[12/29/2017, 2:59 PM] Asma'u Seema1: 🙊 *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA *SAFIYYA (mrs j moon)* *1 ~2* Gudu take zubawa irin na ceton rai bata ko duba inda take jefa qafafunta ita dai burinta tasami wurin tsira daga sharrin azzalumai, arba tayi da wani sark'aqiya na bishiyar tsamiya aiko take ta kutsa kai ciki sark'aqiyar batare da tunanin komi ba, duk sukan da k'ayoyi da suke mata bataji ita dai burinta tasami wurin buya yarda baza su ganta ba ballan tana su yagamata martabarta, da kyar ta sami ta shige. Abin mamaki sai ta sami wurin da fili sosai gashi kamar anshare domin tas tas yake, sai dai uban sanyi wurin kamar k'anqara. Zama tayi tana maida numfashi tare da tunanin maganganun da umminta tafada mata fashewa tayi da kuka tana cewa "ummi kiyafemin kinfini sanin abinda zai amfaneni amma nasa k'afa nayi fatali da maganarki nayi wutowata batare da saninki ba gashinan za akuma maimaita abinda yafaru da adda Salma,, wayyo ni Addawiyya nakawo kaina ga halaka.... nishin da taji ne kamar na mutum yasa ta d'auke kukanta tasoma zare idanu tana waige waige bataga komi ba saita gyara zamanta tajingina jikin wani abu mai taushi tare da d'an uban sanyi. Wani zabura tayi tana bin abinda ta jingina dashi da kallo. Arbatayi da wata murd'ed'iyar micijiya ta nad'e jikinta kamar tayan babban mota ta zuro kanta tsakanin circle d'in datayima jikinta ta kafe Addawiyya da idanunta masu tsananin haske kamar tough light. Addawiyya wacce tuni tasaki fitsari a wando tasoma ja da baya mucijiyan tayi wani girgiza iska mai tsananin k'arfi yatashi wanda saida yad'aga Addawiyya sama ya dawo da ita k'asa ya watsar,, tamik'e agigice tana neman hanyar fita daga sark'aqiya tsamiyar mucijiyar ta saki wani uban qara ta nufota bakinta bud'e zata had'iyeta........ razanannniyar ihu ta saka wanda yasa ummi tare da salma suka shigo d'akin datake. Gumi take had'awa sai kace wacce ta fito wanka sabida zufa takeyi kamar ta watsa ruwa. "Lafiya kike Rabi'atu? Shiru ba amsa sai zare idanu takeyi tana gwama numfashi. Tsaki Salma taja tare da fad'in "ummi iskancinta ne ya motsa kawai. Harara ummi ta sakarwa Salma ta maida hankakinta wurin Addawiyya ta matsa tare da dafa kafad'unta tace "autan ummi mike faruwa? Quri tayima ummin da idanu tana son tuno mufarkin da tayi amma takasa tuno komi illah hasken idanun macijiyan da har yanzu yake mata hizo afuska. "Ko mufarki kikayi mara kyau? Ahankakili ta gyad'a kanta alamar eh. "To shine bazaki farka da du'a,iba sai da ihu? Cikin rawar murya tace "nakasa ne ummi. "Kingani ba, taya zaki tuna addu'a alhakin kin kwanta barci a irin wannan lokacin mai tattare da hatsari. Nasha tunasar dake barci yaban sallar ka'asar abu ne mara kyau, domin ko marasa lafiya wanda basa iya tashi tadasu akeji a jinginar dasu har akira magrib sabida masana sirrin barci sunce yana haifar da mutuwar fuji'a haka kuma junnu suna iya shiga jikin bil'adam a irin lokacin sannan manzon Allah S.A.W. yayi hani da barci bayan sallar la'asar domin yana gadar da bak'in ciki haka na bayan subahi kafin fitowar alfijir tare dana tsakiyar rana su kuma barcin asarane don haka sai ki kiyaye barci alokutan. Kai ta gyad'a tana jan hanci wanda majina yake barazanar zubowa sabida sanyin da ta shak'a amufarkin da alama ya saukar mata da mura. Kuma abin mamaki jikinta ajiqe alamun fitsari tayi, tana wanka tana mamakin wannan kalan lamari mai figitarwa. Bayan sallar magarib Addawiyya ce zaune tatasa touch light sabon zubi a gabanta tana yanke farcenta tare da k'anqaresu, Zuciyanta cumkushe yake da tunanin mufarkin da tayi wanda har lokacin takasa tunano ya yake amma idanun macijiyan nan yaqi bace mata. Afusace ta iso wurin ta d'auke touch light d'in tayi gaba zuwa wurin garken shanu. Da gudu Addawiyya tabi bayanta tana fad'in "Allah baki isaba, insama kayana batur shine zakizo ki d'auke alhalin kina ganin aiki nake da shi. Aiko tana cinmata suka soma dambe tuni Salma ta danne Addawiyya ta matse mata baki don kada tayi ihu Abbi ya jiyosu. Abinda basu sani ba duk Abinda sukeyi Abbi yana tsaye agefe yana kallonsu, ganin abinnasu bana k'are bane yasa ya iso ya d'aga salma ya dalla mata mari ta tsala ihu ta arce da gudu yayin da Addawiyya tasoma bashi hakuri itama mik'ar da ita yayi ya falla mata mari tare da jan hannunta zuwa rumfar da suke cin abinci. Fad'a yayi musu sosai sunata bashi hakuri. "Adda Salma yau muje rafin cigogo muyi kallon wasan iyo man, "bazanje ko inaba ni, "ummm kai Adda keko muje mugana na bankwana man, kinga ashekara su 1 akeyi kuma ina son sake ganin rafin sabida na dade ban gantaba gashi nan da kwana uku zan koma school ke kuma ki koma kwantagora. "Ke Allah zan makeki yanzu inbaki bacemin da gani ba, wato so kike inje suyi ta kallona suna cemin fanko ko? "A'a adda banufina kenan ba, amma tunda kince haka to abar zancen. ****** Rafin cigogo ruwane mai fad'i da tsawo gashi da burgewa tare da d'aukan hankali. masinta sunayin su awurin lokaci zuwa lokaci amma fa rafin tana da had'ari musanman ayayin gabatar da wasan iyo na shekara shekara domin duk lokacin da akazo aiwatar da wasan to tana cin mutane a qalla mutum biyu zuwa uku amma duk da wannan had'arin baisa mutanen qauyen Jangab'a sun daina wasan ba, sabida sun d'aukeshi a wani al'ada mai mahinmanci. Yau ake wasan iyon wasan ruwan na zagayowar shekara,, bakin ruwan cike yake da mutane jinsin fulani kad'o, kanbari tare da dikkawa mazauna yankin da kuma masu zuwa kallo amma junsin fulani sunfi yawa sabida ayankinsu rafin take kuma sune suke gabatar da wasan tare da wasu 'yan k'alilan na sauran qabilun. Inda duk wanda yazo na 1 zai zabi budurwan dayakeso a cikin jinsunsu ya nufi daji da ita wai zai cire mata kashin mundirik'i, kuma bawanda ya isa ya hanashi hatta da iyayensu domin wurin yana samun halartan sarakunan yankunan tare da iyayen da matasa harm da yara qanana. Shiyasa yara mata basa zuwa wurin indai da sanin iyayensu. Wasa yayi wasa bakajin komi sai ihu da sowar mutane. and'auki kimanin awanni biyu ana gabatar da wasan tseren ruwan amma bawanda yazamo zakara sabida zakarun ana samun mutane sama da goma wand'anda suke kai bakin gaba atare. acikinsu aka fidda mutane bakwai domin su fafata suma atare suke kai bakin ruwan ganin haka sai aka soma yin mutane 2~2 wanda yariga kaiwa sai yakoma gefe ahaka aka sami mutane hud'u suka fafata ananma aka sami mutun 2 sukayi bracket sai suka koma domin asamu zakara komawarsu ke da wuya aka hango wata qatuwar kada tayi kasan ruwa dasu sai sowa ya koma kuka aka tura masana ruwa su dubosu suma acikin mutane biyar mutun 1 ya tsira ya fito yana cewa "ba aljannun da muka sani bane aruwan bana wasune kuma mugayene don haka kowa yayi ta kanshi domin yasu ambaliyan ruwa yanzu, aiko yana gama rufe bakinshi ruwa yasoma toro yana malala zuwa cikin mutane, tsere aka soma ana fad'uwa cikin masu fad'uwan kuwa har da Addawiyya da Salma wad'anda suke labe awata bishiya suna kallon wasan. Sunacin tuwan dare suna hira k'asa k'asa gudun kada iyayensu suji "amma wallahi ke kam Addiy 'yar buhu ce, "to minayi kuma adda? "A'a kin manta wuk'a ce ba Adda ba, kinsan Allah nakumajin kin kirani da Adda sai na fashe miki baki na zubda miki da haqora. Ja da baya Addawiyya tayi tace "nima kidaina cemin Addiy in kuma kink'i sai na jefaki arafin cigogo wannan kadar ta cinyeki tare da baqin mucijin nan na rijiyan kugu kuma nace Adda adda adda lolo. Afusace Salma tayi kanta ta kwasa da gudu tana dariya tayi cikin garken shanu bata ko tsoron dare ga duhun damina. Ganin haka Salma ta dawo tacigaba da cin tuwonta. Ita kam Addawiyya zama tayi agefen wata bishiyar tumfafiya ta kankwashe k'afafunta kamar mai d'aukan darasi, sai gyad'a kai takeyi tana murmushi. Motsin mutum taji kusa da ita tatashi da sauri ta shige cikin shanu ta sulale tafice zuwa d'akinsu. Tana kwanciya Abbi ya shigo yayi shiru yana kallonta sai kuma ya fice bayan ya tofesu sa Addi'o,i *mrs j moon* [12/29/2017, 2:59 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA *This page is for you Sadia lawal bala, Allah yakaimu ranar bikinki muzo kt mu kwashi rawar d'aga buje😅 inaji dake sosai a ruhina 'yan matan kwarni.*😘 *3~4* Misalin k'arfe 8:30am. Zaune suke a wani bukka wanda yazamo wurin cin abincinsu ako da yaushe. Yanzuma karyawa sukeyi cike da jin dad'i. Ko rafin shan tea d'in Addawiyya batayiba ta mik'e tafice bata jima ba ta dawo hannunta riqe da kwaryan madarar shanu tazo ta zauna tasoma sha har ta shanye tas sannan ta dubi Salma wacce take da tura bread tare da k'osai sannan tabi da ruwan tea. Dariya ta saki tana nuna Salma da yatsa, "amma Adda kina harkan 'yan k'auye fa, diba yarda kike ta tura abinci kamar kwancen hauka, kai Allah kinada matsala ta rashin iya cin abinci cikin natsuwa. Wani mari Salma ta kawo mata ummi ta riqe hannuta tana hararanta tace "amma wai Salma bana hanaki biyewa Rabi'a ba? "To ummi kinajifa tana cemin mara natsuwa don kawai ina bawa tymmyna hakkinshi, ko tana tunanin kowama irinta ne wanda bai kula da cikinsa. "Uhmm inajinta, nadaice ki kyaleta ki daure kina rik'e girmanki, waishin injin ko kin manta shekaru biyar da wata biyu kika bata ne? "Ban manta ba ummi "to daga yau duk abinda tayi miki ki fad'amin zakiga yarda zanyi da ita "tam ummi, Allah yasa ki iya hutamin ita tan. Dariya Abbi yasa sanda yaji k'arshen zancen Salma yace "aikam gara da kikace hakan domin zuwaira da 'yar autanta kam sai Allah. Hararan wasa ummi ta dokawa Abbi tana k'iftamishi idanu. Dariya Addawiyya tasa tana cewa "haramunne k'ifce da yafice da kuma zund'e haka mai k'awa'idi yafad'a ko Abbi? Gyad'a mata kai yayi yana dariya. Daquwa ummi tayi mata "kagamin ja'ira dai wato karatun naki akaina zai sauka ko auta? Ta kama baki tare daja baya tace "nop ummi kawai ina dai tunasar dake ne da kibari kada... make bakinta Salma tayi tahanata fad'an abinda tayi niyya aiko wani tsalle ta daka ta cukumeta ummi ta mik'e da hanzari tasoma jan Addawiyya amma ta maqale jikin Salma kamar mayen qarfe Abbi ya kishin gid'a yana kallansu yana murmushi da kyat ummi tayi nasaran janye Addawiyya yayin da Salma take hawaye tana liliya qirjinta sabida a nononta Addawiyya ta manna mata cizo. "Zonan Rabi'atu, cewar Abbi. Ta isa gabansa ta durk'usa ta sunkuyar da kanta k'asa. Kunninta yaja da kyarfi ta kwalla qara yace "daga yau nakuma ganin kina dambe da yayarki sai na cire miki kunni, kinaji na ko? "Eh Abbi, bazan qaraba insha Allahu. Sakin kunnin nata yayi yace "kutafi ku d'auko littafanmu kuzo ku biyamin k'arin danayi muku jiya in kun iya sai mu d'ora. Atare suka amsa da "to Abbi. Suna fita ummi ta dubi mijinta tace "amma malam baka ganin lamarin auta abin abincika ne? "Kamar ya? "Gani nayi tafiye jan fad'a ga k'arfi kamar shari'a. Dariya Abbi yasa "amma kindai san duk qarfinta Salma maketa takeyi ko? "Eh hkane kuma "to kibar wani tunani can naki mara tushe, kawai kicigaba dayi musu addu'a shi yafi. "Tam malam Allah ya shirya manasu tare dabasu kariya cikin amincin ubangiji "Amin. Acan d'akinsu kuwa fad'ane ya kaure a tsakaninsu sakamakon dariyan da Addawiyya tayi ta sheqawa Salma tana liliya qirjinta irin yarda Salma takeyi aiko cikin fushi Salma ta cukkumeta ta d'aga ta buga a bisa katifarsu tabita ta danne ta zauna bisa ruwan cikinta tana cewa wallahi sai na rama a wad'annan naniqak'k'un nonuwan naki, duk qoqarin Addawiyya naganin ta hana Salma rama cizonta ta kasa sabida k'arfin ba d'aya ba. Abbi kam ganin sun dad'e basu fito ba yasa ya miqe yace da ummi in sunzo su biya wurinki inna dawo daga ta'aziyyan wad'anda rafin cigogo ta cinye jiya wurin wasan banznsu sai na k'ara musu "tam Allah yadawo da kai lafiya su kuma Allah yaji k'ansu "Amin. Da kuka ta shigo kanta bako d'an kwali, ta zube jikin ummi ta cire riganta ta d'ago tana nunawa ummi qirjinta wanda yasoma cika da dukiyan fulani. Idanu waje ummi take duban inda shaidan haqora suka fito a samar fatan, waya cije ki? "Adda ce. "To maida riganki ta maida tana share hawaye alokacin Salma ta shigo d'auke a littansu na karatun addini. "Salma wani irin wasan banza ne wannan zaki bud'e baki kamar karya ki cijemin auta a inda ruhinta yake? "Ummi ita tasoma ai, kallafa kigani ta d'aga riganta bako kunya tana nunawa ummi kan nononta inda Addawiyya ta cijeta d'azun, wanda suka gama nuna sun kuma cika qirjin dam. da sauri ummi ta rubemata rigan tana hararanta "amma dai kekam anyi babban banza yanzu don ta cijeki sai ki rama don tsaban rashin wayau kuma sai kizo kina nuna nunamin wanda tayo miki? "Ummi to bagashinan itama ta nuna miki nataba. "Naboni ni zuwaira ashe dai har yanzu bakiyi hankaliba Salamatu? Shin ke da auta shekarunku 1 ne? To Allah kifita idanuna tun banyi rawar banjo akanki ba tam. Dariya Addawiyya take tayi mata k'asa2 tare da kwalo ita dai sai cika takeyi tana batsewa, tana hararan Addawiyya. zuwa can ummi ta umurcesu dasu matso suyi karatunsu.bayan sun kammala ta yi musu nasiha dasu bar fad'a da juna balle har yakaisu ga cizo. Bayan sallar azuhur suka zauna cin abincin rana dambun zogale ne wanda yaji gyada da soyayen man kad'e gami da man shanu yayi laushi sosai, sai damammiyar fura agefensu wacce taji nonon shanu mai kyau da gard'i. K'asa k'asa Addawiyya take magana "Adda jiya naga abin mamaki atushen itaciyar tumfafiyan can "uhmm mi kika gani awurin? sarkin iya labari. Qasa ta k'arayi da muryanta tace "karatun Al-qur'anin karim naji anayi wanda yasa na zauna ina saurare cike da nishad'i, kuma abin mamaki wurin yacika da k'amshin turare mai dad'in shak'a, kai ai jiya kwanar mamaki nayi donma Abbi yabiyo wurin yakatsemin jin dad'ina. Quri Salma tayi mata da idanu tana saurarenta ganin haka Addawiyya tacigaba "kuma karatun cikin suratul isla'i akeyi, bakiji yarda ake fidda tajwid ba, kai naso naji qarshen karatun nan kam. Da gudu Salma tatashi ta nufi bukkan dasu Abbi suke ta labe abayan ummi tana maida numfashi. Atare suka ce "lafiya kuwa? "Babu lafiya kam Abbi, ummi Addawiy tayi gamo. Gamo!!! Kuma? Sai kuma suka fice da sauri, turus sukayi suna kallon wacce akace tayi gamo tana zaune tana cin dambunta tana korawa da fura cikin kwanciyar hankali. Tsaki suka ja suka koma cikin bukkansu Salma zata biyosu ummi ta daka mata tsawa ta dawo da baya tana kallon Addawiyya wacce tayi kamar bata gantaba. Cikin sanyin jiki tazo ta zauna ta cigaba da cin dambunta. "Uhmm Adda Salma kenan gabaki d'ayanki sai ahankaki domin ina zargin lissafinki yagoce shi yasa baki iya tabuka komi amakaranatar da Aunty hindu ta saki, inaganima cireki zatayi ayi miki aure tunda dama shi kike buqata acikin ranki. Banza Salma tayi mata. Addawiyya ta sheqe da dariya ta taskama cinyar Salma duka tanagani zata rama tamiqe suka soma tsere har saida suka gaji duk suka zube aqasa suna maida numfashi. Adda kitashi kije kisanja kaya kada yaya mushaffahu ya iso yaganki cikin wad'anan fingilallun kayan. "Banson iskanci Addawiy yaushe kikaji labarin zaizo? "To kada kibi shawarata yarinya zauna tambayata, inyazo kyaji kunyarki ke 1 nikam kinga tafiyata tafice zuwa bayan bukkokinsu tana waqen alami abbiyad wa ahadar. Shiru Salma tayi tana tunanin anya Addawiyya ita kad'aice kuwa? Sallamar mushaffahu ya katse mata tunani da gudu ta yi baya inda Addawiyya take batre da ta sami damar amsa mish sallamar da yayi ba. "Addawiy yazo wallahi yazo zomuje kiganshi ta fizgo mata hannu, yana cikin bukkan su Abbi suka shigo suka zube agabanshi atare suka gaisheshi ya masa cike da walwala. " 'yar qauye tashi kikawomin ruwa qishi nakeji, dariya Addawiyya tasa nata kallon Salma tace cikin harshen fulatanci "tashi kisamowa saurayinki abinda zai jiqa maqoshinshi ya kwaso rana, harara ta dalla mata tare da miqewa ta fice. "dad'ina dake Rabi'a gulma wallahi, yanzu sabida kinsan banaji abinda kike cewa shine zaki maidani bare ko? Tana dariya tace "a'a kad'o bawanmu fulani. Dariya su Abbi suka sa mata. Washe gari mushaffahu ya wuce tare da Salma wai zata raka mama kano bikin qanninta, suka bar Addawiyya cikin kewa mara misaltuwa. Wanki ta yini yi tayi guga domin itama gobe zata koma makaranta. Sai dai duk abinsa takeyi cikin sanyi jiki takeyi aiwatar dashi wanda har ummi saida ta lura da rashin karsashinta kuma tayi mata tambayar duniya nan taqi cewa komi sai dai tabi ummin da idanu ko kuma tace mi kikagani ne ummi? Ganin taqi fadamata damuwarta sai tafita harkata tacigaba kintsa mata abubuwan dazata wuce makaranta da su. Dayammaci ummi tayi mata sallam zata leqa gidan biki a kusa dasu. Bayan tagama kwashe tuwon da ummi ta tuqa musu ta adana tare da miyar sai taje tayo wanka ta dawo ta zauna qasan bishiyar mango tana bitan wani English novel sabida arayuwarta tana makuqar son labarai musanman na hikayan zamanin mutanen da. K'awayentane suka shigo kowacce taci d'amara kamar 'yan kokuwa da kallo tabisu tana tabe baki tana kallonsu sama da qasa. "Dalla malama miye kike kallanmu kamar kinga kashi, kodon kina boko mu kuma bamayi, shine zaki samu agaba da wannan kallon rainin wayau d'in irin na 'yan hanyar jahannama? Banza Addawiyya tayiwa yariyar mai suna haule. "Ke kam haule kinboni kam, ace ana yawan gudun bikinki amma baki bar masifaba, kai Allah yayi wadaran naka ya lalace. "Surare kifita harkata wallahi ko yanzu muware qashi mu kwashi 'yan kallo. Wani dariya Addawiyya ta kwashe dashi tana nuna haule wacce taci kyalliya kamar birin wasa wai itanan Amarya. "Auh wai bikinki dama ummi tace zata leqa wai? Tayi wani marmar da idanu kamar kura ta amsa "ya wuce wai, amma wanke wanken kayanna zata gani, biki kam sainan da jibi kuma yanzu munzo ne kitashi mutafi yawon gudu tunda jiya umminki ta hanaki binmu kasuwa sayayya. "Yawon gudu kuma? Ni Addawiyya inbiku? Taf ba inda zani kam, ko kunmanta agarin wannan yawonne Adda Salma tarasa budurcinta? Shiru sukayi zuwa can haule tace "ayya Addawiy ai bazamuyi nisaba iyakarmu tungan jauro kuma ai yanzu anhana mazajen danne 'yanmatan Amare sannan kuma wa'yanda sukayi k'aurin suna akan aikata iskanci kwanaki sunyi sata abirni ankamasu yanzu haka suna gidan kaso, don haka ba dan niba don Allah kitaso muje kiqara ganin inda kika manata. Kamar baza tajeba sai kuma ta miqe ta maida littafanta d'aki ta kulle qofofin bukkokinsu ta zira wani flat shoes tare da qaramin gyale tace "tam kumuje amma wallahi kowa sai ta kwance wannan d'amaran da tasha a k'uqunta kamar wasu bibrai. Dariya suka saka mata suna cewa "sai 'yar birni kuma 'yar boko. Ita dai murmushi take musu agefe d'aya kuma gabanta yatsananta fad'uwa sannan ga tsoron yarda zasu kwashe da ummi intadawo bata gantaba. Haka suka miqa suna ta wak'e2nsu irinta al'adarsu insun fita irin wannan wayon dasuke mishi laqabi da yawon gudun amarci. Shidai wannan yawo anayinsa ne kafin d'aurin aure da kwana biyu kuma mazane abokan ango zasubi bayan 'yanmata sukuma da sungansu sai suyi ta gudu suna ihu har mazan suyi nasaran kamo Amaryan acikinsu wanda kafin sukawota gida sai sun gama latse mata nonuwa wasuma har fad'e suna mata amma anfi samun hakan in amaryan bata son mijin to in sun kamota sai suba mijin yayi abinda yaso da ita wai nufinsu dole zaisa ta zauna dashi kuma ta soshi tunda yayaga mata munta. To kuma wanj zubin har 'yanmatan wasu suke bi su danne a irin hakane Salma yayar Addawiyya tafita yawon gudun qawarta akayi mata aika aika to tundaga lokacim ummi da Abbi suka soke wannan baqar yawon akan 'ya'yansu wanda bakomi cikinshi sai tanbad'a. Wai acewarsu al'adace. *Nace kodai jahilci* *mrs j moon* [12/29/2017, 3 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *Shafin nakine k'awar arxiki, Jamila A Ladan (Aysar~Aysar) Inajinki cikin ruhina ainun, banmanta had'uwarmu da junaba tun zamanin muna irga dangi*🙊😅 *5 ~ 6* Tafiya sukayi mai nisa saida suka soma shiga daji sannan suka yada zango awani fili mai fad'i wanda itatuwa sukayi masa rumfa, iska mai dad'i yake busowa awurin. K'awayen Amarya tare da Amarya haule suka soma chashewa da gad'a sunayi suna saka wak'arsu kala kala. Ita dai Addawiyya samun wuri tayi ta zauna jugum tana binsu da kallo domin ita bata saba irin wannan wasanba sabida su Abbi basa barinsu fita dandali. Chan gad'a tayi dad'i haule ta iso gaban Addawiyya ta ja hannunta zuwa fili, tsaye tayi tana murmushi ganin taqiyin rawar suka soma yi mata dariya suna waqeta wai tazama,,tazama tazama,, tazama kifin rijiya'' batasan komi sai kwadd'iiiiii. Aiko batasan sanda ta bushe da dariya ba tana rangwad'a kad'an2 irin namasu aji. Sowa sukasa mata suna tsalle domin rawannata baqaramin burgesu yayi ba. Salatin da A'ilo ta doka ne yasa duk suka tsaya da shewar dasukeyi. "Shegiya A'ilo, miye haka? zaki bamu tsoro muna cikin nushad'inmu. Cewar Amarya haule. A'ilo Nuna musu tasomayi da hannunta tana cewa "gawasu can zuwa kamar su hisk'ilu da juma "eh wallahi kuwa sune harma da ilya, gajeje ta amshe. "Gambutsinnan mun bani mun lalace, "ke surare daina kiran mana lalacewa dallah, haule ta katseta cikin fushi. Addawiyya wacce jikinta yasoma rawa tace "yo ba ance suna can gidan yari ba? "Uhmm yau kwanarsu biyu da dawowa. Cikin rawar murya Addawiyya tace "shine haule kika cemin basanan? "Tannatsa!! Ni kam bansami labarin sun dawoba sai yanxu, amma dai kam baraka kincika munahikan Allah, ace kinsan da labarin isowarsu tunganmu amma kika kasa sanar dani sanda kikaji ina cewa Addawiyya basa nan. "Ke haule kifita idanuna, kuma ni banji sanda kike mata bayaninba ai dana sanar dake "kedai anyi 'yar wofi masara saiti kam. Tunni baraka ta d'au zafi tayo kan haule surare ta shiga tsakanin su tace "kubar fad'an hakanan yanzu kowa dai sai ta shirya zeton budurcinta ko kuma ta dawo fanko yanzun nan bada jimawa ba. Duk suka soma shirin gudu. Haule ta duni Addawiyya tace "don Allah ki min affuwa, ko kallonta Addawiyya batayiba tasoma bin hanyar komawa gida da sauri surare ta kamo hannunta tajata da k'arfi tasoma gudu da ita tana cewa gasunan abayanmu kuma mu suke son kamawa wata qila ke suke raji don haka kibi can hanyar ki sami bayan ganye ki labe ni kuma nabi nan, ta saki hannun Addawiyya, tayi ta kanta domin neman wurin tsira. Addawiyya gudu takeyi kamar barewa da kyat tasami wata bishiya ta labe abayanta tana maida numfashi hawaye kuwa tuni yagama wanke mata fuska. Daf da inda take labe taji sunja sun tsaya. "Baba ina ganinfa munrasa wannan hajar mai kyau da nagarta "uhmm ilya kenan ai baka sani ba wannan hajar ko ta halin k'aqa sai nasameta na yimata kaca kaca sabida domin ita nabiyo bayansu "kai hisk'ilu baka da mutuncifa, wato so kake ka kuma shan romon qanwar kenan bayan a lokaci irin haka ka ketawa yayar nata tantani "ashe dai kagane nufina kam abokin arziki juma. Dariya suka kyakyace dashi sannan suka tafa. Atare suka ce "yau zamuga k'aryan boko. Jin zasu iso inda take yasa ta fito fit ta falla da gudu suka rufa mata baya, tako kad'an suka kamata cike da zalama suka soma kaiwa nonuwant chafka wad'anda suka soma cikowa kad'an. ta kwalla ihu wanda sai da dajin ya amsa. Ganin da gaske mutuncinta suke da niyyar ketawa yasa taji wani k'arfi yazo mata ta zabura tayi watsi dasu ta arce da wani uban gudu tuni kuma ta bace musu. Cikin wani shark'aqiyar bishiyar tsamiya ta shige duk da k'ayoyin dake sukanta bata sauraraba har saida taga tashige tasami mafaka. Sanyin wurin yasoma damunta domin kamar k'anqara wurin yake, zama tayi sosai tana waige2 sai kuma taji barci yana son kamata. tazabura ta miqe tana kallon wata gatuwar mucijiya nannad'e ta zuba mata idanunta masu uban haske. Atake mufarkin data tabayi kwanaki yafad'o mata arai sai kuma lokacin ta tuna da yarda mufarkin yake. "Wayyo ummi!!!!! Abbi!!!! Adda Salma!!!!! Kuyafemin yau kwanana ya qare. Jin maganarta yasa su juma kutsowa cikin sark'aqiyar tsamiyar, suna gama shigowa mucijiyan tayi wani girgiza iska yatashi ya kwashesu yayi sama dasu ya watsar a wajen sark'aqiyar. Atare suka mik'e kowa yad'iba hanyar tsira, mucijiyan ta mara musu baya da gudu kamar walk'iya. ***** su haule Amarya kuwa a daf dashiga garinsu suka had'u dukkansu sabida sun san hanyoyi da dama cikin dajin fiye da Addawiyya. Numfashi suke maidawa zuwa can gajeje tace "kai ina Addawiyya? Cikin gigita surare tace "munshiga uku wallahi ita suka bi domin naji ihunta sanda suka kamata "Wayyo ni hauleee!! Nabani na d'aid'aice nazamo sadin tsiya, yau mizancewa ummin Addawiyya? Duk sai suka soma kuka ganin basu samo mafitba yasa suka yanke shawaran zama q bakin kogin cigogo su jira zuwan su ilya su tambayesu ina suka baro Addawiyya. ******* Cinkin 'yan seconds mucijiyan ta nad'e su hisk'ilu amma abin mamaki Addawiyya tuni ta bacewa ganinta, tana nad'e dasu tayi ta shawagi ko zata ganta amma bata ba sanmatanta, don haka sai ta zama iska ta bace dasu juma, wad'anda tuni sun suma sabida gigita. Addawiyya kam gudun datakeyi ya wuce misali bataji bata gani ita dai burinta tasami wurin tsira,, bama tasan inda take jefa k'afafunta ba wand'anda tuni sun koma babu takalmi cikinsu duk k'ayoyi da itace sun shige cikin tafin k'afafunta. Ganinta tayi abakin wata wawukekiyar rijiya mai tsananin tsawo da fad'i sai lokacin tasoma dube2n dama da hagunta, taga duk bishiyoyi ne manya kuma masu mugun duhu gewaye da ita, kanta tad'aga sama tayi arba da wani abu dogo sosai shiba bakiba, ba yelloba, ba jaba, ba koreba, gashinan dai wani iri yana nufo inda take zuwa can taji tim yafad'a cikin wannan rijiyan sai lokacin tasoma tunano labarin rijiyan Abbinta yataba fad'a mata akwai wata rijiya mai suna kugu kuma shekaru masu yawa k'wank'wamai sun kashe hanyar da rijiyan take da zama, anama zargin a cikinta akwai masha ruwa wanda yake shanye ruwa in an had'a hadari. Sai lokacin addu'a yadawo mata cikin brain d'inta, da k'arfi tasoma furta "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, Allahumma ajirni fi masibati wa ka... bata qarasaba taji wani iska mai tsananin qarfi yataso ya mud'eta yatafi da ita luuuuu zuwa cikin rijiyan nan mai mugun duhu. Su haule da k'awayenta kuwa hakanan suka zauna zaman jiransu hisk'ilu amma har maggariba tayi basuga alamun ko inuwarsu ba. Angwaye ne suka iso inda suke suna mitan ina suka shige suka wahalar dasu domin su ango da abokanshi dajin yamma suka tafi neman amarya da qawayenta, su kuma gabas sukayi. Surare ce ta fad'amu abinda ke faruwa, sunyi jimami sosai suna ta la'antar su juma. Suna shirin tafiya sai wani abin al'jabi ya faru, igiyan ruwa ne yaja Amarya tare da qawayenta biyu, cikin kiftawan ido sunyi qasan ruwa sun nutse. Ihu yanmatan suka saka tare da kururuwa suna neman agaji. Ango yanemi ya fad'a cikin ruwan wani cikin abokanshi ya riqeshi yace "kalli abinda ke yawo a ruwan, kuma kasan doka ne ba'a zama a rafin cigogo da maggariba don haka muma mu watse ko dukkanmu muzamo gawa. Aiko da gudu suka doshi zuwa cikin garinsu domin kai rahoto da gaggawa. Kuyi hakuri da wannan please. *mrs j moon* [12/29/2017, 3:00 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA *page d'in nakine ke ka d'ai k'anwata mamie waru😝 lallai Ked'in ta dabance, godia nake da yabawarki gareni. sosai nakejinki a cikin ruhina.*❤😘 *7 ~ 8* Ummi koda ta dawon daga wurin wanke wanken kayan Amarya batasami Addawiyya a gida ba sai bata kawo komi aranta ba illah tayi tunanin tana bayane wurin bishiyar gwaiba. Har maggariba takawo jiki bataga alamun Addawiyya zata dawo gidaba sai ta bita domin ta dubota. Abu kamar wasa saiga ummi tagama duba ko ina babu autanta ba sanmatanta, cikin mugun fad'uwar gaba ta fito waje tasami yara dasuke wasa akusa da qofarsu ta tambaye su ko sunga mata inda Addawiyya ta nufa aiko wani yaro cikin sauri ya fesa mata lallai yaganta tare dasu haule sunnufi bayan gari. Salati ummi tasa tana tafa hannaye sai kuma ta nufi inda aka nuna mata sunbi da sauri. Da Abbi tacikaro yadawo da shanunsa daga wurin kiwo, cikin zubar hawaye ummi ta tareshi tana labarta mishi abida taji, cike da mugun mamaki yake kallon matar nashi nashirin yi mata magana suka cinkayi hargowan mutane sun nufi garkan hard'o. Jikinsu Abbi asabule suka nufi gidan hard'on suma domin jin abinda yake afkuwa. Kuka ummi takeyi kamar ranta zai fita sanda taji abinda yake faruwa. "Shikenan narasa autana, Allah yajik'anki da rahama Rabi'atul Addawiyya. "Ummi babu Addawiyya a wad'anda kogin cigogo ya hallaka. "To ina kuka barota surare? "Shine bamu sani ba muma, amma tabbas tana tare dasu hisk'ilu domin naji ihunta sanda suka kamata. Salati aka d'auka duka wurin, hard'o kuwa ji yayi kamar yayi hauka jin wannan bala'i daya kuma fad'owa yankinshi. Mutane suncika wurin da ihu tare da kururuwa musanma ma ga iyayen yaran dasu fad'a cikin kogi. Dakyat hard'o yashawo kan hayaniyar da akeyi sannan ya raba mutane kashi biyu yace wasu su nufi kogin cigogo domin nemo yaran dasuka fad'a kogin wasu kuma su shiga daji domin nemo inda Addawiyya take tare dasu ilya. ***** wucewan 'yanmatan Amarya tare da Abokan Ango ba jimawa mucijiyan nan ta iso bakin kogin cigogo cikin wani irin iska mai mugun k'arfi ta watsar dasu juma ta kuma rikid'a zuwa siffan wata kyakykyawan budurwa ta shek'e da dariya iska mai qarfi yana fitawo cikin bakinta zuwa can ta sauke dubanta kan su hisk'ilu wad'anda ta mai dasu tsirara haihuwar uwarsu tace "sai ni zailumat mai zalinci batare da anyimin komi ba balle kuma kud'in kun tabani tunda kun shigo har fadata to ga qarshen kunan azzaluman banza da wofi. Takuma bushewa da dariya tace "gani nan zuwa gareki kema yarinya in aika dake barzahu. Ta yi kurukuwa tabace cikin iska tabarsu nan yashe abakin kogi. ****** Addawiyya jitayi anayin qasa da ita wani uban hucin zafi yana dokanmata jiki, sai kuma taji an gizgeta anyi sama da ita, atake tasomajin iska yayi mata yawo domin jin shigarsa takeyi cikin bargo da jijiyoyin jikinta, bata kuma sanin abinda yake faruwa ba illa dai taganta tsaye agefen wani qaton fili rasharre tas dashi. Waige2 tasomayi can ta hango wani lambu mai kyau ta taka ahankali ta isa wurin, k'aton lambun ne mai d'auke da kayan marmari kala kala, cike da gajiya ta zaune qasar wata bishiyar d'orawa ta dafe kanta tana hawaye "oh ni Addawiyya rayuwata tana cikin garari, nan kuma ina nakawo kaina? Wani qishin ruwane ya tasomata kamar mak'oshinta zai kama da wuta don azabar bushewa tamiqe cike da ganin jiri tasoma bin wurin da kallo, kamar asama taga tulo agabanta tako d'agashi sama ta kafa baki, jikinta narawa tasoma shan ruwan ciki, saida taji cikinta ya k'ulle sannan ta direshi k'asa ta koma ta jingina da itaciyar d'orawan tana lumshe idanunta,, batako jimaba barci ya d'auketa awurin ta zame ta kwanta. ****** rukunin mutanen dasuka nufo bakin kogin cigogo suna isowa suka tarada da gawarwakin Amrya haule, A'ilo tare da hanne abakin kogin, atake suka tsamosu waje. Suna shirin barin wurin suka ci karo dasu hisk'ilu, juma tare da ilya tsirara babu kyan gani jikinsu duk jini halittansu duk ya sanja kamar basuba. Cikin gigita suka ja baya suna k'aremasu kallo da kyat wani ya iya ganosu juma ne suka koma haka. Suka d'auke zuwa bakin wuron hard'o jama'a suna ta zuwa ganinsu yayin da danginsu sukayi ta kukan rashinsu. Hard'o yayi umurni da ayi musu sutura yanzu amik'asu zuwa makwancinsu. ******** Tawagan su Abbi kuwa sunyi dube duben daza suyi har sun gaji basuga ko alamar mai kama da Addawiyya ba, ganin dare yasoma kuma bawanda yayi sallah sai suka yanke shawaran komowa gari gobe in Allah yakaimu sai su dawo lokacin ido naganin ido. Abbi bayako gani gabansa yabiyo bayansu, tuntube yaci da wani abu koda yaduba sai yaga takalman Addawiyya ne ya duk'a ya d'auka yana nunawa abokan tafiyanshi duk suka tsaya suka soma duba wurin nanma wurin wata bishiya suka sami gyalenta ganin haka sai suka k'ara qaimi amma basu kuma ganin komi nata ba, hakanan suka haqura suka baro dajin cikin jimami tare da burin komawa gobe. *****wani farin haske ne yabayyana gaban Addawiyya zuwa can ya rikid'a yakoma mutum atake kuma k'amshi ya cika wurin kamar anyi barin turare. Takowa yayi asannu cikin mulki zuwa gabanta ya tsaya yana murmushi ya bud'e hannayenshi sama ya runtse manyan idanunshi yace "welcome to my place mai babban suna. Ya soma takawa yana bin wurin da kallo zuwa can ya cinkayi wata guguwa ta nufo wurinshi cikin hanzari yadawo yatare inda Addawiyya take kwance tana shakan barcinta kamar tasami gadon umminta. Iskan tasoma lafawa tana gama lafawa wata budurwa fara tas mai tsananin kyau ta bayyana ta nufo wurinshi gadan gadan tsawa ya daka mata taja ta tsaya tana kallonshi zuwa can tace "ba wurinka nazoba malam kayata nazo d'auka "tana ina kayan naki? Gatanan ka kareta "oh wai mai babban suna kike nufi itace kayan taki ko wa? "Eh itace kayata, kuma yau zan aika da ita k'iyoma sabida kuskuren datayi na shigamin fada har tayimin barna "fadarki ko fadar wasu domin kwacensa kikayi sabida tsaban zakunchinki, to kisani daga yau baki qara aikata zalinchi har abada, ni masoyin Allah da manzon Allah Habibullah ina mai umurtanki daki bar yankinnan tun fushina bai sauka akanki ba. Cike da tsoron kalamanshi ta matsa baya ta rikid'a takoma rabi mutum rabi micijiya ta nufoshi da wata irin iska ya d'aga hannunshi ya nunata atake sarqa ya zubo tayi maza takoma mutum sarqan ya cukui kuyeta ya nunata da yatsa yace "k'arshe zaluncinki yazo yanzu zan aikaki zuwa ga mahaifinki dama yana nemanki ruwa ajallo don haka ki kuka da kanki sabida kinfi kowa sanin waye malam, hukuncin dazai miki sai kin gwammace bakizo duniyaba. Cikin kuka take roqonshi da yasaketa bazata k'ara zalinchiba zata koma ga Allah tacigaba da bautansa yanda yakamata. "Inkin koma yankinku sai ki tuban da kyau amma nan kam kinbarshi kenan har abada, dama wannan ranar nake jira kuma gashi tazo. Da yatsa ya nunata iska tayi samada ita cikin sarqan tabace bat kamar walkiya. Jan numfashi yayi yadawo gaban Addawiyya ya duqa yace "na ceceki ahannun yaran sarkin yankin rijiyan kugu kuma yanzu Allah ya kuma bani ikon tsirad dake daga muguntar micijiya zailumat sannan kuma bada jimawaba zan maidaki zuwa ga iyayenki,kisani mai babban suna inatare dake ne tun kina cikin mahaifiyarki 'yar wata hud'u kuma zanci gaba da kasancewa dake har izuwa k'arshen rayuwarki. Ya bud'e baki ya hura mata iska wani haske ya fito ya sauka zuwa jikinta atake suka bace bat shi da ita kuma alokaci d'aya wurin yakoma babu dukkanin wani shukan kayan marmarin yadawo fili wanda baya da yawan bishiyoyi. ******Daren ranar kam dukkanin d'aukakin al'umman garin yankin jangaba k'alilan ne sukayi barcin dad'i cikin marasa barcin dadinkuwa har da su Ummin Addawiyya domin kwana kuka ummi tayi yayi da Abbi ya kwana sallah shima in yagaji sai yatsaya yayi ta shere hawaye sai kuma ya tashi ya d'ora, yana addu'ar Allah yabayyana mishi d'iyarsu cikin gaggawa. Ahaka suka kwana basu rintsaba ko kad'an. *Kai haba kubar jin tsoro man*🙊 *mrs j moon* [12/29/2017, 3:00 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *Shafin nakine K'awalliyata Zainab VC.ina jidake sosai my sis, Allah yabarmu tare*😘 *9 ~ 10* Asannu tasoma motsa idanunta har ta bud'esu duka tayi mik'a tare da salati ta d'ora da addu'ar tashi daga barci, ta dafe kanta tana son tuno wani abu. Azabure ta duro daga bisa gadon tasoma bin d'akin da kallo, jikinta yasoma rawa sai kuma tafashe da kuka ta durgushe k'asa tana yarfe hannunta "wayyo Allahna ni Addaiyya naga takaina, nan kuma ina nakawo kai? Ya ubangijin sammai da k'assai ka kawomin d'auki bisa wand'an nan abubuwa dasuke faruwa dani, ka kanemomin hanyar dazankoma zuwa ga mahaifana. "Amin taji amsa mata tamiqe tana kalle2, Alamar tafiya taji yasa tayi tsam tana saurare can ta kumajin Kamar ana magana kusa da ita ta sai ta bud'e kunniwanta sosai tana saurare amma sai taji shiru,, ta miqe a tsorace tana k'arewa d'akin kallo k'aton d'akine wanda yake d'auke da kayan alatu masu mugun kyau da had'uwa, tunda Addawiyya take bata taba ganin wuri mai kyawun hakaba duk kyau da tsarin d'akin mama Ramlat batajin yakai ko kwatan wan nan a had'uwa. "Oh ni ko inane nan? "Baza'acutar dakeba mai babbab suna, kidai hanzarta rama sallolin da'ake binki. Agigice ta mik'e tana duba ta ina maganar yake fitowa, jitayi anja hannunsa har zuwa bakin toilet ance "kiyi wanka ki d'auro arolla sai kizo ga abinci can yana jiranki. Muryan mace taji mai dad'i tace da ita haka. Murya ta bud'e ta kwalla ihu "wayyo ummi nafad'a gidan aljannu, nashiga uku, rashinjin magana baiyiba wallahi musanman na iyaye, gashinan nazo inayin nadama. Wani ubanTsaki taji anja mai qarfi tare da turata bayin, jikinta ya d'auki bari. "Inbaki hanzarta sauke bashin sallar da ake binkiba Allah zan maidaki biri yanzunnan ki koma daji dazama. Tanajin haka jiki na bari tasoma cire kayanta ta hau wanka tana gamawa ta d'auro arollah ta fito kaya tagani agefen gadon tabishi da kallo saiji tayi ance "oya d'auki kisaka bamusu ta sanya ta duba geden damarta taga sallaya shinfid'e tare d hijab tamatsa ta hau kai tasoma ranka sallolin da ake binta ta d'ora da sallar azuhur ta ranar sabida lokacim k'arfe 1:45pm. Tana idarwa ta takure wuri 1 ta zuba uban tagumi,,, kice take da kewar su Abbinta tasan yanzu duk inda suke sunanan cikin tashin hankalin rashinta musanma ma umminta domin tasanta da rud'ewa. Uhmm ko ya adda Salma zakaji intami labarin bacewata oho, Allah gani gareka. Duk cikin zuciyarta take wannan zancen sai tafashe da kuka,, sanda tayi tunanin qilama gidan yankan kai ne ta fad'o, Kukan nata sai yaqaru tayi2 bamai rarrashinta. "Uhmm nidai kam yaya yahad'ani kula da sangartattan bil'adama oooo. Wani tsalle tayi ta koma gefe tana raba idanu, tanason ganin wake mata magana amma bataga kowa ba sai sautin tsaki dataji ankuma ja tare da buga k'ofar fita daga room d'in da qarfi ta ja baya tana gwama numfashi. K'amshin abinci taji yasa ta kai dubanta inda qamshin ke fitowa arba tayi da girke2 masu rai da lafiya ai cikin sarsarfa ta qarasa wurin tasoma bama cikinta hakkinsa bata kojin tsoro domin jitayi kamar tana d'akin umminta ne. Tana gama ci taji wani barci yazo mata tazame awurin ta kwanta, rufe idanunta ke da wuya barci yayi gaba da ita. ****** washe gari Abbi da mutanen gari suka koma dajin neman Addawiyya, sunsha yawo har sun gaji basu gantaba don haka sai suka haqura suka dawo gida, ard'o yayi ta jajantawa Abbi tare da iyayen yaran dasuka rasa 'ya'yansu kuma yace ya soke dukkan wani yawon gudu Amarya ayankinshi sannan hatta wasan iyon ruwa ta kogin cigogo ya soke kuma dole kowa yasa yaronshi makarantar addini,, zaije gari yasamo malamai. Ahaka aka watse taron kowa yana fad'an albarkacin bakinshi. Salma kam sumarta biyu kafin su iso jangaba. Sosai ta d'imauce dajin labarin, koda suka iso kuka tafashe dashi mai cinrai barinma da taga kayan shopping d'inta tare da a kwatin kayan makarantar ta sai ka sake sumewa da kyat aka sami ta dawo hayyacinta Abbi yasa agaba yayi tayi mata nasiha nata dauki qaddara tazamo mai juriya tareda tawakkali. Mushaffa'u shine yaqara yi mata nasiha harta soma haquri ta rage kukan. Kwanar su uku mama Ramkat tare da aunty hindu da mushaffa'u suka yi sallama dasu suka koma garin kwantagora yayin da Salma tak'i binsu fafur tace ita sai 'yar uwanta tadawo zata dawo, ba'ason ran mushaffa'u ba yabi su mama amma ya qudurta kwana biyu zaiyi yadawo su wuce. Wasa wasa Addawiyya takai kwanaki goma da bace kuma har yanzu ana zuwa nemanta cikin dajin amma ba'ayi sa'ar ganintaba. Salma kuwa ta rame sosai, ta maida bakin itaciyar tumfafiyan nan inda Addawiyya take yawan zuwa wurin zamanta, intaje ta had'akai da guiwa tayi ta kuka tun Ummi nayi mata fad'a har ta zuba mata idanu. Abbi kam baima iya ce mata komi sabida duk in yaganta awurin Addawiyya ce ta fad'o mishi arai. Adda'a kam tanasha na Allah yabayyanata intana raye in kuma ta rasune Allah yaji qanta da rahama. **** zaune take gefen gadon dayazama nata ayanxu. Inuwar Mutane take gani suna ta gilmawa ta gabanta kamar kullum, ta runtse idanunta ta bud'e sai kawai taga wata qatuqar mage kwance ta turo k'afafunta gaba ta zuba mata idanu, itama idanum ta zuba mata tana qare mata kallo,, tabbas itace take yawan gani duk inta kwanta barci tunsanda tasamu kanta awannan d'akin. Yauma magen rik'id'a tasoma yi mata kamar yarda take gani amufarkinta ta koma mata bak'a, kore, yelo, ja sai kuma ta dawo golden zuwa can ta dawo faranta yarda take, ita dai Addawiyya quri tayi tana kallon ikon Allah sabida yanzu tabarjin tsoron duk abinda zata gani a d'akin. Koda ta kuma kallon inda magen take sai tanemeta tarasa, ta miqe cike da sanyin jiki ta shige bayi tayo arollah tayi sallar la'asar sabida taji anata kir Awani charming garden take ta shawaginta cike da nushad'i can nesa ta hango shi yana zaune bisa buzu yana jan tasbaha kansa sunkuye. ahankali ta qarasa wurin ta zauna gefenshi tace "Abbi d'agowa yayi taja baya bakinta bud'e yasakar mata murmushi yace "ni uncle ne ba Abbi ba, Abbinki gashi can cikin kasuwa yana saida dabbobinshi zaiyi hijira da mahaifarshi zuwa nesa da it. Sai ta qurshe tana wani irin kuka mai taba zuciya, ya kai hannunshi ya dafa mata kai yana girgizawa alamar rarrashi, sai kuma yakamo hannunta atake wani sanyi ya jiyarci jijiyoyin jikinta tare da bargon ta, tayi wani irun zabura ta farka sai ganinta tayi agadon umminta kuma cikin bukkan ummin. K'ara ta saki mai k'arfi tana fad'in ummi!!!!!!!. Salma wacce take waje tana share tsakar gida ta saki tsintsiyar ta nufi d'akin da gudu sakamakon jin muryan 'yar uwarta da tayi,, tanaganin Addawiyya zaune, ta kuma yo waje da gudu tana fad'in "tadawo wallahi, ummi,, Abbi gata can a samar gadon ummi. Atare su ka tambayeta "wa? "Addawiy ta amsa musu tare da jan hannayenzu zuwa cikin bukkan. *mrs j moon* [12/29/2017, 3:00 PM] Asma'u Seema1: [11:36AM, 12/7/2017] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA *Shafin nakune my aunties Aunty Maijidda musa tare da aunty jamila gombe, sosai nake godia da karamcinku gareni Allah yabar k'auna Amin.lallai kusani Inaji daku ainun acikin ruhina*❤😘 *11~12* Suna shiga Addawiyya tana sakkow abisa gadon. atare suka rungumeta suna ta jera kalaman godiya ga Allah mad'aukakin sarki daga dawo musu da gudan jininsu zuwa garesu batare da zato ka tsammani ba. Ita kam Addwaiyya sai kuka takeyi tana qara k'amk'ame su ummi zuwacan ta dawo ta rungume Salma, cikin fizgan magana irin namai kuka tace "Adda nayi kewarki sosai wallahi, inna tuna daku nayita kuka bamai rarrashina. Itama Salma kuka takeyi har da sheshsheka ta amsa "nima nayi kewarki sweet Addawiy, har suma nayi tayi danaji kin bace, ashe zakidawo gare, kai wallahi Allah shine abin godiya, Allah mun gode maka, Allah kak'ara tsare dukkan musulmi da afkawa irin wannan yanayi. "Amin, su Abb suka amsa atare. Cikin k'ank'anin lokaci yankin k'auyen labari ya bazu na anga Addawiyya, ta dawo gida batare da ko rauni ba. Kafin kace me gidansu Addawiyya yacika taf da al'umma masu zuwa tayasu murna tare da ganin ya Addawiyya tadawo. Hatta ard'o dakanshi ya tako yazo ganinta. Atsakiya suka sakata suna tayi mata tambayo na ya'akayi ta bace kuma aina tasami mafaka ta boye akayi ta xuwa nemanta batare da anganta ba? Cikin sanyi tace dasu "sanda su hisqilu suka kamani nasamu na kufce sai nayi ta gudu har nafad'a inda mucijiya take kwana, tako biyomu tarw dasu, nasamu na tsira ahaka nayi ta rayuwa cikin daji innaji yunwa sai na ci a kayan itatuwan dajin haka innaji k'ishi sai inqarasa awata rafi nasha ruwanta sannan nayi arollah in sallah inna fahimci lokaci yayi,, nakan bata lokaci ina addu'ar Allah yakawomin mafita, to ahaka dai harna kwashe wasu kwani ina rayuwa ni d'aya batare da wani abin citarqa yasameni ba. Nasoma bin hanya domin indawo cikin mahaifana to cikin ikon Allah sai gashi d'azun da sanyin safia na iso gida. Cike da al'ajabi mutanen wurin sukayita hamdalah suna kumayi mata sannu, ita dai sai murmushi takeyi tana kallon gefen damarta wanda tun sanda tasoma basu labarin take kallon wurin bako k'iftawa. Bayan kwana biyu. Addawiyya ce tare da Salma suke hiransu cikin nishad'i zuwa can Addawiyya ta dubi salma tace "Adda ashe jikin micijai sanyi yake dashi kamar k'anqara? Idanu waje Salma take dubanta takasa tankawa, ita kam tacigaba dacewa "uhmm ai wallahi har yanzu inajin sanyin jikinta a fatata kuma hasken dake idanunta yakasa bacemin afuska, kai Allah yayi halitta awurin kam, Adda bakiganta ba wata qatuwa gaske kamar tayan babban mota kalanta fara tare da rod'i rid'in golden,, wallahi bantaba ganin micijiya mai kalantaba sai a mufarkina naran nan sai kuma lokacin dana nemi wurin tsira daga sharrin su hisk'ulu. Jadabaya Salma tasomayi har tamatsa sosai sannan tamiqe ta kwasa da gudu tashige bukkan Abbi, tabe baki Addawiyya tayi tana mai furta "matsoraciyar banza kawai. "Abbi wallahi Addawiy tana tare da matsala domin taboye muku gaskiyan abinda yafaru da ita. "Kamar nami ba? Cewar ummi. "Allah ummi yanzu take bani labarin wai jikin micizai yana da sanyi kamar k'anqara. Azabure ummi ta jababaya tana kallon Salma tace "banson sharrinki fa yarinyar malam. "Wallahi Allah ummi kuje ku tambayeta kuji. "Tam munji kiramana ita, Abbi ya umurceta, wanda shima yasoma tsorata dajin labarin, dama can shi bai gamsu da yarda tayi musuba bayanin bacewan nataba yadai kyaletane kawai. Daga nesa da ita Salma ta tsaya tace "Addawiy kizo inji Abba, harara ta wullamata sannan ta miqe tace da k'arfi "ga miciji nan ya nad'e miki k'afafu. Aiko wani tsale Salma ta daka ta fad'a bukkan Abbi da uban gudu tana ihu. Me Addawiyya zatayi inba dariyaba, hartana kwanciya aqasa ta dafe cikinta hawaye da majinu suna ta zirara don tsaban dariyan mugunta. Cirko2 su ummi sukayi suna kallonta tana d'agowa ta dubi Abbi tace "laaa! Gashinan ajikin Abbi zai shige mishi aljihu. Wayyo zo kuga wani wuntsilawa da tsohon yayi ya fad'i ya k'asa ya miqe arud'e yayi hanyar waje da gudu. Ummi kam ai tuni takai cikin bukkanta ta kulle qofa dama ita kam Salma bata fitoba tunsanda tashige bukkan da gudu. Addawiyya kam don tsaban dariya saida tasaki fitsari awando, haka yake gudu ajikinta ya wanke mata qafafu. Abbi ne yadawo yana mazurai Addawiyya ta dubeshi ta kuma kyalkyalewa da dariya tace "Abbi wallahi duk kanku nafiku jarumta nida naga micijiyan da idanuna har natabata banyi irin wannan rud'ewanba amma ku daga ina muku wasa shine duk kuka zure haka? gama Adda Salma can cikinta yana murd'awa tana son kaiwa ma'aikatan sarrafa kashi (msk) ziyara. "Rabi'a kinci gidanku nace, wato kinmaidamu kakan ninki ko? Girgiza kanta tayi tare da barin dariyan ta tsunu kamar ba itace ke kyakyacewa ba. Jan hannunta Abbi yayi zuwa cikin bukkanshi. Salma naganinta ta miqe ta fice hannunta dafe da cikin, a makewayi tayada zanzo ji kake fatsatsatsa!!! Burrrr!! Burr!! Burrrriririii!!. Tana share zufa ta shigo bukkan, Addawiy ta dubeta ka kama bakinta tana qunshe dariya. timmm!! Salma ta timawa Addawiyya duka a baya zata qara mata wani ummi ta riqe hannunta tana hararanta, cike dajin haushi ta zauna gefen Abbi tana wullawa Addawiyya harara, ita kam sai murmushi take dokawa tare da kanne mata ido 1. Gyara murya Abbi yayi ya sauke dubanshi kan Addawiyya yace "Rabi'a muna saurarenki da kifad'amana gaskiyan abinda yafaru dake sanda kika bace. Zama Addawiyya tagyara ta jingina jikin ummi tasoma basu labarin da ta sanu har zuwa falkawan datayi ta ganta agadon umminta. Baqaramin al'ajabi suka fad'aba sanda sukaji wannan sirad'i da tsallake musanman na wurin rijiyan kugu. Salma ta matso ta kama hannunta tace "amma Addawiy taya kika tsara labarin nan sanda su ard'o suka tambayeki kuma miyasa kika boye musu gaskiyan lamarin? Shiru tayi taqi cewa komi. Ummi ta dafa kanta tace "autana abin alfaharina kuma haskena yi magana mana. Quri tayi tana kallon rifin tsoron d'akin zuwacan ta gyad'a kai tana mai amsawa da "tam. "Alokacin fa wannan mutumin ne daya tai makeni yazo ya bud'emin tafin hannunshi ina karanta dukkan bayanin danayi sabida yacemin bakowane zai yarda da abinda zan fad'aba kuma wasu zasu iya mai dani 'yar mai ganye sunazuwa suna cewa inbasu magani alhalin bansan komi akan cutarsu ba. Jinjina kai sukayi dukkansu cike da gamsuwa da bayaninta. Abbi ya numfasa yace "hakikanin gaskiya Rabi'a kinga abubuwan al'ajabi kuma tabbas kin had'u da aljannun musuncine, lallai nagode musu da Allah yabasu ikon taimakonki, Allah yasaka musu da Alkhairi. Suka amsa "Amin. "Abbi dama a aljannu akwai masu kirki haka? "Sosaimakuwa Salma, dasu kuma wasun suma sun mafimu tsoron Allah sabida su d'in suna ganin mala'ikun Allah kuma suna jure bautan Allah mad'aukakin sarki fiye damu bil'adam illadai Allah mad'aukakin sarki ya tabbatar da munfisu matsayi da d'aukaka ta ko ina sabida masoyinsa habibinsa d'angatansa ma'aiki SAW ajinsinmu yafito. "Allahu Akbar!! Suka fad'a atare. Addawiyya tace "to Abbi miyasa ake samun azzalumai macuta cikinsu alhalin sunfimu ganin ilmomin Allah SWA quru k'uru? "Haka Allah yake wanzar da k'udinsa da iradanshi kuma asanda yaso, kisani yarda mukammu bi'adama cikinmu akwai azzalumai marasa imani koda kuwa suna musulmai to suma haka yake a cikin jinsinsu. "Aikam indai hakane to micijiyan nan data biyomu itadin azzalumace kuma tana daga jinsun junnu domin daganinta ba normal micijiyabace kuma hakik'a itace tayi azajalin su ilya sabida inajiyo kurukuwansu sanda ta kamasu. "Biri yayi kama da mutum kam don koni nayi zargin ba micijiyan kyau bace Allah bata kyau bace Abbi, bakaga idanunta ba zar haske kamar fitila kuma wallahi haskensu sunqi bacemin a cikin idanuna. "Auta dayardan Allahu zakibar ganin gizon da idanun su ke miki kinji? "Tam ummi, Allah yasa hakan "Amin. Salma ta wulla mata harara zatayi magana Addawiyya ta rigata tace "madam Salma matar mr. Mushaffa'u to be insha Allah minayi miki kuma da kike hararata? "Wallahi ummi kirabi da autanki ko yanzu in sanza mata kamanni tam. Kallo Addawiyya ummi tayi tako kwashe da dariya tana cewa "ummi Allah nagama fahintar adda Salma tana da mugun tsoron jin labarin aljannu tare da micizai ne shiyasa na walata d'azun sai kuma Gashi ashe ba ita kad'aice maijin tsoronba har da ke. Murd'e mata kunni ummi tayi da k'arfi, tako kwalla k'ara Abbi ya toshe kunninsa yana cewa "kai zuwaira kibari kada ki yi mata illaman "barni da ja'ira malam wato sabida kin maidamu abokanan wasanki shine zaki wana mu ko? To dad'in abinma ubanki yafi koqa tsorata tunda shi waje yayi da gudu kamar goyon barewa. Duk sukasa dariya, Salma harda kwaciya. "Su Adda anji mugunta anata dariya to gashinan zawo zai zubo miki dai, aiko da gudu Salma ta tashi ta fice zuwa bayi tasoma zugawa ba k'aqk'autawa. Me Addawiyya zatayi inba dariya ba, Abbi ya miqe cike da dariyan qaran fitar zawon Salma da suke jiyowa daga inda suke yace "Rabi'a biyoni kinji in harbo mana zabon daza ayi mana miya dashi anjima. Cike da zumud'i tabiya bayanshi tana cewa "yawwa Abbi aharbosu da yana sabida isowar dasu mama Ramlat zasuyi anjima sannan kuma yakamata ace angabatar da walimar dawowata gida cikin qoshin lafiya shima. Kaga kenan sai ayi amfani dasu wurin taron ko? Shiru Abbi yana mamakin lamarin Addawiyya kamar wato 'yar duba wani karon take dawo mishi domin lokuta da dama inta fad'i abu sai ya tabbata dad'in abinma natama bata fad'an na sharri kuma iyakarta agine zancen nata. Ilai kuwa suna cin abincin rana saiga su hajiya Ramlat tare da yaranta dukkansu. Cikin murna suka tarbesu yayin dasu kuma duk suka rungume Addawiyya suna murnan bayyanarta. Bayan sunci sun qoshi aka bud'e babin Hira tare da maida zancen abinda yafaru sannan suka cike da addu'ar Allah yaqara tsare musu zuri'a daga k'ara afkawa mummunar kaddara irin wannan. "Yawwa malam to yanzu kenan tunda Addawiyya ta bayya kayi watsi da qudurinka na tashi daga mahaifar naka kenan? Hajiya Ramlat ce take tambayarshi sabida tun sanda Addawiyya tabace da kwana uku yasoma saida wasu daga cikin tabbobinshi yace zai bar yankinsu yayi nisa da jaharsu sosai koyin haka zaisa ya rage mishi rad'in rashin Addawiyyarsa. Amsawa yayi "maganar tananan Ramlatu, domin ko yau zan Koran wasu zuwa kasuwa kuma harna turawa aminina Alhaji gambo kud'i masu kauri dayasaya min fili ko ginannen gida mai d'an girma sabida nafiso da zarad na isa garin in zauma acikin muhallina. "To Allah yatai Mata "Amin. Mushaffa'u yana sosa kai yace "to Abbi amma dai baza kayi misa damuba ko? kuma zaka auramin Salma kafin lokacin tashinnaku naku yayi amma. "La'ilaha'illallahu!!! Mushaffa'u baka da ta ido she bansani ba? Cikin sosa kai yace "Allah mama ni dai kibari Abba ya amsamin tambayata kawai, duka hajiya Ramlat takawo mishi ya goce, hindu dake gefenshi ta rankwasheshi a kai yayi saurin taba warin yana hararanta, itama Salma ta tura baki tayi tana hararan Hindu tagefen idanu, aikan Addawiyya tana ganin haka tasoma tafi tana cewa "masoyan zamani ooo, Abbi wallahi ka d'aura musu auren nan yau kawai gobe sai su wuce tare da ita sabida dama tuni sun shirya tunqaranka da zancen ita da shi. Idanu waje Salma take dubanta zatayi magana tamatsa da bakinta daf da kunninta tace "Allah kina musawa zan fasa kwai, domin kisani nasan yana latsa miki nono in har yaritsaki a inda babu idanun mutane kuma sarai kinajin dad'in latsawan ko? Ahaukace Salma tasoma kai mata duka, ira kam tashi tayi ta gudu zuwa d'akinsu tana dariya tako rufa mata baya iyayennasu suka bisu da kallo cike da sonjin abinda Addawiyya ta fad'ama Salma a sirrince. Da yammaci ranar suka fita yawon shan iska cikin rigagen fulanin dake zagaye dasu tare da leqawa yankin da dikkawa tare da kammabari suke gabatar da al'adunsu. Basu dawo gida ba sai daf da magariba. dukkansu arollah suka d'auro Abbi yajasu Sallah, koda suka idar anan suka zauna suna jiran zuwan lokacin isha'I tayi su d'ora. Sai jan chasbahansu sukeyi yayin da Addawiyya ce kad'ai ta bud'e Alqur'anin karim tana karantawa cikin zuciyarta zuwa can ta tsinkayi wani qamshin turare mai dad'i yana busowa ta gefenta kallon tabi wurin dashi ta hangoshi tsaye gefenta yana murmushi itama murmushin ta maida mishi zata yi magana ya girgiza mata kai tare da jan hannunta ya nufi wata bishi datake bayan bukkokinsu. abin mamaki suna isa ya amshi qur'anin ya ajiye agefe sannan suka zauna abisa wasu kujeru masu kyalkayali. Kallonshi tayi tace "uncle yau banji sanyi ajikinka ba kamar ranan nan. "Dariya yayi kad'an yace badai ki lura bane amma sanyi yana tare da ni ako da yau she sabida nid'in iyayena a tsibin mafi sanyi suke rayuwarsu nikuma nakanyi tawa rayuwar ak'asan ruwa, sannan mud'in jinsinmu haka Allah yayi rayuwarsu gaba d'aya cikin sanyine kinga bayarda za'ayi sanyi yarabi dani. K'uri tayi mishi da idannu bako kifatawa ya hura mata iska taja numfashi da sauri tare da lumshe idanunta ta bud'esu tace "uncle wai miyasa ni kad'aice nake ganinka agidanmu? "Sabida kece kad'ai idanunki abud'e sakamakon bud'e miki danayi tun kina 'yar shekaru biyar a duniya kinga yanzu kimanin shekaru tara kenan da watanni uku tare da kwanaki goma sha d'aya da awa biyu da mitoci arba'in tare da sakonni tara cif. Baki bud'e take kallonshi ya gyada mata kai alamar gamsarwa. "To har karatun danaji ranan awurin itaciyar tumfafiyar nan wai duk kaine ka bud'emin kunnin naji? "Eh, nine mai babban suna, kuma karatun da kikaji ranar anayi a wurin to makarantarmu ta haddar al'qur'ani ce awurin, kema in kinaso sai kin bud'e miki wurin kiriqa zuwa d'aukan karatu amma fa kisani zakiga halittu kala kala awurin damasu kyawun sura da munana da farare da baqaqe harma da jinsin micizai duk zaki riga gani amma bazasu cutar da keba Sam. Dafe qirjinta tayi tace "banaso uncle. "Tam kwantar da hankkinki bawanda zai kaiki, mai babban suna. Murmushintayi tana maijin dad'in sunar datake kiranta dashi ainun. "Amma wai uncle intambayeka man, shin kai mutum ne ko aljani? Dariya yasaka sosai yace "mai babban suna kece zaki lalubo amsar da kanki domin ma naji Abbinki yayi sharhi akanmu rannan sosai. Shiru tayi tana son tunano abinda Abbin yafad'a zuwa can tace "au natunama kai junnu ne kuma musulmi mai tausayi. Gayda mata kai yayi ta kuma cewa "oh to ita wanna micijiyan wanda idanunta yaqi bacemin a maganaina fa? Shin muguwace ko? "Eh, muguwace ta kyau kuma musulma ce "to yanzu da na ina kuma miyasa nakasa mantawa da ita? "Tana can yankinsu a tsubirin sanduluna sannan brain d'inkice take da riqe abubuwa sosai wanda batacika mantuwa ba shiyasa kika kasa manta hasken idanunta. Shiru tayi sai kuma tace "uncle to ya akeyi ajinsunku ake samin micizai? Haka Allah yayosu mucizai wasu kuma komawa sukeyi dakansu kamar yarda micijiyan data biyoki takeyi inzatayi zalunci. "Tafd'ijan, to Allah ya shiryata "Amin mai babban suna, hakan takwaranki sayyada rabi'atul Addawiyya take, komi akamata na zalunci sai ta nemawa mutane shiriya wurin Allah. "To aina itad'in kenan take? Itad'in jinsun kuce ko namu? Gyara zama yayi yana murmushinsa mai kyau ya amsa "Wata baiwar Allah ce mai tsananin tsoron ilahu da gudun duniya sannan ajinsinku bil'adama take. Cike da zaquwa tace "to uncle bani labarin nata man insha. Miqewa yayi yace "Yanzu dai tashi kitafi ki sanja arollah kibi 'yan uwanki sallar isha'i nima zantafi inyi tawa, zuwa dare ko cikin barcinki zan fad'amiki taqaitaccen tsoron Allah nta. "Amufarki kuma uncle? "Eh, acan fa kuma zanfad'a miki wacce take yawan janmiki tsaki sanda kike zauna ad'akin nan sanda kika bace. Da magen dayi tazuwa miki cikin barci "To uncle, amma dai da kazomin azahirine zaifi ba a cikin barci ba "tam hakan za'ayi mai babban suna, yau in kowa yayi barci ki fito zuwa wurin bishiyar gwaiban dakike yawan zama sai muyi hiranmu ko? "Eh zanzo kuwa indai har banji tsoro fitowa ba. Ya jinjin mata hannu ya zama haske ya bace ita kuma ta ganta tsaye gefen randarsu sai kawai ta d'auki buta ta shige bayan gida abinda hankakinta kwance kuma bako tsoron komi dataji na ganinta tsaye alhalin tasan itad'in a zaune take awurin bishiya. Tana arollah tana qudurtawa aranta lallai anjima kuwa zata tambayeshi dalilin dayasa take gaininta awuri batare da itace tayi tafiya takawo kanta wurinba. Bayan sallame sallarsu sai kowa yatashi ya gabatar da shafa'i da wutri sanna suka zauna cin abincin dare cike da nishad'i. Addawiyya kam kad'an taci tuwon ta tsame hannunta taje ta wanke ta dawo ta zauna gefen Hindu tare da leqa agogon dake d'aure a tsintsiyar hannun ta sai kuma taja tsaki tana cewa "kai haba wannan wani irin barci ne yazomin da farkon dare haka, duka2 fa qarfe tara saura kwata ne yanzu amma don tsiya jibeni dakyat nake bud'e idanuna kamar wacce tasha maganin barci. "To Addawiy tafi kije ki kwanta man. "aikam yazamamin dole kuwa aunty. Tayi sallama dasu ta tafi zuwa bukkansu ta fad'a masar katifansu tana ta sakin hamma, cikin 'yan seconds barci ya d'auketa. *mrs j moon* [12/29/2017, 3:00 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUK ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *Wannan shafin na duk wata mai suna RABI'ATUL ADDAWIYYA ce, gashi nan kyauta nabaku domin jin dad'inku sannan kuma kuyi alfahari da sunar sabida sunane mai matuk'ar daraja. Inasonku a ruhina takwarorin Addawiyya*❤. *23 ~ 14* Miqa tayi tana hamma ta dubi gefenta ta hango wani kujera fari ta roba ta jawo ta zauna qasan bishiyar gwiba tana ta waige2 zuwa can tajiyo qamshinsa ta miqe cike da zumud'i har zata kamo hannunshi sai kuma ta nok'e tana kallonshi fuskanta d'auke da murmushi. "Mai babban suna kenan bakyason jin sanyin jina ko? "Eh wallahi uncle kuma kagama hakan baida kyau a addinin islama "hakene kam, yarinya k'arama da sanin yakamata, lallai kinkerewa Adda nki Salma ta ko ina. "Yawwa uncle wai da gaske ne yaya mushaffa'u yana latsa mata jiki? "Tabbas gaskiya ne amma ita d'in bata son haka hasalima tsoronshi takeji sabida har yanzu takasa manta wuyar da mariyan yarannan suka bata. "To amma miyasa bazata hanashi ba? "Shammatanta yakeyi kuma koshi iyakar ita yake tabawa sabida yana da k"yank'yami sosai kuma yana da yana da tsoron Allah illa iyaka yana son kasancewa da ita ne ainunn kuma yana cikin jinsi masu qarfin buk'atuwa. "Miye shi buk'atuwan uncle? Wani kallo yabita dashi sai kuma ya kauda maganar yace "Mai babban suna gyara zama insoma yi miki bayanin wacce keyi miki tsaki da kuma magen datake sanja miki launi a cikin barcinki da farken ki. "Tam ina jinka mai kyau. "Murmushi yayi yace "kinfini komi ai mai babban suna "nikam banyarda ba "uhmm kedai bari kiji "sanda na cetoki daga zalinci 'yan uwana junnu sai na ajiyeki afilin da kikasha ruwa kika kwanta sai nakuma cetonki a hannun micijiya nan sai na d'aukeki nakaiki gidana dake k'asan teku to sanda na kaiki lokacin shiga halwata yayi sai nacewa qanwata da ta kulamin dake to shine fa take tajin haushi wai nakawo musu bi'adama cikin yanki gashinan kindameta da kukan shagwaba sabida ita ta tsani hayaniya balle sautin kuka shi yasa baruwanta da yawo ballantana ta had'u da bil'adama iyayen gajen hak'uri da hayaniya,, cewarta fa amma. Sai ita kuma magen ta kasance matar dazan aura ce. Da sauri Addawiyya ta katseshi tana zare idanu tace "magen!!? "Eh da ita aka had'amu amma ita ba mage bace ta dai koma mage ne don ra'ayinta in kuma taso sai ta dawo irin jinsinmu. "Taf d'ijan, uncle lamarinku yana da ban mamaki gaskiya. Dariya yayi yacigaba "takan biki cikin barcinki don ta tsorataki kuma ta kan fito miki azahiri sannan itace ke gilgilma miki duk domin ta tsorataki wai ita tana kishi da ke ne sai ni kuma na fidda miki jin tsoron komi aranki. "K'uri tayi mishi tana aikin kallonshi, hura mata iskan bakinshi yayi a fuska taja numfashi ta lumshe idanunta ta bud'esu tace "uncle amma matan nan taka so kuwa ce, ta k'arshe, to ta yaya zata soma kishi dani ni ba matarka ba. "Mai babban suna kenan, yanzu dai kinji wad'anda kika zauna tare dasu. "Eh naji su amma baka fad'amim sunayensu ba "ita mai yi miki tsaki sunarta khadija, budurwata kuwa sunarta mabaruka. "Kai kuma sunarka wane? "Habibullah (masoyin Allah) "amma kam yana da dad'i sunar. "Ni kuma nafi jin dad'in naki sunar sabida k'arfin imanin mai sunar taki da kuma jajircewan ta. "Yawwa uncle bani labarin nata dakacemin zaka bani. 'Daga kanshi yayi ya kalli sama itama ta tabi inda yake kallon sai kawai taga wasu abubuwa masu girma kamar mutane gasu da fuka fukai suna ta shawagi kamar tsuntsaye. 'Dan matsawa kusa dashi tayi tace "uncle miye su? "Halittun Allah suke harkan gabansu kamar yarda mukeyi ni da ke. Sai taga ya bud'e yatsunsa biyu ya nuna samar atake suka bace ya dawo da dubanshi gareta, ta matso zatayi magana ya d'aga mata hannu yace "mai babban suna kinfiye sonjin k'wam, amma nasan abinda zan miki kibari "bata rai tayi tace "nidai ina jinka bani insha. "Kad'an zan fad'a miki k'arfin imaninta "tam inaji. "Ita d'in mace ce mai tsoron Allah tare da son ma'aikinsa sosai kum har cikin ruhinta son nasu ya nashe domin wata rana tana tafiya sai ta taradda da wani bawan Allah yana kiran sallah, bayan ya idar da kiran sallan sai tace da mutanen wuri wannan mutumin bai kira sallan nan domin Allah ba, sabida in yakira domin Allah to wancan dandamalin da yahau yayi kiran bazai d'aukeshi ba. Sai mutanen wurin suka cika da mamaki maganarta ganin haka sai tace bari kugani ni inkira kuga ikon Allah aikam sai ta tafi zuwa dandamalin ta hau tasoma kiran salla batako idar da kiran sallan ba dandamalin ya watsar da ita gefe duk ta ji rauni ta miqe tace dasu kungani ko, jinjina mata sukayi suna mai cike da mamakin lamarin. Haka nan wata rana tana sallah mak'iya Allah da mazonsa suka zuba mata micizai da kunamu sukayi ta cizonta suna harbinta amma ko gezau batayiba bama tasan anayiba sabida zuciyarta gabaki d'aya yanaga Allah ne, sahi kad'ai takeji dani lokacin don haka dakansu suka kwashe kayansu suka barta tana cigaba da ibadarta. Tace badan aure sunar mai k'arfi bane to dabaza tayi aure ba domin bata da lokacin kula da miji sabida yawan ibadarta amma hakanan tayi aure domin ANNABIN ALLAH yayi alfahari da ita ranar sakamako. Magabata na kwarai sunyi ittifa'k'i cewa da ace Allah SWA zai bawa mace Annabta to da Rabi'atul Addawiyya zata zamo daga cikinsu. Kinji tak'aitacce tsoron Allah n mai sunarki. "Allahu Akbar kabiran, lallai inada suna mai girma da matsayi, Allah nagode maka, Allah yabamu danshin Sayyada Rabi'atul Addawiyya. "Amin ya rabbi mai babban suna. "Nazamo tare dake ne domin k'aunar danakema mai sunarki kuma sunar kakata ce wacce ta haifi maihaifina. "Ikon Allah, uncle to kai waya baka wannan tarihin? "Kakana na biyar shine yabani domin yayi zamani da ita lokacin "Dafe qirji tayi zata kuma tambayarshi ya katseta da cewa "kinason sanin yarda akeyi kike samun kanki a wuri batare da kinyi tafiba ko? "Eh inason sani "to ilmine wanda Allah yahore mana mu junnu kuma ko da nabud'e miki tunanki bazai iya da'auka ba don haka kibarshi asirrinmu ne kawai. "Tam uncle, amma wata rana inajin maganarka akunnina kuma kana fad'amin abinda zai faru kafin ya afku, to ya akayi kasani "shima sirrine, sai dai in kuma kina son komawa cikinmu sai in fad'a miki. Wani zabura tayi tajita tim tafad'o asamar katifan da ta kwanta. Ta tashi zaune tayi tana matsa hannunta data bige sai kuma tasoma tunano maganganun da sukayi da unlce d'inta, dasuri tamik'e tana kallon agogon dake rataye awani k'usa taga 5:00am. ta duba gefenta ta hango Hindu tana ta sharan barcinta ta kuma duba inda Salma take taganta kwance duk ta mamaye wurin ta turota bakin katifan aikam ta zabura zata doketa. "Kul mai babban suna, ba kyau tashin barci da duka, ware idanunta yayi tace "uncle. "Fito ki arollah kiyi sallah nima masallacin makka yanzu zani, yin sallah. Da qarfi ta ambaci "Makka!! Sai jitayi an hura mata iska ta tafi luuu. Koda ta farka sai ganin su Abbi tayi zaune sunyi jigun jigun sun sata atsakiya, suna gani ta miqe suka soma yi mata sannu ita kam mamaki ne ya cikata tace "waye baida lafiya? "Kece auta, kin suma tun subahi sai yanzu da hantsi kika farfad'o. Jikinta tabi da kallo taganshi duk ya jiqe d ruwa almun tasha kwara ruwa kenan. sai tasoma tunanin mi ya sumar da ita kuma? Ganin tagaza samo amsa sai tamiqe tayo tsarki tayi arollah tagabatar da sallah safe. Nata nan zaune ummi ta kawo mata abinci ta ci sosai tasha ruwa tayi hamdalah ga Allah sannan ta miqe tafice zuwa wurin su Salma. *Mrs j moon* [12/29/2017, 3:00 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. Affuwan sisters ansami matsala a last page inda amaimakon 13~14 sai nasa 23~14. Dafatan za'ayimin kuziri. *Ina kike mum Abdul (Bahijja, bebeelo) Wannan page naki ne domin jin dad'inki kuma Addawiyya tace tana gaisheki sosai tana sonki da qawa😝. Lallai kisani Kina zaune daram a cikin ruhina ainun*😍😘 *15 ~16* Tana isa inda suke zaune suna ta hiransu cike da nishad'i sai ta zauna kusa da Hindu ta dubi Salma ta tabe baki ta amida hankalinta wurin mushaffa'u tace "yaya bani tarihin mai sunana inka sani inji. "Amfaninmi tarihin zai miki? "Kai dai in kasani kabani insha kawai "nasani amma na manta sabida tun ina islamiyya aji uku wani yaro yayi tambaya sai aka fad'ama a tare. "Uhmm to Allah yayima sauqi "Amin dai kam, hindu ta amsa tana hararan mushaffa'u. Sosa kansa yayi ya ja tsinin hancinshi yace "to aunty da inyi mata karya ai gara in fad'amata gaskiya ta. "To fad'amin miye buk'atuwa? "Tofa yau Rabi'a da tambayoyi kika farka kenan. "Nidai amsamin tambayata kawai. "bazai amsaba 'yar rainin wayau, kintafi can wurin rawar maitanki kindawo zaki damemu da fi'ili. "Adda nice mayuwan? Ta fad'a haka idanunta cike da kwalla "Eh kefa, sabida da k'arara d'abi'unkin yanuna irin ta mayune. "Aunty kinajinta tana son laqamin alkaba'i ko? "Salma banson wasan banzan nan, kinko san illar maita kuwa? To Allah naqarajin kinkirata da hakan sai na saba miki. "Tam aunty bazan qaraba "hakan shi yafi kam. Addawiyya ta watsawa Salma harara tace kinjama kanki yau kamar na tona asirin da ke boye,;kuma kinfi kowa sanin hukuncin da Ummi zatayi miki, ciki ma harda hanaki ko... "dalla!! banza kawai wacce bata da sirri sam, bata san rufamawa d'an uwa asiri ba, Salma ce takatseta cikin hargagi. Dariya Addawiyya tasa tana cewa "zakiyi bayani ne in Ummi tasa kaki aloko. Fuuuu Salma ta tashi tabar wurin, tana cewa "wallahi kika fidda zancen nan fili Allah na lahira sai yafiki jin dad'i. mushaffa'u yabi bayanta yana kiranta amma taqi tsayawa. Ita kam Addawiyya sai dariya take kyal kyalawa, hindu ta dubeta tace "wani sirri zaki tona na Salma? "Aunty share kawai walata nakeyi sabida tacemin mayya amma babu wani sirri. Jan kunninta hindu tayi tace "Autan ummu baki jin magana ko? "Washh aunty wallahi inaji magana sosai, kawai Adda ce tafiye jata da fad'a, shine nikuma nake tsikananta. sakin mata kunninta tayi ta janyo kwaryan damammiyar fura dake gefe tasoma sha. Gyara zama Addawiyya tayi tace "aunty mijinki fa yana nan bisa hanya yau zaizo neman qarin bayani akan cikin jikinki amma inaga sai gobe da hantsi zai iso nan inyasami kabarin kuna nan garin, kuma gashi naga alamar baki d'auke da komi. Tarine yasark'e Hindu tayi tayi har saida ta amayo furan data sha. Sai sannu Addawiyya keta jera mata, ita kam sai gyad'a kai takeyi tana cigaba da kwaro amai. Bayan tagama Addawiyya ta d'ibo mata ruwa ta wanke bakinta da fuskanta, ita kuma ta zuba qasa ta rufe aman. Jan hannunta hindu tayi suka fita zuwa wani wurin wata bishiya dake nesa da bukkansu. Zama sukayi a manyan jijiyojin bishiyar, Hindu ta kama hannun Addawiyya ta runtse tace "waya sanar da ke Adnan zaizo yau? Shirub Addawiyya tayi kamar ba ita ake tambaya ba. "Autan Ummi kefa nake sauraro. "Aunty jiyane nayi mufarki zaizo yau kuma nasan tabbas zaizo sabida wata rana mufrkina yana zama gaskiya. K'uri hindu tayi mata d idanu zuwa can taja nufashi tace "nafahinceki amma hak'iqanin gaskiya autan Ummi lamarinki yasoma bani tsoro. "Kidainaji tsoro komi aunty baiwace kowa da irin nashi "haka ne kam. "Autan ummi amma fa inaji ajikina inyazo da matsala. "Eh wallahi aunty ba mutunci zaizo kuma yasan kina da cikinsa d'an wata d'aya koda kuka rabu, yanzu kuma yana tunanin ya kai watani biyar kenan. "Ya ilahil alamina!! Ni hindu yazanyi? "Aunty ki tubure mishi ke bakida komi tunda ko su mama basu san kin zubda cikin ba. Idanu waje Hindu take duban Addawiyya, cikin rawar baki tace "autan Ummi wai wayake fad'a miki sirri mutane ne? Abarcina naganki tun sanda kika aikata abin domin ma har kwanciya kikayi a asibiti na kwanaki biyu, to nad'auka shirmen mufarki ne, sai yanzu nagano da gaskene don naga adnan din yana ta kuri sai kindawo gareshi kodon abinda zaki haifa amma fa bata lalama zaibi ba ta tsiya da tijara wai ganinshi kece kika cuceshi da kika gudu da aurenshi kika kumayi biris da lamarin shi. Ahankali Hindu tace "autan Ummi baki da wayon dazan fad'a miki abinda yasa na guji zama da Adnan amma inamai tabbatar miki shine ya zalunceni yayimin qarya alhalin shid'in mara asaline wanda bawanda yasan inda iyayenshi suke kuma rayuwarshi gaba d'aya sabon Allah ne. "Aunty rabuwarku shine mafita kuma gara da kika zubda cikin domin had'a zuri'a da irinshi hatsari ne, kuma yanxu koda yazo ki rufe idannu kici masa qaniya ta haka zaiji shakkan sake tunqaranki kuma atake zai baki takardanki ki huta da shegen aurenshi. Cike da mamakin basiran yarinyar Hindu tace "autan ummi wai shekarunki nawa yanzu? "Goma sha hud'u da watanni. "Ok, amma fa kina da azancin iya magana gashi wayonki ya girmi shekarunki. Kwantar da kanta tayi a cinyar Hindu tace "haka mutane ke fad'i, hatta Abbi yafiso yayi shawara dani fiye da Adda Salma. "Aikam Salma sokuwa ne ba wayau sai uban iya fushi, abu ba abu ba tayi ta hawa kamar garin kwaki. Dariya Addawiyya tasa tana cewa "kuma kinsan fa abincin Adda ne kwaki, sosai take son shanshi dayin qosanshi. "Nima na shaida hakan, tunda gashinan mushaffa'u yakoyi cin qosan, kamar wasu dikkawa. Dariya sosai sukayi sannan suka cigaba da hiransu amma lokaci2 Addawiyya sai duba gefen damarta ta gyad'a dai, ita kam hindu batama san tanayi ba. Washe gari suna shirin tafiya motar Adnan ta iso bakin bukkan su Addawiyya, baiko gyara parking ba ya kashe motar ya fito yasoma tsula rashin mutuncimshi. Duk tsayawa sukayi cirko2 suna kallonshi cike da ta'ajibin dalilin faruwan hakan alhalin sune suke jiranshi dayazo yayi musu bayanin abinda kefaruwa tunda ita Hindu taqi cewa komi duk tsawon lakacin da ta kwashe zaune agida. Zuwa can mushaffa'u ya shammaceshi ya d'agashi sama ya soka da k'asa yayi ta bugu. Mutanen qauyen suka sami abin kallo, saida yahad'a mishi jini da majina sannan Abbi yayi nasaran rabasu. Atake Adnan ya rubuta takardan saki ya cillawa Hindu ta d'auka ta shige ciki tana kuka. Abbi ya matsa domin yabashi haquri ya tureshi kad'an yarage bai fad'i ba. Mushaffa'u ya zabura zai kuma dukanshi mama ta riqeshi tace "wandama kayi mishi ya isa, barshi ya wuce duniya ce. Afusace yaja motarshi ya wuce, bakinsa tare da hancinshi zai zuban jini yakeyi sannan aqasan zuciyarshi kuma tunanin abinda zaiyiwa mushaffa'u yakeyi. Aciki kuwa Hindu kuka take tayi kamar ranta zai fita. Addawiyya dake zaune gefenta ta soma share mata hawaye tana cewa "kyaleshi aunty kansa yayi mawa kuma yanzu haka yana tace da masifa tunda garin yawon banzanshi yaje ya kwaso k'anjamau. "Nashiga uku, yasamin kenan yanzu? "A'a aunty ke bakya tare da cutar komi domin sanda ya aureki lafiyarshi lau, bayan kin barshine ya kwaso abinsa. Shiru hindu tayi tana mai cike da mamakin lamarin Addawiyya, yarinya kamar goyon aljannu. Dariya Addawiyya tasaki tace "nikam wallahi goyon bin'dama ne. Idanu waje Hindu tace "nashiga uku, ko dai maganar Salma zai tabbane da tace ked'in rabinki mutum ne rabinki junnu. "Au wai sai yau kika fahimci Addwiy tana da matsala aunty? Cikin tsiwa ta tari gaba Salma tace "waya kasa dake? "Yanzu zan zubarmiki da haqora wallahi, kindai sanni sarai bana d'aukan rainin wayonki. "Eh na sanki kam, amma a fannin kare martabanki baki iya tsinana komi sai tura baki kina wani cewa "banso2 kamar wata sakarya. Afusace tayo kanta tayi saurin maqalewa a bayan Hindu tana yimata kwalo. Ficewa Salma tayi tana cewa "mai rabani da yarinya yau sai wanda yabusan numfashi. "Kedai tafi wurin mijinki, kud'ora daga inda kuka tsaya jiya. Afusace Salma ta dawo ta fizgota abayan Hindu tayi d'akinsu da ita, hindu tabiyo bayansu Salma ta kulle qofan. Daga ciki Addawiyya tace "yi tafiyanki aunty na isheta riga da wando domin ba'abin da zata iyayimin duk tarin burgane. Hindu dai dariya tayi tabar qofan ta nufi inda su Abbi suke zaune. Inda sukayi ta bata baki tare dayimata tuni akan yarda da k'addara. Sai bayan la'asar suka sami tafiya wanda har da Addawiyya suka wuto sabida takafe ita sai ta koma makaranta aranar, sabida an wuceta sosai akaratu. Ita suka fara saukewa a school tana ta kuka dakyat suka shawo kanta tayi shiru sanna suka k'arasa cikin gari. Washe garim ranar Salma da Mushaffa'u ne zaune cikin garden suna hiransu ta masoya. Ya rungumeta a jikinshi yana lalibenta, kamar yarda yasaba. Cikin fushi ta kwace jikinta tasoma magana "wallahi yaya bana sin abinda kakemin ko don kasanni d'in ba virgin bace shiyasa kakemin haka? "Honey mi yakawo wannan maganar kuma? Nifa ke nakeao da k'auna ba jikinki ba. "To indai kayarda da haka kabar tabani har sai shedu sun shaida na zama mallakinka, in kuma kacigaba damin haka zan fasa auren muhaqura da junaid. "Nabari honey wallahi, inkuma kinga naqara kimin duk hukuncin da kikaso. Murmushi tayi tana mai jinninawa qanwarta Addawiyya databa wannan shawaran. Haka ko yafaru domin tsawon kwanakin da suka biyo baya ya kame gabbanshi daga lata mata jikinki saima yasoma azumi donmin samun kariya daga afkawa cikin sha'awar datake yawan taso mishi wanda bai samun sauqi har sai ya kai hannunsa jikinta,sannan ya qagara su Abbi su iso ko atsaida lokacin bikinsu ya Hutu. Ita kam Salma hakan yayi Mata mugun dad'i tunda gashi har yamaida hankali da bautan ubangijinsa ta hanyar yin azumin nafila. Sai takuma qara jinjiwa Addawiyya da kuma godemata sabida ita ce sanadin tsamosu ga fad'ama sabon Allah SWA. **** Bayan sati biyu su Abbi sukayo parking din kayansu sukayi ban kwana da mutanen garin jangaba suka nufo kwantagora amma kafi su isa sai suntsaya a makarantar su Addawiyya sun d'auketa domin ason ran Abbi kwana 1 zasuyi agarin su d'uki hanyar birnin kano don tuni ansama musu gidan dazasu zauna. *TUNA BAYA* (Nasabarsu) *mrs j moon* [12/29/2017, 3:00 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *Ina kuke 'yan mata Adon gari, ga page d'inku nabaku shi kyauta.* *Maryam Rano* *Maryam Kaumi* *Ummiey Ahmad* *Fatima kaka malam* *Khady kd (my inlaw)* *Aisha gombe* *Pretty (meena)* *Exclusive (zainab)* Allah ya kaimu lokacin bikinku musha bidiri bired'e Ameen👏🏻😊 *17~18* Malam Yusuf shine cikakken sunar Abbi? Haifaffen garin jangaba ne, mahaifiyanshi tare da k'anninshi uku biyu maza d'aya mace wutane ta yi ajalinsu lokacin shi yana can cikin garken shanu yana gad'insu, wutan ta tashi kokafin akawo agaji wutar ta lashesu sanadin haka mahaifinshi yakamu da ciwon zuciya shima bai jimaba yace ga garinku nan sakamakon haka sai yataso maraya. ga dukiya ubanshi yabari sosai amma 'yan uwanshi sukace nasune yake yi musu kiwo kuma bawanda ya musanta hakan a garin sabida haka suka k'wace komi su bar mishi wata tsohuwar saniya wai ladan kiwon da yariqa yi yayi kuka har yagode Allah kawunshi yayan mahaifiyarshi daya rage mishi shine yayi tabashi baki ya nuna mishi wuta sukaci kuma da yardan Allah bazai amfanesu ba. Haka nan yacigaba da rayuwanshi a gidan kawunshi ya kuma jefa karsanan shi cikin garken kawun duk da suma basu da yawa domin basufi bakwai ba. Bayan shera saiga sanuwa ta haifi 'yan maruk'qa biyu suna isa yaye suka saida uwar suka bar 'ya'yan sabida ta tsufa. suka sayo wasu mata biyu suma shekara na kewayowa suka haihu 'yan bibiyu. abufa yayi albarka sai gashi a cikin shekaru uku shanun yusufa suntasarma kusan ashirin banda tumaki da raguna ga kaji tare da zabbi. Ganin haka sai yacewa kawunshi zai shiga duniya neman ilimi sabida ilimi Addin yayi qaranci sosai ayankinsu, bai hanashi ba saima addu'a daya bishi dashi. Ya soma isa garin kwantagora a inda yahad'u da wani matashi mai suna Abubakar ya taimakeshi ganin yana tare da k'auyenci, ya kaishi gidansu ya kwana washe gari ya kaishi tasha ya sashi amotar garin Zaria birnin ilimi sabida yasanar mishi cewa ilimin addini yafito nema shine yaga ba inda zai samu mai nagarta irin birnin zazzau. Ya iso garin zaria daf da la'asariyya, ranar ya nemi gidan shehin malamin dazai soma karatu, wani mutum yayi mishi jagora zuwa gidan lamamin mai suna Alhaji malam Haruna mai riguna. yanemi iso atake kuma akayi maraba dashi domin gidane na karamci da nagarta, kowa nasune domin irin adalcin mai gidan, yasa ake karrama bak'o kodaga ina yazo sabida yakance shima ai zuwa yayi gashi har yazama wani abin wanda har ake zuwa wurinshi. Anan yusufa yasamu karatun AL-QUR'ANI dawasu littafai na addina sai yakoma gida amma akwantagora ya sauka. Abokin shi Abubakar yayi ta mamakin ilimin da yasamo. Washe gari yayi misu bankwana ya nufo qauyensu kafin ya shiga mota yaji wani yana bawa abokinshi labarin ya kosa yakoma kano yacigaba da sa'arshi. Sai yayi tsam da ranshi atake kuma yaji bazai koma garinsu baida komi ahannumshi ba sai kawai yanufi wurin saurayin nan yayi masa sallama ya fad'a mishi intafiya zaiyi to zai bishi, atake saurayin mai suna gambo ya amince suka shiga motan kano. Ya shigo garin kano da qafar dama sabida a shera 1 yasami alkhairi mai tarin yawa, fad'i yake lallai tacika tumbin giwa. Sai ya shirya yayiwa abokinshi Gambo bankwana ya nufo gida. Koda kawu ya ganshi bai ganeshi ba sabida yazama magidanci sosai mai tarin natsuwa daka ganshi kaga cikakken mai ilimi, gashi dama farine sai farin yakuma qaruwa. Shikuma yayi mamakin irin shanun da kawu yanuna mishi yake nashine domin sunkai garke biyu banda tumakai da kaji tare da zabbi ga kuma kud'in kwan zabbin da yake saidawa insumyi sai ya ajiye mishi, ya tara mishi kud'I masu yawa. Take yaraba komi biyu yabawa kawu kyauta, dakyar kawun ya amsa, saida yayi tayi mishi magiya. Dangin mahaifinshi hankakinsu yatashi dasuka ganshi da wannan dukiya sabida nasu dasukaci zalin duk sun kare basu ka komi sai wahala, sai suka nemi da ya auri y'a'yansu yanuna shi baitashi yin aure yanzu ba. Ya rushe kangon gidansu yayi sabbin bukkoki guda biyar kuma manya. Yacigaba da zamanshi aciki shi kad'ai wata rana kuma ya leqa wurin kawunshi, ahaka yasoma koyar da yaran garin ilimin addini kuma ba laifi suna ganewa sai dai yaran makwaftansu sunfi zuwa akan na yankinsu. Bikin abokinshi Abubakar ne yatashi ya kuma zo har dajinsu ya gaiyaceshi shikuma ya shirya yatafi bikin tun ana saura sati 1, komi dashi akayi sabida sosai ya waye ya kuma iya karatun hausan boko da yakoya tun kafin yayi saukan qur'ani. Bayan angama biki ya komo garinsu yacigana da hidimomin shi. Watanni biyar baya abokinshi Abubakar yazo misho da zancen qanwarshi zuwairat taface sai shi domin wai tunda taganshi a bikin dayazo takamu da dasonshi. Bai watsawa abokinsa k'asa a ido atake ba ya amince da soyayyar qanwar tashi sabida shima tun a lokacin yakamu da sonta amma ya boye abinne sabida yaga tana birni bazata dawo qauye ba. Ba'adauki lokaciba akasha biki aka kawota gidan mijinta. Rayuwa suka gudamar mai kyau da tsari ga kuma so da qaunar juna da yayi musu jagora. Sai da ta kwashe shekaru shida sannan ta haifi danta na miji amma kwanarshi biyu ya koma. Ta kuma haihuwar wani d'an shima ya koma aqalla saida ta haifi 'ya'ya hudu dukannsu maza suna rasuwa sai da kyat Salma ta tsaya kuma sai bayan shekaru biyar da wata biyu sannan ta kuma haihuwar Rabi'atul Addawiyya. Tunda aka haifi Addawiyya arzikin Abbi yaketa qara habbaka fiye da da, har ya kaima yana da shago a cikin gari na saida kayan masa rufi ya danqawa abokinshi gambo amana kuma yariqe amana domin sosai riba yake samuwa a cikin lamarin. Sosai yake fatantawa iyalinshi bai gagyesu da komi ba komi sukesu yanayi musu baima bari sunema zai kawo musu. Abubakar matarshi Ramlat 'yar kano ce shima biki yaje kano suka had'u har sukayi aure. Ta haifa mishi 'ya mace mai suna Hindatu sai mushaffa'u ke bi mata amma da shekaru tsakaninsu da juna bayanshi ta haifi Aliyu da mudansir. Tun salma tan 'yar shekaru hud'u Abbi yake d'aukanta akeke ya kaita gari makarantar boko sabida ya qudiri aniyar yaranshi sai sunyi karatun zamani. Sanda yasoma kai salma makaranta garinsu ya d'auka wai zai maida yaranshi karuwai, musanma d'angin mahaifinshi dama sun tsani matarshi wai itama karuwa ce dukdon tazama y'ar boko kuma 'yar birni gashi kuma tana adawa da al'adarsu ta yawon gudun amare ta kance jahilcine wannan abin. Duk sukan dasuke ta kawowa Abbi akan boko baikoji d'arba tunda yasami goyon baya a wurin kawunshi. Sanda Salma ta gama primary lokacin aka saka Addawiyya kuma a shekaran kawunshi ya koma ga mahaliccinshi, gashi kuma dama baya d'a bare jiki sai mata hud'u yabari. Sosai Abbi yaji mutuwarshi, bayan gama zaman makoki aka raba gado aka bawa Abbi nashi sabida shikad'ai yaragewa mamacin d'an 'yar uwanshi ciki d'aya, ya amsa tare da maidawa matan kawum nashi kyauta yace suqara,, Allah yajiqan kawu mamman yabashi aljanna mad'aukakiya, suka amsa Amin. To tun a lokacin Abbi yaso barin yankin amma sai ummi tace a'a ya barzancen kawai kowa ai da mahaifanshi yake tunqaho. Ahaka rayuwa tayi ta tafiya har Salma tagama makaranta hajiya Ramlat ta d'auketa takoma da ita wurinta da zama, wai bazatayi aure a qauye ba, sudai su Abbi nasu idanu kawai suka zuba. A lokacin kuma Addawiyya ta soma karatuta a boarding school ake garin zuru. K'addaran dayasami Salma yafarune awani xiyara data kawowa mahaifanta ta cinma ana bikin qawarta tako bisu yawon gudu anan hisk'ilu tare da abokanshi suka yagamata martaba cike da rashin tausayi. Sanda aka dawo da ita gida baqaramim tashin hankali su Abbi suka shigaba. Hajiya Ramlat data zo tace sai tayi qaran yaran tare da iyayensu amma Abbi ya hana dole ta haqura ta d'auketa suka tafi akayi treatment d'inta sosai sabida raunin datasamu. To tundaga lokacin su ummi ke taka tsantsan da Addawiyya amma duk da haka saida azal ya kusa afka mata, Allah ya kareta da fad'awa ciki. Mushaffa'u yasoma son Salma ne tun kafin qaddarar ya afkamata kuma yacigaba da sonta ahaka sabida yace bayin kanta bane qaddaran Allah ne bawanda ya isa ya hanashi afkuwa. Iyayensu sosai sukayi tasa mishi albarka akan jarumtar da yanuna tare da taimakon jininshi da yayi. Hindu kuwa bayan ta kammala karatunta na degree a jami'a minna sai tayi aure da abokin karatunta Adnan suka tare a cikin minna amma zamansu na jin dad'I na sati uku ne katsal yasoma bullo mata da iskanci kala2 inda anan tagane iyayen qarya yayi amafani dashi suka zo amsar mishi aurenta, domin shi d'in baya da cikakken asali karatunma da yayi a jami'a wata magajiyan karuwaine ta d'auki nauyinshi. Zaman lafiya yayi qaranci a tsaninsu don haka tunda tagane tana da shigar ciki d'an wata 1 sai ta gudu wani asibitin kud'i suka mata allura na zubewan ciki lokacin watansu hud'u da aure. Takosha wuya sosai domin saida ta kwanta na kwana biyu a asibitin, kuma duk mijinta bai saniba sabida ya lula wani ajon karuwai a garin kaduna. Aranar da aka sallameta ranar tabar garin minna zuwa kwantagora kuma taqi fad'an dalilin zuwan nata sam. Har zuwa sanda minjn nata yazo yayi rashin mutuncinsa, mushaffa'u yagyamishi zama. Yanzu Salma ta kusa kammala school of nursing yayin da ita kuma Addawiyya take ss1. *Continuation* *mrs j moon* [12/31/2017, 10:22 AM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *Alhamdulillahi ala kulli halin* *inamai baku hak'uri masoya labarin ADDAWIYYA najina shiru da kukayi na tsawon wasu kwanaki hakan ya farune abisa wani matsa dana fuskanta kuma yanzu komi ya daidaita don haka zaku riqa jina kullum insha Allahu. sannan ina miqa sak'on godiata mara adadi agareku wad'anda suka kirani domin jajantamin dama wa d'an da suka qudurta zasu kirani amma Allah bai lamunce musuba, da dukkanin masu bin labarin RABI'ATUL ADDAWIYYA nagode nagode nagode ainun Allah yabar zumunci Amin,, kusani I'm astonishment with you Sosai wallahi, luv u so much fans* ❤😘 *19~20* Lamo tayi jikin ummi idanunta rufe hannunta dafe da gefen cikin, kallo d'aya zakayi mata kagano she is not in good mood. yayin da agefe kuma qawayenta ne Asiya tare da Alawiyya suke ta hidimar samata kayanta abayan boot. Ummi ta shafi face d'in cike da kulawa tace "autana bakya da lafiya ne? Kai ta motsa kad'an sannan ta tashi zaune tana cije labba ta dubi ummi tace "inajin kewan school ne tare da qawayena sai kuma tasoma share hawaye suma qawayen nata dasuke zaune kusa da ita hawayen sum sharewa, ummi ta soma rarrashinsu cike da tausayi domin sosai tasan zafin rabuwa da abokanan arziki suna haka wata budurwa ta qaraso wurin ta russuna ta gaida ummi, ummi ta amsa cike da fara'a tace "Abida ya karatu? Ankusa gamawa ko? "Eh mama, nan da watanni uku zamuyi candy mu kuma jira sakamako kafin mu d'ora da wani "to Allah ya nuna mata lokacin lafiya ya kuma bada nasara"Amin Amin mama. Abida ta dubi inda Addawiyya take tare da miqa hannu ta shafi kanta tana mai cewa "haka akeyi ko daughter? Addawiyya ta soke kanta tana murmushi, d'ago mata da kanta tayi tayi tana mai sauke dubanta akan dubi ummi tace "mama abinda Rabi'a tayimin ta kyauta kenan? "Uhmm duk da bansan abinda tayi ba amma ina neman mata affuwa 'yata. Cike dajin kunya Abida ta amsa "ya wuce mama "to madallah Allah yayi muku Albarka, "Amin suka amsa su dukkansu. "Mama aramin ita kafin Abba yagama da principal "to gata nan 'yar mama, dariya tayi tare da jan hannun Addawiyya suka nufi wata bishiya dake nesa da mutane, qawayenta su Asiya suka rufa musu baya. Hango Abbie dasukayi tafe yasa suka taso jikinsu duk a sanyaye, Sakamakon jin labarin da Addawiyya ta basu. Suna tsaye har saida sukaga bacewan motar su ummi sannan suka bar wurin cike da hawaye na kewan rabuwa da Addawiyya, agefe 1 kuma malaman makarantar da wasu cikin d'aliban suma jimamin tafiyar Addawiyya sukeyi suma domin ita d'in mai kyawun mu'amallane da kowa ga tarin azanci tare da kaifin basira, da kuma kwarjini, koya kazauna da ita sai kaji ta shiga ranka. Asiya ce ta dubi Alawiyya fuska cike da hawaye tace "wallahi muna gama exam akayi hutu bazan dawoba day zan koma, alawiyya ta amshe "nima haka 'yar uwa bazan dawoba dama mami bata son boarding d'inan nice na nace sai nazo. "Yanxu haka zakuyimin? Duk kugudu kubarni da kewarku? Abida tace dasu cikin laushin murya. Alawiyya tace da ita "Mommy Abida ba haka bane dole ce ta samu zamu bar school d'in duk kuwa da son da muke mata, dama gatanmu Allah kuma Addawiyya ce idanunmu sabida tun muna js 1 take kula damu domin duk abinda zai cutar damu zata fad'amana kada muje wurin sannan ita d'in haskenmu ce gashi ta tafi tabarmu don haka agaskiya bama mu iya zama bama ganinta ba "tabbas hake sis bazamu iya jure rashinta ba a school d'innan sannan kuma ga wannan masifar datake tashe yanzu ta mafiya, kawai atsotse mawa mutum jini abanza da wofi, kai ni gobema zan bar school d'innan domin mufarkin Addawiyya yana bani tsoro sabida yakan zama gaskiya. Shiru Abida tayi tana sauraren yaran, kuma tagaza tofa ko kalma 1 cikin zancen dasuke mata illama wani mugun sanyi da jikinta yayi, lallai da alamun zancen daughter zai zama gaskiya sabida najima ina zargin shakira tana cikin qunqiyan matsafa. Azuciyanta take zancen zuwa can taja numfashi ta dubi yaran tace "a'a Alawiyya kidai bari zuwa ayi hutu tunda kinga kun soma text sai in kun tafi kuyi zamanku domin nima nasoma tsorata da lamarin na yarda ake mutuwa akai akai a makarantar bakuma ga d'abibai kad'aiba harda wasu cikin malaman musanman 'yan bautan qasama"tam mommy Allah ya kaimu yakuma qara tsaremu da sharrin dukkanin wabi abu mai cutarwa ta amsa "Amin. Sannan ta jasu suka nufi masallaci don gabatar da sallar azuhur. **** Addawiyya tunda suka fice get d'in makarantar ta kwantar da kanta acinyar ummi ta runtse idanu ta ahaka har barci ya d'auketa. Bayan 1hr ta farka afirgice tana haki kamar wacce tayi gudu. Ummi ta riqeta gam tasoma tofa mata addu'o'i har ta sami nutsuwa ta koma ta kwanta tana danqe da gefen cikinta sai zufa takeyi, Abbie wanda yake zaune gefen driver ya juyo yace "Rabi'atu mike daminki? Dan na lura tun zuwanmu bakya cikin yanayi mai kyau. "Bakomi Abbie sai dai ina son kacigaba dayimin addu'an nan ta kariya daga sharrin shed'anun mutane da aljannu "to Allah yayi mana katangan qarfe dasu, ummi ta amsa da "Amin. Tafiyan 2hrs yakawosu cikin garin kwantagora, suna isowa suka cimma salma tsaye abakin get da alama su take tsumaye. Suna fitowa Da gudu ta isa ta rungume ummi tana ihu kamar wata qaramar yarinya. Addawiyya ta tureta gefe tace "angirma ba saiti sai tarin shashanci, dundu ta dage ta dimawa Addawiyya abaya wanda sai yasa Addawiyya ta durqushe awurin ta saki wani razananniyar ihu tare da dafe gefen cikinta tana kiran "ummi cikina zan mutu wayyo!!! Da sauri Abbie ya kamata ya d'agata tsaye ummi ta janye hannun data dafe cikin dashi saiga jini har ya jiqa farar rigan makarantar datake yanye dashi. Cikim gigita Salma taja baya tana cewa "yau na bani daga dukan baya sai jini a ciki? Sai kuma ta saki kuka "wallahi ummi bani naji mata ciwonba da abinta tazo dama can. Wani tsawa ummi ta daka mata yasa tayi shiru hannunta dafe da bakinta tana matsan kwalla. Ganin Salma tayi iya bakin qoqarinta don ganin jinin ya tsaya amma ta kasa gashi Addawiyya tasoma galabaita yasa aka d'auketa zuwa hospital. Cikin hanzari suka amsheta suna tambayar abinda yasameta. Abu fa yayi mugun firgita doctors sosai domin duk iya dibaransu nagnin jinin ya bar zuba amma yaqi tsayawa ga ciwo ba wani mai yawaba domin d'an yankane kad'an kamar na ya kushi to shine yake fitar da jini haka. Cirko cirko sukayi anrasa wanda zai iya fita yasanar da su Abbi halin da ake ciki. K'uri tayima gefen damarta tana kallo bako k'iftawa, shi kuwa sai matsowa yakeyi fuskansa ahad'e babu alamar fara'an nan data sanshi dashi, har ya iso gabanta ya miqa hannunsa ya shafa wurin ciwon tare da tofa addu'a atake jinin ya d'auke doctors sunagin haka suka soma hamdalah shi kuwa yaja baya ya sakar mata murmushi tare da hura mata iskan bakinsa atake taja wani numfashi ta lumshe idanunta bakinta d'auke da kalmar "thank you uncle. Jinijina kansa yayi yazama farin haske ya bace. Doctors sukayi dressing d'in wurin tare da yi mata allura domin tasami hutu. **** cikin zumud'i ta kama hannunshi sai kuma tayi saurin saki tana yamutsa fuska, dariya yasaki yace "sanyi ko? Kai ta gyada mishi, yakuma darawa "mai babban suna ya jikin naki? Saida ta shafa gefen cikin sannan tace "uhmm na warke ai, " to madallah. "Amma uncle kana ina kabari kuraye suka kusa halakani? "Affuwan mai babban suna nayi tafiyane yazomin abazata, naraka kakana garin makka ne domin lokacin shiga bautan dazai sake sabon jiki yayi. "Jikin mi? Ta tambayeshi cike da mamaki. "Mu zauna sai inbaki labarin yarda zakifi fahimta. Zama sukayi samar wasu kujeru masu kama da azurfa. Ya kafeshi da idanu tace "uncle bani insha wata qila ba'arasa ilimi ciki. "Tam mai babban suna yanzu kuwa, mudai jinsin musulman junnu idan mun kai shekaru d'ari hud'u aduniya lakacin mun tsufa sosai sai mutafi qasa mai tsarki cikin kogon dutse mu d'aura niyyar azumi na kwanaki talatin cif ba ci ba sha sai muyi ta sallah tare da zikiri har na tsawon kwani, idan mun cika sai musha zamzam da dabino sai mu fito wajen kogon muyi girgiza muna mai miqa godiya ga Alllah mad'aukakon sarki wanda baya barci bare gyangyad'i, akake kuwa Allah sai yamaidamu abinda muka qudurta acinkin zuciyarmu ta yarda muke son kasan cewa wasu matasa suke komawa wasu kuma dattijai sai mudawo ga 'yan uwanmu cikin aminci mu cigaba da rayuwarmu kamar da. "Tabd'ijan amma lamarinku yana da ban mamako uncle wato haka zakuyi tayi kenan har izuwa ranar tashin qiyama? "Eh mai babban suna "to yanzu kai sau nawa kayi girgizan? Dariya yayi mata ya miqe yace "dawo duniyarku ga danginkinan sun cika d'akin suna jiran farka wanki ya soma ja dabaya yanayin sama tare da d'aga mata hannu har ya bacewa ganita cikin cloud. **** tabud'e idanun tayi arba da su ummi, Abbi, mama, Abba, aunty hindu, mushaffa'u tare da Salma duk sunyi tsuru cike da jimami. Suna ganin farkawanta sukayo kanta suna ta jera mata sannu, kai take gyad'a musu cike da murmushi, shigowar doctor yasa suka bashi wuri ya dubata tare da tambayarta inake mata ciwo yanzu ta amsa "banajin ciwon komi yanzu "Alhamdulillah ya furta sanna ya juyo yace dasu Abbi zuwa magariba zamu sallameta bayan ta amsa alluranta na marece amma yanzu abata abu mai ruwa ta sha kamar tea mai d'umi dai dai ba mai zafi sosai ba, daga haka ya fice. Hundu ce take bata tea d'in tana mara magana qasa qasa ita kam sai dariya takeyi mai sauti zuwa can ta kalli inda Salma take zaune tazuba uban tagumi ta yafitota da hannu ta taso ta iso ta tsaya gefenta idanunta cike da hawaye tace "ayya Addawiy na kiyi hakuri wallahi bansan zanji miki ciwo haka ba "mintsilin cinyarta tayi cike da tsokana tace "ke nifa da ciwona nazo dama don haka kibar kukan hakanan matar bishiyar baure uwar arhan zubar ruwa. Duk aka dariya, mushaffa'u ya amsa "matar sarakinta ne oga Muhammad mushaffa'u. Mama tayi masa daquwa yasoke kansa yana murmushi yafice waje Salma tabi bayansa Addawiyya ta ware murya tace "yayi matar mai abocin azumin lada badon ya shiryaba, da sauri taqarasa ficewa batare da ta kula taba. Bayan magarib aka sallameta suka nufo gida cike da annashuwa naganin yarda Addawiyya tadawo normal. Aunty hindu ta had'a mata ruwan wanka tajata zuwa toilet ta tsareta da idanu tace "oya dube in miki wanka, zare idanu tayi zana shirin yin magana ta tareta "ko har kingirman da kika wuce in wanke kine? Tura baki tayi tasoma buga qafa "Allah ni dai ban ceba amma nikam kifita zan iya da kaina don ba'inda kemin ciwo yanzu, "ok autan ummi dai ta girma tana boyemin sirrinta, dasauri ta sa hannu ta rufe fuskanta wai taji kunyar maganar. Washe gari bayan sungama break fast Abbi ya dubi Addawiyya yace "Rabi'a wacece shakiran da kike ta kira sanda jini yake zuba miki jiya? Gyara zamanta tayi tace "itace wacce take bani tsoro acikin barcina kullum tun a cikin daren dana koma makaranta.... "To miye had'inki da ita autan ummi? Shiru tayi kamar bazatace komiba sai kuma zuwa can taja ajiyar zuciya ta soma da cewa.... *mrs j moon* [1/2, 12:07 AM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *This page is for you: Haermeebrah, Mmn Ihsan(yaya sadiya), Aisha Umar, Hauwa'u Gombe, Imranat, tare da my lovely sis Asma'u (seema) sosai nakeji daku Allah yabar zumunci Amin* Happy birthday Halimatus Sadiya Lawal Bala ('yan matan k'warni).😅 Allah yayiwa shekaru Albarka ya kuma qaro wasu masu cike da ni'imomi Amin. 👏🏻 *21* Ranar da nadawo makaranta da dare mun fito daga masallaci sallar isha'i har mun kusa isa hostel sai natuna namanta da littafin addu'o,ina sai nace dasu Asiya su jirani nakoma na d'auko sabida ina son induba wani nafila dazanyi da dare, naje na d'auko zan dawo sai na hangi wata bishiyar mur datake nesa da masallacin tana haske sai na nufi nurin donmin naga mike haske haka koda na isa sai naga senior Shakira ce take ta wasu abu buwa kamar tsafi ina ganin haka sai nasoma addu'a inaja baya domin kada taganni amma na makaro don taganni, ta juyo idanunta kamar garwashin wuta ta nufoni ni kuma na kwasa da gudu ina karanta ayatul kursiyu afili. Su Asiya suna hangoni ina gudu suma suka d'iba a sukwane. Sai numfashi muke saukewa sanda muka isa cikin hostel, sunso nafad'a musu abinda yabani tsoro har nake gudu amma naqi fad'a sabida nayi tunanin duk wanda yarufawa wani asiri Allah zai rufa mishi amma agefe na qudurta zan mata wa'azi data bar tsafi domin shi hanyar zuwa wutan jahannama ne. Ban dak ganinta ba ko awurin assembly sai dai kullum inaganinta cikin barcina tana bani tsoro dan komamin namun daji takeyi masu mugun ban tsoro, duk tadagulamin lissafi nakoma mara karsashi kuma naqi sanar da kowa labarin. Ranar dana cika kwanaki hud'u daganin ta tana tsafi, awani yammaci mundawo d'ibo ruwa afamfo naganta dif agabana tana wani murmushi wanda na fassarashi dana mugunta, a'uziyya naja mata da sauri tare da soma addu'a a cikin raina,, wani mugun tsaki taja ta bangajeni ta wuce su Alawiyya suka bita da kallo cike da tsana domin bata da farin jini sam a school din. ni kam gaba nayi ina tunanin mi hakan ke nufi. Adaren ranar ta zomin cikin barcina, wannan karon so take ta kasheni domin tsafka take kawomin awuya ina gofcewa tare da tofa mata ayar Allah, mun jigata ni da ita har tagaji ta bace ni kuma na farka zufa yajiqamin jiki, nayita mamakin lamarin, to tundaga nan tahani sukuni abarcina sosai take son illatani Allah yana kareni. A daren shekaranjiya mukayi dambe nayi ta d'agata ina bugawa da qasa nakuma gargad'eta da ta kuma zuwamin cikin barci sai na kasheta na juya domin tafiya shine ta zama min zaki tasa farce ta ya kusheni a gefen cikina ko kafin in kamata ta bace tanamin dariya to da na farka sai naga da gaske tajimin ciwo kuma yana min zafi sosai amma naqi nunawa kowa har kukazo tafiya dani. sanda mommy Abida ta jani zuwa wurin bishiya nan shine nake fad'a musu abinda ke faruwa kuma haka sanda na farka amota afirgice ita ce nagani tanamin dariya wai nakusa zama gawa domin itace zata tsotse min jini, kuma sanda nake kiran sunarta kafin mu isa hospital ita nake gani tana son tara k'ok'o a jinin dake zuba ajikina amma ta kasa sabida da ta matso kusa dani sai ta koma da baya tana qara kamar taga wuta. Shiru kowa yayi cike da tsoron lamarin sanda Addawiyya takawo qarshen labarin. zuwa can mama tace "Allah yaqara tsare mana ke, suka Amsa da "Amin. Salma tace "amma ya barcin ki najiya ya kasance? Shin ta kuma zuwa miki ko ya? "A'a banganta ba hasalima inaga banyi mufarkin komiba jiya sai na wata asararin smaniya yayi haske sosai har yana kashemin idanu. Abba yace "Alhamdulilla, alamu yanuna kinfi qarfinta kenan amma duk da haka za'aneman miki maganin kariya daga miyaqu. "Ai dukka gidan za'anemawa domin riga kafi yafi magani, cewar ummi. Haka dai sukayi ta tattauna zancen tsawon wani lokaci kafin iyayen su tashi suka bar yaran suna cigaba da maida zancen. Su Abbi basu bar kwantagora ba sai da sukacika sati 1 da zuwa sabida maganar auren Salma da Mushaffa'u Abbi ya tsaya ganin an tsaida rana kafin ya wuce. Sun tsaida nan da lokacin dazata gama karatunta watanni biyu masu zuwa sai ayi biki. Mushaffa'u tunda yaji haka bakinsa yaqi rufuwa sai tsokananshi Addawiyya ketayi shikam sai biye mata ya keyi cikin nushad'i. Salma tasha kuka sanda su Addawiyya suka tafi barinma dataga har da Hindu aka tafi, da kyat mama tayi ta bata baki tare da tuna mata cewa in Allah yasa Mushaffa'u yasami aikin dayake nema a arewa bank itama zata koma kanon dazama kusa dasu umminta, sannan tayi shiru yayin da Mushaffa'u yake ta mata dariya yana mata waqa wai tazama mai kukan banza, dakyat mama ta samu ya bar tsokanta bayan tayi mishi jan ido. ******* Baqin kano sun isa lafiya, bayan sun huta gajiya a gidan aminin Abbi Alhaji gambo da la'asar suka d'unguma zuwa gidansu wanda iyalen Alh. Gambon suka kyarashi tsaf tunkafin su iso. A unguwan Nasarawa gidan nasu yake, unguwan da masu kud'i suka cikashi, tun a hanya Abbi yace da Alh. Gambo "abokina "amma ba'anan unguwan gidan namu yakeba? Ya amsa "Anan ne aminina "tofa amma kasan unguwan ta masu hannu da shuni ne ko? "Eh, nasani kuma kaima ai mai hannu da shunin ne shi yasa na saya maka gida a wurinsu. Abbi ya had'e fuska yace "to ka sai dashi kasamamin wani a kusa da kai zanfijin dad'i. Murmushi Alh. Gambo yayi sannan yace to muqarasa gidan sai muyi maganar anatse. Gida fa mai kyau da tsari gashi gato komi yaji irin na zamani, bayan sun gama dubawa Alh. Gambo ya dubi Abbi yace "gidan nan na mai gida nane yaji ina cigiyan gida ne zansaya shine yace inzo ya saidamin da nashi wai yayi mishi qarami zai koma wanda yafishi girma, atake mukaje nagani mukayi cikini na biya amma ya ragemin sosai akan yarda yace yayi mishi kud'i, shi azatonshi nine zan zauna sai daga baya yasan bani bane don haka in ka huta na kwana biyu sai inyima jagora kaje da kanka kaqara yi mishi godiya. Numfashi Abbi yaja ya amsa "tam aminina sai kasamana ranar dazamuje kuma ina qara yima godiya sosai Allah saka da Alkhairi ya bar zumunci "Amin su ummi suka amsa. Asatin dasuka iso Alh. Gambo ya samawa Addawiyya wata makaranta mai kyau tacigaba da karatunta kuma suka barta a ajin da take, sosai takejin dad'in karatun harma tayi qawa mai suna maryam Rano. Aunty Hindu kuwa aiki ake neman mata kuma tana cigaba da idarta yayin da ummi take kula dasu sosai, basu rasa komiba na dangin kayan more rayuwa. Abbi kuwa har ya bud'e shago na saida atamfofi akasuwan kwari, don haka baya samun zama dasu sai da dare. Yau hutun qarshen mako kuma ranar suka shirya zuwa gaida uban gidan Alh. Gambo mai suna Alh. Muktar daloli. Mrs j moon [1/4, 8:42 AM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* Na SAFIYYA. *Masha ALLAH Your love, is sweet and true🤝 You are an ideal couple👫 Always stay together,🤳🏻 and the roads ahead shall shower only happiness 💃🏻Happy wedding anniversary to you my everlasting Bahijja (bebeelo)* 😍😘 This page is for you members of sophy nd vc novel luv u sosai uncountable, like yawan malalin gashin tunkiya😅. *22* Tafiya sukayi mai cike da nushad'i Abbi da Alh. Gambo cikin motar babban yaro Alhjin Suka shiga mai suna ayub ummi kuma na ubayyu suka shiga yaronshi na biyu kuma auta domin daga kanshi mamansu tasami matsa a mahaifarta bata sake haihuwa ba. Sun sami ilimi sosai both side boko d na islama dukkansu suna aikin gobnati kuma suna da rufin asiri dai dai misali, Ayub yayi aure har da yaranshi biyu ubayyu ne yake bisa hanya. Maman su hajiya Raliya mace ce mai kirki da dad'in zama yanzu haka tajawo ummi ajiki ta maidata tamkar 'yar uwarta ta jini inkagansu kace sun dad'e tare da juna ne. Sun sami tarba ta karamci sosai a gidan Alh. Muktar daloli. Mahaifiyar hajiya sharifat wanda ake kira da hajja ita ce tayi ta hidima da su. Hira suke ta sha abinsu cikin falon hajja bayan kammala cin lunc dinsu. Azuciye ta shigo ba d'a'a ta zaune gefen Hajja tana ta cika da batsewa cikin daqunar rai Hajja ta danqashi kanta tana cewa "wai miyasa har yanzu baki da nutsuwa ne khairiyya? Tura baki yarinya da aka kira da khairiyya tayi tace "minayi kuma hajiyan complain? "Kinci gidanku nace, ke makauniya ce halan sanda kika shigo bakiga bak'i a tare dani ba ne ko ya? . "Oh sorryn ku mutane, tafad'i cikin salon iskanci. Hajja sauke kanta tayi qasa cike dajin kunyar abinda khairiyya tayi ma baqinta, su kam su ummi ko ajikinsu don ba'abinda ya damesu tunaninsuma wata qila tana da motsin rashin saiti ne dubi da yarda take ta gyad'a kai kamar mai sauraron music, nan kuwa da hankalinta ras tsaban rashin tarbiya ne ke damunta. Ad'age take kallon Addawiyya wacce bama tasan tanayi ba don hankalinta nakan indian film da ake nunawa a Bollywood. Aunty Hindu ce take lura da abinda take yi kuma take taji tsanar yarinyar ya d'arsu a ranta, ta had'e rai ahankali ta matsa kunnin ummi tace "ummi kira Abbi mutafi hakanan wallahi natsani gidan yanzu, kallon mamaki ummi tabita da shi batare da tace komi ba tasoma dealing number n Abbie. Sai bayan sa'asar sukayi haramar tafiya domin su Abbie sunfita da Alhjin wani wuri. Abin arziki sosai Hajja tabasu, don ledar Hindu daban tabata abinda yayi mugun bawa hindun mamaki ainun. Haka Alhjin yayi musu kyauta ta bajinta yayi ta musu godiyan ziyaran dasu kawo mishi. aha sukayi musu sallama sukabar Hajja cike da kewa. Ita kam 'yar fitsara khairiyya tana tsaye a balcony tana ta jifansu da harara kamar sunyi mata laifi, yayin da uwarta matar gidan hajiya Karima, basu kai isar dazata tafito su gaisa da ita ba, tana can kwance tana barcin asara, da alama wurinta khairi ta d'auko d'abi'un banza. "Wallahi ummi tunda nake bantabajin tsanar gida irin na Alh. Muktar daloli ba duk da tarin karramawan da akayi mana "to Hindu duk akanmi kika damu kanki da zancen? Mu zumunci ya kaimu kuma munyi an wuce wurin don haka bana son sakejin maganar kinji ko? "Eh ummi insha Allahu ya wuce. "Uhmm ummi wata qila zata zama 'yar gidanne domin nayi mufarkin wai Alhjin yazo neman aurenta tana ta kuka bata sonshi. Da sauri hindu takawoma Addawiyya duka ta kauce tare ta miqewa ta gudu d'aki tana dariya. Ajiyar zuciya ummi taja tace "Hindu lamarin auta yana jefani cikkn rud'ani fa. Kamar zatayi kuka ta amsa "nima haka ummi kuma wallahi yawanci mufarkinta gaskiya yake zama, amma ina addu'a Allah yasa wasa takemin batayi mufarkin komi ba "Amin dai. Da hanzari ta sauko down stairs tana gyara zaman qaramin hijab d'in na school. Ta sussuna gefen ummi tace "ina kwana ummi? "muntashi lafiya auta? Lafiya lau "madallah. Tana qoqarin fita ta tsinkayi muryan Hindu "autan ummi dawo maza ki karya, a mairaice ta juyo "Aunty zan makara in na tsaya yin breakfast gashi yau monday "koma miye sai kinsha koda tea ne kafin ki tafi don haka oya zo ki amsa, kallon ummi take tana son tasa baki amma taqi cewa komi sai ma yi tayi kamar bata wurin ta maida hankalinta kan karatun dala'ilul khairat d'inta. Baki ature tayi ta shan ruwan tea din bako bread har ta hanye tas ta fice da gudu tana kallon agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta. Tana fitowa get din gidansu motar ubaiyu yana tsayawa don haka batare da bata lokaci ta fad'a back seat tare da cewa "don Allah sauke a school sai kadawo kasami Abbie n. Baice mata komi ba ya jata amma zuciyarshi cike da mamakinta yake na yarda ta bashi umurni batare da ya shirya ba sanna saqon gaggawa dadyn shi ai turoshi amsa wurin Abbie nta. Suna isa ta fice tare da d'aga mishi hannu tace "kayi sauri kada Abbie n yafita, tayi gaba da sauri, girgiza kanshi yayi yana sakin wani smile sannan yaja motar da gudu ya bar wurin. Tana dawowa school taci karo da Hindu zaune qasar bishiyar umbrella ta zuba tagumi hawaye yana tayi mata zarya. Zama tayi gefenta jiki a sanyaye ta kai hannu tana share mata haqaye tare da cewa "waya yataba minke aunty? Ummi ko Abbie? Girgiza kanta tayi cikin rawar murya tace "mufarkinki ne ya tabbata, wani dariya Addawiyya ta saki ta miqe tayi ciki da gudu, Hindu tabi bayanta da kallo sai kuma ta miqe ta rufa mata baya cike da tuhuma. Manage it please. Mrs j moon [1/4, 1:05 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *23* Ko kallon gabanta batayi shi yasa bata lura da ummi ba wacce ke zaune cikin parlorn. "Zo nan Hindu, ummi ta ce da ita, sai asan nan ta lura da ita zaune, qarasowa tayi ta zauna gefen ummin tare da d'ora kanta bisa cinyarta tana qoqarin maida hawayen dake shirin zubo mata. Kallon tsaf ummi tayi mata sannan tace "ya kukayi da Alh. Muktar din kuma mi yake saki kuka? Kamar bazata amsa ba, zuwa can tace "nafad'a mishi ina cikin idda ne sai na fita zaiji amsar sakonshi, jinjina jinjina kai tayi tare da cewa "Haka yayi, amma mi yasaki kuka to? Sai da tashare hawayen dasuka zubo a face dinta sannan ta amsa "banajin son shine sam araina gashi kuma babbn mutum mai matuqar daraja a wurin ku inyadawo bazan iya fad'a mishi bana sonshi ba, sanna koda na aminta na aureshi bazan iya jure rashin d'a'ar yarinyar gidan ba amma dai nasan ina jin son mahaifiyarshi araina sosai. "Uhmm Hinduta kenan kina da wafta har yanzu, to kiyi istahara don neman zabin Allah sannan ki dage da addu'a cikin sallarki ayayin da kikazo sujjada "to ummi zanyi "Allah sa kiga alkahairi "Amin. Wani qamshin turare sukaji yana nufosu duk suka maida hankali wurin, Addawiyya ce ta bullo taga cikin kitchen hannunta d'auke da cup mai d'an girma tana motsa kunun Alkhama wanda yaji nonon shanu, milk tare da zuma ta sami wuri ta zauna tana cigana da motsa kunun sabida yana da zafi sosai sai turiri yake ta fiddawa. Harara Hindu ta dalla mata tace "yaushe kika wucemu har kika shiga kitchen bamu lura ba? Sai da ta had'iye kunun data sa abakinta sannan tace "sanda ummi keyi miki wa'azi, tana fad'in haka ta miqe ta fice da hanzari Hindu tabi bayanta da sauri yayin da ummi ta rakasu da idanu ta saki murmushi ta na mai furta "Hindu ta koma miki Salma kenan yanzu wacce kika maida abokiyan wasanki. Idanu kawai Hindu ta samata har tagama shanye kununta sannan tace da ita "autan ummi mi kike boye min agame da Alh. Muktar? Murmushi Addawiyya tayi sannan ta amsa "ba abin da na boye miki aunty illa dai nasan Hajja mahaifiyarshi ce ta umurce shi da ya zo neman aurenki, sabida tayaba da hankalinki tare da natsuwarki shiyasa tayi miki kyau na daban jiya, bama ta san cewa kintaba aure ba sai da yakoma yake sanar da ita kuma atake taqarajin son daki zamo surukanta. "to pa ni Hindu naga ta kaina, gashi ni kuma bazan aure shi ba don bajin son tsoro mutum irinshi. "uhmm aunty kenan, inace Allah shine yake wanzar da dukkanin abinda yaso batare da wani ya isa ya sanja ba? "Eh haka ne Allah ne yake da ikon komai ba mutum ba, amma gaskiya nikam mutumin yayimin tsufa, ya girmi su Abbi fa sosai kuma ni sam iyalanshi lamarinsu bai yimin ba, kidi ba fa abinda shegiyar khairi dinnan tayima kakanta jiya ina kuma ga ni matar ubanta. Dariya Addawiyya tasaka sosai sannan tace "ni kam ta burgeni da calour d'in stile din haukanta domin ni ban d'auketa mai cikakken hankali ba tunda batasan mi takeyiba, bata da ilimin addini tare dana nasara kuma bawai ba'a sata bane a'a tadaiqi maida hankali ne sabida sangarta ta da momynta tayi wai ganinta gata ne takeyi mata. "To ke autan Ummi waya baki duk wannan labaran nasu? "Duk amufarki na nagani jiya da dare "Allah qarya kikeyi autan ummi, kedai kifito fili ki sanar dani kawai Aljaninki ya sanar dake. "Ashe kingane amma kika isheni da tambaya to abindama baki sani ba shi kanshi Alhjin tunda yaganki yaji sonki da qaunarki ta kamashi,, daren jiya bai iya barci ba sabida tunaninki tare da na matarshi na fari uwar 'ya'yan shi domin sai yake ganin kinyi mishi kama da ita barinma da yazo d'azun yaga yanayinki mai sanyi da alamaun haquri ga kunya atare da ke da kuma iya zance mai ma'ana intact dai komi naki ya burgeshi. Kama haba Hindu tayi tana kallon Addawiyya bako qibtawa. "Aunty Hindu wallahi taimako zakiyi sosai in kika aure shi domin yana buqatar taimako sosai, mace irinki yake so wacce zata kwantar mishi da hankali kuma ta dawo mishi da martaban gidanshi a idanun muta ne yarda al'umma zasuyi ta zuwa yana taimakonsu haka kuma mahaifiyarshi zata sami nutsuwa da jin dad'in gida fiye da yarda takeji yanzu, hatta yaranshi zasu dawo gidanshi da zama kuma abinda yafi buqata kenan yanzu arayuwarshi ganin 'ya'yanshi akusa dashi, sabida haka don Allah da zarar ya dawo alokacin dakika bashi to ki ce mishi kin amince dashi, so da qaunarshi asannu zaki sami kanki cikinsa dumu2. Ta qarashe zancen cikin dariyan tsokana. Shiru Hindu tayi tana nazarin zantukan Addawiyya, kai ta gyad'a batare da ta iya cewa komi ba don hakika tashiga rud'ani da lamarin Addawiyya ainun. "Aunty ni kaina haka kawai nakejin tausayin wani a cikin gidan kuma wallahi bansan ko waye ba amma nasan wata qila yana cikin matsala ne tarashin wani abu a rayuwanshi dubi da yarda nakeji wani feeling na maraici. "Ikon Allah autan Ummi anya ke mutum ce kuwa ba rabi rabi kike ba kamar yarda Salma take fad'a? Murmushi tayi kawai tamiqe tasoma tafiya, Hindu ta sha gabanta tana zare mata idanu, dariya ta kwashe dashi harda duqawa tace "kingako yarda idanunki suka kuma fitowa kamar jikar nufe, kai kina da idanu masha Allah. ranqashi ta kaima kanta tana dariyan itama tace "yo ai layinmu d'aya don komi nawa irin taki ce ko kin manta kamar da mukayi dake har tafi wanda kukayi da Salma? "Eh ina sane kawai tsokanarki nakeyi don insaki dariya gashi kuma nayi nasaran saki. "U r too nice Addawiyna. Duqawa Hindu tayi ta rungumeta ta manna mata kiss agoshi sannan ta miqar da ita suka nufi ciki cike da nushad'i. ****** kwanci tashi ba wuya gashi har bikin Salma yazo lokacin su Addawiyya sun sami hutu don haka tun ana saura kwana hud'u suka isa garin kwantagora. Biki yayi biki, bikin 'yar gata haihuwar dangi. Acikin gidan aka gina mata flat d'inta mai kyau sabida ba dad'ewa zasu yiba zasu dawo kano domin aikin da mushaffa'u yake nema na banki yasamu a bakin arewa. Bayan gama biki da sati biyu suka dowa kano suka bar Salma da kewarsu kafin itama tabawa su mama kewa nan bada jimawa ba. Yau hutun qarshen mako, Addawiyya tana kwance cikin bargo amma ba barci take yiba ta daiyi lamone kamar mai barci. Hindu ta fito wanka ta zauna samar stool ta soma shafe2nta ta tsara kyalliya sosai ta d'auko wata doguwar riga baqa ta sanya tare rolling da gyalen kayan tana cikin fesa turare ta tsinkayi muryan Addawiyya. "Aunty wallahi kinyi kyau kamar baki taba yin aure ba, "uhmm autan Ummi kenan kinfiye zolaya "Allah aunty ba wani zolaya sai gaskiya "tam nagode. Aunty ko kinsan yau baqonki zai zo domin yana lisafin sanda zakigama idda yasan tuni kingama ya dai tsahirta ne don kada kiga gajen haqurunshi, yanzu hakama yana hanyar isowa kuma yau su Adda Salma zasu iso, bama ta da lafiya wata qila malerian qaruwa ne yakamata sannan yau Dadyn su ubaiyu zai zo miki da albishir d'in kinsami aiki amma bansan ko aina kika samu ba, wata qila a company n mr Habibinki ne don nasan yanzu kin somajinshi aranki tun bayan da kikayi istiharan nan sonshi yake ta miki gizo a cikin ruhi, kina wani kaucewa. Ganin Hindu tayi mutuwar tsaye yasa Addawiyya sauka ta fad'a bathroom tana yi mata dariya. Hindu ta matsa jikin toilet d'in tace kigama kizo ki bani labarin kanki tunda kinzama mai leqen asirin sirrin zuciyar mutane. Bud'e qofar tayi ta fito tana goge hannunta da qaramin towel, ta wuceta da bud'e freeze ta d'auko Apple saida ta ci kamar rabi sannan ta miqawa Hindu tana cewa ci kiji dad'in sa kamar mad'i harara hindu ta wulla mata ta murd'e mata kunni tana mai cewa"oya ina sauraronki bani labarin kanki ko in maidaki mai 1 ear yanzu. "Washhh!! Aunty H. Sakeni to sai na fad'a miki, sakinta tayi ta zuba mata manyan idanunta. "Nidai bawani labari atare da ni sai na wannan banzan ubaiyu n dayake sona kuma yakasa sanar dani kuma gara hakan sabida ni dai banson so ba ban san aikinta ba basan muhinmancin taba bansan qalubalenta ba kuma ban fatan in sani don ni bazanyi aure ba balle tunanin maza yanemi illatani har na Kai ga kamuwa da hawan jini. Duka hindu ta kaiwa bakinta tace "ke autan ummi banson hauka, kuma in ba'ayin aure za ahaifeki ne daka kikewa baza kiyi ba? Wata rana kina abu kamar wanda lissafinta ya afka halin makuwa. "To zanyi auren Aunty amma bayanzu ba sai nagama karatuna kamar ku "tam Allah yanuna mana lokacin lafiya "Amin. Suna fitowa parlor mai gad'i yana shigowa yace da Hindu yallabai Alh. Muktar Ya iso yana sit room. Kallon Addawiyya tayi tako kashe mata ido 1 tace "saura isowar su Adda Salma da labarin samun aikin ki, kinga tun anan zaki gane tarayyanki da Alh. Muktar haske ne. Girgiza mata kai kawai hindu tayi batare da tace da ita komi ba. "ummi sai na dawo "tam ki gaishe da shi "aha zaiji, ki tawo mishi kayan motsa baki, tace da Addawiyya "tam aunty babba angama matar tsoho mai zuciyan alkhairi. Duka hindu ta kawo mata ta koma bayan ummi ta qamqameta tana yi mata kwalo, ficewa tayi tana dariya domin lamarin Addawiyya yanzu dariya take bata. Ummi zo mu shiryawa su Adda Salma kalolin girki masu qayatarwa tare da d'and'ano, "aiko kin tunamin dazun ta kirani take ce min suna nan tafe yau, muje kigani asan abinyi. "To ummi amma bari na nasoma kaiwa ogan aunty H. kayan maqulashe "ohk tafi kidawo mu soma kada su iso bamuyi komi ba. "to umminmu, ta amsa tare da ficewa d'auke da qaton tire wanda ta jera d'angin kalolin drinks da snacks. *mrs j moon* [1/8, 8:40 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA *This page is for you khadeeja Candy (qanwas) Allah yacika miki burinki na Alkhairi Amin,, kisani inaji dake sosai aruhina my dear candalah*😍 *24* K'arfe 9:00pm duk kansu zaune suke a dinning area, Abbie ne kad'ai baya wurin sabida shi baya zama a dinning yaci abinci sai dai akai mishi room d'insa ko a shinfida mishi ledar cin abinci a parlor ajera mishi akai. Bakajin komai sai sounds d'in spoons da yake tashi. Tsawon wani lokaci bawanda yayi ko tari mai qarfi zuwa can Addawiyya ta kammala tayi hamdala ta sauke dubanta zuwa inda Salma take tace "Adda kidaure kici ko kad'anne tunda ke da kanki kikace ayi miki zakici shi. 'Dan tsaki Salma taja kad'an sannan ta amsa "wallahi Addawiy ina mugun jin yunwa amma nakasa cin komi tun daren jiya sai ruwa nake durawa har yazo ya dungureni shima. "Kidaure ki dai ci ko kad'an ne domin hakan zai sakiji qarfin jikinki, "to ummi bari nagani ko innaci zai zauna. "insha Allah bazakiyi amai ba honey mushaffa'u ya ce haka yana matsa kusa da ita. Harara Hindu ta dalla mishi ya kauda fuska ya qara matsawa sosai jikinta yace "ko nabaki abaki ne? Kaita girgiza mishi tasoma diban faten Irish d'in tana cika kamar tanaci magani.ganin ta soma ci sai Ummi tamiqe ta barmusu wurin. "Wallahi mushaffa'u karage rashin kunya, yanzu d'azun da salma ta amince sai ka bata abinci abaki ummi tana wurin ko? "Eh Allah zan bata, miye aciki, ainaga bata da lafiya ne ko? "Eh bata da lafiya amma kasani hakan rashin ta ido ne don haka kada kaqara kwatantawa, indai agabanmu ne wannan bakomi amma agaban su ummi baiyi tsariba abin. "To auntynmu amma Allah agida agaban mama nake bata abinci wata ranama maman rake sani na bata "to mama daban ummi daban, ko kamanta ummi tana da kawaici irinta fulani ne? don haka ka kiyaye rashin kunya agabanta. "uhmm aunty nace bazan qaraba sharhin ya isa haka, duka hindu ta kai mishi ya gofce yana dariya sai kuma ya nunata da yatsa "aunty Allah kibari, yanzu ba da bane sabida yanzu na kusa zama father. Caraf Addawiyya tace "hakane kam ka kusa zama baba kuma hankali tare da natsuwa yanama asharuwan tsintsaye, tunda har yanzu baka bar buga ludo ba. Afusace yayo kanta da duka ta qamqame jikin hindu tana kwalla ihu, Salma ta saka dariya ta janyosi baya "my dear kasan halin tsokanar Addawiy dai sarai amma kake biye mata "sweetie sakeni in shafe mata face da maruka wata qila zata barmin katsalandan alamarina, tana can labe ta amsa "aiko da bakuyi barcin dad'i ba. "kinji ko honey? Salma tace "Addawiy kiyi shiru kada ya had'a miki jini da majina "ai ko wallahi da kungama zaman soyaya mai da.... Hindu tayi hanzari rufe mata baki ta tare da jan hannunta suka barmusu wurin. Da harara mushaffa'u yabi bayansu dashi sannan ya juyo yayi qasa da murya yace "honey tashi mutafi in miki wanka sai ki kwanta, gyad'a mishi kai tayi ya d'agata cak tanemi zamewa yariqeta gam suka shige room d'in dasu kayi masauki. Addawiyya ce tsaye tana sanya kayan barci "Aunty wai ya kukayi da habibinki Alh. Muktar? "Autan ummi sai naci gidanku fa. Dariya ta kyalkyale dashi ta tafa hannaye "aunty yanzu fa nice aminiyarki don haka komi naki kada ki boyemin ina da shawarwari masu nagarta da zan riqa baki. "To mama. Dariya Addawiyya takuma sawa "a'a aunty h. Bankai can ba, yanzu dai kibani insha "in naqi fa? "To riqe kayanki, nadai san kin amince mishi kuma yabaki saqo ki bani kikaqi amsa alhalin kinsan ina buqatan abin. "Autan ummi!! Waike wata kalan halitta ce? Inaga sai Abbie yanemo masu ruqiyya sunyi miki sun rabaki da aljanin nan dake tonawa mutane asiri "aunty h. Inko kikayi haka to lece wanda zaki soma da kin sani, in kuma ina ganin wasane to tafi kija arabani dashi kiga abin mamaki. Sassauta murya Hindu tayi tare da janyota jikinta tace "uhmm wasa nake miki, bawanda zai rabaku tunda baya tutar dake saima taimako da yakeyi mana, kice masa mungode sosai, "zaiji kuwa aunty. Suka kwanta hindu tana ta sake2 abisa lamarin autan ummi. Addawiyya ita da maryam awani yammaci suna tsaye abakin titi suna jiran napep zasu dawo daga islamiyya sai ga wata motar ta ja ta tsaya agabansu suka bi motar da kallo zuwa can mamallakin mota yafito, ubaiyu ne ya bayyana cikin kyalliya mai d'aukan hankali. Ya iso yayi musu sallama maryam ce ta amsa afili yayin da addawiyya ta amsa azuciyarta, tawani had'e rai kamar taga mutuwa. "Qanwata ku zo in kaiku gida, yace yana mai duban Addawiyya, da sauri maryam ta amsa to tare da jan hannun Addawiyya. Sunsoma tafiya ya juyo kad'an yace "qanwata ina yini, ya karatu? Tayi mishi banza kamar bada ita yakeyi ba, girgiza kai yayi ya dora da "tunda ke kin kasa gaishe dani sai qawarki ce tayi hankalin gaishe ni to yakamata ki amsa tawa danayi miki. Nan ma shiru tayi mishi tana motsa baki kad'an2 alamun karatu takeyi. Maryam ta faskamata duka acinya ta saki qara bashiri, ta zabura zata rama suka had'a idanu da ubaiyu ta mirror ta koma ta zauna tana kallon gefen titi zuciyarta kamar wuta sabida haushin da ya kasheta na ubaiyu, ita dai haushi yake bata sosai bata qaunar ganin yazo wurin Abbie ko yanzu ma maryam ce ta kwafsa tasa suka shigo motarshi. "Qawarmu ina muka nufa? Yace d maryam. Maryam tasoma kwatan ta mishi hanyar gidan su har suka isa tafita tayi mishi godiya ta makawa Addawiyya harara ta shige get d'in gidansu. Gyara zama Addawiyya tayi tabi bayan maryam da murmushi, ubaiyu ya shagala wurin kallonta shima yana zuba murmushin domin shidai tana matuqar burgeshi barinma intana magana sai yariqajin muryanta tana busawa kamar ba hausa takeyi ba don dad'i. "Kallo dai in yayi yawa yana zama ta haram. Maganarta ya dawo dashi hayyacinsa, ya shafi sumar kansa tare da yiwa motar key. Har suka iso gida yayi horn, get man ya bud'mishi ya shige ciki, yana gama parking ta bud'e zata fice yayi hanzari cewa "minti biyu don Allah Rabi'atu, komawa tayi zauna ta zuba mishi manyan idanunta ya kauda fuskanshi gefe yana cewa aranshi ai komi zakiyi yau sai nayi ta maza na bud'e miki asirin zuciya ta. "Uhmm ina jinka ya sunkuyarbda kansa kamar mara gaskiya ya soma cewa "da... ma... ina... s.. o.. n... ki.. ne da.. Au.. re.. ne. "Kai!! nifa yaya bangane wannan karatun 'yan chanar da kakeyi minba, Inzaka bud'e baki kayimin yarda zangane to, in kuma baka iyawa ni zan shiga ciki ina da abinyi. "To ki kauda idanunki akai man Addawiy, qara bud'e idanunta tayi akanshi tawani had'e rai tace "nasan kalmar so da kauna zaka biyamin karatunshi to ni dai kaina bazai riqe ba, don haka kabar karatunka ka tattara kamiqawa mai sonka da qaunarka kana yi mata wulaqanci. Baki bud'e yake kallonta zaiyi magana wayarshi tayi qara ya duba yayi rejected. Yarda ta zuba mishi idanu har yaji tsoro, ta saki murmushi ta lumshe idanunta ta kwanta a jikin seat tace "yaya miyasa ba datse kiranta alhalin kansan tana muradin jin muryanka? "Uhmm Rabi'a wa... Wayarshi ta kuma yin qara yana shirin kashewa tace "pick it pls, she's need ur assistant. Mamaki ya kashe shi har kiran ya tsinke, asanyaye ya bi bayanta, addawiyya naganin haka tayi ficewarta. Tana daf da shiga parlor taji an fizgo mata hannu ta juyo afusace sai taga ashe ubaiyu ne. Hannun nata yasaki ya langabe kai yace "waye yafad'a miki Aisha tana sona? Kuma ya akayi kika san tana neman tallafina na? " A idanunka nagani duka, tana fad'ar haka tashige parlor da sauri, tabarshi tsaye, da idanu yarakata kawai domin yarasa mizai kuma cewa, asanyaye ya koma cikin motarshi ya dafe kanshi dayake barazanar rabewa biyu. "Wannan yarinyar kuwa bata da matsala? Ganin yarasa gano amsa yasa ya ja motarshi yafice ya mufi gidan su Aisha donjin kiran datakeyi mishi. Addawiyya kuwa tana shiga bathroom tayi ta watsa ruwa tazo ta tada sallah domin anata kiran magrib tana idarwa ta shafa lotion ta zura doguwar riga tafito parlor ta zauna ta d'ora qafa d'aya kan d'aya ta jingina sosai idanunta lumshe. Haske take gani yana nufota ta kuma qamqame idanunta tana sakin murmushi. Ummi da Hindu wanda isowarsu parlorn kenan suka tsaya suna kallon ikon Allah. *Mrs j moon* [1/9, 10:52 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *25* Zuwa can ta saki dariya mai sauti sai kuma ta soke kanta atsakanin cinyoyinta tana girgiza kai tare da cigaba dayin dariyan. "Ke!!! Auta kina da lafiya kuwa? Cewar ummi tare da kai hannu tana qoqarin d'ago kanta da ta soke. Tura baki tayi tamiqe da sauri tashige room d'insu, ummi zata bi bayanta Hindu ta riqota ta zaunar tayi qasa da murya "ummi ki kyaleta wataqila tunanin wani abu takeyi kika katseta. "hindu hakiqanin gaskiya inajin tsoron ayyikan auta kada fa muyi sakaci wata rana awayi gari ta hauka ce. "A'a ummi ba'abinda zai faru insha Allah, adage dai dayi mata addu'a shi yafi "to Allah ya warware mana lamuranmu "Amin. Bayan sungama cin supper, suna zaune a parlor, ummi tana damawa Abbie fura, hindu ta duqufa akan laptop d'inta tana wani aiki don yanzu lecture ce a fce wacce watan ta nabiyu kenan da soma aiki. Addawiyya tare da Abbie kuwa kallon wani drama na larabawa sukeyi, duk abinda bata ganeba cikin maganarsu sai ta tambayi Abbie. Ubaiyu yayi sallama saida aka amsa mishi sannan ya shigo ya zauna tare da zamewa ya gaida su ummi da Hindu, shi kuma Addawiyya ta gaishe shi. Abbie ya tashi ya shiga room d'insa bai jimaba yafito da sak'o ya miqawa ubaiyu. Yayi musu sallama ya fice, hindu ta dubi Addawiyya tace "malama tashi kiraka shi bakin motarshi, baki ature ta miqe tafita bako mayafi jikinta, ummi ta rakata da idanu fuskanta d'auke da murmushi, cikin ranta tana addu'ar Allah ya had'a kansu zumuncinsu dasu Alh. Gambo yakuma qarfi, haka abin take agefen Abbie, sosai yake murad'in su qulla zumunta tsakaninsu da zuri'ar Alh. Gambo. Kamar yasan zata biyo shi a baya, da yafita sai ya tsaya a daf da parlorn yana ganin tafito yayi gaba cikin taqama taja ta tsaya tana kallon solon wani iskaro daykeyi mata, sai da ya shiga motarshi sannan ya ankara bata biyo shiba yafito da sauri yana waige waige can ya hangota tsaye bakin parlornsu ta kafeshi da mayun idanunta mai jefashi cikin rud'ani dazarar yayi arba dasu. Sauke taqamarsa yayi yadawo inda take yayi kamar zai rungumeta ta ja baya yasa dariya yace "baki san kin girma bane halan, da kika fito babu mayafi? Harara ta watsa mishi, ya kuma matsowa kusa da ita tayi saurin juya mishi baya tace "zan saita maka maths d'inka da yasami matsala in har kace haka zaka riqa yimin, "minayi miki yanzu? Banza tayi mishi zuwancan kuma tace da shi "Sai da safe, kagaishemin da Aisha inkaje wurinta, kuma wayar da ka sayomin zaka bani, ina roqonka dan Allah kabawa Aisha ne domin ita tafini buqatar ta. Ko kafin yayi magana ta shige parlor ta barshi nan tsaye cike da mamakin inda ta sami labarin sayar wayan da yayi mata. Kamar kullum duk in sun fito break a school a qasan wata bishiyar mango suke zama suyi ta hiransu ita da maryam har zuwa sanda lokaci komawa class zaiyi. Yauma zaune suke suna hira akan test d'in dasu kayi d'azun kafin fitowarsu. maryam tace "ke kam my Addawiy kinji dad'inki ba'abin da yake baki wuya jiba yarda kika riga kowa gama test alhalin da gwaraza masu tsananin kwazo a ajin amma tun sanda kikazo duk suka koma laqas kamar sun mace, ba salo da fi'ili. Dariya Addawiyya tasaka sosai, "my Rano kina da abin dariya kam, yo nikam ai banga wani kwazo danake dashi ba tunda banyi ko quarter nkiba a komi d komai. "Kefa 'yar wofi ce wata rana my Addawiy, wato abin naki har da tsokana ko? "Ba tsokana sai gaskiya 'yan matan rano. Dariya maryam tayi "my Addawiy da alama kina son garinmu, yakamata ki sa rana na kaiki kiga yatake, "aikam inasonta sosai, kuma insha Allah wannan hutun tare dake zamuyi acan. Cike da murna maryam ta rungumeta ta manna mata light kiss a kumatu. "Yawwa babe look at my new phone, maryam tace tare da fiddo da phone d'in tana nuna wa Addawiyya "uhmm tayi kyau sosai qawas amma dai wata qila zata zama hanyar lalacewarki ko kuma jiyo qamshin barzahu. Wani kollo maryam da sauke mata tace "mi kike nufi? Ko dai kinamin baqin ciki ne nashigo gari da zazzafan waya ke kuma baki da ko gidan layi balle ki saran samun irinta. Had'e rai Addawiyya tayi kamar bata taba dariya ba, maryam ta ja baya domin taji tsoron ganin mood d'inta sosai. Allah ya tsareni tabewa na rashin aikinyi ace ni da kaina zan miki black stomach, tirr!! Wallahi, kuma kinsan nafi qarfin wannan banzan wayar taki ta sata, kisani in yanzu nace ina son waya wallahi kafin atashi school zaki ganni da apple bama tecno ba, don haka ina gargad'inki da kada ki kuma cemin inayi miki baqin ciki. "To hajiya Ammi "bankai can ba amma ina so kina natsu in fad'amiki had'arin dake ga wayar nan "uhmm inajinki mai gani har hanji, "komi zaki ce na d'auka "to fad'an inji. Sai Addawiyya ta kallace daga sama har qasa sannan tace "wayar takai kwana uku atare dake kina boyonta kada Ammi tagani sai jiya da dare kika fito da ita shima don d'an iskan da yabaki yayi miki qorafine da ki budeta zai kiraki. to ki rubuta ki ajiye tabbas in kika koma da ita gida yau Ammi ta gani mai rabaki da ita sai Allah domin sai kin leqa barzahu na wucin gad'i sabida yanzu haka inda yayi satan wayar sungano shi yakuma ce ke yakawomawa anzo wurin su Abba, Ammi ta bincike d'akinki kaf bataga waya ba amma sunce ajira ki dawo abincikeki in da gaske ne sai abasu, don haka sai kisan mafita. Ai tuni jikin maryam ya jiqe da zufa, tafad'a jikin Addawiyya ta rushe da kuka tana cewa "nashiga uku na lalace, ashe Ameer barawo ne bansani ba? "Ba barawo bane sonkine yaja mishi satan sabida da yarda kika matsa sai kinyi waya donmin kema a adama dake a social media alhalin kina sane Abbanki yace inkingama secondary zaki riqe waya ko wacce iri kike so amma son zuciya da hud'uban qawayenki su haule ya kaiki yabaro gashinan kinjawa yaro muta ne tabon tsiya yaci duka har ya gode Allah. "Uhmm aminiyata bar wannan zancen kedai bani mafita "bansanya za'ayiba amma tashi muje wancan tap d'in ki wance face d'inki, insha Allahu zuwa kafin mutashi mafita zai zo mana. Jiki asanyaye tabi bayan Addawiyya, bayan ta wanke face d'inta, suka taho Addawiyya tanayi mata nasiha data bar biyewa qawayen banza marasa kamun kai. "ya ilahi!! Ranota kalli bishiya tana tafiya, maryam ta dubi wurin da Addawiyya take nuna mata tayi arba da wata qatuwar bishiyan kuka tana rangaji jijiyoyinta duk awaje ta nufo wurinsu zata kwalla ihu Addawiyya ta rufe mata baki tasa hannunta ta shafa mata idanu tace "dalla can matsoraciyan banza daga wasa har kin saki fitsari, jikinta ta duba taga qafafunta duk ruwa alamar fitsarin tasaki dai. "Ban yafe ba Addawiy, ace don Allah ajannun da kike ta ammali dasu zaki sa subani tsoro har inyi fitsari ban sani ba? Dariya Addawiyya take tayi mata har suka iso class ta d'auki ruwan roba a lokansu ta wanke qafafunta. Malamin physics ya shigo period d'insa yana daf da qarewa wayar maryam tasaki sauti mai qarfi, cikin fushi ya miqawa Addawiyya hannu ta saka mishi wayar, ya jefa a aljihu ya fice baiko gama darasin ba. 'Yan ajin sai cece kuce sukeyi wasu na Allah ya qara wasu kuma nayi mata jaje, ko kallo basu isheta saima ta soma yiwa maryam magana qasa2 "kinga munsamo mafita ko? "Eh wallahi qawata, "kinga sim din na cire in munfita sai mu karya dama kunnawa nayi yaji sautinta duk don ya kwace, inkin koma gida sai ki tubure ke bama kisanshi balle har yabaki waya "tam haka za'ayi 'yar gari "kuma kinsan shima sace wayar za'ayi bazaiyi mishi amfanin komi ba duk kuwa da rawan jikin da yakeyi yaje ya bud'e media, wawa wanda matsolanci ya hanashi siyan waya babba. Wata uwar dariya maryam tasaka duk ajin suka maida hankalinsu kanta ta gintse fuska tana hararansu, Duk suka kauka fukokinsu domin sun san yanzu baqaramin aikinta bane ta feshesu da matsifarta. ******Rayuwa tacigaba da tafiya sannu sannu gashi yanzu har su Addawiyya ta kusa kammala secondary. Tuni Salma ta haihu d'anta namiji yaci sunar Abbie ana kiranshi da Annur. Hindu kuwa kimanin watanni biyar kenan da yin aurenta da Alh. Muktar har tasamu rabo. Addawiyya ce tafito da sauri tace da ummi "natafi school daga can zan wuce wurin Aunty Hindu kuma sai ranar lahadi zan dawo tunda yau Friday "to kigaishe da ita sosai ga bushashen zogale ki kaimata kozatayi miya "ohk, ummi sena dawo "auta don Allah kada kiyi fad'a da mutanen gidan nan kinji? "To, amma fa in sun tabani bazan kyale kowa ba "a'a auta bance ki ramaba kinji ko? "Eh, zan kiyaye ummi "to madallah, Allah ya tsaremin ke "Amin ummina, ta janyo hanun ummin ta manna mata kiss tafice da gudu tana kiran drivernsu. Akwwnakin baya Abbie yasaya motoci biyu tashi d'aya nasu d'aya, ya nemi driver mai hankali yana kaisu duk inda zasuje. *****misalin 1:00pm suka tashi daga school, bayan sun sauke maryam driver ya wuce da ita gidan Hindu. Driver yana gama parking ta fito ta dubeshi tace "malam khalid sai jibi da yamma kazo mu koma gida "to insha Allahu zanzo akan lokaci "aha sai kazo d'in. Tashige parlor d'auke da sallama. Bata tadda kowa cikin parlorn ba don haka sai ta cilla school bag d'inta samar kujera ta zare qaramin hijab d'inta tare da d'ankwalinta gashina ya bazu abayanta, ta fad'a bisa kujera tana kiran "washh wallahi nagaji. Zuwa can ta yunqura ta zare sandal dinta tare da socks, "inje na watsa ruwa wata qila zanfijin daidai, ta furta hakan tare da miqewa ta nufi room d'in Hindu. Daf dazata shiga room d'in ta juyo caraf idanunsu ya had'u ta kwasa da gudu ta shige cikin room d'in. Shi kam murmushi yayi ya miqe ya fice yana tambayar kanshi wannan kuma wacece? *mrs j moon* [1/10, 8:29 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *26* Motsin shigowarta ya tashi Hindu wacce take barci, ta yamutsa fuska tana hararan Addawiyya "autan ummi wai har sai yaushe zaki hankali ne? Zaunawa tayi gefen bed d'in ta kamo hannun Hindu tace "affuwan maman 2, wani mutum nagani a parlornki yana da d'an kyau kuma naga yayi kama da habibinki mr tsoho. Duka Hindu takawo mata ta matsa tana dariya. "Yaron Alhji ne na biyu sunarsa Abdul Hameed, jiya yadawo daga Egypt wani course da yaje, cikakken doctor ne. "Oh ina mishi murna zamowar shi doctor, Allah yasa nima wata rana naganni hakan kamarshi "Amin autan ummi. "Yawwa Aunty H. Kinsan abinda yakawoni gidan nan kuwa? "A'a sai kin fad'a. Qasa tayi da murya tace "makiran matarcan ta sato takardun qaddarorin Alhaji ta saka miki a cikin sip, anjima zaizo nema in bai ganiba sai tayi jagora zuwa part d'inki ayi bincike, don haka yanzu zan d'auka in miqashi zuwa part d'inta, ai intasan wata bata san wata ba. Cike da tarin mamaki Hindu tace "autan ummi samuwarki alkhairi ce a rayuwarmu, godiya nakeyi miki mara adadi. "Kada ki damu aunty H. Allah yana tare da mai gaskiya. Gaba gad'i Addawiyya ta shiga parlorn hajiya Karima, bakowa ciki don haka direct ta wuce bedroom d'inta ta bud'e bedside drawer ta saka ta fito da sauri tabace kamar walqiya. "Autan ummi mi hakan ke nufi? "So take uncle tsoho ya sakeki ki barmata gidan tacigaba da mulkinta don tace tunda kika zo komi ya lalace mata ta rasa gane kan mijinta. "Ikon Allah sai kallo, to ta Allah ba nata ba,, zama daram a gidannan, "zancenki haqqun aunty. Da yammacin ranar suna kitchen suna gabatar da girkin dare. hayaniyar hajiya karima tayi musu sallama fad'i take "wallahi yau dubun barauniya yacika, dama don arzikinshi kika aureshi 'yar matsiyata, to kisani mu kam bazamu lamunci sata ba a irin wannan gidan mai cike da nagarta. "Kimin shiru nace karima ko in saba miki, miye kikeyi haka? Alh. Muktar yace haka cikin qunar rai. Tsaye su Addawiyya sukayi kirko2 suna kallon ta, zuwa can Alhaji yace "Hindu wasu takardu nake nema bangani ba shine nace ko kin gansu? A'a Alhaji bangansu ba sam "qarya takeyi ita ta sace don haka dole abincika ko ina na cikin d'akinta. Wani kallo Addawiyya ta doka mata tana girgiza kai tare da cije labba. "Ke uwarki kikewa wannan kallon? Tace da Addawiyya. "A'a inamawa marka ce matar basharu. A fusace tayo kan Addawiyya Alhaji ya tareta "ke!! Banson sokarci anan wurin, inace tambayarta kikayi ta kuma baki amsa? Cikin kuka hajiya karima tace "su malam fa ta kira sunarsu, sunacan kwance cikin qabarinsu ta tashesu. Kallo mamaki Alhaji ya saukewa Addawiyya, zaiyi magna tariga shi "a'a Abba nikam bansan sunar iyayenta nakiraba, sunar zuwamin yayi kawai abaki amma ni banma san wasu masu suna hakan ba. Jinjina kai Alhaji yayi yace "to kindaiji badasu takeyi ba don haka sai ki kama mana baki haka nan, kina bareshi kamar anyaga faranti. Ga dariya amma ba halin yinshi. Tana hararan Addawiyya tace "To naji, amma sai anyi binciken nan angano barawo yau, "karima fice kibani wuri tun ban saba miki ba. Hindu tayi saurin cewa "Azo ayi binciken Alhaji ko za agano mai halin beran. "Dear baza'ayiba nace, kaya dai nawane to bakomi kowa ya d'auka nauyi yaragemin. Afusace hajiya karima ta fad'a bedroom d'in Hindu tana masifa, "ai wallahi sai naduba haka kawai acucemu inaji ina gani taf bazai sabuba kam. Alhaji zai bita Hindu ta riqeshi tana girgiza mishi kai, akan dole yaja ya tsaya amma ranshi inyayi dubu ya baci. Tsawon 15 minutes karima tana bincike amma bataga komai ba hankalinta yayi mugun tashi. ayyanawa take cikin ranta 'anya kuwa khairi ta kawo file d'akin nan kuwa? "Malama kifito mata a d'aki hakan nan tun kafin ranki ya baci, jiki ba lakka ta fito, her face was dripping with weat, sai sharcewa takeyi da hanunta, tawani maqure gefe tana zare idanu narashin gaskiya. Kallo 1 Alhji yayi mata ya kauda kai yace "Allah ya shiryaki karima, Allah yasa kibar qage arayuwarki. Da qarfi Addawiyya ta amsa "Aminn Abba. Taja jiki asanyaye zatabar parlor Addawiyya tace"Abba aje abincika part dinta itama mugani ko yana can "ohk je ki duba Rabi'a, kuma kibincika dakyau "angama Abba. Hajiya karima tasoma masifa ita tafi qarfin sata don haka ba wanda zai yamutsa mata d'aki. "Ai kam baki isaba madam, yarda kika bincika na wata to kema sai anduba naki, kuma ni da kaina zan jagoranta don haka ke yarinya zo muje. Abdul Hameed ne yake cewa haka donmin tun farkon dramar yana tsaye abakin qofa yana kallo. "Alhaji karabani da d'anka tun kafin in d'au mataki akanshi, tace cikin hargagi. Bai kula taba yace "Abdul kuje kuduba, ke kuma karima dawo ki zauna har su dawo, zatayi magana ya daka mata wani tsawa bashiri ta dawo ta zube bisa kujera tana faman hararan Hindu. Acikin 5 minutes suka dawo d'auke da file suka miqawa Alhaji. Tuni hajiya karima tasoma rantsuwa tana hawaye, wai baki suka had'a suka qulla mata sharri. Kad'a kansa kawai Alhaji muktar yayi tare da ficewa zuwa part d'insa batare da yace komi ba, Abdul hameed yamara mishi baya. Addawiyya ta dubi hajiya Karima ta sheqe da dariya tace "inzaka gina ramin mungunta to ginashi kad'an don gudun wata rana zai iya zurmawa da kai ciki, ta qara kwashewa da dariya. "Dani kikeyin zancen yarinya, zakiga yarda zan maidake "uhmm hajjaju ma abociyan sabon Allah, to ki rubuta ki ajiye ni Addawiyya badai mutum ba sai dai Allah, kuma kisani ni da kaina na kai miki file d'in d'akinki kamar yarda kika turo fingilallaliyar 'yarki ta kawo nan, don haka ina baki shawara kada kibari kicigaba shege kafasa. Cike da fusata Hajiya Karima ta kawo mata wani mari taji anriqe mata hannu gam koda ta juyo tayi arba da Haydar yayi mugun had'e rai, cikin kakkauran voice yace "fice da arzi ko in baki mamaki. Kafin kace me tafice har tana tumtube, sabida sosai take shakkan Haydar fiye da kowa agidan hatta Alhajin kuwa. "Aunty please kidaina biyewa sokuwan matan nan kuna fad'a kinji? "Insha Allahu zan kiyaye Haydar "madallah, ya juya yafice baiko duba inda Addawiyya take ba. Gaban ta yariqa bugawa fat!! fat!!, asannu ta zame jikinta tashige room tana maijin wani yanayi wanda tarasa gano ko miye shi. Da dare suna cin abinci, Addawiyya tace da Hindu "aunty H. Matar can fa tayi mugun tsorata da ni, bazata qara marmarin qulla miki sharri ba "uhmm autan ummi wallahi lamarin matar nan yasoma isata, amma yanzu nayanke shawara nabar sakeyi mata shiru balle ta zaci tsoronta nakeji. "yawwa aunty, gara kiriqa zare musu ita da 'yarta "kedai bari ai komi yazo qarshe, zasu sha mamaki na. Wshe gari tana part d'in hajja suna hiransu cikin nushad'i ita da hajja, khairi ta shigo bako sallama, ta dage ta dallawa Addawiyya mari, ko kafin ta sauke hannunta Addawiyya ta maida mata da martani kuma bata tsaya a 1 ba a'a cigaba tayi da dalla mata zafafan maruka, Abdul Hameed yana tsaye yana irgawa har sai da tayi mata hawa 12 kwarara sanan ta dakata. Tuni khairi da zube tana tsala ihu, face d'inta kuwa har ya kumbura. A. Hameed yasoma dariya har da riqe ciki, yace "very good beauty, take my phone as a gift, ya tako ya ya fidda sim da m.card d'insa ya d'ora mata phone d'in ajikinta, tabi wayar da kallo taga Apple ce ash calour, ta d'ago tana kallonshi ya sakar mata murmushi yana yi mata jinjina da hannu, ya d'ora da cewa"najima ina son ganin wanda zai cimin uwar shegiyan yarinyan nan sai yau Allah ya kawoki don haka tashi ma yanzu muje shopping domin jindad'in abinda kikayi jiya da yau dole in karramaki ainun. "Gidanku nace Hameedu, hajja tace dashi tare da yi masa daquwa, ta kuma cewa "amma kai kam anyi wofi mara raba fad'a sai zigawa. Dariya ya saki tare da janyo hannun Addawiyya yace "oyo come on beauty mubarwa wannan old woman d'in matsuguninta taci tsiyarta ita 1. "Qaniyar kace zataci tsiyarta ba ni ba, yana dariya suka barmara d'akin. Kamar doluwa Addawiyya tabiyo bayanshi, suna shiga part d'in Hindu sukayi kicibis da Haydar. Wani fad'uwan gaba ya kawowa Addawiyya ziyaran bazata, tayi sauri dafe qirjinta tana kwama numfashi, "wash ta furta ahankali. "Kai dai bakajin magana ko? "To minayi kuma uban yan sa ido? "Hameed wallahi zancima qaniya fa, inbanda iskanci kasan kana da aiki a hospital amma tazo gida ka rashe sannan kuma ka kashe wayarka don tsaban rainin wayau. Sai da yashafi sumar kansa yana dariya ya amsa "to second Abbana ayimin affuwa bazan sake ba oga Ali gadanga qusar yaqi. Dukan wasa ya kaiwa kad'an Hameed tare da ja mishi kunni, sannan ya wuce yana murmushi. Da sauri ya juya zai bishi tayi hanzarin tura mishi phone d'insa a aljihun wandonsa ta baya ta ruga ciki da gudu. Dariya ya saki kad'an ya furta "zanzo miki da sabuwa dal anjima beauty. "Aunty yana da kyau sosai harma yafi Hameed kyau amma dai suna mugun kama da juna kamar 'yan biyu. "Eh sosai suke kama da juna kuma Aliyu haydar shi ne babba da Abdul Hameed. "Taf ai kam Hameed yafishi jikin girma sosai "ko, autan ummi? "Eh, Allah yafishi har tsawo, shi dai haskene kad'an zai nuna mishi "to kodai kina ciki ne? Oya fad'amin wane ne gwanin naki cikinsu? Dafe kanta tayi kamar zatayi kuka tace "Wayyo aunty H. Amma Kingama dani wallahi. Dariya Hindu tasaka mata tana shirin yin magana suka tsinkayi hayaniyar hajiya karima, "tofa ni Hindu nashiga uku!!!! "Kai aunty H. Kina bada mata wallahi. "Ina kike? gayyar tsiya mai siffan aljannu Wallahi yau ko ni ko ku, zanga uban da ya d'aure muku gindi a gidannan da har zaki kusa sumarmin da 'ya don kawai tazo shashin kakanta. Kalllon tuhuma Hindu ta saukewa Addawiyya, tayi saurin sauke kanta qasa tana motsa yatsun hannunta tana kuma dariya qasa2. *mrs j moon* [1/11, 4:47 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *27* Kunninta ta kama ta matse da kyau "oya fad'amin mi kikayiwa 'yar muta ne? Kukan shagwaba Addawiyya ta saki har da hawaye, da sauri hindu ta sakar mata kunni, tana cewa "ayya sorry qanwata da zafi ko? "Eh aunty "to affuwan kinji? "Uhm! Uhm!! Ni bakimkin komiba "ina sonki autan ummi "nima ina sonki sosai aunty H. Uwar ta gari. "Ja'iran banza to waye ba ta gari ba? ceqar hajiya karima wacce ta kaicinsu tuni yagama cikata ji take kamar ta bisu da duka. juyowa Addawiyya tayi ta sakarwa hajiya karima harara, ahasale tayo kanta da bugu, hindu ta tareta da hanzari "hajiya ya isheki abinda kikemin agidan nan, ki kama ragowar girmanki dayarage, tun kafin ya qarasa zubewa a idanuna tam. "Bazan kamaba kinji ko? kiyi duk abinda kike da niyya, gaiyar tsiya kawai, jinin hatsabibai, masu mugun abu, to wallahi dani kuke zancen, kusani ni karima naci dubu sai ceto ballantana ku qananan k'wari, na d'auki aniyar bazan bar kowa ya shaqata ba a cikin ku saina baku mamaki matuqa. Tsaki Hindu taja "Allah shine gatanmu hajiya ke baki isa kiyi mana komi ba sai da izininsa kuma maji roqon bayine shi don haka mugun nufinki sai dai ya qare mikk can amma mu kam muriqe babban takobin yaqi wato addu'a. "Zaki gani yarinya "naga Alkhairi. Ta kalli Addawiyya cikin had'e gira tace "Autan ummi mi kikama 'yarta? "Mari na tayi ni kam nayi mata hawa 12, kuma ko yanzu ta kuma zuwa part d'in nan sai nayi mata hawa 24 wanda sai ta suma, in kuma kina ganin wasa nakeyi ki turota ki sha kallo, ta qarasa tana yiwa hajiya karima kallon tabbatarwa. Baki sake hajiya karima take kallon 'yar qaramar yarinya tana fad'a mata magana amma takasa cewa komi, domin zuwa yanzu lamarin yarinyar yasoma bata tsoro sosai. "Ficemin a parlor ko in baki mamaki, wawiya kawai. "Ni ce wawiyar Hindatu? "Eh, har wofima kece, mara tunani. "Qara mata da shasha sha, doluwa wanda girmanta bai mata komi ba sai mai data mashirmanciya da yayi. Alh. Muktar ne yake fad'an haka sanda yafito daga room d'inshi, ko su hindu basu san yana ciki ba sabida tabaya ya shiga. "Alhaji, ni kake watsawa qasa a idanu haka gaban wad'an nan banzayen? Tasss!!! Sautin marin da Alh. Yayi wa hajiya karima kenan yakuma nuna mata qofa yace "get out ko in miki abinda yafi haka. Afusace tayi waje tana cewa "had'uwarmu da ku bazai muku kyau ba. Dariyan Addawiyya ta ki da qarfi duk don hajiyan tajiyota kuma taji d'in. "Dear bana ce dake kada ki kuma kulata ba? "Affuwan Abban Hameed kaga wacce ta tabota nan, ta nuna Addawiyya. "Uhm Rabi'a mi ya had'aki da ita? Duk abinda yafaru ta fad'a mishi. Yaja numfashi yace "kinmin dai2 don khairi bata da kunya sam, ta rainamin uwa sosai amma zan d'auki mataki sosai akai, shi kuma Hameed zanci qaniyarshi mai makon ya raba sai ya kuma zigawa, kai halin Hameed sai shi, sannan ni da kaina nabaki umurni duk sanda takuma gigin tabaki kiyi mata duka wanda bazata taba mancewa da keba, kinji? "Tam Abba. A'a Abban Hameed ba'a haka kada ka zuga autan ummi tayi aika aika, abinda yafi dai ka tarasu kayi musu nasiha tunda dukkansu yarinta yana damunsu. "To zan duba yiwuwar hakan maman 2. Kauda kanta tayi gyefe tana murmushi. Nan ya zauna yakuma yi musu hasiha sosai. "Beauty!! Beauty!!! Yashigo yana kwallawa Addawiyya kira, ita kam tana zaune a parlor tana buga game a laptop d'in hindu. Zama yayi gefenta tare da rufe laptop d'in "yakinaji ina kiranki kikaqi amsawa? Sai da ta juya mishi manyan idanuta san nan ta amsa kamar mai ciwon hak'ori "banzaci nice keda suna hakan ba. Kallonta yakeyi bako qirtawa, ta miqe ta shige bedroom tabar mishi wurin. Tsaki yaja mai sauti ya ture laptop d'in gefe ya miqe ya fice bayan ya ajiye mata kwalin sabuwar wayarta da yasayo mata zai bata amma tawani tsaya yi mishi yanga, acewarshi. Ni ne yarinyar nan zata yima yanga? lallai kuwa zan fita harkanta don kada taga kamar ina sonta ne, wani tsakin ya kuma ja, afili ya furta "ko cika budurwa bata gama yiba amma ta san kan iskaranci haka. Haydar ya dubeshi ya tabe baki ya miqe ya shige bedroom d'inshi, da harara Hameed yabi bayanshi yanajin kamar yabishi ya rufeshi da duka na halin ko'inkula da yake nunawa mutum in dai balamarinsa bane to baruwanshi ko mi zakayi bazai tambayeka ba sai indai kaine ka bara kasanar dashi to zai saurareka shima bawani abin arzikin da zai tabuka sai dai kalmar yi sorry, kalmar datake mugun batawa Hameed rai kenan duk sanda ya fad'a mishi ita. Ranar sunday da yammaci Addawiyya tashirya zata koma gida, Hindu ta rakota har bakin mota tana jadda mata zatayi kewarta sosai. "Aunty kada kidamu ina tare da ke ai, komi ya shige miki duhu ki kirani awayar ummi zan warware miki "tam, Allah bar kauna "Amin. Sai da ta gyara zama a cikin motar sannan ta miqowa Hindu ledar da Hameed ya ajiye mata jiya wacce yake d'auke da sabuwar waya ta kece raini. "kibashi kayarshi, kice masa Abbiena zai sayamin in lokaci yayi kuma ina bata mishi rai yayi haquri. Amsa Hindu tayi batare da tace qalaba ta. Suna d'agawa juna hannu har tafice get. "Aunty mike damun sistern ki? "Babu komi "to minayi mata data kasa amsan kyau tata? Ko dai tayi mata qarama ce sai na sanja mata wanda ta fita komai? "A'a babu ko 1 Hameed, inaga dai sabida Abbie yace sai ta soma university zata soma riqe phone shine yasa taqi amsar gift d'inka. "Uhmm tam zanko ajiye mata har sai ta soma jami'ar. Dariya Hindu ta saki tace "azubo maka abincin ne? Ta kauda zancen "No am ok, yanzu naci snacks a wurin Ya Haydar "ohk to kaci anjima ai "eh, zanci insha Allah. Gyara zama yayi ya koma serious yace "aunty ina son inyi aure, wacce yarinya kikaga ya dace ta zamo abokiyar rayuwata? "To pah!! Hameed ni kam bansan zabin da ranka ke soba "aunty bana da zabi sai wanda kika zabamin domin mai yanayin rayuwarki nake so wacce bata da hayaniya ga iya tattali da natsuwa, ko da kuwa cikin qanninki ne ina muradi. shiru Hindu tayi tana nazari zuwa can tace "bana da qanni sai Addawiyya, ita kuma a kwai d'an aboki Abbie dayake sonta. Ya mutsa fuska Hameed yayi kamar mace yace "a'a nima bana rajinta, kidai nemomin wata koda cikin students d'inki ne amma mai aji da kyau kuma mature enough nake so ba yarinya qara irin qanwarki ba Addawiy take ko wa? Dariya tayi sosai. "To Hameed zan duba nagani, amma hakiqa ka had'ani da aiki. Dariya yasaka tare da miqewa yace "kawo saqon da zan kaiwa su Abbie don yau zanje nagansu duk da basu sanniba "aiko suna ganika zasu gane daga inda kazo, sabida kamannin Abbanka dazasu gani atare da kai. Aunty hoo, Ya haydar shine ziryan Abba amma ni hajja nabiyo, "haka dai kace amma sosai kuke kama da juna ku duka hud'un. Ya shafi sajansa ya amsa "To nayarda Aunty, saura ki haifo mana brothers nd sisters masu kama da ke, kinga an surka kenan. "Uhmmm tace, tare da miqe tanufi room d'inta saida ta kusa shiga tajuyo tace "agaishemin dasu Abbie sosai, acewa ummie tayimin dambun zogale ka zomin dashi, ta zubamin man shanu ne ba man gyad'a ba. "Ohk don't worry I'll tell her. "Thanks, se kadawo, ka sayomin yalo farare tas nake so. "Angama our special mummy. Nuna shi tayi da yatsa tana murmushi ta shige ciki. "That's why i luv u too much aunty, kina da kirki ga hankali da natsuwa, Abba yayi dacen mata yanzu, Allah yaji qan ummanmu da rahama yabata aljanna mad'aukakiya. "Amin bros. Haydar ya amsa mishi. Juyowa yayi ya rungume d'an uwan nashi sai kuma ya saki kuka mara sauti. Bubbuga bayanshi Haydar yakeyi asannu kuma yanayi mishi magana qasa qasa da alama haquri yake bashi. *mrs j moon* [1/12, 11:27 AM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *28* Parking sukayi a daf da bakin get, Hameed ya fito yayi nocking, get man ya lek'o yana tamabayar waye? "Baba barka da hantsi, yace dashi "barka kadai samari, wakake nema? "Mai gidan, dafatan yana nan? "Eh, yana ciki, bari nayi mishi magana, "ohk nagode baba, "bakomi yaro, amma ace wane ke nemanshi? "Kace jikanshi ne "to jirani a nan. Tare suka iso wurin Abbaie, yana ganinsu yaga ne ko daga ina suke, cikin fara'a ya miqa misu hannu tare da sallama duk suka noqe kansu qasa suka ce atare "munsameka lafiya? "Lafiya lau, ku shigo ciki man, kwa tsaya awaje kamar baqi. Bayanshi suka biyo suna qus qus, "yana da kirki kamar aunty Hindu, "to suda sarkin zance kasoma ba "ya haydar zan zarema halina fa yanzu kada kaga wai munzo baqunta tam. Banza Haydar yayi mishi, ya qara sauri ya cimma Abbie suka jera, harara Hameed yabi kyeyarshi da shi sannan ya qara da d'an gudu ya cimmasu. Tana kwance bisa doguwa kujera face d'inta yana kallon ceiling idanunta lumshe kamar mai barci. Sallamar su Abbie yayi daidai ya saukan wani dum!! Sataji a qirjinta ta dafe wuri tare da furta "washh Allah, awahale ta amsawa su Abbie sallamar, ganin su Hameed atare dashi yasa ta miqe zaune da sauri tana neman inda hularta ta fad'a. Kamar mara gaskiya ta zame ta gaishesu tana wani matse jikinta wuri d'aya. Hameed ne ya amsa mata yayin da Haydar yazuba mata idanu yanajin bugun zuciyarsa ta canja a cikin second. Saukawar ummi daga upstairs yabawa Addawiyya damar tashi da sauri ta haye sama ta bace kamar walkiya, jinkina tayi da door tana kwama numfashi har lokacin hannayenta suna dafe da qirjinta "washh ni Rabi'atu mike faruwa dani? Karo na 3 kenan dana kejin haka da zaran na ganshi, oh Allah ka warwaremin abinda ke boye. "Auta kina ina? "Gani ummi "to fito ki had'awa su Hameed abinci ki miqa musu "to ummi. Sai da ta shaqe wani babban tire da abinci kala2, ta iso parlor n ta jera musu kan wani table mai d'an fad'i. Tana gamawa ta d'ago ta dubi gefen da Hameed yake tace "Bissimillanku "tam mungode, ya amsa. Ta gefen idanu ta kai dubanta inda Haydar yake, caraf suka had'a idanu, gabanta ya buga tayi sauri kauda kanta tana kiran sunar Allah a cikin ranta. "Ke!! Tafi kisanja dress. Idanu ta zuba mishi quri, ya watsa mata harara "ko bakiji mi nace bane? Sauke kanta qasa tayi tare da juyawa tabar wurin batare datace dashi qalaba. "Miye haka bros? Ko kamanta ita d'in ba khairi bace abin ikonta ka? Bayan sa ya jingina sosai a kujeran dayake zaune ya lumshe idanunsa yana wani sakin murmushi. Tsaki Hameed yaja ya kuma cewa "to tun wuri kacire idanunka akan yarinyar mutane, kuma nibanga aibun shigarta ba "in anqi fa? ya amsa mishi cikin isa. "Duka zaka sha wurin samarinta. Wani zabura Haydar yayi yace "kai! banson tanbad'a fa, 'yar wannan yarinyar ce take da samari? "Uhmm naka wasa ne bros. Komawa yayi ya gyara zamansa, Hameed yabishi da kallo cike da zargi. Sai da ya bud'e kwankwanin Amstel ya zuba awani qaramin glas cup ya kai bakinsa ya sha kamar rabi sannan ya dubi Haydar "mike damun ka? Kai tsaye ya amsa mishi "so da k'aunarta yayimin shigan bazata haka nan atake nakejin matsanancin kishinta tunda idanuna ya hangomin shigar dake jikinta daga shigowarmu. Kut!!! Sautin had'iyan yamun da Hameed yayi kenan sai kuma yasoma tari zuwa can ya lafa mishi, Haydar ya miqa mishi ruwa ya sha yana ta jera mishk sorry, shikam sai gyada mishi kai yakeyi. Ya lalibo handkerchief ya miqa mishi, ganin yarda yaketa zufa kamar ya had'iya kunama. Idanun Haydar ya tsareshi da su yace "Mike faruwa Hameed? Ko kaima zuciyarka ta kamu da son tane? Cikin hanzari ya amsa "A'a bros, ni batayiminba sam kuma bazata taba yimin ba "topah, minyakawo wad'annan zancen haka? "Uhmm ya Haydar mubar zancen nan sai in mun isa gida tukunna "ohk, amma ina son kada ka boyemin komi dake ranka, in har kana sonta ka sanar dani tun wuri "ni kam koda zan so mace bazanso kamar Addawiy ba sabida Allah tayimin qarama da aure "kai banson iskanci ita d'ince tayi qaramar? Yana dariya ya amsa "sosai ma, kofa secondary school bata gama ba "to sai me? "Sai bakomi mr. luv a cikin kallo d'aya, murmushi mai sauti ya saki "zanci gidanku ne yaro "uhm 2nd Abba sannu. Direct gaban mirror ta isa ta zame after dress d'in data sanya kafinta fito warta tana qarewa kayan jikinta kallo, T-shirt ce mai dogon hannu amma ta kamata sosai sai sket wanda bai gama kai gwaiwarta ba, tsaki taja tace "shegen kallon qurillansa har yagano kayan nan ajikina, ta kuma jan tsaki ta koma bakin bed ta zauna ta dafe kanta. "Uncle kazo inji labarin wannan mutumin da zuciyata take fad'awa halin firgici duk sanda tayi arba dashi. Qamshin turarensa tajiyo daf da ita, ta juya cikin zumud'i sai kuma taga wayam ta tura baki cikin shagwaba tace "haba uncle minayi maka karage zuwamin yanzu, alhalin kasan ina buqatan bayanai masu yawa atare da kai, to Allah nikam mun kwance amintan daga yau. "Mai babban suna tashi kije umminki tana jiranki a madafi. "Banzuwa ni sai ka sanar dani labarin wad'ancan mazajen musamman Ali. "To zan sanar dake ko mai amma bayan zuba, ciki shagwaba tace "uhmm don Allah dai uncle kafad'amin yanzu. "Auta ina kike ne? "Gani ummi "oya zo ki yima Hindu dambu su Haydar zasu tafi mata da shi donka ki hamzarta ki gama akan lokaci komi na had'insa yana kitchen zogalen ne yanzu Audu zai d'ebo na gyara miki "to ummi gani nan zuwa. Koda ta fito parlor n ko kallon inda suke zaune bata yiba amma tanaji ajikinta kallonta sukeyi. "Bros gafa ta can ta fito, yimaza kabita kasoma kafa gabnatinka tun yanzu "kai fa d'an air ne Hammed, kai haka kayi sanda ka soma son Najiba, ina ce aji kayi taja har yanzu kaqi bada kai bori ya hau. "Kam bala'i!! Ya haydar nine nake son wannan 'yar buhun yarinyan? mai shegen yawon bin club kamar wanda iyalan sarkin aljannun ibilisai su kayiwa fitsari akai. Murmushi mai sauti Haydar ya saki domin shi bai fiye dariya ba. "Hameed Allah ya shirya ka kai kam, "Amin tare da kai. "Yanzu Najiban ce take bin club don tsaban sharrin ka? "Ba sharri sai gaskiya domin ni naganta da idanuna ta shiga club "to kasani wani abu taje amsa "a cikin club d'in? "Eh "in jikina duka kunne ne bazan taba yarda da zancen ba, don haka Allah kada ka kuma had'ani da mashir maciya yarinyan can "to nabari qanina, dama tsokanarka nakeyi "kaiko bros, Hameed yanunashi da pinger. Duk suka saka dariya. Cikin 1hr Addawiyya tagama gambun, sai gamshi yake tashi ta juye akula babba ta zuba soyayyiyar man shanun awani roba qarami ta jefa cikin kulan ta saka cikin leda ta d'auka zuwa parlor. Suna ta hira da ummi tare da Abbie kamar sun saba da juna amma Hameed shine jigon maganar domin Haydar iya kanshi murmushi sai eh ko a'a in ansakoshi ciki. Ajiyewa tayi zata bar wurin da sauri, Hameed yakira sunarta ta dawo da baya tana kallonshi. Ya sakar mata murshi ya dubi ummi yace "ummi autanki bata da kirki, kijiba tun zuwarmu gidan nan taqi zama damu ayi hira sai gudunmu takeyi kamar taga dodonni sannan mu kuma bama yi mata haka duk in tazo gidanmu. "Auta baki kyauta ba kam, ai baqonka Annabinka sabida haka yimaza ki basu hak'uri. Kamar zata fasa ihu tace "kuyi sorry to, tana fad'an haka ta hau upstairs da sauri har tana hard'ewa da sket d'in atamfan Kayan da ta sanja. Haydar yabi bayanta da kallo yana murmushi, Hameed ya take mishi qafafu da k'arfi, ya saki ajiyar zuciya da qarfi wanda sai da su Abbie suka kalleshi, ya sauke kanshi qasa cike da kunya sai kuma ya miqe yayiwa su Abbie sallama shima Hameed sallmar yayi musu Abbie ya rakosu har bakin motarsu, saida yaga bacewar motarsu sannan yashigo gida cike da yabon halinsu na kirki. *mrs j moon* [1/13, 1:27 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *29* Tana isa room d'inta ta zube bisa gado tasoma juye2 kamar mai ciwon ciki zuwa can kuma ta miqe da sauri ta sauko qasa, direct kujeran dasuka tashi ta isa ta kwanta ta qamqame jikinta kamar maijin sanyi. Qasa qasa takejin dariyan uncle takulle idanunta tana tura baki, ahankali take furta "mun bata da kai, baruwa da kai, don haka kayi tafiyar ehe. Iska taji yatashi fiyy, ta bude idanu tana hararan inda taji motsin tashin iskan. Tanajin motsin isawar ummi tayi saurin sake kulle eyes d'inta. "Auta baki da lafiya ne? Da kika kwanta haka kamar maijin sanyi. Idanunta yana kulle ta amsa"Lafiyata lau ummi, ina dai jin kasala ce "ayya inaga shawara take damunki, bari na tafa miki maganin da Abbienki yazo dashi rannan. Shiru tayi kar wacce barci ya d'auka, ganin haka ummi ta shafi face d'inta cike da kulawa tace "atashi lafiya autana. ***** Hameed ya dubi Haydar yaja tsuka mara sauti ya maida hankalinshi bisa titi zuwa can yakuma duban Haydar ya tabe baki. Haydar ya bud'e idanushi dasu lumshe ya zubawa Hameed na 'yan dqiqu sannan yace "inkasake kallona sai na cirema eye 1. "Uhmm sai kasoma cire naka sannan kadawo nawa, banza yayi mishi tare da komawa ya lafe cikin seat. "Uhmm ya Haydar kenan wallahi mamakinka ya isheni yau sosai "kamar na mi? Ya tambaye cikin rashin kula. "Na haukacewar da zuciyanka tayi akan Addawiy, ka koma mara aji, kamar bakaine mata 'yank'walisa da class suke fad'a akan kaba amma kaqi kulasu amma yanzu akaron banza ka mace akan kwaila wacce bata gama cika budurwa ba. "Hameed! Yakira sunarshi cikin kaushin murya. "Uhmm my name. Har yabud'e baki zaiyi magana sai kuma ya koma ya kwanta tare da tura yatsunsa cikin sumar kanshi. "Uhmm kaga Waziri ba kafi mai abu iko. "Kallon Hameed yayi cike da son qarin bayani game da maganar shi. Driving yacigaba dayi yaqi kallo inda Haydar yake balle ya fahinci manufarshi. Shi kuma miskilanci yahanashi ya tambayeshi, haka yayi ta mai maita kalmar aranshi har suka iso gida. Hameed direct parlorn Hindu ya wuce yayin da Haydar ya nufi part d'insu. Yana wanka zuciyarshi tana gargad'inshi akan kada ya afkawa abinda zai tona mishi asirin dake binne wanda dagashi sai mahaliccinsa suka sanda shi, wani kuma shashin ya amsa da ka sota har yakaiku ga aure juna tanan ne zaka tabbatar da zarginka. Ajiyar zuciya yaja mai qarfi ya furta "lallai ina sonki sosai Rabi'atul Addawiyya, Allah yasa ki soni da gaskiya ki kuma iya riqemin sirrina, Amin. A parlor ya cimma Hameed ya barrarraje sai kwasan dambu yakeyi, da sauri ya iso ya d'auke plate d'in ya ruga da gudu suka soma zagaje parlorn Hameed yana cewa "ya Ali kabani abincina, shi kuma yana fad'in "anqi badawan, kai da kace mata kwaila sai kaje yanzu wurin balugun wa balagun ta dafama. Hameed yanaji yana gani Haydar ya cinye dambu ya hana shi, cike dajin haushi yace "zan baka mamaki, don sai na kawo maka wacce za kayi zuban yamu don kyau, cika, diri, sura tare da girma irin ta isassun mata. "Eh, naji dai, kuma wuce nan, namajo kawai, jeka garin neman qiba ka samo rama. "Ina ruwanka, koma mizan samo "kai kaga tafiyata in duba tsohuwata hajja, yafice d'auke da empty plate d'in dambun. Afusace Hameed ya fito zuwa part d'in Hindu domin samo wani dambun sabida sosai yayi mishi dad'i. *** Cikin barci taji ana jan mata baki ta bud'e idanunta ta saukesu bisa Annur wanda yake ta bangala mata dariya, d'aukanshi tayi cike da murna tace "my handsome ina miminka? "Yala ummi daki. Dariya tasaka mishi ta ja kumatunshi "kai Abbiena wai sai yaushe zaka iya magana ne? gashi har kaciki 2yrs. Cikin shirmen yarinta ya amsa "yau aunty adda, dariya ta kuma sawa tamiqe sabe dashi tanufi upstairs. "Adda Salma naga kin qara haskene kamar tasa... "Qaniyarki Addawiy, baki da kunya ko? Cikin dariya ta amsa "ni kam ke da kunya tunda ko kallon maza ban iya d'aga eyes d'ina inyishi sai dai su suyi ta kallo na kamar sun sami tv. "Oh my Addawiy soyayya kika soma kenan, oya gist me , tana karkad'e kunninta. Cike dajin kunyar maganar Addawiyya ta juya mata baya tace "nikam Allah ya tsarene fad'awa wahala. Kyal kyalewa da dariya Salma tayi tana cew "very soon wahala zatayi miki kamun kazar kuku yarinya. "Bakinki ya sari legs d'in mijinki ya daina zuwa kallon ball. "Amin Amin my Addawiy, wallahi kinsan kuwa abin yana bani haushi sosai, ya zauna ya kalla agida amma yaqi innafiye qorafi yace kallo tare da friends yafi dad'i wai anayi na ihu hakan yana shashi nushad'i. "Uhmm Allah dai ya kyauta. "Amin. ***Kwanci tashi ba wuya gashi Addawiyya ta kammala secondary har tasoma zuwa computer training center kafin result ya fito. Yau tadawo gida agajiye ta zube a parlor ta dafe kanta datakejin kamar zaiyi mata ciwo. "Mai babban suna mazumunciyarki ta haihu yanzu ta sami 'yan biyu dukansu maza, yi sauri ki isa tun kafin makiran matar can ta kashe mata su da guba. Wani zabura tayi tafice waje da gudu tana kwallawa driver kira ya iso a rud'e, tace "gidan aunty Hindu, da sauri yayi reverse suka fice. Ummi tafito daga cikin tayo compound da sauri sakamakon jin ihun kiran da Addawiyya keyiwa driver, don ita ba tasan ta dawo ba, jin hayaniyarta tayi kawai. Ko kafin ta iso sun fice, asanyaye ta qarawa wurin get man tace "baba mike faruwa? Cikin girmamawa ya amsa " Hajiya naji tana kiran gidan Hajiya Hindu zasuje "to ko lafiya? "Wallahi bansani "ok to Allah yasa muji Alkhairi "Amin Hajiya. Jiki ba k'wari ummi takoma ciki, tana isa wayar na qara alamar kira, ganin sumar mijin Hindu yasa jikinta d'aukan rawa. Hamdalah tayi ta jerawa sanda taji cewa Hindu ta sauka lafiya kuma a gida. Sai sannan tagano sanadin fitar Addawiyya agigice. "Auta manya halinta sai ita, mai makon ta tsaya ta sanar dani sai kawai tafice kamar yaqi. Ko gama gyara perking bai yiba ta balle door d'in tafice da gudu bako gyale jikinta. Shigarta parlorn yayi Dai dai d'aga feeder da Hajiya karima tayi mai cike da madara zata bawa hussain. Wani tsalle ta doka kamar 'yar chana ta buge feedern ya fad'i qasa murfin ya bud'e yasoma zubewa tayi sauri d'awa gudun kada yazube duka tarasa tujja. Jikin Hajiya karima ba'inda baya rawa don tsaban firgici. "Nashiga uku! Anya yarinyar nan mutunce kuwa? Tafurta hakan cikin rawar baki. Wani kallo Addawiyya ta sauke mata sannan ta d'auki yaron daga jikinta tace "ki tanaji bayanan da zakiyiwa polices, ta shige bedroom din Hindu tabarta nan zaune kamar gari. *mrs j moon* [1/14, 12:25 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATU ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *Shafin na masoya ne dake dukkanin lungu da saqo, ku sani sosai nakejin dad'in yabawarku tare da addu'o,in ku agareni, domin haka shi yake qaramin qarfin guiwa, godiya nake agareku sosai fans. Allah yabar kauna, luv u always* 😍😘 *30* Turus Hindu tayi sanda ta fito daga toilet ta cimma Addawiyya zaune hawaye jage jage a fuskanta. Cikin rawar jiki ta isa inda take zaune ta dafa kad'anta tace "autan ummi mi aka miki? Mai makon ta amsa mata sai ta fashe da kuka mai sauti. Gaban Hindu ya yanke ya fad'i rass!!! Ta zauna gefenta jiki ba k'wari ta kamo hannunta ta rintse qam tace "fad'amin damuwarki Addawiyya, ko bakiso nasami qaruwan twins bane? Da sauri ta girgiza kai tana jan hanci tace "tunani nake da ace hussain ya rasu ko ya zakiji aranki. Cikin daburcewa Hindu tace "autan ummi wani abu ya farune? "Eh, ta amsa mata tare da bata labarin tundaga sanka taji uncle Habibullah yayi mata magana zuwa sanda ta ceci jaririn ahannun hajiya karima ta d'ora da cewa "amma ina mai roqonki dan Allah tare da manzonsa kada kisanar da kowa zancen, ita da kanta zata fad'a da bakinta intaji azaba. "Autan ummi kinaganin rashin d'aukan matakin ba zai kuma bata dama wata rana tadowo ta cutar dasu ba? Jim tayi tana nazari "bana tunanin zata kuma samun kuzarin sake cutar dasu, sabida yanzu haka tana cikin rud'anin kamata danayi tare da fargaba kada Alhaji yaji kuma tana mugun tsoron 'yan sanda, tana can ana fetsa yawo. Tagarasa maganar cike da dariyan mugunta, hawayen daya maqale yazubo a fuskanta ta sa hannu ta share tana cigaba da dariya. Kama kunninta Hindu tayi tace Allah shiryamin ke Addawiy "Amin. " Allah yacigaba dabamu kariya gabaki d'aya. "Amin.aunty shine addu'ar da yadace muyi tayi kawai domin ita kaddaran Allah wanzarciya ce inta tashi zuwa babu tsimi babu daraba sai ta ilahu. Atare Salma da Ummi suka iso, sai murna sukeyi suna hamdalah ga Allah. Addawiyya tun shigowarsu dasun had'a idanu da Salma sai ta sa dariya. Ummi ta dubeta tayi mata daquwa "kinci gidanku auta, yazakisa mutane agaba kiyi tayi musu dariya kamar wata mai tanbotsai. Dariya takuma kwashewa dashi har da riqe ciki, ummi ta zabura tayo kanta ta kwasa da gudu tabar room d'in. "Ummi kibarni da ita, nasa abinda take ma dariya kuma zanci mutuncinta inbata kiyayeni. "Oh to kunfi kusa ai, nawa idanu. Hindu ta sauke kallonta bisa tumbin Salma ta kauda kanta gefe tana dariya qasa2 tace "eh dole autan ummi tayi ta dariyan murna ashe mun kusa samun wani qaruwan ne. Cike dajin kunya Salma ta miqe ta fad'a toilet, suka bita da dariya. "Allah yaraba lafiya, "Allahumma Amin umminmu. Mugun karo sukayi da juna ta kwalla qara ta zube aqasa, domin tayi mugun tsorata da ganinsa abazata, cikin hanzari ya d'agata yana kiran "sorry sorry, ta zame jikinta hannunta dafe da qirjinta, tafiya soma yi da baya da baya eyes d'inta yana kanshi har ta shige cikin kitchen. Ya dafe kansa tare da cije labbanshi, ya saki murmushi mai sauti "i really luv u pretty, yafurta ahankali sai kuma ya yamutsa fuska "uhmm Allah kin wuce pretty akomai my heart, beauty zaifi dacewa dake my kwaila sai yasaki dariya ya dungule hannu ya naushi iska yana mai furta"amma fa Hameed d'an air ne, yanzu wannan zankad'ed'iyar budurwan yake kiranta da kwaila? "Eh, Nakiratan mi za'ayi? Kai kwanso ma sunarta daga yanzu. Muryan Hameed ne ya doke kunninsa, ya juyo yana jifanshi da harara. "Mantawa kayi fara ce. "Eh, hakan ma yafi dad'i, naushi ya kai mishi ya kauce da sauri yana dariya. "Zan gyarama zama Allah "uhmm mr love ina saurare. Bai kuma kula shiba ya shige bedroom d'in Hindu d'auke da sallama, Hameed yabi bayanshi yana tsokanar shi. Addawiyya tana shiga cikin kitchen ta jingina da bango idanunta lumshe sai murmishi take dokawa tamotsa labbanta kad'an tace "he is very charming guy, uhmm ina son.... Sai kuma tayi saurin bud'e eyes d'inta ta tafe bakinta tana girgiza kai, jin motsin za'a shigo yasa tayi saurin bud'e qofa tafice ta baya ta nufi part d'in Hajja. Khairi ta cimma zauna tana kallo bata dubi inda takeba ta wuce kitchen inda takejin motsin ana aiki da alama hajja ce. Dogon tsaki khairi taja tace "shishshigi ba kwarjini, banza 'yar maula ka wai. Bataga dawowar ta sai jin saukan mari tayi a face d'inta tassss!!!! Ta dafe wurin tana laliben hanya sabida ganinta ne ya d'auke na wucin gadi, tana ko samun hanya ta d'iba karce har tanajin tuntube yatsarta ta fashe amma ko dubawa batayi ba, burinta ta kawai taga ta tsira daga shan maru kan Addawiyya domin har yanxu bata manta da artabun suba na kwanaki ba. Dariya ta saka har da dafe ciki tana nuna hanyar da khairi tabi da gudu. Hajja ce ta fito d'auke da babban kula, ganin Addawiyya na dariya yasa ta koma kitchen da hamzari jikinta yana kyarma sabida ji tayi sautin dariyar wani iri kamar ba na muta ne ba. Shigowa kitchen d'in tayi anatse hajja taja baya. "Uhmm hajja dariyan nawane yabaki tsoro ko mi? To bara kiji abinda yasani dariya. Tana gama bawa Hajja labari itama tasoma dariya tace "amma Rabi'a kinyi mugun tsorata min qawar hirata. Cikin dariya ta amsa "gyara mata zama nakeyi, kuma yanzu muka soma buga game d'in har sai ta dawo cikin natsuwarta zan sarara mata. "Lallai hakan yayi kyau d'iyar albarka, Allah yabaki sa'ar saita mana tunanita ta bar yiwa mutane fitsara. "Amin hajjajunmu. *****Ranar suna yara suka amsa sunarsu hassan da hussain. Anyi barin naira, mutanen arziki sukayi ta zuwa suna kwasan gara. Hajiya karima kam kamar zata had'iye zuciyarta don tsaban baqin ciki da yayi mata yawa gashi Addawiyya takasa ta tsare ta hanata halaka su kotaji dama dama, sabida dazaran ta doso part d'in Hindu sai wani hucin zafi ya dameta akan dole zata koma tana tsinewa Addawiyya, taje wurin malamanta sun kasa gono dalili afkuwar hakan, hakanan tanaji tana gani aka gama taron suna cike da masara. Alh. Muktar ya biyawa Abbie, ummi, Addawiyya, mushaffa'u, Abba, mama, tare da Salma kujerun makka, yayin da zarar Hindu ta gama wanka yace zasu wuce umrah kuma baza su dawoba har sai sunyi aikin hajji wanda yanzu saura kimanin watani shida asoma tafiya. Labarin yayi mugun jefa hajiya karima cikin rud'ani wanda atake jininta yayi mugun hawa ta yanke jiki ta fad'i aka kwashe sai asibiti, dakyat doctors sukayi nasaran ceto ranta amma fa taji jiki sosai, khairi sai kuka takeyi gunin ban tausayi. Kakan su Hindu mahaifiyar maman su itace take kula da ita tare da yaranta. Hajjama ba'abarta abayaba, ga ummi tana yimata soqo akai akai nakayan gyara da samun ruwa nono sabida Alh. Muktar yace baza'abama yaranshi madara ba nonon uwa yafi komi inganci ajikin jarirai. Ita kam Addawiyya kuwa ta tarewa tayi agidan, islamiyya da computer school duk tana take zuwa ta dawo, ummi tayi mitan har tagaji na tadawo gidan yayi mata girma ita d'aya amma taqi. Sunyi mugun shaquwa na ban mamaki da Hameed yayin da duk sanda suka had'u da Haydar ko taji muryanshi sai gabata yafad'i ga kuma wani tausayinshi datakeji acikin ranta. zuwa lokacin tagama ganewa ta afka kogin son shi abinda take ta boyewa kada kowa yasani domin aganinta baqaramin zubda aji bane mace ta fidda soyayyarta fili ga namiji. Shi kam Haydar yaqi sanar da ita ne sabida ganin yayi kamar tanajin tsoronsa yafiso su saba da juna sosai kamar yarda ta sake da Hameed. Yau tana zaune cikin garden laptop ne agabanta tanayin assignment, gefenta had'ad'd'iyar phone d'inne take ta sauraren cool music, sai gyada kai takeyi abinta cike da nishad'i. Yana zaune a balcony yana aikin kallonta yana doka murmushi, zuciyarshi sai azalzalanshi take da ya isa wurinta amma miskilanci ya hanashi motsawa. Ya kulle eyes d'inshi yana tasbihi cikin ranshi. Hango khairi yayi zaune suna fuskanta juna da alama wani abu take koya mata computer, dubi da yarda yaga take d'agowa time to time tayi mata magana. Mamaki ne ya cikashi, "yaushe khairi tayi hanakali haka da har suka zama qawayen juna? Lallai gaskiyan Hajjace da tace yarinyar tana da tare da wank baiwa wanda bakowa zai gane hakan ba sai tazauna awuri koda na kwanaki biyu ne. Yana nan zaune yana ta aikin kallonsu, wutar qaunarta yanacigaba da ruruwa a ruhinsa, zuwa can yaga sun miqe atare, Addawiyya ta ruga da gudu ta rungume wata budurwa da alama qawarta ce, sai murna sukeyi ita da budurwan, ko kafin ya ankara sun shige cikin gida. Saukowa yayi bi bayansu cike da k'warin gwaiwa. So yake yau su soma qulla alaqa ta abota inyaso da zarar sun saba da juna sosai sai ya samu hanyar sanar da ita sirrin zuciyarshi. *mrs j moon* [1/15, 4:48 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATU ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *Aunty maijidda musa keta dabance agareni kisani kullum comment d'inki yana jefani cikin nishad'i ainun kuma yana qaramin kwarin guiwa sosai. Ina alfahari dake, thanks* 😍😘 *31* Yana shiga parlor n dai dai ta fito daga kitchen d'auke da tire madaidaici shaqe dakayan motsaba baki. Gabanta taji ya fad'i, jikinta yasoma rawa ta tsaya tsak, kanta aqasa, tasan Ali ne yazo wurin tunda taji jikinta ya sanja, baki ta tura tare da d'ago kanta ta dubi qofar shigowa, ta sauke eyes boll d'inta akanshi ya coge tare da hard'e hannayenshi bisa qirjinsa ya zuba mata idanu bako qiftawa, sai ta qara daburcewa gabanta nacigaba da fad'uwa, tayi saurin tasake yin qasa da kanta. Takowa yayi asannu har ya iso inda take tsaye ya miqa hannu ya amshi tire d'in ya matsa daf da kunninta yace "halan ni dodone da kike jin tsorona har jikinki yana rawa haka? Wani yarrrr taji ajikinta, tayi saurin ja baya qara matsowa yayi zata gudu ya take mata qafa ta rintse idanunta dan azaba, ya saki murmushi mai sauti ta bud'e idanun tana hararanshi. "Waww beauty kinfi kyau ahaka, tura baki tayi ta ma rairaice face tace "d'agamin yatsu kada kajimin ciwo. Da sauri ya d'aga mata yana kiran "am sorry bazafi ko? Wani kallo ta sauke mishi tayi gaba yabiyo bayanta yana dariya qasa qasa. Zama tayi gefen maryam tana wani yamutsa fuska, sai tayi mishi mugun kyau ahaka, ya ajiye tire d'in akan table dake gabansu yana qoqarin bud'e robar coke tayi saurin riqe mishi hannu sai kuma ta saki da hanzari tana yarfe yatsunta. Murmushi yayi mai burgewa, yaja baya ya zauna akujeran dake kallonta, ya kai dubanshi inda khairi take zaune, wacce tumd'azu ta sake baki da hanci tana kallon abin al'ajabi, wai ya Haydar ne yake nuna soyayyarshi a zahiri haka bako kunya. "Ke tashi kibawa mutane wuri, kina wani kallon mutane idanu biyu. Maganarshi ya katse mata tunani. Da sauri ta miqe tabar wurin tana dariya, cije labbansa yayi yana bin bayanta da harara. "Uhmm qawarmu kin iso lafiya? Yace da maryam, ta amsa "lafiya lau, ya office da ayyuka? "Alhamdulillah amma ba dad'i kam. "Ayya to Allah tai maka "Amin, thanks. Addawiyya wacce take saurarensu ta motsa sannu cike da class ta soma zubawa maryam drink ta miqa mata sannan ta bud'e container mai d'auke da danbum nama azuba ta tura gabanta tana satan kallon Haydar wanda yayi balance ya zuba mata manyan idanunshi. "Godiya nake aminiyata, maryam tace da ita. Murmushi tayi mata batare datace qalaba. Sosai ta takura da zamanshi a wurin, duk motsin daza tayi eyes d'inshi na kanta, tana son gudu amma ta kasa tashi. Hira suke tayi da maryam kamar sun dad'e da sanin juna, ita dai komi takasa cewa koda kuwa sun sakota cikin hiran iyakarta gyada kai ko girgizawa, tazama kurman qarfi da yaji. Shigowar Hameed yasa ta tashi da sauri tashige bedroom. Dariya Hameed yasa yana nuna Haydar yace "waww nawa yasoma bada assignment kenan, tam Allah yasa ayi nasara. Had'e fuska Haydar yayi tare da wulla mishi harara yace "kaifa banza ne wallahi, gashi nan da zuwanka ka kora mana abokiyar hira ko qawarmu? Murmusawa maryam tayi tare da gyad'a mishi kai. Tabe baki Hameed yayi yamufi dinning area yana cewa "kadai tsaya kallon ruwa kwad'o yayima qafa. ***** "Qawata mi yake faruwa? "Kamar na mi fa? "Tsakaninki da guy d'incan Haydar mana. "Oh babu komi illah zumunci a matsayinshi na d'an mijin aunty Hindu. "Ba wannan nake son jiba, tunda kinfi kowa sani nasan hakan. Miqewa tayi zata shige toilet maryam ta fizgowa ta zauna bashiri. "Miye haka Rano? "Mele ne "uhmm yau dai da jin fad'a kikazo kenan? "Bansani ba. Shiru sukayi kowa da abinda yake saqawa aranshi. Addawiyya ce ta katse shirun tahanyar dafa kafad'an maryam tana cewa "kiyarda dani qawalli Allah babu komi a tsakaninmu hasalima bama magana sam da juna yaune naga yana son kawo qarshen 'yar shariyan dake tsakanmu ni kuma banjin zan iya sakewa da shiba kamar yarda na sake da d'an uwarsa Hameed ba. "Ko akanmi yasa baza ki iya ba? Shiru tayi zuwa can tace "forget kawai qawata. "Uhmm dole kice haka man, tunda kinsan baki da gaskiya "ya salam my Rano minayi kuma? "Boyemin sirrin zuciyarki da kikayi "uhmm ke nifa bangane inda kika dosa ba kam "zakigane yanzu yarinya, xuciyarki ta kamu da sonshi, koba haka bane? Kauda kanta tayi gefe ta amsa kamar mai ciwon hakori "eh, haka ne amma nasan nice nake sonshi, shi bai san inayiba dan haka naboye abin araina sabida gudun kada yagane ya wulaqanta ni, haka nan naqi sanar da kowa ne dan bana son yaji class d'ina ya zube, dafatan kinfahimce ni yanzu. "Eh, na fahimta amma dai ina da qorafi "tami ba? "Ta yarda baki d'aukeni da mahinmanciba, kikayi ta boyemin sirrinki alhalin ni nawa bana iya boye miki, kadafa kimanta kece ta farko da nasoma sanarma had'uwata da my ustaz kuma kika bani shawara mai kyau gashi yanzu inata cin moriyarta, soyayya mai tsabta ya kankama a tsakaninmu dashi. "Am so sorry my lovely friend, bazan qara hidden miki komi nawaba daga yanzu. "Uhmm Allah yasa, "wallahi kinji na rantse bazan kuma ba "tam nayarda "aha thanks besty. Qasa tayi da murya tace "qawata yanzu miye mafita, abinfa yana son zamamin chronic. Dariya maryam tasa sosai har da kwalla zuwa can ta tsagaita tace "aini hakan yayimin sweet ainun, dama na dad'e inayi miki addu'a Allah ya saka miki so mai zafi kiji abinda mukeji ko kyabar mana iskanci akai. Duka ta kawa mata, maryam ta miqe da sauri ta nufi hanyar fita tana cewa "bara naje na sanar dashi, shine kawai bafita. Aguje tabiyo bayanta tana son kamata amma ina harta fice compound. Dawowa d'aki tayi ta dafe kanta tana furta "wayyo ni Rabi'atul Addawiyya nagama yawo, sai kuma ta miqe da sauri ta hau had'a kayanta tana gamawa ta fito parlor janye da trolley d'inta. Rurus taja ta tsaya tana kallon maryam tare da Haydar durqushe gaban aunty Hindu kamar masu neman gafara. Maryam ce tasoma ganinta ta sakar mata murshi tare da kashema ido d'aya ta motsara baki ta furta wata kalma. Harara Addawiyya ta dalla mata, ta saki 'yar dariya ta miqe ta iso inda take tsaye ta kai bakinta kusa da kunninta tace "qawata d game is over, munyi winning dan haka yana cewa kule kice cas. Wani hararan ta kuma doka mata tare da Janye jikinta zata koma ciki "hindu ta kira sunarta ta tsaya batare da ta juyo ba "ki shirya Haydar yanemi alfarka zaki rakashi unguwa yanzu, ga maryam nan sai ku sauketa agida daga nan. Juyowa tayi cike da shagwaba tace "ni gida zan koma yau, nagama had'a kayana yanzu zan wuce, yanemi khairi ta rakashi. "Autan ummi nice zanbaki umurni kikawomin taki na daban? To yayi miki kyau, wuce ki tafi ga hanya nan. Ganin ran Hindu ya baci yasa ta saki trolley d'in qasa ta qarasa gabanta ta zube tahannayenta bisa guiwoyinta, muryanta na rawa tace "don Allah kiyi hak'uri Aunty banufina in bata miki ba, sai dai ina neman alfarma da yayi hakuri zuwa gobe sabida yanzu baifi nan da 10 minutes za'akira sallar magrib, kinga koda zamu dawo sallar ta wucemu kuma maryam kwana zatayi dan mami ta hanata tafiyan dare. Dafa kanta Hindu tayi tana murmushi tace "nafahimceki autan ummi. Dafatan Haydar zaiyi hakuri zuwa goben? "Eh' aunty zanyi, da yau da goben ai duk 1 ne, Allah yakaimu da rai da lafiya "Amin, maryam ta amsa. Sai da yayi nasaran kallon kwayar idanunta ya sakar mata murmushi sannan ya miqe ya fice, tabi bayarshi da kollo tana murmuhin gefen baki. "Uhmm autan ummi angirma ko? Da gudu ta tashi tashige d'akinta, suka saka mata dariya, kaka Abu ta fito daga kitchen tana tayasu ita ma duk da bata san abinda suke dariya akai ba. ****Shaquwa mai tsanani yashiga tsananin Addawiyya da Aliyu, abinda yayi mugun bawa mutanen gidan mamaki sabida shi mutum ne mai wuyar sha'ani ba'agane kanshi sam amma sai gashi cikin d'an lokaci soyayya ta sanjashi sosai kuma har lokacin yaqi furta mata kalmar ina sonki, ita kuma tsaf tagane imda yadosa so yake ta bara da kanta, abinda ko bazai samuba kenan koda zasu shekara ahaka in har bai furtaba itama baza ta ce ci kanka ba. Hameed kam dariya yakeyi musu yana mamakin wannan salo tasu abinda ko amufarki bazai iyaba, shi in yana son abu ba boye boye zai fad'a, he was very frank about any things shiyasa yafi Haydar rashin sirri. Yau Hindu tagama wanka kuma yau zasu maida kaka Abu gida daganan su wuce gidan Abbie su yini, dan haka Addawiyya tana fitowa wanka ta tsaya ka tsara kwalliya mai kyau da burgewa ta sanya wata super d'inkin riga da zani ta kafe d'aurinta ya zauna d'as akanta ta yafa gyale kalan atamfar ta sanya hill shoe kalan da yadace da kayanta tana cikin fesa turare taji iska ya shigo bata juyaba ta cigaba da abinda takeyi dan tasan uncle babibullah ne. "Uhmm mai babban suna angirma ansoma soyayya ko? Tura baki tayi tana kallon shi tace "uncle mi yasa kayi watsi dani? "Sabida kin girma yanzu, bakya da lokacin kanki. Idanu waje tace "nid'in? "E, "to aikin mi nakeyi? "Ta tunanin masoyinki Ali. Kauda kanta tayi cike da jin kunya, ya saki 'yar dariya yace "Allah yabarku tare, shima yana sonki sosai amma akwai jarabawar rayuwa azamanta kewarku, ina yi miku fatan cinyewa da kuma samum sakamako mai amfani, yaja numfashi yace "sorry mai babban suna, daya yau zanyi nesa dake agame da ganina dakikeyi azahiri amma dai zakiriqa jin maganata lokaci zuwa lokaci. Idanuta ya ciko da kwalla zatayi magana ya rigata "kada ki damu mai babban suna ina tare da ke ako ina, bye. Ko kafinta tayi magan ya bace bat. zaunawa tayi jiki asanyaye tana son gano inda maganganun uncle d'inta ya dosa amma ta kasa gano komi. Jarabawa wacce iri kenan? Ganintana batawa kanta lokaci yasa ta miqe ta fito parlor ta tadda duk sun shirya ita suke jira. Haydar ne zai kaisu, yana ganinta yayi saurin bud'e mata front seat sai da ta zauna sannan ya bud'ewa su Hindu back suka shiga, khairi tace "ya Haydar mata tafi uwa ko? Ahanzarce ya juyo yana kallonta ta gyad'a kai tana cewa "eh'man kana ganin aunty amma sai da kayiwa Addawiy wuri sannan ka tuna da ita. Kauda kai yayi yana murmushi su kaka Abu suka saka mishi dariya itama Addawiyyan dariya tasa tayi qasa da murya tace "abin boye dai yau yafito fili. Mintsilin cinyarta yayi ya amsa "muna isa zakiyimin bayanin me zancenki yake nufi. Cikin kwabe fuska kuma cike da shagwaba ta ture hannunshi tace "Mugunta dai baya da kyau. "Haydar ko mufita mubaku wuri ne, ku gama soyayyar? Cike da jin kunya ya shafi sumar kanshi yace "uhmm aunty gyara zama takeyi fa, banza tayi mishi, ya waiga ya watsawa khairi kallon zakisani ne yarinya sannan ya yiwa motar key suka fice. *mrs j moon* [1/16, 4:02 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *Pape d'in nakine sis Barakah, Allah yabar so da k'auna, inajinki sosai a❤👈🏻😘 kuma Addawiyya tace ki saurari zuwanta garin barno don duk sai ta tone asirrin boye da masu bama bamai suka binne maku* 😅lol. *32* Kaka Abu suka soma saukewa agidanta, sun cikata da kayan arziki sosai sai godiya take tayi tare da samisu albarka. A gidan Abbie ummi tarasa inda zata sakasu tayi don murna, ta d'auki hassan ta koma ta d'auki hussain sai kiran "masha Allah takeyi cike da murna. Addawiyya sai dariya take mata tare da tsokanarta tace "su ummi anga yara masu kalan larabawa duk anbi an rud'e to kisani dai ko yaye baza mu baki su ehe. Ta amsa cikin wasa "nima banso, kuyita riqe 'ya'yanku nawa sun isheni. Suka saka dariya su dukansu. Anan suka yini sai bayan la'asar Haydar yadawo d'aukansu. Yana shigowa idanun shi ya hango mishi Addawiyya zaune da wani suna hira sai dariya takeyi, wani abu yaji ya sokeshi azuciya yasami kanshi da kasa fitowa bayan da yagama gyara parking. Addawiyya kam Sarai taga isowarshi, tayi kamar bata gani ba, ta cigaba da sauraren hiran Aisha wanda ubaiyu yake mata. Afusace ya fito ya wucesu zuwa ciki, bayanshi tabi da kallo tana murmushi. Ubaiyu ya dubeta "Addawiy ko shine wanda ya kasani? "Uhm tace tana sunkuyar da kanta qasa. Ah lallai yaciri tuta kam, Allah yabar so da qauna mai nagarta, ta amsa Amin cike dajin kunya. "Abinda yaja kenan nafad'a tarkon sonki a baya, wato kunyarki da natsuwarki. "Uhmm Allah yabaka wacce tafini komi ai, gata babba ba yarinya kwaila kamata ba. "Kece kwailan? Aikam Ko makaho ya laliba yasan kinfi qarfin akiraki da kwaila. kauda kai gefe tayi ta nunashi da yatsa "kaikoh? Baka da dama ya ubaiyu Allah. Dariya ya saki yana sosa gemunsa ya miqe yayi gaba sannan ya juyo "tafi wurin mijinki kada yazaci muna soyewa ne. "Uhmm kafa samu abinyi tsokanata kenan yanzu, to a inkaje kagai damin da Aisha kasanar da ita zanzo cikin satinnan muga juna. "Zataji, amma ni zanzo nayi mikk jagora ko? "Ai kasan nasoma makanta hqr nasoma shelan neman d'an jagora. Dariya yasa sosai yana nunata da yatsa, "a'a bance ba autan ummi, harara da dalla mishi tace "banson jin sunar nan abakinka tam. Sai da ya russuna ya dunqule hannu yayi mata jinjina sannan ya amsa da "angama ranki shi dad'e. Baqaramin dariya abin yabata ba, tana cikinyi ta hango fitowar su Hindu, ta d'agawa ubaiyu hannu alamar bye tayi ciki da sauri. Qarasawa yayi wurin su Hindu ya gaishe da ita yaga su twins ya fidda kud'i mai yawa ya miqawa khairi yana cewa "asayawa su twins pampers. Godiya Hindu tayi mishi, ya juya tare da miqawa Haydar hannu sukayi musa baha, ya shige motarsa ya fice yana jin jina lamarin Haydar ganin yarda ya amsa mishi sallamar kamar baya so. A bisa hanyarsu ta komawa gida sai harara yake ta wullama Addawiyya, ita kam sai murmushi take sakar mishi da zarar sun had'a idanu abinda ya qara tunzira zuciyarshi yaji kamar ya tsaya ya fiddata a cikin motarshi. Suna isa tayi saurin ficewa tayi ciki harda had'awa da gudu. Cije labbanshi yayi yana jijjiga kai, yana ayyana irin hukuncin da zaiyi mata in suka had'u. Wasan 'yar buya suka soma, duk inda tasan yake bazata je wurinba haka nan da zarar ya shigo part d'in Hindu ko Hajja indai tana ciki bazata bari ya ganta ba. Yashiga cikin damuwa sosai, har yaji ya tsani kansa, da ace bai nuna mata yana qumunta ba da duk haka bai faru ba. "Yau ko ta tsiya sai naganta, ya furta tare da miqewa yafad'a toilet. "Khairiyya wallahi inbaki fita shirgin 'yar banzan yarinyar nan ba mai siffan aljannu ba zanci mutuncinki. Tura baki khairi tayi tana qunquni. "Fito fili ki zageni kawai khairi ba ki tsaya yimin gunaguni ba. "Ni ba zaginki nake yiba momy kawai cewa nayi nakusa komawa gaba d'aya part d'in aunty Hindun ma, sabida can yafi nan dad'i kuma mutane suna kai da kawo sosai fiye da nan part d'in, ba'a zama shiru kullum cikin nishad'i ake, muyi karatunmu tare da ita, muyiiwa su twins wanda mu shiryasu mu goyasu har suyi barci sannan acan nakoyi abu buwa masu yawa wanda ke kika kasa koyamin kamar girmama babba, girki mai dad'i, sallah cikin time d'in tare da koyon had'a baqin ajami wanda mugun gatan da kika nunamin yasa bansan komai ba akai amma yamzu alhamdulillahi taraiyata da Addawiyya nasami abu buwa masu tarin alfanu wanda ada nagaza samunsu don.... Saukan marin da Hajiya karima ta falla mata yasa take maganarta ya cinke ba shiri. Baya taja tana kallon uwar nata idanu waje hannunta dafe da quncinta. "Momy ni yau kika mara? "Eh, kuma ina daf da lakad'a miki dukan kawo wuqa indai har baki rabi da wad'ancan harsabiban muta nen ba. Ja baya takuma yi tana girgiza kai, hawaye tuni yagama wanke mata fuska tace "billahil azim bazan rabu da mutanen kirki irin su ba, koda kuwa zaki zamo ajali nane. Salati hajiya karima tasaka tana tafa hannayenta, ta nuna qirjinta tace "wato kina nufin nid'in mutumiyar banza ce kenan ko khairi? Muryanta na rawa ta amsa "a'a momy baha nake nufiba. Ta soma matsowa inda take tana ja baya "to ya kike nufi fad'amin inji sallamammiya wacce aka gama bata rubutun kashe zuciya ta shanye. "Momy kibar fad'an haka baya da kyau don shine ake kira zato zunubine koda yakasance gaskiya ne. "Yau nagama ganin Ikon Allah mai mana ruwa, ni karima nagata kaina, wato wa'azi suka turoki kiyimin kenan? "A'a momy nadai san hakan ne ayayin had'uwata da Addawiyya dan ita mai tarin ilimi ne sosai musanman na islama, to ita take koyamin da zarar mundawo daga islamiyya kuma ina ganewa sosai don haka ina roqonki dan girman Allah da manzon sa kidaina aibata su kije kigode musu na dawo miki da 'ya dAsu kayi hayya miqaqqiya amai makon da datake aband'are. Wani marin ta kuma sauke mata ta fizgota tayi cikin bedroom d'inta da ita, sai ihu take tana kiran wallahi ina tare dasu koda zaki zama ajalina ne. "Bazan zama ba amma zaki gane kurenki yau, sai naga uban da yatsaya miki agidan nan. Afusace aka banko qofar aka shigo Hameed ne yashigo cikin fushi ya kwaceta ahannunta, da gaggawa khairi ta koma bayarshi ta lafe tana maida numfashi. "Uban wa yabaka izinin ka shigomin part. "Ubana, mari ka kawo mishi ya tare yana zare mata idanu ta zabura zata kamota abayarshi ya daka mata tsawa "wallahi kibar ganin ke kika haifeta to bashi zai hana in faffalla miki mari akan taba. "Ni d'in zaka doka Hameed? Gyada mata kai yayi tare da juyawa ya kama hannun khairi yace "muje ki kwashe kayarki daga part d'in nan ki koma na aunty kuma koda lokacin tafiyarsu yayi gidan su Addawiyya zaki tafi har sai sundawo. Ta amsa mishi da "to jikinta duk yayi sanyi. Duk jaraban da hajiya karima take musu bai sa sun tsaya da abinda sukeyiba, khairi ce ma tayi qasa da murya tace 'ya Hameed momy fa tana sona kada intafi hawan jininta ya tashi. Shima murya can qasa ya amsa "walata zamuyi ai, wata qila zata san Allah d'aya ne. "Ohk nafahimta. Ranar haukane kawai batayiba gashi har yanzu part d'in Hindu baya shiguwa mata balle taje ta d'auko 'yarta, haka dai tayi ta zage zagenta bawanda ya kulata hattako da 'yar nata khairi. Hajja ta kaiwa qara itama ta goyi bayan Hameed inda tace "da part d'inki dana Hindun ai duk d'aya ne. Cikin fushi tabaro part d'in tana jiran Alh. Yadawo daga tafiyar da yayi qasar Germany ayi wacce za'ayi sabida bazata taba lamunta ba arabata da 'yarta d'aya tilo. "Khairi miyasa kikayi haka? Ba'a fad'a in fad'a da mahaifiyya, girma ake bata koda aya take, inkina son dawo da ita hanya ai asannu zaki bita, ko yanzu kinsan kuwa kina cikin fushin Allah sabida tayi fushi dake, kuma hakan zai iya shafan karatunki burinki na son kiyi saukan alqu'ani zaki iya rasarashi, don haka tashi maza in rakaki ki bata haquri. "Addawiy baza ta haqura ba, zata dokeni ne. "Ba hujja bace hakan khairi, tashi maza autan ummi tayi miki jagora, insha Allahu baza tayi miki komi ba. "To aunty, nagode da kulawarku gareni, Allah yasa da khairan. "Amin. Sun cimmata zaune ta tsokala d'ankali gaban goshi, ture kaga tsiya kenan sai huci takeyi ita 1. "Kuficemin a parlor tun banji muku ciwo ba!! Tace dasu cikin tsawa. Juyawa khairi tayi a tsorace zata fita Addawiyya ta kamo hannunta tana girgiza mata kai, suka iso gabanta suka russuna "momyn khairi kiyi haquri bazata qaraba kinji? Kallon banza ta saukewa Addawiyya, zatayi magana ta kafeta da idanu, atake tayi shiru tana jan wa'innahu sulaimanu acikin zuciyarta dan gani tayi idanunta sun koma mata kamar bana muta ne ba, anya 'yannan cikakkiyar mutum ce kuwa? Tambayar da tayi cikin zuciyarta kenan kuma tagaza lalibo amsarshi. Murmushi addawiyya ta sakar mata ta tashi ta koma samar kushin ta zauna tana ci gaba da kafeta da idanu. "Momyna ki yafemin ba burina na bata miki ba, sharrin zuciya ne yasa nayi sa'insa dake amma ina roqon affuwarki don Allah badan halina ba. Kamo khairin tayi ta rumgume tana shafa bayanta tace "Nayafe miki 'yata amma bisa shara'in zakidawo part d'ina "zan dawo momy "ohk tam komi ya wuce "thank you my momma. Sai kuma ta zame jikinta ta zauna tare da lankwashe qafafunta ta soma magana "ina son don Allah momy ki cire tsanar da kikayiwa su aunty Hindu aranki domin sud'imuta nen kirkine, kinga wannan tanuna Addawiyya da yatsa tacigaba Allah sanadi ita ce silar komawata mai hankali amai makon mara shi, mai matsuwa amai makon mara tarbiyya, mai ilimi amai makon jahila, mai kwarjini amaimakom mai bakin jini, mai ibada amai makom mai wasa da sallah, nasamu abubuwa da dama atarayyana da dasu na 'yan lokaci qanqani duk kuwa da ada nayi ta zaginta amma dayake Allah yasoni da shiriya sai tayi galaba akaina batare da nasani, don haka ina roqonki da ki daure ki cirekomai aranki muzauna lafiya dasu, kinji ko momyna? "Uhmm naji, kutashi ina son yin runani akai, sukayi mata godiya suka fice, ta tabe baki tana mai cewa "ba shiri atsakaninmu har abadan abidina, kedai da suka mallake kiyi ta zama dasu amma ni kam ina kan bakana sai naga qarshensu har iyayensu. *nikam nace uhmm wanda yayi nisa baijin kira sam* Daf dazasu shiga part d'in Hindu, Addawiyya taji caraf an damqe mata hannu ta juya atsorace tayi arba da Haydar,ta tura baki tare da qoqarin kwace hannunta, yaja ta da qarfi zuwa part d'insu batare da yace da ita kanzil ba. Khairi tasoma yimusu dariya har suka bacewa ganinta, ta d'aga hannuta sama tace "ya ilahu kasadani da mai sona da qauna mai tsafta kamar yarda ya Haydar yake son Addawiyya. *mrs j moon* [1/17, 4:07 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *33* Sai da ya zaunar da ita abisa cushion sannan ya saki hannu. Miqewa tayi da sauri zata fita yayi hanzarin shan gabanta ya miqa hannu zai riqota taja baya tana hararan shi "Ya Ali wallahi banson haka. Shiru yayi mata ya koma ya zauna, batare da ta kalle inda yake bas ta nufi hanyar ficewa. "Don Allah kada kitafi, magana nakeso muyi dake. Tsayawa tayi cak, ya tako zuwa wurinta ya dafan kafad'anta tayi saurin zamewa ta had'e rai tace "nace kabar son tabamin jiki, baya da kyau hakan sam a cikin addininmu. Rungume hannayensa yayi aqirjinshi ya langabar da kai ya motsa labbanshi kad'an yace "Sorry my heart bazan qaraba. Kallon shi tayi sosai bako qiftawa, ya gyada mata kai murmushi d'auke afuskanshi, itama mirmushin ta saki tana mai kauda fuskanta cike dajin kunyar kallon data yi mishi na ido cikin ido. "Uhmm my angel zo kizauna in bud'e miki asirin zuciyata yau, maqe kafad'a tayi kanta qasa, "au bakya sonjin sirrin kenan? Ta girgiza kai, "uhmm kinsoma azumin rashin magana ne? "Eh ta amsa, yasa dariya sosai ya saita voice dinsa cikin serious yace "Rabi'a zo nan magana nakeson muyi dake mai mahinmanci. "To kazo muje garden sai muyi maganar acan. Kallonta yayi na 'yan daqik'u kamar zai zanyi magana sai kuma yayi shiru tare da miqewa ya doshi qofar fita tabiyo bayarshi. Zama sukayi samar kujerun roba dasuke cikin wata madai daiciyar rumfa a cikin garden d'in. "Rabi'atu bakiyar dani bako? Kina tunanin zan iya cutar dake ko? Yace da ita cikin sanyin murya. Amsawa tayi itama cikin sanyi "A'a ya Haydar banufina kenan ba ina dai qoqarin ganin mun kiyaye haqk'ok'in addininmu ce ta islama, inda ya tabbatar da cewa duk inda mace da namiji suka kebe su biyu musanman baligai to shed'anne na ukunsu, alokacin komi zai iya faruwa atare dasu koda kuwa sud'in kamilallu ne domin sharrin kaidin shed'an la'ananne saninsa sai Allah kad'ai ba mutum ba, don haka naga ya dace muyi taka tsantsan da hakan, amma in hakan baiyima dad'i ba ina neman affuwarka please. Jan doguwar nufashi yayi yace "lallai ked'in tadabance Addawiyya, duk yarda zakiyi magana sai ilimi ya fita cikinsa, sosai naji dad'in samunki arayuwata, nafahimce ki kuma bakiyin komi ba, Allah yacigana da karemana gabbanmu daga sharrin shed'an da afkawa barna. "Amin ya rabbi yayana. Sosai sukasha hiransu ta masoya inda kowa aranar yanunawa d'an uwarshi irin matsanancin son da yake danqare cikin ruhinshi. Basu sukayi haramar barin wurinba sai daf da magriba. Ta dubeshi cikin murmushi tace "Ya Aliyu lokaci salla ta gabato, yakamata mutashi hakanan. "Ya salam!! Beauty namanta banyi sallar la'asar ba gashi har lokacin magrib ta shiga. "Ya ilahi, affuwan mantawa nayi ban tuna maka ba don ni ina fashin sal....tunawa da tayi dawa take magana yasa tayi saurin rufe fuskanta da tafukan hannayenta ta kwasa da gudu tabi ta qofar kitchen tashige ciki. Murmushi ya saki mai sauti ya furta "kunyarki tana dad'a jefani cikin sonki tare da begenki ainun, i luv u wit ol my herat. Sai da yabatar da sallar la'asar sannan ya nufi masallaci don yabi jam'in magrib. Bashi yabaro masjid ba sai da ya sallaci isha'i kuma yaga batar da shafa'i yabar wuttiri sai yazo kwanciya. Yana shigowa get ya hango Hameed yaci uban kwalliya zai shiga car d'insa. Da sauri ya qaraso wurin ya kama kunninsa ya murd'a da qarfi yako saki 'yar qasa don yaji zafi sosai. "Hameed mi yasa har yanzu hankali ba zo maka ba? "To minayi kuma Abbana. Yace cikin fushi tare da fizge kunninsa yana liliyawa. "Kafi kowa sanin abinda nake nufi, yanzu ace ga baki ga hanci amma ka kasa zuwa bin jam'in sallah masjid? " kai bros ya sayyidi, Kadai san sanyi akeyi don haka na had'a arollar sallar magrib da isha'i nakeyi nayisu lokaci d'aya. "Ya rasulillahi!! Hameed yaushe zaka daina wasa da ibada ne wai? "Uhmm kai ne kake ganin ina wasa da ita amma ni kam nasan inayinta yarda ta dace. " uhmm ko? To kasani Wannan abin da kakeyi baka da hujjar kare kanka ranar gobe qiyama a gaban Allah don haka ka hanzarta dawowa bisa hanya na kwarai tun kafin lokaci ya qure maka, don mutuwar fuji'a yanzu ake yayin yinta kuma ita alamar tambaya ce gawanda ta riska. "Allah ya tsaremu da ita dan alfarman Annabi SAW. "To Amin, adai gyara kaji ko? "Tam Allah yabani iko "Amin. "Uhm yanzu da ka kasa zuwa masjid sallah sabida sanyi to yanzu kuma ina zaka? Sai da yasaki lafiyayyiar murmushi ya wani kwanbare sannan ya amsa "gidan su heart d'ina, sabida gidansu ba'a wuce 9:30pm ana hira so shine zanje da wuri kafin tym d'in nasan abinda na yaga. Idanu waje Haydar yace "mi zaka yaga Hameed? Sirrin tsaki yaja yace "kai dalla malam ba abin ashsha zanyi ba kawai hirace ta ma'abota k'auna zan yarfar mata itama ta yarfomin shine ma'anar yagowar. "To Allah ya shirya ka, inka isa kace ina gaishe da ita. "Amin bros, insha Allahu zataji. Yana tsaye har ya fice, ya juyo jikinsa a sanyaye saka makon tuno mahaifiyarshi da yayi. Tun suna yara ummansu hajiya Rahmatu take yaqi da Hameed akan sallah har suka soma mallakan hankalinsu tana aikin abu 1, baya son juwa jam'i haka bayayinta cikin lokacinta sai yaga dama, bayan rasuwarta Alh. Muktar ya d'ora akai, kullum sai yazo dakanshi ya tashesu zuwa masallaci sallar subahi amma Hameed baya zuwa sai Abban yayi da gaske, dakyat aka samu yake zuwa batare da qorafin shi barci bai isheshi ba, sanyi yakeji. Amma sauran sallolin kuwa wannan agida ko office yake yinsu baya yinsu cikin jam'i suma wata rana rankasu yakeyi, Haydar kullum fad'a yake yi masa ya bar wanna d'abi'ar ta ranka salloli amma yaqi dai nawa. Matsar dake damunshi kenan amma inbanda ita shid'in mutum ne mai kirki da tausayi ga iya barkwanci, kowa nashi ne haka nan baya shashanci da 'yan mata sam, soyyar shan minti bata cikin tsarin shi, bar shi dai da iya yiwa mace kallon qurillah in abokanshi sunyi masa qorafin kan hakan sai yace abarshi ya tantance d'iri, sura, siga tare da class d'inta sabida anan zai gano wacce zai bawa kyautar ruhinshi. **cikin sati d'aya da bayanawa junarsu sirrin zuciyoyinsu, sukayi wani mugun shaqu na ban mamaki, basa gajiya da hira duk in haydar yana gida haka in yatafi office suna maqale da waya ana zubawa juna kala man soyayya. Abin da yayi mugun bawa Hameed mamaki, ai ko ya hana Haydar saqat da tsokana ya kance "sumumu kasau ashe munafunci ne da kai haka, da kayi ta wani noqewa kamar sufi nan ko majnun ne. Aduk sanda yaji haka sai dai ya bishi da murmushi kawai bai iya ce mishi komi. Lokacin tafiyar su Hindu yana zuwa suka yi bankwana da dangi suka tafi tare da Addawiyya da khairi sabida rainon su twins. Hajiya karima taqaraci jarabarta ta haqura. Haydar duk sai yaji kamar yabisu, badan aikin office yayi mishi yawaba ba tabbas da dashi za'ayi tafiyar. Kewa tayi mugun daminshi duk sai yadawo shiru2 kamar yarda yake ada can, jin dad'in shi 1 shine kullum dare sai sunyi video call da juna. Yayi tazuba mata shagwaba tana biye mishi. Lokacin aikin Hajja yana zuwa su Abbie suka tashi atare dukkansu, acan suka had'u dasu Addawiyya wa d'anga qasa mai tsarki ta amshesu suka saje da larabawa. Duk inda Addawiyya tayi idanun Salma na kanta har ta tsargu ta matso jikinta ta kwantar da kanta akafad'arta tace "Adda mai tulelen ciki na sanza miki ne halan? Duka ta faska mata a cinya ta zabura taja baya tana tura baki "Allah kinci albarkacin takwaran ummi dake cikinki da sai na rama ko mi za'ayi. "'Yar buhu zokirama mana "uhmm nidai fad'amin mi jikina yayi kike tabina da kallo kamar wata mayya. "Ohk kinrama ke nan ko? Dariya tayi ta amsa "eh'man ban mantaba ai har yanzu "to yayi miki kyau, matso kiji abinda nagani atare da ke. Matsowa tayi ta kanga kunninta daf da bakin Salma. "Addawiy wallahi kin qara girma, haske, wayewa sannan uwa uba komi najikinki yaciko kin zama big lady mai kayan alatu ainun, anya kuwa Haydar zai ganeki in kuka had'u? Da gudu tafice daga d'akin tana cewa "Allahumma yahadiki Adda Salma. Dariya duka d'akin su kasa, Hindu tace "bakwa gajiya da shiririta duk in kun had'u da juna ko Salma? "Aunty wasan saqo da saqo kenan ai. Haqiqanin gaskiya Addawiyya tayi mugun sanzawa, duk alamun cikan 'yan matanci sun bayyana gareta, har abin sai da yabama Hindu tsoro ta tsareta sai ta fad'a mata abinda take sha da boobs d'inta tare da ships d'inta suka koma haka, sai da tayi ta rantsewa sannan ta yarda, kuma khairi ta tabbar mata da ba abinda takesha tunda duk inda zasuje tare suke zuwa, sai tabar abin alokacin zuwansu ne yayi, haka itama khairi ta cika ba laifi don tafi yarda tazo. Cike da nasara suka kammala aikin hajjinsu suka nufo gida Nigeria cike da d'okin ganin dangi. Addawiyya kam d'okin ganin bubby nta takeyi kawai, ji take kamar tayi tsuntsu ta ganta gabanshi. Jirginsu ya sauka lafiya, duk abinda za'a anyi angama suka d'auko kayansu suka fito inda su Haydar suke jiransu. Abin mamaki Addawiyya takasa kallon inda Haydar yake sam, kuma koda akazo tafiya sai shiga motar ubaiyu amai makon tashiga na Haydar, suka nufi gidan Abbie. Haydar kamar zai kwalla ihu awurin amma sai yayi ta maza ya daure yashiga motarshi yaja suka tafi gidan amma inransa yayi ya baci. *mrs j moon* [1/18, 10:24 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *34* Kwance take cikin bedroom d'in Ummi ta rufe jikinta har zuwa samar kanta da qaton bargo amma duk da haka sai rawan sanyi takeyi. A qalla ta d'auki mintoci 20 sannan tasoma zufa alamar zazzabin dake damunta zai sauka. K'ara gyara blanket d'in tayi tare da jan siririyar tsaki ta furta "duk da ban kyauta mishi ba ai tunda na kira phone d'insa sai ya d'auka yaji uzirina ba wai yayi watsi da niba, takuma jan wani tsakin cike da d'acin zuciya. Wani sarawa taji gefen kanta yayi mata ta dafe wurin tana matsan kwalla. "Wai dama haka fushin masoyi yake? Ta tambayi kanta afili. Lallai in haka abin yake masoya suna shan azaba, "wash ni Addawiyya, Allah kakawomin mafita, ka karkatomin da hankali ya Ali ya bar fushi nan ko nasami sa'ida a ruhina. Kimanin kwanaki uku kenan da dawowarsu amma ko sau d'aya Haydar baizo gidansu ba kuma bai kirata a waya ba ita ce ta kirashi ranar da suka kwana biyu da dawowa yaqi d'agawa abinda yayi mugun bata mata rai har ya haifar mata da zazzabi mai zafi kuma tunda lokacin bata sake kiranshi ba duk da muradin son jin muryanshi da takeyi kamar me. Sai bayan azuhur ta falka saboda barci da ya kwasheta bata sani, da hanzari ta shige bathroom, tana fitowa ta shimfid'a sallaya ta hau, bayan ta idar ta miqe ta shafa lotion ta zura wata doguwar riga roba mai d'auke da qananar stones golden ta yane kanta da qaramin gyale shima golden tafito parlor. Gyefen ummi ta zauna a kasalance tace "Ummi barka da war haka, nabarki da aiki ko? Cike da kulawa ta amsa "Alhamdulillahi auta, yajikin naki, kin warware ko dai nakira miki Salma ko Hameed wani yazo ya dubaki? "A'a na warke, kasala ce kawai taragenmin yanzu kuma itama zata bari. "Tam Allah yaqara lafiya "Amin. "Ga abinci can a dining kije kici zakiji qarfin jikin, "ohk tam ummina. Tura abincin takeyi kawai kamar tana cin magana sabida gaba d'aya zuciyarta taqi yi mata dad'i ga bakinta ba d'and'ano sam. Tana gamawa ta gyara wurin ta dawo ta zauna ta bud'e data,, wata qila zatasami abin d'ebe mata kewa. Ganin Maryam a online yasa ta tura mata saqo. '''Ki turomin document d'in Babban goro (khadeeja candy) da cigaban Gidan k'unci (bebeelo) da kuma document d'in Wata uwar (Haemeebrah) ke da dai novels masu dad'i. Yana shiga ta duba Haydar taga yana online, kamar zatayi mishi magana kuma sai ta fasa ta wank had'e fuska tana hararan wayarta kamar shine agabanta. Tana shirin sauka taga ya turo mata da massage da sauri ta duba *malamansu kicire photo nan dake dpnki now* quri tayiwa gajeren saqon kamar wacce ta warke makanta cikin tura baki ta shiga setting tayi remove ta sauka da sauri batare da ta duba massage d'in maryam da taga ya shigo. Haydar ganin ta sauka yaja tsuka. "Wato tafi qarfin ta amsamin kenan? Uhmm to ko sabon saurayi tayi balarabe, shi yasa tasomamin wulaqanci irin tasu na mata? Wani shashi na zuciyar shi ya amsa mishi "kaima baka kyauta mata ba Ali, komi tayi maka ai ka nemeta ka saurari uzurinta ba wai kayi ta fushi da babu gaira babu daliliba. "Yesss!!!! Ya amsa da qarfi ya miqe ya zari key d'in motarshi yafice har yana had'awa da gudu. A parking lot ya had'u da Hameed yace "ya haydar sai ina zuwa haka kuma? "Inda ka aike ni, ya masa mishi bai kuma jira cewar shiba ya shige motarshi ya fizgeta da qarfi, get man ya wangale mishi get ya fice. "Allah yayi maka sauqi kai kam, Hameed ya furta cikin tabe baki. Tana kwance a bisa cushion, suna hira da Ummi ta tsinkayi sallamarsa, Ummi ce ta amsa mishi ya shigo a natse ya russuna ya gaida ummi ta amsa cikin fara'a tare da miqewa ta bar parlor n. Kallon kallo sukayiwa juna sai taga yarame mata amma yayi mata kyau sosai. Shima kallo daya yagano ta rame sai dai yana cike da mamakin girma da cikan da tayi wanda sam bai lura da suba sanda suka had'u airport. Itace ta soma janye idanunta, cike da yanga ta motsa lips d'in tace "ina yini, ya office? Bai amsa mata ba illah idanu ya kuma bud'ewa yana qare mata kallo, kamar yau yasoma ganinta. Wani matsanancin kunya ne ya kawo mata jiyara domin ta tuna rigan jikinta ta kamata tsantsan gyalenta bai rufe mata komi ba. Cikin shagwababbiyar murya tace "please ya Ali d'an jirani a sitting room. Ko motsi baiyi ba balle ta saran zai tashi. Tashi tayi ta haya upstairs cikin sarsarfa don ta sanyo hijab. Murmushi ya saki mai sauti yana mai furta "komi naki mai kyau da burgewa ne Rabi'atu,ya Allah ka mallakamin ita da sauri. *sleep*😴🤦🏻‍♀ *mrs j moon* [1/19, 11:10 AM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *35* Koda ta sauko tuni yabar parlor n, wani sanyi takeji yana sauka mata cikin heart ta runtse idanunta ta daka tsalle ta soma rawa tana d'iban shaky tana juyi cike da nishad'i tana waqan soyyaya soyayya. Sautin dariyan Ummi taji abayanta yasa tayi saurin dakatawa da rawar ta juyo cike dajin kunya sai kuma ta diba da dugu zata fice. "Auta zo ki tafi mishi da wani abu mana, juyowa tayi kanta aqasa ta shige kitchen, tana jera drinks tare da snacks tajiyo ummi na fad'in "uhmm auta dai da qarfi da yaji taqi yaron nan ubaiyu, to Allah yasa haka shine mafi Alkhairi. Can qasan maqoshi ta amsa da "Amin sai kuma ta rufe fuskanta wai taji kunya, haka ta fito kanta a qasa taqi kallon inda Ummi take, rankwashi Ummin ta kai mata tana mai cewa "kunyar qarya ba, bacin yanzu kika gama cashewarki har da d'iban shaky. Da sauri tafice tana dariya mai sauti, itama ummin dariyan tasa ta furta "auta hoo ita dai abinjin kunya bayayi mata wuya sam. 'Dauke da sallama ta shiga sitting room d'in, ya amsa mata can qasa, ta qaraso ta d'ora tire d'in bisa table ta tsiyaya mishi lemon mango with apple data had'a da hannunta, ta miqa mishi mai makon ya amsa sai ya damqe hannunta yana son su had'a idanu ita kuma ganin haka ta qara soke kanta qasa murmushi ya saki mai sauti yace "kinsan Allah idan har baki d'ago kin kalleni ba sai dai mu kwana ahaka. Taqi motsawa ya matse hannunta da qarfi ta ritse idanu, jus d'in dake hannunta yasoma zubeqa sabida rawar da hannunta yasomayi. miqa hannun nata yayi zuwa bakinshi ya kafa kai yana tsotsan jus d'in eyes d'insa bisa kanta, tana jinsa duk abinda yakeyi amma taqi d'ago kanta ta kalleshi. Sai da ya shanye tas sannan ya saketa ya koma ya lafe cikin cushin yana tsotsan labbanshi cike da nishad'i yace "oya hajiya Rabi'atu sami wuri ki zauna haka nan kada qafafunki yayi tsami, miqewa tayi ta zauna nesa dashi kanta qasa tanayin wasa da ya tsun hannunta. "Uhmm sarkin jin kunya sai kisaki jikinki hakan ko maji dad'in yin hiran yaushe gamo duk da nasan yanzu batani kikeyi ba kinsami kyakykyawan d'an balarabe tuni ya sace miki zuciya. Da sauri ta d'ago idanu waje tace "inji wa? "Inji ki. Ta langabe kai cike da marairaita tace "kai ya Ali yaushe mukayi haka da kai? Shima langabe kan yayi ya amsa "ranar da kuka dawo daga saudi a airport kika tabbatarmin da bana gabanki sam yanzu. "Uhmm ya Haydar kenan baka rabo da zolaya. "Allah ba zolayanki nakeyi ba pretty, kece da kanki kika nunawa duniya bakya yayina tunda ko darajan kallon arziki samuba ba daga gareki, ya qarasa zance cikin dacin rai. Tuni idanunta ya kawo ruwa ta dawo gabanshi ta zauna ta soma magana "wallahi Allah ya Ali ba abinda kake tuna akai shine ba, kawai kunyar yima magana naji agaban su Abbie amma sosai ranar naji dad'in ganinka. Ya amsa adaqile "Uhm naji, kallonshi tayi sosai tace "don Allah kayarda dani ba wanda ya sace maka heart d'inna, wallahi taka ce har abada bata taba son waniba sai kai kuma bazata qara son waniba bayan kai, kayafe min dan girman Allah kaji my life. Murmushi ya kufce mishi ba shiri ya jinjina kai ya amsa "komi ya wuce sweetie. "Aha thank you habibi. Sosai suka sha hiransu ta masoya kamar wani abu bai taba faruwaba. Suna tsaka da hira Addawiyya ta had'e rai tayi shiru, jikinsa yana bari yasoma magana "beauty mi nayi kuma? Sai da taja lokaci sannan tace cikin shagwaba "jiya nakiraka kaqi d"auka, kasa zazzabi ya kamani ya wahalar dani nakasa hassala komi nayi ta kuka har hawayena ya kusa d'aukewa. Dariya yasaki mai sauti tabishi da kallo cike da so da qauna, ya kanne mata ido d'aya yace "ramawa nayi, kuma Alhamdulillah kinji abinda naji dafatan nan gaba zaki kiyaye yimin hakan. Cike da mamaki ta jefa mishi tambaya "da gaske wai kayi kuka da hawaye kaima? "Yes, ya wuce wai hakik'a nayi kukan zucci wanda yafina na zahiri zafi da rad'ad'i,kad'an yarage heart d'ina bata tasami attack ba. Zamewa tayi bisa gwaiwoyinta muryanta na rawa tace "don girman Allah da manzonsa ka yafemin bansan zaka fad'a mawuyacin hali haka ba da tuni nayakice kunyar gefe na kula ka. Shima zubewa yayi gabanta yace "hakan yayimin dad'i sannan qimarki ta qaru sosai ya ruhina, lallai ina alfahari da samun mace mai kunya da kawaici tare da hangen nesa irinki, azancinki yana qaramin jin sonki har namanta da kaina. Miqewa tayi ta koma mazauninta tana murmushi mai cike da kunya wanda yin hakan yariga yazama d'abi'arta. Sai da Abbie ya dawo suka gaisa sannan ya wuce gida cike da annashuwa. A parlor ya zauna dirshen bisa carpet ya zuge zip d'in d'an madai daicin akwatin data bashi sanda zai wuto tace tsarabarshi ne ciki. Kayan barci ne masu laushi sai vests d boxes masu kyau da wasu littafan addu,o'i sai wata qaramar leda mai kyalli ya bud'eta ya fiddo wani box ya bud'e agogone mai uban tsada tare da zobben azurfa mai kyau, cike da jin dad'i ya zura zobben a yatsrshi nagefen qaramar ya tsarshi yayi mishi cif kamar angwada shi, subba ya kaiwa yatsar ya lumshe idanunsa ya furta "i really love you my angel. "Uhmm soyayya ruwan zuma, in ansha aba masoyi oooo. Bud'e idanunsa yayi da sauri ya watsama Hameed harara, yako sheqe da dariya har na buga qafa sai kuma ya matso ya soma duba kayan tare da cire night wear biyu vest da boxer bibiyu ya kwasa ya nufi room d'insa yana waqar "shi zumunci yana qarfafa son 'yan uwa. Murmushi Haydar yayi tare da tattare sauran kayan ya nufi room d'inshi da su, yana shiga ya hango phone d'insa yana haske koda ya duba yaga Addawiyya ce ta kirashi har 3 miss call da hanzari yayi back call yanajin yasoma ringing yahaye bed d'insa yakwanta hanunshi d'aya cikin sumarsa. ***** Addawiyya tasoma karatunta na pharmercy a BUK duk medicine taso sai suka bata parmacy yayin da Maryam kuma suka bata medicine amai makon choice d'in na pharmacy, ita kuma khairi abinda tanema shi suka bata wato mass communication. Sosai suka maida hankali akaratunsu amma fa Addawiyya tafi son medicine aranta don haka kullum Haydar yazo sai tayi mishi qorafi ita fa yasan yarda zaiyi a maidata medicine burinta ya cika inyaso sai maryam ta koma pharmacy d'in. Yauma da yazo da shi tasoma yi masa maraba, ganin yaqi ce mata komi ta soma kukan shagwaba har da hawaye, baice mata kanzil ba har tagaji tayi shiru baki a ture. Jan bakin yayi tayi sauri gyarashi yayi qasa da murya yace "Addawiyya ki zamo mai godiya ga Allah akan dukkanin abinda yazamo qaddaranki, ki amshi wannan qaddara tako da hannu bibiyu kicigaba da neman zabin Allah tare da nasaranshi sannan ina roqonki daki maidahankali sosai akan karatunki kada kiga ba choice d'inki bane shi ki soma shiririta, dafatan daga yau zakibar qorafi akai. "Insha Allahu bazan kuma ba sannan nayi maka alqawarin dagewa sosai abisa karatuna. "That's good my heart. Idanu ta kad'amishi face d'inta d'auke da murmushi, tayi ihu kad'an ya kwanta baya tare da dafe qirjinsa ya furta "washhh!! Mashin so ya sokeni a ruhi, wannan irin fari ai sai a d'au gawata yanzu. Dariya tasa tana mai kulle idanunta da tafukan hannayenta. ******* 11:00am at school. Addawiyya, maryam tare da khairi suna zaune a wurin love garden suna ta hirasu na qawaye cike da nishad'i. Qamshi turarenshi taji ya doso wurin sai kuma iska mai qarfi ta tashi agefenta tabi wurin da kallo uncle habibullah ne ya baiya a zaune bisa kujeranshi mai d'aukan idanu. Addawiyya ta juya ta kalli su maryam taga sai hiransu suke tayi da alama basu ganshi ba. "Mai babban suna tashi ki matsa wurin bishiyar mango d'incan magana nazo miki da ita mai mahinmanci. Batare da tayi magana ta miqe ta nufi wurin mango tree d'in yayin data ga su maryam sun juya musu baya suna ta hiransu basu ko lura da tashinta a wurin ba. "Mai babban suna aurenki yazo, za'ayishi nan da kusa kwanaki arba'in masu zuwa, to abinda nakeso dake shine da zarar magabatanki sunzo miki da zancen ki amince batare da gardama ba domin baki san me Allah ya boye ciki ba kamar yarda nima ban san komi akai ba, dafatan kin fahimceni da kyau. Muryamta na rawa tace "a'a uncle nakasa gane inda zancenka ya dosa, wai kana nufim ni Addawiyya autan Ummi zanyi aure ciki qanqanin lokacin nan? "Eh mai babba suna. Idanu waje tace "to waye miji nawa "Aliyun kine "uhmm uncle ya Ali fa ya tabbatarmin sai na kammala karatuna har zuwa sanda zan gama service sannan zamuyi aure. "Inkinje gida kinji zancena ya tabbata sai mucigaba da magama, bye sai nazo tayaki hira abarcinki yau. Kokafin tayi magana ya bace bat. Jikinta ba inda baya rawa, ta qaraso wurin su maryam ta d'auki purse tare phone d'inta tayi gaba batare data ce dasu qalaba. *mrs j moon* [1/20, 4:40 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *36* Ko kafin su maryam su iso inda take tamuza key ta fizga motar da gudu ta ta nufi get d'in fita. Khairi tuni ta hassala tasoma fad'a, "ai wannan iskancin banzane tana ganinmu amma takasa tsayawa jiba yarda mutane ke kallonmu suna dariya. Maryam da dubi mutanen ta tabe baki ta dafa kafad'an khairi cikin sigan rarrashi tace "Uhmm share kawai sis basa da aikin yine zo mukoma inda muka taso kafin nan da 25 minutes yaqarasa na shiga lecture. Bata ce da ita komiba suka juya. Saida suka zauna tace "Maryam mi kika sani agame ta ficewar addawiyya cikin fushi? "Wallahi bansan komiba khairi. "Ok, let me call her muji. Tace tare dasoma dialing number ta. Addawiyya kam driving takeyi kamar zata tashi sama, ikon Allah kawai yakawota gida lafiya. Tana shiga harabar gidan taci karo da motoci gabanta yana bugawa ta sami gefen bishiyar umbrella tayi parking ta kife kanta bisa Stereo ta rasa meke mata dad'i. Kiran khairi ya kuma shigowa tana kallo har ta tsinke batayi picking ba. Kira na biyar kenan tayi mata tana kallo har ya tsinke amma taqi d'auka. Khairi ta dubi maryam hankalinta atashe tace "bara na bita inajin ko lafiya. "Ohk, ni inna fito class zan biyo inji mike faruwa"tam sai kinzo, ta qarasa parking lot taja motarta ta fice tana zancen zuci. Jin maganganun su Abbie yasa ta d'ago tana hangensu daga inda take, Abbie, Abban su ubaiyu, Abban su Hameed tare da wani dattijo mai kama da Haydar sosai ta hango faces dinsu d'auke da fara'a, jikin wata mota babba suka tsaya zuwa can sai ga Hajja, Ummie tare da umman su ubaiyu sunyo mata rakiya. Tana isowa suka shiga mota suka wuce Abbie da Abban su ubaiyu sukayi ciki tare da su Ummie. Hakanan sai taji jikkinta yayi mugun sanyi, tasaka fitowa saima ta kuma gyara kwanciya a seat d'in data kwantar baya ta lumshe idanunta kamar mai barci nan kuwa tunanine ya baibayeta kuma tarasa wanne zata kama ciki. Qaran bud'e get dataji yasa ta bud'e idanunta wanda suka koma red color. Kusa da ita khairi ta parker motarta, bayan ta kulle ta fito tanufi ciki batare da ta lura da Addawiyya. 'Dan tsaki taja sanda taga su Ummie sunfito suna dube dube, tasan sarai ita suke nema donmin tasan khairi ta riga da ta kai gulma. Kafin su qaraso wurinta ta fito tanayin murmushin yaqe, aqoqarinta na ganin ta boye halin da take ciki. Umma ce ta kamo hannunta cike da kulawa tace "Ayya Rabi'atu mike faruwa kika boye kanki cikin mota alhalin kin jima da shigowa gidan? Sai da ta saita muryanta sannan ta amsa "kaina yakemin ciwo ga kuma kasala yana damuna shine na zauna ciki amma yanzu dama zan shigo. "Ayya sannu, Allah yaqara lafiya. "Amin umma. Juyawa tayi ta kalli inda ummi take tsaye ta zuba musu idannu, da aurin ta d'auke kanta sakamakon kallon tuhuma dataga ummin tana binta da shi. Jan hannunta umma tayi suka nufi ciki, khairi ta matso daf da kunninta tace "madam Haydar mushiga ciki ki fad'a misu abinda kika boye mana amatsayinmu na qawayenki. Harara ta wulla mata, itama hararan nata tayi ta kuma bud'e murya tace "dole dai kifad'a musu duk boye boyenki ehe. Abinci umma ta matsa mata taci sannan ta bata magani tasha, ta umurceta data tafi ta kwanta, intasami barci zataji tadawo normal. Koda ta shiga room d'in mai makon ta kwanta sai kawai tashige bathroom ta sakarwa kanta shower. Bata jimaba ta fito ta tadda khairi zaune bakin bed tana aikin yi mata bincike a cikin phone, ko kulata batayiba ta qarasa gaban mirror tayi 'yan shafeshafenta ta sanya inner wear tare da zira english wear na riga da sket masu santsi ta tako asannu ta haye bed ta ja blanket ta rufa ruf har zuwa face d'inta. Da hanzari khairi ta janye blanket d'in tayi jifa da shi gefe. A fusace ta tashi zaune tana doka mata harara tace "wani salon iskanci kenan haka khairi? "Salon iskancin da kika koyamin ne. Kallonta tayi na daqiqa ta girgiza kai tare da komawa ta kwanta tana mai dafe goshinta da left hand d'in. "Malama tashi zakiyi ki sanar da ni abinda ke damunki ba wai kiyi ta cin magani ba. "Wai ina ruwanki da lamari nane da kikabi kika takurawa kanki dole sai kinji matsalata? "Au haka kikace? Tam yayi kyau haka kuma nagode, tamiqe cikin fushi har ta kama handle zata murd'a Addawiyya tace "am sorry qawata dawo kiji matsalata, ko juyowa batayi ba tayi ficewarta cike da fushi. tabe bakinta Addawiyya tayi tana mai cewa "jikin ya motsa kkenan? sarakan fushin sun matso kusa, to Allah ya saukeku lafiya. "Mikike cewa? Dariya ta saka ta amsa "abinda iska yakawo miki, wato labe kika koma ko? "Bansani ba, nidai Abbie yace kizo, dafe qirji tayi idanu waje tace "wayace kice mishi idanuna biyu? "Au qarya kike nufin zanyi mishi ko mi? "Bamsani ba dalla magananyi kawai, ta furta cike da jin haushi. Dariya khairi tasa mata sosai tace eh, din nadai ji alamaun ilimi kenan. "Uhmm ni kirabi danj tam. "To momy sai kisami da tashi ko nakoma nasanar dashi kince sai yazo da kamshi don dama ina fita naci karo dashi zaizo kiranki da kanshi shine nace bara na kira mishi ke. "To kin kyauta ai, sai kibani hanya in wuce, duk kinbi kin isheni da uban surutu kamar parrot. Gwalo tayi mata takoyo kanta da sauri ta kwasa da gudu tayi downstairs ta rufa mata baya. **** Hajja bakya ganin in akayi haka ba'a tauye mata hakki taba? "Aliyu kasani yin haka shine zai baka damar sanin lafiyarka sannan shi aure, haihuwa, mutuwa tare da k'addara duk in lokacinsu yayi bawanda ya isa ya tsaidasu sai ikon Allah. "Haka ne Hajja, amma dai ina duba alkawarin danayi mata ne nacewa sai ta kammala karatunta har tasoma aiki sannan zamuyi aure. "Uhmm Ali ka kwantar da hankalinka ka natsu ka ajiye wannan zancen agefe, ka d'auka cewa haka Allah ya tsara baza ta kammala ba zakuyi aure. Nisawa yayi ya amsa "tam Hajja Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi "Amin Amin Ali gadanga qusar yaqi, murmusawa yayi tare da miqewa yafice. Cike da jin tausayi Hajja tabi bayamshi da kallo ta d'aga hannunta sama tace "Allah kabawa bayanka Aliyu lafiya alfarmar manzon rahama. **** Cikin parlon Abbie Addawiyya ce zaune ta lankwashe qafafunta kanta duqe a qasa, ta daiyi zama irin ta ladabi. Sai da Abbie ya dubi gefensa inda ummie take zaune ya sauke ajiyar zuciya ahankali sannan ya soma da cewa "Alhamdulillahi ala kulli halin, yayi jim zuwa can yace "Rabi'atul Addawiyya, tad'ago kanta da hanzari tayi tana dubanshi, yayimata murmushi ta koma da kanta qasa ta amsa "Na'am Abbie. "Rabi'a ya kuma kiranta akaro nabiyu,, ina mai baki haquri abisa katse miki cikan burinki da zanyi dafatan zaki gafar ceni? Muryan na rawa ta amsa "Abbie tsakanin iyaye da abin ikonsu wato 'ya'yansu, babu abinda zasuyi musu indai bai sabawa shari'aba ace zasu tsaya roqonsu gafara, don haka bakayimin komiba kuma baza kataba yimin shi ba sabida nasan kai d'in uba nagari ne mai hangen nesa kafin ya aywatar da komi. Tana rufe baki suka had'a baki wurin cewa "Allah yayi miki albarka har izuwa qarshen rayuwar. "Amin ta amsa fuskanta yana mai nunajin dad'in addu'ar. "Rabi'a bakomi bane illah d'azun na amshi sadakin aurenki da Aliyu wurin su Alh. Muktar sannan har mun tsaida lokacin biki nan da sati biyar masu zuwa, dafatan baza ki bani kunya ba. Ahankali ta amsa "insha Allahu zaka sameni mai ladabi da biyayya a lamarin zamantakewar aurena. Sai kuma tamiqe tafuce da gudu don sosai maganar ya jefata cikin jin kunyar su Ummie. "Auta hoo, jibafa kunya wai taji, ya amsa "hakan shi yanuna tana maraba da lamarin kena, "eh, malam dama ai nace maka bazata qiba sabida tana sonshi sosai, "to Allah ya barsu tare da karesu cikin amincin Allah "Amin. Koda ta shiga room d'inta khairi da maryam tasamu suna cin food, suna ganinta suka sa shewa ta had'e rai ta zauna suka kuma sakin dariya maryam tace "munji komi abakin Adda Salma ai. "Adda Salama fa kuka ce? "Eh ita "to yaushe tazo gidan? "Inanan tun bitarki zuwa school baji mawa, don haka agabana akayi komi Abbie ya kyautarwa Haydar dake. "Malamandu gyara zancenki akadai neman mishj aurena. Yeeeee!! Tafad'i da bakinta, su Amaren Ali kenan manya, maryam tace. Ficewa tayi da gudu tana cewa "magul matan banza kawai sai kuyi da wata ai ba ina ba. Tana jiyo dariyan dasuke kyalkyalawa tashige kitchen ta fice zuwa garden tasami wuri ta zauna ta kulle eyes d'inta tace "Haydar yana tare da lalura ko ta miye? Saukam Iska taji agefenta ba tare da ta bud'e idanunta ba tace "sanar dani lamarin uncle. "Kasheki zanyi yanzu kowa ya huta. Wata murya mai bantsoro ta amsa mata. *mrs j moon* [1/22, 3:47 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *37* Arazane ta kai dubanta inda sautin voice d'in yafito, wani zabura tayi sakamakon yin arba da wani halitta da tayi shi ba mutum ba bakuma dodo ba, yana d'auke da fuskan mutane kanshi na rago jikinsa na jaki har da bindi dogo qafafunshi na mutace. Bud'e baki tayi zata kwalla qara raji an hannu ya kulle mata baki tare daijn shigar wani sanyi cikin qirjinta, cikin second tasami kanta cikin jarumta na rashin jin tsoro. Komawa tayi ta zauna ta had'e fuska cikin kaurin voice kamar banata ba ta dubi halittan tace "to bissmillah, gani kamiqani barzahu, tunda kai ka halicceni. Wani zaro idanunshi halittan yayi cike da kid'ima sabida yazaci firgicin ganinshi zaisa ta suma yarda zaiji dad'in sheqawa da ita qiyoma. "Kana batamin lokaci fa, kallonta ya kumayi sosai, atake yagano wani baqon lamari cikin idanunta, yasoma ja baya tana biyoshi bakita na motsi alamar addu'a takeyi. Ganin burinta ta damqeshi da hannunta yasa yayi girgiza ya zama qaton shaho ya bud'e fuka fukanshi yayi sama. Abin mamaki sai da tabari ya lula sosai sannan ta bud'e bakinta ta hura iska sama atake shahon ya fad'o tim, ya saki razananniyar qara, yaja baya ya kuma girgiza ya koma kura yayo kanta kamar walqiya ta bace bat zuwa can wani qosasshen zaki ya bayya, yayi kan kurannan suka soma fafatawa wani baqin hayaqi ya rufesu ruf, tsowon lokaci suna abu d'aya zuwa can farin haske ya bayyana. Habibullah ne zaune bisa chair d'insa mai ruwan gold fuskansa kamar dare don rashin walwala. Ya dubi kuran da take yashe aqasa bakinta da hancinta sai zuban jini yake, yasa qafa ya shureta tayi wani sama sama sannan ta fad'o tim iska ya tashi ya rufeta, koda ya baje saiga wata mata baqa qirin fuskanta kamar na gorilla, zubewa tayi gaban Habibullah tana yin wani yare kamar na 'yan China. Wani tsawa ya daka mata ta zabura ta koma wata budurwa mai mugun kyau. Kallon sosai yayi mata yace "waya aikoki wurin kayana? "Kayimin rai ya kai adalin shugaba. "Tambayarki nayi, kuma amsa nakeso ba ban haquriba. "Matar Aliyu ce, wani Aliyun? "Wanda zai auri jaririyanka Addawiyya. "Uban wa ya d'aura musu aure? Shiru tayi ya kuma tambayarta saitayi qasa dakanta, taqi cewa komi. Shiru yayi kamar bazai kuma magana ba zuwa can yace "tashi ki tafi amma inamai gardad'inki kada ki kuma zuwa domin cutar da mai babban suna. Zubewa tayi gabanshi tana godiya, d'agamata hannu yayi atake ta bace bat. Kallon wata bishiyar itaciyar tumfafiya yayi saiga Addawiyya ta bayyana sai zare idanu takeyi. Dariyansa taji agefenta yasa ta juyo ta kama hannunshi bakinta na rawa tace "uncle naga abin tsoro yanzu anan wurin har yana cewa yazo kashe ni ne, don Allah sanar dani mike faruwa. "Mai babban suna, hakiqa rayuwarki tana gamuwa da ababen ban al'ajabi, don haka nakeso ki dage da yawan ibada da tsayuwar dare tun daga yanzu har izuwa gidan mijinki. "Tam uncle zan dage dayinsa daga yau in Allah yaso. "Madallah, yanzu shiga ciki. "A'a uncle sanar dani labarin wannan halittan dana gani da kuma matsalar Ya Ali danaji d'azun a parlon Abbie kacemin na amince dashi shid'in mai raunine domin lafiya bata isheshi ba. "Mai babban suna tabbas Aliyu baya da qoshin lafiya sosai, ada bansan miye matsalarba sabida hijabi da abin yake dashi amma bayyanar wannan halitta agareki nagano komi don haka kibar sonjin komiyeshi, ki dai zamo mai yawar addu'a Allah yana tare da mai yawan miqa lamuransa gareshi. "Idanu ta zuba mishi taqi cewa komi. Iska ya hura mata, lumshe idanu tayi tare da jan ajiyar zuciya tace "shikenan uncle nabar sake matsa maka akan sai naji ko miye amma don Allah kasanar dani waye wannan halittan? "Baiwace ta wata basarakiya, anturo tane domin ta cutar dake abisa dalilin banza da wofi na sarauniyar, atunaninta nayi nisa dake sabida taji nace zanyi tafiya to shine ta turo a kasheki sai gashi Allah ya kareki. "Uncle miye had'inta dani? "Kaddaran maganar aurenki ya had'aku. "Kamar ya? "Kamar yar yawan bincike baya da kyau sam. "Uhmm Uncle wallahi ban fahimce kaba. "Dama bana son ki fahimceni yanzu sai nan gaba. Zata kuma magana ya rigata "tafi ki shirya tarban zuwan masoyin Haydar. Yana fad'an haka ya zama haske ya bace. Barin wurin tayi jikinta duk yayi sanyi. Adaren ranar Haydar yakawo mata ziyara. Cikin parlor suka zauna yayin dasu ummie sukabar musu wurin. Haydar yasha mamaki jin batayi masa qorafin ya daqile mata karatu ba sam, shi kuma baitada zancen ba. Bai bar gidansuba sai bayan ten na dare. Daren ranar Addawiyya bata rintsaba sai bayan da ta sallaci subahi. Anan bisa sallaya ta bingire barci mai dad'i ya kwasheta. Hiran soyayya sukeyi cike da nishad'i wanda ya shagalar dasu suka manta inda suke. Qaran zuwar wata ququwa ce ta dawo dasu hankalinsu. Guguwar na zuwa tayi sama da Haydar ganin haka Addawiyya ta bishi zuwa saman, haka suke gudu cikin girgije, guguwar tana qoqarin tsere mata ita kuma tana qoqarin kamota ta kwace Haydar wanda tuni iska yayi mishi yawa har ya suma, cikin ikon Allah Addawiyya ta cukume guguwar bakinta d'auke da ayatul kursiyyu. Atare sukayo qasa koda suka sauko sai wata budurwa fara sol mai kyau ainun ta bayya ta nuna Addawiyya da yatsa "wallahi sai kin barmin mijina ko ta halin qaqa ne, wato in raini abina tun yana tsumman goyo sannan tun da naga yafara gima na fidda mishi sha'awar ko wacce mace aranshi, shine ke cikin lokaci qanqani zaki aureminshi duk kuwa da adalcin danayi miki na barin zuciyarshi ta soki, to narantse da karagar mulkin Abbuna baki isaba, kinyi kad'an ki shiga tsakanina da masoyina. tanagama fad'an haka ta bace bat. Afirgice Addawiyya ta falka tana share sweat daya jiqa mata fuska har yana d'iga. Kalmar innalillahi wa'inna ilaihin raji'un take ta ambaata har tasamu natsuwarta yadawo. "Shine dama labarin da uncle yake boyemin kenan? Shine dalilin da yasa tun kafin in had'u da Ali nakejin tausayinsa? To wai ma miye hakan kenufi? Shin wannan budurwa mutum ce ko aljan? Tambayoyin datake ta jerawa kanta kenan afili kuma tarasa samo ko amsa d'aya daga cikinsu. Hakanan ta tashi jikinta ba kwari ta shirya ta wuce school ko break bata samu damar yiba. Eleven dai dai tafito direct motar ta nufa, tashiga ciki ta kulle kanta ta lume cikin seat ta d'aga kanta sama tana maijin wani maqaqin d'aci a maqoshinta. "Ya ilahil alamina badai kishi nake da wacce banda tabbaci akan zancentaba? Baki isaba, kinyi kad'an ki rabani da masoyina. Shine kalmar datafi tsaya mata arai. "Ooo ni Addawiyya minyasa junnu suke bibiyata ne haka? "Mai babban suna kiragewa kanki tunani tun kafin ciwon kai yasoma hanaki karatu. "Uncle katai makeni man, kafad'amin amsar tambayoyina don Allah. "To mai babban suna, mufarkin da kikayi duk yana daga cikin sharrin shaid'an don haka kiyi watsi dashi gefen sannan budurwan da kike tunani akanta itad'in d'iya ce ga sarkin aljannu mai mulki ayankin larabawa amma ina son ki sani kece zaki galaba akanta sai dai abinda zai faru ne bayan afkuwan nasaran Allah bai lamuncemin sanin shiba amma tabbas abin yana da rud'ani. "Uhmm uncle mufarkina dai ya tabbata tunda gashi kabani labarin budurwan data ta dagulamin lissafi. "Mai babban suna kibi abinda nace kawai kinbarshi a sharrin mufarki ne kawai. "Tam, Nagode uncle Allah yabiyaka da Aljanna mad'aukakiya. "Amin, Allah yabawa dukkanin musulmai masu imani daga dukkanin cikin jinsin mutum da aljan. "Amin ya rabbi. Sosai suke ta hiransu da uncle kuma tuni ta nemi quncin da yadameta ta rasa, suna haka phone d'inta tasoma ringing, ganin sunar Haydar bayyane a bisa screen d'in ta kulle idanunta da hannayenta, wai tanajin kunyar uncle. Musmushi yayi mai sauti ya bace, jin fitar iska ta window yasa ta d'auki wayar wacce aka kira akaro na biyu. Cike da salon yanga tare da shagwaba ta furta "mijinaaaa. *Mrs j moon* [1/23, 11:50 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *38* Amsawa yayi cikin hanzari, jin yarda ya amsa tasa mishi dariya. "Uhmm my angel dariya kikemin ko? Cigaba tayi da dariyan, shima dariyan yasa. Sun d'auki fiye da 1hr suna hiran qauna, inda yayi ta tsokanarta da zancen jin kunya ita kuma tayi ta mishi shagwaba wai yabari ko tasa mishi kuka, sosai ta sashi cikin nishad'i yayi ta biyemata zuwa can sukayi sallama badon sunsoba sai don time d'in shiga lecture d'inta yayi. Sauke phone d'in tayi bisa qirjinta ta lumshe idanu ahankali ta furta "lallai duk wanda yace zai rabani da ya Ali ya tabowa kansa transformer mai tartsatsin wuta kam. Wani dogon tsaki akaja agefenta, ta kalli wurin da sauri, abin mamaki budurwan nan datagani cikin mufarkinta d'azun ita ce yanzu ta kuma gani azahiri zaune gefenta fuska ahad'e. Tsakin ta maida mata da martani, tad'ora da cewa "malama ficemin a car ko yanzu in koya miki hankali. Wani dariya mara dad'in amo budurwan tasoma, sai da tayi mai isarta sannan ta gintse fuska tace "motar banza, in kikai wasa Allah yau sai na batar dake tare da motar kuma inkince qarya cigaba damin tsiwa. Cike da fushi Addawiyya ta d'auko kwalbar red musk ta bud'eshi ta yarfa mata afuska take ta kwalla qara ta bace, ita kuma ta koma ta kwanta tana maida numfashi tare da bin kwalbar musk d'in da kallo, asannu ake janshi har aka d'agashi sama aka fice dashi ta window. Murmushi ta saki tana mai furta "thank you uncle. Abu kamar wasa budurwan junnun nan ta hana Addawiyya sukuni domin duk inda take tana biye da ita, kuma duk in tasoma yi mata bara zana sai taga kwalbar musk agefenta tako d'auka da watsa mata afuska ko jiki take zata bace tana kururuwa, sanan takasa sanar da kowa lamarin. Agefen Haydar kam, abubu sosai suka soma yi masa yawa ada dai rashin jin kuzarinsa na d'a namiji ne yake damunshi wanda yake yawan sakashi zazzabi da rashin karsashi to kuma yanzu cikin kwanakin nan harda ciwon mara yake damunshi sai ya danganta abin da dire ce tayi masa yawa jin yarda yake jin son kasan cewa da mace sosai kuma Addawiyya ce take zuwa mishi arai sai yayi ta hango surarta cikin shigar daya soma ganinta a gidansu, sannan sam halittanshi baya motsawa yanzu yakumankoma kamar na yara, abinda yakuma tada mishi da hankali kenan yayanke shawara zai je yaga doctor dai akan matsalar in kuma yaga ba'a samu nasara ba sai ya tumtubi Hajja ta soma amso mishi taimako na gargajiya. Shi yasa time to time sai yayi ta tunanin kamar ya cuci Addawiyya, anya zamansu zai yiwu kuwa? Tambayar datake mugun d'aga mishi hankali kenan, sabida sosai yakejin mai rabashi da ita sai Allah. Zaune suke su 3 qawayen juna cikin parlor n aunty Hindu, ko wacce hankalinta yana bisa laptop d'inta da alama browsing kowa keyi na assignment, dubi da yarda sukayi shiru bakajin komi sai sound of chewing gum d'in da khairi keta qas qara qas qas!!!! dashi. Cike da gajiya maryam ta d'ago ta dubi khairi tace "don girman Allah sis khairi ki fidda gam d'in nan koma masami sauqin takuramun da kikayi mana da qaransa. Fiddawa tayi ta tare da kwallawa hassan kira ya iso da gudu ta miqa mishi "kaishi cikin dustbin yaron ya amsa ya fice da gudu. Addawiyya ta saki murmushin gefen baki taceb"su hassan sun girmafa yakamata Aunty H tayo musu qanni. Caraf khairi ta mashe "jiranki takeyi kizo sai kuyi tare. Wani dariya maryam tasaka har da riqe ciki tana kallan mood d'in Addawiyya wacce tayi mugun bata rai tana zabgawa khairi harara ita kuma taqi kallonta balle tasan abinda ke faruwa. Afusace ta miqe d'auke da laptop d'inta tashige bedroom d'in Hindu, suka kuwa sake kyalkyale da dariya tare da tafawa. Biki dai ya matso sai hidima ake tayi ta kowanni part. Ana saura sati biyu aka kawo lefe nagani na fad'a domin babu ne kawai ba asakaba. Addawiyya kam tarewa tayi gidan Hindu kuma duk kwakwan Haydar Hindu ta hanashi ganinta sai dai suyi waya ko su raba dare suna hira a online ananma yayi yayi da ita ta turo mishi pictures d'inta ya ganta sai ta fake dacewa wayar bata da camera alhalin tuni yagano aunty ce ta hanata, abinda ya rasa dalilin yimasa hakan. Ana jibi d'aurin aurin Hindu ta maidata gidan Abbie. Ummie sai kallonta takeyi kamar wata baquwa sabida gaba d'aya ta sanja mata sakamakon gyaran jikin da akayi mata, abin bana wasa bane, komawa tayi kamar fure don kyau da qamshi. Dariya tayi tama ummie ganin yarda taketa murza idanunta tana kuma kallonta. Haka nan suma su maryam sukayi ta yaba gyaran tare da tsokanarta. Ita kam iyakarta murmushi take tayi domin ita kanta tasan fatarta tasanja ainun. Daren ranar ta fito wanka kenan ta tsaya gaban mirror tana qoqarin bud'e robar lotion ta tsinkayi maganarta abayanta qin juyowa tayi tacigaba da abinda ke gabanta sabida yanzu ta daina kulata komi zatace da ita tun sanda uncle yace tabar bi ta kanta kada ta maidata mahaukaciya domin ya fahimci burinta kenan sabida bata fito mata yanzu sai tana cikin mutane. "Uhmm jaririya kina son jefa kanki awahala ko? Tacebda ita. Tayi mata shiru "zan maidake abi kwatance in har kika bari aka d'aura miki aure da abin sona. Nanma ko qala bata ce mata ba, haka tacigaba da tsoratata da kalamai masu nuni da gargad'i amma ko kalma 1 taqi tofawa. Tana gama shirin barcinta ta soma Addu'a atake junnun ta bace tana mai jin haushin yarda take kasa yiwa Addawiyya komi duk in ta bayya gareta alhalin da mugun nufi take zuwa. Addu'a Addawiyya tayiwa mugun riqo sannan ako da yaushe bakinta bai rabo da ambatar addu'ar da uncle ya fad'amata ta kariya daga sharrin muguntar junnu. Yau dai aka d'aura auren RABI'ATUL ADDAWIYYA da Angonta ALIYU HAYDAR wanda dubbannin manyan mutane suka halarta halartar harda su Baffa jatau wanda yaragewa Abbie kenan cikin dangin mahaifinshi, yazo tare da 'yayan baffannisa da matarsu, yanzu babu wanda sukeso kamar yusufu wato Abbie sabida yanzu sunga babu mai arziki kamarshi duk cikin qauyensu. Sanda aka sanya bikin Addawiyya ne ummie ta matsa mishi yaje danginshi ya sanar dasu, dakyat ta shawo kanshi ya tafi sai gashi sunzo tun ana gobe d'aurin aure. Cikin tsanaki aka gabatar da taron biki. Qawayen Amarya sunsha kyau sosai sai raha suke da junarsu kamar yarda dai aka san 'yan matan amare sunayi duk in taron biki ya had'asu. Da la'asar Addawiyya ta zame jiki ta nufi garden ta zauna bisa kujeran roba. Kallo d'aya zakayi mata kasan tana cikin rud'ani, a hankali ta bud'e baki ta furta "uncle gani, mizaka fad'amin? "Nasiha zanyi miki da kuma ban haquri. "Rashi ne za'amin ko mi? "Babu ko d'aya amma ita rayuwa dole sai da haquri musanman ke da kike fuskanta barazanar gimbiya zuhfa. "To pa!! Sunarta kenan? "Eh "to wai uncle ita d'in tafi qarfinka ne dabaza karabani da ita ba? "A'a bata isheni komai ba sai dai kisani komi na duniya yana da iyaka inkin cire ikon Allah shikad'ai ne wanzajje bawanda yasan qarshensa sai shi kad'ai. "Hak ne kam "to don haka iyakar ce bai zoba amma Allah yabani iko nayi miki katanga da ita tayarda koda tazo domin cutar dake baza ta iya yi miki komi ba "tam nagode uncle sosai. "Bakomi mai babban suna. "Sai kuma ina so ki kula da Ali sosai ki maidashi tamkar yaron da yake buqatar kulawa, kiyi haquri da halin dazaki riskeshi ciki, shine jarabawar rayuwar dana taba fad'a miki zai riskeku amma in kinyi haquri zai wuce kamar ba'ayiba. "Tam uncle Allah yabamu ikon cinye jarabawar. Ya amsa "Amin. Zata kuma yin magana ta tsinkayi muryan khairi agefenta inda ta kai mata duka tana cewa "kefa wata kalan mutumce ayi ta nemanki arasa sai kace wacce taci eggs d'in makwarwa. Kallon uncle tayi, ya sakar murmushi yace "itama ta kusa aure ita da d'an uwarta hameed za'asha bikinsu bada jimawa ba. Dariya ta saki tana kallon khairi, sai kuma tamiqe tayi gaba ta juyo tace "bye, gyada mata kai yayi tare da bacewa. Khairi ta waiga taga bataga kowa ba tace "kefa aljana ce inaga, ke da qaye kike bye. "dake nakeyi koba ki fahimci narigaki barin wurin ba ne? "eh haka ne "yawwa yarinyata, duka ta kawo mata ta gofce tana cewa "hattara dai yarinya domin Amarya dai tsautsayi gareta, ki lallabani ko yanzu in sume miki. "Duka takuma kawo mata tace "oya mace man man, kuma Allah haka nan zamu kaiwa ya Haydar ya more sadakinshi. 'Yar buhu kawai, banza wanda batsa yayiwa zubar 'ya'yan kanya a baki kawai. Dariya khairi tasa sosai ta amsa "naji dai, kuma zuwa jibi kamar yanzu wata yarinya tagama zama ragowa. Afusace takaima bakin khairi duka takauce tare da fallawa da gudu tana dariya. Murmushi tayi ta furta "uhmm drama kenan ni Addawiyya a bed d'in aure, sai tasoma kyalkyala dariya, ahaka Hindu ta sameta ta janyo hannunta ta suka fito zuwa d'akin Abbie. Daf dazasu shiga tace da ita "hala uncle d'inki ne yazo miki sallama yasakaki wannan dariyan kikayi tayi kamar sabuwar kamun almatsutsai? Qince mata komi tayi har suka shige parlor n d'auke da sallama, gaban Abbansu ta kaita ta zaunar ita kuma ta dawo gefen ummie ta zauna. Nahisa sosai Abba yayi mata sannan Abbie ya d'ora da tasa, mama tayi irin nata, ummie tayi kai hatta da Salma saida ta tsoma baki kuma sosai tayi magana mai cike da natsuwa da shiga jiki. Addawiyya sai kuka takeyi, tanajin wani irin kewa yana shigarta. Ana idar da sallar magrib motocin d'aukan Amarya suka soma layi wanda dukka daga abokan Ango ne suke. Tana kuka kamar ranta zaifita mama ta sakata a cikin motar Hameed tare da babban qawarta Maryam wacce itama kukan take tayi kamar itace Amaryan. Part d'in Hajiya karima aka fara kaita. Tana jinsu taqi fitowa har suka gaji Hindu tace "sufito su tafi ai anfita hakkinta. Suna fita khairi ta fad'a bedroom d'in nata cikin kuka take fad'i take "ni kika wulaqanta momy ba kowaba, masifa ta rufeta dashi wanda yasa dole tafice bashiri domin taga inta tsaya zata bata na gidan bread. A part d'in Hajja sun sami tarba mai kyau inda tanemi da Abar mata ita da kanta zata sadata da d'akin mijinta, atakeko suka barta suka koma akabarta tare da qawayenta. Misalin tara saura Hajja ta umurceta data shiga wanka, ruwan zalla turare irin tasu na kanuri tazuba mata acikin ruwan wankar, bayan ta fito ta zuba mata wani na tsugun. Cike da kunya ta tsuguna, wani d'an ubansun swiss lace ta fito mata dashi bayan ta sata ta mulke jikinta da had'in su humra da kulacca. Koda tafito wurin su maryam duk miqewa sukayi suna yaba kyawunta Hajja tayi ta fad'in Tubarkallah masha Allah. Suna shirin kaita part d'inta Hameed ya shigo afujanjan. "Kai lafiya kuwa? Hajja ta tambayeshi cike da rud'ani. Dariya yasoma batare da ya amsata ba ya nufi inda Addawiyya take ya kai hannu zai kamata ta noqe, Hajja ta qaraso wurin ta dima mishi duka abaya ya ja baya yana fad'in "Kai hajja mugunta dai bai da kyau, kuma zuwa nayi na d'auki Amaryanmu lokacin zuwa dinner zai qure. Cikin fad'a Hajja ta amsa "Uban dinner za'a nace, ficemin dagani ko yanzu ranka yabaci. "Hajja don girman Allah kada kiyi mana haka, kibani ita kada ayi ta jiranmu. "Hameed kaficemin anan ko ranka ya baci, dinner banza da wofi, to bata zuwa ko qofa ta kashi kaji dai na fad'a maka. Cike dajin haushi ya fice, ta dubi 'yanmatan tace "irin wannan bidi'ar yake kwashe karamar aure don haka sai ku kiyaye habbaka shi. Suka amsa da "to cike da yabawa hangen nesa irin na tsohuwar. A ta qaice dai a part d'in Hajja suka kwana duk don kada ta kaita atafi dinner aboye. Da yamacin ranar akayi bud'an kai inda Alhaji muktar ya mallaka mata wani gidan hayarsa mai d'auke da parts shiga. Wayyo zo kuga yarda hankalin h. Karima yatashi, khairice tayi ta lallabata kada taraba abin fad'a qarshema sai tajata kawai suka bar wurin, tana mai cike da qunar rai agame da d'abi'ar mahaifiyarta. Taro yawatse lafiya qawayenta duk sun tafi sai maryam tare da khairi kawai suka rage. Qara gyara gidan sukayi, ya d'auki qamshi. Salma tashigo ta shiryata cikin wata koriyan atamfa mai tsad'a da kyau, ta kuma amsheta sosai d'inkin yayi mata cif2 ajiki, ta yafa gyale kalar atamfar, tafesheta da perfumes masu taushin qamshi. A gefen gado ta zaunar da ita tace "jirani inzo yanzu my Addawiy, gyad'a mata akai tayi. Maganganun isowar abokan Ango ya ankarad da ita wayau Salma tayi mata, gudu su kayi suka barta, atake idanunta suka kawo ruwa alokaci d'aya kuma taji gabanta ya bada sound dam!!! Murd'a handle d'in yayi tare da sallama, can qasar maqoshi ta amsa, tsaye yayi yana qare mata kallo zuwa can ya tako a sannu ya yaye gyalen data rufe fuskanta dashi ya d'ago kanta, tayi saurin kulle eyes hawayen dasuka maqale suka zubo ya sunya sosai ya zaro harshenshi ya lashesu. Cikin hanzari ta bud'e idanun ya sakar mata murmushi tare da furta "shine cikar so da qauna. Kayda fuskanta tayi gefe, ya juyo dashi tare da miqar da ita ya gyara mata zaman gyalen sosai ya rufe mata jiki sannan yaja hannuta suka fito parlor inda abokananshi suke jiransu. nasiha tare da addu'o,i sukayi musu sannan syka ajiye mata kayan siyan baki kamar dai yarda al'adar mafi aka sarin hausa fulani yake. Sunagama fita ya kulle qofar parlon ya dawo ya cimmata inda yabarta. Zama yayi a gabanta samar carpet ya zuba tagumi yana aikin kallonta. Tura baki tayi tare da sakar mishi hararan love tace "miye kuma? "Uhmm uhmm qaunar kice ce zata maidani kurma. Bata san sanda dariya ta kufce mata ba ganin yarda ya kwaikwayi voice d'in mata. "Masha Allah ya furta da qarfi tare da d'agata cak kamar baby, bai sauketa ko ina ba sai cikin bathroom, yace "oya muyi arolla sai muyi sallah domin nuna godiyarmu ga Allah. Bayan sun idar da sallah ya d'au ledar da suka shigo dashi yace "bismillah, girgiza kai tayi alamar ta qoshi. Ture ledar gefe yayi ya miqe yashiga wanka bai jimaba yafito yazo ya zauna gabanta yace "ehem fara aikin ladarki tun yanzu,kallon qari batani tabishi da shi, ya miqa mara cream "shamamin zakiyi, kauda fuska tayi gefe, ahankali tace "niban iyayiwa gato shafa ba, "yau zaki koya zuwa gobe kisoma da koyon yarda ake wanke gato. Ganin da gaske yakeyi yasa ta marairaice fuska takoma kalan tausayi tace "ya Ali nidai kazo kaci abinci tukunna "in har baza kiciba nima na haqura, shiru tayi tana kallonshi. "Mai babban suna tun safe baici komi ba don haka ki lallabashi yaci. Haran gefen da sautin yafito tayi, murmushi mai sauti yaka saki tare da cewa "affuwan Amarsu ta ango yanzu zan wuce dama sallan godiya ga Allah na tsaya binku jam'i amma ba burina naga sirrin kuba. Da sauri tasoke kanta qasa cike dajin kunyar qarshen Ancen shi. "Asuba tagari mai babban suna, motsa bakinta tayi alamar amsawa sai kuma ta juyo wurin Haydar taga har yagama shafanshi ya sanya night wear, turare yake fesawa. Tashi tayi ta d'auko plate ta juye kazar ta zuba fresh milk a cup tazo gabanshi tasoma bashi abaki saida ya qoshi sanna yabata taci kad'an tace taqoshi. Miqewa tayi tashiga toilet, yabita da kallon tausayi, gamace har mace amma lafiyar mijinta sai a slow, abinda yake ayyanwa a zuciyarshi kenan. Kansa bisa qirjinta yake wasa yakeyi da sumarta, sai hira yake mata kad'an kad'an ita kam gabanta sai bugawa yakeyi sam bata fahimtar inda hiran nashi ta dosa. Cire kanshi yayi a bisa qirjinta ya kwance zaren gaban riganta ya tura hannunshi ciki ta rutse idanu, yace "mi yasa gabanki yake beating haka? Tak'i cewa komi, sai da yakuma tambayarta ta amsa ahankali "bakomi barci nakeji kawai, shafa fuskanta yayi ya kai bakinsa daf da ear d'inta yasoma hura mata iska yana mai furta "yi barcinki my life, "uhmm uhmm to kabar huramin iska nan zata iya hanani barci "ohk na bari, ya rumgumeta tsam tsam yana ceqa muyi addu'ar shiga barci tukunna, suna shafawa ya kuma cewa "to asuba tagari kayan Haydar, murmushi tayi tare da kulle idanunta. ASUBA TA GARI ADDHAY😍 *Mrs j moon* [1/24, 9:09 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *39* Qamk'ameshi tayi sosai, ita kuma sai qoqarin rabasu takeyi tsawon lokaci takasa yin nasara akansu sai ta ja baya ta koma kura bakinta yana fidda wuta ta nufosu ko kafin ta iso iska yazo yayi sama dasu tabisu ta gudu haka sukayi ta keta dazuka kamar walkiya tana biye dasu cikin siffarta na kura awani fili mai yawan itatuwa iskan ta saukesu, ita kuma kuran tuni hasken wurin yasa ta daina gani sai juye juye takeyi tana tsala ihu mai firgitarwa, zuwa can tabace bat. Jin nishinsa nafita da qarfi kamar mai tsere, shiya ya falko da ita. Har yanzu yana kwance bisa qirjinta shafa kanshi tayi tana mai cewa "ya Ali lafiya kuwa? Shiru bai motsaba saima qara cukumeta da yayi yana magana wanda bata fahimtar miyake cewa. Addu'a tasoma tofa mishi afuska zuwa can yaja ajiyar zuciya ya tashi firgigit. Da lalube yayi turn on d'in globe haske ya gauraye d'akin. Kallon kallo suka somawa junarsu, ta matsa jikinsa ta miqa hannu tasoma share masa sweat d'in daya jiga mishi face har zuwa jikinsa. Da sauri ya rungumeta yana sunsuna wuyarta zuwa qirjinta sai kuma ya d'ago ya kama face d'inta ya had'a da nashi yacigaba da sauke numfashi. Da kyat ta iya motsa bakinta tace "wai mike faruwane mijina? Muryansa na rawa ya amsa "mufarki nayi mai ban tsoro naga wasu mutane masu girma zasu jefaminke cikin rami mai zurfi ga duhu shine nake ta dambe da su inason na kwaceki amma nakasa daf da zasu jefaki naga kin kwace kin zama iska mai qarfi iskan ya turasu cikin ramin su duka take wani baqin hayaqi ya turnike wurin a dai dai nan na falka. Shiru tayi tana auna mufarkin da irin wacce tayi yanzu. Voice d'insa ya katse mata tunani inda yake cewa "Rabi'atu wallahi ni bancika yin mufarkin ababen tsoroba haka ba inko kikaga nayisa to abin zai iya zama azahirance shiyasa yanzu duk na rud'e kada wasu suzo su sacemin ke, yaqara rungumeta yacigana dacewa Allah in hakan ya kasance bansan halinda zan fad'aba, ya saketa daga rungumar da yayi mata ya d'aga hannayenshi sama yace "Ya Allah yasa na mutu nabar matata Addawiyya ba wai ta mutu ta barni ba. Da sauri ta amsa "ba Amin ba, Allah ka d'auki ranmu atare ya amsa "A'a indai mutu nabarki ki rainar mana yaran dazan bari inhar ina da rabon barin kwaina a duniya. Kuka ta fashe mishi dashi sosai, zai kamota tayi hanzarin sauka tafice zuwa parlor. Amfani yayi da inda sautin muryan kukanta yafitowa qasa qasa ya isa wurin sabida parlon babu haske. Rungumeta yayi tasoma kicikicin kwacewa ta kasa. Jin yarda yake sauke numfashi kamar mai shashshekan kuka yasa ta d'auke nata kukan bashiri tasoma magana "wayyo Allah natuba kayafemin nasa mijina kuka a darenmu ta amarci, don Allah ya Ali kada kayi fushi dani na fad'a cikin fushin Allah tare da tsinuwar mala'iku akan kukan dakakeyi, don Allah badan niba kayi shiru. Cak ya d'ata zuwa bedroom ya zaunar da ita bisa cinyoyinsa ya kai hannu cikin riganta yana latsa mata tumbi yace "kezan bawa hakuri akan sakaki kukan danayi amaimakon nishad'i, sannan ki rubuta ki ajiye Ni Aliyu kami kikayimin tundaga yau har izuwa ranar da za'azaremin rai na koma ga mahaliccina nayafe miki. Cikin muryan kuka ta soma magana "banson haka ya Ali, banson zancen mutuwa, banson haka, yazaka tasani agaba da tsawon darennan kayi tamin maganar mutuwa, agaskiya bana so. Yana shafa sumar kanta alamar rarrashi yace "affuwan my heart beat bazan qaraba insha Allahu kinji? Tura baki tayi taqi amsawa, yayi saurin kai lips d'insa kan nata. Da kyat tasamu ya saketa ta ruga toilet da gudu yabi bayanta. Arollah suka d'auro yajasu sallar nafia raka'a 4 bayan sun idar kowa ya bud'e alqurnin kareem yasoma karantawa cikin ransa. Sai da suka sallaci subahi sannan suka koma barci. Aunty Hindu tayo aike yakai sau 3 da break fast d'insu amma sai adawo ace mata anyi nocking basu bud'eba dan haka sanda taga 11am tayi sai ta fito da kanta Salma nabiye da ita abaya, bugu d'aya tayi Addawiyya tazo tabud'e mata, rigan barci ne ajikinta kanta ba d'an kwali sumarta duk ta yamutse sai hamma take zubawa alamar junya takeji. Idanu waje Salma tace "ke Addawiy kina da lafiya kuwa? Jibi yarda kike amma kika iya zuwa bud'e door, to da wasu canne kumafa ba muba? Yamutsa fuska tayi ta amsa "nasan daga ku saiko su khairi zasu zomin part da safen nan "au 11am kike kira safia? "Uhm nifa yunwa yataso dani ina daf da shiga kitchen naji ana nokin nataho na bud'e. Hindu taja hannunta ta zaunar tace "akul nakuma ganin kin fito bud'e qofa a haka, kuma yanzu kije kiyi wanka sai kizo ga break d'in kunan tun 7am na aiko muku dashi sai adawo acemin kuna barci. Amsawa tayi "tam, mungode sosai Allah yabar zumunci "Amin suka amsa tare da miqewa suka fice ita kuma ta nufi ciki. Atare suka fito da Haydar cikin shigar shadda coffee colour sunyi mugun kyau sai qamshi suke zubawa, direct dining suka zarce sai da sukayi nak sannan yaja hannunta suka nufi part d'in Abba. Sosai yaji dad'in ganinsu, yayi musu nasiha mai ratsa jini da jijiya tare da samusu albarka ya miqo keys guda biyu yace "amsa Haydar motoci ne kai d'aya ita d'aya, cike da murna sukayi masa godiya da adduar Allah yajiqan magabata. Daganan part d'in Hajja sukayi itama tayi ta samusu albarka, anan suka zauna har lokacin sallar azuhur tayi, haydar ya nufi masallaci ita kuma tayi tare da Hajja. Da dare suna zaune a parlor yanata aikinsa cikin laptop d'insa ita kuma tana yanka mishi fruits. Hira suke ahankali kamar masu rad'a, "uhmm ajiye computer nan kasha fruits inka gama sai ka d'ora"ohk angama beauty. Abaki tabashi yasha sosai sai da yaqoshi sannan yariqe mata hannu ya janyota ya bud'e qafafunsa ya sata ciki, ta zabura zata miqe ya maidata da sauri yace "oya open ur mouth aramawa kura aniyarta. Kulle eyes dinta tayi "no ya Ali am ok kasan bandad'e dagama cin super ba"uhmm kinsan Allah kozakiyi amai ne sai kinsha. Kwabe baki tayi cikin shagwaba tace "Allah inkasani amai kai zaka kwashe kayi mopping d'in wurin "eh naji bud'e dai kigani. Tas ta shanye tana lasan lips. Dariya yasa mata ta shammaceshi ta mannawa cinyarsa cizo ta ruga da gudu yako mara mata baya yana fad'in "la la la la laaa kika cijenni to sai na rama. Tana qoqarin kulle qofa ya danno tasaki ta ruga toilet nan ma kafin ta kulle ya shigo. Cak ya d'au kota, tasoma yi masa ihu yayi sauri rufe mata baki da nashi, tuni ta natsu tasoma amsar saqon. Satin ta biyu ta koma school inda shi yake kaita ya kuma d'aukota, baya damu dako yana da aiki a office. tarairayanta yakeyi kamar egg, itama tana qoqarin bashi kulawa sosai, rayuwa mai cike da inganci suke gudanawa. Su maryam suyi tayi mata tsiya wai yanzu ta koma mara kunya tunda agabansu takeyiwa Haydar fari da shagwaba don iskanci acewarsu har rumgumeshi takeyi da zarrar sun tashiga cikin motar in yazo d'aukanta, takan ce dasu "adaiji tsoron Allah arage liqamin sharri ko asami na cin exam, su kanyi dariya in sunji tace haka. Yau ma kamar kullum qarqarfe 3pm ta fito hole d'aukan darasi. Cike take da gajiya ga kuma maranta data matsa mata da ciwo akwanakin nan wanda tasa dalilin ciwon tadai san 2 days kenan dagama mensuration period d'inta don haka bazata danganta ciwon da shiba. Zaune suke ita su maryam suna ta hiransu ita kuma tayi shiru tana jin wani feeling yana damunta cije labbanta tayi tare da qamqame jikinta wuri 1. Khairi ta dubeta cike da kulawa tace "ya dai kayan ya Haydar? Banza tayi da ita, maryam ta dafata tace "baki da lafiya ne ko har mun kusa zama mummies ne? Kallonta tayi da eyes d'in wanda suka sanza launi da kyat tace "dadies zaku zama dai. Dariya suka sa mata, ta miqe ahankali ta nufi inda ta hango Haydar yana gyara parking. Daf da zata isa ta hango gimbiya zuhfa zaune a back seat suna had'a idanu ta sakar mata murmushi taji muryanta cikin kunninta tana cewa "yau mun hole da masoyina don haka wannan dire data tasomiki nice sanadinta kuma haka zakiyi ta fama da ita har ajalinki yariskeki sannan romancing danabarku kunayi itama narasa yarda zanyi na hana kune shiyasa nasamo mafita kinga yanzu nike da nasara akanki kenan. Kallonta tayi sosai tako jinjina mata kai alamar tabbatarwa fuskanta d'auke da walwala, wani maqaqin abu taji yataso ya tokare mata numfashi wanda tabbas ta san zafin kishine ya taso mata, adaidai kuma lokacin Haydar ya iso gabanta ya d'an sunkuya yana gyara mata zaman shoes d'inta. Ya d'ago face d'insa yayi cike da murmushi yace "sannu haskena, ya karatu? Kallonshi tayi abirkice sai kawai taga yayi mata wani baki kamar tukunyar data shekara 10 ba'a taba wanke bayarta. Cike da fushi ta tureshi kad'an yarage bai kai qasa ba, ko kulawa batayi ba tanufi motarshi kamar zata tashi sama. Kokafin ta isa makirar tuni ta bace bat sai sautin dariyanta takeji yana mata amsa kuwwa cikin ears. Tsaye tayi tana gyada kai sai kuma ta juyo face d'in sake kamar ba ita ba. "Uhmm mijina zo mutafi kaga 'yan matan jami'a sai kallacemin kai sukeyi. Cike da sanyin jiki ya yaqaraso ya bud'e mata qofa tashi ya rufe, ya shiga yayi key suka bar wurin zuciyarsa cike da tarin tambayoyi. Ita kam kwanciya tayi sosai a seat d'in sai gyada kai takeyi tare da sakin murmushi lokaci zuwa lokaci bisa ga dukkan alamu sako take amsa. ********Watansu uku da aure aka sawa su khairi rana sati hud'u, Khairi zata auri d'an yayar momynta namiji yayin da Hameed zai auri budurwansa Zuhuriyya 'yan boko wayayyiya mai kayan alatu cewarshi. Addawiyya da Haydar zaman su lafiya sai dai matsalar rashin kuzarinsa fa har yanzu babu alamar nasara kuma yaqi sanar da Addawiyya komi akai haka uncle sai boye mata yakeyi yaqi bata haske akai, yadai bata shawaa da tabar yin mafani da maganin da ummie takawo mata haka nan tabar shan wanda Hindu take bata domim suke kawo mata yawan jin ciwon mara. Tuni ta bari kuma ciwon maran yayi sauqi sosai amma dai abinda takasa fahinta shine wai ko Haydar namiji ne? Amsar datake son sani kenan kuma kunya ta hanata tambayarshi. matsalar junnj zuhfa kuwa yanzu kam sai tarihi sabida taji ruwan ayoyin Allah da Addawiyya tayi taja mata alqunut dasu sai gashi dakanta ta bayya mata tana kuka wai tabarsu har abada dama mamanta bata son abinda takeyi, tuni Addawiyya ta yafemata tare da neman mata shiriya na Allah yasa tayi tuban na har abada kenan. Yau bata da class don haka a part d'in Hajja ta yini. tana cikin kitchen d'an wake takeyi mata sai tajiyo muryan Haydar qasa qasa yana ma Hajja bayani abinda taji ne yayi mugun tada mata da hankali ta dafe qirji, tuni hawaye sungama wanke mata fuska fad'i takeyi "wh zakayimin haka ya Aliyu, sirri yana da dad'i ai. Wani qarin rud'ani kuma sai ji tayi yana cewama Hajja "nariga da nagama yanke shawara zan saketa kawai amma dai yanzu miye shawaranki akan hakan? Dafe qirjinta tayi dake barazanar barewa biyu, ta jingina jikin da cabinet sabida jirin dayasoma bilayi da ita, ahankali take ta maimaita hailala hawaye yanata cigaba dayi mata sintiri a fuska. *mrs j moon* [1/26, 10:42 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *40* Shiru shiru ko zataji amsar da Hajja zataba shi amma bataji komi ba da alamar ma sun bar parlon. Cikin rashin karsashi ta tsame d'anwaken ta wanke tare da zubawa a kula, dama tuni tagama had'a kayan had'in daza'aci dashi sai kawai ta d'aukesu ta kai dining ta jera, duk abinda takeyi bakinta bai yanke da ambaton sunar Allah ba, shi yasa asannu tariqajin natsuwa yana shigarta tare da kuzari. Koda ta kammala komai sai zuciyarta tayi ta ingizata datayi wucewarta kawai batare da tayiwa Hajja sallama ba har ta kai bakin qofa zata fita sai kuma ta dawo da baya ta nufi bedroom d'in Hajjar inda take zaton tana zata sameta. Saida ta saita kanta sosai ta boye halinda take ciki sannan tayi nocking daga ciki Haydar ya amsa mata, ta shiga kanta a qasa ta matsa jikin Hajja ta d'an kwanta sannan cikin sigar wasa tace "komi yayi ready 'yar tsohuwarmu ke yake jira kizo kiyi ta jifan yunwa dashi. Cike da dariya Hajja ta shafi kanta ta amsa "nagode sosai d'iyar albarka, Allah ya sa ki gama da iyayenki lafiya ya kuma baki zuri'a d'ayyiba. Sunne kanta qasa ta kumayi ta amsa "Amin can qasar maqoshi ko Hajja datake kusa da ita bataji mi ta ceba. Haydar kam cike da zumud'i ya amsa "Amin da qarfi. Kallonshi tayi ta watsa mishi harara ya zaro idanu ta kuma watsa mishi wani harara tare da jan siririn tsaki wanda iyakarshi lips d'inta ya tsaya. Ganin ya yunqura zai iso wurinta tayi hanzarin miqewa ta nufi hanyar fita tana cewa Hajja "bara na watsa ruwa kafin akira magrib, batajira amsawarta ba tafice da sauri har da had'awa da gudu. "Kagani ko Ali, yanzu mace kamar wannan mai tarin nutsuwa da hankali ga girmama manya, uwa uba kuma maccen sirri ita ce zaka nemi yin nesa da ita don rashin tunani, to wallahi summa billahil azim akul nakuma jin zance makamancin wannan daga gareka, kaji ko? Cikin sanyi ya amsa "naji Hajja kuma insha Allah zanbi shawaranki na sanar da ita lamarin "tam haka babu laifi, Allah yayi muku Albarka "Amin. Koda yashigo part d'insu bai ganta cikin parlor ba sai ya zarce cikin bedroom d'inta, nanma bata ciki. Wasa wasa ya duba ko ina bata nan, tuni hankalinsa yasoma tashi ya fito compound yana ta waige waige, juyowar da zaiyi ya ganta abayarshi riqe da hannun hussain. Wani ajiyar zuciya ya saki wanda sai da tajiyoshi amma baisa ta d'aga kai ta kalleshi ba, tayi wucewarta ciki. Cike da wasi wasin laifin da yayi mata take fushi dashi yabi bayanta. Tana shiga room d'inta ta kulle qofa koda ya murd'a handle d'in yajishi gam sai ya wuce room d'inshi, arollah ya d'auro yafito ya ja hannun hussain suka nufi masjid. Addawiyya kam tadad'e cikin toilet tana kuka har sai da taji kanta yasoma yi mata ciwo sannan tayi wanka tare da d'auro arollah ta fito. doguwar riga kawai ta zira ta tada sallah, bata bar wurinba sai da ta sallaci isha'i ta kuma gabatar da shafa'i da wuttiri. Cream ta shafa tayi simple make up ta sanya wata riga mai gajeren hannu tsawonta bai gama kai laps d'intaba, ta fesa turare sosai sabida zamowarta ma'abociya son qamshi ne sosai. Direct kitchen ta zarce ta tayi worming food d'in datayi before taje part d'in Hajja. A dining ta shiryasu ta d'auki qaramin cup ta had'a tea wanda yaji garin titta tadawo parlor ta zauna tana kurba kad'an kad'an. Haydar ya shigo d'auke da sallama ta amsa mishi dakyat ya iso ya zauna gefenta ya qurawa cinyoyinta idanu yanajin wank abu na kai komo cikin jikinsa, hannun yakai samar cinyarta ya latsa tayi wani zabura ta miqe tsaye ta sanja kujera baki a ture, cikin sanyi jiki yabita. Tun kafin ya iso ta miqe ta shige room d'inta da sauri ya bi bayanta yana cewa "wai meke damunki ne haka beauty? Bata amsa shiba. tana shiga ta murza key ta zame jikin qofar ta saki kuka fad'i take why kayimin haka? Ina alkawarinmu da juna na cewa duk wuya duk rintsi muna tare da juna haka matsalarmu tare zamu warwareshi, amma duk ka watsar, sai ta kuma fashewa da kuka, ni kai nakeso ba wai ka... Sai ta kasa qara sawa ta sunne kanta tsakanin cinyoyinta cewa take "in narasaka ya Ali bansan wani irin hali zan fad'aba, wash Allah na qirjina zafi yakemin kamar zai fashe,,, tafad'a hakan cikin kuka mai cin rai. "Don girman Allah heart beat ki bud'e door d'in nan, kibar kukan nan haka, ki fito ki sanar dani laifina kinji? wallahi bansan laifin danayi miki ba, ki bud'e ki sanar dani dan Allah. tana jinsa ko motsi taqiyi. Yafi 30 minutes yana aikin yi mata maqiya ta bud'e amma taqi bud'ewa haka nan yagaji ya koma parlor ya had'e kai da gwaiwa yana son tunano laifin da ya aikata mata haka da zafi. Ko dai taji zancen danakewa Hajja ne d'azun? To in kuma taji ai tsayawa zatayi muyi magana na fahinta ba fushi ba, to wai ni minayi mata ne? Abubuwan da yayi ta saqawa kenan cikin ransa har dare ya tsala batare da yasani ba. Ranar dai kowa room d'insa ya kwana cike da kewar juna sun kasa rintsawa tsawon lokaci sai juye juye suketayi. Bawanda yasan sanda barci barawo yasaceshi, sai kawai farkawa sukayi sukaji anata kiraye kirayen sallar subahi. Koda tafito taduba dining taga komi bai taba ba sai kaji ba dad'i, d'auka tayi ta zubda wanda ya lalace wanda bai lalaceba ta kai kitchen. Tsaye tayi a kitchen d'in tarasa mizatayi sai kawai ta dafa ruwan zafi ta juye a fulas ta soya eggs kad'an dai dai cin mutum 1 sabida yarda takejin bakinta baza ta iya cin komi ba yanxu, d'imama ferfesun kayan cikin datayi jiya tayi ta kawosu dinning ta jera. Daf da zata shiga room d'inta shi kuma yafito cikin shirin zuwa office kallon kallo sukayiwa juna, tayi saurin janye idanunta shi kuma ya wuceta batare da yace da ita kanzil ba. Sosai yayi mata kyau cikin shigarsa ta dogayen kaya na wani yadi milk, sai tasami kanta ta binsa da murmushi. Daf da zai fice parlon ta daure tace da shi "ya Ali, cike da mulki ya juyo batare da ya amsa ba, had'iye yamu tayi bakinta na rawa sabida yayi mata mugun kwarjini tace "bakayi break fast ba, kamar mai ciwon hak'ori ya amsa "naqoshi daga haka yasa kai ya fice. "Kam bu!!!! Mi guy d'innan yake nufi ne? Wato tabarman kunya da hauka ake nad'eta kenan? Uhmm zanko nuna mishi ni Autan ummi nafi gaban wulaqanci, kuma wallahi kadawo yayita ta qare in auren aure in kuma rabuwan rabuwa, kai bama zan iya zama da kai ba ehee!!!! Tafad'a cikin qaraji, fuuuu tashige room d'inta sai kai da kawo takeyi tana jan tsaki. "Mai babban suna ba'ayi haka ba, kiyi haquri, zaman aure sai da hakuri, kuma dama ance zo mu saba zo mu zauna, rayuwa bata taba inganta sai tare da qalu bale cikinta don haka nake roqonki da kiyi haquri ki saurari bayaninsa. "Uncle!!!! Yau banaji kuma bana gani dan haka kayi tafiyarka kawa kawai kabarni domin kaima mun bata da kai tunda kasan komi ka boyemin. Iska mai qarfi yasoma kad'awa, sanyi yasoma shiga jikinta tunk tasoma rawar sanyi bakinta na rawa tace "please uncle stop doing dis, i'm begin u, washhh!!! Shikenan nazama iceeeeeee sai ta tafi luuu zata fad'i Haydar yayi saurin tareta ta fad'a jikinsa. Manage 👏🏻 Momyn sadiq this page is for you😍😘 Allah yabar zumunci ya raya mana su sadiq rayuwa mai cike da ni'imomi. Amin *mrs j moon* [1/27, 4:18 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *41* K'amqameshi tayi bakinta yana karkarwa cewa take "Ya Ali katai makeni sanyi nakeji kamar ina cikin snow. Taba wuyarta yayi yaji babu alamar sanyi saima dumi da yaji. "Washhh!!!!! Banso nace, kabari don Allah, zan mutu wayyyo ummie sanyi zai mashe ni, sai kuma maganar ta daina fita sai motsa baki takeyi jikinta yana rawar saniyi hak'oranta sai had'uwa da juna suketayi. Haydar iya rud'ewa yayi yama rasa mizaiyi sai kawai ya d'auketa akafad'arshi ya isa inda ac yake yayi switch d'insa ya kuna ta dumama d'aki, duk tana qamqame dashi, ya koma ya shimfid'eta a bisa gado, ya tube kayan jikinshi yarage dagashi sai vest da boxer. Ya d'agota ta kufce ta cure wuri d'aya sai kiran sanyi sanyi take tayi cikin muryanta dabata fita sosai. Da kyat yasamu ya cire mata rigan barcin dake jikinta yarage daga ita sai pant. Boobs d'inta suka bayya baiko lura dasuba hankalinshi yana kan ganin ta dawo normal. Vest d'in jikinsa ya kuma cirewa yaja blanket ya rufesu ruf ya rungumeta sosai yana ta murza skin d'insa da nata yana kiran "sorry sorry, sorry my angel yanzu zan ragemiki jin sanyin, haka qaddaranmu take, ki yafemin dan Allah. Ita kam sai tura kamta takeyi cikin qirjinsa tana kuma jin sanyin yana raguwa kad'an2. Tsawon lokaci ya d'auka yana abu 1 kuma cikin ikon Allah sai tadaina jin sanyi, tayi lamo a jikinsa ganin haka yasa ya bud'e su kad'an, yaga tayi barci sai lokaci ya lura da kayan ruwanta a fili suke, jim yayi yana qaremusu kallo cike da sha'awar su, ya kai hannunsa kansu yana shafawa asannu sannu tare da lumshe idanunsa. Afili ya furta "Allah kabani lafiya na biyawa wannan cikakiyar yarinyar buqatarta, donshi tunaninsa dire ce ta dameta har ta fad'a cikin wannan yanayin. Xuwa can ya koma ya kwantar da face d'inshi tsakanin boobs d'inta tare da lumshe idanu yana mai jin wani yarrr yarrr cikin jininsa, bai jimaba shima barci yayi gaba dashi, bako tuna saqon da Abba ya turoshi d'auka ba, shine daliline ma dawowarshi har zai wuce yaji yana son ganin beauty d'insa duk da bata mishi rai datayi daren jiya, ashe da rabon zai risketa cikin halin damuwa ne haka. "Uncle haka dama kake da iya cin zalin? Tafad'a cike da shagwaba. Dariya yasaka mata sosai ta bata rai tayi bakinta a ture ta kuma cewa "inaga kasheni kasoyi da sanyi, bakaji yarda nakejin dhigarsa ba har cikin bargona kamar ana bud'esu ana ziraramin ruwan qanqara. "Mai babban suna kin batamin rai ne sosai, tayarda inayi miki magana kina maidamin da martani cikin tsawa har dacewa baruwanki dani shine na yanke shawaran bari na horaki koda nan gaba in kin tuna baza ki kumamin haka ba. Kamar zatayi kuka tace "to kayi haquri insha Allah bazan qaraba fushin abinda ya Ali yayimin ne ya shafeka. "Nima bazan kuma cutar dakeba mai babban suna kiyimin affuwa, wannan ma danayi duk yabi yadameni ga khadijata nan sai fushi take dani wai nayi mugunta abinda ba halina bane kuma wai narasa inda zanyi sai akanki. Shiru tayi tana kallon inda yake nuna mata da hannunsa can ta hango wata budurwa zaune akujera wasu mata gewaye da ita da alama fadanci sukeyi, suna had'a idanu da ita tasakar mata murmushi tare da d'ago mata hannu, itama hakan ta maida mata da martani sannan tajuyo tace da uncle "yaushe zakuyi aure ne da juna? "Ankusa mai babban sun, dafatan zakixo bikinmu ko? "Uhmm kanaso acigaba da cemin jinsin junnu kenan? "Eh, inaso indama da dayarda zanyi ki koma jinsinmu ai da tuni nayi kinkoma cikinmu da zama. Wani zabura tayi tare da miqewa tana cewa "uncle inaga yanzu kadaina bani kulawa kamar da. Dawo da ita yayi ya zaunar, ta fizge hannunta tana hararanshi murmushi ya saki yace "affuwan matar Aliyu Haydar. murmushi ta saki tare da gyara zama tace "uncle sanar dani gaskiyan zancen danaji Ya Ali yanayi da Hajja. "Uhmm mai babban suna kinfayi alqawarin bazaki kuma tambayata maganar laluran Ali ba. Dafe goshinta tayi tana mai furtan"oh!! sam na manta, to barshi kawai. "Anqi a barin sai nafad'a, kafeshi tayi da idanunta tare da baza ears. Ya koma serious sosai sannan yasoma magana "mai babban suna abinda kikaji yana fad'a hakane tabbas baya da qarfin dazai iya saduwar aure dake kuma shine yasa kakarsa ta matsa sai yayi aure sabida ya sanar da ita laluranshi abinda yayi ta boyarshi tsawon lokaci, duk don ya gane ko abin da gaskiya ne. Bari kiji yarda yakejin laluran... halittanshi ne yake komawa qarami ya kuma sirance sannan wata zubin ya nad'e ya kom ciki to in yayi haka shine yake yawanjin ciwon mara da kuma son kasancewa da mace. Ada nayi tunanin gimbiya zuhfa ce take maida mishi da halitta haka sai gashi yanzu bata tare dashi amma still yana fuskanta hakan. Cikin zubar hawaye tace "uncle to baije hospital bane? Yaje mai babbn suna sai dai har yanzu basuyi nasara ba kuma kakarshi tana amso mishi na gargajiya shima bawani sauqi sai na Allah. "Ikon Allah sai kallo, to yanzu uncle miye mafita? Jim yayi yana tunani zuwa can yace "zan nemi gimbiya zuhfa na tuntubeta naji intana da sa hannu cikin lamarin to ta taimaka tacire ko yasami lafiya in kuma haka Allah ya halicceshi to bamu da mafita sai abinda Allah SWA ya wanzar donmin shi cuta lokaci d'aya yake shigar bawa amma warakarsa sai a sannu, to muna fatan samun warakar cikin amincin Allah. Nisawa tayi jikinta duk yayi sanyi tace "Allah yakawo mana mafita cikin lokaci qanqani "Amin mai babban suna, uhmm wata yarinya ta qosa tafad'a cikin kogin amarci, yafad'a hakan cike da zolaya. Saurin rufe fuskanta tayi tana mai cewa "wallahi banson haka uncle "to nabari, yanzu dai sai ki daina fushi dashi "uhmm Allah uncle sai nayi, sabida tun kafin muyi aure yakamata yasanar dani "mai babban suna yana gudun kada kiqi amincewa dashi ne lokacin "to lokavin da mukayi aure fa? "Shima tsoronsa kada kiqi zama da shine "uhmm to yanzu da yake son rabuwa dani fa "bazai iyaba fad'a kawai yakeyi ganin kamar yana zalintarki na rashin baki hakkinki da yagaza yi. Kauda face d'inta tayi gefe tana qunquni. Dariya Habibullah yayi sosai yace "kinganki ko? baza ki daina fad'amin magana bako? Cike da shagwaba tace "cewa fa nayi banson zance kwanciyar nan, kabari "to nabari shi kenan ko? Nodding kanta tayi tana dariya qasa qasa. Mai babban suna koma duniyarku kinji nima natafi tamu duniyar, yana gama fad'an haka yazama haske ya bace. Asannu tasoma bud'e idanunta har ta bud'esu tar, jin kamar qirjinta yana mata zafi yasa tamiqa hannunta ta sauke shi bisa kan Haydar d'an zabura tayi abinda ya hayfar da farkawarshi ya zuba mata idanu tayi saurin kulle nata murmushi yayi kad'an ya d'ago ya kai face d'insa daf danata yace "ya sanyin hope yabari yanzu ko da saura? Tura bakinta tayi taqi cewa komi, fidda finger d'insa 1 yayi yasoma zagaye mata baki da sauri ta bud'e idanunta tare da tureshi daga jikinta tana cewa "ni ka d'agani duk kabi ka taramin gajiya. Dariya ya saki tare da sauka daga gadon, itama saukan tayi tana miqa ganin ya kafeta da idanu yasa ta dubi kan ganin ta zir sai panta ta kwalla qara ta fad'a bed tare da rufe jikinta ruf da blanket. Dariya abin yabashi sosai, cikin dariyan ya shige bathroom, har yafito tana qudundune shirya wa yayi ya fice batare da yakuma kulata ba amma tanajin sautin dariyarshi qasa qasa. Yana fita ta diro tamurza key a qofarta ta isa gaban mirror tana kallon kanta sai kuma tayi saurin duqawa qasa ta tura kanta tsakanin cinyoyinta, "ya ilahi yariga da yagama ganina tsaf yan,, ta furta cike dajin kunya. zuwa can kuma ta miqe ta nufi toilet da gudu. Yinin ranar a d'aki tayi shi taqi fitowa parlor wai ita kunyar kada su had'u da haydar takeyi, kuma tana da aji ranar amma taqi zuwa sam. Haka tayi tajin motsinsa don bai kuma fita ko ina ba shima, ga yunwa tanaji amma taqi fita tasami abinda zara ci, sai bayan la'asar taji fitarsa sannan tafito sad'af2 kamar wata mai laifi tanufi part d'in Hindu, acan taci abinci kuma bata baro part d'in ba sai bayan sallar isha'i. Tana fitowa zata koma part d'inra taci karo da Hameed, qin tsayawa tayi duk da tanaji yana yi mata magana. bayanta yabiyo suka iso har cikin parlor n tare. Haydar suka samu zaune yana cin take away, kallansu yayi na 'yan daqiqa sannan yace "haskena zo kiyi aikin lada, kallonshi tayi ya gyada kai "oya taho kiyi feeding d'in mijinki, cikin dibara ta cilla mishi harara yana 'yar murmushi yataso ya kama hannunta ya zaunar samar cinyarshi tare da kai bakinsa daf da kunninta yana yimata magana. Kunya kamar me taji tana son tashi amma ya saka hannunsa a qugunta ya riqe gam, hakanan ta zauna amma takasa kallon inda Hameed yake tsaye. "Uhmm yayi masoyan asali, to kuyi abinku nima nan da 1 week zan wuce gori ai. Hameed yace dasu haka. Harara haydar ya cilla mishi yaja baya yana dariya tare da nuna Addawiyya yace "Allah sai kinsani in muka had'u, wato kinsan soyayya kike muradi yin shine ina yimiki magana kika mai dani washa hana gashin baki ba geme ko? Sauke kanta tayi bisa kafad'an Haydar ta amsa "baruwanmu dakai tunda aure yasoma sanja ka, ace mukwana gida 1 mutashi amma baza muganka ba sai dace irin haka. Zama yayi yana sosa kansa cike da jin kunyarta yace "ayimin affuwa hidmace tayimin yawa wallahi kitambayi mijinki kiji. Kallo Haydar tayi ya kashe mata 1 eye tare da d'aga mata gira, da sauri ta sauka daga jikinsa tanufi room d'inta daf dazata shiga ta juyo tace "kada kadamu d'an qanina na yi maka uziri, tashige ciki da sauri domin gujewa kallon dake cikin idanun Haydar wanda yake saukar mata da kasala sosai. Duk dariya suka kwashe dashi mara dashi, tanajinsu itama dariyan tayi tana mai furta "Allah ka barmu tare da juna har izuwa qarshen rayuwarmu. Haydar da Hameed kuwa tare suka qarasa cin food d'in sannan suka d'ora da zancen yarda bikin zai kasance, sai after 10pm Hameed yayi masa ya fice. Tana kwance cikin kayar barcin mai laushi riga da wando, chatting takeyi dasu maryam tana ganin ya shigo tayi sauri rufe data. zaunawa yayi gefen bed tare da kamo hannunta yasoma muzawa ahankali, rintse eyes d'inta tayi tana maijin wani abu yana hawo bisa kanta zuwa dukkanin parts d'in jikinta. ganin yanayin data shiga sai yayi saurin sakinta ya sunkuyar da kansa qasa yana maijin wani d'aci cikin maqoshinsa, sosai take bashi tausayi yasan duk sanda ya rabeta tanajin feeling amma domin adalci irin nata bata taba nuna mishi rashin yarda ba, "Allah kabani lafiya in ina darabon samunsa. Can qasan maqoshi ta amsa da "Amin ya rabbi. Kallon mamaki ya sauke mata sai kuma ya haye bed d'in sosai ya kamota ya miqar zaune ya mannata da qirjinsa tare dayin gyaran murya yasoma magana a natse.... *mrs j moon* [1/28, 8:39 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *42* "Rabi'atul Addawiyya kimin affuwa don Allah, ki agazamin ki zauna dani, kada ki gujeni, inkika gujeni tabbas zuciyata zata buga, ina roqonki domin soyayyarki da fiyayyan halitta Annabin rahama S.A.W Ki haquri da matsalata ki zauna dani kinji? Shiru tayi masa tana aikin kallonshi bako qiftawa. Cike da fargaba ya had'a hannunsa da nata ya qamqe gam ta saki 'yar qara kad'an, duk da haka bai sake taba ya kuma matse yatsun nata sosai, "washh Allah!! ta furta da qarfi, sai lokacin ya saketa tare da zamewa ya kwanta rigingime kansa na kallon ceiling. Asannu ta matsa ta kwantar da kanta bisa qirjinsa cike da sanyin murya tace "mi ke damunka? Daga kwancen ya kallota ya kai hannu bisa sumarta yana shafawa ahankali yana mai bata amsa "bana da kuzarin irinta ko wanni cikakken d'a namiji, bazan iya yin sunnar aure da keba ataqaice dai bana da kwazon da zan iya biya miki buqatarki. Had'e rai tayi kamar bata san komi ba a kai tace "kasan hakan mi yasa kaqi sanar dani tun kafin muyi aure ko sai bayan aurenmu kasami laluran? Tashi zaune yayi ya tallabo face d'inta da hannayenshi yace "ina gudun kiqi aure nane lokacin, gashi ni kuma ina tsananin sonki bazan iya barinki ba sannan tun da na soma mallakan hankalin kaina nafahimci ina da matsalar. Shiru tayi tana kallomsa sai kuma sauke kanta qasa ta kuma cewa "amma mi yasa kaqi sanar dani sanda mukayi auren? "Tsoron kada kice naci amarki ne ko ki tubure kiqi zama dani shiyasa nayita boye miki. "uhmm to yanzu kana da yaqinin cewa bazan yima bore ba ne komi? Shiru yayi zuciyarsa na kai komo, yakasa bata amsa. Jan numfashi tayi tare da d'agowa ta kalleshi tace "to kuma miye na zuwa kana tona sirrinka wurin Hajja alhalin kasan ta soma tsufa ba komi ne yanzu zata iya dannewa ba, baka tunanin sanin matsalar zai iya jefata cikin damuwa? "Wallahi tunanin haka sam baizomin ba beauty "uhmm to yayi amma miye nane man shawaran son rabuwa dani alhalin kasan bazaka iya ba? Dafe kansa yayi cike da nadama domin yanzu yagama gano tsaf taji zancenshi da Hajja, wataqila shine yahaifar da fushin data keyi dashi. "Ina sauraron ka mr Haydar, tace dashi cike da tsiwa. Had'a hannayensa yayi wuri 1 yace "affuwan one's again haskena kuma sirrina, lallai nasan na kusa in tafka aikin dana sani sai Allah ya nufeni da rahama yadawo dani cikin natsuwata amma kisani billahil azim ko daidai da second 1 bantaba tunanin zan iya jure rashinki ba sannan abinda kikaji nasanar da Hajja na fad'ane kawai inji ra'ayinta akai sai gashi tayimin wankin babban bargo wanda dakyat nashawo kanta ta sauka kema ina qara neman affuwanki daki yi haquri ki yafemin duk abinda nayi miki wanda yajefaki kicin bacin rai. Tura baki tayi tana d'an hararansa tace "ni komi ya wuce sai dai banson ka kuma fad'ama wani matsalarka irin haka donshi d'in sirrine. "Tam bazan sakeba heart beat. D'an murmusawa tayi tace "Ya Ali, ya amsa "na'am kayana, ta mintsili cinyarsa yasaki qara cikin wasa, ta gyara zama tace "ina son ka rubuta aranka cewa ni Rabi'atul Addawiyya zan rayu da kai acikin ko wani irin hali ka tsinci kanka har izuwa ranar maha'shar, zan zamo mai boye maka sirrinka har izuwa sanda lafiya zai wadaceka haka zan dage dayima ka addu'ar samun sauqi wurin mai duka sannan kasani koza mu dawwama ahaka ne ina tare da kai domin ban mance alkawarin damukayiwa juna ba a cikin garden, don haka kacire duk wani damuwa tare da wasi wasi kawai mucigaba da fadama Allah matsalarmu insha Allahu zaimana maganin komi kaji kayan Addawiyya, ta qara fadan haka tana kashe mishi 1 eye tare da sakin mishi wani murmushi mai kwantar da hankali. Wani runguma ya kai mata, ya soma sunsuna ko ina na jikinta yana shafawa cike da nishad'i kuma da hanzari yake aika mata da saqon. Gani zai jefata awani hali yasa tayi dibaran janyewa tana sauke mumfashi da sauri da sauri. Kallonta yayi cike da tausayawa ya kuma yanjota jikinshi tana qoqarin kwacewa yace "a'a my angel kibari inbaki hot romances yarda zaki sami relief. "Uhmm ya Ali tafi kayi wanka sai kazo inbaka labari mai dad'i "ya maqe kafad'a kamar wani yaro yace "a'a naqi wayon salon kafin indawo kinyi barci ko? "Allah bazanyi ba, zan jiraka "ohk tam zomuje kitayani. Idanu ta zaro tana girgiza kai, lakace mata hanci yayi tare da miqewa yana cewa "matsoraciya kawai, very soon zan soma yi miki wankan ai kuma tas zan wanke komi nawa da kyau nakuma zo na liliyeshi da mai. Da sauri ta kauda kanta gefe cike dajin kunyar zancensa, yana dariya ya shige cikin bathroom zuciyar cike taf da qaunarta domin hakika tayi mishi bazata data yarda zata zauna da shi ahaka d'auke da lalura. Kwanakin dasuka biyo baya zamane sukeyi mai cike da tsafta tare da tsantsar bawa junarsu kulawa wanda yake bawa mutanen dasuke tare dasu sha'awa ainun. Bikin su Hameed da khairi yazo don gashi har nan da kwanaki biyu masu zuwa d'aurin aure, hidima yayi ma Addawiyya yawa sabida Aunty Hindu dazata shige gaba akan abin tana fama da laulayi mai wahala don haka sai itace ke gudanar da komi tare da taimakom Hajja domin Hajiya kareema Alh. Muktar yaqi sakar mata ragamar hidimar har kuwa da abinda yashafi 'yarta khairi yaqi aminta da lamarinta, tayi ta haukanta har tagaji. Ita kam khairi ko a gyalenta indai tabata kayan gyara na Amare tana sha amma data kawo mata qorafin anyi kaza da kaza zata bar mata wurin sabida tasan tana tofawa to tsiya zata bita dashi. Da yammacin alhamis suka gabatar da walima mai kyau da tsari. Ranar gajiya mai suna ita kam Addawiyya tayi ta, don haka tana idar da sallar isha'i ta bingirea wurin ko wanka bata samu tayi ba. Koda su maryam sukazo tabasu gift d'in da khairi ta samu awurin qawayenta zata kaiwa momynta, sunyi2 ta tashi ta kasa saima layi take musu suna haka Haydar yashigo ya korasu suka fice cike dajin haushi, shi kuma ya ragemata kayan jikinta ya d'agata cak sai toilet. Ita dai tajitane kawai cikin ruwa mai zafi sosai ta zabira tare da sakin qara. Dariyan dataji yana mata ta fahinci wanka zai mata tako soma mishi shagwaba ita bataso yabarta zata iya da kanta, bai kula taba saida ya sulleta tsaf ya nad'ota kamar baby. Koda yagama shiryata sai ya shiga nashi wankar kafim yafito tuni takuma lulawa duniyar barci. Rugumeta yayi yana cike da yabawa kwazonta ayayin aiwatar da hidimar bikin hae barci shima ya lula dashi. Washe gari bayan sakkowa daga sallar juma'a aka d'aura auren khairi da angonta kabir sannan aka wuce aka d'auro na Hameed da Amaryanshi zuhuriyya wacce yabata sunar masoya wai riyya. Taron biki yayi armashi sosai, qawayen Amarya khairi a part d'in Addawiyya suka tare, sai hidimarsu sukeyi cike dajin dad'i. Da hayaniya yayiwa Addawiyya yawa sakamakon ciwon da kanta yake mata tun safe sai ta shige room d'in Haydar ta kwanta. Kwanciyarta ke da wuya ta tsinkayi maganar babibullah yana cewa "sannu mai babban suna, ta amsa "yawwa uncle. "Mai babban suna nacika miki alkawarinki na tambayo gimbiya zuhfa tace min ba sa hannunta cikin lamari, k'addarar daga Allah ne, zata dai tai maka da addu'a insha Allahu zai sami lafiya yazamo kamar ba'ayiba. "Tam uncle Allah yasa hakan ya tabbata "Amin Amin. "Bari nabarki ki huta amma kada kisake kiyi barci a irin wannan lokacin kinji? "Tam bazanyi ba, nagode da samuwarka arayuwa sosai, Allah yasaka maka da alkhairi "Amin. Yana bacewa ta lumshe idanun face d'inta d'auke da murmushi ta furta "rayuwa kenan mai cike da qalubale, Allah kabamu ikon cinye wannan jarabawar. ***bayan kwana biyu duk 'yan biki sun watse sai gidan yakoma kamar da, tsit bakajin hayaniyar komi sai nasu hussain shima sai ranakun hutun qarshen mako. Awani safiya Haydar tare da Addawiyya suke matsa jiki sanye suke cikin sport wear suna ta tsale kad'an kad'an a filin dake gefen garden, in tagaji ta duqa, ya miqar da ita su cigaba. Da dai tagaji sosai sai ta kwanta tana maida numfashi ya iso ya d'ora kanshi bisa ruwan cikinta ya kai hannunsa bisa boobs d'inta yana cewa wai mi kike sha haka ne suke qara cika? Ture hannunsa tayi cike danshagwaba ta amsa "ba kaine ka damesu da yamutsa ba, ai dole suyi ta kumburi kamar fanke. 'Yar dariya ya saki tare da matsasu da qarfi kuma alokaci d'aya yana mai mannawa cibiyarta kiss ya zarce zuwa samar qirjinta yana qoqarim d'aga mata riga xai tura kansa ciki tayi sauri tureshi tamiqe da gudu ya bita suka soma zagaye filin suna dariya. Koda yayi nasaran kamata baiyi wata wata ba ya had'e bakinsu wuri 1 sai son kwacewa takeyi amma ta kasa, sai da yagaji don kansa sannan ya saketa tayi baya kamar zata fad'i yayi saurin tareta, idanunta lumshe ta motsa bakinta kad'an tace "Ya Ali yanzu in wani yashigo yaganmu haka mizamu ce? Mai makon ya amsa mata sai kawai ya kuma had'e bakinsa da nata, ahaka yayi mata d'aukan jarirai ya nufi ciki da ita, ita kam sake maqalqaleshi tayi domin ji tayi kamar zai yar da ita. Wano uban tsuka taja tare da furta "Wallahi nayi mugun tsanar ki Addawiyya kike koma wa oho. "Eh dole kice kin tsani 'yar mutunci d'iyar mutanen arziki. Cike da kad'uwa ta juyo tana kallo Hameed wanda yake tsaye abayanta tun sanda take leqen su Haydar kuma duk yaga abinda ya wakana. "Mi yakawo wannan maganganun kuma my AH? "Kinfi kowa sani sannan mi Addawiyya tayi miki da zafi da har kika tsaneta? Banza tayi dashi zata raba ta wuce ya fisgota ya sakar mata mari yana huci yace "sai kin fad'amin maza nawa sukayi hawan daba akanki kafin in aureki? Agigice taja baya tana mai jifarshi da wani mugun kallo, acikin ranta kam tsoro ne cike fal domin bata taba zaton wannan ranar zata risketa ba. "Zaki amsamin ko sai na karya miki wuya kin mace na huta daganin ragowar wasu? Banza kawai karya mai fuska biyu, wato kinsan baki da gaskiya shiyasa kikayitamin zille2 ko? To wallahi kisani bazan zauna da keba harbsai natabbatar da ingancin lafiyarki sabida haka wuce kishirya inje abinkikamin ke ciki da bai don bazanyi da kaina ba. Zuhuriyya kuka ta fashe dashi mai cin rai, ko kallo bata isheshi yasakai yashige room d'insa yana maijin tsanar kanshi da kanshi duk da bai bi kyalkyala banza ba da haka bai sameshi ba, yanace shi sai mai nonuwa da duwawu to ga irinta nan ya kwasowa kanshi ta kaici, shiba mazinaci ba amma gashi ya auro mazinaciya. *Hattara dai 'yan mata budurcinki 'yancinki ako ina* This page is for you Aisha manumfashi, inajin dad'in soyayyarki ga Addawiyya sosai Allah yabar zumunci 👏🏻😘 sannan tace inbakibar ce mata dangin aljanu ba sai ta kai samar dutsen rafin cigogo kinkwana acan 😅 lol *mrs j moon.* [1/30, 9:18 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *43* Koda ya fito a inda yabarta tana risgan kuka nan ya sameta, shiru yayi yana kallomta ransa abace, doguwar tsaki ya ja tare da daka mata tsawa ta miqe bashiri ya nuna mata hanyar room d'inta yana mai bata umurni "dalla wuce kishirya tun ban sauke hushina akanki ba, cikin rawar jiki ta wuce tana mamakin bala'i irin na Hameed, ashe dai haka yake da tijara? Tambayar da tayiwa kanta kenan cikin ranta. Ahanyarsu ta zuwa hospital kowa yayi shiru, sai saqe saqe sukeyi cikin zuciyoyinsu, ya d'an juyo ya kalleta har yanzu bata bar zubar hawaye ba ga kumatun ta nan inda ya mareta har ya tasa kauda kansa yayi yana mai jin tausayinta cikin ransa sabida sosai yake sonta da gaskiya. Anyi binke iya bincike kuma antabbatar da lafiyarta lau haka shima sumul yake, koda suka dawo gida baibi ta kanta ba room d'insa ya shige ya kwanta yana ta tunanin wannan lamari abinda sam baiyi zatoba sabida dubi da irin tarbiyyan gidan data fito ashe duk ta bogine, uhmm lallai shi natsuwa ba'a fuska takeba dace ne kawai abin. Sosai lamarin da ya risketa yabashi mamaki in bai mantaba yataba riqe mata hannu tayi ta mishi masifa wai ita ba 'yar iska bace waye2 amma ji yarda yasameta kamar qofar gari, dafe kansa yayi zuviyarsa tayi masa nauyi atake yasoma kiran sunar Allah cikin lokaci qanqani yaji sanyi yana ratsa mishi zuciya. "Abdul hameed don soyayyarka da ma'aiki SAW kayimin affuwa, maganarta ya doki cikinn ears dinshi. Kallonta yayi sai daga kwancen sai tausayinta yanemi karya mishi zuciya. Janyota yayi jikinsa yace "fad'amin gaskiya miyasa kikayi yawon ta zubar? Lafewa tayi jikinsa cikin muryan kuka tasoma magana "ba'ason raina na aikata ba, sharrin qawayene wata rana a skul qawarmu tayi birthday shine muka had'a party domin tayata murna to anan suka samin abin maye ya bugar dani mazan wurin sukayi watandensu dani, lokacin dana fahimci haka nayi kuka mara adadi sannan naja musu Allah ya isa yafi cikin Duran, baya kwana biyu sai na fad'a halin son kasancewa da d'a namiji abinda ya kaini da nemansu da kaina to tundaga nan na sami abinyi lokaci zuwa lokaci nake aikatawa, kuma agida bawanda yasani domin Abu yana da tsanani kuma yayarda dani ainun shi yasa na boye musu halin dana ke ciki tun farko don gudun jefasu cikin tashin hankali. Ranar wata littini da bazan manta da shiba arayuwata, na sawo kai kenan cikin hostel sai naji qawayena suna gulmar wai zubamin magani mai tada dire sukeyi shi yasa nakejin son kasancewa da d'a namiji, jin hakan hankalina yayi mugun tashi na koma da baya don kada suganni. To kundaga ranar na koma gida daga can nake zuwa skul sannan tuni na na d'aukewa qawayen nawa wuta baruwana dasu har xuwa yanzu banayi musu magana don ko bikina ban bari sun sani ba. Ta fashe da kuka mai qarfi tana buga kanta aqirjinsa, riqeta yayi cike da tausayi yace "ya isa hakanan riyya Allah zaiyi miki sakaiya, qarshensu bazai kyauba, sannan nayafe miki Allah ya yafe mana baki d'aya. Cike da matsanancin kuka ta qamqameshi, shima qamqametan yayi tare da cewa "fad'amin abinda Addawiyya tayi miki da zafi da har kika tsaneta? "Uhmm ni batayimin komi ba haka kawai naji bansota sam. D'aure fuska yayi ta mau ya nunata da yatsa " banson sakejin makamancin wannan maganar abakinki, ina ruwarki da ita da zuciyarki zata tsaneta? To kisani ita mai kyawun mu'amalace ga kowa kuma lashakka babu nasan bata damu da keba bama tasannkalar kiba tunda har yau nasan bata shigo part d'innan ba, kota shigo? Girgiza kanta tayi tare da amsawa da A'a "to kinga tabbacin bata saki aranta ba kenan, don haka ina son kisama ranki sonta kuma ki bita tunda itace babba dake a aure duk da kin girmeta a shekaru, dafatan kin fahimceni? "Eh, ta amsa ahankali "tam Allah ya had'amana kanku "Amin ta amsa amma aqasan ranta sam batajin sonta kuma tarasa dalilin hakan. Daganan suka koma kamar wani abu bai faruba sai dai Hameed yasaka mata idanu sosai don gudun kada azo tubar mazuru tayi. Awani dare Haydar ne zaune yana aiki a computer. Addawiyya ta iso wurin cikin shigar barci, ta zira kanta a kafad'arshi tana leqen abinda yakeyi kallonta yayi ta hasken computer n tare da shafar fuskanta "my angel barci yazo ko? "Uhmm ta amsa tare da kai hannunta cikin rigarsa tasoma wasa da sumar dasuke kwance aqirjinsa, kuma kallonta yayi yaga idanunta kulle kashe computer n yayi ya janyota ta dawo samar cinyoyinsa "ya akayi ne beauty? Murya can qasa ta amsa "wani kewa nakeji yana baquntata wanda narasa ta miye, ina fatan Allah yasa ta alkhairi ce dai "to Amin haskena. Miqa tayi tare da hamma yabita da kallo yanajin tausayinta sabida yasan bakomi ke damunta ba sai dire amma ita da alama bata gano hakan ba. "Tashi muje na ragemiki kewar dake damunki. Kallonsa tayi kad'an ya kashe mata ido 1 tura baki tayi tace "kai ya Ali ni bawannan abin ne ya daniba kawai ji nake kamar zanyi rashin abu mai mahinmanci arayuwata, wata qila Ummie ko Abbie zan rasa. Sai saka mishi kuka sosai. Shima sai jikinsa yayi sanyi eyes d'insa ya kad'a ji yake kamar ya tayata kukan amma yasan in yayi haka zai jagula komi don haka sai ya d'agata cak ya nufi bedroom da ita, da kyat yayi nasaran rarrashinta ta daina kukan barci ya kwasheta sai sauke ajiyar zuciya take tayi. Washe gari haka ta tashi ba walwala kuma taqi zuwa skul duk kuwa da test d'in dakake dashi don haka 12pm Haydar yataso daga office ya d'auketa suka nufi gidan su Abbie, acan suka yini sai dare duka dawo tuni ta kawo normal suka cigaba da shinfid'a rayuwarsu mai cike da nagarta. Lamarin zamansu da zuhuriyya kuwa ba yabo ba fallasa domin tuni Addawiyya ta gano tsanarta atare da ita don haka sai ta fita shirginta tabawa banza ijiyarta inba sun had'u part d'in Hajja ba har mantawa take da wata halitta zuhuriyya. Al'amura suna ta tafiya cike da nasarori yanzu haka matar Hameed zuhuriyya ta haihu tasami baby girl ansamata sunar ummansu suna kiranta da ummul bait haka itama khairi ta haihu ansami takwaran Abba suna kiranshi da Abbul bait. Aunty Hindu dama ita ta rigasu haihuwa twins ta kuma sinbulowa duka mata yayin da Adda Salma itama ta kuma samun qaruwa yanxu yaranta uku biyu maza mace d'aya. Addawiyya ce dai tun suna saran ganinta da ciki har sun haqura sun duqufa fad'ama Allah itama ya bata intana da rabo. Karatunsu kuwa tuni har yazo gaba goshi ita da khairi maryam ce dai ake ta fafatawa don karatun medicine sai anjajirce. Hajiya karima angamu da iftila'i domin tana zaune taji tasa tashi kafin ace me qafafunta sun kunbure suntom, anyi maganin asibiti har saudi an kaita amma ba cigaba illa dai anyi nasaran kunburin ya baje tafiya dai ne bata iyawa dole aka bata keken guragu take amfani dashi. Ranar da ta hau tayi kuka mara adadi har tabawa kowa tausayi, atake kuma nadama yazo mata tayi ta fad'an dukanin tuggun datayi ta had'awa tun tuni tare da roqon gafararsu musanman Hindu wanda taso hala kawa 'ya'ya Addawiyya ta cecesu sai lokacin kowa yaji abinda tayi akayi ta mamaki lamarin kuma hakanan suka yafe mata tana hawaye tana yi misu godiya. Abba yasamo wata dattijuwa dazata riqa kula da ita domin danginta kowa yaqi yarda yazo sabida sanda take da lafiyarta sunce bata tsinana musu komiba sai mulki da gadara. *uhmm duniya kenan mai abin al'ajab kuma rawar 'yan mata na gaba ya koma baya, Allah kasa muyi kyakykyawan qarshe* Yau da jin soyayya Haydar ya tashi domin duk inda Addawiyya tayi yana laqe da ita yana aikin latsata gashi aiki takeyi na snacks d'in birthday d'in su hassan, duk yabi ya takurata yana hana mata aikin yayi sauri. Agajiye taja ta tsaya tana hararanshi "Ya Ali don Allah kabarni haka nan, ingama aikin dake gabana sai kayimin koma miye bazan hanaka ba. "Kintabbata? "Eh wallahi zanma duk abinda kake so "tam gama kuwa in kasheli da love. Siririyar dariya ta saki tace "wai ba kamar gaske "au haka kikace? To zan ko shayar dake mamaki kam "uhmm nidai naji matsa kagani inyi ingama lokaci yana tafiya. Sa hannu yayi yasoma ta yata har suka mammla da komi suka gyara inda za'a gabatar da party n sannan sukayi wanka tare wurin shiryawa da kyat yabarta tagama yin kyalliya. Yara sun taru sosai na dangi da makwafta. Abin kuma yayi kyau sosai, Addawiyya ce ja gaba sai photos ake tayi misu da videos. Daf da za'a watse taro zuhuriyya ta baiyana d'auke da yarinyarta mai kama da ubanta sak. Addawiyya na ganinsu ta soma hararan su cikin wasa tace "akoma bama so tunda kuna gidan amma sai amakare za kuzo tayamu murnan. Kallon tsana ta cilla mata tana murmushi, amma cikin kissa yarda ba kowane zai gane hakan ba. Addawiyya kam tsaf tanago inda ta dosa sai kawai ta saki murmushi itama mai d'auke da matsalarki ce. Hannu ta miqa don tabata ummul bait amma sai ta noqe ta wuceta abinda yayi mugun jefata cikin jin kunya ta sauke kanta qasa tana wasa da yatsun hannunta. Azuciye Hameed yazo ya fincike yarinyar ya iso inda Addawiyya take tsaye ya miqa mata ita tare da cewa "ni Hameed indai nine mahaifin ummul to daga yau nabaki ita kyauta na har abada, yanzu kece uwarta kuma banson kiyimin musu akai indai na isa nayi miki kyau ki amsa. Tsit wurin ya d'auka kamar mutuwace ta gifta. Muryan Hajja ya katse shirun "Hamidu lallai wannan kyauta ta faran tamin rai sosai kuma Rabi'atu ta amsa ta gode ainun Allah yata yata riqo. "Amin mutanen wurin suka amsa, ta d'ora sai dai ina roqon abarta zuwa sanda za'a yayeta sai ta amshi kayanta. "Hakan zance Hajja, cewar Haydar. Hameed ya jinjina kai ya amsa "tam ai abin kamar gobe ne in muna da rai. Cike da murna Addawiyya ta d'aga ummul sama tace "Allah ya albarkaci rayuwarki 'yata, ina sonki sosai, jama'a kushaida. Sai addu'ar Allah tayata riqo ake tayi mata, yayin da zuhuriyya tuni tabar wuri zuciyarta cike da jin zafin mulkin mallakan da Hameed yayi mata batare da shawaranta ba. Daren ranar Haydar yazo mata da wani baqon lamari wanda yagigi tata, domin daga romances sai ya zarce, tuntana d'auka lamarin wasane sai ga abu ya tabbata lafiya tasamu gareshi. Taso ta d'aure amma ta kasa sai kawai ta saka mishi kuka tana bashi haquri amma ina Haydar yayi nisa bayajin kira, ya fad'a wata duniya da bai taba zaton da ita ba. Koda yadawo natsuwarshi sai kawai ya fashe da kuka yana jera godiyarsa ga Allah subbahanahu wata ala da ya jarabbeshi da lalura kuma gashi ya yaye mishi alokacin dabaiyi zatoba. Shi ya taimaka mata ta gyara jikinta sannan ya d'aukota ya shifed'e bayan ya fidda bedsheet d'in daya baci ya sanja wani, tsarkake jikinsa yayi shima ya zo ya rungumeta yasoma magana "Rabi'a Allah yasa kigama da iyayenki lafiya, Allah yayi albarka arayuwarki, Allah yacika miki dukkannin burukanki na alkhairi Allah yasa murayu da juna in da rabon haka, Allah yasa kece matata cikin aljanna, wallahi ina sonki Addawiyya, bana son inbarki, Allah yasa sanda zamu koma ga mahaliccinmu a tare da juna za'a zare ranmu. Can qasar maqoshi ta amsa "Amin. Bayan sun sallaci subahi Haydar yace mata kansa yana ciwo abu kamar wasa sai gashi yasoma fizge fizge duk tabi ta rud'e. Number Hameed ta kira qara biyu yayi ya d'auka cikin kuka tace "Hameed kazo ya Ali zai tafi yabarni, ai bai gama jin metace ba yafito da gudu zuhuriyya tana tambayarshi bai ma san tanayi ba. Tai makon gaggawa yasoma bashi har numfashinsa ya dawo normal sannan ya d'aukeshi suka nufi hospital dashi. Addawiyya tun tana kuka da hawaye har ya komo hawayen ya qafe, ga jikinta da batajin dad'isa sam, abu dai duk yataru yayi mata yawa, takasa zaune ta kasa tsaye sai kai kawo takeyi. Hailala tare da istiggifari take ta ambata afili, addu'ar Allah yabashi lafiya kuwa tayisa har tabawa uku lada, cikin 'yan awanni har tayi wani mugun rama. *mrs j moon* [1/31, 4:54 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *44* Zaune take bisa kujeran roba a gaba gadon dayake kwance ta sarqe hannunta da nashi tare da kwantar da kanta samar qirjinsa idanunta lumshe, fatarsu duk ya kumbura da alama barci ne ya d'auketa ahakan. Can daga d'an nesa take hangoshi cikin shigar sutura masu kyau tare da kyalkyali har suna kashe idanu don walqiyarsu. Tafiya tasomayi don ta isa wurinsa amma sai taga yana mata nisa sai ta soma gudu gudu kad'an nanma dai takasa isa inda yake sai kawai ta soma kuka tana kiranshi tare da falfalawa da matsanancin gudu, yana dai ta cigaba dayi mata nisa tare da yi mata murmushi yana kuma d'aga mata hannu ita kam sai gudu takeyi don ta isa wurinshi amma sai taga kamar ana janta baya ahaka har ya bacewa ganinta ta zubbe bisa guiwoyinta a filin mai cike da ciyayi kwance lufluf tare da kalla mishi kira da qarfi "Ya Alee!!!!!. Kiran da yayi amsa kuwwa cikin room d'in tare da haddasa farkawanshi a firgice sabida amsa kuwwan da sautin yayi cikin kunninsa, bakinsa d'auke da salati. Shafa kanta yayi ahankali tare da kiran sunarta, tabud'e idanunta wanda suke cike da hawaye sai sauka sukeyi bisa quncinta. Hannu ya kai yasoma share mata hawayen tare da girgiza mata kai face d'insa cike da annuri. Kallonsa takeyi kamar yau tasoma ganinsa sabida sai taga yaqara mata kyau sosai kamar bashine aka kawo rai a hannun Allah ba, agefe 1 kuma zuciyarta cike take taf da mamakin mufarkin da tagama yanzu. Shin ko me hakan ke mufi? " beauty bani ruwa insha maqoshina kamar zai kama da wuta. Maganarshi ta katse mata tunanin data afka ciki. Jikinta ba kwari ta motsa domin d'auko mishi ruwan roba. Tana shirin bashi ruwan kenan Hameed ya shigo tare dasu Abba. Hameed yayi hanzarin cewa "A'a Addawiyya kar kibashi bari na dubashi tukunna. Komawa tayi ta zauna ahankali tana rintse idanu sabida zafin datakeji kad'an2 aqasarta har yanzu sai kuma tayi saurin zamewa ta sunkuya ta gaishe da Abba tare da aunty Hindu suka amsa suna tambayarta mai jiki "yaji sauqi ta amsa. Hameed ya dubashi tare zare mishi drip d'in sannan ya bashi ruwan da kanshi. Ya tambayeshi "yanzu ina yake mishi ciwo? Ya amsa "ba ko ina, naji sauqi sosai. "To Allah ya qara lafiya, cewar Abba suka amsa "Amin. Aunty Hindu ta had'a mishi tea sabida koda zaiji karfin jikinsa. Ita take bashi abaki fitar Abba da Hameed yasa ta miqawa Addawiyya ta bashi ba musu ta amsa tasoma bashi har yasha rabi sanna yace "haskena shanye sauran don nasan kema bakici komi gashi kuma bakya da lafiya. "Mike damun autan ummin? Hindu ta tambayeshi. Murmushin qarfin hali yayi sannan yace "aunty tana buqatar kulawa dan Allah kitaimakeni tasamu. Had'e rai tayi tana zabga mishi harara ya saki 'yar dariya kad'an tare da janyota jikinsa tayi sauri tashi ganin haka Hindu ta fice d'akin yarage daga ita sai shi. "Haskena wurin yabaryi miki zafi ko? Banza tayi mishi, ya matse ta ta saki 'yar qara, ya sake cewa "yabari ko kuwa? "Eh, yabari "da gaske? "Eh "to madallah sannu kinji na wahalar dake jiya ko? Kauda kanta tayi gefe sannan tace "Ya Alee kabar yawan surutu kasan kana buqatar hutu inji doctor ko? "Uhmm beauty to nayi shiru amma d'an matsamin qafafuna jinsu nake kamar ba nawaba. Cike da tausayawa tasoma matsa mishi qafafun shi kuma yayi mata quri da idanu yana aikin kallonta bako qiftawa. Suna a haka zugan su ummie suka shigo, tayi saurin komawa samar kujera ta zauna suka kayi tayi masa ya jiki yana amsawa cike da murna. Ita kuma ta gaishe dasu cikin ladabi. Yafito aunty Hindu yayi da hannu ta matso daf da bakinsa ganin yana tunata yasa tayi saurin barin d'akin sabida tasan maganar d'azunne bai bariba. Koda tafito gefe ta samu ta zauna tazuba uban tagumi. Hameed ya qaraso wurin ya zauna gefenta yace "yakamata ki cire damuwa aranki haka nan ko don ingantuwan lafiyarki. "Uhmm kawai tace. Ya gyara zama yana qare mata kallo cike da mamaki, donmin ya kauda zarginsa sai yace "amma kamar qafafunki sunayi miki ciwo ko? Kallons tayi tama rasa mizatace mishi. "Nagano hakan ne tayarda kike tafiya kamar ba dai dai ba. Kauda fuskanta tayi cike da yabawa rashin kunyarshi wato amatsayinsa na doctor yariga da tuni ya gano komi kenan amma don tsaban rainin wayau tare da fitsara shine zai zo yasata agaba da tambayar wofi. "Kaga malam banason sharhi, ni lafiyata lau don haka sai ka barni naji da abinda ke damuna. "Uhmm "aunty Addawiyya kenan daga zan tai makeki sai ki hauni da masifa, to Allah yabaki lafiya amma dai ina cikin mamakin yar da abin yakasance haka alhalin kun wuce 3yrs da aure yanzu. Tsaki taja tare da miqewa tayi gaba tana qoqarin dai daita tafiyarta tun kafin wasu sa'idanawar su gani. Murmushi yayi tare da shafan sajensa ya furta "kin canci asoki da girmamaki, ina tayaka murna brother da samun 'yar albarka. Tana shiga Hindu ta kama hannunta tayi qasa da murya "autan ummi mike damunki Haydar yaketa jaddadamin cewa in baki kulawa bakyajin dad'i? Kallon inda yake kwance tayi yako sakar mata murmushi ta wulla mishi harara tareda tura baki ya yafitota ta kaqe kafad'a. Ita dai Hindu sai kallon ikon Allah takeyi, ganin sunqi daina maganar kuramen sai taja hanunta zuwa bakin gadon tana mai cewa "ku sanar dani ko laulayin ciki takeyi dama naga tayi rama ta kuma qara haske. Cike da shagwaba tace "aunty abar kaza cikin gashinta kawai amma dai nasan ni banda komi. "To ai shikenan tunda bakyason musani muyi addu'a akai. Zama tayi gefen gadon taqi kuma cewa himdu komi. "Kaiko Ya Alee burinka ka tona mana sirri ko? "A'a haskena, inadai son abaki kulawa ne wanda rashin layar nan tahana in baki "to bana so nace, kabari kana sani jin kunya "tam nabari hajiyata, d'an murmushi tayi tana jifarshi da hararan wasa. Kwanaki biyun da yayi 'yan uwa da abokan arziki sai tururuwar zuwa dubashi suketayi kuma alhdulillah yasami lafiya sosai. A yammacin daya cika kwanaki hud'u yana zaune ya d'ora qafafunsa bisa cinyoyin Addawiyya wacce take yanke mishi farce da cut nail hira sukeyi qasa qasa xuwa can ya ja numfashi mai qarfi tayi saurin dubashi ya sakar mata lallausan murmushi yace "yanzu ace in na mutu wazaki aura? Wani kallo tacilla mishi fuska ahad'e tace "banson zancen mutuwanan fa ya Alee "uhmm heart beat ai kam zancen mutuwa tazama dole sabida ko kana so ko baka so dole sai ka d'and'ani d'acinta don haka amsa min tambayata kawai. Cike da fushi ta miqe tana cewa "daga kai nagama aure don haka sai ka daina kiran mutuwa in kuma kaqi Allah yau bazan kwana da kaiba, gidan Abbie zan tafi sai da safe nadawo. A'a zo kusa dani matata, bazan sake maganar ba. Matsawa tayi ya sun kuyo daf da kunninta yafad'a mata wani magana wanda yasa ta zabura ta ja baya sai kuma tafice tana zubar hawaye. Tana fita taci karo dasu maryam, khairi tare da zuhriyya da fara'a ta tarbesu tana boye musu hawayen da tafito dashi tare suka dawo d'akin. Hira suke tayi cike da raha har da zuhriyyan yayin da ummul ta maqale mata taqi yarda dako mamarta ta amsheta. Tanaji ajikinta idanun Haydar yana kanta amma taqi duban inda yake sabida bata huce zancen takaicin ya yayi mata d'azun ba. Kwanarsa shida aka bashi sallama suka nufo gida. An sallamoshi da kwana biyu da hantsi tana cikin kitchen taji ya kwalla mata kira ta kashe stove da hazari tare da amsawa. Afalo ta cinmashi ya takure wuri d'aya yana rawar sanyi ta sunkuya tana tambayarshi "sanyi kakeji? Kai ya gyada mata tare da yanyota ta fad'o kanshi yayi mata wani runguma kamar zai ballata fad'i yake "ina sonki Rabi'a. Bakin na rawa itama tace "nima ina sonka sosai ya Alee. "To in haka ne ina son ki amince da zancen da nayi miki ranan a hospital. "Ya Alee bazan iya bane. "Zaki iya my angel Allah zaki iya. Yafad'a hakan cike da kwarun guiwa. Tureshi tasomayi tana fad'in sakeni in tafi wurin ummie tunda ka gaji dani neman kai kale dani. Gam yariqeta ya hanata kufcewa yana fad'in am sorry am sorry abin alfaharina nabari Allah nabari. Zuwa can tace "to sakeni in samowa abinda zakaci. "Bazanci komi ba "sabida mi? "Hakanan kawai "to tashi muje ciki ka kwanta tunda kabarjin sanyin "uhmm Rabi'a ni kad'ai nasan minakeji acikin jikina, kawai tafi ki kiramin Abba tare da aunty da kuma Hameed. Gabanta ne ya wani yanke ya fad'i rass!! Bakinta narawa tace "mizasuyi maka? Shafa fuskanta yayi cike da juriya ya amsa "kada kidamu ganinsu kawai nake son yi. "Ohk to bara nakira aunty ta waya sai ta sanar a Abban, hameed shima kiransa zanyi "badamuwa kirawomin su d'iyar albarka, wallahi komi kikayimin tuni na yafe miki kema kiyafeni. Banza tayi dashi don tasan neman magana yake da ita tunda yasoma zancensa mai kama da wasiyya,, tasoma dialing numbers. Cikin mintoci biyar duk sun taru cike da fargaba suna zaton ko jikin ne amma sai sukaga sabanin hakan. Addawiyya kitchen takoma tacigana da aikinta har ta kammala komi tana shirin fitowa dasu zuwa dining ta tsinkayi salatin da Hindu ta kafka da qarfi aibata san sanda ta iso wurin ba ta zube gaban Haydar wanda yake jikin Abba kwance. Jijjigashi tasomayi tare da kiran sunarshi taji bai amsa ba ta d'ago cike da fargaba tace da Hameed "mike faruwa ne? Mai makon ya amsa mata sai kawai yafice yana kuka, juyowa tayi tace da Hindu "Aunty badai nayi rashin ya Alee ba? Sauke kanta Hindu tayi qasa ta kasa kallon Addawiyya. Sallallamin Hajja tare dajin kalmar "Allah yagafarta maka Aliyu shine ya tabbatar mata da cewa ya Alee ya barta har abada. k'ara ta kwalla mai qarfi bakinta d'auke da Kalmar innalillahi wa inna ilai.... Bata qarasa fad'aba ta sulale qasa babu numfashi. Abba ya miqe arikice d'auke da Haydar a hannunsa yana mai cewa Abdul "d'auko Rabi'atu mukaisu asibiti, ke kuma Hindu biyomu amma Hajja kijira mudawo yanzu. *I'm sorry readers please*🤦🏻‍♀ *mrs j moon* [2/1, 3:45 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *45* Suna isa hospital aka amshe su bajimawa wani doctor yafito ya sanar dasu Haydar yajima da rasuwa amma ita matarsa doguwar suma tayi wanda zata iya d'aukan lokaci mai tsawo kafin tafarfad'oba, wata qila ta d'auki kwana 1 ko 1wk koma fiye da hakan. Tashin hankali kenan wanda ba'asami rana ga dai jimamin rasuwar Haydar ga kuma firgicin lalurar da Addawiyya ta afka ciki duk alokaci d'aya. Bayarda suka iya da hukuncin ilahu sai haquri tare da addu'ar Allah yabasu ikon juriyan wannan k'addarori dasu afko cikin rayuwarsu. Allahumma Amin. Anyiwa Aliyu haydar sutura dibbannin mutane suka miqashi zuwa makwancinsa na gaskiya suka baroshi daga shi sai halinsa sai kuma abinda ya shuka. Mutuwar ta gigita duk kanin d'aukakin al'umman gidan musanma Hameed wanda ko maqabarta bai iya rakashi ba, tunda yadawo daga asibi ya kulle kansa cikin room d'insa sai da ya kwana ya yini bai bud'e kansa ba, anyi ban bakin har an gaji yaqi bud'ewa sai da Abba ya tako dakansa zuwa part d'in, yasaka mishi kuka abakin qofar sannan ya bud'e tare da fad'awa jikin Abba yana fad'in "Abba yanzu brother yatafi yabarni kenan? Tambayar da ta kuma saka kowa dake wurin kuka kenan, Abba baibashi amsa ba illa wucewa da yayi da shi zuwa part d'insa yayi tayi masa nasiha tare da bashi misalai har yadawo natsuwarshi yasoma yi masa addu'a yana mai zubar hawaye wanda yarasa yarda zaiyi ya tsaidasu. Hajja kam sosai tabawa kowa mamaki domin itace mai rarrashin duk wanda yazo da kuka tayi ta cewa addu'a yakeso ba zubar jurwaye ba. Salma da Hindu kuwa baka gane wanda yafi wani fad'awa ciki firgici cikinsu, suke zaune wurin Addawiyya. Anyi anyi subar ummie ta zauna sunqi. Khairi da maryam suma sai da suka sume sanda zancen ya samesu, sunyi kuka har sun gode Allah. Duk wanda yasan Haydar sai da yayi jimamin rasuwarshi hatta da abokanan aikinsa sunshiga rud'anin rashinsa. Kowa yayi mishi shaidan arziki baya da abokin fad'a sam, shi bai damu da shiga shirgin da ba'a kasa dashi ba, duk abinda zaiyi to mai ma'ane gashi da riqon gaskiya da amana. Lallai yasami yabo ta ko ina don haka akeyi masa kyakykyawan zato. To koma dai miye Allahn da yafimu sonshi ya amsa abinsa sai dai fatan Allah yajiqansa da rahama in kuma tamu tazo Allah yasa mucika da imani, Amin. Yau kwanar Addawiyya goma sha d'aya batare da ta farfad'oba lamarin da yadagula zuciyoyin dangi babba da yaro. Ranar da tacika sati biyu na'urorin dake kewaye da ita suka soma tsuwwa alamun ta farfad'o. Cikin qanqanin lokaci doctors suka kewayeta zuwa can dasuka tabbatar da bugun zuciyarta ya dawo normal sai suka sanja mata d'aki tare da yima mata alluran da zai taima ka ta kuma dawowa cikin natsuwarta. Asannu tasoma bud'e idanunta wanda suka yi mata nauyi har ta bud'esu tar. Quri tayiwa gefe 1 tana kallo zuwa can ta motsa bakinta ahankali ta furta "da gaske ya Alee ya tafi yabarni cikin wannan duniyar mai cike da rud'ani? Jin maganarta ya ankarada da mutanen d'akin farkawanta. Sannu sukayi ta jera mata amma takasa amsa ko 1. Salma tana hawaye ta dafa goshinta tace "my Addawy kiyi magama mana muji muryanki. Kallon salman tayi tare da motsawa tace "kamani in tashi zaune bayana ciwo yake yimin. Kama tayi ta zaunar tare da kara mata filo ta baya. Hindu tashigo tare da doctor ya dubata yayi umurni da abata abu mai ruwa ruwa kamar tea sannan sai dawo ya bata magani. Tunda ta falka take tambayarsu da gaske Haydar yatafi ya barta? Amma an rasa wanda zai amsa mata, data matsa da tambayar sai duk suka saka mata kuka ita dai da ido take binsu, suna haka ummie ta iso ita da Hajja da kuma mama don bata koma kwantagora ba tun datazo ta'aziyyan tace sai taga farfad'owar Addawiyya tukunna. Fad'a ummie tasoma yiwa su Hindu kamar zata'ari baki wai akanme zasu tasata a gaba suna kuka alhalin sun san batagama dawowa daidai ba. Hajja ce ta daka tar da fad'an tare da matsawa ta janyo Addawiyya jikinta tayi qasa da murya ta soma yi mata magana "Rabi'atu ki zamo mai tawakkali, mai yarda da kaddara khairan ko akasinta kinji ko? Gyad'a kanta tayi, hajja tacigaba "Aliyu dai yarigamu gidan gaskiya yau satinsa biyu kenan da rasuwa kamar yarda kema satinki biyu yau kina cikin halin doguwar suma, don haka abinda nakeso dake ki jure kada kiyi masa kuka domin add'arki yafi buqata a yanzu ba kuka ba, kinaji nako? Gyad'a kai ta kuma yi wasu hawaye masu zafi suka zubo mata ta qamqame Hajja tare da sakin kuka mai cin rai, muryanta can qasa take fad'in "kuka yazamamin dole Hajja, bazan iya daurewa ba, kibarni inyi kada ciwon zuciya ta kamani. Kukan datakeyi yayi mugun karyawa kowa zuciya har kuwa da Hajjan, itama kuka takeyi sosai, kukan dabata samu tayiba sanda abin yake d'anye. Haka Addawiyya ta qara kwana biyu sannan aka sallameta kuma har lokacin hawaye yaqi qafewa a idanunta, duk kuwa yarda taso ya tsaya amma yaqi. Gidan mijinta aka wuce da ita, anso barinta a part d'inta amma ganin suna doso part d'in ta tafi luuuu ta sume musu yasa dole aka sakata amota zuwa gidan Abbie bayan anyi nasaran ganin ta farfad'o. *****Rayuwa kenan kana naka Allah na tasa kuma na Allah itace gaskiya. Gashi har Haydar yayi arba'in ya tasarma watanni na biyu. Addawiyya kuwa yanzu ta koma shiru2 kullum tana cikin d'aki, duk tabi ta rame sai uban qashin wuya da kayan boobs da d'uwaiyu ga kuma wani haske da taqara tar tar kamar atabata jini ya tsillo. bata cin komi sai pineapple kad'ai ta maida abincinta sai kuwa ruwa. Ummie sosai take bata tausayi, haka Abbie duk in yafita ya dawo d'akinta yake soma shiga ya zube mata duk abinda yazo dashi amma bata taba komi ciki sai Abarba, sunyi sunyi ta riqacin abinci taqi in sun matsa sai taci sai taka musu kuka tana kiran "ya Alee katafi kabarni da kewarka gashinan su ummie suna ta matsamin, da sunji haka sai su soma rarrashinta, don haka yanzu sun daina matsa mata da sai taci abinci, Abarba dai agidan ko gonarta sai haka, abinda hakan yayi mata mugun dad'i. Kwance take tayi rigingine fuskata na kallom ceiling eyes d'in kulle kamar mai barci, wayarta kife samar qirjinta. Daf da ita taji qamshinsa ta bud'e idanunta tare da kallon inda qamshin yake fitowa. 'Dan bata rai tayi tare da kwabe fuska cikin sonyin kuka tace "uncle wannan ita ce amana ko? Ace ya Alee ya rasu kaqi zuwamin gaisuwa ko? Tam nagode. Sai ta koma ta kulle idanunta, tanaji yanayi mata magana taqi kulawa zuwa can taji fitar iska ta window ta bud'e idanu tare da bin window nda harara sai kuma ta fashe da kuka mai tsanani, muryan Alee taji yacewa "addu'arki itace abar da nafi so da qauna ba wannan kukan da kiketayi ba haskena. Miqewa tayi azabure tana waige2 can ta kumajin ance "mai babban suna nine ba Alee ba nayi miki muryanshi ne don kisan nima nayi kewarsa kuma natayaki jimamin rashinsa, kisani mai babban suna, rayuwa bata taba inganta sai taci karo da qalubale haka cikakken mumuni ne Allah yake jarabtarsa da k'addara domin ya gwada qarfin imaninsa don haka ki zamo cikin bayi nan nagari masu yawan godiya ga Allah in k'addara tazo musu. Tana kuka ta amsa "tam uncle nagode, Allah saka da alkhairi da tunatarwa. "Bakomi mai babban suna daga haka yabace ita kuma tamiqe ta fito zuwa kitchen inda ummie take had'a lunch. Hakan yayi ummie dad'i sosai wanda takasa boyewa sai da ta furta "masha Allah autana tasoma dawowa cikin farin cikinta. D'an murmushi tayi tare da cewa "uhmm ummiena kenan. Ranar tayi hira sosai tare dasu kuma taci abinci kad'an, abinda yayi mugun faranta musu rai ainun. Awani yammaci tana zaune a compound hannunta riqe da Alqur'ani tana bita, sam hankalinta yayi nisa cikin karatun datakeyi sabida yanzu shine aikinta kuma sosai take samun natsuwa da sanyi cikin zuciyarta duk intana karatun. AL-QUR'ANIN KAREEM KENAN MAGANIN DUK KAN WANI CUTA. Allah ta dawwamar damu cikin bitarshi Amin. Kamar daga sama ta tsinkayi muryan su hassan suna kira sunarta "aunty Adda tare da rungumeta suna kyalkyala dariyar murnan ganinta. Cike da murnan ganinsu itama ta rungumesu tare da cewa "ku dawa kuka zo? Atare suka amsa mata da "mu da yaya Hameed da kuma ummul bait, yace ma wurinki yakawo miki ita kyauta, mamanta tana ta kuka sanda muka barota Hajja nata bata haquri. Cikin bargaba ta dubi parking lot ta hangoshi jingine jikin motarshi sabe da ummul bait. Sai taga yakoma mata Haydar sak, hatta kallon dayake mata hak irin ta haydar. Rintse eyes d'inta tayi ta sake bud'ewa sai taga ya koma mata biyu gashi sabe da ummul ga kuma Haydar tsaye gefensa yana yi mata murmushi da qarfi ta miqe tana furta "ya salam!!. "Mai babban suna zuciyarki ce take hasko miki photon Alee amma shi tuni yadad'e da koma ga mahaliccinmu don haka ki cire tunanin zai kuma dawo. Muryan uncle kenan yake tunatar da ita. Jiki a sanyaye ta koma ta zauna tare da rungume su hussain hawaye yana bin fuskanta. *mrs j moon* [2/2, 9:49 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *Assalamu Alaikum fans ina mai jinjina muku abisa comments d'inku daya riske ni ta ko ina agame da rasuwar Alee, hakan ya dad'a tabbatarmin dacewa kuna tare dani sau da qafa, to ina godiya sosai. Sannan ina son kusani ita rayuwa ko ya take tana tafiyane cike da qalubale haka duk abinda kakeso to tabbas wata rana sai yayima nisa ko kai kayi masa nisa. K'addara ita sikeli ce ta ma'aunin mizanin imanin mummunan bayi, don haka rashin Alee shine k'addarar Addawiyya. Aqarshe ina mai bawa fans wad'an da suka taya Addawiyya kukan rashin Haydar dama wad'an sukayi juriya basu zubda jurwayeba da duk kanin masoya labarin hak'uri, kuma wannan shafin na sadaukar muku dashi kyauta kuyi yarda kukaso da shi bamai hanaku domin nakune*💃 😅 LOVE YOU ALWAYS FANS❤😍😘 *46* Hucin saukan numfashinsa taji daf da ita yasa ta waiga da sauri. Subbahallahi!! Ta fad'i cikin ranta, sai kuma tayi sauri miqewa tsaye tana jifarshi da wani kallo wanda yarasa gano ma'anarshi. Ahankali yace "wannan kukan baya da amfani agareshi illah azaba da yake qaramishi don haka nasan kin sani wata qila mugunta ce yasa kikeyin hawayen don yayi ta qonashi. Afusace ta wulla mishi harara tana mai point d'insa tace "Hameed ya isheka tijaran da kazo yimin har cikin gidanmu kuma kasani kada kaga wai uwa 1 uba 1 kuke da ya Alee kayi tunanin kafini sonsa tare da jin zafin rashinsa, to wallahi ko kwatan2 abinda nakeji game dashi kai bakaji sabida haka kada kasake cemin inayi masa mugunta ehe, ta qarasa cike da tsiwa ga kuma kwalla yataru cikin idanunta sai qoqarin maidasu takeyi don bata son su zubo. Shiru yayi yana binta da kallo fuskasa cike da murmushi. Ganin ya maidata sauna sai tamiqa hannu ta fizgo ummul wacce take ta sharan barcinta bisa kafad'arsa, tayi gaba sai kuma ta juyo fuska a had'e tace "nagode sosai da kyauta amma kasani bana son yawar bibiya inkana son ganin 'yata sai kanasar dani in ina da lokaci domin bazan lamunta ka riqa zuwamin baqatatan ba, dafatan kajini da kyau? Shafa kwantarcen sajensa yayi cike da mishad'i sannan ya amsa "naji hajiya Rabi'atul Addawiyya matan malam badamasi. 'Dan sakin fuska tayi batare da ta kuma magana ba tawuce ciki su hassan suka rufa mata baya. Yajima duqe a wurin yana sake sake zuwa can ya miqe ya isa wurin motarsa ya bud'e boot ya d'auko akwati biyu d'aya babba sosai d'aya kuma d'an madai daici, yayiwa falon tsinke. Ummie ya tarad zaune tana bitan wani littafin addu'o,i. Har gabanta ya isa ya zauna sannan ya gaisheta, ta amsa cike da fara'a tare da tambayarsu mutanen gidan ya amsa "suna lafiyalau. Kallonsa ummie ta kuma yi tace "Hameed haka akeyi ka d'auki mutum sukutum kayi kyauta da shi? Baka tunanin ita uwar yarinya wani hali zata fad'a saka makon rashin gudar jininta kusa da ita? Sauke kansa qasa yayi kuma cike da ladabi ya amsa "babu komi ummie, ai ni da Addawiyya duk 'ya'yan kune kuma nasan zuhuriyya bazata taba bijirewa umurnina ba haka babu halin dazata fad'a don bata tare da ummul hasalima anrage mata d'awainiya ne sabida yanzu haka batajin dad'i bata iya hidimar ummul sam, nike mata dukkan wani abun da yashafi raino, ga aikina ga hidimarta sai kawai nayanke shawaran bari na cika alkawarin dana d'auka kawai. "Tam yayi Allah yatayata riqo ya kuma raya ummul cikin ni'imar Allah. "Amin, ya amsa. Hira sosai suka sha da ummie, inda ta tashi da kanta ta kawo mishi kayan motsa baki, yanaci suna hira har lokacin sallar magrib tayi. Ummie tamiqe ta shige room d'inta dake qasa don ta gabatar da sallah. Yana ganin haka ya haye upstair da sauri. Koda ya hau sai yatsaya yana nazarin wani room zai shiga, qasa qasa yake jiyo dariya sai ya doshi d'akin kai tsaye, tabawa yayi yajita bud'e don haka sai ya saka kansa kawai batare da neman iziniba. Su hassan yagani zaune tsaliyar bed d'inta duk sunyi caka caka da chocolates tare da biscuits suna ta aikin sha, sunsa ummul a tsakiyarsu in sun bare nasu sai su bare mata su miqa mata ta amshe. Ingina da qofar yayi yanata aikin kallonsu cike da jin dad'i, kuma cikinsu bawanda yalura da zuwarshi. Motsin fitowarta daga toilet yasa ya zubawa qofar bathroom d'in idanu. Fitowa tayi d'aure da guntun towel wanda iyakarshi cinyoyinta ya rufe. Ba tare data lura da shi ba, ta isa gaban mirror tasoma shafa mai, ta matso lotion zata shafa a qirjinta ta tsinkayi maganarsa inda yace "kai kai!!! Jira infita tukunna basai kin nunamin kayan ruwan naki ba. Zabura tayi wanda kad'an yarage towel d'in bai sunbule qasa ba, sabida sosai ta firgita dajin muryanshi don batayi zaton da mutum ba. Kallonsa tayi kamar zatayi kuka tace "kasan Allah in har nacre bamyafe makaba sai Allah yafitarmin da hakkina da ka d'auka ta hanyar tsoratani. Kashe mata ido 1 yayi tare da matsowa inda take tayi sauri d'aga mishi hannu tana mai cewa "kul ka taka shari'a kuma kaficemin a room tun ban saukema kwadon rashin matunci ba. Matsowa ya kuma yi a fusace ya kama dantsen hannunta ya matse da qarfi tako kwalla qara don azaba yasa qafarsa ya take mata yatsu tare da murzawa ta rintse idanunta cike dajin azaba ta dubeshi tace "sakeni Hameed banson irin wannan bad'alar. Mai makon ya saketa sai kawai ya kai bakinsa daf da kunninta yana mai cewa "kinsan Allah in har kikace tsiwa zaki tsiromin dashi to ni kuma zan soma baki wuya kala kala don haka sai ki kiyaye kinsanni bana d'aukan wargi musanman kan mace, macenma kwaila irinki, yafad'a hakan tare dabin jikinta da kallo. Da qarfi ta fizge daga riqon da yayi mata, tayi saurin janyo hijab d'inta ta saka ta nuna mishi hanyar qofa tana mai bashi umurni "malam kaficemin a d'aki nace, bana da lokacinka. Wani damqan ya kawo mata tayi sauri fad'awa cikin su hussain tana ihu, aikam yaran da tun dazu suke kallonsu suka saka mata dariya hassan yace "laaa yaya Hameed yafi qarfin Aunty Adda, hussain ya amshe da "eh, Allah yafita, bakagani ba har yakusa sata kuka, sai suka kuma kwashewa da dariya har da Hameed d'in. Wani uban tsawa ta daka musu take sukayi shiru suna mazurai, yayin da baby ummul ta fashe da kuka don taji tsoro. Hameed wanda yake ta kyal kyala dariyan zancen su hussain yayi hanzarin kai hannu zai d'auketa, tako buge mishi hannu tare da cewa "dalla malam kar ka tabamin 'ya, baya yaja yana dariya qasa qasa ta kuma bata rai tace "wai ka soma mensuration ne halan da kanajin time din prayer zai wuce amma katsaya d'aukan magana kamar nid'in ba auntynka bace? Kallonta yayi kamar zai yi magana sai kuma ya miqawa su hassan hannu suka kama ya d'agasu suka fice batare da yakuma kallon inda take ba. Tsaki taja mai sauti tare da cewa "iskancin banza da wofi kawai, yawani zo duk ya dagulamin lissafi har yana wani cemin kwaila a'a kwanso ce ba kwaila ba. Tare dashi da Abbie sukaci dinner, su kuma su hussai sukaci tare da ummie ita kuwa Addawiyya ta qule cikin d'aki da 'yarta tana aikin bata priso. Tana cikin gyarawa ummul kwanciya ya kuma shigowa ta d'ago tare da cilla mishi harara bai kulata ba illa iyaka yamatsa kusa da 'yarshi ya manna mata kiss daga haka ya fice tabi bayanshi da harara kamar kwayar idonta zai fad'o. Ummie ce ta shigo da kanta ta tasata a gaba duka sakko don tayi sallama da Hameed. Baki ature ta isa wurin ta miqawa su hussain ledar chocolates tace dasu "kugaidamin da momynku, dadynku, hajiyarku tare da tsohuwar kirki Hajjanmu, atare suka amsa da "to aunty adda. Juyawa tayi tabar wurin batare da ta dubi inda Hameed yakeba. Da sauri ya biyo bayanta ya kama hannunta yace "bakice a gaida my heat riyya ba, da sauri ta amsa mishi "a'a zanba zance agaisar ba riyya ba, ta fizge hannunta tayi gaba bud'e murya yayi da qarfi yace "gudan jininta dai tana hannunki don haka akul kika soma kishi da ita tun zuciyar mijinta bai gama tantance zancen ba. Wani juyowa tayi afusace, ya kwasa da gudu ya fad'a motarshi yafice a 100 yana ta kyal kyalan dariya domin sosai yau rigimarta yajefashi cikin mishad'i. Ita kam zubewa tayi awurin tana maimaita kalmar kishi cikin ranta, "kardai ace ya Alee shima yayi mishi maganar da yataba yimin a hospital ne? To inko yayi masa ita lallai ina cikin matsala,, Saita dafe kanta cike da rud'ani takuma cewa "To ma wai duka duka yaushe ne ya Alee yarasun da har Hameed yasami kuzarin da zai soma min zancen banzan nan? Ganin bata san amsarba sai tamiqe jiki ba kwari ta shige ciki tana aiyana abinda zatayiwa Hameed duk randa yakuma zuwa inda take. Kamarko yasani sai ya d'auke qafarshi tsam daga gidan baima ko kiran wayarta balle yaji irin tanajin da tayi masa. Baby ummul kuwa sunyi mugun shaquwa da Addawiyya,, batayi mata rigimar komi,, sosai takejin dad'in zama da yarinyar, sai su qulle cikin d'aki suyi ta ifece ifacen su, hakan kuwa yana faran tawa ummie da Abbie rai sosai sakama kon zuwan yarinyan sun fahimci ya tafi mata da damuwarta sama da kaso 80 cikin d'ari, shi yasa kullum suke godewa Hameed da samishi albarka. Cikin sauri tagama shiryawa ta d'auki ummul itama ta shiryata cikin kayan sanyi masu laushi ta ratayo bag d'inta maroon ta sauko downstairs, ummie ta taradda zaune bisa dinning tana yin break fast, qarawa tayi ta zaumar da ummul bisa cinyar ummie tace "ga rainonan nakawo miki kema kisami ladan. "Tam auta na amsa, tad'ora da cewa "sai ina kuma yau haka da sassafe? Sai da tayi gaba sannan ta amsa "skul zani. Cikin mamaki ummie ta mai maita skul kuma? "Eh, ummie nayanke shawaran komawa ne domin nafahimci kuna son haka, "tam hakan yayi kyau auta, Allah ya tai maka, "Amin ta amsa tare da d'agawa ummul hannu itama hannun ta d'aga mata tana tsalle jikin ummie. Driving takeyi ranta fal da tunanin mafarkin datayi da Haydar daren jiya, lokaci zuwa lokaci sai tasaki murmushi cike dajin dad'i. Ta mirror ta lura da wata mota tana binta abaya, hakan tacigaba da tafiyarta tana tunanin ko waye wannan dake bin nata? Daf dazata shiga get d'in skul motar tazo ta wuceta da gudu tuni bace bat kamar walqiya. Tabe baki tayi tare da shigewa ciki tana mai furta "can ta matse ma koma waye a matse matsin matsalar shi. *mrs j moon* [2/4, 10:37 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *47* parking tayi a qasar wata bishiya tayi jim kamar baza ta fitoba zuwa can kuma sai ta bud'e qofar ta zuro santala santalan qafafunta waje tana qarewa students d'in dake kai kawo a harabar wurin kallo, caraf idanunta suka had'u dana wani malaminsu yako kafeta da idanu quri, da saurin ta koma ciki ta kulle door din ta kwanta sosai ta d'aga kanta sama ranta abace. Qaran shiqowar message taji cikin phone d'inta ta d'ago ta fiddota cikin bag ta duba. Baquwar number tagani qin bud'ewa tayi tare da yin cilli da wayar cikin jikka, ta koma ta kuma kwanciya tana tuno yarda taga Haydar cikin mufarkinta. Qiba, haske, jin dad'i duk sun bayyana ajikinsa ga wani qamshi da yake fitarwa mai dad'in shaqa, hatta wurin da yake zaune abin kallo ne, ni'ima mai dad'i yake ta fitarwa sai ta qamqame jikinta cikin jin dad'i tana mai furta kalmar "Alhamdulillah a fili sai kuma ta d'ago ta kife kanta samar sitiyari tayi shiru kamar mai barci tsawon lokaci ta d'auka ahaka sannan ta lalibo phone d'inta ta duba saqon daya shigo d'azun. *kwailata lallai kinyiwa kanki qiyamun laili tunda kin koma skul amma da yau na yanke zanje nasameki insa ki koma ko tatsiya ne sai gashi kin hutashshe dani, don haka inayi miki fatan samun nasarori masu yawa ki kulamin da kanki sosai Allah yadawo dake lafiya, Abu ummul bait ne mijinki bada jimawa ba da yardan mai duka* Wani dogon tsaki taja tare da furta "iska na wahalar da mai kayan kara, kuma asannu zan gyarama zama indai har baka bar kirana da kwaila ba, ai wannan ma sunan rainin wayau, fuska a had'e ta fito waje ta kulle motar batare da ta kuma kallon inda taga mayen kallon ba sunar da tabawa malamin kenan ta doshi wurin dasuke zama dasu maryam tun can da, sabida tasan kotace zata shiga class yanzu lokaci ya qure sun kusa fitowa. Zama tayi tare da juyawa mutane baya ahaka maryam ta qaraso wurin sakamakon hangota datayi tun sanda ta fito daga mota. Cikin mamaki ta zauna gefenta tare da dafata tace "qawalliya dagaske ke nake gani a cikin skul yau? Bata ta juyoba ta amsa mata da "eh, nice ya kike dasu mamie? Sai da ta miqe ta dawo gabanta ta duqa sannan ta amsa "muna lafiya lau. "Masha Allah. Shiru sukayi Addawiyya taqi d'ago kanta ta dubi maryam ita kuma taqi tashi daga tsugunon datayi a gabanta, zuwa can ta sa hannun ta tureta aikan abazata ta ganta qasa zaune, dariya tasaka mata irin ta mugunta, maryam bata ce komi ta koma ta zauna agefenta ta ta aikin kallonta, ganin haka tuni ta gintse fuska sai abin yabawa maryam dariya kuma. Qawayensu ne sukayi ta zuwa suna yi mata ta'aziyya tana amsawa ita da maryam ganin sunqi qarewa masu zuwan yasa ta miqe tana mai cewa maryam "besty bara na koma mota kafin lokacin shiga ta lecture yayi domin naga mutanen nan so suke su sani kuka kuma alhalin nayiwa ya Alee alkawarin nadai yi masa kuka sai addu'a. Biyo bayanta maryam d'in tayi tana cewa "hakan shi yakamaceki dashi dama, Allah dai yaji qansa da rahama "Amin. Atare suka isa wurin motar suka shiga. Maryam ta dubeta tace "amma besty ya akayi kika sanja ra'ayinki kika dawo skul? Tana murmushi ta amsa "wallahi tunda na falka misalin 3 daren jiya naji jin son komawa skul ya d'arsu azuciyata kuma inajin duk don ganin ya Aleen danayi ne a ciki mufarkina cikin shiga mai kyau da jin dad'i da alama yasa mi kyakykyawan makoama sannan maganar da mukayi dashi ita ce ta karatu na, to inaga shine yahassa samin son komowata. "Uhmm yayi kyau hakan amma inajin junnu uncle d'in kine dai yafito miki a siffarshi shine kike ganin kamar ya haydar ne. "To nidai koma waye nasan mufarkin ya jefani cikin nishad'i haka nan yakasa wucemin arai. "To Allah yacigaba da sadamu da mufarkan Alkhairi "Amin. Koda zata koma gida wannan motar data biyota ita ce tayi mata rakiya har bakin get sannan ta juya. Cike da saqe saqe tayi parking ta mufi ciki. yaran Salma tare dana Hindu tayi arba a falon suna ta iface ifacen su da ummul. Cogewa tayi a qofa tana ta kallonsu cike da jin dad'i. Dama ace Allah ya k'addara cewa ya Alee yabar gudan jininsa a jikina fa, uhmm lallai da nafi kowa jin dad'i da kuma wata rana da shi ko ita za'ayi wasar nan. Cikin zuciyarta take wannan tunanin, atake kuma sai hawaye suka soma zubo mata tayi sauri sharesu tana mai furta "affuwan ya Alee, bayin kaina bane zuciyata ce takasa manta ka. Muryan ummie taji kusa da ita yasa tayi saurin fad'awa jikinta tana ta sauke ajiyar zuciya. Shafa kanta ummien tayi2 har ta dawo natsuwarta sannan tayi qasa da murya tace "nasan damuwarki haydar ne to don Allah ba dan niba ina son duk sanda kikaji ya fad'o miki arai kiyi mishi addu'a ne ba kuka ba, kinji? Gyad'a kai tayi tare da janye jikinta ta qarasa wurin yaran suna ganinta suka soma ihun murnan ganinta ta durqusa tayi ta manna musu kisses cike da murna. Washe gari da sassafe tafita don ko ummul bata tashi barci ba. Misalin 10am ta fito daga lecture. Tafiya suke ita da maryam suka tsinkayi muryan khairi tana kwalla musu kira atare suka juyo ta qaraso tana dariya harara addawiyya ta cilla mata ta kuma saka dariya tana cewa "ke madam ashe dai kin dawo skul ne bako sanarwa. "Yo ai yanzu idanunki yaga ne miki, dalla kina tawani kwallawa mutane kira kamar wata yarinya, girma yariga hankali zuwa dama ai. Dukan wasa ta kawo mata tayi sauri gofcewa duk suka sa dariya. Cikin motar maryam suka shiga sunata yi mata murna tare da addu'ar Allah ya tsare ya ka tsone idannun maqiya sai amsawa take da Amin Amin, da yammacin jiya Abbanta ya danqa mata key d'in motar. Sosai Addawiyya ta mai da hankali akaratunta sabida komi yazo daf da qarshe, a tsawon lokaci data d'auka nata zuwa uncle d'inta shi yayi ta fitowa a mutum yana zana mata duk kannin wani tests da exams da akayi da bata nan shi yasa komi yazo mata cikin sauqi. Mai binta abaya dai ya bari kuma har lokacin bata san ko waye ba haka taqi tambayar habibullah sabida bata son ya tado mata da zancen aure sam. Su Abbie kam yarda ta dawo real Addawiyyanta sosai hakan yake faranta musu rai, shi yasa tunda suka fahimci bata son zancen aure sai suma sukay biris da ita amma hakiqa akwai abinda suke shiryawa agame da aurenta. Tafiya take cikin jin dad'i ta kunna begen Annabin Allah mai taken murna muke da zuwan shugaba d'aha...... Akan hanyar ta na zuwa saloon sai gyad'a kai takeyi tayi tare da bin begen,sai da tayi nisa da gida sannan motarta ta bata matsala gangarawa tayi gefen hanya ta gyara parking tayi shiru tarasa yarda zatayi gashi tayi nisa da gida. Har ya wuce sai kuma ya dawo da baya ya iso dai dai inda take yayi parking tare da fitowa. Nocking yayi mata ta d'ago tare da sauke glass ta zuba mishi idanu, murmushi ya sakar mata tayi saurin kauda fuska tayi tana maijin wani tashin tsiyar jiki yarrrr, yace "matsala kika samu ne? Banza tayi mishi sabida taya zai ganta anan wuri amma ya tsaya yi mata tambayar rainin wayau irin haka. Tanajin murmushin da yasaki mai sauti ya matsa gaban motar ya bud'e yayi 'yan tabe tabensa sai ya koma motarshi da sauri ya dawo yacigaba da abinda keyi duk tana jinsa kuma taqi motsawa zuwa can ya dawo wurinta yace "d'anyiwa motar key mugani, bata musaba tayi ai kam cikin sa'a sai gashi ta tashi. Cike dajin kunya ta fito ta russuna tace dashi "nogode, nawa zan biya? "Kai kai haba mai kyau ai banyi don ki biyani ba. Murmushi tayi batare datace komi ba tashiga tayi gaba tana ganin yana tsaida ita amma sai tayi kamar bata ganshi ba tayi tafiyarta tana fad'in wahalalle kawai cikin ranta. Shikan mutumin dariya yasaki ya isa wurin motarshi ya dafata sai kawai ya bace bat. Agajiye ta dawo hannunta d'auke da babbar leda dagani kayan zaqi ne ta yowa ummul bait tsaraba. Tana sawo kai taga mutane cikin falon zaune kallonsu tayi sosai sai tagano kamar idanunsu sunyi kama da mage, atake kuma taji fad'uwar gaba yazo mata, tasbihi taja cikin ranta sannan ta qaraso cike da sanyin jiki ta gaishe dasu suka amsa ta nufi room d'in ummie can taga Salma, Hindu tare da maman su ubaiyu suna kus kus daga ganinta sai sukayi shiru cike da zargi take kallonsu sai kuma ta sunkuya ta gaishesu tare da cilla musu tambayar "suwaye nagani afalo? Mama ce ta amsa mata "iyayen mus'ab ne "waye haka kuma? "Au wai mufinki baki sanshi ba dama ya turosu mana wad'ancan matan su nema mishi aurenki? Tafe qirji tayi bakinta na rawa tace "wallahi ni ban taba jin sunar da yayi kama dashi ba sam. "Ikon Allah, to muma muna zaune suka iso wai ya turosu ne neman musu aurenki shine fa muka cika da mamaki naganin mata da zuwa neman aure, zaman damu kayi ma anan jiranki mukeyi kidawo muji ya abin yake. Zubewa tayi ranta in yayi dubu ya baci, to wai yaushe ta tsaya da wani da har zata bashi izinin zuwa wurin iyayenta? Tambayar da ta rasa amsarta kenan sai kawai ta miqe fuuu tanufi falon suka rufa mata baya amma sai me suna fitowa suka nemi matan suka rasa babu su babu san matan su duk sai suka shiga rawar jiki ita kam komi batayi ba illama wucewa datayi upstairs ta barsu nan tsaye cike da rud'ani. Tana shiga ta zaune gefen bed tafad'a kogin tunani. "Mai babban suna warning yayi miki na ya tai makeki amma sai kika wulaqantashi ta hanyar qin tsayawa alhalin kinagani yanayi miki magana kikayi biris dashi. "Wayyo Allah ni Addawiyya wai mike bibiyata ne haka daga wannan sai wannan kai wallahi rayuwar duniya cike take da rud'ani. "Haka ne amma banson kiqara yiwa wanda ya tai makeki irin haka, kinji "eh, to amma shi waye? "D'an uwa nane nina turoshi da ya tai makeki donmin shi d'in engineer ne na motoci manya da qanana. "Tofa!!!, wai uncle shin kuna sana'a ne kamar yarda mukeyi tare da karatu? "Sosai ma, komi da kukeyi munayi wata ranama tare daku muke hada hada kasuwanci da karatu musanman ta nasara. "Taf d'ijan, to ace yayi haquri bazan sakeba "ai tuni yayi ya dai yi miki haka ne don kigane ba kowwa ne yake cikin jinsin bil'adama ba don haka sai ki kiyaye ba kyau wulaqanta kowa ka gani koya yake sabida dawani mugu ne sai ya nemi cutar dakai musamman jinsinmu na junnu. Tam nagode bazan sake ba da yardan Allah "Allah yasa "Amin, amma yanzu ya zanyi da su ummie in sun sake neman qarin bayani agareni? "sharesu kawai ai tuni yasa musu mantuwa zancen ya bar zuciyarsu sai dai Hindu ce ya kasa tasiri mantuwan akanta. "To sabida mi? "Sabida taga kofato dake qafafun 1 cikinsu, shine abin yaqi tasiri akanta, yanzu haka zata zo kuyi magana akai dama kuma akwai maganar da yakawota wurinki. "Ohk tam uncle bari na shiga wanka kafin tazo "aha bye in kin fito wanda ke binki baya in zaki makaranta yana nan tafe anijma sai ki shirya tarbanshi. "Bazan fita ko inaba don haka ma ka tsai da shi can bisa titi yayi ta garararanba kamar leda. "mai babban suna bansonki da haka, kifito ki saurari batunsa kuma bayanshi biyu sunan tafe zasuzo da buqatar son aurenki. "Na boni uncle haja ce ni da za ayi tazuwa tayawa haka? Dariya yasaki yace "farin jinin da Alee yayi miki katanga dashi ne yanzu yake fitowa fili. "Mi kake nufi da cewa hakan uncle? "wata qil nan gaba inyi miki bayani amma ban d'au alqawariba, yanzu dai wanda zaizo sunarsa dr. Suwaid'i kuma wurin aikinsu d'ya da Hameed ata qaicema photonki yagani a cikin office d'in Hameed yaji bawanda yakeso sai ke sannan ubaiyu zai dawo da qarfinsa haka lecuran ku Salim yana ciki ga kuma shugaba Hameed kai mai babban suna kin had'a jarumai fa. Yana gama fad'an haka ya bace bat. Komawa tayi ta zauna hannunta bisa goshinta kamar zata sa kuka, ahaka Hindu tashigo ta sameta ta zaun gefenta tace "autar ummie natsuwarki nake buqata dafatan zan samu? Gyad'a mata kai tayi tare da zuba mata manyan eyes d'inta tana sauraronta. *Readers ayi ta haquri da Safiyya wlh uzurirrika nake dasu sosai*🤦🏻‍♀ *mrs j moon* [2/5, 11:35 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *48* Autan ummie ina son kisanar dani gaskiyar zancen agame da zuwan wad'ancan mutanen sabida tun zuwarsu nagane ba mutane ba ne domin da idanuna naga d'aya cikinsu na d'auke da fafafun doki. "Eh aunty h. Hakika ba mutane bane laifi nayiwa wani d'axun... Ta fada mata duk yarda sukayi dakuma abinda uncle yafada mata. "Uhmm lallai kam biri yayi kama da mutum, to Allah yaqara tsarewa "Amin. "Kuma autan ummie kikiyayi wulaqanci domin a irin haka ake had'uwa da masifu iri iri masu wuyar magani, duk inda kikaga mutum to ki rabi dashi lafiya sabida wasu ba mutane bane kamar dai yarda kika had'u da wannan. "tam aunty ai nabari "To hakan yayi kyau. Ta murkuta kad'an ta kama hannun Addawiyya tace "Sai kuma maqasudin zuwana wurinki shine Abban Hameed ya aikoni da inzo na tambayeki shin ke kika amincewa Hameed ya fito neman aurenki? Sabida yasameshi da zancen shine yace ya dakata yaji daga gareki. Da sauri ta amsa "a'a "ohk, to Abbansu yace yana neman alfarmarki daki amince ki kuma zamowa surukarshi akaro na biyu, dafatan baza ki watsan qasa a idanu ba? Shiru tayi zuwa can tace "ni ba aure zanyi yanzu ba hakanan kuma banjin zan yi aure a lokaci kusa. "Eh, mun sani dama wai in kin amince dashi ne sai abari har sai sanda kika kammala karatunki sai ayi bikin. "Aunty ni dai nace bazanyi aureba kuma Hameed baya cikin 'yan kayana, bai min ba, yatafi can ya qarata da matarsa. Hindu zata kuma magana tayi hanzari tashi ta shigewa toilet tare da murza key. Baki sake Hindu tabi qofar toilet d'in da kallo kai ta jijjina tana mai cewa "ina nan zaune har sai kinfito naji gamsasshiyar amsa sannan zan kyaleki. Koda tafito bata zaciga zata tadda Hindu ba don haka sai ta coge a jikin bayin ta tura baki fuska a murtuke, Hindu yi tayi kamar bata gantaba tacigaba da latsa wayarta, tsawon lokaci ta d'auka tsaye ganin bazata kulata ba sai ta isa gaba mirror ta murza lotion tare da jira rigan shan iska mai gajeren hannu ta zo ta zauna gaban Hindu ta marai marai ce murya tace "aunty don Allah ki fahimceni ni bason Hameed ne banayi ba a'a nadai harantawa kai na auren shi ne duk da burin ya Alee kenan bayan ransa in auri d'an uwarsa Hameed ni kuma atun sanda yake fad'amin haka nace bazan auri qanin mijina ba, kuma banson zancen don haka yanzuma banson kinamin zancen don Allah. "Shikenan hujjanki? "A'a "ok tam ina sauraronki "aunty matarsa zuhuriyya ta tsaneni alokacin ina matsayin matar wan minjinta balle kuma ace yanzu na zama abokiyan zaman, ai kinga sai ta kyes samin ashana kuma. "Autan ummie ni dai koma miye ina son kice kin amince kawai, zancen bakyason zancen duk bakison zancen ba. "Allah aunty bazan auri Hameed ba sai dai abisa k'addara. "Uhm to yayi miki kyau amma ki sani tuni su Abbie sun amince amsar ki kawai suke jira kuma yanzu zantafi nasar dasu amincewarki don haka sai ki shirya zama Amaryan Hameed nan bada jimawa ba kuma kishiyar riyya. Tamiqe ta barta durqushe tarasa bakin magana. Leqowa ta kumayi tace "indai da Amana abinda yafi shine kiso jinin Haydar kuma kiyi biyayya ga cikar burinsa ta hanyar auren jininsa kamar yarda yakoma ga mahaliccinsa da burin hakan a ransa. Runtse idanunta tayi tare da toshe kunninta, Hindu tasaka dariya tace "ki saurari kiran su Abbie kuma in har kika qaryatani to wallahi babuni babu ke ehe, ta buga mata qofar da qarfi tayi gaba. Bata san tsawon lokacin data d'auka a zube bisa carpet ba tana aikin tunani, ita dai jin muryan Salma tayi akanta tana cewa "ummie tace in sanar miki kifito kici abinci tun bata iso da kanta ba. Bata tanka taba ta miqe ta rufa mata baya ranta abace suna saukowa mai gadi yana kwad'a salma ko bari a amsa mishi bai yiba yacigaba "Hajiya ummie, wani yazo neman hajiya Rabi'atu. Caraf tace "jekace masa ina zuwa, takoma upstairs da sauri ta d'oro abaya abisa kayan jikinta, koda ta dawo falon ummie kadai ta kalla tace "natafi kiran, cikin murmushi ta amsa "adawo lafiya kada ki dad'e dai auta "aha ummiena bye tafice da sauri ganin Hindu tana daf da fashewa. Zaune ta taddashi samar motarshi yana waya cikin harshen fulatanci. A sannu ta qare mishi kallo, farine tas mai kama da larabawa ko kuma india, muryanshi ce zata tona asirin ko daga wani jinsin ya fito wato jjnsin fulani, hakiqa yana da kyau amma sam batajishi cikin ruhintaba. Bata san ya sauko ba sai jin maganarsa tayi daf da ita tayi saurin ja baya tana tura baki, dariya yasaki kad'an sannan ya russuna cike da barkwanci yace "ina yini, nasameki lafiya? "Lafiya ta amsa masa ataqaice, ya ce "Addawiyya d'anyi mana wuri zama man yarda zanji dad'in yin maganar data kawoni. Batace qalaba sai tayi gaba zuwa wurin wasu kujerun roba dasuke jere cikin wani rumfa. Uhmm 😴😴😴 *mrs j moon* [2/6, 8:15 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *Where are u d best friend of Addawiyya,, Maryam Rano, this page is belong to you, u can do what so ever u want do with it, don abin nakune mrs ustax mai tsefaffen geme* 🙊😅 😍 *49* "Sunana Doctor Garzali Baffa ard'o, abinda yasoma cewa da ita kenan sanda suka zauna, yacigaba "ni haifaffen garin jalingo, Taraba state, ai kine ya kawoni garin Kano, ina aiki a general hospital. nasoma ganin photonki a office d'in Dr. Abdul Hameed tun da jimawa kuma nayi ta nacin daya had'ani dake sai yasanar dani wai kina da aure to sai gashi kwatsam kwanaki nayi cikibus dake har nabi bayarki naga kinshiga buk shine nadawo nayi bincike akanki aka tabbatarmin dacewa lallai kintaba aure amma mijinki Allah yayi masa rasu. Jan numfashi yayi tare da kallonta yana murmushi. ita kam shiru tayi tana nazarin surutu irin nashi daga zuwarshi na farko. Yacigaba "ina miqo ta'aziyyata na rashin Aliyu damu kayi Allah qansa da rahama ya kuma yabashi aljanna mad'aukakiya. Cikin mugun fara'a ta amsa da "Amin, kamar ba itace fuskanta yake d'aure ta mau ba, ta qara da cewa "nagode sosai da addu'a. Shima fara'ar ya saki cike da gano lagonta ya amsa "bakomi sayyada Rabi'a. D'an sauke kanta tayi qasa cike da jin kunya, gyara zama yayi yace "da fa qarfina nashigo fagen dafatan zan sami ticket d'in shiga gasar? D'agowa tayi idanun su ya had'u tayi hanzarin kauda nata. "Ehm inajinki mai babban suna,yace hakan ahankali. Ahanzarce ta kuma kallonshi zuciyarta na bugawa. Kardai ace shima junnun ne? Zancen datayi cikin zuciyarta kenan. "Sunar ki 1 da wacce ta goyani ita d'in matar wan babana shine Baffan danake amfani dashi a sunana. Cikin ranta ta cewa ikon Allah yau Allah ya had'ani da suda fad'i ba'a tambayeshi ba radio mai jini. Ahankali ta sauke numfashi tace "ohk, kace nid'in maman ka ce? Yana dariya ya amsa "hakk'un mai babban suna. "Uhmm ta furta tare da miqewa tace "zanshiga daga ciki sai wata rana. Miqewa yayi shima ya matso daf da ita yace "a'a ya haka, zaki tafi batare da kin bani amsa taba? Tabatare da ta tsaya ba tace "banshirya yin aure yanzu ba haka kuma bansa lokacin yinsa ba don haka sai dai ince Allah ya sadamu da alkhairi amma fa lallai kasani bance inaqin kaba haka kuma bance inajinka araina ba. Dai dai sanda ta iso qofar shiga falo taja ta tsaya, shima tsayawar yayi cike da dumuwa yake dubanta domin zancenta yana kama da bigtin. murmusawa tayi tare da cewa "doctor kayi haquri dani domin nasan anriga da an zartar da hukunci akaina, na wanda zan aura shiyasa na sanar dakai gaskiya kada in boye maka daga baya kaji kace na yaudareka, dafatan yanzu kafahinci inda nadosa? "Eh, na fahimta amma kisani bashine zaisa na yanje daga gareki ba, zancigaba da gwada k'wanjina har sai naga abinda yaturewa buzu nad'i sabida nasan ba mijin akayi miki ba kawai kora da hali ne kike son yimin, ni kuma naqi koruwa. Ya qarasa zancen cikin sigar qasa. murmushi tayi kawai batare da ta kuma ce mishi komi ba ta sakai cikin falon tabarshi anan tsaye. A zuciyar mamakin hukuncin datace anzartar akanta take tayi "Allah na tuba, ta furta a hankali. Sai bayan Sallar isha'i Abban su Hameed yazo d'aukan Hindu wacce take ta fishi da Addawiyya taqi kulata tun sanda tadawo daga wurin dr. Garzali. Salma kam 'yan baruwan muce sai zolayar addawiyya take tayi wai taga taqara qibane komi nata yaqara cika ko dai Alee yabar mata ajiyar shine ba'a sani ba tazo ta duba ta, da harara Addawiyya keta binta dashi amma taqi bari saima sake lalibo abin neman magana take tayi da ita har saida ummie tashiga tsakani sannan ta sarara mata. Ita kam kwana zatayi a gidan sabida mushaffa'u yayi tafiya sai kuma yayi sati zai dawo shine tazo gida wai bazata iya zama ita 1 a gidanta ba tsoro takeji. Washe gari a skul tana cikin bawa su khairi labarin zuwar dr. Garzali da yarda sukayi, sai dariya suke tayi mata barinma khairi datake ta mai maita sunarsa wai Garzali. Ita ma sai yanzu sunar yake bata dariya, ita kuwa maryam cewa tayi taji ya kwanta mata arai kuma sunarshi special ne don bakowa yake dashi ba. Cike da zolaya khairi tace "ato shi kenan su Garzali anyi kasuwa to ke mrs AH sai kibar mata shi kiriqe Ah d'inki zam zam dama ni team d'insa nake don hausawa sunce so so ne amma son kai yafi, ga gida ana so ai ba'abawa dawa ba. Wani duka Addawiyya ta taska mata acinya wanda yasa ta kwalla ihu hankalin students ya dawo kansu, tana liliya wurin tace "wallahi bashi kikaci don kamar narama ne. Gwalo tayi mata tace "warning nayi miki next time kika kuma had'a da yayanki sai nayi miki mafiyinsa kinsan dai karonmu dake ba dad'i. "Eh, nasani kam amma kisa dai yanzu bada bace sabida komi ya sanja sinadarin aure ya nusheni yagama ratsa jini da jijiyata nayi karfi fiye da doki don haka kibini asannu kada in ji miki targad'e. Dariya suka saka su dukansu, zuwa can maryam tace "khairi gabaki d'aya kin lalace tunda kikayi aure kika soma sakin zance bako jin kunya, fari tayi ta amsa "lokaci nane yayi kema kina shiga daga ciki zamujiki bulum buqui kunya tayi gefe 1 atare da ke. "Uhmm badani ba kam, kedai da kike kayarshi Allah ya yaye miki. "Amin, yayaemana baki 1, "kudai amma nikam tuni dama ina da kunyata ras, "uhmm addawy kenan, Allah ina tausaya miki in ya Hameed ya danqeki wallahi baya da wasa kinsan zuhuriyya 'yar gida tace, to tasha sanar dani lamarin ya hameed to anan nafahimci shid'in jarumi ne, kinga in kika shigo zaki raina kan... Fas tabuge mata baki abunda yahanata qarsa zancenta, ta nunata da yatsa tana mai cewa "wallahi khairi zan shuka miki rashin mutunci inabaki bar had'ani da wannan mutumin ba tam. Afusace khairi ta kaimata duka a baki itama tayi saurin kaucewa tako sakar mata dukan a qirji, tafe wurin tayi idanunta sukayi raurau sabida ba qaramin duka tayi mata ba. Maryam ce tasoma magana "wai miye haka kukeyi ne kamar yara? Banza sukayi mata ta kuma cewa "ke khairi tunda bataso kina danganta ta da shi man basai ki bari ba, haka kema Addawiyya kirage saurin hannu yanzufa bada bane, hankali da girma duk sun wada cemu don haka we r ol mature enough, sabida haka kamewa itace ta kamace mu ba wasan yara ba. Duk sukayi shiru kowa da abinda yake saqawa aranshi. Wata budurwa ce ta iso wurinsu ta katse musu shirun ta haryar duban Addawiyya tace "kizo malam Salim yanakiran ki yace kisameshi a office d'insa, tana gama fad'an haka tayi gaba fuuuu. Tabe baki su kayi atare, zuwa can Addawiyya ta miqe tace don Allah kuzo ku rakani, miqewa sukayi tare da amsawa "tam. Tafiya suke anatse mai cike da class har zuwa bakin office d'in masa sannan sukaja suka tsaya ta dubesu don neman qarin bayani, khairi ce tace "nan zamu tsaya har ki fito sabida baida mutunci yana iya tijaramu abanza inya ganmu tare, maryam ta d'ora "wannan shine za'ayi don haka ki shiga kawai munamiki fatan jin alkhairi amma ki kula da kanki domin kurane shi indai akan mace ce. Gyad'a musu kai tayi tare da kwankwasa qofar daga ciki ya amsa da "yes come in. Tura kai tayi ciki tana maijin fad'uwar gaba atake kuma tasoma jan addu'ar tsari. Tunda tashigo yakafeta da idanu har ta qaraso bai d'auke idanunsa akanta ba. Atake taji tayi mugun jin tsanarsa dama can tasan mayen kallo ne ita kuma bata shiri da mai yawan kallo shiyasa ta tubure akan Hameed don tuntuni tagama fahimtarsa yayi degree a kallon mace. Maganarsa taji cikin kunninta "Rabi'atu zauna mana kya tsaya haka ai sai ki gaji, kallonsa tayi a fakai ce sannan ta russuna tace "Good afternoon sir. Washe baki yayi yana wani kashe mata ido 1 ya amsa "lafiya lau, ya karatu? "Alhamdulillah "tam haka akeso, masha Allah. Shiru yabiyo baya na wani lokaci, ta katse shirun ta hanya cewa "Sir, ance kana kirana "eh, dama wata magana nakeso muyi amma zaifi da na sameki agida dai, don haka sai kibani time dazan zo insameki kada kidamu da bani address d'in gidan domin sanishi bamai wuya bane agareni. "Uhmm malam inhar magana bata tawuce 30 minutes ba kawai kasanar dani insha Allahu ina tare da amsarta. "Ohk tunda kinfison ayita anan ai shikenan. Shiru tayi masa kanta aqasa tana ta nazarin d'abi'unsa, domin d'an zamanda sukayi har tagano mutum ne mara kunya dubi da yarda yake mata magana yanajan yaji. "Dama ina son muqulla wata alaqa ce ta zumunta wanda nake fatan ta kaimu har zuwa aure. D'agowa tayi tare da qare mishi kallo, bakine har yana qalkiya amma yana da kyau ainun sai dai kallo da'ya zaka kayi masa kagano d'an barike na bugawa a mujalla. Katse mata tunani yayi ta hanyar tasowa ya dawo ya zauna gefenta har yana shafar mata kafad'a da hanzari ta miqe tayi hanyar fita yayi sauri tareta yana wani langabar da kai "haba kekoh miye haka? Kallonsa tayi sai kuma tayi saurin kauda fuskanta gefe sannan tace "Kayi hakuri don Allah malam domin ban tsaida lokacin aureba gaskiya ayanzu, tana fad'an haka taraba gefensa ta wuce sauri, biyota yayi yaga har tayi nisa ita da qawayenta cije labbansa yayi yana mai furta "Allah sai kinsoni koda ta bayan gidane, bari in bar office tun yanzu na dangana da wurin malam halee nasanar dashi tun lokaci bai quremin ba. Direct inda ta perker motarta suka nufa ta bud'e motar suka shiga ciki. "Ya kukayi dashi? Maryam ta tambayeta, "uhmm tatsuniyar gizo ai bata wuce ta qoqi kalmar so dai ya jaddamin ni kuma nace a'a. Dariya khairi tasa sosai zatayi magana maryam rayi hanzarin rufe mata baki,Addawiyya ta dubesu ta tabe baki ta kwanta tana cewa maryam "don Allah besty yi driving dinmu mu sauke wannan 'yar neman fitinar a gidanta ko nasamu kaina yabarmin ciwo, wanda neman maganarta ya haddasamin. "Eh, na daiji kuma dole ya Hameed yayi winning ehe. Banza tayi da ita, tako kwashe da dariya, girgiza kai maryam tayi tare da yiwa motar key suka fice daga cikin skul d'in. Abin kamar had'in baki tana shan kwanar shiga layinsu bayan maryam ta sauka agidansu sai tacikaro da ubaiyu tsaye a get din wani gida ko kallonsa batayi ba ta wuceshi da gudu, tana mai dad'ajin haushi. Ita kad'ai take cewa "ni haja ce halan da kowa zai soma son samuna? abinda ban fuskanta a zamanin 'yan matancina ba shine yanzu zai zamemin qalubale? Amsar da take buqatan sani kenan amma ta kasa samowa. A tsiyace tayi parking ta fito afusace ta tasarma ciki. Tana shiga parlor tayi turus kanta yakuma sarawa kamar zai tsage biyu, hannu tasa ta dafe goshinta tare da zubawa Hameed idanu wanda yake zaune a gaban ummie da ala magana mai mahinmanci sukeyi dubi da yarda ya sunyar da kanshi kamar mai d'aukan ilimin addini ga malaminsa. Quri yayi mata shima yana kallonta tare da nazarto tarin damuwa a face d'inta. Sallamar Ubaiyu shi yasa tayi saurin isa wurin ummie ta kwanto da kanta a bayanta tana cewa "ummie yimin addu'a kaina ciwo kamar zai rabe biyu. Sai da suka gama gaisawa da ubaiyu sannan tayi mata addu'ar, ta miqe ta nufi upstairs, ummie tace da ita "auta bakiga Hameed da Ubaiyu bane halan dabaki gaishe dasu ba? Dawowa tayi cikin rangaji mai nuni da alamun gajiya atattare da ita tace "sannunku ya aiki da iyalanku? Bata tsayajin amsarsu ba ta haye sama da d'an gudunta, tana shiga room d'inta ta kife ruf da ciki samar bed ta lumshe idanunta tana jin wani mai dad'i yana kad'a mata suma kuma tana jin shigarsa cikin jikinta abinda ya haifar mata dajin kasala, tayi lamo, acan qasan zuciyanta kuwa tunani ne fal har ta rasa wanne zata kama sai kawai tasoma istiggafari, bata jimaba tanayi barci yazo yayi awon gaba da ita. *mrs j moon* [2/7, 10:22 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA* NA SAFIYYA. *50* Barci ne tayishi mai mugun dad'i wanda ya d'auketa lokaci mai tsawo don sai bayan magrib ta farka, miqa tayi tare da salati sai kuma tayi jim tana tunanin wannan wani irin barci ne tayi shi haka gashi har duhun dare ya shigo, d'an tsaki taja tana mai furta "ummie bata son inayin irin wannan barci amma yariga da ya zamemin jiki. Hannayenta ta d'aga sama tace "Allah kayaye min shi cikin amincinka, ta amsa ma kanta da "Amin. Wanka tashiga tabata lokaci sosai cikin bathroom sannan ta fito, shiryawa tayi tsaf sai qamshi take ta zubawa, asannu ta taka ta isa wurin d'an qaramin freeze d'in dake d'akinta ta bud'e ta d'auko babban kwalin hollandia drink ta zauna gefen bed ta bud'e kwalin ta zuba a wani glass cup mai d'an girma tasoma sha tana lumshe idanu, sosai take son duk abinda ya dangainci milk. Wasa2 sai da ta kusa shen kwalin drink d'in dika sannan ta tsagaita ta d'aga kwalin ta girgiza sai kawai tasoma dariya ita d'aya tare da kai hannu tana shafa cikinta tafurta "waya gayamin barno gabar take, ai dole 'yan hanji sunemi abincinsu, tun safe kwankwani maltina kad'ai yake cikina fa, uhmm wallahi yunwa bata da kyau, Allah ubangiji kanesan tamu da ita alfarman Annabin Rahama, Amin. Falon qasa ta sauko direct dinning area ta nufa, ta soma bud'e kulolin dake wurin, tuwon shinkafa ne da miyar agushi taji namar saniya sai qamshi yake tashi, sai soyayyen naman jabbi sunji kayan qamshi da kunun aya mai sanyi. Bata rai tayi domin ita kam ta tsani tuwo arayuwarta gashi kuma tanajin k'yuyar shiga kitchen, da ta dafa ko noodle ne. Hakanan ta d'iba tuwon kad'an ta saka cinyar naman jabbo 1 ta d'auko ruwan roba ta dawo cikin parlorn ta zauna, sosai taji dad'in food d'in domin sai da ta cinye shi duka ta kora da ruwa, ta d'au kayan ta shiga kitchen ta wanke ta kife sannan ta dawo falon ta kwanta samar doguwar kujera, tunani ne yake son zuwa mata arai amma taqi barinsa yayi galabar zuwa. Tananan kwance ummie tafito d'auke da baby ummul sai kuka take ta tsalawa, da sauri ta tashi zaune ta miqawa ummie hannu tana cewa "ayya my sweetheart kinyi kewata ko? to zuwa muji d'imin juna. Tanako amsarta yarinya tayi tsit ta kwanta lamo a jikinta. Dariya Addawiyya ta saki tana kallon ummie tace "aha yarinya taji d'umin momma nta tayi tsit, anyama kuwa ummie ba mintsilinta kikayi ba? Ta qarasa maganar cike da zolaya. Cikin hararanta ummie ta amsa "Eh, mintsilinta nayi, 'yar nema kawai, kuma kisani daga yau duk inda zaki da 'yarki zaki tafi don bazan iya da rigimarta ba. Cikin marai raita tace "Ayi haka kuwa ummie? "Sosai ma kuwa, yi yazama dole ai "uhmm muna neman affuwan ummienmu baza muqara yi miki kukan banza kinji? Qin kulasu tayi ummien. Ganin haka sai ta kuma rungume ummul sosai tana sunsuna wuyarta tace "yarinya 'yar gatan ummie sai qamshi takeyi kamar fure, kyal kya lewa da dariya tayi ummul kamar taji mi akace. Tsillata sama tayi cike da jin dad'i tace "kai inajin sonki 'yata har cikin tsokar zuciyata, Allah yasa ina da rabon ganin aurenki dai. "Amin, ummie ta amsa tare da cewa "zauna ina son muyi maga dake, "tam ta amsa tare da zaunawa a gaban ummien ta zuba mata idanu yayin da ummul tuni ta sauka tasoma wasanta dama kukan rigimar son ganin addawiyya takeyi. "Auta shin abinda kikayi d'azun kin kyauta kenan? "Minayi kuma ummie? "Au kin manta irin gaisuwar asharuwan tsintsayen da kikayiwa Hameed da Ubaiyu d'azun? Sunkuyar da kanta tayi qasa tana sosa tsinin hancinta, taqi cewa komi. Kallonta ummie tayi sosai tana son gano damuwarta amma bata gano komi ba sai kawai ta cigaba da cewa "lallai hakika d'azun raina ya baci kuma naji kunyarsu sosai sabida ina ganin qimarsu fiye da tunaninki don haka banason sake ganin kin maimaita hakan koda abayar idanuna ne. Ahankali ta amsa "tam ummie bazan sakeba ayi min affuwa, nadawo ne da matsanancin ciwon kai shi yasa. "Allah ya sauwaqa to "Amin. Miqewa tayi sabe da ummul wacce tasoma gyangyad'i. "Koma ki zauna bangama maganar ba ai. Kallon ummien tayi taga babu wasa sam atare da ita sai ta koma ta zauna gabanta yana fad'uwa. *Ayi haquri da wannan don Allah* *mrs j moon*