Safeera ta ƙaraso ta zauna, suka ɗan cigaba da hira duk da hankalin Islaha baya tare da ita ko kaɗan, wani abun daban take tunani. •••••• *JEDDAH, SAUDI ARBIA* *AL HAMRA, CORNICHE RESIDENCES.* Unguwa ce mai kyau da tsari, unguwa ce mai ɗaukar hankali tun daga kallon farko zaka san ko a cikin ƙasar saudia ba ƙananun mutane ne suke zaune a cikin ta ba. Unguwa ce mai cike da tsafta, da tsaro na musamman. Ko ina na kan titin unguwar al hamra cike yake da cameras saboda tsaro, unguwa ce da take kusaa da ƙaton tekun Corniches, babban ocean da yake ɗaya daga cikin manya manyan ruwan da ake ji dasu a garin Jeddah. Unguwa ce da take ɗauke da gidaje masu kamar hotel, wanɗanda ake yi musu laƙabi da hotel style. To ko wanne ɓangare unguwar Hamra ta yi. Rehaan yana tsaye daga cikin apartment ɗinsa, yana tsaye a bedroom ɗinsa ya yaye labule yana kallon ƙaton ocean ɗin da ya mamaye bayan ɗakinsa. Hannunsa riƙe da mug yana shan tea a nutse, hannunsa ɗaya yana cikin aljihun wandonsa yana kallon yadda mutane suke hutawa a wajan, suna kai kawo ana shan drink. Ya sauke numfashi yana lumshe idanunsa, haka kawai fuskar Islaha ta zo idanunsa, ya ɗan runtse ido yana cize bakinsa, irin ka tuna abinda baka so ka tuna ɗin nan. Ya yi ƙoƙarin kawar da hotonta daga idanunsa, ya cigaba da shan tea ɗin amma still ita yake gani tana harararsa. Kalamanta ya tuna, sai ya murmusa ya girgiza kai yana taɓe bakinsa. Shi bai taɓa ganin yarinya mara hankali kamar ta ba, da zai san danginta da ya basu shawarar a kai ta asibiti a dubu lafiyar ta, dan tana da matsalar ƙwaƙwalwa. Door bell ɗin da aka danna ya katse masa tunani,ya fito daga ɗakin a nutse, ya sauka downstairs ya ƙaraso ya buɗe ƙofar falon. Ubaid da Maleek ya gani, maƙotansa mafi kusa, wanda gidansu yake kusa da na juna. Apartment ɗin Rehaan shine a tsakiya, sai na Ubaid a ɓangaren dama, sai Maleek a ɓangaren haggu. Ubaid likita ne shima, sun taɓa aiki a asibiti ɗaya shi da Rehaan, ta dalilin haka suka saba dashi. Sun saba da juna sosai, tare suke haɗuwa a buga ball, a ɗan sha tea, a yi hira. Dukkansu larabawa ne, Maleek balaraben Saudiya ne haihuwar Riyad, Ubaid kuma balaraben Egypt ne. Maleek yana da aure, Ubaid kuma bashi da aure. Rehaan da ya buɗe ƙofa ya gansu sai ya yi murmushi yana kallon su kamar yadda suke kallonsa suna murmushi. Cikin turanci harshen Maleek ya ce, "Rehaan barka da zuwa." Gaisawa suka yi, suka shiga falon suka zauna. Rehaan ya zauna shima ya ce, "ya aiki?." "Alhamdu lillah. Baka faɗa mana zaka zo ba, da mun shirya maka abubuwa na musamman." Ya ɗan murmusa ya ce, "na zo aiki ne, bazan jima ba zan koma." Ubaid ya ce, "ina Jafar?." Rehaan ya ce, "Yana Englaand." Maleek ya ce, "kai kaɗai zaka zauna?." Rehaan ya ɗaga musu kai yana ɗan murmushi bai ce komai ba. Sai kuma Rehaan ya ce, "yauwa ina son house maid, ku tura min maid daga wajan ku, zan dinga biyansu in sha Allah." Ubaid ya ce, "Bani da House maid, amma za a kawo min daga Nigeria. Ka san na fi son aiki da yan ƙasar ku, musamman mata." Rehaan ya bisa da harara cikin takaicin wanann ɗabi'a ta Ubaid. Ubaid ya yi dariya ya ce, "da gaske nake, za a kawo min house maid daga can. In sun zo sai mu dinga sharing, is normal." Rehaan ya yi masa banza, dan in akwai abinda yake jin haushi bai wuce matan ƙasar sa da suke barin ƙasarsu su taho aikin gidajen larabawa ba, abin yana yi masa ciwo matuƙa, dan bashi da damar da zai hanawa ne, amma wallahi da sai ya hana ɗan nigeria zuwa Saudia aiki a gidan larabawa. Ƙasa mai girma da daraja kamar Nigeria, amma matan cikin ta sun saka ƙasa suna tuntsurar da mutuncinta. Da ace aiki ne mai tsafta da tsari da sauƙi, to yawancin wannan aikin da shirme da watsewa yake ƙarewa. Duk da ba duka ne ɗaya ba, amma majority haka ce take faruwa. Ya san kalar rayuwar da suke yi a ƙasar, ya san babu abinda larabawa suka raina a yanzu kamar ƴan Nigeria, saboda ƙasƙantar da kansu da suke yi a ƙasar da sunan aikatau. Yana zama cikin larabawa, yana jin yadda suka mayar da matan nigeria kamar toys, wasu matan sune suke kawo musu kansu dan su samu kuɗin abinci. Ya san halin Ubaid sosai, mayen ƴan mata ne lamba ɗaya, duk macen da ta yi aiki a gidansa sai dai Allah ya kyauta kawai, dan yana da kuɗin da yake sakar musu, lokaci ɗaya mata suke rikicewa, su ruɗe duk abinda yake so zasu yi masa shi. Shiyasa har rige rigen kawo masa ƴan mata ake yi daga nigeria. Dan wanda ya kawo ma zai samu, itama in ta bada kanta babu abinda bazai yi ba, baya jin ƙyashin kashewa ƴan mata kuɗi, ƴan matan ma na Nigeria, musamman baƙar fata. In aka ce mace baƙa ce ta shiga uku a wajen Ubaid, ya dinga nacewa mace kenan har sai ta amince masa, dan yana da kyau da kuɗi, da wuri suks faɗawa. Shi kuma Rehaan haushin hakan shiyasa basu cika shiri da Ubaid ba, Maleek ne mai halin kirki, sun fi shiri dashi sosai akan Ubaid. Bai shiga shiga harkar Ubaid ba, dan ya tsani ɗabi'unsa sosai. Maleek ganin yadda Rehaan yake hararar Ubaid sai ya yi dariya ya ce,"Kar ka damu Dr, zan turo maka housemaid daga gidana, duk da nima babu sosai, amma za a kawo. Matsalar suna jin tsoron cheetah da ka ke kiwo ne fa." Ya ɗan yi murmusui yan shafa kansa, sai a lokacin ya tuna bai ma je ya ɗauko ajiyarsa ba, daman Jafar ne yake takura masa akan a ɗauke su, amma shi kam yana son kiwo, musmaman kiwo irin na su Cheetah wanda ba a ko ina ake yin su ba sai a gidajen larabawa. Kiwon damisa ko zaki a manyan gidajen larabawa ba komai bane, sun saba yi sosai. Ya so ya yi a gida Nigeria Abba ya hana, sai da ƙananun abubuwa irinsu ɗawisu. Ya ce, "in anjima zan je na ɗauko ta, kuma baza ta yi musu komai ba. Ƙarama ce sosai, bata cutarwa." Maleek ya ce, "nima tsoron gidan nan naka nake ji indai har suna nan." Ya sake yin dariya kaɗan, kafin ya tashi da niyar kawo musu black tea, sai da ya shiga kitchen ɗin ya yi tsaki, dan shi ya tsani aiki, yafi so komai ayi masa. A kawo masa tea kuma a ɗauke cup ɗin, inda dama a bashi a baki hakan yafi masa daɗi. Ya tsani sai ya dawo daga aiki ya dafa tea, shiyasa yake tsaywa a cafe ya siya,  yana tuƙa mota yana sha. Gabaɗaya ya sangarce, babu abinda ya iya sai dafa tea ɗin kawai, shima daga ruwa sai lipton da sugar, bayan hakan babu abinda ya iya sakawa. Shiyasa ya damu da rashin housemaid ɗin, sai danasani yake da bai taho da chef ba. Yana dafa ruwa a kettle yana tsaki, yana ji ransa yana ɓaci, yana jin dole ma a samu masu aiki, dan shi bazai iya wata wahala ba, daman Jazy ne ya sallame, gashi ya rasa yadda zai yi. A haka ya kawo musu suna sha suna ƴar hira kaɗan kaɗan. Nana Haleema. [6/25, 11:15 AM] KRBBK: RDB2P021 Nana Haleema. Ummi ta bi Muslim da kallo lokacin da ya shiga office ɗinta, bayan ya zauna ta miƙe ta rufe ƙofar ta jingina da ƙofar ta ce, "meye plan na gaba?." Ya bita da kallon mamaki da tsoro ya ce, "kina nufin baki zubar da makamanki ba duk abinda ya faru?." Ta sauke numfashi tare da harɗe hannu a ƙirji ta ce, "Yanzu aka fara wallahi, dan an kama ni an kai ni gaban hukuma ba hakan yana nufin zan ja da baya ba." Muslim ya girgiza kai ya ce, "kina bani tsoro Ummi, har yanzu akwai zargi a kan ki fa" "Sai me?." "Hmmm! Na ɗauka kin yi sanyi ai." "Har abada wallahi, sai na ga bayan Islaha." "Dakyau! Kin san in aka kama mai keken nan akwai damuwa ko?." "Yana ina yanzu haka?." "Na ce ya ɓuya, kar ya sake ya fito inda mutane zasu ganshi, in aka kama sa kema kin san mu ma nun kamu." Ta dafe kai ta ƙaraso ta zauna ta ce, "Ni so nake na ji ka shirya wani abu akan Islaha, so nake na ji ka haɗa gagarumin plan ɗin da zai tarwatsata ita da rayuwarta gabaɗaya." Muslim ya ce, "ɗaukar mataki a kanta ba abu ne mai wahala ba, amma zamu ɗan jinkirta saboda idon mutane da yake kanta a yanzu. Duk wani motsinta an saka hukuma tana bibiya, samun galaba a kanta a wannan lokacin abu ne mai wahalar yuwa. Amma akwai babban shirin da zan yi a kanta, farin jinin da take dashi a duniya nake so na lalata, ta yi baƙi a idanun al'ammu, a daina ganin farin ta ko kaɗan." Ummi ta ce, "da zarar an ga fuskarta a dinga bad comments, sannan a dinga cewa ba a buƙatar fuskarta." "Haka nake so na yi Ummi. Ina so na samu wani abun da zan yi posting wanda zai tarwatsa rayuwar ta gabaɗaya." "Me zai hana baza muyi amfani da AI ba?." "Kusan kowa ya gano AI yanzu, ana gani za a iya fahimtar sa ba tare da dogon nazari ba. Ita da kanta nake da buƙata ta aikata ba AI ba." Ummi ta yi shiru tana tunani kafin ta ce, "to ya za a yi yanzu?." Ya sauke numfashi ya ce, "ni na san abinda ya kamata nayi, tunda acid bai yi aiki ba, wani abun zai yi mana amfani. Ke dai ki zama cikin shiri, ko yaushe zaki iya jin labari akan Islaha." Ta yi dariya ta ce, "ko yaushe a shirye nake, indai akan ganin bayan Islaha ne, na ɗaura ɗammara." Ya yi mata jinjina ya ce, "dakyau mace mai kamar maza, ina zuwa" ya faɗa yana miƙewa ya fita. Ummi ta bi sa da kallo tana girgiza kai cike da mugunta. Dan an kama ta akan Islaha ba hakan yana nufin ta yi sanyi ba, a lokacin ta ɗaura ɗammarar yaƙi da Islaha.          •••••• Bayan kwana biyu. Islaha ta cigaba da harkokin aikinta, dan cikin kwanakin bata samun zama duk wani ɗaukar rahoto ita ce take zuwa, fuskarta ta sake fita musamman a shafukan yaɗa labarai. Ta sake sama cele a idanun al'ammu, ta sake yin farin jini, saboda kyaun fuskar ta da iya aiki da kuma farin cikin da take dashi. Bayan ta tashi daga waje aiki asibiti ta wuce, a nan ta tarar da Saheer da Mama a wajan Baffa da ya fara samun sauƙi. Ta shiga da sallama aka amsa, Baffa ya kalle ta cikin ƙarfin hali ya ce, "Islaha kin dawo?." Ta ɗaga kai ta ce, "na dawo Baffa, ya ƙarfin jikin?." "Alhamdu lillah." "Allah ya ƙara lafiya." "Amin. Allah ya yi miki albarka." "Amin Baffa." Mama ta yi tsaki ta ce, "waɗanda ka haifa kuma Allah ya kwashe musu tasu albarkar kenan ko me?." Baffa dai bai kulata ba dan ta lafiyarsa yake yi ba ta surutan banza ba. Islaha ta ce, "na shiga wajan Kawu yana bacci." Baffa dai kallon ta yake yana murmushi, yana jin alfahari a ransa, yana ji ina ma shine ya haife ta. Adda ta bashi labarin wahalar da tayi a kansa, ta faɗa masa komai da faɗi tashin da ta dinga yi akan nemo kuɗin aikinsa. Ta yi abinda ƴaƴansa na cikinsa basu yi masa ba, ta yi masa abinda bazai taɓa mantawa dashi ba har abada. Islaha bata jima a asibitin ba ta fito ta tsaya a ƙofar ɗakin ba tare da tana yin komai ba, babu jimawa Saheer ya fito yana kallon ta ya ce, "mu tafi gida ko ba yanzu zaki tafi ba?." Ta gyaɗa kai a sanyaye ta ce, "yanzu zan tafi, na gaji sosai." "Sannu" ya furta yana kafe ta da idanunsa. Ta sunkuyar da kai, ta ɗaga kai bata ce komai ba ya yi gaba ta bi bayansa. Suna fara tafiya a motar da ta zama kamar tasa ya ce, "kin ce na baki kwana biyu zaki faɗa min, kwana biyu ta wuce har ina shirin komawa inda na fito, har yanzu baki faɗa min dalilin da ki ka ce zaki faɗa min ba. Wato kin yi min wayo ko? Tunda gashi an bar batun case ɗin gabaɗaya." Ta ɗan dafe kanta ta ce, "Ba wayo nayi maka ba Hamma, zan faɗa maka." "Ina jin ki." "Hamma Saurin me ka ke yi? Na ce zan faɗa maka. Kuma yanzu kaina ciwo yake min wallahi" ta faɗa yana dafe kai tana lumshe idonta dan kar ya sake maganar. Ya yi shiru bai ce komai ba har suka je gida, amma zuciyarsa sai saƙe-saƙe take yi masa akan case ɗin, yana kawarwa ne saboda zargi. Islaha ta fita ta ahiga gida, shi kuma sai ya nemo mata maganin ciwon kai ya bata sannan ya shiga ya kwanta dan shima ya gaji. Da daddare Mama ta dawo, tana zaune a ɗaki ita da Hajiya Karima tana amsa waya Islaha ta shiga a hankali ta zauna a kusa da ƙafarta tana jira ta gama wayar. Mama da take waya ta ce, "ai visa ta fito, ko gobe za a iya siyan tikiti su tafi, a filin jirgi zasu haɗa su da Oga Musa ya rarrabasu inda ya kamata." Mama ta kuma cewa, "Ai gani ga Kariman fa, babu wani abun zai faru sai alkhairi." Mama ta sake yin shiru kafin ta kashe wayar. Mama ta kalli aminiyar ta da take kallon ta, suna mamakin ganin Islaha a ɗakin a zaune, ta kalli Islaha cikin mamakin abinda ya kawo ta ta ce, "Islaha lafiya?." Islaha ta gyara zama, cikin sanyin murya ta ce, "Mama alfarma nazo nema a wajan ki in zan samu." Mama ta ce, "ina jin ki, faɗi in zan iya." Islaha ta buɗe ledar hannunta ta miƙawa Mama ahinda yake ciki. Mama da Karima suka kalli juna, kafin Mama ta saka hannu ta karɓa tana juya abinda ta kawo mata a hannunta ta ce, "faskon tafiya wata ƙasa nake gani, na waye?" Ta faɗa tana buɗewa sai ga hotom Islaha da sunanta. Mama ta kalle ta cikin mamakinta ce, "Fasko ɗin ki ne ai, yaushe ki ka yi?." Islaha ta ce, "ranar litinin na yi Mama." Karima ta ce, "ƙasar waje zaki je kenan?." Islaha ta girgiza kai, ta sunkuyar da kai a sanyaye ta ce, "ina so a tafi dani aikin da za a je yi Saudia, daman naji ana neman mai irin kamannina, na shirya indai akwai dama." Mama da Karima suka kalli juna cike da mamaki da tsoro, Mama ta ajjiye passport ɗin a kusa da ita ta ce, "ban gane ba, yi min bayani yadda zan gane Hajiya Islaha." "A asibitin fa Baffa yake na ji kuna cewa akwai gidan da aka samu amma babu mai zuwa. Shine na je nayi komai na kawo miki, indai ba a samu mai zuwa gidan ba nima ina so naje nayi aikin, ina da buƙatar kuɗin a halin yanzu." Karima ta yi dariya cikin jin daɗi ta ce, "Amma kin kyautawa kan ki Islaha, yadda ki ke da kyaun nan, da kala mai kyau rububin ɗaukar ki aiki za a yi. Wallahi baki taɓa burge ni ba sai yau, ban yarda ke wayayyiya bace sai yanzu." Mama da mamakin Islaha ya kusa kashe ta ta ce, "wai kina nufin kema saudian zaki tafi?." Islaha ta ɗaga kai kamar mara jini saboda sanyin jiki ta ce, "indai akwai dama ina so na je." Mama ta yi dariyar jin daɗi ta ce, "dama mai kyau ma Islaha, akwai damar da zaki je ki yi aiki ki samu kuɗi masu kauri." Mama ta saki fuska ta dafa Islaha ta ce, "Ko ke fa, da irin haka ki ke yi ai da bamu dinga samun saɓani dake ba. Kar ki damu, aiki kamar kin tafi kin gama wallahi. Bara ma kiga, ai ba a bori da sanyin jiki" Mama ta faɗa tana ɗaga waya. Mama ta ce, "Ga data page nan zan turo, a buga mata visa. Itama da ita za a yi tafiyar, cikon ta ukun ce" tana faɗa tana kashewa, ta ɗauki hoton fasko ɗin Islsha ta tura. Mama tana murmushi tans kallon Islaha ta ce, "kin taki sa'a, yanzu visa tana saurin samuwa, da an tura suke bayarwa babu wata wahala yadda ya kamata, muna zaune a nan za a iya turo visa ki. Kuma akwai aiki mai kyau a ƙasa, ina tabbatar miki da a cikin wata biyar zaki iya haɗa naira miliyan goma. Aiki da larabawa ba ƙaramin kuɗi yake kawowa ba, kin san su akwai kyautar girma ta ban mamaki, haka kawai zasu iya baki kyautar miliyan guda ban da albashin ki." Islaha ta sauke numfashi, tana ji a ranta lokacin sauke nauyin bashin da taci yazo ta ce, "yaushe ne tafiyar?." Hajiya Karima ta ce, "an samu visa mutane biyu, zamu jira taki ta fito, na tabbatar zuwa gobe za a samu takin ma. Dan yanzu ma yamma ta yi ne, da za a iya nemo visa ki. Ana samun visa nan da jibi ma za a siyi tikiti ku wuce, daman ku uku ne, keda Labiba da babar ƙawar ki." Islaha ta ɗaga kai ta ce, "Allah ya kaimu." "Amin. Ki zauna cikin shiri, ga jakar tafiya a can ki zo ki ɗauka ki haɗa kayan ki da abinda zaki yi amfani dasu." Islsha a sanyaye ta ce, "Amma ni bana so aikin ya wuce shekara ɗaya, iya na lokacin da nake so zan yi na dawo gida." Mama ta yi dariya tana yi mata kallon baki da hankali ta ce, "kar ki samu damuwa, Allah ya kaimu." Islaha ta ɗan yi shiru sannan tace, "Mama don Allah bana so Hamma ya sani, tunda ya ce tafiya zai yi a bar tafiyar sai Hamma ya bar garin nan. Daman ga Baffa yana asibiti, shima bazai san mun tafi ba. In na je can zan san yadda zan yi da Hamma, amma don Allah koda wasa bana so ya san da tafiya Mama." Mama ta sake dafata ta ce, "nima bazan bari ya sani ba, na san halin Saheer zai iya kifar da burin ki. Jeki abin ki, na san abinda zan yi babu abinda zai faru." "Na gode" Islaha ta faɗa tana miƙewa a sanyaye ta fita daga ɗakin. Tana fita Mama ta yi shewa suka tafa da Karima, Mama ta ce, "ke ki ga ikon Allah, ashe arzuƙin wannan gida da ake yi mata talla a Jeddah ta tabbata daga hannunmu za a ci sa. Ki duba Islaha dai, yarinya fitsararriya da muka yiwa tayin zuwa ta watsa mana ƙasa a ido, yau gata wai itace da kanta ta kashe kuɗi ta yi fasko har ta kawo a tafi da ita. Kai lamarin nan ya yi min daɗi sosai." Hajiya Karima ta ce, "nima ya buge ni, na yi mamaki sosai da ta sakko cikin sauƙi haka. Kin ga wannan gidan, da kuɗin aikin sai yadda muka yi dashi." "Ga mai gidan daman babu lafiya, har islaha ta tafi ba sani zai yi ba balle ya ɗaga min hankali. Ssheer ma barin gari zai yi, su je can su ƙarata ni na tura ta inda zan samu." "Amma fa lamarin nan ya ɗaure min kai, meye sakko da ita haka?." Cikin rashin damuwa Mama ta ce, "koma meye wannan ita ta ga zata iya, ni dai taje ta samo min kuɗi kawai shine burina." Karima ta ce, "Kai amma za a yi rububin yarinyar nan, dan Oga Musa ya faɗa min akwai fararen fatar da suke son mata irin Islaha, dan gidan da yake magana a kai yace mai gidan irin fatar Islaha yake so, da ta je zai ɗauka. Yarinya ga shegen kyau da gashi, ga kalar fatar ta abin kallo ko baka yi niya ba...." Hajiya Karima ta yi dariya ta ce, "Inda zata bi ƙananun hanyoyin da ake da wuri zata zama Hajiya wallahi." Mams ta ce, "nifa daman burina kar gidan nan na Jedda ya wuce mu, kuma tunda an samu mun gode Allah, sai a cigaba da shagali kawai." Karima ta ce, "Ki ji fa, wai ita aikin shekara ɗaya take so ta dawo. Shashasha, bata san in ta shiga sai Allah ya fito da ita ba." Mama cikin dariya ta ce, "Ai basu san roman baka ba." Suka tafa suna dariya, suka cigaba da tattauna yadda lamarin zai kasance. Islaha haka ta shiga ɗaki jiki a sanyaye, zuciyarta a cushe take akan abinda ta aikata, wani abu take ji ya tokare mata zuciyarta.  Ta san ba daidai ta aikata ba amma hakan shine kawai mafitar ta, bata da mafita da inda zata samu kuɗi ta sauke nauyin da yake kanta sai hakan. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ka kawo min sauƙi cikin lamarin nan, Allah ka bani abinda zan iya, Allah ka bani abinda zan iya ɗauka, dan darajar ka. Ya Allah ka bani ƙaddara mai sanyi, ka kaini hannu na gari, ka bani ikon kiyaye mutuncina a duk inda nake. Allah ka yaye min gagagwa da aikata abu a cikinta, ka bani ikon yin tunani mai zurfi kafin na aikata, amin." Ta zauna a gefen gadon, sai kuma ta miƙe tsaye dan tana buƙatar magana da Safeera, tana so ta faɗa mata abinda yake faruwa amma bata son tayar mata da hankali, bata so ta ji labarin har an yiwa Umma visa fita ƙasar waje. Ta tabbatar Safeera bata sani ba, dan da ace ta sani da tuni ta bata labari abubuwan da suka faru akan hakan. Ta yi ajiyar zuciya, duk da haka tana da buƙatar yin magana da Safeera da kuma Sadik, dole ta yi magana dasu ko dan abinda zai faru bayan tafiyarta, bata so Saheer ya san zata bar ƙasar sai bayan ta bari. In ta je can kome zai faru zata iya jurewa, kuma zata rarrashe shi har ya haƙura ya fahimce ta. Ta sauke numfashi tana lumshe ido, tunda bata da iyayen da zasu saka ta ko hana ta, gwara ta yi abinda take ganin shine ya dace da halin da take ciki. Islaha a Jeddah Rehaan a Jeddah🤭❤️‍🔥 [6/26, 12:30 PM] KRBBK: RDB2P22 Nana Haleema Da sallama Umma ta shiga wajan Baba da yake zaune, ya amsa yana kallon ta har ta ƙaraso ta zauna. Umma ta ɗan kalli Baba ta ce, "ina son nayi magana da kai." Baba ya ɗan kalle ta sannan ya ce, "ina jin ki." Umma ta ce, "akan batun tafiyata ƙasar waje ne, daman...." Kafin ta ƙarasa ya ɗago ya kalle ta sai ta kasa ƙarasawa ta yi shiru. Baba bai ce komai ba ya cigaba da abinda yake yi, ganin bai yi magana ba sai Umma ta ce, "tafiyar tana matsowa, shine na ce..." nan ma bata ƙarasa ba ya ɗaga kai ya kalle ta. Baba ya ajjiye abinda yake hannunsa ya ce, "shine me?." Umma ta yi shiru bata ce komai ba, duk da ƙarfin guiwar da take ji kafin tazo, yanzu da take gabansa sai ta ji tayi sanyi ta kasa magana. Sai take jin nauyin faɗa masa har an buga mata visa an yi ticket, bakinta sai ya sarƙe ta kasa faɗar abinda zata ce. Baba ya ce, "na faɗa miki hukunci na akan maganar nan, indai ki ka amince da tafiya ƙasar waje to ki tabbatar babu aurena a kan ki." Umma da mamaki take kallonsa ta ce, "wai da gaske zaka iya sakina? Ƴaƴa huɗu ne a tsakanina da kai, kuma dukkansu mata ne. Yanzu sai ka sake ni saboda wannan ƙaramar matsalar?." Baba ya miƙe tsaye ya ce, "indai zaki iya tsallake su ki tafi wata ƙasa saboda neman duniya, ina so na faɗa miki nima zan iya rabuwa dake. Kuma ina kan bakata wallahi, indai ki ka zaɓi barin yaran ki nima zan zaɓi barin ki. Baza ki bar nigeria da aurena a kan ki ba, gwara ki tafi babu nauyin kowa kema zaki fi jin daɗi" yana gama faɗar haka ya mike ya fita daga falon. Umma ta miƙe tsaye ta ce, "tabɗijam! Wallahi bazai yu ba, dole na je ƙasar nan na samo kuɗin da mata suke samowa. Da gaskiyar woman leader, indai zaka biyewa namiji zaka ƙare a wahala da takaicin rayuwa. Yanzu dubi baban Safeera, me yake tsinana min da har zai hana ni tafiya neman na kaina?. Ai wallahi tunda na yi niya sai na je, bazan zauna a nan talauci ya kashe ni ba." Sai kuma ta sauke numfashi tana kama ƙugu ta ce, "amma bana son auren nan ya rabu, auren shekara ashirin da tara zai rabu saboda haka? Kuma sai da yara duk suka girma sannan hakan zai faru?." Ta dafe kai cikin damuwa ta furzar da iska waje ta ɗauki waya ta kira ƙanwarta. Tana ɗauka ta ce, "Atika ina cikin matsala wallahi, Babansu Safeera ya sake tabbatar min da indai na tafi sai ya sake ni." Daga can ɓangaren Atika ta ce, "to meye abin damuwa? In ya sake ki ai ba wani abun ne zai faru ba, ƴaƴa dai ƴaƴanki ne, kuma zaki je ki samo kuɗin aurar dasu ne tunda dukkansu mata ne. Ƴan mata uku ne a gabanki, a cire batun autar ki ita bata kai su girma ba, amma Safeera da ƙannenta duk sun isa aure. In ki ka zauna da me zaki aurar dasu?." Umma ta ce, "shine tunanina Atika, amma bana son rabuwar auren nan wallahi. Ace aure shekara da shekaru zai rabu saboda tafiya ƙasar waje aiki? Kuma sai da yara suka girma, duk sun san meye aure da rabuwarsa sannan zai faru? Abin akwai nauyi Atika." "meye dan ya sake ki, in ya sake ki ba sai ki sake wani auren ba?." "Haba Atika, da tsufana, ina shirin aurar da ƴa kuma ki ce nayi wani auren?." "To a kan ki aka fara? Kin ga Maimuna, Kar wannan ya dakusar dake, nima harkar nake so dan bazan samu dama bane shiyasa zan yi haƙuri, amma ke tunda kin samu kar ki yi wasa da ita." "In ya kira Yayana na Katsina ya faɗa masa fa?." "To ina ruwansa? Zai hanaki abinda ki ka yi niya ne?." Umma ta ce, "shikenan dai, ina zuwa" ta faɗa tana kashe wayar cikin tunani. Baba ko da ya fita a ƙofar gida ya tsaya cike da tunani, ya san halin matarsa tsaf zata iya tsalleke auren ta tafi. In hakan ya faru bazai ji daɗi ba, bazai taɓa jin daɗi ta tafi ta bar yaranss a gantale ba tare da uwa ba. Shi mutum ne mai ɗan tafiye-tafiye neman na abinci, in ta saka ƙafa ta tafi in zai yi tafiya da wa zai bar ƴaƴansa mata?. Ya yi ajiyar zuciya, ya saka hannu aljihu ya ɗauko waya ya kira Yayanta na Katsina dan ya sanar dashi halin da ake ciki, da farko ya ɗauka ta bar maganar shiyasa bai saka magabatanta a ciki ba, amma ya ga alama yanzu dole ya saka makusantata a maganar. Basu jima suna wayar ba ya sauke wayar ya cigaba da tsayuwa a wajan har mota ta tsaya a kusa dashi. Aka fito daga motar, mutumin ya ƙaraso kusa da Baba da fara'a Baba ya ce, "Ashe kana cikin garin na mu." Alhaji Yakub ya ce, "na shigo garin jiya, kuma na yi niyar na shigo mu gaisa sai ga wayar ka, shine na ce ai ko ban yi niya ba ya kamata ace nazo." Baba ya ce, "barka da zuwa." "Barka dai. Ka yi haƙuri, ban san abinda yake fatuwa ba kenan, ai da na yiwa tufkar hanci." "Mu ƙarasa ciki." Bai musa ba suka shiga cikin gidan da sallama. Umma da fitowar ta tsakar gida kenan ta ji sallar tasu su ta amsa tana kallon su, gabanta ya yanke ya faɗi ganin Yayanta da kuma mijinta. Cikin yaƙe da faɗuwar gaba ta ce, "Yaya Sannu da zuwa." Ya yi murmushi ya ce, "Yauwa sannun ki." Ta nuna masa falo ta ce, "Yaya mu shiga ciki." Suka shiga shida Baba ita kuma ta dafe ƙirji tana ajiyar zuciya. Daƙyar ta ɗauko faranti ta ɗora masa pure water guda biyu, ta koma kitchen ta ɗauko ƙaramin flakass wanda ta zuba kunu tun na safe da kofi ta shiga da sallama. Suka amsa ta ajjiyewa Yaya ta ce, "Yaya ban san zaka zo ba, da na yi maka tanadi na musamman" ta faɗa tana zama da murmushi. Yaya ya ce, "jiya nazo, daman kuma nayi niyar na shigo mu gaisa, sai yanzu Allah ya yi na ƙaraso." Ta durƙusa har ƙasa ta ce, "Ina yini." "Lafiya lau, ya gida ya yara?." "Alhamdu lilah. Ya mutanen Katsina?." "Kowa lafiya lau. Da nace musu in na zo Yola zanzo mu gaisa sun ce duk a gaishe ku." "Muna amsawa." "ina Safeera da ƙannenta?." Umma ta ce, "duk suna islamiyya. Safeera kuma tana wajan aiki." Yaya ya ce, "ma sha Allah! Allah ya taimaka." "Amin Yaya." "Yaushe ne bikin Safeera ne?." "Ba a saka lokaci ba har yanzu, Yaron yana aiki ne." "Gwara haka, gwara ya yi komai a nutse. Allah ya kaimu lokacin." "Amin Yaya. Ga kunu na kawo maka ka sha, bara na kawo abinci" ta faɗa tana miƙewa. Yaya ya ce, "yi zaman ki, kunun dai zan sha, abinci kam na ƙoshi." "Ka dai ci har abincin." Baba ma ya ce, "ya kamata dai ka ci wani abun." Yaya ya ce, "wallahi a ƙoshe nake, zan dai sha kunun tunda daman ina sonsa." Umma ta yi murmushi bata ce komai ba, ƙirjinta yana dukan goma goma. Yaya sai da ya sha ruwa sannan ya kalle ta ya ce, "Maimuna!." Gaban Umma ya yanke ya faɗi, ta ɗaga kai ta kalle sa ta ce, "Naam Yaya." Ya gyara zama ya ce, "Meye matsalar ki? Me ki ka nema ki ka rasa a cikin gidan nan?." Umma ta sauke numfashi kanta yana ƙasa ta ce, "babu komai." Yaya ya ce, "A'a akwai, ki faɗa min abinda yake damun ki, ina ji." Umma ta yi shiru bata amsa ba, dan bata san me zata ce masa ba. Alhaji Yakub ya haɗe mata rai ya ce, "magama nake yi miki, me yake damun ki?." Umma ta ce,"babu komai." Ya girgiza kai ya ce, "da girman ki, da shekarun ki, da ƴaƴan mata duk sun kai munzalin aure, ke da kanki kike so ki tsallake su ki bar ƙasa saboda abin duniya Maimuna?." _Shikenan, ta faru ta ƙare._ Umma ta faɗa a zuciyarta, cike da jin haushi da takaici, dan ta san tunda mutanen Katsina suka ji maganar ta shiga uku. Alhaji Yakub ya ce, "Wallahi ko a mafarki ban yi tunanin zaki aikata wannan ɗanyen aikin har haka ba, ban yi tunanin shirmen ki da rashin girman naki ya kai haka ba sai yanzu. Ke yanzu za ki iya ɗaukar ƙafa ki bar ƙasa, ki bar mijin ki da ƴaƴan ki saboda duniya don Allah?." Umma ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, dan ta san bazai taɓa bata damar magana ba, ko ta faɗa bazai fahimce ta ba ko kaɗan. Cikin faɗa ya ce, "dan tsabar shirme da neman duniya? Ki rufe ido ki ɗauki ƙafa ki tafi wata ƙasa ki bar yaran ƴan mata a Nigeria, in ba shirme da rashin hankali me meye amfanin wannan?." Nan ma bata tanka ba ya ce, "kin rasa ci da sha a gidan nan?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "faɗa min dalilin ki na tafiya, faɗa min dalili mai ƙarfi da ya saka ki ke son barin ƙasar nan ki tafi aiki wata ƙasa." Umma ta kasa cewa komai, dan duk da Baba bashi da kuɗi amma yana ƙoƙarin ganin ya tsare musu komai na rayuwa. Ilimi, abinci, suttura da sauransu duk basu rasa a gidan ba, in ta faɗi wani abu makamanincin haka ta yi masa ƙarya. Ya ce, "ina jin ki." Umma ta ce, "babu komai." "Haka kawai ki ke neman ɓata rayuwar ki, da girman ki da shekarun ki kike son mayar da kan ki baya?. Abinda baki yi da kina ƙarama ba, shi zaki yi yanzu da ki ka isa ajjiye jika? Kar ki manta, an saka kawo kuɗin auren ƴarki Safeera, ko kunyar hakan bakya ji za ki saka wannan shirmen da ya zama ruwan dare a zuciyar ki?." Umma ta ce, "Yaya da farko ban yi niyar zuwa ba, sai da na faɗa masa ya ƙyale Safeera ta je amma sai ya ce indai shi ya haife ta wallahi bazata je." "To faɗa miki aka yi shi mahaukaci ne irin ki? Ko an faɗa miki bai san abinda yake yi ba kamar yadda baki sani ba?. Haka kawai ki ɗauki yariya budurwa ki sahale mata ta tafi wata ƙasa aiki? Ba tare da kin san da wa ki ka haɗata ba, baki san a ina zata sauka ba, baki san a hannun wa zata zauna ba? Kedai kawai ta je ta samo miki kuɗin da baki san ta hanyar da za a samu ba ko?." Umma ta kalle sa ta ce, "Aiki ne fa kawai Yaya, aikin gida ne irin na gidan larabawa ko gidan turawa, ba wani abu ake aikatawa a can ba." Ya yi shiru kawai yana kallon ta bai ce komai ba dan bai san me zai ce ba, dan shima ya ga lamarin nata da gaske take ba da wasa ba. Jin ya yi shiru sai ta ɗago ta kalle sa taga ita yake kallo, ta sunkuyar da kai sai kuma ya ce, "Mahaifi. Safeera ya hanata zuwa ne saboda ya isa da ita, tunda shine ya haife ta babu mai iko da ita kamar sa." "Ni kuma Yayanki ne, na girme miki da shekaru masu yawa, iyayenmu basu da rai, dan haka ni ne uba a gare ni. Dan haka nima na hana ki zuwa saboda na isa dake, zan gani in na isa dake in ban isa dake ba." "Banda lalacewa da shirme, da girmanki da shekarun ki zaki ɗauki ƙafa ki ta fi wata ƙasa aikin gida? Anya kina da hankali kuwa?." Baba dai yana zaune ya yi shiru bai ce komai ba, Yaya ya kalle sa ya ce, "Anya tana da hankali?." Baba ya ɗan murmusa ya ce, "tana da hankali, kawai wani abun ne ya rufe mata ido." "A'a, mai hankali bazai aikata abinda take aikatawa ba. In da ace tana da hankali baza ta yi kwatankwacin wannan shirmen ba. Tafiya aiki fa take tunanin yi wani waje, ba cikin yola ko cikin nigeria ba, jirgi zata hau ta bar ƙasa. Kuma wai ita irin huce haushin nan zata yi, wato an hana Safeera tafiya ita bara ta je da kanta, tunda kaine ka haifi Safeera kuma ka hanata zuwa, to ita ai baka haife ta ba. Abinda take nufi kenan, shiyasa take wannan maganar." Baba dai ya yi murmushi kawai bai ce komai ba, dan kuwa haka Umman ta faɗa masa, Safeera ya haifa ba ita ba. Yaya ya ce, "in ban da lalacewa ma, ƙasa kamar Nigeria amma ace wai matan cikinta ne suke fita su tafi wata ƙasashen larabawa yin aikii kamar wasu gantallalun mutane?. Tsakani da Allah wanne farar fatar ne ya taɓa zuwa nigeria yake aikin wanke-wanke da shara a gidan baƙaƙe fata ƴan Nigeria?." Baba ya ce, "babu." "Amma mu mun mayar da kan mu baya, babu abinda ƙasashensu suka fi mu dashi, dan dai kawai lalacewa irin ta ƙasar ta mu, an ɗauki hakan a matsayin ba komai bane." Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Ahir Maimuna! Kar na ji kar na gani, kar na sake jin wannan maganar mai kama da wasan yara. Ki adana wannan shirmen a gefe, ki cire shi daga ranki ki kalli gaban ki. Wallahi in n kuma jin wata magana makamanciyar wannan sai na ɓata miki rai. Kin ji ko?." Umma ta ɗaga kai ta ce, "na ji." "Yauwa, maganar ta tsaya iya haka, maganar ta ƙare a iya falon nan, maganar ta tsaya a nan wajan. In kina niyar tafiya ma ki tabbatar kin daina, wallahi in wani abun ya sake faruwa sai na saɓa miki, kin ji na rantse." Umma ta ce, "in Allah ya yarda babu abinda zai kuma faruwa." Ya ce, "ya fi miki. Kome ki ke hange da zai saka ki kai rayuwar ki can, in so ki san komai lalacewar nan ɗin shine dai jin daɗi ki, baza ki je ki ɗauko farin ciki da walwala ba, in kika sake ki ka bar gidan nan, wallahi kin yi bankwana dasu har abada. Abinda suke faɗa miki zaki samu a can roman baka ne, suna kwaɗaita miki abinda zai saka ki ji ranki yana so, amma in kin je akasin hakan zaki tarar. Kin girma, wannan shirmen duk ba naki bane, kin taso a gidan tarbiyya ,kin samu ilimi daidai gwargwado, wannan shirme da ɓata lokacin duk bai kamace ki ba." Umma tayi shiru bata ce komai ba. Ya ce, "kin ji me nace ko?." "Na ji Yaya, in sha Allah ta wuce." "Haka ake so." Ya kalli kunun ya ce, "zan tafi da kunun nan, in anjima zan bayar a dawo da flaks ɗin. Wannan ki bawa yaran" ya faɗa yana miƙa mata kuɗi. Ta karɓa fuskar ta babu walwala sosai, dan ji take an takura mata an matsawa rayuwar ta an hanata abinda take so. Sama-sama take amsawa, babu walwala ko kaɗan a tare da ita. Daga haka dai suka yi sallama Yaya ya tafi ya barta da tunani. Nana Haleema. [6/26, 12:30 PM] KRBBK: RDB2P23 Nana Haleema. Islaha tunda Saleem ya taho kawo su gida daga asibiti wajan Baffa ta yi shiru bata cewa komai. Saleem da Safeera ne suke magana sama-sama, ita dai bata saka musu baki. Saleem yana tsayar da motar Islaha ta ce, "Safeera zo mu je gida mu yi magana don Allah." Safeera ta kalle ta ta ce, "me ya faru?." Islaha ta ce, "ki zo mu je" tana faɗa ta buɗe motar ta buɗe gidan dan babu kowa duk basa nan ta. Saleem ya kalli safeera bayan Islaha ta shiga gida ya ce, "ƙawar ki tana da damuwa, tun daga dawowar ta daga ɓacewar da ta yi, na tabbatar tana da wata matsala da take ɓoyewa." Safeera ta ce, "nima naga hakan, in na tambaye sai ta ce min ita babu komai. Amma bara na je na ji me zata ce min. Ka gaishe da Mama don Allah." Ya wani kalle ta ya ce, "ba wani na gaishe ta, ko sau ɗaya baki taɓa zuwa kin gaishe ta ba." Ta buɗe ido waje ta ce, "bafulatana ce ni fa, da kunya aka san mu. Ina ni ina zuwa gidan ku gaida Mama?." "Ko ba bafulatama ba" ya faɗa yana hararar ta cikin wasa da soyayya. Murmushi ta yi ta buɗe motar ta fita shi kuma ya wuce gida. Safeera a zaune ta samu Islaha ta riƙe ciki tana cize bakinta, Safeera ta ce, "ya dai? Period ɗin ne?." Ta girgiza kai ta ce, "ovalution ne." "Tabɗi! Kina ƙoƙarin gane lokacin ovalution cycle ɗin ki, ni wallahi mantawa nake yi" ta faɗa tana zama a kusa da ita. Safeera ta ce, "ina jinki, lafiya?." Islaha ta ɗan sauke numfashi ta kalli Safeera ta ce, "a duniya bani da wani daga ke sai Hamma. Bani da iyaye, inda na taso kuma gida ne na kowa da kowa, ba wani nake dashi da zan je na yi sirri dashi ba. Ke kaɗai nake da ita wacce nake faɗawa damuwata na ji daɗi. Safeera..." sai kuma ta yi shiru bata ce komai ba. Safeera a sanyaye ta ce, "ina jin ki, zaki jefa zuciyata cikin dogon tunani Islaha." "Akan kuɗin mutumin nan ne, wallahi kullum sai na yi mafarki mara kyau akan hakan. Ban san tautsayin da ya kaini aikatawa ba, gashi gabaɗaya na kasa nutsuwa." "Kin saka abin a ranki ne shiyasa ki ke mafarki akan abun. Wani mafarin yana zuwa ne in ka saka wani abu a zuciyar ka kana tunaninsa, yawan tunanin sai ya jawo ka yi mafarki akan hakan." "Hanyar da zan biyasa kuɗinsa nake nema Safeera. Ta wacce hanya zan samu kuɗin?." Safeera ta ce, "babu gaskiya, duk hanyar da zaki bi ki samu maƙudan kuɗi kamar wannan a lokaci ɗaya ba hanya ce mai ɓullewa ba. Sata, iskanci, fashi, damfara da sauransu. Sune zasu kawo miki kuɗi masu yawan wannan lokaci guda. In kuwa ta hanyar halak ne dole sai kin jira, a hankali a hankali in kin tara sai ki biya." Ta ja nunfashi mai ƙarfi ta ce, "Yaushe kenan? Yaushe zan tara wannan kuɗi masu yawa?. Shekara goma ko ashirin?." "To gashi nan dai." "Safeera ni dai na samo mafita, kuma in Allah ya yarda a shekara ɗaya zan haɗa masa kuɗinsa. Zan neme sa a duk inda yake na damƙa masa koda zai saka a kama ni." Safeera ta bita da kallon mamaki ta ce, "wacce mafita ce wannan?." Islaha ta ɗan yi shiru tana kallon ƙasa, ta ɗago ta kalli Safeera da take kallon ta tana jin nauyin faɗar abinda yake bakin ta. "Faɗi mana Islaha, kin saka ni a tunani fa." "Na shiga cikin waɗanda Mama zata kai Saudia aiki a wannan lokacin, tafiyar baza ta wuce nan da kwana biyu ba." Safeera ta zabura ta miƙe tsaye cikin mamaki da kiɗima haɗi da tashin hankali. Islaha ta riƙo hannunta ta ce, "ki zauna mana." Safeera ta ce, "ban gane me ki ke nufi ba, maimaita na ji da kyau" ta faɗa tana komawa ta zauna. Islaha a sanyaye cikin rauni da rashin mafita ta ce, "cewa nayi zan tafi aiki ƙasar larabawa, a can nake tunanin zan iya haɗa kuɗin...." Safeera ta dakatar da ita ta ce, "kina cikin hankalin ki kuwa Islaha, kin san abinda ki ke faɗa min?." "Na sani mana, ni da kaina nake faɗa miki abinda na yanke." "Gaskiya ban yarda kina cikin hankalin ki ba Islaha, ban yarda kin san abinda ki ke faɗa ba wallahi. Anya a inda aka sace ki basu gurɓata miki tunani ba? Anya basu masu baki kayan maye kin sha tunanin ki ya gushe ba?." Islaha ta runtse ido, ta san dole Safeera tana shiga ruɗani akan hakan, tunda sune masu yaƙi da son kawo ƙarshen matsalar. Dole zata firgita in ta ji ita da kanta zata je. Cikin sanyin murya ta ce, "Safeera! Wallahi ina cikin hankali da nutsuwa, abinda nake faɗa miki shine asalin gaskiya ta. Har nayi international passport na bawa Mama, ɗazu da safe Mama take sanar dani da har an yi min visa." "Innallilahi wa'inna ilaihir raji'un, Islaha!" Sai ta kasa faɗa ta zubawa Islaha ido bata ce komai ba. Islaha ta ce, "babu yadda zan yi Safeera, ina da buƙatar sauke nauyin da yake kaina shiyasa na yanke hukunci ban faɗa miki ba. Wallahil azim ni kaɗai na san nauyin da ƙirjina yake yi min, ni na kaɗai na san zafin da nake ji akan abinda na aikata. Ke kin san wacece ni, kin kowa sanin halina, ban taɓa ɗaukar zaren wani ba balle naira biyar. Dole hankalina ya tashi, dole na rasa nutsuwata. Mafarkai nake yi marasa kyau, har mafarki nayi na mutu kuɗin sun hana ni kwanciya a kabarina." Safeera ta ce, "Akan wannan zaki dakusar da rayuwar ki, akan wannan zaki kashe kanki ki lalata tarbiyyar ki Islaha?. Meyasa baza ki bi wata hanyar ba, meyasa baza mu neme sa mu ba sa haƙuri akan hakan ba?." Islaha ta goge hawayen idanunta ta ce, "Yanzun nan kika faɗa min hanyoyin da suke kawo kuɗi, a cikin wanda ki ka faɗa wanne zan ɗauka?." "To meyasa baza ki sauke tsiwa da girman kai mu je a basa haƙuri? Meye a cikin ido ban da ruwa? In ka san ka yi laifi baka ɗaga kanka sama kace kai baza ka ƙasƙantar da kai ba. Wacece ke da ki ka ɗorawa ranki girman kai? Meye a cikin kalmar haƙuri Islaha?." Islaha ta yi shiru bata ce komai, Safeera ta ce, "rashin ba da haƙurin nan, da wannan maganar, sun saka na ji kamar komai da ya faru ke ki ka tsara." Ta ɗan murmusa ta ce, "Safeera kamar baki sanni ba?." "Meyasa za ki yanke wannan hukuncin ba tare da na sani ba?." Islaha ta ce, "Na san zaki hanani ne, shiyasa na je na yi duk abinda ya kamata ban faɗa miki ba." Safeera ta dafata ta ce, "ni da ke muke so mu yaƙi yawan fitar da yara da ake yi ƙasar waje da sunan aiki, yara nawa muka tattauna dasu waɗanda aka fita dasu? Mata nawa ne suka bamu labarin yadda rayuwarsu take juyewa sama ta dawo ƙasa saboda hakan?. Kin manta ina zaki je ne? Kin manta irin abubuwan da aka faɗa mana suna faruwa a can Islaha?." Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, Safeera ta ce, "wannan ba tarbiyyar ki ba ce, tafiya ki bar ƙasa ba daidai yake da tarbiyyar ki ba. Ni da ke muka zauna a kan case ɗin Umma, mu ka yi magana dake akan zamu je Katsina wajen iyayenta don a hanata zuwa. Meyasa ki ke son tafiya bayan wannan ƙaramar matsala ce?." "Safeera dole ce ta saka, kuma wannan matsalar ba ƙarama bace Safeera." "Ƙaramar matsala ce mana, in mu ka neme mutumin nan muka bashi haƙuri komai wucewa zai yi. A yadda ki ke ba da labarinsa na tabbatar yafi ƙarfin naira miliyan goma sha bakwai, yadda ki ke faɗarsa dan ya ce ya bar miki abu ne mai sauƙi a wajansa. Meyasa baza mu bi hakan ba, sai ta hanyar tafiya wata ƙasa aiki?." Islaaha ta yi shiru bata ce komai ba, Safeera ta ja tsaki cikin takaicin taurin kan Islaha ta ce, "baza ki iya ba sa haƙuri ba ko?." Islaha ta ce, "kema kin san bazai yu ba." "Wallahi Islaha ji nake kamar na tsinke ki da mari, wannan girman kan da ki ka ɗorawa kan ki babu inda zai kai ki sai danasani. Yanzu kin zaɓi ki bar ƙasar ki ki tafi wata ƙasar aiki a gidajen fararen fata ko?. Kin yarda ki watsar da tarbiyyar ki akan titi akan ki furta kalmar haƙuri a wajan wanda ki ka yiwa laifi?." "To ina zan gan shi balle na ba sa haƙurin?." "In ki ka nemo kuɗin a ina zaki gan shi ki ba shi?." "Neman sa zan yi duk inda zan gan shi." "Wannan ma sai ki neme sa ki basa haƙuri, ai ba aljani bane balle ace ya ɓace daga duniyar da muke ciki." "Safeera ni ya yi laifi fa, kuma bayan ya yi min laifin ya sace ni. Kuma haka ki ke so na basa haƙuri?." Safeera ta ja tsaki ta miƙe tsaye, Islaha ma ta miƙe ta riƙe ta ta ce, "Safeera kema kin san bazan iya ba, shiyasa na nemo mafita a gare ni da rayuwata. Ki yi haƙuri, na san kece mutum na biyu da baza ki ji daɗin hukuncina ba, bazan iya ɓoye miki ba shiyasa na faɗa miki, amma tafiya babu fashi. Na yi miki alƙwararin bazan watsar da kaina ba, na yi miki alƙwarain iya albashina kawai zan karɓa bazan karɓi kuɗi ta wata hanya mara kyau ba. Ko a wata ɗaya na tara kuɗin zaki ganni na dawo, bazan ɓata lokaci a can ba. Ba neman kuɗi naje yi ba, neman kuɗin da zan biya bashi zan je nayi." Safeera ta kalle ta ganin da gaske take magana, ga rauni ya bayyana a tare da ita. Safeera hawaye suka sakko daga idanunta ta ce, "Islaha ta ya zaki tara wannan kuɗi a wata ɗaya da iya albashi? Kuma in ki ka tafi baza ki dawo ba sai kin gama biyan su Mama kuɗin da suka kashe suka kai ki, sai kin biya kamfani kafin ki fara morar kuɗin. Kina ganin duk zaki iya hakan a ƙaramin lokaci?." Islaha ma kuka take yi a hankali ta ce, "in sha Allah zan iya, zan nemi halak ba haram ba. Ki yarda dani, bazan yi komai da zai lalata tarbiyyata ba." Safeer ta goge idonta ta ce, "na yarda dake bestie, ni na san wacece ke. Amma ina so ki sani daga ranar da ki ka tafi duk mai yi miki kallon mai mutunci zai daina, an riga an yiwa tafiyar nan kuɗin goro, ko da iya halak ɗinki ki ke nema a can, an lalata hakan a idanun mutanenmu na nan. Shaida mai kyau daga bakin kuma mutune rahama ce, bana so a fara yi miki wani zargi mara daɗi." "Duk wanda ya zarge ni shi da Allah, duk wanda ya yi min ƙazafi akwai ranar tsayuwa Safeera." Safeera ta ce, "na ji. Ya zaki yi da Saheer? Na san ko za a sake yaƙin duniya bazai taɓa amincewa da tafiyar nan ba. Ya zaki yi dashi? Ya zaki yi da su Zainab da abinda ki ke bincike a gidan? Kina so ki ce min ƙudurin ki ya danne na gidan marayu? Tafiyar ki ta fi bincike akan zargin lalata yaran da ake yi mahimmaci?....." See you on monday guys😍 [6/29, 11:53 AM] KRBBK: RDB2P24 Nana Haleema Islaha ta ja numfashi mai tsaho ta sauke, ta ɗan yi shiru kafin ta lumshe ido ta buɗe ta kalli Safeera ta ce, “Na san Hamma bazan taɓa ɗaukar maganar nan ba, shiyasa nake fatan Allah yasa tafiyar ta kai jibi, kin ga gobe ya ce min zai koma Niger, in dai ya tafi shikenan.” Safeera ta bita da kallon tausayi ta ce, “nufin ki ko ya dawo bazai sani ba?.” “Dole zai sani, da kaina zan faɗa masa amma sai na tabbatar bana nan. Indai har na tafi damuwar ba mai yawa bace, kafin na tafi ne wallahi bazai taɓa bari ba. Faɗa zai ta yi, ya kuma takura min sai na faɗa masa dalilina na tafiyar.” Safeera ta ce, “yanzu ya za a yi kenan?.” “Sadik zan yiwa waya, zance masa ina so mu haɗu, sai na faɗa masa komai da komai. Na san da wahala ya fahimce ni, amma zan roƙesa sosai, zance don Allah kar ya faɗa masa har sai na tafi.” “A shawara ta kar a faɗawa Sadik, babu lallai ya iya riƙe maganar bai faɗawa Saheer ba. Ki bari in kin je sai su ji labari, duk da na san zasu zo su tutsiye ni akan maganar, ni kuma zan faɗa musu abinda yake faruwa kawai.” Islaha ta ɗan yi shiru alamum tunani kafin ta ce, “To mu gwada hakan mu gani, amma ina jin tsoron ɓacin ran Hamma.” Safeera ta ce, “dole ransa ya ɓaci, shi da yake so ayi bikinku nan da wasu kwanakin masu zuwa, amma a wayi gari kin bar ƙasar, ai dole ransa ya ɓaci.” Ta ja numfashi mai tsaho ta ce, “babu yadda zan yi ne, ni kaina dole ce ta saka ni zan yi. Har istikhara nayi akan tafiyar, shiyasa na saka a raina in har Allah ya nufa naje to akwai alkhairi a zuwana, in kuma ban je ba babu alkhairi a zuwan, tunda na nemi zaɓin Allah kuma na san zai zaɓa min.” “Babbar matsalar ki a rayuwa shine gaggawa, duk da in mutum yana cikin yanayi na neman mafita yana aikata duk abinda ya zo ransa ne. Amma ke tun asali haka ki ke, kawai da zuciyar ki ta ɗarsa miki abu sai ki hau kai ki zauna, ki kasa fahimtar kuskuren abun har sai kin aikata. In ba dan haka ba, meye ya kai ki ɗauko kuɗi don Allah? Sannan me ya kai ki yanke hukuncin tafiya saudia? Dan kina ganin baki da iyayen da zasu hana ki ko?.” “Ina da Hamma, na san shima in ya ji bazai bari ba. Kamar iyayena yake, duk abinda yace na bari ina bari.” “Dole ki rage gaggawa, duk inda gaggawa take daga shaiɗan take.” “Ga sakamakonta ina gani Safeera, da ban yi ba da ina nan hankalina a kwance. Yanzu kuwa mafarkai nake yi marasa kyau, har mafarki nayi na kasa tsallake siraɗi. Shiyasa hankalina ya tashi, nake nemawa kaina mafita.” Safeera ta ce, “Zainab da Hafsa fa? Case ɗin da ki ke ta bibiya fa? Kina nufin zaki tsallake ki tafi ki bar yara a cikin garari?.” Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Zan bar maganar a hannun Barr Suraj, na san zai yi komai kamar ina nan. Kuma kema kin nan, zan dinga saka ki kiyi magana dasu.” “Amma kin san ba kamar ke ba ko? In dai ki ka bar ƙasar nan an ajjiye batun case ɗin Islaha.” “Allah zai kawo min yadda zanyi.” Safeera ta ce, “Allah ya kyauta. Aikin ki fa?.” “Zan yi droping ɗinsa, in na dawo zan cigaba in sha Allah.” “Kafin shekara ɗaya za a manta da fuskar ki, kina kan matakin ɗaukaka a yanzu, in ki ka yi ƙaura aka daina ganin zaki dakusar da kan ki. “To ya zan yi?.” “A ganina ki yi creating content a can, ko da video flowers ne ki dinga ɗauka ana yawan ganin fuskar ki a media. Tunda kina da followers, hakan zai saka baza a manta dake da sauri ba.” Islaha ta ɗaga kai ta ce, “Allah ya bani iko.” Safeera ta amsa da amin a lokacin aka buɗe ƙofar aka shigo da sallama. Suka amsa suna kallon Mama da ta shigo da babbar trolly bag ta ce, “islaha ga jakar zuba kaya nan, in anjima za a siyi ticket ɗin ku, jirgin jibi da daddare zaku hau. Ki zuba duk abinda ki ke da buƙata, ki zuba kaya masu kyau kar ki tafi da marasa kyau. Sannan zaki iya yin siyayya in kin je Jedda ki siyar ki riƙe kuɗin ki. Ana siyan goro, doya, fara, man shafawa, da sauransu. Goro dai ya fi kawo kuɗi, amma wucewa dashi tun daga nan Nigeria yana da wahala, amma da kin wuce in Allah ya taimake ki a Jedda ma ya wuce zaki yi murna.” Islaha cikin yaƙe ta ce, “Na gode Mama, ba sai na siyi komai ba.” Mama ta ce, “shikenan, ni zan ba da sautun da za a siyar min ki saka a jakar ki, in aka siyar ki mayar da kuɗin naira ki turo min kuɗina. Sannan akwai yaji, saboda abincin larabawa babu ɗanɗano, ina dashi na siyarwa in za ki siya.” A sanyaye islaha ta ce, “To Mama. Hamma yana nan?.” Mama ta ce, “ke kar ki damu da Saheer babu abinda ya isa ya yi, ba haifar ki ya yi ba, kuma ba auren ki yake yi ba. Bai isa ya hanaki abinda ki ke so ba.” Ta langwaɓar da kai ta ce, “Don Allah Mama bana so ya sani, tunda gobe zai koma Niger don Allah kar ki faɗa masa.” Mama ta ɗaga kai ta ce, “naji……” Mama ta juyo ta kalli Safeera ta ce, “Ke Safeera ana ta tafiya ke baza ki je ba? Ga ƙawarki nan zata tafi ta bar ki a nan, ko da yake da babar ki za a yi tafiyar” ta faɗa tana juyawa ta fita. Safeera ta bi bayanta da harara ta ce, “babu inda Umma zata je in Allah ya yarda. Matar nan makira ce, wato dan zaki je ki samo mata kuɗi shine harda sakar miki fuska. Ki ji kayan takaici, wai in kina son yaji ina da na siyarwa.” Ita dai Islaha bata ce komai ba dan bata so Safeera ta ji da Umma za a yi tafiyar a bakinta. Sai da suka yi sallah suka fito, a harabar gidan suka haɗu da Saheer da Sadik a tsaye suna tattaunawa akan jikin Baffa da ya warware kamar ba shi ba. Suka ƙarasa inda suke tsaye suka gaisa, Saheer ya kalli Islaha da kana kallon ta ka san tana cikin yanayin damuwa mai yaws. Ya ɗauke kai daga kallon ta, amma sai ya kasa daurewa ya juyo ya ce, “Ya dai?.” Ta kalle sa ta ce, “babu komai, kaina ne yake ciwo.” Ya zuba mata ido ya ce, “me ya kawo ciwon kan? Kwana biyu kina yawan cewa kan ki yana ciwo, me yake kawo shi?.” “Gajiya ce, ɗazu na je ɗaukar labarai ne, kuma ka ga yau anyi rana kamar ba lokacin sanyi ba.” Ya ɗan sauke nunfashi ya ce, “kin sha magani?.” Ta ɗaga masa kai alamun eh ta ce, “zan raka Safeera na dawo.” “Ki dawo mu yi sallama, gobe da asuba zan wuce in sha Allah.” Ta ɗan gyaɗa kai ta raka safeera ƙofar gida, ta dawo ta tarar suna tsaye har lokacin suna magana. Bata tsaya ba ta wuce su zuwa cikin gida Saheer ya bita da kallo har ta ɓace daga idanunsa. Ya juyo yana kallon Sadik ya ce, “ban amince da yanayin Islaha na kwanakin nan ba, tabbas ta canja ta koma kamar ba ita ba. Zuciyata tana faɗa min akwai abinda aka yi mata a lokacin da aka sace ta, a can ta samo wannan damuwar da take ɓoyewa.” Sadik bai ce komai ba, amma shi kansa har lokacin yana tunanin kuɗin da ta kawo masa aka biya kuɗin aikin Baffa, har lokacin zuciyarsa rawa take yi akan Islaha, tunaninsa a ina ta samu kuɗin ita da aka ce an sace ta?. (Waye y sani Malam Sadik?🤣) Islaha sai ta ƙagu dare ya yi Saheer ya zo su yi sallama ta huta, so take kawai ya bar ƙasar ya tafi Niger ko zata fi mayar da hankali akan abinda yake gabanta. Ta gama shirin bacci kenan ya kira wayarta ya ce ta zo harabar gidan su yi sallama. Ta saka hijjab a sanyaye ta fito, a daidai lokacin Hanan ta shigo da manyan ledoji tana wani takun isa da taƙama ta wuce su ta shiga ciki. Ya ja tsaki ya ce, “gabaɗaya Mama ta lalata yaran nan.” Islaha bata ce komai ba, ya kalle ta ya ce, “na kira ki mu yi sallama, bana so na takura miki ki fito da asuba saboda sanyi. Zan tafi, amma bazan jima ba zan dawo saboda jikin Baffa. Islaha a sanyaye tankalle shi ta ce, “Allah ya kai ka lafiya, Allah ya baka abinda ka je nema. Ya sauke numfashi ya ce, “Amin matar Hamma. Kin san nawa bill ɗin asibitin da Baffa yake?.” Ta girgiza kai tana kallonsa gabanta yana faɗuwa ya ce, “kuɗi ne masu yawa fa, a haka ma wai dan an biya kuɗin aikin. Asibitin yana da kyau da tsari, amma akwai kashe kuɗi sosai.” A sanyaye ta ce, “an ce mai asibitin kamar bature yake, shiyasa tsarin asibitin ya zama na turawa. In ban da shi ban taɓa ganin asibitin da nurses ne sukw jinyar mara lafiya ba, ko national hospital Abuja nasan ba haka ake yi ba, amma wannan gashi an yi. Kuma duk tsadarsa tunda an samu biyan buƙata ai mun gode Allah. Ga Baffa ya tashi kamar ba shi ba, ga Kawu ma ya miƙe kamar ba wani abun aka rage daga jikinsa ba. Ban taɓa ganin wanda aka yiwa dashen ƙoda ya miƙe ba, sai Baffa.” Ya yi murmushi ya ce, “haka ne kam, hausawa sun ce a wajan biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba. Kuma tunda an samu biyan buƙata baza a ji fitar kuɗin ba, mun gode Allah da ya bamu ikon yin komai ba tare da wani ya cutu ba.” Islaha ta murmusa ta ce, “Gaskiya ne Hamma.” “Amma fa an ƙarar da ƙaramin arzuƙin mijin ki kaf, abinda ya rage min bai wuce gidan da nake ginawa ba. Shima dan Allah ya taimaka mana Sadik ya yi ƙoƙari an samu kuɗin aikin ne, da yanzu an siyar dashi mun koma bamu da komai. Akwai wani fili da muka siya ni da shi da jimawa, ya ce min shi aka siyar aka ƙarasa biyan kuɗin.” Ta yi murmushi ta ce, “kuɗin da suka ƙare a hidimar iyaye Allah zai ninka su sau babu adadi.” Ya yi murmushi yana shafa kansa cikin jin daɗin maganar ta ya ce, “Gaskiya ne Matar Hamma. Amma da a ina zamu zauna?.” Ta juya ta kalli ɗakinsa ta ce, “Ga ɗaki can.” Ya yi dariya ya ce, “Haba dai! Sabuwar amaryar zan ajjiye a wannan tsohon ɗakin? Lallai ya kamata naci tarar ki, kin ƙasƙantar min da mata, kin sakko da ita daga high level zuwa low levwl.” Islaha ta yi dariya mai sauti, ta kalle sa tana murmushi amma bata ce komai ba. Sai dai tana jin daɗi ya sake ya daina fushi da ita. “Har zan tafi baki faɗa min komai ba akan maganar case ba.” Islaha ta yi shiru bata amsa, ya ɗan murmusa ya ce, “Na sake baki lokaci ko?.” Ta ɗaga kai alamun eh, ya girgizaa kai ya yi kafin ya ce, “Ki je ki huta kanki yana ciwo, in sha Allah da asuba zan tafi. Na faɗawa Sadik kar wani abu ya sake faruwa a ɓoye min, in hakan ya faru bazan yafe ba.” Ƙirjinta ya buga da ƙarfi, amma ta daure ta ce, “in Allah ya yarda babu abinda zai faru.” “Allah ya sa, nima haka nake fata matar hamma. Ki je ki huta.” Ta ɗaga ido tana kallon kyakykyawar fuskarsa mai cike da haske da kyayawan idanu ta ce, “To Hamma, da asuban zan fito mu sake yin sallama.” Ya bita da kallo ya ce, “To matar Hamma.Ina ƙaunar ki.” Ta sauke ido dago kallonsa ta ce, “ina ƙaunar ka Hamma.” Murmushi ya yi yana ji kamar ya rungume ta, sai yake jin wata irin kewar ta mai yawa tana ratsa jikinsa, sai yake ji kamar rabuwar su ta ƙarshe kenan a duniya. Ya kalle ta ya ce, “ina jin kewar ki a raina wacce ban taɓa ji ba, ina ji zuciyata tana bugawa fiye da duk lokacin da zan yi tafiya.” “nima haka haka nake ji Hamma” ta faɗa a sanyaye tana ji kamar ta kwantar a jikinsa, tabbas da zata samu zarrar jawo sa jikinta babu abinda zai hana bata ware hannayenta ta rungume sa ba. Amma kai tsaye bazata iya ba, da ace shi zai yi mata zata so hakan sosai a lokacin. Ya ɗan matso kusa da ita yana kallon idanunta da bakinta da yake ɗaukarsa ya ce, “ina ji kamar na rungume ki matar Hamma, kin bani dama in yi?.” Ta sauke iso ƙasa tana sauke numfashi a hankali zuciyar ta tana bugawa da ƙarfi. Da zata iya magana da ce masa eh, da ta faɗa masa ta bashi dama dan ita kanta tana so, amma baza ta iya furtawa ba. Bata iya cewa komai ba tana tsaye ƙyam bata motsa daga inda take ba. Yana jin sirritaccen ƙhamshin da yake fita a hankali daga jikinta, kasancewar ta mai yawan samun attack bata cika amfani da turare mai ƙarfi ba, sai ka zo kusa da ita zaka ji tashinsa a hanlkali yana shiga hancin ka. Jin shaiɗan yana neman tsirga masa wani abu sai ya yi sauri ya ja baya, amma sai ya riƙo hannunta duka biyun ya ce, “na sake yin haƙuri, sai kin zama mallakina, amma ko hmm” ya faɗa yana murmushi ita dai kunya duk ta cika ta. Ya ɗan shafa fuskarta ya ce, “ki je ki kwanta.” Ta ɗaga kai ta ce, “sai da safe.” Ya saki hannunta a hankali sannan ya ce, “sai da safe.” Ta juya tana hankali ta koma tana jin wata irin kewarsa tana ratsa zuciyarta. Tana ji kamar bazasu sake haɗuwa ba, kamar daga lokacin baza su sake furtawa junansu suna ƙaunar juna ba, kamar bazasu sake tsayuwa a matsayin masoya ba. A haka ta kwanta cikin tunani da buguwar zuciya, kewa da tunani kala kala a ranta. Nana Haleema 09030398006. [6/29, 11:53 AM] KRBBK: RDB2P025 Nana Haleema. Da asuba basu haɗu ba, sai text ya yi mata ya ce ya tafi, ta ji haushin rashin haɗuwarsu sosai sai take ji kamar baza su sake haɗuwa ba. Bayan ta fito ta ga Mama da iyalanta suna karyawa, ta gaishe da Mama ta amsa tana kallon ta ta ce, “ki fa shirya kayan ki, tafiyar ku gobe ce.” Gabanta ya faɗi ta ce, “To Mama.” Labiba ta ce, “ashe maganar duk ta ƙarya ce, da an yi magana ta ce ita bazata je ba, sai gashi zata tafi ba tare da Hamma ya sani ba.” Hanan ta ce, “bar munafuka, ita wai ga ta gari. Mtsw kamar bamu san dawar garin ba.” Islaha dai bata ce musu komai ba dan bata cikin yanayin magana. Ta juya ta koma ɗaki ta zauna tana tunani, taƙi bawa zuciyar ta damar tunanin abinda take niyar yi ba daidai bane, bata so ta zauna ta yi nazari a akai har ta gani kuskure zata aikata. Gudun hakan sai ta miƙe da hanzari ta shiga banɗaki ta yi wanka ta fito ta shirya ta wuce wajan aiki. A can ma bata da walwala, kowa ya lura da ita Safeera ce kaɗai ta san halin da ake ciki. Tare suka je wajan chairman suka same sa a zaune Islaha ta ce, “Chairman barka da aiki.” Da murmushi ya ce, “barka dai ƴar jarida mai ƙwazo.” Ta murmusa ta ce, “daman wata magana nazo da ita.” Ya gyara zama ya ce, “Allah ya sa labarin da zamu fara fitarwa ne. Kin san ya kamata ki koma ɓangaren da ki ka baro, ɓangaren wasanni ana ta tambayar ki.” “Ba akan aiki bane Chairman.” “To meye?.” Ta kalli Safeera sannan ta ce, “zan ɗan yi tafiya na wani lokaci, zan yi dropping aikina in na dawo zan cigaba. Ba barin aikin zan yi ba, zan tafi za a daina biyana, in na dawo zan ɗora daga inda na tsaya.” Mamaki ya saka Chairman miƙewa zaune ya ce, “ban gane ba, kina nufin zaki daina aiki damu?.” Islaha ta ce, “aikin gabaɗaya zan bari na wani lokaci, kuma ba gidan wata jaridar zan koma ba, zan yi ƙaramar tafiya ne zuwa wani waje. Da zarar na dawo zan ɗora in sha Allah.” Chairman ya ce, “Islaha ina zaki je haka? Ina zaki tafi ki bar ɗaukakar ki?. Kin san labaran da ki ka yi jiya adadin mabiya da masoya da mu ka tara? Islaha kece ƙwarin mu, saboda fuskar ki da muryar ki mutane suke bibiyar mu. Yau in aka ce bakya nan ina zamu saka ran mu?.” Islaha ta kalle sa a sanyaye ta ce, “Chairman tafiyar ta zamar min dole, ni kaina wallahi ba a son raina zan yi ba, kawai dan babu yadda zan yi ne. Amma na yi maka alƙwarin zan dawo.” Chairman ya ce, “in kika tafi kika canja wajan aiki fa?.” “Babu inda zan canja, ina nan bakin rai bakin fama in Allah ya yarda. Tafiyar ta zama dole ne, nima da bazan tsallake aikina na tafi ba.” Ya yi shiru yana sauke numfashi cikin damuwa ya ce, “Shikenan Islaha, Allah ya kiyaye, ya baki abinda ki ka je nema.” Ta yi murmushi ta ce, “amin, na gode.” “Yaushe ne tafiyar?.” “Gobe in sha Allah.” “Yanzu labaran goben ma baza su samu ba?.” Ta ɗan yi dariya ta ce, “in sha Allah zan shigo, nima ina so na yi na bankwana kafin na dawo.” Ya yi dariya ya ce, “shikenan Islaha. In kuma Mr Rehaan ya amsa gayyata bakya nan fa?.” Haka kawai ta ji gabanta ya faɗi ba tare da ta san dalili ba, bata nuna ba ta ɗan murmusa ta ce, “sai a samu madadina.” Ya yi dariya ya ce, “duk wahalar da ki ka sha ta tashi a banza? Zan yi fatan Allh yasa ya jinkirta amsawa har sai ki dawo.” Ita dai bata ce komai ba ta miƙe suka fito ita da Safeera. Da Ummi da Muslim suka haɗu, suka gaisa da Muslmin Ummi kuwa bata ce komai ba suka wuce. •••••• Yadda fuskarsa take a ɗaure ya saka Alma shiga hankalin ta, a rayuwarta tana tsoron baƙin mutum kuma ɗan nigeria, musmaman irin waɗanda deal irin nan ya haɗa su. Cike da ɓacin rai ya ce, “meye amfanin saka ki aikin da na yi, ace har yanzu an kasa samun ƙaramin videon Rehaan ko ya ya yake, har yanzu kin kasa yin komai game da hakan?.” Alma ta ce, “Im sorry sir, Rehaan ya bar Uk kuma bai dawo ba. Ina yawan zuwa apartment ɗinsa amma sai na tarar brother ɗinsa ne kawai shi baya nan. Ni kaina na damu da raahin dawowarsa, kuma tunda ya tafi yaƙi picking call ɗina. But na duba location ɗinsa a snapchat na ga yana Jeddah.” “To me ki ke jira baki bisa Jeedah ba?.” “Sir Saudia baza su bani damar zama tare dashi ba tunda ni ba matarsa bace.” “A apartment ɗin ma’aikata yake?.” “Aa, a gidansa na Jeddah yake. “To ina ruwan Saudia da zaman ki? Ki haɗa kayan ki kawai tafi can ku zauna tare. Bana son kuskure Alma, wannan lokacin ki tabbatar da kin samu Rehaan, ki tabbatar da kin turo min video.” Alma cike da ƙarfin guwa ta ce, “okay sir, i will try my best.” Ya yi tsaki ya tashi ya futa ya barta a wajan. Ta sauke numfashi tana haɗa plan ɗin tafiya Jeddah, dan ko babu wannan aikin itama ta yi missing ɗinsa sosai, tana da buƙatar ta je ta gan shi a duk inda take. ••••••• Tun bayan tafiyar Yaya daga wajan Umma bata sake nuna wani abu ba, ta nuna kamar ta bar tafiyar, nan kuwa shirin tafita take yi hankali kwance babu wanda ya sani sai ƙawar ta. Ranar da zasu tafi da safe take ta shiryawa tana kallon ƴaƴanta da suke shirin tafiya makaranta. Sai take jin tausayinsu, dan ta san kafin su dawo ta tafi, kuma gashi bata san ranar da zata dawo ba, bata san ranar da zata sake haɗa ido dasu ba. A haka suka gama shiryawa, suka yi mata sallama suka tafi, Safeera ce ta tashi bata jin daɗi tace baza ta fita ba. Ƙarfe goma na safe, jirginsu kuma zai tashi ƙarfe sha ɗaya na dare, ya rage saura awa sha uku zuwa sha haɗu jirginsu ya tashi, Umma ta shiga wajan Baba ta same sa a zaune yana duba wayarsa. Ta zauna a kusa dashi ta ce, “magana nake so mu yi.” Baba ya kalle ta ya ce, “ina jinki.” Umma ta sauke numfashi ta buɗe wayarta ta shiga whatsapp ta buɗe wani hoton ta haska masa ta ce, “waɗanda suka ri gasuka yi min visa da komai sun ri ga da sun siyi ticket ɗin tafiya, sun ce dole sai naje bazan saka su asarar kuɗi ba. Maganar da nake maka nan da awa sha uku zuwa huɗu jirgi zai tashi. Ana jirana zamu tafi Abuja, da mun je zamu wuce airport mu hau jirgin saudia.” Baba ya zuba nata ido yana kallon ta cikin firgincin maganar ta, ya ɗan ɗaga kai ya ce, “ina jin ki.” Umma ta ce, “tafiya ta zamar min dole, babu yadda zan yi dole sai naje. Kaima shaida ne tunda Yaya ya yi min faɗa na ajjiye batun zuwan, amma yanzu dole na tafi saboda bazasu yi asarar kuɗinsu ba.” Baba ya katse ta ya ce, “bata zama dole ba, babu wanda zai yi miki dole tunda kin ce bakya so. Nawa suka kashe, ba sai a biya su ba?.” Ta wani kalle sa ta ce, “ka san nawa ce visar? Ko iya ticket yafi miliyan balle a haɗa da visa. Bamu da kuɗin da zamu iya biyansu.” Baba ya ce, “ba dai matar Alhaji Mustapha bace Hajiyan ta ku ba? Nawa ne kuɗin.” Umma ta ƙufule ta ce, “biya fa bai tashi ba, kawai tunda haka ya riga ya faru zanje na dawo kawai, kamar yau zaka ga naje na dawo. Baba ya murmusa yana kallon ta ya ce, “zaki je ina?.” “Saudia ɗin mana.” Ya bita da kallon baki da hankali bai ce komai ba ya yi shiru. Umma ta miƙe ta fita a lokacin kiran Mama ya shigo wayarta tana shaida mata da ta haɗo kayanta ta taho gidanta zasu tafi Abuja gabaɗaya. Sai a lokacin gaban Umma ya faɗi, tsoro ya mamaye mata zuciya, tausayin ƴaƴanta ya ɗarsu a ranta, ta shiga tunanin ya zasu ji in suka buɗe ido bata nan?. Amma babu yadda zata yi, duk abinda take yi ma dansu take yi, saboda gobensu. Safeera ce ta shiga wajanta neman maganin ciwon kai, ta ga Umma tana rufe jaka gata da hijjab tana sakawa alamun fita zata yi. Safeera da mamaki take kallon ta ta ce, “Umma ina za ki je da safiyar nan?.” Umma ta kalle ta tana harararta ce, “aikin da ki ƙi zuwa ni zan je. Islaha da ta dinga zuga ki akan kar ki je, to yau da ita zamu tafi.” Kan Safeeera ya sara, daman gashi yana yi mata ciwo, ta dafe kai ta ce, “Umma ban gane ba, kina nufin tare da Islaha da Labiba zaku tafi yau?.” Umma ta ce, “ga zahiri kina gani, daga nan sai Madina in Allah ya yarda. Ki kula da ƙannenki kafin na dawo, in buƙatar kuɗi ta tashi zan dinga tura miki, daman nemansu zan tafi.” Safeera ta ƙarasa ta riƙe mahaifiyar ta tana kuka ta ce, “Don Allah Umma ki ce wasa ki ke yi, ki ce wasa ki ke yi min ba tafiya zaki yi ba.” Umma ta ce, “tafiya zan yi Safeera, zan je na nemo kuɗin da zan aurar dake da ƙanneki. Ki kula da kanki da ƙannenki kafin na dawo.” Safeera ta duƙushe ta riƙe ƙafarta ta ce, "Don Allah Umma kar ki yi mana haka, mun fi buƙatar ki sama da komai a rayuwar nan. Ni na yarda zanje, na amince zan je ba sai kin je ba." Umma ta kalle ta tana hararar ta ta ce, "lokacin da nake lallaɓa ki ai iskanci ki ke yi min, dan haka ki sakar min ƙafa na wuce." Baba ya ɗaga labulen ya shigo yana kallon ta da mamaki da ɗaure kai ya ce, "Maimuna da gaske tafiya za kiyi?." Ta kalli Baba duk da faɗuwar gaban da take ji, amma hakan ta daure ta ce, "yanzu na gama yi maka bayani fa." "Duk abinda Yayanki ya faɗa miki daman baki ji ba?." "Ni fa ta dole zan tafi, ba dan son raina zan je ba." "Yanzu dai sai kin je ɗin?." "Jirana ma suke yi zamu tafi Abuja, ta can zamu hau jirgin saudia mu tafi Madina.” Baba ya girgiza kai ya ce, "Maimuna kin zaɓi ki watsar da ƴaƴanki mata ki tafi wata ƙasar aikin gidan larabawa, kin zaɓi ki barsu a nan ki je inda baki da kowa saboda neman duniya?. Ki bar naki yaran, ki je ki yi bautar yaran wasu?." Umma ta ce, "ga Safeera nan, meye baza ta yi musu ba? Ai ba lallai sai ni ba." Baba ya bita da kallo dan bai ga alamun zata fasa ba, bai ga alamun tana jin tausayin ƴaƴan ba balle shi ta ji tausayinsa a matsayin mijinta. Zuciyarta ta bushe, kuɗi kawai take kallo. Baba ya gyaɗa kai ya ce, "na faɗa miki baza ki bar ƙasar nan da aurena akan ki ba, anyi haka ko?." Sai a sannan ta ji gabanta ya faɗi matuƙa, ta ɗago ta kalle sa taga ita yake kallo sai ta kasa cewa komai. Baba ya daure ya ce, "tunda kin zaɓi tafiya a kan aurenki da ƴaƴanki da ƴan uwanki baki ɗaya, ki je Maimuna, ki je ki nemo duk abinda ki ke ganin zaki samo a aikin gidan larabawan saudia." "In kin bar gida nan ki taho da duniya gabaɗaya, ƙarewar arzuƙin da ki ke hangen zaki samu a aikatau. Kin zaɓi yin aikatau a wata ƙasa akan zama da yaranki…..” Baba ta dakata yana gyaɗa kai, ya ɗago ya sake kallon ta ya ce, “Kamar yadda na faɗa miki, indai ki ka zaɓi barin ƴaƴanki ki ka tafi neman kuɗi Saudia, ni kuma na rantse baza ki bar ƙasar da aurena kan ki ba. Ki tafi saudia, amma ki sani, na sake ki Maimuna!." Wata irin ƙara Safeera ta yi, tana ɗora hannu a kanta cikin gigicewa da tashin hankali. Su Umma za a tafi aiki, sai mu ce Allah ya sa a dace.😁😁 [6/30, 9:54 AM] KRBBK: RDB2P26 Nana Haleema. Islaha haka take yin komai a sanyaye, ji take kamar ta cewa Mama ita ta fasa tafiyar, gabaɗaya tafiyar ta fita daga ranta, daman ba a ran nata tafiyar take ba lallaɓawa kawai take yi. Amma yanzu da tafiyar tazo sai raunin ya yi mata yawa, ta sake zama mai rauni sosai. Tana ganin Labiba sai hidima take yi tana shiga ta fita, harda su yin sabon kitso. Ita dai kallon ta kawai take yi, zuciyarta tana saƙa mata abubuwa da yawa, tana ji da tana da dama da iko zata fasa tafiyar da ta yi niya, dan Allah ya gani gabaɗaya tafiyar ta ta fita daga ranta ko kaɗan. Ranar ko asibiti basu je ba, suna gida suna hidimar tafiya. Islaha tunda ta dawo daga wajan aiki ta kasa yin komai, tana zaune sai dai ta kwanta ta tashi ko kayan ta kasa haɗawa. Jikinta ya yi sanyi, ta rasa abinda yake yi mata daɗi, komai ya tsaya mata cak, bata jin daɗin duniyar gabaɗaya. Buɗe ƙofar da aka yi hakan ya saka ta ɗago ido ta kalli Labiba da har wanka tayi, ta shirya cikin doguwar riga kuma tayi mata kyau sosai. Ta bi Islaha da kallo ganin babu alamun shiri a tare da ita ta ce, "ke bama ki shirya ba kenan, jirgi dai ha mota bace balle a jira ki. Gashi nan in ji Mama, ki saka mata a kayan ki" ta faɗa tana cilla mata kayan ta fita ta barta. Islaha ta sauke numfashi ta miƙe a sanyaye, ta buɗe kayanta tana kallo ta kasa taɓa komai balle ta san abinda zata ɗauka. Kamar mara jini haka ta dinga jawo kayan tana zubawa, ita kanta baza ta ce ga abinda take zubawa ba, kawai ta san ta saka dogayen riguna da hijjabai. Tana gama zubawa ta zauna a kan gado ta yi tagumi, ta rufe idanunta ta rasa abinda yake yi mata daɗi a lokacin. Tana zaune Mama ta shigo tana faɗin, "Yauwa Islaha kizo kuci abinci, motar tafiya Abuja tana jiran mu, gabaɗaya zamu tafi sai kun tashi sai mu dawo." Mama ganin yanayin Islahan sai ta bita da kallo mamaki ta ce, "ke jirgi ne fa ba adadaita sahu ba ne, akwai tafiya miƙaƙƙiya a gaban mu, daga nan Abuja zamu wuce ba jimeta ba. Ki tashi ki shirya, dan wallahi in ki ka rasa jirgi kamfani bai san asara ba, sai kin biya abinda aka kashe miki." Islaha ta ɗaga kawai bata ce komai ba Mama ta fita ta barta. Bata an shigo ba, kawai ji ta yi an faɗo kanta ana kuka, a firgice Islaha ta kalli Safeera da ta rungume ta tana kuka mai tsuma zuciya. Islaha cikin tashin hankali da tsoro ta ce, "lafiya Safeeraa, me ya faru ki ke kuka haka?." Safeera bata yi magana ba sai kuka da take yi mai sauti, Islaha ta yi shiru ta bar ta tana kuka, dan itama haka kawai take ji tana da buƙatar zubar da hawaye. Taso ace tana da iyayen da zasu hanata abinda take niya, taso ace tana da uwa ko uba da zasu yi rantsuwa su ce baza ta je ba kamar yadda Baba ya hana Safeera zuwa. Amma ita bata da kowa, ita kaɗai take yanke hukuncin da ya yi mata a zuciyar ta, ita kaɗai take saƙawa kuma take warwarewa. Safeera sai da ta gaji da kukan sannan ta koma jan numfashi, islaha ta bata ruwan da yake kusa da ita ta ce, "ki sha." Bata ƙi ba ta karɓa ta sha tana sauke numfashi. Islaha ta ce, "me ya faru?." Safeera ta ce, "Islaha Umma da Baba." "Me ya faru?." "Ashe da Umma zaku yi tafiyar nan?." "Na sani Safeera, ban faɗa miki bane dan babu amfanin na ɓata miki rai. Amma na san da Umma za a yi tafiyar tun ba yau ba." Safeera ta goge hawaye ta ce, "Islaha ni kaɗai na san abinda nake ji a raina. Baba ya hana Umma tafiyar nan, har Yayanta na Katsina ya kira har gida ya zo ya hanata. Amma ga Umma can ta haɗa kaya zata taho gidan nan. Islaha...." Sai ta kasa magana tana jan nunfashi cikin ƙunar rai da ɓaci mai yawa. Islaha cikin rauni ta ce, "Ki yi haƙuri Safeera." "Islaha Baba ya saki Umma!." Gaban Islaha ya yanke ya faɗi, ta dafe ƙirji cikin kiɗima da tashin hankali ta ce, "Saki Safeera!." Ta ɗaga kai ta ce, "Daman ya ce mata indai zata bar ƙasar nan to babu aurensa a kanta, a gaban idanuna Baba ya cewa Umma ya sake ta. Islaha ji nake kamar ana gasa zuciyata wallahi, me Umma ta nema ta rasa a duniyar nan, me zai kai Umma wata ƙasar aiki don Allah!?." Islaha ta shafa bayanta ta ce, "ki yi haƙuri, babu amfanin ɓacin ran tunda ta riga ta aikata. Ki kwantar da hankalin ki, kar damuwar ta saka miki ciwo." Safeera ta ce, "ni kaɗai na san me nake ji Islaha. Yanzu in Umma ta tafi ya zanyi?. Bakyan nan itama bata nan, ina zan saka raina naji daɗi? Wajen wa zan dinga kai damuwata? Babu ke babu ita, ina zan saka raina....." ta kasa ƙarasawa saboda kuka, muryar ta tana rawa ta cigaba da cewa, "Waye zai dinga yiwa Baba abinci, waye zai dinga kula da Baba in na tafi wajan aiki?." Hawaye ya sakko daga idanun Islaha, cikin raunin murya ta ce, "shiyasa nake cewa ki yi haƙuri, in ki ka cigaba da damuwa ke zaki samu matsala." "Sai da ta ga lokaci ya ƙure, babu damar na faɗawa danginta, dan tasan kafin su zo ta tafi. Na kira Abban Katsinan na faɗa masa, amma na san wallahi Umma bazata saurare sa ba. Mama Atika ƙawarta ce take zugata, duk abinda take yi wallahi itace take saka ta. Kuma da ba haks Msma Atika take ba, tana da kirki, ban ssn me ya canjata haka ba.” Islaha dai bata ce komai ba, Safeera ta riƙe hannunta ta ce, "zan zama marainiya ta ƙarfi ta yaji, babu Umma, kema babu ke, babu inda zan saka raina na ji daɗi....." hawaye ya sakko mata ta ce, "da na san haka zai faru dana amince na rarrashi Baba ya amince nima naje, da Umma tana gida, sai tafi nida ke." Islaha ta share mata hawaye ta ce, "ki yi haƙuri, nima kin san ba a son raina zan je ba, kin fi kowa sanin dalilina na tafiya." "Islaha ga Ummata nan, na bar amanar ta a hannunki...."sai ta kasa magana sai kuka. Islaha ma ta ɗora kanta a bayan Safeera tana kuka mai taɓa zuciya. Cikin kuka Safeera ta ce, "Don Allah ki kula da ita, in kin ga zata kauce hanya ki dawo da ita madaidaiciya. Ki ba wa Umma kulawa don Allah, ki dinga bata shawara kina nuna mata abinda ya kamata. Kin san dai ya ake faɗar aikin nan, don Allah ki kula min da uwata, kar ki bari ta aikata wani abun da zai zamar mana tabo har ƙarshen rayuwarmu!." Islaha gyaɗa kai kawai take yi tana kuka ta ce, "zan yi Safeera, zan yi iya abinda zan yi. Ki daina kuka, ki taya mu da addu'a Allah ya sa mu faɗa hannu na gari." Safeera taja numfashi irin na wacce ta yi kuka ta ce, "bani da kowa yanzu, kin tafi, Umma ma ta tafi, zan zama marainiya. Allah ya kiyaye ku, Allag ya nisanta ku da haram, ya kusanta ku da halal." "Amin Safeera. Zan dawo, zan dawo mu cigaba da rayuwa kamar yadda muka fara. Ki ta yi mana addu'a kawai, zamu cigaba da magana a waya. Sannan zan bar amanar su Zainab a hannunki, na bar miki amanar su, don Allah ki kula da su, musamman Zainab. Tana cikin matsala, tana buƙatar mai bata shawara, tana buƙatar mai rarrashinta. Kema kin san akwai case a kanta, ki bibiyi case ɗin, duk abinda ya faru ki dinga faɗa min. Akwai abinda nake tunani kuma nake hange a kai, ki tabbatar da komai ya tafi yadda ya kamata, kar ki bar tabiyyar Zainab ta lalace kamar yadda Hafsa ta lalace. Don Allah ki kula min da ita, ina son Zainab kamar ƙanwata ta jini." "Zan yi Islaha, in kina ganin zai yu zan iya yiwa Baba mu ɗauko ta kawai ta dawo gidanmu da zama, in sha Allah bazan bari ta yi kukan maraicin ki ba. Sannan duk abinda zai faru zan bibiya kamar kina nan, duk abinda na samu zan dinga sanar miki in sha Allah." Islaha ta goge hawayenta ta riƙe hannunta ta ce, "Na gode. Zan yi magana da Barr Suraj in na je, komai zai tafi kamar ina nan in sha Allah. In kina fa kayan bayarwa, ki haɗawa Zainab ɗin ki bata.” A lokacin Mama ta shigo ta bi su da kallo ta ce, "To a taso zamu tafi, ki ɗauko wannan takardar gwajin da nace ki yi. Ke Safeera zaki raka babar ki Abujan ne?." Safeera dai bata ce komai ba, ta goge ido tana riƙe da hannun Islaha kamar yadda take riƙe da nata cikin kewar juna. A sanyaye Islaha ta miƙe ta wanke fuskarta, ta buɗe handbang ɗinta ta ɗauki sabon facemask ta saka, ta yi rolling kanta da mayafin abayar da ta saka. Safeera ta miƙe ta jawo mata jakarta, kanta yana sarawa saboda kukan da ta yi a haka suka fito falon. Da Umma suka haɗa ido, Safeera ta bi Umma da kallo kamar yarda take kallonta. Umman ta zama wani iri, jikinta a sanyaye yake matuƙa, ta zubawa Safeera ido tana kallonta cikin wani irin yanayi mai wahala fassarawa. Safeera ta ɗauke kai daga kallon Umma, ta riƙe hannun Islaha, itama Islahan kallon Umma take yi da take a zaune cikin shirin barin ƙasa. Mama da take ta shige da fice ta kalli Safeera ta ce, "dake za a yi rakiya zuwa Abuja ɗin ne?." Safeera ta girgiza kai, ta kalli Islaha muryar ta a shaƙe ta ce, "Islaha zan tafi." Tare suka fara takawa zuwa harabar gidan, Islaha ta riƙe hannun Safeera cikin rarrashi ta ce, "baki yi sallama da Umma ba." Safeera ta goge hawaye ta ce, "babu amfanin sallama da ita Islaha, ta zaɓi duniya sama da mu, ta zaɓi aiki akan mijinta, ta zaɓi ta bar mu taje inda bata sani ba. Ta je kawai, ba sai mun yi sallama ba." "Amma hakan ba daidai bane, ko meye ya fari kar ki manta uwace ita, ya kamata ki tuna hakan." Safeera ta sauke numfashi ta ce, "Islaha itama bata da buƙatar magana dani, da zata yi magana dani da...." "Safeera!." Umma ta kira ta tana daga bayan su, hakan ya dakatar da Safeera daga maganar da take yi. Safeera ta runtse ido hawaye ya sake wanke mata fuska, ta juya ta kalli Umma da take tsaye, Umma  ta ƙaraso ta ce, "zan tafi Safeera, ki kula da kanki da ƙannen ki." Safeera kasa magana tayi bata ce komai ba, Umma ta shafa fuskarta ta ce, "duk abinda zan yi zan yi shi ne saboda ke, zan yi ne saboda rayuwar ku keda ƙannenki. Na fi kowa sonku a duk duniya, duk wanda zai so ku a bayana yake. Zan dawo nan ba da jimawa ba, ki kula da kanki" daga haka ta juya a sanyaye ta koma. Safeera ta yi murmushin takaici bayan Umma ta ɓace ta ce, "ki ji wai saboda mu take yi, mu mun sakata, mun ce muna buƙata ne?." Islaha bata ce komai ba, dan ta lura in ta tanka zata iya jawowa Safeera ta faɗi wata magana wacce bata dace ba akan Umma ba, ita kuma ba haka take da buƙata ba. A hankali suka ƙarasa bakin gate, Islaha ta rungume Safeera ta ce, "Zan yi kewar ki Bestie." "Nima zan yi kewar ki Islaha. Allah ya kare ki a duk inda ki ke, ya yi miki abinda ki ke so. Allah ya sa tafiyar nan ta zama alkhairi a gare ki." "Amin Ƙawata, na gode." Safeera ta raba kanta da ita ta ce, "Allah ya sake haɗa fuskokin mu cikin alkhairi." "Amin Safeera. Sai mun yi waya." "Ki saka kati sosai, an ce ana jan kuɗin kiran waya." "Zan yi." Ta gyaɗa kai ta saki hannun Islaha ta fita daga gidan a sanyaye. A haka Islaha ta koma ciki a sanyaye, ta tarar duk sun miƙe tsaye ana niyar fitowa, tana shiga Hajiya Karima ta ce, "ki ɗauko kayanki da hanzari, daga nan fa Abuja muka y, tafiya cs miƙaƙƙiya a gaban mu." Islaha ji take kamar ta ce musu ita fasa, amma in ta tuna bashin da yake kanta sai ta daure ta kawar da komai daga ranta. A sanyaye ta ɗauko handbag ɗinta, ta jawo trolly bag ɗin ta fito da ita, ta samu duk suna ƙofar gidan gida, ga wata mota mai ɗan girma wacce zata kwashe su gabaɗaya. Aka saka jakar Islaha a booth, Islaha ta kalli ƙofar gidansu Safeera ta ganta a tsaye, ta ɗaga mata hannu itama ta ɗaga mata, hawaye ya sakkowa Islaha, ta share hawayen ta buɗe motar ta shiga aka ja motar suka bar unguwar. Nana Haleema. [6/30, 9:54 AM] KRBBK: RDB2P27 Nana Haleema. Ikram kwance a bedroom ta zubawa hotonsa ido tana kallo cikin shauƙi da soyayya. Hoton ya yi matuƙar kyau, yana sanye cikin manyan kaya, ya saka hula, kwantaccen gashinsa ya sauka a bayan wuyansa. Ya ɗora hannunsa ɗaya akan hannun kujera, ya yi murmushi mai ƙayatarwa. Duk wanda ya kalle sa sai ya so ya sake kallo, dan iya ganin hotonsa kaɗai ma wata dama ce da ba kowa ne yake samu ba. A bayyane Ikram ta ce, "yana da kyau, ilimi, kirki, wayewa. Ban damu da kuɗin da yake dashi ba, amma ni dai ina sonsa. Ina ƙaunar Hamma Rehaan, ina mafarkin ya zama mijina, ina so na rayu dashi har ƙarshen rayuwata.” "Wa ki ke so?." A bazata ta ji tambayar, hakan ya saka ta firgita ta juyo da sauri tana kallon Mummy da ta zuba mata ido tana kallon ta cikin tuhuma, Ikram ta sunkuyar da kai tana miƙewa zaune. Mummy ta ƙaraso ta zauna kusa da ita, ta saka hannu ta zare wayar hannunta tana kallon fuskar wayar dan ganin wanda take kallo tana cewa tana so har haka. Ganin hoton wanda take kallo ya saka ta kalle ta, cike da mamaki da ɗaure kai, a sanyaye ta ce, "Rehaan ki ke so Ikram?." Ikram ta shagwaɓe fuska tama ɗaga kai ta ce, "eh Mummy." "Tun yaushe?." "Nima ban sani ba." Mummy tayi ajiyar zuciya cikin damuwa ta ce, "to meye na ajjiye maganar a ranki, meyasa baki faɗa min ba?." Ikram ta yi shiru bata ce komai ba. Mummy ta sauke numfashi ta dafata ta ce, "Ikram Rehaan yayan ki ne, dan kin so shi ba laifi bane. Amma soyayyar da ki ke yi masa kamar bata kamace ki ba, kin san Rehaan ba wannan soyayyar yake yi miki ba, yana sonki soyayyar ƴan uwantaka ba ta aure ba. Saka irin wannan soyayyar a ranki zai iya cutar dake, kin san bazai kalle ki a wannan matsayin ba.” Hawaye ya sakko mata, ta ɗago ta kallo Mamy ta ce, "Na sani Mummy, ina so na koyawa kaina hakan amma na kasa. Yana kallona kamar yadda yake kallon Riyya, yana kallona kamar Janan da Banisha, nasan bazai taɓa kallon a wani matsayi in ba wannan ba. Amma ni kuma ina sonsa Mummy, ina ƙaunarsa sosai, kuma aurensa nake mafarkin yi.” "Kin san baya kallon ki a matsayin wacce zai aura meyasa ki ka fara yi masa irin wannan soyayyar? Ko dan kin ga yana sakar miki fuska?. Kar ki manta kaf cousins ɗinsa da ƴan gidan nan kaɗai yake shiri, kuma ki tuna in ba ke ba babu wacce in ta kira shi kai tsaye zai ɗauka. Kin san Rehaan ba ƙaramin mutum bane, yana cikin matasan da suke da kuɗi a garin nan. Anya ba ki yi gangancin fara sonsa ba?." Ta goge idonta da suka jiƙe da hawaye ta ce, "Mummy ni ba dan kuɗinsa nake sonsa ba, ko bashi da komai zan rayu dashi." "Na sani Ikram, soyayya da ki ka fara yi masa itace illar. Koda Rehaan zai so ki kakarsa baza ta taɓa yarda ya aure ki ba, kin san yadda aka sha wahala da ita kafin ta yarda da auren Jafar da Juwariyya. Inda Rehaan zai yarda dake a matsayin matarsa muna daga cikin mutane na farko da zasu so hakan, bani da matsala da Nadira, na san zata yi farin ciki sosai, mahaifinsa ma zai yi murna da hakan. Amma Kakarsa bazata taɓa yarda, saboda ba ita ta haifi mahaifin ki ba. Kin san kishi take yi da ƴaƴan kishiyoyinta kamar me.” "Mummy ni duk ban damu da wannan ba, indai har zai yarda dani shikenan. Sai ya ɗauke ni mu koma Uk da zama, ba lallai sai na zauna a nan ba." "Ki dage da addu'a kawai, amma bana tunanin Rehaan zai amince ya karɓe ki matsayin matarsa." Cikin kuka Ikram ta ce, "Mumny ki daina yi min baki, wallahi ina son Rehaan so mai yawa, in na rasa shi ban san halin da zan shiga ba.” Mummy ta shafa kanta ta ce, "ba baki nake yi miki ba, na san halinsa ne kawai. Kar ki ga Yayan ki zai auri ƙanwarsa ki ji a ranki kema zai iya auren ki, kowa yana da ra'ayin sa. Rehaan bashi da ra'ayin auren ƴan uwansa, nasan kema kin san da haka. Kafin ke an yi irin ki da yawa amma bai karɓa ba.” "Mummy ai da shima Hamma Jafar ɗin haka yake faɗa, amma yanzu Riyya zai aura." "Na faɗa miki shi daban da Rehaan, abinda zai yi Rehaan bazai yi ba. Ki cigaba da addu'a, in Allah ya amince komai zai wuce." Ikram ta kwantar da kanta a kafadar Mummy tana kuka sosai ta ce, "Amma ina sonsa Mummy, wallahi zan iya cutuwa in ban aure sa ba." Mummy ta shafa kanta ta ce,"shiyasa na ce ki ta addu'a." "Mummy ki faɗawa Mamy, ko zata saka shi ya so ni, tunda yana son abinda Mamy take so.” "Ikram! Ke bakya fatan ya so ki dan kansa sai an saka shi?." "Ni ko bazai kula ni ba, indai zan amsa sunan matar shi hakan ya yi min." Mummy ta yi dariya tana girgiza kai cike da tausayin Ikram ta ce, "Lallai kin yi nisa. Kar ki damu komai zai wuce in sha Allah, ki tashi muje ki ci abinci." “Mummy ki faɗawa Mamyn.” “Zan faɗa mata in sha Allah, zamu tattauna akan hakan.” Zata yi magana Mummy ta ce, "kar ki ce komai, ki tashi muje muci abinci kawai." Ta goge hawayenta suka fito tare da Mummy.       ••••••• Basu isa Abuja ba sai bayan sallar i'sha, kai tsaye aiport aka wuce dasu basu tsaya hutawa ko wani abun ba. Bayan sun fito daga mota, kowa a gajiye yake saboda zama, gashi babu batun hutu wani sabon zaman ne a gabansu. Mama ta kalle su ta ce, "to zamu rabu daga nan, yanzu wanda zai tafi daku zai zo. Da zarar kun isa ku kira mu a waya, ban da saɓa alƙawari." Labiba ce ta ce, "To Mama. Anty Karima sai mun yi waya" ta faɗa ciki ɗauki da zumuɗi. Hajiya Karima ta kalli Islaha da tunda suka taso bata ce komai ba, gwara da suka tsaya a gidan Mai ta sauka ta yi sallah, daga nan bata sake cewa komai ba. Hajiya Karima ta ce, "ba fa haka za ki je kina haɗe musu rai ba, tunda mu ka taho ban ji kin ce komai ba, ya kamata dai ki san irin abubuwan da zaki yi in kin je can. Aiki zaki yi musu su biya ki, dole ki saki jikin ki." Islaha ta ɗauke kai bata ce komai ba, ita sallar magrib da i'sha take so ta yi, ba wannan surutan banzan ne a gabanta ba. Hajiya Karima ta kalli Umma da take duk ta damu kanta kamar wacce aka yiwa dole a tafiyar ta ce, "kar wani abu ya dame ki fa, mutuwar aure ai ba kan ki farau ba, kuma ba kan ki ƙarau ba. Kar ki wani damu wallahi, ki je ki haɗo kan ƴan canjin ki, ki dawo a cigaba da zama. Sai me dan ya sake ki? In ki ka samu kuɗin ki ba sai ki yi wani auren ba?." Umma cikin rauni ta ce, "Aure kuma?." "To wuce auren ki ka yi? Nawa ki ke?." Mama ta ce, "mata ne da ɗorawa kansu fitina walllahi, ni ban ga abin ɗaga hankali dan ya sake ki ba. Kina da yarinyar da zata kula da ƙannenta ba, shikenan an huta ba. In ni ce ita, wallahi a saudian zan ɗaura aure, dan na nuna masa baya gabana. In ka nunawa namiji ka damu dan ya sake ka ba ƙaramin raini bane, komai ace saboda ƴaƴa, na rasa lokacin da mata zasu waye su daina kallo ƴaƴa su kama gabansu.” Umma dai ta kasa magana, ɗauki da zumuɗin da take yi gabaɗaya ya kau daga zuciyarta, da tana da iko a lokacin tabbas da ta koma gidan mijinta ta cigaba da zama ita da yaranta, amma lokaci ya ƙure. "Salamu Alaikum. Hajiya Karima da Hajiya Zulai barkan ku da zuwa." Ganin wanda ya yi maganar sai suka washe baki, cike da girmamawa Mama ta ce, "Barka dai, mun same ku lafiya?." Ya yi murmushi ya ce, "Lafiya lau. Ya hanya?." "Hanya alhadu lillah." "Waɗannan ne?." Mama da Karima harda saurin haɗa baki wajan cewa, "Eh sune." Ya bisu da kallo yana nuna Islaha da Labiba ya ce, "kai amma waɗanan sun yi, zasu yi daidai da gidajen da ake nema. Gaskiya kun yi aiki mai kyau, daga gani baza a sha wahala dasu ba wajan turanci." Mama cikin son gwaninta ta ce, "ita fa wannan ƴar jarida ce, babu wanda bai santa a Yola ba. Kaima na san zaka iya saninta, tunda yanzu a waya ake sanin mutane." Hajiya Karima ta cafke ta ce, "ai indai ɓangaren turanci ne an bar mata kayanta." Ya yi dariya yana girgiza kai ya ce, "ƙwarai ina ganin fuskarta a waya. Irinsu ake so, wanda za a iya magana dasu da turanci. Dan gidan da za a kai ta likita ne, yana jin turanci sosai, ba lallai sai ta iya larabci ba......" ya ɗan kalli Umma ya ce, "Amma wannan zata iya kuwa?." Ya faɗa yana nuna Umma. Hajiya Karima ta ce, "Me zai hana Oga?." "Da gani babba ce, babu lallai a samu wani yare akan harshen ta. Kun san yanzu gidajen aikin nan basa ɗaukar waɗanda basa jin larabci ko turanci, kuma daga ganin wannan bata jin ko ɗaya. Dama dai kamar waɗannan ɗin ne, an fi buƙatarsu." Mama ta ce, "lah itama ta iya turancin ai, kawai dai yaran sun fita ne. Amma babu abinda baza ta yi ba." Ya gyaɗa kai yana kallon Umma dan shi bata yi masa ba, yafi so a kawo yara kamar su Islaha, baya so aje ta zamar masa kaya, ai ta yawo da ita ba a samu abinda ake so ba. Ya kalle su yana ɗaga kai ya ce, "Sun san komai dai ko? Sun san tsari da kason kamfani?." Mama ta ce, "sun sani, duk mun yi musu bayani yadda ya kamata. Mun faɗa musu albashi za a kasa gida uku, mu ɗauki biyu su ɗauki ɗaya. Duk na karanta musu." Ya ɗaga kai ya ce, "dakyau!. Ban da sata, gulma da komai duk kun faɗa musu?." "Duk sun sani, mun tabbatar baza su yi aikata ba." "Yanzu jirgin na su ya sauka, mu je a auna kayan kafin a fara boading. Ku yi sallama, dan baza su bar ku shiga ba. Zulai bani takardun nan.” Mama ta miƙa masa, kafin ta ta kalli Labiba ta rungume ta ta ce,"Saduwar alhairi ɗiya ta gari, Allah ya kiyaye ya bada nasara. Kin san gargaɗina, ban da zubar da mutunci." Ta yi fari da ido ta ce, "zan yi kewar ki Mama." Mama ta ce, "nima haka." Ta kalli Islaha ta ce, "Islaha sai an dawo, Hajiya Maimuna saduwar alkhairi." Duk suka yi musabaha kafin su fara tafiya ciki a hankali, Labiba ce kaɗai take murna amma Islaha da Umma kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki a haka haka suka ciki. Basu sha wani wahala ba dan ba kaya ne sosai a ciki ba, aka gama auna kayan aka basu tag aka tafi boarding room. A nan Islaha ta ga akwai banɗaki, bata yi duhun kai ba ta yi alwala ta yi sallolin da suke kanta. Ganin tayi ya saka Umma ma ta yi, suka dawo suka yi jugum suna kallon jirgi ta glass ɗin da yake gabansu. Basu jima ba aka fara shiga jirgi, wanda yake tare da su ya ce, "mu je." Ba musu suka miƙe a sanyaye suka fita daga wajan suna takawa kamar basa so. Labiba ce take ta video da selfie, su kuwa a hankali suke takawa cikin wani yanayi. Lokacin da suka shiga jirgi ganin abun suke yi kamar a mafarki. A econamic class suke, kujeru huɗu ne, Islaha ce a ciki har ta tana kallon Window. Sai Umma a kusa da ita, sai Labiba sannan shi. Duk sun yi shiru babu wnada yake magana, Islaha ta kunna data ta turawa Safeera cewa sun shiga jirgi. Ba jimawa aka rufe jirgi, aka fara yi musu bayanin da komai da komai na mintina ashirin, daga nan aka kunna jirgi ya fara juyawa a hankali. Islaha ta runtse ido lokacin da jirgin ya fara gudu, ta riƙe hannun kujerar lokacin da ya ɗaga ya lula zuwa sararin samaniya, tana ji kamar jirgin ya ɗaga da duk wani burinta na duniya….. Safe flight mutanen Saudia🙌🏻❤️ [6/30, 9:54 AM] KRBBK: RDB2P28 Nana Haleema. Safeera tunda ta koma gida take kuka, ƴan uwan Umma suna tayi mata waya suke yi amma ta ƙi ɗauka, a ganinta babu amfanin ɗaukar tunda dai Umma ta riga ta tafi. Tana tsaka da wannan tunanin ƙanenta suka dawo, Rukayya ta shigo a hankali ta ce, "Adda Safeera baki da lafiya ki ke kuka?." Jin muryar ƙanwata ya sake karya zuciyar Safeera, ta cigaba da kuka babu ƙaƙƙautawa. Yaran duk suka zageye ta suna kallo, Ruƙayya ta ce, "Adda ki daina kuka, naga Umma bata nan, bara na faɗawa Baba baki da lafiya" ta faɗa tana miƙewa ta fita. Babu jimawa suka dawo da Baba, ya tsaya daga bakin ƙofa yana kallon ta cikin tausayawa sa karayar zuciya ya ce, "Safeera!." Jin muryar Baba ya saka ta ɗago fuskarta ta yi kaca-kaca da hawaye. Baba ya bita da kallo ya ce, "ki bar wannan kukan, ki yi haƙuri ki tashi ki rarrashin ƴan uwanki. Ke ce uwa a gare su a yanzu, shigar ki damuwa zai dame su. Ki daure ji kawar da duk abinda yake damun ki, ki zama jaruma ko dan saboda su." Rukayya cikim mamaki ta ce, "Baba Umma bata nan ne?." Ya kalle ta ya ɗaga kai ya ce, "Umman ku tayi tafiya, kuma zata jima bata dawo ba." Humaira mai biye mata ta ce, "Katsina ta tafi Baba?." Ya girgiza kai ya ce, "Umman ku ta ɗan yi nisa da ku, zata kwana biyu bata nan. Ku kwantar da hankalin ku, zaku dinga waya da ita in sha Allah." Rukayya gabanta ya faɗi, dan sai take ji kamar Umman mutuwa ta yi ta ce, "Baba ina ta je?." Ya kalle ta a tausashe ya ce, "kar ki damu, zo ki dafa muku abinci dan ko girki ba a yi ba. In akwai abinda babu ki faɗa min sai a siyo." Rukayya ta fito a hankali ƙannenta suka biyo bayanta cikin damuwa mai tsanani. Baba ya kalli Safeera bayan sun fita ya ce, "ki bar wannan kukan kar ki jawowa kan ki ciwo, kukan ki bazai saka babar ki ta dawo ba tunda ta yi niya sai ta yi. Ki kwantar da hankalin ki, babu abinda zai faru in Allah ya yarda. Tafiyar ta babu abinda zata rage daga cikin farin cikin gidan nan, dan ta tafi ba hakan yana nufin mun daina walwala da farin ciki ba, zamu cigaba da yin komai kamar yadda muka saba in sha Allah. In kina zama a haka ya ƙannen ki zazu kasance? Ke kin samu sallama da ita, su kuwa basu san ma zata tafi ba sai yanzu." "Rukyya zargi take yi kamar babar ta ku mutuwa tayi aka ɓoye musu. Sai kin saki jiki kina walwala sannan suma zasu sake, in kina a cikin damuwa suma zasu shiga damuwa. Ke ce babba, duk halin da suka ganki a ciki suma a ciki zasu kasance. Safeera ta goge hawayenta ta ce, "To Baba." "Mun yi waya da mutanen Katsina, sun ce suna ta yi miki waya bakya ɗaukar wayar. Ki ɗauka ku yi magana, rashin ɗaukar wayar zai dame su sosai. Ko kin ɗauka ko baki ɗauka ba Maimuna ta tafi, gwara ki ɗauka ku yi magana dasu." Safeera ta kuma ɗaga kai ta ce, "zan ɗauka Baba." Baba ya ce, "Yauwa. Ki fito wajan ƴam uwanki ku dafa abinci ku ci, ba sai kun ajjiye min nawa ba, bana jin yunwa. In akwai abinda za a siya sai ki faɗa min." Hawaye ya sake sakko mata, ya bita da kallo ya ce, "ki daina kuka, ki ɗauka kamar taje Katsina ta dawo ne, kin ji?." Ta ɗaga kai alamun to Baba ya juya ya fita. Sai da ta jima a zaune sannan ta fito, ta tarar har sun gama jollop ɗin taliya sai ƙhamshi take yi. Rukayya ta bita da kallo ta ce, "Adda mun gama, kizo ki ci." Ta girgiza kai tana zama a kan kujera ta ce, "bana ci Ruky, ku ci kawai." Rukayya ta yi sak tana kallon ta, cikin sanyin jiki ta ce, "Adda don Allah me ya faru?." Safeera ta lumshe ido ta buɗe ta ce, "Babu komai, ku ci abinci kawai." Rukayya ta zauna suna ci a tray ɗaya, basu jima da fara ci ba Safeera ta miƙe ta shiga ɗaki. Rukayya ma ta tsame hannunta bi bayanta, ta same ta a tsaye a ɗaki ta ce, "Adda don Allah ki faɗa min abinda yake faruwa, ki taimaka min ki sanar dani hankalina ya kasa kwanciya wallahi." Safeera ta kalle ta ta ce, "Rukayya Umma ta tafi saudia aiki, ta bar gidan nan bamu san ranar dawowar ta ba." Rukayya ta ce, "Yanzu sai da Umma ta tafi?." Safeera ta ɗaga kai ta ce, "Ta tafi Ruky. Ki je ku cigaba da cin abincin saboda su Aysha." Rahma jikinta a sanyaye kafin ta ce, "To wa ta bari wanda zai dinga kula da Baba?." Safeera ta ce, "Umma bata yi wannan tunani ba ta tafi. Mu kwantar da hankalin mu, tunda Baba yana nan komai zai zo mana da sauƙi." "To Adda ta ya hankalin mu zai kwanta kina nan kina nan kuka? In baki kwantar da hankalin ki ba mu ma hankalin mu bazai taɓa kwanciya ba." Safeera ta yi ajiyar zuciya ta ce, "kaina ne yake ciwo, magani zan sha zuwa anjima zan dawo mu zauna mu yi hira." "to Adda, Allah ya ƙara lafiya" ta faɗa tana fita a sanyaye. Ba jimawa ta dawo, ta kalli Safeera ta ce, "Adda Abba na Katsina yana son magana dake." Safeera ta buɗe iso ta yi mata alama da ta ce bacci take yi. Rukkya ta juya ta fita Safira ta kwanta, bata ga amfanin magana da dangin Umma ba tunda dai Umma ta riga ta tafi balle su dakatar da ita, shiyasa babu da wanda zata yi magana, kowa bata buƙatar magana dashi tunda maganar bazata dawo mata da Umman ta ba. •••••••• *KING ABDULAZIZ INTERNATIONAL AIRPORT JEEDAH.* Awansu shida da rabi a sama suna tafiya, Islaha tunda aka tashi bata iya motsi ba, abincin jirgin ma bata iya ci ba, cake kaɗai taci sai ruwa. Ƙarfe shida na safiyar Saudia suka garin Jeddah. Dukkansu suna bayansa suna tafiya a hankali, sai da suka ƙaraso wajan da za a buga musu stamp sannan ya kalle su ya ce, "ku je ku hau layi, ga wannan ku miƙa musu." Basu musa ba suka hau layi suna kallon wajan cikin burgewa. Kaf ma'aikata mata ne, wasu sun rufe fuska da niƙab wasu kuma fuskar su a buɗe. Sai larabci suke yi, ga mutane mabanbanta ana ta kai kawo a wajen, komai nasu very neat babu dauɗa ko ƙazanta. Islaha ta ƙarasa ta miƙa passport ɗinta, matar ta karɓa Islaha ta bugawa Islaha Stamp ɗin shiga Sauida bayan ta yi thumb print, Islaha ta koma gefe ta tsaya tana jira a gama dasu. Ba jimwa suka tafi wajan da zadu ɗauki kayansu. A lokacin ya kalle su ya ce, "in kuna da kayan siyarwa a cikin jakukunan ku zasu iya ƙwacewa a wajan nan, ku nutsu kawai." A hankali suka wuce cikin ikon Allah babu wanda aka buɗewa kayan har suka fita dags screnning ɗin. Bayan sun fita ya juyo yana kallon su ya ce, "wannan rumfar zamu shiga, in kuna da kayan siyarwa akwai waɗanda zasu siya. In an gama sai mu tafi." Labiba dai kallon wajan take yi cikin burgewa, mamaki take yi wai itace a ƙasar Saudia cikin garin Jeddah. Larabawa suna ta kai kawo, tana ta jin yadda suke yarensu abin yana sake burge ta. Ta ce, "eh akwai kayan Mama, nima kuma ina da kaya." Ya nuna musu ciki ya ce, "mu shiga ciki ku huta, sai a siyar da kayan." Islaha dai ta kasa magana, a sanyaye suka ƙarasa ciki suka zauna. Abinda ya bawa Islaha msmski jin suna ta hausa kamar ba a Jeddah suke ba, sai a lokacin ta lura duk hausawa ne masu zaman can. Labiba ta kalli Islaha ta ce, "kin ja kin zauna kin yi tagumi, kin san akwai kayan Mama a kayan ki." Islaha ta sauke numfashi dan ita ta manta, ta buɗe ta ɗauko ta miƙawa Labiba bata ce mata komai ba. Tana ji suna ciniki da mutumin, aka gama aka basa kuɗin, Oga Musa ya ce musu zai turawa Mama naira shi zai riƙe riyal ɗin. A nan suka yi sallar asuba, bayan sun idar basu jima sosai ba suka miƙe suka fito zuwa harabar wajan. Sai ga watsu mata su biyu sanye da abaya baƙa, ta rufe fuskarsu da niƙab kamar yadda suka saba ganin larabawa. Suna ƙarasowa inda suke suka ɗaga niƙab ɗin, duk suka bita da kallon ganin hausawa ne ce kamar su, sai dai sun sha bleaching har wani yellow suke yi, kuma kana ganin su ka ga waɗanda ta waye a harkar zaman Saudia. Ɗaya ta bisu da kallo tana tauna chewing gum su ta ce, "Sannun ku da zuwa." Suka amsa kafin ta kalli mutumin suka canja yare zuwa larabci suna gama. Sun jima suna magana kafin ya kalli Islaha da Labiba ya ce, "Ku zamu tafi tare daku, gidan da zaku zauna a nan gari yake ba sai an je Makka ko Madina ba. Amma Hajiya ke a Madina gidan aikin ki yake, zaku tafi da wannan zata kai ki har gidan da zaki yi aikin." Duk da tunda suka taho Umma bata cewa Islaha komai ba amma sai jikinta Islaha  ya yi sanyi, ta kalle sa ta ce, "me zai hana itama baza a barta a nan ba? nafi so a haɗa mu waje ɗaya tare." Oga Musa kalli Islaha ya ce, "Ya sunan ki ma?." "Islaha." "Islaha gidajen aikin da aka samu a nan Jeddah gida biyu, kuma kamar ku ake buƙata ba mai shekarun ta ba. Inda zata je a Madina shine daidai ita, kuma gida ne da zata ji daɗinsa sosai." Islaha ta kalli Umma da bata ce komai ba, matar tayi dariya ta ce, "Kar ki damu Islaha, duk zaku saba fa. Da kun saba dan ki ɗauki ƙafa daga Jeddah kin je Madina abu ne mai sauƙi. Kawai dai duk inda zaku je ku dinga tafiya da passport ɗinku kafin visa ta ƙare. Visa shekara ɗaya aka yi muku, zaku jima kuma zaman yanci a ƙasar nan." "Abinda zan ja hankalin ku a akai shine, Ku ku ji sata, babu ruwansu da ba yan ƙasa bane sai an yanke muku hukunci wallahi. Ku guji abubuwa saɓawa doka, wallahi ku ka aikata a gidan yari zaku ƙare rayuwar ku, in hukuncin kisa ne ya hau kan ki kashe ku zasu yi wallahi. Gidan da za a kai ku manyan gidaje ne, sai kun yi taka tsantsan." Suka amsa cikin gamsuwa da bayanan su.Labiba cikin iyayi ta ce, "in Allah ya yarda zamu yi komai yadda ya kamata." Matar ta kalle ta ta ce, "da alama baza ki bamu kunya ba, na gan ki a waye kamar kin taɓa zuwa." Labiba ta yi farr da ido jin an yabe ta, tana ta murmushi cikin jin daɗi. Ɗayar da suke tare ta ce, "Ku mu je safiya yana yi, mu da zamu ɗauki hanya ma mune abin ji." A hankali suka fara tafiya, suka iso bakin titin airport ɗin. Hajiyar ta kalle su bayan ta tsayar da mota ta ce, Mu mun wuce Madina sai kun ƙaraso." Ta kalli Umma ta ce, "Hajiya muje." Islaha ta kalli Umma, itama ta kalle ta Islaha ta ce, "Allah ya kiyaye Umma." Umma ta ce, "amin." Daga haka Umma da Hajiyar suka shiga mota suka ɗauki hanyar Madina. Oga Musa suka gama magana da ɗaya matar ta tafi, shi kuma kalle su ya ce, "yanzu zamu wuce gidanjen da zamu je. Labiba da Islaha, ina sake jan kunnen ku ban da ƙazanta, ban da sata, ban da gulma." Ya faɗa yana tsayar da moyar ya faɗawa driver inda zai kai su. Bayan sun gama ciniki, aka saka kayansu a booth, ya shiga gaba Islaha da Labiba suka shiga baya suka fara tafiya. Duk safiya ce ko ina cike yake da haske da mutane, Islaha tunda ta kalli titi sau ɗaya bata sake kallon titi ba ta sunkuyar da kai tana ji ana tafiya amma ta kasa ɗago kanta. Tana kallom Labiba tana ta hotuna, ita kuwa ba ta wannan take ba, yanayinta gabaɗaya babu daɗi tana ji kamar zuwan bazai zama alkhairi ba. Sai da motar su ta tsaya sannan Islaha ta ɗago a hankali tana kallon estate ɗin da suke a tsaye. Ki ina na unguwar tas, gashi shiru babu alamun mutane, ga sanyi unguwar kasancewar ta a kusa da teku. Motoci kaɗan-kaɗan ne suke wucewa, ko ina ya yi tas dashi kamar kar ka daina kallo. Oga Musa ya nuna musu gidajen ya ce, "waɗanan sune gidan da zaku yi aiki. Ya sunan ki ma?." Ya faɗa yana kallon Labiba da ta saki bakin da hanci tana kallon gidan da ya nuna zasu shiga kamar wanda take gani a film. Ganin bata ji ba sai ya sake cewa, "ke dake nake fa." Labiba ta yi sauri ta ce, "Labiba sunana. Wannan gidan na tsakiya shi zamu shiga? Na gan shi mai kyau, har yafi waɗannan kyau." Oga Musa bita da kallon sama da ƙasa, dan ya lura tana da rawar kai sai ya ja mata kunne ya yi mata gargaɗi zata shiga hankalinta. Ya ɗaure fuska ya ce, "ki adana wannan rawar kan na ki, ki nutsu ki san abinda ki ke yi. Wallahi ki ka aikata wani abun ba daidai ba kama ki zasu yi. Nan saudia ce, in hukuncin kisa ne ya hau kan ki kashe ki zasu yi, ba cin hanci ake basu ba balle su sake ki. Ki kula da tsarikan gidajen, zasu faɗa miki tsarikansu, kuma dole ki bi, in ba haka ba kece a ruwa." Labiba sai ta ɗan nutsu ta kalle sa ta ce, "zan kiyaye in sha Allah." Ya ce, "ku fito." Duk suka fito aka fito da kayansu. Ya kalli Islaha da take kallon gidajen da suka tsaya a wajen ya ce, "ki jira mu a nan, bara na fara shigar da ita na dawo na shiga dake." Islaha ta ce, "kuma ba matsala in na tsaya a nan? Kar su kama ni." "Kar ki damu, babu damuwa." Ya kalli Labiba ya ce, "mu je." Ta ja jakarta suka shiga gidan da yake ɓangaren dama. Tunda suka shiga take kallon gidan cikin burgewa, dan gidan ya tsaru, ya haɗu irin su take kallo a turkish drama, bata taɓa zaton zata shiga cikinsa ba sai gata a ciki. Lokacin da suka shiga falon numfashinta sai da ya kusa ɗaukewa dan bata taɓa ganin gida mai kyaunsa ba, komai ya tsaru irin tsarin larabawa. A falon baƙi suka zauna har lokacin Labiba kalle-kalle take yi cikin burgewa. Ba su jima ba Ubaid ya fito sanye cikin ƙananun kaya yana amsa waya, suna ganinsa suka miƙe tsaye har ya ƙaraso ya zauna sannan suka zauna suma. Bai jima yana wayar ba ya kashe, suka gaisa dashi ya nuna Labiba ya ce, "Gata nan, itace wacce aka kawo daga nigeria." Ya bi Labiba da kallo da take murmushi, ya kalle ta cikin turanci ya ce, "What is your name?." Labiba ta ce, "Labiba." "daga wani gari?." "Adamawa, Nigeria." Ya ɗaga kai yana binta da mayen kallo ya ce, "Albashin ki Riyal dubu ɗaya ne duk wata kin yarda?." Labiba ta ce, "na yarda." "Good" ya kalli Oga musa ya ce, "Ina takardar ta?." Oga musa ya ɗauko takardar gwajin jinin da Mama ta bashi, ya ɗauko ta Labiba ya bashi ya karɓa yana dubawa. Ya ɗaga kai ya kalle ta ya ce, "Za a raka ki inda zaki zauna, gobe zaki fara aiki." Cikin murmushi ta ce, "na gode." Ba jimawa sai ga wata mata ta fito sanye da uniform, farar riga da baƙin siket, sai kanta da ta rufe da baƙin mayafi. Ubaid ya nuna mata Labiba ya ce, "New housemaid." Jikin matar har rawa yake yi ta buɗe wata drawer ta ɗaukowa Labiba wata tarkada ta miƙa mata da biro. Oga Musa ya kalli Labiba ya ce, "Ki karanta ki saka hannu." Ita sai ta ji tsoro ganin yadda matar take rawar jiki, dan bata san me yake saka ta rawar jikin ba. Labiba ta saka hannu ba tare da ta karanta ba. Tana saka hannun ya yi alama da takai Labiba ɗaki, ta taimaka mata aka shiga da jakarta ɗaki. Ubaid ya miƙe tsaye ya yiwa Oga Musa kyauta sannan ya fita ya ce, "in tayi zan kira ka na faɗa maka, in an samu matsala zan faɗa maka. Ina fatan ka faɗa mata tsarikan mu?." "Ta sani." "Ya yi kyau" ya faɗa tana shiga ciki shi kuma ya koma wajen Islaha. Yana fita ya samu Islaha a tsaye a inda ya bar ta, ya kalle ta ya ce, "naga ke kina da nutsuwa sosai, kuma baki da hayaniya irin Labiba, in ki ka mayar da hankali zaki samu alkhairi sosai. Suna son mace mai nutsuwa da zafin nama, da ance a yi kawai ayi kar a ɓata lokaci. Ki kula da komai yadda ya kamata, kar ki bari a aikin farko su gano kuskure kin ji?." Islaha ta ɗaga kai ta ce, "In sha Allah." "Muje na kai ki gidan." Haka kawai gaban Islaha ya faɗi, ta kalli gidan da yake tsakiya wanda taga sun tunkara, gidan babba ne sosai, gashi da kyau duk adon glass ake hangowa tun daga waje. Ta kalli gefen gate ɗin ta ga house number, daga gefe kuma an rubuta DR REHAAN da wani irin front mai kyau da ɗaukar hankali. Ta yi ajiyar zuciya, ta ga Oga Musa yana niyar buɗe gate ɗin, dan ta kula kamar su babu mai gadi, kawai buɗewa ake a shiga, taga haka ya yi a gidan da aka shiga da Labiba. Ta yi ajiyar zuciya, ta bishi da kallo gabanta yana faɗuwa sosai...... Nana Haleema✍🏻❤️ [7/1, 1:07 PM] KRBBK: RDB2P29 Nana Haleema. Oga Musa ya dawo da baya yana sake kallon Islaha ya ce, "ba wannan gate ɗin bane, wancan ne." Ita dai bata ce komai ba, ta kalli gate ɗin tana mamakin kyaun gate ɗin kamar da gold aka tsara sa, har fuskar ka kana iya gani a jiki kamar madubi, sai dai shi gold ne har ɗaukar ido yake yi. Islaha ta bi bayansa suka shiga gidan tana tafiya slowly kamar bata son shiga ciki. Tun daga harabar gidan ya burge ta sosai, gida ne mai cike da shuke-shuke da parking space mai matuƙar girma da tsari, komai na gidan ya burge ta sosai, kana kallon gidan ka san gidan larabawa ne saboda yadda aka tsara shi kuma babu hayaniya. A hankali suka ƙarasa har bakin wata babbar ƙofa mai girma da faɗi. Ya danna door bell suka ɗan tsaya na wani lokaci kafin a buɗe ƙofar. Da kyakywan balarabe suka yi tozali, fari ne tass mai madaidaicin jiki, ko a cikin larabawan yana daga cikin kyawawa, dan in ka kalle shi sai ka so ka kuma kallo saboda baiwar da yake da ita. Maleek ya bisu da kallo, cikin harshen larabci ya ce, "daga ina?." Cikin ƙaramin lokaci Oga Musa ya canja yare zuwa larabci ya ce, "barka ranka ya daɗe, itace mai aikin gidan da aka ce za a kawo." Ya faɗa yana nuna Iskaha da kanta yake ƙasa bata ɗago ba. Maleek ya bi islaha da kallo kafin ya dawo da kallon sa ga shi ya ce, "haka nace maka ina da buƙata ne? Waye ya ce a kawo min?." "Matar gidan nan ce ranka ya daɗe." Maleek ya yi tsaki kaɗan ya ce, "ni ban ce a kawo min kowa ba, zaku iya komawa." Har zai rufe ƙofa sai kuma ya kalli Oga musa ya ce, "daga Nigeria ku ke?." Da sauri ya ɗaga kai ya ce, "eh, shigowar mu kenan." Ya ɗan kalli Islaha da har lokacin bata ɗago ta kalle shi ba ya ce, "itace mai aikin?." Ya ɗaga kai, ya kalli Islaha ya ce, "ki gaishe sa." A hankali ta ɗaga ido ta kalle sa suka haɗa ido dashi, a sanyaye cikin english ta ce, "ina yini." Sai ya ɗan yi murmushi ba tare da ya amsa ba, ya kalli Oga Musa ya ce, "tana jin turanci?." "Eh ranka ya daɗe, ta iya sosai." Maleek ya ɗan basu hanya ya ce, "ku shigo." Daɗi ya mamaye zuciyar Oga Musa, dan da ya ce su koma bai san inda zai kai Islaha ba, kaya zata zamar masa tunda babu aikin a ƙasa, suka shiga Maleek ya rufe ƙofar. Islaha tana saka ƙafarta falon wani shegen sanyi ya ratsa ta, da sauri ta ɗaga facemask ɗinta ta mayar hancin ta, ga wani ƙhamshi da wajan yake yi kamar kar ka daina shaƙa saboda daɗi. Suka zauna Maleek ma ya zauna ya ce, "Nawa ta ce zata bata salary?." Oga Musa ya ce, "ta ce za a bada riyal dubu ɗaya da ɗari biyar." Ya ɗan ɗaga kai ya ce, "Okay ya yi kyau. Za a bata kuɗin. Ka bani katin ka." Oga Musa hannu yana rawa ya ɗauko compliment card ɗinsa ya bawa Maleek, shi kuma ya ajjiye a gefe ya ce, "zan neme ka." Musa ya ɗaga kai ya kalle ta ya ce, "Islaha zamu yi waya, kome ake ciki zamu tattauna." Ta ɗaga kai tana jin faɗuwar gaba mai yawa har ya fita. Falon ya yi shiru gabanta yana faɗuwa sosai, ta ɗaga ido ta kalle sa taga ba ita yake kallo ba waya yake dannawa, kafin ta ji ya fara magana cikin larabci. Sai da ya gama wayar sannan ya kalle ta ya ce, "ga ɗaki nan, ki je ki zauna." A sanyaye ta miƙe da jakarta ta nufi ɗakin da ya nuna mata da hannunsa. Tana buɗe ɗakin ta tsaya tana kallon ɗakin tana mamakin girma da kyaun ɗakin, komai yana shirye tsaf kamar daman an san da zuwan ta. Wata irin gajiya take ji a jikinta, ta ɗan sauke numfashi tana kallon kanta a ƙaton madubin ɗakin. Ji take yi kamar ba ita ba, jin ta take yi kamar a mafarki, wai itace a wata ƙasa ba nigeria ba, kuma wai aiki tazo yi aikin da ta fi kowa tsana. Ƙofa ta gani daga gefe, ta taka a hankali ta buɗe, girman banɗaki sai ya bata tsoro, ta tsaya tana ƙare masa kallo ganin babu abinda babu a ciki, harda kayan wanka da komai a ajjiye. Ta zauna a gefen gado a sanyaye, ta ɗauki wayarta ta kunna data amma data ta ƙi ta yi. Ta sauke numfashi sai ta ga wata takarda da scan ɗin wifi, ta ɗauka ta juya sai kuma ta yi scaning sai ga wifi ya kama a wayarta. Message ɗin da ta tura Safeera ta duba taga bata buɗe ba, ta ɗan dafe kai ta danna vn ta ce, "Bestie ya ki ke, ya ciwon kan?. Bestie ina jeedah, har an bani gidan da zan yi aiki." Har zata tura sai ta goge, ta yi tsaki ta sake yin wani ta kuma gogewa, daƙyar ta yi wani ta tura mata ta ɗan kwanta a kan gadon tana sauke numfashi. Sai kuma ta miƙe a gajiye ta warware rolling ɗin kanta, ta kwance gashinta ya sauka har bayanta, ta fara ɓalle maɓallan abayar jikinta kenan taji an buɗe ƙofar ɗakin. Da hanzari ta kalli ƙofar suka haɗa ido da Maleek, maimakon ta ga ya koma saboda ganin tana cire kaya, sai ta ga ya shigo yana binta da kallo. Maleek ya ce, "Za ki iya haɗa min Coffee?." Islaha gabanta ya faɗi sosai, ta gyara rigarta sannan ta ɗaga kai alamun eh zata iya. Ya ɗaga kai ya buɗe closet ɗin wajan ya nuna mata uniforms na masu aiki ya ce, "You can take your size." Ta kalli wajan ta kalle sa ta ɗaga kai bata ce komai ba. A hankali ya juya ya fita, da gudu miƙe ta sakawa ƙofar lock tana sauke nunfashi hannunta yana dafe da ƙirjinta har lokacin zuciyarta bugawa take yi. A bayyane ta ce, "Bai damu dan ya shigo ina cire kaya ba, shi ko a jikinsa bai nuna alamun rashin kyautawa ba. Na shiga uku ni Islaha, ina na kawo kaina?." Sai kuma ta wara ido tunawa da yace yana son coffee ta ce, "wai bazan huta ba kenan, daga zuwana sai na fara bauta?." Tunawa babu mai bata amsa sai ta yi sauri ta shiga wanka, da ruwa mai zafi ta yi wanka ta fito ya kalli agogo a ƙarfe tara na safe. Ta sauke numfashi tana jin bacci yana fizgarta, gajiya ta yi mata yawa tana buƙatar yin bacci, tana so ta kwanta amma babu dama. Ta ƙarasa wajan closet ɗin tana kallon uniforms ɗin da ya nuna mata, farar riga ce da baƙin siket mai faɗi, sai mayafi baƙi da aka haɗa dashi. Ta ɗauko tana warwarewa, sai ta ga kala biyu ne akwai doguwar riga mai yanayin apron, daga sama take fara, daga ƙasa kuma baƙa ce. Sai ta ga gwara ta saka doguwar rigar, ta saka a jikinta ta ga ta zauna sosai kamar dan ita aka ajjiye. Ta ɗauki ribbon ta saka a gashinta, ta saka ɗan mayafin da ake yafawa ta rufe gashinta, ta saka room slippera kalar kayan tana tunanin ta yadda zata fita. Kallon kanta take yi, kayan sam basu kamata jikin ba amma sun yi mata kyau sosai, ta fito sak a ƴar aiki. Ta lock key ɗin da ta sakawa ƙofar, ta fito a hankali tana takawa a hankali kamar bata. Falon da suka bari ta ƙaraso, sai ta ga babu kowa sai a.c da take aikinta. Islaha sai ta tuna da yanayinta, tana buƙatar saka facemask gudun samun matsala. Ta juya zata ɗauko facemask suka yi karo da mutum. Islaha ta tsorata sosai, ya bita da kallo ganin ta shirya cikin kayan kamar yadda ya ce, kafin ya yi murmusui ya ce, "where are you going?." Muryarta tana rawa, "I'm going to get my face mask." Ya girgiza kai ya ce, "You don't have to wear it, you're very beautiful" ya faɗa yana shafa kumatunta. Da hanzari taja baya gabanta yana faɗuwa sosai, ta ce, "I have asthma, so I need it because of the cold" ta faɗa muryarta tana cracking ganin yana ta kallon ta. Ya ɗan bata hanya alamun ta wuce, a guje ta koma ɗaki ta rufe ƙifar tana sauke nunfashi. Sai kuma ta ɗora hannu a kanta ta ce, "na shiga uku!." Knocking ƙofar taji ana yi, da hanzari ta ɗauki face mask ɗin ta saka, tana buɗe ƙofar suka haɗa ido da balarabiya fara kyakykawa sanye da uniform irin nata. Islaha bata san ta yiajiyar zuciyar ba, dan a tunaninta Maleek ɗin ne ya dawo yana ƙwanƙwasa ƙofar. Cikin larabci ta miƙawa Islaha hannu ta ce, "barka da zuwa Jeddah. Sunana Sunaira." Islaha kwata-kwata bata ji me tace ba, ta dai ji ta ce Sunaira. Sunaira ganin Islaha bata gane ba sai ta kuma miƙo mata hannu. Islaha ta bata hannu suka gaisa ta ce, "Islaha." Ta yi murmushi ta ce, "ki zo zan nuna miki kitchen." Islaha bata ji me tace ba ya saka ta ce, "i'm sorry, no arabic." Itama ta ɗan yi murmushi cikin ƙaramin ingilishinta ta ce, "No english." Islaha ta ɗan murmusa suka fito tare. A falon farko a nan kitchen ɗin yake, suka shiga ita dai Islaha kallon kitchen ɗin take yi saboda girmansa. Daga nan ta nuna mata ɗakin wanki wanda aka tanadi komai na wanki a cikinsa. Suka dawo kitchen ɗin Sunaira ta ɗauki wayarta ta shiga google ta yi rubutun arabic to english ta haskawa Islaha wayar. Islaha ta karanta ta ɗaga kai suka fara haɗa coffee. Islaha ce ta ɗauki tray ɗin zuwa falon da tayi mata kwantancen nan zata kai. Da sallama ta tura glass door ɗin ta shiga, daga ciki taji ya amsa sallamar, ta ƙarasa tana kallon ƙasa har ta ajjiye masa a kan table bata kalle sa ba. Maleek ya ajjiye wayar hannunsa ya kalle ta ya ce, "what is your name?." Islaha tana daga tsaye ta ce, "Islaha." Maleek ya bita da kallo jin sunan mai daɗi, kafin ya maimaita ya ce, "Islaha!." Ta ɗaga kai alamum eh, ya murmusa ya ce, "from which state in Nigeria?." Islaha ta ce, "Adamawa state." Ya ɗan bita da kallo kafin ya ce, "Fulani?." Da mamaki ta kalle sa suka haɗa ido, sai ta ɗaga kai alamun eh. "Wow! I have a friend from Adamawa state, but his skin color is not the same as yours. Why do you look like this?." Ta yi shiru bata ce komai ba, ya kalle ta ya ce, "You look so beautiful. Why do you look even better than him?." Islaha nan ma ta yi shiru bata ce komai ba, dan bata ce komai ba, wannan iyayin nasa ya fara isar ta wallahi. Maleek ya ɗan ɗaga kai ya ce, "well, you looks so beautiful. I like your skin type." Islaha a gajiye take hakan ya saka ta ce, "thank you." Ya nuna mata hanya ya ce, "you can go." Kamar an saka ta a aljanna haka taji, ta yi saurin barin wajan ta koma ɗakin da aka ajjiye ta. Uniform ɗin ta fincike ta canja kaya ta kwanta tana ji kamar ana sassara jikinta saboda gajiya. Labiba suna shiga ɗakin da aka ajjiye ta taga tangamemen ɗaki mai kyau da tsari kamar ba na mai aiki ba, ta buɗe ido tana juyi a ɗakin ta ce, "sabuwar duniya." Matar da take bayanta ta yi darita ta ce, "ki ka shigo cikinta." Da hanzari ta juyo tana kallonta jin tana hausa, Labiba da mamaki ta ce, "Daman kina jin hausa har haka?." Tayi dariya ta ce, "Sunan Aisha, kefa?." "Labiba sunana. Amma na yi mamaki da na ji kina hausa a ƙasar nan." "Ni ƴar Niger ce, kuma na yi zaman nigeria." "Kai amma na ji daɗin haɗuwa dake a gidan nan sosai. Naji daɗi dana samu wacce take jin hausa." Aisha ta yi murmushi ta ce, "nima na samu ƙawa. Ki shiga kiyi wanka ki fito ki shirya, kin san gidaje irin wannan ba a zama haka. Sai kin jure, zaki sha wahalar aiki, dan wallahi ba a hutawa." Labiba ta ce, "daman shi ya kawo ni ai, kuɗi nazo nema, dan haka ko meye bazai dame ni ba." Aisha ta yi dariya ta ce, "da alama kan ki a waye yake Labiba, da wuri zaki tara kuɗi a gidan nan. Ki shiga kiyi wankan zan jira ki." Aisha ta fasawa Labiba kai jin ta ce a waye take, cikin iyayi ta ƙarasa banɗaki ana yanga ita lallai wayayayyi. Aisha ta bita da kallo tana murmushi, ta girgiza kai ta ce, "Sannu da zuwa gidan Ubaid, gidan kuɗi kuma gidan jin daɗi, gidan nasara kuma gidan rashinta, gidan fantamawa gidan morewa." Ta yi yar ƙaramar dariya ta juya ta fita ta bar mata ɗakin. Labiba bata jima ba ta fito, taga an ajjiye nata uniform irin na jikin Aisha, ta ɗauka ta saka tana kallon kanta dan ita kanta ta san ta yi kyau. A lokacin Aisha ta dawo ta bita da kallo tana murmusji ta ce, "kim yi kyau sosai. Kin karanta tsarin gidan nan dai ko?." Labiba ta ce, "ni saka hannu kawai na yi, ban wani duba soaai ba." "Lallai kam sannun ki. To babu sata, babu gulma, babu yawo waje barkatai. In ki ka saɓa kaɗan daga cikin rules ɗin gidan nan za a iya kama ki. In mun fita zan baki takardar ki sake dubawa dan ki kiyaye dakyau. Mu je na nuna miki inda ya kamata, sannan sai kizo ki ɗan huta na ɗan lokaci." Tare suka fito daga ɗakin tana nuna mata duk inda ya kamata ta sani, zuciyar Labina fari ƙal ganin gida irin wanda take mafarki, gida kamar ba a duniya ba, ga abokiyar aiki ƴar nigeria. Ta kusa da Ubaid da yake zaune yana danna laptop suka zo wucewa, ya ɗaga ido ya kalli Labiba ya ganta ta yi kyau a cikin shigar da ta yi, ta yi kyau cikin kayan kamar ka sace ta ka gudu. Da hannu ya yi musu alamun da suzo, suka nutsu suka ƙarasiɓo wajen suka tsaya cikin girmamawa.. Suna zuwa ya bi Labiba da shegen kallon up and down ya ce, "ya sunan ki?." Labiba ta ce, "Labiba." Ya ɗan yi jim ya ce, "Habiba?." Ta girgiza kai ta ce, "Labiba." Ya ɗan ɗaga kai ya ce, "from nigeri, right?." Ta ɗaga masa kai alamun eh tana kallonsa. Da hannu ya yi mata alamun ta tafi, ta miƙe tana tafiya ya bita da kallo yana shafa kansa, ya girgiza kai don tayi daidai da tsarinsa sosai. •••••• Tunda ya dawo daga wajan aiki yana tsaye ransa a ɓace, ya tsani ya dawo daga wajan aiki kuma ya tsaya neman wani abun da zai sha da kansa, yafi son da ya dawo a kawo masa komai baya son ɓata lokaci. Ya sauke numfashi, dan cikin kwana biyu cleaners ya ke ɗaukowa su zo su gyara masa gidan, dan shi baya so a haɗa shara da girki, ya fi son chef daban cleaners daban. Ya ja tsaki ya ɗauki waya ya kira Jazy, yana ɗauka ya ce, "Jazy meyasa wai ka sallami housemaids ɗin gidan nan? Kana neman haukata ni, ina zan saka raina ne?." Jin Rehaam yana faɗa abinda ba sabon sa ba sai ya bawa Jazy mamaki ya ce, "me ya faru?." "Na dawo daga aiki, ina buƙatar sha tea amma babu kowa a gidan nan. Waye zai bani?." "Ka yi order ko ka fita kasha" "baka da hankali Jafar, ki fi kowa sanin ina son abu bana son ɓata lokaci ko?." Jafar ya ce, "yanzu ya zan yi maka? Ni ka ke so na zama maid nazo ina yi maka aiki, ko kuma daga nan zan turo maka mai aikin gida?. Ina cleaners ɗin da suke zuwa yi maka aikin gidan?." "Cleaner chef ne?." Jazy ya ɗan yi shiru kafin ya ce, "Okay ka yiwa Maleek ko Ubaid magana mana, na san akwai housemaids a gidansu sosai, sai a baka ɗaya." Ya ɗan girgiza kai ya ce, "mun yi magana da Maleek, but bai ce min komai ba har yanzu. Kuma ni permanent nake so, bana son sharing chef, bana so na dawo ina son wani abun ace sai na jira." "Mr Rehaan samu housemaids ko chef a Jeddah bazai yi maka wahala ba, ka bincika zaka samu. Gidan Maleek ko Ubaid mata ne, kai kuma ka fi son maza." "Ina son matan, indai za a samu." "Lallai ka ji uwar bari, sai ka san yadda zaka yi." Ray ya ja tsaki ya kashe wayar cike da takaicin Jazy. Ya dafe kai, shi babu abinda ya iya dafawa balle ya ce zai je dafa, tea kwai ya iya shima a dafa ruwa zafi a saka lipton da sugar shine abinda ya iya. Komai yi masa ake yi, ta ya zai juri ko yaushe in ya dawo shi zai dafa abinda zai ci ko sai ya tsaya a hanya, ko sai ya jira rider ya kawo masa?." A Englaand suna da housemaid ɗin da yake musu girki ko yaushe, cleaner kuma kullum ana zuwa sau uku ko huɗu ana gyara inda suka ɓata shiyasa bai iya yin komai ba. Daman Jazy ne mai ƙoƙarin girki, da yana nan da bashi da matsalar abinci ko matsalar abin sha ko wani abun. Ya ɗan yi tsaki yana neman number Maleek, dan ba kasafai ya cika sakewa da Ubaid ba, rawar kan Ubaid ya yi yawa, ya fi son shiri da Maleek dan yana da nutsuwa akan Ubaid. Ya kira number Maleek yana fatan Allah ya sa a samu housemaid ɗin da za a tura masa a take su zo su fara yi masa aiki, bai damu da mace ko namiji ba, ko ma waye yana maraba dasu. Tunda nema yake bashi da zaɓi, amma da a gida ne baya haɗa hanya da housemaid mata, ya fi son maza su yi masa komai. Kuna Maleek zai ba da Islaha kuwa? Ina labarin Hajiya Umma? Labiba fa? Mu je zuwa🤭💃🏻 [7/1, 1:08 PM] KRBBK: RD2P30 Nana Haleema. *MADINA* *AL KHALIDIYYAH AREA.* Umma tunda aka gama gabatar da ita ga mutanen gidan take a gantale a falon gidan, tana kallon falon sanyin a.c yana ratsa ƙasusuwanta. Dan sanyin ba ɗan kaɗan bane, sanyi ne mai yawa wanda ya fi ƙarfinta. Falon yana da girma da manyan kujeru masu girma, ga wani ƙaton dining table mai guda ashirin, alamun iyalai gidan suna da yawa ba na yara ba. Ga wasu ƙofofi a falon wanda bata san na meye ba, ga ƙatuwar tv, komai na falon ya yi yadda ya kamata. Umma dai tana zaune ga yunwa ga gajiya, sanyin duk ya dame ta kuma ba a bata wajan zama ba balle ta shiga ta zauna. Wata balarabiyar budurwa ce ta fito daga ɗaki, ta bi Umma da kallo kafin ta ƙwalawa Mamanta kira cikin harshensu ta ce, "Mama Wannan baƙuwar a ina zata zauna?." Daga ciki ta ji muryar babar cikin harshen su uwar ta ce, "ki raka ta ɗakin baƙi ta ajjiye kayanta." Ta kalli Mama ta ce, "Mu je." Umma bata fahimta ba, ita dai taga tana kallon ta kuma tana yi mata magana, amma bata san me take faɗa ba. Yarinyar ta yiwa Umma nuni, hakan ya saka ta miƙe ta ta bi bayanta tana sake kallon ko ina na falon. Ɗaki ne madaidaici da komai a cikin sa, Umma ta shiga tana ajjiye kayanta gana kallon ɗakin cikin wani irin yanayi mara daɗi. Umma ta zauna a gefen gado tana kallon ɗakin, sai kuma ta miƙe tana kallon ƙofar tana tunanin banɗaki ne, ta buɗe tana kallon banɗakin kafin ta shiga ta yi wanka. Tana fitowa taga yarinyar nan a tsaye a ɗakin tana kallon ɗakin. Umma tana fitowa ta bita da kallo kafin ta yi mata alama da tazo da hannunta. Umma ta canja kaya a gajiye, ta yi tunanin za a barta ta huta amma sai ta ga akasin haka. Ta fito tana takawa a hankali dan ta gaji sosai ma kuwa. Tana fitowa ta ga mutane harr a falon manya da yara, kowa ya zuba mata ido yana ƙare mata kallo kamar sun ga wata mujiya. Iyayen gidan tana kallonsu ta san sune iyaye, uwa da uban suna zaune a waje ɗaya, sai sauran yaran duk mata ne da namiji ɗaya, suna zaune sun yi kaca-kaca da wajan suna ciye ciye kamar ba manya ba. Umma tana fitowa matar ta kalle ta tayi mata nuni da ta kwashe kayan wajan. Umma a sanyaye ta duƙa ta fara kwashe kayan, aka nuna mata kitchen ta kai ta ajjiye. Tana fitowa yarinyar cikinsu ta zubar da lemo a kan tiles har kan carpet. Aka ɗauko abinda gyara waje aka bawa Umma ta goge tiles ɗin, aka bata ƙramin towel alamun ta goge wajan ta duƙa tana gogewa. Tana gamawa aka nuna mata wata yarinya, ita dai ta kalli yarinyar amma bata san me ake faɗa ba.Cikin tsawa matar take yiwa Umma Magana, duk ta ruɗata dan ta kasa gane me take nufi balle ta yi. A lokacin aka buɗe ƙofar aka shigo, matar gidan ta kalli wacce ta shigo ta hauta da bala'i ita dai Umma ta yi shiru bata san me suke faɗa ba. Hajiya Shafa da aka damƙa Umma a hannunta ta kalli Umma da ta yi tsuru-tsuru ta ce, "ki riƙe yarinyar ki yi mata wanka, wannan matar bala'i ne da ita sai kin yi da gaske, in ba haka ba tsaf zata dake ki wallahi." Da mamaki Umma ta ce, "Duka kuma?." "Kina mamaki kenan? Lallai baki san larabawa ba. Ki riƙe yarinyar nan ki je ki wanke ta." Umma ta riƙe hannun yarinyar ta ce, "ina ne wajen wankan?." Hajiya Shafa ta ce, "mu je na nuna miki." Tare suka tafi yarinyar tana turjewa tana ƙwalla ihu, duk ta cika musu kunne da magana. Hajiya Shafa ta kalli Umma ta ce, "ki ɗauke ta, basa jurar ɗansu yana kuka fa, a kan haka zaku ɓata dasu wallahi." Umma ta kalli yarinyar ta ga a taƙaice zata yi shekara goma, sannan gata lukuta ce, ta kalli Hajiya Shafa ta ce, "ta ya zan iya ɗaukar yarinyar nan, kalle ta fa?." "Haka zaki gwada, in wacce ta fita aka ce ki ɗauka haka zaki ɗauka. Kamar baiwa ki ke a gidansu, ko taka ki suka yi suka wuce haka zaki yi haƙuri." Umma ta duka ta ɗauki yarinyar daƙyar tana hakki. Ɗakin yaran ta raka ta, suna shiga ta gansa kaca-kaca, an ci abubuwa an watsar ga toys an zubar kamar ɗakin mahaukata. Hajiya Shafa ta ce, "gashi nan, kije kiyi mata wanka sai ki saka mata kaya. Sannan ki gyara waɗannan kayan da suka watsar. Maimuna kwana da sanin baza ki yi bacci ba, domin kuwa zasu je makaranta." Umma ta kalle ta cikin firgici ta ce, "Baiwar Allah zuwa na kenan fa, ko hutawa ban yi ba, ko ɗan abinci ban ci ba balle bacci. Wallahi ƙafafuna a gajiye suke, zaman motar nan gabaɗaya ya sagar min da ƙafafu. Tun safe muka taso, aka samu matsalar mota muka kwana a hanya, yanzu gashi har gari ya yi haske. Kuma ace bazan kwanta ba? In ban kwanta ba ai sai na faɗi." Hajiya Shafa ta bi Umma da kallo ta ce, "aiki kika zo yi ai ba hutu ba, kar ma ki saka a ranki wai zaki huta a gidan nan, wallahi aiki zaki zage ki yi kamar jaka, dan kaf aikin gidan nan a kan ki yake, ga kula da yaransu. Su basu san uzuri ba, kuma basu san ɓata lokaci ba, in suna so sai an yi kawai babu na gaji." Umma ta sauke numfashi tana jinjina kai ta ce, "to bara na yi mata wankan." Hajiya Shafa ta ce, "ya fi miki dai. Sunana Shafa, ni ce waccce suka faɗawa suna neman mai aiki a kawo musu, ni kuma na faɗawa Oga Musa, shi kuma ya saka aka nemo ki. Duk abinda zaki aikata a gidan nan ni zasu nema su faɗawa, dan haka ko rufa min asiri ki zauna dasu lafiya, bana so a ɗaga min hankali." Umma ta shiga banɗakin tana kallon banɗakin, yarinyar ta ƙarasa cikin bathtub ta kunna ruwa alamun a ciki ake yi mata wankan. Umma bata tsaya ƙarewa banɗakin kallo ba, dan a gajiye take matuƙa tana so ta huta. Ta kunna ruwa ya fara zuwa sai yarinya ta ƙwalla ƙara mai ƙarfi. Umma ta firgita ta taɓa ruwan dan ta ɗauka ƙonata ta yi, saita ji ruwan sanyi ne kuma bai yi sanyin da zata yi wannan ƙarar ba. Kafin ta tsayar da ƙarar har an shigo banɗakin, da uwar da uban da yayyenta duk sun hallara an nufe ta ana tambayar abinda ya faru. Tana gani yarinyar tana faɗa musu ita dai tana tsaye bata san me ake cewa ba. Matar gidan ta juyo tana yiwa Umma bala'in da bata san me take faɗa ba, ta dai zuba masa ido tana kallo bata fahimci ko kalma ɗaya ba. A lokacin Shafa ta shigo, suka koma kan Shafa suna faɗa mata itama tana mayarwa. Suka fito da ƴar tasu daga ciki suka fita da ita. Shafa ta bi Umma da kallo ta ce, "Na faɗa miki wallahi Allah ba a taɓa musu yaransu, ba a taɓa yayansu a zauma lafiya. Ƙauna ƴaƴansu suke yi kamar su ɗiga musu sabon rai, akan ƴaƴansu zasu iya yi miki komai wallahi. Na yi miki bayanin nan, amma daga fita ta har kin canja. Akan cutar musu da yara zasu iya kama ki, kuma a ƙasar Saudia ki ke ba Nigeria ba, kulle ki zasu yi a gidan yari, babu ruwan su dake ba ƴar ƙasa bace." A sanyaye Umma ta ce, "ban san ruwan sanyi na kunna mata ba, wallahi ban san ya yi mata sanyi ba." "Waye ya ce ki bari ta shiga ciki? Ai sai kin fara haɗa mata ruwan sannan zaki bari ta shiga ciki. Yanzu da na zafi ki ka kunna mata fa?." "Wallahi ban sani ba, da na san me sanyi ne bazan kunna ba. Tunda kin ga ban san kan gidan ba, ko awa ɗaya ban yi da zuwa ba, sai a hankali zan saba." "Wallahi da ruwan zafi ki ka zuba mata da yanzu sun kira ƴan sanda sun tafi dake. Basa jurar ƙaramar matsala, son jikinsu ne dasu." Umma ta yi shiru bata ce komai ba, Shafa ta ce, "akan yaran nan sai zaman ki zai ƙare a gidan nan, kin ga dai yau ki ka zo ko? To zaki iya komawa yau. Kinga ke ce da asara, kafin a sake samun wani gidan kin galabaita, gashi baki san gari ba, kuma baki da ko sisi." Umma ta ce, "to ya zanyi?." Shafa ta ce, "mu je." Umma ta biyo ta a sanyaye tana ji kamar ta kifa saboda gajiya mai nauyi, ga kanta yana ciwo, ga yunwar da take ji mai ƙona ciki. Shafa tabi ɗakin yaran da kallo ta ce, "ki gyara ɗakin nan, sannan ki je ki dafa musu abinci, lokacin cin abincin su ya kusa." Umma a galabaice da rauni ta ce, "Hajiya Shafa na gaji, wallahi bazan iya aikata komai a yanzu ba, ina buƙatar hutu. Gaɓoɓina ciwo suke yi min, ga kaina yana ciwo, ga yunwa, ga gajiya. Tafiyar Jeddah zuwa madina ba kusa bace kin sani, tafiya muka dinga yi kamar zamu bar duniya. Gashi mota ta lalace, haka muka zauna a daji ana gyarawa. Don Allah ki ce musu a bari na huta zuwa anjima sai nayi." Hajiya Shafa ta gyaɗa kai tana bin Umma da kallo tana buɗe ido tace, "Hajiya meye ma sunan ki?." "Maimuna nake." "Maimuna buɗe kunnen ki dakyau ki ji abinda zan faɗa miki, dan na ga alama baki san inda ki ka kawo kan ki ba...." "Ina so ki san a inda ki ke, nan ba Nigeria bace, a ƙasar Saudia kike, a cikin garin Madina. A cikin Madinan ma ba ziyara ki ka zo ba, ba hutu kika zo ba, a gidan larabawa kike kuma aiki zaki yi su biya ki." Ta yi ƙwafa irin baki san dawar garin ba ta ce, "Maimina ina sake faɗa miki basu san ɗaga ƙafa ba, basu san kara ko wani abu hutu ba. Mai aiki akwai sunan ki a wajensu, a haka suke kallon ki ba wacce tazo ta huta ba. Kamar baiwa haka zaki koma a gidan nan, tunda kuɗi zasu baki ba kyauta zaki yi musu ba. Dole ki yi abinda suke so a yanzu, babu ruwansu da yanzu ki ka zo ko kin gaji. Indai kina son samun kuɗin dole ki buɗe ido ki san a inda ki ke." Umma a gajiye ta ce, "ina son samun kuɗi, kuma na san aiki zan yi, amma tsakani da Allah a bari na huta zuwa gobe ko zuwa dare mana. Tun da muka ɗauko hanyar garin nan a zaune nake, wallahi na gaji, gajiya mai yawa. Babu abinda zan iya yi yanzu, ko sallah da akwai dama yi min za a yi, ƙafafuna jinsu nake kamar ba nawa ba." Shafa ta ce, "zancen ki ke so, wannan maganar hutun ki haƙura sai dare. Mu je na nuna miki kitchen ki dafa musu abinci, lokaci yana gudu." Umma ta bi bayanta a sanyaye tana ji kamar zata kifa saboda gajiya da tashin hankali. Suka shiga kitchen ɗin, Umma taga babban kitchen ne mai kyau da tsari irin na larabawa. Ta nunawa Umma komai ta ce, "ki ɗauki kajin nan ki gyara su sannan ki gasa a nan" ta faɗa tana nunawa Umma oven. Shafa ta ce, "sai ki dafa shinkafar nan, basa son yaji, basa son ɗanɗano ya yi yawa. In ki ka saka musu yaji mai yawa wallahi babu ruwana. Ga kayan ƙhamshin, sai ki yi amfani dashi yadda ya kamata." Umma dai tana ji ne kawai ba wani fahimta take yi sosai ba, kanta juyawa yake yi tana ji kamar ta faɗi a wajen. Da taimakon Shafa suka fara dafa abincin, dan bata san me Tana cikin dafawa sai ga budurwar yarinya ta ƙaraso, ta yiwa Shafa magana da larabci ta amsa bayan ta bar wajan ta ce, "wai tana da wanki a ɗaki, ki je ki wanke musu." Umma ta tsame hannunta daga wanke shinkafar, ta bi inda aka nuna mata. Ɗakin wanki ne wanda yake ɗauke da injinan wanki guda biyu, sai wajan goga da kayan gugar. Umma ta sauke numfashi ganin kayan tuli masu yawa sosai, gashi sun yi kaca-kaca kamar kayan ƙananun yara masu rarrafe. Umma ba iya amfani da komai sosai ba, amma bata fita ta tambayi Shafa ba ta dinga bi a hankali har ta kunna ya fara wankin. Ganin ta fara wankin sai ta samu waje ta zauna tana lumshe iso bacci yana figarta sosai. A haka tana zaune a wajen har aka yi kiran sallar azahar, ta ji kiran ya karaɗe ko ina. Umma ta miƙe daƙyar ta fito ta koma wajan Shafa ta tarar har ta gama abinci ta gama gyara waje komai tsaf. Shafa ta kalli Umma ta ce, "wai har kin gama wankin?." Umma a sanyaye ta ce, "sallah na ji ana yi, shine na fito nayi zallah sai na koma." Ta kalli Umma tana girgiza kaita ce, "hmm, Allah yasa su yi miki wannan uzurin, sufa sun fi so da ance kawai a yi, basa son ɓata lokaci." Umma ta wara ido waje cikin mamaki ta ce, "har sallar ma?......" Nana Haleema✍🏻❤️ [7/1, 1:08 PM] KRBBK: RDB2P31 Nana Haleema Hajiya Shafa ta yi dariya ta ce, "baki san a ina ki ke bane. Jeki ki yi alawar." Umma ta juya ta shiga ɗakin da aka nuna mata, daƙyar ta iya alawala ta fito ta yi sallah, Tana idarwa bata san bacci ya ɗauke ta a inda ta idar da sallar ba, ko hijjab bata cire ba saboda yadda baccin ya ci ƙarfinta.      A firgice ta farka jin ana shafa hannunta, ta buɗe ido tare da miƙewa zaune tana raba ido jin baƙon abu wanda bata saba ji ba. Suna haɗa ido taga mai gidan ne da kansa a tsugune a gabanta yana yi mata murmushi. Gaban Umma ya faɗi, ta ja baya da sauri tana so ta yi magana amma bata san me zata ce ba, ta san ba yaren ta yake ji, sannan itama ba nasa take ji ba balle ta tambaye sa dalilin zuwan sa waje. Umma ta ruɗe sosai, tashin hankali ya bayyana ƙarara a tare da ita. Shi dai ya bita da kallo kafin ya miƙe ya fita. Umma ta bisa da kallo sai kuma ta tuna da wanki, ta firgita ta miƙe ta koma ɗakin wankin ta tarar an sake tulo mata wasu. A haka Umma ta gama wankin, ko gama bushewa basu yi ba ta fito jin kanta yana sarawa kuma ta san yunwa ce. Tana fitowa suka haɗu da matar gidan, ta yi mata alama da ta biyo bayanta, Umma ta bita har kitchen. Ganin kayan wanke-wanken da suke jibge sai da gabanta ya faɗi, ta ji hawaye har taruwa suka yi a idanunta saboda tashin hankali da damuwa. Matar gidan ta nunawa Umma kayan alamun ta wanke, sannan ta nuna nata wani kwano alamun ga abincinta nan. Umma ta bi kayan wanke-wanken da kallo dan kayan suna da bala'in yawa sosai. Umma ta ƙarasa ta buɗe abincin ganin shinkafar da aka dafa ce sai rabin kaza. Hannu yana rawa Umma ta fara ci a hankali dan yunwa take ji sosai. Kafin ta ci rabin abincin ta ji ana jan hannunta, taga yarinyar nan da zata yiwa wanka ɗazu, Umma ta bi bayanta suka fita sai taga yadda suka lalata falon, kuma taga alama ake yi mata da ta gyara wajan. Umma ta yi ajiyar zuciya cikin wani irin yanayi, ta bi dining ɗin da kallo ganin sa kaca-kaca kamar yara ƙananu ne suka ci, bayan cin abincin suka haɗa da dambe a kai. Ta lumshe ido tana ƙarasa wajan ta ɗauki abinda aka nuna mata na aiki, ta fara share wajan sannan ta goge dining ɗin ta gyara kujuren, ragowar tarkacen kayan da suka bari ta ɗauke ta koma kitchen ta fara wankeawanken dan ta manta ma abinci take ci. Kamar an tuna mata da wayar ta, gabanta ya faɗi ta ji tana so ta yi magana da ƴaƴanta. Ta juya zata fita ta ɗauko ta ga mai gidan a tsaye a falo shi kaɗai yana binta da shegen kallo da ya saka ta tsaya cak, gabanta ya faɗi matuƙa, ta juya ta cigaba da aikin jikinta yana rawa cikin tashin hankali. Tunani take a zuciyarta ina ta kawo kanta haka?. •••••• "Sadik ina Islaha ne, ban ganta ba kwata-kwata. Ko ta tafi aiki ne?." Sadik ya kalli Baffa ya ce, "Wallahi Baffa nima bamu haɗu da ita ba, amma na san tana wajan aiki, zata biyo in ta tashi. Baffa ya ce, "Islaha sarkin ƙorƙari, Allah ya yiwa rayuwa Albarka." Sadik ya amsa yana fitowa daga ɗakin suka haɗu da Hanan zata shiga ya ce, "Hanan don Allah ina Islaha?." Ta ɗan taɓe baki ta ce, "Ban sani ba" ta faɗa tana shiga ɗakin ta bar sa a tsaye yana binta da kallon mamaki. Sadik ya ɗauke kai ya ɗauko wayarsa ya kira Islaha amma wayar bata tafiya gabaɗaya. Mama ce tazo zata shiga ɗakin, Sadik ya tsayar da ita ya ce, "Mama Islaha tana gida ne?." Mama ta ce, "Islaha ai bata nan, zaka jima baka ganta ba." Kafin ya sake magana ta shiga ɗaki ta barsa a tsaye cikin mamaki. Sadik ya bi Mama da kallo cikin rashin fahimta, ya fita daga asibitin ya hau mota ya nufi gidansu Safeera. Yana tsayawa a ƙofar gidan kiran Saheer yana shigowa wayarsa, bai ɗauka ba dan ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ya san bazai wuce yace masa lambar Islaha bata shiga ba, in ya ɗauka bashi da amsar da zai bashi. Sai bayan wayar ta yanke ya kira Safeera tana ɗauka ya ce, "Safeera kina gida ko wajan aiki?." Ya yi shiru alamun ana basa amsa, sai kuma ya fita daga motar ya hango ta ta fito daga gidansu. Ya ƙarasa wajan sai ya ga motar Saleem ta tsaya, shima ya ƙaraso suka gaisa. Saleem ya kalle Safeera ta ce, "ya jikin ki?." A sanyaye Safeera ta ce, "Da sauƙi." Saleem ya ce, "Ana ganin ki an san baki da lafiya." Sadik ya ce, "Sannu Safeera, ban san baki da lafiya ba da ban kira ki ba." Safeera ta ɗan murmusa ta ce, "ciwon kai ne kawai." Sadik ya kalle ta ya ce, "Ƙawar ki fa? Na kira ta sau babu adadi bata ɗauka, ga sarkin rashin haƙuri ya fara damuna da waya akan baya samunta." Saleem ya ce, "A'a, Islaha ba tayi tafiya ba?." Sadik da mamaki ya ce, "Islahan ce tayi tafiya, to zuwa ina?." Saleem ya ce, "nima ban sani ba, amma kowa na gidan tv ya san Islaha bata nan, har Safeera." Sadik ya kalli Safeera ya ce, "Safeera Ina Islaha take?." Safeera ta sauke numfashi ta ce, "Eh Islaha tayi tafiya Hamma Sadik." Sadik mamaki ya mamaye masa zuciya ya ce, "ina ta je? Ina ta tafi bamu sani ba?." Safeera ta ɗan yi ajiyar zuciya ya ce, "itace tace bata so ka sani kai da Saheer, shiyasa baku sani ba." Da mamaki Sadik ya ce, "tafiya zuwa wani gari to? Me ya kaita garin, kuma yaushe zata dawo?." Safeera ta kalle sa ta ce, "Ƙasar ta bari gabaɗaya ai, ba wani garin ta tafi ba, Islaha bata Nigeria." A tare suka haɗa baki suka ce, "Kamar ya ta bar ƙasar!?." Safeera ta yi shiru bata ce komai ba, dan bata san me zata ce musu su yarda ba. Sadik a ƙagauce ya ce, "ki yi mana magana mana Safeera, kalli wayata, Saheer ne yake yi min magana ban san me zance masa ba. Wacce ƙasar Islaha ta tafi? Wacce ƙasar islaha ta tafi bamu sani ba?." Safeera ta sake yin shiru bata ce komai ba, ita kanta gabanta faɗuwa yake yi dan bata san me zata ce ba. Sadik ya dafe kai ya ce, "Safeera ki buɗe baki ki yi magana, kar ki saka jinina ya hau don Allah." Safeera ta ce, "ta tafi ƙasar saudia, yanzu haka ma tana can. Dan tun safe na ga voice note ɗinta, ta ce min har ta sauka a masauki." Saleem cikin firgici da tashin hankali ya ce, "Saudia Safeera! Umra ta tafi babu labari?." Sadik yabi Safeera da kallo dan ya kasa magana, ya girgiza kai cikin mamaki ya ce, "wai me islaha ta ɗauke mu ne? Me take ɓoyewa wanda bata so mu san dashi?. Tunda aka sace ta na lura da akwai abinda ake ɓoyewa wanda bata so mu sani. Yanzu waye ya kai Islaha saudia Safeera? Kin tabbatar ta bar ƙasar nan?." Safeera ta ce, "Wallahi Islaha bata nigeria, kuma ta tafi Saudia ta ƙarƙashin kamfanin su Mamansu Saheer. Ba ita kaɗai ba, harda Labiba da...." Sai maganar ta maƙale saboda nauyi, ta sunkuyar da kai ta ce, "Da Ummana" ta faɗa hawaye yana sakko mata ta yi sauri ta goge. Sadik ya dafe kai da hannu biyu ya ce, "aikatau ɗin ta tafi kenan?." Ta ɗaga masa kai ta ce, "ta ce bata so ka san ta tafi, bata so ka san dalilinta sai ta bar ƙasar." A fusace Sadik ya ce, "wanne dalili ne da ita da zai saka ta yanke wannan hukuncin?. Ni fa ban yarda da ita ba, zuciyata faɗa min take yi yawon banza Islaha ta fara yi, shiyasa ta bar gida ta je ta kwana biyu da sunan an sace ta. Taje ta gama zaman ta a inda ta ga dama, sannan ta dawo da kuɗi masu uban yawa ta ƙi faɗar a inda ta samu, yanzu kuma ta bar ƙasar duk bamu sani ba." Safeera ta ce, "wallahi Islaha bata fara yawom banza ba, ka daina jifanta da wannan kalaman. Tafiyar ta aikin ma rashim mafita ne ya saka ta tayi ta, ba a son ranta ta tafi ba." Sadik ya zuba mata ido dan ya kasa magana, hakan ya saka Saleem ya ce, "Wacce mafita ce wannan da zata saka ta tsallake mu ta tafi wata ƙasar aiki a gidan larabawa?." Safeera ta ce, "Kamar yadda ta faɗa mana yadda aka sace ta, da gaske ta hakan aka sace ta. Ranar da zata dawo ta ga kuɗin a falon mutumin, shine kawai sai ta ɗauko tana tunanin yanayin da ta bar Baffa a ciki, kar ta dawo ba a samu kuɗin aikin ba." "Bayan aikin Baffa ya kammala kuma sai hankalinta ya tashi sosai, ta dinga mafarkai akan kuɗin. Shine ta same ni tana neman hanyar da zata samu kuɗin ta biya sa. Na faɗa mata samun kuɗi kamar wannan a ƙaramim lokaci bazai yu ba, nima ban sani ba, ashe har ta gama shirya komai an yi mata visa, sai tafiyar kawai ta faɗa min." Sadik ya bita da harara ya ce, "Safeera kar ki mayar damu ƙananun yara mana, kar ki mayar damu shashashai waɗanda basu san abinda suke yi ba, ki faɗa maganar da kanmu zai ɗauka, ki daina yi mana magana ta rainin hankali. Mu ba mahaukata bane da zamu yarda da wannan shirmen." Saleem ya jinjina kai ya ce, "ya sace ta, ya ajjiye ta a gidansa bai yi mata komai ba, kuma ya saka aka dawo da ita. Ita kuma saboda ƙarfin hali, tana hannun wanda ya sace ta bata kuɓuta ba, shine harda ɗauko masa kuɗi?. Bayan ta dawo kuma ta ɓoye mana, ta dinga ɓoye-ɓoye a kan case ɗin. Yanzu kuma ta shirya tafiya ta bar ƙasar, duk babu wanda sani ba." Ya ɗan girgiza kai ya ce, "Safeera hankali bazai ɗauki maganar nan taki mai kama da wasan yara ba, nima ban yarda ba balle Sadik, balle kuma aje kan uwa uba Saheer. Kuna ɓoye mana wani abun ke da ƙawar ki." Kamar Sadik jira yake yi ya fara bala'i ya ce, "mu zata mayar shashashai ƴan iska? Mu za a tsaya ana tsarawa ƙarairayi kamar wasu marasa hankali?." Safeera ta ce, "wallahil azim ban ɓoye muku komai ba, wallahi Allah abinda ya faru kenan. Islaha ta tafi dan ta nemi kuɗin da zata biya wancan bashin sa da taci, ko nace ta je neman kuɗin da zata mayar masa a inda ta ɗauke. Wallahi duk wani tunani mara kyau da kuke yi ba haka ba, Islaha bata canja ba, tana nan yadda take. Don Allah ku daina zarginta da mummunan abu, Islaha mace ce ta gari" Sadik ya ce, "Naji mace ce ta gari. Yanzu in taje ta samo kuɗin ta dawo, a ina zata samu mutumin ta ba sa kuɗi? Ko daman ta san shi daman tun farko? "Wallahi bata san shi ba, ta ce min zata neme sa." "Ƙarya ne, wannan ƙarya ne wallahi!. Ta tafi yin wani abinda daban a ƙasar waje kawai, amma ba wannan tatsuniyar ba." "Wallahi ba tatsuniya bace, gaskiya ce maganar nan ba ƙarya ba. Wannan dalilin da na faɗa muku shine ya saka ta tafiya." Saleem ya ce, "Shikenan munji haka ne, ta ya zata biya shi in bata san shi ba?." Safeera ta ce, "wallahi bata san shi ba." Sadik ya ɗaga mata hannu ya ce, "Ki daina yin rantsuwa Safeera, rantsuwa akan ƙarya bata kamace ki ba. Abu ne guda biyu, ko ke da ƙawar ki kuna raina mana hankali, ko kuma ƙawar ki ta haɗa har ke ta rainawa hankali. Wannan maganar ƙarya ce wallahi, babu ta yadda za a yi mu amince da wannan wasan kwaikwayon. Sau nawa Mama tana yiwa Islaha tayin aikin tana avoiding, tafi kowa tsanar tafiya aikatau ɗin nan. Kwanaki har progeam ta fara akan hakan, ko Saleem?." Saleem ya ce, "shine abinda ya ɗaure min kai, nida ita muka fara wayar da kai akan tafiyar nan a kafofin sada labarai, meyasa ita ta yi bayan itace mai so ta yaƙi abin? "Ni ban yarda da wannan shirmen ba, akwai abinda aka ɓoye wanda ba a so mu sani." Safeera ta ce, "Hamma Sadik ba a ɓoye mu ku komai ba, gaskiyar kenan." Sadik ya ce, "to kema ta ɓoye miki, kema bata faɗa miki gaskiyar abinda yake faruwa ba, ta haɗa damu dake ta raina mana hankali tana so ta ɓoye laifinta. Bazan taɓa yarda da wannan ƙaryar ba Safeera, Islaha ta ɓoye miki gaskiyar lamarin nan, dan na tabbatar akwai wani abun bayan hakan." Safeera zata yi magana aka kira wayar Sadik, ya kalli wayar ya kalle su ya ce, "Saheer ne, yanzu me zance masa don Allah?. Wannan tatsuniyar da Safeera ta faɗa mana zan faɗa masa, ko wani abun daban?!." Nana Haleema✍🏻❤️ [7/2, 10:40 AM] KRBBK: RDB2P32 Nana Haleema.. Saleem ya bi Sadik da kallo ya ce, "ka ɗauki wayar ka faɗa masa gaskiya, wannan ba maganar sace ta bace balle ace a bari kar a faɗa masa daga baya. Magana ake na ta bata ƙasar gabaɗaya, dawowar ta yanzu bazai yu ba." Sadik ya dafe kai cikin wani irin takaici da ɓacin rai ya ce, "Islaha tana bani wuta wallahi, komai ni take sakawa a ciki." Kiran da ya sake shigowa wayarsa ne ya saka ya ɗauka, ya saka wayar a speaker, Saheer daga can ɓangaren ya ce, "ina ta kiran ka baka ɗauka. Kuna tare da Islaha ko tana wajan aiki? Tunda na tafi sau ɗaya muka yi magana da ita, yanzu ina kiranta amma bana samunta. Kuna tare ko na kira Safeera?." Sadik ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "muna tare da Safeera da Saleem, amma babu Islaha." Saheer ya ce, "tana ina ita? Ko ta tafi wajen aiki ko taje orphanage?." Sadik ya ce, "kana ina yanzu?." Saheer ya ce, "ina gida, ka bani amsa." "In a tsaye ka ke ka samu waje ka zauna Saheer." "Meyasa kenan? Wani abun ne ya sake faruwa?." "Eh wani abu mai girma ya faru, shiyasa na ce ka samu waje ka zauna." "Sadik me ya faru, wani abun ne ya sake samun Islaha? Ka yi mana, ka faɗa min abinda ya same ta bana son ɓoye ɓoye, ka faɗa min!." Sadik ya ce, "Islaha dai bata ƙasar nan." Saheer muryarsa har rawa take yi ya ce, "ban gane ba, tana wacce ƙasar?." Sadik ya ce, "sun ɓoye mana komai ita da ƙawar ta, sai yanzu muke jin labari a bakin Safeera. Islaha tana ƙasar Saudia, ta biyewa Mama ta tafi aikatau." "Ka ga Malam ka yi maganar da zan fahimta, kamar ya ta tafi aiki? Aikin jaridar ne ya kai ta saudia ko wani abun ne, ni ban gane ba?." Sadik ya bashi labari irin wanda Safeera ta faɗa musu, sannan ya ce, "a lokacin da aka sace ta daman ni ban yarda da ita ba wallahi, dan a lokacin ta saka na ɓoye maka itace ta biya kuɗin aikin Baffa. Tana dawowa daga wajen wanda ya ɗauke ta muka je asibiti, a lokacin na ga rafar dala ɗari a hannunta. Dana tambaye ta sai ta ƙi faɗa min, ta wuce wajen biyan kuɗi ta biya kuɗin aikin Baffa. Da nayi converting dala zuwa naira, a lokacin da kuɗin hannunta naira miliyan sha bakwai kenan. Nayi nayi ta faɗa min inda ta samo kuɗin nan amma Islaha taƙi faɗa, daga ƙarshe sai ta ce min don Allah kar na faɗa maka, wallahi ba ta hanyar banza ta same su ba, ta dinga haɗa ni da Allah har na amince bazan faɗa maka ba. Yanzu kuma dan ta raina mana hankali, ta ɓullo da wannan maganar mai kama da wasan yara." Saheer ya yi shiru ya kasa magana, kansa ya kulle ya rasa abinda zai ce. Bakinsa ya yi nauyi, bakinsa ya ɗaure matuƙa ya rasa abinda zai ce. Daƙyar ya buɗe baki ya ce, "da gaske ka ke Islaha ta bar ƙasar nan?." "Wallahi da gaske bata ƙasar nan Saheer." "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Meyasa ka ɓoye min maganar kuɗin da ta zo dasu tun farko?." "itace ta dinga roƙona akan don Allah kar ka sani, shiyasa na yi shiru ban faɗa maka ba." "An sace ta, sannan ta dawo da bandle na dala ɗari har ta biya kuɗin aiki. Taƙi faɗar wanda ya sace ta, ta dage akan sai an rufe case ɗin sace ta da aka yi, ta koma zama cikin yanayin damuwa, ko walwala bata yi. Kenan daman saboda wannan kuɗin ne ya saka take so a kulle case ɗin?." Sadik ya ce, "ko kuma saboda ba sace ta ɗin aka yi ba, ni fa zuciyata tana faɗa min tana sane duk abinda ya faru tsarinta ne. Haka kawai mutum zai sace ta ya ajjiye ta bai yi mata komai ba, kuma saboda ƙarfin hali irin nata da ta tashi dawowa har ta samu guts ɗin sato masa kuɗi?....Babu ta inda hankali zai ɗauki wannan maganar, babu ta inda za a faɗi maganar nan ace tayi kama da gaskiya. Ni na fi zargin kawai a wajansa ta samo kuɗin, ta damu da rashi lafiyar Baffa ne shiyasa ta tafi, amma ba sace ta aka yi ba." "Me ka ke nufi?." "ina nufin ta yadda mata suke samun kuɗi mana, su bayar a basu." "Kana nufin ƴar iska ta koma?." "Ga amsa a bayyane." "Kar ka sake jifan Islaha da wannan kalma mara daɗi, tun muna shaida juna da kai ka iya harahenka akanta!." Sai ya kuma cewa, "Duk abinda ya faru ba laifin ka bane? Da ka kula da amanar da na bar maka ai da hakan bai faru ba." Sadik cikin takaici da haushin Islaha ya ce, "duk ƙoƙarin da nake yi a kanta baka gani ba kenan?." Saheer ya ɗan sauke numfashi cikin yanayin damuwa ya ce, "Safeera meyasa za a haɗa kai dake a yi min haka? Meyasa zaki ɓoye min wannan magana mai girma, meyasa zaki bata goyan bayan wannan ɗanyen aikin?." Safeera ta ce, "Hamma Saheer ni kaina ban sani ba sai da ta gama yin komai sannan ta faɗa min, ta san in na sani zan dinga kushe abin har ya fita daga ranta, shiyasa ta yi min shiru ban sani ba har sai da aka gama yin komai." Saheer cikin rauni da sanyin murya mai cike da damuwa ya ce, "ƙawar ki bata kyauta min ba Safeera, ƙawar ki ta bani mamaki mai yawa, ta karya min zuciya, ta yi abinda ban yi tunani ba. Islaha bata kyauta min ba, isla....." sai ya kasa maganar ya kashe wayar. Sadik ya ja tsaki ya ce, "bayan duk abinda ta aikata, wai har yanzu ya yarda da ita, har yanzu akwai sauran yarda a tsakaninsu. Mtsww! Wallahi Islaha ta fita daga raina gabaɗaya, duk wani girma da ƙimarta da nake gani ya riga ya zube ya bi rariya, ta bani mamaki mai matuƙar yawa." Safeera ta fito da waya tana kallon number Islaha ta buɗe voice note ɗin. Duk suka ji muryar Islaha tana magana a sanyaye. Safeera ta kalli Sadik ta ce, "Ka daina zarginta, ni na yarda da ita, na san bazata taɓa aikata wani abun mara kyau ba. Tana da ilimi, ta san duk abinda take yi, wallahi baza ta yi abinda zai lalata tarbiyyar ta ba." Sadik ya ja tsaki ya ce, "lalata tarbiyya na nawa kuma? Ai tunda ta saka ƙafa ta bar ƙasar ta, zancen tarbiyya ya ƙare. Ni ta saka ni a tsaka mai wuya, ko me zan cewa Baffa yanzu oho." Sai kuma ya ɗan gyaɗa kai ya ce, "babu amfanin tsayuwa a nan, tunda dai bata nan ta je duk inda zata je. Allah ya kiyaye hanya" ya faɗa yana bar wajan. Saleem ya kalli Safeera ya ce, "ƙawar ki bata kyauta ba Safeera, abinda ta aikata bai kamata ba ko kaɗan. Hakan bai yi daidai da tarbiyyar ta ba ko kusa." Safeera bata ce komai ba dan ba yarda zasu yi ba, gwara ta yi shiru da bakinta tunda zargin Islaha suke yi, kome zata faɗa musu ba amincewa zasu yi ba. Safeerata kalle sa ta ce, "bara na shiga ciki, zamu haɗu zuwa gobe ina sha Allah." Ya ɗaga mata kai ta juya ta shiga gidan a sanyaye. Safeera a sanyaye ta koma gidan, ta tarar da Rukayya ta shirya ta fito zata tafi makaranta ta ce, "Adda ina ta neman Umma ta whatsapp bana samu, ya kamata ace zuwa yanzu mun ji yadda ta sauka ko?." Safeera ta ce, "in kin dawo sai mu neme ta, sai kin dawo." Ruƙayya ta fita ita kuma islaha ta tsaya tana tunanin abinda ya kamata ta yi, dole ta ajjiye aikinta ko dan saboda Baba, bazata so ya dinga dawowa daga wajen neman halak babu abinci ba. Sannan ga ƙannenta, in suka dawo daga makaranta waye zai dinga basu abinci? A ina zasu dinga zama tunda zata rufe gidan ta tafi da key ɗin? Ta sauke numfashi ta shiga ɗaki tana tunanin mafita a cikin lamarin, dan mahaifinta da ƴan uwanta suna buƙatar zaman ta a gidan ko dan saboda abinci. Mama suna tsaye ita da Hajiya Karima suna jin voice note ɗin Labiba na jiya. Mama ta yi dariyar jin daɗi da farin ciki ta ce, "kai amma na ji daɗi, ke daga jin muryar Labiba kin san tana cikin farin ciki mai yawa wallahi." Hajiya Karima ta ce, "ita da take tamu kenan, ki duba tun da muka ajjiyewa ƴar riƙon can taku saƙo, amma har yanzy bata duba ba balle ta bamu amsa ba. Kuma Oga Musa ya ce mana gidan da aka kaita gida ɗaya ne ya raba su da Labiba, Maimuna aka kai Madina su suna Jeddah. Mai yarinyar nan take nufi damu?." Mama ta ce, "kar ki damu, na san halinta zata yi magana. In bata yi magana ba ai daidai mu ke da ita, tunda har ta riga ta bar ƙasar nan ta tafi a ƙarƙashin mu ai duk ahinda muke so kuma sai ta yi." Karima ta ce, "yarinyar nan ba a gane gabanta fa, ƴar iskan kanta ce." Mama ta yi dariya ta ce, "kar ki wani damu, zamu yi magana da ita. Ai wannan ba abin damuwa bane, tunda har ta tafi ai iskanci da iyayi ya ƙare." "Kuma Alhaji Musa ya ce zasu iya ƙarawa Islaha kuɗi, dan yace mai gidan yana da kirki sosai, in ga in aka ƙara gaba ta kaimu." Suka tafa da Mama ta ce, "ke da yarinyar nan zata saki jiki ta nemi kuɗi a ƙasar nan, zata yi saurin samu a hannun karɓuwa a wajen mutanen ƙasar wallahi. Kin san kalar ta mai ɗaukar hankali ce, su da suka saba ganin farare ƙal ƙal kalar Islaha zata yi saurin ɗaukar hankalinsu." "Za ta yi fa, ba dai ta je ba? Ki jira dai mu gani, na tabbatar tana daga cikin waɗanda zasu maƙale su ƙi dawowa." Suka sake tafawa cikin nishaɗi mai yawa dan suna cikin farin ciki mai yawa. Mama ta kalli wayarta da ake ta kira, ta taɓe baki ta ce, "Saheer ne fa, da alama ya samu labarin bata nan, shine yake kirana zai fara yi min ƴar murya kamar ni ce uwar Islahan." Karima ta ce, "Ki ɗauka, baki san me zai ce ba." "Allah akan Islaha ne, bara kuma ki ji." Ta faɗa tana ɗauka suka gaisa sannan ya ce, "Mama da gaske Islaha ta tafi wata ƙasar aiki?." Mama ta kalli Karima alamun kin ji ko, sai ta yi ƴar dariya ta ce, "ta tafi Saheer, tana can gidan wani balarabe, dan an ce ko aure ma bashi dashi. Tun a kallon farko ta burge sa har ya amince ya ɗauke ta. Ka san budurwar taka ba dai ɗaukar ido ba, yanzu zata burge namiji ya ɗauke ta ko bai yi niya ba" Saheer ya ji zafi a ransa, kishi yana mamaye masa zuciya, haushin Islaha ya mamaye masa zuciya, ya daure ya kawar da fushin ya ce, "Mama meyasa za ki tura islaha don Allah?." "kai malam dakata, Islahan yarinyar goye ce da zan ɗauke ta na tura ta ba tare da amincewar ta ba? Sau nawa ina yi mata tayi tana guduwa, sau nawa ina cewa tazo tana watsa min ƙasa a ido?. Wannan ma da kanta ta same ni tace tana da buƙatar tafiyar nan. Ina ruwana dan ta nema na kai ta? Ko wuta Islaha tace min tana son shiga, da hannuna zan riƙe hannunta mu je ta shiga na dawo. Ko kana so ka ce min ta ƙarfi na ɗauke ta ana kai ta?." "Mama wai harda Labiba, yanzu Mama hakan daidai ne? Dan sun nuna suna so kawai sai a basu dama su yi ahinda suka ga dama?." "Ka ga malam bana son surutan banza, ka dakata da wannan maganar. Tafiya dai an riga an yi ta, babu dawowar su a yanzu." "In sha Allah sai na dawo da Islaha, ina dawowa gida Islaha zata fara shirin dawowa gida itama." Mama ta yi tsaki ta ce, "sai ka dawo da ita ai" ta faɗa tana yanke wayar. Ta kalli Karima ta ce, "Yaro bai san wuta ba sai ya taka, shi a tunaninsa dawowar Islaha yanzu zai yu? Bai san sai ta gama biyan kuɗin da aka kaita ba, sannan take da ƴancin yin duk abinda ta ga dama?." Karima ta ce, "ki ka sani ko duk zai biya? Yadda yake magana cikin gadarar nan na san zai iya biyan kamfani kuɗinsu ya dawo da ita." "ina ya ga kuɗin?." "Ki ka sani?." "Ai ko yana dasu wallahi bazai biya ba, sai ta biya da kanta, ai ba a banza ta hau jirgi ta bar ƙasar ba." Karima ta yi dariya suka cigaba da tattaunawa akan batun. [7/2, 10:41 AM] KRBBK: RDB2P33 Nana Haleema. A hankali ta ji ana tashinta daga bacci, Islaha ta buɗe iso a sanyaye ta kalli Sunaira da take tsaye a kanta tana murmushi. Sai a lokacin Islaha ta tuna a inda take, ta bi ɗakin da kallo sannan ya miƙe zaune a lokacin take jin ana ta kiran sallar asuba. Ta kalli Sunaiha ganin har ta shirya cikin uniform, Islaha ta miƙe tsaye tana ɗan murmushi, kafin Suhaira ta yi typing a waya ta bata. "Barka da Safiya Islaha, lokacin sallah ya yi, sannan lokacin haɗa breakfast ya yi." Islaha ta gyaɗa tana murmushi ta shiga banɗaki tana tafiya kamar bata so. A sanyaye ta yi wanka ta fito ta saka uniform sannan ta tayar da sallah, tana idarwa ta fito ta tarar da Sunaira tana ta aiki itama ta shiga tana taya ta. A lokacin suka gama haɗa lafiyayyen tea, suka haɗa simple breakfast kamar yadda aka saba da taimakon Sunaira. Suka jera a dining a lokacin ƙarfe bakwai na safe, suna tsaye a jikin dining ɗin ya sakko daga sama yana amsa waya cikin shirin fita aiki. Sai da ya zauna sannan ta ji Sunaira ta gaishe sa cikin harshen larabci, itama ta gaishe sa cikim english. Maimakon ta ji ya amsa kamar yadda ya yiwa Sunaira, sai ta ga ya kalle ta sannan ya ce, "morning, Islaha...Right?."  Ya faɗa yana kallon ta da sigar tambaya. Ta ɗan yi murmushi tana gyaɗa kanta, tana mamakinsa na kallonta har yana maimaita sunanta. Bai ce komai ba Sunaira ta yi serving ɗinsa sanann suka bar wajan. Kitchen suka koma a lokacin Sunaira ta fara karyawa, ita dai Islaha tana tsaye dan lokacin ya yi wuri da yawa, baza ta iya cin komai a lokacin ba, tafi so sai rana ta fito. Tashin motarsa suka ji alamun ya fita, Sunaira ta fito itama ta fito, suka kwaahe kayan da ya gama suka shiga aka wanke aka ajjiye. Sunaira ta yiwa Islaha typing ta bata dan ta karanta, Islsha ta karɓa ta ga ta ce, "Ki je bedroom ɗinsa ki gyara." Islaha ta kalle ta Sunaira, sai ta rubuta da turanci ta mayar dashi arabic ta bata. Sunaira ta karanta sannan suka fita ta raka ta har bedroom ɗin ita kuma ta koma. Islaha ta sauke numfashi ta shiga ɗakin tana kallon ɗakin hotonsa da wata balarabiya da yaro ta gani, ta ƙarasa tana kallon hoton ganin matar kyakykawa ga yaronsu mai kyau. Ta ɗauke kai a bayyane ta ce, "Ko ya Hamma yake? Na san zuwa yanzu ya ji labarin abinda yake faruwa. Na san zai ji babu daɗi, zai yi min hukunci mai tsauri" ta faɗa tana kallon bedroom ɗin. A sanyaye ta gyara ɗakin, ta buɗe bathroom shima ta gyara sannan ta fito a lokacin Sunaira ta shigo. Ta kalle ta taga ta buɗe wani waje ta ɗauko kaya masu yawa sosai. Ta yiwa Islaha alama da ta taho, ta bi bayanta suka tafi laundry room ta bawa Ilsaha alamun ta wanke. Islaha cike da mamaki ta ce, "kutumelecy, wankin ma ni zan yiwa wani ƙato?." Sunaira ta yi murmushi alamun bata ji abinda Islaha ta ce ba, Islaha ta karɓa suka kunna washine machine aka wanke su. Lokacin da ta gama ta kalli kayan ganin duk basu fita ba, ta yi tsaki ta wanke inda bai fita ba da hannu, ta yi drying kayan sannan ta goge. A falo suka haɗu da Sunaira ta yi mata murmushi, Islaha ta ɗan yi yaƙe sannan ta wuce ɗakin ta tsaya tana kallon closet ɗinsa. Ta taɓe baki ta buɗe ta saka kayan ta fito dan ta gaji da wannan azabar, daga girki sai shara da wanki. Ta manta rabon da ta yi wanki, tunda ta baro gidan marayu Hamma ya shagwaɓata, wanki indai ba na undies ba bata yi. Shi yake biya a wanke a goge mata, a kawo mata ta ajjiye sai dai ta saka kawai. Amma daga zuwan ta ta fara yiwa wani ƙato wanki, ga kayan duk sun yi dauɗa kamar ƙaramin yaro. Ganin Sunaira a zaune ya saka itama ta zauna, sai kuma ta tashi ta haɗa tea ta sha ta ɗauki wayarta tana duba messgaes. Gabanta ya faɗi ganin messages ɗin Saheer har guda biyar sun shigo a jere. Ta zubawa saƙon ido amma ta kasa buɗewa balle ta ga abinda ya ce, ta kalli ƙasan sunansa ta ga saƙonn Adda, sai na Maman su Safeera, sannan na Safeera harda Saleem da Sadik. Na safeera ta fara buɗewa ta ga vn ne na sakan talatin, ta buɗe ta ji Safeera ta ce, "Islaha ya ki ke, ina ta kiran wayar ki kiran baya zuwa. Ina fatan komai lafiya lau. Hamma ya san kin tafi, ransa ya ɓaci sosai. Ban taɓa jin rauni a muryarsa kamar yadda naji ba, yace min baki kyauta masa ba, kin karya masa zuciya." Islaha ta sauke numfashi cikin damuwa, ta lumshe ido tana tuna tazarar da take tsakaninta da Hamma, ta san yana can ransa a ɓace, gashi bata nan bata san lokacin da zata koma ba balle ta bashi haƙuri. Ta buɗe ido ta kira Safeera ta audio call amma baya yi, ta kalli Sunaira ta ga tana waya, sai kuma ta tuna itafa ƴar ƙasar ce. Sunaira tana kashe wayar, sai Islaha ta shiga google ta yi english to arabaic ta miƙawa Sunaira dan ta karanta. Sunaira ta karɓa ta karanta sannan ta yi murmushi, ta yiwa Islaha downloading botim, ta koma google ta yi mata rubutu ta sake bata. Islaha ta kalla ta ga ta ce, "Ki faɗawa wanda zaku yi waya, ya ɗauko botim ya buɗe sai ku yi waya." Islaha ta gyaɗa, ta yiwa Safeera voicenote ta faɗa mata, ba jimawa sai ga message ɗin Safeera tace mata ta buɗe.  Islaha ta shiga app ɗin ta kira Safeera, sai gashi tana ringing har Safeera ta ɗauka. "Islaha ya ki ke?." Isalaha jin muryar Safeera ya saka ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Safeera har yanzu baki da lafiya? Muryar ki bata yi daidai ba." "Gani nan dai kawai, ko aiki ban je ba. Ina fatan komai normal ko?." "Eh to kusan hakan. Gidan da nake babban gida ne sosai, kuma mai gidan balarabe ne. Allah ya taimake ni akwai wata balarabiya itama tana aikin, tana da kirki sosai, itace take ɗan nuna min wasu abubuwa. Sai dai aikin na su babu hutu, komai kai zaka yi musu. Abin takaicin ma wai har wanki." "To ya za a yi, Allah ya taimaka." "Amin. Hamma ya yi miki waya ko?." "Sadik ne ya fara zuwa, sannan ya kira Saheer ɗin, ransa ya ɓaci sosai, bai ji daɗi ba. Ya ce min ƙawata ta yi abinda bai yi zato ba, ƙawata ta karya masa zuciya. Gaskiya bai ji daɗi ba, a muryarsa kaɗai zaka fahimci ya ji ciwo sosai." "Na san hakan zai faru, na ga messages ɗinsa bazan iya buɗewa ba, dan ban san me zan ce masa." "Saleem da Sadik ma ransu ya ɓaci sosai. Sadik yana ta masifa, shi wai wallahi bai yarda dake ba. Shi kamar zargin ki yake yi, wai komai ke ki ka shirya." "Shi tun farkon abin nan abai yarda dani ba, gani yake kamar kaina na bayar aka bani kuɗin aikin Baffa. Bai san ina da hankali ba, kawai sai na lalata rayuwata?." "wallahi ɗazu ma ya faɗa, yana ta cewa wai kin bayar an baki, Sai da Saheer ya taka masa burki akan hakan." "Hmmm na fisu tsanar aikin nan wallahi." "Ki samu ku yi magana da Hamma ko zai ji daɗi, dan gaskiya bai ji daɗin wannan hukuncin nan naki ba." "Sai ya huce, yanzu in na kira shi bazai fahimce ni ba, sai zuwa jibi sannan zan kira sa, yanzu yana dokin fushi bazai ji me zan ce masa ba." Safeera bata ce komai ba, Islaha ta ce, "baki ce min ina Umma ba, ko kun yi waya?." Safeera ta ce, "hmm to me zan ce? Abinda yake so ne fa Islaha, dan ta tafi neman kuɗinta ni neman ta ɗin me zan yi kuma?." "Duk da haka Bestie, Uwa ce fa, ko babu komai zaki so ki ji ya ta sauka ko?." "tafiya ta yi ta bar mu, ta zaɓi yiwa larabawa bauta akan gidan auren ta. Yau ko aiki ban je ba, ina gida ban san waye zai dinga kula da gidan in bana nan ba. Ina tunanin ma aikin kawai zan ajjiye saboda dafawa Baba abinci. Kin ga tafiyar ita ta yiwa kyau, tambayar ta ɗin me zan yi." "Umma tana Madina, ni ina jeddah ni da Labiba. Amma zan kira ta in sha Allah." Safeera ta ce, "Bestie zamu yi magana anjima" ta faɗa tana yanke wayar, Islaha ta bi wayar da kallo tana sauke numfashi tana kallon message ɗin Hmmanta amma ta kasa buɗewa. •••••••• Yana zaune yana kallon screen ɗin laptop ɗinsa, murmushi yake yi yana kallon kyakykyawar budurwa wacce kallo ɗaya zaka yi mata ka san bahaushiya bace. Kana ganinta ka san bata jin hausa ko fulatanci, dan ko kaɗan bata yi kama da ruwa biyu ba, ita ruwa ɗaya ce. Ta saki gashinta har baya tana ta dariya tana kallon Rehaan. Fatima kenan, ƴar autar su Mamy kuma age mate ɗin Rehaan. Sun saba da Rehaan sosai, ya kan ɓata awa ɗaya suna hira da Fatima, ta zama kamar ƙawarsa, baya kallon ta a matsayin ƙanwar Mamy. Ya ɗan taɓe baki yana kallon ta ya  ce, "ni babu wani aure da zan yi." Ta yi dariya ta ce, "Mamy ta faɗa min auren ka ya kusa, shine na ce yaron nan ashe aure zai yi babu labari." Ya yi murmushi ya ce, "sai ki aurar dani. Baki tafi aiki ba?." "Sai anjima kaɗan zan tafi." "Okay byee" ya faɗa yana niyar katse kiran. Ta yi dariya ta ce, "Mr Busy, za a tafi aikin ne?." Bai bata amsa ba, sai ta ce, "ka gaishe da matar ka." Ya harare ta ya ce, "you are not serious" ya faɗa yana kashe laptop ɗin yana jingina da kujera idonsa a rufe. Tashi ya yi ya buɗe ido, ya miƙe zaune yana kallon wani wajen daban dan bai sam me zai yi na kwata-kwata. A yadda yake zaunen nan kamata ya yi ace yana shan tea ko coffee, dole ya samo housemaid ko dan haka. Ranar da ya yi nufin kiran Maleek a waya fasawa ya yi, amma a yanzu yana jin zai yi ko dan taimakon kansa. Kiran Jazy ne ya shigowar wayarsa, yana ɗauka Jazy ya ce, "Mr Man how far?." "Fine. Ya ka ke?." "Yau hausa ka ke ji da ita kenan, lafiya lau. Ka yi magana da Maleek ɗin?." Ya ɗan sauke numfashi sannan ya ce, "ban yi ba, bana so a kawo min wacce bazan iya cin abincinta ba." "Kai ma ka san duk housemaids ɗin ƙasar nan they are very neat wallahi, ba su da ƙazanta ko kaɗan." "Ni yaushe zaka zo?." "zan zo, amma ba yanzu ba." "ka hanzarta ka zo, akwai lissafin da zaka ta ya ni mu yi." "Alright. Amma kafin nan ka fara magana da Maleek ko Ubaid a baka housemaid ɗaya, na san halin ka, kafi son komai a yi maka ba wani abincin kirki ka ke ci yanzu ba. Ni kuma Mamy ta bani amanar ka, shiyasa na damu." Ya ɗan murmusa kaɗan ya ce, "ka raina ni, wai an baka amanata, kana mantawa ni yayan Riyya ne ko?." Jafar ya ce, "Tunda ba kai ka haife ta ba ai shikenan. Sai wani lallaɓa ka nake yi kamar cikina abincin zai je. Rehaan kar ka yi magana dasu, nan ba Yola bane balle kace Mamy zata dafa maka." Ya ɗan taɓe baki ya ce, "zan yi waya Shams ya kawo min chef daga can." "Har sai an kawo maka chef daga nigeria? Dan dai kawai kana da kuɗin biya ko?." "Ya ka ke so na yi ne?." "yadda ka ke so Rehaan." Rehaan ya kashe wayar, ya miƙe ta fita daga falon kai tsaye ya nufi gidan Maleek da niyar tambayarsa ya bashi housemaid face to face.... Nana Haleema [7/2, 10:42 AM] KRBBK: RDB2P34 Nana Haleema. Labiba tunda suka tashi da safe suke aiki, duk ta jigata amma haka ta daure suna yi tana sauke numfashin wahala. Aisha ta kalle ta ta ce, "Duk kin gaji, kamar kin yi wani aiki mai yawa." "A haka babu yawa aikin?." "Na ki wasa ne. zan je na zubar da sharar nan a waje, ina zuwa." Labiba ta ɗaga mata kai ita kuma ta fita. Labiba ta zuba abinci ta fara ci, kanta har sarawa yake yi saboda gajiya ga yunwa. Hannu ta ji a sako ta bayanta an riƙo ƙugunta, ta firgita sosai ta juyo suka haɗa ido da Ubaid yana binta da wani shegen kallon kamar zai cinye ta. Duk da ba yau namiji ya fara yi mata haka ba, amma gamin Ubaid sai ta diririce ta ta rasa abinda zata yi, ya ja ta a hankali zuwa jikinsa, yana shaƙar ƙhamshin humar da ta shafa a wuyanta. Labiba jikinta ya fara rawa, ta ɗan daure bata nuna ba, tana jin yadda yake yawo da hancinsa a wuyanta yana sake haɗa bayanta da jikinsa. A hankali ya kai hannunsa wuyanta yana shafawa a hankali kafin ya ce, "Labiba." Yadda ya faɗi sunan ya burge ta, dan yadda ya faɗa ɗin ya yi mata daɗi har bata san ta lumshe ido ba. Ya yi mata kiss a wuyanta sannan ya ce, "meet me in my room, now" yana faɗa ya sake ta ya juya ya fita. Labiba ta juya ta bisa da kallo tana dafe ƙirji, sai suka haɗa ido da Aysha da take tsaye a wajan. Labiba ta ruɗe ta kasa magana, har Aysha ta shigo kitchen ɗin ta kasa cewa komai. Aysha ta bita da kallo kafin ta ce, "kin zo ƙasar nan saboda ki tara kuɗi ko saboda ki yi asarar kuɗi?." Labiba a diririce ta ce, "ni ban san ma ya shigo ba, kawai na ji...." Aisha ta dakatar da ita ta ce, "kawai ki bani amsa." Labiba ta ce, "ina so mana, kuɗi na fito nema." Aisha ta ƙare mata kallo sannan ta ce, "Amma ki ke tsaye a nan?." Da mamaki ta ce, "Ina zan je to?." "meyasa baki bi shi ɗakin ba kamar yadda ya ce?." Labiba ta bita da kallo alamun ƙarin bayani, Aisha ta ce, "ta wannan hanyar zaki fara tara kuɗin irin wanda baki yi tunani ba. Ubaid mutum ne mai kuɗin gaske, wallahi kuɗin da yake dashi zan iya cewa bai san adadinsu ba, kuɗin da yake dashi da a nigeria yake zai zama na farko a ƙasar. Indai zaki yi abinda yake so babu abinda bazai yi miki ba...." "Ni ɗin nan da ki ke gani nabu abinda baya bani, na canjawa iyayena gida, na siya musu mota, na kawo su umra duk da kuɗin da nake samu a gidan nan. Kema dan jinin mu ya zo ɗaya ne ya saka har na bar ki a gidan nan, har nake faɗa miki sirrin gidan, amma da wallahi bazan taɓa bari ki raɓe sa, ba saboda ni kaɗai na san alkhairi da nake samu tare dashi." Labiba ta ɗan yi shiru tana tunani kafin ta ce, "Aysha kuma kina ganin babu matsala?." "Wacce matsala ana zaune lafiya? Kuɗi ki ka zo nema kuma su zaki samu, Ba shikenan ba?. In ki ka biye ta albashi kuɗin kayan sakawa ma gagarar ki zai yi, dan kayan ƙasar nan shegen tsada ne dasu wallahi. Amma in ki ka saki jiki shikenan zaki ga kin zama hajiya, kina daga nan kina turawa gida abin arzuƙi ana bin ki da albarka. In ki ka saki jiki, Ubaid ƙasar waje zai ɗauke ki ya tafi dake." Labiba ta yi shiru bata ce komai ba, har lokacin jikinta a sanyaye yake ta kasa aikata kataɓus balle ta amsa ta amince ko bata amince ba. Aysha ta bita da kallo tana dariya a ranta, tana ayyana bata san dawar garin ba, dan inda ta san waye Ubaid da bata tsaya a wajen ba. Aishata girgiza kai suka cigaba da gyare gyarensu. Labiba da ta shiga ɗaki waya ta ɗauka ta shiga lambar Mama ta ganta online sai ta kira ta ta inda Aisha ta koya mata. Mama tana ɗauka ta ce, "ke kuma haka ake yin abu? Daga tafiya sai a jiki shiru babu wani labari?." Labiba ta ce, "ina nan lafiya Mama, ya jikin Baffa?." "Da sauƙi. Ya aikin?." "Mama aiki ake yi kamar jakai, akwai gajiya a aikin su wallahi." "amma akwai damun kuɗi ba, kar ki bada ni mana, kar ki saka na yi danasanin tura ki, dan Hanan da take nan gida kuɗin da take kawowa yana da yawa, ke gaki a can har kin fara ƙorafi. Kar ki saka zuwan naki ya zama bashi da amfani." Ran Labiba ya ɓaci sosai ta ce, "Mama wai ko mai sai ki ce Hanan, me take baki wanda ni bana bayarwa?." "To itace take kawo min abin arzuƙi, ba dole na dinga ambatar sunanta ba?." "Nima zan aiko miki da kuɗin da sai kin ce gwara ni akanta." "Dakyau! Kina yin hakan kin tabbatar min da ke ɗin mai ƙaunata ce, ke jinina ce, ke mai kishi ce." "Zan yi Mama, indai zaki daina yabonta a kaina." "Tuni zan daina, indai zaki yi abinda ya fi nata ita ɗin banza. Ai ni duk wacce ta fi kawo min kuɗi itace ta gaban goshi a wajena. Ke dai kawai ki riƙe kan ki." Labiba ta murɗa baki kamar tana wajan ta kashe wayar. Sai ga kiran Hannan tana ɗauka ta faɗa mata abinda ya sake ɓata mata rai ta kashe tana. Aysha ce ta shigo ta bita da kallo ta ce, "ki tashi mu je mu ƙarasa aikin can." Labiba ta miƙe a sanyaye ta fito, bayan sun gama Aysha ta ce, "zan je na yi wanka, kema ki yi." Ta ɗaga kai ta shiga ɗaki, ta shiga wanka tana yi tana tsakin abinda Hanna ta ce mata har ta fito, tana fitowa ta ga an kashe hasken ɗakin. Abin ya bata mamaki, dan ta san ita a kunne ta bar sa da zata shiga. Ta ƙarasa wajen switch, zata kunna kenan ta ji an riƙo ta, ta firgita zata ƙwace ta ji muryarsa a kunnenta. Ya kunna hasken ya bita da shegen kallo ya ce, "ke mai kyau ce." Gabanta ya faɗi, amma da ta tuna ƙudurinta akan nsman kuɗi sai ta ɗan yi murmushi tana kallon sa. Ya ɗago da fuskar yana kallon idanunta ya ce, "i’m waiting for you" yana faɗa ya fita daga ɗakin. Yana fita Aysha ta shigo ta bita da kallo ta ce, "zan je mall na dawo." A sanyaye ta ce, "nima zani." "A'a ki zauna, ba ya ce ki same sa a ɗaki ba?." "Ni tsoro nake ji fa." "Tsoron me? Kina so ki ce min baki taɓa yi ba?." "ban taɓa ba, sai dai ƙananun abubuwa. Amma ban taɓa bada kaina ba." "Dakyau! Tunda kin saba da ƙananun abubuwa sai ki fara da manyan yau, kuma tukwicin babba ne tunda shine na farko. Ki saki jiki ki je a wuce wajen, in ba haka ba wallahi zaki yi danasani mai yawa." “Zan je, kawai ina ganin kamar abin zunubin ya yi yawa saboda a ƙasar saudia nake." Aisha ta taɓe baki ta ce, "Sai me da a ƙasar ki ke? Ai ba a makka ko Madina ki ke ba, nan Jedda ce. Allah na tuba ko a Makka da Madina nan ki ke meye a ciki? Mu sau nawa muna yi a can? Akwai abinda ya same mu?." Labiba ta ce, "ni tunani nake yi wallahi." "Mtsww! Ke ki ka sani, ni na fita." Labiba ta koma gefen gado ta zauna tana tunani, tana son tara kuɗi masu yawa sosai, tana so ta yiwa Mama abinda Hanan bata yi mata ba, ga hanya ta samu amma zuciyarta tana rawa sosai. Ta saba ƙananun abubuwa da maza, babu abinda namiji bai taɓa yi mata ba, babu inda hannun namiji bai je a jikinta ba. Ta saba da hakan sosai, kuma ta ƙware a kai kawai bata taɓa bada kanta ba, sun yi da wani alhaji akan hakan tafiyar nan tazo. Duk da ba wai faruwar abin take jin tsoro ba, tsoron ta ɗaya Ubaid ba ɗan ƙasar su bane, sai take ganin kamar bai dace ta saka masa jiki ba. Ta tuna kalaman Aysha, sai ta samu ƙarfin guiwa mai yawa, tana ji a ranta lokacin zaman ta hajiya ne kawai ya yi, shiyasa Allah ya jinkirta mata har aka zo yanzu.A sanyaye ta shirya ta saka kaya ta nufi ɗakin nasa.  Zaune ta same sa daga shi sai short, ta bi sa da kallo dan fatarsa kaɗai ma abin kallo ne, fari ne sosai ga kyaun larabawa. Tana shiga ya taso ya riƙo ta yana kallon ta ya ce, "kina jin tsoro?." Ta ɗaga kai a sanyaye ya ce, "Sau nawa ki ka taɓa yi?." Ta girgiza kai ta ce, "Ban taɓa ba." "Kin tabbatar?." Ta ɗaga kai alamun eh, ya murmusa ya ce, "nawa ki ke so na baki?." Ta kalle sa suka haɗa ido ya ce, "ki faɗa." Labiba bata ce komai ba, ya sake ta ɗauko kuɗi riyal ya buɗe hannunta ya saka mata, kallon kuɗin take yi dan bata taɓa ganin Saudi riyal ba tunda take, bata san riyal nawa bace, kawai kallon ta kawai take yi ta ga dai ɗari biyar a rubuce. Ya yi converting kuɗin da ya bata to naira ya nuna mata wayarsa, zaro ido ta yi ganin kuɗin mai yawa a kuɗin nigeria, ta kalli hannunta ta gansu ɗan kaɗan ba wani yawa ne dasu ba, amma a kuɗin nigeria da ywa sosai. Suka haɗa ido, kafin ta ce wani abun ya jawo ta ya ƙanƙame yana zare rigar jikinta a hankali. •••••••••       Umma tana zaune tana kallon hannunta cikin gajiya, hannunta duk ya yi ja saboda wankin yaran da ta yi. Ta sauke nunfashi mai tsaho, gidan shiru duk sun fita sai ita kaɗai shiyasa ta samu damar hutawa. A gajiya yake jinta sosai, gaɓoɓinta duk sun gaji saboda aikin da ta sha a gidan. Ko abincin kirki bata samu ta ci ba saboda aiki, sallah ma ba a nutse take yi ba saboda ihun su. A sanyaye ta jawo wayar ta kunna data amma data taƙi yi kwata kwata. Ta sauke ajiyar zuciya ta kira lambar Safeera, wayar ta shiga dan ta saka kati sosai a layinta. Wayar tana ta yi ba a ɗauka ba, ta sauke ajiyar zuciya ta rasa wanda zata kira. Kallon lambar Baba take yi abinda ya faru yana dawo mata a ranta, ta rufe ido ta buɗe ta nemo, dan baza ta iya kiransa ba, sai ta kira lambar Atika. Bata jima ringing ba Atika ta ɗauka, Umma ta ce, "Atika kina jina." Daga can ɓangaren Atika ta ce, "Ina jinki, Hajiya Maimuna mutanen makka da madina. Ya ki ke?." Umma ta sauke numfashi ta ce, "lafiya lau, kowa lafiya?." "Lafiya ƙalau. Ya aka yi wayar ta shigo? Na ji ance fa layin nigeria ba ya yi." "Eh da yake na saka kati sosai a wayar, kema kuma yanzu zasu ɗauki katin wayar ki." "Allah sarki. Ai da kati sosai a wayar tawa, ɗazu na saka na dubu uku shiyasa ta shigo." "Na kira Safeera bata ɗauka ba, ban yi magana dasu ba tunda nazo. Don Allah ki duba min su." Atika ta ce, "kar ki damu zan duba miki su in Allah ya yarda. Da fatan komai lafiya dai ko? Aiki ya samu ko?." Umma ta ɗan taɓe baki cikin wani irin yanayi ta ce, "Aiki ya samu kan Atika, ina kan yin aikin ma yanzu." "haka muke fata. Kin shiga masallacin annabi?." "Ban je ba, amma zan je in sha Allah." "Ayi mana addu'a, Allah ya biya mana buƙatun mu na alkairi." "Amin. Don Allah ki duba min su, in kin same su ki kira ni." "Kar ki damu ƙawata, ki ɗauka kamar kina Nigeria, wallahi zan kula miki dasu sosai, zan yi komai dan na samar musu da nutsuwa." Sai hankalin Umma ya kwanta, ta yi murmushin jin daɗi ta ce, "na gode sosai." Daga haka suka yi ssllama ta kashe wayar. Tana son kiran ƴan uwanta na Katsina amma tana jin shakkar aikata hakan, dan ta san bata shuka abin kirki ba, babu wanda zata iya tunkara a halin yanzu. Ta yi ajiyar zuciya, ta miƙe tsaye daƙyar tunawa da kayan wanke-wanken da ta bari a kitchen, ko zasu shekara ita zata wanke babu abinda zai ragu sai ma ya ƙaru. Ta shiga banɗaki, bata jima ba ta fito tana goge ruwan fuskar ta. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Hasbuhallahu wa'imal wakil! Na shiga uku Maimuna!" Ta faɗa a tare cikin tsananin firgici da tashin hankali wanda bata taɓa tsintar kanta a ciki ba. A guje ta koma banɗakin tana sauke numfashi ƙirjinta yana up and down, ta rufe ta buɗe cikin firgici, ta ɗan daki fuskar ta ta tabbatar ba mafarki take yi ba, da gaske ne ba wasa ba. Bata san ta fara hawaye ba sai ɗuminsu ta ji akan fuskar ta, tashin hankalin da ta gani dole ya saka ta zubar da hawayen da bata shirya zuwan su ba. Tunda take a duniya bata taɓa ganin namiji tsaye a haka a gabanta ba, ko mijinta da suka kwashe shekaru sama da ashirin da wani abun bata taɓa iya tsayawa ta kalle sa muraran babu suttura, haihuwar uwa da uba ba, saboda kunya mai tsanani. Yau ga wani wanda ba muharamin ta ba, tsaye a gabanta babu suttura ko kaɗan a jikinsa yana yi mata murmushi, yana nuna mata jikintsa ta sigar iskanci.😂 Ta dafe ƙirji dan har lokacin ƙirjinta bai daina bugawa, ta jingina da ƙofa hawaye yana cigaba da sauka daga idanunta cikin tsananin ɗaci da tashin hankali. Da tana da damar goge abinda ta gani daga ƙwaƙwalwar ta da ta goge, da ta rufe ido shi take kallo a idanunta. Tana jinsa a kusa da ƙofar banɗakin yana bugawa yana yi mata magana cikin yarensa, bata jin me yake faɗa amma ta san ba kalaman kirki yake faɗa ba. Umma hawayenta ya ƙaru, ta rufe bakinta da hannunta cikin wani irin yanayi da tashin hankali. Bata san ta zame ta zauna a wajan ba, bata san lokacin da ta ɗauka a wajan ba ta dai san ta jima a wajen a zaune tana kuka. Ni dai Umma ta bani dariya🤣🤣 Nana Haleema✍🏻❤️ [7/3, 2:04 PM] KRBBK: RDB2P35 Nana Haleema Sai da ta gaji da kanta sannan ta miƙe a sanyaye ta buɗe ƙofar, ta fito tana leƙowa kamar munafuka, ganin ba ya ɗakin ya saka ta yi ajiyar zuciya tana takowa a hankali ta fito tsakiyar ɗakin. Har lokacin abinda ta gani bai daina yi mata gizo ba, har lokacin abinda ta gani da idanunta bai daina yi mata yawo a kanta ba. Ta rufe ido ta buɗe tana kallon daidai inda ta gan shi a tsaye da abinda yake nuna mata. Tsoron gidan ya mamaye mata zuciya, a haka ta buɗe ƙofar ta fito tana leƙe cikin ruɗewa. A sanyaye take takawa  ta koma kitchen ta fara wanke kwanukan a tsorace. Ƙarar rufe ƙofar kitchen ɗin ta ji, ta waigo a hankali ta gansa a yanayi irin na ɗazu, yanayin yanzu har ya fi na ɗazu muni, kuma yana tsaye ƙyam yana kallon ta. Umma ta ƙwalla ƙara ta gudu daga wajan tana kuka, ya biyo ta yana kallon ta yana murmushi yana yi mata magana cikin larabci. Ƴar tsere suka shiga yi a kitchen ɗin, tana gudu yana binta yana maganar da bata san me yake faɗa ba, gashi babu wata suttura da ta suturta jikinsa, ita kuma firgici da tashin hankalinta ninkuwa suke yi. Ba ta yi tsammani ta ji ya cafko hannunta, ya haɗa ta da jikinsa yana cigaba da yi mata murmushi kamar zai yi mata kiss. Umma ta yi dogon salati ta gigice, ta ja jikinta da ƙarfi ta fizge, ta fita daga kitchen ɗin a guje ta afka ɗaki ta rufe ƙofar tana kuka mai sauti. Jikinta karkarwa yake yi, ta rasa abinda ya kamata ta yi sai kuka da take yi kamar ranta zai bar gangar jikinta. Lokaci ɗaya zazzaɓi ya rufe ta ruf, ta kashe ac ta hau kan gado ta rufe jikinta tana cigaba da zubar hawaye. Ta kasa baccin kuma ta kasa mantawa da abinda ya faru, jikinta ya cigaba da karkarwa na tsahon lokaci tana a haka. Tana ji ana kiran sallah amma baza ta iya tashi ba, a haka har aka idar ta fara jiyo hayaniyar yaran gidan alamun sun dawo. Dukan ƙofar ake yi da ƙarfi tana jin muryar masifaffaiyar matar gidan tana magana ita dai ta kasa motsawa, tana cikin bargo zazzaɓi ya rufar mata a jikinta. Can anjima ta ji muryar Shafa tana cewa, "Maimuna taso ki buɗe, Shafa ce." Jin hakan ya saka Umma ta diro daga gadon ta zo ta buɗe cikin rawar jiki. Hajiya Shafa tana shigowa Umma ta kulle ƙofa a firgice. Hajiya Shafa ta bita da kallo ta ce, "Lafiya? Me ya same ki ki ke wannan rawar jikin?." Umma bata ce komai ba saboda tashin hankali, Hajiya Shafa ta ce, "wai meye haka ki ke yi? Kin kama kin rufe ƙofa kamar gidan ki, suna ta buga miki ƙofa kin ƙi buɗewa, shine suka je suka nemo ni aka ce na zo nayi miki magana. Kar ki haifar mana da matsala fa, kar ki aikata abinda za a ɗaure ki a ƙasar nan wallahi." Umma ta kasa cewa komai sai rawar jiki kawai take yi, ta kasa buɗe baki ta ce komai. Hajiya Shafa cikin tsawa ta ce, "ki yi magana mana, meye wannan na rawar jikin?." Umma tana jan numfashi ta ce, "ni dai a canja min gidan aiki, bana son gidan nan, don girman Allah a canja min gida ko a mayar dani Nigeria." Ta bita da kallo ta ce, "ban gane ba, ban gane a canja miki waje ba. Meye ya faru?." Umma ta ce, "nidai bazan iya ba, a canja min gida don girman Allah, bazan iya zama a gidan nan ba, wallahi bazan iya ba. Gida zan tafi, bazan iya zama a nan ba." Hajiya Shafa ta bi Umma da harara ta ce, "to uban meye ya saka baza ki zauna ba? Ki yi min bayani yadda zan fahimta, meye ya faru?." "Mai gidan nan nake gani tsirara yana shigowa, har bina kitchen yake yi babu komai a jikinsa, yana jawo ni jikinsa yana taɓa ƙirjina, yana ƙoƙarin sumbatata. Ni dai bazan iya ba, a canja mim waje, bazan iya zama a nan ba wallahi" ta faɗa jikinta yana rawa, jikinta yana karkarwa. Hajiya Shafa ta ja tsaki ta ce, "wani abun ya yi miki?." "Na faɗa miki ya taɓa min jiki." "Ina nufin komai ya faru?." "Allah ya kiyaye, Allah ya yi min tsari da wannan saɓon." Hajiya Shafa ta ce, "Tunda komai bai faru ba meye na ɗaga hankali? Dan yana shigowa tsirara ai ba wani abun ya yi miki ba, jikinsa ne ko?." Umma ta kalle ta ta ce, "babu komai a jikinsa fa, sannan dambe mu ka dinga yi dashi, yana bina ina guduwa." Hajiya Shafa ya ce, "sai me? Ai bai yi miki komai ba ko?." Umma ta yi sak tana kallonta cikin sabon yanayi, jikinta yana yin sanyi ta kasa cewa komai. Hajiya Shafa ta ce, "bana son ƙauyanci Maimuna, ki daina wannan shirmen kamar wata ƙaramar yarinya. Yau ki ka saba ganin namiji babu kaya ko me?." Umma dai ta kasa magana sai kallo kawai take binta dashi, dan ta kulle mata baki, bakin ya rufe ruf ta kasa magana. Hajiya Shafa ta ja tsaki ta ce, "ki nutsu, daga yin kwana ɗaya har sun fara yi min complain a kan ki, ki nutsu in ba haka ba zaki kore ki wallahi." Umma ta ce, "ni dama zasu kore ni ɗin." "A kore ki ɗin mana meye ya dame ni? In aka kore ki sai ki san inda zaki zauna, nan ba Nigeria bace da zaki je ki kama hayar gida kara zube. Sannan kuɗin da aka kashe miki aka kawo ki sai kin biya, wallahi ko sisi baza a yafe miki ba, in ba haka ba hukuma ta raba ku. Kuma in ki ka bar gidan nan ki ka aikata wani abu mara kyau aka kama ki wallahi baza ki tsira ba. In zaki nutsu ki nutsu, nan ba a Nigeria ki ke ba, uban ki zasu ci wallahi." Umma ta dafe kai muryar ta tana rawa ta ce, "yanzu haka zan cigaba da zama? Ga aiki kamar jaka, daga jiya zuwa yau aikin da nayi ban san adadinsa ba. Ni dama a iya aiki abin zai tsaya da sauƙi, zan jure na cigaba da yi tunda ni na kawo kaina. Amma wannan lamari ya girmi aikin da  wahalar sa, namiji magidanci kamar wannan yana yawo a gabana babu kaya ai dole hankalina ya tashi. In ya faɗo min cikin dare fa?." "Kema sai ki faɗa masa, sai meye?Ai ba yau ki ka fara haɗuwa da namiji ba." Umma ta zuba mata ido kawai bata ce komai ba, dan har wani zafi take ji a jikinta, zazzaɓin da ya rufe ta gabaɗaya ya sauka saboda tashin hankali. Har gumi take ji yana tsatstsafo mata, maganar Hajiya Shafa ta fi ɗaga mata hankali. Hajiya Shafa ta ce, "ki dakatar da wannan shirmen, ki saki jiki ki yi aiki. Tunda ki ka zo baza ki samu ƴanci ba sai kin gama biyan bashin kuɗin da yake kan ki, yanzu a ƙarƙashin kamfani ki ke, dole ki nutsu. Zan kira Alhaji Musan, zan faɗa masa ya yiwa waɗanda suka yi miki hanya magana, bazan ɗauki wannan shirmen ba wallahi, na gaji da kawo ƙara." Umma dai bata ce komai ba dan an kulle nata baki. Hajiya Shafa yi tsaki ta ce, "ki fito ki yi musu aiki, ki daina wanna ɗari ɗarin, ba jin yaren ki suke yi ba. In kina ɗarare jiki zasu zargi baki da gaskiya, in suka yi miki wani abun ke ki ka jiyo" ta faɗa tana yin gaba. Umma dai tana tsaye kamar an dasa ta a wajan cikin tashin hankali, Hajiya Shafa ta juyo ta ce, "ki zo mu je." Umma ta tako a hankali ta biyo bayanta cikin yanayi na ruɗewa da tashin hankali. •••••••• Mamy tana zaune tana waya da yan ƙasar su, bayan ta gama wayar Abba ya kira ta ya ce ta zo yana neman ta. Mamy tq miƙe ta nufi apartment ɗinsa ta same sa a zaune. Ta ƙarasa ta zauna ta ce, "gani Abba." Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Daada ce." Mamy ta ɗan murmusa ta ce, "akan maganar Rehaan ko?." Ya ɗaga kai ya ce, "ta ya ki ka canka?." Ta yi murmushi ta ce, "indai har aka ce Daada to tabbas na san maganar Rehaan ce. Me ya faru?." Ya yi murmushi sannan ya ce, "akan auren sa da yarinyar can ne, ta matsa a kai sosai ma kuwa. Dan yau ta ce min ko ta mutu na tabbatar ya auri yarinyar, hakan shine zai saka ta kwanta a kabarinta lafiya." Mamy ta ce, "ikon Allah! Wai a ina ta san yarinyar nan haka?." Ya girgiza kai ya ce, "Ke dai ki bar girma Nadira, Daada ta girma shekaru sun ja, shiyasa take fama da rigima kala kala." Mamy ta ce, "to yanzu kun yi magana da iyayen yarinyar ne?." "Na faɗa min ance mai riƙonta yana kwance a asibiti, da wa zan yi magana?." "To sai ka faɗa mata hakan ko?." "Na faɗa mata, ta sake maimaita min ko bata da rai na tabbatar an yi auren nan. Tana son yarinyar, kuma ita take so Rehaan ya aura. Ko yau ta mutu, gobe a ɗaura musu aure." Mamy ta yi murmushi ta ce, "To me zamu ce tunda Daada ce ta yanke? Sai mu yi fatan Allah ya sa ta gari ce." Abba ya ce, "Amin ya rabbi. Zan saka a yi min bincike mai ƙarfi a kanta.” Mamy ta ce, "ni wallahi Ikram nake yi masa sha'awar aure, yarinyar tana da hankali sosai, kuma ni na lura kamar itama tana son shi." Abba ya yi dariya ya ce, "za a ki saka a maimaita Juwairiyya da Jafar kenan. Ke kin san yadda aka kai ruwa rana akan auren nan, yanzu in aka sako maganar Ikram da Rehaan ai babu zaman lafiya." Mamu ta ce, "Inda zai amince ɗin da sauƙi, yadda ta amince dana Riyya shima zata amince." Ya yi murmushi ya ce, "indai har Rehaan ɗin zai amince da Ikram ɗin sai ya aure su duka, Ikram itace tamu, mun san halinta ta san namu. Ita kuwa wannan bamu san daga ina take ba." Mamy ta ɗan taɓe baki tana jin takaici a ranta ta ce, "ni tun kafin tazo ma bana sonta, sam bata yi min." Abba ya ɗan buɗe ido ya ce, "akan me? Yarinyar da baki santa ba zaki ce baki so bata yi yi miki ba?." Ta yi shiru bata ce komai ba, Abba ya girgiza kai ya ce, "Saboda Rehaan baya so ko?." Mamy ta kalle sa ya ce, "Na san halin ki ai, duk abinda yake so shi ki ke so, abinda baya so kema bakya so. Kefa koda kina son abu, da ya kushe sai ya fita daga ranki. In kuma bakya so, shi kuma yana so sai ki so kema." Ta ɗan yi murmushi dan tasan haka ɗin ne, ko me Rehaan yake so tana so, in baya so bata so. Abba ya ce, "yanzu dai kin san dole nayi abinda mahaifiyata take so ko?." Ta girgiza kai ta ce, "gaskiya ne." "To ki ba da haɗin kai akan auren nan, na fahimci Daada da gaske take, babu wasa ko rikicin tsufa. Ki yi haƙuri." Mamy ta girgiza kai bata ce komai ba, amma ko kusa bata son auren nan, haka kawai yarinyar bata yi mata ba, bata santa bata taɓa ganinta ba, amma tana jin ƙinta a ranta, saboda tana ganin ta silarta za a yiwa ɗan da ta fi so a duniya dole, bata taɓa yiwa ɗanta dole akan komai ba, amma akanta za a yi masa dole. Wannan dalilin ne ya saka Islaha bata yi mata ba. •••••••• Mama tana tsaye a ɗaki riƙe da waya ta ce, "ina jin ki, ya ake ciki yanzu?." Daga wayar aka ce, "an tabbatar min da yarinyar nan ta tafi ƙasar waje aiki, kin ga tayi daidai da wacce mu ke nema." "Aikin gwamnati ko na kamfani?." "Aikin gidan turwa mana. Aikin da ake lalata rayuwar mata, shi nake nufi." Mama ta buɗe ido ta ce, "da gaske ki ke?." "Wallahi da gaske nake. An tabbatar min da yarinyar bata ji, tana ɗan taɓa abubuwan zamani. Dan gidan da take zaune ma babu tarbiyya, ana yiwa mai riƙonta take da woman leader. Ƴaƴanta ne jarinta, sune suke fita su kwana a waje su kawo mata kuɗi, kuma itama a gidan take." Mama ta ƙyalƙyale da dariya ta ce, "ina zuwa." Ta faɗa tana kashe wayar, bata ɓata lokaci ba ta kira lambar malam, suna gaisawa ta ce, "Malam akan batun auren Rehaan da yarinyar nan, ina so a yi aikin da ko ba yaso sai an yi auren nan ta ƙarfi da yaji." Malam ya ce, "kar ki samu damuwa. Ki ɗauka kamar an yi wannan aikin an gama, in kin ga ya tsallake auren to zai iya tsallake mutuwarsa." Daɗi ya mamaye zuciyar Mama, cikim farin ciki da jin daɗi ta ce, "yauwa Malam, yarinyar tayi daidai da ra'ayina, tayi daidai da wacce nake nema. A taimaka ayi aikin nan Malam, in ba a yi auren ba hankalina bazai taɓa kwanciya ba." Malam ya ce, "kar ki damu Hajiya Saddiƙa, wannan ƙaramin abu ne, kawai ki ɗauka an gama. Dan wallahi sai an yi auren nan, auren nan babu fashi." Mama ta ce, "zan turo da abin sakada a rabawa almajirai, sannan akwai naka ka yi cefane." Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar. Mama cikin farin ciki ta ce, "dakyau! Kai wannan lamari ya yi min daɗi, bana so Rehaan ya auri mace ta gari domin hakan ma amfaninmu ne. Dole na tabbatar da auren nan ya yu, ko koda zai mutu akan ba ya so sai dai ya mutu, amma auren nan kamar an yi sa an gama!!" ta faɗa cikin nishaɗi, dan ita kaɗai ta san amfanin da hakan zai yi mata. Mu je zuwa. 💃🏻 [7/3, 2:05 PM] KRBBK: RDB2P36 Nana Haleema. Kamar yadda Umma ta faɗawa Atika bata yi ƙasa a guiwa ba ta shirya ta nufi gidan. Da sallama ta shiga suka amsa suna kallon ta cikin sakin fuska. Safeera ta ce, "sannu da zuwa Mama Atika." Atika ta murmusa ta zauna ta ce, "Yauwa Safeera, ya gida ya ƙannen naki?." Saferra ta ce, "Lafiya lau. Ina Kausar?." "Tana gida, ta ce na gaishe ki." "Ina amsawa." Atika ta ce, "Mun yi waya da da Umman ku, ta ce ta kira ki baki ɗauka ba, shiyasa ta ce nazo na ga lafiya." Rukayya da ƙannenta suka haɗa baki suka ce, "Mama Atika don Allah ki kira mana ita." Atika ta murmusa ta ce, "to bara na gwada, kun san yanayim ƙasar da take sai a hankali" ta faɗa tana ɗaukar wayar ta kira wayar Umma amma ba a ɗauka ba. Ta kalle su ta ce, "ba a ɗauka ba, amma gobe zan kira muku ita da kaina." Jikinsu duk ya yi sanyi alamun ba haka aka so ba. Atika ta kalli Safeera ta ce, "Ya aikin naki?." Safeera ta ce, "Alhamdu lillah." "Amma za ki cigaba da zuwa ko?." Safeera zata yi magana Baba ya yi sallama ya shigo. Mama Atika ta sauka har ƙasa ta gaishe sa, ya amsa ya ce, "yau ke ce a gidan?." Cikin fara'a ta ce, "Ni ce. Mun yi magana da Maimuna ne ta ce don Allah nazo naga ya yaran suke, shiyasa na fito." Baba ya gyaɗa kai ya ce, "kin kyauta" ya faɗa yana shiga ɗaki. Atika ta ce, "Safeera kar ki ce zaki ajiiye aikin ki akan wannan abun, ki yi haƙuri ki cigaba da zuwa." Safeera ta ce, "Mama Atika in na tafi waye zai dinga kula da gidan? Sannan in Baba ya dawo abincinsa fa?. In suka dawo daga makaranta ban dawo ba Baba bai dawo ba ina zasu je?." Mama Atika ta ce, "ki ji wata magana, ni ba uwa ce a wajen ku ba kenan ko Safeera?." Safeera ta ɗaga kai ta kalle ta Mama Atika. Mama Atika ta ce, "kalle ni da kyau, ni ba uwa bace da baza su iya zama a wajena su ci abinci kafin ki dawo ba? Kina tunanin akwai abinda bazan iya yi muku ke da ƙannen ki ba?." "A'a Mama, kar a ɗora miki nauyi ne shiyasa." "Babu batun nauyi, yadda Kausar take ƴa a wajena haka kuma ku ke gabaɗayan ku. Babu yadda ban yi da babar ku ba amma ta ƙi ji tace sai ta tafi, ni daman ku nake ji ba wani abun ba. Mahaifin ku yana yin tafiya wani lokacin, in ya tafi da wa zai bar ku?. Wanna dalilin ya saka na ce tunda ita bata yi wannan tunanin ba ni nayi, duk abinda ya samu kizo ki faɗa min, in tafiyar ta kama Baban ku, sai ku taho wajena mu zauna. Danginta ba a garin nan suke ba balle ace ku je can, kinga ni kaɗai ku ke da ita." Daɗi ya mamaye zuciyar Safeera, amma bata nuna ba ta ce, "Mama bama so mu takura ki ne, kuma..." Mama Atika ta daktar da ita ta ce, "Kar ki sake faɗar maganar nan, ni mai tsayawa akan lamarin ku ce a ko yaushe. Yanzu akwai abinda ku ke so?." Safeera ta murmusa cikin jin daɗi ta ce, "Babu komai." "Gobe ki shirya ki tafi aiki, in zaki tafi ki kawo min makullin gidan. Ke Rukayya in kin dawo daga makaranta ki zo ki karɓa a wajena." Ta ɗaga kai alamun to. Baba da yake jin komai, ya fito da fara'a ya ce, "Atika ba a ɗora miki nauyi ba?." Ta yi dariya ta ce, "babu komai. Auren Saeera za a yi nan da wani lokaci, suna buƙatar uwa a tare dasu, kuma in sha Allah zanyi iya abinda zan iya dan basu kulawar da ta kamata.  Na yiwa Maimuna alƙawari, kuma zan cika in sha Allah." Baba ya ɗaga kai cikin jin daɗi ya ce, "madallah, Allah ya ƙara zumunci." Ta amsa da amin. Baba ya fita cikin jin daɗin kalamanta. Safeera ma ta ji daɗi sosai, lokaci ɗaya ta sake dan sun saba da Atika ƙawar Umma ce. Safeera ta ji daɗin karamcinta, hakan ya rage mata nauyin da take ji a ranta. Daman dangin Umman sun ce ko zasu koma Katsina, itace daman bata so kuma ga mafita an samu hakan ya yi mata daɗi sosai. •••••••• Islaha suna tsaye a gaban dining table yana zuba abincin dinner, sai da ya gama ya fara ci a nutse sannan yankalle su ya ce, "you made this?." Islaha ta ɗaga kai alamun itace, ya girgiza kai ya ce, "perfect." Ta yi murmushi tana sunkuyar da kanta shi kuma yana cigaba da cin abincinsa. Sai da ya kama kaf suka kwashe kayan suka wanke, Islaha ta ɗan ci abincin dan kayan ƙhamshinsu ba wani daɗi suke yi mata sosai ba. Bayan sun kammala ta shiga ɗaki ta yi wanka ta canja kaya zuwa mofty ta zauna tana tunanin Saheer. Waya ta ɗauko ta buɗe saƙon Mama, ta buɗe voice note ɗin ta ji ta ce, "an samu waje ko waya baki yi min ba, ke haka za a yi dake? Haka za a yi dake tun ba a yi cikin ba harza a haihu?." Kafin ta ba ta amsa kiran ta ya shigo kamar jira suke su ganta online. Tana ɗauka Mama ta fara masifa tana faɗin,  "dan wulaƙanci baza ki iya kirana ki faɗa min a inda ku sauka ba, haka za a yi dake kenan ko? Kin je kin fara shan laban kina cin kaji kin manta yadda tsarin yake ko?." "Mama ina yini." "Da ban yini ba ai da ban kira ki ba." "Ki yi haƙuri, aikin ne da yawa shiyasa sai an yi a hankali." "Wannan ke ta shafa bani ba, kuɗi ne in ki ka samu sai an raba an bani nawa, duk abinda zai biyo baya keki ka jiyo." "Ki yi haƙuri." Mama ta ja tsaki ta kashe wayar. Islaha bata damu ba ta kira Saherr, ta kasa jurewa sai an kwana biyu kamar yadda tace sannan zata kira sa, hakan ya saka ta kira ko zata ɗauka. Har ta gama ringing bai ɗauka ba, ta buɗe saƙonsa tana karantawa ƙirjinta yana bugawa cikin tsananin kewarsa. A hankalinta danna vn ta ce, "Hammana ka yini lafiya, ya aiki?. Ka yi haƙuri Hamma, na san na yi kuskure, ka bani dama na wanke laifina." Tana turawa ta ga ya yi blue alamun har ya buɗe, ta tsaya tana jiran amsa amma shiru bai ce komai ba kuma ta tabbatar ya ji. Ta sake yi masa wani ya sake buɗewa, daga ƙarshe sai ta ga dp ya koma fari saɓanin hoton addu'a da yake kai, in ta tura saƙon sai ya yi tick ɗaya alamun an yi blocking number. Hankalin Islaha ya tashi, ta gigice ta rasa yadda zata yi. Daga ƙarshe ta zauna ta ci kuka son ranta, ta share hawaye ta kwanta tana jan numfashi cikin rashin mafita.     Ball suke bugawa a babban wajen ball ɗin da aka tanada a gidan Rehaan, Rehaan yana tsaye sanye da complete set ɗin kayan barcelona, ya tufke gashinsa a tsakiyar kansa. Yadda suke ball ɗin da jikinsu da ƙarfinsu sai ka ɗauka turanwan gaske ne, ko kuma biyansu ake yi. Lokacin da suka gama Rehaan yana riƙe da ruwa yana sha, suka taho suna hira har suka ƙaraso tsakiyar compound ɗin gidan Rehaan. Duk suka yi masa sallama, ya rage daga shi sai Ubaid da ya cika sa da uban surutu. Rehaan ya ce, "ina ta so na tambaye ka sai na manta, har fita nayi zan shiga wajen Maleek na dawo. Kana da extra maid? I want it for my chef." Ubaid ya shafa gemu ya ce, "yes i have it. She's from Nigeria, Yarinyar ta haɗu sosai, zaka ji daɗin ta." Rehaan ya kalle sa sai ya ja tsaki bai ce komai baz Ubaid ya ce, "Riyar dubu ɗaya ta raba ka da ita, zaka mori lokacin ka yadda ka ke so. Kuma ta iya soyayya sosai Rehaan, zata shagwaɓa ka. Zan iya ara maka ita na lokaci ɗaya ta zo ku kwana tare. Wallahi ta yi, ga skin ɗinta very soft and smooth." Rehaan ya ja tsaki ya ce, "ka bar su bana so." Ubaid ya yi dariya ce, "i'm telling you, ƴan Nigeria sun fi arab zama too hot, komai so sweet." Reehan bai kuma ce masa komai ba ya koma ciki zuciyarsa cike da takaici. Allah ya sani baya son wannan ɗabi'a, yana kishin ƴan ƙasar sa sosai, yana so a martaba ƴan ƙasarsa, amma duk sun gantalar da ƙimar ta bi rariya. Cikin takaici ya shiga ɗaki, ya yi wanka ya shirya ya tafi asibiti. Islaha ta ɗan sake, ta saba da wasu abubuwan sosai. Ta fahimci Maleek yana da kirki sosai, bai taɓa ƙoƙarin yi mata wani abu ba, sai dai a gaisa daga nan ba ya cewa komai zai fita. Damuwar ta bai wuce Hamma ba, ya ƙi ya yi unblocing ɗinta, gabaɗaya ta damu, har sim card na ƙasar suka je ta yi register amma da kira shi sai ya ƙi ɗauka, ƙarshe ma sai ya kashe wayar. Ta yi ajiyar zuciya ta fito falon, a nan suka haɗu da Maleek zai fita, suka gaisa ya kalle ta ya ce, "Are you able to work as a chef in another house as well, or would that be too much for you?." Islaha ta ɗan yi jim bata amsa ba, sai kuma ya ɗaga kai alamun zata iya. Ya girgiza kai ya ce, "The house in the middle close to us, gidan abokina ne. He's looking for someone to cook and make tea for him. If you're willing, you can also work there, he pays well and he's very kind. Islaha ta ce, "yeah i can." "Okay. Let's go, I'll show you the house." Islaha ta koma ciki ta ɗauko hijjab ta fito ya fita itama ta bi bayansa. Tunda kuɗi take nema, dole ta haɗa da gidan tunda ya ce yana biya dakyau. A wannan lokacin ta ga Labiba ta fito saka shara a babban trash ɗin da yake wajan, suka haɗa ido Labiba ta ɗauke kai ta koma ciki itama ta ɗauke kanta. Tunda suka nufi gate ɗin gidan gabanta ya yanke ya faɗi, ta dinga addu'a ranta, bata san dalilin da ya saka take jin faɗuwar gaba ba, gashi bata san mai gidan ba balle tace tsoron aikin take yi, haka kawai tana cike da fargaba. Bayan sun shiga compound ɗin gidan ya juyo ya kalle ta ya ce, "Shima ɗan nigeria ne kamar ki, amma yana kiwon damisa." Islaha ta ɗan buɗe ido cikin mamaki, Maleek ya murmusa ya ce, "yeah." Bata tanka ba suka cigaba da tafiya. Gidan shiru babu sautin komai sai na tsuntsaye kaɗan kaɗan, sai kallon gidan take yi tana girmama girmansa, duk yadda take ganin kyaun na Maleek sai taga wannan yafi sa komai, ya tsaru sosai, ya sha adon flowers a ko ina. Suna zuwa wajen babban ƙofar ta ga Maleek ya saka card ya buɗe ƙofar falon, ya kalle ta ya ce, "ki shiga, akwai kitchen ki yi abinda ya kamata. Ki yi komai kamar yadda ki ke yi min, na yarda dake shiyasa na zaɓe ki. Note, ba ya son milk tea or milk coffee, baya shan madara" ya faɗa yana miƙa mata katin, ta karɓa ya juya ya barta a wajan. Gaban Islaha ya faɗi, ta taka ta ƙarasa cikin falon a hankali ƙhamshi yana dukan hancinta. Falon da duhu sosai, hakan ya saka ta nemi switch ta kunna take haske ya gauraye ko ina. Ta bi falon da kallo ganin yadda ya tsaru, komai a tsaftacce, komai yana mahallinsa. Laptop ce a ajjiye akan table ɗin, bayan ita babu komai a wajen. Ta kalli sama ta ga upstairs ɗin wanda yake sama zai iya gano na ƙasa, irin mai balcony ɗin nan ne saman, na saman in yana tsaye tsaf zaku yi hira. Islaha ta ɗaga kai ta fara tafiya dan neman kitchen ta yi abinda zata yi ba kallon falo ba. Ƙofar farko da ta buɗe ta ga kitchen ɗin ne, mai mahaukacin girma da tsari, ta kunna haskensa tana sake kallon ko ina cikin mamakin girmansa. Gashi babu wasu tarkace, gas stove, sai oven da microwive, sai mixer da blander kawai ajjiye a wajan. Ita dai a tsorace ta ke kallon ko ina, kafin ta ƙarasa ta buɗe drawer a nan ta ga glass tea pot mai madaidaicin girma, ta ɗauka ta ƙarasa gaban sink ta ɗauraye sannan ta dawo ta ɗora akan gas ɗin. Hijjab ɗin ta cire, ta sake ɗauka ta zuba ruwa madaidaici ta dawo ta ɗora ba tare da ta kunna ba. Buɗe buɗe take yi amma bata ga komai na kayan tea ba, ta ɗan yi tsaki kamar ance ta kalli gefe, a nan ta ga wani carbinet na glass, ta ƙarasa ta buɗe ta ga da kayan tea kamar hauka. Tea leaves ma sun fi kala talatin. Black, green, red duk akwai. Ta ɗauko normal black, ta ɗauko cimmanon stick guda ɗaya, cardamon ɗaya, clove guda biyar sai citta. Ta ƙarasa ta zuba a ciki ta sake dawowa, ta ɗauki mint powder ta dawo ta zuba a cikin tea ɗin ta kunna wuta. Tana tsaye ya tafasa, ƙamshi ya mamaye ko ina. Ta ɗauko flaks ɗin da ta gani, ta juye a ciki. Sai bayan ta juye take kallon flaks ɗin ganin kamar gold aka yi sa saboda kyau da ɗaukar hankali, gashi ɗan ƙarami daidai mutum ɗaya ko biyu. Sai da ta gama ta tafi tunanin me kuma ya kamata ta dafa. A bayyane ta ce, "ko me zan dafa oho. Ni bana son sabgar mutanen nan, sun cika iyayin tsiya. Allah ya taimake ni can gidan da Sunaira, shiyasa nake jin daɗin yin abubuwa tana taimaka min." Sai ta tuna ance ɗan nigeria ne, ta duba ko ina taga akwai komai na amfani, nan take ta ɗora mandi rice. Cikin lokaci kaɗan ta gama, ta yi grill kaza ta yi ganishin komai a warmer. Ta wanke kayan ta mayar da komai mazauninsa kitchen ya zama kamar ba ayi komai ba. A kan dining ɗin da yake kitchen ɗin ta ajjiye, ta ɗauko plate da komai ta yi serving a wajan, sai da ta tabbatar ta yi komai yadda ya kamata sannan ta saka hijjab ɗinta ta fito daga gidan. Tana shiga gidan Maleek Rehaan yana dawowa, ya shiga gidan a gajiye ya kunna haske, coat ɗin jikinsa ya cire, ya ware gashinsa ya sauka, ya cire takalminsa ya saka room slippers, ya shiga kitchen dan ya ɗauki ruwa. Turus ya yi ganin abinci a ajjiye, ya ta fi tunanin ko Jazy ne yazo, sai kuma ya tuna ai basu yi maganar zuwan sa ba. Text ɗin Ubaid ya gani, sai ya buɗe yana karantawa, ya ja numfashi yana kallon yadda aka tsara komai cikin tsafta daidai da ra'ayinsa. Ɗan tsaki ya yi yana ɗaukar flaks ɗin ya zuba tea a glass mug ɗin da ta ajjiye masa. A yadda yake so ya fi so komai a yi masa, da akwai dama a bashi tea ɗin a baki hakan ya fi masa, ba ya son wahala shi kam ko kaɗan. A hankali ya kai tea ɗin bakinsa ya sha, sai ya ɗan yatsine fuska jin cloves ɗin ya fito sosai, amma sugar ɗin ya yi masa yadda yake so, ya haɗɗiye a hankali yana kallon tea ɗin kamar mai karantar wani abun a ciki. Da mug ɗin a hannunsa ya juya ya fita daga kitchen ɗin ya hau sama a hankali. Yana shiga ɗaki kalaman Ubaid suka faɗo masa a rai, sai ya ta ya yana kallon tea ɗin a bayyane ya ce, "itace ta yi min kenan?." Ya ɗan yi tsaki kaɗan ya ajjiye cup ɗin akan mirror yana cire rigar jikinsa. Sai da ya yi wanka ya shirya, ya kalli tea ɗin da ya rage a ciki, ya ɗan yi tsaki dan sauka da mug ɗin ma a wajansa babban aiki ne. Ya ɗauke ido ya sauka ya shiga kitchen ya buɗe abincin yana kalko jin ƙkhamshin spices ɗin sun daki hancinsa. Abincin ko a ido ya yi kyau sosai, a yi garnishing ɗinsa da parsley da green peper, ko ba a ce ba abincin zai yi daɗi. Rehaan ya ɗauki spoon ɗin da aka naɗe a tissue, ya warware ya ɗan ɗibi kaɗan ya kai bakinsa yana ci. Irin abincin ƙasar ne dai, ƙhamshin da taste ɗin da komai iri ɗaya. Ya taɓe baki ya ce, "ta yi order a wani resturant." A lokacin ya ɗauki plate ya yi serving kansa ya zauna yana ci a hankali. Bai ci da yawa ba ya tashi ya fita daga gidan dan akwai inda zai je. Labiba tana zaune tana waya ita da Mama, Mama ta ce, "Labibatuna a cikin kwanakin da basu wuce takwas ba har kin samo waɗannan kuɗin? Naira miliyan ɗaya nake gani fa, Labiba ban taɓa riƙe miliyan tawa ta kaina ba sai yanzu, Labibatuna Allah ya ui albrka." Daɗi ya mamaye zuciyar Labiba, ta yi fari da ido kamar tana gabanta, ko yanzu ta tabbatar ta fi ƙarfin Hannan ta ce, "Babu yawa fa Mama, zuwa nan da wani satin zan sake turo miki wasu." Hajiya Kariman ta ce, "Allah ya saka miki albarka Labiba, wannan ke ce farar haihuwa mai son taimakawa iyayen ta. A ina ki ka samu kuɗin haka?." "Kyauta ce kawai, kin san in ka iya aiki kuma kana jin turanci suna yi maka kyauta mai aji. Wannan kawai kyauta na samu, shiyasa na saka aka raka ni aka mayar da kuɗin naira na turo muku." Mama ta ce, "kin kyauta ɗiyata, Allah ya cigaba da dafa miki kin ji. Ki cigaba da kyautata musu, ki ɗora daga inda ki ka tsaya, kuɗi su cigaba da shigo mana babu ƙaƙƙautawa." Ta yi dariya, a lokacin Aisha ta shigo ta zauna a kusa da ita tana kallon ta, Labiba bata daina waya ba ta ce, "Amin Mama. Yanzu kin tabbatar da na fi Hanan amfani? Kin tabbatar zan yi abinda ita bata isa ta yi ba?." Mama ta ce, "Hanan ɗin banza, iyakacin kyautar hanan dubu ɗari biyar ce, itama ɗari biyar ɗin sau ɗaya aka bani. Yau ke kuwa har miliyan guda, ai ko yanzu kasuwa ta tashi ɗan koli ya ci riba, balle yanzu kasuwar ta fara ci, babu ranar tashinta." Daɗi ya mamaye mata zuciya ta ce, "Zuwa nan da jibi zan sake turo miki wasu Mama." Mama ta yi guɗa ta ce, "Alkhairin Allah ya kai miki Labiba, Allah ya cigaba da kare ki." "Zan kira ki" ta faɗa tana kashe wayar tana kallon Aisha da take kallon ta. Aisha ta ce, "da ke kin san da haka ki ka tsaya ɓata lokacin ki?." Ta kalle ta ta ce, "yanzu na fahimci amfanin hakan." "Kina da buƙatar ƙarin kuɗi, ba iya na gidan nan kawai ba. Yadda Mama take murna ya kamata ace kuɗin sun fi haka, yadda zaki saka ta gigice saboda farin ciki." Labiba ta ɗan yi jim ta ce, "Kai Aysha a bari a ɗan kwana biyu, har yanzu ban gama sabawa da Ubaid ba balle kuma wasu daban. Wahala nake sha sosai, kin san abinda da farin shiga." Aysha ta yi dariya ta ce, "na yi mamaki sosai da baki taɓa sanin namiji ba sai a kan Ubaid,  shiyasa ya gigice miki ya rikice yake yi miki ɓarin kuɗi." Ya kalle ta ta ce, "kema a haka ki ka saba?." Ta ɗan yi dariya ta ce, "ke yanzu nawa ki ka ajjiye naki?." Labiba ta ce, "miliyan ɗaya ce, sai kuma riyal dubu ɗata da suke hannuna a yanzu." Aisha ta girgiza kai ta ce, "Hajiya, kina tara kuɗi abin ki." Labiba ta yi murmushin jin daɗi, ita ita wuce Hanan da tayi a wajen Mama yafi mata komai daɗi. Ta ji daɗi da ta bada abinda Hanan bata taɓa bayarwa ba, ta ji daɗi da ta zama itace a gaba ba Hanan ba. Aisha ta ce, "zan raka wata ƙawata zata yi sim card, zan je na dawo." Labiba ta ce, "to sai kin dawo." Daga nan ta fita ta bar Labiba a zaune. Ƙofar ta ji an buɗe ta ɗaga kai tana kallonnsa, gabanra ya faɗi sosai, ta miƙe tsaye tana kallonsa ya tako ya riƙo ƙugunta ya riƙo ta yana shafa fuskarta. Kiss ya yi mata a kumatu yana kallon idonta ya ce, "What wrong Beb?." Ta yi shiru bata amsa ba, ya rungume ta yana shafa bayanta a hankali cikin salo. Ya ɗago ta ya buɗe hannunta ya saka mata dala dubu dubu biyu, sannan ya raɗa mata ya ce, "can i have you now?." Ta kalli kuɗin ta kalle sa, sai ta marairaice ta ce, "na gaji." Ya ɗan yi shiru  yana binta da kallo ya ce, "i'm sorry." Ya faɗa yana shafa fuskarta tare da fara kissing ɗinta. Shi fa Rehaan ya yi tunanin Ubaid ne ya turo Islaha ba Maleek ba🤭🤣🤣🤣 [7/3, 5:35 PM] KRBBK: RDB2P37 Nana Haleema. Dr Isma'il ya kalli Baffa da yake zaune kamar ba shi aka yiwa aiku ba, gefensa Kawu ne a zaune a kan kujera, gabaɗaya baza ka ce sune suka kasance a kwance kwanakin baya ba. A gefensu Mama ce da Adda, sai matar Kawu da Saheer da Sadik da suke tsaye. Dr Isma'il ya ce, "Baba Alhamdu lillah, in sha Allah yau zamu sallame ku." Baffa ya ce, "Alhamdu lillah, daman na gaji da zaman wajen nan." Ya ɗan murmusa kaɗan, Dr Isma'il ya ce, "Baba ya kalar fitsarin ka yake?." "Fari ne." "Fari babu wata kala?." "Eh." "ma sha Allah. Daman normal urine fari ne, in fitsari ya canja daga fari akwai dalilin canjawarsa. Baba amma sai an kula da ƙa'idoji da shan magani gaskiya. Dashen ƙoda ba abu ne mai sauƙi ba, sai an kula da shan magani yadda ya kamata." Ya gyara tsayuwa ya ce, "Akwai buƙatar kula da lafiya sosai, a gujewa abubuwa wanda zasu raunata jiki. Baba kamar kai, ana buƙatar ka samu hutu kamar na sati uku zuwa huɗu kafin ka koma harkokin ka. Mun duba mun tabbatar da sabuwar ƙodar da aka saka maka tana aiki. Komai naka ya dawo daidai shiyasa nake faɗa maka abinda ya kamata a yi nan gaba." "Akwai magununan da zamu bayar, suna da ɗan tsada gaskiya amma in ana sha za a warware in sha Allah. Akwai abincin da ya kamata aci da wanda ya kamata a bari. In za a ci nama ya zama dahu sosai, in na ce nama ina nufin kaza ko kifi, a tabbatar ya dahu ya yi laushi yadda ƙodar zata sarrafa shi cikin sauƙi. Sannan a samu abinci mai sauƙin narkewa, tuwo, dankalin da sauransu. Sannan a yawaita cin kayan lambun da aka wanke kuma aka dafa. Kamar zogalen da aka dafa ko aka yi miya, alaihaun da aka dafa ko aka yi miya. Koma dai meye a tabbatar da an dafa sa kafin a kai ga ci. Babu salad wanda ake ɗorawa akan abinci aci. Sai ƴaƴan itaciya, lemo, apple, da banana." "Sai madarar da aka dafa, kar ya a ɗanyen maradar da ba a dafa ta ba. Sannan a dinga shan ruwa sosai, ya kasance a yini ɗaya ana shan ruwa lita 2 zuwa 3 a rana. In an dawo asibiti aka duba, in likita ya ga da yuwa a ƙara adadin ruwan za a ƙara ko a rage. A dinga kula da lafiya yadda ya kamata, a dinga zuwa asibiti duk bayan sati biyu ana ganin likita, in kuma aka samu kwanaki bayan an warke yana da kyau a dinga zuwa asibiti ana duba lafiya gabaɗaya. Yana da kyau a dinga duba yanayin yawan jini, sugar, da sauransu." "Abinda ya kamata a gujewa gishiri, ɗanɗano mai yawa a abinci, barasa, ɗanyen naman da bai dahu sosai ba. A guji aiki mai nauyi ko yawon da zai wahalar da jiki Baba. In dai aka kiyaye wannan, aka yi komai yadda ya kamata, ana shan magani ana zuwa checkup in sha Allah za a samu lafiya sosai." Baba ya gyaɗa kai ya ce, "na gode sosai likita." Dr ya kalli donar ya ce, "na dawo kan ka." Kawu ya yi murmushi ya ce, "to ina ji likita." "A yawaita shan ruwa kamar lita biyu zuwa biyu da rabi a rana. A dinga cin nama mara kitse, a dinga cin kayan lambu, ƴaƴan itaciya, madara amma ba da yawa ba. Baba a gujewa cin gishiri da sugar mai yawa, lemo mai gas, inda hali duk wani soft drink a dakatar da shansa na wani lokaci. A gujewa maganuna ba tare da umarnin likita ba, ko ciwon kai aka ji yana da kyau kafin a sha magani azo a ji me likita zai ce, maganunan hausa su ma a ajjiye su a gefe. In za a sha ruwan ya zama ana rarrabawa, kar a ɗaga kai asha ruwa mai yawa lokaci ɗay,  an fi so a sha da kaɗan kaɗan. Sannan zaka ɗan dinga jin zafi ko kasala wani lokacin, ana buƙatar ka huta sosai, aƙalla sati huɗu zuwa biyar. Baba a guji aiki mai wahala, a dinga zuwa ana duba lafiya akai akai, a dinga zuwa ana duba yanayin fitsari, da yanayin hawan jini, da sikari." "Amfanin gujewa abu mai kitse saboda kar a ƙara ƙiba, amfanin gujewa gishiri ƙaruwar hawan jini, amfanin gujera sugar saboda ɗagawar sugar. Akwai maganin da yake ƙara sikari a cikin maganin da za a baka, shiyasa ake so a rage shan farin sikari mai yawa. A yanzu jinin ku da sugar ku duk ya yi yadda ake so, fitsari ya koma kalarsa shine jin daɗin mu." Kawu ya ce, "in sha Allah za a kiyaye." Dr ya ce, "Allah ya ƙara lafiya." Suka amsa da amin Dr ya ce, "in kun gama clearing bill za a baku takardar sallama, daga nan zan iya cewa sai wani lokaci." Sahaeer ya ce, "za a iya zuwa wanann asibitin don duba lafiya?." Dr ya ce,  "Sosai ma, tunda suna da file a nan za a iya zuwa ko yaushe in sha Allah." Sadik ya ce, "mun gode." Sadik da Saheer suka fita zuwa reception dan su biya abinda ya rage. Suna gama biyan kuɗin Dr ya kalli Sadik ya ce, "Sadik minti ɗaya don Allah." Sadik bai ƙu ba ya ƙarasa inda yake, Dr Isma'il ya ce, "Don Allah ina Islaha? Kwana biyu bana ganin ta." Sadik ya ɗan murmushi ya ce, "kwana biyu ta ɗan yi tafiya." "Aiki ko ƙaro karatu?." "Duka biyun." "Shiyasa bana ganin programs ɗinta. Zan iya samun number ta don Allah?." Sadik ya murmusa ya ce, "ba kana da social media handles ɗin ta ba? Kawai ka yi mata magana, dan inda take a yanzu waya bata shiga." Ya ɗaga kai ya ce, "na gode. Allah ya ƙara musu lafiya." Ya amsa suka yi musabaha sannan ya dawo wajan Saheer da yake ta kallonsa. Saheer ya kasa haƙuri ya ce, "me likitan nan ya ce maka?." Sadik ya kalle sa bayan ya haɗe rai ya ce, "Islaha yake nema." "A matsayinsa na waye zai neme ta?." "a matsayin wanda yake sonta mana, zaka hana mutane son Islaha ne?." Saheer ya zuba masa ido yana kallo cikin kishi mai tsanani, ya kasa cewa komai ya cize baki cikin baƙin ciki. Sadik ya ɗan taɓe baki yana kallon Saheer ya ce, "kai duk wannan kyautatawar da yake yi mana ka ɗauka a banza yake yinta?....." Sadik ya yi ƴar dariya ya ce, "Wallahi son Islaha yake yi, tun ba yanzu ba na lura da hakan." Saheer ya yi shiru bai ce komai ba zuciyarsa bugawa take yi da sauri sauri. Kishi yake ji mai tsanani, zuciyarsa tana yi masa zafi da raɗaɗi akan kamalan Sadik. Sadik ya ce, "Yarinyar akwai farin jini, da wahala taje wani waje ba a ce ana so ba." Saheer bai ce komai ba ya haɗɗiye mugun abu da ya tsaya masa, da ace Islaha tana nan babu abinda zai hana bai saka an ɗaura masa aure da ita ba, daga lokacin babu wanda zai sake cewa yana sonta. A wannan yanayin suka shiga mota aka wuce gida. Saheer har aka je gida bai ce komai ba, yana riƙe da Baffa har ɗakinsa. Bayan sun kwantar dashi shi da Sadik suka raka Kawu gidansa, bayan sun yi masa siyayya mai yawa wacce take nuni da jin daɗinsu akan abinda Kawu ya yi. Bayan sun dawo gida suna zaune a mota Sadik ya kalle sa ya ce, "sai wani ɓata rai ka ke yi dan kawai an nemi lambar Islaha. Islahan da bata gaban idanunka a yanzu, ka san abinda take aikatawa a halin yanzu?." Ya juyo ya kalle sa yana ɗaga masa hanmu ya ce, "Ya ishe ka, ka daina faɗar wannan maganar akanta. Bana son wannan shirmen da ka ke faɗa, na faɗa maka bana so amma ka ƙi yarda ko?." Sadik ta ce, "gaskiya ce ai, kaima ka saukewa kanka wannan damuwa da takaicin da take ɗura maka, ka share ta ka nemi wata ka huce takaici. Nan na dinga converncing ɗinka akan ka barta a dinga tafiyar aikin nan da ita amma ka ƙi, da a cikin mu take da duk ba haka ba. Yanzu gashi tana can wata ƙasa ƙarƙashin larabawa, Allah kaɗai ya san abinda yake faruwa a can. Duk yadda ka ke wannan haukan a kanta, ita ko neman ka ma bata yi, tana can tana hutawa cikin ac tana cin kaza kullum." Saheer ya kalle sa rai a ɓace ya ce, "kai ka san dan kaine shiyasa na tsaya kana faɗa min wannan maganar ina ƙyalewa ban fasa maka baki ba, kaima ka kusa kaini bango, in baka iya bakin ka na wallahi zan baka mamaki. Sadik ka daina yiwa Islaha wannan mummanan zaton, ko ina Islaha zata je ni na yarda da ita, baza ta taɓa aikita wani abu mara kyau ba. Na amince da ita har cikin raina, na yarda da ita ɗari bisa ɗari,  ko a cikin maza dubu zata kwana ta tashi bazan zargi Islaha ba. Kaima ka iya harshen ka, in ba haka ba wallahi sai na ɓarar da kai a wajan nan." "Gaskiya ce baka so, kuma wannan ba mummanan zato bane gaskiya ce." Saheer bai ce masa komai ba ya fita daga motar ya shiga cikin gida, dan in ya cigaba da sauraren sa zai iya yi masa duk abinda zai yi danasani nan gaba. Wajan Baffa ya wuce ya tarar da Mama da Adda a zaune, yana shiga Baffa ya ce, "Saheer ina Sadik?." Saheer ya ce, "ya tafi Baffa, yanzu muka rabu dashi bayan mun kai Kawu gida." Baffa ya ce, "Aboki ne na gari, yana da kirki sosai. Ya yi abinda ko kai da kanka iyakacin abinda zaka yi kenan, iya abinda zaka yi kenan daga kwanciyata zuwa yanzu. Allah ya yi masa albarka, Allah ya sa ya fi haka, Allah ya sake haɗa kan ku." Saheer ya amsa da amin yana jin haushim Sadik a ransa. Baffa ya ce, "in na samu lafiya zan je har gida wajan iyayensa na yi musj godiya, zan je na yi musu godiyar abinda ɗansu ya yi mana na karamci." Mama ta ce, "ya kamata" ta faɗa a taƙaice. Baffa ya ce, "Ina Islaha ne? Ina ta tambaya sai ku yi min shiru." Saheer ya ɗan sauke kai ƙasa ya ce, "Baffa Islaha bata nan." Baffa da yake kwance ya ɗan motsa kaɗan zai miƙe zaune, Saheer ya miƙe ya riƙe sa ya ce, "Ka yi hankali Baffa." Mama ta ce, "saboda an ambaci ƴar gold ɗin ka bata nan, shiyasa zaka hallaka kan ka." Baffa bai kula ta ba ya ce, "ina jin ka, ina ta je?." Saheer ya kalli Mama, ya juyo ya kalli Baffa ya ce, "Mama ta tura ta aikin ƙasar waje." Mama ta buɗe ido cikin masifa ta ce, "kamar ya na tura ta? Kai Saheer bana son iskanci da wulaƙanci. Kamar ya na ɗauke ta na kaita ƙasar waje? Jaririya ce ita da zan goya ta a baya na kaita inda nake so?." Baffa ya kalli Mama ya ce, "Ya isa! Saheer ka yi min bayani yadda zan gane." "Baffa Islaha bata ƙasar nan, yau kwananta goma da tafiya. Mama ce ta...." Mama ta katse sa cikin faɗa ta ce, "na rantse da Allah in ka sake ambatar Maman nan sai na tsinke ka da mari, ka ji min yaro da wulaƙanci. Ni na ɗauki Islaha na kai ta, ba itace ta zo ta same ni ta ce na kai ta ba?. Lokacin da na so ta je ba ƙi ta yi ba? Kuma ina zaune ta kawo min fasko ta ce min gashi ta yi in da dama na saka ta tafi a cikin wanda zasu tafi a kwanakin. Dan ka raina ni sai ka dinga cewa ninna saka ta? Ta ƙarfi na jata na kai ta ko kuma sakawa na yi aka ɗauke ta aka kai ta?." Baffa ya ɗan ja numfashi ya ce, "Ya isa haka, ki daina yi min ihu a kaina." "Ji na yi yana neman ɗora min laifi, dan Islaha ta bar ƙasar nan ta hannuna sai ya zama ni na kaita?. Ban san ta yi ba, ban ce zo mu je ba, ta je ta yi fasko ta kawo min ta ce na kai ta. Ni kuma a lokacin kanfanin mu yana buƙatar mace irinta, dan na ɗauke ta sai ya zama laifina?. Meye nawa? Me na yi da za a ce ni ce na kai ta?. Dan kawai akuyata ta yi kuka kan waccen tsintacciyar?." Baffa ya nuna mata ƙofa ya ce, "jeki in baza kinyi shiru ba." Ta yi shiru tana ɗauke kai ya kalle ta ya ce, "baki da adalci, baki san karamci ba, ba ki san saka alkhairi ga alkhairi ba, ba ki san mai ƙaunar ki ba, ba ki san wanda ya kamata ki so ko kar ki so ba." Ya ɗan yi shiru saboda ciwon da yake ji sannan ya ce, "yarinyar nan itace ta dinga faɗi tashi akan rashin lafiyata, abinda ta yi ƴaƴan da ki ka haifa da cikin ki basu yi ba. Ita kuwa sai dai ace na riƙe islaha na wani lokaci, amma bazan amsa sunan mahaifi a gare ta ba, dan bani na haife ta ba. Su kuwa kaf ɗinsu ni na haife, basu da wani mahaifi sai ni ɗin. In na kwanta na mutu su aka yiwa mutuwa, domin su suka rasa mahaifi, daman ita Islaha marainiya ce a haka ta tashi, su kuwa in na mutu su aka yiwa mutuwa ba ita ba. Yarinyar nan  ta ba da duk wani ƙarfinta da kuɗin ta akan ciwona, ta ruɗe ta fita daga hankalin ta saboda kawai bani da lafiya." Ya yi shiru yana kallon Mamq na wani lokaci kafin ya ce, "Kuma a haka kina nuna mata ƙiyayya, amma ita bata nuna miki ƙiyayya akan wanda ki ke aure ba. Ta sadaukar da kuɗinta da lafiyar ta da lokacinta saboda ni, ni kuma ke nake aure...." Ya girgisa kai ya ce, "Islaha bata cancani wannan abun daga wajan ki ba, ko bakya kallon ta a matsayin wacce zata auri ɗanki zaki iya kallon ta a matsayin marainiya wacce bata da iyaye. Kuma ƙarya aka yi ba ke ki ka kaita ƙasar wajen ba? Sau nawa kina so ki kaita, bani nake hanawa ba?. Da yake kin ga bani da lafiya ban san me aka yi ba gashi kin kai ta ai. Wa za a ce in na ke ba? Ba dole ace kece ki ka kai ta?." Mama ta sassauta murya ba kamar ɗazu ba ta ce, "Ni fa ban saka Islaha ba, itace ta kawo kan ta." "wajan wa ta kawo kanta?." "Wajena." "Waye ya kai ta?." "Ni za a ce na zama sila." Baffa ya ce, "gashi kin amsa da kan ki. Ba na faɗa miki indai ina da rai yarana baza su wannan aikin ba? Meyasa ki ka yi dan kin ga ina kwance?." Mama ta wani kalle sa ta ce, "Islaha ce fa." Baffa ya dafe kai jin duk jawabin da ya gama yi mata a banza, gashi tana maimaita masa Islaha ce ai ba ƴarsa bace. Ya ɗan yi shiru na wani lokaci, ya ɗan sauke numfashi ya ce, "wato ita ba ƴata ba ce ba ko?." Ta yi shiru bata amsa ba, Baffa ya kalli Saheer ya ce, "meyasa ban san maganar ba?." "Nima ban sani ba Baffa, sai bayan ta tafi aka faɗa min. Cewa aka yi kar a faɗa min, kuma ba ita bace kaɗai ba ce, harda Labiba da babar Safeera ƙawar Islaha ɗin." Baffa ya sauke numfashi ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Harda Labiba?." Saheer ya ɗaga kai bai ce komai ba. Baffa ya zubawa Mama ido ya kasa cewa komai, ta ƙi kallonsa ta ɗauke kai bata ce komai ba tana ji yana kallon ta. Baffa ya ce, "Harda Labiba ki ka kai?." Ta ce, "To ai na ji na ta ita ka ke yi ba ai, ta ƴat riƙo ka ke yi tunda ita ka fara tambaya." Baffa ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "Yanzu sai da ki ka kai Labiba ƙasar waje aiki? Me ta nema ta rasa a gidan nan, me ki ka nema ki ka rasa a gidan nan da zaki saka ta fita daga ƙasarta zuwa wata ƙasa aiki?." Mama ta yi shiru bata ce komai ba, Baffa ya ce, "duk kashedin da na dinga yi miki akan hakan sai da ki ka aikata?." A sanyaye Adda ta ce, "Ka yi haƙuri Baaffa, ka ga baka da lafiya. A bar maganar don Allah, in ka warware sai a samu mafita in sha Allah." Baffa ya ce, "wacce mafitar kenan? Ta ɗauki ƴan mata har biyu ta kai wata ƙasar da basu da kowa ki ce a bar maganar? Ban san inda suke ba, ban san a hannunwa suke ba, ban san a inda suke kwana ba. A wajen kirki suke ko a wajen na banza duk bamu sani ba. Kuma ki ce na kwantar da hankalina?." Saheer ya ce, "kayi haƙuri ka bar maganar Baffa, zamu yi magana daga baya in sha Allah." "Ta ya zan bar maganar? Ƴaƴana ƴan mata suna wata ƙasar da ba tamu ba, ku dinga cewa na kwantar da hankalina? Ƴaƴana har biyu kuma ƴan mata da basu taɓa aure ba, an ɗauke su an kai su wani waje ba tare da na sani ba. An yi amfani da rashin lafiyata an yi abinda bana so. Yanzu da raina da lafiyata ace yaran nan basa nan? Don Allah ya ake so a dinga kallona a garin nan?." Saheer a sanyaye ya ce, "duk da haka ka yi haƙuri Baffa, ya riga ya faru sai mu yi haƙuri." "Dan baka san irin maganar da za a dinga faɗa a kaina ba. Mu fa fulani ne, fulani ne gaba da baya. Fitar wannan maganar babban abin kunya ne a gare ni da dangina. Ace ƴaƴana mata guda biyu sun bar ƙasar nan sun tafi aiki a gidan larabawa, ba fa wajen Yola suka tafi ba, ba wani garin suka tafi ba Saheer, wata ƙasar suka tafi ban sani ba. Saheer in ban damu ba me zan yi?." "Baffa likita ya gargaɗe mu akan gujewa abinda zai saka jinin ka ya hau, ka ga iya wannan maganar zata iya jawowa jinin ka ya hau. Don Allah don Allah ka bar maganar, ni zan san abinda zan yi in sha Allah." Baffa ya kalli Mama da bata ce komai ba ya ce, "yadda ki ka ɗauke su ki ka kai su ki saka a dawo min dasu, in ba haka ba kuma zan yi miki abidna baki taɓa tunani ba." Adda ta ce, "babu batun dawowa Baffa, dole sai sun zauna sun biya kuɗin da aka kashe aka kai su. Ka san kuma Mama itama aiki kan aiki take yi, ba wai itace shugaba, tana da na sama da ita. Ƴar sallamar da ake bata in ta samo matan bata taka karya ta yi ta karya ba. Dole sai sun biya kuɗin da aka kai su sannan zasu samu ƴancin da zasu dawo." Baffa ya yi shiru ya dafe kansa cikim yanayin da bai san meye ba. Saheer ya ce, "Don Allah Baffa ka yi haƙuri, a bar magnar don Allah." Baffa bai ce komai ba Mama ta miƙe ta fita, Baffa ya bita da kallo kafin ya kalli Saheer ya ce, "wani abu nake dubawa akan mahaifiyar ku, wani abu kawai nake kallo shiyasa duk abinda take yi min nake ƙyalewa. Amma naga ta kasa ganewa, tana neman ta kai ni bango na kasa ɗauke kai na yi abinda zuciyata take faɗa min nayi." A tare suka haɗa baki suka ce, "Ka yi haƙuri Baffa." Baffa ya ce, "Kun yi magana da Islaha? Dan na san Labiba bazata neme ku ba." Adda ta ce, "ɗazu ma mun yi magana da ita, ta tabbatar min da bata da wata matsala ta samu gida na kirki. Na dinga yi mata faɗa akan meyasa ta tafi, sai ta ce na tambayi Saheer dalilinta na tafiya, wallahi ba a son ranta ta tafi ba. Kuma ta ce na baka haƙuri, tasan ta yi maka laifi mai girma." Baffa ta kalli Saheer ya ce, "Faɗa min dalilin." Adda ta kalli Saheer ya yi mata alama da ta yi shiru kar ya faɗa, Adda ta ce, "ai bamu yi maganar dashi ba, yanzu zan tambaye sa in sha Allah. Ka huta Baffa, bara mu je, Saheer mu je" ta faɗa tana miƙewa, shima ya miƙe suka fita suka bar Baffa cikin tunanin da ya kasa barin zuciyarsa. Ya sauke numfashi cikin wani irin yanayi, ko kaɗan bai ji daɗin maganar nan ba, zuciyarsa zafi take yi akan hakan. Amma bai ga laifin Islaha ba, dan ya yarda da ita, ya tabbatar akwai dalilin tafiyar ta. Nana Haleema. [7/3, 5:36 PM] KRBBK: RDB2P38 Nana Haleema. Adda suna fitowa ta tsayar da Saheer ta ce, "Faɗa min wacce matsala ce ta kai Islaha tafiya aiki Jeeda, bayan ni da kai mun san ta tsani aikin nan?." Ya ɗan sauke numfashi cikin takaicin hakan ya ce, "nima ban sanar mata ba, ki tambaye ta." Adda ta ce, "ka faɗa min Saheer, na san ka san komai." "Raina min hankali kawai take yi, ta aikata wani abu a ɓoye sannan ta tafi ban sani ba. Lokacin da aka sace ta, ta faɗa min komai akan sace ɗin da aka yi, tun lokacin zuciyata take rawa. Nayi-nayi ta faɗa min dalilin ta na so a rufe case ɗin ɗauke ta ɗin taƙi. Kwatsam sai na ji ta tafi Saudia, bayan ta tafi sai nake jin labarin ashe itace ta biya kuɗin aikin Baffa gabaɗaya. Ta ya hankalina zai ɗauki maganar nan? Ya ki ke so na kalli Islaha a wannan maganar?." Adda da mamaki ta ce, "kamar ya ita ta biya kuɗin aiki?." "Kamar yadda ki ka ji. A lokacin ƙin faɗa min ta yi, sai yanzu Safeera take cewa wai ɗauko kuɗin ta yi a gidan da aka ɗauke ta. Just imagine, wacce aka sace ita ita a ɗauko kuɗi? Sace ɗin da aka yi  daɗi ne da shi kenan, tunda har ta iya gani ta ɗauka." Adda ta ce, "to waye ya sace ta ɗin?." Ta ɗage kafaɗa ya ce, "shima taƙi faɗa, sai ta ce wai bature ne baya jin yaren mu. Ya ɗauke ta har na tsahon kwanaki, ya ajjiye ta a gidansa yana bata abinci mai kyau tana kwana a ac, ya rabu da ita ba tare da ya riƙe ko hannunta ba. Ita kuma da yake ga shugabar masu shirme, da ta tashi dawowa sai ta ɗauko masa kuɗi masu yawan da ta biya kuɗin aikin Baffa. Magana ake ta miliyan sha ba ƙananun kuɗi bane, don Allah da wanne ido zan kalli maganar nan? Da wanne kunne zan ji wannan dramar ta gamsar dani?." Adda ta ɗan yi jim kafin ta kalle sa ta ce, "kana zargin Islaha ta aikata wani abu ne ta samo wannan kuɗin?." Ya girgizs kai ya ce, "ko kaɗan ban taɓa zarginta ba, itace take neman saka min zargin ta a zuciyata Adda. Ta tafi da sunan an sace ta, ta dawo da kuɗi masu yawa, taƙi faɗar wanda ya ɗauke ta, ta ƙi faɗar dalilinta, sannan ta ce a rufe maganar. Yanzu ta bar ƙasar da niyar wai zata biya bashin da ta ɗauko. Don Allah ko Ihsan ɗin ki aka faɗawa wannna maganar zata amince?." Adda ta ce, "ni abinda nake so na ji, me ta yiwa wanda ya ɗauke ta har ya saka aka sato masa ita? Sannan da ya sace ta kawai ajjiye ta ya yi yana bata abinci?." "Hmmmm! Kema dai kya tambaya, ajjiye ta kawai ya yi yana bata abinci tana bacci, da ta tashi dawowa kuma sai ga kuɗi." "Ka faɗa min, me ya haɗa su?." "Ta ce wai faɗa suka yi, rashin kunya ta yi masa a hotel, lokacin da ta je neman Mr Rehaan Yola, sai kuma a asibiti. Na rasa wanne irim tunani ma ya kamata ace na yi." Adda ta sauke numfashi ta ce, "indai da gaske baka zarginta kamar yadda kace to ya kamata ka amince da abinda ta ce, kaine mutum na farko da zaka fara b da shaidar ta, in da Islaha ƴar iska ce zuwa yanzu kowa ya sani, kai kanka ko zuwa yanzu in baka zama ɗan iskan ba to ka rabu da ita. Ni a jikina ina ji maganar ta gaskiya ce, duk abinda ta yi ta yi ne saboda mahaifinka. Na san halin islaha da gaggawa, wani lokacin sai bayan ta aikata abu take zuwa ta yi nadamar hakan. In zuciyar ta tana son abu kawai tana aikatawa ne nan take, kar ka yanke mata hukunci cikin rashin sani, islaha bazata yi wani abu mara kyau ba." Ya kalle ta ya ce, "kawai rashin kunya sai ya saka a sace mutum?." "Eh mana, ai baka san wanda ta taɓo ba. Kuma ka san halin kayar ka, ba kunya ce da ita ba ko kaɗan. Tana da tsiwa mai yawa, zata aikata abinda ya fi haka ma. Kuma wani saboda haka zai iya sace ta, ba lallai sai ya yi mata komai in ya ɗauke ta ba. Ai ba ko wanne namiji ne yake ɗaukar mace dan ya yi amfani da ita ba, wataƙila shi ya ɗauke ta dan kawai ya yi mata gargaɗi." "Kuma sai ta satowa mutum kuɗi?." Adda ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Saheer zuciyar ka ta daina rawa akan Islaha, ni wallahi na amince da ita. Ka fi kowa sanin yadda bata ƙaunar aikin nan, ba tun yau ake yi mata talla tana ƙi ba, ƙaramin dalili bazai saka ta cilla kanta a cikin wannan yanayin ba. Ka tsaya ka saurare ta." Saheer ya taɓe baki yana ajiyar zuciya ya ce, "ni na yi blocking ɗinta, bani da lokacin yin magana da ita a yanzu." Adda ta ce, "kar ka yi haka, ka yi haƙuri ka tausaya mata don Allah." "To ni an yi min adalci kenan? Ta bar ƙasa ban san lokacin da zata dawo ba. Me take yi a can, a hannun wa take, wacce irin rayuwa take yi duk ban sani ba. Auren ta zan yi fa, itace nake mafarkin ta zama mahaifiyar yaran da zan haifa a duniyar nan, meyasa zata yi min haka?." Adda ta tausasa murya ta ce, "bata kyauta ba, amma ka yi haƙuri." "In na yi haƙurin yaushe zata dawo? Ina da kuɗin da zan je na ɗauko ta ne Adda?." Adda ta kalle sa jin muryarsa ta yi sanyi, sai ya bata tausayi, dan ta san Saheer yana son Islaha sosai. Ta ɗaga masa kai ta ce, "komai warware in sha Allah, ka yi magana da ita don Allah, na tabbatar tana tare da damuwar rashin kula ta ɗin da baka yi." Ya kalli gefensa sannan ya ce, "na ce mata me? Na faɗa mata tsarabar da zata siyo min, ko na ce mata a ina take aiki, ko na ce mata aikin me take yi?." Adda ta ce, "Haba Saheer, ban sanka da mita ba, ka bar maganar nan, ka je ka yi magana da ita ka ji?." Ya kalle ta ya ce, "kin san mahaifin Safeera ya saki babarsu saboda tafiyar nan?." Adda ta zaro iso ta ce, "ban gane saki ba, wanne irin saki?." Ya taɓe baki ya ce, "Wallahi ya sake ta, ya faɗa mata sai babu igiyar aurensa a kanta sannan zata tafi, kuma ta tafi ɗin shi kuma ya sake ta." "Innalillahi! Me Mama ta saka ta aikata ne haka?." Saheer ya ce, "lamarin Mama sai addu'a kawai, amma abim yana yi min ciwo sosai. Ta raba aure guda saboda wani banzan aikin da ba duniya zaka je ka samo ba." Adda ta ce, "ban da abin Umma meye na tafiya? Da girmanta da komai don Allah." Bai ce komai ba ya fita daga gidan ita kuma ta shiga cikim gidan. ******      Safeera a gaggauce ta shiga gida, tana shiga ta tarar da Gwaggonsu ƙanwar Baba tana gidan. Ta yi murmushi ta ce, "Gwaggo ina yini." Ta yi murmushi ta ce, "lafiya lau ƴar jarida. Ya na ga ki a firgice haka?." Safeera ta ce, "Baba yana azumin tsakiyar wata, zan dama masa kunu, ya ce min baya jin daɗin na Ruƙayya, shiyasa nake saur" ta faɗa yana ajjiye mayafinta. Ruƙayya ta ce, "Adda ai Maman su Kausar ta aikowa da Baba kunu, gashi nan na kai masa ɗakinsa." Safeera ta ji daɗi a ranta ta ce, "da gaske?." "Wallahi da gaske, harda da ƙwai ta soya masa. Kuma daman na yi masa fanke mara sugar irin wanda yake so." Safeera ta zauna tana ajiyar zuciya ta ce, "kai amma na ji daɗi sossi, a gagaguce na dawo wallahi saboda aikin Baba." Gwaggo ta ce, "ai ya faɗa min zancen ƙawar Babar ku, tana da kirki sosai, bata jima da fita daga nan ba." Safeera ta yi murmushi ta ce, "tana da kirki sosai Gwaggo, baki ga yadda take yi mana ba wallahi, tana kula damu sosai kamar sun haɗa jini da Umma." "Ta kyauta, haka ake son ƙawa ko aboki su kasance na gari. Tunda ita uwar taku ta watsar daku ta tafi gantali ita ta sani." Basu ce komai ba suka yi shiru. Gwaggo ta ce, "Baban na ku nake jira ya dawo mu gaisa sai na wuce gida." Suna nan zauna suna ta hira sai ga Mama Atika ta shigo da sallama. Suka gaisa da Gwaggo cikin sakin fuska, ta miƙawa a Gwaggo kwano ta ce, "Tuwon alkama nayi, shine na miki." Gwaggo ta karɓa ta ce, "kai amma na gode sosai Atika, Allah ya bar zumunci." "Amin Gwaggo." "Da haka ake samun ƙawaye masu kula da yaran ƙawayensu da an more wallahi, ke kam kin yi dace abin ki." Ta yi murmushi bata ce komai ba, a lokacin Baba ya shigo. Har ƙasa Atika ta zube tana gaishe sa, ya amsa da sakin fuska ya ce, "Ya hidima Atika?." "Alhamdu lillah, ai babu komai." "Allah ya saka da alkhairi." Ta amsa da amin tana murmushi. Gwaggo ta ce, "ka ga kaɓakin arzuƙin da aka aiko min dashi, tuwon alkama da miyar kuɓewa harda man shanu. Bayan ta aiko maka da kunun buɗa baki, har su doya da ƙwai." Baba ya cika da mamaki, wannan dafe-dafen abincin da Mama Atika take yi ya yi yawa, ya ce, "Atika kar na ɗora miki nauyi fa, hidimar nan ta yi yawa. Iya saurraren yaran da ki ke yi ma ya isa, dan Allah ki daina hidimar dafe dafen nan." Ita dai murnushi take yi sannan ta ce, "Babu komai Baban Safeera, duk an zama ɗaya. Kuma ina dashi ne shiyasa nake yi, da babu da bazan yi ba." Baba ya ce, "duk da haka dai ki ɗan rage, kar hidimar ta yi yawa." Bata ce komai ba sai murmushi da take yi. Mama Atika kalli Gwaggo ta ce, "Gwaggo zan koma, na bar Kausar ita kaɗai." Gwaggo ta yi murmuahi ta ce, "To Atika, Allah ya saka da alkhairi." Ta amsa da min ta miƙe ta fita daga gidan. Baba suka gaisa da Gwaggo kafin ya shiga ciki ya yi alwala ya fito ya je masallaci, bayan an idar ya dawo ya shiga ɗakinsa yana cin abinci. Ba jimawa Gwaggo ta shiga ta same sa ya gama cin abincin yana zaune. Gwaggo ta zauna ta ce, "har ka gama buɗe bakin?." Ya ɗaga kai ya ce, "Na gama Gwaggo, yanzu zaki wuce?." "eh yanzu zan wuce, jira nake ɗan wajan naka ya zo ya ɗauke ni. Amma kafin nan ina da wata magana." Baba ya ce, "ina jin ki Gwaggo." "Matar ka ta watsar da ƴaƴanta ta tafi yawon gantali, zaman yaran nan su kaɗai in baka nan akwai damuwa tunda ba namiji ne a gidan ba. Kuma ana so duk inda ƙarami yake ya kasance akwai babba a tare dashi." "Gwaggo kullum da tunanin nan nake kwana nake tashi, yanzu haka nan da sati biyu zan yi tafiya, amma ban san ya zan yi ba. Ina ta tunanin ko na tura su Katsina sai na tuna da aikin Safeera da makaratar su Rukayya, sai na yi tunanin gidan ki sai kuma na ga kar hiidmar ta yi miki yawa. Na dai rasa inda zan aika su." Gwaggo ta ce, "ai yawon dangi ba nasu bane, duk inda zasu je barin nan ne." "To zan bar su su kaɗai a gidan nan ne Gwgago?." "Aure zaka yi kawai, tunda kana  da gida da halin riƙe mace ai, meye laifi dan ka yi?." Baba ya ɗan miƙe zaune sosai ya ce, "Gwaggo aure fa?." Gwaggo ta ce, "Auren fa, ko akwai haramci ne?." "Babu gwaggo. Amma sai na ga auren ya yi wuri, har yaushe Maimuna ta tafi d zan yi aure? Sai mutane su ga kamar daman jira nake ta tafi na yi aure ai." "To sai me? Duk abinda mutane zasu ce su ce mana, na ga dai kai ka san matsalar da ka ke ciki ko? Kuma maganinta zaka yi, in zaka biyewa maganar mutane ko baka yi ba sai an yi maganar." "Haka ne. To ni Gwaggo yanzu in na ɗauko batun aure wa zan aura?." Gwaggo ta ce, "Ga matar nan Atika, meye laifinta?. Ka san halinta ta san naka, ga gidanta da take zaune ga gidanka. Meye aibu dan ka aure ta ka haɗa da ƴar ta ka riƙe?." Baba ya zubawa Gwaggo ido har ya gama kafin ya murmusa ya ce, "Gwaggo Atika ƙawar Maimuna ce fa, ƙawar ta ce wacce zan kira ta da aminiya, ko nace nace ta zama ƴar uwa." Gwaggo ta ja tsaki ta ce, "ko uwa ɗaya uba ɗaya suke ƙarewar ƙawance, in baban su ɗaya uwa ɗaya tunda babu Maimuna zaka iya auren ta, balle wani ƙawance, abu indai ba haramun bane shikenan. Yadda take kula da yaranka na tabbata zaka samu kwanciyar hankali a auren ta, mai son naka ai ba abin wasa bane ba." Baba ya yi murmushi ya ce, "Gwaggo ni gaskiya babu batun aure a gabana balle har na yi tunanin zan iya auren Atika." Gwaggo ta ce, "ya kamata ka kawo sa kuwa, dan bazan zuba ido kana barin ƴan mata su kaɗai a gida ba. In aka fahimci baka nan hauro musu fa?. In kuwa da babba idanunsa  ma makami ne babba." Baba ya girgiza kai dan ya san gaskiya ta faɗa, ya ce, "zan san abinda zan yi in sha Allah, komai zai yi daidai Gwaggo." "Daidaita komai kawai ka auri Atika, ai ba aibu a lamarin." "Ikon Allah! Gwaggo ita an faɗa miki zata iya aure na ne hala?." "Ka gwada ka gani, zan iya rantse maka akan zata amince. An ce tafi shekara sha biyar tana zawarci, wallahi kana yi mata tayi zata amsa. Ai kai ba irin wanda za a ƙi bane, ta san yanayin yadda ka ke tsayawa akan iyalanka ai." Ya girgiza kai ya ce, "Shikenan gwaggo, zan yi tunani zan kuma yi addu'a." Gwaggo ta ce, "ko kai fa, haka zaka ce daman. Allah ya sanya mana alkhairi" ta faɗa tana miƙewa shima ya miƙe. Sai da ya raka ta har waje ɗanta ya zo ya ɗauke ta a mota ta tafi. Ya bi motar da kallo yana murmushi, yana tunanin maganar Gwaggo yana ganin kamar ba abu ne da zai yu ba. *JEEDAH..* Slowly take tafiya kamar bata so, hannunta riƙe da ledar Nahdi pharmacy ta shiga gidan Maleek ta wuce ɗakin da yake nata ta cire hijjab ɗin jikinta. Ta buɗe ledar ta ciro pad da panadol da pack ɗin facemask da ta siya. Ta sha panadol ɗin ta zauna a gefen gado ta dafe kai dan yanayin ta babu daɗi as usuall. Kwana biyu Maleek ya yi tafiya, aikin ya ɗan ragu sai gidan Rehaan da take shiga, kuma har lokacin bata taɓa ganin mai gidan ba. Yanzu ma can take niyar zuwa amma bata jin daɗin jikinta, a wannan yanayin ba kasafai ta cika son zama cikin jama'a ba, dan yanayinta ko yaushe zai iya canjawa ta fara yiwa mutane faɗa. Gashi tana ƙasar da ba nigeria ba, kar ta je ta aikata abinda zai zamar mata matsala. Tana jin kanta cikin kaɗaici, sai ta ji tana buƙatar rarrashi ba tare da an yi mata komai ba. Ta jima a zaune a haka, kafin ta miƙe ta shiga banɗaki ta saka pad ɗin ta fito tana jan numfashi daƙyar. Ta ji daɗin maganin da ta sha, amma duk da haka tana jin ciwo sosai. Hijjab ɗin ta saka aka turo ƙofar aka shigo, Sunaira ta gani suka yi maganar bebayen da suka saba. Islaha ta ce mata zata shiga gidan da take zuwa, daga nan ta jawo ƙafa slowly tana takawa a hankali zuwa gidan. Magriba ta yi lokacin, duhu ya yi amma ko ina haske kamar dare bai yi ba. Tana shiga motar cleaners tana fita, ta bisu da kallo ta ce, "ko meyesa bazai ɗauko chef daga wani wajan ba oho, ba dan kuɗi nake nema ba da me zai kai ni aiki kamar wata baiwa?." Sai da ta yi typing lock code ɗin ƙofar sannan ta tsaya tana jira ƙofar ta yi ƙara sannan ta buɗe, ta yi tsaki ta ce, "Aikin banza, gida kamar gidan tuba duk an bi an rufe sa da lambobi." Sautin lock ɗin ta ji alamun ta buɗe, ta shiga falon yana nan yadda yake kamar kullum babu kowa. Haka kawai ta ji falon yana bata haushi, ta yi tsaki tana hararar falon ta ce, "aikin banza, kullum baya nan, ni ga ƴar aiki sai dai na yi masa aiki na ajjiye, yana can yana hutawa ina gaban stove zafi yana tafasa ni." Islaha ta taka a hankali zuwa inda kitchen ɗin yake. Ta kunna hasken ta ga komai yana inda yake ko cup ɗin da sha tea babu. Ta kama ƙugu ta ce, "wai yana cin abinda nake dafawa ma kuwa ko wahalar banza nake yi?." Sai kuma ta sake yin tsaki ta ƙarasa ta haɗa komai na tea ta ɗora akan stove ta kunna. Ta rasa me zata dafa ranar, duk ranta a ɓace yake bata san me ya kamata ta yi ba. Loades fries nw ya zo ranta, hakan ya saka ta ɗauko irish potatoes irin na ƙasar manya manya, babu wahalar peeling sannan ga auki. Guda uku kacal ta gyara ta yanka yadda ake soya dankalin turawa. A lokacin ta ji marar ta tana ɗaurewa, idanunta ya ciko da hawaye, ta fara kuka mai sauti ita kaɗai tana yi tana share hawayenta. A haka ta soya ta ajjiye, ta buɗe fridge ta ɗauko chicken breast ta yanka ƙananu ta saka spices ta zuba a fan ta ɗora akan stove ɗin. Ta koma gefe tana jan numfashi tana jin yadda take flowing a hankali. A hankali ta ƙarasa ta kwashe kazar, ta buɗe fridge ɗin ta ɗauko mayonnaise ta zuba a ƙaramin bowl, ta zuba ketchup a kai, ta ɗauki lemon ta zuba kaɗan, ta saka chili powder da maggi ta yi mixing a haɗe. Casrool ta ɗauka mara girma sososai, ta zuba dankalin a ƙasa sannan ta kawo wannan kaza ta zuba a sama, ta zuba cheese, sannan ta zuba cream ɗin da ta haɗa ta sake zuba cheese. Ta ɗauka ta saka a cikin oven, mintina kaɗan ta cire ta kalla ta ga loaded fries ɗin ya yi kyau sosai. Dafa kitchen island ta yi tana jan numfashi mai ƙarfi, bata daina kuka ba har lokacin, dan ita kaɗai ta san irin abinda yake ji a jikinta. Buɗe murya ta yi tana kuka mai matuƙar sauti dan ta san babu kowa a gidan, tana kiran sunan Hamma da Safeera. A lokacin Rehaan ya shigo gidan, yana buɗe falon ya ji sautin kuka har tsakiyar kansa. Gabansa ya faɗi lokaci ɗaya, ya fara tunanin waye a gidan yake kuka haka?. A hankali ya ajjiye wayarsa akan table ya shiga ciki a hankali ya nufar inda yake jin kukan. A tsaye ya ganta ta juya baya ta riƙe kitchen island ƙam jikinta yana rawa. Kallo ɗaya ya yi mata ya gane itace housemaid ɗin, uniform ɗin jikinta sun tabbatar masa da wacece. "Are you Okay?." Rehaan ya furta a tausashe yana kallonta, dan daga ganin yanayinta bata da lafiya. Islaha ta firgita jin magana a bayanta, kuma ta san babu kowa a gidan sai ita kaɗai. Firgtar da ta yi, sai tsantsin tiles da ɓawon dankali guda biyu da suke a ƙasa, suka ja ta da ƙarfi, ta yi gaba zata faɗi da fuskar ta, Rehaan ya yi hanzarin ƙarasawa ciki, ya taro ta ta faɗo ƙirjinsa gabaɗayanta...... An haɗu fa❤️‍🔥 Nana Haleema✍🏻 [7/6, 9:35 AM] KRBBK: RDB2P39 Nana haleema. _Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments ɗin ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link ɗin ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode ɗin baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/POak37bdMTE?si=dU33KLoRcvufRf7S …… Kanta yana kwance a kirjinsa, jikinta ya saki gabaɗaya, sai ƙhamshin turarensa da yake shiga hancinta yana ratsa kanta da zuciyar ta a hankali. Rehaan sai da ya yi da gaske ya rike ta, yadda ta faɗo jikinsa gabaɗaya sai da ya kusa faɗuwa, dan bai ɗauka jikinta zai saki haka ba, sai ya ji ta sakar masa jiki tana kwantar da kanta a ƙirjinsa. Hannunsa ɗaya yana waist dinta, ya zagaya dashi har cikinta ya rike ta yana kallon gashin kanta da yake baƙi sosai, ga kitson da ta yiwa kanta, irin na fulanin daji guda biyu kacal. Ya ɗago ta yana kallon fuskarta, amma idanunta a rufe yake sai hawaye da yake sauka a hankali, ya ɗan zubawa fuskar ta ido na wani lokaci, sai kuma ya ɗauke kansa daga kallonta. Daga yanayin uniform ɗin jikinta ya san itace housemaid ɗin da Ubaid yace masa ya turo, ya riƙe fuskarta yana ɗan jijigawa. Camly ya ce, "can you hear me? What's wrong with you?." Islsha tana jinsa amma tana buƙatar kwanciya a halin da take ciki, tana jin muryarsa da ƙhamshinsa har cikin zuciyarta, amma kuma ta kasa buɗe ido ta ga waye. Har lokacin yana riƙe da ita sai dai ya raba ta da jikinsa, bai kuma magana yin ba ya riƙo ta a yana sake riƙe hannunta suna takawa a hankali suka fito falon, ya zaunar da ita yana kallon yadda take kuka har lokacin. Coat ɗin jikinsa ya cire, ya kwance necktie ya cire, ya rage bottuns ɗin saman rigar. Ya cire tucked in ya koma kitchen, ya dauƙo ruwa mai madaidaicin sanyi ya ƙaraso ya miƙa mata ya ce, "take it." A hankali ta fara buɗe ido tana kallon abinda ya miƙo mata, bata gani sosai yadda ya kamata, amma tana ganin mutum a tsaye yana miƙa mata ruwa amma baza ta ce waye ba. Ta karɓi ruwan ta sha ta ajjiye, ya bar wajan ya ƙarasa ya ɗauko panadol ya dawo ya bata guda ɗaya, dan ya ga alama tana cikin radaɗi, yana kula da yadda ta riƙe kanta yasan tana buƙatar pain reliever. A hankali ta karɓa ta sha ta koma ta jingina da kujera, gabaɗaya ƙhamshin falon ya canja ya koma ƙhamshinsa. Gashi ya kunna ac ta fara fita a hankali, sai ƙhamshin ya haɗe da sanyin ya ba da wani yanayi mai daɗi. A hankali ta fara jin relief ta koma sauke ajiyar zuciya a hankali, ta buƙe ido ta kai kallon ta gare sa, sai ta ga ya dora ƙafa kan ƙaya yana danna waya hankalinsa kwance. Sai kuma ta ga ya ɗora waya a kunne yana magana cikin turanci, bai jima ba ya sauke wayar. Islaha gefen fuskarsa take gani, gashinsa ya rufe gefen fuskarsa, ta miƙe zaune sosai gabanta yana faɗuwa matuƙa. Ta miƙa hannu ta ɗauki glass cup ɗin da ya miƙa mata, ta kai bakinta zata sha kenan Rehaan ya juyo suka haɗa ido. Gabanta ya faɗi, glass cup ɗin hannunta ya faɗi ƙasa, ruwan da ta sha ya sarƙe ta ta fara tari. Islaha kallonsa take yi tana tari kamar yadda yake kallon ta Sai kuma ya ɗauke kansa daga kallon ta ya cigaba da abinda yake yi ita kuma ta sake firgicewa. Da sauri ta miƙe tsaye tunawa da babu ɗankwali a kanta balle hijjab ɗin da ta shigo dashi, da sauri ta koma kitchen ta saka ta fito a hankali tana kallonsa kamar bai san da ita a wajan ba. Kallonsa take yi ƙirjinta yana bugawa, kamar bai san ta fito ba duk da yana jin motsinta kuma ba kallon ta yake yi ba. Ita dai ta kasa banbance yanayin da take ciki, gizo yake yi mata kamar yadda take yawan ganin fuskarsa a mafarki yana tambayarta bashinsa, ko kuma shi ɗin ne dai?. Tunda ta zo Jeddah take mafarkin sa, ta san kuma saka abinda ta yi masa a ranta ne ya saka take ganinsa, amma yanzu abin ya fara bata tsoro matuƙa, tunda gashi ta fara ganinsa a zahiri. Gab da zata wuce ya sake juyowa ya kalle ta suka sake haɗa ido, yadda ta firgita hijjab ɗinta ya taɗeta ta baya ta zube a ƙasa, kuma bata daina kallonsa ba. Sai kuma ta miƙe da sauri ta juya ta fita da sassarafa bata sake waiwayonsa ba. Shi dai bai motsa daga inda yake ba, shi kansa yana ganin kamar ya san fuskar, kawai bazai tsaya ya tsaurara tunani a kanta ba ne, bashi da wannan lokacin. Sai ya yi tsaki tunawa da maganar Ubaid, ya sake kallon inda ta zauna yana tuna duk abinda Ubaid ya faɗa a kanta. Ya yi ƙaramin tsaki ya miƙe yana tuna yanayinta, ya shiga kitchen yana kallon abinda ta haɗa komai tsaf sai ɓawon dankali guda biyu da yake ƙasa. Ya saka hannu ya ɗauke ya saka a dusbin, ya ƙaraso ya zuba tea yana buɗe casrool ɗin yana kallon abinda yake ciki. Fork ya ɗauka ya ci abinda ta yi, sai kuma ya zauna a kan dining ɗin da yake kitchen ɗin ya ci sosai, ya sha tea sannan ya miƙe da tea ɗin a hannunsa ya hau sama. Islaha a yanayi na ruɗani ta koma, ta cire hijjab ɗinta ta ajjiye tana kallon kanta yana tuna fuskar wanda ta gani. Ta dafe kanta da hannu biyu a bayyane ta ce, "da gaske shine ko kuma...." Sai kuma ta katse waccen maganar ta ce, "nan fa ba Yola bane, ya aka yi ya zo nan kuma?." Ta ɗan runtse ido jin mararta tana murɗawa, ta buɗe idon ta ce, "Ya aka yi ya zo nan? Shine wai ko ba shi bane?" Ta faɗa da ƙarfi jin tunanin yana neman yi mata yawa. Buɗe ƙofar ta ji anyi, ta kalli wanda ya shigo ta ga Maleek ne, ta bisa da kallom mamaki dan ta san baya nan. Ya ƙaraso ya riƙe kafaɗarta ya ce, "Islaha are you Okay?." Sai a lokacin ta tuna maganar da ta yi da ƙarfi ne ya ji har ya shigo, ita ta manta ma da ƙarfi take magana, a ruɗe take sosai. Ta ɗan matsa baya tana ɗaukar hular ta saka a kanta, sannan ta ɗaga kai alamun lafiya lau take. Ya bita da kallo ya ce, "you look so stress, and why are you shouting?." Islaha kamar zata kuka ta ce, "i'm not feeling wll." "Okay, let me take you to the hospital." "No, i'm feeling better." "No, let me call my friend, he is a dr." "No Sir, i'm Okay." "are you sure?." Ta ɗaga kai alamun eh sannan ya ce, "don't stress yourself, ki kwanta ki huta." Ta ɗaga kai shi kuma ya fita. A hankali ta zauna tana tunanin wannan lamari, ita ta kasa banbance abinda idonta ya gani dan gani take kamar ba shi ɗin bane. Ta ya zata ganshi a Jeedah bayan ta san a Yola yake? Shine ko kuma gizo yake yi mata saboda kuɗinsa da ta ɗauko? Sai ta sauke numfashi, ta jawo wayarta ta shiga lambar Hamma ta ga har lokacin bai yi unblocking ɗinta ba. Ta rufe ido ta sauke nunfashi a hankali cikin kewar sa mai tsanani, kamar wasa ta ga kiransayana shigowa. Ruɗewa ta yi, ta gigice ƙijrinta yana bugawa ta miƙe tsaye, hannunta yana rawa tana kallon sunan Hamma da yake yawo a kai, murmushi take yi tana zubar da hawaye ganin sunan masoyinta yana kiran ta. Wayar ta katse bata ɗauka ba saboda ruɗewa, wani kiran ya sake shigowa, daɗi ya mamaye mata zuciya a bayyane ta ce, "Ya sake kirana, ya kuma kira, Hamma yana kira" ta faɗa hannunta yana rawa kafin ta ɗauka. Ta saka wayar a speaker ta toshe bakinta da hannunta ta kasa cewa komai, shima daga can ɓangaren kasa yi mata magana ya yi shiru yana jin saukar numfashin ta a hankali. Saheer ya murmusa har ta ji sautin murmushin. Calmly ya ce, "Matar Hamma!." Sai kawai ta fashe da kuka mai matuƙar sauti, ya sauke numfashi a tausashe ya ce, "na kashe wayata, na sake yin blocking ɗinki?." Kai take girgizawa kamar yana ganinta, ta kasa magana sai kukan da ya sarƙe ta ya hanata cewa komai. Saheer ya ce, "Islaha!." Muryarta tana cracking ta ce, "Hamma!." "Matar Hamma, ki bar wannan kukan mu yi magana. Kar ya sarƙe ki samu attack, ki nutsu mu yi magana." Ta kasa cewa komai sai ya kashe wayar, sai ta ga video call yana shigowa, ta zauna sosai ta ɗauka fuskar hammanta ta bayyana mai cike da annuri. Kanta a sunkuye yake ta kasa ɗagawa ta kalle sa, ya ce, "bakya so ki ganni ko?." Ta girgiza kai ta ce, "kunyar ka nake ji Hamma, bazan iya haɗa ido da kai ba, ina jin nauyin kallon ka." Ya yi murmuahi ya ce, "ɗago ki kalle ni." A hankali ta ɗaga kai ta kalle sa suka haɗa ido, ya ce, "filter ki ka saka ne?." Ta girgiza kai alamun bata saka komai ba, kuma bata yi magana ba, ya ce, "fuskar ki ta kumbura kaɗan, sannan ta yi ja alamun kin yi kuka sosai. Baki da lafiya?." Ta ɗaga kai a hankali ya ce, "me yake damun ki?." A sanyaye ta ce, "ciwon kai ne." Ya girgiza kai ya ce, "kin sha magani?." Ta ɗaga kai tana tuna wanda ya bata magani, tana ganin abin kamar a mafarki ya faru, kamar zata buɗe ido ace mafarki ne haka take hango abin a idanunta. A sanyaye ta ce, "na sha, kuma har ya fara dainawa." "To ki je ki huta kar na dame ki, na san ku dare ya yi ko?." Ta ɗaga kai ta ce, "an yi sallar i'sha." "to ki kwanta, gobe zamu yi magana ?" Ya faɗa da sigar tambaya yana kallon ta. Ta girgiza kai tana shagwaɓa ta ce, "Ni dai kar ka kashe." Saheer murmusa ya ce, "ina so ki huta, gobe in kin samu lokaci ki yi min magana, sai kira ki mu yi hira." "In ka kashe baza ka kuma kira na ba." "Zan kira ki mana." Ta kalli idonsa ta ce, "baza ka sake ƙin kula ni ba?." Duk da ya kula da hasken da ta yi, da ramar da ta yi bai yi mata magana ba ya ce, "bazan sake ba matar Hamma, ki huta kin ji?." Ta ɗaga kai tana murmushi. Ya bi jelar kitson ta da kallo ya ce, "da kan ki kika yi kitson?." Ta kalli jelar kalbar sannan ta ce, "da kaina na yi...." da shagwaɓa ta ce, "na sha wahala, hannuna ya dinga ciwo. Na yi awa biyu ina yi." Ya yi dariya ya ce, "Wannan gashin naki ai yafi ƙarfin ki daman, ke daman ba ƙwari ba." Ta yi murmushi ta ce, "To bani da wanda zai yi min." Ya sake yin dariya kaɗan ya ce, "Sai da safe." Zata amsa kenan aka ɗan ƙwanƙwasa ƙofar, ta kalli ƙofar dan a tunaninta Sunaira ce sai ta ce, "come in." Maleek yana shigowa gabanta ya faɗi, ta juya ta kalli Saheer da yake kallon Maleek da ya shigo, ya ƙaraso inda ta ke yana bata magani ya ce, "take this and sleep." Ta karɓi maganin ta ce, "thank you." Ya yi murmushi ya juya ya fita. Ta kalli Saheer da ta san jiran amsar ta yake yi, iaya kallon da yake yi mata kaɗai ta san na jiran amsa ne. Islaha ta ce, "Sunansa Maleek, nan gidansa ne, a gidan nake aiki dani da wata Sunaira. Yanzu ma na yi tunanin itace shine na ce ya shigo." "Oh! Da gidansa ne sai ya dinga shiga ɗakin ki kai tsaye?." Ta sunkuyar da kai ta ce, "ba ya shigowa, yanzu ma ni na bada dama, na ɗauka Sunaira ce." Ya yi shiru bai ce komai ba, Islaha ta ce, "Ya ga bani da lafiya shine ya kawo min magani." Ya sake yin shiru bai amsa ba sai kallon ta da yake yi, a sanyaye ta ce, "ka yi haƙuri." Ya girgiza kai ya ce, "ki kwanta ki huta." Ta ɗaga kai ya kashe wayar... Ta kwanta da baya tana kallon sama, cikin farin ciki tana jin daɗi, ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Hamma ya daina fushi dani, Allah na gode maka." Ta juya a kan gadon ta kwanta tana murmushi, sai ta manta da batun Rehaan da ta gani, farin cikin ganin Hamma ya matar da ita wani Rehaan, daman tunanin ta gizo yake yi mata ba gaskiya bane, dan bata ga dalilin da zata ganshi a Jeddah ba. Ta miƙe ta kashe hasken ɗakin ga kwanta ta yi bacci. _Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments ɗin ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link ɗin ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode ɗin baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/POak37bdMTE?si=dU33KLoRcvufRf7S Nana Haleema. [7/6, 9:38 AM] KRBBK: RDB2P40 Nana Haleema. _Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments ɗin ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link ɗin ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode ɗin baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/POak37bdMTE?si=dU33KLoRcvufRf7S •••••••••••• Bata farka ba sai ƙarfe uku na dare, ta miƙe zaune tana murza ido tana tuna mafarkin da ta yi. A bayyane ta ce, "da gaske dai gizo ya yi min, tunda gashi na sake yin mafarki yana cewa na biyasa kuɗinsa." Ta sauke numfashi tana ɗan runtse ido dan har lokacin tana jin ciwo kaɗan kaɗan. Ta ɗan ja numfashi ta ce, "Allah ka bani kuɗi na biya mutumin nan kuɗinsa na huta, Allah kawo min hanyar da zan biyasa na huta da wannan bala'in. Sai mafarkinsa nake yi, fuskar da bata cancanci na ganta a mafarki ba ita nake gani. Na tsane shi, haka kawai bana son ganinsa. Bana son mutumin da ya cika alfahari" ta faɗa ta miƙewa a sanyaye dan jikinta kamar an yi mata duka, ga kasala da take ji kamar ta yi kuka haka take yi. Ta kunna hasken ɗakin ta ɗauki hular kanta ta saka, ta saka hijjab ta fito zuwa main falon. Babu kowa a falon, ta wuce kitchen dan yunwa take ji sosai. Tana shiga ta ga babu abinci, babu komai sai da ta dafa. Takaici da baƙin cikin ya saka ta kukan da yake cin ranta, ta jingina da bango tana kuka dan bata dafa komai a halin da take ciki. So take a dafa a bata, inda hali a bata a baki. Ita ta saba, Hamma ya shagwaɓata, indai yana kusa baya bari ta yi komai, dan ya san yanayin da take ciki yana haifar mata da kasala da son jiki. Motsin da ta ji ya saka ta kalli wajan, ta ga Maleek da shigar fita da alama dawowarsa kenan. Ganin tana kuka sai ya ƙaraso ya ce, "Islaha are you Okay?." Ta ɗaga kai ya ce, "and why are you crying?." Islaha ta goge idonta ta ce, "i'm so famished, and i don't want to cook." Bai ce mata komai ba, ya ƙarasa fridge ya ɗauko mata fresh laban ya ƙaraso ya ja kujerar dinging ɗin kitchen ɗin ya ce, "have a seat please." Haka ta ja ƙafar ta kamar mara jini, ta zauna akan kujerar, ya tsiyaya a cup ya miƙa mata. Ta karɓa sai ta ji ya yi sanyi sosai, ta ajjiye ta ce, "is too cool." "Oh sorry" ya faɗa yana ɗauko mara sanyi ya yi mata mix ya bata. Islaah haka take so a duk lokacin da take cikin wannan yanayin, tana son kulawa, tana so komai ayi mata, hakan yana sakawa ta ji ta comfort bata da damuwa ko kaɗan. Ta ja cup ɗin tana sha a hankali, yana tsaye yana kallon ta har shanye. Maleek ya ce, "me ki ke so kuma?." Ta girgiza kai ta ce, "nothing, i'm okay." "Are you sure?." Ta ɗaga kai ta ce, "Thank you." Ya murmusa ya ce, "my pleasure." Ta sauka daga kan kujerar tana takawa a hankali ta fita shi kuma ya shiga ciki. Washe gari da suka gama komai ita da Sunaira, yana fitowa breakfast sai da ya tambayi ya jikinta ta ce taji sauƙi. Ya zauna akan dining ɗin sanann ya ce, "za ki iya zuwa gidan Dr?." Ta ɗaga kai ta ce, "zan iya." Ya ɗaga kai ya ce, "Fine." Ya zauna ya gama cin abincinsa sannan ya fita. Islaha tana zaune kafin ta tafi gidan Rehaan, ta yi shiru tana tunani Umma ta faɗo mata rai. Duk da Umma bata sonta amma mahaifiyar Safeera ce, baza ta iya share ta ba, kuma Safeera ta bata amanar Umma, ko lafiyar ta ya kamata ace ta kira ta ji. Ta ɗauki wayar ta ta shiga kiran wayar Umma amma bata samu, duk sai ta ji ta damu tana so ta san halin da Umma take ciki kodan saboda alƙawarin da ta yiwa Safeera. Tunawa da Alhaji Musa ya basu lambar sa sai ta kira sa, ta yi sa a ya ɗauka suka gaisa ta ce, "Islaha ce, wacce suka zo daga Yola aka kawo su nan Jeddah." "Okay na gane, ya aka yi?." "Don Allah Lambar wacce ka haɗa Umma da ita suka tafi Madina nake so, ina ta neman Umma bana samun ta ko kaɗan." Ya ce, "okay zan tura miki." Ta yi masa godiya ya kashe wayar. Tana zaune lambar ta shigo, bata yi ƙasa a guiwa ba ta kira ta. Tana ɗauka Islaha ta ce, "Barka ina yini." Ta ce, "lafiya lau." "Islaha ce, ƴar uwar wacce Alhaji Musa ya haɗa ki da ita ki ka kaita Madina." "Yaushe kenan?. "Sati biyu da suka wuce, har ni na zauna a Jeddah nida ƴar uwata." "Na gane. Ya aka yi?." "Ina nemanta a waya bana samu, don Allah ko za ki haɗa ni da ita?." "Sai aka ce miki tare mu ke kwana ko me?." "A'a ina so na san ne kawai." Matar ta ce, "shikenan, zan tura miki da lamba Shafa sai ki yi mata magana, zata iya haɗa ki da ita." Bata gama maganar ba ta kashe wayar. Islaha ta tsaya jiran lamba amma shiru, sai daga baya sai ga lambar ta shigo, Islaha ta kira kai tsaye. Hajiya Shafa bata ɗauka, hakan ya saka Islaha ta gaji tanmiƙe ta shiga cikin ɗakinta. Ta tsaya tana kallon kanta, tana tuna abinda ya faru a gidan Rehaan wanda take ganinsa kamar a mafarki. Ta yi saurin taɓa waist ɗinta jin kamar har yanzu akwai hannun Rehaan a wajan, ta ɗan lumshe ido tana tuna ƙhamshin turarensa da sassanyar muyarsa da yake tambayarta tana lafiya. Ta yi ajiyar zuciya, ta sake gyara kitson kanta sannan ta canja kaya zuwa sabon uniform ta saka hijjabi ta ɗauki wayarta. Sai kuma ta ya tsaya tunawa ina kuma zata je? Gidan da take zuwa ta san ba lokacin zuwan ta bane, tunda yanzu rana ta buɗe. Ta yi ajiyar zuciya ta fita dan sai ta ji gidan ya fita daga ranta. Tana fitowa gidan ta ga Labiba ita da Aisha sun fito daga gidan Ubaid, suka haɗa ido da Labiba, sai da gaban Islaha ya faɗi ganin wani irin kyaun da Labiba da ta yi kamar ba ita ba. Itama Labiban kallon Islaha take yi dan ganin ta yi kyau itama sosai, sai dai ta ɗan rame kaɗan kuma fuskar ta ta nuna alamun rashin lafiya. Aisha ta kalli Labiba da take kallon Islaha, kowa ya tsaya kuma babu wanda ya cewa ɗan uwansa Hii. Aisha ta ce, "wannan zuƙeƙiyar fa? Itace wacce ku ka zo tare?." Labiba ta kalli Aisha ta ce, "itace. Tsintacciya ce a gidan mu, kuma ita Yayana zai aura." "Kai amma tana da kyau fa, kalle ta fa, kalli skin ɗinta har wani shining yake yi kamar tana shafa chocolate. Wow, gaskiya ta burge ni sosai." Labiba ta ɓata rai ta ce, "kin ga Aisha, mu je inda zamu je." Aisha ta ce, "ita baza ta shigo ba? Ya kamata a sako ta a sabgar nan itama ta samu, wallahi ni kaina ta burge ni balle namiji." "Ki ka sani ko gidan da take itama irin mu ne?." Aisha ta yi dariya ta ce, "gaskiya, daga ganin yanayinta baza a barta haka ba." Labiba ta yi dariya ta ce, "Daman ta saba, tun a gida tana yawon ta." Islaha dai tana tsaye tana kallonsu har suka fara tafiya kafin su samu taxi su tafi. Islaha ta yi ajiyar zuciya ta motsa daga wajan ta ƙarasa gidan Rehaan ta buɗe gate ɗin ta shiga a hankali. Tana tafiya tana sake ƙarewa gidan kallo, ta kalli car park ɗin da yake can gefe, ta ga mota biyu a ajjiye, sai ƙaton filin da ya rage wanda zagaye ko ina da fulayoyi masu kyau da tsada. A hankali take takawa wajan ƙofar ta saka code ɗin ƙofar ta buɗe ta shiga a hankali. Hasken falon a kunne yake saɓanin yadda ta saba tarar sa falon, sai laptop da take buɗe a ajjiye, da alama ba a jima da gama amfani da ita ba, sai mug ɗin tea da yake wajan a ajjiye. Islaha ta bi wajan da kallo, ƙhamshin turaren Rehaan yana nan, duk inda ta gifta a falon ƙhamshinsa yake yi. Tana shiga kitchen ɗin ta kunna haske, ta bi ko ina da kallo kamar mai neman wani abun. Sai ta jingina da bango tana tunani, a bayyane ta ce, "Har ƙhamshin turaren iri ɗaya, bazan manta da ƙhamshin turaren nan ba tunda ya jima kafin wayata ta daina ƙhamshin. Ya aka yi nake jin ƙhamshin a nan? Shima ƙhamshin gizo yake yi min ko me?." Sai ta zame ta zauna akan tiles, ta haɗa kai da guiwa bata san asalin abinda yake damun ta ba. Rehaan yana tare da baƙi a sama suna meeting, yana zaune ya ji wayarsa ta yi alert ɗin lock ɗin da yake haɗe da ƙofar falo, wanda duk wanda ya shigo indai yana gidan zai sani, hakan ta ba shi tabbacin an shigo gidan. Rehaan ya miƙe tsaye ya sakko ƙasa ya shiga kitchen ɗin, dan daman ita kawai yake jira, da yana da number ta da ya kira ta, dan yana buƙatar ta a lokacin. Bai kula da ita ba ya shiga kalle-kalle sai ya hango ta a zaune a ƙasa ta haɗe kai da guiwa. Ya bita da kallo yana mamaki, yana tunanin dalilin da ya saka ta zauna a ƙasa. Islaha da ta ji motsi ta ɗago suka haɗa ido dashi da yake tsaye ya saka hannu aljihu yana kallon ta. Ta zuba masa ido ta ga ya haɗe gashin kansa, yana sanye da complete black suit, sai ƙhamshi yake yi. Islaha ta miƙe tsaye daƙyar tana kallonsa, ta gaji da gizon nan da yake yi mata, gwara ta yi masa warning kawai. "Don Allah ka daina zuwa idona, don Allah ka ƙyale ni na huta da ganin ka ko yaushe. Na ganka a Yola, na ganka a Jeddah, na ganka a mafarki, na ganka a zahiri, ka bari na huta don Allah. Na san na yi laifi, kuma zan gyara kuskurena, zuwana nan ma saboda na biya bashi da na ɗauka ne. Ka ƙyale ƙwaƙwalwata ta huta, kar ka saka na haukace. Ko yaushe kai nake gani, ka rabu dani na huta, da kaina zan nemo ka duk inda ka ke, ba sai ka dinga damuna da tunani ba don Allah!" Ta ƙarasa faɗa hawaye yana sakkowa daga idanunta. Rehaan ya bita da kallo jin tana magana ita kaɗai, sai ya kama ƙugu yana tunanin anya lafiya lau take, in ba haka wacce irin magana take yi haka kamar zautacciya?. Babban abinda ya bashi mamaki Yola da ya ji ta ambata, sannan kuma hawayen da take yi ya fi komai basa mamaki. (Ɗan rainin hankali, nufinsa ya manta Islaha😒). Islaha ganin bai ce komai ba sai ta goge hawayen ta, tana sake tabbatarwa da kanta gizo yake yi mata bashi bane, dan da shine da yanzu ya chakumi wuyanta ya ce ina kuɗinsa. Ta ce, "koma meye ya faru kaine da laifi, kai ka yi min duk abinda ka yi har ka saka na aikata abinda ban taɓa yi ba. Na karɓi laifin dan daga ƙarshe na yi kuskure nima. Ka ƙyale ni, ka je can ka cigaba da zama a Yola, zan zo har inda ka ke na same ka. Ka ƙyale ni don Allah, ka daina zuwa mafarkina, ka daina yi min gizo!" Ta faɗa cikin masifa dan ita a tunaninta gizo ne ba gaskiya bane. Yatsunsa biyu ya yi snapping a daidai fuskarta suka bada sauti mai ƙara. Islaha ta firgita kamar wacce aka tsirawa allura, ta sake kallonsa idanunta duk hawaye. Ta ga ita yake kallo, ya zuba mata ido kawai bai ce komai ba. Ita har lokacin bata gasgata shi ɗin bane, ta kai hannunta a hankali kamar wacce zata taɓa wuta, ta ɗan taɓa sa dan ta tabbatar na gaske ne ko kuma na bogi ne. Shi dai ya tsaya cak yana kallon ikon Allah, ya zuba ido yana so yaga a ina zata tsaya. Hannunta ya ɗan taɓa hannunsa sa ta ji kamar jan wutar lantarki, ta ja baya da sauri tana sake kallonsa dan ta tabbatar ba gizo yake yi mata ba, shine ɗin a gabanta, a Jeddah ba a Yola. Ya ɗauke ido daga kallon ta, ya sake kallon ta ya ce, "We have seven guests, make tea for them, now......" yana gama faɗa mata haka ya fita ya bar ta cikin tunani da ruɗani mai yawa. Drama don start🔥😍 _Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments ɗin ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link ɗin ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode ɗin baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/POak37bdMTE?si=dU33KLoRcvufRf7S Nana Haleema.✍🏻 [7/7, 10:21 AM] KRBBK: RDB2P41 Nana Haleema. _Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments ɗin ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link ɗin ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode ɗin baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/S0HoWfmkTOI?si=vJKdn7h8rPpmDhS5 ••••••••••••• Islaha ta bisa da kallo har ya ɓace daga wajan daga wajen ta daina jin sautin takunsa, ta dafe kai cikin ruɗani da tashin hankali, a bayyane ta ce, "ta ya ya zai zama shine?." Ta shiga zagaye kitchen ɗin, tana kai kawo kamar mai ɗawafi, sai kuma ta sake tsayawa ta ce, “amma bai nuna ya sanni ba, kuma in har shine na tabbatar zai neme ni saboda kuɗinsa....." Ta sake yin shiru tana tunani kafin ta ce, "Amma ya aka yi na ga ya share ni, yana yi min kallon housemaid kawai ba wacce ya sani a Yola ba?." Ta safe kama ƙugu cikin son tabbatarwa. Ta sake kallon inda ya bi, ta ja numfashi tana jin turaren yana shiga hancinta a hankali ta ce, "turaren iri ɗaya, wallahi ƙhamshin iri ɗaya ne da nasa. Na haddace ƙhamshin nan, tunda wayata ta jima kafin ta daina ƙhamshinsa. Sannan ga gashin wancan mutumin irin wannan, sannan maganar ma iri ɗaya, turancin ma irin na wancan kamar na ƴan Englaand. Iyayin da komai iri ɗaya ne." Sai kuma ta sake jan numfashi, ta lumshe ido tana tattaro nutsuwa ta ce, "Nutsu Islaha, ba lallai shi ɗin bane. Ki nutsu ki dawo hankalin ki, nan Jeddah ne ba Yola ba" ta faɗa tana kwantarwa da kanta hankali dan ta kasa fahimtar komai. Sai kuma ta ɗauki waya da niyar faɗawa Safeera, sai kuma ta fasa tana kallon wayar a bayyane ta ce, "A'a kar ki faɗa, in ki ka faɗa mata zarginsu zai iya zama gaskiya, zasu ce daman can na sanshi, kuma zasu ce da haɗin bakinsa na zo nan. Kenan da gaske shine?." Sai kuma ta wara hannu ta ce, "indai har ni Islaha zan iya zuwa Jeddah shi meyesa nake ganin ba shi bane? Bayan shi mai kuɗi ne, zai iya zuwa duk inda ya ga dama?. Tabbas shine, ko tantama bana yi shine wanda ya sace ni." Ta sauke ajiyar zuciya ta bi inda ya tsaya da kallo, ta taɓe baki ta ce, "yadda ya nuna bai sanni ba nima zan nuna ban sanshi ba, zan cigaba da harkata har na tara kuɗinsa na biyasa na kama gabana....." Ta sake riƙe baki cikin mamaki ta ce, "kai! Me gayen nan yake nufi wai, bai gane ni ba?. Lallai an yi ɗan rainin sense, ya sace ni ya ajjiye a gidansa ya ce bai gane ji ba?.” Ta girgiza kai ta ce, “Amma mutumin nan ya yanke ni fa, abin ya firgita ni sosai. Allah mai iko, Allah ya sake haɗa mu waje ɗaya, a inda ban yi tunani zan ganshi ba sai gashi na gani" ta faɗa tana kallon stove, sai kuma ta tuna da abinda ya ce. Ta yi tsaki ta ce, "wallahi shine, maganar ma iri ɗaya ce. Wai we have seven guests, ko shi da wa suke da baƙin oho masa. Ɗan rainin hankali mai sace mutane kawai, zaka shigo hannuna ne, bari dai na biyaka kuɗin ka, wallahi sai na yi maganin ka." Tea ɗin ta dafa kamar yadda ya ce, ta samu babban tray ta ɗora kai. Ta buɗe fridge ta ga akwai loaf cake a ciki, ta ɗauka ta ɗorawa kowa slice ɗaya. Ta cire hijjab ɗin jikinta, dan bazai barta ɗaukar trayn  yadda ya kamata ba, ta gyara zama rigarta ta naɗa mayafi kamar ko yaushe. Ta ɗauki tea ɗin ta nufi upstairs a hankali saboda nauyin tea ɗin. Stairs ɗin ma na ɗaurawa, kamar kana taka glass haka suke kana ganin fuskarka. Saman ya rabu biyu, wani ya yi gefe wani ma ya yi gefe, ta zaɓi na dama ta bi ta ƙarasa ƙatuwar balcony ɗin da in kana tsaye a jikin staircase ɗin wajan kana kallon kowa na ƙasa, hira zaka iya da mutumin da yake ƙasa shima kuma yana kallon ka. Islaha sai da ta hau saman ta ga ashe a ƙasa ba komai take gani ba, ga asalin kallo a nan a sama, dan tunda take bata taɓa ganin lafiyayyen falo mai ɗaukar hanlali kamar sa ba. Harda BAR a gefe, wacce aka yi adogon glass cups da kwalabe kamar na giya. Ta tsaya cak tana kallon falon dan bata san inda zata bi ba, ga dai corrior nan tana gani, amma bata san in ta bi ina zata je ba, ta ajjiye tea ɗin akan table tana sake kallon falon dan ta gaji da riƙewa. Bar ɗin take kallo, a bayyane ta ce, "Malam Bature har giya ana sha kenan, an yi asara" ta faɗa tana taɓe baki. "Hey." Islaha jin magana daga bayanta, sai ta juya tana kallonsa. Bature ne na asali, kana kallonsa sa ka san bai yi kama da wani jinsi ba ba sai bature. Ta ce, "hello." "Are you looking for meeting room?." Ta ɗaga masa kai, ya nuna mata inda zata shiga ta ɗauki tray ɗin ta ƙarasa wajan. Autimatic door ce a wajan, tana zuwa wajan ƙofar ta buɗe ta shiga da sallama a bakinta. Babban meeting room ne mai ɗauke da table da kujeru masu yawa, su bakwai ne a zaune a ciki, har wanda ya fita bakwai, ko wanne sanye da transilater a kunnensa dan wani baya jin turanci. Rehaan yana tsaye a jikin kujerar CEO, yana kallon wani da yake tsaye tsaye shima yana abinda za a yi a projector. Tana shiga duk suka zuba mata ido, har shi Rehaan ɗin sai da ya juyo yana kallon ta, kafin ya ɗauke kai yana jira ta ƙaraso. Gajiya kallon nasu ta yi ta tako ciki a hankali, suna ganin uniform ɗinta suka san housemaid ce, amma duk da haka kallon ta suke yi. Wani irin sanyi ɗakin yake yi, ita bata san meyasa suke saka ac mai hawa kai haka ba, sanyi zaka ji kamar ka buɗe fridge, sanyi mai ratsa ƙwaƙwalwa da ƙasusuwan jiki. Haka gidan Maleek yake, kamar ka shiga cikin ƙanƙara. Sanyin ya buge ta, ta ji kamar numfashinta zai ɗauke, ta ƙarasa a hankali ta ajjiyewa kowa a gabansa. Bata ce komai ba sai su da in ta ajjiye zasu ce sun gode, Allah Allah take ta bar wajan kafin ta samu attack, dan sanyin ya yi mata yawa sosai, yanzu numfashin ta zai fara sarƙewa, ƙirjinta ya fara ciwo. Tana gama ajjiye musu da sauri ta juya ta fita daga wajan, ta tsaya a falon da yake da ɗumi tana sauke numfashi har ta ɗan nutsu snanan ta sauka ƙasa a hankali tana sake ƙarewa ko ina na gidan kallo. Tana shiga kitchen kiran Hajiya Shafa ya shigo wayarta, ta ɗauka ta saka a kunne da sallama, jin Hajiya Shafa ta fara larabci sai ta ce, "Sunana Islaha, don Allah ina so ki haɗa ni da Hajiya Maimuna da ki ka kai wajan aiki. Tare mu ka zo nan da ita, ni ƴarta ce, ina garin Jeddah, tunda mu ka zo bamu yi magana ba." Hajiya Shafa ta ce, "Shikenan, zan haɗa ku in na shiga wajen ta." Islaha ta yi mata godiya ta kashe wayar. Islaha ta yi ajiyar zuciya tana kallon kitchen ɗin har lokacin ƙhamshin tea ɗin yake yi, ga ƙhamshin turarensa da ya cika ko ina. Hijjab ɗinta ta mayar, ta fito falon kenan shi kuma ya sakko yana amsa waya kamar baya so, tafiyar ma a hankali yake yu kamar mara lafiya, komai nasa a sanyaye kamar nata laka. Islaha ta yi kamar bata gan shi ba, har zata wuce ta fita ya ce, "go and take the used cups from the meeting room, then go into my bedroom and clean it up." Islaha wani juyo ta kalle sa, sai ta ga shi ba ita yake kallo ba, wani wajen daban yake kallo kamar ba shine ya yi magana ba. Ta maimaita gyara masa ɗaki a ranta, ta bi sa da kallon up and down har ya ɗago ido suka haɗa ido, ya sake ɗauke kansa daga kallon ta. Islaha ta ce, "ba fa baiwa bace ba ni, girki aka ce zan dinga yi ba aikin gyara ɗaki ba." Bai kalle ta ba balle ta saka a ranta ya ji me ta ce, ko kaɗan bai nuna mata alamun ya ji ba, shiyasa bata yi tunanin ya ji ɗin ba. Islaha ta ce, "ban san ƙaddarar da ta sake haɗa mu yanzu ba, na so sai wani lokacin ba wannan ba. Na so sai lokacin da zan nuna maka kuskuren ka muka haɗu, na so sai lokacin da zaka yi danasani sannan zamu haɗu da kai. Amma yanzu ma bata ɓaci ba, zaka san wacece Islaha." Rehaan tsaf ya gano wacece, yana kuma jin duk abinda take faɗa, yana murmushi a ransa dan shi baya yi mata kallon mai hankali. Daman shi tun a Yola ya lura kamar bata da hankali, yanzu da ya ganta a Jedda ya tabbatar da babu hankalin ko kaɗan, dan gashi nan sai magana take yi ita kaɗai babu mai ta ya ta. Bai damu da tunanin abinda ya kawo ta Jeddah ba, ko kaɗan bai ji yana wannan tunanin ba, dan ko a jikinsa rayuwarta ce ba ta sa ba. Maimakon ya kalle ta sai ta ji yana waya ya ce, "Mamy i'm so tired, i need rest." Yadda ya yi maganar ya bawa Islaha mamaki, ta bisa da kallo jin yadda yake shagwaɓa kamar yaro ƙarami. Kai ko ƙaramin yaro baya irin wannan shagwaɓar, sai wani narke fuska yake kamar mai. Babban abin haushin ma wai ya gaji, ko me ya yi da ya gaji oho masa. "Mamy I've been in a meeting with a guests for 30 minutes." Islaha bata san ta buɗe baki ba ta ce, "ji wai minti talatin, ai daga ganin rariya ka san zata zubar da ruwa. Kallon farko da nayi masa nasan wannna maza ya rako duniya. Gashi nan kamar ruwa, sai aukin kwanciya. Wannan in waje ɗaya muke wata ran sai na yi masa dukan tsiya, bazan iya ɗaukar wannan abubuwan ba" ta faɗa tana kallonsa. Rehaan ya tsaya da wayar ya kalle ta, shi fa ta fara bashi tsoro, dan ya fara tunanin mahaukaciya ce. In ba mahaukaci ba waye zai dinga magana shi kaɗai? Har yana faɗa yana nuni da hannu. Suna haɗa ido ita ya ce, "what are you waiting for?." Ƙasa-ƙasa ta ce, "takaici nake ji in ina kallon ka, nan ba Yola bane balle ka hanani fita" ta faɗa tana wuce sa ta hau sama. Ya kalli inda ta bari ya ɗauke, kai kafin ya fita daga falon gabaɗaya. Islaha tunda ta shiga meeting room ɗin take ta mita, "Aikin banza, wai ya gaji. Gaskiya na jima ban ga ragon maza kamar wannan ba. To daman wannan me zai tsinana? Abu kamar fulawa saboda laushi. Mtsw! Haushin namiji mai yanayin mata nake ji, shiyasa na tsani wannan mutumin da ko sunansa ban sani ba." A haka ta kwaso cups ɗin ta ajjiye a falo, ta shiga tunanin ina ne kuma bedroom ɗin nasa da ya ce ta shiga. Ta ja tsaki ta bi hanyar corrior ta buɗe ƙofar farko ta shiga. Ƙhamshi mai sanyi ya shiga hancinta, ta dinga takawa a hankali kamar mai jin tsoro dan ta ɗauka wani falon ne saboda girman ɗakin. "ma sha Allah!" ta furta tana kallon ɗakin cikin yanayi na burgewa. "Wow!" Ta furta lokacin da ta juya bayanta ta ga lafiyayyen ocean kana hangonsa ta glass. Ta taka a hankali tana kallon wajan ganin mutane suna ta harkokinsu a waja, ga ruwan mai daɗin kallo. Islaha ta ce, "gaskiya ya yi kyau sosai wajan nan, ya burge ni." Sai ta bar wajan tana kallon ɗakin, ita bata ga me za a gyara ba, duk da komai na ɗakin fari ne amma babu alamun dauɗa, komai neat. Ta ƙarasa ta ɗauki cups guda biyu, sai kuma ta haɗe rai ta ce, "ɗauke cup ɗin ma bazai iya ɗauka ba, mtsw! Me ake da ragon namiji don Allah." A haka ta sakko tana ta masifa akan abinda bai shafe ta ba, ta shiga da cups ɗin ta wanke su ta goge sannan ta mayar dasu wajansu. Ta fito daga kitchen ɗin ya sake shigowa falon still waya yake yi. Bata kalle sa ba, zata wuce ta fita kenan ta ji ya murza yatsunsa sun bada sauti alamun yana yi nata magana. Islaha saboda ƙarfin hali sai ta yi banza kamar bata san da ita yake ba, gab da zata ƙarasa wajan ƙofar ya ajjiye wayar ya ce, "ki dawo, ki haɗa min loaded fries irin na jiya." "Kan bala'i! Wai wannan mutumin me ya mayar dani ne?" Ta faɗa a hankali tana juyowa a fusace. Karaf suka haɗa ido, sai ta ji gabanta ya faɗi dan gabaɗaya ya zaro idonsa a kanta yana kallon ta. Duk da faɗuwar gaban da ta ji tsiwar tana nan bata saduda ba, zata yi magana ya miƙa mata kuɗi ya ce, "take it." Ta harari kuɗin kamar baza ta je ba, shi kuma ya zuba mata ido yana so ya ga ƙarshen gudun ruwan yarinyar nan. Ya ɗan kalle ta ta ƙadan ido, ya ga ta ja ta tsaya tana hararar gefe. Sai ta bashi dariya, ya ɗan murmusa dan da gaske baya yi mata kallon mai hankali, so yake ya ga zata karɓi kuɗin ko baza ta karɓa ba. Nana Haleema. [7/7, 10:22 AM] KRBBK: RDB2P42 Nana Haleema. _Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments ɗin ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link ɗin ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode ɗin baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/S0HoWfmkTOI?si=vJKdn7h8rPpmDhS5 ••••••••••••• Islaha ta juyo ta kalle sa, suka haɗa ido ta ɗauke ido, ta ɗan yi ajiyar zuciya sai kuma ta tuna aiki nake yi saboda ki biyasa kuɗinsa, ta rarrashi zuciyar ta ta ƙarasa ta karɓa. Ya wani kalle ta ganin ta karɓa, ya yi tunanin rashin jin ta ya kai ta ƙi karɓa. Riyar dubu bakwai ta gani a hannunta, daga zaman ta a ƙasar zuwa lokacin tana fahimtar kuɗin ƙasar sosai, farin ciki ya mamaye zuciyarta, ganin ta fara tara kuɗin da ta zo nema. Dan kuɗin da ya bata masu yawa ne sosai, a kuɗin nigeria sun tafi miliyan biyu da wani abun, amma a ƙasar kamar dubu bakwai suke, duk da kuɗi ne masu daraja ko a can ɗin, dan zaka yi siyayya mai matuƙar yawa. Lokaci ɗaya fuskarta ta washe, farin jinin zaya sauke nauyin bashi ya mamaye mata zuciya, ta ɗan ja baya daga wajan ta ce, "na kusa biyan bashin da na ɗauko in sha Allah, da na tara na biya sa zan kama gabana ka koma gida, nima na gaji." Bayan ta gama bayaninta sai kuma kalle sa ta ce, "Thanks." Hannunsa ya ɗaga mata kawai bai ce komai ba, ta harare sa ta ce, "ɗan wulaƙanci, zan rama ne." Ta wuce ciki ya bita da kallo bayan ya ɗan tafi tunani, indai ba tana da matsala ba to gaskiya daman mahaukaciya ce. Bai amince da lafiyar ta ba, dan mutum mai lafiya bazai dinga magana sakaka haka ba. Ita kuwa farin cikin fara samun kuɗi ya mamaye mata zuciya, ta fara converting saudi riyal to naira tana lissafa riyal dubu bakwai. Ƙaramar ƙara ta yi ganin kuɗin da ya bata a kuɗin nigeria, daɗi ya mamaye mata zuciya tana ji kamar ta taka rawa. Ta rufe baki da hannunta ta ce, "anya ya san kuɗin da ya bani? Ya san dubu bakwai ce kuwa?." Ta yi dariya ta ce, "ni da zai karɓa ma dana bashi wallahi, da na fara rage masa bashinsa da na ci, a hankali sai na ƙarasa bashi." A wannan yanayin ta yi abinda ya ce ɗin, ba tayi kuskure ba saboda murna. Lokacin da ta fito aiki yake a laptop, sai yatsine fuska yake yi shi a lallai ya gaji. Islaha ji take kamar ta tsinka masa mari, dan bata son ta ga namiji mai saurin nuna gajiyarsa akan komai kamar sa. A ganinta mata ne ya kamata su nuna sun gaji ba namiji ba, maza jarumai ne, kuma da juriya aka san su. Ta ajjiye masa a kusa dashi, bai motsa ba kamar bai gan ta ajjiye ba, ita kuma bata ce komai ba ta juya a hankali ta fita daga falon. Tana fita ya kira Jazy yana ɗauka ya ce, "Jafar wata housemaid Ubaid ya aiko min, kamar mai taɓin hankali fa, sai ka ga tana magana ita kaɗai." Jafar ya yi dariya ya ce, "ina ruwan ka da maganar ta, kai dai ba tana yi maka abinda ka ke so ba? Shugaban masu son jiki da shagwaɓa na africa." Rehaan ya ce, "uhum ba laifi, tana da ɗan ƙoƙari." "Shikenan sai ka haƙura. Zuwa next week zan shigo in sha Allah." "Zaka shiga Yola before ka zo nan?." "i think so." "Okay, in ka shiga ka taho da Kiddo, na yi mata alƙawarin zuwa amma bana so ta zauna ita kaɗai." "Ga housemaid ɗin ka nan, ba sai su zauna tare ba?." Kamar Jafar yana ganinsa ya wani ya wara ido ya ce, "god forbid, ta ya zan bar kiddo da wannan yarinyar mai taɓin hankali? Infact ni fa manage nake yi, in na tuna abinda suke aikatawa da Ubaid sai na ji kamar bazan iya cin abincinta ba." "Rehaan ka shiga uku, kai a ina ka ga suna aikata wani abun? Ka kiyaye harshen ka fa, kar wata ran ka yi danasani mara amfani." Rehaan ya ce, "babu yadda za a yi Ubaid ya ajjiye housemaid ƴar Nigeria irin wannan bai yi mata komai ba, na san waye Ubaid. So zan iya rantse maka itana irinsa ce, dan da kuɗi yake siye matan Nigeria, duk abinda yake so suna yi. So bazan iya barin ta tare da Kiddo ba." Jazy ya ce, "rayuwarta ce, babu abinda ya shafe ka da abinda take aikatawa. Ka iya harshen ka akan irin wannan maganar, in ma tana yi ɗin ina ruwan ka? Babu ruwanka da abinda take yi, ita ta ga zata iya." Ray lokaci ɗaya ya ji ransa ya ɓaci, loaded fries ɗin maya ji bazai iya ci ba. Ya ture sa daga gabansa ya ce, "na tsani ɗauko mata daga Nigeria a kawo nan suna wannan shirmen, bana so Jazy, kuma yana jin haushin hakan sosai." "Ka ji mai kishin ƙasa. Kai fa ba ɗan nigeria bane, haifaffen ƙasar Uk ne ne kai, Mamy haifaffaiyar ƙasar india ce. So meye na damuwa akan ƙasar da ƙafar ka ɗaya ce a ciki?." "I was born in England, but I'm Nigerian by blood...... Jini ba wasa bane malam, na fi ka kishin ƙasar tanka" ya faɗa da hausa saɓanin da da yake magana da turanci. Jazy ya yi dariya ya ce, "An gaishe da mai kishin ƙasa. Ka fara gyara ƙasar taka tukunna, ka mayar da hankali ka samarwa da kowa aikin da zai ishesa ya riƙe kansa iyalansa. In ka yi haka ka tabbatar kowa ya samu, sai ka ji haushi in sun je wata ƙasar nema." "Ni ba shugaban ƙasa bane." "Dan haka sai ka yi kamar baka gani ba, tunda ka san baza ka iya canjawa ba meyasa zaka damu kan ka?. Wallahi basu da laifi, in basu bar ƙasar su sun nema ba mutuwa ka ke so su yi ne Ray? Kai ka san yadda ake cikin talauci a Nigeria kuwa?." Ray ya yi masa banza bai tanka ba, Jazy ya ce, "ya maganar auren ka? Ance an kusa ko?." Jin yana yi masa dariya sai ya kashe wayar. Ya bi bowl ɗin da kallo, haka kawai ƙyanƙyaminta ya mamaye masa zuciya, ya ɗauka ya kai dusbin ya zubar ya haɗa har bowl ɗin, ya hau sama yana jin haushin kasancewar ta a gidan Ubaid kamar wata ƙanwarsa. Islaha lokacin da ta koma tana shiga kiran Hajiya Shafa ya shigo. Ta zauna a gefen gado ta ɗauka ta ji Umma ta yi sallama. Islaha ta amsa ta ce, "Umma ina yini, Islaha ce. Ina ta kiran wayar ki bana samu." Umma ta ce, "Lafiya lau Islaha. Da yake ban siyi layin ƙasar nan ba." "Ai ya kamata ki siya Umma saboda kiran gida." "Ina samu ina kiran su ta whatsapp in na samu hutu. Ƙawarki ce dai har yanzu taƙi bani dama na yi magana da ita." Islaha ta ce, "Kuma tana tambayata ina ki ke, sai na ce mata ai ba tare muke ba." "Don Allah ki ce mata ko sau ɗaya ta karɓa mu gaisa, ina so na ji muryarta." Islaha ta ɗaga kai ta ce, "To Umma, zan faɗa mata in sha Allah. A wacce unguwa ki ke a madinan?." Umma ta cr, "wallahi ban sani ba, ban taɓa fita ba tunda na zo, aiki ne nake yinsa kamar inji." Islaha ta ce, "To Umma ki tambayi mai wayar sai ta faɗa miki sunan Unguwar, ina so na zo na ganki." A sanyaye Umma ta tambayi Hajiya Shafa, ta faɗa mata itama ta faɗawa Islaha. Islaha ta ce, "In Allah ya yarda zan zo na ganki, duk da nima bana fita amma zan san yadda zan yi na zo." Umma ta ce, "to Islaha, amma ki cewa ƙawar ki ta daure ta yi magana dani kin ji?." Islaha ta amsa sannan suka kashe wayar. Bayan sun gama wayar Hajiya Shafa ta bi Umma da kallo ta ce, "ya naga kin rame haka?." Umma ta ce, "kullum a cikin fargaba nake kwana a gidan nan, kwana biyu hankalina ya kwanta saboda mai gidan baya nan, amma yanzu gabaɗaya a ruɗe nake saboda ya dawo yau." Hajiya Shafa ta yi tsaki ta ce, "ke baki san yadda za ki kare kan ki daga wajan ba? In baki kame kan ki ba, kin nuna masa ke ba irinsa nace wallahi bazai ƙyale ki ba wallahi." Umma ta ce, "to ya zan yi?." "Sai ki san abinda zaki yi. Kuma ki tashi na raka ki kije ki yi layin waya saboda ƴan uwan ki, bazai yu na dinga zarwa a kan ki saboda waya ba." Umma ta ce, "ai bani da kuɗi." "Mu je na ranta miki, in aka baki albashin ki sai ki biya ni." Babu yadda Umma ta iya haka ta tashi suka fita. Tunda ta zo sai ranar ta fita, Umma sa kallon unguwar take yi cikin burgewa, ko ina shiru sai larabawa kaɗan-kaɗan kafin ta ce, "Hajiya a ina masallacin annabi yake?." Ta kalli Umma ta ce, "da tafiya, sai kin hau mota." Umma ta ce, "Allah ya bani iko wata ran na je na gano kabarin Annabi." "Kina saka ran zaki je kenan?." "Eh mana Hajiya, na zo har garin ace ban je ba, ai na yi asara babba." "Ai ba ziyara ce ta kawo ki ba, aiki ne ya kawo ki." "Duka biyun ne suka kawo ni wallahi." "Ki cire ran zuwa wallahi, dan fitowa daga gidan nan ma babu lallai ki sake yi." Umma ta yi shiru tana tunani, kenan burinta na zuwa masallacin bazai cika ba, gata a Madina amma ace kar ta saka ran zuwa ta yi ziyara? To meye amfanin zuwan ta ƙasar in bata je ta ga masallacin ba? Ita da buri biyu tazo ƙasar, ta tara kuɗi kuma ta yi ziyara, gashi duka biyun basu yu ba. Bata ce komai ba suka je aka yi mata layin waya suka dawo gida ita kuma ta wuce. Umma jin gidan shiru sai ta kwanta da niyar hutawa, bacci yana ɗauke ta ta ji ana tashin ta, ta buɗe ta ga matar gidan a tsaye tana yi mata nuni da tashi. Umma ta miƙe tsaye ta biyo bayanta zuwa kichen. Abinda ta gani ya saka gabanta ya faɗi, kaji ne masu yawa sosai, ta nuna mata alamun ta gyara. Umma ta ji kamar ta kurma ihu saboda takaici, ta bi kajin da kallo dan a ƙalla zasu kai hamsin. Matar ta ware wanda in aka gyara za a saka a fridge, da wanda Umma zata gasa. Umma ta ƙarasa ta fara gyarawa, tana yi tana hawaye saboda gajiya. Tana tsaka da yi aka ce ta zo ta gyara waje an ɓata. Ta fito ta gyara ta koma ta cigaba da aikin. Aikin sai da ya ɗauke ta awa biyu da wani, ta gaji matuƙa, bayanta kamar zai ɓalle saboda gajiya mai tarin yawa. Daƙyar ta ke jan ƙafa ta shiga ɗaki, ta cire kaya ta shiga wanka dan khamshin gashin kaza kawai take yi. Tana fitowa daga wanka ta ji an rufe ƙofa, tana juyowa ta ga mutuminta a tsaye yana kallon ta. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Umma ta faɗa hawaye cikin tashin hankali. Ya fara takowa zuwa inda take a hankali, Umma ta fara ja baya tana kalle kalle tana so ta samu wani abun da zai zamar mata makami. Babu komai a wajan sai ta ɗauki wayar ta tana muna masa, cikin turancinsu na manya ta ce, "Police, zan kira Police zu zo su kama ka wallahi, kar ka matso kusa dani." Jin ta ambaci police sai ya tsaya, kafin ya juya ya fita daga ɗakin. Umma ta zube a kan gado kwai ta fashe sa kukan takaici da sanasani. Whatsapp call ɗin Atika ne ya shigo, tana ɗauka kawai ta fashe da kuka. Atika daga can ɓangaren ta ce, "Maimuna me ya faru ki ke kuka?." Umma cikin kuka ta ce, "Na gaji Atika, gida nake son dawowa. Na gaji da zama a nan, aikin ya fita daga raina, ina so nazo na riƙe ƴaƴana. Wahala nake sha, ga tsawa, ga aiki, ga raini. Na gaji wallahi." Atika ta ce, "da wuri haka? Gabaɗaya kwanan ku nawa da tafiya da ki ke son dawowa? Ko har kin tara da yawa ne?." "Wallahi babu abinda na tara, hasalima bani da ko sisi a hannuna. Ɗazu layin waya na je siya, sai ranta min kuɗin aka yi dan bani da komai. Na gaji Atika, Ki ta ya ni da addu'a, Allah ya kuɓutar dani daga hannunsu." "Kin san dawowar ki yanzu bazai yu ba ko? Dole sai kin gama biyan waɗanda suka kai ki kuɗinsu ko?." Kukan Umma ya ƙaru ta ce, "na sani, shiyasa na ce ki taya ni da addu'a." Atika ta ce, "ki yi haƙuri, zaki saba a hankali." "baza ki gane halin da nake ciki ba. Ga wahala, ga fargaba, ga tsawa, ga aiki, ga raini. Haka kawai zan buɗe ido na ga magidanci tsirarara a gabana. Ya zan yi?." Atika ta ce, "haƙuri zaka yi, a hankali komai zai zama labari." Umma ta ja numfashi ta ce, "Safeera har yanzu fushi take yi dani, ki bata haƙuri ki ce ko sau ɗaya ne ta yi magana dani." Atika ta ce, "zan yi mata magana in na shiga gidan. Ki cigaba da haƙuri, ki ta addu'a, Allah ya kare ki daga sharrin shaiɗanin can." Umma  ta ɗaga kai kamar tana gabanta ta ce, "ki ta ya ni, ki saka su Rukayya su ta ya ni. Ina so na nemi afuwar su Yayan Katsina ban san ta ya zan fara ba." Atika ta ce, "Allah zai kawo mafita, ki cigaba da haƙuri." Umma ta amsa suka yi sallama zuciyarta cike da abubuwa kala kala...... Nana Haleema. [7/7, 6:25 PM] KRBBK: RDB2P43 Nana Haleema. _Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments ɗin ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link ɗin ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode ɗin baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L •••••••••••• *YOLA.* "Ummi meyasa bakwa yin aiki yadda ya kamata ne? Har yanzu ƴan kallo complain suke yi akan rashin Islaha, mun rasa mabiya da yawa saboda rashin ta. Da Saleem ya duba shafin mu na tiktok mutane sama da dubu uku sun yi unfllowing ɗinmu saboda rashin fuskar Islaha. In mu ka yi posting a ko yaushe magana ɗaya ce, su dai a dawo da Islaha ko su daina bibiyarmu. Shirin Rayuwatatalkshow views sun ragu sosai, lokacin da Islaha tana nan sai a samu masu kallo sama da dubu ɗari biyar, amma tun bayan tafiyar ta ba a wuce dubu hamsin, wani har dubu ashirin. Me yake faruwa ne?." Tunda ya fara magana Ummi da Jamila suka yi shiru, sai da ya gama sannan Jamila ta ce, "Chairman tsakani da Allah sun fi son fuskar Islaha, saboda son da masu kallo suke yi mata ya saka ta sama permanent a ɓangaren interview da talkshow, sai ta ƙure ake canja ta a ɓangaren. Ba laifin bane, mun iya aiki daidai ƙarfinmu, kawai zuciyarsu tana tare da Islaha ne shiyasa ake samun matsala. Kuma baza mu maye gurbinta ba, sai dai mu yi abinda zamu iya." Chairman ya ce, "Yanzu haka za a cigaba da zama kenan? Muna samun masu kallo dubu ɗari uku zuwa ɗari mun dawo dubu ashirin?. Ko interview ɗin da Muslim ya yi da minister tsaro akan satar yaran nan, har yafi interview ɗin Ummi views. Asara mu ke ta tafkawa, kwata-kwata bata yi sati uku da tafiya ba, amma muna ta samun naƙasu akan harkokin mu." Ummi ranta ɓaci yake yi, baƙin ciki da hassadarta suka sake ninkuwa fiye da baya, hassada ta ɗaure mata harshe ta kasa cewa komai balle ta yi magana. Chairman ya ce, "ina magana Ummi kin yi yi shiru." Daƙyar ta buɗe baki ta ce, "To Chairman na rasa me zan ce ba, gani ka ke kamar ba ma yin ƙoƙari a aikin nan, ka manta tun kafin Islaha mu ne muke tafiyar da komai yadda ya kamata, zuwan ta ne ta asirici kowa ya zama babu mai son fuskar mu sai fuskar ta." "Ke Ummi bana son shirme, wanne irin asiri kuma?." Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, shi kuma ya ce, "baza ki iya bakin ki ba? Baki daddara da abinda ya faru ba ko?." "Chairman ai ba wani abun na ce ba, gaskiya ce ba wani abun ba." Chairman ya ce, "ke ki ka sani kuma, ni dai in aka cigaba da samun akasi wallahi zan canja ku gabaɗaya na zuba wasu. Bazai yu na dinga asara saboda ku ba." Jamila a tausashe ta ce, "ka yi haƙuri Chairman." Ya ja tsaki ya ce, "ku je. Sannan ku aiko min da Safeera."Basu jima da fita ba Sfeera ta shiga da sallama. Ta ce, "Chairman gani." Chairman ya ce, "Safeera ban tabbatar rashin ƙawarki zai taɓa mu har haka ba sai yanzu da mu ke ta samun raguwar mabiya. In ki ka duba comments section zancen Islaha ne, in bamu dawo da ita ba su dai zasu daina bibiyar mu." Safeera ta ce, "ina lura da komai Chaairman." "babu batun dawowar ƙawar ki nan kusa Safeera? Kina gani bata rufe sati uku ba har yanzu, amma mun rasa mutane masu yawa. Ya ki ke ganin abinda zai kasance in ta sake kwanaki bata nan?." Safeera ta ce, "In sha Allah baza a sake rasawa ba, zan tambaye ta in na koma na ji yaushe zata dawo, in sha Allah zata dawo a cigaba da komai kamar yadda aka sa ba." "Don Allah ki tambayar mana ita, rashinta zai iya sakawa mu rasa abubuwa da yawa. Guest uku muka kaiwa katin gayyata amma sun bamu uzuri, abinda bai taɓa faruwa damu ba kenan. Da zarar Islaha ta kaiwa mutum iv yake saka mana lokaci, wani ma shi zai ce ta saka lokacin da ya yi mata. Don Allah ku yi magana da ita." Safeera ta ce, "in Allah ya yarda zamu yi magana, zata dawo komai zai dawo." Chairman ya ce, "na gode Safeera, ki je ku cigaba da aiki." Lokacin da ta fito office ta koma, tana shiga Saleem yan shigowa ta kalle sa ta ce, "Chairman ne ya yi min magana akan rashin Islaha, ba ka gani ba kamar ya yi kuka. Da yana da iko da ya yi fuffuke ya je ya ɗauko Islaha ta dawo, ta ɗora daga inda ta tsaya." Ya yi murmushi ya ce, "Rashin ta ya taɓa gidan gabaɗaya, har bana son buɗe tiktok saboda yadda za ki ga ana wulaƙanci dan ba ita bace." Safeera ta yi dariya ta ce, "Hajiya Ummi uwar hassada, tana murna ta rabu da targaɗe sai ga karaya ta samu. Bata rabu da bukar ba an haifi Habu." Saleem ya yi dariya ya ce, "Ai na san ji zata yi kamar ta kashe Islaha ta huta." "Ai da tana da dama wallahi zata iya. A haka zata ƙare, babu abinda ta isa ta yiwa Islaha wallahi. Bara na koma gida na kira ta na bata labari." Saleem ya yi murmuahi suka cigaba da hirar su.    Ummi tana barin office ɗin Chairman office ɗin Muslim ta nufa, yadda ta shigo ya fahimci akwai damuwa, kuma daman ya san zata zo saboda irin cin kashin da ƴan comments section suke yi mata. Kamar sun fi tsanar Ummi akan kowa, har gwara shi in ya yi ba a cewa a canjasa, amma in Ummi ce yanzu za a cika comments section da magana. Ummi a firgice ta ce, "babu yadda za a yi a kashe Islaha ne? Babu wanda zamu biya ya kai ta har a shafe labarin ta daga duniya gabaɗaya?." Muslim bai ce komai ba, sai da ya miƙe ya buɗe office ɗin ya leƙa dama da haggu ya ga babu kowa sannan ya dawo ya saka mukulli ya ce, "me yake damun ki? Wannan ɗaga muryar da ki ke yi na meye? In wani ya ji abinda ki ke faɗa fa?." Ummi cikin ƙunar zuciya ta ce, "Islaha! Ta tafi ɗin ma ban daina ƙunsar baƙin ciki saboda ita ba, bata garin nan, bata cikin gidan nan amma tana bakin kowa, harda masu kallon mu. Ka kalli wulaƙancin da aka yi min a hirar jiya? Ka kalli yadda ake saka hoton Islaha a commets section ana cewa in ba ita ba an daina kallon mu?." Muslim ya ce, "na gani." "Haukacewa ake so na yi ne? So ake na kashe kaina saboda baƙin cikin Islaha?. Chairman ne ya kira mu yanzu, wai faɗa mana yake yi in aka cigaba da samun low views sai canja wasu presenters ɗin. Ya manta kafin Islaha ni ce highest presnter da ta fi kowa na gidan nan farin jini da samun views, ya manta ni na fara aiki a nam kafin ita?. Tunda ta zo na koma baya, yanzu akan rashinta yake cewa zai canja mu, ni Ummi ni za a canja na koma bayan camera saboda ita!. Wallahi bazan bar yarinyar nan ba, bazan ƙyale ta ba, sai na yi mata abinda har ta mutu bazata manta dani ba." Muslim a tausashe ya ce, "kwantar da hankalin ki, mafita ya kamata mu samu akan hakan ba wannan ɗaga muryar ba. Ki zauna mu yi magana." Ta zauna kamar zata farka kujerar, sai jan numfashin mugunta take yi hassada da baƙin ciki suna nuƙurƙusar zuciyata. Muslim ya bita da kallo ya ce, "a hankali zamu yi maganinta, yadda ta bar aikin nan baza ta sake dawowa ba. Baƙin fenti ya kamata mu shafa mata, yadda ƴan kallon ma zasu dinga son ganin fuskar ta ba balle har su ce suna son ganinta." "Me zamu yi? Ni a ganina batun acid ɗin nan ya kamata a dawo dashi, da zarar ta dawo a lalata fuskar shegiya, sai na ga wacce fuskar za a dinga gani ana yabawa." "Wannan ma shawara ce mai kyau. Bayan haka ma akwai abinda nake tunani, amma dole sai na yi bincike na ga ina ta tafi, me ta tafi yi, me ya kai ta garin, yaushe zata dawo?." "Ka tambayi Salim, na san shi ya san inda take ai." Ya yi murmushi ya ce, "ta yadda za ki san abun munafurci ne ya ƙi faɗa min, sai ya ce shi bai san inda take ba. Safeera ma da na tambaye ta sai ta ce min ta yi tafiya, nace zuwa ina, wai bata sani ba. Hakan ya jefa min zargi a zuciyata, ya tabbatar min akwai abinda aka ƙulla. Ko dai ba waje na gari ta tafi ba, ko kuma akwai abinda ya faru." Ummi ta ɗan daki table ta ce, "ya kamata ka samo mana inda take, jikina yana bani wani abu akan hakan." Ya gyaɗa kai ya ce, "dole zan nemo, wannam itace hanya ta farko ta yaƙi da ita. In muka samo labari mara daɗi a kanta, zamu yaɗa sa ya shiga duniya gabaɗaya. Iya wannan zai rage mata farin jini da masoya sosai." Ummi ta ce, "yaushe zaka nemo ɗin?." Ya bita da harara ya ce, "bana son gaggawa, na ce zan yi ai. Ki tashi ki koma, kar ace muna kulle ƙofa ni dake a office." Ta miƙe ta ce, "meye in ance ɗin, mun kai mu kulle ɗin ai." Ya ɗan yi dariya bai ce komai ba ta fita. Ya jingina da kujera yana tunanin hanyar da zai bi ya gano inda Islaha ta tafi. Safeera tana komawa gida ta tarar su Humaira suna nan, ta cire hijjab ɗinta, Rukayya ta shiga wajanta ta ce, "Adda Maman su Kausar ta aiko mana da dafaffiyar awara ta ce mu soya. Gata na soya in za ki ci." Safeera ta murmusa ta ce, "bana jin yunwa Ruky, ki bari sai anjima. Baba ya dawo?." "A'a bai dawo ba. Nima so nake ya dawo, Maman su Kausar ta ji ina maganar kuɗin handout, shine ta bani kuɗin ta ce na ƙyale Baba ya huta. Kin gansu dubu biyu." Safeera da mamaki ta ce, "Mamansu Kausar ɗin ce ta ba ki?." Ta ɗaga kai ta ce, "itace wallahi." Safeera ta ce, "Kai hidimar da take yi mana nan ta yi yawa sosai, ta bakin Baba ya kamata ta rage kar ta ɗorawa kanta nauyin mu." Ruky ta ce, "Nima haka na ce Adda, amma bara ya dawo mu ji me zai ce." Safeera ta ɗaga kai ta ce, "bara na ɗan huta kafin lokacin sallah. Ko akwai abinda ku ke so?." Ruky ta ce, "Babu komai Adda." Safeera ta shiga ɗaki ta kwanta sai kuma ya jawo waya ta kira layin Islaha na saudia. Tana ɗauka ta ce, "ki hau whatsapp, yanzu za a janye min ɗan katin nawa" tana faɗa ta kashe wayar. Ba jimawa sai ga kiran Islaha video call ya shigo, Safeera ta yi murmushi ta ɗauka tana kallon Islaha da take zaune kanta babu ɗankwali tana cin apple. Safeera ta ce, "Lallai matar nan kina huta, kin ga yadda ki ka ƙara kyau? Ga wani haske, anya larabawa baza su ƙwacewa Hamma ke ba?." Islaha ta yi dariya ta ce, "ke yanzu kina tunanin akwai halittar da zata iya kasa Hamma? Duk kuɗi da kyaun mutum bazai taɓa kaiwa matsayin Hamma ba" "Ban da cika baki dai, kar mu ga kin maƙalewa wani balaraben fa." "Wuce wannan wallahi, Hamma shine farko kuma shine ƙarshe." "Amma duk da haka kin yi kyau. Waye ya yi miki kitson kan ki?." "Ni na yi Safeera, ina yi ina kuka saboda sagewar hannu." "Kema waye ya kai ki, wannan tulin gashin naki mai yawa da tsaho ai tufke shi zai yi miki wahala." "In san in ina yanayin nan kaina in ba a haka yake ba damuna yake yi wallahi, hasken ma da ki ka ga na yi shine" ta faɗa dan bata so su dinga cewa ta yi haske, kar a ga kamar hutawa take yi, ita kuma ta san wahala take sha. Nana Haleema. [7/7, 6:26 PM] KRBBK: RDB2P44 Nana Haleema. _Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments ɗin ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link ɗin ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode ɗin baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L Safeera ta yi dariya tana kallon Islaha ta ce, "ashe period ki ke yi, to a kan wa ki ka sauke kwandon masifar da ki ka saba?." Ta ɗan yi dariya ta ce, "ni kaɗai na dinga ihu a kitchen, har sai dai mai gidan ya zo yana tambayar lafiya." Safeera ta yi dariya ta ce, "duk abinda period yake sakawa ban yarda da gaske bane sai a kan ki, in aka faɗa gani nake ƙarya ne, amma a kan ki na yarda. Ya yi spoiling mood ɗin ki, ya canja ki, ki sake komawa masifaffiya daman kuma itace, ya saka ki haske, ya saka ki ciwo, ki zama lazy, ki zama mai rigima......Kai Hamma zai yi fama, Wannan watan waye ya dinga rarrashin ki to?." "Dallah can ban sani ba. Kin san me?." "Sai kin faɗa." "yanzu na gama waya da Hamma, ya yafe min mun koma kamar da. Yana ta jaddda min kar na yi abinda zan bashi kunya, na cigaba da riƙe kaina kamar yadda na saba. Ya ce da zarar ya samu kuɗi zai biya su Mama kuɗin da suma kashe a kaina, zai siya min ticket na dawo. In ya so sai mu je a bawa wanda na ɗaukowa kuɗin haƙuri." Safeera ta ce, "Ke hankalin Baffa ya tashi, ga ciwo ga damuwa, Baffa harda hawaye akan ya ji kin bar ƙasar." "Allah sarki Baffa, yanzu zan kira Hamma na ce ya bani shi mu gaisa." "Yana sonki wallahi, yana jin ki kamar ƴar cikinsa. Kuma ya san duk gwagwarmayar kin yi ta ne saboda shi." Islaha ta ce, "ya cancanta ne, riƙe ni ya yi kamar ƴar da ya haifa, ya bani tarbiyya da ilimi." "Haka ne kam. Allah ya sa ki dawo nan da lokaci kaɗan. Kin san hankalin ƴan da toron guiwa ya tashi, ƴan commentse section sun buɗe wuta su in ba ke ba zasu daina bibiyar mu." Islaha ta yi siririyar dariya ta ce, "Yanzu Hamma ya bani labari. Ni ban ma duba ba." "Hankalin Chairman ya tashi, ya ce daga tafiyar ki zuwa yanzu an rasa followers masu yawa, ina ga in aka kwana biyu?. Don Allah shi dai na yi convencing ɗin ki ki dawo." Islaha ta sake yin dariya tana saka hularta ta ce, "na yi kewa sosai." Safeers ta ce, "ni sai nake ganin me zai hana baza ki ƙirƙiri wani program ba, ki samu topic ki dinga magana a kansa don wayar da hankali. In ya so sai ki yi amfani da sunan tv da kuma logon mu, ki yi video ki watsa. Hakan zai saka a cigaba da ganin fusksr ki, kuma baza a yi saurin mantawa dake ba." Islaha ta ce, "ina naga cikakken lokacin da zan yi?." "Za ki samu, kamar yanzu da ki ke zaune za ki iya saka camera a gaba ki ɗan wayar da hankali koda na minti biyar ne, yadda Allah ya saka miki kalaman hikima akan harshen ki yanzu za ki ga kin faɗi abu mai mahimmaci. Don Allah ki yi Islaha, rashin ganin ki zai iya taɓa carrier ki, in ana ganin ki akai akai baza a manta dake ba." Ta sauke nunfashi tana shafa fuskar ta ce, "zan yi shawara da Hamma, in ya bani dama zan yi Safeera." "To matar Hamma.." Islaha ta zuba mata ido ta ce, "Safeera meyasa har yanzu ba ki yi magana da Umma ba?." Ta kalli Islsha ta ga yadda ta mayar da fuska irin babu wasan nan. Safeera ta yi dariya ta ce, "to tsoron ki zan ji? Wannan haɗe fuskar na meye?." "Ki amsa min kawai." "Islaha Umma zubar damu tayi ta tafi wata ƙasar neman kuɗi, mahaifinmu ya sake ta saboda hakan, bata saduda ba ta girgije mu ta yi tafiyarta. Neman ta ɗin me zan yi?." Islaha ta ce, "Mahaifiyar ki ce fa, ko me ta yi miki bata cancanci ki watsar da ita haka ba. Ta damu da rashin magana dake, da mu ka yi waya sai jaddda min take yi don girman Allah na taimaka na saka ku yi magana. Safeera ki ajjiye wannan ciwon da ki ke ji a ranki, ki yi magana da ita, tana son jin muryar ki, don Allah ki yi magana da ita." "Islaha zafi nake ji a raina, in na tuna ta zaɓi duniya akan mu da mahaifin mu." "Ke kina da mahaifiyar da zata so ta ji maganar ki, ni kuwa bani da ita. Ban san kowa nawa ba, suna nan ko basa nan ban sani ba. Na tashi cikin marayu, na tashi cikin maraici, ban san kowa na sai Maman da ta raine mu a gidan. Wani lokacin ina ji kamar ina tuna mahaifiyata, amma sai naga kamar a mafarki ne ba gaskiya ba...." "Nima da da tana nan da ban zo inda nake yanzu ba, da tana tare da ban fuskanci ko wacce matsala ba balle har a ɗauke ni......Safeera! Dan ba ki san abinda nake ji bane a duk lokacin da nake jin kewar iyaye, ke ga ki kina tare dasu suna so ki yi magana amma kin ƙi." Ta share hawayen da ya zubo mata ta ce, "Safeera ki manta da Umma ta bar ku, ki yi magana da ita matsayin ki na ƴar cikinta." Safeera jikinta ya yi sanyi, tausayin Islaha ya mamaye nata zuciya. Ko sati uku bata yi babu mahaifiya ba, amma ita kaɗai ta san kewar ta da take ji a ranta. To ina ga Islaha da ta rabu da ta ta tun tana yarinya? Ta rayu tsahon shekaru babu ita, kuma bata san inda take ba, bata da tabbacin akwai wanzuwar mahaifiyar ta ta a duniya, wani lokacin tana jin abin a kamar a mafarki. Tabbas Islaha itace ta san meye kewar iyaye. Safeera ta ce, "zan yi, zan je wajan Maman Kausar ta bani lambar Umman ta saudia sai na kira ta." "Ko ke fa, Allah ya cigaba da bamu ikon jure jarabawar rayuwa." "Amin Bestie. Ina Labiba kuwa?." "Tunda na zo au ɗaya na ganta, na fita na ganta ita da wata mata sun hau taxi." "Lallai an samu duniya. Hanan tana nan itama tana cin karen ta babu babbaka, Mama kullum cikin saka mata albarka take yi." "ke baki san gasa suke yi akan kawo kuɗi ba? In wannan ta kawo dubu goma yau, gobe sai wata ta san hanyar da ta bi ta samo ashirin. Gasa suke yi akan nemo kuɗi ba ta hanyar halak ba." "Uwarsu ce ta ɗora su akan hakan ai, kuma ita wai gani take haka kawai mazan suke ɗaukar kuɗi su basu." Islaha ta taɓe baki ta ce, "Su suka sani dai, matsalar su ba tamu ba. Zainab fa? Tunda na tafi kun yi magana da ita kuwa? In na kira ta sai na ji wayar bata zuwa." "Wallahi ba mu yi magana ba har yanzu, Brr Suraj dai mun haɗu mun gaisa." "Don Allah ko za ki je ki duba min ita?." "Shikenan, zan je in Allah ya yarda. Ya batun binciken ki akan gidan?." "Shine na ce ki je ki ganar min ita ai, itace makamina." "To shikenan, zamu yi magana in Allah ya yarda." Daga haka suka yi sallama suka kashe wayar.     Lokacin da Baba ya dawo suka nuna masa duk abinda Maman Kausar ta yi. Baba ya girgiza kai ya ce, "Safeera ƙawar babar nan ta ku hidimar da take yi ta yi yawa sosai, kar na hana ta ga kama bana yabawa da kulawarta gare ku, amma ta ɗora kanta nauyin ku wanda Allah bai ɗora mata ba." "Wallahi nima haka na ce Baba, in na yi magana sai ta ce ai duk an zama ɗaya." Baba ya sauke nunfashi ya ce, "Allah ya saka mata da alkhairi." "Amin Baba." "Zan yi tafiya kwananan Safeera, ina ta tunanin inda zan bar ku. Gaskiya bazan bari ku zauna wajan Atika ba, hidimar zata yi mata yawa sosai." Safeera ta ce, "Ka je ka dawo Baba, zamu zauna a wajan nata, in ya so kafin tafiya ta gaba sai a ɗauki mataki." Ya kalli Safeera ya ce, "wanne mataki kenan?." Safeera ta sunkuyar da kai ta ce, "Baba kamar yadda Gwaggo ta ce, me zai hana baza ka auri Mamansu Kausar ɗin ba kawai?." Baba ya girgiza kai tana kallon ta ya ce, "ƙawar babar ki ce fa Safeera, kina ganin hakan ya dace?." "Baba ko Unma tana nan dan ka aure ta ai ba damuwa bane, kuma ko da auren tsakanin ka da Umma ba laifi bane balle babu auren. Kawai in dai akwai hali ka aure ta ɗin Baba, ka ga baka da fargaba in zaka yi tafiya, sannan itama zata dawo ƙarƙashinka, babu batun hidimar ta ta yi yawa." Baba ya sauke numfashi ya ce, "Shikenan Safeera, zan yi shawara akan hakan." Ta gyaɗa kai ta ce, "To Baba, sai anjima" ta faɗa tana tashi ta fita ya bita da kallo yana tunanin mafita akan hakan.      Hajiya Karima suna kan waya ita da Mama suna tattaunwa akan Islaha, Hajiya Karima ta ce, "Labiba ta ce min yarinya ta waye, har gidajen larabawa take shiga. Gidaje manya manya. Ke kin san yarinyar zata yi farin jini, ga kyau ga gashi." Mama ta ce, "ai na san za a rina, na san karuwanci kawai zata je tana tafkawa a gidajen larabawa wallahi." "To ki kwaɓi Saheer, babu shi babu ita koda zata dawo. Aure tsakaninsu a dakatar dashi babu batun yinsa. Baza mu zuba ido ya ɗauko mana ita a matsayin sirika ba, shine kaɗai namiji da ki ka mallaka, in ya kawo ta mun shiga uku." "Har sai kin faɗa ma, ai yadda ta tafi ɗin nan ta bar zuri'a ta har abada, daman ba so nake yi ba, zan amince ne saboda wani burina. To yanzu bazan amince ya auri ragowar larabawa ba wallahi." "Hakan shine ya kamata. Kar ki bashi fuskar da zai ce zai aure ta wallahi, ki rufe ido ki ce in ya aure ta sai kin tsine masa. Ke da ina da yarinya mace ma ai da Saheer ya yi mata, matsalar da aka samu bani da ita. Yanzu ba abin na yi hanyar yaran ƙawaeye ba, yarinya ta zo ta ƙoshi ta zama ƴar iska." Mama ta ce, "Bar ni dashi kawai Karima. Daman Iskaha ta ga babu Idon Saheer ba sai abinda Allah ya yi ba? Ni fa shiyasa na ji daɗi da ba a haɗa su gida ɗaya da Labiba ba, dan ɓata min yarinya zata yi wallahi." "Tsaf zata lalata ta wallahi, kin ga yanzu kowa ya san inda dare ya yi masa. Ke Alhaji Musa ya faɗa min wai Maimuna ta ce ita so take ta dawo, na sheƙe da da dariya na ce waye ya faɗa mata borno a gabas take." Mama ta ce, "Bata san ita da dawowa sai ta biya kuɗin nan cif ba, in ba haka ba ta wuce gidan yari." "Bar ƴar wahala, ta ɗauka zuwan ai sauƙi ne dashi. Ina zuwa" ta faɗa tana kashe wayar. A lokacin Saheer ya shigo, Mama ta bi sa da kallo ta ce, "yauwa zauna, ina neman ka daman." Ya zauna ta ce, "kana da labarin abinda budurwar ka take aikatawa a Jeddah?." Gabansa ya yanke ya faɗi, ya kalli Mama ya ce, "na me kenan?." "Na iskanci mana, Labiba ta faɗa min gida gida take bi na larabawa dan ta tara kuɗi. Ka ga sai ka cire ta daga ranka, dan wallahi bazan bari ka auri ragowar wasu ba." Saheer ya yi shiru ƙirjinsa yana bugawa sosai ya kasa cewa komai, dan bai san abinda zai cewa Mama ba, ya san duk abinda zai faɗa baza ta yarda ba, gwara ya yi shiru zai fi alkhairi. Mama ta ce, "ka saka a ranka babu kai babu Islaha, wallahi baza ka aure ta ba ka ji na ce wallahi!." Ya ɗago ya kalle ta jin ta rantse, suka haɗa ido ra ce, "Gwara tun wuri ka nemi wata, da in na faɗa maka na ce ƴar iska ce ai baka yarda, yanzu in ta dawo maka da cikin balarabe ai ka amince. Ka ji da kunnen ka, babu kai babu ita indai ina da rai da numfashi, zan ga da ni da ita waye ya fi mahimmaci a rayuwar ka!." Mama ta miƙe ta shiga ɗaki ta barsa da bugawar zuciya......... Nana Haleema. [7/8, 11:05 AM] KRBBK: RDB2P45 Nana Haleema. _Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments ɗin ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link ɗin ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode ɗin baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L •••••••• Islaha tana kashe wayar Saheer ya kira ta, ta yi murmushi sannan ta ɗauka ta ce, "yanzu nake shirin sake kiran ka Hamma." Ya yi murmushi ya ce, "gashi nima na kira ki." "Muna ta waya da Safeera ne. Ka san me ta ce?." Saheer ya ce, "sai kin faɗa." "Wai na yi creating content na dinga yi daga nan, saboda kar a manta da fuska ana ta, yan social media suna ta tambayar inda nake. Shine na ce mata Hamma ya faɗa min." Saheer ya ce, "Hakan shawara ce mai kyau, zai saka kowa ya san kina nan kuma zaki dawo in sha Allah." Islaha ta yi murnushin jin daɗi da farin ciki, Hamma yana bata goyan baya a duk wani abu na cigaba rayuwar ta, yana ƙara mata ƙarfin guiwa yi ko da bata so. Koda ta sare yana ƙarfafa mata guiwa har ta ji zata iya, ko da zata yi sanyi yana sakawa ta ji zata iya. A sanyaye ya ce, "Shine na ce mata sai na tambaye ka, in ka bar ni sai na yi." Ya yi ƴar dariya ya ce, "Ki yi Islaha. Ki samu topics masu kyau ki dinga tattaunawa a kai, hakan zai taimakawa aikin ki harda gidan tv ku." "To Hamma, zan yi tunani in sha Allah." "Allah ya taimaka." "Amin Hamma. Na gode da bayan goyan bayan ka, ko yaushe kana riƙo da hannuna ka kaini inda nake son zuwa." Ya murmusa yana sauke ajiyar zuciya sai ta ce, "ka san me? Na fara tara kuɗin nan fa." "Har nawa ki ka samu?." "riyal dubu bakwai, in ka yi converting kuɗin zuwa naira sun kai miliyan biyu da ɗari shida a yanzu." Saheer ya ce, "a ina ki ka same su? Ko albashin na ki ne?." "A'a ba albashi bane. Kasan akwai gidan da nake zuwa ina ɗan dafa musu tea na dawo, can ba zama nake yi ba, ina dai zuwa na ɗan yi na dawp asalin inda nake. Shine....shine matar gidan ta bani kuɗin" Ta samu kanta da ɓoye masa asalin wanda ya bata kuɗin. Ya ɗan yi shiru yana nazari, maganar Mama tana sake yi masa yawo a kansa, yana tuna yadda Mama tace tana yawo a gidanjen larabawa, amma bai bari tayi tasiri ba ya ce, "har gida nawa ki ke zuwa?." Ta ce, "nan ne fa kawai, shima kawai tea nake dafawa na fito. Matar gidan tana da kirki sosai, shiyasa ta yi min kyauta." Saheer ya ɗan kausasa murya ya ce, "Islaha!." Jin yadda ya kira ta sai ganbanta ya faɗi sosai ta ce, "Na'am Hamma." "Kin san ba son aikin nan nake yi ba ko?." "Na sani Hamma." "Na yarda kina zaune ne dan babu yadda zan yi, kuma tun farko ban san da maganar ba, da baza ki je ba." "na sani Hamma." Saheer ya ce, "meyasa ki ke zuwa wani gidan aiki bayan inda ki ke? Ke ba kalar yin aiki a gidan mutane bace, ke kalar hutu da kwanciyar hankali ce, sai dai azo a yi miki girki ba dai ke ki yi ba. Burina na aure ki na killace ki a gidana, fita ma sai naga dama za ki yi saboda kar wani ya ganar min ke. Yanzu magama ake ta bakya ƙasar gabaɗaya, kin yi nisa dani balle na zama inuwa a gare ki. Me ya kai ki aiki har gida biyu?." Calmly ta ce, "mai gidan da nake ne ya yi min magana akai, ni kuma da naga ina son tara kuɗin immediately shiyasa na amince. Kuma can ba aiki nake yi sosai, akwai cleaners da suke gyara gidan, kawai tea zan dafa da ɗan wani abun." Ya yi shiru bai ce komai ba, jin haka sai jikinta ya yi sanyi sosai a sanyaye ta ce, "ka yi haƙuri." Ya sauke numfashi ya ce, "dole na yi haƙuri, babu yadda zan yi. Ki cigaba da zama a Islahan da na sani, kar ki canja kin ji?." Kamar zata yi kuka ta ce, "Hamma ka fara zargina ne?" Ta faɗa hawaye yana sakko mata. Jin ta fara yi masa kuka sai ya tausasa murya ya ce, "Har abada bazan taɓa zargin ki ba Islaha, na yarda dake ɗari bisa ɗari, in ana yarda da mutum dubu bisa dubu ma na yi miki. Ina tsoron zaman ki a wajan da babu kowa na ki, kar wasu su canja miki tunani ki yi wani abun dan ki samu kuɗi da gaggawa." Muryar ta tana rawa ta ce, "ni bani da kowa ma, wacce nake tare da ita ko turanci bata iya ba sai larabci. Wallahi Hamma bazan taɓa aikata wani abu mara kyau ba, na san abinda nake yi, kuma na san haramcin hakan." Ya sanyaya murya ya ce, "Oh matar Hamma, meye na kukan, uhum!." "Kaine ka ke magana kamar kana zargin zan samo kuɗi ta wata hanya daban." "Don't deflecte my issue, kin san har abada bazan iya zargin ki ba. Wallahi na yarda dake, bana jin wani ɗar a raina dan bakya kusa dani. Ki daina kuka, kin ji matar hamma!." Ta goge ido cikin shagwaɓa ta ce, "to ba kai bane." Ya yi murmushi ya ce, "To na bari Matar Hamma, ki daina kuka kin ji?." Ta ɗaga kai kamar yana gabanta ta ce, "to na daina." Ya murmusa ya ce, "kin san meye?." A hankali ta ce, "A'a." "In sonki." Ta yi dariya harda rufe idonta kamar yana kallon ta. Shima ya yi dariya ya ce, "Kina ganin Labiba kuwa?." Ta girgiza kai ta ce, "sau ɗaya na taɓa ganinta, bayan nan ban kuma ganjnta ba. Kuma ni ba fita nake yi ba shiyasa." "Ki cigaba da zama a gida, kar wani balaraben ya ganar min ke ya ƙwace." Ta yi dariya ta ce, "shi ɗin banza, ai wannan Islahan ta Hamma, sai dai ya nemi wata. Ai babu halittar da zata iya rabu mu Hamma, in dai ina da rai ni mallakin ka ce. Muna tare daga nan har aljanna in sha Allah." Ya yi dariya ya ce, "Allah ya tabbatar matar Hamma. Zan je na gaishe da kawu." "Amin. Kace ina gaishe sa da kyau, kuma in ka shiga wajan Baffa ka haɗa mu don Allah." "In sha Allah, sai na dawo" daga nan suka yi sallama suka kashe. A lokacin ta miƙe tsaye ta naɗa mayafinta ta fita zuwa gidan Rehaan dan gabaɗaya bata je ba gashi har i'sha ta yi. Da sallama ta shiga falom kamar ko yaushe babu kowa, ta wuce kitchen ta ga cup ne kawai wanda bashi da kyau. Ta ɗauke ta wanke tana tunanin abinda ya kamata ta yi. Kamar wasa ta ji ana knocking ƙofar falon, da mamaki ta fito ta tsaya tana kallon falon dan ta san dai bashi bane, duk da sau biyu suka taɓa haɗuwa, amma tasan shi bazai yi knocking ƙofa ba, zai buɗe ya shigo ne kawai. Kamar mai jin tsoro ta kai hannu a hankali ta buɗe ƙofar, idonta ya faɗa kan wacce take tsaye. Alma ce a tsaye gajeriyar riga wacce bata wuce cinyar ta ba, ga rigar bata da hannu, sannan daga cikin ta a yanke take ana ganin cibiyar ta, sai handbag sannan da trolly bag, sai farin gashinta da ya sauka har baya. Bata cewa Islaha komai ba ta shiga falon, sannan ta kalli Islaha dan uniform ɗinta sun yi maya indecating matsayinta a gidan. Cikin english ta ta ce, "Dr is here?." Islaha ta bita da kallo tana mamakin wacece wannan kuma, sai ta ɗan taɓe baki kafin ta girgiza kai alamun baya nan. Alma ta ja jakarta ta hau sama ita kuma ta bita da kallo ta ce, "ikon Allah, wannan kuma daga ina oho." Ta koma kitchen ta cigaba da abinda take yi ta. Ba jimawa ta ji an shigo kitchen ɗin, Alma ta buɗe fridge ta ɗauki drink ta dawo falon tana sha. Islaha ta bita da kallo ganin ta canja kaya, yanzu riga da wando, wandon ya kai guiwa amma rigar bata kai ciki ba iyakacinta ƙirji. Ko ba a faɗa ba ta san baturiya ce, kamaninta gabaɗaya sun nuna yaren ta. Islaha ta taɓe baki ta cigaba da abinda take yi, sai ta fito falo dan ta ajjiye tea ɗin da ta gama dafawa a dining ɗin falon. A daidai lokacin ya shigo yana amsa waya, hannunsa yana cikin aljihu kamar yadda ya saba. Alma tana ganinsa ta miƙe tana kallonsa, shi kuma ya tsaya cak yana kallonta cikin mamaki da al'ajabi. Kafin ya gama mamaki ta ce, "Beb i missed you" ta faɗa tana nufarsa a guje ta faɗa jikinsa tana ɗafe sa tsaf. Islaha ta yi saurin ɗauke kai jin gabanta ya faɗi, ta kawar da kai gefe tana jin wani iri a ranta, sai kuma ta kuma kallonsu ta ji ya ɗan yi tsaki ya ce, "Alma what are you doing here?" ya faɗa yana cire ta daga jikinsa. Ita kuma ta kai masa kiss a bakinsa ya kauce ya ce, "why are you here?." Ta riƙe hannunsa ta ce, "i missed you my love, i'm here beacuse i wanted to see you." "Why you did not call me?." "Suprise." Ya ɗan sauke numfshi ya kalli Islaha suka haɗa ido sai ta ɗauke kai, ya ƙaraso inda take tsaye kamar zai magana sai ya fasa, bai ce komai ba ya wuce Islaha ya hau upstairs Alma ta bi bayansa. Nana Haleema. [7/8, 11:07 AM] KRBBK: RDB2P46 Nana Haleema. _Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments ɗin ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link ɗin ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode ɗin baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L •••••••••• "Alma!." Islaha ta maimaita tana binsu da kallo, ta girgiza kai ta ce, "shi kuma baturiya ce matarsa, baturiyar ma irin wannan...." Ta faɗa tana bin Alma da kallo har ta ɓace sannan ta ce, "Ji ƙirjinta ko abin kirki babu, gabaɗayan ta kamar an zana number. Ban taɓa ganin bature mai munin wannan ba, shi kuma ita ta yi masa, iko sai Allah. Ko ni da nake baƙa na fi ta kyau wallahi, ban da ma namiji meye abin so a wannan? Ko ni da nake mace bata burge ni ba, mtwww tirrr." Kafin ta bar wajan Alma ta sakko, ta kalli Islaha ta ce, "hey! Make something delicious to my Husband now." Islaha ta ce, "a matsayin ki na wa zaki bani umarni?." Alma cikin rashin fahimta ta ce, "you say?." Islaha ta ce, "ban sani ba. Ke ko shi mai gidan ba ya bani umarni sai abinda na ga dama nake yi, balle ke koɗaɗɗiya ruɓaɓɓiya, za ki zo ki ce ga abinda zan yi. In ki ka yi wasa sai na ɓallaki:" "I don't undersand, what are you saying?." "Sanin bakya fahimtar ne ya saka nake faɗa ai. Wai Alma, ke dama alif aka saka miki da ya fi dacewa dake, bazan yi ba" tana gama faɗa ta wuce kitchen tana ta mita ita kaɗai a ranta. "Duk iyayin nasa akan wannan ya ƙare, duk turawan da suke duniya wannan ce tafi masa?. Tirrr an yi asara babba, ban ga abin so a wannan doguwar ba."  (Ko ina ruwan Islaha🤔🤣). Macroni salad kawai ta yi, ta ɗora a tray da tea ɗin ta hau sama. Sai da tray ɗin ya kusa kubcewa daga hannunta, ganin Alma a zaune a jikinsa yana ƙoƙarin ta ɗagasa amma ta ƙi. Islaha ta ji takaici ya mamaye mata zuciya, haka kawai ta ji Alma bata yi mata ba kwata kwata, haushin Rehaan da take ji a ranta gabaɗaya ya koma kan Alma. Ta yi siririn tsaki tana takawa zuwa cikin falon, a lokacin ta ji ya ce, "Alma stop this nonsense!." Da sauri ta miƙe daga jikinsa, ya kalli Isalaha ya nuna mata bedroom alamun ta kai sama can. Ta juya tana takawa a hankali tana jin me Alma take cewa. "My love i missied you, i want to kiss you, please allow me." "You know i don't tolerate this nonsense right? Who invited you here?." A lokacin ta daina jin maganarsa, dan ba da ƙarfi yake magana ba, ta shiga bedroom ɗin ta ajjiye a kan table. Ta juyo zata fito ya shigo ya zauna akan kujera, har zata wuce ya ce, "help me with water." Ƙasa ƙasa ta ce, "in naƙi fa? Ka je koɗaɗɗiyar matar ka ta baka mana." Sai kuma ta nufi fridge ɗin ta ɗauko ra kawo masa. Ya buɗe ya sha ya ajjiye, ya yamusaha gashin kansa ya ce, "What the fuck!." Ta taɓe baki ta wuce ta sauka tana tsaki a ranta. Waya ya ɗauka ya kira Jafar, yana ɗauka ya ce, "kaine ka bawa Alma address ɗin gidan nan?." Jafar ya ce, "kawai sau na bata address ɗin gidan ka ko?." "To ta ya aka yi ta san gidan in ba kai ka faɗa mata ba? Bata taɓa zuwa Jeddah ba balle ace daman ta san gidan. Gata nan ta zo zata chaja min kai." "Malam ka daina yi min faɗa, ba budurwar ka bace, dan ta zo sai me? Na ga daman kuna zama kai da ita a london ko?." "This is not london, saudia ne." "Kai ka sani kuma, kai ka saba mata da hakan, da kana yin abinda nake cewa da hakan bai faru ba ai. Sai ka kore ta ko ta ta ya ka zama." Rehaan Ya dafe kansa cikin takaici ya kashe wayarsa. A lokacin Alma ta shigo ɗakin, ya lumshe ido ya buɗe, ya ɗago ido yana jifanta da wani irin kallo, kallon kaɗai ya saka ta tsaya cak bata ƙarasa ba, sai kuma ta koma sa baya ta fita bata ce komai ba. Ya ja tsaki ya ɗauki spoon zai ci macorni salad ɗin sai kuma ya fasa, ya yi fatali da tray ɗin ya kufe a wajan ya tsallake ya shiga bathroom.     Alma hankalin ta ya tashi, yadda ta so ya karɓe ta ya yi rawar jiki in ya ganta bai yi hakan ba. Ta fara zagaye ɗakin da ta yiwa kanta a gidan, cikin damuwa da neman mafita. Ko ba ya so a wannan lokacin sai ta yi abinda take so, zata yi masa video sannan kuma zata same shi. Wajan handbag ɗinta ta ƙarasa, ta ɗauko ɗauko wani tab tana kallon maganin. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "dole na yi amfani da wannan, na ga alama a london ya fi kirki, a nan bashi da kirki dole a haɗa da tab." Ta mayar da maganin ta zauna a gefen gado tana huci, bata so yin amfani da maganin wajan cimma burinta ba, so take ta same shi a hayyacinsa ba tare da ta bugar dashi ba, so take ta same shi cikin soyayya ba tare da wani abu ya taimaka mata ba. Amma ta ga alama ya zo da taurin kai, dole ta koya msa hankali. Washe gari Islaha da safe da ta farka bata je gidan ba, aikin gidan suka gama ita da Sunaira sannan ta yi nufin zuwa. Sai kuma ta tuna zata yi sabon content, ta yi creating topic da kanta ta ta saka hijjab ta zauna ta saka camera a gaba ta ɗan yi magana mai ɗauke da ilimi sannan ta yi posting. Tun kafin ta fira take ta ganin comments yana zuwa espacilly a tiktok da ig. Ta yi murmushi ta ta miƙe ta fita zuwa gidan Rehaan. Falon babu kamar ko yaushe, ta shiga kitchen sai kuma ta tuna da bowl ɗin jiya yana sama, ta san bai saulo dashi ba, ita kuma bata so sai ta gama zata fita ace ta je ta ɗauko wani abun, hakan ya saka ta hau sama. A hankali take takawa har ta ƙarasa ciki, falon babu kowa dan babu haske ma a falon sai kaɗan. Sai ta ja ta tsaya tana tunanin yana nan ko ba ya nan, duk da bata ga mota ba amma bata yi tunani ba ko bata nan. A hankali take tafiya har ta ƙarasa ɗakin ta murɗa handle ɗakin ta shiga da sallama, side ɗaya gadon yana yamutse alamun an kwanta a kai, dan ɗaya side ɗin yana nan normal ko pillow sa bai nuna alamun an kwanta ba. Ta kalli ƙasa ta ga macroni ɗin da ya ɓarar a kan carpet, ta kalli ko ina ta ga babu kowa alamun dai ba ya nan. Ta ja dogon tsaki ta ce, "ji wani abu don Allah, ji yadda ya zubar da abu akan carpet. Kwashe kayan zan yi shara ba aikina bans, ya je ya samu ya san abinda zai yi." Ta sunkuya ta ɗauko bowl ɗin, ta ɗauke tray da tea ɗin ta ajjiye. Tsaki ta yi tana ganin yadda salad ɗin duk ya bushe, ta harari wajan harda murguɗa baki. Kamar wasa ta ga an buɗe an shigo, ta ɗaga kai ta kalle sa suka haɗa ido ta ɗauke kai daga kallonsa. Shima ɗauke kai ɗin ya yi, ya wuce ya ɗauki wayarsa da take kan bedside. Islaha ta bisa da kallo ta ce, "aikin banza, ji wani abu kamar ƙaramin yaro, sai ka nemo wanda zai gyara maka wajen, ni dai bazan iya ba." Rehaan ya waiwayo ya kalle ta, ta maze kamar ba ita ta yi magana ba, dan ta san bai ji abinda take faɗa ba. Rehaan ya ce, "cleaner zasu gyara wajan." Ta harare sa ta ce, "ai ko baka ce ba, ni ba gyarawa zan yi ba wallahi, ai ba ƙaramin yaro bane ba kai." Shi dai bai tanka mata ba, ya ɗauki wayarsa ya fita. Itama downstairs ɗin ta sakko ta dafa tea, ta juye a mini kettle, wacce yake da mug guda huɗu madaidaita. A lokacin Alma ta shigo, ta bi Islaha da kallo kallo ta ce, "he is calling you." "Ubana ne yake kira na?." Alma bata ce komai ba dan ba ji tayi ba ta ja ta tsaya ita kuma Islaha ta fita. Islaha tana fita ta ɗauko tab ɗin ta ƙarasa gaban tea ɗin tana marmasawa a ciki. Daidai na Islaha ta dawo ta ga tana juya tea ɗin da tea spoon, ta tsaya cak tana kallon ta tana girgiza kai cikin mamaki. A hankalinIslaha ta ce, "kai! Me matar nan ta zuba a tea?." Ta yi shiru tana kallon Alma sannan ta ce, "in fa ya sha wani abun ya same shi ko ya mutu ni za a ɗorawa alhakkin hakan, ni za a kama a kulle ban ji ban gani ba. Dole na san abinda zan yi, bazai sha wannan tea ɗin ba wallahi." Tana ganin Alma ɗauke da tea ɗin, Islaha ta yi saurin hawa sama, gab da zata ƙarasa falon sa ta tsaya tana hangosa a zaune. Ta ƙarasa ta hau saman tana ganin Alma ta taho sai ta yi kamar zata koma ta sakka downstairs, sai da Alma tazo daidai da ita, Islaha ta bangaje ta tea ɗin ya zube a ƙasa, mug ɗin ya fashe. "Ouchhh! You burned me with the tea" Alma ta faɗa da ƙarfi wanda hakan ta ja hankalin Rehaan ya kalle su. Islaha a ruɗe kamar da gaske ta ce, "I'm sorry, it was an accident." "To hell with the accident! Can't you see how you burned me with the tea?." "I'm sorry Madam." Rehaan daman ciki yake da Alma, ya ƙaraso cikin fushi ya ce, "Alma Pack your things and leave Jeddah immediately!." Ta bi sa da kallon mamaki ta ce, "I'm Alma." "That's exactly why I told you to leave. I don't want to see you here." "I'm not going anywhere until you promise to marry me." "I'm not marrying you, i don't feel that way about you. You're just my schoolmate, stop this drama and leave Jeddah now!" "I'm not going anywhere!" Ta faɗa da ƙarfi tana tsallke tea ɗin sa ya zube ta wuce. Islaha ta bi Ray da kallo dan bata taɓa ji ya yi doguwar magana haka ba, gabanta ya faɗi tana tunanin daman wai ba matarsa ba ce ba ko me?. Ya kalli Islaha da take kallonsa ya ce, "go down." Bata motsa ba kallonsa take yi dan yadda yake magana cikin faɗa ya bata mamaki sosai. Ya buɗe idanunsa a kanta ya ce, "Ba ki ji me nace miki ba?." Islaha ta wani kalle sa jin da hausa ya yi magana, kuma hausar ta fita alamun ba koya yake yi ba ya iya, suna haɗa ido ya nuna mata stairs ya ce, "na ce ki sauka!" Ya faɗa yana kallon ta, wanda hakan ya saka numfashinta ya tsaya cak, ta buɗe ido tana kallonsa cike da mamakin yaren da ya yi magana. Rehaan yana jin ku duk rashin m din da kk yi masa🤣🤣🤣 [7/9, 11:24 AM] KRBBK: RDB2P47 Nana Haleema. Islaha ta tsaya cak tana kallonsa cikin mamakin da ya kusa kashe ta. Ta kasa matsawa daga inda take, ta tsaya cak ta zuba masa ido jin yana magana da yaren da take tunanin ba ya ji. Gabaɗaya bata ɗauka yana jin fulatanci ba balle hausa, kwata kwata bai yi kama dasu ba balle ta yi tunanin ya iya. A hankali ta ɗauke ido sdaga kansa, jikinta ya yi sanyi tana tuna irin maganar da ta dinga faɗa masa tun daga kan zaman Yola har nan ɗin. Riƙo hannunta ta ji ya yi ya ya jawo ta baya, sannan ta kalle sa ta ga yana nuna mata pieces ɗin mug ɗin da suke ƙasa, Islaha ta kalli wajen dan da tuni ta taka. Ya matsa daga wajan ya ce, "ki kawo min coffee." Ta gyaɗa kai ta sauka a sanyaye cikin yanayin sanyin jiki. Tana shiga kitchen ɗin ta tsaya tana mamaki, a bayyane ta ce, "daman yana jin yaren da nake ji? Wallahi na ɗauka bature ne kwata kwata ba ya jin fulatanci balle hausa. Gaskiya na kwafsa, ashe daman share ni kawai yake yi, ya ɗauke ni kamar mahaukaciya. Sai na ji kunya" ta faɗa tana dafe kai kafin ta ɗora ta yi making black coffee kamar yadda ya ce. Da ta gama ta hau saman bata same sa a falon ba, ta ƙarasa ɗakin ta ɗan yi knocking kaɗan ta ji ya ce, "yes." Ta tura a hankali ta gansa a zaune yana danna waya, ta ƙarasa ta ajjiye masa coffee ɗin. Bai kalle ta ba sai wayarsa da yake dannawa, dan ya rasa meyasa indai zai kalle ta to maganar Ubaid yake tunawa, wani lokacin har image ɗin su yake gani a idonsa, bai san meyasa ya damu haka ba, bai san meyasa in ya kalle ta yake jin haushi in ya tuna yarinyar Ubaid ce ba, mata nawa ya sani wanda Ubaid yake mu'amala dasu ba ya damuwa? Amma ita bai san dalilin da ya saka yake jin haushi ba, ko dan ƴar nigeria ce kuma ƴar yola oho, shiyasa ya yanke shawarar daina kallon ta. Ta juya zata koma ya ce, "serve." Ta dawo ta zuba tana hararar sa ƙasa ƙasa, bai ma san tana yi ba ta ajjiye ta juya ta fita. Inda glass ɗin nan ya fashe ta ƙarasa, ta ɗauki machine ɗin falon ta kwashe glass ɗin, ta goge tea ɗin da ya zube. Har zata bar wajan sai ta dinga jiyo kukan Alma daga room ɗin da yake wajen. Har zata wuce ɗakin sai ta dawo, dan ƙofar bata rufe da kyau ba. Islaha ta ji tana cewa, "Wata housemaid ce ta zubar da tea ɗin da na saka maganin, ba laifina bane, ban san ya zube ba." Sai Alma ta yi shiru sannna ta ce, "but in anjima kaɗan zan zuba masa powder, i promise, tognight he will be mine, sannan zan ɗauki video komai zan tura maka." Alma ta ce, "na gode, da dama ta ƙarshe" ta faɗa tana sauke wayar. Jikin Islaha a sanyaye ta bar wajan a hankali ta sauka downstairs tana tunani, ta zauna a kan dining ta yi shiru tana tuna abinda Alma ta ce. A bayyane ta ce, "video take so ta yi masa ko kuma turancin ne ban fahimta ba?." Ta sake yin shiru kafin ta ce, "i promise, tonight he will be mine....." ta ɗan sake tafiya tunani sannan ta ce, "Kenan mai zata sake ba shi? Na ji ɗazu yana cewa bazai aure ta ba, kenan ita tana so ya aure ta shi kuma ya ƙi." Ta ɗan daki kanta, tunawa bafa Hamma bane baturen da ya sace ta ne. Ta girgiza kai tana taɓe baki ta ce, "ina ruwana? Su kashe kansu mana, tare na gansu." Tana gama faɗa ta miƙe ta shiga kitchen, amma sai ta kasa yin komai tana tuna abinda Alma ta ce. Gashi dai ta gama abinda zata yi amma sai ta kasa barin gidan, har aka yi sallar la'asar tana kitchen a zaune tana duba yadda video ta yake ta trending ana ta zuba likes da comments. A hankali ta miƙe tana sauke numfashi ta ce, "Islaha ina ruwan ki ne? Duk abinda zata yi masa me ya dame ki?." Ta sake jan numfashi ta ce, "duk fa abinda ya faru cewa za a yi ni ce, gwara na je na hana kafin a ɗora min sharri." Da wannan tunanin ta koma upstairs ɗin, daidai lokacin da Alma ta wuce daga hanyar ɗakinsa tana murna tana cewa, "Yes ya shaƙa, zan jira wasu mintina" ta faɗa yana shiga bedroom. Jin hakan sai gaban Islaha ya faɗi, ta buɗe ido ta ce, "na shiga uku, ba dai ta kashe shi ba, ni fa da wuri nake burin barin ƙasar nan, ban shirya zaman prison ba wallahi." Da sauri Islaha ta ƙarasa ɗakinsa, ta same sa ya dafe kai da duka hannu biyu ya rufe ido ruf. Miƙewa ya yi ta ga yana layi kamar zai faɗi, daƙyar ya kai kansa gado ya kalli Islaha yana ganin ta guda biyu ya kasa banbance wacece, ya sake runtse iso ya ce, "Subahanallah!." Islaha ta yi sak tana kallonsa ta ce, "ashe fa ya san Allah." Ya kwanta da baya jin kansa yana barazanar watsewa,wani irin bacci ya ji yana fizgarsa idonsa sai rufewa yake yi, shi kuma ba ya son yin baccin amma ya kasa rinjayar maganin. A hakali idonsa ya rufe ruf dogon bacci ya ɗauke sa. Islaha ta bisa da kallo ganin baƙin gashinsa a baje a kan gadon idanunsa a rufe, ta ɗan ja baya dan bata san abinda ya kamata ta yi ba. A lokacin Alma ta shigo, Islaha tana daga gefe bata ganta ba.Ganinsa a haka sai ta yi dariya ta ce, "I am certain this moment is mine. I will have you, my love, nothing can stop me. And I will make sure to record every second of it" ta faɗa tana fara cire rigar jikinta, ya rage daga ita sai bra, ta sai ta wayar ta ajjiye daidai inda zata ɗauki komai da komai, har da light ta kunna yadda komai zai tafi yadda ya kamata, ta girgiza gashinta tana ƙarasa inda yake tana murmushi. Islaha da take nesa da ita gabanta ya faɗi, ta wara ido waje ganin ana niyar yin BF a gabanta. Ta runtse ido ta fito daga inda take, Alma da take niyar fara unbotton rigarsa ta kalli Islaha ta ce, "what are you doing here? Go out!." Islaha bata ce mata komai ba ta ƙarasa ta ɗauki wayar da ta ajjiye, Alma ta ƙaraso a guje amma kafin ta cimmata Islaha ta goge videon da ta fara ɗauka. Alma ta zo zata ƙwace wayar Islaha ta riƙe da ƙarfi, ita kanta bata san tana da ƙarfin iya riƙe Alma ba sai a lokacin, ta haska wayar a fuskar Alma ta cire face id, ta goge videon daga deleted recent ɗin wayar. Islaha cikin kakkausar murya ta ce, "get out, before i call the police." Ta bi Islaha da kallo ta ce, "who are you?." "I said get out!." Jin an kira police ya saka Alma karɓar wayarta ta ɗauki rigarta ta fita daga ɗakin. Islaha ta dafe kai ta ce, "ban yarda da gaske ana yiwa namiji fyaɗe ba sai yau, ji wannan motsatstsiyar don Allah." Sai kuma ta kalle sa da yake kwance ido a rufe yana bacci. Ta harare sa ta ce, "wallahi ba dan kai na yi ba, zuciyar musulunci ce ta saka na yi. Kuma ka burge ni ne, yadda ta dage akan ka ya nuna min baka sauraren ta......" sai kuma ta sake jan tsaki ta ce, "Ji sa don Allah, ya wani ba je yana bacci. Mtsw! Ragon maza kawai." Islaha falon ta koma ta zauna, a kan idonta Alma ta sauka da jaka da sauri ita dai bata ce mata komai ba. Islaha ta yi shiru tana tuna abinda ya faru kamar a mafarki, ta sake kallon ɗakin da yake ta ɗauke kai ta yi shiruu. Tana tana zaman jin daɗin a wajen har ta gaji, ta yi sabon content duk dan ta rage lokaci amma babu wani cigaba. Har aka yi i'sha tana gidan, sai bayan takwas ma dare sannan ta miƙe ta sauka ta fita daga gidan gabaɗaya. Ita kanta bata san me ya zaunar da ita ba, ta san dai ta zauna saboda kar Alma ta dawo, kar ta yi masa wani abun a ce itace.       •••••• Maman orphage ta bi zainab da kallo da take zaune kanta a sunkuye ta ce, "Zainab ni ban ga abin ɗaga hankali a nan ba, matar nan tana so ki je ki ɗan zauna mata kafin ki dawo, kuma kitso zaki yi mata ita da yaranta; to meyasa bakya son zuwa?." Zainab ta kalle ta ta ce, "Mama ni bana son zuwa, na fi son zama a nan kawai." Ta miƙe ta ƙaraso ta dafa kafaɗarta ta ce, "A nan me ki ke samu? In kin fita sana'ar me ki ke samu? Sana'ar kitson da baya wuce a baki ɗari biyu, ƙarshen kyautar a baki ɗari biyar, hajiyar gaske ce zata baki dubu ɗaya. Ta ya za ki tallafi rayuwar ki da wannan kuɗin da bai wuce na purewater ba?. Bakya ganin ƴan uwan ki yadda suke jin daɗi? Bakya sha'awar kema wata ran ace kece kamar su?. Manyan makarantu suke yi, ga wayoyi masu kyau da tsada a hannunsu. Meyasa baza ki amince kema ki samo na ki arzuƙin ba?." "Mama in na je aikin me zan yi musu da zasu bani kuɗin?." "sana'ar ki mana, da ita zaki samu arzuƙi." "To Mama zan duba na gani." Ta bita da kallo kamar ta tsinka mata mari, amma da yake lallaɓa ta take yi sai ta ce, "tunanin me zaki yi? Ni ce fa uwar ki, ba ki da wacce za ki yi shawara da ita kamar ni." Zainab ta ce, "zan nemi Adda Islaha." "Komai sai kin yi magana da Islaha? Ina ki ka ga Islahan da za ki yi shawara da ita?. Tana can ƙasar waje aiki, ta tafi ta tallafawa rayuwar ta tana can tana neman kuɗin ta, ke ta ɗora ki akan aƙidar da ba itace a ranta ba. Waccee Islaha a wajan ki? A nan gidan ku ka haɗu kawai, kuma gidan ya raba ku. Ke tana hana ki taimakom rayuwar ki ne , ita kuma tana taimakon ta ta rayuwar!." Ta faɗa a fusace tana kallon Zainab. Zainab ta yi shiru bata ce komai ba. Mama ta ja tsaki ta ce, "jeki ciki." Zainab ta miƙe ta fita ita kuma ta da ki table ta ce, "Ban san me matar nan ta gani a tare da Zainab da ta dage a kanta haka ba. Yarinyar nan zata iya saka min ciwon kai" ta faɗa tana ɗaukar waya. "Yarinyar nan Zainab taƙi ba da haɗin kai fa, ni tsoro nake ji kar maganar nan ta fita wallahi." "Har yanzu?." "yanzu ta bar nan, na ɗauka rashin Islaha zai saka ta ɗan shiga hankalinta, sai na ga sake ɓotsarewa ma take yi. Bana so maganar nan ta fita, dan haka a ƙyale zainab kawai." "Baza a ƙyale ta ba, za a samu mafitar da zata amince ko bata so." "Kar ta jawo mana matsala fa." "zan san abinda zan yi." Ta kashe wayar tana tsaki ta ce, "Wannan shegiyar Islahan ta zamar min damuwa wallahi." Zainab tana fita daga office ɗin fita ta yi ta nufi gidan su Safeera. Da sallama ta shiga tsakar gidan ta samu Safeera a zaune tana shan tea. Nana Haleema. [7/9, 11:24 AM] KRBBK: RDB2P48 Nana Haleema Ganin Zainab sai ta yi murmushi ta ce, "Zainab sannun ki da zuwa." Zainab ta yi murmushi ta ce, "Yauwa Adda Safeera, ina yini?." Safeera ta miƙe ta ce, "mu shiga ciki sai mu gaisa." Suka shiga falo Safeera ta ce, "ɗazu Islaha take yi min maganar ki, tana cewa kin zo kuwa." Zainab cikin damuwa da ruani ta ce, "Yaushe zata dawo Adda?." Safeera ta ce, "wallahi ban san rana ba, amma ta kusa in sha Allah." Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ina cikin damuwa ne Adda Safeera, an takura min akan dole sai na je wani gida wai na yi aiki, gabaɗaya ban yarda da matar ba, gani nake kamar akwai wata manufar da ake so a tura ni. Mama tana faɗa min zan samu kuɗi, zan samu abubuwan mure rayuwa a can. Ni na ga ji, komai sake lalalcewa yake yi. Ina jin tsoron kar a kaini inda za a lalata ni, gabaɗaya zuciya ta bata amincewa da gidan." Safeera ta yi shiru kafin ta ce, "kun taɓa magana da Islaha akan haka?." "Mun yi, har take faɗa in ance na je gidan na amince na je, sai na yi mata waya. Kinga yanzu bata nan, shiyasa hankalina bai kwanta da na je ɗin ba." Safeera ta girgiza kai ta ce, "Bata ce ki yi magana da Barr Suraj ba?." "Bata ce ba. Amma na yi recording maganar mu da Mama ta yau, zan tura miki sai ki tura mata. Ni bana samun ta a waya." "Eh ta whatsapp za ki dinga kiran ta, za ki same ta." Zainab ta ce, "akwai masu saka min ido sosai, gwara na tura miki sai ki tura mata zai fi." Safeera ta ce, "shikenan turo min, nima in kim turo sai ki yi delete for me saboda gudun kuskure." Zainab ta tura mata a lokacin, sannan ta ce, "don Allah ki faɗa mata ta dawo, itace garkuwa a gare ni." Safeera ta ce, "Itama ke ce a ranta, ko yaushe cikin maganar ki take, na tabbatar zata dawo ke dan ke Zainab. Ki cigaba da yi mata addu'a, Allah ya bata abinda ta je nema." "Amin Adda Safeera, ki gaishe ta." "Safeera ta ɗaga kai daga nan Zainab ta yi mata sallama ta tafi. Safeera ta yi ajiyar zuciya, sai yanzu take sake tabbatar da zargin Islaha gaskiya ne, amma a cikin waɗanda suke zagaye da Islaha akwai munafakin su Maman, waye ko wace shine basu sani ba.         •••••• "Kar ki ce min komai Alma, na ba ki yarda da amana amma kin kasa yin komai. Na jima ina biyan ki kuɗi amma kin kasa yi min abinda nake so. Daga yau na yi canceling duk wani abu da yake tsakanina dake, bazan sake ba ki aiki akan Ray ba." Alma murya tana rawa ta ce, "i try my best, wata housemaid ce ta ce ta kira min ƴam sanda, shiyasa na dawo amma ba wai dan ina son haka ba. Ka sake bani dama ta ƙarshe." "Lokacin ki ya ƙare, ki goge number ta, ki goge duk maganar da muka yi dake." Jin ya kashe wayar hankalin Alma ya tashi, ba ƙaramin kuɗi take samu da mutumin nan ba, yanzu da ya daina bata aiki ta shiga uku. A bayyane ta ce, "this housemaid! Sai na yi maganinta, sai na kashe ta, sai na tabbatar na yi mata abinda ba a taɓa yi mata irinsa ba." Ta girgiza kai ta ce, "zan koya mata darasi mai yawa, zan tabbatar mata da ni ba sa'ar wasan ta ba ce!. Zan yi mata abinda baza ta manta dani ba, zan yi mata abinda zata dinga tuna wacece Alma." ••••••• Rehaan bai farka ba sai azahar, ya miƙe zaune yana dafe kansa da ya yi masa nauyi mai girma, ya jima a haka a zaune sannan ya kalli agogo. Ganin lokaci sai ya tafi tunani, ƙarfe ɗaya na dare ko kuma ɗaya na rana shi bai gane ba. Sai da ya huta sosai, dan kansa ya yi nauyin da in ya miƙe zai iya faɗuwa, sai da ya jira kan ya saki sannan ya miƙe ya ɗaga labuble ya ga rana ce sosai. Ya firgita harda zaro ido waje, ya rufe bakinsa da hannayensa ya ce, "What! 1pm" ya faɗa yana juyowa yana kallon ɗakin. Lokacin da Alma ta shigo ya ce ta fita yake tunawa, sai ya tuna lokacin yamma ce ko sallar magrib ba a yi ba, ya tuna ta zuba masa powder a fuska daga nan bai sake buɗe ido ba, sai yanzu da ya buɗe ƙarfe ɗaya na rana. Gabansa ya yanke ya faɗi, tsoro da tashin hankali ya ziyarce sa, ya bi jikinsa da kallo ya ga yadda ya ke a jiyan haka yake a yanzu, babu alamun an yi undressing ɗinsa. Ya dafe kai yana so ya tuna abinda ya faru amma ya kasa, da hanzari ya motsa sai ya tsaya saboda yadda kansa ya yi nauyi haka jikinsa. Ya ƙarasa a hankali ya fito falon, falon shiru ko haske babu, ya shiga ɗakin da ya ke tunani a nan Alma ta zauna amma bata nan babu ko jakar ɗinta. "Oh my god!" Ya furta yana fita daga ɗakin, zai sauka dan down stairs ya ji kiran sallah. Da hanzari ya dawo tunawa da sallolin da suke kansa. Ya shiga banɗaki da hanzari, har zai yi alwala sai ya ja ya tsaya, ya buɗe ido yana kallon kansa cikin tunani. Bai san me Alma ta yi masa ba, bai san me ya faru a tsakaninsu ba, san ya tunda ya yi losing control Alma zata yi iya masa komai, dama kaɗan take nema ta far masa, burinta a duniya bai wuce ta same sa ba, kuma ya san zata aikata komai dan hakan. Yanzu kenan sai ya yi prepacatuon bath for that? Ya dafe kai dan ya sama confuse and lost, ban san me ya kamata ya yi ba. Saboda kokwanto haka ya yi wankan ya yi alwala, sai da ya yi drying kansa sannan ya fito ya yi sallolin da suke kansa. Sallar ma ba a nutse ya yi ta ba saboda tunani, ƙirjinsa bugawa yake yi ba tare da ya san dalili ba. Haka kawai yake jin kansa ya zama so corwing, fargaba ta mamaye sa sosai, ya rasa me yake damun zuciyarsa, a cushe take saboda bai san abinda aka yi masa ba. Allah ya taimake sa ya koma night duty, da bai san ya zai yi da ranar nan da ya yi skiping without reason ba. Walkin slowly ya fito falo, ya zauna ya dafe kai cikin damuwar da bai san daga ina take ba. Ya kira wayar Alma amma baya samun ta, ya dafe kansa ya yi shiru bai san me yake damunsa ba. A lokacin Islaha ta shigo falon, ta gansa shiru babu haske kamar ko yaushe. Kallon upstairs ɗin ta yi tana tunanin ko yana nan ko baya nan bata sani ba. Kitchen ɗin ta shiga yana nan kamar ko yaushe babu komai a cikinsa, ta dafa tea ɗin ta buɗe fridge ta ɗauki apple ta yi slicing ta a ƙaramin plate. Sai kuma ta ce, "shi ba ya cin abinci ne sai tea? Bai damu da a bashi abinci ba sai dai ya sha tea kawai?." Ta taɓe baki irin ina ruwan nan ɗin nan, sai ta yi tunanin jiya ta bar cup a sama, ta bar kayan a wajan dan bata ɗauka yana nan ba ta hau sama. Sai da ta je ƙarshe sannan ta ji maganar sa, dan a hankali yake magana sai da matso sosai sannan ta ji ya ce, "Ban sani ba, abinda na sani ta zuba min powder, daga nan ban san me ya faru ba. Ina jin tsoro, ban san me ta yi min ba." Tana jin magana daga waya ya ce, "Yarinyar nan bata da mutunci amma, kuma da ka tashi ba ga alamun an yi undressing ɗin ka ba?." "Ban ga komai ba, ni dai Im afaird Jafaar" ya furta a sanyaye yana lumshe ido. "Ni abinda nake tsoro kar mu je ta yi snapping nude ɗin ka." "Wannan shine abinda nake jin tsoro nima, ban san me zan yi yanzu ba, kaina ya kulle, na sama confuse and lost, ina jin kaina uncomfortable, kamar dai wani abu ya faru dani." "Kuma babu cctv a bedrom balle a ce ayi checking, amma akwai a falon ko?." "Kamar babu cameras a gidan nan." "Oh god!." "Help me please!." Jazy ya ce, "calm down, zamu san abinda ya kamata a yi in sha Allah." Ya girgiza kai ya ce, "Alma baza ta yi powdering ɗina ta bar ni ba, She knocked me out, I'm sure she did something bad to me. Ni saboda confusing sai da na yi perupacating bath sannan na yi sallah. Na rasa tunanina, na rasa me ya kamata na yi na ji daɗi." Jazy ya ɗan yi dariya ya ce, "Da yake haka abin yake da sauƙi daman, da ace wani abun ya faru a tsakanin ku za ka ga alama ko ya ya take. Abinda nake tunanin ta yi maka hoto ko video, amma ni bana tunanin wani abun ya faru a tsakanin ka da ita." Rehaan ya yi ajiyar zuciya bai ce komai ba cikin damuwa. Islaha da take tsaye sai take ji kamar ta faɗa masa gaskiyar abinda ya faru, yadda yake magana a sanyaye sai ya ɗan bata tausayi kaɗan, a haka ta ƙarasa ta yi sallama, ya juyo ya kalle ta ya amsa. Kamar zata yi magana sai ta fasa, maimakon ta yi abinda ta yi niya sai ta juya zata koma ƙasa. Camly ya ce, "Wait!." Ta tsaya ba tare da ta juyo ba, bai damu dan bata juyo ba ba ya ce, "have you ever seen Alma? Jiya ko yau baki ganta ba?." A hankali ta waiwayo suka haɗa ido ta ce, "i did not." Ya gyaɗa kai bai ce komai ba, ita kuma ta sauka bata sake magana ba. Sai ya bata tausayi sosai, yadda ya zama confuse ya saka ta ji kamar ta faɗa masa, amma sai ta share tana tuna shine ya sace ta baza ta faɗa masa ba. Tana komawa suka yi magana da Safeera akan zuwan Zainab. Hankalinta ya tashi musamman da ta ji recording ɗin. Har zata kira Brr Suraj sai ta fasa, tana tuna yadda aka goge hotuna a wayarta kwanakin baya, baza ta faɗa masa ba kar hakan ya kuma faruwa. Bata tsaya shawara ba ta kira shi ta whatsapp ya ɗauka, yana ɗauka ya ce, "Hajiya Islaha." Ta yi ƴar dariya ta ce, "Hamma Suraj ya aiki?." "Alhamdu lillah! Ina ki ka shiga kwana biyu? Wayar ki bata zuwa sam sam." "Na ɗan yi tafiya ne, kuma zan ɗan kwana biyu." "Zuwa ina kenan?." Ta ɗan yi jim sannan ta ce, "ina ƙasar Saudia, a garin Jeddah." "Lallai Islaha, shine ko a faɗa min? Ko a waya ki ce min zaki yi tafiya ki ka ƙi?." "Tafiyar ce ta zo bazata wallahi, shiyasa ban faɗa maka ba." "Allah ya taimaka." "Amin. Ina son magana dakai ne" ta faɗa tana katse maganar zuwan Jeddah. Suraj ya fahimta hakan ya saka ya ce, "ina jin ki." "zan tura maka wani recording yanzu, in ka ji sai mu yi magana." Ya amsa ta kashe wayar ta tura masa, sai da ta tabbatar ya gama ji sannan ta kira sa. Yana ɗauka ya ce, "na ji Islaha. Hakan yana nufin zargin ki gaskiya ne ko?." Ta sauke numfashi ta ce, "har yanzu bamu kama su red in hand ba, ka ga baza mu tabbatar ba. Shiyasa na tura maka ka ajjiye, kaga haka aka goge hotunan Hafsa a wayata, shiyasa zan tura maka kaima ka ajjiye min wanann." "Hakan ya yi kyau. Yaushe za ki dawo? In baki dawo an yi komai ba rayuwar Zainab zata iya lalacewa." "Shiyasa na tura maka, na san zaka yi komai ko bana nan. Don Allah Hamma ka bincika, ka tabbatar ka fitar da maganar nan ta je kunnen gwamnati, don Allah ka taimaka min." "Eslaha ai ko baki faɗa ba zan yi, nima a gidan na tashi, duk wani ɗan gidan ɗan uwana ne. Amma kin san sai an haɗa hujjoji masu ƙarfi kafin a kai ga tuhumar su." "Zan yi ƙoƙarin haɗa wani abun daga nan, sannan kaima ka taimaka min ka yi wani abun daga inda ka ke." "Baki da matsala, in sha Allah i will try my best." "Na gode Hamma, na gode sosai." "My pleasure. Kin wuce komai a wajena." "Sai na ji ka." Daga nan suka yi sallama ta kashe ta kira Hamma Saheer. Shima irin bayanin da ta yiwa Suraj ta yi masa, ta tura masa recording ɗin just for evidence, ta ce ya ajjiye ko da na wajen ta zai ɓata. Bayan sun gama waya ta yi shiru tana tunani, bata taɓa jin hankalinta ya yi gida ba sai yanzu, gabaɗaya zaman Jeddah ya fita daga ranta, hankalinta ya yi kan Zainab, tana so ta san asalin abinda yake faruwa.... Mu je zuwa🤭😂 [7/10, 11:05 AM] KRBBK: RDB2P49 Nana Haleema. Mamy da Mummy suna zaune a falo suna hira cikin raha da wasa da dariya kamar yadda suka saba. Mummy ta ce, "yaushe Rehaan zai dawo ne?." Mamy ta ɗan yi murmushi ta ce, "wani lokacin dawowar ta sa babu notice, sai dai kawai ki gan sa." Ta yi dariya ta ce, "Ya batun aurensa da Daada zata yi masa? Yana nan ko kuma an fasa?." Mamy ta taɓe baki ta ce, "Yana nan, babu batun fasawa. Kuma ko, wallahi dani dashi duk ba ma son auren nan, shi kansa Abban ba son yake yi ba, kawai dan babu yadda zai yi da mahaifiyarsa ne shiyasa. Amma kwata kwata babu mai goyan bayan auren nan." Mummy ta ce, "to wannan aure waye zai so shi? Aure ba a san mata ba ai dole baza a so ba. Amma wataƙila sai ki ga ya zama alkhairi." "ina wani alkhairi? Ni wallahi bana so, shi ba ya so, babansa ba ya so, ta ya zai zama alkhairi?." "Ba ki san me Allah ya ɓoye ba, wataƙila ta zama matar so a gare sa." "Bana wannan tunanin Mummy, Rehaan bazai taɓa son yarinyar da za a bashi ba. Saboda ya san bana so, shina kuma baya so ɗin. Mummy ta yi dariya ta ce, "To yanzu ya za a yi?." "Ba dan na ga idon ki ba ko, amma ni Ikram nake yi masa sha'awar ya aura. Na san halinta, itama ta san na sa, na san ba dan kuɗi ko ɗaukakar da yake da shi zata aure sa ba." Mummy ta yi murmushin jin daɗi, tana ganin kamar maganin damuwar Ikram ya zo. Mamy ta ce, "To kin san mutumin na ku, ya ƙi, wai shi kallon ƙanwa yake yi mata bazai iya aurenta ba. Ranar da zai tafi Jeddah sai da muka yi maganar, Amma Rehaan ya ce shi dai kallon Riyya yake yi mata, bazai iya auren ta ba. Mummy ta murmusa ta ce, "haka halinsu yake shi da Jafar, Jafar ɗin ma ai haka yace, amma daga baya ya canja, ya zo ya ce shi fa Riyya yake so, gashi kwanaki kaɗan ya rage." "Haka nace masa, sai cewa ya yi shi ya ga zai iya auren ƙanwarsa, amma shi bazai iya ba. Amma har cikin raina ina yi masa sha'awar auren Ikram sosai." Mumny ta yi murmushi cikin jin daɗi ta ce, "sai mu dinga addu'a, duk abinda ya kasance alkhairi Allah ya tabbatar mana. Itama wannan ɗin bamu sani ba ko tana da nata alkhairin." Mamy ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Haka ne. Amma ko ya aure ta akwai zaɓina da zai aura, ina so ya samu kwanciyar hankalin da ya rasa a cikin gidan nan. Kuma ni a ɓangarena ban amince da ko wacce yarinya kamar Ikram ba, akwai mata kala kala da ake kawo min na haɗasu, haka ɓangaren mahaifinsa da ƴaƴan abokansa, dana ƙawayena, dana ƴan uwa kamar sun gaji da yaransu." Mummy ta yi dariya ta ce, "ba gajiya suka yi da yaran ba, Rehaan ɗin ake kwaɗayin samu." "Akwai wata ƙawata da za ki ji su Ikram suna ce mata Ammi, matar former deputy gov of Adamawa state. Tana da ƴa mai suna Zuhra, age mate ɗin su Riyya ce, ko zata girmi su Riyya da kaɗan ne. Ammi ta dage akan a haɗa auren ta da Rehaan, har deputy gov sai da ya yiwa Abba maganar." Mummy ta ce, "shiyasa na faɗa miki, kwaɗayin Rehaan ɗin ake yi." Mummy ta girgiza kai ta ce, "Ni kuma bazan bada goyan baya ba, dan ina son wacce zata zauna dashi tsakani da Allah, ba dan yana da kuɗi ba." Mummy ta ce, "Allah ya zaɓa abinda ya fi zama allhairi." Ta amsa da amin suka cigaba da tatttaunawa, Mummy dai bata faɗa mata ƙudurin Ikram akan Rehaan ba, amma ta ji daɗin abinda Mamy ta ce, da alama haɗin zai iya yuwa nan gaba. Bayan Mummy ta tafi Mamy ta kira Jafar a waya, yana ɗauka ta ce, "Jafar ya aiki?." Daga cikin wayar ya ce, "Alhamdu lillah Mamy. Ina yini?." "Lafiya lau, kana lafiya?." "Lafiya lau." "Za ka shiga Jeddah wajan Rehaan ne?." "Yes Mamy, ina tunanin cikin week ɗin nan zan je in sha Allah." Mamy ta sauke nuɓfashi ta ce, "Jafar da gaske har yanzu babu macen da Rehaan yake so da aure? I mean so na aure?." Ya ɗan yi murmushi ya ce, "Gaskiya babu." Ta ce, "ka tabbatar?." "i'm very much sure Mamy." Ta sauke numfashi ta ce, "ina da wacce nake so na zaɓa masa, bana so ya ga kamar na takura masa ne, shiyasa na tambaye ka in akwai na sani kafin na kai ga furtawa." "Babu kowa Mamy, da akwai da zan sani, kuma zan faɗa miki. Sai dai akwai wata baturia Alma, ta dage sosai akan sai ta aure sa, yarinyar nan zata iya yi masa komai dan ta mallake sa." Mamy ta yi tsaki ta ce, "i'm here for him, ina faɗawa Allah ya basa kariya a ko yaushe, babu wata baturiya da zata yi tasiri a kansa in sha Allah." Jafar ya ce, "in sha Allah." "Mamy ta ce, "Jafar ina so Rehaan ya auri Ikram." Da mamaki ya ce, "Ikram Mamy! Which Ikram?." "Your junior sister." "Ikram!" Ya maimata cikin mamaki. Mamy ta ce, "ba na faɗa maka a matsayin ka na yayan Ikram ba, ina faɗa maka ne a matsayin ka  na abokin Rehaan kuma ɗan uwansa. Ina so ka yi convencing Rehaan akan Ikram, ka saka ya sota har ya amince da auren." Jafar ya ce, "Mamy ba ƙi bane, amma Rehaan bazai amince ba, ko yaushe a ƙanwarsa yake kallonta." Mamy ta ce, "munafurci ne fa, kaima haka ka dinga faɗa sai gashi Riyya she is your fiancés. Kuma kai dashi duk bakin ku ɗaya, abinda ɗaya ya yi shima ɗaya zai yi." Ya yi ƴar dariya ya ce, "Mamy a wannan ɓangaren Ray bazai hau layina ba, bashi da ra'ayin auren cousin sisters at all." "Ka saka shi ya yi ra'ayi. Ka san ba son auren nan na wajan Daada muke yi ba, kawai an fi ƙarfinmu ne. Dan haka nake so na haɗasa da wacce in ya aure ta zai zai samu peace of mind. Bana so Rehaan ya sha wahala bayan wacce yake sha a yanzu, ina so ya samu kwanciyar hankalin da ba ya samu in ya zo ƙasar nan. Kuma ni kaf garin nan ban ga wacce na yarda da ita kamar Ikram ba. Zata so shi tsakani da Allah, zata kula dashi, zata bashi duk wani abinda ya rasa a gidan nan. Shiyasa na kira ka dan ka taimaka min." Jafar ya sauke numfashi ya ce, "Shikenan Mamy, in sha Allah zan yi abinda zan iya. Amma ninety percent out of hundrend bazan amince ba, ten ɗin shine amincewarsa." Mamy ta ce, "ka dai gwada ɗin, na baka dama." Ya yi murmushi ya ce, "in sha Allah." Daga nan suka yi sallama Mamy ta kashe wayar. Mama tana zaune a falon Daada suna tattaunawa akan binciken da ta saka ta yi mata akan Islaha. Daada ta ce, "ina jin ki Saddiƙa, wanne bincike ki ka yi?" Mama ta gyara zama ta ce, "Daada akan yarinyar da Rehaan zai aura ne." Daada ta washe baki cikin jin daɗi ta ce, "to me aka gano?." Mama ta murmusa ta ce, "Ai Daada baza ki taɓa zaɓo abu mara kyau ba, Allah ya yi miki baiwar da ba kowa ya yiwa ita ba. A kan ido kawai, kina fahimtar abinda yake daidai da ba daidai ba." Daada ta washe baki jin an fasa mata kai, ta gyara zama ta ce, "ni fa a idon mutum ina gane munafuki, ina gane maƙaryaci da ɓarawo. Da za a ɗauke ni aikin ɗan sanda da na taimakawa aikin su sosai, ba sai an sha wahalar bincike ba, ina ganin idon mai laifi zan ce mai laifi ne wannan. Wannan baiwar tun yarinta, har nemo ni ake yi na nuna ɓarawo." Mama ta yi mata hararar ƙasan ido, amma a zahiri ta yi murmushi ta ce, "ko shakka bana yi akan hakan." "Ina jin ki, ya aka yi?." "Yariya ce mai kirki, ta sauke alkur'ani guda, sannan cikakkiyar ma'aikaciyar jarida ce. Gata da shigar mutumci, ga ta da hankali da girmama mutane. Sa....." kafin ta ƙarasa Daada ta dakatar da ita tana murmushi, tana hararo fuskar Islaha tana jin daɗi na mamaye ta. Daada ta ce, "ni shaida ce, in dai tarbiyya da girmama na gaba ne tana dashi wallahi. Yarinyar da ta ganni a akan titi ta tsaya, ta sauko ta riƙe ni ta kawo ni har nan. Ai a iya nan an nuna tsantsar girmama ɗan adam da sanin martabar na gaba." "Gaskiya tana da hankali, dan ma ance ta je ƙaro  ilimi." "Kai ma sha Allah! Ashe dai irinsa ce ƴar boko." "Irinsa ce kam Daada, kin ga itace daidai shi." "Ai bari kawai. Wannan aure kamar an yi sa an gama, babu wanda ya isa ya dakatar dashi." Mama ta ɗan yi jim sannan ta ce, "amma sai nake gani kamar babarsa baza ta bari ayi auren nan ba, dan bata so." Daada ta wani kalle ta ta ce, "a ƙarƙashin wa take?." Mama ta ce, "mai gidan." "Shi kuma a ƙarƙashin wa yake?." "Wajan ki Daada." Daada ta haɗe rai ta ce, "in ina magana ki daina saka min ita a lissafi. Wallahi Allah, kin ji na rantse ko? Babu wanda ya isa ya saka a fasa auren Ishlaya da Muhammad, ko mutuwa na yi sai an tabbatar dashi. Ko shi mijin nata bai isa ba balle ita kanta, dan haka ki ɗauka auren nan kamar rubutu ne a kan dutse." Mama ta murmusa cikin farin ciki ta ce, "har na ji daɗi, da na yi bincike akan yarinyar ba ki ji yadda ta shiga raina ba wallahi. Ta burge ni, ina son mace nutsatstsiya wacce za ki ji kowa yana yaba mata. Ance in ka mutu ma da shaidar bakin mutane mala'iku suke amfani. Shaida mai kyau ai rahama ce, tunda na ji yadda ake ta yabonta na ce wannan matar aure ce. Kuma daman na san Daada da kaifin basira, baza ki taɓa yi masa zaɓen tumin dare ba." Daada ta yi murmuahin jin daɗi ta ce, "wannan gaskiya ne Saddiƙa, shiyasa nake sonki, dan kin fi su fahimta da saurin gane haske. Yanzu ki je a cigaba da shiri, aure babu fashi. Ke kafin auren Juwairiyya da Jafar za a yi bikin nan nasu, tunda uwarsa ta fara nuna bata so tsaf zata saka matsafan ƙasarsu su tsafe auren a kasa aikata komai." "Da hakan ma ya fi Daada, dan komai zai iya faruwa wallahi." "Matsala ɗaya, ance bata ƙasar, kuma an ce babanta yana asibiti." "Gaskiya ne, amma da ta dawo ba sai ayi a wuce wajan ba." Daada ta ɗan yi jim ta ce, "zan san yadda zan yi. Jeki abin ki, na gode." Mama ta miƙe ta fita ta koma ɓangarenta. Tana shiga ta ɗauki waya ta saka a kunne ta ce, "auren nan bazai fasu ba, na gama da batun auren a yanzu." Wanda take magana dashi a wayar ya ce, "in kina hali da dama, za ki iya zuwa gida?." Mama ta ce, "yanzu kuwa Malam, in zuwa." Tana kashewa ta kira Abba ta faɗa masa zata fita, bai hanata ba, ta saka Saleem ya ɗauke ta a mota suka fita. Daman indai fitar wajan malamai ce Saleem ne yake kai ta ba driver ba, saboda tana buƙatar sirri, bata so a san inda zata je. *Madinah.* Umma tana ta murna an bata albashinta na wata a hannu, duk da babu abinda ta rasa a gudan amma ta ji daɗi sosai. Duk ta rame saboda wahala, Allah ya taimake ta tunda ta yiwa mai gidan barazana bai sake zuwa inda take ba sai shegen kallo kamar maye. Tana tsaye tana aiki sai ga kiran Hajiya Shafa ya shigo wayar ta, ta ɗauka ta saka a kunne ta ji me tace sai ta kashe wayar. Umma ta koma ɗaki ta saka hijjab ta fita zuwa ƙofar gidan, ta ga Hajiya Shafa da Alhaji Musa a tsaye. Umma ta ƙarasa ds fara'a ta ce, "barkan ku da zuwa." Alhaji Musa ya ce, "barka. Ina albashin?." Umma ta yi sak tana kallon su, kafin ta ce"Yana ciki, ɗazu aka bani." "Jeki ki ɗauko mu gani." Bata musa ba ta juya ba jimawa ta dawo dasu. Ya karɓa ya ga riyal ɗari bakwai ne, ya zari riyal ɗari biyar ya bata ɗari biyu ya ce, "wannan itace tamu ta kamfani, wannan kuma sune naki." Kafin Umma ta yi magana Hajiya Shafa ta ce, "bani riyal tamin ɗin da na ranta miki, ki ka siyi layin waya." Kafin Umma ta yi magana ta zare riyal ɗari a hannunta, ta canja ta bata riyal ashirin ta ce, "sai ki adana waɗannan." Umma a ɗan zaman da ta yi tana ɗan gane kuɗin ƙasar, tunda haka kawai yaran gidan zasu aike ta kuma dole sai ta je, ta haka take ɗan fahimtar kuɗin kaɗan kaɗan. Ta juya kuɗin a hannunta ta ce, "Daga riyal ɗari bakwai na dawo riyal ɗari ashirin, shine kuɗina?." Alhaji Musa ya ce, "shine naki mana." "Amma ni nake shan wahalar aikin nan, gwara Hajiya Shafa na san bashi ne na ci dole na biya ta. Ina laifin ku ɗauki riyar ɗari biyu ku bar ni da ɗari biyar ɗin? Ni nake shan wahala, kalli hannuna duk ya goge saboda yi musu wanki, duk da akwai injin wanki amma wani abun dole sai ka saka hannu ka wanke. Ta ya riyal ɗari da ashirin zata kai ni wata? Bakwa jin tausayina ne?." Nana Haleema. [7/10, 11:05 AM] KRBBK: RDB2P50 Nana Haleema. Alhaji Musa ya bita da harara ya ce, "ban gane ba ma tausyain ki ba? Tun farko ba an faɗa miki yadda tsarin yake ba? Me ki ke siya da za ki raina kuɗin hannun ki? Kim san naira nawa ne wannan?." "Duk da haka, na san da batun za a dinga rabawa uku, na ɗauki kashi ɗaya ku ɗauki biyu, amma cemin aka yi riyal dubu ɗaya da ɗari biyar za a bani, yanzu kuma na ga riyal ɗari bakwai, ko dubu bai kai ba." Hajiya Shafa ta riƙe baki ta ce, "Ke ɗin za a bawa riyar dubu ɗaya da ɗari biyar? Bakya jin turanci, babu larabci, ga ƙorafi, a haka za a baki wannan kuɗin?." Hajiya Shafa ta kuma cewa, "Kuma ƙarya suka yi miki, tun farko da aka ce ana neman ki ba dubu da ɗari biyar aka ce musu ba. Su ma na Jeddah da za a basu haka ne saboda yara ne, kuma suna jin turanci, kuma a gidan ma'aikata suke. Ke kuwa har yanzu zo bakya ganewa da larabci, a haka za a baki kuɗin da ki ka ambata?." Umma ta ce, "Amma ni ba haka suka faɗa min ba, dubu da ɗari biyar suka ce." "Roman baka ne, dan ki yarda ki zo kuma kin zo." Umma  ta yi shiru bata ce komai ba saboda takaici, Alhaji Musa ya ce, "saboda haka na zo a canjata tun a Yola, irin waɗnan matan buri ne dasu, gani suke in suka bar nigeria kamar kuɗi zasu yi, sun baro ƙasar su sun zo nan inda zasu yankewa talauci cibiya. Ki gode Allah, na rantse da Allah da riyar ɗari bakwan da aka baki sai kin kawo ta, ruwanki ne ki nemi kuɗin kashewa ta wata hanyar, ruwank ki zauna haka. Babu ɗaga ƙafa a lamarina, tunda ka ki ka amince sai abinda ki ka gani." Umma kamar zata yi kuka ta ce, "amma babu adalci a lamarin nan. A kuɗin nan zan si yi magani in bani da lafiya, ga abubuwan amfanin yau da kullum." "Ke ki ka san adalci, wani watan in Allah ya kaimu zan zo na karɓa, kuma dole ki bayar, in ba haka ba yan sanda su kama ki. Shaafa mu je." Umma tana gani suka tafi, ta koma jiki a sanyaye tana duba kuɗin. Ashe daman roman baka su Mama suka yi mata a harkar nan, ita bata ga jin daɗi da tara kuɗin da suke cewa zata yi ba, ina tara kuɗi tana fama da wahala kamar jaka? Kullum ana tula mata aiki kamar wata mara galihu. Kuma duk wannan aikin ace a iya kuɗin da zasu tsaya kenan?. Ta juya kuɗin kafin ta ajjiye, ta yi tagumi tana tuna ƴaƴanta da ta tsalleke ta baro saboda neman kuɗi, gashi kuɗin baza su taru yadda take tunani ba. *Jeddah.* Yadda suka je wajan Umma suka karɓa haka suka je wajan Islaha, ita bata musa ba ta bayar dan ta san daman haka aka ce. Labiba kuwa gabaɗaya ta ce su riƙe suka dinga yi mata godiya. Islaha bayan sun rabu, sabon content ta ɗauka ta gama editing ta yi sharing. Ta sauke numfashi, tana son komawa gida kuma tana son zuwa Madina ta ga Umma, haka kawai take so ta je ko dan amanar ƙawarta. Ta saka hijjab da niyar zuwa gidan Rehaan, kwana biyu ko ga je bata ganinsa, bata san ina yake zuwa ba, amma bata ganinsa kwata-kwata. Hakan yana yi mata daɗi, dan ita ganinsa ma fusata yake yi, sai ta dinga tuna abinda ya yi mata ta ji kamar ta zane sa. A haka ta shirya ta nufi gidan tana tafiya a hankali. Rehaan yana sama, suna zaune shi da Jafar da ya gama hutun gajiya yake hutawa a zaune. Rehaan ya ce, "sai yanzu ka ga damar zuwa, bayan na faɗa maka ina da abubuwan da zamu yi?." Jafar ya ce, "Malam yanzu na ga dama, kuma yanzu zan yi. Na shiga america ne, kuma ana snow mai ƙarfi, ko jirgi ba ya tashi, shiyasa na jima ban shigo ba." Ray ya taɓe baki bai ce komai ba, Jazy ya ce, "ya Alma? Kun yi magana bayan ta tafi?." Ya girgiza kai a sanyaye ya ce, "bata sake yi min magana ba, na kira ta sau ɗaya bata ɗauka ba, sai na watsar. Ka san bana kira sama da sau ɗaya, tunda bata ɗauka ba ta yi duk abinda ta ga dama." "Ya kamata ka kira ta." "Ƙyale ta, duk abinda zata yi ta yi kawai Jazy, in na saka damuwar nan a raina zan soiling mood ɗina a banza." Jazy ya yi murmushi ya ce, "tunawar babu amfani ka, tunda ba a san abinda ta riga ta aikata ba. Amma ni a jikina nake ji bata yi komai ba, maybe ta fasa ne." "Anya kuwa? Alma baza ta samu wannan damar ta ƙyale ba." "Gaskiya bana tunanin haka." Ya yi shiru bai ce komai ba, sai kuma Jazy ya gyara zmaa ya ce, "ina housemaid ɗin taka ne? Yunwa nake ji sosai, na zo daga America, ya kamata a sauke ni da arbian rice da grill chicken na ci." Ray ya yi masa banza baice komai ba, Jafar ya ce, "Kai ya batun auren ka ne? Ni fa wallahi bazai yu a ɗaga bikina saboda wannan gantallen auren naka da ko matar baka sani ba. In aka ce za a ƙara lokaci, wallahi ɗauke matata zan yi mu gudu, bazai yu a saka min ciwon kai ba." Nan ma ya yi masa banza bai ce komai ba, Jafar cikin tsokanar sa da son fusata shi ya ce, "kana shirin auren naka amma ko?." A fusace ya ce, "ina shirin haihuwa ba aure ba, ƙarewa ina shirin mutuwa!." Jazy ya ƙyalƙyale da dariya jin yadda ya fusata, daman kuma so yake ya fusata ɗin, ya kwana biyu bai ga ya fusata ba, ya ɗago ya kalle sa ya ce, "bani na kar zoman ba, rayata aka bani malam." "Kana sane ka ke yi min wannan wulaƙancin, ka san bana son maganar auren nan meyasa ka ke damuna da ita?. Ni bazan auri yarinyar da ban sani ba, sai dai Daada ta yi duk abinda zata yi." Jafar ya daina dariya ya ce, "na baka shawara?." Ya yi masa banza bai ce komai ba, Jafar ya ce, "ka ji matsalar ka, ina magana ka yi min shiru baka ce komai ba." Ya juyo ya kalle sa yana buɗe idanu waje ya ce, "ai kunne ne yake ji ko, i'm all ears." Jafar ya ce, "tunda baka son auren nan me zai hana baza ka kaiwa Daada matar da kake so ba, daman damuwarta akan baka yi auren bane, in ka kai mata matar aure ka ga shikenan sai a fasa da wancan." "Daadan nan ba ita ta haife ni ba, Babana ta haifa. Meyasa take son takura min? Ina ruwanta da ban yi aure ba?." "Da ruwanta mana, gani take kamar akwai abinda ka ke aikatawa a nan." "Ko ina aikawa ita ta aikata? Tunda na zauna a Englaand tsahon wannan lokaci ban lalace ba, bana tunanin akwai abinda zan gani da zai lalata ni. Jafar ya ɗan girgiza kai ya ce, "gaskiya dai babu, dan har biyan ka baturiya tace zata yi indai zaka yi sharing bed da ita, shiyasa wani lokacin nake tantama akan kana da lafiya? Anya kai ba     Asexual bane?." Wani banzan kallo ya yi masa mai cike ds harara, Jazy ya buɗe hannu ya ce, "tambaya ce kawai, ko irin canjawar yanayin nan bana gani a tare da kai, kuma ni na san ka saba ganin mata niked. A gabana kana zaune a sun chair a gaban beach, wata tazo ta kwanta a jikinka flat amma ka miƙe tsaf da kai." "Ka ji tsoron Allah Jafar, niked fa." "So meye banbancin? Wannan beach ɗin da ka nacewa kana zuwa kayan da suke sakawa dasu ba gwara babu ba? Bikini ce fa, to da bikini da babu ai gwara babu." "Hmm!" Shine abinda ya ce yana ɗaukar waya yana dubawa. Jafar ya ce, "tun daga lokacin na fara zargin anya kana da lafiya?." Ya ɗan murmusa ya ce, "har yanzu ban ga macen da zata burge ni bane, ka jira na samu, daga nan zaka tabbatar akwai lafiyar ko babu." "Kuma baka jin komai? Ka fi shekara talatin fa, har yanzu ko ɗan tsigar jiki baka ji?." Ya bisa da harara ya ce, "ɗan iska kawai, ƙanwata bata yi dacen miji ba." Jafar ya yi dariya sosai kafin ya ce, "let's be serious, Allah ka ɗauki shawara ta akan nemo matar auren nan." Rehaan ya ce, "babu wata Daada za tayi min dole, ai ba ni ta haifa ba balle ace sai na yi mata biyyayya ta dole. Laifin Abba ne, shine yake biye mata tana yi min abinda ta ga dama. Kamar ni ne kaɗai jikanta, in na lalace ɗin ina ruwanta? Bazan yi auren ba!." "Rehaan, kamar kai ace ka haifi ɗa, sai Mamy ta ce ga abinda zai yi, ya zaka ji in ya ce bazai yi ba?." Ya ɗaga kai ya kalle shi, Jafar ya ce, "shine misalin laifin Abba da ka ke gani, na tabbatar in wuta Mamy ta ce ɗanka ya faɗa sai ka riƙe hannunsa ka kaisa har gaban wutar ka saka shi, saboda kana son Mamy, kuma ta isa da kowa naka. To haka Abba ma, mahaifiyarsa ce." Rehaan ya yi shiru dan ya san gaskiya ya faɗa, Jafar ya ce, "ka daina faɗar haka, zai dinga jin babu daɗi a ransa. Yadda ka ke son Mamy haka yake sonta, Mamy haifarka ta yi, shima Daada haifarsa ta yi." Nan ma ya share bai ce komai ba sai kaɗa ƙafa da yake yi. Jay ya ce, "Meyasa baza ka nemi matar aure ba?." Ya ɗago ya kalle sa clamly ya ce, "a ina zan nema?." "Englaand, Jeddah, India, Nigeria. Babu inda zaka nemi aure ba a baka ba, ko balarabiya ce ƙarshen tsada a aure kenan, za ka iya da ita." Ya girgiza kai ya ce, "ka san baza ta bari na auri wani tribe in ba fulani ko hausa ba. Infact, bani da ra'ayin auren waɗannan da ka lissafa. I'm tired of the same faces and the same beauty I've always known. I want something different... something that makes my heart feel new again." "Ka nema a yola, akwai masu duhun fata irin wanda ka ke so. Black beauties, duk akwai a Yola da wajen Yola. Ƴaƴan masu kuɗi, ƴaƴan masu sarauta, duk wanda ka ke so a akwai." "See you, ni akwai wani kuɗi da zai buɗe min ido ne?." "Na san babu, amma kuma nasan baza ka auri low class ba ko? Dole zaka samo daidai kai, ko wacce ta fi ka. Ai zamanin auren ƴaƴan talakawa ya wuce, ƙwarya ta bi ƙwarya." Ya taɓe baki bai ce komai ba ya cigaba da abinda yake yi a waya. Jafar ya yi masa shiru shima, suka yi shiru dukkansu kusan minitina goma, kafin Rehaan ya yi breaking slince ɗin ya ce, "Jazy samun wacce zata aure ni saboda Allah zai yi wahala, shiyasa na bawa Mamy zaɓi, duk wacce ta ji a ranta tana so zan karɓa." "Ka san wacece zaɓin Mamy?." "Ikram. Kuma na faɗa mata ni bazan iya auren ƙanwata ba." Jafar ya yi murmushi ya ce, "Mamy ta kira ni akan hakan, ta ce na saka ka amince da auren Ikram." Ya wani kalle shi sannan ya ce, "a matsayin ka na wa kenan?...." Kafin Jafar ya basa amsa ya ce, "wai ka saka na amince, Mamy tana da abin dariya. A duniya akwai wanda zai saka na yi abinda bana so ne in ba ita ba? Kaine zaka saka na amince? Oh god!" Ya faɗa tana kallon Jafar da yake dariya. "Kaine ka raina mahimmacina, su kuma ƴan gida gani suke yi sai abinda nace maka ka ke yi, basu san taurin kan tsiya ne da kai." "Yes, ka sake maimaitawa, baka isa ka saka ni ba wallahi. Ka faɗawa Mamy, babu aure tsakanina da Ikram har abada, kamar yadda babu aure a tsakanina da Riyya, Banisha da Janan. Ni ba irin ka bane da zan je na auri ƙanwata. Ta ya zan iya auren ƙanwata?. I want my married life to be filled with love deep, endless love. A life full of romance, laughter, and unforgettable moments...." Jazy ya wani kalle sa, suka haɗa ido sannan ya ce, "soft nights, sweet words, and a home that feels like heaven. I want it to be beautiful, joyful, and a little bit lavish... the kind of love people only dream about. Kuma duk wannan tsarin da nake so na ɗora rayuwata a kai, sai na auri ƙanwata? Abin kunya, God forbid." Jafar ya ɗan yi murmushi bai ce komai ba, sai ya miƙe tsaye ya sauka zuwa ƙasa dan da gaske yunwa yake ji. Kitchen ya shiga ya ga babu komai, ya yi tsaki ya fito daga kitchen ɗin za fita daga falo kenan Islaha ta buɗe ƙofar zata shigo, ya ɗan ja baya ya bata hanya ta wuce, ita kuma ta ɗaga ido ta kalli fuskar sa suka haɗa ido.... Nana Haleema. [7/10, 6:47 PM] KRBBK: RDB2P51 Nana Haleema. Islaha ta zuba masa ido dan tsaf fuskarsa ta zo ƙwaƙwalwarta, ta gane shi sosai, ta ɗan ɗauke kai ta shiga falon shi kuma ya tsaya yana jira ta wuce. Sai da shiga falon sannan ta ce, "good evening." A kaikaice ya kalle ta bai amsa ba, yana binta da kallon up and down ya ce, "ke ce housemaaid ɗin?." Islaha ta ɗan ɗaga kai alamun eh, ya wani kalle ta ya ce, "sai yanzu ake zuwa aikin?." Ta ɗan kalle sa, zata yi magana ta ga yana yi mata wani kallo irin yaro da mai gidansa, sai ta fasa cewa komai. Shima bai sake bi ta kanta ba ya fita. Yana fita ta shiga kitchen ɗin slowly, sai da ta shiga sannan ta tsaya cike da mamaki ta ce, "Wannan ai Mr Jafar ne, wanda mu ka haɗu a diamon hotel...." Ta sake kallon bayanta sannan ta ce, "Me ya kawo sa nan? Shima ya san mai gidan kenan ko meye?." Sai kuma ta yi tsaki ta ce, "ɗan wulaƙanci, irin bai sanni ɗin nan ba, sai wani shan ƙhamshi yake yi. Amma a diamond hotel ba haka ya yi min ba, ya karɓi hannu biyu, suka gaisa da wasa da dariya. Amma yanzu kalle sa, sai wani jin kai yake y." Ta taɓe baki ta fara dafa tea, sai ta harari shayim ta ce, "sai son shayi kamar wani buzu." A sanyaye ta dafa tea ɗin ta ajjiye. Sai ta tafi tunanin abinda ya kamata ace ta dafa kuma, dan ta ga kamar mai gidan yana nan, ta rasa me zata yi duk basirar girkin nata ta ƙare. Ta so ma ta yi joining online classes saboda iyayin mutumin nan, amma sai ta fasa ta ga saboda shi baza ta yi asarar kuɗi ba. Tana nan tsaye Jafar ya shigo yana amsa waya, da fulfulde yana magana hakan ya saka take jin duk abinda yake faɗa. AirPod ne a kunnensa, wayar tana aljihu har ya gama ya yi shiru yana abinda ya kawo sa. Bai ce mata komai ba ya ɗauki plate ya juye abincin da ya shigo dashi, sai kuma ta ga ya ɗauko waya yana danne-danne sannan ya ce, "za ka ci abinci ne?." Bata ji amsar ba ta ga ya cigaba da abinda yake yi, ita dai tana tsaye tana kallonsa tana mamakin wannan rainin hankalin nasu. Shi wancan ya nuna bai gane ta ba, shima wannan ya nuna bai gane ta ba. Fridge ya buɗe ya ga babu apple, sai ta ga ya buɗe wata ƙofa da bata taɓa buɗewa ba. Buɗe iso ta yi ganin lafiyayyen garden mai ɗauke da bishiyoyi masu kyau da ƙhamshi. Ya shiga ciki bai jima ba ya dawo da basket na fresh apples green and red. Ya juye mata a sink gabaɗaya, ya kalle ta ya ga ba shi take kallo ba, ya nuna ɗan taɓa sink ɗin ya yi ƙara, ta kalle sa ya nuna mata apples ɗin alamun ta wanke. Ya ɗauki abincin har zai fita sai ya tsaya ya ce, "cups of tea" yana gama faɗa ya fita ya hau sama. Ta yi tsaki ta ce, "aikin banza, ni ba ƴar aiki bace ba wallahi, wata damuwa ce ta kawo ni nan, da ba ka isa ka yi min wannan wulaƙancin ba." Maimakon ta fara kai musu tea ɗin sai ta ƙi, ta fara wanke apple ɗin ta zuba a fridge ta ɗauki ɗaya tana ci. Sai da ta gama ci sanann ta ɗauki tea ɗin ta nufi saman. Jafar lokacin da ya hau yana zama ya ce, "wannan ce housemaid ɗin ta ka?." Rehaan ya kalle sa ya ce, "Housemaid ɗin Ubaid ce, ba tawa ba." Jafar ya fara cin abincinsa ya ce, "tunda dai kaima tana yi maka aiki housemaid ɗin ka ce." Bai ce masa komai ba ya cigaba da danna wayarsa, shi kuma yana cin abincinsa. Sallama ta yi a sanyaye tana takowa a hankali zuwa cikin falon, hijjab ɗinta har ƙasa, ta ajjiye tray ɗin tea ɗin babu wanda ya ce mata komai. Babu wanda ya yi magana hakan ya saka ta juya, ta sauka bata sake waiwayonsu ba. Jafar ya kalli Rehaan da ya fara cin abincin kamar ba ya so, ya ce, "ita wannan housemaid ɗin haka take? Bata zuwa da wuri, kuma haka ake aiki ba tare da gaisawa ba?." "Hakan ya fi min" ya faɗa yana cin abincinsa normal bai damu da abinda Jazy ya ce ba. Jafar bai ce komai ba shima ya cigaba da cin abinsa. Sai da suka gama gabaɗaya sannan Rehaan ya ce, "yaushe zaka shiga Madina?." Jafar ya ce, "nan da four days in sha Allah." "zan je." Jafar ya kalle sa ya ce, "za ka je umrah kenan?." Ya girgiza kai ya ce, "A'a, iya madina zan shiga na dawo." Jafar da mamaki ya ce, "meyasa? Ai ya kamata ka yi umrah ko dan matsalolin da suke gabanka." Ya ɗago iso ya ce, "wanne matsaloli kenan?." "Kai matsalolin ka har irguwa zasu yi? Ai suna da yawa sosai. Yana da kyau ka shiga ka yi addu'a ko dan ka sake firgita da maƙiyanka." Ya ɗan sauke numfashi ya ce, "zan je, amma ba yanzu ba. Iya madina zan je na dawo. Ina samun peace of mind in na shiga garin, hankalina yana kwanciya, duk wata damuwa tana gushewa." "Na sani, amma yana da kyau ka yi umrah." "Bazan shiga makka ba Jazy. In zan yi Umrah sai na cire gashin nan, ni kuma bana so." Da mamaki ya ce, "Kai yanzu saboda wannan tsinannen gashin sai ka fasa yin Umrah? Gashin banza da wofi.....mtsw! Daman gashin nan ya yi yawa, gashi kamar na mata, don Allah ka rage, ya yi yawa." "In anjima zan je na rage." "Amma ya kamata mu je mu yi tare. In muka shiga da madina da makka five days zamu yi, ba jimawa zamu yi ba." Ya ɗan sauke numfashi ya ce, "kai zan yi yanzu ba, ai ba dole bace ba ko?." Jafar ya ce, "kar ka yi." Ya ɗan yi murmushi bai ce komai ba. Jafar ya miƙe bai ce komai ba ya shiga ɗaki. Islaha ce ta dawo saman saboda ta ɗauke kayan, ta same sa shi kaɗai a zaune yana cigaba da danna wayarsa hankali a kwance. Ta yi sallama ya amsa ba tare da ta ji ba, ta ƙarasa tana kallon ɗan abincin da ya ci tana taɓe baki. Ƙasa ƙasa ta ce, "iyayin banza, ji wani cin abinci, shi lallai ɗan gayu." Ta ƙasan ido ya kalle ta, bai ce komai ba ta kwashe kayan, ya ɗan kalle ta ganin ta hijjab har ƙasa, ya taɓe baki yana tunanin abinda Ubaid ya faɗa masa akanta. Sai ya ja tsaki har ta kalle sa, bata ce komai ba ta sauka. Tana sauka ya bi bayanta da kallo ya ce, "a haka kamar ta kirki, ji hijjab har ƙasa. Mtsw!" Ya faɗa yana tashi ya shiga ɗakinsa. Islaha lokacin da ta koma matar Maleek ta dawo ranar, suna zaune ta same su a falo ta jingina da jikinsa yana wasa da gashin kanta, sai yaro guda ɗaya wanda bai fi three years ba yana ta tsalle daga gefe. Tana shiga matar ta kalle ta, Maleek ya ce, "Meet Islaha, our new housemaid." Ta ɗan gyaɗa tana kallon Islaha sannan ta ce, "sannu Islaha." Islaha ta yi murmushi ta ce, "Yauwa." Maleek ya ce, "Islaha she's my wife, Maryam, and my son Muhammad." Ta ɗan yi murmushi tana kallonsu cikin burgewa. Ta wuce ciki tana waiwayonsu dan sun burge ta sosai ma kuwa. Sai yamma sannan Maryam ta kira Islaha, ta fito daidai lolacin da take fesa airfreshner spary. Islaha tana fitowa ƙhamshin da iskar spar ɗin ya shiga hancinta, gas ɗin ya dake ta sosai, sai ta ja numfashi, ta yi baya da sauri tana nemawa kanta mafita, dan lokaci ɗaya numfashin ya sarƙe ta. Cikin lokaci kaɗan ta gigice, numfashinta ya fara fita sama sama yaƙi sauka, hawaye ya fara sauka daga idanunta, idanaunta su ka yi ja sosai saboda rashin fitar numfashi. Maryam ta ruɗe, hankalinta ya tashi ta sa ki spray ɗin ta riƙe Islaha cikin gigicewa. Islaha tuni ta kai ƙasa saboda rashin numfashi, Maryam ta fara ƙwalawa mijinta kira ba shiri ya fito. Yana ƙarasoqa cikin kuka ta ce, "ka ga abinda ta ke yi, ban san me ya same ta ba." Ya ƙaraso wajan yana ganin yadda numfashin Islaha yake yi kamar zai bar jikinta. Maryam ta ce, "tana da Asthma ne?." "Yes tana da ita. Ɗauko standfan." Da sauri ta juya ta ɗauko aka kunna kusa da Islaha daga baya dan a samu turaren ya wuce. Ita dai daƙyar take sauke numfashi cikin wahala, Sunaira ta kawo mata ruwa mara sanyi. Sai a lokacin ya kalli Sunaira ya ce, "tana da inhaler?." "Ban sani ba" ta faɗa a sanyaye cikin tausayin Islaha. Daƙyar aka samu numfashinta ya ɗan dawo daidai, fuskarta ta yi kaca-kaca da hawaye, ido ya yi ja sosai. Maryam ganin tana sauke numfahsi ta bata ruwa ta ce, "ki sha." Da kanta ta ɗan bata ruwan ta sha. Ta saka tissue ta goge mata hawayen idanunta. Maleek da yake tsaye ya ce, "sannu Islaha." Ta ɗaga kai a hankali tana jan numfashi a hankali. Ga ja hular kanta da aka cire mata ta mayar ta rufe gashinta. Maleek ya ce, "kina amfani da inhaler ne?." Ta girgiza kai ya ce, "meyasa?." Bata iya magana ba matarsa ta ce, "a kaita asibiti kawai, ku je asibiti a duba ta." Bai yi dogon nazari ba ya kira wayar Rehaan bai ɗauka ba, sai ya kira Ubaid, yana ɗauka ya ce, "kana asibiti? Ina da mara lafiyar da zan kawo maka..." Maleek ya ɗan yi shiru alamun ana bashi amsa, sannan ya ce, "Okay i'm coming" ya faɗa yana kashe wayar ya kalli Islaha ya ce, "zamu je asibiti a duba ki, tashi mu je da sauri." Nana Haleema. [7/10, 6:47 PM] KRBBK: RDB2P52 Nana Haleema. Sunaira ce ta ɗauko mata mayafi ta yafa akan hular kanta, ga sabon kitson da ta yiwa kanta ya sauka ta gaba, har ta cikin mayafin ana hangowa. Har bakin mota Maryam ta raka su sannan ta juya ta koma dan ta tsorata da yanayin Islaha. Rashin facemask ya saka ta toshe hanci da mayafinta, ya ɗan kalle ta ya ce, "seat belt." Sai a lokacin ta tuna ashe fa ba Nigeria ba ce, ta jaqo a sanyaye ta saka sannan ya ja motar. Ta yi shiru, shi kuma kallon gefen ido yake yi mata, musamman gashinta da yake a naɗe ya sauka har ƙasa. Ya ɗan juyo ya ce, "akwai abinda ki ke so?." Ta girgiza kai dan har lokacin bata dawo nutsuwar ta ba. Kallon titin Jeddah take yi yadda komai yake tafoya cikin tsari, ko kai kaɗai akan titin im street danger ta tsayar da kai sai ka tsaya saboda bin doka, babu wrong drivring, babu guje guje na wuce ƙa'ida. Rage ac ya yi ganin kamar tana damunta, a haka sauke tafiya har suka iso asibitin. Kallon asibitim yake yi ganin yanayin tsarinsa da kyau da yake dashi, ta ɗan gyaɗa kai tana bin ko ina da kallo, kai ba sai ance maka ba a Nigeria ka ke ba. Yana tsayar da motar ya ce, "let's go." Ta buɗe a hankali ta fito, shima ya fito suka shiga ciki. Sai da ya yiwa Ubaid waya ya faɗa mada abinda zai yi, ya ƙarasa reception, aka shiga da ita wani ɗaki aka duba yanayi jikin marasa lafiya, aka saka mata nebulizer domin daidaitar numfashinta, aka duba lafiyarta sannan suka wuce office ɗin. Sai da suka zauna, already daga inda aka yi mata checkup an tura sunanta zuwa office ɗin likita, suna zuwa suka zauna har aka kira ta suka shiga gabaɗaya. Yana shiga suka ga Ubaid a zaune a table ɗin fuba marasa lafiya, cikin larabci suka gaisa da Maleek, sannan ya nuna islaha ya ce, "itace mara lafiyar, kamar dai tana da asthma." Ya kalli Islaha, duk da ya san sunanta tunda an turo masa amma sai ya ce, "What is your name?." Islaha a hankali ta ce, "Islaha Muhammad Maddibo." Ya ɗan bita da kallo ya ce, "your age." Ta faɗa masa ya shigar a computer sannan ya ce, "meye yake damun ki?." Islaha a sanyaye ba tare da ta buɗe hancinta ba ta cw, "ina wahalar numfashi in na shaƙi iska ko turare ko gas da hayaƙi. Ina shan wahala in na yi tafiya mai nisa, sannan ina yawan tari da ciwon ƙirji." Ya gyaɗa kai yana shigarwar sannan ya ce, "kina da asthama kafin yanzu?" Ta girgiza kai alamun a'a, ya ce, "kin taɓa yin gwaji akan hakan?." "Eh, na yi." "Yana ina?." "Yana Nigeria." Ya bita da wani irin kallo ya ce, "you are from nigeria?." Ta ɗaga kai alamun eh, shi kuma ya ce, "wow!." Maleek aka kira sa a waya ya tashi ya fita ya bar su. Ubaid ya ce, "Which country in Nigeria?." "Adamawa." Ya ɗaga kai kawai bai ce komai ba, a lokacin Ubaid ya ce, "za a yi miki spirometry test for that, ki je lab zasu yi miki." Islaha ta miƙe suna bin arrow ɗin asibitin har lab ɗin. Ita dai islaha kallon ikon Allah take yi, asibitin tsarinsa ya yi iri ɗaya da asibitin da Baffa ya kwanta, kusan komai iri ɗaya ne, Tana zuwa lab tana faɗar sunan ta ta ga har an basu details ɗinta tun kafin ta zo. Nan da nan aka yi mata test ɗin, aka ce ta jira result ya fito. Bata jima sosai ba aka sake tura su Office ɗin Ubaid, saboda an tura masa sakamakon. Suna shiga ya duba ya kalli Islaha ya ce, "Asthma ta rabu kaso uku, akwai mild persisten asthma, itace mafi ƙanƙanta a ciki, itace wacce bata yi ƙarfi sosai ba. Akwai moderate persisten asthma, matsakaiciya kenan, wacce ta fara ƙarfi a jikin mutum, ta fi mild ƙarfi, amma bata kai matakin ƙarshe ba. Last one ɗin itace severe persisten asthma, itace stage ɗin ƙarshe a Asthma. In asthma ta kai severe, ta kai ƙarshe a matakin asthma, babu wata a gaba sai ita kaɗai." "Akwai allergic and non allergic asthma. Allergic one ɗin itace wacce take tashi in aka shiga ƙura, danshi bango, ko shaƙar wani abu kamar ƙhamshin furannci, wasu ko wani abin suka ci yana iya tayar musu da allergic asthma. Ƙaiƙayin ido, hanci, kunne, maƙogwaro, cunkushewar ƙirji. Amma ita allergic mafi yawan lokaci, tari ko mura sun fi tayar da ita." "Non allergic itace wacce take tashi ta hanyar hayaƙi, motsa jiki, gajiya, sanyi, ƙura mai tsanani, zafi mai tsanani, damuwa, tsoro mai firgitarwa, gas da sauran abubuwa." Ya ɗan sauke numfashi ya kalli Islaha ya ce, "Islaha ta ki tana mild presisten ne, ƙarama ce bata yi ƙarfi a jikin ki sosai ba. Amma in ba ki kula da abubuwan da suke sakawa ki samu attack ba zata koma moderate presisten, daga nan ta tafi severe presisten. Ki gu ji shiga hayaƙi, ƙura, sanyi, gas, zafi mai tsanani. In ki ka gujewa wannan, a za ki yi controlling asthma ɗin ki ba tare da controller inhaler ba. Abu kaɗan yana iya tayar da Asthma, sai kin kula sosai, wani lokacin abinda ka raina shine yake sakawa ka samu attack." Islaha ta ɗaga kai tana fahimtar maganar sa sosai. Ya ɗan yi rubutu sannan ya yi mata printing test. Ya kalle ta ya ce, "ku je pharmacy ku karɓi magani. Akwai reliever inhaler, zata dinga taimaka miki a lokacin da ki ka samu attack. Bakya buƙatar controller one, saboda bata yi ƙarfi sosai a jikin ki ba." "Thank you Dr." "My pleasure." Malek ya ce, "yanzu zaka koma gida?." Ubaid ya ce, "she's my last patient." Maleek ya ce, "thank god! Ku je da ita, she's my housemaid." Ubaid ya zaro ido ya ce, "housemaid!" ya maimaita yana kallon Islaha da kanta yake ƙasa. Maleek ya ɗaga kai ya ce, "take care of her, i'm coming" ya faɗa yana fita. Ubaid ya bita da kallo, kalar ta ta ɗauki hankalinsa sosai, yadda ta kalli ƙasa bata kallonsa, eyelashes ɗinta sun kwanta a ƙasan fuskar ta, ga wata kyakykyawan eyebrow da take cikakkiya baƙa wuluk. Ga bakinta yana moving a hankali, dan ta cire mayafin a fuskarta. Gashinta ya sauka har bayanta, ana iya ganowa dan mayafin kawai ta yi. Jin shirun ya yi yawa sai ta ɗago kai suka haɗa ido, ya ɗan yi murmushi ya ce, "Mu je phamarcy." Ta miƙe a sanyaye, shima ya miƙe suka fita tare zuwa phmarcy. Ya karɓo ya rubuta dust sannan ya koma office ya rufe komai suka fita. Har bakin mota suka ƙarasa, ya buɗe mata gaba ya ce, "bismillah." Ta shiga shima ya shiga ya ja motar suka fita. Sai da suka ɗan yi nisa sannan ya ce, "so you are from nigeria?." Ta ɗaga kai ya ce, "Wow! Amma kina da kyau Islaha, ban taɓa ganin ƴar nigeria mai kyaun ki ba." Ta ɗan murmusa bata ce komai ba suka cigaba da tafiya. Suka cigaba da tafiya yana ta janta da hira ita dai taƙi sakewa yadda ta kamata. A ƙofar gidan Maleek ya tsaya, ya kalle ta ya ce, "Yaushe za ki kawo mana ziyara? Wannan shine gidana, can i have your digit?." Ta ɗan sauke numfashi ta ce, "Dr my medicine, please." Ya ɗan yatsine fuska ya ce, "sorry my lady.." Ya faɗa yana nuna mata yadda inhaler ɗin take. Ta karɓa ta saka takardar gwajin a ciki ta ce, "thank you." "my pleasure, ki kula da abinda na faɗa miki saboda samun attack, har turare mai ƙarfi ki daina sakawa. In ki ka bi doka a hankali wani abun zai ragu." Ta ɗan gyɗa kai za ta buɗe motar amma ta ji a rufe, ta ɗan kalle sa ta ga ya zuba mata ido yana murmushi, sai ta ga ya fita da kansa ya buɗe mata, ta fito tana kallonsa ta ce, "thanks." Ya yi murmushi yana kai hannunsa kumatunta ya shafa, abin ya zo mata bazata, sai hannunsa kawai ta ji bata san zai yi ba, sai ji ta yi ya ja kumatunta. Rehaan yana tsaye a balcony yana kallonsu, tun tsayuwar motar ya san Ubaid ne a ciki, dan su larabawa duk kuɗinsu canje-canje mota, mota ɗaya suke amfani da ita ko yaushe, duk kuɗin balarabe da mota ɗaya aka san shi. Kuma da yake motar larabawa babu baƙin glass, yana iya hango akwai mace a ciki. A bayyane ya ce, "Ubaid! Allah ya shirya ka." Yana tsaye yana kallon su, haka kawai yake so ya ga wacece zata fito daga motar. A kan idonsa ya fito ya buɗe mata motar, tana fitowa ya ja dogon tsakin da bai san dalilinsa ba. Ya miƙe tsaye sosai yana sake buɗe idanunsa a kanta ya ce, "Oh god!" Ya furta lokacin da yake jan kumatunta yana murmushi. Bai san ya ja tsaki ba sai sautinsa ya ji a kunnensa, ya ɗan ɗauke kai har yana rufe idanunsa, yana ɗan gyaɗa kai yana cewa, "a haka kamar mai hankali." Lokacin da ya juyo bai ga gidan da Islaha ta shiga ba, ya ga dai bata nan. Ya taɓe baki ya ce, "dole na dakatar da ita daga zuwa gidan nan, bana son shirme." Jafar da ya zo wajen ya ce, "kai kuma kai da wa?. Sai magana ka ke yi kai kaɗai." Bai san ya sake yin tsaki ba, ya raɓa Jazy ya wuce cikin jin haushinta, haka kawai ya ji haushinta yana mamaye masa zuciya, bai san dalilin da ya saka yake jin haushinta da ta kasance yarinyar Ubaid ba, shi kansa yana tambayar kansa ina ruwansa? Amma bashi da amsar da zai bawa kansa akan hakan. Jazy ya kalli abinda yake kallo har yake tsaki, ya juya ya kalli inda Rehaan ɗin ya bari, ya sake kallon wajen ya girgiza kai yana tunani.... Nana Haleema. [7/13, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P53 Nana Haleema. Islaha tana shiga ɗaki ta wuce, ba jimawa sai ga Maryam ta shigo tana yi mata sannu. Ita dai murmushi take yi dan ta ji daɗin yadda suke nuna mata kulawa sosai, sun nuna mata iya mai aiki bace, ita ma tana da daraja sosai. Hutu aka bata aka ce ta kwanta, sallah ce ta tashe ta ta tashi ta yi sallah kafin ta ɗauki waya ta kira Hamma. Bata jima tana ringing ba ya ya ɗauka, yana ɗauka ya ce, "Matar Hamma ya ki ke?." Ta ɗan yi murmushi a sanyaye ta ce, "Alhamdu lillah." Ya ce, "ya dai, na ji muryar ki ta yi ƙasa kamar kin samu attack. Kina lafiya?." Ta yi murmushi, ba dole son Hamma ya cigaba da ninkuwa a ranta ba, ko maganar ta ya ji ta canja sai ya tambaya. Wani lokacin sai ta ɓoye masa damuwar ta, amma da ya ga fuskar ta sai ya ce me yake damun ki. Kulawar da yake bata tana sakawa ta ji ta kai wani mataki a zuciyarsa, tana jin ta kamar sarauniya, tana jin ta kamar gimbiya. Ta sauke numfashi ta ce, "na samu attack, ban jimawa da dawowa daga asibiti ba." "Subahanallahi! Ya jikin naki, kin samu sauƙi?." "Na ji sauƙi sossi. Har test aka yi min, kuma ka san an ga asthma ɗin, amma bata da yawa. Har inhaler an bani." "Kin ga banbancin ƙasar mu da ƙasar waje kenan. Amma sun baki magani ko?." "Sun bani Hamma, har da inhaler. Mutanen gidan suna kirki sosai wallahi, ba ka ga yadda hankalin matar gidan ya tashi ba. Yanzu ta shigo ta duba ni ta tafi." "Larabawa ai suna da tausayin mara lafiya, kuma dan kin kasance mai yi musu hidima bazasu ƙi taimakon ki ba." Ta ɗan sauke nunfashi ta ce, "Ya batun Zainab? Ana bibiyar ta kuwa Hamma?." Ya ɗan yi shiru sannan ya ce, "ina bibiya Islaha, amma gaskiya kwana biyu hankalina ba ya kai tunda na koma Niger, sai na koma zan ɗora daga inda na tsaya sha Allah." A sanyaye ta ce, "To Hamma, Allah ya taimaka." "Amin ya rabbi. Bara na bar ki ki huta tunda ba ki da lafiya." Ta amsa ya kashe wayar ta yi shiru. Tana son bibiyar lamarin Zainab amma bata san ya zata yi ba, kwana biyu ko wayar Suraj bata samu balle ta yi masa magana a kai. Gabaɗaya zaman ya ishe ta, tana so ta koma gida, kuma tana so ta je Madina ta ga Umma. •••••••    Mama Atika ta yi shiru tana sauraren abinda Safeera tazo mata dashi, ta sunkuyar da kai tana jin maganar Safeera kamar a mafarki, kwata-kwata bata taɓa tunanin Safeera zata same ta da maganar ba, ko kaɗan bata kawo a ranta hakan zai faru nan kusa ba. Safeera ta ce, "Mama kin yi shiru ba ki ce komai ba. Baba yana gani kamar yana takura miki, hidimar iyalansa da ki ka ɗauka ya yi yawa. In kuwa ki ka aure sa kin ga kema kin dawo ƙarƙashinsa, duk abinda ki ka yi baza a ce haka ba." Mama ta ɗaga kai ta kalle ta ta ce, "Safeera dole na kasa magana. Baba mijin ƙawata ne fa, ta ya zan iya aurensa? Kuma ni duk abinda nake yi, ina yi mu ku shi tsakani da Allah ba dan baban ku ya aure ni ba, ban yi dan na auri baban ku ba." "Na sani Mama. Alfarmar ki muke nema, kema za ki shiga inuwar aure, Kausar zata samu uba, mu ma zamu samu uwa, Baba zai samu mata. Kin ga kowa zai amfana da auren, ba kan ki za ki duba ba, ki duba mu da Kausar da baban. Don Allah ki amince Mama ." Ta sauke numfashi a sanyaye ta ce, "Shi Baban naki ya amince ne?." "Ya amince, amincewar ki kawai ake jira. Ba ma so a ɗauki lokaci, ranar juma'a mu ke so a ɗaura auren kawai." Atika ta ɗan yi murmushi ta ce, "da wuri haka?." "To me za a jira? Kin halinsa, shima san halin ki, ba yau ki ka saba jin halinsa a bakin Umma ba, ba yau ki ka san abinda Baba yake yi a bakin Umma. Tunda haka ne ba sai ayi auren a wuce wajan ba?." Ta ɗan yi shiru tana murmushi, ta kalli Kausar da take kallonsu ta ce, "Kausar ba ki ce komai ba." Kausar wacce bata wuce agemate ɗin Rukayya ƙanwar Safeera ba ta ce, "ki amince Mama, ina goyan bayan hakan." "Bakwa ganin na ci amanar ƙawata? Ta yarda dani, ta bar min amanar gidanta, kuma ta dawo ta ga na auri mijinta?." Safeera ta yi caraf ta ce, "babu wani cin amana, ko tana nan dan kin auri Baba ai ba laifi bane, balle kuma bata nan." Ta ɗan yi murmushi tana jin daɗi a ranta, dan yadda ta san halin Baba yana tsarewa iyalansa komai na rayuwa, zata so ace ta aure sa ɗin. Bai ragi iyalansa da komai ba, duk ƙarfinsa akan ya nemo ya kawo musu yake ƙarewa. Za ta so ta rayu a ƙarƙashin wanda zai riƙe ta hannu biyu, ya girmamata kuma ya san darajar ta. Mama Atika ta ce, "shikenan Safeera, na amince." Safeera ta rungume Mama cikin farin ciki ta ce, "mun gode sosai Mama, Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya ba ki haƙurin zama damu." Ta shafa bayan Safeera tana murmushin jin daɗi, dan gaskiya abin ya zo mata bazata, kuma ta ji daɗi, ta karɓi auren hannu biyu. Safeers ta miƙe ta ce, "bara na je na sanar da Baba, sai ya zo ku yi zance ko?." Mama ta kai mata duka tana dariya, Safeera ta kauce ta fita tana dariyar farin ciki. A zaune ta samu Baba, ta shiga kamar an cillo ta tana kiran sunansa, ya ɗaga kai ya kalle ta ya ce, "Safeera lafiya?." Ta zauna a kusa daahi ta ce, "Baba ina da wani albishir da zan yi maka." Ya kalle ta ya ce, "ina ji Safeera." "Mama Atika dai ta amince." Baba ya girgiza kai cikin mamaki dan ko kaɗan tunaninsa bai kai wajen ba ya ce, "ta amince da me?." Ta ɗan ɓata fuska ta ce, "auren mana." Ya riƙe haɓa ya ce, "Yanzu Safeera zuwa ki ka yi ki ka same ta? Ni na ce miki ki je ku yi maganar nan ne?." "Baba ai ka amince, itama amincewar ta na je nema kuma na samu. Yanzu kawai ayi magana a ɗaura auren ranar juma'a a huta." Ya kalle ta ya ce, "Ranar juma'a! Har kin yanke lokaci?." "Eh mana, to me za a jira?." "an faɗa miki haka ake auren ba a bada komai ba?." "To Baba ai kana da abinda zaka bata ɗin, kawai ka je ku yi magana." Ya yi murmushi bai ce komai ba, dan bai san me zai cewa Safeera ba. Safeera ta ce, "Ni sai na raka ka ma." Ya kalle ta, sai ta miƙe da sauri ta fita tana dariya.  Ya girgiza kai yana murmushi, zai yi ne kawai dan ya ga suna farin ciki da hakan, kuma danginsa gabaɗaya sun bada goyan baya a kai, kuma yana so ya aure ta ɗin ko dan ta kula yaransa in ya bar garin. Baba ya sauke numfashi, ya cigaba da abinda yake yi yana tuna Umma, zuciyarsa tana faɗa masa ko tana ina yanzu, ko ta samu kuɗin da take nema bai sani ba. Ya ɗan sauke numfashi yana tuna kishin Umma, duk da ba matarsa bace a yanzu, in ta ji labarin Atika zata aure sa sai ta yi jinyar kanta. Ya ɗan yi murmushi, ya cigaba da abinda yake yi.          ••••••• Suna zaune zaman meeting na ƙungiya, sun yi shiru ana sauraren abu a cikin wayar. Yadda suka nutsu da kyau zai baka tabbacin abin mai mahimmaci suke ji, dan daga yadda suka ba da hankali su a kai ba za ka san ba ƙaramin abu bane. Sai da aka gama jin muryar tass, aka juyo ana kallon juna, kowa da abinda yake tunani. Babban cikin su ya kalli Mama, ta ɗan tsorata ta ce, "ya ku ke kallona kuma, laifina ne?." Wanda yake zaune a gefe ya ce, "in ba laifin ki ba laifin waye? Ace yarinya ƙarama har ta samu damar yi miki recording kina yi mata irin wannan maganar? Yanzu ba dan ya zo hannunmu ba ya kenan?." Mama a kiɗime ta ce, "ban yi tunanin tana da wannan wayon ba, kuma wallahi Islaha ce ta saka ta." "Komai ki ce Islaha, komai Islaha. Ita wacece da baza a ɗauki mataki a kanta ba? Haka zamu zuba ido ta ɓata mana gari?." Mama ta kalle sa ta ce, "babu yadda ban yi ba, har sace ta na saka a yi, amma yarinyar nan duk abinda na haɗa mata kaucewa take yi." Ɗaya daga ciki ya ce, "Zainab ce a gabanmu yanzu ba Islaha ba. Me ya kamata a yi? Na tabbatar akwai masu recoding ɗin nan da yawa, ba a san iya adadin mitanen da aka turawa dan su ajjiye ba. Tunda har bincike Islaha take yi baza a bar recording ɗin a wajen mutum ɗaya ba, za su rarraba shi inda ba a yi tunani ba, ko da ya ɓace daga wajen ɗaya, ɗaya yana dashi." Mama ta ce, "wa zata turawa in ba Islahan ba, ita ce dai kawai. Yarinyar nan har hotunan Hafsa ta ɗauka a hotel, ba dan Allah ya kiyaye ba da yanzu muna prison." "Kina prison dai, wa za a ɗaure in ba ke ba? Ke ce uwa a gidan, kuma ke ce ki ke fito mana da yaran nan, ke gwamnati zata kama ba mu ba" Ɗaya daga ciki shima ya faɗa yana kallonta. Mama ta dafe kai cikin takaici da tashin hankali ta ce, "wai ni Zainab zata yiwa recording, ni zata nemi tonawa asiri?. Na rantse da Allah bazan bar yarinyar nan ba, sai na yi mata abinda nata taɓa tunani ba. Ni zata naɗa a waya? Ni zata wulaƙanta?." Baban cikinsu ya ce, "kawai ku yanke shawara, me ya kamata ace an yi?." "A ɓatar da yarinyar kawai, dan zaman ta ba ƙaramin bazarana zai zamar mana ba. Ita kanta ma shaida ce, ko babu wannna muryar shiada ce mai girma. Magana ake ta gidan nan na gwamnati ne, ko ya ya gwamnati ta san da maganar nan ba za a tsaya neman wata hujja mai ƙarfi ba, ko Zainab ɗin ce kaɗai ta ba da shaida shikenan mun gama yawo. Tunda an kasa mallake ta har ta amince da ƙudurin mu, kawai a san yadda za a yi da ita." Mama sai jikinta ya ɗan yi sanyi jin ana zancen za a kashe Zainab, murya a sanyaye ta ce, "a kashe ta kenan?." Wanda ya yi maganar ya wara hannu ya ce, "meye amfaninta? A kashe ta kawai, itama ta ƙasar wajen in ta dawo a yi maganinta, a kashe su duka su biyun ai basu ƙarfin kisan ba. Saboda rai biyu zamu haƙura da aikin mu ne?." Babban ciki ya ce, "gaskiya ne wannan, abinda ka faɗa shi ya kamata ayi. A ɓatar da yarinyar nan daga garin nan, in hakan bai yu ba a kashe ta!. Itama mai goya mata bayan, a wannan lokacin bana son kuskure, a tabbatar an yi maganinta!." Mama a sanyaye ta ce, "kisa ya yi tsuri boss, a bani dama na san abinda zan yi." Cikin faɗa ya ce, "sau nawa ana ba ki damar? Dama nawa aka ba ki ki ke wasa da ita?. Nan aka ba ki kwangilar sace yarinyar, nan ashe ba ke ki ka ɗauka ta ba. Yanzu kuma kina so a sake ba ki dama dan ki ɗauki mataki?...." Ta yi shiru bata ce komai ba ya ce, "Na gama baki dama, a wannan karon da kaina zan ɗauki mataki, ai ba fin ƙarfina suka yi ba. Ke kin san muna yin komai saboda idanun mutane, amma yanzu bazan sake saurare ki ba. Kisa shine daidai da Zainab, dole mu tabbatar ta daina numfashi!." Nana Haleema. [7/13, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P54 Nana Haleema. Mama ta kalle sa a sanyaye ta ce, "Tuba nake, amma a wannan karan baza a same ni da kuskure ba." "Me za ki yi mata?." "Daji zan aika ta kawai, yadda baza a yi zargin wani abu akan gidan ba." "Kina nufin ta haukace kenan?." "Ƙwarai." Ɗaya daga ciki ya ce, "in wata ran ta samu lafiya ta dawo daidai fa?." Ta kalle shi ta ce, "ban da aikin wajen wanda zan je, in ya yi aiki tamkar rubutu akan dutse ne. Wallahi sai ta haukace." Duk suka yi shiru Mama ta ce, "a bani wannan damar don Allah, bazan ba ku kunya ba in Allah ya amince. Kisa ya yi tsauri, ba mu san wa ta turawa recording ɗin ba, in aka kashe ta za a yi zargin mu ne. Amma in ta haukace, ta shiga daji, shikenan mun huta." Boss ya ce, "me ku ka ce?." Suka ce, "duk abinda ka ce boss." Ya kalli Mama ya ce, "An baki dama, amma in aka samu matsala..." kafin ya ƙarasaa ta ce, "wallahi babu matsala a harkar nan, ku bar komai a hannuna." Cikin gamsuwa aka amince da shawarar haukata Zainab, suka cigaba da tattaunawa akan yanayin tsarin aikinsu, kafin kowa ya watse. Mama tana barin wajan kai tsaye wajan bokan ta wuce. Ta yi bayani yadda ya kamata, sannan ta saka a yi aikin da zai ɓatar da hankalin Islaha daga kan su, ta manta da duk abinda yake faruwa ta yi harkokin ta, shi ya bata abinda ya kamata ta yi sannan ta koma orphange. Tana shiga aka kira wayarta, ta ɗauka ta ce, "na gama komai, zuwa gobe za ku ji labari mai kyau. Zainab baza ta shura ba, tunda ta fitar da recording ɗin muryata ai ta shiga uku. Ku bar komai a hannuna, zan ɓatar da ita wallahi. In kuma nata haukace ba, zamu kashe ta!." Zainab da ta ji komai, gabanta ya faɗi ta bar wajan da sauri. Hannunta yana rawa ta kira wayar islaha amma sai larabci ake yi mata. Jikinta yana karkarwa ta yi mata voice note tana hawaye, tana gamawa ta ɗauki kuɗi a jakarta ta fita a guje.            ••••••• Islaha bacci ne ya ɗauke tunda dare ya yi, bata farka ba sai sha biyu na dare, tana miƙewa zaune wayar ta ta jawo tana dubawa. Da voice note ɗin Zainab ta fara karo, ta buɗe tana sauraran abinda take faɗa. Bata san ta miƙe tsaye ba, a firgice ta tsaya akan ƙafarta jikinta yana rawa sosai. "Innallahi wa'inna ilaihir raji'un!." Shine abinda take maimaitawa cikin kiɗima da tashin hankali, jikinta har rawa yake yi, kanta yana sarawa saboda tashin hankali. Zagaye ɗakin take yi, duk da akwai sanyin ac amma gumi tsatstsafo mata yake yi cikin tashin hankali da tsananin firgici mai yawa. Ta kira lambar Zainab amma bata shiga, ta yi mata voice note amma babu alamun datar ta a kunne take. Ta ɗora hannu a kanta ta fashe da kukan damuwa da rashin sanin abinda zata yi. Sai kuma ta zabura ta kira lambar Safeera, daga can ɓangaren Safeera ta gama shirin kwanciya kenan tunda suma dare ya yi. Ganin kiran Islaha sai ta murmusa, daman tana da niyar kiran ta bata labarin auren Baffa da Atika. Tana ɗauka Islaha cikin kuka ta ce, "Safeera na shiga uku, zasu kashe Zainab Safeera. Ki taimaka min ki je ki gano ta, ki taimaka ki je gidan ki ga in tana nan!. In zainab ta rasa ranta ta silata bazan yafewa kaina ba." Hankalin Safeera ya tashi ta ce, "Ban gane zasu kashe ta ba, su waye zasu kashe ta ɗin?. Ki nutsu, ki yi min bayani yadda zan gane." "Safeera ki fara zuwa ki gano min in tana nan, bazan taɓa samun nutsuwa ba indai ba lafiyar Zainab na ji ba." "Goma na dare ta wuce Safeera, Baba bazai barni na fita ba. Kuma ko da na je kin san a rufe gida gate, baza a bar ni na shiga ba. Ki kira ƴan uwanki na gidan ki ji in tana ciki mana." Islaha ta sake fashewa da kuka ta ce, "Bata nan, An ce min ta bar gidan Safeera!. Ina zan saka raina in wani abun ya samu Zainab?." Saferra jin yadda Islaha take kuka sosai sai hankalinta ya sake tashi sosai, ta ruɗe itama, cikin taushin murya ta ce, "ki faɗa min me ya faru?." "Komai ma ya faru, na lalata rayuwar Zainab, tunda ni na bata shawarar ta dinga yi min recording tana turo min, da ban saka ta yi ba da bata yi ba, da ba a yi ƙoƙarin kashe ta ba. Ina zan saka raina in aka cutar da ita ta silar hakan?." Safeera zata yi magana Islaha ta kashe wayar tana kuka sosai. Ta nemi number Saheer ta kira sa, bai ɗauka ba ta ajjiye wayar ta cigaba da kuka mai tsuma zuciya. Tashin hankalin ta bata ƙasar balle ta je ta ɗauke Zainab, damuwar ta ta yi nisa da Zainab balle ta kai mata ɗauki. Babu jimawa Saheer ya kira ta, tana ɗauka ta sake saka masa kukan da yake jin sautinsa sosai. Shiru ya yi mata bai ce komai ba, yana jin yadda take sauke numfashi tana fitar da kuka mai sauti. Ya san in ya ce zai yi magana bazata ji sa ba, gwara ya yi shiru ta gama kukan sai su yi magana. A hankali ya ji tana sauke nunfashi alamun kukan ya tsaya ya ce, "ki nutsu, kar ki jawo numfashin ki ya sarƙe. Kin san ba cikakkiyar lafiya ce dake ba." A hankali take sauke numfashi kafin ta ce, "Hamma!." Jin yadda ta kira sa ya saka ya ce, "Na'am, ya aka yi?." Ta lumshe ido ya buɗe, a sanyaye ta ce, "Hamma Zainab!." "Me ya samu Zainab ɗin?." "Za su kashe ta Hamma." "Kisa kuma! Su waye?." "Su Maman orphage." "Mafarki ki ka yi akan hakan?." Hawaye ta sakko mata ta ce, "wayar nan da muke yi mafarki ce?." Ya ce, "Aa, a gaske ne." "To da gaske ne abinda na faɗa maka, za su kashe Zainab Hamma." Saheer cikin rashin fahimta ya ce, "da gaske ne me? Ki yi min bayani yadda zan gane. Ki nutsu, sai ki faɗa min abinda ya faru." "Hamma sun samu recording ɗin da Zainab ta turo min har na tura maka na ce ka ajjiye min, saboda shi zasu kashe Zainab saboda ta naɗi muryar Mama ta turo min." Saheer ya ce, "su waye suka samu recording ɗin?." "Maman orphanage." "ya aka yi ki ka san sun samu har zasu kashe ta?." Hawaye ya sake sakko mata ta ce, "Zainab ɗin ce ta faɗa min, kuma an tabbatar bata cikin gidan yanzu, na saka a n duba an ce bata nan." Saheer ya ce, "Islaha anya ba mafarki ki ka yi ba? Ba fa film mu ke kallo ba, zahiri ne." Islaha sai ta yanke wayar, ta tura masa voice note ɗin Zainab. Sai da ta tabbatar ya gama ji sannan ta kira sa, ya kiɗime ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yaushe ta tura miki?." Islaaha ta ce, "tun ɗazu, ban gani ba sai yanzu dana farka daga bacci. Hamma in wani abun ya samu Zainab mutuwa zan yi, ni na saka ta ta dinga yi min recording ko yaushe, ni na saka Zainab ta dinga tura min duk abinda ya faru. In suka yi mata wani abun bazan yafewa kaina ba, ko meye ya same ta ni ce sila, Hammaaaaaaaa!" Ta ja sunan cikin heart breaking, muryarta tana cracking cikin tashin hankali. "Kwantar da hankalin ki, in Allah ya yarda babu abinda zai same ta. Yanzu zan saka Sadik ta je ya sanar da hukuma halin da ake ciki, zan saka a baza neman ta ko za a dace a ganta. Kar ki damu, ki kwanar da hankalin ki, zan yi komai kamar kina ƙasar, kin ji?." Ta girgiza kamar yana gabanta ta ce, "bana so hukuma ta shiga maganar nan tun yanzu, na fi so na gama tattara komai sannan hukuma ta sani." "Shikenan, zamu bayar da cigiyarta. Amma na tambaye ki." Kafin ya yi tambayar ta ce, "Ya aka yi aka san ta yi recording ɗin, har aka san ta turo min ko?." Saheer ya ce, "haka zan tambaya. Ya aka yi suka san da recordong ɗin a wajan ki?." Ta ce, "ban sani ba Hamma, wallahi ban sani ba......" ta faɗa tana kuka, sai kuma ta ce, "Ka ga kenan lokacin da aka goge hotunan Hafsa shima  masaniya suka samu a akan hakan, shine aka saka wani a cikin office ɗin su Safeera ya goge." Saheer ya ɗan yi shiru yana tunani sannan ya ce, "bayan ni, waye ya san da recording ɗin a wajan ki?." Islaha ta ce, "kamar dai hotunan Hafsa, daga kai sai Safeera, ta ce min ta faɗawa Saleem har ta tura masa saboda gudun ɓata, sai Brr Suraj." Ta yi tunanin zai yi faɗa akan Suraj kamar yadda ya saba, amma sai ta ji bai ce komai ba ya yi shiru kafin ya ce, "lokacin hotonan Hafsa ma iya mu haka muka sani ko?." Kamar tana gabansa ta ɗaga kai ta ce, "A daren kai da Suraj ku ka sani, washe gari Safeera da Saleem suka sani. Ko mintina ashirin ba a yi da saninsu ba aka rasa hotunan." Saheer ya ce, "Yanzu kuma gashi recording ya fita, ta silar sa har ana ƙoƙarin cutar da Zainab." Ya sauke numfashi yana ya ce, "Islaha!." "Na'am!." A sanyaye ta amsa ya ce, "a tsakanin ni, Suraj, Safeera, Saleem akwai munafuki a cikin lamarin ki. Akwai wanda yake da hannu a cikin lamarin nan, zai nuna yana tare dake amma a bayan idonki yana tare dasu. Tabbas akwai suspect a tsakanin mu." Islsha ta dafe kai cikin tsananin damuwa, ta kasa furta komai, dan tabbas maganar Saheer gaskiya ce. Saheer ya katse mata tunani ya ce, "ya zama dole ki nemo waye munafukin a cikin mu, kafin nan ki daina faɗa mana komai akan abinda ya shafi binciken ki. Ki dinga ajjiyewa a wajan ki, kar ki yarda da kowa, ki yarda da kan ki. Ko ni ɗin kar ki yarda dani, kar ki yarda da Safeera, balle Suraj. Ki nutsu, ki cigaba da abinda ki ke yi ke kaɗai, ko da kin dawo ki daina faɗawa kowa damuwar ki." Islaha a sanyaye  ta ce, "amma ni bana zargin kowa Hamma, wallahi bana zargin kowa a cikin ku." "Hmm! Ba ki san mutum bane, ni ɗin nan da ki ke gani wataƙila sai ya zama ni ne mai fitar da dukkan sirrin ki. Safeera da ku ke tare ko yaushe zata iya zama itace, Suraj da ki ke kallo a matsayin Yayan ki shima zai iya zama shine munafukin ki. Balle Saleem, da ya kasance abokin aikin ki kawai...." Ya ja numfashi ya ce, "Ki yarda da zuciyar ki, ko me za ki samu ki daina faɗa, in ba haka ba baza a taɓa bari ki yi achieving mafarkin ki ba. Kuma za a cigaba da cutar da irinsu Zainab ɗin. Kar ki sanar da kowa sai kin tabbatar komai ya kammala. Tunda har aka fara haka zargin ki a kan gidan nan gaskiya ne, wanda yake aikata laifi shine yake ƙoƙarin kawar da duk wani abun da zai kawo masa cikas. In ki ka cigaba da faɗa mana za ki dinga cilla rayuwar mutane a haɗari, tunda bamu san waye suspect ɗin a cikin mu ba." Ta ja numfashi ta sauke ta yi shiru dan bata da bakin magana. Shima ya yi shiru, dan ya san tana cikin ruɗani mai yawa. Sai daga baya ta ce, "ina son dawowa nigeria Hamma, na gaji da zaman nan, zan dawo gida." "Dawowa gida ba na ki bane, dole sai kin ƙarasa abinda ki ka fara." "Bazan iya cigaba da zama ba, zan dawo Hamma!" Ta faɗa tana kashe wayar, ta kwanta a kan tiles tana tunani. Waye abin zargi, wa zata zarga a cikin mutane huɗu bayan duk duniya babu waɗanda ta yarda dasu kamar su huɗun?. Saheer masoyinta kuma mijinta na gobe, ko aminiyarta Safeera wacce ta rikiɗe ta zama ƴar uwa, ko Suraj aboki kuma Yayanta wanda ya taimake ta tun tana ƙarama, ko Saleem da ya zama ɗan uwa a gare ta? Wa zata ɗauka ta yi cycling sunansa a matsayin munafuki?. Ni kaina ban san waye na ɗauka waye na bari ba🤔 Nana Haleema. [7/14, 2:53 PM] KRBBK: RDB2P55 Nana Haleema. Islaha haka ta kasa komawa bacci, sai tunanin halin da Zainab take ciki take yi. Ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a nigeria, zaman ya gama isar ta, ta gaji tana buƙatar komawa gida. A haka ta kwana cikin tunani, haka ta tashi kanta ya yi nauyi ta rasa me zata yi. Tana idar da sallar asuba ta kira Saheer amma bai ɗauka ba, sai a lokacin ta tuna ashe fa su asuba bata yi ba. A hankali ta ji ana buga ƙofar, ta miƙe ta buɗe suka haɗa ido da Maleek da Maryam. Maryam ta shiga ciki tana kallon ta, Islaha ta ce, "good morning madam." Maryam ta riƙe fusksr Islaha ta ce, "you look so stressed, i hope you are feeling well?." Islaha ta ɗaga kai ya ce, "Ahamdu lillah! I'm feeling better. Good morning" ta faɗa  tana kallon Maleek da yake kallon ta. Ya ɗan murmusa ya ce, "Ya jikin ki?." "Alhamdu lillah." "Ma sha Allah. Ki kwanta ki huta, kar ki damu kan ki." Ta ɗan yi murmushi suka fita dan ta san bacci zasu je su yi, dan tana jin su tana jinsu sai uku na dare suka dawo daga yawo. Ita kam kasa baccin ta yi gabaɗaya, tunani kawai take yi cikin rashin mafita da rashin sanin abinda ya kamata ta yi. Ta jima a haka, sai ga Sunaira ta kawo mata breakfast har cikin ɗaki, tana murmushi ta karɓa ta yi mata godiya ta koma. Tea ta sha, sai kuma arabian rice ɗin ta burge ta, ta ɗan ci kaɗan sannan ta sha maganinta ta koma ta cigaba da tunani mara ɓullewa. A haka ta miƙe ta yi wanka ta ɗan kwanta ta yi bacci, zuwa sha biyu na rana ta farka, a lokacin ta ga kiran Hamma dana Safeera da na Suraj. Hamma ta fara kira, yana ɗauka ta ce, "Hamma an samu Zainab ɗin?." Ya ce, "ba a same ta ba islaha, amma ana bincikawa." Zata fara yi masa kuka ya katse ta ya ce, "Allah in ki ka yi kuka zan ƙi nemo ta ɗin, baki da lafiya fa, in wani abun ya same ki fa?." Islaha ta goge ido ta ce, "na damu ne." "Ai na faɗa miki zan yi ƙoƙari ko? Ko ba ki yarda dani ba?." "Na yarda." "To ki kwantar da hankalin ki, saboda wannan maganar zan koma nigeria, in na zauna a nan bamu san inda lamarin zai je ba, tunda ke bakya nan gwara na koma kafin abin ya yi nisa." Ta yi ajiyar zuciya jin zai koma gida saboda haka ta ce, "To Hamma, Ina kwana." Ya ɗan murmusa ya ce, "Matar Hamma, sai yanzu za ki gaishe ni?....." Ta ɗan yi murmushin da ya ji sautinsa, amma ya san murmushin bai kai zuciya ba, ta yi ne kawai dan ya ji daɗi. Saheer ya ce, "lafiya lau, ya jikin ki?." "Da sauƙi sosai, na ji daɗin maganin." "Haka ake so. Allah ya ƙara lafiya." "Amin Hamma." "Zamu yi magana anjima." Ta gyaɗa kai sannan ya kashe wayar. Sai ta ɗan samu nutsuwa, jin Hamma zai koma Nigeria a nemo Zainab sai ta ji daɗi sosai, ta san in sha Allah rayuwar Zainab baza ta salwanta ba. Sai a lokacin ta samu ƙarfin guiwar iya zuwa gidan Rehaan, ta miƙe ba tare da ta saka uniform ba, ta yafa mayafi a kanta tana kallon kanta. Atamfa ce a jikinta mai kyau, rigar bata kamata ba amma bata yi mata yawa ba, daidai jikinta, irin mai tsaga a gefen nan, an ɗan yi nata adon stones a waya, sai dogon hannu da ya zo har tsintsiyar hannunta. Ita kanta ta san ta ƙara haske a zamanta na Jeddah, fatarta kamar madubi saboda ɗaukar ido da santsi. A bayyane ta ce, "ina zaune waje ɗaya dole na yi haske." Ta faɗa tana ɗaukar wayarta, ta fita daga gidan zuwa gidan Rehaan. Yau a falon downstairs ta tarar dasu duka biyun a zaune, abinda bata taɓa gani ba, bata taɓa ganinsa a ƙasa a zaune ba, ko yaushe yana upstairs. Babu da wanda bata haɗa ido dashi a cikinsu ba, ta ɗauke kanta ta sunkutar da kai ƙasa ta ƙarasa ciki ta ce, "Good morning." Jafar ya wani kalle ta ya ce, "morning! Yanzu safiya ce?." Ta ɗan yi shiru bata ce komai ba ya ce, "haka housemaid suke zuwa aiki sai lokacin da suka ga dama?." Ta ɗan sauke nunfashi ta ce, "bani da lafiya ne, shiyasa hakan." Rehaan ya ɗago ya kalle ta jin wai bata da lafiya, kai tsaye suka haɗa ido, sai ta ga ya sake yi mata wani haske mai ɗaukar ido, gashi ya rage gashin kansa, ya dawo da iya wuyansa, kuma an datse shi ya zama daidai babu inda ya fi wani tsayi. Shi kallon ta yake yi jin ƙaryar da ta zabgawa Jafar, wai bata da lafiya bayan ya ganta jiya da Ubaid yana ja mata kunatu tana dariya. Sai kuma ya yi tunanin ina ruwansa, ya taɓe baki ya ɗauke kai bai ce mata komai ba. Jafar ya ce, "Okay." Daga haka ya yi shiru bai ce komai ba. Ita dai ta ga ji da tsayuwa ganin duk sun share ta sai ta kasa motsawa, bata son yin abinda zasu dizga ta dan ba ɗauka zata yi ba, gwara ta cigaba da tsayuwar. Jafar ya ɗago kai ya kalle ta ya ce, "ki je ki yi aikin ki, ki samar mana da wani abu mai daɗi." Ta ɗan ɗaga kai ta ce, "Okay." Rehaan ya miƙe tsaye, ya kalli Jazy ya ce, "Ta samar maka dai, ni kam bana so" ya faɗa yana ɗaukar wayar sa ya hau sama bai sake kallon ta ba. Islaha ta bi sa da kallo, dan da fulfulde ya yi maganar, tana ta mamaki dan ita bata ɗauka yana ji ba. Kitchen ta wuce bayan ya bi shi da harara, ta shiga ta ja kujera ta zauna dam bata san me zata dafawa Jazy ba. A lokacin Jafar ya shigo da sallama, ta amsa tana kallon sa, ya ɗan tsaya daga gefen ta ya nuna mata screen ɗin wayarsa ya ce, "Are you?." Islaha ta kalli wayar, ta ga content ɗinta na farko da ta yi magana akan zuwa hotel, wanda ya fi samun views da ɗaukaka sama da ko wanne. Ta kalle sa ta ga ita yake kallo, sai ta ɗaga kai ta ce, "Eh ni ce." Ya ɗan taɓe baki yana ɗan girgiza kai ya ce, "Islaha Muhammad Madibbo, right?." Ganin ba ita yake kallo ba sai ta ce, "Haka ne." "A jounlist, working in toran giwa channel.  You are from Adamawa state?" Ya faɗa yana kallon ta. Ta ɗaga kai ta ce, "Eh." Ya ɗan girgiza kai ya ce, "so fulani is your tribe?." Nan ma ta ɗaga kai alamun eh. Ya ɗan zuba mata ido yana nazarinta, sai ya ga ta buɗe baki zata yi magana amma ta fasa. Jazy cikin yaren hausa ya ce, "faɗi, ina jin ki." Islaha ta ce, "Watannin da suka gabata, a cikin Diamond hotel, an kawo maka katin gayyatar Mr Rehaan Yola for interview. Miss Islaha." Ya ɗan zuba mata ido alamun yana tunawa, sai ya ɗan ɗage gira yana ɗaga kai ya ce, "Yes na tuna. Ke ce Miss Islaha da ta bani katin gayyatar Rehaan a Diamond hotel?." Ta ɗaga kai alamun itace tana kallonsa. Ya ɗan jingina da kitchen island ya harɗe hanunsa a ƙirji ya ce, "neman Rehaan Yola ne ya kawo ki Jeddah kenan?." Ta ɗan buɗe ido kaɗan ta ce, "No, i'm here for a job." "A job!" Ya maimaita yana kallon ta, kafin ya miƙe tsaye sosai ya dafa kitchen island ɗin yana kallon ta ya ce, "which job?." Islaha ta ɗan lumshe ido ta ce, "it's my personal issue Mr Jafar." Ya ɗan ɗage kafaɗa alamun bai damu ba, sai ya ce, "Kin haɗu da Rehaan ɗin akan hakan?." Ta girgiza kai ta ce, "Ni ban haɗu dashi ba, ba da kai muka yi alƙawari akan zaka neme ni in lokaci ya yi ba, ko ka manta?." Ya girgiza kai ya ce, "Fuskar ki na manta, ba alƙawarin ba. Amma kin taɓa ganin Rehaan? Ina tunin kafin yanzu kin taɓa ganin Rehaan Yola?." Ta girgiza kai alamun  ta ce, "ban taɓa ganinsa ba had yanzu." Ya ɗan buɗe ido yana binta da kallo cikin mamaki, dan ya san raina masa hankali kawai take yi. Ya ɗan girgiza kai ya ce, "Wow!." Sai kuma ya ɗan murmusa ya fita bai ce komai ba. Jazy yana fita daga kitchen ɗin sama ya hau har ɗakin Rehaan, ya same shi a tsaye yana amsa waya. Sai da ya gama wayar sannan Jazy ya ce, "a ina ka san housemaid ɗin na da take zuwa gidan nan?." Rehaan ya kalle sa ya ce, "Gidan Ubaid." Jafar ya ce, "ka san ƴar Nigeria ce, kuma ƴar Yola?." Ya ɗan juyo ya kalle sa sannan ya ce, "me ya dame ni da sanin hakan?." Jafar ya ce, "Ya kamata ya dame ka, a yadda ka ke ya kamata ka dinga tantance waɗanda zasu raɓe ka. Dan a biyata kuɗi daga Nigeria, ta zo Jeddah ta fara aiki a gidan Ubaid, daga baya ta shigo nan abu ne mai sauƙin faruwa. Za a iya haɗa baki da ita a cutar da kai." Ray ya ɗan sauke numfashi bai ce komai ba. Jazy ya ce, "Lokacin da ka shiga Nigeria ka sauka a diamond hotel, itace ƴar jaridar dana faɗa maka mun yi magana da ita, har na yi mata alƙawarin itace zata hira da kai. Me ya baro ta daga garinsu duk da aikin da take dashi mai kyau?. Sannan ta zo Jidda ta fara aiki a kusa da gidan ka, sannan daga baya ta fara yi maka aiki......" Jazy ya yi shiru yana girgiza hannunsa, ya gyaɗa kai ya ce, "Akwai alamar tambaya akan yarinyar nan, zuciyarta bata amince da ita ba..." sai ya yi shiru, ya shiga video da ta yi, ya yi screenshot fuskar ta, ya tura ya ba da umarnin bincike a kan Islaha a take. Rehaan shi kansa ya ɗan ji wani iri, musamamn da ya tuna itace dai wacce ya sace, ya tafi tunanin  meyasa ta shiga rayuwarsa har haka?. Ya kalli Jazy ya ce, "Sannan itace yarinyar da na ɗauke ta, har ka dinga cewa in ban sake ta ba zaka faɗawa Mamy." Jazy ya zaro ido waje ya ce, "what! Kana nufin itace?." "Itace." Jazy ya furzar da iska, ya tafi tunani sannan ya ce, "da farko ta fara haɗuwa da kai a diamond hotel, ta zubar maka da tea har ta faɗa maka magana, kafin ta haɗu dani. Daga baya ta haɗu dani ta ce tana so ta yi hira da kai. Daga nan ka sace ta, sannan sai gata a Jeddah a kusa da gidan ka tana aiki, sai kuma gata a gidan ka a matsayin housemaid....." Ya girgiza kai ya ce, "Ban yarda da ita ba, in ta aikata wani abu mara kyau wallahi i will have her arrested" ya faɗa zai fita sai kuma ya fasa ya ce, "bara na ƙyale ta. Amma ta san kaine Rehaan Yola?." Ya ɗage kafaɗa alamun oho, Jazy ya fita daga ɗakin ya koma wajan Islaha. A zaune ya same ta kamar yadda ya bar ta, sallamar sa ya saka ta kalle sa, ya gyara tsayuwa ya ce, "Miss bani labarin a inda ki ka san me gidan nan." Ta ɗan kalle sa jin wata tambaya ta rainin hankali ta ce, "Mr Jafar meyasa ka ke yi min wannan tambayar?." Maimakon ya amsa sai ya ce, "ina jinki." Ta ɗan yi tsaki kaɗan ta ce, "ni ban san shi ba, a diamond hotel na fara ganinsa, daga nan na gansa a Nadira hospital and medical center, daga nan ya sace ni, daga nan na gansa a gidan nan. Shine kawai." Ya girgiza kai ya ce, "me ki ka yi masa har ya sace ki?." Ta miƙe tsaye ta ce, "Wannan shi zaka tambaya, nima ban sani ba." "Haɗuwar ku a hotel kafin ki haɗu dani, me ya haɗa ku?." Ta ɗan dafe kai cikin ƙosawa ta ce, "why me? Ka je ka tambaye sa mana, lallai sai ni?." Ya zuba mata ido ganin ko nauyinsa bata ji ta fara yi masa rashin kunya. Islaha ta juya ta ce, "na faɗa maka iya abinda na sani, meyasa zaka takura min da tambaya?" Ta faɗa zata wuce sa ya riƙe gefen mayafinta. [7/14, 2:53 PM] KRBBK: RDB2P56 Nana Haleema. Islaha ta mayafinta ta juyo ta ce, "Mr Jafar me ka ke so nace maka? Ƙarya ka ke so na yi maka?." Ya zuba mata ido yana sake karantar yanayinta ya ce, "kin haɗu dashi a hotel, kin haɗu dashi a asibiti, ya sace ki, sannan ya ƙyale ki. Sai kuma ga ki a Jeddah, kin fara aiki a kusa da gidan nan, daga baya kin fara a nan. Meyasa rayuwar ki take haɗuwa da ta sa har haka?." "Bani na halicci kaina ba balle na sani, Kuma wannan ai ba yin kaina bane, yin Allah ne. Ni kaina inda ina da dama, ko wanda ya san shi ma bazan nuna na sani ba balle shi da kansa. Hanya bazan so ta haɗa ni da wani nasa ba, balle shi ɗin." Ya ɗan murmusa yana kallon idanunta ya ce, "Miss Islaha in na gano wani abu akasin haka a kan ki, wallahi i will have you arristed." Da mamaki ta ce, "akasin abinda na faɗa, au har ni zan tsaya na yi maka ƙarya akan mutumin da ban san shi ba? Kawai sai na yi maka ƙarya dan na burge ka, ko dan ka bar ni na cigaba da aiki a gidan nan?....." Ya yi shiru bai ce komai ba, ta cigaba ta ce, "Ni ban ce zan saka a kama shi ba sai kaine zaka ce zaka saka a kama ni saboda shi? Kai ga mai aboki, ni da sace ya sace banza kenan, tunda shi mai kuɗi ne ni kuma talaka ce. Ban san shi ba, ban san ko sunansa ba, kuma bani da buƙatar na sani. Aikina a gidan nan ma wani dalili ne kawai ya saka nake yi, in ba da dan dalilin ba da ban zo ƙasar nan ba balle har na zo gidan nan. Kuma ina so ka sani, shine dalilin, shine dalilin da ya saka na zo ƙasar Jeddah. Dan haka ni nake da bakin da zan ce ya shiga rayuwata, ba shi ba." Jazy dai ya yi shiru yana kallonta ganin yadda take yi masa tsiwa cikin rashin tsoro. Ta ce, "inda na yi niyar cutar dashi da baka zo ka same sa lafiya ba, tunda har in na dafa na bashi yana ci, da yanzu sai dai ka ji labarin mutuwarsa. In da ina niyar cutar dashi da ban taimake sa daga wajan wata ƙoɗaɗɗiyar baturiya ba, da na bari ta aikata ƙudurinta na jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Wallahi bai kai na baro ƙasata da iyalaina na zo nan saboda shi ba, ko biyana za a yi na bibiyi rayuwarsa bai kai wanda zan tsaya na ɓata lokacina na bibiye sa ba. Babu wanda nake jin haushi a duniya kamar shi ɗin, ina so ka faɗa masa, bai isa na zo dan na cuce sa ba wallahi, bai kai matsayin da zan riƙe sa a rai har na cuce sa ba" tana gama faɗar hakan ta nufi exit door. "Wanne irin taimako ki ka yi masa, mai Alma zata yi masa ki ka taimake sa?." Ta juyo ta kalle shi ta ce, "don Allah na yi, na yi saboda kasancewarsa musulmi ɗan uwana, bayan wannan babu wani abun. Dan haka no need sai na faɗa maka" tana gama faɗar hakan ta fita daga kitchen ɗin. Jafar ya ɗaga ƙafa zai fita aka kira shi a waya, yana ɗauka aka ce, "Mr Jafar kamar yadda ka faɗa haka sunanta yake, yarinyar ƴar jarida ce bata da wata damuwa. Matsalar ta kawai bata da kunya, tana da tsiwa bata saurarawa wanda ya ɗaga mata murya. Dalilin neman kuɗi ne ya kawo ta Jedda ba dan tana so ba, a kwanakin baya tana daga cikin masu wayarwa da iyaye kai akan illar kai yaransu mata wata ƙasa aiki. Itace dai wacce Mr Ray ya ɗauke ta, ta yi kwana biyu a hannunsa,  amma duk da hakan bai saka ta yi sanyi ba. A yadda na ji ance ta ci bashi kuɗi ta biya kuɗin aikin mai riƙonta, ta zo ƙasar saudia dan ta samu kuɗin biyan wannan bashin. Bata tare da kowa, kuma ba aiko ta aka yi ba." Jafar ya sauke numfashi ya ce, "ka tabbatar?." "Na tabbatar ranka ya daɗe." Bai ce komai ba ya kashe wayar yana tuna abinda tace daki-daki. Islaha rai a ɓace ta koma, gani take kamar Jafar ya gama raina mata hankali da yake tunanin an tiro ta dan ta cutar da wanda bata sani ba. Ta cire mayafin ta ajjiye, ta zauna sai kuma ta ja dogon tsaki ta ce, "wai he will have me arriested, ko shi waye da zai kama ni oho." Sai kuma ta ce, "ko kuma dan ɗan uwan Ray ne ba. Mtsww! Ai ba shine Rehaan ɗin ba balle ya yi taƙama da kuɗi, kuma Allah na tuba ko Baban Rehaan ne ya yi min...." Sai kuma ta dakata ta ce, "bakyau yiwa iyayen wasu irin haka, amma ko shi Rehaan ɗin ne ya yi min daidai nake dashi balle wani ɗan uwansa. Meye abin cutarwa a wancan ragon? Mtsw! Mai zubin mata, yadda yake da gashin nan a kansa, kamata ya yi ya saka kayan nata kawai, tsaf zai saje da su." Haka ta ƙaraci mitar ta ita kaɗai, kafin tunanin Zainab ya dawo ranta ta ɗauki waya ta kira Safeera tunawa ta kira ta ɗazu. Safeera tana ɗauka ta ce, "Ɗazu na kira ki, ina ki ka ajjiye wayar?." Islaha ta ce, "ya aka yi?." "Muna magana kin katse kiran, me ya faru da Zainba ɗin?." "Bestie mutanen nan kamar yadda suka saka aka goge hotunan Hafsat a wayata ba tare da na san ya aka yi suka sani ba, sun sake samun wannan recording ɗin, har ana yiwa Zainab barazanar a kai. Yanzu babban tashin hankalina kar a cutar da ita." Safeera ta ce, "subahanallah! Lallai lamarinsu azimun ne. Yanzu an samu Zainab ɗin?." "Hamma ya ce min zai dawo ya dubata." "To waye ya fitar da audio ɗin? Wani ya san dashi ne bayan ni?." "Ina zan sani?. Daga ke, sai Hamma, Suraj da Saleem ne kaɗai ku ka san dashi. A cikun ku akwai abin zargi ne?." Safeera ta sauke numfashi, a sanyaye ta ce, "babu kam. Amma kuma dole a cikin mu akwai munafukin, mu ɗin dai akwai wanda yake tare dake, kuma yake tare dasu.. Ni dai wallahi...." Islaha ya dakatar da ita ta ce, "kar ki fara yi min rantse rantse malama, kin ji na ce ke ne? Kina da matsala wallahi." "Ba ki ce ba, amma ina cikin abin zargi, kuma zata iya yuwa ni ɗin ce, kin yarda dani ne shiyasa ki ke ganin bazan yi ba." "kowa ma yana cikin zargi ai ba ke kaɗai ba, ki dakata da wannan maganar kawai. Ni wallahi gabaɗaya zaman nan ya dame ni, ina so na je Madina na duba Umma, daga nan ina son dawowa gida." Safeera ta ce, "Hajiya Umma, sai ga Vn ɗinta a wayar Mama Atika, wai a ta ya ta a da addu'a Allah ya dawo da ita. Na ce Umma tun kafin daren ya yi har an fara fatan wayewar gari." Islaha bata ce komai ba, Safeera ta ce, "ki samu ayi miki bincike yadda ya kamata, daga nan sai a san abinda za a yi." Islaha tana so ta bata labarin haɗuwar ta da Mr Jafar, amma bata son bata labarin wanda ya ɗauke ta kuma take aiki a gidansa, dan bata san ya zata ɗauki abin ba. Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar         •••••• Adda dai kallon Mama kawai take yi, jin tana ta lissafin kuɗi cikin farin cikin da yake kwance akan fuskar ta. Ta ɗan sauke numfashi ta ce, "Mama duk Labiba ce ta aiko miki da wannan kuɗin da ki ke lissafi?." Mama ta ce, "itace mana, farar haihuwa ba, wallahi itace." Ran Hanan ga ɓaci ta ce, "mu da muke baƙaƙen haihuwar sai a yar damu, kuma duk abinda Labiba zata ba ki a bayan wanda na ba ki yake wallahi. Kuma in kuɗi ne sai na kawo wanda Labiba bata kawo rabinsa ba." Mama ta kalle ta tana murmushi ta ce, "mu gani a ƙasa Hanan. Dah dai kin yi, amma yanzu ƙanwar ki ta wuce ki, ko a hanya baza ku haɗu ba, ta wuce ki tuni wallahi. Madarar kuɗi take aiko min dasu, ba ƙananun kuɗi ba." "Amma kafin ta ba ki ni ce na fara ba ki." "Ke ki ka fara, amma ki ɗauka ba ki yi komai ba, kawai ƴan tsaba ki ka bani, hajiyar tana Jeddah." Hanan ta miƙe ta shige ɗaki, jim kaɗan sai gata ta fito ta fita fuuu cikin ɓacin rai. Adda ta kalli Mama ta ce, "Mama anya hanyar da ki ka ɗora yaran nan zata ɓulle kuwa? Kamar fa kin je ku je ku yi karuwanci....." Mama cikin tsawa ta katse ta ta ce, "Ya isa Sa'ida, ni ban aika yarana da su nemi maza ba, ina ja musu kunne ko yaushe akan raba kansu daga mazan banza. Ni dai na ce su san hanyar da zasu bi su karɓi kuɗi a wajan maza, amma ban da basu kansu." "To yanzu Mama wacce hanya zasu bi su samo kuɗi a wajen maza? Sana'ar me suke yi? Ko kuma mazan da suke basu kuɗin haifarsu suka yi da zasu ɗauki kuɗi haka kawai su basu?." "Soyayya ce zata saka su bayar ba wani abu ba, in kana son mutum dan ka ɗauki abu ka ba shi baka jin komai. Shi ƙaninki meye ba ya yiwa watsatstsiyar yarinyar can? Duk da ya san ta gama watsewa kuɗi yake ɗauka yake bata, saboda yana sonta. Dan kin fifita bare akan jininki, shine za ki ce min wai kamar na aike su karuwanci ne?. Ahir ɗin ki wallahi, kar na sake jin wannan ƙazamar maganar a bakin ki." "Shikenan Mama. Amma ita Labiba a ina take samun kuɗin da take baki haka? Albashin ta bai kai yawan da zata dinga turo miki da manya kuɗi haka ba." "Ke duk duniya akwai wanda ta kai balarabe kyauta ne? In balarabe ya yi miki kyauta sai kin gigice kin fita daga hankalin ki saboda farin ciki da ruɗewa. Balarabe da kyauta, balarabe da kyautatawa mutane, ai wannan hidimar da Labiba take yi min duk cikin kyaututtukan da suke samu ne." Adda ta ce, "ita Islaha bata samun kyautar ne, ko ita Ummansu Safeera ba a bata kuɗin?. Na ji an ce ita wahala ma take sha a gidan da take aikin, ita bata samun kyautar ne?." "Waye zai ɗauki kuɗi ya bawa tsohuwa mai budurwar ƴa kamar Safeera? Kema dai wasa ki ke yi. Ita kuma Islaha zata bani ne? Zan san inda ta samo kuɗin ne balle ta ɗauka ta bani?. Shegiyar yarinya mai zubin mayu." "Labiba ce tawa, ita da yake ni na haife ta gashi ina ganin amfanin haihuwa. Shiyasa hausawa suka ce, ko baka so haifi ka yar." Adda ta yi shiru bata ce komai ba, sai ta miƙe ta nufi wajan Baffa, dan Mama ba ji zata yi ba. A zaune ta same sa yana cin dafaffen zogale, ta zauna ta ce, "Baffa ya ƙarfin jikin?." Baffa ya kalle ta ya ce, "Jiki da sauƙi. Ya na ganki haka?." Adda ta ce, "Baffa haka za a bar Mama tana ɗora Hanan da Labiba akan hanyar da bata dace ba? Ace har faɗa take haɗa yaran nan akan kawo mata kuɗi ta hanyar da bata san ya suke samowa ba?." Baffa ya ce, "babu yadda zan yi, na yi maganar tun ba yanzu ba abin duk a banza. Na yi faɗan, na dake su, na hana fitar amma da yake suna da goyan baya da kanta yake buɗe musu ƙofa su futa. Ta kai ta kawo ko maganata sun daina ji, sai abinda suka ga dama suke yi. Daman Saheer suke  ɗan tsoro, shima yanzu ba wata shakkarsa suke yi ba, dan ta riga ta gama saba musu." Adda ta ce, "abin ya yi yawa Baffa, yanzu Labiba kuɗi take aiko nata dashi ba tare da ta san a inda take samu ba. Na yi magana ta ce wai kyauta ce daga larabawa, wallahi hankalina bai kwanta akan hakan ba. In kyautar ce meyasa Islaha bata samu? Meyasa Umman su Safeera bata samun kyautar?." Baffa ya murmusa ya ce, "a ko da yaushe Islaha itace lalatacciya watsatstsiya a idonta, a idanun mu da idanun kowa na garin nan kuma Islaha itace nutsatstsiya mai hankali. Yaran nata da take gani sune na karki, na tabbatar sune lallatattun." "Ka daina faɗa Baffa, ka cigaba da yi musu addu'a." Ya sauke numfashi ya ce, "Allah ya shirya." Ta amsa da min tana ɗan jansa da hira kafin ta miƙe ta fita. Nana Haleema [7/15, 11:45 AM] KRBBK: RDB2P57 Nana Haleema. Washe gari Islaha ko shirin zuwa gidan Rehaan bata yi ba, gabaɗaya hankalinta yana kan Zainab ta kasa samun nutsuwa. Har mafarki ta yi saboda ta saka a bin a ranta, gani take in wani abun ya samu Zainab itace sila. Ranar ma Maleek da matarsa fita suka yi, tana zaune a falo tana tunani ta ji an shigo, ta ɗaga kai ta kalli wanda ya shigo, kamar yadda tunda ya shigo yana kallon ta. Islaha ta miƙe tsaye bata ce komai ba, shi kuma ya murmusa yana ƙarasowa inda take ya ce, "hii beauty." A ciki ta amsa ya zauna yana kallon ta ya ce, "Na zo na duba ki, ya jikin ki?." Islaha tana daga tsaye ta ce, "Alhamdu lillah, na ji sauƙi sosai "Good. Have a seat" ya faɗa yana nuna mata kusa dashi. Bata zauna ba ta cigaba da tsayuwa ya ce, "Kina da kyau sosai." Ɗan kawar da kai tayi tana haɗe rai cikin takaicinsa. Bata farga ba sai gani ta yi ya tsaya a kusa da ita, ya miƙa mata hannu alamun su gaisa ya ce, "Can i be your friend?." Ta ɗan ja da baya kaɗan ta ce, "Sorry Dr, i'm not interesting. Thank you" tana gama faɗa ta bar wajan cikin jin haushinsa har zuciyarta Shi kam fita ya yi yana neman hanyar da zai bi ya ga Islaha ta saba dashi sosai. Gidan ya koma, ya shiga ɗaki yana kallon window cikin damuwa mai yawa. Sai kuma aka buɗe ƙofar aka shigo, ya juya ya kalli wacce ta shigo ya ga Labiba ce, ya yi tsaki yana kallon ta da yarinyar tana tsaya masa a ransa. Tunda ya ga Islaha ta fara sire masa, amma yana jin daɗin mu'amala da ita sosai. Zama ya yi akan sofa, ta zauna a kusa dashi ta ce, "Me yake damun ka?." Ya gyara zama ya kalle ta ya ce, "Kin san haousemaid ɗin gidan Maleek? Sunanta Islaha, itama ƴar nigeria ce, kuma fulani ce." Gaban Labiba ya faɗi, ta ɗan haɗe rai ta ce, "Eh na santa." Ya yi murmushin jin daɗi ya ce, "Ina sonta, ina son kasancewa da ita, ina jin yanayi mara misaltuwa a akanta. In dai za ki jawo min hankalin ta, zan ba ki kuɗaɗe masu yawa, zan ba ki kuɗin da ban taɓa ba ki kamar su ba." Labiba ta ɓata rai, cikin jin haushin Islaha ta ce, "Ni ba ƙawata ba ce." "Amma za ki iya sakawa ta zo nan, Indai ki za ki saka ta ta zo..." ya dakata ya ɗauko kuɗi masu yawa ya bata ya ce, "zan ƙara miki wasu." Ta kalli kuɗin, ko lokacin da ya fara kwanciya da ita bai bata wannan kuɗin ba, amma gashi yau saboda Islaha yake bata wannan kuɗi masu yawa har yana cewa wai zai ƙara mata. Bata ƙi karɓar kuɗin ba, ta riƙe a hannunta sannan ta ce, "zan yi, amma tana da taurin kai, babu lallai ta amince." "Zan jira, ko yaushe ne indai zata amince. I like her, tana da kyau sosai." Labiba ta girgiza kai sai ta miƙe ta fita. Tana shiga ɗaki ta kira Mama, Mama yana ɗauka ta ce, "Mama sai kin tashi tsaye, balaraben da yake yi min kyauta ya gano Islaha Mama, Shikenan Mama, zai daina bani komai." Daga can ɓangaren Mama ta ce, "ban gane ya gano Islaha ba, a ina ya ganta?." Daidai lokacin Saheer ya kai abinci bakinsa, jin abinda Mama ta ce sai ya tsaya cak ya kasa ci ya zubawa Mama Ido kallon ta. Labiba ta ce, "Ban sani ba Mama, amma shekaran jiya an ganta a motarsa, yau kuma ya zo yana faɗa min indai zan saka ta zo gidansa ta kwana dashi kamar yadda take kwana da saura abokinsa zai bani kuɗi masu yawa. Mama kin ga kuɗin da ya bani saboda ita? Kin ga yawan kuɗin, har yana cewa zai ƙara min in dai ta zo gdain?. Mama shikenan ta mu ta ƙare, don Allah Mama ki yi wani abun." Mama ta ce, "ke dallah kar ki damu, islahan ta isa ta shiga tsakanin mu da arzuƙin mu?. Ki kwantar da hankalin ki, zan yi maganin abin wallahi. Amma in ya ba ki kuɗi akan ki kawo masa ita ki karɓa, amma ko da wasa kar ki bari ta kusanci gidan, ta je ta ƙarata da abokinsa, shi kam ya fi ƙarfinta. Sannan me ya kaita shiga motarsa?." "Mama ko ni ban taɓa shiga ba, amma ita ta shiga. Sai gano su na yi ta camera yana yi mata kiss. Kin san ta da farin jinin maza, inda take aikin ba ki ga yadda mai gidan yake rawar jiki a kanta ba, ita tsabar haɗama namiji ɗaya ya yi mata kaɗan, har wani gidan take zuwa kullum, nan ma ta samo kuɗi. Wallahi Hamma bai yi dacen mata ba, gabaɗaya Islaha ta gama zubar da mutuncinta, ta zama ƴar iska mai lasisi." "Farin jinin samarin banza ba, ai in saurayi na kirki ne bazai kalli Islaha ya ce yana so ba, ke da ganinta ka san babu irin duniyancin da bata aikata ba, yadda idanunta suke a kakkafe akan mutane, babu iskancin da basu gani ba. Yanzu dai ki kwantar da hankalin ki, ta je ta ji da wasu amma wannan na ki ne ke kaɗai, ke kaɗai zai dinga yiwa kyauta, baza ta hana mu rawar gaban hantsi ba." "Kuma Mama ta ci a can, ta ci a nan kenan? Ni ina zuwa gidan da take ne?." "Bar shegiya tsintacciya, zan yi maganin abun." "yauwa Mama, Yanzu zan je na canja kuɗin xuwa naira sai na turo miki." Mama fara saka mata albarka kafin ta kashe wayar. Saheer ya ƙame ya kasa yin komai, ya ajjiye cokalin yana juyasa a plate yana jin duk abinda dukkansu suke faɗa, har wanda Labiba ta faɗa ya ji. Baffa da ya shigo yana tsaye shima duk ya ji abinda ta ce, ya girgiza kai cikin ƙunar zuciya da ɓacin rai ya ce, "a cikin samarin banza da suke kula Islaha, ina so ki san ɗanki ne lamba ɗaya, ɗanki ne babban ɗan iska tunda shine zai aure ta." Mama ta kalli Baffa ta ce, "yanzu ban da lalacewa yana ji an ce ta zama ƴar iskar larabawa sai ya ɗauka ta ya kai gidansa a matsayin mata? Ya aure ta ya ce ya auri me? Gwangwani ko fanko?." Baffa ya girgiza kai yana kallon ta ya ce, "ina guje miki ranar da za ki yi danasani akan harshenki, ranar da rashe zai juye da mujiya, ranar da kalaman bakinki zasu zamar miki izina akan Islaha. In kina da rabo, daga lokacin da fari zai koma baƙi, za ki yi hankali ki san me zaki dinga faɗa a kan ƴaƴan wasu." "ai babu wannan ranar kuwa, yarana na gari ne gaba da baya. Kuma aure tsakanin Saheer da Islaha babu, indai ni na haife sa." Baffa ya gyaɗa kai, ya kalli Saheer ya ce, "Kai Saheer ba dai ginin gidan ka ya kammala ba?." Cikin wani yanayi na damuwa ya ce, "saura kaɗan Baffa, an gama komai, kawai kayan wuta za a saka." Baffa ya kalle sa ya ce, "zan yi waya da Islahan,  juma'ar jibi za a ɗaura auren ka da ita in sha Allah, in ya so duk ranar da ta dawo nigeria sai ta tare." Mama ta miƙe ta ce, "a ɗaura aurensa da wa, Ragowar wasu mazan? Ai wallahi indai ina da rai bai isa ya auri yarinyar nan ba, in ka ga na bari ya auri Islaha, to ka ɗauka bana numfashi!." Baffa ya murmusa, ya kalli Saheer ya ce, "Saheer kira min Islaha a waya." Saheer ya ce, "Baffa ka kwantar da hankalin ka, ka ga ba wata lafiyar kirki ka ke da ita ba, kuma ba a son abinda zai saka ka a damuwa, ka yi haƙuri." Baffa ya ce, "ni ba a damuwa nake ba Saheer, ka kira min wayar Islaha kawai." Saheer ya sauke numfashi ya kira lambar Islaha ta ƙasar Saudia amma bata ɗauka ba, ya sake kiranta ta whatsapp amma bata ɗauka ba. Saheer ya ce, "Bata ɗauka ba Baffa." Baffa ya ce, "sake kiran ta." Saheer bai musa ba ya kuma kira amma bata ɗauka ba. Ya kalli Baffa ya ce, "bata ɗauka ba Baffa." Baffa ya ce, "daga nan zuwa ko yaushe indai ta ɗauka ka sanar dani, ni Mustapha Maddibo, na rantse da girman Allah, daga yanzu zuwa sallar azahar, indai har Islaha ta ɗauki waya mun yi magana da ita, ba za a ƙara mintina goma ba sai ta zama matar Saheer. Daga lokacin da igiyoyin auren ɗanki suka ɗaure Islaha, sai zubawa kan ki fetur ki ƙona kan ki da kanki. In kin ga hakan bai faru ba, ki ɗauka kawai Islaha bata ɗauki wayar nan ba, amma indai ta ɗauka sai na nuna miki ni ne uban Saheer!...." Baffa ya juyo a fusace ya kalli Saheer ya ce, "mu je" ya faɗa yana kallonsa suka fita daga falon. Mama ta da ki kujera ta ce, "in ɗana Saheer ya auri Islaha Allah ya tsine min albarka, wallahi sai dai duk abinda zai faru ya faru, amma bazan taɓa bari Saheer ya auri Islaha ba!" Tana faɗa ta shiga ɗaki dan nemo mafita. Baffa bayan sun fita ya kalli Saheer ya ce, "ba ka gama haɗa lefen ba?." Saheer ye ce, "an gama Baffa, daman kuɗin aikin ka ne ya tsayar da komai. Amma ka yi haƙuri kar ka yanke hukunci cikin fushi, ka kwnatar da hankalinka saboda lafiyar ka." Baffa ya kalle shi ya ce, "kana son Islaha ko babarka ta saka maka zargi ta?." Ya girgiza kai ya ce, "Har abada bazan taɓa zargin Islaha ba, na san halinta fiye da kowa." "Kana sonta ko baka so?. "Baffa kaima ka san amsa ta akan hakan." "Ka shirya karɓar aurenta a yau?." "Ko yanzu ne a shirye nake?." "Za ka iya jira har sai ta dawo da auren ka akanta ko baza ka iya ba?." Ya sauke numfashi ya ce, "akwai yarda a tsakanina da ita, wallahi ko shekara dubu zata yi da aurena a kanta zan jira har ta dawo." Baffa ya murmusa ya ce, "da zarar ta kira ka ka sanar dani, zamu yi magana da ita, bana so na yanke hukunci ya zama kamar ban kyauta mata ba. Amma da yanzu yadda zan fita masallacin nan, wallahi bazan dawo ba sai igiyoyin auren ka uku sun hau kanta, daga nan sai babarka ta saka bindiga ta kashe kanta." Saheer ya murmusa, wani irin daɗi yana mamamaye masa zuciya, Allah Allah yake ya fita ya sake kiran Islaha. Baffa ya ce, "Jeka, in ka same ta kazo ka haɗa mu." Ya gyaɗa kai ya fita yana sake kiran wayarta amma bata ɗauka. Ji yake kamar ya shiga cikin wayar ya jawota ta ɗauki wayar, gabaɗaya zumuɗi da shauƙin aura masa ita a ranar ya cika masa zuciya. (Tofa, ana wata ga wata🤣) ••••••• Islaha lokacin da Saheer yake yi mata waya suna kitchen ita da Sunaira, ta bar wayar a ɗaki bata san yana kira ba. Sallar la'asar ce ta shigar da ita ciki, kuma bata kalli wayar ba ta yi alwala ta yi sallah ta zauna tana azkhar. Har biyar na yamma tana zaune, Sunaira ta shigo ta yi mata tayin fita su je Mall su dawo, Islaha ta amsa ta miƙe ta saka hijjab suka fita. A ƙasa suke tafiya a hankali, ba hira suke yi ba dan ko wanne bai iya yareen wani ba, har gwara Islaha yanza ta ɗan iya ƙananun abubuwa a kalmar larabci. Islaha kallon estate ɗin take yi sosai, ya tsaru iya tsaruwa, kai ba sai an faɗa maka gidan da suke wajan suna da tsada ba. Sai da suka yi nisa suka hau mota suka tafi. Sai da suka shiga mota ta tuna ta bar wayar ta a gidan, ta ji haushi sosai dan ta so ta ɗan yi video ta samu na streaks. Waye mai nasara? Daada ce ko Baffa?. Nana Haleema✍🏻❤️ [7/15, 11:52 AM] KRBBK: RDB2P58 Nana Haleema. Islaha basu dawo ba sai magrib, a ƙofar gidan Rehaan motar ta ajjiye su, ta harari gidan cikin jin haushin mai gidan da abokinsa, suka shiga ciki suna ajjiye komai a mazauninsa. Sai da ta yi sallah sannan ta ɗauki wayarta, ta wara ido ganin kiran Hamma babu adadi. Da hanzari ta kira sa, ta yi ringing bai ɗauka ba har ta katse. A bayyane ta ce, "Allah ya sa ba laifi na yi masa ya ƙi ɗauka ba." Kafin ya kira ta sai ga kiran Umma, Islaha ta ɗauka da sallama ta ce, "Umma ina yini." Umma a sanyaye ta ce, "Lafiya Lau Islaha, ya zaman Jeddah?." "Lafiya lau Umma." "Ya ƙawar ki? Kuna waya kuwa?." "Eh muna gaisawa, bata kira ki ba?." "tunda na zo sau biyu kawai muka yi waya. Islaha zaman ƙasar nan gabaɗaya ya ishe ni, ina so na samu hanyar da zan koma gida, amma abin ya ci tura." Islaha ta sauke nunfashi ta ce, "Ina so nazo na gan ki Umma, na yiwa Safeera alƙawarin an ba ki kulawa daidai ƙarfina. Ina so na zo ban san yaushe ba, kuma ban san a inda ki ke ba." Umma ta ji daɗi ya mamaye ta, ta ji kamar an ce Islahan ta zo, ta ce, "Allah ya kawo ki Islaha, sunan unguwar wai Khadiyya, in ki ka shigo sai ki kira ni, an koya min yadda ake tura location ta whatsapp." Jin yadda Umman take murna daga cewa zata zo sai zuciyar Islaha ta karye, ta ji ranta dole ma ta je Madina ganin Umma. Ta ce, "zan zo in sha Allah Umma." Umma ta ce, "na gode Safeer....su Islaha, sai na ganki." Daga nan suka yi sallama ta kashe wayar. Tana kashewa kiram Saheer ya shigo, tana ɗauka ya ce, "ina ki ka shiga ne? Tun ɗazu nake yi miki waya bakya ɗauka." "Ban ga kiran ba sai yanzu, dan yanzu na dawo daga mall, sallah kawai na yi." "Baffa ne yake son magana dake tun ɗazu." "Wallahi ban gani ba, yana ina yanzu? Ka haɗa ni dashi." "lokacin sallar magriba ya taho, kin san da huri yake shiga masallaci." "amma ban ji daɗi ba." "kin san meyasa yake neman ki?." Kamar tana gabansa ta girgiza kai alamun a'a ta ce, "ban sani ba." Ya ce, "bara na kira ki video call." Bai jira me zata ce ba ya yanke wayar, ya kira ta ajjiye wayar tana kallonsa, ta ɗan yi murmushi ta ce, "Hamma kullum ƙara kyau ka ke yi, meye sirrin?." Ya yi murmushin da yake ƙara masa kyau, ya ɗan girgiza kai yana kallon ta da fararen idanunsa ya ce, "ni ba ta wannan tsokanar ta ki bake yi ba, Kin san meyasa Baffa yake neman ki?." "sai ka faɗa Hamma." Ya yi murmushi yana shafa kansa yana kallon ta cikin shauƙi mai yawa, iya faɗa mata maganar da zai yi ma shauƙi yake ji, ina ga an ɗaura kuma?. Islaha ta shagwaɓe fuska jin ya ƙi faɗa mata, ta ce, "ka faɗa min mana." Ya ce, "Da ace ɗazu kin ɗauki wayar, daman tambayar ki zai yi, in za ki amince a ɗazun za a ɗaura aurenmu dake bayan sallar azahar. Shiyasa na dinga jera miki kira amma amma ban same ki ba, wallahi ji na yi kamar na zo na ɗauko ki." Haka kawai ta ji gabanta ya faɗi matuƙa ta buɗe ido waje tana dafe ƙirji ta ce, "Aure Hamma!." Shima ya buɗe ido kamar yadda ta yiya ce, "Eh mana." Islaha ta ce, "da gaske ka ke?." "Na taɓa yi miki wannan wasan?." "Baka taɓa ba, abin ne na ji sa har jinina, wallahi gabana sai faɗuwa yake yi." Ya harare ta ya ce, "Meye na faɗuwar gaban? Bakya son auren nawa ne?." Ta girgiza kai ta ce, "Abin ne yazo min coincidences, ban taɓa tunanin hakan ba shiyasa. Kuma da gaske Baffa yake?." "Wallahi da ɗazu da kin ɗauki wayar da na yi miki, kin kuma amince, da yanzu kin zama matar Saheer" ya faɗa yana zuba mata ido. Sai kallon ya yi mata nauyi sosai, ta sauke ido ƙasa tana wasa da abin hannun da ya bata. Saheer ya bita da kallon mamaki ya ce, "Hmm! Da ace Baffan ma ya yi magana dake cewa za ki yi ba ki amince ba ko?." Ta ɗago ta kalle sa tana zaro idanu ta ce, "Ni haka na ce?." "Gashin nan kin zama wani iri daga ba ki labari." "Kawai jikina ne ya yi sanyi, amma da a guje zan amince." "Meye na sanyin jikin? Aure fa kawai za a ɗaura, kina nan Jeddah ina Nigeria. Sai kin dawo sannan za a yi biki." Ta sauke kai ƙasa ta ce, "Hamma duk inda aka ce za a ɗaura aure, ai dole jiki mace ya yi sanyi." "yanzu in ya tambaye ki me za ki ce? Kin amince a ɗaura yanzu ko sai kin dawo?." Yadda ya zuba mata ido ya saka ta kasa cewa komai, in dai a ra'ayinta ne baza ta yarda a ɗaura mata aure yanzu ba gaskiya, ta fi so sai ta gama komai da yake gabanta, dan ta san halin Hamma da kishi, in aurensa ya hau kanta wani abun bazai bar ta ta yi ba, musamman ɓangaren da Barr zai shigo ciki. Amma baza ta iya ƙin amincewa ba, zata amince ko dan saboda Hamman yana so, daga jin yadda yake bata labari cikin zumuɗi ta san ya ji daɗin maganar sosai. "Beddo am!." Ta kalle sa ya ce, "Tunani ki ke yi akan za ki amince ko baza ki amince ba?." Ta yi murmushin dole ta ce, "A'a, kawai ina tunanin yadda zan fara rayuwa da auren ka a kaina a ƙasar nan ne, dan ni na hango har an ɗaura auren." Sai kuwa fuskarsa ta washe, annuri da farin ciki suka bayyana akan fuskarsa sosai. Ya gyara zama ya ce, "Ni kaina ina lissafin yadda zan ji kewar matata a kusa dani, har na siyi bankin da zan fara tara kuɗin da zan zo Saudia wajan matata." Ta yi dariya sosai, shima dariyar ya yi ya ce, "Ni dai kar ki kwafsa min, in Baffa ya tambaye ki ki tausaya min ki amince don Allah. Haɗuwa ta gaba ina so ya kasance da aurena a kan ki, yadda zan nuna miki adadin kewar ki da na yi ba tare da kin ce, Hamma babu kyau fa" ya ƙarasa faɗa yana kwaikwayon muryarta. Dariya ta yi sosai tana rufe fuska da hannunta, ya yi murmushi yana kallon kyawawan hannayenta marasa kauri dogaye. Cikin sanyin murya ya ce, "ƙarya na yi, ba haka ki ke faɗa ba?." Ta cire hannunta tana sunkuyar da kai tana murmushi ta ce, "Amma meyasa Baffa ya ke son a ɗaura aurenmu a yau?." "Mama ce wallahi, itace ta tunzura shi har ya yanke hukunci.....Islaha ana kiran sallah, in an idar zan kira na haɗa ki da Baffan." Ta amsa da to ya kashe wayar. Ta jingina da gado tana tunanin wannan sabuwar chakwakiyar da ta kawo mata kai, Allah ya sani bata ra'ayin wedding fatiha before ceremony. Kuma ana ɗaura auren nan takura ta Hamma zai yi, duk da bashi da matsala da aikin ta amma akwai mutanen da zai iya hanata magana dasu, kuma dole ta hanu tunda matarsa ce. Kuma yadda yake nuna shauƙinta a kwanakin nan bazai iya barinta har sai an yi biki bai yi mata komai ba, ita kuma bata son hakan Allah ya sani. Tana wannan tunanin aka yi sallar i'sha. Ta san daman bazai kira ta ba sai bayan sallar i'sha ta nigeria, saboda Baffa ba ya dawowa daga masallaci sai ya yi sallar i'sha. Ko ya wayarta ta yi ƙara sai gabanta ya faɗi, gabaɗaya bata so kiran Saheer ya shigo kwata kwata, dan bata son ya haɗa ta waya da Baffa. A haka ta miƙe ta je suka ci abinci dan har lokacin matar gidan basu dawo ba. Ƙarfe sha ɗaya na Saudia, wanda ya yi daidai da tara na Nigeria. kiran Saherr ya shigo, tana kalla gabanta ya faɗi ta ji kamar kar ta ɗauka, ta runtse ido ta buɗe, ta ɗauki wayar a sanyaye ta sama a kunne. Tana sakawa a kunne Baffa ya ce, "Islaha." Ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ta ɗan runtse ido sannan ta ce, "Baffa barka da dare." "Barka dai Islaha, ya aiki?." "Alhamdu lillah, ya ƙarfin jiki?." "Jiki ya warware Islaha." "Allah ya ƙara lafiya." "Amin Islaha, yaushe ne dawowar ta ki?." Islaha ta ce, "na kusa in sha Allah." Baffa ya murmusa ya ce, "Allah ya dawo dake lafiya." Ta amsa da amin sannan ya ce, "Islaha wani hukunci nake so na yanke a kan ki da Hamman ki, shine na kira na ji ra'ayin ki a kai." Islaha ta ce, "Baffa kana da dama da ikon yanke ko wanne hukunci a kaina, ba sai ka tambaye ni ba, kawai ka yanke min hukunci a matsayin ka na uba a gare ni." "Na sani Islaha, na san na isa dake gaba da baya. Amma hakan bazai saka na tauye ki ba, dan kina yi min biyayya hakan bazai saka na cutar da rayuwar ki ba. Ki faɗa min ra'ayin ki, kina so a ɗaura auren yanzu ko sai kin dawo?." "Baffa wallahi na ba ka zaɓi, ka zaɓa min abinda ka ga ya yi daidai dani." Baffa ya yi murmushi mai sauti, ya ce, "baza ki zaɓa ɗin ba ko?." Islaha kamar tana kusa dashi, ta sake sunkuyar kai ta ce, "Baffa ka zaɓa min kawai, na san baza ka yi min abinda zai cutar dani ba." Baffa ya yi murmushi cikin jin daɗi da farin ciki ta ce, "Shikenan Islaha. In Allah ya nuna mana jibi juma'a, bayan sallar juma'a za a ɗaura auren ki da Saheer. Hakan ya yi miki?." Gabanta ya faɗi, ta runtse ido ta ce, "Ya yi Baffa. Allah ya nuna mana, Allah ya ƙara maka lafiya da tsahon rai mai amfani." "Amin Islaha. Allah ya yi miki albarka, ya cigaba da ba ki kariya a duk inda ki ke." Ta amsa da amin kafin su kashe wayar. Baffa yana kashe wayar ya kalli Saheer da yake kusa dashi, ya yi murmushin jin daɗi ya ce, "Yarinya mai tarbiyya, ina ji a raina ina Islaha ƴata ce, ina ma ni ne na haife ta." Saheer ya murmusa yana ji kamar ya miƙe ya taka rawa saboda murna, ji yake kamar ya jawo jibi ta zo Islaha ta zama mallakinsa. Baffa ya ce, "gobe zan aika ka a siyo goro da alewa na ɗaurin aure, jibi babu abinda zai saka a dakata daga ɗaura muku aure in sha Allah." Ya yi murmushin jin daɗi da farin ciki ya ce, "Allah ya kaimu Baffa." Baffa ya ce, "Amin. Ka je ka sanar da waɗanda zaka sanar, dan lokacin ya ƙure ba sai an yi gayya gagaruma ba, in bikin ya zo sai a yi taro." Cikin zumuɗi ya miƙe, yana ji kamar ya rungume Baffa dan daɗi da farin ciki. Saheer yana fitowa suka haɗu da Mama a tsaye da alama ta ji komai. Ya sunkuyar da kai ita kuma ta ce, "biyo ni." Ƙirjinsa ya buga da ƙarfi, ya bita a sanyaye zuwa falon ta. Suna shiga ta juyo ta kalle sa ta ce, "Ban amince da auren Islaha ba, ban amince ka aure ta ba Saheer. Ka je ka samu mahaifinka, ka faɗa masa baza ka aure ta ba." Ya buɗe ba ki zai yi magana ta ce, "Wallahi in ka amince da auren nan sai na tsine maka, ka ji na ce wallahi, babu abinda zai saka na dakata dafa tsine maka albarka Saheer, in kana ganin bazan iya ba ka aikata Saheer!." Saheer ya zare ido yana kallon Mama jin abinda take faɗa, ya haɗɗiye yawu daƙyar, yana ji idanunsa suna cikowa da ruwa, ya buɗe baki zai yi magana ta ce, "kar ka ce min komai, ikon da nake dashi a kanka nake so na gani. In har kana jin tsoron bakin uwa kar ka amince, in kuma baka jin tsoro tsinuwata ka aure ta ka ji!" Tana gama faɗar hakan ta shiga ɗaki. Saheer ya bi ta da kallo, yana ji zuciyarsa tana girgiɗi kamar zata faɗo daga ƙirjinsa, ya sauke numfashi mai tsaho, yana ji kamar wuta ce a kusa dashi saboda tiririn sa yake ji, ya ja ƙafarsa daƙyar ya fita daga falon, yana ji kamar ya yi kuka..... Ga ƙoshi, ga kwanan yunwa😩🤭🤣 [7/16, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P59 Nana Haleema. Saheer a sanyaye ya fita ƙofar gida, ya tarar da Sadik a zaune a mota yana jiransa, ya shiga motar yana jan numfashi mai tsaho. Sadik bai kula da yanayin da yake ciki ba ya ce, "An kawo kaya, zamu tura zuwa inda ya kamata. Ka ga list ɗin mutanen da...." Maganar Sadik ta maƙale ganin ko kallonsa ma ba ya yi. Sadik ya ce, "Yane?." "Akan maganar ɗaurin auren nan ne." "Ba ka son auren nata ne kuma ko meye?." Ya kalle sa ya ce, "a duniya akwai mai son auren Islaha in ba ni ba?." Sadik ya ce, "to meye na damuwa akan hakan?." Ya sauke numfashi ya ce, "Islaha ta amince auren....." Sadik ya tari numfashinsa, bai bari ya ƙarasa ba ya ce, "daman ya za a yi ta ƙi amincewa? Ai dole ma ta amince da auren, tunda ta gama...." Cikin tsawa ya ce, "ya ishe ka malam!." Sadik ya murmusa ya ce, "to na yi shiru, ina ji." Ya yi masa banza ya ƙi magana, Sadik ya yi dariya ya ce, "ina da abin yi, in baza ka faɗa ba na kama gabana." Saheer ya sauke numfashi ya ce, "Baffa ya ce jibi za a ɗaura aurena da ita, Mama kuma ta ce indai aka ɗaura auren sai ta tsine min." Sadik ya zaro ido cikin kiɗima da mamaki ya ce, "kai! Abin har ya kai ga haka?." Saheer bai ce komai ba sai lumshe ido da ya yi ya buɗe sannan ya ce, "ban sani ba, ban san me zan yi ba yanzu." Sadik ya ce, "Haƙura za a yi zuwa lokacin da zata janye kalamanta, ai ba a yi auren ka Islaha tana wannan fushin ba, ga furucin da ta yi a kan ka, dole sai mun jira ta janye sai a san abinda ya kamata ayi." Saheer ya ɗan ɗaga kai ya ce, "Sai abinda Baffa ya ce, ni wallahi kam kaina ya kulle." Sadik ya ce, "Dole kan ka ya kulle, kana son Islaha, ga damar aurenta ka samu, amma Mama ta hana. Sai haƙuri, ka cigaba da addu'a kawai." Saheer ya yi shiru yana kallon ƙasa, ya rufe ido ya buɗe zuciyarsa tana bugawa da sauri sauri. Ya kalli Sadik ya ce, "Ina son Islaha Sadik, rasata daidai yake da rasa rayuwata gabaɗaya." Sadik ya ce, "Haka zalika Mama mahaifiyarka ce, tsinuwar ta daidai yake da tarwatsewar rayuwar ka." "Na sani, ba ina nufin na zaɓi Islaha akan Mama ba, kawai dai ina faɗa maka yadda nake sonta, in na rasata ban san wanne hali zan shiga ba." Sadik ya taɓe baki, dan shi gabaɗaya Islaha ta sire masa, da abokinsa zai yarda ma da ya ce masa ya nemi wata wallahi. Bai yarda da ita ba, akwai abubuwan da take ɓoyewa, kuma tana da ɓoyayyiyar ɗabi'a wacce bata so a san da ita. Saheer bai kuma cewa komai ba ya fita, Sadik ya yi murmushi ya ɗauki waya yana dannawa yana jin daɗi, a bayyane ya ce, "Auren babu lallai ya yu, ni daman na fi son haka wallahi, dan zaman sa da Islaha ƴar ƙaramar matsala" yana gama faɗar hakan ya ajjiye wayarsa ya ja mota ya tafi.                 ••••••• Islaha tunda Baffa ya kashe wayar take jingine da gado cikin sanyin jiki, a kasa motsawa saboda rashin ƙarfin jikinta. Ta kasa yarda jibi juma'a za a ɗaura mata aure, ta kasa amincewa igiyar auren Hamma har guda uku zasu hau kanta nan da wasu awanni masu zuwa. Bawai bata son Hamma bane, tana sonsa so na tsakani da Allah, kawai bata shirya aurensa a lokacin bane, ta fi so sai ta gama abubuwan da suke gabanta, sai auren ya biyo baya. Ta zame ta kwanta a wajan tana tunani, tana so ta faɗawa Safeera amma sai ta ji baza ta iya ba, ta yi shiru cikin tunanin da bata san dalilinsa ba. Ta yi tunanin Saheer zai kira ta, amma sai ta ji shiru, hakan ya yi mata daɗi sai ta ji bata so ma ya kira wayar ta Sai dare mutanen gidan suka dawo, aka kira ta suka bata tsarabar doguwar riga baƙa mai kyau irin ta larabawa. Ta je ta ajjiye a ɗaki tana tunanin halin da Zainab take ciki, da kuma auren da Baffa zai ɗaura mata. Washe gari bayan ta gama komai ta yi nufin zuwa gidan Rehaan, duk da bata so amma tana son samun kuɗi, tana ji a jikinta dole ta je ko dan kuɗin da take so ta haɗa ta bashi ta bar ƙasar da wuri. Ko dan saboda Zainab dole ta dage da neman kuɗi, dan hankalinta ya yi kan ta koma fa je ta ga halin da take ciki. Tana typing code ɗin ƙofar ta buɗe, ta shiga a hankali da sallama. Babu kowa a a falon hakan ya saka ta wuce kitchen. Sai da ta tsorata ganin Jazy a tsaye ya ɗora mai akan wuta zai soya irish. Ya juyo suka haɗa ido ya ce, "Miss Islaha, ƙaraso mana." Ta shigo a hankali ta kalle sa, kamar bazata yi magana ba sai ta ce, "ina yini." Ya juyo ya kalle ta ya ce, "jiya sai ki ka ƙi zuwa, ina ta jiran zuwan ki." Bata ce komai ba, ya miƙa serving spoon ɗin da yake juya dankalin dankalin ya ce, "za ki iya taimaka min?." Ta gyaɗa kai ta karɓa, shi kuma ya ɗan matsa gefe ya ce, "na gode" ya faɗa ana fita daga kitchen ɗin. Ta bi sa da kallo dan gabaɗaya ƙhamahinsa ya mamaye kitchen ɗin. A bayyane ta ce, "Ka rasa turaren dubu nawa suke siya, turare ya maƙale ko ina kamar yanzu aka saka" ta faɗa tana zuba dankalin a mai. Man ya yi zafi sosai, hakan ya saka ya taso sama, ya yi hayaƙin da ya shiga hancinta kai tsaye ya sarƙe ta. Ta ɗan ja baya da sauri ta fara tari, ta ɗauka abin kaɗan ne tunda hayaƙin bai kai ya sarƙe ta haka ba, sai ta ji numfashinta yana neman tsayawa, ta miƙa hannu ta kashe wutar stove ɗin, ta fito ta zauna a falon tana jan numfashi da ƙarfi. Ta sama Jazy ya hango ta ta fitoc ganin yadda numfashinta yake sauka sai ya sakko da sauri, ya ɗauki ruwa ya ƙarasa inda ta ke ya ce, "Sannu, ki nutsu." A hankali take jan numfashin yana sauka a hankali, a hankali nunfashinta ya dawo daidai, ta saka hannu ta kwance roll ɗin kanta ta bar mayafin a kanta bai cire gabaɗaya ba. Ya bata ruwa ya ce, "karɓi ki sha." Ta karɓa a hankali ta sha, ta jingina da bango kujera tana lumshe ido cikin wani irin yanayi mara daɗi. Sai da ya ga ta nutsu sosai sannan ya ce, "kina da asthma ne?." Ta ɗan sauke nunafshi tana ɗaga kai alamun tana da ita, ya ce, "ban sani ba, da ban baki aikin da zai saka ki sanu attack ba." Ta ɗan sauke numfashi ta ce, "ina yin aiki sosai, yau an samu incidence ne kawai." "Sannu. Ina inhaler ɗin ki? Meyasa bakya yawo dashi?." "Na manta shi." "Meyasa?." "Ba a tabbtaar da akwai asthma ɗin ba sai few days back, a nigeria an ce babu, amma a nan ance akwai itama babu yawa, tana first stage. Ban saba da yawo dashi ba, shiyasa ban ɗauko ba." Ya ɗan girgiza kai yana kallon ta, ita kuma ta miƙe ta ce, "zan ƙarasa." Ya dakatar da ita ya ce, "A'a ki bar shi, na gode." Bata zauna ba tana tsaye, ya kalle ta ya ce, "Dawo ki zauna." Ta zauna a hankali tana sunkuyar da kanta. Ya sauke numfashi ya ce, "zan iya tambayar ki?." Ta ɗaga kai alamun eh za iya, Jazy ya ce, "kuma za ki faɗa min gaskiya?." Nan ma ta ɗaga kai alamun eh. Ya ɗan girgiza kai yana kallon ta kafin ya ce, "Wanne irin aiki ne ya kawo ki ƙasar nan?." Ta ɗago suka haɗa ido sannan ta ce, "ga shi nazo gidan nan ina yi." "Dalilin zuwan naki nake so na ji. Na bibiyi contents ɗinki daga shekaran jiya zuwa yau, na bibiyi na dah dana yanzu, kuma na ga har tattaunawa kin taɓa yi akan disadvantges na aiko yara aiki wata ƙasa. Yanayin kalaman ki yana nuni da bai kamata a dinga tura yaran ba aiki irin wannan ba, hakan sai ya tabbatar min da ba ƙaramin dalili ne ya kawo ki nan ba. Miss Islaha Ina so na san dalilin ki na fara aiki a nan." Ta ɗaga kai ta kalle sa tana gyara mayafinta da yake son zamewa, ta ɗan sauke numfashi ta ce, "ni dai na san ban zo saboda bibiyar abokin ka ba, dan ban san zan haɗu dashi a nan ba, na zo da niyar na samu kuɗi kawai, ban san yana zuwa Jeddah ba balle na san gidan nan." Ya gyaɗa kai ya ce, "na san ba ki san shi ba, na ji kin ce silar zuwan ki yana da alaƙa dashi ne, shiyasa nake so na sani." Ta sauke numfashi ta ce, "in na faɗa maka babu lallai ka yarda." Ya ɗan yi murmushi ya ce, "Na yi bincike a kan ki, na san komai na ki Islaha. Halayen ki, da wanda za ki aura, ƙawar ki, wajen aikin ki, inda ki ka taso, da komai na sani. Zan yarda da duk abinda za ki faɗa min, in bazan yarda dake ba bazan ce ki faɗa ba." "Meyasa baka bincika ka san dalilin zuwana nan ɗin ba? Yadda ka san komai a kaina shima ya kamata ka nemo ka sani, Mr Jafar." "Ina so na ji daga bakin ki, ki faɗa min Miss Islaha." Ta ɗan yi shiru kamar bazata ce komai ba, sai kuma ta ce, "Na faɗa maka ya sace ni daman, a lokacin da ya sace ni ni kuma mahaifina yana Nadira hospital da yake Yola, za a yi nasa dashen ƙoda, ana neman kuɗin har miliyan goma sha biyu, ban da ƙananun abubuwa da aka kashe a asibitin. Ana tsaka da neman kuɗin aikin Baffa sai ya sace ni, ya kaini aka ajjiye ni a wani gida, sai dai a buɗe ni a bani abinci a rufe. Da na ga ji sai na nemi ganinsa, muka haɗu na nemi ya ƙyale ni sai yake nuna kamar sai na basa haƙuri." Ta dakata tana turo baki tana kallon Jazy ta ce, "Haka kawai ban yi masa laifi ba haƙurin me zan ba shi?." Ya ɗan girgiza kai bai ce komai ba yana kallon ta. Ta ce, "Ni kuma na ƙi ba da haƙuri, daga ƙarshe da na dinga mafarkin Baffa ya mutu na haƙura na bashi haƙuri, amma ba akan laifin da ya yi min ba, sai dan dalilin Baffa. Rana tsaka ya aiko wanda yake bani abinci ya ce za a kai ni gida. Ni kuma a lokacin ina falon sa, ina ta tunanin kuɗin aikin Baffa da nake mafarki har Baffa ya mutu saboda rashin kuɗin. Kawai sai na ga kuɗi akan sofa a ajjiye, kuɗi ne masu yawa har rafar dala guda biyu....." Sai ta dakata bata cigaba ba dan bata san ya zai ɗauki maganar ba. Jazy yadda take naganar dariya take bashi sosai, a nutse take maganar amma cikin shagwaɓa da nuna zallar gaskiya akan maganar. Ganin ta yi shiru sai ya ce, "ina jin ki." "Ni kuma a lokacin ban san me ya shiga kaina ba, rashin mafita ya ja ni, tunanin halin da Baffa yake ciki ya rufe min ido, na kasa tunanin abinda zan yi ba daidai bane, kawai na ɗauki rafa ɗaya...." Jazy ya wani ya zaro ido, sai ta yi sauri girgiza hannu ta ce, "wallahi ba sata na yi ba, bashi na ɗauka, kuma na ce zan biya sa." Jazy ya murmusa ganin yadda ta ruɗe wai ba sata ta yi ba, Islaha ta ce, "har camera falon na kalla na faɗa masa ni ban saci kuɗinsa ba, rashin mafita ne ya saka na ɗauka saboda na biya kuɗin aikin Babana. A lokacin ban san me ya shiga kaina ba, amma wallahi ban taɓa ɗaukar abin wani ba, shima ban san meyasa na yi ba a wannan lokacin. Tunda na ɗauki kuɗinsa na je aka biya kuɗin aikin sai na kasa nutsuwa, da ina da burin na kai ƙarar sa gaban hukuma, saboda a bi min haƙƙina na sace ni da ya yi ban yi masa komai ba, amma saboda kuɗinsa ya saka na fasa" ta ƙarasa faɗa tana wani karyar da murya. "Ina ji" Jazy ya faɗa yana murmushi dan shi wallahi dariya take bashi. Islaha ta ce, "tun daga ranar sai na fara mafarki akan kuɗinsa, ko yaushe in na kwanta sai na ga yana cewa na biya sa kuɗinsa. Ƙawata ta ce min sata na yi ba bashi bane, hankalina sai ya tashi, na fara neman hanyar da zan biya bashin. Na yi tunanin shiga film ta hana ni, sai kawai na yanke shawarar zuwa nan, dan kawai na tara kuɗi na biya sa bashin da na ɗauko. Bayan wannan ni babu wani abu a raina wallahi, ko sunansa ban sani ba." Ya sauke numfashi yana wani irin murmushi ya ce, "Miss Islaha." Ta ɗaga kai ta kalle sa suka haɗa ido, ya ɗan girgiza kai ya ce, "You are so funny." "Ba wasa nake yi maka ba, da gaske ne abinda na faɗa." "Na san da gaske ki ke, kin bani dariya ne kawai." Ta ɗan sauke numfashi ta ce, "ban san tsautsayin da ya sake haɗa ni dashi a nan ba, dan ni mugun haushinsa nake ji sosai wallahi. Ina zama a nan ne dan na tara kuɗi na biyasa, daga nan na kai ƙarar sa a bi min haƙƙina, dan bazan bar case ɗin sace ni ya sha ruwa ba." Ya yi dariya mai sauti, dan wallahi ƙyalƙyala dariya yake so ya yi, kawai ba ya son zubar da ajinsa ne. Ya ce, "Miss Islaha yanzu kin fara tara masa kuɗin na sa?." Ta ɗaga kai ta ce, "na fara." "Nawa ki ka tara?." Ta ɗago tana kallonsa, sai kuma ta chunkushe fuska ta ce, "basu da yawa, riyal dubu takwas ne, dubu bakwai a ciki....." sai ta dakata tana jin haushin abinda zata ce. Sai kuma ta sake kallonsa ta ce, "dubu bakwai a ciki, shine ya bani." Jazy ya ƙyalƙyale da dariyar da take damunsa, yadda ta yi maganar ya bashi dariya matuƙa, ya yi dariya son ransa yana kallon ta ganin ta sake haɗe rai. Ya dakata ya ce, "i'm sorry Miss, abin ne ya bani dariya sosai. Ya sace ki, kuma ki ka saci...." Ta dakatar dashi ta ce, "bashi ne, ni ba sata na yi ba." "Oh Sorry, kin ci bashin sa, kuma shine yake ba li kuɗin da zaki fara biyansa?." Ta kawar da kai ta ce, "ai ba kyauta ya bani ba, aiki na yi masa ya biya ni kuɗin aikina." Har lokacin murmushi yake yi yana kallonta, ya ɗan girgiza kai ya ce, "Kina da sa'a Miss." Ta ɗago ido tana kallon Jazy ta ce, "dan ya bani kuɗin?." Ya girgiza kai ya ce, "haɗuwa dashi gabaɗaya sa a ce." "Rashinta dai, ni a wajena rashin sa'a ne. Na faɗa maka gaskiya Mr Jafar? Wallahi babu wanda nake jin haushinsa kamar sa." Ya ɗan yi clapping hannunsa yana gyaɗa kai ya ce, "So ya batun interview ki da Mr Rehaan Yola?....." ya faɗa yana kallom ta yana so ya ji me zata ce. Nana Haleema. [7/16, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P60 Nana Haleema. Islaha ta kalle sa tana girgiza kai ta ce, "wannan yana hannunka, kai ka yi alƙawari akan hakan." Jafar ya ce, "To ai yanzu ai kina Jeddah, bakya Yola." "Zan koma, in sha Allah." Ya gyaɗa kai ya ce, "ai yanzu kema kin san shi, bakya buƙatar taimakona. Kina da damar da za ki bashi invitation ke da shi." Da mamaki take kallonsa ta ce, "A ina na san shi ɗin? Ni fa ban san shi ba, ban taɓa ganinsa ba har yanzu." Ya ɗan yi murmushi kaɗan yana girgiza kai cike da mamaki ya ce, "Unbelievable!." Ya sake kallon ta sannan ya ce, "Wanda ku ka haɗu a diamond hotel, ku ka haɗu a asibiti, ya sace ki, ki ka ranci kuɗinsa, ya yiwa babanki tiyata, ki fara aiki a gidan sa..." ya ɗaga kai yana kallon Rehaan da yake tsaye a upstairs yana amsa waya. Jazy kalli Islaha ya yi mata alama da ta kalli inda ya kalla, ta ɗaga kai ta kalli Rehaan sannan ta kalli Jazy alamun na gani meye. Ya ce, "Rehaan AbdulAziz Yola, wanda ki ka fi sani da Ray!." Wani irin dum Islaha ta ji a kanta da kunnenta, ta buɗe ido sosai ta saka ɗaga kai tana kallon Rehaan da yake amasa waya yana murmushi. Yana sanye da riga mai ƙaramin hannu, sai dogon wando, ya saka hannu a aljihun yana zagayawa daga nan zuwa nan. Ta sake kallin Jafar alamun tana son tabbatarwa, ya ɗan murmusa yana ɗaga mata kai ya ce, "Ba ki yarda ba?." Bata amsa ba dan mamaki ya kashe ta a zaune, Jazy ya ɗan ɗaga murya ya ce, "Rehaan!." Rehaan ya ɗan zabura ya juyo yana kallonsa, ya yi masa alamun what kafin ya bar wajan. Ya sake kallon Islaha da ta daskare a wajan, ta kalle sa dan har lokacin bata dawo daidai ba, mamaki take yi da ya kasance shine Rehaan Yola, zuciyarta bugawa take yi, dan kwata-kwata bata taɓa wannan hasashen ba. Ya ce, "har yanzu ba ki yarda ba? Ko dan kina ganin babu security kamar a Nigeria?." Ta ɗan sauke numfashi ta kasa magana, dan harshen ta ya sarƙe, kamar an ɗaure sa ta kasa furta komai. Rehaan Yola kawai take maimaitawa a ranta, tana ganin abin kamar rainin hankali. Jazy ya ɗauki wayarsa a gefe kafin ya miƙa mata, ta karɓi wayar tana kallo, ta sake jin faɗuwatr gaba mai yawa, dan ta tabbatar shine Rehaan Yola. Ta kalli Jafar tana miƙa masa wayar sa, ta koma ta zauna tana ganin abin kamar wasa. Jazy ganin ta shiga ruɗani sosai ya ce, "Islaha nan gidan Rehaan, duk abinda ya faru ya faru tsakanin ki da Mr Ray. Shiyasa na ce kina da sa'a, babu macen da ta taɓa rayuwa dashi kamar ki. Ke kam kin zauna dashi, kun yi magana, sannan ya yiwa mahaifin ki tiyata. Ta ko ina kin shiga rayuwarsa, shima ya shiga ta ki. Itace sa'ar da nake faɗa miki, dan ni na san waye Rehaan, na san abinda zai yi da wanda bazai yi ba." Ta ɗan kalle sa ta ce, "Da gaske shine Mr Ray?." Ya ɗaga mata kai ya ce, "a gidan Mr Ray ki ke, Miss Islaha." Islaha ta gyaɗa kai ta ce, "Ikon Allah! Wallahi ban taɓa sani ba. Ban ɗauka ma wannan yana jin hausa ba, har na gama zama a hannunsa ɗauka nake yi ba bahaushe bane, dan sau ɗaya na ji ya yi magana, kuma ban san sunansa ba. A nan ma sai akan wannan baturiyar na ji ya yi min hausa." Ya yi murmushi ya ce, "na san ba ki sani ba, shiyasa na faɗa miki." Ta sunkuyar da kai ta yi shiru bata ce komai ba, dan jikinta har rawa yake yi saboda mamaki. Ya gyara zama ya ce, "kin san meyasa nake tambayar ki kuma nake faɗa miki?." Ta girgiza kai alamun bata sani ba, ya ce, "Tunda na yi bincike a kanki sai na ji na yarda dake, sai nake ji a raina aikin nan da ki ke yi kamar bai dace dake ba. Kina da carrier mai kyau, kina da farin jini, ana son fuskar ki a duniya, meyasa za ki zo nan ki dakusar da rayuwar ki?." Ta ɗan rausayar da kai ta ce, "na faɗa maka ina nan saboda shi, wallahi ba dan kuɗin nan ba da babu abinda zai kawo ni Jeddah da sunan aiki." "Tun farko da kin faɗa masa maganar kuɗin da ba ki tsinci kan ki a nan ba. Na faɗa miki shine ya yiwa mahaifinki tiyata, ranar da ya yi aikin ranar ya tawo nan, bai sake komawa ba har yanzu. Na tabbatar da bazai karɓi komai na ki ba." "Haka kawai ban san mutum ba sai na roƙe sa? Ni ɗaukar da na yi ma ban san dalili ba. Kuma wallahi da na san shine Mr Rehaan, da na san shine zai yiwa Baffa aiki, da bazan ɗaga hankalina na taho nan neman kuɗin da zan bashi ba." Jazy ya kalle ta, ta ɗaga kai ta ce, "Eh, da na san shine da bazan zo ba. Na ci bashin kuɗinsa, kuma na ba da kuɗin a asibitinsa. Na ɗauko, kuma na mayar." Jafar ya yi dariya yana kallon ta ya ce, "yanzu ki ajjiye batun nan, kina da asthma aiki irin wannan bai dace dake ba. Ki koma gida, ki cigaba da aikin jaridar ki, kamar zai fi miki." Islaha ta ce, "ina son hakan, amma bazai yu ba sai na sauke nauyin da yake kaina. A nan ne zan iya haɗa masa kuɗin nan within one year, can kuwa fa?." "Au ki ka ce baza ki biya ba." "ai cewa na yi da san haka ne tun farko, amma ba wai na fasa biya ɗin bane." Jafar ya nuna mata kuɗi akan table, ta kalla ta ga kuɗin saudia ne masu yawa a wajan a ajjiye. Ya ce, "tun jiya kuɗin nan suke a wajan nan, ɗabi'ar Rehaan ce ajjiye kuɗi ya manta. I'm very much sure kuɗin nan da ki ka ɗauka ya manta dasu, in dai ba ɗauka aka yi aka bashi ba shikenan sun sha ruwa. Sai dai Shams ya ɗauke ya ajjiye a wajensa, dan duk inda Rehaan zai zauna indai zai fito da kuɗi, daƙyar bai bar wasu a wajen ba." Islaha ta kalle shi ta ce, "dan shi bai sani ba ai Allah ya gani, akwai haƙƙin hakan a kaina." Ya gyaɗa kai ya ce, "In dai za ki koma Nigeria, na yi miki alƙawarin zan biya Rehaan kuɗinsa, Shikenan ko?." Ta ɗago ido yana kallonsa bayan ta buɗe su waje, ta ce, "za ka biya sa kuma? Ni ban ce ka biya ba, zan yi aiki da kaina dan biyasa." "Kina son zaman nan ɗin kenan, in kina so fine bai dame ni ba, sai ki zauna." Ta sunkyyar da kai ta ce, "bana son zama, ina da abubuwan yi da yawa a can. Kawai bazan amince ka biya min kuɗin bane Mr Jafar, na gode da niyar alkhairi, amma gwara na yi aikin na samu na biyasa." "Ban ce zan biyasa saboda wani dalili ba, zan biyaa ne saboda na yi niya. Yanayin rayuwarki, da ciwon da ki ke dashi ne ya saka min son biya miki kuɗin. Dan haka kar ki damu, bazai san ma na tura masa kuɗin ba. A account ɗin PA ɗinsa zan tura, ba shi ne ma zai ga alert ɗin kuɗin ba." Ta sauke nunfashi cikin wani irin yanayi, ta kalle sa zata yi magana ya katse ta ya ce, "Indai bakya son aikin nan da gaske, kawai ki fara shirin komawa Nigeria, in kuma kina so ban yi miki dole ba." Ta sauke numfashi a hankali, ta ɗago ta sake kallonsa ta ce, "kamar na ɗora maka nauyi, ba ka sanni ba fa." "Na sanki mana" ya faɗa yana ɗaukar wayarsa da dan gaske yake zai biya mata ɗin, gwara ta koma gida ta bar Jeddah Islaha a sanyaye ta ce, "Na gode Mr Jafar, Allah ya saka maka da alkhairi..." "Amin Miss Islaha." Ta kalli hanyar da take jin takun tahowa, ta ga Rehaan ne yake sakkowa, ya ƙaraso ya wuce su ya fita bai ko kalle su ba. Yana fita ta girgiza kai ta ce, "Da gaske shine Mr Ray?." Jafar da yake jinta ya ɗan murmusa ya ce, "Sai ki fara shirin interview." Ta ɗan buɗe ido cikin firgici ta ce, "har yanzu yana interview tana hannunka." Ya kalle ta ya ce, "Ki faɗa min abinda Alma ta yi nufin yi masa please, hankalin mu ya kasa kwanciya da ita." Ta kalle sa ta ce, "na faɗa maka tsakani da Allah na yi." "nima tsakani da Allah zaki faɗa min." "Na ganta a kitchen tana zuba masa tablet a tea, sai na haɗa accident ɗin da na zubar da tea ɗin." Ya harɗe hannayensa yana binta da kallo ya ce, "meyasa ki ka yi abinda ki ka zubar da tea ɗin?." "Saboda in wani abun ya same sa ni za a ce, ban san me ta zuba a ciki ba, shiyasa na yi hakan." Ya ce, "na biyun fa?." "Ya ce na kai masa tea bedroom, na kai na fito ba jimawa na dawo na ɗauki cup ɗin, sai na ga ta fito daga ɗakin cikin murna tana cewa yanzu zai fara aiki. Sai ban yarda da ita ba na shiga ɗakin, sai na same sa kamar wanda aka yi knocking out ya riƙe kansa, daga ƙarshe ya kwanta bacci ya ɗauke sa....." "Sai na ɗan ɓuya a ɗakin, a nan na ga ta shigo tana undressing kayan jikinta, sannan ta saka waya da light ta fara ɗaukar video. Ni kuma sai na fito, na ɗauke wayar na goge video, na ce in bata fita ba sai na kira police. Shine kawai." Ya girgiza kai ya ce, "Thank you so much, mun gode da wannan taimakon da ki ka yi." Ta ɗan taɓe baki ta ce, "ba dan shi na yi ba, saboda Allah na yi. Kuma na san in wani abun ya faru dashi ni za a ce, tunda ni ce housemaid a gidan." "Mun gode." "Kar ka faɗa masa, ka ƙyale sa kawai." Ya gyaɗa mata kai alamun to. Ya miƙe tsaye itama ta miƙe tana yin rolling mayafin kanta ya ce, "ki koma, zuwa gobe in Allah ya kaimu ki siyi ticket ki koma Nigeria. Zamu sake haɗuwa in lokacin interview ya yi." Ta yi murmushi ta ce, "na gode sosai." Bai ce komai ba ya fita ya biyan Rehaan dam ya san ita ya tafi. A zaune ya same sa a cikin garden ya harɗe hannayensa yana girgiza kai kamar wanda aka yiwa laifi. Jazy ya zauna a kusa dashi bai ce komai ba. Ray ya wani kalle sa ya ce, "so you found a new girlfriend, you are cheating Riyya." Jazy ya yi dariya cikin mamaki ya ce, "girlfriend kuma?." "Yes, awa nawa ku ka yi a zaune kai da ita? Sai wani hira ku ke yi kamar ka santa, kana ta dariya abinka." Jazy ya ce, "tana bani labarin yadda ka sace ta ka kaita gidan ka ne." Ray ya ja tsaki ya ɗauke kai cikin takaici mai yawa, sai daga baya ya ce, "yarinyar tana da mental disorder, ta dinga magana ita kaɗai, kai kuma ka biye mata kun zama ɗaya." Jazy ya kawar da maganat ya ce, "gobe zan tafi Madina." Rehaan ya fusata ya ce, "ina yi maka magana akan kana cin amanar ƙanwata kana zancen gobe za ka tafi madina? Na riƙe ka ne? Yanzu ma ka tashi ka tafi mana." Jazy ya bi shi da kallon mamaki jin ya fusata lokaci ɗaya, ya ce, "calm down, me ya fusata ka haka Ray?." Ya ja tsaki bai ce komai ba, yana jin zafi haushin Jazy da ya biyewa Islaha suna hira. Jazy ya ce, "Ni ban ga abin faɗa a nan ba Ray, dan na yi hira da ita ban ga dalilin da zai saka ka fusata kana faɗa haka ba. Yau na saba hira da mata?." "You were talking in a low voice so I wouldn't hear, right?. Me ka ke faɗa da baka so na ji?." Jazy ya bi sa da kallon mamaki ya ce, "wait! Ya ka ke magana kamar wanda yake kishi?." Wani banzan kallo ya yi masa, kafin ya yi tsaki ya miƙe ya bar wajen. Jazy ya bi sa da kallo yana dariya, dan shi bai ga abin ɗaga hankali ba. Nana Haleema. [7/17, 11:50 AM] KRBBK: RDB2P61 Nana Haleema. Islaha a sanyaye ta fita daga gidan, ta sake kallon ƙofar gate ɗin ta ga Dr Rehaan a rubuce, ta yi ajiyar zuciya, ta shiga gidan Maleek. Tana tafiya tana tunani, ganin abin take yi kamar a mafarki wai wannan mutumin da take rainawa hankali, take faɗa masa duk abinda ta ga dama, wai shine Rehaan Yola da kowa yake son yin magana dashi. Ta zauna a gefen gado tana tuna yadda ta dinga faɗa masa magana, da yadda Chairman ya ke son a kawo shi channel ɗin su, da yadda kowa yake son ace ya ga Rehaan Yola. Ta ɗan taɓe baki ta dafe kai ta ce, "Shiyasa Hamma yake yawan yi min faɗa, yana cewa na iya harshena, ban san mutanen da zan haɗu dasu ba, amma bana jin magana." Ta ɗauki wayarta, ta sake yin searching Rehaan Yola ta ga dai shi ɗin ne ya fito, a bayyane ta ce, "Anya Jafar ɗin nan ba raina min hankali yake yi ba?." Sai kuma ta kalli wayar ta ɗan gyaɗa kai ta ce, "kuma dai ɗin ne, kenan da gaske shine Rehaan Yola? Wanda na fita tun asuba ina nema, muka haɗu ya zuba min tea" ta nuna wayar da yatsanta ta ce, "wai duk shine ashe?." Ta girgiza kai ta ce, "Allah mai iko, Allah gwanin hikima. Ko kaɗan ban taɓa hararowa shine Rehaan Yola ba, ko da na ga Jafar ban ji a raina shine Rehaan ba. Ashe wannan soloɓiyon mai jikin matan shine Rehaan Yola, amma dai an yi ragon maza." Ganin Hamma yana yi mata waya sai gabanta ya faɗi, ta tuna da batun ɗaurin aurensu gobe, sai ta kasa ɗaga wayar tana kallo ta lumshe ido tana jin ƙirjinta yana bugawa sosai. Ya sake kiranta ta kasa ɗauka, sai ma komawa da ta yu ta kwanta tana tunanin da gaske dai wancan shine Rehaan?. Rehaan Yola dai da yake yiwa mutane wahalar gani, shine ya zama kamar purewater a wajenta, shine ya zama kamar wani toy a wajen ta. Ta lumshe ido tana tuna waye shi a Yola, ta girgiza kai tana ganin abin kamar a dream. Jazy a tsaye ya samu Rehaan yana kallon wani waje daban kamar mai tunani, Jazy ya kalle sa ya ce, "ina faɗa maka gobe zan tafi Madina kana share ni." Ya juyo ya kalle shi, kamar zai yi magana sai kuma ya yi masa banza. Jafar ya yi dariya bai ce komai ba ya wuce ɗaki, dan in ya biye masa faɗa zasu yi, mamaki ma yake bashi da yake wannan abun, kamar yau ya saba hira da mace bayan Riyya. Haka suka zauna Rehaan yana jin haushin Jafar ba tare da ya san me ya yi masa ba, ba su haɗu ba har dare kowa yana ɓangarensa. Shigowar Jafar kenan ya siyo turare ya zauna yana buɗewa bai kula Rehaan ba, dan yadda ya share shi shima haka ya share sa. Rehaan ya ɗan kalle sa, kamar baya son magana ya ce, "meyasa baza ka jira mu je tare ba?." Jazy ya yi masa banza kamar bai ji ba, dan sai ya rama wulaƙancin da ya dinga yi masa. Rehaan ya ce, "magana nake yi maka." Ya yi masa shiru bai ce komai ba, buɗe turarensa yake yi kamar bai san yana yi masa magana ba. Rehaan ransa ya sake ɓaciya girgiza kai yana jan ƙwafa kafin ya cigaba da danna wayarsa. Yana ji Jafar yana waya da wanda suka sani a Madina, yana faɗa masa hotel da room ɗin da zai yi masa reserving kafin ya zo. Sai a sannan Jafar ya kalle sa ya ce, "Abba ya ce yana ta kira ka baka ɗauka ba, in ka ga dama ka kira shi, in ba ka ga dama kar ka kira." Rehaan ya kalle sa cikin ƙuluwa ya ce, "wai akan waccan yarinyar ka ke yi min magana haka?...." Jazy ya ɗago ya kalle sa ya ce, "Rehaan me na yi maka?." "Me ba ka yi ba?." "Sai ka faɗa na ji ai." "Ka zauna da ita kuna hira harda dariya kama wata sister ka, ka manta yarinyar Ubaid ce, zama da ita a waje ɗaya ma babban zunubi ne. Dan na yi maka magana ka ke jin haushina?." Jafar ya ce, "sai me ye dan yarinyar Ubaid ce? Ni bai dame ni ba, kai ka ga hakan zai dama ka bani ba. Ko ganinta na yi da Ubaid ido da ido ba damuna zai yi ba, kaima kuma ban ga dalilin da zai dame ka ba. Kamar yadda ka ce ba sister na bace, kai ma ba sister ka bace. Ban ga abin ɗaga hankali dan tana yarinyar Ubaid ba, balle har ka ji haushi kana daina yi min magana." "Kuma ni yarinyar nan tausayi ta bani, da na saka aka yi min bincike a kanta, sai na gane rayuwar ta gabaɗaya a maraici ta tashi. Kuma kai da ka san taimakon da ta yi maka, da baka ce mata haka ba" ya faɗa yana cigaba da abinda yake yi. "Taimako! Ita wacece da zata taimake ni?." "Ƴar adam ce kamar kai, zata iya taimaka maka a ko wanne hali. Ba maganar kuɗi ko iko ake a nan ba, maganar taimako ake yi." "Kai ka san duk duniya babu yarinyar da nake jin haushi kamar ta, dan baka da class, ka zauna da ita kana hira, bayan ga matar da zaka aura can a Yola." "Kai wai dan zan auri Riyya shikenan bazan yi hira da ko wacce mace ba?." "Ka yi hira da matan duniya ma Jazy, amma ban da wannan." "ita meye laifinta? Kawai dan kana zarginta akan abinda baka da tabbaci a kai?." Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba, Jazy ya ce, "In ma kana da tabbacin yarinyar Ubaid ɗin ce, abinda ka ke zargi ta aikata, sai me? Ina ruwan ka, rayuwar ka ce ko rayuwar ta?." Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba, Jazy ya taɓe baki ya ce, "Ni dai gobe zan wuce, kafin ka tashi daga wannan wahalallan baccin naka na hau train na wuce." Ya ɗan hararesa sannan ya ce, "In ka je a binne ka a can, kar ka dawo da rai." Jafar ya yi dariya ganin ya ƙular dashi, kuma shi dai bai ga abin jin haushi a lamarin nan ba, ya tayar da hankali kamar wata sister sa ce. Ya ce, "Inyee, jinin indiyawa ya ji hausa. Na ji, dan an binne ni a can ai ba komai bane, garin da Annabi yake kwance ai abin so ne nima na kwanta. Kuma wallahi duk bala'in ka bazan ɗaga tafiyata ba, in ka ga dama ka biyo bayana, in baka ga dama ba ka sha zaman ka" ya faɗa yana haɗa kayansa ya miƙe ya bar masa wajan. Ya bi sa da harara yana ji kamar ya je ya yi msa dukan tsiya. Washe gari Friday, tunda Islaha ta farka take cikin fargaba da bugawa ƙirji. Da safe sai kallo agogo take yi tana tunanin aurenta da Hamma saura awanni kaɗan. Haka take yin komai sukuku babu ƙarfi, a haka suka gama haɗa breakfast suka fara shirin zuwa masallaci. Sunaira ta ta takurawa Islaha akan su je sallah, babu yadda ta iya, ta saka sabuwar abayar da aka bata suka tafi da wuri dan su samu huɗuba. Lokacin da suka dawo a lokacin wayarta ta fara ringing, gabanta ya faɗi ganin sunan Hamma yana yawo akan wayar. Ta san lokacin sallar juma'a bai yi ba a Nigeria, amma haka kawai take jin faɗuwar gaba mai tsanani. A hankali ta ɗauka ta saka a kunne, daga can ɓangaren ya ce, "Ya dai Matar Hamma? Saura lokaci kaɗan ko?." Ta ɗan yi dariya kaɗan ta ce, "ina yini Hamma." "Lafiya lau Matar Hamma, kin ganni ina shirya kaina cikin farar shadda, saboda yau za a bani auren Islahata." Ta ɗan murmusa, cikin son kawar da abinda yake ranta ta ce, "ai gwara ka shirya da kyau, dan ma bana kusa ne." Ya yi dariya ya ce, "ai ni ko bakya nan ɗin, indai za a ce Islaha matar Saheer ce Allah ya yi min komai. Zan zauna na jira ki, duk lokacin da ki ka dawo a yi biki, a kai min ke mu fara shimfiɗa rayuwar aure mai tsafta. Ke ba sai an yi bikin ba ma, a bani ke haka." Ta sake yin murmushi ta ce, "Yanzu dai yau za a ɗaura?." "In sha Allah, saura lokaci kaɗan." Ta yi shiru bata ce komai ba, Saheer bai damu ba ya ce, "zan je wajan Baffa, ana ɗaurawa zan yi miki message, ki kasance active." Ta amsa da to a sanyaye, ya kashe wayar cikin shauƙi da zumuɗi.. Daga can ɓangaren yana kashe wayar ya nufi wajan Baffa, da ya shiga falon Baffa ba ya nan sai Mama kaɗai a tsaye. Tunda ya shiga yake binsa da kallo, ganin sabuwar farar shadda ya saka sai ɗaukar ido take yi, kai da ka gansa ka ga ango ko wanda yake shirin angwancewa, bai taɓa yi mata kyau kamar ranar ba, bai taɓa yi mata haske da annuri kamar na wannan lokacin ba. Suna haɗa ido gabansa ya faɗi sosai, ya daure cikin dakiya da dauriya ya ce, "Mama Baffa yana ciki?." Mama ta girgiza kai tana ƙwafa ta ce, "Saheer yanzy kenan ka zaɓi tsinuwata akan ka rabu da Islaha? Ka amince na tsine maka ka bi duniya akan ka rabu da ita ko?." Saheer ya sunkuyar da kai bai ce komai ba, amma ƙirjinsa har ɗagawa yake yi saboda tashin hankali, ya rasa me zai yi. Mama a fusace ta ce, "ina magana ka sunkuyar da kai kamar wani mutumin kirki, ka zaɓi na tsine maka akan a fasa auren nan ko!?." "Ya zaɓi yiwa mahaifinsa biyayya ne, dan kin tsine masa babu abinda Allah zai yi masa, dan ba wani abun mara kyau ya aikata ba!" Baffa ya faɗa yana shigowa yana kallon ta. Mama ta sake fusata matuƙa ta ce, "Bazan amince da auren nan ba wallahi, bazai yu na haifawa wata banzar yarinya ɗana ba. Tun yanzu yana rawar ƙafa da rawar kai a kant, ina ga an yi auren?. Wallahi Allah, In Saheer ya auri yarinyar nan sai na tsine masa alabrka!." Baba Yayan Baffa da yake tsaye, sun shigo tare ɗaukar goro da alewaya ce, "Subahanallahi! Me ya yi zafi haka?." Baffa ya ce, "ni kuma sai na aura masa Islaha a yau, in kin tashi tsinuwar ki haɗa har ni ki tsine, amma babu abinda zai dakatar dani daga bawa Islaha auren Saheer a yau." Mama ta girgiza kai ta ce, "Mu zuba mu gani" ta faɗa tana fita cikin takaici da ɓacin rai. Baba ɗan uwan Baffa ya kalli Baffa ya ce, "Hakan bai kamata ba Mustpaha, kar a yi abinda za a zo ana danasani. Tunda har ta yi wannan furucin akansa, ka yi haƙuri a bari zuwa gaba, kar a yi abinda zai lalata rayuwar Saheer. Uwa ce, ko ya ta yi nasa bakin sai ya bi shi, in aka bari ta furta, duk ƙanƙantar abinda ta furta sai ya taɓa rayuwarsa." Ran Baffa a ɓace ya ce, "saboda ita sai na fasa abinda na yi niya kenan?." "Ba saboda ita zaka fasa ba, saboda shi zaka fasa. In aka yi auren ta tsine masa wa gari ya waya? Kwata kwata baza a ga albarkar auren ba, tunda akwai tsinuwar uwa a cikinsa. A bi komai a hankali, islaha matarsa ce in sha Allah, amma a bari a daidaita komai sai ayi auren." Baffa ya sauke numfashi ya ce, "Itace zata juya ni kenan?." Baba ya dafa Baffa ganin ya fusata da yawa, daga ganin yadda ya fusata ya san an kai shi bango, dan Baffa ba mutum ne mai saurin ɗaukar zafi ba, tunda ya ga ya fusata sosai ya san abin ya taɓa ransa. Ya ce, "ba juya ka ta yi ba, hankali da nutsuwa ka fita. In aka yi auren nan rayuwar Saheer a gaba za ka duba, tsinuwar uwa ai ba abin wasa bane. Kai ka fita hankali, bai kamata ka biyewa zuciya shaiɗan ya zuga ka ba. A yi haƙuri, abar maganar ɗaurin auren nan a yau, in Allah ya kaimu lokaci sai a yi, amma yanzu a dakatar dashi." Baffa ya ce, "Baza a fasa auren Saheer da Islaha ba, bata isa ta saka na fasa abinda na yi niya ba, akan Zulaiha bazan fasa aurawa Saheer Islaha ba. Akan auren Saheer da Islaha, zan iya sakin Zulaiha!." Nana Haleema. [7/17, 11:50 AM] KRBBK: RDB2P62 Nana Haleema. Saheer ya kalli Baffa da sauri jin abinda ya ce, Baba ya kalli Saheer sannan ya kalli Baffa ya ce, "Haba Mustapha, wannan wacce irin magana ce mara kan gado?. Zulaihan za ka saki??." Baffa ya ce, "A kanta aka fara?." "Ba a kanta aka fara ba, kuma ba a kanta za a gama ba. Shi kansa Saheer ɗin ya kalle sa ka gani, ai bazai so ace ta silar aurensa auren mahaifiyarsa ya ƙare ba. Shaiɗan ne yake zuga ka, ka kwantar da hankalinka, Allah zai nuna mana gaba." Baffa ya shiga ɗaki bai ce komai ba. Baba ya riƙe hannun Saheer suka fita daga falon, dan ya ga yadda Baffa ya fusata sosai bazai yi magana a gabansa ba. Baba ya kalle Saheer ya ce, "ka yi haƙuri ka bar maganar, zuwa gaba sai ayi auren ai ba gagawa ake yi ba. Na san baza ka so auren babar ka ya lalace saboda auren ka ba." Ya ɗan ɗaga kai ya ce, "haka ne Baba, Allah ya kaimu lokacin." "Amin. Ka cigaba da yi mata biyayya, ka cigaba da tausarta har ta amince da auren. Kar ka yi abinda bata so, kar ka yi abinda zata yi maka baki a kai, dan baza ka ji daɗinsa ba. Ka cigaba da addu'a, in alkhairi ce Allah ya zaɓa maka, sannan ita ya saka mahaifiyar ka ta amince, in ba alkhairi bace Allah ya canja maka da mafi alkhairi." Ya amsa da amin suka nufi masallaci don yin sallar juma'a. A gidansu Safeera ƴan uwan Baba mata suna nan, dan ranar za a ɗaura auren Baba kuma ranar zata tare. Suna gidan sun zo karɓar amarya, dan ba ƙaramar murna suke yi da auren ba. Ita kanta Safeera tana murna da auren, dan tana son kwanciyar hankalin mahaifinta sosai. Daga cikin falon Umma suke zaune, Gwaggo Yayar Baba ta ce, "ni na ji daɗin haɗin nan wallahi, ko babu komai Maimuna zata san ta tafka kuskure, inda ta bari saboda abin duniya aminiyarta ta shigo." Ɗaya daga ciki ta ce, "Maimuna bata da matsala fa Gwaggo, matsalar ta ɗaya, shine zaɓar abin duniya akan yaranta da mijinta da ta yi, itace matsalar da aka samu da ita. Amma bayan wannan tana da kirki kowa ma ya shaida." Ɗaya ta ce, "Kuma na ji labarin an ce wahala take sha a can ƙasar, duk ga rame ta damu ta dawo." Gwaggo ta cs, "To ko haƙƙin mai gidan nan zai barta ne? Barin auren ta yi ta tafi wata ƙasa aiki, ai ko wuƙanata aure da ta yi sai Allah ya hukunta ta. Yanzu ga amarya zata shigo, Kowa yana yabon halin Atika na kirki da dadtaku. Na ji daɗi wallahi, Allah ya saɓa halaye." Suka amsa da amin suna cigaba da tattauawa. Safeera tana ɗaki duk tana jinsu, bata ji rashin jin daɗi ba kaɗan, dan ta san gaskiya suka faɗa ba ƙarya ba, da Umman bata aikata ba da hakan bai faru ba. Sai da ta ji dawowar Baba, su gwaggo suna ta yi masa Allah ya sanya alkhairi da addu'a sannan Safeera ta yi murmushi, ta ɗauki waya ta kira Islaha. Islaha tana kwance akan gado, lokacin la'asar ya kusa a Saudi, tana jiran kiran Saheer amma shiru. Jin kiran Safeera sai ta tsorata, ta miƙa hannu a sanyaye ta ɗauko wayar daga gefenta ganin Safeera ce sai ta ɗauka. Islaha tana saka wayar a kunne Safeera ta ce, "Islaha an ɗaura auren." Ƙirjin Islaha ya buga dummm, ta ji wani irin abu zuuu yana yawo a jininta, ta ji wani shock kamar jan wutar lantarki, wani irin ɗumi mai kama da zazzaɓi yana lulluɓe ta, zuciyarta ta tafi tunanin yanzu kenan ta zama matar Hamma? Ta zama mallakin Hamma halak malak, ta zama matarsa ta sunnah, ko yanzu akace babu shi sai ta yi masa takaba?. Sai ta kasa magana, bakinta ya yi nauyi sosai, ta riƙe waya a kunne tana jin sautin bugun zuciyarta a kunnenta. Bawai auren Hamma ne bata so ba, gaggawar da aka yi a ɗaura auren ne bata so. Safeera da zumuɗi ta ce, "Yanzu Baba ya dawo, an ɗaura aure yau." Islaha ta ja numfashi mai ƙarfi bata ce komai ba, Safeera ta ce, "Ya dai?." Islaha ta ce, "Nima ban sani ba Safeera, haka kawai nake jin bana murna da auren." Da mamaki Safeera ta ce, "meyasa bakya murna?." "Wallahi ban sani ba, ni kaina bazan ce ga dalili ba. Gabaɗaya ji nake kamar a warware auren nan, bazan iya zama da aure a kaina ba." "auren Baban?." Islaha ta buɗe ido tana miƙewa zaune ta ce, "Wanne Baba kuma?." Safeera ta ce, "ke akan auren wa ki ke magana?." Islaha ta ce, "Shekaran jiya Baffa ya kira ni, ya ce za a ɗaura aurena da hamma a yau, dan ɗazu ma ya kira ni akan hakan, yana ta shirin tafiya masallaci za a ɗaura. Shine gabaɗaya jikina ya yi sanyi, ko ke na kasa faɗawa maganar ɗaurin auren." Safeera ta ce, "tabɗi! Wai da sai dai na ji an ɗaura auren ki? Na rantse da Allah sai na yi miki abinda ba ki taɓa tunani ba." "Wallahi ni nauyi maganar ta yi min, sai nake ji gabaɗaya bana son a yi aurensa yanzu, bana murna da auren gabaɗaya." "Auren Hamman ne bakya so ko son Hamman ki ka daina?." "Ina da wanda zan so in ba shi bane? Ina son Hamma sosai, kawai dai aurensa a yanzu ne bana so." Safeera ta ce, "Yanzu an ɗaura auren?." "Ban sani ba wallahi, amma tabbas yau za a ɗaura sai dai in an fasa." "to meyaasa za a yi auren yanzu?." "ina zan sani? Baffa ne ya yanke hukunci." Safeera ta yi dariyar shaƙiyanci ta ce, "ki ce amarya ce da kanta, tunda an sakko daga masallaci na san kin zama matar aure." Islaha ta ce, "hmm Safeera kenan. Baba ya auri Mamansu Kausar ko?." "Wallahi fa, an ɗaura auren." "Ke kamar bakya ta ya Umma kishi." "Kishin me zan ta ya ta? Ba fa matar Baba bace." "Amma Maman kausar aminiyar Umma ce, komai tare suke yi. Dan kawai Umma bata nan sai ta aurar mata mijinta maye gurbinta?. Ni fa haushin ki nake ji akan hakan, sai rawar kai ki ke yi." Safeera ta yi dariya, dan ta san halin Islaha da kishi, in itace a matsayinta baza ta yi ba. Safeera ta ce, "Wallahi ni ko a jikina, murna nake yi Baba ya samu sabuwar matar da in na tafi aiki ƙannena suna makaranta zata kula dashi yadda ya kamata. Kuma dan ba ki san irin kyautatawar da ta dinga yi mana bane, mahaifiyarmu ta ajjiye mu ta bar ƙasa, ita kuma ta kamo hannunmu ta riƙe. Ai wallahi ta cancanci Baba ya aure ta, ko Umma tana nan ta cancanci su yi zaman kishi, balle bata nan, kuma ba a san ranar da zata dawo ba." Islaha ta ce, "Allah ya sanya alkhairi." Ta amsa da amin kafin ta ce, "bara na kira Sadik na ji in an ɗaura na ki, yadda zan dawo na tsokane ki son raina" ta faɗa tana kashe wayar Islaha ta bi wayar da kallo cikin wani irin yanayi. Tana idar da Sallah Sahir ya kira ta, ta ɗauka cikin faɗuwar gaba, amma yadda ta ji maganarsa a sanyaye ya saka ta ce, "Hamma ya dai?." Ya ce, "kin ji shiru ko? Baba ne ya ce a dakata da ɗaura auren sai kin dawo. Gabaɗaya raina a ɓace yake a akan hakan." Ta yi ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, yanayinta ta ya canja zuwa na jin daɗi ta ce, "meyasa ya ce haka?." "Wai gaggawar me ake yi, a jira ki dawo." "To ai shikenan, Allah ya sa zamu gani." "Amin. Amma ni ba haka naso ba gaskiya." "Wataƙila yanzu in aka ɗaura bazai zama alkhairi ba." "Haka ne." Islaha ta ce, "Hamma ya batun Zainab?." "Bana so na faɗa miki ki tayar da hankalin ki, shiyasa na yi shiru." "Bazan tayar ba, ka faɗa min don Allah." "Ba a ga Zainab ba, duk inda nake tunanin zan ganta ban ganta ba. Har gidan ƴan uwanku na gidan na je aka ce bata je ba, har Barr na tambaya ya ce shi ya jima bai ga Zainab ba." Ta yi shiru bata ce komai ba, ya san ta daman zara damu sosai akan hakan, sai ya tausasa murya ya ce, "amma ki yi haƙuri, kafin na koma zan sake dubawa, in sha Allah rayuwar Zainab zata salwanta ba, Allah zai yi riƙo da hannunta, zai kare ta a duk inda take." "Allah ya shiga tsakanina da wanda ya zama munafuki a tare dani" ta faɗa hawaye yana sakko mata. Ya tausasa murya cikin rarrashi ya ce, "ki yi haƙuri, in sha Allah zan nemo miki ita." "Hamma in wani abun ya same ta ni ce sila, Allah bazai yafe min ba." "Ki yi haƙuri, Allah ya gani ya san taimako ki ke yi, ko dan hakan bazai bari ki wulaƙanta ba." Kuka take yi masa sosai yana rarrashinta, sai da ya ji ta ɗan nutsu sannan ya ƙyale ta. Abin ya haɗar mata, ga jin daɗin an fasa ɗaura aure ga tunanin Zainab. Daƙyar ta iya miƙewa, ta wanke fuskar ta ta fito tana kallon kanta, kallo ɗaya za ka yiwa idanunta ka san ta yi kuka. Ta ɗauki facaemask ta saka, ta saka hijjab ta fita zuwa gidan Rehaan. Tana shiga falon gabanta ya faɗi, dan yana zaune shi da wani bature yana nuna masa abu a file shi kuma yana gani. Tana ƙarasa shiga falon Baturen ya tashi da file ɗin ya fita. Sai ta ji zuciyarta ta yi nauyi sosai, haka kawai take ji kamar tana jin nauyinsa akan abinda ta dinga yi, ta lumshe ido ta buɗe ta kalle sa ta ga kamar bai ganta ba ta ce, "Good day." Ya ɗago ido ya kalle ta, ta yi saurin kawar da kai tana mamakin wannan faɗuwar gaban da take yawan ji indai zasu haɗa ido. Ya miƙe tsaye ya harɗe a hannu a ƙirji yana kallon ta, ya ɗan riƙe kai ya ce, "ohhh my god, na gaji sosai." Ta kalle sa ta ƙasan ido, ta turo baki gaba tana hararasa ta ce, "rago kawai, shi komai ya gaji." Bata faɗa yadda zai ji ba, ita kaɗai take maganarta. Rehaan ya ji ta, ya yi kamar zai yi magana sai kuma ya ɗauke kai ya taɓe baki ya ɗauki wayarsa zai bar wajan. Daƙyar ta iya buɗe baki ta ce, "kana buƙatar wani abu ne?." Sai ya tsaya ba tare da ya juyo ba, sai kuma ya juyo ya dawo da baya, ya saka hannu aljihu ya ɗauko kuɗi ya ajjiye a gefen kujera kusa da ita, ya ɗan fara tafiya da baya sannan ya ce, "no need, you can go" ya faɗa yana bar mata wajan ya hau sama. Ta bi sa da harara ta ce, "Ɗan rainin hankali, kar ka so ɗin, da na san haka ne ai da ban fito na zo inda ka ke ba. Dan ka kasance Rehaan yola babu ruwana wallahi, baza ka yi min na ƙyale ka ba." Ta kalli kuɗin ta ga riyal ɗari biyar biyar da yawa, ta harari kuɗin ta ce, "ba dan ina son kuɗin ba wallahi bazan ɗauka ba, kawai dan amfani dasu ya zama min dole, ko dan na biya su Mama kuɗin da suka kawo ni na wuce gida" ta faɗa tana ɗaukar kuɗin tana kallonsu. Ko bata lisssfa ba ta san da yawa, dan gani take kamar sun fi waɗancan yawa. Ta yi ajiyar zuciya tana kallon kuɗin tana tunanin aikin me take yi masa da yake bata waɗannan uban kuɗin?. Sai kuma ta taɓe baki, a bayyane ta ce, "ba sata na yi ba, ba kyauta ya bani ba, ba roƙonsa na yi ba, aiki na yi masa kuma ya biya ni, haƙƙina ne, kuma halak ɗina ya bani" ta faɗa tana saka kuɗin aljihun rigarta ta fita daga gidan tana takawa a hankali. After two days... Nana Haleema. [7/17, 7:20 PM] KRBBK: RDB2P63 Nana Haleema. Suna zaune a falon Maleek suna faɗa musu zai yi tafiya shi da matarsa. Islaha tana zaune ta yi shiru bata ce komai ba, sai da ya gama sannan ta ɗaga kai ta ce, "zan iya faɗar wani abu?." Maryam ta ce, "za ki iya." Islaha ta ce, "ina so na je Madina na yi kwana biyu, amma ban san ta inda zan fara ba." Maleek ya kalle ta ya ce, "Is okay, duk lokacin da za ki je sai ku je da Sunaira ki yi ticket ɗin train ki je." Islaha ya yi murmushin jin daɗi ta ce, "na gode." Ya kalli Sunaira ya ce, "Ku je da ita station ta siyi ticket duk lokacin da zata tafi." Sunaira ya amsa ya bawa Sunaira kuɗin ticket ɗin. Ita dai Islaha godiya take yi dan ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Basu jima ba suka tafi aka bar gidan a hannunsu. Daman kwana biyu ba zuwa gidan Rehaan take yi ba, rabon ta da zuwa tun washe garin da ya bata kuɗi, daga nan Maleek ya ce mata ya yi tafiya baya nan. A washe garin ranar ta siyi jaka ta baya, irinta ta ƙaramar tafiya, ta saka doguwar riga guda ɗaya a ciki, ta saka kayan amfani in za ka iya kwana dasu, ta goya jakar ta fito zasu je statiom ɗin kamar yadda ya faɗa. A hanyar su ta tafiya Islaha ta ce, "Sunaira ina na ne unguwar Khadiyya a Madina, ya zan yi?." Sunaira ta yi mata typing kamar ko yaushe, Islaha ta dub ta ga ta ce, "in kin sauka ki tari mota ki faɗa musu, zasu kai ki ko ina ne. In kuma za ki je masallaci, kawai ki cewa masu mota haram zasu kai ki." Islaha ta gyaɗa kai tana murmushi, a haka suka si yi ticket Sunaira, ta bata da sauran kuɗin da zata siyi na dawowa. Sai da Islaha ta shiga train sannan Sunaira ta koma. Islaha kallon jirgin kawai take yi, dan ticket ɗin first class aka siya mata, gashi nan kamar jigin sama saboda kyau. Babu jimawa jirgin ya fara gudu dasu a ciki. Tana zaune da facemask a fuskar ta tana ta kalle kalle, wani abun ta yi video wani abun ta ajjiye wayar. Awa ɗaya da wani abun suka ɗauka suna gudu, kafin ta ji sanarwa sun iso station ɗin Madina. Suna fita ta ga inda mutane suke bi, da yawa matafiya ne waɗanda suka shigo ƙasar, ita dai su take bi har aka fito inda motoci suke, ta samu taxi ta faɗi sunan da Umma ta ke, ya faɗa mata kuɗin da zata biya ta shiga suka tafi. Sai da suka zo sannan ta bashi location ɗin da Umma ta tura mata, ai kuwa har ƙofar gidan da Umma take ya kai ta. Islaha ta bi gidan da kallo, gidan babba ne babu laifi, ta fita daga motar ta bashi kuɗinsa ta ƙarasa. Gate ɗin bashi da tsayi, sannan lock ɗin yana saman gate ɗin kana saka hannu zaka cire. A hankali ta cire, ta taka a nutse ta ƙarasa wajan ƙofar tana danna door bell. Ba jimawa aka buɗe, ana buɗewa suka haɗa ido da Umma da take tsaye sanye da ƙaramin Hijjab. Umma ta buɗe ido cikin tsananin mamaki ta ce, "Islaha ke ce?." Islaha ta ɗaga kai tana murmushi ta ce, "Ni ce Umma." Umma ta ji wani irin daɗi yana mamaye mata zuciyarta, ta rungume Islaha tana ji kamar ƴarta Safeera ya gani. Daman kuma duk wanda ba ya ƙasar sa in ya ga wanda ya sani sai ya ji kamar ya yi me saboda murna, Umma ta gigice tana jin daɗi kamar ta mayar da Islaha ciki. "Me ki ke yi a nan! Baza ki dawo ciki ba!?." Muryar matar gidan ya ratsa su cikin yaren ta, zuwa lokacin Umma tana fahimtar wani abun a arabic sosai. Ta saki Islaha tana cewa, "Wannan masifaffiyar mata, Islaha mu je Allah ya sa ta bari ki zauma." Tare suka shiga falon, ta yi kan Umma kamar zata dake ta tana masifa da arabic. Umma ta bata haƙuri da larabci, ita kuma ta nuna Islaha tana tambayar wacece. Islaha ta bi matar da kallo, ganin ta yar ƙarama da ita bata da jiki, kuma a haife ma ta san Umma ta haife ta, amma ji yadda take yi mata wannan masifa har da ƙoƙarin duka. A lokacin bababr ƴar gidan ta zo wajan, Umma ta ce, "Islaha ki yi mata bayani da turanci, ki mata ke ƴata ce, kin zo ki ganni ki koma." Islaha ta kalli yarinyar ta ce, "Mamana ce, na zo na ganta na koma." Yarinyar ta taɓe baki ta ce, "to ai kin ganta ko? Sai ki koma gida." Islaha ta haɗe rai ta ce, "Ba yanzu ba, ina so mu gaisa kafin na koma." Yarinyar ta faɗawa babarta abinda Islaha ta ce, sai kuwa ta fara zazzaga bala'i da larabci. Umma ta kalli Islaha ta ce, "ki yi haƙuri, haka suke da wannan tashin hankalin wallahi, gabaɗaya ruɗa ni suke yi, na rasa ya zan yi." Islaha ta ce, "ke zan bawa haƙuri Umma, na zo na jawo miki faɗa." "Wannan ma kaɗan ki ka gani, shekaean jiya wannan budurwar marina ta yi." Islaha ta zaro ido ta ce, "Mari Umma?." Umma ta ce, "Mari Islaha, mu je na kai ki ɗaki kafin na gama aiki." Islshs ta ce, "mu je na ta ya ki." "Aa, mu je ki huta dai." "Zan ta ya ki Umma." Suna tsaye suna kallon su, kamar yadda basa jin me su Umma suke faɗa haka suma basa jin me suke faɗa, amma kowa ya san maganar juna suke yi. Zasu wuce kitchen matar gidan ta tare hanya ta hana Islaha wucewa, Islaha ta ce, "ki je Umma, zan jira a nan." Umma ba dan ta so ba ta wuce kitchen, su kuma suka bar wajan ana bin Islaha da kallo kamar sun ga wata dabba a gidan zoo. Ita ba ta su take yi ba, tunanin yadda Umma ta rame kawai take yi, gashi dai da hijjab a jikinta amma ta ga ramar da ta yi, ramar ta yi yawa sosai. Ta ɗan jima a zaune kafin su bar wajen, Islaha ganin basa nan sai ta bi Umma, ta same ta a tsaye a gaban kayan wanke wanke tana wankewa, ga girki a kan stove. Islaha ta ce, "Umma kawo na yi miki wannan, ki ƙarasa girki." Umma ta kalle ta ta ce, "kar ki damu, na saba da haɗa aiki." Islaha jikin ta ya yi sanyi ta ce, "Tunda na zo zan ta ya ki Umma." "A'a Islaha, daga Jeddah ki ka zo, baza ki yi aiki ba." "ai ba a mota na zo ba, jirgin ƙasa na hau." "Duk da haka, ki huta." Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, sai ji ana kiran sallah, ta kalli Umma ta ce, "Zan yi Sallah Umma." Umma ta tsame hannunta ta ce, "mu je na raka ki ɗakin sallar." Suna fitowa suka tarar da matar gidan da yaran gidan suna tsaye suna jiran su, Islaha ta ɗaure fuska tana bin su da kallo dan hauka hauka zata yi musu, baza ta bari su latsa ta ba wallahi. Suna wucewa Umma ta ce, "Ikon Allah, na yi mamaki da basu rufe mu da duka ba." Islaha ta ce, "hauka za ki dinga yi musu Umma, in ki ka zuba musu ido raina ki zasu yi. In ni ce a gidan nan da yanzu na gyara musu zama Umma, sai dai na ƙare a gidan yari.” Umma ta cire hijjab jikinta ta ce, "ga hijjab ki yi sallar, ni bani da lokaci yanzu, sai zuwa anjima." Islaha ta ce, "mayafina ma zai yi sallah. Amma Umma na ga kin rame sosai, rashin lafiya ki ka yi haka?." Umma ta ɗn murmusa ta ce, "na yi ciwon dai na warke, sannan...." Ihun matar gidan da ta ji  ya saka ta ce, "zan dawo Islaha, ki yi haƙuri ban ba ko ruwa ba, ina zuwa" ta faɗa tana fita ita dai Iskaha ta bita da kallo ganin duk ta firgice. A nan ta yi alwala ta shiga wajan ta yi sallah, bayan ta idar tana zaune tana jiran Umma amma shiru babu labarinta. Islaha ta miƙe ta fito ta tarar da Umma tana share falon, tana sharewa yarana suna marmasa cake, haka zata dawo ta sake bi ta sharewa. Duk ta yi wujiga wujiga, sai kuma ta ajjiye ta koma kitchen tana duba abinci. Ta dawo sai ga babbar budurwar da kayan wanki ta watsawa Umman, Umma ta tattare ta shiga laundry room lafin ta fito. Daƙyar Umma ta samu lokacin sallah, tana idarwa ta kalli Islaha da take kallon ta ta ce, "ba ki sha ruwan ba." Islaha cikin tausayin halin da Umma take ciki ta ce, "Umma haka ki ke shan aiki a gidan nan?." Ta sauke numfashi ta ce, "kaɗan ma ki ka gani Islaha, komai ni ce, babu abinda aka ɗauke min a gidan nan. Bara na kawo miki abinci." Islaha ta ce, "a'a Umma, wucewa ma zan yi ba sai na ci ba, amma ke ki samu ki ci." "ina na ga lokacin cin abinci? Tun dafe har dare aiki nake yi kamar agogo. Kalli ki ga" ta faɗa tana nuna mata hannunta. Islaha ta ga hannun Umma duk ya yi wani iri, ta ce, "wanki ne, kin ga dai akwai injin wanki ko, to bashi da amfani, dan dauɗar kayansu sai na saka hannu." Islaha ta ce, "Amma wallahi wani abun ki dinga ƙin yi, ki dinga yi musu wuta wuta da yaren ki yadda baza su gane ba, zasu dinga shakkar ki." "Islaha ni zaman ma ya ishe ni, ki dinga yi min addu'a Allah ya kawo silar da zan koma na ƙasata na rungumi yarana. Na watsar dasu a can ban san halin da suke ciki ba, na zo nan na rungumi na wasu ina yi musu bauta. Na bar mijina a Nigeria, na zo ina yiwa mijin wata bauta. Bauta na ke yi a gidan nan ba aiki ba Islaha, bani da banbanci da baiwa. Gashi basa wani damuwa da bani da lafiya sai sun ga dama, ni zan siyi magani na yi jinyar kaina, shiyasa ko bani da lafiya bana faɗa, sai dai na ɗauki ƴan kuɗi na siyi magani. Ga kuɗin babu yawa, gabaɗaya riyal ɗari nake tsira da ita, ɗari biyar ɗin kuɗin ta su Maman Saheer ce." "Riyar ɗari shida suke ba ki? Aka ce riyal dubu?." "Roman ba ka ne Islaha, ƙarya ce wallahi. An zuga ni na zo naga duk abinda aka ce ba haka bane. Na zo da niyar na tara kuɗi, amma har yau ban tara riyar ɗari biyar ba. Masifar da nake ciki a gidan nan yawa ne da ita, gwara na koma gida na bawa kowa haƙuri, na riƙe ƴaƴana." Jikin Islaha ya yi sanyi matuƙa, cikin tausayin Umma ta ce, "Allah zai kawo mafita Umma." "Allah ya kawo Islaha. Ke kam daga ganin ki an san bakya shan wahala." Islaha ta ce, "gaskiya bana shan wahala Umma, inda nake aiki basa bani aiki mai wahalar naki, dan bai kai rabin wannan ba, kuma mu biyu ne. Sannan suna da kirki akasin naki, ranar da na samu attack har asibiti suka kai ni da kuɗinsu, yanzu ma da na ce zan zo madina, kuɗin ticket ɗin da na zo nan sune suka biya min. Kuma akwai maƙotansu ina shiga ina aiki, kyautar kuɗi kawai mai gidan yake bani ba albashi ba." Umma ta goge hawayen da ya sakko mata ta ce, "Kin ji daɗin ki. Ni nan abubuwan sun yi yawa, da girmana amma ban wuce wulaƙanci ba. Babban abinda yake ɗaga min hankali bai wuce mai gidan nan ba, nemana yake yi Islaha.....!" Ta faɗa tana kuka. Islaha gabanta ya faɗi sosai, Umma ta cigaba ta ce, "kwanaki da suka wuce na yi masa barazana da police ya daina, amma a yanzu ta kai ta kawo in ban rufe ƙofata ba sai dai na ji shi a kusa dani. Babu damar na shiga ɗaki sai ya biyo ni, sai dai ina shiga na kulle, in ba haka ba ya farmin." Islaha ta ƙame ƙam ta buɗe ido waje cikin mamaki, hawaye suka taru a idonta ta ce, "Umma!." Sai ta kasa faɗa ta fara kuka. Umman ma tana kuka ta ce, "bai taɓa sanun nasara a kaina ba, kuma Allah bazai bashi iko ba….” Umma ta faɗa cikin kuka mai tsuma zuciya. Nana Haleema. [7/17, 7:20 PM] KRBBK: RDB2P64 Nana Haleema. Islaha ta rungume Umma tana kuka sosai, dan bata taɓa jin abinda ya tayar mata da hankali kamar wanann ba. Mace kamar Umma ace wani namijin yana ƙoƙarin yi mata fyaɗe? Uwa kamar ta, wacce take ƙoƙarin kare mutuncin ƴaƴanta, amma ace ita da kanta wani namiji yake ƙoƙarin haike mata?. Shine abinda ya saka Islaha kuka, Umma tana shafa bayanta ta ce, "ki yafe min da ƙiyayyar dana nuna miki, ki yafe min Islaha. Na nuna bana sonki ba don kin yi min komai ba, yanzu ga shi kece ki ka ɗauko ƙafa tun daga Jeddah ki ka zo madina da ki ganni. In ban da naka waye zai yi maka haka? Sai mai ƙaunar ka." Islaha ta ɗago tana kuka ta ce, "Umma ki zo ki bi ni kawai, bazan iya barin ki a wannan halin ba." Umma ta girgiza kai ta ce, "in bi ki na je ina? Gwara na zauna a nan ɗin, na gama haɗa musu kuɗinsu, daga nan sai na gudu na kai kaina wajan ƴan sanda nace a dawo dani ƙasata." Islaha ta ce, "yaushe za ki tara kuɗin Umma?." "Nima ban sani ba Islaha, kawai ki ta ya ni da addu'a." Islaha ta ja numfashi ta goge idanunta ta ce, "Allah yana tare dake Umma." Umma ta ce, "kar ki faɗawa Safeera, duk da fushi take yi dani, amma hankalinta zai tashi in ta ji ana ƙoƙarin keta min haddi." Ta ɗaga kai ta ce, "ba fushi take yi ba Umma, kewar ki take yi." "In fushin ta yi ma bata yi laifi ba Islaha, tsallake su na yi na taho nan, sai gashi ina yiwa wasu bauta na bar nawa." "Umma ga lamabar ƴan sandar ƙasar nan, da zarar ya sake zuwa inda ki ke ki nuna masa lambar, zai tsorata bazai sake yi miki ba." Umma ta kalla ta ce, "bara na saka a wayata, dan in abin ya ci tura kiransu zan yi." Umma ta saka lambar ta kalli Islaha ta ce, "a ina za ki kwana? Ko yau za ki koma?." "Sai gobe, ina so na shiga masallaci annabi. A can zan kwana, ance min zan iya zamana a can, har na yi wanka na shirya duk a ciki." "Ki yi min addu'a in kin je, ina so na je amma babu dama, ko kuɗin mota ma bani dashi. Albashina na farko ma a magani suka tafi, saboda mura da tari." Islaha ta sauke jakar bayanta, ta ɗauko kuɗi ta ce, "ki riƙe wannan Umma." Umma ta kalli kuɗin, ta kalli Islaha ta ce, "Islaha a ina ki ka samu wannan kuɗin?." Islaha ta ce, "na faɗa miki kyautarsu da ake yi min, ranar farko riyar dubu bakwai ya bani." Umma bata karɓi kuɗin ba, ta zuba mata ido ta ce, "Islaha kar fa ki ɓata rayuwar ki a ƙasar nsn, na lura in ka ja mutuncin ka zaka zauna lafiya, amma in ka watsar ya watse." Islsha ta sakawa Umma kuɗin ta ce, "Wallahi Umma babu abinda nake aikatawa, ki yarda dani, kyauta aka bani." Umma ta kalli kuɗin ta ga riyal dubu biyu ne, ta sauke numfashi ta ce, "na gode, Allah ya albarkaci rayuwar ki, ki yafe min." Islaha ta murmusa ta ce, "Amin Umma. Ina tunanin komawa Nigeria a kwanakin nan, wannan kuɗin da aka yi min kyauta dasu zan biya su Mama kawai na wuce gida." Umma ta ɗaga kai ta ce, "Hakan ya fi miki, Allah ya saka mu a danshin ki."ta amsa da amin a sanyaye. Umma ta ce, "Labiba fa?." Islaha ta ce, "sau ɗaya na taɓa ganinta, har yanzu ban sake ganinta." Umma bata ce komai ba, Islaha ta sha ruwan sannan ta miƙe ta ce, "Umma ni zan tafi." Umma ta miƙe ta riƙe hannunta ta ce, "Allah ya kai ki lafiya, na gode miki, in ba ke ba waye zai yi min abinda ki ka yi? Allah ya albarkaci rayuwar ki." "Amin Umma. In sha Allah sai na zama silar barin ki gidan nan." "Allah ya sa Islaha." Tare suka fito, Islaha ta bi falon da kallo ganin kamar ba yanzu Umma ta gyara sa ba, anyi kaca kaca dashi da abinci. Umma ta ce, "kin gani ko, ga shara ga wanke wanke, ga wankin kayansu, sannan ga kula da yaran. Kullum a haka nake." Islaha tausayim Umma ya sake kamata, a lokacin matar ta fito ta fara yiwa Umma masifa. Umam ta fusata ta ce, "bazan yi aikin ba, ki dake ni. Haifata ki ka yi da za ki dinga yi min faɗa? Dan ina aiki a ƙarƙashin ki sai ki dinga ɗaga min murya?. Wallahi ba ki isa ba, na daina ɗaukat wulaƙancin ki!." Sak matar ta yi, duk da ba ji take yi ba amma Umma ya bata tsoro, ta ja baya ganin Umma tana yi mata faɗa sosai, sai ta bar wajan bata ce komai ba. Islaha ta ce, "Yauwa Umma, haka za ki dinga yi musu, duk da ba ji suke yi ba amma zasu yi shakkar ki, ki dinga ƙunduma musu ashariya." Umma ta ce, "Na gaji islaha, mu je na raka ki." Tare suka fito Umma ta raka ta har kan titic ta tari taxi ta hau Umma ta koma ciki cikin kewa. Islaha tunda suka ɗauki hanya ta yi lamo a jikin kujera tana kallon titi, tunanin halin da ta ssmu Umma take yi da abinda take faɗa mata. Ta sauke numfashi tana tunanin ita kam Allah ya tarfawa garin ta nono, Allah ya kai ta hannu na gari, basu taɓa ƙoƙarin cutar da ita ko neman ta da wani sharri ba, ga kuɗi da take sami hankali kwance ba tare da ta ba da kanta ba. Tabbas Allah ne ya ga zuciyarta ya haɗata da mutanen kirki masu farar zuciya, in itace a halin da Umma take ciki bata san wanne mataki zata ajjiye abinda zai faru ba. Kallon titi take yi ganin ko ina mai kyau da ɗaukar hankali, ta girgiza kai tana tabbatar da an yiwa nigeria nisa ta ko wanne fanni. Sun ɗan jima suna tafiya kafin ya tsaya, a nan take hango gate ɗin masallacin, ga mutane ana ta shige da fice dan a idar da sallar la'asar lokacin. Cikin zumuɗi da sanyin jiki ta fito, ta bashi kuɗin da suka yi sannan ta taka a hankali tana nufar gate ɗin. Tafiya take yi tana kalle kalle, ta san duk wanda ya ganta ya san faron zuwa masallacin ce, amma sai ta ga babu mai kallon ta kowa harkokinsa yake yi. A sanyaye take takawa tana sake kallon ko ina, sai yanzu ta san ta shiga madina, dan Umma a ƙauyen Madina take. A haka ta riski inda banɗaki yake, ta ga mata yadda suke hawa excletor yana sauka da su banɗakin, itama ta bisu ta yi alwala ta fito ta yi sallah a harabar masallacin. Babu inda ta sani, bata san kuma me zata yi a gaba ba. Tana zaune tana kalle kalle, sai kuma ta tashi ta shiga cikin mata ganin ana ahiga cikin masallaci. Shiga ta yi ta zauna ganin mata a zaune wasu suna addu'a wasu suna karanta alkur'ani. Ta zauna ta ɗauki alkur'ani tana karantawa har aka yi sallar i'sha tana ciki, yunwa take ji, amma saboda bata son fita haka ta maƙale a ciki gani take ksmar in ta fita bazata dawo ba. Jin yunwar ta dame ta ya saka ta fito, ta si yi abinci ta koma harabar masallacin ta ci ta sha ruwa. Sai kuma ta miƙe tana zaga ko ina dan in ba haka ta yi ba bazata rage dare ba. Tun daga farkon masallacin sai da ta kai ƙarshe, nan ta ga mata sun hau layi ita dai bata san me za a yi ba itama ta hau. Sai gashi ta shiga rauda wothout nusik permit, ita bata san ma rauda za a shiga ba, sai da aka shiga ɗin wannan ta ji hakan a zuciyarta. Bayan sun fito ta dinga jin farin ciki yana ratsata, tunda ta zo ƙasar bata taɓa jin daɗi da alfaharin zuwa kamar lokacin ba. Ta dinga yawace yawace, ta shiga binwood, ta shiga movepick har taba da wayar ta ayi mata hotuna. Haka ta raba dare tana zaga ko ina, in ta ga wani hotel da ya yi mata kyau kawai ta shiga ta gama yawo da ɗaukar hoto sannan ta fito. Sai biyu na dare ta koma cikin msallacin, a nan bacci ya ɗauke ta bata farka ba sai kiran farko na asuba. Duk da baccin da take ji haka ta fita ta yi alawa ta dawo ta fara sallah tana addu'a. Sai bayan sallar asuba sannsn ta fito ta shiga banɗaki ta yi wankanta, ta canja kaya ta saka wasu kayan a cikin jakar. Ta so komawa Jeddah da safe, amma da ta tuna juma'a ce sai ta fasa, ta yi niyar sai bayan juma'a sai ta tafi. Sai bayan an idar da juma'a sannan ta fara shirin tafiya, sai take ji kamar kar ta tafi, ta dinga jin zuciyarta babu daɗi kamar ta koma. Ta ji daɗin zaman kamar ta cigaba da kwana kar ta koma, dan ita kam ko shekara zata iya yi a haka; ta kwana a masallaci abinta. Har zata tafi sai ta fasa, ta sake komawa ta kwana asabar, ta saka sabuwar rigar da ta siya sannan ta fara shirin tafiya saboda marar ta da ta ji tana ɗaurewa alamun period zata yi. Duk sai hankalin ta ya tashi kar ciwo ya riske ta a haka, a station ɗin ta si yi tucket na daidai kuɗin wancan, ta shiga ta zauna a seat number ta. Idonta a rufe yake ruf, ta jingina da kujera tana jin yadda mararrta take ɗaurewa tana rutse ido. Ƙhamshin turaren wanda yake kusa da ita ya mamaye hancinta, sai ta ja facemask ta rufe hancinta, ta saka hannu ta kashe a.c inda take saboda sanyi, ta ja labule ta rufe window ɗin. Babu jimawa sai ta ji an kunna ac, ta ɗago jajayen idanunta ta kalli wanda yake zaune a gefenta, a lokacin jirgi ya fara tafiya........... Nana Haleema. [7/19, 10:59 AM] KRBBK: RDB2P65 Nana Haleema. Kansa yana ƙasa yana danna waya kamar bai san abinda ya yi ba, Islaha ta ɗauke kai ta sake kashe a.c, dan yadda kansa yake a duƙe kuma ya saka glasses bata gane waye a kusa da ita ba. Ta sake komawa ta kwanta tana runtse ido cikin ciwon da ya fara takura mata. A lokacin train staff suka fara raba musu abin sha, Islaha idonta yana rufe bata sani ba, sai magana ta dinga ji a kanta sama-sama. Sanyin ta sake ji ya dame ta, ta ɗaga kai ta ga an sake kunna ac, ta waiwayo ta kalle sa a lokacin ya ɗago kai yana magana da wani da yake ɗaya side ɗin. Yana juyowa suka haɗa ido, dan ya cire glasses ɗin idanunsa. Islaha gabanta ya yanke ya faɗi, ta yi saurin ɗauke kanta tana mamakin wacce irin ƙaddara ce take haɗasu ko yaushe? Ita ba wata danginsa ba, amma ko yaushe sai su haɗu. Bata ce komai ba, tacure a waje ɗaya, ta kifa kanta a jikinta tana kuka mai sauti. Rehaan yana jinta, duk da ta rufe rabin fuskarta da face mask amma ya gane ta, haushinta ya sake mamaye masa zuciya. Ya ja tsaki ya ɗauke kai yana jin kukanta a kunensa, bai san ƙaddara da ta saka shi siyan ticket na kusa da ita ba, ji yake kamar ya miƙe ya koma wani wajan saboda takaici. Kuka take yi sosai, sanyin ya yi mata yawa ga ciwon da yake damunta. Ta yi shiru bata ce komai ba, bata cikin yanayin masifa dan tana kan ciwo, sauƙi take nema, amma bata san inda zata same shi ba. Ga sanyi, ga ciwo, gashi bata da mai taimaka mata. Muryar ta a sarƙe ta ce, "Don Allah ka kashe ac, zan mutu." Banza ya yi mata kamar bai ji ba, bai ma motsa ba balle ta fahimci ya ji har ya kashe ɗin. A daidai lokacin mararta ta murɗa sosai, bata san ta riƙe hannunsa ta matse ta saka kuka mai ƙarfi ba. Kukan ta duk sai ta jawo hankalin mutanen da suke zaune a train ɗin, da sauri ma'aikatan suka ƙaraso wajan ta ana tambayar ta abinda yake damunta. Shi dai takaici ya gama mamaye masa zuciya, gashi ta riƙe masa hannu ga mutane a kansu sai kallonsa ake yi kamar wani tv. Ya ja siririn tsaki dan bai san me zai ce musu ba, gabaɗaya zaman jirgin ya ishe shi, ba ya son ganin fuskar yarinyar ko kaɗan. A lokacin wani ma'aiakcin train ɗin ya ƙaraso, ganin hannunta a cikin na Rehaan, sai ya kalli Rehaan sai ya ce, "Me yake damun ta?." Rehaan ya ɗago ya kalle sa, ya harare sa ya yi masa banza bai ce komai ba, dan indai a kanta ne bazai yi magana ba, bai ga dalilin da zata shiga shiga rayuwarsa ko yaushe ba. Train staff ɗin ya ce, "she's your wife?." Nan ma ya share sa yana ƙoƙarin zame hannunsa a hankali ba da ƙarfi ba, amma ta riƙe sosai ga zafin da hannunta ya yi yana ratsa fatar hannunsa. Ta daina kukan sai hawaye kawai take yi, tana jan numfashi kamar mai naƙuda, a hakan ma dauriya take yi, ita kaɗai ta san adadin ciwon da yake nuƙurƙusar ta. Ganin sun kafe shi da ido sai ya ɗan kalle ta, muryarsa a hankali ya ce, "suna tambayar ki, ki faɗa musu me yake damun ki." Islaha idonta yana rufe, ta buɗe ido ta kalle sa suka haɗa ido dan ita yake kallo, yadda ya ga fuskar ta ta koma sai jikinsa ya ɗan yi sanyi, ba sai ance maka bata da lafiya ba, kana kallon ta kasan babu lafiya. Ta ɗan miƙe zaune sosai sannan ta ce, "paracetamol za a bani kawai." Da gaggawa aka kawo mata aka bawa Rehaan dan ya bata. Kamar ba ya so haka ya karɓa, ya miƙa mata yana kallon ta. Islaha hannunta yana rawa ta raba hannunta da nasa ta karɓa ta sha, ta koma ta kwanta ta lumshe ido, sai kuma ta tattare ƙafarta, ta haɗe da ƙirninta ta saka kanta a ciki. Wayarsa kawai yake dannawa kamar bai san abinda yake faruwa ba, sai daga baya ya kashe ac tana kwance a haka tana jin sauƙin ciwon a hankali sai ciwon kai da ya dame ta. Dan ita bata san irin ta ba, bata son ac a mota balle kuma a jirgi. Yanzu sai ac mota ta saka ta ciwon kai, ko za a saka tafi son a saka kaɗan, kar ta yi yawan da zata dame ta. Kafin su je Jeddah ta ɗan ji sauƙi, train yana tsayawa ya fita bai sake waiwayenta ba, itama ta miƙe tana tafiya a hankali, larabawa suna ta yi mata sannu, sai dai ta ɗaga kai tana fatan Allah ya sa bata yi staining wajan ba. A haka ta fito, a lokacin rana ta buɗe sosai, ta tsaya daga can gefe tana ji kamar jiri yana ɗaukarta. Bata san inda zata bi ta hau mota ba, dan ba a nan suka zo da Sunaira ba, nan arrived area ne, gabaɗaya bata gane wajen ba, ga ciwon da yake damunta. Rehaan kuwa kai tsaye inda ya bar motarsa ya je ya ba da pass ɗin ajiyar aka bashi, yana zaune yana kallon ta. Kallon ta yake yi, ba sai an faɗa ba, kai da ka ganta ka san gaske bata jin daɗi, yana so ya taimake ta amma kuma ba ya son abinda zai haɗasu a waje ɗaya, shiyasa yake kaucewa, amma Allah ya sani yana so ya taimake ta musamman da take tsaye a kan titi kamar zata faɗi. A hankali ya ƙarasa da motar kusa da ita, ya sauke glass a hankali yana kallon ta. Islaha idanunta a rufe suke, amma tunda motar ta zo kusa da ita ta ji ƙhamshin turarensa, ta buɗe ido suka haɗa ido, ta sunkuyar da kai ƙasa tana ji kamar ta faɗi. Kamar ba ya son magana ya ce, "mu je." Bata da yadda zata yi, in a son ranta ne itama baza ta shiga motarsa ba, amma da yake neman taimako take yi sai ta motsa daga inda take, ta yi kamar zata faɗi ta yi saurin dafa motar. Rehaan ya ce, "ki shiga back seat" ya faɗa ganin kamar kafin ta ƙaraso front ɗin zata iya faɗuwa. Islaha a hankali ta shiga bayan motar, ƙhamshin turarensa ya mamaye motar, ta jingina a hankali shi kuma ya ja motar suka tafi. A hankali yake tafiya, babu sautin komai a motar, sai ƙarar wayarsa kuma baya amsawa. Idonta a rufe suke, tafiya kawai take ji ana yi, tafiyar mai laushi babu gargada, sai zaman ya yi mata daɗi sosai, dan ba a motsa ta balle ta ji wani abu. A  har suka je unguwar ya tsayar motarda yana kallonta ta mirror, idanunta a rufe suke har lokacin, yanayinta gabaɗaya ya koma na marasa lafiya, yana so ya ji me yake damunta amma sai ya ga kamat bai shafe shi ba. A lokacin ta buɗe ido suka haɗa ido, ta sauke ido ƙasa ta kalli unguwar ta ga har sun zo. Ta ɗauki jakarta ta kalle sa ta ce, "Na gode." Bai ce komai ba ta buɗe ƙofar ta fita, shi kuma ya danna remote ɗin gate ɗinsa ya buɗe ya shiga, bai tsaya ya ga inda ta shiga ba. Islaha tunda ta shiga ta kwanta a kan gado, Sunaira ta zo tana yi nata sannu da zuwa ganin bata da lafiya sai ta fita ta ƙyale ta. Shi kuwa Rehaan yana ajjiye motar ya shiga cikin gidan, ya hau sama ya shiga wanka bayan ya fito ya yi sallar azahar ya kwanta bacci. Sai la'asar ya farka, ya sake yin wanka ya saka jallabiya ya sakko ya shiga masallaci ya yi sallah sannan ya fito. Yana fitowa ya shiga coffee bar ɗin da yake kusa da gidan su, ya zauna tana duba menu, kafin ya yi order aka kawo masa black coffee da brownie, sai kuma biryani rice. "Hii Rehaan." Aka faɗa ana zama a kusa dashi. Ya ɗago kai suka haɗa ido da Ubaid, sai ya basa hannu suka gaisa kafin ya ce, "Hii." Ubaid ya ce, "kwana biyu ina ka je? Bana  ganin ka." "Madina" ya bashi masa a nutse yana cigaba da cin abincinsa. Ubaid ya ce, "Nima na je, mun je tare da Babyna, na rigata dawowa ne kawai." Rehaan ya kalle sa yana mamaki, ya rasa meyasa Ubaid ya raina sa, ba ya iya ɓoye yana neman mata, har faɗa yake yi ya je da wacce ba matarsa ba Madina suna aikaita saɓon Allah, ko kunya ba ya ji faɗa yake yi kamar ba babban abu ya aikata ba. Sai kuma ya tuna shi ƙasar ce, ba wani abu bane a wajansa. Ubaid ya ce, "wallahi ina son ƴan matan ƙasar ku, Allah ya yi musu wata baiwa ta musamman, wacce sai ka shiga za ka gane. Rehaan black sun haɗu sosai, akwai albarka a tare dasu. Irin abinda za ka samu a tare dasu bazai misaltu ba wallahi." Rehaan ya ji kamar ya shaƙe masa wuya, ba ya son wannan maganar ko kaɗan, ɓata masa rai take yi ta fusata shi lokaci ɗaya. Ya daure ya share bai ce komai ba, haka kawai ya ji abincin ya fita daga ransa, ya kalle sa ya ce, "na faɗa maka ka daina bani labari ko?." "Ina so kaima ka ɗanɗana ne shiyasa. In kana so zan turo maka ita ta kwana biyu a wajan ka, na yi maka alƙawarin za ka so hakan." "No need" Rehaan ya faɗa yana harararsa Ubaid shi kuma yana dariya, dan wani lokacin da gangan yake tsokanarsa, dan ya san ba ya so. Rehaan ya miƙe ya biya kuɗi ya fita yana jin haushi. Yana shiga gida ya ji wayarsa ta yi ƙara alamun shigowar saƙo, da ya ga Ubaid ne sai ya yi tsaki ya jawo laptop ya fara abinda yake gabansa dan gobe yana da morning duty. Waya yake yi ta ko ina, maganar harkar kasuwancinsa yake yi, gabaɗaya ya takura saboda amsa waya, wannan ya kira sa wannan ya kira sa. Ya jima a haka, sai dai ya tashi ya yi sallah ya dawo, har aka yi sallar i'sha yana a haka. Maganar Ubaid ce ta faɗo masa a rai, sai ya tuna da saƙonsa ya ɗauki wayar ya ga ƙaramin video ne, kuma viewonce ya tura masa. Kamar ya share kar ya buɗe sai kuma ya buɗe, video yana loading shi kuma yana kallon laptop ɗinsa. Wani irin yarr ya ji a jikinsa lokacin da ji abinda yake fitowa daga video, ya kalli wayar sai ya yi saurin ɗauke kai ya kashe video, ya dafe kansa ya yi shiru cikin takaicin Ubaid wanda bai taɓa ji ba. Ƙaramin video ne, babu fuskarsu amma akwai muryarsu cikin fitar hayyaci wanda ya ke nuni da dukka basa hankalinsu. Wani irin dum dum dum haka ya ji zuciyarsa tana yi, ya runtse ido ya saki wayar ta faɗi a ƙasa, jin muryoyin yake yi yi har tsakiyar kansa, ya sauke numfashi yana jin haushi da tsanar Islaha tana mamaye masa ko wanne ɓangare na jikinsa. Bai taɓa jin tsana mai muni lokaci ɗaya kamar tsanar ta ba, danasanin taiamka mata ya mamaye masa rai. Sai yanzu ya ke tunawa ashe ma tare suka je Madina da Ubaid ɗin, tunda ga shi ya ganta ita kaɗai babu shi. Ya cize bakinsa cikin takaici, baƙin cikin taimaka mata yana yi masa dirar mikiya, ji yake kamar ya dawo da wajen baya, ya jawota ya zabga mata mari sannan ya cilla ta kan titi mota ta take ta. Da ana dawo da abinda ya wuce, da ya dawo dashi ya goge taimaka mata da ya yi a ranar. A bayyane ya ce, "Allah ka yi maganin matan da suke zuwa ƙasar waje suna lalata mana sunan matan ƙasar mu, Allah ya shiga tsakanin mu dasu, ka yi mana tsari dasu gaba da baya." Duk yadda ya so yakice takaicin Islaha daga idanunsa amma sai ya kasa. Shi mutum ne da yi rayuwa a cikin turawa, lokacin da yana makaranta suna sha ganin mace da namiji suna abinda suke so, ya gani sau babu adadi musamman a school, amma bai taɓa jin takaici akan hakan ba, bai taɓa jin ya tsani wanda ya aikata ba, bai taɓa jin haushi ko zafin abin ba. Amma yanzu kam ya ji takaici da baƙin ciki wanda bai taɓa ji ba tunda ya zo duniya. Shi kansa tunani yake yi, meyasa ya damu da ita har haka? Amsar itace; bai sani ba, amma yana tunanin dan ta kasance bafulata kamar sa ne, shiyasa yake jin haka.     Islaha kuwa ta ɗan ji sauƙi babu laifi, a haka ta yi bacci sanin ba sallah zata yi ba ta sa ki jiki ta yi baccinta, dan Sunaira da ta ga bata da lafiya bata takuta mata ba kuma daman masu gidan basa nan. Cikin bacci ta ji ana kiran sunanta, ta buɗe ido a hankali tana kallon inda ta ji maganar, da hanzari ta miƙe ganin Labiba a durƙushe a gabanta. Da mamaki mai yawa Islaha take bin Labiba da kallo ta ce, "Labiba!." Labiba ta kifa kanta a kan gado, cikin ciwo da tsananin azaba ta ce, "Islaha, ki taimaka min mu je asibiti, taimaka min ki raka ni don Allah. Zan mutu, zan mutu Islaha!." Hankalin Islaha ya tashi, tsoro da firgici suka shige ta, ta riƙe Labiba ta ce, "meyasa same ki? Me ki ke ji?." "Marata! Ki taimaka min zan mutu." Ta diro daga kan gadon, ta shiga baɗaki ta wanke baki a gaggauce ta fito ta saka hijjab. Ta kalli Labiba ta ce, "za ki iya tashi?." Labiba ta ɗaga mata kai kawai, dan ita kaɗai ta san azabar da take ji. A haka suka fita Islaha ta tsayar taxi ta ce a kai su asibiti ma fi kusa. Labiba tana jikin Islaha tana ta yi mata sannu, sai shafa fuskarta take yi ganin yadda take gumi kamar wacce zata haihu. Nana Haleema✍🏻❤️ [7/19, 10:59 AM] KRBBK: RDB2P66 Nana Haleema. Islaha jin abu mai ɗumi yana taɓa ƙafarta ya saka ta kalli ƙafarta, ganin jini ya saka gabanta ya faɗi, sai take tunanin wanne irin jini ne wannan a jikinta? Ita ba mai haihuwa ba mai zai saka ta ga wannan jinin?." A lokacin suka iso asibitin, da hanzari aka zo aka shiga da Labiba ganin yadda jini yake zuba a jikinta duk ya ɓata Islaha. Sai bayan an shiga da Labiba, a lokacin Islaha ta bi jikin Labiba da kallo, ta duba jikinta ta ga ba daga jikinta jinin ya zo ba, daga jikin Labiba ne. Ta kalli kayanta duk hijjab ɗin ya ɓaci, ta biya mai taxi ta shiga ciki da sauri. Bata ga inda suka shiga da Labiba ba, ta zauna a reception ta dafe kai tana tunanin abinda yake damun Labiba har haka. Ta sake kallon jinin, ta ga yadda ya ɓata, ta yi tsaki ta rasa me zata yi. Sai ta miƙe ta ƙarasa reception ta tambayi inda zata ga Labiba aka faɗa mata tana emergency. Aka tambayi details ɗinta a wajan Islaha ta faɗa sannam ta wuce can. A tsaye ta tsaya tana kai kawo cikin rashin sanin abinda yake faruwa, sai da likita ya fito ta ƙarasa wajan sa ta ce, "me yake damunta Dr?." Zuwa lokacin har an turawa Dr details ɗin Labiba, dan haka ya kalle ta ya ce, "Labiba?." Ta ɗaga kai alamun eh, Dr ya ce, "she had miscarrige!." Wani irin bugawa ƙirjin Islaha ta yi, ta maimaita kalmar miscarriage a ranta, tana tunanin meye ma take nufi, dan kanta ya manta meye ma kalmar misscarrige take nufi. Dr ya ce,  "ta samu bacci yanzu, za ki iya zuwa wajan ta" ya faɗa yana nuna nata ɗakin. Har ya ɓace Islaha ta kasa motsin kirki, sai daga baya ta shiga a sanyaye tana ji kamar ta yi kuka saboda yadda take ji zuciyarta tana bugawa. Ta tsaya tana kallon Labiba tana tuna kalmar ɓarin ciki da aka faɗa mata, har an canja mata kaya zuwa uniform na asibitin, tana kwance tana bacci an saka mata ruwa. Islaha ta zauna a gefenta tana kallon ta cikin wani irin yanayi na bugawar zuciya. Sai maimaita kalmar take a ranta, ta rasa wanne irin tunani ya kamata ace ta yi. Sai bayan azahar Labiba ta farka, suka haɗa ido da Islaha da take zaune ta yi tagumi tana kallonta, amma ta cire hijjab ɗin ta ajjiye a gefe. Islaha ta ce, "Sannu." Labiba ta ɗaga kai ta ce, "me ya same ni?." Islaha kai tsaye ta ce, "kin samu miscarrige ne." Labiba ta kasa ɗauke ido daga kan Islaha jin abinda ta ce, sai kuma ta sunkuyar da kai tana jin kunya ina ma bata kira Islaha ɗin ba, ina ma ita kaɗai ta zo da Islaha bata san sirrinta ba. A lokacin nurse ta shigo, aka tafi da Labiba ɗakin scanning, Islaha dai tana zaune a ɗakin bata je ko ina ba. Gajiya ta yi da zaman, ta miƙe tana kallon abayar jikinta, sai ta shiga banɗaki ta wanke inda jinin ya ɓata, tana yi tana mita ta ce, "Aikin banza, ni ba yin ciki ba ni da wanke jinin shege. Allah ka kiyaye mu, ka cigaba ba mu kariya gaba da baya." A haka ta ɗan wanke, sai kuma ta ga rigar ta jiƙe da yawa, kawai sai ta ɗauki uniform na asibitin ta saka, ta shanya rigar a kan ƙofar banɗakin, ta fito ta hau kan gadon da niyar in Labiba ta dawo zata tashi. Tunani take akan lamarin Labiba, tana mamakin ciki, kuma a ƙasar Saudia aka same shi, kuma yadda Labiban ta sunkuyar da kai ya bata tabbacin ta san da cikin, ta girgiza kai tana jin babu daɗi a ranta. Bata taɓa ganin wacce ta samu ciki ba ta hanyar aure ba ido da ido sai Labiba, shiyasa abin yake ɗaure mata kai sosai. A lokacin aka buɗe ƙofar ɗakin, ta juya ta kalli wanda ya shigo dan a tunaninta su Labiba ne, bata gane waye ba dan scrub ne a jikinsa irin na likitoci, sannan ga hular tiyata ga face mask. Kafin Islaha ta yi magana an juya an fita daga ɗakin an rufe ɗakin, sai ta taɓe baki ta koma ta yi kwanciyar ta, dan gaskiya bazata tashi ba sai Labiba ta dawo. Rehaan da ya yi mistake ɗin ɗaki ya tsaya bayan ya fita ya yi shiru, ya tafi tunani yana girgiza kai, yana sake tambayar kansa kamar yarinyar can ya gani, yarinyar da ya taimaka mata a train. Sai zuciyasa take faɗa masa me ya same ta har haka? Ko ciwon train ɗin ne har yanzu bai bar ta ba?. Ya shiga office yana cire hular kansa ya zauna yana tunanin da bai san dalili ba. Ya kalli landline yana tunanin ya tambayi reception amma yana tunanin ina ruwansa? In ma itace ina ruwansa da zai damu?. Ya sauke numfashi, ya girgiza kai yana so ya kawar da ita daga ransa amma sai ya kasa, ya tallafi haɓa yana tunani, sai kuma ya yi tsaki ya ɗauki wayar ya kira reception. Daman sun san daga inda kiran yake, suna ɗauka ya ce, "what happened to the patient in room 202 of the emergency ward?" "Wait a minute." Ya yi shuru yana ji ana danna computer sannan aka ce, "She had a miscarriage Sir, She was three weeks pregnant... and she took the wrong medication without knowing it was harmful to her condition." Rehaan ya ji wani irin dummm a tsskiyar kansa, ya runtse ya furzar da iska, ya haɗɗiye yawu don son tabbatarwa ya ce, "Are you sure it's the patient in room 202 who had the miscarriage?." "Yes Sir. There is no mistake, her name is Maddibo Mu....." Rehaan kafin ta kai ƙarshe ya dakatar da ita ya ce, "is okay, thnak you." Ya ajjiye wayar yana tuna sunan Islaha Muhammd Maddibo, ya shafa kansa yana ji kamar wutar tsanar ta ake hura masa a zuciyarsa. Kenan condition ɗin da ta shiga a train ciki ne? Ya ɗaga kai sama yana jin wani irin yanayi, kuma ya tuna abinda Ubaid ya tura masa. A bayyane ya ce, "Oh Allah! Meyasa nake haɗuwa da yarinyar nan ne? Meyasa ƙaddara take haɗa mu da ita ko yaushe?" Ya faɗa yana dukan table, yana ji ina ma bai taɓa saninta a duniyarsa ba. "Kuma cikin Ubaid ne!." Ya rufe ido ya buɗe, sai ya sauke numfashi ya ce, "bazan sake ganin ta ba daga yau, in sha Allah!" Ya faɗa yana jan numfashi, sai kuma ya ɗauki kayansa ya fita daga asibitin. Labiba ta kasa yiwa Islaha magana itama bata ce komai ba, sai dare sannan aka aka yi discharging ɗinsu Labiba da kanta ta biya duk wani bill. A taxi suna tafiya Labiba ta kalli Islaha ta ce, "Don Allah kar ki faɗawa kowa wannan maganar, tsautsayi ne, kuma baza a sake ba." Islaha ta wani kalle ta ta ce, "ina ruwana Labiba? Lokacin da ki ka yi na sani, In ba dan neman taimakona da ki ka yi a lokacin ba kin taɓa nema ne?. Nima saboda zuciyar musulunci ya saka na kalle ki, kuma ina kallon ki a matsayin ƙanwar Hamma. Labiba bata ce komai ba, itama ta share ta suna zuwa ta fita daga motar bata sake kallon ta ba. Haka Islaha ta kwana da wannan tunanin, da ta motaa abin take tunawa tana ganinsa kamar a mafarki. Da safe bayan sun gama komai ta nufi gidan Rehaan dan yin aiki, da kuma sake yi masa godiya akan abinda ya yi mata. Tana shiga ta ji falon shiru babu kowa, lokacin sallar azahar ne ta tabbatar bacci yake yi. Ta dafa tea ta ajjiye, tana zaune ita kaɗai har aka yi sallar la'asar. Da yake ba sallar zata yi ba bata tashi, tana zaune a kitchen tana danna waya ta ji an shigo falon. Ta ɗago kai, sai kuma miƙe a sanyaye ta fito tana fitowa falon suka haɗa ido. Ta ɗan yi murmushi, da son nuna masa ta gode akan taimakonsa, ba dan haka ba shi ya isa ta kulasa. Islaha ta ce, "ina yini" ta faɗa da hausa tana kallonsa. Ya yi shiru bai ce komai ba, yana kallon fuskar ta sau ɗaya ya ɗauke kai, domin yanayinta da komai na ta ya yi kama da wacce ta samu miscarrige ɗin. Islaha ta ce, "na gode da taimakona da ka yi." Ya juyo ya kalle ta, sai kuma ya dawo da baya ya zo kusa da ita yana kallon ta ya ce, "I don't ever want to see your face again. Stay away from this house. Your face is the first face I've ever hated seeing in my life......" Ya dakata yana kallon ta kamar yadda take kallonsa, ya girgiza kai ya ce, "Bana so na sake ganin ki, daga yau!." Islaha ta bi sa da kallo tana mamakin kalamansa, daman yana da guts ɗin cewa ya tsane ta? Ta yi tunanin itace zata ce ta tsane sa ba shi zai faɗa ba. Sai ta ga ya ja bayac ya ajjiye kuɗina inda ya taɓa ajjiye mata ya ce, "ki ɗauka, ki je ki cigaba da abinda ki ka saba. But I don't want my name dragged because of you." Da mamaki take kallonsa ta ce, "Dragged your name? Akan wanne dalili kenan." Bashi da lokacin bata amsa, ya wuce ta sai ta ga kamar in ta bari ya tafi bata tanka ba ya gama ci mata fuska. Ta ce, "Ji mana! Dan na zo gidan ka ina aiki ba haka yana nufin kana da ikon faɗa min abinda ka ga dama ba. In kana so kace na daina zuwa gidan nan ka faɗa kai tsaye, ba sai ka yi ƙoƙarin ci min mutunci ba. Ka ke zancen ka tsane ni, kai ka ɗauka nima sonka nake yi? Wallahi nima babu wanda nake jin haushi kamar ka, in ba ka sani ba yau ka san da hakan. Ina zuwa gidan nan saboda wani dalili, kuma na samu mafitarsa, dan na daina zuwa kai zaka ragu da rashin zuwana, ba ni ba." Ya waiwayo ya kalle ta yana mamakin ƙarfin hali da rashin kunyar yarinyar nan. Ya record ɗin miscarrige ɗinta ya zo har office ɗinsa, amma ta dinga faɗa masa wannan maganar banzar?. Kamar bazai kula ta ba, sai kuma ya ɗan ɗaga kai ya ce, "Thank God you've found your solution. Now leave! I don't want to see you again. Go and continue your filthy prostitution." Islaha ta wani zaro ido, cike da tsiwa da rashin kunya, da tafasar zuciya ta ce, "Kar mu zo nan, kar ka kuskura ka kira ni da kalmar karuwa!" Ta faɗa da hausa tana kallonsa. Ya ɗan buɗe ido, wani irin haushinta yake ji ba kaɗan ba, sai ya ya jingina da staircase yana yi mata kallon ƙasƙanci ya ce, "Let me say it again, you're a prostitute and a thief. Za ki dake ni?.." "Bazan dake ba, amma harshena zai dake ka. Ni ba karuwa bace, kar ka sake kirana da wannan sunan. Sannan ni ba ɓarauniya bace, sau ɗaya na taɓa ɗaukar abinda ba nawa ba, kuma saboda shi nake a ƙasar nan. Ba ka isa ka faɗa min magana wacce bata yi min ba na ƙyale ka. Kar ka yi tunanin saboda kai ne Rehaan Yola zan saurara maka, wallahi bai dame ni ba, ko kai waye a duniyar nan ba ka isa ka ɗaga min murya na ƙyale ka ba." Sai ya ga kamar yana zubar da ajinsa in ya tsaya yana magana da ita. Ya ɗauke kai ya ja tsaki ya fara hawa sama, sai kuma ya tsaya ya kalle ta kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya hau sama bai sake waiwayonta ba, dan Allah ya sani ba ƙaramin haushinta yake ji ba. Ta kalli kuɗin da ya ajjiye, ta kalle sa tana ganin a lokacin zai shiga bedroom, ta zubar da kuɗin a ƙasa ta ce, "bani da buƙatar kuɗinka, kuma Allah sai ya saka min ƙazafin da ka yi min...bazan yafe wannan kalma ba, sai Allah ya tsayar damu a ranar hisabi, ka yi bayanin sunan da ka kira ni dashi." "Kuma ka jira Rehaan Yola, wallahi sace ni ɗin da ka yi bazai tafi a banza ba, sai na nuna maka waccece Islaha!." Yana jin duk abinda take faɗa, ya shiga ɗaki ya rufe ƙofa, ta tsaya tana kallonsa cikin wani irin baƙin cikin da bata taɓa jin irinsa a rayuwar ta ba. Ta kasa tafiya saboda takaici, bata san ta fara hawaye ba, sai ɗuminsu ta ji akanfuskarta. Ta goge ido, ta sake kallonsa sai ta fashe da kuka, tana tunanin wacce halitta ce a jikinta da ake yi mata kallon karuwa?. A haka ta ja ƙafar ta ta fita daga gidan, tana ji a ranta ta fita kenan har Allah ya tashi duniya baza ta dawo ba. Rehaan fan's yaneee🤣🤣🤣 Nana Haleema. [7/20, 10:26 AM] KRBBK: RDB2P67 Nana Haleema. Islaha ko da  ta koma gida Maleek sai kawai ta sake fashe da kuka, kuka ta yi sosai, kuka mai mai tsuma zuciya da baƙin cikin da bata san na meye ba. An daɗe ana kiran ta da karuwa, ba yau aka saba kiran ta da sunan ba, sunan ba baƙo ne a gare ta ba. Bata san dalilin mutane na faɗa mata ba, amma bata taɓa jin zafi da haushin kalmar kamar yau ba. Ko dan Rehaan Yola ne ya faɗa mata bata sani ba, amma yadda kalmar ta yi mata zafi a ranta ko kalaman Mama basu taɓa yi mata zafi haka ba. Tunanin ta ɗaya ko yaushe, wacce halitta ce a jikinta da ya saka ake yi mata kallon karuwa? Aikinta ne ya jawo ko kuma ina ta tashi? Haka ake yiwa waɗanda suka tashi a gidan marayu kallon karuwai ko kuma ita kaɗai ta fita zakka?.... Ta yi kuka ta gode Allah, kalmar ɓarauniya tana sake tsaya mata a zuciyata. Ta lumshe ido tana goge idanunta, tana jin zafi da ɗaci yana mamaye mata ko ina na jikinta da jinin jikinta. Ashe da ƙaryar haushin sa da take yawan faɗa take yi, sai yanzu ta san meye asalin jin haushi, bata taɓa jin ta tsani abu kamar yadda take jin ta tsani Rehaan ba, yanzu ta san meye tsana da jin haushi, da bata san komai ba. Ta goge idonta ta kanta a hankali tana ji hawaye yana sake sakkowa. Bata san lokacin ta kwashe a haka ba, tana ji wayar ta tana ƙara amma bata iya ɗauka ba saboda yadda jikinta yake a sanyaye, haushi da baƙin ciki ya gama mamaye mata zuciyarta. Gabaɗaya zaman ƙasar ya fita daga ranta, komawa gisa take da buƙatar yi cikin gaggawa, bata son zaman ko kaɗan. Ta jawo waya ta ga wanda ya kira ta, bata bi kiran ba ta kira Alhaji Musa. Bata jima tana ringing ba ya ɗauka, suka gaisa sannan ta ce, "Don Allah zan iya ganin ka zuwa gobe?." Alhaji Musa ya ce, "wani abun ne ya faru?." Islahs ta ce, "eh, ina so na ganka don Allah." "Zan shigo zuwa dare, ina garin Jeddah, amma ina airport, zuwa anjima zan zo." Ta amsa ta kashe wayar ta koma ta kwanta, sai kuma ta miƙe ɗauko kuɗin da suke hannunta gabaɗaya. Wanda ya bata a ƙarshe suna nan bata taɓa su ba, ta bi kuɗin da kallo, da tana da dama da iko da ta ƙona su ko ta yi sadaka dasu, dan bata buƙatar amfani da abin hannunsa, amma tana buƙatarsu dole zasu yi mata amfani. Riyal dubu sha bakwai ta irga, sune gabaɗaya  kuɗin har albashinta. Ta ɗauki waya ta yi converting kuɗin zuwa naira, ta ga kuɗin suna da yawa sosai, ya ishe ta ta biya su Mama ta koma gida da duk abinda zata yi. Ta sauke numfashi tana kallon kuɗin, a haka gasu ƴan kaɗan, amma a kuɗin nigeria kuɗi ne masu yawan gaske. _Ƙarfin kuɗin nan dai shine ya ba ki, a cikin sha bakwai shine ya ba ki sha huɗu. Kin ga kenan da kuɗinsa za ki kashe wutar gabanki. Kuɗin mara mutunci, wanda ya ce miki karuwa. Kawai ki watsar!._ Abinda zuciyarta take faɗa mata kenan, ta rutse ido tana ji kamar ta yi hauka saboda takaici da ɓacin rai, tabbas kuɗinsa ne, ba dan ta haɗu dashi ba da bata samu kuɗi masu yawan waɗannan ba. Daƙyar ta rarrashi zuciyarta bata watsar dasu ba, ta haɗe su ta ajjiye ta yi tagumi tana tuna Labiba ta zubar da ciki. Zuwa dare ya yi mata waya ya ce gashi ya zo, ta fita zuwa ƙofar gidan suka shigo compound ɗin tare. Ya kalle ta ya ce, "Ya dai?." Ta ssuke numfashi ta ce, "yanzu misali, in zan biya kuɗin da ku ka kashe ku ka kawo ni nan, nawa zan bayar?." Ya kalle ta ya ce, "a cure wai?." Ga ɗaga kai ya ce, "Miliyan uku ne da wani abun, a nan kuma zai kama riyal dubu takwas kenan." Ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "in na bayar shikenan na biya gabaɗaya?." Shi dai kallon ta yake yi ya ce, "eh." Ta gyaɗa kai ta ce, "ina zuwa" ta faɗa tana komawa ciki. Ba jimawa ta dawo ta bashi kuɗin, ya kalli kuɗin ya kalle ta ya ce, "Wai kin biya gabaɗaya kenan?." Ta ɗaga kai ta ce, "gasu ina ba ka." Ya miƙa hannu zai karɓa sai ta fasa bashi, ta ce, "shaida nake so ka bani, wacce in na bayar kowa zai san na biya ka, bazan ba da kuɗin nan ba tare da shaida ba." Ya murmusa ya ce, "buɗe idon ki da kyau yarinya, na fi ƙarfin na cuce ki, na wuce na damfare ki na karɓi wannan kuɗin. In ki ka je makka ki sha shiga kasuwar mai zogale, ki ka ce Alhaji Musa ki ke nema, babu wanda bazai nuna miki ni ba. Nawa riyal dubu takwas take a wajena da har zan cuce ki?." "Nima ban ce zaka cuce ni ba, abu ne na shaida, ka saka hannu nima na saka hannu. Ina zuwa" ta faɗa tana sake komawa shi dai ya bita da kallo. A bayyane ya ce, "da wannan yarinyar zata zauna zuwa wani lokaci da ba ƙaramin kuɗi zata haɗa ba, kalli yadda take ba da riyal dubu takwas ba tare da ta ji komai ba. Lallai an jiƙata, ta zama shalelen mutanen jeedah. Ko wata uku basu cika ba ace har ta samu waɗanann uban kuɗin?." A lokacin ya hango ta tana tahowa, ta ƙaraso da takarda ta bashi ya saka hannu ta saka hannu, sannan ta yiwa takardar hoto sannan ta bashi kuɗin. Ya lissafa ya ga sun cika cif, ya bita da kallo ya ce, "na tambaye ki?." "Ina ji." "A ina ki ka samu waɗanan kuɗin? A kuɗin albashi dai bai kai ki tara wannan kuɗin ba, kuma ba ki yi kama da mai bin maza ba, amma waɗanann kuɗin da na gani a hannunki sun bani mamaki. Ba ku cika wata uku a ƙasar nan ba har yanzu, amma kin tara wannan kuɗin mai uban yawa." Ta ɗaure fuska ta ce, "tunda na biya ai shikenan. Mun rabu lafiya, ni zan koma nigeria a cikin kwanakin nan." Ya bita da kllo ya ce, "ke kuwa kina samun wannan kuɗin me za ki koma nigeria ki yi?." Bata ce komai ba, yana ta jinjina kuɗin sai ta kalle sa ta ce, "don Allah nawa zan samu ticket ɗin Abuja?." Ya kalle ta ya ce, "Zai kai riyal dubu ɗaya da wani abun, kin ga lokacin umrah ne yanzu, ana ta shigowa dole ticket ya yi tsada. Amma za ki samu, musamman in ki ka nemi jirgin saudia." Ta gyaɗa kai ta ce, "in zan siya a ina zan je na siya?." Alhaji Musa ya buɗe baki ya ce, "wai da gaske ki ke?." Ta sauke numfashi ta ce, "da gaske nake." Ya gyaɗa kai ya ce, "ni kuwa na ba ki shawara mana Islaha?.." Ta sake haɗe rai ta ce, "ina ji." "Me zai hana baza ki je umrah ba, tunda visa ki bata ƙare ba, kuma kina da kuɗi. Ki je ki yi umra sannan sai ki koma gida." Ta ɗan jim alamun tunani sannan ta ce, "ni dai ka amsa min kawai." "Kamfaninsu kawai za ki je, daga nan in ki ka tambaya za a kai ki." Bata jira mai zai ce ba ta ce, "na gode" ta faɗa tana juyawa ta koma ciki. Tun kafin ya fita ya kira Mama a waya, tana ɗauka ta ce, "Alhajin Allah, tunda na ga kiran ka na san ta samu." Ya gyaɗa kai ya ce, "ta samu kuwa. Wacce yarinya ki ka samu mai zafin hannu haka?." Mama ta ce, "kamar ya kenan?." "Cikin ƴan matan da aka kawo mana, wacece wannan mai sa'a haka?." Mama ta ti dariya ta ce, "ai ƴata ce ta cikina." Ya gyara tsayuwa ya ce, "ke ki ka haife ta?." "Eh mana." "Amma za ki bari ta yi mana asarar dukiya? Tana matsayin ƴarki za ki bari ta dawo gida duk da maƙudan kuɗin da take samu?." Mama da mamaki sosai  ta ce, "ta dawo gida kuma, Yaushe kenan?." "Ga shi ina faɗa miki, kin ganni a tsaye a gidan da take aiki, ta kira ni ta bani kuɗin da aka kashe wajan kawo ta. Kin gansu riyal dubu takwas, naira miliyan uku ta ɗauko ta bani. Yarinyar nan babu wani ɗar ta lissafa ta bani, kuma tana zancen zata siyi ticket ta dawo gida, in ki ka bari hakan ya faru ba ki kyauta mana ba Zulai." Mama cikin firgici ta ce, "ban sani ba, kuma da muka yi waya ɗazu bata faɗa min ba." "To maza maza ki kira ta, ta canja sahwarar dawowa gidan nan. A cikin wata biyu da kwanaki ta haɗa waɗannan kuɗin, ina ga an sake kwana biyu?." "Yanzun nan ma kuwa alhajin Allah, yanzu zan kira ta." "Ki yi maza ki kira ta" yana faɗa ya yanke wayar. Islaha kuwa da ta shiga sai ta fara tunani, sai take ji ko dai ta shiga makka ta yi umran ne kamar yadda ya faɗa mata? Tunda gashi tana ƙasar kuma ba wani kuɗi zata kashe ba, an ce babu nisa daga Jeedah zuwa Makka. Ta sauke numfashi a bayyne ta ce, "To amma hotel fa? Zan je na dinga zama a masallaci ne?." _Kuma in ki ka je da kuɗin Rehaan ki ka je, gwara ki bari Allah ya kawo ki daga baya._ Ta runtse ido jin shawarar zuciyarta, ta dafe kai dan Allah ya sani Alhaji Musa ya saka mata kwaɗayin hakan, amma kuma zuciyarta gaskiya take faɗa mata, da kuɗin Rehaan zata je Umra, ita kuma bata so. Ta zauna tana sauke numfashi, ta dafe kai cikin rashin mafita. Gashi bata so a san zata dawo balle ta kira Safeera ta yi shawara ta je umrar ko kar ta je, bata so kowa ya san da zuwanta sai dai kawai su ganta. Cikin tunani ta kwanta, tana tunanin zuwa umrah da kuɗin Rehaan. Sai tunanin zagin da ya yi mata, da cikin Labiba da kuma Zainab. A haka ta kwanta ba dan tana jin baccin ba.     Mama kuwa tana kashe wayar ta kira Labiba, Labiba tana zaune ita da Aysha, ta ga kiran Mama. Ta ɗan lumshe ido ta ce, "Mama ce." Aysha ta ce, "Allah ya sa ba yarinyar nan ce ta faɗawa Mama abinda ya faru ba." Labiba ta girgiza kai ta ce, "Islaha baza ta faɗa mata ba, sai dai in wani abun ne." Ta ɗauki wayar ta saka a kunne ta ce, "Mama ina yini." Mama ta ce, "lafiya. Ya na ji maganar ki kamar mara lafiya?." Labiba ta ce, "mura nake fama da ita." Mama ta ce, "Na ji maganar wai za ki dawo gida, akan me?." Labiba da mamaki ta ce, "zan dawo gida kuma? In ji wa?." Mama ta ce, "ban gane in ji wa ba, ba yanzu Ale Musa ya bar wajan ki ba?." Labiba ta ce, "ni bai zo inda nake ba, rabon da na gan sa tun ranar ya zo ya karɓi kuɗin nan." Mama ta ce, "Yanzu muka gama waya dashi fa, ya ce min har riyar dubu takwas ki ka bashi, wai kin gama biyan kamfani kuɗin da suka kashe miki." Labiba ta ce, "Kuma ni ya ce miki?." "to wacece ƴata in ba ke ba?." "Ki ka sani ko Islaha yake nufi?." Mama ta yi ɗif tunawa da hakan da Islaha, dan ko kaɗan bata yi tunanin ta ba. Labiba ta ce, "Itace ma, ko tantama bana yi Islaha ce." Mama ta ce, "Islaha! A ina zata samu kuɗi kamar wannan? Ko kin haɗa ta da mai gidan naki ne?." "aa Mama, ni bai sake yi min maganar ta ba ma, dan a cikin kwanakin nan ma baya nan ya yi tafiya, bai jimawa da dawowa ba." Mama ta ce, "taɓɗijam! A ina yarinyar nan ta samu kuɗi irin wanann? Kin ji yadda yake faɗa min kuɗin da ta samu?." Labiba ta ce, "Mama in ta so babu abinda bazata samu a nan ba. Nima dan kina yi min addu'a, da yanzu na fi haka." "Lallai yarinyar nan tantiriya ce, ki ce yawon ta zubar ɗinta kawai take yi." Labiba bata ce komai ba, Mama ta ce, "Na yi mamaki wallahi." Labiba ta ce, "Mama kaina ciwo yake, sai anjima" ta faɗa tana kashe wayar. Nana Haleema. [7/20, 10:26 AM] KRBBK: RDB2P68 Nana Haleema. Bayan Labiba ta kashe wayar Aysha ta kalli Labiba ta ce, "Lafiya dai?." Labiba ta ce, "yarinyar nan da muka haɗu ranar nan, wacce ta raka ni asibiti. Wai itace zata koma nigeria, har ta gama biyan kuɗin da aka kawo ta." Aysha ta buɗe ido ta ce, "a cikin wata biyu har ta biya kuɗin shekara guda?." Ta ɗaga kai Aysha ta ce, "lallai yarinyar tantiriya ce, ki ce har ta fi mu iya harka." Labiba ta ce, "ni ba wannan ba. Aysha tsoro nake ji, kar na sake yin ciki." Aysha ta ce, "me zai kai ki sake yin ciki kuma? Wancan ɗin ma kuskure aka samu, amma yanzu ai na san baza ki sake bari ki yi ciki ba." Labiba ta ce, "ta ya kenan? Mutumin nan ba ya barina na huta, ni wallahi gabaɗaya na fara gajiya." Aysha ta ce, "kin gaji da kuɗin?." Ta ɗago ido ta kalle ta ta ce, "Ba haka bane, kawai ban ji daɗi da na yi ciki ya zube ba." "Au so ki ka yi ki haife sa?." "A'a." "To ai murna za ki yi da ya fita da kansa, ba ke ki ka zubar dashi ba ai." Labiba ta yi shiru bata ce komai ba. Aysha ta ce, "kin ga." Ta faɗa tana nuna mata wasu pills a hannunta. Labiba ta kalle ta ta ce, "na meye?." "Hana ɗaukar ciki, babu ruwan ki da fargabar za ki sake yin ciki nan gaba." Labiba ta zubawa maganin ido sannan ta ce, "ni bazan sha magani ba." Aysha ta ce, "meyasa baza ki sha ba? Kina so ki dinga ɗaukar ciki ne?." "Bana so, amma bazan iya shan maganin tsarin iyali ba. Kar na lalata mahaifata tun ban yi aure ba." Sai ta bawa Aysha dariya, ta yi dariya son ranta sannan ta ajjiye mata maganin ta ce, "yadda ki ka gani, gashi nan in kin ga za ki sha daidai ne, in baza ki sha ba ma duk ɗaya." Ta miƙe ta fita daga ɗakin ta bar Labiba cikin tunani.      Washe gari Maleek da matarsa suka dawo, bayan sun huta suna zaune, su Islaha gama gabatar musu da abinci. Bayan sun kammala Islaha ta zauna ta ce, "ina da maganar da zan yi." Maleek ya ce, "ina jin ki." Ta sauke numfashi ta ce, "ina so zan bar aikin nan, zan koma nigeria." Maryam ta ce, "Meyasa za ki koma?." Islaha ta ce, "ina da wani abu da zan je na yi a can, zamana a nan ya ƙare." Maleek ya ce, "Kin tabbatar babu abinda aka yi miki?." Ta ɗaga kai alamun eh. Maleek ya ce, "yaushe za ki tafi?." "Cikin satin nan." Ya ɗaga kai ya ce, "shikenan, in za ki tafi ki faɗa min zan nemar miki ticket." Ta yi murmushi tare da godiya ta tashi ta koma ɗaki. Duk sai ta ke jin babu daɗi a ranta, amma komawar gidan ya fi mata alkhairi akan zaman. Da yamma ta je Mall ta ɗan yiwa mutane masu mahimmaci a gare ta tsaraba madaidaiciya ba mai yawa ba, tana ta shirin tafiya gida a hankali har lokacin babu wanda ta faɗawa. Bayan ta dawo tana shirya kayan Mama ta kira ta, ta ɗauka kafin ta yi magana Mama ta ce, "har kin samu dama da saken da za ki biya kuɗi gabaɗaya baki faɗa min ba ko?." Islaha maimakon ta bata amsa sai ta ce, "Ina yini Mama?." "ai da ban yini ba da ba ki ji mi ba. Waye ya ce ki ce za ki dawo gida ba tare da na sani ba?." "Mama na gama abinda ya kawo ni, dawowa gidan...." "Me ki ka gama da ya kai ki? Me ki ka gama da ya kai ki ƙasar?. Yawon watsewar ki ka gama?." "Mama ni bana yawon watsewa, waɗanda suke yi dai suna yi, amma ni babu." "Kan uba! Ni ki ke faɗawa wannan maganar?." Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, dan ranta a ɓace yake sosai. Mama ta ce, "in ba wayon banzan ba a ki ka samu waɗannan kuɗaɗen masu yawa? Ale Musa ya faɗa min duk abinda yake faruwa, ya faɗa min duk abinda ki ka bashi da abinda ki ka ce masa." "Ni gida zan dawo." "to ki nemi wani gidan, gidana ba gidan ubanki bane balle ki ce za ki dawo ki zauna. Ki san inda za li samu ki zauna, amma ba dai zama a gidana ba wallahi." Islaha tana sane ta kashe wayar, dan in ta cigaba da jin maganar Mama zata iya zaginta bata san ta yi ba. Rehaan yana zaune hankalinsa gabaɗaya yana kan aiki, ya yi busy sosai, yana ta aiki ko motsin kirki ba ya yi. Gabaɗaya abin ya yi masa yawa, ya samu saƙo daga kamfaninsa na Englaand, ya samu saƙo daga asibiti, ya samu daga mall da sauran kasuwancinsa. Ya cillar da wayar jin kansa ya ɗau chaji, ya hargitsa gashin kansa yana ji kiran waya yana shigowa amma bai iya ɗauka ba, dan bai san me zai ce ba. Dan lokacin rufe ko ina ya kusa, dan ayi lissafi a fitar da zakka. "Ya dai Mr Busy" Jafar ya faɗa yana zama a kusa dashi. Ray ya ɗago ya kalle sa yana lumshe ido, sai kuma ya ce, "Uk, yaushe zaka koma?." Jazy ya taɓe baki kaɗan ya ce, "Sai bayan aurena, na gama tattara komai nawa na can yana gida, ni da sake zuwa wata ƙasar sai na je honeymoon." Ray ya ce, "ka taimaka ka je don Allah, abubuwa sun yi yawa a can." Ya girgiza kai ya ce, "meye amfanin Alex? Na ga shine yake riƙe da komai a can ko?." "amma ba kamar kana can ba, ban san me zan ce ba." Jazy ya ce, "Daga nan ka wuce can, dan ni dai bazan shiga ba gaskiya, ni da Uk sai zamu tafi da Riyya." Ray ya sauke numfaahi mai tsaho bai ce komai ba. Jazy ya ce, "lokacin lissafin ka ya yi." A fisace ya ce, "ba shiyasa na ce ka je ba, dame zan ji? Da waɗanda suke Yola, ko dana Uk?." "Ka tuna da partnership ɗin kamfanin nan na France, shima zai shiga lissafi." Ray ya ji kamar ya shaƙo wayan Jazy ya matse sai ya daina numfashi, amma sai ya daure ya shafa kansa yana girgiza kai cikin takaici. Ya san yana cikin yanayi na cakuɗewar tunani, amma ya dinga tuna masa da abinda ya manta dashi, yana sane yake tsokanarsa, dan kawai ya fusata shi. Jazy ya murmusa ya ce, "My billionaire, yanzu dai ka zama mai saurin fusata, da ba haka ka ke ba wallahi. Yanzu da an yi magana sai faɗa, ka dinga sassautawa kan ka." Ya sake yin dariya sannan ya ce, "Haka za ka yi haƙuri, ai daman masu kuɗi irin ka kullum a haka suke, ba sa samun lokacin kansu yadda ya kamata. Kullum sune tunani, lissafi da chajawar kai. Kai ka gode Allah, abubuwa suna zuwar maka da sauƙi, baka cika rasa lokacin kan ka ba." Ray ya yi masa banza, yana ji ana yi masa waya bai amsa ba. Jaxy ya ce, "ni na san wannan shekarar ma sai dai ka kimanta kawai ka fitar. Ribar da ta shigo kamfaninka wannan shekarar ta fi ta last year...." "Hmm dole ƴan uwanka su dinga cewa ka yi ƙanƙanta da samun irin wannan kuɗin, gabaɗayanka nawa ka ke? Amma kana da abinda ko Abba sai dai ya kalle ka. Yana da kyau ace ka yi aure, ka fasai ka ɗora matarka akan wani abun daban, yadda za ka dinga samun sauƙin wasu abubuwan." Ray jin Jazy ya koma maganar hankali sai sauke numfashi ya ce, "Alhamdu lillah!. Amma fa is not easy, kwana biyu gabaɗaya kaina a rufe yake. Na shiga Dubai, daga na shiga Madina na dawo nan. Ni shiyasa nake sso ka yi auren ka tafi da Riyya can, sai ta taimaka min da wani abun." Jazy ya kalle shi yana harararsa ya ce, "baza ka wahalar min da mata ba." Ya harare sa sai kuma ya ja tsaki ya ce, "dole ta yi, min, bazai yu kai ba ka yi min ba, ita ka ce baza ta yi ba." Ya yi dariya ya ce, "ina da abin yi ai, ba a ƙasan ka nake ba." "Na fitar da kuɗi ina so na bawa mutanen gidan mu, amma bana son ƙaramar magana." Jazy ya yi dariya ya ce, "ka san sai sun yi kuwa, ƴan gidan nan naku ko ruwa za ka faɗa sai sun ce ka zuba musu ƙasa. Amma kar ka fasa, ka yi ɗin kaine a gaba gaba dasu." Ya girgiza kai bai ce komai ba. Jazy ya ce, "Bilal ya ce min ana ta sadaka da abinci. Na ce daɗina sa Rehaan Mamy akwai hankali kaɗan." Ya ɗan yi murmushi kawai bai ce komai ba. Jafar ya ce, "Yauwa, ina housemaid ɗin nan ta ka? Tana zuwa kuwa?." Nan da nan annurin fuskar Rehaan ya gushe, ya ɗauere fuska bai ce komai ba. Jafar ya ce, "ina so na ganta ne." Ya ɗago suka haɗa ido, Jazy ya ce, "Ya na ga ka ɓata rai, dan na ce ina so na ganta shine na haɗe rai haka?." Ya sake tamke fuska ya ce, "ban taɓa jin tsanar ko wacce halitta kamar yadda nake jin tsanarta ba. Ko kaɗan bana so na tuna na taɓa ganinta." Jazy ya zaro ido cike da mamaki, dan tunda yake da Rehaan bai taɓa ji ya ce masa ga wani ko wata da ya tsana ba, ko a film in suna kallo ba ya cewa ya tsani wani actor ko actress balle kuma a zahiri. Jafar da ya cika da mamaki ya ce, "Meyasa? Me ta yi maka haka da ka tsane ta?." Ya yi tsaki bai ce komai ba, yana jin tsanarta tana sake shiga jikinsa. Jazy ya ce, "kuma wallahi tana da kirki sosai, na yi binckena kanta. Ni da na ji a gidan marayu ta girma sai na ji ta bani tausayi, shiyasa ka ga na sake da ita har muna hira haka, dan rashin iyaye babu daɗi." "Oh, na ɗauka ka shiga jerin mazan da suke tare da ita, kamar Ubaid." Jazy ya yi tsaki yana binsa da kallon mamaki ya ce, "ko da na shiga cikinsu ɗin bana tunanin ranka zai ɓaci kamar haka, ko da ni da ita za ka gani a ɗaki ɗaya bana tunanin ranka bazai ɓaci har haka ba Rehaan. Ni na rasa me ta yi maka da ke ke ɓata rai saboda ita, kai ta faɗa kamar wata mata mahimmaci a gare ka. Kuma ta faɗa min ta zo ƙasar nan saboda kai, lokacin da ka sace ta akwai kuɗin ka da ta ɗauka, ta ce ka duba cctv zaka gani. Wannan kuɗin shine ya kawo ta nan dan ta biya ka. Ni kuma nace maya ta koma gida, zan biya ka kuɗin ka, kuma already na tura Bilal kuɗin." Rehaan ya ɗago ya kalle shi, sai kuma ya ja tsaki ya ce, "wani lokacin wannan ɗabi'ar ta ka ta saurin sakewa da kowa haushi yake bani, a haka kamar namiji amma banza ne kai." Kafin ya yi magana ya ce, "Kawai saboda ba ka san zafin nema bane, shiyasa ka ke abinda ka ke so da kuɗin Daddy, shiyasa fitar da kuɗi ba ya yi maka wahala. Ni da na san zafinsu ai bazan yi ba." "Dallah can, har ka faɗawa wani kashe kuɗi?. Naira miliyan sha bakwai ne fa ba wani abu ba." "Oh! seventeen millions ka ke cewa ba wani abu ba? Baka zafin nema ba Jazy." Ya yi dariya ya ce, "dan kana keeping malice da ita ns ya saka ka ce cewa haka, amma ban kama ƙafarka a kashe kuɗi ba. Kuma na biya bashin da ya saka ta baro gida dominsa." Ray ya ce, "ƙarya take yi fa, ta saka ka yi asarar kuɗin ka, dan na rantse da Allah baza a dawo maka dasu ba." Jazy ya ce, "ka ji na ce a dawo dasu ne? Ni dai na biya mata na sauke mata nauyin da take ganin ta ɗorawa kanta." Ray ya taɓe baki ya ce, "Lokacin da na ganta a diamond hotel, ina ranar da aka ce anyi sata an gudu, har ka ke bani labari?." Jazy ya ce, "wani ɗan siyasa ko?." "To itace ta yi, a kan idona ta fito daga ɗakin, shima ya fito yana cewa ta manta face mask ɗinta." Jazy ya zuba masa ido yana kallonsa kafin ya ce, "da gaske ka ke?." "Ita ɗin banza na yi mata ƙarya? Tun daga nan na santa, nima kuma gashi ta faɗa maka ta yi min sata. Na haɗu da ita a train da zan dawo daga Madina, har na taimaka mata ganin bata da lafiya, ashe miscarrige ta yi." Jazy ya zaro ido ya ce, "miscarrige?." "Na ga record ɗin ta a asibiti da komai, ta sha wrong medicine ne ya saka cikin ya zube. A ina ta samu ciki? Ko shima ni ne silar da ya saka ta yi?." Jikin Jafar sai ya yi sanyi dan ya san bazai taɓa yi masa ƙarya akan Islaha ba. Jazy sai ya ji bai ji daɗin maganar ba, da gaske shi tausayi ta bashi shiyasa ya taimake, ta ashe ƙarya ta yi masa. Ray ya ja tsaki ya ce, "ka daina yi min magana a kan wacce bata cikin rayuwata, a bar maganar don Allah, ka daina ɓata min rai." Jazy ya ce, "na yi mamaki ne sosai, ban yi tunanin tana da ɓoyayyen hali ba, dan ni da zuciya ɗaya na taimaka mata." Ray ya miƙe ya bar masa wajan, dan shi ko tuna ta ma ba ya son yi ko kaɗan. Nana Haleema. [7/20, 10:27 AM] KRBBK: RDB2P69 Nana Haleema. Islaha a hankali take tafiya da daddare akan titi, titin yana burge ta yadda komai yake cikin tsari, duk da akwai nisa da mall ɗin amma haka ta ke son zuwa a ƙafa saboda kawai titin yana burge ta. Daidai wani shawarma and home of ta ga Jafar a tsaye, ta ɗan yi jimm tana kallonsa dan bata so su haɗu, ba dan ya yi mata laifi ba sai dan ɗan uwansa da take jin haushi. Ganin bai ganta ba sai ta ɗauke kai tana fatan Allah ya sa kar ya ganta, dan bata san me zata ce ba. A hankali ta ji an ce, "Miss Islaha." Ta ɗan runtse ido kafin ta juyo a hankali, ta kalle sa da murmushi ta ce, "Mr Jafar." Ya yi murmushi yana kallon ta, ta ɗan ƙarasa kusa dashi ta ce, "ina yini." Ya ce, "lafiya lau. Ina zuwa ke kaɗai?." Islsha ts ce, "zan je mall ne." "Mall ɗin za ki je da ƙafa?." "Uhum, ina son ganin gari ne kawai." Ya ɗan girgiza kai ya ce, "i through kina Nigeria." Ta girgiza kai ta ce, "Jibi zan koma in sha Allah." "Allah ya kaimu. Na tsayar dake, sai kin dawo, a yi min tsaraba." Ta ɗan yi murmushi ta juya ta cigaba da tafiya ta a hankali. Jafar ya tsaya yana tunanin abinda Rehaan ya faɗa masa, ya san Rehaan bazai yi masa ƙarya ba, dan shi damuwar wani ba damunsa ta yi ba, ba ya shiga lamarin da bai shafe sa ba, tunda har ya faɗa ɗin ya san ta faru. Amma Islaha bata yi kama da irin matan da yake kwantanta dasu ba, she looks very decent and neat, bata yi kama da abinda yake yawan faɗa a kanta. Abinda ya yarda dashi akan Islaha kawai bata da kunya, kuma tana da tsiwa, shima ba ko yaushe ba. Lokaci na farko da ya ji bai yarda da maganar Rehaan ba, duk da ya san abinda ya faɗa masa ya faru, dan bazai yi ƙarya akan Islaha ba, amma ba a kan Islaha ba, sai dai in kuskure ko akasi aka samu a kan hakan. In itace wacce yake cewa ta yi sata a hotel da yanzu an kamata, tunda ba ɓoyayyiyar fuska ce da ita ba, tana da ɗaukakar da baza ta yiwa ɗan siyasa sata ya ƙyale ta. Kuma shi ba daga gidan Ubaid yake ganin ta ba, a gidan Maleek yake ganinta, hakan sai ya tabbatar masa da kuskure Rehaan ya yi. Ya kawar da tunanin daga ransa, amma yana ji a ransa sai ya yanke ta a idanun Rehaan, ba dan wani abu ba, sai dan baka dan me gobe zata haifar ba. Ice cream da shawarma ya siya ya koma gida ya tarar da Rehaan yana shirin tafiya aiki, yana tsaye a gaban consool ɗin falon yana gyara zaman necktie ɗin wuyansa. Ya yi kyau cikin black ɗin suit, ya haɗe gashinsa a tsakiya, ga wani luxury watch da ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa. Jafar ya kalle sa ya ɗauke kai, ya zauna a kan kujera yana waya da inda ya ba da order kayan da zai saka. Sai da ya gama wayar Rehaan ya kalle sa ya ce, "kai kaɗai ka ke siyayyar ka, ba ka faɗa min." Jazy ya ce, "sau nawa ina faɗa maka kana avoiding ɗina? Shiyasa na ƙyale ka, bikina ne ba naka ba, ni ya kamata na yi duk abinda zan yi." Ya gyaɗa kai ya ce, "bikin ka ne kam" ya faɗa yana ɗaukar wayarsa. Jay ya ce, "Kaima harda kai, tunda tare za a haɗa mu." Hararar sa ya yi, hakan ya saka ya ɗan yi murmushi bai ce komai ya fara cin shawarmarsa hankali kwance. Rehaan yana sauka Mamy ta kira wayar Jafar, ganin video call ne sai ya gyara zama sosai kafin ya ɗauka. Fukar Mamy ta bayyana kan screen, ganinsa da ice cream da shawarma sai ta ce, "shan zaƙi, sanyi, ciye ciye duk ka iya Jafar." Ya ɗan yi dariya ta ce, "Ina yini Mamy." Ta ce, "Lafiya lau Jazy, nima yau na zama Rehaan, na ce Jazy." Ya yi murmushi Mamy ta ce, "Tunda mu ka yi magana da kai baka ce min komai ba, ya amince da zancen Ikram kuwa?." Jazy ya ce, "Wallahi Mamy na yi masa, amma ina farawa ya ce shi baya so, Ikram ƙanwarsa ce ba zai iya auren ta ba." Mamy da damuwa ta ce, "Jafar Rehaan ya girma fa, ga arzuƙin da Allah ya yi masa, aure ne kaɗai ya rage masa. Meyasa bazai amince ya auri Ikram ba? Duk wacce zata aure shi a yanzu dan kuɗi zata aure shi, amma ikram mun santa, mun san wacece ita." "Mamy ko ni na faɗa masa, da yana zancen zai yi lissafi za a fitar da zakka nake faɗa masa ya kamata zuwa yanzu ya yi aure." Mamy ta ɗan yi jim kafin ta ce, "Ni na fara wani tunani Jazy." Jafar ya ce, "na me kenan Mamy?." "Anya yana da lafiya?." Maimakon Mamy ta ji kunyar tambayar shine ya ji kunya, amma ganin ita ko a jikinta sai ya basar yana ɗan murmushi ya ce, "waye ya sanar masa Mamy? Amma na tabbata lafiya lau yake, yana da ilimin da in bashi da lafiya zai nemi magani bazai zauna ba." "Haka ne kam Jafar. Daman ni ya bawa damar zaɓa masa mata, kawai zan zaɓa nasa ita, koda zai zo ya ce baya so na san daga baya zai amimce. Zan yi magana da Ikram, in ta shirya aurensa za a yi bayan auren ku." Jafar ya ce, "Mamy amma da kar a yi gaggawa,  ki bari ya amince ɗin. Kin san hali, ɗan rigima ne." Mamy ta ce, "ƙyale ni dashi, bazan zuba masa ido haka ba. Ita wacce Daada zata aura masa bamu san wacece ba, wataƙila tana daga cikin waɗanda zasu so su ga bayansa saboda kuɗi. Ina so ya samu wacce zai samu peace of mind." Jafar ya ce, "Shikenan Mamy, Allah ya zaɓa mana abinda ya fi alkhairi." Ta amsa da amin ta kashe wayar. Jafar ya sauke numfashi ya ce, "za a sha rikici dashi kam, kafin ya karɓi auren nan za a jima sosai." Ya faɗa yana kiran Juwariyya, dan tunda Rehaan ya fita bashi da abokin hira, gwara ya kira ta su sha soyayya.        •••••• Daada tana zaune ita kaɗai a falon ta, Abba ya shiga da sallama ya zauna a kan carpwt ya ce, "lokacin da ki ka aika in zo na shiga wanka, yanzu na fito." Daada ta kalle sa ta ce, "akan maganar yarinyar nan da Muhammad zai aura, an sake komawa kuwa? Tunda ka ce min babanta yana asibiti baka sake cemin komai ba. Ka san da bikin Zuwairiyya nake so a haɗa, gabaɗaya biki yanzu bai wuce sati huɗu ba." Abba ya ce, "Daada wanda take hannunsa ba mahaifinta bane." Daada da mamaki ta ce, "waye ɗin ta?." Abba ya ce, "Yarinyar a gidan marayu ta tashi, bata san kowa nata ba, tana gidan ne a matsayin ƴar riƙo ba ƴar gida ba." Abba sai ya ji shiru Daada bata ce komai ba, jin shirun ya yi yawa ya ɗago ya ga Daada tana hawaye. Hankalin Abba ya tashi ya ce, "Daada lafiya, Me ya faru haka? Na faɗi wani abun da ya saka ki kuka ne?." Daada ta dakatar dashi da hannunta ta ce, "ashe shiyasa ta shiga cikin raina, shiyasa nake jin sonta har cikin jinina, ashe marainiya ce. Allah sarki, maraya bawan Allah, Allah sarki Ishlaya, sai na sake jin sonta, sai na sake ji dole ma Muhammadu ya aure ta." Abba ya ɗan girgiza kai jin kukan ba wani mai babban dalili bane ya ce, "Zan saka a sake bincikawa in Allah ya yarda. Tunda kina so za a yi in Allah ya yarda, in mahaifin nata ya dawo daga asibitin za a je a same shi in Allah ya yarda." Ta goge idonta ta ce, "haka nake so na ji, Allah ya nuna mana lokacin." Abba ya amsa ya tashi ya fita. Abba yana fita ya shiga apartment ɗinsa, a zaune ya tarar da Mama tana jiransa, ya ƙarasa ya zauna ta ce, "ka dawo." Ya ɗaga kai ya ce, "Na dawo. Daada da rigima, wai batun auren Rehaan take yi da yarinyar nan. Ni da yake ban mayar da hamkali ba, tunda na saka a ka bincila sau ɗaya ban sake bincikawa ba." Mama ta ce, "Tunda ka ga ta dage akwai alkhairi a ciki, gwara ka saka albarka Allah ya sanya alkhairi." "Maganar auren take yi a na nan da sati uku fa, Kawai sai na je na ce musu nan da sati uku zuwa huɗu ɗana zai auri ƴar ku?." "Ai ba wani abun damuwa bane, akwai abinda za a dawata su dashi har a yi auren a wannan lokacin." "Ba a yi binciken kirki a kanta ba, bazai yu ace daga nemo yarinya a yi aure babu bincike mai ƙarfi ba." Mama ta ɗan ɓata fuska ta ce, "haka ne kuma" ta faɗa dan kar ta musa ya yi saurin gano ta Abba bai ce komai ba ya miƙe ya shiga ɗaki, ta bi sa da kallo ta ce, "Wallahi sai auren nan ya yu, sai na tabbatar da auren nan ya tabbata ko da zan rasa wani abu nawa. Bazan bari a yi binciken ba, ni na san abinda zan yi" ta faɗa tana tashi ta fita cike da mugunta a ranta. Nana Haleema. [7/20, 10:27 AM] KRBBK: RDB2P70 Nana Haleema.     Riyya suna tare da Ikram da Janan, suan ta zaɓen fabrics na biki, ga kaya nan a gabansu a jibge kamar ba a so, ana ta haɗawa ƙawaye packs ɗinsu, dan bikin manya ne, bikin ƙanwar Rehaan Yola komai na package ɗin ƙawayen amarya kyauta za a bayar, babu batun siyan anko. Bayan kayan sakawa a pack ɗin, harda kuɗin ɗinki za a sakawa ko wacce a cikin pack ɗinta. Janan ta ce, "Ya batun musician ɗin ne? An gama komai?." Riyya ta ce, "an gama yin komai, babu abinda ba a yi booking ba. Indian night ma an gama yin komai, kuma ba ki siyi outfit ɗin ki ba." Ikram ta ce, "waye ya ganni a kayan india, ban taɓa sakawa ba fa." Riyya ta cee, "kuma dole ki saka. Kin ga nawa nan" ta faɗa tana buɗe musu wani milk kaya mai kyau. Janan ta ce, "Wow, amma ya yi kyau. Zai yi miki kyau sosai. Ina na Hamma Rehaan?." Janan tana faɗar hakan gaban Ikram ya faɗi, amma bata nuna ba ta ce, "zan so na gansa cikin kayan india, na tabbatar ba ƙaramin kyau zai yi ba." Janan ta ce, "ba ki taɓa gani ba? Ni na taɓa gani ya saka sau ɗaya, yana sakawa ya cire wai babu daɗi." Riyya ta yi dariya ta ce, "bara na kirasa yanzu, bai faɗa min gift ɗin da zai bani ba" ta faɗa tana ɗaukar waya ta kira sa ta saka a speaker. Yadda wayar take yin ringing da bugun zuciyar Ikram, ta ɗan yi shiru tana jira ya ɗauka amma sai ta katse bai ɗauka ba. Riyya ta ce, "Mr busy, Matarsa ta shiga uku, ko yaushe yana kan waya akan kasuwanci, in ba waya ba laptop, ki rasa inda zai kai kuɗi." Janan ta ce, "ya za a yi ya yiwa matarsa? Ai duk wannan abubuwan nasa sauke sa zai yi a sha love." Riyya ta yi dariya ta ce, "Kuma fa haka ne." Zata sake yin magana kiransa ya shigo wayar. Ta ɗauka ta saka a speaker ya ce, "Riyya." Ta ce, "Na kira ba ka ɗauka ba." "Ina ganin kiran, kawai dai na kira ki ne yanzu. Ya aka yi?." "Ba ka bani gift ba." "Wanne gift?." "For my wedding." Ya ɗan yi dariya ya ce, "oh amarya." Ta ɗan yi dariya kaɗan bata amsa ba, sai ya ce, "ni ban san me zan ba ki ba Riyya, amma ki tura min abinda ki ke so." Ta ce, "ka san me nake so?." Ya yi shiru bai amsa ba, Riyya ta san jiran ƙarshen maganar yake yi sai ta ce, "ni kawai ka zo bikin, shine kyautar da zaka yi min." "Riyya abun babu sauƙi, ina da aikin da zan yi, zuwana zai zama under probability." Cikin shgwaɓa ta ce, "Ni dai don Allah ka zo, bazan ji daɗin ace bikina baka nan ba." Ya ɗan sauke numfashi ya ce, "Okay. Ina Kiddo?." "Tana wajan Mamy." "ke kina ina?." "Ina tare da Ikram da Janan." Ya ɗan yi shiru kamar bazai yi magana ba sannan ya ce, "suna ji babu wanda zai yi min magana?." Janan ta ce, "ni fushi nake da kai, na kira ka har sau huɗu baka kira ni ba." "Sorry Jan, amma kin san bana so a tara min kira." "Zan kiyaye." "Good gal." Ikram ta ce, "Yaya Rehaan." A hankali ya ce, "Ikram." Ta ce, "Uhum, ya aiki?." "Alhamdu lillah, ki gashe da Mummy." Yana gama faɗar ya kashe wayar gabaɗaya. Janan ta ce, "wai kuwa yana da budurwa?.• Riyya ta ce, "bashi da kowa, Hamma Jazy ya faɗa min bashi da wata budurwa har yanzu. Sai dai wannan aure da Daada take so ta ƙaƙaba masa." Janan ta kalli Ikram da ta ƙi cewa komai, ta taɓa ta ta ce, "Sis kin yi shiru." Ikram ta ɗan yi murmushi ta ce, "Kawai ina tunanin wacce lucky gal ce zata ɗauki Ya Rehaan a matsayin miji." Riyya ta yi yar dariya ta ce, "gaskiya kam sai dai lucky ɗin. Amma kuma ga shi nan zai yi auren, duk da ba ya so amma dai matarsa ce." Janan ta kalli Ikram ta ce, "Iky ni wallahi na jima ina ji ina ma ya aure ki, tunda Hamma Jazy ya ɗauki Riyya, na san shima zai iya auren ki, nikam ina so ya aure ki sosai." Ikram ta ɗan yi murmushi ta ce, "rufa min asiri, ina ni ina shi?." Ta harare ta ta ce, "ka ji wata magana, Akwai aibu da kin aure sa ne?." Ta girgiza kai ta ce, "Babu, kawai na san ba abu ne da zai yu ba." Riyya ta ce, "zai iya yuwa mana, ki ka san me Allah ya rufe?. Mu zamu so ki aure sa ɗin, saboda kowa ya san wacece ke balle azo ana wata magana, ko bakya so?." Ta kalli Riyya ta ce, "Riyya kenan, Wacce mace ce zata ce bata son Hamma ne? Sai dai in ta san bazata samu ba." Janan ta ce, "ke kam za ki samu, daman na lura kamar you have stong feelling for him." Ikramta ɗan yi murmushi kawai bata ce komai ba, she wish abinda suka faɗa ya zama gaskiya, da sai ta yi azumi guda goma na godiya ga Allah.       ••••••••• Islaha tana ta shirye shiryen dawowa gida, har an siya mata ticket, har ticket ɗin jirgin da zata hau zuwa Adamawa ta siya. Ranar da zata bar ƙasar tun bayan sallar i'sha ta shirya, da taimakon Sunaira da Maleek ta yi komai yadda ya kamata. A lokacim ta fita zuwa wajan Labiba, dan ta ji ko akwai saƙon da zata kai wa Mama. Falon gidan babu kowa shiru, Islaha ta ɗan zauna tana jira ko za a fito amma ba a fito ba. A lokacin Aysha ta shigo falon ta ga Islaha a zaune, Islaha ta kalle ta ta ce, "Don Allah ina Labiba?." Aysha ta ce, "in ki ka shiga ciki, ɗaki na biyu" ta faɗa tana ɗaukar wayarta ta fita. Islaha ta miƙe ta shiga ciki kamar yadda ta ce mata. Islaha a hankali take takawa a nutse, gidan ya yi mata kyau sosai, tana ta mamakin su haka gidanjensu yake manya ga kyau. A hankali ta tuea ƙofar ta shiga da sallama tana kiran sunan Labiba. Gaban ta ya yanke ya faɗi, ta yi saurin ja baya, tana jin kamar wata ta ja tasaboda shock ɗin da ta ji ya ratsa ta, ta fara zare ido tana so ta tuna abinda ta gani, amma bata so ta gasgata abinda ta gani ba gaskiya ne, ta fi so ta bar shi a hasashe ko mafarki. Ta jima a haka cikin rashin nutsuwa, kafin ta firgita ta dawo hanlalin ta, ta kalli ɗakin sai kuma ta zabura ta bar wajan a guje cikin kuka. A wannan yanayi ta koma, ta faɗa kan gado tan kuka kamar ranta zai fita, ita kanta bata san kukan me take yi ba, kawai dai ta ji tana kuka ne wanda yake zuwa daga zuciyarta. Abinda ta gani bata taɓa gani ba ko a film balle a zahiri, mace da namiji a tare suna aikata wani abu mara kyau bata taɓa gani ba ko da wasa. Ganin da ta yi ya saka zuciyarta ta tsinke, jikinta yana rawa, zuciyarta tana rawa, cikin wani irin yanayi mara daɗi wanda bata taɓa jin kanta a ciki ba. Ita dai bata san adadin lokacin da ta ɗauka a wajan ba, sai ji ta yi an buɗe ƙofar an shigo. Tunda ta shigo ta zuba mata ido kawai tana kallon ta, ganin ta normal da ita kamar ba ita ta gani ita da namiji a ɗaki ba. Labiba ta dake ta ƙarasowa inda take ta ce, "Kin je nemana, lafiya?." Wani irin abu Islaha ta ji yana taso mata daga cikin kanta yana mamaye duk jikinta, ji take kamar ta tashi ta shaƙe Labiba har sai ta mutu. Labiba ta ce, "Sai wani kallona ki ke, meye baƙo a abinda ki ka gani ɗin? Kin saba yi fa, ina jin farar fatarsa ce ta ruɗa ki. Amma wannan a wajan ki ai....." Islaha bata san hannunta ya sauka a akan fuskar Labiba ba, sai ganin kanta ta yi a tsaye a kusa da ita tana nuna mata yatsa ta rasa abinda zata ce. "Kai! Ni ki ka mara?" Ta faɗa tana kai mata mari  amma Islaha ta riƙe hannun, ta sauke hannunta tana jin ƙyanƙyamin Labiba yana shiga zuciyarta. Kasa ce mata komai ta yi, kawai ta shiga bathroom tana jin fitar Labiba. Ruwa ta dinga zubawa kanta kamar itace ta aikata, haka ta jiƙe gashinta jagab, a sanyaye ta sake shirya ta fito falon tana zare idanunta. Sama sama suka yi sallama da mutanen gidan, duk ta karɓi lambobinsu dan zasu dinga gaisawa a whatsapp, aka kai ta har airpot. Ita dai a sanyaye take yin komai, Sunaira ce mai taimaka mata tana nuna mata abinda bata sani ba, a haka har ta gama komai ta yi boarding. Sai da ta shiga boarding room sannan ta samu ta sha tea, ta yi tagumi tana tuna abinda ta gani da abinda kunnenta ya ji mata. Gabaɗaya ta ruɗe ta fita daga hankalinta, ita dai ta san tana zaune kawai sai gani ta yi an fara shiga jirgi. Ta miƙe a sanyaye ta shiga itama ta zauna tana kallon window. Sai ta fara tunanin ko tana da rabon dawowa ƙasar ko babu Allah ne ya sani. Ga shi ta shigo ta fita bata je ta ga ka'aba ba, babban abinda yake yi mata daɗi ta shiga madina har ta kwana biyu. A haka jirgi ya ɗaga zuwa ƙasa nigeria.      A jirgi suka yi sallar asuba, ƙarfe tara na safe jirginsu ya dira a Abuja. Bayan ta gama komai ta ɗauki kayanta kuma ta zauna jiran jirgin da zai kai ta Adamawa state. Sai ƙarfe sha biyu sannan komai ya zama ready, mota ta ɗauke su zuwa inda stairs ɗin jirgin yake. Awan su uku a sama sannan suka sauka, tun a airport ta canja wasu kuɗin zuwa naira, ta yo drop ɗin taxi zuwa gida zuciyarta tana bugawa, dan bata san abinda zata tarar a wajan Mama ba, bata san yadda zasu kwashe da Hamma ba, wacce irin amsa zata bashi in ya tambaye ta? Ta bashi labarin Rehaan Yola ko kuma ta yi shiru?. Da wannan tunanin aka cigaba da tafiya, tana kallon Yola cikin yanayin kewa. Ya ku ke ganin Hamma zai karɓi maganar Rehaan? Mama zata bari ta zauna a gidan ta? Ana ta shirin auren Rehaan, ya abin zai kasance? Drama don start🔥❤️❤️ Nana Haleema✍🏻❤️ [7/21, 12:04 PM] KRBBK: RDB2P71 Nana Haleema. _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ Islaha a ƙofar gidansu Safeera aka sauke ta, daman ta yi canjin riyal zuwa naira tun a airport, ta biya kuɗin mota aka sauke mata kayanta aka shiga dasu gidan su Safeera. Da sallama Islaha ta shiga cikin gidan, Safeera da Kausar da Rukayya suna zauna a tsakar gidan suka ji sallama sai kuma ga kaya an shigo dasu. Safeera ta yi wani ihuu ta miƙe cikin gigicewa, a guje ta ƙarasa ta ƙanƙame Islaha tana ihun murna. Islaha tta ce, "Dallah za ki cillar dani" ta faɗa tana murmushi. Safeera ta riƙe hannun Islaha tana kallon ta cikin wani irin yanayin murna da ɗimaucewa ta ce, "Islaha ke ce?." Ta harare ta bata ce komai ba ganin Mama ta fito daga ɗaki. Islaha ta ƙarasa kusa da Mama ta ce, "Mama ina yini." Mama ta bita da murmushi ta ce, "Ai dole Safeera ta yi ihu, ina ciki na jiyo ihunta, ashe kece a tafe. Sannu da zuwa Islaha." Islaha ta murmusa ta ce, "yauwa Mama." Kausar ta ce, "Kin ga yadda ki ka yi kyau? Kin sake zama kalar madara." Ta yi dariya bata ce komai ba Rukayya ta ce, "Adda Islaha ina Umman mu? Tare ku ka dawo?." Islaha ya girgiza kai ta ce, "Ni kaɗai ce, Umma tana can, amma tana gaishe ku, akwai saƙo ta bani na kawo miki." Sai jikinsu ya yi sanyi ta ce, "ita meyasa bata dawo ba?." Islaha bata iya bata amsa ba, dan bata san me zata ce musu ba, gwara ta yi shiru ya fi zama alkhairi. Mama ta ce, "Ku bar ta ta huta, shiga ciki Islaha." Islaha ta shiga ɗakin Safeera, tana shiga ta cire mayafin kanta, ta cire ribbon ɗin kanta tana barbaza gashinta dan zafi take ji a cikin gashin. Safeera ta shigo mata da kayan da aka shigo dasu ta ce, "Kin dawo ƙasar mu mai zafi, gashi nan har kin fara cire ribbon." Islaha ta kalli Safeera ta ce, "bacci nake ji, taimaka min za ki yi da ruwan zafi na yi wanka na yi sallah na kwanta." Safeera cikin murnar ganinta ta ce, "An gama mutanen Jeddah." Babu jimawa ta kawo mata Islaha ta yi wanka haɗe da alwala. Tana fitowa Safeera ta shigo mata da abinci, Safeera ta bita da kallo tana zama kusa da ita ta ce, "ke kin ga yadda ki ke wani shining na kyau? Kin ga yadda skin ɗinki ta yi kyau?." Ta harare ta ta ce, "ki bar abincin nan Bestie, sai na tashi daga bacci." Safeera ta bita da kallo ta ce, "Wallahi na kasa gasgatawa ke ce ɗin, gani nake kamar mafarki nake yi." "Ki cigaba da mafarkin." Safeera ta yi dariya sosai ta ce, "kawai sai na gan ki, ba labarin za ki dawo." Islaha ta ce, "daman na ce babu wanda zan faɗawa sai na dawo, har Hamma ban faɗawa ba." Ta girgiza kai tana murmushi ta ce, "To ki sauri ki kwanta ki tashi, ki bani labari." Gabaɗaya zumuɗi ganin Islaha ya cika mata zuciya, ji take kamar kar ta bar ta ta yi bacci. Islaha ta yi dariya ta tayar da sallah, bayan ta idar da sallah kwanciya ta yi bacci ya ɗauke ta. Har aka yi magrib bacci take yi, sai bayan sallar i'sha ta tashi. Kai tsaye banɗaki ta shiga ta yi alwala ta fito ta yi sallah. Safeera ta shigo tana faɗin, "kin sha bacci, tun ɗazu nake shigowa sai in ga ba ki tashi ba." Islaha ta ce, "na gaji ne Safeera. Daga Jeddah na zo Abuja, ban wani huta sosai ba na taho Yola." "Na kawo miki abincin ko za ki fito falo?." Islaha ta ce, "kawo min nan. Baba ya dawo?." "eh ya dawo." "mu je na gaishe sa sai na dawo." Ta saka hijjab ya fito har ɗakin Baba. Baba yana ganin ta ya murmushi ya ce, "Islaha saukar yaushe?." Ta yi murmushi suka gaisa sannan ta ce, "saukar ɗazu Baba." "Sannu da zuwa." "Yauwa Baba. Ina yini?." "Lafiya lau Islaha, ya hanya?." "Alhamdu lillah." "Ma sha Allah.." Khadija autarsu Safeera ta ce, "Adda Islaha Umma bata dawo ba, yaushe zata dawo?." Islaha ta kalle ta ta ce, "ta kusa dawowa, ki kwantar da hankali ki." Sai kawai ta fara kuka ta ce, "ina so na ga Umma, ki kaini wajanta." Islaha ta riƙe hannunta ta ce, "kar ki kuka, ki bari in zan koma zan tafi dake wajanta, kina so?." Ta yi murmushi tana ɗaga kai, Islaha ta ce, "Yauwa, to daina kuka." Ta daina kuka Islaha tana murmushi ta koma ɗaki. Mama har ɗakin ta shiga ta kaiwa Islaha abinci sannan ta bar su ita da Safeera suna hira. Islaha bata ce komai ba ta buɗe abincin ta ga shinkafa da miyar kifi, ta yi ajiyar zuciya ta ce, "kai amma na ji daɗin abincin nan, saura shinkafa da wake da mai da yaji" ta faɗa tana ci a hankali har ta ci rabi. Safeerata kawo mata ruwa ta sha ta sauke numfashi alamun ta ƙoshi. Islaha ta ce, "Na ƙoshi wallahi, miyar nan ta yi daɗi sosai." Safeera ta ce, "sai na gan ki ƙwatsam, ni ki bani labarin ya aka yi ki ka dawo." Islaha ta kalle ta ta ce, "Kai bestie, kin cika gulma wallahi, lallai sai na ba ki labari? Ki jira na gama hutawa mana, ko gidansu Hamma ban shiga ba fa." Ta yi dariya ta ce, "Ai tunda na gan ki a nan na san ba ki shiga ba." "wallahi matsalar Mama ce bana so, shiyasa na zo nan na huta, in Baffa ya dawo sai mu gaisa, na fi jin daɗin gidan in Baffa yana nan." Safeera ta harare ta ta ce, "wai baza ki faɗa min ba, sai ja min aji ki ke yi." Islaha ta yi dariya ta ce, "zan faɗa miki, abin ne kamar tatsuniya wallahi, kar ki ce na raina miki hankali." Safeera ta ce, "Ke wallahi harshen ki ya fara komawa na larabawa, har wani la la ki cewa." Suka yi dariya gabaɗaya Islaha ta ce, "Wallahi ban san ya shiga bakina ba, kuma zama da Sunaira ne, amma dan ta Maleek larabci bazai zauna a bakina ba, saboda da turanci mu ke magana." "Ina jin ki, bani labari." "Kar na faɗa miki ki ce drama ce." "Kema in dramar ce ai kin sani." Islaha ta yi murmushi tana ɗaukar wayarta tana dubawa ganin chaji ya kusa ƙarewa. Ta kalli Safeera ta ce, "na gama abinda ya kai ni, shiyasa na dawo." Safeera da mamaki ta ce, "kin gama kamar ya kenan, Har kin samo kuɗin?." Ta ɗaga mata kai alamun eh, da mamaki Safeera take binta da kalko kafin ta ce, "ta ya kenan? Ko duk wata miliyan biyar ake ba ki, bai ci ki haɗa wannan kuɗin ba, dan ba ki yi wata uku ba har yanzu." Ta furzar da iska ta ce, "Ba na faɗa miki akwai gidan da nake shiga na yi aiki bayan wanda nake ciki ba?." Ta ɗaga kai alamun ta sani. Islaha ta ɗan yi shiru dan bata san ta ina zata fara ba, kar ta ga kamar ta raina mata hankali tana ɓoye mata wani abun. Safeera ta ce, "ina jin ki." Islaha ta ce, "A gidan da nake zuwa na samu kuɗin da na biya bashin, kuma na dawo gida." "ban gane ba, a gidan da ki ke zuwa ki ka samu wannan kuɗin?." "Ke ba wani kuɗin na kuma ɗaukowa ba, na ga kina yi min kallon tuhuma." "Ai dole na yi miki, abin da mamaki ai. A cikin wata biyu da ƴan kwanaki har kin haɗa miliyoyin kuɗi?." "Ke dallah, ko yankan kai nake yi ai bai ci na haɗa kuɗin nan ba. Biya min aka yi. "Waye ya biya miki? Wa ki ka sani a Jeddah da zai biya miki wannan kuɗin?." Islaha ta miƙe tsaye tana share zancen ta ce, "bar ni na fara buɗe kayan nan, na bar na ajjiyewa a nan, san bana so Mama ta saka ni a gaba da tambayoyin banza. Bani reza na farka silling ɗin nan." Ta faɗa tana zuwa wajan kayan da suke a ajjiye. Safeera ta bata reza ta farke kayan tana fitowa dasu daga ciki. Safeera cikin tuhuma ta ce, "kin share maganar da muke yi Islaha, kin saka min ayar tambaya akan ki." Ta kalli Safeera ta ce, "ban san ya za ki ɗauki maganar ba, bana so ki sake zargina, dan maganar bata yi kama da hankali ba, ina faɗa miki za ki ji kamar na raina miki hankali." "Shirun na ki ne zai saka na zarge ki, gwara ki faɗa min kin san ni mai fahimtar ki ce." Islaha ta dakata da fito da kayan ta ce, "gidan wanda nake shiga aikin, shine wanda ya sace ni ɗin nan, har na ɗauko masa kuɗinsa....." ta ɗan ja numfashi sannan ta ce, "Kuma a gidan na samu kuɗin da na biyasa har na dawo gida." Safeera ta yi shiru tana binta kallo, Islaha jin ta yi shiru sai ta ɗago ta kalle ta ta ce, "ba ƙarya nake yi miki ba Safeera, wallahi da gaske nake. Ashe likita ne, yana aiki a ƙasar, shine wanda mai gidan da nake yiwa aiki ya ce na je na dinga dafa masa tea. Kuma babban mai kuɗi ne ko a ƙasar nan, kuma babban ma'aikaci ne. Safeera wallahi ni ban ɗauka yana jin yaren mu, dan bai yi kama da ƴan ƙasar mu ba gabaɗaya." Safeera ta sauke numfashi ta ce, "Abin ne ya ɗaure min kai, maganar ta yi wani iri Islaha. Shi ya sace ki, ki ka ɗauki kuɗinsa, ki ka je Jeddah dan ki tara masa kuɗinsa ki biya sa, sannan kuma kin fara aiki a gidan sa, kuma kin samu kuɗin da ki ka biyasa a gidan sa. Ta ya hankali zai ɗauki wannan? Kar ki saka zuciyar mu ta yi zargin wannan plan ne, da sace ki da zuwan naki da komai da komai." Islaha ta ɗan rufe ido ta buɗe ta ce, "Safeera wallahi Allah da gaske nake miki, ni ban san shi bane, da farko in na shiga gidan bana ganinsa, sai ranar da nake fama da ciwon mara ne muka haɗu. Da ya nuna bai gane ni ba nima sai na numa ban gane sa ba, na cigaba da harkokina. Kuma in dai zan iya zuwa Jeddah, shima zai iya." "Na ji, za ki iya zuwa, shima haka. To ta ya ki ka samu kuɗin da ki ka biyansa a cikin gidan?." "Wai kin san waye shi kuwa?." Safeera ta ce, "Ta ya zan sani bayan ba ki faɗa min ba?." Islaha ta ce, "zan faɗa miki waye shi, amma bana so kowa ya sani don girman Allah." "Ina jin ki." Islaha ta yi ajiyar zuciya, ta ce, "wayar ki da data?." Ta ɗaga mata kai alamun eh, Islaha ta ɗauki wayar Safeera ta shiga google ta yi searching sannan ta ce, "karɓi ki duba." Safeera ta karɓa tana kallon screen ɗin, ta kalli Islaha ta ce, "Rehaan Yola nake gani." Islaha ta ɗan zuba mata ido dan bata san ta ya zata ɗauki wannan maganar ba, ko ita aka zaunar aka faɗawa wannan shirmen baza ta yarda ba, kai tsaye zata ƙaryata mutum sai dai su yi faɗa. Islaha ta ce, "Dashi na haɗu a diamond hotel a lokacin da muje can neman, ya zuba min tea a jikina na nuna masa kuskurensa. Da shi muka haɗu asibiti lokacin da ki ka same ni ina kuka har ya fasa min wayata....." ta ja numfashi tana kallon irin kallon da Safeera take yi mata sannan ta ce, "shine ya sace ni, kuma shine likitan da ya yiwa Baffa tiyata, kuɗinsa na ɗauka, kuma a gidansa nake shiga aiki!." "Mtsw!" Safeera ta ja tsaki bata ce komai ba, ko kallon Islaha bata kuma yi ba ta ɗauke kanta jin ta mayar da ita kamar wata yarinyar goye. _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ Nana Haleema. [7/21, 12:04 PM] KRBBK: RDB2P72 Nana Haleema. _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ Islaha ta yi murmushi tana kallon Safeera ta ce, "ba ki yarda ba ko?." Safeera ta kalle ta ta ce, "kema ba ki yi abinda zan yarda ɗin ba, in ba dan ke ce b da bazan tsaya na saurari wannan shirmen ba. Rehaan Yola fa ki ke magana, kina zancen dashi ki ka haɗu ki ka yi kaza kaza kamar wani ɗan gidansu Hamma. Rehaan ya wuce tunanin ki, a ina za ki gansa balle har wannan abubuwan su faru?. Kuma kina nufin duk yadda hotunansa suka baza duniya ba ki taɓa ganinsa ba? Ke ma'aikaciya ce, kuma ƴar social media, kina nufin ba ki san fuskar Rehaan ba?...." Ta ɗan girgiza kai alamun kin raina min wayo ta ce, "Haba Islaha, ki faɗi abinda hankali zai ɗauka, wannan hankali bazai ɗauka ba." Islaha ta yi ajiyar zuciya mai tsaho sannan ta koma koma tana cigaba da fito da kayanta sannan ta ce, "Ban yi tunanin in kowa bai amince dani ba kema za ki ƙi yarda dani, na ce miki wallahi amma ki kasa yarda." Safeera ta ce, "Abin ne bai yi making sense ba Islaha, ta ya zan yarda da abinda ki ka faɗa?. Rehaan Yola fa, kina magana akan wanda ganinsa ma wahala yake yi, kuma ke kina faɗa min wai shine ya sace ki. Don Allah ta ya zan yarda da wannan maganar ta ki?." Ta ɗago ta kalle ta ta ce, "Wallahi Allah da gaske nake miki, kin san ba ki isa na yi miki rantsuwa akan ƙarya ba, shima R Yolan bai isa na yi rantsuwa akan ƙarya saboda shi ba. Ban taɓa ganinsa ba, ko na taɓa ganin hotonsa ban tsaya na kalla yadda ya kamata balle har na haddace sa ba. Kin san Allah? Har na gama zama a hannunsa ban san waye ba, ban taɓa ji ya yi magana ba sai sau ɗaya, kuma ban ji wani ya kira sunansa ba. A Jeddah ma in ban da zuwa Jafar ban san waye ba, shine yake faɗa min da wanda nake tare. Ki yarda ko kar ki yarda bai dame ni ba, bazan zauna ina yi miki rantsuwa kina ƙaryata ni ba" ta faɗa tana fito da wata ledar alawa ta ajjiye. Safeera ta girgiza kai cikin al'ajabin wannan lamari ta ce, "Na yarda Islaha, kawai abin ne yazo wani iri shiyasa." Islaha ta yi mata banza ta cigaba da abinda ta ke yi. Sai daga baya ta ce, "ke kowa yana tambayata ya Umma amma kin kasa buɗe baki ki tambaya, na rasa a ina ki ka samo wannan baƙin halin. Kina ji har Maman su Kausar sai da ta tambaya, amma ke kin kasa cewa tana ina, bayan ita kullum cikin maganar ki take." Safeera ta murmusa ta ce, "na san tana cikin ƙoshin lafiya." "Ta ya ki ka sani? Waya ku ka yi da ita ta faɗa miki haka ko ganinta ki ka yi?. Ki daina irin wannan, uwa ce ita.." Safeera sai ta ji zuciyarta ta karye, dauriya kawai take yi, amma ita kaɗai ta san ya take jin kewar Umma. Ta ɗan yi murmushi ta ce, "Islaha kullum da tuanninta nake kwana nake tashi, kullum da kewarta da son ganinta muke kwana muke tashi. Ita fa ta haifemu, amma ta ajjiyemu, ta ajjiye aurenta ta tafi neman kuɗin da babu lallai ace ta same shi. Sai dai na nuna kamar ban damu ba saboda ƙannena, amma ni kaɗai na san yadda rashinta yake yi min illa. Duk yadda Mama zata kula damu ba kamar ita ba, kullum Khajida zaman jiran dawowarta take yi, kullum a zancenta take; so ki ke dinga nuna na damu su ma su shiga damuwa?." Islaha ta ɗan yi murmushi ta ce, "ke kenan, kin san ta ki mahaifiyar tana da rai, ni kuwa na ce me?." Safeera ta goge idonta bata ce komai ba. Islaha ta ce, "ko ba ki nuna kin damu ba, ki dinga magana da ita hakan zai saka ta ji daɗi." Safeera ta ce, "da ki ka je wajen ta ya ki ka same ta?." "Umma tana lafiya lau, bata san zan je ba, ta so ta bani saƙo mai yawa na kawo mu ku. Amma ga wannan ta ce na kawo miki." Safeera ta karɓi ledar alawa da yawa, gasu nan kala-kala masu kyau tun daga leda.. Islaha ta bata tsaraba ta ce, "Ga doguwar riga na siya miki." Safeera ta karɓa tana murmushi ta ce, "Na gode sosai, hajiya Islaha mai capacity. Amma ba ki gama bani labarin ba." Ta tattare kayan waje ɗaya ta ɗauki kayan gidan Mama sannan ta ce, "Ba yau ba. Zo ki raka ni gidan Mama, sauran kayan ki ajjiye min, duk wanda zan bawa zan karɓa." Safeera ta amsa, ta ɗauke kayan ta ajjiye a waje mai kyau, sannan ta saka hijjab suka fito zuwa gidan Mama. A falo suka samu Mama a zaune ita da Hanan suna cin abinci. Islaha suka shigo da sallama ita da Safeera, suka amsa suna kallon su. Hanan ta buɗe ido ta ce, "Islaha!." Islaha ta ɗan murmusa ta ce, "Na'am, Hanan." Islaha ta kalli Mama ta ce, "Mama ina yini." Mama ta sauke numfashi tana kallon ta ta ce, "da mu ka yi magana a waya mai na ce miki? Bana faɗa miki in kin dawo ki nemi wani gidan ba? Me ki ka zo yi min nan?." Islaha ta ɗan yi ajiyar zuciya bata ce komai ba, tana tunanin shekanan kuma, ta dawo za a ɗora daga inda aka tsaya. Mama ta ce, "kin je kin gama yawon ki, za ki ɗauko ƙafa ki zo min gida?. Kuɗin da za ki biya a shekars ɗaya, shi ki ka biya a wata biyu kacal, kuma ki samu na dawowa ƙasar nan. Kalli yadda ki ka koma, ai ana ganin ki an san ba iya abinci ne ya mayar dake haka ba, akwai wani abun a bayansa." Islaha ta ɗan runtse ido ta ce, "Mama ni ba yawo na yi ba, ban aikata komai ba, na samu dama ne shiyasa na dawo. Daman ba a son raina na tafi ba, abinda ya kaini shine ya dawo dani." Mama ta zuba mata ido tana kallon ta, kafin ta ja ƙwafa ta ce, "to sai ki bar min gidana, ai ba da kuɗin ki aka gina gidan ba ko?." Islaha bata ce komai ba, ta miƙawa Mama tsarabar da ta siyomata ita da Hanan ta ce, "Ga tsarabar Jeddah, babu yawa." Hannan ta ja ledar tana buɗewa ta ce, "Lallai Mama da gaskiyar ki, wanda ya je aikatau ina shi ina tsaraba? Gaskiya da walakin goro a miya." Mama ta kalli kayan ta kalle ta ta ce, "bazan ƙi karɓar kaya ba, amma zama a gidan nan ne baza ki yi ba, ki je ki nemi wajen zama, amma ban da gidan nan." "Wa nake gani kamar Islaha!." Islaha jin muryar Baffa a bayanta sai ta miƙe tana murmushi ta ce, "Ni ce Baffa." Baffa ya zauna yana kallon ta da fara'a ya ce, "Islaha saukar yaushe?." Ta zauna aƙasa ta ce, "Tun ɗazu na dawo, ina gidansu Safeera. Ya ƙarfin jiki Baffa?." "jiki ya warware Islaha, na ji sauƙi kamar ban yi ba." "Allah ya ƙara lafiya Baffa." "amin Islaha. Ina kwance sai na nemi ki na rasa, sai da na dawo nake jin labari mara daɗi. Me yaasa ki ka biyewa zuciya ki ka bi shanun sarki? Meyasa ki ka amince dar huɗubar waɗanda basu cancanci a ji kalaman su ba balle a ɗauka?." Islaha ta san Baffa da Mama yake maganar, sai ta ɗan yi murmushi ta ce, "Baffa wani abu ne ya kaini, kuma shine ya dawo dani." Baffa ya ce, "na ji daɗi da ki ka dawo lafiya, daga ganin ki an san ba ki sha wahala ba. Ki shiga ciki ki kwanta." Mama ta ce, "tunda ni ce shanun sarkin, baza ta shiga ta kwanta ba, ta tafi wani wajan amma ba nan ba." Baffa ya ce, "a nan zata zauna, in kin ga Islaha ta bar gidan nan to ta yi aure, in kuwa bata yi aure ba bata da wani gida in ba nan ba." "Bazan ajjiye wacce ta je ta gama wayon duniya a gidana ba. A ina ta samu kuɗin da ta biya kuɗin da aka kaita harda na dawowa gida da tsaraba?." "Cewa ki ka yi a gidan ki, kin ga nan ai ba gidan ki bane. Sai ki jira ki gina na ki, daga lokacin sai ki hana duk wanda ki ka dama zama a cikinsa, dan wannan kam ba gidan ki bane." Baffa ya kalli Islaha ya ce, "Safeera jeki ki rakata ɗaki." A sanyaye suka wuce zuwa ɗakin Islaha suka tarar dashi yana nan yadda yake, sai dai ya yi ƙura sosai. Safeera ta ce, "ki fita, bara na gyara miki, na ji har kin fara tari." Islaha ta ce, "Bara na miƙawa Baffa wannan ɗin sai na dawo." Safeera ta fara gyara mata ɗakin ita kuma ta fita da tsarabar Baffa. Da sallama ta shiga wajan Baffa, ya amsa yana kallon ta da murmushi, ta durƙusa ta ce, "Baffa ga tsarbar da na siyo maka." Ya klli kayan ya ce, "Tsaraba kuma Islaha! Ke da ki ka je aiki maimakon ki adana kuɗin ki sai ki yi tsaraba?." Ta yi murmushi ta ce, "Babu yawa Baffa." Baffa ya ce, "Na gode Islaha, Allah ya yi miki albarka." "Amin Baffa." "Ki cigaba da haƙuri, kar ki biyewa Maman ku, ki kau da kai ki cigaba da zama jiran lokaci. Tunda kin dawo auren ku bazai wuce sati biyu ba, gwara ta daina ganin ki a huta." Ta yi murmushi ta ce, "Babu komai Baffa." Baffa ya ce, "Jeki ki huta." Ta miƙe a sanyaye, Baffa ya ce, "Ina Labiba da Maimuna?." Gaban Islaha ya faɗi, ta dawo ta duƙa ta ce, "Duk suna gaishe ka." Baffa ya murmusa ya ce, "gwara da ki ka yi dawowar ki, ni zuciyata bata amince da zaman nan ba, kuma ban taɓa zargin za ki aikata wani abu mara kyau ba, ko yaushe kyakykyawan fata nake yi miki. Tashi ki je ki huta, Allah ya cigaba da dafa miki." Islaha ta amsa da amin, sannan ta miƙe ta fita ta koma wajen Mama. Tana shiga falo suka haɗu da Mama, ta bita da kallon sama da ƙasa ta ce, "ya ba ki goyan bayan zama a gidan nan, kina zaune kina zaman jiran Saheer ya aure ki ko?." Islsha ya sukuyar da kai bata ce lomai ba, Mama ta ce, "indai ni na haifi Saheer wallahi bazai aure ki ba, in kuwa ya zaɓi ya aure ki sai dai ya nemi wata uwar bani ba." Islaha ta ɗaga ido ta kalle ta jin abinda ta ce, Mama ta buɗe idanu waje ta ce, "kalle ni da kyau, buɗe idonki cikin nawa. Wallahi bazai aure ki ba, in kuwa ki ka ga kin aure shi to ki tabbatar bana numfashi!." Islaha ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, ta ɗan motsa zata bar wajan Mama ta riƙo ta ta ce, "ki daina ganin yana ba ki goyan baya, ga dai gida nan ki zauna, amma ban da auren ɗana." A hankali ta bar wajan ta shiga ɗaki, ta tarar Safeera ta gyara shi ta zauna akan gado ta yi shiru. Safeera ta ce, "Ya dai?." "Kwana biyu na fara mantawa da damuwar Mama, hankalina ya kwanta, kunnena ya daina ji min baƙaƙen maganganu irin na Mama. Daga dawo ta yau na fara fuskantar ƙalubalen da na bari. Ya zan yi da Mama? Me na yi mata bata sona?." Safeera ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ina jinta, duk abinda ta faɗa na ji, amma bata isa ta hana abinda Allah ya nufa ba." Islaha ta yi shiru bata ce komai, Safeera ta gama yi mata abinda zata yi sannan ta kalle ta ta ce, "zan koma gida, zan bar ki ki sake hutawa. Amma gobe ki tabbatar sai kin ƙarasa bani labari." Islaha ta kalle ta ta ce, "Gobe za kiraka ni opharnge, ina da buƙatar yin bincike akan inda Zainab ta tafi." "Allah ya kaimu. Aiki fa?." "Ba gobe zan koma ba, sai na huta." Safeera ta ɗaga kai ta yi mata sallama ta fita. Ya ku ke ganin rantsuwar Mama? Zata karye ko baza ta karye ba?..... _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ Nana Haleema. [7/21, 12:05 PM] KRBBK: RDB2P73 Nana haleema. Washe gari Islaha bata bari sun haɗu dasu Mama ba ta bar gidan ko karyawa bata yi ba. Islaha da Safeera suka haɗu suka tafi gidan marayu kamar yadda ta ce. Tun da suka je gate take gaisawa da da ita har ciki gidan. Office ɗin Mama suka je, aka ce ta fita bata nan, hakan ya saka Islaha ta tsaya ta rasa abinda zata yi. Tana na tsaye sai ga ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan, ganin Islaha a tsaye sai ta ce, "ƴata Islaha." Islaha ta kalli matar, sai ta yi dariya ta ce, "Baba Tabawa, ina kwana." Baba Tabawa ta ce, "Yaushe ki ka dawo? Ance min da bakya nan." "Jiya na dawo Baba Tabawa, na zo neman Zainab ne." Baba Tabawa ta ce, "Zainab dai ta ki?." "Ita fa, nazo ina neman ta ance bata nan, kuma naga Mama bata nan." Baba Tabawa ta girgiza kai ta ce, "ai Zainab ta kwana biyu bata nan, an nemi inda take an rasa, har maganar an kai gaban hukuma amma babu ita babu labarinta." Islaha ta sauke numfashi cikin wani irin yanayi ta ce, "Don Allah Baba Tabawa babu wanda suka yi magana da ita kafin ta bar gidan nan?." Baba ta girgiza kai ta ce, "gaskiya ba mu yi magana ba, amma...." Sai ta yi shiru, ta kalli Islaha ta ce, "ku zo mu je." A hankali suke bin bayanta, suna tafiya Islaha tana gaisawa da waɗanda suka sani har ta ja su kitchen inda Baba Tabawa take aiki. Baba tabawa ta ce, "Na jawo ku nan ne saboda akwai saƙon Zainab da ta bawa Yafindo, Yafindo ta faɗa min ta ce ta bata saƙo ta ce mata don Allah duk ranar da ki ka dawo ta ba ki." Islaha da zumuɗi ta ce, "bara na je wajan Yafindon na same, ba Yafindon kitchen ɗin nan ba?." Baba Tabawa ta yi saurin riƙo hannun Islaha ta ce, "Islaha tsaya." Islaha ta tsaya tana kallon Baba cikin wani irim yanayi. Baba ta ce, "Yafindo bata nan, ta je ƙauyensu." Islaha ta dafe kai ta ce, "Kuma bata ba ki saƙon ki ajjiye ba?." "bata bani ba Islaha, ita kanta wannan maganar cewa yi kar na faɗawa kowa, kema kawai na faɗa miki ne. Dan ba mu yi tunanin dawowar ki nan kusa ba, shiyasa itama ta tafi ƙauye." Islaha ta ce, "Ina ne ƙauyen na su?." Ta girgiza kai ta ce, "ba a cikin garin nan take ba gabaɗaya." Islaha ta yi ajiyar zuciya mai ƙarfi, ta jingina da bango ta yi shiru bata ce komai ba. "Amma ta faɗa min a yadda Zainab ta bar gidan nan akwai matsala a tare da ita." Islaha ta girgiza kai ta ce, "Ina Hafsa da Fadwa?." Ta girgiza kai ta ce, "waɗnanan sun zama ƴan kansu, sai abinda suka ga dama suke yi a gidan nan, kuma da yake sun samu goyan baya babu abinda ake yi musu. Fadwa itace shugaba, duk abinda suke yi a ƙarƙashin Fadwa suke yi." Islaha ta kalli Baba Tabawa ta ce, "na gode Baba, zan dinga shigowa akai akai, dan na duba ko Yafindon ta dawo." Ta girgiza kai ta ce, "Duk da dai tana jimawa in ta tafi, amma na san zata dawo nan kusa." Islaha ta gyaa kai suka fita daga gidan. Suna fitowa Islaha ta ga motar Saleem a ajjiye tana jiransu, Islaha ta kalli Safeera, Safeera ta ce, "Ni ce na kira sa." Bata ce komai ba suka shiga motar. Suna shiga Salewm ya ce, "Hajiyan Jedda, sai ki ka dawo babu labari ko?." Ta ɗan yi murmushi ta ce, "Dawowar ce ta zo a haka, amma na so na faɗa mu ku Allah bai yi ba." "Ba wani nan, kin tafi kwatsam babu labari, kin dawo babu labari." Ta ɗan yi murmushi dan bata cikin yanayin wasa, suka gaisa ya ce, "ina fatan komai ya zama normal ko?." Ta ɗaga kai ta ce, "Alhamdu lillah!." "Haka ake so. Ina zamu je?." Islaha ta ce, "Safeera wajan wankin kai zani, kaina ya dame ni." Safeera ta ce, "mu je sai ayi mana." Tunda suka fara tafiya bata ce komai ba, ta yi shiru tana tunanin halin da ta jefa Zainab a ciki. Safeera ce ta waiwayo ta kalle ta ta ce, "Yanzu ya ki ke ganin za a yi?." Islaha ta kalle ta sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ban sani ba, amma da zan san garin su Yafindo zan je ko dan ta bani saƙon da Zainab ta bata ta bani, hankalina ya kasa kwanciya, zuciyata tana faɗa min akwai wani abun da yake faruwa." Safeera ta ce, "gaskiya dai akwai, sai dai fatan Allah ya kiyaye." Ta yi shiru kawai ta kwantar da kanta, tana ganin Safeera da Saleem sun kalli junansu suna kallon ta, ita dai ta lumshe ido bata ce komai ba tana tunani. Saleema wajan wankin kan ya sauke su ya tafi. Basu jima sosai ba su fito, kai tsaye ta ce su wuce office ɗin Barr Suraj. Shima ya yi mamakin ganinta sosai, ta ƙi bashi damar yi mata tambayar yaushe ta dawo ta ce, "Hamma Suraj ba a ga Zainab ba, tun bayan wannan recording ɗin ba a kuma ganinta ba." Barr ya ce, "dole hukuma za a saka a cikin case ɗin nan, ki bar komai a hannuna, zan kai maganar gaban ƴan sanda, za su san abinda za a yi." "Ko yaushe sai ka ce na bar komai a hannunka, amma in na bari ɗin bana ganin wani cigaba. Kwana nawa da tafiyata, na bar maka komai ɗin, amma ni ban ga wani cigaba ba har yanzu." "Islaha baza ki gane ba, wannan case ɗin ba ƙaramin case bane, ba a yi masa shigar sauri, dole sai an bi a hankali." "Yanzu daga gidan nake, kuma an tabbatar min da bata nan, sannan akwai saƙon da ta bayar a bani, wacce aka bawa ɗin bata nan." "Wa aka bawa?." "Za ka iya gane Yafindo, wacce take aiki a kitchen?.." Ya ɗaga kai ya ce, "na gane ta sosai ma, Ina ta je?." "Wai ta je ƙauye, kuma ashe ba a garin nan take ba." Ya tallafi haɓarsa ya ce, "Amma zan so a same ta, ba mu san me ta bayar ba. Kar ki damu, tunda har ta bawa wani saƙo abin ya zo da sauƙi, za a san abinda zamu yi. Ina tare dake ko yaushe, zan san duk hanyar da zan bi na nemo Yafindo." Islaha ta ce, "na gode, zamu yi magana anjima" ya amsa yana miƙewa suka fita. Suna fitowa Safeera ta ce, "Islaha da kin sani ba ki faɗawa Barr maganar saƙon nan ba, kar a sake samun matsala irin wancan." Ta kalli Safeera ta ce, "Duk da abinda ya faru ni bana zargin ko ɗaya a cikin ku, Hamma ya faɗa min na dinga ɓoye sirrin da na samo, amma bazan iya ba, dan aikin ya fi ƙarfina ni kaɗai. Ko waye yake da hannu a maganar nan, Allah zai bayyana shi da gaggawa." "Haka ne, Allah ya ba da sa a." "Amin." Islaha haka ta dinga jan Safeera yawo, daga nan su je nan kuma duk akan ɓatan Zainab, sai da suka yi azahar sannan suka wuce gida. A cikin napep ɗin ma ta yi shiru tana tunani, Safeera ta ce, "ki ta addu'a lamarin nan, in sha Allah komai zai dawo daidai." Ta gyaɗa kai ta ce, "ban san me zancewa Hamma akan dawowa ta ba, in na faɗa masa maganar Mr Rehaan Yola kina ganin zai amince?." Safeera ta ce, "gaskiya babu lallai, kuma zai iya jin shakku a ransa. Amma kar ki ɓoye masa, kin ga kin ɓoye masa batun ɗauke ki da tafiyar ki, kuma ya ji haushi sosai kawai dan yana sonki ne yake mantawa. Yanzu kar ki ɓoye masa, ki faɗa masa gaskiya ko da zai ji haushi." "Zai ji haushi kam, sai dan kawai faɗa masa ɗin shine mafita. Ni kaina ina neman hanyar da zan fara yi masa bayani, shiyasa har yanzu ko waya ban yi dashi ba, dan ban san me zance ba." "Dole ki damu ai, amma in ki ka faɗa masa irin abinda ki ka faɗa min zai ji kamar kin raina masa hankali, in ki ka canja maganar kuma daga baya ya san asalin gaskiyar bazai ji daɗi ba. Dole ki faɗa masa, tunda daman kin ce masa neman kuɗin biyan bashi ne ya kai ki. Abinda zai tambaye ki ta ya ki ka samu kuɗin a wannan lokacin, dan ko aikin gwamnati ki ke yi a can baza ki haɗa wannan kuɗin a albashin wata biyu ba. Sai dai ki faɗa masa ɗin zai fi." Ta sauke numfashi bata ce komai ba suka cigaba da tafiya, a daidai ƙofar gidan ta hango sa a tsaye cikin jallabiyya baƙa, Sadik yana kan mota a zaune shi kuma ya jingina da motar suna magana. Gaban Islaha ya faɗi ta ce, "Safeera Hamma ya dawo." Safeera ta kalli wajan ta gan shi a tsaye, ta kalli Islaha ta ce, "ki nutsu, kar ya ga kamar kin tsorota ya yi tunanin wani abun." Daga can nesa suka sauka daga napep ɗin, Islaha ta biya kuɗin suka nufi wajan su Hamma ƙirjinta yana bugawa sosai. A hankali suke nufar inda suke a nutse, Islaha ta sunkuyar da kai har suka kusa ƙaraso daf dasu. Sadik ne ya fara gano ta, ya buɗe baki cikin mamaki da ɗaure kai ya ce, "A'a, wa nake gani kamar Islaha?...itace ko gizo take yi min?." Faɗar Islaha da ya yi sai ya ja hankalin Saheer ya kalli wajan da yake kallo, Saheer ya yi arba da bugun zuciyarsa, sai tsayar da idonsa a kanta yana kallon ta, kanta a ƙasa tana ƙarasowa har suka cin musu. Suna ƙarasowa ta ce, "barkan ku da yamma." Saheer ya kasa magana sai kallon ta da yake yi, zuciyarsa tana bugawa, yana so ya tantance da gaske itace ko gizo take yi masa. Sadik ne ya diro daga kan mota ya ce, "Islaha ke ce ko kuma ƴan biyun ki ce?." Ta yi dariya ta ce, "Ni ce Hamma Sadik." Ya kalli Saheer da ya zuba mata ido kamar zai cinye ta, sai kuma ya ƙaraso inda yake yana kallon ta, muryarsa a tausashe ya ce, "Matar Hamma?" Ya faɗa da sigar tambaya yana nuna da yatsa. Islaha ƙirjinta ya buga, jin muryar masoyinta har tsakiyar kanta, ga kewar ganinsa da take addabar zuciyarta. Ta ɗago ido a hankali ta kalli idonsa, sai ta sauke kai ƙasa ta ce, "Na'am, mijin matar Hamma." "Oh my god! Ke ce da gaske? Na kasa yarda fa." Ta ɗan yi dariya ta ce, "Ni ce fa Hamma." Saheer ji yake kamar ya jawo hannunta ya rungume ta, sai ya tuna a ƙofar gida suke bazai iya aikata hakan ba. Amma yana so ya ji ta a jikinsa ko zai tabbatar itace ko kuma ba ita bace. Ya riƙo hannunta yana kallon bracelet ɗin daya bata ya ce, "Yaushe ki ka dawo?." Ta sukar da idanunta ƙasa ta ce, "Jiya na dawo Hamma." Ya wara ido ya ce, "har jiya? Kuma shine ban sani ba?." Ta ɗan kalle sa tana zame hannunta daga cikin nasa ta ce, "Mamaki nake so na baka." Ya bita da kallon da ya mamaki ita kuma ta kalli Sadik ta ce, "Hamma Sadik ka gama mamakin ko da saura?." Ya yi ƴar dariya ya ce, "Na tabbatar Islaha. Kuma ki ka sauka tun jiya babu labari?." "Sai dare na nutsu, kuma da safe ina tashi na fita." Sadik ya kalli Safeera ya ce, "laifin ki ne, da ba ki faɗa mana aminiyar ki ta dawo ba." Ta yi dariya ta ce, "Wallahi nima ganinta kawai na yi, babu labari babu sanarwa." Sadik ya ce, "Ma sha Allah! Tunda ta dawo lafiya ai haka mu ke fata. Gashi nan kam Jeddah ta karɓe ta." Ta yi murmushi ta kalli Saheer da ya rungume hannunsa a ƙirji yana kallon ta ta ce, "zan shiga ciki Hamma." Ya ɗafa mata kai ta juya zata shiga, Sadik ya ce, "sai na zo na karɓi tsarabata." Ta yi yar dariya kawai bata ce komai ba. Safeera ta ce, "na shiga gida Islaha, zan shigo da daddare mu ƙarasa maganar mu." Ta ɗaga mata kai ta shiga cikin gida. Sadik ya daki kafaɗar Saheer ya ce, "Saheer wallahi ƙasar Saudia ta karɓe Islaha fa, anya wani minister bazai yi maka overtaking akan yarinyar nan ba?." Saheer ya hararesa  ya ce, "ko kunya ba ka ji, kana yabon kyaun matata a gaban idona." Ya yi yar dariya ya ce, "Amma ya aka yi ta dawo da gaggawa haka? Ba ta yi wata uku ba fa." Saheer ya ce, "Nima na yi mamaki sosai, kuma ban ji Mama ta ce min Labiba ta dawo ba. Amma bara na shiga na tambaye ta, dan gaskiya ina da tambayoyin da zan yi mata." Sadik ya ce, "Ni na wuce, gobe ƙarfe nawa zaka koma?." "sai dare zan tafi." "Allah ya kaimu" ya faɗa yana shiga mota ya tafi shi kuma ya shiga gidan. Gidan babu kowa da Mama bata nan, Baffa ma ba ya nan sai Islaha kaɗai a tsaye tana tunanin abinda zata ci. Jin motsin Hammanta sai ta juyo ta kalle sa ta ga ita yake bi da kallo, irin kallon kewa da ƙauna da kuma shauƙi. Islaha ta ɗan turo baki ta ce, "Yunwa nake ji, kuma ni bazan iya girki ba." Saheer ya zo kusa da ita yana kallon idanunta, sai ta sauke ido ƙasa ya ce, "me za ki ci?." Bata ɗago ba ta ce, "komai ma zan ci." Ya sauke numfashi ya ce, "Islaha!." Bata ɗago ta kalle shi ba, Saheer ya ce, "ɗago mana." Ta ɗago a hankali ta kalle sa, ya ce, "ina jin kewar ki a zuciyar ki, kin yi min bazatar da ba ki taɓa yi min irinta ba." Ta yi murmushi bata ce masa komai ba, shi kuma ya ɗaga kai ya ce, "bara na samo miki abinci, na san kin saba da abinci mai daɗi ko?." Ta yi dariya ta ce, "ni komai ma zan ci." "To ki jira ni." Ta yi murmushi tana kallonsa, har zai tafi sai ya kasa daure abinda yake yawo a jininsa, ya dawo da baya, ya riƙe fuskar ta ya ce, "Ina ji kamar na rungume ki, ina jin kewar ki da yawa, ganin ki kaɗai bai gamsar dani ba, ina so na ji ki a jikina. Shiyasa na so kafin ki dawo an ɗaura auren mu, yadda zan nuna miki adadin kewar ki da na yi." Islaha ta sake sunkuyar da kai ƙasa bata ce komai ba. Saheer ya yi ƙasa da murya yana kallon ta ya ce, "in rungume ki?." Islaha ta ƙi kallonsa, sai wasa da take yi da hannunta amma ita kanta ta yi murnar ganinsa sosai ta jin daɗin haɗuwarsu. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Me ki ka saka shi gida kina yi masa ku kaɗai a gida babu kowa?.” Nana Haleema. [7/21, 12:06 PM] KRBBK: RDB2P74 Nana Haleema. Jin muryar Mama cikin amo duk sai suka waiwayo suna kallon ta. Mama ta ƙasaro da zafin nawa ta janye Saheer daga kusa da ita. Ta kalli Islaha ta ce, "rungumarsa za ki yi? Na ce rungumarsa za ki yi ko sumbatarsa za ki yi?. Kin je kin saba bin maza, kin ɗanɗana fulani kin ɗanɗana larabawa, dole ki zo ji cigaba da lalata min yaro. Yaarinyar da ta gama lalacewa a ƙasar waje, in ban da masifa da bala'i me zata yi min a gidana?." Saheer da yake ji kamar ya yi kuka saboda kalaman Mama, a sanyaye  ya ce, "Mama ki bari don Allah." Ta harare sa ta ce, "dallah can yi min shiru, mara zuciya da kishin kai. Me za ka yi da wannan ragowar? Me za ka yi da wannan watsatstsiyar wacce ta gama raba kanta a ƙasar waje?. A cikin wata biyu ta haɗa kuɗin da aka kai ta ta biya, sannan ta siyi ticket ta dawo gida kuma harda tsaraba. Daman Labiba ta faɗa min, gida gidan larabawa take shiga, wannan ya ɗauka wannan ya ajjiye." Islaha hawaye ya sakko daga idonta ta ce, "Wallahi Mama ni ba yawon....." ta kai mata mari Islaha ta yi saurin komawa bayan Saheer tana kuka. Mama ta nuna ta da yatsa ta ce, "sai na tsinke ki da mari. Ni ki ke faɗawa haka, ni ki ke kallon idona ina faɗa kina musawa?. In ba watsewar ba faɗa min me ki ka yi?." Bata ce komai ba sai kukan da take yi kawai, kuka mai tsuma zuciya, kukan da yake fita da wani irin sauti mai tayar da hankali. Mama ta jawo ta daga bayansa ta ce, "bar jikinsa ko na fasa miki ba ki. Ni dai an cuce ni, an kawo min tsintacciyar mage, an haɗa ni da mugun iri." Saheer ya ce, "Mama don Allah ki bari, ki daina faɗar hakan babu daɗin ji." Ta harare sa ta ce, "ga ka gata nan, sai ayi auren na gani" ta faɗa tana barin wajan. Ya kalli Islaha da take kuka sosai, ya kasa yi mata magana ganin yadda take jan nunfashi hawaye yana sakkowa daga idonta. Cikin sanyi jiki ya ce, "Ki yi haƙuri, je ki ɗaki ki zauna na kawo miki abincin, ki daina kuka kar ki sarƙe.” Bata shiga ɗakin ba, ta ɗauki mayafinta da ta ajjiye a wajan ta fita daga falon a guje. Da sauri ya bita yana kiran sunanta, ta tsaya ya ce, "kar ki fita Islaha, ki jira ni na kawo miki abinci." Ta ja numfashi ta ce, "na...na ƙoshi" ta faɗa muryar tana cracking saboda kuka. Ya ce, "sai kin ci, shiga ɓangaren Baffa na kawo miki." Ta ƙi motsawa daga inda take, ya ƙaraso kusa da ita ya ce, "ki je ki zauna ki jira ni." A lokacin Baffa ya shigo gidan ya ƙaraso ya ce, "Saheer me ya same ta take kuka haka?." Saheer ya kalli Baffa ya ce, "Baffa Mama ce." Baffa ya sauke nunfashi ya ce, "wani abu ne ya faru?." "Ka san halin Mama Baffa, kalamai marasa daɗi ta dinga faɗa mata, shine ta ɗauko mayafi zata fita." Baffa ya ce, "Islaha mu je falona ki zauna, kai ina zaka je?." Saheer ya ce, "abinci zan kawo mata, ta ce yunwa take ji." Baffa ya ce, "jeka ka kawo mata, Islaha mu je ciki." Bazata iya yiwa Baffa musu ba, ta karɓi ledar hannunsa suka cigaba da tafiya a hankali shi kuma ya fita. Suna shiga Baffa ya ce, "Zauna Islaha." Ta zauna a kan carpet ya zauna a kan kujera. Ya ce, "ki cigaba da haƙuri kin ji, ki cigaba da ɗauke kai ƙiris nake jira na ɗaura auren ku. Amma bara Saheer ɗin ya zo mu san abinda za a yi." Ta yi shiru tana goge hawaye, Baffa ya dinga rarrashinta cikin kalamai na kwantar da hankali. A lokacin Saheer ya shigo da sallama, suka amsa ya ƙaraso ya zauna ya miƙa mata ledar abincin ya ce, "ga abincin nan." Ta ja ledar kusa da ita amma bata buɗe ba, Baffa ya ce, "ki ci abincin ki, ina zuwa" ya faɗa yana tashi ya shiga ɗaki dan ya bata dama ta ci. Saheer ya bita da kallo, a sanyaye ya ce, "Islaha ki ci." Ta buɗe ledar ta ga fried rice ce da chicken, ta sauke numfashi ta fara ci a hankali dan da gaske yunwa take ji. Harda ruwa da lemo a ledar, ta sha ruwan ta rufe ragowar abincin. A lokacin Baffa ya dawo ya zauna, Saheer ya ajjiye masa tasa ledar abincin da ya siyo masa a kusa dashi. Baffa ya kalli Saheer ya ce, "Ina so ɗaurin auren ku kar ya wuce nan da sati ɗaya, ka shirya?." Cikin ƙarfin guiwa ya ɗaga kai alamun eh, sai kuma ya ce, "Baffa ina jin tsoron furuncin Mama." Baffa ya ce, "ka bar ni da ita, kar ka damu da wannan furucin nata, babu abinda Allah zai yi maka." Baffa ya kalli Islsha ya ce, "Ƴata Islaha kin amince da auren ku nan da kwana sha huɗu?." Islaha sake saukar da kanta ƙasa bata ce komai ba, Baffa ya ce, "Kar ki ji kunya, na san kema kin gaji da takura da zagi da tsangwar da Zulaiha take yi miki sun ishe ki. Bana so ki dinga jin kamar dan ba ki da iyaye ne ya saka ake yi miki haka, bana so ki ji na gaza a matsayina na uba a gare ki. Ina so ki samu farin ciki da kwanciyar hankalin da nake so ki samu, ina so ki samu walwala da nutsuwa kamar kowa. Shiyasa nake so a yi auren yanzu, amma sai kin amince." Islaha ta sake sauke kai ƙasa ta kasa cewa komai, Baffa ya ce, "ki amsa." Kanta yana ƙasa ta ce, "Duk abinda ka yanke daidai ne." "A'a, faɗa min ra'ayin ki." "na ba ka zaɓi Baffa." "sai kin zaɓa." Ta kasa ɗago ido ta kalle sa ta ce, "na amince Baffa." Baffa ya murmusa ya ce, "ki fara ƙananun shirye-shirye, daman ya ce min an gama haɗa lefen ki, ginin gidansa shima ya zo ƙarshe. Kai ko ba a gama ba, na yarda ku kama haya ku zauna, nan gaba sai ku tare a gidan na ku." Islaha dai kanta yana ƙasa, Saheer ne yake murmushin jin daɗi, amma in ya tuna da Mama sai gabansa ya faɗi. Saheer ya kalli Baffa a hankali yace, "Baffa ina jin tsoron Mama." Baffa ya ce, "ka kwantar da hankalin ka, babu abinda zai faru, zata yi haukata ta gama." Baffa ya kalli Islaha ya ce, "na yi miki alƙawarin baza ki sake sati biyu a gidan nan ba, za ki je inda za ki samu ƴancin rayuwa yadda ki ke so." Ita dai bata ɗago ba ta dai yi murmushi, tana jin ƙaunar Baffa tana shiga zuciyarta sosai. Baffa ya ce, "ki yi zaman ki a nan, zan je na yi sallah na dawo" ya faɗa yaa  miƙewa ya fita. Saheer ya ce, "to ya fita, sai ɗago ki kalle ni mu yi magana." Ta ɗago a hankali tana kallonsa, Ssheer ya ɗaga mata girarsa sama ya ce, "To ya dai ƴan mata, kin shirya?." Sai ta yi murmushi ta kuma sunkuyar da kanta bata ce komai. Ya yi murmushi shima sannan ya miƙe ya ce, "zan je na yi sallar magrib." Itama ta miƙe ta ce, "nima sallar zan yi, amma bana son komawa can." "Na raka ki ɗakina ki yi alwalar?." Ta girgiza kai alamun a'a ta ce, "Kar Mama ta ganni. Bara na yi da ruwan nan, ya ishe ni" ta faɗa tana ɗaukar ruwan suka fito tare. Mama tunda ta shiga ɗaki take waya ta ce, "Karima abubuwa suna neman lalace min, wannan yarinyar da ta je ta dawo maganar auren nan tana sake tasowa fa, ni kuma wallahi bazan  bar Saheer ya aure ta ba." Karima ta ce, "wata maganar ce ta taso kuma?." "Za dai ta taso, dan yanzu haka tana ɓangaren Baffa ya sakata a gaba yana rarrashi. Ni dai taimako bai yi min rana ba wallahi, na ɗaukowa kaina abinda ya fi ƙarfina." "Ai na faɗa miki, tun yarinyar bata kai haka ba nake ja miki kunne akan zamanta a gidan ki, amma ba ki ɗauki mataki ba, yanzu gashi nan kina ji kina gani zata aure miki ɗa bayan ta gama yawace yawancen ta." "Bata isa ba wallahi, sai dai ayi ragas, mutuwar kasko." "Lallai ma, ke da ɗan cikin ki ki ke fatan ayi ragas? Ai babu batun ragas, ke ce mai nassra kawai." "Yanzu meye abin yi? Ni ko meye zan yi akan Islaha, in kashe ta za a yi a kashe, in haukata za a yi a haukata. Duk abinda za a yi ayi, indai zata fasa auren Saheer." Karima ta ce, "Kuɗi za ki fito dasu, mu je mu bi hanyar da Saheer ɗin da kansa zai ce bazai aure ta ba." Mama ta ce, "yaushe za a yi hakan?." "Gobe ma in kin shirya mu wuce, na faɗa miki wannan kurarin babu abinda zai yi, tsaf za a yi auren nan ba ki sani ba wallahi. Dan haka mu je a yiwa tufkar hanci tun bata warware ba." Mama ta ce, "ƙarfe nawa goben?." "Ki fito da sassafe, dan cikin ƙauye zamu shiga. Fulani ne mu, akwai wanda ya kai mu surkulle da iya shige shige ne?. Zan yi miki maganin Islaha wallahi, sai dai wata mai irin sunanta, amma ba dai Saheer ya aure ta ba." Mama ta sauke numfashi cikin jin daɗi ta ce, "Allah ya kaimu goben, zamu yi waya" ta faɗa tana kashe wayar tana tunani. A bayyane ta ce, "Akan ta auri Saheer wallahi gwara na sabauta ta, gwara ta nemi hankalinta ta rasa." ••••••••• Abba yana zaune yana amsa waya, Mamy tana gefensa a zaune tana jin duk abinda yake faɗa. Abba ya ce, "Sunan mutumin Mustapaha Maddibo, ka san shi?." Daga can ɓangaren ya ce, "Sani kai, yanzu haka tare zamu shiga masallaci." Abba ya ce, "Yauwa, zan iya wakiltaka in babu damuwa." "Haba dai, faɗi kawai babu damuwa." "so nake a same shi akan maganar yarinyar da yake riƙo, a tuntuɓe shi in ba a yi mata miji ba zan bawa ɗaya daga cikin yaran nan aurenta." "Islaha ka ke nufi?." "Eh kamar haka sunan yake." "Ai kuwa kowa waye ya yi dacen yarinya mai kirki da hankali. Yarinyar tana da hankali da nutsuwa sosai, dan ta fi yaran da ya haifa tarbiyya da sanin darajar na gaba. Ina ta ya wanda za ka karɓawar auren ta murna, dan ya samu macen kirki." Abba ya yi murmuahi cikin jin daɗi sannan ya ce, "sai ka saka na ji daɗi da ka ke yabonta. Wallahi Daada ce ta matsa akan sai Rehaan ya aure ta, daga yarinyar ta ganta a hanya ta taimake ta shikenan wai ita Rehaan zai aura. Nayi-nayi a bar batun auren nan amma Daada ta ƙi. Ka san in abu ya haɗu da girma, sai ana yi ana lallaɓawa a rabu lafiya." "Rehaan da kansa? Kai lallai Islaha ta ta ki sa'a. La la la! Ashe babbar giwar ce da kanta." "Wallahi shine. Ta dole Daada take son haɗa auren nan." "Kar ka hana, ka ba da goyan baya baka san me Allah ya ɓoye a ciki ba, ka saka a yi ta addu'a, sai ka ga hakan ya zama alkhairi." "Shiyasa na ji daɗi da na ji kana yabonta wallahi. Ka san ya rayuwar Rehaan take, ta ko ina kawo masa suka ake yi." "Na sani wallahi, ai duk wanda kaga ya ɗaukaka ka kalle sa kawai, ba ka san ƙalubalen da ya fuskanta ba. Amma yarinyar tana da hankali da nutsuwar da zan ce maka baza ta auri Rehaan dan kuɗinsa ba wallahi." Abba ya ce, "Duk da haka Alhaji Rufa'i, ni so nake kar su san sunan Rehaan, ka je musu a matsayin ban faɗa maka sunan wanda nake so na haɗa ba, kawai tambaya ce in babu miji za a yi magana." Alhaji Rufa'i ya ce, "Hakan ma shawara ce. In Allah ya yarda gobe zan same shi, duk abinda ake ciki zan kira ka." Abba ya ce, "na gode Alhaji Rufa'i." Daga nan suka yi sallama ya kashe wayar. Abba ya kalli Mamy da ta yi shiru ya ce, "Kin ji dai, yarinyar ana ta yabonta. Ban taɓa jin wanda ya faɗi aibunta ba tunda na fara sakawa ayi bincike a kanta." Mamy cikin ko in kula ta ce, "Allah ya kyauta kawai, amma ni kam bana son auren nan wallahi." "Uwa ce ke, ki yi masa addu'a da fatan alkhairi, ki yi fatan Allah ya sa ta zamar masa alkhairi." Ta amsa da amin kafin ta ce, "Amma yadda ya bani zaɓi zan zaɓa masa wacce ta dace da rayuwarsa, zan zaɓa masa wacce zai samu farin ciki daga gare ta." Abba ya murmusa ya ce, "Nadira! Mu fa fulani muna da kara, amma ku indiyawan nan ba ku da kara akan yaranku. Nuna min ki ke yi Rehaan fa ɗan ki ne, ni kin cire ni kin ajjiye a gefe." Ta ɗan yi murmushi ta ce, "Bazan yi karar da zata cutar min da ɗa ba, ba zan yi abinda zai ji ban kyauta masa ba. Ina so ya samu farin cikin da ya rasa, ina so ya zama ya fi jin daɗin zaman gidan nan akan ko ina. Ka duba, saura sati biyu bikin Jafar, amma saboda ba ya son zuwa ba ya maganar dawowa." Ya yi murnushi ya ce, "zai dawo ne, tsakaninsa da Jafar ai ba a shiga. Kuma dole ya dawo shima ya angwance." "haka za a yi bikin ba wani shiri? Yanzu an ce nan da sati biyu, ko shirin kayan amarya da ake kaiwa ba a yi ba." "Kar ki wani damu, wannan duk mai sauƙi ne. Mu jira mu ji mana, in an yi mata miji fa shikenan an huta." Mamy ta murmusa tana fatan Allah ya sa an yiwa Islaha miji a kuɓutar da ɗanta daga aurenta, dan Allah ya sani bata son auren, dan an fi ƙarfinta ne kawai. REHAAN KO SAHEER?💃🏻🔥 Nana Haleema [7/22, 10:14 AM] KRBBK: RDB2P75 Nana Haleema. _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ Sameer ya kalli Mamansu ya ce, "Mama wai meyasa ki ke so auren nan ya yu har haka?." Mama ta kalle sa ta ce, "yaro yaro ne, yuwar auren nan na Rehaan yana daga cikin cikar birina a gidan nan, shiyasa zan iya bin ko wacce hanya dan ganin na tabbatar da auren nan?." Sameer ya ce, "ta ya zai zama cikin burin ki? Ban gane ba, ki yi min bayani." Mama ta murmusa sannan ta ce, "ka zuba ido ka sha kallo, amma babu wanda ya isa ya hana auren nan yuwa matuƙar ina da rai. Ku je ku cigaba da shirin auren kawai." A lokacin Hamma Zayyad ya shigo, ya zauna a kan kujera ya ce, "Mama ashe wai bikin Riyya saura sati biyu?." Sameer ya ce, "Abba bai faɗa maka ba?." Ya girgiza kai ya ce, "ban sani ba, yanzu nake ji a bakin masu gadi." Mama ta kalli ɗan nata tana ji kamar ta juya sama ta dawo ƙasa, da tana da iko da yanzu ta ƙwace ɗaukaka Rehaan ta bawa ɗanta, shine babba amma ya zama kamar shine ƙarami saboda bashi da kuɗin da Rehaan yake dashi. Ba wai kuɗi ne bashi dashi ba, yana da kuɗi kamar sauran ƴan gidan, kawai Rehaan ya fita zakka a cikinsu. Ita kuma kallon talakawa take yi musu saboda Rehaan, shiyasa take baƙin ciki da hakan sosai. Ta girgiza kai cike da takaici ta ce, "Kaima dai ban da abin ka, meye abin damuwa dan za a yi bikin ka Riyya baka sani ba?." "Ba damuwa na yi ba, sai meye san an yi ban sani ba. Kawai babu daɗi ne Mama." "Kar ka ji daɗi. Duk ba kai ka jawo ba? Ga hanyar yin kuɗi da shahara nan da yawa amma ka kasa bi ka zama kamar Rehaan. Hannunka kamar rariya, da an ba ka kuɗi da sun ƙare. Haba, ƙannenka wanne irin abun duniya ne basu dashi?." Hamma Zayyad ya ɗan taɓe baki ya ce, "To Mama zan canja Allah ya yi ni ne?." Ta ja dogon tsaki, ta cize leɓe tana buga ƙwafa. Auren nan na Rehan shine target ɗinta, shiyasa ta ɓuya ta yi shiru tana jira ayi sannan ta cigaba da aiwatar da abubuwan da suke gabanta, dan wallahi bazata bar Rehaan lafiya ba, sai ta la'anta rayuwarsa ta ɗaiɗaice •••••• Islaha bata bar ɓangaren Baffa ba sai goma na dare, Baffa ya riƙe hannuta da kansa ya kai ta har ɗaki ya sannan fito. Mama bata ce komai ba dan ta daina ɗaga jiyoyin wuya, ta ƙarƙashin ƙasa zata yi maganin Islaha. Ita dai Islaha kwanciya ta yi tana tunanin rayuwarta, haka zata yi zaman aure da mijin da babarsa bata ƙaunarta? Anya zata samu farin cikin da take fatan samu a aurensa? Anya zata samu kwanciyar hankali da nutsuwar da take fatan samu?. Hamma yana sonta, zai bata kulawa irin wacce bata yi hasashe ba. Amma babarsa bata so, duk da ba da Babarsa zata zauna ba amma ita ta haife sa. Tun tana faɗa masa aibunta baya yarda, wata ran zai yarda, wata ran za a samu akasin da zata yi abinda zai ce daman Mama ta ce. Ta girgiza kai Zainab ta faɗo mata a rai, ta miƙe ta kira Suraj a waya amma bai ɗauka ba, ta koma ta kwanta tana tunanin mafita a rayuwarta. Washe gari da safe bata ji motsin Mama ba, daman bata cika yi mata karanbani ta shiga ɗakinta ba sai dole. Gidan babu kowa alamun Hanan ma bata nan, ta shiga kitchen ta sha tea, dan ya yi safiya baza ta iya cin komai ba sai rana ta fito sosai. Tea ɗin kawai ta sha, ta shirya ta fito da niyar tafiya aiki. Tana fitowa suka haɗu da Saheer, suna haɗa ido ta ɗan yi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ina kwana." Bai amsa ba sai kallon ta da yake yi sannan ya ce, "kin ci abinci?." Ta girgiza kai ta ce, "Ya yi safiya da yawa, zan ci in anjima." "Ina za ki je da safe haka?." "wajan aiki zan je." "Yanzu?." Ta ɗaga masa kai alamun eh. Ya ce, "Ya yi wuri yanzu, na san ba ki da aiki a wannan lokacin. Mu je ki raka ni wani waje, daga nan sai na kai ki." Bata ce komai ba suka fito, bai rufe gidan ba dan Baffa yana ciki. Tunda suka shiga motar ta lura da yanayinsa ya canja, ya haɗe rai sosai kuma ko kallonta ba ya yi. Ta ce, "Hamma motar wajen Sadik ɗin ce?." Kai kawai ya ɗaga mata bai ce komai ba, ta yi shiru bata sake kula shi ba. Sun fi mintina goma a haka, shi bai kunna motar ba kuma bai fita ba. Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Sai na ganki kwatsam, har shekara ɗayan ta yi?." Islaha ta ɗan murmusa, daman ta san dalilin ɓata ran nasa kenan, babu inda zata raka shi kawai maganar yake so su yi shiyasa ya saka ta shiga mota. Islaha ta ce, "bata yi ba." "Bani labari, ya aka yi na ganki a nan bayan na san zaman ki a can bai isa kin tara waɗanan kuɗin ba." Ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Hamma...." Ya yi saurin dakatar da ita ya ce, "kar ki ɓoye min komai, in na same ki da ɓoye min wani abu kamar yadda ki ka dinga yi a baya zamu yi faɗa mai muni." Ta girgiza kai ta ce, "bazan ɓoye maka komai ba, in sha Allah." Ya ɗaga kai ya ce, "ina jin ki." Ta yi shiru kamar baza ta yi magana ba, dan bata san da wacce fuska zai ɗauki maganar ta ba, ita kanta jin maganar take kamar wasan yara balle kuma shi. Ta sanyaya murya ta ce, "kamar yadda na faɗa maka ina samun kyautar kuɗi a gidan aiki, to a haka na tara kuɗin." Ya sake kallon ta ya ce, "cikin wata biyun ki ka tara miliyoyin nan?." Ta girgiza kai ta ce, "ba wannan ba, wanda na siyo ticket na dawo gida nake nufi." "Okay, waɗancan fa?." Ta sake kallon sa ta ga ita yake kallo, sai ta daure saboda kar ya zarge ta ta ce, "Mun haɗu da Jafar ne, wanda muka taɓa haɗuwa dashi a Diamond hotel, lokacin da na je neman Rehaan Yola zamu yi interview. Shine ya ce min na dawo gida aikin bai dace dani ba, shi zai biya Rehaan kuɗinsa." Saheer ya tsaya yana kallon ta jin wata magana mara kan gado, ta sako wasu mutane da bai san da su a cikin labarin ba. Ya ce, "Me ya kawo Jafar cikin maganar nan kuma? Ya aka yi ya san da batun kuɗin?. Sannan me ya kawo Rehaan Yola a ciki?." Islaha ta ɗan shiru sannan ta ce, "Shi wanda ya sace ni ɗin, ashe shine Rehaan Yola ban sani ba, kuma..." Saheer ya dakatar da ita ya ce, "ban gane ba, kamar ya shine Rehaan Yola, Rehaan Yola dai wanda na sani ki ke nufi?." "Shi ɗin dai Hamma. Shine ya ɗauke saboda mun haɗu sau biyu na yi masa rashin kunya, sannan gidansa ne gidan da nake zuwa yin aiki a Jeddah. A nan muka haɗu da Jafar, ya yi bincike a kaina ya san wacece ni, shine ya ce aikin bai dace dani ba, ni kuma na faɗa masa dalilin zuwana Jeddah, shine ya ce na dawo gida zai biyasa kuɗinsa. Shine kawai na dawo." Saheer ya ce, "lokacin da kina Jeddah, kin ce min matar gidan ce ta ke yi miki kyautar kuɗi saboda tana da kirki, yanzu kuma kin ce Rehaan ne. Meye gaskiyar maganar?." "Ƙarya na yi maka a wancan lokacin, bana so ka yi min faɗa kace ina zuwa wani gidan ne shiyasa na ce maka haka. Amma shi ko aure bashi dashi." Ya zuba mata ido kawai yana kallon ta, ita kuma ta ƙi kallonsa ta kawar da kai gefe tana jira ta ji amsar da zai bata. Sun kwashe minitina ashirin a haka kafin ya ce, "Wanne series ne, waye ya ya yi directing film ɗin?. Na san dai labari da tsarwa na ki ne, to waye ya ba da umarni?." Ta juyo suka haɗa ido jin abinda ya ce, ya ɗaga mata kai ya ce, "a wacce channle ake haskawa nima na gani, ko a youtube ne?." Islaha ta sauke numfashi jin bai yarda ba, ta lumshe ido ta ce, "Hamma da gaske nake fa." "Nima da gasken nake ai, ki faɗa min sunan series ɗin na je na kalla. Ko sunansa rainin hankalin Islaha?." "Hamma...!" Ya dakatar da ita ya ce, "Ni za ki mayar ƙaramin yaro Islaha, ni za ki zauna kina rainawa hankali dan kin ga ina ɗaukar ko wacce damuwa daga wajen ki?." Islaha ta ce, "Da gaske nake Hamma." "Da farko kin ce min ba ki san wanda ya sace ki ba, kin ce ba ɗan ƙasar nan bane ba, aka yi ta fama dake akan ki ba da wata hujja da za a iya gano waye ki ka ƙi faɗa. Yanzu sai Rehaan Yola ya shigo cikin wasan kwaikwayon ki, sai ga Jafar ma ya shigo cikin wasan dan a yi acting ɗin dashi. Da yake kin mayar da Rehaan abokin wasan ki ko, An faɗa miki ƙaramin mutum ne shi?. Ko kina faɗa sunansa ne dan na ji a raina ai kina tare da mai kuɗi bara in bar magana? Ko kina faɗa min Rehaan ne dan na ji a raina baza ki yi min ƙarya dashi ba?." Islaha zata sake magana ya hanata ya ce, "indai wannan shashancin za ki cigaba da faɗin min bana son ji, ki riƙe kalamanki kawai. Gwara ki fito fili ki faɗa ki ce Hamma bazan faɗa maka ba, ya fi min daidai akan ki dinga raina min hankali kamar wani sa'anki." Islaha ta ce, "Wallahi da gaske nake, bazan yi maka ƙarya ba." Ya kalle ta ya ɗauke kai sannan ya ce, "Da dai bakya yin rantsuwa akan ƙarya, amma yanzu kin fara. Ke da bakin ki kin ce ƙarya ki ka yi min dan kar na yi miki faɗa, wannan ma dan lin yi min ƙarya ba yau aka fara ba." Islaha sai ta yi shiru dan bata san me zata ce masa ba kuma, tunda har ya yi tunanin ta rantse a kan ƙarya gwara kawai ta yi shiru da bakinta zai fi alkhairi. Ta yi shiru shima ya yi shiru, ya zubawa ƙaramin titin masu ido ita kuma tana wasa da jakarta bata sake ce masa komai. Baza ta sake cewa komai ba tunda ya yace tana rantsuwa a kan ƙarya a je a hakan, gwara ta yi shiru kar ta yi masa rashin kunya tazo tana danasani daga baya. Shi kuwa tunanin wannan rainin hankalin nata kawai yake yi, ji yake ba a taɓa raina masa hankali a duniya kamar yadda Islaha ta yi masa ba, ji yake ba a taɓa yi raina masa wayo da wulaƙanci kamar abinda ta yi a lokacin ba. Zuciyarsa ta fara ɗarsa masa abubuwa kala kala a kanta, ya fara zargin kalaman Sadik dana Mama gaskiya ne, tunda gashi ta saka shi a gaba tana raina masa hankali kamar wani yaro ɗan shekara ɗaya. Ya yi ajiyar xuciya bai ce komai ba, sun jima a haka kowa ya yi shiru babu wanda ya sake magana a cikinsu. Sai daga baya ya ja motar suka tafi wajan aikin bai sake yi mata magana ba. A bakin gate ɗin ma'aikatar ya tsaya baice mata komai ba, ta ɗauki handbag ɗinta sannan ta kalle shi, kamar kar ta yi magana sai kuma ta ce, "in na yi ƙarya da sunan Ray wacce riba zan samu Hamma? Wanne irin amfani hakan zai yi min da zan rasa da wanda zan yi maka ƙarya sai shi?. Amma tunda kana jin abinda na faɗa maka a matsayin ƙarya shikenan, har kana cewa ina rantsuwa akan ƙarya. Duk tunanin da zuciyarka ta baka a kaina ka yarda hakan ne, kar ka tilasta zuciyarka ta amince da gaskiya na faɗa, ka yi amfani da yardar ka ya fi" ta faɗa tana fita daga motar har lokacin bai ce mata komai ba. _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ Nana Haleema. [7/22, 10:14 AM] KRBBK: RDB2P76 Nana Haleeema. Sai da ya ga ta shiga wajan aikin sanann ya ja tsaki, a bayyane ya ce, "Islaha ƴar rainin hankali ce, ni zata saka a gaba tana bugawa kamar ball dan ta raina ni? Da farko an sace ta, ta biya kuɗin aikin baffa, ta saka aka kulle case, ta tafi Jeddah, ta yi min ƙaryar wata mace ce take bata kuɗi, yanzu ta dawo tana kallon idona tana faɗa min wai Mr Rehaan ne. Mtsww!"ya faɗa yana jan motar ya bar wajan. Yana barin wajan da Sadik suka haɗu, Sadik ya shiga motar ya zauna ya ce, "Ya dai na ganka da ɓacin rai a safiyar nan, bayan jiya kace min akwai labari?." Saheer ya kalle shi ya ce, "kalli fuskata Sadik, na yi kama da shashasha?." Da mamaki ya ce, "ban gane ba, me ya faru?." Saheer ya ce, "yarinyar nan Islaha ce take neman mayar dani mahaukaci." Sadik ya yi yar dariya ya ce, "sai yanzu ka sani kenan....Hmmm me ya faru?." "Na tambaye ta akan ya aka yi ta dawo gida bayan bata gama abinda ta je yi ba, a ina ta samu kuɗi, ka san me ta ce?." "Sai ka faɗa." "Wai Rehaan Yola shine ya sace ta, kuma dashi ta haɗu a can, Jafar ya biya mata kuɗin kuma ya ce ta dawo gida." Sadik ya ce, "ban gane ba, wanne Reheen Yola ɗin?." "Wanda ka sani, wanda ta je hotel yin interview dashi kwanaki. Wai da shi ta haɗu dashi a can, daga nan suka haɗu asibiti, ya sace ta, ta sace masa kuɗi, ta je Jedda suka haɗu......." Sai ya ja dogon tsaki yana dukan motar, ya dafe kai ya ce, "Islaha ta mayar dani mahaukaci gabaɗaya." Sadik ya ce, "bayan mahaukaci ta mayar da kai sakarai wanda bai san abinda yake yi ba. Ta rasa da wanda zata yi ƙarya sai da Ray? Kuma duk wannan shirmen da ta lissafa ta ce duk da shi ya fau? Ta rasa wanda zata ƙullawa sharri sai shi?." "Hmm!" Ya faɗa yana jan numfashi kawai bai ce komai ba dan bai san abinda zai ce ba. Sadik ya ce, "wannan maganar bata da kan gado balle makama, da sunan wani zauna gari banza ta faɗa ma sai a yarda, amma sunan wanda ta kira ba abin wasa bane. A ina zata ga Rehaan ma, mutumin da ko yaushe yana Uk? Ko da ma shi ɗin ne, ace bata taɓa ganin hotonsa ba balle ace har ya sace ta bata san shi bane?. Islaha fa ƴar jarida ce, kuma ƴar social media ce, duk wanda yake hawa kafafen yaɗa labarai ƙarya yake yi ya ce bai san Rehaan Yola ba. To akan me ma zai zubar da class ɗinsa ya ɗauke Islaha fisabinillahi?." Saheer dai bai ce komai ba, dan gani yake Islaha ta gama katantanwa da hankalinsa gabaɗaya. Sadik ya kuma cewa, "Allah ya kyauta kawai, amma akwai wani abun a ƙasa. Ina jin ka, meye labari mai daɗin?." Saheer muryarsa a shaƙe ya ce, "share kawai, zuwa anjima zan wuce in sha Allah, komai normal ko?." Sadik ya ce, "komai ya yi normal, sai mun haɗu" ya faɗa yana fita daga motar shi kuma ya ja motar ya tafi. Islaha tunda ta shiga ake ta murnar ganinta, Chairman har office ɗinta ya shiga yana ta murnar ganinta, ya zauna ya ce, "Malama Islaha, saukar yaushe?." Ta yi dariya ta ce, "Shekaran jiya." Daɗi ya mamaye ransa ya ce, "ni da ake ta cewa ga Islaha na ɗauka wata muka samu daban ba ke ba, sai na yi tunanin kaf gidan nan ke kaɗai ce mai irin wannan sunan, ashe ke ɗin ce dai." "Ni ce Chairman." "Barka da sauka Islaha." "Yauwa Chairman." "Amma dai an dawo kenan ko? Baza ki sake guduwa ki bar mu ba? Allah in za ki sake sai dai ki nannaɗe toron giuwa ki tafi da ita, dan baza mu zuba ido ki saka mu watse ba." Ta yi dariya ta ce, "na dawo in sha Allah, babu inda zan sake zuwa, muna nan tare." Ya sauke numfashi ya ce, "har na ji daɗi wallahi, da na san kina nan ai da ke za ki yi labaran ƙarfe shida. Amma akwai na sha biyun rana ai, Allah ya nuna mna." Ta yi murmushi ta ce, "Amin Chairman." "Ki gode Allah Islaha, kina da sa a sosai a rayuwar ki. Kina daga inda ki ke ma ɗaukakar bata bar ki ba, wannan ɗan content ɗin da ki ke yi ya sake farfaɗo damu daga doguwar suman da muka afka da bakya nan." Ta yi dariya bata ce komai ba, Chairman ya ce, "yau yau ɗin nan za a fara ganin ki, akwai labarin wasanni da za a gabatar kai tsaye, tashi ki hau camera." Ta ɗan buɗe ido ta ce, "Aikin Jamila da Muslim ne fa." "Yau kema za ki ɗana, ni na san za ki iya. Taso maza maza." "Chairman faɗar sunan ƴan ball ɗin nan wani lokacin yana bani wahala, kar na kwafsa fa." Ya kalle ta ya ce, "Sai dai in wata Islahan, ba dai ke ba, mu je." Ta dole y saka ta gabatar da shirin ba dan tana so ba. Da yake shirin live ne a radio da tv da kafafen sada zumunta, an sha ruwan comment ana murnar sake ganin fuskar Islaha. Shigowar Ummi kenan ta samu baƙin labari, ta nufi office ɗin Islaha dan ta ganarwa idonta. Tana shiga suka haɗu, Ummi bata ce komai ba ta juya ta bar wajan da hanzari. Islaha ta taɓe baki, bata bi ta kanta ta wuce record office wajan Safeera, a hanya suka haɗu da Safeeran ta taho nemanta, sai suka koma office ɗin su Islahan dan su tattauna." Safeera ta ce, "Ya dai? Na ga duk kin canja." Islaha ta ce, "Hamma ne bai yarda da labarin da na bashi ba, wai har yana cemin ya sunan film ɗin." Safeera ta ce, "ba kowa ne zai yarda ba fa Islaha, ni kaina sai da na kai zuciya nesa sannan ya amince da maganar nan. Kowa zai yi tunanin me ya kawo Ray cikin zancen ki, da ace ƙarsmin mutum ne babu wanda zai damu, amma sunan babban mutum kamar sa ki ka ambata, iya faɗa kawai mutum zai ga kamar kin raina masa hankali ne kawai." "amma meyasa ke ki ka yarda shi bai yarda ba? Wai har yana cewa ina rantsuwa akan ƙarya, wallahi Safeera baza ki bini bashin rantsuwa ba, bazan yi abinda zai cutar dani dan na kare kaina ba. Safeera duk abinda na faɗa miki an yi, wani abun ma ban faɗa miki ba. Meyasa Hamma bazai yarda dani ba? Shima ya fara zargina kamar Mamansa kenan?." "ba zargi bane, kawai zai ji kamar kin mayar dashi mahaukaci ne. Amma zai amince, ki sake yi masa bayani." Ta yi tsaki ta ce, "ai tunda ya ce na rantse a kan ƙarya babu abinda zan sake faɗa masa, in ya ga dama ya yarda, in bai ga dama ba kar ya yarda bai dame ni ba. Abu ɗaya na sani, gaskiyata na faɗa, duk wanda yake yi min wani kallo na daban shi da Allah, kuma ban yafe ba wallahi." "Babu zancen shi ya sani, dole ki yi masa bayanin da zai gane kuma ya fahimce ki, shine wanda za ki aura fa." Ta kalli Safeera ta ce, "to me zan ce masa? Kina ji na faɗa miki yadda muka yi dashi." "Haka za ki sake faɗa masa har ya gane." "Hmmmm! Ga Baffa ya ce bazan sake yin sati biyu a gidan nan ba, aurena da Hamma za a yi." Safeera ta buɗe ido ta ce, "Baffa ya matsa fa, kuma na san duk saboda Mama ne." Ta taɓe baki ta ce, "itace mana, kin ji kalaman da ta dinga faɗa min?. Ni yanzu fargaba ma nake yi wallahi, ta ya zan yi rayuwar auren da mijin da babarsa bata ƙaunata?." Safeera ta ce, "Babban ƙalubale ne mai girma, amma kuma ai shi yana sonki." "Na raina son da yake yi min, tunda ya kasa bani listing ears ɗinsa har yake cewa ina rantsuwa a kan ƙarya, kuma yake zargin kamar yawon banza na je na yi har na samu waɗanan kuɗin." "Ba zargi bane, dole zuciya zata yi rawa." "ke meyasa ki ka yarda dana faɗa miki?." "Nima da farko ban yarda ba." "yanzu fa?." "Na yarda." "saboda me ki ka yarda?." "Saboda na san halinki, kuma na yarda dake." Islaha ta ce, "kin ga kenan shi bai yarda dani ba, ga shi ke kin amince shi ya kasa amincewa. Bazan bashi tsarabar da na siyo masa ba ma, in na ba shi wani zargin ne zai sake shiga tsakani. Har Sadik ɗin bazan bawa ba, zan ajjiye kayana na siyar ko na bayar. Tunda ya fara zargina in na ba shi wani zargin ne zai biyo baya." Safeera ta yi dariya jin ta fusata sosai da Hammanta ta ce, "Ki ba shi mana, kar ki fasa alkhairin da ki ka yi iya." Ta yi tsaki ta ce, "Bana son rainin hankali ne wallahi, bai taɓa bani haushi kamar yau ba, ya ɓata min rai sosai, da wani ne ba shi ba da sai ya raina kansa wallahi." Sai kuma ta kalli Safeera ta ce, "Kin gama abin ki ke yi?." Safeera ta ce, "na gama." Islaha ta miƙe ta ce, "Mu je ki raka ni office ɗin Barr, daga nan mu je gida na ɗauki tsarabar Adda na kai mata." Safeera ta miƙe suka fito tare. Ummi tana barin wajan office ɗinMuslim ta shiga, ta same shi a zaune ta shiga a fusace ta ce, "Islaha ta dawo, ka ganta?." Ya ɗago ya ce, "Haba Ummi, babu sallama babu neman izini?." "Ba shi ya kawo ni ba, ka ga Islaha?." "na ganta. Itace ta gabatar da shirin da nake gabatarwa yau." "ka kasa yin komai a kanta, kai ka ce za ka nemo mafita kafin ta dawo, baka yi komai ba gashi har ta dawo. Na ga ji da waɗanan alƙawarin naka, ni zan yi abinda nake ganin ya dace." Ya miƙe ya ce, "Allah ya baki sa'a, amma duk abinda ki ka aikata kar sunana ya fito, dan babu hannuna a ciki. Jeki tunda ba ki da hankali, ki je ki aikata abinda zuciyar ki take raya miki ya kamata ki yi. Ke ba ki san a hannun hukuma ki ke ba ko?" ya faɗa yana zama bai kalle ta ba." "Ka kasa yin komai, kai ka ce baza ka bata damar dagowa ba, amma gata ta dawo, ta ya hankalina zai kwanta?." A fusace ya ce, "an faɗa miki cikin gaggawa ake yin abun? Ko an an faɗa miki ƙaramin abu nake so na yi?. Tunda baza ki iya jira ba ki je ki yi abinda ki ka ga ya dace, amma wallahi duk abinda ki ka aikata kar ki sake sunana ya fito a ciki." Ummi ta koma ta zauna tana jan numfashi, ya yi mata banza bai ce mata komai ba ya cigaba da abinda yake yi. "Yi haƙuri. Hankalina ne ya tashi wallahi." "Da sannu sannu ake yin komai, a hankali zamu ɗana tarkon da zai kama mata wuya. Program ɗina aka ɗauka aka bata, ni kaɗai na san abinda nake ji a raina. Dan haka ki nutsu, wallahi Allah bazan bar Islaha ba, sai na yi mata abinda baza ta iya ɗaga ido ta kalli camera ba har abada." Ummi ta ja numfashi ta ce, "yaushe?." "Ki ƙyale ni kawai" ya faɗa yana miƙewa ya bar ta zaune. ••••••• "Sabon labari ya bayyana, na samu labarin yarinyar nan Zainab kafin ta bar gidan nan ta bawa Yafindo ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan nan saƙo ta bawa Islaha. Har Islahan ta biyo bayan saƙon, ta dawo cikin garin nan kuma zata cigaba da tone tone. Hankalinta ya tashi tana neman ƙauyen su Yafindo dan ta a bata wannan saƙon." Ya girgiza kai ya ce, "Yarinyar nan da gaske dai dangerous ce a gare mu. Ita Yafindon ina ne garin na su?." "Kwata-kwata ba ƴar Adamawa bace." "Duk yadda za a yi mu rigata zuwa, ko ta iska zata hau ta je wajen Yafindo, mu zamu hau guguwa mu rigata sauka, kafin ta je mu mun je mu karɓi abinda aka bata ko ta lallami ko ta ƙarfi." Mama ta ce, "tsohuwa ce fa." "tsohuwar fa, in ta ƙi ayi mata sbinda aka yiwa Zainab ɗin. Itama Islahan lokacin ta ya yi, dole ta rasa ɗaya daga cikin waɗnanan abubuwa guda biyu. Ko rayuwarta, ko kuma hankalinta!." Mama ta sauke numfashi ta ce, "Mu fara da maganin Islahan, amma maganar ta tsaya iya ni da kai, kar ka faɗawa wani muna shirin yiwa Islaha wani abun." Da mamaki yake kallon ta ya ce, "saboda me?." Ta ja numfashi ta ce, "zan faɗa maka dalilin, amma dai magana ta tsaya iya ni da kai. Zan san hanyar da zan bi na yi maganinta da gaggawa, in ba haka ba zata yi mata illar da bamu taɓa zato ba." Ya ɗaga kai ya ce, "a wannan karon bana so a samu matsala." "an gama ranka ya daɗe" ta faɗa tana ɗaukar handbag ɗinta ta fita. Ya bita da kallo har ta ɓace sannan ya ce, "Meyasa bata so sauran mutanen ƙungiya su san za a kashe Islaha? Me amfanin hakan zai yi mata?." Babu mai amsa masa sai Maman kawai, kuma ta ce zata faɗa masa ba yanzu ba. Ya sauke numfashi yana girgiza kai, dan zai iya aikata komai indai aka ce za a lalata masa kasuwancinsa. Tofa! Labari ya sake fita, waye ya sake fitar da sirrin Islaha ne? Meyasa ba a so mutanen ƙungiya su san za a kashe Islaha?😱😱 _Don girman Allah ku shiga Youtube ki yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ Nana Haleema. [7/22, 10:15 AM] KRBBK: RDB2P77 Nana Haleema. _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ A hankali Islaha take ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Saheer kamar babu jini a jikinta. Bata jima a tsaye ba ya buɗe suka haɗa ido, sai ta ɗan ja baya shi kuma ya fito ya jingina da ƙofar yana kallonta. Ta ɗan kalle sa sai ta ɗauke kai sannan ta ce, "Daman saƙo na kawo maka." Saheer ya karɓi abinda take miƙa masa yama juyawa a hannunsa ya ce, "na meye?." Ya buɗe yana kallon abubuwan da suke ciki, ya sake kallon ta ya ce, "waye ya ba ki ki kawo min?." Ta juyo ta kalle shi ta ce, "ni na baka." "Ke ki ka bani!" Ya maimaita yana kallon ta, sannan ya sake kallon kayan ya ce, "na meye?." Ta ɗan sauke numfashi ta ce, "Tsarabar ka ce na taho da ita daga Jeddah." Ya zuba mata ido bai ce komai ba, har sai da ta ɗago ta ga ya zuba mata ido yana kallon ta, itama ta zuba masa turo tana turo baki gaba. Ya miƙa mata kayan da ta ba shi ya ce, "Na gode." Ta ƙi kallon kayan sai kallon fuskarsa da take yi ta ce, "Ba ka so?." Ya ɗaga kai fuskarsa a ɗaure ya ce, "eh bana so." Har lokacin kallonsa take yi, ta ɗan buɗe ido waje ta ce, "Kyauta ce fa." "Kuma na ce bana so." "Amma meyasa ba ka so? Ni ce fa na baka, kuma itace kyauta ta farko da na fara yi mata, ko dan hakan ya kamata ka karɓa ko da baza ka yi amfani da abubuwan da suke ciki ba." Ya ajjiye mata a kusa da ita ya ce, "Bazan karɓi abinda ban san da wanne kuɗin da aka siya ba." Ta buɗe baki cikin mamakin kalamansa ta ce, "Hamma....!" Ta faɗi sunan cikin yanayi na mamakinsa. Sai kuma ta nuna kanta da yatsa ta ce, "Zargina ka ke yi Hamma?." Yadda ta yi maganar sai da zuciyarsa ta karye, dan ko kaɗan ba ya zarginta, kawai yana so ta faɗa masa gaskiyar abinda ya faru kuma ta ƙi. Bai nuna mata ba ya ce, "Ke ce ki ke ƙoƙarin dasa min zargin ki a zuciyata." "Amma Hamma na faɗa maka komai ko?." "kina tunanin zan yarda da wannan dramar ne?." "Drama ce Hamma?." "Drama ce! Bazan yarda da wannan kalaman naki ba, tunda kin zaɓi ki ɓoye min gaskiya shikenan, ki ɗauki tsarabar ki na gode." Ta yi shiru bata ce komai ba, ya juya zai shiga ɗakin sai kuma ya kalle ta ya ga ta zuba masa ido bata ce komai ba, ya daure shige ɗaki ta bar ta a wajan. Islaha a fusace ta bar wajan ba tare da ta ɗauki kayan ba. Haka ta koma ɗaki cikin jin haushi, ko a mafarki bata yi tunanin Hamma zai iya zarginta ba, ta yi tunanin shine mutum na farko da zai fara shaidar halayyarta, sai ga shi shine yake yi mata mummanan zargi akan abinda ta faɗa masa gaskiya a kai. Bata taɓa jin haushinsa kamar ranar ba, bata taɓa jin ya bata haushi kamar a lokacin ba. Ta zauna a gefen gado tana tuna abinda ya ce mata, tana jin zafi sosai. Haka ta kwana tana fushi dashi, ko da ta tashi da safe bata neme sa ba. Tana fitowa suka haɗu da Mama, ta gaishe ta bata amsa ba ta wuce, itama bata damu ba ta shiga wajan Baffa suka gaisa sannan ta fita daga gidan. Baffa ya shirya ya fito da niyar tafiya wajan aiki ya haɗu da Alhaji Rufa'i a ƙofar gidan a tsaye. Baffa da mamaki yake kallonsa ya ce, "Alhaji Rufa'i." Alhaji Rufa'i ya juyo da fara'a suka gaisa, Baffa ya ce, "Wani ka ke nema na ganka a tsaye a nan?." Alhaji Rufa'i ya ce, "Kai nake nema, ina ta tunanin yadda zan same ka sai gaka ka fito." Baffa da mamaki ya ce, "ni kuma?." "Kai fa." "Allah ya sa Lafiya." "lafiya lau wallahi. Alkhairi ne yake tafe dani. Magana ce mai girma a bakina, kuma itace ta kawo ni gare ka." Baffa mamaki ya sake mamaye masa zuciya, amma bai nuna ba ya ce, "To mu shiga daga ciki?." Alhaji Rufa'i ya ce, "Ma sha Allah." Baffa ya yi masa iso har cikin falonsa. Baffa ya ce, "Bara na saka a kawo maka ruwa daga cikin gida." Alhaji Rufa'i ya ce, "ba sai ka wahala ba, kar ka damu, na gode sosai." Baffa ya zauna ya ce, "Babu komai. Abin farin ciki ne a gare ni ace yau ka zo gidana tafe da alkhairi." Alhaji Rufa'i ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya dai lamari ne mai girma ya kawo ni, alkhairi ne babba, wanda in ya kasance ba kai kaɗai ba, duk dangin ka zasu san Allah ya saka maka albarka a rayuwar ka." Baffa ya girgiza kai yana nazarin wannan wanne irin alkhairi ne haka, amma bai ce komai b sai murmushi da ya yi ya ce, "ma sha Allah!." "Ban taɓa ganun wanda aka yiwa dashen ƙoda ya warke kamar ka ba, ni duk waɗanda na sani in aka yi dashen basa tashi, sai ka ga sanadin tafiya kenan, Amma kai gaka kamar ma baka yi ba." Baffa ya yi murmushi ya ce, "haka mutane da yawa suke faɗa, ni kaina ban taɓa gani ba sai a kaina. Dan nima na yi tunanin lokacin ya zo, ban yi tunanin zan kawo haka da rai ba." "Ma sha Allah, Allah ya ƙare mu da lafiya." "Amin ya Allah." "Na barka kana ta tunanin dalilin zuwana ko?" Ya faɗ yana murmushi. Baffa ya ce, "Gaskiya dai, ka barni cikin tunanin wanne irin abu ne haka?." Ya yi murmushi ya ce, "Batu ne akan ƴar gidan nan da ka ke riƙo, Islaha." Baffa ya girgiza kai ya ce, "Allah ya sa lafiya." "Lafiya lau. Alhaji AbdulAziz Yola, shine ya yi min magana akan yana nemawa ɗansa aurenta." Baffa ya buɗe ido yana riƙe haɓa jin maganar kamar a mafarki, ya girgiza kai ya ce, "Alhaji AbdulAziz dai na mu?." Alhaji Rufa'i ya ɗaga kai alamun tabbatarwa ya ce, "shi fa, AbdulAziz Yola dai da ka sani, a kansa nake magana. Ya faɗa min ya yi bincike akanta kuma ya yaba da komai na ta, wannan dalilin ne ya saka yake yiwa ɗansa ƙwaɗayin aurenta. Shine da kansa ya taso ni, ya ce na zo na same ka na ji, in ba a yi mata miji ba auren bazai wuce nan sati biyu ba. Akwai bikin ƴarsa da za a yi, yarinyar zata auri ɗan Yayansa, yana so a haɗa lokaci ɗaya ayi." Baffa ya girgiza kai cikin mamakin gingimemen abun da ya tunkarosu, sai maimaita sunan AbdulAziz Yola yake yi a ransa, yana maimaita sunan Islaha yana girgiza kai cikin mamaki mai yawa. Baffa ya ce, "Alhaji Rufa'i ni na rasa abinda zan ce. Alhaji AbdulAziz da kansa shine ya ga Islaha ya yaba da ita, har ya yiwa ɗansa ƙwaɗayin auren ta?." Ya yi murmushi ya ce, "Yarinyar ta taimaki mahaifiyarsa ne, ta taimake ta a lokacin da ba kowa ne zai taimake ta ba. Tun daga nan suka yaba da ita, kuma da ya bincika ɗabi'unta sai ya ga halayenta da komai ya yi masa. Shiyasa yake yiwa ɗansa sha'awar aurenta." Baffa ya yi murmushi, wani daɗi ya mamaye masa zuciya, yana ji kamar Allah ya kawo masa mafita lamarinsa, ya na ji kamar Allah ne ya aiko da haske dan ya haska duhun da ya mamaye shi gabaɗaya. Baffa ya gyara zama yana murmushi ya ce, "Islaha dai ba a yi mata miji ba, da dai ɗan wajena Saheer zai aure ta, amma mahaifiyarsa ta nuna bata so, ta ce akwai wacce ta zaɓa masa ita zai aura, to maganar Saheer ta wuce, dan ya haƙura ma tuni. Ba a yiwa Islaha miji ba, za a iya shiga neman auren ta." Alhaji Rufa'i ya yi murmushi ya ce, "Amma na ji daɗi sosai, dan ni kaina na yaba da halayen Islaha sosai, shiyasa yana faɗa min na ce bazan yi ƙasa a guiwa ba, sai na zo da kaina mun yi magana." Baffa ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya dai Islaha ba daga nan ba, ba dan ta kasance tawa nake yabonta ba, amma wani lokacin ina ji ina ma ni ne na haifi Islaha." Alhaji Rufa'i ya ce, "dan ka yabe ta ai baka yi laifi ba, baka ji ance yabon gwani ya zama dole ba?." Suka yi murmushi a tare Alhaji Rufa'i ya ce, "Zan sanar da kai saƙonsa, sannan za a turo yaro dan su daidaita kansu. Za ka iya bincike akan ahlin gidan gabaɗaya, dan a tabbatar da ingancin auren. In Allah ya sa sun daidaita dashi shikenan, in kuma ta ce bata so babu lallai babu dole." Baffa ya ce, "Waye bai san gidan Alhaji AbdulAziz ba? Ai ba ɓoyayyen mutum bane, da halayensa dana ƴaƴansa duk basa su ɓuya ba. Zan yi magana da Islahan, in ta amince zan kira ka na faɗa maka, in bata amince ba ma zan sanar da kai. Ka san yaran yanzu, ba kasafai suke amincewa da irin wannan haɗin ba, ni kuma bana so na yi mata dole dan ta kasance ba ni na haife ta ba." Alhaji Rufa'i ya ji daɗin kalaman Baffa ya ce, "wannan gaskiya ne. Ka faɗa mata zai zo su ga juna, ta ɓangarensa daman mahaifinsa ya bawa zaɓin fitar masa da mata, ka ga ita ake jira a yanzu." "In Allah ya yarda zamu yi magana da ita, ta tafi aiki da yanzu zan kira ta." "Babu komai, ayi abun a nutse. Muna da saura kwanaki a gaba. Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Baffa ya amsa da amin, ya raka shi har ƙofar gida sannan ya dawo. Baffa ya sauke nunfashi yana jin daɗi a ransa, domin mafita Allah ya kawo masa a lokacin da yake tsaka da nemanta. Ya ji daɗi da Saheer baya nan, yana fatan kar ya dawo har sai an ɗaura auren Islaha da wannan yaron da ko sunansa bai sani ba. Mama sai ta jiƙa Saheer ta shanye, Allah ya ɗaga Islaha ya kai ta babban gida, inda rayuwarta zata yi haske, inda zata yi farin ciki ta samu cigaban rayuwa. (me ya canja Baffa ne?😱🤔). _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ Nana Haleema. [7/23, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P78 Nana Haleema. _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ •••••••• Abba yana zaune a gaban Daada yana faɗa mata yadda aka yi. Daada yi guɗa cikin murna, ta yi hamdala sannan ta ce, "An yi nasara a matakin farko da ya kasance ba a yi mata miji ba. Yanzu sai jiran amincewarta, in Allah ya yarda zata amince da auren nan." Abba ya yi murmushi kawai bai ce komai ba. Daada ta ce, "An faɗa musu bikin bazai wuce kwana sha uku ba dai ko?." "An faɗa Daada, shiyasa mai riƙonta ya ce bazai yanke hukunci ba sai ya yi magana da ita, sanann sai ta ga Rehaan ɗin ta tabbatar zata aure sa. Dan ba a faɗa musu sunansa ba, na saka an ɓoye ne dan mu gwada yanayin su, kuma gashi ya bamu mamaki ya amince." Ta washe baki ta ce, "Ai daga ganin laraba ka san da juma'arta, ni na san yarinyar nan ta samu tarbiyya mai inganci wallahi. Yau kwana zan yi akan sallaya ina faɗawa Allah, sai Ishlaya ta shigo ahlina sannan hankalina zai kwanta." Abba bau ce komai ba, amma yana jin daɗi in ya ga Daada tana farin ciki. Daada ta ce, "a je a cigaba da shiri kamar yadda ya kamata." Ya amsa yana tashi ya fita. Yana fitowa suka haɗu da Jafar zai shuga wajan Daada. Jaazy ya duƙa har ƙasa ya gaishe da Abba, Abba yana murmushi ya ce, "Ango ka dawo ashe?." Jazy cikin da kunya da girmamawa ya ce, "Na dawo Abba." Abba ya ce, "Jeka ku gaisa da Daadan ka zo ina neman ka." Jazy ya amsa da to, Abba ya fita shi kuma ya shiga wajan Daada. Bai wani jima a wajenta ba, dan ba fuska yake samu a wajanta ba, kawai ya shiga ne dan Mamy tana cewa ya shiga, amma da bazai je ba. Yana fitowa ya shiga ɓangaren Abba ya same shi a zaune a kan kujera. Shi kuma ya zauna a akan carpet yana jiran Abba ya yi magana. Abba ya ce, "Jafar ina ɗan uwan naka? Yaushe zai dawo?." Jazy ya ɗan murmusa ya ce, "ya ce min nan da jibi in sha Allah zai shigo, daƙyar na saka zai zo ma, ya ce shi ba sai ya zo ba." Abba ya murmusa yana gyaɗa kai ya ce, "Baturen bafulatani kenan, jini uku ne yake yawo a jikinsa. Ga jinin fulani, ga na indiyawa, ga jinin turawa tunda a burtaniya can ya girma, dole a samu iyayi kala kala a tare dashi." Jazy ya yi dariya sosai amma bai ce komai ba. Abba ya ce, "Ai kuwa zuwa ya zamar masa dole, dan tare za a haɗa aurenku da kai dashi, kamar yadda Daada ta ce." Da mamaki Jafar ya kalli Abba ya ce, "Tare kuma Abba?." Abba ya ce, "Tare kuwa Jafar, dan har an yi magana da dangin yarinyar da Daada ta nace a kai, amma sun ce sai sun yi magana da ƴarsu in ta amince. Hmmm a ganinka akwai wacce zata ƙi wannan tayin ne?." Jafar ya ce, "gaskiya babu Abba." "Ka ga shima aurensa ya zo kenan." Jafar ya ce, "Amma Abba wacece yarinyar? An yi bincike mai kyau a kanta?. Kar a biyewa Daada a yi abinda za a yi danasani, wacce zata zama natar Rehaan dole a tsaurara bincike a kanta, musamman irin wannan auren." "An yi sosai Jafar, yanayin yadda Rehaan yake dole ayi bincike kafin ayi auren. Na yi bincike da kaina kuma na saka anyi, babu wanda ya buɗe baki ya faɗi aibun yarinyar. Duk wanda zai buɗe baki yabonta yake yi, kowa in zai yabe ta zai ce tana da kirki da hankali. Kuma marainiya ce gaba da baya, a gidan marayu ma ta tashi har ta girma. Daga baya ne ta dawo gidan su wanda ya yi adopting ɗinta, da shi zai aure ta amma ance mahaifiyarsa bata so an haƙura. Duk da ance gidan da take babu wata tarbiyyar kirki, matar da take riƙonta tana harkar kai yara ƙasar waje aikin gidajen larabawa, amma duk da haka ana yabon halinta fiye da na yaran da ya haifa. Wajen aikinsu, mutanen unguwa, gidan marayun da ta tashi duk na bincika, kuma alhamdu lillah!." Jafar ya gyaɗa kai sannan ya ce, "ma sha Allah! Wacece Abba?." Abba ya ce, "Sunanta Islaha Maddibo, ƙaramar ƴar jarida ce a wata ƙaramar gidan tv, ban riƙe gidan tv ba gaskiya, amma yarinyar ta ɗaukaka a idanun mutane, musamman matasa. Jafar ya zaro ido ƙirjinsa yana bugawa ya ce, "Islaha Abba!." Abba ya kalle sa ya ce, "haka aka ce sunanta. Ka santa ne?." Jafar ya ce, "Na santa Abba, na taɓa ganinta a wani waje, har muka yi magana tana so na kawo mata Rehaan su yi interview." Abba ya ɗan girgiza kai yana murmushi ya ce, "to itace." Jafar ya girgiza kai yana mamakin ikon Allah, yana mamakin wannan kwaɗo da chakwakiya, yana hango yadda abin zai kasance, yana hango rigimar da Rehaan zai yi akan wannan abun. Lallai Allah Allah ne, in ba Allah waye zai haɗa Islaha da Rehaan a matsayin mata da miji?." Jazy ya ce, "itace wacce Daada take ta magana daman a kanta?." Abba ya ce, "Wallahi itace, yarinya kamar ta yiwa uwata asiri, gabaɗaya hankalinta ya tashi a kanta. Kuma babban abin mamakin har yanzu yarinyar bata san da maganar auren ba, bata san za a yi aura mata wani daga gidan nan ba, balle kuma ta san Rehaan zata aura." Jafar ya ce, "Ikon Allah!." Abba ya ce, "me ka sani a game da ita?." "Babu laifi Abba, ana yabonta sosai. Amma zan saka a yi bincike na musamman, in na ga wani abu mara kyau ko lokacin auren ya yi za a san yadda za a yi a fasa. Dan gaskiya bazai yu a yi auren mutum kamar Rehaan da wacce ba a san halinta sosai ba, zan tsaurara bincike mai kyau, in aka samu akasin alkhairi za a fasa." Abba ya cr, "hakan yana da kyau, ka saka a bincika yadda ya kamata, bana so ayi abinda za a zo ana danasani." Jafar ya ce, "Gaskiya ne kuwa." Abba ya ce, "amma kar ka faɗa masa sai ya dawo, na san halinsa, ana faɗa masa ya fasa zuwa." Jafar ya yi dariya yana hango dramar da za a kwasa dashi, musamman da ya kasance Islaha ce. Ya ce, "Bazan faɗa masa ba in sha Allah." Suka yi sallama Jafar ya shiga wajan Mamy. Da Banisha suka haɗu a falon Mamy, ya yi murmushi hancinta kamar yadda Rehaan yake yi mata ya ce, "Kiddo ina Mamy?." Ta ce, "Uncle Jazy Mamy tana apartment ɗin Hamma Rehaan." Ya riƙe hannunta ya ce, "zo ki raka ni." Tare suka je har part ɗinsa, ya hau sama ya tarar da Mamy a zaune a falon Rehaan na sama, Mamy ta dafe kai ga Riyya tana rarrashinta. Ya shiga da sallama ta ɗago ta kalle sa ta ce, "Jafar ƙaraso, ƙaraso ka ga abubuwan da na samu a ƙasan gadon ɗan uwanka." Gaban Jafar ya faɗi, ya ƙarasa yana kallon layoyin da suke ajjiye akan center table. Ya kalli Riyya da take kuka, ya kalli Mamy dan itama kukan take yi. Ya sanyaya murya ya ce, "A ɗakinsa aka samu wannan Mamy?." Riyya ce ta ce, "Eh! Mun zo yi masa gyara, shine Mamy ta samo wannan." Ya kalli layoyin ya sake kallon Riyya ya ce, "Samo ashana da reza yanzun nan, ki taho da plate." Ta ɗaga kai ta ɗauko ta kawo masa. Ya ɗauki layoyin bayan ya kira sunan Allah, ya farke ya zaro takardar ciki, bai tsaya karantawa ba ya saka musu wuta akan plate ɗin suka ƙone, yana ƙonawa yana karanta Auzubika bi kalmatillahil tammaat min sharri ma kalaƙ. A kan idonsa suka ƙone ƙurmus ya ɗauki tokar, ya shiga banɗaki ya zuba a masai ya yi flushing. Ya fito yana kallon Mamy, cikin son kwantar mata da hankali ya ce, "Koma meye Mamy ya koma kansu in sha Allah, don Allah ki daina kuka." Kamar jira take ta sake fashewa da kuka ta ce, "Jafar kashe Rehaan suke so su yi ne?." Ya sauke numfashi ya ce, "waye yake shigowa nan?." Riyya ta ce, "Babu kowa, ni ce kaɗai nake zuwa, wani lokacin sai Janan ko Ikram." Ya gyaɗa kai ya ce, "Kar ku damu, za a yi maganin koma waye. Mamy ki daina kuka." Ta share hawayenta tana sauke numfashi ta ce, "Na daina Jafar. Ka samu labarin aurensa ko?." "Yanzu Abba yake faɗa min, zan ƙara bincike a kan yarinyar in Allah ya yarda." "Wai Rehaan za a yiwa irin wannan aure, Rehaan ɗin da nake tanadin aurensa, shi za a yiwa wannan wulaƙantaccen auren da ko matar bai sani ba." "Sai haƙuri Mamy." Ta girgiza kai bata ce komai ba, sai kuma ta tashi ta sauka daga saman ta barsu a saman. Ya kalli Riyya da take ta hawaye ya ce, "Meye na kukan kuma?." Ta ce, "ni kaɗai fa nake shigowa, an zuba masa pioson a drink ɗin da na bashi, sannan yanzu ga kayan asiri a ɗakin da ni kaɗai nake zuwa. Ba dole na yi kuka ba." Ya ɗago fuskar ta ya ce, "Kina tunanin za a ce ke ki ka saka masa ne?." Ta buɗe baki zata yi magana ya ɗora yatsansa a kan lips ɗinta ya ce, "kar ki ce komai, wannan ba tunani ne mai kyau ba." Ta cire hannunsa sannan ta ce, "to meyasa suke so su kashe mana shi, kowa a gidan nan ba sauraren mu yake yi ba, laifin mu ne dan mun zo a jinin Mamy?. Shi kaɗai ne Yayanmu, sauran Yayyem ƙannensu ne, meyasa zasu kashe mana shi?." A ya zauna a kusa da ita ya rungume ta yana pitting bayanta a hankali ya ce, "ki daina kuka, koma meye ai ya wuce, tunda na ƙona da sunan Allah." Ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tana kuka sosai yana rarrashinta. Sai da ya ji ta daina sannan ya ɗago ta, ya yi pecking goshinta ya ce, "ki bar kuka, babu abinda zai samu Rehaan in sha Allah, babu wanda ya isa ya yi masa abinda Allah bai yi ba. Ki cigaba da ta ya shi da addu'a, ba wai yana kyautata miki kawai ki ji daɗi ba, ki dinga dagewa da yi masa addu'a kin ji?." Ta ɗaga kai alamun to, ya share mata hawaye ya ce, "Ko ke fa. Yanzu kin gama gyara masa ɗakin?." "Na gama." "Me za ki yi yanzu?." "Zan je na wajan wata vendor ne, zan ga wasu samples ɗinta." "Meyasa baza ta kawo miki ba sai kin je?." "Ai akwai inda zan je." Ya ɗaga kai ya ce, "Mu je na raka ki." Bata ƙi ba suka sakko daga saman, ta shiga wajan Mamy shima bai bi ta kan matan gidan ba suka fita. _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ Nana Haleema. [7/23, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P79 Nana Haleema. _Don girman Allah ku shiga Youtube ki yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ •••••••••• Mama tana zaune a gaban Daada tana jira ta idar da sallah dan ta idar mata da abinda yake zuciyarta. Daada tana idarwa ta kalle ta ta ce, "Saddiƙa lafiya?." Ta yi murmushi ta ce, "Ga dambun nama." Daada ta karɓa ta ajjiye a gefe ta ce, "Na gode da hidima." Ta yi murmushi ta ce, "sai wata magana da nake tafe da ita, ban san ta ya za ki karɓe ta ba." Daada ta ce, "ina sauraren ki, ko ya take faɗa min kawai." Mama ta sauke numfashi ta ce, "Akan auren nan na Rehaan ne. Daman tambaya zan yi, in ana ɗaura auren a ina zai tare da matarsa?." Daada ta yi dariya ta ce, "Gidajen da Rehaan yake dasu har sai ance a ina zai zauna? Ko mata goma zai aura yana da gidan da ai ajjiye su." Baƙin ciki ya mamaye zuciyar Mama, amma bata nuna ba ta ce, "gaskiya ne. Amma ni a shawara ta mai zai hana bazai yi zamanasa a gida nan ba, ɓangarensa har mata huɗu zai ajjiye. Kaf gidan nan daga ɓangaren Abbansa sai ɓangarensa ne masu sama, kin ga akwai wajan ajjiye mata a nan." "Meye amfanin hakan? Yana da gidaje mai zai yi a nan?." "Amfanin hakan kin ga ba son auren nan yake yi ba, in ya tare a wani gidan Allah kaɗai yasan wulaƙancin da zai yiwa yarinyar nan. Ba a san yadda zasu dinga zama ba, kuma zai iya tsallake ta ya bar ƙasar babu wanda ya sani. Hakan kuma zai taɓa ƙimar ki da ƙimar gidan nan sosai, dan wulaƙanta mutum ba halinmu bane. Kuma ga maƙiyan da ya tara, in ya bar yarinyar nan ita kaɗai a waɗannan tanƙama tanƙaman gidan za a iya cutar da ita. In kuma tana gidan kin ga akwai idonmu, wani wulaƙancin na sa ma zai ragu, kuma ko da ya tafi ya barta muna nan tare da ita, balle ma wani abun in ya aikata za ki tsawatar masa." Daada ta yi murmushin jin daɗi ta ce, "wato a kaf gidan nan babu mai hankali kamar ki Saddiƙa, babu mai hangen nesa da sanin ya kamata sai ke ɗin kawai. Ai ko ni kin fini zurfin tunani." Ta yi dariya ta ce, "Wane ni Daada?." Daada ta yi dariyar jin daɗi ta ce, "na ji daɗin wannan shawarar ta ki, kuma da ita za a yi amafani. In na bari ya tafi da ita wani waje ai sai ya dinga cin zalinta, nan kuwa ko baya nan muna nan babu abinda zai same ta." "Abinda na gani kenan, kuma hankali kwance babu tunani mara kyau. Shiyasa na ce bara na zo na same ki, zuwa nan gaba in komai ya warware sai ya tare a inda yake so." Daada ta ce, "wannan shawara ta yi ɗari bisa ɗari. Haka za a yi ma babu makawa." Mama ta yi murmushi ta ce, "Bara na je Daada, sai anjima." "Babu damuwa, in da wata shawarar ina nan ina jiran ki." Ta amsa tana murmushi ta tafi. **** Islaha haka ta je ta samu Safeera ta dinga yi mata mita skan abinda Saheer ya yi mata Safeera ta yi dariya ta ce, "to ni da ki ke ta yi min mita ni ce Saheer ɗin?." Islaha cike da jin haushi ta ce, "Wallahi Hamma bai taɓa bani haushi kamar yau ba, wai bazai karɓi abinda bai san da kuɗin da aka siya ba. Ni yake faɗawa wannan maganar kai tsaye, yana nufin yana zargin a hanyar banza na samu kuɗin." "Na faɗa miki dole ya shiga ruɗani saboda abubuwan da suka faru." Ta ja tsaki ta ce, "Shi ya sani. Bazan sake saurarensa ba wallahi, in ya ga dama ya zarge ni ɗin sai me." Safeera bata ce mata komai ba ta yi dariya kawai, dan ta san zasu shirya ne. Kuma ita bata ga laifinsa ba, dole ya zargi wani abun a ransa, saboda abinda ta faɗa ita kanta sai da ta kai zucoya nesa sannan ta amince. •••••••• Motar su tana cikin tafiya a cikin daji da duhuwa, masu bacci suna bacci, masu chating suna yi, masu jin waƙa suna yi. Ƙarar babura da ihuun mutane ya saka kowa ya firgita ya miƙe, kafin wani lokaci babura sun kewaye motar. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Masu garkuwa da mutane ne!." Jin kalaman driver sai kowa ya ɗauki salati, wasu suka fashe da kuka saboda tsananin tashin hankali. Saheer yana zaune gabansa yana faɗuwa, ya kalli mutanen ya ga a ƙalla baburan zasu kai goma, kuma ko wanne mutum biyu ne a kai. Ya dinga salati a zuciyarsa, hankalinsa ya tashi sosai. Duk suka sauka daga kan baburan, dukkansu da ƙatuwar bindiga a hannunsu, sun yi carko carko a gaban motar suna kallonsu. Ɗaya daga cikinsu ne ya buɗe ƙofar driver, cikin muryar fulani amma da yaren hausa ya ce, "Malam Driver sakko." Driver jikinsa yana karkarwa ya sakko daga motar, suka buɗe bayan motar suka ce kowa ya sakko daga ciki. Duk sauka sakko suka kwanta, suka dinga binsu ɗaya bayan ɗaya suna kallo. Ɗaya daga cikin su ya ce, "Yellow a karɓi waya da kuɗi." Wanda aka kira da Yellow ɗin ya ci sunan nasa yellow, dan yana da haske sosai, gashi ɗan siriri mai jikin fulani, ya fara binsu ya ce, "Kawo waya da kuɗi." Hannun su yana rawa suke basu, har aka zo kan Saheer ya bayar. Yellow ya ce, "Magaji wannan matar ciki gare ta" ya faɗa tana nuna masa wata mata da bindiga, tana zaune tana kuka saɓaninsu da suke kwance. Magaji ya ƙaraso yana kallon yadda take kuka, ga cikinta nan ya fito sosai alamun ta kusa haihuwa. Ya kalle ta ya ce, "Ya sunan ki?." Muryarta tana rawa ta ce, "Magajiya." Duk sai suka saka dariya suna sowa. ya kalle ta ya ce, "ki ce sunan mu iri ɗaya ne. Kin ci albarkacin sunan ki, baza mu tafi dake ba, kuma baza mu kashe ki ba, zamu bar ki tafi. Tashi ki tafi." Jikinta rawa yake yi ta kasa miƙewa, ya ce, "ki tashi babu abinda za a yi miki." Ta miƙe tsaye, ya nuna mata hanya ya cr, "ki bi nan, ki ta gudu kar ki tsaya." Bata iya magana ba ta tafi da gudu ɗin kamar yadda ya ce, tana kuka sosai. A take aka ɗaure hannayensu Hamma ta baya, aka miƙar da kowa a cikinsu suna binsu da kallo. Yellow ya kalli wata babbar mace, a shekaru ta girma kuma tana da jiki sosai. Ya ce, "Magaji wannan fa kaya ce." Magaji ya kalle ta ya ga tabbas kaya ce, in aka ce za a yi tafiya mai nisa da ita wahala za a sha. Ya kalli Yellow ya ce, "Ka san yadda zaka yi da ita kawai." Yellow ya saita bindiga a kanta, ta ɗaga hannu sama ta zube guiwa a ƙasa ta ce, "Don Allah kar ka kashe ni, ina da ƴaƴan da suke tsananin buƙaata ta." Kafin ta sake magana bullet ya fasa kanta, a take ta zube a wajen matacciya. Matan da suke cikin su Hamma suka ƙwalla ihuu, cikin kiɗima da tashin hankali mai tsanani. _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭 Nana Haleema. [7/23, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P80 Nana Haleema. _Don girman Allah ku shiga Youtube kunyi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ •••••••••• Tsawa suka yi musu duk suka shiga hankalinsu suna kallonsu cikin tashin hankali. Yellow ya ce, "In ba ku yi shiru ba, kuma makomar ku kenan." Kowa ya yi tsitt gabansa yana faɗuwa, aka kaɗa su daji aka fara tafiya. Tun dare suke tafiya har gari ya yi haske, babu waya babu agogo balle su san ƙarfe nawa, haka suke tafiya cikin wani irin yanayi. Duk sun gaji, sun jigata amma tsoron faɗuwa suke yi saboda kar a kashe su. A haka suka iso sansanin su, zuwa lokacin gari ya fara haske sosai, aka nuna musu inda zasu zauna kowa ya zauna cike da gajiya. Saheer ya dinga kallon wajen, ganin mutane da yawa a zaune a filin Allah, sai wata bukka guda biyu daga gefe, sai au da suke da yawa a wajen kowa da bindiga. Ɗaya daga cikin matan da aka kamo ta ce, "fitsari na ke ji." Wanda suka taho tare ya ce, "ki yi a nan." Ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta yi ftsarin kamar yadda suka ce. Saheer salati kaɗai yake yi a zuciyar, ambaton Allah ya yi cikin neman mafita yana kallon mutanen. Dukkansu fuskarsu a rufe ta ke, sun rawani irin naɗin buzaye sun rufe har fuskarsu. Ɗaya ya dafa Saheer ya ce, "Kai bafulatani ne?." Saheer ya ɗaga kai ya ce, "Eh." "A wanne gari ka ke?." "Yola." Sai ya ɗago ya kalli yan uwansa ya ce, "Wannan bafulatani ne, yana jin yaren da muke magana dashi. Saheer dai kallonsu yake yi, ganinsu da manyan bindigu, ga over over a hannun ko wannensu, ga kayan harbe-harbe koda za a kawo musu hari ta sama. Ƙarar machine ya cika wajen gabaɗaya, duk ya ga sun miƙe sun nutsu cikin girmamawa. Su biyu ne akan machine ɗin, suka sauka daga machine suka saka musu kujera suka zauna. Ɗaya dinga binsu ɗaya bayan ɗaya da kallo, kafin ya kalle su ya ce, "Ka kawo tsohuwar ajiya." Ya kalli Magaji ya ce, "Mutum nawa aka samo jiya?." Magaji cikin girmamawa ya ce, "Su ashirin ne Arɗo." (Arɗo shugaba). Ya girgiza kai yana kallon kowa a cikinsu, ya ce, "kar a taɓa matan nan, kar yi musu komai, duk wanda na kama da akasin haka zai tauna gyaɗa." Duk sun fahimci me yake nufi da gyaɗa, a yaren masu garkuwa da mutane na wani ɓangare in suka ce gyaɗa suna nufin bullet kenan, yana nufin duk wanda ya lalata mace ɗaya a cikin matan sai ya harbe su. A lokacin aka kawo mace da namiji aka gurfanar a gabansa, ya kalle su ya kalli Arɗo ya ce, "kwance shi." Ya kwance namijin, ya kalle su yana girgiza kai ya ce, "Ku ƙi ku ba da lambar wayar ƴan uwan ku ko? Kun so ku mutu ne?." A hankali namijin ya ɗago ya kalle sa, wanda yake zaune a kusa dashi ya ce, "Wannan yaro ne ma sosai." Arɗo ya ce, "Sai taurin kai, kwanan su biyu amma sun ƙi ba da lambar waya, wai babar su bata da waya balle su bayar." "Wannan macen ƴar uwarsa ce." "Ƙanwarsa ce." Abokin Arɗo da suke kira da Black ya ce, "Ƴan mata ya sunan ki?." A hankali ta ɗago kai ta kalle su, a lokacin Saheer ya kalle ta yana jin tausayinta, ganinta yarinya ƙarama dan bata wuce shekara sha shida ba. Black ya ce, "Arɗo wannan ai kyakykyawa ce sosai, a bani ita mana." Arɗo ya yi dariya ya ce, "Babu hakan a shugabancina, kai k fi kowa sanin haka." "A bani auren ta, zan riƙe ta hannu biyu." Arɗo ya kalli ɗanuwanta ya ce, "Kai ka ji, Black yana son auren ƴar uwarka. Ya sunan ka ma?." Muryarsa tana rawa sosai ya ce, "Sudais." Black ya ce, "ita fa?." "Sudaisa." "Ku ƴan biyu ne?." Sudais ya ɗaga kai yana hawaye sosai, Black ya ce, "Ina son Sudaisa, za ka bani auren ta?." Sudais ku ka kawai yake yi, ya girgiza kai ya ce, "Ni bazan ba da auren....." kafin ya gama faɗa an buga masa kan bindiga, a take ya faɗi a wajen a sume. Black ya yi kam Magaji da masifa ya ce, "Gashi nan ka sumar dashi, aurena za a ɗaura yanzu fa." Magaji ya ce, "Tuba nake Black, na ji yana yi maka taurin kai." "Ka saka ya farfaɗo yanzu a ɗaura auren nan." Arɗo ya ce, "Ga wani a zaune, tun ɗazu yake kallon mu, ya baka auren ta mana" ya faɗa yana nuna Saheer da idanunsa yake wajen. Sudaisa kuka ta yi sosai, Black ya tsuguna a gabanta ya ce, "In na aure ki zan ɗauke ki daga nan, zan je na ba ki rayuwa mai kyau, za ki daina wannan wahalar da ki ke ciki." Ita dai kuka take yi sosai, ta ɗago ta kalli Saheer suka haɗa ido, sai ya ɗan zuba mata ido yana ganin kamar ya santa, amma sai ya ɗauke kansa daga kallon ta yana jin tausayinta sosai. Arɗo ya ce, "Black ka bari ya farfaɗo za a ɗaura auren, amma kafin nan sai an bani haƙƙina, dan bazan yi asarar mutane har biyu ba." Ya kalli Sudaisa ya ce, "Kafin ɗan uwan ki ya farfaɗo, ki zama matar black, za ki ba da lambar wayar ko ba za ki bayar ba?" Ya faɗa yana sakawa ana saita kanta da bindiga. Sudaisa muryar ta tana rawa ta ce, "Ba mu da kowa, Maman mu kuma bata da waya." Arɗo ya haɗe rai ya ce, "in na kuma tambayar ki ki ka maimaita abinda ki ka faɗa sai na kashe ki." Ita dai kuka take yi, a lokacin aka farfaɗo da Sudais ya ce, "za ku ba da lambar ko......" Over over jikin Arɗo ta fara ƙara alamun ana magana, ya ɗauka yana magana, sai kuma ya miƙe da hanzari suka hau machine suka bar dajin. Saheer kallon yaran yake yi cikin tsananin tausayi, ya ji Sudais yana cewa, "gwara su kashe mu kawai, bamu da wanda zamu ba da lamba balle a kirasa, gwara mu mutu." Kuka take yi sosai ta ce, "Ni ban son auren Hamma, kar ka bari a yi auren." Ya juya ya kalli Saheer da yake kusa dasu ya ce, "Sannu." Saheer ya ɗaga musu kai, Sudais ya ce, "yau ku ka zo wajen nan, ba ku san me yake faruwa ba, mu kwanann mu uku. Sun takurawa ƙanwata, ba dan an hana su yi mata komai ba da yanzu sun yi mata fyaɗe. Ka ta ya ni kula da ita don Allah." Kuka suke yi dukkansu, Saheer tausayinsu ya kama su sosai, ya lumshe ido kawai bai ce komai ba. A lokacin aka ɗauke sunaka mayar dasu inda suke, aka bar su Saheer ko ruwa ba a basu ba, yana kallon mutum biyu sun mutu saboda rashin ruwa, an ɗauke su an cilla a wani ƙaton ramin da suke cilla gawa. A kansu rana ta buɗe ƙwal, babu wanda ya yi ƙoƙarin ɗauke su, a lokacin Arɗo ya dawo, yana sauka daga machine ya ce, "ana bawa ajiyata abinci kuwa?." Ɗaya daga ciki ya ce, "Arɗo baka ce a bayar ba." Ya zauna yana kaɗa ƙafa ya ce, "Na ce yanzu, a saka mata su shiga daji a samo zolage su dafa a ci. A kawo mana waya." Wasu suka ɗauki mata uku a cikin matan da suke wajen, dan su ba a ɗaure su aka nufi daji dasu dan su nemo zogale. Wani kuma ya bashi waya ya kalli su Saheer ya ce, "Ban ɗauko ku dan na ajjiye ku ba, ku jarina ne, dole na killace ku yadda ya kamata. Ko wannen ku zai bani lambar wayar gidansu, bazan ɗauki lokaci na bar ku a nan ina baku abinci ba, ƴan uwanku su kawo kuɗi su ɗauke ku." Ɗaya bayan ɗaya aka dinga ba da lamba ana kiran wayar yan uwa, Saheer kallonsu yake yi yana mamakin wannan lamari. Wai ƴan ta'adda ne suke da wayoyi da makamai haka, kuma wai a ce an kasa kama su. Ya kalli Saheer ya ce, "Bafulatani bani lambar ƴan gidanku." Saheer ya ba shi lambar Sadik, dan bazai ba da lambar Baba aka kira wayar Sadik. ••••••••• Washe gari da safe da wuri Baffa ya fita basu haɗu da Islaha ba. Ta fito daga gida kenan ta ga Sadik, suka gaisa ya ce, "kun yi waya da Saheer kuwa?." Ta girgiza kai alamun a'a ta ce, "ni ban san ya yi tafiyar bama sai da na dawo daga aiki, ba mu yi magana ba gaskiya." Ya sauke nungashi ya ce, "gabaɗaya ba a samunsa a waya wallahi, kuma ba haka ya saba in ya yi tafiya ba." Ta taɓe baki cikin ko in kula, dan haushinsa take ji sosai ta ce, "zai kira ka ɗin ne, sauri nake zan tafi aiki" ta faɗa tana barin wajan ya bita da kallo cike da mamaki, ganin ana maganar ba a samun Saheer a waya tana nuna ko a jikinta. Bata tashi dawowa daga aiki ba sai dare, tana shiga ta tarar da mutanen gidan an yi cirko cirko, ga Baffa, ga Sadik a tsaye, kana kallonsu za ka ga tashin hankali a kwance a fuskarsu. Islaha gabanta ya faɗi sosai, ta bi su da kallo kafin ta ce, "Hamma Sadik lafiya?." Baffa ya sauke numfashi cikin wani irin yanayi ya ce, "masu garkuwa da mutane ne suka kama Saheer a hanyarsa ta tafiya Niger!.... _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ Nana Haleema. [7/24, 9:52 AM] KRBBK: RDB2P81 Nana Haleema. _Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_ Islaha ta ji kamar an soka mata kibiya a ƙirjinta, ta tsaya cak ta kasa ƙarasawa tana kallonsu cikin tashin hankali.  Sai kuma ta zabura ta shiga ciki ta ce, "Ban gane an yi garkuwa dashi ba, waye ya yi garkuwa dashi ɗin?." Adda ta riƙo hannunta ta ce, "Ki nutsu Islaha." Ta kalli Adda ta ce, "waye ya yi garkuwa dashi?." Baffa ya ce, "Islaha ki nutsu, za a faɗa miki duk abinda ya faru." Ta ce, "Baffa ka faɗa min, don Allah." Baffa ya ce, "ɗazu suka kira Sadik akan Saheer yana hannunsu, zasu sake kira a jira su." Islaha ta ja numfashi mai tsaho ta ce, "innallillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Ta faɗa hawaye ya sakkowa daga idonta. Sai kuma ta juya ta kalli Sadik ta ce, "kuma an tabbatar masu garkuwan ne? Kar a sake maimaita abinda aka yi lokacin da na ɓata." A sanyaye Sadik ya ce, "da gaske su ne Islaha." Ta zauna a kan kujera ta dafe kai tana kuka mai taɓa zuciya, hannunta yana rawa saboda kuka ta rasa abinda zata ce. Baffa ya ce, "mu je a sanar da ƴan sanda." Sadik ya ce, "Baffa ka share batun hukuma kawai, a bari aji abinda zasu ce a biya kuɗi a karɓo shi. Haka aka yi da aka sace ƙanwar abokina, ba a iya karɓota ba sai da aka biya wannan kuɗin. Babu abinda hukuma suke yi a wannan gaɓar, in dai sun faɗi kuɗi sai an bayar." Baffa ya ce, "Duk da haka Sadik, gwara hukuma ta shiga maganar nan." Sadik ya ce, "ban ƙi ba Baffa, amma abinda suka faɗa shi ya kamata mu yi." Mama da take kukan rashin Saheer ta ce, "kar a faɗa musu don Allah, kar su kashe min Saheer." Sai abin ya sake karyawa Islaha zuciya, ta yi kuka mai tsuma zuciya, tana ji kamar ta tashi ta yi tsuntuswa ta ganta a gaban Hamma, ta karɓosa ita ta bada kanta a kamata a ɗaure. Baffa ya yi dauriya ya ce,  "ku daina wannan koke koken, ku je a cigaba da addu'a kawai. Allah ya shiga lamarin mu gabaɗaya." Sadik ne kaɗai ya amsa da amin, su basa cikin nutsuwarsu gabaɗaya.. Adda ta riƙe hannun Islaha suka koma falon Mama, dan yadda take jiri ita kaɗai zata iya faɗuwa. Ita kaɗai ta shiga ɗaki ta zauna tana ta kuka babu ƙaƙƙautawa, abinda yake ɗaga mata hankali bai wuce in ta tuna yadda suka rabu ba, in ta tuna hakan sai hawaye ya sake sakko mata, cikin wani irin yanayin da bata taɓa jin irinsa ba.  A lokacin Safeera ta shigo a gigice, Islaha ta miƙe tsaye ta rungume ta sake fashewa da kuka tana faɗin, "Hamma..an kama Hamma Safeera....Zasu kashe min shi, zasu kashe min Hamma!.." Ta faɗa muryar ta tana rawa sosai. Safeera cikin rauni ta ce, "yanzu Baffa ya yi sallama da Baba yana faɗa masa, shine na zo wajen ki." Islaha kuka kawai take yi a jikin Safeera, tana ganin abin kamar a mafarki, ganin abin take kamar wasa wai an yi garkuwa da Hamma, garkuwa ba irin wacce aka yi da ita ba, garkuwa ta gaske wacce za a iya kashe shi. Safeera ta ce, "ki yi haƙuri, addu'a yake buƙata ba kuka ba, don Allah ki kwantar da hankalin ki, Allah zai kuɓutar dashi. In ba ki daina kuka nan ba za ki samu attack, kuma kukan ba shine maganin damuwar mu ba." Ita dai bata daina kuka ba, Safeera ta zanar da ita tana rarrashi. Islaha cikin kuka ta riƙe hannun Safeera ta ce, "In na tuna yadda muka rabu dashi sai na ji wani iri, sai na ji ban kyauta masa ba." "Haƙuri za ki yi, ki ta yi masa addu'a, ita yake da buƙata yanzu ba wannan kukan ba. Kar ki je ki samu attack a wannan koke-koken, ki yi haƙuri." "Masu garkuwa da mutane fa Safeera, ƴan bindiga ne suka ɗauke Hamma." "Na sani, ki yi haƙuri." Safeera ta dinga rarrashinta har ta samu ta ɗan haƙura, bata koma gida ba ta zauna a tare da ita tana kwantar mata da hankali. Islaha ta kalli Safeera cikin muryarta da ta dashe saboda kuka ta ce, "Ashe haka ku ka ji lokacin da na ɓace? Ashe haka ku ka ji lokacin da aka sace ni?. Haka wancan banzan ya dasawa mu ku ciwo, kuma ya saka ku kuka?. Me zai saka na so wannan mutumin, har abada wallahi." Safeera dai bata ce mata komai ba, ta dinga rarrashinta har ta nutsu sannan ta tafi. Ranar gidan haka ya rayu shiru, kowa ya nutsu ya koma ga Allah ana zaman jiran tsammani, gabaɗaya kowa hankalinsa baya jikinsa, ana tunanin ta inda lamari zai sake ɓullowa. Islaha bata iya baccin kirki ba, da ta yi zata farka ta yi kuka ta koma bacci. Ƙarfe uku ta tashi tana sallah tana roƙon Allah akan ya bayyana mata Hammanta, ta kuɓutar dashi faga hannunsu, ya kare shi daga zaluncinsu. Da safe da ta tashi haka ta tashi da fuska a kumbure saboda kuka, ko shirin zuwa aiki bata yi ba, saboda bata da wannan nutsuwar a lokacin. Ta shiga wajan Baffa dan su gaisa, ta same shi shida Sadik da Kawu da Baba a zaune ana ta tattaunawa akan batun. Ta ƙarasa ta gaishe su, kafin su amsa ta ce, "har yanzu shiru?." Baffa ya kalle ta cikin tausayin yanayinta ya ce, "har yanzu shiru Islaha, muna ta addu'a a kai." Ta sauke numfashi ta ce, "Allah ya bayyana mana shi." Suka amsa da amin. Baffa ya ce, "akwai maganar da nake so zamu yi dake, shigowar wannan lamari ne ya saka ni na manta jiya, amma in kin dawo daga wajen aiki ki zo ki same ni." "Ai bazan je aiki ba Baffa, bazan iya ba" tana faɗa hawaye yana sakko mata. Ya ɗaga kai ya ce, "shikenan, ki je ki zauna zamu yi maganar in anjima. Ki daina kuka, Allah yana sane da komai, shi ya ƙaddara mana, kuma shi zai ba mu mafita." Ta ɗaga kai ta miƙe ta fita ta bar suna cigaba da tattaunawa. A harabar gidan ta zauna a inda suka saba zama ita da Hamma. Sadik yana fitowa ta miƙe tsaye tana kallonsa har ya ƙaraso sannan ta ce, "Hamma Sadik da gaske sace shi aka yi?." Ya bita da kallo ganin duk ta firgice, sai ya tausasa murya ya ce, "da gaske ne Islaha." "Kuma zasu sake shi?." "Za su sake shi in sun faɗi kuɗi an biya in sha Allah." "Yaushe zasu faɗa?." Ya sauke numfashi ya ce, "ko yaushe zasu iya yin waya." Ta ɗaga kai ta ce, "an yi magana da ƴan sandan?." Ya ɗaga mata kai ya ce, "An yi Islaha." Ta ce, "shikenan Hamma Sadik, amma don Allah kome yake faruwa ka faɗa min, ka ji?." Sadik ya bita da kallo cikin tausayin yanayinta, magana take yi masa amma kuka take yi, gabaɗaya ta canja daga jiya zuwa yau, ta firgice lokaci ɗaya kamar ba ita ba. Tunda ta bar ƙasar yake jin haushinta, amma yanzu sai ta bashi tausayi saboda yadda ta koma wani iri, har rama ta yi akan daga daren jiya zuwa safiya, har ta so ta fi Mama shiga damuwa akan lamarin, dan tunda ya zo gidan ko Mama bai gani ba balle a tambayesa ya ake ciki. Ya ce, "Zan faɗa miki in sha Allah, ki je ki ci abinci." "Bazan iya cin komai ba." "In Hamma ya ji bazai ji daɗi ba." Faɗar hakan da ya yi sai hawayenta ya ƙaru ta ce, "ni bazan ci komai ba sai ya dawo." Ya murmusa bai ce komai ba, dan bazai iya da rigimarta ba, shi yana da saurin hawa yanzu sai ya rufeta da faɗa, Saheer ɗin ne daidai ita. Ya fita daga gidan ta bishi da kallo, ta koma ta zauna a wajan cikin tunanin da bata san adadin lokacin da ta ɗauka a wajan a zaune ba, yana wajan har sai da rana ta fito sannan ta koma ciki. ••••••• Su Saheer haka suka buɗe ido a filin Allah, gwara matan ya ga an tattare su an saka su a wata ƙaramar bukka, amma su a wajen suka kwana bayan an ɗaure musu hannu da ƙafa saboda kar su gudu. Suna jere shi da Sudais, dan yaron tausayi yake bashi sosai, bashi da wata magana sai ta ƙanwarsa, hirarsa akan ƙanwarsa ce, indai zai buɗe baki ya yiwa Saheer magana akan ƙanwarsa ne. Gabaɗaya wari Sudais yake yi, dan babu batun zuwa yin fitsari sai dai ka yi a wajen, kashi ne in sun ga dama za su kwance ka a kara ka da bindiga ka je ka yi ka dawo. Suna zane a wannan yanayi na rashin sanin me anjima zata haifar musu. A lokacin Magaji ya zo yana kwance musu hannaye saboda zasu ci abinci. Sudaisa ta kawo abinci a ganye ta ajjiye a gabansu, fuskar ta duk ta tashi, ga cizon sauro da ƙananun ƙwaruka. Saheer ya kalle ta ya ga hawaye kawai take yi, tana ajjiye musu abincin ta koma. Bayan sun bar wajen Sudais ya ce, "Sune suke dafa abinci, ba ka ji jiya Arɗo ya ce a kai su su nemo zogale ba?." "Na ji." "To ba a tsaurarawa mata tsaro sosai, an fi tsaurarawa maza saboda kar su gudu." Magaji ya dawo ya kalle su ya ce, "Akwai wanda zai shiga banɗaki? In lokacin shiga banɗaki ya wuce babu wanda zamu sake kaiwa." Kowa ya ɗaga hannu a wajen, ɗaya bayan ɗaya aka dinga raka su da bindiga ana tsayawa su gama abinda zasu yi a dawo dasu. Saheer ya kalli abincin ya ga shinkafa ce fata tas, gabaɗaya bata fi spoon uku ba, babu komai a kanta. Bai ƙi ci ba, dan in bai ci ba bai san zai ci ba nan gaba, aka basu ruwa suka sha. A wajen suka yi taimama suka yi salla kafin a sake ƙulle musu hannu. Ihuu suka ji daga wajen matan, take Sudais ya zabura yana kallon Saheer cikin tashin hankali, dan ya san ihun ƴar uwarsa ne. Suna kallon su sun nufi wajen suna tambayar lafiya. Ita kuwa Sudaisa ta fito tana tsalle tana kiran maciji. Wani daga cikinsu saboda takaici bai san ya maka mata kan bindiga ba, goshinta ya fashe, jiri ya kwashe ta ta faɗi a wajen. Babu zato babu tsammani suka ji sautin harsashi kawai, take wanda ya buga mata bindiga ya faɗi a wajen a mace. Sudaisa saboda gigicewa ta yi baya ta suma. Nana Haleema. [7/24, 9:52 AM] KRBBK: RDB2P82 Nana Haleema. A take suka yi cincirindo akansa, aka kalli wanda ya yi harbi suka yi kansa da faɗa da bala'i kamar zasu harbe shi. Ya nusa Sudaisa ya ce, "Itace wacce black zai aura, kuma ya faɗa min duk wanda ya taɓa ta na ga bayansa." Hayaniya ta kaure a tsakaninsu ana shirin fara harbe-harbe tsakaninsu. A lokacin Arɗo ya ƙaraso ya ce, "Faɗan me ake yi?." Aka nunawa Arɗo abinda ya faru, ya kalli sa ya kalli Sudaisa ya ce, "Amanar Black ce, amanar Black amanata ce, babu wanda zai taɓata ya kwana lafiya. Ku ɗauke maji daɗi ku binne, sai mun taho." A ɗauke maji daɗi aka tafi da gawarsa daga wajen. Arɗo ya ce, "Magaji a farfaɗo da yarinyar nan." Magaji ya ce, "An gama Arɗo." A lokacin aka kawo wata mace da take a cikinsu, Arɗo ya kalle ta ya ce, "Wannan fa?." "Arɗo ta yi yunƙurin guduwa daga nan." Ya kalle ta ya ce, "a hukunta ta." Ya damƙi gashin kanta yana janta a cikin dutsu, ya kai ta gaban bishiya ya ɗaure ta da igiya mai ƙarfi, suka cire mata riga, suna zuba mata ruwan sanyi suna yi mata duka da bilalai kala-kala. A haka suka kashe ta, suka jawo gawar ta aka cillar a gaban Arɗo. Arɗo ya kalli gawar ya ce, "Ban ce kashe ta ba, meyasa za ku kashe ta? Kun san asarar nawa ku ka yi min?." Duk suka yi shiru ya yi tsaki ya ce, "Kar wanda ya sake irin wanann shirmen, neman kuɗi nake yi, ba zaman banza nake yi ba, ita da ku ka kashe kamar jarina ce. Duk wanda yake wajenan jarina ne, zan iya kashe ku su na bar su da rai.” Suka haɗa baki suka ce, "Tuba mu ke." Ya ba da umarnin a ɗauke ta suka saka ta a ramin da suke cilla gawa. Sudaisa kuwa ta farfaɗo, amma zazaaɓi ya rufe ta gabaɗaya ga jini duk ya ɓata mata jikinta. Babu wanda ya damu da jinin jikinta ko rashin lafiyarta, harkokinsu kawai suke yi, motsi kaɗan harbi kawai suke yi, har gwara mata suna raga musu, amma baza taɓa ɗagawa maza ƙafa. A lokacin Black ya dawo dajin, har lokacin Sudaisa tana inda take a ajjiye, tunda ta farfaɗo ba a takura mata sai ta tashi daga wajen ba. Black ya kalli Arɗo da ya nannaɗe dubu ɗaya, ya kunna mata wuta yana sha kamar taba. Ya ce, "a ɗaura auren nan na ɗauke ta, zamu fanshe. Zan aiko maka da wata guɗa ɗaya, sai a yi canje ka bani ita na baka ita." Arɗo ya kalle sa ya ce, “Ni bana son canje nan, kar ka kawo min wacce iyayenta basa sonta, su kasa ba da kuɗi su karɓe ta.” “Zan samo maka mai ƙwari, bazan ba ka kunya ba. Yarinyar nan ta shiga raina, ina buƙatar ta zama matata yau ɗin nan.” Arɗo ya bada damar a matso da Sudaisa aka matso da ita jikinta yana rawa sosai, ga ciwo ga fargaba da tsoro. Ya zaune a kusa da su Sudais, a nan yake zaka kujera ya zauna in ya zo dajin. Ya kalli Sudais ya ce, "Nawa za a baka sadakinta?." Sudais kuka kawai yake yi bai ce komai ba, dan bai san abinda zai ce ba. Black ya ɗauko dubu ashirin ya bawa Arɗo ya ce, "Ga sadaki nan, a ɗaura a bani matata" ya faɗa yana murmushi yana kallon Sudaisa. Arɗo ya girgiza kai ya ce, “Lallai ka shirya, ya kamata a yi gayya, auren ka ya kasance kowa ya sani.” Black ya ce, “A gayyato mazaje.” “Dole.” Arɗo ya ɗauki over over irin ta ƴan sanda ya kunna ya ce, "Kuna ina mazaje, ku ƙaraso Black zai angwance." Cikin lokaci kaɗan ƙarar machina ta cika wajen, suna ihuu aka ɗaura auren Sudaisa da Black, aka bawa Sudais sadakin ta ya karɓa dan babu damar musu. Black ya bita da kallo yana wani murmushi ya ce, "in anjima zan dawo na tafi da ita, a daina takura mata...." Sai ya juya ya kalli Magaji ya ce, "Babu sani babu sabo, duk wanda ya taɓa min mata sai ya baƙunci lahira, wallahi babu wanda zan ɗagawa ƙafa." Suka amsa dukkansu, ya kai hannunsa ya shafi kumatunta, suka sake yin ihu suna harba bindinga sama, ya hau machine ya tafi. Arɗo ya kalle ta yana murmushi, dan shi fuskarsa a buɗe take ko yaushe ya ce, "Yanzu kin zama sirikar mu kuma amaryar mu, za a kawo miki abinci mai kyau ki ci, har ki ragewa yayan ki." Ita dai bata ce komai ba kanta yana ƙasa ta gaji da yin kuka. Bayan Arɗo ya tashi ba a takurawa Sudaisa sai ta bar wajen ba, dan tana da babban matsayi babu mai takura mata. Sudais ya ce, "Yanzu baza su dinga takura miki ba, in kin samu dama ki gudu kafin wancan ya dawo ya tafi dake, kar ki yarda a tafi dake wani waje, ki gudu." Ita dai bata ce komai ba, tana zaune wajen kawai, dsn baza ta iya guduwa ta bar shi ba, sai a kashe su gabaɗaya. Ganin basu hanata zama a cikinsu Sudais ba sai ta yi zamanta a cikin mazan, tana kusa da Sudais da Saheer da har lokacin bata san sunansa ba. Ta kalle sa ta ce, "Ya sunan ka?." Ya ɗan lumshe ido saboda ciwon kai ya ce, "Saheer." Ta ɗan murmusa bata ce komai ba, a loakcin aka kawo mata gurasa da nama da ruwan roba. Yellow ya miƙo mata ya ce, “Ga shi.” Ta miƙa hannu ta karɓa, bai takura sai ta bar wajen da take zaune ba ya juya ya tafi. Sudaisa ta buɗe ta kalli su Saheer ta ce, "Hamma Saheer ku ci." Ya girgiza kai kawai bai ce komai ba ta fara ci. Sudais ya kalli Saheer ya ce, "Hamma Saheer ko da zasu kashe ni ka kula min da ita, na baka amanar ta." Sudaisa sai ta fara kuka, sai Sudais ya yi mata shiru kawai bai ce komai ba. Wani wanda yake kusa da Saheer ya ce, “Haka yaron nan yake, duk wanda ya zauna a kusa dashi yana bashi amanar ƙanwarsa, sai ya ce ko da zai mutu ka riƙe masa ƙanwarsa dakyau. Lamarin yaron abin tausayi, yana ƙaunar ƙanwarsa sosai.” Saheer ya juya yana kallon Sudais cikin tsananin tausayinsu shi da ƴar uwarsa, dan sun fi kowa ƙanƙanta a cikin mutanen da suke wajen. Sudaisa sai dare sannan ta bar cikinsu ta koma wajen mata, ko sau nawa za a ga tana kai kawo babu mai yi mata magana balle tsawa, dan tana da matsayin da dole kowa ya girmamata. Maganar Sudais take tunawa da yace ta gudu, amma baza ta iya guduwa ta bar shi ba, shiyasa ta haƙura da tsaf zata iya guduwa tunda babu mai takura mata. •••••••• Washe Islaha gari ta shiga wajan Baffa kamar yadda ya ce ta je yana neman ta, tana shiga ta same shi shi kaɗai a zaune ya yi shiru yana tunanin Saheer. Islaha ta zauna ta ce, "Gani Baffa." Ya yi murmushin yaƙe, dan ba ya son saka ta a damuwa ya ce, “ba ki daina kukan ba ko?." Ta ɗan yi murmushi ta ce, "na daina Baffa." "Yauwa gwara ki daina, ki cigaba da ta ya shi da addu'a." Ta ɗaga kai bata ce komai ba. Baffa ya ce, "Islaha shekaran jiya an zo min wata magana mai girma a kan ki, rashin nutsuwa ne ya saka ban same ki da batun ba. Yanzu ma ina yi miki maganar ne dan babu wanda ya wuce ƙaddara, dan an sace Saheer ba hakan ne zai hana yuwar wani abun a rayuwar ki ba." Ta yi shiru tana saurarensa bata ce komai ba. Baffa ya ce, "An zo min da wata magana mai girma da kuma alkhairi, kuma ni na amince har cikin raina, ina so na ji ra'ayin ki daga ɓangaren ki ba. Islaha bana son yi miki katsalandan a rayuwar ki, shiyasa nake ɗan ja baya ina tambayar ki shawara akan rayuwarki ta yau da ta gobe." Baffa ya cigaba ya ce, "Kin san Alhaji AbdulAziz Yola?." Ta ɗan ɗaga kai alamun eh, a ranta tana ayyana ta ya zan ƙi sanin sunan da yake rubuce a gaban sunan maƙiyinta?. Baffa ya ce, "za ki iya tuna wata tsohuwa da ki ka taimaka a kan titi, har ki ka kaita gida a napep?." Ta ɗaga kai bata kalli Baffa ba ta ce, "Na tuna Baffa." Baffa ya ce, "Yauwa. To itace mahaifiyar AbdulAziz Yola." Baffa ya cigaba ya ce, "Ya turo an same ni akan yana nemawa ɗansa auren ki nan da kwanaki goma masu zuwa, kuma ni na ba su ke!." Da hanzari ta ɗago ta kalli Baffa idanunta a waje, ta kasa cewa komai sai kallonasa da take yi tana mamakin furucin Baffa mai kama da labari ko tatsuniya. Baffa ya ce, "na san za ki yi tunanin ka basu ni kuma Baffa, to Saheer fa, bayan kai ka ke cewa za ka aura min Saheer a kwanakin nan, me ya kawo maganar wani?....." ya faɗa yana kallon ta dan ya san abinda yake ranta kenan. Islaha bata ce komai ba, dan ya riga ya karanta abinda yake zuciyar ta, sai ta sunkuyar da kai ƙasa tana jira ta ji dalilin Baffa akan abinda ya faɗa. Baffa ya ce, "Islaha na zaɓi na ajiiye batun auren ki da Saheer a gefe saboda wani dalili da ni kaɗai na san meye, ba dan saboda gidan AbdulAziz Yola suna da kuɗi, Allah ya sani ko basu zo nemawa ɗansu auren ki ba, ban yi niyar aura miki Saheer ba. Ranar da na tambaye ki ki ka ce kin amince za ki aure sa, a ranar da gaske nake zan aura miki Saheer, amma daga baya na canja shawara, saboda na ga kwata-kwata Saheer bai dace da ke ba. Ni ne uba a gare ki, ni nake da haƙƙin zaɓa miki mijin da nake ganin ya dace rayuwarki, shiyasa na ajjiye batun Saheer har abada, a gefe na jawo wani daban." Ita dai ta kasa magana ta zubawa Baffa ido, tana jin abin kamar a mafarki. Sai maimaita an ajjiye maganar Saheer a gefe kawai take yi a ranta, ga tashin hankalin da take ciki, ga wata magana da ta kasa gane mata gabaɗaya. Ganin Baffa yana kallonta sai ta sauke ido ƙasa, Baffa ya ce, "na yi hakan dan cigaban rayuwarki da samun rayuwa mai inganci, kuma kowa yana son cigaba a rayuwarsa, za ki so ki auri wanda ya fi Saheer wani abu a duniya." "A'a Baffa, ni bana son komai daga hannun kowa, kuɗi ko mulki basa gabana, ko shi wanda ka ke faɗa ɗin bazan iya zaɓarsa na bar Hamma ba." Baffa ya murmusa ya ce, "a yanzu ba za ki gane abinda nake nufi ba Islaha, ba za ki fahimci abinda nake gujewa rayuwar ki ba. Amma indai kin ɗauke ni a matsayin uba, kin yarda bazan cutar dake ba, kin yarda bazan kai ki inda za ki sha wahala ba, kin yarda bazan hana ki auren Saheer saboda son zuciya ba, to ki kalli maganar da na kawo miki da zuciya ɗaya, kar ki kalle ta ta fuskar kuɗi ko na zaɓi wanda ya fi kuɗi akan ɗana. Duk wanda zai so auren ki da Saheer wallahil azim a bayana yake, ko ke da kan ki bana tunanin kina so ki aure shi kamar yadda nake so ki aure shi. Tunda ki ka ga na ja baya, ki amince da abinda nake faɗa miki kawai." Ita dai bata san me zata ce ba, ta yi shiru kawai tana tunani dan ba wani jin kalaman Baffa take yi ba, tana cikin tashin hankalin rasa Hamma ana yi mata wani abu na daban. Baffa ya ce, "Kina jina?." Ta ɗaga kai ta kalle sa ta ce, "Wallahi Baffa bana fahimtar komai, ni tunanin Hamma kawai nake yi." Ya yi murmushi yana kallon ta ya ce, "Tashi ki je Islaha." Ta miƙe kamar jira take yi, da gaske bata fahimtar abinda Baffa yake faɗa. Mama duk ta ji abinda suke faɗa ta yi shiru tana tunanin wannan lamari cike da tashin hankali. Da hanzari ta koma ɓangarenta ta tarar da Karima da Hanan a zaune. Nana Haleema. [7/24, 9:52 AM] KRBBK: RDB2P83 Nana Haleema. Mama tana shiga suka bi ta da kallo har ta samu waje ta zauna sannan Hajiya Karima ta ce, "Kun yi magana kuwa?." Mama cikin wani irin yanayi ta ce, "Waye ma Alhaji AbdulAziz Yola?." Hanan ta yi caraf ta ce, "Shine mahaifin Rehaan Yola." Ta zaro ido cikin bugawar ƙirji da tashin hankali ta ce, "kan bala'i! Kun san me na jiyo a falon mai gidan nan?." Hajiya Karima cike da zumuɗi ta ce, "Faɗi muna jin ki." Mama ta ce, "Magana na ji ana yi akan ya turo a nemawa ɗansa auren Islaha." A tare suka zaro ido waje Hanan ta ce, "Ɗansa fa! Wanne daga cikin su?." Karima ta ce, "Ke Zulaiga bana son ruɗewa, ƴaƴansa fa ance kaf sun yi aure, kuma tsakani da Allah me za su yi da Islaha? Su da suke auren ƴaƴan masu kuɗi me zasu yi da tashin gidan marayu? Ai sun fi ƙarfinta Islaha, mai gadin gidan ma ya fi ƙarfinta balle kuma ɗam gidan da kansa, anya kin ji da kyau?." Mama cikin tabbatarwa ta ce, "Wallahi da gaske nake. Har Baffa ya amince da batun auren, itama yana saka mata ra'ayin ta amince ta bar Saheer." "Danƙari!." Mama ta gyara zama cikin baƙin ciki ta girgiza kai ta ce, "aiki ja Karima, na hana auren ta da Saheer kuma ta auri wanda ya fi Saheer? Ina wallahi bazai yu ba, dole na san abinda zan yi, AbdulAziz Yola fa." Hanan ta ce, "Amma kuma akwai wani mahaukaci a gidan, shima ɗansa, kuma an ce ya girma sosai ana nema masa matar aure, amma yana da taɓin hankali. An ce in haukan ya tashi sai ya yiwa kowa duka, har mai aikin gidan ya taɓa kashewa kuma ya kashe banza. Ina jin shi ake so a aura mata." Mama ta kalli Hanan ta ce, "Yana da ɗa na cikinsa wanda yake da taɓin hankali daman?." Karima cikin tabbatarwa ta ce, "yana dashi, na taɓa ganinsa. Ya girma sosai, dan zai girmi Saheer amma babu hankali sam." Sai kuma Karima ta kuma cewa, "Irinsa ne daidai da islahan ai, irin wanda zai kashe ta ya kashe banza shine daidai ita." Mama ta kalli Karima ta ce, "bazai yu ba, in ta auri ɗan gidan dole za a ce matar ɗan uwan Rehaan Yola ce." "Amma kuma matar mahaukaci ba.... Islaha bazata taɓa samun kwanciyar hankalin aure ba, kullum cikin fargaba da tunani take, kuɗin mahaifinsa bazai amfane ta da komai ba sai danasani. Kin ga kin samu hanyar kuɓutar da Saheer daga auren ta cikin sauƙi. Kar ki manta, in ya kashe ta ya kashe banza har lahira." Mama ta yi shiru ta kalli Karima ta ce, "ni ban damu da wanda zata aura ba, ko waye ta aura ban da ɗana. Kawai wanann ne na ji ya yi girma da yawa, ta wuce class ɗin Saheer fa." Karima ta ja tsaki ta ce, "To wannan ɗin ya kai Saheer hankali ne? Ana faɗa miki mahaukaci ne tuburan kina kawo wata magana. In za ki amince da auren nan ki amince kawai, ta je can ta ƙarata, meye amfanin kuɗi babu farin ciki?." Mama ta sauke numfashi cikin jin daɗi ta ce, "Ni dama zai kashe ɗin ai da zan so hakan, ɗana ne wallahi baza ta aure shi ba, akan ta aure shi zan iya zama ajalinta. Ta je ta auri duk wanda zata aura amma ban da ɗana, dan nasan Alhaji AbdukAziz bazai bawa ɗansa mai hankali auren ta ba." Hanan ta ce, "kin ga matan da ƴan gidan suke aure kuwa? Kyawawa, farare tass, kuma ƴaƴam masu kuɗi, dan har da wanda yake auren yar gwamna. To ban da abin ki Mama waye zai ɗauki Islaha in ba mahaukacin ba?." Karima ta ce, "Bar Maman nan ta ki, ko kuma tana so ta ce Rehaan ɗin ne zai aure ta?.” Hanan ta ce, “Bar faɗa, ai ko a mafarki bazai taɓa faruwa ba balle a zahiri. Wai! Ina ita ina ganin Rehana balle aurensa?. Ban ƙi ba ta zo a wankewa matarsa toilet.” Hajiya Karima ta yi dariya ta ce, “Ba ki da kirki Hanan. Amma a wajea mai wankin toilet ɗin ma matsayi ne, ta ƙare a a matar mahaukacin ya fi riba.” “Wallahi ya fi. Ban da abin Mama tunda har aka zo neman aurenta ai kin san ba abin kirki bane, basai an faɗa ba kowa ya san mahaukacin zata aura.” “Maman ta ki ma na ga ta ɗau haske." Suka yi dariya suka tafa. Hanan ta sake yin dariyar mugunta ta ce, "duk wannan iyayin a matar mahaukaci zata ƙare, duk wanann gashin har baya, da wannan idanun, da shagwaɓa duk na mahaukaci ne." Karima ta ce, "ta yi masa shagwaɓa ya ci kutmar ubanta, ya kashe ta ya kashe banza, ta mutu tana amsa sunan matar mahaukaci." Suka ƙyalƙyale da dariya a tare suna tafawa. Baffa yana tsaye ya zo kiran Mama akan maganar Saheer ya jin duk abinda suke faɗa, ya sauke numfashi yana girgiza kai yana mamakin wannan ƙiyaya da suke yiwa Islaha. Ya dawo da baya ya kira lambar Alhaji Rufa'i dan shaida musu amincewar Islaha.      ••••• "Mamy Hamma Rehaan bashi da lafiya." Riyya ta faɗa a gigice tana shigowa ɗakin Mamy a guje. Mamy gabanta ya faɗi, ta miƙe da gaggawa ta ce, "me ya same shi?." Ta faɗa suna fita a guje zuwa apartment ɗinsa. Dawowarsa kenan daga Jeedah, ko wanka bai yi ba, yana zaune ya ji cikinsa yana yi masa ciwo sosai. Mamy ta shiga da hanzari ta ƙarasa ta tallafo shi jikinta, ya kwantar da kansa a ƙirjinta tana shafa kansa ta ce, "Rehaan ciwon cikin ne?..." Bai iya bata amsa ba saboda ciwo Mamy ta ce, "Sannu. Riyya je ki ki ɗauko min pcm injectiom da sauri." Ta koma da sauri ita kuma ta kwantar da shi a jikinta ta ce, "Banisha shiga ɗaki ki ɗauko towel, ki taho da ruwan sanyi." Banisha ta je ta dawo, Rehaan yana ta juya kansa a ƙirjinta tana riƙe dashi cikin azabar da take addabarsa. Banisha ce ta fara dawowa, Mamy ta kwantar da kansa a cinyarta, ta jiƙa towel ɗin da ruwan sanyi, ta ɗaga rigar jikinsa tana goga masa a cikinsa da ya ɗauki zafi kamar bakin wuta. Ya ɗan riƙe hannun Mamy, dan wani irin ciwon ciki yake yi da ba ya so a taɓa masa cikin ko kaɗan, ko ya aka taɓa cikinsa ko aka motsa shi sai ya ji kamar za a zare masa rai. Mamy cikin tausayi ta ce, "Yi haƙuri, zai daina." Bai ce komai ba idonsa yana rufe yana kwance akan cinyarta tana shafa kansa da hannu ɗaya, hannu ɗaya yana kan cikinsa da towel dan ya ji sanyi. A lokacin Riyya ta dawo da abinda Mamy ta saka ta ɗauko. Mamy ta saka Riyya haɗa mata allurar, ta gama haɗa mata allurar ta bawa Mamy. Mamy ta karɓa ta riƙo hannunsa guda ɗaya, ta cire masa agogon hannunsa, ta kalli Riyya ta ce, "cire takalmin ƙafarsa." Riyya ta cire masa ta ajjiye. Mamy da dabara ta yi masa allurar a jijiyar hannunsa, daƙyar take motsawa saboda kar ta motsa ta motsa shi ciwo ya dawo baya. Mamy ta kalli Riyya, murya a can ƙasa yadda baza ta dame shi ba ta ce, "kawo min ruwa a cup." Riyya ta kawo mata ruwan, Mamy ta yi masa addu'a a cikin ruwan kamar yadda ta saba, ta tallafo kansa ta ce, "Ɗago ka sha." Ya ɗago a hankali ta zuba masa kaɗan a bakinsa, yana haɗɗiyewa a hankali, ruwan yana sauka cikinsa ya saurin runtse ido, saboda in wani abun ya shiga cikinsa kamar saukar garwashi haka yake ji. Daƙyar ya sha kaɗan, sauran ta zuba masa a fatar cikinsa tana gogewa da towel a hankali. Shi dai ya riƙe cinyarta sosai, ya kifa kansa a kai tana shafa gashin kansa tana yi masa tofi a hankali. Mamy ta kalli Riyya da Banisha ta yi musu alamun su zo su zauna, suka zagaye Rehaan suna yi masa addu'a Banisha sai kuka take yi. Sun fi minitina talatin a haka, in cikin ya riƙe Mamy tana jin yadda zai riƙe jikinta sosai, sai ta riƙe shi tana cigaba da yi masa duk addu'ar da ta zo bakinta, a hankali jikinsa ya saki alamun ya samu bacci. Mamy ta yi pecking goshinsa tana janye gashin kansa da ya rufe masa fuska, ta saka hannu a gashin kanta ta cire band ɗin da ta ɗaure gashinta, ta ɗaure masa gashinsa tana shafa fuskarsa a hankali. Sai kuma ta yi pecking kuncinsa, tana kallon fuskarsa yadda ta yi ja saboda tsananin ciwon da yake damunsa. A hankali Riyya ta taso ta zo tana shafa fuskar Yayanta cikin tausayi da ƙauna. Ƴaƴan ɗakin Mamy ji suke da Rehaan, in ba shi da lafiya kamar su ɗauko cutar su dawo da ita kansu haka suke ji. Suna zaune a wajan baccinsa ya yi nisa sosai alamun ya samu sauƙi, Mamy ta ɗauki waya ta turawa Riyya message, dan bata so ta yi magana ya farka. Riyya ta karanta ta ga Mamy ta ce, "ku je ku kwanta, dare ya yi. Ni zan kwana tare dashi." Riyya ta yi mata reply ta ce, "Zamu kwana tare Mamy." "A'a, gobe kina da inda za ki je kar ki damu kan ki. Banisha zata je makaranta, ku je ku kwanta." Riyya ba yadda zata yi, ta rage musu hasken ɗakin fita ta ita da Banisha saka bar Mamy a zaune a wajansa. Nana Haleema. [7/24, 5:59 PM] KRBBK: RDB2P84 Nana Haleema. Rehaan baccin yake yi sosai a jikin Mamy, ita ma ta jingina da kujera ta lumshe ido. Ta saba masa da wannan ɗabi'a, in bashi da lafiya a jikinta yake bacci, tun yana ƙarami har yanzu bai daina ba, har hakan ya zamar masa jiki. Shiyasa in yana rashin lafiya a inda bata nan yake shan wahala sosai, dan shi ya saba, har bacci itace take saka shi ya yi. A haka itama bacci bata sani ba, kuma bazata iya motsawa ta bar jikinsa ba gudun kar ya tashi, shiyasa ta nutsu ko motsi bata yi, wayarta ma ta kashe ta saboda kar vibrating ya tashesa. Sai ƙarfe uku na dare ya buɗe ido a hankali yana kallon ɗakin, sai a lokacin ya tuna ashe fa ya dawo gida ba a Jeddah yake ba. Ya ɗaga ido ya kalli Mamynsa da take bacci a zaune, ga kanta ya yi gefe. Rehaan ya yi murmush ya miƙe zaune yana runtse ido, dan har lokacin yana jin zafi a cikinsa sosai. Ya miƙa hannunsa a hankali ya ɗago kanta yana shafa fuskar ta ya ce, "Mamy!." A hankali ta buɗe ido ta kalle shi a firgice ta ce, "Rehaan me ya faru, Ciwon ne?." Ya girgiza kai ya ce, "za ki yi ciwon wuya Mamy." Maimakon ta amsa sai ta ce, "akwai ciwon ciki?." Saboda kar ta damu sai ya girgiza kai ya ce, "Babu. Mu je ki kwanta" ya faɗa yana miƙewa, yana ɗagawa tsaye a hankali kamar tsoho ko wanda aka yiwa tiyata. Sai kuma ya koma ya zauna ya ce, "oshhh!." Mamy ta miƙe a gigice ta ce, "koma ka zauna, ka san ciwon nan ba ya ƙyale ka lokaci ɗaya. Me ka ke so na kawo maka?." Ya bita da kallo a hankali ya ce, "Mamy kina buƙatar hutu." "Waye ya ce maka na gaji? Har bacci na yi. Me ka ke so yanzu?." Ya girgiza kai yana magana numfashi yana sauka ya ce, "Babu, Ina so ki huta ne." "Na san kana son shan tea, ina zuwa." Zata tafi ya riƙo hannunta ya ce, "No Mamy, ki dawo." Ta dawo ta zauna ya ɗora kansa a ƙirjinta ya ce, "Bana son komai Mamy." Ta shafa bayansa ta ce, "ba ka ci komai ba Rehaan, me za a dafa maka?." Bai ce komai ba ya yi shiru, itama sai ta yi shiru tana shafa bayansa a hankali. Ya jima a haka sannan ya ɗago daga jikinta ya ce, "Mamy mu je ki yi bacci." Ta kalli agogon da ta saka aka cire masa ta ce, "yanzu uku ta wuce, baccin me zan yi? Kai ka je ka kwanta ka cigaba da baccin ka." "Me za ki yi?." "Addu'a zan yi maka, kana bacci ina bawa Allah gadin ka." Rehaan ji ya yi kamar ya yi hawaye, ya zagaya da hannunsa ya rungume ta, sai kuma ya yi pecking goshinta ya ce, "i love you Mamy." Ta riƙe sa a jikinta ta ce, "You are my world Babyn Mamy." Ta taɓa jikinsa ta ce, "Body temperature ɗin ka ta canja Rehaan, kana jin zazzaɓi ne?." Ya girgiza kai alamun a'a, dan shi gani yake kamar babu wanda ya yi dacen uwa mai ƙaunarsa kamar yadda Mamy take ƙaunarsa, gani yake da za a ajjiye iyaye mata na duniya gabaɗaya, a yi gasar nuna so da ƙaunan da suke yiwa ƴaƴansu, yana da tabbacin Mamy ce zata yi nasara. Bai san ya sauran iyaye suke yiwa yaransu ba, kawai ya san Mamynsa daban take a cikin iyayen duniya gabaɗaya. Ta taɓa fuskarsa ta ce, "tashi mu je ka kwanta." Bai musa ba ya miƙe daƙyar tana yi nasa sannu, ji yake kamar ana kuna wuta a cikinsa, ko iy ƙarasa miƙewa tsaye bai yi ba, a duƙe suka shiga bedroom ɗin. (Waɗanda suke fama da irin wanann ciwon cikin mu kaɗai mu ka san me muke ji. Allah ya bamu lafiya baki ɗaya😭). Mamy zaunar dashi a gefen gado, ya ɗan juyo ya kalle ta ya ce, "zan yi wanka." Ta girgiza kai ta ce, "A'a, ka yi bacci gobe sai ka yi. Yanzu dare ya yi sosai, ka kwanta" ta faɗa tana taimaka masa ya kwanta amma sai ya ƙi kwanciya ya ce, "nima zan yi sallar." "Zan roƙa maka duk abinda ka ke so, ka kwanta kawai." Babu yadda zai yi da ita, haka ya kwanta ta rufe shi da duvet mai nauyi. Sannan ta ce, "ka yi addu'a?." Ya girgiza kai alamua a'a ta ce, "ka yi." "Ki yi min" ya faɗa yana lumshe idanunsa. Mamy ta zauna a gefensa tana yi masa addu'a tana shafa masa. Ta kunna masa a.c kaɗan, ta kashe masa haske, ta shiga banɗakinsa ta yi alwala ta fito ta tayar da sallar a ɗaki, dan gani take baza ta iya fita falo ta bar sa shi kaɗai ba. Yana kallonta tana sallah, har bacci ya sake ɗauke shi.      •••••• Saheer yana kallon yadda ake gudanar da rayuwa a hannun masu garkuwa da mutane, yana ganin yadda Sudaisa ta samu ƴancin yin duk abinda take so, Sudais yana haska mata akan ta gudu amma ta kasa. Lokacin da Arɗo ya zo aka jawo masa Sudais aka jefar daahi a gabansa. Magaji ya ce, "Yana bawa matar black shawara akan ta gudu." Arɗo ya kalli Sudais ya ce, "Ina ɗaga maka ƙafa amma ba ka gani ko? Har shawarar guduwa ka ke ba wa matar abokina?." Ya yi shiru bai amsa ba, Arɗo ya ce, "in ya sake aikata abinda ya yi a kashe shi kawai." Suka amsa da to, aka ɗauke sa daga wajen aka mayar dashi inda yake. Sudais ya yi ƙudurin dole kuɓutar da Sudaisa kafin Black ya dawo ya ɗauke ta, bazai bar yar uwarsa a hannunsu da sunan mata ba. Arɗo ya kalle su gabaɗaya ya ce, "za mu kira dangin ku gabaɗaya, kowa za a fanshe shi akan naira miliyan ɗari ɗari. Ni na gaji da ganin ku, ban kawo ku nan dan na ciyar da ku a banza ba, kuɗina nake buƙatar fanshewa." Saheer ya kalle sa jin abinda ya ce, ya sunkuyar da kai yana tunanin inda ahlinsa zasu samu wannan kuɗi masu matuƙar yawa, dan ya san basu da hanyarsu, basu da inda zasu samu sai dai a kashe shi. Ya ɗauki waya ya ce, "zan kira lambarsu, kowa zai yi magana da ƴan uwansa, kafin mu yi gajeren video mu aika musu dashi." A take aka fara kiran waya ana bawa su suna magana. •••••••• A wannan lokacin ahlin gidan Baffa a daidai wannan lokaci sun yi cirko cirko cikin yanayi na damuwa. Islaha gabaɗaya ta manta da batun wani auren da Baffa ya yi mata, zancen ɓacewar Saheer kawai ake yi. Hankalin kowa a tashe yake, suna zaune a wajan Baffa wayar Baffa ta hau ƙara alamun kira ya shigo. Gabansa ya faɗi, amma haka ya ɗauka ya saka a speaker, daga can ɓangaren aka yi sallama cikin fulfulde. Baffa ya amsa cikin yaren, sai kuwa ya ce, "Ina magana da ƴan uwan Saheer dai ko?." Baffa ya ɗaga kai ya ce, "su ne." "Ga ɗan ku zai yi mu ku magana." Duk sai suka ji muryar Saheer ya ce, "Baffa!." Baffa ya ce, "Saheer kai ne?." Ya ce, "eh Baffa, ina Mama?." Mama da take kuka ta ce, "Gani Saheer." Islaha kuka take yi wanda sautinsa ya bayyana, gashi tana kusa da Baffa a zaune, kukanta ya shiga cikin wayar har Saheer ya ji. Saheer ya ce, "Islaha ce take kuka ko? Ina Sadik ?." Sai kuwa ta ƙara ƙarfin kukanta ta kasa magana, kuka take yi mai matuƙar ɗaga hankali. Arɗo ya ce, "Kun ji muryar ɗan ku ko?." Baffa ya ce, "mun ji." Ya ce, "to ba mu kashe shi ba, yana nan da ransa. Amma in ba ku cika alƙawari ba zamu kashe shi." Baffa ya ce, "wanne alƙawari kenan?." Mutumin ya ce, "Za ku kawo mana kuɗi naira miliyan ɗari ku karɓi ɗan ku, in kuwa ba ku kawo ba....." sai ya yi shiru ya fara harba bindiga suna jin ƙararta a kunensu. Ya ce, "Ka ji sautinta ko?." A sanyaye Baffa ya ce, "na ji." "To zamu kashe shi. Kuɗin shine fansar ɗan ku naira miliyan ɗari!." Baffa ya kasa cewa komai, dan bai san me zai ce ba. Ya ce, "ka yi shiru baka ce komai ba, ko mu kashe shi?." Mama ta yi caraf ta ce, "A'a, zamu kawo, don Allah kar ku yi msa komai bawan Allah." Arɗo ya ce, "ba sunana bawan Allah ba, Arɗo za ki ce, in da hausa ne ki ce Shugaba, inda turanci ne ki ce master ko ki ce leader." Mama ta ce, "To Arɗo, don Allah kar ku kashe sa zamu kawo." "Yauwa. A shirya kuɗin nan da kwana biyu, zamu sake kiran ku" yana faɗa suka kashe wayar. Baffa ya yi shiru bayan an gama wayar ya kalle su sanyaye ya ce, "Ina zamu ga waɗanan kuɗin? Ai sai dai mu ce Allah ya gafarta maka Saheer, Allah ya sa ƙarshen wahalar ka kenan. Dan na san lokacin mutuwar ka ne kawai ya yi!." 100 millions ta fansar Saheer! Saheer fans a haɗo kuɗi kar a kashe mana bawan Allah😭 [7/24, 5:59 PM] KRBBK: RDB2P85 Nana Haleema. Cikin tashin hankali da ruɗewa suke kallon Baffa jin furuncin a kashe Saheer da yake faɗa. Mama ta ce, "Haba Baffa, ya ka ke faɗar irin wannan kalaman, maimakon ka yi fatan Allah ya kawo mafita sai ka ce haka?." Baffa ya kalle ta cikin yanayi na damuwa da tashin hankali ya ce, "A ina za ki samu naira miliyan ɗari? Ko gidan nan za a siyar baza a taɓa samun wannan kuɗin ba, in za a zaga dangina da na ki ana neman waɗanan kuɗi baza a samu ba, dan ba mu dasu, ba mu da dalilinsu. In aka bayar ɗin ma kashe mutane suke yi, gwara mu yi masa fatan cikawa da imani." Mama tana girgiza kai tana kuka ta ce, "Baza su kashe Saherr ba, zai dawo in Allah ya yarda, bazai mutu ba." Islaha kuka take yi kamar ranta zai fita, tunda ta ji muryar Hammanta shikenan ta gigice take kuka mai sauti, bata tare da nutsuwa ko kaɗan, Hamma kawai zuciyarta da ƙwaƙwalwarta take kira. Baffa ya dafa Islaha ya ce, "ki daina kuka Islaha, ki cigaba da addu'a, in akwai rabon zamu sake ganawa zai dawo." Mama ta yi tsaki cikin jin haushi, ita da take mahaifiyarsa bai ce ta daina kuka ba sai wata banzar Islaha. Baffa ya ɗauki waya ya kira Sadik, babu jimawa sai ga shi ya zo gidan. Baffa ya kalli Sadik da sanyin jiki ya ce, "Sun kira waya Sadik, suna neman kuɗin fansa har naira miliyan ɗari." Sadik ya wara ido ya ce, "ɗari Baffa? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Miliyan ɗari!" Ya sake maimaita cikin tashin hankali. Sai kuma ya girgiza kai ya ce, "dole hukuma ta shiga maganar nan, in Allah ya taimaka sai ka ga an dace." Mama ta ce, "ni dai kar a faɗawa ƴan sanda, kar su kashe min ɗana." "Baza su kashe sa ba in sha Allah, za a san yadda za a yi a kuɓutar dashi in Allah ya amince." Sadik ya juya ya fita, Islaha ta zabura ta bi bayansa ko takalmi bata saka ba. Sadik da ya fita gab da zai shiga mota ya ji maganar Islaha a bayansa. Ya tsaya ya waiwayo ya kalle ta, Islaha ta ƙaraso kusa dashi ta goge ido ta ce, "zan bi ka mu je." Ya kalle ta ganin duk ta firgice, ta koma wani iri kamar ba Islaha ƴar gayu da aji ba. Sadik ya ce, "to ki koma ki saka takalmi." Sai a sannan ta san babu takalmi a ƙafarta, ta koma ta je ta ɗauko ta shiga mota suka tafi. Bayan sun dawo wajan Baffa Sadik ya shiga, ya same shi a zaune yana tunanin mafita akan wannan lamari. Sadik ya zauna ya ce, "Gani Baffa." Baffa ya ce, "Sadik akan maganar kuɗin nan ne, ya ka ke ganin za a yi?." Sadik ya ce, "Wallahi kaina ya rufe Baffa, ban san me zan ce." Baffa ya ce, "Akwai gonata guda biyu, kwanaki a ta ya ɗaya miliyan biyar, ɗaya kuma miliyan bakwai ban siyar ba, ka ga yanzu zasu iya yin miliyan asirin. Sannan ga wannan gidan, tunda a babbar unguwa yake, kuma yana da girma sosai, a tunanina zai iya zuwa miliyan hamsin zuwa sama haka. Ka ga an ɗan samu kuɗin, sauran kuɗin sai a siyar da gidansa, da ɗan abubuwan da za a rasa ba.." Sadik a sanyaye ya ce, "Baffa in aka siyar da gidan nan ina za ku koma?." "Sai mu koma ƙauye cikin ƴan uwa, ran Saheer ya fi komai mahimmaci Sadik." Ya sauke numfashi ya ce, "kwana nawa suka ce?." Baffa ya ce, "Kwana biyu suka bayar." Sadik ya ce, "in sun kuma kira mu faɗa musu ba mu da halin wannan kuɗin su taimaka su rage, in aka yi sa a zasu rage. Tunda daman ciniki ake yi dasu, ba da sun faɗa ake ɗauka a bayar ba." Baffa ya sauke numfashi bai ce komai ba, dan bai san wanne irin tunani zai yi akan haka ba. Abinda suke ji a waje ga shi ya zo gidansu, har cikin ɗakinsu. Sadik ya dinga rarrashin Baffa ganin ya ɗaga hankalinsa sosai, shi kansa hankalinsa a tashe yake, amma yana ɓoyewa ne saboda halin da Baffa yake ciki. ••••••• Suna kashe wayar suka kalli Saheeer Arɗo ya ce, "Baban ka ya ce basu da miliyan ɗari, kuɗi sun fi ranka kenan." Saheer ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Basu da wannan kuɗin, basu da hanyarsa." "Ba bafulatani bane? Ya siyar shanunsa mana." "Ranka ya daɗe wanne shanu ne zasu yi miliyan ɗari a wannan lokacin?." Arɗo da yake goge bindiga ya kalle sa ya ce, "in ba a kawo ba za a cilla ka cikin ramin marasa amfani." A lokacin wani matashi ya ƙaraso wajen da machine, Arɗo ya kalle su har suka ƙaraso. Aka gurfanar da matashin a gaban Arɗo. Arɗo ya yi murmushi ya ce, "Barka da zuwa." Mutumin ya ɗan dake ya ce, "Barka ranka ya daɗe." "Kuɗin fansar Bala ka kawo ko?." "Sune ranka ya daɗe." "Nawa ne?." "Miliyan biyar aka ce, da waya guda huɗu, da wannan machine ɗin" ya faɗa yana nuna machine ɗin da ya zo a kai. Arɗo ya ja jakar ya buɗe ya ga dubu dubu ne a ciki, ya ɗauke wayoyin ciki yana kallonsu sabbabi duk a kwalayensu. Ya tura masa kuɗin ya ce, "ka lissafa, naira ɗaya in babu ka yi kuka da kan ka." Mutumin ya fara irga kuɗin kamar yadda aka ce, yana yi yana gumi jikinsa yana rawa sosai. A lokacin Magaji ya ƙaraso wajen ya ce, "Arɗo mai cikin can da take cikin matan can ta haihu, ta samu ɗa namiji amma ita ta koma." Arɗo ya ce, "Har yanzu ba a ɗauko mana likitoci ba? Har yanzu ba a samu mai amfani a cikin sanƙammmun ba?." Kafin Magaji ya yi magana ya kalli Saheer ya ce, "Kai baka iya aikin asibiti ba?." Saheer ya ce, "Ban iya ba." "Mtsw! Ba ka da amfani." Ya kalli baƙo da yake irga kuɗi ya ce, "Baƙo fa, ka iya likitanci?." Ya ɗago ya kalle sa jikinsa yana karkarwa, Arɗo ya ce, "Kar ka ji tsoro, babu abinda za mu yi maka, in ka iya likitanci ka taimaka mana ka duba wacce ta haihu." Murya tana rawa ya ce, "Na iya." Ya yi dariya ya ce, "Dakyau baƙo...Magaji a ɗauke shi a je dashi ya duba ta, ina akwai wanda bashi da lafiya yau mun samu likita. Bar irga kuɗin, alfamar likitancin da ka iya ko nawa ka kawo mun karɓa." Aka tafi dashi inda matar ta haihu. Ya je ya same ta a kwance kaca kaca cikin jini, ga matan sun zagaye ta suna kallo, ga jaririn an naɗe shi da ɗankwali yana ta kuka, ita kuma tana kwance tana jan numfashi daƙyar. Ya duba ta ya kalli Magaji ya ce, "Da ranta, ba mutuwa ta yi ba, gajiya ce da yunwa, tana buƙatar a saka mata ruwa." "Mu je a faɗawa Arɗo." Tare suka dawo wajen Arɗo aka faɗa masa, ya ɗan ɗaga kai ya ce, "Tunda bata mutu ba a ƙyaleta kawai, ina da ciwo a hannuna, me za a siyo a wanke min likita?." Jikinsa ya yi sanyi tunawa da halin da matar take ciki, amma babu damar magana ya faɗi abinda za a siyo. Ya ɗauki waya ya kira, babu jimawa sai ga duk abinda ya faɗa an kawo masa, harda ƙarin maganin ciwon kai da ƙananun abubuwa. Ya wanke masa ciwon kamar yadda ya ce, Arɗo ya kalli magaji ya ce, "Kukan jaririn can ya cika min kunne, a kawo waya a kira mijinta, in bazai kawo kuɗi ba duk mu kashe su, kar su zamar mana kaya." Shi dai yana duƙe yana wanke masa ciwo, ƙirjinsa yana bugawa har ya gama. Arɗo ya ce, "A kawo amaryar Black ya wanke mata ciwon ta." Aka je aka ɗauko Sudaisa da kanta yake a fashe, yana wanke mata tana kuka bayan ya gama ya ce, "Za a iya bata magani?." Arɗo ya ce, "ka bata komai, wannan ai ta gida ce." A cikin magungunan da aka kawo ya buɗe ya bata na zazzaɓi ta ce, "Arɗo a duba Hammana, da wannan Hamma" ta faɗa tana nuna Saheer. Arɗo ya ce, "Ayi yadda take so...." Ya juyo ya kalle ta yana murmushi ya ce, "Amarya kuma amanar Black." Alfarmar Sudaisa aka bawa Saheer maganin ciwon kai da zazzaɓi, aka bawa Sudais aka wanke masa ciwukan jikinsa. Arɗo ya bita da kallo ya ce, "Black ya yi min shigar sauri, kamata ya yi a ce ni na aure ki ba shi ba. Amma matar abokina matata ce, nima mijin ki ne, yau zamu yi daren amarcin mu" ya faɗa yana binta da shegen kallon da gabanta ya faɗi. "An samu labarin shigowar sojoji nan da mintina goma, kowa ya shirya!." Abinda aka faɗa ta over over hannun Arɗo kenan, ya kalli su Magaji ya ce, "A kwashe min kadarorina a killace su waje ɗaya, kar a bar wani abu ya samu ɗaya daga cikinsu, mu zamu ji da sojojin." Magaji ya ce, "Ya za a yi da jaririn can? Kukan sa zai iya tona mana asiri." Ya kalli Magaji ya ce, "A bashi ƙaramar gyaɗa kawai, a aika shi inda zai huta daga wannan wahalar." Magaji ya amsa ya bar wajen, su dai sun ji ihunn matan wajen, sai tsawar da Magaji yake yi musu, ashe har ya murɗe kan jaririn an cilla shi cikin rami. Wannan rashin imanin ya ja zuciyar mai jegon ta buga, itama ta bi ɗanta. Saheer sai da ya yi kuka, shi kuma Likita tuni an sallame shi shida ɗan uwansa sun tafi. Haka aka tattare su aka shiga dasu wani waje, Sudaisa da Sudais da Saheer a waje ɗaya aka bar su, saboda baza a takura masu ba saboda Sudaisa. Duk an kwashe su an ɓoye a cikin bukka saboda su ɗin jari ne, ana jiran shigowar sojojin da aka samu masaniyar zuwansu. ••••••• Mamy tunda aka yi kiran sallar asuba take kallonsa Rehaan, ta kasa tashinsa ya yi sallah saboda ta san bai jima da yin bacci ba. A hankali ya buɗe ido, sai ta kunna hasken ɗakin tana kallonsa ta ce, "Good morning Rehaan, lokacin Sallah ya yi." Ya ɗan miƙe zaune daƙyar yana saule numfashi a hankali, sai ya ɗan nutsu sannan ya kalle ta ya ce, "Morning Mamy." Mamy ta ce, "Ya ciwon cikin?." Ya girgiza kai ya ce, "da sauƙi." "to tashi ka yi alwala kar a tayar da sallah, an yi kira." Ya miƙe a hankali ya sauka daga kan gadon, Mamy ta zuba masa ido tana kallo har ya miƙe tsaye sosai yana runtse idonsa. Bai kalle ta ba ya shjga bathroom ɗin ita kuma ta fita daga ɗakin. A falo ya same ta bayan ya fito ya ƙarasa inda take ita kuma tana kallonsa ta ce, "za ka iya zuwa masallaci?." Ya girgiza kai alamun bazai iya zuwa ba, shinfiɗa masa sallaya ta ce, "To ka bi jam'i daga nan." Bai musa ba ya hau kai ya tsaya ya tayar da ra'akatal fijir. Yana idarwa aka tayar da sallah suka yi sallah tare da masallaci. Bayan ya idar ya jingina da kujera idanunsa a lumshe, ya jima a haka kafin ya buɗe ido ya kalle ta ya ce, "Good Morning Mamy." Ta ɗora hsnnunta a gashinsa ta shafa ta ce, "Ya jikin ka?." Ya yi murmushi ya ce, "na ji sauƙi." Ta yi murmuahi ta ce, "za ka sha tea ko?." Ya ɗan rausayar da kai ya ce, "Kar ki wahalar da kan ki." Bata ce komai b ta miƙe ta sauka ta shiga kitchen ta kawo masa black tea mai zafi, dan ta san ba ya shan madara. A kan kujera ta same shi, iyama zauna ta ce, "ka yi azkhar?." Ya ɗaga kai alamun ya yi, ya miƙa masa tea ɗin ta ce, "ka sha sai ka koma bacci." A lokacin Abba ya shigo falon da sallama, duk suka ɗaga kai suna kallonsa har ya ƙaraso. Ya zauna gefensa, ya zama sun saka shi a tsakiya sannan ya ce, "ni ai ban san ya dawo ba, sai yanzu Riyya take faɗa min......" Ya kalli Rehaan ɗin ya ce, "Sannu Rehaan, ya ciwon cikin?." A sanyaye ya ce, "Na ji sauƙi Abba. Lokacin da na dawo je zan gaishe aka ce baka nan, shine na shigo nan." Ya kalle shi cikin tsananin tausayi ya ce, "wannan ciwon ciki yana wahalar da kai, kalli yadda ka rame lokaci ɗaya. Na rasa wanne irin ciwo ne wannan, an yi duban duniya ba a ga komai ba." Rehaan ya ɗan sauke numfashi bai ce komai ba yana sipping tea a hankali. Sai kuma ya ce, "Ina kwana Abba." "Lafiya lau. Yanzu ya daina yi maka ciwon?." "Ba ya yi sosai, sai kaɗan." "Allah ya ƙara lafiya." "Amin Abba." "Ka kwanta in ka gama shan tea ɗin, in ka sake yin bacci za ka ji daɗi sosai." Abba ya kalli Mamy da take gefensa a zaune ya ce, "Nadira mu bar shi ya huta, mu je ko?" Ya faɗa yana miƙewa, babu yadda Mamy zata iya haka ta miƙe ta fita ba dan ta so ba, in a son ranta ne yadda suka kwana tare a haka zasu yini. Suna fita ya ajjiye tea ɗin hannunsa ya kwanta kan kujerar ya lumshe idonsa. Bacci ya yi sosai har bayan sallar azahar yana bacci, sai ƙarfe biyu na rana sannan ya farka, kuma sai ya ji daɗin baccin dan babu sauran ciwon kamar ɗazu. A haka ya tashi ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya ya zauna a falon. A lokacin Mamy ta shigo ita da Riyya da Banishs da kuma Jafar. Ya ɗaga kai yana kallonsu kamar yadda suke kallonsa. Mamy ta yi murmushi ta ce, "Lallai jiki ya yi kyau." Ya yi murmushi ya ce, "na ji sauƙi Mamy. Ina yini." "Lafiya lau, ka tabbatar ka ji sauƙi?." Ya ɗaga kai yana kallon Banisha da take kallonsa. Ya miƙa mata hannunsa ya riƙota ta zauna a kusa dashi, ta kallesa ta ce, "ya daina yi maka ciwon?." Ya ɗaga mata kai yana murmishi. Ya kalli Riyya da take riƙe da tray a tsaye, ganin yana kallonta sai ta ajjiye ta riƙe hannunsa ta ce, "Ya jiki?." "Na ji sauƙi Riyya." Ta ce, "Ga lunch na kawo maka." Ya ɗaga kai ya ce, "Na gode." Ta ta yi serving ɗinsa white rice da vegetable sauce wacce aka yi ta da chicken breast. Maimakon ya karɓa ya ci sai Mamy ta karɓa, ita ta dinga bashi abincin har sai da ya ci da ɗan yawa sannan ya ce ya isa. Jafar dai yana tsaye yana kallonsu cikin burgewa, gabaɗaya ahlin Mamy abin sha'awa ne, suna son junansu sosai, suna ƙaunar farin cikin juna, suna son kowa ya rayu lafiya ba tare da wata lalura ba. Babu kamar Rehaan, kamar duk sun fi son Rehaan akan kansu, in Rehaan babu lafiya su kan iya kasa bacci, su saka shi a gaba suna kuka har gari ya waye. Jafar ya ce, "Mamy ki ƙyale sa ya ci da kansa, sai wahalar mana dake yake yi." Ta yi murmushi ta ce, "kaima zo ka zauna na ba ka da kaina." Ya yi dariya dan shi wallahi Mamy burge shi take yi matuƙa, bata wani siriki dashi kamar Rehaan take kallonsa. Tsaf in ya zauna zata bashi abinci a baki kamar yadda ta bawa Rehaan, sai dai shi ya ji kunya ba dai ita ba. Yana ganin banbanci sosai tsakanin iyayensu da suka kasance jinin fulani, da kuma Mamy da take yar wata ƙasar, yana ganin yadda ake jan yaro a jiki ana nuna masa soyayya a zahiri, ba kamar fulani da suke yin fulako ba. Mamy bata jure rashin lafiyar Rehaan ko kaɗan, ko a gaban waye tana nuna Rehaan ɗanta ne, sai dai ka ce duk abinda zaka ce. Ya zauna yana murmushi sannan ya ce, "na ƙoshi Mamy." Rehaan ya karɓi tea ɗin hannun Mamy ya ce, "zan sha da kaina Mamy." Ya cigaba da shan tea ɗin suka yi shiru suna kallonsa. Jin an yi sallama ya saka duk suka juya suna kallon Abba da ya shigo. Abba ya ƙaraso ya ce, "lallai Rehaan jiki ya warware, na yi tunanin bacci ka ke yi, na leƙo ɗazu na ga kana ta bacci." Rehaan yana murmushi ya ce, "na ji sauƙi Abba." "Na ga alama kam, gashi nan ka yi kyau abin ka." Rehaan ya yi murmushi yana kallon tea ɗin hannunsa kamar mai ganin wani abun a ciki. Mamy ta ce, "zamu fita ni da Riyya, zamu je mu taro baƙi." Abba ya yi murmushi ya ce, "mutanen India sun fara sauka kenan." Ta ɗan gyaɗa kai tana murmushi ta ce, "Eh sun fara, zan kai su guest house su zauna." Da mamaki Abba ya ce, "baza su zo nan ba?." Ta ɗan girgiza kai ta ce, "gwara su zauna a guest house ɗin." Bai ce komai ba ta miƙe ita suka fita dasu Banisha da Riyya. Abba ya kalli Rehaan ya ce, "ka dawo bikin Jafar ko bikin Riyya?." Shi dai murmushi yake yi amma bai ce komai ba. Abba ya sauke numfashi ya ce, "Rehaan maganar auren ka ta tabbata, da gaske dakai za a haɗa aurenku ranar juma'a in sha Allah. In Allah ya kaimu jibi saura sati ɗaya." Nana Haleema. [7/27, 11:49 AM] KRBBK: RDB2P86 Nana Haleema. Rehaan ya ɗago ya kalli Abba sai kuma ya sauke kai ƙasa bai ce komai ba. Abba ya tausasa murya ya ce, "Ka yi haƙuri Rehaan, na san za ka ji ba a kyauta maka ba, amma ka yi haƙuri baka san me Allah ya ɓoye ba." Calmly ya ce, "Abba amma ban san yarinyar ba, kawai sai na aure ta? A jira ni na kawo matar da kaina mana, duk daren daɗewa ai zan yi auren." Abba ya ce, "haka ne Rehaan, amma ka yi haƙuri kamar yadda na ce, ka karɓa da zuciya ɗaya, kar ka kalle sa da wani abun daban. Na san za ka ce meyasa sai kai kaɗai, kaf ƴan uwanka babu wanda aka yiwa haka sai kai. Ina so na tuna maka tabbacin kai ɗin na daban ne kenan, ɗaukakar da Allah ya yi maka ce ta kawo haka. Babu yadda zan yi, mahaifiyata nake yiwa biyayya, kaima ka yi min biyayya ka amince." Ya ɗan sauke nunfashi bai ce komai ba dan bai san me zai ce ba, wanne irin aure ne wannan kamar na wasan yara. Abba ya kalli jafar ya ce, "ga Jafar nan, ya yi bincike mai yawa akan yarinyar, kuma ya tabbatar tana da ilimin addini dana zamani. Ƴar jarida ce cikakkiya, kuma tana da tarbiyya da kamewa, in Allah ya amince baza ka yi danasani ba." Rehaan ya ɗaga kai ya ce, "To." Abba ya ce, "yauwa Rehaan, Allah ya yi albarka, yadda ka ta ya ni yiwa mahaifiyata biyayya Allah ya sa ka ga amfanin yi min biyayya." Jafar ne kaɗai ya amsa da amin Abba ya ce, "Sannan in sha Allah duk macen da ka gani ka ce kana so ka aura zan shige maka gaba har sai ka mallake ta. Baturiya ko ƴan india jinin babar ka, kai ko wanne yare, ko wanne ƙabila, indai ka kawo bazan ba da goyan bayan a juya maka baya ba. Kai ko ba musulma bace, indai ta yi maka za ka aure ta, tunda addini bai hana ba zan ba ka goyan baya koda kowa zai ƙi goya ma ka baya a kai. Sai na tabbatar ka samu abinda ka ke so." Rehaan ya ce, "To Abba" ya sake faɗa a taƙaice dan bai san me zai ce ba. Abba ya ce, "Jafar zai raka ka kaje ka ga yarinyar, daga nan sai ka dawo a ɗan yi shirye shirye a kai mata da lefe da komai na al'ada, In kuma kuɗi za ka bata a matsayin kayan lefen sai a bayar a yi." To kawai ya sake cewa kawai bai ce komai ba. Abba ya ce, "ka tuna kwana tara auren ya rage, aje ayi abinda za a yi kafin lokaci ya ƙure." Rehaan ya ce, "To Abba." Abba ya shafa kansa ya ce, "ka cigaba da haƙuri, ɗaukakar kenan, hausawa sun ce ɗaukaka abar gudu ce kuma abar nema." Ya kalli Jafar ya ce, "sai ka ɗora daga inda na tsaya." Jafar ya amsa sannan Abba ya miƙe ya fita. Jafar ya kalle sa cikin tsokana ya ce, "Ango." Bai kula ba sai shan tea ɗinsa da yake yi kamar baya so. Jafar ya ce, "ɗan gata Abba da Daada, aure kawai za a yi maka cikin kwana tara, gaskiya kana lokacin ka." Nan ma ya yi masa banza bai ce komai. Jafar ya ce, "ka dai yiwa Abba biyayya kawai malam." Sai a lokacin ya kalle sa ya ce, "wai aure, sai ka ce wani toy, ni Rehaan za a yiwa haka." "Babu mita Rehaan, kawai ka amince." "Kamar a film, ko sanin yarinyar ban yi ba. Kamar sadakata aka bata fa." "Na faɗa maka wacece?." "Kai ka santa ne?." "kaima ka santa." Ya ɗan zuba masa ido kafin ya ɗauke kai bai ce komai ba. Jafar ya ce, "Yarinyar nan da sace, yarinyar nan da ku ka haɗu a Jedda, itace dai matar ka." Rehaan ya juyo yana kallonsa alamun ban gane ba, Jafar ya yi dariya yana ɗora ƙafa kan ɗaya ya ce, "da gaske nake maka, wallahi itace, ka san dai bazan ce wallahi akan ƙarya ba. Abba yana faɗa min sunanta na gane ta, na saka a yi bincike a kanta a kan hakan." Ya ajjiyd mug ɗin hannunsa ya ce, "Jaazy ka daina yi min wasa." Jazy ya ce, "ba wasa nake maka ba, wallahi da gaske nake. Itace wacce Daada take so ta haɗa auren ku." Ya ɗan yi shiru yana kallon waje Jazy, har Jazy ya ce, "ka zuba min ido kana kallona." "Jazy akwai plan ɗin da yarinyar nan take haɗawa a kaina, jikina yana bani turo ta aka yi." Jafar ya girgiza kai cikin tabbatarwa ya ce, "Wallahi babu wanda ya turo ta, infact har yanzu bata san da batun auren ka ba, ita ta neman saurayinta da aka yi garkuwa dashi take, ta ajjiye ka a gefe kamar bata taɓa saninka a Jeddah ba." Ya zuba masa ido ya kasa magana, yana ganin abin kamar rainin hankali. Ta ya za a ce itace matar? In ba shirya wannan abin aka yi ba ta ya hakan sai faru?. Jafar ya ce, "ni ka daina zuba min ido, ka yi magana kawai." Rehaan ya ce, "Kawai ina tuna irin abubuwan da suka faru ne, kai tsaye ka san plan ne wannan. Ta ya rayuwarta zata dinga haɗuwa da ta wa? Daga hotel sai asibiti, daga asibiti sai guest house, daga guest house sai Jeddah, daga Jeddah sai aure?. Jazy akwai abinda yarinyar nan ta shiryawa." Jazy ya yi dariya yana girgiza kai ya ce, "na faɗa maka babu abinda take shiryawa, ta taimaki kakar ka akan titi, daga nan suka haɗu ta kawo ta gida, daga lokacin kuma Daada ta fara wannan maganar." Rehaan ya ce, "Meyasa take shigowa rayuwata ko yaushe?." Ya ɗage kafaɗa ya ce, "oho, kaima kuma ka shiga rayuwarta ai." Ya girgiza kai ya ce, "Wallahi ban yarda da yarinyar nan ba, akwai abinda take shiryawa a kaina." Jafar ya yi dariya ya ce, "In za ka saka a bincika sau dubu, amsar itace bata da wani mugun nufi a kanka. Wallahi bata san kai zata aura ba, ta san da maganar auren amma ba ta auren take yi a yanzu ba. Duk wanda zai faɗa maka akasin abinda na faɗa maka ƙarya ce, abinda na faɗa maka a kanta shine gaskiya." Rehaaan ya ce, "Ta ya zata dinga shogowa rayuwata ko yaushe? Da farko otel, hospital, guest house, jeddah sannan yanzu aure. Aure fa Jazy!" Ya maimaita yana kallon Jafar. Jazy ya ce, "ka san dai bazan yi maka ƙarya ba, ka san dai bazan faɗi abinda yake ba gaskiya ba, ka san bazan taɓa yin abinda zan cutar da kai ba, ka yarda yarinyar nan bata da nufi ko kaɗan a kan maganar nan, bata san da batun auren ka ba har yanzu." "To ya aka yi ake zancen auren bayan bata sani ba?." "ban sani ba, amma ita bata sani ba, amma wanda yake riƙonta ya sani." Ya girgiza kai yana kallon Jazy ya ce, "Bazan aure ta ba Jazy, ban yarda da ita ba, bazan yarda da wannan auren ba." "Ya kamata ka yarda." "Bazan yarda ba, wallahi bazan yarda babu plan cikin a haɗuwata da yarinyar nan ba, wani ne ya turo ta cikin rayuwata." "Daman kwai plan ɗin Allah mana, kuma daman Allah ne ya turo ta rayuwarka ba wani ba." Ya girgiza kai ya ce, "haka bazai faru ba, akwai wani abun bayan nan. Meyasa sauran mata basu shiga rayuwata ba sai ita kaɗai?." "Ni dai ban ga wani plan ba, kuma na faɗa maka na saka an bincika min maganar nan sosai." Rehaan ya ce, "ta ya hakan zai faru lokaci ɗaya? In ba plan bane wannan meye?." Jazy ya taɓe baki bai ce komai ba, dan ya gaji da maimaita magana guda ɗaya. Rehaan ya bi sa da kallon tuhuma ya ce, "anya babu haɗin bakinka a maganar nan? Na lura tun Jeddah kamar akwai abinda ku ke haɗawa kai da ita." Jazy ya ɗaga hannu sama yana murmushi ya ce, "ban sani ba, Abba ne ya bani labari." "Amma meyasa ba ka faɗa masa karuwa bace!?." Jafar ya zaro ido waje ya ce, "ni Jafar na faɗi abinda ban taɓa gani ba? so ka ke Allah ya tsayar damu ya yi mana hisabi na yi bayani da larabci?. Ba da ni ba, na san illar da take cikin yiwa mutum ƙazafi akan abinda ba ka da tabbas a kai." Ya bisa da harara yana kallonsa amma bai ce komai ba, dan ya san yana nufin ƙazafi ya yi mata kenan. Ya ja tsaki yana ji an gama raina masa hankali a duniya, mutum kamar sa da iliminsa da komai a ace wai mata za a zaɓa masa kamar yaro ƙarami. Ya ja tsaki mai tsaho ya ce, "Bazan amince da auren nan ba, dole a fasa shi!" Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Sai kuma ya tsaya cak jin cikinsa ya motsa, ya ɗan runtse ido yana dafe cikinsa. Sai kuma ya fara tafiya, Jazy ya miƙe tsaye ce, "ina za ka je?." "Zan je na faɗawa Mamy, bazan iya auren yarinyar nan ba, bazan iya auren karuwan da ta zubar da ciki ba, sannan ɓarauniyar da take yiwa ƴan siyasa sata ba." Jafar ya ce, "Yanzu ka yiwa Abba alƙawarin za ka aure ta." "Ni ban yi alƙawari ba!." "Amma ka amince tunda ka ce to, kuma ka ce ka masa za ka ta ya sa yiwa mahaifiyarsa biyayya." Ya ɗan dafe kai jin jiyoyin kansa suna harbawa, zuciyarsa tana bugawa, tsanar Islaha tana sake tasowa daga ƙasan zuciyarsa tana mamaye ko ina na jikinta. Ya hargitsa gashin kansa ya kalli Jazy, calmly ya ce, "Jazy na tsane ta, wallahi na tsane ta bana so na ganta. Ka ji na ce wallahi ko? I mean my words." Jafar ya ce, "To ya za ka yi? Biyayya za ka yiwa Abba." Ya ɗago yana kallonsa, Jafar ya bishi da kallo ganin har idonsa ya canja kala zuwa jajeye, ya san ba komai ne yake canja yanayin Rehaan har haka ba, ba komai ne yake taɓa shi har ya ɓata masa rai ba. Ya yi mamaki da ya ga ransa ya ɓaci haka, ya yi mamaki da ya ga har mood ɗinsa ya canja, hakan da ya gani ya tabbatar masa da gaske ya tsani yarinyar. Jafar a hankali ya ce, "meye na ɓata ranka haka? Ni na jima ban ga ranka ya ɓaci kamar haka ba, ka sassauta wannan ɓacin ran please." Ray ya kalle sa ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "na tsane ta, bana son ganinta ko kaɗan a cikin rayuwata. Ta ya za a ce zata zama matata?." Jafar ya ce, "ni abinda nake so da kai, ka daina faɗar abinda ba ka sani ba, ka daina faɗar kalmar da ba ka tabbatar ba a kanta." "Zan sake maimaitawa ,she is a prostitute….Kuma zan je na faɗawa Mamy, ni bazan aure ta." "Kar ka faɗa mata." Ya juyo ya kalle sa alamun meyasa ya ce, "hakan bai kamata ba, kuma za ka iya yin danasani nan gaba." Ya wani kalle sa yana harararsa, ya kasa cewa komai yana kallonsa jin wai zai iya yin danasani, ko danasanin me zai yi oho. Jafar ya ce, "Just obey your father's command, ka aure ta kawai, ba ka san me hakan zai kawo ba. Wataƙila ka ga ya zama alkhairi, haƙurin da za ka yi sai ka ga ya zama riba a nan gaba." Ganin ya yi shiru bai ce komai ba ya san mamaki yake yi akan ya ce zai yi danasani. Jafar ya ce, "kana ji, ni ba wai aurenta nake so ka yi ba, ba goyan bayanta nake yi ba, ina faɗa maka ka daina yi mata zato akan abinda ba ka da tabbas a kai, sannan ka yarda babu wani plan a lamarin yarinyar nan, sannan ka amince ka yi abinda Abba ya ke so. Bayan nan babu wani abu a raina, babu wani dalilin da zai saka na ce ka amince saboda ra'ayin kaina. Kuma na ba ka shawara ka daina kiranta da karuwa, kuma kar ka faɗawa kowa wannan maganar, bai kamata a jita a bakin ka ba. Ba class ɗin ka bane, in aka ji maganar karuwa a bakin ka za ka zubar da class ɗin ka." Ya sauke numfashi ya ce, "a ko yaushe ra'ayinmu ɗaya da kai, meyasa yanzu ka canja?." "Ban canja ba Ray, ina faɗa maka abinda ya kamata ka yi ne kodan saboda mahaifinka. Ka daina kiran yarinyar nan da karuwa, ko da karuwar ce bai kamata ka dinga faɗa ba, tunda ba gani ka yi ba, hasashe ne." "sai ka ce na daina cewa haka, ka san abinda na gani da idona meyasa ka ke ce min haka? Irin wannan yarinyar ka ke cewa na aura?. Rehaan Yola ne, ko ka manta ne?." "Ban manta ba mana." "Abba bai yi bincike a kanta ba, bai ga halayen ta ba?." "Ya ce shi bai ji wani hali mara kyau a kanta ba, in ka faɗa masa a yanzu zai ga kana yi mata sharri ne dan ka gudu daga auren." Ya dafe kai cikin takaici ya ce, "wai na gudu! Oh my god." Jafar ya yi masa bai ce komai ba. Rehan ya dinga sauke numfashi kamar wanda ya yi gudu, ya rufe ido yana ji kamar ya kurma ihu saboda takaici da ɓacin rai. Da wata daban ce ba Islaha ba sai ya yarda da auren, amma tunda aka ce Islaha ce sai ya ji bazai iya ba. Jafar ya ce, "yanzu sai mu je gidansu ku tattauna ko? In ka yi mata ta ga zata iya auren ka sai ta taimaka maka ta aure ka, in ba ka yi mata ba a kai kasuwa" ya faɗa yana gimtse dariya dan so yake ya sake tsokano sa. Sai kuma ya kalle sa, saboda takaici ma bai ce komai ba sai numfashi da ya sauke yana cize lips ɗinsa kamar zai fasa shi da haƙora. Jafar ya yi dariya ya ce, "Ango! Ango!!." Yana faɗa yana dariya, sai wayarsa ta yi ƙara, yana dubawa ya ga Abba ne yake yi masa waya, ya ɗauka ya saka a kunne ya yi magana sannan ya kashe. Jazy ya kalli Rehaan ya ce, "Abba ya ce ka same shi a ɓangaren Daaada, ni dai zan wuce gida, Ba kasafai na cika gaisawa da kakar nan ta ku ba, in ka fito ka same ni sai mu tafi gidansu budurwarta ka, in ba ka same ni ba...." Kallon da ya ɗago yana yi masa ya hana Jafar ƙarasawa, ya yi dariya sosai harda tafa hannu ya fita, ya bar Rehaan da kayan takaici.......... Nana Haleema. [7/27, 11:49 AM] KRBBK: RDB2P87 Nana Haleema. Walking slowly ya shiga falon kansa a ƙasa, ɓacin ran da yake ciki bazai barsa ya ɗaga kai ya kalli mutanen falon ba, ya nemi waje ya zauna bai kalli kowa ba. A hankali ya ce, "Ina yini." Daada ta bisa da kallo ganin ya ɗan rame, ta ji labarin ya yi ciwon ciki kuma gashi nan ta gani a kan fuskarsa. Amma duk da haka sai ta ce, "Gaisuwar tawa ce ko ta iyayenka?." Ya yi shiru baice komai ba, kuma ya ƙi ya ɗaga kai ya kalli kowa dan duk haushi suke bashi. Daada ta ce, "na yi maka uzurin raahin lafiya. Ka ji maganar auren ka ai ko?." Bai motsa ba balle ya amsa mata, bata damu ba ta ce, "Ranar juma'a mai zuwa za a ɗaura aurenka Muhammad, sai ka fara shirye shirye, in za ka yi shagali ka yi, in baza ka ba dai kai ka sani." Nan ma bai ce komai ba sai Mama da ta ce, "Shagali kai Daada, bikin Rehaan guda in ba a yi shagali ba a bikin wa za a yi?." Daada ta kalle ta ta ce, "kin san halin nunƙufurcinsa, bazai bar shi ya yi abinda ya kamata ba. Da ya yi shagali, da kar ya yi duk ɗaya ne, aure ne wallahi sai an yi." Ta sake kallonsa ganin ko kallon ta bai yi ba ta ce, "batun gidan da za ka zauna, umarni ne ba wai shawarar wani nake nema a nan ba. Ban ce kowa ya ce min komai ba, ban ce kowa ya kawo min shawararsa akan hukuncina ba...." Ta faɗa tana kallon kowa. Kowa ya yi shiru yana jira ya ji me zata ce, har shi Rehaan ɗin so yake ya ji abinda zata faɗa. Daada ta ce, "Ban amince Rehaan ya fita daga gidan nan zuwa wani gida daban ba, ban damu da gidajen da yake dasu a garin nan da wajen garin nan ba, ban damu da yana da gidaje masu yawa ba, umarni ne ba shawara ba, a cikin gidan nan nake so ya zauna. Ɓangarensa ya ishe sa ya zauna da matarsa, dan haka a nan zai zauna ban amince ya fita ba." A lokacin ya ɗaga ido yana kallonta, suka haɗa ido ta ga yadda fuskarsa da idanunsa suka canja, ya ɗan lumshe ido ya buɗe a kanta. Ta ce, "ka ke kallona da wasu idanun ka masu kama da na maguna, ka ji abinda na ce ai ko?." Ya ɗan ɗaga kai yana kallon ta, muryarsa a sanyaye ya ce, "meyasa bakya sona ne Daada? Duk abinda zan yi farin ciki a duniya sai kin hana shi, duk abinda zai saka min walwala sai kin hana. Abinda zai saka ni baƙin ciki a ko yaushe shine burinki, abinda zai ɓata min rai ya hanani walwala shine burin ki. San....." Abba ya dakatar dashi ya ce, "Rehaan!." Ya kalli Abba ya ce, "Abba ka bar ni na faɗa mata, ta ce aure zata yi min da wata yarinya, duk waɗanda suka yi aure a gidan nan kowa an bashi dama ya auri zaɓinsa, amma ni da yake ba a sona an ce ban isa ba, sai dai na auri wacce aka zaɓa min. Ka ce na yi haƙuri kuma na yi, ka ce na yi haƙuri na karɓi auren na haƙura na karɓa, yanzu kuma kana ji tana cewa na zauna a nan..." ya ƙarasa faɗa cikin ɓacin rai, amma maganarsa a hankali take fita, kuma a kakkatse. Mama ta ce, "Rehaan ba ka da kunya ashe? Daada da mahaifinka ka ke faɗawa haka?. Daadan ba ita ta haifi mahaifinka ba, bata isa da kai ba kenan?." Ya kalli Mama zai yi magana Abba ya ce, "Ya isa haka Rehaan, kar ka ce komai." Ya ɗaga kai ya mayar da kansa ƙasa, muryarsa a sanyaye ya ce, "a yaushe haka ka ke cewa kar na ce komai, na yi shiru Abba." Daada ta saki baki tana kallonsa, sai kuma ta gyaɗa tana girgiza kai tana kallonsa ta ce, "lallai jinin indiyawa wuyan ka ya isa yanka....." Ta sake kallonsa ta ce, "Na isa ɗin ne, shiyasa nake yanke duk abinda na ga dama a kan ka. Kuma wallahi sai anyi auren nan, ko za ka sha fiya-fiya ka kashe kan ka sai an ɗaura auren nan da gawar ka. Kuma billahillazi in ka ƙure ni ka ɓata min rai, a yanzu zan kira iyayen ka a ɗaura auren kowa ya huta!. In kana musu ka nuna min ban isa nayi hakan ba." Yana jin yadda Abba yake kallonsa shiyasa bai ce komai ba, ya sunkuyar da kai yana ji kamar ya tashi ya fita amma ba ya son yi saboda Abba, kuma ya san ƙarshe zagin a kan Mamy zai ƙare duk da bata wajan. Mama ta girgiza kai ta ce, "ai sai ya nuna miki shi ba jinin fulani ne gabaɗayansa ba, sai ya nuna miki akwai baragurbi a cikin jininsa." Abba ya ce, "Saddiƙa ya isa...." Ya faɗa yana kallon ta. Abba ya kalli Daada ya ce, "Daada ki cigaba da yanke hukuncin da ki ka ga dama, dole kowa ya bi." Daada ta ce, "daman abinda zan faɗa kenan, kuma dole ayi wallahi, in kuma ban isa ba zan gani." Abba ya ce, "kin isa, tunda ki ka faɗa hakan za a yi." Kafin a sake yin magana Rehaan ya miƙe ya fita daga falon. Yana fita ya ji wayar ta yi ƙara ya ɗauko ya duba, ganin Abba ya kiransa kuma ta katse duk a lokaci ɗaya, sai ya fahimci saƙo ne dan ya dakatar dashi daga barin gidan, ya koma da baya ya tafo ɓangaren Abban ransa a ɓace sosai. Bai jima da zama ba Abban ya shigo ya ga ya jingin da kujera ya lumshe idonsa. Abba ya ƙarasa ya zauna akan kujera yana kallonsa, cikin sanyin murya ya ce, "Rehaan da mahaifiyata ka ke sa'in sa?." Ya ɗago a hankali ya kalli Abba ya ce, "bata yi min adalci ne Abba, bata sona." Yadda ya yi maganar sai dai Abba ya ji tausayinsa, ya san Rehaan ya wuce irin wannan auren, ko a ƙauye an daina irin wannan aure balle a cikin birni, a cikin birnin ma namiji mai kyau da aji da kuɗi kamar Rehaan. Shi da in ya tashi aure zai iya ɗauko ko wacce mace a faɗin duniya ya aura, saboda abinda Allah ya mallaka masa, amma ace shine zai yi irin wannnan auren da ko matar ma bai sani ba. Abba ya tausasa harshe ya ce, "tana sonka mana Rehaan, ya za a yi ta ƙi ka bayan kaima jikan ta ne?." A hankali ya ce, "saboda ni jinin Mamy ne, kuma bata son Mamy." Abba ya ɗan dafe kai cikin rashin jin daɗi ya ce, "ka daina faɗar haka Rehaan, babu wanda Daada bata so a gidan nan." Ya yi shiru bai ce komai ba, dan ya san Abba yana kare mahaifiyarsa ne kawai, amma duk dinga kowa ya san bata son Daada. Abba ya ce, "Rehaan yadda Mamy ta isa da kai haka na Daada ta isa dani, tana da ikon yiwa kowa a cikin ku hukunci. Na tabbata ko me Mamy zata yiwa ɗan da ka haifa baza ka ji komai a ranka ba." So yake ya faɗawa Abba shi Mamy baza ta taɓa yiwa ɗansa dole akan abinda ba ya so ba, amma sai ya kasa ya sunkuyar da kai kawai. Abba ya ce, "nima ita ta haife ni, kana ji tana rantsuwa, zan karya mata rantsuwa ne?." A hankali ya ɗago ya ce, "Amma Abba bana so, meyasa sai ni?. Wallahi Abba ban taɓa jin tsanar abu kamar auren nan ba." Abba ya ce, "ina ba ka haƙuri a madadinta, ina ba ka haƙuri matsayina mahaifinka, dan na san bamu kyauta maka ba. Don Allah ka yi haƙuri ka karɓa. " Rehaan ya ɗaga kai a hankali yana ji kamar ya yi kuka. Abba ya ce, "na faɗa maka in ka aure ta kana da damar auren duk wacce ka ke so daga baya." Ya sauke nunfashi ba tare da ya yi magana ba. Abba ya sake tausasa murya ya ce, "ka yi min alƙawari za ka bar auren nan ya yu, ka ɗaukar min alƙawarin baza ka lalata auren ba, ka yi min alƙawari baza ka sake yin wata magana a kai ba." Ya kalli Abba ya ga shi yake kallo, Abba ya ɗaga ka alamun haka yake nufi. Ya yi shiru ya kasa amsawa, bai san ya zai yi da Abba ba. Abba yace, "alfarma ta farko da na taɓa nema a wajanka wannan ce Rehaan, na san ban kyauta maka ba, amma mahaifiyata nake yiwa biyayya. Ka yi min alƙawari akan hakan?." Ji yake kamar ya yi kuka, Abba ya saka shi a tsaka mai wuya, Abba ya ɗaure sa da jijiyoyin jikinsa. Tsakani da Allah ta ya zai ɗauki alƙawari akan abinda ba ya so, ta ya zai ɗauki alƙawarin da ya san bazai iya cikawa ba?. Abba ya ce, "ina jinka, za ka yi min Rehaan abinda na nema?." A hankali ya ɗaga kai alamun zai yi, Abba ya ce, "ka yi alƙawarin?." Ya jima a haka bai motsa ba, sai kuma ya ɗaga kai alamun ya yi. Abba ya murmusa ya ce, "Na gode sosai, kar ka zama mai saɓa alƙawari a wanann lokacin, a duk lokacin da ƙin auren ya taso maka a zuciyar ka, ina so ka tuna alƙwarin da ka yi min." Shi dai bai motsa ba yana zaune yana ji kamar an saka shi a cikin wuta sbaoda zafin da yake ji. Abba ya ce, "Za ka yi taron biki ne?." Ya ɗago kai ya ce, "Bana so, inda zai yu bana so kowa ya san za a yi auren nan Abba, in dai ba a cikin gidan nan ba, don Allah kar a sani. Ka yi min wannan alfarmar nima!." Abba ya ce, "ta ya auren ka zai ɓuya? Kaima ka san bazai yu ba." "A saka ya yu, a rufe shi ya zama babu wanda ya sani. Ko a falon nan ne ku ɗaura auren ba sai a masallaci ba." Abba ya bisa da kallo ganin da gaske yake maganar ya ce, "Meyasa ba ka so a sani." "Saboda bana so." "Ba ka yi haƙurin ba?." "Na yi Abba, yin haƙurin ne ya saka na ce bana so a sani." Abba ya ce, "shikenan Rehaan, tunda ba ka so a sani zan san abinda zan yi a kai in sha Allah." Rehaan ya ce, "ka san wacece yarinyar?." Abba ya ɗaga kai ya ce, "eh na sani, har na turawa Jafar adireshinta, sai ku je ku gaisa. Tana da kirki sosai, sai da na tabbatar da nagartarta sannan na amince ka aure ta. Rehaan ya yi wani murmushin takaici jin ana yabon yarinyar da ya san wacece ita, wai tana da nagarta. Ya buɗe baki zai yi magana sai ya fasa, ya yi shiru yana jin Abba. Abba ya ce, "ka kwantar da hankalin ka, nima da ace yarinyar bata dace dakai ba bazan amince ba. Kuɗi ne kawai bata kai ka ba, amma komai nata da na haɗa shi da naka iri ɗaya." Ya kawar da kai yana mamakin ya aka yi halinta na banza ya ɓuya ne?. Abba ya ce, "tashi ka je, Allah ya yi albarka. Ina so ka tuna da alƙawari kaya ne." Ya amsa da amin ya tashi ya fita, ɓangarensa ya koma sai kuma ya sakko ya shiga mota aka ja shi ya fita. •••••• Islaha tana gidansu Safeera a kwance kamar mai zazzaɓi, gabaɗaya jikinta babu ƙarfi sai kwanciya take yi a duk inda ta samu dama. Safeera ce take ta rarrashinta, ita dai sai dai ta ɗaga kai amma Allah kaɗai yasan yadda ta damuwa ɓatan masoyinta. Sai da ta yi sallar magrib sannan ta fito, a hankali suke tafiya babu wanda yake yiwa wani magana dan bata da nutsuwa balle ta ce wani abun. A lokacin wata baƙar motar ta wuce su ta yi parking gab da ƙofar gidansu Saheer, basu kula da ita ba suka cigaba da tafiya a nutse har suka zo inda motar take. Suna zuwa wajan aka buɗe motar murfin motar ta tare musu hanta, suka kalli motar a tare suka ɗauke kai. Wani mutum sanye da baƙaƙen kaya ya fito ya ce, "Barka Islaha." Ta ɗan tsaya ta kalle sa, ganin bata san shi ba sai ta sake ɗaure fuska a daƙile ta ce, "barka" ta faɗa tana niyar barin wajan. "In ba za ki damu ba ina so zan yi wata ƙaramar magana dake." Ta ɗan juyo ta ce, "gaskiya zan damu, na gode." Ya yi murmushi jin amsar da ta bashi ya ce, "magana ce akan ɓatan Saheer." Cak ta tsaya tare da waiwayowa ta kalle shi ta ce, "me ya faru?." Ya kalli Safeera ya sake kallon Islaha ya ce, "Ina so ki shiga motar nan, akwai inda nake so mu je, in sha Allah za ki samu mafita akan matsalar ki." Islaha ta kalli Safeera da take kallon mutumin ta ce, "kamar ya ta shiga mota?." Ya kalli Safeera ya ce, "yi haƙuri Safeera, ba cutar sa ita zan yi ba." Safeera ta buɗe ido jin ya kira sunanta, sai ya yi murmushi ya ce, "Babu abinda zan yi mata na cutarwa, kawai ina so ta shiga motar ne, ni kuma zan kai ta inda zata samu maganin damuwarta in sha Allah." Islaha ta kalle sa a kaikaice ta ce, "sai aka ce maka ina buƙatar taimakon ka ne?." Ya ɗan murmusa dan kafin ya zo an karanta masa halayenta ya ce, "ko ba ki ce ba kina da buƙata, ki shiga kawai." Ta harare sa, hararar up and down ta ce, "Bazan shiga ba, da kai da maganin damuwar ta ka ku je bana buƙata." Ta juya zata bar wajan ya ce, "in ba ki shiga ba za ki yi danasani Islaha, zai fi miki ki zo ki shiga mu je." "Sai maimaitawa ka ke yi kana cewa baza ka cuce ni ba, yadda ka ke faɗa ya tabbatar min da kai ɗin macuci ne. Bazan shiga ba, in ka ga za ka ɗauke ni ka saka a motar sai ka yi. Aikin banza kawai, baka san me yake damun mutum ba ka zo ka ishe sa da surutan banzada wofi!" Ta faɗa a fusace tana kallonsa. Maimakon ya ji haushi sai ya yi murmushi ya ce, "ki yi haƙuri, ban faɗa dan na ɓata miki rai ba. Amma don Allah ki shiga motar nan mu je." Ta ja wani dogon tsaki ta yi gaba abinta. Safeera ta kalle shi ta ce, "to kai akan me ka takura sai ta shiga motar ka ne? Ka ƙyaleta mana, ko ana dole?." Ya ɗan yi murmushi ya ce, "Ba a dole, amma ana buƙatar ta shiga ɗin." Safeera itama ta yi tsaki ta bi bayan Islaha da ta shige gida abinta. Waya ya ɗauko yana dannawa kafin ya saka a kunne, cikin ladabi da gimamawa ya ce, "ta ƙi shiga motar Sir." Ya yi shiru alamun ana bashi amsa kafin ya ce, "Okay Sir" ya faɗa yana kashe wayar ya shiga mota ya bar unguwar. Nana Haleema. [7/27, 11:49 AM] KRBBK: RDB2P88 Nana Haleema. Washe gari har aka yi sallar azahar bata fito ba, tana ɗaki a kwance ko breakfast ta kasa yi. Tana ji ana zancen za a siyar da gidan da ake ciki a karɓo Saheer bata iya fitowa ba, sai daga baya ta miƙe ta yi wanka ta shirya ta fito daga gidan. Gidan radio ta yi nufin zuwa dan ta kai koken ta ko Allah zai saka mutane su ji su taimaka mata, bata so ta je gidan radion da take aiki, shiyasa kawai ta hau napep ta tafi ko Safeera bata faɗawa ba. Kallon window napep ɗin take yana tafiya a hankali, a haka ya ɗauki passenger maza guda biyi ita dai tana zaune bata ce komai ba, dan inda sabo an saba haɗa mata da maza a napep guda ɗaya. Islaga sai ta ga ya canja hana, gabaɗaya bai ɗauki hanyar da ta ce masa zata je ba. Kasancewar bata da duhun kai sai ta ce, "A'a, Malam ina za ka je ne? Ni ba nan na yi ba." Ya yi shiru bai ce mata komai ba sai cigaba da tafiya da ya yi bai motsa ba. Islaha ta ce, "magana nake yi maka fa, ina za ka kai ni?..." Nan ma ya yi shiru bai ce komai ba, ta fusata ta ce, "Wallahi zan yi....." Ɗiff maganar ta tsaya, yi jin wani abu kamar bindinga daga gefenta. Ta buɗe ido ta kalli wajen a hankali, ta ga bindinga ce wanda yake zaune a gefenta ya saka mata alamun ta yi shiru. Ta kalli fuskarsa ta ganta a buɗe bai rufe ba, amma ba ita yake kallo ba titi yake kallo. Ta yi ɗif, duk rashin kunya da tsiwar sai ta yi shiru gabanta yana faɗuwa. Islaha ta fara tunane-tunane, tana tunanin ta faɗa ta gefe kawai, dan gwara ta faɗa ta window tunda bata san inda zasu kai ta ba. Ta dinga kallon gefenta tana so ta faɗa amma tana jin tsoro, dan motoci suna ta kai kawo a wajen. Tana wannan tunanin suka shiga estate ɗin da babu yawan mutane a cikinsa sai manyan gidaje kamar su yi magana da bakinsu. Abin mamaki wani bababn gida ta ga an yi horn an buɗe sun shiga da napep, har lokacin bindigar tana gefenta bai cire ba kuma bai yi magana ba. Suna tsayawa duk suka fita, ɗaya ya kalle ya ce, "fito." Duk da tsoron da take ji hakan bai hanata ta ce, "bazan fito ba, ina ne nan?." Ya ɗan yi murmushi dan an zana musu halayenta tsaf, duk sun san zata yi taurin kai. Ya ce, "za ki fito ko sai na fasa kan ki?." Ta runtse ido ganin yana nuna ta da bindiga, fito daga napep ɗin ba dan komai ba, sai dan bata so ta mutu bata sake ganin fuskar Hamma ba. Ya nuna mata wata ƙofa ya ce, "ki je ki shiga wannan ƙofar yanzun nan." Bata ce komai ba ta bi wajen da ya nuna mata, dan sai take ji kamar umarni kawai yake bata. A hankali ta shiga falon da yake da haske ko ina, ta tsaya a falon tana kallo dan bata san me zata yi ba. Gashi dai bai yi kama da sato ta da aka yi a wancan lokacin ba, amma wannan ɗin ma sata ce tunda ba a son ranta aka ɗauko ta ba. A wannan lokacin Jafar ya fito daga kitchen yana amsa waya, jin maganar mutum sai ta kalli wajan suka haɗa ido. Jafar ya ɗan zaro ido waje cikin mamakin ganinta, ya katse wayar ya kalle ta ya ce, "Miss Islaha." Fuskar ta babu walwala ta ce, "Mr Jafar me na yi maka ka saka aka kawo ni nan?." Yadda ta yi maganar cikin sanyi ya saka ya ce, "ki zauna miss, amma bani na saka aka kawo ki ba." Islaha bata zauna ba, ta kalle sa ta ce, "To waye?." Kafin ya bata amsa aka buɗe wata ƙofa, ta kai kallonta wajan ta gan shi ya fito cikin jallabiyya brown mai kyau da ɗaukar ido. Kwata-kwata ba inda take tsaye yake kallo ba, ita kuma shi take kallo cikin mamaki da a'aljabi haɗi da takaicin sake arba da fuskarsa a duniya. Lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta take faɗa mata kenan dai shine ya sake sato ta a karo na biyu, tunda ga shi ya saka an nuna mata bindiga an kawo ta inda bata yi niya ba. Jafar tunda ya fito yake kallonsa, sai ya yi murmushi ya kalli Islaha ganin ta zuba masa ido tana binsa da kallon mamaki da wata irin fuska ta marasa mutunci. Ya gyara tsayuwa dan yana so ya ga yadda za a kwashe tsakanin mai girman kai da mai rashin kunya. Kafin ya gama tunanin yadda abin zai kasance Islaha ta ce, "Wannan abin ne ya saka a ɗauko ni kenan...." sai ta kalli Jafar ta ce, "akan wanne dalili zai ɗauko ni? Sata ko kisan kai?." Jafar ya yi dariya ya ce, "ban sani ba, nima na gan ki ne kawai" "To ya saka a mayar dani inda aka ɗauko ni, ina da abubuwan yi da yawa ba zaman banza nake yi ba. Meye haɗina dashi da zai saka a kawo ni nan? Ko an faɗa masa yanzu dah da zai sace ni ya kwana lafiya?." Jafar murmushi yake yi ya ce "ask him." Ta juya ta kalle shi, ta ga ya zauna akan kujara kamar ma bai san dashi take magana ba. Wani irin takaici ya mamaye mata zuciya, ita ko magana dashi ma bata so balle har ta tambaye shi dalili, tunda ya ce mata ƴar iska karuwa take jin bata taɓa jin tsanar kowa kamar yadda take jin tsanarsa ba. Ta kasa magana, ta yi shiru ba dan ta kasa ba, sai dan takaicin da yake gangaro daga zuciyarta. Falon ya yi shiru babu wanda yake magana a cikinsu, kowa ya yi shiru ba kamar Rehaan da ya yi banza da ita. Islaha ta katse shirun ta ce, "Ina da wani personal agender da kai da za ka saka a kawo ni nan?." A lokacin ya ɗago ya kalle ta suka haɗa ido, ta ƙi ɗauke idonta daga cikin nasa ta ce, "Tun muna shaida juna da kai, ka saka a mayar dani inda ka ɗauko ni, ni ba ƴar tsana bace da za ka sace a duk lokacin da ka ga dama." Ya ɗauke kai daga kanta ya yi mata banza, takaicinta da haushi da tsana ya hana shi magana, bai san haka yake ji a kanta ba sai yanzu da take tsaye a gabansa, sai ya ji a baya ba komai yake ji ba kamar abinda yake ji yanzu. Takaici ya kusa kai Islaha lahira, ga shi bata da wani ƙarfi yadda ya kamata balle ta yi masa hauka, raunin zuciyarta ya taɓa mata gangar jikinta, ta yi sanyi sosai, ba dan haka ba da sai ta ɗauki wani abun ta fasa masa kai. Jafar dai yana zaune yana so ya ga ta inda Rehaan zai fara, haka kawai ya ɗauko ƴar mutane shi ya fi ƙarfin ya je gidansu. Rehaan kamar zai yi magana sai ya fasa, ya ɗago ya sake kallon Islaha yana maimaita kalmar future wife ɗinsa ce a tsaye a gabansa, ya ɗauke kai ya gyara zama bai ce mata komai ba. Islaha ta kalli Jafar ta ce, "don Allah ka saka a mayar dani gida, ina da abinda zan yi da yawa. Bani da lokacin wannan shirmen, bani da lokacin ɗaga murya a yanzu, ko wanne second na lokacina yana da mahimmaci a gare ni." Jafar ya yi murmushi yana jan kujerar dining ya zauna ya ce, "Bani na ɗauko ki ba Islaha, shine ya saka aka ɗauko ki." "To me zai yi min da zai saka a ɗauko ni?." "Ki tambaye shi." "Wallahi baƙin ciki da haushinsa zai iya sakawa na shaƙe shi har sai ya daina numfashi. Bana ɗaukar abinda kowa zai iya ɗauka, zuciyata daban take da ta sauran mutane, abinda nake ji daban da na sauran mutane, bazan shiga lamarinka ba, kaima kar ka shiga nawa." Jafar da ya ga dai Rehaan ɓata mata lokaci zai yi sai ya ce, "ya ɗauko ki ne akan maganar auren ku." Ta ɗan yi jim tana kallonsa kafin ta ce, "auren mu, ban gane ba." Jafar ya ce, "eh auren ku, kin manta za ki yi aure ranar friday?." "Ni ban gane ba fa, kamar ya zan yi aure ranar friday?." Jafar ya ce, "kin gane mana, ai na san kin san da auren da aka ce za a yi miki ko?." Islaha sai ta tuna da maganar Baffa ta ce, "oh! Wai shine daman wanda ake so a liƙa min ɗin nan?." Jafar ya girgiza kai yana dariya bai ce komai ba, yadda ta yi maganar ta bashi dariya sosai, wai wanda ake so a liƙa mata. Ta ce, "yanzu na gane, sunan ya zo ɗaya da sunan mahaifin wanda aka faɗa min....." Ta yi wani murmushin rainin hankali ta ce, "To ba a faɗa masa cewa na ce bana yi a kai kasuwa ba? Ko faɗa masa aka yi na rasa masu sona ne da har za a yi min tallansa har cikin gida?." Jafar ya ɗage kafaɗa ya ce, "ask him Miss." Ta kalle Rehaan da ba ita yake kallo ba ta ce, "babu wani aure a tsakanina da kai, magana ta baki ma baza ta sake haɗa ni da kai ba har abada balle aure. Ni ina da wanda zan aura, tallan aurenka da aka kai min kuna a kai kasuwa, ni a wajena bani da lokacin magana da kai balle auren ka....." Ta dakata tana harɗe hannu a ƙirji ta ce, "Malam zan ce maka ko Alhaji? Ka saka a mayar dani kamar yadda ka ɗauko ni." Sai a lokacin ya ce, "So go and tell your father to inform Abba about what you said, so the marriage can be called off." Ta bisa da harara tana yi masa kallon up and down ta ce, "gani ga ka ai, ba sai an faɗawa kowa ba. Na ce maka bana yi, sai a haƙura ko?." Rehaan ya lumshe ido yana jin ɗan dama dama a ransa, jin ta ce bata so kuma baza a yi auren ba ya yi masa daɗi, ko haushin rashin kunyar ma ba ya ji, tunda bata so abin ya zo da sauƙi. Ya ce, "Kina da plan mai girma a kaina, kina shigowa rayuwata ta ko wanne ɓangare. Yanzu kuma kin zo ta ɓangarren aure...ina so na faɗa miki, ni Rehaan na fi ƙarfin ki, ki canja tunani." "Hey Mr man! In na shiga rayuwar ka na ce na shiga rayuwar wa?...." Ta nuna sa da yatsa ta ce, "na ce na shiga rayuwar Rehaan Yola? To na samu ribar me?." "Mr man ina so ka faɗa min da ni da kai waye ya shiga rayuwa wani, sannan ka tuna har gida aka kai min katin gayyatar auren ka, ka ga ni nake da bakin da zance nafi ƙarfin ka, tunda kai aka kawo min tallah, ba ni aka kai maka tallah ba....." Ta yi dariyar rainin hankali ta ce, "Ai ban san arhar ta ka ta kai haka ba, ban san rashin class da ƙaryar iyayin naka a nan ya tsaya ba. Tunda aka ɗauko tallan auren ka, aka zo har gida aka samu mahaifina, ana neman na amince na taimaka na aure ka, ka dawo zero percent a idanuna..." "Ka jira lokacin da aka kai maka tallan Islaha, daga lokacin ne ka ke da bakin cewa ta canja tunani, amma daga lokacin da aka je aka zauna da mahaifinta, aka ce an gani ana so na amince nace ina yi, na fi ƙarfin waɗannan kalaman na kan harshen ka. Ba ni da lokacin ɓatawa, ka bar maganar, dan bazai yu ba har abada!." Shiru ya yi bai ce komai ba, zata sake magana ya buɗe idanunsa cikin nata ya ce, "shut up! Bana buƙatar ki yi magana...." Ya nuna ta da yatsa ya ce, " Kin yi nasarar shiga rayuwata, kin yi nasarar da ki ka saka iyayena suka amince dake, kuma kin yi nasara ina yia iyayena biyayya akan duk abinda suka ce na yi." Zata sake magana ya katse ta ya ce, "I will marry you for five months as a contract, because of my father's command." Banzan kallo ta yi masa sannan ta ce, "bana buƙata, bani da ra'ayi balle har na aure ka na zauna da kai a ƙarƙashin contract. Ka je ka samu wata amma ba Islaha ba, ita tace bata yi ka haƙura ko ka yi danassani. She's not your type, and she's not your class. An kawo min talla na ce kuma bazan siya, a kai wani gidan zasu iya tayawa!." Ta kalli Jafar da yake kallon ikon Allah, duk da ba ɗaga murya take yi in tana maganar ba, amma ya san maganar tana shigar Rehaan. Shi dai yana so ya ga an yi auren nan dan ya ga ya abin zai kasance, amma ya san abu ne mai wahala matuƙa wajan yuwar auren. Islaha ta kalli Jafar ta ce, "please ka saka a mayar dani, bana son tsayuwa a nan ko kaɗan." Jafar ya miƙe yana murmushi ya kalli Rehaan da kamar bai san abinda aka yi ba. Ya buɗewa Islaha ƙofa ya ce, "ki je mota, zasu mayar dake Miss." "Na gode....." Ta ɗan waiwayo tana kallo Jazy, ta nuna masa Rehaan da hannu sannan ta ce, "Ka faɗa masa kar ya sake gangancin sace ni, ni ba toy ba ce da zai ɗauko duk lokacin da ya ga dama, ni ba sa'arsa ba ce, ya sace wasu ya zauna lafiya, amma ban dani. Maganar aure kuma a kai tallah social media, a rabawa bloggers details ɗinsa wataƙila a dace, baza a rasa masu buƙata ba. Wannan Islahan ta Saheer ce, ya je ya dage ya cigaba da advert, zai iya dacewa wata ƴar wahalar ta gani ta ya, amma ba da nan" ta faɗa tana nuna kanta sannan ta juya ta fita da sauri. Wai ta ya auren nan zai yu ne? Rehaan ya ɓullo da auren yarjejeniya, ya abin zai kassance ne?💃🏻🤣 [7/28, 12:20 PM] KRBBK: RDB2P89 Nana Haleema. Jafar ya kalle shi bayan ta fita ya ce, "Rehaan wanne irin auren yarjeniya kamar a america? Meye hakan?." Bai kalle sa ba sai shiru da ya yi ya zubawa waje ɗaya ido, yana tuna kalamanta yana jin zafi a ransa, kuma ba kowa ya jawo masa wannan rainin ba sai Abba. Jafar ya ɗauki takardar da ya ajjiye ya ga takardar contract ɗin ce, har ya tsara rules da komai, an yi printing, ga inda zata saka hannu ga inda zai saka hannu. Jafar ya kalle shi cikin fusata ya ce, "wani lokacin in ka yi wani abun kamar a rufe ka da duka wallahi, yanzu meye wannan don Allah? Kana musulmi gaba da baya za ka wani ƙirƙiri auren yarjejeniya?." Ya ɗago ya kalle shi ya ce, "Na yiwa Abba alƙawari, Abba bai taɓa neman abu a wajena ba sai wannan lokacin, kuma na ce zan yi. Ka fi kowa sanin bana son auren nan, kuma bazan so ba, bana son yarinyar, kuma bazan so ta ba. Gwara a gina auren a ƙarƙashin contract, in na san auren yana tafiya akan lokacinsa zai fi min sauƙi." Ya girgiza kai ya ce, "hakan bai kamace ka ba ko kaɗan, bai kamata ka gina auren a ƙarƙashin yarjejniya ba. Kuma in na yarjejeniyar ne, ina laifin na shekara ɗaya, sai ka saka wata biyar?." Ya ɗago ya kalle sa ya ce, "kwana na yi ina tunanin maganar nan, ban taɓa tunanin wani abu a rayuwata kamar wannan ba. Wata biyar ɗin ma ya yi min yawa, in kwanakin basu yi ƙasa ba bazai yi sama ba." Jafar ya ce, "to ga shi nan ai ta ƙi yarda." Ya ɗan girgiza kai ya ce, "daman saboda Abba nake yi, kuma ya ce baya so ya ji wata matsala daga side ɗina, in daga ɓangarenta ne wannan bai dame ni ba daman ba so nake yi ba. Me zan yi da wannan abar?." Jafar ya murmusa ya ce, "Ikon Allah, ni dai zan ga ta wannan abin nan zai yu." "Shiyasa nake ji kamar na je na matse tsohuwar can na zuba mata poison ta haɗɗiye ta mutu. Allah ban taɓa jin haushinta kamar wannan lokaci ba." Ya yi dariya ya ce, "gaskiya dai, haka kawai ta ɗauko maka aure." "Auren ma da wannan yarinyar, wacce ta gama...." Jafar ya yi dakatar dashi ya ce, "za ka yi bayani da larabci a gaban Allah, babu ruwana." Ya girgiza kai Jafar ya cigaba da karata rules ɗin takardar, ya kalle shi ya ce, "auren ka bazai zama na sirri ba fa, dole za a sani." Ya girgiza kai bai ce komai ba Jafar da yake kallon abinda yake cikin takardar ta ce, "wannan aure dai za ku gina shi akan abinda ku ka ga dama ne, babu ruwan wani da wani kenan?." Rehaan bai ce masa komai ba, Jafar ta gama karanta takardar kafin ya ajjiye masa ya miƙe ya shiga ciki. Shi kuma Rehaan fita ya yi daga gidan yana so ya je inda dangin Mamy suka sauka. Islaha tana fitowa ta ga baƙar motar tana jiranta, ta kalli mutumin da ya tare ta a daren jiya yana cewa ta shiga motarsa. Ba dan bata san hanya ba wallahi babu abinda zai saka ta shiga motar, ta yi ƙwafa ta shiga suka tafi. A ƙofar gidan suka ajjiye ta, tana sauka daga motar suks haɗa ido da Sadik shi da Safeera sun fito daga gidan. Ta ƙaraso wajan duk kallonta suke yi Safeera ta ce, "Daga ina haka?." Islaha ta kalle su ta ce, "wani waje." Safeera ta ce, "ina ne wajan?." Ta kalle ta sannan ta kalli Sadik ta ce, "in na faɗa mu ku ba yarda za kuyi ba, za ku ce ƙarya nake yi. Gwara na yi shiru da maganar." Safeeta ta ce, "baza mu ƙaryata ki ba, ki faɗa kawai." Ta ɗan shiru kamar mai tunani sannan ta ce, "ina zuwa, bara na yi sallar la'asar" ta faɗa tana shiga gidan suka bita da kallo. A zauneta same su a harabar gidan cikin inuwa, ta ƙaraso ta zauna ta ce, "Hamma Sadik ya batun mutanen nan? Sun sake yin wayar ne?." Ya girgiza kai ya ce, "basu yi ba, har yanzu shiru." "Batun kuɗin fa." "To an dai saka gidan nan a kasuwa, har yanzu ba a samu masu siya ba wallahi. Gona dai an taya, muna jira mu ji ko zasu siya." Islaha ta ta yi shiru bata ce komai ba. Safeera ta ce, "muna jin ki." Ta ɗago ta ce, "Ban san me yasa ba, amma ina ji a raina akwai wani abun ba daidai ba." Safeera ta ce, "na me kenan?." "Akan Baffa nake magana, washe garin ranar da aka rasa Hamma ya kira ni wai wasu sun zo neman aurena kuma ya amince musu, dan kar ya bada ni ne naga kamar bai kyauta min ba, amma da yanzu ya ce ya basu ni." Sadik ya ce, "Nima ya faɗa min maganar." Ta ɗan kalle sa ta ce, "ashe ka sani ma. Ban san meyasa Baffa ya yi haka ba, kamar ya manta da Hamma? Kamar ba shine yake cewa zai aurawa Hamma ni na kusa ba." Safeera ta ce, "wai Baffa da kansa ne ya ce haka?." "Shine." "to ya batun auren ki da Hamma?." "Nima ban san meyasa ya ce haka ba, ban san meyasa Baffa ya canja ra'ayinsa akan aurena da Hamma ba. Abinda na sani ko waye bazan amince ba, auren Hamma ya fi min auren kowa a duniyar nan. Duk kuɗin mutum ba ya gabana, indai Hamma yana da rai ni mallakinsa ce." Sadik ya numfasa ya ce, "abin ne da ɗaure kai, ba a satin nan Baffa ya ce zai ɗaura auren ku ba?." Islaha ta ce, "juma'a mai zuwa ya ce, amma yanzu an canja ya koma wani daban ba shi ba." Ya ɗaga kai ya ce, "Kuma na tabbatar Saheer ɗin bai sani ba, kuma wannan maganar cutar dashi zata yi ba kaɗan ba." Islaha ta ce, "shine abinda nake ji, tsakani da Allah ta ya za a ce haka?." Safeera ta ce, "Wai waye wanda za ki aura ɗin? Su waye suka zo neman auren ki?." Ta ɗan kalle su sai kuma ta ja tsaki ta ce, "Lokacin da ya faɗa min bai faɗa min sunan waye ba, ya dai faɗa min sunan mahaifinsa mutumin. Ɗan gidan Alhaji AbdulAziz Yola ne." A tare suka zaro ido waje cikin mamakin sunan wanda ta faɗa Sadik ya ce, "kai! Wai shi ne da kansa ya aiko nemawa ɗansa auren ki?." Islaha ta ce, "abin kamar plan ko? Ni kaina ina ganin abin kamar tsarawa aka yi." Sadik ya ce, "Gaskiya akwai ayar tambaya a kan maganar nan." "Ni dai taimako bai yi min rana ba, haka kawai na tsinci wata tsohuwa a hanya na taimaka mata, ashe wai itace babar AbdulAziz Yola ɗin." Safeera ta ce, "Gaskiya dai lamarin nan kamar plan, kawai dan kin taimaka mata sai a aura miki jikanta?." Sadik ya ce, "Wanne ɗan nasa a cikin yaran? An ce yaransa kaf suna da aure, wanne daga ciki ne zai ƙara aure a cikinsu?." Ta ɗan yi jimm tana tunanin ta faɗa musu ko ta yi shiru, ta kalle su ta ga duk ita suke kallo alamun suna jiran amsa. Sai ta ɗan ja tsaki ta ce, "ku share kawai, sanin waye ba shi da mahimmaci a halin da mu ke ciki. Yanzu ma da ku ka ga an sauke ni a mota shi mutumin ne ya saka aka kai ni can...." Sai ta kalli Safeera ta ce, "Jiya da wani yake bina yana cewa na zo na shiga mota?” Ta faɗa da sigar tambaya. Safeera ta ce, "eh." "Ashe shine ya aiko shi wajena. Har yana faɗa min mahaifinsa ne yake son auren ba shi ba, shi bazai aure ni dan yana so ba, dan haka zai aure ni saboda mahaifinsa ya ce ya aure ni. Mtsw! Sai ka ce an faɗa masa nima aurensa zan yi, ko maza sun ƙare a duniya ba gwara na mutu babu aure ba, balle ina da Hammana." Sadik ya ce, "Ba ki faɗa mana waye ba." Ta ɗan sake yin shiru kafin ta ce, "ba shi da wani mahimmaci, ku manta kawai. Mu caigaba da neman kuɗin fansar Hamma." Suka cigaba da tattaunawa akan yadda za a yi. Islaha abu kaɗan sai ta yi tsaki saboda takaicin Rehaan, a haka suka gama zaman basu samo mafita ba, ta shiga gida Safeera ta tafi shima ya tafi gida. Rehaan tunda ya shiga gidan da dangin babarsa suke yake jin kansa cikin ƴanci da walwala. Dukkansu indiyawa ne, gabaɗaya basa jin wani yare in ba hindi ba sai english. Har gwara Yayar Mamy tana iya yin hausa kaɗan-kaɗan. Suna ta hira gabaɗaya, sun hanashi motsi kowa yana bashi labari ana bashi tsarabar da aka kawo masa. Shi dai tana kusa da Mamy a zaune, sai Yayar Mamy a zaune a gefensa sun saka shi a tsakiya. Yana murmuahi ya ce, "Fateema bata zo ba?." Mamy ta ce, "Tana wajan aiki, ta ce aiki ya yi mata yawa, amma ta ce zata zo." Ya ɗan gyaɗa kai bai ce komai ba yana kallon su gabaɗayansu. Yayar Mamy mai suna Sanah ta ce, "ga mu gabaɗaya mun haɗu, amma babu Sofia, ko tana da rai, ko bata da rai Allah ne ya sani." Rehaan ya ce, "Mama wai meye silar barinta cikin ku? Ya aka yi ta ɓata har aka neme ta aka rasa?." Wacce ya kira da Mama ta ce, "Tunda mahaifiyarka ta auri ɗan Nigeira kuma bafutalani take sha'awar auren irinsu. Gabaɗaya sai aka ƙi bata goyan baya kamar yadda aka bawa Mamy goyan bayan auren mahaifin ku...." Ta ɗan sauke nunfashi kaɗan ta ce, "Shine aka wayi gari ta bar gida, daga baya sai ta tura mana hotunan ɗaurin aurenta da mijin. Amma ita mijin ta ɗan Kano ne ba nan ba, mun nemi ta dawo bata dawo ba, kuma bata faɗa mana inda take ba. Tun muna samunta a waya har muka daina, mu neme ta ko ina bamu samu ba. Gashi bamu san mijinta da ahlinsa ba balle mu neme ta. Shekarun da yawa, dan ba a jima da haihuwar ka ba aka yi hakan. Rehaan ya ɗan yi shiru sannan ya ce, "in tana da rai za a ganta wani lokacin, in bata da rai kuma Allah ya nuna mana ahlinta in ta bari." Ya riƙe hannun Mama da Mamy ya ce, "ku cigaba da addu'a, Allah zai bayyana ta." Sanah ta shafa kansa ta ce, "Allah ya sa." Ya ɗan yi murmushi kawai. Sanah ta ce, "ashe da kai za a haɗa ayi auren." Ya ɗan sauke kai ƙasa kafin ya ce, "Mama bana so kowa ya san da maganar nan, zan bi umarnin Abba ne ba dan ina so ba." Sanah ta ɗaga kai tana shafa kansa ta ce, "Allah ya cigaba da ɗaukaka ka." Suka amsa da amin kafin ya yi musu sallama ya tafi bayan ya ci abinci. Da daddare Baffa ya kira Islaha akan maganarsu, Islaha ta shiga da sallama ta zuna akan carpet. Ya kalle ta ya ce, "Islaha mun yi magana ranar nan ba ki ce min komai ba, ni kuma ina jiran amsar ki na ke yi." Islaha ta kalli Baffa ta ce, "Baffa wacce magana kenan?." "Akan auren ki da ɗan AbdulAziz Yola, ranar juma'a suke son ɗaura auren." Ta sunkuyar da kai ta ce, "Baffa don Allah ka daina faɗar maganar nan, in wani laifi na yi maka ka ke so ka aurar dani ga wanin Hamma don Allah ka yi haƙuri ka yafe min. Baffa in kuma shine ya yi maka laifi har ka ke so ka aurar ga waninsa don Allah ka yafe masa, amma ka daina faɗar maganar auren don Allah." Baffa ya ɗan yi shiru yana kallon ta sai ya yi sauke ajiyar zuciya ya ce, "Islaha Saheer ba ya nan, babu lallai ya dawo, ni a jikina nake jin Saheer ya tafi kenan, sai dai mu yi masa fatan Allah ya sa ya cika da imani." Islaha ta ɗago kai ta kalli Baffa hawaye ya sakko daga idonta, ta girgiza kai ta ce, "Baffa Hamma bazai mutu ba, ka daina faɗa don Allah." Baffa ya ce, "Islaha kalle ni." Ta ɗago a hankali ta kalle sa sai ta sauke kai ƙasa saboda biyayya bata son kallon idanunsa. Baffa ya ce, "A wanne matsayi ki ka ɗauke ni a duniya?." Muryar ta tana cracking ta ce, "a matsayin mahaifina, ban san waye ya haife ni ba, kai nake kallo a matsayin mahaifi wanda ya kawo ni duniya." Baffa ya ji daɗin amsar ta sannan ya ce, "To ki yarda bazan yi miki zaɓi wanda zai cutar dake ba. Na fi kowa ƙaunar auren ki da Saheer, na fi kowa son ki auri Saheer saboda yadda nake son tarbiyyar ki, ina ƙwaɗayin ki amsa sunan ƴata kuma matar ɗana, in ƙwaɗayin na samu iri daga jinin ki. Islaha tunda ki ka ji na janye kalamaina akan auren, tunda ki ka ji na ce ga wani ba Saheer ba, kin san ina da hujja mai ƙarfi akan hakan. Ko kina ganin zan cuce ki ne?." Ta girgiza kai tana hawaye, ta kasa magana sai hawayen da yake sakko mata, kalaman Baffa hr jininta take jinsu. Baffa ya ce, "To ki saka a ranki ina guje miki faɗawa inda za ki sha wahala ne shiyasa na zaɓi wani na bar Saheer. A matsayina na uba a gare ki, bazan so na ga za ki faɗa wuta na ƙyale ki ba, duk yadda zan yi zan riƙe hannun ki na tabbatar kin wuce ba tare da wutar ta taɓa ki ba." Islaha ta yi shiru bata ce komai ba tana goge hawaye ta kasa magana kwata-kwata. Baffa ya ce, "Ki yi haƙuri, na san kina son Saheer, kuma kina burin mallakar Saheer a matsayin mijinki. Kuma na san abin zai zo miki bazata, amma nan gaba za ki gane abinda nake hango miki a yanzu. A yanzu bazan amince da auren ki da Saheer ba, ko da yana nan bazan yarda ya aure ki ba balle kuma baya nan. Masu garkuwa da mutanen nan in suka kama kashewa suke yi, ni jikina yana bani bazasu taɓa sakin Saheer ba. Shiyasa nake so ki amince da abinda na zo miki dashi, dan ni na ari bakin ki na ci albasa, na sanar da su kin amince." Iskaha ra fashe da kuka mai sauti ta rarrafa ta riƙe ƙafar Baffa ta ce, "Baffa Hamma ba ya nan, an sace Hamma, an yi garkuwa dashi ana neman kuɗin fansa. Don Allah Baffa ka bar maganar nan, ni bazan iya auren wani in ba Hamma ba, bazan iya yin aure Hamma ba ya nan ba, ko da yana nan bazan iya kallon wani namiji a matsayin mijina ba in ba shi ba. Don Allah Baffa ka daina faɗar za ka aurar dani ga wani, don Allah ka bar maganar nan, tana saka min bugun zuciya." Baffa ya bita da kallo ganin yadda take kuka da zuciya da jikinta, sai ta ba shi tausayi mai tsanani, amma duk da haka ba ya tunanin a ransa zai amince ta auri Saheer. Ya shafa kanta ya ce, "Shikenan, ki yi shiru ki bar kuka. Na ji na bar maganar sai Hamman ki ya bayyana. Ki daina kuka." Ta kifa kanta a guiwar Baffa tana kuka sosai. Ya yi shiru ya ƙyaleta tana kukan, sai da ta gaji dan kanta sannan ta ɗago ta goge idonta, ta kalle sa ta ce, "Na gode Baffa." Ya yi murmushi ya ce, "tashi ki je." Ta miƙe a hankali ta fita daga ɗakin. Baffa ya sauke numfashi ya ce, "A haka za a yi auren, bazan zuba ido rayuwarta ta lalace ba. Zuwa nan gaba zata saba, in bata so nan gaba zata so, in bata gane ba nan gaba zata gane” Baffa ya faɗa yana kallon Inda Islaha ta bi, dan bazai taɓa bari ta auri Saheer ba, duk hanyar da ya san zai bi dan kuɓutar da Islaha daga auren Saheer zai yi, bazai taɓa bari rayuwarta ta lalace ba. Nana Haleema [7/28, 12:20 PM] KRBBK: RDB2P90 Nana Haleema. "Ki gudu Sudaisa, kina da damar da za ki gudu yanzu, ki tafi bana so wani ya yi nasarar amsa sunan mijin ki." Sudaisa tana kuka ta ce, "bazan iya ba, bazan iya tafiya na bar ka ba." "Za ki iya, ki tafi Sudaisa." "A'a, bazan iya tafiya ba bar ka ba." Kafin Sudais ya yi magana aka damƙo wuyansa ana jansa a ƙasa, Sudaisa ta bi yo bayansu tana kuka ta tarar an ajjiye sa a gaban Arɗo da yake zaune. Aka nuna maaa Sudais ya ce, "Shawara yake bawa amaryar Black akan ta gudu." Arɗo ya kalli Sudaisa ya kalle ta, bai ce komai ba sai ƙarar sautin bingida suka ji, Sudais ya faɗi a ƙasa alamun shi aka harba, ita kuma ta zube a ƙasa a sume. Arɗo ya kalli kowa na wajen ya ce, "Na jima ina tausayinsa, amma shi ba ya tausayin kansa. Ƙarshen mara jin magana kenan, duk wanda ya bawa wani shawarar gudawa ƙarshensa kenan." Ya kalli Sudaisa sa take a sume ya ce, "Ina ɗayan nan da nake ganin su a tare? A je a zo dashi." A lokacin aka je aka ɗauko Saheer, ganin gawar Sudais bai san ya fara kuka ba, ga Sudaisa a ƙasa a sume. Hankalinsa ya tashi sosai, ya duƙa akan guiwarsa yana kuka. Arɗo ya ce, "Matar Black ta suma saboda rashin ɗan uwanta, na ga kuna shiri da ita, ka rarrashe ta." Aka zuba mata ruwa ta farfaɗo, ta gigice ta miƙe ta yi wajensa tana girgiza shi, ganin da gaske ya mutu sai ta sake suma. Sai da ta suma sau huɗu tana farfaɗowa, kafin ta koma kamar mahaukaciya, ko magana bata iya yi, saboda alfarmar Sudaisa sirikin black ne aka binne shi da kayana jikinsa ba a cillar dashi ba. Sudaisa ta zamarwa Saheer kaya, ko yauahe tana kusa dashi bata iya magana, bata cin abinci bata shan ruwa sai kallo kawai. Har lokacin Black bai dawo ba, kuma Arɗo ya ƙyale ta akan nufinsa. Shi kansa Saheer ya ji mutuwar Sudais, ya yi kuka sosai, yana tuna amanar da ya bar masa. Har washe gari Sudaisa tana cikin wanann yanayin, ana bawa Saheer damar rarrashinta amma ta ƙi ko magana bata yi. Saheer ya yi iya yinsa amma ya kasa taimaka mata, dole ya haƙura yana yi mata addu'a. A ranar suka yiwa kowa duka, sannan suka ɗauki  video suka turawa ƴan uwan kowa dan su ga halin da suke ciki. ••••••• Sadik da Baffa suna zaune suna tattaunawa akan kuɗin fansar Saheer, suna ƙoƙarin nemo mafita akan abinda yake damunsu. A lokacin Mama da Hanan suka shigo har Islaha. Kamar jira ake yi su ahigo sai ga kiran waya ya shigo wayar Baffa. Baffa ya kalli wayar gabansa ya faɗi, ya kalli Sadik ya ce, "sune fa." Kowa sai da ƙrijinsa ya buga saboda ba a san da abinda suka zo ba, Baffa ya ɗauka ya saka a amsa kuwa ya ce, "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki salam. Yauwa na ce ƴan uwan Saheer ne ko?." Baffa ya ce, "su ne." "Mun turo mu ku video, ku buɗe" ya faɗa yana kashe wayar. Sadik ya kunna wayarsa sai ya ga shi nan suka tura video, ya kunna musu suka ga yadda ake dukan Saheer da bulalai ga hannunsa a ɗaure. Suka dinga kuka, hankalin kowa ya sake tashi. A lokacin suka sake kiran wayar, Baffa ya ɗauka ya ji sun ce, "Mun ga kamar bakwa son ɗan ku, in bakwa sonsa sai mu kashe sa." "Muna sonsa, kuɗin ne suka yi yawa." "Daman mun faɗa mu ku yau za mu kira mu faɗa mu ku inda za ku kai mana kuɗi, an gama haɗa kyɗin?." Baffa a sanyaye ya ce, "Ba a haɗa ba, kamar yadda muka yi magana da ku bamu da halin waɗanan kuɗin da ku ka ambata. Mun nemi inda za mu samu kuɗin mun rasa, har gidan da mu ka ciki mun saka a kasuwa amma har yanzu ba a tayawa." "Bakwa son ganin yaron ku kenan?." "Muna so, amma muna neman alfarmar a rage mana kuɗin, baza mu iya biya ba." "Mun rage miliyan ashirin, za ku ba da miliyan tamanin ranar alhamis. Kun amsa za ku kawo ko mu kashe shi?." Baffa ya ce, "wallahi su ma ba mu da hanyar su." "To ai shikenan, za mu kashe shi mu ƙona gawarsa...." Sai ya dakata ya ce, "ku zo min dashi." Baffa ya ce, "ku yi haƙuri, kar ku kashe shi don Allah." "naga kun ɗauki abin wasa ne ai, bara ku ji daga bakinsa. Kai zo ka yi magana da yan gidan ku, ka faɗa musu mutane nawa mu ka kashe a gaban idanuna." Saheer saboda wahala da tashin hankalin da yake gani, da damuwa rauni da yunwa, ruɗewar mutuwar Sudais, tashin hankali da damuwar da ƙanwar Sudais ta shiga, cikim gajiya da sanyin jiki ya ce, "Baffa na san ba ku da hanyar wannan kuɗin da suka faɗa, na san babu inda za a same su. Kar ku tayar da hankalin ku, kawai ku bari su kashe ni ɗin daman lokacina ne....." dakata ya yi da magana saboda bindigar da suka buga masa a kai. Saheer ya yi ƙara wacce ta ratsa kunnensu gabaɗaya. Arɗo ya ce, "Mu za ka yiwa wannan maganar? Sai mu karɓi kuɗin kuma mu kashe ka, kuma mun kaahe banza da wofi." Arɗo ya ce, "Ba ku ga irin dukan da mu ka yi masa ba ko?." Baffa murya tana rawa ya ce, "Mun gani." "Kuma har yanzu ku kasa haɗa miliyan tamanin?." "Ba mu da ina zamu samu." Arɗo ya ce, "Shikenan, mun dawo hamsin, daga nan ba za mu sake rage mu ku komai ba. Za ku kawo kuɗin ko mu kashe sa, baza mu ƙara mu ki lokaci ba, in dai ba a kawo kuɗin nan ba zamu kashe shi. Ba mu ɗauko shi dan mu dinga ciyar dashi a banza ba, da kun ba da kuɗi da yanzu ya dawo.” Baffa zai yi magana Islaha ta firgita ta fizge wayar daga hannunsa, jikinta yana rawa, muryarta tana rawa, hannunta yana karkarwa ta ce, "Kar ku kashe sa, za mu kawo mu ku in sha Allah. Kar ku kashe Hamma, ku ƙyalesa zan nemo kuɗin na kawo." Ya yi dariya ya ce, "Yauwa Yarinya, ke kaɗai ki ke son ɗan uwan nan na ki. Za mu sake kiran ku." Ya faɗa yana yanke wayar. Islaha ta cillar da wayar, jikinta yana rawa kamar wacce aka jonawa wutar lantarki, ta rasa inda zata saka kanta, ta rasa me zata yi ta ji daɗi, sai kai kawo take tana tunanin mafita. Muryar ta tana sarƙewa, numfashin ta yana barazanar barin jikinta, yana sarƙe mata maganar da take kan harshenta. Ta kalli Baffa a wannan yanayi ta ce, "Baffa zan nemo kuɗin, zan yi komai saboda Hamma, zan je na nemo miliyan hamsin a duk inda take a kai  musu, in dai za su saki Hamma, zan nemo." Baffa ya riƙe kafaɗunta ya ce, "ba ki da hanyar Islaha, ba naira dubu hamsin aka ce ba, ba dubu ɗari biyar aka ce ba, ba miliyan biyar aka ce ba, miliyin hamsin suka ce. Miliyan ɗay ɗay sau hamsin. Islaha ba ki da hanyar da za ki samu waɗanan kuɗin, ki karɓi ƙaddara ki cigaba da yi masa addu'a, in yana da sauran kwana a duniya Allah ya kuɓutar dashi, in kuma babu Allah ya sa ƙarshen wahalarsa kenan." "Bazan iya ba Baffa, zan nemo kuɗi ne a ko ina suke, na yarda zan yi ko meye indai zan samu kuɗin. Bazan iya bari rayuwar Hamma ta salwanta ba, bazan iya zuba ido Hamma yana cikin wani hali na ƙyalesa ba, bazan iya ganin Hamma yana neman taimako na ɗauke kaina ba......" Ta girgiza kai tana ja da baya tana kallonsu tana hawaye duk a lokaci ɗaya ta ce, "Zan nemo miliyan hamsin, ko raina ne zan bayar indai shi zai dawo" ta faɗa tana fita daga falon da sauri. Baffa ya kalli Sadik ya ce, "Sadik ka bi bayana don Allah, kar bari ta je ko ina, ka dawo da ita." Da sauri ya bi bayanta ya samu zata fita daga gidan, ya yi sauri ya cimma ya ce, "ina za ki je?." Muryarta tana rawa tana kuka mai tsanani ta ce, "zan je na samo kuɗin ne." "A ina za ki samu? Ba ki da hanyar da za ki samu wannan kuɗin." Sai ta sake fashe masa da sabon kuka ta ce, "haka zan bar Hamma kenan a kashe sa a banza? Haka zan bari Hamma yana neman taimako na ƙyalesa? Haka zan bari suna dukan Hamma na kasa yin komai?. Meye amfanina a duniya in ban sadaukar da farin cikina akansa ba, meye amfanina a duniya in ban fito da Hamma daga cikin halin da yake ciki ba?. Ni bazan iya ƙyale Hamma a wanann yanayin ba, babu amfanin zamana a duniya bayan na kasa taimaka masa, wallahi bazan iya ba" ta faɗa tana rufe fuskar ta da hannunta, ta durƙushe a wajen tana kuka sosai. Sadik ya ce, "haƙuri za ki yi, babu abinda za ki iya a kan hakan." Bata ce komai ba sai kuka, sai da ta ga ji sannan ta miƙe zunbur ta kalle shi ta ce, "ina da mafita, ban sani ba ko za ka bani goyan baya akan abinda zan faɗa maka." Ya kalle ta ya ce, "in dai hanyar bata saɓawa Allah ba ce zan amince, ina jin ki." Ta ja numfashi mai tsaho ta sauke shi a hankali, ta rufe ido tana tunanin yadda zai ɗauki maganar, ta buɗe iso ta ce, "Ahlin gidan AbdulAziz Yola suna da kuɗin da za su bani miliyan hamsin?." Ya ɗan kalle ta cikin mamaki abinda ta ce ya ce, "su za ki je su ba ki kuɗin?." Ta girgiza kai ta ce, “ka amsa min Hamma Sadik." Ya ce, "Suna dashi mana, meye miliyan hamsin a wajansu?." Ta yi shiru na wani lokacin, ta rufe ido ta buɗe tana furzar da iska. Ta kasa magana, ita kanta bata son furta abinda zata ce, amma kuma ya zamar mata dole ta yi, dan ita kaɗai ce hanyar da zata bi dan karɓo Hamma, akan Hamma zata iya ba da ranta. Ta sake rufe ido ta buɗe, ta kalle shi ta ce, "Ai daman na faɗa mu ku batun aurena da suka zo nema, kuma shi wanda za a aura min ɗin da kansa ya kawo maganar auren contract na wata biyar…..” Ta dakata tana ji zuciyarta tana bugawa, ta ja numfashi da ƙarfi ta ce, “Zan karɓi auren contract ɗin da ya yi min tayi, zai aureni saboda mahaifinsa, ni kuma zan auresa inda zai bani kuɗin fansar Hamma!." Sadik ya bita da kallo ganin kamar bata cikin hankalinta ne ya saka ta ke wannan maganar. Ya tausasa murya ya ce, "ki ɗan samu waje ki zauna Islaha, kamar ba nutse ki ke ba." Ta ce, "a nutse nake, ina faɗa ma ka ne kar na je na yi a bayan idonka daga baya kai da Hamma ku dinga ganin laifina har ku dinga zargina da mummunan abu, shiyasa na sanar da kai abinda zan yi. Ba wai shawara nake nema ba, na faɗa maka ne dan ka sani, na riga na gama yanke hukunci a zuciyara. Zan amince na yi auren, shi kuma ya bani kuɗin da za a karɓo Hamma. Bayan wata biyar in muka rabu, sai na dawo na auri Hamma." Sadik dai kallon ta yake yi dan har lokacin bai yarda a nutse take ba. Ya ce, "wannan maganar bata da ma'ana Islaha, kina musulma ina ke ina auren yarjejeniya?. Kuma shi mahaukacin ina ne da zai ɗauki kuɗi masu yawan waɗanan ya ba ki dan kawai ki aure sa?." Ta kalle sa ta ce, "kai ka ce min a wajansu miliyan Hamsin ba komai bane." "Dan na ce haka ai ba hakan yana nufin zai yu bane, kawai dan za ki auresa sai ya ba ki waɗannan kuɗin?. Islaha ki nutsu don Allah." "A faɗa maka a nutse nake, kuma haka na yanke, kuma hakan zan yi. Bazan bar ran Hamma ya salwatanta a banza ba, tunda dai auren ba mai ɗorewa bane zan jure saboda Hamma. Na riga na yanke hukunci akan zan yi ɗin, ina faɗa maka ne dan ka zama shaida koda Hamma zai dawo ya ce ban kyauta masa ba. Ka zama shaida, na yi ne saboda shi, kuma zan dawo gare shi ba tare da komai ya same ni ba." Sadik ya ce, "Islaha wannan ba shawara mai kyau bace, akan me za ki yi irin wannnan auren kamar a Kdrama ko american series?....." "Akan Hamma zan yi, kana ganin yadda suke dukansa, kana ganin yadda Hamma ya rame kamar ba shi ba, kana ganin yadda Hamma ya koma kamar wanda ya shekara yana ciwo. A kansa zan sadaukar da kaina balle auren wata biyar." "Islaha ke za ki aurar da kanki? Ko za ki cewa Baffa auren jarjeniya za ki yi saboda Saheer?. Ba Kdrama bane, ki nutsu ki fahimci a Yola ki ke." Ta kalle sa ta ce, "ka ɗauka Kdrama ɗin ne kawai, ka ɗauka film ka ke kallo kuma ni ce jarumar ciki. Baffa ya amince da auren, zan ce masa na amince ba tare da ya san ƙudurina ba. In dai har zai bani kuɗin fansar Hamma zan yi, Hamma Sadik!." "To shi waye wanda za ki aura ɗin? A cikin ƴaƴan Abdul Aziz Yola wanne za ki aura har da ki ke ganin zai ba ki miliyan hamsin lokaci ɗaya?." Islaha taɗan ja numfashi sannan ta lumshe ido ta ce,.. Nana Haleema. [7/28, 12:20 PM] KRBBK: RDB2P91 Nana Haleema. Ganin ya zuba mata ido yana jira ya ji sunan da zata faɗa sai ta ɗan ɗauke kai zuciyarta tana faɗa mata ba yanzu ba, kar ta faɗa masa sunan ko waye sai ta ce, "faɗar bata da wani amfani, na faɗa maka ƙudurina dan ka zama shaida, zan yi abinda nake ganin shine daidai." Sadik ya ce, "Kar ki dakusa rayuwarki, ki jira mu ga abinda Allah zai yi." Ta ɗan murmusa ta ce, "akan Hamma zan iya yin komai, ba dakusar da rayuwata ba, in rasa rayuwata ne zan iya yi indai a kansa ne. Bazan iya jira ba, zan jarraba wannan ɗin, in ya yu daman haka nake fata, in bai yu ba sai na gwada wani." Ganin ya shiru ya kasa magana, sai ta koma da baya ta koma cikin gidan da sauri. Tunda ta koma take kai kawo a ɗaki, ɓangare ɗaya na zuciyarta yana faɗa mata abinda zata yi ba daidai bane, ɗaya ɓangaren ya faɗa mata hakan shine daidai, in ba ta aikata ba a ina za a samu kuɗin da za a karɓo Hamma?. Ta kawar da tunanin kar ta aikata, ta ƙarasa jakar ta ta buɗe, ta ɗauki biro da takarda ta zauna tana rubutu a kai. Bayan ta gama rubutawa ta karanta yadda ya kamata, ta ajjiye takardar tana ajiyar zuciya a hankali a hankali. Kamar lokacin da zata tafi Jeddah, haka wannan lokacin ma ko kaɗan ta ƙi bawa zuciyarta damar da zata ce tunaninta ba daidai bane, ta dage akan ƙudurinta, ta dage akan abinda take kai shine daidai, ta ƙi amincewa da ba kan daidai take ba. Haka ta gama zamanta a ɗakin, sannan ta kwana a kan gadon ta yi shiru tana tunanin halin da suka ga Hamma a ciki. Sai kuma ta miƙe ta yi alwala ta zo ta tayar da sallah raka'a biyu, bayan ta idar ta karanta addu'ar da annabi ya koyar damu domin neman zaɓin Allah, ta nemi zaɓin Allah akan abinda ya zama alkhairi sannan ta kwanta. Washe gari tana tashi wanka ta yi a gaggauce, ta saka hijjab ta ɗauki handbag ɗinta ta fita da sauri ta fita. Da farko gidan tv ta fara zuwa, ta ɗan jima a can sannan ta tafi asibiti. A can ma ta ɗan jima sannan ta fito ta dawo gidansu Safeera ta kira Saleem a waya. Saleem ɗauka ta ce, "Hamma Saleem don Allah email address ɗin Jafar za ka bani." Daga can ɓangaren ya ce, "Wanne Jafar?." "Wanda mu ka gani a diamond hotel, lokacin da mu ke neman Rehaan Yola." "Okay, bara na duba in na gan shi zan turo miki. Amma yana jimawa jafin ya buɗe mail, sai a kwashe sati ɗaya bai amsa ba." "Na gode" tana faɗa ta kashe wayar. Safeera ta ce, "kin ce za mu yi magana kuma kin yi shiru, wani abun ne ya sake faruwa?." Ta kalle Safeera sannan ta ce, "Jiya sun ce in ba a ba da kuɗin fansar Hamma za sa kashe sa, har video suka turo suna dukansa." Safeera cikin damuwa da sanyin jiki ta ce, "Waɗnanan mutane Allah ya shiga tsakaninmu dasu......" "Amin." "Yanzu ya ake ciki, An samu kuɗin?." "Ba a samu ba. Amma ni zan samo." Safeera ta ce, "ban gane ba, a ina za ki samu miliyan ɗari?." "Sun rage hamsin, miliyan hamsin ne yanzu." "Ina za ki samo waɗanan kuɗin?. Islaha ta yi shiru bata amsa ba, dan bata san da wacce fuska zata fahimta ba, kuma ta san halin Safeera in ta faɗa mata zata dinga kushewa, ta dinga yi mata wa'azi ita kuma bata so. Safeera ta ce, "ko saudian za ki sake komawa ki haɗo kuɗin?." Ta girgiza kai alamun a'a, sannan ta goge idanunta ta ce, "contract marriage zan karɓa, zai aure ni saboda iyayensa, ni kuma zan auresa dan ya bani kuɗin fansar Hamma." Safeera ta buɗe baki saboda mamakita ce, "Ban gane ba, yi min bayani yadda zan kwashe." Islaha ta rufe ido ta ce, "Shi wanda Baffa ya ce zan aura, dashi zan yi auren yarjejeniya." "Islaha kina da abin mamaki, ko na ce kina da abin dariya wallahi. Kwana biyu kalaman ki kamar na waɗanda suke acting, yadda ki ke yin komai kamar rubuta miki aka yi ki ka karanta ki ke acting a kai." "Shiyasa bana son faɗa miki, dan na san baza ki bani goyan baya ba." "Akan me zan ba ki goyan baya akan abinda bai kamata ba? Auren yarjejeniya ki ke cewa za ki yi fa." Islaha yi magana saƙon Saleem ya shigo wyar ta, ɗauki wayar bata cewa Safeera komai ba, ta buɗe saƙon ta yi copy ɗin email address ɗin Jafar, ta je mail ɗinta ta paste ta fara rubuta masa message. Sai da ta gama ta tura sannan ta kalli Safeera ta ce, "Abinda na faɗa miki shi zan yi, zan je wajensa mu yi magana, in dai ya amince zai bani wannan kuɗin ni kuma zan aure sa na ɗan lokaci kaɗan, daga baya sai mu rabu na dawo na auri Hamma." Safeera da take kallon Islaha ta ce, "ban gane ba Islaha, wai aurensa za ki yi dan ya ba ki kuɗi, sannan daga baya ya sake ki ki dawo ki auri Saheer?." Ta ɗaga kai alamun eh tana kallon ta. Safeera ta zaro ido waje ta ce, "na shiga uku, Islaha me ki ke faɗa ne haka? Wannan wacce irin magana ki ke yi kamar ta masu taɓin hankali?. Contract marrige a addinin mu, kuma a al'adar mu ta fulani? Sunnar Annabin za ku gina akan bayan wasu kwanaki za ku rabu?." "Dallah malama ki daina ɗaga min murya, na san duk abinda nake yi, kuma auren gaske za a yi tunda Baffa ya sani. Ba wa'azi na ce ki yi ba, na riga na yanke hukunci, ko me za ki ce ba sauraren ki zan yi ba." "Dan Baffa ya sani ai ba akan hanyar kirki ku ka gina auren ba. Kuma ke yanzu akan Saheer sai ki yi wannan kwamachalar? In ya fito ya ji kin yi aure nufin ki zai ji daɗi ne?." "Akansa zan yi, in ma abinda ya fi kwamachala ne indai akan Hamma ne zan aikata. Kuma ko da ya fito ɗin ma ba wani abun damuwa bane, dan ba jimawa aure zai yi ba ya watse, ni kuma na dawo na auri Hamma." Safeera ta bita da kallon bata da hankali, amma sai bata yi magana a kai ba ta ce, "Shi kuma kawai sai ya ɗauki waɗannan kuɗi ya ba ki dan ki aure sa? Mahaukaci ne shi ko yana shaye-shaye?.” Islaha ta ce, "ban sani ba, amma na san yana da kuɗin da zai bani. In ya bani fine, in bai bani ba za a yi soke yarjejeniya." "Okay, mu yi tunani akan bai baki ɗin ba, a ina za ki samu kuɗin fansar?." Islaha ta ɗaga kai ta kalle Safeera sai ta girgiza kai ta ce, "bani da hanyar da zan samu, balle ma a jikina nake jin zai bani." Safeera ta ce, "saboda kawai zai aure ki sai ya ɗauki waɗnanan kuɗin ya ba ki? Ke ga ƴar gold ko ƴar diamond da azurfa ko?. Miliyan hamsin fa ba dubu hamsin ba." "Ba ƴar diamond ba ce, amma zan gwada na gani. A rashin ta yi ake barin arha, abinda ka ke ganin bazai faru ba in ka gwada sai ka ga ya faru." "Shi wanda ki ke magana akan zai ba ki kuɗin, waye shi?." Ta ɗaga ido ta kalle Safeera, kamar zata faɗa mata sai kuma ta ce, "ƙaryata ni za ki yi in na faɗa miki." Safeera ta ce, "faɗi ina jin ki." Islaha ta ce, "ki jira komai ya tafi yadda nake so, zan ɗauke ki muje tare dan ki gani da idon ki. Amma yanzu....." bata ƙarasa maganar ba wayarta ta fara ƙara, ta duba ta ga sabuwar lamba ce sai ta ɗauka ta saka a kunne. Jafar ya ce, "Miss Islaha." Jin hakan sai ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Mr Jafar, Ina yini." "Lafiya. Na ga mail ɗin ki, kuma sai na ga kin yi dropping digit ɗin ki sai na kira." "Thank god! Gaskiya ni mai sa a ce, an faɗa min kana jimawa jafin ka buɗe mail. Amma ni within ten minutes ka buɗe har ka kira ni." Bai ce komai ba ta ji dai ya yi murmushi ta ce, "Allah yasa ban takura ka ba, dan Ina son magana da kai ne." "Kar ki damu, Am all ears." Ta ɗan sauke numfashi ta ce, "ina so na haɗu da ɗan uwanka akan wannan maganar." Jafar ya ce, "Gaskiya a yanzu ban san inda yake ba, amma na san yana cikin garin nan." Islaha ta ce, "Ina so na haɗu dashi akan auren yarjejeniyar sa ya ce." Ya ɗan yi murmushi ya ce, "kina ina yanzu?." "Ina gida." "Okay, zan turo a ɗauke ki sai a kai ki inda za ki same sa." "Thank you. Amma don Allah ina so ka kasance a wajen, ina so na ganka a tare dashi "Miss gaskiya am not availabe, beside an fara events ɗin bikina, bani da wani time yadda ya kamata." Islaha ta ce, "Don Allah." Ya ɗan yi shiru sannan ya ce, "Okay." Ta yi godiya ya kashe wayar. Ta kalli Safeera da take kallon ta ta ce, "Ki shirya mu je tare, za ki ganawar idanunki waye shi ba sai na faɗa miki ba." Safeera ta kasa cewa komai, dan tunda ta yi waya da Jafar sai tunanin ta ya tafi Rehaan ne, tunda ta san sunan mahaifinsa ta faɗa masu lokacin da ta ce an zo neman aurenta. Safeera doguwar rigar da Islaha ta bata ta ta saka, jim kaɗan aka kira ta a waya aka ce an zo ɗaukar ta suka fita. Farar mota suka gani a ajjiye a ƙofar gidan tana jiransu, suka ƙarasa wajan driver ya ce, "Islaha ko?." Ta ɗaga kai ya ce, "Mr Jafar." Bata ce komai ba suka shiga motar suka tafi ƙirjinta yana bugawa da gaggawa. Gidan da ya saka aka kai ta nan ta ga an sake shiga, Safeera dai kallon Islaha kawai take yi har motar ta tsaya. Driver ya ce, "bismillah." Suka fito a hankali ya nuna musu hanyar da zasu bi suka wuce suna tafiya kamar basa so. Gab da zasu shjga falon Safeera ta riƙe Islaha ta ce, "Islaha kar ki yake hukunci cikin gaggawa, kar mu zo mu yi danasani nan gaba. Ke kan ki kin san kina da gaggawa akan komai, ki tsaya mu nutsu kar mu yi abinda zai cutar damu." Islaha ta cire hannun Safeera daga riƙon da ta yi mata ta ce, "Tunda mu ka zo nan magana ta ƙare, tunda na yi niya sai na yi, indai akan Hamma ne zan yi ko wacce gaggawa ce. Akan wani daban ma na yi gaggawa na tafi Jeddah balle Hamma? Ki zo mu je kawai." Safeera ta ɗaga mata kai suka shiga falon da sallama. Falon babu kowa, amma akwai haske sosai. Suka tsaye suna kalle-kalle ba su san inda zasu bi ba, Driver da ya kawo su ya leƙo ya ce, "ku shiga waccan ƙofar, Mr Jafar yana ciki." Suka shiga ciki da sallama, Jafar da yake kallon ƙofar ya amsa yana kallonsu. Islaha ta ɗan yi murmushi ta ce, "Thank you mr Jafar." Ya nuna mata wajen zama sannan ya ce, "Your welcome, Miss Islaha da ƙawar ta Miss Safeera." Safeera cikin mamaki ta kalle sa, sai ta kalli Islaha ta ga bata ji wani mamaki dan ya faɗi sunanta ba. Duk ba su lura da Rehaan a kwance akan kujera ba, dan ya kifa littafi akan fuskarsa, ya yi shiru yana jinsu kawai bazai miƙe bane shiyasa ya yi kamar bai ji ba, bai motsa bama balle su gane idanunsa biyu. Islaha idanunta ya kai kansa, ta ɗan yi tsaki ta ce, "Mr Jafar na zo nan dan na saka hannu a takardar yarjejeniyar auren wata biyar." Jazy ya nuna mata Ray da yake kwance ya ce, "gashi nan ai, dashi ku ka fara kuma dashi za ku gama. Ray ka tashi, your wife is here." Ya yi masa banza kamar bai ji ba, nan kuwa yana jin duk abinda suke faɗa. Jazy ya ce, "na san kana jina fa, dallah malam ka tashi." Kamar bazai tashi ba, sai kuma ya miƙe ba tare da ya cire book ɗin fuskarsa ba. Ya sauke ƙafafunsa a ƙasa, ya cire littafin a hankali ya kalli Jafar. Jazy ya ce, "ita za ka kalla ba ni ba." Ray ya ɗan juya ya kalle su sai ya ɗauke kai kamar bai gane su ba. Nana Haleema. [7/28, 5:31 PM] KRBBK: RDB2P92 Nana Haleema. Lokacin da ya kalle su Safeera sai ta ji kamar an jona shocking a jikinta, ta buɗe ido sosai tana sake tabbatar da ba fa gizo yake yi mata ba, shi ɗin ne dai a zaune a gabanta. Tsabar mamaki da ruɗewa bata san ta buɗe baki ta ce, "Mr Rehaan!." Ta gefen ido ya kalle ta ya share bai ce komai ba shima Jazy bai ce komai ba. Islaha ta ɗan taɓa Safeera ganin zata zubar mata da class ta ce, "Ka yi magana akan auren yarjejeniya ko? To gani na zo zan saka hannu a kai." Bai ce komai ba sai kallon falon da yake yi kamar mai neman wani abu, can ya hango takardun a  kan tav stand. Ya kalli Safeera suka haɗa ido, ya nuna mata takardar ya yi mata alama da ta ɗauko masa. Safeera kwarjini ya yi mata, bata san lokacin da ta yi nufin miƙewa ta ɗauko ba, Islaha ta zaunar da ita ta ce, "ai ba aikin da ki ka zo yi ba kenan, ba ke za ki ɗauko ba, in shi bazai tashi ya ɗauko ba ni zan ɗauko. Abinda ya shafe shi ne ba ke ba, baza ki yi masa aiki a banza ba." Ta faɗa tana miƙewa ta ɗauko ta dangwarar a gabansa. Ya shafa kansa yana mamakin wannan yarinya mai taɓin hankali, ya jingina da kujera yana rufe ido yana ji a ransa in aka bar shi da yarinyar nan wata ran tsaf zai iya shaƙe ta ta daina numfashi, ya lura tana da rawar kai, amma zai gyara mata zama a wata biyar kacal.  Jafar dai ya yi shiru yana danna waya kamar bai san dasu ba, hankalinsa baya kansu yana kan abokansa da suka zo daga wata ƙasar yana ba da inda za a kaisu. Ya buɗe ido ya ɗauki takardar ya miƙa mata ba tare da ya kalle ta ba. Islaha ta karɓa bata kalle sa ba, ta kalli takardar tana karanta abinda yake ciki. Five months contract marriage, shine abinda ta gani da manyan baƙi a rubuce a sama. Sai rules ɗinsa da ya rubuta mata wanda dole sai ta bi su indai ta yarda da auren. Rule na farko akan ba ya so kowa ya san shine mijinta, auren sirri ne. Na biyu kar ta faɗi sunansa a ko ina a matsayin matarsa, ko me zai faru kar ta ce faɗi sunansa. Na uku kar ta saka masa baki akan komai nasa, duk abinda ya ga dama zai yi mana babu ruwanta. Na huɗu dole ta yi duk abinda ya ce mata babu saɓawa, dole ta bi umarninsa a duk lokacin da ya ga hakan ya kamata, dole ta yi pretending ɗin matarsa a wajan waɗanda suka dace. Babu ruwanta da maganar gidansu, komai zai faru kar ta saka baki. Ta gama karantawa ta kalle sa tana hararesa, ta sake kallon takardar ta ga ƙaramin rubutu inda ya ce zai aure ta saboda mahaifinsa ya ce, saboda ya yi alƙawari akan hakan. Sai wajan da zata saka hannu da inda zai saka hannu. Islaha ta kalle sa ta ce, "na karanta sharaɗan ka." Bai kalle ta ba ya ce, "ki saka hannu." Ta yi dariya ta ce, "ji mana, ni ma ba ka ji nawa rules ɗin ba ai ko?" Ta faɗa tana buɗe handbag ta ɗauko takarda ta miƙa masa.  Ya bita da kallo yana mamaki, tunanin har wasu conditions ne da ita akan aurensa?. Ya yi kamar bazai karɓa ba, sai kuma ya karɓa yana dubawa. _Na amince zan yi auren yarjejeniya da Rehaan Yola, amma in ya amince zai bani kuɗin fansar wanda zan aura naira miliyan hamsin._ Rehaan yana gama karanta wajen ya ɗago ya kalle ta ya ce, "Are you a thief? Fifty million for your marriage?" A lokacin Jafar ya kalle su jin zancen miliyan hamsin, ya kalli Islaha da take kallon Rehaan, ya kalli Rehaan da yake kallon ta, ya girgiza kai yana tunanin wannan lamari nasu kamar a wasan kwaikwayo, ko a film bai saba ganin mutane kamar Rehaan da Islaha ba. Kuma shi daɗi ya ke ji da ya kasance Islaha tana da wayo da magana, in ba dan haka ba da Rehaan ya gama da ita. Amma yanzu da yake faɗa tana mayarwa, tana nuna masa itama tana da rules ɗin da zata ba shi, Rehaan ɗin zai san ba dan wani abu na sa zata aure shi ba. Islaha ta kalle sa cikin ko in kula ta ce, "za ka aure ni saboda mahaifinka, wannan shine reason ɗinka. Ni kuma zan aure ka saboda fifty millions, kuɗin fansar wanda zan aura in contract ya ƙare. In za ka bani kuɗin da zan karɓo sa daga wajan kidnappers fine, if not daman ban saka hannu ba." Ya zuba mata ido kawai yana kallon ta, sai kuma ya kalli Jafar, Jafar dai murmushi yake yi bai ce komai ba, sai kuma Jazy ya ɗauke kansa dan babu ruwansa, ya cigaba da danna wayarsa yana dariyar wannan lamari. Rehaan ya ce, "Ke ƴar fashi ce?." Islaha ta ɗaga hannu tana ɗage kafaɗa ta ce, "babu dole a maganar nan, in baza ka iya ba a fasa daman ba a yi ba. Saboda shi kaɗai zan saka rayuwata a cikin rayuwarka, shima rashin mafita da son ceto rayuwarsa ne ya saka zan zauna inuwa ɗaya da kai, bayan wannan da babu wani abu da zai sake haɗa ni da kai har abada. Ya ɗan buɗe ido ya ce, "fifty millions for you? Oh God!" Ya faɗa yana ɗan kulle ido. Inda wata ce ba ita ba kuɗin ba komai bane, amma gani yake in ya bata kuɗin ta yi nasara kuma ta samu riba akansa, ga aurenta ga kuma kuɗin da zai bata. Kamar ma shine ya nemo ta ya ce zai aura, tunda daga aljihunsa zai fitar da kuɗin ya bayar, kamar shi ya ke son auren. Bai ce komai ba ya cigaba da kallon takardar yana karanta rules ɗinta bit by bit. Dan ya san sharaɗin irin wanna auren, indai ka saka hannu dole ka bi duk abinda mutum ya ce. Abu na farko da ta rubuta zan cigaba da aikina, ko ƙasar waje aikinna zai ta babu ruwanka. Ina da wanda nake so kuma zan aura, zan cigaba da magana dashi kuma na haɗu dashi a duk lokacin da na ga dama, babu wanda zai yi min iyaka da ganinsa. Zan yi duk abinda nake so, baza a takura min ace sai na bi umarni ba, dan ba auren gaske na yi ba balle na yi biyayya. Ni ba ƴar aiki bace, bazan yi share-share da girki ba. Baza a hana ni fita duk inda na ga dama ba, in kwana ya kama na yi a waje zan yi babu ruwan mutum da ni. Rehaan ya gama karantawa dan kaf cikin rules ɗin bai ga wani rule na kirki a ciki banan ba. Rule na ƙarshe ya kalla, ya ga shi da capital letter ma aka rubuta shi saboda girmansa, an rubuta NO INTIMACY RELETIONSHIP!. Rehaan ya ɗan ɗago ido ya kalle ta, shi wallahi ya manta da wani intimacy saboda ba ya gabansa a aurenta, ko kaɗan bai kawo hakana a ransa ba balle ya yi tunanin saka shi a cikin rules ɗinsa. Amma ita da yake abin yana zuciyarta gashi har ta rubuta, ko intimacy ɗin me zai yi da ita oho mata. Ya ɗan yi ƙaramin tsaki ya ce, "it's that all your rules?." Ta ɗaga kai alamun eh. Ya ɗan yi shiru yana tuna alƙawarin da ya yiwa Abba sannan ya kalli Jafar ya ce, "Jazy pen." Jazy ya ya miƙe masa shi kuma ya yi signing takardar da ta ba shi, sannan ya yi signing akan wata a kusa dashi. Ya sake yin signing akan guda huɗu ya cillar da biro akan table ɗin. Itama ta ɗauki biron ta saka hannu zuciyar ta ko ɗar babu kamar yadda ya yi.  Ta ɗauki ɗaya wacce ya rubuta rules ɗinsa, dan ko wacce copy biyu ce, da wacce zata riƙe da wacce zai riƙe, ta saka a handbag. Daɗi ya cika mata rai dan iya saka hannun sa ya yi ya bata tabbacin zai ba da kuɗin, sai ta ke gani kamar Hamma ya fito ya gama, ta zama silar fitar Hamma daga cikin uƙuba. Jazy ya ɗan yi tafi yana kallonsu ya ce, "Finally, mr and mrs Rehaan." Islaha ta ce, "ku zama shaida a gaban idanunku aka yi komai, Mr Jafar ka karanta don Allah" ta faɗa tana nuna masa takardar. Ya girgiza kai ya ce, "No need Miss, kar ki damu. Rehaan bazai yi breaking ko wanne rule ɗin ki ba, ya san duk abinda yake yi." "A'a Mr Jafar, bana so a samu matsala nan gaba, dan gaskiya bazan jure ba." "Baza a samu ba Islaha, tunda kuna ganin auren contract shine daidai da ku shikenan." Rehaan dai kallon ta kawai yake yi yana mamakin ƙarfin hali irin nata, wai mutum kamar shi take faɗawa irin wannan maganar dan bata da hankali, har tana cewa wai bata so a samu matsala saboda baza ta jure ba. In ba dan alƙawarin da ya yiwa Abba ba ita ta isa ya zauna yana faɗa tana ja? Ta isa ta sake ganinsa balle har ta samu damar yi masa shirme?. Ya yi tsaki mai sauti ya miƙe tsaye ya ce, "ki turawa Jazy account details ɗin" ya faɗa yana barin wajan ko takarda ɗaya bai ɗauka ba..... Nana Haleema. [7/29, 12:06 PM] KRBBK: RDB2P93 Nana Haleema. Islaha ta bi shi da kallo cikin takaici da ɓacin rai, kafin ta yi tsaki ta kalli Jafar da yake kallon ta ta ce, "shiyasa na ce ka kasance a nan, saboda ina so ku zama shaida da kai da ƙawata. Bana so a samu matsala nan gaba, duk ƙanƙantar matsala bazan jure mata ba. Na saka hannu na amince da auren nan saboda Hamma, zan rayu tsahon wata biyar saboda shi, in ba dan haka ba da ba mu sake haɗuwa ba." Jafar ya ce, "saboda wanda za ki aura ki ka amince za ki auri Rehaan?." Ta ɗan yo murmushi ta ce, "ba iya auren yarjejeniya ba, zan iya sadaukar da komai saboda shi." Ya girgiza kai ya ce, "Wow! Ban taɓa ganin irin wannan sadaukarwa ba. Yanzu fifty millions suka nema kuma za ku basu?." Ta ɗan yi ajiyar zuciya ta ce, "haka suka ce, da farko sun ce one hundrend millions, amma daga baya sun rage ya dawo haka." "Ƴan sanda fa, kun yi magana dasu?. Haka kawai za ku ɗauki kuɗi a bawa wasu mutane a cikin daji, meyasa baza ku basu dama su yi aikin su ba?." Islaha ta ce, "an yi komai Mr Jafar, abin ne kamar bazai yi aiki ba. Ni kuma ganin na samu dama sai na ce bara na gwada, in ya yi aiki shikenan, in bai yi ba sai mu nemi wata hanyar." Jafar ya ce, "shikenan, za a tura miki kuɗin." Islaha ta ce, "Thank you." A lokacin Rehaan ya dawo falon ya ɗauki wayarsa. Jafar ya kalle sa sannan ya kalle ta ya ce, "Thanks him." Islaha ta kalli Rehaan sannan ta ce, "Da na godewa wannan ai gwara na kwana babu ci babu sha." Jafar ya yi dariya mai sauti, ya kalli Rehaan da ya ɗauki wayarsa ya koma ko kallonsu bai sake yi ba, kamar ma bai san dasu a wajen ba. Islaha ta miƙe tsaye tana jinta wani iri, sai take ji kamar zuwa ta yi ta roƙosa kuɗi ya bata, sai ta ke jin kamar ta zubar da ajinta a wajensa. Sai kuma ta tuna zama dashi zata yi na wata biyar, shi kuma ya ba ta kuɗi. Ta kalli Jafar ta ce, "na gode." Bai ce komai ba ya ɗaga mata kai, ta kalli Safeera da ta maƙale a waje ɗaya ko motsin kirki ba ta yi ta ce, "Safeera mu je." Safeera ta miƙe suka fita daga falon. Tana fita Jafar ya ɗauki takardun yana karantawa, rules ɗin ya dinga bi yana karantawa, dan gabaɗaya shi bai wani nessecery abu a ciki ba, daga nata rules ɗin har nasan. Ya ɗan yi murmushi ya ajjiye musu, ya miƙe tsaye a lokacin Rehaan ya dawo. Rehaan ya kalli Jazy ya ce, "amma wannan yarinyar nan bata da wani plan a ƙasa? Daga zancen contract sai ta kawo maganar kuɗi?." Jafar ya ce, "Da gaske an yi kidnapping ɗin wanda take so kuma zata aura, a gidanau take rayuwa, shine ya ɗauki duk wani responsibilities ɗinta. Zata iya ɗaukar komai saboda dashi, dan ta yarda ta zauna da kai na wata biyar saboda shi a wajenta ba komai bane." Rehaan ya girgiza kai cikin ko in kula ya ce, "dole ta yi komai saboda shi, abokin ɗan iska shima ɗan iska ne." Jafar ya kalle sa ya ce, "auren ta da dai za ka yi, bai kamata a dinga jin waɗanan kalaman a bakin ka ba." Ya ce, "Ikon Allah, shi kuma ita yake so, ya rasa abinda zai so sai wannan." Jazy ya ce, "ni na tafi, ina da abinda zan yi. In ta turo min details ɗin zan tura maka, ni ba ɗan aikin ka bane" ya faɗa yana fita daga falon. Islaha yadda aka ɗauko su haka aka mayar dasu, Safeera duk ta gigice ta kasa cewa komai sai da suka sauka daga motar, suna shiga gidan su Saheer ta riƙe hannun Islaha ta ce, "Islaha daman da gaske ki ke? Wayyo Allah, ban taɓa tunanin zan ga Rehaan ido da ido ba sai yau. Ashe haka yake da kyau? Ashe a zahiri ya fi kyau Islaha. Wow! Gaskiya kina da sa'a ƙawata, ke me sa'a ce." Islaha ta kalle ta cike da takaici ta ce, "ji don Allah, akan wancan banzan duk kin wani rikice, ni ki sakar min hannu" ta faɗa tana ƙwace hannunta. Sai kuma ta ce, "Don Allah ki bar wannan shirmen, ni bana so kowa ya ji maganar nan, ki riƙe wannan amanar don girman Allah. Bani da buƙatar a san na yi aure balle a san wanda na aura, ki rufe maganar nan, ko Saleem kar ki faɗawa, na yarda dake shiyasa na je har can da ke." Safeerq ta ce, "Meyasa bakya so a sani?." "Kin ga yanayin da auren ya zo, ba aure ne da zai dawwama ba, ba aure ne kamar ko wanne ba. Na rantse da Allah bana son ganin fuskarsa, ko sunansa bana so a kira, ni kaɗai na san wulaƙancin da ya yi min, ni kaɗai na san irin ɗacin da dasa min a zuciyata...." Ta dakata da maganar tana tuna yadda ya dinga jifanta da kalaman banza sannan ta ce, "amma na amince saboda Hamma kawai, zan je na zauna dashi saboda Hamma, zan dawo saboda Hamma." "In sha Allah bazan faɗa ba, za ki same ni da riƙe miki amana in sha Allah, kar ki damu." Sai kuma ta dafe kai ta ce, "Ni wallahi danasani nake yi, sai nake ji kamar na cutar da rayuwata, kamar ban yi daidai ba, kamar abinda na yi zai canja rayuwata, kuma duniya zata ce na aure kafin na auri Hamma, za a dinga cewa bazawara Hamma ya aura. Innallahi, wallahi bana son hakan ko kaɗan." Safeera ta girgiza kai tana binta da kallon daga baya kenan sannan ta ce, "Islaha kenan, sai da na faɗa miki, na ce ki tsaya ki yi tunani, amma ki ka ƙi." "Ni ba danasani nake yi ba, kawai bana so a dinga jifana da kalman da zasu yiwa Hamma ciwo. Ina yin auren nan zan koma bazawara a idanun mutane, ba kowa ne ya san ya zaman auren zai ya kasance ba. Amma tunda zai bani kuɗin a karɓo Hamma duk abinda mutane zasu ce ba komai bane." Safeera ta ce, "Amma kina ganin zai ba da kuɗin nan kuwa?." Ta gyaɗa kai ta ce, "zai bayar, sanin zai bayar ɗin ne ya saka na amince. Zai amince saboda Babansa, ni kuma na amince saboda Hammana." "To wai shi wanne irin kuɗi ne dashi haka? Miliyan hamsin fa da yawa." "Shi ya sani, ni dai ya tura min kuɗin na bayar a yi fansar Hamma." "To me za ki cewa Baffa in aka bada kuɗin?." Ta ɗan yi shiru sannan ta ce, "zan faɗawa Sadik ya faɗa masa kawai sun sako shi ba tare da an bada komai ba, a rufe maganar kar ya sani.....Ke ni fa da akwai yadda zan yi, da na yi dan na tabbatar Hamma bai san da maganar nan ba, da na faɗa masa wani abu a madadin na ce masa na yi auren yarjejeniya." Safeera ta ce, "Gaskiya za a yi daru dashi akan auren nan, yadda yake kishin nan na ki in ya ji kin auri wani kafin shi, sai ya haɗɗiye zuciya ya mutu." "Wannan shine tashin hankalina Safeera, shine kaɗai abinda nake jin tsoro wallahi. Amma in sha Allah zai fahimce ni." Safeera ta ce, "Allah ya sa." Ta amsa da amin ta ce, "zo ki raka ni wajan Baffa na faɗa masa na amince da auren." Safeera ta ce, "amma bakya so." "Wallahi Allah bana so, Allah ya sani bana ƙaunar auren nan." "Sai haƙuri, dan dai ki ki karɓi kuɗin nan shikenan komai ya fara." Ta yi shiru bata ce komai ba suka tafi wajen Baffa. A zaune suka same shi dan tunda aka samu damuwar nan ta sace Saheer ya daina fita, ko ya fita da wuri yake dawowa saboda ana neman maganin damuwar da suke ciki. Islaha ta zauna ta ce, "Baffa ina yini." Baffa maimakon ya amsa sai ya ce, "yau ban gan ki ba." "Eh Baffa, na ɗan fita ne." Baffa ya ce, "Na san da kina gidan nan da yanzu muna tare akan maganar Saheer." Islaha ta ce, "Baffa akan maganar auren nan ne."  Baffa ya ce, "ina jin ki." Ta haɗɗiye yawun takaici da baƙin cikin kalaman da zasu fito daga bakinta ta ce, "Ka yi haƙuri da abinda na ce maka a akan auren." "Babu komai Islaha, kar ki damuwa, ai ba matsala bane." Ta yi shiru bata ce komai ba tana kallon ƙasa, Baffa da yake kallon ta ya ce, "Faɗi abinda yake ranki, ina jin ki." Islaha a sanyaye ta ce, "Daman...." Sai ta kasa magana ta kuma yin shiru. Baffa ya ce, "ki nutsu, ina jin ki. Faɗi abinda yake zuciyarki, kar ki saka tsoro ko fargaba." Islaha ta ce, "Daman cewa zan yi na amince da auren Baffa." Baffa ya yi murmushin jin daɗi ya ce, "da gaske ki ke?." Islaha ta ce, "Da gaske nake." Baffa ya ce, "Allah ya yi miki albarka. Duk da ba ki san waye mijin ba ki ka amince da abinda na ce miki, ki ka yarda da maganata ki ka amince da kalamana. Islaha ba ƙin ki nake yi da Saheer ba, akwai abinda nake dubawa akan auren ki dashi shiyasa na soke shi da kaina." "Islaha In sha Allah wanann auren da za ki yi baza ki yi danasani ba. Kuma daman na faɗa miki ni tuni na faɗa musu kin amince, amma tunda yanzu kin amince da kan ki kin ga faɗuwa ta zo daidai da zama. Allah ya yi miki albarka, Allah ya taimaka miki, Allah ya shiga lamarin ki, Allah ya sa auren nan ya zama silar farin ciki a rayuwar ki." Islaha tana so ta amsa da amin, amma kuma addua'ar ƙarshe ce bata so ta tabbata, sai kawai ta yi shiru bata amsa ba. Baffa ya ce, "tashi ki je, Allah ya yi miki albarka." Ta miƙe a sanyaye suka fito suka shiga wajan Mama. Nana Haleema. [7/29, 12:06 PM] KRBBK: RDB2P94 Nana Haleema. Islaha suna shiga wajen Mama suka bita da kallon raini da ƙasƙanci, sai suka yi dariya ita da Hanan har suna tafawa. Irin dariyar nan ta rainin hankali, mai saka ciwo da raɗaɗi a zuciyar wanda aka yi dariya dan shi. Mama ta ce, "Ka ga matar mahaukaci, yanzu duk wannan iyayin a auren mahaukaci za a ƙare." Islaha bata ce komai ba ta waiwayo ta kalli Safeera da take tsaye bata ce komai ba. Hanan ta ce, "Yayanmu dai ya fi ƙarfin wata, sai dai mahaukacin wallahi." "To in ba mahaukacin ba ya za a yi mata tayin auren ɗan AbdulAziz Yola? Sai dai mai taɓin hankalin, shine daidai da ita, shine bazai banbance budurwa da ragowar wasu ba. Hanan ance sunansa Salman ko?." "Eh Mama, ance haka sunansa yake, kuma in ya kashe ta ya kashe banza wallahi. Ita ba uba ba balle ya shige gaba a ƙwaci haƙƙin ranta, kuma waye yake shari'a da mahaukaci?." Suka yi dariya suka sake tafawa kamar ba uwa da ƴa ba. Mama ta ce, "Ga idanu ga hanci, ga gashi har baya ga iyayi, ga farin jini da zaƙin murya, amma duk mallakin mahaukaci ne." Islaha ta ja Safira suka shiga cikin ɗaki, ta tsaya ta jingina da bango bata ce komai ba. A fusace Safeera ta ce, "Matar nan bata da kirki wallahi, wato mahaukaci ne zai aure ki ko? Basu san....." Islaha ta dakatar da ta ce, "Don Allah kar ki faɗa, ki barsu a je a hakan, sai me?." Sai ta ɗauki waya ta kira Sadik yana ɗauka ta ce, "Hamma Sadik zan iya samun account details ɗin ka?." "Me za a yi dashi?." "Kuɗin fansar Hamma za a saka, account ɗin ka zai cire wannan kuɗin lokaci ɗaya?." Cike da mamaki ya ce, "Islaha a ina ki ka samu wannan kuɗin masu yawa haka?." Ta ce, "zan yi maka bayani. Amma yanzu ka turo min kawai" ta faɗa tana yanke wayar, ta ga Safeera tana kallon ta. Ta kalli Safeera ta ce, "meye ki ke kallona kamar na ci bashin ki?." Safeera ta ce, "kina da sa'a wallahi." Ta yi tsaki ta shiga banɗaki ta bar mata wajan..... Bata jima da shiga ba ta fito, ta ga Safeera riƙe da takardar yarjejeniya tana karantawa. Safeera ta kalli Islaha da take tsaye a wajen kayanta tana bincika kayan ta ce, "ni ban ga wani rules na ɗaga hankali a rules ɗinsa ba. Ya ce ba ya so mutane su san ya aure ki kema bakya so, ya ce babu ruwansa dake kema kin faɗa...." Islaha ta yi tsaki bata ce komai ba, Safeera ta ce, "Amma Islaha rule ɗin nan na ki na ƙarshe anya zai yu kuwa?." Islaha ba tare da ta juyo ba ta ce, "wanne kenan?." "Da ki ka saka no intimacy, kina ganin zai ba ki waɗnanan kuɗin ba tare da wani abu ba?. Kuma in ki ka duba a cikin na sa rules ɗin bai saka haka ba, ni sai nake ganin kamar bazai yu ba." Islaha ta waiwayo a fusace ta harare ta ta ce, "Ita yarjerjeniya ko ɗaya bai saka rules ba indai ɗaya ya saka kuma ka saka hannu ciniki ya faɗa. Ba gwara ya hana ni aikina da fita daga gidan akan abinda ki ke faɗa ba? Na yi miki kama da wacce zata saurari wancan banza?. Na rantse da Allah Safeera kina da abin haushi, har kin ɓata min rai." Safeera ta ɗan yi dariya sannan ta ce, "Ba banza bane, tunda aurensa za ki yi." "Auren contract ba. A cikin wata biyar ɗin nan ko hannuna ya riƙe ya karya mana rules, kuma in ya sake ya yi wannan gangancin daga ranar bazan sake zama dashi ba. Daman saboda me na yarda da auren? Saboda Hamma ne, kuma na san zuwa lokacin ya dawo, bazan tsaya ina ɓata lokacina a gidansa ba. Da gangan zan yi abinda zai karya ɗaga daga cikin rules ɗina ko da ba ya so, daga nan zan yi terminating contract ɗin kowa ya kama gabansa." Safeera ta yi dariya ta ce, "mugunta kawai ki ka shiryawa bawan Allah. Da dai kawai ya saka hannu ne, amma ajjiye macen da ka san matar ka ce ta aure, addini da al'ada sun baka ko wacce irin dama a kanta, ka ajjiye ta har tsahon wata biyar kana kallon ta ba tare da wata alaƙa ba akwai wahala, a wannan zamanin dai kafin a samu wanda zai yi wannan jan halin za a jima." Islaha ta ji kamar ta tsinkawa Safeera mari ta ce, "Yana rayuwa a cikin turawa, ya san girman karya rules ɗin da ka yi signing akan amincewar ka a kai. Ni mallakin Hamma ce, babu wani banza da bawa kaina matuƙar Hamma yana da rai." "Hmmm Islaha kenan!. To kina nufin za ki cigaba da son Hamma bayan wannan yarjejeniyar?." "Ban gane ba, da sai na ajjiye son nasa kenan?." "eh mana, na ga matar aure ce ke, son wani ta fuskar soyayyar babban zunubi ne." "Da yake zuciyar tawa whatsapp ce, da zan kunna data na hau lokacin da nake so na sauka lokacin da na ga dama ko?. Kuma da ki ke zancen aure, ki dinga haɗawa da contract." Safeera zata yi magana ta ce, "Dallah malama ki yi min shiru, kina ɓata min rai." Islaha ta ɗauki wayarta ta ga Sadik ya turo acc details ɗin. Ta ɗan dafe kai tana tunanin anya abinda ta yi daidai ne kuwa? Sai yanzu abin yake damunta take ganin kamar ba daidai ta yi ba, sai yanzu take gani kamar ta dakusar da rayuwarta ta lalata carrier ta. Ta bi account number da kallo tana tunanin turawa Jafar, ta zauna a kan gado ta ce, "Safeera ina cikin damuwa, kamar ban aikata abinda ya kamata ba. Contract marrige na yi, wayyo Allah!." Safeera ta ce, "Ai na faɗa miki ki ƙa ji, yanzu da muka dawo ma na sake maimaita miki. Kin yi gaggawar yanke hukunci babu dogon nazari gaskiya, amma tunda kin bawa Allah zaɓi wataƙila shine alkhairin ki." Ta ɗago a fusace tana hararar ta ta ce, "Ta ya wannan auren zai zama alkhairi a gare ni?." "ki daina faɗa, ba ka yankewa kan ka hukunci akan abinda ba kai za ka yiwa kanka ba. Kawai ki cigaba da addu'a Allah ya shiga cikin lamarin." Islaha ta yi shiru, ta yi forwading acc detaila ɗin zuwa ga lambar Jafar da ko saving ma bata yi ba. Ta jima a zaune a wajan daga ita har Safeera babu mai cewa komai, sai daga baya Safeeta ta ce, "Su wai ƴan gidan nan ɗauka suke yi ɗansa da akace yana da taɓin hankali za ki aura? Da yake ga ki ƙarshen mara gata, sai kawai Baffa ya ɗauke ki ya aurawa mahaukaci." "don Allah Safeera mu bar maganar nan haka, kin yi min alƙawarin babu wanda za ka faɗawa." Safeera ta yi ziping bakinta ta ce, "shikenan, bara na koma gida." Tana miƙewa wayar Islaha ta fara ƙara, Islaha ta ga kiran Sadik ne sai ta ɗauka ta saka a kunne. Daga can ɓangaren ya ce, "Islaha an saka min kuɗi fa, an saka kuɗi har naira miliyan hamsin. Fito ina waje." Ta kalli Safeera da take tsaye ta ce, "An saka kuɗin, mu je waje mu same sa" ta faɗa tana miƙewa ta yafa mayafi. Suna fita basu tarar da babu kowa a falon suka fita zuwa ƙofar gida. A jikin motarsa suka sake shi a tsaye, suka ƙarasa dan wajan da ya tsaya rana sosai. Tana zuwa wajen Sadik ya ce, "Islaha kuɗin waye wannan?." Islaha ta ce, "kuɗin fansar Hamma ne, ya za a yi a mayar dasu cash, ka yi musu waya kace musu an haɗa kuɗin? Amma bana son Baffa ya san kuɗin aka samu." Sadik ya dakatar da ita ya ce, "in na yi magana sai ki ce ina yi miki wani kallo na daban, yanzu meye wannan?. Wancan lokacin na gan ki da rafar daloli, yau kuma ga ki da naira miliyan hamsin. Islaha kina so kaina ya tarwatse ne?." "Ai na faɗa maka abinda zan yi ko? Ban ɓoye maka ba na faɗa maka saboda gudun zargi. To shi na aikata, ga kuɗi nan sun zo ni kuma na ƙulla yarjejeniya." "Na shiga uku ni Sadik!...." ya faɗa yana dafe kansa tare da juya musu baya. Sai kuma ya waiwayo ya ce, "Islaha ba mafarki bane ba wannan, rayuwa ce ta zahiri wacce take faruwa a gaske ba a mafarki ba. Ki ɗago kai ki kalle ni da kyau, a gabanki nake a tsaye ba a cikin mafarki nake ba..... Ki daina raina min hankali, ki faɗi abinda zai yu don Allah. Wanne irin mutum ne zai ɗauki wannan kuɗin ya ba ki saboda auren contract." Islaha ta ce, "Na dai faɗa maka gaskiya, ka daina yi min tambayoyi akan wannan abun da ya riga ya zama tarihi, abinda na sani shi nake faɗa maka. In ba ka yarda ba ga Safeera nan, a gaban idanunta aka yi komai, wataƙila in ita ta faɗa maka baza ka ƙaryata ba." Safeera ta ce, "Hamma Sadik a gabana aka yi komai, har takardar yarjejeniyar na karanta. Ta ƙulla aure na wata biyar saboda kuɗin fansar Hamma." "in aka je yarjejeniya ana nufin yarjewa akan abinda kowa yake da ra'ayinsa. Na ji ita akan Hamma ta yi, shi kuma akan me ya bata kuɗin dan ya aure ta?." "Mahaifinsa. Zai aure ta saboda mahaifinsa" Safeera ta ta bashi amsa tana kallonsa. Ya kalli Safeera ya ce, "wai waye wannan mutumin ne? Waye wanann da akan mahaifisa sai yi aure ta harda wannan kuɗin matsayin na yarjejeniya?." Islaha ranta ya fara ɓaci ta ce, "bazan tsaya na tsara maka ƙarya ba, in ma abinda ka ke tunani na je na aikata babu wanda zai bani waɗnanan kuɗin a lokaci ɗaya saboda na bashi kaina. Abinda nake so da kai kawai ka amince, a je a yi abinda ya kamata." Ya kalle ta ya ce, "Ba ki amsa min ba, waye shi?." Islaha ta ce, "In na faɗa amfani me hakan zai yi?." Sadik ya ce, "Ki faɗa min." Islaha ta ɗan yi jim tana tunanin ta faɗa ko kar ta faɗa, ta kalle shi ta ga ita yake kallo alamun yana jiran amsa, ta sake tafiya dogon tunani kafin ta ce, "Rehaan AbdulAziz Yola, wanda ka fi sani da Ray!. Nana Haleema. [7/29, 12:06 PM] KRBBK: RDB2P95 Nana Haleema. Sadik sai da wayar hannusa ta kubce ta faɗi ƙasa saboda yadda sunan ya ratsa kunnensa ya shiga har ƙwaƙwalwa. Safeera ce ta duƙa ta ɗauko masa wayar, tana murmushi tana aiyana inda shine ya gansa ido da ido da bata san ya zai firgice ba. Sadik ya zuba mata ido yana kallon ta cikin rashin sanin abinda zai ce mata. Sunan Ray kawai yake maimaita a ransa, da Raay ta ƙulla auren contract take nufi ko me? Da Ray zata zauna a matsayin miji da mata ko kuma dai wasa take yi masa? Ya kasa magana sai tunani yake yi, duk da ta faɗa masa sunan mahaifin wanda za a yi auren amma ko kusa bai kawo Rehaan bane. Ya ɗauka sauran yaransa ne tunda ance yana da yara da yawa, bai yi tunanin babbar giwar ne da kansa ba. Sadik ya kalle ta ya ce, "Ray fa ki ka ce?." Islaha ta nuna masa Safeera ta ce, "ka tambaye ta, a gabanta aka yi komai." Ya kalli Safeera ya ce, "Da gaske shine ko AI ne?." Ta ɗan yi dariya kaɗan ta ce, "shine. Yadda ka shiga wannan firgicin haka nima na shiga, lokacin da na haɗa ido dashi sai da na ji kamar ba a duniyar nake ba. Mr Ray da muke gani a tv da magzine, shine na zauna a falonsa har na haɗa ido dashi. Har ya yi mata magana da yaren da nake ji, ban ɗauka ya iya wani yare in ba turanci ba, sai gashi na ji ya yi har zan ba da shaidar ya iya ko ina. Rehaan shine wanda ya saka hannu Islaha ta saka hannu, shine ya tura kuɗin da aka turo maka." Sadik ya karɓi wayarsa a hannaun Safeera, ya duba bank name ɗin wanda ya turo kuɗin, amma sai ya ga sunan kamfani ne kuma bai yi kama da sunan Ray ba. Ya kalli Safeera ya ce, "Bank name ɗin ba nasa bane." Safeera ta ce, "Kaima kamar ba mai ilimi ba, ta ya zai turo maka kuɗi da kansa? Sai dai ya saka a tura." Sadik kalli Islaha yana girgiza kai ya ce, "Abokina ya yi haƙuri, ko da ya dawo daga hannun masu garkuwa Islaha kin fi ƙarfin....." Islaha dakatar dashi a fusace ta ce, "kar ka ƙarasa!." Ta nuna kanta da yatsa ta ce, "Har abada ni matar Hamma ce, babu wani namiji da zan kasance a ƙarƙashinsa a matsayin mijina sai Hamma. Auren wata biyar ne kawai, daga ya ƙare kowa zai kama gabansa kamar ba a zauna ba. Na auresa saboda Hamma, kuma zan zauna da shi saboda Hamma, zan dawo saboda Hamma. Zan dawo a ɗaura mana aure da Hamma, mu zauna a matsayin ma'aurata kamar yadda muke mafarkin halam, shi kuma ya je ya cigaba da rayuwarsa kamar yadda yake yi!" Ta faɗa cikin fushi tana kallonsa. "Amma Islaha ko da ace kun rabu za a ce ex wife ɗin Ray ce, iya wannan matsayi da ki ka samu na ex ɗinsa babban mataki ne a duniyar nan. Kuma ta ya zai sake ki? Ni bana hango rabuwa a zaman ku." "Na faɗa maka auren wata biyar ne kawai, ya san mahimmacin rules tunda a turawa yake rayuwa, ya san meye contract marriage tunda a cikin masu yi ɗin yake zama ko yaushe. Bazai karya ɗaya daga rules ɗina da na ba shi ba, zai yi komai base on yadda muka gina auren ni da shi, bazai taɓa breaking ko guda ɗaya ba, dan ya san illar yin hakan. Zan kiyaye rules ɗinsa, shima zai kiyaye nawa, lokaci yana yi komai zai ƙare." Sadik ya girgiza kai ya ce, "Islaha ya kamata ki tuna, bayan contract akwai aurensa a kan ki. Mu musulmai ne, ba a kan contract mu ke gina aure ba balle mu ce da an yi canceling shikenan auren ya ƙare. Dole sai ya sake ki ta hanyar furta miki ko ya rubuta miki." Islaha ta ce, "Na san da wannan, kuma zai yi ɗin kamar yadda na faɗa maka." "Yanzu yau laraba, jibi kenan ɗaurin auren ku dashi?." Ta masa ɗaga kai alamun eh. Sadik ya ce, "Baffa ya sani?." "ya sani, amma bai san batun yarjejeniya ba. Don girman Allah ka yi min alƙawari babu wanda zai sani, daga kai sai Safeera ne ku ka san maganar nan, don Allah ka riƙe min amana. Ko Hamma ne zai dawo kar ka faɗa masa, ni zan san abinda zan ƙirƙira na faɗa masa amma ba aure ba. Kuma ko da wasa kar ka faɗawa wani ka san Rehaan ya yi auren contract dani ko da wata, wallahi bana so a san da auren nan kamar yadda ba ya so." Sadik ya ce, "Na yi miki alƙawari babu wanda zai sani in sha Allah." Ta ce, "Sai batun waɗanda za a kira domin kuɗin fansar Hamma, Baffa suke kira yanzu ba kai ba, ya za a yi yanzu?." Sadik ya ce, "ni suka fara kira kafin Baffa, zan kira su gobe, sannan zan je a ciro kuɗin a bank sai a kai musu. In Allah ya yarda Saheer zai fito lafiya." Ta ɗaga hannu sama ta ce, "In sha Allah." Sadik har lokacin bai fita daga shock ba, ya kalle ta alamun yana son yin magana amma ya ga ta haɗe rai alamun babu tambaya, dole ya yi shiru ya shiga mota yana tunani akan wannan lamari mai ɗaure kai. A gidansu Ray shagali bikin kawai ake yi, masu henna ma daga india suka zo aka yiwa amarya da ƙawayenta ds iyayen amarya. A ranar suke yin indian night kamar yadda suka saka shi a cikin jerin event ɗin da zasu gabatar. Ango da amarya sun sha kwalliya a cikin kayan india, kowa ya kalli Riyya ya san jininsu ce, shima Jay da yake yana da haske da kyau sai ya zama kamar ɗan india ɗin. Kowa in ya kalle su sai ya sake kallo saboda kyau, ita kanta Mamy ɗin shigar india ta yi, kowa na wajan shigar india ya yi dan kyauta aka raba kayan. Mama da Umma ne suka ce baza su saka ba, sai suka saka lafaya kawai amma basu naɗa sari kamar sauran mutane ba. Rehaan ma kayan india ya saka, irin rigar nan tasu mai ɗan tsaho har guiwa. Yana zaune a kame a wajan, har ya fi amarya da angon farin jini dan shi kaɗai ake haskawa. Cikin lokaci kaɗan hotuna da video suka zaga duniya, ana ta yaba kyau da tsarin bikin dan ya ƙayatar sosai. Umma da Mama sai taɓe baki suke yi, suna ganin yadda ake ɓarin kuɗi a wajan dan dukkansu da kuɗin india suke liƙi ba naira ba. Lokacin da Riyya ta je ta riƙo hannun Yayanta ya shigo kan stage wajan ya ɗauki ihu, iya Mamy ne dasu a kan stage ɗin sai Jazy da ya zama ɗan family Mmay shima. Gently Mamy take taka rawar india, shi dai yana tsaye yana murmushi yana riƙe da hannun Banisha da take kusa dashi. Sai daga baya ya fara yiwa Mamy liƙi da kuɗin da bai san adadinsu ba, Mamy ta ruungume su aka yi musu hoto. Daga nan aka kira mawaƙin daga gayyata tun daga ƙasar india har nigeria. Mawaƙin da india take ji dashi, mawaƙin da india suke mararinsa, mawaƙin da bollywood take ji dashi, mawaƙin da mu kan mu ƴan nigeria waƙoƙinsa suke burge, wato arijit sight. Aka chase aka raba abubuwa masu yawa, sai ƙarfe ɗaya na dare aka tashi kowa ya tafi. Mama da Umma suna zaune basu tashi ba, duk da sun gaji amma sun ƙi tafiya, amma saboda gulma suna zaune sai sun ga ƙarshen abin. Mama ta ce, "Abu babu tsari, wai indian night. An cuci ahlimu da aka ɗauko mana wannan." Umma ta ce, "ni ba wannan ba, wai ina matar Rehaan ɗin ne? Ita meyasa ba a yi bikin da ita ba?." Mama ta ce, "ƙyale jinin matsafa, kin san da yake ba son auren yake yi ba, bazai bari ayi biki dashi ba. Ni kuma wallahi sai na tabbatar da auren nan saboda cikar burina." Umma ta ce, "Haushin yaron nan nake ji, da ace mutuwa a hannuna take da yanzu na kashe shi kowa ya huta. Komai ace Rehaan, komai shi? Yaran mu sun zama koma baya, ba a yin komai dasu sai shi?. In ki ka ɗauki waya ki ka duba kafafen yaɗa labarai, gabaɗaya akansa ake magana yau. Shirme!" Ta faɗa tana miƙewa ta fita. Mama ta bita da kallo tana murmushi ta girgiza kai ta ce, "duk yadda zan yi na mallake yarinyar nan ta zama yar ɗakina sai na yi, ba a banza na tsaya kai da fata a aurota ba, ina da shiri na musamaman akan hakan. Zan riƙe ta da kyau, zan jawo ta a jiki, zan nuna mata ƙauna, yadda duk abinda na ce tayi akan Rehaan zata yi, duk wani sirrinsa zai zama yana tafin hannuna." Ta sake yin dariya ta ce, "Mu je zuwa, yanzu ne za a fara kafcen, da ba a yi komai ba." Washe gari. Saheer tunda ya ji labarin za a kawo kuɗin fansarsa sai jikinsa ya yi sanyi, duk sai ya damu yana tunanin in ya tafi wa zai bar wa amanar sa Sudais ya bar masa? Kuma Allah ya sani ba ya so su Black su yi nasara akanta, ba ya so wani abu ya shiga tsakaninta da mai garkuwa da mutane da sunan mijinta. Duk da mijinta ne na aure, an ɗaura aure da sadaki da shaidu, amma rashin mafita ce ta saka aka amince dashi. Kwana biyu ta ɗan sa ki jiki, duk bata magana har lokacin amma in suka bashi abinci suka ya bata tana ci kaɗan, kuma shi kaɗai ne yake yi mata magana ta ji. Gabaɗaya sai ya ji ya damu, ba dan ba ya son komawa gida ba, sai dan bai san ya rayuwarta zata kasance a wajen ba. Ƙarar machine ɗin Arɗo da ya ji ya saka shi ya ɗago ya kalli Arɗo da ya sauka daga kan machine ɗin, ya zauna a inda ya saba zama yana kallon su ɗaya bayan ɗaya ya ce, "Ban kawo ku nan na ajjiye ku ba, ban kawo ku nan dan mata su dinga dafa mu ku abinci kuna ci ba. Duk wanda ƴan uwansu baza su kawo kuɗi ba za mu daina ganin ku, ƴan uwanku kamar ba sa son ku." Kowa ya yi shiru babu wanda yake magana, ya kalli Saheer ya ce, "Kai yau mu ka yi zasu kawo kuɗin ka, ga shi akwai inda zan je na dawo. Sai dai in sun kawo su tafi, ka bi bayansu daga baya." Saheer dai ba shi da bakin magana, wannan kashe kashe da yake yi kamar suna kashe sauro bazai bar ka ka yi magana ba. A take ya saka aka fito da mazan ciki, suka yi musu dukan tsiya aka yi video aka turawa ƴan uwa, shi kuma ya tashi ya fita. Kamar yadda Sadik ya shirya haka shirya kuɗi ya ta fi dajin da kwantance da suka dinga yi masa, su da kansu suka faɗa masa inda zai tsaya, ya je wajen ya tsaya, suka ce masa zai ga mai jar riga kawai ya bi bayansa, haka aka yi yana ganin mai jar riga ya bi sa, daga nan aka hau machine aka tafi sansaninsu. Islaha da Safeera ne kaɗai suka san an tafi kai kuɗi, ko su Baffa basu san me yake faruwa ba, ba a so su sani saboda kar su tambayi a ina aka samo kuɗin. Islaha tunda Sadik ya tafi gabaɗaya bata da nutsuwa, duk ta ruɗe saboda tashin hankali har rama ta yi, tunda Sadik ya tafi bata iya zama ba kai kawo take yi. In ta gaji ta huta ta kuma miƙewa tana cigaba da tunani. A ranar gidan su Rehaan a ranar aka haɗawa Riyya grand kamu, babu yadda Jafar bai yi da Rehaan ba amma ya ƙi zuwa. An shirya kamu a babban ɗakin taron da ake ji dashi a garin Yola, an kashe kuɗi masu nauyi, anyi harkar gold, social media ta san ana bikin ƙanwar Rehaan Yola. Amarya ta yi kyau, ta samu gift ma su yawa marasa adadi. Gidan su Rehaan suna can suna shagali, islaha kuma tana tunani, har dare babu Sadik babu labarinsa. Hankalinta ya tashi, ko abinci ranar bata ci ba, gani take kamar Sadik ɗin bazai dawo ba. Nana Haleema. [7/30, 11:15 AM] KRBBK: RDB2P96 Nana Haleema. Sai sha ɗaya na dare sannan ta ga Sadik yana yi mata waya, ai ko hijjab bata tsaya sakawa ba ta fita a guje ta gansa a harabar gidan a tsaye. Ta tsaya tana kallonsa ganinsa shi kaɗai, shima ya gaji kuma wahala ta bayyana a tare dashi sosai. Ta ƙaraso ta ce, "Hamma Sadik ya ake ciki, Ina Hamman nawa?." Sadik ya kalle ta kamar yadda take kallonsa, ita kuma gani ta yi duk ya firgice, ruɗewa da tsoro sun bayyana ƙarara akan fuskarsa. Sadik Ya ce, "sun ce sai gobe ko jibi za su sako shi." "Kamar ya? Daman in aka ba da kuɗi ba ranar mutum yake dawowa ba?." "Ban sani ba Islaha, ban taɓa zuwa inda suke ba sai yanzu. Daji ne Islaha, ban taɓa shiga daji ba sai yau, wajen kamar ba a duniya yake ba." "Ka ga Hamma Saheer?." Ya ɗaga kai ya ce, "na gan shi." Hawaye ya sakko daga idonta, ta saka hannu ta rufe bakinta ta ce, "basu kashe sa ba?." Ya ɗaga mata kai yana murmushi ya ce, "yana nan da rai, kuma zai zo ya ganki. Wai shugaban nasu ne ba ya nan, shiyasa baza a ba da shi ba. Duk yawan kuɗin nan sai da na irgasu, a haka ma ban gama ba kawai na ce musu na gama ne." Islaha ta zube a wajan ta yi sujjud shukur tana farin ciki da murnar Hamma yana da rai, sai ta miƙe ta ce, "Yanzu sai gobe ko jibi?." Ya ɗaga kai ta dafe kai ta ce, "meyasa basu ƙyalesa yau ba? Kar su karɓi kuɗi su hana mu shi." "Za su bayar in sha Allah." "Ya Hamma yake, Ya rame ko?." Sadik ya yi murmushi yana kallonta ya ce, "Samun mace mai ƙaunar mutum tsakani da Allah kamar ki za a jima, ƙarnin irin ku ya jima da ƙarewa, waɗanda suke saka rayuwarsu a hatsari saboda wanɗanda suke so ya jima da shuɗewa. Har abada Saheer bazai samu wacce take sonsa kamar ki ba, har abada Saheer bazai samu masoyiya kamar ki ba, har abada Saheer bazai samu mai ƙaunarsa da zuciya ɗaya kamar ke ba. Na jinjina miki sosai, kin sadaukar da farin cikin ki da rayuwarki gabaɗaya saboda shi, Allah ya bar ƙaunaa." Ta yi murmushi tana goge hawaye ta ce, "Hamma ya wuce komai a wajena, Hamma ya yi min abinda babu wanda ya yi min shi a duniyata. Ya ɗauko ni kuma ya riƙe ni, ya taimake ni ya kaini matakin da ban yi tunanin zuwa ba. Duk ahinda  zan yi masa ban faɗi ba, kuma ban saka masa ba." Ya ɗaga kai ya ce, "Gaskiya ne wannan. Ina so na faɗawa Baffa saboda kar ya yi asarar da kadararsa ya siyar, amma ban san me zan ce ba." Islaha ta ce, "Ka samu dabarar da zai daina cewa zai siyar ɗin." Ya ɗaga kai ya ce, "zan san abinda zan yi in Allah yarda, Baffa yana nan?." "Yana ciki." "bara na je na same sa, shi da Maman." Islaha bata ce komai ba, ya wuce ya shiga ciki itama ta bi bayansa. A nan ya samu Mama a zaune suna tattaunawa akan batun siyar da kadarorin da aka saka a kasuwa. Kamar dare bai yi ba, dukkansu idanunsu biyu ana lissafa abubuwan da ya kamata a siyar. Bayan sun gaisa Baffa ya ce, "Sadik tun ɗazu nake yi maka waya." Sadik ya ce, "ina can wajan ƴan sanda ana maganar yadda za a fito da Saheer ba tare da ko sisi ba, kuma da alamun nasara in sha Allah." Mama ta ce, "Sadik ni ban yarda da wanann maganar ba, kawai a samu kuɗin nan a basu." Baffa ya kalle ta ya ce, "kina dasu ne?." Sai ta yi shiru bata ce komai ba, Baffa ya kalle sa ya ce, "Kana ganin hakan zai yu?." Sadik ya ce, "In Allah ya amince, a cigaba da addu'a kawai. In sha Allah Saheer zai dawo gida ba tare da ko sisi ba." Baffa ya yi masa addu'a sannan Sadik ya tafi, da a gajiye yake sosai, yana so ya je ya huta. A take Baffa ya kira Islaha ya bata labari mai daɗi, bata nuna masa ta sani ba, sai ta nuna ta ji daɗin maganar yadda zai yi tunanin da gaske take, a haka kowa ya kwanta, duk mutanen gidan babu wanda yake cikin walwala da jin daɗi. Washe gari Friday. Jazy yana ta shirin ɗaurin aure, ya saka lafiyayyar luxury shadda fara mai kyau da ɗaukar ido, yana tsaye a gaban mirror yana ɗaura agogon hannunsa, sannan ya ɗauki hula ya saka a kansa yana kallon kansa. Ya yi murmushi dan shi kansa ya san ya yi kyau, ya kalli Ray da tunda ya saka kayan ya koma ya zauna ko magana bai sake yi ba. Jazy ya kalli agogo sannan ya kalle sa ya ce, "Ray lokaci yana tafiya, tun ɗazu ka zauna ba ka tashi ka gama shiryawa ba." Rehaan ya kalli Jazy kamar mai tunani, suka haɗa ido ya ga Jazy ɗin ya yi kyau sosai, sai miƙe tsaye yana ajjiye wayar hannunsa. A tsakiyar kansa ya naɗe gashinsa, ya ɗauki hula ya saka ya rufe gashin gabaɗaya babu ta inda ya fito, ya saka agogo yana kallon babbar rigar da Jazy ya saka aka ɗinka masa, ya ɗauka ya saka yana kallon kansa. Ray ya murmusa dan ba sai ance ya yi kyau ba, shi kansa ya san ya yi kyau, bazai iya tuna rabon da ya saka babbar riga a rayuwarsa ba. Ko bikinsu Sameer bai saka ba, ya saka dai manyan kaya amma bai saka babbar riga ba. Kayansu iri ɗaya ne sak da Jazy, hatta takalmin ƙafarsu iri ɗaya ne, sai banbancin hula da agogo da lins. Jazy ya ce, "Ma sha Allah! Angon Islaha, ka yi kyau sosai." Rehaan ya haɗe rai, murmushin da yake yi ya gushe daga kan fuskarsa, ya ɗan harari Jazy amma bai ce komai ba. Jazy ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Wallahi kyaunka na yau na daban ne dana kullum, ka yi kyau sosai ba tsokanar ka na ke yi ba. Dole na yi mana selfie, na yi posting ko zan samu likes da comments, ka san yin hoto da irinka sai mai sa'a" ya faɗa yana ɗauko wayarsa. Ray ya matsa daga wajean alamun bazai yi hoton ba, Jazy ya riƙo shi ya ce, "Dallah ka kalla, tarihi ne fa." Bai ƙi ba ya kalli camerar Jazy ya ce, "ka yi dariya mana, Yayan matata." Sai ya yi murmushi jin sunan da ya kira shi dashi, Jazy ya ɗauke su hoton duk sun yi murmushi kuma ya yi kyau sosai, kowa annuri da kyaunsa ya bayyana a cikin hoton. Rehaan camly ya ce, "ba ka da tarbiyya, Yayan matar ta ka ka raina haka." Jazy ya yi dariya ya ce, "my billionaire." A lokacin wayar Jazy ta fara ringing, da ya duba sai ya ga sunan Abba ne hakan ya saka shi ya ɗauka. Yana sakawa a kunne Abba ya ce, "Jaafar kuna tare da Rehaan ne?." Jazy ya ce, "Eh Abba." "Kuna cikin gida?." "A'a muna guest house." "Ku yi hanzari ku zo nan kafin ku je masallaci, kuna zuwa gidan ku shigo main palour ba sai kun shiga ciki ba. Ku yi sauri." Jazy ya amsa ya kashe wayar. Jazy ya ce, "mu je in ji Abba, ya ce mu je yanzun nan." Ray bai ce komai ba ya ɗauki wayarsa suka fito daga ɗakin. A harabar gidan ya tsaya yana amsa waya, security guard ɗinsa suka ƙaraso suna yi masa barka da fitowa. A lokacin Mansur driver Rehaan ya fito da tsaddiyar sabuwar motar Rolls Royce 2026, aka ajjiye ta a wajen ana jira ya gama wayar ya shiga su tafi. Jazy ne ya ƙarasa kusa da motar yana yiwa Ray magana, aka buɗe musu sabuwar motar suka shiga baya suka tafi gidan. Kamar yadda Abban ya ce a main falo ɗin suka shiga da sallama, mutanen ciki suka amsa suna kallonsu, su kuma suka shiga ciki suka zauna. Sameer ne da Zayyad da Baba, sai Alhaji Rufa'i, Daddy, Abie, Baffa, da Kawun Saheer da malamin da yake ɗaura auren ƴan gidansu. Gabaɗaya mutanen falon basu fi su goma ba, sai goro alewa da suke a ajjiye a wajen. Sai Ray da Jazy suka zauna sannan Abba ya ce, "Yauwa, za mu fara ɗaura auren Rehaan a wajan nan kafin mu tafi masallaci." Zayyad cikin mamaki ya kalli Abba ya ce, "Abba ba a masallaci za a ɗaura ba?." Abba ya ce, "a nan za a ɗaura na Rehaan, na Jafar ne za a yi a masallaci. " Rehaan dai tunda ya sauke kai ƙasa bai ɗago ba, yana ji ana hidimar ɗaura aurensa bai ce komai ba, yana ji ko wanne ɓangare yana gabatar da kansa a matsayin wakili, yana ji ana zancen sadaki ana tambayar shaidu sun shaida. Yana ji yana gani aka ɗaura aurensa da Islaha akan sadaki naira miliyan ɗaya, aka bawa Baffa sadakin Islaha. Ji yake jinin jikinsa kamar ya daskare ya daina zagawa, ya kasa ɗago kai saboda yadda yake jin jikinsa ya yi sanyi sosai. In ya tuna aurensa aka ɗaura da Islaha sai ya ji kamar a tashi duniyar, sai ya ji kamar kowa ya mutu a bar duniyar babu kowa. Bayan an ɗaura auren Abba ya kalli Baffa yana  murmushi ya ce, "Alhaji Mustapha mun gode, Allah ya saka da alkhairi." Baffa ya yi murmushi ya ce, "Amin. Allah ya tabbatar da alkhairi a cikin auren, Allah ya sa ya zama silar farin cikin kowa." "Amin ya Allah." Abba ya kalli su Jafar ya ce, "Zayyad ku je masallacin gamu nan, an bar mutane suna ta jira." Duk suka miƙe suka fita, aka bar Rehaan da Daddy a zaune. Abba ya ce, "Alhaji Mustapha ga Rehaan...." Abba juyo ya kalli Rehaan ya ce, "Rehaan ga mai riƙon matar ka, kuma uba a gare ta. Ka yi masa godiya akan karamci da haliccin da ya nuna mana. Ba tare da ya san mu ba ya ɗauki ƴarsa ya bamu, bai san kai ne za ka auri ƴarsa ba, amma ya amince da zuciya ɗaya. Ka yi masa godiya." Rehaan ya ɗago ido a hankali ya kalli wanda aka muna masa, ya rasa me zai ce, dan shi bai ga abin godiya a auren Islaha ba. Amma sai ya daure ya ce, "an gode" ya faɗa a taƙaice dan babu yadda zai yi. Baffa ya yi murmushi ya ce, "Babu komai, Allah ya sanya albarka a cikin auren, Allah ya ɗorar da zaman har aljanna." Duk aka amsa da amin ban da Rehaan da ya ja bakinsa ya yi shiru. Baffa ya ce, "Na san ka san marainiya ce, a gidan marayu ta girma, bata san kowa na ta ba. Islaha yarinyar kirki ce, yarinya ce ta gari mai tarbiyya da sanin ya kamata. Yadda take yin ɗawainiya dani ko ƴaƴan dana haifa basa yi, yadda take yi min biyayya ko ƴaƴana basa yi min. A ko yaushe ina ji a raina ina ma ni na haifi Islaha, ina jinta kamar jinina, ina ji kamar ɗaya daga cikin yaran da Allah ya bani. Ka riƙe ta hannu biyu, na tabbatar da baza ka taɓa danasanin aurenta ba, sai dai ka yi alfahari." Daddy ce, "Duk mun shaida, tarbiyyarta ce ta saka Daada ta ganta, ta burge ta har mu ka zo wannan matakin. In sha Allah ƴarku ba zata yi danasani ba, baza ta yi hawaye ba, baza ta yi maraici ba. Zata rayu cikin farin ciki da walwala, za a maye mata gurbin ku da zata baro ta dawo nan." Baffa ya ce, "Allah ya tabbatar mana da haka." Duk suka amsa da amin kafin Abba ya kalli Ray ya ce, "ka je masallaci, ga mu nan." Ya miƙe a hankali ya fita ya bar su. Bayan sallar juma'a aka ɗaura auren Riyya da Jafar, bayan an ɗaura auren anata hotuna kafin a tafi reception, Ray dai yana killace dan ba hayaniya yake so ba, duk inda ya yi masu tsaron lafiyarsa suna bin bayansa. A haka aka watse daga reception, ya wuce guest house dan Jazy ba dawowa zai yi ba. Nana Haleema. [7/30, 11:15 AM] KRBBK: RDB2P97 Nana Haleema. Baffa bayan ya koma gida ya shiga har falon Mama ya samu Mama ta ita kaɗai a zaune ya ce, "Ina Islaha?." A daidai lokacin Islaha ta shigo da sallama, kafin su ji sallamar ta ta Mama ta ce, "Ta tafi yawon ta zubar, ko ta ɓatan Saheer ba ta yi, sai ƙaryar Hamma." Islaha ta ce, "Gani Baffa." Baffa ya juya yana kallon ta yana murmushin jin daɗi, ji yake kamar ya sauke nauyin da Allah ya ɗora masa, ji yake ya sauke haƙƙin da Allah ya ɗora masa a matsayin uba. Islaha ta durƙusa a gabansa Baffa ya ce, "Kina da sa'a Islaha, ke mai sa'a ce gaba da baya. Duk mai nufin ki da sharri ko waye shi sai dai ya koma kansa, Allah ya yi miki abinda babu wanda ya isa ya ƙwace sa daga hannunki, alkhairin da ki ke nema ya ba ki, da ya tashi ba ki sai ya ninka ya kuma ninkawa. Karɓi nan" ya faɗa yana miƙa mata. Ta saka hannu ta karɓa tana kallon kuɗin ganinsu sa yawa. Baffa yana murmushi ya ce, "kin san meye wannan a hannun ki?." Islaha ta ce, "A'a Baffa." Baffa ya murmusa cikin jin daɗi ya ce, "sadakin auren ki ne." Gaban Islaha ya faɗi, ta buɗe ido waje ƙirjinta yana bugawa da ƙarfi. Ta kalli kuɗin ta kalli Baffa da yake kallonta, ta sake ɗauke kai tana jin wani iri a jininta, ga wani irin yanayi da take ji yana manaye ko ina a jikinta. Mama ta yi tsaki ta ce, "Sadakin auren mahaukacin har wani abin murna ne? Mahaukaci ne fa wanda aka bata, sai meye dan ya aure ta?. A banza zai kashe ta kuma ya kashe banza, babu abinda aka isa ayi ranta ya tafi a banza. Ni tunda dai bata auri ɗana ba ko waye ta aura bai dame ni ba, Saheer dai ya fi ƙarfinta wallahi." Baffa bai kulata ba ya ce, "Islaha kin yi shiru." Gabanta faɗuwa yake yi, da farko bata yi tuannin zata ji irin wanna faɗuwar gaban ba tunda ta san a yadda aka gina auren, amma sai ta ji tsoro yana mamaye mata ƙirjinta, fargaba da sanyin jiki suna yi mata dirar mikiya lokaci ɗaya. Cikin sanyin murya ta ce, "Har an yi auren?." Baffa ya yi murmushi ya ce, "An ɗaura. Yanzu ke matarsa ce halak malak, sun ce min gobe zasu turo da motoci a ɗauke ki, tunda babu bikin da za ki yi sai ki tare a gidan ki gobe." Ta wara ido tana kallon Baffa jikinta har rawa yake yi ta ce, "Baffa gobe kuma?." "Ko kina da shirin da za ki yi ne?." Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Baffa ya ce, "na riga na amsa musu, amma in akwai abinda za ki yi sai a faɗa musu." "Shikenan Baffa." "Na faɗawa Yayar ki, za a zo ayi miki ado irin na amare, bai kamata a kai ki a haka ba." Islaha ta ce, "ba sai ta zo ba Baffa." Baffa ya ce, "Haka za a yi auren na ki babu kwalliyar amare?." Ta yi shiru bata amsa ba dan gaskiya babu abinda zata yi. Baffa ganin haka sai ya ce, "Shikenan, ki je ki haɗa komai na ki, yau Allah ya ɗaga darajar ki daga ƙasa zuwa sama. Waɗanda suke ganin ki a wulaƙance zasu fahimci sun tafka kuskure, zasu gane sune a wulaƙance ba ke ba." Islaha ganin Baffa zai fita sai ta ce, "Baffa kuɗin." Ya kalli kuɗin ya ce, "Sadakinki ne, ke za ki riƙe." Ta bi kuɗin hannunta da kallo ta sake kallon Baffa ta ce, "Baffa ka bar su a wajan ka." Ya yi murmushi ya ce, "Haƙƙinki ne Islaha." Daga haka ta fita ita kuma ta sauke numfashi tana kallon kuɗin. Ta kalli Mama da take tsaye tana kallon ta, ta ɗauke kai tana miƙewa tsaye. Mama ta bita da kallo ta ce, "Amaryar mahaukaci! Yau Allah ya yi zan rabu da alaƙaƙai daga cikin gidana, sai a je can a ƙarata. Ko banza za ki dinga kwana a ac kina cin kaji." Islaha ta haɗɗiye yawu bata ce komai ba ta raɓa gefen Mama zata wuce Mama ta ce, "daman na rantse, babu ke babu Saheer, kuma rantsuwata bata faɗi a ƙasa ba. Ki je ki ƙarata da mahaukacin ki, a bi wani sarkin, Saheer kam ya fi ƙarfin ki wallahi." Bata tanka ba ta shiga ɗaki, ta rufe ƙofar tana jingina da bango ta lumshe ido. Ta buɗe idanunta ta kalli kuɗin hannunta, tana ayyana sadakin aurenta ne a hannunta, aurenta kuma ba da Hamma, da wanda ta fi tsana a duk duniya. Ta juya kuɗin a hannunta, tana tuna wanda ta aura a zuciyar ta. Ta yi tsaki a bayyane ta ce, "igiya uku ta aurensa ta hau kaina." Ta dafe kai cikin takaicin da ta ji yana mamaye ta, ta cize bakinta tana ji kamar ta zane kanta saboda takaicin da ya cika mata zuciyarta. "Rehaan!" Kalaman da ya faɗa mata a ƙasar saudia suna yawo a kunnenta, ta runtse a bayyane ta ce, "na yi saboda Hamma, na yi saboda Hamma ya kuɓuta, na yi saboda rayuwar Hamma ta dawo, saboda shi ne kawai, ba dan ya isa ba. Na yi komai domin shi, kuma zan dawo gare sa in sha Allah" ta faɗa dan ta kawar da tunanin da yake damun zuciyarta. Ƙwanƙwasa ƙofar ake yi a hankali, Islaha ta bar jikin ƙofar ta buɗe ƙofar suka haɗa ido da Safeera. Islaha ta bata hanya ta shiga, sannan ta mayar da ƙofar ta rufe. Islaha bata ce komai ba ta ƙarasa gefen gado ta zauna, ta zame ɗankwalin kanta, ta ajjiye kuɗin akan cinyarta tana ji duniyar tana juya mata. Safeera ta ce, "ya dai?." Ta ɗago ta nuna mata kuɗin ta ce, "an ɗaura auren." "Shine ya saka ki a damuwa?." "Ina ji kamar ban kyauta ba, sai yanzu nake jin na tafka kuskure babba. Jikina yana bani kamar...." Sai ta kasa faɗa ta dafe kanta. "Islaha komai ya riga ya faru, wannnan tunanin da ki ke yi duk ihu ki ke yi bayan hari. Yanzu ke matar Rehaan ce, kamata ya yi ki fara tunanin abinda zai biyo baya, ba wanda ya riga ya wuce ba." "Ya zan yi, ina ji kamar ban kyautawa Hamma ba, ban kyautawa rayuwata gabaɗaya ba." "Hmm kina son maimaita magana ɗaya Islaha, ke ki ka ce za ki iya yin komai saboda shi. Yanzu kuma kin yi saboda shi ɗin, meyasa ki ke damun kan ki?." "Zan iya yin komai saboda shi" ta sake maimaitawa don Safeera ta tabbatar." Safeera ta dafata ta ce, "ki saka a ran ki wannan ɗin ma saboda shi ne." Ta ɗago idanunta da suka fara cikowa da hawaye ta ce, "ya zan yi in Hammma ya dawo, da wacce fuska zai karɓi maganar nan?. Aure na yi fa, duk da auren contarct ne, amma kafin ya fahimce ni ni kaina na san za a sha wahala" ta girgiza kai tana ɗaga hannu sama ta ce, "Allah ka taimake ni Hamma ya fahimce ni, Allah ka sa kar ya yi min mummanar fahimta." Safeera ta ce, "Haka za ki faɗa masa ya fahimta, komai zai yi daidai in sha Allah. Ki daina damun kan ki, komai ya riga da ya faru, danasani akan abinda ya wuce ɓata lokaci ne Islaha. Na farko baza ki dawo da abinda ya wuce ki gyara ba, sannan tunaninsa ɓata miki rai kawai zai yi, tunda ba ki da magani. Kuma auren nan na suna ne, tunda za ku zauna matsayin ma'aurata amma ba wai na gaske ba." Islaha ta girgiza kai ta ce, "Baffa yana zancen gobe zan koma gidan, ni wallahi komai ya fice min daga rai" ta faɗa tana kwnaciya da baya cikin wani irin yanayi. "Daman ai a can za ki zauna, tunda a matsayin matarsa ki ke yanzu." Ta yi ƙaramin tsaki ta rufe ido ta ce, "bana son maganarsa wallahi, ban san haka na tsane sa ba sai yanzu." Safira ta yi dariya ta ce, "taimakon ki ya yi dai, ba dan shi ba da ynzu an kashe Hamma har lahira." Banza ta yi mata bata ce komai ba tana saƙawa da warwarewa. Itama Safieera bata ce komai ba suna zaune a wajen har aka yi sallar la'asar, a nan suka yi sallah ta sake komawa ta zauna tana buga tagumi cikin sabon yanayin da take jin jikinta. Safeera ta katse shirun ta ce, "Amma bakya ganin Mama zata faɗawa Saheer kin yi aure?." Islaha ta miƙe zaune sosai tana gyara ɗankwalin kanta ta ce, "ko shakka babu, Mama sai ta faɗa masa. Kin san halinsa da saurin ɗaukar zafi, kafin na samu ya fahimce ni ma babban aiki ne wallahi." Safira ta ce, "dole zai birkice, tunda yana da kishi, kuma magana ake ta kin auri wani. Amma daga baya komai zai zama ya yi daidai in sha Allah. Duk inda wanda ka ke so yake, in aka ce ya yi aure dole za ka ji zafi da kishi a ranka." Islaha bata ce komai ba suka jiyo hayaniya daga falo, da sauri suka miƙe suka fita falon suka ga Baffa ne sai su Mama da suke a tsaye. Baffa ya ce, "Islaha an saki Saheer, yanzu haka yana asibiti tare da Sadik!." Nana Haleema. [7/30, 11:15 AM] KRBBK: RDB2P98 Nana Haleema. Wani irin dumm ta ji a kanta kamar an doka mata abu mai nauyi a tsakiyar kanta, sai da jinta da ganinta suka ɗauke na wani lokaci, kafin ta dawo hayyacinta, jikinta ya fara rawa, ta koma da baya da hanzari ta ɗauko hijjab, ta dawo ta samu Baffa da su Mama har sun fita daga falon ta rufa musu baya da sassarfa. Gabaɗaya suka tafi asibitin da Saheer ya ke, suna shiga suka tarar da Sadik a tsaye yana amsa waya yana faɗawa mutane an sa ki Saheer ya dawo. Yana ganinsu ya kashe wayar, Baffa ya ƙarasa ya ce, "Yana ina?." Sadik ya ce, "an yi masa allurar bacci, yana ciki ana ba shi kulawar da ta kamata." Islaha da ta fi kowa zaƙewa ta ce, "Zan iya shiga na gansa?." Hanan ta buɗe baki ta ce, "ka ji wani abu, ga mahaifiyarsa bata shiga ta gansa ba sai ke?." Islaha bata kula Hanan ba kallon Sadik take yi tana jiran amsa. Sadik ya ce, "an ce dai kar a tashe sa, amma za a iya shiga ɗaya bayan ɗaya a gansa." Hanan ta yi caraf ta ce, "Mama mu je ki gansa, babu wata bare da zata fara shiga wajansa bayan ga ki. Ke ki ka haife sa ba, ba ita ba." Islaha ta ja gefe ta jingina da bango ta bawa Mama hanya ta wuce, Mama da Hanan suka shiga. Babu jimawa Mama ta fito tana kuka tana faɗin, "kun ga yadda ya koma? Gabaɗaya ya rame ya yi baƙi, jikinsa ya yi ƙuraje. Allah ya isa! Allah ya isa! Allah ya isa!!. Allah ka shiga tsakaninmu da waɗannan mutane, ka yi mana maganinsu cikin gaggawa.” Bafffa ya kalli Islaha da ta ke hawaya ya ce, "ki shiga ki gan shi Islaha." Ta kalli Baffa jin abinda ya ce, muryar ta a shaƙe ta ce, "ka shiga kawai Baffa." Baffa ya murmusa ya ce, "ki shiga, Safeera ki raka ta." Safeera ta riƙe hannunta suka shiga ciki. Suna shiga ta hange shi a kwance yana bacci, hawaye ya cigaba da ambaliyya daga idanunta, ganin yadda masoyinta ya canja kamar ba shi ba. Ta ƙarasa gaban gadon tana kallonsa, an saka masa ruwa yana shiga jijiyoyin jikinsa, kayan jikinsa duk sun lalace, fuskarsa ta yi duhu sosai, ga goshinsa an ɗaure da bandage, fatar jikinsa duk ta yi wasu ƙananun baƙaƙen ƙuraje. Islaha ta miƙa hannu da niyar dafa kansa Safeera ta riƙe hannunta, duk da ba saba taɓa shi ta yi ba, amma yanayin da ta gan shi a ciki ne ya saka take so ta dafa kansa. Ta juya suka haɗa ido Safeera ta girgiza mata kai alamun kar ta taɓa shi. Bata fahimci dalilin Safeera na hanata taɓa shi ba, sai ta janye hannunta suka fito a sanyaye. Ko da suka fito bata daina kuka ba, Safeera bata ce mata komai ba, sai da ta gama kukan son ranta sannan ta kalli Safeera ta ce, "meye dalilin da ya saka ki ka riƙe hannuna da zai taɓa Hamma?." Safeera ta ce, "saboda ke matar wani ce, taɓa wanda ba muharramin ba babban zunubi ne da ba ki san girmansa ba." Islaha ta yi sak tana kallon Safeera da ta kashe mata baki, ta kasa magana sai kallonta take yi, ta rasa wanne irin zagi zata yiwa Safeera da zata fahimci kuskurenta a cikin kalamanta. Islaha ta ce, "Ina ma na iya zagi, ina ma na iya zagin maguzawa, zagin ƴan iska, zagin karuwai, wallahi da sai na zage ki tas!......" Ta nuna ta da yatsa ta ce, "Daman akan auren nan ki ka hana ni?." Safeera ta ce, "Laifi ne hakan, ke ba matar auren ba ce?." "Safeera meyasa ki ka yi min haka, ɓeyasa ki ka fara canja min tun yanzu?. Ni na ɗauka saboda haramcin hakan ki ka hana ni, ashe akan wancan banzan auren da ban ɗauke sa a matsayin aure ba ki ka hana ni taɓa Hamma?." Ganin ta fara fusata tana masifa a cikin mutane sai Safeera ta tausasa murya ta ce,  "Aure ya wuce ace masa banza aure, ki daina faɗa, sunna annabi ne ba a zaginsa. Kuma akwai haramci a ciki taɓa shi, ko babu aure a kan ki taɓa Saheer haram ne balle ke matar aure....." Hannu Islaha ta ɗaga kamar zata mare ta, sai Safeera ta yi shiru dan ta san a fusatar Islaha tsaf zata mare ta akan kalamanta. Islaha ta nuna ta da yatsa ta ce, "Na rantse da Allah in ki ka ƙarasa sai na gaggaura miki da mari." Safeera ta yi murmushi bata ce mata komai ba. Baffa ne ya ƙaraso wajan da suke tsaye, hakan ya hana Islaha magana. Ya kalli Islaha ya ce, "Islaha." Ta ɗaga kai ta kalle shi tana jiran ta ji me zai ce, a daidai lokacin Adda ta ƙaraso wajan ta tsaya a kusa da Baffa. Baffa ya ce, "Yauwa ga Yayarki nan, ku je ta ta ya ki abubuwan da ya kamata ki yi, kafin gobe ki tare a gidan mijin ki." Wani irin abu ya soki Islaha a zuciyarta, ta runtse ido da ƙarfi tana jin yaji yana tasowa daga zuciyarta yana mamaye idanunta. Saboda zafin yajin har ruwa idonta ya tara, ta rasa inda zata saka kanta saboda baƙin ciki. Ga shi bata iya yiwa Baffa musu balle ta ce bazata je ba. Adda ta kalli Baffa ta ce, "Baffa wai sai da aka yi auren nan, yanzu me za a faɗawa Saheer?." Baffa ya kalle ta ya ce, "wannan duk zai biyo baya, ya kamata ku fara shirin da ya kamata." Islaha ta kalli Baffa tana hawaye ta ce, "Baffa don Allah ka bari zuwa anjima sai mu tafi, tunda ka ga sai gobe ne tafiyar ba yau ba." Baffa ya murmusa yana kallon ta, yana karanto rauni da soyayyar Saheer a idanunta. Shi kuma wannan dalilin ne ya saka yake so ya nisanta ta a Saheer dan ita yanzu matar wani ce, zama inda Saheer yake bai kamace ta ba. In ya bar su tare za a tafka saɓon Allah, ko iya magana ta yi da Saheer da fuskar masoya babban zunubi ne. Baffa ya ce, "ku je Islaha, har shida na yamma ta yi. Ku tafi kawai." Babu yadda zata yi da Baffa, ta miƙe a sanyaye Safeea ma ta miƙe suka fito tare da Adda. Ray tunda aka ɗaura aurensa ya daina walwala, yana sakewa ne kawai zaboda Jazy zai ji babu daɗi in yana ƙin sakewa a bikinsa, amma gabaɗaya komai ya tsaya masa ba ya jin daɗin komai. Yana zaune a falo ya canja kaya zuwa na shan iska, hannunsa riƙe da mug na tea yana sipping a hankali. Jazy ya shigo yana hararsa ya ce, "Mamy tana ta neman ka, ɗan family picture ɗin nan na biki baka tsaya an yi ba. Haba Ray, baka kyautawa Riyya ba, gabaɗaya bata ji daɗin haka ba." Bai ce masa komai ba ya dai kalle sa kafin ya ɗauke kai. Jazy ya zauna bayan ya cire babbar rigar jikinsa, ya ɗauki wayar sa yana dannawa sannan ya ce, "media gabaɗaya a kan ka take magana yau, hotunan ka kamar ruwa. Amma na yi mamaki da maganar auren ka bai fita ba." Ya juyo ya kalle sa ya ce, "ka daina cewa aurena, please." Ya yi murmushi ya ce, "Ray she is your wife, auren contract ne ko akasin wannan kai ta dama ba mu ba." Bai ce masa komai ba ya kuma yi masa shiru dan bai san me zai ce ba. Jazy ya kalli agogo ya ce, "ƙarfe nawa zamu tafi dinner party?." Ray ya buɗe baki zai yi magana Jazy ya ce, "wallahi bazan karɓi uzurin ka ce min baza ka je ba, gwara ma na faɗa maka tun kafin ka furta. Kar ka wahalar da bakin ka ka ce min baza ka je ba." Sai ya fasa faɗar abinda zai faɗa ya ajjiye kofin hannunsa ya miƙe ya shiga bedroom. Bayan sallar magrib Jazy ya shirya cikin ash men lace, yana saka agogo a hannunsa ya shiga ɗakin Ray ya same sa sanye da bathrobe ko kaya bai saka ba. Ya bi shi da ya ce, "kasan akwai pictures before event ko?." Ya yi tsaki ya ce, "kai wa da me zan ji ne? Ka ce sai na je, kuma ka ce min photoshoot?." Jazy baice komai ba sai danna waya da yake yi, ya kira Riyya ya saka a speaker ya ce, "Riyya ɗan uwanki ya ce ba zai yi attending event ɗin ki ba, ki yi masa magana yana jin ki." Riyya ta ce, "Ray please, tunda ba ka tsaya an yi pictures ɗazu ba yanzu ka zo mu yi, ka ji?." Jin muryarta kamar zata yi masa kuka sai ya ce, "Riyya zan je event ɗin, meye wani pics brfore event?." "Please!." "Okay, i will be there" "Thank you. I love you." "I love you" ya furta yana kallon Jazykafin Jazy ya kashe wayar. Ray ya yi ajiyar zuciya yana kallon Jazy da ya yi kyau cikin shigarsa ta angwaye. Kafin ya yi magana Jazy ya ce, "ka shirya mu je." Bai ce komai ba ya ɗauke kansa sai wayarsa da ya ɗauka jin ana kiransa. Jazy ya ƙwace wayar bai bari ya ɗauka ba ya ce, "in ka fara waya akan business sai a tashi daga event ɗin ba ka gama ba. Don Allah ka tashi ka shirya." Nan ma bai ce masa komai ba Jazy ya ce, "Abba ya ce na tura a ɗauki Islaha ta je event ɗin, ni kuma na manta." Sai lokacin ya ce, "wace?." Ya wani kalle sa ya ce, "ɗan rainin hankali, da ina yi maka magana ka yi banza amma ina ambato sunanta ka yi magana." "Ita wa?." "ba ka san ta ba?." Ta girgiza kai alamun bai santa ba yana miƙewa tsaye. Jazy ya ce, "matarka nake nufi." Ya dakata daga kwance igiyar bathrobe ɗun da yake niyar yi yana kallonsa, sai kuma ya ce, "point of correction, contract wife za ka ce, ba matata ba." "Kai ka san wannan, ni a matarka nake kallon ta." "As who will she go to the event?." "Amaryar Ray." Bai ce komai ya ƙarasa yana kallon kayan da zai saka. Jazy ya ce, "ni fa murna nake da auren nan, ko babu komai Alma zata ƙyale ka." Ray ya sake yi masa shiru, sai da ambaci Alma ya tuna masa kwana biyu ko kiransa bata yi, yadda take damunsa da waya da texts yanzu duk bata yi. Bai ce komai ba ya shirya cikin men lace amma na sa brown colour. Jazy ya kalle shi bayan ya gama ya ce, "ka yi kyau fa." Bai ce masa komai ba wrist watch yake ɗaurawa sannan ya saka takalmi. A hankali ya ɗago yana yatsine fuska ya ce, "cikina." Jazy ya buɗe ido waje ya ce, "ciwo yake yi maka?." Ya ɗan girgiz kai ya ce, "ina jin alamun ciwon." Jazy ya ce, "don Allah ka taimaka mana kar ciwon cikin nan ya tashi, in ya tashi a wannan lokacin ai mun shiga uku." Bai ce komai ba ya ƙarasa shiryawa suka fito tare, suka hau mota suka tafi ayi hotunan kafin event. Mama tana tsaye ta shirya cikin lace mai kyau, fuskar ta ta sha makeup kamar ba ita ba. A kan idanunta motar Mamy ta fita zuwa wajan event ɗin. Ta girgiza kai ta ce, "an dai ɗaura aure, wannan aure shine target ɗina na ganin bayan Rehaan. Wallahi indai ina da rai sai na ga bayan Rehaan, wallahi sai na kai shi ƙasa." "Mama" Sameer ya faɗa yana shigowa. Ta juya tana kallonsa ya ce, "Za mu tafi tare ne?." Ta ɗaga kai ta ce, "mu je mu tafi tare kawai." Tare suka fito suka shiga mota zuwa wajan event ɗin. [7/31, 11:42 AM] KRBBK: RDB2P99 Nana Haleema.. Islaha tunda suka koma Adda ta saka a gaba da tambaya akan ya aka yi aka yi auren. Adda ta ce, "Ya aka yi? Me yasa Baffa ya yanke hukuncin aura miki wani ba Saheer ba?." Islaha cikin rauni ta ce, "nima ban sani ba Adda." "Meyasa ki ka amince bayan kin san wannan hukuncin nan na ki sai ya fi yiwa Saheer zafi fiye da zaman wajen masu garkuwa mutane? Aure fa Islaha." "Adda babu yadda zan yi ne" "Ban yarda ba Islaha; Da kin nunawa Baffa bakya son auren da bai yi ba miki ba. Yanzu da ki ka auri wani ya ki ke tunanin makomar Saheer zata kasance?. Daga wajen masu garkuwa da mutane ya fito, kuma dan rashin imani yana farfaɗowa sai a ce masa kin auri wani?." Adda ta ɗora da cewa, "Gaskiya ba a kyautawa Saheer ba wallahi, yanzu shikenan duk yadda ya sakawa ransa auren ki sai dai ya haƙura?." Islaha bata ce komai ba ta yi shiru, tana so ta faɗa mata babu wanda ya isa ya hanata auren Saheer, aurensa yana nan babu fashi. Tana so ta faɗa mata duk wuya duk runtse sai ta fito daga gidan Rehaan ta zo ta aure shi, tana so ta faɗa mata babu wanda zai rabata da Saheer. Sai dai kash! Bata so kowa ya san sirrin auren ta, bata so kowa ya san irin auren da ta ƙulla, dole ta ja bakinta ta yi shiru. "Na san dai kuɗi ba sa gaban ki, balle na ce dan ɗan masu kuɗi ne ya saka ki ka amince. Amma duk da haka kin dakusar da kan ki, ba kowa ne zai yarda ba auren kuɗi ki ka yi ba Islaha. Mahaukaci ne fa aka ce, in ya kashe ki ya kashe banza, babu abinda aka isa ayi masa, tunda ba a shari'a da mahaukaci. Kin san da haka ka amince har aka ɗaura aure, ki ka bar Saheer da yake tsananin sonki, yake burin auren ki, yake burin ya ga ya samu kuɗin da zai mallake ki. Ko yaushe maganar bikin ku ce akan harshensa, shine ginin gida, shine lefe, shine kyautata miki, amma ke kuma ba ki riƙe amana ba wallahi!." Safeera jin Adda ta fara wuce gona da iri sai ta yi caraf ta ce, "Adda duk abinda Islaha ta yi har ki ke ganin laifinta ta yi ne dan taimakon Saheer, ke kin san baza ta zaɓi kuɗi ta bar Saheer ba. Masu kuɗi nawa ne suka nuna suna sonta ta ƙi basu dama? Sai yanzu da aski yazo gaban goshi zata juya masa baya?." Adda kalli Safeera ta ce, "kamar ya saboda shi ta yi? Ban gane ba, kina so ki ce ta auri wani zata tare a gidansa gobe saboda Saheer? Wannan ma tana daga cikin soyayyar da take yi masa kenan ko?." Safeera zata yi magana Islaha ta ce, "ni dai ki yi haƙuri kawai, duk abinda ki ke tunani ba haka bane, za ki fahimta nan gaba, amma ban da yanzu." "Me zan fahimta Islaha? Ai kin riga kin goge min hadda, kin ɓarar da duk yardar da na yi da ke, kin ri ga kin nuna min za ki iya zaɓar kuɗi akan Saheer. Meye Saheer bai yi miki ba?." Mama da take shigowa falon ta ce, "faɗa mata dai, yau kin tabbatar da tsintacciyar mage bata mage, in ina faɗa miki halinta bakya ganewa, yau gashi ta nuna miki ita ƴar kunama ce. Ta zaɓi auren mahaukaci akan Saheer." Adda ta kalli Mama ta ce, "wallahi ta bani mamaki, ban yi tunanin zata zaɓi mahaukaci akan Saheer ba. Kawai dan mahaifinsa yana da kuɗi, kuma dan ɗan uwan Rehaan Yola shikenan sai ta zaɓi auresa ta bar Saherr? Yanzu in ya tashi me za a ce masa?." Hanan ta ce, "a faɗa masa gaskiya mana, ta zaɓi ɗan masu kuɗi mai taɓin hankali a kansa. Daman duk wanda ya siyi rariya ya san zata zubar da ruwa, duk wanda ya kalli Islaha ai ya san zata aikata goman haka." Safeear fusace ta ce, "ke da ki ke maganar ba dan Islahan ba da yanzu..." Islaha ta katse ta ta ce, "Safeera mu je gidan ku" ta faɗa tana jan hannunta suka fita da ƙarfi suka fita daga falon. Suna fita harabar gidan ta fashe ta kuka, ta nemi waje ta zauna ta dafe kanta tana kuka mai tsuma zuciya wanda yake fita da sauti mai ratsa kunne. Safeera ta tsaya a kanta ta ce, "ki bari a faɗa mu su, ki bari su san kin sadaukar da rayuwar ki ne saboda Saheer, ki bari su san kin yi abinda su basu yi ba saboda shi, ki bari su san kanki ki ka ɗauka ki ka kai wani waje saboda Saheer. Sai wani ƙananun mganganu suke yi, ai kowa ya san baza ki taɓa zaɓar mai kuɗi ki bar Saheer ba. Ban taɓa jin haushin Adda kamar yau ba, na ɗauka zata yi shaidar ki, sai ga shi ta biyewa Mama. Ba dan ke ba da yanzu ai Saheer ɗin bai dawo ba." Islaha dai bata ce komai ba, kuka kawai take yi tana jin ciwon auren da ta yi da ba Hamma ta aura ba. Tabbas kowa zai ce kwaɗayi ta yi, musamman in aka san asalin wanda ta aura, kuma aka san ta bar Saheer ta aure sa, kowa ya san halaccin Saheer a gare ta, dole a faɗa mata baƙaƙen maganganu a kai. Islaha kalli Safeera ta ce, "gaskiya ce maganar su, duk wanda ya ji asalin wanda na aura zai ce kuɗi na zaɓa na bar halacci. Na yi danasanin ƙulla yarjejeniyar nan, na yi danasani wallahi. Safeera In wayata?." Safira ta ce, "me za ki yi da ita?." "Zan kira Jafar ne." "Ki ce masa me?." "Ya haɗa ni da Rehaan, zan yi canceling auren nan." Ta yi mata kallon up and down ta ce, "kuɗin sa da ki ka karɓa fa? Ko kin manta ya ba ki kuɗi dan ki zauna dashi har na wata biyar, ko kina da kuɗin da za ki dawo masa da kuɗinaa ne?." Islaha ta dafe kai bata ce komai ba zuciyarta tana yi mata ɗaci, tana suya, tana zafi da raɗaɗi mai yawa. Sai a lokacin take danasanin aikata abinda ta aikata, sai a lokacin take tunanin ya Hamma zai ji, sai a lokacin take tunanin me mutane za su ce akan auren da ta yi?. "Islaha lafiya ki ke kuka?." Jin muryar Baffa duk sai suka juya a tare, Baffa ya ƙaraso ya ce, "me ya faru ki ke kuka?." Islaha ta yi bata ce komai ba, amma ƙirjinta bugawa yake yi, jikinta rawa yake yi sosai. Baffa ya ce, "Safeera me ya faru?." "Su Mama ne suka ce wai ta zaɓi mai kuɗi ta bar halacci." Baffa ya girgiza kai ya ce, "shine take kuka?." Safeera ta ce, "eh Baffa. Suna ta faɗar magana mara daɗi, wai ta zaɓi mai kuɗi ta bar Saheer, ta manta wahalar da ya yi da ita a rayuwa." Baffa ya yi tsaki ya ce "ku zo mu je ciki." Safeera ta riƙe hannun Islaha da ta fara jiri, suka bi bayansa har ɓangaren sa. Baffa ya zauna ya ce, "Islaha kar wata magana ta fatar baki ta dame ki, in ance kin zaɓi kuɗi ki ce kin zaɓa ɗin, waye yaƙi kuɗi?." Ita dai bata ce komai ba kanta yana ƙasa tana goge ido, kanta yana ciwo, ƙirjinta yana harbawa, numfashinta yana sarƙewa. Baffa ya ce, "ki kwantar da hankalin ki, ba ina sane na zaɓa miki auren yaron nan ba. Na yi ne dan na tsaraɓar dake daga mahaifiyar Saheer, bana so ki sha wahala a rayuwar ki, shiyasa na aikata hakan. Kin fara shirin tarewar gobe?." Gabanta ta faɗi sosai, ta runtse ido tana girgiza kai alamun a'a. Baffa ya ce, "ki fara shiryawa. Safira ki taimaka mata, sannan ki faɗawa Gwaggon ki Atika za a raka Islaha gidan nijinta gobe. Na san Sa'ida bazata ta fahimta ba itama, tana kishin ɗan uwanta baza ta je ba. Iya ku kun isa ku yi mata rakiya, ba taro ake so ba, albarka ake nema." Safeera ta ce, "To Baffa." Ya kalli Islaha ya ce, "kar ki wani damu, na san kina tunanin ba ki kyautawa Saheer ba, amma hakan shine daidai." Baffa ya dinga rarrashinta ita dai jin sa kawai take yi, yana gamawa duk fita ta koma gidan su Safeera dan bazata iya komawa cikin gidan ba. Haka ta zauna da zazazzaɓi da ciwon kai, ta koma shiru bata magana, sai tunani da kuka, Safeera ce mai rarrashinta amma bata rarrasuwa. Safeera ta ba ta magani ta sha, daga nan ta share ta dan ita bata ga abin tayar da hankali akan abinda ba ka da mafita a kai ba. *Washe gari.* Abba ne tare da Jazy, ya kira sa suna magana akan ɗauko amaryar Rehaan. Abba ya ce, "Jafar kana jina, a je gidansu yarinyar nan a ɗauko ta a kawo ta. Na baka ragamar komai, kuma da kan ka nake so ka ɗauko ta a kawo ta gidan nan. Kafin a kai maka taka amaryar, ka kawo ta ɗan uwanka." Jafar ya yi murmushi ya ce, "In sha Allah Abba, zan yi yadda ka ce." "Yauwa Jafar, da kai kaɗai na amince shiyasa na ba ka wannan damar. Don Allah ka kula, yarinyar nan ta shigo gidan nan lafiya, kar a fara da matsala." "In sha Allah." "An gyara apartment ɗin nasa ne?." "A'a, ya ce shi baza a canja masa komai ba." Abba ya girgiza kai yana murmushi ya ce, "ai ya yi ƙoƙari ma, yana da haƙuri sosai, shiyasa bana so na dinga ƙure shi, bana so na dinga yi masa dole akan abinda ba ya so, shiyasa nake ƙyale shi duk abinda ya ce nake bi dan a yi masa yadda yake so. Ba ya son auren nan, ni na tilasta masa ya amince, shiyasa bana son na ƙure shi." Jafar ya ɗan murmusa kawai amma bai ce komai ba. Yana ayyana Abba bai san akan yarjejenuya ya ɗora auren ba, ba don Allah ya yarda har ransa ba. Abba ya ce, "ka je kawai, duk abinda ya kamata aje ayi." Jafar ya amsa da girmamawa sannan yana miƙewa ya fita. Gidansu Rehaan ɗin shiru, duk baccin gajiyar dinner suke yi, shi kansa ba dan Abba ya kirasa ba bazai fito ba dan sai biyu na dare aka tashi daga event ɗin jiya, kowa a gajiye yake yi. Sanin Rehaan yana can yana baccinsa na ƙa'ida shiyasa bai shiga wajansa ba, ya fita daga gidan yana aiyyana yadda zai tsokane sa in anjima. Garin Allah yana wayewa Islaha bata jira kowa ba ta wuce asibiti, a can ta tarar da Sadik ne kawai a wajansa. Tana shiga suka haɗa ido, Saheer ya yi mata murmushin da gabanta ya faɗi. Yana zaune ya idar da sallah, ya yi wanka ya canja kaya amma ya rame sosai, ya yi wani iri, kamar wanda ya jima yana kwance cikin ciwo, damuwa ta bayyana akan fuskarsa sosai. Islaha ta tsaya cak tana kallonsa kamar yadda yake kallon ta. Cikin nutsuwa ya miƙe a hankali, ƙafarsa ciwo take yi masa sosai, saboda ɗaurin da ya sha a wajen mutanen, hannunsa ma kamar har lokacin a ɗaure yake haka yake ji, amma saboda murnar ganin Islaha haka ya miƙe a kan ƙafarsa ya matso kusa da it ya ce, "Matar Hamma!." Yadda ya faɗi sunan, da yadda muryarsa ta fita, da yadda yake kallon ta, da yadda yadda yanayinsa ya koma ya saka gabanta ya faɗi, ta lumshe ido ta buɗe hawaye suka taru a idonta. Ganin tana hawaye sai ya miƙa hannunsa kan fuskarta ya goge mata ya ce, "ki amsa mana, ba ki ji na kira sunanki ba?." Islaha kasa magana sai ta fashe da kuka mai sauti, zuciyarta gabaɗaya ta gama karyewa, jikinta ya yi sanyi, zuciyarta tana rawa kamar zata faɗo ƙasa. Tana tunannin shikenan ta cuci kanta, ga Hamma ya dawo amma ita zata tafi, zata tafi gidan wani matsayin matarsa ba Hamma ba, zata tafi wani wajen da zata zauna da wani namiji a matsayin mijinta ba Hamma. Saheer ya riƙe hannunta duka biyun, cikin wani irin yanayi na rauni da gajiyar da take jikinsa ya ce, "Islaha zan tsallaka iyaka, i want to hug" Ya faɗa yana a hankali yana kallon ta. "Saheer me ka ke yi haka?" Sadik ya faɗa da sauri dan ya dakatar dashi, dan shi ya san akwai auren wani a kanta, riƙe hannunta ma da ya yi sai dai Allah ya yafe, amma ba ƙaramin zunubi aka aikata ba. Saheer ya juyo ya kalle sa ya ce, "iya yau ne kawai, in ban jita a jikina ba zan iya mutuwa Sadik. Ina tsananin kewar ta, ni kaina bazan ce ga adadin kewar ta da nake ji ba.” A lokacin Baffa ya shigo ɗakin ya raba gardamar, da sauri Islaha ta ƙwace hannunta ta koma gefe tana cigaba da zubar da hawaye. Baffa ya bita da kallon mamaki, dan shi bai san ta fito daga gida ba balle ta zo nan ya ce, "Islaha har kin ƙaraso?." Ta ɗaga masa kai ta yi bata iya cewa komai ba. Baffa ya ƙarasa wajan Saheer ya ce, "barka da fitowa Saheer, Allah ya cigaba da kiyaye mu." Saheer cikin jin daɗin ganin mahaifinsa ya ce, "Amin Baffa. Ina Mama?." Baffa ya ce, "suna hanya, yanzu zasu ƙaraso." Saheer ya ɗaga kai yana kallon Islaha da take kuka, ya kalli Baffa ya ce, "Baffa ka ce ta daina kuka don Allah." Baffa ya kalli Islaha, ya juya ya kalli Safeera da ta shigo lokacin ta ke tsaye daga bakin ƙofa ya ce, "Safeera ki rarrashe ta." Safeera ta ƙarasa inda Islaha take ta dafata kawai dan ta san baza ta daina kuka ba. Saheer kam idanunsa yana kanta, duk inda ta motsa ita yake kallo. Ya kasa samun nutsuwa, ji yake kamar ya riƙo ta jikinsa ya rarrashe ta daina kuka. Duk da abubuwan da yake tunawa wanda suka faru a can, bai saka sun danne kewar Islaha da yake ji ba. A lokacin Mama suka ƙaraso, suka riƙe Saheer suna kuka, shi kansa sai da ya yi kukan na kewar ƴanuwansa da iyayensa. Likita ya sallame su, bayan ya ba shi magani, ya kuma ce ya dinga yawan shan ruwa, sannan ya dinga cin abinci mai gina jiki. A lokacin da suka tafi, rana ta yi sosai dan har an yi sallar azahar. Ita dai Islaha kasa komawa gidan ta yi, tana gidansu Safeera tana kukan da ya ƙi tsayawa. Sai da Baffa ya kira ta a waya ya ce ta dawo gida sannan ta koma. Baffa kaɗai ta samu a zaune ta ƙarasa ta zauna, Baffa ya ce, "Ƙarfe huɗu zasu zo tafiya da ke Islaha. Ki yi haƙuri, ki bar wannan koke-koken. Za ki ta fi gidan mijin ki in sha Allah. Nana Haleema. [7/31, 11:42 AM] KRBBK: RDB2P100 Nana Haleema. Islaha ta ɗago ta kalle sa cikin rauni, murya tana cracking ta ce, "Baffa, Hamma!." "Zan yi masa bayani da kaina." Tana girgiza kaita ce, "Don Allah kar ka faɗa masa, kar ya sani don Allah Baffa!." Ya yi murmushi ya ce, "ai kuwa dole ya sani, ba abinda za a ɓoye masa bane." Ta cigaba da kukan da ya zamar mata ɗan uwa Baffa ya ce, "kina da matsalar sarƙewar numfashi, ki dakata da wannan kukan, ki tashi ki je." Islaha ta kasa tashi saboda kuka, Baffa ya ce, "Islaha ya isa, ki bar wannan kukan kar ki jawowa kan ki matsala. Ba ke ki ka halicci kan ki ba, Allah ne ya yi ki, kuma tun ka fi ki zo duniya ki ka rubuta ƙaddarar ki, kuma ba ki isa ki tsallake abinda ki ka rubuta da hannun ki ba. Babu Saheer a cikin rayuwar ki, halaccin da ki ke tunanin ya yi miki don Allah ya yi ba don ki aure shi ba, ba ki isa ki yi abinda Allah bai nufa ba. Dan haka ki daina kuka, ki tashi ki je ki shirya." Duk da Baffa wa'azi yake yi mata amma ba ji take yi ba, Hamma kaɗai take hangowa a idanunta. Ta miƙe ta fita daga falon, tana fitowa ta haɗa ido da Hamma da Sadik a ƙofar ɗakinsa, Sadik yana riƙe dashi saboda bashi da ƙwari sosai, yana miƙa ledar maganinsa. Ganin ya tsayar da idanunsa a kanta sai ta ƙarasa wajen da suke har ta je yana kallon taya ce, "me yake damun ki haka? Wannan koke-koken da ki ke yi na meye?. Ba gani na dawo ba, gani a gaban ki a tsaye ina yi miki magana, meyasa ba ki nuna farin cikin ganina ba ki ke kuka?." Ta goge idanunta ta ce, "Ka yi haƙuri Hamma, don Allah ka yi haƙuri!." Abinda ta iya faɗa kenan, ta juya a guje ta bar wajan tana kuka. Hankalinsa ya tashi sosai ya kalli Sadik cikin muryarsa da bata fita sosai ya ce, "me ya same ta, me ya faru ta ke bani haƙuri?." Sadik ya ce, "ban sani ba, ka jira ta nutsu sai ka tambaye ta." Saheer cikin damuwa ya ce, "na lura tana da damuwa sosai, akwai abinda ya faru da bana nan?. "Ka sha magani ka ka huta, likita ya ce ka samu bacci mai tsaho, sai ka yi bacci jinin ka zai sauka. Ko wacce magana ce zata biyo baya, amma ba a yanzu ba. Ka tabbatar ka sha maganin nan, dan ya kashe maka ƙananun cuttukkan da suka shige ka." Saheer ya yi shiru, Sadik ya raka shi ɗaki, ya ba shi abincin da Mama ta aiko dashi ya ɗan ci kaɗan, ya ba shi magani sannan ya kwanta. Sadik ya bi shi da kallon tausayi sannan ya fito, ya rufe masa ƙofar cikim rauni ya ce, "Allah Sarki Saheer, sai dai ka yi haƙuri, amma Islaha yanzu ba ta ka bace, bazata taɓa zama ta ka ba har abada. Dan ni na san babu yadda za a yi Islaha ta dawo, ta tafi kenan." Islaha da kuka ta koma gidansu Safeera, Safeera ta runtse ido dan ita har ta gaji da wannan koke-koken da Islaha take yi. Ta yi tsaki cikin fusata ta ce, "in kin san za ki damu har haka meyasa ki ka amince? Da kanki ki ka ɗauki ƙafa ki ka je ki ka saka hannu, ba wani ne ya yi miki dole ba. Kukan me ki ke yi bayan ke ki ka kai kan ki?." Bata ce komai ba sai kuka, itama Safeera ta yi mata banza bata sake ce mata komai ba, dan wallahi haushi take bata. Sai da suka jima a haka, sai daga baya Safeera ta ce, "Ki cigaba har ki samu attack." Zazzaɓi ya rufe Islaha, kanta ya yi nauyi yana ciwo sosai. Cikin rauni da sanyin jiki da ciwo ta ce, "Wai ƙarfe huɗu za a zo a tafi dani, ni dai bana son tafiya ko ina Safeera, ina son zama tare da Hamma." Safeera ta ce, "me ki ke so na ce miki yanzu?." Islaha bata ce komai ta cigaba da goge hawaye. Safeera ta ce, "tunda ki ka yi aure zancen zama da Saheer ya ƙare, haka za ki yi haƙuri zuwa lokacin da komai zai yi daidai." Ta goge ido ta ce, "da wacce fuska zai fahimce ni?." "Zai fahimta, amma za a sha wahala." Islaha ta ce, "daman ni marainiya ce, amma ban yi tunanin haka aurena zai zama na marasa gata kamar wannan ba." "Oh da gaske auren ki ka yi kenan?." Ta girgiza kai ta ce, "Ba haka nake nufi ba, kawai abin ne babu daɗi." Safeera bata ce komai ba ta cigaba da danna wayarta dan bata san me zata ce mata ba kuma, ta gaji da rarrashinta. Sun jima a haka a zaune, har aka yi sallar la'asar, Baffa da kansa ya kira Safeera ya ce ta saka Islaha ta shirya ta rako ta gidan. Jazy bai haɗu da Ray ba sai bayan sallar la'asar, ya same sa a zaune a falo yana video call a laptop, ya zauna a gafensa har ya kammala ya rufe laptop ɗin. Jazy ya ce, "a ina Rolls Royce take?." Ray ya ce, "Ka tambayi Shams." Jazy ya ce, "Okay let me call him, ya kawo min ita. Ka san Abba ya wakiltani na je na ɗauko amaryar ka, da ita za a ɗauko ta." Ray ya yi shiru bai ce komai ba har ya gama kiran Shams. Bayan ya gama wayar Jazy ya ga Ray yana kallonsa suna haɗa ido Ray ya ce, "meyasa ba ka ɗauki private get ba sai RR?." Jazy ya yi dariyar shaƙiyanci ya ce, "ai wallahi da ace Islaha a wajen Yola ta ke ba cikin Yola ba, da private get za a ɗauko ta, yanzu ma dan abin ya zo late ne, da hilicopter zan tasa ya ɗauko ta, Matar Ray ce fa." "Mtsww! Yanzu me ya hana ka tashi helicopter ɗin? Ɗan neman suna" ya faɗa yana miƙewa tsaye tare da saka hannu a gashin kansa yana yamutsawa.  Shima ya miƙe ya ce, "na faɗa maka lokaci ne ya ƙure, amma da wallahi bazata zo gidan nan a mota ba, sai a jirgi." "Ta zo a iska ma." Jazy ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "lallai ka ji hausa mutumina, baki yana ta buɗewa....." "Zan je na dawo, ka san ina da amarya sabuwa da za a kai min ita in anjima, bazan ɓata lokaci ba. Matsayina da naka yanzu da banbanci, ni auren sadaki na yi, kai kuma auren yarjejeniya ne, bazan ɓata lokaci a nan ba." Banza ya yi masa ya shige ɗaki bai ce masa komai ba, shi kuma ya yi dariya ya fita. Baffa ne ya saka Safeera shiryawa Islaha kaya ƴan kaɗan da zata tafi dasu, ta dole aka saka ta yi wanka dan gabaɗaya ta fita hayyacinta, tana jin daɗi da Hamma yake bacci tunda ya sha magani. A haka ta shirya cikim atamfa doguwar riga da veil ɗinta mara tsaho sosai. Safeera ta bita da kallo ganin mayafin da ta ɗauko ta ce, "wannna mayafin bazai rufe miki fuska ba, babban mayafi ake sakawa." Islaha ta harare ta da jajayen idanunta da suka kumbura ta ce, "sai aka ce miki zan rufe fuska ne daman?." "Haka amarya take zuwa gidanta fuska a buɗe?." "Wace amaryar?." "Shafa ki ji." Islaha ta share ta ta ɗauki handbag ɗinta kamar wacce zata je unguwa, sai kuma ta ajjiye jakar ta ce, "ai gobe ma zan fito, ba sai na ɗauki wani abun ba." Safeera dai tana kallon ikon Allah kawai take yi, ganin yadda Islaha take yin abubuwnta kamar ba amarya ba. Har sai da Baffa ya shigo da kansa sannan suka fita daga ɗakin. Tana fitowa daga ɗakin Saheer yana shigowa falon yana tafiya a hankali cikin yanayin rashin lafiya, zuciyarsa tana tuna masa abubuwa da yawa a can, yana ta tunanin amanar da aka bari a hannunsa, wacce ya taho ya bari a hannun masu garkuwa da mutane. Saheer ya tsaya yana kallon Islaha, ganinta tare da Baffa da kuma Safeera. Bai yi tunanin komai ba, dan ya yi tunanin fita zata yi. Baffa ya kalle sa ya ce, "Saheer ka tashi kenan?." Ya ɗaga kai cikin dashewar murya ya ce, "na tashi." Baffa bai ce komai ba ya kalli mutanen falon da suke zaune, sannan ya ce, "ku yi mata fatan alkhairi, yau Allah ya ɗaga darajarta zata bar gidan nan zuwa gidan mijinta." Ita kanta Ialaha sai da gabanta ya faɗi, ta kalli Saheer ta gefen ido ta ga ya zubawa Baffa ido yana kallon sa. Baffa ya kalli Saheer ya ce, "ka jira ni, in na dawo zan yi maka bayanin komai." "Wanne bayani za a yi masa da ya wuce wanda ya gani yanzu? Da kai da Islaha kun zaɓi kuɗi akan halacci, kun ɗauke ta kun aurar da ita bayan ka san yadda yake tsananin ƙaunar yarinyar nan. Me za a ce masa kuma?." Saheer ya ji kalaman Mama kamar an doka masa guduma a tsakiyar kansa, daman ga rashin ƙarfin da yake fama dashi, ya dafa bango jin jiri yana ƙoƙarin kayar dashi, ya kalle ta ya ce, "aure kuma Mama?." Mama ta ce, "eh aure, ya aura mata ɗan gidan AbdulAziz Yola. Wani yaro mahaukaci, shi ya aura mata saboda ya fi ka kuɗi. Maganar da nake yi maka yanzu matar aure ce a gabanka!." Saheer ya buɗe ido tana kallon Mama, ya dawo da kallon sa ga Islaha da kanta yake a ƙasa, sannan ya kalli Baffa alamun ƙarin bayani. Baffa ya ɗaga masa kai alamun tabbatarwa ya ce, "eh gaskiya ne, shiyasa na ce zan yi maka bayani. Yanzu zan saka ta a motar da zata kai ta gidan miiinta, in na dawo sai mu tattauna. Islaha mu je" ya faɗa yana riƙo hannunta suka fara tafiya. Saheer ya dafe kai da hannayensa duka biyun ya ce, "Baffa wai da gaske ka ke?." "Da gaske nake Saheer." Saheer ya ji ɗakin yana juya masa, ya dinga maimaita salati a bayyane yana kalle-kalle dan ji yake kamar ana juya ɗakin da yake ciki, kamar ana juya duniyar tana sama da ƙasa. Baffa ya sake riƙe hannun Islaha da ta sunkuyar da kai ta ƙi ɗagowa, bata son haɗa ido da Saheer dan bata san me zata ce masa ba. Saheer ya ji kamar numfashinsa zai ƙwace, ya runtse ido yana kallon Islaha ya ce, "Islaha da gaske gidan wani za ki tafi ko wasa ku ke yi min? Kin san bana jure wannan wasan ko? Kin san bana son wasa da zuciya, ki faɗawa Baffa ya ce min wasa yake yi." Islaha ta tsaya cak ta kasa cigaba da tafiya, ta ɗaga ido tana kallonsa da idanunta da suka canja amma ta kasa magana. Baffa ya ce, "Saheer ba wasa nake yi maka ba, ka jira na saka ta a mota na dawo ko meye za aka ji." "Baffa wasa ne wannan, na san tsokanata ka ke yi. Kai da kanka ka faɗa min ka fini son na auri Islaha, meyasa za a yi min wasa a daidai irin wannan lokacin?. Baffa likita ya ce ina buƙatar hutu, meyasa ka ke yi min wannan wasan a daidai wannan lokacin?.” Baffa ya kalli Saheer ya ga in ya tsaya sauraren Saheer zasu ɓata lokaci sai ya ce, "Islaha mu je." A hankali take take bin bayan Baffa, ko gabanta bata kallo janta kawai yake yi tana tafiya tana kallon ƙasa tana kuka. Saheer ya biyo bayansu yana fitowa harabar ya ce, "Islaha!." Ta tsaya cak ta ƙi bin Baffa, jikinta ya hau rawa, raunin zuciyar ta ya bayyana, ta kasa cigaba da daurewa, ta zube guiwar ta a wajen ta ɗurƙushe tana kuka. Baffa ya waiwayo ya ce, "Saheer matar wani ce, ka daina karya mata zuciya, zan zo mu yi magana." Saheer bai kula Baffa ba ya ce, "Islaha da gaske ke matar wani ce ba ni ba ko wasa ake yi min? Islaha ki ce min mafarki ne, in kuma a gaske ne ki faɗa min film ake ɗauka, ki faɗa min script ki ka karanta ki ke acting a kai, ba gaskiya bane.” Bata iya magana ba sai kukan da take yi a ɗurƙushe tana ji kamar Allah ya ɗauki ranta a take a wajen, Baffa ya ɗago ta taƙi motsawa ta ce, "Baffa na fasa, bazan tafi ba, don Allah ka bar ni a nan!." Yadda jikinta yake rawa haka muryarta take rawa, Baffa bai fasa ba ya ɗago ta ya ce, "Islaha mu tafi" ya sake riƙe hannunta dakyau yadda baza ta iya ƙwacewa ba, ya cigaba da janta har suka fita daga gidan. Suna fita ƙofar gidan suka tarar da motar a ajjiye, Jazy yana zaune a ciki yana danna waya. Ganinsu ya saka shi ya fito, ya yimurmushi suka gaisa da Baffa cikin girmamawa. Baffa ya ce, "Gasu nan." Jazy ya bi Islaha da kallo ganin tana yadda take kuka jikinta yana rawa sosai, sai ya yi mamaki sosai, dan bai yi tunanin haka ba tunda ta san a yadda suka ɗora auren nasu, a ganinsa meye na kuka?. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" "Shikenan ta kashe min ɗana!." "Saheer! Saheer!! Saheer!!!." Lokaci ɗaya muryar Mama ta shiga kunnensu cikin ƙaraji mai nuni da tsananin tashin hankali. Wata irin zabura Islaha ta yi zata koma, Baffa ya riƙo ta ya haɗe rai cikin ba da umarni ya ce, "shiga ki tafi." Islaha cikin wani irin yanayi, ta girgiza kai murya tana rawa ya ce, "Baffa……” “Ham….ma…!." "Na san da Hamman na ki na ce ki tafi, na san abinda nake yi, ba ki fini sanin daidai ba." Baffa ya kalli su Mama Atika ya ce, "Safeera, Atika ku shiga ku rakata, Allah ya kiyaye ya sa an shiga a sa'a. Dan ma ban shirya zuwa bane, da ni zan kai ta da kaina." Baffa ganin Islaha da gaske ta ƙi shiga motar, sai ta buɗe motar da kansa ya saka ta shiga ciki, ya rufe motar ya kalli Jafar ya ce, "Allah ya kiyaye hanya." Jazy ya ce, "Amin Baffa. Mun gode Allah ya ƙara girma.” Safeera ce ta shiga gaba, saboda ta san dai Jazy ba driver bane balle ta shiga baya, kuma ta ga motar ta ƴan gayu ce kamar mutum biyu kaɗai ne suke zama. Mama Atika ta shiga kusa da Islaha, Jazy ya shiga motar ya ja ya suka bar unguwar a guje.... End of book 2 Tofa!😂🔥💃🏻 _Wai ta zata kasance ne? Ya zaman Islaha zai kasance ita da Ray? Ya batun zaman nasu, zai ɗore ko zai lalace? Ya zata yi da Saheer?. Ya haɗuwar Mamy da Islaha zai kasance? Ina labarin Labiba da Umma? Ina labarin Zainab da ta ɓace?. Wacce irin rawa Islaha zata taka a gidansu Rehaan? Ya labarin Mama da take jiran shigowar Islaha gidansu Rehaan?. Shin zata auri Saheer ne ko a'a?. Ina labarin Alma? Ina labarin Ummi da Muslim?. Waye yake ƙoƙarin ganin bayan Rehaan? Za su yi nasara ko kuma baza su yi nasara ba?._ Mu haɗe a book 3. Ni dai ina ba ku shawara, ko ba ku karanta book 1&2 ba, to ku maƙalewa book 3.😍😍🔥 Nana Haleema.