[17/11/2017, 03:16] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: QIYAYYA SA GANIN LAIFI··! 01 @QURRRATUL-AYN SHAMFI'DA BISMILLAHIRRAH MANIRRAHIM Wannan littafi 'ka gaggen labarine, amma idan yayi dai_dai da rayuwar ka/ki kuyi hakuri kuskuren idea ne, banyi dancin fuskar wani ko wataba, fatana darasin dake cikin littafin ya ammafani al'umma Littafin QIYAYYYA SA GANIN LAIFI··! littafine daya kawo maku wani saban salo naban mamaki kusani Annabi muhammad (S.A.W) awani hadisi yace (kada kutsananta son abu, haka kuma,kada ku tsananta qiyayya) domin abinda kake qi wata rana zai iya zama shi kakeso sosai, haka kuma abinda kake so sosai wata rana zai iya zama kana qinsa sosai, sannan yace awani hadisin (Idan zaka so mutum kasoshi domin Allah idan zaka qi mutum ka qishi domin Allah) ALLAH yasa mudace, acikinn wannan littafi akwai ILMANTARWA, FADAKARWA, WA AZANTARWA SANNAN UWA UBA NISHADI DA BAN DARIYA (camedy) da TSAN_TSAN SOYAYYA kudai kubiyoni cikin litttafin QIYAYYA SA GANIN LAIFI··! *** *** *** *** NURATU! NURATU!! NURATU!!! wata 'yar dattijuwar mata tafad'i tana mai sanya kanta cikin d'akin, kai taye gado ta nufa tasanya hannu tana mai janye bargon tare da fad'in "nasan kinajina, to kada kitashi, 'karfe takwas saura" jin hakan da tayi yasanyata mi'kewa tsaye da sauri atsakiyar gadon, tana mi'ka, duka-duka bazata wuce shekara tawas da watanniba, dattijuwar bata sake fad'din komaiba tafice daga d'akin, Nuratu takoma da'bas tazauna kan gadon dai-dai sanda agogon d'akin yabuga takwas dai-dai, aguje tanufi toilet , nan da nan sai gata tafito jiki aji'ke da alamu wanka tayi, a gurguje ta shafa mai, ta sanya kayanka tad'auko jakarta tari'ko hijabinta a hannu, tayo waje da gudu tana fad'in "ni nawuce Ammy na" kai kace wani abin tashin hankaline yafaru, banda Ammy tasan halin d'iyar tata da tsorata zatai da yanayin data fito, ta nufi kitchen dan acan tajiyo motsinta, da zuwa kiss tayiwa Ammy agoshi, zata tafi Ammy takira sunanta, Nurat da takusa kaiwa wajen kitchen d'in ta tsaya da sauri tare da juyowa, Ammy tami'ko mata foodplask, Nuratu tad'anyi jim..kaman bazata amsaba sai kuma ta amsa da murmushi akan fuskarta, ta bud'e jakarta tajefa foodplask d'in, tayi waje aguje sai da tafita sannan tatuna bata saka hijab ba, ta tsaya tasanya duka_duka hijab d'in iya kacinsa wuya, wai gawarnan da zatayi taganshi zaune saman motarsa a bakin gate, da waya ahannunsa yana dannawa, gabanta yabada dammm, “yaushe yadawo?”Nuratu ta furta afila, tatako kaman wacce kwai yafashewa zata wuce ta gabansa tashiga gidan, wani mugun kallo ya watso mata tare da daka mata wata uwar tsawa, wadda sai da tasanya Nuratu sakin d'an guntun fitsari tana zare ido, “'karfe nawa yanzu?”ya watso mata,tambayar da bata shiryaba“amm ta..tahh takwas”tabashi amsa cikin rawar murya, kai kawai ya gyad'a gami da fad'in “mai yahanaki fitowa da wuri, yanzune lokacin zuwa skull?”“Aa ya Nura, Ammy ce bata tasheni....”mugun kallon daya watso matane yasanyata dakatawa, bata gama dai_daita tunanintaba sai saukar rankwashi taji atsakiyar kanta, yana fad'in “ni zakiwa 'kary?” ai kuwa ta runtuma wani uban ihu tana fad'in “Allah ya....”kafin ta 'karasa yakawo mata bugu a bakin, da gudu tayi cikin gate d'in, tana fad'in “wayyo Mama zai kasheni....!” [17/11/2017, 14:04] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: QIYAYYA SA GANIN LAIFI··! book 1 02 MALLAKA.....QURRRATUL-AYN *** *** *** Tana shiga haraban gidan Mama da Aunty nakawo kai da saurinsu, sabida ihunta da sukajiyo suna sama, Nuratu ta'buya bayan Mama tana ihu, dai-dai sanda Ya Nura yabiyota, cikin 'bacin rai Mama ta dubeshi da fad'in “wai kai Nura baka girmane?, kai kullum rigima da 'kannanka, yanzu sabida Allah mai Nuratu tayi maka, ko kuwa tsabar cin zaline? daga dawowarka jiya da dare zaka fara zaluntar yara” Aunty ta kar'be da fad'in “a'a Mama kinmance halin 'yar taki kenan? nasan Nura bai da laifi yanzu haka Nuratun ce”Nura da yayi tsaye yanajinsu yayi murmushi yana fad'in “yauwa Aunty gayawa Mama dai, ita akan wannan yarinyar sai duk ta rufe idonta” Mama ta galla masa harara, tana mai kamo hannun nuratu ta dafa kanta tana cewa “rabu dasu kinji, gayamin mai yayi maki?”“Mama wai kawai akan namakara fitowa makaranta shine ya dake ni,kuma fa Ammy ce bata tashe niba”Mama ta 'bata rai tana duban Nura “yanzu sabida Allah kana nufin kakaisu Hilal makaranta kabar Nuratu?”Nura yad'an sosa kansa da murmushi wanda ba kasafai yakeyinsaba sai da dalili, Mama tayi kwafa tajawo hannun Nuratu ta dan'ka mata naira d'ari biyun da idi almajiri yadawo mata da ita, tana mai fad'in “barni dashi maza kije kihau keke-napep yakaiki makarantar banda wasa kinji, kada ki makara” Aunty tayi murmushi tajuya tana fad'in “nikam nakoma ciki bazan iya da rigimar 'yannan taki marajiba, ni wallahi ihun da tayi nadauka wanine ya mutu ko d'auketa akazo yi”bata sake bi takansuba tayi ciki abinta, Nuratu ta kai-kaici idon Mama tayiwa Ya Nura gwale, kwafa kawai yayi yafice daga haraban zuwa bakin gate. Mama ta gogewa Nuratu fuskarta, tana rarrashinta tare da fatan Allah kiyaye ta kula da hanya. Nuratu tayi murmushi tafito zuwa gate itama, ta bud'e gate d'in tasanyo 'kafa kenan taji andan'keta 'kam, tare da rufe bakinta, Nuratu tazaro ido ganin Ya Nura ne, idanunsa sunyi ja da alamu na'bacin raine, hannu yami'ko mata yana fad'in “bani kud'innan, yau zanga 'karshen rashin kunya”ba musu Nuratu tami'ka masa, domin tamatsu ya saketa sabida zafin ri'kon dayayi mata, sanya kud'in yayi a aljihunsa yana fad'in “wallahi kikamin ihu ko wani yun'kuri har Mama taji ta fito, Allah yau na lahira sai yafiki jin dad'i”Nuratu ta girgiza kai alamun bazata yiba, Ya Nura ya cikita yana fad'in “wuce kibani waje, kitafi a'kafa kuma wallahi zanbiyo sahunki naga bakijeba tammm”yafad'a cikin tsawa,yayi kwafa, Nuratu ta goge 'yar kwallarta ta murgud'a baki kamin tajuya takama tafiya tana fad'in “Allah ya isa mugu kawai”ciki ciki tafad'a dan kada yajita, shi kuwa saman mota yakoma yazauna yabi bayanta da kallo yana 'karewa shigarta kallo. unifoam d'in jokinta black blue & white ne riga da siket, siket d'in iyakacinsa gwiwa, aka sanya safa fara zuwa gwiwar, sai riga fara sai aka d'ora falmaran kalan siket d'in, sai hijab fari babu batun d'an kwali ko hula, hijabin iya kacinsa wuyanta da kad'an yasauka kafad'a, shigar ba 'karamin yiwa Nuratu kyau tayiba kasancewar itad'in farace, ga diri ga kyawu, duk da 8yrs take amma hakan bai hana wasu daga cikin halittun jikinta bai yanaba, Nuratu ma'abociyar doguwar fuskace amma ba canba, sannan tana da cikar gashin gira dana ido, ga siririn hancinta dake 'karawa fuskarta kyawu tare da d'an ma dai-daicin bakin 'karami pink colour kamar tasanya jambaki, uwa uba abinda ke jan hankalin kowa akan Nuratu bai wuce blue eyes d'intaba mai jan hankali, gasu ma dai-daita tubarkalla sannan bata cika sirantaba amma bazakace mata mai 'kiba ba, tun yanzu kenan, ina ga kuma shekaru sunja, shiyasa duk wanda ya kalli Naratu yasan za'ayi had'add'iyar mace da kowanne namiji zaiyi burin mallakarta. Ya Nura kuwa wani dogon tsaki yaja tare da fad'in “yarinya sai kace aljanah, mummuna kawai, gawasu shegun unifoam, shiyasa nace Abba yasanyasu makarantar mutumci amma ya'ki waishi wannan tafi ilmi”yasake jan tsaki (kunjifa Ya Nura kodai-kodai 🤣) . har Nuratu tabar layin yana binta da kallo, yana mita acikin ransa. Nuratu nafita titi tafiya tacigaba dayi, tana 'yan wa'ko'kinta, da alamu babu abinda yadameta, jin tsayuwar mota tayi abayanta tare dayin hon, ta juya da sauri tad'auka Ya Nura ne yazo kaita wani matashin saurayi tagani kyakkyawa yana fad'in “zo ki hau 'yan mata na rage maki hanya, naga kin makara ma" Nuratu tayi ajiyar zuciya had'e da hamdala azuciyarta, afili kuwa murmushi tayi tabud'e gaban motar tashiga tahakimce abinta (araina nace su Nuratu an iya danna lamba tara 9number). Nuratu ta gaida mutumin tana sanar masa sunan makarantar tasu, shaf tamancema Ya Nura yace zai biyo bayanta, domin yariga yasan kunnen 'kashi irin na Nuratu, ile kuwa duk abinda tayi akan idonsa, har aka sauke Nuratu 'kofar school d'insu, tafito tayi godia mai motar yaja yatafi, tana juyawa suka had'a ido ko d'arr bata nuna jin tsorontaba, sai ma murgud'a masa baki da tayi, Ya Nura yabita da kallo kawai yana mamakin Nuratu wacce irin yarinyace, bai kuma bi takanta yasan 'batawa kansa lokaci zaiyi yawuce yabarta agun, amma ya 'kudurta aransa yau zai koya mata hankali kuwa. Nuratu na ganin yabar wajen da gudu tayi bayan school d'in sai gata asaman katanga, ta wulla jakarta sannan ta sauka, tana duddubawa ko wani ya ganta, da taga babu kowa ta sunkuya tana tafiya asunkuye har zuwa wajen windown class nasu, dayake dai-dai saitin window wajen zamanta yake, ta jiyo uncle nasu a ajikin class d'in, abokiyar zamanta tasan halinta sau tari haka takeyi, ta matsa mata ta wullo jakarta, da yake window d'in irin mai glass ne, bata sha wahalaba wajen shigowa uncle nacan na rubutu bai kulaba, 'yan ajin kuwa babu wanda bai saniba, amma kowa natsoron Nuratu domin bahaushe naceawa (dokin mai baki yafi gudu), Nuratu ba wani 'karfi garetaba amma akwai baki, sannan babu malamin da baisan Nuratuba wajen rashinji da tsokana domin duk laifin daka tarar anyi a school d'in idan ka bincika da sa hannun Nuratu, ga surutu sai dai inda take burgesu d'aya akwai 'ko'kari Nuratu, dan ita ke d'aukan first class koyaushe, da ka karanta data iya, ko haurowan katanga babu wanda yasani acikin malaman, amma 'yan school kowa yasani, domin Nuratu ogace fannin makara, gudun duka yake sanyawa take haura katanga, gashi kuma class nasu daf da katangar school d'in, domin,idan akwai abinda Nuratu tatsana aduniyarnan to dukane, sabida duk aka ta'ba lafiyar jikinta to har jinya sai tayi, shiyasa take kiyaye lafiyarta. “wai kuwa Nana yaushe Ya Nura ya dawo?”Nuratu tayi tambayar tana ri'ke ha'barta na mamaki, irin wata babbar nan, Nana ta d'an ta'be baki tana fad'in “nima muna tashi da safe muka ganshi zaune a daining, bakiga masifar da mukashaba da Abba yace yakawomu school, shinema yace bazai jirakiba " “mugu kawai ni wallahi har bana so yadawo idan yatafi, duk yazo yahanaka sakewa”Hilal yafad'i yana tsaki, Nuratu tace “kaima dai kafad'a ai yau nasha wuya, banda Allah yasoni da tuni a'kafa zanzo tun daga gida”“zuwa nan school d'in???”Nana da Hilal da Rahma suka had'a baki wajen fad'a, Nuratu tayi dariya “bari in baku labari”nan Nuratu ta basu labari kaf, sunji mamakin abinda Nuratu tayiwa Yayan nasu, Hilal dayake shine 'karaminsu gashi yafisu tsoro sai zare ido yake, hakan yasanya dariyar tadawo kanga, 'kararrawar komawa class da aka buga itace tayi sana diyan tashinsu daga hiran kowa ya nufi class d'insu, kasancewar ba class d'aya sukeba, Nana da Nuratu ne suke class guda, Hilal class d'insa daban Rahma ma haka. [19/11/2017, 23:33] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1 MALLAKA......QURRATUL-AYN 03 *** *** *** Yana parking motar cikin harabar gidan suka fito aguje zuwa ciki, kai tsaye babban falo suka nufa suna shiga suka hau wurgi da jakar makarantar tasu tare da ciccire unifoam d'in, ko wanne acikinsu yazauna dagashi sai best da pant wanda bai kai gwiwaba, babu batun sanya d'an kwali ko hula, illa gashinsu da ya zuba bisa kafad'unsu, dan su Allah yahore masu yalwar gashi, Hilal kai tsaye d'akin Mamansu ya nufa yana kwala mata kira, su kuwa zama sukayi suka kunna kallo. idanun Nuratu yasauka akan wayar dake jone jikin chaja afalon, ta dubi Nana “Lah Nana kinga wata waya mai kyau”tafad'a sanda takai hannu tana d'aukota, tadawo kusa dasu tazauna tana dariya, “kunnata mugani ta wace, ammafa tayi kyau wlh kinsan tafi ta su Mama”cewar Rahma, Nuratu takunna waya 'kirar Iphone6 suna ganin babu password ai kuwa suka hau kokawa kowa nafad'in abashi ya gani, Nuratu kuma ta hana, har abin yakai kaman zasuyi fad'a basuyi auneba sai ji kake tasss, 'karar fad'uwar wayar, da sauri Nuratu tasunkuya tad'auko wayar gaba d'aya screen d'inta yafashe, gaba d'aya suka zaro idanuwa, tsaki Nuratu taja tana fad'in “gashinan kunja tafashe, ko gani bamuyiba, gashi bamusan ko ta wace bama....”tayi shiru tana duban waya “mu mayar jikin chajin mugudu kawai, kuma kada wanda ya nuna yasan tafashe acikinmu”Nana tafad'a, Nuratu tace “good idea”ta mayar jikin chajin da gudu suka kwashi kayansu sai d'akinsu suna dariya, kan gado suka fad'a. “yanzu idan ta Ya Nura cefa”fad'in Nuratu, Rahma tazaro ido tana dafe 'kirji “munshiga uku ai yau sai yakusa kashemu, dan kinsan sojoji basu da imana”Nana tayi ta gumi jin abinda Rahma tafad'a Nuratu tace “ku daina majin tsoro ai babu wanda yasan mu muka fasa, kuma sarkin tsoro Hilal baya nan”jin hakan yasanya suka saki jikinsu suna harkokinsu. Dawowarsu kenan daga islamiyya, suna tafe akan hanya kasancewar islamiyyar tasu babu wani nisa tsakaninsu da gida, wata yarinya tazo zata wuce takusa da Nuratu itama da alamu daga Islamiyyar take dan kalan unifoam d'insu d'aya, doguwar riga koriya da farin hijab, cikin zafin nama Nuratu tajawo yarinyar tana fad'in “ke ummi kike kowa?, d'azu wakike cewa aljana?”“nifa ba dake nakeba”yarinyar tafad'a, Nuratu tasa hannu tad'auketa da mari, Rahma da Nana suka 'kara mata wani, dai-dai sanda yayun yarinyar maza suka kawo kai su biyu, nanfa fad'a yakaure, kasancewar unguwar babu jama'a sai 'yan makarantar kawai dasuka zagayesu suna kallo, ana masu wa'kar su sasu, cikin fad'an yayan yarinyar d'aya yad'au dutse ya bugawa Rahma agoshi nan kuwa jini ya'balle, cikin zafin nama Nuratu tana fad'in “wallahi sai munrama”tad'auki dutsen itama tarotse kan d'aya yayansu shima sai jini kuwa, tana niyar bugawa yarinyar taji anri'komata hannu bata jutaba takalli kowayeba tahau fizgewa tare da fad'in “ni cikani wallahi duk sai na fasa musu kai”jikake tasss and'auketa da mari da sauri ta juyo taga Ya Nura cikin 'bacin rai nan tayar da dutsen tana kallonsa, hannuwansu yahad'a baki d'anyansu yazubasu amota har su Ummi d'in, kai tsaye clinic yanufa dasu aka wanke masu ciwon tare da basu magunguna, duk suka had'a ido da Nuratu wani mugun kallo yake watsa mata, wanda yake sanyawa hanjin cikinta 'kullewa. sai da yakai yaran gida tare da bawa iyayen yaran ha'kuri, duk da dai bai tambayaba amma yana da tabbacin Nuratu ce da laifin komai, sannan suka nufi gida, lokacin an idar da sallar maghriba ma, Mama da Aunty da Abba sunyi jugum-jugum a babban falo, Aunty Amarya tashigo tana wani yau'ki da taunar cingum d'aurin d'an kwalin kanta irin wanda ake kira (gobarar mata ne), kusa da Abba tazauna tana fad'in “lafiya dai Alhaji na, yau duk nayi kewarka amma kazo kazauna anan kasanfa ruwan wanka da abinci nanan na jiranka”yanda take maganan da wani shishshige masan da take yasanya Mama da Aunty kallon juna, Abba yad'an matsa kad'an cikin jin kunya, tare da fad'in “ai kinsan ina kan hanya, nazo natarar da yarana har maghriba basa gidane, wai fad'a sukayi har da fasa kai ”cikin salo na kissa Aunty Amarya ta dafe 'kirji tana mai fad'in “subhanallahi waye yakawo maka wannan mummunan labarin Alhaji na?”“gashinan Hilal ne”Aunty Amaryar tahau matsar kwalla kamar gaske tana rarrashen Abba wai ita adole mai miji, su Mama kuwa sai suka zama 'yan kallo, tama nuna tafisu damuwa, Mama kai kawai ta girgiza tare da d'an guntun murmushi daya tsaya iyacin le'banta, Aunty kuwa harara taketa aikin aikawa Aunty Amarya zuciyarta na 'kuna. Da sallama yashigo falon, baki d'ayansu suka amsa masa, yayinda su Nuratu suka rufo masa baya ga Rahma goshi afashe, suka zauna Abba yahau tambayarsu “ya akai hakan rafaru”“sai dai ka tammbayesu Abba, nima akan hanya nagansu Nuratu d'auke da dutse a hannu”Abba yakai dubansa gun su Nuratu yana tambbayarsu, Nuratu da dai niyarta tashirga masu 'karya amma sai tasamu kanta da kasa yin hankan, nan tafad'i gaskiiyar abinda yafaru, nan fa ran Ya Nura ya'kara 'baci yahau fad'in “dan ankiraki da aljana sai me daman ai dasu kikafi kama, wawuya maraji kawai wallahi sai in'ballaki kowa ya huta 'yar kauye”“kai Nura ya isa haka agaban nawa, kada kasake yi mata irin wannan”cewar Abba, ita dai Mama ta rungume Rahma tanajinsu kawai, batace komaiba hakama Aunty, Abba yace “tunda Allah yatsai da abin haka shikenan kada insakejin anta da zancen, ita kuma uwata Allah bata lafiya, kowa yaje yayo sallah”Abba ya mi'ke zai fita, Aunty Amarya tami'ke tabi bayansa tana kwarkwasa, Nuratu taja wani mugun tsaki da har sai da yasa Aunty Amarya juyowa ta zabga mata wata uwar harara, Ya Nura yabugewa Nuratu baki, ta murgud'a masa bakin tare da fad'in “Allah ya isa na”tayi d'akin Mama da gudu, zai bita Mama ta dakatar dashi tana fad'in “ka wuce masallaci kada kabi yarinyar nan”Ya Nura ya dubi Mama kawai yajuya yafice. “Gaskiya Yaya ke kike 'kara sangarta 'yar nan wallahi”cewar Aunty, Mama tayi murmushi “kema dai Auntyn Nura, kin mance wacece Nuratu ne, kinsan dai ko kasheta zaiya Nuratu baza fasa fad'in Allah ya isa ba, tare da rashin kunya, da ace Nuratu zata daina rashinji da tuni ta daina, ni kaina wani lokacin Nuratu tsoro take bani wallahi, addu'ar shiriya kawai zamu dinga yi mata”“to Allah dai yashirya mana, bari inje inyi sallah”cewar Aunty tana mi'kewa, Mama tace “amin dai nima tashi zanyi yanzunnan”Aunty amarya tafice daga falon. Mama....mama..! Ya Nura ke kwala mata kira yana mai niyar shiga d'akinta, sai gata itama ta fito tana fad'in “lafiya kuwa Nura?, wannan kira haka?”“kalli wayata Mama daga jonawa achaji, mancewa nayi da ita nafita wallahi, nasan aikin yaran nanne”Mama tari'ke baki ganin screen d'in waya akwankwatse, suna tsaye sai ga Hilal yakawo kai zai nufi d'akinsu Nuratu, Ya Nura yari'keshi yana tambayarsa, Hilal har da kukansa yana fad'in bashi bane, kuma bai san wayeba, ganin hakan yasa Ya Nura rabuwa dashi dan yasan Hilal da tsoro da tuni yafad'a masa gaskia, “tashi jeka kiramin su Nana”Hilal yatashi da gudu yatafi kiransu, Ya Nura yazauna a kan d'aya daga cikin kujerun falon yana kallo, sai gasu sun fito jiki babu kwari, suka zube agabansa tare da fad'in “gamu yaya”wani mugun kallo yawatsa musu, gami da harara bai ce musu komaiba hannun Nana yakama yanufi d'akinsa da ita, nanfa 'yan hanjinsu tafara 'kullewa, sai da yaje dai-dai bakin 'kofar sannan yajuyo yana fad'in “idan nafito naga kintashi daga inda kike zaki sani”yashige cikin d'akin yana mai jan hannun Nana, Nuratu tabisu da kallo tana addu'a aranta. mintuna biyar sai gasu sunfito fuskar Nana hawaye sha'be-saha'be, suna had'a ido da Nuratu ya buga mata wata uwar harara, ta sunkuyar dakai da sauri, ya dubi Nana “maza wuce d'aki kiyi barci, zanzo d'akin ingani idan baki barcinba”Nana tawuce da gudu, yazo kan Nuratu yatsaya kafin yasa hannu yari'kota itama, d'akin nasa ya nufa da ita, yana shiga ya mai da 'kofa ya kulle, hakan yasaka hankalin Nuratu 'kara tashi matu'ka, kai tsaye gefan tamfatse tsan gadonsa yazauna, ita kuma ta tsuguna agabansa kanta a 'kasa, “ke”yakira sunanta, da sauri tad'ago idanunta, wata 'karamar bindiga ta gani ahannunsa nan Nuratu ta 'kara fiddo da idanuwanta daman ita ga ido tubarkalla, dubanta yatsayayi sosai kafin yafara magana “yau laifinki uku ne aguna, amma babban laifin fasamin wayata, mai yasa kika fasa?”“bani kad'ai nafasaba wallahi Yaya”Ya Nura ya watsa mata wani kallo kafin yace “nasan bake kika fasaba, amma kece sila, ba daman nace laifi uku ne akankiba, kuma yazama dole na hukuntaki akansu” yayi shiru yana dubanta kafin yad'ora da fad'in “za'bi d'aya gareki, ko dai in harbeki yanzu ki mutu ko kuma ki kwana azaune babu barci”jin hakan da Nuratu tayi shiyayi sanadiyya zubowar fitsarin dake ri'ke a mararta, matsowa tayi tari'ke 'kafarsa 'kam tana fad'in “kayi ha'kuri Yaya wallahi bazan sakeba, nidai banaso in mutu yanzu inbar Ammy na dasu Nana da Abba da mama”maganar taso tabawa Ya Nura dariya amma sai ya matse abinsa, ya dubeta dakyau, ya'kara tabbatarwa Nuratu yarinyace sosai, wani guntun murmushi yayi yana fad'in “saifa kinza'ba ”Nuratu tayi shiru tana sharar 'kwalla kafin tace “naza'bi inkwana azaune, dan bana so in mutu yanzu”yanda tayi maganar da abinda tafad'a sai da yasanya Ya Nura murmusawa, yace “is ok, yanzu saiki tsugunna kid'aga hannuwanki sama, ahaka zaki kwana”ba musu tayi abinda yace mata, dan duk atsorace take gani take kaman zai iya harbeta koyaushe, shi kuwa kwanciya yagyara ya'dora bindigar akan 'kirjinsa yakashe hasken d'akin yaja bargo abinsa yabarta nan tsugunne, motsi kad'an idan tayi sai taji yace “ina kallonki idanma guduwa zakiyi bismillah.” [20/11/2017, 18:18] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1 MALLAKA.....QURRATUL-AYN 04 Barcinsa yake shi hankalinsa kwance abinsa, jin da yayi anta'bashine yasanyashi farkawa, ganinta yayi tsugunne bakin gadon kanta kuma nakan hannunsa dake gefan gado tana baccinta, ya kunna globe d'in d'akin haske yagauraye amma ko kusa bata farkaba, domin baiyi kwakw-kwaran motsin dazata farkaba, duban agogon dake manne jikin bango saitin gadonsa yayi, yaga uku da mintuna goma lokacin, ajiyar zuciya yayi kafin yadawo da kallonsa kan Nuratu, gashinta kwance bisa fuskarta, tana sanyane da wata guntuwar rigar bacci, mai 'karamin hannu iyakacinta gwiwarta, yasa d'anyatsansa d'aya yajanye mata gashin daya rufe mata fuska, yana bin ilahirin fuskar da kallo, kafin yayi tsaki mai tsayo yakoma yakwanta, amma bai kashe hasken d'akinba, yanajin tsanarta sosai aransa, shi dai yarasa dalilin dayasa yatsani Nuratu duk da tana 'yaar'uwa agareshi, amma yatsaneta shi ko kyawunta da yakanji mutane nafad'a har da abokansa shi dai baita'ba ganiba, mai makonma idan yakalleta yaga kyawun sai dai kawaai yaji tsanarta nabin dukkan jikinsa, “meyesa natsaneta?”yayi tambayar kusan afili, wani gefe nazuciyarta yabashi amsa “sabida rashin kunya da raashin ji mana”yayarda da amsar da zuciyarsa tabashi, tsakin dai yasakeyi yana mai janye hannunsa da 'karfi, hakanne yayi sanadiyar buguwar goshinta jikin katakwan gadon, a gigice tafarka tana goga wajen, ta turo baki gaba yayin da take murza idanunta, firgigit ta koma ta tsuguna sabida tunawa da tayi a cikin d'akin wanda take, shi kuwa ya kafeta da shanyayyun idanuwansa, yana binta da kallo, tsoro ya'kara kama Nuratu sosai “kayi ha'kuri Yaya, nadaina insha Allahu bazan kumaba, dan Allah kabarni inje inkwanta.....!”ta'karashe maganar tana mai share kwallar dake shirin zubo mata. Ya Nura yayi murmushi kafin yace “kwanta nan inda kike, kuma bana son wannan kukan ”Nuratu tagyad'a kai, takwanta ta takure waje guda, ko mintuna biyu da kwanciya ba tayiba barci yad'auketa. ko da tafaarka da asuba ganinta tayi anrufeta da tattausan bargo, sai tashin 'kamshi yake, har tasake juyi sai tatuna da abinda ya faru jiya, ta mi'ke da sauri jin motsin ruwan da tayi a toilet yasa ta nufi 'kofa tana sand'a, tana zuwa tafice da gudu sai d'akinsu. 。。。after 1 week。。。 “Ammy wai dan Allah mai yasa Ya Nura baya sonane?, yana takuramin wallahi, ni duk natsaneshi....y”buge mata bakin da Ammyn tata tayine yasanya Nuratu dakatawa daga abinda take shirin fad'i. “in kumaji kince kintsaneshii, d'an uwan naki guda, kina da wanda yafishi ne?, sakarya kawai to ba dole kowa yadinga jibgarkiba tunda kinza'bi hakan Nuratu, ni aduniya nata'ba ganin yaro maraji irinki, idanshi baice yatsaneki ba ke har kina da bakin fad'ar hakan, tashi ki bani waje, na kuma jin bakinki yafurta hakan”. Nuratu tatura baki gaba tana fad'in “ni wallahi Ammy dan bakisaan abinda yakemin bane, cewafa yakeyi zai kasheni da bindigarsa”“to yakashekj mana ina ruwan wani, kowama ya huta”jin abinda Ammy tafad'ane yasanya Nuratu 'kulewa, tami'ke daga wajen Ammy dake yankan farce, mai makon tayi d'aki sai tayi waje abinta. Tana fita gidansu Nana ta nufa, domin rabonta da gidan tun randa Ya Nura yasata baccin zaune, tana shiga gate d'in ta gamu da Nana da Hilal da Rahma suna wasa, ta 'karasa wajensu da sauri tana,harararsu “shine sati guda banzoba kuka 'ki zuwaa gidanmu ko?”cewar Nuratu tana kallon Nana “ya Nura ne yahanamu zuwafa”Rahma tafad'a, Nuratu tazauna akan ciyawar wajen, duk suka kewayeta, kamar wata sarki da mu'karrabansa, “kunsan wani abu?”“A'a”suka fad'a atare, “yau lambun gidansu zainab nake son zuwa musha mangwaro, kuzo muje”Nana ta dubeta ad'an tsorace tana fad'in“A'a kin mance karan gidan ko?”“ke dallah d'azu naga anfita dashiifa ya mutu”“Allah to muje daman inason shan mango na gidan yafi nanan dad'i”inji Rahma. suka fice baki d'ayan su, suka nufi bayan gidansu, ashe nan ne gidansu Zee d'in. suna zuwa suka tura gate d'in Nuratu ce kan gaba, tagama le'kenta babu kowa mai gadi yana band'aki, hakanne yabasu damar shiga gidan, kai tsaye cikin lambun suka shiga, sai ga Nuratu akan bishiyar mangwaro kamaan wata biri, sannan Nana tahau da gyar Hilal da Rahma na kwashewa idan sunjefo, basuyi auneba saijin,haushin kare sukayi, Rahma da Hilal sukai tsuru-tsuru, ganin karen da sukayi yana nufosu ne yasanyasu zubar da mangwaron suka kwasa da gudu, Nuratu ta diro aguje itama, Nana garin saukowa tafad'o kan 'kafarta ta kwala wata uwaar 'kara data janyo hankalin mai gadi zuwa wajen, su Nuratu kuwa tuni sunyi waje aguje. ko da mai gadi ya'karaso sai ganin Nana yayi akwance karen nata faman zagayata, yana kad'a wutsiyarsa, mai gadi ya kori karan ya tsuguna agabanta ya ta'bata yaji babu ko alamun numfashi a tattare da ita. [21/11/2017, 13:05] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1 MALLAKA.......QURRATUL-AYN 05 Mai gadi yatashi arud'e zuwa cikin gidan, da shigarsa kaitsaye falo yashiga, Hajiya Saude mahaifiyar Zee nazaune falon ta amsa masa sallamar, ganin sa da tayi arud'e yasanyata watso masa tambayar “Lafiya kuwa malam Badaru?”“ba lafiyaba dai Hajiya, domin wata yarinya na cikin lambu akwance cikin suma ko mutuwa”mai gadi yabata amsa “subhanallahi...! muje ingaanta, garin ya hakan tafaru?”tafad'a tana mai d'aukan hijabinta dake kusa da ita, tayo waje mai gadi yabiyo bayanta yana fad'in “wallahi bansan ya akai hakan tafaruba Hajiya, kawai ina zaune najiyo ihu, ina zuwa naga kare nazagayata ita kuma babu alamun numfashi atare da ita”ya 'karashe maganar dai-dai sanda suka isa wajen. Hajiya ta sunnkuya ta d'ago Nana tana mai ta'ba wuyanta, kafin ta dubi mai gadi da fad'in “Nana ce da alamu suma tayi, to me yakawota nan? yi maza malam Badaru, kiramin Naseer ad'akinsa, kace yad'auko mukullin mota”“to Hajiya”. mintuna kad'an sai gasu sunfito, aka sanya Nana amotar domin kaita asibiti. Duk kan abinda yafaru akan idonsu Nuratu, suna ganin sunfita da ita, suka nufo gida da gudu suna kuka, suna shiga da Aunty sukayi karo ta tsai dasu tana tambayarsu “ku lafiya dai, mai kuma yafaaru? naganku duka kuna kuka” “Aunty Nana ce, Nanaa ce”cewar Rahma data kasa fad'in abinda yafaru, Aunty cikin kad'uwa tahau fad'in “mai kuma yafaru da Nanan?”hakan yasanya hankalin 'yan gidan baki d'aya dawowa wajensu, Mama takama hannun Nuratu tana tambayarta “mai yasamu Nana? Nuratu”Nuratu cikin kuku takama fad'in “ta mutu Mama, Nana ta mutu”. Ganin da Mama tayi duk arud'e suke yasa taja hannunsu zuwa falo, kowa binsu yayi amma banda Aunty Amarya da tanajinsu tad'akinta tayi shiru abinta, tana addu'ar Allah yasa gaskiyane ta mutum. Mama tazauna tana rar-rashinsu, sai da taga sunnutsu, sannan tasake tambayar Nuratu “yanzu Nanan tana ina?”“tana gidan mangwaro, amma sunsakata amota sunfita”“gidan mangwaro mai yakaiku gidan mangwaro kuma?”cewar Aunty, Hilal ne yabada wannan amsar yana fad'in “yaya Nuratuce da Nana sukace muje mutsunko mangwaro”wayar Mama dake gefantace tayi 'karasa, yasa kowa ya mai da hankalinsa kanta, ganin number Hajiya Saude da Mama tayine yasanyata d'aukan wayar da sauri. “kuna ina yanzu Hajiya”cewar Mama, basuji amsar da aka bayarba sai dai Mama da tace “to shikenan gamunan zuwa”Mama takashe wayar, tana mai sake kiran Number takara wayar akunnanta “hello Nura kana ina? ”“ina kan hanyar zuwa gidan na kusa 'karasowa ma, da wani abune Mama?”“to kayi maza kazo babu lafiya, ankwantar da Nana a asibiti ne”takashe wayar. falon yad'au shiru kafin Mama tace “wai suna Nana Khadija hospital, anbata gado, karaya tayi a'kafa, amma jikin da sau'ki, inji Hajiya saudan”Aunty tayi ajiyar zuciyar tana fad'in “to Allah 'kara kiyayewa yabata lafiya” dai-dai sanda Ya Nura yayi sallama yashigo “daman kai muke jira Auntyn Nura tashi muje ko”mi'kewa sukayi baki d'ayansu, da yake kowacce da mayafita kai tsaye waje suka nufa. su Nuratu suka bisu da kallo babu wanda yayi gigin fad'in zai je sabida sunga Ya Nura ne zai kaisu. 。。。 。。。 。。。 “ni wallahi Momy dama zata mutum mufara rage banzaye”cewar Kamal d'a na biyu awajen Aunty Amarya, “ni duk ba wannan ba nafison wannan yarinyar mai kama da 'yayan aljanun ta mace wallahi, aduniya babu wadda natsana irinta”fad'in Habiba kenan, wadda Kamal ke bi mata, Aunty Amarya tayi murmushi tana fad'in“kudai kusha kuruminku, ku kwantar da hankalinku kowanne acikinku sai burinsa ya cika, barinma dai ke Habi na”Habi tayi murmushi “Momy ya kamata dai yanzu kisanarwa da Abba batun aure na da Ya Nura, Allah ji nake idan ban aureshiba mutuwa zanyi”“kai Aunty Habi, soyayyar har takai haka?”Habi tayi dariya tana duban Momyn tasu, kafin Momyn tace “kai ai soko ne, duk wani plant mungama shiryawa, ya kake ganin idan Habi ta auri babban d'an gidan nan, tahaifo jikoki duk maza, kasan cewa arzi'ki namune ”suka tafa tare da Habi, Kamal yari'ke baki “Momy yaushe kukayi wannan tunanin? ammafa abin gaskiya yayi”“ai kaine baka da sirri saura inji zancen wajen Yayanka, kasan cikin satinnan zai dawo”“haba dai Momy ai ko kusa bama zaijiba domin kinsan shi baya cikin jam'iyyarmu, yana jam'iyyar 'yan adawa”suka saka dariya baki d'ayansu, haka suka shafe awanni, su'kulla wannan sukwance wannan, duk zancen babu abin arzi'ki sai na tsiya. Su Mama na isa hospital d'in waya ta bugawa Hajiiya saude tazo ta tafi dasu d'akin da aka kwantar da Nana, cikin mintuna kad'an sai gata, tayi musu iso zuwa d'akin, har lokacin Nana bata farkaba, tana kwance 'kafarta ta hagu d'aure da bandeji, da alamu anan karayar take,Mama tace “mungode Hajiya, tunda munzo yakamata kuje gida ku huta”“ehh yanzu nake cewa idan kunzo zanje gida daman, nafito babu wanda yasani, anjima zandawo ai”tayi musu sallama, Mama tasake godiya kafin tafice tatafi. Ya Nura yahau tambayar mai yafaru da ita “Mama tasanar masa iya kacin abinda tasani”“Abba yasani kuwa?”cewar Ya Nura “A'a sai dai yanzu kasanar masa, shaf namance wallahi”Mama tafad'a, “ok ba damuwa bari inyi masa waya ”yafad'a yana fita. wunin ranar su Nuratu sukuku sukayishi, sai yamma Nuratu ta nufi gida wajen Ammyn ta jiki duk babu kwari, tana shiga falon tafad'a kan kujera takwanta, Ammy,dake zaune 'kasan kafet tana cin abinci ta dube ta, tasan babu lafiya Nuratu tashigo waje takwanta kawai, batayi abin maganaba “ya dai 'yar gidan Mama, lafiya kuwa, mai yafaru?” “Ammy Nana ce aka kwantar a asibiti wai takarye”Ammy tabarcin abincin tana dubanta tare da fad'in “ta karye kaman ya?”“ehh fad'owa tayi daga kan bishiyar gidan mangwaro, yanzuma tana asibiti har da su Mama”“subhanallahi....!wanne asibitin suke?”“wai Nana Khadija hospital”Ammy tami'ke tana fad'in “banga tazama ba, bari inbi bayansu”“kai Ammy na, kema tafiya zakiyi, su Mamafa da Aunty nacan, duk saiku tafi kubar mu, dan Allah Ammy kizauna”“kinci gidanku inzauna inyi miki mai kuma? mara lafiya nacan kwance sai inzauna tare dake, inzauna inyi miki uban me? ke da kike ficewa kibarni fin sati guda baki le'koba ban damuba, sai ni kice bazan fitaba”Nuratu tashare kwallar idonta, bata sake maganaba, har Ammy tagama shirinta, da yake tasan asibitin sosai nan ake kwantar dasu duka idan basu da lafiya, sai da tafito sannan ta dubi Nuratu dake kwance falo, ta duba taga har tayi barci Ammy dariya tayi da fad'in “yaro yarone, ana mitar bazan fitaba gashi ita kuma baccima tayi abinta” Ammy tagyara mata kwanciyar tafice tabarta, kai tsaye bakin titi ta nufa ta tsai da kekenapep tahau suka tafi. [22/11/2017, 01:08] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈QIYAYYA SA GANIN LAIFI🌈🌈🌈Book 1 MALLAKA......QURRATUL-AYN 06 {Da yawa mutane na tambayata wai WACECE NURATU?, abasu tarihinta, sannan yaya ala'kar GIDAJE GUDA BIYU take?, to kuyi ha'kuri dukkan amsarku nanan tafe, kudai kubi QURRATUL-AYN asannu zata war-ware maku ZARE DA ABAWA ina godiya sosai masoyana harma da maqiyana ngd sosai 😘} *** *** *** kusan tare Ammy da Abba suka shiga asibitin, bayan sun gaisa Abba ya kira ya Nura yayi musu iso zuwa d'akin da Nana ke kwance, lokacin jiki alhamdulillah, tafarka daga baccin har taci abinci,tana zaune abinta. Gaisawa suka hauyi, kafin Ammy ta tambayi yanda abin yakasance, Aunty ce ta bata labari kamar yanda Nuratu tafad'a. Ran Ammy ya'baci sosai tace “haba biri yayi kama da mutu, tunda Nuratu tashiga gida jiki amace da yanda ta bani labari nasan idan anbibiya itace UMMUL-ABA'ISIN faruwar abin ”“A'a kada kice haka Ammyn Nuratu, wannan abin 'kaddarace ko da Nuratu ko babu idan Allah ya'kaddara sai yafaru, amma dan Allah kidaina wannan maganar”cewar Abba kenan yayin da yake niyar fita, yacigaba da fad'in “ni zanje gida nad'anyi wanka ina dawowa, inyaso zuwa bayan sallar isha'i zan mayar daku gida Nura yakwana, da safe kwa dawo”“to Allah kiyaye sai kadawo”suka fad'a baki d'ayansu, ya bud'e 'kofar yafita, Ya Nura yabi bayansa. “”“”“” “”“”“” “”“”“” sati guda Nana tayi a asibitin, ranar alhamis likita yasallamosu, a motar Ya Nura da Aunty Hafsa dake aure a sharad'a phase 1, itama ranar taje tare suka nufo gida, Aunty Hafsa ce tari'ko Nana dake dogarawa da sanda zuwa babban falo, sannan su Momy nazaune falon tare da iyalanta, wani mugun kallo tawatsawa Aunty Hafsa kafin tami'ke zata fice, Haby tasaki wani mugun tsaki tabangaji kafad'an Aunty Hafsa tafice, Aunty Hafsa tayi murmushi tana fad'in “ai daman ance tsintacciyar mage bata mage, kuma d'an kauye idan ya kile yafi d'an iskan binni iya iskanci” A fusace Haby ta juyo cikin masifa tana fad'in “ehh munji amma ahakan d'an 'kauyen yazo yafi d'an birnin ko mai ta'kama mulki, arzi'ki”“ke rufemin baki, ni ba dake zanyiba kinsan nawuce ajin yi dake sai dai da mahaifiyarku”cewar Aunty dake shirin zaunar da Nana, cikin,'bacin rai Haby tad'aga hannu zata mari Aunty Hafsa, Momy tari'ke hannunta tana fad'in “barta zata san ta zageni, ni bazanyi da itaba sai dai da ubanta, shine dai-dai dani” Tafad'a dai-dai sanda su Mama suka kawo kai, Aunty Hafsa kuwa tana tsaye tana jiran ta mareta taga yanda zatayi da ita, Aunty Hafsa tayi tsaki tana fad'in“ wannan ke yadama kuma, amma idan banda butulci da cin amana, daga zuwa cin arzi'ki, kuma ba iya cin arzi'kin ba sai da aka had'a da cin amana, aikin banza aikin wufi”“ki rufe bakinki Hafsa bana son kalan fad'a”fad'in Mama kenan, yayin da take 'ko 'karin zama kan kujera. Momy takama hannun Haby suka fice fuuu Kamal yatake masu baya, Aunty natsaye tana dubansu, batace komaiba, suna fita Ya Nura yashigo da kayan da sukazo dashi ya ajiye afalon ya nufi d'akinsa. “Da kinbarni Mama na koya masu hankali wallahi, wa 'yannan zuma ne Mama sai da wuta ha'kuri bazaiyi amfani akansu”Aunty tace “wallahi kuwa, ni kaina badon ina tsoron igiyar aure naba da tuni anyi wacce za'ayi”“uhmmm,bazaku gane bane, duk abinda kwanciyar hankali bai bayarba, rashin sa bazai bayarba, rigima bata da dad'i ko kad'an, ha'kuri da addu'a shine yadace akan wad'annan”cewar Mama, Aunty Hafsa tayi ajiyar zuciya kawai, tayi saurin kawo wata hiran, dan ita idan Mama nafad'in suyi ha'kuri ranta idan yayi dubu 'kara 'baci yake. ko da Abba yadawo Momy da kukanta take sanar masa wai Hafsa tayi mata rashin kunya, ai kuwa fad'a ranar Aunty Hafsa tasha shi, har sai da tayi data sanin zuwa gidan ranar, ha'kuri kawai,tayi ta aikin bawa Abba dan da cewa yayi ta tattara ta tafi tun alokaacin da'kyar ya ha'kura tajira mijin nata yazo sai dare sannan mijin Aunty Hafsa yazo yad'auketa suka tafi. Da dare Ammy zata fita 'kara dubo Nana, yayin da Nuratu kezaune kan kafet tana Assingment, ta baje littafai gabanta, Ammy ta dubeta “ni zanje dubo Nana, saura kisa 'kafa kifita daga gidan nan, dan naga tun yamma rawar kan naki tadawo”tafice tabar Nuratu Nuratu tayi murmushi tacigaba da aikinta, aranta tarasa dalilin da yasa Ammy tad'aure mata fuska yanzu, tun ranar da tadawo daaga asibiti aranar da abin yafaru, baki d'aya Ammy tabar sake mata fusks, ita kanta Nuratu batajin dad'in gidan yanzu, shiyasa take Allah-Allah asallamo su Mama daga asibitin, ai kuwa yau da yamma da Aunty Hafsa tashigo gai da Ammynta take sanarwa Ammy ansallamosu, Nuratu naji ta cika da farinciki, domin ita gani takeyi Ammy na matse mata lamba, tana takurata sosai acan tafi sakewa,tayi dukkan abinda take so. 《》《》《》 《》《》《》 《》《》《》 “uhmmm Alhaji ni kuwa da ina son shawartarka akan,wani al'amari, sai dai bansan yandaa zaka d'au maganarba”Abba dake shingid'e kan kusun yana karatun jarida, ya ajiye yana mai duban Momyn Kamal “fad'i dukkan abinda zaki fad'a nasan alkhairi ne, domin baki bani gur'batacciyar shawara, dan haka kada kiyi shakkar sanarmin komai da bani shawara, zanyi 'ko 'karin ganin nayiwa maganarki kyakykyawar fahimta, ina jinki” Momy tad'anyi murmushi mai sauti na ri'kak'kun 'yan duniya, kafin tace “dama kan batun Nura ne, tunda ya kammala komai yanzu aiki yake, kuma ba'ananba gida ba, yakamata ace ya ajiye iyali ko?”tad'anyi shiru tana duban Abba, tana so tafiskanci idan maganar zatayi tasiri awajensa, Abba yayi murmushi “kinyi kyakykyawan tunani gaskiya, nima sati guda kenan dayi masa magna kan batun aure, to amma ya nunamin bashi da wata wadda yake so yanzu, da alamu ma baya ra'ayin aure yanzu”“haba Alhaji na, ya za'ayi abarshi haka yakamata dai kanema masa, ya za'ayi mubarshi haka kasan yanda rayuwarnan tacanjafa, mai aurenma ya ya'kare bare kuma mara auran”“kinyi gaskiya kam, to nidai ayanzu bani da wacce zan nema maasa, amma idan kin hango wacce ta dace dashi sanarmin”. Momy tayi murmushi tana wasa da zoben hannunta “to Alhaji mai zai hana kahad'asu da Habiba”“wacce Habiba kuma?”cewar Abba “Habiba ta wajena mana”“ohh Allah sarki amma kuwa Rabi Allah yamiki albarka, naji dad'in wannan hangen naki da ni yamata inyishi gaskiya nagode sosai”Momy tayi masa wani shu'umin murmushi, aranta tana fad'in “ta 'kare maka Alhaji, da kasan abinda wannan had'in yataka da bakayi saurin amince wa ba”afili kuwa 'yar dariya tayi tana fad'in “haba dai Alhaji kada kadamu babu komai wallahi, Allah tabbatar da alkhairi dai”“amin”cewar Abba daya cika da farinciki kamar ance nasa ga aljannah shiga. [22/11/2017, 19:54] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1 MALLAKA......QURRATUL-AYN 07 (Godiya ta musamman a gareki ZEEE-YABOUR, Allah ubangiji yabar 'kauna ya'kara basira da za'kin hannu Amin, Inayinki sosai tawan MISS XOXO, bazan mance dakeba HAFSAT RANO, ZAHRA BUKAR kina raina wallahi Allah ya'kara lafiya yasa kaffara amin ACTION BABY Parrot na gaisheki kyauta😘 ) 。。。 。。。 。。。 Safiyar ranar wata alhamis, Ya Nura ne gaban Mama yaje gaisheta da ita“Mama daman shawara nake nema, ko na koma d'akin dake harabar gidannan, na kusa da gaiden ne, inyaso idan Khaleel yadawo sai yazauna nan d'akina, tun da ya kusa dawowa ”ya Nura yafad'a yana mai wasa da mukullayen hannunsa, “ehh gaskiya kam, hakanma yayi, tunda daman idan bakanan inyadawo hutu d'akinka yake sauka, yanzu kuwa yadawo gaba d'aya bazai yiyu kuna d'aki d'ayaba hakan zai zamo takura, yanzu yaushe za'a gyara maka, sannan kasanarwa Abbanku ko?? ”Ya Nura ya sosa 'keyarsa “yasani Mama dashi muka fara magana, zuwa anjima masu gyaran d'akin zasuzo, daman amincewarki nake jira kawai”“babu damuwa Allah taimaka”“amin” yana fita Aunty tashigo domin gaisawa da Mama, nan Mama take sanarwa Aunty batun komawar d'an gidan nata d'akin waje, Aunty tayi murmushi tana fad'in “ya sanarmin d'azu, shine nace yazo yaji ta bakinki”“au ashema kinsani?, ko dayake namanta kunfi kusa da Nura, ni ina gefe 'yar kallo”suka sa dariya baki d'ayansu, nan sukayita hiransu abinsu, kishiyoyi biyu masu abin sha'awa kenan. Ya Nura kuwa yana fita waya yabuga, mintuna kad'an sai ga mota nan d'auke da kaya cikin kwalaye, nan ya nuna musu inda zasu saka kayan yafice, da yake sauri yake yayi musu bayani idan sungama subawa mai gadi mukullum, ya fita yabarsu. Nuratu ce tafe tana 'yan wa'ko'kinta zata shiga gidan kenan taga d'akin waje bud'e, cikin zumud'i ta nufi wajen dan ganin waye aciki kuma ya bud'e, domin tun taso warta d'akin rufe take ganinsa, da isarta le'kawa tayi taga anata bud'e furniture dariya tayi aranta tana fad'in “waye zaiyi aure kuma, ko dai Ya Nura ne?”cikin gidan ta nufa da gudunta batayi zatoba saiji tayi tayi karo da mutum, kafin tawaye da sanin wanda ta bangaza sai saukar mari taji, arazane Nuratu tad'ago taga ashe Haby ce, tsaki Nuratu taja gami da d'an guntun murmushi tayi tsalle tad'auke Haby da marin itama, tawuce ciki aguje ta nufi babban falo wajen Mama. “lafiya Nuratu?”cewar Aunty kenan da taga Nuratu aguje tafad'a kan cinyar Mama, kafin tayi magana Haby tashigo, har kan cinyar Mama taje tajawo Nuratu, zata mareta Aunty tafizge Nuratu tana fad'in “lallai Habiba rashin kunyar taki takai, kizo har falonnan zaki daki Nuratu agabanmu kome tayi maki kifad'a mana mana, ko kuma kijira awaje kyayi mata rashin kunyar taki”wani mugun tsaki Haby taja kafin tace “sai dai inga wanda zai hanamin karya yarinyar nan wallahi akan namareta shine tasa hannu ta rama, ko ni sa'ar uwar tace?” Aunty zatayi magana Mama ta tareta da fad'in “ki rabu da ita Auntyn Nura, kinsan dai ba sa'ar yinki bace, Nuratu kuma gatanan ki kasheta kinji 'karewar duka ko, sai insan kin isa rashin kunyar taki takai”Momyn Haby ce tashigo falon tana fad'an “mene haka Habiba, bana son wannan abin ai ba sa'an yinki bane, wuce muje”ta nunawa Haby hanyar waje, Haby tafice tana tura baki, Momy ta juyo tana fad'in “sai kuna ha'kuri kunsan halin yara sai ha'kuri”ta fad'a tana tura d'an kwali gaba, tafice itama tabarsu. Aunty tazauna ta dafe kai, Mama ta dubi Nuratu kaman zatayi magana sai kuma tafasa, ganin hakan yasa Nuratu fad'in “Mama waye zaiyi aure kuma?”“mai kika gani?”cewar Mama, Nuratu tayi dariya da fad'in “naga d'akin waje ana saka furniture ne”“ohh yayanku ne zai koma nan d'akin, nan kuma Khaleel ne zai zauna”“laahh Mama yaushe Ya Khaleel zai dawo ne?”Nuratu tayi tambayar cikin zumud'i “nan da jibi yace, d'azu daya bugo waya” “wowww Mama, amma naji dad'i wallahi, mun huta da takuran Ya Nura”tafad'a tana fita daga falon aguje, Mama tayi murmushi tana girgiza kai, “Nuratu kenan Allah nuna mana randa zamuga nutsuwar Nuratu”“Amin aini wallahi wataran sai indinga tunanin anya Nuratu ita kad'aice kuwa ?”Aunty tafad'a, tana mai duban 'kofar da Nuratu tafita yanzu, Mama tayi dariya mai sauti “ita kad'aice kima daina wannan tunanin, kawai tsabar 'kiriniya ke cinta da rawar kai”“to Allah dai yakyauta yashirya mana ita”amin dai. 『』『』『』『』『』『』『』『』『』 zaune take falon Ammyn ta da littafi a hannunta tana karatu, domin daf suke da fara exam, sallama yayi fuskarsa d'auke da wannan shu'umin murmushin nasa mai tsada, Nuratu ko d'aga kai batayi ta dubeshi ba, sai ma kwanciya datayi tacigaba da karantunta, sai Ammy ce dake can cikin d'aki, tana shirya kayan gugarsu cikin wardrobe ta fito tana amsa sallamar. “a'a Nura yau kaine kale'komu kuma? zauna mana katsaya kamar wani ba'ko”Ya Nura yayi murmushi yazauna kan d'aya daga cikin kujerun d'akin yana fad'in“wallahi kuwa Ammy yau ina free ne nace bari inzo mugaisa da Ammyn tawa”“ai kuwa ka kyauta wallahi ”Nuratu tayi tsaki jin yace Ammyn sa “iyayin banza”tafad'i aranta, Ammy ta dubeta tana zama “amma Nuratu baki da kirki, kina jin ana sallama baki amsaba, bare kuma gaisuwa”“to Ammy shinefa yayi sallamar ahankali, kuma ina karatu banjiba”Ammy takai mata duka“kinci gidan, ni da nake d'aki naji sallamar bare ke da kike falon tsabar iskanci”Ya Nura yayi murmushi yana fad'in “kirabu da ita Ammy babu komai”“haba wallahi ni iskancin yarinyar nan har yafara isata anya kuwa kanta 'kalau?”“ha'kuri zakiyi Ammy”cewar Ya Nura, Nuratu kuwa harararsa tayi tana tura baki gaba ta nufi d'aki, Ammy tabita da kallon takaici, shima bin nata yayi da kallo yanajin wani d'aci aransa, afili kuwa murmushi yayi kawai yana girgiza kai. Ammy tadawo da kallonta kansa tace “kazo a dai-dai d'an gidana yanzun nan na kammala abincin da kake so bari inkawo maka”bata jira mai zaiceba tafice. mintuna kad'an sai gata tadawo d'auke da flat arufe tami'ka masa takoma, Ya Nura yabud'e wani 'kamshi ya doki hancinsa tuwon shinkafane miyar agushi taji kifi sai tashin 'kamshi take, ya Nura yanason tuwo da miyar agushi sosai har dai girkin Ammy yakan jishi daban dana kowa. Ammy tadawo d'auke da jug kunun gyad'ane aciki da yaji kwa-kwa da dabino, Ya Nura a'koshe yake, amma bai san sanda yatashi da tuwon da lemon ba, sukai ta dariya shida Ammy, Nuratu najinsu tacika tayi fam, dan ita arayuwa ta tsani ya Nura mugune take cewa. BAYAN KWANA UKU [23/11/2017, 21:56] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1 MALLAKA......QURRATUL-AYN 08 (Godiya mai tarin yawa agareku 'YAN BIYU kyautar Allah HASSAN ATK TANKO & HUSSAINI ATK TANKO Allah yabar zumunci ngd sosai inayinku ko yaushe 😘👍🏻) *** *** *** BAYAN KWANA UKU *** *** *** “ke haby yakamata ki nutsu, duk wani rashin mutunci ki ajiye gefe wannan akwai lokacin yinsa, yanzu kissa da kisisina zaki d'auka, dole muyaudari mahaifiyar Nura domin musamu amincewarta, dan itama zata iya kawo mana sikas a shirinmu, duk da Alhaji ya amince nasan bazai canja maganaba amma dole kinemi soyayyar surukarki tahakanne zamu cimma gashi”Haby ta rumgume Momy cikin murna da farinciki, tana fad'in “kome kikace inyi Momy zanyi wallahi nidai burina in auri Ya Nura, ina son gayen wallahi yahad'u Momy”Momy tayi murmushi tad'an bugi Haby da fad'in “ko kunyata bakiji kike fad'in saurayinki yahad'u, to dai kada kizurfafa sonsa aranki kizo kina rusa mana plan d'inmu”“haba dai Momy, aini burina kawai in aureshi ko da adaran farko ya butu bazan damuba”suka sanya dariya baki d'aya, gami da tafawa. Momy ce zaune falon Mama yayin da Haby ke zaune kusa da ita a'kasa, kanta na sunkuye Aunty da Mama suna zaune kan 2siter suna kallon Momy dake magana “Maman Nura munzone ban ha'kuri, ha'ki'ka nagane nayi babban kuskure arayuwa, dan haka naga yazama dole inzo mubaku ha'kuri munyi nadama sosai ni da yarana, nasan hakan kokad'an abinda muke maku babu kyau, kuma ba tarbiya bace, amma kuyi ha'kuri d'an Allah hakan bazata sake faruwaba zamuyi zama na amana da mutunci insha Allahu”. Mama tayi murmushi tana fad'in “amma gaskiya naji,dad'i sosai da kuka fahimci gaskiya, ai zaman,mutunci da kwanciyar hankali yafi komai, wallahi komai yawuce araina daman banri'ke kuba Allah bamu ikon kyauta tawa juna da ha 'kuri”“amin”suka furta atare, Aunty tace “komai yawuce ai, sai akiyaye gaba”Haby ma dur'kusawa tayi tanemi gafara duk sukace komai yawuce, nan sukaita hira kai kace babu abinda yahad'asu arayuwa nan kuwa ta ciki na ciki Momy da d'iyarta Haby. yau take ranar dawowar Khaleel daga malesia inda yaje yakaranci Doctor, gida ya cika da hayaniya sai 'kamshi ke tashi kala-kala, asauke a d'ora aikin kenan tun safe, babu wanda yazauna cikinsu Mama ko wanne da aikin da yake Haby ma ba'abarta abayaba har da ita a kitchen d'in, su Nuratu ne dai su a fannin fitina da ci aka barsu, komai aka sauke sai sunci Mama bata hanasu, idan ma za'a hanasu cewa takeyi kada atakurawa 'yan iyalanta abarsu suci, hakan ne yabawa su Nuratu damar yin tsiya kala-kala a kitchen d'in wani abun ma da tsoka sukeyi dan Haby tasa baki, amma ta danne domin hud'ubar Momynta na nan akunnanta. 'karfe sha biyu komai ya kammala, nan aka shirya komai aka gyara ko ina, sannan kowa ya nufi part nasa domin shiryawa, sabida 'karfe d'aya jirgin nasu zai sauka afilin jirgin malam aminu kano. “idan kunshirya Mama kufito mu tafi, Abba na mota da Momy yana jiranku”cewar Ya Nura kenan, yana mai fita daga falon, Mama tafito cikin wani rantsats-tsan leshinta ba'ki mai rashin ash-silba, ba'karamin kyau tayiba kasancewar Mama farar fata ga kyau ga son gayu, bazaka ta'ba ganewa ita tahaifi Ya Nura ba, sai idan ansanar maka, itama Aunty irin shigar Momy tayi kasancewar dama sun saba duk inda zasuje anko suke shima Abba hakan nayi masa dad'i shiyasa duk d'inki anko yake yimasu. Abba da Ya Nura ne agaba, sannan Mama da Aunty sai Momy duk abaya suke, Ya Nura ne keyin dreving, su Mama na baya suna hira tsakaninsu abin dai abin ban sha'awa, hakan ba 'karamin yiwa Abba da Ya Nura dad'i yayiba. Dai-dai sanda jirgin ke sauka, su kuma suna isa filin jirgin, fasinjojin, suka kama layin saukowa, cikinsu har da Khaleel dake sanye cikin ba'kin jeans da farar t.shart sai farin glass d'in dake manne a fuskarsa wanda ya'kara masa kyau ainun, ga kwantaccen gashinsa ba'ki wuluk dayasha kud'i, gaskiya shima Khaleel ba bayaba wajen,kyau sai dai muce masha Allah. Da murmushinsa ya'karaso waajensu, ya gaida Abba dasu Mama cikin farinciki suka amsa, sannan ya rungume Ya Nura kowa ya cika da farin cikin,yanda suka ganshi yayi kyau abinsa, sannan ya kammala,karatunsa lafiya tare da tarin albarka. a mota,babu wanda ya fara tambaya,illa Nuratu, Aunty tayi dariya tana fad'in “ai Nuratu tana nan inda kabarta,illa ma abinda ya'karu”Khaleel yayi dariya,“kuce haryanzu kuna nan kuna fama?”“wallahi kuwa sai fatan shiriya,kawak”cewar Mama kenan, Momy kuwa,haushi ya cikata, yarasa wadda zai tambaya sai wata can, bayan ga 'yan'uwansa nan najini, a fili kuwa murmushi kawai take kamar babu komai aranta. suna isa gidan kai tsaye babban falo suka nufa da gudu Nuratu ta she'ko tarungume Khaleel tana “oyoyo yayanmu”Hilal da Rahma ma suka rungumeshi, Nana tataso da 'kyar tana dogara sandarta zuwa wajensa, Khaleel yajanye su Nuratu ya'karasa gareta da sauri yana fad'in “mai yasameki haka kuma Nana?”“ciwo naji”tafad'a tana 'karasawa,gareshi, Mama tace “ai yanzu,jiki alhmdlh taji sau'ki sai 'karashe kuma”duk sai yaji babu dad'i a ransa afili kuwa fad'i yayi“Allah 'kara lafiya”sukace “amin dai”. Haby ma zuwa tayi ta rungume d'an uwan nata tana murna, shi kunya ma sai takamashi, duk da 'yar uwace ta jini, amma yasan hakan da kunya domin ai tawuce yin hakan a addinance, ita kuwa ko ajikinta, awajenta waye wace da cinyewa hakan, Khaleel yajanyeta yana mai amsa sannu da zuwan Kamal dayake yi masa, kafin kuma ad'unguma zuwa daining table baki d'aya, sannan Kamal yakai masa kayansa d'akinsa, shima yadawo yazauna dan bawa ciki ha'k'kinsa. Dawowarsa kenan ya shiga cikin gidan domin kaiwa Aunty aikenta, “Mama daman ashe Ya Nura d'an iskane...?”Mama ta dubeta “mai kike cewa?”Nuratu tafito da wasu,fefan cd guda biyu tana nunawa Mama, yayin da Rahma da Hilal suka hau fad'in “a cikin d'akinsa muka gani wallahi Mama, duba ki gani”dai-dai sanda suke nunawa, sannan Ya Nura yakawo kai zai wuce, Mama duba d'aya tayiwa caset d'in tad'auke kai, “innalillahi wa'inna ilaihi razee'un”Ya Nura yafad'a yana mai fizge caset d'in yad'auke Nuratu da mari da sai da tayi,kaman zata fad'i, Mama ta tarota kallon datayiwa Ya Nura ne yasanyashi sunkuyar da kai 'kasa yana fad'in “kiyi ha'kuri Mama, Amma wallahi wannan ba nawa bane, a d'akin Kamal nad'aukeshi randa Abba yace inkirashi nataddashi yana kallo shima sai da na zaneshi, shine nad'auke nakai d'akina da zummar zan 'kona kuma namance”Mama tayi shiru kafin tace “kaji jeka yawuce”Ya Nura baiji dad'in yanda Mama tayi masaba, koba komai tafi kowa sanin wayeshi, tafi kowa sanin halinsa, har Aunty yasama yasanar mata akan tabaiwa Mama ha'kuri, Mama kuwa sai ta d'aurewa ya Nura fuska kullum yazo gaisheta sai yayi aikin bawa Mama ha'kuri, duk sai yake yaji gidan babu dad'i, hakan yasa tsanar Nuratu ta'kara yawa aransa, gashi Mama tahanashi ya hukuntata koya huce. 『』 『』 『』『』 『』 『』 BAYAN KWANA BIYU Zaune suke baki d'ayansu a babban falo, Abba zaune kan kujera yayin da Mama,Momy,Aunty,Ammy kowan nensu nakan kujera, sai Ya Nura da Khaleel,sai Kamal da Haby zaune duk suke 'kasa kan kafet, Aunty Hafsa ma tazo, da dukkan alamu maganace mai mahimmanci tahad'an family guda waje d'aya, yara ne kawai,babu su, asalima suna gidan Ammy suna wasansu basu san wainar da ake toyawaba. Abba yabud'e taro da addu'a,kafin yafara magana “nasan duk zakuyi mamakin tarakun da nayi ayau duk da dai ba abin mamaki bane”Abba yad'anyi shiru yana binsu da kallo kafin yad'ora yana murmushi,“taron yau ba akan komai bane illa kai Nura”Abba yafad'a yana mai nuna Ya Nura, kowa yasha jinin jikinsa,yad'auka wani laifi Ya Nura ya aikata Abba yacigaba da fad'in “Nura kwanaki nasha yimaka batun aure amma sai dai bana samun gamshash-shiyar amsa naga kuma kai kamar auren baya gabanka ayanzu,dan haka nayi shawara na kuma yanke hukuncin had'a aurenka da Habiba”dammmmm gaban ya Nura yafad'i, yad'ago kai ya dubi Mama, yaga ko kallon inda yake batayiba, tunaninsa yatsaya akan ko abinda yafaru kwanakine yasanya Mama sanarwa Abba yayanke wannan hukunci, daman yasan tunda Mama tayi fushi dashi haka yana iya fuskantar ko wanne irin hukunci jiran tsammani yake dama. tunaninsa yadawo adai-dai sanda yaji Abba nafad'in “mai kayanke akan hakan Nura, dan bazan takura makaba”ya Nura yahad'iye wani yawu mai d'aci abakinsa,kafin yace “duk abinda kuka yanke akaina dai-daine Abba, ni mai biyayyane agareku”“to alhamdulillahi, ke kumafa Habiba? ina sonjin ta bakinki”cewar Abba “nima dai babu komai awajena zanyi biyayya insha Allah”Haby tafad'a kanta a'kasa, Abba yace su Mama ko suna da abin fad'i kowacce tace babu,sai fatan alkhairi, Abba ya rufe taro da addu'a kowa ya watse . “wai kai da gaske kake fad'a master za'a had'a aurenka da Haby ta gidanku?”Ya Nura yayi tsaki yana mai kur'ban lemon dayake sha cikin kofin glass, ya ajiye yana fad'in “na ta'ba yimaka 'karyane Khamis? wallahi nima zancen kawai naji daga sama kuma wannan aljanar yarinyar itace tajamin komai na tsani Nuratu Khamis na tsaneta”Khamis yayi dariya “kaga Master zancen tsana bai tasoba, ni banga laifin Nuratu ba anan, tunda ba ita ketsara maka dukkan rayuwar kaba, kad'au wannan matsayin 'kaddara,kuma haka Allah yatsara maka, amma ni abinda yake bani mamaki daman wai Haby ba'kanwarka bace?”Ya Nura ya furzar da wata iska daga bakinsa mai zafi yana fad'in “ba 'kanwa bace”“to idan ba 'kanwarka bace ya kuke da ita?”. ya Nura ya'kurawa Khamis ido jin tambayar daya watso masa, kafin yakwantar da kansa saman kujerar dayake zaune 'kasanta yarufe idanunsa kamar mai bacci SHEKARUN BAYA CAN DA SUKA WUCE ASALIN LABARI KENAN [25/11/2017, 01:05] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1 MALLAKA.....QURRATUL-AYN 09 【【SHEKARUN BAYA DA SUKA WUCE】】 (Farkon labari kenan) *** *** *** Malam Salisu Ibrahim haifaffan jahar jigawa ne cikin garin ringim, bafulatani ne tsan-tsa, kuma babban malami da malanta takawoshi garin kano, ya tare a unguwar rijiyar zaki d'orawar 'yan kifi trasformer ta......( bari dai indakata anan kada inbada full address 'yan tsurku suje sa eyes 😜musamman MISS XOXO da HAFCY RANO,😏)shine mahaifi ga Abba, su uku ne kawai ya haifa a duniya tare da matarsa mai suna Aisha da suke kiranta INNA, Aminu shine babba wato (Abba) sai mai bi masa Auwal (mahaifin Nuratu kenan) sai kuma 'kanwarsu wato auta mai suna Suwaiba, su kad'ai Allah yabasu sun tsaya tsayin daka wajen tarbiyar yaransu, malam Salisu baiyi 'kasa a gwiwaba wajen sanya yaransa karatun boko, sai da Aminu yakai matakin digree sannan yakama harkar kasuwanci dayake fannin business yakaranta, hakan yasa ragamar kula da gidan tadawo hannunsa sabida rashin lafiyar da mahaifinsu malam Salisu ke fuskanta, yau ciwo gobe lafiya, cikin ikon Allah Aminu kasuwanci yafara ha'baka, hakan yasanya malam Salisu tayar masa da maganar aure, shima dayake kamar kad'an yake jira, nan da nan ya gabatar da wadda yake so mai suna Zainab, d'iyar mai gidansace, mahaifinta ko dayaji batun yayi murna sosai, domin yasan Aminu da mahaifansa, mutane ne da kowa zaiso had'a zuri'a dasu, ba wani 'bata lokaci akai auransu, ya sanyata awani 'bangare na cikin gidan daya gyara, domin gidan babu laifi akwai girma. Zainab asalinta shuwa arab ce, kasuwanci yakawo iyayenta nigeria, kuma Allah bai nufesu da komawaba, itace ta biyu a gidansu, tana da 'kanne uku duk maza, bayan yayanta namiji ita kad'aice mace kenan a cikin gidansu, ba acika wata guda da auransuba Zainab tasamu ciki, karkuso kuga murna wajen Malam da Inna kamar su d'au keta su goya, hakama wajen Auwalu da Suwaiba, cikinta na wata biyar akai bikin Suwaiba ta tare a can jahar jigawa ta auri wani malamin makaranta dake koyarwa a dutse, shi kuma Auwal Malam yaso ya cigaba da karatun boko shima kamar Aminu, amma shi yanuna yafison karatun addini akan na bokon, babu takura a'bangaran Malam, bai takura masaba haka yabarshi yana neman ilminsa, da Aminu yaji nan ya had'a masa kud'ad'an dayake tarawa ya turashi Saudia, domin yin karatun dayake so, Malam yaji dad'i sosai yayita sanya masa albarka. Bayan tafiyarsa da watanni hud'u, Zainab ta haifi d'iyarta mace,mai kama da mahaifiyarta sai dai takwaso wani 'ban gare na kyawun mahaifinta, gida ya cika da murna, nanfa 'yan barka sukayi ca agidan, Suwaiba tanaji kwana uku da haihuwar sai gata agarin kano, Inna tayita fad'an mai makon tabari ana igobe tazo, tace ita dai bazata iya bari bane, ranar suna yarinya taci suna Hafsatu, Inna tayita fad'a akan me bai sanya sunan ta ba, sai da Malam yasanar mata cewa shine yarad'a sunan da kansa ai, sannan aka samu lafiya, domin Inna babu laifi akwai fad'a idan kata'bota. yarinya ta taso cikin gata da so, ta kowanne fanni, cikin ikon Allah kuma dukiyar Abba sai 'kara ha'baka take, kasuwanci na'kara bud'ewa tako ina. BAYAN SHEKARU HUD'U shekarun Auwalu hud'u a saudiya yadawo gida ya kammala karatunsa lafiya da taimakon Allah da kuma Aminu yakaranci Qur'anic science, sunyi murna sosai ranar da akace Auwalu yadawo, har da Inna da Malam babu wanda yakaisu murna, domin tun da yatafi basu sake ganinsaba, sai dai dayake Aminu nad'an zuwa domin kasuwancinsa nakaishi sauran 'kashashen 'ketare, sai dai daya tashi zuwa yazo musu da abin mamakin daya girgiza kowa, bakomai bane illa ganinsa da sukayi tare da wata balarabiya shine ya girgiza kowa, amma kuma babu wanda ya nuna damuwarsa afili, har sai da sukaci abinci suka huta, sai zuwa kashe gari, sannan Malam yatarasu baki d'aya a falonsa, dayake Abba yasake gyara gidan babu laifi, yayi ginin zamani na wancan lokacin. Malam yana kishingid'e dayake baya iya zama sosai jikin ya'kara rikicewa, bayan bud'e taro,da addu'a, Malam ya bud'e,baki da 'kyar da muryarsa da bata fita sosai“Auwalu munyi farin cikin kammala karatunka asa'a, sannan mun godewa Allah daya dawo mana da kai gida lafiya, sai dai wani hanzari ba guduba, kazo mana da wani abin mamaki da muka damu akansa, bakomai bane illa muna so musan wacece wannan dakazo tare da ita?”Auwalu yayi shiru kansa a'kasa, kafin ya d'ago ya dubi yayansa Abba, Abba ya gyad'a kai alamun yayi magana, ya gyara zamansa yana mai duban Inna data tsareshi da ido, ya sunkuyar da kai yana fad'in. “naji dad'in tarbar dana samu agareku Malam, abinda banyi tunaniba, duk da nasan irin karamci na zur'armu, nayi tunanin zaku tambayeni tun ajiya, amma sai naga,kunyi kawaici ha'ki'ka naji dadi, wannan ba kowa bace illa Amina, Amina balarabiyace danginta kaf larabawane na had'u da Amina tunfarkon zuwana saudia, ta nunamin so da kauna tsan-tsa, tare da iyayenta,asalima agidansu nazauna, har zuwa kammala karatuna, munsha'ku da ita sosai Malam, sai dai iyayenta sun nuna bazata biyoni nugeria muyi aureba sai dai ni inkoma can na aureta, duk yanda naso infahimtar dasu bazan iya rabuwa da kuba da mahaifata sungaza fahimtata, nafad'a musu koda natawo da Amina nigeria hakan bazai saka nakasa kai musu itaba, amma sun'ki yar da, nayanke hukuncin rabuwa da ita, amma sai abin yazama illa agareta har ciwo takwanta, ana igobe zantawo kwana tayi tana kuka Malam, ganin hakan yasaka mahaifinta ya yarda mutawo da ita duk da dai,mahaifiyarta ta'ki yarda, amma akan sharad'in duk shekara zamu dunga zuwa da ita, da dai kamar bazan aminceba, amma sai tausayinta yakama ni har dai na amince da hakan, yanzu dai Malam gani gareka duk abinda kayanke akaina ni mai biyayyane” kowa yayi shiru haka falon yad'au shiru, illa kukan Amina dake tashi, wadda duk wanda ya lura da ita tun da suka zo kukan take, ba fahimtar abinda ake fad'i takeba, amma tasan fad'a ake, magana ake akanta, hakanne yasaka kukanta 'kara sauti, gani take kamar bazasu aminta da itaba, kafin Malam yace wani abu, Abba yarigashi da fad'in “malam kuyi ha'kuri kukar'bi Amina matsayin 'ya agareku, ha'ki'ka Amina taso Auwalu tayi masa halaccin da ba du macace zatayiba, ta nuna masa so wanda da wuya yasamu wadda zata soshi tsakani da Allah haka, sannan ina ro'kon masa, afuwa idan har yayi laifi”falon yasake d'aukan shiru, kafin Malam yayi gyaran murya yana murmushi yake fad'in “ai babu abinda zamuce illa fatan alkhairi kawai, Auwalu baiyi laifin komaiba agare mu, illa yayi 'ko'kari yadinga cika al'kawarin daya d'aukowa iyayen Amina”yayi shiru yana d'an tari, Inna tace “gaskiya nayaba da nutsuwa da hankalin yarinyar, na amince Auwalu ya aureta Allah bada zaman kafiya da zuri'a,tagari”“amin” suka amsa, kafin Malam yace “babu wani 'bata,lokaci nan da sati biyu masu zuwa insha Allah za'a d'aura auren Auwalu da Amina”😁 [27/11/2017, 22:10] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈QIYAYYA SA GANIN LAIFI🌈🌈🌈Book 1 MALLAKA......QURRATUL-AYN 10 (kuyi ha'kuri abisa yanda nake baku labarin ASALIN SU NURATU inshort ina fatan hakan bazai bada matsalaba zaku fahimce ni nagode sosai NURATU FANS😘) RANA BATA 'KARYA Kamar yanda Malam yafad'a, sati biyu na zuwa ranar juma'a bayan saukowa daga mallaci aka d'aura auren Auwal da Amina, ta tare itama awasu d'akuna dake cikin gidan nasu, Amina taga so da 'kauna daga d'angin Auwal, babu tsangwama bare nuna ban banci, ta zauna cikin so da yarda da aminci, kamar yanda Malam da Inna suka d'auketa matsayin 'ya agaresu, ita batayi 'kasa agwiwaba wajen yimusu biyayya. BAYAN SHEKARU UKU Hafsa na da shekaru uku a duniya tayi wayo sosai tana yawonta ko ina, gata da surutu tubarkalla, bakinta yafara bud'ewa ne da kiran Mama da Abba. Ranar wata laraba aranar ciwon malam yatsananta sosai, amma duk da haka yana daure yatara dukkan iyalensa, yayi musu nasiha mai ratsa jiki, da yanda kowa zai zauna da duniya lafiya, Abba yaso akaishi asibiti amma Malam ya'ki yanuna lafiya 'kalau shi dai yake. kwana biyu dayin hakan ranar juma'a da asuba Malam yace ga garinku nan, mutuwar malam ta girgiza al'umma da dama bama iyalensaba, Amina tayi kuka tamkar mahaifintane ya mutu, ko dayake mahaifin tane mana, tunda shine yahaifi mijinta. haka aka had'a Malam domin kaishi gidanshi na gaskiya, iyalensa sunyi kuka sosai, har akayi sadakar bakwai mutane na zuwa gaisuwa sai sati biyu da rasuwar sannnan 'yan jigawa suka koma gida. Ranar da Malam yacika kwana arba'in da rasuwa, ranar Mama tatashi da wani irin ciwon ciki, wanda tun tana daurewa sai da aka nufi asibiti da ita, ana zuwa sukace na'kudace, kowa ya cika da mamaki da murna, domin babu wanda yata'ba tunanin da ciki atare da itama,bare kuma labarin haihuwa, kowa addu'ar sauka lafiya yahauyi mata. sai da tashafe kusan rabin awa da kawota asibitin sannan tahaifo d'anta namiji mai kama da mahaifinsa, aka wanke yaro sannan nurse tayo waje dashi, Abba yacika da murna sai godiya yakeyiwa Allah, amma murna babu kamar Auwal dayakeji kamar shi akayiwa haihuwar, sai da aka gama gyarata sannan aka kawota d'akin hutu, sai lokacin su Abba suka samu damar ganinta akahau yimata sannu. kamar akan yaron aka fara haihuwa ranar suna yaro yaci suna NURA, babu irin fad'an da Inna batayiba akan bai mai da sunan Malam ba, sai da 'kyar taha'kura shima sai da yace mata malam dakansa yabar wasiyyar sanya sunan Nuran sannan aka samu lafiya. yaran suntaso cikin gata da so da 'kauna, har dai Amina tanason yaran kamar tahad'yesu, musamman Nura yyatone mai shiga rai, domin kusan kayansama d'akinta suka koma, ita keyi masa komai lokacin bakinta yafara gogewa da yaren nan 'kasar wato Hausa, daman gata da son al'adun nan, wajen shiga da irin girke girkenmu da dai sauransu, hakan yasaka komai baya yimata wahalar kowa, kasan ance duk abinda kake so, bazai baka wahala wajen koyaba. BAYAN SHEKARU BIYAR “haba Ammy, kidaina zubda ha wayenki akaron banza, haihuwafa ta Allah ce, ni da Allah yabani yara,biyu aiba cemiki akai yafi sona dakeba, dan Allah kidaina wannan kukan, a gidannan akwai mai miki ba'kar magana kan haihuwane ?”cewar Mama kenan, dake zaune tare da Amina tana aikin kuka, da yake yanzu Nura da Hafsa sun sanya mata Ammy, hakan yasa kowa na gidan ke kiranta da hakan. Ammy ta goge kwallar dake gefan idonta ta dubi Mama “ba wai ina fushi dayin hakan bane, yaufa shekara takwas kenan da aurena babu ko da 'batan wata, haka kawai nakeji araina ina son nahaihu kodan insamu maiyimin add'a, tunda banda ku yanzu bani da.....”sai kuma tayi shiru, Mama tatsareta da ido kafin tace “naji koma dai menene kifauwalawa Allah dukkan lamarinki, kimai da komai ba komaiba, sai kiyita addu'a sai kiga komai yawuce yazama labari”Ammy tashare hawayenta tana fad'in “nagode sosai da shawaranki agare ni”shigowar Nura da Hafsa shine yayi sanadiyyar yin shirunsu, suka hau wata hiran domin basaso yaran sufara sanin damuwa tun suna yara. “nidai kam yanzu jigawa nake son komawa, inyaso duk mai son ganina yaje can, akan me kuke son rabani da mahaifata?”fad'in Inna kenan dake zaune saman kujera, yayin da su Abba ke zaune 'kasa a gabanta, Abba ya girgiza kai yana fad'in “bawai zamu rabaki da mahaifarki bane Inna, amma idan kin koma can aibazamuji dad'iba, muna son zamanki anan sosai Inna”Abba 'karami kamar yanda su Nura ke kiransa yakar'be da fad'in “ki daiyi ha'kuri Inna, kizauna damu zamufi jindad'in rayuwa tare dake”wata harara Inna tawatsa musu da fad'in “wato kunfi son ganin 'bacin raina ko akan kufarantamin”ta'karashe maganar tana mai fashewa da kuka, hakan yasaka hankalin su Abba tashi baki d'aya, nan da nan Abba yace tashirya sukaita babu komai, su dai addu'arta suke bu'kata, sai sannan tahau sanya musu albarka, aranar Abba 'karami ya aike da kud'in siyan gida madai daici, yasaiwa Innarsu, da yake shima yanzu babu laifi arzi'ki yabud'e masa, domin shine headmaster nawata makarantar islamiyya private ce, nan da nan aka yiwa gidan d'an gyararraki, akayi fenti da yamma kuwa suka kaita jigawa ta tare agidanta, basu baro garinba sai da suka ajiye mata dukkan wani abu dazata bu'kata, Suwaiba tayi murna sosai jin cewa Inna tadawo jigawa, yanzu kewa tad'an kau aranta, tun da haryanzu Allah baibata haihuwaba, har mijin nata ya'karo aure ma wata mace mai kirki mai suna Jamila, suna zaman lafiya abinsu domin tana baiwa Suwaiba girmanta yanda yakamata, haka itama Suwaibar tana jan girmanta. “wai har yaushe zaki barni incika al'kawarin dana d'aukowa iyayenki da Malam, Amina?”fad'in Abba 'karami kenan yana mai kai cokalin abincin daya d'ebo bakinsa, Ammy tad'anyi ajiyar zuciya “bawai na'ki barinka kacika al'kawari bane, kasan cewa idan har zanje gida ayanzu tabbas sai dai kadawo batare da niba, domin kuwa indai zanje batare da ciki ba ko d'a tabbas aurena dakai yazo 'karshe, ni kuwa bana son abinda zai rabani da kai”tayi shiru jin kukan datake 'ko'karin 'boyewa zai fito, Abba 'karami yayi ajiyar zuciya, “ki kasani ko yanzu su sauya ra'ayi akan hakan?, yau shekara takwas kenan amma duk shekara sai Yaya yayi batun tafiyar taki, har yafara ganin laifina, gani yake nasan illar rashin cika al'kawari amma ina takewa, har cewa yake idan kud'in tafiyar takine babu shi zai biya, to mai kike so ince mai kuma Amina?”Ammy tagoge kwallar data kawomata, “nidai kayi ha'kuri, karo na farko arayuwa zanyi maka musu, bazanje gidaba, domin bana son rabuwa da kai”Abba yayi shiru yana dubanta, shima bawai yana son rabuwa da ita bane, amma yana ganin kamar yana tauye mata ha'k'kine, ruwan data zuba masa mai sanyi yad'auka yasha dayake ana zafi agarin, sannan yace “shikenan bazan takuraki ba, amma zamuje dake kifad'awa Yaya dukkan abibda kika fad'amin, domin bana so Yadinga kallona da laifin tauye maki ha'k'ki”Ammy ta gyad'a kai alamun to. SHEKARU BIYU cikin shekarun abubuwa da dama sunfaru, ciki kuwa har da 'karuwar arzu'kan da Abba da 'kaninsa suka samu, domin kuwa Abba 'karami harya sayi filin dake gaban gidansu, yayi gini ma dai-daici amma kuma gidan mai kyau sosai, ya tashi daga cikin gidansu suka tare asabon gidan, Abba yayi murna sosai domin su 'yan uwane da basa kyashin samun 'yan'uwansu, suna so ace nasu ya cigaba sosai, Abba ma ya gyare gidan sosai, lokacin Hafsat nada shekaru goma aduniya yayin da Nura ke da shekaru bakwai, domin ta girmashi da shekaru uku idan baku manceba. lokacin Abba yataso da batun 'karin aure, dake Mama macace ta gari mai kawaici da sanin ciwon kai, ko kad'an bata damuba saima fatan alkhairi da tayi, domin tasan namiji ma aurin mata hud'une ba biyuba, Inna cema taso tabashi matsala, acewarta dukansu mata d'aya ta ishesu, kaman yanda tazauna ita kad'ai batason tara mata agida, taron rigima, ankai ruwa rana kafin ta amince da auren, domin sai da Yayanta yashigo maganar, sannan ta amince (Innar rigima kenan). kuma dayake Abba namijine domin baya mantawa da dukkan ha'k'kin dayasan ya rataya akansa, aurensa bai sanya ya sauyawa Mama ba ko kad'an. Dayake abune namasu hali, ba'awani ja lokaciba akayi bikin domin wata bazawara ce mai suna Habiba ya aura, Mama tacewa su Nura sudinga kiranta Aunty, yaran kuwa na bata girma sosai, kaman yanda take girmama mahaifiyarsu Mama. suna zamansu lafiya, cikin girmama juna Abba kansa najin dad'in hakan sosai. [29/11/2017, 03:04] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈QIYAYYA SA GANIN LAIFI🌈🌈🌈Book 1 MALLAKA......QURRATUL-AYN 11 【NURATU nami'ko gaisuwa agareku masoyanta tanayi muku fatan alkhairi, QURRATUL-AYN tana godiya sosai da addu'arku agareta😘】 BAYAN SHEKARU GOMA SHA BIYAR Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da auren Hafsat da akai tare da wani doctor mai suna Hamza, tunda Hafsat ta kammala scondry school Inna ta matsa akan dole ta fidda miji ayi mata aure, domin ita macace bata son wani zurfin boko akan mace gwanda namijin, cikin ikon Allah kuwa doctor Hamza ya fito da gaske, Abba baiyi 'kasa a gwiwaba wajen bincikar asalibsa ba, bayan gamsuwa dashi da Abba yayi yaga yafito daga gidan tarbiyarne, nan da nan aka sanya rana akasha biki. har wannan lokaci gidan Abba ko 'batan wata ba'asakeyiba, babu kuma wanda yadamu da hakan, domin sunsan samu da rashi duk na Allah ne. Ammy ce zaune cikin falonta kankujera mai cin mutum biyu, yayin da wata mace ke zaune kan kujera mai cin mutum d'aya, da dukkan alamu tattaunawa suke akan matsalolinsu, Ammy tad'anyi murmushi tana fad'in “ni kuwa Momyn Haby kina bani mamaki, menene acikin haihuwa kuma, ni da nake nema nizan damu, amma nima nabarwa Allah dukkan lamurana, amma ace ke dakika samu kike wannan maganar”matar da aka kira da Momyn Haby tayi wani murmushi,mai kama da takaici, ta dubi Ammy tana fad'in “ke kike ganin hakan, amma ni nasan wuyar danake sha ahalin yanzu, domin wani lokacin abincin da zamuci ga gararmu yake, banda Allah yahad'amu daku da bansan yanda zanyiba arayuwa”“uhmmm ke kike tunanin hakan, amma Allahn daya baka 'ya'yan shiyasan yanda zai tafi da rayuwarsu, mu namu kawai rainone da tarbiya”Ammy tafad'a cike da murmushi akan fuskarta, Momyn Haby takau da zancen tana fad'in “ni kuwa Abban su Nura nanan, inason yi masa godiya ne, abisa hidimar dayake agaremu”“yana nan, jiyama yadawo daga dubai”Ammy tabata amsa, ta d'an ta'be baki, kafin tace “to ni zanwuce gida, idan munhad'u nayi masa godiyar”Ammy tayi mata rakiya har soro, sukai sallama ta tafi. Asalin Momyn Haby 'yar barnoce sunanta Rabi'atu, aure ne yakawota garin kano, ita da mijinta ma aikancin gwamnatine,sunansa Safiyanu, yaransu uku, khaleel shine,babba sai Habiba sai Kamal, Khaleel kusan sa'an Nurane, amma nuran ya girmashi da shekaru biyu, sai Habiba da tsiransu da kamal shekara biyar, sannan Kamal tsiransu da Habiba shekaru uku. Gidansu nanan 'kasan layinsu Ammy, mutuwar mijinta shine asalin had'uwarsu da Ammy, da take bala'in tausayawa rayuwar yaran da ita kanta u wartasu, kasancewa mijin nata yarasu bai barmusu komaiba arayuwa, hakan yasa Ammy take d'an taimaka musu, tare da Mama, Mamace ma tasanarwa Abba akan ad'inga taimaka musu kamar yanda Ammy takawo kukan hakan. Ammy ta aminta da Momyn Haby sosai, hakanne yasaka babu wani sirri nata da bata saniba, komai za'ayi a gidan suna tare, sabida amintarsu. Nura kuwa yadage akan cewa shifa soja yake son tafiya 'kasar malesia, kasancewar ya kammala karatunsa na scondry, Abba da farko 'kin amincewa da hakan yayi, sai da Abba 'karami yasanya baki sannan Abba ya amince aka tura Nura malesia. Tafiyar Nura malesia da shekara uku, ciki ya baiyana atare da Ammy karkuso kuga murna cikin gidaje guda biyunnan, har dai 'bangaran Mama tafi kowa murna da samuwar cikin, Ammy taga gata domin aikin komai hanata yisu Mama sukai, suke yi mata komai, Abba 'karami kuwa har 'yan aiki yace zai kawo, Ammy ta'ki amincewa da hakan. Ammy na mamakin Abba ayanzu, shida da baya nuna wata damuwa,akan rashin haihuwarta, amma yanzu yafi kowa damuwa akan cikin nata, idan tatuna hakan sai dai tayi dariya kawai, tasan halin Abba wajen kawaici da zurfin ciki, amma baya nunawa akan cikin nan. ana cikin hakan kuma Abba ya 'bullo da wani al'amari daya girgiza kowa, ba komai bane illa cewa da yayi zai auri Momyn Haby, al'amarin ya girgiza Ammy da Mama, musamman Ammy har taso sanya abin aranta, yana bara zanar ficewar cikinta, sai da Abba 'karami yanuna jan ido akan hakan sannan tad'an rage damuwa, amma kullum suka zauna ita da Mama zancensu baya wuce batun cin amanar da Momyn haby tayi musu, Aunty cema bata fiye nuna damuwarta akan hakan ba. Momyn haby tad'auke 'kafa 'bat, daga zuwa gidan, hakan ya'kara tabbatar musu da batun auren da gaske ne. wata mata dake makwabtaka da Momyn haby ita taje wajen Mama tana sanarmata cewar su tashi tsaye da addu'a domin Momyn haby ba haka tabar Abba ba, har alwashi tayi indai tashiga gidan to babu su ba farinciki, kuma sai daula da mulki sunkoma hannunta sai Abba yadaina ganin kowa sai ita, daman kawai lumbu-lumbu tayi musu. Mama bata d'au maganar da muhimmanciba, ganinta gulmace kawai ta mata da ba 'arabasu da ita. *** *** *** “Ni kuwa Maman Nura mai kike gani akan batun auren nan na Alhaji?”cewar Aunty dake gyaran alaiyahu, a kitchen yayin da Mama tamai da hankali kan tu'kin tuwanta, Mama tad'an dubeta kafin tace “mai kuwa zanyi ayanzu banda abin da yawuce addu'a da fatan alkhairi”Aunty tad'an ta'be baki “nikam abin nabani mamaaki wallahi, yanzu Alhaji baki d'aya hankalinsa yakarkata kan aurennan da zaiyi, bama yabi takanmu”“kidaina sanya damuwar wannan abin aranki, ki dinga addu'a kawai, amma sanya damuwa bashine zai saka yafasaba, saima sanyashi yayi auren da damuwar taki zatayi, amma idan kika watsar da lamarin kika fuskanci abinda yake gabanki hakan zai saka yaji shakkar wani abun, ko kinajin damuwa aranki dannewa zaki dingayi, nasan ai kishi dole ne, domin halittar muce tazo da hakan, amma dai kidinga ha'kuri”Aunty tad'anyi murmushi tace “kai amma nagode sosai Maman Nura, shiyasa nake son zama dake, inajin dadin shawaranki agareni nagode sosai”“karki damu ai anzama d'aya”nan suka cigaba da aikinsu,kamar babu wata damuwa arabsu, domin dama sunsaba,idan kaje gidan bazaka gane wacece da girkiba, komai tare sukeyi. Abba 'karamine zaune falo, da kwanukan abinci,gabansa yayinda Ammy,kezaune gefansa, da cikinta wanda yafito sosai yana wata na shidda kenan, Ammy tad'anyi gyaran murya tana fad'in “yanzu dan Allah babu wanda zai iya hana Abba wannan auren?”yad'an dubeta yana mai ajiye cokalin hannunsa tare da fad'in “babu mai hana wannan auren ayanzu, d'aurin aure yarage sati guda, Inna ce kawai kuma itama ta amince da auren, to waima menene abin damuwa da hakan?, shi namiiji ai ma'aurin mata hud'une, kuma yana da yanda zaiyine shiyasa zai aureta”“bazaka gane abinda yasaba”Abba 'karami yayi dariya yana fad'in “yaushe kuwa zangane tunda kina taya 'yar uwarki kishine, kika sanima ko nima tare za'a d'aura da,nawa”Ammy wata harara ta watsa masa, wadda batasan tayi taba, Abba yasa dariya yana mai jawota jikinsa tare da fad'in “ke kad'ai kin ishe ni rayuwa”Ammy tayi murmushi kawai. Cikin satin da Abba zai 'kara auren, yasake gyara gidansa sosai, ya fitar da inda Amaryarsa zata zauna, akai fenti da komai, sannan ya canjawa ko wacce kayan d'aki, kamar yanda yayiwa amaryar tasa komai, sai wani rawar 'kafa yake kai kace yanzune zaiyi auren fari. Aunty Hafsat dataji wadda mahaifinsu zai aura, taji haushi sosai, har tad'au alwashin ba ita ba zuwa gidan ranar bikin bare tayi kallon kayan takaici. Nura kuwa nacan malesia asalima baisan wainar da ake toyawaba anan gida nigeria. Sati na zuwa aka d'aura aure, da 'ker kwarya kwaryan walima, a daran amarya tatare, randa aka kawota su Mama sung a bariki, ganin idansu, tun daga kan masu kawota har zuwa ita kanta amaryar, tare da yaranta ta tare baki d'aya. ashema Abba ya mai dasu school baki d'ayansu, dayake da duk ankoresu sabida rashin biyan school fees. Tun da Momyn Haby tazo gidan abubuwa da dama yacanja, basa rigima amma dai yawanci sai abinda tace za'ayi agidan, ga yaranta basu da kunya ko kad'an, har dai Habiba tun suna yara kenan Khaleel ne shi babu ruwansa, asalima yafi zama d'akin Mama akan d'akinsu, domin shi Allah yayishi da ha'kuri da rashin son fitina tun zuwan Momyn Haby ta tare d'akin Aunty bini bini suna d'akin ita da yaranta, cikin wata guda Aunty tad'aurewa Mama fuska yaza mana babu shiri tsakaninsu, wata rana ranar girkin Aunty da dare, Abba na kwance yace Aunty tami'ko masa wata jaka tasa, dayazo da ita da safe ya ajiye kud'ine cike aciki na 'yan kasuwarsu abokansa suka bashi ajiya za'aiko masu wasu kaya, ita Aunty batama san da jakarba Abba na bud'ewa yaga kud'in babu bandir uku, Abba ya mi'ke da sauri yana duban Aunty tare da fad'in “kin ta'ba jakarnan ko?”“a'a mai kagani Alhaji ni da kosanin kazo da itama banyiba”Abba ransa ya'baci “kinga banson wasa, kud'ine na ajiya nazo dasu, yanzu na duba babu babdir uku”“wallahi ban d'aukaba Alhaji domin bansan kazo da kud'in bama”“to waye yashigo d'akinan?” “babu kowa dan gaskiya banga wanda yashigoba”. sukaita jayayya hakan yasaka Abba tara dukkan mutanan gidan adaren amma kowa yace bashi yad'aukaba, Abba ransa ya'baci, yacrr kowa yaje har ita Auntyn yace takoma d'akinta, baya bu'katar kowa. nan da nan Momyn Haby ta lalla'ba tashiga d'akin nasa, mai tace masa oho, sai gashi ya fito yanufi d'akin Aunty, yana zuwa yahau bincike, Aunty tayi tsaye tana kallon ikon Allah sai da yahargitse d'akin baki d'aya, har zai fita sai kuma yakoma yad'age katifar gadonta sai kuwa ga kud'in. Aunty tayi tsai tana kallon ikon Allah, tana tunanin yanda akai,kud'in yazo d'akinta,kuma,'kasan katifarta. Abba kuwa tsareta yayi da idanunsa, yanayi mata kallon tuhuma, Aunty tadur'kusa tana mai neman yafiya da fad'in ba ita tad'aukaba, asalima batasan yanda akai suka zo d'akiinba, Abba jin zancen nata kawai yake kamar rainin hankali, hakanne ya'kara fusatashi yace gobe da safe taje gida kawai. Momyn Haby na la'be tanajin dukkan abinda yafaru, tayi dariya aranta tana fad'in “kad'an kika gani, ingama dake kafin inkoma kan uwar gijiyar taki wato Mama” gari nawayewa Aunty tanufii gidansu, har tsawon wata guda Abba yawatsar da lamarinta, Mama da Ammy sunje har gidan nasu Aunty bata ha'kuri, amma Momyn haby ko le'ke, hakan yasanya jikin Aunty yin sanyi da al'amuran Momyn haby. sai da Abba 'karami yasanya baki, yaje kuma yahad'oshi da Yayan Innarsu, sannan Abba ya dawo da Aunty, lokacin watanta biyu a gida. tun da tadawo tafita hanyar Momyn Haby, Aunty tabaiwa Mama ha'kuri suka koma kamar da abinsu suka aje Momyn haby a gefe. Wata ranar alhamis tunsafe da Abba 'karami yatashi yake fad'in baya jin dad'in jikinsa, gashi kuma zasuje d'aurin auren wani amininsa zai sake aure matarsa tarasu, Ammy ce tad'inga 'karfafa masa gwiwa duk da itama bawai dad'in take jiba, daurewa kawai take, da 'ker yasamu yafita, kafin yatafi dawowarsa uku, sannan yatafi adaddafe. 'karfe biyun rana sai ga ambulan a 'kofar gidan, motar Abba na biye da su, cikin gidan Abba aka shiga da gawar Abba 'karami dake lullu'be da farin yadi, mintuna biyar da shiga sai ga Ammy tashigo ko mayafi babu, tana fad'in, anuna mata mijinta tasan ba mutuwa yayiba, kowa yacika da mamakin wanda yasanar da ita, domin ance kada afad'a mata, basuyi auneba sai ganinta akayi ta zu'be 'kasa jini ya 'balle bashiri sai hospital, ana zuwa akayi ciki da ita, doctor yadawo yasanarwa Abba sai dai ayi operation aciro abinda yake cikin domin zai iya rasa ransa, nan da nan Abba yasanya hannu. mintuna goma sha biyar sai ga nurse d'auke da jaririya kyakkyawa, Mama takar'bi jaririyar tana tambayar “Ammyn tana lafiya kuwa?” nurse tace “ yanzu itama za'a fito da ita tana nan lafiya” Ammy data dawo haiyacinta,babu abinda take sai kuka, har dai idan takalli jaririyar data haifa sai zuciyarta takarye tausayin yarinyar yakamata. har akai sadakar bakawai Ammy na hospital yawanci idan anzo gaisuwa sai kuma awuce hospital dubiya, ranar da jaririyar ta cika kwana bakwai a duniya Abba yace Ammy dakanta zata za'bi sunan da za'a sanya mata, nan take Ammy tace “NURATU”shine sunan da take so, Abba yasanya mata kuwa. Haka Ammy tad'au ha'kuri da dangana tasanyawa ranta, ta tsaya kai da fata wajen rainon marainiyar jaririyarta. shekarar Nuratu guda aduniya ya Nura yazo hutu gida, tun da yazo yatarar anhaifi Nuratu, ko d'aukanta bai ta'ba yiba, asalima yakanji yatsani kallon yarinyar, amma yarasa dalilin hakan, bayan tunda akayi masa waya akace anyi haihuwa yake Allah Allah yazo gida yayi 'kanwa, amma yarasa mai yasa,ko kallon yarinyar bayasonyi yanzu, bayan yana ganin mutane da dama kowa da yaga nuratu shidai burinsa yad'auketa amma shi banda shi. wata shida yayi yakoma sannan Mama Allah yataimaketa da shigar ciki, shekarar Nuratu biyu a duniya Mama tahaifi NANA, bayan shekaru biyu kuma ta haifi 'yan biyu sune RAHMA da SAlisu sunan malam suke kiransa HILAL. Har lokacin Aunty ko 'bari batayiba, hakama Momyn haby, kullum sai 'karyar zubewar ciki. Nuratu ta girma,Nana da shekaru biyu, sannan Nana ta girmi su Hilal da shekaru biyu. yanzu tsakanin yaran Nuratuce babba shiyasa suke binta da duk abin da tace dasu tun tasowar Nuratu yarinyace mai rigima, ga uwa uba tsokana da rashin ji, wanda ada suke ganin yarintace kawai zata daina, amma har ayanzu da Nuratu takai shekaru takwas aduniya, mai makon abin yaragu saima 'karuwa kawai da take. Tunda ya Nura yakoma bai sake zuwaba sai bayan shekaru uku yazo yayi wata biyu yakoma, a wannan zuwan su Nuratu sunci kwakwa, domin da ahoto kawai suka sanshi, basu zaci haka yakeba, shiyasa da yakoma sukayita addu'ar Allah yasa kada yadawo. Da Khaleel suke d'asawa, domin shi babu ruwansa duk abinda sukace hakan za'ayi, shima kuma Abba yad'aukeshi yaturashi karatu, ranar su Nuratu ansha kuka, kamar ance idan yatafi bazai dawoba. Dama can a gidan basa shiri da Kamal da Habiba, Haby cema indai zasu had'u da Nuratu saii anji kansu, acewarta tatsani yarinyar. wannan kenan shine ASALIN NURATU yanzu zamu koma ASALIN LABARIN [30/11/2017, 22:18] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈QIYAYYA SA GANIN LAIFI🌈🌈🌈Book 1 Mallaka.......QURRATUL-AYN 12 MU KOMA BAYA 【】【】【】 【】【】【】 Ya Nura yad'ago kansa daga kwanciyar da yayi, yadubi Khamis yana mai fad'in “ba'kanwa tabace, da ita mahaifiyarta tazo gidan nan”“ohh kacemin agolace dai kawai”Khamis yafad'a yana dariya, bai jira mai Nura zaiceba yad'ora da fad'in “nidai shawara agareka kawai kayi biyayya da abinda iyayenka suka za'ba maka”Ya Nura yayi murmushi “biyayya ai tazama dole, ko dan murabu lafiya” Khaleel zaune falo, yayin da su Nuratu suka kewayeshi sunata faman zuba masa surutun da suka saba, Nuratu tace “yanzu ya Khaleel mai kaje ka karanta ne? dan kasan nidai bana son aikin soja wallahi natsani sojoji”Khaleel yayi dariya “Nuratun Ammy kenan, ni doctor na karanta, amma mai yasa bakyason soja?”Nuratu tad'an ta'be baki “kawai dai natsanesu domin mugwayene azzalumai har dai wannan Yaya Nuran na.....”bata 'karasa maganartaba taji anbuge mata baki, Nuratu da sauri tami'ke tsaye taganshi tsaye kansu kamar mala'ikan mutuwa, murgud'a baki tayi tana fad'in “Allah ya isa mugu”tawuce d'akin Mama da gud yabita shima, amma kafin ya kai harta kulle 'kofar. ya Nura yadawo ransa a'bace yana duban su Nana dake zaune, wata uwar tsawa yawatsa musu, wadda tasanya Rahma sakin guntun fitsari awando “ubanwa kuke kallo kuna muzurai, kosaina 'ba'b'ballaku kuma, tashi kumar falon nan”da gudu suka mi'ke suka fita, Nana ce aka d'an barta abaya, sabida 'kafarta da haryanzu d'ingisawa take. Khaleel yad'anyi dariya yana mai fad'in “ni kuwa broda al'amarinka da Nuratu nabani dariya, kasan halin Nuratu sarai, amma kadinga shiga shirginta, Nuratu nada sau'kin kaifa kuma bata da raini, idan kaga tayi wad'annan abubuwa biyun to shiga hanyarta akai”Ya Nura yajefi Khaleel da wata irin harara yayi kwafa yana mai fad'in “to babanta, ai na fahimci ma komai yarinyar nan keyi da had'in bakinka, idan ba hakaba mai yasa zaka sasu gaba tana zagina kanaji”Khaleel dariya yasakeyi karo na biyu yana mai girgiza kai “broda kenan, dad'ina da kai d'aukan zafi, yanzunan har wani abu tafad'a dazai 'bata ranka abanza”Ya Nura yakalli Khaleel kawai yad'auke kansa, bai kuma tanka masaba yafice, domin jiyayi maganganun Khaleel d'inma sunfi na Nuratun 'kona masa rai. Wasa-wasa dai sai ga soyayya na'kulluwa tsakanin Ya Nura da Haby, wadda kowa yake mamakin hakan, amma awajen Abba yaji dad'in hakan sosai, Mama da Aunty nema suke shakka akan son da Nura ke nunawa Haby ahalin yanzu, domin soyayyar tana so tayi yawa, hakan yasaka Mama du'kufa da yimasa addu'a sosai, a'ban garan Haby da Momynta kuwa sunfi kowa murna da hakan, ji suke tamkar burinsu ya gama cikama tun ahalin yanzu. 8:40pm Zaune yake cikin gaiden, kan had'addaan carpet ma dai-daici, ga kayar fruit cike agabansa, sanye yake da blue d'in jeans, mai ratsi irin kayan sojoji da farar t.shert gaban rigar anrubuta MEGA POWER STAR da ba'in rubutu, wayace ahannunsa yake daddan nawa, gefe guda kuma Haby ce zaune kusa dashi, tana yanka masa Apple, taci ado kamar wadda zataje gasar kyau, domin babu laifi Haby itama nada kyawunta dai-dai gwargwado, gata ma'abociyar son make-up ce sosai, da shiga takece raini, yanzuma riga da siket ne ajikinta, na wata super koriya mai ratsin fari da ba'ki, abinka da farar mace duk da dai an'kara da mai, atamfar tayi mata kyau sosai, gaban rigar kamar da tayi kwakw-kwaran motsi albarkatun 'kirjinta zasu fad'o waje, ciket d'in kuwa kamar kad'an yake jira ya yage tsabar kamata da kayan yayi, tayi d'aurinnan da ake kira gobarar mata, wanda da dukkan alamu yazamewa haby jiki, domin d'aurin d'ankwalinta kenan kodan tafahimci yanayi mata kyaune oho, fitilun dasuka haske wajen sune suka 'kara 'kayata wajen da kyau. matsowa tayi kusa dashi har jikinsu na d'an gogar juna, tasanya masa apple d'in dai-dai bakinsa yana ci ahankali tamkar baya so, ya juyo kad'an ya dubeta sai kuma yayi saurin d'auke kai yana fad'in “mai yasa kikeson irin wannan shigarne?”tad'anyi farr da ido kafin tace “naga hakan ba illa bane, kuma aikai zan aura, menene dan nayi maka kowacce irin shiga?”Ya Nura yatsareta da mayun idanuwansa yanajin wani abu nafizgarsa, hakan yasanyashi d'auke idonsa daga dubanta yana mai fad'in “ai yanzu baki zama matar tawaba tukunna, kijira a gidana sai kidinga yimin, kinsan ina da kishi sosai ko? ”Murmushi tayi mai jan hankali, wanda yakusa sumar da ya Nura, takamo hannunsa tasanya anata tana murzawa kad'an-kad'an “zankiyaye insha Allah Dear”jin dayayi kamar tana neman tafiya da wani 'bangare na jikinsa, yasanyashi janye hannunsa ahankali, yad'auko ayaba yakama ci, yana mai 'ko'karin mai da numfashinsa. Garararrrffff aka turo gate aguje tashi go, yayin da wasu garada su biyu suka biyo bayansu, Gateman ne yayi saurin ri'kota, sukuma garadan suka ja birki suka tsaya, ganin hakan yasanya Ya Nura mi'kewa da sauri ya nufi bakin gate d'in, Nuratu sai wani fiffi'kewa takeyi zata gudu, mutum d'aya daga cikin mutanan yana fad'in “kaga Baba kabarmu mu fyed'eta kawai, harmu zatayiwa rashin kunya”cikin maye yake fad'in hakan ga kuma wu'ka a hannunsa, Ya Nura nazuwa ko kallon inda Nuratu take baiyiba, yahau tambayar samarin mai yafaru d'aya daga cikinsu yace “muna cikin tafiyane yalla'bai,kawai sai ga wannan sikar tazo, shine tahaucewa 'yan maye masu warin kashi, 'yan maye basa wanka, 'yan maye masu kwanan bola, aka cemata mu sa'annintane eyee, kawai Baba kabamu ita muje mufyed'e muyi kilishinta kawai 'yar banza, yalla'bai kada kace komai”“wallahi 'karya yake, 'karya sukemin Allah ya Nura”cikin d'aga murya Nuratu take fad'in haka. Abba ne ya'karaso da sauri shi da su Mama da Khaleel suna tambayar “lafiya Nura nakejin haya niya?”Samarin suka sake mai-maita abinda Nuratu tayi musu, Aunty da Mama ri'ke baki kawai sukayi, Abbane yatsaya basu ha'kuri suna rashin mutumci, hakan yasanya ya Nura fito da I.D card nasa, sai gasu sunzube bisa gwiyoyinsu, suna bashi ha'kuri, Nuratu kuwa sai dariya take ri'kewa tanayi musu gwalo, Ya Nura yace sutashi sutafi, amma kada su sake yawo da makami suna fad'in zasu kashe mutum, tuni suka cika wandonsu da iska sukayi waje. Abba yakama hannun Nuratu sukayi cikin gida, Ya Nura ma baikoma wajen Haby ba, dake can zaune tana kallonsu ta cika tayi fam, aganinta Ya Nura ya wula'kantata, akanme zai tafi wajen Nuratu yabarta, aganinta yabarta kawai su nakasata. Abba falonsa yawuce da ita, baki d'ayansu suka bishi, illa Khaleel daya nufi d'akinsa, domin yana da aikin yi, Abba ya zauna kan kujera Nuratu nakusa da 'kafarsa, Mama da Aunty ma kan kujera suka zauna, ya Nura shima 'kasa yazauna, domin girmama mahaifansa. Abba yace “Nuratu tawa, Nuratun Ammy”Nuratu tayi dariya tana fad'in “na'am Abba”Abba ya cigaba da fad'in “mai yasa kuka barta tafita adarannan?”Mama tace “nifa cewa tayi dani wajen Ammyn ta zataje, yau acan zata kwana”“to kuma sai kibarta tafita, kuma ita kad'aima awannan daren, yanzu da wani abu yafaru da itafa?”cewar Abba cikin fad'a, Mama tad'anyi murmushi “Allah dai yakiyaye Alhaji, amma kai kanka kasan halin Nuratu, idan taso abu kamar d'a yaso fitowa daga cikin mahaifiyarsa, to yakake so nayi da ita?”“babu yanda zakiyi da ita, amma dai kada kimance Nuratu marainiyace, kada ganin mahaifiyarta da kuke yasanya kumanta, kusan ri'kon maraya sai da ha'kuri, kuma gata yarinya 'karama, ni kuma dubata ko sunyi mata wani abu, domin hankalina bai kwantaba”“Nuratu ta, ko sunyi maki wani abune?”ya tambayi Nuratu, Nuratu tad'an tura baki cikin shagwa'ba “A'a Abba basuyimin komai ba, ai gudowa nayi kasan na iya gudu, kawai dai nad'an buge a'kafane kuma ya Nurane yabugamin takalminsa”tafad'a tana kallon Ya Nura da shima ita d'in yake kallo cike da mamaki da takaici, ya kuwa watsa mata harara mai d'auke da inkiyar zaki gane kurenka “to shikenan rabu dashi 'yar gidan Ammy, amma kidaina fita da dare, kuma kirage tsokana”“to Abba”tafad'a fuskarta d'auke da murmushi, “Abba kagafa hararata yake, dukana zaiyi Allah idan baka nan”ta sake fad'i, Abba yace “a'a kar naji kar nagani, laifin me tayi na duka, bafa nason doke dokennan, kaji ko?”“to Abba”ya Nura yafad'a kansa a'kasa. Nan kuma suka shiga wata hiran, har Nuratu tayi barci kanta nakan cinyar Abba, sai da kowa yatashi zai nufi d'akinsa, Abba yace ya Nura yad'au Nuratu yakaita d'akinsu, babu yanda ya iya akan dole ya d'auketa, akad'arsa yad'orata, ya nufi d'akinsu da ita, suna shiga d'akin nasu, ta sakar masa wata uwar tusa mai shegen wari dai-dai salansar hancinsa, ai kuwa ya Nura bai san sanda yasake taba, Allah yasa yaje dai-dai kangadon tafad'a kan gadon ruf da ciki, ya Nura yayi tsaki yafice da sauri, Nuratu tami'ke zaune tana dariya har da ri'ke ciki. ashe tun sanda yad'auketa tafarka amma tayi masa likimo.🤣😘❤ [01/12/2017, 15:16] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈QIYAYYA SA GANIN LAIFI🌈🌈🌈Book 1 mallaka.....QURRATUL-AYN 13 Tafiya yake cikin motarsa, yana tu'ki cikin kwarewa irin tasa, fuskarsa d'auke da murmushi, wanda da dukkan alamu na farin ciki ne, gefe guda kuma abokinsa Khamis ne yana ta danne-danne awayarsa can yad'ago yana duban Ya Nura “kai amma gaskiya Master natayaka murna wallahi, yanzu malesia ce kenemanka domin yi masu aiki tsawon shekaru bakwai?”“yes...nan da wata uku sukeson najema, domin da wata guda sukace, ni na nace akan subani wata uku”“to mudai fatan Alkhairi Allah yataimaka yasa aje lafiya adawo lafiya”“amin...”wayarsa dake hannun Khamis itace tayi 'kara, alamun tana neman agajin gaggawa, Ya Nura yace “d'aga mana” “a'a kadai d'aga master Abba ne”“ok”yafad'a yana kar'ban wayar, yakarata akunnansa, Abba ke fad'in “kana jina Nura?, kaje makarantar su Nuratu, uncle d'insu yakirani yana nemana, to nariga nashiga meeting ne yanzu, kaje kaji lafiya?”“to Abba babu damuwa, kahuta lafiya”Abba yakashe wayar, Ya Nura ya ajiye wayar, yana mai jan wani uban tsaki, Khamis yace “lafiya dai master?”“inafa lafiya?, yanzu haka waccan mai ba'kin kunnance tayi wani abu a school nasu,Abba yace inje inji komenene”“to maza mujuya ko? Allah yasa dai lafiya?”cewar Khamis, Ya Nura yayi guntun tsaki, yana dukaan sityarin motar, yajuya suka koma, domin da suna hanyar zuwa (gadon gaya ne, school d'in kuma kuntau take). zaune suke kan kujeru cikin office d'in principal a school d'in gefe guda kuma Nuratuce zaune, tare da wata yarinya kusan sa'ar Nuratun goshinta afashe and'aure da d'ankwalli sai jini duk yaji'ke d'an kwalin, sai kuma Uncle d'insu dake tsaye gefe guda, principal yaace yarinyar ta mai-maita abinda yahad'asu da Nuratu, cikin kuka tahau fad'in “wai akan jiya batayi note ba, to ni nayi shine tace in ara mata book d'ina, na aramata tayi shine naga ta yagamin, kuma ba'ayage nabataba, dan nace mai yasa ta yagamin shine tahauni da kokawa ta bugamin goshi abango, wai mai yasa zance ita tayagamin, tayaga inyi abinda zanyi”principal yace “to kaji dai, Nuratu bataji wallahi fitinarta tayi yawa, kusan kullum saimun kashe case nata, abunne yake yawa yasaka bama sanarwa mahaifinta, domin shi babban mutum ne kuma yana da daraja awajenmu”Ya Nura dai kasa cewa komai yayi sai Khamis ne ya ari bakinsa da fad'in “ayi dai ha'kuri yalla'bai, kunsan sha'anin yaro sai da ha'kuri, a gidama haka muke fama da ita, idan dukanne sai dai mugaji amma bata daina abinda tasaba, yanzu dai ga wannan awanke ciwon”Khamis ya d'auko wallet d'insa yazaro 5k (dubu biyar) yami'kawa principal, suka bawa yarinyarr ha'kuri tare da sallama suka fito, sai sannan Ya Nura ya dubi Nuratu yana fad'in, “zakizo kisame ni agida yarinya”suka fice. Kafin su'karasa inda sukai parking motarsu, Khamis ya dubi Ya Nura “wai ya dai naga kakasa cewa komaine?”“to mai zance Khamis, kasan idan dukan yarinyar nan zanyi, Allah sai inkasheta abaanza, inda zuciya takawomin wuya shiiyasa nayi shiru kawai, domin shirun shiyafi alkhairi”“to da babu ni kuma fa?”Ya Nura jin tambayar da Khamis yayi masa yasashi murmushi wanda iyakacinsa le'bansa, kafin yabashi amsa, sai ji yayi anrungumeshi ta bayansa, ya juyo dan ganin waye, Nuratu tayi maza ta zube 'kasa tari'ko hannunsa gam, tana fad'in “kayi ha'kurri ya Nura, nadaina bazan kuma ba, kada kadokeni dan Allah....”ri'kon da tayiwa hannunsa, da abinda yakeji na daban akanta, wanda ko Haby ce tari'ke bayajin hankan,yasanyashi janye hannunsa ahankali, jikinsa yaji ya mutu, amma mai makon yaji tausayinta saima tsanarta daya sake ji, wani mugun kallo ya watsa mata kafin yace “tashi kibani waje, kuma da kin dawo gida kije d'akina kisame ni, zaki gane kuranki yau” Nuratu tami'ke da sauri, ta murgud'a masa baki kafin ta juya tana 'ku'kuni. Ya Nura yabita da kallo kawai, yana tunanin abinda zaiyi mata, wanda zai saka ta nutsu, yarasama irin horon dazaiyiwa Nuratu, Khamis kuwa dariya yasa, har da ri'ke ciki, hakan yasanya ya Nura 'kara 'kulewa, ya wuce abinsa yashige mota, ganin da Khamis yayi ya Nura nashirin tafiya yabarshi, yasanyashi 'karasawa da sauri yashige motar, har lokacin bai daina dariyarba, sai da yayi mai isarsa, kafin yace “kayi ha'kurifa master Allah abubuwan yarinyar nan yana bani dariya da mamaki, har dai idan kuna wata dramar sai inji kamar inyi maku video”ya Nura yayi tsaki yana fad'in “da yake film muke ko? kaga bana son rashin mutumci wallahi”Khamis yasake dariya “dad'ina da kai d'aukan zafi, ko dayake aikai sojane, soja kuwa sai aslow, amma kana ganin yarinyar nan anya bata da aljannu?”ya Nura yayi tsaki, ganin da yayi Khamis nata 'kara masa 'bacin raine, yasa yayi shuru, bai sake tanka masaba, Khamis keta zubarsa shi kad'ai, domin mutum neshi mai surutu, har suka isa inda suka nufa, ya Nura bai cemasa komaiba shi adole yaji haushi. WEEKEND 8:00Am kwance yake kan doguwar kujera, da dukkan alamuma barci yakeyi, sanye yake da farar best da gajeran wanda wanda iya kacinsa gwiwarsa shima farine, dake shi dogone amma ba canba 'kafafuwansa, har sund'an haura kujerar, kansa kuma nakan hannun kujerar yasanya pillow, fuskarsa watsai, ma'abocin kyawun fuskane doguwa tana tafene da tsayin jikinsa, ba siriribane amma bazaka kirashi mai 'kiba ba, ga wani saje dayayi 'kawanya afuskarsa ba'ki wuluk, sai siririn hancinsa dake 'karawa fuskarsa kyau, bashi da manyan idanuwa amma kuma ba 'kananu bane gasu farare tas, ba'kin ciki kuwa har yafi sumarsa ba'ki, kannan nasa masha Allah gashin kan akwance luf, kai kace yana shampoo ne, sai zara zaran gashin gira dana idanu dake 'kara fito da tsan-tsan kyawunsa, gashin giransa harya kusa had'ewama, sannan ma'abocin dogwayen yatsune fes dasu abin sha'awa, ma'abocin faffad'an 'kirjine da gashi yakwanta luff ba'ki dashi. A gaskiya dai duk inda namiji kyakykyawa mai jini ajika yakai to ya Nura yakai, domin irin mazan nanne da kowacce mace zataso ace yazama maallakinta, kuma tayi tin'kaho da nunashi aduniya matsayin mijinta. “Innalillihi wa'inna ilahi razi'un”cewar Nuratu, tana mai mi'kewa daga kwanciyar datayi kan gado, baki d'aya Nana da Rahma suka dubeta da fad'in “lafiya ”“dan Allah kuzo kurakani wajen ya Nura wallahi namance yace inje, nashiga uku”tafad'a tana zaro ido game da dafe 'kirji, suka sanya dariya “a'a kije babu ruwanmu, salan muje ya had'a damu”cewar Nana, Nuratu ta girgiza kai tare da kwafa, tafice da sauri daga d'akin “A'a Nuratun Ammy ina zuwa kuma yanzu?”cewar Khaleel daya gamu da ita aharaban gidan tana sauri, “d'akin Ya Nura zanje yace inje, na mance sai yanzu natuna, dan Allah kad'an rakani kada ya dake ni”tafad'a tana lankwa'be kai,“wuce kije abinki babu abinda zauyi miki, indai kin bashi ha'kuri, kuma saura ki murgud'a masa bakin”Nuratu tad'an harareshi tare da murgud'a masa bakin tawuce, Khaleel yayi dariya yana fad'in “Nuratu kenan, anriga ansaba da wannan murgud'a bakin, naga ranar dainawa”,ya fad'a yana mai wucewa zuwa cikin gidan. A hankali tamurd'a 'kofar d'akin takuwa jita abud'e, ta tura tashiga tana sand'a kamar mai shirin kama 'barawo, d'akin sai buga 'kamshi yake, ga wani sanyi mai dad'i dake ratsa jikin mutum, Nuratu ta'karasa cikin d'akin taje dai-dai kujerar dayake kwance ta tsuguna tana fad'in “gani ya Nura” tayi furucin can 'kasan ma'koshi, yajita bai jitaba oho, illa dai ko motsi baiyiba, ita kuwa ta gyara zama abinta, tayi ta gumi tana dubansa, tsoro take kada ta kuma magana yatashi ya rufeta da duka, hakan yasaka kawai tazauna tana dubansa, sai da ta'kare masa kallo daga sama har 'kasa, sannan tayi tsaki tana fad'in “mugu kawai, abu bakyauba sai mugunta” ganin da tayi yamotsa ya juyo da fuskarsa gabanta yasanyata rufe baki tami'ke da sauri, tunaninta tashi zaiyi, sai kuma taga idanuwansa arufe, hakan yasaka tasaki wata ajiyar zuciya, jitayi ana turo 'kofa alamun za'ashigo, sanin da tayi batasan waye zai shigoba, kuma ta fahimci barci yake, tana tsoron ya farka ya ganta, yasa ta gudu bayan kujerar dake gefansa mai zaman mutum biyu ta'buya. Haby ce taturo 'kofa tashigo, taci wani uban make-up, gawani takalmi mai shegen tsini kamar idan tataka zai iya karyewa, kara sowa tayi cikin takun 'kasaita tazo dai-dai kan kujerar dake kwance ta zauna, tana shafa sajen fuskarsa, jin da yayi and'an matseshi sannan ana ta'bashi yasashi bud'e ida nuwansa tar akan Haby, ajiyar zuciya yayi yatashi zaune yana dubanta, hannunsa takamo tasanya anata cike da shagwa'ba take fad'in “haba My...laifin me nayi maka ne? tun randa katashi kabarni acikin gaiden baka kuma bi takainaba, babu kira babu nema haba dan Allah”tahau sharar hawayen 'karya, Ya Nura ya dubeta “ke dai zan tambaya da kika d'au fushi dani”“haba dai kawai nidai naji haushine naga kafi bawa waccan kwailaar muhimmanci akaina”tafad'a tana mai zama kan cinyarsa, Nuratu dake bayan kujera tana kallon abinda sukeyi ta zaro ido, Ya Nura zaiyi magana tarufe masa baki da tafin hannunta, takai bakinta saitin nasa da zummar yi masa kiss, ai kuwa Nuratu ta kwala ihu da fad'in “innalillahi wa'inna ilahi razi'un ya Nuraaa...!”tafice da gudu kafinma yayi 'ko'karin kamata. Da sauri suka mi'ke baki d'aya, Ya Nura yakoma yazauna yari'ke kansa, Haby tadawo daga kallon 'kofar da nuratu tafita zuwa kansa, tayi tsaki tana fad'in “ni wallahi natsani ba'kar yarinyarnan Allah jibafa abinda tayi mana muna cikin soyayyarmu, gaskiya kad'auko mataki akanta”ya Nura yad'ago idanuwansa yana dubanta, sai da ta tsorota ita kanta da yanda kalar idanuwansa suka canja daga fari zuwa ja, cikin d'aga murya da tsawa yake fad'in “gate out in my side Habiba”ta tsaya tana kallonsa da mamaki, cikin 'bacin rai yasake d'aga murya yana nuna mata hanyar fita “gate out nace da ke”Haby na'barin jiki, tad'au takalminta ahannu tafice daga d'akin, Ya Nura yakoma yazauna, ya dafe kansa dake sara masa yana fad'in “duk ke kika jamin Haby, mai yasa bana iya hanaki aikata komai akainane?, bayan hakan ba halina bane”sai kuma yahau tunanin yanda akaima Nuratu tashigo masa d'aki bai saniba, “anya kuwa bata da aljannu kamar yanda Khamis yafad'a”ya tambayi kansa, sai kuma yayi saurin kau da zancen da fad'in “no...tsabar iskanci ne kawai, da raina mutune da tayi”yayi maganar afili, mi'kewa yayi yafito zuwa cikin gida, domin jikinsa nabashi Nuratu nacan nashirya masa wata tsiyar. Nuratu kuwa nashiga gida da gudunta, ta gamu da Aunty a tsakar gida zata shiga kitchen, tana haki takama fad'in “Aunty kin kuwa san mai Ya Nura yayi yau tab....!”“ke...yimin shiru bana son shirman zancenki mara kan gado, wuce kiban waje ” Nuratu ta zunguri baki tawuce tana fad'in “ita Aunty komai sai tayiwa mutum fad'a, baza'a fad'i laifin Ya Nura ba”“ehh ni bana son ji”Aunty tafad'a tana wucewa kitchen, Nuratu tanufi falo tana fad'in “bari ni insanarwa Mama nasan sai tayi masa fad'a wallahi”tashiga falon tana kwalawa Mama kira [02/12/2017, 16:51] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈QIYAYYA SA GANIN LAIFI🌈🌈🌈Book 1 mallaka....QURRATUL-AYN 14 sai kuma yahau tunanin yanda akaima Nuratu tashigo masa d'aki bai saniba, “anya kuwa bata da aljannu kamar yanda Khamis yafad'a”ya tambayi kansa, sai kuma yayi saurin kau da zancen da fad'in “no...tsabar iskanci ne kawai, da raina mutune da tayi”yayi maganar afili, mi'kewa yayi yafito zuwa cikin gida, domin jikinsa nabashi Nuratu nacan nashirya masa wata tsiyar. Nuratu kuwa nashiga gida da gudunta, ta gamu da Aunty a tsakar gida zata shiga kitchen, tana haki takama fad'in “Aunty kin kuwa san mai Ya Nura yayi yau tab....!”“ke...yimin shiru bana son shirman zancenki mara kan gado, wuce kiban waje ” Nuratu ta zunguri baki tawuce tana fad'in “ita Aunty komai sai tayiwa mutum fad'a, baza'a fad'i laifin Ya Nura ba”“ehh ni bana son ji”Aunty tafad'a tana wucewa kitchen, Nuratu tanufi falo tana fad'in “bari ni insanarwa Mama nasan sai tayi masa fad'a wallahi”tashiga falon tana kwalawa Mama kira, tana shiga falon taga Mama bata nan, sai Hilal da Rahma dake zaune gaban tv suna game, gefe guda kuma Nana ce kecin abinci, bata kulasuba tawuce abinta duk da kiran da Nana kemata, d'akin Mama ta nufa, tana zuwa tatura 'kofar da sallama. Mama dake zaune tana duba wasu kaya nata, ta amsa mata sallamar da fara'a, Nuratu ta'karasa tazauna gefanta tayi tagumi tayi shiru, Mama tace “lafiya dai Nuratu kike ta gumi haka?” Nuratu tad'an ta'be baki, tare da ajiyar zuciya, kamar wata babba tana fad'in “Mama kin kuwa san abinda yafaru? kinsan abinda ya Nura ya aikata...?”sai kuma tayi shiru, Mama cikin fargaba tace “fad'amin mai kuma ya faru? ”“Mama ganinsa nayifa, tare da Aunty Haby, ta zauna akan 'kafarsa ta......”kafin ta'karasa aka turo 'kofa da 'karfi, hakan yasaka Nuratu mi'kewa da gudu tahau kan gado ta'boye bayan Mama. ko lura da Mama ya Nura baiyiba tsabar 'bacin rai yanufi Nuratu zai kamota, jin muryar Mama yayi nafad'in “kada ka fara”ya Nura yatsaya ya dawo da dubansa wajen Mama, kallon da Mama ke watsa masa shine yasanya jikinsa yin sanyi, Mama ta dubi Nuratu “tashi kifita”Nuratu ta'kara 'kan'kame Mama abayanta tana fad'in “Allah dukana zaiyi Mama”“jeki abinki, babu abinda zaiyi miki kinji, ai gani azaune”tafad'a tana jawo Nuratu daga bayanta taturata hanyar fita, Ya Nura yawatsa mata wani irin mugun kallo, hakan yasa Nuratu ficewa aguje. Mama ta dubi Ya Nura, ya Nura yayi 'kasa da kansa Mama tasoma magana da fad'in “kaji tsoron Allah Nura, kada kamance Allah na duban bawa da dukkan abinda yake aikatawa, sabida tsabar abin naka yabun'kasa, agaban wannan 'kanwarkama yi kake wai kai d'an zamani ko?”“A'a Mama wallahi ba haka bane nidai bana aikata abinda kike tunani akaina Allah, kidaina yarda da maganar Nuratu”Mama tayi ajiyar zuciya “bawai ina zarginka bane Nura, kasan nafikowa sanin kai waye da sanin halinka, kawai dai ina fad'ane kaji tsoron Allah aduk inda kake, sannan idan auren kake so yanzu saika sanar da Abbanka, ahuta ai daman ina lura da kai kwanakin nan kanka rawa yake sosai”ya Nura yad'an sosa sumarsa“Allah Mama ba haka bane, nibansan ya akaima Nuratu tashiga d'akinaba”Mama harara ta watsa masa, kafin tace “nidai zansanar da Abbanka kawai ayi biki katafi da matarka can malesian ku 'karata, sannan na fahimci baka addu'o'i ko? azkar d'innan da karatun al'kur'ani duk kawatsar”ya Nura yayi murmushi “ana 'ko'karin yi Mama”Mama tad'auke kanta daga kallon Ya Nura domin tausayi yake bata ayanzu, tasan cewa angama cutarsa 'karshe, domin kuwa Haby ba matar aure bace, mace babu tarbiya, babu ilmin addini, bokonma ya aka 'kare, ita dai kawai angama da ita da d'anta, afili kuwa murmushi tayi da fad'in “to dai 'kara daurewa sosai kaji, domin rayuwarnan kana addu'ama yaka 'kare, bare kuma mutum bayayi”“insha Allahu Mama zandage, sannan kada kimance dayiwa Abba zancen bikin”yafad'a yana ficewa da sauri, waishi a dole kunya, Mama sakar baki tayi ta bishi da kallo kawai, tana girgiza kai tare da fad'in “d'an yau kenan”. Nuratu na fita, bata tsaya falonba ta fice zuwa gidansu wajen Ammynta, domin tsoro take kada ya Nura ya fito ya tad da ita. Da shigarta gidan, kai tsaye kitchen ta nufa, mai zatayi oho, sai fitowa tayi da gudu tana kiran Ammy, idanunta arufe, Ammy ta fito da sauri tana fad'in “lafiya kikemin wannan kira haka,mai makon sallama”turus Ammy taja ta tsaya ganin Nuratu tayi jikinta duk yaji, takamo hannunta takarkad'e mata yajin tana fad'in “haba Nuratu, mai ya kaiki kitchen yanzu, har kika 'baro da wannan uban yaji, rabin kwano nefa, na bayar aka dakomin d'azu aka kawoshi”“Ammy flat fa naje d'aukowa abinci zanci”Ammy ta doke mata baki, “anan flat d'in suke, inda na ajiye yajin ina duk kayan dake-dake nane agun, kice dai kinje fitinar taki baki samuba shine kikazo kikayi awajena ko?”“A'a Ammy wallahi bansan yaji bane”Ammy ta cikata tsabar takaici ta nufi kitchen taga yanda yajin yayi, ta tadda dashi baza-baza, babuma halin kwashewa, babu inda yajin bai shigaba a kitchen d'in, Ammy tama rasa mai zatace da Nuratu. komawa d'aki tayi tabarta tsaye atsakar gidan tana ihun yaji, Ammy tayi banza da ita, da ta gaji da ihunta ta cire kayanta atsakar gidan taje ta tara jikinta a famfo, sai sa tagaji dan kanta takashe famfon tashiga d'aki tasanyo wasu kayan, lokacin duka jikinta yahau rad'ad'in dayafi na da ma, nan tasaka Ammy gaba taci kukanta ta'koshi, wuni guda babu inda taje, abinka da faarar fata kuma babu kwari, nan da nan jikin yayi jajur, yayi rud'u rud'u, amma kokad'an Ammy bata tausaya mataba, sai ma cewa da tayi tagama kukan taje ta gyara mata kitchen d'inta, nanfa Nuratu ido ya raina fata, tazaro idanuwa waje😳🤣 [29/12/2017, 11:27] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 🌈🌈🌈《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》🌈🌈🌈Book 1 MALLAKA__QURRATUL_AYN 15 。。。。。。。。。。。。。。。。。。。。。。。。。。。 (Am sorry masoyana kunjini shiru, hakan yafaru ne sanadiyyar rashin lfy data kamani, amma yanzu alhmdlh, insha Allah zaku dinga jina any time indai bada wani uzuriba, sannan duk mai so 4rm begining yayiwa admin group nasu magana dan Allah ko kuma wanda yake dashi a grp yataimaka ya tura idan ana nema, nagode sosai masoyana Allah yabar zumunci da kauna, naga call &message naku ina qara godiya sosai espicially HAFSAT XOXO godiyata bazata yankeba agareki ngd da kauna😍😘) *** *** *** Ganin da Nuratu tayi Ammy tashiga bedroom nata hakan yabata damar mi'kewa tafice daga gidan, tana kuka, kai tsaye gidansu Nana ta nufa, da shigarta bata tsaya ko inaba sai falon Mama tayi sa'a tana shiga Mama nazaune falo tana kallon tashar arewa 24, da gudunta tafad'a kancinyar Mama tana kuka, Mama tad'agota da sauri tana fad'in "lafiya kuwa Nuratu"?,ganin da tayiwa jikin Nuratu yayi rud'u_rud'u shine ya tsorata tahau fad'in "menene yasamu jikinki Nuratu, lafiya kuwa?" cikin kuka Nuratu tahau fad'in "yajine yazubomin bansaniba Mama, shine Ammy tace sai na gyara mata kitchen d'inta kuma ni ban iyaba" Mama tad'anyi murmushi kawai, domin tasan fad'ar Nuratuce kawai, wannan zancen ba gaskiya bane, Mama tajawota jikinta tana rarrashinta, taji jikinta yad'au zafi sosai, har tafara tsumar sanyi, Mama taja hannunta zuwa d'akinsu, takwantar da ita kan gado, tarufeta da bargo, sannan tafito tana mai janyo 'kofar d'akin, tadawo falo, tad'auki wayarta tana neman number Khaleel yazo ya dubata, yaga abinda yake damunta. Ko da Ammy tafito falo, ta tarad babu Nuratu, murmushi tayi aranta, domin tasan antafi kaita 'karane. Khaleel na zuwa aunata yayi, yafahimci fever ne ajikinta kawai, sanadiyyar wankan da tayi a famfo yajamata hakan, magunguna yaje yasiyomata, da lallashi da komi sannan aka samu Nuratu tad'ansha maganin, domin aduniya magani yana d'aya daga cikin abinda Nuratu ta tsana arayuwarta. sai da Nuratu tayi kwana biyu akwance kafin ta war_ware, cikin kwanakin kuwa, kowa hidima yake da Nuratu, kai kace ita kad'aice d'iya a family d'in, kowa Nuratu, amma banda Ya Nura, dominshi ko zancenta bayayi, bare kuma yaje yayi mata sannu, domin aganinsa babu wani ciwo da take kawai freetndeng ne irin nata, domin ta ta'bayin hakan, tayi 'karyar ciwon ciki, ta tsorata kowa a gidan, 'karshe tami'ke tana yimasu dariya, ai kuwa sai da Ya Nura ya zaneta sosai. 。。。 。。。 。。。 。。。 Ansanya bikin Ya Nura da Haby sati hudu masu zuwa, kenan ana kammala bikin da sati biyu zasu d'aga zuwa malesia, kowa cike yake da murna a gidan, musamman su Nuratu manya wanda yake takura masu zai tafi, sunfi kowa murna aganinsu. wani had'add'an falone, dayasha kayan alatu kala_kala na more rayuwa, kai da ganin falon kasan ba'karamin 'barnatar da naira akaiba domin 'kawata falon, ga wasu had'add'un manya_manyan kujeru dake gewaye cikin falon, wani kyakykyawan matashin saurayine zaune a d'aya daga cikin kujerun, dagashi sai best da wani guntun gajeran wando, yana zu'kar shisha cikin 'kwarewa irin tasa, gefe guda kuma Haby ce kwance bisa cinyarsa daga ita sai wasu lalatattun kaya ajikinta wanda dasu da babu duk d'aya, mi'kewa tayi zaune ta kar'bi shisha daga hanun saurayin, tasanyata abakinta tayi mata wata muguwar zu'ka ta fesar da haya'kin tana mai fad'in "haba Nabeel, mene abin tashin hankali akan wannan maganar, yin aurena ba shine zai rabamuba, haka zalika tafiyata malesia bazai rabamuba to mene abin saka damuwa arai kuma?". Nabeel yayiwa Haby wani irin kallo wanda ita kad'ai tasan ma'anarsa, ya furzar da wata iska mai zafi kafin yace ‘’tunaninki rabuwa dake shine damuwata?‘’ yayi murmushin da baikai cikiba, ya dubeta yakai hannu bisa fuskarta yad'an shafeta yana duban 'kwayar idanunta yace "da muwata itace zakiyi tarayya da wani 'kato baniba, kinsan ina kishinki sosai Baby na inasonki sosai, domin ke ta dabance, ke kanki kinsan hakan" Haby tayi murmushi, wani dad'i na ratsata saboda jin kalaminsa agareta, tad'anyi dariya tana fad'in "wai shin ma kasan dalilin da yasa zanyi auren nan, ko kuwa kasan ummul'aba'isin yin auren?" Nabeel bai ce komaiba dubanta kawai yake yana girgiza kai, alamum a'a, Haby tami'ke tayi taku biyu zuwa uku agabansa cike da kwarkwasa, tad'an sunkuyo da fuskarta dai_dai fuskarsa, har nimfashin su yana had'uwa ta furta "sabida kai zanyi auren nan NB nawa...!" [29/12/2017, 11:51] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》Book 1 MALLAKA__QURRATUL_AYN 15 (Am sorry masoyana kunjini shiru, hakan yafaru ne sanadiyyar rashin lfy data kamani, amma yanzu alhmdlh, insha Allah zaku dinga jina any time indai bada wani uzuriba, sannan duk mai so 4rm begining yayiwa admin group nasu magana dan Allah ko kuma wanda yake dashi a grp yataimaka ya tura idan ana nema, nagode sosai masoyana Allah yabar zumunci da kauna, naga call &message naku ina qara godiya sosai espicially HAFSAT XOXO godiyata bazata yankeba agareki ngd da kauna) *** *** *** Ganin da Nuratu tayi Ammy tashiga bedroom nata hakan yabata damar mi'kewa tafice daga gidan, tana kuka, kai tsaye gidansu Nana ta nufa, da shigarta bata tsaya ko inaba sai falon Mama tayi sa'a tana shiga Mama nazaune falo tana kallon tashar arewa 24, da gudunta tafad'a kancinyar Mama tana kuka, Mama tad'agota da sauri tana fad'in "lafiya kuwa Nuratu"?,ganin da tayiwa jikin Nuratu yayi rud'u_rud'u shine ya tsorata tahau fad'in "menene yasamu jikinki Nuratu, lafiya kuwa?" cikin kuka Nuratu tahau fad'in "yajine yazubomin bansaniba Mama, shine Ammy tace sai na gyara mata kitchen d'inta kuma ni ban iyaba" Mama tad'anyi murmushi kawai, domin tasan fad'ar Nuratuce kawai, wannan zancen ba gaskiya bane, Mama tajawota jikinta tana rarrashinta, taji jikinta yad'au zafi sosai, har tafara tsumar sanyi, Mama taja hannunta zuwa d'akinsu, takwantar da ita kan gado, tarufeta da bargo, sannan tafito tana mai janyo 'kofar d'akin, tadawo falo, tad'auki wayarta tana neman number Khaleel yazo ya dubata, yaga abinda yake damunta. Ko da Ammy tafito falo, ta tarad babu Nuratu, murmushi tayi aranta, domin tasan antafi kaita 'karane. Khaleel na zuwa aunata yayi, yafahimci fever ne ajikinta kawai, sanadiyyar wankan da tayi a famfo yajamata hakan, magunguna yaje yasiyomata, da lallashi da komi sannan aka samu Nuratu tad'ansha maganin, domin aduniya magani yana d'aya daga cikin abinda Nuratu ta tsana arayuwarta. sai da Nuratu tayi kwana biyu akwance kafin ta war_ware, cikin kwanakin kuwa, kowa hidima yake da Nuratu, kai kace ita kad'aice d'iya a family d'in, kowa Nuratu, amma banda Ya Nura, dominshi ko zancenta bayayi, bare kuma yaje yayi mata sannu, domin aganinsa babu wani ciwo da take kawai freetndeng ne irin nata, domin ta ta'bayin hakan, tayi 'karyar ciwon ciki, ta tsorata kowa a gidan, 'karshe tami'ke tana yimasu dariya, ai kuwa sai da Ya Nura ya zaneta sosai. *** *** *** Ansanya bikin Ya Nura da Haby sati hudu masu zuwa, kenan ana kammala bikin da sati biyu zasu d'aga zuwa malesia, kowa cike yake da murna a gidan, musamman su Nuratu manya wanda yake takura masu zai tafi, sunfi kowa murna aganinsu. wani had'add'an falone, dayasha kayan alatu kala_kala na more rayuwa, kai da ganin falon kasan ba'karamin 'barnatar da naira akaiba domin 'kawata falon, ga wasu had'add'un manya_manyan kujeru dake gewaye cikin falon, wani kyakykyawan matashin saurayine zaune a d'aya daga cikin kujerun, dagashi sai best da wani guntun gajeran wando, yana zu'kar shisha cikin 'kwarewa irin tasa, gefe guda kuma Haby ce kwance bisa cinyarsa daga ita sai wasu lalatattun kaya ajikinta wanda dasu da babu duk d'aya, mi'kewa tayi zaune ta kar'bi shisha daga hanun saurayin, tasanyata abakinta tayi mata wata muguwar zu'ka ta fesar da haya'kin tana mai fad'in "haba Nabeel, mene abin tashin hankali akan wannan maganar, yin aurena ba shine zai rabamuba, haka zalika tafiyata malesia bazai rabamuba to mene abin saka damuwa arai kuma?". Nabeel yayiwa Haby wani irin kallo wanda ita kad'ai tasan ma'anarsa, ya furzar da wata iska mai zafi kafin yace ‘’tunaninki rabuwa dake shine damuwata?‘’ yayi murmushin da baikai cikiba, ya dubeta yakai hannu bisa fuskarta yad'an shafeta yana duban 'kwayar idanunta yace "da muwata itace zakiyi tarayya da wani 'kato baniba, kinsan ina kishinki sosai Baby na inasonki sosai, domin ke ta dabance, ke kanki kinsan hakan" Haby tayi murmushi, wani dad'i na ratsata saboda jin kalaminsa agareta, tad'anyi dariya tana fad'in "wai shin ma kasan dalilin da yasa zanyi auren nan, ko kuwa kasan ummul'aba'isin yin auren?" Nabeel bai ce komaiba dubanta kawai yake yana girgiza kai, alamum a'a, Haby tami'ke tayi taku biyu zuwa uku agabansa cike da kwarkwasa, tad'an sunkuyo da fuskarta dai_dai fuskarsa, har nimfashin su yana had'uwa ta furta "sabida kai zanyi auren nan NB nawa...!" [29/12/2017, 23:53] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book 1 mallaka_QURRATUL_AYN 16 Haby ta cigaba da fad'in "zanyi aure dominka ne NB, domin 'karuwar muce, zakayi ar'zi'ki sosai da Nura, domin ahankali saina kwashe dukiyarkisa, inkawo maka sannan mukashe banza, muzo muyi aurenmu, wannan sirrin ko momy na batasan da shiba, domin itama burinta kawai dukiyar, sabida idan nabawa momy dukiyar dole sai yanda tayi damu, amma idan tana hannunmu fa?" ta 'karashe maganar tana d'agawa Nbeel gira, Nabeel yayi wani shu'umin murmushi yajawota zuwa jikinta, nanfa salon yacanja xxx (Allah ka tsaremu da aikin dana sani amin). ****** BAYAN SATI 'DAYA***** Mama ce tare da kishiyoyinta, Aunty da Momyn su Haby,sai Ammy tattaunawa suke agame da auren ya Nura da Haby, Nana tayi sallama tashigo zuwa falon, tana d'ingisa 'kafarta, domin yanzu 'kafarta d'aya tad'an nakasa, tun fad'owar da tayi daga saman bishiya, Ammy tad'anyi tsaki data dubi Nana, Mama tace "lafiya kuwa Ammyn Nuratu" Ammy tayi ajiyar zuciya gami da fad'in "a kullum na kalli Nana tausayi take bani wallahi, rashin jin Nuratu baiyiba arayuwa wallahi, haka kawai tajawa yarinya nakasa" Mama murmushi tayi "ki daina fad'in haka Ammy, dama can haka Allah ya'kaddarowa Nana zai faru da ita, ki daina zargin Nuratu akan hakan" Aunty tace "ai daman koba Nuratuba, idan Allah yayi hakan zai faru sai yafaru, dan Allah kidaina saka damuwar Nuratu aranki Ammy" Momy tace "gaskiya kika fad'a Aunty komai ai na Allah" nan kuma suka sauya hiran zuwa shirye shiryen bikin da za'a ga batar nan da sati uku masu zuwa. komai suna gudanar dashi tare, Momyn Haby bata ware kantaba, ta saki jiki dasu sosai kamar babu komai aranta suma su Mama haka. "Ango, ango, ango manya" cewar Khamis kenan dake zaune saman kujera yayin da Ya Nura ya kammala waya da gimbiya amaryarsa, ya dawo da dubansa kan Khamis da fad'in "to yaranka?, kai dai kazauna amatsayin tuzurunka, yanzu mune manyanka" Khamis yasanya dariya sosai yana fad'in "to mene a ciki, nudai haryanzu, banga mata taba" ya Nura harara ya watsa masa da fad'in "ai bazaka ta'ba ganin taba, zauna dai sai dai kaji ana kiranmu Abba, kai kuwa sai dai kawu" wannan karon dariya suka saka baki d'ayansu, Khamis yakau da zancen da fad'in "yauwa wai me da me gimbiyar taka tashiryane, haryanzu bata fad'a maka abinda za'a bata ba?" "ehh bata sanarminba tukunna tadaice 'kawayenta zasuzo suyi maganar abinda za'a basu, ita kuma zata sanarmin wanda zatayi anfani dashi, idan tadawo daga school zata fad'i nawa zanbata" Khamis yace "ai gara ayi shirye_shiryen tun da wuri domin rawar kan naku tayi yawa da kai da ita" Ya Nura yajawo pillown kujera ya jefi Khamis da shi yana dariya su Nuratu ne zaune cikin harabar gidan suna wasa, kusa da d'akin ya Nura, lilo sukeyi abinsu, basajin dukkan abinda akeyi ma, Ya Khaleel ne yazo yazauna a d'aya daga cikin fararen kujerun dake wajen, yana kallon dukkan shirmensu, basu lura da shiba sai can suka kula da mutum awajen, ganin Khaleel ne yasaka suka bar yin lilon, suka nufi inda Khaleel yake zaune suna fad'in "ya Khaleel yaushe kazo kazauna anan?" suka kewayeshi kowa da abunda yake fad'i, yana basu amsa dai-dai da abinda kowannensu ya tambaya, cikin nishad'i, da kaunar yaran da yakeji aransa, domin shi Khaleel ko kusa bai d'au duniya da zafiba, kai kace ba yayan Haby bane, baki d'ayan rayuwarsa ta ban-banta da tasu, halinsa kamar Ammy ce ta haifeshi. 'karar bud'e 'kofar d'akin ya Nura da suka jine yasanyasu juyawa baki d'ayansu, sanye yake da t.shert da jeans masu ratsi tamkar kayan sojoji, sumar kannan nasa kwance kamar wanda yakeyi mata relaxer sai 'kyalli take ba'ka wuluk, sai sajensa daya kewaye doguwar fuskarsa, takalminsa ba'kine sau ciki, a ta'kaice dai Ya Nura ya had'u, dukansu sakar baki sukai suna dubansa, har shi kansa uban gaiyar Khaleel, ya Nura yayi gyaran murya gami da d'a gira yana fad'in "wannan kallonfa?" Khaleel yayi murmushi yana fad'in "kayi kyau ne sosai broda" "nagode" ya Nura yacewa Khaleel, suma su Hilal haka suka hau fad'in "gaskiya kayi kyau Yaya" bai kulasu ba, Nuratu kuwa murgud'a baki tayi, ta bishi da harara, amma mai makon yayi fushi, sai kawai ya girgiza kai yawuce, ya nufi parking space, yashiga motarsa ya tayar, gateman ya bud'e gate yafice abinsa. Khaleel ya dawo da dubansa kansu Nuratu, yana mai mi'kewa tsaye yake fad'in "kuyi wasanku ko, ni zanshiga ciki ina da wani aikine" bai jira surutunsu na shirmeba yawuce yabarsu. Nan suka hau wasan guje-guje, Hilal bai saniba ya daki 'kofar d'akin ya Nura ta bud'e, nanfa suka saki baki suna mamakin yanda akai ta'bud'e, basu san cewa mancewa yayiba yana sauri, ai kuwa Nuratu tace su shiga suga abunda yake d'akin, babu musu suka bi bayanta, cikin sand'a suka shiga kamar wasu 'barayi, nanfa suka hau aiki, subud'e nan su rufe nan har cikin bedroom nasa, Nuratu da Rahma toilet suka nufa ta kunna shower wai wanka zasuyi, Nana da Hilal a d'akin suka zauna sunayimasa ta'be ta'be son ranau, sunma mance a cikin d'akin wanda suke. 'karar hon d'in da sukajiyone, da kuma bud'e gate yasanyasu fitowa a guje, suka nufi cikin gida, sai kuma sukaga ba shi bane Hamza ne mijin Aunty Hafsa, hakan yasaka suka mance da batun zuwansu d'akin ya Nura. suka hau tsallen murnar zuwansa, nanfa suka kafe sudai yatafi dasu wajen auntyn su, kan dole Mama tabasu 1set na kayansu, cike da murna suka ruga zuwa gate, suka shige cikin mota, sai da yagama abinda yake, kafin yafito su tafi. suna son zuwa gidan Aunty Hafsat ne, domin gidanta babu takura, daga ita har mijinta babu mai takura musu, sunayin abinda sukeso da wanda suka ga dama, domin Aunty Hafsa babu ruwanta kan hantarar yaro da takura masa, hakama mijin nata. suna tafe a mota suna hiransu, yana biye masu, har suka isa gidan su dake 'Dorayi, yana parking motarsa suka fito da gudu zuwa cikin gidan, lokacin Aunty Hafsa na kitchen tana shiryawa mijinta abinci, sai jitayi kawai an rungume 'kafafuwanta ana ihun kiran sunanta, da sauri ta juto ta sunya zuwa garesu tana fad'in "a'a iyalan Mama, saukar yaushe, waye yakawomin ku zuwan bazata?" sai kuma taga mijinta tsaye bakin 'kofa yana murmushi, itama murmushin tayi tana fad'in "sannu da zuwa amma gaskiya ka shammacenifa, wannan bazata haka" murmushi yayi, kawai ya juya zuwa falo, ita falon ta nufa tare dasu Nuratu, suka zube gaban tv suka hau aikin game, ita kuwa Aunty Hafsa d'akin mijinta ta nufa domin yimasa sannu. ya Nura kuwa bashi yadawoba sai bayan sallar isha'i, yadawo agajiye, ya sanya key domin bud'e d'akin yajishi a bud'e, ya cika da mamaki, yana tunanin ya akai hakan tafaru, sai kuma ya tuna mancewa yayi, yana sauri. yana shiga falon ya gunna globe haske ya gauraye falon, yafad'a saman kujera abinsa sabida gajiya, 'karar ruwan daya jiyone yasanyaahi mi'kewa da sauri ya nufi bedroom d'insa, yana sanya 'kafa yaji laima a 'kafarsa, har ruwa nad'an bullowa daga cikin capet d'in, da gudu ya 'karasa toilet d'in ganin shower da famfo yayi nata zuba, toilet d'in ya cika da ruwa, yanata mala lowa zuwa cikin d'akin, da kudu yaje ya kashe ya dawo falo yana tunanin yanda hakan ta faru, yasan dai shi yamance 'kofa a bud'e amma komai na amfani a d'akin akashe yake, nan tunaninsa yabashi may be aikin su Nuratu ne, da sauri yami'ke ya fito zuwa cikin gidan 'kafarsa ko takalmi babu yana kwalawa mama kira [30/12/2017, 20:47] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book 1 mallaka------QURRATUL-AYN 17 Ko da yashiga falo Mama batanan, hakan yasanyashi nufar d'akin Aunty, da sallamarsa ya shiga tana zaune da waya a hannunta, da dukkan alamu waya ta kammala. Ya Nura ya dubeta da fad'in "wai ina Mama tashigane?" "tana d'akin Abbanku" Aunty ta bashi amsa, Ya Nura yaja wani d'an guntun tsaki, Aunty tace "wai lafiya kuwa Nura" Ya Nura yakalli Aunty kafin yamai da kallonsa zuwa wani wajen yana fad'in "to mema zance Aunty, dawowata kenan na tadda bedroom zuwa toilet cike da ruwa" "subhanallah, garin yaya?" "wallahi bansaniba, abinda nasani kawai da zanfita ina sauri namance 'kofa a bud'e, ban rufeba kuma su Nana nabari awajen suna wasa" Aunty tad'anyi shiru, kafin tace "kana ganin anya ba yarane suka shigaba, nasan fitinarsu yawa gareta" "ai sud'innema Aunty domin famfo da shower duka kunne nagansu, wai ma ina suke Aunty?" "ai basanan sunje gidan Hafsatu, amma nima zan iya cewa sud'inne domin nagansu sunshigo aguje kuma Rahma da Nuratu jikinsu aji'ke da ruwa" Ya Nura ya gyad'a kawai tare da fad'in "zasu dawo su sameni ai" yayiwa Aunty sallama ya koma d'akinsa, a falo yakwanta har barci yad'aukeshi, yana tunanin abinda zaiyi masu yawuce. Su Nuratu kuwa ana gidan Aunty anayin abinda aka saba, da gari ya waye tun da asuba sukahau rige-rigen girka indomie, Aunty hafsa bata hanasuba, ta kunna masu risho ma suyi akai, ita kuma ta kunna gas, domin shirya masu breakfast. haka kowannensu yakwa'ba indomiensa yahau ci, wai dad'i, alhalin ko a ido bata da kyan gani, Aunty Hafsat da mijinta kuwa dariya suka dinga yi nasu, dominsu kwa'bar yaran burgesu take, ko dan basy da yarane haryanzu?. Ya Nura kuwa gari na wayewa yasanya akayo waje da kayan baki d'ayansu, akai masa moping d'in d'akin, Mama da taga yanda d'akin ya cika da ruwa, al'amarin ya bata mamaki sosai da salon fitina irin tasu Nuratu. sai bayan sallar maghriba Hamza yadawo dasu gida, bot d'in motar cike taf da tsarabarsu daya biya mall yayi masu, da gudu sukayi cikin gidan, tsarabar ma Hamzane da shida mai gadi suka biyosu dasu, lokacin kowa yana zaune falo, har su Ya Nura da su Khaleel, Haby da Kamal ne kawai basanan, kan cinyar Mama suka fad'a cike da murna. lokacin Hamza yashigo da sallamarsa, suka amsa masa,ya gaishe da surukansa, yana bawa Ya Nura da khaleel hannu, and'an ta'ba hira dashi kafin yayi musu sallama yatafi, yana mai fad'in "ya'yan Mama ga tsarabar kunan, sai yaushe kuma?" Nuratu tayi saurin fad'in "sai ankwan biyu, idan Mama tabarmu" Ya Nura yad'an bugeta da 'kafa, yanda babu wanda ya lura, Nuratu takalleshi tare da d'an murgyd'a masa baki, shi kuwa d'aure fuska yayi tamau, Hamza yace "to Nuratu Allah kawoku" yafice, ya Nura yataka masa baya. suna fita su Nuratu aka hau labarin abubuwan da sukayi a gidan Aunty Hafsa, Mama tace "shiyasa ai bana so kuna zuwa gidan, gidan iya babu kwa'ba, ace abinda kuke so zakuyi" Nuratu tad'an zunguri baki, Nana da Rahma suka sanya dariya. mintuna kad'an Ya Nura yadawo, yazauna akan kujerar da yatashi, domin babu wanda ya zauna, Mama tace "ya tafi ko?" "ehh" ya Nura yabata amsa ata'kaice, Nuratu da rawar jikinta ta nudi ledojin da suka zo dashi zata bud'e ya Nura ya kar'be, ta koma tazauna tana zungure-zungure, Mama tace "zaka fara ko?" "A'a Mama tayasu gani zanyi", yafad'a fuskarsa taf murmushi, yafara fiddo da kayan daga sweet sai choculate da buscuit, sai kuma kayan Make-up, da gani aikin Aunty Hafsa ne, sai da yagama fiddo da komai yamayar ya d'auki choculate d'aya yasanya abakinsa kafin yace "duk kumatso nan" ba musu suka matsa, Nuratu ce ta'ki zuwa, yace "zo mana 'kanwata" sannan ta'karasa tana mai turo bakin nata, wanda da dukkan akamu hakan yazame mata tamkar jiki ne. ya Nura yakama hannuwansu 'kam yari'ke, ya had'e fuska tamkar bashine ke dariyaba d'azu ba, sannan yafarafad'in "shine kuka shiga d'akina ko?, kuka cikamin shi da ruwa, waye acikinku ya kunnamin shower da famfo?" nanfa suka hau kallon-kallo, "nace waye bazaku fad'aminba" cikin tsawa yake magana yanzu, haknne yasanyasu razana sosai, Hilal harya fara d'an kuka, sabida zafin ri'kon da ya Nura yayi musu, su Mama najinsu basuce komaiba, illa hiransu da sukeyima, Hilal yace "wallahi bani bane Yaya,Nuratuce da Rahm sukace zasuyi wanka, mu bamu shigaba ni da Nana" Ya Nura yabisu da kollon tuhuma d'aya-bayan d'aya, kafin yace "yanzu kowa zaimin tsalle sau goma, sannan wannan kayan babu wanda zai cishi" ya kalli su Mama yaga hankalinsu baya wajen, sannan ya sunkuyo dai-dai kansu,"saura kuma kusanarwa Mama nahanaku kayan, dukanku harbeku zanyi kunsan halina, bana magana biyu" atare su gyad'a kai, cike da tsoro, ya mai da kansa kankujera yana kallonsu sunata faman tsalle, sai da sukagaji sosai, sannan yace suje sukwanta, Mama tatafi d'akin Abba tuni dama, domin girkintane, Aunty ma tawuce d'akinta, Khaleel kuwa tuni yashige d'akinsa dake falon yakwanta, hakan yabashi daman tafiya da kayan nasu, yasan yin hakanne zai samu yawuce, domin duk abinda zaimusu baji zasuyiba. [01/01, 14:07] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book 1 mallaka------QURRATUL-AYN 18 ******RANA BATA 'KARYA****** Duk wani shirye-shirye daya kamata ayi na auren Ya Nura da Habiba anyishi, 'kawayen amarya dubu d'ari biyar suka nema abasu, Khamis yayi musu da, amma Ya Nura yace babu matsala abasu, ita kuwa amarya dubu d'ari biyu da hamsin tace yabata kud'in gyaran jiki kawai, duk da komai Abbansu yace zaiyi, amma hakan bai hana Haby wankar Nuraba san ranta, sabida tasan tariga takamashi ahannu, komai tace babu musu zai mata. zaune take kan cafet yayin da Nabeel ke zaune bisa kujera yana aikin zu'kar sigari, Habi ta zuge jakarta ta fiddo da bandir-bandir na 'yan dubu bugun abuja ta watsa kan center table dake gaban Nabeel, tayi masa wani kallo mai d'auke da guntun murmushi, tana fad'in "gashinan dubu d'ari biyar ne, naka kason kenan tunyanzu, ni zanyi amfani da dubu d'ari biyu" Nabeel yayi murmushi yana mai kashe sigarin, yami'ko mata hannu alamun tazo, ba musu tami'ke zuwa gareshi, yajanyota tafad'o bisa cinyarsa, yasa bakinsa bisa fuskarta yana kiss nata, tad'an janyeshi ahankali tana fad'in "no Nabeel babu wannan harkan yau, ka jira bayan biki kawai, domin ina cikin kintsa kainane kaji, kasan matsalar da hakan zata haifar idan ban shirya kainaba ko?" Nabeel da idanuwansa suka kad'a sukai ja, yabita da wani mugun kallo, amma kasa furta ko kalma d'aya, yana kallonta tagama gyara kanta, tarataya jakarta tayi masa kiss a goshi tajuya tana yimasa byee-byee. tana fita kekenapep ta tara takoma school, cike da tsoro domin sunyi da Ya Nura zaije d'aukantane, shiyasa tayiwa Nabeel 'karya tafito, domin idan tasanar masa Nurane zaije d'aukanta tofa ransa zai'baci, ita kuma ta tsani 'bacin ransa. Inna tun saura sati guda ta sauka agarin kano gari mai albarka, domin bikin d'an jikallenta, sai nan da nan ake da ita musamman ma Abba da take uwa agareshi, tare da Maman Jigawa tazo, wato Suwaiba 'kanwar Abba, dayake aurenta ya mutu kwanaki, akan dai matsalar rashin haihuwar tata, mijin yace yagaji da ci da ita tatafi gidansu, kasancewar Jamila kishiyarta tahaifa masa yara biyu duka maza, Inna da Abba sunso amai da auren amma tace ita tagama aurensa, domin bazata iya da wula'kanci da cin mutunciba. Nuratu ce tazo da gudunta tafad'a bisa cinyar Inna tanayi mata oyoyo, kasancewar sanda suka zo basanan, Inna tace "ke d'agani kada ki'ballani, tsofai-tsofai dake" Nuratu ta tura baki tana fad'in "ai gara mu'ballakin, daman kin ishema kin kafe akan sai kinci zamaninmu" aka sanya dariya baki d'aya, Inna tace "nadaiji amma ad'agani, duk falonnan kancinyar tawa kikaga tafi burgeki, kikazo kika zauna" Nuratu tami'ke takoma cinyar Maman jigawa tana fad'in "mai zanji acinyar tsohuwa ban da 'kashi" Abba yace "a'a da alamu yau zamu 'bata Nuratu, Innar tawa" Ya Nura yayi sallama da fara'arsa yake fad'in "a'a tsohuwa,mai ran 'karfe saukar yaushe" nanma dariya suka sanya, Ya Nura yazauna anata hira da bandariya. "wai ni wanne irin gyara zanyine zuly da Nura bazaigane koni waceceba" Haby tayi maganar fuskarta cike da damuwa, wacce takira da zuly tayi dariya da fad'in "haba dai amaryanmu kada kidamu, nagama shirya maki komai, koda Nura yasan mace bazai ganekiba, bare kuma ina tunanin baho ne shi" suka sanya dariya baki d'ayansu, wata budurwa doguwa siririya tashigo falon da wasu lala tattun kaya ajinkinsa, da alamu abuge take ma, Zuly tace "A'a Baby na, yadai naganki hakan" wacce aka kira da baby tad'anyi murmushi da fad'in "babu komai nazo ayi da nine" Zuly da Haby sukatafa, zuly tace "wannan kyawunfa Amarya, gaskiya yau kintafi da nifa, Baby tad'an 'kara matsowa garesu da fad'in "gaskiyane zuly, kinrigani afili na rigaki a zuci" zuly takai hannunta bisa cinyar Haby, yayin da Baby tajanye d'an kwalin dake d'aure bisa kan Haby, nanfa shed'an, yadinga kid'a akunnuwansu, yana ingizasu busa aikin masha'a (wa'iya zubilla Allah katsaremu da aikata zina, kakaremana zuciyoyinmu, karabamu da sharrin 'kawaye amin)Zuly macace gajeriya ba'ka 'yar duma-duma, bawani kyau garetaba amma sai bariki fal ciki, domin itacema asalin gur'bacewar tarbiyyar Baby da Haby. sun had'une tun a scondrym school har zuwa jami'a basu rabuba, aganinsu bazasu iya rabuwa da junaba, kasancewar abinda suka san suna aikatawa, kuma agida babu wanda yasan Haby tana bariki, sabida iya taku nata, babu wanda yasan gaskiyar Haby sai zuly da Baby, ko Nabeel zirashi kawai take akwalba, domin biyan wasu bu'katu nata, Zuly da Baby kuwa ahalin yanzuma basa gaban iyayensu, shiyasa suke son janyo ra'ayib Haby akan itama tabijire tadawo zaman kanta, domin zasufi jin dad'in harkokinsu acewarsu kenan, kasancewar Haby tafisu kyawu aji da d'aukar wanka, ita suke turawa wajen manyan Alhazai da Hajiyoyi, take wanko masu su, yanzu a'kalla account d'insu nad'auke da kusan millon goma cikin shekaru uku, kawai suka tara wannan, burinsu kawai kud'i, da rayuwar holewa su suka sanya agaba, yanzu haka harsun tsunduma kansu cikin wata 'kungiya sabida kud'i kawai, a tsarin 'kungiyar kuma babu aure, sai dai harka da mazan banza kawai, duk wanda zuciyar d'aya daga cikinsu yaraya zaiyi amfani da wani to tabbas mutumin sai ya amince akan dole, kuma hakan kud'i kawai zai kawomusu da 'kungiyar tasu, wannan shine asalin ainahin wacece Haby da Zuly da Baby. (WAI SHINMA MASU KARATU KO KUNSAN ASALIN GASKIYAR DALILIN DAYA SANYA HABY AMINCEWA DA AUREN NURA, DUK DACEWAR A 'KUNGIYARSU BABU AURE) kudai biyoni sannu ahankali zakusan asalin gaskiyar komai . Amarya da 'kawayenta sungama shirya komai da za'a gudanar abikin 'kawarsu, dinner za'ayita har sau biyu, sai party shima da za'a gudanar sau biyu, sai kamu walima da yini da d'aurin aure, kowanne kuma rana daban za'ayishi, ankon kowacce rana daban, kuma kowanne gurare daban za'ayishi angama shirya komai gidansu cike yake da al'umma mutan jigawa da dangin mahaifiyar amarya dana babanta duk sunzo, gidan ko ina kashiga mutanene, shikanshi angon dan dai d'akin waje yakene, Khaleel ma d'akin Nura ya koma. ba'ki har gidansu Ammy, sai hidima ake kala-kala, kowa kagani fuskarsa cike da annuri na farinciki, domin abinda ba'a ta'ba agidan gashi yazo za'ayishi. Haby kuwa gidan Zuly ta tare, acewar gidan 'kawayen tane, duk wani gyara da taimako sunnema dan kare mutuncin 'kawarsu, acewarsu kenan, 'kungiyarsu tabasu tabbacin babu abinda zai gane, Zuly kuwa tabata shawaran koda yagane, ta nuna masa dabarunsu na'yan bariki mana. gefe guda kuma Nabeel yamatsawa Haby akan dole tazo gareshi, shine yakamata yafara kwasar garar ango, acewarsa zai tona asirinta idan bata zo, hakan yasanya Haby mi'kawa zuly wayarta takar'bi ta zulyn take amfani da ita, nan suka shirya yanda zasu raina masa hankali, su tura Baby matsayin Haby tare da taimakon 'kungiyarsu, domin shima abinda bai saniba amfani ake dashi a 'kungiyar.....! ***BIKI BIDIRI BIRI'DI*** inji masu iya magana Amarya da angonta sunyi kyau sosai awannan rana, domin kayan da suka sanya kansu abin kallone, gashi daman Nura ba bayaba wajen kyau, anko sukai Amarya tasanya leshi blue mai ratsin pink, shi kuwa ango shadda yasaka blue sunyi kyau sosai, a layi aka shiga wajen, amarya da ango na gaba ri'ke da hannuwan juna, yayin da aka jere su Nuratu manya abayansu, sukuma suna sanyene da dogwayen riguna pink, and'aure masu gashin kansu da ribon sunyi kyau sosai musamman Nuratu da dama ruwa biyuce tafi kowa d'aukan hankali awajen. nanfa wajen yakaure da tafi da shewa, bayan bud'e taro da addu'a da d'an jawabai sai kuma ango da amarya suka yanka cake nan waje ya hargitse aka fara kad'e kad'e can nahangi Nuratu sai rawa take d'iba, masu hotuna da bidio kuwa gunta suka koma suna d'auka, sai da Aunty Hafsa tahanjenta, sannan aka samu lafiya, ba'a tashiba sai 11pm na dare , sannan aka fara mai da kowa gida, sai kuma gobe idan Allah yakaimu [03/01, 01:35] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book 1 mallaka------QURRATUL-AYN 19 ***** *** ***** kashe garima dinner aka sakeyi a hamdala hotel, sai kuma party biyu da aka gudanar a nigh-tell, sanna aka gunar da walima iya mata kawai cikin harabar gidansu, ranar asabar aka gudanar da yinin biki, Amarya tayi kyau sosai ranar, sai shiga takeyi ta alfarma tana cirewa, haka sauran dangi ba'abar su abayaba, ranar lahadi kuma take ranar d'aurin aure, za'a d'aura 'karfe goma na safe ne. -----RANAR 'DAURIN AURE---- Nuratuce zaune gaban Ammynta tana sanar mata abinda za'a bata ita da su Nana zasuyi nasu parting, Ammy ta dubeta kawai tayi murmushi tare da dafata tana fad'in "haba 'yar gidan Mama, wanne party kuma zakuyi" duk partyn da akasha bai ishekuba, kinsan nifa bana son harkan fitina" Nuratu tad'an turo baki gaba, tana d'an bubbuga 'kafafunta a'kasa tsabar shagwa'ba, Ammy tace "to tunda ke bakisan harkan lallashiba, tashi kificemin ad'aki" ba musu Nuratu tafito a d'akin tana murzar idanuwa, mutanan falon namata magana ko kulasu batayiba ta fice daga gidan, ta nufi wajen Mama, a harabar gidan ta taddasu Nana, suka bita zuwa cikin gidan. a hanyar shiga gidan tana tafiya da baya da baya tana fad'awa su Nana abinda zasu gayawa Mama domin ta amince ta basu kayan parting, sai ji tayi tayi karo da mutun, cikin zafin nama taji anfizgi gashin kanta tayi baya ta daki bangon wajen da goshinta, kafin ta dawo haiyacinta aka d'auketa da mari, cikin firgici da gigita ga kuma azabar buguwa batasan sanda tahau fad'in "Allah ya isana mugu azzalimi" duk da cewar idanunta basu washe taga ko wayeba, dai-dai sanda yasake kai hannu zai 'karamata wani marin, taji ana fad'in "kai Kamal lafiyarka kuwa, mai tayi maka haka?" Nuratu tad'ago kanta da sauri, sai taga ya Nura ri'ke da hannun Kamal, ashe da Kamal sukai karon. shine yayi mata wannan mugun bugun, da kyar ta dafa bangon tami'ke, tana binsu da kallo, bakinta na jini, goshintama haka, Ya Nura yasake tambayar Kamal cikin tsawa "nace mai tayi maka?" Kamal da idanuwansa suka kad'a sukai ja, wanda da dukkan alamu abuge yake ya fizge hannunsa daga ri'kon da Ya Nura yayi masa yana fad'in "waini zata buge wannan yarinyar, sannan inhukuntata tazageni" cikin layi yake maganar, Ya Nura ya dubi Nuratu yaga jini duk ya'bata gaban rigarta, ya kamo hannunta suka fito zuwa harabar gidan, bai kuma bi takan Kamal ba, d'akinsa ya bud'e yaja hannunta zuwa ciki, Nuratu kuwa cikinta yagama d'urar ruwa ta sada'kar yau Ya Nura ko bai kashetaba sai ya illatata. suna shiga har bedroom nasa ya nufa da ita, yaje yad'auko wata 'yar akwati 'karama suka dawo falon, ya zauna akan kujera, yajawo hannunta zai zaunar da ita tafara kuka ta zube agabansa tana magiyar "dan Allah Yaya kayi hakuri, wallahi nadaina rashin kunya da 'kinji, kabarni dan Allah inrayu tare da Ammy dasu Mama" maganganunta sunso bashi dariya sosai, amma sai ya kanne yasake zaro idanuwa yana fad'in "ni bakison kirayu dani ko?, to matsonan" Nuratu tasake ja dabaya tana fad'in "har dakai wallahi inaso inrayu da kai, kayi ha'kuri dan Allah" Ya Nura sai da yayi murmushi, yami'ke yajawo hannunta, yazaunar da ita, bisa kujerar da yake zaune kusa da shi, yasa hannu yashare mata hawayen, yana fad'in "kukan ya isa to" sannan yabud'e akwatin sai taga ashe first aid ce, tasaki wata ajiyar zuciyar da sai da Ya Nura ya dubeta kawai, nan yasanya hydrogien yana goge mata ciwon, ai kuwa tahau ihun zafi, ganin yad'aure fuska yasanyata yin,shiru ammafa har 'kan'kameshi take, duk tabi ta'bata masa jiki, sai da yagama sannan ta lura da 'bata masa rigar da tayi cikin tsoro tahau fad'in "kada kadukeni yaya kawo rigar inwanke maka" Ya Nura yayi dariya yana fad'in "ko ke bakya wanke naki kayan, bare kuma nawa" dai-dai sanda aka turo 'kofar d'akin akashigo, Khamis ne tare da wasu abokansa su biyu, dukkansu cikin bluen shadda da hula d'inkin zamani sunyi kyau sosai . Khamis ya tsaya daga bakin 'kofar yana fad'in "haba master, kana duba agogo kuwa? daga bari kaje kayi wanka kashirya sai kabarmu tsaye" Ya Nura bai maganaba illa duba agogo da yayi yaga tara da rabi har da mintuna biyar, hakan yasanyashi mi'kewa yanufi bedroom nasa, Khamis yabishi da kallo, sauran abokan kuwa guri suka samu suka zauna, sannan Khamis ya'karaso zuwa kujerar da Nuratu ke zaune, ya zauna yana fad'in "Nuratun Abba, Mama, Ammy, ko Nuratun Nura zance?" Nuratu ta dubeshi cikin harara ta d'an murgud'a baki, kafin tad'an rage murya tana fad'in "kace dai Nurantun Abba da Mama da Ammy kawai, amma babu wata Nuratun Yaya, mugune infad'a maka" baki d'aya su Khamis dariya suka sanya, har ita uwar gaiyar, Khamis yace "wai lafiya kuwa mai yasameki ne?" Nuratu tad'an ta'be baki, tana fad'in "wani mugunne kuma yaso illatamin fuska ana cikin bikin murna" "wayeshi kuma?" "Kamal mana" Nuratu tabasu ansa, tacigaba da basu labarin abinda yafaru, har chakwakiyarta da Ya Nura bayan yajawota d'akin, su Khamis nata dariya. 'karar bud'e 'kofar d'akinsane yasanya Nuratu yin shiru daga labarin datake bawasu Khamis, yana fitowa wani 'kamshi ya kewaye d'akin, sanye yake cikin farar shadda da malun-malun, tasha aiki blue, takalminsa blue ne, sai hular kansa itama fara mai aikin blue, yasanya farin glass afuskarsa, daya 'kara fiddo da kyawunsa, Nuratu tasaki baki tana dubansa, karo na farko a rayuwarta data ta'ba ganinsa da glass, tsawar daya daka mata itace tayi sanadiyyar d'auke kanta tana murgud'a baki, Ya Nura yace "to parrot tashi kifice, duk inajinku ai, ku kuma da girmanku kunwani biye mata" sum-sum Nuratu tatashi tafice tana 'ku'kuni. Khamis yace "ai dole mubiye mata Nuratu akwai burgewa" Ya Nura yaja wani mugun tsaki yana fad'in "sai ku tashi mufita ai, saura five minute" ba musu sukayo harabar gidan. Nuratu kuwa nashiga gidan kowa Nuratu, anayi mata sannu, hakan yasanyata dawowa da kukan da bata samu tayiba, Maman jigawace taja hannunta takaita d'akin da Inna take takwantar da ita, tana ta ta'bara da shagwa'ba Inna na lallashinta. 10:00 aka d'aura auren ya Nura da Habiba akan sadaki dubu hamsim, wanda Abba ne yabayar dasu, nan waje yakaure da kad'e-kad'e da bushe-bushe, jama'a kuwa bila adadin gasunan, sun cika 'kofar gidan fam, babu masakar tsinke domin Abba mai mutane hakama ya Nuran kansa [04/01, 00:09] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book 1 mallaka-----QURRATUL-AYN 20 Haby nacan cikin d'akin Momynsu anayi mata d'auri, tasha make-up tayi kyau sosai tamkar ba itaba, su Zuly ne cike ad'akin tare da wasu 'kawayensu su biyar, shewa suka sanya baki d'ayansu suna zolayar amarya jin maro'ka nata kirarin an d'aura auren. Mamace tashiga d'akin Inna neman Nuratu domin tuni su Nana suka kaimata zancen abinda yafaru da ita, ai kuwa Nuratu naganinta ta taso ta rungumeta cike da shagwa'ba, Mama tace "subhannallahi, haka yayi maki da fuska?, ai kuwa sai na sa'ba masa wallahi" taja hannunta suka fito zuwa part d'inta, toilet ta kaita tayi wanka ita kuma takoma wajen ba'kinta, koda Nuratu tafito su Nana tagani zaune kan gado cikin bluen shadda anyi mata stone work, sunyi kyau sosai, da murmushi Nana tami'ka mata tata shaddar suka fice da sauri, jin anfara d'aukar hotuna, Nuratu agurguje ta shafa mai, tasanya powder da jan baki pink, tad'an gyara giranta, ta taje gashin kanta dake zuba har gadon bayanta, ta sanya under wear, ta zura doguwar rigar shaddarta, ta sanya ribom d'aya takama gashinta, sannan tasake d'aurewa da d'ankwalin shima tayishi kamar ribom, tayi kyau sosai duk da cewa bawani make-up tayi ba(kada kumance Nuratu ruwa biyu ce bafulatana kuma balarabiya). takalminta ma flat tasanya pink, bata tsaya wani duba mayafiba tayo waje, duk da ciwon dake goshinta hakan baihana baiyanar kawuntaba, ai kuwa,nan akahau jan ta kowa Nuratu tazo suyi hoto, domin Nuratu irin yaran nanne masu shiga rai. Ango nashigowa aikuwa abokan wasansa suka fara zolayarsa, kasancewar Nura bamai magana bane murmushi kawai yake binsu dashi, Khamis ne da sauran abokai suka sayi bakinsa suke rama masa, lokacin Amarya itama aka fito da ita cikin tata shaddar pink da aikin blue akai mata, ata'kaice dai angon blue da pink akai ranar, nanfa hotuna da videos yakoma kansu, akaita hotuna kamar baza'a dainaba. kafin angwaye sufice zuwa d'akin ango, nan aka shirya musu abinci mai rai da lafiya sukaci suka gimtse. kafin zuwa maghriba kuma aka fara shirye-shiryen kai amarya gidanta dake sharad'a phase II, wanda Abba ne yabaiwa Ya Nura shi kyauta, nan zasu tare kafin zuwan tafiyarsu malesia, Ya Nura yasa angyare masa gidan sosai, tamkar a turai, domin damacan Ya Nura d'an son hutune da gayu, kuma gashi yaje yayi rayuwa cikin turawa. Su Nuratu sunkafe akan sai sunje har da kukansu, Mama kuwa tace ba'kine zasuje su 'yan gida suyi ha'kuri zuwa kashe gari zasuje, nan su Nuratu suka 'karashi kukansu sukai barcin dole dana gajiya, domin sungaji sosai ai. motoci reras akazo d'aukar amarya, Momynta tayi mata nasiha sosai kamar gaske, hakama Abba da Mama, Innama ba'abarta abayaba, lokacin angama shirya jama'a acikin mota, sannan aka fito da amarya tana kuka kai kace gaskene sai ha'kuri ake bata, aka sanyata amota daga ita sai 'kawayenta kafin su d'au hanya zuwa kaita kuma, kowa yayaba da tsarin gidan da kyawunsa komai abin birgewa ne a gidan. 10:30 goma da rabi dai-dai angwaye sukai sallama cikin falon, lokacin gidan anwatse kaf, sai amarya da 'kawayenta, sunata shewa da zance narashin mutunci, sallamar angwaye ce takatsesu, amarya tayi maza tarufe kanta, suka 'karaso zuwa cikin d'akin. nan suka bufe wajen da addu'a sukayiwa amarya nasiha da angonta, tare da d'anyin barkonci, sannan suka aje ledojin da sukazo dasu, sukayi musu sallama suka fito tare da 'kawayen nata dan mai dasu gida. Ya Nura har bakin motocinsu yarakasu sannan yadawo yarufe ko ina, ya koma cikin d'akin daya bar Haby, koda yakoma harta zanye mayafin kanta tayi kwanciyarta, da sallama yashiga d'akin amma ko kulashi batayiba, ya d'an jima yana kallonta fuskarsa cike da murmushi, amma kuma yanajin wani irin fad'uwar gaba azuciyarsa, sai ya d'auki hakan amatsayin kawai dan yaune karo na farko arayuwarsa da zaiyi kwana d'aki guda da macene. 'karasowa yayi haryanzu bakin gadon, yazauna agefanta yad'an juyo da ita, tabud'e idanu ahankali tana dubansa, Ya Nura yayi ajiyar zuwa had'e da murmushi kafin ya furta "gajiya ko amaryata?" gyad'a kai tayi tad'anyi masa murmushi, hannunta yakamo yasanyashi cikin nata yana d'an murzawa ahankali, duk da Haby maza sunsaba ri'ke hannunta, amma sai taji wannan ri'kon daban, taji wani yarr ajikinta, wanda yasanyata dubansa ahankali, ya Nura yasa hannu yatasheta zaune yana fad'in "tashi yau ba ranar barci bace, kitashi mugodewa Allah" Haby tad'anso yin gardama, amma sai tayi tunanin kada tabayar da kanta awajensa tun ranar farko, hakan yasanyata mi'kewa zuwa toilet tayo alwala tafito, sannan Ya Nura yashiga mintuna kad'an shima yafito d'aure da alwala. ya shimfid'a musu sallaya, tasanya mayafinta ita kuma, sannan yaja musu limancin sallah raka'a biyu domin nuna godiyarsu ga Allah, yakama kanta yayi mata addu'o'i kamar yanda addini yakoyar, sannan yami'ke yafita mintuna kad'an yadawo d'auke da flat da spoon sai cup, ya ajiye agabanta, sannan yad'auko ledojin da sukazo dasu yabud'e, ya fiddo da wasu kaji biyu gashashsu, ya zuba madarar holandia a cup d'in, yace mata "bismillah matso" ba musu tad'an matso gareshi, yafara bata naman abaki, yana bata madarar sai daya tabbatar ta'koshi, sannan yaci nasa yatashi yamai da kayan kitchen, ya wanke sannan ya dawo. wardrobe ya nufa ya fiddo da jallabiya fara 'kal ya ajiye gefan gadon, sannan ya kuma aje wata daban kalar ja, ya mi'kawa Haby da fad'in "ungo kirage kayan jikinki sabida zafi kisanya wannan" yami'ka mata takar'ba, shi kuma ya nufi toilet. yana shiga tami'ke taware rigar duka-duka bazata wuce gwiwartaba, shara-shara ce, sai wasu siraran igiyoyi a wuyan rigar, rigar tayi kyau sosai sai 'kamshi take gata mai taushi, bata jira komaiba tasanya, ta tsaya a gaban mirrow tana duban kanta domin gaskiya tayi mata kyau sosai. can shima yafito jikinsa ji'ke da ruwa da dukkan alamu wanka yayi, kallon Haby yatsayayi yana kallon irin kyawun datayi, ya tako zuwa gareta ya rungumota tabaya, yasanya kansa bisa kafad'arta yana rad'a mata wasu irin kalamai, dabanji mai yake cewa ita kuwa murmushi kawai take. can yasaketa yahau shafa mai ajikinsa, yafeshe jikinsa da turaruka, lokacin takoma gedan gado ta zauna tana dubansa kawai, harya sanya jallabiyarsa sai kuma yacire yasanya 3quarter da best, yazo ya hure mata idanuwa yana fad'in "wannan kallonfa, kamar ance maki za'a saceni, yau ai ranarkice kece da Nura" Haby tayi dariya, Ya Nura yajanyota tafad'o zuwa jikinsa, suka saki wani sassanyan nunfashi atare, tare da 'kurawa junansu idanuwa nanfa Ya Nura yaji yakasa d'aure kallon, yakai bakinsa bisa nata yafara kiss tamkar yasamu sweet mai dad'i daya dad'e bai shaba kafin kace mai labari yacanja, sai ganin duhu nayi yamamaye d'akin XXX, hakan yasani yin waje. ASUBA TA GARI NUR-HABY [04/01, 18:57] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book1 mallaka-----QURRATUL-AYN 21 Bugun 'kofar da akene yayi sanadiyyar farkawarsu daga nannauyan barcin da suke, Ya Nura ya duba agogon dake manne bisa bangon d'akin, yaga 11am harda mintuna, salati yayi yana mai saukowa daga bisa gadon, sanye da farar jallabiya ajikinsa, domin tunda yayi sallar asuba yakoma bai farkaba sai yanzu, itace dai uwar garin ko sallar ma batayiba, daman kuma bata dametaba, anata ganin yin sallama takurawa kaine kawai. yana fitowa Haby tabiyo bayansa, ko zani bata nemaba bare kuma hijab, hakanan tafito sanye da guntuwar rigar barcinta, Ya Nura yace "waye?anazuwa" yaji ance "hafsat ce" hakan yasanyashi bud'ewa da sauri fuskarsa cike da murmushi, yana bud'ewa su Nuratu suka danna kai ciki, suna rige-rigen shiga, Aunty Hafsa tasanyo kai hannunta d'auke da basket na kulolin abinci, ya Nura yakar'ba yawuce daining dasu, su Nuratu nashiga falon sukaga Haby tsaye bakin 'kofar bedroom cikin wannan rigar da duk surorinta waje, gashi babu komai jikinta banda ita d'in, sakar baki sukai suna dubanda kawai cike da mamaki, Aunty Hafsat ce takai dubanta wajen, dai-dai lokacin da Haby ta tako ta nufi wajen Ya Nura tawani rungumeshi ta baya kamar babu kowa a falon da sauri ya Nura yajanyeta daga jikinsa yana fad'in "haba haby bakiga Aunty Hafsat da yara bane" tsaki Haby tayi sannan cikin shagwa'ba tafara fad'in "haba dear sabida mutane sai mu kasa jindad'in rayuwar aurenmu, su mai yakawosu gidan amare da safiya haka, ai sunsan abinda zasuzo sutarar" ta'karashe maganar tana hararar Aunty hafsat, cikin takaici Aunty Hafsat ta dubesu, tama rasa abinda zatace hakanne yasanyata tattara hannuwan su Nana tafito daga cikin falon da sauri, Ya Nura yabiyo bayanta, kafin yazo har takai cikin harabar gidan tabud'e motarta tasanyasu, cike da magiya Ya Nura ke lallashin Aunty Hafsat kamar zaiyi kuka, Aunty Hafsat tace "kada kadamu ba laifinkabane laifinane nazuwa gidanku da safe kagane muhad'u a gida kawai" tafad'a tana mai tada motarta tafice daga cikin gate d'in. Ya Nura yajima,nan tsaye cike da takaici, yana tunanin hukuncin da zaiyiwa Haby idan yakoma, a zuciye ya koma cikin gidan, ko da yashiga falon tana nan cikin shigar daya barta, sai ma zama da tayi bisa d'aya daga cikin kujerun dake falon, ta kunna tv tanata karkad'a 'kafa, Ya Nura nashigowa zaiyi magana kenan ta dubeshi ido cikin ido fuskarta d'auke da wani irin mugun murmuahi, sai gashi yama mance da abinda yafaru, ya'karasa bisa kujerar datake zaune yazauna, yad'ora kansa bisa kafad'arta takama wasa da gashin kansa kamar wani yaronta. Ranar kashe wayoyinsa matayi, ta kuma hanashi fita, shi kuwa duk abinda tace babu musu, koda yaso yin musu da sunhad'a ido zai saduda, yinin ranar sunyitane cikin gurzar amarci, acewarta itafa bata gajiya dan haka sai dai yayi ha'kuri da ita, sai ta zama angon ya koma amaryar (TAB...! DA MAMAKIFA WAI MENENE SIRRINNE?, BAZAKU TAMBAYABA?, KO DAYAKE KUBIYONI DAI). ko da Aunty Hafsat ta isa gida cike da takaici tafito daga motar tashige gidan, kai tsaye falo ta nufa, tunawa da tayi akwai ba'ki agidan ashine yasa tasaki fuskarta ta wuce cike da murmushin ya'ke, taja hannun su Nuratu zuwa d'akin Mama domin babu kowa takora musu gargad'in kada taji wanda yayi maganar abinda yafaru, sannan tafito ta nufi d'akin Inna anata tambayarta yata barosu fatan dai lafiya tadawo da wuri haka, sai tabasu amsa da lafiya kawai, sannan tami'ke tanufi d'akin Aunty nanne babu kowa, su Nuratune azaune falon suna game, bedroom nata tashiga takwanta tana kallon cilling, tunanin abinda yafaru kawai take, tausayin d'an uwanta yakamata sosai, domin tasan akwai aiki agabansu, shiyasa ita tunfarkon maganar auren abin bai kwanta mata araiba, kawai tayi shirune kasancewarta bata da 'yancin yin wani abu akai. har Aunty tazo d'akin tazauna bisa gefan gadon kusa da ita amma Aunty Hafsat bata saniba sabida nisan da tayi a tunani, sai da Aunty ta dafata sannan tafarka firgigit tami'ke zaune, had'e da dafe kanta dataji yasara mata. Aunty tace "lafiya kuwa Hafsatu?, kinsan dadewata zaune anan? tunanin mai kike haka?" Aunty Hafsat tad'ago kanta tare da ajiyar zuciya tana fad'in "wallahi Aunty wani abune ya girgizani yau agidan Nura, al'amarin yabani mamaki da tsoro sosai" Aunty tace "kamarya fa, ban fahimcekibafa?" Aunty Hafsat tayi ajiyar zuciya, sannan tafara bawa Aunty labarin dukkan abinda yafaru, Aunty tayi shiru itama kanta yakulle sosai, can Aunty tayi ajitar zuciya tana fad'in "al'amarin da mamaki da d'aure kai, amma dai koma menene addu'a itace mafita, ki cire komai aranki, kuma shawara kada kisanarwa Mamanku, kada hankalinta yatashi kinji, hakan zai iya jamata damuwa, ace daga kai amarya jiya anfara samun sa'bani, kije tana nemanki tund'azu, nima banzaci kinananba" tafad'a tana mi'kewa ta sake duban Aunty Hafsat, "kiyi 'ko'karin danne zuciyarki, amma nima wallahi tunkafin yau nadad'e ina kokwantan wannan had'in, amma babu yanda zamu iya da tsarin ubangiji, domin komai na Allah ne kitaya d'an uwanki da addu'a kawai" Aunty Hafsat ta gyad'a kai, ita kuma tafice daga d'akin. Aunty hafsat tad'an jima azaune, kafin ta fito daga d'akin ta nufi d'akin Mamansu jikinta duk babu kwari, amma hakan yasanyata tadaure ta saita kanta domin kada Mama ta fahimci halin da take ciki. koda tashiga d'akin Mama na zaune gefan gado da waya ahannunta, Aunty Hafsat ta 'karasa tazauna kusa da ita, Mama tace "wai yanaga kundawo da wuri haka?, ko wani abunne ya faru? naganki kuma cikin damuwa" Aunty Hafsat tayi murmushi tana fad'in "babu komai Mama, lokacin da mukaje sannan suka tashi daga barcine shiyasa kawai muka dawo" Mama ta gyad'a kanta kawai tana fad'in "neman wayarsa naketayi tundazu akashe, amma tunda naji kince lafiya suke shikenan, kije can d'akib Abbanku Hamza na nan yana jiranki, wai yakira wayarki baki d'agaba" sai lokacin Aunty Hafsat ta tuna da wayartama, murmushi tasakeyi tace "ayya namanceta a cikin jaka wallahi, natafi d'akin Aunty nakwanta nagajine" to kifita kije yanzu" Mama tafad'a tana mai ficewa daga d'akin. Aunty Hafsat tayi ajiyar zuciya, sannan ta nufi mirrow ta gyara fuskarta, kafin ta nufi wajen mijinnata. [06/01, 17:53] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》Book1 mallaka-----QURRATUL-AYN 22 *****KASHE GARI***** Har kashe gari Haby bata bar Ya Nura yafito daga gidanba, neman duniya Khamis yayi masa a waya amma shiru, ga ba'kinsu nanesa nasonyin sallama dashi zasu koma gida hanne yasanya Khamis nufar gidan Nura domin jin ko lafiya? Da isarsa abakin gate ya tsaya yana tambayar gate man, lafiya kuwa mutanan gidan suke? gateman yabashi amsa shidai yana da tabbacin babu wata matsala, hakan yasanyashi 'karasawa cikin harabar gidan Khamis yayi parking motarsa cikin parking space, ya fito ya nufi cikin gidan. lokacin Ya Nura nazaune kan kujera a falonsu da jarida ahannunsa yana karantawa yayin da 'yar mulkin nasa ke kwance bisa cinyarsa, cikin wasu riga da wando dasuka kama jikinta, wuyan rigar nada girma sosai, wanda yafito da rabin 'kirjinta duk awaje, kanta ko d'ankwali babu, sai ribom data sanya taka gashin nata, cingum ne a bakinta tanata aikin taunarsa. Khamis yai sallama bakin 'kofar falon batare da ya shiga ba, jin sallama yasanya Ya Nura ajiye jaridar agefansa yana duban Haby, dako motsi bataiba bare ta kula da wata sallama da ake, sai da Khamis yasake mai-maita sallamar sannan Haby ta buga wani tsaki tana fad'in "wai waye haka?" Khamis yace "nine Khamis" "sai ka shigo ai" Haby tabashi amsa, batare data tashi daga kan 'kafar Ya Nuraba, shi kuma yakasa furta ko da kalma d'aya. Khamis ya danna kai cikin falon, cikin murmushi, ganin Nura da yayi zaune abin yabashi mamaki sosai, Haby ta dubeshi a wula'kance da fad'in " lafiya dai?, kazo katsaya akan mutane mai kake bu'kata?" Khamis sakar baki yayi yanaa duban ikon Allah, Haby ta tashi tazauna ta d'ora 'kafa d'aya kan d'aya tana girgizasu game da 'kare masa kallon wula'kanci tace "tambayarka,nake kayi shuri kana dubana" Khamis yaja wani mugun tsaki yana fad'in "ni ba wajenki nazoba wajen Nura nazo ki rufe mana baki malama" Haby ta sanya wata muguwar dariya tana fad'in "ok to dakyau hakan ai gaka gashi kuyi magana". khamis yace "Master wai lafiyarka kuwa?, kana ganina amma ka tsaya kana kallona" Ya Nura mai makon yayi magana sai ya mai da dubansa kan Haby, da dukkan alamu umarninta yake jira. Khamis yayi ajiyar zuciyar kawai yana kallon ikon Allah, can Haby tayi murmushi tare da hura cingum d'inta yaba da kwai ya fashe, ta dubi Khamis tana fad'in "kafad'i dukkan abinda yake tafe da kai, domin sai da umarnina zaiyi komai ayanzu" Khamis dubanta kawai yayi yad'auke kai aransa yana fad'in "kyan banza kyan d'an maciji" afili kuwa gyaran murya yayi yasake duban abokin nasa cike da tausaya, yaga alamun dukkan abinda tafad'a akwai 'kamshin gaskiya ciki, kuma shidai burinsa yafita da Nura sufita kunyar abokai, ya zaiyi dole yabi umarnin nata, Khamis yasake duban Haby akaro na biyu cike da tsana yafara fad'in "inason zamu fitane, domin yin sallama da abokanmu, zasu wuce gida" Haby ta dubeshi sama da 'kasa kamar bazata furta komaiba, sai kuma tamai da dubanta kan Nura tana fad'in "sai ka tashi kashirya ai" Ya Nura yami'ke da saurinsa ya nufi bedroom, baki d'aya da kallo suka bishi Haby ta kece da wata muguwar dariya, tana duban Khamis kafin tace "ji mana mallam, ruwankane ka rufawa abokinka asiri, ruwankane ka tona, amma bakayi mamakiba yanda abokinka ya koma mijin tace ko ince mijin kantace a dare d'aya" tasake sanya dariya, Khamis jiyayi kamar ya rufeta da duka, ko kuma yahad'iyi zuciya tsabar takaici, sai yajima tsabar tsanar da yayiwa Haby ayau gidanma yatsaneshi yaji kaman akan 'kaya yake. mintuna kad'an sai ga Ya Nura yafito cikin wani bluen yadi, yayi kyau sosai, Haby tace "kada dai akai dare " da sauri Ya Nura ya furta "to, madam" suka fice Khamis ko takanta bai sake biba. tafiya suke amotar amma babu mai furta komai, Khamis yamai da kansa ga driven, Ya Nura kuwa kwantar da kasa yayi bisa kujerar idanuwansa arufe, jefi-jefi Khamis na aikin jan tsaki, tare da duban abokin nasa, cike da tausayawa rayuwarsa. har suka iso hotel d'in da abokan nasu suka sauka, suka gaisa sunata zolayar ango, shi dai murmushi ne nasa kawai, Khamis kuwa kan dole yake ya'ke, har dai suka kammala komai suka raka abokan nasu airport, sannan suka juyo kan motar tasu zuwa gidansu Ya Nura akan hanyarsune Khamis yakasa daurewa domin shirun da Nura yake yafara damunsa duk da yasan shi bamai surutu bane, yad'an dubeshi ta gefan ido yana fad'in "wai Master taya hakan yafaru?" Ya Nura ya dubi Khamis tsahon wasu lokata kafin yakau da kai, kamar bazaice komaiba, har Khamis zau sake magana sai yaji yana fad'in "nima bansan yanda akai hakanba, amma idan ina tare da ita inajina kamar baniba, kawai kadingayimin addu'a" Khamis ya dubeshi cike da tausaya, daga haka basu sake furta komai har suka iso gate d'in gidan, gate man yabud'e gate, Khamis yasanya hancin motarsa zuwa ciki, ya nufi parking space yayi parking, amma Ya Nura ko motsi baiyiba, illama 'kurawa gidan idanu da yayi kamar yana nazarin wani abu akan gidan, sai da Khamis yayi masa magana sannan yasanya 'kafa ya fito, suka nufi cikin gidan. suna shiga mutan jigawa suka kama yi musu tsiya, nan d'inma Khamis ked'an kareshi amma shidai murmushine nasa kawai da haka suka gaisa da kowa suka nufi d'akin Mama, tana zaune falo dasu Ammy da Aunty harda Aunty Hafsat domin bata tafiba, cike da kunya Ya Nura yake gaishesu, suna ansawa sai yaji yanajin nauyin had'a ido da Aunty Hafsat, ita kuwa 'kura masa idanuwa tayi kamar tana so tafahimci wani abu akansa, Ammy ta dubeshi da fad'in "lafiya dai Nura, naganka jikinka duk amace?" Mama tace " nima naga kamar babu wal-wala atare dasu" Khamis yayi saurin fad'in "babu komai Mama, gajiyace kawai" suka mi'ke domin zuwa d'akin Inna, anan dai sund'anyi barkwanci kafin su fito su nufi d'akin Momyn Haby, anan kam sunga kallon wula'kanci da 'kas'kanci, Khamis yasake cika da mamakin wannan lumbu-lumbu irin nasu, ya fahimci duk wanda yace baya son ka da safe da yamma yazo yace yana sonka to 'karyane. haka suka fito jiki amace, da Aunty Hafsat suka gamu a tsakar gida tace "ku sameni a falon Abba zamuyi magana" ba musu suka nufi can. Aunty Hafsat dubansu take d'aya bayan d'aya kawai, musamnan 'kanin nata, Khamis yayi ajiyar zuciya yana fad'in "to kinji dukkan abinda yafaru yau" kuma duban Ya Nura tayi daya sunkuyar da kansa, bazaka iya tan-tancewa a wanne hali yakeba. ajiyar zuciya Aunty Hafsat tayi kamin tace "nidai ahalin yanzu Khamis babu abinda zan iya cewa, illa kawai mu tayashi da addu'a domin yana cikin tsaka,mai wuya, amma insha Allahu zansan abinyi, matsalar d'ayace tafiyar da zaiyi, amma duk yanda za'ayi zansaka atayamu da addu'a domin babu abinda yafi 'karfin Allah" Khamis yace "hakane Aunty, nima insha Allahu zanyi wani abu kai, domin ba aboki nad'auki Master ba, d'an uwa" sun tattauna abubuwa da yawa, duk da Ya Nura baya cewa komai, dubansu kawai yake domin shi aganinsa babu abinda zaiyi, babu abinda zai iya, sun koma sunyiwa su Mama sallama kafin su fito zasu tafi, a harabar gidan suka hangi su Nuratu can cikin lambu suna wasa Ya Nura yatsayawa yayi yana dubansu cike da nazari, wanda Khamis yakasa tan-tance wanne irin nazari yakewa abu idan ya 'kura masa ido, sai da Khamis yaja hannunsa sannan suka wuce zuwa gidan Nura, a bakin gate Khamis ya ajiyeshi yajuya acewarsa babu abinda zai koma yayi agidansa. Haby nazaune falo da waya akunnanta tana baiwa Zuly dukkan abinda yake faruwa agidan nata, da irin wainar data toya jiya zuwa yau, sunata shewa da 'karawa Haby wani makircin, yayi sallama yashiga ta dubeshi tad'auke kai tana fad'in "to Zuly tawa sai zuwa anjima zamuyi waya zakuji wani zazzafan story d'in domin yanzu holo'kwan nawa yadawo" suka sake sanya dariya kamar zasu fasa wayar. [07/01, 00:20] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book1 mallaka-----QURRATUL-AYN 23 Wasa-wasa al'amarin Ya Nura sai 'kara ta'bar'barewa yake, cikin sati biyu Ya Nura yazama ko kad'an baya iya sarrafa kansa akan al'amuran Haby, akaran kansa yanajinsa kamar bashiba, amma kuma,baya iya dogwan nazari akan hakan, yana kallon kansa komai yayi dai-daine. malesia takirashi akan batun zuwansa gobe, Haby tacika da murna domin tana ganin barinta nigeria shiyafi alkhairi da cigaban dukkannin wasu har'kallolinta, domin zamanta zai iya kawo cikas da tonuwar sirrinta. Da dare suka shirya shida gimbiyartasa domin zuwa,gidansu danyin sallama da iyayensu, wanda dukkan umarnin Haby ne, badan mahaifiyarta dake gidanba da bata zoba. Da sallama suka shiga cikin babban falon gidan, dake dukkansu suna falon suna hira, amma banda Momyn Haby domin itama ungulu takomo gidanta na tsamiya, sama-sama Haby ta gaida su Mama tami'ke zata nufi d'akin Momynta, da rawar jiki Nura yami'ke zai bita, Mama tace "a'a ba dai tafiyaba?" wani kallo Haby tawatsa masa yakoma yazauna, sannan tasanya kai tafice, Mama da Aunty sakar baki sukai suna duban ikon Allah, domin daman masu zuwa gidan nata kawo musu gulmar halin da d'an nasu yake ciki, Aunty daman tasani, Mamance take ganin kamar gulmar mutanece kawai, duk da itama wani lokacin tanajin ajikinta kamar gaskiyane, yau kuwa gashi agabanta tagani, ga irin duban da matar tasa ke masu, uwarta kuwa yanzu rashin mutunci take masu sanranta danma Abba yanzu yadawo daga rakiyarta,tana d'an shakkarsa. Mama tayi ajitar zuciya suka dubi juna da Aunty, su Nuratu nacan suna aikin game, Ya Nura daya koma yazauna shima ajiyar zuciyar yayi, sai lokacin yasaki jikinsa suka kama hira kamar bashiba, can su Nuratu suka dawo wajensa suna yimasa 'korafin bayaso suje gidansa, murmushi yayi kawai batare daya kulasuba, domin baisan abinda zaice dasuba shi gashi bayason 'karya yatsani maiyin 'karyama, dayaga zasu takura masa tuni yayi musu jan ido suka koma game d'insu. Mama ta watsa masa harara tana fad'in "sai dai kayiwa 'kannanka jan ido, amma ka kasa sarrafa gidanka ko?" a firgice ya dubi Mama sai kuma yayi 'kasa da kansa, haka kawai yaji zuciyarsa na'kuna, Auntyce tayi saurin kau da zancen da fad'in "goben kamar da yaushe zaku tafi, ko ba'ason rakiyarmu airport ne?" Ya Nura yayi murmushi yace "a'a shidda nasafe zamu tashi, addu'arkuma ta isa, Mama dan Allah kidinga yimin addu'a, kada kiyi fushi dani ako da yaushe...." ya'kareshe maganar kamar zaiyi kuka, dai-dai sanda wayar hannunsa takama ringing, yana ganin number Haby ce da rawar jiki yad'aga, cikin tsiwa da rashin mutunci take fad'in "idan kagama gaisawa da tsohuwar taka, sai kazo ka gaida tawa ko, sha-sha kawai" takashe wayar, da rawar jiki yafice daga d'akin ba tare daya sake cewa komaiba. Mama tayi ajiyar zuciya da fad'in "nidai ancuceni wallahi, Allah ya isarmin" Aunty tace "addu'ar daya ro'ka itace yadace mudinga yimasa ko da yaushe, domin itace kad'ai zata fidda shi daga halin dayake ciki ayanzu" "hakane gaskiya kika fad'a" Mama ta bata amsa, Aunty takau da hiran da kawo wata hiran daban, dan kada Mama tasa damuwa acikin ranta. Haby ta dubi Momynta dake tsara mata kwar-kwasa da yanda zata janye hankalin Nura akan kowa, tayi tsaki kawai tana binta da kallon wula'kanci, can tayi murmushi tana fad'in "ai ni duk Momy bazan zauna ina wannan abunba akan d'a namiji, domin ni yanzu nagama da Nura bana bu'katar dukkan wad'annan" Momy tace "iyeee kaji yarinya 'yar zamani wai menene sirrinne?" dai-dai sanda Ya Nura yayi sallama falon, wani kallo Haby tawatsa masa wanda yasanyashi rud'ewa da rawar jiki ya'karasa yana bata ha'kuri, awula'kance tami'kamasa jakarta tana fad'in "ungoni maza kaimin mota kadawo bana son 'bata lokaci kuma" cikin tsawa tayi maganar, Ya Nura yakar'ba jiki na'bari yafice, Haby da Momynta suka tafa, MOmy tace "d'iyata taya hakan tafarune?" Haby ta ta'be baki da fad'in "wannan kuma sirrinane, wanda jinsa dai-dai yake da rasa ranki, zamu wuce malesia idan munje zankiraki a sim nawa banson yawan kira kinsan bana son takura" Momy tasaki baki tana duban 'yar tata cike da mamaki koma mafarki takene, Haby ta ajiye mata,bandir 'yan duba akan cinyarta tace "ga wannan akashe nasan shine burinki" tayi murmushi kawai, Momy tace "ah aishikenan kitara mana da yawa, tunyanzu nasamu kyautar wannan bare kuma zuwa gaba" Haby tayi murmushin da iyakacinsa fuska kawai, tana duban Momynta dake lissafin kud'in, tasake zaro wasu rafar tace "ungo kirabawa Kamal da Khaleel" dai-dai sanda Nura yadawo tace "muje ko" suka fito Momy na aikin sanya musu albarka. ko sallama bata,bari sunkoma sunyiwa su Mamaba tace su tafi, haka yata da Mota yabar gidan, dan ma Allah yasa Abbansa bayanan addu'ar da yaitayi aransa kenan, har suka tawo kuwa baidawoba, sai bayan tafiyarsu ya dawo Mama ce tasanar masa da zuwansa yayi farinciki sosai, domin shi aganinsa alkhairi yahad'a, sai awaya yakira Nuran yayi masa addu'ar fatan alkhairi. 6:00am shidda dai-dai jirgin Malesia yad'aga, Khamisne ya kaisu airpory, bayan magiya da Ya Nura yayi tayima kan dole yazo yakaisu dominshibaki d'aya yagama tsanar Haby, bayan haka kuma yayarda yakawosune kozai samu makama domin sanin wacece Haby?, sai dai babu abinda yasamu har jirgin nasu yad'aga zuwa malesia, yadawo gida cike da tunane-tunanen ta inda yakamata yafara. 《MALESIA》 Airport d'in malesia fasinjojin tane suke sauka a hankali, garin gwanin ban sha'awa da d'aukar ido, cikin fasinjojin har da Ya Nura da Haby, Haby tasha'ki iskar malesia tare da sauke wata ajiyar zuciyar, motocin sojoji ukune manya ajere sai 'kananu biyu sune sukazo tarbar Ya Nura, abin yabawa Haby mamaki, ashe shid'in wani babbane a sojojin abinda bata ta'ba saniba sai yau, suna saukowa sojojin sukahau sara masa cike da girmama aka bud'e masu murfin motar da zasu shiga, kayansu kuwa d'aya motar daban aka sanya, driver yaja mota, basu tsaya ko inaba sai barrek d'insu, anan akaiwa Ya Nura masauki na musamman gida guda nasa, duk inda suka wuce sara masa ake, gateman kansa sojane banda wad'anda ke shawagi aharabar gidan. Haby bata 'karatsinkewaba sai da suka shiga gidan, taga gida kamar a film nanfa ta cika da murna da farinciki, har tafara ayyana irin rayuwar da zatayi agidan. bayan sunyi wanka sun shirya kukune yazo yana sanarmusu angama shirya abinci bisa daining, can suka nufa nanfa Haby taga abinci kala-kala wanima batasan mene ba illa kawai takalla. ciyar da junansu sukai cike da so da 'kauna, domin Haby jinta take wata daban, auren Ya Nura yaga mata komi, saura cin duniyarta da tsinke kawai, da suka kammala d'aki suka nufa domin yin barcin gajiya. [07/01, 22:06] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book 1 mallaka-----QURRATUL-AYN 24 《NIGERIA》 Bayan kwana uku da tafiyarsu Ya Nura,misalin 3:30pm Abbane zaune falonsa bisa daya daga cikin kujerun d'akin, hannunsa ri'ke da jarida, fuskarsa d'auke da wani farin glass wanda da dukkan alamu na 'karin ganine, Mamace tayi sallama tashigo, Abba ya ajiye jaridar hannunsa yana amsa mata, tami'ko mai lemon data tsiyaya awani cup na glass, yakar'ba yana godiya, tazauna bisa kujerar kusa da shi, sai da yasha ya ajiye sannan tafara magana da fad'in "Alhaji yaronnan kuwa ya kiraka tunda suka tafi shiru babu wani labari, duk nashiga damuwa wallahi" Abba ya d'anyi murmushi da fad'in "bai kiraniba, amma nasan zaikirani domin inaji ajikina lafiya suke, sai dai idan aikine yari'keshi" Mama tace "to Allah yasa dai lafiyan" amin " Abba ya furta tare da d'aukan jaridarsa yacigaba da karanta, turo 'kofar falon aka sakeyi, cikin sallama, Mama ta amsa, Momyce fuskarta fal murmushi tashigo hannunta ri'ke da waya, ta fara fad'in "Alhaji gashi Haby ce takira waya, tace abaka" Abba yakar'bi wayar yana dariya yakarata bisa kunnansa, yana fad'in "kuna lafiya dai ko?, to masha Allah ina Nuran yake?" can tabashi amsa da fad'in "yafita office tun safe, idan yadawo nasanarmasa yakiraku" "toto Allah taimaka ki gaisheshi", takashe wayyar. Abba yami'kawa Momy wayar dake tsaye, ko zama bataiba tafice, Mama tad'anja tsaki aranta kawai, Abba yace "kinga abinda nake sanarmiki ko, nasan ai suna lafiya dama, shid'in aikine yayi masa yawa, kinsan aikin can da nan ba d'ayaba" Mama tace "uhmmm" kawai tama rasa mai zatace, hakan yasanya tami'ke ta koma d'akinta. "Ammy waike ina 'yan'uwanki sukene? kowa naga 'yan'uwansa nazuwa gurinsa amma bandake, Mama nada nata Auntyma haka, Momyn Haby ma haka, kuma naga ke duk bakwa kama ke kamarku d'aya da indiawa kuma.....!" "ke ya isa, meye haka Nuratu? bana habaki yimin irin wad'annan tambayoyinba?" Nuratu ta tura baki gaba "amma Ammy Allah nidai inason ganinsu, nifa naga bana kama dasu Nana, kuma kowa haka yakece dake da 'yan'uwanki nake kama, wai kyau yayimin yawa sai kace aljana, hakane Ammy?" " ya Ilahi ohhh! ni Amina..!wai ke bakyajin maganane? nace ban saniba" "kinga idan bazaki rufemin bakiba zaki d'agani wallahi" Nuratu tasake gyara kwanciyarta bisa cinyar Ammynta, tana sonyin magana, amma tasan Ammy bazata kulataba, hakan yasanyata yin shiru tacigaba da kallonta. 《MALESIA》 'Dinnn....d'innnn..! 'karar 'kararrawar 'kofar falon ketashi wanda da dukkan alamu ba'kine, Haby dake kwance bisa tafkeken gadonta, cikin wani lallausan bargo tana aikin barci, tafarka cike da barci idonta, ta zuro 'kafafunta tasanya wani takalmi mai taushi, daga ita sai wata guntuwar rigar barci tafito zuwa falon tunaninta Nurane cike da tsawa take fad'in "wai wayene?" "bud'e kigani" Haby tabud'e 'kofa da sauri, jin muryar wadda bata zataba, ai kuwa Zulynce da gaske, su ukune Zuly sai Baby sai wata da bata santaba, suka rungume juna cike da murna, saiga Nabeel tsaye bakin 'kofa, nanfa ta'kara cika da mamaki sosai, shima sund'an cafke irin na ri'ka'k'kun 'yan barikinnan, kafin su zauna kuku yafara yimusu serving d'in abin ta'bawa. Zuly ta'karewa falon kallo, ta dubi Haby tana fad'in "shegiyar irin wannan daula haka, ai dole kimance da mu" Bby tace "wallahi kuwa, jidai yanda ta'kara kyau" NB yace "duk za'kin sabuwar zuma, tsohuwar zuma tafita" suka sanya dariya baki d'aya, yayin da Nabeel keta bin Haby da wani irin mugun kallo, wanda duk sai da suka fahimci kona menene, nanfa suka fara tsokanarsa Zuly tace "kai malan kamai da maitarka kasan gidan wanda muke dai kada kaja duk aharbemu" Haby tasanya dariya da fad'in "shid'in banza" suka sake sanya dariya, Nabeel yace "ai wallahi naji dadin shirya plant d'in zuwanmu", Haby tace "baku kainiba". Zuly tace "duk ba wannanba muyi abinda yakawomu, Haby ga Sholy nan, itace wadda nakawo muki matsayin 'yar aiki, kasancewarmu mijinki duk yasanmu ma dinga zuwa, amna itama Sholy 'yar hannuce sosai zakiji dad'in harka da ita" "wowww Wallahi kin kyautamin sosai, daman ina cikin kewa wallahi, har dai idan wancan saunan yafice aiki" suka sanya dariya, Nabeel yace "to ni ya za'ayi dani" Haby tad'an harareshi da fad'in "wuce bedroom muyi magana, sud'an jiramu" Bby tace "ayi haka kuwa?" Haby tayi dariya tami'ke tana fad'in "gobe ko jibi kuma saimu tattauna daku" suka sanya dariya, Sholy ta bud'e jakarta ta fiddo da kayan shaye-shaye tami'kawa Zuly da Bby, Nabeel kuwa da Haby tuni sunwuce bedroom XX, (ohh Allah ka shiryamu, kashirya bayinka irinsu Haby amin, kan gadon mijinka kakai wani katon gardi Allah ya kyauta). kafin Ya Nura yadawo gida babu kowa kaman ba'ayi zuwansu Zulyba, domin Ya Nura baimasan suna 'kasarba, bare kuma har suzo gidan, agajiye yashigo cikin falon ya yada laptop d'in hannunsa da sauran tarkacen yakwanta bisa doguwar kujera dake falon, can Haby tafito daga kitchen hannunta d'auke da d'an flat da yankakkun kayan fruit aciki tanaci, zuwa tayi tazauna ahannun kujerar dai-dai kansa tafara magana "Nura...!" tafurta babu kod'an risinawa, Ya Nura yabud'e idanuwansa ahankali yana dubanta, batajira taji mai zaiceba tafara fad'in "daman maganace zamuyi, nasamu 'yar aiki itama 'yar nigeria ce, zata dinga tayani wasu abubuwan, tun da kai naga yanzu bana gaban nasamu mai tayani hira" Ya Nura yami'ke zaune yana dubanta kawai kafin yace "shikenan hakanma yayi, amma batun bana sonki bai tasoba kawai dai ayyuka sukaimin yawa amma insha Allah nan da 2week komai zai zama normal, kinji karki damu" ya'kareshe maganar yana d'anjan kumatunta, murmushi tad'anyi kawai, har yami'ke ya nufi bedroon d'insa, tabi bayansa da harara tare da guntun tsaki tana fad'in "ni dama kadauwa a aikin nahuta nima ai", haka kawai kwanakinan takeji auren da zaman gidan duk ya gundureta. zaune yake cikin wani katafaran office, kai kace wani had'ad'an gidane, kansa na jingine abisa kujera tana jujjuyashi idanuwansa kuma arufe, yad'auki tsayin mintuna ahaka, kafin yabud'e idanuwa ahankali ya janyo wayarsa dake kusa da laptop d'insa, yana daddannawa can yakara akunnansa, takama ringing daga can 'bangaran aka d'aga da fad'in "hellow" Ya Nura yayi murmushi, kafin yace "assalamu alaika, kana lafiya Khamis?" Khamis yace "kaine Master, nayi zaton kamance mune ai" Ya Nura yayi 'yar dariya da fad'in "a'a wallahi yazanyi namance daku, ayyukane sai aslow, amma yanzu alhmdlh, yanzudai bama wannanba dan Allah kamin sending number mutan gidanmu" Khamis yasanya dariya "wato numbet kowa kana nufin kamance ko ince ka goge" "ba hakabane wallahi bansan ya'akayiba, narasa dukkan contact nawa anyi formating wayar tawa baki d'aya, takanma yanzu nayi searching brain d'inane wallahi" ya Nura yabashi amsa, Khamis yace "ok zanyi maka sending dazaran munkammala waya, yakake fatan dai lafiya?" "lafiya 'kalau, yi katuromin dan Allah Mama nakeson kira, nasan tayi fushi dani" Khamis yace "to d'an gidan Mama" sukai dariya baki d'aya, Khamis yakashe wayar. [08/01, 16:09] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book1 mallaka----QURRATUL-AYN 25 《NIGERIA》 Mintuna biyar da kashe wayar text d'in Khamis yashigo, da sauri Ya Nura yabud'e ciki da d'auki, number Mamace sai ta Abba da aunty Hafsat, Mama yafara kira, tayi ringing kamar zata tsinke aka d'aga cike da tsiwa da fad'in "waye yake damunmu haka?" muryar Nuratu tadaki kunnuwansa , kafin ya bud'i baki yace wani abu ya jiyota tana fad'in "lahh Mama, anya kuwa number mutanece, kinga numbarfa wallahi kamar ta 'yan yankan kai da ake fad'a" Mama tace "kinga baninan, ke bakya gajiya da shirme" Mama takar'ba takara akunnanta tare da fad'in "salamu alaikum, wake magana?" jin muryar Mama yasanya Ya Nura dai-daita nutsuwarsa yafara fad'in "amin wa'alaikassalam, Mama...!kuna lafiya?" "Nura...! kaine kuwa nakeji yau?" "ehh nine Mama, yakuke yasu Ammy?" "lafiya 'kalau, amma mai mukai maka haka kamance damu" "a'a Mama kada kice haka, wallahi bayin kaina bane, baki d'aya narasa contact nawane, yanzuma Khamis nasanya yaturomin, ina fatan bakiyi fushi daniba?" "a'a fushi name kuma?, kawai dai munyi kewarka sosai, ga 'kannanka nanma, suna kallona jin kaine, kullum sai sunyi zancenka" murmushi ya Nura yayi, yace "akira Auntyna mugaisa, basu mugaisa suma" nanfa aka fara rige-rigen kar'bar wayar, Mama Hilal tafara bawa, sannan Rahma, sai Nana, Nuratu Mama ta aika kiran Aunty, tare suka dawo da Auntyn, Mama tami'ka mata wayar sun gaisa sosai kafin yakashe wayar cike da jindadi, haka suma su Maman, Nuratu kuwa fushi tayi ganin kowa angaisa dashi amma,banda da ita, hakan yasanya ta'kara jin haushin ya Nura da tsanarsa aganinta baya sontane, yafi son 'yan'uwansa, ranar kuwa barin gidan tayi tatafi wajen Ammynta. Ko da Abba yadawo gidan yaga Mama nata wal-wala yagane dalili, domin Ya Nura yakirashi yana gun aiki, shikanshi jinsa yake cike da nishadi bama suba, ranar anyitane cike da hirar Ya Nura dayi masa addu'a. "Ni gaskiya Momy dubu hamsim nake so, idan babu kawai ko gwal d'inkine kibani insiyar" Momyn Haby baki sake take duban Kamal, kafin tayi tsaki tad'auke kanta cike da takaici tana fad'in "wai kai wanne irin yarone, mai kake da kud'i haka?, naga jiya-jiyannan dubu goma kakafe nabaka, amma kacemin kacinyesu yau kuma hamsin ma sabida ta'barar taka tabun'kasa" Kamal yad'an cije le'be yana fad'in "haba Mom idan ba wajenkiba wajenwa zannema, please Momcy na" "sai kayi kuma" Momy tafad'a tana mai maida kallota bisa tv, zai sake magana Khaleel yayi sallama a falon, Momy ta amsa masa awuka'kance, tana harararsa, ya dur'kusa ya gaishe da ita, ta amsa kamar dole tana fad'in "soko kawai, wanda yarako mata, sai yanzu aka baka izinin zuwa gaisheni?" Khaleel yayi murmushi yana fad'in "a'a Momy nad'anyi wani aikine, yanzuma office zanwuce, ankiranine ankawo wasu marasa lafiya yanzu" Momy tayi ajiyar zuciya tana fad'in "to ina bu'katar dubu hamsin yanzu" Khaleel yad'anyi murmushi "yanzu babu awajena, sai dai idan nadawo aiki zanje banki inciromiki" "a'a amfani zanyi dasu yanzu, baga 'kaninka nan zauneba, kabashi ATM card d'in yaciromin yanzu mana" Khaleel yad'an dubi Kamal, kafin yace "a'a Momy nayi miki al'kawari zantawo miki dasu" "nice baka yarda daniba ko d'an'uwannaka, kafita daga idona wallahi Khaleel, yazanyi tunda anriga anshanye minkai, waya sanima ita uwar taka nawa kake bata" Khaleel yace "a'a Momy haryanzu Mama kwandala bata ta'ba tambayataba wallahi.." "kai da Allah rufemin baki, zaka bani card d'in ko inha'kura?" "a'a zanbaki bari ind'auko a d'aki" yami'ke yafita. Momy tabishi da kallo, kafin ta dawo da dubanta kan Kamal tana fad'in "bazan baka hamsin ba, sai dai ka kar'bi talatin" "haba Mom birthday d'in wani best friend nawanefa haba dan Allah kiban hamsin d'in, bayanma ATM za'abaki sai yanda kikaga dama zaki cira" momy tace "hakane kuwa d'annan tunani mai kyau" Khaleel yasake sallama yashigo, yami'ka mata card d'in yafice, Kamal yabishi da harar yana fad'in "wai Mom mai nayiwa Khaleel ne duk yabi yatsaneni, da alamu ko ganina baya sonyi" Momy tace "kada kad'au fushi dashi bayin kansa bane ai, aikin wad'ancen mubafukan matanne, sunrabani da d'ana mai 'kaunta, nima dandai kurwata tafi 'karfinsune" Kamal yayi dariya kawai, yana fad'in "kawo inje indawo dawuri zuwa anjina za'ayi birthday d'in kada namakara" Momy tami'ka masa tare da fad'in "dubu d'ari zaka d'auko" Kamal yace "to yafice" Khaleel nazaune cikin office, yaji 'karar alert, ya duba yaga anciri dubu d'ari, girgiza kai kawai yayi, yana yiwa Momyn tasu da 'yan'uwannasa fatan shiriya, domin yafahimci son abin duniya ya rufe masu ido. Kamal kuwa dub hamsin d'in yad'auka, yabawa Momynsu hamsin, nan ta'karashi fad'anta tagama, taha'kura, domin tasan halin Kamal ba bata zaiyiba. Zaune suke babban falo bayan sallar isha'i, Khaleel ne yatara yaran gidan suna hira, duban Hilal yayi yana fad'in "yanzu zantambayi kowa abinda yakeso yazama bayan kammala karatunsa idan ya girma" nan da nan yaran suka nutsu, takan Hilal yafara yace "to Hilal gaya mana abinda kakeson zama?" Hilal yad'anyi shiru, kafin yace "nafiso inzama professor" dariya su Nuratu suka kama yimasa, suna fad'in "kafin kazama, sai ka koma mai 'kafa uku"aka sake sanya darita sosai, har Hilal yayi fushi, ya Khaleel yajawoshi zuwa jikinsa yana rarrashinshi yabashi chocolate, sai akace ,saura Rahma "mai kikeso kizama kema, bayan kammala karatunki?" Rahma tace "inason zama 'yar jarida" nanma Nuratu har da tuntsurawa dan dariya, Nana tace "bakinki yagaji da surutu kuwa" Mama tace "babu komai Rahmata rabu dasu, su ai maji mai zasuce" Ya Khaleel yace "to Nanan mufa mai kikeson zama?" Nana tad'an karya kai cike da nazari kafin tace " Doctor, domin taimakon 'yan'uwana mata" ya Khaleel yace "woww Nanata, kece yakamata,nabaiwa kyauta yau" Aunty dake gefe ita da Mama tanajinsu tace "inda Nana ke burgeni kenan wallahi Nutsuwa, komai nata ba irinsu Nuratuba" Mama tace "akwai nutsuwa kuwa, badan tana biyewasu Nuratunba" sukayi murmushi,Ya Khaleel yace "to saura Nuratu, gaya mana naki burin ke kuma" Nuratu ta gyara zama tafara lissafi "nidai komema nazama inason taimakawa marayu da talakawa, sannan inason kai Mama Ammy da Abba saudiya, sannan duk wani d'an'uwa,nawa zan kaishi sannan kuma...." sai kuma tayi shiru, "sai kuma me?" Ya Khaleel yatambaya, su Mamama shiru sukai suna dubanta, murmushi tayi kafin tace "indai nayi arzi'ki ina da burin kyautatawa rayuwar duk wani na'kasa dani, naga yanzu masu kud'i basa zakka bare sadaqa, inason cika wannan burin, amma buri d'aya kuwa nabarshi araina" Ya Khaleel yace "ku tafa mata" nan yaran sukahau tafi, Mama tace "a'a kice Nuratun tawa ashe akwai hankali, nake kallon kinfi kowa wauta" suka sanya darita baki d'aya, nan kuma suka hau wasansu suna kwatanta yanda zasuyi rayuwarsu idan sun girma, Ya Khaleel yakwantar da kansa bisa kujerar dayake jingine ajikinta yana nazarin magan-ganun Nuratu domin sunratsa kunnansa sosai da zuciyarsa. [08/01, 16:09] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book1 mallaka-----QURRATUL-AYN 26 Yau su Nuratu amakare sukaje school, cikin su Rahma yacika da ruwa ita kuwa uwar garin ko ajikinta, tunkafin a'karasa tace asaukesu, suna sauka Nuratu tace "mubi ta baya muhaura sai kowa ya nufi class d'unsu, kunsan halin Uncle bilya wallahi da mugunta" sukace "to" ta bayan makarantar suka shiga, Hilal suka fara turawa da jakunkunansu, kafin su tura Rahma sai Nana, sannan Nuratu tad'ane katanga kamar biri, tana sauka sun sunkuya suna d'iban school bag d'insu, ai kuwa suka jiyo ana "kaiii daman abinda kuke kenan, kune kuka fasa bilo ko, dan kuji dad'in haurowa, yau na lahira sai yafiku jindad'i kuwa" tuni jikinsu yafara rawa ganin Uncle bilya ne, nan tahad'a kawunansu sai office d'in principal, principal yace "ai daganin wannan aikin Nuratune, dan haka yau babu duka, babu kiran kowa agidanku, tsalle zakuyitayi abakin office d'ina" Nuratu kuwa tacika tabatse abinta, kamar zata fashe Uncle bilya yasanyasu gaba sunata aikin tsalle har akatashi daga school d'in, sannan aka barsu suka tafi gida. ko da sukaje gida basu fad'aba, kashe gari kuwa ko da suka tashi daga barci, 'kafafun Nuratu 'kintakuwa sukai, sai lokacin Mama ta tsaresu sannan suka fad'a mata abinda yafaru, ranar Nuratu ko falo bata takoba, tasha kuka kamarme, har sai da Abba yakira principal yayi mai tatas, acewarsa zasu illata masa yarinya, principal yayita aikin bada ha'kuri, Ammy kuwa koda tazo dubata cewa tayi sunyi mata dai-dai, rashinji na Nuratu ai sai da hakan, nanfa ta'kara sanya kuka wai Ammy bata sonta. 《MALESIA》 zaune suke falo suna kallo, Haby nabisa carfet, shi kuma yana kan kujera, Sholy tazo tawuce zuwa d'akin Haby zata share, ai kuwa Haby tafara amai, Ya Nura yami'ke da sauri yana fad'in "lafiya, mai yasameki?" ganin da yayi zata galabaita yasanya Sholy ta taimaka masa ya gyarata suka fito da ita zuwa hospital, baki d'aya yagama tsorata, kasa zama yayi sai zarya yake, doctor nafitowa yabashi result na tabbacin tana da shigar ciki wata uku, habawa karkuso kuga murna wajen Ya Nura, tun a hospital d'in yafara kiran mutane yana sanar musu, har su Mama yakira da Aunty Hafsat, tuni gida yakaure da murna, Momy cewa tayi yakamata tatawo gida ai, ya Nura yace insha Allah, tarema zasu tawo, su Nuratu kuwa sai lissafin partyn da zasuyi suke, Mama tace "duk ba wannanba kuyi addu'ar dawowarsu lafiya, ta kuma haihu lafiya sai kuyi koma mene". tun da Haby tasamu wannan cikin Ya Nura babu zama kullum yana faman aiki akanta, motsi kad'an maitakeso?, baki d'aya yazama busy, ga aiki ga kuma Haby babu lafiya domin irin cikinnan tasamu mai laulayi. 『AFTER 3YRS 』 *****【BAYAN SHEKARU UKU】***** Aunty Hafsat ce a daining, yayin da mijinta ke zaune bisa dainig, da yaronta dabai wuce shekaru biyuba da rabi, tana aikin serving d'insu, bayan ta kammala ta zuba nata sunad'anci, Hamza ya dubeta cike da kulawa yana fad'in "naga damuwarki ta tsananta akwanakinnan, fatan dai lafiya?" Aunty Hafsat ta ajiye cofin dakw hannunta ta dubeshi "dole kaganni cikin damuwa mana, Mama ta tada hankalinta sosai akan Nura, da muwarta ta tsananta fiye da da" "to mene nasanyawa kanta damuwa haka?, dan baya zuwa kinsan yanayin aikin sauran'kasashen waje da nan bad'ayaba, ba suna wayaba?" Aunty Hafsat tad'anyi murmushi da iyakacinsa le'banta tace "rabon da Mama koma wani yaji muryar Nura da Haby yau shekara uku kenan, tun ina da cikin Hameed nad'an watanni, lokacin bansanma ina da shigar cikinsaba" Hamza yad'an zaro idanuwa waje, can yayi shiru yanata aikin jujjuta tea d'in gabansa, kafin yace "ga shawara mai zai hana muje jigawa gurin Baffa na tsamiya goma, insha Allahu kome ake ciki ko wanne hali yake ciki zamuji" Aunty Hafsat tace "hakanefa, wallahi tsahon shekaru damuwar Mama duk tasanya namance da Baffa" nan suka 'karasa karyawa, Hamza yafice office yana fad'in "idan nadawo zamuyi magana" har bakin motarsa suka rakashi d'ansu Hameed nayi masa,byee-byee. Nuratu tashiga d'akin da gudu tana fad'in "wayyoo Inna....!" tafad'a bisa cinyar Inna dake zaune bisa sallaya ta idar da sallah, Inna tace "ke ni d'agani, saikin karyani abanza, kullum baki da aiki sai tsalle bisa 'kafata,kin girma amma haryanzu bakibar halin yaraba" Nuratu tatashi tazauna tana fad'in "kaii Inna kullum sai kinmin gorin wannan 'kafar duk 'kashi, kuma wai na girma duka-duka shekara nawa nake?, 13yrs nakefa" "oho kekika santa" Inna tafad'a, Nuratu tasanya dariya tana fad'in "ashefa bakisan turanciba, to shekara goma sha uku nake nufi" Inna tace "sha uku kuwa angirma, mu'azamaninmu shekara goma muna d'akin mazajenmu" Nuratu tasaka dariya, Nanace ta shigo d'akin tana d'ingisa 'kafarta, hararar Nuratu tayi tana fad'in "nidai dan Allah kibani littafina" Nuratu tajanyo littafi acikin janinta tana karanta sunan "MATAR SO" Nuratu tasanya dariya da fad'in "kowacce mace ai daman matar soce" Nana ta fizge littafin da fad'in "wasu dai ba kowacceba" tafice a d'akin, Nuratu tasake mai da kai kan'kafar Inna tanayi mata tsiya. Tun bayan da Maman jigawa tayi aure anan kano, ta auri wani Alhaji mai mata d'aya da yara shida, matar mai kirki suna zaman lafiya sosai, yaransa kuwa nabawa Maman jigawa girmanta. shinefa Inna takafe akan kano zata dawo, Abba yaji dadi sosai, domin dama can bajin dad'in zamanta waje daban dashi yake jiba, nan da nan aka gyara mata d'akinta dake kusa da nashi ta dawo. su Nuratu kuwa sun kammala J.S, yanzu scondry zasu wuce ita da Nana, Rahma da Hilal ne dai sai nan da shekaru biyu zasu gama, yanzu suna gida abinsu Amma Abba yace nan da sati biyu zasu fara zuwa school, tofa su Nuratu angirma lollz. "ehhh gaskiya Nura yana cikin matsala sosai, addu'arku yake bu'kata sosai, domin shi ba asiri akai masaba tsafi, domin shi tsafi abune mai wuyar karyewa, sai andage sosai, amma kuma babu abinda yake gagarar ubangiji, domin mu dashi muka dogara" Aunty Hafsat suka dubi juna da mijinta, Baffa yacigaba da fad'in "shima kuma da nasa sakacin baya addu'a kokad'an, sannan yana da sanya son abu aransa sosai, da wannan damar akaci galaba akansa sosai, kuyi ha'kuri zuwa gobe insha Allah zanyi istihara akansa, duk halin da ake ciki zansanar miki awaya" Aunty Hafsat tace "to mungode sosai Allah ya'kara girma" sun shiga gidansa, sunyi salla suka sha fura, kafin su sake d'auko hanya zuwa garin kano, suna tafe suna tattauna maganganun da Baffa yasanarmusu, ana kiran sallar maghriba suka isa kano, kai tsaye gidan Mama suka wuce domin Hameed nacan, acan suka barshi. Aunty Hafsat tashige gida, shi kuma ya nufi masallaci?, tana shiga Hameed yakama yi mata oyoyo tad'aukeshi suka nufi d'akin Mama, lokacin Mama nakan abin sallah ta idar da sallah, Aunty Hafsat kasancewarta na hutun sallah zamanta tayi bisa gadon Mama, Mama nayi mata sannu da zuwa, nan tafara sanarwa Mama dukkan abinda Baffa yafad'a mata, Mama kamar tayi kuka dan takaici da tausayin d'annata, nanta sake kallon gabas tana sake koro addu'o'i akansa akan Allah ya shiga tsakaninsa da ma'kiyansa yakarkato mata da d'anta zuwa garesu. [09/01, 22:31] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book1 mallaka-----QURRATUL-AYN 27 《MALESIA》 Abubuwa da dama sun faru azaman Haby da Nura koma ince suna kan faruwa, tunda Haby tasan tariga ta gana da Ya Nura, sai kuma tamai da kai akan harkokinta, yanzu babu 'kasar da bata zuwa dasunan kasuwanci, ayanda ta sanarwa Ya Nura kenan, sai dai abinda bai saniba shine, duk wani shaid'anci da bin maza tanayine ta wannan hanyar, da zaran zuly ta bugo mata waya tana sanarmata, anyi order kayan mata zuwa 'kasa kaza, to wasu hajiyoyinne ke bu'katar harka da ita a'kasar, ko kuma tace mata kayan maza zuwa 'kasa kaza to tasan wasu alhazawanne a'kasar ke bu'katarta. Haby ta'bud'e tacika tayi fam, kud'i sun zauna mata, yanzu bata kallon Ya Nura amatsayin komai, domin ayanzu bazai nuna mata kud'iba, sabida ana hayar Habyne kan naira mai gugar naira ahar million guda, babu harkar da Haby batayi tun daga kan lesbian har zuwa kan mazan, ga uwa uba babbar 'kungiyarsu data bun'kasa ako ina, domin da bazar 'kungiyar suke taka rawa acewarsu baza'a ta'ba gano sirrinsuba, wannan abubuwan da Haby keyi, duk yana daga cikin umarnin 'kungiyane domin haka harkokin 'kungiyar yake koma waye yake ciki, abinda zaiyi kenan namiji ko mace, Haby tasamu damar fin kowacce mace dake cikin 'kungiyarne, kasancewar dukkan abinda aka sanyata tanabi, kuma sannan ta bawa 'kungiyar had'inkai 100%, kuma tabasu dukkan abinda sukeso. Ya Nura kuwa haryanzu baisan su Zuly na malesia ba, haka kuma baisan abinda ke tsakanin Sholy da Haby ba, haka kuma baisan gaskiyar cin amanar da Haby keyi masaba. a halin yanzuma Haby nada motar kanta har guda biyu nakusan million shida-shida, da sunan da kud'in kasuwancinta tasiya. Yanzu Haby babu ruwanta da Ya Nura taharkar auratayya idan kuwa yana bu'kata sai yabiya, daya gama abinda zaiyi zatace masa barci takeji, da zaran taje d'akinta to sholy zata kira, suyita harkarsu shed'an na'kara kad'a musu gangarsa, domin yariga yagama shinfid'arsa acikin zuciyoyinsu, har takai takawo ko yana zaune afalone sukan shige d'akinta surufo 'kofa suna harkarsu, sukwana tare abinsu, harka da Haby keyi da Sholy ya'kara bud'e idanuwanta sosai, har take ganin su Zulyma 'kananun kwarine, yanzu harya zamana bama tason harka da maza sosai sai mata musamman Sholy, sabida yanzu a'kungiyarsuma ta d'aura musu aure tare, zuna zaman miji da,matane (subhannallaha, astagfirulkah wa'atubi ilaik). Ya Nura kuwa idan ba wanda yasanshi sosai ba, bazaka iya shaidashi ba, yayi fari sosai yad'ashe, yad'an rame kad'an, sai hakan kuma ya'kara masa kyau sosai loll. ya Nura yana harkokinsa kawai, amma yamance da yana da 'yan'uwa a nigeria, asalima yamance cewar nigeria mahaifarsace, an mantar dashi kowa da komi, illa aikinsa da Haby sune kad'ai bai manceba. Haby kuwa bawai tamance da kowa bane, a'a kawai dai aganinta yanzu tafi 'karfinsu, tunawa dasu zai iya wargaza mata duk wani shiri natane, sannan za'a iya fahimtar halin da take ciki, hakanne yasa tayi banza da duk wani nata, tasanya harkokin gabanta kawai takeyi. (NASAN MASU KARATU ZASUCE INA CIKIN DA HABY KE DASHI?, KARKU DAMU KUDAI KUCIGABA DA BIBIYATA, ZAN WARWARE MAKU DUKKAN ZARE DA ABAWA NAN DA LOKACI KA'DAN). 《NIGERIA》 Tsaye yake cikin harabar gidan, jingine jikin motarsa ba'ka, cikin 'kananun yara blue d'in riga da ba'kin jeans, hannunsa ri'ke da waya yana daddannawa, Hamzane yafito cike da fara'a yabashi hannu suka gaisa, kafin yace "sai dai ban shaidakaba" yad'anyi murmushi kafin yace "Khamis ne abokin Nura, nazo wajen Aunty Hafsat ne" "ohhh Allah sarki, shigo mana" Hamza yace, suka jera da Khamis har zuwa cikin falonsu, yace "bismillah zauna, bari inkirawo maka ita" yahaura zuwa sama, d'ansu Hameed yazo da gudu yad'ane cinyarsa yana fad'in "uncle yakake?" Khamis yace "lafiya, yasunanka?" "Abdul-hameed, amma Hameed akecemin" "woww suna mai dad'i" Khamis yafad'a, Aunty Hafsat tasauko tana fad'in "a'a kace babban ba'kone agidan namu, kazo kahad'u da d'an surutu ko?" Khamis yayi murmushi yana gaishe da ita, Aunty Hafsat ta amsa kafin tace "maza Hameed jeka wajen Dadynka yana kira" yaron yami'ke da gudu yahau saman. Aunty Hafsat ta kwalawa mai aikinta kira, sai gata da saurin, tace "maza kawowa ba'kona abin ta'bawa" mintuna kad'an sai gata d'auke da 'katon tire taja table gaban Khamis tad'ora ta fita, Khamis yad'an zuba lemo yasha, sannan Aunty Hafsat tace "kaima ka'buya kamar abokin naka" Khamis ya ajiye cofin lemon yana fad'in "nasan dama zakuce haka, amma nidai 'buyana akwai dalili, kamar yanda nayi miki al'kawari, saura kad'an na'karasa cikawa" Aunty Hafsat tad'an dubeshi da fad'in "banganeba, al'kawarin me kuma kamin?" Khamis yad'anyi dariya kafin yace "maganar gaskiya daman nazone domin muyi magana mai muhimmanci" Aunty Hafsat tad'an gyara zamanta kafin tace "to Allah yasa inji alkhairi inajinka". Khamis yad'an muskuta yafara magana"nayi maki al'kawarin binciki ko halin da Master yake ciki idan baki manceba?" "ehhh inajinka" tafad'a a gaggauce, alamun ta matsu taji labarin. Khamis yacigaba da fad'in " tabbas nasamu labari akan hatsabibiyar matarsa, dukkan halin da Master yake ciki to Habyce silar jefashi, kafinnan yakamata ma kisan wacece Haby" yad'anyi ajiyar zuciya, ya cigaba da fad'in " shekaru uku kenan bana 'kasarnan, naje malesia batare da Master yasan inacanba, acan naga abin mamaki, idan baki manceba kinsan 'kawayen Haby ai? ZULY da BABY, to sudai bansamu wani labari akansuba, amma suma suna can malesian, sai dai abinda nafahimta Master baisan suna 'kasarba, dalilin daya sanya nasaka ayar tambaya akansu kenan, amma Haby yanzu tana fita 'kasashen waje sosai, london india america germany da dauransu, har nan nigeria tana zuwa da sunan business, amma a sirrance kinsan mai takeyi?" Aunty Hafsat ta girgiza kai "hayar Haby ake akan naira million guda, ga duk wanda yabu'kaci yin harka da ita, tana bin manyan alhazaine, da kuma hajiyoyi" "subhannallah" Aunty Hafsat tafad'a, "kacemin dai Haby mazinaciyace tsan-tsan kuma maci amana,to amma mai takeyiwa hajiyoyin?, shine abinda ban fahimcekaba" Khamis yad'auki cofin lemon daya aje d'azu yad'ansha kad'an, ya ajiye cike da murmushi yace "lesbian mana" "les...me..!?, kace Haby tagama 'kazanta, subhanallah, to yanzu ina cikin dayace tana dashi tahaihune?" Aunty Hafsat tasake tambaya "a'a ai ahalin yanzuma babu ciki agidansa bare kuma d'a ko 'ya" "zubewa yayi to kome?" wannan ne bansaniba, amma nima haryanzu bangama bincike akantaba, mutum d'aya nake nema shine kad'ai zai iya gayamin dukkan sirrinsu da kuma wacece ita kanta Haby d'in, shine Nabeel, to amma su kanshi nemansa suke basu ganshiba har 'kungiyarsu nemansa take" "wace irin 'kungiya kuma?" Aunty Hafsat ta tambayeshi, Khamis yace "ai duk abinda Haby keyi 'kungiyarsuce tasanyata, domin sunshiga wata 'kazamar 'kungiyane kawai sabida kud'i, shi kanshi Nabeel d'in Haby tayi harka dashine da umarnin 'kungiya domin wasu biyan bu'katu nata, haka shima Master 'kungiyar amfani take dashi sosai, don biyan wasu bu'katunsu" shiru falon yayi inbanda 'karar famka da AC dake tashi, sai 'karar tv kad'an-kad'an dake kunne, Aunty Hafsat tayi ajiyar zuciya kafin tace "wato dai Haby tazarce dukkan inda tunani zai kai, atunanina bokaye takebi, ashe ita mai gaba d'aya takeyi, da sake wallahi, amma baka tubanin Momynta tasan komai?" "babu abinda Momynta tasani akanta, asalima Momynta koda gidan boka bata ta'ba zuwaba dasunan wai mallake wani, tana amfanine kawai da makirci, aganinta iya wannan ya isa agun mace, indai tasan kanta, abinda Momy kawai takeso kud'i, akan wannan tarbiyar tad'ora Haby, gashi yanzu tazarce inda take tunani, 'kungiyarsu na sirranta abu fiye da tunanin mai tunani, nikaina ba'karamar wahala nashaba akan samin wannan d'an labarin kawai, duk 'kasar da Haby taje ina biye da ita, nasaka aka had'amin layin Zuly da nawa, bayan nayi basajar had'ata da wani abokina amtsayin zasuyi harka dashi, ta wannan haryar nasamu numberta, to kinji yanda akai" Aunty Hafsat tace "to yanzu ina kake ganin zamu sami shi Nabeel d'in?" "ehh to gaskiya wannanne bansaniba, amma inanan ina bincikarsa, ya'buyane sabida 'kungiyarsu Haby domin lokacin cika aiki yayi akansa, bansan ya'akai yagane sirrinsuba shima, domin shi kanshi baisan suwaye suba" "to Allah yakyauta yashige mana, su kuma Allah yatona asirinsu, yanzu haka nasanya anata addu'a, Baffa yatabbatarmin nan da d'an lokaci zamuga Nura acikin gidanmu" Khamis yace "amin Allah yasa, Allah tabbatar mana" suka amsa da "amin" dukansu. [10/01, 21:32] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: 《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》Book 1 mallaka-----QURRATUL-AYN 28 "amin" suka amsa baki d'ayansu, suka cigaba da tattaunawa akan matsolin Ya Nura da Haby, kafin su kama hiran duniya kuma, Aunty ke tambayar Khamis shi yaushe zaiyi aurene? Khamis yad'an sosa 'keyarsa yana fad'in "aini baki d'aya aure yaficemin araima Aunty, badan raya sunnaba danace naha'kura, amma ina ganin kezanbawa za'bin matar da zan aura, danni yanzuma tsoron Matan nake" suka sanya dariya Aunty tace "Allah shige mana gaba dai" nan sukaita hiransu, har Hamza yasauko shida d'ansu Hameed aka cigaba da hiran dashi, nan Khamis ya wuni, kafin yayi musu sallama yatafi, tare dayiwa Aunty al'kawarin duk halin da ake ciki zata jishi, ko da awayana. 《MALESIA》 HABY, ZULY, BABY, SHOLY, Zaune suke cikin wani dan'kareren falon, wanda kallo d'aya zakayi masa kasan naira tayi kuka acikinsa, falon shiru kai kace babu wasu halittu aciki, inbanda 'karar fanka da AC dake tashi kad'an-kad'an. Haby tayi ajiyar zuciya tana bin dukkansu da kallo kafin tace "Ina cikin damuwa sosai, narashin sanin inda NB yake, tsawon watanni uku kenan ko labarinsa babu, gashi 'kungiya ta matsa akan anemoshi, yanzu ni INA ZANGANSHI?" Zuly ta tauna cimgum d'in bakinta yaba 'kara 'kasss, ta sauke 'kafarta daga karkad'a tan da take kafin ta gyara zama tana fad'in "abin da mamaki kuwa, domin Nabeel baya tafiyar kwana guda batare daya sanarmana ba, amma bakwa tunanin yagano sirrinmune?" Sholy ta zu'ki shisha da 'karfi tafurzar da haya'kin yabi iskar wajen yabaje, ta dubesu da fad'in "mai yasa kuke da saurin karaya da tsorone, kunmance ko da Nabeel yagane komu suwaye, ya kuma gane sirrinmu, 'karyarsa yatona asirinmu" Haby tace "hakane, amma kinsan dolene mudamu, domin saura sati guda agudanar da aiki akansa, wanda shine cikar dukkan burinmu" Baby da tunda suka fara magaba bata sanya bakiba, ta dubesu cikin yau'ki, kamar ana mata dole akan magana, tace "ni kuwa ga shawara, mai zai hana murabu da wani batun Nabeel, musamo wani mana, sai kace SHI KA'DAINE NAMIJI?" Zuly tace "hakane mubi shawarar Baby kawai, aha'kura da aikin yanzu har anemo wani da zai maye gurbi Nabeel" Haby tace "to taya 'kungiya zata yarda da wannan batun?" Sholy tasanya dariya tace "kinji halin naki Haby, saurin karaya da tsoro, kece zaki sanarwa 'kungiya komai, domin 'kungiya naji dake kuma anajin maganarki sosai" Baby tace "kwarai kuwa, ko kinmance Haby kece first lady acikin 'kungiya?" Haby ta girgiza kai tana dad'in "to shikenan, amma kunsan burinmu bazai cikaba nawannan shekarar, tunda anfasa aiki da Nb, sai dai zuwa shekara mai zuwa,idan ansamu wani" "ehh to meye aciki, mutara wata shekar mana" cikin had'a baki suka baiwa Haby amsa. (kunjifa kai kace sune da rayuwarsu, sun tabbata zasukai anjima ma bare gobe zuwa shekara mai zuwa, Allah kasa mufi 'karfin zukatanmu amin). Nan Haby da Sholy sukawaisu Zuly sallama suka nufi gida. *****BAYAN WATA 'DAYA*****(After 1mnth) 《NIGERIA》 ***KANO*** Bayan sallar maghriba Kekenapep ne yayi parking adai-dai 'kofar gidan, Baba mai gadi dake zaune bisa binci dake wajen ya'kurawa napep d'in idanuwa, domin ganin wanda ke ciki, ya ziro 'kafafuwansa yafito, fuskarsa sanye da farin glass, yana sanye da kakin sojoji a jikinsa, ya rataya jakar systerm d'insa, Baba mai gadi yayi masa 'kuri da idanuwa yanayi masa kallon sani, ya zaro wallet d'insa ya d'auko d'aya daga cikin kud'in wallet d'in yami'kawa mai napep, mai napep yayi murmushi yana fad'in "yalla'bai bansan wannan kud'in bafa" murmushi shima yayi kafin yacw mai "kaje ka canja, wannan guda d'ayan amatsayin dubu ashirin da biyu take, idan kacanja kad'auki dubu goma nabar maka dubu sha biyun kai kayimin sadaka, idan kana tunanin cutarka zanyi kuwa, kaga inda ka ajiyeni dai, nanne idanmu mazo zanbaka irin kud'inku nanan, yanzu banida canjin nigeria ne, wannan kud'in malesia ne" mai napep yawashe baki, yana godiya yakar'ba yayi gaba. Baba mai gadi yataso da gudu yana fad'in "sannu da zuwa yalla'bai, ai ban shaidaka bane wallahi, sai da naji kayi batun malesia, fatan kazo lafiya?, gida kowa nacike da kewarka" ya Nura yace " lafiya 'kalau" Baba mai gadi yakar'bi jakar systerm d'in suka nufi cikin gidan. lokacin kowa nazaune falo suna hira, suka tsinkayi sallama bakin falon, kowa yamai da kallonsa bakin 'kofa, ganin wanda yad'aga labulen ya shigone yasanya duk mutanan dake falon mi'kewa tsaye cike da kad'uwa suka furta "NURA....!" Ya Nura ya'karasa cikin d'akin, yaje yarungume Mama siraran hawaye suka ziraro bisa kuncinsa, ganin hakan yasa Gateman aje masa jakarsa yafice, cike da farinciki, Mama tad'an bubbuga bayan Ya Nura, kafin tad'agoshi tana 'kare masa kallo, cike da farinciki ta furta "Alhamdulillah, Allah nagode maka daka nunamin wannan rana, ka dawomin da d'ana, ai daman Allah maji rokon bayinsane, addu'ar bawa bata ta'ba fad'i, zo zauna" ta zauna bisa,kujera tasanya Ya Nura gefanta, Aunty tace "Nura da gaske kaid'inne kuwa?" Ya Nura yagyad'a kai cike da murmushi a fuskarsa, nan akahau gaisawa, Khaleel yadawo kusa dashi yazauna a'kasa suna hira,Hilal da Rahma ma zagayeshi sukayi suna kallonsa. jin hayaniya yasanya Nana fitowa daga d'aki tana aikin karatun littafi, tafito hannunta ri'ke da Hameed dayazo hutu, da gudu ta'karaso tana d'ingisa 'kafarta, zuwa tayi tarungume Ya Nura cike da murna, Ya Nura yajanyeta ahankali ya dubi Mama da fad'in "yarannaki sungirma sunyi hankali" Mama tayi murmushi tace "ba doleba shekara uku zuwa hud'u" Hameed ne ya rungumeshi kamar yanda yaga Nana tayi masa, ya Nura yad'aukeshi yana murmushi, yace "wannanfa? nasan dai d'anane, sai dai bansan wanda yahaifaminba" Ya Khaleel ysce "anbaka gari, kafad'a 'DAN WAYE?" ya Nura ya'kurawa yaron idanuwa kafin yace "kai boy ya sunanka?" "Abdul-hameed, amma Hameed akecemin" ya Nura yayi murmushi ya dubi Khaleel yace "nagane yanzu ai, d'angidan Hafsat ne, babban jika muka samu ashe da bana nan" aka sanya dariya Nana tace "bamu yardaba, dama kasan sunan da Aunty keson sanyawa yaronta shiyasa yana fad'a kagane" bai bata amsaba illa murmushi kawai da yayi, Mama sai bin d'annata take da kallo, tasan damacan ya Nura bamaison surutu da hayaniya bane, amma sai taga yanzuma yafi zama silent akan da. Momy dake zaune cikin falonta ita da Kamal sukaji hayaniya tayi yawa a falon, suka fito dan ganin abinda yake faruwa, ganin Nura zaune cikin falon ya girgizasu Momy tace "A'a Nura yau kaine a gidan?, ba'kin malesia, ina Haby take kuma?" ya dur'kusa yagaisheta kafin yace "ai ni kad'ai nazo, ita taje london ne" jin haka yasanya kowa sakar baki, tare da tambayar "london kuma?" "ehh business take, zatazo nan da kwana biyu" Momy tawashe baki tace "a'a ikon Allah kace Haby anzama hajiya" Mama kuwa baki d'aya kanta yakulle, Aunty ce dai tayi murmushi kawai na takaici, cike da tausayawa Nura, domin tasan komai Aunty Hafsat ta sanarmata Mamace dai batasan dawar garinba. kiran sallar ishar da akaine yasanya Ya Nura da Khaleel mi'kewa suka nufi masallaci, Nana tace "Rahma kuzo muje gidan Ammy musanarwa Nuratu zuwan Ya Nura" suka fice cike da d'aukin kaiwa Nuratu kyakkyawan labari. [10/01, 21:55] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》*Book1 mallaka-----QURRATUL-AYN *29* *KASHE GARI* kashe gari misalin 'karfe goma da rabi nasafe, Ya Nurane sanye cikin wani farin yadi, wanda ana iya hango best d'insa ta ciki sabida shara-sharansa, 'kafarsa sanye da wani ba'kin takalmi, idanuwansa cikin farin glass daya 'kara masa kyau, sannan yad'ora ba'kar hula akansa, duk da ramar dake baiyane ajikinsa hakan bai hana kyawunsa baiyanaba. ya fito daga d'akinsa ya kulle, mai makon yayi cikin gida gate ya nufa, suka gaisa da mai gadi yafice kai tsaye tsallakawa yayi yanufi gidansu Nuratu. Da sallamarsa ya shiga cikin gidan, Ammy dake falo ta amsa masa cike da farincikin ganinsa, yazare takalminsa yashiga a'kasa yazauna yana gaisheta ta amsa fuskarta cike da fara'a, tana tambayarsa anzo lafiya? ya amsa da "lafiya 'klau, naso shigowa ajiyan to gajiya tahanani wallahi" "babu komai, hutu na dakyau ai" Ammy tafad'a. ta mai da kanta cangefe tana fad'in "ke bakya ganin yayan naku, amma ko gaisuwa babu" sai lokacin Ya Nura yakai dubansa zuwa inda yaga Ammy nakallo tana magana, Nuratuce kwance bisa doguwar kujera, da wani 'karamin littafi ahannunta mai suna (HISNUL-MUSLUM) tana karantawa, tana sanye da wani riga da wando pink, wandon yad'an kamata, rigar kuma daga sama zuwa cikinta dai-dai jikinta, daga 'kasa kuma tabud'e antsaga gefe da gefanta, tayi rolling da blue d'in mayafi, jelukan kalbar kanta sunzubo abayanta, Ya Nura yayi murmushi kawai Ammy tace "magana nake maki, kuma sannan kiwuce kikawo masa d'an abin ta'bawa, da dukkan alamuma baka karyaba" Ya Nura yasake murmushi yace "wallahi kuwa, cewa nayi bari inzo mugaisa naje inyi breakfast daga baya, domin ina shiga gidan zasu shagaltar dani da hira" "ai dole munyi kewarka sosai ai" Ammy tafad'a, Nuratu ta ajiye littafin ta ziro 'kafafunta da suka sha jan lalle 'kasa, tana tura baki da 'ku'kuni ta furta "ina kwana" "ban ganshiba" Ya Nura yabata amsa, yana dubanta, Nuratu ta murgud'a masa baki, tazo ta wuce ta gabansa zata fice, yad'an bugi 'kafarta tayi kaman zata kifa, sai kuma ta tsaya tajuyo ta dubeshi da harara ta fice, Ammy tace "tsabar masifa har zata fad'i, ni dama kinfad'in mara kunya kawai" Ya Nura daya bita da kallo yadawo da dubansa gun Ammy yana fad'in "haryanzu dai Nuratu na nan yanda nasanta, tsiwa da rashin kunya bai raguba, sai girma dai da akai" ya 'karashe maganar yana janyo littafin data ajiye yaduba, tare da murmushi aransa yana fad'in "ko yaushe rabonsa da karanta wannan litrafinma, bare azo batun karatun al'qur'ani" ya mance, Ammy ce tadawo dashi daga tunanin da fad'in "ai Nuratu na nan yanda kabarta, sai dai girma da akai, inda take burgeni kad'ai waje d'ayane, bata wasa da addininta, idan ba karatun boko ba, babu ruwanta da karance-karancen banza, tafiso tad'au littafin addini tana biyawa, amma idan tsiyarta ta motsa kai kace aljanune akanta" sukai dariya tare, Nuratu tashigo da sallama ta ajiye babban faranti agabansa, amma fuskarnan tata atur'bune, kamar zata sanya kuka, ta ajiye takoma inda tatashi tayi kwanciyarta, Ammy tace "au bazaki zuba masaba" ya Nura yace "a'a barta,na zuba" Nuratu tami'ke da 'ku'kuni tana fad'in "ya zuba mana ai yana da hannun dukan mutane, amma abinci ace sai an zuba masa" tafad'a tana mai ficewa daga falon tayi waje abinta. ya Nura dariya yayi yace "au kice ri'kona ake?" Ammy tace "share shirman waccan kai dai ci abincinka" ya Nura yabud'e flask d'in ya tsiyayo, sai yaga ashe kunun gyad'ane, ga soyayyan dankalin hausa da kwai daban, sai wani had'add'an danbun nama daketa tashin 'kamshin bai saniba yanaci suna hira da Ammy sai ganin kwanuka yayi agabansa, suka sanya dariya da Ammy, Ya Nura yace "wallahi abincin yayi dad'i, gashi daman har namancw rabona da cin irin wannan girkin, shiyasa nakeson dawowa nigeria ai, kodan cin girkinki Ammy" Ammy tayi murmushi kafin tace "kai dai canti kake kawai, to wannan ba girkina bane, girkin 'yar gidan takace" Ya Nura yad'an zaro idanuwa waje yana fad'in "wai Nuratuce da wannan girkin, a lallai yarinyar taki ta girma" Ammy tace "ai kuwa, dan yanzu nan gidan da gidan Mama muna kwasar garar girki, dan bata da muwa da aiki ita dai tayi girki ace yayi dad'i, shine burinta" Ya Nura yayi dariya yana girgiza kai. sunsha hira da Ammy sosai, dan sai wajen shabuyi yayi mata sallama yafito ya koma gida. Da sallamarsa yashiga falon lokacin har Aunty suna falon, yana shiga Nuratu na gaban TV suna game da Rahma yayi sallamar, kallo d'aya yayi mata yad'auke kansa, Mama ta bishi da kallo tana fad'in "yau kuma ina kaje haka tun safe?" "ina wajen Ammy wallahi muna hira, sannan naci wani abinci mai shegen dad'i" Mama tayi murmushi tace "ai nama gane girkin wadda kaci, girkin Nuratune" Ya Nura yasake duban Nuratu, amma wannan karon fuskarsa ad'aure yake dubanta, itama d'aure fuska tayi tami'ke daga game d'in tayi cikin d'akinsu tabarsu nan falon. Ya Nura yadawo da kallonsa, kan Mama yana fad'in "wai mai nayiwa 'yar taki take jin haushina?" Mama tasanya dariya tana fad'in "wakenan?" Nuratu mana" Ya Nura yabata amsa, Mama tace "ai daman tace indai kadawo babu ruwanta dakai, bazata shiga harkarkaba bare kace zaka harbeta" suka sanya dariya baki d'ayansu. Ya Nura yace "bari inje gidan Hafsat Hilal yarakani domin ba lallai ingane gidanba" Mama tace "ai kuwa dai ka gaishe da ita to, Abbankuma yana hanya yau shida Inna" ok Allah kawosu lafiya kafin sudawo nadawo ai insha Allah" yaja hannun Hilal suka fice, Aunty nafad'in "kagaishemin da ita". [11/01, 22:13] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》*Book1 mallaka-----QURRATUL-AYN *30* Baki sake cike da mamaki Aunty Hafsat ke duban Ya Nura, dake tsaye cikin falon, Ya Nura yatako da murmushi ya zauna bisa kujera tare da fad'in "rufe bakin haka, nine dai Nura, yau a gidanki" Aunty Hafsat tazauna tana dariya, aranta kuwa godiya take ga Allah daya amsa addu'arsu, dan jiya da Aunty tayi waya tasanar mata, jin batun tayi kamar wasa, sai yanzu da taganshi ta gas-gata. suka gaisa cike da farincikin ganin juna, Aunty waya tad'auko, tahau daddannawa takara akunnanta, ringing d'aya aka d'aga cikin murmushi ta furta "kazo yanzu kaga abin mamaki" takashe wayar, tunanin Ya Nura,Hamza takira mijinta, sai kuma yaga mijinta yasauko da murmushi yana fad'in "a'a kice yau gidannamu cike yake da manyan ba'kin malesia?" ya Nura yayi murmushi yabashi hannu sukai musabiha, kafin yace "toni zan wuce, ana jiranane" sukai sallama,yafice yana tsokanar Aunty Hafsat da fad'in "yau anga d'an uwa, babu ko rakiya ko?" Aunty Hafsat dariya tayi tana yimasa byee-byee. ta dawo tazauna kenan suna hira, a kai sallama bakin falon, Aunty Hafsat tace "bismillah shigo mana" Khamis yad'ago labule yashigo fuskarsa d'auke da murmushi, ganin Ya Nura zaune yasanyashi sakar baki ya washe baki da fad'in "master...!" Ya Nura yataso cike da farincikin ganin aminin nasa suka rungume juna, Aunty Hafsat tana kallonsu fuskarta fal murmushi. nan suka zauna ana hira, Aunty Hafsat tad'auki waya tana kira, can aka d'aga, suka gaisa tace "gashi zaune yazo jiya Baffa" Baffa yayi hamdala kafin yace "to kada kuyi masa tambayoyi akan komai, domin bai san komaiba akan kansa da matarsa tunda dai Allah yasa yadawo sai akuma dagewa da addu'a domin haryanzu tsunne bata 'kareba, bashi wayar mugaisa ko" Aunty Hafsat tami'kawa Ya Nura waya, tana fad'in "ungo Baffa na jigawane" cikin girmamawa Ya Nura yakar'bi wayar yana gaisheshi, kamar yana gabansa, yana 'kara jajjada masa muhimmancin addu'a, da cemasa yadingayi sosai, sukai sallama yakashe wayar. nan suka cigaba da hirar yaushe gamo, wayarsa dake aljihunsace tayi 'kara, ya cirota ahankali, kamar bayason d'aga wayarma, ganin number da sunan wadda takira, yasashi dai-daita nutsuwarsa, su Aunty Hafsat ma gani sukai kamar jikinsa har 'bari yake, wajen d'aga wayar. a hankali cikin sanyin murya ya furta "assalamu alaiki" bata amsaba illa tambayarsa data hauyi "wai kana inane mallam, tun jiya haryau baka dawoba kuma ko ka kirani kasanarmin" "am sorry ina Nigeria yanzu haka" cikin kad'uwa da d'aga murya ta furta "what...! nigeriafa kace?" "ehh mana, naji kewar gidane shine natawo, kema nacewa Momynki jibi zaki zo, saiki shirya kizo" "a'a ni bayanzu zanzoba gaskiya domin ina da ayyuka agaba" ta furta maganar dagaji atsoracectake Ya Nura yace "okey duk yanda kikai" yakashe wayar. Aunty Hafsat da Khamis dubansa kawai suke, ya kammala wayar yajefata gefan inda yake zaune yana fad'in "Haby tafiye rigima wallahi, shiyasa natawo bansanar mataba nasan bazata barni inzoba" bai jira mai zasuceba yacigaba da fad'in "wallahi jiya ina zaune a office kawai sai naji baki d'aya hankalina yatashi, narasa mai yakemin dad'i aduniya, naji nidai kawai gida nakeson zuwa inganku, hankalina baki d'aya ya'ki kwanciya, sai da na sauka a nigeria sannan naji nutsuwa tazomin, najini cike da nishad'in da rabon da inji hakan harna mance wallahi, da kayan aikinma natawo dagani sai systerm d'ina" Aunty Hafsat da Khamis suka dubi juna, Khamis yace "yauwa ya akayi suka barka katawo to?" murmushi Ya Nura yayi kafin yace "abi mai sau'ki kenan a 'ka ida aftr 1yrs ina da hutun 1mnth ne, to ni tunda naje banta'ba hutun kwana gudabama, sai jiya kawai nace hutu zanje, yanzu sai sanda naga dama zankoma har nan da 5mnth" . Aunty Hafsat tace "to mudai sai anyimana 5mnth d'in za'a koma" yanda kukace" Ya Nura yabata amsa nan suka cigaba da hira abinsu, har lokacin sallah yayi suka nufi masallaci da suka dawo, Aunty Hafsat tagama readyn abinci suka cika tunbinsu, sai yamma li'kis lokacin Hamza yadawo, sukai musu sallama, suka nufi gida a motar Khamis, zai saukeshi shi kuma yawuce gidansu. A bakin gate yafaka motar, Hilal yashige gida, su kuma suka tsaya suna d'an tattauna magan-ganunsu, Nuratuce tafito da saurinta daga gidansu zata shiga gidansu Ya Nura, ganin Khamis yasanyata daka tawa da fara'arta ta gaishe da Khamis, haryana tsokanarta ta girma anyi hankali, cikin ido da ido suka dubi juna da Ya Nura, tad'an harareshi tad'auke kai, Ya Nura kuwa murmushi yad'anyi, danshi yanzu Nuratu dariyama al'amuranta suke bashi. Nuratu ta wuce tana fushi, Khamis ya bi Nuratu da kallo, ya dawo da dubansa kan Ya Nura, ya Nura yace "kai saika dinga shiga harkar wannan yarinyar kana jamin raini ko?" Khamis yasanya dariya kafin yace "banganeba?, nifa wallahi yarinyar kawai burgeni take, ga kyau ga tsari, ga nutsuwa da ilmi, rashin kunya kuwa ai sai dai mutum yakulata, koya shiga harkarta, amma indai zakabita yanda takeso nafahimci babu raini atare da ita..." Ya Nura yad'anja tsaki yana fad'in "to ya isa haka naji, inkana ciki ai saikayi magana tun da wuri, bawai katsaya kame-kameba" Khamis murmushi yayi yana duban kwayar idon Ya Nura, yace "mai da wu'kar, ni banshirya aureba, amma da ace na shirya itace matar" "zancen kakeso, kaga tafiyata muyi waya kawai" Ya Nura yafad'a yana mai shigewarsa gida, yabar Khamis tsaye murmushi Khamis yayi yana fad'in "master kenan, narasa dalilin dayasa baison yarinyarnan, nikam banga aibu agaretaba" yafad'a yana mai shigewa motarsa yaja yatafi. 《MALESIA》 Haby kuwa ko da Ya Nura yakashe wayar, tsaye tayi da wayar ahannunta tana kallon screen d'in cike da firgici. Sholy ta dafa kafad'unta tabaya tana fad'in "yadai, kafiya kuwa?" Haby tazauna da'bas abisa kujerar dake kusa da ita tadafe kanta tana fad'in "shikenan Sholy, shikenan asirina yana daf da tonuwa" Sholy tayi mata duban rashin fahimta tana fad'in "kamarya asirinki na shirin tonuwa?" "Nura yana nigeria yanzu haka, acan yakwana" cikin takaici da damuwa tabata amsa, Sholy tazaro idanuwa waje, tana duban Haby, har tsayin wasu da'ki'ku, kafin tayi ajiyar zuciya tana fad'in "Dolene ayi zama na musamman akan matsalolinmu wannan watan, domin abubuwa sunfara kwancewa, Nabeel ya gudu, sannan kuma Nura ya tuna da 'yan uwansa heeeyyy da sake gaskiya" ta 'karashe maganar tana girgiza kai ta cigaba da fad'in "ki kira 'yar shila, shugabar 'kungiya tunyanzu musan abinyi, asaka mana ranar zama na musamman" Haby tace "sosai kuwa, kin kawo magana, bazan ta'ba bari asirina yatonu akan Nuraba, dole a gaggauta zartarmin da aiki akansa, dama ni aurensa yagama fitarmin arai, tunda namallaki abinda nake buri meye yarage kuma, iyakaci muyi zaman makokin kwana uku mushare hawaye mud'ora daga inda muka tsaya, amma babu wanda yasan silar mutuwarsa" suka sanya dariya suna tafawa, Haby tazaro waya, tananna takara akunnanta, tana fad'in "bari inkirata, abari yahuce shike kawo rabon wani". [14/01, 01:52] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *《《《《《QIYAYYA SA GANIN LAIFI》》》》》*Book1 mallaka-----QURRATUL-AYN 31 zaune suke dukansu acikin falon Abba, anayi masa sannu da zuwa, domin dawowarsu kenan daga umara, Inna har da kukanta domin farincikin ganin Nura, Abba 'kara godewa Allah yake sosai domin amsa addu'arsa dayayi, domin sabidashi sukaje umara gashi kuma yadawo yatadda Ya Nura agida gashi gabansa kuma. wayar Khaleel tayi 'kara yatashi yafice domin amsa wayar. Inna tad'ago jajayen idanuwanta tana duban Abba kafin takira sunansa "Aminu...!" Abba ya d'ago ya dubeta yana fad'in "na'am Inna" Inna ta gyara zama tare da gyaran murya tana fad'in "ayau zansanar da kai, wani 'boyayyan al'amari dake raina, daman kuma irin wannan ranar nake jira naganku baki d'aya, naga ranar da jikana zai zama mutum, duk da nayi nauyin baki har wani abu ya gilma kafin nayi maganar, amma nasan hakan bawani abu bane" Inna ta cigaba da fad'in "wannan abu zanfad'eshine gaban kowa, gaka ka Mamansu ga Amarya da Momyn Haby, ga kuma,uwa uba Ammy, ku zaku zama shaida akan wannan magar, ba wata magana bace illa inason Aminu kahad'a auren *NURA DA NURATU*" baki d'aya kallon kallo aka hauyi afalon, Abba yace "Inna kikace ahad'a auren Nura da Nuratu kuma?" "ehh haka nace, indai kanason ganin farincikina, wannan shine kad'ai ragowar burina aduniya, domin banaso GIDA BAI 'KOSHI BA ABAIWA DAWA" Ya Nura kuwa dake zaune gefe yafi kowa kad'uwa da al'amarin, jin zancen yake kamar amafarki, har wani 'kara karkad'a kunnuwansa yake. Abba yace "amma Inna nake ganin kamar yin hakan zai bada matsala" "kayi abinda nace kawai Aminu, indai kanason ganin farincikina" cewar Inna, Abba ya maida dubansa kan Ya Nura yace "to kajidai da kunnanka ko Nura?" Ya Nura yace "Abba wai ni in auri Nuratu, haba Inna Nuratufa kikace?" yafad'a yana girgizakai, Inna ta kama gefan mayafinta tafara sharar hawaye tana fad'in "babu komai, akan wannan maganar shine zaku tsaya kai da mahaifinka infad'a kufad'a, shikenan ai kushirya mai dani jigawa, nagama zama daku" Abba yace "a'a Inna,baza'ayi hakaba, munason zamanki tare damu, dan haka wannan magana angamata" ya Nura zaiyi magana, Abba yace "umarni nake baka, matsayina na mahaifinka, idan har nina haifeka kuma na isa da kai" "Abba bawai ban'ki jin maganarka bane, amma duka duka yaushene akai aurenmu da Haby, kuma,nasan bazatayardaba sannan..." "da kata..!" Abba ya dakatar dashi game da d'aga hannun, yacigaba da fad'in "sanda nahad'a aurenka da Habyba bakaimin wannan musunba, dan haka yanzuma inaso kayi min biyayya a matsayina na mahaifi agareka" "Abba amma Nuratufa kace? guda nawa take kuma kasan halin yarinyar sannan ai Haby tafi Nuratu kuma.." "kai...!ya isa nace" cikin tsawa da 'bacin rai Abba yayi maganar yanzu, wadda sai da dukkan falon sukad'an razana, ya cigaba da fad'in "nagama magana Nura, sai dai idan kanason nunamin iyakata" yana kaiwa nan yatashi yashige bedroom nasa, yabarsu nan zaune, Ammy da Mama kuwa,kasa cewa komai sukai, Aunty ce dai taketa murmushi, kamar maganar tayi mata dad'i ma, Momyn Haby cike da 'bacin rai tami'ke tana fad'in "ina bazai yuyuba wallahi, yaushe har akai auren da Haby da Nuran, da har za'a 'ka'kaba masa ala'ka'kay ayiwa Haby kishiya wallahi da sake" tafice daga d'akin tana sababi, Inna kuwa,murmushi tayi tana fad'in "babu wanda zai gane wannan had'in nawa, inaji araina akwai alkhairi aciki, kuma kowa zaiyi farinciki da hakan, domin nasan babu wanda zai iya ri'kemin marainiyar jikata Nuratu da amana kamar Nura, domin bahaushe yace NAKA SAI NAKA" Inna tami'ke tafita tanufi zuwa d'akinta tabarsu nan zaune, haka Ammy ma tayi musu sai da safe ta nufi gida, Mama da Aunty kowacce d'akinta ta nufa, akabar ya Nura nan zaune yadafe kansa dayaji yana saramasa, baki d'aya yaji duniyar tayi masa zafi, har wani duhu-duhu yake gani, baisan irin zaman da yayi falon Abba ba, kafin yami'ke ya nufi d'akinsa. Ammy kuwa jiki babu kwari tayi sallama falonta, lokacin Nuratu nazaune gaban TV tana kallon wani girki da ake koyawa Ammy tayi sallama, Nuratu ta amsa tana fad'in "har kindawo Ammy banjeba, nayiwa Abba da tsohuwa sannu da zuwa, so nake akammala koya girkinnan inje, inason iyawa wallahi, kuma gashi kintaho" Ammy bata kulataba, illa zama d tayi kan kujera ta dafe kai, tana hasko yanda Nuratu take a gida da yanda al'amuranta da Haby suka dinga tafiya, tasan akwai matsala sosai domin Nuratu da Haby ko kad'an basa jituwa, bare kuma ace yanzu suyi zaman kishi yakenan?. Ganin Ammy tayi mata banza yasata matsowa tana tambayarta lafiya ?, Ammy tace "babu komai kaina ked'anmin ciwo, zanje ind'an kwanta ad'aki" "to kisha paracetamol ko Ammy, kafin ki kwanta, dakin tashi zaki d'anji sau'ki" ta'karashe maganar tanami'kewa tafita, anjimakad'an sai gata d'auke da cofi da paracetamol, koda tadawo Ammy tawuce d'aki, har can tabita tamatsa mata akan tasha maganin, kan dole Ammy takar'ba tasha, don bawani ciwonkai da takeji tadai fad'i hakanne, don sanin halin Nuratucwajen nacin tambaya. Ya Nura kuwa yana shiga d'aki, kan doguwar kujera yakwanta, kansa na kallon silling, baki d'aya yaji duniyar tayi masa duhu, har yakejin dama baizoba, domin Inna da Abba sun'ballo masa tashin hankali, tayama zai iya tunkarar Haby da maganar 'karin aure?, sannan taya zai sanar mata cewa Nuratu zai aura?, sannan shi dai yasan bayason Nuratu ko kad'an aransa, abinda yasani kawai yama tsaneta, taya zai iya zama da ita matsayin matarsa?, anya zai iya kuwa?, anya zai iya yiwa Abba biyayya akaro na biyu?, wad'annan tambayoyin sune yadinga yiwa kansa, sai dai babu amsa haka yayita juyi akan kujera, ranar barci sai dai 'barawo. To 'bangaran Mama ma haka abin yakasance, bawai bata son auren bane a'a, kawai tanajin tausayin za'ajefa Nuratu cikin garari, za'a cuci rayuwartane kawai, sannan ayanda tasan Nuratu da yanda suke da Nura tasan zai wuya Nuratu ta amince da auren ta dad'i, gani take kamar za'a tauyewa Nuratu rayuwar tane kawai. Amma 'bangaren Momyn Haby da shigarta d'aki, takasa zaune takasa tsaye zarya take kamar mai hauka sabon kamu takai takawo, baki d'aya taji ta'kuntata ad'akin tunaninta mafita kawai yanda zata wargaza komai, domin bazataso ace ayiwa 'yarta mafi soyuwa aranta kishiyaba, hakan yasanya hankalinta baki d'aya 'kin kwanciya, sai surututai take ita kad'ai. Aunty zama tayi gefan gadonta fuskarta d'auke da murmushi, gani take tamkar asirin Nuratu ya tonune indai Nuratu tashiga gidan Nura, domin tasan zata koyawa Haby hankaline, dan Nuratu ba 'kyalle bace turmin zanice har da d'ori, tanaji ajikinta had'in da Inna tayi zai zamo abin alfahari a cikin family baki d'aya, duk da tasan kafin hakan tasamu sai anjure 'bacin rai da damuwa sosai, domin akwai jan aiki agaba. TOFA...! WAI SHINMA NURATU ZATA AMINCE DA WANNAN AUREN? HABY ZATA AMINCE DA NURATU MATSAYIN KISHIYARTA? IDAN HAR NURATU TA AMINCE DA AUREN, TA KUMA SAMU DAMAR SHIGA GIDAN YA NURA MATSAYIN MATARSA WACCE IRIN CAKWAKIYA ZA'A BUGA AGIDAN? ZAMAN NURATU DA HABY ZAIYI DA'DIKUWA? MAMA ZATA BADA GOYON BAYAN AUREN? MOMYN HABY ZATA CI GALABA AKARO NA BIYU? YAYA AL'AMURAN HABY DA ZULY, SHOLY, BABY ZAI KASANCE ? INA NABEEL YAKE? WAYE ZAICI GALABAR NEMOSHI? KHAMIS NE KO SU HABY ? Domin jin amsan dukkan tambayoyinku kubiyoni nidin dai QURRATUL-AYN *ALHAMDULILLAH* SAI KUMA KUNJINI CIKIN LITTAFI NA BIYU INSHA ALLAH *GARGADI* banyarda wata kowani yajuyamin littafiba kota wacce hanya idan bada izininaba duk wanda yayi hakan za iya cewa Allah ya isa ban yafeba. GODIYATA TA MUSAMMAN AGAREKU HASSAN ATK TANKO HUSSAINI ATK TANKO AUNTY MAIJIDDAH MUSA *SADAUKARWA* KARKI MANCE WANNAN LITTAFIN NAKINE *HAFSAT XOXO* *KUNA RAINA* ANEESAH A. RIMI HAFSAT RANO ZAHRA BUKAR SHAFA'ATU UMAR UMMU ABRAR DA SAURANSU AM SORRY KUNA DA YAWA AMIN UZURI MASOYANA DUK INDA MASOYANA SUKE INA MI'KO GAISUWA AGAREKU ALLAH YABAR 'KAUNA KUNA RAINA. *NAGODE* NURATU FANS INA GODIYA SOSAI