💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* Daga marubuciyar littafin CAPTAIN ABBAS. *Masoyana bani da bakin gode muku domin irin 'kaunar da kuke nuna min tana matu'kar sanyani farin ciki..... fatana kawai shine kuma Allah ya faranta muku fiye da yanda kuke min.........Gashi dai yau na sake dawo muku da wani labari shima mai suna NOORUL fatan zaku bani ha'din kai ku kuma raka ni da da'da'dan sharhohin ku kamar yadda kuka saba....😍 🤞🏻 ~*AKAFTA*~ 👇🏼 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *1* Babban waje ne ba na wasa ba, zaka iya ambatan sa da suna wani tsararren mansion ko wani abu daban, sai dai ina sam ba haka bane......wannan tsarin na daban ne kamar yadda yake na musamman, bazaka ta6a fahimtar menene shi ba a tsanake daga yanayin wurin saboda sam ba'a yi shi yanda kallo 'daya zaka fahimce shi ba in ba kayi duba da Babban farin sign board 'din dake kafe gefe da gate 'din building 'din ba ko kuma in dama asali kasan mene shi ba, nima a sign board 'din na fahimci ashe asibiti ne nan 'din......... A hankali wata ba'kar mota ha'd'diya mai sanyin yanayi take shigowa harabar wurin tamkar ba son jan motar ake yi ba, duk da ba'kin tinted glass 'din da ya lullu6e jikin motar amma hakan bai hana securities 'dagawa mamallakin motar hannu ba alamar gaisuwa, duk kuwa da cewa ba ganin sa suke yi ba amma saboda girmamawa yasa sukayi masa hakan, da yake ma sun san halin sa bayan hakan baya bu'katar komai dan ko kayi wanda yafi hakan ma ba bu'dan baki zai yi ya amsa maka ba wata'kila ma ko kallon inda kake ma bayi zai yi ba sa6anin hakan kuwa zaka iya samun kyautar murmushi daga gareshi...... cikin sa'a kuwa yau 'din sai gashi yayi 'kasa da ba'kin glass 'din motar ya 'dago musu hannu shima murmushi sukayi na jin da'di suna ayyana canjin yanayin sa na yau 'din. Sosai yake birge da yawa daga cikin su dayake a zahiri sun san halin sa mutumin kirki ne na bugawa a jarida koka'dan bashi da matsala a idanun su bayaga rashin son hayaniyar sa.....wannan kuma su a wajen su ba wata babbar matsala ba ce tunda sam baya shiga ha'k'kin su ta fuskar ayyukan su abinda ke gaban sa kawai yake yi. Wannan kenan. Kamar yadda ya shigo a hankali hakan ya 'karasa har parking space inda musamman aka tanada dan ajiye motoci, gefe ka'dan da sauran motocin yayi parking nasa. Bai bu'de marfin motar ba koda yayi parking 'din sai da ya 'dauki a 'kalla kusan mintina takwas sannan ya bu'de motar a hakan ma sai da ya 'kara 3mins akai kafin ya zaro 'kafar sa 'daya sannan ya ya fito gaba 'daya ri'ke da brief case 'din a hannun sa na hagu yayin da 'dayan hannun ke ri'ke da key 'din motar tasa gami da wayar sa, a nutse ya juyo ya fara tafiya bayan ya danna wa motar security ya nufi hanyar da zata sada shi da cikin ma'aikatar. 'Kofar da kanta ta bu'du kasancewar ta auto ce ita ke operating kanta ba sai ka wahal da kanka ba. Stairs ya nufa da 'dan hanzari tare da duban agogon dake 'daure a tsintsiyar hannun sa wanda kana gani ko ba'a sanar da kai ba kasan cewa na musamman ne. Shiru ya samu saman bayan hawowar tasa inda direct ya nufi office 'din sa yasa hannu ya bu'de tare da bismillah cikin zuciyar sa ya nufi faffa'dan table 'din dake cikin office 'din ya zagaya yaja kujerar data kasance mazaunin sa kenan in har ya shigo office 'din. Jakar dake hannun sa ya ajiye sannan ya zauna tare da 'dago wayar sa da yaji ta fara 'kara alamar 'kiran sa akayi. "Hi" Yace tare da jingina da jikin kujerar ya lumshe idanun sa fuskar sa ba yabo ba fallasa ya sake fa'din " Yes na iso mana...." " ah ah ba yanzu ba" yana gama fa'din hakan yayi ending call 'din tare da gyara zaman sa akan kujerar yana juyi. Bai jima da gama wayar ba aka fara gabatar masa da files 'din marasa lafiya da yake lokaci ya 'dan ja kusan 'karfe tara yanzun shiyasa batare da wani 6ata lokaci ba yafara duba patients. 'Karfe shabiyu ya dakatar da duba marasa lafiyan saboda gajiyar da yayi sai a sannan kuma yasake 'daukan wayar sa yayi dialling wata number tare da ha'da wayar da kunnan sa. "Assalamu alaikum Yah Deen!" Kamar jira akeyi ya 'kira daga 'dayan 6angaren aka 'dauka tare da doka sallama cikin natsuwa inda tayi maganar fuskar ta cike da annuri. Amsa ta yayi da fa'din " Na'am.... Nureen Deen i missed u alots" Shima yayi maganar yana sake lafewa kan kujerar dayake zaune akai harda lumshe idanu. Murmushi tayi ita kam sannan tace " Ni dai yaushe zaka dawo please ka fa da'de wannan karan kusan fah satin ka biyu". Idanun nasa a rufen yace " kina kewata ne?" Kwafa yayi tare da juya idanu tana murmushi tace "Ba dole ba, ai kaima abinda kasani ne ko sai na sake tuna maka?" Sai yace "Da zanfi son hakan ai idan naji shi a zayyane daga furu in ki". " Allah yah Deen baka jin magana...kai kullum sai na ta maimaita maka abu 'daya ne?". Ta 'karashe maganar tamkar zatayi kuka. Hankalin sa a kwance yace " toh ai ni nafi son hakan ya za'ayi" Ganin kamar shi bai ma wani damu ba yasa tace " ni dai please ka dawo in yaso sai ka koma kaji.....?" "Sai nayi tunani tukun na" ya bata amsa atakaice. Tana shirin sake yin magana sai ya dakatar da ita da fa'din " ya isa plz......! kar ki damu soon zan dawo kinji nima am so eager to meet u Nureee...." Murmushi mai sauti tayi before saying a word sai ya rigata yin magana da fa'din " where is my diamond?" Dama tasani tunda yace ya isa please 'din nan tasan 'yar sa zai tambaya bakomai ba. 'Dayan hannun ta ta 'dago ta 'daura shi akan cikin ta sannan ta amsa shi da fa'din " ai tana school yah Deen bata dawo ba". Ta 'karasa maganar tana 'dan ha'de gira. Shima goshi ya 'dan dafe daga 'daya 6angaren tamkar suna wuri 'daya da ita tare da furta " upps sorry Nureee kinga ma na mance ne amma please ki 'kirani idan ta dawo kinji?" Da " uhm" ta amsa shi daga nan tayi shiru shine dai ya furta " i love u Nuree i have something to do now.....bye owk" Shiru tayi masa bata tanka ba daga haka kuwa ya yanke 'kiran. 'Karfe 12:50pm Ta sake duba agogon dake cikin wayar ta karo na barkatai domin kuwa abin yafara bata haushi duk da ba wai yau ne hakan yafara faruwa ba amma zuwa yanzun abin na 'dan fara 6ata ranta ganin yanda lokaci ya tafi amma har yanzu Jas bata dawo ba kuma tasan dawuri driver yake tafiya school 'din nasu yayi zaman jiranta har a tashi, amma ta rasa mai yasa sai sun da'de kafin suke dawowa gida, kusan kullum sai sun 6ata lokaci wanda ta fahimci hakan a 'yan kwanakin nan dayake bata shiga school sosai ita 'din, Nursery school dai kowa yasan ba'a haura 12:00pm batare da an tashe su ba amma tana ganin kamar na Sani yana yawa lokacin......bata gama tunanin nata ba Driver yayi sallama hannun sa 'dauke da wata 'yar kyakkyawar yarinya da bazata haura shekara biyar ba yayi mata 'daukan jarirai da lunching box 'din ta a hannun sa be dire ta ko ina ba sai gefen mahaifiyar ta dake zaune kan kujera, bata wani nuna alamun rashin jin da'din ta game da hakan ba cuz tasan kusan kullum a hakan yake kawo ta ya zaunar da ita, cikin natsuwa yayi wa matar dake zaunen barka da gida tare ta amsa shi sannan ya bar 'dakin yana bayyanar da murmushin sa afili. Binsa tayi da idanu haka kawai sai take 'dan jin haushin sa a ranta, daf da zai bar 'dakin sannan ta furta " Sani yau kuma mai ya rike ku har haka?" Sosa kai Sani yayi sannan ya juyo ya kalle ta suna ha'da ido da jas sai yayi murmushi ita kuwa 'dan yatsan ta 'daya ta 'daga ta kalli mahaifiyar tata tare da fa'din " Mummy kinsan me yasa muka da'de ne.......?" Sani na jin haka yayi saurin dakatar da maganar nata da fa'din " Ranki ya da'de wallahi mun 'dan yiwa wani abokina lift ne shiyasa". Jas kam shiru kawai tayi tana rarraba idanu tsakanin Sani da mahaifiyar ta jin 'karyar da ta tafka duk da 'karamcin shekarun ta amma sarai tasan 'karya ya shirga. Matar ne ta sake cewa " amma ai Sani ka dawo da ita gida tukunna kayi yawon naka ai ko? Jasmine 'karama ce kasani kuma ko mahaifin ta yaji cewa kana yawo da ita cikin gari ba zaiji da'di ba". Sani cewa yayi "Insha Allahu Hajiya baza'a sake ba" Kauda kai tayi tace " Allah yasa " A 'kasan ma'koshi tayi maganar tare da maida duban ta kan 'yar ta, shima Sani ba tare da ya sake furta komai ba ya fita ya bar 'dakin. Matar bata wani damu da shi ba har ya fitan wanda bayan fitar tashin ne tace da 'yar yarinyar " Jas tun 'dazu Daddy yake ta tambayar ki fa....." bata 'karasa abin tayi niyyan fa'dan ba ta kai hannu kan fuskar Jas 'din da kulawa ganin sauyi tattare da ita atake ta sauya akalar maganar da fa'din " Jas me ya sami bakin ki yayi ja haka ?" A ru'de tayi maganar Jas kuwa sai ta 'daga hannun ta itama i zuwa bakin sannan ta ce " bakina?" Jas 'din ta tambaya Da sauri ta amsa ta da fa'din "Ehh mana... ko kin bige ne a school?" Kai ta juya mata alamar "ah ah" Uwar sai tasake fa'din " Toh menene? Har fa 'dan kumburi naga yayi" Jas shiru tayi kamar mai tunanin wani abu sai da uwar tasake tambayar ta a 'dan tsawace sannan ta bu'di baki tace bu'di baki tace "Sa......." Bata 'karasa ba ringing 'din waya ta ya 'dauki hankalin su gaba 'daya inda atake suka kai duban su kan wayar. Cire hannun ta tayi daga fuskar 'yar yarinyar sannan ta kai hannu ta 'dago wayar. Picking call 'din tayi ba tare da tayi magana ba kawai ta ha'da yarinyar da wayan tare da fa'din " Daddy kin ne" Yarinyar najin haka tayi saurin kar6an wayan tace " Daddy.... i missed u when ar u coming back?" Murmushi mai sauti yayi sannan yace " gobe insha Allahu Diamond zan dawo kinji? Me zan kawo miki?" Ta6e baki matar tayi jin abinda ya fa'dawa Jas 'din, ita lokuta da dama tana mamakin Deen yanda ya 'dauki buri, kula da so gaba 'daya ya 'daura akan yarinyar nan, duk dama ita ta haifa abinta amma is too much...ace tana matsayin matar shi amma ya kasa sanar da ita cewa zai dawo gobe sai dai wa 'yar yarinyar nan nan zai fa'da... "Hmm" tace a fili tare da cigaba da sauraran su. Jas kam cewa tayi "Daddy ni dai ka dawo kawai" Sai yace " zan dawo ai Jas da iznin Allah amma me kike so in kawo miki?" Jas cewa tayi " Ni ba komai Daddy... gurin Grandpa nake so muje kawai" 'Yar dariya yayi daga 'dayan 6angaren sannan yace " To shikenan bari idan na dawo insha Allahu zamuje kinji Mama na?" "To Daddy sai ka dawo"! "Gud girl....ina Mummyn taki ?" Mi'kawa Mahaifiyar ta wayan tayi tana murnar Daddyn ta zai dawo suje 'kauye fuskar ta cike da fara'a. 'Bangaren mahaifiyar tan kuwa tana ha'da wayar da kunnan ta taji shi yana fa'din " Nuree i ll be back tomorrow kinji?" "uhum" tace da shi a takaice. Daga haka suka yanke 'kiran kuma sanadin da kenan ta manta da tambayar Jas 'din a salin me ya samu bakin ta saboda wayar da Deen 'din yayi gaba 'daya ya 'dauki hankalin su kowa da abinda ke ranshi . Ita tana tunanin halayyar mijin nata ne yayin da Jas ke murnar zata je wurin su Granny. Zuwa tayi ta watsa mata ruwa ajikin ta tare da 'debo mata abinci. Sam koka'dan bata kishi da 'yarta domin bata da hujjan da zatayi hakan, amma wani lokaci abinda Deen keyi na matu'kar bata mamaki atimes kuma haushi yake bata yanda yake matu'kar fifita Jas a kanta bisa komai. Yes tasan 'yar sa ce mafi soyuwa a gareshi musamman da yake ya 'dan yi shekaru a 'kalla biyu batare da ya haihu ba sannan ya same ta kuma daga itan har yau bata ko 'kara yin 6ari, amma hakan ai ba dalili bane da zai ce zai ringa fifita Jasmeen ya kuma fifita soyayyan ta akan na kowa ba, kuma ma har da ita data yi na'kudan ta ya maida ta banza a kanta, duk da tasani cewa ita kanta shaida ce akan irin son da Deen yake yi mata amma compare to soyayyar Jas kam tana ganin nata 'din ba komai bane, saveral times tana yi masa uzurin cewa dan itan gudan jinin sa ne shiyasa yake hakan, itama tasan cewa abin alfahari ne ace ka haihu kuma uban ya matu'kar nuna farin cikin sa game da abinda ka haifan tasan da akwai birgewa da faranta ran mahaifiya hakan amma atleast itama yana 'dan sauraran ta mana....bata da yanda zatayi dashi dan haka ko yanzun ma sai ta saka cikin ranta cewar Jasmeen gudan jinin sa ce kuma dole ya 'kaunace ta fiye da komai. Abaki tayi ta bata abincin har ta 'koshi sannan ta sata agaba sukayo alwala suka sallaci azahar daganan sai ta fara gyara mata kitson rubber band dake kanta da haka hartayi bacci sannan ta barta. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [11/17/2019, 9:33 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Labarin nan 'kir'kirarre ne, banyi shi da sunan wani ko wata ba dan haka duk wanda yaji yayi kama da wani abu na rayuwar sa ya sani cewa co-incidence ne babba ma kuwa.... dan haka ayi amin afuwa dan Allah ba da niyya nayi hakan ba.* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *2* 'Karfe uku kusan da rabi Jas ta tashi a baccin, inda mahaifiyar ta tayi 'ko'karin ganin ta shirya ta cikin hanzari zuwa makarantar islamiya dake bayan layin su ganin ta makara lokaci yaja, bata fiya son tana missing makarantar ba da sai tace yau 'din ta bari kar tace amma kuma ba laifi yarinyar akwai 'ko'karin 'daukan hadda idan anyi musu, shiyasa uwar tafi so kar tayi fana yawan fashin zuwa sosai ta ke matu'kar 'ko'kari wajen ganin ta kula da karatun nata. Jas 'din ce ma yau 'din take 'dan rigimar ita bazata je islamiyar ba, amma da ta ta lalla6a ta sai ta samu da 'kyar ta amince zata je 'din amma wai sai dai Maman nata taraka ta. Kwafa tayi tana kallin ta sannan tace " haba Jas ni kuma in rakaki? Baki ga ko sallah banyi bane? Kafa'da Jas ta 'daga da damamman fuska take shirin yin rigima. Sai ta janyo ta jikin ta tace " yi ha'kuri mamana watarana zan rakaki kinji...ki bari yau zan dafa miki abinci kafin ki dawo wannan irin na T.Vn nan kinji? Murmushi tayi tana kallon maman nata. Sai ta sake fa'din " Yauwa maman Daddy....Hauwa ta rakaki ko? Sai ta 'dage kai sama alamar "ehh". Murmushi matar tayi sannan ta 'kwala 'kiran mai yi mata aikin tace ta raka Jas makarantar islamiyar su inda ta 'kara da fa'din kar su 6ata lokaci a hanya saboda tayi late sosai. Amsa mata yarinyar tayi tare da kama hannun Jas 'din suka fita daga parlourn. Hauwa yarinya ce matshiya da bazata haura 15yrs ba ba laifi tana da kyaun ta daidai gwargwado sannan baza'a 'kirata ba'ka ba tana haske, ta kan 'dan taya Noor aikace-aikacen gida irin su Wanke-wanke, sharan cikin parlour da mopping har ma da haraban gida. Sannan tana wankin uniform da socks 'din Jas kullum boko da islamiya duk dama Uniform 'din tana da kusan kala uku-uku amma bata son a dinga ajiye su da datti shiyasa take sawa a wanke su kullum. Jas ba gwanar surutu bace sam, yarinya ce 'karama amma abubuwa dayawa takan bisu da idanu ne kawai, surutun ta yakan zo mata ne lokaci-lokaci, sai dai kuma ko idan tana tare da mahaifinta wannan kam har sai ka gaji da dajin surutun ta idan suna tare dan shi da kansa yake koya mata ma surutun za'ace cuz a kullun biye ta yake yi a komai baya takurata ba kuma yason ganin ta zauna shiru 'din nan, a fa'dar sa wai yafi son ya dinga ganin walwalar ta koda yaushe. Sa6anin mahaifiyar ta kenan dan ita kam bata barin ta yawan surutun nan, itace mai yawan kwa6an ta sau tari zata bu'di baki da niyyan fa'dan magana amma sai uwar ta dakatar da ita wanda hakan yake tilasta mata yin shiru har abin ya wuce. Suna fita daga gidan ta warware kamar ba ita ba suna tafiya hannun ta cikin na Hauwa suna 'dan hira ka'dan-ka'dan. Daf da 'karshen layin nasu suna shirin fita daga layin suka ji an danno musu horn daga bayan su, a tare suka waiga dan ganin kowaye ke yin hakan. Ga mamakin su sai suka ga Sani driver ne inda ya 'karaso gefe da su yayi parking yana wani murmushi tare da 'dagewa Hauwa gira. Hauwa kam saurin kauda kanta gefe tayi a ranta tace " d'an iska kawai". Ganin Hauwa ta kauda kai sai ya dawo da kallon sa kan Jas yace " Jasmin makaranta za'aje ne?" Kai Jasmin ta 'daga masa alamar "ehh" Baki ya washe yace " babu nisa kun ma iso badan haka ba dana kaiki ko?" Jas bata kula shi ba sai ta juya ta kallo makarantar kawai. #20 ya ciro ya mi'ka mata yace " gashi ki sayi sweet ko Jasmin?" Yana dariya ya mi'ka mata wanda yasa ta kalle shi tare da kallon ku'din. " kar6i mana"! Ya sake maimaitawa da 'dan 'karfi. "Daddy ya hana ni ri'ke ku'di " Tace dashi tana kallon shi. Sai yayi dariya yace " kar6i abinki ki kashe.....ai Daddyn bazai sani ba kinji?" A hankali ta matsa ta sa hannu ta kar6a tare da fa'din " nagode" Hauwa matsawa tayi taja hannun Jas da sauri suka fara tafiya tana tuttura baki gaba suka barshi a gurin. Kwafa Sani yayi tare da cizon lips 'din sa yabi bayan su da kallo. Jan motar yayi zuwa saitin su ya 'dan tsaya tare da le'ko kai yace " ki yi mata a hankali fa Hauwa dan wannan da kike gani tafiki daraja ko awaje na ma balle a gun iyayen ta". Yana gama fa'din hakan yaja motar yayi gaba abinsa yana sakin murmushi. Hauwa hararar bayan motar tayi a fili tace " kai kasani ai banza 'dan iska kawai". Bata bar Jas ba har sai da ta dangana ta da 'kofar shiga makarantar islamiyar tasu kafin ta juyo tana yi mata bye-bye ta dawo gida. Koda ta dawo ma Sallah tayi tare da fara aikin ta na yamma wanda bata jima da da fara aikin ba sai ga Sani ma ya shigo da sallamar sa hannun sa ri'ke da leda ga dukkan alamu ma ashe aikan sa akayi shine ya tsaya yi musu iyayi a hanya. Suna ha'da ido da Hauwa sai ya 'dage mata gira da yake ita ka'dai ce a parlourn lokacin tana kammala shara tana mopping parlour wanda jin sallamar tasa ne yasata 'dagowa sai kuma yai mata signa. Ita kam 'kasa tayi da kanta taci gaba da aikin dake gaban ta tare da sakin tsaki cikin ranta. Sai ji tayi yace mata " ina matar gidan". Shiru tayi kamar bata jishi ba. Sai da yasake maimaitawa kafin tace masa " tana ciki" 'Kasa-'kasa tayi maganar kamar bata so. Shi kuwa da yaga haka sai ya taho a hankali ya tsaya daga bayan ta still yana ri'ke da ledan a hannu. Hauwa bata san ya taho bayan ta ba dan haka cigaba tayi da aikin ta hankali kwance, sai da ta 'dan matsa baya ka'dan sai taji tayi karo da mutun. A firgice ta juyo tare da sakin mop 'din ya fa'di 'kasa zata tsala ihu sai Sani yayi saurin sakin ledan hannun sa ya toshe mata mata baki yana zare mata idanu 'kasa-'kasa yace " y'ar 'kauyen banza". Dai-dai fitowan Noor da idanun ta ya fara sau'ka akan su Hauwa na 'ko'karin 'kwatar kanta a hannun sa yayin da shi kuma yayi mata ri'kon 'karfi. Da matu'kar mamaki ta ke kallon su bata san meke faruwa ba amma ga dukkan alamu Sani ne mara gaskiya ganin yanda ya toshe bakin yarinya ya hana ta magana, dan haka sai ta nufo su da hanzari tare da fa'din " meke faruwa anan wai?" Sani na jin haka yayi saurin sakin ta yana sunkuyar da kansa 'kasa tare da sosa kansa. Noor kam kallon su take yi 'daya bayan 'daya yayin da abin ya 'daure mata kai ganin Hauwa na hawaye tana banka masa harara shikuma yana wani sussunne kai 'kasa. Duban Sani tayi tace " Sani yaushe ka dawo gidan ne ma wai plz da har kake yin wannan abin?" Kai ya 'kara sosawa tare da tsugunnawa ya kwaso ledojin daya zubar a 'kasa cikin sauri yana fa'din "Yanzun nan na dawo Hajiya ban gan ki bane a parlourn". Alamar rashin gaskiya 'karara kan fuskar sa dan ko idanu ya kasa ha'dawa da ita. Goshi ta ha'de tare da sake fa'din " yanzu?, da baka ganni ba kuma shine ka tsaya cin zali? Sani cewa yayi " Ah ah Hajiya ba cin zaki bane wallahi" Noor ma sai tace "To ita kuma Hauwa me tayi maka?" "Kai ya 'dan juya gefe alamun dai rashin gaskiya yace " Hajiya zagi na tayi" Bata yi magana ba sai ma binsa da kallon mamaki da take 'kara yi, ba yau tasan Hauwa tasan halin ta ba, yarinyar babu laifi tana da tarbiya kuma bata raina na gaba da ita kamar yanda tasan bazata ta6a bu'dan baki ta zagi Sani haka kawai ba, babban abinda yasa take 'kara birgeta ma shine sanyin halin ta amma ko kunya bayaji zai ce wai ta zage shi. Har ta bu'di baki da niyyar sake tambayar sa abinda yayi mata kafin ta zage shin sai kuma tafasa dan haushi. Kallon ta ta dawo dashi kan Hauwa tace " Me ya ha'da ki dashi Hauwa?" Hawaye ta share tare da jan numfashi tace " ni fa babu abinda nayi masa kawai da shigowar sa sai yake min signa ni kuma banaso sai na harare shi na cigaba da aikina...shine kuma kawai bansani ba najishi ya tsaya a bayana hadda toshe min baki" Noor ji tayi wani iri abin ba ma ma'ana ga dukkan alamu dai koma ma Sani ne mara gaskiya kamar yanda ta zarga tun farko. Cewa tayi " kai subhanallahi...... dan Allah Sani ka fita harkar yarinyar nan ka barta ta huta hakan nan.....idan son ta kake yi ka je can gurin mahaifin ta kayi masa magana na san ba zai hana ka ba, amma ni dan Allah Sani ka daina 'daga min hankali a gidan nan........in kuma ba haka ba gobe Deen zai dawo zan sashi yayi muku iyaka dan ba kai ka kawo ta gidan ba bansan damuwa da tashin hankali " Cikin sanyin murya yace " ayi ha'kuri Hajiya insha Allahu zan kiyaye". Tsaki ta ja kawai tare da kar6an kayan hannun sa, ranta duk a jagule ta tsani Sani haka kawai batare da ta san dalili ba, gashi da shegen kinibibi da uban bada ha'kuri wannan kalmar tasa ta za'a kiyaye harta gaji da jin ta amma kullum baya sake hali. Kitchen ta nufa ta kai kayan ta ajiye sannan ta sake fitowa tace da Hauwa ta hanzar ta ta gama aikin ta tafi gida kar yamma tayi sosai. Kitchen ta koma dan fara shirin shirya musu abincin dare tana yi tana sakin tsaki ka'dan-ka'dan.... 'Karfe 5:30 Jas ta dawo gidan da sallamar ta inda tasami mahaifiyar ta zaune a parlour hannun ta ri'ke da waya tana dubawa. Jas na shigowa ta cire hijab 'din kanta, ya saura mata riga sai wandon Uniform 'din tace " Na dawo Mummy " Washe baki Noor tayi tana duban 'yar tata itama tace " sannu da dawowa to yarinyar Mummy" Jas bata kula ba sai tace " ruwa zan sha". Noor cewa tayi "Uhum je ki sha amma ba mai sanyi sosai ba" #20 dake hannun ta ajiye akan hijab 'din ta daga gefen maman nata sannan ta tafi izuwa fridge 'din. Noor kam bata kula da ku'din ba sai ta cigaba da duba wayar ta batare da ta 'daga kai ba har sai da taji motsin tahowar Jas 'din kafin ta 'daga kai ta kalle ta sai kuma ta ajiye wayar tare 'dago hijab 'din Jas 'din tana murmushi da niyyar ninkeshi anan taga 20 naira ya fa'do. Zuciyan ta tsinkewa yayi sosai da ganin ku'din, cuz ita tasan bata bawa Jas ku'di wai musamnan dan ta kashe, kamar yanda yau ma bata bata ba lokacin da zata tafi islamiya " to daga ina ya fito" ta tambayi kanta. Jas na isowa hannun ta ri'ke da ragowar ruwan a hannun ta takce " Nasha ruwan Mummy" Bata kula maganar Jas 'din ba sai ta 'dago ku'din ta nuna mata tare da fa'din " Jasmin wannan fa waye ya baki?" Jas sai tace " Sani ne ya bani 'dazu da muna hanya ". Ranta taji ya 6aci sosai fiye ma da yanda taji 'dazu dan haka sai tace. Har amsa sunan Sani 'kwa'kwalwar ta keyi mata bakin ta na rawa ta furta " a wani dalili kenan?" Jas ma sai tace " Nima ban sani ba Mummy, cewa yayi in sayi sweet dashi ni kuma bana son sweet 'din?" Wani 'kululun ba'kin ciki da takaici ne ya ziyarce ta har ma bata san lokacin da ta furta " dan ubansa kuma sai a kace sai shi zai baki ku'di kafin ki sha sweet? ko kuma ce masa akayi naki uban bashi da ku'din da zai sai maki sweet 'din?" Kallon cikin idanun Jas tayi tace da ita " Wallahi idan kika 'kara kar6an ku'din sa zaki ga abinda zan miki agidan nan ke bama shi ba ko wani ne daban ki ka kuskira kika sake ansan ku'di awurin mutun ni da kene". Masifa take ji har cikin ranta, takaici da tu'ku'kin ba'kin ciki duk ya cika zuciyan ta, ji take kamar taje ta sha'ke Sani har sai ya suma, domin ga dukkan alamu so yake ya shiga rayuwar ta a du'kun'kune ta ko wani fanni, taya tana 'ko'karin ganin ta gyara rayuwar 'yar ta ta kula da ita zai ringa rusa mata, farko yawo yake 'ko'karin koya mata, ehh yawo mana tunda baya dawo da ita gida akan lokaci kullum idan sun tashi daga school sai ya 6ata lokaci, in tayi magana kuma ya kawo wani silly excuse 'din sa ya lullu6e ta dashi. Yanzu kuma ya 6ullo da batun bawa Jas ku'di how dare he?" Ce masa akayi sun kasa ne? Ko kuma ance masa Jas 'din na bu'katan ku'din sa, ai ba ku'di kawai bane yin alkhairi... balle Jas ai 'karamar yarinya ce irin su ba ayi musu haka cuz yaro wawa ne bai iya sabo da abu ba matu'kar ka saba masa da wani abin to kuwa wataran kai zai dama. Yanzu tana ganin Sani ya kaita ma'kura, ita bazata iya ko da yaushe tana maimaita masa magana ba gardi dashi ita kuwa akwai aure a kanta, sannan akan hakan idan har tace zata yi masa magana ne to kuwa bazata iya controlling 6acin ranta ba. Dan haka da Deen zata ha'da shi, kawai yayi masa magana in bazai canza ba sai a nemi wani driver shi yayi gaba abinsa yafi. *Ayi ha'kuri da typing errors pls* ❌ 👇🏼 *Naji da'din comment 'din ku kuma ina godiya sosai ga dukkan addu'o'in ku Allah ya bar kauna...wasu na amsa musu wasu kuwa bansamu damar amsawa ba amma dai kusani dukkan ku ina son ku.* 🥰 Wannan page 'din kyautar ku ne saboda jin da'din comments d'inku na jiya, shiyasa ma nayi muku yau duk da ba yau ya kamata nayi posting ba. _Comment, Vote and share_👌🏻 *Salmerh ce*😍 [11/17/2019, 9:34 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Thanks masoyana nagode sosai da kulawa Allahu ya bar 'kauna.* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *3* Kamar yanda ya fa'da washe gari Deen ya dira a cikin garin Bauchi, da yake ma da wuri ya taso shiyasa ya iso tun 11 da 'yan mintina na safiya. A lokacin kuwa gidan babu kowa sai Hauwa mai yi musu aiki ka'dai, amma bai da'de da isowa ba sai ga Jas ma ta dawo. Yau 'din da wuri Sani ya dawo da ita batare da ya bata wani tsawon lokaci ba. Jas kam da murnar ta ta isa wurin sa tana mai farin ciki da ganin sa ha'de da murnar zata je taga kakannin ta. Deen ma sama ya 'dagata yana dariya yana da farin cikin ganin gudan jinin nasa cikin walwala da 'koshin lafiya, sai daya gama juyi da ita kafin suka zauna kan kujera inda ya 'dora akan cinyar sa. Tambayoyi ya rin'ka yi mata kan makaranta da abubuwan da ake yi musu tana bashi amsa,sai daga baya ya kar6i textbook 'din ta yana dubawa tare da yaba 'ko'karin ta ganin bata fiye failing ba tun ba wurin tracing ba sosai ta iya shi fa dukkan alamu za'a yi gwana wajen rubutu. Yana cikin yaba matan sai Jas ta jefa masa tambayar " yaushe zasu je wurin su Uncle Saif 'din?" Deen sai ya bata amsa da fa'din " sai gobe Jas insha Allahu". Inda yayi maganar ba tare da ya kalli inda take ta ba. Murna ta sake saki har 'kananun ha'koran ta na bayyana a fili ta sake fa'din " Daddy kenan bazanje school gobe ba?" 'Dago kai yayi ya kalle ta yana murmushi yace " ehh mana bazaki ba... sai idan mun dawo zaki cigaba da zuwa abinki kinji?" Jas sai tace " Har da Mummy zamu je ko daddy?" Da " uhm " Deeen ya bata amsa a takaice. Take kuma sai Jas ta 'dan ha'de fuska tace " Daddy.....!" Deen yace " na'am 'yar gidan daddy". Sai tace " Daddy kullum idan zamu dawo daga makaranta da Sani ko sai ya dinga........" "Dukan ki?" Ya tare ta da tambayar hakan. Sai ta jijjiga kanta alamar " ah ah" tana mai cinno baki gaba. Murmushi yayi tare da dafe bayan ta ganin yanayin da tayi da bakin tan sai yace " Sorry kinji, duk abinda yake miki zan yi masa fa'da ya daina kinji?" Kai ta 'dage sama alamar " toh " Deen sai yace mata taje ta samu Hauwa ta cire mata uniform 'din jikin ta sai ta dawo. Tashi tayi ta fita da 'dan hijab 'din ta a hannu, Deen sai ya bi bayanta da kallo yana murmushi tare da tuno abinda yake yawan sata kawo 'karan Sani wurin sa, wato yawan tsokanan ta da Sani yake yi wai " cry-cry mai 'karamin baki" Tun ba yau ba take yawan kawo masa 'karan sani dan ita sam bata so ace mata cry-cry 'din nan shiyasa ma yanzu bata fiya yin kuka ba dan gudun tsokana dan ko Deen 'din ma wani lokaci har da a tsokanan nata. Tun farkon da aka saka a makaranta idan an kaita ne sai ta tayin kuka in ta gaji da zama tayi fa'din "Daddy" toh duk lokacin da a kaje 'daukan ta sai a same ta tare da Auntyn su, anan Auntyn zata basu labarin kukan da tayi shine su kuma suke 'dan mata wasa da hakan, musamman ma Sani da kusan kullum sai ya tsokane ta da hakan while ita kuma Jas bata so....balle da yanzu ta 'kara wayo idan ya tsokabe fushi take yi masa. Zaton Deen yanzun ma akan abinda zatayi magana kenan shiyasa ya dakatar da ita batare da ya ida jin furucin dake bakin ta ba. Jas ta 'dan 'dauki lokaci kafin ta dawo cus sai da Hauwa ta yi mata wanka kafin nan ta dawo. A jikin Deen ta lafe shima ganin Hauwa ta watsa mata ruwa sai kawai ya gyara mata kwanciya ajikin sa dan ta huta da kyau mintina ka'dan kuwa bacci yayi gaba da ita. 12:47pm Noor ta dawo gidan, dama hankalin ta na gida tun fitar ta bata samu nutsuwa ba saboda sanin da tayi cewa Deen na hanya a yau 'din, ji tayi ma badan test 'din da za'ayi ba da kuwa babu inda zata fita dan sosai tayi missing 'din sa a 'dan sati biyun nan a yayi baya nan. Da sallamar ta ta shigo parlourn inda ta hange shi zaune yasa system a gaban sa Jas kuma na daga gefen sa a kwance tana bacci. Noor da fara'ar ta ta 'karaso yayin da shima fara'ar dake kan fuskar sa ta sake fa'da'da fiye da na baya ya 'daga kai yana kallon ta yana murmushi tare da maida dukkan.hankalin sa gareta batare da ya motsa ba. Har ta 'karaso inda yake ta zauna daga gefen sa tare da rungumar daga gefen sa a hankali ta furta " welcome back Yah Deen...tun yaushe ka iso?" " Na da'de " ya bata amsa a takaice yana kallon cikin idanun ta still yana murmushi. 'Dan 6ata rai tayi tace " haba dan Allah Yah Deen shine kuma baka 'kirani na dawo ba?" Hannu yasa ya rufe system 'din dake gaban sa sannan ya sake kallon ta yace " me yasa zan 'kira ki kuma keda kike fama da lectures? Yanzu da kika gama bagashi kin dawo ba?" 'Dan juyawa yayi ya kallo Jas yace " Jasmine ta taya ni hira kin gama har tayi bacci". Kallon Jas 'din tayi itama sai yanzu ma ta lura da ita a cikin ranta ta ayyana yau kam da wuri suka dawo afili kuwa sai ta matsar da kanta jikin sa Fuskar ta manne da tashi daga gefen kunnan sa ta furta " me ka ci to daka dawo?" Kai ya juya mata alamar babu komai. A 'dan razane ta bar jikinsa tana kallon idanun sa tare da zaro idanu tace " haba Yah Deen... meyasa kuma ?" Ba tare da damuwar komai ba yace "Jiranki nake yi mana kizo ki bani". Ya bata amsa yana duban ta shima. Murmushi tasaki mai 'kayatarwa na jin da'din abinda ya fa'da 'din tare da 'dan sake mai harara ka'dan na zaman da yayi hakan batare da cin komai ba. Matsar da kanta ta sake yi ta bashi peck a gefen fuskar sa sannan ta mi'ke tsaye tana murmushi.......da sauri Deen ya kamo hannun ta dawo jikin sa yana 'ko'karin kissing 'din ta sai ta jijjiga mai kai tare ta yi masa nuni da Jas dake 'dan motsawa. Deen murmushi yayi ya sake ta tare da komawa baya ya kishingi'da da jikin kujera yana binta da idanu. Noor kam dinning ta nufa taje ta fara duba abincin dake wurin, murmushi ta sake saki ganin dagaske 'din bai ta6a komai ba suna nan yanda ta barsu. Da yake tun safe kafin ta fita ta tanadar masa da abinci da komai da tasan zai bu'kata ko da bata nan, da yake tasan ba mamaki ya dawo bata gidan sai kuma gashi hakan ne ya faru. Fridge ta wuce ta 'dauko ruwa da lemon zo6o datayi masa mai da'din gaske ta zo ta dire akan table sannan tayi masa bismillah tare da fara zuzzuba abincin. Har ya taso ya iso wurin bata gama serving musu ba, isowan shin ne yasata ta ja masa kujera amma sai yayi kamar bai gani ba, instead ya zauna ah ah sai ya tsaya daga bayan ta ya rungumo ta ta bayan tare da sau'ke kansa akan kafa'dan ta yana sau'ke mata hucin numfashin sa dake fita a hankali yace " Nureen Deeen " " umm" Ta amsa shi dashi tana mai mayar da duk kan hankalin ta gareshi. " i really....missed.... u" Ya sake fa'di a 'dan hahhar'de yana goga mata hancin sa a wuyan ta. Ba tace da shi komai ba sai shine ya sau'ke mata 'karamin kiss a wuyan nata daya sata lumshe idanu. Sakin ta yayi ya zauna a kujerar da ta ja masan yayinda Noor taci gaba da ha'da masa abincin a gaban sa, bata zauna ba sai da ta zuba nata plate 'din ma sannan ta zauna. A hankali suke cin abincin fuskokin su cike da annuri har suka 'kare gaba 'daya. Deen na kammala cin abincin ya shirya ya fita sallan azahar jin an fara 'kiraye-'kiraye. Koda ya dawo daga masallacin sai ya samu Jas ma ta tashi a baccin har sunyi sallah da mahaifiyar ta. A gaba yasata taci abinci har ta 'koshi sannan yasa Noor tasake yi mata wanka dan ta warware.....shiri sukayi cikin kyakykyawar shiga mai 'daukan hankali, sky blue captan ya sanya ajikin sa tare da karye hula gefe guda tamkar wani 'dan sarauta ya fito sai walwali ya keyi, yayin da aka shirya Jas cikin wata doguwar riga pink colour mai fa'di da kyau da tsada ga birgewa ga duk wanda ya kalla, 'dan 'karamin farin veil ne a kanta da farin cover shoe abin sai sai wanda ya gani. Noor photo tayi ta 'daukan su kala tana yaba kwalliyar su tare da mitan itama aje da ita amma Deen yace ah ah wannan fitar ta musammance. Daga 'karshe sai sukayi selfie dukkan su gwanin birgewa suna dariya. Sai da suka gama 'daukan photon ne sannan suka fita Jas na yiwa Noor bye-bye tana dariya hannun ta ri'ke cikin na Deen suka fita daga parlourn suka nufi harabar gidan. Sani driver na hango su ya mi'ke da sauri yana washe baki zaton shi koda tare dashi zasu fita, amma sai Deen ya dakar dashi da fa'din " karka damu yanzu zamu dawo ka huta abinka". Deen na gama fa'din haka yayi gaba ya bar tsaye agurin, har ya fara tafiya sai kuma ya tsaya tare da waigowa yace " Sani! Da 'dan hanzari Sani ya 'karaso inda suke tsayen yana fa'din " na'am ranka ya da'de!" Deen na murmushi yace " wato Sani har yanzu baka daina tsokanan Princess 'dina ba ko...'dazun nan ta sake kawo min 'karar ka". 'Dan sosai kai Sani yayi yace " Insha Allahu baza'a sake ba yalla6ai, yanzun ma ai ta girma ta zama 'yan mata bata kukan ta daina....ko Jasmine?" Kai Jas ta 'daga masa alamar "ehh" Deen ma Jasmin ya kalla yace " kinji ai yace ba zai sake ba ko.....so no more complaint.....okay?" Sai ta sake 'dage kai sama tana murmushi. Juyawa Deen yayi suka cigaba da tafiya tare da cewa Sani " sai mun dawo to" Sani ma sai yace " to yalla6ai...Allah ya tsare yasa a dawo lafiya" 'Dan 'daga murya yayi yace " Jasmin a kawo min tsaraba ko?" Jas bata waigo ba sai kawai tace " zan kawo maka sweet da choculates " Deen murmushi yayi yayin da Sani ya sake wangale baki yace " to 'yar albarka sai kun dawo ina nan ina jira" Jasmin bata sake bi ta kan maganar tasa ba har Deen ya bu'de mata mota ta shiga sannan ya zaga shima ya shiga tare da tada motar, horn ya dannawa mai gadi lokacin da suka isa bakin gate 'din. Suna fita daga gidan Jas tace " Daddy tunda ka dawo yanzu kai ne zaka na kaini school ko?" Deen take sai yace " ah ah.... mamana ni ai soon zan koma, Sani ne zai na kai ki kinji?" 'Dan tura baki tayi tace " Daddy ni fa bana son Sanin nan kullum cinye min........ baki na yake yi" Dai dai tace " _kullum cinye min_ .....'din nan Deen ya daina sauraran ta cuz sun iso junction 'din da zai sada su da babban titi ga kuma 'karan wasu motocin dake sakin horn shiyasa bai ji 'karshen maganar ta ta ba sai da ya dai-dai ta tu'kin sannan sai ya kalleta da mamaki yace " cinyewa kuma mamana kamar yaya?" Jas sai tace " nima ban sani ba Daddy.....ni dai kai nake so ka na kaini kullum". Deen bai sake bi takan maganar ta ta farkon ba cuz be yi zaton faruwar wani abu daban ba bayaga shirmen Jas dan haka sai ya 'dan saki murmushi yana tu'kin yace da ita " kin fiya rigima Jas, ni ai zanje aiki..." 'Dan waigowa yayi ya kalle ta yacigaba da fa'din "..... ko ba kya so in kaiki Makkah da Mummyn ki?" Jas da murnar ta tace " inaso Daddy har da Madina ma" Deen mirmushi yayi yace " Yauwa yarinya ta ko ke fa.... muje muga 'dakin Allah ko?" Tace " ehh Daddy" Tana murmushi. Shima murmushin yacigaba dayi daga nan ya maida hankalin sa kan driving 'din da yake yi. Asibitin da ya fara aiki anan Bauchi ya kaiwa ziyara da niyyar yiwa Safwan abokin sa bazata cuz shi yana nan 'din har yanzu amma kuma sai akayi rashin sa'a bai same shi a asbitin ba kasancewar yata shi a aiki dan haka sai ya bi ya 'dan dudduba sauran ma'aikatan nasu da ya sani inda anan suka ha'du da wata nurse Fadila da suka ta6a yin aiki tare da ita. Da fara'ar ta suka gaisa tare yi masa murnar canjin aikin da yayi cuz a lokacin ita bata nan tana hutu lokacin da ya koma aiki a Abujan shiyasa sai yanzu tayi masa murna. Daga nan gidan Safwan suka wuce suka 'karashi wunin su acan. Basu suka dawo gidan ba sai da yamma lis 'karfe biyar da kusan mintina arba'in sannan suka dawo. Jas da gudu ta taje ta fa'da jikin Noor tana dariya tace " Oyoyo Mummy" Itama Noor tana driyan ta rungume ta da fa'din " y'ata oyoyo" Deen kam tsayuwa yayi a kansu yace " ni kuma maraya ko?" Dariya suka sanya masa dukkan su shi kuwa Deen kunu yasha sai ya 'dan du'ka ya ajiye ledan dake hannun sa tare da sake kamewa daga tsayen wai shima sai anyi masa oyoyo sannan zai zauna. Noor koda ta gama dariyar tata bata kulashi ba, tana murmushi ta yiwa Jas ra'da a kunnen ta da cewar taje 'dakin ta ta jirata tana zuwa yanzu. Tashi Jas tayi kamar yanda Noor 'din ta fa'da mata Noor ma da idanu ta rakata har ta shige ciki. Tana ganin hakan kuwa ta mi'ke da sauri ta fa'da jikin sa shima Deen kamar jira yake ya rungume ta har sai da ya rabata da 'kasa suna juyi rare cikin farin ciki, sai da ya bata lafiyayyan kiss saman lips 'din ta sannan ya dire ta a hankali sai yace " ke baki san kara ba ko?" Da mamaki ta kalle shi tare da fa'din " karan me kuma Yah Deen ?" Amsa ta yayi da fa'din " wanda nake yi miki mana"! Tace " niii" Tare da 'dan waro idanu tana kallan sa. Sai yace " ehh mana...ko angaya miki badan nayi kara na 'daga miki 'kafa da ko fitan zanyi ne ?.....darajan baby Jas 'dina kike ci shiyasa na 'kyale ki ba dan ita ba Allah da yanzun nan zan......." 'Dan yatsan ta ta kai bakin sa cikin hanzari ta rufe bakin da shi tana murmushi tare da kallan cikin idanun sa. Deen kam juya kai yayi gefe tare da cire hannun nata dake saman bakin sa yace " let me talk please......ai bakya jin magana ne, kuma ba kina gani na kika share ni ba kika wani rungumi 'yarki bacin kin san how i badly missed u but sai ki rin'ka basar dani ko?" 'Yar dariya tayi ka'dan takai hannun ta gefe fuskar sa tace " haba My Deen bafa haka bane, Jas ai ita tazo inda nake bani naje na taro ta ba.......kuma ma baga shi kaima nazo ba" " Dana ro'ka 'din?" Ya fa'di tare da sake rungumota jikin sa. A hankali ta furta " sorry baza'a sake ba kaji?" Yace " kima sake ki gani nima sai in daina 'daga miki 'kafa ba ruwa na". " Kai Yah Deen ai nace bazan sake ba " Baiyi magana ba sai da ya kamo lips 'din ta ya 'dan ciza ka'dan sannan yace " Allah yasa " 'Kasan ma'koshi ta amsa da " insha Allahu". Maghrib nayi Deen ya wuce masallaci, yayin da Noor ta saka 'yar ta a gaba sukayo alwala suma suka gabatar da sallahn su tare da jero addu'o'i da kallum Noor bata ta6a gajiya da yin su saboda a wurin Allah ka'dai take neman maganin damuwar ta. Bayan sun idar da sallan ne Noor ta zaunar da Jas kan stool gaban dressing mirror tana warware mata kitson dake kanta kowa yayi shiru tsakanin su babu mai cewa komai, cuz Jas bata dogon surutu da Noor musamman da yake tana yawan kwa6an ta idan zata fara yi mata surutu duk dama bawai yawan magana ne da Jas 'din ba amma sosai Noor ta bada gudummawa wajen sake maida ita shiru-shirun 'karfi da yaji musamman idan suna tare su biyu. Ko yanzun ma hakane wanda hakan yasa dole sai da Noor ta tilasta ma kanta abinda ba son ranta bane sannan sam bata so yazama halin ta, amma kuma a yanzun tana jin idan ba tambayar tayi ba bazata ta6a samun natsuwa a zuciyar ta ba duk kuwa da tasan ba abu bane mai kyau ba aikata hakan amma yazata yi...? samun natsuwar zuciya yafiye mata komai a yanzun takeji. Taso Jas da kanta ta sanar da ita amma tasan Jas bazata ta6a yin hakan ba tunda ita ke hana ta yawan kawo gulma ko surutu marasa ma'ana kuma yarinyar ta hau turbar hakan sosai ta zaunu akai. Shirun nasu ta yanke da tambayar Jas wai ina da ina suka je da Daddy 'dazun?" Jas cewa tayi " gidan Uncle Safwan muka je Mummy har nayi wasa da little Afrah ma" Noor washe baki tayi da jin hakan sai tace " ah ah lallai kun sha yawo, .....sai kuma.......". Noor na shirin sake yin wata tambayar sai suka ji motsi. Itace tayi saurin juyawa cike da firgici cuz' bata yi zaton ganin Deen a dai-dai wannan lokacin ba dayake idan yafita sallar maghrib baya dawowa gida har sai anyi isha'i tukunna, amma kawai yau 'din kwatsam bata san dalili ba sai gashi kuma ya dawo. A hankali ya 'karaso cikin basarwa ya furta "gyaran gashi kuke yi ne?" Yayi maganar tare da kallon fuskar Jas hannun sa cikin aljihun wando. Kai Jas ta 'daga masa alamar "ehh " yayin da Noor ta amsa da " umm" a 'kasan ma'koshi. Deen bai sake magana ba kamar yanda bai sake kallon 6angaren da Noor take ba sai ya dan ja baya ya zauna daga kan side drawer yana duba cikin wayar sa. Noor kuma ta cigaba da warware gashin Jas 'din, shiru wurin ya 'dauka na 'dan lokaci har ta kammala tsifan mata kan ta taje tare da yin parking wuri guda da 'dan 'karamin ribbom Deen na zaune yana kallon wayar sa kowa abinda ke cikin ransa daban. Sai data gama mata komai kafin tace da ita ta je parlour ta jirata bari ta wanke hannun ta tana zuwa. Har Jas tafara tafiya sai Deen ya 'kira ta zuwa inda yake, Noor bata damu ba illah shigewa bathroom da tayi dan tsaftace hannun ta. Koda ta fito kuma bata samu Jas a 'dakin ba sai shi ka'dai a zaune kamar yanda ta barshi. A hankali ta 'karasa inda yake ta zauna daga gefen sa sai take jin wani iri da shirun nasa sosai take jin guilty conscious na sar'ke mata ga6o6i game da tambayar da ta yiwa Jas 'dazun wanda take kyautata aton yaji ta dan bata san tsawon lokacin da ya 'dauka tsaye a wurin ba. 'Dan 'dago wa tayi ta saci kallon sa sai da kuma mai da kallon ta gefen sa bakin ta na sar'kewa tace " Yah Deen!" Kallon ta yayi ba tare da yayi magana ko amsawa ba illah 'dage gira 'daya da yayi yana kallon ta a karkace. Itama idanun ta sau'ke a 'kasa sam takasa 'daga idanu ta kalle shi balle har su ha'da idanu dashi balle irin kallon da yayi mata yanzun sam yasa ta jin ba da'di. Kanta a 'kasan tace dashi " d'azu daku ka fita ka manta 'dayan wayar ka a gida kuma an ta 'kiran ka". Bai kalle ta ba yace " waye ya 'kirani ?" Amsa ta bashi a takaice da fa'din " _Jiddah_ !". *Kuyi min afuwa plz......nasan ban kyauta ba amma insha Allahu zan na 'ko'kar tawa wajen ganin nayi muku typing ko ba yawa ma.* Comment Vote Share *Salmerhn ku ce* 😍 [11/17/2019, 9:34 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *It's ur day dearies so enjoy it 🎂🍩 *HAPPY BIRTHDAY 2 u* 🍩🎂 *Sis Faateemah and my besty Dr Khausar.......may Allah bless u with d very best of evrything in your life. 🥰.* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *4* Ha'de rai Deen yayi ya wani tsare ta da idanu tare da fa'din " dalilin kenan da ya sanya kike neman sanin inda muka je ni da Jas?" Kai ta jijjiga masa da sauri alamar "ah ah". " to menene?" ya sake tambayar ta. Noor sharesa tayi ta 'kurawa gefen inda yake zaune idanun ta da suka cika taf da hawaye 'kiris suke jira su gangaro. Daya ga bata da niyyan tankawa ne yasa shi fa'din " am i not talking to u ?" yayi maganar a 'dan tsawace. Sai a lokacin Noor ta juyo da idanun ta kan fuskar sa ta kalleshi jin yanayin da yayi maganar sai suka ha'da idanu. A hankali ta furta " Yah DEEN......." daga haka bata 'kara fa'din komai ba illa saurin 'dago hannun ta 'daya da tayi ta toshe bakin ta da shi. Kukan daya ma'kale mata tun 'dazu ne ya kubce mata inda ta ringa yin kukan mai sauti da ko Jas dake parlour zata iya jiyo ta amma daya ke akwai 'karan T.V kuma Ninja Turtles 'din da take kallo a MBC 3 ya matu'kar 'daukan hankalin ta shiyasa bata jiyo ta ba. Deen kuwa kai ya kawar gefe tare da cizon la6en sa na 'kasa sam koka'dan baiji da'din abinda ta aikata yau 'din ba, amma babu yanda zai yi cuz ya tsani jin kukan ta sosai yake ta6a masa zuciya. A hankali ya juyo ya kalle ta ba tare da wani 6ata lokaci ba ya sa hannu ya rungumo ta jikin sa batare da ya furta komai ba sosai yayi 'ko'kari wajen ganin ya danne 6acin ransa yana rumgume da ita har sai da yaga ta 'dan tsagaita da kukan yanayin ta ya 'dan daidaita ta fara sau'ke numfashi kafin ya fara 'ko'karin raba jikinsa da nata. A hankali itama Noor ta furta sunan sa ganin yana 'ko'karin sakin ta Sai tace " Yah Deen dan Allah kayi ha'kuri ka yafe min......." Bata gama rufe baki ba ya tare ta da fa'din " amma kinsan koma miye ne ai bazan ta6a 'daukan 'yata ta cikina na kai inda be dace ba ko ?" Cikin 6acin rai sosai yayi maganar sai ma ta gode Allah da ya furta mata hakan domin Deen sosai yake 'daure ta da shirun sa idan tayi masa laifi amma yau 'din ga dukkan alamu zata 'dan samu sassauci. Da muryar kuka ta bashi amsa da fa'din " na sani Yah Deen.... i'm sorry please ba nufi kenan ba....kawai fa na tambaya ne". Ta 'karasa maganar tare da barin jikin sa ko dan taga yanayin fuskar sa a lokacin. Deen kuwa bai ce da ita komai ba sai 'dan 'karamin tsaki da ya saki tare da mi'kewa tsaye yana gyara rigar jikin shi yace da ita " na tafi masallaci". Bai ko jira jin abinda za tace ba ya sa kai yayi gaba abinsa. Noor da idanu ta raka shi har ya idasa barin 'dakin kafin ta dawo da hankalin ta gaban ta. Tagumi ta rafka tare da rintse idanu tana tuno rayuwar su na baya da shi a hankali siraran hawaye ke bin kuncin ta masu 'dumi, wani abin idan ta tuno shi murmushi yake sata yayin da wani abin kuwa ji take tamkar tayi ta rafka ihu ko zata ji 'dan sami sassaucin abinda take ji a cikin zuciyar ta. Ta 'dau tsawon lokaci a haka batare da ta sani ba, sau'kan hannun Jas da taji saman nata hannun ne ya sata yin firgigi ta dawo daga tunanin data fa'da. Murmushi ta 'ka'kalo ta sanyawa fuskar ta na dole tare da dai-dai muryar ta kafin tace da Jas 'din " Baby har kin gama kallon ne?" SJas cewa tayi " yunwa nake ji Mummy kuma Daddy yace zai kawo min ice cream amma har yanzu bai dawo ba ". Ajiyan numfashi Noor ta sau'ke sannan tace " ohh sorry Baby zai dawo kinji sallah yaje yi daya idar zai kawo miki...muma bari muyi sallahn kafin ya dawo ko?" Kai Jas ta 'daga sama tana kallon Noor 'din. Sai ta sake fa'din " Mummy idon ki fa akwai hawaye me ya same ki?" Noor saurin kaiwan hannu tayi ta goge fuskar tata sam tama manta da hawayen sai tace mata " bakomai Jas abu ne ya shiga min idon kuma na cire shi". Tana gama fa'din hakan sai ta mi'ke tare da kama hannun Jas suka nufi bathroom dan yin alwala. Sallahn isha'i suka gabatar tare da jero addu'o'i kamar yanda ta saba yi kullum Jas na tayata da fa'din Ameen sannan suka shafa. Ganin har a lokacin Deen bai dawo ba yasa ta tasa Jas agaba ta karanto mata suran da suka tsaya da karatu a islamiyar su dan ta gyara mata inda take 'dan kuskure wa. Take kuwa Jas tayi bismillah cikin muryar ta ta yarinta ta karanto mata suratul *Fajr* daga farko har zuwa aya ta goma sha tara a duk cikin ayoyin kuwa bata yi mata gyaran komai ba dan kuskuren ta yawancin yana bin yanayin harshen ta ne dayake yarinyace har sai da ta kai inda suka tsaya kafin Noor ta yi mata gyara wajen _wata'a kulunat-turatha aklal-lammah_ Wannan ayar ne yayi mata wahalan fa'da sosai sai da tayi ta maimaita mata kafin ta ri'ke shi daga shi sai ...... _watu hibbunal mala hubban jammah_ wato aya na ashirin kuma anan suka tsaya da karatun a cikin satin. Jas akwai 'ko'kari ba laifi dan Noor bata 'dauki wani tsawon lokaci ba wajen gyarawa Jas karatun sai gashi ya zauna abakin ta. Ganin haka yasa Noor sai ta kama hannun ta suka koma parlour dan suyi zaman jiran Deen kafin ya dawo. Ga mamakin su kuwa suna shiga parlourn sai suka ganshi zaune a ya sanya T.V a gaba yana kallon labarai. Ko da yaji motsin fitowar tasu ma bai 'daga kai ya kalle su ba yi yayi tamkar bai san da fitowar sun ba. Jas ce ma da ganinsa sai ta wuce gurin sa da gudu ta 'dane jikin sa tana tambayar ice cream 'din ta. Murmushi yayi tare da kamo chicks 'din ta da hannun sa 'daya yace " y'an matan Daddy mai kwa'dayi to na manta ban siyo ba " Kafa'da Jas ta no'ke tana cunno baki gaba tace dashi " ni kan ah ah". Waro idanu Deen yayi yace " ya za'ayi kenan to ?" Tace " Daddy tunda ka tuno yanzu ai sai kaje ka siya min". Sai yace " Smile then...in ba haka ba nima ba zani ba". Murmushi Jas ta saki tare da fa'dawa jikin sa ta kwanta. Shima Deen murmushin yayi sannan ya kai hannu gefen kujera inda ya ajiye ledan daya zo dashi ya 'dago shi. Itan ma 'dago ta yayi zaune tare da 'dago ledan saitin fuskar ta yana murmushi. Jas na ganin ledan bata yi wata-wata ba ta sa hannu ta kar6a ta rungume tare da fa'din " thank u Daddy". " yes Dear" Yace tare da mi'kewa da ita tsaye suka nufi dinning ganin cewa tun 'dazu Noor take wajen tana jiran su. Bai zauna ba sai da ya samawa Jas gurin zama a kujerar dake tsakanin su kafin shima yaja 'dayan kujerar ya zauna. Already Noor tagama arranging dinner 'din ta rurrufe dan haka bu'dewa kawai suka yi ha'di da bismillah suka fara cin abincin. Kuma ko a lokacin ma Deen ne da 'yar sa kawai sukayi ta shagalin su yayin da Noor ta sanya abincin a gaba tana kallo bai fi spoon uku ta kai bakin ta ba abubuwa duk sunyi mata yawa a zuci. Deen kam da Jas kamar ma sun manta da ita a wurin dan baya ci sau biyu batare da ya kai wa Jas a bakin ta ba ita ma kuma Jas haka suna ci suna raha abinsu. Noor ce shiru kamar bata wurin duk kuwa ashe Deen na lura da ita batare da ta sani ba. Jas ma kamar tasan abinda ke cikin ransa sai da ya mi'ka mata ta kar6a tana murmushi tace da shi " saura Mummy ma ". Juyawa yayi ya kalle ta sai amma bata ma san yayi ba domin ga dukkan alamu tunani takeyi aranta. Tana cikin tunanin kuwa taji an take mata 'kafa daga 'kasan table. Firgigi tayi tare da kallon inda yake ganin yanda ya nufo bakin ta da spoon cike da abinci fuskar sa ba yabo ba fallasa amma ya'ki kallon fuskar ta. Abincin ta kalla sannan ta sake maida kallon ta kan fuskar sa still ya'ki su ha'da idanu. Da niyyar ta ta'ki kar6an abincin amma sai taji muryar Jas na fa'din " Mummy is ur turn now " Dolem ta ta bu'de baki a hankali yasa mata abincin. Shine yaci gaba da bata tana kar6a ana uku sai tace ya ishe ta ganin har a laokacin ya'ki kallon cikin idanun ta sai yake sake sata cikin ru'dani. Parlour suka koma bayan sun 'kare cin abincin inda suka zauna jigum babu mai yiwa wani magana a tsakani Jas ma jikinsa take har tayi bacci. 'Karfe tara da 'yan mintina ya 'dauke ya kaita 'dakin Noor ya kwantar da ita, da kansa ya rage mata mata kayan jikinta amma rashin sanin inda kayan baccin ta suke yasa shi barin ta da 'yar rigar ciki ya fita ya koma nasa 'dakin. A parlour ya wuce Noor da ta kwantar da kanta jikin kujera tana binsa kawai da kallo. Ganin ya koma nasa 'dakin ne yasa ta tashi itama ta kashe dukkan switch 'din sannan ta shiga 'dakinta. Sai da ta gama shirin baccin ta kafin ta 'dauko wa riga da wando marasa nauyi ta sanya mata da hula. Zama tayi tai mata addu'o'in bacci ra shafe ta sannan ta rage 'karfin fan tare da kashe wuta ta fita bayan taja mata 'kofan. D'akin Deen ta nufa inda ta same shi kwance luf tamkar mai bacci dan ko sallamar da tayi ma bai amsa ba, a hankali ta 'karasa shigowa ta tura 'kofar ta kamar yanda ta samu. plz kar kuce yayi ka'dan fah. Comment Vote Share *Salmerhn ku ce*😍 [11/17/2019, 9:34 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* Dedicated to MeemarTJ Nagode sosai da Addu'o'in ku masoyana ubangiji Allah saka da mafificin alkkhairi. *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *5* 'Dakin ba wani haske sosai dan haka kawai sai ta 'karasa bakin gadon ta tsaya 'dan takaitaccen kallo tayi masa cuz rashin hasken 'dakin bai hana ta kallon fuskar sa dake 'dauke da lumsassun idanu da kyau ba, sam sai taji bata yadda baccin yake yi dagaske ba, 'dan murmushi ta saki da ya tsaya mata iya kan fuskar ta sannan a hankali ta haura gadon tare da matsawa jikin sa ta kwantar da kanta bisa hannun sa tayi shiru tana 'dan tunani. Ga dukkan alamu yau 'din _Mu'inuddeen_ 'din da ta sani tun baya ne ya motsa, musamman data ga yanda yake ta faman share ta ta fuskan magana, shi bai nuna 'karara cewa yana fushi da ita ba amma azahiri yanayin da yake yi matan sosai yake ta6ata. Ajiyan zuciya ta sau'ke a hankali....shiru tayi na 'dan lokaci itama tana sau'ke ajiyan zuciya tare da 'dan lumshe idanu. Tunanin irin matsayin da _Jiddah_ take dashi a wurin sa takeyi, wannan shine karo ba biyu da taga 'kiran Jiddah a wayar shi, sai dai kuma na yau 'din taga ko bi takan wayar be 'karayi ba har yanzu tana nan ajiye a parlour kan center table tunda ta kashe ta ajiye a wurin shima bai sake dubawa ba, sa6anin ranar farko da Jiddahn ta ta6a 'kiran sa, a lokacin kam taga 'kiran ya 'dan 'dauki hankalin sa ka'dan. Bata san manufar sa a yau 'din ba da be duba wayar ba. Baki ta ta6e tare da ayyana " ALLAH YASA IYAKAN ALA'KAR KENAN". Ganin har a lokacin DEEN bai motsa ba sai ta fara 'kiran sunansa a hankali tare da yi masa yawo da hannun ta saman 'kirjin sa. Deen kuwa bai amsa sunan shin da ta 'kira ba duk kuwa da cewa sarai yaji ta amma still sai yayi kamar bai ji ta ba a yanda ta samo shin ko motsin kirki bai yi ba, 'ko'kari yake yi kawai ya nuna mata kuskuren ta akan abinda ya faru 'dazun.... amma ba wai dan yaja maganar ko kuma dan ya 6ata ranta ba. Duk da hakan kuma ma sai yaji ba zai iya yin fushi da ita na dogon lokaci ba cus he missed her alots, and kuma bama ya son ace daga zuwan sa har sun samu sa6ani akan abinda bai taka kara ya karya ba, abin doesn't make any sence at all. ( shi a ganin sa) Sunan shin data 'kara ambata ne ya sanya shi bu'de idanu amma da yake tayi 'kasa da fuskar sa sai bata san hakan ba yayin da taci gaba da yi masa yawo da hannun ta saman jikin sa da har yake 'ko'karin canza masa yanayi ba tare da ta sani ba. Deen sake lumshe idanu yayi tsawon da'ki'ku yana ji da sauraron abinda take yi masan har ya fara jin tana neman 'kure shi musamman data ke yi masa wasa da nipple 'din sa tana 'dan ja ka'dan-ka'dan, dama gashi gwanin son ayi masa hakan sai kuma yaji bazai iya jurewa ba. Karo 'daya kawai ya birkito ta take ya maida ita 'kasan sa. Kallon fuskar ta ya tsaya yi kamar mai karantar wani abu har zuwa cikin idanun ta. Kallon-kallo suka tsaya yiwa juna na 'dan lokaci batare da sun furta komai ba. Noor ce ta bu'di baki a hankali tace " i'm sorry plz Yah Deen.....kayi ha'kuri kaji?" Deen bai tanka mata ba sai kawai ya lumshe idanu ya kuma bu'de su akan nata. Tana shirin sake magana sai yayi saurin matsar da fuskar ta ya ha'de bakin su waje guda, kissing 'din ta ya fara azafafe tare da sarrafa dukkan ilahirin jikin ta zuwa wani yanayi na daban mai wuyar fassaruwa. ***** Noor wutan da Deen ya 'dauke mata ne 'dazun ya 'dauki hankalin ta har ya sa kwata-kwata ta manta da batun Sani balle ma har tayi magana a kan sa kamar yadda ta tsara cikin ranta tun kafin isowar Deen 'din. Har kuwa suka gama faranta wa juna rai suka yi bacci bata tuna da hakan ba... sam bai zo kanta ba. Washegari da shirin tafiya suka tashi, kafin 'karfe takwas kuwa har sun kammala komai. Noor ce ma take 'dan mitan wai ai da an bar tafiyan sai gobe saturday ko kuma kawai abari sai Jas tayi hutu sai suyi tafiyar mai ma'ana yafi amma Deen sai cewa yayi " ai wannan tafiyar ta Jas ce ba tasu ba ita ke son aje dan haka kuwa shi ba zai 'ki faranta mata ba dan kawai makarantar friday ba, dan haka idan ita bata son zuwa tayi zaman ta". Shiru Noor tayi ta 'kyale shi kawai ta ta6e baki yayin da Jas ke ta murnar zata ga su granny da su uncle Saif da Zaid. Noor kam tun lokacin da ta ga Sani da sunan shi zai ja motar sai taji haka kawai ranta ya 6aci sai lokacin kuma ta tuna da batun maganar da ta tsara a ranta game dashi wanda bata samu daman sanar da Deen ba har yanzu. Tsanar Sani take ji cikin ranta haka kawai batare da tasan takamamman dalili ba. Lokacin da zata shiga motan 'dan 'karamin tsaki taja wanda daga ita ka'dai babu wanda yaji shi musamman data ji yanda Sanin yake tsokanan Jas yana yi mata wasa. Deen kuwa bashi da matsalar komai dan shi Sani baya gaban sa abinda kawai ya sani shine Sani amintaccen yaron gidan sa ne mai matu'kar raha da iya zama da mutane. ( ganin Deen kenan). Sani driver 'din ne ya ja su inda Deen ya umarce shi daya tsaya a shopping mall zasu yi siyayya. Da niyyar shi su biyu da Noor zasu shiga amma da Jas ta'ki zama a motar tace zata bisu sai kawai ya 'kyale ta suka shiga tare, siyayya suka yi mai 'dan yawa na tsaraba da wasu kayan amfani daga nan suka 'dauki hanyar garin Shuwaryn. Gari ne mai matu'kar yalwa da ni'ima ga da'din rayuwa, ita kanta Noor na jin da'din ganin ta cikin garin nasu, daya ke ma ta 'dan kwana biyu bata zo ba, sau tari Deen da Jas kanzo suyi weekend su koma abinsu batare da ita ba. Yau kuma Alhamdulillah gata a cikin mahaifar ta ta asali. Lokacin da suka isa 'kofar gidan Alhaji Baba tuni Jas tayi nisa a baccin da take yi tun a hanya. Koda a kayi parking 'ko'karin 'daukan ta Deen ya fara yi amma yana 'dago ta daga jikin sa kuwa sai ta bu'de idanun ta a hankali, da yanayin bacci ta fara rarraba idanu caraf tayi arba da 'kofar shiga gidan kakan ta Alhaji Baba wanda tana ganin haka tafara 'ko'karin barin jikin sa shima sai ya 'kyale ta kawai ya bita da murmushi. Batare da wani 6ata lokaci ba Jas tayi cikin gidan da gudu tana fa'din Ammee na, Alhaji Baba, Uncle Saif. Murmushi suka yi kusan dukkan su harda Sani ganin yanda Jas ta shige batare da sauraran kowa daga cikin su ba, 'dan 'karamin mayafin Jas 'din na ri'ke a hannun Noor yayin da 'dayan hannun nata kuma ta ri'ke handbag 'din ta da shi, itama tana murmushin tace " Jas ko shirme". Deen ne ya jagorance su zuwa cikin gidan da sallamar su, suna shiga ma sai suka ci karo da Alhaji Baba a harabar gidan tare da Jas ya 'dago ta sama da hannun sa 'daya 'dayan hannun kuma daddumar sallah ce ri'ke da shi ga dukkan alamu cikin shirin zuwa masallaci yake, dan kuwa sanye yake da shaddah sabuwa mai tsada ruwan zuma d'inkin riga da wando da babbar riga, yasha hula mai kyakkyawan zubi da birgewa sai tashin kamshi yake yi, sosai kayan suka kar6i faran fatan jikinsa. Idan ka kaga Alhaji Baba bazaka ta6a yin tunanin a 'dan wannan garin yake rayuwa ba. Yana ganin shigowar su kuwa ya sake fa'da'da fara'ar sa fiye da na baya ganin iyalan nasa tare da fa'din " ah ah ah..... yau har da 'ya ta kuka zo kenan.....bar kanku da zuwa 'yata" Yace tare da juyawa zuwa ciki. Suma murmushin suka yi tare da binsa a baya zuwa yalwataccen parlourn gidan suka zazzauna. Deen ne yana shirin zama yace " Alhaji nifa baka yi min barka da zuwa ba sai 'yar ka ka'dai ko in koma abina". " bani da damuwa ai ko ka koma tunda ga 'yata ga kuma amaryata tare da ni". Alhaji Baban ya bashi amsa yana murmushi. Sai suka maida masa da martanin murmushin gaba 'dayan su batare da wata kalma ba. Suna zama Jas tayi cikin 'dakin Ammee da gudu tana 'kiran sunan yayin da sauran dake zaune suka hau gaggisawa Alhaji Baba na tayi musu maraba da zuwa cikin farin ciki sosai dake fita tun daga zuciyar sa. Jas kuwa koda ta shiga 'dakin Ammee bata ganta ba sai de taji motsin ruwa a bayi dan haka sai ta fito ta dawo wurin Alhaji Baba da ke ta faman hira da yaran nasa cikin walwala da raha Jas sai tace dashi " Baba Alhaji ina su Uncle Zaid suke ?" Murmushi Alhaji Baba yayi sannan yace da ita " ai kya bari mu gaisa da kyau kafin ki tambaye sun ko amaryata". Jas cewa tayi " ah ah ai na gaishe ka kuma ina so in gansu ne". "Ai kuwa baki zo da sa'a ba domin kuwa duk suna makaranta". 'Dan 6ata rai Jas tayi tace" ai zanje makarantar in gansu". Juyowa tayi ta kalli Deen sannan tace da shi" Daddy ai zaka kaini ko?" " insha Allahu zan kaiki Mamana amma ba yanzu ba kinji?" Deen ya bata amsa da kulawa. Kai ta 'dage sama tana murmushi tace da Alhaji Baba " ai Daddy na yace zai kaini"! Shafa kan ta yayi yace " to 'yar Daddy Allah ya bada iko". Daga nan sai ya tambayi Deen yanayin sabon wurin aikin sa da ya koma. Deen yace " ba matsala komai na tafiya dai-dai". " masha Allah...Allah ya taimaka ya bada sa'a ya kuma rufa asiri". Baba Alhaji ya fa'di da kyakkyawar niyyar sa a zuci. Fitowar Ammee ne ya katse su gaba 'daya inda Jas ta tashi da gudu ta nufi Ammee ta 'kan'kame ta tana dariya Ammee ma dariyar tayi tace ' 'yar tsohuwa an zo kenan". " ni ba tsohuwa ba ce Ammee ai ni 'yan mata ce". Jas ta bawa Ammee amsa tana 'dan turo baki. " Iyeh lalle kuwa ai ban san kin zama 'yan mata ba sai yanzu". Ammee ta fa'da tare da 'dago Jas 'din sama suka 'karasa shigowa. Nan aka sake dasa wani sabon gaishe-gaishe daga nan Ammeee ta kawo musu ruwa daya ke ma dukkan su suka shigo har Sani so babu wata damuwar kai masa nasa ruwan duk anan kowa ya 'dan sha iya yanda yaga zai masa illah Noor ce ka'dai bata kai komai bakin ta ba. Alhaji Baba ne ya fara mi'kewa ganin lokaci ya 'dan ja ka'dan, yaso iyanzu ace ya da'de cikin masallaci amma zuwan 'ya'yan nasa sai ya katse sa dan haka yanzun sai ya tusa su a gaba daga Deen har Sani driver suka tafi masallacin gaba 'daya. Jas ma ta so bin su amma sai Deen ya hana ta tare da fa'din kar ta damu yanzu zasu dawo sallah kawai zasu yi. 'Kin yadda Jas tayi har taso ta 'dan fara yin rigima, Ammee ce tayi saurin janyo ta ta rungume tare da lallashi har ta nutsu. Ganin ya rage su biyu ne yasa Ammee tambayar Noor yanayin zaman su da Deen da fatan baya cutar da ita. Noor sai tace " Alhamdulillah babu matsalar komai Ammee". Hamdala Ammee tayi a fili da zuci daga nan sai ta fara yi mata nasiha tare bata 'kara bata ha'kuri akan zaman auren nata inda tace taci gaba da addu'ah Allah yana tare da bayin sa nagartattu tace itama nan tana tayata insha Allahu komai zai dai-daita. Noor cikin ranta tace " Allah yasa" yayin da a fili kuwa murmushi kawai tayi. Ammee taso su 'dan ci wani abin mai 'dan nauyi kafin dawowar su Alhaji ganin cewa ita ka'dai ce bata saka komai a bakin ta ba tun 'dazun amma sam Noor ta'ki cin komai agaban Ammee. Murmushi Ammee tayi tace " wai kin manta wace ni ko Hudah?, ni ce fa Ammeen ki nada 'din nan kike min irin wannan kunyar ko manta ni kika yi?" Sunkuyar da kai kawai Noor tayi tare da 'dan sake fuskar ta, cikin ranta ta furta " ai da da yanzu ba 'daya bane Ammee, yanzu Noor nake mahaifiyar Jasmine....ba Huda da kika sani a baya ba". Jas kam babu ruwan ta zagewa tayi ta ringa cin 'ya'yan itatuwan da aka kawo musu a hankali suna 'dan ta6a hira har lokacin sallah yayi sannan dukkan su suka su suka yi alwala suka gabatar da sallar azahar daga nan Ammee taja Jas suka tafi da fa'din zata watsa mata ruwa. Hanyar 'daki sukayi tare da ro'kon Noor akan ta 'dan ta6a wani abu koka'dan ma dan ita bata san wannan salon ba'kuntan tagaji da shi". cewar Ammee ta na 'dan dariya. Ko bayan shigan Ammee ma ruwa kawai Noor ta iya sha daga nan bata iya 'kara cin komai ba. ***** Su kuwa a can masallacin bayan sun idar da sallah suna wurin sanya takalma dan zuwa gida sai aka 'kira Sani driver cewar mahaifin sa babu lafiya suna asbiti ma har an kaishi amma yana ta ambatan Sani dan haka idan zai samu dama yazo ya duba shi da wuri. Jin hakan ne yasa Alhaji Baba yace da shi maza ya tafi yaje ya duba mahaifin sa, ku'di masu 'dan nawi Deen ya bashi hakama Baba Alhaji ya bashi na shan ruwa daga nan ko gida bai koma ba suka yi sallama ya tafi da fatan Allah ya tsare hanya ya kuma bawa mahaifin sa lafiya. (Ameen). 2:38pm suka dawo daga masallaci ganin su biyu ne yasa Ammee tambayar ina driver 'din kuma anan Alhaji Baba yayi mata bayanin meke faruwa itama da taji ta tausaya sosai sai ta bishi da addu'ah da fatan alkhairi. Tun kafin su kammala cin abinci Jas ke damun Baba Alhaji akan zata je gidan gona. Sai fa'di take " Baba Alhaji kayi sauri mu tafi da kai tunda Uncle Zaid baya nan". Ai kuwa yana kammala cin abincin dole suka tafi, sallar la'asar ma a can suka yi ta. Babban abinda yafi birge Jas a gidan gonan shine kaji da take ganin su da yawan anan na 'kwai (layers) da broillers, sosai suke birge ta idan tazo ta gansu, shiyasa a duk lokacin da ta zo garin to fa sai an kaita gidan gona nan tafi son zuwa yawo. A baya idan tazo 'kannan mahaifin ta ne ke kaita idan suna gida kenan wato Saif ko Zaid, yanzu kuwa da duk basa nan sai ta ri'ke bawan Allah Alhaji Baba. Ko da yamma da Deen zai kai Noor gidan mahaifin ta ma su biyu suka tafi cuz har a lokacin Jas bata dawo ba. Tare suka shiga har cikin gidan Deen ya gaida Ummahn Noor sannan ya fita. Deen bai wuce ba sai da ya aiko aka shish-shigo da tsaraba da kayan abincin da suka zo dashi, sai da aka shigo da komai kafin yaja motar yatafi bayan sunyi sallama da Noor kasancewar ita a gidan mahaifin ta zata kwana. Sai kusan maghrib kafin Alhaji Baba da Jas suka dawo gida, Jas na hango Deen zaune a harabar gidan kuwa sai ta 'kwaci hannun ta daga ri'kon da Alhaji Baba yayi mata ta tafi da gudu tana fa'din " Daddy oyoyo". 'Daga ta Deen yayi sama shima da fara'ar sa yace " my baby Jas oyoyo". Tana dariya tace " Daddy na kawo maka mango". Dariya Deen yayi ka'dan yace mata " ai ni bana cin mango mamana sai dai ki bawa Ammeen ki". Yana maganar ne tare da nufan inda Alhaji Baba yake ta howa a hankali. Barka da dawowa yayi masa sannan suka 'karasa cikin tare. Dawowan sun ne Alhaji Baba ya samu labarin tafiyar Noor gida take sai ya tasa yaron sa da suka dawo tare daga gidan gonar da kayan lambu, k'wai da kaji biyar yace akai mata can gidan. Baby Jas kam ko da ta dawo taga Noor bata nan bata wani 'daga musu hankali ba da yake tana ganin Deen a kusa, sai da dare yayi ne ma ta 'dan so tayi musu rigima amma daya 'kira Noor ya ha'da su a waya shikenan ba'a 'dau dogon lokaci ba tayi bacci. Washe gari da safe da zaije can gidan sai ya sata a gaba suka tafi tare, inda anan ne Ummah ta samu daman yi masa godiyan 'dawainiyan da suke da ita daga na jiya har na baya. Deen yace " ah haba Ummah ai bakomai" Tare suka fito dukkan su Ummah ka'dai suka bari a gida sai Ummie wata jikar Ummah dake zama a wurin ta, lokacin da zai tafi Jas nata yi masa bye-bye har yayi nisa, ranar JASMINE tare da mahaifiyar ta ta wuni, inda suka je gidajen 'yan uwa da abokan arzi'ki yinin ranar kaf basu yita a wuri 'daya ba sai da yamma suka yada zango gidan su Deen ganin yanda ya matsa mata da waya cewa su dawo gida hakanan yawon ya isa. Wata 'kawar Noor tun ta yarinta mai suna Binta datayi aure da jimawa yaran ta uku a lokacin, in ka ganta ma bazaka ta6a yin zaton sa'anni suke da Noor ba tsabar yanda rayuwa ke juyawa.....itace tayiwa Noor rakiya har gidan Alhaji sai wata 'yar sistern ta da ta biyo su tunda suka je gidansu itama take binsu da ita suka je ko'ina yarinyar batafi 7years ba, sai kuma Ummie da dama tare suka fito tun daga gida 'yar wani brothern Noor ne da ya rasu da jimawa, mahaifiyar ta ma already tayi aure a wani gidan ita kuma tana hannun Ummah ne. Ummie yarinya ce 'yar kimanin shekaru goma sha biyu goye take da Jas suna 'yar fira. Gidan Binta ne 'karshe da suka je shine tayi musu rakiya har gidan Alhaji Baban. Koda suka je gidan kuwa Ammee ka'dai ce a gida itace ma ke sanar da su ai Deen 'din sun tafi gaisuwa da Alhaji Baba zuwa gidan Malam Barau. Yayin da Ammee ta 'kara da fa'din " kin san har hanzu Alhaji ya kasa nutsuwa da abinda ya farun nan kullum damuwar sa Alhaji Barau". "Hakane Ammee, hakan yanada kyau ai". Daga nan shiru Noor tayi bata 'kara furta komai ba, ita kam sam bata son tuno da wasu abubuwan ma da ace 'dan Adam na iya shafe rayuwa da babu abinda zai hana ta binne rayuwar su ta baya tayi updating musu sabuwa fill, amma ba zai yiwu ba, dole idan wani abu ya faru abaya matu'kar mutane na raye to an dinga tunowa dashi kenan ko da kuwa an manta shi. Binta bata wani da'de ba tayi musu sallama ta koma gidan ta dan maghrib ta gabato, ganin hakan ma yasa Noor ta sallami 'dayar yarinyar da ta biyo sun har ma da Ummie dan itama bata san lokacin da zata koma gida ba tunda Deen baya nan. kar kuma ta ri'ke yarinyar mutane, dama gidan Ummah suke ne da babu damuwa tunda kakar tace, kuma ma itama Ummie ba mamaki Ummah ta nemi taimakon ta akan wani abin gashi sun wuni basa gida. Zama sukayi da Ammee suna 'dan hira tare da 'karasa aikin abincin da Ammee ke yi. Su Deen kam sai da suka yi sallar isha'i kafin suka dawo gidan, gaisuwa kawai sukayi da Alhaji Baba sai ya tambaya sun ci abinci ganin har Jas tayi bacci, Ammi ce ta bashi amsa da fa'din "ehh". Take kuwa sai yace " Mu'inuddeen ka kaisu gida kaga dare yayi". Ba tare da musun komai ba Deen ya tashi suka fita bai shiga motan ba sai da ya bu'de mata nata 6angaren ta shiga ya rufe kafin shima ya zaga ya shiga. Hannun ta ya kamo cikin nasa yana murzawa a hankali tare da janyo ta zuwa jikin sa cikin ra'da ya furta " Nifa bansan ki tafi Nuree mu koma 'daki na mu kwana please". Noor na jin haka ta bar jikin sa da sauri tare da marairai ce fuska. Gira ya 'dage yana kallon ta da mamaki sai yace" ya akayi kuma? sai yaushe zaki saki jikinki a gidan nan please....kuma ma banda abinki wama zai an abinda ya faru tsakanin mu ko da ma an sani 'din ni ba mijinki bane?" " Ni dai Allah kunya nake ji Yah Deen please kayi ha'kuri". Murmushin gefen baki yayi tare da sake kamo hannun ta yace " kunyan wa kike ji a gidan Babanki ne fa da Ammeen ki ko kin manta?" Pouching gefen cikin sa tayi sai yayi saurin dafe gurin tare da furta " awsshh ". " ai na girma sosai yanzu". Tace tana murmushi. Sai yace " ni banga hakan ba gaskiya tunda kunyar su ma kike ji yanzun". 'Dago ta yayi daga jikin sa tare da fa'din " ni dai tashi kiji kinsan ban jurewa ko ya zakiyi dani to yanzu". "Na yau ka'dai kam ka bini bashin sa amma ni bazan iya yin komai a gidan Alhaji Baba ba". " Naji to....then kiss me". ya fa'di kamar me irgo maganar. Kallon fuskar tashi ta tsaya yi with smile on her face, a hankali ta matsar da kanta kusa da shi ta kama lips 'din sa. Deen ba yau yasan halin ta ba dama matu'kar suka zo garin nan to baya sake samun kanta koda kuwa kwana nawa zasu yi, hakan ne ma yasa shima yake hanawa kansa bu'katar muddin suka zo tare har sai sun koma Bauchi, yau 'din ma bai san me yasa yake jin son kasancewa da itan ba. Idanun sa har sun 'kan'kance jin yanda take sarrafa harshen ta cikin bakin sa da niiyar sa ba zai tayata ba amma tsabar shauki bai ma san lokacin daya fita za'kewa ba, sosai yake sumbatar da da dukkan iyawar shi tare da bin ilahirin jikin ta da shafa. Ko lokacin data ji yaja mata Zip ma bata damu ba cuz tasan idan ba barin sa tayi ya rage zafi ba ba nutsuwa mata zai yi ba. A zafafe yake romancing 'din jikin ta dan gaba 'daya hankalin sa a tashe take yama manta da cewar cikin mota yake. Sai daga baya ne ya an kara da cewa a mota suke jin bai sake sosai ba, kuma ma a 'kofar gidan mahaifinsa Alhaji Baba. Barin ta yayi da sauri amma still sai ya lafe a jikin ta kamar 'dan yaro a hankali yace " me yasa baki tuna min cikin mota muke ba?" " ai nima mantawa nayi" Tace da shi tana 'ko'karin gyara jikin ta. Deen kuwa sai ya matsa ka'dan daga jikintan tare da jan hancin ta yace " kuma a hakan kike cewa kina kunyar su Alhaji bacin gashi baki yi acikin gida ba kuma kina shirin yi a 'kofar gida idan ya ganki fa". Juyawa tayi ta kallo 'kofar gidan sai ma yanzu ta tuna da hakan. A 'dan gagguce tace " Zipping min rigan to mu tafi da sauri ". Murmushi Deen yayi sannan yaja mata Zip 'din ya rufe mata. " muje to Yah Deen da sauri". "Dan ma na tuna miki". Yana maganar ne tare da 'ko'karin kunna motar. A hankali yaja suka bar haraban wajen, sai da suka yi tafiya mai 'dan nisa kafin ya sake tsaida motar. Kallon tambaya Noor tabishi dashi sai yayi 'dan guntun murmushi tare da fa'din " muje gidan mu?" Yayi tambayar yana mai kallon cikin idanun ta. Noor kam wani tashin hankali ne ya ziyarce ta da jin furucin nasa, idanu ta waro a kansa itama sai ta jefa masa tambayar" gidan mu kuma Yah Deen? saboda me?" Muryar ta na rawa tayi maganar saboda tsinkewar da zuciyar ta tayi. Deen kuwa bai damu ba sai ma ya kwantar da kansa akan sitiyarin motar a hankali yace " me yasa kuma zaki ce Nuree?.....i need u kema kinsani ai". Kansa a kan sitiyari ya fa'di hakan batare da ya kalle ba cuz shi ka'dai yasan abinda yake ji a lokacin. Sai tace "Amma Yah Deen ai naga gobe zamu koma, kuma fa kaga gidan yayi 'kura sosai dan an da'de ba'ayi amfani dashi ba.... ta ina zamu fara gyara shi...please kayi ha'kuri idan mun koma gida mana kaji?" Ta 'karashe maganar da sigar lallashi ha'di da shagwa6a. Deen kuwa 'dagowa yayi a take tare da juyowa ya fuskance ta da kyau sannan yace" ni bazan iya ba Nuree ke bakya jin tausayina ne? sati nawa rabona dake dan Allah da kike wani kawo min silly excuse....nima 'din ai gobe zan koma ko haka kike so in tafi da damuwa ta?" Kai ta jijjiga masa a hankali alamar " ah ah" Sai yace " muje to ai gyaran 'daki 'daya bazai bamu wahala ba". Yana maganar tare da 'ko'karin sake tada motar. Noor kam wani zazzafan hawaye taji ya sau'ko mata akan kuncin ta, wani 'daci take ji a zuciyan ta sam ta tsani wannan gidan ko ganin sa bata son yi a rayuwar ta me yasa shi bazai fahimce ta ba?, ko laifi tayi da take tsananin son shi da kishin sa. Rintse ido tayi tana tunanin hawaye na bin fuskar ta suna sau'ka da gudun gaske. Deen ma fasa tada motar yayi ya 'kura mata idanu yana kallon ta, sam bai yi mamakin halin data shigan ba amma yanzun sai yake ganin kamar harda rashin damuwa da lamarin sane ya sanya ta hakan. Tsawon mintina uku suna a haka ganin kukan nata ba mai 'karewa bane ya sanya shi 'kiran sunan ta. Bu'de idanun tayi ta sau'ke su a kan fuskar sa, saurin kawar da nashi idanun yayi gefe, domin ganin cikin 'kwayar idanun Noor cike da hawaye na matu'kar gigita masa lissafi, baya so ya 'kara wani abu akan abinda yake ji a yanzun. A hankali ya bu'di baki kamar bazai yi maganar ba da 'kyar ya furta " bu'katata ce ta sanya ki kuka ko Nuree?" Bata bashi amsa ba sai kawai tayi 'kasa da idanun ta tayi shiru. " Tambayar ki nake ki bani amsa". Hawayen ta tafara sharewa da hannun ta 'daya tare da dai-dai muryar ta amma still da yanayin kuka cikin maganar sai ya kasance shagwa6a ziryan ne ya fanshi muryar tata " ba haka bane fa Yah Deen... ni dai dan Allah kar muje wancan gidan ban son shi". Juyowa yayi ya kalle ta sau 'daya tak sai ya kuma ya 'dauke idanun sa. Batare da ya 'kara furta komai ba ya tada motar yaja bai tsaya ko'ina ba sai a 'kofar gidan Ummah. Parking kawai yayi yana jira ta fita ya wuce kansa na kallon gefen hanya. Noor kam ji tayi hankalin ta ya tashi sosai da ganin yanayin nasa, sai dai hakan ba zai ta6a sawa ta amince ta bishi wancan gidan ba duk kuwa da tasan kalar yanayin sa ha'kurin sa ka'dan ne ta wannan 6angaren. Kallon gefen fuskar sa take yi duk da babu wani haske sosai amma farin watan da ke haskawa shine ya bata daman ganin sa da 'dan kyau. Sun kai mintina kusan shida a hakan batare da wani yayi magana ba, shi Deen jira kawai yake ta fita shima ya wuce yayin da ita kuma Noor take ta sa'ka da warwara cikin zuciyar ta har ta yanke shawaran da taga ya fi mata sai dai tana ganin bazata iya wucewa gida ta barshi a cikin wannan halin ba ita kanta hankalin ta bazai kwanta ba. Ganin tana 6ata masa lokaci ne ya sanya shi waigowa a nutse yace mata " ki wuce gida dare nayi ina so inje in huta nima.....". Kafin ya rufe bakin sa sai tayi saurin kwantar da kanta bisa kafa'dan sa tare da dabaibaye shi da hannayen ta duka biyu. Shi kam shiru yayi bai kula ta ba jira yake yaji manufar hakan. Hawaye ne ya sake gangaro mata sai tayi saurin rintse idanu.....shima danshin dayaji ne gefen wuyan sa ya sanya shi fahimtar kukan da take sake yi. Sai ya kai hannun sa kan nata hannun yana 'ko'karin raba ta da jikinsa amma ta no'ke. A hankali tace " Yah Deen please kayi ha'kuri kar kayi fushi dani.....ni ban isa in gujewa bu'katar ka ba kai kanka kasani koda kuwa a ina ne ina maraba da kai amma dan Allah kar muje wancan gidan kaji?" Cikin natsuwa tayi maganar shi kansa sai da yaji natsuwa ta shige shi, musamman da ya fahimci maganar tata inda ta dosa, sai dai shi kuma ba zai iya kusantar ta a mota ba in ma hakan take nufi kenan. 'Dago hannunsa yayi tare da kai wa kan fuskar ta ya shafa a hankali sai ya cire hannun sa, nata hannun ya sake 'dagowa ya kai gefen fuskar sa yasha da hannun nata suna kallon juna yace " karki damu i'm ok...ki je gida sai safe". Bata fita ba sai take binsa da idanu kamar me san karantar wani abu a fuskar sa, ganin hakan yasa Deen ya saki hannun nata sai ya kai hannu ya bu'de mata 6angaren da take tare da sake nuna mata bu'da'dden 'kofar. Karyar da wuya tayi gefe tana kallon idanun sa sai ya jijjiga mata kai left and right. Slowly taja jiki ta fita daga motan tare da rufo masa 'kofan sai ta tsaya tana jiran wucewar sa. Yasan halin ta sarai yanzu sai ta'ki shiga gidan ta tsaya bin bayan motar da kallo idan yayi gaba, shima 'din kuma baya jin zai iya tafiya ya bar ta a wurin tsaye ba tare da yaga ta shiga gida ba cuz dare nada sharri kala-kala, dan haka sai yace da ita " 15seconds ban yadda ki 'kara anan ba maza ki shiga gida". Motan ya tayar dai-dai itama ta juya ta kama hanyar shiga gida, bai ja ba sai daya tabbatar ta shige kafin ya tafi. *Ayi ha'kurin jina da akayi shiru na tsawon lokaci plz...........JASMINE NA GAISUWA SOSAI* 🤠 *Salmerh ce* 😍 [11/17/2019, 9:35 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *6* A hankali Deen ke tafiya da motar tamkar bai san yin tu'kin haka yake yi, sam baiji da'din abinda Noor tayi masa ba duk da yayi 'ko'karin ba'kin cikin sa amma sam ransa ya kasa sakewa da hakan. Tsaban yanda yaji haushi 'kirjin sa har nauyi yake yi masa na takaici, ban dama marar sa data ri'ke sa. Bai tashi sanin abin sosai bane har sai da yazo shiga gida, da yake babu gate man dake kula da 'kofar gidan so dole sai shine da kansa zai fito ya bu'de kafin ya shiga. Yun'kurin da yayi da niyyan fita daga cikin motar ne ya sanya shi jin tamkar an sar'ke shine gaba 'daya, sosai yake jin feelings na damunsa, tsigar jikin sa duk ta mi'ke, ga cikin sa ma ba'a barshi a baya ba. Koma wa yayi ya kwantar da kansa kan sitiyarin motar tare da lumshe idanun sa, Jiddah ce abu na farko da ta fara zuwa cikin ransa a lokacin amma sai yayi saurin girgiza kan sa a 'ko'karin sa na ganin ya gujewa tunanin ta. Bai gama fitar da Jiddah a ransa ba yaji wayar sa dake cikin aljihun gaban rigar sa na vibration. Share wayar yayi batare da ya duba mai 'kiran ba har ya tsinke take kuwa wani ya sake biyo baya. 'Dan 'karamin tsaki yaja jin yanda wayar ke 'kara shiga rayuwar sa bayan halin da yake ciki a lokacin. Hannu ya kai ya lalu6o wayar wanda sunan *NOOREE* ya bayyana akai da manyan haruffa. Kamar ba zai 'daga ba kuma sai ya yaja yayi receive tare da sada wayar da kunnan sa yayi shiru. " Yah Deen"! Ta 'kira sunan shi cike da damuwa. Shiru yayi mata bai amsa ba. Sai ta sake fa'din " Yah Deen kana jina.......ka isa gida lafiya ko?" " miye matsalar ki da hakan?" Yayi maganar cikin 'karfin hali. Take idanun ta suka fara tara hawaye tace da shi " Haba Yah Deen...laifi ne dan na tambaye ka hakan dan Allah?". " To ni kaina ban sani ba tukunna, may be lafiyar na iso". Ya bata amsa da da kewa. Sai tace " Yah Deen bakace min shikenan ka ha'kura ba miye hakan kuma please kake min, kasan bazan juri fushin ka har hakan ba ko?" Bai yi mata magana kawai sai dafe 'kirjin sa da yaji yayi masa wani suka mai azaba da ya ratsa har brain 'din sa, hatta wayar da ke hannun sa ma bai san lokacin da ta zame ta fa'di ba, take kuwa ta mutu a inda ta fa'din, 'kirjin sa ya dafe da hannun sa 'daya a hankali yake jero bayyananniyar salati cikin azaban ciwon da ya ha'de masa guda biyu. Noor kam nata" hello!, hello!!!, Yah Deen....." Taji shiru, bin wayar tayi da kallon mamaki, cikin ranta ta ayyana kar dai Yah Deen kashe wayar sa yayi. Koda ta sake gwadawa kuwa ga mamakin ta switch off aka ce mata. Sosai hakan ya ta6a ta bai tsaya iya zuciyar ta ba har sai da ya nuna a gangan jikin ta. Dawowa tayi 'dakin da ta baro Ummah a ciki tana tafiya a hankali tamkar wacce 'kwai ya fashewa a ciki, inda ta sami Ummah nata a kishingi'de, yayin da Ummie ke kwance a gefen ta kan katifa tuni tayi bacci abinta. Ummah na ganin ta ta mi'ke tare da gyara zaman ta da kyau tana kallon ta cike da murmushi. Yanzu ta bar 'dakin jikin ta ko kayan kirki babu cuz fitowan ta daga bayi kenan ta watso ruwa shine ta 'dauki wayar ta fita 'kiran sa. Inda dama manufar yin 'kiran shine dan taji ya ya isa gida ta kuma 'kara jin yanayin da yake ciki, dan ita kanta ta kasa samun natsuwa tun rabuwar su. Rashin samun gamsasshiyar amsa daga gareshi da kuma tukuicin datse wayar da yayi ne ya sanya ta dawowa 'dakin cikin sanyin jiki. " Menene haka 'yar nan? naga kin wani dawo wata iri meya faru?". Ummah ta jefa mata tambaya tana kallon ta tuni kuma murmushi dake kan fuskar Ummah ya riki'da ya dawo damuwa. Sai da ta sami bakin gadon dake 'dakin Ummah ta zauna kafin tace " bakomai Ummah, kawai na 'kira shi ne naji ko ya isa lafiya sai kuma yace min har yanzu bai kai ba". Tana maganar ne tare da lalu6an abin shafa daga cikin jakar da suka zo da ita. " Shine kuma kika dawo haka dan har yanzu bai 'karasa gidan ba? Miye abin damuwa a ciki? Mu'inuddeen ai ba ba'ko ko kuma yaro, 'dan gari ne fa .....kuma kin san shi da sabgogi...... ni fa har kin firgita ni wallahi da na ganki" Ummah ta 'karasa maganar tata da 'dan sakin fuska. Tunowa da tayi cewar man sha fan baya cikin jakar ne ya sanya ta sakin 'dan 'karamin tsaki a hankali. Zipping jakar tayi sannan ta mi'ka hannu ta 'dauko mai 'din kuma sai a lokacin ne ta bawa Ummah amsar ta da fa'din " sabgogin mene da shi Ummah yanzu bacin duk abokan hul'dar tasa basa nan". " kede ki bi a hankali uwata, ki daina sanya damuwa a ranki bisa wasu dalilai na daban marasa amfani da ma'ana, idan kince haka zaki cigaba da yi wallahi zaki sha wahala arayuwar nan.... hmm Allah kiyaye dai". Ummah ta 'karasa da fa'din hakan tare da komawa ta kishingi'da abinta kamar 'dazun. Noor kuwa har ta kammala da shafa mai 'din ta 'dauko kayan baccin ta sanya bata furta komai ga Ummah ba. Mi'kewa tayi a gadon batare da ta 'kara fa'din komai ba cuz abinda Ummah take tunani daban yake da abinda ke tsakanin ta da Deen, ita kuwa tana ganin ba abin sanar wa haka ga kowa bane shiyasa kawai tayi shiru duk da kuwa ta fahimci Ummah kamar na ganin kishi take yi, duk da kuwa a yanda tasan halin sa ko da ace kishin ne a ranta to ba laifi ne amma ma bata sanyawa ranta faruwar wani abu daban ba a wannan lokacin, sam babu hakan cikin ranta a, dana sanin rashin 'kin amince masa ma takeyi duk da kuwa har a lokacin tana nan a kan bakan ta na farko, amma yanayin da taji yake magana ka'dai ma ya fi sanyata damuwa dan tasan babu mamaki fama yake da kansa akan 'kin amince masa da tayi. Shiru ne ya 'dan biyo baya na wasu 'yan lokuta kowa da abinda yake sa'kwa cikin ransa, Ummah ce ta sake fa'din " ni kuwa ya jikin mijin naki fatan dai yanzu ciwon yayi sau'ki ?" Sai da ta 'dan mi'kar da hannayan ta ta kuma lumshe idanu kafin tace " da sau'ki sosai sai godiya gaskiya, dan har ma na manta rabon da ya tashi masa....ina jin dai an dace ciwon ya tafi". Ummah cewa tayi " masha Allah, Allah ya 'kara lafiya da nisan kwana". Da "Ameen Ameen " Noor ta amsa mata daga nan bata 'kara magana ba har bacci yayi gaba da ita. ***** 'Bangaren Deen kuwa da 'kyar ya samu zafin 'kirjin ya ragu masa inda ya lalla6a a 'dan ran'kwafe ya samu ya fita daga motar yaje ya bu'de gate 'din tare da jan motar ya shigar ciki. Yanayin yanda yake tafiya idan ka ganshi har zakayi zaton cikin halin maye yake tsaban yanda yake tafiyar cikin rangaji shi ciwon da cikin sa keyi ne kawai ya dame sa. Koda ya isa 'kofar parlourn ma sai da yayi 'ko'kari ya seta komai nasa, tafiyar sa da muryar sa ya daidaita ta yanda iyayen nasa ba zasu fahimci yanayin da yake ciki da wuri ba, amma a zahiri kallo 'daya zaka yi masa ka fahimci ba dai-dai yake ba musamman idan kayi duba da cikin idanun sa yanda suka riki'de zuwa ja suka kuma 'kan'kance, shi kansa ya san hakan amma bai damu ba saboda dare ne yasan gane hakan zai matu'kar yi musu wahalan gaske Ciki-ciki yayi sallama yana daga wajen, jin an amsa shi ne yasa shi 'dago 'kafar sa ya shigo. "Ka dawo ?" Alhaji Baba ya tambaye sa sai ya amsa da " umm na dawo Alhaji" A takaice. Hanyar 'dakin sa ya nufa tare da furta "sai da safe Alhaji...."bai jira yaji nashi amsar ba ya 'kara fa'din" Ammee mu kwana lafiya". "Zonan Deeni meke damun ka ne wai?" Alhaji ne yayi wannan tambayar dan tun a muryar da yayi sallama Alhaji Baba ya gane ba lafiya ba. Cak Deen ya tsaya da jin muryar Alhajin tare da 'dan juya idanu ya lumshe su ya kuma bu'dewa ba tare da yayi niyyan fa'din komai ba. Alhaji ne ya sake fa'din" da kai nake magana ko?" " Baba 'kirji na ke min zafi amma ba wata matsala bace, zan sha magani yanzu idan na shiga". Ya bashi amsa da fa'din hakan dan hakan ka'dai zai iya furtawa ya kare kanshi batare da sun 'dago damuwar sa ba. "Subhanallah" Ammee ta ce cikin damuwa tare da tasowa ta nufo inda yake" me yaja hakan ? Me yafaru bayan fitan naka ko dama haka yake yima kullum?" Ammee ce ke jero masa wa'dan nan tambayoyin cikin tashin hankali. Girgiza mata kai yayi a hankali tare da fa'din" Kar ki 'daga hankalin ki please Ammee, ba abin damuwa bane zai daina ne, bari inje insha magani yanzu". "Wani irin kar in damu Mu'een ka ga idanun ka kuwa....?" Bata gama kai aya ba ya tare ta da fa'din" idanu na bacci nake ji sosai ne shiyasa.......let me go nd take mu drugs.....okay". Yayi maganar tare da 'ko'karin wucewa 'dakin sa. " To Allah ya sawwa'ka" Alhaji ya fa'di yana daga inda yake zaunen cuz shi bai taso ba daman, batare da ya sake yun'kurin jefa masa wata tambayar ba ya barshi ya wuce 'din kamar yanda ya bu'kata. Deen 'dakin sa na da dake gidan ya wuce, sai da ya shiga bathroom ya watso ruwa inda ya ya 'dauki tsawon lokaci kafin ya fito sai yayi kwanciyar sa a kan gado daya ke yanzu ma ya 'dan rage jin abinda yake ji 'din sai 'dan abinda ba'a rasa ba..... ba dai kamar 'dazun ba, amma duk da haka zuciyar shi bata hana shi lalu6o wayar sa yayi dialling wata number ba tare da lafewa sosai kan gadon. (Kuyi ha'kuri fa dan nima banga sunan ba ballantana in fa'da muku). Ammee sosai ta so 'daga hankalin ta da jin cewar 'kirjin Deen na ciwo, tsoro take yi kar ciwon zuciyar sa ne ke shirin motsawa. Haka ta zauna ta dafe kanta, gaba 'daya ta nemi natsuwar ranta ta rasa shi. Alhaji Baba ke kwantar mata da hankali akan kar ta damu ba abu mai tsanani bane tunda ma gashi ai da kansa ya shigo gidan. Taso ta je ta sake duba shi bayan shigar tasa amma sai Alhaji ya hana ta da cewar " koma meke damun sa ai a yanzu ba zai so a dame sa ba ta bar shi kawai zuwa safiya in da rai komai zai dai-dai ta". Haka Ammee ta ta ha'kura ba dan taso ba ta tafi ta kwanta. Alhaji Baba kam anan ta bar shi yana zaune tsawon lokaci yana tunani, shi kansa fa abin ya dame sa kawai ya danne ne a zuciyar sa. Sai daya kusan raba dare a nan palourn sannan ya tashi ya 'karasa 'dakin Deen 'din, a hankali ya tura 'kofar inda ya same shi kwance jikin sa ba ko riga sai dai dogon wando kawai na bacci da ya sanya. Hannun sa duka biyu dafe da cikin sa yana kwance rigingine. Duk kuwa da cewa bacci yake yi amma zaka ga goshin sa a tattare, kallo 'daya zaka masa ka fahimci cewa ba'a yanayi mai da'di yayi baccin ba. Alhaji Baba kai ya jijjiga ganin yanayin Deen 'din, domin a fili yanayin sa ya fallasa asirin zuciyar sa, Alhaji Baba bai sha wani wahalar gane 'karyar da Deen ya sharara ba na cewa 'kirjin sa ne ke ciwo, amma dubi yanda ya dafe cikin sa. Godiya ya jerowa mahallici Alhamdulillah har sau uku, da kuma fatan Allah yasa ba zuciyar bace da gaske, idan ya kasance hakan kuwa zai matu'kar jin da'di. Jijjiga kai Alhaji Baba yayi tare da fa'din " Allah ya shirya min kai Mu'een Allah ya yafe mana kura-kuran mu gaba 'daya".(AMEEEN). ***** " Daddy ina Mummy na?" Jasmine dake tsaye daga bakin gadon da yake kwance ta tambaye sa hannun ta kan sa tana wasa da suman kansa, fuskar sa na 'daya gefen daya ke yana cikin baccin yaji hannun nata a kansa wanda sanadin hakan ne ma yasa shi farkawa. A hankali ya juyo ya tsura mata idanu yana kallon ta cikin kyakkyawan shirin ta da yasan aikin Ammee ne a yau 'din, sosai yake son 'yar tasa da dukkan zuciyar sa, ba'kin cikin ta sam baya fatan gani har 'karshen rayuwar sa, buri, 'kauna da soyayyar sa kaf a kanta suka 'kare, zaka ga walwalar sa koda kuwa waye kai matu'kar ka sanya Jasmine cikin farin ciki. Juyi yayi tare da 'dan yin mi'ka ka'dan, hannun sa ya kai yaja hancin ta yana murmushi yace " baki gaida ni ba kike tambayar mummyn ki ko?" Kafin ma ya rufe bakin sa tayi gaggawan fa'din "Ina kwana Daddy...." batare da ta jira amsa ba ta 'kara da fa'din" ai na gaida Baba Alhaji ma da Ammee, Baba Alhaji ya bani dabino da zam-zam". "Iyeh Baby na ta dawo 'yar gatan su Alhaji kenan.....wato dan haka ne yasa har kika manta ki gaida ni ko?" Jas jijjiga kanta tayi tare da fa'din " ah ah ai jan gaishe ka har da Mummy na ma". " Mummyn naki ai bata nan itama taje wajen maman ta". Cewar Deen yana kallon ta. " To Daddy ka kaini wurin ta ". Jas ta fa'di cike da shagwa6a kamar ba itace me surutu yanzun ba. Shiru Deen yayi kawai ya kauda idanun sa a kanta ya mayar gefe yana tunanin yanda zaiyi da ita. D'ayan wayar sa da ya kalla ne a gefen gadon yasa shi mi'ka hannu ya 'dauko ta, dialling numbern Noor yayi tare da 'kurawa wayar idanu, sai yanzu ma ya tuno abinda ya faru jiya, sam bai ga laifin ta ba domin ya san laifin sa ne gaba d'aya, amma me yasa itan bazata iya yi masa uzuri na rana 'daya ba?" Noor kuwa fitowan ta kenan daga wanka daya ke tasan yau zasu koma kuma da wuri zasu tafi cuz idan sun koma Deen ma zai wuce Abuja duk a yau 'din, so shiyasa take 'ko'karin shiryawa da wuri dan kar su rigata shiri. 'Karan wayar ta da taji ne yasa hankalin ta ya koma can, tana ganin sunan Deen sai tayi saurin danna receive don dama tun jiya ta kwana da shi a cikin ranta. Sassanyan muryar ta da yaji tana sallama cikin wayar ne yasa shi lumshe idanu " Barka da safiya Yah Deen". Ta 'kara fa'di bayan sallamar daga 'dayan 6angaren. Bai amsa mata ba sai yayi saurin mi'kawa Jas wayar shi kuma ya tashi ya shige bayi kamar an tsikare shi. " Mummy". Jas tace tana turo baki. Ajiyan zuciya Noor ta sau'ke tare da fa'din " Na'am Mamana ke ce?" " Umm " Jas ma tace a takaice. Sai Noor ta sake fa'din " Ya a kayi baby kina lafiya ko? ina Daddy?" "Yana bathroom". Jas ta bata amsar 'daya daga cikin tambayoyin nata wanda taga zata iya badawa. Noor murmushi ta saki a 'dayan 6angaren, tasan ba mamaki Deen fushi yake yi da ita, shiyasa ya shige bayi bayan ya ha'da Jasmine da wayar tunda ai tasan Jas ba iya 'kira zatayi da kanta ba dole sai an mata. " Mummy ni zan zo gurin ki.....". Da taji Jasmine na fa'di ne ya sanya ta yanke tunanin da take yi da kulawa tace da ita. " me kika ce Baby ban jiki da kyau ba". " Ni gurin ki nake so Mummy". Jas ta sake maimaitawa a sakalce. Murmushi Noor tayi tace " Ai baki ko gaishe ni ba dan haka babu gurina da zaki zo nima ba ruwana". " sorry Mummy, good morning". " Yauwa my princess....ko ke fa, hope kowa na lafiya?" "Ehh har da nima Mummy, Ammee ta min wanka ta samin turare a jikina". "Ahh masha Allah ashe yarinya ta tayi kyau sosai ko?" Jas washe 'yan ha'kwaran ta tayi na jin da'din maganar. Noor sai tace " kin zama 'yar gatan Ammee kenan". " Harda Baba Alhaji ma ai shima ya bani zuma da zam-zam da dabino na ci". " iyeh....duka ke ka'dai mamana, gaskiya Alhaji ya kyauta, me kika ce masa to". Noor ta 'karashe da tambaya sai Jas tayi saurin fa'din" nace masa nagode". "Yauwa Babyn Mummy, May Allah's blessing be with you....hum". Deen da fitowar sa kenan daga bathroom 'din kunnuwan sa suka jiyo addu'ar Noor, a saman la66an sa ya amsa da " Ameen summah Ameen". Noor kuwa sai tace da Jas 'din" bari nima in shirya ko sai ki jirani zan zo kinji.... sai mu koma gidan mu ko ba kya so?" A hankali Jas ta amsa da " inaso". " Yauwa Baby bye" Daga haka ta yanke 'kiran tare da cigaba da shirin ta. ***** Lokacin da yaje 'dauko Noor a gida tare da Jasmine suka tafi, kuma ga mamakin Noor sai taga fuskar sa wasai a sake ba kamar yadda ta tsammaci ganin sa ba, cuz tayi tunanin zai yi fushi da ita ne tunda har ya kashe wayar sa jiya suna cikin magana. Sosai taji da'din hakan da yayin har take jinjinawa wannan ranar mai tattare da sa'a a gareta, da har tayi masa laifi amma bai 6ata ransa ba. Sallama yayi wa Ummah suka fito a tare dukkan su da Jas bayan Ummah ta cika su da tsaraba irin nasu, da tulin dabino, Ummie ce ta fito musu da shi aka sanya bayan mota. Haka suka rabu da Ummah cikin farin ciki tana tsokanar Jasmine wai tsohuwa mai sunan flower, Jas kuwa tace ita ba mai sunan flower ba ce ita mai sunan maman Daddy ce". Dariya suka 'dan yi kafin Ummah ta bisu da Addu'ahn sau'ka lafiya. Ko cikin motan ma Noor shiru tayi fuskar ta cike da annuri, har kwantar da kanta tayi jikin kujera tana murmushi ita ka'dai. Haka har suka isa gidan Alhaji Baba basuyi wani dogon magana ba tsakanin su, nan ma dukkan su suka shiga cikin gidan, Noor ta gaida in-laws 'din nata tare da yi musu sallamar tafiya. Alhaji Baba bai bar su sun tafi ba har sai da ya 'kara jan hankalin su sosai a kan rayuwar duniya da kuma ha'kuri da juna cikin zamantakewar su. Ammee ma sai da ta 'kara da nata kamar wasu sabbin aure su Alhaji basa gajiya da sake tunatar musu da muhimmancin kasancewar su a tare da junan su. Daga 'karshe Ammee tace da Deen dan Allah ya daina wasa da shan maganin sa dan jiyan nan sosai ya so 'daga mata hankali dan ma Allah yasa ciwon bai yi tsanani ba. Murmushi Deen yayi yace da ita " kar ki damu Ammee na insha Allahu ina nan araye har sai kingan ni cikin jikokina nima". Murmushi sukayi dukkan su Ammee kuwa tace " ja'iri kakar ka ka mai dani ko?". Basu 'kara 6ata wani dogon lokaci ba suka 'dauki hanyar Bauchi, Noor kam da'di take ji har cikin ranta, lokaci-lokaci ta kan tsura masa idanu sai kuma ta 'dauke, ba'a 'daukan lokaci kuma sai ta sake. Sosai yake bata mamaki musamman da taji bai tado maganar jiya ba ya share tamkar babu abinda ya faru. Deen kam kasa ha'kuri yayi da kallon har sai da ya tambayi dalili shima 'din fuskar sa a sake wasai yayi tambayar . Tana jin ya tambayi dalilin kallon tamkar dama jira take yi sai ta juyo da kyau ta fuskance shi sannan tace " wai jiyan nan me ya sami wayar ka ne Yah Deen muna cikin magana naji ta yanke ko dana sake 'kira kuma bai shiga ba.....miye dalili". Shi kam ma sai a lokacin ya tuna da batun wayar tasa dake jefe cikin motar, bai ce da ita komai ba sai da ya 'dauko wayar kafin yace " kin ganta ma ni ai sam na manta da ita, tun jiyan tana mota ina jin ba caji ne shiyasa". Shiru tayi bata sake yin wata magana ba, tasan dai ba rashin caji bane ya sanya hakan, in ma rashin cajin ne ai kuma ba zai kasance ya bar wayar jefe a mota ba. Sai dai bata tsawaita tunanin a ranta ba, duk kuwa da cewa tana da ya'kinin akwai wani dalili 6oye bayan wannan amma tunda kam shima 'din be nuna mata 6acin ransa ba ai shikenan. Batayi mamaki ba lokacin da ya jona wayar a caji sai taga yana da kimanin 50% na caji a ciki, kauda kanta tayi tamkar bata gani ba ta koma kallon gefen hanya. Kafin su isa kuwa aka ringa 'kiran Deen kan wani emergency aikin da ya taso dole tasa suna sau'ka ko hutawa bai yi ba sallahr azahar ka'dai yayi sai ya fito da shirin tafiya da jakar sa ka'dai a kafa'dan sa da yake motar kasuwa zai bi bai taho da mota ba san da zai zo. _sai fatan Allah ya sau'ki Mu'een lafiya......Ameeen_ ***** Jikin mahaifin Sani yayi tsanani sosai, cuz a lokacin da aka kai shi asbitin ma ko gane ahalin sa bai yi illah sunan Sani da yake iya furtawa a hankali. Gashi dama yana da hawan jini tun a baya sai kuma wannan ciwon da ya 'kara sako shi a gaba. Da farko duk sun raina ciwon domin ganin kamar abin bana kirki bane sai babu wanda ya damu, amma tashin farko da ya gigita shi da azaba 'kafar sai take 'kara 'kumburi ga shi baya iya bacci koda dare ne. Dole tasa suka kaishi wani asbiti dake cikin garin Jos. Ko a asbitin ma ansha fama dashi kusan wata guda amma abin ba sau'ki sai an 'daga shi an kuma kwantar, daga 'karshe sai suka tattara shi zuwa gida domin a gwada yi masa na gargajiya. Alhamdulillah kuwa ba laifi,sai aka dace domin kumburin 'kafar tasa ya ragu sosai ba kamar da da yake girma kullum ba. Sai dai bakin da ciwon ya sanya ne yake sake bu'duwa amma shima suna 'ko'karin sanya masa maganin da aka basu a kullum. Ganin kamar an 'dauko hanyar warkewa ne ya sanya Sani fara haramar komawa Bauchi bakin aikin sa, amma sai mahaifiyar sa ta taka masa birki. Domin kuwa shi ka'dai ne 'dansu namiji da Allah ya basu a gidan gaba 'daya, 'yan uwan sa kaf mata ne, kuma duk suna gidan mazajen su, mahaifin nasa kuwa komai sai an taimaka masa kama daga wanka, bawali, alwala sallar ma kanta da sauran su. Abinci ne ka'dai yake iya kaiwa baki da kansa yaci ya sha ruwa baya ga haka kuwa ba iya yin komai. Sani dole ba dan ya soba ya sake wani zaman dan kulawa da mahaifin nasa. ***** 'Bangaren makarantar Jasmine kuwa Noor ce taci gaba da kaita makaranta tana kuma 'dauko ta har sukayi exams suka kar6i hutu, daga nan ne sai take barin ta a gida suna zama da Hauwa ita ta tafi nata makarantar ta dawo, dan su ma 'din jarabawar suke yi a halin yanzun so bata wani jimawa take dawowa gida. Rayuwar su a kullum dai-dai take tafiya musu basu da matsalar komai, sai 'dan abinda ba'a rasa ba saboda halin rayuwa. Lokacin da hutun Jasmine ya 'kare a lokacin kuma Noor ta fara nata hutun dan haka sai taci gaba da kaita makarantar da kanta kamar baya. Bata ta6a gajiya ko 'kosawa da hakan ba, bata san me yasa ba amma haka kawai sai tafi jin da'din hakan, tafi jin natsuwa da kai Jasmine tana kuma 'dauko abinta. Deen ma na 'ko'karin zuwa yana duba su duk bayan 2-3weeks baya ta6a wuce hakan batare da yazo Bauchi ba. Idan yazo yayi weekend 'din sa sai ya koma Abuja. Sha'kuwar sa da 'yar sa kuwa babu abinda ya ragu sai ma gaba domin kuwa koda baya gida ma toh kullum sai sunyi waya dashi kusan sau hu'du ko uku a rana. Zaku yi mamakin irin masifaffen son da yake yiwa Jasmine 'din tamkar wanda akace masa ita ce 'daya k'wal 'kwansa a duniya gaba 'daya, yanzun ko bacci Jas bata yi sai taji muryar Deen, shima d'in da yake yasan abinsa to baya ta6a tsallake lokaci in dai bada wani 'kwa'k'kwaran dalili ba. 8:o clock bata gotawa batare da 'kiran sa ya shigo wayar Noor ba, haka zasu yi ta hira abinsu har sai bacci ya 'dauke ta kafin nan, wani sa'in ma shine yake karanto mata addu'o'in bacci awayar idan ya fa'da itama ta maimaita har su kammala gaba 'daya, a kullum 'karshen maganar sa da Jas shine " I love you Diamond 'din Daddy" Itama sai tace " i love you Daddy". Noor kuwa sai dai ta zama 'yar kallo da sauraren su, sau tari tagumi take yi ta zubawa Jas idanu tana kallon ta idan suna wayar, gani take yi da ace Deen ne yayi jigilar rainon cikin Jasmine tare da haihuwar ta da bata san abinda kuma zai aikata ba a rayuwar Jas tsabar so. Zuwa yanzun baya bata mamaki sai dai kawai tana matu'kar jinjina masa afili da zuciyar ta. A kullum sai bayan ya gama da Jasmine kafin nata turn 'din yake yi, wanda itan ma ba laifi Deen yana matu'kar 'ko'kari wajen ganin ya bata isassan lokacin sa a wayar, sosai yake nuna mata zallan son da yake mata tare da kewar ta a kusa da shi. Haka rayuwar su taci gaba da tafiya da da'di ba da'di har aka kafe result 'din su Noor inda cikin rashin sa'a tafita da carryover har guda uku. Ita da kanta batayi mamaki ba, dan tasan dama da yaya ma take iya karatun, bata kasance cikin 'dalibai masu haza'ka sosai ba.... ba kuma za'a ce da ita doluwa ba, tana nan ne a tsakiya tana lalla6awa and ta 'kara ha'dawa da rashin attending wasu lectures 'din, hatta test tayi missing har guda biyu ta dalilin 'dauko Jasmine daga makaranta, cuz bata tsayawa ta saurari komai matu'kar lokacin tashin Jas yayi to kuwa barin komai take yi tayi tafiyar ta. Hakan bai ta6a damun ta ba, dan kuwa sama taka kawai ta tsinci kanta da son kaiwa da 'dauko y'ar ta ta da kanta batare da tunanin makomar nata karatun ba. Hatta da Carryover 'din ma bai wani 'daga mata hankali sosai ba duk kuwa da cewa tana masifar son karatun amma farin cikin 'yar ta da walwalar ta yafiye mata komai. Deen ne ma ya 'dan yi mamaki da yaji labarin dan kuwa last semester result 'din ta ba haka yake ba, batayi carrying ko wani course ba, tashi 'daya kuma wannan karan sai gata da 'yan rakiya har guda uku...... yaso yaji dalilin hakan amma sai ta nuna masa cewa ita kawai bata gane karatun ne yanzu sosai shiyasa. Da kansa ya zurfafa tunani ya gano inda matsalar take, sai ya bari akan da hutun ta ya 'kare zai nemo wani driver 'din ya fara tafiya da Jas kafin Sani ya dawo, idan kuma ma ya dawo shikenan Alhamdulillah. ***** Wasa-wasa har sai da Sani yayi wata uku cif bai dawo ba, sau 'daya Deen yaje duba mahaifin nasa daganan kuwa bai sake zuwa ba dan garin yayi lungu sosai gashi hanyar ba kyau ba gyara, akwai 'kura sosai hakan ya sanya bai 'kara sha'awar komawa ba. Ya kan yawai ta 'kiran sa a waya su gaisa tare da jin ya jikin mahaifin nasa musamman ma saboda zaman tare, wani sa'in har ku'di yake aika masa tare da 'kara kwantar masa da hankali akan ya nutsu ya kula da mahaifin sa da kyau. Ya kance da shi kar ya damu kansa a duk lokacin da ya samu daman dawowa Bauchi aikin sa na nan yana jiran sa. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 [11/17/2019, 9:35 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *7* Watan Sani uku da 3weeks sannan ya samu daman dawowa Bauchi.. ganin mahaifin sa ya samu sau'ki sosai ya warware. Shi kansa Sani a rame ya dawo duk ya fita hayyacin sa, gashi dama asali ba jikin kirki ne da shi ba, yaro ne matashi 'dan shekara ashirin da uku (23yrs) amma yanda mahaifiyar sa ta sako shi gaba da batun aure ma ka'dai yafi 'daga hankalin sa. Sam baya son maganar aure a yanzu, yanda yake jima in zaiyi auren nema to Hauwa ce yake ganin zai iya aura dan sosai yarinyar tayi masa, itan ma da ace zai samu daman ke6ewa da ita yana jin da shikenan an wuce wurin. Sam bai shiryawa yin aure a yanzun ba, hakan ma da 'kyar ya samu ya lo6a mahaifiyar tasa da sunan zai dawo nan da wata 'daya sai ayi maganar auren, jin hakan da ya fa'da ne yasa ta amincewa har ta barshi ya taho, Sani kuwa har cikin ransa koka'dan baida niyyan komawa Jos a kwana kusa. Ranar da Sani ya dawo Bauchi Deen na gida dan a lokacin shima yazo Bauchi, a yanda Deen ya gansa kuwa sosai ya tausaya wa yanayin sa, dan haka sai ya bashi hutun 1week acewar Deen idan ya huta ya nutsu sai ya fara fita aikin sa. Godiya sosai Sani yayi masa sannan ya koma masau'kin sa dake gidan....yana murmushin jin da'di, cuz shi kansa yana yabawa da karamcin Deen agare shi, bazai ta6a mantawa ba a jinyar mahaifin sa yaci a 'kalla kusan 80 thousand daga Deen 'din da yake aika masa wanda a fa'dar sa wai salary 'din sa ne, sosai yake yaba wa da hakan hatta mahaifiyar sa lokacin da zai taho ta matu'kar jan hankalin sa akan ri'kon gaskiya da amana ta kuma ce ya dinga kula da aikin nasa da kyau saboda ta fahimci ogan nasa na da karamci matu'ka, shi kansa Sani ya san hakan kuma yana yaba masa domin ba kowa keda hali irin nasa ba a wannan zamanin da damuwar junan mu bata dame mu, kowa kansa ya sani, kowa burin sa akansa ne, ka'dan daga cikin mu ne ke damuwa da yanayin halin da wanin sa ke ciki. (Allah kasa mu dace). ***** B'angaren Noor kam zuwan Sani bai wani 'da'data ba balle ya dame ta, dan ko ta kansa ma bata bi ba taci gaba da kai 'yar ta school tana kuma 'dauko ta, har tsawon sati biyu bata bi takan Sani ba, duk kuwa da cewa Deen yayi mata bayanin hutawan da Sani zai yi na sati ne da ya bashi daga a fa'dar sa sai ta bashi key amma Noor tayi banza dashi. A sati na uku ne shi da kansa ya 'kira Deen da batun dan ya lura kallo ma bai ishi Noor ba a gidan, shi kuwa zama wuri 'dayan sai yaji ya ishe shi. Deen bai yi mamaki ba dayake yasan daman ba kowani namiji bane ke juran zama wuri 'daya batare da wani abin yi ba, baya ga haka ma shi Sani yaro ne matashi tashin 'kauye mai ji da 'kuruciyar sa da wuya ya iya juran hakan. Noor ya 'kira yayi mata bayani akan cewa Sani zai cigaba da kai Baby school itama sai ta huta ta maida hankali akan nata karatun. Shiru Noor tayi bata bashi amsar komai ba kasantuwar wani bugu da zuciyar ta tayi da bata san silar faruwar shi ba, sai dai bata raba 'dayan biyu hakan bai rasa nasaba da jin batun sani daga bakin mijinta. Abu 'daya da ta sani a yanzu kawai shine bata 'kaunar Sani har cikin zuciyar ta ba kuma ta 'kaunar kusancin sa da duk wani abinda ya shafe ta. Sai da Deen ya sake magana jin shirun nata yayi yawa ne kafin itama ta bu'di baki tace dashi" wai dan Allah yah Deen sai shine zai na kaita?.......ni fa bance hakan ya takura ni ba Yah Deen please kabashi wani aikin daban ni zan cigaba da kai ta ina 'dauko ta". Da mamaki Deen yace " miye dalilin hakan kenan Nuree?, i thought aikin da ya saba yi kenan a gidan bayan hakan ma kuma wani aikin kike tunanin zan bashi?" Baki ta turo gaba tace dashi " Ni dai ka canza masa please Yah Deen, wallahi sam hankali na bai kwanta da Sanin nan ba....ni zan cigaba da kai yarinya ta ina 'dauko ta, idan babu wani aikin da zaiyi kawai ka bar shi ya huta abin sa in yaso sai kana biyan sa tunda baka son rabuwa dashi". Ran Deen ne ya 'dan fara 6aci saboda jin maganganun nata, a 'dan hargitse shima yace mata" wai me kike nufi ne Nuree?...don't you dare think zaki shiga hakkin naki karatun ne?..... ko angaya miki ban san cewa baki attending 12-1 lectures bane?" Turo baki ta 'karayi daga 'dayan 6angaren tamkar tana gaban shi tace " ai ba kullum ne nake da 12-1 'din ba sau biyu ne kawai a week". " Look Nuree....bansan rashin ji kin sani ko? Na riga na yanke decision and that's final, from now on Sani zai cigaba da fita aikin sa....kin fahimta ko?". Tana shirin sake yin magana ya hana ta da fa'din " shhiiii.... ban son musu please". 'Dan sau'kar da murya yayi yace " ke baki son ki nutsu ne wai". Fizgar maganar tayi dayake da haushin maganganun sa na 'dazun a zuciyar ta sai tace " Wani nutsuwa zanyi Yah Deen...bacin yarinya ta bata da wannan damar". Cike da mamaki Deen yace " kamar yaya kuma....Nuree me kike nufi?" Tambayar da yayi 'din ne ya sanya 'dan sau'ko wa a 'dan nutse tace dashi " Yah Deen kabar Sanin nan.....kwanakin can kafin ya tafi 'din nan ba 'karamin 6ata min rai yakeyi ba Allah". Sai kuma tayi shiru. Deen folding 'dayan hannun sa yayi a 'kirjin sa tare da fa'din" inajin ki miye dalili?" " tsiran tafiya min yawo da Jasmine yayi, idan ya 'dauko ta baya dawo min gida sai kusan 1: o'clock koma fin haka, bacin da ba haka yake yi ba ai da da wuri yake kawo ta, kuma ai har makarantar naje na tambaya aka ce da zarar an tashi basu 'kara 6ata lokaci suke kama hanya amma sai ya zarce wani gurin.......kuma fa da wuri yake tafiya 'dauko ta tun 11:30 yake barin gidan nan 12:20 kuma zaka ga har sun dawo, amma a lokacin gaba 'daya sai ya canza yake zarce hakan batare da wani dalili 'kwa'k'kwara ba, dan ko na tambayi jin dalilin ma banda wasu silly excuse babu komai da zai gaya min, 'karshen ta yace sunyi wa wani lift ne ko kuma wai anyi accident suka 'dan tsaya a wurin ko kuma wani abu daban marar tushe. Bana jin da'din hakan da yake yi sam sannan bamu gama da wannan 6angaren ba ya wani fara bawa Baby ku'di, inda ma Allah ya taimake ni bata iya kashe ku'di ba ai da sabar mata zai yi da hakan batare da na sani ba, ni gaskiya na gaji da halin Sani na tsani abinda yake yi, shi kansa ma na tsane sa dan haka kawai a canza masa wani aikin nafi jin da'din kai ta da kaina Yah Deen". Deen sai yace " amma kin san babu kyau tsanar musulmi haka kawai ko?" Cike da haushi tace " na jima da sanin hakan tun ba yau ba, ban san dai ko kaine ka sani yanzu akan Sani ba". Goshi ya ha'de yace " meaning". Cikin rigima tace da shi" Ni dai ba ruwana, ai tun a lokacin ma naso sanar da kai amma sai na sha'afa na manta da batun gaba 'daya". Idanun ta har ja suka yi da ta ke maganar tsaban yanda abin yaci ranta balle data tuna gaba 'daya sai haushin Sani ya 'kara kamata sosai fiye da na baya ma. Ajiyar zuciya Deen ya sau'ke tare da fa'din" to kiyi ha'kuri zan masa magana kinji, in dai hakane gaskiya baya kyautawa zan mishi magana dole ma ai tunda har yasa ana yimin habaicin abinda ya wuce ta dalilin sa". Ya 'karasa maganar yana murmushi. Kwafa tayi in ka ganta zakayi zaton wuri guda suka da shi tace " wasa ka 'dauki maganar ko Yah Deen ?" Bayyanan niyar murmushi yayi sannan ya 'kara da fa'din" a ah ni dai ba haka nake nufi ba Nureee ai nace zan masa magana, Allah ya huci zuciyar hasken Deen, ashe kin iya masifa har haka?" Azafafe ta kara bu'dan baki tace " Wallahi Yah Deen ni hankali na bai kwanta da shi ba...." Bata gama maganar ba Deen ya tare ta da fa'din "Control your anger madam ai nace zan masa magana ko?". Noor bata sake ce dashi 'kala ba kawai ta yanke 'kiran dan ita ba haka take son ji daga bakin sa ba. Da kallo Deen yabi wayar sai yayi murmushi a fili ya furta " *NOORUL HUDAH* ta kenan sarkin rigima". Batare da wani 6ata lokaci ba yayi dialling numbern Sani. Sani da ke zaune gefen mai gadi yayi saurin ciro wayar sa daga aljihu jin tana rurin neman agaji, sunan _Oga Dini_ da yaga ya bayyana kan fuskar wayar ne ya sashi amsawa cikin hanzari. "Hello ranka ya da'de.....barka da war haka". " Uhum Sani barka dai.....kana jina ko?" Deen ya tambayesa. Da " ehh yalla6ai inaji" Sani ya amsa shi cike da 'kaguwa ga son jin makomar aikin na sa. " Nayi magana da mahaifiyar Jasmine tace min sam bata jin da'din abinda kake yi, ba ka kyautawa Sani.....me yasa baka dawo da Baby gida akan lokaci.....tell me". Sosa kai Sani yayi tare da fa'din " ayi ha'kuri yalla6ai, wallahi akasi ake samu a lokacin amma insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba". " Batun ku'di fa?" Deen ya sake tambayar sa a takaice. Cikin rashin fahimta Sani yace " ku'di kuma wani iri yalla6ai? Inajin wannan ai za6in ka ne sai yadda ka ce". Ya 'karasa maganar da 'yar guntuwar dariya. A tsare Deen ya katse shi da fa'din" ba wannan nake nufi ba Sani, ku'di da kake bawa Jasmine nake magana a kai". Sani sai cewa yayi " ohh yalla6ai insha Allahu shima 'din bazan sake ba". " Ina fatan hakan Sani, dan bama Noor ka'dai ba....ko ni bazan lamunci faruwar hakan a gidana ba, in kuwa ya sake faruwa ina tabbatar maka da kaina zan 'dauki mataki akai". Cikin tabbatar wa Sani ma yace "Ayi ha'kuri yalla6ai duk zan kiyaye". " I hope so". Kalmar Deen kenan ta 'karshe a hankali ya fa'di tare da yanke 'kiran gaba 'daya. Sani dake zaune gefen Mai gadi sai ya juya ya kalle shi fuskar sa ko nuna alamun damuwa be yi ba cuz ya san da wuya ne Deen ya dakatar da shi a aiki batare da 'kwa'k'kwaran dalili ba shiyasa bai wani 'daga hankalin sa ba. Da 'yar dariya yace da maigadi " Ji min matar gidan nan dan Allah, ba'kin ciki take dani shine harda ha'dani da mijin ta". Mai gadin da yake shima ba wani babba bane cuz har yanzu bai cika 30yrs ba yace da Sani " ai naji kana ta neman afuwa...mene ya faru wai? naga ma tun dawowar ka ba fita aiki kake yi ba" " K'yale ni da wannan matar mana ai ba tun na lura da ita ba sam bata 'kaunar kasancewa ta a gidan shiyasa ta lalu6o wani tsohon hujja dan ta 'daure ni dashi, Allah ma yasa mijin nata ba irin ta bane in ba haka ba ai da tuni nayi gaba". Baki mai gadi ya ta6e tare da fa'din " ikon Allah!, to laifin me kayi mata har haka?" Sani zaman sa ya gyara sannan yace " wai fa tun lokacin kafin na tafi jinyar Baba kasan ni ke kai wannan yarinyar makaranta shine wai tace ina 6ata lokaci bana kawo ta gida da wuri......,menene...menene, kasan mata da shegen gulma da munafurci ai" Ta ma fa ta6a yi min magana kuma na daina amma hakan bai ishe ta ba sai da ta ha'da ni da shi dan ya koreni". Kallon sa kawai mai gadi ke yi yanda yake maganar a yatsine, shine ka'dai a gidan yasan cewa fuska biyu ce da Sani, baya ga haka babu kowa da ya sani. Kai ya jijjiga tare da fa'din " kaima ai Sani da laifin ka, me yasa baka kawo musu yarinya gida da wuri tunda kasan ba amincewa zasu yi da wani abu sa6anin hakan ba?". Goshi Sani ya ha'de sannan yace " ai nace zan daina ko?, kuma ma idan ta kwantar da hankalin ta zama na na 'dan lokaci ne yanzu tare da su, ku'din mota kawai nake so in ha'da in ware Lagos". Da zararren ido mai gadi yake kallon sa da mamaki musamman da yaga yanda yake nuna halin ko in kula da maganar. " ka dai bi a hankali Sani". Mai gadi yace masa. Sani kuwa sai cewa yayi " in an'ki fa?" " Ba fa'da bane ai Sani, sai in bika da fatan alkhairi". Cewar mai gadi. Sani ma sai yace " da yafi maka". Mai gadi bai yi mamaki ba koka'dan dan dama sun saba irin hakan da shi, shima sai bai sake magana ba kawai ya kauda kai gefe a fili ya furta " Allah shi kyauta". *Members 'din group 'dina wad'anda da kuka ga ban amsa* *muku comments 'din ku na previous page ba kuyi ha'kuri please........chat* *d'ina ne ya goge gaba d'aya* . Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 [11/19/2019, 12:31 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *8* ***** Ko bayan da akayi maganar ma sai da Noor ta 'kara kusan kwana hu'du a kai batare da ta bawa Sani daman yin aikin sa ba. Idan aka ha'da da shigowar kwanakin weekend kuwa zai bada kusan sati guda da yin maganar. Ranar wata monday ne Sani ya fara fita da Jasmine, cikin sa'a kuwa babu complaint 'din komai da ya biyo baya har suka yi kusan sati uku. Wanda sai a lokacin hankalin Noor ya 'dan fara kwanciya ba laifi, dan ko Hauwa ma da yake matsawa ada duk yanzu baya takura ta. Wani lokaci Deen da kansa yake 'kara bata kyakkyawan tabbaci akan Sani, inda yake cewa ai ko da 'din ma bata fahimce shi bane shiyasa amma yanzu ba gashi komai ya dai-dai ta ba. " Hmm" Kawai take ce dashi batare da wata doguwar amsa ba akan hakan, ita fa kawai ta barshi yaci gaba da aikin sa ne, amma yanda take jin tsanar sa Allah ne ka'dai ya san iyakar hakan cikin zuciyar ta, rashin kyakkyawar hujja da kuma hanin da addini yayi akan tsanar 'dan uwa musulmi ne ya sanyata zuba musu idanu kawai. Itama 'din tana zuwa nata makarantar cikin natsuwa ta dawo, bata da damuwar komai yanzu sai na abinda ke zane cikin ranta wanda ya kasance sirrin ta ne. Haka ma soyayyar su da Deen sai abinda yayi gaba, bata ta6a jin tsanar sa ko wani abu daban ba cikin zuciyar ta illah soyayyar shi duk kuwa abinda zai mata ko kuma ya faru tsakanin su soyayyar su da 'kaunar su sosai tayi 'karfi a zu'katan su gaba 'daya. Wani irin so take yi masa mai zafin gaske da ita kanta bazata iya misalta shi ba balle tasan iyakar sa. Shima 'din ba laifi dan yanzu duk wani abu da yasan zai kawo sa6ani a tsakanin su duk ya kawar dasu, ciki kuwa harda batun Jiddah, tun lokacin da ta ta6a 'kiran Noor take tambayar ta wai akan wani dalili Mu'een zai ce ba zai sake aure ba, wani irin ri'ko tayi masa da har zai ce da ita matar sa ta ishe sa rayuwa har mutuwar sa. Noor sai tace da ita " nima ban sani ba 'yan mata, amma zaki iya tambayar sa tunda naga ai saurayin ki ne shi may be ki samu amsar tambayar ki" Tana gama fa'din hakan ta yanke 'kiran tare da kashe wayar ma gaba daya. Bata ta6a ko gwada sanar da Deen cewa sunyi haka da wata ba balle yasan da faruwar lamarin. Sai kuma shi da kansa yazo mata da batun cikin yanayi na ban ha'kuri tare da sanar da ita cewa shi bai san da faruwar hakan ba, Pics 'din Jasmine ya gani cikin wayar Jiddah sai ya tambayi inda ta samu dan ko shi bai da wancen photon a wayar sa balle yace daga cikin wayar sa ta samu. Koda ya tambayi Jiddah in da samu shine sai tace dashi " a DP 'din matar ka na 'dauka dan Babyn tamin kyau naga tana kama da kai sosai yarinyar". Ha'de rai Deen yayi yace da ita " a ina kika samu digit 'din ta Jiddah... bana son fitina fa". Itan ma 6ata rai tayi tace da shi " ni nace maka fitina ne ya sani na 'dauka ko kuma ita tace maka dana 'kirata na yi mata fitina?" " Yah salam!.... Ya fa'di tare da dafe goshi, cikin 6acin rai yace" haba Jiddah.... kar dai kice min har 'kiran Nuree kinyi?" Cikin nuna halin ko in kula tace " in ma menene dai ni kam na 'kira ta, kuma ai ba fa'da muka yi da ita ba, tambayar ta kawai fa nayi naga ne da ita ka'dai kake da burin 'karashe rayuwar ka shine na 'kira inji dalili daga gare ta". " sai aka gaya miki kuma itace ta tilastani ko?" Cike da haushi ya fa'di hakan. " Ah to ni na sani ne? kasan matan yanzu basa zama sai uban shige-shige dan ganin sun mallake miji su ka'dai, itan ma waya sani ko tana zagawa dan bana tsammanin haka kawai ta bar ka". Kafin ta rufe baki taji sau'kan lafiyayyan mari akan kuncin ta da ya kusan gigitata mata lissafi. Tsaye ta mi'ke dafe da fuskar ta idanun ta har sun tara ruwa cikin muryar kuka tace " akan waccan bushash-shiyar ka mare ni Mu'een?" Wani marin ya kuma sau'ke mata a 'dayan gefen fuskar tata shima 'din tuni jijiyoyin kansa sun mi'ke. Jiddah sai ta kurma ihu tayi zaman dirshan 'kasan tiles tana kuka. Deen kam tuni idanun sa sun riki'da zuwa ja, a masifance ya nuna ta da yatsa tare da furta" how dare u zaki rin'ka furta wannan irin mugun abin kan iyalina?, kin san ta kuwa? kinsan matsayin ta cikin raina?.....Wallahi Jiddah kika kuskura kika sake gigin 'kiran layin ta dan 'daga mata hankali ko fa'dar wani abu makaman cin 6atanci akan ta....ina tabbatar miki da cewa a lokacin zaki gane the other side of me.....idiots kawai.....get out of my house....". Ya 'karashe da tsawa tare da nuna mata hanyar waje. Da gudu Jiddah ta tashi ta fita cuz sosai ya bata tsoro ayau 'din, bata ta6a zaton haka halin sa yake ba, ashe masifaffe ne na gaske. Tun daga ranan bai 'kara sauraren Jiddah ba, ita kuwa haushin abinda yayi mata kan matar sa ya sanya ta takaici sosai, barin ma da taga yanda ya nuna alamun bai ma san da batun 'kiran ba, kenan matar tasa bata sanar da shi ba ne ko me yake nufi?. Ita Jiddah ba haka ta so ba, taso ne a yanda tasan mata da kishin mazajen su to dole idan ta 'kira abin zai dame ta har ma hakan ya sanya matar tasa yi masa bori sai su zama cikin rashin natsuwa kullum wala alla ko ta sanadin hakan ta samu shiga gidan sa, amma sai matar Mu'een ta nuna mata cewar ita bata isa ta shiga tsakanin su ba, sai ta ri'ke maganar ita ka'dai a zuciyar ta. Sam Jiddah ta rasa me hakan ke nufi, tunani ta zurfafa sai ta tsaya akan kawai Mu'een ke haukan son ta, 'kila ita bata son shi shiyasa ma bata kishin sa, dan kuwa da tana kishin sa da bazata yi shiru kan wancan maganar ba. 'Kwafa tayi tana tunani tare da cije bakin ta haushin dukkan su take ji. Murmushi tayi lokacin da wani tunanin yazo ranta, cikin gaggawa ta lalu6o wayar ta tare da shiga gallery, ganin abinda take so 'din na nan ya sanyata har da buga tsallen murna take fara'ar fuskar ta ta dawo. A fili ta furta" yarinya kenan, ai in kinsan wata baki san wata ba, zan gani idan dagaske bakya kishin nasa, sai dai ba yanzu zan yi ba nasan a dai-dai wannan lokacin banda 'ko'karin faranta mata babu abinda zai sa agaba tunda shike son ta kuma yana ganin shi mai laifi ne agareta, dole kusancin su zai 'karu fiye da baya...." "Yes" ta sake fa'di cikin tsananin murna kuma a fili tamkar zautacciya, sai tacigaba da fa'din hakan zanyi nasan a lokacin dole zata ji zafin koma me zan aikata". Wannan dalilin na Jiddah ne ya sanya ta itama ta ja jiki sosai daga gareshi, ta sake bashi daman 'kara kusanci da matar sa sosai, shima 'din bai sake waiwayar inda take ba......... Wannan kenan. ( Toh fa Jiddoriya na shirin yin wani 'kulli fa, Team Jiddah pls a taushi zuciyar ta) Bayan faruwar hakan ne Deen yazo da kansa inda yazo wa Noor da batun, tare da 'ko'kon sa na barar ha'kuri akan 'kiran ta da Jiddah tayi, cuz ya san kallon sa take yi da hakan koda kuwa bata furta ba. Babu bu'katar yi mata 'karyan cewa Jiddah ba budurwar sa bace dan haka shima bai 'dauki wannan layin ba kawai sai yace da ita shi bai san lokacin da har Jiddah ta 'dauki Number a wayar sa ba, tare da 'ko'karin nuna mata cewar ai shi da Jiddan ba wai wata 'ka'k'karfar ala'ka bace tsakanin su... kawai dai ta kan yawai ta zuwa office 'din sa ne, yace ba mamaki a irin hakan ne ta samu daman 'daukan numbern nata....cuz so many times ya kan bar wayoyin sa kan table cikin office idan zashi wani wurin. Noor bata wani damu sosai ba, dan ita kanta tasan dama abu ne mai wahalar gaske ace Deen bai da budurwa a Abuja kamar yanda da yake da wahala ace shine da kansa ya bada numbern ta, ko kuma ace da yardar sa wata ta 'kira layin ta, sai dai in baya cikin hayyacin sa ne, dan haka har zuciyar ta tayi masa uzurin wannan batun. Abu 'daya ne damuwar kuma shima tunda bata da hurumin goge shi dole ta sanya wa ranta ha'kuri akai....wato the fact that Deen yana neman Jiddah. Sosai tayi 'ko'kari wajen nuna masa rashin damuwar ta akan hakan ta kuma 'kara da fa'din kar ya wani damu ita bata sa batun ma aranta ba, ai shi 'din mijin mata hu'du ne, matu'kar zai iya da su sunnah ce babu wanda ya isa ya hana shi......" Abinda yafi tsaya masa arai shine da ta 'karasa maganar da fa'din " ai da wani irin rayuwar ma gara kayi auren yafi mana gaba 'daya". Da kansa yasan magana ta gaya masa inda ta bashi statement 'din a hannun sari, kuma sosai ya sara da ku'din sa, dan kuwa ya fahimce ta, amma bai damu ba tunda itama ta fahimce shi akan batun wayar Jiddah. Wannan ne ka'dai damuwar sa a lokacin dan zai zama ne kamar cin zarafi akayi mata shiyasa ya kwantar da kansa gareta. Itama Noor bata sanyawa ranta komai ba duk ta share su illah sunan Jiddah ka'dai ne da bazata ta6a iya mantawa da shi ba a rayuwar ta, tuni ta sanya ta cikin jerin sunayen dake zane cikin allon zuciyar ta. Duk wannan abin ya faru ne cikin sati biyu kacal bayan ta bawa Sani ragamar kaiwa Jasmine makaranta, duk ta watsar da komai ta zuba a dustbin ta fuskanci rayuwar ta. Domin a fa'dar ta har yaushe zata rayu cikin farin ciki matu'kar tace zata sanya damuwar wasu a kanta, dole ne ta fuskanci nata rayuwar itama ta nutsar da nata rayuwar, addu'ah ce ka'dai bata ta6a gajiya da yin ta kuma tana da ya'kinin Allah zai waiwaye ta komin daren da'dewa, tun yanzu ma tafara ganin sauyi tattare da rayuwar Deen, domin duk wani kulawa da ya dace yanzu yana bata shi ita da 'yar ta, yanzu ko 2weeks baya kaiwa a Abuja yake zuwa weekend, duk sati yana Bauchi. Idan ta dubi rayuwar su farin cikin su da kuma canjin da ta 'dan fuskan ta game da Deen kawai sai dai ta godewa Allah " Alhamdulillah kawai take furtawa, daman tasan addu'ah makami ce ta mai imani, kuma garkuwa ga duk mai yin ta, ta sani dama wataran Allah zai dubi al'amuran ta ya amsa addu'o'in ta. Lectures 'din ta kawai tasa agaba da kuma batun carryover 'din ta, dan so take ta gyara su tun yanzu ba sai tayi gaba ba. ***** *Bayan sati shida* Ya kasance ne ranar Wednesday .....rana na biyu da bazata iya mantawa dasu ba cikin ranakun ba'kin cikin rayuwar ta, bama su da dalilin mantuwa ita a ganin ta muddin rayuwar ta. Ranar tun kafin a 'kira assalatu ta farka daga bacci, bata san dalili ba amma haka kawai taji baccin ta ya yanke, kuma duk da haka bata iya tashi ta ta6uka komai ba tsurawa Jasmine idanu kawai tayi tana kallon ta cikin so da 'kaunar 'yar tata, yanayin baccin ta irin na yara ya 'dan saka Noor murmushi inda ta ha'da bakin ta ta cura shi gaba tana baccin kamar wacce ke fad'a da wani. Tsawon lokaci tana kallon 'yar tata wani farin ciki take ji can 'kasan zuciyar ta data ke kallon Jas 'din, domin kusan itace sanadin farkon samun farin ciki a rayuwar ta iya zaman ta tare da Deen, lokuta da dama ta kan ji da ganin ta ne matsayin sanyin idaniyar ta. Juyi tayi ta komar da kanta 'dayan 6angaren daya ke tana hutun sallah ne so har akayi sallah a masallaci aka idar bata bar kan gadon ba, azkar kawai take ta jerowa cikin ranta. Sai da gari ya 'dan fara haske kafin ta yun'kura ta tashi, bathroom ta wuce ta watso ruwa inda tafito bayan ta kintsa kanta, shirin ta tayi cikin simple doguwar riga na atampa mai kalar sararin samaniya. Jasmine ta tayar itama tayi mata wankan basu fito ba sai da ta sata tayo alwala sannan suka fito daga bayin. Sai da ta goge mata jiki ta shafa mata mai tare da sanya mata pant da wata riga ha'di da hijab 'din ta tace tayi sallahr asuba. Kai Jasmine ta 'dago ta kalle ta tare da fa'din " Mummy yau ma ni ka'dai zanyi sallahn?" " ehh mamana yi abinki kinji, ni 'din tun 'dazu na tashi kina bacci nayi nawa sallahr". " Nima to Mummy ki ringa tashi na muna yi da wurin tare kinji". Sai Noor tace " to naj...amma kiyi na yau 'din karki makara". Ganin Jas ta fara sallah ne yasata barin 'dakin ta nufi kitchen sai data kammala ha'da musu breakfast kafin ta ha'da wa Jasmine na makarantar ta ta shirya komai, kintsa ko'ina tayi a kitchen 'din sannan ta fito. Koda ta dawo 'dakin ma sai ta tarar da Jasmine har ta gama saka uniform 'din ta, dayake Jasmine akwai wayo sau da dama bata jira wai sai an sanya mata, sucks ne dai bata iya sanya shi a dai-dai sai Noor ta gyara mata tare da yaba wa 'ko'karin ta. Parlour suka koma ta bata break 'din ta wanda basu jima da zuwa parlourn ba wayar Noor ta fara ruri, dayake tasan wannan 'kiran sassafen na Jasmine ne sai ta 'dauka tare da ha'da shi da kunnan ta. "Hello Daddy! Cewar Jasmine da ke 'ko'karin kaiwan 'dan gutsuren soyayyan 'kwan da ta gutsura yake hannun ta. Noor tace "haba Jas bar abincin mana kuma sai kin gama wayar ko?. Mayar wa Jas tayi ta ajiye tare da maida hankalin ta hankalin ta gaba daya kan wayar. " Baby ya kike?" yace daga 'dayan 6angaren. Sai tace " lafiya... Daddy good morning". Murmushi Noor tayi da jin salon Jas 'din da ta riga ta saba dashi a yanzu. Kamar yanda suka saba kullum yau ma 'din hakan ne yakan 'kira yaji muryar tane kawai kafin ta tafi makaranta inda daga k'arshe kullum ya kance "Allah ya bada sa'a ya albarkaci karatun Baby" . Watarana shiru take yi masa koda yayi addu'ar amma mafi yawan lokuta ta kance da shi " Amin" Sa6anin yayu da Jasmine cikin farin ciki ta amsa addu'ar tashi da fa'din "Amin Daddy...Allah ya kawo ku'di ka kaimu makkah da Madina da ni da kai da Mummy". Deen ma da fara'a ya amsa ta da fa'din" Ameen ya rabbi mama na, Allah yayi miki albarka" Noor dake jin su ne tayi saurin amsawa da "Ameeen-Ameeen". 7:00am suka fito daga parlourn suka nufi wurin motar da ake kai Jasmine makaranta, kamar yanda kullum Noor ke rakota yau ma d'in hakan tayi, wanda kullun sai taga bayan motar kafin take komawa ciki ta fara nata shirin tafiyar. Yau 'din kuwa sai akayi rashin sa'a domin motar da Sani ke kai Jasmine makaranta sam ta'ki tashi. Sani yayi-yayi amma duk 'ko'karin sa a banza. Ganin kamar lokaci zai tafi ne ya sanya Noor komawa ta 'dauko key 'din motar da take tafiya dashi Benz ce mai tinted glass ta bawa Sani, ta kuma ce dashi ya kai Jasmine 'din dan ita sai 10:00 take da lecture yau, in yaso idan ya dawo sai itama ya kaita ya dawo gida da motar in lokaci yayi sai ya wuce ya 'dauko Jasmine 'din kafin a duba 'dayan motar. Sani kar6an key 'din yayi suka shiga Jas nayi wa Noor bye-bye har suka bar gidan sannan ta koma ciki. Da yake bada wuri zata shiga school ba yau 'din shiyasa koda ta shiga ciki sai tayi zaman ta a parlour tare da bu'de data 'din wayar ta. Sa'kwanni ka'dan ne suka shigo wayar cuz ba da mutane da yawa take chat ba ita contacts'din ta 'yan 'kalilan ne. A hankali tabi ta dudduba chat 'din har da na group 'din da take dashi na class mates 'din ta na makarantar da ta kammala secondary school 'din ta. Sai wasu friends 'din ta na yanzu da ta yi a school. Wata new number data gani ne 'karshen bu'dewa ganin messages har hu'du aka turo akai wanda tana bu'dewa sai taga ashe uku daga ciki duk pictures ne yayin da 'dayan ya kasance video ne na 49seconds aka turo kuma duk sun bu'du inda suka samu kyakykyawan mazauni cikin ma'danar pictures dake cikin wayar tata. Arba da idanun ta suka yi da wanda ke kan pics 'din ya sanya ta bugun zuciya mai tsananin gaske, amma haka ta daure ranta dan wannan ba ba'kon lamari bane agare ta, daurewa tayi ta bu'de Video 'din duk da kuwa tana jin idanun ta sun k'an'kance suna barazanar daina gane mata komai. 20 seconds bata iya kaiwa tana kallon Videon ba ta ji komai nata ya tsaya cak har yana 'ko'karin tsayar mata da numfashi......bugun zuciya, tashin hankali duk suka ziyarce ta a lokaci guda, hatta yawun bakin ta sai da ya kafe kaf. Rintse disassun idanun tayi ta kuma bu'de wa akan fuskar wayar still babu abinda ya canja, abinda take gani 'din gaskiya ne ba 'karya ba. Jifa tayi da wayar da k'arfin gaske wanda da ace ha'duwa wayar tayi da tiles ko kuma bango da labarin wayar tuni ya shu'de, amma sai a kayi sa'a ta sau'ka akan kujeran dake fuskantar ta a parlourn. Bata kuma bi ta kan wayar ba ta dafe kanta da dukkan hannayen ta biyu, _innalillahi wa innah ilaihi raji'un_ take son fa'di amma sai ta kasa bakin ta sosai yayi mata nauyi.....sunan sane kawai ya iya zuwa bakin ta a wannan lokacin, inda da 'karfin gaske ta furta " Yah Deeen!" Da ce kusa suna da neighbour na kusa da babu abinda zai hana aji amon muryar ta. Daga nan kuwa sai hawaye zir ya sauko mata kamar sau'kan fitsarin da ba'a shirya masa ba. Fitan hawayen ne ya bata damar iya jero salati cikin kuka ta zube da6as k'asan tiles 'din dake parlourn tana kuka tana furta _innalillahi wa inna ilaihi raji'un............._ Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 [11/20/2019, 5:00 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Wannan shafin naku ne Team NOORUL na baku kyauta musamman saboda tsananin 'kaunar ku ga NOORUL......._ _ina son ku sosai_ 😍 *_Fatan alkhairi masoyana Allahu ya bar 'kauna_ 🤝* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *9* Husnah kawai take hangowa a idanun ta lokacin da take faman kukan. Wancan rayuwar, wancan lokacin, ashe ba'kin cikin ta bai 'kare ba har yanzun, ashe zata sake ganin wannan mummunan abin da idanun ta. Ta kai 20mins tana zaune a a gurin, wanda tuni kukan nata ya riki'da ya koma na zuci, ga 'karan wayar ta tana ji yana ringing amma sam ta 'ki ko da kallon inda wayar take ma balle har taje dubawa, ganin kamar 'karan wayar na gauraya da damuwar ta yana sake 'daga mata hankali ne ya sanya ta barin parlourn ta koma cikin bedroom 'din ta. Zuwa yanzun kam kukan ya tsaya mata sai dai na zuci, shiru ta zauna tana tunani kanta tallafe cikin tafukan hannayen ta, wai da gaske Yah Deen ne ta gani ko wani daban? Tambayar da kenan take yiwa kanta take kuma son warware ta, sai dai bata jin zata sake iya kallon wayar tata ma ballantana har ta bin ciki abinda ke ciki. 'Karfin halin tashi tayi kamar an tsikare ta inda ta nufi closet 'dinta ta fara ha'da kaya nata da na Jasmine cikin akwati guda domin bata jin zata iya sake zama a 'kar'kashin Deen matsayin matar sa ta aure, ji tayi gaba 'daya ya fita aranta gaba 'daya. ***** B'angaren Sani kuwa koda ya sau'ke Jasmine a makaranta niyyar sa ya dawo gida da motar amma sai yayi wani tunani. Agogo ya duba sai yaga ai da sauran lokaci kafin tafiyar Madam nata makarantar dan haka sai ya zarce inda ake saida wayoyi, dama tun jiya yayi shawaran canza waya, yana da 'yan canjin sa naira dubu biyu shine yake tunanin idan ya ha'da da tasa wayar da kuma ku'din zai iya samun wata daban cuz tashi wayar na 'dan cijewa sosai take bashi haushi wani lokacin. Koda yaje wurin saida wayoyin kuwa sai bai yi sa'an samu da wuri ba, inda ya 6ata kusan 2hrs 30minute yana ta faman dubawa da k'yar kafin ya samu wayar da tayi masa. Ganin lokaci ya ja sosai ne ya sanya shi kar6a a gaggauce, speaker, mouthpiece da gurbin saka caji kawai aka gwada masa ganin komai normal ya sanya shi jefa wayar cikin aljihu kawai daga nan ya kamo hanyar gida batare da ya sake 6ata lokacin komai ba. Da 'dan hanzari ya shigo gidan yana yin parking kuwa ya nufo mai gadi yana tambayar " matar nan ta fito bana nan ko Bala?" " Wace mata kenan?" Mai gadi ya jefa masa tambaya shima as if bai gane wacce Sani yake nufi ba. Sani sai ya 'dan juya kai ka'dan tare da fa'din "Kai da Allah ni ka fiya shirme wallahi kai, matar gidan nan nake nufi mana". " ohh Hajiya wai?" Mai gadi ya sake tambaya yana kallon sa. Sani ma sai yace "Koma wacece ni, tambaya nayi kawai ta fito ne?" "Ah ah bata fito ba tukunna". Cewar Bala maigadi tare da kawar da kansa . Ajiyan zuciya Sani ya sau'ke tare da fa'din " yauwa barka". Sannan ya zauna. Sai kuma yaci gaba da fa'din " kasan ta da jaraba, yanzu sai ace nayi laifi bandawo da wuri ba, nima 'din wallahi ina ta sauri in ga nadawo da yake tun kafin na fita ta sanar dani 'karfe goma zata fita makaranta, to kuma sai na 'dan samu matsala kasan abinka da jama'ah sai a hankali....." Hannu ya kai cikin aljihun sa domin ciro wayar tasa yayin da mai gadi ke binsa kawai da idanu. Sani cigaba yayi da fa'din " waya na je na sauya amma nake gaya ma da 'kyar na dace da wannan, akwai dayawa amma basuyi min ba". Maigadi bai kar6i wayar a hannun sa ba cewa kawai yayi" ba laifi ai dan gata bata wani sha jiki ba kuwa...Allah ya sanya alkhairi". Da " Ameen" Sani ya amsa tare da maida wayar cikin aljihun sa sannan ya mi'ke tsaye, ha'di da fa'din " bari in kama ruwa ina zuwa, idan ta fito da Allah kayi min magana, in kuma bata fito ba to zan 'dan tsaya watsa ruwa ". " Sai ka fito to". Cewar mai gadi tare da komawa ya kishingi'da kamar yadda yake tun farko. Shiru-shiru har sha 'daya Sani bai ga Noor ta fito ba, har yayi wankan ya fito ya sake zama da maigadi amma shiru. 'Dan 'karamin tsaki yaja tare da mi'kewa tsaye yace " bari kaga in yiwa matar nan magana tun 'dazu naga shiru, kaga in bazata ba nima in hutawa raina". Yayi maganar yana me cigaba da tafiya ya tunkari cikin gidan. Sallama yayi daga bakin 'kofar parlourn tare da turawa ya shiga, sai yaga babu kowa, sallama ya dinga dokawa kusan sau hu'du amma shiru. Noor na daga ciki duk ta gama hautsina ko'ina garin shirye-shiryen kayan su ita da Jas, tana jiyo sallamar Sani amma bata jin zata iya amsawa sai ma wani 'karin takaicin da taji ya sake kama ta musamman data ji sallamar tasa ta'ki 'karewa. A 'dan zuciye ta ture takardun dake gaban ta ta taso ta nufo parlourn kamar wata jaruma, tana isowa parlourn sai taga Sanin ya juya yana 'ko'karin fita ga dukkan alamu gajiya yayi da jero sallamar ne. A dake tace " Sani!. Ciki-ciki tayi maganar amma hakan bai hana Sani jin muryar ta ba. Sai ya juyo kafin yayi magana sai ta riga shi da fa'din" ya akayi?" Ta sake tambayar sa fuskar ta ko alamun fara'a babu, daman ma yaya asali ba fara'a take yiwa Sani ba ballantana yanzu da take jin ranta yake 'kololuwar bace. Shi kansa Sani da yaga yanayin fuskar ta sai da yagane cewa ba a dai-dai take ba. Bu'dan baki yayi yayi yace.... " Hajiya naga baki fito bane har yanzu, kuma naji 'dazu kince 'karfe goma zaki shiga makaranta shiyasa nazo in tuna miki". "Karfe nawa yanzun?" itama ta sake tambayar shi. Sai yace " Sha 'daya fa har ta gota Hajiya". Kauda kai tayi gefe tare da fa'din " Ni 'din bazani ba, amma please ka hanzar ta zuwa 'dauko min 'yata zamuyi tafiya ne". Tayi maganar cikin 'karfin hali sosai wai dan kar ya fahimci halin da take ciki. Da " to" kawai Sani ya amsata tare da juyawa ya nufi hanyar fita. " Ka hanzar ta dan Allah". Ta 'kara fa'di tare da juyawa ta koma ciki. Kamar yanda ta fa'da 'din batare da wani 6ata lokaci ba Sani ya shiga mota kai tsaye ya nufi makarantar su Jasmine da tunanin 'kila ko mutuwa akayi musu shiyasa dan yaga idanun ta sunyi ja alamar tasha kuka, kuma ma in ba haka ba bai ta6a ji ko ganin sunyi irin wannan tafiyar ba. 11:25am ya isa makarantar su Jasmine, shi kansa yaje ne a lokacin dan cika umarnin ta amma bawai dan cewa yaran sun tashi ba. 'Karamin tsaki ya saki a fili daya tuna cewa zai yi zaman jiran su a 'kalla na kusan mintina 30. Jikin kujera ya kwantar da jikin sa tare da 'dago 'kafafun sa ya 'dora a gefen stairy, wa'kar 'yar budurwa nasu M.Shareef ya kunna ha'di da kunna A.C ya wani lumshe idanu yana saurare tare da bin bakin wa'kar a fili tsawon mintina uku. 'Karan shigowan sa'ko dayaji cikin wayar sane ya katse shi a hankali ya lalu6o wayar ya duba sai yaga ma ashe sa'kon MTN ne. Koda ya ga sa'kon sai kuma bai maida wayar tasa cikin aljihun ba ya cigaba da duba ciki dan tunda ya siya bai ga komai a wayar ba, Sim 'din sa ka'dai ya sanya ciki. Sa'konnin dake inbox 'dinsa mara sa anfani kaf yabi yabi ya goge su sannan ya koma cikin file manager 'din wayar. Gani yayi kan wayar da akwai abubuwa da 'dan dama da ba'ayi clearing ba kafin a siyar da wayar, kama daga kan videos har photuna da kuma wa'ko'kin audios ka'dan. A fili ya furta " sai kace ba a shirya saida wayar ba.....mthew" ya 'karashe da jan tsaki. Duba wa ya rin'ka yi yana goge abubuwan da basuyi masa ba yana kuma barin na bari. Cikin haka har ya iso wani folder dake 'dauke da videos guda uku, bai yi wata-wata ba kawai ya shiga ya bu'de, ai sai yaga ashe porn videos ne duka ukun a jere. Batare da wani tunani ba ya dinga bi yana kallon su 'daya bayan 'daya, in ya gama sai ya sake maimaitawa, abin babu kyan gani amma Sani kam sosai suka 'dauki hankalin sa harma bai san cewa lokaci yaja sosai ba domin ba k'aramin shagala yayi da kallon ba. Jasmine kuwa ana tashin su ta nufo inda tasan Sani yake parking ya jira ta sai kuma ta ga motar da Mummyn ta ke hawa ne tsaye a gurin, abinka da yarinta har ma ta manta cewar da motar aka kawo ta da safe kuma Sani ne ya kawo ta. 'Dan dariya tayi " a fili ta furta " mummy!" Sai ta taho da gudun ta zuwa wajen motar. Ji kawai Sani yayi an bu'de 'kofan motar ta gaba gefen inda yake kishingid'e. Kafin ya ankara sa jin sau'kan muryar Jasmine yayi a tsakar kansa tana fa'din " Mummy yau nayi karatu har Uncle ya bani kyautan exercise book". Bu'de motan ha'di da maganar tata ne ya sanya shi saurin dawowa hayyacin sa ya kauda ido daga kallon wayar ya mayar kan Jasmine dake ta faman kokuwa da marfin mota. Da taga bazata iya bane shiyasa ta kawai ta barshi wanda sai a lokacin kuma ta ga ashe ba maman nata bace Sani ne yazo. Duk da haka sai bata fasa maganar ba ta 'dago takardar ta nuna masa, ha'koran ta washe tace " kaga takaddan da Uncle 'din mu ya bani...yace min nayi 'ko'kari sosai". Tana yi tana juya kai cikin tsananin murna da farin ciki. Sani bai yi magana ba kawai sai ya lumshe idanu tare da saka wayar tasa cikin aljihu sannan ya bu'de idanun nasa ya sau'ke su kan fuskar Jasmine da har yanzu take kallon sa itama da sauraran abinda zaice da ita, Sani tsura mata idanu yana kallon ta ba tare da ya furta komai ba. Gaba 'daya sai ta juye masa ta dawo babba a idanun sa a yanayin da yake kallon tan. Irin yanda yake kallon ta da kuma yanda taga idanun san sunyi wani iri harma da rashin maganar da be yin ba ya sanya Jasmine fa'din " baka da lafiya ne?" Kai Sani ya 'daga mata sama alamar " ehh". Jasmine sai tace da shi" sorry....kar kayi kuka kaji idan Daddy na yazo zai baka magani, amma kace kar yayi maka allura akwai zafi". Shiru kawai Sani yayi ya kai hannu ya rufo 'kofar da kyau tare da 'ko'karin tada motar. Itama Jasmine sai tayi shiru taci gaba da binsa da idanu har suka fara tafiya sannan ta koma tana bin hanya da idanu da sauran 'yan makarantar tasu. A hankali Sani yake jan motar har suka hau titi, ji yake yi kamar bazai iya juran irin 'ka'k'karfan feelings 'din da yake ji ba a lokacin, duk wasu 'kananun iskancin sa yau 'din sai yaji sun motsa masa gaba 'daya har suna 'ko'karin zarce tunanin sa. Gangarawa yayi ya koma bye-pass 'din da zai sada su da hanyar gida, dama tana nan yake bi kullum shiyasa baya wani 6ata lokaci yake isa gida da wuri koda wani lokaci, bayan zai kaita da kuma 'dauko ta by- pass 'din ne sau'k'a'k'ken hanya mafi kusa. Sani bai sake ko kallon inda Jas take ba duk kuwa da tana zaune gefen sa. Damuwar sa ne kawai ta dame shi a lokacin jijiya da 'kwa'kwalwa gaba 'daya yake jin sa cikin wani yanayi na daban, still kuma a hankali yake jan motar tamkar ba a son ransa yake tu'kin ba, kuma bashi da niyyan 'kara speed har cikin ransa shi. Jasmine kam sanyi sosai ne ya dame ta cikin motar da yake ya 'kure 'karfin A.C, da farko ta 'dan jure amma daga baya sai taga bazata iya ba, dan haka cikin irin shagwa6ar ta da ta saba yiwa iyayen ta tace dashi " Sani ka kashe A.C.....nifa sanyi nake ji". Ta 'karashe maganar da turo baki. Tun lokacin da tayi maganar sai hankalin Sani ya dawo kanta tsura mata idanu yayi yana kallon fuskar ta zuwa bakin ta, lokaci-lokaci ne ya kan 'dan 'daga kai ya dubi hanya, bai ma damu ba saboda ba wani sosai ake bin hanyar ba. A haukar sa da kuma hu'duban shai'dan da yake yi masa sai yake ganin ta tamkar wata 'yar 18yrs ce a gaban sa. Bai iya yaci gaba da tu'kin ba sai yaja birki inda ya parker motar a gefen hanya daga 6angaren hagu. Juyawa ya sake yi ya kalle ta da kyau sai yaga tana 'dan kame jikin ta alamar dagaske sanyin takeji. Hannu yakai yayi 'kasa da 'karfin A.C sannan ya sake kallon ta sai yace " wai sanyin sosai kike ji ne haka?" Kai Jas ta 'dage masa tana kallon cikin idanun sa ba tare da tayi magana ba. Sai ya sake fa'din " ko de zazzabi ne ke damun ki kema irin nawa......." bai jira yaji amsar da zata bashi ba ya cigaba da fa'din" zo nan inji ko jikin na ki da zafi". Yayi maganar tare da 'dago ta cak daga wurin zamanta yayi mata masau'ki a kan cinyar sa. Jasmine kam kallon shi kawai take yi domin bata san manufar sa ba, sai dai 'dora ta da yayi kan cinyar tasa da yayi a yanzun sai yasa ta tuno da abinda yake yi mata tun watanni 'kalilan da suka shu'de. Ha'de rai tayi nan take ta kalle shi, shima 'din ita yake yake kallo. Hannun ta ta 'dago ta rufe bakin ta dashi sannan cikin yarintar maganar ta tace dashi " Ni bana son ka cinye min bakina irin na rannan, in ka cinye min bakina sai na gaya ka da Daddy......". 'Dan ha'de rai Sani yayi yace " ke da Allah can, waye yace miki bakin ki zan cinye miki? Bake kika ce kina jin sanyi ba? Shine fa zan cire miki yau 'din a bakin naki ba irin wancan ba". Sai tace dashi " ai na daina jin shanyin". " k'arya ne akwai ka'dan...in kuma ba haka ba cire hannun naki mugani". Ya fa'di tare da kaiwa nasa hannun saman nata. Jasmine sai ta cire hannun tana kallon shi domin ita zaton ta gaskiya yake fa'da. Rashin tsoron Allah, biyewa zuciya, 'karamin tunani da kuma sharrin shai'dan ya sanya Sani ko kunya bai ji ba ya kama bakin 'yar yarinya Jasmine ya ha'da da nashi. Kafin ya sake mata bakin kuwa har ta fara kuka cuz dama ita koda da yake yi mata ma ba so take yi ba sai dai yanda yayi mata yau 'din daban dana kullum sosai taji zafi shiyasa ma har tayi kuka. Yana sake mata bakin kuwa ta kai hannu kan bakin da hawayen ta a fuska take fa'din " sai na gaya ka Daddy na". Sani ko kulawa da maganar da take yi ma baiyi ba kawai ya kai hannu cikin wandon makarantar dake jikin ta. Kuka take yi tana ture hannun shi tare da fa'din " ni bana so zan gaya ka da daddy na". 'Ko'karin cizon shi tafara sai ya yayi saurin yin baya da ita ya danne mata bakin ta da hannun sa. ( ayimin afuwa pls labarin ne yazo da haka) Yatsa Sani ya tura mata a gaban ta ba tare da yayi tunanin komai ba, wanda hakan ya sanya ta tsala ihun kuka, ko tausayin ta Sani baiji ba balantana ya tuna cewar yarinya ce 'karama sa'ar abinda zai haifa sai ya sake danne bakin nata da 'karfin gaske jin amon ihun nata ya fito fili inda ya ha'da har da hancin ta ya rufe gam. Jasmine kam nan take numfashin ta ya tsaya cak a wurin, duk da haka Sani bai fasa abinda yake yi ba, bai ma san da faruwar hakan ba sam. Sani ya fahimci bata numfashi ne lokacin da ya ga alamar bata motsi, wanda hakan ne ya sanya shi 'daga hannun sa saman bakin ta. Ko 'dar baiji ba balle yaga rashin dacewar abinda ya aikata, hannun sa dake jikin ta ya cire duk jini ya bata hannun, amm bai damu ba sai yayi saurin gogewa a jikin sa ya fara 'ko'karin cire belt 'din sa 'kato dashi ko kunya baya ji balle tsoron Allah, bansani ba ko ya manta cewar Baby Jas ne ba wata daban ba. Duk kuwa abinda ke faruwa babu wanda ya lura da shi, domin hanyar ba wani cika binta akayi ba, by-pass ne da 'dai-'dai kun motoci ne ke bin ta, kuma ma yaushe kai da ke da naka uzurin yaushe zaka tsaya karantar faruwar wani abin da bai shafeka ba, abin ma cikin mota. Shiyasa ko motocin dake wulgawan ma da gudunsu suke zuwa su wuce kamar yanda suka taho, gashi ha'di da ba'kin glashin da motar ke da shi wanda ya 'kara bada babbar gudummawa wajen rashin ganin haukar da sani ke aikatawa cikin motar. Yana 'ko'karin 6alle belt 'din nasa ne sai yaji 'kara daga bayan sa, sai hakan ya matu'kar gigita shi sosai abinku da marar gaskiya. A tsorace ya sa hannu kan key 'din motar ya tada da niyyan barin wurin duk da bai fahimci takamamman abinda ke faruwa ba, amma hakan bai hana shi zaburar da motar cikin gaggawa ba. Wata mota dake 'ko'karin tsaya wa daga gaban sa ganin abinda ya farun shi kuma Sani a gigice ya tafi da 'karfi sai suka gwabza uban karo mai firgitarwa. Take motar Sani ta gangara gefen hanya gaba 'daya sai ya kasa controlling 'din ta, kafin ma ya nutsu ya dakatar da motar har ta isa ta bugi wani bangon sabon ginin manyan shaguna da a keyi ya rubzo kan motar......nan take labari yasha bam-bam. Domin kuwa tun daga lokacin Sani bai 'kara sanin abinda ke faruwa dashi ba. Salati kawai tsirarun jama'ar dake wurin ke yi, yayin da wasu harda 'dora hannu sukayi aka, domin abin babu kyan gani. Motar da su Sani ke ciki bazaka ta6a tunanin za'a rayu a cikin ta ba tsabar yanda yayi. Take an gwabza accident har kala biyu wanda na farko an yishi ne sanadin mai tura baro mota ta ka'de shi, shi kam ma nan take bai ko shura ba ya amsa 'kiran Allah, dan kuwa duk yawancin masu bin by-pass 'din basa shigan ta a hankali, da gudun su suke tafiya saboda samun sarari yayin da wasu daga cikin su uzururruka ke sasu yin gudun. Hatsari na biyun shine ya faru ta sanadin rikicewar Sani sakamakon rashin gaskiya da kuma jin 'karar hatsari na farkon sai gashi mota tayi kaca-kaca 'kar'kashin gini bazaka ta6a zaton an rayu cikin motar ba, shi kansa mai ginin ba 'karamin tafka asara yayi ba. Wanda suka gwabza da Sani ne ka'dai nashi da 'dan sau'ki domin kuwa gaban motar ne ka'dai ya lalace da yake shi cikin hayyacin sa yake so sai yayi saurin yin baya lokacin da suka yi karon, shi kuma Sani garin kaucewa ne ya karkace yayi gefen hanya, wancan bawan Allah kuwa da ya ka'de mai baro motar sa bata samu ko 'kwarzane ba amma azumi sittin da ya hau kansa matsayin sa na musulmi ma ka'dai ya ishe shi fargaba. Dr. Safwan abokin Deen ne ke wucewa shima da shirin sa na zuwa aiki cuz aikin rana yake yi a lokacin, sai shima yaja ya tsaya ganin faruwar lamarin, wanda ganin mutane an taru da 'dan yawane ya sashi shima yayi parking domin ganewa idanun sa. Har ya iso 'din kuwa babu wanda ya kai ko da farcen sa kan wanda aka ka'de 'din, tsayawa sukayi suna kallon yanda jinin sa ke malala a 'kasa kamar ba mutun ba. Dr. Safwan na isowa ya kutsa tsakankanin mutanen wanda shine ya duba wanda aka ka'de 'din yaga tuni rai yayi halin sa sai ya jijjiga kansa tare da fa'di wa wa'danda suke wurin. Kafin wasu 'yan mintina guri ya sake cika ma'kil da jama'ah na ban mamaki, inda wasu suka maida hankali kan motar da gini ya zubzowa. Dr. Safwan kam shirin komawa mota yake yi cuz bai lura da 'dayan motar ba, jin hayaniyar mutane agurin ne ya sashi waigowa yaga mai suke wa hayaniyar. Caraf sai idanun sa suka yi arba da motar Deen abokin sa wanda matu'kar yana gari to da ita yake zuwa ko'ina idan zashi. Tsinkewa zuciyar Dr.Safwan tayi sai yayi hanzarin tafiya da gudu izuwa wurin motar ya tarar da mutanen dake wurin suna hayaniyar ta inda zasu fara taimakon mai motar. Sanin da Dr. Safwan yayi cewa Deen baya gari ne ya sanya shi tunanin cewa Noor ce cikin motar sai da ya isa daf kafin ya ganewa idanun sa kasancewar tuni glashin ya tarwatse. " Innalillahi Jasmine". ya furta a fili tare da 'ko'karin taimaka musu. Da taimakon Dr. Safwan aka fitar da su duk daga cikin motar inda ya sanar da jama'ar gurin cewa 'yar sa ce tare da nuna musu I.D card 'din sa na aiki da addreshin asbitin da yake aikin saboda kada su zarge shi. Cikin motar sa aka sanya Sani, yayin da shi da kansa ya rungumo Jasmine ya isa motar da ita, wani dake gurin ya ro'ka akan ya taimake ya ja su zuwa asbiti sai yace bai iya mota ba. Wani aka nemo ya jasu zuwa asbitin cuz Dr. Safwan baya jin zai iya tu'ki a dai-dai wannan lokacin. Dukkan su Emergency ward akayi da su inda aka rufu akansu ana basu taimakon gaggawa. Har alokacin kuwa cikin su babu wanda ya farfa'do balle su san halin da ake ciki. Dr. Safwan da kansa ya duba Jas yayin da wani likitan ya duba Sani. Sosai suka yi 'ko'kari wajen ganin sun shawo kan lamarin, cikin sa'a kuwa komai ya dai-dai ta wanda sai a lokacin hankalin Dr. Safwan ya kwanta ganin cewa dukkan su suna da sauran numfashi. Sani ne dai sai aka sanya masa oxygen, ga kuma mummunan raunin da hannun sa yayi harma suna tunanin sai an yanke hannun gaba 'daya. Ajiyan zuciya Dr.Safwan yayi jin abinda ya faru da Sani sai yace " Allah ya bashi lafiya" Nan yayi musu bayanin cewa ai 'yar Dr Mu'een ne da drivern gidan sa, yace ga dukkan alamu daga makaranta ya 'dakko ta sai hakan ya faru" Likitoci uku dake tare da shi 'din sosai suka tausaya tare da 'kara bada himma sosai wajen kula da su. ***** Noor dake can gida kuwa zuwa yanzun har ta fara gajiya da duba agogo, har ta gama shirin ta tayi sallah amma har yanzu shiru, lokacin da ta 'daya ta gota har da rabi ne sai ta ji wani tu'ku'kin ba'kin ciki ya 'karu mata akan na baya. Yanzun kam tana ganin cewa rainin hankalin Sanin da gangan ya keyi, in ba haka me ya tsaida su har wannan lokacin basu dawo ba. Tayi tunanin 'kiran sa amma kuma bata 'kaunar sake ganin wayar tama a idanun ta, tsakin da ta ringa ja yafi cikin container daga 'karshe sai ta fito parlour, amma instead ta 'dauki wayar tata ta 'kirashi " ah ah.....sai ta kauda kai daga kallon wayar ma gaba 'daya ta zarce waje. Wurin Mai gadi ta nufa tace da shi " har yanzu Sani basu dawo bane wai?" "Ehh Hajiya, gaskiya basu dawo ba nima ina mamaki yau 'din" Yayi maganar cikin bata girma matsayin ta na matar ubangidan sa. " k'ira min shi mana please Bala kaji ina suka tsaya" Tace dashi cikin dakewa tare da 6oye damuwar ta. Batare da 6ata lokaci ba mai gadi ya 'kira layin Sani amma switch off aka ce dashi " Hajiya wayar a kashe". Ya fa'da tare da raba wayar da kunnan sa. Noor sai tace " Sake gwadawa mana dan Allah ba mamaki matsalar network ne" Koda ya gwada 'din kuwa still baya tafiya wanda wannan karon kam ba sai ya bu'di baki yayi mata 'karin bayani ba, kasancewar a speaker ya sa wayar. 'Dan 'karamin tsaki Noor ta ja tare da yarfe hannu sannan ta juya ta koma ciki tana mita cikin ranta. Tana shigan ta sake jiyo rurin wayar ta karo na abinda bazata iya tunawa ba. Zaton ta ko Sani ne ya 'kira dan haka sai taje inda take jiyo rurin wayar ta kalla, ganin sunan wanda ke 'kira ne ya sanya ta ta6e baki tare da wucewa abinta ciki. Deen kam tun safiyar yau daya gaisa da Jas bai sake jin natsuwa ba wanda hakan ya sanya shi yake zaune a office ko mutun 'daya bai iya ya duba ba. Bai san dalilin da ya sanya ta 'kin 'daga wayar sa ba wanda da farko ya zaci ko bata kusa ne, amma daga baya da ya 'kara 'kira bayan kusan hour guda still yaga batayi picking ba, daga nan ne ya fahimci cewa da gangan ta'ki 'dagawa. Dan haka sai ya cigaba da 'kira tare da tura mata text har guda uku amma shiru ba replay sannan 'kiran sa har alokacin bai samu response ba. Ganin haka ne yayi tunanin ko de ba lafiya ba, dan haka sai ya 'kira mai gadi ya tambaye shi matar sa tatafi makaranta ne sai maigadi yace "a ah tana ciki" Ro'kon sa yayi akan ya duba masa ko ba lafiya ba dan yata 'kiran layin ta amma ba'a 'dagawa. Wannan abin ya faru ne bayan fitar Sani izuwa 'dauko Jasmine daga makaranta.......koda mai gadi yaje mata da batun ma 'kin amsan wayar tayi tace dashi ita lafiyar ta 'kalau wayar tata ce bata san inda ta jefa ba. Mai gadi na 'ko'karin juyawa ya fita ilsai ga 'karan wayar tata daga kan kujera, kallon ta yayi ya kuma kalli inda wayar take......Noor kuwa kauda kai tayi tamkar bata san meke faruwa ba kawai ta koma bedroom abinta. Fita mai gadi yayi wanda tun ma kafin ya gama barin cikin parlourn wayar sa ta sake ruri. 'Dauka yayi yace " yalla6ai tana nan lafiya...wai wayar tata ce bata gani ba amma yanzu ta ganta". Ya fa'di hakan ne da tunanin babu mamaki yanzu ta 'dauki 'kiran. Godiya Deen yayi masa tare da kashe wayar sa, bai sake 'kiran maigadi ba kawai yaci gaba da 'kiran nata wayar amma har yanzun dai bata canza zani ba. Barin office 'din yayi kawai ya koma gida ya fara shirin tahowa Bauchi, abokin sa da ke aiki a airport ya sanya yayi masa booking cikin sa'a ma sai ya samu 'karfe 'daya da rabi jirgin zai tashi, sosai yayi murna da hakan kuwa wanda kafin kace kwabo har ya isa filin jirgin. 'Karfe 'daya da ashirin yana cikin jirgin har ma ya fara haramar kashe wayar sa, sai ga 'kiran Dr. Safwan ya danno. Kamar ba zai 'daga ba sai kuma dai ya 'daga dan sun 'dan kwana biyu basu gaisa ba. Jin abinda ya sami 'yar sa daga bakin Dr. Safwan ne ya sanya gumi karyo masa nan take ha'di da bugun zuciya.......a fili ya furta salati tare da tambayar yanayin jikin. Dr yace masa da sau'ki sai godiyan Allah domin nata abin bai yi tsanani ba kamar na Sani" Cikin ransa yayi hamdala tare da tambayar " Noor ko tana wajen ne?" Sai Safwan yace " ah ah, bama ya tunanin tasan abinda ke faruwa" Deen bai bi ta kan hakan ba sai ya tabbatar masa da cewa ai shima yanzu haka yana cikin jirgi zai sau'ka nan bada da'dewa ba, ha'di da yimasa godiyan kulawa da yayi da su. "Haba bakomai kar kadamu da wannan please" Safwan ya fa'di tare da tsinke wayar shi. Tun lokacin hankalin Deen ya kasu gida biyu har ji yake tamkar jirgin ma ba ya sauri, duk kuwa da cewa shi da kansa ya san da bambamci in da ace mota ce. Amma yanda ya 'kagu ya gansa gaban iyalin nasa ya sanya har yake raina tafiya irin ta jirgi. Daga 'karshe rintse idanu yayi ya kwantar da kansa yana addu'an Allah ya takaita masa Allah ya bawa Babyn sa lafiya mai 'dorewa. *Sani ya aikoni yace a sanar da ku cewa kunnuwan sa a toshe suke* 🎧 *haka ma idanun sa😎, dan haka* *ba zaiji komai ba kamar yadda ba zai gani da idanun sa* *ba.* _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerhn ku ce* [11/24/2019, 1:09 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Godiya mara iyaka gareku 'yan uwa na, sosai naji da'din addu'o'in ku gare ni....Allahu ya saka muku da mafificin alkhairi, baiwa_ _da rahamar sa._ 😍 *_Fatan alkhairi masoyana Allahu ya bar 'kauna_ 🤝* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *10* Iya k'ololuwar tashin hankali babu inda na Noorul bai kai ba a ranar, amma taurin kanta da kuma haushin abinda ta gani ya sanya ta ta tsani sake 'daga wayar ta ma balle har ta 'kira Deen kan batun Jasmine 'din. Haka ta daure ta sake 'kara mintina kusan talatin akai batare da ta kira Deen 'din. Ga mamakin ta kuwa har a lokacin shiru babu labarin su. Wnda zuwa lokacin kuwa duk wani dauriyar ta 'karfin su ya tafi, wani sabon kuka take jin yake taso mata, ita kanta tausayin kanta ta keji, da wanne zataji? Da damuwar miji ko kuwa damuwar Sani?. 'Dan guntun hawayen da ya zubo mata tasa hannu ta goge shi da bayan hannun ta sannan ta mi'ke cikin hanzari ta zari mayafin ta, cikin jakar ta laluba ta zaro 2k sannan ta fita bayan ta rufe jikin ta da mayafin. Ko da ta isa parlourn ma ko kallon inda wayar tata take bata yi ba, kawar da kanta tayi gefe ta fice abinta cikin sauri. Kafin ta fita sai da ta saka mai gadi ya sake 'kiran Sani, amma har yanzun dai wayar sa bata tafiya, sai tace ya 'kira mata Deen tana so tayi magana da shi. Ko daya gwada layin Deen ma a lokacin bata shiga, dan already jirgin su ya lula sararin samaniya zuwa Bauchi. Noor da bata san da batun zuwan nashi ba sai taji wani sabon takaici ya kama ta, idan zata biye abinda 'kirjin ta ke mata da ko tafiya taku biyar mai kyau bazata iya ba. Amma rashin sanin halin da 'yar ta Jasmine take ciki a lokacin shi yafi komai 'daga mata hankali......fiye da komai. Cikin 'karfin hali ta ringa karanto maso sauran layukan Deen 'din yana gwadawa amma ko 'daya babu wanda ya shiga. Rintse idanu da karfi ji take kamar iska zai yi sama da ita tsaban yanda take jin kanta, bata bari mai gadi yaga hawayen daya sauko mata ba....sai da ta juya ta fuskanci gate kafin ta furta " nagode Bala". Bai ma ji da kyua ba amma kuma kuma bata kuma maimaitawa ba ta cigaba da 'daga kafafun ta a hankali ta fara tafiya izuwa bakin gate 'din. Tunanin 'kiran Saif take yi amma bata rike numbern ki ba kuma baya san komawa ciki a yanzun balle ta dubo cikin wayar ta. Wani tunani ne ya sake zuwa ranta cak sai ta tsaya sai kuma ta juya ta kalli Bala tare da fa'din " Bala....dan Allah Sani bai ce.....da kai zai biya wani.... wuri ba kafin ya fita?" Muryar ta na cracking tayi maganar kana ji ba sai an sanar da kai ba zaka fahimci cewa tana tare da matsanciyar damuwa. Mai gadi jijjiga kansa yayi, shima 'din duk jikin sa yayi sanyi domin irin hakan bai ta6a faruwa ba iya zaman sa a gidan, ace har 'karfe biyu na shirin haurawa amma babu labarin mai tashi 'karfe sha biyu daga makaranta.....abin gaskiya bai yi ba kuma dole hankalin ta ya tashi matsayin ta na uwa. Yana jijjiga kai 'din ya ke wannan tunanin. Sai kuma ya 'kara da fadin ....." Babu inda yace min zashi Hajiya, ni Sani ma tunda nake da shi a gidan nan bai ta6a sanar dani inda zashi ba...." Ya 'karashe maganar a hankali domin tuno wani abu da yayi cikin ransa Sai yace "...sai dai kwanaki ya ta6a ce min daga nan in ya bar aiki Lagos zai wuce amma ban san yaushe yayi niyyan tafiyar ba gaskiya". Take lumsassun idanun Noor suka bayyana 6aro- 6aro, bakin ta har na 6ari tace da Bala " Lagos dai? Shine ya gaya ma hakan kuma?" " Ehh 'kwarai kuwa Hajiya...shine da bakin sa ya sanar dani, sai dai bai har ga Allah bai gaya min ranar da zai yi tafiyar ba". Ya bata amsa cikin tabbatar wa. Noor ji tayi tamkar ta sa hannu aka tayi ihu...bata sake waiwayan Bala maigadi ba balle maganganun sa, tasa kai kawai tayi waje da sassarfa tana share hawaye.....a fili kamar zautacciya take fa'din " Allah ka sa hasashena ba gaskiya bane, Yah Allah ka dawo min da yarinya ta....ina son 'yata Yah ka taimake ni ka sada ni da ita". Tafiya take tana zubda hawaye har ta 'karasa bakin titi ta tari 'dan adaidaita, shigewa kaia tayi bata ma ko tuna ta gaya masa inda zai kaita ba dan tsananin tashin hankalin da take ciki, sai da yayi tafiya mai 'dan tsayi kafin yace da ita " Hajiya ina muka dosa ne?". Firgigi tayi cikin damuwa ta sanar da shi sunan makarantar. Ciki-ciki yayi tsaki dan kuwa shi ba hanyar ya 'dauka ba sai da ya 'dan 'kara tafiya ka'dan kafin suka yi U- turn zuwa hanyan makarantar su Jasmine 'din. Bata yi mamaki ba lokacin da ta isa bakin gate 'din makarantar ganin tamkar mutane basu ta6a rayuwa a wurin ba domin kuwa shiru arean gurin babu kowa, ita kanta tasan babu mamaki koda ta ga hakan, cuz almost 2hrs kenan da tashin 'daliban makarantar to kuwa wa zata samu? Kafin ta shiga sai da ta juya ta kakkali gefe da gefen hanya wai ko zata hango motar dasu Sanin ke ciki amma ina, bata ga komai ba. A hankali ta tura gate 'din ta shiga hango mai securites biyu da tayi zaune kan table ne ya sanya ta nufan inda suke, 'daya sai faman zuba surutu yake yayin da dayan kokuwa da da asuwaki cikin bakin sa. Kafin ma ta 'karasa mai asuwakin ya taso ya iso gare ta yana fa'din barka da zuwa Hajiya....wani matsala ne?" Yana gama fa'din hakan sai ya karkata kai gefe ya tufar da yawu. Noor kai ta 'dage masa tare da fa'din " ehh Baba yarinya ta ce har yanzu bata koma gida ba....bansan meke faruwa ba wallahi kuma tunda 'karfe sha 'daya na turo driver 'daukan ta". Batare da wani dogon tunani ba securityn yace " ya sunan ta?" Noor da sauri ta bashi amsa da fa'din " Jasmine ake 'kiran ta amma sunan Aisha Muhammad Tahir, nursery 2 take Baba shekarun ta kuma biyar ne!" Inda ta bashi amsar tambayar tasa hadda ma wanda bai tambaya ba. Sai yanzun ne ya 'dan kai hannu bakin sa alamar nazari, sannan yace " ehh toh a gaskiya dai ban gane ta ba......amma kuma yara yau duk babu wanda ya zarce 'ka'ida anan....kusan kowa ya watse tun ma kafin mu shiga Sallah, dama manyan sun ne ma ke 'dan 6ata lokaci amma yaran kam gaskiya duk basu da'de anan ba, sai dai ko ki tuntu6i drivern 'kila wani uzuri ya ri'ke su....." Tun ma kafin ya rufe bakin sa tace " Na shiga uku ni kam, Allah ka rufa min asiri?" Tayi maganar ha'di da dafe 'kirji. Kallon da security 'din yayi mata ne ya sanya ta sau'ke hannun data 'dora a kanta dama na 'kirjin gaba 'daya. " Me ke faruwa ne wai?" Ya sake tambayar ta da kulawa, sai tace " Numbern drivern baya tafiya tun 'dazu wallahi an ta gwadawa". Da sauri ya furta " subhanallahi......ashsha, Allah dai yasa lafiya....." Bata amsa ba sai kawai ta juya ta fita tana share hawaye yayin da Baba security ya cigaba da fa'din rayuwar yanzu sai a hankali komai ya lalace gaba 'daya, zu'katan mutane ya gur6ace da son abin duniya....Allah dai yasa ba salwantar musu da rayuwar yarinya wannan mutumin yayi ba". Daga inda take cigaba da tafiya tana iya jiyo duk abinda security 'din ke fa'di, daf da zata bu'de gate 'din ta amsa da " Amin". Sannan ta fice tana tunanin ashe ba ita ka'dai ke zargin hakan ba.....ita dai ro'kon ta Allah ya ku6utar mata da 'yar ta ya kuma bata kariya a duk inda take. Maganar da Securityn yayi sai ya 'kara birkita mata lissafi.........what if sayar min da yarinya yayi!. Da sauri ta jijjiga kanta ha'di da fa'din no no it can't be....Sani ba zai yi hakan ba. Wani zuciyar yace da ita idan kuma Lagos 'din ya tafi da ita fa........innalillahi Allah ka rufa min asiri......Allah kar ka tabbatar min da duk wadan nan abubuwan, Allah ka dawo min da baby lafiya. Ita ka'dai take tafiya tana sa'ka da warwar ta a zuci sam bata cikin natsuwar ta wani mota da ya auno ta da ka'dan yayi wulgi da ita sai yayi saurin jan birki, ita kam ma duk bata kulaba. Masifa ya so balbale ta da shi amma ganin tana kuka ya sanya shi jan bakin sa yayi shiru....haka taui wucewar ta ta gaban motar batare da ta kula da yanayin kallon da yakeyi mata ba. Mace har mace amma duk ta zama wata tamkar mahaukaciya.......jijjiga kansa yayi sannan yaja motar sa yayi gaba. 'Kin taran abin hawa tayi taci gaba da tafiya tana yi tana 'dan dube-dube wai ko zata hangi motar a wani wuri, lokaci-lokaci ta kan share hawayen dake gangaro mata, gaba 'daya ta fita hayyacin ta, wuni guda amma idan ka ganta sai kayi mamakin yanda duk ta birkice. Bata ta6a tunanin akwai ranar da zata tsinci kanta cikin tagwayen damuwa irin wannan ba, bata ta6a tunanin haka ba, ashe farin cikin mu da ba'kin cikin mu duk suna faruwa ne daga yanayin rayuwar mu. Yunwa take ji sosai domin tun safe bata saka komai cikin bakin ta ba, amma sam bama ta jin cin komai a wannan yanayin, damuwar ta Jasmine ne, burin ta ta ganta tasan halin da take ciki. Har yanzun kuwa hawaye na cigaba da sa'k'ko mata wanda yake tilasta ta yawan goge shi, domin da saurin sa yake sau'kowa hakan yasa bata jinkirin 'daga hannun ta takai saman fuskar ta ha'di da ro'kon Allah ya ji'kan ta ya ta'kaita mata wannan abin, Allah ya bayyana mata 'yar ta gudan jinin ta. Mafi yawan lokuta wasu dake wucewa na binta da kallon mamaki wanda wasun ma sam bata san suna yi ba, yayin da wa'dan su masu 'karfin gwiwar har na tsaya wa da nufin jin damuwar ta amma sai ta rasa mai zata ce dasu, kusan mutane uku suka yi mata magana amma mutun biyu daga ciki bata tanka su ba wucewa kawai take yi ta barsu tsaye a wurin, me zasu yi mata take tambayar kanta, idan har mai gadin makarantar ma bai san inda Jasmine tayi ba to waue zai iya sani banda Sani, hakan data sanya cikin ranta ne ya sanya ko kula su bata yi ba kuma bata damu da halin da zata shiga ba in dai saboda yar ta ne. Mutum na farko cewa yayi " Allah ya kyauta yayin da na biyun ya bita da kallon tausayi kawai gami da jijjiga kansa inda cikin ransa ya furta " Allah ya rufa asiri". Mata ta uku da tayi mata magana kuwa itace ta 'danyi sa'an samin amsa daga bakin ta inda tayi mata bayanin rashin ganin Jasmine 'din a takaice. Cike da tausaya wa kuwa matar tace Allah sarki, Allah ya bayyana ta....amma kiyi ha'kuri ki koma gida kinji, ki sanar da mahaifin ta sai ku kai report wurin 'yan sanda, in akayi sa'a za'a dace tun da kinsan aikin su ne, amma ai hakan kam wahalar da kanki kawai zakiyi" " Idan batada mahaifi fa". Ta tambayi matar tana kallon cikin idanun ta wanda tsintar kanta kawai tayi da fadin hakan. Sosai fuskar matar ya nuna alamun tsananin tausayawa tace " Allah sarki....idan na fahimce ki dai-dai kenan kina nufin marainiya ce ko....Allah ya bayyana miki ita, duk da haka kiyi ha'kuri ki je ga jami'an tsaro babu mamaki a dace, ki daina wahal da kanki please". Noor tsaban yanda take jin ranta yasa ta kasa fahimtar gaskiyan da matar ta sanar da ita ballantana ta fahimci tsananin tausayin ta da ya mamaye ilahirin fuskar matan. Cikin ranta tace " ai dama nasani, mutane bazasu ta6a fahimtar halin da kake ciki ba, komai ya faru da kai sai dai a cema " kayi hakuri.....ban damu da dan na wahal da kaina ba matu'kar akan yarinya ta ne zan juri komai koda kuwa menene shi" A fili kuwa share hawayen ta tayi sannan tace da matar "....nagode" tare da juyawa taci gaba da tafiyar ta tana tunanin yaushe zataje ga 'yan sanda ta kai report har su fita su nemo mata y'ar ta, gani take duk 6ata lokacin ta zatayi. Matar kam sosai ta tausaya mata dan kana ganin ta zaka fahimci tsananin tashin hankalin da take ciki..........a fili ta furta " Allah ya bayyana miki ita". Sannan itama ta juya ta wuce abinta. ***** Misalin 2:28pm jirgin su Deen ya sau'ka garin Bauchi, da 'dan sauri shima ya fita daga airport ya tari abin hawa direct zuwa asbitin batare da 6ata lokaci ba ya zarce inda Dr. Safwan yayi masa baya nin suna ciki ko da yaje gado 'daya ya tarar a 'dakin kuma Baby ne ka'dai take kansa. Jakar dake hannun sa ya sake tayi 'kasa lokacin da yayi arba da Babyn sa kwance idanun ta a rufe, hannun ta, goshin ta, kafa'dar ta da 'kafafun ta duk da farin abu dangin fari, ga dukkan alamu sitirta ciwuka akayi da su. A hankali ya 'karasa gaban gadon ya zauna daga gefen ta ya kamo hannun ta mai 'dan lafiyan ya sanya cikin nashi hannun, yayin da 'dayan hannun nasa ke shafa kanta a hankali. " Baby" Ka'dai ya iya cewa wanda daga hakan kasa furta komai yayi tsabar yanda tausayin Jasmine 'din ya cika masa zuciya, kuka yake jin yi amma baya so yayi kuka gaban ta dan kar ya karya mata 'karfin gwiwar ta na sake rayuwa a doron 'kasa. Yanda tausayin ta ya girmama a zuciyar sa har ji yake tamkar 'kirjin sa zai tsage, daga gefen ta ya kwantar da kansa a hankali cikin ransa ya furta " Allah ya baki lafiya Mamana, Allah ubangiji ya tashi kafa'dun ki". Dr. Safwan dake tsaye daga bayan sa ne ya 'kara so tare dafa kafa'dun sa ganin yanda jikin sa duk yayi sanyi, sosai yake tausaya masa shima. Yana dafa shi kuwa sai Deen ya 'dago jajayen idanun sa ya kalli hannun sannan ya kalli fuskar Dr. Safwan. Ganin shine sai ya sake sau'ke kanshi ya ci gaba da kallon fuskar Baby Jas dake kwance jikin ta bako riga tayi fayau duk ta ko'de ta 'kara haske. Saman la66a ya furta " Safwan Jasmine 'dina soon zata warke ko?" " Insha Allahu zata warke Mu'een karka damu, addu'ah zakayi mata kaji". Fa'din Dr. Safwan cikin tausayawa. Shiru Deen yayi kawai ya tsura mata rinannun idanun sa masu 'dauke da zafafan hawayen da sam baya son su sau'ko masa. A hankali ya sake fa'din " Bakin Baby ya kumbura Safwan kuma naga ba'a saka komai ba" Yayi maganar tare da kaiwa hannu yana shafa bakin a hankali. Safwan sai yace " Nayi mata allura kuma zai warware da iznin Allah, inajin buguwa tayi a bakin domin a 'kasan sit aka 'dauko ta a sume......sai dai kuma a mi'ke ta fa'da wurin ga dukkan alamu tun farkon faruwar lamarin tsoro da firgici ya sanya ta suma wanda sanadin fa'dawan nata ne ma ya sanya blocks 'din basu illata ta sosai kamar Sani ba". Shiru Deen yayi bai ce komai game da maganar Dr. Safwan ba kawai yaci gaba da kallon gurbin ciwukan dake jikin nata har zuwa 'kafafun ta wanda dai-dai feet 'din ta yaga nan manne da bandage, jikin ta babu komai sai tarin fararen bandage da auduga. Muryar Dr. Safwan ne ya ratsa masa kunnuwan sa inda yake fa'din " akwai wani abinda ya kamata mu tattauna da kai Mu'een, dama zuwan ka nake jira tun 'dazun da kuma farka war yarinyar 'kila zata san me ya faru, sai dai ba yanzu zamu yi maganar ba dan naga baka cikin natsuwa a halin yanzun gashi muna bu'katar jini". Sakin hannun Jas Deen yayi da sauri ya juyo ya kalli Safwan yace " me kake nufi Safwan, me ke faruwa da Baby....don't tell me that yarinya ta mutuwa tayi". " Haba Mu'een ka manta matsayin kane wai? dan Allah ka daina fa'din hakan, in kuma ma mutuwa Baby tayi har ni sai na gaya maka ne, ai gata nan a gabanka you can check her da kanka in baka yadda ba". Kai Deen ya dafe da dukkan hannayen sa tare da sakin zazzafan huci daga bakin sa batare da ya furta komai ba. Safwan ne ya cigaba da fa'din " magana zamuyi amma sai in Allah ya tashi kafa'dun yarinyar na tabbatar tukunna". " Kallon mamaki Deen yayi masa tare da furta " what's going on ne Safwan me yasa kake son min wasa da hankali ne, da wanne kake so inji please". Maimakon ya bashi amsar maganar shi ah ah cikin salon kauda waccen maganar yace dashi " Muna bu'katan jini Mu'een dama zuwan ka nake jira dan bana so a sanya mata wani daban sai naka kuma naga duk baka cikin hayyacin ka....ya za'a yi?" Tsaye Deen ya mi'ke yace " muje lab karka damu dani". Wata sister suka bari a cikin 'dakin suka fita. Suna zuwa ba a wani 6ata lokaci ba aka gama duk abubwan da ya kamata sannan aka 'dibi jinin Deen 'din leda 'daya. Safwan yayi-yayi dashi ya 'dan zauna ya huta amma sam ya'ki dole suka fito tare. Safwan da kansa ya jona mata jinin, ganin da yayi Deen bashi da niyyan zuwa ya huta ne yasa shi fa'din " kayi magana da mahaifiyar tan ne?" Kai Deen ya jijjga masa tare da kawar da kansa daga barin kallon Safwan 'din. " No wonder shiyasa har yanzu banga tazo ba....amma kasan duk inda take hankalin ta a tashe yake ko? Kuma itama Jasmine idan ta farka dole zata bu'kata ganin mahaifiyar ta ka sani...so ka daure ka 'karasa gidan sai ka sanar da ita kaga kaima ka 'dan huta kayi freshing up kafin ka dawo, babu mamaki ma Baby ta farka kafin dawowar taku..........". Deen kam sai yanzu na ma Noor ta fa'do ranshi, yanzu ne tunanin asalin ma'kasudin tahowar sa Bauchi yazo ransa, shi kansa yana so ya ganta yaji dalilin 'kin amsa wayar sa da bata yi a yau 'din ba" Batare da 6ata lokaci ba ya tashi sannan ya sunkuya dai-dai kan Jas yayi pecking 'din ta agoshi tare da furta " speedy recovery my angel". Kafin ya 'karaso har Dr. Safwan ya 'dago masa jakar sa da ya jefar tun farkon shigowan sa sai ya mi'ka masa. Hannu ya mi'ka ya kar6a tare da furta " ina Sani fa". Safwan amsashi yayi da fa'din " an kaishi male surgical". " Ok muje in ganshi kafin in wuce". Koda suka je yaga halin da Sani yake ciki ba 'karamin tausaya masa yayi ba, bai bar cikin asbitin ba kuwa sai da ya bada nasa ha'din kan, domin hannun Sani ba 'kara amfanar sa zatayi ba. Yana gamawa da wannan batun ya nufi hanyar gidan sa zuciyar sa cike fal da tausayin wa'dan nan rayuka guda biyu, wato Jasmine da Sani, wanda yake tunanin duk abinda ya same shi shine sila tunda shine ya bashi makullin mota ya kuma bashi suna DRIVER, duk dama yasan bawa bai ta6a wuce 'kaddarar sa amma yakasa raba zuciyar sa da 'daukan wannan laifin. ***** B'angaren Noor kuwa tafiya ta cigaba da yi idanun ka kan titi wai ko zata ga motar ta gifta amma bata gani ba, bata san iya tsawon tafiyar da tayi ba sai da ta tsinci kanta daf da round about, anan ta tsaya da tafiyar batare da mamakin doguwar tafiyar da tayi ba, wanda bata tunanin iya tsawon rayuwar ta ta6a yin koda makamanciyar ta. A daidai ta sake tara ta hau zuwa gida da tunanin Allah yasa ta same su a gida, yanzu kam in har ta koma gida taga basu dawo ba to dole ne ta 'kira Deen ta sanar dashi sai ya dawo asan abinyi tun kafin lokaci ya 'kure musu. *Ayi manage plz readers....Allah idona yana ciwo ne Amma insha Allahu gobe zaku ga wani update 'din* ~*PROMISE*~👌🏻 Comment Vote Share *Salmerhn ku ce* 😍 [11/25/2019, 3:37 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *11* Tunawa da tayi cewa shi 'din ma layukan sa duk basu tafi ba 'dazu da Bala ya gwada ne ya sanya ta furta" ko ta landline 'din asbitin su dole zan neme shi". Bata san cewa a fili tayi maganar ba har sai da 'dan sahun dake janta yace " na'am Hajiya dani kike yi ne?" Kafin ta ankara da abinda ya faru. Basar da shi tayi ta kauda kanta gefe tamkar bata ji me yake fa'di ba. Shima 'din shiru yayi ya cigaba da tu'kin sa. ***** Tun daga mashigar gidan da Deen yaga Bala mai gadi cikin wani iri ya fahimci shima cikin damuwa yake, dan ko fara'ar sa ma kaso hamsin babu a yau 'din, sai dai Deen bai tambaye shi dalilin hakan ba daga gaisuwa da sika yi sai kawai ya sa kai ya wuce ciki, cuz ya san koma menene damuwar ta shi ba zai rasa nasaba da accident 'din dasu Sani sukayi ba. Yana shiga parlourn yaji shiru ko'ina tamkar babu mutum mai rai cikin gidan, bai wani damu ba dan yasan mutnn 'daya dama ai baya hayaniya balle ita da yasan zuwa yanzun damuwar 'yar ta ka'dai ma ya ishe ta. Cikin bedroom 'din ta direct ya 'karasa sai ya tarar bata nan ga 'dakin duk a hautsine ga akwati cike da kaya da hand bag a gefe. Da kallon mamaki yabi 'dakin sannan ya sake fitowa da niyyar duba sauran 'dakunan, sai dai bai kai ga yin hakan ba 'dan motsin da yajiyo daga kitchen ya 'dauki hankalin sa. Duk wannan abinda yake yi cikin sanyi yake yin su, lokaci guda Deen ya sauya ya zama wani shiru-shiru tamkar bashi ba. Batare da sallama ba kawai ya tura 'kofan kitchen 'din. Turus yaja ya tsaya ganin wacce ke kitchen 'din. Hauwa ce ke wanke-wanke wanda tana ganin sa ta fara gyara 'dan kwalin kanta tana sunne kai. " Sannu da zuwa". tace dashi batare da ta kalle shi ba. Deen ma sai ya amsa gami da fa'din " yauwa Hauwa sannu, ina Maman Baby take ne?". " Nima ban sani ba, nazo ban same ta a gidan ba kuma Jas ma bata nan amma inajin sun 'dan fita ne". Juyawa kawai yayi ya koma parlour batare da ya 'kara furta komai ba. Har yanzun kuma jakar sa na kafa'dar sa bai sau'ke ba, sai da ya koma parlourn kafin ya ajiye jakar yayi mata masau'ki kan center table dake tsakiyan 'dakin. Kujera ya nufa da nufin samawa kansa matsuguni cikin tunanin inda Noor ta shiga a dai-dai wannan lokacin. Yana shirin zaman ne yaji abu 'kar'karshin sa, hannu yayi saurin kaiwa ya 'dago abin sai ya ga ashe waya ce kuma ma ta Noor. 3% ne ya rage na caji cuz tun 'dazu da safen data 'din wayar a bu'de take, yayi mamaki 'kwarai da gaske ganin wayar yashe a gun while mai ita bata ma gidan. Dayake wayar Noor babu wani security dan haka yana 'dagawa batare da wani dogon bincike ba yaga tarin missedcall 'din da wayar ta tara kusan 29, harda wanda ma ba nashi ba, akwai nashi dana 'yan makarantar su sai kuma wani new number. Bai bi takan massages ba sai kawai yayi minimize, ganin akan whattsapp ta bar wayar sai shima ya shiga. Farkon inda ya tsinci idanun sa shine kan wani photo da Jiddah ta 'dauka musu shi da ita awayar ta da bazai ta6a mantawa da ranar ba. Cikin ru'du yake duban photon musamman ma dayaga cewa har guda uku ta turo da kuma videon su shi da ita da aka 'dauka yana kusan tar ta. Jiyayi idanun sa nayi masa yana-yana kafin ya ankara sai yaji sun rufe gaba 'daya tsabar tuku'kin takaici da ba'kin cikin abinda ya fahimci Jiddah ta aikata wa rayuwar auren sa. Kife wayar yayi kan cinyar sa tare da lumshe idanu, tuno abinda ya faru da abinda ta gaya masa lokacin da ya fahimci cewa ta 'dauki videon......... Baya raba 'dayan biyu wannan dalilin ne ya sanya Nuree yin fishi dashi tsawon wunin yau. Tunanin irin yanda zai ci uban Jiddah kawai yake yi, ga kuma mamakin yanda har ta sake samu bayan da kansa ya san ya raba ta da shi....... Sam fushin Noor bai dame shi sosai ba cuz yasan tana da ha'kuri kuma zata fahimce shi ta yafe mai, amma yasan dole zai ji kunyar ta, zaiji kunyar sake cin amanar ta da yayi ha'di da cin zarafin ta Jiddah tayi. Sam baiji da'din abinda Jiddah ta aikata ba cuz yasan koda ace Jiddah kishiyar Noor ce suna 'kar'kashin sa duk kan su dole in taga irin wannan abin zataji kishi sosai balle kuma ace babu batun aure tsakanin su........ Yana cikin wannan tunanin yaji alamun an shigo parlourn. Tar ya bu'de idanun sa ya sau'ke su akan Noor dake tsaye tana kuka da hawaye duk ta birkice ta fita hayyacin ta. Take wani fargaba ya shige shi ha'da idanun da sukayi da ita, sake rintse idanun yayi gami da jijjiga kansa sannan ya bu'de idanun tare da fa'din " ohh Allah help me" cikin zuciyar sa. Sosai ya nemi 'kwarin gwiwar tunkarar ta wurin mahallici. Shigowan ta kenan shine Bala mai gadi ya sanar da ita cewa har yanzu su Sani basu dawo ba amma Deen na ciki shiyasa tayi hanzarin isowa har da gudu ta ha'da batare da damuwar komai ba, burin ta taga 'yar ta, sam ta manta da wata aba wai Jiddah balle abinda ya shafe ta. Suna sake ha'da idanu sai yayi saurin raba bayan sa da jikin kujerar ya mi'ke tsaye ganin yanda ta koma kamar ba ita ba ta tsaya tana kallon sa tamkar yau ta fara ganin sa. Sauri ajiye wayar dake hannun sa yayi a gefe, lokaci guda wani mahaukacin tausayin ta ha'di da soyayyar ta suka ratsashi, musamman yanda yaga yanayin da ta koma ga dukkan alamu tayi kukan nan yau sosai ba da wasa ba domin duk saman idanun ta sun kumbura idanun kuma sunyi ja sun kuma 'kan'kance. Tunkaran inda take tsaye yayi da niyyan taro ta amma Noor bata jira faruwan hakan ba. Da 'dan gudu ta taho itama ta rugume shi tare da sakin wani kukan gwanin ban tausayi, wanda cikin kukan take fa'din "Yah Deen banga Baby ba, Jasmine 'dina ban ganta ba......please kace Sani ya dawo min da Baby na....". Kamar 'karamar yarinya Deen yake bubbuga bayan ta ha'di da lallashi amma takasa yin shiru da 'kyar ya raba jikin sa da nata dan ba 'karamin ri'ko tayi masa ba, yana raba ta da jikin sa sai ya ha'de bakin su dan baiga alamar zatayi shiru ta bar kukan da ta keyi ba, bama ya tunanin tana fahimtar me yake fa'di, to a hakan kuma taya zata fahimci abinda zai gaya mata daya faru da Jasmine 'din. Shiru wurin ya 'dauka tsawon mintina uku yayin da Noor ke ta 'ko'karin jan jikin ta daga nashi cuz wannan abin ba shine a gabanta ba a halin yanzun, in akwai abinda tafi so da 'kauna bai wuci ganin babyn ta. Abinda bata sani ba kuwa shine shi kansa Deen 'din ba yana yine da jin da'din sa ba yana yine kawai dan nemo natsuwar ta da yaga alamun sun fara barin ta badan komai ba. Duk 'ko'karin ta kuwa bata iya k'watan kanta ba dole ta ha'kura amma hawayen ta bai daina na zuba yana bin kuncin ta ba. Tsawon mintina uku yana kissing 'din ta kafin ya barta tare da kaiwan hannu yana share mata hawayen yace " in kina son in kaiki gurin Baby ki daina wannan kukan......bani son shi kinji". Da jajayen idanun ta take kallon sa, tana jin wani k'ulli na taso mata game dashi amma jin cewa ya san inda baby take ya sanya ta sakin murmushi. " Dagaske Yah Deen zaka kaini wurin ta?" Ta tambaya tamkar wata yarinya 'karama cikin zubar hawaye da tsananin farin ciki mara misaltuwa. Shima 'din hakan yaga ta zame masa domin duk yarintar ta ta dawo mata sabuwa a dai dai lokacin. Kai ya 'dage mata sama alamar " ehhh" fuskar ta na tallafe cikin hannun sa. Sai ta kai hannu tayi saurin share hawayen ta da kyau Deen kam da kallo ya tsaya binta, zakuyi mamakin irin yanda yake ji a zuciyar sa game da ita, sosai yaga 'ko'karin ta data iya jurar 'daukan manyan damuwa har iri biyu cikin wuni 'daya. Yana cikin tunanin yaji ta kamo hannun sa tana janshi tare da fa'din " muje Yah Deen ka kaini inga 'yata kaji". Dakewa yayi guri guda kawai yana binta da kallo...hannun tan da ta kama nashi ya janyo ta ta dawo jikin sa, bai yi wata-wata ba kawai ya 'dago ta ya rungumo a jikin sa, bai dire ta ko'ina ba sai a cikin bathroom 'din dake 'dakin sa, baya son ya kaita nata 'dakin taga akwatin data shirya kuma ya tuno mata da 'dayan lamarin da ya faru shiyasa ya kaita nashi 'dakin. Yana direta kuwa sai tace " me zamuyi kuma a 'daki dan Allah Yah Deen? Ni fa Baby nake son gani" Ta 'karasa maganan cikin damuwa da rawar murya. " Sai munyi wanka first" Ya bata amsa a takaice. Noor kam wani sabon hawaye ne ya sake sau'ko mata tana 'kiyasta tsawon lokacin da zata 'dauka kafin taga baby, shi bai masan halin da take ciki ba wato shine zai wani ce sai anyi wanka. Tana ji shi da kansa ya rabata da komai na jikin ta ba tare data saka ko 'dan yatsan ta ba, a tare yayi musu wankan sannan suka fito. Zaunar da ita yayi cikin d'akin nasa yace ta goge jikin ta ta gama kintsawa kafin ya dawo bari yaje ya 'dauko mata kayan da zata saka. Koda yaje 'dakin nata bai bi ta kan kayan da suke cikin closet 'din nata ba sai ya bu'de akwatin data shirya ya zazzage shi kaf kan gado. A ciki ya za6a mata dogon riga da mayafi ha'di da inner set sannan ya koma 'dakin nasa ya kai mata. Yanda ya bar ta a haka ya dawo ya same ta ta 'kurawa waje guda idanu, Deen sai ya zuba kayan a kan gado sannan ya kama hannun ta zuwa gaban dressing mirror yace " maza ki shirya da wuri mu tafi kinji, ga kayan ki can idan kin gama sai ki shirya ina zuwa yanzu kinji ?". Yana gama fa'din hakan ya juya ya sake fita. Hauwa kam tuni ta fice abinta ta 'kofar kitchen, dama yau 'din ba wani aiki bane a gidan ko da safe da tazo ma Noor bata barta tayi aikin komai ba dan bata son damuwa alokacin shiyasa kawai tace mata taje gida anjima da yamma ta dawo, toh ita Hauwa sam sai taji hankalin ta bai kwanta ba shiyasa ta dawo da rana sai kuma ta tarar gidan ba kowa. Kafin ma ta gama kuwa taji shigowar Noor 'din bayan Deen ya bar kitchen 'din, lokacin data fito ta ga Noor na kuka a jikin sa sai tayi baya a hankali yanda babu wanda zai ji motsin ta ta koma ta fita ta kofan baya ta zauna a wurin. ***** 'Bangaren Deen kuwa 'dakin Noor ya koma kaf kayayyakin sai da ya maidasu mazaunin su har da na Jasmine gaba 'daya ya kai 'dakin ta itama. Kafin ya fito sai ya 'dan za6o kayan Jas 'din kala biyu marasa nauyi ya zuba cikin jaka sai ya bar su a palour da nufin zasu tafi dashi saboda garin a 'dan kwai sanyi-sanyi. Kitchen ya koma ya duba Hauwa da niyyan sanar da ita taje ta kintsa 'dakin Noor 'din amma sai ya tarar bata nan, dan haka kawai sai ya sha ruwa saboda rabon da yasha ruwa tun safe, ko a jirgi bai sha ba saboda rashin natsuwa. Yana komawa 'dakin shima ya shirya sharp-sharp ganin tana sallah sai ya duba agogo, kafin ya gama shiryawan ma har ta idar. Alwalar ya 'dauro shima sannan suka fita a tare da ita. Shaf kuma sai ya manta da kayan Jasmine 'din da ya bari a parlour bai tuna dashi ba. Har sun fita harabar gidan sai kuma Deen ya tuna babu driver yanzu a gidan, duban sa ya kai kan 'dayan motar dake ajiye a garag. Kamar wasa yace da Noor ta 'dauko mishi key 'din wancan motar inda yayi maganar yana nufan inda motar take. Da 'dan hanzari ta koma ta 'dauko masa ta bashi yana gwadawa kuwa sai mota ta tashi inda suka shiga suka tafi aciki. Kafin su isa asbitin sai da ya tsaya a wani masallaci yayi sallah sannan ya dawo suka cigaba da tafiyar. Tambayar.... shi waye ya sanar dashi inda Baby take... ta jefa masa, kafin ya bata amsa kuma sai ta 'kara fa'din me yasa to basu koma gida ba da ita ba kuma an ta 'kiran wayar Sani bata shiga. Deen cewa yayi " ki bari idan muka je zaki gani ai da idanun ki". Jan bakin ta tayi tayi shiru sai dai still wasu tarin tambayoyin ne cike fal a zuciyan ta, amma kawai ta ri'ke a ranta ta cigaba da binsa da idanu, 'kaguwan taga Baby Jas ka'dai ne yafi cika ta a lokacin. Deen kuwa a wani plaza ya tsaya ya shiga shi ka'dai, 'dan tsaki taja bayan ya bar cikin motar, ko wani tsayuwan sa 'daya ita ka'dai tasan irin haushin da hakan ke bata. Bata damu da me yaje siya ba balle ta damu da sanin ko menene da kuma manufar su ita dai kawai akaita wurin yarinyar ta. Sa'an ma datayi shine daga wannan plaza 'din bai k'ara tsayuwa ba sai asbitin da da yake aiki. Nan kam 6ata rai tayi ganin ya shigo harabar asbitin yaja ya parker sai ta kasa ha'kuri tace " haba Yah kaifa kace zaka kaini......" " mun zo ai " ya tare ta da fa'din hakan tun kafin ta a takaice. Da kallon mamaki ta bishi sai kuma ta 'kara bin asbitin da kallo goshin ta ta tattare tana duban sa. Fargaba ne ya ziyarce ta harma bata san lokacin da ta fito daga cikin motar ba tana fa'din " dan Allah Yah Deen ka gaya min me ya samu yarinya ta? Me take yi a asbiti?" A ru'de take maganar kamar zatayi kuka. Bai tanka ta ba sai kawai ya kamo hannun ta suka fara tafiya, bai 'dauko komai daya zo dashi ba duk ya bari cikin mota a hakan suka nufi ciki yana kwantar mata da hankali tare da fa'din " k'addara tana kan kowa Nuree, kuma Jas ma bata fi 'karfin Allah ya 'dora mata komai daga cikin buwayar sa ba, abin luran kawai shine tata 'kaddarar ba jarabawan ta bane a 'kananun shekarun tan nan, 'kaddarar ta iyayen ta ne, jarabawar iyayen ta ne...ina fata zaki kar6e ta hannu bibbiyu ki kuma gode Allah......cikin sa'a ma Baby bata yi wani raunin kirki ba sa6anin Sani da hannun sa 'daya ma kacokam cire shi za'a yi saboda ya lalace gaba 'daya". Tuni ta fara hawaye wanda cikin kukan ta tace dashi " Yah Deen me yasa me su?" " They had an accident Nuree, ni kaina bansan ainahin me ya faru ba amma in munje yanzu zamu iya jin bayanin gaba 'daya amma fa sai kin nutsu kinji? Sai ta 'dage kanta sama. Cigaba yayi da fa'din " Baby zata warware in sha Allahu domin nata bai yi tsanani ba, kar kuma ki ganta ki fara wannan kukan kin san banaso ko?" " Uhm bazan yi ba insha Allahu". Ta fa'di tare da goge hawayen da 'dayan hannun ta. Direct 'dakin da aka kai Jasmine ya wuce dasu inda suka tarar da wata Nurse da kuma Dr. Safwan a kanta yana 'ko'karin gyara mata mazaunin hannun ta. Hawaye kawai Noor ke sau'kewa da taga jikin 'yar ta duk farin bandages tana kwance kamar ba ita ba, kamar ba ita ce suka rabu da safe cikin raha ba. Da gudu ta 'karasa bakin gadon taje ta kama hannun Jas 'din tana kuka tana fa'din " Baby please ki bu'de idan ki ki ganni kinji.....gani nan Baby nazo wurin ki, nice Mummyn ki baby please ki bu'de idanun ki ki kalle ni....." Safwan ne ya mi'kawa Deen hannu suka gaisa sai yace " kaga ai ka nutsu ba kamar 'dazun ba". Bayyananniyar murmushi kawai Deen yayi masa na 'karfin hali sai yace " ya jikin nata....naga har yanzu bata farka ba?" Safwan sai yace "Ah ah ai kana fita ta farka inaga ma ko gida baka isa ba, da sunan ka kuwa tafara magana " wai Daddy kaga Sani ba, ni kam kace masa bana so".......Ta'ki barin kukan ne shine kawai na sata bacci". Deen cewa yayi " hmm ai Jas ban san irin dramar dake tsakanin ta Sani ba". Safwan cikin ransa yace " wannan kam babban drama ne abin Allah wa dai Mu'een....sai fatan Allah ya gyara lamarin kawai" A fili kuwa shiru yayi ya 'kyale sa dan tun farkawar Jas da yaji sunan Sani a bakin ta sosai ya shiga ru'du duba da yanayin da ya ganta ciki. Cikin hikima ya rin'ka tambayar ta har ta sanar da shi komai iya wanda ta sani. Safwan ji yayi tamkar ya zubda hawaye dan tsananin 6acin rai, rashin imanin yayi yawa sosai........babu mamaki abinda ke nan ya sumar da ita tun kafin afkuwar hatsarin. Da kansa ya sake duba ta bayan ya sata bacci, nan kuwa ya tabbatar da zargin sa.....sosai ransa ya 6aci ya kuma ji haushi sam baiji da'din faruwan hakan ba, wasu mutanen ma sai yake ganin basu da tunani, in ba haka ba mai mutun zai samu ajikin 'yar yarinya kamar Jasmine in banda hauka da rashin tunani. Da kansa yayi mata duk wani abinda ya kamata, da yake ba sai anyi mata 'dinki ba dan ba'a wani shige ta sosai ba kuma yarinya ce a hankali wurin zai ciko da kansa idan tana 'kara girma. Yana so ya sanar da Deen amma abin gatsau yake jin sa yafi son Jas da kanta ta sanar dasu tunda tasan duk abinda ya faru. Juyawa suka yi da niyyar barin 'dakin, suna tafiya a hankali inda Safwan ke yiwa Deen bayanin cewa " Sani shi har yanzu bai farfa'do ba balle asan wasu abubuwan dake damun sa". Sai Deen yace muje ma in duba shi, yaushe za'a yi masa aikin?" Safwan yace " sai gobe idan Allah ya kaimu". " Okay...Allah ya nuna mana goben yasa kuma ayi a sa'a". Safwan sai yace "Ameen tare kuma da 'kara bawa Deen 'karfin gwiwa akan faruwar lamarin gaba 'daya. Zuwa yanzun kuwa Noor kwantar da kanta tayi gefen na Jas 'din yanzun bata kukan da sauti, bakin ta kusa da kunnan Jas a hankali take karanto mata addu'ar neman sau'ki gurin mahallici. Tuni Noor ta 'dago kanta ji da tai Jas ta kama mata hannu tana 'dago kanta kuwa sai suka ha'da idanu da ita. " Mummy"! Jasmine tace a hankali. Sai Noor tayi saurin tashi ta zauna cikin tsananin farin tare fa'din " Alhamdulillah Jasmine.....Yah Deen zo kaga baby ta tashi!". Suna daf da 'karasa barin 'dakin sai suka jiyo abinda Noor 'din ta fa'di, a tare dukkan su suka dawo cikin hanzari zuwa gaban gadon. Comment Vote Share *Salmerhn ku ce* [11/27/2019, 7:09 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *12* Farin ciki ne mai tsanani ya ziyarci zu'katan su, Deen kam ji yake tamkar ya taka rawa, _Alhamdulillah....Alhamdulillah_ kawai yake furtawa a fili ba tare da damuwa ba. Yayin da Noor ke faman hawaye da murmushi lokaci guda idanun ta kan Jasmin 'din hannun ta kuwa na gefen fuskar ta. Ta 'dayan gefen bed 'din Deen ya koma ya ri'ke hannun ta yace " Jas 'din Daddy kin tashi?" Jasmine sai ta 'dage kanta sama a hankali tana kallon shi daga kwancen. " ina ke miki ciwo yanzu ?" Ya sake tambayar ta da kulawa cikin sassanyar murya. Shiru Jas tayi tana kallon fuskar shi batare da ta bashi amsar tambayar tasa ba. A hankali ta maida idanun ta kan Safwan inda nan take ta 'dan tura baki a hankali ta bu'di tace " Daddy kaga Uncle Safwan yayi min allura ba? kuma ni ai lafiya na 'kalau Sani ne yace bashi da lafiya 'dazu". Tana maganar cikin shagwa6ar ta da ta saba yi masa. Murmushi Deen yayi inda ya da'da ran'kwafowa ha'di da kai hannun sa 'daya yana shafo kanta yace " kar ki damu kinji mamana, shima ai Sanin an yi mishi alluran har guda uku ma, yanzu ina ke miki ciwo?" Deen ya 'karasa maganar tasa da tambaya yana me cigaba da shafa kanta. Jas sai tace " Ciwo?" Ta sake mai maita abinda ya fa'da 'din. Shima sai yace " uhmm fa'da min inji ko mamana, kanki na ciwo ne?" Jijjiga kai Jas tayi a hankali alamar ah ah " cikin ki fa ?" Ya sake tambayar ta. Sai kuma tayi shiru tana 'kara turo baki. Noor kam tagumi tayi tana binta da kallon jin da'di jin har tana yi musu hira, ashe da gaske ne da Yah Deen yace " nata ciwon da sau'ki ba kamar na Sani ba......hamdala kawai take ta zubawa mahallici. Jas ne taci gaba da fa'din " ai 'kafana na min ciwo da 'dan 'dina..." Tayi masa nuni da bandages 'din dake kanta. " Ayyah....sorry baby kinji, soon zai warke insha Allahu". Sake 6ata rai Jas tayi sosai sannan tace " Daddy!" Deen ma sai yace " Na'am 'yar gidan Daddy ina jinki akayi ?" " Ba sani bane ya cinye min bakina a mota ba kuma ya rufe min bakin da 'karfi har ina jin zafi....., banyi pupu ba a school kuma ko fitsari ma banyi ba amma ya min tsarki mai zafi......ni kam Daddy kace mishi bana so.......". Wani dumm dukkan su suka ji tamkar sau'kan wani abu mai nawi a tsakar kawunan su, yayin da idanuwan Noor duk suka firfito waje ta zuba su akan Jasmine tana kallon ta. Deen ma kansa tsura mata idanu yayi yana faman harha'da bayanan nata wuri guda domin so yake ya fahimci ma'anar su. Inda karon farko tunanin sa ya basa a kan zancen nata da inda ya dosa gaba 'daya sai yaji wani bambabara'kwai kamar ba hakan bane........'dan jijjiga kansa yayi tare da fa'din " no ths can't be". Still yana ri'ke da hannun Jasmine cikin nasa. 'Dagowa yayi ya kalli Noor da bakin ta ke faman 6ari tana son furta magana amma ta rasa me zata ce ma kwata-kwata, domin ita tashin farko batare da wani dogon nazari ba ta fahimci inda maganar ta dosa. Mayafin da ke rufe da jikin Jas ta kai hannu da sauri ta yaye shi sai taga gaban ta a kumbure ka'dan. Sake shi tayi da sauri tare da zubewa da gwiwowin ta 'kasa ta 'kasa furta komai wani mahaukacin jiri ke 'diban ta yayin da maganganun Jas 'din ke sake yi mata yawo aka " ........banyi pupu ba kuma banyi fitsari ba amma ya min tsarki mai zafi....". Kanta tayi saurin dafewa da dukka hannayen ta biyu, yayin da hawayen ta ge turereniya wurin ganin sau'ka, sosai jikin Dr. Safwan yayi sanyi amma babu yanda zai yi dole ne zai tabbatar musu da asalin gaskiya. Bin ta Deen yayi da kallo sannan ya sake bin jikin Jasmine 'din ma gaba 'daya da idanun sa da suka gama dawowa jajazur.....shi kam 'kwa'kwalwar sa ma dum yake jin ta ya kasa koda yin nazari ne tsabar confusion. 'Daga kai yayi ya kalli Safwan dake tsaye tun 'dazun bai furta komai ba. A 'dan rikice yace " Safwan me ke faruwa wai?" Nuna Jas yayi da hannun sa yace " kasan me maganan Baby ke nufi Safwan?" Kai ya Safwan ya jinjina masa alamar " ehh". Deen sai ya sake fa'din " kenan dagaske Sani......." Bai 'karasa ba Dr. Safwan ya amshe da fa'din ".......he try to rape her but Allah bai bashi nasara ba sai dai duk da haka ya ji mata ciwo ka'dan......ni kaina lokacin da aka ciro shi a motar nayi mamaki sosai domin belt 'din wandon sa a kunce sai dai banyi zargin wani abu ba a lokacin gaskiya duk da kuwa abin ya kulle min kaina.....duba Jasmine da nayi sai naga abinda akayi mata wanda sai a lokacin na tuno da bu'da'd'den belt 'din Sani da na gani......ha'ki'ka wani mummunan lamari ne ya so faruwa sai Allah ya takaita shi...... Na gama tabbatar wa ne lokacin da Jasmine ta farfa'do.....ita ce ta sanar dani duk abinda ya faru wanda take da masaniya akai........". Noor bata kai ga jin 'karshen maganar tasa ba ta sanya aka ta kurma uban ihu kamar zautacciya tare da zama dirshan 'kasan tiles tana kuka, wanda cikin kukan take fa'din " ta tabbata kenan an lalata min rayuwar 'yata....Sani ka cuce ni Sani, Sani Allah ya isa tsakani na da kai.....ubangiji sai ya saka wa Baby zalincin nan da kayi mata....insha Allahu sai kaga sakayyar ka tun anan ba sai an mutu ba.....Allah ba zai barka ba Sani". Deen kam na gama jin abinda Safwan ya fa'di sai ya sake waigawa yana kallon Jas dake tsiyayar da hawaye ganin mahaifiyar ta na kuka.....kallon sa ya mayar kan Noor dake ihun kuka Sannan ya 'dago ya kalli Safwan dake tsaye kusa da shi sai ya jijjiga kansa......suna ha'da idanu sai Safwan yace " kar ka 'daga hankali dan Allah Mu'een abin ba mai tsanani bane, inajin yatsa ya tura mata da karfi amma bai kai ga mummunan ku'durin nasa ba.....kaga Allah ya takaita....kuma da iznin sa komai zai zo da sau'ki". Tsaye Deen ya mi'ke sai Safwan yace " Zo da Allah ka bawa Noor ha'kuri tayi shiru ko kuma ka 'dauke ta ku koma gida ku huta zanji da Jasmine karka damu please". Deen bai ko waigo ba yaci gaba da tafiyar sa inda yake 'daga kafafun da 'kyar tamkar ana ri'ke masa 'kar'kashin takalmin da gum. 'Kirjin sa yake ji tamkar na aro ne aka bashi ba nasa ba, a hankali yake tafiyar kamar bazai yi ba dan sosai lamarin ya karya masa ga6a6o6in jiki gaba 'daya, ba'ki'kirin yake ganin gaban sa....sam baya ma fahimtar meke gaban sa dan tsananin ka'duwa amma a hakan ya cigaba da tafiyar dan gani yake tamkar haske zai baiyana masa a gaban sa...tamkar zaiji cewa wannan abin dayajin ba gaskiya ba ne....ba Jasmine 'din sa Sani yayiwa haka ba". Noor dake ihun kuka tana sumbatu cak ta tsaya da kukan da take yi kamar wanda aka 'dauke mata wuta, tashi tayi da sauri ta tafi ta tari gaban sa ta tsaya tare da kama kunkumi da dukka hannayen ta biyu tamkar ba ita ce mai kukan yanzun ba, amma kallo 'daya zakayi mata ka fahimci tsananin 6acin rai dake tattare da ita. Gaba 'daya idanun ta run rufe da 6acin rai...... abinda bata ta6a yi masa ba tsawon rayuwar ta amma ayau tana jin zata iya aikata masa fiye da zaton duk mai zato akan yarinyar ta. Cike da 'karfin hali dakiya da kuma masifa tace " kagani ko? Yah Deen Kaga result 'din mugun halin ka ko?" Nuna Jas tayi da hannu tace " ai kaji da kunnan ka abinda tace Sani babban amintaccen ka yayi mata ko? Me kuma zaka ce yanzun? wani dama ce ta rage maka......wace dama ce ta rage maka ka bu'di baki ka bani amsa Yah Deen?" Ta 'karashe cikin daka masa tsawa tamkar itace gaba da shi. Rage sautin muryar ta tayi tace " Miye ban gaya maka ba Yah Deen?, miye ban sanar da kai game da Sani ba amma 'kememe ka'ki ka saurare ni, sai ma kake ganin tamkar kawai 'kiyayya ce nake yi masa, ban sani ba ashe bakin ku 'daya ne da shi, yanzu daya 'kwa'kule min yarinya kuma me zaka ce dani....miye laifin Jasmine...me ta tare muku a rayuwa dan Allah.....? Kuka ne yaci 'karfin ta sai da ta 'dan yi kuka kafin na taja numfashi sannan taci gaba da fa'din " wallahi har abada Yah Deen bazan ta6a yafe maka ba kai da Sani, kun cutar min da 'yata kun cuci yarinya ta kun cuci rayuwar ta....ha'k'kin ta ba zai ta6a barin ku ku sami farin ciki ba da izini Allah..". Da yatsa ta sake nuna shi sannan ta cigaba da fa'din " kuma ka sani wallahi duk abinda ya sami yarinya ta kaine sila kuma sai na 'dau ka mata fansa a kanka.... ba zan yafe ma ba sai inda 'karfi na ya 'kare.....banza munafukai marasa tsoran Allah masu lalata 'ya'yan mutane babu gaira babu dalili........". " Noor....... Da Safwan ya fa'di ne ya sanya ta waigo wa ta kalle shi inda a masifance tace da shi " miye...?" Cikin 'dacin rai. Sam Safwan bai yi mamakin abinda take furtawa ba dan kuwa ya san fiye da hakan ma ba laifi ba ne matsayin ta ta uwa ga Jasmine da aka cutar, amma miye na 'dora lafin kacokam akan Mu'een kuma bayan shine mahaifin yarinyar, ai koma miye ne tasan shi ba zai ta6a bada gudummuwa wurin ganin an cutar da Jas 'din cuta mafi muni irin haka ba. Saurin matsowa yayi kusa da ita cikin salon kwantar mata da hankali yace " haba Noor relax mana....mijinki ne fa kuma mahaifin Jasmine, ki sassauta mana......". Deen kam tsaye yake tun 'dazun tamkar mutun mutumi, tun farkon fara maganar tata ya tsurawa bakin ta idanu, gani yake kawai bakin na motsi yayin da sautin muryar tata ke ratsa dukkan wani ga6o6i dake jone cikin jikin sa, har bibbiyu yake ganin ta amma sam bai da niyyan tanka ta. Noor kuwa 'kan'kance idanu tayi tace da Safwan " Miji na kace Yah Safwan?, kuma kace na sassauta masa? Haka kace da gaske.....? Gashi nan ka tambaye shi Yah Safwan na san ya sani.......a yau 'din nan kafin yazo me budurwar sa ta turo min....Yah Safwan ga shi ka tambaye shi". Ta fa'da tare da kamo hannun Deen amma ko motsi bai yi ba daga inda yake tsayen. Dawo da kallon ta tayi gare shi tace " wallahi tunda nake Yah Deen ban ta6a dana sanin kasancewa da kai ba irin ta yau kuma hakkin 'yata sai ya biku bazai ta6a barin ku ba.......mazinatan banza kawai". Tana gama fa'din hakan ta wuce wurin Jas da tun 'dazun take faman kuka a kwancen da take. Deen bai iya cewa da ita komai ba, illah binta da idanu da yake 'karayi, shi ka'dai ya san me yake ji zuciya da gangan jikin sa. Shi kansa Safwan jikin sa yayi sanyi sosai, har ma bai san lokacin da Deen ya bar 'dakin ba. Komawa yayi gurin Noor yana bata baki akan tayi ha'kuri amma ko sauraran sa batayi sai surutu take yiwa Jas tana kuka tamkar ta zauce bata hankalin ta, ganin hakan ne yasa shi niyyar barin office 'din domin bata lokaci ta 'dan nutsu. Juyawan da yayi ne yaga Deen baya 'dakin sai dai taku uku mai kyau bai yi ba yaji muryar Noor na fa'din " Yah Safwan yaushe za'a sallami Jasmine?" Inda tayi maganar ba tare da ta waigo ta kalle shi ba. Shi 'din ne dai ya sake waigowa gami da bata amsar " sai nan da sati 'daya idan ta warke" " ba gaskiya ka fa'da ba Yah Safwan?" Ta sake fa'di cikin dakiya sannan ta tashi ta juyo ta fuskance shi " ka gaya min gaskiya dan Allah, ina so ne inje in kula da tarbiyar yarinya ta guri guda in da bazata ha'da ala'ka da duk wani munafuki ba bana son zaman asbitin nan bani son zaman Baby anan". Safwan kam zuwa yanzun mamakin ta ma yake yi yanda duk ta juye masa zuwa wata abu daban tamkar zakanya, har ji yake kamar wannan ba Nureen Deen ba ce, yarinya mai matu'kar sanyin hali, ha'kuri, kunya da kawaici ga girmama duk wani wanda ya girme ta, sa6anin wannnan da take kallon cikin idanun mijin ta take zagin shi, ta dubi tsabar idon mutun ta 'karya tashi. Cikin rawar murya ya bata amsa da fa'din " ki bari dai sai ta warware....first idan ma zaki..tafi da itan ". Noor bata sake tanka shi ba sai ta koma ga Jasmine ta kwanta gefen ta tare da kwantar da kai gefen ta tana shafa cikin ta tace "Allah zai saka miki Mamana, baki da hakkin kowa akanki kuma da iznin Allah duk wanda ya cutar da ke sai Allah ya saka miki...zai bi miki ha'k'kin ki". Safwan jijjiga kai yayi kawai sai ya sa kai ya fice daga 'dakin. ***** 'Bangaren Sani kuwa......... Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 [11/30/2019, 10:34 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *13* 'Bangaren Sani kuwa.....tunda aka kawo shi asbitin bai farka ba iya tsawon zaman sa bai san meke faruwa da shi ba sai yanzun da yake dai-dai da 'karfe hu'du da mintina hamsin da uku na yammacin ranar. 'Kafafun sa ne suka fara motsawa a hankali kana ya bu'de idanun sa da yake jin sun matu'kar yi masa nauyi saboda buguwan da kansa yayi. Kasa-kasa bu'de idanun nasa yayi saboda wani suka da yake jin kansa nayi masa ga jikinsa ko'ina yayi masa nawi, takamamme ba zai ga inda ke yi masa ciwo ba. Allah ma yasa dai-dai lokacin farkawar ta shi likita mai kula dashi yana nan cikin ward 'din wato Dr. Felix. Matsowa yayi cikin saurin sa zuwa gaban gadon da Sani yake kai 'din ganin ya 'dan motsi da 'kafafuwan sa, wanda ganin hakan ne ya tabbatar masa da cewar ya farka. Jin motsi kusa da shine yasa shi 'karfin halin bu'de idanu da 'kyar, bama ya gani sosai dishi-dishi yake gani, amma a hankali da ya cigaba da 'kif-'kif da idanun sai suka 'dan washe ya fara gani da kyau. Bai wani sha wahalar gano inda yake ba a halin yanzun, musamman da yake yaga likita akansa cikin kayan aikin sa na likitoci. Idanun sa ya mayar ya rufe su sai tar hawaye ya gangaro ta gefe da gefen idanun nasa, yana so ya 'dan jijjiga kansa amma ya kasa, yayi 'ko'karin 'daga hannun sa da yaji yayi nawi sosai amma hakan ma ya gagare shi, banda ciwon da ga6o6in sa ke masa baya jin komai. 'Ko'karin tuno sanadin faruwar hakan yayi inda ya fara tunani tun daga farko, lokacin da ya 'dauko Jasmine daga makaranta, feelings 'din da ya kama shi sanadin kallon abinda bai dace ba cikin wayar sa, amfani da yayi da sanyin da tace tanaji, kissing, har zuwa fingering nata da yayi and most of all yun'kurin kusan ta kansa da ita da yayi wanda bai kai ga aikatawa ba yayi musu sanadin accident saboda firigici da ya kamashi. Hawaye yake sau'karwa masu matu'kar zafi da ciwo a zuci, tambayar kansa yake yi shin anya shine kuwa, Jasmine fa, da 'din kenan kusantar ta zanyi ko me? Sani da hankalin ka kuwa? Anya kaine Muhammad Sani na da 'din nan? me ya ru'deni har haka? Me ma zan samu a jikin ta? Ashe kissing 'din ta da da nake yi ma bai isheni sanin haukar da nakeyi ba? Yanzu yarinyar Oga Deeni nayi wa haka? Waiyo Allah na.....wallahi shai'dan ka cuce ni, baka min adalci ba, yanzu fisabilillahi wani kallo Oga Deeni zai yi min...? Nasan ba zai ta6a yafemin ba...." Dr. Felix kam bai bi ta kan hawayen da yaga Sani keyi ba, dan zaton sa duk akan zafin ciwo ne, dan haka kawai sai yaci gaba da aikin sa inda ya 'kara duba lafiyar sa da sauran wasu abubuwa, tambayan sa Dr. Felix yayi kan cewa baya ga ciwukan sa na zahiri akwai inda ke yi masa ciwo ne? Sani ko kulasa ma bai yi ba yaci gaba da kukan sa yana tariyo ta'asar da ya aikata cike da tarin nadama. ***** Tunda ya baro 'dakin da aka kwantar da Jasmine yake tafiya tamkar mutun mutumi, tunani yake cikin ransa wai dagaske Babyn sa aka lalatawa rayuwa, dagaske ne Sani ya lalata masa rayuwar 'yar sa?, da gaske ne kamar yanda Nuree ta fa'da wannan abin ya faru ne sanadin halin sa? Kai ah ah me ze sa hakan to? Abu 'daya ne yafi tsaya masa a rai shine lalata masa 'ya da Sani yayi. Sam Deen bai san inda yake jefa 'kafafun sa ba, bai san inda yake nufa ba balle yasan wa'danda ke wuce wa ta gefen sa ko suke masa magana, domin bajin su yi ba ba fahimtar su wanene yake yi ba. Ga6o6i, zuciya da gangan jikin sa duk sun saki, tuno irin yadda da aminta da yayi da Sani fiye da ma mai gadin gidan sa, tuno irin yanda Jasmine ke yawan kawo masa 'karan Sani ne ya 'dan bashi 'karfin gwiwa ajikin sa. Sani! Ya sake maimaita sunan cikin zuciyar sa......lumshe idanu yayi ya kuma bu'de su a take sai hawaye ya gangaro masa. 'Daci yake jin na taso masa daga zuciyar sa ga harbi da takeyi da 'karfi gami da nawi da yake jin 'kirjin sa na yi masa, amma duk hakan basu dame shi ba kamar idan ya tuno wai Sani drivern gidan sa ne ya lalata masa rayuwar 'yar sa da bata 'karasa ma ciki 5years ba har yanzun. Saurin goge hawayen nasa yayi cikin bawa kansa 'karfin gwiwa gami da juyawa ya koma baya zuwa male surgical ward tunowa da yayi cewa Sani na can....." i ll kill today Sani.....sai na kashe ka ta yadda bazaka sake samun daman illata 'ya'yan mutane ba". Cikin zuciyar sa yake wannan maganar yana tafiya cikin hanzari. Dr. Felix na 'ko'karin sake jefa ma Sani wata tambayar ne sai Sani ya dakatar da shi da fa'din " dan girman Allah likita ka cire min wannan abin....ina so inga Jas inga halin da take ciki....ban kyautawa....rayuwar ta da ta iyayen... ta ba". Da 'kyar Sani yayi maganar cuz in ba ka kawo kunnan ta kusa da dashi ba bajin abinda ya fa'di zakayi ba. Dr. Felix ma bai ji abinda ya fa'di ba.....kawai sai shi da kansa yaga dacewar cire masa abin zu'ko numfashi dake manne saman fuskar sa. Kallo 'daya zaka yiwa Sani ka fahimci cewa cikin tsananin damuwa yake......har a lokacin kuwa bai daina hawaye ba, ana cire masa abin ya furta " Likita ina Jasmine take? Wani hali take ciki? Allah yasa yarinyar mutane bata mutu ba sanadin abinda nayi mata? Wannan karon Dr. Felix ya 'dan ji abinda Sani ya fa'di dan haka sanin da yayi cewa tare da 'yar Dr. Mu'een suka yi accident 'din ya sashi takaita tunanin sa kan cewa ita Sani ke tambaya.....cikin salon kwantar da hankali yace da shi " don't worry...tana lafiya, Dr. Safwan ya bata kulawa". Rintse idanu Sani yayi hawaye na sake bin gefen fuskar sa. Dr. Felix na sake shirin jefawa Sani tambaya akan nasa jikin ne sai idanun sa suka sau'ka kan Dr. Mu'een da ya bayyana daga bakin ward 'din tsaye cikin hali mai wuyan fassaruwa. Idanun sa ka'dai zaka kalla kasan cewa ba a dai-dai yake ba. Kallon Sani yake yi cikin tsananin tsana da haushin sa while Sani kam bai ma san yanayi ba domin idanun sa a rufe suke. Dr. Felix da bai san asalin abinda ke faruwa ba lokacin da ya gansa yaga halin da yake ciki sai yayi saurin nufo inda yake tsayen domin shi zaton sa damuwar sa nada nasaba ne da jinyar su Sani, dan haka cikin tausaya wa halin da ya gansa a ciki ya nufo inda yake da nufin calming 'din sa. Sai dai ga mamakin sa da sauri Deen ya zo ya wuce shi batare da ya bi ta kansa bama balle ya samu koda kallon arzi'ki ba daga gareshi. Da idanu Dr. Felix ya bi bayan sa da sakakken baki, sai dai mamakin sa ninkuwa yayi akan nada lokacin da yayi arba da hannayen Dr. Mu'een jikin wuyan Sani yayi masa sha'ka na gaske domin kallo 'daya zaka masa ka tabbatar ba da wasa yayi hakan ba hatta jijiyoyin kansa sun fiffito hakama idanun sa. Waro idanu Dr. Felix yayi tare da dawowa baya da gudu yana fa'din " haba Dr baka ganin halin da yake ciki ne? Me yayi zafi haka please?" Yana maganar ne at the same time yana 'ko'karin cire hannun Mu'een daga wuyan Sani amma sam ya kasa. Sani kam gaba 'daya ya cire rai a sake rayuwa a doron duniya domin kuwa ba 'karamin sha'ka Deen yayi masa ba, gashi hannun sa 'daya ne mai lafiya ballantana ya yun'kurin 'kwatan kansa. Hawaye kawai yake sau'kewa cike da azaba sai kakarin fizgo 'dan numfashin daya rage masa da 'kyar. Dr. Felix daya kasa raba hannun Deen da jikin Sani sai yayi saurin ciro wayar sa daga aljihun sa ya danna 'kiran Safwan inda yana 'daga wa yace " Dr. Please we need you here, ka zo da sauri please Dr. mu'een zai yi kisa". Safwan dake 'ko'karin yiwa matar sa Hafsat jagora zuwa ward 'din da Noor suke 'kiran Dr. Felix ya riske shi, ai da hanzari ya bar ta yace tayi tambaya za'a nuna mata" da 'dan gudu-gudu ya kama hanyar male ward 'din dan kai agaji. Wanda sunan Mu'een da yaji cikin lamarin ne ya 'kara rikita shi gaba 'daya. Dr. Felix kuwa cigaba yayi da 'ko'karin 'kwatan Sani hannun Deen da har yanzun bai bu'di baki ya furta komai ba, da 'kyar yayi nasaran 'kwatan sa amma Deen ya'ki sakin sa gaba 'daya, mari ya rin'ka sau'ke masa hagu da dama idan Dr. Felix yayi yun'kurin dakatar da shi sai yayi masa wani kallo mai rikitarwa tsoro sai yasa shi matsawa baya. Sani ya kwashi mari a 'kalla fiye da biyar a hannun Deen wanda sai lokacin da yake marin sannan bakin sa ya bu'du fa'di yake " i ll kill u right away.....i'm going to kill u today....Sani u cheated me u ruined my daughters life....u fool me da kyakkyawar fuska kasa na yadda da kai Sani...... idan ban kashe ka ba yau Sani ni mutuwa zanyi.....gara ka mutu ko zanji sanyi a raina......" Da 'karfi ya girgiza shi yana hawaye yace " Sani mai yasa kaci amana ta, me yasa zaka min haka? Why only my daughter? Me na tsare maka a rayuwa Sani laifin me nayi maka? Mari ya sake sake masa ya kuma fa'din " ka bani amsa Sani, open ur eyes and tell me meyasa ka min haka Sani?" Ashe baka da tausayi baka da imani da sanin ya kamata? Jijjiga shi Deen yake da 'karfi yana surutai kamar wani mahaukaci. Dr. Felix kam hanyar waje yayi dan dubo wanda zai taimaka masa kan wannan lamarin. Sai dai bai kai ga fitan ba suka ci karo da Safwan a bakin 'kofan shigowa, wanda ganin sa da ya sakeyi a rikice yasa bai ko tsaya tambayar sa komai ba ya zarce ciki, shima Dr. Felix ya rufa masa baya. Yana isowa dai-dai Deen ya 'daga hannu zai kai wani marin wa Sani cikin kuka amma kafin ya sau'ke nashi sai Safwan ya riga shi sau'ke nasa marin kan kuncin Deen. Gami da fa'din " baka da hankali ne Mu'een, me kake shirin aikatawa ?" Cikin tsawa yayi maganar da 6acin rai. Take Deen ya sau'kar da hannun sa gami da sakin Sani da ya jima da sumewa a hannun sa ya tafi la'kwab ya kwanta. Mi'kewa tsaye Deen yayi da jajayen idanun sa yake kallon Safwan kallo na 'kas'kanci. 'Kirjin sa ya nuna da hannun sa 'daya gami da fa'din " Did u just slapped me Safwan....did u?" "yes i did...." Fa'din Safwan cikin masifa, hannu ya 'daga ya nuna Deen 'din dashi tare da cigaba da fa'din "........and ina tabbatar maka more is coming idan har kace zaka 'kara yi mana irin wannan haukan anan.....meke damun ka ne Mu'een? Kai baka ganin halin da yake ciki ne? Da wanne kake so yaji?". Cikin tsawa gami da watsa hannu Mu'een ma yace " i don't bloody care Safwan! I don't.....i thought da bakin ka ka tabbatar min da abinda ya aikata wa rayuwar 'ya ta? How dare he? bashi da sence ne ko kuma rainin hankali me ya sashi aikata min hakan? Yadda sosai sosai nayi da yaron nan Safwan fiye da kowa cikin ma'aikatan gida na, amma ji abinda ya aikata min, dubi abinda ya saka min da shi, ko tsoron Allah be ji ba talkless of yaji kunyar abinda yake aikata wa ya farma that little soul, ka tambaye shi Safwan me ya samu me ya tsinta a jikin ta? ribar me ya ci?.......wallahi Safwan ganin mutuwar wannan yaron ya fiye min komai a yanzu, bana 'kaunar sake ganin sa a rayuwa ta....Safwan....me na zama, miye matsayina? Me nene amfani na matsayin uba ga Jasmine, Safwan ina raye amma wani 'dan iskan banza ya lalata min rayuwar yarinya ta, ina jin tamkar bazan iya yafewa kaina ba, duka laifina na ne, nine na yadda da shi na amince da shi na bashi yadda na kuma dam'ka masa ragamar jigilar 'yata a hannun sa...yanzu me zan cewa ubangiji na, wani irin ri'ko zance na yiwa Baby idan ubangiji ya tambaye ni game da rayuwar ta....... ". Kuka ne yaci 'karfin sa sosai da yasa shi dakatawa da maganar. Zama yayi kan wani kujera dake 'dakin ya dafe kansa da dukkan hannayen sa biyu ya cusa su cikin gashin kansa, cike da damuwa ya sunkuyar da kansa gami da jijjiga wa, gaba 'daya ya nemi nutsuwar sa ya rasa. Sosai tausayin sa ya kama Safwan dan ya sani koma waye irin haka ya faru da shi dole hankalin sa zai tashi, musamman ma idan kayi duba da 'kan'kantar Jasmine 'din, amma ya za'ayi? wannan ba komai bane face daya daga cikin 'kaddarorin dake tafe da rayuwar 'dan Adam, babu kuma wanda yafi 'karfin 'kaddara matu'kar yana raye a doron 'kasa. A hankali ya tako ya 'karaso kusa da Deen 'din, kafa'dar sa ya dafa tsawon minti guda batare da ya furta komai ba. Dr. Felix kansa jikinsa yayi sanyi amma a haka ya daure yayi kan Sani yana sake duba shi tare da bashi taimakon gaggawa. Cikin 'karfin hali Safwan yace " I'm so sorry Mu'een..... please kayi ha'kuri.....the deed is alredy done babu yanda zamuyi.....'kaddara ta riga fata, sannan kai kanka kasani 'kaddara dolen banu Adama ce dole ka kar6e ta ko kaso ko ka 'ki imma mai kyauce ko kuma akasin haka, ba zamu iya ta6a canza ta ba.....kar ka girgiza kafuwar imanin ka akan faruwar hakan Mu'een, ka daure nasan ba da'di...it really hurt but Allah ya sani yasan meke faruwa and insha Allahu komai zai dai-dai ta tunda Jasmine yarinya ce, still tana da wani chance 'din da zata yi regaining duk abinda ta rasa.....ka daina damun kanka akan Sani as u can see tun daga yanzu sakayyar Allah ta kama shi, can't u see shirin cire mai hannu ake yi ne? Wannan ka'dai ya ishe shi sanin cewa Allah bai barin hakkin wani......idan kuma kai ka 'dauki hukunci a hannunka ka kashe shi kasan hukuma bazata barka ba.....Allah ma kansa ba barinka zai yi ba duk kuwa girman laifin da ya aikata maka...to ribar me ka samu ......?" " i don't care Safwan ....koma me zai faru I'm ready to face it......su hukuntani su sani rayuwa cikin u'kuba da tsananin bauta da wahala wallahi bazan ta6a damuwa ba matu'kar akan Jasmine ne....Safwan" Kai Safwan ya girgiza ha'di fa'din " Calm down malam don't u dare say that again...idan ka juri wahalar duniya ka iya 'dauka to tsakanin ka da mahallicin ka fa? Zaka iya da wannan ne ? Shiru Deen yayi ya zuba wa 'kasan farin tiles 'din dake ward 'din idanu shi kansa yasan gaskiya Safwan ke fa'di amma me yasa yake 'kara jin zafin abinda Sani ya aikata masa. Safwan cigaba yayi da fa'din " ......kowa fa nada laifi Mu'een dama haka rayuwa a kullum take tafiya.....kar ka tsaya duba girman laifin wani sam duba naka kayi ma kanka hisabi and then cigaba da tafiya......Don't ever think i was supporting Sani......just want to wake u up daga dogon baccin da ka tafi..idan har kai zaka ji zafin abinda Sani ya aikata maka first then turn back kayi recalling kaf 'din rayuwar ka, ka duba da kyau kayi tunani akai.......". Tsaye Deen ya mi'ke da sauri yana sake tattare goshi ransa a matu'kar 6ace yace " me kake nufi ne Safwan bangane ba...me kake shirin sanar dani?" " What i mean is clearly opened Mu'een....kai dai kayi 'ko'karin godewa mahallici kawai domin ba 'karamin son ka yayi da rahamar sa ba....ina jin kamar gaskiyan Noor ne...bana haufi akan abinda ta fa'da, babu mamaki sakayya Allah ya so yi shiyasa ya sanya maka ninkin son Jasmine a zuciyar ka fiye da komai, ya kuma baka ita matsayin 'ya mace sannan ita ka'dai a gaban ka domin kawai sha'kuwar ku tayi tsanani ta yanda ko menene ya samu rayuwar ta zaka fi kowa jin zafin hakan.....ina maka kwa'dayin rahamar ubangiji Mu'een gami da fatan wannan abinda ya farun ya kasance babban darasi kuma iznah cikin rayuwar ka......." Tarin da Mu'een ya fara ne ya dakatar da Dr. Safwan ga cigaba da maganar da yake yi, da sauri ya taho ya ri'ke shi. Tari yake yi yana dafe 'kirji cikin tsananin azaba har yana 'ko'karin kaiwan 'kasa amma Safwan ya rirri'ke shi yana mai sannu Dr. Felix ma da wata likita da bta jima da shigowa ba dan suke kula da Sani tuni suka yo kansa domin taimaka masa. Kan 'dayan gadon dake 'dakin Safwan yasa aka kwantar dashi amma Deen ya'ki kwanciya. Tarin na lafa masa ya tashi ya zauna idanun sa jajajur yake kallon Safwan yayin da hannun sa 'daya ke dafe da 'kirjin sa. Da 'kyar ya iya bu'dan baki ya furta "....Safwan! " Ka daina damun kanka please Mu'een kafa san halin da kake ciki ko?" Fa'din Safwan cike da tausayi da kuma damuwa yana kallon Deen 'din. Cike da 'karfin hali yace " Safwan is it true kamar yanda Nuree ta fa'da kaima hakan ka maimaita min.....kenan...kenan...dagaske abinda nake aikata wa ne ya dawo kan ahalina.....my..my little princess......sanadin abinda na yi.......". Sai shar hawaye ya sa'k'ko masa. " Not exactly Mu'een kar ka manta akwai fa kaddar naga maka wancem kawai hasashene da kuma duba da fa'din mqnzon Allah (S A W), amma ai 'kaddara na iya kawo komai cikin rayuwar mutun, da yawan mutane ma zaka ga hakan ya same su batare da sun ta6a koda tunanin 6ata 'yar wani bq ballantana su aikata, to su kuma me zasu ce sai su cewa Allah me yasa kenan ko me? " To ni kuma dana aikata din fa ke za'a 'kira nawa 'kaddarar?" " haba Mu'een wai me yasa kake hakane....kai ba abin halitta bane ko kafi karfin jarabawa ne? Allah fa da kansa yace zai jarrabi bayin sa da duk abinda ya ga dama......to kai baka daga cikin bayin sane....? Shiru Deen yayi yana dan yi tari 'da'd'day da hawaye masu dumi dake sa'k'ko masa wana ganin hakan yasa Safwan cigaba da kwantar masa da hankali inda yace " ...kayi ha'kuri Mu'een ka kasance bawa nagari, duk abinda kaga ya samu bawa to rubutacce ne tun daga ranar da aka halicce shi....Sai dai kwai muyi fatan rayuwar mu tayi kyua mu kuma cika da imani muna amintattu....." Sosai Safwan yayi 'ko'karin kwantar masa da hankali amma Deen yakasa kwantar da hankalin sa, tashi yayi yana tafiya da 'kyar dafe 'kirjin sa ya bar ward 'din. Safwan bin sa da idanu yayi har ya bar ward 'din sannan ya jijjiga kansa ganin 'karfin hali irin nasa, tafiyar ma da 'kyar yake yin ta amma taurib kai ya hana shi tsayawa a mai abinda ya dace. Tambayar Dr. Felix yayi yanayin jikin Sani sai yace masa " bai farfa'do ba tukunna amma kuma hannun sa nata bleeding sosai daga hakan babu wata matsala...sai dai ya kamata a 'kara masa jini". Safwan cewa yayi " Bakomai kayi duk abinda ya dace we ll talk later". Dr. Safwan na gama fa'din haka sai yayi saurin bin bayan Mu'een 'din sai dai koda ya fita bai gansa ba, bai kuma yi tunanin zai koma ward 'din da su Noor suke ba dan haka sai ya tsaya duba harabar asbitin gami da tambaya ko angan shi. Deen kam yana fita ward 'din da Jas take ya nufa cikin ransa yake ta maimaita " maganganun Safwan yana 'kara na Noor akai, sosai ya fahimce su, ya kuma fahimci kuskuren sa bisa ga faruwar lamarin, sai ya 'dau laifin kacokam ya dawo dashi kansa har da na yarda da Sani da yayi da na 'kin yin bincike game da abinda Noor ta ta6a gaya masa game da Sani, sai ya 'dauki abin wasa a lokacin, yayi zaton ko kawai jinin su ne bai ha'du ba, ashe bai sani ba tattali da kiwon silar mummunan 'kaddar sa yake yi. Ita Noor dayake bata da hakki sai Allah ya sanya mata tsanar sa sa6anin shi da yake jin sa cikin zuciyar sa tamkar su Saif da Zaid......bansani ba ashe cuta ta zai yi....Allah ya ka yafemin, Allah ya yafemin laifukana...Allah ka bawa Baby lafiya...". Abinda yaci gaba da maimaitawa cikin zuciyar sa kenan yana tafiya. *Afuwan please kun jini shiru ban gama typing bane shiyasa* . _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [12/4/2019, 1:22 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Dedicated to sis Nanerh &_ _Aisha Aliyu (sarauniyar comment)_ 🌹 _Sosai nake yabawa da 'ko'karin ku.....luv u irin unlimited 'din nan mutane na_ 🥰😍. *ACIGABA DA GASHI.........*👌🏻 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *14* Noor dake faman kuka rungume da Jas a 'kirjin ta, tausayin ta take ji sosai, ji take kamar ta cire duk wani abu da yafaru da Jas 'din ya dawo kanta amma babu hali wanda sanin hakan ke matu'kar 'kara karya mata zuciya sosai take jin ciwon abinda ya farun jini da jijiyar ta. Cikin wannan halin matar Safwan ta shigo ward 'din ta same su. Ganin halin da take ciki ya sanya ta saurin ajiye basket 'din da take 'dauke da shi a hannun ta ta 'karaso kusa da ita a hanzarce " Haba Hudah ki sawa ranki salama please ki bar kukan hakanan, idan kina haka ai itama Jas 'din bazata samu natsuwa ba". Kai Noor ta jijjiga mata batare da ta furta komai ba sai kawai ta cigaba da kukan ta. " Kar kice zaki ja da ubangiji Hudah game da 'kaddaran da duk ya 'dora miki, dan Allah ki kwantar da hankalin ki, wanda ya 'dora mata shi ne zai yaye mata ke addu'ah kawai zaki ci gaba da yi mata matsayin ki na uwa kinji". Hafsat na maganar ne cikin sigar lallashi gami da 'ko'karin raba jikin Noor 'din da Jasmine cikin nutsuwa ba tare da 'dayan su ya illatu da hakan ba domin da 'karfi Noor ta rungumo ta. Kwantar da ita tayi da kyau tana shafa kanta tace " yi shiru mamana ki daina kuka kinji, Allah zai baki lafiya ki warke abinki, ga Afrah ma na kawo miki ita kuyi wasa kinji". Jas sai ta 'daga kai a hankali tana kallon Afrah dake tsaye daga gefe itama tayi rau-rau da idanu ganin dukkan su suna kuka. Tsurawa yarinyar ido tayi ko 'kiftawa babu tana tuno lokacin da tata 'yar ma take kamar ita....maganan Hafsat ne ya dawo da ita daga 'dan tunanin da take yi.... " dan Allah ki daina Hudah, kukan nan bashi da amfani kar kuma ya jawo miki ciwon kai a banza......" Bata kai ga rufe baki daga maganar tata ba Noor ta tare ta da fa'din " sun ha'da baki sun cutar min da 'yata ya zanyi Hafsat...sun lalata min rayuwar 'ya taya bazan yi kuka ba? Ta ya zan iya jure iri, wannan babban cin mutuncin Hafsat? Sai da na gaya wa Yah Deen ban yadda da wannan tsarin ba amma ya'ki amince min....yanzu gashi nan sun gama cutata sun cutar min da 'yarinya sun lalata mata rayuwa...". Hafsat da bata san inda zancen ya dosa ba sai kawai taci gaba da fa'din " ha'kuri zakiyi koma menene ya faru, ba kuka zakiyi ba, kima gode Allah tunda gata agaban ki kina kallon ta.....inda ace bata rayu ba fa? Me kuma zaki ce game da hakan? Cuta ba mutuwa bace Hudah kuma babu 'kaddaran kowa a hannun wani abin halitta kowa da nashi yake zuwa yake kuma tafiya dashi, dan driver ya sanya sunyi hatsari ba ze ta6a kasance wa cewan ya cutar da Jas bane, shi kansa da yasan hakn zai faru nasab da ko hawa motar ba zai yi ayau 'din ba....amma ya zaa yi Allah ka'daine masanin gaibu kiyi mata addu'ah kawai kinji, Allah zai bata lafiya da iznin sa 'yarinyar ki zata tashi kamar yanda take ada....." cikin kwantar da murya ta cigaba da bata ha'kuri tare da nuna mata muhimman cin yadda da kaddara har ta samu ta 'dan rage kukan da take yi d'in sannan ta fara lalla6an Jas ma yayin da Afrah ta matso ta kwantar da kanta bisa cinyar ta tayi shiru, duk da 'karancin shekarun ta amma sosai ta fahimci yanayin da suke cikin bana walwala bane. Tashi Hafsat tayi ta 'dauko abincin da tazo da shi ta zuba cikin plate tace da Noor ta daure taci abincin koda 'dan ka'dan ne tunda ita Jasmine Dr. yace abar ta tukunna sai zuwa anjima a bata. Noor bata yi musu ba tasa hannu ta kar6i abincin ko kallon arzi'ki bata yi masa ba sai kuma ta ajiye daga gefen ta. Hafsat na ganin haka sai tayi saurin fa'din " Ki daure ki ci dan Allah koka'dan ne dan nasan tun 'dazun baki nutsu kin ci wani abinba...." Noor kam bata bi ta kan maganar da Hafsat 'din ke yi ba sai kawai ta ce " bani wayar ki dan Allah zanyi 'kira". Da yake tun da tazo bata ga Deen ba sai tayi tunanin ko shine Noor 'din zata 'kira dan haka batare da wani tunani ba ta mi'ka mata wayar. Numbers ta jera tayi dialling wanda ana 'dagawa ta fashe da kuka har kamar zata kasa magana ma. Ba hafsat ka'dai ba hatta shi wanda ta kira 'din rikicewa yayi ya dinga tambayn ta me ke faruwa....har ro'kon ta yake dan Allah tayi shiru ta gaya masa gaba daya jikin sa yayi sanyi, zaton sa ko 'dan uwan sa ne ya rasu dan wannan kukan in ba mutuwa ba babu abinda zai saya yin irin sa. Duk da kuwa sunyi waya da Deen 'din daren jiya amma sam sai yaji hankalin sa ua tashi da kukan nata......." dan Allah Antyn mu kiyi shiru ki gaya min me ya faru, me ya samu Yayah...hankali na ya tashi sosai". Da 'kyar cikin kukan ta bu'di baki tace " Jas....mine....." "Me yafaru da ita gaya min please ". "...Saif please ka zo... dan Allah ka zo Baby ba lafiya Saif.....sun cutar min da........." Da sauri Hafsat ta 'kwace wayar ta kashe 'kiran gami da kashe ta gaba d'aya sannan tace " Haba dan Allah, ashe ba kiji me na gaya miki ba, me yasa zaki rin'ka fa'din haka......ashe bazaki amince ki kar6i wannan 'kaddarar ba sai kin dangana ta da wasu....?" Saif kam arikice ya sanya salati yana tambayar ta yana sake tambayar yana jikin Jas 'din da kuma tambayar su wanene suka cutar da ita kuma wani irin cuta suka yi mata..... Shiru yaji bai sani ba ashe tuni wayar ta tsinke".......hello...hello Antyn mu!" Yake ta fa'di amma yaji shiru bata amsa shi ba. Noor da ta rasa mai zata ce da Hafsat sai kawai taci gaba da kukan ta. girgiza kai Hafsat tayi cike da damuwa gaba 'daya zuciyar ta ta karye.....'dago kan da zatayi sai idanun ta suka sau'ka kan Deen da tsayuwar sa kenan a wurin. bayan sa wata Nurse ce dake 'ko'karin shigowa itama "....excuse me". Tace dashi amma ko motsi bai ba. koda ta sake excusing 'din nasa ma still kamat bai ji ba dan haka sai ta tsaya jiran ya matsa kawai kafin ta shigo. Yayin da ya tsurawa iyalan nasa idanu yana kallo da sauraren sautin kukan Nureee da ke ratsa masa har zuciya yana sake illata shi ta ciki. Hafsat ne tace "...ah ah Doc..tor! Tayi maganar da rawar murya gami da 'dan jin natsuwan zai taimaka mata wajen kwantar wa Noor 'din hankali. " k'araso mana" ta sake fa'di a take gami da mi'kewa tsaye. Cak kukan Noor ya tsaya da jin sunan da Hafsat ta fa'di duk da tasan likitoci nada yawa musamman da ya kasance cikin asbiti suke, amma tasan da irin sunan Hafsat ke 'kiran Deen. Tsaye itama ta mi'ke tana jefa masa wani mugun kallo da shi ka'dai ya san ma'anar sa. 'Bangaren Saif kuw batare da ya tsaya sake bi ta kan Noor 'din ba kawai ya doka wa 'dan uwan sa dake can ABU Zaria 'kira inda yana 'dagawa ko sallamar da yake yi bai amsa ba kawai yace "......Ni kunyi magana da Yah Deen ne? Zaid take yace " ah ah gaskiya bamuyi magana ba...." " Antyn mu fah?" " itan ma bamu yi waya ba gaskiya....wani abin ne ya faru?" Zaid ya 'karashe da tambaya sai Said yace "....ina zargin haka gaskiya....cuz recently ta 'kirani tana kuka amma ban fahimci inda ta dosa ba....bari dai in gwada 'kiran Alhaji inji ko sun 'kirashi..." " ok ni kuma bari na gwada Yayan inji" Da haka kowa ya yanke wayar. 'Bangaren Deen kuwa ganin kallon da Noor ke jifan sa da shi ne ya sanya shi 'karasowa ciki a hankali kuma har a yanzun hannun sa dafe yake da saman 'kirjin sa. Shigowar tasa ne ya bawa Nurse daman 'karasowa ciki ta ajiye abin hannun ta 'dan madaidai cin tea flask ne da wani leda. Sannu kawai tayi musu bata kuwa wani damu ba duk da bata samu amsar kowa daga cikin su ba. Cigaba tayi da abinda ya kawo ta wato duba Jasmine. A fusace Noor ta juyo gareta dan zaton ta ko tafiyar su 'daya da Deen ne dan haka rai 6ace tace da ita " da izinin waye kike 'ko'karin ta6a min jikin 'yata?" Kallon Jas Nurse 'din tayi sannan ta sake kallon Noor tace "...da iznin Dr. Safwan". Nurse d'in ta bata amsa a takaice. Nuna Deen tayi da yaja ya tsaya daga kofa yana kallon ikon Allah, batare da ta kalle shi ba tace " wannan kuma fa....?" Nurse da mamaki ta kalle shi sannan ta kallo Noor tace " Dr Mu'een wai?...i think familyn sa ne ku 'din" Cikin d'an hargagi Noor tace " Ba wannan na tambaye ki ba madam" Da yatsa ta nuna ta sannan tace" idan har kinsan shine ya kawo ki ward d'in nan to wallahi tun wuri ki bani waje kafin in 6ata ranki anan....bani son salon makirci......". Hafsat ne tayi saurin dakatar da ita da fa'din " Haba Noor...kar zafin ciwon Baby ya sanya ki zaucewa mana....likita ce fa ita, kuma aikin ta tazo yi me yasa zaki yi haka....ina jin ita ce ke taimaka wa Safwan..ki kwantar da hankalin ki please ki barta tayi abinda ya kawo ta". Nurse kam bata ko ko second biyar bama ta juya ta fice abinta batare da ta kara fa'din komai ba. Wanda fitan nata ne ya bawa Jas daman ganin mahaifin ta dake tsaye tun d'azun. Tana ganin sa kuwa take sai ta 'dan saki fuska da fara'ar ta tace " Daddy!" Har tsakan kansa yaji sunan da ta 'kira shin dashi amma girman laifin da yake ga yake dashi agare ta bazai bar shi ya amsa wannan babban matsayin ba, gani yake bai cancanci kar6an wannan matsayin ba daga Jas. A hankali ya 'karaso bakin gadon da Jasmine ke kai Noor na tsaye tana kallon sa ta wani yi kicin-kicin da idanu. Hannu ya mi'ka da niyyar kama hannun Jasmine sai Noor tayi saurin shiga tsakanin su ta janye hannun yarinyar gami da fa'din " malam me ya faru? Deen bai tankata ba illah hannun nasa da yabi da kallo sannan ya kalli Jasmine dake kwance " Baby... " ya furta saman la66an sa tare da lumshe idanu sai ga hawaye masu sanyi sun subo masa. "....karka sake tunanin kusanto inda muke dan banaso ka kaini bango.....daga ni har baby bama bu'katar sake ganin ka ko rayuwa da kai har abada....ai kayi naka...ba burin ka ya cika ba?....sai ka kama gaban ka kaje ka cigaba da rayuwar ka son ranka...baza mu sake shiga rayuwar ka ba balle mu takura ka... please muma ka bar mu hakan nan....". Ta 'karashe maganan cikin kuka gwanin ban tausayi. A hankali ya bu'de idanun nasa dake cike taf da hawaye ya sau'ke su akan fuskar Noor da ke faman ruzgan kuka mai tsuma zuciya a hankali ta dur'kushe 'kasa taci gaba da kukan. Ilahirin jikin sa kaf babu inda sautin muryar tata baya ratsa shi....sosai yake jin zafin hakan sai dai a zahiri sam bai nuna ya damu ba karo na farko cikin rayuwar sa da ya iya jure jin kukan ta batare da ya lallashe ta ba, saboda yasan yayi mata laifuka masu girma a yau 'din da bai isa ya iya hanata kokawa ba, idan ma yayi hakan kamar ya so kanshi ne, gara tayi kukan ko zata 'dan ji sassauci cikin zuciyar ta bisa ga abinda take ji. .....Kan Jasmine ya maida duban sa da ta turo baki tana kallon sa har ranta take jin fushin bai zo inda take baga kuma kukan da mahaifiyar ta keyi a gefe. Suna ha'da idanu da ita take ya gane abinda ke cikin ranta musamman ma da yaga yanayin fuskar ta, cuz sosai ya san halin 'yar sa ya kuma san damuwar ta. Baya ka'dan yaja sannan ya durk'ushe 'kasa a hankali gaban gadon still yana zubda hawaye. Kai Hafsat ta jijjiga gami da 'daukan Afrah suka bar 'dakin dan ganin kamar ahalin suna bu'katan privacy na musamman. Babu ma wanda ya bi ta kan ta har ta idasa barin 'dakin ga dukkan alamu ma basu san da faruwar hakan ba. Jas ne tace " Daddy kaima kana kuka irin na Mummy ko? Idan kana kuka zan gaya ka da Baba Alhaji idan naje wurin sa". Cikin kukan Deen yayi 'ko'karin dai-dai ta muryar sa batare da ya goge hawayen ba yace" Baby ki yafe min dan Allah kinji.....ke da Mummyn ki ku yafe min....nasan bazan ta6a goge laifukana a gareku ba amma dan Allah ku yafe min ko Allah zaiji 'kaina". " Daddy ka daina kuka kar little Afrah tayi maka dariya kai da mummy...na yafe maka kaji ka daina kuka, malam Hashim yace Allah yana son bayin sa masu yafiya....mummy ma ta yafe ma ka kuma kaga ta daina kukan.... idan kai kanayi kuma bazamu je Makkah da Madina da kai ba mu da Mummy ka'dai zamu tafi abin mu". Murmushin 'karfin hali Deen yayi mata sannan yace " Allah albarkaci rayuwar ki...ya sanya haske ya kasance abokin tafiyar ki....Allah ya tashi kafa'dun ki mama na insha Allahu cikin shekaran nan sai kinje makkah koda kuwa ni bazan samu zuwa ba insha Allahu sai na cika miki burin ki kinji". Koka'dan bai yi yun'kurin ta6a jikin ta ba dan Noor ta hana shi aikatan hakan ba kuma ya son ya sake 6ata ranta shiyasa ya tsaya iya magana. Tambayar sa Jas ta sake yi da fa'din "....Daddy nima ka yafe min?" Lumshe idanu yayi yana murmushi da hawaye ya 'daga mata kai gami da fa'din " har abada bazaki ta6a yin laifi a wurina ba Baby....na yafe miki koma menene...na yafe miki uwata fatana albarkar Allah ya kasance tare da ke har karshen rayuwar ki". Noor da ta zuba musu idanu tana kallon su ita kanta taji dadin addu'ar tasa har cikin ranta....sai dai duk da haka bata jin zata iya yafe masa abinda ya aikata mata. Muryar Jas da taji tana fa'din " Daddy saura Mummy ma kace ka yafe mata". " bata yi min laifi ba Baby....in ma tayi na yafe mata ". Juyaea tayi ta kalli Noor tace " Mummy ki yafewa Daddy na kinga yana kuka". 'Ko'karin share hawayen sa ya fara sannan ya ya kalle ta da niyyar ro'kon ta gami da bata ha'kuri sai tayi saurin dakatar da shi da hannun ta gami da saurin fa'din " adana tuban ka malam, ni banda bu'kata....burina ka fita daga cikin rayuwar mu ka bar mu mu huta....wallahi Yah Deen da kasan yanda nake ji cikin raina idan na ganka ko da bazaka sake gigin kusanto inda nake ba....i hate to see u by my side....." Hanyar waje ta nuna masa sannan ta cigaba da fa'din " barin ka ward din nan zai fiye min sassauci fiye da ganinka a gabana....dan Allah ga hanya nan zaka iya tafiya" Kalaman tan sun masa ciwo sosai amma haka ya daure ransa bai sake zubda hawaye ba. 'Ko'karin tashi ya fara yi sai tari ya sar'ke shi harma yaci 'karfin sa matu'ka, 'kirjin sa ya dafe da yake jin tamkar zai tsage biyu inda ya rin'ka jera tarin kusan sau hu'du har sai da ya dangana kansa da bakin gadon da Jasmine take kai. Da ya 'karayi kuwa sai ga jini a bakin sa. kaf a idanun Noor hakan ya faru dan kokadan bata kawar da kai daga kallon sa ba, ganin jinin ne ya sanya ta saurin rintse idanu ta kawar da kanta gefe, ita kanta tasan me hakan ke nufi, amma sam bata son tausayin sa ya kamata ballantana har soyayyar shi ta rinjaye ta duk kuwa da tanajin ra'da'di cikin ranta tana kuma jin tamkar ta taimaka masa amma haka ta basar ta kawar da idanun ta tamkar bata san cewa shine a gabanta ba. Jas kuwa sai kallon shi takeyi tana jin babu da'di, ganin tarin ya tsaya ne ya sanya ta cikin sanyin murya tace " Sorry Daddy...inaso in tashi amma 'kafana ciwo yake min....". Cikin 'karfin hali shima yace " kar ki damu mamana ai ya daina ma kingani ko?" Cike da takaici Noor taja dan guntun tsaki " Mthew" kana ta koma tayi zaman ta gefen Jas tana gyara mata mayafin jikin ta ta'ki ko da kallon inda yake ma. Tsaye Deen ya mi'ke da 'kyar cikin 'karfin hali dafe da 'kirjin na sa ya saiti hanyar fita. Taku 'daya zuwa uku yayi sannan sai ya juyo ga Noor ya kalle ta yaga ko bi ta kansa ma batayi ba illah hannun Jas da ta kamo cikin nata, a hankali cikin sanyi da nutsuwa yace " Ki gafarce ni Nuree.....ina so ki sani....banta6a aikata wani abu ba....dan na 'kuntata miki ko rayuwar ki ba koka'dan, sai dai wannan karon bansan ta yanda zanyi in wanke laifina a gareki ba duk dama nasan....cewa ehh ni 'din....ni mai laifi ne....amma ya zanyi? Ya zanyi Nuree bazan ta6a iya goge abinda ya riga ya faru ba tunda bani da ikon yin hakan....but instead i regret everything.....i regret every step of my life Nuree.... har abada nasan ni mai laifi ne agareku dukkan ku amma please ki yafe min ko Allah zaiji 'kaina Nureee, ki yafe min ko zanyi sa'an samun gurbi a gefen manzon tsira.....trust me Nuree insha Allahu daga yau d'in nan i promise u bazaki sake shiga damuwa saboda ni ba, bazan sake shigowa cikin rayuwar ku in hargitsa muku farin cikin ku ba....zan barku har abada Nuree tunda hakan kika fi bu'kata......." Jas ne ta yanke maganar tasa da fa'din " Daddy is still begging mummy please forgive him". Tayi maganar tamkar zatayi kuka. Noor kuwa cewa tayi "Shut up da Allah....rufe min baki....baki ga baki da lafiya bane Baby...ina ruwan ki da surutun sa". Kai Deen ya girgiza sannan ya 'daga 'kafa a hankali ya juya da 'kyar yake 'daga 'kafafun na sa ga jiri dake faman 'diban sa amma a haka ya daure yake tafiyar, lokaci-lokaci ya kan rufe idanun nasa sai ya kuma bu'dewa a take dan ganin hanya da kyau. Bai damu da halin dayake ciki ba a lokacin, burin sa kawai ya isa gidan sa, ya gansa cikin gidan sa. Safwan ne ya iso bakin ward 'din da sassarfa, wanda sai yanzun yayi tunanin zuwa duba shi anan 'din dan tun fitar sa hankalin Safwan bai kwanta ba musamman daya ga a halin da ya fita.......sai kuma yayi turus ganin Hafsat tsaye daga waje da mamaki yace " har yanzu baku same su bane?" Murmushi Hafsat tayi tace " ah no mun same su, kawai mun fito ne dan naga kamar suna bu'katan sarari, ban dai san meke faruwa ba amma naga Noor ta hana Mu'een ta6a jikin Jasmine bansani ba ko wani abin daban ke faruwa". " Yana ciki ne?" Safwan ya tambaye ta. Sai tace " ehh yana ciki". Bai sake jiran jin komai daga bakinta ba kawai yayi cikin ward 'din da 'dan hanzari, daga bakin 'kofa suka ci karo da Deen dake faman jan 'kafafu at the same time yana tari 'da'd'daya ga jini a hannu da kuma gefen bakin sa amma kuma dan taurin zuciya a hakan ya'ki tsayawa da tafiyar. Aikuwa Safwan na ri'ko shi sai yayi luu ya fa'da jikin sa, idanun sa lumshewa sukayi nan take. 'Kasa suka zube dukkan su Safwan ne ke fa'din" innalillahi Mu'een meke faruwa ne?" Noor na jin su amma ko motsin kirki batayi ba daga inda take zaunen sai ma sake kwantar da kanta da tayi gefen Baby ta dauke mata hankali da labarin su Alhaji da uncles 'din ta. Hafsat dake biyo bayan Safwan ne ta iso ta tarar da su Safwan cigaba da fa'din " dole fa ka tsaya a duba lafiyar ka kaima Mu'een in ba haka ba abin naga 'karuwa yake yi". Deen kam bai ma san da waye bane sukayi karon sai da yaji muryar sa kafin ya gane shi . " Me yafaru ne haka wai....a kira likita ya duba shi to idan bazaka iya ba" Hafsat ta fadi a d'an rikice. A hankali cikin murya mai kama da ta maye Deen yace " Saf..wan....Nureee". " Me tayi, me ya faru?" Safwan ya tambaya a k'agauce". " Ta'ki kula ni Safwan...ta'ki ta..yafe min..ya zanyi...? idan na mutu ka kula....min da su kaji...dan Allah ka kula min da su...ba zan iya juran fushin ta ba it hurts me....tell her i really love her...i love her...with all of my heart...and...and i was so sorry for all my mistakes...i...i....." Sai kuma yayi shiru 'dif sai numfashin sa dake fita a hankali. Hafsat kuwa tsorata tayi da ganin hakan instead ta kalli Deen 'din ah ah sai ta tsurawa Safwan idanu dan jin me ze ce game da hakan. Shi kam bai ma san tanayi ba domin waya ya ciro cikin hanzari ya yi 'kira domin azo atafi da Deen 'din inda za'a bashi taimako cikin gaggawa. Mintina biyar mai kyau basu cika ba kuwa sai ga shi anzo. Kan gadon tura marasa lafiya aka 'daura shi sannan batare da wani 6ata lokaci ba suka wuce dashi cikin sauri. Tun a kan hanya Safwan ya 'kira Alhaji Baba ya sanar dashi abinda ke faruwa, shima kuwa yanaji duk ya rikice ya tabbatar wa Safwan cewa insha Allahu gobe suna hanya suma. Duk abinda ya faru a kunnen Noor ne, kuka take jinyi amma kukan ta na yau tana jin ya 'kare, dan tun safe kuka takeyi, har ta gaji da shi, kanta ciwo yakeyi a yanzun tausayin ahalin ta gaba 'daya yake ratsata. Yini 'daya tak cikin rayuwar su yayi nasaran rusa musu dukkan farin cikin su wanda a kullum take yi musu fatan ya dore har abada,..amma hakan bai faru ba.....yini 'daya tak dukkanin farin cikin su yayi musu 'kaura, sai dai duk da haka al'kawari ta 'daukar wa kanta insha Allahu daga yanzu bazata sake yin kuka ba, bazata sake zubda hawayen ta ba, duk kuwa da cewa a duk lokacin da ta kalli Jasmine ta tuna abinda ya faru da ita, ta tuna ta'asar da akayi mata sai taji wani sabon kukan yana shirin zubo mata ji take inama...inama....inama ana maida rayuwa baya da sai ta bawa Deen mamaki, da sai ta kasance uwa 'daya mai tambari biyu, sai ta kasance abin kwatance a duk inda ta gifta, domin sai ta zamewa Jas uwa da kuma uba gaba 'daya, da bazata ta6a barinta tayi kuka ba...duk da hakama tana ganin bata makara ba, tana jin daga yanzu babu wani shegen da zai 'kara ra6a mata 'yar ta koda kuwa wanene shi, hatta Deen 'din kansa kuwa bata tunanin zai 'kara samun wannan daman, zata je ta rungumi 'yar ta ta kula da ita da tarbiyar ta, ta goge wannan mummunan tambarin da akayi mata, ......dana sanin auren ta da Deen kawai takeyi dana sanin rayuwa dashi dana sanin kasance wa dashi da kuma sonta da kuma yarda da tayi da shi gaba 'daya takeyi ahalin yanzun. " Wai daman Doctor nada ciwon zuciya ne?" Muryar Hafsat da taji ta fa'di hakan ne ya sanya ta dawowa daga dogon nazarin da ta tafi, sai tayi saurin bu'de idanun ta. Four eyes suka yi da Hafsat 'din sai ta kawar da nata idanun gefe. Ciki-ciki cikin halin ko'in kula ta amsa da fa'din " ummm yana da shi". Hafsat sai tace " amma gaskiya baki kyauta masa ba Hudah, shine kin san hakan kuma yazo duba halin da 'yar sa take ciki bayan tayi hatsari kuma sai ki hanasa ta6a ta? kin san yanda ta6a yarinyar zai sanyaya masa rai kuwa? anya Hudah kin yi adalci da wannan hukuncin? Mahaifin ta ne fah? " That was gone Hafsat....not anymore....yanzu shi ba mahaifin ta bane, ni nan da kike gani ni zan maye mata gurbin sa, ni zan zame mata uwa da uba bata da kowa daga Allah sai ni a duniya nan". A zafafe Noor ta fa'di hakan cikin dakiya. Sosai Hafsat tayi mamakin jin kalaman Noor 'din, sosai kanta ya kulle gaba 'daya. Zama tayi daga gefen ta cikin kwantar da murya tace " ban fahimce ki ba Huda, ganar dani manufar hakan.... bacin ga mahaifin yarinya nan araye sannan kike wani zance... ko ce miki akayi mutuwa yayi?" " I said shi ba mahaifin ta bane ko....please ki daina danganta min ya da shi" Tayi maganar cike da masifa sannan taci gaba da fa'din " bamu da ala'ka da shi har abada". " Wai saboda menene, what do you mean Hudah bacin ko makaho ya kalli Jas ya kuma kallon Doctor gani na farko zaka fahimci cewa jinin sa ce, me yasa kike son raba abinda Allah ya riga ya ha'da?" Noor wannan karan shiru tayi tana kallon fuskar Hafsat tsawon mintina uku suna kallon kallo, sannan Noor ta sau'ke ajiyan zuciya gami da fesar da numfashi mai huci cikin sanyin murya tace" bazaki gane bane Hafsat....ke sunan Mu'inudeen kawai kika sani amma sam baki san halin sa ba" Hafsat kam binta kawai take da idanu yayin da Noor ta juya ta kalli Jas da bacci ya fara daukan ta, kanta ta shafo a hankali sannan ta dawo da kallon ta kan Hafsat tace ".....wai anya kuwa kinsan asalin me ya samu Baby ne?" Hafsat cewa tayi " yes nasani mana, they had an accident on there way back home ita da driver ko ba haka bane...." Murmushin takaici Noor tayi gami da fa'din " zahiriyya kenan....shi kika sani Hafsat kamar yanda dukkan mutane suka sani...kuma suka shaida." Da mamaki Hafsat ta kalle ta sannan tace " akwai wani abu ne bayan hakan?" Murmushin takaici Noor tayi tace mata " 'kwarai kuwa Hafsat a ba'dini abinda ya faru shine Sani driver raping min yarinya yayi, Jasmine yayi attempting ya kusanta sai dai Allah ya tsare min ita, amma sai da yayi nasaran fingering nata deep inside.....Dr. Safwan ne ya sanar dani hakan, Hafsat to me ya rage min yanzu? Hafsat babu wanda zai fahimci abinda nake ji a zuciyata game da hakan sai ni ka'dai.....ina jin ciwon cutar min da ya da akayi aka lalata mata rayuwa, bazan 6oye miki ba Hafsat shima kansa Yah Safwan 'din ban gama yadda da furucin nasa ba inaga kamar 6oye min yake yi shiyasa yace fingering ne kawai". " innalillahi wa inna ilaihiraji'un, ya subhanallahi" Hafsat tace dafe da kanta sai ga hawaye ya gangaro mata cike da tausayin Jasmine 'din nuna ta tayi da hannu tana salallami tace " 'yar wannan abin...nikan na shiga uku da wannan rayuwar.....wannan wace iriyar hauka ce, mutane duk sun zama abin tsoro wallahi....kai Allah shirya Allah ya saka mata yabi mata hakkin ta". Tana maganar tana share hawayen ta duk da kuwa sake fitowa suke 'karayi amma bata fasa goge su ba tsawon mintina kusan shida tana kuka da hawaye batare da ta 'kara furta komai ba. Yayin da Noor taui shiru tana sauraran ta batare da ta yi yun'kurin bata ha'kuri ba illah wasa da hannayen ta da take yi kanta k'asa. Sosai tausayin Jasmine ya shige ta harma da ita kanta Noor 'din domin duk uwa abar tausayi ce indai har akazo irin wannan 6angaren, ace an lalata maka yarinya....ko da ace da girman ta ma ai abin da ciwo balle wannan da bata ma san komai game da rayuwar ba tukunna...A fili ta 'kara furta "Allah zai saka miki Jasmine ubangiji Allah ya shiryar da shi". " Ya shiryar dasu dai zaki ce ....ai suna da yawa" Cewar Nuree tana murmushin takaici, dan ita tayi al'kawarin cewa bazata sake kuka game da hakan ba, samun sauki Jas kawai take jira su tattara su tafi suyi musu nisa. Hafsat ne ta sake fa'din " Allah ubangiji ya shiryar da duk masu hali irin na Sani da mu ma baki 'daya". " To Ameeen za'a ce dan addu'ah nada kyau da matukar muhimmanci ga duk wani musulmi " Fa'din Nuree cikin halin ko in kula. Hafsat ne ta sake fa'din " To amma Hudah miye laifin Doctor anan kuma?" " Saboda shine mafarin komai Hafsat....Yah Deen shine sanadin komai, kar in ja ki da nisa Hafsat let me cut it shot ko zaki gane, a yau-yau 'din nan da safe Hafsat wallahi da videon ZINAN yah Deen nayi breakfast, inajin idan ban manta ba har yanzun shine a ciki na ban 'kara cin komai ba........can u emerging wai mijin ka ne da kake so kake kuma 'kar'kashin ikon sa zai je ya aikata ZINAH da budurwar sa kuma su 'dauka su turo min me suka 'dauke ni? Mara hankali ko me? Hafsat ban ta6a sanin al'amarin Yah Deen har ya kai haka ba sai yau.....i thought Yah Deen ya zubar da wancan rayuwar tun abaya bansani ba ashe yaudarar kaina nakeyi...har wai ni zasu raina wa hankali dan ina sar'ke da igiyoyin auren sa. Hafsat bana son in sake tuno rayuwa ta ta baya koka'dan amma inajin dole in sanar dake a yau 'din nan domin ki tabbatar da cewa wanene Doctor, menene halin sa, meyasa na dangan ta faruwar lamarin baby dashi? Me yasa kuma na hana shi ta6a jikin baby? Mai yasa zan fita in bar rayuwar shi na har abada?" 👇🏼 *Ba mamaki ku 'dan jini shiru kwana biyu saboda wasu dalilai, may be baza ku ga update da wuri ba, amma in nasamu lokaci zaku* *jini, idan kuma kuka ji shirun to ayi min uzuri please kamar yanda kuka saba* 🥰 *Comment* *Vote* *Share* *Salmerh ce* 😍 [12/14/2019, 12:17 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *15* Kukan rigimar da Afrah ta fara ne ya dakatar da maganar da Noor 'din ke yi. Gaba 'daya sai hankalin su ya koma kan Afrah...tashi Hafsat tayi ta 'dauke gami da fara rarrashin ta amma sam ta'kiyin shiru.....tana daga tsayen take faman jijjiga ta tana lalla6an ta yayin da Noor tayi shiru ta tsura musu idanu. Idan ka ganta alokacin zaka zaton ko kallon nasu takeyi but azahiri ba haka bane.....'dan 'karamin tunani take yi game da rayuwar ta gaba 'daya. ***** B'angaren Deen kuwa likitoci uku suke kansa banda Safwan da ya kasa barin 'dakin da aka kaishin. Da 'kyar suka samo kansa numfashin sa yayi dai-dai sai dai har yanzun zuciyar tasa bata daina harbawan da take yi ba bisa 'ka'idan ba. Shi ka'dai ne a 'dakin dayake shiru bakajin 'karan komai illah ceilling fan da ke aiki yake kuma bada sassanyar iska mai shiga jiki. Dr. Safwan duk jikin sa yayi sanyi, gaba 'daya faruwar lamarin ya tsaye masa a zuci...sosai ya karaya da matsananciyar tausayin abokin nasa. Da 'kyar ya bawa kansa ha'kuri ya daure ya bar kan Deen 'din ya fita cikin jimami. Ward 'din da Sani yake ya koma ya sake duba shi... bai samu Dr. Felix a 'dakin ba sai dai akwai wani likitan tare cuz yace kar ana barin sa shi ka'dai a 'dakin saboda gudun faruwar wani lamarin daban. Jinin da aka sanya masa ko rabi bai yi ba har yanzun, kuma bai farfa'do daga suman da yayi na sha'kan da Deen yayi masa ba. Jijjiga kai kawai Safwan yayi sannan ya juya ya fita ba tare da ya ko tambayi yanayin jikin nasa ba cuz ko bai tambaya ba kallon farko da ya yiwa Sanin ya fahimci ba wani ci gaba cikin lamarin...domin tun a yanda ya barshin a haka ya dawo ya sameshi...... 'dakin da aka kwantar da Jas yako ma yana me fatan Allah ya basu lafiya dukkan su.....da yake case 'din Jasmine a hannun sa yake so shiyasa dole sai shi ne ka'dai yake duba ta kuma bai wakilta kowa akan hakan ba....in badan haka ba da babu abinda zai sashi barin inda Deen 'din yake har sai ya tabbatar da cewa an bashi kulawar da ta dace. Zuwan sa 'dakin ne sai ya samu Hafsat tsaye tana faman lallashin Afrah da ta 'kiyin shiru da rigimar da takeyi. Hannu Safwan ya sanya ya kar6e ta gami da lallashin ta amma kamar ziga ta yake 'kara yi. Mi'kawa Hafsat 'din ita yayi tare da fa'din " ki sata ta 'danyi bacci dan inajin ba yanzu zamu koma ba sai zuwa can anjima dan Mu'een is unconcious......Alhaji kuma yace in kula da su baki 'daya shima wai gobe yana hanya insha Allahu". Hafsat cikin tsananin tausayawa tace "Ayyah Allah ya basu lafiya gaba 'daya, shi kuma Alhajin Allah ya kawo shi lafiya" " Ameen" Safwan yace tare da matsawa gaban gadon da Jas 'din take dan dubata...wanda sai a lokacin yace da Noor " madam yau fa duk kun 6ata raina kun rikita min patient". Inda yayi maganar batare da ya kalle ta ba. Bata sha wani wahalan fahimtar cewa da ita yake maganar ba cuz dama bata zurfafa tunanin nata da nisa ba tun farkon shigowar sa ta yanke tunanin. Murmushin 'karfin hali ta 'kir''kiro ta sanyawa fuzkar ta wanda ya tsaya mata iya kan fuzkar bai kai zuciya ba, sannan a hankali cikin sanyin murya tace " ayi ha'kuri Doctor baza'a sake ba insha Allahu.... naga ma kamar bacci ya fara 'daukan ta?". Cewa yayi " ehh dama tana da bu'katan hutu sosai ...kar ku sake damun ta please ga Afrah ma na kuka...ku koma wancan 6angaren ku bar min patient ta huta please". Yayi maganar tare da nuna musu 6angaren da zasu koma 'din. Allura yayi wa Jas 'din sannan ya 'kara dudduba ciwukan jikin nata daga nan ya fita bayan ya tabbatar sun koma 'daya 6angaren sun bar ta ita ka'dai akan nata gadon. Da 'kyar Hafsat ta samu Afrah tayi bacci sai ta kwantar da ita sannan ta 'kira wayar Safwan tace da shi ya 'dauko musu daddumar dake cikin motar sa zasu anfami da shi ganin cewa lokacin sallah ya gabato. Safwan aikawa yayi aka 'dauko musu daddumar ha'di da bada sa'kon abubuwan da ya san zasu bu'kata sannan aka aka ha'da aka kawo musu gaba 'daya. Sallar maghrib suka ya haramar gabatar wa, inda a lokacin Noor ta fahimci cewa al'adar ta ta dawo mata bata yi mamaki ba dan kuwa 'dazun tana kyautata zaton rikicewan da tayi ne ya hana ta tunowa da ainahin kwanakin da tayi wanda ganin kamar ya tsaya ne ya sanya ta yin wankan tsarki.... Hafsat da ta 'kagu taji labarin Noor 'din tana idar da sallar ta sai tace da ita ta bata labarin ai Doctor yace ma ba yanzu zasu tafi gida ba....so suna da isashshen time. Hafsat tayi maganar ne cikin 'kaguwa. Noor gyara zaman ta ta 'danyi ka'dan gami da fa'din " kai ya...ba wani abin ji na jin da'di cikin labarin mu Hafsat, sai dai tarin abin haushi da takaici". Lumshe idanu Hafsat tayi ta kuma bu'desu nan take inda ta sau'ke su akan fuskar Noor sannan tace " duk da haka zanso inji ni dai...... babu mamaki kece kike ganin sa matsayin abin haushi da takaicin, 'kila ni bazan ga hakan ba". Murmushi tayi mai ciwo a zuci..but sosai ya 'kawata mata fuskar ta duk da kuwa kallo 'daya zakayi mata kasan cewa na 'karfin hali ne...a hankali cikin sanyin murya ta sau'ke ajiyan zuciya tare da fa'din. " hmm...karki damu Hafsat zakiji labarina insha Allahu..... 'Dan yamutsa fuska ta sakeyi sannan ta cigaba da fa'din " amma inajin cikina na min zafi yanzun ban san....." Tun ma kafin ta kai 'karshen maganar Hafsat tayi saurin mi'kewa taje ga flask 'din da Nurse ta shigo dashi 'dazu ta ha'da mata tea mai kyau ta kawo mata. Duk abinda takeyi Noor bata ko bi ta kanta ba illah tsurawa inda Jas ke kwance kawai da tayi idanu, tana matu'kar tausayin Baby sosai..a inda take 'din sai ya kasance tana fuskantar fuskar Jasmine 'din ne, gani tayi yarinyar tayi fayau sosai, hasken ta ya 'karu fiye dana asali. Kuka take jinyi a duk lokacin da ta kalli Jasmine ta tuno mummunan 'kaddarar da ya hau kanta, sosai abin yake ta6a mata zuciya.....amma sai take daurewa take bawa kanta 'karfin gwiwa da ya'kinin Allah zai yi mata jagora wajen kulawa da ragowar rayuwar Jas 'din har 'karshen rayuwar su. Dawowa Hafsat tayi inda take zaune gami da dafa 'kafa'dun ta...Noor sai ta rintse idanu a hankali, 'dan guntun hawayen da ya cika cikin idanun ta suka gangaro sai tayi saurin share su. 'Dagowa tayi ta kalli Hafsat 'din yayin da ta 'dago Cup 'din tea 'din ta mi'ka mata ba tare da ta furta komai ba illah yanayin fuskar ta da juya zuwa yanayi na tsantsan tausayi. Kar6a Noor tayi ba tare da 6ata lokaci ba ta kur6a, tana jin yanda 'dumin Tea 'din ke ratsa mata ciki kasancewar babu komai acikin nata tun safe...cigaba tayi da kur6an tea 'din yayin da zafin da cikin keyi yake 'kara yawaita mata, duk da haka kuwa bata fasa sha ba dan tasan ba komai ya jawo hakan ba face tsantsan yunwa.... ka'dan-ka'dan take sha har ta shanye rabin sa sannan ta ajiye cup 'din a gefen ta. Babu wanda ya sake magana acikin su, shiru wurin ya 'dauka kusan na tsawon mintina goma, kowa da abinda yake sa'kawa cikin ransa, wanda cikin 'yan mintinan Noor ta danne zafin da take jin cikin nata na mata duk da kuwa yaso yafi 'karfin dauriyar tata amma sam bata nuna haian ba, kafin cikan mintina goman kuwa har ya 'dan sarara. Ganin yanda Hafsat ta tsura mata idanu take kallon tane ya sanya ta tunowa da abinda Hafsat ke zaman jira daga gareta...wato labarin rayuwar ta. Noor sama ta 'daga kanta gami da rintse idanun ta a hankali wasu siraran hawaye masu sanyi suka sake sau'ko mata. Bata sharesu ba wannan karon sai ta barsu suka cigaba da sau'ka a hankali. Hafsat kuwa ita kawai ta zubawa idanu take kallo gami da sauraron jin labarin Hudah daga bakin ta....amma ganin kukan da take yi sai itama taji wani iri jiki da zuciyar ta, gani take yi kamar Noor bata son tunowa da rayuwar ta na baya ne, sai take ganin tamkar takura mata tayi akan hakan. Ajiyan numfashi Noor ta sau'ke sannan ta sau'kar da kanta gami da goge hawayen da ya gangaro mata....wanda tana cikin hakan ta tsinkayi muryar Hafsat na fa'din " idan da takura Huda ki bari sai wani lokacin babu damuwa ai muna tare....". Murmushin gefen baki na 'karfin hali Noor tayi mata batare da ta bata amsar wancen tambayar ba taci gaba da fa'din......... ***** Asalin suna na Nurul Hudah, iyayenmu mu biyar suka haifa, Yah Usman shine babba sai Addah Maryam, sauda, Amina (Nanne) sai ni autar mu da mahaifina ya sanya min suna *Nurul Hudah* . Na taso cikin gatan Ummah na da Babana dan su ka'dai na bu'di idanu na ganni tare da su, cuz tun kafin nayi wayo aka aurar da yayuna mata biyu, Yah Usman kuwa ba zama yake yi sosai damu ba, shi ya kan ziyarce mu ne lokaci zuwa lokaci saboda yanayin sana'ar sa, daga ni sai yayata Amina da nake bi mata, haka muka taso gaban iyayen mu cikin so da 'kaunar juna. Mahaifina asalin manomi ne tun a wancen zamanin, bashi da wata sana'ar da ta wuce noma, kuma Alhamdulillah ba laifi dan a hakan muke lalla6a rayuwar mu cikin rufin asirin Allah, bamu fiye neman abu mun rasa ba. Da yawan mutane kan 'kira shi da Malam Mamman Jaji...mun kasance asalin fulani ne na garin bauchi, mahaifiyata 'yar asalin 'karamar hukumar Darazo ne yayin da mahaifina ya kasance haifaffen garin Shuwarin.....rabon aure ne kawai ya ha'da mahaifana lokacin da wata tafiya ta kai shi garin Darazo har Allah ya 'kaddara auren su. Sana'ar Ummah ta shine kunu da suyan waina kullum safiya a 'kofar gidan mu....wanda ya kasance nice ke taimaka mata koda wani lokaci idan mun gama komai sannan sai inje inyi shirin makaranta ta shiyasa mafi yawan lokuta na kasance cikin lattin zuwa makaranta kusan mafi yawa daga cikin 'dalibai na riga ni isa makarantar. Sam Ummah bata saka Amina Nanne cikin sabgar sana'ar ta harda ma ayyukan gida gaba 'daya, kasancewar bata da isashshen lafiya kamar ni. Shiyasa Ummah bata fiya matsa mata akan komai ba sai dai ni duk da kuwa baya nake da ita. Duk wani abinda ya kamata ace Nanne ce ke yi matsayin ta na wacce take sama dani to ni ke yinsa. Hatta da wankin kayan mu Ummah da kanta ke mana da kanta, wani lokaci kuma ina taya ta da 'dauraya har mu kammala....tun tasowata ban tashi da 'kiyuya ko son jiki ba. Na kan birge Baban mu a duk lokacin lokacin da yaga na bada himma ina ayyukan gida tun kafin shekaruna su suyi 'kwari...wanda har hakan ke sanya shi yawaita sa min albarka cikin matu'kar jinda'di. Wainar Ummah ta yayi farin jini ba laifi domin da yawan mutane kanzo wurin ta dan ha'da abin karin su yayin da wasu ke ci a wurin batare da sun yi dakon sa zuwa wani wurin ba. Akwai wa'danda har booking suke yi tun kafin ayi.....yayin da wasu ke zuwa su jjira har layi ya iso kansu. Gurbin wainar Ummah ta baya ta6a rabo da masu siya har sai in ta kammala gaba 'daya. Alhaji Baba ya kasance 'daya daga cikin masu siyan wainara Ummah ta, kuma babban abokin Baban mu ne, mafi yawan lokuta tare zaka gansu indai har babu wani uzuri dake gaban 'dayan su. Ya kan siyi wainar Ummah ta da da 'dan yawa dan kullum yakan sawa ayi masa sadaka dashi sannan akai masa wani gida. Tun ban da wayo nike zuwa gidan Alhaji Baba har na fara wayo kaina, domin kusan kullun sai ya siya an kuma kai masa gar gida. Mutum ne shi mai matu'kar kamala da sakin fuska gami halin girma, ga faram-faram da jama'ah bashi da mugun hali sam. Shi na fara sabawa da shi kafin kowa cikin gidan sa, domin duk ranar da muka ha'du na kan zauna da shi muyi ta hira abin mu shima baya gajiya da biyewa yarinta ta. Abu 'daya dake kulle min kai game da shi shine yanayin rayuwar su...sam ba kamar yanda mu muke rayuwa bane, sosai tsarin rayuwar mu ta bambanta da su. Yanayin sa shi kansa da yaran sa, yanayin gidan sa, tun daga harabar gidan, ciki da kuma abubuwan more rayuwa dake cikin gidan sosai suke bani mamaki, domin ni in ba agidan nasa ba ban ta6a ganin dayawa daga cikin su ba. Komai na gidan Alhaji Baba na musamman ne...idan kana cikin gidan sa har manta cikin garin da kake zakayi in ba ka fito ba, domin zakayi tsammani cewa cikin babban gari kake. Yanayin yanda yake dressing 'din sa ma daban ne ba irin na su Baban mu ba, domin shi Alhaji Baba kusan kullum zakaga kayan jikin sa sababbi ne masu kuma matu'kar birgewa. Na rasa dalilin da ya sanya su 'din komin daban domin hatta da wankin kayan su da engine suke yin sa, kasa ha'kuri nayi da hakan har naje na tambayi Ummah ta. Abakin naji naji ta'kaitaccen tarihin Alhaji Baba kamar haka......... *~One Luv masoya na~* 🥰❤😍 *......yau dai ga NOORUL ta dawo fatan ha'kurin naku bai kammala* *'karewa ba* 😉 *Daga yau insha Allahu zaku cigaba da samun update akai-akai koda read more 'daya ne ma* 🥴 *....agafarce ni pls.* *Kuyi manage da wannan kafin ku sake jina.* 👌🏻 😎😎😎 Deen 'dina na gaisuwa fa 🙋🤠 *Salmerh ce* 😍 [12/17/2019, 10:50 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *16* Kafin Ummah ta fara magana sai ga Nanne ma ta zo inda muke zaunen ni da Ummah, zama tayi a gefena tayi shiru itama kamar yadda taga nayin muka cigaba da sauraran Ummah a tare....domin zuwan Nanne bai sa Ummah ta taka birki daga fa'dar labarin da tayi niyyan bani ba........ ***** Alhaji Taheer Manga.....haifaffen cikin garin Azare ne na jihar Bauchi....wanda yanayin aiki ya kawo mahaifin sa mai suna Mukhtar garin mu inda anan yayi katari da samun matar aure Fatima wacee itama ta kasance matashiyar malama ce a makarantar da yake aiki bata ko yi rabin shekara da fara aikin ba......batare a wani 6ata lokaci ba suka dai-dai ta kansu, iyaye suka shiga maganar akayi bikin Mukhtar da Fatima cikin farin ciki da 'kaunar juna. Sunyi zama na tsawon shekaru wanda har ya kasance sun zama tamkar 'yan asalin garin ne, shima bai hanata fita aikin ta ba suka cigaba da fita abinsu atare har Allah ya azurta su da samun 'Ya'ya. ....Mahaifin Alhaji Baba bai ta6a samun matsala da kowa agarin ba, har yazo yayi dacen samun matsayin Headmaster na makarantar......ga shi kuma yana da kyakkyawar ala'ka da manyan cikin garin sosai suke girmama junan su. Wanda har wa'adin Allah ya kasance akansa bai sake samun wata haihuwar ba duk kuwa da yana son samun 'ya mace amma Allah bai nufe sa da samu ba..... ya rasu ya bar yaran sa maza guda biyu wato Taheer (Alhaji Baba) sai mai bi masa Ja'afar da yanzu haka yake zaune can garin Kaduna da iyalan sa. Lokacin da ua rasun shekarun Taheer goma shabiyu yayin da Ja'afar yake da shekara tara fa haihuwa. Tun bayan rasuwar sa Fatima taci gaba da kulawa da yaran da karatun su da tarbiyyar su bisa jagorancin mahallici. Bata sake tunanin sake yin wani auren ba duk da kuwa alokacin tana da 'yan 'karancin shekaru wanda hakan yasa mutane da da dama ne suka bu'kaci auren ta amma sam bata bawa kowa dama ba dole tasa kowa ya janye nasa 'kudurin Haka har yaran ta suka girma suka zama mutane, bata kuma koma can garin iyayen ta ba saboda tana ganin tamkar yaran nata da nan suka bu'di idanu so bata so ta canja musu salon rayuwa, kuma ko dan saboda nata aikin da take yi shiyasa ma kawai suka cigaba da zaman su nan. Suma yaran nata ba laifi suna 'ko'karin yin 'kananun sana'o'i basu zama haka nan....cikin rayuwar su babu abinda ya canza face kewar mahaifin su, karatun su ma sun cigaba da yi atare domin tsakanin su babu wani rata sosai shekaru uku ne zuwa hu'du kawai hakan yasa karatun su yake tafiya lokaci guda. Suna kammala secondary ta basu zauna ba suka zarce da karatu Taheer BUK yatafi yayin da Ja'afar yayi karatun sa a nan cikin garin Bauchi inda ya karanci Accounting, basu samu matsala da komai ba har suka kammala kasancewarsu yara masu bada himma haza'ka da kuma 'ko'karin karatu. Cikin sa'a kuwa suna kammala makarantar kowanen su yayi dace da samun aiki dai-dai da abinda ya karanta....inda Ja'afar yayi dacen samun aiki a banki cikin garin Bauchi, yayin da Taheer kuma ya samua gidan mai a Kano a matsayin 'kananun ma'aikata. Duk da hakan sam ba raina ko kuma yin girma kai ba, hannu bibbiyu ya rungumi aiki gami da godewa mahallicin sa. Samun aikin nasu ya matu'kar yi musu da'di domin kuwa suna gani cewa lokaci yayi da ya kamata mahaifiyar su ta huta.....ai kuwa gata sosai take samu daga dukkan 6angarorin biyu sai godiyan Allah ita kanta sai da tasan cewa ehh lallai haihuwa na da rana. Sai dai kawai tayi ta binsu da addu'ar samun sa'a da kuma dacewa. Taheer ne yaso ya 'dauke ta ma kwata-kwata daga wannan garin amma ta nuna masa ba komai ya barta a nan 'din kawai, kuma ma me yasa zata bishi bacin ba iyali ne dashi ba sai ta 'karasa da fa'din ka bari idan ka ajiye iyali sai ij bika ko kuwa?" Shiru kawai yayi mata dan sam shi ba haka yaso ba amma dolen sa ya ha' kura tunda ta nuna bata ra'ayi ai shikenan. Ba su shekara da fara aikin ba Zmz sai Allah ya kar6i ran mahaifiyar ta su bayan jinya (Allahu Akbar) mutum mai rai kenan.....sunci kuka sunyi takaici domin sunso mahaifiyar su ta fara cin moriyar su kafin kafin kowa yaci, amma hakan bai yiyuba Allah ya nuna ikonsa dole suka ha'kura suka yi tawakkali, domin *hukuncin Allah* ba a ja da shi...mutuwa kuma dolen kowa ce.. Bayan sun gama kar6ar gaisuwa sai duk suka koma bakin aikin su zuciyoyin su cike da alhaini. Cikin sa'a kuwa Taheer bai wani jima da fara aikin ba ya samu 'karin girma...sun yi matu'kar farin ciki sosai, bayan hakan ne Ja'afar ya shawarce shi da cewa gara ya ajiye iyali saboda halin rayuwa kuma ma ko don cika sunnar ma'aiki (SAW).....Ya 'karashe da fa'din " kaga ni tuntuni fa kai nake jira in ba dan haka ba da tuni anyi nawa". Washe baki Taheer yayi yana kallon sa yace" haba malam.... kace kenan dama hanya kake so in baka"! "Ashe ka gane manufata". Cewar Ja'afar yana dariyar shima. Sai Taheer yace masa " kar ka damu to....ba sai ka jirani ba.....inaga ai za'a iya ha'dawa duka rana 'daya ko?" " Gud idea...."! Ja'afar ya furta yana murmushi sannan ya 'karasa da fa'din " gaskiya shawarar ka tayi 'dan uwa, aini da banyi tunanin hakan ba sam". " Hmm " kawai Taheer yace dan shi sam ba mai son yawan hayaniya bane, ta inda bambancin su yake kenan da 'kanin nasa. Taheer bai yi 'kasa a gwiwa ba yaje ya tuntu6i wacce suke 'dan soyayya da ita..har yake tunanin inda hali ita zai aura.....wata matashiyar yarinya ce 'yar 'kabilar Igbo da bazata gaza 23yrs ba, mazauna garin Kano ne su....ama Kano aka haife su....duba da karamci da mutunci gami da ha'ku'ri irin na mabiya addinin muslunci da kuma mazauna garin Kanon ya sanya mahaifin su kar6an muslunci tun kafin yaran sa suyi wayo...anan matar sa ta nuna 'kin amincewar ta da wannan batun inda batare da 6ata wani lokaci ba ta tattara ta koma mahaifar ta wato Imo State. Shi kuwa ya hanata tafiya da kowa cikin sa, dolen ta ta tafi ta tafi ta barshi da yaran nata guda uku, biyu maza da mace 'daya wacce mahaifin ta ya za6a mata suna Aishatu yayin da 'kannan ta maza biyun suka ci suna Aliyu da Umar, shikuma uban ya za6i sunan fiyayyen halitta annabi Muhammad (SAW) yace wannan ne yayi masa. Haka suka cigaba da rayuwar su cikin haske da alfarmar addinin muslunci har yaran sa suka yi wayo, babu wanda ya 'kara ziyar tan su daga 6angaren dangin uwa har ma da na mahaifin nasu, hatta ita kanta mahaifiyar tasu ma bata sake waiwayan su ba haka shima mahaifin su bai yi gigin taka 'kafar sa zuwa can garin nasu ba domin yasan bazata 'kare musu da da'di ba. Tunda ya kar6i addinin muslunci ya ri'ke sa da hannu bibbiyu domin koda wasa baya sakaci da islamiyar yaran sa sosai yake bada muhimmanci ga wannan 6angaren shi kansa ma neman ilimin yake bai zauna haka nan ba......shiyasa yaran nasa suka taso cikin tarbiya dai-dai gwargwado, amma bai yadda ya sake yin aure duk kuwa da malamai na nuna masa muhimmancin hakan amma sam ba bada himma ga hakan ba har girma ya kama shi. Aishatu tayi matu'kar farin ciki da jin cewa Taheer na so iyaye su shiga maganar su... dan kuwa ba 'karamin so take yi masa dama, shi 'din ne dai yake 'dan taka mata birki da irin salon sa na shariya da basarwa. Bata wani 6ata lokaci ba taje ta samu mahaifin ta da maganar take kuwa ya basu dama domin shima baya da burin da ya wuce yaga ya aurar da ita a lokacin.......cikin 'kan'kanin lokaci aka tsaida maganar auren su harda na Ja'afar ma. Bayan wata uku akayi bikin su kowa ya tare da matar sa. Tun daga nan kowa ya dasa gidan sa cikin so da kulawa da iyalin sa...kuma ba laifi suna zumuncin su dai-dai gwargwado duk da ma ba gari 'daya suke ba amma suna 'ko'karin kulawa da zumuncin dake tsakanin su. Taheer Kano yake da zama yayin da Ja'afar yake zama Azare da matar sa dan shi anan ya samu aikin nasa tun farko. Shekara na zagayowa Aishatu ta haifi 'dan ta namiji kyakkyawa da shi, yaro mai kyau da haiba sak Baban sa sai dai farin sa gaba 'daya na uwar sa ya kwaso har ma ya 'dan so ya zartata. Murna gurin wannan familyn ba'a cewa komai sai wanda ya gani...domin kuwa babu wanda bai yi farin cikin da samun wannan 'karuwar ba. Tun washe garin haihuwar Zainab matar Ja'afar ta zo shima 'din ba a barshi abaya ba domin kuwa ana gobe suna shima ya dira garin Kano dan asha shagalin suna dashi. Ranar suna yaro yaci sunan kakan sa wato mahaifin Aishatu.... *Muhammad Taheer*, matar 'kanin baban sa Ja'afar ne ta fara ambatan sa da suna *Mu'inuddeen* ( the helper of d religion).......tace da sunan zaa 'kira shi....sosai akayi shagalin suna cikin bawa Naira kashi...kowa ya nuna bajintar sa sosai abin ba'a cewa komai. Shi kansa mahaifin Aishatu da yaro yaci sunan sa ma ba'a barshi a baya ba wajen bada nasa manyan gudummuwan domin shima wani irin so yaji yake wa yaron na ban mamaki hakama Umar da Aliyu da suke ji tamkar su dawo zama tare da babyn. Yaro ya taso cikin so da 'kaunar duka dangin sa musamman ma Baban sa Ja'afar da har yanzu Allah bai ba shi haihuwa ba, matar sa ko 6atan wata bata ta6a yi ba, amma bai wani 'daga hankalin sa da hakan ba domin ya san Allah shike bada haihuwa a duk lokacin da yaso haka kuma saiga wanda yaso. Matar san ce dai take 'dan damun sa wasu lokutan amma ba laifi ya kan kwantar mata da hankali da nuna mata cewar hakan ya faru ne saboda buwayar mahallici kuma bawai dan bai san su ba a a sai dan kawai ya jarrabe su, ya kance da ita kuma ma dududu shekar su nawa da yin auren da har zata damu kanta ai komai yana da lokaci kuma hanzari ko rashin ha'kurin mu baya ta6a sawa mu samu abu face Allah ya so, mu ci gaba da addu'ah insha Allahu watarana ke ma zaki haihu". Idan ya fa'di mata hakan kuma Alhamdulillah tana fahimtar sa. ***** Allah cikin ikon sa haihuwar *Mu'inuddeen* sai ya zowa mahaifin sa da *wani haske*...domin sai ya ringa samun 'karin girma a hankali wurin aiki ga kuma hanyoyi da suka 'kara bu'de masa na ban mamaki, inda cikin natsuwa tattalin arzi'kin sa ya ringa bun'kasa yana 'kara girma. Kafin shekaru uku kuwa har ya zama wani abu da shi kansa ya san cewa ya shiga sahun wasu daban masu fa'da aji ko wani bai fa'da shi 'din ya san hakan. Manyan store ya bu'de kusan guda uku ya zuba kaya inda ya wakilta masu kula masa da shi cikin ri'kon amana da gaskiya. Bashi da matsalar komai a yanzun illah ya kula da tarbiyar iyalan sa da hakkokin su. A gidan Alhaji Muhammad Ugoh Chukwu (mahaifin matar sa) ya bar Mu'een lokacin da zasu tafi aikin hajji da matar sa...wanda hakan ya 'kara sanya 'ka'k'karfar so da sha'kuwa tsakanin Mu'een da kawunan nasa. Kafin su dawo kuwa Alhaji Muhammad U.C ya bada kyautar wani babban plot 'din sa dake can Zaria road har ma ya musanya sunan an 'daura na Mu'een. Koda suka dawo kuwa sunyi matu'kar farin ciki da jin hakan baran ma Aishatu da take 'kara jin da'din yanda mahaifin ta ke so da kula da jinin ta. Taheer ne dai ya 'dan so yayi 'korafi amma Alhajin ya dakatar da shi da fa'din " Kyautar sa ga mai sunan sa ne shi bai ce ya sa baki ba". Yayi maganar ne cikin karkatacciyar hausar sa da har yau bata 'dauki hanya ba da kuma murmushi kan fuskar sa. Taheer baya so yaja da maganar Alhajin amma sai yake ganin kamar ai kyautar tayi yawa sosai Mu'een 'din ma nawa yake da har zaa yi masa irin wannan kyautar amma dole haka ya ha'kura da maganar ganin 'korafin sa bai samu shiga ba, domin Alhajin ba sauraran sa zai yi ba ga dukkan alamu. Shi haka tsarin sa baya son ayi masa godiya sam koda yayima kyauta baya son yawan godiya shiyasa wa'danda suka san halin sa idan hakan ya faru kawai sai su bishi da addu'o'i cikin ransu. Shima 'din yafi gane hakan....dan haka shima Taheer sai ya ja bakin sa yayi shiru gami da jinjinawa karamci irin na mutumin tamkar ba 'kabila ba haka yake rayuwar sa. ***** Alhaji da Mu'een yaji 'kannan mahaifiyar sa na kiran Baban sa da shi ne ya sanya shima ya 'kara Alhaji kan sunan da yake kiran sa da shi wato daga Baba zuwa Alhaji Baba. Babu kuwa wanda ya hana sa har hakan ya zauna bakin sa abu kadan sai yace Alhaji Baba...Alhaji Baba. Kwanci tashi rayuwa babu wuya.... har Mu'een ya shekara biyar da haihuwa, yaro kakkykyawa da shi abin so da birgewa.. yayin da yana 'kara girma kywaun sa na 'kara yawai ta.....sai dai kuma har a lokacin ba'a sanya shi makaranta ba haka rayuwar sa ta kasance yau yana gun iyayen sa gobe yana gidan kakan sa, sosai yake samun *gatan kowa* daga cikin su, har da ma Uncle 'din sa dake Azare shima ba'a barshi abaya ba. Wani zuwa da Ja'afar yayi ne ya kai musu ziyara sai ya dinga masifar me yasa ba'a sanya shi makaranta ba, yanda yake yi 'din idan kun ganshi har zaku zaci cewa ko shine babba, sosai ya nuna musu rashin dacewar hakan, su kansu ma sunsan ba dai-dai suka yi ba kuma bama su da dalilin 'kin sashi a makarantar amma kawai hakan bai zo kansu bane shiyasa, zuwan Ja'afar 'din ne sai ya fargar dasu, musamman da yace idan ba su so shi zai 'dauke sa ya tafi dashi. Kowa bai so yayi missing yaron dan haka cikin satin suka 'dauri aniyar kaishi makaranta. Ashe ma basu sani ba Kakan sa ya gama masa komai, shima daya gaji da jiran ganin sun sanya shi yaga shiru shine kawai ya nema masa makarantar da ta dace da kansa batare da ya shawarci kowa daga cikin su ba. Monday da suke tunanin zasu fara yi masa cuku-cukun makarantar, aranar da sassafe Alhaji ya aiko driver aka 'dauke shi sai dawo musu yayi da uniform a jikin sa yazama d'an makaranta. Tun daga ranar Mu'een yaci gaba da zuwa makarantar, wata tsadaddiya da kakan sa ya sanya shi. Sosai suka ji da'din hakan a lokacin.....Aishatu ce da kanta ta 'kira mahaifin nata tayi masa godiya amma bai ma tankata ba kawai ya kashe wayar. Bayan ya gama da layin Mu' een sai hankalin sa ya dawo kan processing wa yaran sa tasu makarantar domin suk sun gama secondary school yana so su cigaba. A Canada ya samar musu dukkan su Umar da Aliyu.. inda suka tafi cikin matu'kar farin ciki suka bar mahaifin nasu da kewa sosai domin gida yayi shiru babu kowa, shima 'din kawai sai ya wuce South Africa inda ya tafi domin gudanar da harkokin *Kasuwancin sa* na can. Bai dawo ba sai da ya tabbatar su Aliyu zasu dawo hutu kafin nan shima ya dawo, su kam ma ba haka suka so ba domin can suka so zuwa su same shi amma yace kawai su ha'du agida domin shima akwai abinda zai kawo sa. Ranar da suka dawo Taheer, Mu'een da mahaifiyar sa duk a gidan suka yini sai yamma kafin suka koma gidan su....inda anan Umar ya ce abar musu shi mana su 'dan kara gaisuwa, take Aishatu tace a'a sai dai ya dawo gobe domin basu zo da kayan sa ba, kuma ma kar ya dame su daga sau'kan su gara idan sun 'dan huta sai akawo shi. Da haka suka yi sallama suka koma gidan su. Kwatsam tashin farko Taheer ya tsinci kansa a matsayin Assistant Manager na gidan man Oando dake nan cikin garin na Kano. Wannan abin shi yafi komai yi musu da'di a rayuwar su baya ga haihuwar Mu'een, domin kuwa hakan shine ya kasance silar bun'kasuwan arzi'kin su suma suka zama abin kwatance. Kunsan abu idan Allah ya dafa maka toh shikenan baka da matsalar komai domin babu wanda ya isa ya sha gaban ka face Allah ya kautar maka da shi. Mahaifin Aishatu ne yayi masa hanyar hakan batare da sun sani ba dukkan su.....da yake mahaifin nata babban mutun ne mai fada aji....sai dai kuma bayan hakan bai yi wani tsawon rai ba ya koma ga mahallicin sa da dukkan sauran yaran sa biyu da suka zo hutu wato Aliyu da Umar. Hatsarin mota suka yi akan hanyar su ta zuwa duba wani plot da ya siya zai kaisu ya nuna musu sai hakan bai faru ba, domin kuwa basu kaiga zuwa wurin filin ba ma motar su ta kife da su inda nan take biyu suka rasu, Umar kuwa a asbiti ya 'karasa da kalmar shahada abakin sa. Wannan mutuwar itace ta kasance babban tashin hankalin su domin Aishatu gaba 'daya kasa nutsuwa tayi.... banda suma babu abinda take yi....shi kansa Taheer yaji mutuwar sosai wanda sai bayan mutuwar ne ma ya samu labarin halaccin da dattijo sirikin nasa yayi masa na canza masa wurin aiki tare da sawa a 'kara masa babban matsayi batare da ya sani ba. Banda addu'ah babu abinda yake bin sa da shi domin dattijon iyamurin mutum ne mai mutu'kar dattako da halin girma sai fatan Allah yayi wa Alhaji Muhammad Ugoh Chukwu da iyalan sa rahama Ameen . Hatta Mu'een da yake 'dan shekaru shida ma a lokacin sai da ya fahimci gidan nasu ba dai-dai yake ba, domin shima sosai ya rasa kulawar uwar sa, duk wani kulawar da ta dace ya samu daga gareta to baya samun sa. Mahaifin sa ne ke 'ko'karin yi masa wa'dan su hidimomin da kansa, ga kuma aikin sa da yake yi, ganin hakan bazai fishshe su bane ya sanya shi nemo wata da zata ringa kulawa da yaron da kuma yi musu abinci. Hutu ya bawa Aishatu sosai cuz ya san ko shine irin wannan mutuwar ta riske shi dole sai yaji babu da'di balle ita da take matsayin mace mai rauni. ***** Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya ba yabo ba fallasa, har akayi kwana arba'in da rasuwar, kafin hakan kuwa idan kun ga yanda Aishatu ta rame ta lalace abin har zai bawa mutun tsoro, sosai ta zabge ta fita hayyacin ta...ga uban low BP da ya sako ta agaba tun da 'kuruciyar ta...tana nan yau lafiya gobe babu. Bayan arba'in ne lawyern mahaifin ta yazo da niyyar ya dan'ka mata dukkanin takaddun k'adarorin mahaifin ta harda ma wa'danda bata sani ba....bai wani dame ta ba balle ya d'aga mata hankali domin kyakkyawan nutsuwan ta ma lawyern bai samu ba, Taheer ne ya jagoranci lamarin inda ya kar6a mata wasu yayin da ya dan'ka wasu a hannun lawyern akan ya cigaba da kula mata dasu. Abubuwa da yawa na mahaifin ta da basu san da shi ba, anan Kano harda ma can South Africa cikin su kuwa babu wanda ya bibiyi lamarin duk kuwa da cewa sun san yana da cibiyar kasuwanci acan, abinda yake gaban su ma ka'dai ya ishe su, domin shi Taheer a yanzu bashi da wani burin da ya wuce yaga matarsa ta warware amma abin ya faskara, tsawon wata uku da rasuwar amma ta kasa ha'kuri da rashin su. Hatta Mu'een sai da ta koya masa tagumi da rashin son magana, cuz idan yaga tayi shiru tana tunani shima sai yaje gefen ta ya zauna yayi tagumi yana kallon ta, koda taga hakan bata tanka shi, idan kuwa yaga tana hawaye shima kukan yake yi....idan ta ga hakane sai ta rungumo shi zuwa jikin ta su cigaba da kukan tare. Abin sosai yake ta6a masa zuciya domin ba 'karamin damun sa arai yake yi ba, amma ya rasa yadda zai yi, kullum yana ko'karin ganin ya nuna mata muhimmancin yadda da kaddara matsayin ta na musulma amma a banza kamar bada ita yake ba, ganin kamar yanayin yaron sa na son canza salo irin nata ne ya sanya shi dogon nazari, domin kuwa Mu'een surutaccen yaro ne amma tunda ya fara ganin mahaifiyar sa na yawan kuka shima ya zama shiru-shirun 'karfi da yaji, domin kuwa wani lokacin har mantawa zakayi cewa cikin gidan akwai yaro 'karami...tun farkon rasuwar yayi nacin tambayar su Granny, Uncle Umar da Uncle Aliyu yayi ta rigimar akai sa wurin su kullum amma rashin samun gamsasshiyar amsa daga bakin iyayen nasa ne ya sanya shi yau da gobe ya ha'kura shima duk kuwa da cewar ba wai ya manta dasu bane....tafiyar da ake ce masa sunyi ne ya sanya shi koma cewa " yaushe zasu dawo?". Hakan ma ba amsa mai kyau yake samu ba amma dai duk da haka baya gajiya da yin tambayar. Ita Aishatu idan ya tambaye ta sai dai tayi ta masa kuka, a wurin mahaifin sa ka'dai yake samun amsar " baza su dawo ba Mu'een mune zamuje mu tarar da su" Take sai yace " To Alhaji Baba mu 'din yaushe zamuje da Ammee na?" Idan yaron ya fa'di haka sai kawai Taheer yayi murmushi ya shafa kansa yace koda wani lokaci Babana, tafiyar ba'a mata shiri kaji". Sai ya 'dage kansa da nufin yaji. Sosai jikin Taheer yake yin sanyi aduk lokacin da sukayi irin haka da Mu'een. A hankali ma sai Allah ya taimake shi yaron ya rage tambayar sa sai dai kuma shiru-shirun nasa sam baya jin da'din sa. Hutu ya shirya musu zuwa a Dubai... wai ko zasu d'an nutsu idan sun kauce duk kuwa da cewa ya kasa rabata da zubda hawaye da tunani amma sosai yake iya matu'kar 'ko'karin sa akan hakan. Zuwan su Dubai ne ya sanya ta 'dan warware domin kuwa sam baya bari su zauna wuri guda kullum fita suke yi suna yawo suna zaga gari har na tsawon sati biyu, daga nan ne suka wuce Umrah....inda anan Taheer ya dinga kaiwa kukan sa wurin mahallici kan lamarin matar tasa, bai gushe ba yana addu'ah cikin kowacce sallahr sa har suka gama Umrah suka dawo gida. Alhamdulillah babu laifi, domin kuwa yanzun abubuwan nata da sau'ki ta 'dan rage yawan tunanin..sai dai Mu'een 'din sa ne har yanzu bai dawo dai-dai ba, zama shiru ya riga ya zama halayyar sa. *Kai ni 'din nan kamar azane ni ko* 🥴 *Gaskiya bana kyautawa, amma a 'kara ha'kuri dai plz na kasa settling ne wallahi* _Comment_ _Vote_ _Share_ ~Taku mai 'kaunar ku har kullum~ 👇🏼 *Salmerh ce*😍 [12/20/2019, 1:13 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 👏🏻~JUMMA'AT MUBARAKH TO ALL MUSLIM UMMAH~ 👏🏻 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *17* Amma duk da haka sosai yake yiwa mahallici godiya domin sai yanzu ya gama fahimtar cewa farin cikin mace cikin gida shine farin cikin kowa a gidan...cuz lokacin da Ammee ke cikin wancan yanayin kwata-kwata shi kansa baya samun matsuwar kansa akoda wani lokaci balle kuma 'dan yaro Mu'een. Yanzun kuwa da abubuwa suka fara dai-daita banda godewa Allah babu abinda yakeyi....6angaren Mu'een 'din bai dame shi sosai ba domin kuwa yasan shi yaro ne har yanzun akwai yiyuwar canzawan sa idan yana 'kara girma in kuma Allah yayi nufin hakan shiyasa kawai ya 'kyale sa. ***** Bayan sati uku da dawowar su daga Dubai...... a ranar wata Monday lokacin Mu'een na makaranta shi kuma Alhaji ya fita, kwance take kan kujera tana nazari kan rayuwa, sosai tayi nisa cikin tunanin marigayan dangin ta mahaifin ta, har anata danna bell na 'kofa amma sam bataji ba, sai da 'karan ya yawaita ne kafin tayi firgigi ta tashi zaune. Sam sai taji bata son mi'kewan ma balle bu'de 'kofar amma haka ta daure ta tashi ta isa gurin 'kofan ta bu'de a hankali. Baya ta 'dan matsa ganin wanda ke tsaye daga wajen, cikin murmushin ya'ke tace dashi" welcome Barrister ". Bai furta mata amsar komai ba sai ya mayar mata da martanin murmushi madadin amsar maganar ta. Hanya ta bashi domin ya shigo gami da yi masa iso . Ta'aziya ya 'kara yi mata harda 'dan guntuwar nasihar sa a 'dan 'kagauce ganin 'yar ramar dake tare da ita, wanda har yasa 'dan guntun hawayen da suka ma'kale mata suka gangaro. Amma sai tayi saurin sharesu saboda ba taso a kullum ta kasance cikin kuka....takaddu sun kai guda tara Barrister ya mi'ko mata gami da fa'din ta saka hannu akai akwai abinda za'a yi da shi ne kuma urgent ake bu'katar hakan. Yanda yayi mata maganar sai ya sanya ta ba tare da tayi tunanin komai ba ta 'kar6i takaddun da biron da ya bata ta bisu 'daya bayan 'daya duk tayi signing a 'kasan su. Yayin da Barrister ya tsura mata idanun sa wanda suke 'kulu-'kulu kamar zai cinye hannun ta yana gani da tabbatar wa idanun sa abinda ke shirin faruwa, be ta6a zaton abin zai yi masa sau'ki har haka ba. 'Kayataccen murmuhin da ya bayyana kan fuskar sa bayan 'dage hannun ta daga kan takaddar har ya 'danso ya 'daure mata kai amma sai bata sa a kaba saboda tunowa da tayi cewa yace ana da bu'kata ne urgent, bata damu ba duk da kuwa bai sanar da ita abinda ke faruwa ba, sai kawai tace dashi..." idan abin damuwa ne ko in 'kira Taheer yazo 'kila ya taimaka shima ko". Da sauri Barrister yace " ah no karki damu ba sai yazo ba, zamuyi waya da shi kawai ba komai...". Yana maganar ne yana tattara kan takaddun waje guda bayan hakan bai ko 'kara second biyar ba ya zuba su cikin jakar da yazo da ita yayi mata sallama ya 'kara gaba abinsa. Koda Taheer ya dawo sai ta sanar dashi yanda sukayi da Barrister 'din da safe shi kam yaso yaji ko menene amma sai itama tace bata san me ya faru ba, sa hannun ta ka'dai ya bu'kata. Bata tashi sanin babban kuskuren da ta aikata ba har se da aka shafe kusan watanni uku wayar Barrister bata tafiya, domin tun a ranar da Taheer ya dawo tayi masa bayani sai ya dinga gwada 'kiran sa da zummar yaji abinda ke faruwa amma wayar sa tun ranar ta daina shiga. Wasa suka 'dauki abin dan haka suka cigaba da bibiyan layin nasa batare da sun tuntu6i office 'dinsa ko mazaunin sa ba, amma gaba 'daya abin yaci tura har aka shafe 3month da 'doriya basu sake ji daga garesa ba. Abin haushin ma shine ko cikakken ainahin sunan sa basu sani ba balle akaiga zancen binciken gidan sa.....duk da haka Taheer yaso yabibiyi lamarin bayan ya fahimci abinda ya faru ko dan 'kwato hakkin matar sa ma amma Ammee ta hanasa domin tasan yin hakan dai-dai yake da sanya rayuwar sa cikin garari, irin wannan badakalar shiri babba take bu'kata domin in kayi wasa ma har sai rai yabi, ita kuwa shi ka'dai gareta a yanzun, shine ka'dai ya rage mata sai Allahn ta da 'dan ta kuma bata son ta rasa shi....dan haka sai tace dashi " ka barshi yaje kawai idan da niyya yayi hakan ai Allah yana sane kuma yana ganin komai....shi kansa yasan wani bai cin hakkin wani ya zauna lafiya dole sai yaga iyakar sa, balle shi da ya ha'da har da cin amana, ba'karamin yadda Daddy yayi dashi ba amma kalli halin 'dan Adam...... dan haka ka 'kyale shi yaje kawai Tahir idan da gangan yayi Allah zai mana maganin sa.....idan kuwa ba da gangan bane ni na yafe masa duniya lahira kuma har cikin zuciya ta, bashi da haufi akan hakan, da'din abin ma shine idan babu nan to akwai can...inda bawa bai isa ya 6oyewa kowa ba kamar yadda bai isa ya 6oye laifukan sa ba...to me yasa zamu 'daga hankalin mu? wanda suka rage a hannuna ma Allah yasa musu albarka...let him be ai duniya ce girma gareta......"! Sosai ya gamsu da bayanin ta kuma yayi na'am da shi amma hakan bai hana shi bincike kan Barristern ba, har sai da ya gano dukkan bayanan dake tattare da shi har inda ya koma a halin yanzun. Tsananin mamaki yayi sosai da jin hakan domin a zahiri zaka fahimci manufar sa ta guduwa ya bar garin Kano adai-dai wannan lokacin. Bai yi 'kasa a gwiwa ba gurin burin son zaman sirri da Barristern dan yana so ya nuna masa muhimmancin gujewa haramun da kuma illar cin dukiyar maraya cin amana da kuma illar biyewa zuciya......shi ka'dai ya shirya hakan cikin ransa batare da kowa ya sani ba, amma sai ya bari a kan cewa sai ya samu lokaci tukunna zaije masa da kansa su tattauna. Kwatsam kafin faruwar hakan sai yaci karo da wani mummunan tashin hankalin da ya kusan zautar dashi. Wai shi ake tuhuma da satan fuel na kusan 80million....meze yi dashi? Abinda ya tambayi kansa kenan da yaji batun. Sosai abin ya ta6a ransa bai ta6a tunanin irin wannan zargin zai hau kansa ba kuma shi ka'dai ake tuhuma batare da kowa ba, abin ya 'daure masa kai sosai. Ita kanta Aishatu sai da ta kusan sumewa dan tashin hankali, kuka take yi har tana 'ko'karin kauce hanya cikin maganganun ta dan ganin kamar iftila'in na neman sufi 'karfin su ma, basu gama da wancan ba ga wannan kuma, gaba 'daya tashin hankalin ta sai ya ninka na 6acewan Barrister ta rasa yadda zatayi da ranta. Duk ya fita shiga damuwa amma hakan bai hana shi kwantar mata da hankali gami da nasiha akan hakan ba. Rana tsaka tana ji tana gani aka zo har cikin gidan sa gaban iyalan sa aka sanya masa Handcuff sannan aka tusa 'keyar sa zuwa ofishin 'yan sanda duk da kuka magiya da ro'kon da take yi musu bai hanasu tafiya da shi ba. Mafita ko guda 'daya be iya yazo kanta ba banda aikin kuka da takeyi babu komai, domin ko sau 'daya basu ta6a bari ta gana da shi ba tsaro sosai akayi masa wanda hakan ya sanya ta shiga cikin mummunan yanayi. Kullum yanda taje haka take dawowa gaba 'daya ta fita hayyacin ta, sarai tasan Taheer bai ci ku'din kowa ba domin baya yin abu batare da shawarar iyalan sa ba kuma ma ita bataga a inda yaci ku'di har Naira Million tamanin a gidan ba....taya za'ace shi ya 'dauka. Har akaci sati guda Taheer na kulle ko bailing 'din sa bata iya tayi ba sun ma hana ta bailing nasa gaba 'daya. Ran kwana na tara ne Ja'afar ya 'kirata domin baiji daga 'dan uwan nasa a kaf 'din satin ba, sanadin hakane ya 'kira ta inda anan cikin kuka ta samu tayi masa bayanin abinda ke faruwa. A rikice shima yake mata tambayar " kina nufin sati gudan Taheer na kulle amma ban sani ba?...haba dan Allah me yasa baki 'kira ni tuntuni kin sanar dani ba?" Kuka taci gaba da yi batare da ta bashi amsar tambayar sa ba dan haka sai ya kashe wayar. Aranar ko kwana beyi ba ya dira garin kano rana tsaka dayake Allah ya taimake shi tun safiya ya 'kira ta bai 'kira a 'kurarren lokaci ba. Sau'kar sa keda wuya kuwa ya dira gidan a hargitse...inda yana shiga parlourn ya samu Mu'een zaune cikin damuwa, ga ta ita kuma zaune ta kwantar da kant jikin kujera a hakan bacci ya 'dauke ta wanda tashin farko zaka fahimci cewa shima baccin ba'a nutse take yinsa ba, ba itan ba ba yaron ba hatta gidan gaba 'daya idan ka kalla zaka san cewa masu shi na cikin tashin hankali kowa yayi jugum har zaka rasa gane waye cikin su yafi shiga damuwa...domin shi ma yaron ya damu da rashin mahaifin nasa cuz ba haka suka saba ba ya saba ganin sa kullun agida amma yanzu babu shi kuma basa waya dashi ko Landline yaji tana 'kara ya kanje da sauri ya jira zuwan Amminsa a wurin da tunanin ko mahaifin sa ne, in kuwa tazo ta 'dauki 'kiran sai ya bita da idanu gami da zuba kunnuwa ko zaiji muryar mahaifin sa amma baya jin hakan. Ga yawan kukan Ammin sa dake 'kara 'daga masa hankali shima sau da dama tayata yake yi suyi ta kukan tare shiyasa duk suka fita hayyacin su. Makaranta kuwa itama babu labarin ta, domin tun ranar da aka kama Baban sa bai sake zuwa ba. Shiyasa duk suka zama wasu iri dasu gwanin tausayi, kallo 'daya zakayi musu ka fahimci yanayin da suke ciki. Mu'een na ganin Ja'afar a tsaye ya taso da sanyin jiki ya iso gaban shi, Ja'afar sai ya 'dago shi sama kafin yace wani abu ma Mu'een ya riga shi da fa'din " Uncle kaga Ammina kullum kuka takeyi kuma Alhaji Baba baya nan kullum bana ganin sa agida bansan inda yaje ba inaso in ganshi Uncle". Kwantar da kan Mu'een yayi kan kafa'dar sa gami da sau'ke ajiyan zuciya, sosai zuciyar sa ta karye da jin furucin yaron. Da kansa ya shiga ya watsa masa ruwa a extra room dake gidan dan ganin yana bu'katar hakan sannan ya fito da shi yace yaje ya 'dauko kayan sa ya sanya masa sai suje gurin Alhaji Baban. Mu'een najin haka ya tafi da gudu da yake yana da wayo, da idanu kawai Ammin sa ta raka shi batare da tayi yun'kurin motsawa ba, har yaje ya 'dauko kayan wandon jeans da riga ya sake koma 'dakin " Uncle gashi ka samin da sauri muje wurin Alhaji Baba" Yayi maganar fuskar sa cike da annurin zaiga Alhaji Baba. Palour suka dawo bayan ya shirya shi wanda tana ganin su tare sai ta mi'ke tsaye tare da fa'din " Ja'afar please help me....Allah sharri suke yi masa kuma sun'ki saurarata wallahi Taheer bai saci ku'din kowa ba". Sai yace " Kunyi magana da shi ne?" Tace " ah ah sun hanamu ganin sa ma" Tambayar Division 'din da yake yayi ta gaya masa sai yace to ta nutsu ta 'dauko masa key su je yanzu ko za'a dace su ganshi" Da sauri ta wuce ciki ta duba key 'din da rawar jiki domin ita rabon ta da hawa mota tafi 3weeks tun ma kafin faruwar lamarin kuma koda abin ya faru ma idan zasuje Division 'din da aka kulle shin da taxi suke zuwa bata ko sauraran motar gida. Shine ya jasu har Division 'din, inda aka kai ruwa rana kafin ya samu suka ganshi da dokar mintina biyar cif. Ganin Tahir sai da ya kusan sanya shi kuka amma wannan dauriyar da ya ara ya yafawa zuciya da fuskar sa tun a gida gaban Mu'een yake so ta 'kara rufa masa asiri, yaso kar ya zubda hawaye amma ganin yanayin da 'dan uwan nasa yake ciki ka'dai ma abin ya ta6ashi sosai domin ba kyan gani, gaba 'daya ya rame yayi ba'ki ya fita a hayyacin sa, rashin 'kibar daya ke da ita ita ta 'kara taimakawa wajen bawa tsufa shiga yanayin halittar sa, gaba 'daya ya zama tamkar wani dattijon mutun ga wani uban handcuff da aka maka mai a hannu. Mu'een na ganin sa ya fara murna yana fa'din " Alhaji Baba....Alhaji Baba kazo mu tafi gida kullum Ammi kuka take yi bata bacci..." Kafin ya kai aya sai Taheer ya juya baya dan baya son yaron yaga hawayen da ya sau'ko masa...shi kuwa Mu'een sam ya'ki zama jikin Uncle Ja'afar 'din sai da ya 'kwaci jikin sa yaje ya rungume Alhaji Baban yace " Kaima kana kuka ko Alhaji Baba...Uncle kace yayi shiru mu tafi gida, Alhaji Baba waye ya saka maka wannan abin?" Yayi tambayar gami da shafo handcuff 'din dake hannun sa......jikin sa Alhaji Baba ya jawo shi sosai ya rungume shi yana 'kara sau'kar da wasu hawayen masu zafi. Ammi ma dake gefe kukan takeyi yayin da Taheer yayi 'karfin halin ri'ke nasa hawayen bai bari sun sau'ko ba amma kallo 'daya zakayi masa ka fahimci cewa baya cikin mood mai da'di musamman idan kayi duba da yanda idanun wansa suka yi jajir......a hankali Taheer yace " Ja'afar ban san me zance kan lamarin nan ba dan bansan meke shirin faruwa dani ba kwata-kwata, amma dai inada tabbacin kai da Aishatu kunsan cewa ni bazan ta6a iya aikata irin wannan aikin ba har abada ko?" Kai Ja'afar ya 'dage gami da dafa kafa'dar sa yana shirin magana sai Taheer ya riga da sake fa'din " inaso koda mutuwa nayi sanadin hakan dan Allah kuyi 'ko'karin fahimtar da Muhammad cewa mahaifin sa bashi da laifi kan hakan, ni ban ta6a cin haramun ba, ban saci ku'din kowa ba... 'kaddara ce kawai ta hau kaina kuma na kar6e ta da hannun bibbiyu matsayina na bawan Allah...." Taran shi Ja'afar yayi da fa'din " ka daina fa'din haka dan Allah Alhaji insha Allahu komai zaizo da sau'ki, mu miye amfanin mu? Zamu kai 'karar duk wanda ya zalince ka wurin mahallici da izinin sa kuma insha Allahu zamuyi nasara". Bai ce dashi komai ba sai kawai ya 'dago kansa ya kalli Ammi da tun 'dazun take tsaye tana aikin kuka.....suna ha'da idanu sai ta 'daga kanta sama da niyyan tabbatar masa da kalaman Ja'afar 'din wani kukan na sake 'kwace mata. Saurin cire Mu'een yayi daga jikin sa ganin mai kula dashi dake tsaye gefe dasu na shirin tunkaro su, baya son ayi abinda zaisa Mu'een 'din kuka ko kuma yaji ba da'di tunda bai san meke faruwa ba, dan haka sai yayi saurin mi'kewa tare da fa'din " Mu'inuddeen kuje gida da Uncle ko..nima soon insha Allahu zanzo gidan kaji Babana". Kafin yaron yayi magana har ya juya 'dan sandan ya rufa masa baya suka yi ciki. Kuka Mu'een ya sanya yana 'kiran sunan shi sai Ja'afar yayi saurin 'daga shi sama yayi waje dashi, Ammi ma cikin sakakkiyar gwiwa tabiyo su abaya har wajen motar su, da 'kyar Ja'afar ya samu ya lallashe sa yayi shiru da al'kawarin zai kawo shi wurin Alhaji Baban gobe sannan yayi shiru. Zugum sukayi cikin motar ko'ina shiru babu mai ko motsin kirki illah hannun Ja'afar dake tu'ki har suka je gida. Yana sau'ke su ya sake fita da motar dan neman mafita, domin baya jin zai iya barin 'dan uwan sa ya sake ko kwana 'daya ne cikin wannan halin balle nan da 3weeks da aka ce kafin aje kotu. Wahala sosai yasha kafin ya samu ganin mutumin da yake tunanin zai taimaka musu shima 'din kuma sai ya so ya nuna akwai wani uzurin a gaban sa amma haka ya nace bai bar inda yake ba da 'kyar ya samu Commisionern ya saurare shi da 'kyar ya amince abada bailing sa bayan ya 'kira wani da bai san ko wanene ba amma yana kyautata zaton ma'aikatar da Taheer 'din ke aiki ya 'kira amma da shara'din daga yau 'din har ranar da za'a shiga kotu kullum zai je ya sa hannu domin a tabbatar da cewa yana kusa, dai-dai da rana 'daya idan ya sa6a lokaci ko rana zasu yi abinda suke ganin dai-dai me agare su. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍, [12/22/2019, 3:18 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *18* Batare da tunanin komai ba Ja'afar ya amince dan kuwa sosai yake da ya'kinin cewa Allah yana tare da su kuma shi zai taimake su, farin cikin sa 'daya kawai shine yau 'dan uwan sa zai kwana cikin gidan sa da iyalan sa . Kamar yadda suka fa'da 'din kuwa hakan ne ya faru domin kullun yakan je yayi signing kamar yadda suka bu'kata har tsawon sati biyu batare da yayi fashi ba. Ammi kuwa s duk iya 'ko'karin da zatayi na ganin cewa ya amince an saida abubuwan data gada daga gurin mahaifin ta tanayi domin a biya bashin sharrin da aka tiwa mai gidan naga amma sam Taheer ya 'ki amincewa bai kuma sanar da ita da dalilin 'Kin amincewar yasa ba. 'Bangaren shi Tahir 'din kuwa har cikin ransa yake jin tamkar idan yayi hakan bai kyauta mata ba duba da yanda wancen Lawyern ya damfare ta ya tafi da dayawa daga cikin dukiyar ta sannan 'dan abinda suka rage kuma yace zai yi haka dasu ai bai kyauta ba....shi aganin sa. Ammi kuwa rashin amincewar tasa sosai ya bata haushi har ma take jin tamkar da'ace takaddun dukiyar na wajen ta da tuni tayi abinda zatayi sai da ya 'dau duk matakin daya ga daman 'dauka daga baya amma baby abinda zai hanata aiwatar da nufin ta. Abin na damun ta sosai a duk lokacin da ta tuna cewa mijin ta matsayin mai laifi yake dan har fargaban dare yayi gari ya waye take yi sai take ganin kamar lokacin rabuwan ta da mijin ta ne yake 'kara kusanto ta, dan haka ranar wata talata ta fara bincike sosai cikin 'dakin sa da niyyan duba takaddun dake wurin sa.....domin sunyi magana dashi ko yana da wasu ku'dade cikin account 'dinsa sai yace mata bad baza su haura 10million ba ku'din ita kuwa bata son rasa shi ta ko wani 6angare. Gaba 'daya tayi kaca-kaca da 'dakin amma bata ga komai ba kuma tana da tabbacin a 'dakin suke bai kai su ko'ina ba dan haka sai ta cigaba da dubawa da fatan Allah ya taimake ta can su....kamar daga sama kawai ta ganshi tsaye a bakin 'kofa dan ko motsin shigowar sa ma bataji ba tsaban yanda hankalin ta ya tafi. Suna ha'da idanu da shi sai ta diririce abinda ke hannun ta ya fa'di 'kasa, batayi zaton zai dawo yanzu ba dan kuwa division yaje yin signing shiyasa ma ta saki ranta take binciken cikin kwanciyar hankali ko zata gansu tunda ya hanata ta da'din rai gara ta 'dauka tayi abinda ya dace dasu...ina amfanin ba'di ba rai" acewar ta kenan...... Da rawar murya tace dashi " har...ka....da wo?". Sai yace " Ke ma 'din na miki satan ne?" ya tambaya a tsare batare da yabata amsar tambayar ta ba wanda daga jin yanayin muryar sa ma zaka san cewa ransa a 6ace yake. Sai ta jijjiga kanta a hankali alamar " ah ah" "So...?" Yace da ita da 'dagaggen gira 'daya. Kwa6a fuska tayi kamar zatayi kuka gani da watsa hannayen ta tace dashi " please Taheer give me the documents i want use them...me yasa kake hakane wai?" Cikin 'dakin ya 'karaso a hankali cike da 6acin rai ya nuna mata hanyar waje gami da fa'din " leave this room please"! Tsayuwa taci gaba dayi cikin karya wuya da niyyan sake ro'kon sa amma kafin tayi magana sai ya daka mata tsawan " i said leave from here now"! Fita tayi a hankali tana matse 'kwallan takaici.....yayin da Taheer ya rakata da jajayen idanun sa har ta fita. Tana fita ya koma ya zauna bakin gado tare da dafe kansa, tunanin inda ya kamata ya 6oye takaddun kawai yake yi amma ya rasa, kuma baya so ya bawa kowa ajiya saboda gudun kar labari ya sake maimaita kansa...kar asake yi musu irin na Lawyer. Sosai ya zurfafa tunanin har ya gano abinda ya kamata yayi....dan haka washe gari ya faki idanun ta tana kitchen yaje cikin 'dakin ta ya 6oye su inda yasan tunanin ta bazai ta6a zuwa wurin kwana kusa ba. Ko bayan hakan ma tasha zuwa a 6oye tana bincikawa amma bata ta6a sa'ar ganin koda 'daya daga cikin documents 'din ba, har sai da ya kasance cikin 'dakin babu abinda bata 'daga shi ta canza masa mazauni ba saboda neman takaddun amma tarasa bata gansu ba. Rashin sani ya sa bata ta6a ko kawowa cikin ranta cewa kullum tare take rayuwa dasu cikin 'dakin ta ba, shima dan yasan tunanin ta ba zai zo nan 'din bane shiyasa ya kawo su kusa da ita duk da hakan amma yakan saci jiki kullum ya je ya duba lafiyar su batare da ta kula da hakan ba. ***** Kwanakin shiga kotu na 'kara 'karatowa yayin da abubuwa ke 'Kara shan kansu gaba 'daya, Addu'ah sukeyi ba dare ba rana... Hatta Ja'afar ba'a barshi abaya ba kamar yadda ya 'dau al'kawari ga kuma tunanin inda zasu iya kammala ku'di mash uban yawa har haka sosai abun ke adamun sa. 'Bangaren Ammi kuwa sai take ganin kamar shi har yanzun bai wani damu da lamarin ba dan ko lawyern da Ja'afar ya nema musu ma 'kin bashi ha'din kai yayi acewar sa koma me zasuyi ba nasara zasuyi ba tunda bashi da proof ko 'daya da zai kare kansa dashi, dan haka su bari kawai ayanke masa duk hukuncin da suke ganin yayi musu he ll definitely accept it" Cike da 6acin rai Ja'afar yace " haba Alhaji dan Allah...wai kai baka tunanin future 'din iyalan ka ne?" Sai ya bashi amsa da fa'din... " Duk wanda yake da 'dan uwa irin ka Ja'afar ai bashi da damuwar komai, na tabbata Mu'een bazai ta6a yin maraicin uba ba har abada matu'kar kana raye a duniya". " ita kuma matar ka fa ya zakayi da ita... baka tausayin halin da zata shiga dalilin hakan ne?.... Me yasa ba zaka tausayawa maraicin ta ba?" Ja'afar ya sake tambayar sa. Kafin ya bu'di baki yayi magana sai Ammi ta taho da gudu ta rungume shi tana kuka gami da bugun 'kirjin sa tana fa'din " kawai ka kashe ni Taheer ka kashe ni ka huta dan Allah...wai ya kake so inyi ne fisabilillahi...baka son gani na ina farin ciki ko Taheer....? 'Kasa ta sulale tana kuka mai cin zuciya, haushin abubuwan nan da yake yi take ji, bata san manufar sa akan hakan ba, sam ta rasa wani irin zuciya ce da shi da har zai yi saurin yanke 'kauna da farin ciki so soon haka, me yasa ba zai bari su yi abinda ya dace ba, ko dama ya gaji da rayuwa da su ne shiyasa ko tausayin su baya ji zai bawa ma'kiyan sa daman cin galaba akan sa?" Jikin Ja'afar sanyi yayi sosai dan haka sai yasa kai ya fice a 'dakin ya barsu su biyu. 'Kasan shima ya dur'kusa akan gwiwoin sa a hankali ya furta " Aisha.." 'Dago jajayen idanun ta tayi ta kalle sa da su sannan ta kawar da kanta gefe yana mai cigaba da zubar da hawaye. Kai ya girgiza gami da fa'din " ke kina ganin tamkar duk abinda nake yi dan kaina nake yin sa ko Aisha? Idan kowa bai fahimce ni ba ai ke ya kamata ki fahimce ni, me yasa zan tauye miki hakkin ki in salwantar miki da dukiyar ki bacin bani da tabbacin cewa zan samu hanyar da zan biyaki abinki koda na rayu? Ke kina ganin hakan dai-dai ne idan na amince da batun ki?" A fusace tace " ni nace maka zaka biyani ne?" Murmushi ta'kaitacce yayi gami da mi'kewa tsaye tare da fa'din" bazaki gane bane Aisha, banfa saci abin kowa ba kuma sai in yadda naki dukiyar ya salwan ta saboda wasu can marasa tsoron Allah? kin sanni kin san hali na Aisha kinsan cewa bana saka kaina cikin abinda bai shafeni ba... ban nawa kaina magana tun farko, duk abinda kika ga ya faru dani to daga Allah ne, bance kince zan biyaki ba yanzu ba amma bazan 6oye miki ba wallahi har abada bazan ta6a iya cin dukiyar ki wai dan ni na rayu cikin farin ciki ba......" Juyowa tayi ta kalleshi bai damu ba sai yaci gaba da fa'din ".....karki damu kinji...baki na yimin addu'ah kullum ba, nima kuma kinga inayi, kijira kiga ikon Allah tunda sharri ne ba gaskiya bane na tabbata Allah na tare da mu, in kinga ban tsallake wannan lamarin ba to 'kaddara wannan babban 'kaddara ce daga cikin babin rayuwa ta kuma dukkan mu ya kamata mu kar6e shi....duk abinda aka riga aka fawwalawa Allah shi to sanya wa ranki salama domin zai isar miki koma menene ". Ammi sai tace " What about the court...." 'Kyale su ni ba wani Lawyer da zamu 'dauka su suka sani...domin babu wani taimako da Lawyern zai mana sai dai ma cuta abanza". Ammi bata 'kara magana ba illa binsa da idanu da take yi, sosai take jinjinawa taurin kai da kafiya irin nasa, yau ne ta yadda cewa lallai mijin ta mai tsantsan taurin kai ne, bata ta6a fahimtar hakan ba sai yanzu da wannan abin ya faru. Haka ta ha'kura ta zubawa sarautar Allah idanu ba Wai dan task jakan ba... bata dai fasa addu'ah ba haka kuma zancen case 'din babu abinda ya canza. Ana jibi za'a shiga kotun ne Manager da kansa ya 'kirashi ya sanar dashi cewa an janye maganar saboda an samo inda ku'din fuel 'din sukayi dan haka yayi ha'kuri. Bai ce dashi komai ba illah lumshe idanu da yayi gami da fa'din Alhamdulillah cikin zuciyar sa tare da yanke 'kiran gaba 'daya. Hawaye kawai yaji ya gangaro masa masu sanyi, tun fitar sa daga station bai 'kara zubda hawayen sa ba sai yau 'din da yake yiwa Allah godiya bisa ga babban taimakon da ya yiwa rayuwar sa. Batare da ya sanar da Ammi ba ya shirya ya tafi Division 'din inda suka sake yi masa bayani gami da neman saka hannun sa na 'karshe tare da ban ha'kurin tuhuma inda suka 'karashe da fa'din " haka aikin mu ya gada ka gafarce mu visa abubuwan da suka faru. Bai damu da wannan ba shi dai kawai fatan sa ya isa gidan sa ya sanar wa da Ammi wannan babban abin farin cikin da ya same su a yau. Tunowa da yayi cewa jiya-jiya Ja'afar ya wuce Azare da niyyar gobe zai dawo a shiga court 'din dashi sai taji matu'kar tausayin 'kanin NASA..... dan sau'ka'ka masa tafiya sai yana fita daga ofishin 'yan sandan ya doka masa 'kira gami da fa'din " albishirin ka lil bro". "Goro fari 'kal Alhaji...amma duk girmana mana 'kiranka Lil ai sai Mu'een ya min dariya..... nd kuma irin wannan albishir da kake min Allah yasa dai ku'dine suka bayyana"! " Kusan hakane 'dan uwa domin kuwa an kori wannan case 'din i'm free now ba sai kazo goben ba". Washe baki Ja'afar yayi gami da hamdala daga 'dayan 6angaren sannan ya 'kara da fa'din " ai zuwa dole ne Yayah, dole inzo muyi murnar tare...insha Allahu gobe ina hanya...kai masha Allah..... Allah ka 'kara rufa mana asiri". Amin yace tare da yanke 'kiran. Yana shiga palour da Mu'een ya fara cin karo sai yayi saurin 'daga shi da murnar sa yana dariya. Shima Mu'een dariyar yake yi ganin mahaifin sa da ya jima baiga dariyar sa ba yau yanayi dan haka shima da 'karfin gwiwar sa yake darawa. Hayaniyar sune ya fito da Ammi daga 'daki inda ta 'karaso da bu'd'den bakin mamaki tana kallon sa, fara'ar da take gani yau 'din direct take hango shi har cikin zuciyar sa domin kwata-kwata bai yi kala da na ya'ke ba. Ganin kallon da take yi musu ne ya sanya ya shi sau'ke Mu'een gami da fa'din je kawo min ruwa insha kaji". Da gudu yaron ya tafi yayin da Taheer yayi saurin tunkarar Ammi ya ha'de musu fuska gami da fa'din " ur husby is free now an kori shari'ar mu gaba 'daya". Tsalle ta buga tare da rungume shi cike da farin ciki shima 'din sai ya rungume ta ka'dan dan hankalin sa na kan yaron da ya aika. Yana sakin ta kuwa Mu'een ya dawo da goran ruwan Swan mai sanyi a hannun sa, shi Taheer bai sake bi ta kan farin cikin da Aishatu keyi ba yayin da itan kuwa take jin tamkar ta zuba ruwa a 'kasa tasha, ruwan ya kar6a ya bu'de gami da 'daga kai bai sau'ke ba sai da ya kwankwa'de gaba 'daya. _Alhamdulillah_ ya sake maimaitawa gami da kallon ta yace " kinga ikon Allah ko? ai dama na gaya miki, ba'a dogaro da Allah aga failure, yanzu ya kika gani?". Murmushi tayi tare da sake tahowa ta rungume shi cikin tsananin farin ciki, cuz she is totally speechless, Mu'een ya janyo ya ha'de su duka ya rungume su shima 'din yana farin cikin sosai. A kunne ya ra'da mata" bakya jiko...didn't i tell u not to hug me in front of him?" " Sorry...." tace a hankali itama. Sannan sai tayi saurin samin shi gani da fa'din "amma Alhaji ya kukayi da Manager gurin warware case 'din? Baiji kunyar ka Ba da ya ganka? " " Ai ban ma ganshi ba ni.... Sa'ko ne ya iso ni kawai" "Hmm" tace gani da sakin tsaki. Kallon ta yayi gami da tambayar abinda ya faru sai tace " ya kamata ya ji Mari Allah ko sau ' daya ne". Sai yace " Ba damuwa ba kenan Aisha.... ai da naso yin hakan da har office zan same shi amma bani da wannan lokacin ni..... ***** Washe gari kamar yanda ya fa'da Ja'afar suka zo harda matar sa Zainab, gaba 'daya suka ha'du suka yi farin cikin tare inda anan Taheer yayi musu bayanin yanda akayi gaba 'daya, dukkan su basuyi mamaki ba domin sunsan wannan ka'dan ce daga cikin buwayar mahallici balle bayyanar da gaskiya da take ta zahiri.... Wannan a gurin sa shi yafi komai sau'ki. Anan Ja'afar ma yake sanar musu cewa ai shi har ya fara cuku-cukun kar6an loan sai kuma ta Allah ta kasance.....Ammi ma tace " ai ka bari Ja'afar ni da document sukayi min 6atan laya a gidan nan....gaba 'daya na rasa ina aka sanya su har na fara tunanin ko an sace ne". Kallon sa tayi gami da ri'ke baki tace " wai dan Allah ina ka 6oye su ne... Yanzu kam ai zaka sanar dani tunda komai ya wuce?" Sai yace " D'akin ki na 6oye su saboda nasan hankalin ki bazai je gurin ba" Salati ta sanya yayin da su Zainab suka tuntsire da dariya don ko su ma a lokacin confused sosai suka shiga da tace ta rasa document 'din dan yana yawan tiwa Zainab complaint a duk lokacin da ta gaji da bincikawa..... Abun na bash mamaki duk da take ma suma 'din basu goyi bayan a salwantar mata da dukiya ba yayin da 'dayan 6angaren kuma basa so rayuwar sa ta salwanta...abin sai ya 'daure kansu gaba 'daya shiyasa ma daga baya Ja'afar yayi tunanin kar6ar loan sai su cika sauran da abinda Allah ya hore musu. " Ni dai Allah baka kyauta min ba kuma kar kaga kamar banji haushin abin nan da kayi ba wallahi har abada bazan daina jin haushin hakan ba, ace ina da abu amma mijina ya kasa anfana da ita to miye anfanin ta?" Shi kan Taheer shiru yayi mata illa murmushi da yake yi a cikin ran sa ya furta "sai kiyi kuma ai"! yayin da su Zainab suka cigaba da bata ha'kuri da ban baki har ta ha'kura. Duk kansu babu wanda ya sake bi takan office 'din nashi balle har su nemi jin babban dalilin da ya sanya akayi masa sharrin, sude kawai fatan su Allah ya kare na gaba ya raba su da ma'kiyan su Amin. Kwanan su 'daya suka koma Azare domin shima Ja'afar yawan zirga-zirgan da yayi a kwanakin ya so ya ta6a masa wurin aikin sa, kunsan aikin banki ba'a wasa dashi...dan haka yake so ya dai-dai ta komai..... Shiyasa suna komawa ya fuskanci aikin sa bada wasa ba. ***** Rayuwar su ta dawo sabuwa 'kal, yanzun kam basu da matsalar komai illa Taheer da ya dawo da lamarin Barrister cikin ransa, so yake a matsayin sa na mijin ta ya kare mata maraicin ta, martabar ta da hakkin ta da ya kamata... dan haka yake so yaje ya ziyarce shi kamar yanda yayi planning run farko dan su magantu da shi wala Alla ka zai fahimce shi, amma da kansa yasan cewa abinda zai yi 'din riski ne babba kamar yadda Aishatu ta ta6a gaya masa tun farko, dan haka ya kamata wani nasa yasan da lamarin wanda zai ri'ke sirrin sa batare da ya taka masa birki ba. Kansa ya dafe yana tunanin yanda Ja'afar zai 'dauki lamarin yasan da 'kyar ya fahimce shi amma kaf duniyan nan yanzu shi ka'dai yake da shi kuma shi kad'ai ya yadda dashi dan haka batare da 6ata lokaci ba ya danna masa 'kira ta landline 'din gidan sa dayake lokacin yasan already yana gida. Bayani yayi masa cikin natsuwa akan duk yadda akayi, da kuma abinda yake son aikatawa, anan Ja'afar ya 'danso ya hana shi amma ya fahimtar dashi a fahimce ya kuma fahimta. Yana sau'ke wayar daga kunnen sa Ammi ta fa'do 'dakin cike da 6acin tana kallon sa, sai yayi saurin mi'kewa tsaye. Yaso yayi mata magana amma sai yayi tunanin kar dai taji shi ne...taji shirin nasa. Dan haka sai ya juya inda ya fara rage kayan jikin sa tamkar bai kula da yanayin fuskar ta ba cikin 'karfin hali yace " yauwa ma tunda kinzo...ha'da min ruwan wanka please mai 'dan 'dumi". "...bazan ha'da ba"! Tace dashi a fusace. Da mamaki ya juyo yana kallon ta gami da 'kan'kance idanu batare da ya furta komai ba. 'Kafa ta 'dago ta taho da gudu tana bugun sa a 'kirji tana kuka... Taheer bai hanata ba sai da ta gaji dan kanta ta bari cikin kukan ta nuna shi da yatsa tace " bazaka daina saka rayuwar cikin masifa ba ko? bazaka daina nemawa kanka rashin kwanciyar hankali ba ko...wai anya ma Taheer kana son farin cikin mu, kana son kallon mu cikin farin ciki kuwa kode nice baka so ka gaya min Taheer?" Ta 'karasa maganar cikin kuka. Bai furta komai ba kawai ya rungumo ta jikin sa tsawon mintina har tayi shiru, duk da yana kyautata zaton taji wayar sa ne amma still yana son ji daga bakin ta domin ya tabbatar. " me ya faru ne wai haka?" Ya tambaye ta as if bai san me ya farun ba dagaske. Raba jikin ta tayi da nashi ta matsa baya ka'dan sannan cikin dakiya tace masa " nima ban sani ba...amma ka sani wallahi akan wannan abun ko ciwon farce kayi bazan ta6a yafe maka ba tunda mun gama magana da akai tun ba yau ba". Juyowa tayi ta fuskance shi sannan tace " ina ruwan ka dashi, bashi ke son dukiyar ba ai sai ka bar masa, ni ko ka kar6o ma banso matu'kar zakasa rayuwar ka cikin halaka to wallahi banso Taheer, miye ma anfanin ta tunda ko akwai 'din ma ba abinda ya dace ake yi da ita ba, me zan yi dashi Taheer, kai kace bakaso to ni me zan yi dashi?amfanin me zata min? " Cewa yayi " Hakkin ki kine Aisha ni kuma nawi ne akai na in kare miki hakkin ki ko wani iri ne....." " to hell with it...." ta fa'di a fusace, sannan ta 'dago yatsa ta nuna saitin fuskar sa tace " wallahi idan ka kaje da kanka ka kar6o ban yafe maka ba kuma daga ranar zamana da kai ya 'kare, lokacin da zai kar6a ya wahal da kai ne, me yasa lokacin da ake so kuma kai zaka wahal da kanka? Kai kake cin dukiyar ne....? Zunubin ka ne ko kuma menene?.... I told u ka 'kyale shi ni na barshi da Allah matu'kar da gangan yayi ban kuma ce abi bayan sa ba har abada"... Tana kaiwa nan ta fice a fusace ta bar 'dakin. " Aisha! ..... Aisha!!....yake ta anbata amma ko waigowa bata yi ta k'yaleshi. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 [12/25/2019, 12:27 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *19* Zama yayi bakin gadon gami da dafe kansa da har sara yake jin yana yi masa. Daga nan bai 'kara ha'duwa da ita ba, bai je ba haka itama bata sake dawowa inda yake ba. Mu'een kuwa Ja'afar sun tafi dashi da yake anyi hutun makaranta.....so kowa sai yake jin babu da'di. Washe gari da safe Ja'afar ya 'kira shi dan yaji ko ya shirya tafiyar anan Tahir yake sanar da shi cewa ai ya fasa tafiyar gaba 'daya maganar ma ta wuce. Baiyi masa dogon bayani ba ya yanke 'kiran shima Ja'afar 'din bai damu ba cuz dama can baso yake yi ba, ya ha'kura ne dai kawai dan babu yadda zaiyi, amma ai abun a zahiri yake, duk wanda kaga ya aikata irin wannan abun to kuwa shi ka'dai yasan me ya taka, shi ka'dai yasan shirin sa akan hakan, Tahir 'din ne dai kawai yake da taurin kai shiyasa ya kasa fahimtar su... Amma yanzun da yaji cewa ya fasa sai yaji hankalin sa ya kwanta sosai. 〰〰〰 ...... Basu sani bama ashe ko wancan case 'din da ya faru da Tahir.... Lawyern ne ya assaso shi tunda ya samu labarin binciken da Tahir yayi akan sa sai ya rasa yadda zai yi ya 'kas'kantar da shi da rayuwar sa, ya so yasa akashe shi amma sai ya fasa ganin cewa managern Oando babban aminin sa ne, dalilin haka ya sanya suka shirya deal akan hakan da zummar idan an tuhume shi kan satan fuel dole zai biya ku'din komin yawan su, wanda dalilin hakan zaisa ragowar dukiyar dake hannun sa zata sami gi6i na gaske shikenan daga ranan koda zasu nemi karawa dashi they ll not win against him dan basu da komai, rayuwar yanzu kuwa sai kana da shi ake yi da kai. Ku'din da zasu biya 'din kuma shi manager zai ri'ke sai lawyer ya cika masa ya zama 100million shi kenan deal 'din su ya 'kare daga nan.... amma 'karfin addu'ah da kuma rashin sabo da cin amana ya sanya manager rashin natsuwa bayan sun gama shirya komai, sai gashi kafin deal 'din nasu ya kammala da kansa ya bayyana cewa an samu ku'da'den...sai dai bai sanar da kowa cewa su suka shirya hakan ba. 'Bangaren Lawyer kuwa ganin ha'kar sa bata cimma ruwa ba a karon farko ganin hakan ne ya sanya shi canza tunani zuwa plan B. ***** Bayan wasu kwanaki sai Oando suka rin'ka damun Tahir akan ya dawo bakin aikin sa, shi kuwa gaba 'daya aiki dasu ya fice masa arai harma ya fara 'ko'karin neman wani aikin a wani wajen daban. Itama Aishatu bata goyi bayan ya koma can 'din ba haka ma Ja'afar, sai ma tace suje Kaduna su 'dan kwana biyu daga nan su duba gidajen mahaifin ta dake can 'din daga baya sai su dawo kafin nan ko zasu rage damun sa. bai 'ki shawarar ta ba dan ko shima 'din yana so ya 'dan kauce ko ma dan ya huta, cuz tun bayan faruwar lamarin Kano ta bar ransa kwata-kwata. Dalilin haka ne yasa washe gari suka wuce Kaduna su biyun su batare da kowa ya sani ba da yake ma har yanzu Mu'een na Azare gun Ja'afar shiyasa ya kasance su biyu ne sukayi tafiyar. Sunje sunyi duk abubuwan da ya dace sun kuma huta 'din kamar yadda suka yi buri duk cikin sati 'daya, harma sun fara 'ko'karin dawowa da tunanin barin Kano su koma Kaduna da zama gaba 'day musamman ma da suka ga yanayin garin yayi musu ba laifi sai suke ganin zasu dasa sabuwar rayuwa a can 'din. Ana jibi zasu tafi ne da safe lokacin Aishatu na 'dan fama da zazza6i ko Tahir ma bai san da zancen zazza6in ba yayin da ya shiga cikin gari tun safe ya manta wayar sa a hotel 'din da suke 'din.....Aishatu kuwa zafin zazza6i da ciwon kai da take ji bai barta ta iya koda motsawa ba, tana jin wayoyin su na faman ringing amma bata iya ta 'daga ko guda 'daya ba, duk kuwa da tayi mamakin yanda wayoyin ke faman ruri lokaci guda amma hakan bai sa ta 'dauki 'kiran ba. 'Ko'karin da tayi ma shine tashin da tayi ta kakkashe wayoyin batare da tabi ta kan 'kira ko 'daya ba. Tsawon lokaci sannan ya dawo kusan shabiyu na rana sai da ma yayi sallahr Zuhr kafin yabi ta kan wayar inda ya tarar da ita a kulle... Yaso yayi mamaki amma kuma tuna cewa Aishatu ce ka'dai zatayi hakan ya sanya shi kunnawa kawai ya bar batun mamakin. Kunnawar sa keda wuya kuwa sai ya tsinci 'kiran Manager cikin wayar kamar dama jira yake yi ya kunna.. ...'dauka yayi da tunanin zai masa bayani na 'karshe dan zaton sa ko har yanzu akan komawar sa bakin aiki ne dan haka cikin ransa ya shirya maganar da zai gaya masa akan cewa shi ba zai iya sake yin aiki da su ba har abada......sai dai ga mamakin sa bai kai ga furta abinda ke cikin ransa ba shima 'din hankalin sa ya tashi, cuz yanda yaji muryar Manager cikin damuwa sosai ya sanya shi shiga firgici lokaci guda. Jikin sa sanyi yayi da ya sau'ke wayar daga kunnen sa, koda Aishatu ta tambaye shi ma bai iya yace da ita komai ba dan gudun 'daga hankalin ta. Wannan dalilin ne ya sanya shi mantawa da duba sauran tarin missedcalls 'din da akayi masa. Aranar ya wuce Kano batare da ta sani ba. Manager ne yayi masa kwatancen inda zai same shi batare da 6ata lokaci ba kuwa ya wuce gurin saboda har yanzun baiji hankalin sa ya kwanta ba tun bayan da suka yi waya da manager a Kaduna. Ba 'karamin mamaki yayi ba da yaji abinda Manager yace cikin 6oye ko wanene ke abin yayi masa bayani a ta'kaice kan cewa babban abokin sa ke neman ran Tahir 'din da iyalan sa ma gaba 'daya. Tun jiya wai ake zarya a gidan sa har wayewar garin yau amma basu samu kowa a gidan ba kuma rashin ganin ahalin gidan ya sanya su fahimtar cewa basa kusa ne shiyasa, dan haka da safiyar yau suka sanya wa gidan wuta kuma ya 'kone 'kurmus..... Cikin matu'kar razani Tahir ke kallon manager jin cewa an 'kona masa gidan sa a wayewar garin yau 'din nan.....kenan da bamu tafi ba da ikon Allah ne ka'dai zai iya ku6utar da mu a hannun su. "..... Yah Rabbi.. " Ya furta gami da dafe kansa.... Sai ga hawaye sun sau'ko masa take idanuwan sa sukayi jajur, bai san me ze ce kan wannan lamarin ba sam....musamman da yake ba sanin mai neman halaka shin yayi ba, mamakin sa kawai shine ta ina suka ha'da ala'ka yayin da tambayar abinda ya ha'da su ya tsaya masa a zuci. Bakin sa har rawa yake yake wajen godewa Allah da ya basu ikon tafiya Kaduna cikin kwanakin nan...ya san ba komai bace hakan face kariya daga wurin sa in ba dan yaso kare su ba da babu abinda zai sasu yin tafiyar. Duk dama ya san sun yi asara sosai a gidan wanda shi kansa ba zai iya irga su ba amma ba zai ta6a fasa furta Alhamdulillah ba. Duk cikin zuciyar sa yake wannan tunanin yayin da hawayen sa ke sake gangara a hankali. Manager ne ya dafa kafa'dan sa gami da cigaba da fa'din " ni kaina ina cikin matsala Tahir ta dalilin haka domin rashin samun ka ya sanya shi zargin ni na kawo maka labarin zuwan su, shiyasa ka gudu amma ban damu ba dan nasan babu wanda zai ta6a gujewa 'kaddarar sa ko a ina take shiyasa bazan 'daura ma laifi ba... Amma tun lokacin da na cire ka cikin wancen zargin ni kuma na cusa kaina ciki dumu-dumu batare da na sani ba...... Yanzu haka Tahir wannan ha'duwar tamu da kai babu wanda ya san da ita.... Na tausaya maka sosai jin cewa an 'kona gidan ka fargaba ta shine Allah yasa baka ciki domin ban samu dama na nemi yafiyar ka ba har yanzu, Tahir dan girman Allah kayi ha'kuri ka yafe min 6ata maka suna da nayi duk kuwa da nasan cewa baka da laifin komai amma naso biyewa son zuciya ta... ban cancanci kasancewa shugaba sama da kowa ba saboda na ci amana Tahir.... Sai dai gashi nima ban tsira ba domin yace naci amanar sa kuma zai 'dauki akaina.....please Tahir forgive me, sai daga baya nasan ban kyauta ba sam ban yi maka adalci ba" Kallon sa kawai Tahir yake yi bai yi wani mamaki ba da yake tun farko ya san cewa sune suka bada report 'din a kamashi, in ma mamakin zai yi bai wuce na ji da yayi cewa shima saboda wani yayi hakan ba, babbar damuwar sa a yanzun kuwa bai wuce yaji ko waye wancen 'din ba mecece kuma ala'kar su. Manager bai damu da shirun Tahir 'din ba sai kawai ya cigaba da maganar sa inda yace. " Naji da'di sosai Tahir da ka kasance araye ma'ana baka 'kone cikin wannan gidan ba..... Dan haka ga wannan ka tafi can da nisa inda babu wanda zai takuraka kaje ka gina sabuwar rayuwar ka ka ingan ta rayuwar iyalin ka, nasan yanzu haka abubuwa da yawa ka rasa kuma nasan bazan iya biyan ka ba amma duk da haka bazan barka haka ba Tahir.... Ka tafi da nisa domin *Kido* ba zai barka ba matu'kar ya san kana raye. " Yana gama fa'din hakan kawai ya cusa masa check 'din yayi gaba.... Tahir kam bai iya yace dashi komai ba.... Mutuwar tsaye yayi yana tunanin sunan da yaji manager ya fa'da. .........Me yake nufi wai, *Kido* inkiyar Lawyern mahaifin Aishatu ne wanda suka sanshi da shi tun asali sai ma da yaje bincike ne ya samu bayanin cikakken sunan sa.....kenan barrister shine yake neman ransa?... Shine ya sa aka 'kone gidan sa? Shine.... Shine...yasa aka kama shi da laifin da bai aikata ba? Duk dan saboda dukiya ko me? Ashe gaskiyan Aishatu ne... Gaskiyan tane da ta hana shi tunkarar sa tun abaya.... " Har manager ya 6ace bai dawo daga tunanin da ya lula ba. Tafiya manager yakeyi cikin sanyin jiki yana jin dad'in ya sau'ke nauyin da yake kanshi... Tsakanin sa da abokin san bai wani dameshi sosai ba duk kuwa da ya riga yasan kalan mugunta da rashin imanin sa amma yasan bai isa yayi masa abinda ba Allah bane ya tsara dan haka bai damu sosai ba.... Gudun kar Tahir ya'ki amincewa da batun tafiyan ne ma ya Sanya shi 6oye masa cewa ance ne ko ya kawo shi ko kuma shi abakin ransa..... Yaso ya kai report gun 'yan sanda amma yin hakan dai-dai yake da salwantar da rayuwar iyalan sa cuz dasu akayi masa baraza na kan kar ya yadda ya fara sako jami'an tsaro cikin lamarin. Dan haka sai ya wuce gida kawai yana jiran yaga yadda Allah zai yi dashi. 'Bangaren Tahir kuwa lokacin da ya dawo daga tunanin a lokacin ya fahimci cewa Manager ya jima da barin wajen dan haka a hankali shima ya taka ya isa gaban motar sa da niyyar komawa Kaduna, har zai bu'de motar ya shiga sai kuma ya fasa. Rufe ta yayi ya koma bakin titi ya tari taxi zuwa unguwar tasu inda ya ringa nuna wa mai taxi 'din hanya har kan layin nasu. Nesa da gidan ka'dan ya tsaya ya dubi yanda gidan duk ya lalace bai 'kara mintina biyar masu kyau ba ya umarci mai taxi 'din fa'din su tafi kawai bai samu numbern wanda yazo gurin sa ba, ko mai taxi 'din Tahir bai yi saken da har ya gane abinda ya kawo shi layin ba kuma koda suka koma daga can bakin titi ya sau'ka inda ya gangaro da 'kafar sa ya dawo ya shiga motar sa take ya wuce Kaduna, Sallar la'asar ma a Zaria ya tsaya yayi ta daga nan ya wuce abinsa. Yanzun kam da ya koma bai 6oyewa Ammi komai ba duk ya bata labari inda take ta sanya kuka tana dafe kai jin cewa ana neman su ne kunsan mata da tsoro. Sai da yayi ta kwantar mata da hankali kafin ya samu tayi shiru amma ta kasa sakewa dan ko da dare ma kasa bacci tayi saboda tsoro. Washegari ya fita bayan sun gama yaje ya saida motar dake hannun sa, sannan ya biya Bank ya ciro ku'da'den da Manager ya bashi check jiya na dubu 'dari 'daya daga ya koma masau'kin su kusan la'asar a lokacin inda yaje ya samu Ammi zazza6i sosai ya rufe ta. Batare da 6ata lokaci ba suka wuce asbiti. Inda bayan gwaje-gwaje da 'yan tambayoyin da likita yayi mata sai ya bisu da albishir 'din cewa tana 'dauke da juna biyu na kusan wata uku. Murnar da sukayi har sai da ya kusan mantar da su damuwar da suke ciki. Da komawar su sai Tahir ya 'kira Ja'far ta landline 'din dake gidan sa ganin lokacin ba lokacin aiki bane, anan ya sanar dashi komai duk abinda ke faruwa. Shima Ja'afar 'din sosai ya damu da jin abinda ya farun....ganin kamar zai ja maganar cikin tashin hankali ne ya sanya Tahir dakatar dashi da albishir 'din cikin da Ammi ke 'dauke da shi.....ai kuwa take yanayin sa ya canza amma duk da haka farin cikin bai hana shi tambayar inda suke ba. Jin cewa suna Kaduna a dai-dai lokacin ya sanya hankalin sa kwantawa gami da yiwa mahalicci godiya. Bayan kwana uku da faruwar hakan suka tattara suka wuce can jihar Bauchi batare da sun sake tsayuwa cikin gari Kano ba. Sai da suka sau'ka a gurin Ja'afar suka 'dan huta kafin suka 'karaso garin Shuwarin mahaifar su ta asali.....inda Ja'afar yayi-yayi da shi akan ya bari kawai su zauna tare amma Tahir ya'ki amincewa sam dole tasa Ja'afar ya ha'kura badan ya so ba da kansa ya shigo dasu suka sau'ka gidan mahaifin su dake can bayan makaranta. Su biyu kawai suka taho batare da su Ammi ba sobada gidan na matu'kar bu'katan gyara dan an jima ba'ayi amfani da shi ba. Nan Ummah taja dogon numfashi tace " to kunji dalilin dawowar Alhaji Baba garin nan da zama, bakomai bane face sharrin ma'kiya". Dukkan mu shiru mukayi ni kam harda tagumi duk muna kallon Ummah yayin da fuskokin mu ya cika da tausayin su jin irin yadda suka sha fama da rayuwa. Ummah bata bi ta kan mu kawai ta ci gaba da labarin ta. " Sai da suka nemi masu aiki suka bada aikin gyaran gidan bisa jagorancin mahaifin ku sannan suka koma Azare. Cikin sati guda aka gyare gidan tsab kamar bashi ba da yake ma 'karamin gida ne ba babba ba shiyasa gyaran bai 'dauki lokaci ba, ai kun gane gidan ko....wancen gida mai fenti dake nesa ka'dan da makaranta?" Ta 'karashe maganar da sigar tambaya. Nanne kai ta 'daga yayin da ni.kuma nace " ehh Ummah nagane shi kullum idan zani makaranta ai ina ganin sa a rufe". Ummah sai tace " Yauwa to wannan shine gidan da Alhaji Baba ya fara zama bayan dawowar sa garin nan, kuma anan Ammi ta haifi 'yan biyun ta wato....Saifullahi da Zaidullahi". Murmushi Ummah tayi tace min " abokan wasan Hudallahi". Nima 'din murmushin nayi jin sunan da ta 'kira ni dashi.....kuma ya min da'di...dan bata cemin hakan ba sai yau. "......Sai dai koda Alhaji Baba ya dawo nan bai taho da 'dan sa dake gurin 'kanin sa Ja'afar ba, dan Ja'afar hana musu shi yayi musamman saboda karatun sa shiyasa har yanzu baku san shi ba....." kallo na Ummah tayi tace " ko ke dake zuwa gidan kin ta6a ganin sa?" Da sauri na girgiza kaina gami da fa'din " ah ah". Sai ta cigaba da fa'din ko hutu ma ba'a kawo shi idan sunzo tare suke komawa da iyayen nasa basa barin sa anan koda ana hutu sai suce akwai makarantar islamiya....Alhaji Baba ma bai damu ba dan yasan ilimi shine hasken rayuwar 'dan Adam, Ammi kuwa da take ganin 'yan biyun shikenan sai suka 'dauki hankalin ta bata damu sosai da shi babban ba, musamman ma da yake tana tausaya musu saboda rashin samun haihuwar su shiyasa take ganin dama a bar musu shi kawai su ri'ke shi. Tun zuwan Alhaji Baba garin nan bashi da abokin da ya wuce Baban ku, shine ka'dai suke zama suyi hira wanda har hakan yasa da kansa ya bashi labarin duk abinda ke faruwa da rayuwar sa, Baban ku ya tausaya masa sosai. Koda ya nemi shawarar abinda zai rin'ka yi yana juya ku'd'den sa sai Baban ku yace bari yayi tunani. Ganin ba zai iya noma kamar yadda su suke yi ba ya sanya washegari da suka ha'du ya bashi shawarar yayi gidan gona tunda shi rani da damina ana cin moriyar sa in yaso sai yayi na dukkan 6angarorin biyu, wato lambu da kuma kiwo za'a fa'da'da gurin sosai ta yadda babu wanda zai cutar da wani acikin su. Sosai Alhaji Baba ya ji da'di shawarar Baban ku, dan kuwa kafin sati uku su cika har an nemi filin gona mai girman gaske an siya har an katange shi sauran aikin cikin. A hankali ake yin komai kafin 3month kuwa komai ya kammala an raba filin 6angare biyu. Kaji kala suka zuba farko guda dubu biyu...sannan suka yi shuke-shuke aka dasa wasu kama daga kan albasa, carrots sweets potato, abubiwa da dama suka fara dasu, gefe guda kuma aka daddasa su ayaba da sauran su wa'danda zuwa yanzun sun girma sun zama bishiyoyi masu masifar ni'ima a wurin. Ma'aikata kusan talatin aka zuba kowa da 6angaren sa. Karon farko da Alhaji Baba ya fitar da kajin sa ba 'karamin riba ya samu ba wanda hakan ya sanya shi 'karo wasu masu yawan gaske kamar da wasa sai gashi yana samun alkhairi da dama. Lokacin da kajin sa na 'kwai suka fara 'kwai abin ba'a cewa komai....'diba kawai suke yi safe da yamma babu 'ka'k'kautawa. Dalilin hakan ne ya sanya shi yiwa mahaifin ku alkhairi na zunzurutun ku'di har dubu hamsin, wanda da 'kyar Baban ku ya amshi ku'din....dubu goma ka'dai ya 'dauka ciki ya dam'ka sauran hannun yayan ku Usman yace ya 'kara akan sana'ar sa. Wani filin Alhaji Baba ya 'kara siya ya tada ginin na zamani kafin a shekara kuwa ya gini ya kammala gaba 'daya.....sai da ya gama zuba komai aciki na amfani kafin suka tattaro suka dawo ciki inda aka kulle wancan gidan shiyasa har yau kuke ganin sa a kulle babu kowa ciki. A dai-dai lokacin ne kuma Alhaji Baba ya samu labarin rasuwar Manager inda a lokacin ma ya kai kusan wata shida da rasuwa, Ja'afar ne da yaje Kano ya samo labarin. Alhaji Baba ya tausaya masa musamman da yaji cewa wai cikin sa aka soka da wu'ka har cikin gidan sa yasan babu mamaki aikin *Kido* ne wannan, addu'ar dacewa ya bisa dashi sannan ya ro'ki Allah ya tsare masa marayun 'ya'yan sa dama shi kansa da abin ya kasance sanadin sa ne. Sai dai bai gayawa Ammi ba dan baya son hankalin ta ya tashi, ganin yanzu ta kwantar da hankalin ta baya son sabuwar damuwa kuma...dan haka sai ya ri'ke abin cikin ransa bai 'kara sanar da kowa ba. Gidan gonar Alhaji Babba sosai albarkar Allah ya sau'ka a kansa shiyasa a kullum take 'kara habbaka da yin suna a fa'din garin Bauchi. Bai yi 'kasa a gwiba wurin siyan manyan motoci guda biyu ya bayar ana zirga-zirga da su jahohin kudanci shiyasa a kullum ka ganshi bazakace mazaunin 'karamin gari kamar nan bane.....gashi da karamci da son mutane ga kyautatawa jama'ah gaskiya halin Alhaji Baba sai godiyar Allah........." Ummah na kaiwa nan sai ta dubeni tace " kinji ko Hudah, ai yanzu kam kin fahimci dalilin da ya sanya rayuwar Alhaji Baba da iyalan sa ta banbanta da ta mu ko?" " ehh Ummah na fahimta yanzu". Nace cikin sanyi. Sai tace kunga ba dan wani ikon Allah ba ma da nasan babu abinda zai sa shi dawowa nan garin da zama amma rayuwa ta kan juyawa mutum ne a duk lokacin da taso shiyasa ake son bawa ya ri'ki imani da 'kaddara cikin kowani hali na rayuwa". Nanne ce tace hakane Ummah Allah yasa mu dace". Dukkan mu muka amsa da " Amin". Baban mu dake tsaye tun da jimawa wada bamu san ma da tsayuwar shi wurin ba murmushi yayi shima gami da jijjiga kansa sannan ya 'karaso ciki da sigar wasa yace da Ummah " kinyi mantuwa". Kallon shi mukayi gaba 'daya da mamaki yayin da Ummah cikin sauri tace " Me na manta kuma?" Sai Baban mu yace " Riba ta mana.....kin manta nike kula da 6angaren Kajin ne?" Dariya mukayi dukkan mu har Ummah sannan muka mi'ke muka bar wurin. ***** Ban san me yasa ba amma tun ranar da naji tarihin Alhaji Baba sai na 'kara jin mutumin ya shiga raina sosai, duk da 'karamcin shekaru na amma hakan bai hanani fahimtar labarin nasu ba. Bazan ta6a mantawa ba ranar wata Alhamis da na je gidan da safe, Ummah ce ta aikeni in kaiwa Alhaji Baba sa'kon gidan sa kamar yadda na saba kullum..... Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 [12/27/2019, 8:16 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* This page is specaially dedicated to👉🏻 *Ummien Diga* naki ne ke ka'dai kiyi yadda kike so da shi...👌🏻 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *20* Koda naje banji muryar Alhaji Baba ba....haka ma sai naga Ammi duk ta zama wata iri kana ganin ta zaka san tana tare da damuwa, ni kaina sai da naji babu da'di a raina cuz ba haka na saba ganin ahalin gidan ba. Tun da Ammi ta kar6i abin hannu na ta ajiye akan dinning gami da fa'din " Zaid in kun gama ga breakfast anan". " toh" yace da ita shikenan ta koma ciki ban 'kara ganin ta ba. Hatta su Saif ma da kansu suka yi serving breakfast 'din su suka ci...har suka kammala ina gidan kuma Ammi bata fito ba. Tashi nayi da niyyar tafiya ganin kowa ba kulani yake yi ba yau 'din. Har zan tafi sai kuma na dawo 6angaren da Zaid yake zaune, nesa ka'dan dashi na tsaya nace masa " wai ina Alhaji Baba yake yau?" " me ya faru?" Yace dani cuz dama ba wani shiri sosai mukeyi da shi kamar da Saif ba. Jin ya sake tambaya ta madadin amsata sai na 'dan ja 'karamin tsaki ciki-ciki, sai na koma gefen Saif a hankali nace " Saif yau me ya samu Ammi?" Kallona yayi kawai batare da ya bani amsa ba sai kuma ya 'dauke kansa yaci gaba da abinda yake yi. " Zakiyi late fa better kije kiyi shirin makaranta yafi miki dan bazan hana kowa dukan ki ba yau kam". Jin hakan ne ya sanya ni ta6e baki gami da mi'kewa na fara tafiya a hankali sai kuma na waigo nace dashi " to ina Alhaji Baba yake ni yau duk ban ganshi ba? Kuma ban gaishe shi ba ma". Saif ne ya bani amsa da fa'din " sassafe ya wuce Azare Yayan mu bai da lafiya". " yayan ku?" Na sake tambayar sa da mamaki dan ni har ga Allah mantawa nake da batun wani wai shi Mu'een a gidan. Da " erh ai baki san shi ba". Saif ya sake bani amsa gami da mi'kewa tsaye ya rataya jakar makarantar sa. Ganin hakan ne ya sanya ni fita nima da 'dan hanzari na na koma gida dan shirin zuwa makaranta ta. Kwanan Alhaji Baba uku a Azare sannan ya dawo gida bayan ya tabbatar jikin Mu'een 'din da sau'ki. Wannan karan kam abakin Baban mu mukaji takaitaccen labarin cewa wai ai 'dan Alhaji Baban ciwon zuciya ke damun sa wanda afa'dar likitocin ma wai da abinsa ya girma cuz ciwon ya da'de a jikin sa amma wannan ne karo na farko da ciwon ya ta6a motsa masa dalilin 6ata masa rai da akayi a school abin sai ya bashi haushi sosai, ga kuma club 'din su da sukeyi ma suka sake 'dora wani a madadin sa da yake ya 'danyi zazza6i na kwana kusan tara sanadin targa'de da ya samu a'kafa wajen wasan Ball shine ya ha'da masa harda zazza6i. Su kuma kamar jira suke dama ya kauce duk sai suka maye gurbin sa da wasu, ya juri wancen bai nuna 6acin ransa ba har suka zana jarabawa.....abinda yafi 'kona ranshi ma shine debate 'din da za'ayi na 'karshen zango wanda duk da yana fama da targa'da'd'den 'kafar amma hakan bai hana shi mai da hankali wajen karancewa da kyau ba tunda jimawa yake bibiyar abin....... abin mamaki ranar ma zazza6i na damunsa amma haka ya matsawa Uncle Ja'afar akan zai zo yaji labarin debate 'din saboda gobene yake saka ran za'a fita na jaha ne kuma, zuwan sa sai ya tarar har an maye gurbin sa da wani tuntuni duk da yake kuwa wancan 'din bawai ya kai sa 'ko'kari bane amma dai mahaifin sa babban mutum ne shiyasa yaron ya maida Mu'een tamkar abokin hamayyar sa a makarantar dan sam baya 'daga masa 'kafa a komai kuma bai isa yace ya kamo 'kafar Mu'een a karatu ba amma haka yake kishi da shi....sai gashi wannan karon yaron na 'daga masa doro dan ya maye gurbin sa wurin debate.....karo na farko kenan da Hayatuddeen yaci nasara a takarar da yake yi da Mu'een. Koda Mu'een ya nemi ji daga bakin jagoran nasu sai yace dashi ai ya 'dauka ko shi 'din ya fasa ne ganin lokaci na tafiya kuma basu ji daga gareshi ba". Inda yayi maganar batare da nuna damuwar komai ba. Mu'een bashi da tsoro shi tun tasowar shi haka Allah yayi sa, dan haka batare da fargabar komai ba yace da malamin " haka mukayi da kai? Ko ni nace maka na fasa?" Idanun sa har jajaye suka koma lokacin da yake maganar dan tsananin 6acin rai. Take sai malamin ya juyo gami da dafa gefen kafadar sa yace " kayi ha'kuri zuwa wani lokacin kaji....me kake so kai kam ma yanzu, me kake nema Muhammad?, i thought duk inda ya kamata ace burinka ya cika akan fita debate to ka kai matsayin, in ban manta ba tun kana junior classes ake fita debate da kai toh ina laifi dan ka bawa wani chance wannan karon? Mahaifin Hayatuddeen da kansa yazo ya ro'ki a sanya Hayat 'din for the first time kaga kuwa da girman sa bazamu bijirewa batun saboda kai ba ko?" Cikin ido yake kallon malamin tankar wani sa'an sa wanda jin wai Hayat ne ma akasa a madadin sa ya ta6a ransa sosai, yasan kuma ba dan komai hakan ya faru ba sai dan cewa mahaifin Hayat 'din mai yaga Naira ne.....kenan 'karfin ikon Naira aka nuna masa. Hafsat wannan abin ya 6ata ran Deen sosai fiye da zaton ki.... " Allah sarki" Hafsat tace cikin sanyin murya yayin da Noor taci gaba da bata labarin da fa' din..... " Hannun malamin ya sau'ke daga kan kafa'dar sa sannan ya juya batare da ya ce da shi komai ba kawai ya koma gida". Haushi sosai abin ya bashi fiye da zaton mai karatu sannan bai sanar da kowa halin da yake ciki ba ko Uncle Ja'afar da ya tambaye shi ma cewa yayi dashi kawai wai ai an fasa ne gaba 'daya. Sai dai ya 'kudura cikin ransa cewa bazai ta6a barin Hayat haka ba sai ya rama, sai ya 'dau fansar abin nan da yayi masa, sai ya 'kuntata masa shima ta yadda zai san cewa bakomai bane Naira ke wakiltan sa, cuz ya san dagangan ne yasa mahaifin sa yazo ya ro'ka masa gurbin sa dan ya kawai ya nuna masa shi ba komai bane, sai dai ta ina....iya tunanin sa bai iya ya tuno abinda zai masa ba sai dai duk da haka bai ta6a cire abin aransa ba........tun faruwar lamarin kuma yake jin 'kirjin sa na yawan mai ciwo lokaci-lokaci...da yake bai san miye bane shiyasa bai damu ba. Ba'a da'de da yin hakan ba sai ya samu labarin cewa anje anyi debate 'din acan Bauchi kuma makarantar su ce ta kasance ta 'daya wai sanadin Hayatuddeen abin mamaki, wanda har hakan ya sanya suka samu manyan kyaututtuka na ban mamaki daga manya-manyan mutane wanda basu ta6a samu ba, abin sosai zai baka mamaki musamman idan already kasan waye Hayat, mutumin da ko a class kusan kowani semester shike 'daukan second to d last position taya zai iya winning debate din jaha harma kuma ya samu lambar yabo? amma kuma abin a fili yake domin sai wanda ya sani ne ka'dai zai fahimci cewa mafiya yawan kyaututtukan sun fito ne daga manyan abokan Mahaifin Hayatu.....wanda a fili zaka fahimci manufar hakan ga dukkan alamu yayi ne dan nemawa 'dan sa suna dan kuma ganin ya goge fuskar da'ki'kanci da aka sansa dashi. Ranar da Mu'een yake da niyyan shigowa makarantar aranar yaci karo da 'kira cikin wayar sa...bai san ko numbern waye ba dan haka koda ya 'dauka shiru yayi........sai ji yayai ance " yane Man har yanzu banga kazo taya ni murna bafa ko ba'kin cikin bai barka ba har yanzu?" Bai 'kara 6ata lokaci ya saurari komai ba kawai ya yanke 'kiran. Har ji yayai dama ya fasa shiga makarantar amma kuma idan yayi hakan kamar ya nuna sarewar sa ne dan haka sai ya gama shiri ya ya tafi makarantar. Amma ko iya zama bai yi ba dan haushi, duk inda ya wulga zancen akeyi, ana yaba 'ko'karin Hayatu bacin shi da suke class 'daya dashi ya san sirrin brain 'din Hayatuddeen tun ba yau ba....amma ya akayi hakan ya faru sam ya rasa. Babu abinda akeyi cikin makarantar banda hayaniya dan haka sai ya yanke shawarar komawa aji kawai ya 'dan duba takaddun sa cuz gab suke da fara exams. Dai-dai 'kofar class 'din su yaci karo da Hayat da wasu abokan sa guda uku, bai yi niyyan tanka su ba domin dama can ba magana ce ke hada su ba...take sai suka fara yi masa dariya suna nuna shi " bana an fa'do". Abinda wani daga cikin su ya fara furtawa kenan yayin da Hayatu yace " an gamu da maza ai...wannan karon ansha kashi.....yaro yaci 'kasa sai ha'kuri". "....na gaba ma duka za'a sha ai Bahbah". Cewar wani daga cikin su. Shiru Mu'een yayi yana kallon bakunan su harma sai ya daina fahimtar abinda suke fa'di...banda 'daci babu abinda yake ji cikin zuciyar sa... Lumshe ido yayi sannan sannan kamar an ingiza shi yayi taku 'daya, na biyu sai gashi tsaye a gaban su, yana bu'de idanun sa nan take sai ya sau'ke su kan fuskar Hayatuddeen yana dariya har a lokacin, dun'kula hannun sa yayi cikin zafin rai ya bashi naushi a bakin nasa da yasa nan take sai ga jini....batare da 6ata lokaci ba sai ya ware hannun ya sau'ke mishi mari 6arin makauniya a duka gefe da gefen fuskar tasa wanda hakan ya faru ne tun kafin Hayat ya warware daga jin sau'kar naushin. Sauran abokan tafiyar tasa duk sai suka yi turus gami da matsawa baya ka'dan, yayin da wasu suka kama baki, wani kuwa bakin ya bu'de cike da mamaki. Yana gama yi mai marin kawai ya watsa hannun sa gami da goge guntun hawayen da suka zubo masa, tafiya yaso yayi batare da ya furta komai ba amma taku uku masu kyau bai yi ba kawai ya fa'di 'kasa warwas a wurin dafe da 'kirjin sa. Mu'een ya kasance ba mai tara abokai bane haka kuma ba mafa'daci bane, rayuwar sa kawai yake yi cikin school 'din with respect tsakanin sa da kowa, bashi da shiga shirgin da ba nasa ba, abokin sa 'daya ne tun shigar sa makarantar wanda shima shigan su SS3 akayi mai transfer zuwa wata makarantar a can Maiduguri dan ya kammala acan....shiyasa yanzu bashi da aboki ko 'daya. Amma da yake tun naushin da ya yiwa Hayat na farko hankalin sauran 'daliban da ke gurin ya dawo kansu shiyasa yana fa'duwan akayo kansa ana salati yayin da wasu ke furta" ikon Allah...ganin cewa shine da bugu kuma shine da kaiwa 'kasa. 'Bangaren Hayat kam haushi kamar ya kake shi, haka ya 'daga 'kafafu fuu yayi hanyar waje da fasheshen baki ya nufi offishin mahaifin sa. Ba'a 'dauki dogon lokaci ba wurin isar da sa'kon abinda ya faru ga headboy 'din makarantar wato Mu'een. Nan take aka zo daga school administration aka 'dauke shi zuwa asbiti da ambulance cikin hanzari.....suna zuwa aka fara bashi taimakon gaggawa musamnan da yake jikinsa da uniform na makaranta. Principal da kansa ya nemi Uncle Ja'afar ya sanar dashi halin da ake ciki wanda nan take shima ya garzaya asbitin wurin Mu'een a rikice. Lokacin da yaji abinda ke damun sa ba 'karamin tashin hankali ya shiga ba, wani 'dalibin ne da suke class 'daya dashi akazo asbitin dan shi sosai Mu'een ke birgesa duk da ba sa wata abota amma duk halin da yake ciki yanada labari. Shine yake basu labarin duk abinda ke faruwa da Mu'een 'din, tun daga kan team 'din su na ball, da batun debate har abinda ya faru tsakanin sa da Hayat last kafin faruwar hakan. Uncle Ja'afar ya damu sosai fiye da zaton mai karatu dan masifa ya fara yiwa malamai biyu dake tare da su a wurin su kuma suna bashi ha'kurin cewa basu san da wannan batun ba sam dan ba 6angaren su bane. " munafukan banza munafukan wofi....an gaya muku shi 'din bashi da galihu ne ko ance muku ba'a son shi, wallahi da Mu'een na fa'da min halin da yake ciki da sai inda 'karfina ya 'kare wajen faranta masa.... da bazan ta6a bari a wula'kan ta min yaro ba, wato dan kunga 'dan mai arzi'ki shiyasa kuka fifita shi akan yaro na ko, to gani gaku wani abu ya same shi kuga mai zai faru tsakani na da ku...aikin banza aikin wofi". Su kam ha'kuri sukayi ta bashi daga nan suka dan'ka shi hannun Uncle Ja'afar 'din sukayi gaba abin su. Sam bai tuna ya 'kira Alhaji Baba bama har sai da dare yayi kusan 'karfe sha 'daya jin cewa numafshin Mu'een ya daidaita kafin ya sami hankalin tunawa da Alhaji Baba take kuwa ya 'kira yayi masa bayani. Ammi taso binsa lokacin da zai taho dan sosai hankalin ta ya tashi da jin abinda ya farun amma Alhaji Baba ya hanata....koda yaje ma bai wani nuna damuwar sa a zahiri ba duk kuwa da cewa ya damun amma daga Allahn sa sai zuciyar sa ne suka san hakan.... ganin yanda Uncle Ja'far gaba 'daya ya fita hayyacin sa ne ya sanya Alhaji Baba 6oye tasa damuwar sa kawai ya dinga kwantar masa da hankali. Allah cikin ikon sa kuwa kafin Azahar tayi Mu'een ya tashi wasai dashi kamar bashi ba sai 'dan abinda ba'a rasa ba. Amma harda 'dan rama yayi a kwana 'dayan da yake kwancen, Alhaji Baba fa'da yayi masa sosai akan rashin ha'kuri da kuma biyewa zuciya da har zai je ya bugi 'dan mutane akan kishin ya maye gurbin sa. Mu'een bai ce dashi komai ba, dan yasan ba Alhaji Baba ka'dai ba kowa ma babu mamaki a haka aka 'dauki abin.....idan ya fahimtar da Alhaji Baba to sauran mutane fa dole akan hakan zasu 'dauke shi......amma shi sam ba nufin sa kenan ba, me yasa zan dake shi dan kawai ya sha gabana akan wani abu? Wannan ai ba komai bane face halin rayuwa, amma ya bar ni da haushi na da nake ji mana dan me yasa zai 'debo wasu banzayen abokan sa da ko kallo ma basu ishe ni ba suzo su tsaya agaba na suna gaya min magana son ransu.....zan iya 'daukan komai amma banda rainin hankali". Cikin zuciyar sa yake wannan maganar yayin da a fili kuwa Uncle Ja'afar ya 'dago ya kalla gami da fa'din " ni gida zani Uncle..." " Baka jin komai ne?" Uncle 'din ya tambaye shi cike da kulawa. Sai ya 'dauke kansa gami da kallon gefen gadon yace " ina jin nawi a 'kirjina da kuma zafi sannan numfashi na na sar'kewa". Da sauri Uncle Ja'afar yace " Bari toh sai Doctor ya sake dubaka tukunna". Alhaji Baba shiru yayi yana kallon su har Uncle Ja'afar ya fita 'kiran Doctor....'dakin sai ya zama shiru gaba 'daya. Mu'een ne ya yanke shirun da fa'din " Ya su Ammi?" Inda yayi maganar a hankali batare da ya kalli fuskar Alhaji Baba ba kamar ba'a son ranshi ba. Ajiyan zuciya Alhaji Baba ya sau'ke sannan batare da ya bashi amsar tambayar tasa ba ya 'kira sunan shi da fa'din " Muhammad!" Cikin natsuwa. 'Dagowa yayi ya kalle shi gami da bashi hankalin sa gaba 'daya. " Dan Allah ba dan ni ba Mu'een ka daina saka kanka cikin irin wannan rigimar kaji, mutane kala-kala ne Mu'een ni nan na ha'du da ire-iren mutane wasu zuciyar su babu Allah ciki dan Allah ka daina cusa kanka cikin ire-iren su, ba nason wani abu ya same ka ko ka'dan...." Cikin 'karfin hali yace " Alhaji ka daina ha'da ni da Allah nifa ban shiga rayuwar kowa ba shine ya ke gaya min magana bayan sun 6ata raina shiyasa na maresa". Alhaji Baba cewa yayi " amma me yasa bakayi ha'kuri ba to a lokacin?" " nima ban sani ba Alhaji". Yace A hankali. " shai'dan ne ya ingiza ka Muhammad shiyasa ka kasa ha'kuri har ka biye masa...." Sallamar Zainab ne ya katse maganar Alhajin inda ya amsa mata sallamar tata gami da mi'kewa tsaye....barka da hanya tayi masa gami da gaishe sa wanda suna gama gaisuwar sai yayi waje. Kallon ta ta dawo dashi kan Mu'een tace " ya jikin naka Mu'een?" " Da sau'ki Anty sai godiya, please kice da Uncle mu koma gida ni banson asbitin nan". Murmushi Zainab tayi gami da fa'din " ai kai da gida sai ka warke". Dai-dai nan su Ja'afar da likita suka shigo bayan su kuma Alhaji Baba ne. Bayan likita ya sake duba shi sai ya tabbatar musu da cewa ciwon sa bai kammala kwanciya ba tukunna sai an 'kara bashi kulawa. Da jin haka sai ya lumshe ido gami da furta " ya salam" cikin zuciyar sa. Haka aka cigaba da bashi kulawa har kwana uku daga nan Alhaji Baba ya koma gida. Dan likita ya tabbatar musu da cewa zuwa jibi insha Allahu za'a sallame shi. Washe garin tafiyar Alhaji Baba ne dismissal letter ya same shi har asbiti, abin takaicin ma wai shine Hayatuddeen ne ya kawo masa cike da izza da gadara, wannan abin ba 'karamin 'kona ransa yayi ba har ciwon sa yaso dawowa sabo. Uncle Ja'afar ne ya dinga kwantar masa da hankali dan ko shi Uncle Ja'afar 'din ma abin ya bashi haushi amma magangunun Alhaji Baba kafin ya wuce jiya su suka hana shi yin wani yun'kuri. 'Bangaren Mu'een kuwa sai ingizashi zuciyar sa take sake yi akan ya koyawa Hayatuddeen hankali....sam baiji zai iya barin sa haka kawai ba tunda har yayi sanadin da aka kore shi daga makaranta.....in ma akan yayi fa'da ne ai Hayat 'din shi ya tunzura shi, kuma in dole ne sai anyi hakan mai yasa sai Hayat....me yasa ba za'a 'kirashi ya kar6a da kansa ba. The following day aka discharging nasu suka koma gida, Mu'een bai sake taka 'kafar sa a makarantar ba dan haushi, Uncle Ja'afar ne yaje da kansa ya kar6o mai transfer dan ya canza masa wata makarantar inda anan ya samu labarin cewa babu wanda ya kori Mu'een daga makaranta, Uncle Ja'afar ne ya ciro DL ya nuna musu sunyi mamaki sosai cuz stamp da komai na makarantar ne amma kuma ba su sukayi ba...su shirin bashi horo ma sukeyi na sati biyu kuma gashi nan suka nunawa Uncle Ja'afar. Uncle Ja'afar ma sai ya sanar dasu wanda ya kai wa Mu'een lettern sai yaga basu nuna wata damuwar komai ba sai ma ha'kuri kawai da suke bashi. Abin mamaki, da wata makarantar ce a yanda ya sani ya san yin hakan babban laifi ne ace 'dalibi ya aikata irin hakan sa6anin wannan da yake ganin kamar babu adalci cikin lamuran su. Wannan dalilin ne ya sanya shi 'kin fasa kar6ar transfern acikin satin ya canzawa Mu'een makaranta dan baya son ya 6ata lokaci a gida dan zuwa nan da watanni biyar zasu fara zana waec. Ba yabo ba fallasa ya fara zuwa makarantar babu laifi tayi masa sai dai bata shiga ransa sosai kamar waccen ba amma a hankali makarantar take shiga ransa musamman da ya fara karantar yana yin makarantar. Mai tsada Uncle Ja'afar ya sanya shi dan har tafi wacce ya baro 'din tsada...shiyasa ya bada himma sosai ga abinda ke gaban sa baya wasa sam da karatun sa kuma har yanzun bai yi aboki ko 'daya ba. ***** Akwai watarana yaje Library karatu sai ya tarar da wasu 'yan mata su uku na faman musu kan pronouncing wani word, kowa da abinda yake fa'da ga dukkan alamu kuma 'kawaye ne su dan haka sai ya 'dauke kansa da zummar wucewa bai yi niyyan tanka su ba. 'Daya daga cikin su ne yaji tace " yauwa Bross dan Allah tambaya". Cak ya tsaya gami da waigowa dan baiga alamun cewa da wani agurin bayan shi ba. Tasowa tayi da text book a hannun ta ta iso gaban shi ta nuna masa tace " ya ake pronouncing word 'din nan please?" Bai san me yasa ba amma sai tsintan kansa yayi da fa'din " ke fa'da inji". ...kamar an batsi bakin ta sai ta fa'da. Karo na farko da ya yiwa wani murmushi a makarantar a hankali sai yace " ba haka bane". Baki ta 'dan tura dan ita duk zaton ta nata ne dai-dai. Sauran ma jin yace nata ba dai dai bane sai sukayi hanzarin tasowa dan suji da kunnuwan su. Batare da 6ata lokaci ba ya sanar dasu yanda ake pronouncing word 'din, ai kuwa take sauran suka fara murna jin cewa nasu ne dai-dai. Yatsa ya sanya kan bakin sa gami da fa'din " shiii kun manta ba'a hayaniya a Libry ko?" Tsit sukayi kamar ruwa yaci su gami da komawa mazaunin su. Shima har ya juya sai kuma ya saci kallon wacce ta fara yi masa tambayar ganin ita bata motsa ba har yanzun. Waro idanu yayi ganin ta kafe a tsayen ga dukkan alamu ranta ne ya 6aci....kallon ta yayi da kyau gami da fa'din " wai fushi kika yi ?" Girgiza kai kawai tayi tare da komawa gurin sauran 'kawayen nata ta zauna. Shima sai ya girgiza kansa ya juya ya tafi can inda hayaniyar su bazata dame shi ba dan yayi karatun sa, amma haka kawai fuskar yarinyar sai yake masa kama da fuskar sani amma ya kasa fahimtar a ina ya san fuskar. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 [12/29/2019, 9:36 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ~Dedicated to👇🏼 Hussaina B. Abubakar~ ~Wannan kam naki ne Mrs Habou~ ~(Sa'eenah) wallah kina sani nisha'di sosai....~ ~Allahu ya bar min ke~ 😘👌🏻 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *21* Bai wani tsawaita tunanin ba balle har ya hana shi sukuni kawai yaci gaba da harkokin sa. Bai kuma kara bi ta kan yaran ba haka bai sake ganin su ba, kamar yadda bai sake tunawa da su cikin sha'anin rayuwar sa ba dan basu ne a gaban sa ba a halin yanzun. Karatun sa kawai ya sa agaba littattafan sa sune abokan sa baya shiga rayuwar kowa cikin makarantar. ***** *Bayan sati 'daya* Zaune yake daga gefen bakin Varandern 'kofar class 'din su yana duba wani handbook fuskar sa sanye da farin siririn glashi, yayin da uniform 'din dake jikin san suka matu'kar amsar fatan jikin sa yafito shar da shi. Wajajen goma da rabi ne dan break akeyi a lokacin hankalin sa sosai ya 'dauku ga karatun littafin, batare da yayi zato ba kawai yaga an 'daura masa wani takadda kan nasa handbook 'din har ya kansance ma baya ganin nasa sai wannan 'din. Mamaki ne ya cikashi na ganin hakan mamakin waye mai wannan uban 'ko'karin da har zai masa haka, dan shi ba saba yin hakan yayi da kowa ba, sai dai yana da ya'kinin duk yadda akayi an sa6a lamba ne shiyasa akai masa hakan, may be kama yayi da wani daban da har yasa aka ga kamar wancen 'din ne. A hankali ya 'dago kansa dan ganin kowaye sai yaga ashe ma mace ce, macen ma kuma waccen yarinyar da suka ta6a hast duwa a Libry last week... ita ce tsaye kansa cikin sakalalliyar fuska take duban sa....da wata 'kawar ta su biyu suka zo. Suan hada idanu da ita sai yaga ta tura baki gaba kamar yanda yaga tayi rannan a Libry, sarai ya gane ta amma sai ya ce da su " me ya faru?" 'Dayar yarinyar ne ta juya ta kalle ta sai ta wani yan'kwana fuska sannan cike da shagwa6a tace da shi " Ayyah Bross tun ranar fa nake ta neman ka ban ganka ba, am bamu assignment na mathematics da yawa ni kuma ban iya ba, kullum sai na ta duba ka amma ban samun ka na kaima Yayah Hayatu shi kuma yace wai bai iya ba ni bansan yanda zan yi ba sai yau na ganka anan". Bai furta mata komai ba illa takaddar tata da ya 'daga da niyyar ganin set 'din da take sai idanun sa ya sau'ka kan sunan ta dake rubuce a bangon littafin da manyan haruffa RAHMA SALIS GIMBA...... yaga an rubuta...Dum yaji zuciyar sa ta tsinke haka kawai bai san dalili ba. Tuno sunan Hayat yayi da ya baro a wancen makarantar wato HAYATUDDEEN SALIS GIMBA..... Batare da ya 'dago ya kalle ta ba ya tuno kamannin su take ya fahimci dalilin da ya sanya yake ganin kamar ya san yanayin fuskar ta a wani guri. Kenan itan blood sister 'din Hayat ne....me hakan ke nufi kenan?" Ya tambayi zuciyar sa. " Please kayi min anjima zanzo nan in kar6a wai gobe za'a yi submitting kaji". Tana gama fa'din hakan ta kama hannun kawar ta suka bar wurin. Bai iya yace da ita komai ba har ta 6acewa ganin sa, sai a sannan ya sake duba bayan littafin SS 2A yaga an rubuta. Gaba 'daya sai yaji jikin sa yayi sanyi, Hayat da yafi tsana a duniya ne yau kuma Allah ya ha'da shi da sistern sa anan, me hakan ke nufi wai, na kasa ganewa ?" Ya sake tambayar kansa...gami da cire gilashin dake manne a fuskar sa. Har lokacin break ya wuce bai iya ya yanke shawarar da ta dace ba, tambayar kansa yake shin yayi mata ne ko kuma ah ah kar yayi....koda bai yi mata solving Assignment 'din ba taci Zero sanadin hakan sam ba zai wanke zuciyar sa daga takaicin da Hayat ya 'kunsa masa ba, dalilin sa aka tono masa ciwon da shi kansa bai san yana da shi ba, dalilin sa yasa ya bar school 'din da yafi 'kauna kaf fa'din jihar Bauchi..bar ma batun abubuwan da suka faru cikin makaranta...taya zan iya yafe masa...taya zan iya mantawa da abinda Hayat ya min cikin kwanaki 'kalilan, a duk lokacin da na kalli kaina cikin makarantar nan na ganni matsayin ba'ko abin na matu'kar sosa raina. Bhu yarinyar sam bata da hali irin na yayan ta, ga dukkan alamu halin su ya banbanta dashi.... Ido ya lumshe cikin zuciyar sa ya furta " ohh Allah help me....ko dan hakan ma yana ganin zai iya yi mata Assignment 'din ba dan komai ba saboda Allah kuma saboda yaddan da tayi da shi. Class ya tashi ya shiga inda batare da 6ata lokaci ba duk ya solving mata Assignment 'din, sannan yabi cikin littafin duk ya duba yaga anan ya fahimci matakin brain 'din ta 6angaren Maths, babu mamaki gajiya tayi da ganin Zero cikin takaddan ta shiyasa ta nemi agajin sa....murmushi yayi sannan ya rufe littafin ya ajiye. Shai'dan ne ya dinga zuga shi game da fansar dake ransa na tsakanin sa da Hayatu, har ma yake ganin kamar Allah ne ya kawo yarinyar cikin rayuwar sa dan kawai ya koya wa Hayatu hankali...sam bai 'karyata wannan tunanin ba, take yayi na'am da hakan ya kuma saki murmushin mugunta na gefen baki....sai dai inda gizo ke sa'kar shine bai san wani irin fansa zai 'dauka ba tunda yarinyar ba sa'ar sa bace balle suyi takun sa'ka, ya dai barwa lokaci....da ya'kinin cewa watarana zai iya tuna kalar fansar da ya kamata ya d'auka wanda Hayatu zai ji ciwon abin sosai, zai kuma san ba komai ne ku'di ke siyan sa ba. 12:03pm ta bayyana bakin class 'din su tana neman izinin shiga, class representative ne ya dakatar da ita sai tace da shi wurin brother 'din ta tazo amsar abu. Sai yace " ta bari ba yanzu ba". Take tayi kalan tausayi gami da fa'din " please mana it's urgent Allah". Sunan brother 'din nata class rep ya tambaya....anan sai tayi shiru tana rarraba idanu cikin ajin, bata san takamamme nan ne ajin ba ko ah ah balle har ta san sunan sa da ko za'a yanka ta bazata iya fa'da ba dan ba sani tayi ba, ita dai 'dazu ta ganshi zaune anan dan haka sai ta cigaba da binciko shi da idanun ta...ko Allah zai sa ta hango shi. Mu'een kuwa yana zaune harda kishingi'da yana kallon duk dramar da suke yi....sam bashi da niyyan motsawa balle ya tanka su so yake yaga iya gudun ruwan ta. " baki san sunan nashi ba kenan?" Class rep ya sake tambayan ta. Sai tace dashi " na manta ne fa". Da mamaki sai yace " U ar not serious sunan brothern naki kika manta?" Hannu ta ha'da kamar zatayi kuka...yayin da class rep ya cigaba da fa'din " may be ma baki san class 'din ba shiyasa kika zo nan, ai da yana nan 'din da yanzu kin ganshi dan haka jeki neme shi ba anan yake ba". Juyawa tayi zata fita da tunanin inda zata kuma zuwa neman sa, amma me yasa da nace masa zanzo nan bai ce min ah ah ba.... " _Rahmah_ ". Tana cikin tunanin tajiyo muryar sa ya ambaci sunan ta. Cak sai ta tsaya gami da waigowa caraf sai idanun su ya sarke cikin na juna take sai ta sau'ke ajiyan zuciya harma bata san lokacin da ta furta " haba Bross... kana jina shine ka 'kyale ni ko?" Cike da shagwa6a tayi maganar gami da 'karasawa inda yake zaune. Bai ce da ita komai ba kawai ya mi'ka mata takaddar ta. Kar6a tayi gami da fa'din " Thanks" tare da hanzarin barin ajin yayin da ilahirin mazan ajin suka bi ta da idanu dan sosai kalar shagwa6ar ta ta birge su sa6anin Mu'een da ko akan sa ma bai sa hakan ba. Wani dake seat 'din gaban Mu'een ne ya waigo yana murmushi yace dashi " Amma sister n kan nan da gani rigimammiya ce ko?" " indeed". Yace dashi a takaice shima 'din yana murmushi kamar gaske. Tun daga lokacin sha'kuwa mai tsanani ya shiga tsakanin Mu'inuddeen da Rahma, tun Mu'een na kaucewa har yazo ya saki jikin sa da ita dan ita komai zatayi sai ta neme shi haka kuma duk abinda ya dameta gurin sa take zuwa, sosai take girmama shi matsayin yayan ta. Tsananin sha'kuwar ta sun ne ya sanya shi fahimtar komai game da ita a haka ya fahimci cewa itan ba sosai suke zama gida 'daya da yayanta Hayat ba. Ta kan zauna gidan kakar ta wani sa'in, yayin da wani lokaci take zama gidan Antyn ta wato babbar yar su dake aure da yaranta uku, lokuta 'kalilan nan take zama gidan mahaifin ta, bai sani ba ko wannan dalilin ne ya sanya halayyar su ta banbanta da Hayat....sam basu kama ta fuskar halayya ba bayaga jini da ya ha'da su. Rahma sanyin hali gareta bata da jan fa'da barta dai da rigima wanda ta saba irin na shagwa6a66u sa6anin Hayatu da yake fitinanne, son rigima, ga son shiga abin da bai shafeshi ba sannan ga shi da uban rashin ha'kuri. Abubuwa da dama ya sani game da ita sa6anin shi da bai ta6a gaya mata komai akan sa ba, banda sunan sa Muhammad da ta sani har yau bata san komai game da shi ba....haka kuma " Bross " da take 'kiran sa da shi har yau bata fasa ba. Da gaske yawanci sun 'dauka cewa 'kanwar sa ce blood sister kamar yadda take fa'da harma wasu mazan kan zo wajen sa da sunan wai suna neman hanya wajen sistern sa ta fuskar soyayya, yayin da yake murmushi kawai baya furta komai kamar yadda bai jin komai a zuciyar sa koda hakan ya faru. Kuma bai ta6a isar mata da sa'kon kowa ba, shi kansa bai san me yake ji game da ita ba, ya rasa me yasa har ya sake mata, shin saboda ta kasance 'kanwar Hayat ne ko kuwa dan sau'kin kanta?" Sam ya rasa dalili 'daya da ya sanya shi. Cikin haka har suka zana waec suka gama, suna fara zana Neco Rahma ta fara 'daga masa hankali da iyayin wai ita bata son ya tafi ya barta ita menene.." Haka dai duk ya rasa kan maganganun nata. Da abin yayi yawa ne a wautar sa sai yake ganin 'kilan hanyar 'daukan fansar sa ce tazo masa cikin sau'ki, Rahma 'kanwa ya 'dauke ta amma ya san koka'dan baya jin ta a zuciya kamar yadda ita ta 'dauke shi, dan haka zai yi amfani da wannan damar yayi wasan 'kwallo da zuciyar ta yadda zai illata farin cikin ta cikin sau'ki sannan ya barta, 'kila idan yayi hakan zaiji sau'ki cikin ransa game da abin da Hayatu yayi masa...harma ya cire abin a ransa. Sanadin wannan tunanin ya sanya shi sakin jiki sosai da ita, yanda take nuna masa zata yi kewar sa haka shima yake nuna mata zai yi fiye ma da yanda ita take tunani, ya kan 6ata lokacin sa sosai tare da ita, ya kula da karatun ta, ya sanya ta farin ciki, duk abinda take so ya kanyi mata shi, sau tari ta kanso ha'da shi a waya da Yayan ta Hayatu amma Deen sai ya'ki amincewa ya nuna mata ba yanzu ba, a hankali ya fahimci irin shimfi'da'd'iyar 'kaunar da Hayatu yake yi mata matsayin ta na 'kanwa agare shi kuma auta duk da yake akwai 'kanne 'yan uba amma Hayat baya ha'da soyayyar da yake yiwa Rahma da kowa. Deen sai ma yaga kamar komai na tafiya masa ne yadda ya kamata, cuz yasan duk abinda zai faru da Rahma to Hayat ne biyu da zai fi jin ciwon abin bayaga mahaifan ta.....kenan Rahma tamkar kibiya ta zame masa da zai harba ta tafi direct izuwa ga fansar ransa. Duk shirin da Deen keyi cikin ransa Rahma bata da masaniya akai ko 'daya kuma bata ta6a tunanin akwai abu makamancin hakan cikin ransa ba. Kafin su kaiga kammala Neco ne mahaifin su Rahma ya samu paralize, barin jikin sa na dama ya daina aiki gaba 'daya sanadiyyan hawan jini. Ranar shi ya dinga kwantar mata da hankali yana bata ha'kuri da kalaman kwantar da hankali har ta daina damuwa sosai. Ba 'karamin tausaya musu yayi ba dan kuwa yasan su Hayatu marayu ne mahaifiyar su ta jima da rasuwa ga shi kuma yanzun abinda ya faru ga mahaifin su. Yanda tausayin Rahma ya shige shi har sai da ya sanya yayi watsi da dukkan mugun shirin sa, gaba 'daya sai yake jin zai iya yafewa Hayatuddeen komai ma sanadin mutunci da karamci irin na Rahma, ga kuma tausayin ta da ya kamashi. Jikin mahaifin su kuwa babu sau'ki sam sai dai ace Alhamdulillah, haka aka dawo dashi gida aka kwantar likita na zuwa duba shi, rayuwar kenan dama, shiyasa ake so ka mori lokacin ka kafin abubuwa sufi 'karfin ka ta yadda bazaka iya jayayya da su ba, duk wani izzar da 'kafafan ka gadarar ka lafiya ce, idan babu ita haka zaka zauna komai sai dai kaga anayi amma idan Allah bai so ba ko tankawa baka isa kayi ba balle har ayi da kai, hakan ma idan ya barka da numfashi kenan, idan kuwa yaso sai ya zare ranka kana ji kana gani baka isa kace miye dalili ba, haka zaka tafi ka bar duniyar daga kai sai ayyukan ka, babu dukiyar, babu gadara, babu izzah balle 'kafafa, duk ka barsu anan. ALLAHU AKBAR RAYUWA KENAN.... ALLAH UBANGIJI KA BAMU LAFIYA MAI AMFANI, KA TSAREMU DA AIKATA MUMMUNA, YAH ALLAH KAYI MANA KYAKKYAWAN 'KARSHE....AMEEEN 〰〰〰 Ranar da ya gama rubuta Neco Rahma har kuka tai ta masa dagaske wai ita son shi take yi kuma bata son ya rabu da ita. Ba 'karamin mamaki yayi ba da jin furucin nata dan bai ta6a kawo faruwar hakan tsakanin su ba.....dan duk wani shirin sa da yake yi cikin ransa ma ya jima da watsar da su. 'Kin bata amsa yayi kawai ya shareta dan ganin kamar shirme take yi, amma yarinyar ta matsa masa sosai tun baya kula ta kan hakan har dai ya fara biyeta amma bawai dan yana jin soyayyar ta cikin ransa ba. Har suyi graduate suka yi bankwana da makarantar Rahma bata janye kan batun soyayyar ta ba. Kamar wasa sai take jan shi zuwa gidan kakar ta suna hira, baya damuwa sam dan kuwa yanzu ya gama makaranta kuma ba abokai ne da shi sosai ba balle ya dinga zuwa wurin su, itan ce dai ne abokiyar shi ita ka'dai shiyasa duk ranar da ta nemi ganin sa ya kan bar duk abinda yake yi ya shirya yaje suyi hirar su da shi sannan ya dawo gida. Wasa-wasa soyayyar sa tayi 'karfi a zuciyar Rahma, yayin da shi a kullum yake yi mata kallon 'kanwar sa, duk kuwa da cewa ya san irin girman soyayyar da take masa amma hakan bai sa ya bata wannan matsayin cikin zuciyar sa ba, har yau bai ji Rahma ta canza daga matsayin 'kanwa zuwa wani abu daban ba agareshi. Bai sani ba ko wannan dalilin ne ya sanya duk iya zaman da zasuiyi dashi bai ta6a jin komai ajikin sa ba ko zuciyar sa. Rahma ce ta fara koya masa ta6a jikin junan su, misali kamar idan anyi abin dariya ta kan kwanto jikin sa tayi dariyar, wani lokaci sukan sha hannu da shi a hira, wasa-wasa har wasu lokutan ta kanyi pillow da cinyar sa idan suna zaune su biyu suna hira. Deen bai ta6a hanata ba, duk kuwa da yasan cewa hakan ba abu ne mai kyau ba, hujjar da ya ri'ke kawai itace na cewa ai bai jin komai ajikin sa. Hakan yasa shima ya 'kara sakin jiki da ita sosai wanda har ya zarce ka'idan addini. Daga ita sai kakar ta suke zama agidan shiyasa idan yazo ya kan shiga har ciki ya gaida kakar sannan su fito haraban gidan ta bayan 'dakuna kan wani dakali su sha hirar su anan. Kaka bata damuwa da lamarin su cuz ta san cewa dokar mahaifin su Rahama iya secondary ne kawai tana kammalawa auren ta zai yi shiyasa kaka bata damu da lamarin su ba, balle da take ganin yanda Deen 'din yake duk sai bata yi tunanin cewa yaro ne shi ba. Deen na da cika ido gashi kuma da ladabi hakan ne yasa kaka tayi zaton ko manemin auren Rahma ne shi shiyasa bata ta6a taka musu birki ba. Balle da jinyar mahaifin su Rahman ya sako ta agaba ma sai ya kasance bata zama sosai, bata nutsu bama balle ta zauna wuri guda....koda bata nan kuwa still a cikin gidan suke hirar su kamar yanda suka saba, duk bayan kwana biyu Rahma take zuwa gaida mahaifin ta, koda ta tambayi Deen cewa shi bazai je ya gaida mahaifin nata bane take sai yace mata " a ah, bazai iya zuwa ba..amma yana yi masa addu'ah kullum, bata damu ba koda taji hakan dan zaton ta ko kunyar zuwa yake ji. ***** Akwai wata rana da kaka bata nan taje can gidan daga nan kuma zata wuce wurin rasuwa kuma bazata dawo ba sai anyi bakwai saboda 'yar uwar tace ta rasun, bayan tafiyar tata sai Rahma ta koma gidan Yayar ta kafin dawowar kakan...wacce itama taje gaisuwan amma bata kwana can ba ta dawo gida. Kwanan Rahma biyu a gidan sai ta fara jin babu da'di cuz bata samun yin hira da Mu'een a gidan bata ma ta6a bari yaje can 'din ba dan tana tsoron Antyn nata. Da kewar sa ta dameta sai ta shirya tace da Antyn nata zata koma gida amma gobe zata dawo. Taso tayi mamaki Antyn dan Rahama ta jima bataje gidan mahaifin su ta kwana ba dayake basa shiri sam da matar baban nasu shiyasa tafiya zama da kaka. Antyn bata hanata ba sai dai tace da ita idan taje banda rigima dan naga kamar yau matar nan a cike take" Antyn Rahama ta fa'di hakane saboda dawowan ta kenan daga can gidan. Yayin da Rahma ta bata tabbacin babu abinda zai faru insha Allahu... Jinjina kai Antyn Rahma tayi. Cikin hanzari Rahma ta shirya ta fito bata 'dauki kaya ko kala 'daya ba illa wayar ta da wata 'yar 'karamar jaka ta fito. " kina nufin haka zakije bako kayan sawa shine har goben?" Antyn Rahma ta tambaye ta da mamaki. Rahma sai cewa tayi " zan biya gidan kaka in 'dauki kayana acan". " Owk...ni dai ki kula please Rahma kinga Daddy ba lafiya gareshi ba balle ya taking side 'dinki kan abu, dan Allah karki shiga harkar kowa ko yaran nan sun miki abu kiyi ha'kuri kinji". " To Anty insha Allahu zan kiyaye". Tana fa'din hakan ne tana tafiya izuwa 'kofar da zata sadaka da waje. Tana fita kuwa sai ta wuce gidan Kaka kamar yadda ta fa'dawa Anty. Dama kuma keys 'din gidan a wurin ta yake dan haka sai ta bu'de ta shiga. Tana shiga sai ta 'kira wayar Mu'een tace dashi yazo tana gidan Kaka. " har ta dawo ne?" ya tambaye ta. Sai tace " erh " a takaice. Batare da wani 6ata lokaci ba ya shirya ya nufo gidan Kaka, sallama yayi a bakin parlour gami da shigowa ciki. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 [1/4, 11:27 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ~Godiya ga dukkan masoyana na ha'ki'ka....ba sai na ambaci suna ba~ ~in kinji aranki ke masoyiya ta ce to da ke nake~ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *22* Tafe yake bisa titi yana driving but 'dayan hannun sa ri'ke da waya yana faman trying numbern ta amma ba'a 'dagawa gaba 'daya hankqlin sa ya kasu gida biyu cuz bai san dalilin da ya hanata daga wayar ba. Bai yi 'kasa a gwiwa wurin cigaba da 'kiran nata ba da tunanin 'kilan ko zai yi sa'a ta 'daga har sai da ya kasance ya jera mata tarin missedcalls a 'akalla guda tara.... Jifa yayi da wayar cike da haushi inda ta tafi can 'kar'kashin 'dayan kujeran dake gefen sa ta fa'da a nan. Bai bi ta kan wayar ba kawai yasa hannu cikin suman gashin dake kansa ya ja hannun nasa zuwa baya tare da 'dora hannayen sa duka biyu bisa sitiyari ya cigaba da tu'kin da yake yi cikin k'agauta. A waje yayi parking cikin hanzari ya fito daga motar ya tunkari mashigar gidan cikin hanzari inda ya isa har bakin parlourn gidan ya shiga ciki da sallamar sa. Wani yaro dake zaune tsakiyar palourn yana wasa da jirgin wasan yara ne ya taso da gudu ya nufo shi yana fa'din " Uncle Hayat oyoyo!....Uncle oyoyo". Ta 'kafa ya iya rungume shi kasancewar tsayin su da bambanci yayin da Hayat ya sa hannu ya shafo kansa gami da fa'din " yauwa my Sabir ina Baby da Basmah?" " Lafiyan su 'kalau.... Basma tana bacci Baby kuma tana 'daki". Sabir ya bashi amsa cike da murnar ganin kawun nasa. Sai yace " Owk, ina Rahma fa". " Anty Rahma bata nan". Hayat sai ya sake fa'din " Anty fa?" " Tana Kitchen". Cewar Sabir. Raba jikin yaron yayi da jikin sa gami da fa'din " je 'kiran min ita". Bai zauna ba kawai ya cigaba da tsayuwa yayin da Sabir ya tafi da dan gudun sa dan isar da sa' kon Hayat. Har Antyn nasu ta bayyana parlourn bai sani kasancewar ya juya baya ne.... " Ah ah ya haka Hayat ko zama kuma bakayi ba". Jin muryar ta tana fa'din haka ne ya sanya shi waigowa ya kalle ta. Da murmushi a fuskar sa ya furta " ina yini Anty"! " Lafiya 'kalau... Ta amsa lokacin da take shirin zama bisa kujera.....sannan ta cigaba da fa'din " ban jima da da dawowa daga can gidan ba ma ai amma kuma ban ganka ba". Yace "Ehh wallahi Anty na 'dan fita ne yanzun ma wani uzuri ke tafe da ni.....ina Rahma taje ne wai ina ta 'kiran layin ta tun dazu amma bata 'dagawa ". " Ai kuwa bata jima da fita ba tace itama zata can gidan amma kafin nan zata biya gidan Kaka ta 'dauki kaya....wani abun ne ya faru?" Ta 'karashe da yi mai tambaya tana kallon sa. Hayat sai ya bata amsa da fa'din " Rannan tazo zata shiga gida muka ha'du na bata wasu takaddu ta shiga min dasu cuz a lokacin ina sauri ne...to kuma ina a bu'katar su yanzu kuma ban ga ni a 'dakina ba bansan inda ta ajiye ba na dudduba ban gani ba kuma na 'kira ta bata d'aga wayar". Anty baki ta ta6e gami da fa'din " su Rahma sarkin shirme yanzun kuma ko ina ta ajiye sai Allah". Juyawa yayi kawai tare da fa'din " bari in duba ta gidan kakan 'kilan can ta tafi da su...." Yana maganar ne yana tafiya izuwa hanyar da zata fitar da shi daga palourn...." bazaka tsaya kasha ko ruwa ba Hayat?" Cewar Antyn nasu batare da ya juyo ba ya bata amsa da fa'din.... " ah ah Anty ina sauri ne". Daga haka bai sake magana ba ya fice daga parlourn. ***** Fitowan ta kenan daga bayi sai ta duva cikin kayan ta ta lalu6o 'yar shimi da wando ta sanya ajikin ta kasancewar yau garin akwai zafi ga kuma matsalar wuta da suke fama da shi a unguwar wanda ba dan hakan ba da zafin ba zaiyi tsanani sosai ba, ruwa ta watso ajikin ta mai d'an sanyi amma still bata ji sassauci ba....'dan karamin tsaki ta sake gami da nufar inda ta ajiye 'yar jakar da ta tazo da ita. Wayar ta ta lalubo daga ciki wanda ta jefa ta ciki tun bayan da ta gama waya da Mu'een 'dazu.....wanda ko yanzun ma ta 'dago wayar ne da tunanin ko ya sake 'kiran ta cuz ta jima cikin bathroom 'din tasan babu mamaki ya 'kirata bata ji ba. Sai dai madadin taga 'kiran Mu'een sai kuma taci karo da na yayan ta Hayatuddeen. Da mamaki take duban wayar ganin tarin missedcall 'din da yayi mata. Ido ta juya cikin ranta tace " zanzo ma har gidan Yaya amma kafin hakan wallahi sai naga mai sanyi na...." Tunanin Rahma ko dan ta kwana biyu bataje gidan bane shiyasa yake neman ta....dan haka take sai ta yanke shawarar 'kiran sa tace dashi tana hanya ma yanzu. Sai dai tana shirin sake 'kiran nasa sai taji sallamar Mu'een daga 'kofar parlour. Ai da sauri tayi gefe da wayar ta fita batare da ta ko kula tabi ta kan yanayin suturar da ke jikin ta bama balle ta tuna da 'kiran Hayat. A haka ta bayyana gaban sa a parlourn fuskar ta cike da murmushin ganin sa. Shi kam idanu ya lumshe a hankali gami da kawar da kansa gefe batare da ya tankata ba ya wuce kujerar da tafi kusa da shi mai zaman mutum biyu ya zauna. Da 'dan hanzari ta taho inda yake tare da zama gefen sa kan 'kafarta 'daya yayin da 'dayar ta sau'kar dashi 'kasa. Da smiling face tace da shi " I thought bazaka zo ba ai dan baka bani wani response mai kyau ba 'dazun...." Takaitaccen kallo yayi mata gami da yin baya ya jinginu da jikin kujera sannan a hankali tamkar ba zai yi maganar ba yace da ita " ina Kaka?" Fari tayi da idanun ta tana murmushin tace " bata fa dawo ba dama...kawai nace tana gida ne dan ina so in ganka dan nasan in kasan bata nan ba zuwa zakayi ba...ni kuma Allah kwana biyun nan da ban ganka ba karka ga yanda na kasa natsuwa........". " Shine kuma dan baki da kunya kika fito a haka ko?" Ya tare da fa'din hakan kuma yayi maganar ne a tsare. Jikin ta tabi da kallo wanda sai a lokacin ma ta gani ta kuma tunawa da yanayin suturar da ke jikin ta....'yar shimi ce da ba'kin skinny da yabi jikin ta ya zauna sosai. Yatsina fuska tayi tace da shi " Share kawai Bross mantawa nayi...kuma ma ai kaga ana zafi sosai yau d'in gashi ba wuta zanfi shan iska a hakan ko?". Deen be sake kulata ba yayi shiru gami da kawar da kansa gefe, dole yake so ya tilastawa idanun sa barin kallon ta amma bai san meyasa yau 'din zuciyar sa ta kasa bashi ha'din kai ba. Ido ya lumshe a karo na biyu a hankali amma still bai daina hango ta cikin runtsatstsun idanun nasa ba wani abu yake jin na fisgar sa. " Bross meke damun ka yau 'din please?" Yaji muryar ta ta daki kunnuwan sa cike da kulawa da marairaita. Sai ya bu'de idanun sa ya sauke su kan fuskar ta gami da fa'din " me kika gani?" " Kamar baka yi farin ciki da gani naba?" " haka nace miki?" Bata bashi amsaba kawai sai ta 'dago hannun ta ta ta6a fuskar sa da niyyar jin yanayin jikin sa cuz bata yadda cewa bashi da lafiya ba a yanda ta ganshin. Amma ga mamakin ta sai taji jikin sa normal ba wani zazza6i yayin da Deen ya cigaba dabin ta kawai da kallo batare da yayi yun'kurin dakatar da itaba. Baya tayi ta mi'kar da 'kafafun ta wanda hakan ya canza mata yanayi daga zama zuwa kwanciya rib da ciki sai ta 'daura kanta da hannayen ta duka biyu bisa cinyar sa.....cikin shagwa6ar ta tace da shi " dan Allah Bross ka gaya min me ya same ka....ko laifi nayi maka?" Shiru yayi mata bai furta komai ba dan abinda yake ji cikin jikin sa ne yake sake hauhawa tsawon da'ki'ka uku yana fama da bugun zuciya sannan a hankali cikin 'karfin hali yace da ita " ta shi Rahma...mu fita waje zafi na damu na anan sosai". 'Kin kula shi tayi sai ma ta sake yin luf tamkar bata ji abinda yace da ita ba, ganin hakan ne ya sanya shi sakin tsaki cikin zuciyar sa dan yau 'din sosai yake jin sa wani iri bai san me yasa ba haka kawai yake jin kansa a tsarge. " Rahma please 'dagani mana...je ki saka ko hijab ne mu koma waje......" Taran shi tayi da fa'din " ni fa banson wajen yau dan Allah mu zauna anan kawai ?" Ganin da gaske take yi bazata 'daga shi ba ya sanya shi janye 'kafar sa daga kar'kashin kanta da 'karfi yana shirin mi'kewa sai ta kamo hannun sa gami da rutsa shi da idanun tace " wai yau meke damun ka ne dan Allah ko ni 'din ce baka son gani...? Sai ga hawaye shar ya gangaro mata wanda ganin hakan ya sanya shi fasa mi'kewan ya koma ya zauna gami da kallon ta da mamaki, yayin da ta cigaba da fa'din.."...ni bansan me kake so inyi maka ba da zai sa ka soni, kullun ni ka'dai ke damuwa da kai ni ka'dai ke son ka...ban isa nayi tambaya ka bani amsa directly ba kullum ina lura da kai, gashi yanzu ma abu na damun ka amma bazaka sanar dani ba so kake yi sai zuciyata ta buga tukunna ko?" Tana gama fa'din hakan sai ta cigaba da kukan ta. Jikin sa sanyi yayi shi kansa ya san baya kyauta mata amma ai yau 'din shi damuwar sa daban ce kuma baya tunanin zata fahimce shi, taya ma zai iya bayyana mata halin da ya tsinci kansa a yau 'din wanda shi kansa ba zai iya fasalta shi ba...a hankali ya kai hannun sa 'daya ya kamo nata hannun sai tayi saurin ri'kewa gami da tasowa ta fa'do jikin sa kamar dama jira take yi sai ta rungume shi. Shima 'din hannu yasa ya 'kara ha'de ta da jikin sa sosai.....sau 'daya ya furta " sorry dear don't cry...owk" A hankali cikin ra'da yayi maganar daga nan shiru ne ya biyu baya illah sautin sheshshe'kan ta dake cigaba da tashi a parlourn. Tsawon kusan mintina uku sannan ya sake fa'din " sorry!" Yana bubbuga bayan ta. Ganin bata da niyyan barin kukan ne yasa shi saurin cireta daga jikin sa tare da fa'din " wai kukan duk na menene haka ba nace ya isa ba?" A 'dan hassale yayi maganar idanun su cikin na juna take kuwa sai wani hawayen ya 'kara sau'ko mata wanda yasa Mu'een saurin rintse idanu ya kuma bu'de su nan take. " Ai dama batun yau ba na fahimci kai baka sona". Ta fa'da hawaye na sau'ko mata. Sai yayi saurin tambayar ta " me kike so Rahma in miki...please ki daina wannan abin ban son kukan nan ni". Bata kula shi ba sai ma sabon sheshe'kan da ta fara wanda ya matu'kar bawa Mu'een haushi da ya rasa yanda zai yi da ita kawai sai toshe mata baki da nashi. Cak kukan nata ya tsaya shima da farko tsayawa yayi cuz bai san me zeyi bayan hakan ba. Amma sabon yanayin da ya fara tsintan kansa a ciki sai ya sanya shi jin tamkar bashi bane da Rahma a wurin, gaba 'daya ya manta a ina yake ya manta matsayin Rahma a wurin sa. Ji yake tamkar ana ingiza shi....a hankali ya maida idanun sa ya lumshe tare da kamo lips 'din ta na 'kasa ya fara 'daura mata sabon darasi. Yana jin yanda ta 'kan'kame masa hannu da jin salon darasin nasa wanda hakan ya 'kara bashi 'kwarin gwiwa wurin kamo harshen ta ya cigaba da abinda yake yi. Shi kansa ji yayi take komai ya kwance masa, fiye da yanayin da ya tsinci kansa 'dazu yake sake ji cikin jikin sa.....wannan dalilin ne ya sanya hannun sa ya kasa tsayuwa wuri guda a jikin ta yana sake wargaza mata matashiyar yanayin ta. Rahama bata hana shi ba sai ma tayi luf a jikin sa tana kar6an darasin da bu'da'dden brain 'din ta yayin da ta tattaro hankalin ta da 'kananun kukan banzan da take yi gaba 'daya ta dun'kula su wuri guda suka koma zuciyar ta. Lokacin da ya tsinci hannun sa cikin 'yar shimin dake jikin ta sosai hakan ya ta6a zuciyar sa sai dai duk da halin da yake ciki hakan bai sa ya gaza fahimtar nata yanayin ba a lokacin, dan wani sassanyar ajiyan zuciya ta saki mai matu'kar shiga jiki. Shi kam sam ya manta da cewar lallashi yake yi dan gaba 'daya tsintan kansa yayi a wata duniya ta daban, ganin kamar shimin nata na hana shi sakewa ne ya sanya shi janye shi zuwa sama gami da bin ilahirin jikin ta da sumba, yana niyyan kaiwa kaiwa 'kirjin ta farmaki da bakin sa ne sai yaji tashin sallama daga 'kofar parlour wanda kafin ma yayi wani yun'kuri har an shi go ciki batare da an jira amsar sallamar ba. Caka ya tsaya da abinda yake yi yayin da zuciyar sa ta cigaba da bugawa da sauri da sauri, salati yake so yayi a zuciyar sa amma ya kasa tsaban ru'danin da ya shiga ganin tun a rana na farko da ya fara ta6a mace Allah ya kamashi..... Bai 6ata lokacin sa wajen yin wani nazari ba ya fahimci muryar waye dan ba yau ya san amon muryar Hayatu ba a rayuwar sa.....yau gashi ga Hayat ga kuma Rahma sannan ga uban kunya da ta lulla6e shi. Bai amsa sallamar ba kamar yanda bai ko motsa daga yanda yake ba sai ya bi jikin nata kawai da kallo sannan a hankali ya rintse idanun sa take ya sake bu'desu ya sau'ke su ajikin ta, batare da yayi kyakkyan motsi ba yaja mata shimin 'kasa ya maida shi yanda yake tun farko sannan cikin 'karfin hali yayi 'ko'karin bawa kansa 'karfin 'karfin gwiwa, take ya danne kunyar da ta kamashi ya juya ya kallo inda yake da tabbacin Hayat na tsaye. Itama Rahma jin ya tsaya da abinda yake yi ne ya sanya ta bu'de idanu a hankali tana duban sa har a lokacin bata ji cewa ba dai-dai suke aikata wa ba haka kuma bata san da zuwan Hayat cikin parlourn ba. Hayat da tun shigowar sa ya tsaya turus yana duban bayan sa da mamaki cuz bai gane waye bane kamar yanda bai san me yake yi agidan ba bayan ance Kaka bata nan, toh ma daga ina yake?" Hayat sam bai yi tunanin tare yake da Rahma ba dayake koda ya shigo ma bai ganta ba dan Deen ya tare gaban sa juyawan da Deen yayi ne ya sanya shi bu'de baki cike da mamaki biyu zuwa uku yake nuna shi da yatsa, magana yake son yi amma ya kasa sai la66an sa dake cin karo kamar zasuyi dambe....a fili zaka fahimci meke shirin faruwa musamnan idan kayi duba da yanayin kusancin dake tsakanin su. Mamakin sa bai wuce na ganin Mu'een cikin gidan kakar su ba, sannan kuma da ganin sa tare Rahma da kuma abinda yake shirin faruwa tsakanin su.....me kenan nake gani? ya tambayi kansa cikin 'kin gaskata abinda idanun sa suka gane masa. Da rawan jiki yake nuno Mu'een da already ya mi'ke tsaye yana gyara hannun longslip shirt 'din dake jikin sa cikin nuna halin ko in kula tamkar bai san me ya aikata ba... " _MU'INUDDEEN_ !" Hayat ya furta cikin ka'duwa. Deen kuwa sai yayi murmushi gami da 'dage masa gira 'daya 'kasan ma'ko shi batare da ya bu'di baki ba ya amsa masa da " Ummn". Hayat kallon sa yayi sannan ya juya ya kalli Rahma da tuni ta mi'ke zaune ta ha'de kai da gwiwa tana kuka a rikice da ganin sa. Rintse ido Hayat yayi yana mai Addu'ar Allah yasa mafarki yake yi ba gaskiya ba ne. Ganin hakan ya sanya Mu'een takawa zuwa gaban sa sai ji yayi an dafa kafa'dar sa tare da fa'din " ai bazaka farka daga baccin ba malam Hayat dan kuwa zahiri kake gani ba a mafarki ba". Hayat na jin haka sai yayi saurin cukumo wuyan rigar Mu'een cike da 6acin rai yana jijjiga shi yace " me kayi mata Mu'een, mecece ala'kar ka da 'kanwata menene tsakanin ku?" Hankalin kwance yace dashi " Ka tambaye ta mana babban Yaya ai gata nan zaune ko" Ko yun'kurin dakatar da Hayat bai yi balle yayi niyyan kare kansa sai ma wani murmushin sa na mugunta da ya aro ya sanyawa fuskar sa yake kuma cigaba da zubawa yana duban Hayatu. Da 'karfi Hayat ya jijjiga shi da zararren idanu yace " tambayar ka nake yi ka bani amsa...me ya kawo ka gidan nan?" ya fa'di a tsawace. Cikin rashin nuna damuwar komai Mu'een ya nuno Rahma dake zaune ta takure tana aikin kuka yace " gata nan ka tambaye ta, babu mamaki zata fini iya yi maka bayani....." Bai gama rufe baki baki Hayat ya 'daga hannu da niyyar sake masa naushi sai yayi saurin dakatar dashi da ri'ke hannun sannan yace " kwantar da hankalin ka abokina abin bai kai nan ba, ga dukkan alamu na fahimci a bakina kafi son jin bayanin....bakomai zan sanar da kai......" Ya 'karashe da sakin hannun Hayatu sannan ya cigaba da fa'din " Rahma 'kanwar ka nada kyau Hayat kuma komai nata mai kyau ne, nayi babban sa'a domin tana so na sosai sai dai 6angare na ni abin sam ba haka yake ba.... dan ban ta6a jin ta a zuciya ta ba.....Hayat da naso cutar da Rahma da na yi hakan tun ba yau ba amma ban aikata ba dan sam ba shine a gabana ba, ban ta6a tunanin faruwar haka tsakanin mu ba kuma ina so kaima karka zarge ni.....idan ka lura bani da laifi musamman idan kana da masaniyar cewa ni 'din mutun lafiyayye ta kowani 6angare taya kake tunanin zan iya juran ganin hakan kuma ya zame min ba komai ba bayan na samu damar da ta dace?". Ya 'karashe da nuno Rahma da hannun sa gami da cigaba da fa'din " ka kwantar da hankalin ka amma....abin bai munana ba ka bayyana kan lokaci in baka yadda ba kuma ka tambaye ta, ni zan wuce nice meeting u once again Hayat....na barku lafiya". Yana gama fa'din hakan ya ratsa gefen sa ya fice abinsa. Har cikin zuciyar sa yake jin babu da'di da faruwar hakan, bai so ace sha'ki'kin ta ya gansu cikin wannan yanayin ba, dan yasan abin bazai masa da'di ba, amma wata 6arin zuciyar sa sai zuga shi takeyi akan yayi dai-dai harma take tabbatar masa da cewa a yau fansar sa ta kammala burin sa ya cika ya 'kunsawa Hayat 'kunshin ba'kin cikin da zai jima bai bar idanun sa da zuciyar sa ba. Yanajin da'di idan ya tuna hakan at the same time kuma yana tuna yafewar da yayi tun farkon tarayyar sa da Rahma....hakan sai yake tabbatar masa da cewa sam bai kyauta ba...duk dama yasan itama da laifin ta amma babban laifin nasa ne, tsintan kansa da yayi a wata duniyar bayan fara kissing 'dinta ya sanya shi mantawa da cewa ba akan dai dai yake ba. Da ire iren tunanin nan ya tunkari bakin titi dan neman abin hawa zuwa gida ji yake tamkar iska na hure shi kamar 'kafar sa bazata juri 'daukan sa ba amma a hakan ya cigaba da tafiya. ' Bangaren Hayat kuwa da idanu yabi bayan sa har ya idasa barin 'dakin take wani 'kululun ba'kin ciki ya turnu'ke shi , hawaye masu zafi na takaici da ba'kin ciki ne ya gangaro masa. Da hanzari ya 'karasa gabanta ya finciko hannun ta ta mi'ke tsaye arazane kafin ta ankara sai jin sau'kar mari tayi mai sa hauka ihu tayi niyyan sakewa sai yayi saurin kwarfan 'kafafun ta ta tafi 'kasa ta bugu da tiles 'din dake shimfi'de a parlourn. Kasa yin kukan ma tayi dan azaba amma hakan bai hana Hayat dukan ta ba. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 [1/5, 11:23 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *23* Cable na cajin lanta ya rarumo ya nufo kanta da shi a fusace, bata ankara ba sai jin sau'kan sa tayi a jikin ta haka ya dinga zabga mata cable 'din cike da 6acin rai. Sai da yayi mata lilis kafin ya barta ya zauna bakin kujera yana hawaye dafe da kansa, yayin da Rahma ta takure a gefe tana kukan ceton rai wanda ko muryar ta ma baya iya fita sosai. "....Rahma me kika rasa a gidan nan, da me aka rage ki da har zaki biyewa wannan 'dan iskan yaron, an gaya miki ana soyayya hakane? Ko angaya miki idan ya gama lalata rayuwar ki zai aure ki? Shiru bata bashi amsa ba sai ya sake fa'din " wama ya baki damar kulashi?.... Yanzun ma shiru tayi tana mai cigaba da sau'ke ajiyan zuciya.....Hayat sai ya sake mi'kewa a fusace yace " tambayar ki nake yi a ina kika sanshi?" Yanda yayi maganar da yanda taga ya taso kanta ne ya sanya ta saurin furta " wallahi Yayah a school muka ha'du.....shine fa wanda nake gaya maka yake min Assignment idan an bamu" Hayat kansa ya dafe gami da juyawa a hankali ya fara takawa....'kuna yake ji cikin ransa ji yake tamkar yayi ta zabga ihu, me yasa sai Mu'een Rahma zata kula? Baya tantama kan cewa Mu'een da gangan ya shiga rayuwar Rahma, kenan yau 'din nan da banzo ba da Allah ne ka'dai ya san abinda zai faru da Rahma". Innalillahi wa inna ilaihiraji'un....ya furta a fili gami da komawa da6as ya zauna bakin kujera......hannayen sa ya ha'da wuri guda yayin da zuciyar sa ta 'dai'dai ta sam ya kasa dai-dai ta natsuwar shi. Batare da ya kalle ta ba ya fara fa'din " Duk haukata Rahma ni bana aikata zina bana lalata yaran mutane....amma me yasa zai min haka? nawa ma Mu'een yake da har zaki bashi dama har cikin gidan ku har 'daki yana lalumar ki Rahma?, kinsan waye shi ne...kinsan miye tsakani na da shi? " Dan Allah Yayah kayi ha'kuri ba zan sake ba...." Tayi maganar da 'kyar cikin kuka. Sai ya dakatar da ita da fa'din " Wallahi Rahma idan kika 'kara biyewa yaron nan koda wasa ko Allah zaki ga abinda zan miki zaki sha mamaki na". Da 'kyar take kuka amma hakan bai hanata bu'den baki cikin kukan tace dashi " dan Allah kayi ha'kuri Yaya wallahi ni ina son shi sosai bazan iya rabuwa da shi ba". " Ya ta6a ce miki zai aure ki ne?" Shiru tayi ta cigaba da kukan ta tana tunanin yaushe ma ita kanta tasamu amsar soyayyar ta ballantana har aje ga maganar aure.....shirun da Hayat yaga tayi ne ya bashi damar cigaba da fa'din......" Mu'inuddeen ba auren ki zai yi ba Rahma gara tun wuri ki cire shi a ranki dan ko yace zai aure kin ma ni ba amincewa zanyi ba, dan haka tun wuri ki cire shi a ranki, idan har a wannan shekarun nasa ya iya ya ke6ewa da mace to kiyi tunanin gaba mai zai aikata dan haka daga yau babu ke babu shi har abada". Yana gama fa'din hakan ya tashi ya fice daga parlourn inda ya barta tana faman sake wani sabon kukan da fa'din " dan Allah yayah kayi ha'kuri wallahi shi ka'dai nake so ni....." Ko sauraren ta Hayat bai yi ba yayi tafiyar sa....haka bai ko sake tunawa da takaddun da yazo kar6a a wurin ta ba. ***** A hankali yake tafiya har ya isa bakin titi shi kansa bai jin da'di har cikin ransa bai san me ya kaishi aikata irin wannan aikin ba. Mashin ya tara ya hau zuwa gida wanda da sau'kar sa ya wuce 'dakin sa batare da yabi ta kan kowa a gidan ba, dana sani kawai yake yi na sanin Rahma da kuma abinda ya aikata sai dai koma me ya faru yafi bawa Hayat laifi domin a ganin sa duk shine sanadi dan da be sashi ya bar wancan makarantar ba ai da bazai ta6a ha'duwa da Rahma ba balle ma har hakan ya faru tsakanin su. Wayar sa ya 'dago ya shiga wurin text kan sunan Rahma ya shiga ya rubuta mata sa'kon kalmomi guda biyar kacal ya tura mata sannan ya bu'de bayan wayar ya ciro sim 'din ya 6alla shi gida biyu ya zuba cikin drawer. Daga haka sai ya fa'da bayi yana mai istigfari cikin ransa. ***** Cikin 'karfin hali ta tashi dan duk jikin ta ciwo yake yi mata da kuka ta shirya ta fito a gidan har ta kulle sai kuma ta tsaya saboda tunanin inda ya kamata taje a wannan halin, tsoron zuwa gidan Anty takeyi dan tasan inta ganta a haka dole ne sai ta tambayi abinda ya same ta inko tace ga wanda ya dake har hakan Anty sai ta nemi jin dalilin dukan to ince mata me? ta tambayi kanta. Can gida kuma tsoron sake gamuwa da Hayat take ji tsoron sake ha'duwar su kar kuma taje gidan cikin wannan yanayin damuwar ta ya fallasa sirrin dake 6oye har ma'kiyan ta su fahimci damuwar ta wanda tasan daga nan kuma babu wani kima da zai rage nata a idanun kowa, domin sarai tasan halin matar baban su ba kau da kai zatayi daga gareta ba kuma kowa idan ya ganta a hakan dole sai ya tambayi dalili. Gara Yayah Hayat tana da tabbacin in dai dan ta shine babu wanda zaiji labarin to in kuwa hakane me ze hana itam ta canza tunani. Wannan tunanin ne ya sanya ta sake bu'de 'kofan ta koma ciki ta je da gudu ta fa'da gadon ta cigaba da kukan ta, ta gwammaci ta zauna anan ita ka'dai har sai kaka ta dawo da taje inda za'a 'kara 'daga mata hankali. Sai da tasha kukan ta son ranta kafin ta tashi tayi alwala ta gabar da sallar la'asar. Wayar ta ta 'dago da niyyar 'kiran Mu'een domin duk faruwar wannan abin bai sa ko 'dis daga cikin soyayyar da take yi masa ta ragu ba. Tana 'daga wayar sai ta ci karo da sa'kon sa saurin bu'dewa tayi ta karanta " _Rahma kiyi ha'kuri ki gafarce ni dan Allah_ " Haka kawai taga ya rubuta, sai ta saki murmushi a fili, wani sanyi taji ya ratsa mata zuciya da ganin sa'kon nasa.....fita tayi daga wurin sa'konnin ta fara gwada 'kiran layin sa amma baya tafiya, wasa-wasa har bayan maghrib bata same shi a wayar ba..... wannan dalilin ne ya sanya damuwar ta 'kara yawaita ta so taji ko muryar sa ne a yau 'din amma hakan bai faru ba. (' *Kalubalen mu iyaye....kamata yayi mu kula da rayuwar yaran mu musamman 'ya'ya mata, bai kamata ace 'yar ki yarinya mace na rayuwa tsakanin gidaje biyu ko uku ba wasu ma zaka ga fiye da hakan....saboda* *gudun ta6ar6arewar tarbiyya dan Allah a kiyaye, ni bance dukka ba.....bhu majority akan samu matsala daga irin hakan idan ba Allah ya gyara ba, ta iya yiyuwa ke kinsa rai tana* *can gidan ne, yayin da suma can 'dayan gidan zasu yi zaton* *tana wurin ki ko kuma 'dayan gidan alhalin ita daga 6angaren ta ba haka abin yake ba... sai ta ringa wasa da hankalin ku cikin rashin sani.....sai* *fa an kula sosai 'ya'yan mu amana ne aka bamu dole ne kuma mu dage wurin kula da rayuwar su da tarbiyar su......kar* *ku manta cewar kulawa da rayuwar yarinya mace da bata ingantacciyar tarbiya zuwa aurar* *da ita ga mijin da ya dace na iya yi maka/ki sanadin* *Aljannah).....* 🤷‍♀ ~BA FA'DA TA BACE NIMA~ 🤷‍♀ Tana idar da sallar maghrib taji ana buga 'kofa da tsoro ta tashi taje jikin 'kofar ta tsaya batare da ta bu'de ba, daga wajen ta jiyo muryar Yayan ta Hayat na 'kiran sunan ta sai taji wani sabon firgici cuz bata san dame yazo yanzun ba. Tsinkewa zuciyar ta tayi da 'karfi kana ta cigaba da bugawa akai-akai......yayin da Hayat ya cigaba da ambatan sunan ta at d same time yana buga 'kofar. Dole badan taso ba ta barwa Allah komai ta tsaida zuciyar ta akan koma menene zai yi mata tana maraba da shi in dai akan Mu'een ne. A hankali ta matsa jikin 'kofar ta sa hannu ta bu'de masa gami da matsawa baya ka'dan, Hayat tsaki ya saki ka'dan gami da fa'din " me kike yi tun dazu inata magana baki amsa ba?" Da rawar murya ta bashi amsa da fa'din " sallah nakeyi". Be 'kara furta komai ba kawai ya sako kai ya shigo sannan yace sai yace da ita " je 'dauko abinda zaki 'dauka da keys 'din gidan ki kulle mu tafi". Da sanyin murya yayi maganar dan haka sai ta tafi 'dakin ta ta dauki kayanta kala biyu tasa cikin jaka sai wayar ta da hijab din da tayi sallar ta fito ta same shi hannun ta ri'ke da makulli. Kar6an makullib yayi yasa ta agaba da kanshi ya kulle ko'ina sannan ya ri'ke makullin a wurin sa suka tafi inda ya wuce da ita gidan mahaifin su. A parlour suka tarar da yaran gidan sama-sama ta gaisa dasu sannan ta wuce ciki....ko mahaifiyar su bata nema ba ta tafi 'dakin ta na gidan......wanka tayi da ruwa mai 'dan 'dumi saboda ciwon da jikin ta ke yi mata sannan ta gabatar da sallahr isha'i daga nan tayi shirin bacci ko abinci bata nema ba. Da kwanciyar tan ma sai da ta sake gwada layin Mu'een amma switch off akace mata. Da tunanin dalilin hakan tayi bacci, Allah ya taimake ta washegari da ta tashi garau taji ta illah kumburarren idanu wanda shima ta san hakan ne lokacin data je gaida matar Baban su ta tambayeta abinda ya sameta da idanun ta suka kumbura take sai tace mata da dare ne kanta yayi ta yi mata ciwo bata samu isasshen bacci ba shiyasa....." sorry" kawai tace da ita gami da ta6e baki sannan ta 'kara fa'din " Jiya ban ma san kinzo ba sai abakin yara naji...kuma yau da safe sai Hayatu yake cemin wai kin dawo kenan gaba 'daya meyasa ko de fa'da kukayi da yayar taki?.Ta 'karasa da tambaya gami da tsare ta da idanu....Rahma sai ta girgiza kai. " to menene ko gajiya akayi da yawace yawacen?" Shiru Rahma tayi mata bata bata amsa ba. 'Kasa-'kasa sai matar tace " ku de kuka sani munafukai kawai". Rahma juyawa tayi ta fita abinta batare da ta amsa ta ba ita kanta matar sai da ta bita da kallon mamaki dan tasan Rahma ba haka take ba sam bata 'daukan 'kananun zagin nan shiyasa kullum basu fiye shiri da juna ba, da wuya tace mata munafuka tayi shiru sai tayi 'kun'kuni yau 'din ta tsammaci jin " mu de ba munafukai bane" daga bakin ta kamar yanda ta saba amma ga mamakin ta Rahma bata tanka ba. Wannan dalilin ne ya sanya ta fahimtar lallai akwai abinda ke faruwa. Rahma kam wurin mahaifin ta wuce, inda ta same shi akwance kamar kullum sai yanda akayi dashi, zuwa tayi ta zauna bakin gadon gami da kamo hannun sa d'aya " Daddy! tace dashi a hankali sai ya tsur mata idanu " Ina kwana Daddy!" Ta sake fadi da rawar murya take kuma sai kuka ya 'kwace mata. Cikin kukan take fa'din " Daddy pls kacewa yaya kar ya rabani dashi, shi ka'dai nakeso Daddy...." Maganar sa bata fita sosai dan bakin sa ya karkace amma ahaka yake 'ko'karin lallashin ta har tayi shiru. Matar Daddy dake tsaye la6e daga bakin kofa ta6e baki tayi jin cewa damuwar Rahman kan soyayya ce. " nasan ai dole akwai wani abu" Tafa'da cikin ranta. Wasa-wasa kusan satin Rahma guda agidan bata samu dama ko sau daya tayi waya da mu'een ba...duk ta fita hayyacin ta dan ba da'din zaman gidan take ji ba, babu wanda zata zauna da shi suyi hira illah mahaifin ta shi kuma a kullum ma ta ganshi ta tuno da lokacin da yake da lafiya sai tausayin sa ya karya mata zuciya, kullum da kuka take barin wurin sa. Gashi yanzu bata da ranar barin gidan dan Hayatu da kansa yaje ya kwaso mata kayan ta gidan kaka Anty kuma yace mata ai Daddyn su ne yace ta zauna kusa dashi. Sosai zaman ya gundureta 'dan hutun da suke yi ma jitayi yayi mata tsayi tsabar yanda ta damu sosai....kuma Hayat ya hanata fita ko'ina. Akwai wani 'dan abokin Daddyn su da ya jima yake binta take wula'kanta shi dan bai mata ba...a 'yan kwanakin taga yana ta matsa mata da 'kira sam tarasa dalili. Bata ma bashi fuska ko awayar ma amma kwatsam ranan wata talata sai gashi ya kirata wai tafito yana harabar gidan su..... Share sa tayi ta'ki fita har kusan mintina talatin sannan taga ya sake k'iran ta 'kin 'dauka tayi sai da ya sake 'kira sannan ta 'daga " ina jiranki fa 'yan mata". Yace da ita tsaki tayi gami da kashe 'kiran. Basu fi mintina biyar bayan hakan ba sai ga kiran Hayatu ya shigo cikin wayar ta. Tana 'dauka shima taji yana fa'din " Amin bai 'kiraki bane?" " ya 'kirani"? Ta bashi amsa da sanyin murya sai yace " to angaya miki bashi da aikin yi ne da ya zo 'din?" " Yayah nifa bance masa yazo wurina ba"! A harzu'ke ya ce da ita " zan sassa6a miki Rahma....baki da hankali ne? Maza ki shirya ki fita yana jiranki saura kuma inji kinyi masa rashin kunya". Da kuka ta fita wurin Al'amin 'din zuciyar ta tamkar zata faso 'kirjin ta. Tana isa gaban sa ko gaishesa batayi ba kawai tace " shine ka 'kira Yayah kayi masa gulmata ko?" Dariya ma ta bashi shikam sai da yayi dariyar kafin yace mata " shine kike kuka dan ance kizo wurina?" " To ni nace ina son ganin ka ne? Kawai zaka sa yayi ta min masifa" " sorry matas ba za'a sake ba na matsu in ganki ne shiyasa kuma nasan in ba hakan nayi ba bazaki fito ba....yanzu ba gashi na ga crying face din matata ba " Baki ta tura gami da fa'din " ni ba matar ka ba ce...." " hmm" kawai yace da ita sai ya tsaya kallon ta yana murmushi. Haushi sosai ya kamata kawai ta juya ta koma gida. Dai-dai tana shiga 'dakin ta sako ya shigo wayar ta _Sai nazo gobe ko matars_ . " _sai kazo din ai mu gani_ " tace afili tare da yin jifa da mayafin ta. A daren ranar Hayat ya sanar da ita abinda ke faruwa.....tayi kuka ranar kamar ranta zai fita ko bacci bata iya tayi ba. Duk iya tsawon tunanin ta ta kasa fahimtar da yaushe akayi wannan kullin, duk abinda ke faruwa tsakanin da Amin abaya bata ta6a sanin cewa Hayat nada labarin ba. Sai gashi kwatsam ya 'dauki ragamar ragomawar rayuwar ta yana shirin dam'kawa Amin nan da sati uku masu zuwa......bacin har ya ha'kura da ita tuntini ya daina damun rayuwar ta ta kasa fahimtar ta inda wannan alakar ta sake 'kulluwa. ....to ya zatayi da 'dimbin soyayyar da take yiwa Mu'een?" Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 [1/6, 7:55 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *24* ........Ba 'karamin so take yi masa ba...gashi ba ta samun sa a waya ko ta nemeshi, a yanzu babu mai kwantar mata da hankali ko mutun 'daya, gara ma 6angaren Amin 'din ta kanji 'dan dama-dama domin shi ba laifi yana shiga rayuwar ta da nashi salon soyayyar bayaga shi kuwa kowa tsareta yake yi, mahaifin ta kuwa ba magana sosai yakeyi ba shi ko taje wurin sa ma ita ka'dai zata 'karaci kukan ta tafito shi kam sai dai yayi ta kallon ta. Abin ma da yafi 'daga mata hankali shine dakatar mata da makaranta da akayi, dan Hayat cewa yayi ko an koma ba zata je ba ita, ranan ma tasha kuka ranar da ya gaya mata hakan, " duk menene dalili wai ? Ta tambayi kanta...wani 6angare daga cikin zuciyar ta ne ya bata amsa da fa'din " kawai yana gudun kar rayuwar ki ta lalace ne Rahma.....wani sabon kukan ta sanya ta 'kudura a ranta cewar da zaran ya dawo zata je ta bashi ha'kuri ta kuma ro'ki alfarmar ya barta ta 'kare ko secondary ma, in yaso sai ta killace zuciyar ta daga soyayya musamman irin ta su Mu'inuddeen da bata da ribar komai daga 'karshe sai asara da tulin abin kunya ma.......tayi al'kawari matu'kar ya barta to bazata sake kula kowa ba hatta Mu'een 'din ma yanzu rabuea zatayi dashi tunda ya barta fiye da sati guda bai 'kara waiwayen inda take ba ko ma yaji halin da take ciki ba f duk ya shareta...sai daga baya ma da tayi tunani sannan ta fahimci cewa ha'kurin nan da ya tura mata mai reshe ne....manufar sa ba 'daya bane. Hayat kuwa duk wasu 'kananun iskanci da rashin kunyar sa ya zubar da su tun ranar da idon sa ya gane masa 'kanwar sa da ake shirin lalatawa da a tunanin sa sanadin sa ne, dan babu mamaki yasan Mu'een da gangan ya aikata hakan...... tun ranar da yaga hakan ya nutsar da hankalin sa wuri guda, ya nemo matakan hankali ya cusa cikin rayuwar sa, balle dama gashi mahaifin su babu lafiya yanzu abubuwa sun sha kansa sosai, komai shi ke jagoranta na daga dukiyar mahaifin nasu jinyar sa, ga kuma sha'anin gida ma. Yanzu ne ya san cewa shi babba ne a gidan, ko waccan takaddun ma da yaje ansa wurin Rahma....takaddun wani test ne da aka yiwa mahaifin nasu sai daga baya kuma ya ga inda ta ajiye cikin 'dakin nasa ashe ranar bai nutsu ya duba da kayu bane....wanda baya raba 'dayan biyu hakan ya faru ne saboda Allah ya so nuna masa rayuwar da Rahma take ciki. Shiyasa ya dage yayi ruwa yayi tsaki wurin ganin ya aurar da ita ga wanda ya tabbatar yake yi mata son gaskiya tun bata san kanta ba....wata 'kila auren ne ka'dai zai zama katanga tsakanin ta da Mu'een. ~Wannan kenan~ ***** Yanzu Rahma bata da burin da ya wuce taga an daina batun wannan auren nan...burin ta taji cewa an fasa aurar da ita, ko kuma taji ance mafarki ne take yi kawai ba gaskiya ba. Sai dai cikin rashin sa'a koda ta yiwa Hayat magana bayan ya dawo gida sai ya tabbatar mata da cewa batun auren ta gaskiya ne da fa'din " bazai ta6a iya sake barin ta a hakan ba...yace haba Rahma...kar ki manta fa da idanu na naga halin da kike ciki ba gaya min akayi ba, ta ya kike tunanin zan zuba ido inga lalacewar rayuwar ki? Mu'een ba aure zaiyi yanzu ba balle ace shi ya fito ya aure ki na tabbata ba auren ki zai yi ba burin sa kawai ya ta6ar da rayuwar ki ne....ko kin fi son in barku ku cigaba da rayuwar dabbobin yafi miki?" Rahma 'kasa ta sake yi da kanta sosai bata iya ta bashi amsa ba. Shima sai ya jijjiga kansa sannan ya cigaba da fa'din ....." Darajar 'ya mace shine kafuwar mutuncin ta Rahma ki ringa tunani kafin ki aikata wani abin domin wani lokaci mutun kan manta da dacewar abu sai bayan ya aikata shi wanda in yayi wasa zai 'kare kaf 'din rayuwar sa ne yana me dana sani wacce bata da amfani sam, kuma kinga Daddy bashi da isasshen lafiya a yanzu so bazan so in 'kara masa wani ciwon akan wannan ba gaskiya shiyasa kawai na yanke wannan shawarar dan bana so watarana yayi kuka dani cewar ban kula da ke ba lokacin da babu idanun sa.....sannan kuma na 6oyewa kowa dalilin taso maganar auren gaba 'daya saboda in kare miki mutuncin ki Rahma.....ko kaka da su kawu shafi'u ma basu san ainahin dalilin ba, dan haka kije kawai ki cigaba da shiri...Amin na sonki sosai kuma na san zai kula da ke da amana". Yana gama fa'din hakan yayi gaba abinsa....ya barta tana zubda hawaye. Rahma ji tayi tamkar tayi ta ihu saboda takaici, ga kunya ga haushin sharetan da Mu'een yayi ga shi kuma ance ba za'a fasa auren ba kuka take jin yi sosai amma babu amfani sam...bazata iya watsawa Yayan ta 'kasa a ido ba dan ya rufa mata asiri shima, dan haka dole ta sanyawa ranta salama gami da bawa kanta ha'kuri da 'ko'karin cusawa zuciyar ta kar6an 'kaddarar auren da hannu bibbiyu...kodan ta faranta ransa ta kuma nuna masa cewa wancen abinda ya farun 'kaddara ne ba halin ta bane. Duk 'ko'karin da matar baban su tai tayi wajen gano babban dalilin da ya tado batun auren Rahma tayi amma bata samu abinda take so ba dan kuwa Hayat bai gayawa kowa ba daga shi sai zuciyar sa ne ka'dai suka sani, sai dai a kullun yana sake ro'kon Ubangiji akan Allah yasa daga iya abinda ya gani 'din babu wani abu daban, Allah yasa bai riga ya illata rayuwar ta ba abaya... kamar yanda yace bai aikata ba 'din Allah ya sa ya kasance hakan 'din ne gaskiya....Allah ka 'kara karemu da iyalan mu daga sharrin dukkanin masu sharri....AMEEN" Wani sa'in ya kanji haushin Mu'een sosai a zuciyar sa yayin da wani lokaci haushin kansa ke kama shi, sai dai lokuta da dama yafi bawa Rahma laifin kacokam, dan duk ta inda ka kewaya zaka samu itace da laifi...ta sake mai da yawa, ta bashi fuskar shiga gidan su kai tsaye, har ta iya fitowa gaban sa da irin wancan shigan, abu mafi muni ma shine da har ta barshi ya ta6a mata jiki, idan ya tuna hakan abin na bashi takaici sosai fiye da zaton mutun Hafsat...." Girgiza kai Hafsat tayi cikin tausaya tace " ai babu da'di irin wannan abin Hudah, bazaka ta6a sanin ciwon sa ba sai abin ya same ka". " gaskiya ne " cewar Nuree sannan ta cigaba da fa'din....." shiyasa Hayatu yake jin bai ga wani dalilin da zai hana shi aurar da ita ba adai dai wannan lokacin sai dai in ikon Allah. Tsakanin sa da Mu'een kuwa bai ma san me ze ce ba, kawai ji yake tamkar ha'duwar su da shi na gaba ba zai yi kyau ba, me yasa ze bi 'kanwar sa? ai in fansa yake son 'dauka ni ya kamata ya tunkara ba Rahma ba.... me yasa sai ita? Ai namiji sai namiji matsoraci ne ka'dai ke maida fansar sa ta koma kan mata...a fa'dan Hayatu kenan. ***** Kwanaki na 'kara matsowa yayin da duk kwanan duniya idan Rahma ta tuna bikin ta ya kusa sai taji haushin Deen ya lullu6e ta, da abin yayi yawa har sai ya riki'da ya koma tsana, ko sunan shi bata son tunawa, da gaske ne ashe da ake cewa akwai 'yan used nd dump cikin maza, ita dama ba a riga anyi using 'din ba ma gashi anyi dumping 'din ta, kenan da a wancan ranar ya samu dama ya shige ta ma da shikenan shi kam gaba ta kaisa....me yasa ma na biye masa ne, me yasa ban hana shi ta6a jikina ba? Banza harda ta 6a min...." bata 'karasa ba taja tsaki " mtheew" cike da takaici gami da mi'kewa, haushi sosai take ji har cikin ranta musamman idan tana tuna touches 'din sa she can deny it abin ya kasa barin kwanyar ta....yana abu a nutse cikin sanyi ga dukkan alamu ya 'kware ta wannan fannin dan akwai shi da tsayawa a zuci....ba 'karya tasan gayen ya ha'du... " " Allah ya isana ma wallahi" tace afili....irin su ne wa'danda ake cewa shiru-shiru munafukai ai...'dan iska mayaudarin banza mai fuska biyu". Tana cire kaya take wannan tunanin wanda tana gamawa ta fa'da wanka. ***** Shima 'din ta 6angaren sa abin ba sau'ki, domin damuwar sa 'kara yawaita takeyi a ko wani lokaci musamman idan ya tuna abinda ya shiga tsakanin su da Rahma, hoton surar jikin ta ya kasa barin idanun sa, tunanin sa da zuciyar sa gaba 'daya. Sai abin ya zame masa tamkar cuta, a kowani lokaci sabon yanayi ke sake ratsa shi a duk lokacin da ya tuno da surar jikin ta, bai ta6a sanin haka yanayin sa yake ba sai da wannan lamarin ya faru. Duk iya 'ko'karin da zai yi na ganin ya raba kansa da wannan damuwar abin ya faskara, gashi dai yayi wa kansa katanga da Rahma tunda ya karya sim card 'din sa, ya san ko ta nemeshi bazata same shi ba kuma ba komai ta sani akan sa ba bayaga suna da lambar wayar shi....shi kuwa yayi al'kawarin ba zai sake kai kansa wurin ta ba, ba zai sake shiga rayuwar ta ba dan baya so ya sake yin wasa da hankalin ta karo na biyu. Batun yau ya san irin girman soyayyar da take yi masa ba, shiyasa ma wasu lokutan yake 'ko'karin bata kulawa koda kuwa zuciyar sa ba hakan take so ba, ko ha'kurin da ya tura mata a text ma yayi ne mai manufa biyu duk da yasan zai yi wahala ta fahimce shi amma shi yasan bai kyauta mata ba ta 6angare da dama shiyasa ya bata ha'kuri.... Ya yaudari zuciyar ta da soyayyar 'karya daga 'karshe kuma yaso lalata rayuwar ta a lokacin da yasan cewa bazata ta6a 'kin amince mishi ba...dan tana wa soyayyar ta fadanci ne a lokacin, yana da ya'kinin ko me zai yi da Rahma a wancan lokacin bazata 'ki amince masa ba.....ya kan godewa Allah ma da ya jefo masa Hayat a dai-dai lokacin kafin yayi aika-aika...wata 'kila Allah yayi hakan ne dan ya kare su daga aikata ba dai-dai ba. Amma duk da haka moment 'din ya kasa barin tunanin sa har ma yana barazanar hana shi sukuni. Uncle Ja'afar da kansa sai da ya fahimci cewa a 'yan kwanakin nan Mu'een ba dai-dai yake ba ya kuma tambaye sa dalilin damuwar sa amma bai ce da shi komai ba baya ga " ba komai" bacin 'karara idan ka dube shi a fili zaka fahimci cewa yana tare da damuwa. Tunanin Uncle Ja'afar ko Jamb 'din da bai samu ba ne yake damun sa a zuci shiyasa ya yanke shawarar yi mai registern Computer certificate ya fara da shi na rage lokaci kafin wata shekarar ya 'kara rubuta Jamb 'din...sai dai kuma kafin hakan sai yaga dacewar kaucewar Mu'een 'din saboda gudun abinda yawan tunanin nasa zai haifar. Wannan dalilin ne ya sanya uncle Ja'afar yanke shawarar gara ya tafi yaje ya wurin iyayen sa ya 'dan huta babu mamaki ma harda ka'daici ke damun sa....Zainab na jin hakan tayi na'am da batun dan ko itama yanayin nasa na damun ta. Shi kansa da Uncle Ja'afar ya sanar da shi shawarar da ya yanke yaji da'di sosai, har hakan ya bayyana murmushin sa a fili. Ko da Uncle Ja'afar yayi masa batun canza layi da yayi ma sai cewa yayi ai wancan wayar ne ta fa'di shiyasa...( dayake lokacin da zai canza Sim 'din harda wayar duk ya ha'da ya canza wata). " Ai da ka dawo da lambar taka Mu'een ba naga ana welcome back na simcard ba?" Uncle Ja'far ya tambaye shi..sai yace " ehh ya sani kawai bai san damuwa ne shiyasa kawai ya sayi sabo. " hmm" kawai Uncle Ja'afar yace daga haka bai 'kara magana kan batun wayar ba ya 'kyale shi tunda hakan yafi so. Kwanaki biyu bayan hakan Mu'een ya shirya ya wuce Shuwarin gidan mahaifan sa cike da murnar sa a zuci. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *25* " Allah sarki....ai dole yayi murna zaije yaga mahaifan sa". Cewar Hafsat dake zaune tana kallon Nuree. Noor kuwa " Hmm"  kawai tace gami da daidaita zaman ta, kafin ta sake yin wata maganar sai suka jiyo tashin 'kiran sallahr isha'i. Take sai Hafsat tace " Ikon Allah...ashe lokaci yaja har haka, muyi sallahr tukunna sai ki 'karasa bani labarin kafin Safwan ya dawo ko?" Nuree bata furta mata komai ba dan haka kawai sai Hafsat ta mi'ke ta shiga bayi dan 'dauro alwala. *****          'Bangaren Deen kuwa...har yanzun bai farka ba  da yake ma anyi masa allurar bacci shiyasa abin ya 'dan ja lokaci.   Safwan ne dai hankalin sa ya kasa kwanciya dan allurar baccin ba mai nawi akayi masa ba, in har dan allurar ne to bazai wuci 1hr ba zai farka amma sai gashi kusan 3hrs amma ko motsi bai sake yi ba, sosai Safwan ya kasa natsuwa da hakan shiyasa ma tun fitar sa daga 'dakin da aka kwantar da Jasmine bai sake dawowa ba, yana can yana zirga-zirga tsakanin Deen da Sani mura'din sa kawai yaga farkawar Deen amma abin ya faskara, dan ma kar Hafsat tayi masa zancen komawa gidane yasa tun fitar sa daga 'dakin bai dawo ba in da suke ba, dan harga Allah shi bai jin zai iya tafiya ya bar Mu'een cikin wannan halin saboda amincin dake tsakanin su ga kuma Alhaji Baba da yace ya kula masa da su kafin isowar sa gobe....burin sa ya samu jin dai-daituwar lafiyar Mu'een 'din kafin ya koma gida. 〰〰〰      Jasmine ma bacci take yi har yanzu, koda Hafsat ta 'dauro alwalar ta fito ma bata nufi wurin dadduma ba sanadiyyan ganin Noor gaban gadon da Jas ke kwance, tsaye taje tayi a kanta sannan a hankali kuma sai ta koma ta zauna gami da ta6a jikin Jas 'din, cikin sa'a sai taji zazza6in jikin tan ya sau'ka ba kamar 'dazu ba. Ajiyar zuciya ta sau'ke mai sanyi gami da fa'din " _Alhamdulillah_ " cikin zuciyar ta, ji take tamkar ta 'daukewa Jas ciwon ya dawo kanta, amma tasan hakan ba mai yiyuwa bane.    Iska ta sake furzarwa daga bakin ta a fili ta furta " Allah zai saka miki Baby...Allah ya isan miki".   Hafsat dake tsaye daga can gefe ne ta 'karaso gami da dafa kafa'dan ta cikin sanyin murya tace da ita " kiyi ha'kuri please Hudah ki fawwalawa Allah komai...nasan abin da ciwo amma ya zamuyi 'kaddarar nan dai ya kamata ta kasance a koda yaushe cikin zu'katan mu matsayin mu na musulmai masu kwa'dayin kasancewa cikin za6a66un Allah masu imani...in har muna son samun wannan kusancin kuwa dole sai mun sanyawa ranmu dangana da komai zai faru na rayuwa"    Nuree kallon Jasmine ta sake yi, batare da ta furta komai ba kawai ta kusanta fuskar ta izuwa fuskar Jas ta sumbaci goshin ta cikin ranta ta furta " speedy recovery mamana" sannan ta mi'ke tsaye ta shige bayi. Yayin da Hafsat ta bita da idanu har ta 'karasa shigewa bathroom 'din kana ta girgiza kanta cike da tausayi ta wuce kan dadduma ta tada sallahr isha'i. Nuree bata fito daga bayin da wuri ba, cuz lokacin da ta fito ma har Hafsat ta idar da sallahr tana 'ko'karin gyarawa Afrah kwanciya.... 'Karasowa tayi ta zauna kan kujerar dake ajiye a wurin yayin da Hafsat ta koma kan daddumar ta zauna ta zuba mata idanu gami da bata hankalin ta gaba 'daya...." ina jin ki" Hafsat tace a hankali.       Noor kuwa sai ta sau'ke ajiyan zuciya cikin sanyin jiki sannan ta cigaba da fa'din......"       ♾ Washegari da safe da nazo sai na tarar da Zaid zaune a parlour ya baje yana zane inda ya bada dukkan hankalin sa kan zanen kinsan zanen Intro- Tech na bu'katan natsuwa sosai. Ni kuwa tun shigowa ta hankalina ya koma kansa shiyasa ma ina bawa Ammi sa'kon da na kawo kawai da sauri na na nufo inda yake zaune nima na zauna daga gefen sa kan 'kafaya 'daya....nace dashi" Zane kaka yi ne Zaid?" Kansa 'kasa ya bani amsa da " a a caca nake bugawa"! batare da ya ko kalle ni ba. Ban damu da jin irin amsar da ya bani ba sai na sake cewa da shi " Ina cacar take to nima zanyi". " Bansani ba". Yace da ni a takaice a kuma 'dan harzu'ke.    Yatsina fuska ta nayi gami da jan guntun tsaki sannan nace " Allah kai Zaid 'din nan ka fiya masifa...daga tambayar ka shikenan zaka fara yi min ihu?" Sai yanzun ya 'dago kansa ya kalleni, idanun sa cikin nawa yace dani " to ke 'din makahuwa ce da ba ki ganin abinda nake yi ne?" Shiru nayi na cigaba da kallon littafin nasa, shima 'din bai sake furta komai ba haka ya cigaba da zanen sa bai sake bi ta kaina ba ma. Ban gushe ba ina zaune a wurin har sai da na dangana hannuna da littafin nasa Zaid sai yayi saurin bige min hannu yace " karki dameni ni dallah". Ban damu ba sai ma na sake fa'din " kawo to in tayaka". Cike da masifa yace " see u..an gaya miki suyan waina ne da zaki ce in baki ki tayani......?" Ban ko bi ta kan maganar da yake yi ba cuz tun kafin ya rufe bakin sa na wafce takaddar na mi'ke da gudu nayi hanyar waje.   Kafin Zaid ya ankara sai gani yayi bana gaban sa haka ma littafin sa....da hanzari ya tashi ya bini a harzu'ke yana fa'din "Ammi kin ganta ko?" Nima ina cikin gudun sai nace" ai tayaka zanyi..."     Ban gama rufe baki na ba kawai naji...Kau... nayi karo da abu wanda tun kafin in ankara in gane da me nayi karon sai kuma naji sau'kan mari saman kuncina daya matu'kar gigita min lissafi har ya sanya ban ma san lokacin da na yada takaddar ba na dafe fuskata gami da yin baya ka'dan na 'daga kaina sama na kalle shi.    Gani nayi ya wani ha'de rai sosai tamkar shi aka mara ba ni ba. Kwa6a fuska ta nayi nima gami da 'kif-'kif da idanuwa na da suka cika taf da hawaye sai dai basu gangaro ba. " Non-sence" naji yace kawai tare da wucewa ya bar gurin direct ya nufi table 'din cin abinci. Ni kuwa sake juyawa nayi na bisa da idanu har ya isa ya zauna ban daina kallon sa ba, shikuwa koda wasa bai sake kallon inda nake ba...... ji nake tamkar in bishi in rama marina amma tsoro nake ji, cuz ban san shi ban kuma ta6a ganin sa a gidan ba haka kuma ban tuna cewa su Zaid da Saif nada Yayah ba balle inyi tunanin ko shine.   Zaid da tun 'dazun ya ja yayi turus shima a hankali ya 'karaso ya 'dauki littafin sa gami da fa'din " Allah shi 'kara". Daga haka ya juya ya koma ciki abinsa daga inda yake ya mi'kawa wancan 'din gaisuwa da fa'din " ina kwana Yayah?" Da " lafiya " ya amsa shi a takaice batare da ya ko kalli Zaid 'din ba. Haushi ne sosai ya kamani bayan jin furucin Zaid 'din, take sai hawayen na da suke ma'kale suka 'karasa gangarowa....da gudu na wuce na tafi wurin Ammi dake kitchen ina kuka.   Sai lokacin da nazo wucewa ne kafin ya 'dago ya kalle ni gami da sakin tsaki sannan ya koma ya kishingi'da akan kujerar harda lumshe idanu.   Ina shiga sai na rungume 'kafafun Ammi ta baya ina kukana.    A rikice Ammi take fa'din " Subhanallah! menene ya faru? Me akayi miki? Ban tankata ba kawai na cigaba da kukana, yayin da Ammi tayi 'ko'kari ta cire ni daga jikin ta sannan ta sake tambaya ta " wa ya ta6a ki?" Cikin kukan na bata amsa da fa'din " wani ne ya mare ni"! Ido ta 'dan zaro gami da fa'din " mari dai? A ina yake?  me ma ya ha'da ki dashi da zai mare ki?" Da murya kuka na bata amsa da fa'din " Ni ban masa komai ba kawai dan na 'dauki takaddar Zaid shine mukayi karo ya mare ni" Inda na 'karashe maganar tawa da sheshsh'ka. Ido Ammi ta lumshe gami da girgiza kanta gefe da gefe a hankali ta furta " _MU'EEN_ ". _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *26* Hannu na ta kama da alamar rarrashi take fa'din " sorry daina kukan i ll slap him too...zan rama miki marin ki bar ni da shi kinji?" Kaina na 'daga sama alamar " to" sai ta sake fa'din " yauwa Hudah ta...." Juyawa nayi na kama hanyar barin kitchen 'din da fa'din " zan je in yi shirin makaranta Ammi". " To adawo lafiya" tace min gami da juyawa ta cigaba da aikin ta.        Ranar ma ko gaida Alhaji Baba ban tuna nayi ba kawai na nufi hanyar da zata sada ni da barin parlourn batare da na sake kallon koda  inda suke ba daga shi har Zaid 'din gaba 'daya. Bayan fitata ne Ammi ta zo ta 'karasa shishshirya musu abincin, inda anan take yiwa Mu'een da har a lokacin yake kishingi'de a wurin fa'dan mari na da yayi. Murmushi yayi mata kana batare da damuwar komai ba yace mata" wai dan Allah Ammi ina kika samo wannan yarinyar da sassafe haka?" " Ina ruwan ka". Ammi tace da shi  sannan ta sake fa'din " ni dai kar ka kuskura ka sake dukan min 'ya bana so"!...sassafe yarinya bata karya da komai ba sai ta karya da mari....idan kai aka yiwa hakan zaka ji da'di ne?....shiyasa nake son 'yan biyu na wallahi cuz duk iya wasan da zasuyi agidan nan bazaka ta6a jin sunyi duka ba......"       Rausayar da kansa yayi gefe ganin da gaske Ammi ke masifar an ta6a yarinyar da be san ta bai kuma san me take yi agidan da wannan safiyar ba.          Taran masifar tata yayi da fa'din " kai Ammi na sorry...ni dai abani abinci inci....yunwa nake ji". Ya 'karashe da yamutsa fuskar sa. " Je yiwa Alhaji magana to...". Cewar Ammi Sai yace " na shiga gaida shi ma na tarar baya nan...ina ya tafi da wannan safiyar haka?". Ya 'karashe mahanar tasa da tambaya.                    Kai Ammi ta dafe gami da fa'din " ups na manta ai, yaje wurin ta'aziya ne amma bazai da'de ba zai dawo". Bai damu ba sai ma yasake fa'din " Ni dai abani breakfast please Ammi"! Murmushi Ammi tayi tare da jan kujera tana shirin zama tace da shi......" sai yarana sunzo tukunna"        Mu'een sai ya 'dan ha'de fuska gami da fa'din " haba Ammi...ni 'din bare ne ba 'danki ba?, Allah zanyi fushi fa....". " Zama ka sa'k'ko ai..." Tace tare da juyawa ta kallo 6angaren da Zaid yake zaune  daga can tsakiyar parlour tace da shi....." Zaid 'kira 'dan uwan ka kuzo kuyi break.... time is running". Mintina uku basu cika ba sai gasu sun fito atare, Saif already har yayi shirin sa yayin da Zaid bai shirya ba har yanzun.      Da kallo Mu'een ya bisu dukkan su inda ya sau'ke idanun sa kan Zaid dake shirin zama yace da shi " me yasa baka yi shiri ba kai har yanzu". Kallon sa Zaid yayi sannan ya bashi amsa da fa'din " Assignment nake yi ne Yayah shiyasa". " Assignment kake yi ko kuma wasan banza, ba kaine na ganka kuna guje-guje ba 'dazun?" Zaid cewa yayi " Takkadda ta ta 'dauka min fa shine nabita in kar6a ba guje-guje muke yi ba". 'Dan neman sai ya sake fa'din " me yasa kuma sai yanzu zakayi Assignment 'din...tun jiya me kake yi?" "Mantawa nayi sai yau da asuba na tuna". " Yayi maka kyau ai Zaidu dama ai kai bakajin....." Ammi ce dake gefen sa ta take mai 'kafa wanda yasa shi dakatar da maganar yayi shiru tare da juyawa ya kalle ta da sauri. Ammi kam tsaye ta mi'ke tana fa'din " ni ya isa haka masifar...ka barmin yara suyi abinda ke gaban su su wuce school...kai akwai wanda ya fika rashin ji ne?" 'Dan 6ata rai yayi yace " Ammi ni kuma?"...da alamar tabbatarwa Ammi ta jinjina kai gami da fa'din " Ehh mana waye kuwa banda kai"....Ciki take murmushi dan tasan he may be angry. Ai kuwa sai ya ha'de gira, sosai ya 6ata rai shi adole Ammi ta yarfa shi gaban 'kannan sa.    Dalilin hakan ya ja baki yayi shiru...murmushi Ammi tayi a fili, haka ma Saif da tun 'dazun yake binsu da idanu, sai a lokacin kuma ya bu'di baki ya gaida shi. A takaice ya amsa masa...batare da ya kalle shi ba...sai ma ya 'kara shan kunu. Saif be gaida Ammi ba a lokacin ga dukkan alamu ya riga ya gaida ta tun 'dazun. Da yake Ammi ta riga ta san ra'ayin 'yan biyun ta sai tayi serving nasu ta tura musu gaban su gami da fa'din " oyah hurry up kar ayi late..." Duk abinda take yi Deen na binta da idanu a kishingi'den da yake amma bazaka ta6a lura da hakan tashin farko ba.         Tana gama sallaman su Saif sai  ta dawo da kallon ta kan Mu'een tace da shi " me zaka ci?" Kunun da yaga ta zubawa Saif ya nuna mata da hannu sai ta zuba masa shima...." sai kuma me?" Ta sake tambayar sa. A hankali yace " ya ishe ni ma wannan 'din". " owk tace gami da tura mai roban sugar gaban sa. Sosai yaji da'din kunun ya kuwa shanye duk wanda Ammi ta saka masa, 'dan fushin da yayi ne ya hana shi bu'dan baki ya yaba mata a zahiri.....amma 100% yaji yayi masa.          Daga shi kuwa be 'kara cin komai ba ya tashi ya bar table 'din.                  Suma su Saif na kammala break fast 'din sai suka hanzarta 'karasa shirin su suka wuce makaranta.    Koda Alhaji Baba ya dawo bai same su agida ba da yake sai kusan 'karfe tara ya dawo gidan so a lokaci, sun da'de ma a makaranta.                 A harabar gida ya ha'du da Mu'een sai suka dawo ciki tare suna 'dan ta6a hira.        Anan Alhaji Baba ke fa'din " ai da har zan tashe ka muje ta'aziyar tare amma danaga kamar baccin gajiya kake yi kawai shiyasa na barka nai tafiya ta". Mu'een kam cikin ransa yace " ai gara hakan ma". Afili kuwa murmushi yayiwa Alhajin sannan yace " Ai kuwa gara ma da baka tashe nin ba...mafarki nake yi ina gaban ka'abah, daka tashe ni da har sai nayi kuka". " Lalle yau ka kai babbar ziyara". Fa'din Alhaji Baba yana dariya. Mu'een sai yace " wallahi kuwa, dan ma naji haushi hannu na bai 'karasa ta6awa ba na farka". " Allah ya sa mu dace to". " Amin Amin" Ya amsawa Alhajin da shi. Haka suka cigaba da 'dan hira har lokacin da Ammi ta gabatar masa da abin karin sa, batare da 6ata lokaci ba ya karya sannan yayi shirin tafiya gidan gonar sa. Har ya kama hanya zai fita sai kuma ya juyo ga Mu'een yace da shi" ko zamu tafi tare ne, naga gidan shiru kar kuma ka gaji da zama kai ka'dai 'din babu da'di". " ah ah Alhaji...ni kam ba yau ba sai dai gobe in Allah ya kaimu". " to shikenan Allah ya nuna mana goben ni kam na wuce". Fa'din Alhaji Baba tare da juyawa ya fara tafiya " Allah ya bada sa'a " Ammi tace yayin da Mu'een yace da shi " adawo lafiya". Ko bayan fitar Alhaji Baban ma bai bar parlourn ba zama yayi suka cigaba da hirar su da Ammi.    Ya kanji farin ciki sosai a duk lokacin da yaga yanda rayuwar ahalin sa ya kasance a yanzun gaskiya sai dai Alhamdulillah kawai za'ace, domin bai ga alamun suna tare da damuwar komai ba...gashi Allah ya 'kara bu'da musu gidan gona sai ha66aka takeyi.    Shima 'din ya kanji farin ciki ta 6angaren sa marar misaltuwa, domin kuwa har mantawa yake da damuwar dake cikin ransa.         Kwanan sa 'daya ne tak amma Alhamdulillah cuz bai samu lokaci ya zauna dan tunani kan abinda ke damun sa abaya ba, hakan kuwa yayi masa da'di sosai, shiyasa 'karfi da yaji yake 'ko'karin maida kansa surutacce na dole ba wai dan hakan ra'ayin sa bane, face dan kawai ya ringa 'dauke hankalin zuciyar sa daga damuwar data ke 'kunshe da shi.      Wannan kenan. *****      " Ummah kinga Hudah ta'ki tayi da sauri ko?" Cewar Nanne dake ta faman ha'de fuska tamkar zatayi kuka. " me ya faru ne Nanne me Hudahn tayi miki?" Ummah ta tambaye ta tana mai tattaro dukkan hankalin ta gareta. Nanne sai tace " Tun 'dazu fa nake ta cewa tayi sauri tayi wanka ta shirya amma ta 'ki kuma fa tun 'dazu akayi azahar har an kusa yin la'asar ma,malamin mu kuma bulala zai mana idan mukayi latti". Kafin Ummah tayi magana sai nayi saurin le'kowa nace " Nifa Ummah yau bazani ba gaskiya, tayi tafiyar ta kawai". Ummah 6angaren da nake ta maida idanun ta sannan tace dani " me yasa bazaki ba Hudah ba fa na san shiririta ni" Ummah tayi maganar da 'dan masifa harda da nuno ni da yatsa. Ni kuwa baki na na  turo gaba sannan nayi komawa ta ciki batare da na 'kara fa'din komai ba. Daga wajen Ummah ta sassauta murya gami da fa'din " kinga uwata yi tafiyar ki, wannan ja'irar ba zuwa zatayi ba nasani tunda har ta fadi da bakinta kuma ma ai kinga bata shirya ba har yanzu...tafi abinki Allah ya bada sa'a, banda wasan banza kinj uwata?" Ina daga cikin daki na ta6e baki na gefe da jin lalla6an da Ummah ke yiwa Nanneh da ko ni da nake auta ma bana samun hakan. " to Ummah " Nanne ta fa'di gami da ficewa daga gidan, Ummah ma bata 'kara bi ta kaina ba ta cigaba da abinda take yi. Yayin da nayi kwanciya ta cikin 'daki har bacci yayi awon gaba dani, haka kawai yau na tsinci kaina da rashin son zuwa islamiyar duk kuwa da cewa ba 'karamin son makaranta ce da ni ba amma yau sai naji bana son zuwa.          A kullum ina riga ta shirin zuwa islmiyar, na safe ne ka'dai take rigani shiryawa kasancewar ita bata yin aikin komai da safen illah tayi sallah taci abinci sai saka uniform.....shiyasa lokuta da dama ma tafiyar bata dai-dai ta kusan kullum sai ta riga ni tafiya makarantar. 〰〰〰           Tafe take a hankali kamar yanda ta saba, tana rungume da takaddun ta a 'kirjin ta.....dai-dai kan layin gidan Alhaji Baba take a lokacin  sai dai bata riga ta iso kusa da gidan ba. Yana tsaye a 'kofar gidan yana amsa waya, yayin da ya kwantar da hannun sa jikin 'karafunan bubler 'din dake daga wajen gidan nasu.      Tun daga nesa  yake hango ta, kunnuwan sa na kan sauraran wayar amma idanun sa da hankalin sa gaba 'daya yana kanta,  yanayin yanda take tafiya kawai ne ya birge shi, yana matu'kar son mutum mai natsuwa a rayuwar sa musamman ma mace, bai fiya son mace mai hayaniya sosai ba.      Koda ya gama wayar kuwa tattaro dukkan natsuwae sa yayi ya mayar kanta tashin farko kawai yaji yarinyar ta birge shi jiki da zuciyar sa, bai ta6a jin irin hakan farat 'daya game da mace ba sau 'din, yarinyace 'karama mai cike da natsuwa da haiba.... da kansa ya 'kiyasta shekarun ta a ransa, gani yayi kamar bazata wuce 14-15 yrs ba.    Cigaba yayi da kallon ta yana sake yabawa da kyau da tsarin ta  har 'kaguwa yayi ta iso kusa da shi dan ya ganta da kyau da idanun sa.   Baifi taku ashirin ya rage tazo ta gifta shi ba kawai wata dake can bayan ta itama sanye da kaya irin nata ta 'kwalla 'kiran sunan ta, ga dukkan alamu makaranta 'daya zasu je. Juyawa tayi batare da ta amsa ba dan ganin mai 'kiran nata.    'Bangaren sa kuwa hakan da tayin sai ya sake birge shi har zuciyar sa, sunan da yaji an 'kirata da shi ya cigaba da maimaitawa cikin ransa yana sake binta da idanu..ya maimaita _Nanne_ ya kai sau uku, bai san ma'anar sunan ba amma a hakan yaji sunan ya mai da'di. " d'an jirani mu tafi dan Allah".    Wacce ta 'kira tan ta sake fa'di tare da 'kara saurin tafiyar da takeyi dan tayi saurin cimmata. Bata ce komai ba har 'dayar ta 'karaso kusa da ita suka fara tafiyar tare a hankali tamkar basu don yin tafiyar....'mita Nanne ta fara yi mata k'asa-'kasa da fa'din " Ke dan Allah kullum sai ki rin'ka 'kiran sunan mutun da ihu Allah..nifa bana so".    " yi ha'kuri to na daina yanzun ma ai naga kin min nisa ne shiyasa...ina Hudah kuma yau 'din na ganki ke ka'dai?".   Duk baiji wannan hirar da sukayi ba illah amsar da ta bayar na cewa " Hudah ta'ki zuwa cewa tayi wai bazata je ba yau 'din". Wannan 'din ma yaji ne kasancewar daf dashi suke a lokacin. Bayan su yabi da kallo yayin da sassanyar muryar ta ya ratsa mai dodon kunne har cikin zuciyar sa bai bari ba, idanu ya lumshe a hankali yana jin wani nisha'di na ratsashi, haka kawai sai ya tsinci kansa da binsu da idanu har suka 6acewa ganin sa.                    Wannan shine ya kasance rana ta farko da Deen ya ta6a tsintan zuciyar sa cikin shaukin so da 'kauna na gaskiya....wanda babu algus acikin sa...bai ta6a sanin da'din da ake ji idan an kamu da soyayya ba sai a wannan lokacin.                Yana daina hangosu sai ya sau'ke ajiyar numfashi yana murmushi ya juya ya wuce cikin gida, inda bai jima a gidan ba ya fito bayan ya 'dauro alwalar sallar la'asar, masallacin da yafi kusa da gidan nasu ya nufa dan bin jam'i. Ana idar da sallah bai zauna ba sai ya koma gida, 'dakin sa ya wuce ya mi'ke kan kujera...tun lokacin da idanun sa yayi arba da yarinyar murmushi bai bar kan fuskar sa har yanzun, kallon 'daya zakayi masa ka fahimci cewa yana tare da nisha'di marar misaltuwa.         Sam Mu'een bai hana zuciyar sa tunanin yarinyar ba dan ko yace zai yi hakan ma ba iyawa zai yi ba, bai gushe ba yana tunanin ta har sai da ya tabbatar da cewa da gaske son yarinyar ne ya kamashi so kuma matsananci, he can feel his heart beat yanda ya canza gaba 'daya....bai kuma 'kalubalanci hakan ba, domin 'dari bisa 'dari zuciyar sa tayi na'am da ita, tashin farko zuciyar sa ya bata tambarin masoyiya agare shi kuma sanyin ransa,  damuwar sa kawai a yanzun shine ya san bayaga Nanne menene asalin sunan ta.       Ko lokacin da aka tashi daga islamiyar ma dawowa yayi ya tsaya da ya saiti 'karfe biyar tayi yasan duk tsiya bazasu wuce hakan ba.   Yana tsaye a wurin 'yan biyun Ammi suka dawo suka shige gida...ba'a 'dau lokaci ba sai ga su nan itama da 'kawayen ta sun taho, sauran nata hira amma ban da ita, dan sam ita ba gwanar hakan bace tun asali, ko ta kansa ma babu wanda yabi balle su san da tsayuwar sa a wurin abinka da 'yan yara dake ji da yarinta....Duk da 'kura mata idanun da yayi amma sam baiga alamar ta san da tsayuwar sa a wurin ba.... amma ga mamakin sa suna gifta shi sai yaga ta waigo ta kalle shi suna ha'da ido sai tayi 'kasa da kanta gami da juya ta cigaba da tafiyar ta.        Tsabar yanda Deen yaji da'din hakan har dafe 'kirjin sa yayi...yana sau'ke sassanyar murmushi.....saman la66an sa ya furta " wannan tawa ce ni ka'dai insha Allahu ke zan aura ko dan in cikata gurbin farin cikina". *****       'Bangare na kuwa.....washe gari da safe da nazo gidan a 'kofar gida na samu Alhaji Baba zaune a kan farar kujerar roba yana hutawa.    Ganin sa wurin ne ya sanya ni gaida shi sannan na shiga cikin gida.      Yau kam parlourn babu kowa sai TV dake aiki shi ka'dai, ba gwanar zama inyi kallo ba ce ni shiyasa ma sam ko hankali na ban kai wurin TVn ba, kitchen na wuce wurin Ammi dan nasan tana can a dai-dai wannan lokacin.   Gaida ta nayi sannan na sanar da ita cewa na ajiye a dinning kamar yanda naji suke 'kiran abin da shi. Banko bi takan su Saif dake can 'dakunan su ba kawai nai wucewa ta waje. Gurin Alhaji Baba na koma na zauna daga gefen sa, dama shi babu ruwan sa matu'kar na ha'du dashi to sai na tsaya surutu da yake shima biye ni yake yi.   " Har kin fito ne?" yace da ni yana kallo na. Ina shirin zama kan wata kujerar nace masa " ehh na fito gidan shiru sai Ammi". Sai yace   " Ina jin suna can 'dakunan su basu fito ba tukunna, shiyasa ma ashe naga kin fito da wuri dan nasan idan da kin ha'du dasu Saifuddeen da ba yanzu zanga fitowar ki ba". Dan 6ata rai nayi nace " Ai nayi fa'da dasu ma kuma babu ruwana da Zaid " Nayi maganar ina dama fuska tamkar yanzu ne abin ya faru. " laifin me yayi har haka?" Alhaji Baba ya tambaye ni yana kallona da fara'ar sa sai nace " ai shine jiya ya hana ni in taya shi zane". Alhaji Baba murmushi yayi tare da fa'din " Lallai Zaidu bai kyauta ba, amma ki barshi watarana ai da kansa ma zai ce miki ki taya shi idan yaga kin fishi iyawa dan nasan 'yar tawa gwana ce ko ba haka ba?" " Hakane" na bashi amsa ina washe ha'kora na jin dadin an yabe ni. Shima murmushi yayi Alhaji Baban sai ya sake fa'din " to maza kije ki shirya zuwa makaranta karki makara kinji..bana son ana dukan yata kullum a makaranta" Kai na juya na kalli hanya sannan nace masa   " ni sai na huta zan tafi...ai na gaji da tafiyar". A fili Alhaji Baba yayi murmushi mai sauti sannan yace " to 'yata ki huta amma ka'dan sai ki wuce ....". Bai gama rufe bakin sa ba sai mukaji sallama daga bayan mu. Alhaji ne ya amsa sannan muka kalle shi dukkan mu. Sanye yake da wando 3quarter na rubber jeans da wata armless riga ja, wuyan sa rataye da headphone babba sai tsiyayar gumi yake yi. Baki na ta6e gami da kawar da kaina gefe. " barka da hutawa Alhaji" Yace bayan ya iso ta gaban mu. Fara'ar dake kan fuskar Alhaji naga ta karu fiye da na dazu wanda cikin hakan yace. " Yauwa Muhammad gudun ya isa kenan?" yayi mafanar yana kallon fuskar sa.     Da murmushi kawai ya amsa Alhajin sannan batare da ya furta komai ba ya tunkari mashigar gidan nasu a hankali. Ni kam 'kasa-'kasa nak hararar sa dan sau 'daya kawai ya kalle ni daga haka bai sake bi ta kaina ba. Alhaji ne ya juyo ya kalle ni sai yace " Baki gaida yayan ki ba..." Tun kafin ya dasa aya na bu'di baki na da 'dan 'karfi nace " ina kwana" Ko kula ni.ma bai yi ba k'ilan bai ma san cewa da shi nake ba...ni kuwa ban kara ba sai ma na kawar da kaina. Alhaji Baba murmushi yayi shi kam. Daf da zai shige gidan Alhaji Baba ya 'kira sunan shi " ammm Muhammad!" Cak ya tsaya gami da waigowa cikin raina nace " ashe gaisuwar tawa ma yaji da gangan ya ki amsa min tunda gashi ya ji sunan shi da Alhaji Baba ya k'ira...ban koyi la'a kari da cewa yanayin amon muryar mu ba 'daya bane dashi. ..... Alhaji Baba ne ya ce dashi" sai kayi sauri ka shirya mu wuce da wuri ko....dan yau akwai sa'kon da nake so zan bayar". " Yanzu zan shirya insha Allahu" yace tare da juyawa ya shige cikin gida.   Kallon Alhaji Baba nayi bayan shigewar tasa a hankali nace " Alhaji Baba wannan ma 'dan ka ne?" Cike da kulawa yace dani " D'ana ne Hudah...baki ta6a ganin sa ba ko?" " ah ah jiya na ganshi a parlour". Alhaji Baba sai yayi murmushi yace " to shima yayan ki ne kinji shine babban 'dana...kina ce masa Yayah". Tunzuro baki na nayi gaba tare da fa'din " ni dai ba Yayah na bane...shida ma har marina yayi jiya dan nayi karo dashi kuma yanzu ma ai dana gaida shi k'in amsawa yayi...kuma bazan sake gaida shi ba ma". Da mamaki Alhaji yake kallo na yace " Mari kuma? Deen 'din ne ya mareki?" Kaina na daga sami gami da fa'din " Ehh amma Ammi tace zata rama min"! Na karasa maganar harda jin da'di na. Murmushi yayi dan yasan Ammi ta fa'di hakane kawai dan ta lalla6ani.... Kafin ya sake yin wata magana sai na riga shi da fa'din " Alhaji Baba Deen 'din ma sunan shi ne? Naji Ammi ba haka tace jiya ba, kuma naji ka ce mishi Muhammad duka sunan na shi ne shi ka'dai?" Ta'kaitacciyar dariya yayi tare da fa'din " Sunan sun masa yawa ko Hudah?" Sai na 'dage kaina sama alamar " ehh" Alhaji ma sai yace " Kuma ai duk sunayen shi ne, Muhammad Mu'inuddeen sunan sa....zaki iya ce masa Mu'een sannan Deen duk wanda zaki iya ki fa'di.....gaya min wanne yafi miki sau'kin fa'da ?" Ya 'karashe da tambaya ta...a hankali na bu'di baki na na furta " *Deen* !" Alhaji baba sai yayi murmushi yace dani " yayi to duk 'daya....daga yau kuma shima yayan ki ne idan bakya yi masa rashin ji bazai na dukan ki ba kinji?". "Uhmn" Nace da Alhajin gami da mi'kewa " na tafi " na sake fa'di batare da jiran jin komai daga bakin sa ba kawai nayi gaba abina.      Cikin gida kuwa yau ma Mu'een kunun sa ya sha son ransa harda waina ya hada yaci har guda biyu, cikin ransa yake yabawa da da'din wainar da duk zaton sa Ammin ce keyin kunu da wainar dan sam bai san cewa da safen ake kawo shi ba.         Kofi ya 'daya ya kur6i kunun a hankali bayan ya ha'diye sai ya kalli Ammi yace " Alhaji Baba fa bai shigo yayi break 'din ba kuma naji yana fa'din zamu fita yanzu?" " Azumi yake yi" Ammi ta bashi amsa a takaice.    Sai ya jinjina kansa tare da fa'din " ai na manta ma ashe yau thursday...duk da'din kunun ki ne kuma fa ya sani mantuwar Ammi". Ya karashe maganar yana murmushi. " Da'din kunun masu kunu dai...." Ammi tace da shi. Deen bai wani sa maganar aka ba kuma balle ya fahimci me take nufi...da yake ma tana gama waccan maganar sai ta sake fa'din " ba surutu ba ka hanzar ta dai kasame shi tun da yana can yana jiran ka" Wannan maganar ne ya 'dauke masa hankali harya gama breakfast 'din ya tashi da hamdala bayan ya goge bakin sa....bai tuna maganar Ammi ta farkon ba. *Kuyi ha'kuri fa kun jini shiru jiya...alhini ne ya hana ni posting* *wlh.....amma yanzu Alhmdllh...zamu cigaba da iznin Allah.* 🤔AMMA READERS ME YASA BA KWA SHARING NE❓.......any ways🤷‍♀👇🏼 ~A CIGABA DA GASHI....~ 🤞🏻 _Comment, Vote and share please_ 👌🏻 *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *27* Da yamman ranar kuwa babu islamiya  da yake ranar Alhamis ne kuma bama zuwa, ranar ma ni da Nanne muka kai marka'den shinkafar wainar Ummahn mu...da kuma gya'da dayake yau d'in harda gya'da ta gyara shiyasa muka tafi mu biyu, dama ranar da duk za'ayi markaden gya'da ne muke tafiya mu biyu idan kuwa marka'da'd'iyar gya'dar Ummah bata kare ba ni ka'dai ke zuwa in marka'do mata shinkafa.      A hanyar mu ta dawowa muna tafiya muna 'yar hira, wani sa'in kuma fa'da mukeyi da ita dan ni nawi ya dame ni sosai yayin da ita kuma take faman jan 'kafa tafiyar ta kamar dan dole take yin sa. Burina tayi sauri mu wuce gida ita kuma ta'ki a hankali take tafiyar ta kamar yanda ta saba.       Cikin shirin zuwa ball yazo ya gifta mu ban sani ba ko bai gane ni amma ni kam sau 'daya na kalle shi amma sai na gane shi.    Sai da ya wuce ne sannan Nanne tace da ni " tab amma wannan yana da kyau gaskiya". " Waye wai wancan ?" Na tambaye ta gami da nuna shi da bakina cuz da duk biyun hannaye na ri'ke roban dake kaina. Nanne sai tace " ehh mana koke baki ganshi ba " Juyawa nayi na cigaba da tafiyata sannan nace " Na ganshi mana... 'dan gidan Alhaji Baba ne, mugunta ce dashi ingaya miki sosai".   Baki kawai Nanne ta ta6e bata 'kara magana ba, daga nan kuwa muka cigaba da tafiyar mu.   Na kanyi gaba in barta dan yanayin tafiyar mu ba 'daya bane da ita sam...ban sani bama ashe Nanne kam hankalin ta duk ya koma kan Yah Deen ne, tafiya take tana waigen sa lokaci-lokaci....ni kuwa dake gaban ta bansan hakan ba sam....bazata kawai naji karan fa'duwan abu...waigowata kawai sai naga ashe marka'den dake kan Nanne ne ya kife gaba d'aya sanadin tuntu6e da tayi.....ido na zaro na kalli marka'den sannan na kalle ta...." ta6'di Nanne marka'den wainar kika zubar?" Sai tace dani " ai tunt6e nayi ban kula ba". " To ki 'dauko robar mutafi gida...." Hannu ta kai ta dago robar sai muka ga ashe itama ta face yayin da marfin ta yake nan garau jefe a gefe guda. " ko zamu 'dan kwasa ka'dan?" Nanne ta fa'da tana kallona" Sai nace kamamin mu sau'ke to sai in tayaki". " ka'dan muka kwasa muka bari dan gaba d'aya ya lalace a wurin ba zai 'kara amfani ba. Koda muka je gida kuwa Ummah bata ce komai ba jin cewa Nanne ce ta zubar kawai sai ta kar6i wanda muka kwasa 'din ta ha'da da ruwa da dama ta baiwa ragunan Baban mu suka shanye abinsu.....wannan dalilin ne ya sanya washegari bata yi waina ba harma da kunun baki d'aya.....sanadin kallon Deen da Nanne keyi wanda a lkacin ita kanta ma bazata iya shaidar ya san da zaman ta a duniya ba ko a'a duk da kuwa ha'duwar su da shi ta biyu kenan inda yau.   *****       Tsananin yanda Deen ya saka Nanne cikin zuciyar sa ya sanya kafin sati har ya nemi duk wasu bayanan da ya kamata ya sani game da ita, cikakken sunan ta da sunan mahaifin ta harma da gidan su duk ya sani amma bai ta6a zuwa ba. Da yake da wayo yake yin tambayar ba a fili yake fitowa ya bayyana manufar sa ba...misali ranar da zai fara yin tambayar aranar wani friend 'din sa yazo wurin sa ne sai da ya daidaici 'karfe biyu tayi sai ya jashi suka fito wajen gida suka zauna kamar da gaske, daka yanzun 'karfi da yaji yake tilastawa kansa zaman waje kawai dan ya ganta yaji sanyi cikin ransa..wani sa'in ma idan ya fito sallar azahar baya ta6a komawa gida koda kuwa 'karfe nawa zai kai a wurin to bazai ta6a shigewa ba sai yaga giftawar ta...(ni kuwa nace...aiki ya kama gwari).   Suna zaune a wurin muka zo muka wuce bamu ma kula da su ba.... Ashe Deen kam hankalin sa na kanmu sai ya koma ya kishingi'da ya wani lumshe idanu bazaka ta6a yin zaton yana ganin abu a hakan ba.   Shi 'dayan abokin Deen da bai san meke faruwa bane da wucewar mu sai ya girgiza kansa yace " Allah sarki...wallahi yarinyar nan na matu'kar bani tausayi...gata haka zaka ganta kamar lafiyayya amma wallahi kar kaso kaga wurin jinyarta, hankalin kowa sai ya tashi a dangin ta, gata da masifar shiga rai". Ya 'karashe maganar da sanyin murya. Mu'een na jin haka sai ya gyara zaman sa da kyau da mamaki yace da shi " wace kake magana akai wai?" Juyawa yayi ya kallomu dan shi baya ya juya mana Yah Deen ka'dai ne ke facing da hanyar da muka bi. " Nannen Malam Mamman nake magana akai...gasu can yanzun nan suka gifta mu 'yar doguwa mai hasken....ai kai bazaka sansu ba saboda ba'a garin kake zama ba shiyasa... Yah Deen taran shi yayi da fa'din " to wani irin suna ne kuma Nanne?" Hannu wancan 'din ya 'dago yace kai dakata " cikakken sunan ta Amina Nannen kawai sunan gida ne". Komawa yayi ya kishingi'da yana kallon abokin na sa kamar mai nazarin wani abu a hankali sai yace to me ke damun ta har haka da kace tana baka tausayi?" " Ai kai de ka bari...wallahi sickler ce da ita abin tausayi yarinyar ni ai badan hakan ba wallahi sai na nemi auren ta yarinyar akwai natsuwa tun tana 'yar 'karamar ta". Idanun sa ya miyar ya limshe su a hankali cikin ransa yace " gara hakan ai, kaga ni sai na nemi auren ta in kula da ita....." A fili kuwa " Allah yata lafiya" kawai ya furta daga nan bai 'kara fa'din komai ba. A ranar ne Mu'een yasan haka game da Nannen mu....to ko ranar da yaga gidan mu ma sanadin wani da suke ha'duwa a filin ball ne ya sa mu ganin gidan da yamma bayan sun tashi daga ball 'din sai hanya ta biyo da su ta wurin anan yaga Nannen mu ta fito daga ma'kwabta ta shiga gida. Shi 'dayan bai ma kula da ita ba Yah Deen ne ka'dai ya lura da hakan. Basarwa yayi sai da ta shige gidan kafin ya tambaye shi wai wannan gidan...gidan waye ne?" " Gidan Malam Mamman ne...me ya faru?" Abokin ya 'karasa da tambaya, Mu'een sai yace " bakomai". Tafiya ka'dan suka sakeyi tare wancan 'din ya shige gida sai ya rage saura shi ka'dai...yana tafiya yana tunani....." Nannen Malam Mamman da abokinsa Ashiru ya fa'da da kuma yanzu da aka ce masa " nan gidan Malam Mamman ne, kenan nan ne gidan mahaifinta. Cikin ransa yake ta tunani har ya isa gida....baiji 'kwarin gwiwar da zuciyar sa ke bashi ta ragu ba saboda sam bai hango wani 'kalubale game da hakan ba. Ya riga ya tsara musu a rayuwa cikin da'da'dan mafarkan sa, tun farko Engineering yake da burin karanta amma ha'duwar su Nannen mu yasa shi canza ra'ayi zuwa zama cikakken likita ta yanda zai rin'ka bawa matar sa kulawar da ta dace.....batun yara ma sam bai sasu a lissafin sa ba shi dai Burin sa ya samu Nanne.          Shi kansa wani lokacin sai yaga kamar kawai yaudaran zuciyar sa yakeyi da cewa wai yana sonta amma  tsoron ranar da Uncle Ja'afar zai fahimci hakan yakeyi dan yaga-yaga zai masa cuz karatu mai zurfi yake so yayi in yasan da batun tun yanzu ya kamu da soyayya kuwa ai ya shiga uku, Uncle Ja'afar ba 'karamib raina shekarun Mu'een yake ba har a lokacin kallon yaro 'karami yake masa bansani ba ko dan shika'dai ne agaban sa oho. Sannan sarai yasan halin Uncle Ja'afar bashi da sanyin hali kamar Alhaji Baba....shi kuwa baya jin zai iya cire ta a zuciyar sa cikin sau'ki balle ma irin yadda yake jin mugun kamun da soyayyar ta ta tayi masa...abin sai wanda ya san zafin so ne ka'dai zai iya fahimtar sa.     Satin sa biyu a garin amma gaba 'daya ya mance da damuwar da yake ciki lokuta 'kalilan da suka gabata, damuwar da tayi sanadin zuwan sa garin gaba 'daya, shaf ya manta da Rahma da sha'kuwar su harma da rayuwar da suka yi tare da ita kaf ya manta da su duk a sanadin soyayyar 'yar uwata, abu 'daya ne kawai da ya kasa raba kansa dashi shine yawan jin feelings...wannan  abin kam har yanzu ya kasa raba kansa da shi sai ma 'kara yawaita da yake yi masa. Ta 6angare na ma haka kullum ban fasa zuwa gidan ba, sai dai kwanaki 'kalilan ne muke ha'duwa dashi cuz mafi yawan ranaku na kan zo har nafi ma bangan shi ba, idan kuwa mun ha'dun gaisuwa ka'dai ne ke ha'da ni da shi. Akwai watarana da na gaida shi ma ya amsa a yatsine ya ficewar sa lokacin tare nake da Saif muna zaune, yana wucewa sai na yamutsa fuskata nace da Saif" Allah Deenin kunnan ya fiya yanga da yawa". Ido Saif ya zaro harda kama baki sannan yace dani " yaji ki dai ba ruwana ni...wa ma yagaya miki cewa sunan sa haka?" "Alhaji Baba ne ya fa'da min"... Na bashi amsa ina kallon cikin idanun sa. Sai yace " to ba Deeni zaki ce ba, Yah Deen zaki ce in bahaka idan yaji kina ce mai Deeni duka zai miki ni kuwa ba ruwana". Ban ce komai ba kawai na ta6e bakina na daga nan nayi shiru ban 'kara fa'din komai ba.     Tun daga ranar Yah Deen ya kama baki na dan gudun kar ya dakeni kamar tanda Saif ya gayamin.    Ban ta6a fa'da a idanun sa ba kam dayake ba zaman hira nakeyi da shi ba, amma a duk lokacin da wata hira ta 'dauko aka sako da sunan shi to bana ta6a canza nawa salon 'kiran sunan, ga dukkan alamu kuma ni ka'dai ke amfani da hakan, dan ban ta6a jin wani ya fa'da ba banda ni. Shima 'din tun baya kulawa da lamarina abu na yau da kullun har ya saba da gani na cikin gidan su, bai san me nake zuwa yi ba haka kuma bai ta6a tambayar kowa ba, kuma har yanzun bai san dalilin dake kawoni cikin gidan su kullum da safiya ba.     Sau tari ya kanyi mamaki idan yaga yanda Alhaji da Ammi ke nan-nan dani, ban dama sha'kuwar da yaga nayi da 'kannan sa musamman Saif da jinin mu yafi ha'duwa dashi......    Bai wani damu sosai da yasan dalilin sha'kuwar mu da ahalin nasa ba dan haka shima sai ya 'dauke ni a yanda ya ganni wanda wani lokacin ma ya kan bani fuska ne albarkacin yawan gani na da Nanne da yake yi. ....tsakanina dashi dai gaisuwa ce kurum daga haka kuma babu komai.    〰〰〰         'Bangaren Rahma kuwa.....tun lokacin da ta ga dangi na faman cika gida da 'da'ddaya, taga yanda Hayatu ya dulmiya tsundum cikin shirin biki shikenan ta saduda, yanzu kam ta yarda cewa auren ta da Al'amin babu fashi....tayi danasanin abinda ta aikata yafi sau 'dari uku, a kullun sai tayi danasanin biyewa Mu'een da tayi.   Gashinan ya yi tafiyar sa ya bar ta ana shirin aurar da ita, babu wanda ya damu da 'karancin shekarun ta ga dukkan alamu ma kowa farin ciki yakeyi da hakan. A cikin yanayin idan taje gun mahaifin ta kwantar da kai takeyi kullun ta sha kuka son ranta kafin ta fito, baya magana balle ya lallashe ta dan haka da kanta take bawa kanta ha'kuri ta fito. Ranar wata Juma'ah ne aka 'daura auren ta da Amin bisa sadaki mai daraja.    Ranar tasha kuka sosai kamar ranta zai fita....da yamma kafin a akaita Hayatu ya shigo 'dakin ta wanda ganin a yanayin da ya shigo 'din ya sanya jama'ar dake tare da ita sulale a hankali suka watse baki 'daya. Hayat zama yayi a bakin gado a hankali, Rahma dake can kan stool 'din gaban mirror sai ta cigaba da rera kukan ta bata damu da wanzuwar  sa cikin 'dakin ba. Duk da zuwa yanzun ta tsani Mu'een tsana mai girma amma har yanzu birbishin son shi bai bar 'kasan zuciyar ta ba, yanzu kuwa da take ganin cewa ta zama mallakin wani sai take jin kamar bazata juri rashin sa ba kwata-kwata, 'ka'k'karfar soyayyar ta shi ne ta dawo mata sabuwa dal. A hankali Hayat ya 'kira sunan ta cikin natsuwa, bata amsa ba amma kuma ta rage sautin kukan nata haka kuma bata 'daga idanu ta kalle shi ba. Bai damu ba shima kawai ya cigaba da maganar sa cikin natsuwa da sanyin murya yace " Kiyi ha'kuri Rahma ki gafarce ni, banyi haka dan na 'kuntatawa rayuwar ki ba, nayi ne kawai dan in kare mutuncin ki da mu ma ahalin ki gaba 'daya, na san babu mamaki kina gani na matsayin mutun mai son kan sa ko kuma kice bandamu da za6in ranki ba. Sai dai inaso kisan wani abu Rahma.... lokuta da dama mukan so wasu abubuwa ne mu kuma kafe akan su alhalin ba su kasance alkhairin rayuwar mu ba, sai kiga wanda muke guje masa 'din shine dai-dai garemu kuma za6in Allah masanin komai, amma wanda Allah yaso sau'ka'kawa lamurane ka'dai yake ganar dashi hakan da wuri ya kuma gane.    Ki gode Allah kawai Rahma domin da wuri ya bayyana miki irin yaudararriyar soyayyar da Mu'een ke miki harma ya nufe ni da gani da idanu na matsayi na na yayan ki.       Hukuncin da na yanke kuwa har yau ban ta6a regretting ba, face godewa Allah ma da nake sake yi a kowani lokaci da ya sanya akwai mai yi miki son gaskiya agefe wanda a koda yaushe yake shirye da kar6an ki matsayin matar aure, gudun kar ya zargi wani abu ne ya sanya na sanar dashi dalilin da yasa nake so ayi auren cikin 'kan'kanin lokaci duk da bani da tabbacin idan yaji zai amince amma bani da za6i face bayyana gaskiya ta...nasan idan yana matu'kar son ki ba zai 'ki yadda da auren ki ba tunda akwai masu 'dauko mace agidan karuwai ma kuma su tsarkake ta su aura su kuma rayu cikin farin ciki.   Allah cikin ikon sa ma sai ya sanya Amin cikin masu kyakkyawan zuciya domin kuwa cikin farin ciki yayi na'am da ke inda ya bani goyon baya 'dari bisa 'dari. Hakan da yayi ne ya tabbatar min da cewa zai ri'keki da Amana har 'karshen rayuwar ki........Rahma gashi yau burina ya cika na dam'ka amanar rayuwar ki 'dungurungum a hannun Amin, yanzu matsayin aljannar ki Amin yake, mijinki ne kiyi masa biyayya ki nemi aljannar ki, bana son fitina kuma, ke kanki kinsan Amin ni kaina ya girme ni balle ke dan haka ki bashi girman sa ki kuma nemi aljannar ki da 'karfin zuciya, bisa yardaewar ubangijin ki, karkiyi tunanin zaki yi masa wasu mugayen halaye da baki son shi, to duk abinda kikayi Rahma ki sani kece da asara dan kuwa ko Amin ya rabu dake da wuya ki 'kara samun makamancin sa, ina tabbatar miki da cewa har shi Mu'een 'din da kika yi domin sa ba auren ki zai yi ba alokacin dan matsayin bazarawa za'a kalle ki a lokacin...ki ma yi tunani Rahma, wanda bai aure ki lokacin da ya tabbatar da kuruciyar ki ba yaushe kike tunanin zai dawo ya aureki?......Ni 'dan uwanki ne, kuma inason ki Rahma ke kanki shaida ce akan hakan, ina kuma da burin ganin farin cikin ki a koda yaushe, banason rayuwar ki ta girgiza ne koda wasa shiyasa na aikata hakan wanda na tabbata koda da ran mahaifiyar mu bazata so ganin ki hakan ba hakama Daddy bazai so yaji ance ga mummunan abinda ya faru da rayuwar ki ba, idan kuwa yaji hakan kuma yana da cikakken lafiya na tabbata bazai bar Mueen haka nan ba, amma kinga yanda duk Allah ya gyara komai ba'a yi masa gyara dan haka sai dai muce ALHAMDULILLAH....dan girman Allah ba dan ni ba ki kula da rayuwar auren ki kiyiwa mijin ki biyayya ki daraja ahalin sa hakan shi ka'dai idan kika yi zai tabbatar min da cewa nima kina sona kuma kin bi magana ta Rahma, ina miki fatan 'daurewar farin ciki na har abada....Allah ya albarkaci rayuwar ki.." A hankali ya mi'ke ya kama hanyar fita daga 'dakin, yana share hawaye da takaicin duk shine sanadin auren ta,  bai ma san mai ya kaishi shiga rayuwar Mu'een a wancen lokacin ba da har abubuwan da suka faru suka faru, haka kawai ya tsinci kansa da tsanar Mu'een batare da wani dalili ba a wancan lokacin, yasan kuwa hakan ba komai bane face sharrin shai'dan, sai gashi ta inda Mu'een ya biyo masa, ta inda zuciyar sa bazata iya 'dauka ba....sam baiso ayi auran Rahma tun yanzu ba yaso ace tafara karatun gaba da secondary, yaso ta fita daban agidan nasu amma duk shirin sa ya watse cikin 'kan'kanin lokaci, sai gashi da kansa ya jagoranci aurar da Rahma tun kafin ta kammala secondary 'din ma, tun kafin hankalin ta ya gama daidaita balle ta kai wani matsayi na musamman. Daf da zai 'karasa barin 'dakin yajiyo muryar Rahma cikin sanyi ta 'kira sunan shi....cak ya tsaya tare da waigowa ya kalle ta, tana hawaye shima haka, tsaye ta mi'ke  sannan cikin sanyib murya tace dashi " nayi al'kawarin yiwa mijina biyayya, insha Allahu bazan tozarta maka niyyar ka ba Yayah, zan kula da duk abinda ya kasance hakkine ta 6angare na, nayi maka al'kawarin mantawa da Mu'een mantuwa ta har abada...amma yayah please kace da Amin kar ya hanani 'karasa karatuna inaso in gama yaya......" Ta 'karashe maganar da sheshshe'ka. Hayatu kam take ya cika da tsananin farin ciki mara misaltuwa, har ma bai san lokacin da ya iso gaban ta ba ya fara share mata hawayen ta. Bai furta komai ba kawai ya janyo hannun ta a hankali suka fita daga 'dakin, direct 'dakin mahaifin su ya kaita, dukkan su kuka sukeyi yayin da mahaifin nasu ya tsura musu idanu yana kallon su. Hayatu ne ya fara magana da muryar kuka yace " Daddy ka yafe min dan Allah, idan abinda nayi ba'a son ranka bane, bansani ba ko dai-dai na aikata Daddy, yau gashi zan dam'ka Rahma a hannun mijin ta zata tafi ta bar mu, Daddy ko cikin ranka ne ka daure ka sanya mata albarka...." Ido Daddyn nasu ya lumshe ya kuma bu'desu nan take hannun sa da suka kama ya dam'ke da 'karfi ga dukkan alamu magana yake son yi amma babu dama....wanda hakan sai ya 'kara 'karya zuciyar Rahma take ta sake sakin wani sabon Kuka....cikin kukan take fa'din " Allah ya baka lafiya Daddy, ubangiji Allah ya tashi kafa'dun ka...." Anan 'dakin sauran 'kannen mahaifin nasu suka suka tarar dasu, harda kaka. Nasiha suka sake yi mata inda ta ringa kuka sosai duk kwalliyar da Antyn ta tasa akayi mata duk sun wanku babu su tas, ba'a kuma 'kara bi takai ba kawai aka sake yi mata shiri, kukan da takeyi bai bari an sake yimata kwalliya ba a hakan aka 'dauke ta aka tattara a'kalar rayuwar ta aka dam'kawa Amin inda ya kar6eta da hannu bibbiyu cikin farin ciki. 〰〰〰 Zaune suke dukkan su a dinning Ammi na shirin serving musu abinci kamar kullum sai Mu'een yayi 'yar dariya ka'dan.....Alhaji Baba ne ya kalle shi duba irin na tambaya domin a yanda ya lura 'yan kwanakin kullum cikin farin ciki yake.    Yayin da ya gumtse dariyar tasa yana kallon Ammi yace " Ga dukkan alamu fa Ammi kin samu kan wainar nan, to danni kike yi ne ko kuwa dama kullum haka akeyi agidan..." Ammi bata fasa zuba abincin da take yi ba ba kuma ta kalle shi ba kawai tace " Tambaya kakeyi ne ko.kuwa neman sani? " " Duka biyu Ammi ni duk inason sani, haka kawai kullum baza muji 'kamshin suya ba sai da muga waina...kamar fa sau 'daya ne kawai akayi fashin yin waina agidan nan tun zuwa na?" Ammi ce ta sake fa'din " To laifi ne hakan kuma ko?" " Ah ah ni ban ce laifi bane...ai wainar taki tana shiga sosai Ammi har Allah Allah fa nake gari ya waye in gamu dashi dan nasan babu fashi". Alhaji Baba kam shiru yayi kawai yana ji da ganin su yana murmushi. Ammi ce tace " kai de kasani..." Dai-dai lokacin da take zubawa 'yan biyun nasu abincin... 'Dagowa tayi ta kalle shi sannan ta 'kara da fadin " in ba yaudaran kai ba yaushe ka ta6a ganin na soya waina a gidan nan......ni ba ni keyi ba siyowa akeyi har kunun ma gaba 'daya". Ammi ta fa'di lokacin da take 'ko'karin jan kujera ta zauna bayan tagama zuzzuba musu. Ido Mu'een ya zaro da mamaki yace" siya kuma Ammi....har daga ina haka?" " Can wani gida mana kana tambaya ta kamar wanda idan na fa'da mai gidan zai sani...." Alhaji Baba ne ya tari maganar da fa'din " gidan abokina akeyi " M. Jaji wanda ranar ka gansa a gidan gona.." Baki ya ta6e ha'di da fa'din ni banganeshi ba wallahi". " Amma ai kasan yarinyan nan Hudah da kullun take zuwa gidan nan da safe ko..?" Kai ya 'daga a hankali yana kallon Alhajin da tunanin dama ya rasa dalilin da ke kawota gidan kullum safiya......Alhaji Baba sai yace masa " to mahaifiyar ta ke yi kuma ita ke kawowa, idan kanaso sosai sai adinga kawowa da yawa". "...Haba Ammi dan Allah... yanzu dama ba ke keyi ba shine kuma ba'a ta6a gaya min ba?" " Ai kaji yau kam". Ammi ta bashi amsa cikin halin ko in kula. Shiru yayi bai sake magana ba haka kuma bai kai komai bakin sa ba har kowa ya gama ya tashi a table 'din ya rage saura shi ka'dai da Ammi...shima kansa kuwa bai san me ya hana shi barin table din ba. Ammi ce ta dube shi tace " Idan baka son wainar ga Tea da bread ka ha'da barin soya ma 'kwai yanzu sai ka ha'da ka ci?". Kai ya girgiza mata alamar "a'a" " to me zaka ci?" " ba komai" ya bata amsa a takaice. Ammi 'kyale shi tayi ta mi'ke ta tafi kitchen dan soya masa 'kwan...amma ga mamakin ta kafin ta fito daga kitchen 'din yayi tafiyar sa domin koda ta dawo bata same shi ba a inda ta barshi......har 'dakin sa ta duba bata same shi ba, shi wai a dole fishi yayi sosai harda barin gidan. Bai dawo gidan ba kuwa sai 'karfe uku sannan yazo nan ma da 'kyar Ammi ta sashi agaba kafin ya ci abinci ka'dan. Cikin ranta tace " silly boy....bacin ya gama santin kunu da waina abaya kuma yanzu zaimin iyayi... mthew" ta 'karashe da jan tsaki duk cikin zuciyar ta. A fili kuwa nan nan ta ringa yi dashi dan bata son mutun ya rin'ka zama da yunwa. *****      Bayan kwanaki uku.....ban fasa zuwa gidan ba kamar yadda ban daina kawo waina da kunu ba....na kanzo kamar yanda na saba muyi wasan mu da su Saif in koma gida abina....amma har ib tafi wani lokacin bana ganin sa. Ban sani ba yanzun ashe Deen ya daina zuwa dinning da sassafen nan tunda ya ji cewa ba wainar Ammin sa yake ci ba...yanzu ko ya dawo daga gudun safen sa ma 'dakin sa yake shigewa abinsa sai kusan 10 yake fitowa yasha ruwan tea.....duk yanda yaso ya daure amma ya kasa ya riga ya saba da 'dan'danon waina da kunun nan. Sati guda yana a haka duk 'ko'karin da yake yi wajen sharewa amma ya kasa watarana da sassafe yayi tsaye akan Ammi wai dole sai tayi masa kunun gya'da da kanta...." kajira anjima ka'dan za'a kawo sai ka sha". Ammi ta bashi amsa batare da damuwar komai ba. 'Bata rai yayi yace "  ni Ammi naki nake so dan Allah". ....kallon sa tayi da mamaki tace " haba Mu'een....ka ta6a ganin nayi kunun gya'da da hannuna ne a gidan nan fisabilillahi?" " to shikenan kiyi min waina abar kunun". " Ni duk ban iya ba" Ta fa'di da 'kosawa... Zai sake magana tayi saurin taran sa da fa'din  " in zaka saki ranka ma gara ka saki ranka dan ni babu abinda na iya...ubanka ma ai yana cin wancan 'din balle kai". Ta 'karashe da masifa...    Tamkar zai yi kuka haka ya juya ya bar mata kitchen 'din, gaba 'daya ma sai yaji garin ya fita ransa, Antyn sa Zainab ce ta fa'do ransa dan yasan ita duk ta iya su tunda lokaci-lokaci takan yi musu idan ta ga dama, sai dai wancen da yake ci 'din ko kama 'kafar wannan bai yi ba a da'di...amma dai duk da haka a yanda yake jin son waina da kunun yasan idan ya sami na Antyn ba zai 'ki ba.          Abu 'daya ke taka masa birki shine son yarinyar nan baya so ya tafi ya daina ganin ta domin a duk ranar da ta kasance ganin ta yayi masa wahala to kuwa shima wahala yake sha da zuciyar sa, wani irin so yake yiwa yarinyar mai wuyan fassaruwa.     Bai ta6a tunanin a wannan shekarun nasa zai yi sha'awar yin aure ba har sai da ya kamu da son Nannen mu, 22yrs yake amma yana jin da Uncle Ja'afar zai yadda masa da auren ta zaiyi ya killace ta a gidan sa shi ka'dai ya ringa kallon ta.      'Karfi da yaji yayiwa kansa katanga da wainar mu, duk kuwa da cewa yana tsananin son ta amma haka ya daure ya cireta cikin ransa. Satin sa shida a Shuwarin Uncle Ja'afar ya 'kirashi ya sanar da shi batun computer certificate 'din zai fara, afa'dar Uncle Ja'afar in so samu ne nan da kwana uku ya dawo yayi registration.    Mu'een yaji da'din wannan labarin sosai domin kuwa zama haka a gidan ya ishe shi sai dai gefe daya yana jin tamkar zai bar 6arin zuciyar sa....tun daga ranar ya fara shirin tafiyar sa sai dai rashin natsuwa da ya ziyar ce shi zuciyar sa tun yanzu har ya fara kewar Nanne.      Ana gobe zai tafi a lambu ya yini wurin Alhaji Baba, suna zama suyi hira sosai da Mal. Jaji amma bai ta6a sanin cewa shine mahaifin Nanne ba....to ko ranar ma tare suka wuni dashi yana bashi labarin irin yadda suke samun cigaba a duk lokacin da aka fitar da kayan lambu ko kaji dake gidan gonar. 'Karfe biyar da rabi suka baro lambun shida Alhaji, da 'kafa suke tafiya suna 'dan ta6a hira anan Alhaji Baba yake 'kara yi masa Nasiha game da rayuwar mu ta yanzu, inda ya ringa buga mai misalai da dama musamman ma irin wancan abinda ya ta6a faruwa da shi har ajiyayyen ciwon sa ya tashi masa......Alhaji yace " ina fa'da maka hakane dan nasan ba kowani lokaci bane zangan ka har in gaya maka hakan, saboda bama tare da kai, yanzun ma nasan da kasamu makarantar akan lokaci nasan da zai yi wuya mu ganka...." Sai yace " Haba Alhaji Baba..ai da da yanzu ba 'daya bane, zan dinga zuwa akan lokaci insha Allahu....ni dama zanyi aure na anan garin ai kaga babu batun rabuwa da ku ko?" Ya 'karashe maganar da tsokana. Murmushi Alhaji Baba yayi tare da fa'din " aure a garin nan....?" Kai ya 'daga masa sama yana murumshi tamkar wani yaro...sai Alhaji yace " a ina kaganta dan nasan ka ga wacce tayi maka ne shiyasa ka fa'di haka". " Ai kaman kasani Alhaji...dama inaso in baka amanar ta kafin in tafi..." "Da yake ni kakan kane ko...?" " ah ah ni dai dan Allah Alhaji Baba kar kabari a aurar da ita ma wani, ina kammala karatuna zan dawo ka nema min auran ta ". " Baka da kunya Muhammad, ni ne zan yi ma gadin wacce kake so?" Shagwa6e fuska yayi tare da rausayar da kansa gefe yace " please....please Alhaji... in ba haka ba kuma to kawai ka tanadi likkafani ka ajiye tun yanzu!". " Ja'irin yaro...mu ai namu shan gumba ne kawai". " um-um dai Alhaji gara asha biki da gumban nan, ai nasan kaima baka so in mutu tun yanzu ko ba haka ba?" Alhaji 'yar dariya yayi sannan ya sake fa'din " idan tazo na isa in hana ne Muhammad?" " Allah yasa mu dace...amma ni dai please Alhaji na baka amana idan ka'ki kuma zanje in bawa Ammi na kawai". " Da yafi maka" Alhaji ya fa'di cikin nuna halin ko in kula....Zabura Mu'een yayi yace " haba Alhaji wai da gaske kake yi ne....ni fa gaskiya kai nake so saboda kai zaka fi kulamin da kyau...kaga idan kaji za'a min sakiyar da ba ruwa sai ka shigar da magana ta kawai amma Ammi ai kullum tana gida ina zata san meke faruwa". Shi kam Alhaji Baba sosai yake mamakin jin wannan zancen daga bakin Muhammad 'din sa....dan ya tsokane shi sai yace " to ka bari sai munyi magana Ja'afar". " Subhanallah " ya furta da sauri har da kame bakinsa " Uncle Ja'afar dai? Cikin shagwa6e murya ya 'kara fa'din" Haba Alhaji Baba kanason in sha masifa ne hala, ai kasan halin Uncle Ja'afar ba sau'ki kuma wannan fa sirrine tsakanin mu dan Allah be serious mana". Ya 'karashe maganar kamar zaiyi kuka. Alhaji sassautawa yayi ganin dagske fa yake sai ya tambaye shi "...to wace yarinya ce?" Cike da farin ciki yace " yess...." harda watsa hannayen sa. Da sauri Alhaji Baba ya kalle shi sai yace " to na fasa" Tuni ya nutsu yace " ah ah no yi ha'kuri Alhaji......sunan ta Amina amma anace mata Nanne...mahaifin ta kuma wai sunan sa Malam Mamman, gidan su na can 'kasan...ya 'karashe da yiwa Alhaji kwatancen gidan mu. _Comment,Vote nd Share please_ 👏🏻 *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *27* Da yamman ranar kuwa babu islamiya  da yake ranar Alhamis ne kuma bama zuwa, ranar ma ni da Nanne muka kai marka'den shinkafar wainar Ummahn mu...da kuma gya'da dayake yau d'in harda gya'da ta gyara shiyasa muka tafi mu biyu, dama ranar da duk za'ayi markaden gya'da ne muke tafiya mu biyu idan kuwa marka'da'd'iyar gya'dar Ummah bata kare ba ni ka'dai ke zuwa in marka'do mata shinkafa.      A hanyar mu ta dawowa muna tafiya muna 'yar hira, wani sa'in kuma fa'da mukeyi da ita dan ni nawi ya dame ni sosai yayin da ita kuma take faman jan 'kafa tafiyar ta kamar dan dole take yin sa. Burina tayi sauri mu wuce gida ita kuma ta'ki a hankali take tafiyar ta kamar yanda ta saba.       Cikin shirin zuwa ball yazo ya gifta mu ban sani ba ko bai gane ni amma ni kam sau 'daya na kalle shi amma sai na gane shi.    Sai da ya wuce ne sannan Nanne tace da ni " tab amma wannan yana da kyau gaskiya". " Waye wai wancan ?" Na tambaye ta gami da nuna shi da bakina cuz da duk biyun hannaye na ri'ke roban dake kaina. Nanne sai tace " ehh mana koke baki ganshi ba " Juyawa nayi na cigaba da tafiyata sannan nace " Na ganshi mana... 'dan gidan Alhaji Baba ne, mugunta ce dashi ingaya miki sosai".   Baki kawai Nanne ta ta6e bata 'kara magana ba, daga nan kuwa muka cigaba da tafiyar mu.   Na kanyi gaba in barta dan yanayin tafiyar mu ba 'daya bane da ita sam...ban sani bama ashe Nanne kam hankalin ta duk ya koma kan Yah Deen ne, tafiya take tana waigen sa lokaci-lokaci....ni kuwa dake gaban ta bansan hakan ba sam....bazata kawai naji karan fa'duwan abu...waigowata kawai sai naga ashe marka'den dake kan Nanne ne ya kife gaba d'aya sanadin tuntu6e da tayi.....ido na zaro na kalli marka'den sannan na kalle ta...." ta6'di Nanne marka'den wainar kika zubar?" Sai tace dani " ai tunt6e nayi ban kula ba". " To ki 'dauko robar mutafi gida...." Hannu ta kai ta dago robar sai muka ga ashe itama ta face yayin da marfin ta yake nan garau jefe a gefe guda. " ko zamu 'dan kwasa ka'dan?" Nanne ta fa'da tana kallona" Sai nace kamamin mu sau'ke to sai in tayaki". " ka'dan muka kwasa muka bari dan gaba d'aya ya lalace a wurin ba zai 'kara amfani ba. Koda muka je gida kuwa Ummah bata ce komai ba jin cewa Nanne ce ta zubar kawai sai ta kar6i wanda muka kwasa 'din ta ha'da da ruwa da dama ta baiwa ragunan Baban mu suka shanye abinsu.....wannan dalilin ne ya sanya washegari bata yi waina ba harma da kunun baki d'aya.....sanadin kallon Deen da Nanne keyi wanda a lkacin ita kanta ma bazata iya shaidar ya san da zaman ta a duniya ba ko a'a duk da kuwa ha'duwar su da shi ta biyu kenan inda yau.   *****       Tsananin yanda Deen ya saka Nanne cikin zuciyar sa ya sanya kafin sati har ya nemi duk wasu bayanan da ya kamata ya sani game da ita, cikakken sunan ta da sunan mahaifin ta harma da gidan su duk ya sani amma bai ta6a zuwa ba. Da yake da wayo yake yin tambayar ba a fili yake fitowa ya bayyana manufar sa ba...misali ranar da zai fara yin tambayar aranar wani friend 'din sa yazo wurin sa ne sai da ya daidaici 'karfe biyu tayi sai ya jashi suka fito wajen gida suka zauna kamar da gaske, daka yanzun 'karfi da yaji yake tilastawa kansa zaman waje kawai dan ya ganta yaji sanyi cikin ransa..wani sa'in ma idan ya fito sallar azahar baya ta6a komawa gida koda kuwa 'karfe nawa zai kai a wurin to bazai ta6a shigewa ba sai yaga giftawar ta...(ni kuwa nace...aiki ya kama gwari).   Suna zaune a wurin muka zo muka wuce bamu ma kula da su ba.... Ashe Deen kam hankalin sa na kanmu sai ya koma ya kishingi'da ya wani lumshe idanu bazaka ta6a yin zaton yana ganin abu a hakan ba.   Shi 'dayan abokin Deen da bai san meke faruwa bane da wucewar mu sai ya girgiza kansa yace " Allah sarki...wallahi yarinyar nan na matu'kar bani tausayi...gata haka zaka ganta kamar lafiyayya amma wallahi kar kaso kaga wurin jinyarta, hankalin kowa sai ya tashi a dangin ta, gata da masifar shiga rai". Ya 'karashe maganar da sanyin murya. Mu'een na jin haka sai ya gyara zaman sa da kyau da mamaki yace da shi " wace kake magana akai wai?" Juyawa yayi ya kallomu dan shi baya ya juya mana Yah Deen ka'dai ne ke facing da hanyar da muka bi. " Nannen Malam Mamman nake magana akai...gasu can yanzun nan suka gifta mu 'yar doguwa mai hasken....ai kai bazaka sansu ba saboda ba'a garin kake zama ba shiyasa... Yah Deen taran shi yayi da fa'din " to wani irin suna ne kuma Nanne?" Hannu wancan 'din ya 'dago yace kai dakata " cikakken sunan ta Amina Nannen kawai sunan gida ne". Komawa yayi ya kishingi'da yana kallon abokin na sa kamar mai nazarin wani abu a hankali sai yace to me ke damun ta har haka da kace tana baka tausayi?" " Ai kai de ka bari...wallahi sickler ce da ita abin tausayi yarinyar ni ai badan hakan ba wallahi sai na nemi auren ta yarinyar akwai natsuwa tun tana 'yar 'karamar ta". Idanun sa ya miyar ya limshe su a hankali cikin ransa yace " gara hakan ai, kaga ni sai na nemi auren ta in kula da ita....." A fili kuwa " Allah yata lafiya" kawai ya furta daga nan bai 'kara fa'din komai ba. A ranar ne Mu'een yasan haka game da Nannen mu....to ko ranar da yaga gidan mu ma sanadin wani da suke ha'duwa a filin ball ne ya sa mu ganin gidan da yamma bayan sun tashi daga ball 'din sai hanya ta biyo da su ta wurin anan yaga Nannen mu ta fito daga ma'kwabta ta shiga gida. Shi 'dayan bai ma kula da ita ba Yah Deen ne ka'dai ya lura da hakan. Basarwa yayi sai da ta shige gidan kafin ya tambaye shi wai wannan gidan...gidan waye ne?" " Gidan Malam Mamman ne...me ya faru?" Abokin ya 'karasa da tambaya, Mu'een sai yace " bakomai". Tafiya ka'dan suka sakeyi tare wancan 'din ya shige gida sai ya rage saura shi ka'dai...yana tafiya yana tunani....." Nannen Malam Mamman da abokinsa Ashiru ya fa'da da kuma yanzu da aka ce masa " nan gidan Malam Mamman ne, kenan nan ne gidan mahaifinta. Cikin ransa yake ta tunani har ya isa gida....baiji 'kwarin gwiwar da zuciyar sa ke bashi ta ragu ba saboda sam bai hango wani 'kalubale game da hakan ba. Ya riga ya tsara musu a rayuwa cikin da'da'dan mafarkan sa, tun farko Engineering yake da burin karanta amma ha'duwar su Nannen mu yasa shi canza ra'ayi zuwa zama cikakken likita ta yanda zai rin'ka bawa matar sa kulawar da ta dace.....batun yara ma sam bai sasu a lissafin sa ba shi dai Burin sa ya samu Nanne.          Shi kansa wani lokacin sai yaga kamar kawai yaudaran zuciyar sa yakeyi da cewa wai yana sonta amma  tsoron ranar da Uncle Ja'afar zai fahimci hakan yakeyi dan yaga-yaga zai masa cuz karatu mai zurfi yake so yayi in yasan da batun tun yanzu ya kamu da soyayya kuwa ai ya shiga uku, Uncle Ja'afar ba 'karamib raina shekarun Mu'een yake ba har a lokacin kallon yaro 'karami yake masa bansani ba ko dan shika'dai ne agaban sa oho. Sannan sarai yasan halin Uncle Ja'afar bashi da sanyin hali kamar Alhaji Baba....shi kuwa baya jin zai iya cire ta a zuciyar sa cikin sau'ki balle ma irin yadda yake jin mugun kamun da soyayyar ta ta tayi masa...abin sai wanda ya san zafin so ne ka'dai zai iya fahimtar sa.     Satin sa biyu a garin amma gaba 'daya ya mance da damuwar da yake ciki lokuta 'kalilan da suka gabata, damuwar da tayi sanadin zuwan sa garin gaba 'daya, shaf ya manta da Rahma da sha'kuwar su harma da rayuwar da suka yi tare da ita kaf ya manta da su duk a sanadin soyayyar 'yar uwata, abu 'daya ne kawai da ya kasa raba kansa dashi shine yawan jin feelings...wannan  abin kam har yanzu ya kasa raba kansa da shi sai ma 'kara yawaita da yake yi masa. Ta 6angare na ma haka kullum ban fasa zuwa gidan ba, sai dai kwanaki 'kalilan ne muke ha'duwa dashi cuz mafi yawan ranaku na kan zo har nafi ma bangan shi ba, idan kuwa mun ha'dun gaisuwa ka'dai ne ke ha'da ni da shi. Akwai watarana da na gaida shi ma ya amsa a yatsine ya ficewar sa lokacin tare nake da Saif muna zaune, yana wucewa sai na yamutsa fuskata nace da Saif" Allah Deenin kunnan ya fiya yanga da yawa". Ido Saif ya zaro harda kama baki sannan yace dani " yaji ki dai ba ruwana ni...wa ma yagaya miki cewa sunan sa haka?" "Alhaji Baba ne ya fa'da min"... Na bashi amsa ina kallon cikin idanun sa. Sai yace " to ba Deeni zaki ce ba, Yah Deen zaki ce in bahaka idan yaji kina ce mai Deeni duka zai miki ni kuwa ba ruwana". Ban ce komai ba kawai na ta6e bakina na daga nan nayi shiru ban 'kara fa'din komai ba.     Tun daga ranar Yah Deen ya kama baki na dan gudun kar ya dakeni kamar tanda Saif ya gayamin.    Ban ta6a fa'da a idanun sa ba kam dayake ba zaman hira nakeyi da shi ba, amma a duk lokacin da wata hira ta 'dauko aka sako da sunan shi to bana ta6a canza nawa salon 'kiran sunan, ga dukkan alamu kuma ni ka'dai ke amfani da hakan, dan ban ta6a jin wani ya fa'da ba banda ni. Shima 'din tun baya kulawa da lamarina abu na yau da kullun har ya saba da gani na cikin gidan su, bai san me nake zuwa yi ba haka kuma bai ta6a tambayar kowa ba, kuma har yanzun bai san dalilin dake kawoni cikin gidan su kullum da safiya ba.     Sau tari ya kanyi mamaki idan yaga yanda Alhaji da Ammi ke nan-nan dani, ban dama sha'kuwar da yaga nayi da 'kannan sa musamman Saif da jinin mu yafi ha'duwa dashi......    Bai wani damu sosai da yasan dalilin sha'kuwar mu da ahalin nasa ba dan haka shima sai ya 'dauke ni a yanda ya ganni wanda wani lokacin ma ya kan bani fuska ne albarkacin yawan gani na da Nanne da yake yi. ....tsakanina dashi dai gaisuwa ce kurum daga haka kuma babu komai.    〰〰〰         'Bangaren Rahma kuwa.....tun lokacin da ta ga dangi na faman cika gida da 'da'ddaya, taga yanda Hayatu ya dulmiya tsundum cikin shirin biki shikenan ta saduda, yanzu kam ta yarda cewa auren ta da Al'amin babu fashi....tayi danasanin abinda ta aikata yafi sau 'dari uku, a kullun sai tayi danasanin biyewa Mu'een da tayi.   Gashinan ya yi tafiyar sa ya bar ta ana shirin aurar da ita, babu wanda ya damu da 'karancin shekarun ta ga dukkan alamu ma kowa farin ciki yakeyi da hakan. A cikin yanayin idan taje gun mahaifin ta kwantar da kai takeyi kullun ta sha kuka son ranta kafin ta fito, baya magana balle ya lallashe ta dan haka da kanta take bawa kanta ha'kuri ta fito. Ranar wata Juma'ah ne aka 'daura auren ta da Amin bisa sadaki mai daraja.    Ranar tasha kuka sosai kamar ranta zai fita....da yamma kafin a akaita Hayatu ya shigo 'dakin ta wanda ganin a yanayin da ya shigo 'din ya sanya jama'ar dake tare da ita sulale a hankali suka watse baki 'daya. Hayat zama yayi a bakin gado a hankali, Rahma dake can kan stool 'din gaban mirror sai ta cigaba da rera kukan ta bata damu da wanzuwar  sa cikin 'dakin ba. Duk da zuwa yanzun ta tsani Mu'een tsana mai girma amma har yanzu birbishin son shi bai bar 'kasan zuciyar ta ba, yanzu kuwa da take ganin cewa ta zama mallakin wani sai take jin kamar bazata juri rashin sa ba kwata-kwata, 'ka'k'karfar soyayyar ta shi ne ta dawo mata sabuwa dal. A hankali Hayat ya 'kira sunan ta cikin natsuwa, bata amsa ba amma kuma ta rage sautin kukan nata haka kuma bata 'daga idanu ta kalle shi ba. Bai damu ba shima kawai ya cigaba da maganar sa cikin natsuwa da sanyin murya yace " Kiyi ha'kuri Rahma ki gafarce ni, banyi haka dan na 'kuntatawa rayuwar ki ba, nayi ne kawai dan in kare mutuncin ki da mu ma ahalin ki gaba 'daya, na san babu mamaki kina gani na matsayin mutun mai son kan sa ko kuma kice bandamu da za6in ranki ba. Sai dai inaso kisan wani abu Rahma.... lokuta da dama mukan so wasu abubuwa ne mu kuma kafe akan su alhalin ba su kasance alkhairin rayuwar mu ba, sai kiga wanda muke guje masa 'din shine dai-dai garemu kuma za6in Allah masanin komai, amma wanda Allah yaso sau'ka'kawa lamurane ka'dai yake ganar dashi hakan da wuri ya kuma gane.    Ki gode Allah kawai Rahma domin da wuri ya bayyana miki irin yaudararriyar soyayyar da Mu'een ke miki harma ya nufe ni da gani da idanu na matsayi na na yayan ki.       Hukuncin da na yanke kuwa har yau ban ta6a regretting ba, face godewa Allah ma da nake sake yi a kowani lokaci da ya sanya akwai mai yi miki son gaskiya agefe wanda a koda yaushe yake shirye da kar6an ki matsayin matar aure, gudun kar ya zargi wani abu ne ya sanya na sanar dashi dalilin da yasa nake so ayi auren cikin 'kan'kanin lokaci duk da bani da tabbacin idan yaji zai amince amma bani da za6i face bayyana gaskiya ta...nasan idan yana matu'kar son ki ba zai 'ki yadda da auren ki ba tunda akwai masu 'dauko mace agidan karuwai ma kuma su tsarkake ta su aura su kuma rayu cikin farin ciki.   Allah cikin ikon sa ma sai ya sanya Amin cikin masu kyakkyawan zuciya domin kuwa cikin farin ciki yayi na'am da ke inda ya bani goyon baya 'dari bisa 'dari. Hakan da yayi ne ya tabbatar min da cewa zai ri'keki da Amana har 'karshen rayuwar ki........Rahma gashi yau burina ya cika na dam'ka amanar rayuwar ki 'dungurungum a hannun Amin, yanzu matsayin aljannar ki Amin yake, mijinki ne kiyi masa biyayya ki nemi aljannar ki, bana son fitina kuma, ke kanki kinsan Amin ni kaina ya girme ni balle ke dan haka ki bashi girman sa ki kuma nemi aljannar ki da 'karfin zuciya, bisa yardaewar ubangijin ki, karkiyi tunanin zaki yi masa wasu mugayen halaye da baki son shi, to duk abinda kikayi Rahma ki sani kece da asara dan kuwa ko Amin ya rabu dake da wuya ki 'kara samun makamancin sa, ina tabbatar miki da cewa har shi Mu'een 'din da kika yi domin sa ba auren ki zai yi ba alokacin dan matsayin bazarawa za'a kalle ki a lokacin...ki ma yi tunani Rahma, wanda bai aure ki lokacin da ya tabbatar da kuruciyar ki ba yaushe kike tunanin zai dawo ya aureki?......Ni 'dan uwanki ne, kuma inason ki Rahma ke kanki shaida ce akan hakan, ina kuma da burin ganin farin cikin ki a koda yaushe, banason rayuwar ki ta girgiza ne koda wasa shiyasa na aikata hakan wanda na tabbata koda da ran mahaifiyar mu bazata so ganin ki hakan ba hakama Daddy bazai so yaji ance ga mummunan abinda ya faru da rayuwar ki ba, idan kuwa yaji hakan kuma yana da cikakken lafiya na tabbata bazai bar Mueen haka nan ba, amma kinga yanda duk Allah ya gyara komai ba'a yi masa gyara dan haka sai dai muce ALHAMDULILLAH....dan girman Allah ba dan ni ba ki kula da rayuwar auren ki kiyiwa mijin ki biyayya ki daraja ahalin sa hakan shi ka'dai idan kika yi zai tabbatar min da cewa nima kina sona kuma kin bi magana ta Rahma, ina miki fatan 'daurewar farin ciki na har abada....Allah ya albarkaci rayuwar ki.." A hankali ya mi'ke ya kama hanyar fita daga 'dakin, yana share hawaye da takaicin duk shine sanadin auren ta,  bai ma san mai ya kaishi shiga rayuwar Mu'een a wancen lokacin ba da har abubuwan da suka faru suka faru, haka kawai ya tsinci kansa da tsanar Mu'een batare da wani dalili ba a wancan lokacin, yasan kuwa hakan ba komai bane face sharrin shai'dan, sai gashi ta inda Mu'een ya biyo masa, ta inda zuciyar sa bazata iya 'dauka ba....sam baiso ayi auran Rahma tun yanzu ba yaso ace tafara karatun gaba da secondary, yaso ta fita daban agidan nasu amma duk shirin sa ya watse cikin 'kan'kanin lokaci, sai gashi da kansa ya jagoranci aurar da Rahma tun kafin ta kammala secondary 'din ma, tun kafin hankalin ta ya gama daidaita balle ta kai wani matsayi na musamman. Daf da zai 'karasa barin 'dakin yajiyo muryar Rahma cikin sanyi ta 'kira sunan shi....cak ya tsaya tare da waigowa ya kalle ta, tana hawaye shima haka, tsaye ta mi'ke  sannan cikin sanyib murya tace dashi " nayi al'kawarin yiwa mijina biyayya, insha Allahu bazan tozarta maka niyyar ka ba Yayah, zan kula da duk abinda ya kasance hakkine ta 6angare na, nayi maka al'kawarin mantawa da Mu'een mantuwa ta har abada...amma yayah please kace da Amin kar ya hanani 'karasa karatuna inaso in gama yaya......" Ta 'karashe maganar da sheshshe'ka. Hayatu kam take ya cika da tsananin farin ciki mara misaltuwa, har ma bai san lokacin da ya iso gaban ta ba ya fara share mata hawayen ta. Bai furta komai ba kawai ya janyo hannun ta a hankali suka fita daga 'dakin, direct 'dakin mahaifin su ya kaita, dukkan su kuka sukeyi yayin da mahaifin nasu ya tsura musu idanu yana kallon su. Hayatu ne ya fara magana da muryar kuka yace " Daddy ka yafe min dan Allah, idan abinda nayi ba'a son ranka bane, bansani ba ko dai-dai na aikata Daddy, yau gashi zan dam'ka Rahma a hannun mijin ta zata tafi ta bar mu, Daddy ko cikin ranka ne ka daure ka sanya mata albarka...." Ido Daddyn nasu ya lumshe ya kuma bu'desu nan take hannun sa da suka kama ya dam'ke da 'karfi ga dukkan alamu magana yake son yi amma babu dama....wanda hakan sai ya 'kara 'karya zuciyar Rahma take ta sake sakin wani sabon Kuka....cikin kukan take fa'din " Allah ya baka lafiya Daddy, ubangiji Allah ya tashi kafa'dun ka...." Anan 'dakin sauran 'kannen mahaifin nasu suka suka tarar dasu, harda kaka. Nasiha suka sake yi mata inda ta ringa kuka sosai duk kwalliyar da Antyn ta tasa akayi mata duk sun wanku babu su tas, ba'a kuma 'kara bi takai ba kawai aka sake yi mata shiri, kukan da takeyi bai bari an sake yimata kwalliya ba a hakan aka 'dauke ta aka tattara a'kalar rayuwar ta aka dam'kawa Amin inda ya kar6eta da hannu bibbiyu cikin farin ciki. 〰〰〰 Zaune suke dukkan su a dinning Ammi na shirin serving musu abinci kamar kullum sai Mu'een yayi 'yar dariya ka'dan.....Alhaji Baba ne ya kalle shi duba irin na tambaya domin a yanda ya lura 'yan kwanakin kullum cikin farin ciki yake.    Yayin da ya gumtse dariyar tasa yana kallon Ammi yace " Ga dukkan alamu fa Ammi kin samu kan wainar nan, to danni kike yi ne ko kuwa dama kullum haka akeyi agidan..." Ammi bata fasa zuba abincin da take yi ba ba kuma ta kalle shi ba kawai tace " Tambaya kakeyi ne ko.kuwa neman sani? " " Duka biyu Ammi ni duk inason sani, haka kawai kullum baza muji 'kamshin suya ba sai da muga waina...kamar fa sau 'daya ne kawai akayi fashin yin waina agidan nan tun zuwa na?" Ammi ce ta sake fa'din " To laifi ne hakan kuma ko?" " Ah ah ni ban ce laifi bane...ai wainar taki tana shiga sosai Ammi har Allah Allah fa nake gari ya waye in gamu dashi dan nasan babu fashi". Alhaji Baba kam shiru yayi kawai yana ji da ganin su yana murmushi. Ammi ce tace " kai de kasani..." Dai-dai lokacin da take zubawa 'yan biyun nasu abincin... 'Dagowa tayi ta kalle shi sannan ta 'kara da fadin " in ba yaudaran kai ba yaushe ka ta6a ganin na soya waina a gidan nan......ni ba ni keyi ba siyowa akeyi har kunun ma gaba 'daya". Ammi ta fa'di lokacin da take 'ko'karin jan kujera ta zauna bayan tagama zuzzuba musu. Ido Mu'een ya zaro da mamaki yace" siya kuma Ammi....har daga ina haka?" " Can wani gida mana kana tambaya ta kamar wanda idan na fa'da mai gidan zai sani...." Alhaji Baba ne ya tari maganar da fa'din " gidan abokina akeyi " M. Jaji wanda ranar ka gansa a gidan gona.." Baki ya ta6e ha'di da fa'din ni banganeshi ba wallahi". " Amma ai kasan yarinyan nan Hudah da kullun take zuwa gidan nan da safe ko..?" Kai ya 'daga a hankali yana kallon Alhajin da tunanin dama ya rasa dalilin da ke kawota gidan kullum safiya......Alhaji Baba sai yace masa " to mahaifiyar ta ke yi kuma ita ke kawowa, idan kanaso sosai sai adinga kawowa da yawa". "...Haba Ammi dan Allah... yanzu dama ba ke keyi ba shine kuma ba'a ta6a gaya min ba?" " Ai kaji yau kam". Ammi ta bashi amsa cikin halin ko in kula. Shiru yayi bai sake magana ba haka kuma bai kai komai bakin sa ba har kowa ya gama ya tashi a table 'din ya rage saura shi ka'dai da Ammi...shima kansa kuwa bai san me ya hana shi barin table din ba. Ammi ce ta dube shi tace " Idan baka son wainar ga Tea da bread ka ha'da barin soya ma 'kwai yanzu sai ka ha'da ka ci?". Kai ya girgiza mata alamar "a'a" " to me zaka ci?" " ba komai" ya bata amsa a takaice. Ammi 'kyale shi tayi ta mi'ke ta tafi kitchen dan soya masa 'kwan...amma ga mamakin ta kafin ta fito daga kitchen 'din yayi tafiyar sa domin koda ta dawo bata same shi ba a inda ta barshi......har 'dakin sa ta duba bata same shi ba, shi wai a dole fishi yayi sosai harda barin gidan. Bai dawo gidan ba kuwa sai 'karfe uku sannan yazo nan ma da 'kyar Ammi ta sashi agaba kafin ya ci abinci ka'dan. Cikin ranta tace " silly boy....bacin ya gama santin kunu da waina abaya kuma yanzu zaimin iyayi... mthew" ta 'karashe da jan tsaki duk cikin zuciyar ta. A fili kuwa nan nan ta ringa yi dashi dan bata son mutun ya rin'ka zama da yunwa. *****      Bayan kwanaki uku.....ban fasa zuwa gidan ba kamar yadda ban daina kawo waina da kunu ba....na kanzo kamar yanda na saba muyi wasan mu da su Saif in koma gida abina....amma har ib tafi wani lokacin bana ganin sa. Ban sani ba yanzun ashe Deen ya daina zuwa dinning da sassafen nan tunda ya ji cewa ba wainar Ammin sa yake ci ba...yanzu ko ya dawo daga gudun safen sa ma 'dakin sa yake shigewa abinsa sai kusan 10 yake fitowa yasha ruwan tea.....duk yanda yaso ya daure amma ya kasa ya riga ya saba da 'dan'danon waina da kunun nan. Sati guda yana a haka duk 'ko'karin da yake yi wajen sharewa amma ya kasa watarana da sassafe yayi tsaye akan Ammi wai dole sai tayi masa kunun gya'da da kanta...." kajira anjima ka'dan za'a kawo sai ka sha". Ammi ta bashi amsa batare da damuwar komai ba. 'Bata rai yayi yace "  ni Ammi naki nake so dan Allah". ....kallon sa tayi da mamaki tace " haba Mu'een....ka ta6a ganin nayi kunun gya'da da hannuna ne a gidan nan fisabilillahi?" " to shikenan kiyi min waina abar kunun". " Ni duk ban iya ba" Ta fa'di da 'kosawa... Zai sake magana tayi saurin taran sa da fa'din  " in zaka saki ranka ma gara ka saki ranka dan ni babu abinda na iya...ubanka ma ai yana cin wancan 'din balle kai". Ta 'karashe da masifa...    Tamkar zai yi kuka haka ya juya ya bar mata kitchen 'din, gaba 'daya ma sai yaji garin ya fita ransa, Antyn sa Zainab ce ta fa'do ransa dan yasan ita duk ta iya su tunda lokaci-lokaci takan yi musu idan ta ga dama, sai dai wancen da yake ci 'din ko kama 'kafar wannan bai yi ba a da'di...amma dai duk da haka a yanda yake jin son waina da kunun yasan idan ya sami na Antyn ba zai 'ki ba.          Abu 'daya ke taka masa birki shine son yarinyar nan baya so ya tafi ya daina ganin ta domin a duk ranar da ta kasance ganin ta yayi masa wahala to kuwa shima wahala yake sha da zuciyar sa, wani irin so yake yiwa yarinyar mai wuyan fassaruwa.     Bai ta6a tunanin a wannan shekarun nasa zai yi sha'awar yin aure ba har sai da ya kamu da son Nannen mu, 22yrs yake amma yana jin da Uncle Ja'afar zai yadda masa da auren ta zaiyi ya killace ta a gidan sa shi ka'dai ya ringa kallon ta.      'Karfi da yaji yayiwa kansa katanga da wainar mu, duk kuwa da cewa yana tsananin son ta amma haka ya daure ya cireta cikin ransa. Satin sa shida a Shuwarin Uncle Ja'afar ya 'kirashi ya sanar da shi batun computer certificate 'din zai fara, afa'dar Uncle Ja'afar in so samu ne nan da kwana uku ya dawo yayi registration.    Mu'een yaji da'din wannan labarin sosai domin kuwa zama haka a gidan ya ishe shi sai dai gefe daya yana jin tamkar zai bar 6arin zuciyar sa....tun daga ranar ya fara shirin tafiyar sa sai dai rashin natsuwa da ya ziyar ce shi zuciyar sa tun yanzu har ya fara kewar Nanne.      Ana gobe zai tafi a lambu ya yini wurin Alhaji Baba, suna zama suyi hira sosai da Mal. Jaji amma bai ta6a sanin cewa shine mahaifin Nanne ba....to ko ranar ma tare suka wuni dashi yana bashi labarin irin yadda suke samun cigaba a duk lokacin da aka fitar da kayan lambu ko kaji dake gidan gonar. 'Karfe biyar da rabi suka baro lambun shida Alhaji, da 'kafa suke tafiya suna 'dan ta6a hira anan Alhaji Baba yake 'kara yi masa Nasiha game da rayuwar mu ta yanzu, inda ya ringa buga mai misalai da dama musamman ma irin wancan abinda ya ta6a faruwa da shi har ajiyayyen ciwon sa ya tashi masa......Alhaji yace " ina fa'da maka hakane dan nasan ba kowani lokaci bane zangan ka har in gaya maka hakan, saboda bama tare da kai, yanzun ma nasan da kasamu makarantar akan lokaci nasan da zai yi wuya mu ganka...." Sai yace " Haba Alhaji Baba..ai da da yanzu ba 'daya bane, zan dinga zuwa akan lokaci insha Allahu....ni dama zanyi aure na anan garin ai kaga babu batun rabuwa da ku ko?" Ya 'karashe maganar da tsokana. Murmushi Alhaji Baba yayi tare da fa'din " aure a garin nan....?" Kai ya 'daga masa sama yana murumshi tamkar wani yaro...sai Alhaji yace " a ina kaganta dan nasan ka ga wacce tayi maka ne shiyasa ka fa'di haka". " Ai kaman kasani Alhaji...dama inaso in baka amanar ta kafin in tafi..." "Da yake ni kakan kane ko...?" " ah ah ni dai dan Allah Alhaji Baba kar kabari a aurar da ita ma wani, ina kammala karatuna zan dawo ka nema min auran ta ". " Baka da kunya Muhammad, ni ne zan yi ma gadin wacce kake so?" Shagwa6e fuska yayi tare da rausayar da kansa gefe yace " please....please Alhaji... in ba haka ba kuma to kawai ka tanadi likkafani ka ajiye tun yanzu!". " Ja'irin yaro...mu ai namu shan gumba ne kawai". " um-um dai Alhaji gara asha biki da gumban nan, ai nasan kaima baka so in mutu tun yanzu ko ba haka ba?" Alhaji 'yar dariya yayi sannan ya sake fa'din " idan tazo na isa in hana ne Muhammad?" " Allah yasa mu dace...amma ni dai please Alhaji na baka amana idan ka'ki kuma zanje in bawa Ammi na kawai". " Da yafi maka" Alhaji ya fa'di cikin nuna halin ko in kula....Zabura Mu'een yayi yace " haba Alhaji wai da gaske kake yi ne....ni fa gaskiya kai nake so saboda kai zaka fi kulamin da kyau...kaga idan kaji za'a min sakiyar da ba ruwa sai ka shigar da magana ta kawai amma Ammi ai kullum tana gida ina zata san meke faruwa". Shi kam Alhaji Baba sosai yake mamakin jin wannan zancen daga bakin Muhammad 'din sa....dan ya tsokane shi sai yace " to ka bari sai munyi magana Ja'afar". " Subhanallah " ya furta da sauri har da kame bakinsa " Uncle Ja'afar dai? Cikin shagwa6e murya ya 'kara fa'din" Haba Alhaji Baba kanason in sha masifa ne hala, ai kasan halin Uncle Ja'afar ba sau'ki kuma wannan fa sirrine tsakanin mu dan Allah be serious mana". Ya 'karashe maganar kamar zaiyi kuka. Alhaji sassautawa yayi ganin dagske fa yake sai ya tambaye shi "...to wace yarinya ce?" Cike da farin ciki yace " yess...." harda watsa hannayen sa. Da sauri Alhaji Baba ya kalle shi sai yace " to na fasa" Tuni ya nutsu yace " ah ah no yi ha'kuri Alhaji......sunan ta Amina amma anace mata Nanne...mahaifin ta kuma wai sunan sa Malam Mamman, gidan su na can 'kasan...ya 'karashe da yiwa Alhaji kwatancen gidan mu. _Comment,Vote nd Share please_ 👏🏻 *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *29* Cikin muryar kuka Hafsat tace " wallahi jinayi tamkar yanzu ne abin ya faru....ha'ki'ka mutuwa aya ce....Allah yaji 'kan Nanne..Allah haskaka 'kabarin ta...Allah ubangijin ka kyautata namu 'karshen" " Amin yah rabbal Alameen".....Nuree tace gami da juyawa ta kallo 6angaren da Jas ke kwance.......Sannan a hankali ta cigaba da fa'din. " Allah sarki Rayuwa....ban ta6a sanin na sha'ku da Nannen mu ba har sai da na daina ganin ta, zazza6i me zafi ne ya kamani.....ga sunbatun sunan Nanne da ya kasa barin baki na....ban kuma fasa kuka ba.      Har akayi sati uku da rasuwar Nanne ban samu natsuwa ba, na kan yawaita tambayar Ummahn mu cewa " dagaske Ummah bazan kara ganin Nannen mu ba?....babu ranar da bana yin irin wannan tambayar tamkar kullum ba amsa iri daya ake bani ba amma gani nakeyi kamar watarana maganar bakin su zata canza...acemin zata dawo. Nafi jin kewar ta idan na saka abinci a gaba na domin ada tare muke cin abinci ni da ita....muyi fa'da muyi da'di. ***** Akwai watarana bayan rasuwar Nanne da kusan sati shida.... dan har an fara mantawa ma da rasuwar, tuntuni gida yayi shiru mun koma rayuwa mu ukun mu, Baban mu sai ni sai Ummah ta, to shi Baban mu ba yini yake agida ba sai yamma yake dawowa wataran ma har sai anyi maghrib, ni da Ummah ta ka'dai muke yini tare.....haka kuma tun rasuwar Nanne Ummah bata 'kara yin sana'a ba har yau....bama ta da niyyar 'karayi. Lokacin da hantsi ne ina zaune 'kar'kashin bishiyar mango da ke cikin tsakiyar gidan mu.... Ummah ta naga ta fito daga cikin 'daki hannun ta ri'ke da wasu kayan sawan Nannen mu. Kamar da gaske nace da ita " Umnah ina za'a kai kayan?" Sai tace zan bayar ne Hudah babu amfanin ajiyar su ai ko?" Tayi maganar tana 'ko'karin cusawa a leda. Kuka kawai na sanya gami da tasowa na iso inda take....ina kuka ina fa'din " Ina zata kai min kayan Nanne, nace ta ajiye mata abin ta...in ta kyautar to in Nannen ta dawo ita me zata saka?". Kuka nakeyi sosai wanda sai da na saka Ummah ma kuka, 'daki ta kona ta barni da kayan a waje na tattarasu gabana ina kukan da ambatan Nanne. Ummah bata ta6a barmin koda 'dan kwalin bane da sunan inyi amfani dashi dan gudun rigima ta amma duk da haka bata tsira ba.   Sallamar Ammi naji a tsakar kaina ban kula ba sai na cigaba da rera kukana " Subhanallah me kuma ya faru?" Ammi tace tare da hanzarin isowa inda nake. Bu'dan baki na sai nace " Nanne" Salati Ammi ta sanya gami da tallafo ni haba " Hudah wmhar sai yaushe zaki bar wannan abin dan Allah?" Ban kulata ba inata kukana sai ta sake fa'din " bakowa a gidan ne" ?" Ummah dake tsaye daga cikin 'daki ne ta fito ta faman kakkauda kanta, tayi 'ko'karin tsaida kukan ta ne tun sanda taji shigowar Ammi, amma duk da haka kallo 'daya zakayi mata ka fahimci cewa tayi kuka. Tabarma ta 'dauko ta shimfi'da wa Ammi sannan a hankali tace " barka da zuwa". Kallon ta Ammi  tayi gami da fa'din " yauwa". Bata 'kara ce da Ummah ta komai ba kawai ta dawo da hankalin ta gareni. " Saurare ni please". Tace dani....gami da gyara min zamana...." kalli nan" Ta fa'da bayan ta nuna Ummah " waye wannan?" Ta ce da ni tana kallon idanuna...cikin kuka nace " Ummah ta" Banji ba ni share hawayen ki tsaida kuka ki fa'da da kyau inji. Kamar yanda ta fa'da haka nayi ganin kamar yanayin ta ya canza zuwa 6acin rai. Sake tambaya Ammi tayi kamar yanda tayi da farko nima sai nace " Ummah ta ce" " Kin fison kullum ki ringa sanyata kuka ko?" Sai na jijjiga kaina. " Toh me yasa kullum kike 'daga hankalin ta? Da wanne kike so taji, da alhinin rashin 'yar uwar ki ko kuma da fitinar ki?...Hudah ke ko tausayin ta ma bakiji...dubi fa duk yanda ta lalace saboda tsaban fitinar ki, in dai mutuwa ce ai kema wataran zaki mutu a daina ganin ki...kanki aka fara ne?" Masifa Ammi ke min sosai yayin da Ummah ke 'kara share hawaye...abin nawa duk ya isheta, ko ita da ta haifi Nanne iyaka damuwar ta ta tsaya ne tun bayan sati guda da rasuwar amma saboda ni har yau mutuwar ta kasa barin zuciyar ta.... Ni kuwa gani nake kamar fa'dan da mukayi ne ya sanya ta yin fishi dani ta tafi abinta shiyasa kullun nake ganin kamar 'karya sukeyi Nannen mu zata dawo watarana...duk kuwa da cewa kowa bai bani assurance 'din dawowar tan amma na kasa gane cewa idan an mutu ba'a dawowa har abada an rabu kenan. Kuka na fara da jin masifar Ammin ga kuma Ummah ma da ta ke share hawaye a gefe. 'Dan 'karamin tsaki Ammi taja sannan ta kalli Ummah tace " yarinyan nan fa abin nata gaba yake  yi...ba kuma barin ki zatayi ki nutsu ba  a gidan nan...barin tafi da ita ta 'dan kwana biyu a wurina may be zata 'dan warware in bata ganin ku...." Ummah bata ce da Ammi komai ba....amma haka kawai sai taji wani iri abin yayi mata gatsau, cuz bata zaci jin hakan ba, ya zatayi da zaman gidan ita ka'dai kafin Hudahn ta dawo" Ummah ta tambayi kanta. Ammi kuwa tsaye ta mi'ke hannu na cikin nata, bata ko nemi yardar Ummah ba kawai tace " idan mahaifin ta ya dawo ki sanar da shi cewa tana wurina dan Allah". " Toh" Kawai Ummah ta iya cewa daga nan Ammi ta jani 'kofar 'daki na saka takalmana 'dan kwali ne kawai a kaina sai doguwar riga a hakan muka nufi 'kofa " sai anjima" Ammi tace da Ummah yayin da Ummah ta amsa " uhmmn" daga nan muka fice. Ko bayan fitar mu Ummah bata tashi a wurin da wuri ba, tunani kawai takeyi, tana ga kamar ka'dai cin zai mata yawa, ita kanta halin da nake matan ya isheta amma sam bata ta6a kawo rabuwar mu face addu'ar data 'dauri aniyar yimin koda yaushe. A hankali ta mi'ke gami da fa'din "Allah yasa hakan shine mafi alkhairi". Koda Baban mu ya dawo ta fa'da masa ma bai ce komai....irin kslmar da Ummah ta fa'din nan shima ita ya fa'da daga nan suka cigaba da harkokin gaban su. Washegari aka kawowa Ummah ta Ummi 'yar gidan Addah ta ta fari....dan ta ringa 'debe mata kewa kafin in dawo. ***** Ni kuwa rayuwa ta wurin Ammi sai godiyan Allah, domin Ammi bata nemi akawo min ko kayana ba dan bata so in tmringa yawan tunawa da gidan, tayi tunanin ko duk kayan mu iri 'daya ne da marigayiyan tsoron ta kar inzo yin amfani dasu kuma in dinga cigaba da tunawa shiyasa ma bata nemi abata ba. Washegarin zuwa na Ammi ta bayar da 'dinki cikin ajiyayyun zannuwan da take dasu aka ciccire min rabi rabi kusan kala biyar ta bayar aka 'dinka min. Ammi ta kula dani sosai, ta kula da rayuwata da tarbiyyata tamkar ita ta haife ni, Ammi bata ta6a barina in zauna shiru, da dare ita kanta take min wanka ta sani in kwanta kan tsakiyar gadon 'dakin ta sani inyi addu'ah sannan tayi ta karanta min story har inyi bacci sannan sai ta koma other room. Da safe ita zata tadani inyi sallah da wanka sannan ta bamu abincin breakfast ni da su Saif bayan munci sai mu wuce makaranta, idan mun dawo bana yi mata aikin komai haka zata sani kallon cartoon a T.v har lokacin sallah tayi daga nan idan nayi sallah sai kuma mu shirya mu wuce islamiya.   Ranar da babu islamiya kuwa...ta ware min lokacin da ya dace nayi baccin rana ragowar lokutan ma duk bata barina in zauna haka kurun Ammi occupied them da abubuwan 'dauke hankali. Musamman ta sa aka siyo min game dan in ringa yi lokacin da babu wutan Nepa...gidan mu kuwa sai dana yi sati hu'du cif ban le'ka ba....ko nace zanje sai tace bani da lafiya in bari sai na samu sau'ki tukun. Shagwa6ewa nakeyi ince " Ammi nifa lafiya ta 'kalau". " Ke de ki bari when u recover da kaina zan kaiki". Ban sani ba ashe Ammi in taso zuwa gidan namu sulalewa take yi tatafi abinta lokacin da ta tabbatar ina tare da dasu Saif muna game, wani sa'in har zataje ta dawo ma bansani ba. Ummah ta tun tana saka ran dawowata har ta ha'kura gashi Ammi bata ta6a ce mata ga ranar da zan dawo ba haka kuma bata sanar da ita son zama da ni take yi ba. Dalilina Ammi ta nemi 'yar aiki saboda ta ringa samun isasshen lokacin da zata zauna dani agidan, in kuwa kitchen zata shiga tare muke zuwa Ammi bata barina idan tana girki kuma bata gajiya da nuna min idan anyi kaza anyi kaza kaza zai zama..ta kan gaya min...idan muna kitchen. Alhaji Baba ma ta 6angaren sa abin sai Alhamdulillahi domin tamkar mahaifi haka ya 'dauke ni, lokaci 'kan'kani na dawo 'yar gatan gidan gaba 'daya, har 'yar ramata ta 6oye. Sha'kuwata da 'yan biyun Ammi kuwa sai abinda yayi gaba musamman ma Saif, dan shi tare muke cin abinci cikin plate 'daya da shi...idan wasa zamuyi ma team 'din mu 'daya dashi...sai dai duk da haka Ammi bata ta6a bari na in shiga 'dakin su haka kawai sai dai in da wani dalili.    Zakiyi mamaki Hafsat yanda kwata-kwata na manta da duk damuwa ta ta baya har mantawa nakeyi da cewa ni ba 'yar gidan ba ce....natsuwa ce ta shige ni ta ban mamaki, yanzu sam na daina rashin ji kamar bani ba...dan ko a gidan idan Zaid ya min mugun ta ban kula shi haka kuma ban kai 'karar sa. Ranar da muka fita gidan mu tare da Ammi kuwa...karki ga farin cikin da Ummah ta tayi da gani na...." Alhamdulilah kawai take fa'di cikin ranta...a fili kuwa godiya tai ta zubawa Ammi. Har muka bar gidan ha'koran Ummah na basu daina bayyana kansu a fili ba cike da fara'a. ***** Alhaji Baba kam damuwar sa kullum Yah Deen ce dan har yau bai iya ya sanar da shi halin da ake ciki ba, ko ya tambaye shi amanar sa kuwa sai dai yace masa " Allah zai yi maka jagora Mu'een....." Fargabar yanda Mu'een zai kar6i lamarin yake yi, kullum tunanin bai wuce hakan. Da abin ya dame shi ne sai lokacin ya sanar da Ammi komai da suka yi da Mu'een kafin tafiyar sa, itama Ammi tayi mamaki sosai amma tasan koma miye ne dole idan yaji ai zai ha'kura tunda bamu ke da mutuwar ba, Allah ne ka'dai mafi sani akan hakan. 〰〰〰 *BAYAN WATA UKU DA RASUWAR NANNE.*       Sai lokacin Yah Deen yazo gida cike da murnar zaiga ahalin sa da sahibar sa, ga kuma 'dumbin farin cikin da ya cika shi na samun gurbin karatu a FEDERAL UNIVERSITY DUTSE.... course 'din da yafi k'auna a rayuwar sa wato Pharmacy.....yana kammala wannan programme 'din da yake yi zai tattara ya koma jigawa dan cika burin sa. 👇🏼 *Toh fah readers ina son jin ra'ayoyin ku game da dawowar* *_MU'INUDDEEN......._* *Sai naga ruwan comments sannan zan cigaba da typing, sa6anin hakan kuma ina jin sai kun jini nan da 1 week ko kuma 29 january idan muna cikin rayayyu.....dan harga Allah na raina comments 'din ku* *Labarin dai har yanzu da saura....amma in akayi ha'kurin bina duk zamu ji koma menene....sannan dan girman Rabbi👏🏻 ku ringa sharing ni 'din abubuwa kan min yawa ne shiyasa* _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _Ina son ku masoyana_ 😍 _...Allah ubangiji ya haskaka rayuwar ku da mafi alkhairi daga cikin alkhairai_ 👏🏻 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *30* ........'Bangaren Alhaji Baba kuwa...a yau 'din duk ya kasa sukuni, damuwar sa ta yawaita sosa...tunanin sa ta yanda Mu'een zai kar6i zancen ne, tun ranar da Yah Deen ya bashi amanar ta ya fahimci tsantsan son da yake yi mata cikin idanun sa da kalaman sa ya fahimci hakan, babban abinda yasa ya 'kara gaskata soyayyar tasa ma shine da har Yah Deen ya iya manta dangantakar da ke tsakanin su matsayin sa na mahaifi agare shi, ya iya duban tsaban idanun sa ya ha'da shi da amanar kula masa da ita, ha'ki'ka hakan ka'dai ya wadaci koma waye fahimtar tsantsan son da Mu'een ke wa marigayiya AMINA...musamman idan kasan halin sa cewa bashi da rashin kunya sam a rayuwar sa.       Alhaji Baba lambun sa ya tafi yaje ya ke6e kansa guri guda yana tunani, sai dai daga 'karshe dole ya watsar da batun ya cigaba da harkokin sa.         Shigan yamma Mu'een yayi dan kuwa 'karfe biyar da 'yan mintina ya shigo garin...fuskar sa cike fal da fara'a tamkar bashi ba, ya 'kara kyau da girma, dama gashi dogo ne shi ba laifi sai gaba 'daya ya juya ya koma tamkar 'dan shekara talatin da haihuwa.    Ni kaina lokacin da na gansa tsaye a 'kofar shigowa parlourn bangane shi ba, saboda kwaftareren ba'kin gilashin dake manne a idon sa, shima kuma bai yi min magana ba tunda yayi sallama ya dire jakar sa a wurin sai ya yaja ya tsaya yayi shiru. " saif!...Saif!!...Zaidu!!!" Na fa'da da 'karfi cike da firgici ina 'dan jan baya dan harga Allah tsoro ya bani, ban kuma kawo akaina shi bane saboda nasan shi baya murmushi haka siddan sai da dalili 'kwak'kwara. Ammi da Saif duk lokaci guda suka bayyana suna tambaya ta saboda jin 'karan 'kiran sunayen da nayi kuma nayi da 'karfi, sannan da tsoro nayi. " Wai me ya faru ne?" Saif yace yana kallo na, yayin da Ammi ta ce dani " Hudah Lafiya kike faman ihu?" Ban bawa kowa cikin su amsa ba illa hanyar 'kofa da na nuna musu da hannu na wanda sai a lokacin suka lura da shi.     Still yana nan tsaye with smile on his face yake duban mu da karkataccen wuya. Saif murmushi yayi yayin da Ammi tace da shi " 'kaniyar ka Muhammad!" Cikin marairaita yace " haba Ammi daga isowa ta ?" " me yasa zaka yi tsaye acan to har kana firgita min yarinya?" Murmushin sa ya 'kara fa'da'dawa sannan yace " Ni fa Ammi ke kawai nake jira ki taroni". Ido Ammi ta 'dan zaro tare da fa'din " daga zuwan na ka zaka fara ko?" Ganin bata da niyyan zuwa ne ya sanya shi tahowa inda take yana kwa6a fuska. Ni kam da kallo kawai nake bin sa ina mamakin sa ayau 'din gaba 'daya ya canza min. Saif ne ya girgiza kansa shima cike da jin dadin ganin 'dan uwan sa tare da wucewa inda jakar sa take ya 'dauka ya wuce da shi cikin 'dakin sa. Ammi kuwa hannun sa ta kama kamar 'dan goye ta jashi zuwa kan kujera mai zaman mutun biyu ta zaunar da shi kan kujera....da yaran su na Igbo tace da shi " Sakalcin yau ya motsa kenan?...baka ganin 'kannen ka na kallon ka ne?" Kai ya 'dan sosa gami da satan kallon 'bangaren da nake tsaye...dai-dai fitowar Saif sai ya maida kallon sa gare shi.    Suna ha'da idanu sai yace " Yayah Welcome...hope an iso lafiya?" Da " Alhamdulillah" ya amsa shi daga haka ya ja ya kishingi'da gami da sakin numfashi. Ammi ya kalla yace da ita " barka da gida Ammi". " Yauwa...ya su Auntyn ka?" " Lafiyan su" " karatun fa?" " Shima normal Ammi saura na tafiya Jigawa yanzu". " To Allah ya taimaka ya bada sa'a". 'Kasa-'kasa ya amsa mata da " Amin Ammi na". Ni kam har lokacin ina tsaye a inda nake sai ma raku6uwa da nayi jikin labile ina kallon su.    Ammi ce tace dani " 'karaso mana kika wani tsaya acan, koma gaida yayan ki baki yi ba". Da jin haka sai nayi saurin tahowa kusa da ita kamar dama jira nake a kira ni na zauna nima a hankali cikin sanyin jiki " wai har kin manta waye shi ne?" Ammi ta sake tambaya ta. Sai na girgiza mata kai alamar "a a" Sai tace" to oya..." ta karasa maganar da nuna min shi da kanta. Sai da na 'dago na kalle shi kafin nace " Ina yini". Bai amsa ba sai kawai ya 'dago idanun sa ya kalle ni sannan naga ya kalli yanayin yanda na ra6u da jikin Ammi. Kai ya 'daga ya maida kallon sa ga Ammi gami da 'dage gira 'daya.    Wannan karan da yaran turanci ya tambaye ta wai ni 'din daga ina haka?" Murmushi Ammi tayi masa sannan tace da ni" Je kawowa Yayan ki ruwa mai sanyi ya sha kinji". Tun ma ban amsa mata ba balle akaiga na matsa a gurin yayi saurin furta " ah no barshi...ban bu'kata Ammi". Yayi maganar yana kallon Ammi...yana gama maganar kuwa sai ya 'dauke kansa ya koma duban agogon dake 'daure a hannun sa. " Wai kana nufin baka gane ta bane ko me?" Ammi ta tambaye shi. Sai ya 'dago ya kalle ta, bata damu ba ta cigaba da fa'din "...Hudah ce fa Hudah ta ko yau 'din ma sai ka mare ta sannan zaka gane ta?" Murmushi yayi yana murmushin yace da ita" to dan Allah Ammi ni me nace ne?" " kai de ka sani" Ammi tace a hankali. Sai ya girgiza kansa a sace ya sake kallo na cuz maganar Ammin sosai ta bashi dariya, kuma ita tasa ya tuna da ko ni wacece, kawar da kansa yayi gefe dan yanzu kam har cikin zuciyar sa ya gane ni...ala'ka ta da Ammin sa ne har yau baisani ba kuma ya kasa ganewa. Mi'ka yayi a hankali gami da mi'kewa tsaye..." bari in 'dan watsa ruwa Ammi zan 'dan huta  ma ka'dan amma saboda ina da wurin zuwa anjima". Bai saurari jin amsar ta ba ma kawai ya juya ya fara tafiya abinsa...Ammi sai ta bishi da idanu sannan tace " idan ka gama sai kayi magana akawo ma ko 'dan abin sha ne ma" " okay " kawai yace gami da shigewa ciki. Ni kam shiru nayi duk jiki na yayi sanyi da ganin sa, dan shi ka'dai ne na kasa sabawa da shi har yau a cikin gidan.   Wanka yayi ya fito ya mi'ke kan gado cuz already yayi sallar la'asar tun kafin ya taso. Da hannayen sa yayi pillow yana kallon fan 'din da ke juyawa saman 'dakin, farin ciki sosai yake ji yau zai ga sahibar sa, kamar an mintsine shi kuma sai ya mi'ke ya janyo jakar da ya zo da ita, kayan sawan sa ne ka'dai da sauran kayan amfanin sa, sai wata jaka da ya ciro daga ciki. Kan gadon ya zazzage kayan sai ga Less na mata mai masifar kyau kala 'daya da turmin exclusive atampa 'daya sai takalmi 'daya da kuma mayafi shima guda 'daya. Takalmin ya 'daga yana juya shi a hannun sa yana murmushi, a fili ya furta " Allah yasa banyi kuskuren number ba".    Jin motsin kamar za'a shigo ne ya sanya shi saurin tura kayan 'kar'kashin pillow ya yi tsuru-tsuru kamar mara gaskiya yana kallon 'kofa, he thought Ammi ce zata shigo, sai kuma yaga ashe Zaid ne ma. Ajiyan zuciya ya sau'ke a fili sannan ya ce da shi " ya akayi?" " Ammi ke 'kiran ka" cewar Zaidu. Sai yace " okay.. gani nan zuwa...let me dress up". Yayi maganar yana mi'kewa tsaye.        Bayan juyawan Zaid ne ya saki murmushi, a hankali ya 'dan bigi 'kirjin sa sannan a fili ya furta " silly me!...me yasa zan ji kunyar Ammi idan taga kayan? Ya tambayi kansa. Wani side na zuciyar shi ne ya bashi amsa da fa'din"...may be ina jin kunyan kar tagani ta gane cewa 'dan ta ya fara soyayya ne?" " to Alhaji Baba fa, ya akayi da kaina na iya sanar da shi har ma na bashi amanar kulawa da ita?" Ya sake tambayar kansa. Baya ya koma ya fa'da kan bed 'din da bayan sa" ....wayyo ni!...ashe abin kunya na tafka babba har haka? shaf hakan bai ta6a zuwa kaina ba...Alhaji Baba zai ce banda kunya!...ohh Yah Allah ya zanyi yanzu?" Ya ware idanuwa tamkar da wani yake maganar. Sai kuma ya saki murmushi ya girgiza kansa lumshe idanu yayi sannan yace " Duk laifin kine fa Nanne, da baki shiga zuciyar wannan Deenin ba nasan da bazai iya aika ta irin hakan ba". Da murmushi ya rufe tunanin kana ya shirya ya fito parlour wurin Ammi. Zama yayi gefen ta yana fa'din " Ammi ni da nace zan huta kuma sai kika sa a 'kirani?" Abinci ta nuna masa da hannun ta tare da fa'din " ai nasan idan na barka bacin komai zakayi ba shiyasa".... " Ai ko yanzun ma ba ci zanyin ba Ammi, banjin cin komai Allah, farin cikin da nake ciki ma ya ishe ni....bari sai zuwa anjima can babu mamaki zan nema". Da mamaki Ammi ke kallon sa har ya dasa aya a maganar tasa sannan tace..." Farin ciki ne zai hana ka cin komai Mu'een? yau ne ka fara ganin mu? ko kuma yau ne ka fara zuwa garin nan?" " Ai yau 'din na musamman ne Ammi". Yayi maganar yana murmushi. " Kai de kasani" ta fa'da tana murmushin itama,  while a cikin zuciyar ta ita ka'dai ta san tausayin sa da take ji, tasan cikar farin cikin nasa ba na ganin su ka'dai ba ne, sam bata son wannan fara'ar tasa ta 6ace daga kan fuskar sa, sai dai tasan wannan dole ne, ko ba yanzu ba, ko anjima ko gobe, sati, watanni ko shekara matu'kar mummunan labarin ya isa kunnuwan sa dole farin cikin sa zai yi masa 'kaura. Har ya sumbaci goshin ta ya wuce ciki bata lura ba sai bu'de idanun ta tayi taga baya nan. Tagumi ta zabga nan kan dinning 'din kawai tausayin sa na 'kara shiga dukkanin ga6o6in jikin ta. Alhaji Baba ma yau har sai da aka idar da sallar maghrib kafin suka dawo cikin gidan tare shi da yaran nasa da duk suka ha'du a can masallaci. Suna ha'duwa Alhaji Baba ya saki fara'a ya bashi hannu tare da fa'din...     " ....sau'kan yaushe?" " Tun jiya da safe Alhaji"! Mu'een ya bashi amsa da fa'din hakan. Alhaji Baba sai yace "Ashe har ka tsufa gidan ma ni ban sani ba?" " Ni ai har na yi fishi Alhaji, awanni na kusan biyu a garin nan amma ka 'ki dawowa ai da niyyya ta ma yanzu in bika can gidan gonar inga ko lafiya". " Shi kenan ai yanzu kam tunda gani nazo, ayyukane yau 'din suka 'dan taru mana sai a hankali". " babu laifi Allah ya taimaka" Cewar Yah Deen kenan. Koda suka shiga cikin gidan ma a parlour suka zauna shi da Alhaji Baba suna sake gaisawa, su Saif kuwa 'dakin su suka wuce dan dama basu zama da shi suyi hira, dama Alhaji ka'dai ne amma da Deen kam a a. Ni kuwa da Ammi muna 'dakin ta tana duba Hisnul muslim yayin da nayi kwanciya ta daga gefen ta har bacci-bacci nake ji yana shirin dauka ta. Mu'een bai yadda ya zauna nesa da Alhaji ba saboda tambayar da yake son yi masa dan haka gefen sa ya dawo ya zauna a hankali cikin ra'da yace " Alhaji Baba amana ta"! Ido Alhaji ya 'dan bu'de yana kallon sa a 'ko'karin sa na ganin ya 6oye damuwar dake cikin ransa....cikin 'karfin hali yace da shi " amana wace iri?" " Haba Alhaji, ai amana guda 'daya tak na bari a hannun ka kuma ita nake tambaya fa?" ya 'karashe da shagwa6a wa Alhaji Baban. Kasa juran kallon sa cikin yanayin Alhaji Baba yayi sai kawai ya kauda kansa gefe, sannan a hankali cikin basarwa yace " ai ni har na manta da batun ma gaba d'aya". Mu'een zai sake yin wata magana sai Alhaji Baba yayi saurin mi'kewa tsaye bai jira jin komai ba kawai ya nufi hanyar 6angaren sa yana fa'din " idan ka gama ka sameni ciki mu 'karasa maganar". Ido Yah Deen ya lumshe gami da mi'kewa tsaye shima ya wuce 'dakin sa, wata arniyar shadda ya ciro mai kalar sararin samaniya sabuwa dal ya sanya ajikin sa, agogo, hula da takalmi ma duk ba'a barsu abaya ba...ya dauki a'kalla kusan rabin sa'a kafin ya kammala shiryawan cuz cikin sanyi yake yin komai, can 'kasan zuciyar sa yake jin babu da'di sai dai bai san dalili ba sam.   Sai da ya gama 'daura links 'din hannun rigar sa kafin ya sake taje gashin kansa, turare ya sake fesawa ajikin sa mai sanyin 'kamshi...sannan yaje ya maida kayan da ya siyo matan cikin leda cuz tun 'dazun bai sake bi takan su ba...da gama sasu cikin ledan sai ya ajiye gefen gado da niyyar da ya dawo daga wurin Alhaji kawai sai ya 'dauka ya wuce.    Agogo ya kalla sannan ya fito a hankali yana gyara hular kansa ya nufi 6angaren Alhaji Baba, sallama yayi aka bashi iznin shigowa inda yaje ya samu Alhaji zaune har ya fito daga wanka ya shirya cikin farar jallabiya yana 'ko'karin shafa man zafi kan gwiwan sa. A hankali ya 'karasa ya kar6i man zafin yana fa'din " Alhaji har ka fara abin tsoffi tun kafin ma kayi jika ko 'daya ko?" Murmushin ya'ke Alhaji Baba yayi sannan yace " in bazaka yi ba bani abina ni". " a a gashi inayi ai Alhaji". Mu'een ya fa'di yana shafa man gami da 'dan massaging gwiwar a hankali. 'Dan satan kallon sa Alhaji Baba yayi sai ya cigaba da kallon gwiwar tasa " sai ina haka na ganka cikin shiri kamar me shirn barin gari?" " Unguwa zani" Ya bashi amsa a takaice. " To bani abu na na 'karasa kar na 6ata ma lokaci...maza yi tafiyar ka". Mu'een 'kara yin 'kasa yayi da idanun sannan yace " A ah ai sai naji dahir daga bakin ka kafin zanje, kar inje a koro ni dan bafa sani na akayi ba Alhaji". " Har ina ne haka?" Alhaji Baba ya sake tambaya as if bai gane inda zancen Mu'een 'din ya dosa ba. Sai da ya saki murmushi kafin ya biyo bayan ta da fa'din " zance fa zani...shiyasa ma na shirya da wuri dan ban son dare yayi sosai". Ido Alhaji Baba ya lumshe cikin zuciya ya furta" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." A hankali ya sake furta sunan _Muhammad_ . 'Dagowa yayi ya kalle shi batare da ya amsa ba jin cikin lokaci 'kalilan muryar Alhaji Baba ta canza...'dan matsakaicin hasken 'dakin bai hana shi hango kwantacciyar damuwar da ta bayyana kan fuskar Alhajin ba. ".....Muhammad kar de kace min shirin zuwa wurin Amina kayi yanzun?" Shiru Mu'een yayi bai iya yace da Alhajin komai ba kamar yadda bai iya cigaba da sake massaging gwiwar Alhajin ba illah ri'ke man da yayi yana kallon gefe....cuz shima zuwa yanzun ya fara jin bugun zuciyar sa na 'karuwa, fatan sa dai Allah ya sa alkhairi ne ke tunkaro sa, fargabar sa 'daya kar ace da shi an bada auren ta ga wani wanda ba shi ba..... " Muhammad ka zauna ka saurare ni da kyau kaji...." Yah Deen da jin haka sai ya d'ago ya kalle shi take y'ar guntuwar fara'ar da ta rage kan fuskar sa ta kau, dan ya fahimci akwai wani 6oyayyen abin daban da Alhaji Baba ke son sanar dashi wanda shi bai sani ba. Jin cigaban maganar Alhajin ne ya dawo masa da tunanin sa, abinda ya tsinkaya cikin kunnuwan sa kuwa shine " Amina...fa ta jima da komawa ga mahallicin ta...." Kallon da Yah Deen ya cigaba da yi masa ne ya sanya shi 'karawa da fa'din " ...ma'ana Amina ta rasu Muhammad sanadiyyan tashin ciwon....."   Bugun zuciya mai karfi gami da fargaba ne suka ziyar ce shi lokaci guda...har ma bai san lokacin da ya 'dago hannun daman sa ya toshe bakin Alhaji Baba da shi ba....abinda kenan ya hana Alhaji Baba 'karasa maganar da yayi niyyan fa'da.     Cikin in ina yace " Dan Allah...Alhaji kar kayi....min irin wannan wasan, ba zan...iya jurewa ba....". Ya 'karasa maganar da girgiza kansa. Baya ka'dan Alhaji Baba yaja tare da cire hannun Mu'een daga kan bakin sa, Yah Deen sai yabi hannun sa da kallo sannan ya cigaba da kallon Alhajin wanda ya cigaba da fa'din. " Duk da yake ina yi maka wasa Muhammad amma wannan bai kasance cikin abinda zan yaudare ka dashi ba, ai nine mahaifin ka, kai kanka kasan bazan so abinda zai ta6a rayuwar ka ba, miye ma ribar yin hakan idan nayi?....mutuwa sau 'daya tak ake yinta Muhammad kuma shi Amina tayi, and kai kanka kasan idan an mutu ba'a dawowa....kayi mata addu'ah kaji, na 6oye maka tuntuni ne saboda gudun irin halin da zaka shiga amma banyi hakan da wata manufa ko kuma dan 6ata maka ba....." Ido kawai ya tsurawa Alhajin, bama ya fahimtar komai, tuntuni maganar Alhajin ta farko take faman amsa kuwa cikin kunnuwan sa...... _" Mutuwa 'daya tak akeyi Muhammad kuma shi Amina tayi_ "..... abinda ke nan yake ta yi masa yawo a tsakar kansa. Bai iya ya sake motsa ko da 'dan yatsan sa ba ne, sakamakon jin kalaman Alhajin cikin tabbatar wa, take 'kirjin sa ya ri'ke shi ga bugu da zuciyar sa keyi tamkar zata fito fili, bai ankara ba sai jin sau'kan hawaye yayi saman fuskar sa. Bai damu da hakan ba kawai ya cigaba da kallon Alhajin cikin rawar murya ya nuna kansa sannan ya bu'di baki da 'kyar yake fisgan maganar yace" Alhaji...kana nufin...Amina Amina....ta rasu... tuntuni kuma ban sani ba?"   Kai Alhajin ya jinjina masa alamar tabbatar wa..... Take sai ya kai hannayen sa ya dafe kansa da yake jin yana juya masa ha'di da barazanar tarwatsewa, ga 'kirjin sa da ya yi masa nawi sosai jikin sa na faman kakkarwa.....kafin Alhaji yayi wani yun'kuri sai ji yayi ya saki 'kara mai 'karfi sannan ya saki kan ya dafe 'kirjin sa da duka hannuwan sa biyu hawaye na cigaba da bin kuncin sa. ~Kwana biyu kun jini shiru nima na rama ne~ 🤪 _Comment_ _Share_ _Vote_ *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *31* 'Karan da yayin ne ya janyo hankalin mu gaba 'daya, Ammi da dama take kan hanyar zuwa gurin Alhajin sai tayi saurin 'karasawa ciki. A rikice ta shigo tana tambayar Alhajin " me ke faruwa?" Alhaji Baba ri'ke yake da hannun Deen yana 'ko'karin kwantar masa da hankali amma ina sam ya rasa nutsuwar sa.     Jin muryar Ammi da yayi ne ma ya sanya shi 'karfin halin mi'kewa cikin idanun sa cike taf da ruwan hawaye ya tsaya gaban Ammi. Hannun ta na dama ya kamo ya 'daura saman 'kirjin sa saitin zuciyar sa yace " Ammi...kiji bugun zuciya ta, kiji irin 'ka'k'karfan soyayyar da nake yi mata...Ammi dan girman ki tausaya min kar kice min dagaske ne Amina ta rasu...Nanne ta tafi ta barni Ammi dagaske ne...?" Sai yanzun hawayen sa suka gangaro kan kuncin sa, yana jin hakan amma bai kula ba still hankalin sa na wurin Ammi yana sauraran jin amsar bakin ta...Ammi kam duk jikin ta yayi sanyi bata ma san me zata ce da shi ba, bata san abin nasa har haka ya girmama ba, Muhammad 'din ta ne yau yake kuka da hawayen sa, kuma kukan ma akan mace. Tsura masa idanu tayi tana kallon sa, tausayin sa na sake ratsa ta ji take tamkar ta taya shi kukan itama, amma tasan yin hakan tamkar ta fallasa asirin zuciyar ta ne.      Ganin kamar yana 'ko'karin sulalewa 'kasa ne ya sanya Alhaji saurin 'karasowa ya tallafo shi wanda sai a lokacin Ammi ma ta ankara da hakan a firgice ta ambaci sunan shi tana tallafan 'daya gefen nasa. Kai Mu'een ya girgiza mata idanun sa lumshe batare da ya amsa sunan shin da ta 'kira ba kawai ya fara fa'din ..."..me ya..sa..zaki tafi..ki barni?...Ammi me yasa...bata jira na dawo na sanar da ita 'dumbin soyayyar da na ke yi mata ba..." " Haba Muhammad kai fa musulmi ne, me yasa kake fa'din irin wa'dannan kalaman...bacin kasan Allah ne ke da mutuwa ba mu ba". Alhaji Baba yayi 'karfin halin fa'din hakan yana gyara masa kansa dake jikin sa. Wasu hawayen ne suka sake gangaro masa da gudun su...idanun sa ya bu'de ya tsayar cak akan fuskar Alhaji Baba bakin sa na rawa da alamar magana yake son yi amma ya kasa saboda azabar dam'kar da zuciyar sa tayi masa da 'kyar ya iya fuzgan " Alhaji...dagaske....ta barni...?" Kafin Alhaji yayi wani yun'kuri sai gani yayi Mu'een ya mi'ke sumamme a jikin sa. Ammi kam tuni ta fara kukan itama cikin ranta take fa'din " wannan wani irin masifa ne?" Ganin yanda ya mi'ke ne ya sanya ta rikice tafara fa'din _innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ ... _Alhaji me yafaru what's wrong with him..?"_      Cikin sanyin murya Alhaji Baba yace " ki kwantar da hankalin ki please...ba wani abu bane he just fainted". Yana shafa cikin hannun Yah Deen ya fa'di hakan batare da ya kalli Ammi ba...shi kansa ya kasa nutsuwa gaba 'daya hankalin sa ya tashi, dama irin abinda tuntuni yake gudu kenan shiyasa ma ya kasa sanar da shi tun farkon faruwar lamarin.   Ammi na jin cewa suma yayi ta tashi da sauri ta 'debo ruwa tana 'ko'karin she'ka masa Alhaji Baba ya dakatar da ita. Da mamaki tace " me yasa kuma Alhaji...idan ansa masa ruwan zai ta shi ai". Kai Alhaji ya girgiza mata sannan ya bu'kaci ta bashi wayar sa. Wayar ta 'dakko masa yayi 'kira inda ya bu'kaci ganin wani likita dake unguwar tasu ya kuma sanar dashi abubuwan da yake so ya zo dasu sannan ya cire wayar daga kunnan sa ya ajiye ta gefe.     Daga nan ya dai-dai ta kwanciyar Mu'een 'din ya kasance straight bai ko saka masa pillow ba ya barshi a hakan illah cikin hannun sa da ya cigaba da shafawa...yana tuna abinda ya ta6a gaya masa ranar da ya bashi amanar ta....".... _dan Allah Alhaji kar ka bari a aurar da ita ma wani, ina kammala karatuna zan dawo ka nema min auran ta....please...please Alhaji!, in kuma ba haka ba to kawai ka tanadi likkafani ka ajiye tun yanzu_ ..."      Allah sarki....sosai tausayin sa ya 'kara kamashi ga tsoron halin da zai iya shiga sanadin hakan, jikin Alhaji Baba har rawa yakeyi ga gumin da ke faman keto masa, shi ka'dai ya san halin da yake ciki dalilin wannan lamari.     Ammi kam zama tayi daga bakin gadon Alhaji Baba ta rafka tagumi tana share hawaye  tana kallon sa....amma tunanin ya tafi wani wuri ne can daban, tunanin har yaushe Muhammad ya san soyayya, yaushe ma ya fara son Amina da har zai 'dagawa kansa hankali saboda rasuwar ta....ko cikin ahalin ta babu wanda taga ya suma saboda rashin ta, ko ni da nake ta haukan damuwa da ita ban ta6a suma saboda rashin nata ba...amma dube shi, yana matashin saurayi da shi amma ji yanda ya maida kanshi saboda macen da ba ma tasan yana son ta ba..." Sosai abin yake damun Ammi a zuci. Ina daga parlour ni da su Saif muna zaune munyi jigum dan tun 'dazu da mukaji 'karar Yah Deen muka rage volume na Tv muka yi shiru, babu kuma wanda ya motsa daga inda yake illah hankulan mu da duk suka zama a tashe.... sallama muka ji daga bakin 'kofar parlour. Zaidu sai ya tashi yaje ya bu'de...gami da gaishe shi.   Likitan da ke ri'ke da 'yar jakan aikin sa sai ya bu'kaci ganin Alhaji Baba. Sai lokacin Zaidu ya bashi hanya ya shigo jin cewa Alhaji ne ya 'kira shi, yana maida 'kofar yana rufewa sai yake bani umarnin zuwa in yiwa Alhaji Baba magana. Banyi musu ba na tashi da sauri na isa 6angaren Alhajin na tura 'kofa a hankali da sallama a bakina...babu wanda ya amsamin illah 'dagowa da sukayi suka kalle ni bansani ba ko sun amsa min a zuci...ni kuwa tunda idanu na ya sau'ka a kansa mi'ke sai hankali na ya tashi sosai, Nannen mu kawai na tuna ranar da ta rasu a hannu na wanda ya kasance shine rana na 'karshe da na ganta..tun daga lokacin akace Nannen mu wai rasuwa tayi, da gama wannan tunanin take sai hawaye ya fara bin kuncina, kuma still ina kallon sa ban kuma iya na furta komai ba.   'Bangaren Alhaji kuwa ganin na tsaya shiru ne ya sanya shi tambaya ta da fa'din " uwa ta ya akayi ne?" Sai da na goge hawaye na kafin na ce da shi " wani ne yazo" Nayi maganar ina nuna hanyar da na shigo kamar wata sokuwa. Alhaji sai yace " maza je ki ce masa ya shigo, kuma ki daina kukan nan babu abinda ya faru da shi kinji".    Da sauri na juya na ifmsar da sa'kon Alhaji amma ban iya na sake zama da su Zaid ba sai bin bayan likitan nayi, Allah ya taimake ni ma da ya shiga bai tura 'kofar ya rufe ba hakan sai ya bani daman shiga batare da sun lura da ni ba dan lokacin hankulan su yana wajen Yah Deen ne.   Direct wajen Ammi na wuce na jinginu da jikin ta na yi shiru, Ammi kam hankalin ta na ga 'ko'karin da likita ke yi ne na ganin farfa'dowar Mu'een amma duk da haka Ammi bata kasa bani kulawa ba, bata kalle ni ba kam amma da hannun ta 'daya tayi 'ko'karin tallafoni zuwa jikin ta.     Tsawon mintina uku likita na fama da shi kafin ya farfa'do da sakin ajiyar zuciya mai 'karfi. Ammi da Alhaji Baba duk a fili suka saki hamdala Ammi har tana murmushi inda ta sake tallafa ta....wanzuwar likita awurin ne kawai ya hanata isa ta rungumi 'dan ta cikin jikin ta amma Allah ne ka'dai yasan yanda ta ji da'din farkowar tasa.     A hankali ya bu'de lumsassun idanun sa wanda suke saitin inda muke zaune ni da Ammi.      'Kara waro idanun nasa yayi akan mu saman la66a ya furta _" Amina...."_ Take Alhaji Baba da likitan duk suka juya suka kallo mu. Ammi kam da bata ji maganar tasa ba ganin sun kallo mu ne sai ta tsorata da sauri ta mi'ke gami da kama hannu na muka isa gaban su tana tambayar su abinda ya faru cikin  harshen turanci.    Ni kuwa ido na tsura masa ganin yana dafe 'kirjin sa kuma yana kallo na, a hankali sai na cire hannu na daga na Ammi na tsuguna agaban sa...idona cikin nasa cikin sanyin murya nace " Yah deen baka da lafiya ne?" Bai amsa ni ba dan haka sai na cigaba da fa'din....kar ka yadda ka mutu irin na Nannen mu kaji...su Saif da Ammi suna sonka kuma idan ka mutu kuka zasuyi baza su 'kara ganin ka ba". Maganar da nayi ne ya sanya shi rintse idanu da 'karfi sai a lokacin ya fahimci cewa ni 'din ba Aminan sa bace, ya san Aminan sa bata shirmen magana kamar ni. Idanun sa a rintsen likita ya gwada B.P 'din sa sai yaga bai hau ba...yana cire abin sai ya fara yunkurin mi'kewa da sauri likitan ya tallafo shi har suka mi'ke tsaye. " Ina zaka ne wai Muhammad?" Alhaji Baba ya tambaya yana mi'kewan shima... a hankali da rawar murya yace " 'daki... na". Shiru suka yi masa dukkan su, inda Alhaji Baba ya iso ya kama shi da kyau yayin da likita ya tsaya ya tattari tarkacen sa sannan ya bisu abaya nima ganin Ammi ta bisu sai na bita da sauri. Shigar su parlourn ne ya sanya su Saif saurin mi'kewa duk jikin su sai ya 'kara yin sanyi da ganin yanayin da 'dan uwan su yake ciki, tamkar ba 'dazun yazo garin da 'kafafun sa ba.          Likita ne ya fara shiga sai ya ri'ke musu 'kofa suka shigo sannan Ammi ma ta shiga, ina 'ko'karin shiga sai Zaidu ya ri'ko hannu na a hankali yace " me zaki je yi ke kuma?" Ban bashi amsa ba kawai na sanya kuka ina 'ko'karin 'kwatan hannu na ni dai burina ya barni in je..." let her go please Zaid". Saif ya fa'di yana kallo na. Take kuwa sai ya sake ni...na kuwa kama hanyar 'dakin na shiga.     Lokacin da na shiga Alhaji Baba na cire mai rigar Jumps da ke jikin sa sai ya rage masa sauran farar singlet ne da dogon wandon kayan....a hankali ya komar da shi ya kwantar Ammi ta dai-dai ta masa pillow akan sa. Numfashi yake fitarwa da 'karfi wanda duk sanda zaiyi sai kaji ya fitar da sauti har 'kirjin sa na hawa da sau'ka sosai...in kin ganshi a lokacin gwanin tausayi Hafsat tamkar ba shine Mu'eenuddeen 'din Uncle Ja'afar ba". Nuree ta fa'di tana kallon fuskar Hafsat da murmushi kan fuskar ta. Hafsat ma murmushin tayi sannan tace " Sharrin zuciya ne ba laifin sa bane ai, kinsan so mugun cuta ce sam bata da da'di". "Hmm" Kawai Noor ta ce sannan ta cigaba da bata labarin. " Allurar bacci kawai Alhaji ya bu'kaci ayi masa kafin gobe dan haka batare da 6ata lokaci ba likitan yayi masa nan take. Har a lokacin kuma ina tsaye ina share hawaye na, har ga Allah tausayin shi nake ji sosai duk da bansan meke damun sa ba amma yanayin sa ba 'karamin karya min zuciya yayi ba, ga kuma tunanin Nannen mu da ya tsaya min cak a zuci banaso ace shima ya mutu irin na ta a daina ganin sa...har cikin raina nake jin banason hakan sam. Likita na cire Allurar sai nayi saurin 'karasawa gaban gadon na dur'kushe gwiwa na daga 'kasa tare da kamo hannun sa 'daya na ri'ke da duka hannuwa na.... na cigaba da kuka na. Idanun sa dake lumshe ya bu'de a hankali, yana kallon fuska ta sai yayi murmushi mai kyau mai sanyi mai kuma tsaywa a zuciyar wanda ya san muhimmancin ta.....dishi-dishin da yake gani a lokacin ne ya sanya shi kasa tantantace kamanni na...a hankali ya bu'di bakin sa ya ce da ni ".....Amina ai baki mutu ba ko?....ai dama nasan bazaki tafi ki barni ba..." Yayi maganar yana kallon fuskata. Ban damu ba duk da sunan Amina da naji ya 'kira ni da shi ban kuma san manufar hakan ba, ni dai fatana kar shima ya mutu irin na Nannen mu, bansan me yasa na damu da hakan ba tun a wancen lokacin...nafi son rayuwar sa fiye da rashin sa duk kuwa da cewa ba wani 'kwa'k'karan ala'ka ce tsakani na da shi ba.   Hannun sa naji kan fuska ta yana share min hawaye na batare da ya sake magana ba...su Ammi kam kallon mu suka tsaya yi da mamaki jin sunan da ya 'kira dashi, wanda sai a lokacin ma Ammi da ta 'kura min ido sannan ta fahimci kammanin dake tsakani na da Nanne, bata ta6a lura da hakan ba sai yanzu, sosai kuma muke kama da ita abinki da jini kinsan ko babu kamar ma dole sai an gani ta wani 6angaren, sai dai haske kawai da Nannen mu ta fini dashi da kuma karan hanci.... Yana gama share min hawayen ya sau'kar da hannun sa tare da sake lumshe idanun sa a hankali inba a kusa da shi kake bama baza ka ta6a jin abinda yace ba...ni dai dake tsugunne gaban sa naji yace "....do not ever leave me...plea...se?" Daga haka bai sake magana ba. Alhaji ne ya tambaye ni abinda yace dan yaga bakin sa yayi motsi,  ba ma iya fa'da zanyi ba dan ban fahimce shi ba a lokacin da yake ban gama koyon turanci ba ni, Saif ne ma yake 'ko'karin koya min kuma ya kan min magana da shi wani sa'in shiyasa nake 'dan ji ka'dan-ka'dan....so naji abinda yace kuma zan iya fa'da a baki amma bansan nufin sa kan hakan ba. Ina shirin maimaitawa Alhaji Baba abinda naji ya fa'da ne sai Ammi ta riga ni fa'da masa...ashe itama taji.    Kallon sa kawai Alhaji yayi sannan ya kalle ni, ni kuwa ban ma san yana yi ba.      Suna ganin ya samu baccin Alhaji Baba yayi godiya wa likitan anan yake sanar da shi cewa babu mamaki ma ya tashi da 'dan 'karfin jiki koma babu ciwon tunda da farin ciki yayi baccin cuz har a lokacin idan ka dubi fuskar sa zaka hango kwantaccen murmushi akai.   Godiya sosai Alhaji Baba ya sake yi masa sannan ya sallame shi, tare suka fita daga 'dakin ya raka shi, nima suna fita na mi'ke na fita ina goge fuskata. Ammi ce dai bata fita ba sai da ta 'dan kintsa 'dakin tukunna, wanda ga rin hakan ne ta ci karo da jakar da ya saka kayan da siyawa Aminan sa. Ammi zazzage su tayi da mamaki take 'dagawa take gani, sosai tausayin sa ya 'kara kamata dan a zahiri zaka fahimci zazzafan soyayyar da yake yiwa yarinyar. Tun lokacin da na fito sai na isa gefen Saif na raku6u jikin sa nayi shiru...shima shirun yayi, Zaid kuwa da idanu kawai ya bini. Cikin sanyin jiki Saif ya tambaye ni " wai meke faruwa ne?" Sai na bashi amsa da fa'din " Nima fa bansani ba, amma naga yayan can ba lafiya kuce masa kar ya mutu ya barku irin na Nannen mu...Ammi ma tana son shi kuma?" Zaid dake gefe ne azafafe ya bani amsa da fa'din " an gaya miki mutuwa zai yi ne...ke kin fiya shirme wallahi". Shiru nayi ban kula shi ba haka ma Saif da ya rafka tagumi. Wajen sai yayi tsit bamu sake magana ba. 'Bangaren Ammi kuwa maida kayan tayi cikin jakar sannan ta fito da shi ri'ke a hannun ta, kallo 'daya tayi mana sai ta 'dauke kanta kamar ance ta juyo kuma sai ta waigo take ta ha'de gira ganin yanayin zama na da Saif.....Da 'dan 'karfi ta ambaci sunana sai na waigo na kalle ta," ta so ki biyo ni" Ta ce dani tare da juyawa ciki. Sai da ta kai kayan  ta 6oye su sannan ta dawo gare ni....ba ta son ya sake gani balle har ya tuna da cewa ya siya mata kaya amma kafin ya isa gare ta labarin mutuwar ta ya riske shi dan haka dole ta 6oye masa kayan daga idanun sa. Jikin ta ta janyo ni ta zauna gefen gado.." wai har yanzu kuka kike yi ne?" Girgiza mata kai nayi sai tace " to ba na hana ki zama jikin su Saif ba...ba kya ji ko?" " Ki yi ha'kuri Ammi". Na fa'di da sanyin murya ta. Sai tace " in kina son in ha'kura kar ki sake zama jikin su kinji, ke bakya ganin ke macece nd 'ya mace is a jewel kama kanta take yi bata ha'da jiki da maza kinji?" Sai na 'daga kaina sama. " Yauwa Hudah ta promise me bazaki sake ba". Tayi maganar tana mi'ko min hannun ta...nima sai na 'daga nawa na sanya cikin nata. " Good girl"! Ta fa'di tana murmushi...nima sai na 'dan murmusa daga haka sai ta sa muka 'dauro alwala muka gabatar da isha'i. Alhaji na dawowa daga raka likitan ya umarce su Saif ma da su wuce suyi sallah dan isha'i ta wuce tuntuni. *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* ~This page is 4u *Nanerh, Nanah* and *Nusaibaty* 😍...ina yinku mutane na....Ubangiji Allah~ ~yai ta faranta muku har 'karshen rayuwar ku~ *AMEEN* 👏🏻 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *32* Lokacin da na tashi a bacci har gari yayi haske sosai dan haka sai da na yi sallah kafin na tafi kitchen neman Ammi, gaishe ta nayi ta amsa tana mai cigaba da ayyaukan ta, nima sai na matso na fara taya ta....fuskar ta cike da annuri tace da ni " baki tambayi jikin yayan ki ba" Sai ma a lokocin ni kam na tuna da shi, cuz harga Allah kwata-kwata na manta da shi ma balle abinda ya faru,  maganar Ammi ce ta sani tunawa da wanzuwar sa, banyi 'karya wa Ammi ba nace mata " ai mantawa nayi ne Ammi".   Shiru tayi min bata amsa ba illah murmushi....sai da tafara aikin kafin tace " har kin manta da shi bacin jiya har cikin bacci ajiyan zuciyan kuka kike yi kuma saboda shi?" Bance komai ba dan bansan mai zance da ita ba tunda bansan da wannan batun ba ni, ganin da sakin fuska tayi maganar ya sanya ni nima murmusawa kawai na maida hankali na ga aikin da Ammi ta bani. Ashe Ammi na jin da'din warwarewar 'dan ta ne, domin tun kafin sallahr Asubah ya tashi, ba laifi garau ya tashi sai 'dan abinda ba'a rasa ba na daga ciwon kai da kuma 'kirjin sa dake 'dan yi masa nauyi ka'dan, sanin da yayi cewa bai yi sallahr isha'i bane ya sanya bai ko bi ta kan ciwukan da yake ji ba ya tashi ya 'dauro alwala ya fara gabatar da sallar isha'in wanda yana tada sallar Alhaji Baba ya bayyana bakin 'kofar 'dakin nasa...ganin.yana tsaye yana sallah cikin narsuwa ne ya sanya Alhaji Baba sakin hamdala da bai san lokacin da ta fito fili ba ma..... wannan shine karo na biyar kenan da yazo duba shi daga dare da wannan lokacin. Bai iya ya tafi ba dan farin cikin ganin yanda ya tashi da kansa batare da taimakon kowa ba, hakan ka'dai ya tabbatar ma da Alhaji Baba  cewa jikin nasa da sau'ki babau laifi, abinda yake gudu cikin zuciyar tasa bai faru ba...dama tsoron tashin ciwon sa yake yi amma tunda Allah ya ta'kaita ai hikenan. Yana tsaye a wurin har Yah Deen ya idar da sallah yana sallamewa kuwa ya waigo ya kalle shi...dan tun 'dazun ya san da tsayuwar sa a wurin sanadin hamdalar da ya furta a fili.    " Ya jikin naka?" Alhaji Baba ya tambaya yana mai tahowa kusa da shi. Sai da ya saki ajiyan zuciya ya shafa fuskar sa da hannun sa 'daya kafin ya amsa da fa'din " Alhamdulillah....banjin komai yanzu". " masha Allah haka ake so ai...Allah ya 'kara afuwa..ubangiji ya sa daga hakan shikenan". " Amin" yace a 'kasan ma'koshi. Alhaji Baba juyawa yayi ya fara tafiya jin 'kiran sallah na tashi daga masallaci...yana tafiyar yace " bari inyi shirin masallaci ko". Yah Deen bai amsa shi ba har ya bar 'dakin...cigaba yayi da zama a wurin yana addu'ah tare da istigafari da salatin annabin tsira {SAW} har sai da yaji motsin su suna shirin fita kafin shima ya yun'kura ya tashi ya tare su inda suka ha'du cikin babban parlour n da ya hada duka 6nagarorin gidan. " Zaka iya zuwa  ne?" Alhaji Baba ya tamabaye shi yana duban sa da kulawa. Yah Deen sai ya gya'da kansa alamar " erh"....." jiri fa baka ji?" Alhaji Baba ya sake tambayar sa, cikin dakiya ya amsa da fa'din " ban jin komai Alhaji". Daga haka yayi gaba dan baya son wata tambayar kuma, suma sai suka rufa masa baya inda suka 'karasa fita gaba 'daya. Koda ya dawo daga masallacin ma kwanciya ya 'kara yi yana tunani  ahaka Ammi tazo ta same shi, sai dai bata wani jima wurin sa ba ta fita ganin kamar bacci yake son yi, bai fito fili ya fa'da ba amma cikin.muryar sa ta fahimci yanayin da yake ciki.    Fitan ta keda wuya kuwa wani baccin ya sake  'daukan shi...har kuma muka tafi makaranta bai tashi ba wanda hakan ya sanya ban ha'du da shi ba wannan da safiyar. Da fitan mu likita ya dawo ya duba shi da yake zai wuce wurin aikin sa ne so bai wani jima ba ya wuce ganin jikin yayi normal dan haka sai ya bayar da wasu magunguna kawai yace idan ya tashi ya sha su na sati guda ne maganin, amma kala uku ne, yana bawa Alhaji Baba sai yayi tafiyar sa da fatan Allah ya bashi lafiya. Ko bayan fitar likitan ma 'karfi da yaji ya tilastawa kansa sake yin bacci saboda baya son ya dinga yawan tunanin abinda bashi da ikon canza shi...     'Karfe 10am ya tashi a baccin, kansa sosai yayi masa nauyi haka ma yake jin kirjin sa har sai da ya zauna bakin gado ya dafe kan, gudun kar jiri ya kwashe shi, idanun sa sun firfirto, ya ko'de yayi fayau da shi. Ko yanzun ma da yake dafe da kan nasa tunani yake yi, wani lokaci sai yaji tamkar 'karya ne Aminan sa nan da ranta bata rasu ba, but idan ya tuna cewa mutuwa ta Allah ce, ka kan rasa ranka a duk lokacin da Allah ya ga damar rabaka da ita sai yaji cewa babu mamaki da gaske ne Nanne ta rasu, tunda yasan mahaifan sa baza su ta6a yi masa 'karya da mutuwar ta ba. Ammi ce ta shigo ta same shi a haka, bai 'dago ya kalle ta ba duk cewa ya ji muryar ta ya kuma san itace ta shigo, amma shi sam yanzu a halin nan da yake ciki bai son hayaniya sam....bai son ma kowa ya ringa kusantar sa ka'daici yake bu'kata sosai...in da hali ma kar kowa yazo inda yake da hakan yafi masa...sai dai ya san samun hakan abu ne mai wahalar gaske tunda ya san irin son da iyayen nasa ke masa, bazasu iya 'daukan lokaci batare da sunji halin da ya ke ciki ba. Ko da Asuba ma da yaji Alhaji Baba ya zo duba shi, ba 'karamin tausayin sa ne ya kamashi ba, dan ya san babu mamaki ko baccin kirki bai samu yi cikin daren ba saboda shi. Kusa da shi Ammi ta isa ta zauna gami da ta6a hannun san da ya dafe kansa da shi, yana jin haka sai ya 'dage hannayen san gami da 'dago idanun sa ya kalle ta. " Barka da safiya Ammi?" Yace cikin raunanniyar muryar sa. Ammi bata amsa shi ba sai tace " Muhammad ba zaka daina damun kanka game da wannan abin ba ko..look at your self mana...zaka ja da yin Allah ne?" Ido ya lumshe cike da damuwa ya kuma bu'de su nan take ya sau'ke su kan fuskar Ammi sannan cikin sanyi yace " Ya zanyi Ammi? ke ma kin san dole ne in damu sosai..." Take sai hawaye suka cika cikin idanun sa....Bai damu ba ya cigaba da fa'din " Burina itace Ammi, komai na, farin cikina da damuwa na duk itace Ammi...na sa ta a raina sosai, me yasa tun lokacin rasuwar ta baku gaya min ba Ammi?, Wallahi da ko ma miye agaba na zan bari inzo ayi jana'izar ta dani inyi mata addu'a da kaina Ammi..." Sai hawayen sa suka 'karasa gangarowa. Take yayi 'kasa da kansa yana mai dafewa da hannun sa 'daya. Ammi kam jikin ta sanyi yayi sosai ita kam mamaki yake bata, ada bata 'dauki abin da zafi ba sai yanzu da ta ga yana 'ko'karin illata zuciyar sa sannan ta tabbatar da abin nasa da gaske ne, tausayin sa sai ya cika mata zuciya....saurin kawar da tunanin tayi, ta sa hannu ta 'dago kansa tana share mai hawayen  cikin kwantar da murya tace da shi "...kayi ha'kuri Muhammad, Alhaji ne yace bazai iya sanar da kai ba kuma kaga ni lokacin ma banda labari sai daga baya yake sanar da ni...kuma inajin duk abinda Alhaji ya aika ta akan hakan ai yayi ne saboda kai, saboda farin cikin ka, i'm sure badan ya 6ata maka bane ya sa bai sanar da kai ba, shi kansa abin ya dame shi sosai ina da tabbacin da zai iya dakatar da mutuwa daga 'daukan ran Amina da zai yi alokacin koda kuwa cewa zai fansar da nasa ran ne saboda kawai kai kayi farin ciki, amma kasan hakan ba mai yiyuwa bane, Amina kam ta riga mu gidan gaskiya kuma ko yanzun ma zaka iya yi mata addu'ah ba laifi bane, shima tafi bu'kata daga gareka a halin yanzu". Bai ce da Ammi komai ba kawai ya kwantar da kansa akafa'dar ta ya lumshe idanu a hankali yace...." Allah ya ji'kan ta yayi mata Rahma, Allah ya sanya ta cikin Aljannar sa may daukakiya, Allah ya....sai kuma yayi shiru. Murmushi Ammi tayi tace " ....Allah yasa ku ha'du a Aljannah ko?" Murmushin shima yayi take sai ya mi'ke ya wuce bathroom. Ammi da idanu ta bishi har ya shige bayin tana murmushi sai ta girgiza kanta tare da tashi ta bar 'dakin. Zuwa tayi ta ha'do mai tea lafiyayye ta kawo ta ajiye masa kuma har a lokacin bai fito daga bayin ba. Bata damu ba kawai tayi ficewar ta da yake taji motsin ruwa tasan hakan kawai yayi ra'ayi. *****      Dawowar mu makaranta bayan mun 'dan huta ina ta bawa Ammi labarin makaranta yanda na fara 'ko'kari a ajin mu da yake Saif na 'ko'karin koya min wasu abubuwa yanzu shiyasa nake 'dan 'ko'kari. Ammi sai jinjina kai take yi, ita kam duk hankalin ta na wajen sane, ai kuwa dakatar min da surutun nawa tayi da fa'din muje ki gaida yayan ki" tashi tayi ta nufi dinning ta ha'da abinci a plate 'daya sannan ta umarce ni da in 'dauko mata tayi gaba ina 'dauka sai na bita abaya. Ta riga ni shiga 'dakin...amma koda na isa nima sai na tsaya kamar yadda na ganta tsaye tana kallon sa. Mi'ke yake akan kujerar dake 'dakin yana kallon sama idanun sa a rintse ban san ko bacci yake yi ba ko kuma idanun sa biyu. " _Mu'een_ !" Ammi tace sai naga ya bu'de idanun sa a hankali, kallo 'daya yayi wa Ammi sai ya tsaida idanun sa akaina ya 'kura min su yana kallo na, ni kam sai na yi 'kasa da nawa idanun gami da matsawa bayan Ammi na 6uya ai kuwa da ya daina hango ni sai ya lumshe idanun sannan ya mi'ke ya zauna ya fuskanci Ammi. Duk abinda ya faru Ammi na lura da shi amma sai ta basar cuz tasan with time ne zai daina idan mutuwar tabi jikin sa. " Ya jikin naka?" Ammi tace da shi tana zama gefen sa. Sai yace " ni lafiya ta 'kalau Ammi". " hakan ake fata ai....ga abinci please ka samu kaci ko ka'dan ne" Tayi maganar tare da mi'ka min hannu a 'ko'karin ta na kar6an abin da ke hannu na. Da sauri na 'karaso na bata. Yana shirin yin magana ta dakatar dashi da fa'din " ban son musu Mu'een tun safe me kaci?" Kallon fukar ta yayi batare da ya sake magana ba, sai ta jinjina mai kai tana bu'de abincin gaban sa take fa'din " ai nasan abinda zai fito bakin ka, bai wuci kace ka 'koshi ba...nd u did not anything since morning, tea 'din ma ban yadda ka shanye ba" " Allah Ammi nasha da yawa ma..." ...taran sa tayi da fa'din .."sai ka 'kara wannan ma koka'dan. Goshi ya tattare gami da kawar da kansa gefe. _Comment Vote and Share_ 👌🏻 *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 🤞🏻😍 *Dedicated to 'kawa AMEEN D. ABDULLAHI...fatan Alkhairi 'kawar kirki...Allah ya 'kara dan'kon 'kauna* ~{Ameen}~ 🙏 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *33* Ammi bata damu ba kawai ta daidai ta zaman ta tare da bu'de abincin ta sanya spoon ciki. "..Ina yini?" Na fa'di kaina 'kasa kuma batare da na ambaci sunan kowa ba...haka kuma in ce masa ya jiki ma sai ya min nawi a baki na. Shima 'din 'dan ra'ayi kuma bai amsa ba, sai da Ammi tace da shi..."..da kai fa take". Bai ko 'dago ya kalle ni ba ya amsa da fa'din " lafiya "a takaice. Ji nayi duk babu da'di, duk da yake ma ba yau na fara gaishe shi yana amsan min a hakan cikin halin ko in kulan ba amma na yau 'din ka'dai sai naji na muzanta. 'Daga ido na nayi na saci kallon sa...yanzun ya 'daga kansa sama ya jingina da jigin kujerar hannun sa a 'kirjin sa idanun a kuma a lumshe...hararar sa nayi gami da kauda kaina gefe, cikin raina nace " wannan ko bashi da lafiyan ma ba zai canza hali ba". Muryar Ammi ne ta katse min tunani na..inda naji tana fa'din" yauwa 'yan matan Ammi je kawo wa Yayan ki ruwa...amma ki duba ba mai sanyi sosai ba kinji?" Kai na 'daga mata tare da juyawa sum-sum na fita daga 'dakin.       Ina fita sai Ammi ta 'debo abincin ta nufo bakin sa da shi " open ur mouth". Ta fa'di da yaren su, ganin ta kusanto bakin sa da abincin ne ya sanya shi bu'de baki batare da musu ba ya ansa.       A hankali yake taunawa da'din abincin na ratsa shi, wanda ko 'kamshin abincin ka'dai ma ya isa ya ja ra'ayin mutun ga cinsa, doya ce da taji manja da bushashshen kifi harda kayan lambu...sosai yaji da'din abincin dan haka koda Ammi ta 'kara bashi be yi gardaman kar6a ba, lokacin da ta 'debo zata bashi ne a karo na uku har ya bu'de baki sai cak idanun sa suka sar'ke da nawa da isowa ta wurin kenan. Bakin sa yayi saurin rufewa tare da yin 'kasa da idanun sa, a hankali sannan ya kai hannu ya kar6i spoon 'din daga hannun ta can 'kasan ma'koshi ya furta " Ammi let me..." Ita ma Ammi ba ta hana shi ba ta sake mai tare da sakin murmushi, inda batare da 6ata lokaci ba ya 'karasa kai abincin bakin sa.     Bai sake bi ta kaina ba dan ko inda nake bai sake kalla ba ya cigaba da cin abin sa cikin ransa yake tunanin ai idan yaran nan suka ga Ammi na bashi abinci a baki ai raina shi zasu yi....daga haka ya 6ige da tunanin kama da nake yi da marigayiyar sahibar sa. A hankali na yi sallama tare da 'karasowa gefen Ammi na mi'ka mata cup da ruwan da na 'dauko...tana kar6a na juya na fita batare da na sake jiran komai ba.    Ammi bata fito ba sai da tabbatar ya ci abincin tukunnna.    Bai ma ci ko rabi ba ya ture gami da sanar da Ammi cewa ya ishesa abincin. Ruwa ma ka'dan yasha ya ajiye.   Ammi sosai taji da'din hakan dan haka da fara'ar ta ta fito da ragowar fuskar ta cike da annurin ganin jikin nasa Alhamdulillah sai godiyar Allah. Har lokacin dawowar Alhaji Baba tayi Yah Deen bai fito parlour ya zauna ba, masallaci kawai yake fita da ya dawo kuwa sai ya wuce 'dakin sa, sai bayan sallar maghrib ne ma suka 'dan zauna da Alhaji can harabar gida har isha ya same su wurin, daga can suka wuce masallacin. Dawowar su sai kowa ya wuce 6angaren sa wato su Saif da Zaidu, Yah Deen kam tare suka shiga 'dakin Alhaji amma bai wani jima cikin 'dakin ba ya fito ya wuce nashi 'dakin, ko gun dinner ban gan shi ba...muna gamawa kuwa Ammi tace in jira muka kai masa abinci.... Tun dawowar sa daga 6angaren Alhaji Baba ya shige bayi kusan 30mins ya 'dauka ciki kafin ya fito da niyyar shirin bacci....a tsanake yake yin komai, cuz babu abinda zai aikata cikin rayuwar sa batare da ya ha'da da tunanin Nanne ba, shi kansa bai san wani irin so yake yi mata ba, bai ta6a tunanin zai so abu har hakan ba sam, sai gashi ya tsinci kansa dumu cikin wata iriyar soyayya mai cin zuciya sossai lamarin ke karya masa zuciya, yanzu ne ya fahimci ashe tun zaman sa da Rahma bai ta6a son ta ba, bai ta6a 'kaunar ta ba, bai ta6a jinta a zuciya kwatankwacin yanda yake jin Nanne ba. " Toh menene?...ya tambayi kansa...saboda ko lokacin da sha'kuwar su da ita yayi 'karfi yayai zaton ko soyayya ce ashe ba haka bane, bai kuma ta6a zama na musamman yayi tunani akan Rahma ba ko ada 'din, Rahma bata ta6a shiga cikin rayuwar sa ta mamaye shi ba...gara ma ranar ha'duwar su da ita na 'karshe wannan ya san bai manta da incident 'din da wuri ba...yakan yawaita tunawa da wannan ranar musamman idan feelings ya tsananta masa ya abu na farko da yake fara tunawa shine that moment...baya ga haka kuwa sam-sam babu komai, shi kansa yana mamakin yanda  Rahma tayi saurin fita daga rayuwar sa...sa6anin Nanne da komai zai aikata ta kan fa'do ransa. Tsaye yake yana 'ko'karin 6alle  botiran silky rigar baccin daya sanya a jikin sa ta bacci, ga dukkan alamu bai jima da fitowa daga wankan ba bazaka ta6a gane yanayin da yake ciki nan take ba in dai ba sanin kirki kayi masa ba, a zahiri kenan....sai dai a ba'dini abin ba haka yake ba, shi ka'dai ya san zafin da 'kirjin sa ke yi masa....yana basarwa ne kuma kawai dan ya san koma wace iriyar damuwa zai shiga hakan bai isa ya dawo masa da Amina ba.....sanin hakan da yayi ne ya sanya shi 'ko'karin tilastawa zuciyar sa dangana bayan da ya 'kara tabbatar wa kansa cewa wanda ya mutu ya mutu kenan.       At times yawan tunani ke 'kara masa zafin 'kirjin musamman idan ya tuno yanda ya 'kwallafa ta cikin ransa, ya gama tsara musu rayuwa tun ma kafin ta san da zaman soyayyar tashi, tunanin Mu'een ko da yaushe nata ne, sanyin halin ta na birge shi, yanda take komin ta cikin sanyi da natsuwa...sosai hakan ya 'kara bada babbar guddummawa wajen dasuwar soyayyar Nanne cikin ransa jijiya da gangan jikin sa, yana jin tamkar rasa Amina da yayi shine babban hasara da yayi cikinrayuwar sa ta duniya....muhimmin gurbi ya ke6e mata cikin zuciyar sa. Ire-iren tunanin kenan da ke 'kara sashi jin matsanancin ciwo a 'kirjin sa, amma sam bai damu da ciwon ba shi, he wish shima 'din da ya bita a ganin sa hakan zai fi masa sau'ki. Gaba 'da ya zaman garin sai ya ishe shi, ji yayi daga yau 'di. nan baya jin zai sake iya kwana cikin garin nan kwata-kwata, gara ya tafi ya daina kallon duk abubuwan da ya ha'da ala'ka da Nanne, musamnan ma ni....wani sa'in ji yake tamkar baya 'kaunar ya sake ganina a rayuwar sa, duk lokacin da ya ganni ya ha'da ido dani...fa'duwar gaba ke ziyar tan sa domin kuwa Nanne sak yake gani tare da ni...har sai ji kamar wai itace...Aminan sa ce....shi yasa idan ya ganni ya ke 'kura min idanu har zai zuciyar sa ta garga'de shi da cewa ni 'din ba Nannen sa bace kafin yake kawar da idanun sa daga kaina....idan hakan ya faru kuwa sai yaji dama mutuwar ni ta 'dauka ta bar masa sahibar sa a raye.... " _Astaghfirullah_ " yake saurin furtawa idan yayi wannan tunanin...daga 'karshe sai ya 6ige da fa'din duk laifin Ammi ce ai...bansan me yasa ta 'dauko wannan me kama da magen ta kawo ta nan ba. 'Dan 'karamin tsaki ya ja a fili sannan cikin ransa ya furta " i hate seeing her wallahi" tare da tattare goshin sa wuri guda. Daga haka ya nufi bakin gado ya zauna dafe da kansa yana me cigaba da tunani. Baya so yawan gani na da yake yi ya ta6a 'karfin imanin sa, saboda yasan Allah ne ya halicci mutuwa so kuma shi ne ya kar6i ran Nanne me yasa zai ringa jayayya da yin sa. Ammi ce a gaba dan haka ita tayi sallama, banji an amsa mata ba ni ma kuwa sai banyi ba kawai na biyo bayan ta cikin 'dakin muryar Ammi naji cike da damuwa tana fa'din " koda yaushe kana nan a haka Mu'een sai yaushe zaka gane cewa jayayya kake shirin yiwa Ubangiji towards his decision?. 'Dagowa yayi da rinannun idanun sa ya kalli Ammi gami da cire hannun sa da ya dafe kansa da shi. Ammi da sauri ta 'karasa kusa da shi ta zauna, hannun sa na dama ta kama sannan ta cigaba da fadin " ka kwantar da hankalin ka please...ko ka manta cewa hukuncin Allah ne hakan? yarinyar nan Addu'ar ka kawai take bu'kata a yanzu, kayi mata sannan ka yiwa kanka ma, ka ro'ki Allah ya sanya hakan shine mafi alkhairi a gare ku da mu ma baki 'daya..."      Bata gama rufe baki ba ya 'dago ya kalli fuskar ta, Ammi sai ta jinjina masa kai alamar tabbatarwa sannan ta 'kara da fa'din"....yes!..ko kasan manufar Ubangiji akan hakan ?" Da kai ya bata amsa alamar " a'a"...Ammi tace " then you should keep praying Allah ll surely lead u, he ll be with u in every circumtances...ka daina 'daga hankalin ka...Allah da kansa yace yana tare da masu ha'kuri masu mi'ka masa lamuran su, be strong and take a stand kaji? i konw yaro na is a fighter, and please don't loose hope for any reason just take Sabr, Bi'iznillah u will soon meet ur type, the better khair for u, the person who is always there when u ar in needs, who sticks up for you even when no one should.." Kanshi ta shafa a hankali yayin da shi kuma ya lumshe idanu yana jin sanyi na ratsa zuciyar sa, 'kaunar mahaifiyar sa na sake ratsa shi, cike da kulawa Ammi ta 'kira sunan sa, take sai ya bu'de idanu ya sau'ke su saman fuskar ta...a hankali Ammi ta cigaba da fa'din " Ka daina damun kanka dan Allah saboda mu kan mu hakan na affecting 'din mu, ka fuskanci rayuwar ka ka gina future din ka da kyau Allah zai dafa maka, idan kuwa kace a haka zaka cigaba da rayuwa kanka zaka cutar, before u know ka riga ka tarwatsa rayuwar ka gaba 'daya with that silly reason...sometimes Allah brings people in to our lives just for some purpose, and he also tooks them away when the purpose is done, may be we would never ever know the reason for sure...but Mu'een Allah knows everything, he knows the best and he sees everything....don't worry kaji Baba na...miye ma duniyan....rayuwar mun fa it's all a journey, mu 'din ma we ll leave oneday...may be today, tomorrow nextweek, month or year or years but we ll surely all leave to our own judgement...who ll leave first? me, you, Alhaji, your brothers or someone that u knew..u don't know whom will be...but we are all human and waiting for the death, just focus on that Mu'een and then increase your Du'ah, put your trust in Allah, ask him whatever you want, ask him to ease your troubled heart....Bi'iznillah u will not fail, he will surely lead you, and he will give u the strength and courage to steady your self..." Jikin hannun ta ya kwantar da kansa a 'ko'karin sa na 6oye hawayen da suke shirin gangaro masa...sai da ya tabbatar ya maida su kafin ya 'dago kansa, cikin 'karfin hali da sanyin murya yace " Thank u so very much Ammi na, really proud of u, insha Allah daga yanzu na daina damuwa Ammi..and i ll not cry for Amina again insha Allah". Murmushi Ammi tayi na jin da'di...tana murmushin ta kamo chicks 'din sa tamkar wani 'karamin yaro tace " May Allah bless u with the very best of his blessings...Allah ya haskaka rayuwar ka...". Da " Ameen" Ya amsa ta shima yana mai jin da'din Addu'ar ta har cikin jinin sa. " Whenever something troubles you, you hurt or in pain just narrate....Innalillahi wa inna ilaihi raji'un don't follow your hearts to break you down kaji.." "Insha Allah Ammi na..." Ya fa'di cike da girmamawa da kuma farin ciki....'dari bisa 'dari ya yadda da maganganun Ammi, sai dai sam baya tunanin akwai wani abin daban da zai iya cike masa babban ramin da soyayyar Nanne ya tona cikin zuciyar sa. Ammi kam kawar da waccan batun tayi ganin yanda duk yayi laushi, jikin sa ta duba da kulawa tace " kar dai har kayi shirin bacci tun yanzun?" Da rawar murya yace da ita " Ina so in samu bacci da wuri ne Ammi kaina ciwo yake yi min sosai kuma ko na sha maganin bai tafiya". " Ai bazai tafi ba kam tunda ba ka cire damuwar da ke ranka ba dole headache ya kasance tare da kai...Allah ya sawwa'ka nd baccin ma will help..but before that ga abinci ka samu ka ta6a ko kadan ne". Ammi ta 'karasa maganar tare da mi'ka min hannu alamar in bata. Tausayin sa sosai ya kama ni duk da bansan ma'kasudin damuwar ta sa ba amma har ga Allah yanda ya koma 'din gaba 'daya sai naji tausayin sa, hakan ne ma ya sanya ni matsowa cikin sanyi da niyyar bawa Ammi abinda ke hannu na. A hankali ya dago ya kalle ni sannan ya maida idanun sa kan abin hannu na, take ya kawar da kansa gefe sannan yace "..Banso Ammi i'm not hungry" Ammi na murmushi tace " Da wuri haka Mu'een ai ka bari kaga ko menene kafin kace baka so 'din ko?" Shi kam baya ya koma ya jinginar da bayan sa sannan yace " am ok Ammi banjin cin komai yanzu, kuma ma 'dazu na sha Zuma wurin Alhaji". " K'aniyar ka...zuma na hana jin yunwa ne?" Ammi tayi maganar gami da ware hannun ta saitin fuskar sa. Ajiyan zuciya ya sauke mai sanyi sannan yace " Ni dai Ammi please... kinga kaina na damu na sosai". " In tafi kenan in baka wuri ko?" Ammi tayi maganar tana kallon sa da alamar zolaya. Saurin gyara zaman sa yayi yana fa'din " Haba Ammi ba haka bane...ni dai kawai abincin ne banso". Murmushi kawai Ammi tayi masa tare da mikewa tsaye...plate 'din abincin ta sake mi'ko min ni kuwa ina kar6a sai na juya na fita abina.   Itan ma baya na ta biyo tana fa'din " Mu kwana lafiya...amma fa karka manta da shan maganin ka kafin ka kwanta". Bai amsa maganar da tayi masa ba illah sunan ta daya 'kira "...Ammi"! Yayi maganar tamkar dan dole aka sanya shi as if ba yanzu ya gama surutu ba. Juyawa Ammi tayi ta kalle shi sai taga ma har ya mi'ke tsaye sai tayi shiru ta zuba masa idanu tana sauraran abinda zai ce da ita. Sai da ya sosa kansa kafin yace...." gobe insha Allahu nake so in koma". Zuba masa idanu Ammi tayi na y'an sakanni cike da mamaki tana karantar yanayin sa yayin da shi kuma ya lan'kwashe kansa gefe yayi kalar tausayi. Da mamaki ta furta " Gobe kuma?saboda me zaka tafi?" " Haka kawai ne Ammi...dama ba da'dewa zanyi ba kuma kinga...kinga" Sai ya kasa k'arasa wa ya 'karashe maganar da in ina. Ammi bata damu ba sai kawai tace " Ka sanar da Alhaji ne?" Tun ma kafin ta gama rufe bakin ta yace "..please Ammi inform him". " Allah ya bamu Alkhairi" Kawai Ammi ta fa'di a takaice gami da juyawa ta bar masa 'dakin. Yah Deen na ganin  hakan sai ya koma ya zauna gami da sakin ajiyan zuciya... Idanu ya lumshe ko bayan da ta bar 'dakin, tausayin kansa da na iyayen sa yake ji, har cikin zuciyar sa, har tsawon wani lokaci  zai 'dauka yana bautar dasu da zuciyar su saboda wata damuwa tashi ta daban, ba zai juri ganin kullum iyayen sa na nan nan dashi ba bisa ga damuwar da ya san basu suka 'dora masa ba, shiyasa ya sanyawa ransa 'karfin gwiwar cigaba da rayuwa kamar kowa, gara yaje inda yafi wayo cikin abokan sa 'kila zai fi saurin mantawa da matacciyar soyayyar sa, Addu'ah ce kam yayi al'kawari daga yanzu har ranar da shima zai koma ga mahallicin sa ba zai cire ta cikin Addu'ar sa ba. Tun a daren Ammi ta sanar da Alhaji Baba batun tafiyar, bai damu ba cuz ko shima 'din yana ganin kamar hakan yafi masa dan baya jin da'din ganin sa cikin wannan yanayin.     Washegari da safe bayan gama breakfast, Alhaji Baba ya zaunar dashi ya ringa yi mai nasiha cikin natsuwa game da rayuwa, ha'kuri da kuma yadda da 'kaddara, sosai yayi 'ko'karin jawo hankalin sa akan hakan, ya 'kara da ro'kon sa akan ya maida hankali ya kula da karatun sa da kyau...Uncle Ja'afar ne ya sanar da shi cewa nextweek zasu fara registration dan haka ya bada himma ya kuma ri'ke Allah cikin Allah al'amuran sa. Da yake Alhaji Baba yayi masa nasihan ne da sau'kak'kiyar harshe dan haka sosai Yah Deen ya fahimce shi ya kuma ji sau'ki cikin ransa...har ma sai yaji kamar bai kyautawa iyayen nasa ba da ya 'daga hankalin sa game da mutuwar. Alhaji Baba bai bar shi ya tafi ba sai da ya tabbatar ya 'dauka masa al'kawari akan ba zai bar kowacce damuwa ta 'kara illata masa rayuwar sa ba zai fuskanci rayuwar sa da dukkan farin ciki...zai kuma rin'ka gode wa Mahallici bisa ga dukkan 'kaddarar da ta same shi.      Ku'di masu 'dan nauyi Alhaji Baba ya ciro ya bashi tare da tsaraba masu yawa duk kuwa da cewa tafiyar tasa ta bazata ce amma hakan bai hana Alhaji Baba tanadar masa da abinda ya kamata ba. Jikin sa sanyi 'kalau ya 'karasa shirin sa, haka ya bar gidan da misalin 'karfe tara na safiya, ya tafi zuciyar sa cike da kewar ahalin sa. Mu kam lokacin muna makaranta sai da muka dawo muka tarar ya wuce.     Ko da ya koma kuwa Uncle Ja'afar kansa sai da yayi mamakin dawowar tasa ganin kwanan sa biyu ne kacal da tafiya amma ya dawo, shi da yace zai yi a'kalla 2weeks acan me ya faru to ya tambaye shi...koda yace zasu fara registration ba wai ya fa'di hakan dan ya dawo bane cuz yasan akwai sauran lokaci kafin ma afara 'din. Deen sai yace da shi ai Alhaji Baba ne yace ya dawo kawai ya fara shirye-shiryen registration. Bayyananniyar murmushi Uncle Ja'afar yayi sannan ya 'kara da fa'din  " Har shiri akewa registration 'din kenan?" Anty Zainab kuwa cewa tayi " Amma na ganka wani iri ba kamar yadda ka tafi da farin ciki ba Mu'een fatan dai ba wata matsala ba ce?" tayi maganar tana kallon sa. Murmushi ya 'ka'kalo ya sanyawa fuskar sa sannan yace " Anty ba dole ki ganni haka ba..ni da zama ya gagareni acan, kema ai kinsan ba yanzu nayi niyyan dawowa ba". Ajiyan zuciya ta sau'ke gami da fa'din " Allah ya kyauta" Uncle Ja'afar kam bai yadda sam cewa babu abinda ya faru ba dan haka sai da ya 'kira Alhaji Baba ya sake tambayar shi sannan ya tabbatar da gaskiyar Mu'een 'din na cewa babu abinda ke damun sa, da yake Alhaji Baba ya 6oye masa batun bai sanar dashi gaskiyan lamari ba. Hakan yasa bai 'kara bi ta kan damuwar Yah Deen 'din ba kawai ya 'kyale shi. Yayin da shi kuma ya cigaba da ya'ki da zuciyar sa shi ka'dai ya san me yake ji, amma yana shan magungunan sa akan tsari baya wasa da shi ko bari su 'kare ma beyi idan yaga ya kusan 'karewa sai yaje ya 'karo wasu...haka kuma ya yi 'ko'kari sosai wajen 'daukan shawarwari da nasihohin da iyayen sa sukayi masa, gaba 'daya ya dogara ga Allah ya mi'ka lamuran sa kaf agare shi, yana kuma Addu'ah kamar yadda Ammi tace da shi yana mata yana kuma yiwa kansa, da haka har suka fara registration. Kana ganin sa zaka san akwai abinda ke damun sa ko dan saboda 'yar ramar da yayi ma ga kuma shiru-shirun da ya 'kara zama musamman idan kayi masa sani na gaske...a hakan ma wai ba'karamin 'ko'kari yayi wajen kawar da damuwar ba. Anty Zainab ma abin na damun ta ko da ta yiwa Uncle Uncle Ja'far magana akan hakan kuma sai yace ta bar shi damuwar makaranta ce kawai a ransa. Tun washe garin tafiyar sa Alhaji Baba ma ya tafi Plateau state, inda yaje duba aikin da ake yi masa acan din na bu'de sabon gidan gona amma na zallar kaji. Kusan satin sa guda acan kafin ya dawo, lokacin da ya dawo kuwa ni ina gidan mu wurin Ummah ta, su Addah ta Maryam da yaran ta ne suka zo shine naje gidan...kwana na biyu agidan Ammi tazo muka koma tare. Anan naje na tarar da uban tsarabar kaya da Alhaji Baba yayo min harda kayan wasa set masu kyan gaske, murna kamar baki na zai yage Saif ma na taya ni farin ciki haka ma Ammi. 'Bangaren Yah Deen kuwa a wannan yanayin yayi shiri ya wuce Jigawa State duk da kuwa zuwa yanzun sam makarantar ta fice a ransa haka ma course 'din da yake dama ba ra'ayin sa bane saboda soyayyar sa ne yasa shi tilastawa kansa son course 'din,  yanzun.kuwa da ya rasa soyayyar sai yake jin baya son course 'din ma tsohon nashi burin yake so, tsoron yanda Uncle Ja'afar zai 'dauki maganar ne kawai ya sanya shi jan bakin sa yayi shiru, amma ba wai dan ransa ya so ba. Haka ya bar abin cikin ransa ya shirya ya tafi makarantar, inda anan ne ya ha'du da Husnah wurin wani signing suka ha'du bayan fahimtar cewa daga gari 'daya suka zo. Husnah taji da'din ha'duwa da shi..da yake dama ba ta san kowa anan 'din ba, tun daga ranar suka zama abokai, bata samun sakin fuskar sa sosai amma a hakan bata ta6a nuna damuwa kan hakan ba, cuz Husna irin yaran nan ne masu nacin tsiya, duk inda zai je yin signing sai ta raka shi, haka tayi ta biye masa har ya kammala nashi sannan ta 'karasa nata ita ma. Baya mata hira dan sai suyi zaman 2hrs da shi amma kalaman sa basu fi biyar zuwa shida ba, ita kuwa gwana ce wurin surutu inda anan ma zaka samu amsar sa be wuce eh, a a ko kuma kawai idanu ba, in kuwa abin dariya me sai dai kawai yayi murmushi, ita hakan bai ta6a damun ta ba dan a fa'dar ta ita mutun miskili na birge ta, she thought miskilanci kawai ke damun Mu'een bata san damuwar sa daban ba shi. Har ta fara karatu a AMINU SALEH COLLEGE OF EDUCATION dake can garin Azare inda take karantar PHYSICAL AND HEALTH EDUCATION, amma shekarar ta 'daya acan ta bari da yake ba wai ra'ayin ta bane mahaifiyar ta ce ta sata, wani Yayan ta ta yiwa complaint shiyasa wannan shekarar aka nema mata gurbi a anan Dutse shine ha'duwar su da Yah Deen. Husna kusan sa'ar Mu'een ce dan kuwa ko ya girme ma ta ma bai fi da shekara 'daya ba, a haka da shariyar tasa amma kafin su rabu sai da suka sha'ku da juna cuz har suka kammala registration tare suke har suka koma gida. Ko ranar da zasu dawo ma tare suka taho da ita sai da suka shigo cikin gari ne kafin kowa yayi hanyar sa. Da komawar sa gida ne yace da Uncle Ja'afar shi ba zai zauna Campus ba cuz sun cika hayaniya shi kuma bai so, duk yadda Uncle Ja'afar ya so fahimtar da shi amfanin zaman sa cikin 'yan uwan sa 'dalibai Yah Deen 'kin amincewa yayi daga 'karshe dole Uncle Ja'afar yayi magana da wani abokin sa akan anema masa gida 'dan madaidaici na haya...wanda bai da tazara sosai da makarantar. Yah Deen ne ya sanar da Alhaji Baba cewa shi baya son zama cikin makaranta, take Alhaji Baba sai ya 'kira Uncle Ja'far sukayi magana sai yayi masa transfern ku'di yace a siya masa gidan zai fi akan haya. Wannan dalilin ne ya sanya akalar neman gidan ta sauya daga na haya zuwa na siya. An kuwa yi sa'a an sami gidan sai dai yanada 'dan nisa ka'dan da makarantar amma ahakan yace shi ya masa...dan ba laifi gidan na da kyau da tsari gwanin birgewa. Uncle Ja'far da kansa yayi masa siyayyan sauran kayan amfani da za'a saka a gidan hatta kujeru sai da ya zuba masa masu kyau amma ba manya ba da katifar sa babba da sauran abubuwan amfani. A waya Alhaji Baba  yayi ta masa fa'da akan tara abokan banza, yace kar ya ga ya ke6e gefe  babu idon manyan sa. Yace " Karka manta duk abinda zaka aikata Allah na ganin ka domin shi ba sai angaya masa ba, dan haka ka san da wa'yan da zaka ringa hul'da wa'danda bazasu ta6a maka daidaituwar imanin ka ba...sannan daga 'karshe karka manta da al'kawarin da ka 'daukar min..and please ka dinga kulawa da lafiyar ka kaji Babana? ". Alhaji Baba ya 'karashe da lallashi. Dama bashi da yawan tara abokai hakan yasa nasihar Alhajin saurin kar6uwa a zuciyar sa...daga 'karshe godiya yayi masa sannan ya yanke 'kiran ba tare da damuwar komai ba. .....Husnah Campus take ita cikin sabbin 'kawayen ta, gashi kuma ba course 'daya suke da Yah Deen ba, hakan sai ya rage kaso mafi yawa na ha'duwar su, duk dama ita bata ta6a yadda rana guda ta wuce batare da ta ganshi ba. 'Bangaren sa kuwa abin ba haka yake ba, dan shi bai damu ba da su ha'du ko kar su ha'du sam bai damu da ganin ta ba, illah iyaka idan ta 'kira shi ta tambayi inda yake sai ya gaya mata ita kuwa tazo ta same shi...sau tari ma yakan ui mata 'karyar yana da lecture a time 'din ita kuwa sai tace to tana jiran sa idan ya fito. Amma da kansa bai ta6a zuwa neman ta ba...bai ta6a 'kiran ta kuma dan wai su ha'du ba. A haka suka cigaba da lalla6a karatun su har suka ci semester guda, ba zai ce har a lokacin bai san kowa ba dan kuwa makaranta duk rashin son jama'ar ka dole ne sai ka saba da mutane, to ba laifi ya san mutane musamman wa'danda suke 'daukan lectures tare, amma ba sabo mai 'karfi ke tsakanin su ba dan sai dai a ha'du a gaisa ko kuma idan wani issue ya taso ko kuma wani group discussions haka akan ha'du ayi da shi amma bayaga haka babu komai, baya saka kansa cikin su wai shi yana gudun hayaniya, sannan ko mata ma baya shiga sabgar su, saboda ko ka'dan shi har a lokacin bai ga wacce tayi masa da zasu ha'da ala'ka ba koda ta abota ce, balle aje ga zancen soyayya, wannan kam har yanzu bai ma fara tunanin yi ba, bai ta6a jin koda birgewa wata tayi masa ba, a kullun sai yaga duk babu wata 'ya macen da ta kai masa Nanne a komai, har ji yake tamkar bazai ta6a samun irin ta ba, bai ma sa aransa zai sake yin soyayya ba, dan haka karatun sa kawai ya sa agaba. 🤞🏻 *Toh mabiya labarin NOORUL* *...gani na dawo fatan za'a cigaba da bani ha'din kai....masoya na ina son ku, fata* *na ubangiji Allah ya cika muku birikan ku na alkhairi yasa mu dace da hasken Rahmar sa yayi mana kyakkyawan 'karshe....* *{AMEEN}.* _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Jinjinar ban girma ga...Khady, Amatullah, Nanerh⁩, Khul⁩,* ⁨ *Jamilayusuf1980⁩,Mrs Nafi U⁩, Nusy tee, ⁨Maman*Muhammad⁩, ⁨Nana⁩ and my Besty (Dr.Khausar)* *Godiya nake 'yan Amana.....Allahu ya biya muku bu'katan ku na Alkhairi...sosai nake yabawa da soyayyar ku...Allah ya bar min ku*😍❤ *{AMEEN}*🙏 *Sister SAFIYYAH A.W ubangiji Allah yasa an fara SAI NA ZAMA JARUMA a sa'a, Allah ubangiji ya baki ikon fa'dakar damu Amin...* 😍 *MARYAM ABDUL muna godiya sosai Allahu ya bar zumunci ya 'kare ha'de zu'katan mu...Allah ya nuna mana 'karshen BIYAYYA lafiya*🙏 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *34* Ko da ya koma gida hutu ma bai yi wasa da  Addu'o'in sa ba,  yana 'ko'karin yi babu laifi, kuma ko al'kawarin da ya 'daukar wa Alhaji Baba ma bai yi watsi da shi ba duk kuwa da cewa basu tare cuz gaba 'daya hutun a Azare ya gama shi bai zo wurin su Alhaji Baba ba har hutun ya 'kare suka koma makaranta ya cigaba da karatun sa.       Duk kuwa ranar da wani course ya caza masa kai ya du'kufa karatu.. tamkar zautacce zaki ga yana ta sumbatu shika'dai yana fa'din...." Duk fa kece kika sani wannan abin Nanne, kuma sai kika tafi kika barni tun ma ban fara karatun ba..." Ajiyar zuciya yake sau'kewa sannan ya cigaba da karatun nasa cike da alhini. Ya kan yawaita sallah musamman tsayuwar dare yana ro'kowa Nanne gafaran mahallici, da kuma fatan Allah yasa mu da muke raye mu cika da kyau da imani. *AMEEN* ******     Ni kuwa 6angarena duk abubuwan nan da suka faru abaya ban ta6a sanin cewa kukan mutuwar Nannen mu Yah Deen yake yi ba, har ya tafi kuwa bansani ba kuma haka Ammi ma bata gaya min ba. Bazan manta ba  kwana biyu bayan tafiyar sa a wancan lokacin, muka ha'du da Ma'u 'kawar Nannen mu da suke hirar Yah Deen tare tun kafin rasuwar ta, lokacin muna hanyar mu ta zuwa makaranta ne ni da su Saif...sai ta tsaida ni da fa'din in jira ta mu 'karasa makarantar tare. Ban yi gardama na tsaya saboda nasan ba 6ata min lokaci zatayi ba tunda duk muna kan hanya ne kuma itama makarantar zata je, Ma'u babu ruwan ta da fitina da yake nasan halin ta  'kawar Nannen mu ce. Su Saif kam gaba suka yi suka cigaba a tafiyar su, ganin hakan ya sani shagwa6e murya nace " to kujira mu mana". Na fa'di ina kallon bayan su. Saif ne yace dani " ku same mu a hanya kuma idan kika tsaya wasa ko kika 6ata time kukayi latti sai na ha'da ki da Ammi". Nasan ba fa'dan zaiyi ba dan nasan ba halin Saif bane kaiwan magana,  amma duk da haka sai nace " to ku jirani" Kafin yayi magana sai Ma'u ta iso kusa dani ta na 'dan haki saboda gudu-gudu sauri-saurin da tayi, cikin hakan ta riga shi magana da fa'din " ba ma sai kun jira ta ba ..." Waigowa tayi gare ni ta kama hannu na gami da fa'din " Muje kawai".   Tafiya muka fara amma tafiyar ta mu ba irin ta su Zaidu ba ce dan sosai suka fi mu sauri...dan haka sai muka cigaba da bin su abaya. Can sai Ma'u ta kalle ni tace " Kina tayin kyau abin ki Hudah kamar ba ke ba"! Murmushin jin da'di nayi har cikin raina naji da'din maganar ta, cikin raina nake ayyana yanda Ammi ke ji dani da sauran mutanen gidan, kafin a siyawa su Saif abu sau 'daya wani sain sai an min sau uku, hakan ma idan an tashi sai a ha'da ayi mana dukan mu...sosai nake jin da'din gidan cuz babu mai tsangwama ta illah Zaidu da sam jinin mu bai ha'du da shi ba. Muryar Ma'u ne ya yanke min tunanin nawa da najiyo tana fa'din " Wai ke Hudah baza ki koma gidan ku ba?" Ina gyara zaman jaka ta nace da ita " Ammi ce ta hana ni". Baki ta ta6e gefe tare da fa'din "...Na fa ji ana cewa wai dan kwa'dayi kawai kike zama a gidan.." Turus na ja na tsaya ina yatsina fuska ta nace " Kwa'dayin me zanyi?" " Oho...ni na sani ne?" Tayi maganar cikin nuna rashin damuwar ta. " Sai na fa'dawa Ammi da Ummah ta". Da sauri tace yi ha'kuri dan Allah ni fa kawai na gaya miki ne dan naji wasu na fa'di ba wai dan ki gayawa kowa ba...kuma yanzu idan kika fa'dawa Ummah ta 'dauke ki a gidan waye zai din ga bani labari?" Baki kawai na tunzura dan ban san manufar ta kan fa'din hakan ba. " In tambaye ki wani abu?" Ta fa'di hakan ne tare da dafa kafa'da ta. Ban ce da ita komai ba dan haka sai ta cigaba da fa'din " Hudah wai dan Allah dagaske ne Yayan su Zaidu ya dawo, ance min wai an gashi shekaran jiya zai shiga mota" " Ai har ma ya koma ". Na bata amsa a takaice. Zaro idanu Ma'u tayi tace " Dan Allah da gaske har ya tafi?" Sai na 'dage kaina sama alamar " Erh..." Sau'kar da murya tayi bayan ta sau'ke ajiyan Zuciya sannan tace " Dan Allah Hudah idan ya sake dawowa ki gaya min kinji..kar ki bari sai ya tafi...sa'kon shi ne a wurina nake so zan bashi". " To" kawai nace mata tare da 'kara saurin tafiya ta. Ban 'kara cewa komai ba haka ma Ma'u har muka 'karasa makarantar.   Ko da muka koma gida kuwa kallo daya Ammi tai min ta fahimci akwai abinda ke damuna..." Zo nan Hudah ke da waye ?...Zaidu kai ne ko?" Da sauri ya girgiza  mata kai har yana 'dage hannu... " Kaina kan cinyar ta nace " Ma'u ce fa ta ce min wai ina kwa'dayi Ammi..."! 'Bata rai Ammi tayi tace " kwa'dayi a ina kuma na me?" Kamar zanyi kuka nace " wai anan gidan". " Ma'un 'yar gidan waye da zata fa'di haka? nifa bana son kinbibi da munafurci, yara 'kanana amma sai tsabar tada fitina.." 'Dago ni tayi zaune tace" idan ta 'kara gaya miki irin haka...ba ita ba ko wani daban...make sure that kin sanar dani har gidan uban ta zanje in same ta sai ta gaya min ko gidan nan 'din na ubanta ne da zata ce kina kwa'dayi...". Ammi kam ta jima tana masifa akan hakan ga dukkan alamu abin yaci mata rai sosai, hatta su Saif ma sai da suka samu rabon su dan cewa tayi wai me yasa basu 'dau mataki ba. Zaidu shiru yayi yayin da Saif yace " Mu fa Ammi bamu ma san anyi haka ba, kuma itama bata gaya mana ba". " Ni dai na gaya muku, daga yau ko da wasa wani ya kuma fa'din hakan...ku sanar dani sai naji dalili ".     *****         Wasa-wasa lokaci na tafiya rayuwa na 'kara yin gaba, har Yah Deen ya ci kusan rabin semester 'din sa na biyu. Tun komawar sa makaranta da sati uku aka yiwa Uncle Ja'afar transfer wurin aikin sa daga Azare Bauchi zuwa can Taraba State....ba tare da 6ata lokaci ba suka tattara da Anty Zainab suka tafi bayan sunje har makarantar sukayi masa sallama bayan haka sannan sukaje suka yiwa su Alhaji Baba ma.      Mu'een bai damu sosai ba da yake baya gida a lokocin dan haka ya cigaba da karatun sa batare da wata damuwa ba har 'karshen semester.     Sai lokacin da ya dawo hutu ne kafin yaji babu da'di, kewar su ta dame shi sosai....gashi Uncle Ja'afar ma ya 'kira shi yace da shi ya wuce gida kawai kar yace zai zauna shi ka'dai a gida daya ke yasan kadan ga aiki sane yace a gidan zaiyi hutun. Kwanan sa uku sannan haka badan ya so ba ya tattara ya wuce garin iyayen na sa.   Sai dai Yah Deen 'kin zama yayi agidan wai mu bama ji zamu dame shi da hayaniya. Wani gida da Alhaji Baba ya ta6a ginawa acan wajen hanyar  makarantar mu yace zai koma inda Alhaji Baba yaso nuna 'kin amincewar sa amma Ammi ta ro'ki ya 'kyale shi kawai tunda hakan yayi ra'ayi. Ita kanta tasan ba dai-dai bane hakan amma dan kawai kar su 6ata ran sa ko kuma yaga kamar an 'ki yi masa abinda yake so ya sanya ta amince....amma Alhaji Baba kam sam hankalin sa  bai kwanta da hakan ba, ta ya shi da yake matashin saurayi zai koma zama shi ka'dai acan bacin ga gidan mahaifin sa, ai rayuwar makaranta daban take da na gida...abin ma sam bai masa tsari ba. Amma yadda Yah Deen ya dage da kuma yadda Ammi ta goya masa baya yasa shi amincewa kawai ya 'kyale shi. Hakan kuwa akayi da yake gidan babu kowa wa'dan da ke haya a gidan basu jima da tashi ba dan sun gina nasu, so bayan 'dan gyare-gyare da akayi wa gidan sai aka shishshirya komai...yayi sa'a ma ba'a jima da canza kayan gidan Alhaji baba ba so tsofin nan aka zo aka zuba su, Ammi ce ta aika aka gyara komai sai T.v data sa aka siya masa da curtain, gida yayi kyau tamkar na amarya...sai dai babu da'di saboda shiru babu ko neighbours illah kangon gidaje da'd'daya. A hakan shi kam  ransa yafi jin da'di ya fi farin ciki. Rayuwar Yah Deen kullum akarkace take shi, kusan ko wani lokaci yafi so yaji shi zaune shi ka'dai yayi tunanin da ransa ke so, shi ka'dai batare da an yanke mai ba, yayi rayuwar sa shi ka'dai, ba tare da yaji motsin kowa ba. Mutane na gudun ka'daici amma shi hakan ne mura'din sa koda wani lokaci...a fa'dar sa wai damuwa ce kawai bai so...sannan wai mu mun cika hayaniya.(Ohh ni Salmerh...naga de banda abin Mu'een dama wake son damuwa a rayuwar nan kawai dai ha'kuri ake ana lalla6awa kawai). Kuma fa 'karya ce kawai yake yi amma babu wata hayaniya da mukeyi gara ma idan musu ya ha'da mu da Zaidu mukan 'dan ta6a hayaniyar amma itan ma ba kullum ba, bayaga haka kuwa ba komai, sai ko idan muna kallon movie musamman American Movie mu kan 'dan yi hayaniya saboda kowa na za6an star 'din shi ne tun kafin film yayi nisa so aduk lokacin da star 'din wani cikin mu yayi abin da ba dai-dai ba mukan 'dan yi mai ihun mugunta sai kuma idan film yazo 'karshe duk wanda star ya fito daga 6angaren sa ya kanyi murna sosai...shine kawai hayaniyar da muke yi agidan, wannan kam nasan ko Ammi ma tana mana fa'dan ihun, to a daren ranar da ya zo mun kalli Fast 3 da Terminator 2....kuma munsha shagalin mu aranar shine fa ya fake da shi...har da 'kin zama a gida.(ALLAH YA RAKA TAKI GONA....inji Maman Muhammad fa amma).       Washe garin tafiyar sa da muka zauna ni da Saif lokacin zai koya min karatu kuma sai ya kasance ranar a harabar gida muka zauna, tashin farko tunani na sai ya tafi can wurin sa ban san dalili ba amma har da ta6e baki na. Ban iya nayi shiru ba kuma sai nace da Saif " Amma wannan Yah Deen 'din gaskiya yana da mugun hali". Ido Saif ya zaro yana kallo na...sai na ha'de goshi na ganin yanda yake kallon nawa...A hankali yace " Ni dai ba ruwa na idan yaji ki". Saif ya fa'di yana mai bu'de text book 'din da ke hannun sa. Cewa nayi " A ina zai jini shida ya koma can jejin..." Tun ma kan in rufe baki na Saif ya tare blni da fa'din" To wai ke ina ruwanki...haka ya ga dama, kuma ra'ayin sa ne ba tilasta shi akayi ba kuma ya koma 'din bashi kenan ba". Baki na ta6e ina jin araina cewa da ni Aljana ce da sai na ringa bashi tsoro da dare tunda ya koma can shi ka'dai. Daga haka muka ci gaba da karatun mu bamu sake bi ta kan zancen sa ba. Yakan zo gidan kullum da safe da rana da kuma yamma, bamu fiye ha'duwa da shi da safe ba da yake sai bayan mun tafi makaranta yake zuwa yayi breakfast wurin Ammi, da rana ma sai kusan 'karfe uku yake zuwa a lokacin kuwa har mun tsufa a Islamiya ma, da yamma ka'dai ne muke haduwa da shi sai dai kuma ba kullum ne yake zuwa gidan da yamma ba sai ranar da yaga dama...saboda bai wani damu da cin abincin dare ba shi. Sai ko a weekend mukan ha'du dan muna gida ko wani weekend da safe. Ni kam haushi sosai yake bani yanzu, balle da naga ya 'karawa kansa mugun hali, ko kallan arzi'ki bai mana a gidan, idan kuwa mutun ya kuskure yayi mai wani abu ranar zai kwashi yatsun sa biyar a fuska. Yah Deen sam baya shayin sau'kewa mutun mari akan kowani irin laifi ne, sa'ar da ni nayi kawai shine ban ta6a ha'duwa da marin sa ba tun zuwan sa, amma ranar da ya mari Saif a gaba na ji nayi tamkar in rama masa dan haushi. Wai dan ya bashi wankin singletes da safunan sa kala kusan biyar, Saif kuma hannun sa na ciwo shine fa na kar6a yana zaune ina wankewa da ya fito zai tafi sai yaga ba Saif ke wankin ba batare da yayi magana ba kawai muka ganshi tsaye agaban mu..." Ban isa ni in saka abu kayi min ba ko ?" Yace da Saif da damammiyar fuska. Saif na shirin magana kawai sai ya 'dago hannu ya wanki fuskar Saif da mari....ba zata kawai naji 'karan mari, ina 'daga kaina sai naga Saif ya dafe kuncin sa da hannu... " Dan ka raina ni Saifu in baka ka wanke min shine zaka bawa wannan yarinyar salon ta 6ata min kaya ko me?" Ko da Saif ya bu'di baki zai mai bayani sai ya sake kai masa wani mari gami da fa'din " Shut up da Allah bana son maganar banza...kuma ka tabbatar ka wanke min kaya na da kyau...stupid kawai ". Yana gama fa'din hakan yayi gaba abin sa cikin ta'kun sa na 'kasaitattu. Yanda tsoron sa ya shige ni sai naji ko kallan banza ba zan iya yiwa bayan sa ba ballantana inyi magana, badan haka ba da sai na yi masa bayanin abinda ya sanya nake taya Saif wankin da har ya mare shi akan hakan. Ha'kuri kawai kawai na dinga bawa Saif kamar zanyi kuka sai da naga ya fice daga gidan kafin a hankali nace " ai sai na gaya shi da Ammi....take Saif ya hana ni yace min a a kar in fa'dawa kowa. Tun daga ranar nake jin haushin sa ga kuma tsoron sa da ya dasa min a zuci....ganin akan 'dan wannan abin shine Saif yasha mari har haka to ina ga kayi wani babban laifin ai sai ya tattaka ka abanza....wannan dalilin ne ma ya sa ko ya zo gidan ban fiya fito wa ba koda ina nan, zama na nake a 'daki har yazo ya tafi ban fitowa ko gaida shi dan gani nake kamar idan mun ha'du zan iya masa abinda zai mare ni batare da nasan na aikata laifi ba, tunda shi komai ma laifi ne a wurin sa...ga kuma wani uban 'daure fuska da ya koya ba zaka ta6a ganin fuskar sa asake ba sam sai dai ko in yana tare da su Ammi su 'din ma wataran ba fara'ar yake yi musu ba.    Da yake kusan kullum muka ha'du da Ma'u sai ta tunadar dani cewa kar in manta idan ya dawo in sanar da ita...tun wancan tafiyar tasa take kan tunatar da ni, da yake yanzu mun saba sosai tunda nace da ita ai Ammi tace idan an 'kara fa'da min irin waccan maganar inzo in sanar da ita, Ma'u sosai ta kiyaye bakin ta bata ta6a 'kara gigin sanar da ni ba, dama itama ji tayi ana fadi, to ko mutanen ma sun tayin gulmar a tsakanin su sika yi shiru ganin babu hanyar ya'dawa, Ammi ba shiga cikin shirgin matan garib takeyi ba balle taji, sai dai bansan ko Ummah ta ba...'kilan taji amma dai bata ta6a ce da ni komai ba. Rashin sake maimaita maganar da Ma'u batayi ba yasa nima na saki raina itama mukayi sabo da ita, daga 'kawata Bintu ban kula kowa sai Ma'u. Ai kuwa kwana shida da dawowar sa muka ha'du da Ma'u, da ta tambaye ni kamar yadda ta saba bama ta6a ha'duwa bata kawo maganar sa ba...sai nace mata " ai ya dawo ma amma ya koma wancan gidan na hanyan makaranta..." na 'karashe da yi mata kwatancen gidan. Tun daga lokacin Ma'u bata 'kara tambaya ta shi ba ban kuma san meke faruwa ta 6angaren ta ba. Ni dai ban ta6a zuwa gidan ba dan ko ya 'kira su Zaidu bana binsu, sau tari kayan wankin sa yake ha'da su da shi idan sun wanke sun goge sai su 'kara kai masa can. Har akaci sati biyu da dawowar sa.    Akwai watarana da Zaidu ke 'dan jin zazza6i Saif ne shi ka'dai yayi wanki da gugan kayan Yah Deen 'din da ya bayar, dan mugunta kuma wai shi bai son asanya masa kayan a machine dole Saif yayi wankin da hannun sa ko shanya ban taya shi ba saboda tsoro. Da zai kai masa kayan ne yace in raka shi na'ki, yayi-yayi dani na'ki amincewa, sai da Ammi tasa baki da fa'din " ki raka shi Hudah kinga ma yace yau bazai shigo ba wai atafi masa da Tea kuma ai kinga kayan sun yiwa Saif yawa ko...daure ki raka shi kinji uwata". Kafa'da na no'ke nace da Ammi" Nifa Ammi tsoro nake ji kar ya mareni". Na 'karashe maganar da shagwa6a ta. Ammi sai tace " Ai idan ya kuskura ya mareki rama miki zanyi kinji Hudah...yi ha'kuri ki raka shi ai ma ba zama zakuyi ba...yana ta6a ki let me know.. i ll deal with him insha Allahu". Tayi maganar tana mi'ka min 'dan madaidaicin Teaflask da ke hannun ta. Kar6a nayi ina share hawaye na nudi 'daki na 'dauko 'dan hijab 'dina fari na sanya har na 'kara fitowa hawaye na bai daina zuba ba.....ganin hakan ne ya sanya Ammi fa'din "...To Saif idan kunje sai ta jiraka a waje in ka mi'ka kayan sai kazo ka anshi flask 'din ma ka kai  tunda ita tsoron sa takeji...." Ta 'karshe da gungunin " Ya maida kan sa dodon 'karfi da yaji kam ba dole yara suji tsoron sa ba". Da " To". Saif ya amsa ta sannan muka wuce. A hankali muke tafiyar cuz ni bana sauri yau 'din da yake raina ba son tafiyar yake ba. Har kuwa muka isa layin gidan babu wanda yace da 'dan uwan sa uffan......akan layin gidan muka ha'du da Ma'u bansan me take yi a wurin ba,  tana ganin mu kuwa sai naga ta washe ha'kora ta iso gaban mu..." Hudah ina zakuje haka naga kina ta fushi?...da alama ma kiyi kuka". Tayi maganar tana kallon cikin idanu na. Kafin nayi magana Saif sai yayi murmushi yana gyara zaman kayan dake hannun sa yace" Rabu da ita matsoraciya, gidan nan zamu fa shine take kuka". Da murmushi Ma'u tace" Kuka kuma saboda me?" " Wai tana tsoro" Washe baki ta sake yi tace " haba da Allah tsoro kuma...muje in rakaku to nima kawai dama gida zan koma yanzu". Tayi maganar tana kar6an abinda ke hannu na, ni kuwa da wuri na sake mata kamar dama jira nake yi ta kar6a.    Tunani na ko dan bata san waye a gidan bane shiyasa take wani azar6a6i....ashe Ma'u kam ta sani, mantawa ma nayi da cewa ni na gaya mata a gidan yake,  dama kullum hanyar da zata 'kara ganin sa take nema shiyasa take yawan shawagi a arean gidan tamkar wata mai gadi, duk da haka kuwa sau d'aya tak ta gansa ranar ma zashi filin ball ne dayake ya fara fita ball.     Tun daga ranar bata 'kara ganin sa ba kusan kwana biyar kenan yanzu, sai yau da in ka lura zaka ga har jikin ta rawa yake yi saboda zata shiga wurin sa. Ni har Saif duk bamu lura da yanayin ta ba, illah surutun ta da ta cika mu da shi sai ya 'dauke hankalin mu gaba d'aya. Muna isa 'kofar gidan sai na ja tsaya na basu hanya, duk suka wuce ni, sai na 'kara jan baya ka'dan, Saif ne ya fara shiga da sallamar sa, sai Ma'u a bayan sa, ni kam 'kin shiga nayi nayi tsayuwa ta daga waje...Saif ma bai kulani ba da yake an riga an gama magana tun a gida, Ma'u kuwa hankalin ta ma bai kaina burin ta kawai ta shiga cikin gidan ta ganshi shiyasa bata ko bi ta kaina ba. Da shigar su sai suka tarar shiru tamkar baya gidan, parlourn ma shiru. Tsayuwa suka yi suna jiran sa duk da ko sallamar ta su bai amsa ba amma Saif bai damu ba cuz ya san wannan 'daya daga cikin halayyar sa ne, rashin amsa sallama musamman idan ba babba ne yayi ba, ko yanzun ma kuwa yana da ya'kinin yaji su sarai amsawar ce dai kawai ba zai yi ba. ...Ai kuwa hakan akayi, dan batare da ya amsa sallamar ba kawai ya fito daga bedroom 'din jikin sa ko riga babu illah wandon 3quarter a fili zaka ga dukkan baiwar halittar da Allah ya tsara masa na daga cikin sa har zuwa kansa gaba 'daya, Deen ba 'karamin kyakkyawa bane na 'karshe, sosai yayi sa'an fitowa cikin mutanen da ako ina za'a kirashi da kyakkyawa batare da haufi ba, yanda kansa ke cike da yalwattaccen gashi haka ma 'kirjin sa yake..... a hakan kuma ya 'karasa fitowa fuskar sa ba yabo ba fallasa ya 'karaso ya zauna kan kujera. Ma'u kam tunda idanun ta yayi tozali dashi ai sai ta manta kanta gaba 'daya, ido ta tsura masa tana kallon fuskar sa ji take tamkar tayi ihu saboda farin ciki, haka kawai Allah ya jarabce ta da sonshi, so kuma mai tsanani irib masifaffen nan wanda bai san fulaku ba, tun Nanne na raye suke fama gashi yanzu Nanne ta tafi ta barta kamar wasa abin ya girma cikin zuciyar ta, kullum kwana take tana tashi da lodin soyayyar wanda bai ma san da zamanta cikin garin ba balle ya san matsayin sa a zuciyar ta. " Yayah na yini?" Saif yace da shi yana mai ko'karin ajiye kayan hannun sa. "A'a shigar ciki mana". Yayi maganar batare da ya amsa gaisuwar Saif ba illah gyarawa da yayi ya kishingi'da kan kujerar. Saif sai ya kama hanyar shiga ciki kamar yanda aka umarce shi wanda sai lokacin Ma'u da rawar murya tace da shi " Ina..yi...ni?" Bai amsa ba sai a lokacin kuma ya 'dago tare da kankance idanu yana kallan ta jin sabuwar murya kamar daga sama a tsakar kansa. Suna ha'da idanu sai ya ha'de gira yayin da Ma'u ta fara rarraba idanu a 'kasa cike da bugun zuciya handle 'din flask 'din dake hannun ta ta kama da duka hannuwan ta biyu. " Daga ina ke kuma?" Yace da ita cike da mamaki yana kallon ta. " Ni....?" Tace a tsorace still muryan ta na rawa. Bai amsa ba sai yace " Me kike yi anan nace?" Yayi maganar a'dan tsawace har Saif dake ciki ma sai da ya jiyo shi. "..Na..na rako su ne ". Ta fa'di kamar zata zura da gudu. Dai-dai fitowar Saif daga cikin bedroom 'din Yah Deen sai ya maida hankalin sa wurin sa... " Saif nace ka ringa kwaso min mutane anan gidan ne? ko kuma tsabar rainin hankali ne?" "A'a fa Yayah..Ammi ce ta aiko mu da Hudah ita kuma wai tana tsoro shine Ma'un ta kar6a tace zata rako mu". Ba sai ya sake tambaya ba cuz ba yau yasan sunan ta hakan ba...a zafafe yace da Saif " Tsoron uban me take ji?" Shiru sukayi dukkan su...a 'darare Ma'u ta ajiye flask 'din hannun ta ta kama hanyar fita, sai ya dakatar da ita da fa'din " My friend...come back here!" Tana jin haka jikin ta na rawa ta dawo ta tsaya. Abin shara ya nuna mata tare da mi'kewa sannan yace" Ki share parlourn ki goge shi and don't waste my time...zan fita ne yanzun". Yana maganar ne yana tafiya zuwa cikin bedroom 'din nasa. Ma'u da idanu ta rakashi har ya 'karasa shigewa ciki. Sam bata zaci haka yake da masifa ba, idan ta ganshi awaje shiru-shirun nan sai ta zaci ko sau'kin hali gare shi har zuciya, baza manta ba da jimawa Huda na 'dan bata labarin sa amma sam bata sawa aka, musamman in 6angaren mugunta ce, gani take tamkar duk rashin jin su Hudah ne ya sanya yake yi musu hakan, bata san cewa haka asalin halin sa yake ba sai yau da ta fara gani...duk da haka Ma'u ko ka'dan bata ji haushi ba sai ma gani da tayi kamar ai dama ta samu tunda har ya sakata aiki a gidan sa kuma da kansa... farin cikin ta sai ya rinjayi raunin ta har hakan ya sanya zuciyar ta cika fal da farin ciki..a hakan tafara aikin tana 'dan murmushi. ( Ni kuwa nace, Babbar Cuta ta kama Ma'u gaskiya). Shi kam Yah Deen bayi ya shige abinsa ransa ba'ki'kirin, duk zaton sa nice, shiyasa ko lokacin da ya fito bai damu da ya ga inda take tsaye ba saboda yasan dole zan gaida shi ko bai dubi inda nake ba. Murya ta kawai yake son ji tana masa da'di...bambancin murya ta da ta Nanne kawai shirme ne da nake yi ada amma yanzu ma da sau'ki tunda 'kara girma nake yi ina 'kara wayo ina barin shirmen abaya, yayin da sautin murya ta ke 'kara riki'dewa zuwa na ta sak, Yah Deen ya gama saka rai da yaga Saif tare da wata shiyasa ma bai ko tsaya ya lura da yanayin bambancin halittar mu ba. Sai a lokacin ma yaga wautar sa da tun farkon shigan sa 'dakin ya kasa gane bani bace tun awajen suturar mu, cuz yasan ji Ammi bata ta6a bari na in saka kayan da suka canza launi ko suka 'dan yage ko kuma kayan da ba'a goge ba, hakan yasa kullum zaka ganni fes dani bana ta6a zama da datti..tun daga 'kafafu idan ka duba zakaga bambanci dan ni 'kafata kullum fes take da haske yayin da 'kafar Ma'u tayi futu-futu da ita da yake ta zama wuri guda ita.      Tsayin mu zai kusan zuwa 'daya da Ma'u duk da kuwa tafini shekaru amma mu 'yan gidan mu muna da tsayi cikin halittar mu shiyasa muka zo kusan 'daya da Ma'u, amma tafini kaurin jiki dan ni haka nake tamkar muciya banda jiki sam sa6anin Ma'u da har ta fara ajiye halittar Allah a 'kirjin ta, ban sani ba ko dan kanta da hijab ne ya sanya bai gane bambamcin halittar mu ba...kuma ma daya ke ni ya saba gani a gidan su, kuma yasan ni jinin Nannen sa ce....sannan kuma ba zai ce ya tsane ni ba saboda wannan ala'kar, amma sau tari idan ya ganni na kan tuna masa da ita har hakan yake sawa yake 'dan yawaita kallo na koda asace ne.      Babban abinda yafi tsaya masa arai game dani kuma shine yanda muryar mu tazo iri 'daya da Nannen sa. Shiyasa ma wani sa'in bai amsa gaisuwa ta saboda bugun da zuciyar sa keyi na sakamakon jin murya ta da yayi, amma ni sam bansan haka ba zato na ko kuma zallar tsana ce kawai da yake min da mugun halin sa.    Ranar da 'yan Jahilcin suka zo kuma yakanyi abinsa da gangan ne, idan yayi tunanin dama ni mutuwa ta d'auka ta bar masa sahibar sa, hakan sai yasa shi jin haushi na har ma ya'ki amsa gaisuwa ta...ha'ki'ka soyayyar Nanne ta zame masa ne tamkar ciwo a zuciyar sa wanda batada magani, ta kan motsa a duk lokacin da ta ga dama....da kanshi ya san cewa erh lallai Amina ta rasu ba kuma zata dawo ba har abada, da kansa ma yake yi mata adduah kusan kowace sallar sa, amma wannan dun'kulalliyar soyayyar tata ta kasa bajewa cikin zuciyar sa a lokacin, shi kansa bai san me ke 'kara ha66aka masa ita ba balle wani daban. Saif fita yayi can waje domin ya dubo ni dan kar naji shiru inda ya same ni tsugunne daga waje na buga uban tagumi tamkar wata almajira da ta rasa madafa, ina jin an bu'de 'kofa na zabura na mike a razane. Saif sai yayi murmushi.." Miye kuma?" Ya tambaya yana kallo na da murmushi. Narai-narai da idanu na nace " Ai tsoro ka bani". " Yi ha'kuri to". Ya fa'di tare da matsowa kusa da ni sannan ya sake fa'din" Allah ya taimake ki yarinya". Yayi maganar yana kallo idanu na.    Ban amsa shi ba sai kawai nace da shi" ina Ma'u?" " An saka ta shara". Ya bani amsa yana 'dan dariya. " Maganin ta ai". Nima na fa'da harda mugunta ta. Au haka ma zakice ke da ta tazo taimakon ki...ai badan ita ba da ke za'a saka sharar". Sai nace" Ba wani nan ai dama Ammi tace kar in shiga ciki". "  Naji to, muje ki taya ta" Cewar Saif yana bani hanya. Kafa'da na no'ke tare da 'kara matsawa baya. Dariya ma bashi, sai da yayi dariyar kafin yace " Allaj kin fiya tsoro, nima fa an min masifar nan amma kin gani a jikina ne...mazgewa akeyi in ba haka ba bazaki daina tsoron nan ba". " Ni dai ba ruwa na, ka 'kirata mu tafi ko kuma muyi tafiyar mu idan ta gama sai ta wuce itama". " Rufa min asiri ni kam in ba so kike ya 6a66alani ba...bari in dubo ta". Yana gama fa'din hakan ya juya ya shige ciki. Lokacin da ya shiga sai ya samu ma har ta gama sharan tana kwashewa. Sannu yayi mata sannan ya wuce ya ha'do abubuwan da za'ayi mopping 'din dasu.       Ga mamakin  Saif fuskar Ma'u cike take da murmushi, sa6anin yanda ya zaci zata ji haushin ta rako su kuma an saka ta aiki. Bai damu ba ya wuce ya fara goge 'dakin, sai tayi saurin tasowa ganin abinda yake shirin yi tace.." Me zakayi?" " Wai da zan tayaki ne" " Banso..nace ka taya ni ne?" tayi maganar tana kar6a daga hannun sa. Saif baki ya ta6e yaja gefe ya tsaya yana binta da kallon mamaki. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Dedicated to Hassan ATk & 80k...Allah ya bar Zumunci ya biya bu'katu...( Amin thumma Amin)* 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *35* Haka tayi abinta ita ka'dai har ta kammala goge tiles 'din tas,. " Sannu". Saif yayi mata sannan ya shiga ciki dan sanar da shi zasu wuce sai kuma ya tarar yana bayi ne a lokacin. Saif kam hakan ma yafi masa, dan bai son wata sabuwar mitar kuma da yake baya rasa na yi shi. { a fa'dar Saif kenan}…    Dalilin ma kenan da ya sanya batare da 6ata wani lokaci ba ya fito yace da Ma'u wai yace ya gode za su iya tafiya. Ma'u kam ba haka taso ba dan taso ta 'kara ganin fuskar sa ma ko da kuwa ace wata masifar zai kuma yi mata… amma ganin bata samu hakan ba sai kawai ta basar suka fito daga gidan inda suka suka same ni tsaye tsuru-tsuru duk na gaji da jiran su, sosai na 'kosa su fito muyi gaba.      Ai kuwa ina ganin sun fito sai na saki hamdala a zuciya ta a fili kuwa ajiyan zuciya na sau'ke har ina lumshe idanu. "...Kamo ta nan". Naji muryar Saif ya fa'di da 'dan 'karfi. A firgice nayi baya da niyyar kwasa da gudu kawai sai naji sun kwashe da dariya atare suna nuno ni, baki na tura ina 'dan kalle-kalle dan harga Allah ni tsorata nayi. " Y'ar gidan Ammi matsoraciya". Cewar Saif bayan ya gama dariyar tasa. " Ni dai kam kuzo mu tafi". Nayi maganar tare da juyawa na fara tafiya ina 'dan 'kun'kuni. A hanya daf da zamu sha kwana muka ci karo da manyan shanukai masu yawa ga dukkan alamu kiwo suka nufa. Wannan karan Ma'u tafi kowa tsorata musamman da yake itace agaba . Ihu ta tsala cike da firgici tare da komawa da baya ta ranta ana kare....duk sai muka bita da idanu da mamaki, hakan yasa kafin mu ankare sun mana 'kawanya sai ganin mu kanmu muka yi a tsakanin su. Ganin hakan ya sanya ni daskarewa wuri guda tare da rintse idanu na da karfin gaske. Saif kam mai zai yi in ba dariya ba, Ma'u kuwa bata tsaya ko ina da gudun ba sai gidan Yah Deen....tana tura 'kofar sai suka ci karo da shi da yake 'ko'karin fita, bata lura da shi ba har sai da suka yi wata irin gwabzuwa gaba 'daya ta fa'da jikin sa har tana shirin kayar da shi. Jinta jikin mutun ne ya sanya ta 'kara ru'kun'kume shi da karfin gaske. Yah Deen kam mamaki, 6acin rai da takaici ne duk suka cika shi, sai hakan basu yi wani tasiri a zuciyar sa ba fiye da yanda yaji tudun boobs 'din ta ajikin sa nan hankalin sa yafi tafiya duk da kuwa bai gane ko wacece ba balle yasan manufar ta nayin hakan. Da 'kyar yayi 'ko'karin raba jikin sa da nata bayan shu'dewan kusan mintina uku suna a hakan jin yanda wani abu ke shirin taso masa. Bai iya yaui mata masifa ba balle wani abu kawai sai tsintan kansa yayi da tambayar ta abinda ya faru bayan fahimtar ko wacece, cuz kallo daya yayiwa fuskar ta ya gane cewa itace suka zo da Saif mintina 'kalilan da suka wuce. " Shanu". Da yaji ta fa'da ne ya sanya shi matsawa ya le'ka 'kofar sai yaga ma har sun wuce sauran basu fi uku ba.    Dawo da kansa ciki yayi batare da ya kale ta ba yana duba jikin sa ya furta" sun wuce". Itama Ma'u le'kawa tayi sannan ta sa kai ta fice tuni farin cikin ta ya kori tsoron kaf, ganin cewa da shi ta ha'du har ma yayi mata magana cikin natsuwa ba tare da tsangwama ba.    Tafiya take a hankali tana sakin murmushi, ita ka'dai ta san da'din da taji ayau kuma take kanji har cikin zuciyar ta, a ranta take faman maimaita kalaman da yai mata ayau 'din...tambayar ta da yayi " Me yafaru" da kuma " sun wuce " 'din da ya fa'di...sosai suka tsaya mata arai suke kuma sata nisha'di....da haka har ta isa wurin mu ni da Saif da ke ta faman yi min dariya wai dan na tsorata...sai dai ganin dawowar Ma'u ya sanya dariyar tasa ta koma kanta wai ita kuma 6acewa tayi 6at da ganin shanayen sai aka rasa ta. Ni kam baki na tura bance da shi komai ba haka ma Ma'u kamar ha'din baki...kawai muka cigaba da tafiyar mu. 'Bangaren Yah Deen kuwa fasa fitan yayi ya koma ciki kan kujera ya zauna tare da dafe kansa a 'ko'karin sa na saita yayanin sa, amma ya kasa  daina jin tudun 'kirjin ta a jikin sa...sai daga baya ma ya fara jin haushin kansa da har ya biyewa zuciyar sa bai saisaitawa yarinyar nan zama ba....(daga baya kenan).  Har muka rabu da ita Saif nayi mana dariyar harda ta mugunta, sai da har muka rabu da Ma'u kowa ya kama hanyar gida kafin ya tuna da 'dagun murya yace " Na manta Ma'u matsoraciya...mun gode fa ". Ma'u batace da shi komai ba kawai ta cigaba da tafiyar ta tana ji har cikin ranta cewa batayi komai dan a gode mata ba tayi ne kawai saboda sanyin ranta wato Yah Deen. Koda muka je gida kuwa babu wanda ya sanar da Ammi abinda ya faru duk da kuwa har a lokacin idan muka ha'da ido da Saif sai in ga yana min murmushin mugunta, da abin ya ishe ni shine naje na sanar da Ammi tamkar zanyi kuka ita kuwa tace kar ya 'kara min dariya ai tsoro halak ne ba laifi bane dan na tsorata da ganin shanaye tace ko ita ma ai tsoron nasu take ji.    Jin abinda Ammi ta fa'di ne yasa na saki raina har ma na fara murmushi nima na jin da'din an bi baya na.    Sai yamma Yah Deen yazo gidan anan yake ce da Ammi ta dinga tura ko mai yi mata aiki ne tana gyara can gidan saboda 'kura na yin yawa. Hararan sa Ammi tayi sannan tace " ni na tura ka can 'din nace ka zauna ne?" " Haba Ammi na...". Ya fa'di yana rausayar da kansa gefe. Ammi sai tace " Kaida ka guje mu saboda me zan dinga wahalar da mutane a kanka?" " Allah Ammi ba haka bane yaran kin nan ne sun fiya surutu kuma kinga ina karatu ne shiyasa". " Kaide ka sani". Ammi tace gami da mi'kewa ta bar shi wurin.   Murmushi kawai yayi ya koma ya kishingi'da har Ammi ta dawo da ha'da'd'iyar juice 'din Abarba da ta ha'da 'dazu da bama nan ta kawo masa. *****       Ammi bata tura kowa ba har sai da aka kwana uku da maganar wanda ganin shiru ya sanya shi sake tuna mata kafin nan ta turani ni da Nana mai aikin ta muka je.   Ni kam da muka shiga gidan a varanda na tsaya ita ka'dai tayi sallama, da yace a shigo sai ta shiga, bai san ma da ni akazo ba har sai da ya fito da niyyar fita ya bar gidan sannan ya ganni tsaye a wurin ina ta wasa da hannu na. Turus yaja ya tsaya da mamaki yace. " ke kuma fa?" Inda yayi maganar yana kallo na. Take sai tsoro ya kamani na kasa ce dashi komai tamkar wacce ta ga dodo a gaban ta. _".....A a fa Yayah...Ammi ce ta aiko mu da Hudah ita kuma wai tsoro take ji....."_ Maganar Saif ta rannan ne da ya tuna ya sashi sakin tsaki kawai yayi gaba....dan ya gano dalilin tsayuwar tawa a wurin. Ni kam ajiyar numfashi na sauke har ina dafe 'kirjina ganin ya wuce batare da ya 'kara tanka ni ba. Har ya kusan fita sai kuma ya tsaya sannan ya waigo ya kalle ni yace " Idan kun gama ku rufe ko'ina ki wuce min da keys 'din can gida zanje na kar6a acan". Kai kawai na 'daga sama alamar " to" sannan nayi 'kasa da kaina. Shi kam juyawa yayi ya fita abinsa ba tare da ya 'kara fa'din komai ba. Yana fita kuwa na bi bayan sa sa'daf-sa'daf ina le'ken sa, sai naga tafiya yayi dagaske amma zuwa bakin hanya ba hanyar gida yayi ba inda yana tafiyar ne ma yana amsa waya hankalin kwance ga dukkan alamu baya tare da damuwar komai. Da'di naji har cikin raina da ganin ya tafin, gudun kar ya dawo ya tarar da ni da abinda nakeyi ya sanya ni dannawa 'kofar sakata sannan nayi ciki da gudu ina fizge hijab 'din kaina. Raina fari tas mukayi aikin dan zagewa nayi na tayata amma ina yi ina 'kara jaddada mata cewa kar ma ta yadda tace da ni akayi aikin gudun kar laifi ya shafe ni. Duk abinda naga be yi ba zan nuna mata a gyara wanda duk ina hakan ne dan kare kaina..." Allah ki tabbatar komai yayi dan in yazo yana masifa cewa zanyi ke ka'dai kika yi abinki dan ban isa da masifa ba ni kam"! Haka nake ta maimaitawa Nana har muka kammala gyare komai tsaf muka fito bayan mun rufe ko'ina. A hanyar mu ta komawa gida ne muka ha'du da Ma'u wanda tana ganin mu ta saki fara'a. Tambaya ta tayi daga ina muke...na gaya mata harda abinda ya kaimu gidan ma duk na sanar da ita. Bu'dan bakin Ma'u  sai tace " daga yau idan zaku nima zan na raka ku tunda Hudah ma ai tsoro kike ji ko?" Ta 'karashe maganar tana idanun ta a kaina. Da kai na bata amsa ina murmushin dan bata san asalin halin sa bane shiyasa take son zuwa inda yake. Ko da muka 'karasa gida dan gudun magana ma wa Ammi na bawa makullin nasa nace inji shi wai a ajiye zai zo ya ansa. Anan parlourn Ammi ta ajiye itama bata kai da nisa ba. Yah Deen kuwa bai zo gidan ba har sai dare shi ko tsoro ma baya ji, arean gidan da yake 'din ba mutane sosai bama shi da makwabci na kusa...amma hakan kullum sai ya ringa yin dare wani lokacin ni har mamakin sa nakeyi ma. *****      'Karfe takwas da 'yan mintuna, suna zaune shi da Alhaji Baba da Ammi suna 'dan ta6a hira, ni da su Saif kam duk muna 'dakunan mu, gara su ma su biyu ne sa6anin ni da nake ni daya sai dai inyi ta buga game ko kuma inta jagwalgwala wayar Ammi dan ba sanin kai nayi ba. Alhaji Baba ne ya duba agogo sannan ya ce da shi " Tunda ka guje mu sai ka tashi ka wuce ai naga dare ya fara kawo kai". Kishingi'da ya 'karayi tare da fa'din " Ina waccan yarinyar taki ne Ammi tazo ta bani Key na sai in tafi". Kan center table Ammi ta nuna masa sannan tace " gasu nan ba ta kai da nisa ba ma". Bai ce 'kala ba kawai ya tashi ya suri key 'din sa ya nufi hanyar fita". Nayi nan ni kam...Allah ya bamu alkahiri". " Amin-Amin" Cewar Alhaji Baba. Tun daga ranar kuwa Ammi ke turamu ni da 'yar aikin ta Nana duk bayan kwana biyu ko uku da sunan muje muyi masa shara.     Ma'u da ta gane kwanakin dake tsakanin zuwan namu sai ya kasance bama ko tunanin ina take ko kuma a ina zamu ganta, kawai tarar da ita muke yi tana jiran mu a gefe da gidan, da ta gan mu kuwa sai ta mi'ke mu 'karasa tare. Ni kam zuwan Ma'u ai rana ya min...gani nake tamkar ceto na tayi, cuz har a lokacin tsoro nakeji dan haka ba kullum ne nake sakin raina in shiga hankali kwance ba, sai dai na kan shigo cikin harabar gidan ne yanzu in jira su har su kammala sannan mu tafi, da yake watarana bai fita har suyi su fito. Ranar da na samu ya fita ya barmu mu ka'dai ne nakan saki raina in sha shagali na bayan na saka sakata wa mashigar gidan. A lokacin bansan dalilin da ke sa Ma'u biyo mu ba kuma banta6a tunani akan hakan ba sam, ashe ita burin ta kawai ta ganshi ne...ta kuma kusanci inda yake, masifaffen son shi Allah ya jarabce ta da shi..... *****      Satin da hutun Yah Deen zai 'kare a week 'din su Saif suka fara zana JSCE wanda a lokacin Jss 2 ma suke amma da suka ce suna son zanawa sai Alhaji Baba ya shige musu gaba ya tsaya kai da fata har sai sunayen su ya shiga jerin 'yan Jss3 'din masu shirin fita.         Kwanan su uku da farawa Yah Deen ya tattara ya tafi Jigawa Dutse. Duk da ba gida 'daya muke da shi ba amma sosai naji da'din tafiyar sa da murnar zan huta ma da zirga zirgan zuwa yi masa shara. Bayan tafiyar sa ne su Saif suka 'kare jarabawar suka fara hutu kuma. *****   Bayan wata uku da tafiyar sannan aka kai su Zaid makarantar boarding, ranar kam nasha kuka da 'kyar Ammi ta lallashe ni nayi shiru...tun daga lokacin gida ya zama shiru daga ni sai Ammi sai kuma Alhaji Baba idan ya dawo daga gidan gona. Sam banjin da'din zaman gidan kwata-kwata dan ya zama babu da'di...i missed Saif alot dan shi abokina ne sosai ba kamar Zaidu ba.     Da na kasa gane kan walwala ta sai na dinga tafiya wajen Ummah ta ina wuni acan daga nan mu wuce yawon mu da su Ummie muje gidan Addah da sauran 'yan uwa...inda duk da bana fahimtar hausar ta su sosai amma tun a lokacin na kanji suna cewa wai iyaye na sun bada ni saboda kwa'dayin abin duniya shiyasa suka ringa cusa ni tun ba'a so gashi yanzu har na zama 'yar gida kala ta ta bambanta da sauran 'yan uwa na, wannan maganar sai dai idan bamu je yawo ba sai an fadi min ko kuma idan an ganni ata6e baki sai kiji ance  Lalle fa gaskiya kwalliya ta biya ku'din sabulu". Ko kuma kiji ance " Umm su Hajiya Hudah 'yar gidan masu ku'di gaki nan kin dawo kamar 'kosai" ....Ni sam ba na sa maganganun aka a lokacin nalle in san cewa abin 6acin rai ake gaya min hakan yasa ban ta6a bawa maganar muhimmanci ba.      Sai ma in an anga yanda na koyi iyayi na canza na dawo fes dani sai kiga ana sakin tsaki da juya kai gefe....ni kam ko ajiki na ban damu da abinda ke faruwa ba...inda har zaki ji wasu na fa'din " Da ayi rawa da bazar uban wani dai gwamma kayi da naka saboda ko babu komai nanne tushen ka kuma nan za'a koma daga karshe musamman idan kasuwa ta watse"..Wannan a gidan da Addah ta Sauda ke aure ne aka fa'di hakan wanda ya fito daga bakib kishiyoyin balbalin ta. Addah Saudah shiru tayi bata tanka ba balle ni da bama fahimtar manufar su nayi ba sam. Yawan zuwa gida da nake yi a lokacin ne ya sanya wasu ma'kwabtan mu suka fara gulmace-gulmacen wai ai an fara gajiya dani ne shiyasa aka fara koro ni gidan iyaye na, bansani ba ashe tun zama na agidan mutane da yawa na jin haushi, kuma Ummah ta ta sani amma bata ta6a nunawa ba, haka ma Addah ta ita kuma bata nuna damuwar ta bane saboda tasan abinda suke fa'da 'din ba gaskiya bane shiyasa take juran jin maganganun duk kuwa da cewa suna matu'kar yi mata ciwo har cikin ranta. A hakan idan maganar tazo kunnan Ummah ta ta kanyi 'ko'karin fahimtar dasu cewa Ammin ke son zama dani ba wai cusa ni akayi ba amma sai aga kamar duk 'karya ne take yi. Ummah ta shiru take yi musu tunda Allah ya san gaskiya ai shikenan, wannan dalilin ne ya sanya da wuya kaga 'kafar Ummahn mu a gidan Ammi sai indai da 'kwa'k'kwaran dalili kafin nan...sosai take 'ko'karin kare mutuncin ta dana 'ya'yan ta game da hakan.    Akwai ranar da nazo sai na 'ki komawa can wurin Ammi, 'karfe 8 har ta gota na dare na gama shirin bacci na har na kwanta, Ummah ta bata ce da ni komai ba, tun kafin Maghrib da tace min inyi in tafi kar dare ya same ni sai nace mata ai nan zan kwana Ammi ne tace min in kwana. Na shirga wa Ummah ta 'karya nan kuwa bakomai ne ya sani hakan ba illah sabon 'kaunar ahali na da ya shige ni musamman saboda yawan zuwan da nake yi sai yasa sha'kuwar mu 'kara 'karfi. Ummah kuwa tun lokacin da na fadi hakan sai ta shiga tunanin kardai dagaske zancen mutanen gaskiya ne cewa an fara turo ni gida da dabara...abin ya kulle mata kai sosai cuz tasan ada matu'kar zanzo gida kwana to da Ammi muke zuwa bata ta6a bari na in taho ni ka'dai...amma ga mamakin ta sai gashi yau 'din ni ka'dai ne na taho. Ita kanta zata so in dawo gaban ta ta cigaba da ri'kon kayan ta amma tafi so inma hakan ne zai faru to ayi shi cikin mutunci kamar yadda aka 'dauke ni ana ganin darajar juna yafi. Duk da haka Ummah bata 'kara damuna akan in koma ba kawai tayi shiru. Har na kwanta ni da Ummie ina bata labari tamkar wata sa'a ta saboda shirme...kamar daga sama kawai sai naji tsayuwar mota wanda ya janyo hankulan mutane da dama harda wasu ma'kwabtan mu.    Alhaji Baba da kansa ya janyo motar suka zo da Ammi ganin dare har tayi amma ban koma gida ba, shiyasa Ammi ta damu Alhaji Baba sai da suka zo tare dan ya tayata ro'ko a bar mata ni gaba 'daya ta cigaba da ri'ke ni. Ai kuwa a 'kofar gida wurin Baban mu Alhaji Baba ya bayyana abinda ya kawo su inda ya ha'da da ro'kon kar Baban mu yace a a, dan Ammi ta damu sosai. Cikin gida ma Ammi zaune tayi cikin natsuwa take ro'kon Ummah ta akan tayi ha'kuri bawai raba ta da 'yar ta take son yi ba kawai tsananin sha'kuwa zata duba dan girman Allah ta bar mata ni, tace hankalin ta kasa kwanciya yayi yau ka'dai da bata ganni kusa da ita ba, tasan badai-dai bane hakan bai kamata ta nuna damuwar ta ba tunda hannun iyaye na nake amma duk da haka ta kasa jurewa sai da tazo ta ganni. Ina lafe gefen ta take maganar tana shafa kaina a hankali dan nima tunda naji muryar ta fito da gudu na rungume ta... daga yanda take maganar zaka fahimci cewa daga can cikin zuciyar ta maganar ke fitowa kuma babu zancen wasa a ciki. 'Dan takaitaccen tunani Ummah tayi....tun zama na agidan ban ta6a kawo 'karar abinda aka min wanda bai kama ta ba, ban ta6a zuwa nayi complaint ba akan wani abu da ba dai-dai ba, zama na nake a sake tamkar gidan mahaifina wanda ko makaho ya ganni zai san cewa hankali na kwance yake bani da wata damuwa a gidan Comment. Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Wannan shafin naki ne Antyn mu ( Anty MAIMOUNATH O.G MAHNOOR)* *Allah ya 'kare mana ke a duk inda kike.* 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *36*    ........Dan haka dan me zata hana ni?...dan me zata raba ni da jin da'di na?..ina ma laifin mai son naka?..ai wanda yaso naka ma tamkar kai yaso, in ba mai 'kaunar ka ba waye zai yi maka hakan....idan maganar mutane kuma zaka biye zaka da'de bakayi abin kirki ba, dan su mutane komai ka aikata to a wajen su kuskure ne dole sai ka samu masu zagin ka, in zaka yi abu to kawai saki ranka kayi abu saboda Allahn ka ba wai dan gudun abinda za'a fa'di ba tunda ba haramun a ciki..." Muryar Ammi ne ya katse tunanin da Ummah ta ke yi...inda Ammi tace " Dan Allah Umman Saudah karki ce a'a..kinga gidan yanzu bakowa sai ni ka'dai, idan ma bazaki bar min ita ba to ki bani aron ta  mu cigaba da zama zuwa wani lokacin insha Allahu da kaina zan dawo miki da ita...i ll bring her back to u safely kamar yadda kika bani ita insha Allahu.." Ammi tayi maganar cikin kwantar da muryar ta.   Murmushi kawai Ummah ta tayi sannan ta biyo bayan sa da fa'din " haba karki damu Ammi, ai 'da na kowa ne...Hudah kam yanzu 'yar ki ce, ga tanan Allah ubangiji ya baki ikon kulawa da ita..Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi". Iya abinda Ummah ta fa'di kenan daga haka kuwa taja bakin ta tayi shiru. Take Ammi ta washe baki ta fara godiya wa Ummah ta gami da 'kara janyo ni jikin ta ta rungume ni sosai. Alhaji Baba yau har cikin gidan mu suka shigo shi da Baban mu, shima Alhajin 'kara mi'ka godiyar sa ga Ummah yayi cike da jin da'di, haka ma Ammi ta ringa zuba godiya. Kafin su tafi ya ciro ku'di ya ajiye wa Ummah ta duk yadda tayi kan ya bar ku'din amma Alhaji Baba ko kulawa bai ba, Ammi ce tace " Haba Ummahn Saudah...idan kina haka kuma ai sai ya zama tamkar ba'a zama 'daya ba...dan Allah ki bar shi ki siyawa jikokin ki alawa dashi". Su kam su Alhaji tuni sunyi waje inda suka sake fita tare da Baban mu. Ko ranar kuwa ban kwana a gida ba muka wuce da su Ammi...sai 'kara jana ajiki ma da takeyi kamar zata maida ni cikin ta. Tun daga ranar Ammi ta ninka komai da take yi min ada, komai nawa sai da ya fita daban, ta shagwa6ani ta riritani tamkar ni ka'dai ce abu mai sunan 'da data fara gani a fa'din duniya, sosai Ammi ta 'kaunace ni ta nuna min soyayya na zahiri, sai dai duk abin nan bai sa na zama mara kunya ba, sai ma shiru-shiru da na 'kara zama a ko'ina...Ammi ta hanani yawan surutu sosai take kwa6a ta a fa'dar ta wai tafi so in dinga yin komai da 'kwa'kwalwa ta. Ma'kwabtan mu kuwa da yake ranar da abin ya faru kan idanun wasun su ne sai hakan ya sanya suka canza akalar zancen su da fa'din wai su Ummah ta saida ni sukayi ganin Alhaji Baba ya bawa Ummah ta ku'di...mutanen duniya sam ba'a iya musu wallahi...(na lura abin ma harda hassada a ciki).      *****      Zaune suke, Ummah ta, Baban mu, Yaya Usman dan shima wannan karan yazo gida har Addah ta Saudah dake gidan mijin ta... Baban mu ne yake neman shawarar su game da sabon gidan gona da suka bu'de a can Jos wanda Alhaji Baba yake so ya 'dora shi akai amma shi yana ganin tamkar shekarun sa sunja ya kuma manyan ta yana ganin kamar bazai iya ba. Yah Usman ne ya dinga bashi 'kwarin gwiwa da nuna masa irin babban cigaban da hakan zai kawo a rayuwar su, yace hakan ai hanyar alkhairi ne kuma ya yadda da kai ne shiyasa karka watsa masa 'kasa a idanu Baba". " Allah ya tabbatar da Alkahiri yasa hakan shine mafi Alkhairi ga rayuwar mu gaba 'daya" Ummahn mu abinda kawai tace kenan sai dai batun zama acan ne tace ita kam a a babu inda zataje tsofai-tsofai da ita ga 'ya'ya da jikoki..tace gara shi namiji ne, kuma ai dama su maza da nema aka sansu duk namijin 'kwarai baya zama...kuma komai nisan wuri matu'kar ka kyautata niyyar ka to Allah zai isan maka". Da haka suka rabu da Yah Usman ya koma gidan sa ya barsu nan zaune Baban mu dumu-dumu cikin tunani. Haka ma Addah Saudah da ta kasa fa'din komai har taron ya watse, farga take yi na yadda abin zai kasance a bakunan mutane...anya ba'a yi kuskuren saurin amincewa ba kuwa?" Shi kam Baban mu  tunanin sa na can batun da Ummah ta tayi ne, yana ga hakan cigaba zai kawo a rayuwar sa, to amma ai zama zai iya kuwa, a wannan shekarun nasa yana ga ba mutuncin sa bane yin rayuwa shika'dai a wani wuri daban da ba cikin iyalan sa ba...kuma Alhaji yace an gama komai hatta muhalli an tanadar acan. Ummah kamar tasan meke cikin ransa kawai tayi 'karfin halin bashi shawarar cewa ya samu wata kawai ya aura sai su tafi tare tace kaga ko ba komai bazaka rasa abincin da zaka ci ba duk sanda zaka bu'kata. Bece da ita 'kala ba kawai ya tashi ya wuce 'dakin sa. Hakan kuwa akayi kafin cikar sati biyu har an 'daura auren Baban mu da wata mai suna Jamila,  mijinta rasuwa yayi ya barta da yara biyar....ana 'daura auren da sati guda suka tattara suka koma Jihar Plateau da zama. Umman mu kam ita ka'dai ta san yanda take ji har azuciyar ta ba ta san me zata ce da familyn Alhaji Baba ba, 'kauna ce wannan ko kuwa akasin haka, komai yana faruwa ne da mutuntaka,  girmama juna da kuma zumunci, amma daga 'karshe duk ciwon abin kanta yake komawa, farko Hudah, 'karfin abinda yasa ta bar ni da Ammi kawai yawan damuwa ta ne ita kanta tana so in daina a wancan lokacin, zaton ta ko ri'keni da Ammi zatayi na 'dan wani lokaci ne, amma sai gashi abin ya juya ya koma zaman da bashi da iyaka dai-dai yake da a 'kira shi na dindindin dan bata san ranar dawowa ta gare ta ba...and ita ka'dai ta san ciwon hakan da taji.    Sai gashi kuma karo na biyu abin kan Baban mu ya koma, kuma ko wannan 'din ma zallar 'kauna ce da kuma yadda aka nuna, tunda dukiyar sa ya 'dauka ya dam'ka a hannun  Baban mu, amma sai gashi tun ba'aje da nisa ba abin ya koma kanta, tun zaman su da Baban mu bai ta6a ko tunanin yi mata kishiya ba balle aje ga yin ta, yanzu kuwa tashin farko sanadin Alhaji Baba gashi an mata kishiya, duk da cewa ita ta kawo shawarar amma dole da ciwo hakan nan kamar jira ake ba'a 'dau wani dogon lokaci ba komai ya kammala. Sosai abin yake cin zuciyar Ummahn mu, wani sa'in sai taji tamkar dan ita su Alhaji Baba suka dawo garin mu, tunda gashi dumu-dumu an sar'ke ta ta 6angori biyu masu girma, an wargaza mata gidan ta ta yanda sake dun'kula shi zai yi mata wahalar gaske. Duk kuwa yanda abin ya dami Ummah bata ta6a hirar da wani ko wata ba ciki kuwa hatta yaran ta, ta ri'ke ne daga ita sai zuciyar ta da fatan Allah yayi jagora kawai...idan hakan Alkhairi yake nufi ubangiji Allah ya tabbatar da shi. *****    'Bangare na kuwa bani da matsalar komai cuz duk abinda nake so shi ake yimin, hatta da gashin kaina sai da ya san da banbamci dan kuwa ba 'karamin kula yake samu daga wurin Ammi ba, har yanzu kuwa na kanje gidan mu, ni ka'dai wataran kuma da Ammi muke zuwa, lokacin da su Saif suka dawo hutu ma sai da muka je dasu Ammi ne tace muje mu gaida Ummah ta. Ummah bata ta6a nuna min komai ba dake cikin ranta, haka zamuje mu gama iya zaman mu tana nan nan damu da nuna farin cikin zuwan mu a fili...bazaka ta6a fahimtar alhinin dake 'kunshe cikin ranta ba. A hankali ma abin ya bar ranta da tayi tunanin kowani bawa kafin a halicce shi sai da littafin 'kaddarar sa ta zanu, komai yana tafiya ne bisa tsarin ubangiji to ita waye da zatace ba haka ba...tun da Ummah tayi wannan tunanin sai ta watsar da komai ta cigaba da harkokin ta, Addah ta ma yanzu ta samu sau'ki tunda ta fa'dawa mijin ta halin da take ciki a gidan shi kuma ganin gidan harda matan yayyen sa so ba dama shi yayi magana hakan yasa yaje ya dur'kusa ya zayyanawa mahaifin sa komai...da kansa ya tara su ya musu 'kira da babban murya akan baya son fitina kuma basu bawa mai tada ta goyon baya ba dan haka kowa ta kiyaye bakin ta, idan abin magana ne da wuya ka rasa ko wani mutun da shi me yasa za'a ringa takurawa Saudah a hana ta sakat bacin ba ita ce da alhakin komai ba...daga 'karshe yace kowa taja girman ta kowa ta kama mutuncin kanta baya son ya 'kara jin wani abu makamancin hakan ya taso in kuma ba haka ba to shikenan..yace da kansa zai 'dauki mataki akan koma waye". Wannan jawabin ne ya 'dan samawa Addah ta sassauci a gidan har yasa ta koma ta cigaba da rayuwar ta kamar da can. Baban mu ya kanzo duk lokacin da ya samu dama sai dai baya yin ko sati yake komawa 'kar'karin sa yayi kwana biyu ko uku shikenan ya koma. *****     'Bangaren Yah Deen ma sun sake samun hutu kuma yazo da yake idan ya tafi baya ko le'ko gida har sai semester ta 'kare, hakan ya sa har mantawa nake yi da shi, dan ko awaya ban ta6a gaisawa da shi ba...and kuma still a wancen gidan nasa ya zauna ni kam hakan yafi komai yi min da'di.....sai dai wannan karan Ammi ce masa tayi bazata tura kowa dan yi masa aiki ba, ai gida yanzu babu kowa tunda su Saif basu nan illah ni ka'daice me ze hana shi dawowa ya zauna tunda ba 'yan hayaniyar...da 'kyar Ammi ta amince ta yadda masa bayan uban ro'kon da yayi mata ranar farko ma a gida ya kwana amma washe gari muka je da shi na taya shi gyara gidan inata tura baki na gashi mai aikin Ammi bata zo ranar ba.   Ranar nasha wahala sosai dan ma bai zauna ba shima tare muka yi aikin da yake yana so ya zauna a gidan sai ya zage damtse ya manta da batun fi'ili, nima kuma gudun kar inje inyi abinda zaisa ya ta6a lafiya ta ya sa na saki jiki muka yi aikin tsaf. Ko bayan da muka 'kare na riga shi komawa gida, sai kuma na sa Ammi a gaba na rin'ka yi mata kukan ciwon kai da gajiya, ita kuwa ta ringa masifan wai ya wahalar dani, haka yazo ya sami Ammi na ta sababi ita ka'dai ni kuma ina kuka. Tsaki yayi zai shige ciki cike da 6acin rai dan yasan iskanci ne kawai ke damuna. " Dan uban ka zo nan Muhammad". Ammi tace da shi a fusace cikin harshen su na Igbo. Sai ya dawo yana tattare goshi da 6acin rai yace..." Allah Ammi iskanci  kawai ke damun yarinyar nan...ki tambaye ta mana ita 'daya tayi aikin ne?" Gira Ammi ta 'dage sama tana duban sa da mamaki tace " Ashe ma ka san abinda ka aitaka kenan?" Sai ya kauda kansa gefe ji yake tamkar ya rarumo ni ya jibge ni. " Wato dan ka samu na barta taje shine zaka min iskanci anan ko Mu'een? Ba ma zakace sannu ba sai ka hau yi mata masifa kaima ko? ba lafin ka bane ai na san isar ka ce ta sa hakan, shikenan je ka abinka....gobe ma ai rana ce zanga wa zai sake yi ma sharar ai". A fusace ya shige 'dakin sa batare da ya 'kara furta komai ba. Wanka yayi sannan ya fito ya sake fita abin sa bai ko sake kallon in da muke ga dukkan alamu fishi yayi da masifar Ammin. Ni kuwa Ammi rarrashi na ta dinga yi tana lalla6ani, da kanta ta rakani 'daki tace in je in watsa ruwa bayan na fito ta bani magani nasha na kwanta sai bacci. Ban 'kara ganin Yah Deen ba har sai dare lokacin sallahr isha'i suna shirin fita masallaci yake ce da Ammi wai sai da safe " Saida safe zaka ce ko, ka wahal min da yarinya sannan ko ya take ko ya gajiya bazaka yi mata ba zaka wani ce sai da safe?" Juya idanu yayi gami da rintsewa ya kuma bu'de su nan take cike da 'kosawa yace " Allah Ammi kina 6ata yarinyar nan da yawa ita ba mace bace...dan tayi aikin shara shikenan ya zama wani abin sakalci?" Zata sake magana yace " Zanje masallaci please Ammi sai da safe zanzo in duba ta". " Hmm" Kawai Ammi tace da shi daga haka bata 'kara fa'din komai ba.   Washe garin kuwa da yazo ko bi ta kaina bai yi ba ni ma dama kuma banso, haka ma Ammi bata 'kara tada maganar ba da yake dama da gangan take yi masa saboda gaba dan ya ji shakkan sake bani aiki mai wahala. *****    Bai nemi a sake yi mai aikin ba dan gudun masifar Ammi har kusan kwana uku, kuma sosai ya rage zuwa gidan yanzu, sau 'daya tak yake zuwa wanda ni kam ma wani lokacin bana sanin yazo balle in san lokacin tafiyar sa. Har akaci sati guda yana lalla6a rayuwar sa acan, da kansa yake yin sharar sa, yana so ai masa mopping amma fargabar abinda Ammi zata ce ya hana shi furtawa gashi kuma shi bai iya ba. Kwance yake yana tunani a wani dare da bacci ya gagare shi gaba daya feelings ya takura shi haka ya dinga taso masa kamar abin masifa, ba ranar ya fara ji ba amma sai na yau 'din ya bambanta da sauran ranakun da yake ji. Cuz ya kasa jurewa har cikin sa sai da ya ri'ke shi, bai san me ze yi ba hakan yasa ya ri'ke cikin kawai ya mi'ka rayuwar sa ga Allah mahalicci.....kafin cikar awa biyu kuwa zazza6i mai zafi ya rufe shi jikin sa na kakkarwa. Haka ya kwana yana fama da rayuwar sa, ranar hatta sallar asubah ma a makare yayi ta dan bai samu bacci ya 'dauke shi da wuri ba shiyasa ya makara. Duk jikin sa bai jin da'din sa sosai dan haka sai ya 'kira Ammi a waya ya sanar da ita cewa bai jin da'di ta aiko masa tea kawai. Bai ambaci sunan kowa da ai kawo ba dan gudun masifar Ammi kawai ya yanke 'kiran. Ai kuwa Ammi sai tabi wayar da kallo a fili ta furta kalmar  " munafuki". Sake dialling number tasa tayi kafin yayi magana tace " saura kuma idan na aiko ta ka sa ta aiki a gidan ka gani" Ya riga ya san wa Ammi take nufi dan haka sai yace " Ammi ni na nace sai ita ne...ni ma ba san zuwan nata nake yi ba ai" ya 'karasa maganar  'kasa-'kasa...dan har lokacin bai gane kan jikin sa ba. A masifance Ammi tace " Sai ka fa'di wanda ka ajiye da zai ringa yima aika  agidan ai, idan ba itan ba wa kaga nake dashi yanzu?" " Kuma dai" Ya furta a hankali yadda Ammi ba zata jiyo shi ba ha'di da sakin murmushin takaici...sannan a hankali cikin natsuwa yace " Ammi wai dan Allah yaushe kika daina so na ne? Fisabilillahi cewa fa nayi banjin da'di amma kike ta min irin wannan masifar Ammi, idan babu mai kawo wa kawai abar shi shikenan na fasa ma". Daga haka ya yanke 'kiran harda kashe wayar shi gaba 'daya. ~Ina gaida masoyanah Allah ubangiji yayi ta faranta muku cikin kowani irin yanayi...Salmerh na 'kaunar ku irin sosai 'din nan~ 🥰😘 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerhn ku ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 🤞🏻 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *37* Bansan yanda suka yi dashi ba ni dai kawai tace dani in shirya in kaiwa Yah Deen tea a gidan can wai baya jin da'di. Ban damu ba da na ji tace baya jin da'di dan haka raina fari tas na kar6a na kama hanyar gidan da yake. Koda naje 'kofan a rufe take sai dana ta bubbugawa kafin yazo ya bu'de bayan na shafe a'kalla kusan mintina goma sha uku ina tsaye. Ina jin an bu'de 'kofar sai na nutsu kamar wawuya daga bu'dewa nace " Ina kwana". Nayi maganar ina sunkuyar da kaina, bai amsa ba haka kuma bai ce da ni komai ba  maimakon ma ya kar6i abin hannu na a a sai kawai ya bani hanya ya koma ciki abinsa batare da ya sake kallon inda nake ba. A hankali nabi bayan sa bayan sa na shigo sannan na maida 'kofar na rufe ina 'kuk'kuni cikin zuciya ta. Har parlour na shiga na same shi zaune yayi 'da'd'daya bisa kujera take na kauda kaina gefe bayan kallo 'daya da na mishi a hakan ma banko yi gigin kallan fuskar sa ba...ina shirin ajiyewa naji kakkausar muryar sa dake cike da 6acin rai yace" wai ke dan uwar ki miye ala'kar ki da Ammi?"    Jikina rawa ya fara take idanu na ya cika da hawaye jin tsawan da ya daka min. Sai na fara in ina ina fa'din " Ni...ni" Yace " a a uban ki"! Take kuka sai hawayen tsoro suka taru cikin idanu na. Ganin nayi masa shiru ne ya sanya shi tashi ya dai-dai ta zaman sa yayin da ni kuma motsin da yayin ya sake firgita ni zato na ko hi zai yi ya dake ni hakan ya sa na saki sheshsh'ka ina jan baya ka'dan. A tsawace yace. " ki min shiru da Allah ni..." Tsit nayi na maida kukan gami da toshe baki na da hannu na duk biyu illah hawayen dake zuba min kaina 'kasa. " Munafuka kawai, ba kina jin Ammi ke zagi na ba lokacin bakiyi kuka ba sai yanzu?" Daga jin yanda yayi maganar zaki fahimci cewa cikin 'karfin hali yake yinta amma dan masifa da sabo da yayiwa zuciyar sa da shi ya sanya shi tilastawa kansa yin sa. Ina so ince masa " Allah ni banji ba". amma tsoron yin magana nake yi.    "...Kuma ranar nan da kika je kina yi mata kuka 'din yankan jikin ki nayi?" Naji ya 'kara fa'di. Sai na jijjiga kaina alamar a a still ina hawaye. " Na dake ki ne..ko kuma ke ka'dai na bari kika yi aikin?" Nan ma da sauri na girgiza kaina. "...oww wato munafurci dan ki ha'da ni da Ammi na ko?" Da 'kyar nayi dauriyan furta " Dan Allah kayi ha'kuri wallahi bazan sake ba...." Nayi maganar murya ta na cracking. "...kima sake" Ya tare ni da fa'din haka. "Ai kin isa". Ya sake fa'di. Sai nayi shiru ina kallon sa hawaye na na zuba ji nake tamkar in zura da gudu inyi waje. "..Ba kin sami 'daurin gindi daga wurin Ammi ba? " a a kayi ha'kuri" Nace dashi da muryar kuka. Bai ce dani 'kala ba kawai sai naga ya koma baya ya kishingi'da, da hannun sa ya nuna 'kasan 'dakin sannan yace " Zo nan"! Sheshsheka na saki cike da tausayin kaina a hankali na matsa kusa neasa ka'dan da shi na tsugunna kan gwiwoyi na cuz wannan karan ba 'karamin tsorata nayi da shi ba. Tashi yayi ya dan rankwafo Kano dan gami da kama kunnan sa ya wani  'kan'kance idanu tare da nuno ni da yatsa yace " Daga yau...me nace...?" Namaimaita " Daga yau" kamar yanda ya fa'di. " Idan kika kuskura kwana uku ta cika ban ganki cikin gidan nan kin zo sharewa ba wallahi take wuyan ki zanyi in karairaya ki...kinji abinda nace ko?" Da sauri na 'dage kaina sama wani hawayen na sake gangaro min. "..Useless kawai..." Ya fa'di tare da komawa baya ya jingina da kujera sannan ya 'kara fact 'din " 6ace ki bani wuri". Da sauri har ina 'ko'karin fa'duwa na tashi na nufi 'kofar fita sai kuma naji yana sake fa'din " Saura inji abakin Ammi....kashe ki zanyi da wu'ka babu ruwa na". Da sassarfa na fice daga gidan ina share hawaye na...ko nayi niyyan yin shiru sai in kasa saboda takaici da kuma girman tsorata da nayi gashi ya hana ni sanar da Ammi. Gudun kar in je gida ina kuka ne ya sanya ni zama jikin wani gida na sha kuka na son raina sannan na share hawayen tas na tashi na 'karasa gida ina sakin ajiyan zuciya.    Ko da naje a parlour na tarar Ammi inda tana gani na kuwa ta tsura min idanu, sai nayi 'kasa da kaina ina 'ko'karin wucewa ciki sai tace da ni " zo nan Hudah..me ya same ki?". Ta 'karasa da tambayata cike da kulawa. Kaina 'kasa amma sai na kasa cewa da ita komai..ban sani ba aseh shirun nawa ya sa Ammi tabbatar da cewa akwai abinda ke damu na. 'Dan 6ata rai tayi tace " Shine ko?" Jin haka yasa nayi hanzarin girgiza mata kai alamar a a. " To menene?" Ta sake tambayata tana kallo na. Kaina kasa nace" ba komai fa Ammi". Yanda nayi maganar yasa ta tsaya 'kare min kallo sosai tana karantar yanayi na. Ganin har a lokacin ban 'dago na kalle ta ba ya sanya ta 6ata rai sosai a fili tace " Wato Mu'een bai jin magana ta ko?" 'Dagowa nayi da sauri jin ta ambaci sunan sa baki na har na rawa nace da ita " Ni..fa Ammi ba shi..bane...na ha'du da shanu da yawa a hanya ne irin na rannan... shine suka bani tsoro nayi ta kuka". Ido ta tsura min sosai tana kallo na yayin da wasu hawayen ke sake sau'ko min ban kuma 6atawa kaina lokaci na share su ba dan nasan ko na share ma ba tsayawa zasu yi ba. Can sai Ammi saki ajiyan zuciya ta janyo ni jikin ta cikin kwantar da murya tace" Ya isa haka nan to daina kukan kinji...bama zaki sake zuwa can 'din ba balle ki ha'du da su". Jikin ta na kwantar da kaina ina ta sakin ajiyan zuciya, sam Ammi kam bata yadda da magana ta ba amma ta bari cikin ranta...musamman ma data ga yanda na yini sukuku a gidan babu walwala abin sai ya dame ta sosai dan tasan ba ganin shanu ka'dai ne zai sani hakan ba.    Da yamma kuwa sai gashi yazo gidan cuz ranar basu da buga 'kwallo. Gaida Ammi yayi ta amsa babu yabo babu fallasa fuskar ta wasai, d next thing abinda ya fito bakin ta shine..." Me ka yiwa Hudah ta da na aika ta da safe?" 'Dan 6ata rai yayi cike da basarwa yace " Ammi wa ce kuma Hudah?" " Bansan iskanci Muhammad kai kace in sa akai ma abu kuma sai ka je ka samin yarinya kuka?" " ohh....wai waccen yarinyar ?" " a a uwar ka nake nufi". Ta bashi amsa ada'kile. Ganin haka sai ya sashi zuwa gefen ta ya zauna yana fa'din " Allah Ammi ni duk bangane abinda kike min ba kwanan nan, gaba 'daya kin daina 'kauna ta saboda yarinyar can, komai nayi masifa kike min....ki tambaye ta mana in akwai abinda nayi mata ai da zata sanar dake na sani tunda ba abakin ta nake zaune ba". Ya 'karashe maganar da sanyin murya. Kauda kai Ammi tayi tare da fa'din " kai de ka sani, gaba ai tafi baya yawa.." " Ni dai yunwa nake ji Ammi..abar zancen please". Yayi maganar yana shafa cikin sa. Dinning ta nuna masa tace " Ga can abinci je ka 'diba kaci mana". " Da kaina kuma Ammi?" Wani kallo da tayi masa ne ya sashi sakin murmushi ya mi'ke yana girgiza kansa..cikin ransa yake fa'din " ai dole ma in ringa cin uban yarinyar nan ko dan huce takaici na".    Ban gayawa Ammi cewa yace in dinga zuwa yi masa shara ba gudun kar tayi masa masifa ni kuma ya kashe ni, dan haka duk ranar da ya kamata inje sharar bana magana sai dai kawai inna shirya zuwa makaranta sai in bi ta gidan inje inyi masa kamar yadda ya fa'da, sau tari sai a lokacin break nake samun zuwa idan har nabi yi masa sharan dan wani lokaci harda wankin kayan ball da socks 'din sa yake bani, dan mugunta kuwa yana gani na sanye da Uniform amma bai ta6a cewa in bari in yi tafiya ta makarantar ba...sai dai abu 'daya bai ta6a duka na ba. Idan kuma ranar babu makaranta to sai lokacin islamiya nake zuwa nayi masa aikin, wanda zuwa yanzun na fara fahimtar bashi ka'dai ke zama cikin gidan ba harda wani abokin sa mai suna Imrana dan ina yawan ganin ya shigo ko kuma wani sa'in su fita tare ...'dan iska ne na na 'karshe sam tarbiyya bata wadace shi ba,  kusan kowa kuma ya san halin sa a garin...shima Yah Deen 'din gurin ball suka ha'du dashi har suka 'kulla abota.      Ni dai magana bata ta6a ha'da ni da shi ba illah gaisuwa idan na gaida shi ya amsa min da muryar sa da take abu'de, shima 'din kuma baya shiga harka ta musamman da yake idan nazo komai a tsarge nake yin sa bana sakin jiki na, kuma ma shi ya zaci ko 'kanwa nake ga Yah Deen shiyasa bai ta6a nuna min halin sa ba sam..shima sai yake min kallon 'kanwar sa..gashi kuma ma yana gudun zuciyar Yah Deen sosai shiyasa ya tsaya iya matsayin sa. *****      Ma'u itace mutun na farko da ta fara fahimtar halin da nake ciki na rashin zuwa makaranta akan lokaci, da kuma zuwa gidan Yah Deen da nake yawan yi yanzu, dan ma mun 'dan jima bamu ha'du da ita ba nasan da tuni ta jima da fahimta, amma da yake  mahaifin ta ya hanata yawan fitan nan da take yi shiyasa bata san da faruwar hakan ba.         Akwai wani 'dan wan mahaifin ta da yake son ta da aure, mahaifin ta yaso ya ha'da auren su idan shekarun ta sun kai amma sai Ma'u ta nuna sam bata ra'ayi, hakan yasa ya barta batare da ya takura ta akan hakan ba, sai dai ya taka mata burki akan yawan fitan da take yi illah zuwa makaranta shima 'dib jifa-jifa ne...shiyasa ma muka kwan biyu bamu ha'du da ita a unguwar Yah Deen ba. Wata ranar laraba ne da aka tashi a makaranta muna hanyar komawa gida hanya ta ha'da mu da ita sai take ce min" Yauwa dama ina so in ganki in tambaye ki" Da " To gani ai " na amsa ta sai tace..." wai me yasa yanzu nake yawan yin lattin Islamiya da makaranta tace kinga fa yau Allah da kin sha duka sosai badan na bada ha'kuri ba?" Take na 6ata raina kamar dama jira nake yi kamar zanyi kuka nace da ita " Ba wannan Yayan bane yake sani aiki kullum, kuma yace kar in fa'dawa Ammi shiyasa idan zani makaranta sai in bi inyi masa aikin". Ido ta zaro tana fa'din wai dama har yanzu yana nan ne?" Kai na 'daga mata alamar " Erh" Ma'u kam sai tace kar in damu duk ranar da zanje aikin inbi ta gidan su zata na raka ni sai mu gama da wuri mu tafi. Da murna ta na amsa da to har muka rabu kuwa ina jin farin ciki har cikin raina. Tun daga lokacin muke zuwa gidan ni da Ma'u duk kuma jikin mu da kayan makaranta muke zuwa, cikin sa'a kuwa muna yin aikin kaf mu gama mu kuma wuce makaranta batare da mun yi latti ba, haka kuma wani lokacin har mu tafi bama ha'duwa da shi da yake ni dama in ba ganin sa nayi ya fito ba ban 'kwa'kulo shi dan wai in gaida shi. Sau uku kacal  muka je da Ma'u Allah sai ya taimake ni ya tattara ya koma makaranta, ranar da ya tafin kuwa nafi kowa farin ciki tamkar in zuba ruwa a 'kasa insha haka nakeji. *****      Level 2 ya koma yanzu, sai dai ya fara ta ne da wata sabuwar rayuwa, rayuwa ce mai cike da 'kazanta, domin kuwa Husnah ba Campus ta zauna ba wannan karan gidan sa ta koma da zama...wanda da 'kyar ma ya amince sai da tayi masa al'kawarin bazata na shiga shirgin rayuwar sa ba. Husnah bata damu da wani dokar sa ba cuz ita damuwar ta kawai ta same shi, yawan shariyar da yake yi mata cikin makaranta sosai ya ishe ta, gashi kuma dalilin sa ta rabu da ko wani saurayi bata kula kowa a lokacin. Sai kuma cikin rashin sa'a sai ya kasance wanda take yi domin san bai san tanayi ba, sam bai damu da ita ba, baya neman ta matu'kar ba ita ta bu'kaci ganin sa ba. Zaman su 'kar'kashin muhalli daya ne take ganin tamkar zai kawo mata sau'ki a zuciyar ta, dan tasan dole a kowace rana ta ganshi wanda take saka ran yawan kusancin su zai kawo mata sau'ki wurin saurin dasa soyayyar ta a zuciyar sa. Ko da ta dawo 'din kuwa ba wani yawan shiga harkar ta yake yi ba, baya zama da ita dan wai suyi hira, haka ya tattari rayuwar sa gaba 'daya ya mayar cikin 'dakin sa bata fiye jin 'duriyar sa ba. Sai dai duk wannan bai damu Husnah sosai ba tunda atleast ita ke yi musu girki kuma yana zama yaci...tasan duk tsiya dole watarana sai saki jiki da ita.   Gidan dama 2bedroom ne dan haka sai ta shiga 'dayan ta tsara shi dai-dai da mura'din ta ya zama nata yayin da Yah Deen yake cikin 'dayan. Daga baya abin yaso ya dame ta ganin cewa baya wani shiga harkokin ta, gashi babu wani abokin hira sa6anin da da take Campus da ba ya rabo da jama'ah, harma sai ta fara ganin tamkar an gudu ne baa tsira ba..tunda gashi akusa da ita kamar yanda ranta ke so amma sai dai kuma bata samun sakin fuskar sa sosai...sai daga baya ne ta basar kawai ta cigaba da harkokin ta ta daina damuwa. 'Bangaren Yah Deen kuwa ada yana lalla6a rayuwar sa ne da da'di babu da'di, yakan juri duk ciwo da damuwar da ta taso masa amma wannan karan da ya kasance da mace cikin gidan sai yake yawan sako ta cikin shirgin damuwar sa. Husnah kuwa babu ruwan ta itama rayuwar ta takeyi irin wanda take so,  bansani ba ko mantawa takeyi da cewa shi'din ba muharramin ta ba ne oho...duk irin shigar data ga dama yi take yi, ita zatayi musu abinci ta gyara gidan tsaf tamkar matar sa, gata da tsafta ba laifi. Babu abinda ya dame ta zaman ta gidan a sake take cikin kwanciyar hankali. Shai'dan kuwa ba'a ta6a ce masa ga yanda zakayi inde ba tsarin Ubangiji ka nema da shi ba to kuwa cikin lokaci 'kan'kani zaiyi galaba akanka ya canza ma tunani daga 'karshe ya barka da aikin dana sani. Zaman Husnah da ya Deen tare sai ya kasance tamkar ana 'kara rura masa wutan yawan sha'awar dake damun sa ne, ada ya kan 'danyi kwanaki bai ji komai ba kuma ko yaji ma ya kan jure abinsa, sa6anin yanzu da kusan kullun abin ke damun sa. Wani dare da ya kasa jurewa ya kasa controlling kansa akan hakan sam, take sai zuciyar sa ta hango masa Husnah matsayin waraka ga matsananciyar damuwar da yake ciki. Haka ya tashi tamkar ana ingiza shi ya kama hanyar 'dakin Husnah daga shi sai boxer ajikin sa ka'dai, yana zuwa ya tura 'kofar a hankali ya shiga...da yake ba rufe 'kofan Husnah take ba itama. Tayi 'da'd'daya bisa katifa ta baje ya same ta, bayan 'kare mata kallo da yayi a hankali ya 'karasa kusa da ita ya tsaya daga tsaye yana 'kara ji tamkar ana ingiza shi.   ....First thing da idanun sa suka fara sau'ka akai shine 'kirjin ta cuz babu laifi Husnah irin matan nan ne masu cikan 'kirji sai dai ace _masha Allah_ . Yayi tsayuwan a 'kalla mintina kusan uku yana 'kare mata kallo sannan ya zauna gefen ta daga bakin katifar. Ko ka'dan baiji cewa ba dai-dai bane abinda yake shirin yi 'din sai ma 'karfin gwiwa da zuciyar sa ke 'kara masa, ga shai'dan ma na sake 'kawata masa suffar ta a idanun sa. Batare da damuwar komai ba ya 'daga hannun sa ya sau'ke shi saman wuyan ta a hankali yake yi mata tafiyar tsutsa da hannun yana yawo da shi har zuwa saman 'kirjin ta...har dish-dishi yake gani tsabar masifa. Husnah da farko jin abin tayi tamkar a mafarki hakan yasa bata motsa ba sai ma ta 'kara yin luf tana sau'ke numfashi cikin natsuwa. Jin hannu saman Boobs 'din ta ne ya sanya ta bu'de idanu a hankali sai ta ci karo dashi a gefen ta, bata motsa ba sai kawai ta tsura masa idanu tana 'kare masa kallo da kuma jin abinda yake yi mata. Jin kamar yana shirin shigar da hannun sa cikin rigar ta ne ya sanya ta ri'ke hannun nasa sannan ta sake kallon shi. A 'darare shima ya 'dago ya kalle ta nan ta ci karo da idanun sa da suka gama 'kan'kancewa saboda mayuwacin halin da ya shiga, bata san damuwar sa ba amma haka kawai sai taji matsananciyar tausayin sa ya shige ta...cikin 'karfin hali tace " Me yafaru ne wai?" Sai ya 'dan lumshe idanun sa a hankali ya bu'de su, hannun sa 'daya ya 'daga ya shafa kansa da shi wanda har a lokacin Husnah bata sake mai 'dayan hannun sa ba. Da lumsassun idanun sa masu kama dana 'yan maye ya sake kallon ta" _Husnah Please_ ". Kawai ya iya ce da ita yana 'ko'karin cire hannun sa dake cikin nata. Jikin Husnah sanyi yayi da taji yanda muryar sa ta koma, da yake kuma shai'dan ya riga ya gifta tsakanin su hakan yasa bata 'kara yi masa magana ba, sai ma komawa da tayi ta kwantar da kanta,  soyayyar da take yi masa ne taji yana 'kara habbaka a lokacin wanda hakan ya 'kara bada babbar gudummuwa wajen bar masa ragamar jikin ta gaba 'daya. Tana jin sa ya dawo gefen ta ya kwanta gami da 'dora kansa saman cikin ta. Lumshe idanu kawai tayi jin yanda yake shafa mata jiki cikin 'kwarewa, Husnah bata bu'de idanun ta ba har sai lokacin da taji hannun sa kan boobs 'din ta yana shafawa cikin natsuwa. Ajiyan zuciya ta sau'ke tare da maida idanun ta ta rufe tana sauraran abinda yake yi mata. Shi kam cikin kwanciyar hankali ya dinga bin jikin Husnah yana Romancing 'din ta..batare da ya ankare da girman kuskuren da yake shirin aikatawa ba. Ranar haka ya jagwalgwalata son ransa daga 'karshe ma rigar baccin nata gefe akayi dashi, Husnah kam wata duniya ta daban ta tsinci kanta da bata ta6a sanin ana zuwa ba sai yau....bai kusance ta ba kam amma lungu da sa'ko na jikin ta kaf babu inda hannun sa bai kai ba.... Ranar a 'dakin ta ya kwana sai washe gari da sassafe ya tashi ya tafi nasa 'dakin.    Hajiya Husnah kam da ta farka kasa tashi tayi ba dan komai ba sai dan tsananin tunanin abinda ya fari tsakanin su jiya, zakiyi mamaki dan kuwa murmushi ne tsantsa kwance saman fuskar ta koda wasa bata hango aibun hakan ba. Duk abinda ya faru tsakanin su jiya kaf sai da ta tariyo shi cikin brain 'din ta.    Tun daga ranar bata 'kara yi masa shamaki da jikin ta ba, zaton shi ma ko zata nuna masa 6acin rai ne sakamakon abinda yayi mata amma ga mamakin sa sai ma yaga sabon salon 'kara shishshige masa da take yi.    'Dakin sa take biyo shi ta ma daina bacci a nata 'dakin  duk kuwa abinda zai yi mata bata yi mai musu sai ma ta taya shi idan ya bu'kaci hakan, kafin kice miye duk wani salo da iskancin Yah Deen sai da ya 'dora Husnah akai ta kusa kar6i darasin sa da hannu bibbiyu...shi kuwa Mu'een yaga na banza ai hikenan....cikin hakan har mai aukuwa ta afku tsakanin su.... _wa iyazubillah_ . Tun daga ranar da ya shige ta shikenan suka sake 'dinkewa, Husnah ta zama tamkar matar sa ta sunnah bu'katun sa suka daina shiga garari, a duk lokacin da bu'katar sa ta taso baya shayin zuwa gare ta kamar yadda bata yi masa gardama koda wasa, ada kowa shi ka'dan sa yake tafiya cikin makaranta amma yanzu tare suke fita abinsu kamar sabbin amare suna tafiya suna 'dan ta6a hira. Kulawa ta musamman Yah Deen ke bata abin gwanin birgewa inda ace ta hanyar da ta dace ne. Sai dai kafin cikar wata guda da faruwar hakan Husnah sai ta fara yawan zazza6i ko da yaushe bata cikin walwala abin sai ya damesu gaba 'daya, kullun da kansa yake siyo mata magani amma abanza, shi kuwa yanzu da ya san da'din abin sam sai ya kasa nutsuwa da jinyar tata dan kaso mafi girma ne ya ragu daga cikin rayuwar jin da'din da suke shimfi'dawa kwata-kwata baya samun yadda yake so. Gashi yanzun duk lokacin da ya samu kanta ya kanji ta daban kamar kar ya 'kyaleta haka yake ji, duk tabi ta canza masa... Har kusan sati uku suna abu 'daya jiki ya'ki 'daukan saiti, 'kawayen da suke course 'daya ma duk sun damu...kamar da wasa sai ta fara amai akai-akai...sai dai in bata ci abinci to sai ta harar, ga za6en abinci kamar kyanwa. Wannan karan kam hankalin sa tashi yayi dan ya fara zargin wani abu, hakan yasa shi da kansa yaje Chemist ya siyo PT strip yazo yasa ta gwadawa da fitsarin ta, wanda Husnah ta aikata hakan cikin firgicin kar ace ciki gare ta dagaske. Ai kuwa Yah Deen na ganin positive hankalin sa ya ninka nata tashi. Ya kasa zaune ya kasa tsaye, da yake ya san sunayen magungunan abortion hakan yasa shi zuwa ya nemo can cikin gari inda babu wanda ma ya sanshi balle a zargi wani abu, be ce da ita na kaza ba ne kawai ya bata yace tasha..gudun kar tayi masa gardama. Haka Husnah ta sha maganin bata san na menene ba, awa 'daya bayan haka cikin ta ya fara ciwo sosai kamar zata mutu, lokacin da ta ga jini ya fara fito mata sai hankalin ta ya 'kara tashi, da 'kyar ta daddafa ta shiga bayi anan ciwon ya ci 'karfin ta gashi ita ka'dai ce a gidan Yah Deen baya nan. Kafin ace kwabo kuwa har jinin ya fara bin 'kafafun ta,  'kara rikicewa tayi ga ciwo ga tashin hankali, a bayin ta zube tana rizgan kuka. Allah ma sai ya taimaka bai dade ba ya dawo gidan ashe daya bata maganin masallaci ya tafi, jin kukan sautin kukan ta ne ya sanya shi hanzarin garzayawa 'dakin ta, bata 'dakin amma yajiyo kukan daga bathroom, hakan yasa ya 'karasa jikin bayin ya 'dan yi knocking tare da 'kiran sunan ta. Tana jin muryar sa sai ta sake sakin wani kukan tana fa'din" Mutuwa zanyi ni kam Mu'een ka taimake ni". Saurin tura 'kofan yayi yana fadin " Subhanallah Husnah"! Ganin ta kwance 'kasan tiles 'din bayi kaca-kaca da jini ne ya sanya shi rikicewa shima...tsugunne yayi gaban ta yana 'ko'karin tallafan ta amma Husanh kam ina ji take kamqr an tsagata biyu, kukan ma daina fita yayi dan azaba, hawayen ta ma ya 'kafe yayi ga bakin ta da yayi ja saboda kukan da ta sha, ban da " Waiyo Allah!....waiyo Allah!!, zan mutu, Abbah na..waiyo Allah"...babu abinda take iya fa'di shi 'din ma a wahale take furta shi. Sosai Yah Deen ya tausaywa halin da take ciki, har yayi tunanin kaita asbiti amma sai yayi tunanin a wani matsayi kenan hakan, tsoro sosai ne ya kama shi da ya tuna cewa yin abortion na iya kashe mutum, tsoron idan ta rasu agidan sa kallon da za'ayi masa, me ma zai ce da iyayen sa da kuma nata iyayen?. Tashi yayi tsaye cikin tunani amma bai iya tsawaita hakan ba ya kuma tsugunnawa gefen ta" sannu" ya ringa jera mata sau ba adadi, cikin ransa yake Addu'ahn Allah ya takaita musu. Bayan tsawon lokaci sannan cikin ya fita bayan taci uwar wuya shi kansa Yah Deen din sai da ya fita hayyacin sa. Da 'kyar ta samu ta kintsa kanta wanda sai da Yah Deen ya saki ajiyan zuciya. Basu je asbitin ba har sai da aka kwana uku kafin sukaje nan aka tabbatar musu da cewa ciki kam babu shi ya fita. Sai a wannan lokacin bayan sun dawo yake sanar da ita abinda ya faru. Tayi murna 'kwarai da fitar cikin duk da kuwa tasha azaba amma ita aganin ta rabuwa da cikin shine dai-dai in haka ba ta ina zata fara tunkarar iyayen ta da batun bata san me zata ce da su ba. Haka tayi ta gama jinyar kanta har ta koma dai-dai, da warkewar ta kuwa ya nemi su sake komawa irin rayuwar su ta baya, anan Husnah ta nuna 'kin amincewar ta yayin da tsoro ya bayyana kan fuskar ta 'karara. Duk yadda yaso ya lalla6a ta da cewa da 'din ma bai tuna bane har ya bari ciki ya shiga amma yanzu ba zai sake kuskuren hakan ba...Husnah ta'ki yadda wataran kuwa ce mata yakeyi idan an ha'da kaza da kaza aka sha to cikin ko fara zama ba zaiyi ba zai fita...nan ma Husnah taki amince masa duk ta'ki yadda, har misalai yake buga mata ya nuna mata a wayar sa har cikin laptop 'din sa amma a banza, ta kan barshi yayi duk yadda yake so da jikin ta amma bata ta6a bari ya shige ta, da ya 'dauko hanyar hakan saita bijire ta tashi ta bar shi. Da abin ya ishe sa ne sai ya sata gaba suka je akayi mata allura... tun daga ranar suka 'dora daga inda suka tsaya dan kuwa sosai suka jarabtu da juna shiyasa ma  suke abinda ran su ke so batare da damuwar komai ba musamman da Husnah ta san cewa yanzu an mata katanga da daukan ciki. Haka suka ci wannan semester kaf suna sha'anin su, dan daga baya ma Husnah da kanta take zuwa tayi allauran, sai da akayi hutu kafin suka rabu Yah Deen ya koma gida. Ni kuwa daga ranar da ya dawo to nima daga ranar damuwa ta take farawa. Zuwa yanzu na tsani ganin sa har cikin raina, ji nake dama ya mutu a wancan lokacin da bashi da lafiyan nan kowa ya huta da masifar sa. Kwanan sa yau uku da dawowa amma kwata-kwata sau biyu kacal na ha'du da shi, ba'a kuma gayyace ni aiki ba da yake wannan karon tun kafin ya iso ta tura ni da mai aikin ta, Saif ma ya raka mu da yake sun zo hutu muka je muka gyara masa ko'ina.     Har kwana uku bayan dawowar sa babu abinda ya 'kara ha'damu da shi, har hankali na ya fara kwanciya da ganin hakan na fara sakin raina. Kwatsam ranar wata Talata bayan nayi shirina tsaf na fito da niyyar tafiya islmiya, da yake yanzu su Saif ko sun zo hutu basa zuwa shiyasa ni ka'dai nake tafiya ta, Uniform 'dina yasha guga ina tafiya ta a hankali na rungumi takaddu na da sallaya a kirji na, dai-dai 'kofar fita daga gidan sai muka ha'du dashi, da sauri nayi baya ka'dan kaina 'kasa 'kirji na na dokawa nace " Sannu da zuwa ". Bai amsa ba sai yace da ni" sai ina kuma?" "..ni..ni?"na tambaye shi da rawar murya sai yace " a a ni"! "..Islamiya zan tafi". " Munafuka ashe kin jini". Ya fa'da tare da wuce ni ka'dan kamar zai tafi sai kuma ya waigo..." akan me ma muka rabu da ke?" "..babu komai" Na bashi amsa da sauri sai yace " shara fa? Ko kin manta?" 'Daga idanu na nayi na kalle shi sai naji hawaye na taruwa min da sauri na maida kaina 'kasa kamar zan yi ihu saboda takaici. " Aikin ki zai fara daga gobe...kinji baki ji ba?" " Naji" Na bashi amsa da muryar kuka. Shi kam bai damu ba sai ma ya taka yayi gaba abin sa.     Raina ajagule har na isa islamiya duk da na tuno Ma'u amma duk da haka hankali na ya kasa kwanciya. Ai kuwa ban shiga aji ba sai da na tabbatar na ha'du da Ma'u, ga mamaki na ita kam da jin abinda nace sai ta saki murmushi abin ta tace min in kwantar da hankali na zata ringa taya ni. Sai a lokacin na 'danji dama-dama har ma na samu na nutsu a aji muka yi karatu.      Da yake ana hutun makaranta yanzu sai nace da Ammi zanje in gaida Ummah na, nan kuwa Ammi tace Saif ko Zaidu wani ya raka ni...Zaidu kam sarkin ba'kin hali take yace shi kansa na ciwo ba zai iya fita ba....Saif kuwa cewa yayi in bari mana gobe sai muje shi yau agajiye yake jin kansa. Ni kam ma duk hakan yafi min dan bana son wanin su ya san inda zanje balle har su gayawa Ammi.   Haka na tafi Ammi na fa'din in gaida su nace to zasu ji... Da fita ta sai na wuce gidan su Ma'u...ban ma zauna ba dana gaida matar baban ta kawai sai ta suri mayafi muka fito da yake tasan kwanan zancen...ita fuskar ta wasai idan kin ganmu yayin da ni nake nan kawai zanje ne dan babu yadda na iya. Muna 'ko'karin shiga sai ga Imrana nan yana fitowa daga gidan sai muka bashi hanya ya 'karasa fitowa....idanun sa 'kyat akan Ma'u mu kuwa gaida shi mu kayi tare da shigewar mu ciki...Imrana sai ya bimu da idanu. Yah Deen na kwance abin sa tsakiyar gado da yake akwai 'dan sanyi a lokacin shiyasa bai fito ba.    Ni dai ban damu da ganin sa ba sai naji ma hakan yafi min har Allah-Allah nake yi mu kammala mu wuce kafin ya fito. Har kuwa muka kammala bai fito ba, ina murnar zamu tafi sai naji Ma'u ta 6aro min wani aikin wai " cikin baza'a gyara ba?" 'Bata rai nayi nace " yana fa ciki". " To ke ina ruwan ki da shi ba aiki kawai zamu yi ba? Baki na tura nace " ni gaskiya tsoro nake ji". Ma'u kam hannu na ta kama da nufin mu shiga sai na wafce hannu na da sauri nace ni ki kyale ni, ke 'din kije in kin sharewa sai ki zo mu tafi. Ma'u kam bata damu ba ta 'dauki tsintsiya ta nufi 'dakin ta shiga ni kam sai na yi zama na a parlour ina jiran ta gama mu wuce gida. Koda ta shiga sai ta same shi kwance amma bai rufe kansa ba, ashema duk yana jin mu sai da yaji zata shigo ne sannan ya 'dan lumshe idanun sa. Yana ganin sanda ta shigo ta kalle shi, ganin kamar yana bacci ne yasa ta da san'da-san'da ta isa gaban sa ta tsaya tana 'kare mai kallo, shima kuma haka, yarinyar ba laifi tana da kyau a hakan ya 'karewa fuskar ta da jikin ta kallo, shai'dan sai ya 'kara 'kawata masa siffar ta gashi dama ba 'karamin missing Husnah yayi ba. Yi yayi kamar zai motsa sai tayi saurin tsugunnawa ta fara shara. Haka ya dinga binta da kallo idan zata waigo sai ya lumshe idanu yayi luf kamar mai bacci motsin kirki bayyi da jikin sa. Har ta kammala sharar ta fita bai motsa ba, ni kuwa ganin ta kammala ta fito yasa nayi saurin mi'kewa harma na riga ta barin parlourn ta biyo ni a baya tana murmushi take fa'din " matsoraciyar banza". Yah Deen kuwa sai da ya tabbatar ta fita sannan ya taso ya koma parlour ya zauna....Kamar wasa ya 'daga wayar sa ya dannawa Husnah 'kira tana 'dauka ya zaiyano mata 'karya da gaskiya na halin da yake ciki da  kewar ta da yayi. Bu'dan bakin Husnah sai tace da shi " Zanzo anjima ka jira ni". ..with so much exitment yace " da gaske....Husnah bansan zolaya ni". Yana mganar ya koma ya kishingi'da. " Allah kuwa zanzo nima fa na damu..ba jiya na gaya maka ba..kai de ka jirani zaka ga ikon Allah". Ta gama fa'din hakan da dan dariya tare da yanke 'kiran. Shiri tayi ta fito tace da mahaifiyar ta zata je shopping..." Adawo lafiya" mummyn tan tace tare da gyara zaman ta kan kujera. Key 'din mota ta 'dauka ta fita, tana fita kuwa sai ta kamo hanya ita ka'dai ba tare da tsoro ko damuwar komai ba. Tafiyar 'yan mintina ce ta kawo ta saboda yanda take sharara uban gudu ya sanya bata 'dauki tsawon lokaci kan hanya ba. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 🤞🏻 *Dadicated my In-law( Umm Amatullah) Luv u irin sosai 'din nan* 😍 *..Allah ya raya mana Zuri'a 🙏AMEEN* 🙏 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *38* Tana isowa ta 'kira shi yayi mata kwatance amma da 'kya ta gane gidan da yake farkon zuwan ta kenan, sai da ta ha'da da tambaya kafin nan, gashi kuma ya'ki fitowa balle ya sau'ka'ka mata abin. Mutanen kuwa idan ta tambaye su kawai sai su bita da kallon mamaki kafin a nuna mata hanyar da zata bi...dan sun san ba 'yar garin bace zuwa tayi. Da 'kyar ta isa gidan bayan ta ha'du da Imrana wanda ya kasance shine mutun na 'karshe da ta ha'du dashi shine kuma yayi mata jagora...Yah Deen ne ya tura shi. Ko lokacin da zata fita daga motar sai da ya sau'ke ajiyan zuciya yana mai yabawa da halittar da Allah yayi mata...dan sosai Husnah ta ha'du iyaka ga kyan jiki gashi ko'ina zam-zam masha Allah. Tare suka shiga Imrana da ita amma ganin yanda ta tafi ta rungume Yah Deen a gaban idanun sa ya sa shi fahimtar cewa ala'kar tasu babba ce, balle da yaga irin kallon da Yah Deen ke binta dashi..ai hikenan. Imrana murmushi ya saki sannan ya juya ya fita yana fa'din " sai ka fito malam...ni kam nayi nan". Yah Deen ko kula sa bai yi ba har ya 'karasa barin gidan. Imrana kuwa fita yayi cikin ransa yake fa'din " gayen nan zai kwashi gara anan gaskiya". Husnah bata yadda azahar ta gota tana cikin garin ba, gudun kar tayi laifi agida bacin shopping tace zataje. A hanzarce ta kintsa ta fito taja motar ta tayi gaba zuciyar ta fes dan ta faranta ran masoyin ta. 〰〰〰         Bayan sati biyu....abubuwa duk sun cunkushe ta 6angare na, abin duniya ne yabi ya ishe ni....musamman da ya kasance su Saif na shirin komawa makaranta, gashi kuma ayau 'din zanje shara can gidan sa, a duniya babu abinda nafi tsana kamar zuwa gidan Yah Deen sam banso koka'dan, gashi hatta Saif ban bari ya san abinda ke faruwa ba gudun kar ya sanar da Ammi Yah Deen ya yanka wuya na. Gashi sam ba kara ce da shi ba, duk yadda ka zage kayi masa aikin abu 'kalilan sai yasa ka gaba da masifa musamman ma ni, ban kuma san dalili ba..gashi ya hana ni yi mai kuka a gida yace ko da wasa hawaye na drop 'daya nayi kuskuren da ya 'diga mai a gida to sai ya 6allani. Idan yace 6allanin nan kuwa gani nake tamkar yadda ake 6alla kara haka zai min shiyasa tsoro ya yiwa zuciya ta 'kawanya, koda wani lokaci tsoron sa nin kuwa yake 'karayi cikin zuciya ta, saukin ma da nake samu shine da yake Ma'u na raka ni, zaki yi mamakin duk wannan tsoron nasa fa da nake ji bai ta6a 'daga hannu ya dake ni ba kalaman sa ka'dai ke firgita ni. Duk na koma wata iri da ni, walwala ta ta ragu sosai, ko a makaranta ban fahimtar komai tsabar damuwar dake cunkushe cikin raina, gaba 'daya na fige na 'kara ramewa gani daman ba jikin kirki gare ni ba, hatta Ammi sai da ta lura da ramar tawa da kuma ta tambaye ni ko wani abu ke damuna sai nace da ita bakomai hakan yasa kawai ta 'kyale ni, yayin da Ummah ta ke tunanin ko girma ne ya sanya ni ramar.     Yau ma kamar kullum, ta kasance ranar Lahadi ne so babu makaranta, hakan kuma yasa tun tashi na da safe abin ke ta min yawo a zuci, inata 'dawainiya da tunani, fargabar ta inda zan fara  tambayar Ammi cewa zan fita nake yi, bansan 'karyar da ya kamata inyi mata da zai sa ta barni in fita ba dan bata so in cika yawo da yawa acewar ta...shiyasa ma ta fara complaint da yawan ce mata zani gaida Ummah ta da nake yi..duk kaina sai ya kulle na rasa mafita. Har hakan yasa na makara har kusan sha 'daya ban fita ba, haka shima Yah Deen 'dib bai zo gida ba...ban san me ya ri'ke shi ba kuma.      Ina zaune a 'daki na kasa zaune na kasa tsaye kawai sai jin muryar Ma'u nayi tana gaida Ammi daga can parlour. Ai da sauri na tashi na fito fuska ta cike da fara'a nace " Ma'u"! Murmushi tayi min tare da 'karasowa inda nake. Ammi ma murmushi kawai tayi ganin yanda mukayi farin ciki da ganin juna, daga haka ta juya ta shige kitchen....mintina biyar Ma'u batayi agidan ba tace zata tafi, mayafi na zara sannan naje na sami Ammi dake kitchen nace" zan rakata Ammi". " Har zata tafi ne?" Nace " Erh" Sai tace" To kar kiyi nisa fa kinji?". nace mata" To" Tare da juyawa na bar bakin kitchen 'din da murnar bata hana ni fita ba. Daga nan naje na same Ma'u muka wuce da sauri..da yake nasan dama abinda ya kawo ta. Muna zuwa gidan ma sai muka tarar da shi ya fito yana shirin kulle gidan da ganin mu sai ya fasa yace " Ina dawowa yanzu". Ko gaida shi bamu yi ba muka shige ciki. Mintina sha biyar mai kyau bamu cika cikin gidan ba muka fito, dama aikin wani lokaci na gulma ne kawai, babu wani dattin kirki amma a hakan idan mutun be zo yayi ba sai aga laifin sa..tamkar wanda ya aikata babban zunubi. Kamar de yau 'din daga shara ma babu abinda muka sake yi amma a hakan je ki gani tamkar mun mopping komai..tsabar walwalin da ko'ina ke yi. Nice na matsawa Ma'u muka fito da sauri dan bana so in da'de saboda Ammi..amma da cewar Mau wai mu dan huta tunda baya nan. Bamu ko rufe 'kofan gidan ba mukayi gaba abin mu....sai dai muna barin jikin gidan muka ci karo da Imrana ga dukkan alamu kuwa gidan zashi, 'dan iskan sai ya saki murmushi ya tari gaban mu..." daga ina kuke, kuma zuwa ina?" Yace damu yana karkata wuya yana kallon Ma'u. Da yake ni na saba ganin sa wurin Yah Deen tun ba yau ba hakan yasa nace da shi" daga gidan can ". Na bashi amsa ina kallon sa. " To ya sunan ku?" Ya sake tambayar mu amma idanun sa na kan fuskar Ma'u. Da yake na matsu in wuce gida so kafin Ma'u tayi magana sai na riga ta da fa'din "...Sunana NOORUL HUDAH ita kuma Ma'u...Asma'u.." Na 'kara fa'da daga 'karshe. Sau 'daya kawai ya kalle ni sai ya maida idanun sa kanta yace " Asma'u...ina son ki". Jin maganar nayi tamkar sau'kar ruwan sama gatsau wani iri hakan ya sa na kalle shi sannan na kalli Ma'u. Sai yanzun Ma'u tayi magana bayan ha'de goshi da tayi da jin wai yana son ta a yatsine tace da shi" Hum-um ni dai bana son ka waccan na gidan nake so"! Ido Imrana ya zaro yana duban ta yace " Wa wai kike nufi?...Deeni?" Sai ta 'dage kanta. Murmushin gefen baki yayi ya cusa hannun sa cikin aljihun wandon jeans dake jikin sa gami da fa'din " wahallalliya, angaya miki shi 'din zai so irin ki ne? Da manyan yara yake tarayya ba da 'yan mata irinki ba, gara ma ki tsaya ki fuskanci rayuwar ki...ni nan nine kalar ki....". Bai kaiga rufe bakin sa ba nace " Ma'u ni kam zan tafi kar Ammi tace na da'de". " A a mu tafi nima gida zani". Ma'u tayi maganar gami da kaucewa daga gaban sa. Daga haka muka ra6i gefen sa muka yi wucewar mu. Imrana kam juyowa yayi ya biyo mu da idanu yana smiling, saboda wani tunani da ya 'darsu cikin ransa. Kafin mu rabu ne da mamaki nace da Ma'u " Wai ke Yah Deen kike so?" Sai tamin shiru tana kallo cikin idanu na...Baki na ta6e sannan nace " Indai wannan ne marin sa ka'dai ma zai kashe ki Ma'u...mugu ne fa shi sosai". " Ni dai inason shi"! Abinda Ma'u tace ka'dai kenan kanta a 'kasa. Baki na 'kara ta6ewa nace " Allah ya yaye miki". Bata 'kara tanka ni ba har muka rabu. Ni kuwa har na isa gida ina mamakin  ta a zuciya ta, wai ita tarasa wa za tace tana so sai Yah Deen " Ta6"...har sai ma naji tana bani tausayi. Ko da naje gida kuwa Ammi fa'da sosai ta fara yimin inda tace na da'de daga raka ta kuma sai inje in zauna, ni banga ita bata da'de agidan mun ba shine ni zan bita har gidan su, kenan ta fini wayo tunda jana tazo yi tace ai da tasan zan da'de da ba zama ta barni in bita ba..daga 'karshe sai tace idan ina yawo irin haka zata saka Mu'een ya zane ni". Ammi ta fa'di haka ne saboda ta san ina tsoron sa wai ko idan naji hakan zan kiyaye gaba...bata san cewa tsoron nawa ya zarce misali ba...dan kuwa tunda naji tace zai zane ni nayi narai-narai da idanu ina kallon ta nace " Dan Allah Ammi kiyi ha'kuri..bamu gama sharar bane da wuri fa shiyasa muka da'de..ni dai kar kice masa ya zane ni". Na 'karasa maganar hawaye na sa'k'ko min. Da mamaki Ammi tace " Shara kuma ta me kuma a ina?"   Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 🤞🏻 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *39* " Ai shine ya sani sharar"! Wannan karan ina share hawaye na nayi maganar. " Waye?". Ammi ta sake tambaya ta tana mai bada dukkan hankalin ta gare ni. " Yah Deen 'din ?" Na bata amsa hawaye na na sake gangarowa. Salati Ammi ke zubawa da jin abinda na fa'di, tana tafa hannuwa tace " Hudah dagaske shine ya saki shara?" Da kai na bata amsa alamar " Erh" Wannan karan Ammi baki ta ri'ke cike da mamaki tace" Allah Buwayi...Ina gidan nan ya akayi har yazo ya aikata hakan batare da na sani ba?". Ina tura baki nace " Ai ya da'de da fa'da min kuma yace kar ingaya miki in ba haka kashe ni zaiyi". Dariya ma maganar tawa ta bata amma yanda Yah Deen ya ninke ta abaibai ya yaudaretan sai ya sa ta jin 6acin rai sosai, " Wato barazana yayi miki da kisa" Ta fa'di a fili"..hmm lalle!... shiyasa ya daina neman atura masa kowa...munafiki ashe ya san munafurcin da ya 'kulla...zaizo ya same ni ai" Ni kuwa ina daga tsaye sai goge idanu nake yi kamar zan cire su, a lokacin tsoro biyu ne suka ha'du min, ga na kar Ammi ta sashi ya zane ni ga kuma tunowa da nayi cewa ya hana ni sanar da ita wanda hakan ya sanya hawayen nawa kasa tsayuwa. Zama tayi ta gyara tare da janyo hannu na zuwa gaban ta kusa da ita, kafin ta furya komai na 'dago jajayen idanu na sauke au kan fuskar ta nace " Ammi kar ki ce masa na gaya miki dan Allah cewa yayi kashe ni zai yi" Na 'karasa cikin kuka. ...Cikin lallami da kwantar da murya tace " Haba uwata ina nan din kike tunanin zai kashe min ke kuma in barshi, 'kyale ni da shi zai zo ya same ni ne...kinji?" Kaina na 'dage alamar Erh naji. " Yanzu gaya min me ya faru duk karki 6oye min kinji ". ....Daki-daki na hau bawa Ammi duk amsar tambayar da ta min. Takaici ne sosai ya kama Ammi jin yanda tsawon lokaci yake wasa da hankalin ta kamar 'kwallo...ya muzanta ta ya nuna mata bata isa ba, sannan ya girgiza mata igiyar al'kawarin da ta 'dauka kafin ta kar6o Noorul Hudah da wani irin fuska yake so iyayen na su dube ta ?" Ran Ammi sosai ya 6aci da shi. Abinda kawai ta iya 'karfin halin furta min a fili shine" Rabu da shi zai zo ya same ni"! Ni kam take sai na marairaice fuska tuno irin kashedin da ya zayyana min gashi na warware wa Ammi komai, cikin kuka da marairaita nace " Ammi dan Allah kar kice na gaya miki Allah kashe ni zai yi". Dai-dai nan Zaidu ya shigo 'dakin yana ta6e baki jin abinda nake fa'dawa Ammi, shi haka yake sam bai damu da damuwar kowa ba har ma sai nake ganin gara kowa ma akaina, domin iya tsawon zama na a gidan bai mun sha'ku da shi ya fara yi min kallon 'yar uwa ba yayin da ni nake jin su tamkar 6angaren jiki na. Daga can hanyar corridor Saif dake biyo bayan Zaidu yake fa'din " ...Wai Zaid anya kuwa ka tuna siyan wannan...." Cak maganar tasa ta yanke sakamakon ganin yanda nake rusa kuka...Ammi ya kalla sai yaga itama hankalin ta na kaina. Take akalar tambayar tasa ta canza daga kan Saif zuwa Ammi inda ya karasa shigowa parlourn da sassarfa yake tambayar.." Lafiya Ammi me ya same ta?" Ammi bata tanka shi ba kawai ta cigaba da duba na...shi kuma Saif ya 'karaso ya zauna daga gefen Ammi yana min duba a tsanake da son karantar yanayin da nake ciki. Ammi kuwa 'dan takaitaccen murmushin takaici ta saki gami da kamo hannu na tana share min hawaye tace " Ki kwantar da hankalin ki, ba na gaya miki ba, ai be isa ya kashe ki ba matu'kar ina nan kar ki damu kinji?" Sai na 'dage kaina sama. " Yauwa...sannan daga yau ki daina 6oye min abu kinji..koma miye ya faru kar ki 6oye min bana son irin haka ni...ko me ya miki ki zo ki sanar dani, zanyi maganin sa, yanzu wannan da kin gaya min tuntuni ai da hakan ba zai faru ba, da ba zan ta6a bari ya ringa bautar da ke ba balle har su lattin zuwa makaranta, munafukin kuma ya sani amma ya basar...zai zo ya same ni ne...ni ina nan na saki baki ina tunanin ramar girma ce ta kamaki ashe ba haka bane..wani abin ne daban...hmm yaron nan na wasa da ni Allah". Daga yanda Ammi ke furta maganar ma zaka san cewa ranta a tsananin 6ace yake hakan yasa da mamaki Saif ya 'kara jefa mata tambayar" Ammi wai meke faruwa ne na kasa ganewa". Sai yanzun Ammi ta 'daga idanu ta kalle shi sai tace da shi " me ke faru kuwa Saif a gidan banda matsalar Yayan ku, fisabilillahi nawa yarinyan take da zai maida abokiyar hamayyar sa? ace tsawon lokaci ina gidan nan ban sani ba ashe kullum sai taje tayi masa bauta acan gidan ko makaranta bata zuwa a lokacin da ya dace, kuma abin haushi ma wai sai yayi mata barazanar kisa idan ta sanar da kowa...ji min hauka fa? Bansan me Mu'een ya 'dauki kansa ba gaskiya". Ta 'karashe maganar da yaren su tare da watsa hannu. Ajiyar zuciya Saif ya sau'ke tare da fa'din" Haba!..ai nima wallahi sai da na zargi wani abu tuntuni, Allah Ammi da Hudah fa ba haka take ba, amma kwanan nan naga duk ta canza bata fiye son shiga mutane ba, kuma fa ko makaranta idan nace zan rakata hanya 'kin yadda take yi...ko'ina zata bata son araka ta sam, ashe dan kar aga inda zata je ne shiyasa". Tsaki Ammi taja tana kallon Saif cikin ido tace" See you, tun farko me yasa baka gaya min hakan ba to?" Yana shirin sake yin magana ta Ammi ta kwa6e shi da fa'din" Shut up please ya ishe ni..ai kaima harda laifin ka Saif...wancan wawan kan ma nasan koda ya sani he won't tell saboda mugun hali". Ta 'karashe tmaganar tana nuna Zaidu. Da haushin ance mai wawa yace " Nima fa Ammi bansani ba". " Kai ka sani ai.. useless kawai". Ta fa'di cike da takaici. Saif kam cikin kwantar da murya yace" Ammi sorry ni dai bansan haka bane Allah da kinsan bazan 6oye miki ba". Shiru Ammi tayi bata sake tanka shi ba. Ni kam kuka na na cigaba da yi bayan na kwantar da kaina bisa cinyar Ammi..ban 'kara fa'din komai ba cikin haka har bacci yayi gaba dani. Ta shi na daga baccin kuwa sai na tashi da zazza6i mai zafi saboda tsoron abinda zai biyo baya tsakanin ni da shi, cuz koka'dan ban yadda cewa Ammi zata iya hana shi ta6a lafiya ta ba. ***** Tun a ranar ba'a kwana ba Imrana yaje gidan su Ma'u da sunan zance ita kuwa ta 'kara jaddada masa wanda take so da yake tana tare da yarin ta itama shi yasa sam bata damu da bayyana sirrin dake cikin ranta ba, domin dududu shekarun ta sha biyar ne a lokacin. Mahaifin ta ma daya ga Imrana tare da 'yar sa ai sai hankalin sa ya tashi sosai, ba zato ba tsammani kawai washe gari yasa ta shirya ya tura ta can wurin dangin mahaifiyar ta a Lanzai ko ita kanta Ma'un kuwa bata san dalilin tafiyar tata ba balle wani daban...dan a cewar sa sam be yaba da tarbiyar Imrana ba. Ana gobe su Saif zasu tafi zazza6i na yayi tsanani sosai....hankalin Ammi kuwa ba 'karamin tashi yayi ba. Ko lokacin da su Saif zasu wuce ma kuka na dingayi Ammi duk sai ta 'kara rikicewa har suka tafi basu samu natsuwar Ammi ba. Bayan tafiyar su ne suka sake 'kiran ta awaya lokacin ina bacci.....sai a sannan hankalin su ya kwanta da suka ji tayi musu Addu'ah cikin natsuwa...anan Saif ya sake tambayar ta jiki na ta ce da shi " Alhamdulillahi da sau'ki". Jin hakan ne ya 'kara kwantar da hankalin Saif har ya saki ransa a makaranta. Kwana uku ina kwance ban zuwa ko'ina, Alhaji Baba da kansa ya 'kira likita ya dubani ya bani magunguna da Allura, ni kaina wannan karan ban san me yasa banji tsoro ba akayi min har guda biyu, sai dai magungunan kam ban iya na sha ba illah kuka da nake tayi wanda ganin haka yasa Alhaji Baba yace abarni kawai. 'Bangaren Yah Deen kuwa sai da ya kwana biyar cif bai sa ni a idanun sa ba, koma ba dan sharar da nake yi masa ba atleast idan ya ganni ya kanji natsuwa har cikin zuciyar sa, amma sai gashi yanzu ko gidan yazo baya gani na haka ban zuwa can gidan nashi, shine ranar ya ku'duri aniyar tambayar Ammi dalilin daina gani na da yayi. Zaune suke kan Dinning daga shi sai ita da yake dama babu kowa gidan, Ammi ce da Alhaji da ni, Alhaji Baba kuwa tuni ya fita, ni kuwa ina 'daki ina bacci, shi ma 'din breakfast yazo yi shine suke zaune tare da Ammi, abinda yayi sosai yake bata haushi amma dan takaici ma sai ta tarasa me zata ce da shi...sai dai ko ba'a fa'da masa komai ba shi kansa yasan sakin fuskar da take yi masa kaso mafi yawa daga ciki babu shi yanzu, hatta gaisuwar sa a yatsine take amsawa kuma daga gaisuwar bata 'kara wani hira mai tsayi da shi sai dai be san dalilin faruwar hakan ba sam kuma bai tambaye ta ba. Yah Deen ya saci kallon inda take a 'kalla kusan sau uku amma ya kasa furta abinda ke ransa, musamman dan ganin yanayin da fuskar ta yake ma...sai ana hu'dun ne kafin ya iya dauriyan 'kiran sunan ta cikin tsohuwar shagwa6ar da jima bai yi mata ba. Da idanu kawai ta iya kallon shi sai ta kuma sau'ke idanun batare da ta furta komai ba. Ganin hakan ya sanya shi yin gyaran muryfa tare da gyara zaman sa da kyau ya wani buga uban tagumi sannan yace" Dan wai ni Ammi laifin me nayi kwata-kwata yanzu bakya 'kauna ta..ko dan na daina zama a gidan nan ne?" Ammi bata kula shi ba kawai ta cigaba da abinda takeyi koma kallon inda yake bata sake yi ba. Bai 'dau abin wani serious ba dan iya tunanin sa bai hango laifin da yayi mata ba, hakan yasa yayi saurin kauda wancan zancen da fa'din" Ba ma wannan ba Ammi ni kwana biyu ban ganin 'yar kin nan ko tayi tafiya ne?" Kamar ba zata yi magana ba sai can kuma tace" Wace 'yar ta wa kenan?" Yah Deen cire tagumin yayi jin ta kula shi, har da 'dan ha'de gira as if tilasta shi akayi yin maganar yace..."..Nu..Noor ce wai ko ya ma sunan ne na manta". Ya 'karashe da yatsina fuskar sa. Cikin kwantar da murya Ammi tace" Baka gaji da bautar min da ita ba kenan?" Tayi magnaar tana ajiye spoon 'din da ke hannun ta tare da gyara zaman ta. Yah Deen kam ido ya zaro da mamaki yace " Ni kuma Ammi?" " a a Ubanka...!" "Toh ni Ammi wani irin bautar da ita zanyi?" " Ka fini sani ai.. ko in ba hakan ba me yasa ka tambayar ta...ko kashe tan kazo yi har gida kamar yadda ka yi niyya?" 'Dan 6ata rai yayi dan ya fahimci inda zancen ya dosa a hankali yace " Nifa Ammi ba haka bane...kawai danna tambaye ta laifi ne?" "....Babba ma kuwa!....kai yanzu ko kunya baka ji sai kasa yarinya 'karama irin wannan agaba bacin kasan lokacin zuwa makaranta ce kai haka akayi maka?" Shiru yayi ya 'dan lumshe idanu yana sauraran ta. A tsawace tace " I'm asking haka akayi maka?" Bu'de idanun nasa yayi da tuni har sun canza launi zuwa ja bai kalle ta ba kawai ya zubawa table 'din dake gaban sa idanu. Yayin da Ammi ta cigaba da fa'din"...kai me yasa ka koma can gidan ba cewa kayi dan kayi karatu bane...shine dan iskanci ita kake 'ko'karin hanata nata zuwa nata makarantar karatu yafi karatu ne?...ko kuwa tsabar ka raina ni ne yasa hakan?" Ta 'karashe maganar tana kallon sa. A hankali ya 'daga idanu ya kalle ta tare da fa'din "...Dan Allah Ammi kiyi ha'kuri..nifa ba nufi na kenan ba". Kwafa tayi gami da fa'din " Ohh nufin ka 6ata raina ko?" " Haba Ammi?" " Yi min shiru da Allah, me kuma zaka sake fa'da min tunda duk girman baka san kayi abinda ya dace da kanka ba har sai an tunatar da kai, and this is my last warning Mu'een wallahi ka kiyaye ni, idan ka kuskura na sake jin abu makamancin hakan ya faru zaka sha mamaki na, ni da kaina zan 'dauki mataki tunda ba kai ka kawo ta gidan ba, kaje kayi rayuwar ka acan babu ruwan ka da yarinya ta, ka bar min ita sha iska, ai kaima babu wanda ya takuraka dan haka ka ka bar min yarinya ba ita ta turaka can 'din ba so babu dalilin da zaka 'daura mata nauyin da ko ni ban 'daura mata ba ..." Taran ta yayi da fa'din"..Ni dai kiyi ha'kuri Ammi.." " Sai yanzu kasan da ha'kurin ai...kwanan yarinyar nawa ba lafiya amma baka ta6a tambayar ta ba sai yau da kake so tayi maka bauta kafin ka iya tambayar ta har ka bada ha'kuri ko..?..i thought ni dai muka rufe zancen tun da 'da'dewa..dan munafurci shine ka zagaya da yake isheshshe ne kai shiyasa ka nuna min ban isa ba, jibi yanda yarinyan duk ta 'kare ta lalace, ko tausaya mata baka yi dan mugunta....". Murmushin dole ya 'ka'kalo ya sanyawa fuskar sa, dan ya fahimci masifar Ammin ba mai 'karewa bane...in dai akan wanna 'yar ne Ammi gwana ce wurin masifa...balle shi da ta kama dumu-dumu da laifin da acewar ta bautar mata da 'ya yake yi..." ko itan ba mace bace oho.." Yayi maganar cikin ransa. A fili kuwa cewa yayi "...Ai ban sani bane Ammi shiyasa...ina take in duba ta". Tsaki Ammi taja ta kawar da kanta gefe, Yah Deen kam wani murmushin ne ua kubce masa sai ya mi'ke ya nufi 'dakin Ammin....tura 'kofar yayi a hankali sai ya hango ni zaune ina shirin sau'ka daga kan bed. Tsaye yayi a 'kofa yana 'kare min kallo, koka'dan baiyi regretting abinda ya aikata ba, bai ma ji cikin ransa cewa laifi ya aikata ba in ka 'dauke abu 'daya shine lattin schhol da nake yi bayaga haka kuwa zuciyar sa fes. Ni kam ina ganin sa sai zuciya ta ta tsinke da 'karfi take nayi narai-narai da idanu tamkar zanyi kuka..jiki na ya fara 6ari. Sai da ya kuma waigawa ya kallo baya bansan abinda yake dubawa ba kafin a hankali ya 'karaso ciki ya iso gaba na ya tsaya yana kallon duk yanayin da na shiga. Ni kam tausayin kaina ya sani zubda hawaye ina sunkuyar da idanu na 'kasa..farar shimi ce a jikina da wani skirt 'yar kanti da Ammi ta siya min, kaina ba ko hula sai tsefaffen gashi na da jinyar da nake yi ya hana ai min kitso har ranar. Sai da ya gama 'kare min kallo wai ko zai hango ramar da yaji Ammi tace nayi amma shi kam bai fahimta ba ko dan bai san yanayin jiki na kafin faruwar hakan bane oho, iya abinda ya sani game da jikina tun farko dama shine banda wani jiki, to ko yau din ma iya abinda zai iya fa'di kenan bai ga sauyi ba, yana folding hannun sa a 'kirji yace " Miye hakan kuma ?" In da yayi maganar cikin natsuwa..sai na 'dago kaina na kalle shi..take kuma na sake yin 'kasa da kaina hawaye na gangaro min. Sau'ke hannun yayi a 'kirjin sa ya cusa cikin aljihun wandon sa kafin yace "... Ba cin kin riga ki fa'da har ta yi min masifan kuma miye na kuka? ko zazza6in ne ya tashi da gani na?" Girgiza mai kai nayi alamar a a. " To ya akayi?" Ya sake tambaya ta. Da muryar kuka nace "..Dan Allah Yaya kayi ha'kuri kar ka kashe ni..ba zan sake ba, bazan sake gaya mata ba"! Bai bi ta kan wancan maganar tawa ba kawai yace " Me ke damun ki wai?" Kafin nayi magana naga yayi saurin zama gefe na wanda sai da ga zauna 'din kafin nima na jiyo takun tafiya, take kuwa sai naji da'di har cikin raina dan nasan Ammi bazata bari ya cutar da ni ba kamar yadda take fa'da min kusan kullum. Yah Deen kam harda kama hannu na tare da maimaita tambayar da ya min da farko kafin ya zauna...inda ya sake yin tambayar yana ta6a jiki na zuwa wuya na. Ganin haka yasa nayi saurin bashi amsa da fa'din "..Zazza6i"! " Sannu.." Yace dai-dai sallamar Ammi da shigowar ta cuz batare da ta jira an amsa ba kawai ta 'karaso ciki. Yah Deen kuwa har shigowar Ammi bai saki hannu na ba shi nan adole ya nuna mata cewa he cares for me..but ni ka'dai na san me yake min da hannun nawa, palm 'dina ya ri'ke cikin nashi dan haka sai ya cusa yatsan sa 'daya cikin tsakiyar hannu na a hankali yake yawo da shi wanda babu ta yadda mutun zai fahimci hakan in ba ni da shi da muke zaune ba..cuz ko Ammi da ta shigo bata lura da hakan ba idanun ta kan fuska ta batare da ta ko kalli inda yake ba ma tace " Kin tashi ko?" Kaina na 'daga mata sama sai tace " To ki samu ki watsa ruwa sai ki same ni can parlour...magungunan ki basu 'kare ba..idan kin yi breakfast sai ki sha ko?" Kai na 'daga mata ina marairaice fuska. Wayar ta wuce zata 'dauka acan gaban mirror ganin haka yasa nayi yun'kuri nima da niyyar tashi cuz Allah-Allah nake ya bar inda nake, sai dai wani kallo da ya watsa min ya sanya nayi saurin komawa na zauna kamar yadda nake da farko still kuma bai saki hannun nawa ba bansani ba ko mancewa yayi da ni 'din wacece. Har Ammi ta 'daukp wayar ta juya bai ce da ita komai ba haka nima, ganin tana shirin fita bata tanka shi ba ne yasa shi tambayar " Ammi wai meke damun ta ne?" " Ka tambaye ta mana gata gaban ka ai". Ta bashi amsa batare da ta ko kalle shi ba kawai tayi waje abin ta. Murmushi ya saki batare da damuwar komai ba, dama ya san ba amsa mai kyau Ammi zata bashi ba kawai ya tambaya ne dan rasa abin fa'da shi a dole kar tace bai damu da jinyar tawa bane dagaske. Ni kam baiwar Allah, idanu na 'kur akan connection 'din da yayi da hannu na nawa hannun 'dumi ne da shi yayin da nashi yake sanyi 'kalau, ji nake kamar in wafci hannu na in zura da gidu amma tsoro bazai barni ba, ban kuma san manufar hakan da ya yayi ba sam. Idan kinga hannu na a cikin nasan abin tausayi, duk yadda nake fallin nafi su Addah Saudah Hasken fata compared to him ba'ka na dawo, idan ina tare da Yah Deen sai dai a 'kira ni da mai choculate skin, hasken sa tas ne shi irin na Ammi ya 'debo, dan shima sosai yafi su Saif hasken fata. 'Dan motsi nayi da hannu na dake cikin nashi sai yayi saurin sake min hannun tare da mi'kewa tsaye bai sake fa'din komai ba har ya juya ya kusa fita daga 'dakin sannan yace " Allah ya sauwa'ka". Inda yayi maganar ciki-ciki tamkar dole aka sa shi furtawa. Nima ban ko amsa shi ba kawai na bishi da idanu har bar 'dakin ya maida 'kofar ya rufe. Da ganin haka kuma sai na maida idanu na kan hannu na da ya ri'ke 'din ina mai jin wani farin ciki na ratsani na ganin bai kashe nin ba, da yake dama fargaba ceke 'kara narkar da ni shiyasa da na ga bai kula ba kawai sai naji wani sanyin da'di har zuciya ta..zakiyi mamaki Hafsat kamar wanda ciwon ya cire min take naji ni garau illah rashin 'karfin jiki. Kafin washegari kuwa har na warware abina kamar bani ba, Ammi kanta sai da tayi mamaki. Haka kuwa na cigaba da rayuwa ta cikin kwanciyar hankali..ba na tare da damuwa yanzu dan zuwa ko'ina illah makaranta da Islamiya...ga shi Ma'u ma bata nan balantana ta dame ni...sabuwar rayuwa na fara mai cike da 'yan cin kai da walwala. 〰〰〰 _*Bayan sati biyu.....*_ Zaune muke ni da Ammi tana tsife min kaina sai wayar ta tayi ringing...tana gefe na wayar game na keyi da na gaji na ajiye ta gefe na. Baki na ta6e da ganin suna mai 'kiran nata, bai jima da barin gidan ba kuma miye na 'kiran waya na fa'di cikin zuciya ta tare mi'ka mata wayar. " Wa alaikissalam..." Naji Ammi tace cikin kulawa. " Ammi akwai wasu kaya na da na bawa Zaidu ya wanke min bai kawo ba tuntuni...na manta kuma 'dazu ban tambaya ba, please ki bayar akawo min". Daga 'dayan 6angaren aka fadi hakan cikin natsuwa. Ammi sai tace" Bani da 'dan aike ai ka sani ko?" Dariya kawai yayi sannan ya yanke 'kiran. Ammi sai da ta gama min tsifan tana mitar mantuwar karya me yasa da ya tuna bai dawo ya duba ba. Kusan shu'dewar mintina a'kalla arba'in har mun kammala tsifan ta kame min da ribbom dan nace kitson sai da yamma zanje idan na huta da yake ranar bani da Islamiya. Muna zaune wayar Ammi ta sake yin 'kara sai ta'ki 'dagawa, sau biyu aka kuma 'kira duk bata 'daga ba, sai da na ukun ya tsinke kafin ta ja tsaki gami da fa'din inyi ha'kuri in kai masa kayan in dawo kafin lokacin zuwa kitson yayi, da taga na canza fuska sai kuma fa'din kar in damu duk abinda ya min idan na dawo in gaya mata tana dai-dai da shi. Haka de na tashi na wuce na nemo hijab 'dina wani sky blue na sanya ajiki na kafin in fito ma har Ammi ta fito da kayan ta shirya su cikin jakar da kawo su tun ranar da ya bawa Zaidu wankin, haka na 'kar6a na tafi badan raina naso ba na kama hanyar gidan sa ina tafe ina 'ku'k'uni cikin raina, fuska ta ka'dai zaka kalla kasan cewa raina be so aiken ba. Yah Deen na zaune a parlourn sa yana murmushi shi ka'dai, ba na komai ba sai ni sabon halayyar da Ammi ke yi masa musamman saboda ni, shi har mamakin ta yake yi wasu lokutan yadda ta fifita ni akan kowa, ai ya san babu wanda za'a turo sai ni ne shiyasa Ammi taki 'daga wayar sa...A fili ya saki ajiyar zuciya tare da fa'din" Ko cinye ta zanyi oho". Yana cikin zancen zuci bazata kawai sai yaji tsayawar mota daga waje, cak ya tsaida hankalin sa tare da sauraren wanda zai shigo, ga mamakin sa kawai sai yaga Husnah ta shigo da fara'ar ta ba tare da tunanin komai ba kawai ta fa'da jikin sa ta rungume shi. Ko da nazo nayi mamaki da naga mota daga waje amma ban wani damu ba nayi shigewa ta ciki da tunanin 'kila abokansa ne suka zo, duk da nasan ba amsa sallama yake ba amma hakan bai hanani yi ba har sau biyu, sai dai jin ba'a amsa ya sa kawai na cusa kaina cikin parlourn na shiga. Cak na tsaya daga ba'kin 'kofar ban ko 'karasa sakin labilen dake hannu na ba sakamakon karo da nayi da mugun gani. Yah Deen da wata mace kan doguwar kujera yana lalumar jikin ta. Duk basu lura da shigowa ta, 'dan hasken da ya bayyana sakamakon rashin sake labilen da banyi ba ne ya fargar da su inda a tare suka waigo suka dube ni. Yana gani na sai yayi saurin sakin ta ya dai-dai ta natsuwar sa gami da mi'kewa tsaye, kicin-kicin yayi da fuska sannan yana duba na yace a masifance yace"..Baki iya sallama ba ne ke?" Ya tambaye ni cikin dakiya yana tunkaro inda nake. Kaina 'kasa nace " ai nayi ba'a amsa ba..." "...Shiyasa bazamu ta6a yin shiri da ke ba har abada da shegen sanyin tsiya, da kin yi da 'karfi ai da zanji ki". Kaina na kara sau'karwa ina fa'din " Allah nayi sallama baku ji ba bane". Tsaki yaja ni kuwa abin hannu na nayi saurin ajiye sai na fara matsawa baya da niyyar tafiya kafin yace zai ta6a lafiya ta. Yah Deen sai ya daka min tsawa...cak na tsaya na fara rawar jiki. Sai da ya iso gaba na ya tsaya sannan ya 'dan rage sautin muryar sa yace " Saura inji a wani wuri kinsan hali na ai, da wu'ka zan yanka ki". Ni kam ma ina ruwa na, har cikin raina ni banga abin bada labari anan ba....sai dai sosai abin ya tsaye min araina na kasa mantawa da shi...wannan karan kashedin sa bai wani tsorata ni ba saboda nasan ba ma fa'dan zanyi ba balle har ta kai shi ga yanka ni. Haka na juya na koma gida amma duk kotsi na abin na raina, sosai kuwa nayi jarumtar 6oyewa Ammi halin da nake ciki koda ta tambaye ni abinda ya min ma da 'karfin gwiwa ta nace mata ba abinda ya min yau kam. " Kar fa ki 6oye min..idan na bincika naji wani abu kinsan harda ke zan zane ko?" " Allah Ammi ba komai". Na bata amsa da 'kwarin gwiwa ta. 'Bangaren sa kuwa tun fita ta ya kasa ta6uka komai, gaba 'daya 'kunci ya cika zuciyar sa ya cunkushe, duk wani yanayin jinda'din da yake jin sa mintina 'kalilan da suka gaba ta dun sun dakushe, zaune kawai yayi kan 1seater ya sar'ke hannun sa cikin juna ransa a matu'kar 6ace..damuwar sa ni...what if naje na sanar da Ammi abinda naga yana aikatawa. Husnah kam bata damu ba duk da tayi zaton sister din sa ce ni, amma duk da hakan ganin nawa bai sa taji ta ha'kura da abinda ya kawo ta ba, sai dai duk yadda taso Yah Deen ya kwantar da hankalin sa su farantawa juna abin ya faskara, daga 'karshe ma da masifa suka rabu ya kora ta. Hankalin sa yazo ya 'dan kwanta ne ganin har anyi kwanaki uku bai ga wani canji daga iyayen sa ba, wanda hakan ne yasa shi fahimtar ban sanar da su ba, tun daga lokacin ya sami natsuwa sai dai bai gushe ba a kullum yana sake Addu'ar Allah ya mantar da ni yasa kar na sake tunawa balle har inyi gigin bada labari. Ni kuwa 6angare na ko 'kaunar sake jin muryar sa bana yi yanzu balle ganin sa...haka har ranar komawar sa tayi tun ganin sa da nayi da Husnah har zuwa ranar tafiyar tasa ban 'kara sashi cikin idanu na ba...ko ranar ma ina school ya tafi bamu ha'du dashi ba. Tafiyar sa kuwa yafi komai yi min da'di a rayuwa ta, daga ranar da na san ya tafi shikenan na saki jiki na amma a kullum abinda na gani 'din nan baya barin kaina na kasa cire shi araina sam. Bayan tafiyar tasa ne Imrana ya je gurin Mahaifin Ma'u da gaske wai shi son ta yake yi kuma da aure, amma mahaifin Ma'u sai yace da shi ya riga yayi mata miji tuntuni dan haka yayi ha'kuri, duk da lokacin babu wanda aka bawa auren Ma'u, amma dole a shekarun san nan badan yaso ba dan dole ya zame masa ya shirga 'karya, badan komai ba sai dan kawai ya tseratar da mutuncin 'yar sa ga fa'dawa lalataccen hannu...cuz yasan fa'dar hakan kawai shine katangar da zai iya ginawa tsakanin Imrana da Ma'u. Ashe Imrana yaji haushin wannan maganar sosai, dan haka cikin ransa ya ku'duri aniyar 6atawa mahaifin Ma'u rai fiye da yanda yayi masa akan Ma'u, kafin yazo ai sai da ya bincika ya tabbatar ba wani a'kasa da zai kawo kasa tsaiko, ko Deeni da tace tana so bai damu bane dan yasan Deeni ba zai so irin ta ba dan shi 'dan gayu ne na 'karshe...amma bakomai " Zanyi maganin ka 'dan tsoho". 'Karshen abinda Imrana ya 'kudurta cikin ransa kenan kafin ya bar wurin mahaifin Ma'u. Da wannan damar Imrana yayi amfani tun kafin Yah Deen ya dawo ya dinga shigar masa da Ma'u, shi da kansa ya dinga bayyana masa irin soyayyar da take yi masa tare da yawaita siffanta masa ita ya ringa 'kawata masa halittar ta, tun Yah Deen baya damuwa har yazo ya fara ri'ke zancen ta cikin ransa, bawai dan yana son ta ba a'a kawai dan yawan zancen ta da Imrana ke yawaita yi masa. Allah sarki Mahaifin Ma'u kuwa ganin kamar ya warware matsalar Imrana ne ya sanya shi bayan wasu watanni kamar uku ya dawo da 'yar sa Ma'u gaban sa ya cigaba da kulawa da abin sa da fatan Allah ya bata miji nagari ya aurar da ita ya huta wa ransa. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 🤞🏻 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *40* Lokaci sun 'dan ja sosai, dan kusan watanni shida kenan da ganin da na yiwa Yah Deen da budurwar sa na farko, ko hutun can ma kuwa daya zo na 'kara ganin su, marasa kunya a 'kofar gida ganin dan unguwar babu mutane sosai ya sanya ko kunyar Allah basu jiba suke kissing juna ga dukkan alamu ta fito zata tafi ne. Ni kuwa yanzu har na saba da bi ta gidan da yake matu'kar yana gari idan zani gidan Ummah ta sai nabi ta can dan kawai inga ko wannan farar motar tazo...bansan me yasa na damu da zuwan motar ba duk kuwa da cewa idan na ganin na kanji haushi sosai har cikin raina, sau tari kuwa ina ganin motar, sai dai bansan me suke aikata wa ba a cikin gidan tunda ba gani nayi da idanu na ba amma koma de miye ina da tabbacin ba abin alkhairi bane. Ko Ammi ma yanzu kwata-kwata ta daina aika na wurin sa, idan yana son abu sai dai shi da kansa yazo ko kuma ya aiko yaro amma Ammi bata tura ni sam...musamman ma da ta fahimci irin tsoron sa da nake yi sosai. ***** Yau 'din ma kuwa gidan Ummah ta zani gaida Addah ta Maryam da tazo tun jiya, ni ka 'dai nake tafiya ta cikin hankali kaina 'kasa, sai dai maimakon in 'dauki hanyar gidan Ummah direct a a sai na yanka na kama hanyar da zata sada ni da gidan Yah Deen. Tun daga nesa na fara hango motar take sai naji wani iri cikin raina, sai dai duk da naga motar ban dakatar da tafiyar da nake yi ba inda nake sake tunkarar gidan ban kuma san me ke ingiza ni ba kawai dai nasan bai wuci tsabar gulma ba, cak na tsaya ganin ta fito ita ka'dai ta shiga motar ta taja tayi gaba har ta 'karasa wucewa ban ga ya fito ba ga dukkan alamu dai ranar bai yi mata rakiya ba. Juyawa nayi da sauri na kama hanya 'kafafu na har na sar'kewa saboda yanda jiki na ke rawa da ganin Husnan. Husnah kam yanzu hat ta saba da zuwa wajen sa ma ko ganin wahalar hakan batayi balle rashin dacewar sa, ko da shi bai 'kira ta saboda bu'katar sa ba ita da kanta ma bata iya sati batare da ta zo inda yake ba hakan yasa jama'ah da dama suka farga da zirga-zirgan da take yawan yi a garin musamnan da kowa ua san cewa gidan da take zuwa 'din gidan 'dan Alhaji Baba ne kuma shi ka'dai ke zama a gidan. Sannan zuwan Husnah yana farawa ne da zarar ya dawo hutu gida, idan akace baya nan kuwa ba'a ta6a ganin ta tazo, wannan dalilin ya sanya jama'ah zargin wannan ala'kar tasu tare da dasa tunani a zu'katan jama'ah. Haka na isa gida wata iri da ni sam na rasa walwala ta, su'kuku na yini ranar gaba 'daya, abin na ci na arai amma ban iya na sanar da kowa ba...koda su Addah ta suka tisani gaba da tambayar abinda ke damu na sai cewa nayi kaina ke ciwo, ai kuwa take aka nemo min magani na sha dan dole ba dan raina ya so ba. Ana saura sati biyu zai koma school ranar da sassafe Alhaji Baba ya 'kira shi a waya inda yace yazo ya same shi.... Yanayin da yaji muryar Alhaji Baba yayi maganar ya sanya bai 6ata lokaci ba ya iso gidan dan cika umarnin Alhajin. Bayan sun gaisa cikin sakin fuska sai Alhaji Baba ya tambaye shi cewa " Abinda yaji gaskiya ne ko kuwa, ance wata yarinya na yawan zuwa wancen gidan da kake, wacece ita?" Numfashi Alhaji Baba ya sau'ke tare da cigaba da fa'din " Ni da kaina naga tana shiga gidan rannan ko ba ita bace ke zuwa da farar mota?" Ya 'karashe maganar yana kallon fuskar Yah Deen domin karantar yanayin sa. Yah Deen kam zuciyar da 'karfi ta tsinke saboda ka'duwa, cike da firgici ya 'daga idanu ya kalli Alhaji sai kuma ya sake sunkuyar da kansa 'kasa nan take, baya fatan ace Alhaji Baba da kansa ya gansa da Husnah da idanun sa, in hakan ne kuwa ya shiga uku da tarin abin kunya ai. Hakan da yayi ka'dai sai ya tabbatar wa Alhaji Baba cewa ba zargi ake wa Mu'een ba komai da yaji gaskiya ne....duk da fahimtar hakan da yayi amma sai ya 'kara tambayar sa saboda tabbatar wa duk da ya san da wuya ne Yah Deen 'din ya iya bu'dan baki ya sanar da shi gaskiyar lamari amma ua zama dole ya bincika saboda gano wace iriyar rayuwa yake yi da har mutane ke masa habaicin wai _ko 'dan Alhaji yayi aure ne bamu sani mun sanya albarka ba_ . Cikin dakiya Yah Deen ya bu'di baki batare da ya iya kallon Alhaji Baba ba yace " Ni...Alhaji...Babu kowa da ke zuwa wuri na". Wanda ya fa'di hakan ne bayan Alhaji Baba ya maimaita tambayar da yayi masa da farko. Murmushin takaici Alhaji Baba yayi...yayin da Yah Deen ya ayyana irin yanda zai ci ubana a cikin ransa, tunanin sa gaba 'daya kaina ya tafi dan shi a tunanin sa ni ka'dai nasan ala'kar sa da Husnah sai kuma Imrana, shi kuwa ya san ba zai ta6a zuwa ya sanar da Alhaji wannan zancen ba. Cikin natsuwa Alhaji Baba yayi masa fa'da ta yadda zai gane abinda yake yi 'din ba dai-dai yake aikatawa ba....inda ya 'karasa da fa'din idan aure yake son yi shi bashi da matsala zai iya yi masa jagora a kowani lokaci ko yau ko gobe sati ko wata a shirye yake kuma zai 'dau nauyin fahimtar da Uncle Ja'afar ma ba abin damuwa bane...Yace ya sanar da shi ko 'yar gidan waye shi zai je ya nema masa auren ta yafi akan a zarge ka da abinda bashi bane ko da baka aikata ba da ciwo balle ma babu mai yadda da kai tunda yarinyar ba muharramar ka bace ita. Kansa 'kasa yace " Babu komai tsakani na da ita Alhaji ba wani batun aure.." " Toh me yasa take zuwa gurin ka?" "...Course mate 'dina ce..abu take zuwa kar6a". Baya Alhaji Baba ya koma ya jinginu...sam baya son 'dan sa ya fa'da irin wannan rayuwar da jama'ah ke zargin sa da shi ko a mafarki baya son ace shike aikatawa. Amma saboda baya son ya ja maganar sosai dan ransa 'kara yaci yake yi...ya sanya shi ta'kaita batun da fa'din " Naji...amma Muhammad ka sani.. matu'kar ka kuskura na 'kara ji ko ganin abu makamancin hakan ya faru wallahi duk matakin dana ga dama shi zan 'dauka akan ka sam bazan lamunci rashin 'da'a ba, kana jina ko?" Da " Erh " ya amsa yana mai jin da'din rashin tsananta bincike da Alhaji bai yi ba. Yana cikin tunanin hakan yaji Alhaji Baba na fa'din " Tashi ka bani wuri...Allah ubangiji ya shirye ka bisa tafarkin tsira". Da 'dan hanzari ya bar gaban Alhaji Baba ya nufi wurin Ammi... Yana shiga parlourn ni kuma sai gani na fito cikin shirin zuwa makaranta ina 'ko'karin dai-dai ta zaman jaka ta ya shigo hankalin Ammi ma duk na kaina. Muna ha'da ido da shi sai ya wani banka min harara cike da 6acin rai, take sai nayi 'kasa da idanu na bansan me na aikata ba kuma yau 'din da aka tare ni da mugun kallo. 'Karaso wa yayi ya zauna a kujera dake facing Ammi...sai lokacin kuma Ammi ma ta ganshi...kafin tayi magana sai nace da ita " Ammi na tafi". " Adawo lafiya mama na" Ta bani amsa amma hankalin ta na kansa. Sum-sum nayi ficewa ta da yake tun lokacin da ya shigo gidan mun ha'du kuma na gaishe shi a lokacin kuma banga yayi min mugun hali ba, Ammi ce dai basu ha'du ba kawai ya shiga wurin Alhaji. Ita kam ma sam bata san da cewa yana gidan tun 'dazu ba, bata kuma san da wannan batun ba haka bata san me suka tattauna da Alhaji Baba ba ta dai gansa wani iri sai faman kau da kai yake kamar munafuki, yana gaida ta ko abinci bai tsaya ya ci ba kawai yace da ita ya tafi. Ammi da idanu ta raka shi har ya 'karasa fita, bata damu ba cuz ta sha ba'kin halin nasa ne yau ya motsa. Ko da ya koma gida bai iya ya sanar da Husnah cewa kar ta sake zuwa ba kamar yadda aka garga'de shi, ita kuwa yanzu sosai ta jarabtu da shi dan yana yi mata natan, ta kan yawaita shirga wa mahaifiyar ta 'karya n zata guri kaza idan ta fito sai ta nufo wurin Mu'een, sau da dama ma baya sanin zata zo sai dai kawai kwatsam ya ganta ba kuma yace mata me yasa kawai sai su shiga sha'anin su. Shai'danin bai ta6a complaint akan hakan ba da yake shima 'din baya wuce tayi musamman idan akan Husnah ne. Haka ranar ya wuni wani iri da shi..bai fita ko'ina ba ko neman abinci bai je yayi ba, Imrana ne ya nemo musu 'dan abin tabawa dangin drinks shima 'din ba wani na kirki ya sha ba ya bari, ko da Husna ta 'kira shi a waya kuwa sama-sama ya amsa ta, wanda jn sa wani iri ya sanya ta tambayar ko lafiya ...baka jin da'di ne? sai yace mata "Erh" A takaice. Take ta rikice ta fara yi mai sannu a jere...bai amsa ko 'daya ba kawai ya yanke 'kiran yama kashe wayar tasa gaba 'daya. Duk yadda Husnah ta so jin sa amma bata same shi ba...hankalin ta ya ta shi sosai gashi bata da number kowa a garin nasu balle ta 'kira taji..hakan sai ya hana ta natsuwa ji take tamkar tayi tsutsuwa taje ta ganshi taga halin da yake ciki. A daddafe ta 'karasa yinin ranar duk ba'a nutse ba, wani irin so take yi masa mai wuyan fassaruwa. Shima 'bangaren sa sai da yamma ne kafin suka fita filin ball shi da Imrana dalilin kenan da ya sa shi 'dan warwarewa...har dare kuwa bai kunna wayar tasa ba cuz haushin kowa ma shi yanzu yake ji, ko gida bai koma ba dan baya son ya ganni kuma babu damar hukunta ni a gaban Ammi domin for sure ya san akaina sai ta 6ata da shi, shi kuwa akan wannan munafurcin da yake tunanin ni nayi masa bai ga mai zai sa ya bar ni na sha haka nan ba. Banda tsantsar kunyar Alhaji Baba da ta cika shi, kunyar sake ha'da ido yake yi da shi, dan yana ganin tamkar yana kallon sa matsayin mai kawo mace gidan sa hakan yasa ko hanyar gidan bai iya ya kama ba har washe gari. Bai sani ba ashe Alhaji Baba kusan mutane hu'du ne suka ta kai masa gulman abin...da farko baya sa zancen aka. Dan tunanin sa Muhamad 'din sa ba zai aika ta hakan ba, amma daga baya sai abin ya dame shi yasan idan har ba dagaske bane ba yadda za'ayi ma banbamtan mutane su ta kawo masa magana iri 'daya....shiyasa ya saka ido da kansa a hankali kuwa sai Allah ya nuna masa zuwan yarinyar har tayi parking ta shiga gidan. Ransa ya 6aci sosai da ganin hakan, yasan babu mamaki mutane zasu masa kallon mutumin banza ne da har zai bar 'dansa ya ke6e yana rayuwa shi ka'dai yana kuma aikata abinda ransa yake so wanda za'a iya 'kira da banzar rayuwa duk kuwa da cewa babu wanda yasan abinda ke kawo yarinyar gidan. Yayi niyyan tsawatar wa Yah Deen game da zuwan yarinyar ne bawai dan yana zargin sa da aikata sa6on Allah ba illah dan kawai ya tunadar da shi anfanin kare mutunci da kuma nesan ta kai da abin Allah wadai...shi yasa ko da ya nuna shi ba komai bane ke faruwa Alhajin yayi saurin yadda da shi. *Nasan wasu zasu ce me yasa fa'dan sa ya tsaya iya can....ba cin azahiri abinda Mu'een ya aikata abin a tsawatar masa ne sosai....toh fa nima ina son sanin dalili sai dai nasan duk bazai wuci tsananin yadda da yayi da shi ba* . Washe gari Husnah bata samu daman fita ba dan mahaifiyar ta ta tashi da zazza6i hakan yasa ta tsaya kulawa da ita gashi ko asbiti ma basu samu ganin likita da wuri ba, damuwar ta biyu ta zama amma dole ta danne 'dayan saboda SAWUN GIWA YA TAKE NA RA'KUMI. ***** *Bayan kwana biyu* Tun 'karfe tara na safe Husnah tayi parking 'kofar gidan Yah Deen...yana bayi lokacin yana 'ko'karin hanzartawa ya shirya dan zuwa gaida mahaifan sa cuz ba zai iya 'daukan tsawon lokaci batare da yaje gare su ba ko ma dan ya proving innocence 'din sa ya shi yanke shawarar shiryawa yaje...duk da ya san for now Alhaji Baba ya jima a gidan gona shiyasa ya 'kudira cikin ransa cewa yau 'din har gidan gonar zaije ya bashi ha'kuri ya kuma taya shi ayyuka inda hali ma acan zai taya shi yini bazai dawo da wuri ba har alokacin kuma bai kunna wayar sa ba. Husnah na shiga ta cire mayafin ta...ta ajiye shi anan parlour da 'yar pulse 'din ta ta tinkari cikin bedroom 'din nasa. Tana zuwa nan ma sai taga wayam baya nan hankalin ta ya so ya 'kara tashi sai dai sakamakon 'karan ruwa da taji a bayi ya sanya ta saki ajiyan zuciya. Da baya ta kwanta a kan gadon dake 'dakin tana jiran fitowar sa. mintina biyar mai kyau basu cika ba kuwa sai gashi ya fito 'kugun sa 'daure da towel fari. Yanda ta ganshin sai ta ji wani sanyi cikin ranta ya ratsa ta...zaune ta mi'ke tana sake 'kare masa kallo tana murmushi. Shi kam turus yayi da ganin ta sam bai ji da'din ganin ta ba a wancan lokacin, sai ma haushi da ya kara ji akan wanda ke 'kunshe cikin ransa. Wani mugun kallo ya bita da shi ya ka'da kai yayi gaba tare da 'kara murtu'ke fuskar sa...haka ya nufi inda yake ajiye 'kananun towels 'dinsa ya zari 'daya ya fara tsane jikin sa da shi...bai ko sake kallon inda take ba. Bai zata ba kawai yaji hannun ta kan hannun sa tana 'ko'karin kar6an 'karamin towel 'din daga bayan sa, a fusace ya juyo ya hanka'da ta baya ta tafi taga-taga kamar zata fa'di sai Allah ya taimake ta drawern mirror ya tare ta. Da mamaki ta 'daga kai take duban sa, saman la66a ta furta sunan sa " Mu'een"! Tana 'kan'kance idanu alamun mamaki 'karara ya bayyana kan fuskar ta. Yatsa ya nuna ta da shi a fusace yace "..don't ever call my name again....and kiyi tafiyar ki, wa ma yace miki kizo...na 'kira ki nace kizo ne?" Tsayuwan ta ta gyara cikin marairaita tace " Haba dan Allah Mu'een yau na fara zuwa ne da zaka fa'di hakan?..idan wani abin nayi maka ai sai ka sanar dani in gyara ba wai ka yi treating 'dina ba?" .....Ido ya lumshe ya kuma bu'dewa cike da takaici ya kalle ta, 'karamin towel 'din ya rataya bisa wuyan sa ya tako gaban ta ya tsaya idanun sa cikin nata yace" Kin san wani abu?" Husnah bata iya tace da shi komai ba sai ido da ta zuba masa sosai yake bata mamaki. Bai damu da rashin amsawar ta ba shima kawai ya cigaba da fa'din "...Bani bu'katar sake ganin kin kusanci inda nake Husnah". 'Dago 'kafa tayi da niyyar 'karasowa kusa da shi sosai take sai ya 'daga mata hannu sannan ya girgiza mata kai tare da matsawa baya ka'dan a hankali ya cigaba da fa'din " Kin san abinda zuwan ki garin nan ya haifar min?....kinsan yanda hakan ya ta6a mutunci na Husnah, mahaifina fa da kansa yayi min maganar...kin san nauyin da naji ya kamani a lokacin?" Kansa ya shafa da hannun sa 'daya tare da furzo iska daga bakin sa sannan ya cigaba da fa'din "....ki kama hanya ki koma inda kika fito and please kar ki kuskura ki sake zuwa gidan nan in ba ni da kaina na na neme ki ba...oyah..." Ya nuna mata hanyar fita tare da 'kara matsawa baya. Husnah kam maimakon ta fice a a sai ma ta taho da gudu ta shiga jikin sa ta rungume shi tana sakin kuka cikin salon yaudara....duk yadda ya so ya raba ta da jikin sa ya kasa, dole haka ya 'kyale ta...cikin kukan take fa'din Yayi ha'kuri kar yayi mata haka dan Allah....idan yayi mata katanga da kansa bata san halin da zata shiga ba..." Da kakkausar murya yace " Ohh ke kanki kawai kika sani baki san zancen mutunci ba ko....dallah sake ni 'katuwar banza 'katuwar wofi". Wannan karan da 'karfi ya hanka'da ta sannan ya kamo hannun ta yaja ta zuwa parlour ya tura ta ciki ya koma abin sa ya datse 'kofan ta ciki. Husnah haushi da ba'kin ciki sosai ya kamata dan haka a fusace ta zari mayafin ta da pause ko rufa mayafin bata yi ba kawai ta fita da 'dan gudu-gudu tana kuka. Bata tsaya ta lura da mutumin da ke tsaye jikin mota daga gefe ka'dan da ita ba kawai ta shiga ta tada motar ta fizga da gudu tayi gaba bayan ta ha'da uban 'kura a wajen. Zuciyar sa tamkar zata faso saboda takaicin halin da mafi soyuwa acikin zuciyar sa yake aikatawa, in bama shi ba ina shi ina wannan matar, ai da gani ba sa'ar rayuwar sa ba ce in ba biyewa zuciya ba. Ya kai tsawon mintina uku bayan tafiyar tata kafin Alhaji ya shiga motar sa bai koma gidan gona ba sai ya wuce gida zuciyar sa na ta azalzalar sa dan 6acin rai. Parlour yaje ya zauna shiru Ammi na ciki bata san da zuwan sa ba....ya kai mintina talatin da zuwa gidan sannan Ammi ta fito ta ganshi...da mamaki ta iso inda yake tana tambayar sa " Alhaji Lafiya kuwa?". " Ba komai " ya bata amsa a ta'kaice. Ammi kam jan bakin ta tayi tai shiru cuz ta san tunda yace bakomai ga dukkan alamu ba hurumin sa ba ne. Ruwa taje ta kawo masa ta ajiye gefen sa sannan ta zauna, tana shirin zata sake magana yayi saurin 'daga mata hannu. Tsaye ya mi'ke yana safa da marwa cikin parlourn ransa ya kai 'kololuwa wurin 6aci...bai san me ze ce game da wannan lamari ba. Yana cikin hakan Yah Deen yayi sallama, Ammi ce ka'dai ta amsa shi. Shi kansa sai da yaji wani iri ganin Ammi ta buga tagumi ga kuma Alhaji tsaye cikin yanayi na damuwa....tunanin sa ko tun fa'dan shekaran jiyan ne bai 'kare ba hakan sai ya sashi tsarguwa. A 'darare ya 'karaso gaban Alhajin yana niyyan durkusawa dan gaida shi sai kawai yaji sau'kan mari saman kuncin sa....daga Alhaji Baba. Cikin ka'duwa ya dafe fuskar sa yana kallon Alhajin da cikin idanun sa ka'dai zaka kalla kasan cewa yana cikin yanayi na tsananin 6acin rai, yanayi ne da ya jima bai shige shi ba. "....Waye ubanta?..Muhammad ka gaya min 'yar waye?" Cikin rashin fahimta ya 'dago idanun sa da suka koma jaja ya zubawa Alhajin da alamar tambaya sannan ya juya ya kalli Ammi ma da ta mi'ke tsaye tun sanda Alhaji ya mare sa. "...Irin rayuwar da kaga ta dace ka za6ar wa kanka kenan ko Muhammad?...mutunci na kake son zubar min agarin nan shiyasa ka nuna min ban isa da kaiba, inace da kaina na garga'de ka akan ban son in 'kara ji ko ganin tazo ko ba ji da kai muka yi maganar ba?" Hawaye ya fara yayin da ya sunkuyar da kansa 'kasa gwanin tausayi, yayin da Alhajin ya cigaba da fa'din...." Nawa ma kwata-kwata kake da har zaka lalata rayuwar ka da biyewa matan banza..ko dan kaga na barka kayi rayuwa dai-dai da mura'din ranka shiyasa kake ganin yes kana da 'yan cin kanka yanzu?....laifi ne Muhammad dan nayi maka abinda ranka kake so?, ko laifi ne dan na barka ka zauna a gida kai ka'dai kamar yadda ka bu'kata...wato gani mutumin banza shine ka shirga min 'karyar abu take zuwa amsa to ko kaina malamin dake karantar da ita ai iyaka kenan..." 'Kasa ya zube yana kuka yake fa'din " Alhaji dan Allah kayi ha'kuri ka yafe min...wallahi ba nufi na kenan ba..." " Shut-up da Allah munfukin banza...hala ka manta ni ne na haife ka...ni zaka yaudara da kalaman ka Mu'een...?" Ammi ce tayi saurin isowa gaban sa tana tambayar" wai me ke faruwa ne Alhaji?. Bai amsa ta ba sai ya koma kan kujera ya zauna Ammi sai ta bishi da idanu..ita kam mamaki duk yabi ya cika ta, a bai-bai take fahimtar maganar ta su. Ajiyan zuciya Alhaji ya sau'ke bayan ya zauna 'din. Kallon Yah Deen ya sake yi da har yanzu yake tsiyayar da hawaye, wannan karan cikin natsuwa ya ce dashi " Waye mahaifin ta kuma a ina yake ka sanar da ni?" Baya so ya sake wasa da hankalin Alhajin dan haka sai yace " Mahaifin ta ya rasu". Ammi kam kallon ta take ta rarrabawa tsakanin su sun 'daure mata kai gaba 'daya. Alhaji kam cewa ya sake yi " Sunan sa na tambaya". Kansa 'kasa ya amsa da " Alhaji Hamza Ar'kilah". Alhaji na jin haka ya tashi tsaye tare da 'daukan hular sa ya yi waje...Ammi kam da idanu ta raka shi har ya 'karasa barin parlourn sannan ta samu damar zama bisa kujera itama cikin tashin hankali. Yah Deen tasowa yayi ya tsugunna gaban ta tare da kwantar da kansa bisa cinyar ta yaci gaba da kuka kamar wani 'karamin yaro. Bata iya tace da shi komai ba har sai da ta dai-dai ta natsuwar ta kafin ta 'dau hannu ta 'dora bisa kan nasa dake jikin ta..." wai me yake faruwa ne Muhammad kaina ya kulle na kasa fahimtar komai...me maganganun Alhaji suke nufi?" 'Dago kansa yayi da raunin murya yace " Ammi dan Allah ki bawa Alhaji ha'kuri, Allah ba laifi na bane...ita ce take zuwa wuri na, sau tari na kan mata magana amma bata ji haka duk lokacin da ta ga dama zata 'dauki hanya tazo batare da ta sanar dani ba sai dai in ganta....to ya zan yi Ammi?... kuma babu komai tsakani na da ita kawai fa makarantar mu ce 'daya....shi kuma Alhaji yana zargin wata ala'ka ce daban a tsakani na da ita". Hannun Ammi yayi saurin kamowa yace" Ammi please ki bawa Alhaji ha'kuri ya fahimce ni, abinda yake zargin bashi bane...kuma nayi al'kawarin daga yau insha Allahu bazata sake zuwa ba". Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 🤞🏻 ~MASOYA NA INA GODIYA SOSAI~ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *41* Ammi 'dayan hannun ta ta 'dago ta shafa sumar dake kwance a kansa, cikin sanyin murya da kulawa tace da shi" ka kwantar da hankalin ka in dai ka tabbatar iya abin kenan kar ka damu, babu abinda zai faru, shima Alhajin ransa ne ya 6aci shiyasa amma zan masa magana insha Allahu zai sau'ko". Kai ya jinjina mata alamar gamsuwa da maganar ta sannan a hankali Ammi ta kamo hannun sa ta mi'kar da shi tsaye, idanun sa jajazur kamar wanda ya yinin kuka. Ammi ce tace da shi" je ka huta maza ka daina 'daga hankalin ka". Bai 'kara furta komai ba kawai ya kama hanyar fita daga parlourn yayin da Ammi tayi zugum tana tunanin ma'kasudin zancen, ita a ganin ta ai laifin duk na yarinyar ne tunda ita ke zuwa wajen sa ba shi ke binta ba, toh me yasa laifin zai zama nasa shi ka'dai kuma? Cikin ranta ta gama kudurta cewa zata fahimtar da Alhajin gaskiyar lamari kamar yadda Yah Deen ya bayyana mata, kar yaje yayi fushi da 'dansa a banza bacin ba shi ke da laifin ba...( a ganin Ammi kenan). *****       Bangaren Alhaji Baba ba kuwa da fitar sa bai zame ko'ina ba sai gidan gona, ransa a matukar 6ace yake, duk komai ya jagule amma haka ya danne kawai ya shiga tunanin mafitar da ta dace da matakin da ya kamata ya 'dauka tun kafin abin yazo yafi 'karfin sa. Har cikin ransa baya zargin Mu'een da aikata mummunan aiki makamancin alfasha, amma bai san meyasa ba sam zuciyar sa ta kasa amincewa da abinda Mu'een ya sanar dashi, ya kasa amincewa da ala'kar sa da wannan yarinyar, dole yasan akwai wani sirri a 6oye dake tsakanin su wanda bakowane ya sani ba, rashin cikakkiyar shaidar zahiri ne ya sanya  shi ya yadda ba komai 'din kamar yadda Ma'een ya fa'di, sai dai hakan bashi zai hana shi cigaba da bincike akansu ba, matsayin sa na baligi kuma cikakken namiji baya so ace ya saba da ke6ancewa da mata tun yanzu, koma dan gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, ita Zina kusantar ta ma Allah ya hane mu da yi balle aikata ta gaba 'daya, sannan matu'kar kana so imanin ka ya cika dole ne sai ka gujewa alfasha tun kafin faruwar ta ba, ba wai sai ya faru kazo kana dana sani ba bacin idan an aikata ba'a iya goge shi sam shiyasa gara ya yiwa tukfar hanci ya kare daraja da mutuncin ahalin sa tun lokaci bai 'kure mai ba. Tunanin hakan ne yasa shi yanke shawarar nemawa Mu'een auren ta, cuz in dai har zata iya barin garin da iyayen ta suke matsayin ta na 'ya mace ta taho gurin sa to dole akwai wani 6oyayyen abin...hujjar haka kawai ya ri'ke, kuma ta gamsar da shi, babu mamaki cikin su zuciyar 'daya na son wani ko kuma ma duk ya kasance suna son junan su Yah Deen kawai ke 6oye masa da fa'din course mate 'din sa ce ita. Bai sake bi ta takan Yah Deen ba, kuma ko da Ammi ta fara mai magana ma bai wani jira ya gama sauraren ta ba kawai ya dakatar da ita da fa'din...." Ta yi addu'ahn tabbatuwan Alkhairi kawai, idan ya gama shirya abinda zaiyi insha Allahu zai sanar da ita komai". Abinda yace da ita kenan wanda hakan yasa dolen Ammi taja baki tayi shiru amma abin na nan cikin ranta...da ta tuno yanda Mu'een ya bar gidan kuwa sai ta sake shiga tashin hankali, hakan ne ya sanya ta saurin sake fuskantar Alhajin kana tace " Amma Alhaji please kar kayi fushi da shi,  kasan fushin iyaye ba alkhairi bane ga 'ya'ya, musamman ma shi Mu'inuddeen 'din karka ga yanda ya 'daga hankalin sa". Takaitaccen murmushin takaici Alhaji Baba yayi yana duba agogon dake 'daure a tsintsiyar hannun sa yace da ita " Ni banyi fushi da shi ba, garga'di ne kawai nayi masa saboda gaba". Ammi bata sake magana ba cikin ranta ta furta" Allah ya kyauta" daga haka bata 'kara fa'din komai ba. *****       Husnah ma wannan karan ranta ya 6aci sosai da abinda Tah Deen yayi mata hakan ya sanya ta shareshi, kwata-kwata bata neme shi ba, da kuma ta tuna kwanaki 'kalilan ne suka rage musu su koma school hakan sai ya sanyaya ranta, tasan koma menene da sun koma school za'a wuce wurin shikenan.     Wannan tunanin ne ya sanya ta sakin ranta ta cire damuwar dake zuciyar ta ta cigaba da rayuwa. Yayin da Yah Deen kuwa koda wani lokaci zuciyar sa cike take da tsoro da kuma fargabar irin matakin da Alhaji Baba zai 'dauka a kansa, zaton sa ma ko zai hana shi zama a gidan ne kwata-kwata ko kuma ya hana shi komawa school, amma ga mamakin sa ko ta kan sa Alhaji Baba bai sake bi ba...balle yace ya rufe gidan ya kai keys 'din gida. Shikuwa fargabar tunkarar sa yake yi a wannan halin, sannan har a lokacin ya'ki kunna wayar sa saboda kar Uncle 'din sa ya 'kira shi yaji yanayin da yake ciki yai masa titsiye, cuz ya san halin Uncle Ja'afar muddin ya san abinda yake aikata bazata yi masa da'di ba. Rashin jin komai daga aalhaji game da batun barin gidan ne ya sanya shi tunanin 'kila makaranta ce Alhaji zai hana shi zuwa kuma hakan ya barwa ransa. 'Bangaren Ammi kuwa da taga shiru bai le'ko su a gida ba har kwana uku sai hankalin ta ya fara tashi gashi bata samun wayar sa, and su Saif ba sannan balle tasa su dubo mata shi, babu kuma wani 'kwakkwaran aboki nasa 'daya da tasani agarin balle tai 'kiran sa ta tambaye shi abin sosai yai mata karan tsaye a ma'koshi. Ni ce ka'dai a gaban ta wadda take tunanin zata iya turawa can amma kuma ranta bai kwanta da hakan ba sam.      Ran cikar kwana na ukun ne ta 'kudira cikin ranta cewar koma menene zai faru ayau 'din nan sai ta ga 'danta da iznin Allah, ko ita da kanta zataje ta dubo ya yake tunda wayar sa ma har a lokacin bata tafiya. Ni da nake tare da Ammi mafi yawan lokuta nice zan iya bada labarin sauyin da ya same ta a wancan lokacin, ban ta6a sanin 'kaunar da take yiwa Yah Deen ya kai irin wannan matakin ba ai da lamarin nan ya faru, yanda ta shiga damuwa, yawan gwada layin sa, yawan sakin tsaki, yawaita yi min hirar cewa bata san a wani hali yake ciki ba hatta Addu'ah bata ware ba nima sai da ta sani yin addu'a  akan in ringa tayata adda'ar "Allah ya dai-dai ta tsakanin Yah Deen da mahaifin sa" Ina kuma yi cikin ko wacce sallah ta, hatta Alhaji Baba bai kaini fahimtar 'kololuwar damuwar da Ammi take ciki ba cuz shi idan ta fara complaint baya bari ta 'karasa zai tare ta da fa'din " Karta damu lafiyar sa 'kalau kawai ta barshi ai ya girma ya san abinda ya dace ya aikata ba sai an tuna masa ba". Ya kan yi mata maganar ne ta sigar gatse amma bata fahimtar inda ya dosa. Cike da damuwa zata sake fa'din " Ko abinci fa  bai zuwa yaci". Alhaji Baba murmushi kawai yake yi yace mata " Rabu da shi zaizo". Yayin da ni kuma nake zama in nutsu in saurari damuwar ta kaf, tun bansan asalin me ya faru har yasa shi 'kauracewa zuwa gidan ba har nazo na fara fahimta a hankali cikin maganganun Ammi  cewa sa6ani suka samu da Alhaji Baba akan wai wata budurwa na zuwa gidan shi, ni kaina da naji zancen ban girgiza ba haka kuma ban 'karya zancen Alhaji ba, zan iya kasancewa shaida akan cewa dagaske tana zuwa 'din cuz da idanu na nasha ganin ta amma bazan iya kallon cikin idanun Ammi in sanar da ita cewa hakan gaskiya ne ba sam, banjin zan iya hakan har abada tsoro ma ba zai barni ba in furta ba dan haka kawai sai na bi Ammi da idanu. Yawan damuwar Ammi akan sa yasa ni fahimtar 6oyayyen sirrin 'kauna dake 'kunshe a zuciyar Ammi game da shi, ashe tun asali farin ciki ta yana wanzuwa ne da tabbacin 'danta Muhammad na nan cikin walwala, ban ta6a sanin haka ba sai a wancan lokacin da lamarin ya faru. Ni kaina ina so inga Ammi ta saki ranta ta dawo kamar da cikin sakin fuska da walwala, wanda hakan ya sanya ni niyyar zuwa can gidan dubo sa in kuma ce da shi Ammi na 'kiran sa, na shirya hakan cikin raina ne batare da na sanar da Ammi ba. 'Karfe 7:37 na safiya ina 'ko'karin fita daga parlour da tunanin ya zanje in tarar da shi, yanayin da na same shi da waccen yarinyar a wanacen ranar shine ya sake dawowa 'kwa'kwalwa ta, kenan idan tazo kullum abinda yake yi mata kenan, bana so in yawaita tuna yadda naga hannun sa na yawo saman 'kirjin ta dake bayyane a fili, bana so in tuna balle har in bada labari, amma na kasa mantawa, har yau 'din nan hoton yanda naga Yah Deen na shan boobs 'din Husnah ya kasa barin kaina, na kanji kaina wani iri aduk lokacin da tunanin hakan yazo raina....(Addu'ar Deeni bata samu shiga ba kenan tunda Noor bata manta abinda taga yana aikatawa ba). Ko yanzun ma da nake shirin fita ina 'dagawa Ammi hannu tunanin da ya fa'do raina kenan, tsoron yau kuma a wani hali zan tadda shi, ba dan Ammi ba da babu abinda zai kaini wannan gidan, amma soyayyar Ammi cikakkiya ce cikin zuciya ta saboda ita da da kuma son dawowar walwalar ta dole na bawa kaina 'kwarin gwiwar zuwa gidan. Addu'ah Ammi tai min kamar yadda ta saba idan zani makaranta" Allah ya tsare ya da sa'a autar Ammi". Haka take yimin kullum, sa6anin yau da kawai cewa tayi " Allah ya bada sa'a sai kin dawo". Abinda kawai na samu daga gareta kenan kuma ma cikin sanyin murya ta furta hakan babu wannan fara'ar nan balle ta iya yimin kirarin "......Autar Ammi" shiyasa naji cikin raina ko dan in samu cikakkiyar Addu'ar da take yawan yi min ma dole in tayata farautan Yah Deen yazo gare ta ta ganshi, wala Allah ko zata dawo dai-dai. A hankali nake rakawa na tunkari  mafitar parlour ina gyara zaman babbar jakar dake rataye akafa'da ta wacce take cike tab da tulin takaddu na rubutu da kima textbook wanda Alhaji Baba da kansa ya aika aka siyo min su bai bari na yi rashin koda al'kalamin rubutu ba ne tunda na fara karatu a gidan sa, shiga na Jss one kuwa sai komai ya 'karu, uniform ma kala uku aka 'dinka min, safa na kusan kala biyar, canvas, sandal, tombs da kito mai kyau da tsada duk an tanadar min sai wanda naga daman anfani dashi nake sawa. Sake gyara zaman jakar nayi karo na biyu dai-dai lokacin da na isa tsakiyar harabar gidan ina sake tunowa da Yah Deen, cikin raina nake ayyana " to meyasa zai yi purnishing Ammi akan laifin da ya san dagaske ya aikata ba sharri akayi masa ba?" Da wannan tunanin na isa bakin gate ina shirin sa hannu in bu'de 'kofan sai naga an riga ni turowa wanda hakan ya sani 'dan matsawa baya ka'dan domin bawa mai shigowar damar shiga. Lumshe idanu na nayi da jin yanda 'kamshin jikin sa ya buwayi hanci na take sai naji wata iriyar fargaba bansan ta menene ba, fuskar sa a hautsine ba ko alamun fara'a wanda a fizge na iya kallon yanayin fuskar ta shi take nayi 'kasa da idanu na ina fa'din " Ina kwana Yayah?" Ko kula ni bai yi ba illah wuce ni da yayi  kawai yayi shigewar sa cikin gida. Cikin raina na furta " Bazaka ta6a canzawa ba farin cikin Ammi". Baki na na ta6e musamnan da na tuna yanayin da naga fuskar sa, a hankali na ri'ke 'kofan hannu na ban fita ba haka kuma ban rufe 'kofar ba, bayan sa nake kallo yanda yake ajiye takun tafiyar sa" Salon ka daban ne 'dan Ammi" Na sake fa'di cikin raina, tafiyar Yah adeen ka'dai aji ne da ita, balle idan ransa a 6ace yakan 'karawa tafiyar sa wani salo na sanyi da natsuwa da shi kansa inajin bai san hakan na da matu'kar 'daukan hankali ba...sanye yake cikin riga ba'ka da godon wandon jeans shima ba'ki, suman kansa yasha gyara sai shai'ki yake yi musamman da hasken rana ya 'dan haske shi walwalin sa gwanin birgewa, 'kafar sa ma wata ba'kar takalmi ce mai tudu da igiyoyi da dama sosai ya amshi 'kafar sa, hannun sa babu komai sai Key holder na makullin gidan da yake zama sosai yaui kyau hasken sa ya kara bayyana cikin ba'kar dressing 'din nasa bakace yana tare da damuwar komai ba. " Hmm" Na saki ajiyar zuciyar tare da juyawa na sa 'kafa na fita daga gidan ina ayyana  " Allah yana sona sosai da bai barni naje wannan gidan ba ya ta'kaita min niyya ta". A hankali na tunkari hanyar makaranta cikin tafiya ta ta masu natsuwa. Ammi ka'dai ya tarar tsaye a palourn da yake yanzu ta gama sallama ta bata riga ta bar parlourn ba kuma dan yanzu Ammi komai cikin sanyin jiki take yin sa. Tsaye take amma da ganin sa ya shigo sai ta saki ajiyan zuciya fara'a ta bayyana kan fuskar ta, komawa tayi ta zauna tana sakin ajiyar numfashi, cikin ranta take godewa mahallici da ya ta'kaita mata niyyar ta ya kawo mata shi har gida.    Gefen ta ya 'karasa ya zauna kan kujera yana shafo sumar kansa da hannun sa na dama, yayin da Ammi ke binsa kawai da idanu ita ka'dai ta san me take ji cikin ranta game da shi. Sai da ya daidaita natsuwar sa kafin ya gaida ta ganin irin kallon da Ammi take binsa da shi da bai san na menene ba. A hankali da muryar masu hankali ya gaida ta yayin da Ammi ta amsa shi cikin sakin fuska da fara'ar ganin sa cikin 'koshin lafiya batare da ya illatu ta wani 6angare na jikin sa ba. Fuskar ta wasai bayan ta amsa gaisuwar tace da shi " Me yasa ka 'dauki tsawon kwanakin nan baka le'ko mu ba Mu'een? Ko fushi kake nufin zakayi da mahaifin ka dan ya gaya maka gaskiya?" 'Dago kansa yayi sosai ya kalli fuskar ta yana 'kan'kance idanu yace" Haba Ammi...ya zaki ce haka please? Ni waye da zanyi fushi da shi? ni da nake 'dan gata, har na samu mai gaya min gaskiya wani ma fa nema yake ya samu irin hakan amma bai samu ba...so dan me zan yi fushi da mahaifi na?" Yayi maganar cikin sanyin murya da natsuwa. Ammi ma cikin natsuwan tana duban fuskar sa tace " To me ya hana ka zuwa bacin kasan dole ne mu damu da rashin ganin ka da sanin halin da kake ciki?" " Kiyi ha'kuri Ammi,  amma ni kawai banson in 'kara 6ata ran Alhaji ne kar idan ya ganni ya sake harzu'ka shiyasa banzo ba". Murmushi Ammi tayi da ya ratsa mata har zuciya sannan tace " Amma baka kyauta min ba". " I'm so sorry Ammi na...kin san ai haka kawai bazan guji inda kuke ba". " Ka kwantar da hankalin ka Alhaji bai yi fushi da kai ba...ya dai ce kawai muyi fatan Alkhairi". Sakin numfashi yayi na jin da'di tare da fa'din " Alhamdulillah" A fili tare da komawa ya kishingi'da da jikin kujera. Ammi kuwa cigaba tayi da fa'din " Kwanaki uku kacal Mu'een amma ji bi ramar da kayi anya ma tun tafiyar ka ka 'kara cin abinci kuwa?" Shima murmushin yayi tare da fa'din " Haba Ammi na, da bana ci ai da ban kawo wannan lokacin ba..." " Banga alamaba ni". Ta tare shi da fa'din hakan. Sai yace " Hmm..Ammi agaban idanun ki fa Alhaji Baba ya sau'ke min yatsun hannun sa saman fuska ta alhali tunda nake da shi bai ta6a mari na ba tun haihuwa ta har sai yanzu da na girma na zama cikakken 'dan jami'ah mai shekaru ashirin har da biyar akai kinga kuwa dole in damu dan nasan abin ya ta6a ransa sosai". Ido Ammi ta lumshe cike da jin da'din yanda yake bayyana gudun 6acin ran mahaifin sa a zahiri. Fuskar ta cike da Annuree tace " ka kwantar da hankalin ka komai ya wuce har a wurin sa ma". " I wish..." Kai Ammi ta jinjina masa cike da tabbatarwa. " Ni dai fata na Alhaji kar ya zarge ni da mummunan abu, Ammi kema ai  kinsan bazan aikata irin waccen abin ba sam". Ya 'karasa maganar cikin marairaita ya wani yi kalar tausayi. Tausayn kuwa ya bawa Ammi dan ta kwantar mai da hankali sai tace " Na sani kuma na yadda da kai, Alhaji ma na fahimtar shi kuma ya gamsu ka daina damun kanka...amma ka kiyaye karka bari ya sake kama ka da laifi makamancin wannan cuz a lokacin ko ni da kaina Mu'een bazan 'daga maka 'kafa ba". " Insha Allahu ba abinda zai sake faruwa Ammi na". Murmushin jin da'di tayi masa sannan tace " Allah ya albarkaci rayuwar mai sunan Baba na". Yah Deen lumshe idanu na yayi yana jin wani sanyin da'di na ratsa shi har brain 'din sa, 'kaunar iyayen sa na sake ratsa shi zuciya da gangar jikin sa, baya fatan har abada ya kasance shine silan 6acin ransu.     Shiyasa ko da wasa baya so ace sunji ainahin irin rayuwar da yake aikatawa balle su san cewa first kyautan da Allah ya bashi na haihuwa ta hanyar alfasha ya same shi sannan da kansa da kuma ku'din sa ya sayo maganin da ya narkar da shi ya zubar da shi a rariya...." *Astaghfirullah ya Rabb* " Ya fa'di cikin zuciyar sa har launin idanun sa na sauyawa sakamakon tuno babban nawin zunubin dake kansa...zai iya aikata komai dan akan wannan sirrin cuz ya san bayyanar wannan maganar dai-dai yake da rugujewar farin cikin sa da na iyayen sa gaba 'daya...dan yasan baza su ta6a jin da'din faruwar hakan ba. " Auntyn ka ta 'kira ni jiya da dare tace bata samun layin ka, idan ka samu lokaci please ka ta6o ta dan naji ta damu da rashin jin kan da batayi ba". Ammi ce ta katse masa tunanin da yake yi da fa'din hakan. Yana gyara zaman sa yace da ita " Insha Allahu zan 'kira ta....Alhaji fa?" Ya 'karashe da tambayar ta mahaifin sa. Sai da ta juya ta kalli mashigar 6angaren Alhajin kafin tace " Yana ciki yau be fito da wuri ba kam..". Tsaye yayi saurin mi'kewa shima yana fa'din" Bari inje mu gaisa kafin ya riga ni fitowa". Itama Ammi tashi tayi tsayen tana murmushi tace da shi sai ka fito" Me zan tanadar maka?" " Karki wahalar da kanki Ammi yau azumi nake yi". Kai ta girgiza batare da ta 'kara fa'din komai ba ta shigewar ta kitchen. Da shigar sa sai ya samu Alhaji Baba na 'karasa shiryawa zaune a bakin gado...links 'din hannun rigar sa yake 'ko'karin sawa sai Yah Deen ya yi sallama daga bakin 'kofar. Alhaji 'dagowa yayi ya kalle shi tare da amsa sallamar da yayi, sai dai kallo 'daya kawai Alhaji Baba yayi masa take ya maida kansa ya cigaba da abinda yake yi. Da sauri Yah Deen ya 'karasa kusa dashi kan gwiwoyin sa ya dur'kusa 'kasa gaban Alhajin tare da kaiwan hannun sa ya kar6i links 'din Alhaji Baba ma bai hana shi ba ya sake mai batare da ya kalli idanun sa ba illah tunanin " yau kaga damar zuwa kenan" da yake yi cikin ransa, wanda shirun san yabawa Yah Deen damar 'daura masa links 'din duka biyu sannan ya koma ya zauna da6as kamar 'dan yaro yace" Alhaji Baba fatan an tashi lafiya". " Alhamdulillah" Alhaji ya bashi amsa a takaice. Daga haka yayi shiru bai iya sake furta komai ba...yana so yayi magana amma fargaba ta hana shi, tsoron yanda Alhaji Baba zai yanke hukunci akan makarantar sa yake yi, gashi dai fuskar Alhaji wasai take baka ce ga yanayin da yake ciki ba, amma kamala da kwarjinin sa sosai yayi tasiri a zuciyar Mu'een musamman da yake shi 'din babban mai laifi ne a gare shi. Alhaji Baba kuwa tsaye ya mi'ke ya 'dauki babbar rigar sa dake gefen sa yana warwarewa da niyyan sawa batare da ya sake bi ta takan Yah Deen ba. Ganin hakan ya sanya Yah Deen sake dai-dai ta nutsuwar sa bayan ya gama harha'da kalmar da zai fa'da cikin kwantar da murya da in ina yace " Alhaji 5days ya rage hutun mu ya 'kare gaba 'daya". " Abinda da dama ya kawo ka gidan dan kazo ka tuna min kenan ko?" Alhaji ya fa'di yana mai sanya babbar rigar sa still bai kalle shi ba. Da sauri Yah Deen ya girgiza kansa tare da fa'din " A a ba haka bane fa Alhaji, yanzu ne na tuno shine nace bari kawai in sanar da kai tunda ina gaban ka". Murmushin da ko akan fuska bazaka ga bayyanar ta ba Alhaji yayi illah sautin sau'kar numfashi da zaka ji, bai kalli inda yake ba yace " Allah ya kaimu ranar to...ka sanar da Ja'afar ne?" Yah Deen sai yace " a a sai anjima zan sanar masa". Shiru Alhaji yayi bai kuma magana ba, Yah Deen ne yayi 'karfin halin tattaro dukkan natsuwar sa tare da dun'kule abinda ya tsaye masa a zuci, tattara kalaman sa yayi wuri guda sai da ya saki ajiyar numfashi kafin cikin muryar masu neman alfarma ya furta " Alhaji dan Allah kayi ha'kuri ka yafe min......". Alhaji Baba bai barshi ya kai 'karshen maganar tasa bama dan ya riga ya san kwanan zancen, dan haka sai yayi saurin taran sa da fa'din " Kar ka damu kanka da ni, na yafe maka tuntuni, sai dai ka sani duk abinda na riga nayi niyya sam bazan ta6a fasawa ba". Alhaji Baba yana 'dora hular sa akai ya fa'di hakan cike da tabbatarwa. Yah Deen cikin muryar Alhajin ya tabbatar da furucin nasan har zuciyar sa ne, sannan baya saurin yanke hukunci akan abu balle fushi amma idan ransa ya 6aci abin ba da'di. Kwata-kwata sai ya rasa yanayin da ya shiga a lokacin,  shin na da'di ne ko kuma akasin haka? shi kansa ya kasa ganewa, a zahiri yaji da'din kalmar yafiya da Alhaji ya furta masa duk dama tun kan ya iso ga Alhajin Ammi ta riga ta tabbatar masa da cewa Alhaji bai yi fushi da shi ba, amma ji daga bakin Alhajin yafi komai yi mai da'di har zuciya, gashi dai ya yafe masa kuma bai ga alamun zai hana shi komawa makaranta ba, amma abinda ya ringa yawo a 'kwa'kwalwar sa ya kuma rasa sukuni shine 'karshen furucin Alhajin da bai san manufar ta ba _....."....sai dai ka sani...abinda na riga nayi niyya sam bazan ta6a fasawa ba"._ Tuno maganar Alhajin ya sake yi a hankali ya 'dago ya kalle shi yayin da yaga fuskar Alhajin wasai ga dukkan alamu bashi tare da damuwa...Key 'din motar sa ya 'dauka ya nufi hanyar fita daga 'dakin yana fa'din " Na wuce yau na makara sosai". Cikin 'karfin hali Yah Deen ya iya furta " Allah ya tsare". Wa Alhajin sannan ya cigaba da tunanin ma'anar maganganun Alhajin amma ya rasa me suke nufi sam, cikin haka ya tuno abinda Ammi tace da shi " _yace muyi fatan faruwar Alkhairi_" .....tuno haka ne ya sanya shi furta " Allah ya tabbatar da Alkhairi akan komai". A fili ya furta hakan tare da mi'kewa cikin sanyin jiki ya kama hanyar fita. Koda ya isa parlour Ammi ka'dai ya tarar da itan ma fitowan ta kenan da Alhaji ya 'kira ta sa'ilin da zai fita, ga dukkan alamu Alhajin har ya fita dan babu shi a palourn. Shima Yah Deen bai zauna ba kawai ya nufi hanyar fita yana fa'din " Bari inje in fara shirin tafiya Ammi hutun mu ya 'kare". " Wai dagaske azumin kake yi ne?" Ammi ta tambaye shi da mamaki. Sai ya amsa da fa'din " Erh Ammi dagaske ne mana". Yayi maganar yana murmushin 'karyar da ya manta cewa ya shirga mata...banda girman kunyar ya zauna gaban su ya ci abinci ba mai zai sa shi wannan 'karyar. Girgiza kansa yayi yana mai cigaba da tafiya izuwa ga barin palourn. Har ya 'karasa fita Ammi bata ce da shi komai ba illah idanu da ta raka shi da shi tana tunanin " Ashe komai na iya canza mutum matu'kar abin n da muhimmanci ga rayuwar wanda abin ya same shi, yau ga shi Mu'een na Azumin nafila ta litinin da Alhamis abinda bata ta6a ji yayi ba tunda take da shi...Allah kenan mai juya Al'amura yanda ya ga dama ". Har cikin ranta taji da'din faruwar hakan ta kuma godewa mahalicci. _('Dan Ammi sarkin 'karya, sai dai kuma fa yayi sa'a karyar tasa tazo a dai-dai)._ ~Comment Vote and share please.~ 👌🏻 *Salmerhn ku ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 🤞🏻 ~KE TA DABANCE NUSEE TA, ALLAH YA 'KARA DAN'KON 'KAUNA...SOSAI NAKE JI DAKE HAR CIKIN JINI NA....~ 🤞🏻 ~MASOYIYA NANAH INA GODIYA SOSAI,  'KAUNAR KI A KULLUM SAKE YA'DUWA  YAKE YI CIKIN ZUCIYA TA~ 😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *42*   Yana isa gida ya sanya wayar sa a caji tare da kunna ta, nan take kuwa sa'konni suka dinga shigowa amma ko bi ta kansu bai ba balle ya karanta abinda suke 'kunshe da shi. Cajin awa 'daya wayar tayi sai ya cire ta, number Unlce Ja'afar ya fara dialling inda ringing 'daya ya 'daga kamar dama can zaman jiran 'kiran yake yi. Ko amsa sallamar da Yah Deen ke yi masa ma bai yi ba kawai ya fara zazzaga masa masifar kashe waya da yayi tsawon kwanaki. Yah Deen kam ha'kuri ya dinga bashi cikin kwantar da murya tare da shirga masa 'karyar baida lafiya ne shiyasa, burin sa kawai yaji ko Uncle Ja'afar na da masaniya akan abinda ya farun tare da son sanin ko yasan 6oyayyen shirin Alhaji akan sa....yayin da a masifance Uncle Ja'afar yace da shi " Da baka da lafiyan kuma ka sanar da ni ne?" " So sorry bazan sake ba Uncle". 'Karamin tsaki yaja tare da fa'din ya jikin to?" " Ai ina jin muryar ka na warke kamar ba ni ba". Cewar Yah Deen yana 'dan smilling da bai wuce kan fuskar sa ba. " 'Karyar banza sai kace ban san halin ka ba Mu'een". Yah Deen 'yar dariya kawai yayi batare da ya 'kara fa'din komai ba. Uncle Ja'afar ne ya sake fa'din"...ya batun school kuma, hutu ya 'kare ko?" " Erh mun kusa komawa Insha Allahu 'karshen week 'din nan ma...ina Aunty na?" Ya 'karashe da tambayar sa Anty Zainab. Ja'afar kam yana shirin yanke 'kiran yace" Hala manta sunan da kayi saving number 'din ta a wayar kayi". Bai sake sauraran jin komai daga gareshi ba kawai ya yanke 'kiran yayin da Mu'een ya bi wayar da kallo da mamakin rashin jin wani abu daga bakin sa da ya danganci damuwar da ke damun sa. Ga dukkan alamu Uncle J bai san komai kan lamarin ba tunda baiga alamun hakan ko cikin kalaman sa ba. Murmushi ya saki na jin da'din rashin sanar da Uncle J da Alhaji bai yi ba, nan take yana murmushin ya 'kira layin Antyn sa Zainab inda suka gaisa cikin sakin fuska da walwala itama tana mai mitan rashin samun wayar sa cikin kwanakin.       'Karyar da yayiwa Uncle Ja'afar itama shi yai mata sai dai ita kam cewa tayi" Ya Ammi bata sanar da ni batun rashin lafiyar ba kuma?" Ai da sauri ya bata amsa da fa'din" May be mantawa tayi Anty". " Ammin ce zata manta da batun jinyar ka Mu'een?" Anty Zainab ta tambaya mamaki bayyane cikin kalaman ta haka ma kan fuskar ta. Sai yace " Gashi kuwa, Anty ai babu mamaki...kinsan Ammi tunda ta samu wannan yarinyar ta daina so na, kullum masifa take min ban isa ko aikan yarinyar nayi ba sai ta tsigale ni". Dariya Anty Zainab tayi tace" k'ilan kana muzguna mata ne shiyasa Ammi take yima haka amma ai yarinyar bata da matsala a yadda na fahimce ta". Yace " Ke de Anty kiyi shiru kawai amma ni da nake tare da su ni zan bada labari...". Taran sa tayi da fa'din "....Ai gaskiya ne Mu'een...ni dama nake cewa zan ro'ki Ammi ta bamu aron yarinyar danni fa tayi min gaskiya ina son ta sai mu zauna tare dukkan mu idan mun dawo Bauchi". 'Dan 6ata rai yayi yace " Anty ni kuma fa?" " Har da kai ai sai kazama yayanta inda rabo kuma watarana da iznin Allah sai ka zamo mijin ta na har abada". Da wuri ya furta " God forbid...Allah ya sawwa'ka Anty ina zan kai ta ni kuma?" Zaro idanu Anty Zainab tayi tace masa" Inda ya dace da ita mana, jimin yaro da shiririta, har haka zaka ce Mu'een an gaya ma ana gayawa Allah yadda zaiyi ne?" " Ni dai please Anty ki bar zancen nan...shima Allah zai kiyaye bazai bar hakan ya faru ba". Anty cewa tayi " Ni dai da za'a ban za6i Allah ita zan za6a ka maka dan nasan ba 'karamin sa'a zakayi ba da samun ta". " Hasara dai". Ya fa'di 'kasan ma'koshi amma Anty sai da ta jiyo shi. "...Hmm...Fatana ni dai a kullum inga ranar da za'a ce wannan yaron nawa na fama da zuciyar sa akanta..." Lumshe idanu yayi yana tuno Nannen sa, masoyiyar sa, sahibar zuciyar sa, baya jin zai 'kara yiwa wata 'ya mace kwatankwacin son da ya yiwa Nanne har abada balle har tasa ciwon sa tashi, ko ita Nannen ma bata tada masa ciwon ba balle wata daban can da ya san bazata kai Nanne daraja a wurin sa ba. Idanun sa a rufen cikin sanyin murya yace " Babu ita Anty...ba ma za'a haifeta har abada". 'Yar dariya Anty tayi daga can 6angaren tace"...Zamu gani ai...in da rai kamar yau ne, ko angaya maka abin ana gudun sa cikin sau'ki ne tamkar yadda kake gudun abokai?" Shiru yayi bai amsata ta ba sai ta cigaba da fa'din" Gara ka bari in mana kamun 'kafa wurin Ammi tun kafin wani ya riga mu". 'Kit!.. yayi saurin datse 'kiran cike da jin haushin maganar ta...cikin ransa yake ayyana" ina zan kai wannan abin da jiki ko'ina flat sam babu mamora, da'din me zata jiyar dani banda aikin kuka da ta iya da kayan takaici, yana ji cewa irin Noor ko a 'kafa aka 'daura masa Allah sai ya kunce ta ya tafi ya barta da gudu ma kuwa...har gara 'dayan yarinyar ma wato Ma'u, babu laifi ita tana da abin kallo ajikin ta...." Take salo da tsarin tunanin sa ya canza, wuri guda ya 'kurawa idanu yana tariyo ranar da ya ha'da jiki da ita (Ma'u) yanda ya jima yana jin tudun 'yan matasan boobs 'din ta a jikin sa, tun ranar yake so ya samu damar ganin su da idanu amma sam ya rasa ta yadda hakan zai faru. Tsaki ya saki a fili yana lumshe idanu tare da kishingi'da, a hankali tunanin sa ya koma kan Husnah, tuno yanayin surar jikin ta take sai ya saki ajiyar numfashi mai 'dumi, gani yake yi kamar ni har abada har in 'kare kaf 'din rayuwa ta bazan ta6a kamo Husnah 6angaren halitta ba, a fa'dar sa bai ma ga alama ba da har Anty ke yi masa fatan kasancewa da ni. Wannan 'dan tuno Husnah da yayi sai yasa take yaji shi on, wani irin shau'kin son kasancewa da ita ne ya kama shi. Aikin kenan dama indai tsakanin Yah Deen da Husnah ne ta 6angaren sa babu komai cikin zuciyar sa daya danganci so ko 'kauna illah son kasancewa da ita da yake yi koda wani lokaci, ya kuma rataya hakan akanta ya maida ta abar jin da'din sa kawai a mori rayuwa. Yayin da Husnah ke yi masa so, so irin na asali mai ninkuwa a duk lokacin da take tare da shi, soyayya take masa wanda babu gauraye ko algus acikin sa, da tunanin yiyuwar aure tsakanin su watarana. Akwai wani cousin 'din ta mai suna Hisham dake tsananin 'kaunar ta da aure amma ta'ki sake mai fuska ta 'kwallafa ranta akan Yah Deen bata san shi a 6angaren sa abin ba haka yake ba sam....(ni kuwa nace stop deceiving ur self am mata). Imrana baya nan ya tafi Kano yanzu shiyasa gidan ya kasance shi ka'dai ke rayuwar sa babu mai takurasa....wa'dannan shai'danun tunanin da yayi ta biyewa zuciyar sa akai ne ya sanya shi jin muguwar sha'awa na taso masa. Sai yanzun yaji babu dadi da rashin Imrana a kusa, ya so da yana nan da sun kammala maganar waccan yarinyar da ya'ki bashi ha'din kai akanta kwanaki, amma sai akayi rashin sa'a baya gari a ranar....fatan shi dai kawai shine Allah yasa dagaske Imrana yake yi cewa da yayi yarinyar itace waccan me zuwa gidan shi da 'yar gidan Ammin nan...cuz waccen tafi tsaye masa a ransa, ita yake so ya mora yanda take da 'danyen 'kuruciyar nan yasan zai kwashi gara. (Hmm....Allah ya shiryi wannan 'dan gidan Ammin gaskiya). Yanda abin ya gama ratsa shi ya kashe mai jiki nan take ya sanya shi mantawa da 6acin ran da Alhaji Baba yayi da shi kwata-kwata, neman hanyar da zai kawar da abinda ke damun sa kawai yake yi. Bashi da mafita game da abinda yake ji wanda tasa dole ba dan yaso ba ya dannawa Husnah 'kira tare da sake yin luf kan kujerar da yake kwance..idanun sa duk sun 'kan'kance sun yi wani iri da su...yasan Husnah ka'dai yake da shi da zata taimake shi cikin wannan yanayin batare da yasha wahala ba. Yanajin wayar tafara ringing sai ya lumshe idanu ya kifa wayar kan kunnen sa na dama yayin da hannun sa 'daya ke yawo saman cikin sa zuwa marar sa a hankali. Har sai da wayar ta kusan tsinkewa kafin Husnah ta 'dauka tana yatsina fuska cike da jin haushin korar da yayi mata, bayan haka kuma bai ko 'kira ta ba tun ranar, haka ma sa'k'konin ban ha'kuri da tai ta tura masa ko reply 'din guda bata gani ba, da wannan tunanin ta daure a yatsine ta furta" Hello!" Shiru yayi yana murmushin mugunta, tuno irin cin mutuncin da yayi mata rannan da tazo. " Helloo!! Ta sake fa'di kamar dole aka sanya ta. Yah Deen bai amsa ba illah numfashi da ya furzar mai 'dumi wanda hatta Husnah sai da ta jiyo shi take kuwa jikin ta ya amshi sa'kon kamar wawuya, cikin sanyin murya da dauriya ta sake fa'din" Hello!!!... wai waye ne?" Sai yanzun ya bu'di baki yace " Husnah!" Cikin mayaudariyar muryar sa mai narkar da zuciya. Husnah na jin yanda 'kira sunan ta ta wani lumshe idanu saboda jin wani irin abu da ya tsarga mata tun daga kanta ya ratsa mata har 'kafafu, wani sanyin da'di  da farin ciki taji ta ciki marar misaltuwa wanda ya sanya ta kasa amsa sunan tan daya 'kira. Yayin da Yah Deen ya cigaba da fa'din ".....Husnah har kin manta da ni da wuri haka ko?..kenan goge layi na kika yi cikin wayar ki?" 'Kasan ma'koshi tayi dauriyar amsawa da " um-um". " To me yasa kika share ni? Baki damu kiji halin da nake ciki ba dan baki sona ko?" Muryar ta na 'dan rawa tace" Ka manta abinda kayi min ne Mu'een?" Murmushi yayi daga inda yake cikin son kawar mata da wancen zancen yace" Ba 'karamin kewar ki nayi ba fa Husnah na damu sosai...yaushe zaki koma school please? " " Sunday". Ta bashi amsa a takaice. Sai yace " Fatan kin shirya ha'duwar mu dan ni gaskiya na matsu...dan Allah ki taho da wuri karki sani jiran ki kinji?" Shiru tayi masa kawai tana jin duk wasu damuwar ta na sulalewa suna barin ta, 'kuncin dake 'kunshe cikin zuciyar ta tun ranar rabuwar su kwanaki ka'dan da suka shu'de duk babu su,  irin soyayyar da take yi masa ita kanta bata san adadin yawan ta ba...irin makauniyar soyayyar nan dake ribatar 6angare 'daya cuz sam bata iya yin dogon fushi da shi koda kuwa mai ze mata, ko yanzun ma bai ko furta mata kalmar ha'kuri ko 'daya ba amma tana jin har ta sau'ko daga fushin, sannan bata iya 'kaurace wa bu'katun sa koda wani lokaci, ba kuma ta ganin ai bun alfashar da suke aikatawa...bai ta6a furta mata kalmar so ba amma ita sai take ganin kamar shima yana son ta musamnan idan taga yanda yake lalla6ata wajen sau'ke bu'katar sa sai taji kamar ta gama mallakar sa ne kawai ita ka'dai. Maganar sa ne ya katse mata tunanin da take yi, inda yace" Yanzu me zan samu to?" ..."...ba komai". Ta bashi amsa tana komawa ta kwanta rigingine tana kallon fan 'din dake sama. Bai damu ba sai ma ya sake fa'din" Turo min abin nan in gani". " Wani abu kuma?" Ta tambaya haka kawai bawai dan bata gane abinda yake nufi ba. Muryar sa kamar ta marasa lafiya yace" Kin fini sani ai ko wula'kanci zakiyi min yau 'din?" "....a a naga kana da shi kala-kala a wayar ka ne ai..." Bata ma kai 'karshen maganar tata ba ya tareta da fa'din" ai na san dasu na zo gare ki ko"! Cikin rashin damuwa tace dashi "Ni dai a a banda lafiya yanzu". " Please Husnah karki min haka mana". Ya 'kara fa'di a 'dan tsawace. Yayin da Husnah tayi dauriyar sake fa'din" Allah bazaka gani ba". Ta bashi amsa tana 'ka'kalo murmushin mugunta ta sanyawa fuskar ta na dole duk dama har cikin ranta taji da'din 'kiran nata da yayi, amma ta ganin wannan ka'dai shine iya jayayyar da zata iya yi masa a yanzu kafin ha'duwar su,  wanda take ganin da shine zata rama cin mutuncin da yayi mata rannan a Shuwarin. Yayin da tana furta hakan Mu'een ya yanke 'kiran 'kat batare da ya 'kara koda kalma ba. Ita kam husnah da ganin hakan sai ta 'kara fa'da'da murmushin ta dan for sure tasan haushi yaji kuma har cikin ranta taji da'din hakan a fili ta furta cewa" ur turn dear..kaima kaji inda da'di, 'kila daga yanzu zaka san muhimmanci na". Sai dai me...tun ma kafin ta yi wani motsin kirki a wurin taji wani 'kiran ya kuma shigowa cikin wayar ta, tana dubawa sai taga video call ne ya 'kira. Bayyananniyar murmushi ta saki tare da girgiza kanta gefe da gefe, receiving call 'din tayi tare da mi'kar da hannayen ta sama ta yadda zasu ga juna da kyau. Wayar na gama connecting sai ya bayyana kan fuskar wayar ta..." i knew it dama ai" Ta ayyana cikin ranta sanadiyan ganin yanayin da yake ciki, tun cikin voice 'din sa ta fahimci ainahin halin da yake ciki yanzu kuwa da idanun ta suka gane mata shi sai ta gama tabbatar da zargin ta domin ba 'karamin sani tayi masa ta wannan 6angaren ba. " I thought fushi kayi ai". Ta fa'di tana kallon cikin idanun sa. 'Dan ha'de gira yayi kamar bashi ba yace" me yasa zan yi..ko dama burin ki kenan nayi fushi?" Ya 'karasa maganar yana 'dage gira 'daya sama. Tana shirin yin magana ya dakatar da ita da fa'din" Nuna min"...inda yayi maganar bayan ya sake yin luf da tunanin bazata yi masa gardama ba sai kawai ya 'kura mata idanu. Husnah kafa'da ta no'ke sannan tace" An'ki". A 'dan hasale yace " Haba Husnah kashe ni kike so kiyi ne?" " Nima ai kashe nin ka kusan yi da 6acin ranka". Ta bashi amsa cikin salon son tuna masa kuskuren sa. " Bazan sake ba i promise u, but please mana Husnah kinji". Ya fa'di da kwantar da murya alamar rarrashi. Husnah sai ta 'kara no'ke kafa'da wannan karan bata amsa masa da baki ba. "...Husnah be serious mana u know i missed u kin 'dauka da wasa nake yi ne?" " Sai kaima ka nuna min nagani tukunna". Shiru yayi kawai ya tsura mata idanu tsawon da'ki'kai yana kallon ta irin kallon nan mai matu'kar 'dauke hankali da ma'anoni da dama, wanda irinta da ta san shi ta fuskar bu'katuwa ita ka'dai ce zata iya fassara ma'anar kallon...amma Husnah sai ta basar kawai ta tallafi fuskar ta da hannun ta itama tana kallon sa. Haka suka cigaba da aikawa junan su kallo Husnah kam ji tayi so da 'kaunar sa na 'kara ninkuwa mata a zuciya yana ratsa mata har cikin jini, yayin da ta 6angaren sa banda tarin jarabar dake cin sa babu komai. Cikin wata iriyar murya mai tafiya da hankali yace mata" Husnah ni kike wa wa haka ko?" Ido ta rausayar tana gimtse dariya tace" Ni dai kayi ha'kuri". " Naji to...kin yadda da dare zaki tura min?" Gira ta 'dage masa sama alamun ta yadda....sai yace " To karki manta ki 'kira ni". Bata furta komai ba sai kawai ta 'dago masa yatsun ta ta karka'da alamun " bye". Tana murmushi. Shima 'din murmushin yayi mata tare da yanke 'kiran yayi gefe da hannun sa dake ri'ke da wayar ya mi'kar da shi yana sakin numfashi a hankali...ya jima a hakan kafin bacci 6arawo yayi gaba da shi. Ai kuwa da dare misalin 'karfe tara Husnah ta 'kira shi kamar yadda ya fa'da harma yayi shirin bacci dan haka suna gama tambayar lafiyar junan su bai bari maganar tayi tsayi ba ya tuna mata al'kawarin da tayi masa....taso ta sake ja masa aji amma da yake yasan salon da yake bi da ita haka kafin ya kwanta sai da ya tabbatar ta tura masa photunan jikin ta da dama harda chat suka yi...kafin su rabu ma sai da ya tabbatar ta manta da batun koranta da yayi sun koma sha'kuwar su kamar babu abinda ya ta6a faruwa. *****             Ana gobe zai koma makaranta yana zaune yana faman harha'da kayayyakin amfanin sa cikin jaka duk ya hautsine ko'ina, lokacin 'karfe hu'du da 'yan mintina ne na yamma dawowar sa kenan daga masallaci sallahr la'asar sai ya fara ha'de kayan, so yake idan ya kammala ya tafi can gida gurin Ammi dan yau duk bai je can gidan ba. Yana tsaka da ha'de kayan kawai yaji sallama a tsakar kansa kamar daga sama, tun zuwan sa gidan bai ta6a zuwa ba sai yau tamkar  mafarki. Fara'a ya saki da ganin sa, cikin sakin fuska ya furta" Alhaji da kanka?" Murmushi Alhaji Baba yayi yana bin 'dakin da duba cikin hikima ta yadda ba zai fahimce shi ba daga 'karshe ya dire idanun sa kan Yah Deen inda ya bi ilahirin jikin sa da kallo daga sama zuwa 'kasa. Wando three-quater ne ajikin sa wanda bai ma sau'ka ko kan gwiwar sa ba ko singlete babu ballantana riga. Wanda tun dawowar sa daga masjid ya raba jikin sa da kayan...sam matu'kar yana gida bai fiya zama da kaya wadatattu ba ya riga ya saba da haka, wanda hakan sai ya tafi da tunanin Alhaji kan cewa kenan babu mamaki a hakan kullum yarinyar take zuwa ta tarar da shi, ga ta mace har mace me ze hana shai'dan yin nasara akan su bayan ke6ewar su tare? Ba yaso ya yawaita zargin Deen kan irin hakan musamman da yake babu wata 'kwak'kwaran shaida da ta bayyana hakan, amma baya jin zai iya samun natsuwa matu'kar ya bar sa haka kawao batare da ya idasa nufin sa akan su ba.       Domin shi 6arna tun kafin ta faru ya kamata ka tareta ka kuma  gyara ta in ba haka ba matu'kar kayi kuskuren da ka bari 6arna ta faru to fa gyaruwan ta sai dai in Allah yaso...shiyasa yake ji is better yayi wa abin tufkar hanci in yaso suje can makarantar su cigaba da rayuwar su zuwa kammalawar su kafin aga yanda hali yayi. Kujera ya samu ya zauna still murmushin kan fuskar sa bai gushe ba. Gaishe shi Mu'een yayi ya amsa yana mai daidaita zaman sa da sakin fuska yace" Kawai cewa nayi bari in shigo in duba ka...kuma inaso za in gayama za'ayi gyara agidan amma kuma yau 'din bamu ha'du ba shiyasa nazo da kaina". Yah Deen kai ya sosa cikin tsananin jin kunyar rashin zuwa gaishe su a ranar yace" Afuwan Alhaji wallahi ina kan hanya gaba 'daya ban nutsu bane shiyasa". " No kar ka damu, ba gashi ni nazo ba". Alhaji ya fa'di yana kallon yawan kayayyakin dake wajen a goge tas komai tsaf-tsaf. Cikin ransa ya san ba wai haka kawai dan shiryawa ne yasa bai je can gidan ba, yana lura dashi tun faruwar lamarin sai ya 'danye 'kafafu, sau 'daya tak yake zuwa kuma shima 'din ba kallum ba, lambu kamma yafi 1week bai je ba.    Duk da tuna hakan da Alhaji yayi amma bai damu ba cikin kulawa yace" Duka wa'dannan kayan tafiyar ne?" " A a ba duk ba Alhaji, ai mafi yawan suna can Jigawa kawai ina so in kintsa su da kyau ne saboda 'kura". Alhaji Baba kai ya jinjina cike da gamsuwa yace" Babu mamaki kafin ka dawo ma a kammala komai...ka ha'de sauran duk abin da kake bu'kata kar suzo su 6ace cikin shirgi". " To Alhaji insha Allahu..zanyi kamar yadda kace". Ya fa'di yana shafa kansa. Mi'kewa Alhajin yayi ya nufi 'kofa yana fa'din" na wuce ni kam dama abinda ya kawo ni kenan". Yah Deen sai yace " To Allah ya tsare ya 'kara girma da arzi'ki". Yayi maganar yana bin bayan Alhaji, har ya raka Alhajin ya tafi Yah Deen bai ko tunanin suturta jikin sa ba koda wasa ma hakan bai zo ransa ba abinka da sabo. Har 'kofa ya raka shi amma bai fita ba daga nan ya juya ya koma ciki fuskar sa wasai na jin da'din ganin yanda Alhaji Baba ya sake dashi, ko ka'dan bai yi tunanin Alhaji Baba CID ya zo yi da kansa cikin gidan ba. 'Bangaren Alhaji Baba kuwa koda ya shiga motar sai da ya tsaya yayi 'dan tunani, shi dai ya san 'dan sa ba mazinaci bane kuma ya yarda dashi, ya san halin sa bai tara shirgin abokai kuma musamman marasa dalili shiyasa ma bai yi shayin barin sa ya zauna shika'dai ba, sai gashi koda yazo 'din ma bai tarar da kowa tare da shi ba..( u know Imrana ya tafi Kano shiyasa basu ha'du ba)...amma da yake ya san mutum mutum ne shiyasa ba zai ce ga ainahin halin sa ba, ba zai ce ga abinda yake aikatawa ba musamman ma da ya san ba'a shaidan mutun a duniyar mu ta yanzu. Sannan zargi da sharri sunyi yawa ga hassada da 'kyashi, wani hakan kan same shi ne batare da ya aikata komai ba sai dai idan bincike yayi tsanani a tarar da shi bashi da laifin komai, yayin da wani zargin anayin sa da 'kamshi gaskiya domin idan an bincika wani lokacin akan tarar da gaskiya abin hakan yake faruwa ba sharri bane. Zaiso Mu'een ya kasance cikin sahun mutane na farkon ba wa'danda zargin da ake yi musu yake kasancewa gaskiya ba, hakan yasa ya shirya kawo masa wannan ziyarar ta bazatan da kansa a kuma cikin lokacin da bai tsammaci ganin sa ba da tunanin ko zai ga wani abu da zai tabbatar masa da zargin sa amma baiga komai tare da shi ba. Sosai ya samu nutsuwar zuciya sai dai duk da haka hankalin sa ya kasa kwanciya da batun  zuwan wata mace wurin yaron sa ba. Wanda ya samu 'kwarin gwiwa daga wani 6angare na zuciyar sa cewa indai har shi da yake matsayin  mahaifi a gareshi zai zo wurin sa amma bai yi tunanin suturta jikin sa ba to inaga wata daban kuma?...sannan akwai possibilityn da za'a iya fassara ala'kar su zuwa wani abu daban musamman idan kayi la'akari da yadda duk da darajar da Allah yayi mata matsayin ta 'ya mace amma tayi watsi da shi ta iya tsefe idanu tun daga cikin garin Azare ta biyo shi har Shuwarin to me ze hana ta binsa can gidan sa a Dutse tunda yace makarantar su 'daya da ita. Sannan ba sau 'daya aka ta6a ganin zuwan ta garin ba shima da idanun sa yaga zuwanta har sau biyu to meyasa take zuwa? me yake kawota wurin sa? Wace iriyar ala'ka ce da zai sa bazata ha'kura ta kama mutuncin kanta ba sai ta zo inda yake bacin ba hadda take kar6a wurin sa ba, wannan dalilin ka'dai ya sanya Alhaji Baba yake ji ba zai iya janye 'kudurin sa ba ba zai ta6a bari rayuwar 'dan sa ta lalace hakanan ba. Key yayi wa motar ya tada ya nufi hanyar gida wanda yana isa ko fita daga motar ma bai yi ba ya 'dago wayar sa saboda a ganin sa yin haka ne ka'dai zai sama masa natsuwar zuciya. Layin Uncle ja'afar ya 'kira inda bayan sun gama gaisuwa yace da shi" Fatan kasan Late Alhaji Hamza Ar'kila?" " Nasan shi, amma ya rasu shekaru bakwai kenan da suka wuce..wani abu ne ya faru?". Uncle J ya 'karashe maganar da jefawa Alhaji Baba tambayar haka. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *43* " Babu komai, amma inda hali ina so mu ha'du da kai nan da 1week.." Take hankalin Uncle Ja'afar ya tashi sosai da jin hakan dan ya san dole akwai abinda ke faruwa da har ya sanya Alhaji fa'dar hakan, ta shin farko tunanin sa gun Kiddo ya tafi, cikin yanayin tashin hankali ya jefawa Alhaji tambayar " Akwai matsala ne? In akwai wani abin ka sanar da ni please hankali na ya tashi sosai". Cikin salon son kwantar masa da hankali Alhaji Baba yayi murmushi sannan yace" Ka kwantar da hankalin ka Ja'afar ba komai bane ya faru face abin alkhairi..." " Alkhairi kamar wani iri kenan Alhaji?" Ya sake tambayar sa cikin rashin fahimta...yayin da Alhaji ya bashi amsa da fa'din" 'Dan ka ke neman auren 'yar Alhaji Hamzan shine na ga ya dace mu sanya baki a maganar, kuma bana so a 'dauki dogon lokaci...". Bai kai ga rufe bakin sa ba ma, Uncle J cike da mamaki yace" 'Da na Alhaji..ban gane wa kake nufi ba". " Kana da wani babban 'dan da kaga ya kai ya nemi aure ne banda Muhammad?" Ido ya zaro da mamaki yace" Mu'een kuma..aure Alhaji? Karatun fa?" Hannu Alhaji Baba ya 'daga tamkar Uncle J na gaban sa yake maganar cikin sanyin magana yace" Bar wannan batun tukunna idan mun ha'du ma tattauna, abu mai muhimmanci yanzu shine zuwan ka, ka samu kazo nan da 1week ina jiran ka". Daga haka Alhaji Baba ya yanke 'kiran tare da jinginar da bayan kansa da jikin kujeran motar yana sakin numfashi, cikin ransa yace" Allah ka rufa mana asiri". Ya 'dauki a 'kalla tsawon mintina uku a haka yana tunani, shi kansa baya son auren Mu'een tun yanzu amma yanajin sam ba zai iya biyewa son zuciyar sa akan hakan ba, cuz babu wanda ya san mai gaba zai haifar..dan gara yayi masa auren hankalin sa zai fi kwanciya, sai da ya gama tunanin nasa kafin a hankali ya ja motar yayi gaba. Uncle Ja'afar kam hankalin sa tashi yayi sosai, jin batun yayi wani banbara 'kwai wai Mu'een ke neman aure, yaushe har ya kai wannan matsayin, shi a ganin sa sam shekarun Yah Deen basu kai wannan matsayin ba, ya zai yi da karatun nasa to, ko kuwa tsabar ya raina masa hankali ne yasa yake nuna masa a kullum cewa karatun sa ya sa agaba nan kuwa ba haka ba ne, wa ma ya bashi wannan damar da har zai jajibo musu maganar aure tun yanzu?" Kasa ha'kuri yayi sai da yayi dialling number Mu'een domin ya tabbatar daga bakin sa...sai dai har wayar tayi ringing ta katse ba'a 'daga ba. Cike da jin haushi ya sake 'kira....Yah Deen kam bai ma san ana 'kiran wayar sa ba da yake bata 'kara sosai kuma can cikin bedroom take shi yana palour. 'Kira uku Uncle J yayi masa amma duk ba'a 'daga ba, hakan yasa shi zama bisa couch 'din dake kusa da shi yana mai dafe kansa dake barazanar tarwatsewa...abubuwa duk sun kulle mai kansa ya rasa mai ke masa da'di, yaron da ya kwallafawa Burin ganin ya zama wani abu a rayuwa shine kuma tun yanzu zai watsar da karatun da batun aure..how dare he. Mu'een kuwa bai bi ta kan wayar sa ba har sai da ya kammala komai da yake yi ya watsa ruwa yayi shirin sa cikin jumpa riga da wando kalar mint green yayi fes abinsa. Lokacin daf maghrib ne, so niyyar sa sai ya biya masjid idan ya idar da sallah sannan ya wuce wurin iyayen sa ya gaida su. Sai da ya gama fesa turaruka ya 'dauki key 'din gidan kafin ya kai hannu ya 'dauki wayar sa dake jone a caji gefen gado. Yana 'dagawa ya danna ta kawo haske da niyyan duba agogo nan yaci karo da missedcall a wayar take ya shiga ya bu'de su. Ganin har sau uku Uncle J ya 'kira shi ya sanya shi 'dan firfito da idanu waje...hanyar barin 'dakin ya nufa yana kan dialling numbern, sai dai shima 'din koda ya 'kira ba'a 'daga ba. Da wani ne daban da ko da wasa ba zai kuma 'kira ba amma da yake Uncle J ne ya sa shi sake 'kira a karo na biyu. Yana 'ko'karin danna locked a 'kofar palour Uncle J ya 'dauki wayar wanda zuwa lokacin zuciyar Uncle J ya 'dan sau'ko daga fushin da yayi ba kamar 'dazun ba, hakanne ma ya sa har ya iya amsa sallamar da Mu'een yayi masa har ma ya amsa gaisuwar sa babu yabo babu fallasa. Yana danna padlock 'din 'kofar waje yace" Na ga missedcall 'din ka har uku Uncle wallahi banji ba wayar bata kusa dani...". Bai bi ta kan maganar tasa ba kawai sai ya 'kira sunan shi "...Mu'een"! Yace" Na'am Uncle". " Wai me nake ji daga bakin Alhaji 'dazun?" Yah Deen dake kan tafiya a hankali sai ji yayi zuciyar sa ta tsinke da 'karfin gaske, nan take zuciyar sa ta fara bugawa da sauri...firgici ne ya shige shi marar misaltuwa. Tsoron sa 'daya kar Alhaji ya sanar da shi komai ne, in kuwa haka ne da bai san yadda zai yi da Uncle Ja'afar ba. In ina ya fara cikin rashin abin cewa kawai sai ya yanke 'kiran yana sakin numfashi harda dafe kansa da yake jin ya fara sara masa. Yana shirin kashe wayar gaba 'daya ne 'kiran Uncle J ya sake shigowa cikin wayar. Kamar ba zai 'daga ba sai kuma ya basar ya ja recieve button, cuz ya san in ya'ki 'dauka Uncle J zaiyi saurin gano cewa bashi da gaskiya kuma zai san da gan-gan ya'ki 'dagawa tunda  yanzun nan suke kan waya da shi. Daf da wayar zata tsinke ya 'daga tare da sada ta da kunnan sa. "...Ba ka da hankali ko Deen?" Abinda Uncle J ya fa'di kenan daga 'daya 6angaren...bai kuma jira jin abinda Yah Deen zai ce ba kawai ya cigaba da fa'din" Tsabar ka raina ni shine ina tambayar ka abu zaka wani kashe min waya ko?" Dauriyar yin magana yayi wanda cikin dakiya ya furta" Afuwan Uncle ba da gangan na kashe ba...". "..My friend please  hold ur sorry i just need my answer now...ko kuwa 6acin raina kake son gani?" 'Dan 6ata rai yayi ka'dan jin tsawan da Uncle J ya daka masa, dan yaja hankalin sa ya sanya cike da shagwa6a yace" Uncle nima fa ban sani ba". Kwafa yayi tare da fa'din " Baka san me ba?" Sai yace "Abinda kake magana akai 'din". Ya bashi amsa da sauri ganin kamar ya dan sauko. Sai dai Uncle Ja'afar a tsawace ya sake fa'din "...Dan ubanka ba kai ke neman auren bane da zaka ce min baka san komai akai ba?" Manyan idanun sa ya zaro waje da jin cewa wai shi yana neman aure....bai iya 6oye mamakin sa ba a fili ya ce" Ni kuma neman aure Uncle..a ina?" "...Raina min hankali kaji ai dama ka saba...hala yanzun ma cewa zakayi Alhaji sharri yayi maka ko?" Wani tashin hankali ne ya ziyarce shi marar misaltuwa...maganar da Uncle J ya fa'di 'din sosai ya tayar masa da hankali, kuma wai Alhaji ne ya fa'di masa, to shi yaushe sukayi haka da shi dan Allah, yaushe yace yana neman aure?, babban abinda ya guda kenan wato sanya bakin Uncle Ja'afar cikin maganar cuz ya san 'kaniyar sa zaici bada wasa ba shi ba ai masa wargi, to ma ta ya zai iya 'karyata maganar Alhaji Baba gun 'kanin sa kan wannan batun fisabillahi.... " Tambayar ka nake yi fa Mu'een kayi min shiru". Maganar Uncle J ce ta dawo da shi daga tunanin da ya tafi. Cike da da damuwa da jin haushi Yah Deen yace" Ni dai dan Allah Uncle help me, wallahi bansan da maganar nan ba ni kam sai yanzu, 'kilan ba mamaki auren dole Alhaji yake shirin yi min". Uncle cewa yayi " Banson munafurci ni..." Yah Deen ma sai yayi saurin taran bakin da fa'din" Please Uncle ni dai kazo ka ro'ka min Alhaji ya bar wannan batun nifa ban ce ina son aure ba, hasalima ni ban nemi auren 'yar kowa ba...Allah in kazo zan ma ka bayanin komai da ke faruwa...ni dai help me". Ya 'karashe maganar kamar zai yi kuka. Uncle J kam tunanin sa gida biyu ya kasu, sai ya rasa wani 6angare ne yafi rinjaye, jin yanda Yah Deen yayi maganar ya sanya shi ta shin farko ya yadda da batun sa sannan ga Alhaji Baba ma ba zai iya 'karya ta shi ba. Ji yayi dama a kusa yake da a yau 'dinnnan ba sai an kwana ba zai je a warware wannan maganar tun kafin tayi 'karfi. Duk da haka bai yi 'kasa a gwiwa ba, take ya shirya cikin ransa cewa kafin 1week 'din da Alhaji Baba ya fa'di dole zai je su ha'du. " Zanzo nextweek insha Allahu". Haka kawai ya iy furtawa a fili ga Yah Deen 'din dake ma'kale da waya a kunnan sa yana sauraro... sannan ya yanke wayar kowa zuciyar sa cike da tunani.    Haka Yah Deen ya 'karasa masallaci ya gabatar da sallar maghrib cikin jam'i bai taso ba sai da ya tsaya yayi addu'o'i masu tsayi akan auren da yaji wai ana shiryawa akan sa, tsoron sa kar Alhaji Baba yace Husnah zai aura masa..yace in kuwa haka ne da ya shiga bakwai ba ma uku ba, wannan dalilin ka'dai ya sanya shi kai kukan sa wurin mahallici akan cewa kar Allah ya sa auren sa da Husnah ya yiwu in dai da ita ne Allah ubangiji  ya tarwatsa auren. Inma ya zama dole sai Alhaji yayi masa auren ne to ubangiji Allah ya musanya masa da wata mafi alkhairi. Zai iya zaman aure da kowa koma wacocdb amma banda Husnah, sam ita kam bai jin zai iya rayuwa da ita matsayin matar sa....(ni kuwa nace kaji ja'iri kamar ba shi ne ya 6ata mata tarbiyya ba). Bai iya ya bar masallacin ba har sai da ya idar da sallar Isha'i, nan suka ha'du da Alhaji Baba a masallaci suka yo gida tare kamar yadda suka saba. Sai dai yanzu babu wannan rahar da Alhaji Baba ke yi musu duk sanda suke tare da shi, to ada 'din ma ko shi Alhaji bai yi musu hira ba Yah Deen kan ja shi da hirar yana 'dan takalo shi tamkar kakan sa, amma yanzu kam shiru kana ganin su zaka san da bambamci cuz tafiya kawai suke yi kowa da abinda ke cikin ransa, har gara ma Alhajin ya kan 'dan tambaye shi abu jifa-jifa har suka isa gida. A palour duk suka zauna nan Ammi ma tazo ta same su. Gaida Ammi yayi sai dai tana jin muryar sa ta fahimci ba dai-dai yake ba, take sai tace" Me ke damun ka?" Tayi maganar tana kallon sa. " Headache"! Ya bata amsa a takaice yana me sakin 'dan 'karamin tsaki. " Allah ya sawwa'ka..kasha magani ne to?" Tace tana duban sa da kulawa. " Zan sha idan na koma". Kai ta jinjina tare da mi'kewa ta gabatar musu da dinner ta kuma 'kwalla 'kiran suna na. Kafin in fito ma har sun isa ga dinning 'din sun zauna, da fitowa ta kuwa ganin su uku ne ya sanya na isa na zaune raku6e gefen Ammi kamar wata ba'kuwa...Ammi kam bata kulani ba da yake tasan abinda ke sani yin hakan ba ya rasa nasaba da wanzuwar Yah Deen a wurin. Alhaji Baba ne yace dani" Ba zaki dai na wannan ra6e-ra6en bako Uwata, maza saki jikin ki ki ci abinci". " Hmm". Kawai Ammi tace tare da karkatawa ta kalle ni sai na sake du'kar da kaina. Sai da ta gama zuba min abincin kafin tace dani"  bismillah" A hankali na kai hannu na na wanke kafin na janyo abincin gaba na, har a lokacin Yah Deen bai ko kalli inda nake ba balle in san cewa ya san da zama na, a hankali na 'daga kaina na kalle shi ganin bai ma san da ni wurin ba ne ya sanya ni fara cin abincin a hankali. Shi kam bai fi hannu uku yayi ba ya kawar daga gaban sa tare da 'dauraye hannun sa yaja baya. Babu wanda ya kula shi cikin Ammi da Alhaji nima kuwa kaina 'kasa ban kuma kallon inda yake ba, sai dai har lokacin na kasa sakin jiki na, Ammi ne ta waigo ta kalle ni tana shirin yin magana na riga ta da fa'din " Ni na 'koshi Ammi". " kin tabbatar?" Alhaji Baba ya tambaye ni sai na 'dage masa kaina alamar " Erh". " Yau abincin Ammi yayi ba'kin jini kenan". Alhaji ya fa'di yana 'yar dariya tare da maida idanun sa kan abincin. Ammi sai tayi murmushi kawai. A hankali na tashi na bar table 'din cikin raina nake tunanin wannan shi kullum bai canzawa. Yah Deen ma da yake zuciyar sa cike take da damuwa hakan ya sanya bai 'kara mintina sha biyar cikin gidan ba yai musu sallama Ammi na tuna masa shan magani yace zai sha... daga haka ya wuce can gidan da yake. Yana kwance yana aikin tunani yaji 'karan shigowar sa'ko cikin wayar sa, da yake wayar na hannun sa hakan yasa bai 'dauki dogon lokaci wurin duba text 'din ba. Nan ya ci karo da bank transfern ku'di daga Uncle J kimanin 40K ya tura mai. Take ya 'kira sa yai masa godiya, anan ne Uncle J ya ji yanayin yanda muryar sa take a 'dan dusashe sai yace" Me ke damunka kuma Mu'een?" Kamar zai yi kuka yace" Ni dai Uncle please help me out of this issue...tsoro nake ji kar Alhaji Baba ya 'daure ni". " Ka kwantar da hankalin ka nextweek insha Allahu zanzo mu gana da shi...ina dai ka tabbatar ba kai ka nemi auren ba?" Sai yace " Haba Uncle ina ni ina neman aure tun yanzu?" 'Yar dariya Uncle J yayi yace " Rabu da Alhaji 'kila dan ya koma 'kauye ne shiyasa zai maka irin na su". " Ni dai banso...Uncle please kazo da wuri". Ya fa'di kamar zai yi kuka. Uncle Ja'afar kuwa " Insha Allah" kawai yace da shi wanda daga haka suka yi sallama da shi yana 'danjin dama-dama, sai dai wani 6angaren hankalin sa ya kasa kwanciya da 'karya ta mahaifin sa da yayi, tsoron kar idan Uncle J ya tunkare shi da maganar shi mai ze ce? kar dai ya bayyana masa komai cewa mata ke zuwa wajen sa shiyasa zai yi masa auren...hankalin sa duk ya kasa kwanciya ji yake tamkar ya fasa tafiyar ma gaba 'daya..amma ya san hakan ma ba wata mafita ba ce mai amfani tunda koda yana nan 'din ma bai isa ya hana Alhaji abinda yayi niyya ba. A wannan daren sam bai iya yayi baccin kirki ba, yaso ya 'kira Husnah ya tambaye ta ko taji  wani labari amma sai ya bawa zuciyar sa ha'kuri akan kar yayi gaggawa tunda bai ji daga bakin Alhaji ba. Washe gari da sassafe misalin 'karfe takwas ya fito, da yake weekend ne so a wajen gidan ya samu Alhaji Baba zaune yana hutawa,  anan suka gaisa ya sanar da shi batun tafiyar tasa...fuskar Alhaji babu yabo ba fallasa yayi masa fatan Alkhairi..daga nan ya shiga wurin Ammi da tunanin ko zai samu jin wani sirri game da batun auren da daga bakin ta...ni kam a lokacin ina can ina bacci na a 'dakin Ammi. Ga mamakin sa koka'dan Ammi bata kusanta maganar ta da batun aure ba, ga dukkan alamu itama bata san shirin Alhaji akan sa ba...cikin ransa ya ayyana wannan karan kenan Alhaji Baba shi ka'dai ya ya yanke shawarar sa cikin ransa. Yah Deen ji yayi tamkar ya sa hannu aka ya tsala ihu, shi sam bai son wani batun aure yanzu, ga shi abin haushin bai ma san wace ake magana akanta ba. Ammi kam bata bar shi haka nan ba, duba da abinda ya faru tsakanin sa da mahaifin sa kwanaki ya sanya ta ringa yi mai nasiha akan ya kiyaye duk abinda zai aikata ya guji wanda zai yi leading 'din sa da kaucewa mahalicci...sannan ta 'kara garga'din sa akan Husnah, tace tunda yace course mate ce ita to ta tsaya iya matsayin ta ya daina bawa mutane damar da zasu iya shiga tsakanin sa da iyayen sa tunda yasan babu wanda zai so ganin hakan daga 'dan sa, shima ya kiyaye, tace in dama 'dan uwan ka namiji ne ai kaga babu wanda zai damu matu'kar tarbiyar sa tana da kyau amma ita a matsayin mace be kamata ace tana zuwa har muhallin ka ba da sunan course mate...kayi mata magana ta daina please babu kyau, kamata yayi ta ri'ke darajar ta 'ya mace. Yace " Insha Allahu Ammi zan mata magana bazata 'kara ba". Zuciyar sa duk acunkushe yake jinta, bai san me ke shirin faruwa da shi ba. Ga shi kalaman Ammi sun 'kara bayyana masa cewa itama a duhu Alhaji Baba ya barta bai sanar da ita komai ba. 10k Ammi ta 'dauko ta bashi tace ya hau mota da shi, yayi mata godiya sosai sannan ya fita, cikin ransa yake jin wani iri tamkar yayi mantuwa cikin gidan amma ko za'a yanka shi ba zai ce ga abin ba, haka ya daure ya fito ya sake tarar da Alhaji Baba a wurin. Da ada ne kafin su sami sa6ani irin wannan tafiyar ta kamashi da yasan tare zasu koma cikin gidan da shi amma yanzu kam Alhaji ko ajikin sa kamar ma bai san da batun tafiyar ba, nan ya sake yi mai sallama ya wuce amma ga mamakin sa Alhaji ko sisi bai ciro ya bashi ba abin ya bashi mamaki sosai cuz ba hakan suka saba ba. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* Masoya na godiya nake sosai Ubangiji Allah ya cika muku burikan ku na Alkhairi😍 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *44* Hakan da yafarun ne ya 'kara fahimtar da shi irin 'kuncin da ya sanya Alhaji Baba ciki, gashi dai zai amsa sallamar sa da gaisuwar sa har ma wani sa'in zai 'dan ja shi da hira amma wannan fara'a da sakin fuskan sam babu su. Tafiya yake yana tunanin abinda zai biyo baya...ya riga ya san zancen auren nan babu fashi tunda har Alhaji ya iya furtawa ga Uncle J, ya san babu mai iya dakatar da shi, cuz tun sanin da ya yiwa mahaifin nasa ya san shine akan magana 'daya tak, duk da'din da kuke da shi kuwa baka isa ka sanya shi canza ra'ayin sa ba, he is the man of his word bashi magana biyu. Sanin haka ya sanya shi fatan Allah dai yasa ba Husnah bace Alhajin yake shirin aura masa ya kuma sa ba irinta bace ma kwata-kwata, bashi da mafita a yanzu illah komawa ga mahalicci ya ro'ke sa..ko zai tausaya masa ya canza ra'ayin mahaifin nasa. Da isar sa gida sai ya sa6i jakar sa a kafa'dar sa ya fito tare da kulle ko'ina na gidan yayi gaba abin sa zuwa bakin titi dan samun abin hawan da zai shigar da shi Azare...sai fatan Allah ya tsare hanya kuma. ***** Kafin cikar sha biyu na rana ya dira Jihar jigawa inda direct ya wuce gidan sa da yake zama bai tsaya 6ata lokaci a ko'ina cikin garin ba, balle ma yanda yake jin sa cikin 'kunci ya sa yafi bu'katar jin sa kawai a muhallin sa shi ka'dai inda babu hayaniyar kowa. Gidan ya 'danyi 'kura ka'dan ba laifi dan haka bayan ya 'dan huta kafin lokacin sallar Zuhr tayi har ya 'dan kimtsa nasa 'dakin ya watsa ruwa sannan ya wuce masjid...sauran aikin ya barwa isowar Husnah ne idan ta iso sai ta 'karasa duk dama ya riga ya yanke cikin ransa cewa zaman su da ita zai cigaba tare ne bayan ya tabbatar da cewa babu wani ala'kar da taji yake shirin faruwa tsakanin sa da ita da ya danganci maganar aure, amma hakan bazai sashi hana ta kimtsa masa gidan sa ba...koma dan kar ta barshi da uban aikin da bai san yadda zai yi da shi ba. Koda ya dawo daga masallacin ma 'dakin sa ya kuma shigewa yayi kwanciyar sa dan hutawa, bai ko nemi abinda zai sa a cikin sa ba ya bari sai zuwa yamma idan ya fita...kafin bacci ya 'dauke sa ne sai yaji 'karan Vibration na wayar sa dake gefen kansa. Tsaki ya saki tare da 'dago wayar yana duban fuskar wayar gami da karanto sunan wanda ke 'kiran sa. Sai a lokacin ma ya tuna ashe bai 'kira mahaifan sa ya sanar da su isowar sa ba...shaf ya sha'afa ma gaba 'daya. Tsayawa tunanin da yayi ne ya sanya 'kiran da akayi masa yankewa nan ya ci karo da missedcall 'din da akayi masa 'dazu da yake tunanin fitar sa masallaci ne akayi 'kiran, na Ammi 3missedcall sai na Husnah kuma biyu yayin da na Is'haq kamar yanda yayi saving yake 'daya...sai dai kafin yayi wani yun'kuri take wani 'kiran Ishaq 'din ya sake shigowa while wayar na ri'ke a hannun sa. ***** Ishaq da Imam abokan juna ne irin na 'kut da 'kut 'din nan su yan asalin jihar Borno ne haifaffun 'karamar hukumar Beinishek. Sun kasance course mate 'din Mu'een ne dake matu'kar son ganin sun 'kulla abota dashi, musamman saboda ajin sa da kuma sanin yanda brain 'din sa ke kawo light ba da wasa ba. Hakan yasa suke matu'kar shishshige masa a mafi yawan lokuta sukan so suga sun sako shi cikin shirgin rayuwar su, babu laifi kuma ya 'dan sake musu fuska cuz dama a makaranta ba'a ta6a gudun mutane, dole ne ko kana gudun wasu a wani 6angaren zaka saba da wasu, hakan yasa Mu'een sabawa da su Ishaq a hankali suna 'dan gaisawa, babu laifi har wataran ma sukan 'dan zauna da shi su ta6a hira ka'dan musamman a irin lokutan da ya kasance suna jiran lecturer ya zo ne, ga shi kuma sai akayi sa'a group 'din su yazo 'daya. Tun lokacin da zasu tafi hutun semester Ishaq ya kar6i phone numbern sa sai dai basu ta6a yin waya da shi ba, babu wanda ya ta6a 'kiran wani cikin su, Ishaq bai 'kira shi ba ko da sau 'daya ne kamar yanda shi da kansa ya san cewa Mu'een ba zai yi 'kiran sa wai dan kawai su gaisa ba, su kan ha'du dai a whatsapp su gaisa sama-sama kuma hakan ma ba kullum ba. Yau shine rana ta farko da Ishaq ya gwada 'kiran layin Mu'een da bayan yankewar 'kira na farkon ya kuma sake dialling karo na biyu. Tsaki Deen yayi tare da jan recieve button ya danna wayar a speaker tare da ijiye ta gefen kansa...yana wani cic-cin magani. " Ya akayi Ishaq?" Ya fa'di yana ha'de gira, ko daga sautin muryar sa ka'dai zaka iya fahimtar ba'a son ransa yake maganar ba balle idan ka dubi yanayin fuskar sa. Ishaq kuwa bai damu da yayanyin da ya jishi ba kawai ya cigaba da fa'din" Normal fa Gaye, ka iso ne?" " No ban taho ba...but may be tomorrow or day after...ban gama kintsawa ba tukunna". Hankalin sa kwance ya shirga 'karyar hakan cikin ransa yake ayyana" ban son damuwa ni daga dawowa ta". 'Kasa-'kasa ya saki tsuka yana gyara kwanciyar sa. Ishaq da bai san cewa 'karya bace Mu'een ya shirga masa sai ya saki murmushi tare da fa'din" Kana sha'anin ka Gaye, girman ka ne...mu kam mun diro muna cikin school ma yanzu haka..." Fa'din Ishaq yana 'yar dariya. Deen kuwa sai yace" Yayi kyau ya hanya kuma?" " Alhamdulillah za'a ce gaskiya". Sai yace " Owk yayi kyau". A takaice yana wani lumshe idanun gajiya gami da 'kosawa da yayi da amsa wayar. Yana so ma ya tambayi Imam amma sai ya mance sunan sa kuma ma bai son hirar tayi tsayi tsakanin su shiyasa kawai ya basar, hakan yasa yayi shiru yayin da Ishaq ya yanke wayar da fa'din" Sai ka iso to". Ishaq na kashe 'kiran ya 'dago wayar yana mita cikin ransa wai" Mutum sai nacin tsiya..wannan in maye ne shi ha'dama zai yi". Ammi ya 'kira ya sanar da ita isowan sa, sai Uncle Ja'afar da Alhaji Baba, daga nan bai kuma 'kiran kowa ba kawai ya mi'ke yai bacci abin sa. ***** Sai bayan sallar la'asar Husnah ta iso, da isowan ta kuwa bai fi hutun 20mins tayi ba kawai ta tashi ta fara aikin gidan zuciyar ta 'daya. Wanda tun lokacin isowan ta daga" sannu da hanya" babu abinda ya ha'da ta da shi tun isowar tata har izuwa kammala kimtsa gidan bata ga wani annuri tattare da shi ba. Husnah bata damu ba cuz ta san dama shi tamkar wahainiya yake, launin halayyar sa canzawa take a duk lokacin da ya ga dama....maganar sa kuwa juju ne da ita, idan yaso yin rowar muryar sa kuwa har sai kunyi mamakin yanda yake yin 'dif...in kuwa yan surutun sa na nan ko ita sara masa take yi ta zama 'yar sauraro...'dan ra'ayi ne Mueen ba na wasa ba kuwa. Sanin halin sa da tayi ne ya sanya sam bata ko damu da sharetan da yake yi ba, mafi yawan lokuta ma sai dai ta saki murmushi kawai ita ka'dai, musamman idan ta tuna irin 'dokin da yake yiwa ha'duwar su da kuma da'da'dan kalaman da yai ta zuba mata cikin satin kafin tahowar su amma ganshi yanzu tamkar ba shi ba yazo yana wani ha'de mata gira... Bata samu damar kammala gyaran gidan ba har sai kusan sallar Maghrib saboda ba laifi gidan nada 'dan girma sosai, amma sosai tayi 'ko'kari cuz cikin lokaci 'kan'kani gidan ya dawo fes da shi yana walwali tamkar ba shi ne yayi futu-futu 'dazun ba...harda burner ta kunna a palourn ta saka musu turare mai da'din 'kamshi saboda kawai ta sanyaya ransa, cuz ta san shi da son 'kamshi. Shi kam tun da ya fita sallar Maghrib bai dawo ba har sai da akayi sallar Isha'i sannan ya dawo gidan da ledan take-away da ya musu a hannun sa. Husnah hutun Sallah take yi dan haka a palour ya same ta kishingi'de tana amsa waya daga mahaifiyar ta. Ledan ya ajiye tare da zama facing da inda take ya tsura mata idanu yana jiran ta kammala wayar ji yake tamkar yaje ya rungumeta ya bayyana mara irin kewar ta da yayi. Amma deep down his heart yake tsana ta na taso masa ka'dan, maganar aure ka'dai da akace mahaifin sa na shirin yi masa ya sanya tsanar yin tsiri cikin zuciyar sa inaga kuma ance auren akayi gaba 'daya..kunga ai sai cin mutunci da hantara ne zai biyo baya ko. _'Kalubalen mu 'yaya mata, darajar ki, itace kimar ki, mutuncin ki, gadarar ki, alfaharin ki, har ma da kwanciyar hankalin ki a ko ina, mu daure mu kula da kare mutuncin mu ko dan gudun abinda kan iya zuwa ya dawo, babban ma shine tsoron Allah...Ubangiji Allah ka 'kara tsare mana kawunan mu ka raba mu da sharrin masu sharri...AM33N._ Ai kuwa tana gama amsa wayar ta juyo gare shi tana murmushi tace" Ka dawo?" Da" Umm" kawai ya amsa ta a takaice tare da 'dago ledan da ya shigo da shi ya ciri abinda yaga zai iya ci sannan ya tura mata sauran batare da ya furta mata komai ba. Shima 'din yunwa yake ji sosai shiyasa bai ko saurari Husnah sun ci tare ba kamar yanda suka saba kawai ya fara aikawa cikin hanjin sa. Murmushi Husnah tayi tana kallon sa tace" ba zaka jira ko plate na 'dauko maka ba yau 'din?" " Barshi kawai". Yace bayan ya taune chips 'din dake bakin sa. Husnah murmushi tayi tare da mi'kewa ta je ta 'dakko plate ta zuba iya abinda zata iya ci ta koma gefe ta fara ci, shiru 'dakin ya 'dauka kowa na cin abincin sa jifa-jifa ta kan 'dan saci kallon sa yayin da shi kuwa baya ko kallon inda take tamkar ma ya manta da kasancewar ta cikin 'dakin illah Television da yake kallo lokaci zuwa lokaci a haka har suka 'kare cin abincin baki 'daya. Husnah ce ta ta shi ta tattare komai harda wanda yayi amfani da shi duk ta fitar zuwa kitchen sannan ta dawo palourn, sai dai bata zauna ba kawai ta tunkari 'kofar da zai sada ta da 'dakin ta tana mai shafo kyawawan siraran kitson da ke kwance a fatar kanta. Daf da zata shige taji muryar sa ya 'kira sunan ta" Husnah"! Cikin dakiya da mugun hali. Waigowa tayi batare da ta yi niyyar tahowa ba cuz zuwa lokacin 'dan iskan banzan halin nasa ya fara isanta itama, ganin babu wani abinda ya ha'da su amma sai faman share ta yake yi, tun zuwan ta gidan zuwa yanzu in bata manta ba bai fi sau biyu kacal magana ta shiga tsakanin su ba. Ganin ta tsaya batare da ta taho zuwa inda yake ba ya sanya shi ha'de gira yana sake fa'din" Magana nake so muyi please". Baki ta ta6e sannan ta taho a hankali ta zauna kan kujerar da ke nesa ka'dan da shi. Sai da ya saki numfashi kafin ya ha'de hannayen sa wuri guda yana duban ta yace" Husnah me kika ji yake shirin faruwa tsakani na da ke?" Da mamaki tace da shi" Ni kuma me zanji Mu'een babu abinda naji ni" Tayi maganar tana kallon fuskar sa. Sai ya 'dage gira 'daya tare da zuba mata idanu a hankali ya furta" Mahaifina ya san ala'kar da ke tsakani na dake, akanki Husnah har mari mahaifina yai min da tun haihuwa ta har girma na hakan bai ta6a faruwa tsakani na da shi ba..kin san kenan ransa ya 6aci sosai kenan ko?" Ya 'karashe yana duban ta sannan ya koma ya zauna da kyau still yana kallon ta da itama 'din shi take kallo...Cigaba yayi da fa'din" Ina jin tsoron hukuncin da zai yanke akan hakan ne shiyasa nake tamabayar ki". Husnah sai tace" Babu komai, ni banji komai ba gaskiya". Yace" Kin tabbatar ko Husnah?" " Me yasa kake tunanin zan maka 'karya to". "Hmm" ya saki ajiyar zuciya afili yana jin 'dan natsuwa ka'dan na shigan sa. Baya ya koma ya jinginu sosai da jikin kujerar yana lumshe idanu. " To ni ka 'daure min kai sam ban fahimci inda maganar taka ta dosa ba, me kake nufi da wannan tambayar? Me yasa kake tunanin hukuncin da za'ayi maka zai shafe bacin ko sani na bai yi ba ni". Idanun sa a lumshe yana shafa saman 'kirjin sa da left hand 'din sa ya bata amsa da fa'din " Bazaki gane bane Husnah abar zancen kawai...fata na dai kawai shine Allah yasa abinda kika fa'da min ya zam iya gaskiyar kenan, kuma ya sanya iyakar abinda zai iya faruwa tsakani na dake ya kasance iya nan...." Husnah kam ido kawai ta tsura masa cike da matu'kar mamakin kalaman nasa, sosai ya 'daure mata kai ya sa ta cikin tunanin manufar hakan da ya furta mata. Yayin da cikin ransa yake ayyana cewa matu'kar Husnah tayi kuskuren da har ta bari aure ya kasance tsakanin sa da ita..." Hmm" Kawai ya furta illah bayyana murmushin sa da yayi a fili still idanun sa a rufe. Husnah kam zuciyar ta cike fal da tunani ta tashi ta shige 'dakin da ya kasance mallakin ta ne a gidan, sosai take so ta san me maganganun nasa ke nufi amma sanin da tayi cewa matu'kar ba ra'ayin kansa yayi ba to ko hauka zata yi bazata ta6a jin yanda take so daga bakin sa ba. Ranar haka kowa ya kwana 6angaren sa babu wanda ya nemi 'dan uwan sa, Husnah kam 'kullin dake cikin maganar sa ne ya dame zuciyar ta..kwana tayi tana tunanin tambayar da yayi mata, to me yake tunanin zai faru tsakani na da shi wanda yake tsammanin zan ji shi a gidan mu? Tambayar da take yawan yiwa kanta kenan abin ya dame ta sosai har hakan yasa ta 'kagara gari ya waye ta 'kira mahaifiyar ta taji, tsoron ta kar dai ahalin ta sun san da batun 'kazamar tarayyar da ke tsakanin ta da shine suke ganin ta da abin kawai...yayin da Yah Deen yayi baccin sa cikin kwanciyar hankali jin cewa babu wani labari daga 6angaren Husnah. Gari na wayewa da yake ba sallah zata yi ba, tana watsowa jikin ta ruwa ko gama kimtsawa bata bari tayi ba kawai ta rarumo wayar ta, sosai ta 'kagara taji abinda ke faruwa cuz ba 'karamin duhu Mu'een ya shimfi'da cikin tunanin ta ba. " Hello Mummy"! Husnah ta fa'di jin an 'daga wayar da ta 'kira 'din. " Haba Husnah...sau nawa wai zan miki kashedi akan wannan Hello 'din da kike yi a waya, sallamar ce da wahala ko kuwa menene?" Mahaifiyar Husnah ce ta furta hakan tana mai jin 'daci har cikin ranta na rashin jin maganar ta da Husnah bata yi. " Sorry Mummy na daina...Fatan an tashi lafiya?" Husnah ta fa'di tana mai zama bakin gadon ta yayin da ta folding left hand 'din ta a 'kirjin ta tana mai cigaba da sauraran wayar tare da bada dukkan hankalin ta akai. Mahaifiyar ta sai tace" Lafiya lau Alhamdulillah...ya makarantar?" " Qalau Mummy gamu nan duk ma ba'a dawo sosai ba ba wani da'di school 'din". Tayi maganar tana wani yatsina fuska kamar gaske. Mummyn sai tace" Zasu dawo ai ba abin damuwa bane may be ma duk yau ku gansu". " Hakane Mummy". Husnah tace tana 'dan sosa tsakankanin kitson dake kanta. Bu'dan baki tayi kamar zata fa'di abinda ke cikin ranta "..umm Mummy" Sai kuma tayi shiru. Da kulawa Mummyn tace" Me ke faruwa ne Husnah sanar da ni mana". Sai da ta sanya dauriya cikin maganar ta kafin ta iya furta" Mummy dama tambayar ki zanyi" " Ina jinki, me yafaru?" " Mummy akwai abinda ya faru ne bayan tahowa ta?" " Wani abu kamar me kenan?" " Wai nace ko kinji wani abin, amma shikenan kawai ya wuce". A masifance Mummyn Husnah tace" Kamar ya shikenan ya wuce, ni 'din sa'ar ki ce ko kuwa 'kawar ki ce da zaki sa ni gaba da guntayen magana ko kuwa tsabar kin raina ni?" Cikin shagwa6a tace " Afuwan..ba haka bane fa Mummy, dama nayi tunanin ko kin sami labari ne amma shikenan ya wuce". " Husnah...ban son iskanci fa..." Saurin taran ta tayi da fa'din" Allah Mummy ba komai in akwai ai kin san zan sanar dake". " Kin tabbatar?" " Erh Mummy" " To shikenan ayi karatu banda wasa ko". " Uhmm". Daga haka suka yi sallama kowa ya ajiye wayar. Sai dai wannan wayar da Husnah ta 'kira 'din sosai ya 'daga hankalin mahaifiyar ta, tayi saurin nuna mata ta saki ranta ne dan tana so ta binciko dalilin da yasa Husnah yi mata wannan tambayar. Yayin da 6angaren Husnah abin ya sake 'daure mata kai, ta tabbata kalaman da Mu'een yai mata jiyan nan da akwai dalilin yin su, sai dai kuma tana tunanin maganar daga 6angaren sa ta taso bai shafe ta ba....to ko dalilin kenan da yasa shi 'dauke min wuta tun isowa ta garib nan?" Ta tambayi kanta, take kuma ta bawa kanta tabbacin erh hakan ne ma. To in kuwa hakane ya zam dole ta nemo dalilin daga wajen sa, batare da 6ata lokaci ba ta ci alwashin hakan cikin zuciyar ta...dole ne tasan abinda yake 'ko'karin 6oye mata. Sai dai ga mamakin ta tun a safiyar ranar Mu'een ya dawo mata a yanda ta saba ganin sa, wannan ba'kin halin duk ya kau, yazo mata ne a asalin masoyin ta Mu'inuddeen. Husnah kam taji da'din hakan sosai har ma ya sanya ta manta duk damuwoyin da take ciki da al'kawarin da ta yiwa ranta....haka suka cigaba da rayuwar su cikin farin ciki kamar da can baya. Lokacin da ta samu tsarki kuwa batare da 6ata wani dogon lokaci ba suka 'dora daga inda suka yi madakata, balle dama gashi duk sunyi missing junan su...ai hikenan. ***** 'Bangaren Alhaji Baba kuwa tun washe garin tafiyar Yah Deen ya tura wani amintaccen yaron sa Yusha'u can cikin garin Azare da sunan mahaifin Husnah da yake shima yayi zaman garin so bai wani sha wahalar gano inda Alhajin ya turasa ba, inda yaje domin yai masa kyakkyawan binciken da ya dace game da ita. Cikin kwanaki biyu kacal ya kammala ya dawo, akan 'dan wannan tafiyar Alhaji Baba sadaukarwar 100k yayi saboda tafiyar, hatta da hotel 'din da Yusha'u yayi masau'ki da sauran abubuwa duk cikin ku'din yayi su, hakan ma lokacin dawowar sa ya dawo da canjin kusan 30k amma Alhaji Baba ya bar masa saboda jin da'din labarin da ya zo masa da shi. Dama can mahaifan Husnah mutanen kirki ne na gaske basu da abokin gaba balle 'yan tsama, sai dai mahassada. Duk iya binciken Yusha'u bai ci karo da komai da ya danganci 6atanci ga iyayen Husnah ba, ita ka'dai suka haifa daga ita Allah bai sake basu wata haihuwar ba, sannan mahaifin Husnah ri'ka'k'ken 'dan kasuwa ne da ya shahara ta 6angagori da dama, ya tara dukiya fiye da zaton mai karatu, sai dai Allah bai bar shi ya rayu cikin iyalan sa ba da mafi soyuwa cikin zuciyar sa wato Husnah. Yawan takurawar da wani wansa ke yi masa ne kan ya bashi kaza yau kaza gobe kaza yafi damun sa, ya gina masa gida mai girman gaske kwatankwacin wanda yake ciki da iyalen sa, ya kai sa Hajji har sau uku wanda shi kansa mamallakin dukiyar ma zuwan sa Hajjin sau biyu ne, matar sa kuma sau 'daya amma dan kawai ya faranta ma Yayan nasa rai ya sanya shi biya masa har sau uku, ya kuma biyawa uwargidan sa ma taje sau 'daya, ya 'dau nawin karatun 'dansa Hisham har Cyprus yaje ya kammala kuma cikin saa yanzu haka yana aiki a Abuja...amma duk wannan abin bai sa wan mahaifin Husnah Alhaji Mamman ya bar 'kanin sa ya sake da dukiyar sa ba. Ya kan zo da bu'kata ta ku'di a duk lokacin da ya ga dama kuma ku'di masu nawin gaske, haka mahaifin Husnah zai bashi check idan bashi da cash a hannun sa, bai ta6a nuna masa 6acin ransa game da hakan ba. Amma duk ranar da ya kuskure yace ya bashi lokaci idan ya tambayi ku'di to kuwa ranar mahaifin Husnah ya taro march har da August ma kuwa, domin masifa zai sashi a gaba yanayi kamar 'dan cikin sa da ya haifa, duk wasu alkhairan da yai ta masa abaya mantawa da su yake yi ya dinga ya6a masa maganganu son ransa kan cewa yana yi masa wula'kanci dan yaga Allah ya hore masa dukiya. Sosai irin wannan abin ke 6ata wa mahaifin Husnah rai amma sai yake dannewa kawai yake dauriyar bashi duk yawan ku'din da ya bu'kata. Mummyn Husnah bata ta6a saka musu baki cikin maganar su ba illah idan taga yayi shiru yana tunani sai ta bashi ha'kuri da kalamai masu da'di da kwantar da hankali tana kuma sake nuna masa muhimmancin dangin sa agare shi. Musamman ma da yake tasan cewa lafiya ba isan sa tayi ba. Ciwon hawan jini yake da ga kuma Diabetes duk shi ka'dai. Shekarun Husnah 15 lokacin tana Ss1 aka yi kidnapping 'din ta...imaging fa tashin farko 50million aka nema daga wurin iyayen ta, sosai hankalin mahaifin Husnah ya tashi...hakan yasa ya tattaro duk abinda ya san mallakin sa ne ya dun'kula ya samo million hamsin. Tun faruwar abin sau 'daya tak wansa yazo yayi masa jaje, waya ma sai sai dai mahaifin Husnah ya 'kira shi idan ya matsu, lokacin da ya tattara ku'da'dan kwanan Husnah hu'du a hannun kidnappers 'din, amma idan kaga mahaifan ta sai ka tausayawa yanayin yanda suka koma saboda damuwa. A bayan mota ya jefa jakar da ku'din ke ciki, yana tunanin hana shi sako hukuma da akayi cikin lamarin, haka yaja mota da kansa ya nufi gidan wansa da nufin sanar da shi cewa ku'din sun kammalu zai kai. A gida ya same shi a can 6angaren sa dake da girman gidan da wasu iyalai kimanin mutane goma zasu iya rayuwa cikin farin ciki a ciki...kishingi'de yake idanun sa a lumshe, a haka mahaifin Husnah yaje ya tarar da shi, bayan sun gaisa sai yake sanar da shi cewa ku'din sun samu zai kai yanzu ya kar6o Husnah. Fuskar sa babu alamun alhini yace" To shikenan sai ka dawo, gashi sun ce kai ka'dai suke bu'kata ba dan haka ba ai da na raka ka mun je tare" " Bakomai Yayah..." Bai kai ga rufe bakin sa ba Alhaji Mamman ya tare shi da fa'din" Amma ka tabbatar ba ka sa hukuma cikin lamarin ba kamar yanda suka bu'kata ko? dan banaso a salwantar min da rayuwar 'ya a banza ". Mahaifin Husnah cikin sanyin jiki yace " A a Yayah ban sa da su ba ni ka'dai zani" " To to je ka Allah ya bada sa'a, idan ka kar6o ta ka kawo min ita nan gidan dan na lura ku jin da'din ku kawai kuka sa agaba baku damu da rayuwar ta ba, idan baku so ni ina son kaya na". Ya 'karashe maganar a masifance. Mahaifin Husnah fita kawai yayi yana fa'din" sai na dawo" Tare da ayyana wai har wani ne zai iya kwatanta irin son da yake yiwa Husnah ya kuma ce wai baya son ta bai damu da ita ba?...shi kansa sa yasan soyayyar da yake yi mata ya rinjayi wanda yake yiwa kansa ma. Da wannan tunanin ya fice daga 6angaren ya nufi inda yayi parking motar sa..wan nasa ko irin ya biyo shi yaga ku'din ma bai yi ba. Har ya bu'de mota zai shiga kuma sai yaji tsoro ya diran masa nan take, rufe motar yayi ya koma 6angaren Yayan nasa da nufin ro'kon sa akan ya taimaka suje tare ko zai 'dan ji 'kwarin gwiwa ajikin sa. 'Kofar babban parlour a bu'de take sai labile da ke sau'ke hakan yasa shi 'dagawa ya shige ya tunkari bakin sitting room da ya samu Yayan nasa aciki 'dazu. _Sai dai me?_ Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *_Marubuciyar littafin CAPTAIN ABBAS_* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *45* Irin kalaman da yaji Yayan nasa na furtawa ne suka matu'kar jijjiga shi, take ya 'dimauce idanun sa suka firfito waje, jijiyoyin kansa suka yi ru'du-ru'du.... Da hannu ya nuna inda Alhaji Mamman ke tsaye ya juya masa baya yana amsa waya bai ma san da cewa ya dawo 6angaren ba...dan haka sai ya cigaba da amsa wayar sa cikin kwanciyar hankali yana sake bada orders 'din yanda yake so abin ya kasance. Bai san meke faruwa ba kawai sai jin fa'duwar abu yayi a 'kasa wanda ya sanya shi waigowa a rikice cikin hanzari da firgicin kar wani ne ya jisa har bai san lokacin da wayar ta fa'di a hannun sa ba ta tarwatse a 'kasa. Ai kuwa ganin 'kanin sa Alhaji Hamza kwance a wurin ya matu'kar 'dimauta shi, ga dukkan alamu ma suma yayi, gumi ne ya fara karyo masa nan take saboda tashin hankali. Kafin ya gama tantance abinda ya kamata yayi sai ga uwar gidan sa Hajiya Kareemah ta shigo 6angaren nasa da sallamar ta, ganin baya palourn ya sanya ta direct ta nufi hanyar bedroom 'din sa sai dai bata 'karasa ba lokacin da ta iso daf da 'kofan sitting room 'din sa sai tayi tunanin ko yana ciki, hakan yasa ta 'dage labilen kawai da yake dama da nufin dubawa kawai da le'ka so lokaci guda ta 'daga labilen gami da sallama a bakin ta. A dai-dai lokacin Alhaji Mamman na shirin cire babbar rigar da ke jikin sa saboda yanda yaji tamkar ta takurashi tana sha'kesa, yayin da mahaifin Husnah ke kwance a 'kasa baya numfashi. A rikice ta 'karaso ciki tana binshi da idanu bakin ta cike da tambayar abinda ya faru amma ta kasa furtawa. Da 'kyar ta iya harha'do kalmar " Lafiya...Alhaji me ya faru?" Ko 'kala bai iya yace da ita ba tsabar yanda ya ru'de, fuskar sa ka'dai zaka kalla ka fahimci ba a dai-dai yake ba. Bayan fahimtar cewa suma Alhaji 'karami yayi yasa Hajiya Kareema da 'dan gudu-gudu ta nufi fridge ta 'dauko ruwa mai sanyi tazo ta yayyafa saman fuskar sa, yayin da Alhaji Mamman ke tsaye yana faman firfita da hular sa dake ri'ke a hannun sa, ji yayi komai ya kwance masa. A hankali mahaifin Husnah ya bu'de lumsassun idanun sa ya sau'ke su akan fuskar Hajiya Kareema then kan Yayan sa da suke uwa 'daya uba 'daya wato Alhaji Mamman. Rintse idanu yayi a hankali hawaye ya gangaro ta gefe da gefen idanun sa saboda takaici...".... _Zai zo wurin ku ya kammala ha'do ku'da'den, yanzun nan ma ya bar wuri na bayan ya sanar da ni..so ku kula da komai bisa tsari saboda 'dan uwa na ne shi ban son ku bar kafa ko ka'dan da za'a iya fahimtar cewa da hannu na cikin lamarin..... sannan ina fatan baku illata yarinyar ko ka'dan ba ko?"_ Bai ji abinda aka fa'di daga 'daya 6angaren ba sai ji yayi Alhaji Yayan nasa yace" _To shikenan ku dai ku tabbatar bai zo da kowa ba kafin a sake ta dan bana son hukuma ta shiga cikin maganar kasan tonuwar asirin ku tamkar tonan nawa asirin ne and i hate that..."_ Abinda kawai zai iya tunawa kenan da yaji wan sa ke fa'di...wanda tashin farko kalaman yayan nasa suka bayyana masa cewa yana da hannu dumu-dumu kan sace Husnah da akayi. Yana kwancen yake tambayar zuciyar sa" miye dalilin hakan? Ashe 'dan uwa bazai ta6a sakin ransa ya rayu da 'dan uwan sa cikin amana da gaskiya ba? Kuma wai duk akan dukiya da Allah ne ke bada ita..." Zuciyar sa nawi yake jinta ga numfashin sa take ya sar'ke sa yake fita da 'kyar, banda hawaye babu abinda yake iya yi a wannan halin. Cikin ransa sa yake jin kamar ya tashi yayi ta jibgan yayan nasa har sai ya illata shi saboda cin amanar da yayi masa, ya nuna masa dukiya tafi masa komai a rayuwar nan ciki kuwa harda zumuncin da Allah ne ya ha'da tsakanin su yayo su daga tsatso 'daya, to laifi ne dan Allah ya fifita 'dan uwanka akan ka? Laifi ne dan Allah ya bawa 'dan uwanka dukiya kai bai baka ka? Shin kasan naka kyautar da ya ajiye maka? 'Kilan duk zafin neman ka ba zai ta6a baka dukiyar ba saboda babu ita cikin 'kaddarorin rayuwar ka ta duniya to meyasa zaka takurawa kanka? Idan kayi ha'kuri ma kabi Allah kabi manzon sa kayi tawakkali babu mamaki ka dace da samun taka dukiyar acan matabbata tana jiran ka, inda ko wani abu zakayi da shi ba zai ta6a 'karewa ba sannan Allah ba zai ta6a gajiya da baka ba, haka nan kuma ba zai ta6a raba ka da aljannar sa ba..to menene yafi wannan fisabilillahi..?" ( ALLAH KASA MU DACE DA NI'IMAR KA DUNIYA DA LAHIRA) " Amma wannan wace iriyar rayuwa ce, ashe mutun ba zai iya ri'ke 'kaddarar da Allah ya 'dora masa ba sai ya nuna nasa ikon ta hanyar da be dace da karantarwar musulunci ba, me yasa muke zalunci muke dagewa da cewa sai mun yi arzi'ki ko ta halin 'ka'ka bacin a littafin 'kaddarar mu Allah bai tsara hakan ba?. Hawaye yake ta zubowa amma bai iya ya furta komai ba yana jin muryar Hajiya Kareema nata 'kiran sunan sa" Alhaji 'karami!..Alhaji 'karami!!.." amma sam ba zai iya amsa mata ba kamar yadda ya kasa motsa koda 'dan yatsan sa ne dake jikin sa. Har a lokacin kuma bai ji muryar Alhaji Mamman yace komai ba yayin da shi kuma ta 6angaren sa ido kawai yake iya rolling amma haushin ganin wan sa tsaye akan sa sai ya hanashi sake bu'de idanun illah hawaye da yake fitarwa. Ganin haka ya sanya Hajiya Kareema a rikice ta mi'ke tana fa'din " Alhaji akai shi asbiti mana ga dukkan alamu fa yana jin jiki..." Shiru bai kulata ba saboda damuwar dake cikin ransa ta isheshi, imaging yanda zakaji idan an kama ka da hannu dumu-dumu bisa cin amana, amanar ma ta jinin ka, 'kanin ka, mabiyin ka da kuka fito ciki 'daya, bayan ko Allah ya san irin 'dawainiyar da yake yi maka amma duk da haka ka ci amanar sa kuma ya kama ka...ya zaka ji please?...kun san ba sau'ki.." Wannan dalilin ne ya sanya shi komai ya tsaya masa cak ya kasa aiwatar da komai a 'adakin hatta maganar da Hajiya Kareema tayi ma bai ji ta ba hakan yasa bata samu amsa daga gare shi ba. Ganin hakan ya sanya ta jijjiga shi da 'karfi tana sake maimaita abinda ta fa'di domin tunanin ta ko duk ya ru'de ne saboda ganin 'kanin sa kwance babu lafiya. Jijjiga shin ke da wuya kuwa take sai ya dawo hayyacin sa, kallo 'daya yai mata sai ya 'dauke idanun sa daga kanta, kowa ma yanzu kunyar sa yake ji gani yake tamkar itama ta san abinda ya aikata. Baya yayi ya zauna bisa kujera yana sakin numfashi mai mugun numi...batare da ya furta komai agare ta ba. Da fahimci kamar baya hayyacin sa sai tayi hanzarin barin 'dakin da gudu Hajiya Kareema tayi waje ta 'kira driver mai gadi da masu aikin ta suka cicci6e shi suka kai mota, sannan ta tafi ta zaro mayafin ta suka wuce asbiti da shi while Alhaji Mamman na nan inda yake bai ko motsa ba, kallo 'daya zaka yi masa ka fahimci ba'a hayyacin sa yake ba wanda in baka sani ba dagaske zakayi zaton ko tashin jikin 'kanin nasa ne ya sanya shi hakan...sai dai shi ka'dai ya san girman kunya da takaicin da yake ciki a wancan lokacin. Sai da ya tabbatar sun bar gidan gaba 'daya kafin ya samu ya sawa ransa 'kwarin gwiwa ya sake 'dauko wayar sa a inda ta fa'di, harha'dawa yayi wannan karan sai da ya 'dan le'ka gudun kar wani ya sake jin sa, duk da kuwa yasan cewa kishiyar Hajiya Kareema bata gari a lokacin amma hakan bai hana shi tunanin itama kar tazo ta jishi ba abinku da marar gaskiya. 'Kira yayi ya bada umarnin akai Husnah 'kofar gidan mahaifin ta a sau'ke ta nan kawai suyi tafiyar su yace daga baya zamu ha'du mu kammala deal 'din. Hakan kuwa akayi, domin mahaifiyar Husnah na nan zaune tayi tagumi tana jiran isowar 'yar ta da yake tasan mahaifin ta ya fita da ku'din amsar tata(ransom), tare suke zaune da wasu 'yan taya ta jaje 'kalilan daga dangi sai da wasu makwabtan ta mafi kusa. Kamar daga sama ta fara jiyo tashin kukan Husnah yana tunkaro ta ai kuwa da gudu ta tashi ta fita itama tana kukan ta rungume ta. Sun 'dauki tsawon lokaci suna a haka tana ta godewa mahallici a fili da zuci...sai da ta 'karashi murnar ta saura na tayata kafin ta tambayi Husnah ina mahaifin nata kuma ya tsaya ganin har a lokacin bai shigo ba kuma bata ga motar sa ba a harabar gidan. Husnah ce tace itama bata ganshi ba...tace mutanen sune suka kawo ta har gida. Sauran dake tare da Mummyn Husnah wasu salati suka sanya da mamaki suke fa'din" Har gida suka kawo ki da kasu..tashin hankali?" Mummyn Husnah kam batayi mamaki ba da jin cewa sun san har gidan su damuwar ta mai gidanta ne kawai. Amma menene abin da zai sa ta dami kanta dan sun har gidan su, tunda kam har suka iya sace ta a makaranta ai zuwa har gidan mahaifin ta ma ba zai gagare su ba...duk kuwa da tasan cewa yanda suka yi abin ba abu ne mai 'daure kai ba. Drivern da yake 'dauko Husnah aka tsare da bindiga ya jawo su zuwa makarantar cikin motar da yake kaiwa da 'dauko ta daga scool 'din, bayan an tashi su Husnah tazo ta shiga sai suka 'kara sashi ya ja motar suka yi gaba, Husnah har na gaida su ganin ba'ki har mutun biyu cikin motar duk kuwa da cewa fuskokin su sanye suke da ba'ka'ken face mask, basu amsa gaisuwar tata ba ma dan hakan sai ta kalli drivern ta tambaye shi su wanene...shima 'din bai kulata ba cuz shi ka'dai ya san halin da yake ciki. Dan haka itama ganin babu mai niyyarf magana cikin su ya sanya ta ja bakin ta tayi shiru, yayin da driver yayi tsuru yana cigaba da driving ji yake kamar yayi ta tsala ihu har aka musu 'dauki amma ina no way...cuz gefen cikin sa bindiga ne hakan yasa ya cigaba da jan motar suka yi nisa suka zo inda babu mutane sosai sannan yaga wata ba'kar mota mai ba'kin tinted glass ta sha gaban su, dole tasa yaja yayi parking. Yana tsaya yaga sun bu'de sun fita tare da dakawa Husnah tsawar ta fito a firgice ta fita 'dayan ya tisa 'keyar ta zuwa 'dayan motar yayin da 'dayan ya tsaya ya bugawa driver gindin bindiga akan sa dan kar ma yayi tunanin binsu abaya, take kuwa ya kifa kanshi bisa sitiyari ya suma. Tun daga lokacin da suka sa ta shiga motar Husnah bata 'kara sanin kanta ba bata 'kara sanin komai ba sai tsintan kanta tayi a wani gida da bata san ina ne ba..amma basu ta6a lafiyar ko 'dan yatsan ta ba. Sai bayan wasu mintina sannan drivet ya dawo hayyacin sa bayan har dan taru akansa ganin kansa da 'dan jini-jini. A gigice yayi musu takaitaccen bayani sannan ya ja motar yana zubda hawaye ya koma gida ya sanar da iyayen Husnah abinda ya faru...Alhaji Mamman ne ya fara 'dora zargin sa kan Nasiru driver har yaza aka kama shi aka kulle da fa'din wai duk munafurci ne, tun ranar ake gana masa azaba wai adole sai ya amsa cewa shi ya sace Husnah amma ya kasa amsawa saboda yasan ba shi bane...'yan sandan da kansu sai da ya fara basu tausayi suka zuba masa idanu kawai duk ya fita hayyacin sa yayi zuru-zuru da shi amma babu wanda zai iya fahimtar sa sai Allahn sa. Tun daga ranar da aka sace Husnah iyayen ta basu sake natsuwa ba har yau da Husnah ta dawo gida hannun su, ko jiya ma sai da mahaifin ta yaje station wurin Nasiru driver yana kuka yana ro'kon sa kan cewa idan shine ya taimake shi ya sanar dashi inda Husnah take, yace shi ko duk dukiyar sa suke so duk zai basu amma dan Allah kar su ta6a masa lafiyar 'yar sa, kar su lalata mata rayuwa matsauin ta na ya mace matashiya su rufa masa asiri...amma Nasiru kuka kawai ya ringa yi bai iya ya furta komai ga mahaifin Husnah ba ya riga ya mi'ka ma Allah kansa bashi da wata mafita...dan shi yawan ku'din da yaji mahaifin Husnah yace anne ma a wurin sa ma ka'dai sun 'daga hankalin sa duk dama dai yasan Alhajin zai iya bafawa amma sosai hakan zai na'kasa tattalin arzi'kin sa...yana kukan yake ro'kon Allah ya tsare al'ummar musulmi daga dukkan azzalumai da masu sharri...to shi me zai sashi yincwannan 'danyen aikin da banda 'diban alhaki babu komai cikin sa, duk mummunan yanayin da yake ciki hakan bai sa ya kasa tausaya wa yanayin da Alhaji Hamza ya koma saboda 6acewar 'yar sa ba duk ya zama wani iri da shi ya fita hayyacin sa, hakan ma shine da yake matsayin namiji to inga mahaifiyar ta? Tausayin ahalin ne ya sake ratsa shi...hakan yasa cikin ransa yake addu'ar" ALLAH ya bayyana ki Asma'u, Allah ya tona asirin duk wanda ya zalunce ki ya raba ki da iyayen ki, yarinya mai hankali da natsuwa abin alfaharin ko wani irin mutun, Allah ya tsare miki mutuncin ki kamar yanda mahaifin ki yake fata". Haka har Alhajin ya bar inda yake bai furta komai agare shi ba...da ikon Allah kuma yau sai ga Husnah cikin gidan mahaifin ta cikin 'koshin lafiya. Mummyn Husnah kam banda hamdala babu abinda take yi, godewa Allah kawai ta ringa yi da dawowar 'yar tata duk da kuwa zuwa lokacin hankalin ta ya kasu gida biyu ne amma a hakan ta basar farin cikin ya rinjayi tunanin inda mahaifin Husnah ya tsaya...ta bari akan cewa duk inda yake ai soon zai dawo ta sani. Sai da suka gama koke-koken su kafin ta Husnah ta shiga wanka yayin da take jin tamkar ta shiga bayin ta yi mata wankan da kanta saboda so, wani zazzafan 'kaunar 'yar tata ne ya ninku mata cikin zuciya da yasa bata so ko nan da can ace Husnah ta matsa batare da ita ba, tun shigar Husnah wankan Mummyn ta bata zauna ba, ta gyara nan, ta kimtsa can duk sai ta rasa takamamman abinda ya kamata tayi ma gaba 'daya. Sai dai duk da haka tunanin ta bai kauce kan binciken ingancin lafiyar Husnah ba, farin cikin da shiga bai sa ta mance hakan ba, tsoro take ji kar sunyi mata wani abin, sai dai ta bari cikin ranta da niyyar sai Husnah ta huta kafin su tattauna. Tuni ta fitar mata wata doguwar riga mai kyan gaske da duk abubuwan da tasan zata bu'kata wurin shirya kanta. Koda Husnah ta fito daga bayin Mummyn ta da kanta tai mata drying na gashin ta da hand dryer sannan ta bata dama ta shirya cikin doguwar rigar da ta ciro mata, kafin hakan sai ta wuce kitchen dan samar mata abinda za ta ci. Mintina 'kasa da talatin ne suka 'dauke ta shirya abincin ta kawo mata. Wannan karan a palour suka zauna dukkan su da sauran mutanen da ke cikin gidan tare da su. Kowa yayi matu'kar farin ciki da bayyanar Husnahn, haka aka zauna ana maida zance ana kuma tuno ire-iren abinda ya fari da Husnahn ana bada misalai da su, yayin da Husnah ke cin abincin ta cikin natsuwa tana sauraren su...tana kuma sake tunanin irin rayuwar da tayi acan da mutanen da bata sani ba. Ko mutun 'daya bazata ce ga kalar fuskar sa cuz basu ta6a gangancin zuwa inda take babu face mask ba wanda hakan ya kasance umarnin Alhaji Mamman ne, basu ta6a cutar da ita ko da wasa ba, dan ko bakin farcen ta babu wanda ya ta6a mata sam cikin su babu wanda yayi gigin kusanta kansa gareta, sun bata damar yin sallah sannan basu 'daure ta ba kawai 'dakin da take ciki ne kullum ba'a barin sa a bu'de, daga an kawo mata abinci da ruwa sai a sake datsewa ta waje...sau 'daya magana ya ta6a ha'da ta da wani shine ranar da aka ha'da ta da mahaifin ta cikin waya ranar ne ta san dalilin kama ta da suka yi, domin a lokacin taji mahaifin ta na fa'din ko nawane zai bayar shi dai su taimaka su sakar masa ita ta dawo gida...ranar kusan kwana tayi tana kuka da tausayin iyayen ta, shiyasa ma ta ringa addu'ar Allah ya kawo sanadin da zata bar hannun si cikin sau'ki...sai gashi kuwa da kansu sun 'dauko ta sun dawo da ita gida batare da sun yi mata komai ba. Wannan tunanin da tayin ne ya sanya ta tunowa da mahaifin ta lokaci guda dan haka sai ta dubi mahaifiyar ta tace" Mummy ki 'kira Daddy na awaya mana kice masa na dawo ya daina nema na". Take sai Mummyn Husnah ta 'dago wayar ta bayan ta jinjinawa Husnahn kai alamar gamsuwa da maganar ta. 'Kiran sa tayi da niyyar taji inda ya tsaya duk da ma dai tasan inda aka tura shi kaiwan ku'din da nisa sosai cuz can wajen gari ne amma ai tunda Husnah har ta dawo gida shima 'din kama ta yayi ace ya iso. Sai dai ko tayi 'kiran sa sai bai 'daga wayar ba, missedcall uku ta jera masa ganin bai 'daga ba ya san ya ta tura masa text 'din albishir cewa Husnah ta dawo...ashe ma wayar tasa bata jikin sa tana cikin motar sa dake gidan Alhaji Mamman. A fili tace da Husnah" Na 'kira bai 'daga ba, amma na tura masa text". Shiru Husnah tayi yayin da sauran suka cigaba da hira bayan sun bata 'kwarin gwiwar cewa" Hakan ma yayi idan ya ga text din ma zai 'kira ko kuma yayi hanzarin dawowa ma gaba 'daya...". Duk abincin taji tafi ce kanta shiru kawai tayi komai ya kwance mata. Mahaifiyar ta ne ta lura da daina cin abincin da tayi sai tace" Eat mana Husnah..ki kwantar da hankalin ki kinji very soon zaki ganshi ya dawo da yardar rabbi". "..To Mummy..Allah ya kawo shi lafiya, amma ni na 'koshi da abincin ne". Kafin Mummyn Husnah ta sake fa'sldin wani abu sai wayar ta ta 'dauki 'kara, lokaci mintina takwas ne da 'kiran da tayi masa, da sauri ta 'dago wayar da tunanin ko shine ya 'kira amma sai ta ga sunan Hajiya Kareema ke yawo kan fuskar wayar. Nan take kowa dake palourn suka yi tsit kamar 'daukewan ruwan sama suka baza kunnawa suna kallon Mummy da son jin abinda ke tafe da 'kiran wayar da akayin. Afili Mummyn Husnah ta furta" Hajiya Kareema ce ta 'kira, ta fa'di hakan ne dan su san cewa ba wanda ake tsammanin bane. Nan Hajiya Kareema take gaya mata cewa ai Alhaji 'Karami is unconscious yana asbiti ma yanzu haka....ta 'karashe maganar da sanar mata sunan asbitin da suke. A rikice mummyn Husnah ta sa hannu aka tana sakin salati at same time tana kuka da hawaye wanda ya janyo hankalin Husnah da sauran izuwa gare ta... Tsaye Husnah ta mi'ke a rikice tana fa'din" Mummy lafiya me ya faru kuma?" Tayi maganar tana mai tahowa inda mahaifiyar tan take 'karara fuskar ta ta nuna alamun damuwa...Sauran ma tambayar da suka jefa mata kenan irin ta Husnah. Tana cikin kukan tace da su" Wai bashi da lafiya yana asbiti". Take palourn ya ru'de da salallamin jajantawa. Mummyn Husnah kam cewa tayi" Wanda zashi ya shirya da sauri mu tafi...waiyo Allah na sun illata min shi". Ta 'karashe da fa'din hakan tana nufar 'kofan fita. Su hu'du suka tafi asbitin ciki harda Husnah, isar su asbitin ke da wuya sai ta sake 'kiran Hajiya Kareema ta kwatanta musu inda suke take suka nufi wurin sai dai likita ya hana su shiga saboda gudun hayaniya kuma wai zasu yi yawa a 'adakin. A rikice Mummy tace" Doctor iyalan sa ne mu fa dan Allah karka yi mana haka...ki bar mu mu ganshi please bazamu yi hayaniya ba". Tana hawaye tayi maganar, Husnah kam kuka harda sheshshe'ka take yi bata iya fa'din komai ba, sauran matan ma sai suka shiga ro'kon likitan amma ya kafe shi sam a a. Hajiya Kareema na jin dramar tasu tana daga ciki ta fito da yake itan babbar likita ce a hospital 'din sai tace da likitan ya bar su su shiga 'kilan ganin 'yar san zai sanyaya masa rai duk dama tun zuwan su bai bu'de idanun sa ba, amma halin da yake cikin ya tsananta sosai...ga mutuwar gangar jiki saboda hawan jini sannan ga heart attack abin ba sau'ki gaskiya dole atausaya mai...bata iya ta bayyana farin cikin ta afili da ganin Husnah ba illah kawai ta janyo ta ta rungume ta tale kuma sai ta sake ta ta bata damar zuwa ta gana da mahaifin ta...daga haka ta wuce ta nufi office 'din ta. Duk da Hajiya Kareemah tayi magana amma sai yace baza su shiga dukkan su ba dole sai dai da bibbiyu tunda su hu'du ne. Nan sauran suka ce to Husnah ta shiga tare da mahaifiyar ta in yaso su 'din sa shiga daga baya. Ana barin su shiga kuwa Husnah da gudu ta isa ta fa'da jikin mahaifin ta tana kuka, yayin da mahaifiyar ta ma ta dur'kushe nan 'kasan tiles 'din 'dakin tana kukan itama ganin sa kwance shame-shame kamar ba shi ba, duk da tayi zaton ganin sa jina-jina ne saboda tunanin ko 'yan kidnappers 'din ne suka illata shi da tayi, musamman da ta tuna yanayin da Nasiru driver ya dawo musu gida rannan, amma ga mamakin ta sai ta gansa haka babu wani alamun ciwo tattare da shi..duk da haka bata fasa yin kukan ba cikin ranta take ayyana Allah yasa ba na'kasa ta ciki aka yi masa ba..domin sau 'daya idan ka dibe shi zaka fahimci cewa yana jin jiki sosai. Jin muryar Husnah cikin kunnuwan sa ne ya sanya shi bu'de idanu ya sau'ke su akanta yana 'dan murmushi da daga gani kasan na 'karfin hali ne..." Daddy please ka tashi gani na dawo,l..ka ganni ko Allah Daddy bazan sake tafiya in barka ba.. wake up Daddu please". Haka kawai take ta maimatawa cikin kuka, yayin da mahaifinta ke binta da takaitaccen murmushi da shi ka'dai ya san ma'anar sa. A hankali ya kai idanun sa kan mummyn Husnah dake 'dan nesa ka'dan da shi sai ya tsura mata idanu kamar me shirin bata sa'ko ko kuma wanda yake so ta karanci wani abu cikin 'kwayar idanun sa. Lokacin da yake kallon nata sai idanun sa suka cicciko da 'kwalla, ganin hakan yasa take sai ta matso kusa da shi ta kama hannun sa tana yi mai sannu Alhaji. Tari ya fara a hankali amma akai-akai wanda da kaga yanayin yanda yake tarin zaka fahimci cewa cikin azaban ciwo da ra'da'di yake yin ta. A rikice Mummyn Husnah ta umarci Husnah da taje ta 'kira likita suzo a sake duba shi in bazai yiwu ba sai su wuce Zaria kawai dan bazata iya juran ganin Alhaji cikin wannan yanayin ba. Da gudu Husnah ta fita yayin da mahaifin ta ya cigaba da tarin da yake yi amma a hakan ma sai da ya bi bayan ta da idanu...da 'kyar cikin tarin ya iya furta sunan..." Fa..tee..ma" bayan ganin fitar Husnah wanda tun kwanciyar sa bai iya furta komai ba sai yanzun Allah ya bashi ikon yin magana karo na farko. Ita da bata san asalin abinda ya faru ba kawai sai tace" Na'am Alhaji ka kwantar da hankalin ka ga Husnahn ka ta dawo ai ka ganta da idanun ka ko?" Bai bi takan maganar da tayi masa ba, burin sa kawai ya fidsa abinda ke cikin ransa, dan haka cikin dauriya yace "...Fateema ki kula min da rayuwar Asma'u...dan Allah, kar ki bawa kowa ri'kon ta ki ri'ke min ita da kanki ki bata tarbiya mai kyau kinji?" Mummyn Husanh take tace " Insha Allahu Alhaji ka kwantar da hankalin ka kai ne zaka kula da rayuwar 'yar ka daina fa'din hakan". Idanu ya lumshe sannan yace "...Ki yafe min Fateemah...ki ce da Husnah ma ta yafe min kinji..da...da" Sai kuma ya kasa 'karasawa saboda tsananin ciwo. Shiru yayi na 'yan sekanni kafin ya sake furta" Fateemah!" Wannan karan itama cikin sanyin murya ta amsa shi cuz jikin ta duk yayi sanyi sosai". "....Duk yanda zaki yi Fateema ki 'ko'kar ta kiga kinsa an saki Nasiru kinji, Nasiru bashi da hannu akan wannan abin...ya gafarce ni nayi komai ne cikin rashin sani...gida na dake...ya fa'di sunan unguwar yace na bashi halak malak ki mallaka masa dan Allah...". Baki bu'de take dubam sa tambaoyi ne fal cike a bakin ta amma sai dai kafin ta yi magana likita ya shigo da Husnah a bayan sa, nan ya nemi su basu wuri zai yi aikin sa, hakan yasa duk sukayi waje badan ransu na son hakan ba. Wannan shine 'karshen ganawar mahaifin Husnah da iyalan sa, awa guda bai 'kara a duniya ba bayan fitar sun Allah ya kar6i ransa...batare da ya sanar da kowa abinda wansa ya aikata masa ba...haka ya tafi ya bar Mummyn Husnah da tarin tambayoyin da shi ka'dai ya kamata ya amsa mata su, amma ina ba dama..domin wanda ya fi ta son shi ya 'dauke abin sa. Husnah tasha kuka da jin rasuwar mahaifin ta hakama mahaifiyar ta, da sauran yan uwa...duk wadanda ya kamata ace an sanar da su duk labari ya riske su, Hisham dake Abuja ma shirin tahowa yake hakama step mothern shi da ta kaiwa iyayen ta ziyara cam garin Kano itama shirin tahowa take hakama sauran dangin su..kowa mutuwar ta ta6a shi sosai...farko 6acewar Husnah sai gashi daga bayyanar ta kuma mahaifin ta yace ga garin ku nan, mutum mai nagarta da halin girma, sanin ya kamatan sa ya shahara ga shi da kyautatawa musamman ga wa'danda suke kasa da shi.shiyasa kowa yaji labarin mutuwar sa sai yaji babu da'di..da yawan mutane tausayin Mummyn Husnah suke yi... Shikam Alhaji Mamman kusan wannan shine abin da yafi komai yi masa da'di a rayuwar duniyar nan (kamar shi 'din gadi zai tsaya yi) musamman ma da ya fahimci cewa babu wanda yasan asalin abinda ke faruwa da sanadin jinyar Alhaji Hamza da har ta kai shi da barin duniya. Cire jakar ku'din dake bayan motar Alhaji 'karamin yayi ya 6oye sannan ya shiga aka kammala komai na hidimar rasuwar dashi. Bayan komai ya lafa ne ya 'dauki motar su ya dan'ka musu, bai damu ba cuz ya san ku'din da ya mallaka zasu iya sayan ashirin 'din motar idan yana so. Babu wani dogon bayanin da yayi musu kamar yadda babu tunanin da mahaifiyar Husnah tayi kan kasancewar motar a gidan sa balle aje ga batun maku'dan ku'din da marigayin ya fita da su, cuz duk zaton ta already ya riga ya kai ku'din ne sannan aka sako Husnah. Bayan kwana arba'in akayi rabon gado aka cire hakkin kowa aka bashi ciki harda na Nasiru driver da Mummyn Husnah ta fa'di wasiyar Alhajin kafin rasuwar sa. Nasiru ya sha kuka sannan yai ta zuba godiya kamar zai ari baki..hankalin sa ya da, kwanta yanzu da yake yaji ance masa Alhaji yace a sake ahi saboda ya fahimci ba shi da hannu kan lamarin. Hatta Mummyn Husnah da ta kawo bayanin sai da aka kusan tuhumar ta akan ta fa'di su wanene to tunda bashi bane..tunani su ko Alhajin ya sanar da ita. Da 'kyar suka yadda cewa bata san komai ba amma sai da ta cike wani form...daga nan ta cigaba da takabar ta har ta 'kare gaba 'daya..Husnah ma ta cigaba da zuwa makarantar ta..nan ne Alhaji Mamman ya nemi ri'kon Husnah ya dawo Hannun sa amma mahaifiyar ta 'ki amincewa musamman ma saboda wasiyyar da mahaifin ta ya bar mata. Tace zata zauna da Husnah koda wani auren zatayi babu abinda zai raba su da ita...balle ma bata tunanin zata sake yin aure har 'karshen rayuwar ta. Da jin hakan sai ya nuna ra'ayin sa na son auren ta...Mummyn Husnah ta nuna 'kin amincewar ta amma sai ya kai zancen gin iyayen ta, mahaifanta sune suka bata 'kwarin gwiwa akan auren sa wai ko ma dan saboda kar Husnah tayi maraicin uba a gaba, hakan ne yasa ta amince da batun auren sa duk kuwa da cewa har cikin ranta ba so take yi ba amma kawai dan farin cikin Husnah...ya aure ta ne a matsayin mace ta uku sai dai basu bar gidan da suke ba suka cigaba da zama agidan da 'yar ta Husnah. Yayin da kansa kullum yake kara bawa Husnah 'kwarin gwiwa akan ta daina damun kanta babu wanda ya isa ya sake yi mata irin na baya, da iznin Allah babu wanda zai sake cutar da ita, ya kanyi mata karyar ai ya zuba securities masu kula da ita dan haka ta daina damun kanta da tsoron zuwa makaranta. Da haka Husnah ta saki ranta ta cigaba da zuwa makarantar ta. Yayin da cikin lokaci 'kan'kani Alhaji Mamman ya zama wani hamsha'ki mai ji da 'ya'yan banki fiye da baya, sosai yake taka naira son ransa, babu wanda yasan inda ya samu ku'da'de sai dai kawai aka ganshi cikin sabon yanayi, hakan ne yasa da yawan mutane ke zargin cewa dukiyar 'kanin sa yake facaka da shi...musamman da aka san cewa matar kanin ma ta zama tashi..... ( Wannan shine ta'kaitaccen tarihin rayuwar Husnah) ***** ......Jin labarin halayyar asalin mahaifin Husnah shi yafi komai yiwa Alhaji Baba da'di, yanzu bashi da damuwar komai illa jiran isowar Uncle Ja'afar, dan yasan ko babu komai ai yasan tushan yarinyar nada kyakkyawan tarihi so bazai yi Allah wadai da kasancewar ta cikin ahalin sa ba, duk dama ya fahimci kan ita yarinyar ke rawa amma ai aure yasha gaban komai, da aje a tafka abin kunya ai gara ace da aure tsakanin su. Take a wurin batare da 6ata lokaci ba ya ciro wayar sa ya yiwa Yah Deen transfer 50k da yake dama bai bashi komai ba lokacin da zai koma school...sai yau yayi ra'ayin da kansa da ya kasance yana cikin kwanaki na hu'du kenan da komawa makarantar. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD* *_Marubuciyar littafin CAPTAIN ABBAS_*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *46* *Bayan wasu kwana ki da komawar su makarantar*        Komai ya gama dai-dai ta tsakanin su, rayuwar su suka cigaba da shimfi'dawa son ransu duk sun manta da damuwoyin da suke ciki kowa ya saki ransa..musamman ma Deen da dama shi abin yafi tsaya masa a rai. *****     Ranar ya kama ranar Monday ne kuma lecture 'daya yake da shi na safe...yayin da Husnah sai 12 take da lecture, hakan yasa ta tattaro kayayyakin ta masu bu'katar wanki kafin cikar lokacin danta 'dauraye su, tana kan haka Mu'een yayi mata sallama ya fita makaranta cikin shirin sa mai 'daukar hankali kamar yadda ya saba. Ba ita ta kammala 'daurayar ba har sai kusan 10:23...sannan ta koma ta na hutawa, bata jima da zama dan hutun ba sai kuma tayi wani tunani dan haka sai ta tashi da niyyar zuwa kitchen ta 'dan dafa musu ko  indomie ma, harta shiga kitchen 'din amma sai ta fasa ganin dacewar yin wanka kafin shiga kitchen 'din cuz sam bata jin da'din jikin ta a haka, wannan dalilin ne ya sanya ta fita daga kitchen 'din ta wuce 'dakin ta dan ta watso ruwa sannan ta dawo kitchen 'din. Kafin ta kammala komai har 11:38 tayi hakan yasa a 'kagauce ta shirya ta fita bata ko kwashe kayan ta dake shanye gaban gidan ba ta bari akan sai ta dawo kawai...gidan ta kulle da yake tasan yana da nashi keys 'din a hannun sa shiyasa bata damu ba. Tana fita sai ta tari adai-daita ya wuce da ita makarantar. Su Mu'een kuwa 12 cif suka fito daga lectures, shi da Ishaq da Imam suke tare harma Ishaq nayi masa 'korafin wai yau 'din sun ganshi wani iri ya babu sakin fuska kamar kwanakin da suka gaba ta..lokacin kafin su gama dai-daita wa da Husnah ne kowa mugun hali ya ringayi musu...bayan hakan kuma sai ya 'dan dawo dai-dai, and still gashi yau ma halin ya dawo. Tsaki kawai ya saki ciki-ciki jin Ishaq zai fara takura masa da tambaya, shi ka'dai ya san damuwar da yake ciki shi kam, cuz tun jiya da Uncle J ya sanar da shi ya taso hankalin sa ya kasa kwanciya sam, tsoron abinda zai biyo bayan tattaunawar Alhaji da Uncle J yake yi...ko 'dazu da sassafe ya 'kirashi sunyi waya sai dai yace da shi yana Gombe amma suna shirin tasowa da yake acan ya kwana saboda doguwar tafiya ce.    Yanda yake jin ransa cikin 'kunci ne ya sanya bai 'kara ko da mintina goma tare da su Ishaq ba kawai yayi musu sallama ya wuce gida abinsa...da tunanin ko zai 'dan samu nutsuwa, sai yanzu yaga wautar sa, da tunda Husnah ta tabbatar masa da cewa babu komai ta 6angaren ta sai ya saki ransa da tunanin ba itan bace Alhaji ke hari, shab ya manta da cewar Alhajin jiran zuwan Uncle J yake yi suyi magana, ya manta ashe isowar Uncle Ja'afar da abinda zasu tattuna shine babbar damuwar sa, duk dama dai yana tunanin Uncle J zai goyi bayan sa ne amma idan Alhaji ya sanar da shi komai fa...shikenan kashin sa ya bushe kenan...da wa'dan nan tunanin ya isa gidan nasa ya bu'de ya shiga bayan ya sallami 'dan sahun da ya sau'ke shi. Akwai research 'din ma da yake son yi ga kuma damuwar da ta dame shi  shiyasa yafi bu'katar ke6ancewa shi ka'dai batare da an takura shi ba...addu'ar sa kawai shine Allah yasa tattaunawar ta su ta kasance masa alkhairi...amma sam baya wani son aure yanzu inda ace ra'ayin sa za'a bi...dama lokacin da Nanne ke raye ne zazzafar soyayyar da yake yi mata ya sashi tunanin auren ta a lokacin batare da ya ko dubi 'karancin shekarun sa ba, yanzu kuwa da babu wata cikin ransa sai yake jin yama tsani zancen auren, in kuwa ya zama dole sai an masa ne ma to Allah ya sa ba da Husnah Alhaji zai ha'da shi ba..sam ba zai iya kallan ta matsayin matar sa a cikin gidan sa ba shi kam. Da shigar sa gidan ya maida 'kofa ya rufe harda datsewa da sakata kamar su Ishaq 'din sunce da shi zasu biyo bayan sa..a palour ya yada zango bai ko nemi abinci ba, batare da 6ata lokaci ba kawai ya fara abinda ya kawo sa. Ya 'dauki a 'kalla kusan awa guda da 'yan mintina zaune a wurin yana aikin research cikin laptop 'din sa, bazata kawai sai yaji 'karar wayar sa tana rurin neman agaji. Sai da ya 'dan saki tsaki kafin ya mi'ka hannu ya lalu6o wayar kamar baya son 'dagawa, ganin sunan da ke yawo kan fuskar wayar ne ya sashi saurin dai-dai ta zaman sa sannan yaja recieve. "...Yaro na gani a Dutse...kana cikin school ne ko kuma kana gida?" Muryar Uncle Ja'afar ne ya fa'di hakan wanda daka ji yanayin yanda yayi maganar ma zaka san cewa cikin tsananin farin ciki yake. 'Bangaren Yah Deen kuwa da jin abinda Uncle 'din yace sai da kansa ya sara masa wani gif..yaji tamkar sau'kar duwatsu a tsakar kansa...cikin ransa ya saki salati..sannan a fili yace" Uncle dagaske?" Idan kaji yanda yayi maganar cike da mamaki zakayi zaton ko tsabar farin cikin da yake cikine ya sanya shi furta hakan, amma ina ba haka bane, tsanar ru'dani ne kawai yasa shi shiga wannan yanayin cuz bai yi zaton zuwan Uncle J har garin da yake ba sam bai yi wannan tunanin ba ma koda wasa. Maganar Uncle J da yaji yana fa'din" Da gaske mana ko in koma ne?" Shine yayi saurin dawo dashi hayyacin sa...cikin rawar murya yace" a a na isa ince ka koma ne Uncle... ina gida yanzu haka". Sai da ya fa'di hakan kafin ya tuna babban kuskuren da ya tafka, sai dai yana shirin sake yin magana yaji Uncle J ya yanke 'kiran...bai ko tambayi address 'din gidan ba da yake tun zuwan Yah Deen na farko da shi akayi komai. Tuni ya jima a tsaye hakan yasa ya dafe kansa da hannun sa 'daya thinking of yanda zai yi ya 6oye zaman sa da Husnah a gidan, yasan idan Uncle J yasan wannan labari cin 'kaniyar sa zai yi bada wasa ba kuwa. Wayar tasa ya jefa kan kujera sannan ya fara waige-waige cikin palourn yana duba ko akwai wani abu da ya shafi Husnah da zai yi saurin bayyana zaman sa da ita amma luckily babu komai da ya dangance ta illah earings 'din ta dake kan center table ajiye. Da sauri ya 'dauka yaje 'dakin ta ya wulla shi...zuciyar sa cike da tunanin me yasa Uncle J zai yi masa haka? Me yasa tun jiya da yau da sukayi bai sanar da shi zai zo ba har sai da ya iso tukunna...ai da ya san cewa Jigawa zai fara zuwa da tuni ya sallami Husnah da komatsan ta kaf ta bar masa gidan sa tuntuni. Kitchen ya shiga nan ma ya fara dube-dube sai dai bai ga komai da zai iya tona asirin sa ba, kitchen 'din tsaf-tsaf babu alamun 'kazanta acikin sa tamkar wanda ba'a amfani da shi, duk kuwa da yana da tabbacin aranar ma bata fita ba sai da ta yi girki, shi kansa yana yabawa da tsabtan Husnah cuz ya san A ce ita 6angaren tsaftar jiki da na muhalli gaba 'daya. Daga kitchen sai ya nufi 'dakin sa nan ma bai ga komai da ya danganci mace ba, cuz daga sun tashi a bacci take tattare komai ta gyara tsab...har bayin sa ya le'ka amma duk bai ga komai ba...duk da haka sai da ya tsaya ya 'kara kimtsa 'dakin yanda Uncle J ba zai zargi komai tare da shi ba...gadon shi tsaf a gyare ga shi ko'ina na 'kyalli tamkar ba mutane ke rayuwa cikin gidan ba... Duk abin nan da ya ke yi kuwa cikin hanzari da rikicewa yake yin komai dan yasan Uncle Ja'afar na iya isowa a kowani lokaci..ya tadda shi. Sai yanzu ma yake jin haushin kansa da ya riga ya furta cewa yana gida, da yace masa yana school kawai in yaso sai yayi gaggawan komawa cikin makarantar su ha'du acan amma ina...ya kwafsawa kansa. Kafin ya baro 'dakin nasa sai yaji daga can waje ana buga 'kofar shiga gidan. A 'dan dake ya fito kasancewar mutun 'daya yake tsammani a lokacin,   abinka da marar gaskiya yana tafiya amma idanun sa tsuru tsuru yana sake bin ko'ina da kallo...fargaba yake yi kar asirin sa ya tonu, in har Uncle Ja'afar ya san cewa da mace yake zama agidan ai yasan kashin sa ya bushe, aure kuwa bai isa yace baya so ba koda mata hu'du aka ce za'ayi masa  saboda hukuncin abinda ya aikata...bai isa ya ja da Alhaji Baba ba ko giyar wake yake sha duk bayan mintina. Sai dai yana fita harabar gidan wani tashin hankalin ya ziyarce shi, dalilin cin karo da yayi da kayan Husnah shanye a igiya a gaban gidan...."Subhanallahi" Ya furta afili sannan da gudu-gudu sauri-sauri ya isa ya fara tattare su yayin da ake cigaba da bugun 'kofar daga waje alamun an 'kosa da bugawa. Da hanzari ya kai kayan 'dakin ta ko shiga bai yi ba ma  watsa su kawai yayi sannan ya jawo 'kofar ya datse da key ya cire key 'din ya kai drawer 'dakin sa ya 6oye...sannan ya sake fita karo na biyu yana gyara zaman rigar da ke jikin sa..at same time yana baza idanuwan sa cikin gidan gudun kar yabar wani abin. Yana cire sakatan 'kofar Uncle J yace" Sai yanzu ka ga damar bu'dewa ko..miye ma na kulle gidan bayan na riga na sanar da kai ina hanya soon?" " Sorry Uncle...bayi na ke ne shiyasa". Yayi maganar yana kar6an jakar dake tare da shi. Murmushi Uncle J yayi sannan ya sa 'kafa ya shigo gidan, Yah Deen nayi mai barka da isowa. A palour suka yada zango Yah Deen yaje ya kawo masa ruwa ya ajiye gaban sa, sai dai bai ma shaba kawai yayi murmushi yace da shi..." Mai ya kaini zuwa wurin 'dan makaranta da ishi, nasha ruwa na tun kafin na iso ni kam". Shima Yah Deen 'din murmushi yayi kawai yayi yana sosa kansa, jin sa yake tamkar akan 'kaya yake tsaye, bai san mai yasa Uncle J yi masa irin wannan zuwan ba sam...shi da yace zai taho kan maganar Alhaji Baba kuma ya akayi ya 'karaso nan. 'Ko'karin zama gefen sa yake sai yace da shi" Ka shammace ni gaskiya Uncle..ban ta6a zaton zaka iso Jigawa ba fa..da na shirya maka better ai..." Ya 'kara she maganar da sigar zolaya. Uncle J bai bi ta kan maganar da yayi ba sai ya 'dan 'kan'kance idanu yana kallon fuskar sa yace " Sai naga ma kamar bakayi murna da zuwa na ba Mu'een ko duk farin cikin zuwan nawa ne ya maida ka haka?" " Ya ka ganni Uncle na canza ne?" Shima ya tambaya yana bin jikin sa da kallo. " Ai yanayin ka ka'dai ya bayyana min halin da kake ciki...meke faruwa da kai to ko zafin karatu ne, gashi ma naga ka baza takaddu ko'ina a gidan". Murmushi ya 'ka'kalo sannan yace " Kamar kuwa ka sani wallahi, kasan yanzu mun zama manya karatu babu sassauci har kaina na 'dan min ciwo ma wasu lokutan". " ..'Kilan baka baccin dare da kyau ne ko?" Uncle J ya tambaya yana kallon sa. Sai yace " Ina yi Uncle kawai damuwa ce ta ishe ni sosai". " Subhanallah..damuwa wace iri kuma Mu'een da baka iya ka sanar min ba tuntuni". Uncle J ya fa'di yana duban sa da kulawa. Kalar tausayi Yah Deen yayi yace" Maganar Alhaji Baba nake ta tunani Uncle, ban san inda maganar tasa ta kwana ba, kuma har yau bai sanar da ni komai akai ba.." "...Ka kwantar da hankalin ka abinda ya kawo ni ma kenan fa musamman...amma sai naga dacewar zuwa in ganka tukunna kafin mu gana da shi..." " Uncle to ya ake ciki ne..?" " Ba komai ka kwantar da hankalin ka nace ai duk yanda mukayi da shi zan sanar da kai..amma dai yanzu ina so fara ka sanar dani abinda kace idan nazo zaka gaya min...menene silar tado maganar auren tell me". Shagwa6e fuska yayi yace"...Nifa ba komai Uncle...ina dai zargin yaga lokacin da wata course mate 'dina tazo wuri na amsan wani manual ne shiyasa.." Uncle J ido ya tsura masa yana kallon sa da son karantar yanayin sa..so yake ya fasa maganar dan ya fahimce ta da kyau ya kuma san fassarar da ta dace da maganar tasa Shi kam wuya ya karyar gefe looking so innocent...idanun Uncle cikin nashi yace" Wata daga ina kenan?" " Azare". Yace a hankali. "..Tun daga cikin Azare ta bika har Shuwarin dan kawai kar6an manual...ka gaya min gaskiya Mu'een..banson 'karya nasan haka nan dan 'dan wannan dalilin Alhaji ba zai ce zai yi maka aure ba.." "...Uncle da gaske babu komai..ni kam iya abinda na sani kenan". Tsaye Uncle Ja'afar ya mi'ke yana nanna'de hannun rigar sa yake fa'din" Bari mu hanzarta zuwa masallaci kar mu makara". Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* Those who remember Allah standing, sitting, nd lying down on their sides, nd think about d creation of d heavens nd d earth, (saying): “Our Lord! You have not created all this without purpose, glory to You! Give us salvation from the torment of the Fire.(Ali ‘Imran,3:191)🌷 🅿 *47* 'Dakin Yah Deen suka shiga tare inda yayi masa jagora gami da nuna masa bayin yace" Bismillah". Shiga yayi ya 'dauro alwalar ya fito, yana fitowa sai idanun sa ya sau'ka kan gadon Yah Deen yanda ya sha gyara sosai sai da ya bashi mamaki, yana murmushi bayan ya kawar da idanun sa yace" Ashe fa yaron nawa nada tsafta sosai, irin wannan gyaran gado da ka iya ai har kafi wasu matan ma...kenan ma ko auren Alhaji yayi maka matar bazata sha wahala ba tunda har ka iya 6ata lokaci kayi irin wannan gyaran to sauran ayyukan ma duk zaka iya su...yaushe ka koyi aikin mata har haka ban sani ba...?" Dum zuciyar sa ta tsinke da 'karfi dan yasan ba shine yayi komai ba. Yayin da Uncle ya cigaba da fa'din" Kaida na san ko sharar 'dakin ka ma wahala yake baka ada...amma ji gidan nan fa ko'ina tsaf..."   Murmushin 'karfin hali kawai ya 'ka'kalo ya sanya wa fuskar sa, sai dai inda zaka tona zuciyar sa Allah ne ka'dai ya san yawan beating 'din da take yi wanda ya kasance ba bisa ka'ida ba, a zahirin ma bai iya ya furta komai ba...cikin ransa yake ayyana" Allah ka rufa min asiri...harda rero addu'ar _Allahu Allahu Rabbii..la'ushriku bihi shai'an_..Har baisan sau nawa ya ambace ta bama tsabar rikicewa. Da haka ya nifi hanyar bayi yana mai sunkuyar da kansa 'kasa...cikin zuciyar cike da tunanin..in shine zai yiwa mace irin wa'dan nan aiyukan ashe kuwa ba zata ta6a zama da shi ba har abada...baki ya ta6e sannan ya shige bathroom 'din. Alwalar shima ya 'dauro ya samo Uncle a palour wanda da ganin sa sai ya mi'ke yana sake bin palourn da kallo yace.." Wai har da wannan abin matan ma ka'iya amfani da shi?" Wannan karan kam sai da ya lumshe idanu ya furta" Rabbi help me" Kafin ya juyo ga Uncle 'din bayan ya bu'de idanu cikin dakiya ya amsa da fa'din" Wani abu ne Uncle?" Da baki Uncle J ya nuno masa Burner..sai ya saki salati cikin ransa shaf ya manta da shi kwata-kwata in ba dan haka ba ai da ba zai bari ba ma balle har yazo ya gani, da i ina ya fara fa'din" Na..iya mana..Uncle ai babu wani wahala...Ishaq ne.. ya kawo min tsarabar turaren wuta daga garin su... kasan 'yan Borno ne su, shine fa na siyo wannan 'din". Ya fa'di hakan ne kawai dan kare kansa amma ba wai dan ya san ko yanda ake kunna burner 'din ba..bai ta6a bi ta kansa ba, tsakanin sa da abin kawai yaji gidan sa na tashin da'd'dan 'kamshi idan Husnah ta kunna. Hanyar waje suka nufa Uncle na fa'din" Ko de waccen yar Azare 'din ke zuwa tayaka ayyukan gidan?" Ya fa'da da sigar zolaya. Da sauri Deen ya ja ya tsaya kamar zai yi kukan an fara gano sirrin shi yace " Haba-haba.. Uncle kaifa mahaifi ne...me yasa zaka min irin wannan zargin dan Allah..yarinyar da ma tun dawowa ta bansa ta idanu na ba taya zata taya ni yin wani abu?" Murmushi Uncle J yayi sannan yace" Abin naka ne ai da ban mamaki ga duk wanda ya sanka Mu'een..." Shiru yayi bai sake fa'din komai ba, cuz ya lura idan ya cigaba da tanka masa zai iya tona asirin kansa da kansa. Da haka suka nufi masallacin still Uncle J na sake masa zolayar shifa sai ya fa'da masa inda ya koyi aikin gida har haka". Da 'kyar ya samo abin fa'da cikin ransa bayan ya gama tsarawa sannan daf da zasu shiga Masjid ya furta" Zama ni ka'dai ne ya sani koyan komai Uncle harda girki ma duk na iya yanzun". Yayi maganar ne afili amma cikin ransa da fatan Allah yasa kar Uncle ya sake fa'din komai... Cikin sa'a kuwa murmushi kawai yayi masa da jin amsar da ya bashi. Ganin hakan kuwa sai da ya sa shi sakin ajiyar zuciya ciki-ciki, wani 6ari na zuciyar sa kuma na fatan Allah yasa kar Husnah ta dawo gidan balle Uncle ya ganta ya gaskata zargin sa. Ko da ya idar da Sallah ma sai da ya ro'ki Allah akan ya rufa masa asiri ya kautar da idanun Uncle da tunanin sa akan rayuwar sa. Da ikon Allah kuwa suna dawowa daga Masjid 'din sai Uncle J yace shi kam zai wuce kar yamma ta same shi. Sai da ya sake tambayar Yah Deen akan abinda suka tattauna farkon isowan domin neman 'karin bayani, Mu'een sai cewa yayi" a a ya bari kawai sai sunyi magana da Alhaji Baba tukun..ya 'karashe da fa'din" Ni dai auren banaso yanzu Uncle" Ya fa'di haka ne  kawai gudun kar ya tonawa kansa asiri da abinda zai sake furtawa musamman da ya san cewa yanzun Uncle J ma na jin zargin irin rayuwar da yake yi cikin zuciyar sa duk da be bayyana gaba 'daya ba but dole ya san akwai ayar tambaya cikin ransa. Uncle kuwa cewa yayi" Idan Alhaji ya dage akai dole ne kayi ha'kuri, sannan kasani nima bazan yi ta jajayya da shi ba tunda auren ba haramun bane ha'kuri kawai zakayi kayi na'am da batun... Yatsa ya 'dago ya nuna shi da shi sannan ya cigaba da fa'din" Kuma ka sani idan har ka kuskura bincike na ya bayyana min rashin gaskiyar ka akan maganar nan, ko kuma naji wani abu na daban kai kanka kasan ba zamu shirya da kai ba ko?" Shiru yayi illah jinjina kai da yayi  yana mai sau'ke idanun sa 'kasa... Wanda ganin hakan yasa Uncle J sau'ke ajiyar zuciya bai wani 6ata lokaci ba kawai ya 'dau jakar sa Yah Deen sai yayi saurin amsar jakar daga hannun sa...suka fice daga gidan Deen ya sake kullewa. Suna kan hanya yana raka shi kafin su isa bakin titi sai ya hango Husnah na tahowa cikin tafiyar ta mai 'daukan hankali..take hankalin sa ya tashi fiye da zaton mai karatu" Me kuma ya dawo da ita yanzun?" Ya tambayi kansa..shaf ya manta da cewar dama 'karfe hu'du zata dawo..2-3 ne last lecturen ta na yau...tuni hankalin sa ya koma gare ta sai dai bai bari Uncle ya gano sa ba ya dake kawai suka cigaba da tafiya zuciyar sa cike da fargabar kar ta tona mai asiri, har suka kusan ha'duwa da ita bai daina satan kallon ta ba. Yayin da itama Husnah tun da ta hango shi tafe da wani mutun ta tsura musu idanu da tunanin ko wanene mutumin oho...sai dai Husnah har cikin ranta bata yi niyyar tanka shi ba..cuz da gani mutumin ba sa'an shi bane in kuwa haka ne magana ga junan su agaban idanun sa sam bai dace ba ko dan su bashi girman sa matsayin babba agare su. Shi kam Ya Deen ya kasa natsuwa sam duk sai ya raba hankalin sa gida biyu, ji yake da da wata hanyar agaban su kafin ha'duwar su da Husnah da yace su bita koda kuwa ba ita ta dace su bi ba amma a lokacin kaucewa Husnah shi zai fi komai yi masa da'di cuz gani yake kamar zata tona asirin sa. Ganin sun kusan ha'duwa ne ya sanya shi jan hankalin Uncle J da labarin makaranta, yana fa'da masa ire-iren wahalar da yake sha, shi kuwa Uncle Ja'afar na bashi 'kwarin gwiwa da fa'din me ma ya rage kuma ai saura ka'dan, yace ha'kuri kawai zasu yi sun ma yi mai wuyar ai saura ka'dan ne cuz dudu semester biyu kacal ne ya rage masa....tun kan Husnah ta iso daf yake yi mata wani irin kallo, da ido yake nuna mata alamun kar ta kuskura ta kula shi, da suka kusan ha'duwa kuwa sai ya kauda kansa gefe tamkar bai ganta ba wanda hakan ya bayyanawa Husnah cewa shima 'din baya so tayi masa magana ne, hakan yasa itama ta 'dauke kai tayi wucewar ta kamar yadda ta yi niyyar yi da tunanin waye wannan mutumin to...sai dai ta fahimci koma wanene mutumin to mai matu'kar daraja ne a wurin Mu'een...kuma yana mutunta shi gami da girmama shi irin na musamman 'din nan. Sam Uncle J bai fahimci komai tsakanin su ba, da yake sam baya kawo ko zargin Yah Deen akan irin wannan abin ko cikin ransa...ko abinda ya gaya masa 'dazun ma ba wai ya zarge shi haka kawai bane, illah tunanin da yayi kan cewa haka a banza Alhaji Baba bazai takura shi akan maganar aure ba dole ne akwai wani abin wanda baya fatan yaji abinda zai ta6a masa zuciya akan mafi soyuwa cikin zuciyar sa wato Mu'een. Har ajiyan zuciya ya saki lokacin da yaga ta shin motar su Uncle J, cuz har cikin tasha ya raka shi. Hamdala ya ringa saki ganin bayan motar tasu, musamman da Allah ya rufa mai asiri ba suje ga abokin Uncle da yace zasu je ba.. Lokacin suna wani eatry ne sunje cin abinci bayan barin gidan Yah Deen da suka yi, har sun gama cin abincin suna niyyar tafiya sai yace dashi wai zai raka shi wurin wani abokin sa har da yi masa kwatancen wurin. Nan take hankalin sa ya tashi da jin sunan wanda Uncle J 'din ya ambata da kuma sana'ar sa...kuma already tun daga kwatancen da yake yi ya fahimci wurin. Mamallakin babban medical center da ya ta6a zuwa sayo magani wa Husnah ne da yake tunanin yaje da nisa inda babu wanda ya sanshi ya sayo drugs 'din, sai gashi Uncle J na shirin banka'da asirin sa da fa'din wai zasu je ya gaisa da shi wai abokin sa ne..." to idan ya gane ni kuma fa?" Ya tambayi kansa...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..ya nanata cikin zuciyar sa kusan sau uku.." wai yau 'din nan me ke shirin faruwa da ni ne?" Ya tambayi kansa, sannan ya sake fa'din" Idan kuma ya gayawa Uncle na ta6a zuwa wurin sa sayan magani kaza kuma fa... ya zanyi in 'karya ta shi ni Muhammad". Fargabar sa 'karuwa tayi sosai akan nada duk kuwa da yasan cewa ba lallai ne mutumin ya gane shi ko tuno abinda ya kaishi wurin sa ba, amma kunsan abin ku da marar gaskiya..zuciyar su rangaji take bata tsayuwa wuri guda. Kamar Uncle J ma yasan tunanin da yake yi sai yace" Bari dai in 'kirashi inji ko yana nan". Sai yanzu ya iya samun damar fa'din" Gaskiya is better ka 'kira shi kam dan wurin akwai nisa ga kuma tafiya a gaban ka..." Yana 'kira kuwa bayan sun gaisa sai yace da shi ai yana Dutse, mutumin sai yace shikuwa wallahi yana Kano amma wai gobe zai dawo why not ya jira shi...Uncle sai yace masa a a yana kan hanya ne dama sai dai wani lokacin kuma idan Allah yayi". Da haka suka yi sallama yake yiwa Mu'een bayani...tsabar murna ma bai san lokacin da ya saki ajiyan numfashi ba har har da fa'din _Alhamdulillah_ Uncle J sai da ya dube shi yace" Ya dai". " Bakomai Uncle banson kayi dare ne kasan kasar tamu sai a hankali". Ya bashi amsa yana 'yar dariya...sai yace" Hakane". Daga nan suka nufi tashar mota...ya tafi abinsa. Ko yanzun ma ganin har Uncle J ya tafi bai fahimci komai game da rayuwar sa ya sanya shi a fili ya furta" Alhamdulillah". Sai dai har cikin zuciyar sa ba zai iya bayyana a wani matsayi ya ajiye wannan ziyara ta Uncle Ja'afar ba, shin farin ciki zaiyi da shi ko akasin haka?" Shi da kansa ya san ba dai-dai yake aikatawa ba amma yayi watsi da sanin sa, banda nasihar Ammi gare shi...sannan ga fushin mahaifin sa, duk hakan bai sa ya bar abinda yake yi ba. Allah ma sai ya sake rufa masa asiri ya tsallake dukkan stage 'din da ya kamata Uncle J ya gano sirrin rayuwar sa...'dan baya gane cewa idan duk ka tsallake irin wannan kalubalen bayan kayi watsi da sanin ka, ka yi watsi da fushin manyan ka ka cigaba da aikata abinda ranka ke so to Allah yana so ya maka talala ne, ranar tonuwan asirin ka na nan yana jiran ka duk da'dewan shekaru kuwa dole ranar sai tazo, ranar da baka isa ka 6oye laifukan ka ga kowa ba...(ALLAH UBANGIJI KA SADA MU DA HASKEN KA, KA KUMA GYARA MANA ZUCIYOYIN MU KA SANYA MU CIKIN BAYIN KA SALIHAI AH'LUL JANNAH...(AMEEN YA RABBAL ALAMEEN). Mashin ya hau ya koma gida, bai bi ko ta kan Husnah ba kawai yayi alwala ya wuce masallaci abinsa cuz la'asar ake 'kira a lokacin. Ko da ya dawo daga masjid 'din ma direct 'dakin sa ya wuce, zuwa yanzun rayuwar da yake yi 'din tafara isan sa, shi kansa ya san cewa ba abin kirki yake aikatawa ba...sannan ba ya kyautawa iyayen sa musamman ma da ya tuno nasihar Ammin sa agare shi lokacin da zai taho, sai gashi cikin lokaci 'kan'kani yayi watsi da komai yana aikata abinda yasan Allah da kansa baya so...sosai yake so ya zama mutun nagartacce kamar kowa, so yake ya zama yaron da iyayen sa zasu yi alfahari da kasancewar sa da agare su, ba irin wanda ake Allah wadai da shi ba a duk lokacin da 6oyayyen halayyar su ta bayyana....sai dai tayaya zai iya hakan?" Ya tambayi kansa..da farko dole ya san sai ya sallami Husnah ta bar gidan shi..in hakan ya faru to ina zan je da bu'katu na?" Ya sake tambayar kansa..goshi ya dafe sannan ya furta" Iyaye na fa?..ya zanyi da su duk ranar da suka gano abinda nake aikatawa.." Ya Rabb please help me". Yanzu da ace Uncle Ja'afar ya kama shi kan hakan fa.. da ya zaiyi?" Juyi yayi kan gadon sa yana sake tunanin abin sosai ya dame shi, yana so ya zama nagari amma kuma yana gudun irin halin da zai shiga...not knowing that komai sawa arai ne musamman abu dangin zunubi. Idan kasa aranka shai'dan sai ya 'kara ingizaka ya rura maka wutar 'kaunar abin cikin ranka...juyi ya ringayi yana tunanin mafita da ya gaji sai ya tashi ya fa'da bayi. *****      'Bangaren Uncle Ja'afar kuwa ranar da ya isa Shuwarin basu samu daman ganawa da Alhaji ba sai washegari...sai dai ko a lokacin da suka zauna kan zancen ma.. Alhaji bai fito fili ya bayyana masa asalin dalilin da yasa yake so ayiwa Yah Deen auren ba...kawai ce masa yayi ya fahimci yana da bu'katar auren ne dan haka ba za'a 'dauki dogon lokaci ba yace already ma ya gama binciken da ya dace ayi. Da Uncle Ja'afar yaji Alhaji Baba ya ambaci Azare ne yasa ya tuno da maganar Mu'een da ya fa'da masa kan yarinyar da yace tazo wurin sa daga Azare. Nan ya bu'di baki dan yiwa Alhaji bayani amma ya dakatar da shi yace baya son jin komai shi dai kawai burin sa ya fahimci inda ya dosa. Uncle Ja'afar sai yace" Amma ai Alhaji kamata yayi a tuntu6e shi aji nasa ra'ayin tukun..." " No need..ai mun gama magana da shi tuntuni sai dai kuma in zaku ha'de min baki ne ku juya min baya kai da shi". Alhaji Baba ya tare shi da fa'din hakan. Jin haka yasa Uncle J jan bakin sa yayi shiru...yana tunanin abinda Mu'een ya gaya masa. Ko iya sanar da Yah Deen ma bai yi ba kawai ya dinga juya batun cikin ransa tare da jinjinawa irin zafin da ya fahimci Alhaji ya 'dauka kan lamarin. Babu wani 6ata lokaci washegari suka wuce Azare gidan Alhaji Hamza da sunan nemawa Mu'een auren Husnah. Sun yi sa'a kuwa basu yi tafiyar banza ba dan Alhaji Mamman na gari a lokacin, take yasa akayi musu jagora zuwa asalin gidan da sauran matan sa suke...kafin isowar su ne ya gayyato wani ma'kwabcin sa Alhaji Halliru suka yi jiran isowar su. Tarba ta musamman akayi musu cikin girmamawa da karamci tamkar dama ansan da zuwan su...bai nuna musu alamun komai ba har suka bayyana masa kansu da kuma abinda ya kawo su...su kam ma tafe suke harda sadakin su a hannu...ga dukkan alamu Alhaji Baba dagaske yake yi bada wasa ba. Ba'a 'ki kar6an batun su ba take Alhaji Mamman ya amince musamman da yaga yanayin shigar su da kuma motar da suka zo da shi yasan cewa ba 'kananun mutane bane, dan haka take yayi musu albishir 'din ya basu auren Husnah batare da yayi tunanin komai ba...har ma ya basu sati guda kacal da zasu dawo a tsaida ranar 'daurin aure. Cikin farin ciki suka rabu, su Alhaji Baba nayi musu godiya sosai da yake tare yake da makwabcin sa. Sai daga baya ne ma ya 'dan yi tunanin abin kamar bai yi dai-dai ba, amma bai tsawaita tunanin ba yaci gaba da harkokin gaban sa. Washegari da girki ya dawo hannun Mummyn Husnah anan yake yi mata bayanin abinda ya faru da bada auren 'yar ta da yayi batare da yayi shawara da ita ba...  inda Mummyn Husnah ta matu'kar nuna ba'kin cikin ta da 'kin amincewar ta kan batun..hankalin ta ya tashi sosai..tace da shi" Alhaji a gaskiya bai kamata kayi hakan batare da kaji ra'ayin Husnah ba, ko da ni ban kai ayi shawara da ni kan lamarin ba amma ai ita da babu mai tayata zaman auren ya kamata a tuntu6e ta..." Tayi maganar cikin nuna 6acin ranta. Ganin Mummyn Husnah ta 'dau zafi ne ya sanya shi fa'din" To Fateemah sai ki gaya min abinda ya dace inyi tunda ni banda hankalin kaina kinji?" Sai tace " Ai ba batun haka bane Alhaji, amma ai ya kamata ka duba lamarin kai da kanka, ko binciken kirki fa ba ka yi ba kawai ka 'dauki auren yarinya ka bayar bacin bakasan ko su 'din wasu irin mutane ba ne haka akeyi ne saboda Allah...?" Shareta kawai yayi yayi kwanciyar sa yayi baccin yayin da Mummyn Husnah kuwa saboda tashin hankali ma kasa rintsawa tayi, zugum ta rafka uban tagumi, daren ranar ka'dai sai da ta tuna mahaifin Husnah yafi sau 'dari, cuz tasan shi din da wuya yayi mata hakan, koda yayi hakan ma to zai bita da kalamai masu da'di da kwantar da zuciya ne. Gari na wayewa ta 'dauki wayar ta ta 'kira Husnah tace mata ko me takeyi maza ta bari ta zo gida aranar ba sai an kwana ba. Jin yanayin da  Mummyn ta tayi maganar sai ya sa hankalin ta ya tashi sosai, kuka ta fara tana tambayar ta abinda ya faru, sai tace" Sai dai kin zo kawai..Allah ya tsare hanya". Tana fa'din haka ta yanke 'kiran tare da zabga uban tagumi, wannan wace iriyar rayuwa ce fisabilillahi?" Ta fa'di cikin ranta. Alhaji na bayi tayi wayar lokacin da ya fito ya ganta da tagumi sai ya kauda kansa ya cigaba da abinda yake yi, dan yasan silar hakan. Batare da ya dube ta ba yace" Wai ke Fateema kina tunanin kin fini son Husnah ne ko me? Ko kuwa ke aganin ki dan bana son ta ne yasa na yanke wannan hukuncin?" Ko 'kala bata ce dashi ba dan takaici, kawai sai ma ta tashi tayi ficewar ta ta barshi a 'dakin..tana mitar" Wannan wace iryar tambaya ce haka..sai ana shirin cutar da rayuwar ka sannan za'a wani fake maka da soyayyar 'karya, bayaga haka ta yaya ma zai iya ha'da soyayyar da takewa Husnah da wadda yake mata, 'kilan ya manta cewa ita ka'dai ta sha wahalar na'kudar ta ta haifi abinta da taimakon ubangiji, shikuwa ganin ta yayi tar idanun ta a bude batare da yasha wahalar komai ba". sai ya ta6e bakin sa gefe. Har kuwa ya gama shirin sa ya bar gidan kulashi ba..da yake ma ba kullum yake yin breakfast a gida ba shiyasa shima bai ko nema ba yayi ficewar sa. Haka Mummyn Husnah ta yini ranar zuciyar ta cike da damuwa da tunani..har Husnah ta iso wajajen 'karfe biyu na ranar Mummyn ta bata warware ta saki ranta ba, gani take an dauko hanyar lalata rayuwar Husnah...ai gwamma ma Hisham 'din tunda shi duk lalaci tushen su 'daya kuma zai ga darajar ta matsayin kanwar shi koda kuwa sadakar ta aka bashi, akan wani can da bata san lungun da ya fito ba balle tasan halayen sa...ta ji bata son tarayyar Husnah da Hisham ne kawai dan taga Husnah na nuna kin amincewar ta ba wai dan ta tsane shi ba, yaro mai hankali da sanin ya kamata sam bai 'dauko ko 'kwara 'daya daga cikin halayen mahaifin sa ba..yaro nagartacce bata ma san me yasa Husnah 'kin amince masa ba. Hankalin Husnah  a tashe ta iso gidan burin ta kawai taga ya mahaifiyar ta take ta kuma ji abinda ya same ta, sai data yi ido hu'du da ita kafin taji hankalin ta ya 'dan kwanta ganin garau cikin 'koshin lafiya tsaye bisa 'kafafun ta. Amma duk da haka sai da ta saki kuka ta tafi da gudu ta rungume ta kamar wacce cewa tayi zata tafi ta barta. Da 'kyar ta lallashe ta tayi shiru har ta je ta watsa ruwa taci abinci ta huta...zuciyar ta cike fal da tunanin dalilin da yasa mahaifiyar tan tayi kiran ta. ***** 'Bangaren Yah Deen kuwa har lokacin bai gama yanke hukuncin da yaka ta ya yanke kan rayuwar sun ba, ya dai sanar da ita cewa 'kanin mahaifin sa ne ta gansu tare sannan yana shakkan ranar da akace ya sake dawowa dan kawo masa ziyara musamman ta bazata irin wannan. Ita kanta Husnah sai taji ta damu sosai har ta fara tunanin komawa cikin Hostel cuz da wani tozarci da abin kunyan ya faru gareka gwamma tun farko ka 'kuntatawa zuciyar ka kayi abinda ya dace kawai koda kuwa hakan zai saka ka cikin damuwa ne to yafi maka indai tsakanin ka da zuciya da gangan jikin ka ne. Sannan tasan da kunya a ganta ace ta bi saurayi ta tare gidan sa dan tsananin son da take yi masa..shiyasa tuntuni ta fara tunanin mafita da zauna ta kwashi kunya abanza bacin bata ga ribar rayuwar da suke yi shi ba cuz har yau bai ta6a furta mata kalmar so ba, hira da itama sai lokacin da yayi ra'ayi yake mata, haka zasu kwana tare su tashi amma babu wata kalma mai da'di da take samu daga gare shi sai ranar da yayi niyyar sake mata fuska, in kinji ya kwantar da murya to yazo mata da bu'katar sa ne ita kanta tasani...amma duk da haka 'digo daga cikin son da take yi masa bai agu ba. Tana nan ne dai tana tare da shi da tsammanin wataran zatayi nasara ya so har ya aure ta. Koda ta ta sanar da shi zata je gida mahaifiyar ta ta'ki ra ta ma bai wani damu ba da yake dama tun tafiyar Uncle J maganar kirki bata shiga tsakanin su ba..kowa nada tashi damuwar 'kunshe cikin ransa. Duk da yaga hankalin ta a tashe amma bai wani damu ba sai yayi tunanin ko family issues ne da yake cewa tayi zata je gida mahaifiyar tayi 'kiran ta, dan haka bai nemi jin dalilin tafiyar tata ba illah 5k da ya 'dauko ya bata da sunan ku'din mota...bai san cewa an bashi auren ta ba sam nasan da ko sisin sa ba zai bata ba. *****   Sai bayan kwana biyu da dawowar su Alhaji daga Azare sannan Uncle J ya sanar da shi cewa sunje sun tambaya masa aure a Azare kuma an bashi...bai fa'di gidan da suka je 'din ba haka ma sunan yarinyar duk bai fa'da masa ba..duk da lokacin da suka je yaji Alhaji Baba ya fa'di sunan ta Asma'u wanda shima yaji ne abakin Yusha'u da ya tura yi masa bincike da sunan mahaifinta da yake ba 6oyayyen mutun bane, kuma ita ka'dai ya mallaka kafin ya bar duniya shiyasa ma Yusha'u bai sha wahalar binciken ba. Hakan ma da Uncle J ya samu ya sanar dashi da 'kyar ya ro'ki Alhaji ya amince akan asanar masan, dan da farko cewa yayi ba za'a gaya ma kowa ba ciki kuwa harda Ammin sa, wai har sai bayan an tsaida ranar 'daurin auren kafin a sanar musu. Ranar kam in akwai sahun tashin hankali na 'karshe to shi Mu'een ya shiga, musamman ma da yaji wai a Azare aka tambayo auren, bai nemi 'karin bayani ba cuz ya san ba Rahma bace, dan ita tuni tayi auren ta harda 'yar ta, shi kenan ta tabbata shine mijin Husnah. Bazan iya misalta muku yanayin yanda ya shiga ba kudai ku misalta da kanku ku gwada girman 6acin ransa akan aure tsakanin sa da Husnah, nasan ku kanku kunsan abin sam bazai yi masa da'di ba. Tun daga ranar da yayi jifa da wayar sa bayan jin bayanin Uncle J bai sake bi ta kan wayar ba...bai ko sake tunanin 'kiran kowa ba dan yasan duk babu wanda zai iya dakatar da auren tunda har takaiga anje anyi tambaya...to wama zai 'kira? Dam Alhaji ne ko Ammi kuma suma 'din a yanzu rashin jin su yafiye masa. Allah sarki Ammi kuwa Allah ne ka'dai ya san halin da shiga da ta daina samun wayar sa domin sam bata san abinda yake faruwa ba har tausayi take bani, kwata-kwata na rasa wani irin so take yiwa wannan gagaren 'dan nata. *To ina labarin Husnah?*        mahaifiyar ta bata sanar da ita komai ba har sai da ta tabbatar da natsuwar ta that's washegarin zuwan ta, shima 'din sai bayan da suka idar da sallar Zuhr kafin ta sanar da ita cewa wan mahaifinta ya bada auren ta ga wasu mutane da suka zo daga Shuwarin...sai ta kasa tantancewa, shin Mu'een ne ko kuwa wani daban, dan ita sam bai ta6a nuna mata alamun a shirye yake da auren ta ba...ya akayi haka kuma?...duk da haka sai take jin 6oyayyen farin ciki cikin zuciyar ta gefe guda kuwa fargabar kar yakasance ba shi bane. Taso ta same shi awaya ko zata damu jin asalin labarin daga bakin sa, amma layin baya tafiya ta gaza samun sa, duk yadda taso su gana abin ya faskara. Haka ta yini neman layin sa amma bata samun sa hankalin ta duk sai ya tashi cuz tasan ba'a fiye rasa shi a waya ba, his phone is always on baya ta6a kashe wayar sa" To yau din meke faruwa kuma? Ta tambayi kanta while tana sake dialling numbern but still is switch off. Damuwar Husnah bai wani yi tsayi kan batun auren ba fiye da rashin samun sa da bata yi ba, dan hankalin ta gida biyu ya kasu, idan Mu'een aka bawa auren ta tasan zata dawwama ne cikin farin ciki musamman ma saboda irin dumbin soyayyar da take yi masa shiyasa ma ba ta damun ba, gefe guda kuma tana tunanin inba shi 'din aka bawa auren kuma fa?" Wannan duk bai dame ta sosai ba kamar yadda ta bawa neman layin sa muhimmanci cuz tasan da ta same shi zata ji komai in yaso daga baya sai ta san me ya dace tayi kan batun. Duk abinda take yi  mahaifiyar ta na lura da ita musamman da taga bata wani damu sosai da jin labarin ba sai tayi matu'kar mamaki, bata san haka Husnah zata 'dauki abin da sanyi ba, she thought zata 'daga hankalin ta ne idan taji labarin amma ga mamakin ta sai taga akasin haka. Ido ta zuba mata domin ganin iya gudun ruwan ta, daga ranar da ta gaya mata har zuwa daren washe gari..amma Husnah bata nuna mata komai ba sai dai ta lura tafi bawa wayar ta muhimmanci a cikin lokutan. Zaune suke tare a parlour bayan Sallar maghrib, amma idanun Husnah na kan wayar ta tana dubawa, daga jiya zuwa yau 'din ta tura masa text kusan thirteen times, amma ga dukkan alamu ko guda 'daya bai gani ba, ko yanzun ma text 'din take rubutawa karo na goma sha hu'du inda bayan ta kira dukkan layukan sa basu shiga ba kamar yadda ta saba ji shine ta shiga rubuta" Please Mu'een ka 'kira ne idan ka kunna wayar ka, hankali na ya tashi sosai, gashi ina cikin damuwa we need to talk". Ji take kamar ta fasa ihu dan ba'kin cikin da take ji tana dannan "send" sai taji muryar Mummyn tana cewa da ita" Husnah ko dai dama wannan batun auren naki shine abinda kike tambaya ta kwanaki akan wai ko naji wani abu kuma kika 6oye baki bayyana min ba?" " a a Mummy" Ta bata amsa cikin sauri tare girgiza kan ta side by side. Mummyn Husnah kam sam bata yadda ba dan yanayin Husnah ya nuna mata akwai wani abinda take 6oyewa, dan haka cike da 6acin rai ta cigaba da fa'din" Ashe Husnah dan bani da matsayi a wurin ki shine har zaki iya bawa namiji damar turowa gidan ku batare da kinyi shawara da ni ba?" " Ba haka bane wallahi mummy, nima fa bansan da maganar ba Allah..wanda na sani a can Shuwarin 'din kuma na ta 'kira layin sa bai tafiya bansani ba ko shine ya turo ko ba shi bane...Mummy in har auren zanyi ai kisan kece mutum ta farko da zata fara sani tun ma kafin aje ga Abbah". Jin haka yasa Mummyn ta 'dan sakko sai tace " A ina dama kika sanshi?" " Makarantar mu ne 'daya da shi". " Amma bai ta6a sanar dake cewa zai turo gun mahaifin ki ba?" "A a wallahi Mummy ni bai ta6a sanar da ni ba ko da wasa ma". " Ikon Allah!" Mummyn ta fa'di cike da mamaki sannan ta cigaba da fa'din..." To ki ta gwada layin nasa duk sanda kika same shi kukayi magana, zan miki wata tambaya". " To Mummy". Tace cikin sanyin murya tana mai sake maida fuskar ta kan wayar ta dake ri'ke a hannun ta. *Hmmm....Allah Ubangiji ka raba mu da sharrin social media* 🙏 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *48* Ita kanta ta matsu ta jishi su gana, musamman ma da ta tuno jiya da dare bayan dawowar Abbah da ta gaida shi yanda ya kar6i gaisuwar ta cikin nuna halin ko'in kula, yana gyara zaman sa zuwa kishingi'da yace da ita" Wato mahaifiyar ki ce ta gayyato ki musamman domin ki zo ki gaya min cewa baki amince da za6in da nayi miki ba ko?" Da sauri ta 'daga kai ta kalle shi tana girgiza kai tace" Ba haka bane  Abbah..Mummy fa bata ce da ni in ce ban yadda da za6in ka ba..." Tun kan ta rufe baki yace" To ai shikenan..sai ki je ki jira ranar 'daurin auren dan ba dogon lokaci za'a saka ba,  mahaifan sa sunce min already kun daidaita kanku da yaron dan haka ba wani abinda zamu jira... daga Shuwarin suka zo wai sunan sa Muhammad...sai kije ki bincika cikin maneman ki babu mamaki kiyi saurin gano shi". Sum-sum ta tashi tana juya sunan cikin ranta da matu'kar mamaki sai taji yace" Yauwa tunda kin riga kin dawo to babu kuma batun komawa sai bayan auren, idan mijin ki ya yarje miki komawa Falillahil hamd in kuwa yace a a shikenan sai ki fawwalawa Allah kinji?" Kai ta 'daga masa alamar " Erh taji". Sannan ta juya ta 'karasa fita daga 'dakin nasa wanda ada ya kasance 6angaren mahaifin ta ne. Yanda 'karara wan mahaifin ta ya nuna rashin damuwa kan halin da zata shiga ya nuna rashin damuwar sa kan farin cikin ta ko akasin haka yasa a daren ranar sai da ta sha kuka amma babu wanda ya sani daga ita sai Allahn ta ne ka'dai da ta gaji ta lallashi kanta. Shiyasa yanzun ta damu sosai wajen ganin ta same shi a waya, tafara gano kamar shi 'din ne amma bata da hujjar gaskatawa inba taji daga bakin sa ba....ko kashe wayar tasa ma sai take ganin kamar yana da nasaba da faruwar maganar auren amma duk tayaya zata gaskata hakan?..No way". Ta riga ta san halin sa da kafiya da kuma bakin hali in ba dan haka ba da ko wata friend 'din zata 'kira tace a kai masa waya suyi magana amma tasan inba ra'ayi yayi ba Mu'een ba zai ta6a ansan wayar ba sai dai a idon 'kawartata yayi 'karyar ta bari zai 'kira ta kawai. Ishaq ne ya fa'do mata cikin ranta, sai kuma ta tuna bata da contact 'din sa..haka ta zauna tayi tagumi tana tunani ta ringa sa'ma sa'ka abubuwa tana kuma warware su da kanta. *****       Shi kuwa Mu'een har lokacin ya 'ki 'daga wayar ta sa ma a inda ya wullata balle ya kunna ta, haka zai yi duk abubuwan da suka zame masa dole ya yi shirin sa ya wuce makaranta ko kallo wayar bata ishe sa ba, wani sa'in ma bai zuwa makarantar sai dai ya yini a gida yana tunani...Ishaq ne yafi damuwa da lamarin sa, cuz sosai ya fahimci akwai abinda ke damun sa da yake so ya hana shi sukuni yake kuma faman 6oye musu.     Watarana da bai shiga school ba sai Ishaq da Imran da wani abokin su Anas jibo suka taho gidan sa dan duba shi dan sau tari idan basu gan sa ba suka sha gwada 'kiran wayar sa amma bata tafiya dole suke hakura su bar sa. Yau kam Ishaq yace suje gidan su dubo shi, tun zaman su da shi kuwa ranar shine rana na farko da suka ziyar ce shi har gida, yau din ma bazata suka yi masa da yake already sun riga da sun san gidan, Mu'een bai ta6a basu daman zuwa inda yake ba ko da wasa. Da sallama suka shiga gidan inda suka zarce har ciki. A palour suka tarar da shi kwance fuskar na kallon ceilling, jikin sa kuwa ko singlate babu balle riga wandon jikin sa ne dai dogon ba'kin jeans ya sanya...hannun sa 'daya ya lan'kwaso ta ta ratsa ta saman fuskar sa yayin da 'dayan kuma ya dafe saman 'kirjin sa da shi. Wanda Ishaq da yake yafi son shi da damuwa da shi yana ganin sa a haka yayi saurin zuwa gare shi inda ya taho yana fa'din" Me ke damun ka ne  gaye har haka please?" Yana jin tun daga yin sallamar su har isowan su kanshi amma ya kasa 'daga idanu ya dube su duk kuwa da cewa ya gane su, amma haushin zuwa masa da suka yi yasa yayi luf kamar mai bacci... 'kofar gidan ma sa'a suka ci da ya dawo daga masjid 'dazu ya manta bai kulle ta ba, amma ba dan hakan ba inda ace bugawa zasu yi to da kuwa ko kwana zasu yi suna bugawa ba zai ta6a tashi yaje ya bu'de ba sai dai su ha'kura suyi tafiyar su. Gefen sa Ishaq ya zauna ya dafa hannun sa dake kan fuskar tasa yana sake tambayar " wai lafiya kuwa?" Hannun ya 'dauke a hankali sannan ya bude idanun sa ya kalli Ishaq dake gefen sa, Ishaq gani yayi idanun sa sun koma jajazur tamkar ba nashi ba" Subhanallah"! Ishaq yace a fili yana tattare goshin sa sannan ya sake fa'din " Me ke damun ka dan Allah Mu'een?" Bai kula shi ba sai ya 'dan juya idanu ka'dan a 'dan fizge ya kalli Imran da Anas dake tsaye sai ya sake maida hannun sa kan fuskar ta sa ya rufe idanun sa. Cikin dauriyar magana yace da su" Ya studies?" Anas ne ya amsa da " Alhamdulillah". Yayin da Imran ya jinjina kansa kawai yana 'ko'karin zama kan kujera...Ishaq kam baki bu'de yake binsa da kallon mamakin yanda ya koma a 'yan kwanaki 'kalilan din nan. Duk yadda Ishaq yayi 'ko'kari wajen gano abinda ke damun sa amma Mu'een ya'ki sake furta komai sai da ya ga kamar hankalin Ishaq kwata-kwata bai kwanta da ganin sa hakan ba shine yayi dauriyar fa'din" kar ka damu babu abinda ke damuna". Ishaq bai yadda ba sam amma haka ya 'kyale shi, har yamma suna tare da shi, tare suke zuwa Masjid su dawo amma babu wata hirar kirki ta 6angaren sa, sai bayan Sallar Maghrib kafin suka yi masa sallama suka wuce cikin makaranta.    Sam bai damu ba shi kam, dama dauriya kawai yayi  amma wanzuwar ta su ba 'karamin takura shi yayi ba a gidan, surutun su na damun sa sosai da ya samu suka tafi kuwa sai da ya sau'ke ajiyan zuciya na jin dafi, har girki Anas yai musu suka ci amma shi Yah Deen bai ra'ayin abinci sam-sam, hakan yasa bai ko yiwa abincin nasu kallon arzi'ki ba. Sai bayan ya dawo daga sallar Isha'i kafin ya ha'da Tea ya sha yayi kwanciyar sa....har a lokacin bai yi tunanin le'ko inda ya yada wayar tasa ba. A kwanciyar san nan nema Ammi ta fa'do ransa sai yaji yana so yayi magana da ita 'kilan ko akwai taimakon da zatayi masa wajen hana faruwar auren. Amma yanda yasan Alhaji Baba yasan Ammi bazata iya dakatar da shi ba...hakan yasa shi gyara kwanciyar sa da kyau batare da ya tashi ya 'dauko wayar ba...cuz ya lura babu amfani yin 'kiran ma. Haka ya cigaba da rayuwar sa cikin 'kunci da damuwa kan auren da ake shirin yi masa, ya kan shiga school amma ba kullum ba sai ranar da ya ga daman hakan, su Ishaq ma yanzu na yawan zuwa gidan duba shi musamman idan suka ga shiru bai shiga school 'din ba, cikin hakan har suka samu Mu'een ya bayyana musu damuwar dake damun sa wato auren da mahaifin sa ke shirin yi masa sai dai bai fa'da musu ko wacece ba dan shima bai gama tabbatar wa ba tukunna. Ishaq sun matu'kar tausaya masa amma hakan bai hana su bashi 'kwarin gwiwa akan kar ya bijirewa mahaifan sa ba ya daure yayi musu biyayya 'kila sai yaga auren yayi albarka ya kuma zame masa abin alfahari. Yah Deen kam jin su kawai yake yi wani lokacin kuwa sai yayi murumushin takaici da gefen bakin sa..." Wai auren sa da Husnah ne zai zame masa abin alfahari" In ji shi yace" Banga alama ba". Duk da ko da ace a giyar wake itace abincin sa a kullum dama bai isa yace zai ja da maganar Alhaji ba, zai nuna baya so cikin harkokin sa, zai iya sanar da Ammi bai so, haka ma Uncle J musamman da ya fahimci cewa har a lokacin bai san labarin asalin abinda ya faru ba...Amma ga Alhaji Baba kam...a a dole ne zai yi masa biyayya ko ma dan kar ya 'kara masa 'kunci kan wanda ya 'kunsa masa abaya. Wani sa'in ha'kuri kawai yake yi amma baya son zuwan da su Ishaq ke yi gidan sa gani yake suna takura masa ne sosai. A hakan ma wataran da gangan yake rufe 'kofar ta ciki yana jin su suyi ta bugawa amma motsin kirki bayayi balle asa ran zai tashi yaje ya bu'de musu....ya kai kusan sau biyu hakan na faruwa haka zasu zo su koma batare da sun ha'du dashi ba duk bugun da zasu yi wa 'kofar gidan kamar babu wani abin halitta mai rai dake rayuwa cikin gidan baza'a bu'de musu ba, haka zasu ha'kura su tafi suna masu trying layin sa amma har lokacin bata shiga bai ko tattare wayar a inda ta fa'di ba balle aje ga batun kunna ta..Ishaq kuwa har ransa dan su ringa rage mai yawan tunani ne yake sanyawa gayyato su Imran su taho. Mu'een kam bai ko damu da yawan mutanen da ke neman layin sa basa samu ba, duk da yasan dole dama za'a neme shi, musamman Ammin sa da Uncle J, amma ya zam masa dole ya nuna musu 'karara shi ba ya son auren nan, wanda ganin sa hakan ma ka'dai ya isa ya bayyana meke cikin ransa. To Husnah fa da sauran mutanen da zasu neme shi? Wa'dannan duk basu dame shi ba kwata-kwata, bai ma sasu cikin tunanin sa ba, in sun gaji da neman layin nasa kowa ya ha'kura kawai..acewar sa. *****    Kamar yadda aka tsara... sati na cika su Alhaji suka koma shi da Uncle J da yake har ranar bai koma ba inda suka tafi da duk wani da duk wani da suka san za'a bu'kata ranar...bayan ganawar su da Alhaji Mamman sai aka sanya lokacin biki sati uku masu zuwa kacal...Uncle Ja'afar ne ya biya sadaki dubu 'dari cif   sannan suka koma gida. Uncle Ja'afar kam washe garin da aka basu auren yayi shirin sa tsaf domin ya tattara ya koma Jalingo a fa'dar sa wai sai lokacin biki ya 'karato sannan zasu dawo da iyalin sa cuz shi zai kar6i auren matsayin waliyin Mu'een. Shi kansa ya damu da rashin samun Mu'een a waya duk da ma ya san iskanci ne ya sashi rufe wayar tasa amma duk da haka ya kasa daurewa da da hakan. Da farko ya so ya share shi amma zuciyar sa ta kasa aminta hakan tausayin Mu'een ya fara kama shi, dan zuwa yanzun ya fara yadda cewa ba da yardar sa Alhaji Baba ya shirya wannan auren ba. Wannan tunanin ne ya sa shi yanke shawarar sake komawa Jigawa ya ganshi kafin ya wuce amma Alhaji Baba bai bashi damar hakan ba yayi masa katsalandan da cewa zasu je Jos tare da shi su duba Gidan gonar Alhajin dake can in yaso daga Jos 'din sai ya wuce abinsa Taraba. Hakan kuwa akayi dan tare suka yi tafiyar suka dira Jos wurin Baban mu, inda suka tarar abubuwa na tafiya normal babu matsalar komai, sosai Baban mu ke 'ko'kari wajen kulawa da amanar da aka dan'ka masa. Da yaji labarin batun auren Yah Deen kuwa cikin farin ciki ya ringa sanya albarka yana fatan Allah ya nuna musu lokacin suna cikin rayayyu. A ranar Uncle J ya wuce Taraba yana mai sake dialling number Mu'een amma baya samu zuwa lokacin kuwa abin nasa sosai ya fara bashi haushi,  dan haka sai ya yayi fushi ya share sa bai ko sake gwada 'kira ba har ya isa gida. Alhaji Baba kam kwanan sa 'daya ya dawo gida cikin farin cikin yanda yaga dukiyar sa na 'kara habbaka wurin Baban mu...wanda kafin rabuwar su Baban mu sai da yayi alkawarin insha Allahu kafin ranar auren zai zo ayi komai da shi Alhaji Baba sosai yaji da'din jin hakan kuwa duk da cewa shima auren ba wai ya kwanta masa bane amma gani yake yiwa Yah Deen auren shine babbar mafita saboda gudun fitinar shai'dan da kuma abinda zai biyo baya. Lamarin da ya matu'kar 'daga hankalin Husnah shine jin wai ansa ranar bikin ta kuma kwanaki 'kalilan, ba 'karamin tada hankalin ta hakan yayi ba gashi har a lokacin ta kasa samun sa a waya balle taji ta tabbatar da cewa shi 'din ne ko kuwa wani daban ba. Abin ya dame ta sosai, gashi Abbah ya hana ta komawa Jigawa wai har sai bayan bikin, badan haka ba ai da taje sun magantu da shi, fitan kirki ma yanzu bata yi Alhaji Mamman ya hana ta zuwa ko'ina.  Da farko kamar abin bazai dame ta ba amma daga baya har kuka take 6uya tayi cikin 'dakin ta bayan ta kulle gudun kar mahaifiyar ta ta ganta tana kuka damuwar ta ta ninku. Wasa-wasa sai da aka share kwanaki goma da dawowar ta amma har ranar bata samun layin sa. *****        Yanda yaga Ammin sa cikin mafarkin sa na jiya da dare tana kuka da hawaye tana bin sa da idanu ne ya sanya duk jikin sa yayi sanyi 'kalau, har bayan ya idar da sallar asubah ma ya kasa warwarewa, photon scene 'din ya kasa barin kwanyar sa. Yanzu ne ma yaga rashin kyautawar sa da yayi watsi da tunanin halin da mahaifan sa zasu shiga na rashin jin sa da basu yi ba...musamman Ammin sa da Anty Zainab ga kuma Uncle Ja'afar da yasan cewa sun fi kowa damuwa da shi, Alhaji Baba ne ka'dai bai sa ran zai neme shi ba saboda abinda ya faru kwanaki. Jikin sa sanyi 'kalau ya isa ga wayar tasa inda ya watsar duk tayi 'kura kasancewar tun bayan tafiyar Husnah gidan bai sake samun gatan shara ba ko'ina in ka duba zaka gansa futu-futu illah bedroom 'din sa ne yake iya kintsawa shima 'din dan acan ya fiye zama ne shiyasa, ranaku 'da'dai ku ne zaka gansa kwance a palourn sa. Ko da ya rufe wayar ya kunna ta sai yaga babu caji sannan fuskar wayar ya tsatstsage, mi'kewa yayi ya isa ya saka wayar a caji tare da zama gefen ta ya rafka uban tagumi yana bin wayar tasa da kallo zuciyar sa fal da tunanin Ammin sa. Tsawon mintina 30 yana a haka sannan ya cire wayar yana 'ko'karin shiga dan 'kiran Ammin yaga duk bata 'daukan hannun sa saboda fashewar da tayi, da 'kyar ya samu da dabara ya yi dialling numbern nata tare da 'kara wayar akunnan sa yayi shiru yana jiran ta 'daga. Ringing biyu ana uku sai aka 'daga tamkar dama zaman jiran shigowar 'kiran nasa akeyi...dan Ammi yanzu bata ta6a yin nisa ta bar wayar ta. Shiru Ammi tayi duk da irin jin dadin da ya shige ta da ganin kiran sa yau a wayar ta, sai da yayi sallama sannan Ammi ta amsa masa ciki-ciki kamar dole aka sanya ta amsawa. Gaida ta ya fara cikin kwantar da murya da tunanin 'karyar da zai shirga mata akan rashin samun sa da ba'a yi ba tsawon kwanaki...sai dai kafin ma ya 'karasa furta gaisuwar Ammi sai tayi saurin dakatar da shi da harshen su na Igbo tace" Sai yau ka ga daman tunawa da ni kenan ko Muhammad?" Da sauri ya girgiza kansa tamkar a gaban ta yake tare da fa'din" Ba haka bane Allah Ammi...am sorry..wayar tawa ce ta lalace amma Ammi believe me kullum kuna cikin raina". Inda ya bada amsa cikin harshen Hausa kamar yadda ya saba a duk lokacin da tayi masa yaren Igbo baya ta6a mayar mata amsa da yaren sai dai ya canza harshe zuwa wani yaren daban turanci ko kuma Hausa. Tun lokacin da naji 'karar ring 'din wayar Ammi na farka daga baccin da nake yi har tazo gefen bakin gado ta zauna tana amsa wayar da hannun ta 'daya a 'kirji..ido kawai na tsura mata da son jin da wa take wayar domin babu mamaki 'daya daga cikin yaranta ne da yake duk basa gida a lokacin. Sai dai jin da nayi ta ambaci suna Muhammad yasa na gane da wanda take wayar kasancewar mutun 'daya tak nasan take 'kira da wannan sunan baya ga shi kuwa sai dai wani daban can da ba 'dan gidan ba. Ido na tsura mata ta baya ina sauraran maganar tasu cuz har abinda yake fa'di tar inajin sa dan wayar Ammi akwai lafiyar speaker mai 'karfi sosai...bansan me yasa yake son wahalar da Ammi ba shi Yah Deen sam, domin bazan manta ba ya ta6a yi mata irin hakan lokacin ma yana cikin garin Shuwarin Amma karkiga yanda Ammi ta damu sosai sai gashi wannan karan ma ya sake maimaitawa, yanda nasan Ammi ta damu da rashin sa wallahi nima sai da naji wani sanyin da'di a zuciyata bayan fahimtar cewa shi 'din ne yayi 'kiran ta, a hankali na ja jikina na kwantar da kaina bisa cinyar Ammi zuciya ta cike da farin cikin daga yau Ammi na zata dawo Ammi ta asali. Hannun ta dake kan 'kirjin ta ta sau'ke shi a kaina tana shafa kitso na batare da mun yiwa juna magana ba. Ammi bata wani iya dogon fushi da shi sam shiyasa ko yanzun ma tun daga kan amsar da yabata sai tace dashi " Amma me yasa ka 'dauki dogon lokaci baka gyara wayar ba bacin kasan mutane da yawa ne zasu damu da rashin jinkan...Antyn ka Zainab sosai ta 'daga hankalin ta tunda taji batun auren ka hankalin ta ya kasa kwanciya kusan kullum sai ta 'kira ni sai dai ince mata nima baka 'kira ni ba..me yasa kai sam kanka ka'dai ka sani ne baka damu da damuwar kowa ba ko?" Tayi maganar hannun ta yawo a kan kitso na. Sai yace " Kiyi ha'kuri Ammi na.. insha Allahu bazan sake ba...ya su Alhaji Baba da su Zaidu". A ta'kaice tace " Zaidu suna school basu dawo ba" Yace " Owk...Alhaji fa?" Sai tace dashi " Ka 'kira shi mana". Yace " Toh zan 'kira shi Ammi na.." Tun kafin ya rufe baki tace da shi" Hope kasan lokacin bikin ka ya 'karato ko?" Take salon muryar sa ta canza zuwa wani iri yace da ita" Biki na kuma Ammi?" A nutse tace da shi " Erh mana ko kana nufin baka da labari?". " a a Ammi Uncle Ja'afar ya sanar da ni cewa an tambayo aure amma bamu sake wata magana da shi bayan hakan ba". " To sai ka 'kira shi mahaifin naka..may be zai yi maka bayani da kansa, amma ina jin 2weeks kacal ya rage a 'daura auren ma..". Cewa yayi " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...Ammi wai wace yarinyar dan Allah?" " Ni ta ya zan sani Mu'een, nima fa ba'a sanar dani ba har sai bayan da aka tsaida rana..amma an dai ce a Azare take 'kilan waccen yarinyar ce..ai kasan da batun tun kafin komawar ka...kuma kasan Alhaji baya canza maganar sa shi....". Idanu na lumshe ina take kunnuwa na suka daina cigaba da sauraron maganar Ammi, jin wai zai yi aure...sam ban san yanayin da nake jin zuciya ta ba, na dai tsinci la66a na da furta" Barka" 'Kasan ma'koshi amma na kasa tantance manufata ta fa'dan hakan. Ban ma san ya 'karshen wayar ta su ta kasance ba sai ji nayi Ammi na fa'din" Kitson ki ya tsufa sosai Hudah...anjima za'ayi miki ko manya ma kafin kuma lokacin bikin Yayan ku sai ai miki mai kyau ko?" Sai lokacin tunani na ya tsaya inda na no'ke kafa'da tare da fa'din" Ni banaso Ammi". Ammi sai tace " To shikenan naji..amma zamu wurin Umman Saudah anjima sai tayi miki na bayan hannu ko ai nata babu zafi zan ma ce tayi miki manya kinji". Jin haka sai nayi saurin 'dage kaina alamar to jin cewa Ummata ce zata min kitson. Yah Deen kam suna gama waya da Ammi sai ya 'kira Alhaji Baba suka gaisa faran-faram...Alhaji bai nuna masa alamun komai na 6acin rai ba haka nan bai yi masa zancen auren ba kamar yadda shima Mu'een 'din bai iya ya tambaya ba...kafin suyi sallama sai Alhaji yace da shi nan da kwana ki goma yana bu'katar ganin sa a gida, wanda a lokacin zai yi dai-dai ne da sati guda kafin ranar 'daurin auren. Bai yi musun komai ba kamar yadda bai nemi jin dalilin zuwan nasa ba illah " To Alhaji" da ya amsa shi da shi a takaice, har suka yanke 'kiran baii ya sake fa'din komai ba illah damuwar sa da ta 'karu. Bin wayar yayi da kallo yana sake kallon sekannin da yin waya da mahaifin sa ta 'dauke su, dududu 43seconds ne, sa6anin baya da in suna waya sukan shafe a 'kalla mintina goma ko 'kasa da haka. Tun suna waya da Alhajin yake kallon 'kiran Husnah amma bai 'daga ba ko yanzun ma kuwa da yake ri'ke da wayar yana tunanin yanda sha'kuwar sa da Alhaji Baba ta sami babban gi6in da ke nemen ta6a masa zuciya sai ga wani 'kiran Husnan ya shigo...ku ayyana yanda Husnah zataji bayan ta shafe kusan kwanaki goma tana neman layin sa bata samu sai a yau da ta samu ya kuke ganin zata ji...ai 'kira kam babu sassauci ta ringa yi tana 'karawa kenan. Bai bi ta kan 'kiran da Husnah ke yi masa ba sai ya fara tunani tsakanin Antyn sa da Uncle Ja'afar wa ya kamata ya fara 'kira. Layin Uncle Ja'afar ya 'kira shima da 'kyar dan wayar sosai ta tabu, sai dai ma Uncle Ja'afar bai 'dauki 'kiran ba, daman baya son masifar sa dan ya san dole sai yayi dama...shi yasa bai sake ba. Daga 'kira 'dayan kuwa sai ya bar shi ya koma 'kiran Anty Zainab. Wacce tana dauka ta fara fa'din " Haba, haba Mu'een gaskiya baka kyauta mana ba, me yasa ka kashe wayar ka dan Allah bacin kasan za'a neme ka?" " 'Dan murmushi yayi da bai kai masa zuciya ba kawai yadda Anty Zee ke bayani ne ya 'dan bashi dariya... Sai yace" Anty ai kya tsaya mu gaisa tukunna ko?" " a a bar wannan batun gaisuwar...baka san yadda hankali na ya tashi ba ne da jin wai an tsaida lokacin auren ka har ma ya kusa, ya akayi haka kuma Mu'een kai da kace min ba yanzu zakayi aure ba?" Yana gyara zaman sa yake ce da ita " Alhaji ne fa ya shirya wannan auren Uncle bai gaya miki bane?" Tace" Ya min bayani amma gaskiya banji da'di ba, yace wai kai kace baka son auren Alhaji kuma yace masa kai ke bu'katar auren shiyasa zai yi maka me yasa hakanne to wai kaina duk ya kulle". Idanu ya lumshe not knowing abinda zai ce mata, tsintan bakin sa kawai yayi da fa'din" Ni kaina bansani ba Anty..ni dai ki min addu'ah Allah yasa afasa dan Allah". " Da gasken baka so kenan?" " Har cikin zuciya ta Anty". Sai tace " Wallahi nima ji nayi auren bai kwanta min ba especially da bai kasance 'yar gidan Ammin nan ba gaskiya banji da'di ba ni kam...ita wannan 'din 'yar waye ce?" " 'yar makarantar mu ce Anty". " To Allah ya sanya Alkhairi.." Bai ce da ita komai ba kawai ya yanke 'kiran tare da kife wayar tasa ya lumshe idanu. Yana ganin 'kiran Husnah amma ya 'ki kulawa..tayi masa missedcall a 'kalla goma sha uku duk bai 'dauka ba, har hawaye take tsiyayarwa daga inda take tana jin tamkar tayi tsuntsuwa ta ganta gaban sa dan kawai taji me ze ce da ita. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *49* Text ta tura mishi nan ma bata ga alamun ya kula ba, a hankali hawayen ta ya fara sau'ka saman kuncin ta tsabar haushin rashin samun response daga wajen sa, tunanin halin da yake shirin sanya rayuwar ta bayan ya gama da rayuwar tan ya sa itama a zuciye tayi jifa da wayar ta, sai na ta wayar ta tsaya ne iya kan tsakiyar gadon ta pillow ne ya tare ta bata 'karasa sau'ka ta ha'du da 'kasan tiles ba da anyi biyu. Kwanciya tayi tana sake sakin wani kukan mai tsuma zuciya gwanin ban tausayi. Ji take kamar zata yi hauka..sam ta rasa menene dalilin hakan, ina zata je ta samu sau'ki cikin ranta? ta rasa gaba 'daya, me zata ce da mahaifiyar ta wanda ba zai 'daga hankalin ta ba shima ta rasa kwata-kwata. Mu'een ma 6angaren sa babu wani sau'ki ko ka'dan, dan ya fahimci babu ta inda abin yake da sassauci sam, nan da kwanaki goma Alhaji yqce yake nemen sa,  kenan akan auren ne...." Yah Allah ka taimake ni ka tarwatsa wannan auren". Ya furta a fili yana maida idanu ya lumshe. Kusan cikin kowacce sallar sa sai yayi wannan addu'ar, wanda ko yanzun ma hakan ya sake maimaitawa yana mi'kewa daga inda yake zaune. Bayi ya shiga domin ya watso ruwa, yau yana jin shiga school ne haka kawai, bayan jin muryar Ammin sa sai yaji wata 'yar natsuwa ta shige shi duk da ma ba albishir 'din anfasa auren tayi masa ba, amma haka kawai sai yaji damuwar sa ta ragu sosai. Yanzu da ya san cewa babu mai iya sawa afasa auren ne sai ya barwa Allah kawai sai dai yana wankan ma har murmushin mugunta yake yi dan irin shegen shirin muguntar da zai shiryawa duk yarinyar da ta kuskura ta yadda aka 'daura auren sa da ita. Da fitowar sa sai ya koma wurin wayar tasa yana murmushin ya sa hannu ya 'dago wayar sai da ya shiga wajen text yaga abinda ta rubuta masa ro'ko ne kawai akan ya daure ya 'dauki 'kiran ta...a fili ya saki 'dan 'karamin tsaki afili ya furta" Kanki ake ji ai"  Fita yayi daga wurin text 'din ya koma ya dannawa layin Husnah 'kira yana furzar da huci daga bakin sa. Tana cikin kuka sai taji 'karan wayar ta, bata yi tunanin shi bane cuz ta san da wuya yayi 'kiran ta dan haka share wayar tayi ta cigaba da kuka abin ta, sai taji kuma ta kasa daurewa, daf da wayar zai yanke tayi saurin kai hannun ta ta 'dago, da wuri ta gyara zama da rawar jiki taja recieve dan ganin sunan da ke yawo kan fuskar wayar tata. Tana kukan ta 'kara wayar a kunnan ta batare da tayi magana ba, jikin ta har rawa yake yi haka ma bakin ta. Hannu ta kai ta rufe bakin da shi yayin da 'dayan hannun ke ri'ke da wayar manne da kunnen ta sai ta kasa magana illah kuwa da ta cigaba da yi mai ha'de da sheshshe'ka, da ka ganta zaka san zuciyar ta ta wahala, tausayin ta ne sosai zai kama ka. Mu'een na jin ta tana kukan amma ya share tamkar bai ji ta ba, sai ma ta6e baki da yayi ya'ki furta komai. Ya bata a 'kalla kimanin mintina biyu da rabi yana tsaye yana jin ta tana ta sheshshe'kan kuka, bai ce da ita komai ba tsawon wasu mintina suna a hakan. Yah Deen dai-dai da 'kwayar zarra daga cikin 'digon tausayin Husnah bai ji a zuciyar sa ba, yayin da Husnah kuwa ke  son tayi magana amma kukan sai sake taso mata yake yi, abubuwa ne duk suka yiwa rayuwar ta yawa suka mata rumfa...sunan sa  kawai take iya 'kira sai kuma ta cigaba da kukan ta idan tace.."..Mu...'een" kamar zata sake magana amma sai kuka ya 'kwace mata...tausayin rayuwar ta take yi ganin cewa daga mahaifiyar ta babu wanda ya damu da farin cikin ta, ko shi Mu'een 'din ma zuwa yanzun ta lura da kwai abu a 'kasan ransa. Gajiya yayi da kukan nata at same time kuma ya gaji da ri'ke waya a saman kunnan sa, yayi tunanin sanya wayar a speaker ya ajiye amma kuma sai yaga kamar in yayi hakan ma tamkar ya bata wani dama ne na musamman da zata ji a zuciyar ta cewar he cares, hakan ya sanya a nutse cikin sanyin hali yace da ita" Quite please Husnah kunne na". Fa'dar hakan da yayi ne ya sa kukan nata ya 'dan tsagaita a hankali bayan wasu sekanni, ji yake kamar ya yanke 'kiran ma kwata-kwata ganin kamar bazata natsu da kyau ta saurare shi ba, sai dai baya jin daga yau 'din akwai wata ala'ka ta daban da zata sake ha'da su, abu mai muhimmanci yake son sanar da ita da zai taimaki rayuwar ta da farin cikin ta, wanda idan ta yadda tayi na'am da shi to tamkar ta ceci zuciyar ta ne, ta wani 6angaren kuwa harda shi, fatan sa daga yanzu ala'kar su yanke koma ba haka b shi baya jin akwai wani abin da zai sa ya sake sauraran ta har ayi auren shiyasa kawai ya saka dauriya cikin ransa har ta rage sautin kukan da take yi. Jin ta fara sau'ke numafashi ne ya sashi fa'din" Ki nutsu da kyau ki saurare ni... kina jina?" Da " Umm" ta amsa shi tana goge hawayen dake fitowa ta 'kasan idanun  ta. Sai ya sake fa'din" Magana nake so muyi dake na 'karshe kina ji?" Yanzun kam bata amsa shi ba illah bada hankali da tayi sosai tana sauraron sa...yayin da ya cigaba da fa'din" Wani labari kika tarar a gida bayan komawar ki? ki gaya min inji..". Yayi mata tambaya irin wacce ya ta6a yi mata abaya. Da muryar kuka ta bashi amsa da fa'din" Ance wai an bada aure na ga wani a garin ku mai suna Muhammad..." Idanu ya lumshe yana shafo suman kansa da 'dayan hannun sa yace da ita" Ya kika ji batun to?" Tace" Hankali na ya kasa kwanciya". Murmushin mugunta yayi yana fa'din" Really? Ni fa aka bawa auren ki Husnah?" Shiru Husnah tayi tana jin yanda zuciyar ta dokawa, wani sashi na damuwar ta taji ya na silalewa nan take, sosai taji da'din jin cewa shine aka bawa auran ta, kenn shi zata aura su 'karasa rayuwar su da shi. Take ta saki murmushi mara sauti na farin ciki da jin da'di wanda in ba kana gabanta ba baza ka ta6a sanin tayi shi ba. Shima Yah Deen shiru yayi tun bayan abinda ya fa'di, a 'ko'karin sa na son jin amsar da zai fito bakin ta shiyasa ya bata lokaci. Ganin kamar shirun yayi yawa ne ya sashi sake fa'din..." Tell me to kina son auren da ni ko baki so na?" Yanda yayi maganar bazaka ta6a zaton he is up to something ba, muryar sa wasai yayi maganar bazaka ta6a fahimtar yanayin sa ba. Husnah kam cikin jin da'di ta tana share hawayen farin cikin dake zubo mata ta bashi amsa da fa'din" Mu'een kaima ai kasan ina matu'kar son ka...me yasa zan'ki amincewa da auren ka? wallahi indai da kai ne inaso kuma na amince har zuciya ta....". A 'dan fusace ya tare ta da fa'din " To ni ban so!..Husnah ni ban amince da auren ki ba...kuma ki sani har abada tsakani na da ke Husnab h babu wannan batun, rayuwar aure na ba rayuwa ce da zan yi shi batare da tsari ba, bada irin ki nake so in shimfi'da ta ba ma, ke kanki kinsan bamu dace da juna ba, bai kamata mu kasance ma'aurata ba Husnah ko kin ta6a ganin inda mutum mai hankali ya kwashi datti dake bola ya akai cikin gidan sa ya adana? Infact ma kin ta6a jin ni na furta cewa zan aure ki ne..ko da wasa?" Ya 'karashe maganar yana huci da zararren idanu...da ace Husnah na kusa da shine na tabbata tsoron ganin yanayin da shiga a lokacin ma ka'dai ya isa yasa ta furta cewa ta fasa auran sa. A 'dan gigice tana  'kan'kance idanun mamaki ta furta" Mu'een..."! Tana karkace wuya. Saurin dakatar da ita yayi da fa'din" Just listen...ba amsar ki nake son ji ba." yayi maganar tare da 'dago yatsan shi 'daya kamar tana gaban sa sannan ya cigaba da fa'din" ... Zan miki garga'di ne sau 'daya tak and that's na farko kuma na 'karshe..I won't ever repeat my self again..fatan kin fahimce ni?" Bai damu da rashin amsar ta ba kawai ya cigaba da fa'din" Husnah idan kina son kanki da arzi'ki, farin ciki da walwala to is better ki rufawa kanki asiri ki nemi hanyar raba auren nan, dan ubanki zaki ci a hannu na matu'kar kika kuskura kika yadda igiyoyin aure na na farko masu matu'kar daraja suka fara dake, wallahi sai kin gane waye asalin Muhammad Tahir...abinda kawai zan iya gaya miki ayanzu kenan sauran kuma ki bari in kika yi kuskuran zuwa hannu na zaki fahimta da kanki..." Daga haka ya cire wayar daga kunnan sa yana shirin yanke 'kiran sai kuma ya tuna da wani abu, saurin maida wayar yayi kunnan sa Husnah kam dama mutuwar zaune tayi bata ko motsa da hannun ta ba balle ta raba wayar da kunnan ta...wuri 'daya ta zubawa idanu ko hawayen ma yanzun bai fito ba banda aikin bugu da zuciyar take yi, gani take tamkar a mafarki ne Mu'een ke shirin nuna mata zallar tsana ta zahiri wacce babu ko kara aciki, fatan ta inma mafarkin rake yi to kar Allah yasa ya kasance gaskiya. Tana cikin hakan taji yana sake fa'din"...uhumm kina jina ko? Wallahi kuma kika sake yin kuskuran da  'kiran ki ya ratso min cikin waya ko ki sani ni da ke ne, matu'kar ba cewa zakiyi na fasa auren ba kar ki sake ki 'kira layi na...don't tell me kin fasa but an fasa gaba 'daya as in harda 6angaren mahaifi na da hakan ne ka'dai na baki damar 'kiran wayata in ba haka ba...dont ever call my line ever again fatan kin fahimce ni?" Bata iya ta bashi amsa ba ko yanzun ma sai wani kuka da ya 'kwace mata mai matu'kar cin zuciya, haka ta ringa kuka babu mai lallashin ta, ita ka'dai ta san yanda take ji, ji take rayuwar na neman juya mata baya gaba 'daya. Mu'een da ta sani ne wannan 'din ko kuwa wanin sa, Mu'een ne zai iya duban tsabar idanun ta ya fa'da mata wa'dannan maganganun  bacin ma ta san ba wani girman ta sosai yayi ba, in ba ma soyayya ba da ina ta ina shi? Da me ze ha'da shi da ita da har zai mata la'kabi da dattin bola...wannan abu da me yayi kama..wallahi Nu'een ka cuce ni ka gama da rayuwa ta" Ta fa'di cike da takaici tana dukan katifa da duk hannuwan ta biyu...yau ne rana na farko a rayuwar ta da ta ta6a yin Allah wadarai da soyayya gaba 'daya, musamman ma irin soyayyar da ta masa irin wacce ke cutar da 6angare 'daya 'dinnan, Mu'een da ke haukace wa ya zauce a jikin ta wurin morar halittar da Allah yayi mata shine yau yake mata garga'di akan aure tsakanin su, bata ta6a zaton jin haka daga gare shi ba ko da wasa. Ta tsinewa ranar da ta mallaka masa budurcin ta yafi sau hamsin, ko san tunawa bata yi, yanzu ne take da na sanin sanin sa a rayuwa..kuma ra tabbatar da cewa kalaman da tayi matan babu wasa cikin su sam, atanda ta sanshi ra san cewa daga cikin zuciyar sa maganar ke fitowa kuma iya gaskiyar sa kenan, da gaske dama haka maza suke?...ba su da amana bayan sun gama da rayuwar ka da yan cinka...'karshe gudun ka suke cike da alfaharin sun fi 'karfin zaman aure tare da ke? Yah ilahi... Inannalillahi wa inna ilaiahi raji'un" Haka kawai ta ringa nanatawa tana kuka. Ta 'dauki tsawon lokaci tana a haka kafin ta samu ta bawa kanta ha'kuri ta tashi ta je ta watsa ruwa, ko cikin bathroom 'din ma ta da'de kafin ta fito tunanin ta yadda zata tunkari mahaifiyar ta da wannan maganar take yi, me zata ce da ita da bazai tashi hankalin ta ba, tana son mahaifiyar tana kuma son farin cikin ta ta yadda take jin koda zata 'kuntatawa zuciyar ta ne tana son ganin mummyn ta na walwala, domin ita ka'daice ta fi kowa damuwa da damuwar ta in akwai na biyun ta to Yayan ta Hisham ne. Haka ta fito ta sake shiri jikin ta sanyi 'kalau, kallo 'daya zaka yi mata ka tabbatar ba dai-dai take ba, gaban mirror taje ta tsaya tana 'karewa fuskar ta kallo sam bata so mahaifiyar ta ta fahimci halin da take ciki, dole zata 6oye mata komai dan kar ta shiga damuwa tunda tasan yadda Alhaji Mamman ke treating Mummyn ta ba lallai ne ya saurare ta kan batun ba, ta kuma san da mahaifiyar ta taji asalin meke tafiya dole ne tace zata same shi tayi mai bayani, ko da kuwa cewa akayi bata son auren sa6anin yanda ya yadda akan cewa sun daidata kansu tun farko 'din ma idan yayi niyya sai anyi to ina amfanin ta bar mahaifiyar ta da tunanin an aura mata wanda zai muzguna mata ya kusantata da lahirar ta. Abin ma zai fi cimata rai a duk lokacin da ta tuna cewa Mu'een na azabtar da ita ne saboda already ya san ta matsayin 'ya mace shiyasa ya tsane ta yake azabtar da ita tasan ba komai bane ya kawo hakan face sakamakon yaudarar mahaifiyar ta da tayi take mata fuska biyu bacin a gefe tana holewar ta agaban ta kuma ta zama saliha, shiyasa ma tayi na'am ta kar6i hukuncin ita ka'dai bazata yadda zuciyar mahaifiyar ta ya 6aci sanadin hakan ba tunda babu s hannun ta aciki...( _Mata fa naku...karfa kiyi zaton ko kinje kin yi kalar rayuwar da kika ga dama Allah ba zai kamaki ba...ba wai maza ne ka'dai Allah ke hukuntawa bisa aikata Zina ba a a harma da matan wallahi...gara ma mu nutsu dan babu yadda za'a yi iyayen ki su baki tarbiya su 6ata lokacin su wurin jan ki ajiki su saki farin ciki su wadata ki da komai na rayuwa 'karshe suje suna alfahari dake cewa sun haifi natsatstsa, amma 'karshe ki watsa musu 'kasa a idanu sanadin soyayyar wani banzan mayaudari sai ki zama mai fuska biyu bayan kin biyewa saurayin kun gama aikata son ranku... gaban iyayen ki kuma kina acting as babu yake fannin hankali da natsuwa dan munfurci, kuma a hakan sai kiyi zaton Allah ba zai kamaki ba? wallahi matu'kar baki tuba ba dole ne Allah ya hukunta ki....kar kiji ance in kayi da 'yar wani za'ayi da taka, haka in kayi da matar wani ma za'a yi da taka ki zaci hukuncin kan maza kawai ya sau'ka...to ki sani kema da kika biye masa akwai naki hukuncin gagarumi kuwa yana jiran ki, wasu mazan ma zasu yi ta aikata Zinan son ran su, su kuma yi dacen samun nitsatstsiyar mace su aura, 'karshe ma kika ga 'ya'yan su sun rayu cikin kariyar ubangiji...sai kiga sun yi tunanin ai sunci bulus....duk babu yadda Allah baiyi da bayin sa, kuma yana 'kaddara abu ne a duk kan wanda ya ga dama, yana jarbtar bayin sa ne da kala-kalar 'kaddara, idan ya so ka da Rahama nema zai hukunta ka tun anan duniya ba sai anje can ba....Sannan akwai Zina ta tilastawa misali kamar rape da sauransu, shine wanda hukuncin sa ke sau'ka kan namiji ma'ana shi wanda yayi niyyar yi 'din har ya tilastaki, amma in kin san ke da kanki kam kika je da niyyar ki da kuma yardar ki to fa ke ma kinsan naki hukuncin na jiran ki wurin mahalicci...'YAN UWA NA MU DAURE MU TUBA MU DAINA, ZINA FA DATTIN ZUCIYA TAKE SAWA ZATA NESANTAKA DA RAHAMAR ALLAH TA KUMA KUSANTA KA DA SHAI'DAN DA AIYUKAN SA 'KARSHE YA BARKA DA AZABAR WUTAR ALLAH MAJI RO'KO .... Yah Allah ubangiji muna ro'kon ka kayi mana tsari da kusantar Zina_ ). Ba'kin kwalli ta nema ta ranba'da a idanun ta take ta 'dan sauya kamanni,  harda powder ta shafa ta saka lipstick a bakin ta sannan ta kama hanyar fita tana addu'ar Allah ya rufa mata asiri, fita tayi taje gefen mummyn ta dake zaune a palour tana kan lissafe-lissafe ta isa ta zauna daga gefen ta cikin sanyin murya tace " Mummy barka da hutawa". " Yauwa Husnah...an fito ne?" " Erh mummy...". Kafin Mummyn ta sake magana sai ta riga ta da fa'din " 'Dazun nan munyi magana da shi ina zaune kawai naga ya 'kira ni". Tayi maganar bayan ta 'ka'kalo murmushin 'karya. Ba bu'katar sake tambaya cuz already abin ke ran kowannane daga cikin su, tsawon kusan sati biyu suka 'dauka suna jiran ji daga gare shi, hakan yasa mummyn Husnah cikin farin ciki ta furta " Alhamdulillah...ya kuma kuka yi da shi?" Tayi maganar tana yi mata duba irin na jin da'di. Husnah sai ta sunkuyar da kanta sannab tace " Mummyn ce min yayj wai iyayen sa ne suka zo, kwana kin nan 'din ma an sace wayar sa ne shiyasa ya 'dauki lokaci bai 'kira ni ba...amma yanzun ya sai wata". Cikin sanyi da dukkan dauriyar ta take magana, sosai tayi 'ko'kari wajen 6oye dukkan damuwar ta saboda son ganin farin cikin masoyiyar mahaifiyar ta. Mummyn Husnah kam banda _Alhamdulillah_ babu abinda take ta nanatawa, dama damuwar ta shine kar a aura wa Husnah wanda bata san shi ba ko kuma ace bata son shi..yanzu kuwa da taji cewa wanda ta sanin ne ya sata 'dan ji sanyi cikin ranta. Cikin kwantar da hankali ta yi mata nasiha akan kar ta 'daga hankalin ta dan ta ganta ta koma wata iri komai zai dai-dai ta da iznin Allah..ina ta 'karashe da fa'din" Ko akwai wara matsalar ne daban?" Husnah na jin haka rayh saurjn girgiza kanta tare da fa'din" Babu komai Mummy kawai dai naga kamar lokacin yayi kusa ne sosai". Murmushi Mummyn tare sannan tace" Shiyasa ai nace ki kwantar da hankalin ki, shi aure ai lokaci ne, idan Allah ya riga ya rubuta mutun bai isa ya canza shi ba, da shiri ko babu shiri idan lokaci ya tsaya to fa sai anyi, misalin sa tamkar mutuwa ne...karma wannan batun ya dame ki...ki saki ranki ki runguni 'kaddarar ki kinji Uwata". Kai ta jinjina cike da gamsuwa still idanun ta na kan hannun ta bata iya ta ha'da idanu da Mummyn nata ba. Kawar da wancen maganar Mummyn Husnah tayi inda tana gyara zamanta zuwa kishingi'da tace "..Tambayar da nake so in miki tuntuni da nace sai kun yi waya da shi 'dinnan kin tuna ko?" Husnah cewa tayi " Erh mummy ban manta ba". " Dama ina so idan ya kasance shi 'din ne in tamabaye ki shin Husnah daman can kuna soyayya da shine ne, ma'ana kina son shi yana son ki?" Fuskar ta tayi saurin rufewa da hannuwan ta biyu kamar gaske sai kuma ta ta shi da hanzari ta bar wurin tama fice daga palourn gaba 'daya, ga duk wanda tayi hakan agaban sa zai yi zaton ko kunya ce ta sata tashi, sai dai sam ba haka bane kuka ne yaso 'kwace Husnah gudun kar tayi gaban mahaifiyar ta yasa tayi saurin ta shi ta bar wurin, dan tasan dole in Mummyn ta taga tana kuka sai ta tambayi dalili ita kuwa bata san amsar me ya kamata ta bata. Yayin da Mummyn Husnah tayi tunanin ko tsabar kunyar ne ya sanya ta yin hakan, dan haka da murmushi kawai ta bi bayan ta tana jin farin ciki na ratsa ta ta ko'ina, yanzu kam tasan ba auren dole ake son yiwa Husnah ba dan haka bata da sauran damuwa. Tun daga ranar ta fara sanar da 'yan uwa da abokan arziki tana fa'din date 'din bikin cikin farin ciki marar misaltuwa. Haka ta fara shiri gadan-gadan wanda ya dace tayi ta 6angren ta na uwa, tayi 'ko'kari waje. gyare Husnah tsab cikin 'yan kwanakin duk kuwa da bata san ma cewa ita 'din already ta biyewa son zuciya ta lalata rayuwar ta ba, hatta da kayan fitan biki duk ta bada sa'kon su za'a kawo mata daga lagos bayan an 'din ke su. Ko ha'duwa da Husnah ba sa yi sosai saboda yanda ta saka hidima agaban ta, bata san cewa Husnah na kashe kanta da damuwa akowace rana ba, kallo 'daya zakayi mata kasan cewa ta rame sosai. Tsimin da Mummyn ta ke bata kuwa bata wasa da shan su, cuz tayi tunanin cewa babu mamaki idan yaji ta canza zai iya sakkowa su raya auren su kamar kowa cikin farin ciki, hakan yasa bata yi wasa da gyaran jikin ta ba...wani abin ma ta hannun friends 'din ta ake sayo mata su a 6oye batare da sanin Mummyn ba. *****     'Bangaren Ammi ma shirye-shirye ya kankama sosai...Anty Zainab tuni tazo suka wuce Kano da wata 'kawar Ammi suka yi siyayyar kayan lefe wanda Alhaji Baba da kansa ya bada ku'din masu nawin gaske, Anty Zainab kam sakin ranta tayi tayi siyayya tsakanin ta da Allah na ganj a yaba, duk kuwa da cewa bason auren take yi ba amma ance abinda ka sowa kanka ka sowa 'dan uwanka daga cikin ingantattun hadisan manzo, hakan yasa ta zage ta za6i latest kaya na gani a bada labari masu kyau da tsarin gani ga kuma daraja a jikin wanda ya sanya su. Tun tana can ma ta 'kira Mu'een tana dariya tayi masa albishir 'din yawan ku'din da Alhaji ya bayar na siyan lefen auren sa, Yah Deen kam sai cewa yayi  " Ni ina ruwa na kuma Anty?". Dariya tayi masa sosai  sannan tace" To kai me zan siya maka..?" Tun ma kan ta rufe baki tace" Babu komai ". Inda ya bata amsa a takaice yana kashe wayar sa. Anty Zainab kam Murmushi tayi ganin yau abinda yayi, rasan duk cikin fushin auren ne.." Ban da abinka ai Alkhairin sa zaka nema". Ta fa'di hakan ne cikin zuciyar ta.   Wani shegen yadi ta za6a masa mai kyau da tsada, dan tasan wannan sarkin tempern da wuya idan zai natsu har ya 'dinka kayayyakin da ya dace a sanya su wurin biki. Sai da ta gama za5a masa duk abubuwan da ta ga cewa sun dace da shi sannan ta dawo kaina a fili ta furta" Ba za'a bar yarinyar Ammi a baya ba". Ta 'kaeashe da murmushi. Siya min nima tayi tsadaddun lace kala biyu ta bada 'dinki tun acan aka 'din ka min dan ita Anty Zainab haka kawai take jina har cikin ranta, Ammi ma am mata nata kala uku masu masifar 'daukan hankali abin sai wanda ya gani, gaskiya Anty Zee tayi 'ko'kari sosai dan kayan da ta siyawa Yah Deen ma sun kusan kaiwa akwati guda. Haka Anty Zainab suka dawo gida da kaya kaca-kaca, lokacin da ta nunawa Ammi kayan da ta 'din ko min sai duk farin cikin Ammi ya ninku akan nada, ko nata kayan bai sata farin ciki kamar yadda taga nawa ba, dama already ta bayar da kayan Yah Deen da ya ta6a siyawa Nanne tace a 'dinka min riga da skirt inda ta ha'da da wata super atampa tace duk a'dinkamin na fitan bikin Yah Deen, ta kuma siya min takalma na da mayafai, sai nake jina tamkar wata sarauniya tsabar da'di musamman da naga wanda Anty Zee ta kawo min suma da mayafan su da takalma sai nakasa 6oye farin ciki na...wanda Alhaji Baba ya siya mana kuwa ban san guda nawa ba amma dai daga ni sai Ammi ya siyawa...su Saif yace sai sun dawo. Ma'u itace mutun ta biyu dana gaya wa cewa an 'dinko min kaya da yawa na bikin Yah Deen wanda tuni na kaiwa Ummah ta labarin...ina murna ta na fa'da mata lokacin an taso daga islamiya muna hanyar mu ta zuwa gida, gani nayi Ma'u ta tsura min idanu kawai tana kallo na, ban damu d kallon ba ni kam kawai na cigaba da bata labarin yawan kayan da kuma kyan su cikin jin da'di. Muna kan hanya wani mai suna Ahmad dake matu'kar son Ma'u ya tari gaban mu yana yi mata magana, har a lokqcin kuwa bata ce da ni komai ba ni ke ta zuba abina, kawai tashin farko kamar dama jira take tga ya bayyana gaban ta sai gani nayi ta fara zazzaga masa masifa tamkar wani 'dan cikin ta, ni kuwa da ban iya yiwa wanda ya fini rashin kunya ba sai na zaro idanu na ina kallon ta, ina 'kiyasta shekarun tsakanin su kamar wacce aka gaya min, na dan yafi ta tsayi da girma amma bansan shekarun sa ba, Ma'u ce dai nasan sha shida ne shekarun ta cuz asali bata kai Nannen mu shekaru ba kawai dai Allah ya ha'da jinin su ne balle kuma da yake ita Nanne na da matsalar rashin lafiya shiyasa ma bata da saurin girma sai duk mu ka zama 'daya harda ni. Ma'u na gama masifar tayi gaba abinta nima dake faman tunanin sai na bita abaya, har nayi gaba sai kuma na waigo na kalle shi" Yah Ahmad dan Allah kayi ha'kuri". nace da shi da karyayyiyar murya dan har ga Allah banji da'din abinda ya farun ba. " Bakomai 'kanwata kar ki damu". Yace da ni yana murmushi da alamu masifar tata bata wani 6ata ransa ba. Kai na jinjina masa ina juya sunan da ya 'kira ni da shi wato 'kanwa ta..nasan babu mamaki Yah Ahmad da nacecda shh ne ya sa shi ce min 'kanwar shi..ni kuwa Ammi ce ta ce da ni duj wanda ya fini ince da shh Yah..in macece kuma ince Anty tace min mutane na matu'kar son yaro mai girmama manya..shiyasa na saba da hakan. Kusa da Ma'u na tsaya ta gaban ta da niyyan gaya mata kuskuren da tayi  sai dai kafin nayi magana sai kuma naga tana share hawaye...baki na ta6e gefe batare da na ce da ita 'kala ba...Gaba ta yi sai na bh bayan ta da kallon mamakin kukan kuma, wannan shine fin 'karfi ita da masifa kuma itace ke da kuka. Ban bh ta ba na tafi a nutse kamar yanda saba har na isa gida, dama ma ko mhn tafi tare ma mhna rabuwa a hanya dan 6angare daban muke da ita. Bintu 'kawata da muke aji 'daya amakaranta itama sai da na bata labarin kayan nawa ina mai matu'kar farin ciki. Bayan kwana biyu sannan muka ha'du da Ma'u cuz bata zo jiya ba, bayan an tashi daga Islamiyar ban damu inji mai ya hanata zuwa jiyan ba sai kawai nace mata" Rann nan baki kyauta ba gaskiya Ma'u da kika ta yiwa Yah Ahmad masifa,  naga shi 'din ba sa'anki ba ne, Allah ki daina rashin kunya..in ba haka ba duk ranar da kika ha'du da irin su Yah Deen wallahi dukan tsiya zaki sha babu ruwa na". Baki ta mur'da tare da fa'din" Dama nace da ke akwai ruwan ki a ciki ne?" Jin abinda tace 'din ya sani kawar da kai na gefe nima nace" Ni dai na gaya miki..." Kafin ma in gama rufe baki na sai ta waigo ta kalle ni tare da saurin taran baki na da fa'din" Wai dagaske aure zai yi?" " Wa 'din?" Nima na tambaye ta ina yatsina fuska ta...sai tace " Yah Deen 'din mana". Nace mata" ehh mana Auren kwanan nan za'ayi". Shiru tayi bata sake ce da ni komai ba, har muka rabu nima ban sake yi mata magana ba dan haushin rashin kunyar da ta yi kuma bata ce mjn bazata sake ba shiyasa naji haushi. *****       Wasa-wasa lokaci na ta faman 'karatowa yanzu Mu'een ya saki ransa a makaranta ba'a gane cewa yana cikin damuwa sai dai a kowanni lokaci bashi da aiki sai tunanin irin abinda zai yiwa matar da za'a aura masa, lokuta da dama zaki ga ya saki murmushi shi ka'dai wanda ba na komai bane face na tsantsan mugunta..bai ta6a furtawa kowa shirin sa ba daga shi sai zuciyar sa yake shirya abin sa dan ya san idan Ishaq ya sani wa'azi zai ringa yi masa kullum har yaji ya fasa shi kuwa abinda zai hana shi aiwatar da niyyar sa akan ta to mutuwa ce ka'dai..hakan yasa yaja bakin sa yayi shiru. Sha'kuwar sa da su Ishaq kuwa sai abinda yayi gaba cuz weekend 'din da ya wuce ma a gidan sa suka yi ta...Ishaq na matu'kar jin da'din yanda yaga lokaci guda Mu'een yayi watsi da damuwar sa ya rungumi 'kaddarar sa, shi ka'dai ya san farin cikin da ya shiga da ya fahimci yanzu Mu'een baya tare da damuwar komai, shine kuma ya fara fahimtar yawan murmushi da Mu'een ke saki a mafiya yawan lokuta batare da dalili ba, harma da ya tambaye shi dalilin sai yace wai mamaki kawai yake yi wai shi za'a yiwa aure. Ishaq sai yace" Zaka iya ne ai shiyasa tun yanzu Allah ya za6eka tun kana 'dan shekara ashirin da shida a funiya ya baka damar cika sunnar ma'aikin sa..so is better ka gode masa kawai". Ajiyar numfashi ya sau'ke yana fa'din" dole na ai". Anas sai yace" Kaga mu har yanzu bamu samu wannan damar ba kuma babu wanda ya tuna da mu yayi mana gatan hakan". Ya 'karashe maganar yana murmushi. Mu'een sai yace" Karka damu Anas lokaci ne ai". " Hakane". Imam yace yana 'daukan wayar sa, yayin da Ishaq ya jinjina kansa up and down vike da gamsuwa. *****       Yau ta kama kwanaki tara kenan da yin wayar sa da Alhaji Baba har yau 'din kuwa basu sake ba, kuma yana sane da cewa gobe ne ya kama ta ya tafi Shuwarin kamar yadda Alhaji ya bu'kata amma sam bai shiryawa hakan ba, musamman da ya san cewa a dalilin auren Alhaji yace ya je tun sauran sati guda shiyasa yayi biris da maganar. Yana waya da Ammin sa, Anty Zee da Uncle J da suka shirya bayan yasha masifar raina masa hankali da yayi ya kashe wayar sa acewar sa...da 'kyar Yah Deen ya bashi ha'kuri ya sa'k'ko sannan suka shirya da shi. Tun daga lokacin suka koma normal tamkar baya, shine ma yace Mu'een 'din kar ya sayi komai zai taho masa da duk kayan da zai yi amfani da su wurin bikin. 'Kasan ma'koshi ya furta" Dama ka hutar da ranka" ji yake shi ko da polo da jeans zashi wurin 'daurin auren babu abinda ya dame sa...A fili ya furta" Wannan mutumin ma brain 'din kifi gare sa wallahi". Ni kaina sai da na zaro idanu nace kardai uban naka ne mai brain 'din kifi? Sai kuma naji yana fa'din" In ba haka ba taya baka ta6a ganin mutun yazo wurin 'yar ka ba ba ka san sanin mutum ba sai ka 'dauki aure ka bayar". Kai 'dan kuka mai jawa uwar sa jifa rayuwa kenan... _Allah ubangiji ka shirya mu ka shiryar da zuri'ar mu, Yah allah kar ka bamu 'ya'yayen da zasu ja mana zagi...Ameeen._ ***** Zauna yake kishingi'de kan kujera mai zaman mutun 'daya, kan cinyar sa Tablet ce yana dubawa yayin da wayar sa ke ajiye gefe dashi a hannun kujera. Ishaq na daga can gefe kwance kan 2seater yayin da Anas da Imam suke daga 'kasan carpet zaune suna buga wasan karta gefen su lemun coca cola ne suna sipping lokaci zuwa lokaci. Wayar Mu'een ce ta fara Vibrating sai ya kai duban sa kan fuskar wayar da tunanin ko Alhaji Baba ne ya 'kira. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *50* Sunan Imrana da ya gani yana yawo kan fuskar wayar ne ya sashi sakin 'dan ta'kaitaccen murmushi tare da kai hannun sa ya 'dauki wayar ya 'kara da kunnan sa muryar sa wasai yace" Imrana ya aka yi ne? Ka 6uya a Kano kayi wuyar gani...". Imrana sai yace" Wallahi nake gaya ma abubuwa ne suka sha kaina sosai..amma ina ga na kusan fasowa ma..." Deen kuwa cewa yayi " Ya kamata ka, gaskiya har fa aure na ya 'karato ba ka dawo ba". Da mamaki Imrana yace" Aure kuma Deeni kai 'din garin ya ya?" Yace " Garin tsautsayi Imran...Alhaji ne yace sai ya aura min Husnah, zancen nan da nake maka ma 1week ya rage a 'daure auren". " Ikon Allah ashe ma da ban 'kira ka ba da ko labarin ma bazan ji ba". Cewar Imrana, Yah Deen kuwa sai yace " ah no dole zan neme kai ai domin akwai cashewa sosai, kai dai ka shirya liyafa kawai dan zan baku bonus ku kwashi gara kai da duk mai bu'kata zan baku dama har sai kun gaji...watandan ta zan muku a kyauta mori banza, dan wallahi bazan iya zama da ita ba sai na koya mata hankali ita da duk yarinyar da tayi kuskuren shigowa cikin rayuwa ta sai sun gane kuren su...albishir 'dina kenan dan haka ka shirya". Imarana da ke ba hankali ne da shi ba sai ya saki ihun murna yana yiwa Yah Deen kirari na musamman jin cewa za'a bashi kyautar wannan tsaleliyar da ya jima yqnq yabawa ashe shima zai kwashi gara daga jikin ta son ran sa. Ihun nasa ne ya sanya Mu'een cire wayar sa daga kunnen sa fuska ba yabo ba fallasa ya yanke 'kiran yana sakin murmushi. Ishaq da tuni ya mi'ke zaune yana yi masa duba da alamun mamaki 'karara kan fuskar sa... 'kure Yah Deen yayi da idanun sa yanayi masa kallo irin na tambaya...hatta su Imam ma kallon sa suke yi shida Anas baki bu'de jin shai'daniyar ta'asar da yake niyyan shiryawa, yayin da Yah Deen ya cigaba da abinda yake yi cikin Tablet 'din sa bai ma san suna yi ba. Ishaq ne yayi 'karfin halin furta" Me wai kake nufi da wannan maganar ne Mu'een dan Allah?" Sam mantawa yayi ma da su a parlour shiyasa har ya saki ransa ya bayyana sirrin da ya jima yana shiryawa cikin ransa batare da kowa sani ba..(ni kuwa nace Allah ne dai kawai ya toni asirin ka Alhaji Mu'een shiyasa ya rufe ma idanu ya kuma 'dauke hankalin ka daga gare su). Basarwa yayi kamar bai san cewa da shi Ishaq ke magana ba, da dabara ta 'kasan idanu ya kallo Imam da Anas daga inda suke zaune suma sai yaga duk sun bar abinda suke yi sun zuba masa idanu suna kallo kowa fuskar sa da matu'kar mamaki da baya raba 'dayan biyu sanadin jin kalaman bakin nasa ne. Cikin sanyin murya Ishaq ya sake fa'din" Mu'een kar dai kace min wannan babban jahilcin abin Allah wadai kake tsarawa cikin ranka?" Cikin ransa yace " Yauwa limami zai fara ai" A fili kuwa batare da ya 'dago idanun sa ba yace" Dama ai ni Jahili ne Ishaq ba sai ka tuna min ba". " No ai kaima kasan ba haka nake nufi ba.. amma please ka canza tunani, hakan sam bai dace ba, me yasa zaka shirya ciwa sunnar ma'aiki mutunci wallahi matu'kar ka aikata hakan Allah ba zai ta6a barin ka ba, sannan ka tuna mahaifan ka mana, dan su kare maka mutuncin ka yasa suka nema maka auren nata fa ba wai dan sun 'kuntata ma ba, kuma na tabbata sai da suka fahimci kyakykyawar fahimtar da ke tsakanin ku da ita kafin suka shiga maganar, to me yasa zaka yi musu haka?, me yasa zaka tozarta musu niyyar su?. Cikin ransa ya furta" Saboda bana 'kaunar ta ne kawai 'dan uwa". Amma a fili bai iya yayi magana ba kamar yadda har a lokacin bai yadda sun ha'da idanu da kowa cikin su ba. Kunyar Ishaq yafi ji saboda shi 'din mutun ne mai mutunci a idanun sa...Tana cikin tunanin yaji Ishaq na sake fa'din" Wallahi duk abinda ka aikata maras kyau Allah ba zai 'kyale ka saboda hakkin yarinyar zaka 'dauka, and baka da hujjar kare kanka a wurin koma waye idan maganar ta fito..in kuma akwai ka gaya min .." Duk yadda yake jin nauyin kalaman sa na 'dazun amma duk da haka bai kasa dauriyar furta masa" Saboda bana so ne kawai Ishaq kuma kowa ya kasa fahimta ta". " Shine zaka saka musu da haka Mu'een? Dan kawai baka 'kaunar ta?, wallahi in kayi haka baka kyauta mata ba sam..ka duba lamarin ka auna shi amizanin masu hankali mana...cin zarafi ne wannan kuma bai kamata ba gaskiya...da ka aikata hakan ma ai gara ka fito fili ka nuna musu cewa baka ra'ayi..." Sai yanzun ya iya duban fuskar Ishaq a 'dan fusace ya tare shi da fa'din" Bazan iya ba Ishaq..kuma ai na gaya mata itan tun ba yanzu ba...amma tamin kunnen 'yan iska ta mai da ni ban san me nake ba, zaton ta zan aure ta in zauna da ita matsayin matata ta sunna ne bayan duk abubuwan da suka faru tsakanina da ita abaya...wallahi i have already made of my mind kuma bazan fasa ba, duk yarinyar da ta kuskura aka 'daura aure na da ita wadantan ta zan yi wa abokaina babu ruwa na...that's final ita ta sani..damuwar ta ce...". Ido Anas ya zaro yana kallon sa yace" wai anya Deen cikin hankalin ka kake kuwa?" " A a na haukace ne Anas kaji..mahaukaci ne ni..". Ya bashi amsa a zafafe yana duban sa da jajayen idanu dan maganar da yayin sosai ta taso masa da 6oyayyan 6acin ransa da ya kwan biyu yana 6oyewa shiyasa ib ka lura zaka ga har jijiyoyin kansa na nunawa. Ishaq kuwa ganin cewa Mu'een ya fara hawa temper sai yayi saurin sau'kar da nashi fushin tana shirin sake yin magana sai yaji Imam ya riga shi da fa'din" Common Mu'een just be your name please, taimakon ta zakayi ai tunda ita tana son ka, sannan kuma kayi saboda Allah da kuma kare darajar ahalin ka ba dan ita ba, duk dama nasan kaine taimakon zai fi yiwa amfani, tunda kaida kanka kasan waye Husnah, kasan halin ta, kaga ba wani dogon bincike kar ta san kar ne, sannan ko ba komai kasan kai ne ka fara yaga Husnah ina laifi dan ka 'karasa ha'kan da kai ka fara da kanka?...sannan kaga abinda Ishaq ya fa'di ai gaskiya ta fa'da maka kayi tunani da kyau ka gani wallahi abinda kake shirin yi 'din babban kuskure ne arayuwar ku gaba 'daya...sai dai nasan gane hakan zai yi maka wahala wata'kila har saj bayan ka aikata sannan ka gane Babbar illar dake ciki..". Ido ya tsurawa Imam wannan karon kawai yana kallon sa, bai yi mamakin jin abinda ya furta ba cuz dama yasan sun riga da sun san irin ala'kar da ke tsakanin sa da Husnah tuntuni..amma batun cewa ya zauna da ita zaman aure hakan ne sam bazai iya ba, ya kasa bawa zuciyar sa ha'kurin hakan kwata-kwata gani yake in ba hukunta Husnah yayi ba zai huce takaicin sa ba...musamman ma yanzu da cikin kalaman Imam ya fahimci irin kallon da za'a ringa yi masa shi da ita bayan auren, kenan kowa yasan cewa ragowar titi ya aura?" Idanun sa take suka sake riki'dewa har ruwa suke 'ko'karin tarawa ta ciki, shi dama haka 6acin ransa yake idanun sa ma basa iya 6oye yanayin da yake ciki....gefe guda kuma bai isa ya 'karyata kalaman su Ishaq 'din ba dan yasan tsagwaron gaskiya suke fa'da masa matsayin su na abokan sa. Tsaye ya mi'ke da wayoyin sa a hannu ya kama hanyar bedroom 'din sa, shiga yayi ya kulle 'kofar ta ciki sannan ya koma ya kwanta rigingine saman katifar sa bayan ya zuba wayoyin a gefen sa, hannun sa na 'kar'kashin kansa yana kallon ceiling tamkar wani mai irgawa tunanin maganganun da suka yi da Ishaq da kuma Imam yake yi...komai na dawowa cikin brain 'din sa daki-daki. Duk cikin maganganun nasu babu wanda tafj tsayiwa masa a rai kamar inda Imam yace"...be ur name.." Yana so shima ya wakilci sunan sa na MU'INUDDEEN ya zama mai taimako amma yasan indai akan batun auren sa da Husnah ne to sam bazai iya ba. Ko bayan tafiyar sa ma babu wanda ya sake furta komai cikin su, illah Ishaq da ya girgiza kansa a hankali cike da alhini cikin sanyin murya ya furta" Allah ya kyauta". sannan ya koma ya kwanta kamar yadda yake tun farko, cikin ransa yake ayyana irin girman wannan kalamin da Mu'een yayi, sosai abin ya bashi tsoro, mamakin sa ma shine yaushe tunanin sa ya iya bashi ya aikata irin hakan saboda kawai yaga ya 'kuntata mata..bacin ma kuskuren ba nata kuma ita ka'dai zai ga laifin ta? Hala ya manta cewa shine silan koma menene...Ishaq alwashi yayi cikin ransa cewa matu'kar yana numfashi da yardar Allah Deen bai isa ya aikata hakan ba, in yayi wasa harda iyayen sa zai ha'da shi, yana can yana biyewa abokan banza da bazasu saka hanyar da ta dace ba illah sa6awa mahallici abanza da wofi...yaushe to zaiyi tunani irin na masu hankali?. Haka ranar suka 'karashi yinin su suka koma cikin makaranta batare da sun sake ganin sa ba. Washe gari ya kamata ya kama hanyar Shuwarin amma bai ko fara niyya ba tukunna balle aje ga batun shiri, hakan ma ya san dan Ishaq bai sani bane da tuni ya matsanta masa wajen ganin tafiyar sa. ***** *Bayan kwana biyu* Ganin da Alhaji yayi bai zo ba kamar yanda ya bashi umarni ga shi kuma ko a waya bai 'kirashi ba ya sanya shi 'kiran Uncle Ja'afar yace da shi ya yiwa 'dansa magana ya daina yi masa taurin kai kar ya kuskura ya kaishi bango...hmm". Haka kawai Alhaji Baba ya fa'di sai ya yanke wayar batare da wani dogon 'karin bayani ba , take kuwa Uncle J ya 'kira shi inda yace" Wai Mu'een me ke damun ka ne? Wallahi idan baka daina yiwa Alhaji irin halin kan nan ba Ubanka zaka ci awaje na, ko an gaya ma shi 'din abokin wasan ka ne?" " Yi ha'kuri Uncle..." A tsawace ya dakatar da shi da fa'din" Shut up da Allah ban san wannan ha'kurin ni...kuma maza ka 'kirashi ka bashi ha'kuri sannan ka aikata abinda ya saka ka banson iskanci". " Uncle wai fa in tafi Shuwarin yace kuma naga ai bikin da saura sannan ina so ne mu tafi tare da friends 'dina shine fa ban tafin ba har yanzu". Ya fa'di hakan ne da tabbacin laifin da yayi wa Alhaji Baba kenan dan yasan abinda ka'dai ya aikata kenan shine rashin tafiyar sa a dai-dai lokacin da Alhajin ya bu'kata. Uncle Ja'afar kam cewa yayi" Koma dai menene bansan wani excuse 'din ka, maza kayi abinda ya saka, in banda ma rashin wayon ka hakan da kake yi shi zai sa ya fasa 'daura maka auren ne, kai kanka kasan da kai ko babu kai auren nan kamar anyi shi an gama ne...so kama nutsu kasan me kake yi...wallahi kar ka yadda 'kafata ta riga 'kafar ka taka Shuwarin...in ba ka yadda ba kuma try me an see d real me". Ji yayi tamkar ya fasa ihu saboda takaici, haushin sa 'karuwa yayi akan nada ma, to shi me ze je yayi musu tun yau da bikin ya rage saura har kwanaki biyar? Shi ba mace ba balle ace zai fara shiri...yana cikin tunanin nan yayi dialling number Alhaji Baba...amma bai 'daga ba, har sai da ya jera masa 3missedcall sannan ya tsaya da wayar a hannun sa yana kallo, shi da kansa ya san ya 6atawa mahaifin sa rai matu'ka amma ya zai yi. Text ya rubuta ya tura masa da fargaban mai ze biyo baya kuma...'kila yace na raina shi ne shiyasa nayi hakan...ya fa'di yana dafe goshin sa. Alhaji Baba na kallon wayar sa na ta rurin neman agaji amma bai 'dauka ba saboda yanda yake jin haushi har cikin ransa, baya son ya zama mai zafin rai amma Mu'een na tunzira shi cikin kwanakin nan, text 'din da ya shigo masa ne ya sashi 'daga wayar ya duba nan yaga Yah Deen ne ya turo" _Alhaji dan girman Allah ka gafarce ni...abokai na nake jira mu taho tare shiyasa banzo akan lokaci ba, amma da iznin Allah gobe ina hanya_ ". Idanu ya lumshe bayan ya gama karantawa sai ya 'dora wayar saman 'kirjin sa, cikin zuciyar sa yake addu'ar" _Allah ubangiji kar ka jarrabe mu da fitinannun 'ya'ya wa'danda zasu datse farin cikin mu a lokacin da bama zato...Yah Allah ka shirya min Muhammad ka daidaita min hankalin sa wuri guda ya Allah_ ". Bai bu'de idanun ba ya cigaba da tunanin sa, shi ada ya san Mu'een ba haka yake ba, sam baya mishi taurin kai akan abu, mutun ne shi mai matu'kar biyayya da sanin ya kamata, ga shi da girmama iyayen sa, amma sam yanzu halayyar sa ta bambanta da na baya bai kuma san me yasa abubwan sa ke 'kara rikicewa haka ba. ( Ni kuwa nace sharrin Alafasha ce tsantsa Alhaji, ta kan canza mutun daga nagari ya koma gur6atacce in ba'ayi sa'a bama har ta kan 6ata wa mutun 6angaren ibadun sa..ALLAH YAYI MANA TSARI DA AIKATA ALFASHA). ***** Ran sa be so ba amma haka washe gari ya shirya ya tafi bayan sun yi sallama da su Ishaq akan cewa ranar thursday zasu taho suma. Ko da yake cikin mota ma tunanin auren sa da Husnah yake yi, ta yadda abin ya fara, ya tsinewa randa ya fara sanin Husnah fin sau 'dari a rayuwar sa, gashi duk da irin kashedin da ya mata hakan bai sa yaga 'kiran ta da albishir 'din an fasa auren ba, yasan dama da wahala ta iya sa afasa auren...sai dai in hakane kuwa shima ba zai ta6a janye 'kudurin sa ba. Cikin sa'a sai suka dira rana 'daya da abokin sa Imrana, sai dai basu ha'du ba dan Mu'een can gidan Alhaji ya sau'ka yayi wani kalar tausayi a wurin Ammi, ita kam Nasiha kurum ta ringa yi masa tana sake bashi 'kwarin gwiwa akan lamarin, haka ma Anty Zainab dan zuwa lokacin ta gama fahimtar cewa auren daga Alhaji Baba ne ba za6in Mu'een ba, itama jan hankalin sa tayi sosai akan ya daina damun kansa, ai shi namiji ne kuma shine da ragamar auren da gidan ma complete, tace kana da damar 'kara wata matar a duk lokacin da kayi niyyah babu mai hanaka, 'kaddara kuwa babu yanda zaka yi da ita, idan tazo dole ne ka kar6e ta tunda ba'a guje mata ko a ina dan haka ka 'dauki wannan auren matsayin 'kaddarar rayuwar ka". Jin su kawai yake yi bawai dan ya 'karyata abinda suke fa'di ba a a, kawai dai shi baya jin zai iya ha'kurin ganin Husnah matsayin mata agare shi ne. Yayin da Alhaji Baba daga gaisuwa babu abinda ya 'kara ce masa sunyi zaman a 'kalla mintina kusan goma a haka sannan Yah Deen ya yun'kura, har ya tashi zai tafi ma sannan yaji Alhajin na fa'din" Hope kasan meke faruwa ko Muhammad?" Komawa yayi ya zauna yana mai jinjina masa kai alamar " Erh ya sani" Ya na ji cikin ransa cewa da wani daban ne yayi tambayar da ko kallan shi ma ba zai yi ba balle har ya bashi amsa. Alhaji cewa ya sake yi" Masha Allah...to sai kaje ka cigaba da shiri..ranar friday insha Allahu za'a 'daura auran ka da Asma'u..sai dai bansan ina zaka fi son matar ka ta zauna ba...kaga wancen gidan ba'a kammala gyaran shi ba za'a ha'da da filin bayan duk agina shi aikin da saura sosai, sai dai in ko can makarantar zata tare idan hakan yayi maka". Kansa 'kasa ya amsa da fa'din" Ba damuwa Alhaji duk yadda kace haka za'a yi insha Allahu". Inda ya bashi amsa da sanyin murya kamar gaske. Alhaji Baba kam kai ya jinjina masa tare da komawa baya ya kishingi'da abinsa harda lumshe idanu, wanda hakan da yayin shine ya alamtawa Yah Deen cewa ya sallame sa. Fita yayi yana tunanin a can Jigawan ma sai yafi masa cuz zai fi samun isashshen daman da zai hukunta ta son ransa dan babu su Alhaji, Ishaq kuwa a ganin sa 'karamin alhaki ne bai damu da shi ba...musamman ma da ya san ba wuri 'daya suke rayuwa da shi ba. Duk nasihar da akayi ta masan abanza ta tashi, duk ya watsar babu wanda ya zauna kansa, shiyasa yake jin 'kudurin sa na nan cikin ransa babu abinda ya ta6a shi, kaf laifin akan Husnah ta 'daura sam bai ganin nasa, hala ya manta cewa tun ranar farko shine ya fara tattaki zuwa 'dakin baccin ta, ya manta a Shi ya fara kawo mata batun cikin rayuwar ta shiyasa yake so ya hukunta ta ta yadda zata san babban kuskuren da ta tafka na yadda da tayi ta aure shi despite warning 'din da ya mata amma tayi kunnen uwar shegu da shi tace taji ta gani a hakan zata aure shi. Bai san cewa itama ta daure zuciyar ta bane kawai saboda kar aci mutuncin mahaifiyar ta a banza da wofi shiyasa ta yadda zata aure shi ko da bayan auren kasheta zai yi akawo gawar ta ga mahaifiyar ta hakan yafi mata fiye da ace ganin idanun ta mahaifiyar ta ta shiga 'kunci ta dalilin ta. ***** Da yamma lis ya koma gidan sa, nan ya tarar da canjin da aka yiwa gidan, an fa'da'da shi sannan aka tada wani tsari mai kyau ginin zamani sai dai ba ai komai a ginin ba tukunna, haka ya shiga asalin side 'din da yake anmfani da shi dan aikin bai iso kansa ba tujunna, iya abinda zai iya ya kimtsa kafin zuwa safiya kuma yasan yadda zai yi da sauran aikin. Tun daren ranar suka yi waya da Imrana nan suka sanar da juna cewa suna Shuwarin...washegari kuwa sassafe Imrana ya iso gidan zuciyar sa fal farin ciki har fuskar sa na nunawa...Yah Deen na ciki jin sallamar sa ne ya sashi fitowa ya bu'de masa 'kofar palourn sannan ya bashi hanya domin ya shigo inda ya koma saman kujera ya zauna yana sakin ajiyar zuciya. Nan take Imrana ya fara zuba masa uban kirari yana daga tsaye yana zuba smilling ya wani 'daga hannu gaban sa tamkar yana gaban wani basarake yake cewa" Woo sai kayi nawa, kamili uban 'yan iska, na Alhaji baka yaudara sai dai horo, sai kai bindiga mai kauda abokin gaba, ka zarce Ak47 sai dai 48, gaye uban mazajen duk duniya, sai kai nuclear tarwatsa dukkan taro...kyautar ka ta musamnan ce ta zarce ta kowa...mai kyau mai hali kyakkyawa....". Murmushi Yah Deen yayi masa batare da ya furta komai ba. Yayin da Imrana ya buga tsalle ya yiwa kansa masau'ki kan kujerar dake facing da inda Mu'een ke zaune sannan ya sake fa'din" Kafa ha'du gayen nan gaskiya ka iya shirya mugunta, yanzu dai kace ka bamu dama mu fara shirin ra'kashewa kenan ko?" Yana murmushi yace" Sosai ma, ai ku kwantar da hankali kawai nake gatama kowa zai shana, zaka iya gayyato abokan ka ma in sun shirya". Dariya Imrana yayi wannan karon tare da bashi hannu suka tafa cike da jin da'di. Sai da suka gama shan hirar su kafin suka yi aikin gidan tare...Inda Yab Deeb ke yj yana sakin tsaki...a fili ya furta" Ammi na ta hana 'yar ra zuwa min aiki ai da yanzu ina hutawa ta". Da jin haka Imran sai yace" Ai da kayi auren shikenan ka huta da irin wa'dannan aiyukan matar ka duk zatai maka..." Wani harara da Yah Deen ya jefa masa ne ya sashi saurin canza magana inda yana 'yar dariya yace" Aww na manta ma ashe ramu ce matar". Haka Imrana yai ta tsokano shi wasu lokutan shi kuma yace" Wallahi sai in fasa" Da yaji haka zakiji yace" Sorry Boss na daina" Da gaka har suka gama aikin. ***** Shirye-shiryen biki ya kankankama daga dukkan 6angarorin biyu, Baban mu ana saura kwana biyu bikin ya iso Shuwarin kamar yadda tayiwa Alhaji al'kawari, haka ma Uncle Ja'afar shima tazo Anty Zee kam dama mun da'de tare da ita inda wani sha'kuwa mai 'karfi ya shiga tsakani na da ita, duk abinda tasan zai fito dani abikin tuni ta tanadar min shi. 'Bangaren Ma'u kuwa ta 'dan damu ka'dan da ta ji batun auren amma daga baya da kanta ta yiwa kanta karatun natsuwa tayi ta 'ko'kari wajen ganin ta cire a tunanin ta...sai dai abin ya faskara dan son shi takeyi ita da dukkan zuciyar ta. Duk da haka bata 'daga hankalin ta ba ta kuma yi 'ko'karin 6oye damuwar ra musamman da take tub farko dama can rasan haukar ta kawai takeyi amma aure tsakanin su abu ne mai wahala. Dalilin sanin hakan yasa ta 'kara watsar da batun harma ta yiwa kanta al'kawarin kasancewa cikin 'kawayen Hudah aranar bikin ko dan ta samu ta manta da shi, dama ta san da kyar ne ya aure ta tunda shi kyakkyawa ne kuma mai aji ba irinta da take girman 'kauye ba. Ana gobe 'daurin auren aka kawo mai lalle tayi min ni da Anty Zee da Ammi, kar kiga yanda abin ya amshi jikin mu Muka fito shar abin mu. Already dama an gama gyare min kaina, Ghana weaven Ammi tace ai min da abin 'karin gashi, kitson 'yan madaidaita ne amma tuni sun canza min kamanni na zama tamkar wata 'yar gayu, Ammi data ganni kawai sai ta rungume ni tana fa'din" Masha Allah, 'yan matan Ammi ansha kyau sosai". Da wayar ta ta 'dauka min photo ina dariya na 'dago hannu na 'daya kaina babu ko 'dan kwali. Pic 'din yayi kyau sosai kamar ba ni ce NOORUL HUDAH 'yar gidan Ummah mai waina 'din nan ba, tuni na juye na zama wata kyakkyawa da ni. Da'di naji lokacin da naji Ammi na ta yabe ni sai kawai na saki murmushin jin da'di. Da yamma su Ishaq suka iso da motar su da suka 'dauko daga gidan su Anas da yake shi dama cikin gari gidan su yake shiyasa suka saki ransu suka taso a lokacin da suka ga dama. Haka kawai Mu'een sai yayi farin ciki da zuwan su, gefe ma ga Imrana da tawagar sa abin ba'a cewa komai. Sai dai duk abin nan su Saif na makaranta basu dawo anyi dasu ba, ni kuwa ba 'karamin kewar su nayi ba haka na damu Ammi da batun su tace inje in samu Alhaji in gaya masa. Ai kuwa zuwa nayi nace" Alhaji Baba yaushe za'a 'dauko su Saif?" Murmushi yayi min tare da fa'din" Hudallah me yasa kike so a 'dauko ko saboda bikin Yayan naku?" Kai na na 'dage alamar " Erh". Murmushin ya sake yi sannan yace" Bar su kawai suyi karatun su...wannan bikin duk shirme ne ki bari sai wanj lokacin in da rai ayi da su kinji". Kqfa'da na no'ke..zan yi magana sai yayi saurin fa'din" To je ki sami mai auren ki fa'da masa ya 'dakko su". Ina jin haka na nutsu sannan na koma inda na fito dan tuni na ha'kura da zuwan nasu indai sai naje na sami Yah Deen kan maganar. Na ha'kura nace kawai ko a wayq zan bash labari. ***** Ranar ko bacci su Yah Deen ba su yi ba suna ta shan hira abin su kun san abinku da abokai idan an ha'du sai a hankali. Washe gari bayan sallar asubah ne kowa ya koma bacci har kusan sha daya suna bacci babh wanda ya tashi illah Imrana, hatta breakfast ma da aka kawo musu babu wanda ya waiwaye shi sai Imranan ka'dai. Sha 'daya suka ta shi a baccin wanda Ishaq ne ya fara tashi sannan ya tada su. Comment Vote nd Share. *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *51* Ganin kamar sun kusa makara ne ya sanya shi tada su gaba 'daya tare da fa'din kowa ya hanzarta yayi shiri kar a tafi abar su abaya. Sharp-sharp ya shiga wanka ya fito da yake bathroom 'din ma biyu ne sai suka rarraba suka hau shirin zuwa 'daurin aure gadan -gadan. Sai dai me? Mu'een 'kin motsawa yayi yai kamar baya jin me suke yi kwata-kwata. Har Ishaq ya kammala shirin sa cikin yadi getzner Kalar ruwan madara da suka yi ankon sa tsakanin su batare da ko shi angon ya sani ba. Duk yadda ya so ya ja hankalin Mu'een kan cewa ya tashi ya shirya amma Yah Deen sam ya'ki kula shi balle ya bashi ha'din kai, sai ma cewa da yayi suyi gaba kawai zai taho shima yana bayan su. Haushin sa sosai Ishaq yaji kan hakan kawai ya fice ya bar shi suka wuce can gida bayan sun ci abinci. Sanin da yayi cewar Alhaji ko Uncle dole ne cikin su 'daya sai ya neme shi, dalilin hakan ya sanya shi bayan fitar sun yayi hanzarin shiryawa cikin 'daya daga cikin kayan da Uncle ya kawo masa tsadadden yadi mint green ya sanya wanda akayi 'dinkin harda babban riga. Sosai kuwa ya yi kyau ya fito shar da shi...turaruka ya dinga fesawa kala-kala ajikin sa bayan ya kafe hula akan sa ta zauna 'das, yana baza 'kamshi Imrana na zuba masa kirari suka fito sai wani shan 'kamshi yake yana takun isa da 'kasaita cikin babbar riga tamkar ba shi ba, Imrana bai barshi ganin kyan da yayi ya sa shi yin gaba ya ringa haska masa pic da wayar sa inda yana tahowa Imrana na haska photunan sai ya wani ha'de gira, mota suka shiga a tare wanda shine yayi driven motar ya bisu da yake akwai wata motar Alhaji a hannun sa sai suka isa gidan ba tare da wani 6ata lokaci ba. Ai kuwa ba 'karamar sa'a yayi ba dan kuwa har Uncle Ja'afar ya fara tambayar sa wurin su Ishaq sai gashi ya 6ullo...da ganin sa cikin shiri kuwa sai fara'sr sa ta fa'da'da sosai bai yi rowar baki ba sai da ya yabawa kwalliyar tasa. Gaishe su yayi da duk jama'ar da ya gani 6angaren Alhajin fuskar sa ba yabo ba fallasa ba zaka ta6a cewa baya 'kaunar auren ba ko kuma kayi zaton da akwai wani 6oyayyen sirri cikin ransa ba. Suna kammalawa da. gaisuwar Imrana yace suyi photo..." Kafa dame ni Imran".Yace a dake ya wani 6ata ransa. Imran kuwa yace sai kuma an 'dauka ba...bai jira jin komai daga Mu'een ba ya juya ga su Ishaq da Uncle Ja'afar sannan ya cigaba da fa'din" Uncle muyi photo mana da su Alhaji.." Murmushi Uncle J yayi nan ya matso batare da musu ba aka 'dauke su, Yah Deen kam dan ba yadda zaiyi ne shiyasa ya tsaya, haka aka 'dauke su harda Alhaji Baba da su Baban mu cikin waya ce amma sunyi kyau sosai...da yake babu wanda ya tuna 'dauko camera man...duk haushin Imran kuwa ya bi ya cika shi kafin a 'kare 'dauka dan acewar sa ai duj tsirin sa ne, haka yana ciccin magani har aka 'kare. Sai da ya tabbatar ya ha'da idanu da kowa cikin iyayen nasa sun tabbatar ya shirya ya fito hatta cikin gida sai da ya shiga ya gaida su Ammi kafin ya fito...sannan ya faki idanun su Uncle ya shige mota shi da Imrana suka koma can gidan sa bai sake komawa ba...kaf kayan da yasa 'din kuwa da dawowar sa duk ya cire su ya zauna abinsa da singlate da dogon wandon jumpan kawai. Duk yadda Ishaq ya so su tafi tare amma Mu'een ya 'ki sam ya ringa kakkaucewa, har gidan suka dawo yayi ta nuna masa abinda yake yi 'din bai dace ba amma Yah Deen kam sai yace su je yana bayan su, hakan yasa yayi zuciya ya tafi abin sa...cuz taurin kai irin na Mu'een ya fara isan sa...musamman ma yanda yaga har ya cire kayan jikin sa ya mi'ke a kujera yasan da 'kyar ne ma idan yana da niyyan halattar 'daurin auren. Su hu'du kacal suka tafi daga 6angaren sa, yayin da aka bar shi daga shi sai Imrana a gida da sunan zasu taho daga baya, sai da yaga sun fita kafin ya tashi ya zauna yana wani mi'ka kamar wanda ya shekara guda yana bacci...yana cikin hakan kuwa yaji wayar sa ta fara Vibrating, zaton sa ma ko Ishaq ne. Sai dai yana dubawa  yaga Uncle Ja'afar ne ya 'kira,  zuciyar sa na dokawa ya 'dauki 'kiran gami da ha'da wayar da kunnan sa, nan yaci karo da muryar Uncle J na fa'din" Mu munyi gaba kasan sallar jumma'ah na gaban mu kuma ban ganka ba, so ku hanzarta tahowa kar ku makara....ya 'karashe da sanar da shi sunan masallacin da za'a 'daura auren. Da " To" kawai ya amsa shi, bawai dan yana da da niyyan halatta ba a a, sai dan kawai baya son wani dogon bayani kwata-kwata. Hirar su suka cigaba da yi cikin kwanciyar hankali shi da Imrana, har lokaci ya 'kure sosai sannan suka ankara, da gaggawa ya tashi ya fa'da bayi da fitowar sa kuwa ya sake shiryawa dan Imrana kam dama kayan sa na jikin sa tun da ya shirya 'dazu riga kawai ya cire kuma har ya maida abinsa ma. Cikin kayan da Anty Zee ta bashi ya sake za6an wani mai kyau wanda babu babbar riga ya saka ajikin sa, ba wai dan yau 'daurin auren sa ba ne ya sashi sanya kayan a a sai dai dan kawai yana so ya sallaci Jumma'ah da shi kamar yadda ya saba yin shiga ta musamman duk ranar kowacce Friday. Suna isa masallaci aka tada sallah kamar dama su ake jira su iso. Ana idarwa kuwa basu wani da'de sosai ba suka mi'ke amma duk da haka Mu'een sai da ya ro'ki Ubangiji akan cewa kar ya basu ikon aura masa Husnah. Kun san akwai gejin da mutun zai kai idan damuwar sa ta yawaita har mantawa yake yi da komai, ko addu'ah zai yi zaku ga abin ka'dai yafi damuwa dashi burin sa duk akai zai 'kare, to hakama Mu'een ya kasance a kullum baya mantawa da addu'ar Allah kar ya ha'da auren sa da Husnah, ko bai ro'ki Allah komai ba amma wannan kam baya ta6a mantawa...ko yau 'din ma irin hakanne ya kasance. Mintina biyar basu 'kara a masallacin ba suka wuce gida...suna shiga Yah Deen ya sake zare rigar jikin sa dan duk ta damesa a fa'dar sa. Zama yayi yana duba cikin wayar sa, Ishaq ya 'kira dan jin ko suna hanya kamar yadda yace zasu biyo su ko sun taho, amma sai ce masa yayi bai taho ba tukunna. Da mamaki Ishaq yace" Dagaske kake bazaka zo ba ko Mu'een?" Yana yatsina fuska yace" Bazan iya ba Ishaq...kace da Uncle banjin da'di ne shiyasa ban taho ba". Ishaq sai yace" Baka da hankali". Yace " Na sani.." " Kuma kasan idan ka yi hakan baka kyautawa Alhaji ba ko?" Yace " Naji to ka wakilce ni". " Shiyasa nace baka da hankali". Fa'din Ishaq cike da 6acin rai. Yah Deen sai yace " Kai ka sani kuma yanzu ai...kuna ina ne haka?". Ya 'karashe maganar tasa da tambaya. Iahaq amsa ya bashi da fa'din" Ban sani ba". Ya fa'di azafafe tare da yanke 'kiran yana furzar da numfashin takaici. " Allah ya shirya ka Mu'inuddeen". Ishaq ya fa'di a fili bayan sun gama wayar. Yah Deen dagaske 'kin zuwa 'daurin auren yayi yai kwanciyar sa agida wai shi bai jin da'di zazza6i na damun sa afa'dar sa...hatta Imrana yau dake nan tare da shi shima tausan sa yake ganin cewa dagasken fa bashi da niyyar zuwa wajen auren amma shi sai maimaita irin ta'asar da zaiyi yake yi akan Husnah matu'kar ta yadda ta zama mallakin sa kamar zautacce. Imrana ma daga 'karshe jan bakin sa yayi yai shiru dama su 'yan abi yarima asha ki'da ne ko wani fanni suna nan. Babu wanda ya sake 'kiran sa har 'karfe biyu da kusan mintina ashirin da uku sannan yaji wayar sa na diri, da sauri ya 'dago wayar cuz zaton sa ko Alhaji Baba ne har ya fara tuhumar kansa da me yasa bai kashe wayar ba ma gaba 'daya. Sai dai ga mamakin sa ba Alhaji Baba bane, ba kuma Uncle bane ya 'kira tamkar yadda ya zata, still ba wani bane face Ishaq, a fili ya saki tsaki yana fa'din" Miye kuma ni kam?" Sannan ya 'dauki 'kiran ya ha'da wayar da kunnan sa yayi wani kicin kicin da fuska gami da sauraron abinda Ishaq zai ce da shi wanda yake kyautata zaton bai wuci albishir 'din auren zai yi amsa ba. Ishaq dake zaune cikin masallaci suna sauraron auren Mu'een sai yaji an 'daura auren Asma'u Hamza kamar yadda ya san sunan ta amma da wani daban mai suna Hisham Muhammad ba abokin sa Mu'inudden ba, kuma Alhaji Mamman shine a matsayin wakilin amarya, abin sai ya 'daure masa kai sosai hankalin sa ya tashi, ta ya za'ayi su da suka zo da sunan 'daurin auren Husnah da Deen sai kuma ya juye da Hisham..how comes?" Daga inda yake zaunen ya hango fuskar su Alhaji ma tuni ta canza yanayi, kallo 'daya zakai musu ka tabbatar cewa da akwai  wata matsala. Da yake ya san Deeni ba son auren yake yi ba hakan yasa ya ciro wayar sa ya danna masa 'kira, murya 'kasa-kasa yace " Kai wai me ka shirya ne dama bamu sani ba?" Da jin haka sai ya 'kara 6ata ransa harda kishingi'da da shirin tarar masifan da Ishaq zai masa, ya gama ayyana yanzu kam bazai bar shi ba. Murya a dake yace" Me kuwa zan shirya ni?, me yafaru a can 'din?" Yace " Kai an fa 'daura auren Husnah amma kuma bada kai aka 'daura ba wai da wani mai suna Hisham, me ke faruwa to dan Allah ka sanar dani..na kasa gane wa". Instead ya bashi amsar maganar sa a a, take sai yayi hanzarin dai-daita zaman sa yana washe baki yace" Kai dan Allah da gaske an 'daura auren ta da Hisham kuma?" Ishaq dake magana 'kasa-'kasa sai ya sake fa'din " Wallahi nake gaya ma yanzun nan....gashi naga Uncle J na shirin magana bari zan 'kira ka anjima Please". Yana gama fa'din hakan ya yanke 'kiran tare da maida hankalin sa wurin da yaga Uncle J na faman bayani wa Alhaji Mamman wanda kana ganin sa zaka fahimci cewa ransa a matu'kar 6ace yake. Yana kallon yanayin duk wanda ke tare da tawagar Alhaji Baba sam fuskar su bata nuna alamun jin da'di ba. Yana gani wani da bai san shi ba yaja Uncle Ja'afar gefe suka yi magana tsawon mintina sannan suka dawo atare still suka zauna, sai kuma yaga Uncle J na yiwa wani magana a hankali daf da kunnan sa. Ishaq duk yana rarraba musu idanu amma ya kasa fahimtar takamammam abinda ke faruwa. Anas ma na tambayar sa amma bai ko iya ya sauarare shi ba ballab ntana ya tanka shi. Bayan wasu 'yan mintina da faruwar hakan sai  kunnuwan sa suka jiye masa wani auren kuma na Muhammad Tahir da wata daban da bai san ta ba, ba ma zai iya cewa ga inda ya san sunan ba sam. *****     'Bangaren Yah Deen kuwa tunda yaji Ishaq ya furta cewa an fasa auren sa da Husnah sai yaji shi tamkar yana yawo a saman gajimare saboda da'di. Wani ihu ya saki bayan kashe wayar da Ishaq yayi na jin da'di wanda ya janyo hankalin Imrana dake cikin bedroom ya shigo da gudu yana tambayar lafiya kuwa, ko ka zauce ne?" " Na kusa dai Imran". Ya bashi amsa a ta'kaice cikin farin ciki da sakin fuska. Imrana sai yace" Da akayi me to?" " Da aka fasa aure na da wancen kuncen titin..." Imran da sauri ya tare shi da fa'din" Kai haba dan Allah..garin ya kenan?" Ya tambaya da mamaki. Yah Deen kam bai bi ta kan amsa maganar Imran ba illah cewa da yayi" Alhamdulillah...Allah yana so na Imran kaga ya amsa addu'ah ta, wallahi ko da wani llokaci idan na tuna wai Husnah ce ke shirin zama matata na kanji matsancin ba'kin cikin da bazan iya misalta maka ba...sai gashi Allah ya ceceni ya raba ni da masifa...yau rana ta ce Imran, an riga da an 'daura auren Husnah da Hisham ba da ni ba.....". Imran yana tsaye daga gaban sa ya sake fa'din " Wai dan Allah Deeni da gaske kake ne ?" " Yanzun Ishaq ke sanar da ni...waiyo...Alhamdulillah! Alhamdulillah!!  Allah nagode maka da ka kar6i Addu'a ta ka raba ni da Husnah...hmm Allah ya taimake ni Imran da na kwashi ragowar kaina wallahi da na cutu duniya da lahira idan Husnah ta zama matata, me zan 'kara mora a jikin ta kuma banda kayan takaici?". Imrana murmushi yayi yana duban sa yace" Har fa ina murna zan kwashi wannan garar da kake sha'anin ka da shi 'dan Alhaji....kamar yadda kayi mana al'kawari gashi har na sanar da su Shadow (wani abokin sa) suna ta murna sums". " Manta kawai Imrana, let celebrates dan Allah ku taya ni farin ciki Allah ne kawai ya taimake ta I ba haka da sai ta gane kurenta awaje na dan la'ada waje zan ci Ubanta wallahi..." " Ni dai banji da'di ba gaskiya". Fa'din Imrana da dukkan gaskiyar sa yana me shirin zama daga gefen sa. Mu'een kuwa cewa yayi" Sai kayi ai kuma yanzu, ni dai kasan wani abu Imran? yau rana tace so ina so in cashe in huta sosai, gashi kuma babu kowa a hannu ban ma da wata babe anan ya za'a yi?" Ido Imrana ya tsura masa yana duban sa, sam bai yi mamakin jin furucin da ya furta 'din ba balle ya tsaya wani dogon tunani akai saboda ya san halin sa sarai, tunanin sa ma shi in da zai samo masa abinda zai cika masa burin sa da shi ne kawai. Tashin farko Ma'u ce ta fa'do masa cikin ransa, musamman da ya tuna cewa da tayi ita sai shi take so ga kuma dama yana da burin rama abinda mahaifinta yayi masa, sai dai yana tunanin 'kila Mu'een 'din bazai yarda da ita ba saboda rashin wayewar ta ga kuma 'karancin shekaru da take da shj ba kamar Husnah ba. Cikin ransa ya sake ayyana amma ai yarinyar ba laifi akwai kayan rayuwa tattare da ita...a fili ya bayyana murmushin sa tare da fa'din" Kwantar da hankalin ka angon Husnah, yanzun nan zan cika maka burin ka bani 20 mins kaga ikon Allah". Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Ar-P Birthday YAYA HAYAT...may ur remaining years be d best of ur life...Allah ya albarkaci rayuwar ka..Ameen* ~_WANNAN PAGE 'DIN KYAUTAR KA NE_~ 🤞🏼 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *52* Yana gama fa'din haka yayi waje da saurin sa Imrana bai zame ko'ina ba sai a 'kofar gidan Malam Barau mahaifin Ma'u, koda yaje bai ga kowa arean gidan ba hakan ya sa shi 'kara duddubawa da kyau gudun kar mahaifinta ya gansa ya hanata fitowa, yaro ya samu ya tura aka yi masa 'kiran ta inda ya koma daga gefen gidan nasu yana jiran yaga fitowar ta. A lokacin yawancin mazaje sun isa majalisi sun zauna da take an riga anyi sallah, haka ma masu zuwa wajen 'daurin aure suma duk sun tafi yayin da wasu ke cikin gidajen su basu fito ba tukunna, shiyasa 'dai'dai kun mutane ne zaka ga suke shawagi a layuka lokaci zuwa lokaci wannan dalilin ne yasa Imran ya isa gidan hankalin sa kwance batare da wata damuwa ba. Ma'u kam tasha wankan jumma'an ta da niyyar zuwa taya ni taron biki a gidan da nake kamar yadda tayi al'kawari, fuskar ta ba yabo ba fallasa ta fito jin wai ana 'kiran ta, zaton ma ko Ahmad ne ya dawo, dan zuwa lokacin tagama yanke cewa zata bashi ha'kuri kawai su dai-dai ta tunda wanda take haukan so 'din ma auren sa zai yi, sai dai ganin Imrana tsaye daga gefen gidan su ne ya sa ta 'dan 6ata ranta tana kallon sa tare da tura baki ita adole ya takura ta da yawa. Murmushi imrana yayi irin na 'yan duniya batare da ya damu da yanayin da ta yi da ganin sa ba ya 'dan tako izuwa gaban ta sannan yace" Kwantar da hankalin ki hajiya Asma'u sarauniyar Deeni, yau 'din zuwan na musamman ne..kuma nasan zakiyi matu'kar farin ciki idan kika ji abinda ya kawo ni, wa ma kika ce min kina so kwanakin nan...?" Ya 'karashe maganar yana duban fuskan ta. Kallon sa kawai tayi itama amma bata bashi amsar tambayar sa ba zaton ta ma ko wani zagin zai kuma yi mata kamar yanda ya saba akan Deeni, ita kuwa yanzu da tasan yau akayi auren bazata sake fa'din tana son shi ba. Shi 'din ne dai ya cigaba da magana ganin tayi shiru sai ya sau'kar da muryar sa inda yake fa'din"..Deeni kika ce kina so ko ba haka ba?" Yanda yayi mata maganar kalan na masu hankali ne ya sanya ta d'age kanta sama ta bashi amsa alamar " Erh". Sai yace " Kin kuwa san yau ne 'daurin auren sa, amma yace ya fasa saboda ke ka'dai?" Ido ta zaro tana kallon sa da mamaki, take fara'a ya bayyana kan fuskar ta tana washe ha'kora tace" Dagaske ya fasa auren?" Yace " Wallahi ya fasa shine ma ya turo ni yace inje in 'kira masa ke yana son ya ganki na yau ka'dai kawai...zamu iya tafiya yanzu ko a a". Da hanzari tace " Erh muje ai na shirya ma". Inda tayi maganar tana mai karka'da hannuwa saboda tsabar farin cikin da ya cika mata zuciya. Gudun kar a gansu tare da shine gashi gari irin na ranar friday akwai jama'a sosai, hakan ya sanya yace da ita su raba hanya zai jira ta a 'kofar gidan Deen 'din in yaso idan ta iso sai su 'karasa shiga tare". Take ta amince da batun sa batare da tayi wani tunani akan hakan ba. Aikuwa basu 'karasa gidan tare ba, duk saurin da Ma'u tai ta zubawa sai da imrana ya riga ta isa abinku da namiji ga shi da dogon 'kafa. 'Kafar Ma'u kam duk tayi futu-futu da ita ga zufa shar'kaf, kwalliyar da tayi ma duk ta dame ta kwa6e mata a fuska kaca-kaca ta koma wata iri da yake da yawa ta shafa powdern gasu jan lipstick da sauran su. kallo Imrana ya 'kare mata daga sama zuwa 'kasa sannan yace" Kina jina ko?" Sai ta 'dage kanta sama. Yace ciro 'dan kwalin kinnan ki goge fuskar ki, shi fa Deeni baya son mace mai yawan kwalliya..." Ya fa'di hakan ne saboda ganin da yayi kwalliyar tata ta fita a hayyacin ta, kuma yasan matu'kar Deeni ya ganta cikin wannan yanayin ba zai amince da ita ba shiyasa yayi mata dabara. Ma'u kuwa tana jin haka take sai ta fara goge fuskar ta, kafin kace Kobo har kwalliyar ta yi hanyar ta fuskar ta tayi fayau shine ya ringa nuna mata inda basu 'karasa goguwa ba duk ta goge su, take fuskar ta dawo dai-dai. Duba mai kyau zaka yiwa Imran ka fahimcj murmushin mugunta yake yi, amma ga Ma'u da gankalin ta baj je can ba hakan sai ya sa bata fahimci komai game da shi ba, yana murmushin  yake fa'din" Yauwa koke fa 'yan mata, kinga ma kin fi kyau haka nan fiye da 'dazun.." Murmushi Ma'u tayi yayin da Imran ya cigaba da fa'din" Idan mun shiga ciki ki natsu kinji, kuma ki tabbatar bakiyi masa gardama ba, duk abinda yace miki kiyi to kar kiyi masa musu sam baya son taurin kai shi ai ke da kanki kin sani ma ko? nima nan da nake abokin sa ai kinga bana yi masa wargi ko?" Kai kawai ta 'daga sama alamar" Erh" Duk da bata tabbatar da maganar tasa ba amma yanayin da tayi mata tambayar yasa she hv no choice than to ansawer him yes. " Balle ma ke baki na son shi ba..?" Imrana ya sake tambayar ta. Sai ta sake 'daga kanta sama kamar wawuya. Sai yace" Kuma kema kina so ya so ki ya aure ki ko?" Wannan karan kam ido ta zuba mishi tana kallon sa, sai da ya sake maimaita tambayar kafin ra bashi amsa da " umm" 'kasan ma'koshi. Sai yace "Gud toh banda taurin kai, yau ranar ki ce yarinya kiji da'din ki kinji?" " Uhumm" Ta sake fa'di batare da tasan ainahin manufar sa kan fa'din hakan ba. "Bismillah" yace tare da juyawa ya shiga gidan, a hankali ta 'daga 'kafafu ta bishi a baya suka shiga ciki. Can cikin bedroom Deeni yake yana duba sake duba kayayyakin da Uncle ya 'din ka mai sai yaji sallamar Imrana. Yana daga wurin ya amsa wanda hakan ya bawa Imrana damar 'karasawa ciki ya same shi, yana daga tsaye ya 'dage masa gira yana murmushi ya nuno parlour da babban 'dan yatsan sa yayin da sauran yatsun ya tan'kwashe su. Yah Deen bai wani sha wahala fahimtar manufar sa ba dayake bai manta akan abinda suka rabu ba, dan haka sai ya mi'ke tsaye fuskar sa wasai saboda farin cikin da yake ciki na fasa auren sa da akayi da Husnah. Murmushi ne ya bayyana kan fuskar sa yana kallon Imrana yace " Haba dagaske Imran ka kawo min?" Kai ya jinijna masa tare da juyawa yake fa'din" Wancen ajiyar da kwanaki nake baka labarin nace, yarinyar na tsananin 'kaunar ka tun ba yau ba so ka more abinka, amma please kar ka yi abinda zai sa asirin mu ya tonu kasan wannan ba Husnah bace..ni zanje in dawo nan da 40mins". Bai ce da shi komai ba har ya 'karasa fita illah bayan sa da yabi da kallo hannayen sa duk na ri'ke da 'kugun sa. Dai-dai yaji 'karan rufe 'kofar parlour at sane time Ma'u ta bayyana bakin bedroom 'din sa idanun ta 'kasa, wanda shigowan nata ya samo asali ne daga umarnin da Imrana yayi mata kafin ya fita. Taki uku tayi ta tsaya daga inda take tsayen bata 'karaso ba haka kuma bata 'daga kai ta kalle shi ba illah" Ina yini" da ta furta. Yayin da Yah Deen ya dinga bin ta kallo kawai batare da ya amsa gaisuwar tata ba. Sosai ganin ta gaban san ya sake tada masa tsimin sa, ya jima da mura'din yarinyar cikin ransa sai gashi yau Allah ya bashi dama har cikin gidan sa. Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya 'dan matsa baya ka'dan bayan ya cire hannayen sa daga 'kugun sa, da sanyin murya yace' 'Karaso mana ki zauna ko?" Yayi maganar yana nuna mat bakin gadon sa. Sai da ta kalle shi sai kuma ta kalli inda yake nuna matan, Mu'een kuwa 'dauke kabsa yayi tamkar ba shine yayi maganar ba kawai ya cigqba da abinda yake yi. A hankali ta 'karasa ta zauna bakin gadon tana mai wasa 'yan yatsun hannun ta sam sai taji ta kasa sakewa..it kanta bata san me yasa take matu'kar son wannan mutumin ba. Cigaba yayi da abinda yake yi, sai da ya kammala ya maida kayan mazaunin su bayan ya cire wanda yake son sanyawa ya ajiye gefe kafin ya dawo inda take. Gefen ta ya zauna yana sakin sassanyar ajiyar zuciya. " Ya sunanki?" Ya tambaya yana kallon fuskar ta. Kanta 'kasa tace" Ma'u". " Miye kuma Ma'u? sunan ki Asma'u dai ko?" 'Kasan ma'koshi tace" Umm". Sai yace" Gud!...kina sona wai dagaske?" Ya tambaya still yana kallon ta. Shiru tayi bata iya ta bashi amsa ba saboda kwarjinin da yake yi mata...Mu'een kam bai damu da shirun nata ba kawai ya cigaba da fa'din" Anyways..baki da matsala, ko da 'din ma bansani bane..amma kinga yanzu da na sani ai har aure na fasa saboda ke..fatan kin shiryawa jarrabawar da zan miki?" Kai ta 'dage sama alamar " Erh". Tsaye ya mi'ke sannan yace" Ki shiga ki watsa ruwa jikin ki..in kin fito zan gaya miki what is next". Ya 'karashe da nuna mata bathroom 'din sa. A tsare da furta hakan saboda baya son tayi masa gardama sam, ai kuwa sai ta 'daga kai ta kalle shi sannan tace " Nayi wanka a gida..." Tun kam ma ta 'karasa yace" Banson musu ni..a haka ne zan aure kin?" Tana jin haka ta mi'ke ta nufi bayin nasa kafin ta 'karasa shiga ne ya sake ce da ita" 5mins please ina jiran ki yanzu akwai inda zani". Ranta fari 'kal ta shiga bayin, bata sha wani wahala wurin fahimtar yanda zata yi ba cuz akwai tap, taran ruwan tayi a bucket tayi wankan ta tasa ta maida kayan jikin ta sannan ta fito tana wani sussune kai 'kasa. Ko da ta fito bata gansa cikin 'dakin ba danchaka sai ta koma inda ta tashi 'dazun ta sake zama tana rarraba idanu da tunanin jarabawar da yace zai mata...farin cikin ta bai wuce auren ta da yace zai yi ba. Tana cikin tunanin taga ya dawo 'dakin direct inda take ya nufo yana binta da kallon sha'awa..." Kayan basa damun ki ne?" abinda ya fara fa'di kenan lokacin da ya isa wurin ta. Kai ta jijjiga masa alamar" a a basu damin ta. Zama yayi daf da ita tare da 'dago 'kafar sa 'daya ya 'dora daga saman cinyoyin ta...cikin murya mai 'daukan hankali yace" Ni banson ganin ki da su to..ko baki son cin jarabawar tawa?" Muryar ta na rawa dan jin abinda ya fa'di 'din ga kuma wani sabon al'amari da ta gani 'kafafun sa kan nata ba ta saba hakan ba shiyasa duk sai taji hankalin ta ya fara tashi, zuciyar ta na harbawa da sauri, amma duk da haka sai da tayi dauriyar amsa masa da fa'din" Ina..so". Ido ya lumshe ya kuma bu'de su nan take sannan yace " To ki nutsu..banson taurin kai kinji? Ni kaina ma inaso ki ci jarabawa ta saboda ki aure ni". Yana maganar ne yana tafiyar da hannun sa kan fuskar ta zuwa saman wuyan ta..daga nan ya nufi bayan ta da shi..a hankali yake yawo da hannun nasa yana kuma bin cikin idanun ta da kallo. Ba wani lokaci yake so ya 6ata da ita ba, abu biyu ne kawai burin sa game da ita, na farko burin sa yaga yayi tozali da Boobs 'din ta da suka da'de zane cikin zuciyar sa, yayin da burin sa na biyun ya kasance na matu'kar son jinsa cikin jikin ta ne. Duk abinda yake yi mata Ma'u bata hana shi ba, zaton ta ko dagasken duk jarabawar ce hakan ma...idanu ta lumshe jikin ta na faman kakkarwa amma bata hana shi ba har lokacin da ta taji ya zuge mata zip 'din rigar ta baya lokacin ne tayi saurin bu'de idanun ta tare yun'kurin tashi tsaye cuz har yanzu a zaune take. " Relax mana gani kawai zanyi". Yayi maganar cike da bada umarni yana wani yatsina fuska tare da maida ta baya ya kwantar, take ya zare rigar tata yayi gefe da shi. Hankalin Ma'u sosai ya tashi jin jikin ta babu komai, dama rigar ce kawaj ta sanya sa sai mayafin ta, ko bra bata fara sanyawa ba tukunna, wasu lokutan ne dai take amfani da vest in ta ga dama yau 'din kuwa bata sa ba sam. Yanda ya haukace da ganin halittar jikin ta yasa ya kasa controlling kansa take ya fara yi mata wasu irin wasanni da bata ta6a sanin akwai su a rayuwar duniya ba. Har ma sai ta ji bata damu ba wanda hakan yasa ta bashi dama sosai da jikin ta, bata tashi sanin jikin ta babu komai ba sai lokacin da taji zafi na ratsata lokacin ne ta ankara tayi saurin 'daga kanta dan ganin me ke faruwa nan ta ci karo da yanayib da jikin ta take, tana shirin bu'de baki tayi kuka Mu'een ya yi saurin danne bakin tare da maida kanta 'kasa ya hana ta motsi. Ko da wasa bai gwada yin kissing 'din ta ba illah jikin ta da yayi ta sarrafawa son ransa batare da ko tsoron Allah ba ballantana yaji tausayin ta a hakan ya afka mata. Ma'u kamar zata mutu haka take ji, gashi bata da bakin kuka illah hawayen ta dake zuba ta gefe da gefen idanun ta na azaba...'kwayar idanun ta ka'dai idan ka kalla zaka fahimci cewa tana cikin tashin hankali. Sai da ya gama fitar da ita a hayyacin ta kafin ya 'kyaleta, taimako 'daya da Allah yayi masa kuma shine Ma'u irin matan nan ne masu 'kwari sam batayi masa langwami ba, ta dai sha kukan ta ta 'koshi taf, amma ko bayi da yace taje ta wanke jikin ta ma da kanta ta taka ta shiga. Shi ya bata ruwan zafi tayi amfani da shi sannan ta fito yace ta shirya ta koma gida amma karta fa'dawa kowa abinda ya faru yace duk ranar da ya shirya auren ta da kansa zai zo gidan su ya sami mahaifinta". Tana share hawaye ta fita saboda azaban da take ji cikin jikin ta...ko 'kafar ta ma nauyi sosai take mata kafin ta 'daga shi amma a hakan ta daure take tafiyar cikin hankali yanda bazai dameta sosai ba. Ganin yanda take tafiya da dabara ne yasa Yah Deen tsaida ta kuma ma sai alokacin yayi wani tunani kan rashin amfani da tsarin da be yi ba kafin ya kusance ta, magani guda biyu ya 'dauko ya bata yace ta sha...Ma'u kam bata son ha'diyan magani dan haka data kar6a sai ta ri'ke cikin hannun ta kawai ta sha ruwan ta ajiye kofin sannan ta juya ta fita, da fitar ta wajen gida kuwa ta watsar da su tana mai sake share hawayen ta da ya kasa tsayawa. Shi kam cike da jinda'di yayi tsalle ya fa'da kan kujera yana 'daukan remote zuciyar sa fari 'kal yau ya samu abinda yake so...gani yake yau 'din da babbar sa'a ya tashi, jumma'ar yau 'din da hasken ta tazo masa...an fasa auren sa da Husnah gashi kuma ya samu biyan bu'katar sa wurin Ma'u. Bai damu sam da halin da zata shiga ba ita da iyaten ta balle yayi tunanin babban zunubi ya aikata wanda Allah ke hukunta bawa a kansa..sksai zuciyar sa ta nutse cikin kogin da ba'a gane illar da zurfin sa ke haddasawa har sai anyi nisa cikin sa. Tana cikin share hawayen bata bar ko 'kofan gidan ba sai ga Imrana da shima isowar sa kenan yana 'ko'karin shiga ciki. Da ganin ta da yanayin ta sai ya saki dariyar mugunta a fili ya furta" Aiki ya kammala kenan...Asma'u ta Deeni komai dozen..". Shiru tayi kawai tana cigaba da share hawayen ta..sai yace" Me ya faru kuma kike ta faman kuka haka...cewa yayi bazai aure ki ba ne?" Sai ta jijjiga kanta alamar a a batare da ta ha'da ido da shi ba. Kai ya rausayar gefe sannan yana duban ta yana mata kallon tsaf a 'dan yatsine yake kuma fa'din" Yarinya kwantar da hankalin ki ki daina kukan nan kinji...sakamakon soyayyar Deeni dama kenan..kyauta yake bada tukuici..dan haka ki saki ranki..kukan ki shi zai sa kowa ya san abinda kika aikata harda 'yan gidan ku ma, in kuwa kika yi shiru kika daina kukan babu wanda zai gane abinda ya faru ko a gidan na ku ma.." D gama fa'din hakan sai ya juya ya nufi mashigar gidan yana sake fa'din" Sai mun zo zance...". Yana shiga parlourn ya saki fuska da dariya ya tunkari wajen da Yah Deen ke zaune yana 'dan tsalle irin na tsokana ya bashi hannu suka kashe kowa fuskar sa cike da fara'a sosai. Imrana ne yace" Harfa ka canza nawa". " Sai kace yau na fara". Ya bashi amsa yana murmushi. " a a kaide kayi shiru kawai kafa san 'yan yaran nan fa bala'i ne". Hannu Mu'een ya sake bashi kawai yana murmushi, cuz shi sam be iya fallasa sirrin gadon sa ga kowa duk dama ba ta hanyar da ta dace yake yi amma bai iya fa'di ma kowa tun asali haka yake yanzun kuwa ya lura abinda Imrana ke son ji daga bakin sa kenan..shiyasa kawai ya mi'ka masa hannun suka sake tafawa irin na gogaggun gayu..ya 'dauke masa hankali da hakan sai dai tun kafin su raba hannaye Imrana yace" Gaskiya abani nawa tukuicin nima dan na lura ba 'karamar liyafa ka sha yau 'din nan ba". Yana gyara zaman sa yace" Je ka za6i kaya guda cikin na Anty". Haka kawai yace da shi a takaice, yayin da Imrana ya tashi yana murna yake yi mai kirari da" Alhaji 'dan Alhaji, yaro mai abin mamaki...da haka ya wuce ciki dan 'dauko kayan da aka bashi kyautar su. Imrana na fitowa daga bedroom 'din Deeni hnnun sa da kayan da ya za6o sai suka ji tsayuwar mota daga waje, babu wanda ya damu cikin su dan sun san babu mamaki 'yan 'daurin aure ne suka dawo, Imrana 'karasowa yayi ya zaune nesa ka'dan da Mu'een yana sake godiya yana kuma warware kayan domin dubawa. Yah Deen bai ce da shi komai ba dan duk hankalin sa ya tafi ne ga tsayuwar motar da yaji..murmushi gefen baki yayi da ya tuna cewa Ishaq bai zo ya tarar da shi da yarinyar can ba da ya shiga uku wurin sa yasan, yanzu kam ransa wasai bashi jin wata fargaba tunda yana da tabbacin babu wani mummunan labarin da suka yo masa guzurin sa daga can tunda an riga an raba tsakanin sa da Husnah shi yanzu bashi da wata damuwa. Ai kuwa su 'din ne kamar yadda tunanin sa ya basa, dan yana cikin tunanin yaji sallamar su...Ishaq ne ya fara shigowa sai sauran a bayan sa. Zama yayi kan kujera yana sakin ajiyar zuciya tare da cire hulan da ke kansa. Yayin da sauran ma suka yiwa kansu mazauni kan sauran kujerun duk suka zazzauna Anas nema yana zaman yake fa'din" Ango mai abin mamaki, ango kasha mai'ko, ango mijin amarya". Murmushi Yah Deen yayi yana kallon sa tare da bashi amsar" A da kenan Anas..yanzu single nake kamar kowa" Anas sai yace" Hmm ai shiyasa nace ma maj abin mamaki domin har gobe ango kake mijin amarya kuma". Bai damu da zancen Anas 'din ba sai ya 'dauki abin wasa dan haka kansa ya kauda gefe yana fa'din" Erh daga goben har zuwa ranar da na shiryawa kaina yin wani auren kenan..." Ya 'karashe maganar yana dawo da kallon sa kan Ishaq dake kallon TV ana hasko wasanni yace masa" Kayi shiru Ishaq ko duk gajiyan tafiyan ne?" Kansa ya shafo a hankali tare da bashi amsar " Bari kawai kaina har ciwo yake min wallahi..an tara jama'ah ba laifi". Dariya Yah Deen yayi tare da fa'din" Shine ai da nima kake so inje in kwaso ciwon kan abanza ko?...ni bani labari ma me ya faru ne da yasa har aka fasa?" Ya 'karashe maganar yana gyara zaman sa izuwa fuskan tar Ishaq dake gefe da shi. Ishaq Babbar rigar jikin sa ya cire ya ajiye agefe sannan yace" Ai ka bari mutanen nan 'kananun 'yan gabas ne wallahi... _Kuyi min afuwan ji na da kukayi shiru kwana biyu al'amura ne suka sha kaina...kunsan rayuwa sai a hankali... hada-hada...._ Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *53* Ishaq Babbar rigar jikin sa ya cire ya ajiye agefen sa sannan yace" Ai ka bari kawai mutanen nan 'kananun 'yan gabas ne wallahi...sai da fa muka gama shiri mun baza kunnuwa zamu ji an 'daura auren ka kawai sai ji akayi ya wakilci auren Husnah da wani daban, ashe ma wai wancen Hisham 'din 'dan sa ne na cikin sa, in ba rainin hankali ba yau ne yasan da zaman 'dan nasa da bai yi tunanin aura masa ita tun farko ba sai da ya bada ta ga wani ?...abin takaici ma wai sai daga baya bacin har an gama komai kafin ya zo yana bawa su Alhaji ha'kuri...a lokacin ji nayi tamkar in mare sa..." Anas ne ya tare maganar tashi da fa'din.." Ai Alhaji ba 'karamin birge ni yayi ba, kai baka ga yanda ya nuna masa bai damu ba, sai ma wata kwantacciyar fara'a da fuskar sa ke haskawa...jikin Mutanen ai har sai da yayi sanyi 'yan rainin sense..". Baki Yah Deen ya ta6e, cikin nuna halin ko in kula da batun ya furta" can musu su suka sani...ni dai Alhamdulillah kawai zance tunda an raba ni da ita". Babu wanda ya ko kwatanta sanar da shi cewa an sake 'daura masa auren da wata  kawai suka bar shi da murnar sa na bai auri Husnah ba. *****    'Bangaren Husnah kam tunda taji cewa da Hisham aka 'daura auren ta bada Mu'een ba sai ta ringa kuka gwanin tausayi idan ka ganta, hawayen ta sam ya kasa tsayuwa, sai dai ita kanta bata san ainahin me take yiwa kukan ba, shin kukan an raba ta da Deeni ne ko kuwa kukan auren da akayi mata da Hisham? A yanzu baza ta ce akwai soyayyar Mu'een cikin zuciyar ta ba balle tace taji haushin rabuwa da shi, sannan ta san Hisahm 'dan uwanta kuma mai 'kaunar ta amma me yasa ta kasa jin farin ciki da jin labarin aure tsakanin su? Ta riga ta shiryawa zama da Mu'een tuntuni, ta yiwa kanta al'kawarin zama da shi cikin ko wani irin hali. Mahaifiyar ta kam jikin ta sanyi yayi da jin wani juyin da aka kuma yi, sam ta rasa me yake damun Alhaji Mamman a dauniyar nan, tsananin son kansa ya fiye masa yawa, wancan karon da ya bada auren Husnah batare da neman yardar ta ba ta yi masa uzuri da tunanin ko abokan sa ne iyayen yaron shiyasa amma duk da haka hankalin ta bai kwanta ba, wanda bata samu natsuwa ba sam har sai da ta tabbatar da cewa Husnah na son yaron sannan hankalin ta ya kwanta da auren, yanzu kuma bacin sun gama kwantar da hankalin su kan hakan sun kar6i auren sai ya kuma 6ullowa da wata sabuwar zance...wai auren Hisham da Husnah...she is totally speechless kan hakan Husnah kam kukan ta na 'kara yawaita ne a duk lokacin da ta tuno da mahaifin ta, tasan da ace yana raye da duk hakan ba zai faru da ita ba, ta san da babu wanda ya isa ya ringa juya mata rayuwa batare da yardar ta ba, balle irin wannan juyi irin na rashin mutunci da 'kas'kanci 'karara hatta mahaifiyar ta ba'a bawa darajar da za'a shawara da ita ba, tasan ba kowa ne zai iya 'daukan hakan ba duk kuwa rashin gatan mutum. Yini ta yi tana kuka, yayin da kanta ke tsananin yi mata ciwo amma sam bata damu ba, kafin maghrib kuwa ko motsin kirki bata iya yi da jikin ta saboda yanda kanta ke sarawa, idanun ta ma nawi sosai suka yi mata. Lokacin da Mummyn ta fahimci halin da Husnah take ciki kuka ta sanya kawai itama, gani take kamar bata kula da maraicin Husnah ba, a 'yan kwanakin nan Husnah tayi kukan da be kamata ace tayi sa ba duba da yanayin shekarun ta, gani take kamar Allah zai tambaye ta akan hakan,  haka ta zauna gefen Husnahn tana faman sheshshe'ka itama, wata 'yar uwar tace dake tsaye dafe da kafa'dar ta take bata baki akan taya Husnah kukan bashi da amfani sam, bata ce da ita komai ba illah ro'kon ta da tayi akan ta 'dauko mata wayar ta. Family Doctor 'din su ta 'kira inda ta sanar da ita abinda ke faruwa da Husnah cikin rawar murya. Husnah kam hawaye ta gefe da gefen idanun ta yake sau'ka, ko iya bu'de idanun da kyau ma bata yi yanzu, tana kyautata zaton Allah ne kawai yake jarabtan ta kan abinda ta aikata abaya, shiyasa yake ha'dawa da abubuwan 'daga hankali a duk sa'in da yaga dama batare da ta zata ba, a  hankali ta furta" Mummy...mutuwa zanyi ko?" Saurin kamo hannun ta mahaifiyar ta tayi ta ri'ke cikin nata tana girgiza kanta idanun ta hawaye tace" Bazaki mutu ba Husnah, idan kika tafi ni da wa zan zaki barni a duniyar nan...?" Husnah rintse idanu tayi tana jin ciwo a 'kirjin ta, ga kunyar mummyn ta da yabi ya cika mata zuciya, tasan babu wanda zai so yaji cewa 'dansa ya aikata irin abinda ita ta aikata, amma duk da haka tana ganin dole ne ta sanar da mahaifiyar ta, dole ne ta gaya mata rayuwar da tayi bayan idanunta, 'kila idan mahaifiyar ta yafe mata Allah ma zai ji 'kanta ya yafe mata, gani take duk abin nan dake faruwa da ita alhakin mahaifiyar ta ne yake binta...she have to end it here kar abin ya zarce haka, da jimawa farin ciki yayi mata 'kaura, rayuwar ta shiga garari ne tun lokacin da batun auren ta da Mu'een ya fara, yanzu kuma ga yadda abin ya kasance. Idan tace haka zata cigaba bata san agaba me kuma zai sake faruwa da ita ba...idanun ta a rintsen wani hawayen ya sake gangaro mata mai matu'kar 'dumi....a hankali cikin sanyin murya ta furta" Mummy ki yafe min...na ci amanar ki..naci amanar tarbiyar da kika da'de kina bani mummy..." Kuka take yi mai tsuma zuciya mai ha'de da shashshe'ka..bata iya bu'de idanu ta ha'da ido da Mummyn nata ba a lokacin. Yayin da Mummyn ta tsura mata idanu tana kallon fuskar ta zuciyar ta duk ta karaya, bata son tana kukan nan, tana so ta dakatar da ita haka nan amma sam ta kasa sai ma taji ta karaya gaba 'daya musamman da taji irin kalaman nata da mamakin ta tsaya kallon ta. Husnah kam tana cikin kukan tayi tunanin rashin sanar da Mummyn yafi saboda gudun halin da itama zata shiga sanadin hakan, take sai tayi ma'am da wannan batun dan haka ko da ta bu'di baki dan cigaba da ro'kon Mummyn sai tace " Mummy...dan Allah ki yafe min insha Allahu bazan sake 'daga hankali na ba...nayi al'kawarin zan zauna da Yah Hisham da amana....nasan 'kaddara ce ta ha'da aure na da shi auren mu ha'din Allah ne..dan haka na amince Mummy.." Ta 'karashe da sheshshe'ka, sam ba haka ta so fa'di ba amma nawin maganar yasa ta kasa furtawa mummyn ta, ta ya za'ayi ta dubi tsabar idanun Mummy tace da ita ta aikata zina sau ba adadi a rayuwar ta, sannan daga 'karshe wanda ta yadda da shi ta mallaka masa jikin tan shine kuma yazo ya nuna mata tsana mafi muni a rayuwar ta?...Tasan jin hakan ba komai zai haifar ba face 'dagawa mahaifiyar ta hankali fiye da tunanin ta..." Mummy kam bata iya tace mata komai ba ganin kukan da take yi, hannun ta kawai ta sake ri'kewa ga gam tana jin so da 'kaunar 'yar ta na sake ratsa ta, dama tasan Husnah me biyayya ce bazata ta6a cewa bata so ba...da yake bata wani fahimci maganar da Husnahn ta 'dauko da farko ba dan haka bata yi ko tunani akai ba. Bata da damuwa ta 6angaren Hisham dan tasan bashi da matsala shi, kuma dama asalima yana matu'kar 'kaunar Husnah tasan ko yanzun ma ba zai 'ki auren ta ba. Tana cikin tunanin nan likita ta iso inda take bayan gaisuwa sai kawai tafara aikin da ya kawo ta. Ba'a 'dauki dogon lokaci ba Husnah ta samu bacci sannan likitar ta tafi bayan ta basu shawarwarin da suka dace wanda hakan yasa suka fita suka bar ta dan ta huta illah mummyn ta suka bari dake zaune gaban ta ta zuba uban tagumi tana kallon ta tana kuma juya maganganun da ta gama furtawa, tausayin Husnah take ji sosai, da kuma tausayin maraicin ta, ba 'karamin da'di taji ba da taji cewa Husnah ta kar6i 'kaddarar ta hannu bibbiyu, ta amince da auren Hisham, ita kanta Mummy zata fison hakan saboda Hisham nagartacce ne, abu 'daya ya rage mata a yanzu shine..kare daraja da martabar 'yar ta, dole ne ta tashi tsaye ta sake shiri tunda Allah ya riga ya ha'da auren. Can gidan Alhaji Mamman kuwa zaune yake kan kujera shi da amaryar sa bayan sallar maghrib...dawowar sa kenan daga masjid sai ya tarar da ita zaune tana jiran dawowar sa, hirar su suke yi cike da raha tana 'kara ziga shi akan auren da tasa ya ha'da shi batare da shiri ba wanda har alokacin labarin auren bai isa kunnen shi wanda akayiwa auren ba. Hajiya Kareema ma tunda taji batun auren hankalin ta ya tashi sosai, tayi mamakin dalilin faruwar hakan, tunda la'asar ta baro gidan bikin ta dawo gida batayi zancen da kowa duk da kuwa abin ya dame ta sosai, musamman da taga yanda Husnah ke faman rusa kuka duk saboda jin cewa da Hisham aka 'daura mata aure, duk itama sai ta ji ta kasa natsuwa sai dai bata tattauna zancen da kowa ba, burin ta kawai Alhaji Mamman ne, so take taji daga gare shi menene dalilin wannan sauyin bazata da yayin. Sanin da tayi cewa duk inda yake da zarar maghrib tayi zaka same shi a gida matu'kar yana garin, hakan yasa da idar da sallah bayan tayi addu'o'i kawai ta kamo hanyar 6angaren sa....sai dai me..abinda taji Amaryar ta ke fa'di ne yasa ta fahimtar da bakin ta kan maganar auren kuma bisa ga wata manufa....cak ta tsaya daga bakin parlourn bawai tazo da niyyar tayi musu la6e ba ne a a, sai dai ta tsaya ne kawai dan ta fahimci maganar ta su da kyau... "...kaga ai hakan yafi..kai da kanka idan kayi duba da kyau zaka fahimci me nake nufi...har a yanzu fa da sauran dukiyar yarinyar nan masu nawi  wanda ina kyautata zaton da zarar ri'ko da kula da ragamar rayuwar ta ya bar hannun ka ma'ana idan ta zama mallakin wani daban haka kana ji kana gani dukiyar ma zata bar wajen ka dan nasan ba bari zasu sake yi a hannun ka ba, 'kila ma mijin nata da kansa zai zuga ta su kar6e a wurin ka, amma idan ta zama matar 'danka na cikin ka kuma ai kaga still dai tana hannun ka sai yadda kaga damar yi da ita da dukiyar gaba 'daya, sai ma fa kaso ka bar ta ta cigaba da rayuwa wallahi..kana iya..." Saurin taran maganar tata yayi da fa'din " A'a zatayi rayuwar ta ba ruwa na da ita, dukiyar ne dai kawai 'kwalelen ta, musamman ma wancen gidan mai 'din wallahi nafi jarabtuwa da shi dan ba 'karamin riba ake kwasa ba, in kuwa ya bar hannu na ai shikenan kashin mu ya bushe...." " Sai ka tashi tsaye da kyau idan baka san tonon asiri..in ma zata cigaba da rayuwa dole ne sai ka tsaya da 'kafafun ka dan kasan uwar ta ma akwai kinibibi...". " Ke de ki barni da su kawai...ai kin fargar dani, ba 'karamin da'din shawaran nan ta ki naji ba, ni fa ban ta6a kawo hakan cikin raina ba balle nayi tunanin zai anfane ni..da yanzu na bayar da ita ga wani can da zai kayar dani.... gaskiya kanki naja sosai..." Ya 'karshe da 'yar dariya. Itama murmushi tayi tana gyara zaman ta..take fa'din" Saura Hisham shima..." " Wannan ma barni da shi duk dama nasan bazai min gardama ba amma dai zan bishi a hankali dan ya fahimce ni da kyau..kar ya wargaza min shiri na so ma nake duk sunayen kan dukiyar su canzu daga nata zuwa mallaki na kuma kinsan hakan ba zai yiwu ba sai da amincewar sa matsayin sa na miji agare ta...". Hajiya Kareema da ta kasa cigaba da sauraran su shigowa tayi batare da ko sallama ba kawai sai jin muryar ta suka yi tana fa'din " Haba Alhaji..da girman kake shirin yin wannan ta'asar ga yarinyar da kake matsayin uba agare ta?...kaine fa babban wan mahaifin ta amma Alhaji ka kasa bata wannan darajar a zuviyar ka? Marainiya ce fa kai ka'dai take dashi amma fi sabilillahi saboda tsananin son abin duniya kake shirin sadaukar da farin cikin 'ya'yan ka? Wallahi tallahi wannan sam ba halin girma bane...ka ringa tunawa da ranar 'karshe..miye ribar ka kan aikata hakan dan Allah..idan fa kace shai'danun mutane zaka dinga biyewa wallahi har abada kwa6ar ka bazata ta6a yin kyau ba...". Juyowa tayi kan Amaryar Alhaji tace da ita" Ke kuma ki sani ita rayuwar duniya 'yar 'kalilan ce, masu aikata alkhairi ma suna kokwanto bisa ga ayyukan su, a kullum tunanin su shin an kar6a ne ko kuwa an barsu da shi ballantana dumu-dumu ka dulmiyar da kanka cikin sharri ai da kanka kasan makomar sakamakon ka, kin sashi ya aurar da Husnah ga Hisham saboda son zuviyar ku... sai dai ku sani Allah yafi ku kuma nasan zai bata kariya, sannan nima ko ka'dan ban yi ba'kin ciki da hakan ba, kuma na yi al'kawarin kar6ar Husnah matsayin 'ya agare ni bazan ta6a bari ta sami gi6i cikin rayuwar ta ba, idan dukiya ce kuje can gata nan ai duniya ce..ku ci ta son ranku ku gina farin cikin ku da shi...shawara ta agare ku kawai shine ku ringa tunawa cewa Husnah marainiya ce kuma sannan haramun kuke ci wanda Allah zai tsaida mu akansa ya tambaye mu bisa hakkin ta da aka tauye ta...." Tana gama fa'din hakan tayi gaba abinta, yayin da amaryar Alhaji ta ta6e baki gefe tare da hararan bayan Hajiya Kareema, Alhaji Mamman kam kai kawai ya sunkuyar yana jujjuya maganganun nata cikin ransa...amma koda wasa bai ji nadama ba. Tana komawa sashin ta sai ta 'daga wayar ta ta 'kira Hisham...bayan sun gaisa sai tace da shi.." Hisham kasan yau ne 'daurin auren 'kanwar ka ko?" " Na sani Mummy". " Me yasa baka zo ba to..?" Cikin natsuwa yace da ita "..Afuwan Mummy...wallahi abubuwa ne suka sha kaina amma idan nadawo har gidan ta zanje in duba ta insha Allahu". " Hisham!" Yace " Na'am Mummy". Inda yayi maganar yana me sake nutsar da kansa sakamakon irin yadda yaji ta 'kira sunan san yasan da akwai magana. Cikin sanyin murya tace da shi" Har yanzu kana son Husnah ko?" Idanu ya rintse tare da 'dora hannu bisa 'kirjin sa yana shafawa a hankali yana jin yadda sunan 'kanwar tashi ke ratsa masa gangan jiki...a hankali ya furta" haba mummy..me yasa zaki tambaye ni hakan bacin kinsan yanzu ita mallakin wani ce?..duk abinda zan fa'da yanzu zai iya zamowa laifi wurin ubangiji mummy...fatana kawai shine Allah ubangiji ya basu zaman lafiya ya albarkaci auren su ya ha'da kan ta da mijin ta". Da" Ameen" ta amsa shi sannan ta 'kara da fa'din" Hisham gobe nake so kazo gida please we need to talk...." Yace " Kuma har sai nazo gida Mummy?" Sai itama tace " Hakan nafi bu'kata in da hali". " Insha Allah zanzo goben Mummy idan Allah ya kaimu". " Allah yasa". Ta fa'di cike da jinda'din sau'kin halin da 'dan nata ke da shi..lokuta da dama takan gode wa mahalicci da ya azurta ta  da samun nagartaccen yaro irin Hisham sam bai gaji halin mahaifin sa ba. 'Yar hira ka'dan suka yi wanda tayi saurin yi masa sallama da jin ya fara tambayar ta abinda ke damunta, cuz a muryar ta ya fahimci tana tare da damuwa amma bata sanar da shi ba sai ma sallamar da tayi masa...hakan ne ma ya 'kara masa kaimi wajen ganin ya taho goben duk da kuwa bai shiryawa hakan ba, amma sam baya son yji ko ganin mahaifiyar sa cikin damuwa. Hajiya Kareema kuwa tun daga lokacin ta yiwa kanta al'kawarin yiwa kanta komai da dukiyar ta tunda tasan babu haramun a ciki, bazata 'kara bari Alhaji Mamman yayi mata komai da kansa ba sanin da tayi cikin dukiyar sa akwai son zuciya. *****    'Bangaren Yah Deen kuwa bai sake tada maganar auren ba, har yamma da suka je can gidan gaisuwa sai anan ya fahimci fuskar Alhaji Baba da ke 'kunshe da annahuwa wanda kallo 'daya zaka yi masa ka fahimci tun daga zuciyar sa ne. Bai yi mamaki ba cuz tashin farko ya ayyana cewa ai shima dama ba wani son auren yake ba kawai 'karfin hali ne, ga shi yanzu da aka fasa ai shima yaji da'di...har ya kasa 6oye farin cikin sa. Ya ayyana hakan ne kawai kuma saboda hakan aka sanar da shi, amma sam a zahiri bai ga wani alamar fasa aure tattare da yanayin gidan na su ba, dan akwai wani abokin Alhaji da ke can Jos yana so ya koma ma a lokacin amma harda tsayawa ya yi masa nasiha kamar gaske. Shi dai Yah Deen yaji shi ne kawai bawai dan nasihar ta shiga kansa ba...gani yake kamar rashin abinyi ya sanya mutumin yi mai nasiha baya ga haka menene ze sa hakan tunda ba auren ne akayi masa ba. Ko cikin gida da suka shiga bai ga alamun sauyi ba, hidindimun su kawai suke yi hankali kwance...Yah Deen kam sai ya ta6e baki gefe bai damu ba cikin ransa ya ayyana" Kwayi ku ha'kura ai". Basu da'de ba suka koma gida shi da su Ishaq wanda suke shirin komawa Jigawa washe gari, shima Yah Deen 'din ya riga ya tsara cikin ransa cewa tare zasu koma a goben tunda babu batun auren gara yaje yaci gaba da karatun sa yafi masa. Sai dai hakan bai yiyu ba, dan Uncle Ja'far ne da kansa ya hana shi tafiya yace ya bari sai next week sannan zai koma...yaji haushin hana shi tafiya da akayi hakan yasa ya ro'ki Ishaq da fa'din dan Allah su bari to ranar Sunday sai su tafi,  basu yi masa musu ba kuwa suka amince. Ranar Asabar da safe nayi shiri na da wuri nace da Ammi zanje in gaida Baban mu da yake tunda  yazo 'daurin auren bmu ha'du ba..to tunda bai koma ba gara inje mu gana da shi...hakan yasa nake ta 'dokin zuwa in ganshi dan na kwan biyu ban gan shi ba. Atamfa ta sabuwa fil na sanya a jikina Ammi ta bani mayafi sabo dal shima na rufa a jiki na...kayan biki dangin flour ta cika min a leda tace in kai wa Ummah ta tare da fa'din in gaida su kuma banda yawo tace min inda ya dace kawai zanje banda shige-shige nace to Ammi. _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *54* Daga nan nayi musu sallama Anty Zee na ko'da ni ina murmushi na fita. A harabar gida na ci karo da su Alhaji Baba da yaran sa, wato Yah Deen da abokan sa...ban san me suke tattaunawa ba sai dai ga dukkan alamu shigowar su kenan... na tabbatar da hakan ne lokacin da na kusan isa inda suke naji suna faman mi'ka masa gaisuwa inda yake amsa musu da fara'ar sa hannayen sa duk na cikin babbar rigar sa amma kallo 'daya zaka yi masa ka tabbatar ba shi tare da damuwa...fara'a fal a fuksar sa har kana iya hango hasken ha'koran sa afili. Da gani na sai ya maida hankalinsa wuri na ina gaida shi ya amsa tare da 'karawa da fa'din" Uwata ina zuwa da sssafe haka?" " Murmushi nayi sannan na 'daga kai na dubi harabar gidan inda duk rana ta mamaye ko'ina..." Ba sassafe bane fa Alhaji Babba kalli fa yanda rana ma tayi". Na fa'di ina murmushi tare da nuno wurin.. shima Alhaji sai yayi murmushin..sannan ya sake fa'din unguwa zaki ne?" Nace" Nace a a zanje in gaida Baban mu ne ". Sai yace " Ya kamata kam..dan inajin gobe ma zai koma...amma ki bari ba yanzu ba kinji maza ki koma cikin gida". " To" kawai nace da shi tare da 'daga kaina na kalli su Yah Deen da ke tsatstsatye wanda da shi na fara ha'da idanu sai naga ya ta6e baki tare da kawar da kansa gefe, bansan me nayi masa ba dan haka sai nima 'dauke kaina daga kallon sa zuwa na gefen sa (Anas) shi kuma sai naga yana min murmushi ban damu ba kawai a jimlance nace da su " Ina kwanan ku?" Mutun biyu zuwa uku ne daga cikin su suka amsa min wanda cikin sun kuwa ina da tabbacin babu Yah Deen a ciki. Juyawa nayi na fara tafiya zuwa cikin gida yayin da Alhaji Baba ya nufi hanyar fita tare da 'kiran sunan Ishaq da alamun yana so su ke6e da shi, Ishaq sai ya bi bayan sa su Yah Deen kuwa cikin gidan suma suka 'karaso dan gaida su Ammi...in tafe suna bina abaya amma tsakani na da su akwai 'yar tazara ka'dan...ledan hannu na na gyara dan ya fara min nawi hakan yasa na 'dago shi zuwa saman 'kirji na na rungume dalilin hakan yasa mayafin da ke rufe da jiki na ya kame min jiki sosai...bansan da faruwar hakan ba sam illah tsinkayar muryar Yah Deen da naji a tsawace yace" Ke...wani irin hauka ne wannan kuma?" " Ke" da naji ya furta cikin maganar tasa ne ya sani tsayawa cak sannan na waigo dan ganin shin da wa yake. Kicin-kicin naga yayi da idanu hakan yasa nayi gefe da nawa idanun ina jiran jin irin haukar da yace nayi...." Gyara mayafin ki". Ya sake furtawa still suna tunkaro ni...sai a lokacin ma na 'dan fahimci abinda ya faru take sai kuma naji tsananin kunya ta lullu6e ni, tfiya na cigaba da yi ina me gyara mayafin nawa...shi kam haushi sosai ne ya cika shi da be san dalili ba...tunda ya tsinkayi irin kallon da su Imam ke bin baya na da shi yaji tsananin 6acin rai ya shige shi..sai da kuma yayi mata masifar sannan yaga wautar sa, to shishshigin miye kuma nayi?" Ya tambayi kansa...'yar 'karamar tsaki ya saki a fili da yasa duk 'yan tafaiyar tasa suka kalle shi...dariya m ya bawa Anas sosai dan abinda yayin da yanda yayin tashin farko zaka fassara hakan da tsananin kishi ga wanda yasan asalin tushen kafuwar 'kauna. Ina shiga parlour sai Anty Zee ta kalle ni da mamaki baki bu'de take min kallon ya haka? Bance da ita 'kala ba har sai da na iso gefen ta na zauna sannan ta furta" Kin fasa zuwan ne kuma?" Kai na girgiza mata tare da fa'din" Alhaji Baba ne yace ba yanzu ba". " Ow woh...sai ki huta abin ki kafin lokacin da ya tsara 'din tayi..." Bata gama rufe baki ba sai ga sallamar su Yah Deen da tawagar sa...tun ma kafin su 'karasa shigowa na mi'ke tsaye na nufi hanyar 'dakin Ammi da sauri na, ba naso in ha'da idanu da kowa daga cikin su bayan sun gama kalle min baya. Zazzaunawa suka yi suna gaida Anty Zainab inda take amsawa da fara'ar ta...tana duban Yah Deen tace" Tunda yanzu kayi auren ka sai ka daina firgita mana yarinya kuma ko..kana gani fa yanzu da jin sallamar ku ta tashi ta gudu ciki..." " Ni ina cin mutane ne Anty da zata guji inda nake?" " Ni na sani maka ne..ga dai zahiri yanzu...kuma wallahi kabi a hankali in ba haka ba in kayi wasa ita zamu aura maka a ta biyu". " Ai kuwa da kun kyauta masa Anty". Cewar Anas yana 'yar dariya. Anty ma murmushi tayi tana duban sa tace" 'yale shi mana ana masa gata yana min yanga". Shi kam Yah Deen " Hmm" kawai yace sannan ya 'kara da fa'din " Ina Ammi take?". Anty ce ta bashi amsa da fa'din " Tana ciki yanzu zata fito ma ai". Nima acan 'daki na sami Ammi inda itama tace dani" ya kika dawo kuma me ya faru?" Tayi maganar tanacduba na da kulawa da son jin ko wani abin ne ya hana ni tafiya Sai nace da ita" Inji Alhaji Baba ne wai in bari ba yanzu zani ba". " Saboda me yasa to?" Nace " Nima ban sani ba". Inda nayi maganar ina cire mayafin da ke kaina. " Ikon Allah". Ammi ta fa'di da mamaki harda kama baki. Ni kam ban damu ba nayi kwanciya ta tare da 'daukan abin da muke buga game ni da su Saif na fara bugawa batare da damuwr komai ba, dan nasan hakan bai ta6a faruwa ba, 'kila akwai dalilin da yasa Alhajin ya fa'di haka a yau 'din. 'Yar hira suke yi sama-sama da su har Ammi ta 'karaso nan duk suka gaida ta sannan suka cigaba da hira. A can waje kuwa Alhaji Baba duban Ishaq yayi yace" Ya maganar mu?" " Tana nan Alhaji..babu wanda ya sanar da shi har yanzu". Murmushi kawai Alhaji Baba ya saki...sannan yace baka gane wancen yarinyar ba ko?" " Erh gaskiya ban gane ta ba amma ina dai ganin ta agidan nan jifa-jifa". " Itace Amaryar taku ai, kaga itama har yanzu bata san da maganar auren ba shiyasa na ce ta koma gida kar ra fita." Take fara'a ta bayyana kan fuskar Ishaq yana murmushi yace" Masha Allah...Ubangiji Allah yayi albarka Alhaji..godiya muke da wannan za6i Allah ya 'kara girma". " Ameen..Ameen..zan sanar da su da kaina idan naga dacewar lokaci insha Allahu..." " To Alhaji hakan ma yayi..Allah ya 'kara girma" Cewar Ishaq..Alhaji Baba kuwa cewa yayi " Goben zaku koma ko?" " Erh hakan da muka ce idan Allah yaso". " Bakomai Ubangiji Allah ya kaimu goben...ka shiga ku gaisa da matan gidan tukunna ". " To Alhaji". Ya furta cikin girmamawa tare da juyawa ya koma ciki. Da isar sa kuwa ya tarar da su kan maganar Fitan da Alhaji ya hanani wanda Ammi ce da kanta ta fara kawo maganar saboda tsananin mamakin da ya cikiu Sallamar Ishaq ne ya dakatar da maganar da Ammi ke yi cuz ita kam sosai tayi mamaki, batun yau nake fita unguwa ba amma bai ta6a magana ba bai ta6a hanani zuwa ko'ina ba sai yau ka'dai, sannan kuma duk iya tunanin ta takasa hasko musababbabin faruwar hakan. Ishaq kam da ya san dalilin kawai sai yake ta sakin murmushi, yanzu ne ya fahimci cewa dagaske babu wanda yasan auren dake tsakanin Deeni da yarinyar can, illah su Alhaji Baba...shi dai farin ciki kawai yake taya abokin sa da dacen da yayi...yasan ko shi da kansa aka bawa za6i a irin wancen lokacin ba zai iya za6o irin yarinyar ba, tashin farko ya fahimci natsuwar dake tattare da ita...ha'ki'ka Mu'een yayi dacen samun mace a duniuar nan. Basu da'de tare da su Ammjn ba suka koma can gidan Yah Deen. ***** 'Bangaren Ma'u kam abin tausayi bata bari taje gida tana kuka ba, kuma sai tayi sa'a lokacin da ta isa gidan matar Baban ta ta shiga ma'kwabta, tana shiga sai ta wuce 'dakin ta ta kwanta tana faman bibiyar lamarin cikin ranta, bata da'de ba bacci yayi gaba da ita saboda maganin da ya bata mai 'karfi ne...ba ita ta shi ba sai kusan maghrib...Allah da ikon sa kuwa duk sai taji ciwon ya ragu...wanka ta sake yi tana ta 'ko'karin daidaita kanta gudun kar a fahimci yanayin da take ciki...matar baban ta sai mita take yi wai tun 'dazu ta tsaya baccin asara bata yi musu ko wanke-wanke ba. Bata damu ba ita dai burin ta kawai kar a fahimci abinda ya faru tsakanin ta da Deeni kafin ya dawo neman auren ta kamar yadda yayi al'kawari. Tana yin sallahr la'sar ta dawo ta tattara wanken-wanken ta wanke musu tas ta sake komawa 'dakin ta..tunanin ta kawai shine zuwa yaushe Yah Deen zai zo neman auren ta. Bata sani ba ashe shi kam ma har ya manta da ita, balle tunanin auren ta...abinda ke gaban sa ma yawa ne da su. Ammi kuwa rashin ganin an kawo amaryar Yah Deen gida ne ya matu'kar sa ta mamaki, ko da ta tambaye shi dalili sai cewa yayi shima fa bai sani ba..ya dai ji ance ba'a 'daura auren ba an fasa. Abin sai ya sake 'daure mata kai, ga shi Alhaji bai zauna ba balle ta samu dama ta tambaye shi yana can yana fama da ba'kin sa. Si taji ta kasa natsuwa da Anty Zainab suka tattauna maganar inda tace abin ya 'daure mata kai sosai itama kuma duk babu wanda yayi musu bayani, da farko ta zaci can Jigawa aka kai amaryar sai daga baya kuma tayi tuananin ba'a kaita can ba tunda ga shi maj auren anan ita zaman me zatayi acana ita ka'dai, amma tunda har anje an 'dauro auren kuma me yasa baza'a kawo amaryar gida ba. Da daran ranar da yake ba'kin Alhajin duk sun watse anan Ammi ta sami daman ganawa da shi, tambayar sa tayi kan batun amaryar sai taga Alhaji Baba na murmushi yace mata ai tuntuni amaryar na gida. " Kamar yaya?" Ammi ta sake tambaya cike da mamaki tana duban sa Sai yace " Kamar yadda kika sani". " Nifa na kasa ganewa Mu'een ce min yayi wai an fasa auren yanzu kuma ga ka kana cemin wai amaryar na gida". " Yana saka jallabiya yace mata" To be frank Aisha..auren Muhammad bai yiyu da wancen yarinyar ba dan wan mahaifinta yaci amanar mu..muna zaune a wurin ya 'daure auren 'yar sa da wani daban bacin ya san shi muke zaman jira...sai daga baya ne ma Ja'afar ke sanar dani ashe wai shi wanda ya 'daurawa auren 'dan sa ne na cikin sa..kinga an nuna mana bambanci a zahiri. ...ran kowa da muke tare sai da ya 6aci a wurin hakan yasa Mahaifin Hudah yace tunda muka zo har Azare da niyyar aure to baza'a fasa ba...yace s 'daura auren kawai da Hudah ya bashi ita...na so in nuna 'kin amincewa amma yace matu'kar na nuna bana do to azahiri na nuna masa 'kyama matsayin sa na talaka...dole naja baki na nayi shiru na wakilci amarya Ja'afar kuma ya kar6awa Mu'een gudun maganar da zai biyo baya, yanzu dai Hudah 'yar ki da kike tsananin so marsayin mata take a wurin 'dan ki Muhammad..." Ya 'karashe yana 'yar dariya. Ammi kam rasa abinda zata ce da shi tayi saboda farin ciki..ita kanta ta fahimci jin da'din Alhaji Baba kan wannan auren...to inaga ita da ta jima da son ganin faruwar hakan duk da bata furta ba amma ya da'de cikin zuciyar ta. Maganar Alhaji Baba ne ya katse mata tunanin ta inda yace" Sai dai bazan bashi Hudah ba har sai na tabbatar da cewa halin sa mai kyau ne , zargin da nake yi masa abaya idan ya kasance ba gaskiya ba ne sannan zan bashi Hudah matsayin mata dan bana so ya lalatawa yarin farin cikin ta da gur6ataccen tunani..matu'kar na tabbatar da zargi na akan sa wallahi da kaina zan sa ya rabu da ita in aura mata wani daban..dan haka a yanzu ko sanin cewa itace matar sa bana so yayi harda itama...ke de kawai ki 'kara kulawa da rayuwar ta ki tabbatar babu wanda ke shiga rayuwar ta tunda yanzu da aure akanta, batun zuwa gida kuma gobe da safe zan sa akaita ta gaida mahaifin nata 'kila ma a goben...zai koma". Ammi kam ji tayi kamar ta taka rawa saboda tsananin farin ciki...ba ta iya ri'ke maganar ba sai da ta sanar da Anty Zee a daren ranar..ga mamakin ta kuwa sai taga farin cikin da Anty Zainab ta shiga har yaso ya zarta nata ma. Sam hakan bai sa Ammi mamaki ba cuz tasan irin 'kaunar da Anty Zainab ke wa Mu'een, in sha'kuwa ce kuwa ko ita da ta haife shi baza ta ce tafi ta sha'kuwa da shi ba saboda a gaban ta ya tashi..so fiye da haka ma idan ta gani daga Anty Zainab bazai sa ta mamaki ba. Itama Anty Zainab Uncle Ja'afar ta 'kira a waya tace dashi gaskiya bai kyauta mata ba da har ya 6oye mata wannan maganar. Sai yace" Tunda yanzu kinji ai shikenan". Ita ka'dai tasan me take ji cikin ranta...Alhamdulillah kawai take ta maimaitawa, cuz tafi kowa 'kaunar ganin Mu'een 'din ya samu mata irin Hudah sai gashi Allah ya cika mara burin ta cikin sau'ki, badan Ammi ta gaya mata abinda Alhaji Baba yace game da batun ba da gobe sai ta ha'da sabuwar gagarumar walima na farin ciki dan ta nuna godiyar ta ga mahalicci. Washe gari sunday..kamar yadda Alhaji yayi al'kawari kuwa hakan ne ya faru..cuz wani yaron sa ya sa ya kaini gidan mu dan gaida mahaifi na, anan na tarar da shi ma yana kan shirin tafiya, ban fahimci komai ba duk kuwa da cewa naga anata nan nan dani sannan Baban mu yayi min doguwar nasiha cikin natsuwa kan ha'kuri tamkar wanda ganawar mu da shi kenan ta 'karshe har yasa jiki na yayi sanyi. Ko da wasa babu wanda yace min an 'daura min aure duk kuwa da cewa duk sun sani, ban sani ba ashe duk Alhaji Baba ya ro'ki da kar a fa'di min har sai yaga abinda hali yayi. Abu 'daya na fahimta kawai canji daga wurin ahali na, yanda ake bani wani daraja da kaffa-kaffa dani abin ya 'daure min kai sosai, sai dai ban kawo batun aure ba sam ko a tunani na, na dai yi tunanin girman da na 'kara ne ya sa ake min hakan dan haka naji Anty Zainab ta fa'di lokacin da zan taho. Turare wannan hanani amfani tayi da asalin nawa ta bani wasu marasa 'kamshi sosai wai ai na girma yanzu so in dinga kula da komai na rayuwa ta. ko da nace zanje gidan su Binta ma Ummah ta hanani tayi, ko gidan Anty saudahn mu banje ba Ummah ta ta ri'ke ni a gida tace wai in bari sai wani lokacin kawai. Ban fi 3hrs ba a gidan aka dawo 'dauka ta...haka na shiga mota ina tuttura baki na gaba da mitar ni banganewa wannan sabuwar tsarin ba duk an bi an takura ni. Da isata gida kuwa na tari Ammi da mitan Ummah ta bata barni naje ko'ina ba, ko gidan Addah ta banje ba da gidan su Binta...kafin in kai 'karshen magana ta kuwa sai ga hawaye ya gangaro min. Ammi rasa abinda zata ce da ni tayi kawai sai ta jawo jikin ta ta hau lallashi na, cikin hakan dmtake ce dani kar in da mu wataran ai zanje...nace" Ammi kinga ma fa Ma'u tace min zata zo bikin Yah Deen kuma bata zo ba bansan me yasa ba kuma ban je na duba ta ba duk Ummah ta ta hana ni". " Rabu da ita ai zata zo may be bata samu daman zuwa bane kawai". Anty Zee na ganin yanda nake yiwa Ammi kuka sai ta janyo ni ta ringa bani misalai tana jan hankali na da da'da'dan kalamai take fa'din duk mace mai aji ai bata yawan yawo komin ta bisa tsari take yin sa ba wai ta ringa shige-shige ko'ina kamar akuyar da babu 'dauri ba. Ni dai kawai jin ta nayi ba wai dan na fahimci me take nufi ba. Ranar kuwa gida ya watse kaf kowa ya koma inda ya fito, ko abokan Yah Deen ma ranar duk suka koma dan daga gida da suka gaida su Alhaji sai suka wuce bayan ya sallame su, aka bar shi shi ka'dai sai Imrana kamar da can. Yah Deen ranar bai je ko'ina ba dan haushin an hana shi tafiya bacin ba komai yake yi a gidan ba, haka ya yini a wuri 'daya illah Imrana da ke faman shiga yana fita...cikin kwanciyar hankali abin sa. Uncle J ma da sassafen ranar ya koma Taraba Anty Zee kuwa ba yanzu ba sai daga baya zata koma dan sai ta 'dan kwana biyu a Azare ma tukunna kafin ta tafi, gida ya zama shiru babu da'di..lalle jama'ah rahama. Haka inaji ina gani aka takurani da zaman gida, illah makaranta da nake zuwa...kuma ko makarantar ma ban ganin Ma'u, gashi su Ammi sun hanani yawo balle inje gidan su in dubo ta... Sai da aka yi kwana biyar da bikin Yah Deem kafin Ma'u tafara fitowa makaranta...nan na isheta da tambayar me yasa bata zo bikin Yah Deen ba?" Tace min" bikin da aka ce an fasa 'din?" Nace" Erh amma ai de mutane sun taru kowa yazo nayi ta duba ki bangan ki ba...". Tace" Banda lafiya ne shiyasa banzo ba". Sai nace " To waye yace miki an fasa kuma ?" " Imrana". Ta bani amsa a takaice. Sai nace " Ayyah ai naso in zo gidan na ku amma an hanani yawo yanzu shiyasa banzo ba". Shiru tayi bata sake kulani ba. One thing da na fahimta game da Ma'u yanzu sam bata son yawan surutu sosai sai dai ban san dalili ba dan haka nima sai nayi shiru ko mun ha'du a makaranta ko Islamiya hirar mu ka'dan ce da ita da yake ma ba kullum take zuwa ba sai jifa-jifa...amma duk ta natsu ta daina rawar kai yanzu (ban sani ba ashe Yah Deen ne ya koya mata hankali). _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ _Nagode sosai masoya Allah ya bar min ku..._ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *55* Hisham yazo gida kamar yadda mahaifiyar sa ta bu'kata sunyi magana kuma ya fahimce ta, musamman ma da yaji cewar an riga da an aura masa Husnah, jin hakan ya matu'kar faranta ransa har ma ya kasa 6oye farin cikin sa, bakomai bane kuma yasa hakan face tsananin soyayyar da yake yi mata, shiyasa ma ko guda daga cikin sharu'd'dan da mahaifiyar sa ta gindaya masa akan Husnahn bai yi jayayya da shi ba. Zuciyar sa 'daya ya 'daukan mata al'kawarin kulawa da Husnah da kuma sau'ke duk wani hakkin ta da ya rataya akan sa, ya kuma yi al'kawarin bata kariya iya iyawar sa, duk da Hajiya Kareema bata fito fili ta bayyana masa asalin meke tafiya ba amma tayi 'ko'karin ganin ta nuna masa daraja da muhimmancin da Husnan ke da shi a wurin sa...wanda bayaga aure akwai kyakykyawar dangantaka tsakani wanda shi kansa ya sani. Ko da ya isa ga mahaifin sa ma ba wani ba'kon al'amari yaji daga bakin sa ba wanda zai rikita shi, bambancin kawai shine shi bai yi masa maganar ta fuskar fahimta ba, ya dai ce da shi yayi masa aure da Husnah and kuma yana fatan zai masa biyayya bisa hakan. Hisham bai wani damu ba dan ya riga ya san wace Husnah, kuma sun riga sun gama magana da mahaifiyar sa kafin nan so hankalin sa kwance ya bar gaban mahaifin sa da 6oyayyen farin cikin sa a zuci. Bai samu damar zuwa ganin Husnah ba har sai washegari...kuma Alhamdulillah 95% ya samu ha'din kanta kan auren dan bata nuna masa tsana ko nuna bata 'kaunar zaman aure da shi ba. Batun tarewar ta kuma yace shi da kansa zai shirya komai kafin ya koma. Wurin mahaifiyar sa yaje  suka sake magana akai inda ya nuna mata cewar ba abin damuwa bane tunda ma tana makaranta, so zata cigaba da karatun ta a Jigawa har sai ta kammala kafin. Ai kuwa muhalli kawai aka canza mata daga campus zuwa wani madaidaicin gida zubin zamani, wanda Hisham ya cire ma'ku'dan ku'dade aka biya haya da shi. Gidan ta aka tsara mata tamkar acan zata 'kare rayuwar ta dan sosai gidan yaci ku'di abin ba'a cewa komai, yayin da shi Hisham 'din zai cigaba da zaman sa a Abuja bakin aikin sa, sai dai ziyara kawai zai ringa kawo mata aduk lokacin da ya samu dama. ~Sai fatan Allah ya basu zaman lafiya mai 'dorewa.~ *****           Cikin shirin makaranta ta na fito da yake nayi latti so sai nake ta hanzari inga na fita dan kar in makara sosai, Ammi da Anty Zee na zaune a parlour na fito ina sanya Hijab akaina ko duban su da kyau ma banyi ba na nufi 'kofa ina fa'din" Ammi na tafi yau na makara sosai". " Adawo lafiya". Ammi tace da ni gami da mi'kewa tayi ciki kamar dama jiran fitowa ta take yi...ko juyawa banyi ba na cigaba da tafiya ta ina gyara zaman jakata da tunanin saurin da zanyi kafin in isa, daf da zan bar parlourn naji muryar Anty Zainab na fa'din" Hudah baki ko gaida Yayan ki ba zaki tafi?" Saurin waigowa nayi jin ta ambaci Yaya na..nan naci karo da Yah Deen zaune daga gefen ta ya wani kishingi'da yana danna wayar sa. Sam ban lura da shi ba lokacin da na fito sai yanzun na ganshi. 'Dauke idanu na nayi daga kallon sa na mayar kan Anty sai naga ta min murmushi tana min nuni da in gaida shi...cikin sanyin murya na furta" Ina kwana Yaya"...kamar ba zai amsa ba can 'kasa-'kasa cike da izza ya amsa da" Lafiya" ata'kaice. Sai da na juya na kalli Anty Zainab dan ganin yanayin ta da son tabbatar mata da cewa na gaida shin sannan na juya na sa kai nayi gaba da tunanin halin sa cikin raina. " Wai me yasa kake haka ne Mu'een...?" Anty ta tambaye shi tana kallon fuskar sa bayan fitata. " Me nayi Anty?" Shima ya mayar mata da tambaya madadin amsar maganar ta yana mai 'daga idanu ya kalle ta. " Aww kana nufin kai baka san me ka aikata yanzun ba? Yadda kake wa yarinyar nan ai kai da kanka kasan bai dace ba...kai baka tunanin gaba ko Mu'een?...kar fa...". Bata 'karasa fa'dar abinda tayi niyya ba ya tare ta da fa'din"...Insha Allahu babu abinda zai faru Anty...dan nasan abinda zaki fa'di bai wuci wanda kika saba fa'da ba". " Hmm..amma dai ya kamata ka daina haka nan tunda babu wanda ya san me gaba zata haifar..'kila sai ka gama mata fi'ili yanzu wataran kuma mugan ka kana ro'konta.. kasan ita rayuwa babu abinda bata tafiya da shi..." Gira ya ha'de tare da gyara zaman sa da kyau yana duban Anty yace" A wani dalili zan yi hakan kenan Anty?" " Dalilin aure mana". Ta bashi amsa tana murmushi...take ya sake ha'de ransa tare da kauda kai gefe yana fa'din" Allah ya sawwa'ka wallahi..wannan 6eran kike fatan aure tsakanina da ita Anty ni me zan yi da ita?" " Ko ma menene dai kai kasani..ko da ita kiyashi ce kuwa idan Allah ya tsara kaine mijin ta baka isa kayi jayayya ba..." Da serious tune cike da 6acin rai yace " Please Anty ki daina min wannan fatan dan Allah..ban so". Bata 'kara cewa komai ba kuwa illah bayyananniyar murmushi dake haskawa saman fuskar ta...tana tunanin ranar da Mu'een zai ji da kunnen sa cewa Hudah matar sa ce ta sunnah da aka 'daura musu aure batare da sanin sa ba... ayanda ta sanshi take kuma ganin take-taken sa tasan ranar kuka ne kawai ba zai yi ba saboda ba'kin ciki...ni kuwa nace ( ~time ll tell~ ). Tunda suka yi wannan maganar bai sake doguwar hira da Antyn ba, bai ma jima a gidan ba ba ya tashi yayi musu sallama ya koma gidan can sa ransa a matu'kar 6ace. Daga ranar kuwa naga ya sake canza min, ni ban san abinda ya faru ba sai gani nayi idan mun ha'du ko kallon arzi'ki bai min, duk da ma ko da can baya ma haka ne amma dai ba kamar yanzu ba, ada, haka ma gaisuwa ta sai ya ga dama yake amsawa, ni kam ban wani damu da hakan ba da yake nasan wannan ka'danne daga cikin halin sa da ni na sanshi da shi. Sati guda bayan bikin Yah Deen sai ya tattara ya koma Jigawa ranar wata Sunday...Anty ma washegarin tafiyar sa ta koma Azare wurin dangin ta...gida ya dawo shiru babu kowa sai mu ka'dai. Duk wani abu da ya faru a bikin bai sa na kawo faruwar wani lamari cikin zuciya ta ba, da yake ma har a lokacin ban gama mallakar hankali na ba shiyasa sam ban ta6a wani dogon tunani kan maganganu ko abubuwan da naga suke faruwa a gidan ba. Sai daga baya ne ma bayan kowa ya watse nake tambayar Ammi ashe wai an fasa auren Yah Deen 'din. Ammi sai tace da ni a ina naji..ban 6oye mata ba nace Ma'u ce ta gaya min nima. Ammi sai tace 'karya ne ba'a fasa ba, an 'daura auren tun a ranar babu wani fasawa da akayi. A 'kagauce na sake tambayar ta ta da fa'din " Ammi to ya banga amaryar ba har yanzu?" Sai tace" Tana gidan su tukunna ba yanzu za'a kawo ta ba". Jin haka yasa na yadda cewa amaryar Yah Deen 'din tana gidan su har kuwa na fa'dawa Ma'u yanda muka yi da Ammin kaf da muka ha'du da ita...jim naga tayi bata ce dani komai ba, ashe abin ya dame ta sosai sai dai ta ri'ke cikin ranta kawai...tunani take yi akan 'karyar da suka shirga mata shi da abokin sa Imrana akan wai ya fasa auren kuma  gun mahaifinta zasu zo neman auren ta ashe 'karya ce ba'a fasa auren nasa ba...shiyasa ma ya yi tafiyar sa bai ko sake bi ta kanta ba ashe..bayan uwr azabar da ya bata suka kuma hanata sanar da kowa. Bayan wasu kwanaki... Yanda abin yake cinta arai har yasa ta fara 'dan ramewa sai dai babu wanda yasan takamamman me ke damun ta, ko makaranta ma yanzu ba zuwa take yi sosai ba sai lokaci zuwa lokaci. Yah Deen ya riga Husnah komawa makaranta so hankalin sa kwance ya cigaba da karatun sa. Ya kusan yin a'kallah kwanaki tara da komawa amma bai ta6a ganin ko gilmawr Husnah ba..shi kam ma ko tunawa da ita bai yi ba, sai dai acikin 'yan kwanakin ranar wata laraba labari ya iso masa cewa anga Husnah cikin makaranta. Basarwa yayi bai nuna wata alamar damuwa ba,  dan harga Allah shi yanzu ba ta gaban sa..sai da ma aka same shi da maganar ta kafin ya tuno da ita. Sai dai me ? komawar sa gida sai tunanin Husnah ya bi ya cika shi, a lokacin ya fara missing presence nata, 'kewar ta ya'ki barin sa ya sarara har ya kasa ribatar zuciyar sa shai'dan yayi galaba a kansa ya mantar da shi cewa tana da auren wani daban  akanta wanda bashi ba. Kamar wasa ya 'daga wayar sa...batare da wani tunani ba kawai ya danna mata 'kira da wani layin sa da ya tabbatar bata shi. Daf da 'kiran zai yanke sannan ta 'daga tare da fa'din " Hello". Cikin sanyi..cuz duk yanzu Husnah tayi sanyi kamar ba ita ba. Yah Deen kuwa shiru yayi bai ce komai ba illah murmushin mugunta da yake saki daga 'dayan 6angaren.." Hello"!! Ta sake fa'di akaro na biyu tana yatsina fuska amma still shiru bai amsa ba. 'Dan 'karamin tsaki taja da niyyar yanke 'kiran dan ganin kamar ba'a da alamun furta komai  wanda jin zata yanke wayar yasa Yah Deen saurin ambatan sunan ta cikin muryar da ya san zai sanyatar mata da zuciya. Ai kuwa cak ta fasa abinda tayi niyyar yi zuciyar ta take ya fara dokawa abinku da zafin 'kauna...sai dai bata iya ta ce da shi ko 'kala ba. Cikin wata mayaudariyar muryar ya sake fa'din" Husnah ashe kin dawo shine kika 'ki neme ni ko?..Husnah har haka na zama a wurin ki ban sani ba?" " Meyasa sai ka sani to?" Tayi 'karfin halin furta hakan. Sai yace" Haba Husna..." Saurin tarar sa tayi da fa'din" Malam matsayin matar aure nake yanzu...." " Na sani Husnah bacsai kin tuna min ba.." " So ka fita hanya ta please ka daina damuna.." " Husnah ni ne fa? ko kin manta badan wani 'dan dalili ba da nine mijin naki a yanzu.." Cike da takaici ta cire wayar a kunnan ta tana jan tsaki. Yah Deen kam da murmushi yabi wayar sa dake ri'ke a hannun sa jin yanda ta yanke masa 'kirara a zafafe...shi kansa yasan ya cancanci fiye da haka daga gareta saboda sam bai mata adalci ba a rayuwar ta. Sam maganar auren dake kantan bai dame shi ba dan yasan shi ka'dai take so, shiyasa ma shai'dan ke 'kara ingiza shi akanta yana sake tunzura zuciyar sa akan sake mallakar jikinta cikin ko wani irin hali. Text ya rubuta ya tura mata _"..Ina fatan baki manta abinda yafaru a Azare ba.."_ Yayi zaman kusan mintina ashirin da uku yana jiran reply amma har a lokacin shiru baiga komai ba. Yanzu kam yasan Husnah gagarumin fushi tayi da shi tunda har ta iya masa wannan wulan'kncin. Cikin ransa ya ayyana zai share ta tukunna na kwana biyu yagani..sai dai me? Kafin cikar mintina talatin sai ga text 'din Husnah ya ratso cikin wayar sa, wanda da ganin hakan ya saki murmushi a fili ya furta" ai nasan hali..yarinya indai zaki kulani ko yayane ai shikenan..". Text 'din ya bu'de ya karanta abinda ta turo _" Me yasa zan manta abinda ya faru ai ba ma su da dalilin mantuwa, 'kyamar da ka nuna min zan manta ko kuwa yaudara da muguntar da ka shirya min?"_ Take shima ya rubuta amsa kamar haka.." _Please pick my call Husnah_ ". Ya tura mata haka ya sake dialling numbern ta. Kamar bazata 'dauka ba amma sai gashi ta 'dauki 'kiran daf da zai yanke. Shiru tayi yayin da Yah Deen ya cigaba da fa'din " Kina jina ko...Husnah wannan duk sun faru a can baya ne, amma daga baya da kaina naga rashin kyautawa ta,  lokacin da na gama saka saka rai na sakankance zan mallake ki kuma a dai-dai lokacin mahaifan ki suka yi betraying iyaye na...nasan kin san komai so ba sai sake gaya miki ba....Husnah hankali na ya tashi sosai da naji labarin auren ki da wani daban ba ni ba ban san cewa kece zuciya ta ba sai a lokacin da naga alamun rasa ki zanyi,  amma is too late dole na 'dau dangana tunda an riga an aura masa ke, nayi tunanin zaki 'kira ni kimin bayani da kanki amma ke ma sai naji ki shiru..bazan iya misalta miki halin da na shiga sanadin hakan ba..all I can say is nayi takaicin rasa ki..please ki sassauta min Husnah.. " " Ni babu wani sassauci da ya rage tsakani na da kai cuz matar aure nake yanzu so ka fita hanya ta, ko ka manta cewa da bakin ka ka sanar dani baka 'kaunar aure tsakanina da kai, ka 'kira ni da dattin bola Mu'een da bakin ka, cikin hankalin ka ka nuna min tsana ta zahiri to dan Allah ya musanya min kai da wani kuma me yasa zan damu har ince zan 'kira ka in ma bayani...?" " Husnah..!" " Ni dai please ka fita hanya ta..kar ka sake 'kira na" Tanacgama fa'din hakan ta yanke 'kiran tana tsiyayar da hawaye...ta san har abada bazata ta6a daina son Mu'een ba, amma yaza tayi dole ta 'dauki hakan matsayin kaddarar rayuwar ta. Ta so ace da kanta cire shi a ranta musamman saboda ba'kin halin da ya nuna mata, amma ga dukkan alamu hakan ba me yiyuwa bane still zuciyar ta na nan tarecda shi...fatan ta kawai shine Allah ubangiji ya bata ha'kurin zama da mijinta. 'Bangaren Yah Deen kuwa sam bai wani damu ba...ya riga ya 'kudura cikin ransa cewa zai dawo da Husnah cikin rayuwar sa kuma sai hakan ya faru. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *56* 'Bangaren Yah Deen kuwa sam bai wani damu ba...ya riga ya 'kudura cikin ransa cewa zai dawo da Husnah cikin rayuwar sa kuma sai hakan ya faru no matter what. Haka suka cigaba da rayuwa bai sake 'kiran layin ta ba kuma ko cikin school ma ba kullum suke ha'duwa ba saboda 6angare daban-daban suke..duk kuwa ranar da ha'duwar su ta kasance yakan bi tane da idanu kawai fuskar sa 'dauke da yalwataccen murmushi, musamman idan yaga irin shigar da tayi...cuz yanzu Husnah babban mayafi take sawa harda safa a'kafafun ta, wanda duk hakan ya kasance ne cikin dokar da Hisham ya gindaya mata, sai kuma akayi sa'a itama shigar ta kwanta mata sosai take jin da'din sa dan haka kuwa ba tare da damuwar komai take 'ko'karin bin umarnin sa duk da basa tare. Bata ta6a tunanin komawa rayuwa da Mu'een ba tunda tayi aure...har wasu lokutan ma da kanta take ganin tsabar wautar da ta tafka abaya na biye masa suka ta aikata son ransu. A kullum soyayyar sa na ma'kale da zuciyar ta amma tayi 'ko'kari sosai wajen ganin ta danne hakan, shiyasa ma ko sun ha'du cikin school bata yi masa kallo sau biyu, sau tari ma ta kan ga kamar ha'duwar tasu shiryayya ce kawai dan ya ringa bayyanar da kansa gare ta a lokutan da bata zato saboda kawai ya ringa tunatar da ita wanzuwar sa cewa still yana nan karta manta. Ko 6angaren shi Mu'een 'din ma kuwa bai ta6a gigin sanar da su Ishaq cewa yana so ya dawo da Husnah cikin  rayuwar sa ba, ya bar hakan ne kawai cikin ransa dan gudun mitar Ishaq kuma yasan matu'kar Ishaq yasan hakan birki zai taka masa...ba zai barshi ba. A kullum tunanin sa bai wuce taya zai sake mallakar ta ba..duk wani hanya da yayi tunanin zai 6ulle masa sai kuma yaga abin ba haka ba saboda Husnah duk ta canza yanzu kamar ba ita ba...kwata-kwata ta 'dauke masa wuta, bai ta6a tunanin Husnah zata iya yi guje masa cikin lokaci 'kan'kani haka ba...shiyasa sau da dama ya kan tsinci kansa dumu-dumu da jin haushin mijin da ke auren ta a yanzu dan yasan shine sanadin rabuwar su....(ni kwa nace ka manta Addu'ahr da ka ringa yi abaya kenan?) Kwatsam ranar yana gida dawowar sa kenan daga lecture sai yaji 'karan wayar sa, ko da ya 'daga sai yaga sunan Ishaq na yawo kan fuskar wayar, batare da damuwar komai ba ya 'daga nan Ishaq ke tambayar sa wai ko yana gida ya bashi amsa da" erh yana nan". A takaice. " Gamu nan zuwa to yanzu". Fa'din Ishaq daga 'daya 6angaren. Mu'een sai yace " Kun fasa fitan ne kuma?" " Ah no bamu fasa ba... ai ba zama zanyi ba yanzu zan koma". " Ok sai kazo to". Da haka suka yi sallama kowa ya ajiye wayar sannan ya ci gaba da abinda yake yi ba tare ya ko yi tunanin me ze kawo Ishaq wurin sa a dai-dai wannan lokacin ba tunda yasan basu da'de da rabuwa ba kuma kafin rabuwar su bai sanar da shi cewa zai zo ba. Yana zaune a wurin yaji sallamar Ishaq daga bakin parlourn sa sai ya amsa a hankali tamkar bai son yin magana kamar yadda ya saba yin komin sa cikin ra'ayi. Ishaq ne ya fara shigowa kamar daga sama sai ga Husnah a bayan sa ta sha Hijabin ta ash colour wanda yake babba har 'kasa ya kuwa yi mata kyau ta fito shar abinta gwanin birgewa. Kallo 'daya tayi masa ta 'dauke idanun ta daga kansa...kishingi'de yake har yanzun bai motsa ba sai ma yayi kamar ganin su taren bai sa yaji wani abu makamancin mamaki ba. Ishaq ne ya zauna daga gefen sa tare da bashi hannu sannan a takaice yayi mai bayanin abinda ya kawo su cewar Husnah ce ta same shi da batun ya rako ta zata 'dauki wasu kayayyaki agidan shiyasa ya rakota amma shi yanzu haka ma ana jiran sa zai koma...bai kai ga rufe bakin sa bama wayar sa ta fara ringing sai ya mi'ke tsaye yana ciro wayar daga aljihun sa yake fa'din ai basu san nan na taho ba. Saurin 'kara wayar yayi a kunnan sa yana fa'din" Gani nan tahowa yanzu Anas..". Hanyar fita daga parlourn ya tunkara yana sake fa'din" Sai mun dawo...Husnah feel free ki yi abinda ya kawo ki kinji?". " Ok Nagode Ishaq". Ta fa'di a hankali da sanyin murya. Ba haka ta so ba sam, ta so ne ace da ya rako tan ya tsaya idan ta 'dauki abinda zata 'dauka sai su koma tare saboda sam bata 'kaunar ta ke6ance da Mu'een koda wasa. Bai ko kalli inda take ba har yanzun sai ya 'dauke jansa yayi kamar bai san da tsayuwar ta a wurin ba, wanda hakan yasa itama bata kalle shi ba ta nufi hanyar 'dakin ta dake gidan nasa tana fa'din" Barka da gida Mu'een...ya studies?" Ko 'kala bai ce da ita ba illah 'daga kai da yayi ya kalle ta ka'dan take ya sake maida idanun sa ya cigaba da abinda yake yi. Duk da bai amsa mata gaisuwar da tayi masa ba amma bata damu ba fatan ma shine ya kasance shirun a wurin  har ta kammala kwasan kayan ta ta koma inda ta fito. Taso ta 'dauko wata 'kawar ta su taho tare amma sai tayi tunanin yin hakan tamkar ta tona sirrin ta ne na baya wanda take tunanin ba kowa yasan shi, ba kowa yasan cewa gidan sa take zama ba...shiyasa ta nemi Ishaq tunda shi yasan komai, kuma sarai tasan halin sa bashi da tashin hankali ko neman magana. Ba dan ya zama dole bama da babu abinda zai sake kawota gidan sa balle su ha'du sai dai hakan bai yiyuba saboda waccen tafiyan da tayin cikin rashin shiri tayi sa, duk wasu muhimman abubuwan ta na nan gidan nasa, taso ta bar su ma amma hakan ba zai yiyu ba...dan hatta system 'dinta agidan yake da sauran tarin littatafan karatun ta,  ayanzu kuwa matu'kar bu'kace take da su cuz semester ta ja sosai. Cikin sa'a kuwa a bu'de ta tarar da 'kofan ba'a saka key ba tana mur'dawa sai ya bu'du, 'kasan zuciyar ta ta saki hamdala dan dama bata 'kaunar zuwa kansa ta tambaye shi wani abin sam. Tana shiga ta sake maida 'kofar ta rufe sannan ta cire hijab 'din kanta ta ajiye shi, cikin sauri-sauri ta fara ha'da kayayyakin da tasan zasu mata amfani, bata tsaya shirmen komai ba tayi abinda ya kawo ta dan kar ta 'dauki lokaci, daf da zata kammala ha'da kayan wayar ta ta 'dauki 'kara wanda tana dubawa taga sunan Hisham na yawo kan fuskar wayar. 'Dauka tayi tare da sallama ya amsa sannan ta gaishe shi, tambayar ta yayi ko har ta fito daga lectures 'din tace " Erh ta fito har ta dawo gida tana aiki ma". " Aikin me?" Ya tambaye ta Sai tace " A kitchen ne". Yace" Abinci kenan?" 'Kasan ma'koshi ta amsa da " Umm". Sai yace" To ayi aiki lafiya 'yan mata anjima zan 'kira ki kinji?" Da" Toh". Ta amsa cikin sanyi. Tana cire wayar daga kunnanta sai suka yi ido hu'du da Yah Deen dake tsaye ri'ke da 'kofa amma bai 'karasa shigowa ba. Take sai taji wani iri fargaba mai tsanani ya shige ta, sarai tasan halin Mu'een bashi da da'di ta kuma san salon muguntar sa shiyasa take matu'kar tsoron ha'duwa da shi balle har su ke6ance, tun bayan auren ta ta yiwa kanta al'kawarin tsare mutuncin ta. Ai kuwa suna ha'da idanu da shi sai ya bar bakin 'kofar a hankali ya 'karaso ciki tare da maida 'kofar ya rufe fuskar sa 'dauke da murmushi. Nesa ka'dan da ita ya tsaya tare da cusa hannun sa 'daya cikin aljihun wandon jeans dake jikin sa yana kallon fuskar ta yace" Me yasa ki kai masa 'karya?" Bata tanka shi ba kawai ta tafi ga mayafin ta ta 'dauka da niyyar sanyawa amma sai taji ya fisge daga hannun ta ya rataya shi saman shouldern sa sannan cike da gadara ya sake fa'din" Tambayar ki nake yi baki bani amsa ba". Husnah kam hankalin ta sosai ya fara tashi, dan haka tuni jikin ta yayi sanyi...a hankali ta bashi amsa da fa'din" Waya ta bata da ala'ka da kai Mu'een so please respect ur self". Murmushi ya saki yana mai sake binta da idanu " Hus...nah". Ya ja sunan ta tare da 'dan matsawa kusa da ita...da sauri ta matsa baya...tana ha'de gira cike da 6acin rai. " Husnah kin raina ni...yanzu dan zaki zo inda nake shine sai kin nemo wani ya rako ki? cinye ki zanyi ne ko me?...Husnah gaskiya kin 6ata raina...ni ne fa ba wani ba me yasa 'karara zaki nuna min irin wannan 'kyamar?" Tace" Darajar aure na nake karewa". " I see...yanzu ina auren to?..tunanin ki zan iya ha'kura dake ne?" " Ni dai Please kayi ha'kuri badan hali na ba". Tayi maganar da muryar kuka...ita harga Allah yanzun tsoro yake bata ma, mutun tamkar ba'a ta6a 'diga masa ruwan imani a zuci ba. Baya ta sake yi ta koma gefe tana mai tsiyayar da hawayen takaici. Bai damu ba ya cigaba da binta har takai bango wanda ya sanya dole ta tsaya cak da 'dan 'karfi tace" Wai meke damun ka ne Mu'een da aure fa akaina". " Nasani ai, amma ai kin lura ba ni ne na biki ba kece kika biyo ni gida na so miye laifi na dan na more ki? Wannan abinda ya saki tahowa har muhalli na shi ka'dai zan cire miki and nothing else". Kuka ta sanya mai zuciya ji take da ace akwai wani abin kusa da ita da babu abinda zai hana ta maka mai aka ko dan ta samu ta tsira da mutuncin ta...amma yanzu da ya kasance babu komai so itama bata da coice than ta ro'ke shi ya bar ta, tasan duk abinda ya fa'di gaskiyar sa ne, itace ta zo koma me yafaru kuma laifin ta za'a gani ba nasa ba...hannun ta 'daga duka biyu ta ha'de su wuri guda idanun ta cike da hawaye ta fara ro'kon sa akan dan Allah yayi ha'kuri ya bar ta ta tafi tayi masa al'kawarin bazata sake zuwa masa gida ba, ya taimake yaji 'kan igiyar auren dake kanta". Shiru yayi bai ce da ita 'kala ba idan ka gansa a lokacin zaka yi tunanin ko maganar da tayin ta shiga kansa ne, hakan yasa itama bata sake magana ba kawai ta cigaba da rera kukan ta gwanin tausayi. Tsawon mintina shida suna a haka har ta daina kukan tayi shiru duk ta sake rai cewa ya ha'kura zai barta ta tafi ganin yanda ya tsaya shiru sai dai me tmkar wani 'kanin fir'auna bu'dan bakin sa sai cewa yayi"..saboda kin samu wani banzan shine ni kike shirin guje min ko Husnah?" Shiru tayi masa bata bashi amsa ba ganin yanda yayi mata katanga...tsoro duk ya bi ya sake cika mata zuciya. Zai sake magana tayi saurin taran sa da fa'din " Dan Allah Mu'een kayi ha'kuri kasan fa yanzu ala'kata da kai haramcin ta yafi muni fiye da baya". " Me kike nufi kenan Husnah?" Yayi maganar yana me 'ko'karin ha'da jikin sa da nata. Surin gocewa tayi tana fa'din" Let me go please Mu'een kai wani irin mutun ne dan Allah?". Murmushi yayi da jin abinda ta fa'di wai shi wani irin mutun ne.. " Husnah so kike kisan ni 'din wani iri ne?...ni mayen ki ne kawai..kuma da kike so in barki ki tafin ya kike so inyi da tarin 'kaunar ki da ke cike a zuciya ta Husnah?" Da muryar kuka tace tace" 'Karya kake yi wallahi baka 'kauna ta ko ka'dan..." Inda ta 'karashe maganar hawaye na gangaro mata. Cikin nuna rashin damuwa da kukan da take yi yace" Ki bari in gwada miki zaki fahimta..." Tunkan ma ya rufe bakin sa tace" Ban so..ni ka 'kyale ni..Allah yayi min tsari da kai mayaudari, azzalimi wallahi har abada bazan ta6a yafe maka ba...". " Really?" Ya fa'di yana zare idanu cuz sosai ransa ya 6aci da zagin da tai masa idanun sa har canza kala suka fara...bata kula shi ba ta cigaba da kukan ta duk da kuwa ta fahimci ransa ya 6aci sosai da ita...Hijabin ta dake hannun sa yayi jifa da shi gefe sannan ya sake tunkarar gaban ta, yatsa ya 'dago ya nuno ta da shi da jajayen idanun sa cike da 6acin rai ya furta" In dai har haka kika ce Husnah nima bazan ta6a fasa abinda nayi niyya ba tunda cewa kika yi har abada bazaki yafe min ba...kuma ki sani daga yau duk lokacin da na bu'kaci ganin ki u must come to me dolen ki, kuma bazan kar6i excuse ba, in bahaka ba kuwa zan baki mamaki..." A firgice ta 'daga kai ta kalle shi da mamaki idanun ta na tsiyayar da hawaye tace" Mu'een da auren nawa kake fa'din haka?". A tsawace ya bata amsa da " To hell with ur auren...ko ma uban wa kike aure i don't bloody care ni dai na gaya miki.." 'Kasa tayi da gwiwar ta tare da sau'kar da murya take ro'kon sa hannayen ta biyu ta 'dago " Kayi ha'kuri wallahi na yafe maka komai dan Allah kar ka tozarta min aure Mu'een". " Ki ri'ke yafiyar ki ban so...kuma ki sani duk lokacin da kika yi kuskuren yi min taurin kai wallahi ki tabbatar labarin rayuwar ki na nan Jigawa zai isa ga mahaifan ki da mijin da kike tutiyan auren sa akakin duk cikin sa'o'i 'kalilan kin san zan iya ko?". Hannu tasa aka ta rusa kuka tamkar ance da ita mahaifiyar ta ta rasu ne a dai-dai lokacin. Tayi danasanin ha'da ala'ka da Mu'een yafi sau 'dari abaya lokacin da ya nuna mata 'kyama bayan tasowar maganar auren su but na yau 'din tana jin nadamar da take yi tamkar bazata sake yin irirn sa ba har abada....bata san Mu'een bashi da ko 'digon imani cikin zuciyar sa ba sai yau...kuka ta sha son ranta wanda sam shi hakan bai dame shi ba...duk yadda ta so ta hana shi aikata abinda ya yi niyya kasa wa tayi yayin da ya ringa yi mata komai cike da rashin imani da mugunta. Husnah kam ita da kanta sai taji ta sani kanta ta tsani rayuwar ta, tayi Allah wadai da rayuwar ta gaba 'daya, bata san me zuwa Jigawa ya 'kare ta da shi ba face ba'kin ciki da takaici. Bazata manta ranar da Hisham ya fara kusantar ta ba kafin tafiyar sa...duk da ba laifi ta 'dan yi amfani da wasu abubuwa na gyaran jiki amma duk da haka bai hana Hisham fahimtar cewa ba cikakkiya ya aura ba...Hisham mutum ne mai nagarta da sanin ya kamata, shiyasa bai wani nuna mata rashin jin da'din sa afili ba, duk wani abinda ya dace da yayi mata a lokacin sai da yayi har tana tunanin ko bai gane bane. Amma daga baya cikin natsuwa sai yake tambayar ta abinda ya faru da ita da yasa ta rasa pride 'din ta. Nan take tayi masa musu ta nuna masa ita ba abinda ya ta6a faruwa da ita...sannan in ba shi ba babu wanda ya ta6a kasantar ta, a zahiri ita kanta tasan ba gaskiya ta fa'da masa ba wanda tunanin ta wai kar idan yasan gaskiyar ya tozarta ta shiyasa ta 6oye masa. Bawan Allah Hisham kam ganin yanda ta dage ne yasa take ya amince da batun ta kuma bai sake tada zancen ba. Shiyasa tayi al'kawarin kame kanta ta ri'ki mijinta tayi masa biyayya sakamakon rufin asirin da yayi mata. To yau idan akace labarin ala'kar ta da Mu'een ya isa kunnen sa da wani idanu zata dube shi? Sannan mummyn ta ma wani irin kallo zatayi mata?" Tana hawaye ta koma gida da kayan ta cikin jaka, hatta 'dan sahun da ya 'dauko yakan waiga ya kallo ta lokaci zuwa lokaci ganin yanda take ta share hawaye. Ko wanka ba ta tsaya tayi a gidan sa ba sai da ta koma gidan ta kafin tayi shi idan ka ganta duk ta fita hayyacin ta, da 'kyar ta samu hawayen ta tsaya amma haushi da ciwon abinda Mu'een yayi mata bai bar zuciyar ta da wuri ba. Da dare da Hisham ya 'kira ta ya so ya fahimci yanayin da take ciki daga muryar ta saboda ya ji ta duk tayi sanyi sarai ya fahimci akwai abinda ke daminta, amma sai ta ce da shi ba komai...ita kawai garin ne ya isheta tace makarantar ma ta gaji da shi gida zata koma ita kam. Lalla6an ta ya ringa yi akan ta daure ta 'karasar tunda watanni 'kalilan ne suka rage musu ai kamar yau ne...bata san me zata ce da shi da zai sa shi aminta da 'kudurin ta ba indai ba kanta zata tonawa asiri ba, hakan yasa dole ta ha'kuran kamar yadda ya bu'kata sai dai tasan rayuwar da zatayi a Jigawa yanzu zai kasance ne mafi muni daga cikin rayuwar ta na duniya, bata jin zata sake yin farin ciki kuma matu'kar ta kasance cikin garin Dutse tare da Mu'een. Husnah har 'yar rama tayi saboda damuwa...sai dai cikin sa'a Mu'een bai sake tuntu6ar ta da batun ba kusan kwanaki goma sha 'daya da zuwan ta gidan sa, wanda cikin hakan har Hisham ya zo yayi weekend wurin ta ya koma Abuja. Kaf Mu'een ya san da zuwan Hisham shiyasa ma ya share ta..cuz barazana kawai yai mata dan tana bashi ha'din kai idan ya bu'kaci ganin ta bawai dan yana da niyyar tona ta dagaske ba. Ko zuwan Hisham daya ga halin da take ciki ma hankalin sa ta shi yayi sosai wanda yayi-yayi ta sanar da shi damuwar ta amma ta'kiya sai dai tace ita garin ne kawai ya ishe ta da kuma zaman ka'daici. Al'kawari yai mata akan zai sa abincika mata  yarinya da zata na taya ta zama da kuma wasu ayyukan...bata 'ki ba ta amince cuz ita kanta zata so hakan ko babu komai zasu zauna suyi hira zata rage mata tunani. Sati biyu cif da zuwan ta gidan sa amma basu sake ha'duwa da shi ba, har ta 'dan fara sakin ranta kwatsam ranar wata talata sai ta ga text 'din sa cikin wayar ta. " _Ina jiran ki by 4pm_ ". Innalillahi ta ringa maimaitawa sannan da rawar jiki ta tura masa " _Ina da lectures_ ". Sai yacturo mata reply da " _'karya kike yi...ni dai ina jiran ki_ ". Tun daga gidan tan ta fara share hawaye na ba'kin ciki, haka tana ji tana gani ta shirya ta fita, ni'kab ta sanya ta rufe fuskar ta dashi ita ka'dai tasan ciwon da wannan lamari take yi mata...ganin da auren ta amma Mu'een na so ya lalata mata shi ya na janta izuwa ga mummunar halakar da bazata 6ulle musu ba. A parlourn sa ta same shi yana kishingi'de kamar ba shi ba...da ganin ta sai ya fara murmushin mugunta...kai ta kawar gefe sannan tace da shi" Kai baka tsoron Allah ko Mu'een?" Yace " Idan koyawa mutun akeyi sai ki koya min tunda ke 'din na lura gwana ce ta wannan fannin". Yanda yayi maganar da izza ya sanya ta dole ta sau'kar da muryar ta cuz ta fahimci shi 'din yayi nisa sosai. Da sanyin murya tace" Nifa indai akan batun yafiya ne wallahi na yafe maka har abada dan Allah ka barni in zauna da mijina lafiya" Ido ya tsura mata kawai yana kallon ta..wato auren bazata da akayi matan yafiye mata shi da suka da'de suna tare. Baki ya ta6e yana shafa cikin sa yace" Ni dai yanzu yunwa nake ji..sama min wani abu please ". Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *57* Bata ce da shi 'kala ba kamar zatayi kuka ta juya ta nufi kitchen 'din sa dake gidan, sharp-sharp tayi masa jallop na cous-cous da yaji attaruhu sai 'kamshi ke tashi...a hakan ma bata samu vegetables a fridge 'din sa ba shiyasa tayi masa a hakan. Gaban sa ta kai abincin ta ajiye, har a lokacin kuwa sanye take da hijab 'din ta bata yi gigin cire shi ba. Tana ajiyewa ya tashi ya mi'ke tsaye da kansa ya 'dauko ruwan gora da cup sannan ya dawo ya zauna ko inda take bai sake kalla ba. Bata zauna ba haka shima bai ce da ita ta zauna ba, tana tsaye har ya 'kare cin abincin ya kora ruwa...'dayan plate 'din ya 'daga yana rufe guntun abincin da shi yace " Zaki iya tafiya". Wani sanyin da'di da Husnah ta ji ya sau'ko mata har sai da yasa ta saki ajiyan numfashi a fili. Da sauri ta nufi hanyar fita dan ma kar yace ya fasa shiyasa bata wani 6ata lokaci ba...sai hamdala take da abun ya tsaya iya girki duk da hakan 'din ma tasan ba dai-dai bane amma ya zatayi...abin is complicated to her bata san hanyar 6ullewa ba tako ina ba sau'ki. Haka ta cigaba da rayuwa a kullun Allah take mi'kawa kukan ta akan ya yi mata katanga da sharrin Mu'een...duk da tana tsananin son shi har yanzun amma darajar auren ta yafiye mata komai. Cikin sa'a bai kuma neman ta ba har aka 'kara cin wasu kwanaki, wanda zuwa lokacin har an kawo mata yarinya mai tayata zaman 'yar matashiya mai suna Dija, yarinyar nada nutsuwa kuma tana 'debe mata kewa sosai, ga ta da aiki bata san jiki, ga girmama ta da take yi tamkar 'kanwar ta..hakan ne yasa hankalin ta ya kwanta yanzu sosai. *****     A can Shuwarin kuwa Ammi sosai take bani kulawa, tana jana a jiki da maganganu inda har take shan cikina cikin dubara dan taji ko ina kula wasu samari awaje, ban ma san manufar ta ba amma da yake ba kowa 'din nake kulawa ba shiyasa ban 6oye mata ba. Sosai yanzu ta ri'ke min wuta da shiga kitchen kula da tsafta ta duk da dama can ina da ita amma yanzu Ammi komai na sake yimin gyara take yi akan sa ni kam duk ban ta6a kawo komai cikin raina ba. Ko jiya ma da nace zanje in dubo Ma'u dan bata lafiya Ammi hana ni zuwa tayi tace in bari ba yanzu ba bata son in cika yawo sosai...tace kawai inyi mata addu'ah. ***** 'Bangaren Ma'u kuwa tun cikar sati uku da ha'duwar su da Yah Deen abubuwa suka fara canza mata, ga damuwar yaudaran da yayi mata ga kuma wasu 'yan canze-canze da take jin jikin ta ciki. Sai tana jin 'kananun zazza6i da ke tashi mata lokaci zuwa lokaci. Babu wanda ya damu da zazza6in nata dayake ba kwantar da ita yayi ba amma kafin sati biyu sai abin ya 'karu ta fara jin bakin ta na tara yawu akai-akai ga kasala da ke yawan damun ta. Matar Baban ta ce ta fara mitar hakan dan ko 'dan wanke-wanke da take yi mata ma yanzu da 'kyar take yin sa. Ga wankin kayan ta nan ma duk ta tara su amma takasa wankewa. Ko a school mun fara jarabawa amma banda Ma'u cuz ko taje makarantar bata iya yin komai shiyasa ma ta daina zuwa. Wata biyu ba sati 'daya kenan yanzu da ha'duwar su da Yah Deen, abin nata kuwa sai abinda yayi gaba, mahaifin ta da jansa ya 'dauke ta ya kai ta Chemist dan aduba ta tunda jikin nata ya'ki da'di da tunanin typhoid ke damun ta da yake yaga sai 'karewa take yi wuri guda. Mai Chemist kam ko daya ganta da yanayin ta kawai sai ya bata su paracetamol sannan ya 'debi jini da fitsarin ta yace za'a kai gwaji a cikin Azare. Ku'din da duk za'a bu'kata ya gaya wa mahaifin ta take kuwa Malam Barau ya ciro ya biya sannan suka koma gida da sunan jibi zai dawo ya kar6i result 'din test 'din nata. Ranar ne ya kasance ranar 'kunci da damuwar ga mahaifin Ma'u dan tashin farko likita ya fito fili ya bayyana wa MALAM BARAU cewa 'yar sa Asma'u na 'dauke da juna na tsawon wata biyu. Kusan mutuwar tsaye Malam Barau yayi saboda tashin hankali, gashi ko da yaje gida da labarin ma step mothern Ma'u bata kwantar masa da hankali ba sai ma masifar da ta haushi da shi wai maganin su kenan ai tunda yace sai tayi makarantar boko ai  sakamakon su kenan. Ma'u kuwa kamar ranta zai fita haka taji...wai ita ce ke 'dauke da ciki ajikin ta..tayi kuka fili da zuci. Duk ta rame tayi fayau da ita..saboda ko abinci ma ba iya ci take yi ba da taci yake dawowa. Duk abin nan dake faruwa Ammi bata bar ni naje dubo Ma'u ba...har ma zuwa yanzun na gaji da tambayar na ha'kura. Mahaifin Ma'u bai iya yayi magana da Ma'u ba saboda takaici, matar sa ce ma cikin 'kananun maganganunta har ta tuna masa batun sanin mamallakin cikin wanda shima sai a lokacin hakan yazo ransa. Tun ranar da ya shigo da result na test 'din abinda kawai ya iya ce da Ma'u shine" Baki kyauta min ba Ma'u". Cikin tsananin rashin walwala ya fa'di mata hakan tare da wulla mata takardar gwajin har yau bai 'kara ce da ita komai ba, ita kam ma nawin ahalin gidan ya hanata sakat bata ko iya fitowa ta zauna tare da su..ga shi shirun da mahaifin ta yayi matan sai ya 'kara tada mata hankali, abubuwan duk sun taru sun yi mata yawa. Sai yanzun ne Malan Barau ya iya tashi ya shiga har cikin 'dakin da Ma'u take inda ya same ta du'kun'kune cikin hijabi kamar mai bacci...jin motsin shigowar shi ne ya sa ta yun'kura ta tashi ta zauna amma sam ta kasa ha'da idanu da shi.. yana daga tsaye ta gaishe shi kanta 'kasa inda ya amsa mata babu yabo ba fallasa shima 'din ji yake kamar ya zubar da hawaye idan ya ganta, Ma'u banda hawaye babu abinda ke motsi a jikin ta su ka'dai ke gudu wani na bin wani. " Ban ta6a tunanin zaki bani kunya ba Ma'u, nayi 'ko'kari sosai wurin ganin na bawa rayuwar ki kariya bansani ba ashe shirme na nake yi..." Cikin kuka tayi saurin  taran sa da fa'din" Baba dan Allah kayi ha'kuri ka yafe min wallahi ba hali na bane..." Yanda tayi maganar da yanda take kuka ya sashi juyawa kawai ya bar 'dakin saboda tausayin ta da ya sake tsarga masa a zuci, abin ma da ya kawo shi bai iya ya tambaye ta ba. Yana fita Innar su ta tare shi da fa'din" Waye mamallakin cikin ta gaya maka?" " Bansani ba nima". Ya bata amsa atakaice. Bata 'kara sauraron sa ba kawai ta fa'da 'dakin da Ma'u take kamar wata zararra, kan Ma'u na 'kasa tana faman share hawaye da sheshshe'ka kawai taji muryar innar tasu kamar daga sama tana fa'din" Munafurcin banza da wofi...da kika je kika yo cikin baki san cewa abin kunya kika yo bane sai yanzu da ya bayyana kansa?...kuma da kike ta faman nu'ku-nu'ku da cikin idan anbarki da shi zaki zama uwa da ubansa ne...in ba munafurci ba ai kinsan wanda ya 'dirka miki cikin da bazaki fa'da ba har sai kin sa zuciyar ubanki ta buga saboda ba'kin ciki ko?...to bari kiji tun wuri ki bu'di baki ki fa'di wanda yayi miki in ba haka ba wallahi su Salele zansa suyi miki dukan mutuwa agidan nan tun da baki da amfani...shashasha kawai wacce bata san ciwon kanta ba.." 'Dagowa tayi ta kalli Innar dan sanyin murya tace " Inna dan Allah kiyi ha'kuri wallahi zan fa'di". Kunne Innan ta juya mata tare da furta" Uhum ina jin ki". Sai da ta share haware kafin ta furta " Yah Deen ne". Inna kam ha'de goshi tayi tana ta6e baki ta ce " Waye kuma Ya Deen?" Ma'u kam 'kara yin 'kasa da kanta tayi tace" Deeni 'dan gidan Alhaji Tahir mai gidan gona". " Innalillahi wa inna ilaihi ra ji'un..." Innah ta saki salallami da 'karfin ta tana tafa hannuwa....daga 'karshe ta dire hannun saman bakin ta sannan tace" Yanzu Ma'u har can kika kai kanki saboda tsananin kwa'dayi?" Kuka Ma'u ta saki bata iya ta sake magana ba har Innar ta gama surutan ta ta fita. Tasan dama kowa yaji labarin zai yi zaton kwa'dayi ya kaita wurin sa...nan kuwa ba haka bane tsabar iya salo da yaudara suka nuna mata shi da abokin sa Imrana da sunan aure...alhalin tun ranar har yau bata 'kara ganin ko Imaranan bane ma ballantana uban gayyar. Take Inna taje ta samu Malam Barau ta sanar da shi mamallakin cikin kamqr yadda taji daga bakin Ma'u. Jikin sa sanyi 'kalau yayi, shi kansa ya bari ne akan kwa'dayi yaja Ma'u, haka ya yini yana tunanin abin cikin ransa, da yamma da zai fita sallar maghrib ne ya 'kira ta ya sake tambayar ta dan tabbatarwa nan kuwa tayi shiru bata musa masa ba..kai Malam Barau ya jijjiga sannan yasa kai ya fita zuciyar sa cike da tausayin halin da Ma'u ta sanya rayuwar ta ciki. Sai da ya idar da sallar maghrib kafin ya nufi unguwar mu gidan Alhaji Baba. Lokacin shima dawowar sa kenan daga sallahr maghrib yana zaune cikin gida yana shan iska Malam Barau yayi sallama. Duk da bai ta6a kawo masa ziyara ba amma Alhaji Baba yaso su shiga ciki sai dai Malam Barau ya 'kiya ya nuna ba komai nan 'din ma yayi, nan suka zauna cikin gidan dan aganin sa nan 'din zai fi sirri tunda suna ganin kowa. Bayan gaisuwa cikin natsuwa yayiwa Alhaji Baba bayanin abinda ke faruwa agidan sa da kuma sunan 'dan sa da ya fito cikin lamarin. Abu 'daya da Alhaji Baba bai ji da'din sa ba shine lalata musu yarinya da Yah Deen yayi, amma bayaga haka bai ji lamarin matsayin ba'ko agare shi ba cus ya jima da zargin Mu'een na aikata irin hakan tun ba yau ba. Ba 'karamin 6aci ransa yayi ba, iya 'kolouwar 6acin rai ranar sai da yajita dan har kasa magana yayi ko ya fara sai ya carke zuciyar na 'kullewa, daga 'karshe dole Malam Barau 'din ne ya dinga bashi ha'kuri yana kwantar masa da hankali ganin halin da ya shiga sannan yayi masa sallama ya tafi. Ya san in ba sharrin yara ba ai Alhaji Baba yafi 'karfin aje har gidan sa ayi masa titsiye akan irin wannan abin, mutun ne shi mai matu'kar mutunci sanin girma da kuma kwarjini. Har akayi sallar Isha'i Alhaji Baba bai sani ba, sosai ya fa'da duniyar tunani, halayyar Mu'een tsoro take bashi ayanzu...har a yanzun ma nawa yake da har ya za6awa kansa irin wannan rayuwar...kuma ma ya rasa 'yar wa zai lalata sai yarinyar Malam Barau dake suke cikin gari 'daya, da wani irin idanu yake so adube shi ne sam bai sani ba. Sai da 'karfe tara na dare  ta gota kafin ya iya tashi a wurin ya shiga ciki...alwala kawai ya iya 'daurawa ya gabatar da isha'i daga haka ya kishingi'da har gari ya waye yana istighfari ga mahalicci, bai san inda Mu'een ya samo wannan halayyar ba sam...bai kuma san ya zai yi da shi akan hakan ba da ya wuci Addu'ah...shiyasa ya mi'kawa Allah komai...da fatan ubangiji Allah ya shirye shi. Hankalin sa bai 'kara tashi ba sai da yaje gidan Malan Barau yaga Ma'u, cuz washegari da sassafe ya isa gidan. Ganin 'kan'kantar yarinyar sosai ya karya masa zuciya, ransa ya 'kara 6aci da Mu'een sosai....da yake ta 'dan rame kwana biyu idan ka ganta bazaka ta6a tunanin tafini shekaru ba. ..shiyasa ko Alhaji Baba ma tashin farko da ni ya 'kiyasta shekarun Ma'u. Cikin ransa ya 'kuduri aniyar ko Mu'een zai mutu kuwa idan har Allah ya sau'ke ta lafiya dolen sa sai ya aureta tunda shi ya lalata mata rayuwa..in ba hauka bama yarinya 'karama irin wannan me ze kai tunanin mutun kanta. A fili kuwa ha'kuri ya dinga bawa Malan Barau cuz jiya bai samu daman bashi ha'kuri ba...kafin ya tafi sai da ya ciro ku'di kimanin 20k ya dan'ka a hannun Ma'u da sunan ta kula da kanta dashi kafin aga yanda hali yayi. Bakuma wai yayi hakan bane saboda ya goyi bayan Mu'een akan cikin ba a a, kawai ba yadda zai yi ne tunda abinda ya faru ya riga ya faru bai kamata kuma a 'kara 'daga mata hankali da tozarci ba shiysa ko Malam Barau 'din ha'kuri Alhaji Baba ya dinga bashi akan Ma'un kan cewar kar su 'daga mata hankali, yasan da wahala abinya zama laifin ta. Shi kansa Alman Barau yayi wannan tunanin sai dai shi ya ajiye ne akan raina matsayin su da Yah Deeb yayi ne ya sashi lalata musu yarinya. Idan baka sani zaka yi zaton duk abinda Alhaji Baban ke yi bakomai bane face goyawa 'dansa baya bisa abinda ya aikata...sai dai da zaka bincika zuciyar sa shi ka'dai yasan abinda ya 6oye, shi ka'dai yasan 'kuncin da yake ciki...shi ka'dai yasan yanda ransa ya kai 'kololuwar 6aci da Mu'een kan lamarin. Malam Barau kamdamuwar ta 'dan ragu tunda Alhaji Baba bai goyi bayan 'dansa ba ya yi na'am da batun dama shi tsorin sa kenan kar ace basu kar6i cikin da be san inda zai sa ransa ba saboda ba'kin ciki. Ko Ammi Alhaji bai sanar da ita abinda ke faruwa ba ya bari kawai cikin zuciyar sa, haka bai yi magana da Mu'een akan lamarin ba haka ma Uncle Ja'far. Yah Deen na 'kiran sa suna gaisawa kusan kowacce safiya amma bai ta6a nuna masa alamun komai ba, gasiuwa kawai sukeyi kamar yanda suka saba a 'yan kwanakin, ba wannan zolaya da wasan tuni shiyasa ma ko da yaji yanayin Alhajin wani iri bai sa akan sa ba. A makarantar mu naji ana gulmar wai ai Ma'u tayi cikin shege ne shiyasa bata zuwa makaranta har akayi jarabawa bada ita ba, lokacin kuwa ana gobe za'a bamu hutu ne. Haka nazo na samu Ammi da maganar amma sai ta kwa6e ni da fa'din wai ita bata son gulma..in daina saka kaina cikin shirgin da bai shafe ni ba. Baki na naja nayi shiru ban 'kara tada maganar ba. Ranar hutu kuwa murna ni kaina murnar nake yi saboda ayau ba sai gobe ba su Saif zasu dawo gida...sosai nayi kewar su abin ba'a cewa komai. Ana tashi ko tsayuwa na fahimci abinda ke faruwa ban yi ba saboda murna yau zanga abokai kuma 'yan uwana. Ashe bayan tafiya ta akayi kwanba aka tafi gidan su Ma'u da sunan gaishe ta ashe tsabar gulma ce tsantsa ta kaisu. Daga ranar kuwa kuwa labari ya watsu ko'ina cikin gari cewa Ma'u tayi cikin shege da 'dan Alhaji. Maganar har kunnan Ummah ta sai da bata ce komai kan lamarin ba...ko ni banji a bakin ta ba...Addah ta Saudah ma da ta same ta maganar birki ta taka mata da fa'din ku dinga kyautata zato wa mutun". Dole Addah Saudah taja baki tayi shiru tunda bata ga fuska wurin Ummahn mu ba, sai dai abin ya dame ta sosai cikin zuciya musamman da yake tasan cewa matsayin matar sa nake a lokacin nice kawai ban sani ba. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *58* Mu kam muna ta murna da farin cikin ganin juna ni da su Saif ko fita bamuyi ba, Saif sun girma sun 'kara tsayi da fa'di kamar basu ba...ganin yanda nake 'ko'karin sakan jiki da sune ya sanya Ammi ta 'kira ni ta ja min kunne sosai akan.hakan...tace tsakani na dasu maganar baki ce kawai bata so taga ko hannu mun ha'da dasu saboda Allah ya haramta hakan tsakanin mu a yanzu tunda mun girma. Hakan kuwa akayi dan ko da wasa ban ta6a kuskuren tsallake maganar Ammi ba ina kulawa da komai tsakanina da su Saif...balle Zaid kam ma dama sama-sama muke da shi har yanzu. Duk mu da muke cikin gidan bamu ji labarin komai ba, gara nima ranar naji ana gulma akan Ma'un amma da Ammi ta kwa6e ni kan zancen shikenan ban kuma tada maganar ba haka kuma ban sa aka ba. Anty Zainab ma muna yawan gaisawa da ita, da yake ma already ta koma Taraba so sai a waya muke ha'duwa kawai. Kwatsam ranar sai ga waya daga mahaifi na da wata safiya, inda yake ro'kon Alhaji Baba da ya bari akai Hudah (ni) 'dakin mijina, bai fito fili ya fa'di dalilin sa na yanke wannan hukuncin ba amma duk da haka Alhaji Baba ya fahimci dalilin da ya sa shi fa'dar hakan cuz dama yasan lamarin ba zai ta6a 6oyuwa ba. Cikin kwantar da murya yace da Baban mu " Wai da ni cewa nayi idan yazo kawai ya sakam min ita tunda dama can bai san da maganar auren ba kaga shikenan...." Taran sa Baban mu yayi da fa'din" A a Alhaji kar ayi haka, abashi matar sa kawai rabuwar ai bata da wani amfani". Alhaji Baba zai sake magana sai Baban mu yayi saurin fa'din" Dan Allah Alhaji kar kace komai...kawai ni dai na ce abashi matar sa". Dole tasa Alhaji Baba yin shiru ganin cewa mutun dattijo irin Baban mu ke ro'kon sa akan 'dan wannan lamarin yasan abin ya girmama ne...duk da yasan kawai dauriya ce yayi har ya sa shi iya yanke hukuncin akai ni 'dakin mijina alhalin yasan 6oyayyar halayyar mijin nawa. Sai da ya zauna yayi nazari sosai akan hakan kafin for the first time tun bayyanar cikin Ma'u sai yau ya sami Ammi da maganar inda yayi mata bayani filla-filla harda abinda mahaifina ya fa'di. Ammi kam shiru tayi saboda tsabar mamaki, wai jin Mu'een 'din ta ke da wannan alhakin, sai dai bata jin zata iya barin 'yar ta zama tare da shi, tunda rayuwar da ya zabarwa kansa kenan sai yaje yayi tayi...ita bata san me zata ce da shi ba. Da yake ita ba shiga cikin jama'a take sosai ba dama da Ummah ta suka fi zumunci a kaf 'din garin , Ummah ta kuwa nasan koma menene zai faru bazata ta6a bu'dan baki tayi mata bayani ba...musamman ma da yake abin ya shafi 'dan ta ne na cikin ta. Ammi kam bata 6oyewa Alhaji Baba ba take ta bu'di bakivta bayyana masa cewa ita bazata ta6a yarinyar ta zama da shi ba tunda haka halin sa yake...wannan abin.kunya da me yayi kama, mutun haka kawai batare da an tambaya ko matsa shi bavya 'dau ki kyauyar yarinya sukutum ya basu auren ta amma sai gashi tun ba'aje ko'ina ba sakayyar da zai musu kenan...hawaye Ammi take tsiyayar wa tsabar takaicin halin Yah Deen...cikinvranta take tuno ranar da ya ta shirga mata 'karya akan case 'din sa da Alhaji Baba akan Husnah ashe ninke ta yayi abai-bai har ta yarda shi cewa ba komai ke tsakanin sa da ita ba...ga shicda Allah ya tashi kama shi sai yasa shi aikatawa a inda bai isa ya musanta ko 6oye abinda ya faru ba...tace wallahi yarinya ta tafi 'karfinvta zauna da mazinaci yake can ya nemi irin sa amma ba 'yata ba. Da 'kyar Alhaji Baba yata bata baki gami da convincing nata ta sau'ko bisa umarnin mahaifina yace baya so yaga kamar ko bai ji maganar sa bane shiyasa amma ko shi ba so yake yi ba da niyyar sa araba auren kawai amma bakomai su cigaba da addu'a kamar yadda Baban mu ma ya fa'da....zai bashi Hudah amma bisa shara'di..Ammi hawauen ta kasa tsayuwa yayi, takaicin halin Yah Deen take sosai, tarasa meyasa ya za6arwa kansa irin wannan rayuwar...ace tun a yanzun sa ya san ya bibiyi mata to gaba idan ya fi haka shekaru kuma bata san me zai aikata ba...fatan ta kawai shine Allah ubangiji ya shirya mata shi.  Babu wanda ya bi takan sa har a lokacin, Ammi.bata 'kira shi haka ma Alhaji Baba...Sai dai shi Mu'een ne kan 'kira Alhaji su gaisa dan Ammi kam ma yanzu ko 'daukan wayar sa bata yi...da farko abin na damun sa saboda be san dalilin hakan ba amma daga baya sai ya share da yake suna waya da Alhaji kuma bai ta6a sanar da shi cewa akwai matsala ba..hakan yasa a kullum sai dai ya bada sa'kon gaisuwa yace a gaida su...ga shi Imrana ma tuni yana Kano shiyasa ma bai san da labarin abinda ke faruwa cikin garin nasu ba. ***** Cikin Ma'u nada wata uku sannan Yah Deen suka dawo hutu wanda yazo da tsananin son ganin mahaifiyar sa dan ba 'karamin kewar ta yayi ba...amma cikin rashin sa'a ko da yaje sam Ammi bata wani nuna alamun jin da'din ganin sa kamar yadda ta saba ba. Ko gaisuwa ma da yayi mata bata amsa ba sai ma ta tashi ta bar shi a wurin zaune. Baki bu'de ya bi hanyar da ta fice da kallo cike da mamakin dalilin da ya kawo hakan.   Duk iya tsawon tunanin sa bai iya ya tuno laifin da yayi mata ba....ya kwashe a 'kalla kusan mintina ashirin bai ko yi motsin kirki ba saboda damuwa. Wai yau Ammin sa ce ke share shi bayan tsawon watannin da suka 'dauka basu ga juna ko jin muryar juna ba?  Bai iya ya bar gidan ba har Alhaji Baba ya dawo wanda bayan gaisuwa sai ya fara shigar da 'korafin sa kan Ammi kamar zai yi kuka...Alhaji Baba kuwa ce ma yayi" Abinda ya dace da kai kenan Muhammad..ko nima daka gani ina amsa gaisuwar ka ne saboda wasu dalilai amma abin kunyar da ka jawo mana cikin garin nan hukuncin da yafi haka ya dace ya hau kanka....nan Alhaji Baba yayi masa maganar cikin da yayi wa Ma'u inda yai masa ba da'di cike da 6acin rai ya nuna masa kuskuren sa...jikin Alhaji har na karkarwa saboda 6acin rai...shi kansa Yah Deen hawaye yake tsiyayarwa jin yanda mahaifin sa ke faman yin Allah wadai da halayyar sa..yasan ba 'karamin 6aci ran Alhaji Baba yayi ba. Ammi kam ko kallo ma bai ishe ta ba, tsaf ta fice a harkar sa ta daina ko kallon inda yake, yayin da tashin hankalin jin abinda ya faru a bayan san ya matu'kar 'daga masa hankali, bai ta6a yin tunanin yarinyar zata iya 'daukan ciki ba dayake ya bata magani daga baya kafin ta tafi...wancan karon da Husnah ta samu cikin sa hankalin sa ya tashi sosai har yasa shi zubar da cikin saboda gudun kar iyayen sa su san abinda take aikatawa, to sai gashi da Allah ya tashi kama shi yanzu sai  labarin ya fito daga bakin mahaifin sa...'karshen tika tikin tik...'karya ta 'kare ya zaiyi kenan...ya zaiyi ya iya kallon mahaifin sa ya 'karyata wannan batu, ya zaiyi ya raba Ma'u da wannan cikin kafin ta haife sa...ina zai je da 'dan shege 'dan da ba ta hanyar aure ya same shi ba? _Uncle Ja'afar_ mutumin da ya fa'do ransa kenan a dai-dai lokacin take sai ya rintse idanu yana maimaita kalmar...innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Kwata-kwata ma ya manta da faruwar wani lamari tsakanin su kwatsam sai ga wannan mummunan labarin, ji yake tamkar ya bu'de 'kasa ya shige ciki...yanzu iyayen sa sun riga sun san 6oyayyiyar halayyar sa...yanzu kenan kowa kallon mazinaci zai ri'ka yi masa? Mai lalata 'ya'yan mutane. Abubuwan duk sun taru sun yi masa yawa...ga fushin Alhaji, ga Ammin sa, ga tsoron kar Uncle Ja'afar yaji, ga shi 'karfi da yaji yana ji yana gani za'a haifa masa 'dan da ba na Sunnah ba kuma na shicda ikon hana faruwar hakan sam, ga tarin abin kunya ga kuma wai inji Alhaji Baba dole sai ya aure ta bayan ta haihu uwa uba ma kuma wai ya ha'da da matar sa su zama biyu...abin ya 'daure masa kai sosai, ina ya samu mata shi da har za'ace ya ha'da su su zama biyu...tunda yake a rayuwar sa bai ta6a jin kansa cikin tsananin damuwa da tashin hankali irin na yau ba, tafiya yake amma sam bai san inda yake saka 'kafafun sa ba...gaba 'daya hankalin sa baya jikin sa bai san inda ya dosa ba. Tafiya ya ringa yi kawai cikin duhun daren yana tunani, wanda tashin farko kawai tsintar kansa yayi kan barandar makaranta...nan ya zauna ya du'kufar da kansa yana kallon 'kasa hannayen sa sar'ke cikin juna...nazari yake so yayi amma gaba 'daya ya rasa ta inda zai fara, duk abubuwan zuwa suke yi suyi masa karo a zuci. Nawin da yaji 'kirjin sa nayi masa ne a lokacin ya sanya shi komawa ya kwanta da bayan sa hannun sa 'daya dafe da 'kirjin nasa yayin da ya dafe kansa da 'dayan hannun...bai ta6a tunanin akwai ranar da zai tsinci kansa cikin irin wannan halin ba sai yanzu da ya yaji shi aciki gashi ya rasa hanyar 6ullewa. Bai san tsawon lokacin da ya 'dauka yana a hakan ba sai kawai jin 'kiraye-'kirayen sallah Asuba yayi. Idanun sa nawi suka yi masa ga zogi lokacin da yake bu'de su ganin inda ya tsinci kansa ne ya sa shi saurin tashi zaune, mamaki ya so kama shi amma tuno abinda yake faruwa da shi ya wanki mamakin sa gaba 'daya. Cikin hasken alfijir 'din dake haskawa ya tashi a hankali ya lalla6a ya isa gidan sa...sai da ya watsa ruwa ya saka jallabiya sannan ya tada sallar asubah wanda a lokacin har ma an idar a masallaci gari ya fara haske. Da idar da sallar ko azkar bai tsaya yi ba kawai ya lalu6o wayar sa ya dannawa Imrana 'kira...wanda cikin sanyin murya yayi masa bayanin komai da ke faruwa harda zafin da iyayen sa suka 'dauka akansa da kuma hukuncin da Alhaji Baba ya yanke akan sa. Imrana kam kwantar masa da hankali ya ringa yi da fa'din kar ya wani 'daga hankalin sa ba abinda zai faru...dama ai haka a rayuwa, balle wannan da ya kasance kuskure ne yasa har asirin abin ya tonu amma  Insha Allahu komai zai wuce in auren ne ma ba sai ya aure tan ba kawai indai hakan zai sa hankalin su Alhajin ya kwanta...rayuwar gidan sa kuma ai a hannun sa take sai yadda ya so yayi agidan sa. Duk maganganun Imrana ko guda daga ciki bai ji ta sau'kar masa da natsuwa ba...hakan yasa ma daga 'karshe ya daina fahimtar sa...sallama kawai sukayi ya ajiye wayar yana tunanin 'kiran Antyn sa Zainab dan yasan zata bashi shawarar da ta dace...sai dai ko giyar wake yasha ba zai ta6a 'kiran ta cikin wannan halin ba...dan yasan idan taji labarin kamar Uncle Ja'far yaji ne. Shi fa tun bayan tafiyar sa makaranta bai sake tunawa da batun wata Ma'u ba balle abinda ya shiga tsakanin su..bai sani ba ashe harda ajiya yayi ajikin ta...abinda yafi 'daga masa hankali ma shine jin labarin cikin...sai kuma maganar da Alhaji Baba yayi kan cewa ya shirya da zaran Allah ya sau'ki yarinyar lafiya dolen sa ya aure ta ya ha'da ta da matar sa su zama biyu...In yaso yaje can shi ya sani...kuma ko da wasa ya kuskura ya cutar da guda daga cikin su bazai ta6a yafe masa ba...." _Yah Allah ka yafe min_ " Ya furta a fili. *****    Mamakin sa bai tashi 'karuwa ba sai da iyayen sa suka zaunar da shi bayan kusan 1 week da dawowar sa kan batun matar sa wai...karo na farko da magana ta ha'da shi da Ammin sa tun dawowar sa, inda tayi masa garga'di mai zafi kan 'yar ta ta kuma nuna masa cewa ba son ranta bane zaman sa da Hudah...kawai dai dan mahaifin ta ya matsa akan akai ta 'dakin mijinta ne bayaga haka da bata san mai zai sa ta ha'da jini da shi ba. " _Da gaske auren ne da ni kenan?_ Ya tambayi zuciyar sa...kansa 'kasa lokacin da yji sunan Hudah ya fito cikin maganar iyayen nasa, ya so ya 'daga kansa saboda mamaki amma sam ya kasa bayyana mamakin sa a fili cuz har yanzu nawin mahaifan nasa yake ji...fatan sa Allah yasa ba wannan 6eran Hudahn da ke gidan su bane. Kamar wasa abin shi dai kawai shiru yayi yana bin komai da idanu tare da sauraron kalaman nasu...duk da halin da yake ciki a lokacin amma hakan bai hana shi murmushin takaici ba da yaga zahiri cewa wai Hudahn Ammi ce matar sa...yaushe hakan ya faru sam bai sani ba. Akan yarinyar nan ne shine Ammi ke cewa in ba dole ba bazata ha'da jini da ni ba? Me Ammi ke nufi kenan? Tana nufin yarinyar ce jinin ta ba ni ba? Kansa 'kasa ya lumshe idanu take fuskar Nanne ya bayyana cikin brain 'din sa..." _Allah yayi miki Rahma ya sa hutun ki kenan_ "...Cikin zuciyar sa ya furta hakan yayin da a fili babu wani yanayi da zaka iya fassara shi saman fuskar sa. Sam ya rasa dalilin da ya sa bai ji haushin komai ba koda labarin cewa Hudah matar sa ce isa kunnuwan sa...shi kansa ya kasa tantance ainahin halin da zuciyar sa take ciki kan hakan. Harcya isa gidan sa yana tunanin yausgechakan ya faru? Yaushe aka 'daura auren sa da ita bai sani ba. Tuno maganar da abokan sa suka yi masa ranar da suka dawo daga Azare wurin 'daurin auren sa ya sa ya zargi wani abu..." _Ai shi yasa nace maka mai abin mamaki domin har gobe ango kake mijin amarya kuma..."_ Maganar Anas ya tuno wanda ya fa'da masa ranar 'daurin auren saxda Husnah bayan suna da tabbacin cewa an riga an fasa auren sa da Husnah ...to mecyasa shi fa'din hakan kuma....? Kenan duk 6oye minvsuka yi alhalin sun san gaskiya, sun san cewa da Hudah aka 'daura min aure kuma suka 6oye min. Laifin Ishaq ka'dai yafi gani kan hakan saboda duk cikin su ya fi kusanci da shi....take ya 'kira shi a waya ya tambaye shi gaskiyar lamari. Tunanin Ishaq ko a wai-wai yaji zancen shiyasa yaso 6oye masa but take Mu'een ya nuna masa cewa yasan komai amma miye dalilin su na 6oye masa iya tsawon lokacin nan..?" " Kayi ha'kuri Mu'een..umarnin Alhaji Baba ne kuma kasan yafi 'karfin hakan a wurin mu shiyasa bamu sanar da kai ba.." Tsaki yaja tare da yanke wayar ya ajiye gefen sa..kishingi'da ya koma yayi yana jin ba da'di...tun dawowar sa garin nan bai samu natsuwa ba...har 'yar rama yayi saboda ko abincin kirki baya samun lokacin ci ga damuwa da yayi masa yawa. Ni kuwa gidan mu wurin Ummata aka maidani wai zanyi 2weeks acan kafin akaini gidan miji na...ban sa damuwar komai cikin raina ba...ni dai kawai abinda ba naso shine zama da shi, kuma ma tun kafin na baro wurin Ammi kullum sai ta kwantar min da hankali tana bani baki akan in daina tsoron sa kuma duk abinda ya min inzo in sanar da ita zatayi maganin sa. Ban ta6a sanin cewa Yah Deen na da ala'ka da cikin jikin Ma'u ba har sai da na koma gidan Ummah ta...anan da muka ke6e da Addah ta Saudah take min gulmar wai ai su Ammi sun san cewa manemin mata ne shiyasa suka aura masa ni dan mugunta...yanzu kuwa da halin sa ya bayyana kowa ya sani cewa shine yayiwa Ma'un Malam Barau ciki shine kuma za'a wani ce za'a kaini gidan sa matsayin matar sa..." Abin ya matu'kar kulle min kaina jin batun Addah Saudah...amma duk da hakan ban wani damu sosai ba...sai dai har yanzu cikin zuciya ta banjin cewa ina son zama da shi. Nasan ma in ba dan Addah Saudan ba in dai dan Ummah ta ne bazata ta6a yimin zancen ba...banda ma nasihar zaman ha'kuri kullum babu abinda ke shiga tsakani na da ita. Yayah Usman baya gari haka ma Baban mu...sai dai duk sun 'kira munyi waya da su kuma sun turo ku'din da za'a min siyayyar kayan 'daki na da shi...har Ammi taso hanawa wai ai wannan hakkin tane amma iyaye na suka 'kiya dole ta ha'kura amma tace ita zata min komai na kitchen ta ro'ki kar asayi komai. Wannan 'din kuwa aka bar mata hakan ma da 'kyar Ummah ta ta amince..kusan kullum sai munyi waya da Baban mu inda da kansa cikin natsuwa batare da ya dubi 'karancin shekaru na ba ya bani kaf 'din labarin tun farkon dalilin kafuwar aure na da Yah Deen...saboda acewar sa abin ya shafe rayuwa ta ne kuma kar inga kamar ba'a yimin adalci ba. Yace lokacin da Alhaji Mamman yaci amanar su ya bayar da auren 'yar sa ga wani sai dukkan su ransu ya 6aci gashi ba laifi sun gayyaci mutane da dama kuma kowa zaman sauraron jin 'daurin auren yake yi...yanayin da yaga Alhaji Baba abin sam bai masa da'di ba..yace to a lokacin sai yayi tunanin me ze hana a 'daura dani tunda duk matsayin 'ya'ya muke a wurin Alhaji Baban kuma ba haramcin auren tsakanin mu. Yace Ja'afar 'kani ga Alhaji Baban ya ja gefe yayi masa bayani badan komai yayi hakan ba kuma sai dan rufin asirin juna...take kuwa Uncle Ja'afar ya amince kuma shine ya kai labarin kunnan Alhaji. Take batare da 6ata lokaci ba aka 'daura mana aure kan sadaki dubu 'dari cif Alhaji Baba shine matsayin wakilin amarya yayin da Uncle Ja'afar ya wakilci ango...abin mamaki kuwa sai ya fahimci aure na da Yah Deen 'din yafi kwantawa Alhaji Baba arai fiye da wanda aka so yi a farko. Ya fahimci hakan ne lokacin da Alhaji Baba yazo gaban sa ya rin'ka zuba masa godiya kamar wanda yayi masa wani gagarumin abu...tun a wurin ma ya fara bayyana masa abinda shi bai ta6a sani ba, wato soyayyar Deen ga Marigayiya Nannen mu...a lokacin ba 'karamin mamaki yayi ba da yaji wannan labarin sai dai ya fahimci komai Allah ne da shi kuma shike tsara komai...shiyasa ya yi sanadin ha'duwar aure tsakani na da Deen,  kenan dama can ba Nanne bace matar sa ni 'din ce...tun daga ranar ya san cewa aure na Da Yah Deen ha'din Allah ne. Alhajin da kansa ya nemi a rufe zancen saboda wani dalilin sa a lokacin yace da kansa zai bayyana idan yaga dacewar lokacin....wannan dalilin ne ya sa ba kowa yaji zancen ba har yanzu...sai dai duk da haka 'yan bani na iya na nan ma'kale suna juya zancen. Yace kwatsam yana zaune sai yaga ana ta 'kiran sa awaya ana sanar da shi abinda ke faruwa...da farko ma bai yadda ba amma daga baya daya da yaga kusan mutane hu'du sun 'kira shi da batun kuma iri 'daya sai jikin sa yayi sanyi gankalin sa ya fara tashi, daga 'karshe ma kashe wayar sa yayi na tsawon kwanaki biyu yana nazari kan lamarin. Yace yasan wasu daga ciki ba wai haka kawai suke 'kira dan su sanar da shi ba, ya fahimci harda munafukai masu nuna cewa kwa'dayin su yayi kai harda 'kafafu tunda gashi halin yaron ya bayyana a fili kowa ya sani...ransa ya 6aci sosai amma duk da haka bai ga wata mafita ba illah ya nemi a mi'ka ni 'dakin mijina wata'kila hakan ka'dai shine mafita shiyasa ya yanke wannan hukuncin. Yace da ace ma wani daban da bai sani ba ne da babu yadda za'ayi bayan sanin mummunan halayyar sa still ya sake 'daukan aure ya bashi...amma Alhaji Baba yafi 'karfin haka a wurin sa darajar sa kuma Muhamnad ya ci saboda karamcin sa a wurin jama'ah da kuma mahalicci...yace Allah ne ka'dai shaidar sa kan haka bai ta6a yin niyya ko aikata wani abu saboda kwa'dayi ko son abin hannun su ba duk da yasan ba kowa ne zai fahimci hakan ba amma Allah ya sani... yana so kuma nima inyi ha'kuri...inyi ha'kuri inyi masa biyayya..in zauna da mijina lafiya yace duk abinda zai faru tsakanin mu kafin in kai 'karar sa wurin wani in fara kaiwa wurin mahalicci saboda shine babban gata na...Allah ya sani shi kansa a yanzu ba son zama na da yaron yake ba dayake lokacin da ya bada auren bai san cewa haka halayyar sa take ba sai daga baya, so ba yadda zaiyi domin raba aure bashi ne mafita ba...ya yi tawakalli ne kawai saboda Allah kuma fatan sa Allah ya dubi niyyar sa...idan ya so sai yasa sanadin aurena da shi ya shirya shi ya daina abinda yake yi...Addu'ar saxgare mu kawai itace ubangiji Allah ya bamu zaman lafiya ya saka fahimta tsakanin mu....". Ni kam kuka nake yi sosai har ban iya amsa addu'ar da yai 'din ba shi kansa Baban mu jikin sa sanyi yayi daga yanayin muryar sa zaka fahimci damuwar da yake ciki. Ummah ta da kanta ta ringa lallashi na har nayi shiru bacci ya 'dauke ni ajikin ta...tausayi na take ji amma babu yadda zatayi, ita dai bata san me zata je da su Ammi ba...duk abin nan tarasa matsayin da ya kamata ta bashi..shin so ne ko kuwa...ta wani fannin akwai wani haske tattare da kasancewar mu tare da su amma wani 6angaren sai dai ace Alhamdulillah kawai...sau tari ta kan hango tsagwaron son kai cikin lamarin su amma sam hakan baya bayyana kansa a fili 'kauna ta zahiri kan lullu6e komai...dan duk abinda ke faruwa da tsigar zallar so suke bayyanuwa..ji take da tana da iko da bazata ta6a yadda da batun zama na da Mu'een ba amma babu yadda zatayi ha'kurin nan dai sai addu'ah kuma....fatan ta  Allah Ubangiji ya shirya shi yasa Hudah ta kasance Haske cikin rayuwar sa". Ana gobe zan koma gidan Ammi aka kawo kayan lefen aure na akwati set biyu masu kyau da 'daukan hankali, ni kam ma ko kallo kayan ba su ishe ni ba inaji anata zuzuta kyan kayan da kuma yada habaicin wai _dama haka ake so kuma an samu_ inji mutane...Babu wanda ya tanka su haka kowa yazo zai gani ya fita da maganar kayan a bakin sa. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ 💕💕 ~*This page is 4u Dear Zainab Kabir Ingawa...Alkhairin Allah ya kai mk duk inda kike...nagode sosai da 'kaunar ki gare ni.*~💕💕 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *59* Addah ta Maryam ma tazo da wasu 'yan uwan mu a hakan ma abin yazo ne cikin lokaci 'kan'kani amma duk da haka ba laifi gidan mu ya tara jama'ah ka'dan. Itama Addah Maryam tayi mamakin faruwar lamarin yanda yazo agaggauce, ta yi 'ko'karin ganin ta samu cikakken bayani daga bakin Ummahn mu amma hakan bai samu ba, sai da suka zauna da Addah Saudah shine tayi mata bayani gamsashshe a fahimtar ta, tace Baban mu ne ya matsa akan dole sai an kai ni 'dakin na saboda labari ya iske shi cewa Mijinnawa shine ke da alhakin cikin dake jikin Ma'u 'yar gidan malam Barau shiyasa Baban mu yace agaggauta kai masa matar sa a tunanin sa ko laifin nasu ne da tun farko ba su bashi matar sa ba suka bar ya a gida..inda ta 'kara da fa'din ni.nama yi mamaki wallahi ban zaci Baban mu zai kuma amincewa da zaman Hudah tare da yaron ba bayan jin abinda ya faru sai ga shi da kansa kuma yayi umarni da akaita gidan sa batare da ya koyi tunanin me hakan zai haifar ba". Baki kawai Addah Maryam ta ta6e tare da kawar da kanta gefe bata iya ta furta komai ba, sai dai har cikin ranta bata ji da'din maganar ba sam...aganin ta ba haka ya dace ayi ba..kamata yayi a bar Hudahn agida tukunna inma ba zasu iya raba auren ba har sai an tabbatar da shiryuwar sa kafin abrta zama dashi baya ga haka taya za'ayi a 'dauki yarinya 'karama kamar ni abawa mutumin da bai san ciwon kansa ba Baban mu yana nufin bai damu da abinda ya farun bane ko me? ..taso su tattauna maganar da Ummahn mu amma bata samu fuska ba hakan yasa dole ta ha'kura tayi shiru da bakin ta. Ana gobe za'a kaini gidan Yah Deen Saif yazo gidan mu shi ka'dai hr naso ma nayi msmskin ganinsa shi ka'dai 'din amma sanin ba'kin hali irin na Zaidu yasa mamaki na ya kau ...y Saif yasha Jumpa milk colour da hula kamar wani babba, fuskar sa fayau sai 'dan 'kasumba da ya fara tarawa, yayi kyau sosai abin sa...a 'dakin Baban mu aka masa masau'ki inda aka yi 'kirana bayan sun gama gaisuwa da Ummahn mu. Jin cewa Saif necyazo ya sani tahowa cikin tsananin farin ciki, jiki na da doguwar rigar material sai 'dan 'karamin ba'kin mayafi da na yane kaina da shi...fuska ta da fara'a muka gaisa da shi na tambayi su Ammi da Zaidu..yace min lafiyan su qalau. " Meya sameka kai in kuma?" Na tambaye shi ina kallon fuskar sa. Take ya amsa ni shima da tambayar" Me kika gani?" Nace" Kamar baka da lafiya". Yace" Ni lafiya ta qalau". Ya 'karashe maganar yana suman shafo kansa. Shiru nayi ban kuma fa'din komai ba cikin rains nake tunanin abinda zai iya sashi canzawa haka cikin sau'ki dan nasan Saif ba haka yake ba...tashin farko tunanin na kan Yah Deen ya sau'ka cuz a sani na shi ka'dai ne ke takurawa su Saif a gidan..baki na ta6e cikin raina nake fa'din" Har yanxu ba zai canza hali ba". Lallen dake zane a hannu na naga yana kallo ban damu ba sai ma nayi murmushi da fara'a ta nace 'dazu da safe aka zana min yayi kyau ko?..har an min kitso ma 'kanana zafi ma kaina yake min har yanzu". Ido ya tsura min yana kallon fuska ta kamar wanda ke son gano wani abin acikin idanu na....Nima 'din sai nayi shiru ban kuma cewa komai ba. Cikin sanyi ya ambaci sunana sai na amsa nima a hankali jin yanda yanayin muryar sa ya koma. Yace " Hudah dagaske Yah Deen mijinki ne yanzu?" " Nima haka naji an fa'da...amma bansan lokacin da akayi auren ba". Na bashi.masa bayan yanayi na na canza izuwa na damuwa. Idanu ya lumshe tare da yin 'kasa da kansa hannun sa cikin gashin kansa, kamar an tsikare shi kuma sai naga ya mi'ke tsaye hannun sa ri'ke da hular sa yana duba agogon dake 'daure a tsintsiyar hannun sa yake ce min" Zan tafi gida...dama nazo ne kawai in dan ganki inga matar Yaya na". Yayi maganar yana me 'ka'kalo murmushi. " To bazaka tsaya in kawo maka ko ruwa ba?" Na fa'di ina mi'kewa tsaye da hanzari na. 'Daga idanu yayi ya kalle ni, sai da ya juya ya fara tafiya sannan ya furta..." Karki damu Matar Yayah.. am ok.." Biyo shi nayi abaya ina 'kun'kunin sunan da yake 'kira na da shi, a fili kuwa cewa nayi" Sai nagaya ka da Ammi tunda ka'ki zama ka ci komai". Murmushi yayi ta'kaitacce sannan ya waigo idanun sa yasa cikin nawa idanun yana murmushi yace" Idan naje gidan ki ai zan ci". Dajin haka sai na fara buga 'kafafu na a 'kasa tare da tura baki.na gaba...zan yi magana yayi saurin tara na da fa'din" Common..me hakan kuma...ke fa yanzu kin girma...gobe-gobe za'a kaiki 'dakin mijin ki ko so kike ace yarinyar Ammi shagwa6a66iyace". Daina abinda nake yi na cigaba da kallon sa..sai ya juyo da kyau ya fuskance ni gira ya 'dage sama sannan yace"  Kinsan me nake so dake 'yar gidan Ammi?" Kai na girgiza alamar a a sai yace" Ha'kuri zakiyi...ai nasan kinsan halin Yah Deen da kyau ko?" Wannan karon kam shiru nayi ina mai cigaba da kallon sa. " Kiyi ha'kuri ki zauna lafiya da mijin ki kinji?...kuma nayi al'kawari kullum zan rin'ka taya ki Addu'ar Allah ubangiji Kar ya bashi ikon cutar mana dake kuma ya daidaita miki hankalin sa...ko baki so?" Ban bashi amsa ba still nayi shiru ina jin yanda cikin idanu na ke tsatstsafo da ruwa ...Saif sai yayi murmushi ka'dan sannan ya cigaba da fa'din" Kar kiyi min kuka ni...ai nasan kina so ko...to ubangiji Allah ya baki ha'kurin zama da shi...Allah ya baku zaman lafiya ya sanya muku albarka cikin auran ku..ki kwantar da hankalin ki insha Allahu bazaki yi danasanin auren Yayah ba". Daga haka ya juya tare da sanya hular sa akansa ya fita batare da ya jira jin amsar da zan bashi ba...yana saka takalmin sa ya ke sake fa'din kice da Ummah na wuce kawai dan naga tana cikin hidima kar mu raba mata hankali". Ganin dagaske tafiyar zaiyi ya sani saurin fa'din"  Ka gaida min Ammi na" Abinda kawai na iya fa'di kenan ban kuma san dalili ba sai naji zuciya ta gaba 'daya ta karaya kafinvna ankara sai jin idanu na nayi suna tsiyayar da hawaye. Saif bai sake yadda mun ha'da idanu ba yayi gaba abinsa, har ya 'karasa fita daga gidan kuwa ban kuma cewa komai ba illah bin bayan sa da na tsaya yi da kallo ina tsaye daga bakin 'kofa ina share hawaye na. Saif yaro ne ba wani babba ba amma yana da nagartar da idan ka zauna da shi sai ya birke ka..wani lokaci har zaka iya mantawa da 'karancin shekarun sa, musamman ma idan magana ta fahimta ta ha'da ka da shi...ko cikin yaran Alhaji Baba Saif ne wanda yafi jin natsuwa da shi sosai...da suke je boarding school 'dinnan ma sai abin nasa ya 'karu, halin girma da mutuntaka duk suka shige shi ga su dama akwai jikin girma ba laifi. Ni dai 'dan maganar nan da muka yi da shi sai naji wani iri tamkar wanda akace min daga yau 'din bazan sake ganin su ba...tun daga yanzu har na fara missing presence na su..hakan yasa na koma cikin 'dakin Baban mu na kwanta na dinga rizgar kuka na wanda babu mai lallashi na...da 'kyar na samu kukan ya tafi har bacci 6arawo ya sace ni. *****    Washe gari da yamma aka zo aka tafi dani gidan Ammi..bayan an min kwalliya ta na gani a bada labari...ko kafin atafi da ni sai da aka ha'da ni da Baban mu awaya ya sake kwantar min da hankali gami da nasihar ha'kuri da kuma kawar da kai...duk wannan abin bai sa na sake zubda hawaye na ba...har sai da mukaje gidan Ammi aka ha'da ni da Yah Deen wuri guda lokacin bayan sallar Isha'i ne, Alhaji Baba da kansa ya zauna yayi mana Nasiha mai shiga jiki tun anan nafara kuka na harda shashshe'ka cus yanzu na fahimci kowa nasihar zama da Yah Deen yake min...kenan dagaske daga yau zama tare da shi zan koma yi...kamar yadda Saif ma ya fa'di. Ammi ce ta fitar dani rungume ajikin ta bayan Alhaji Baba ya sallame mu sai ta wuce dani 'dakin ta muka bar Yah Deen ka'dai da Alhaji Baba, bansan me suka tattauna tsakanin su ba amma sun shafe a'kalla kusan mintina ashirin suna tare da shi. Nima 'din Ammi lallashi na take yi a 'dakin ta tana sake lalla6ani yayinvda nake mata shagwa6ar ni bana son zama da shi tace kar akaini gidan sa...Ammi kam lalla6ani ta ringa yi da kalamai masu da'di har na rage kukan da nake yi, cikin hakan tasa na 'daukan mata al'kawarin duk abinda yamin wanda banji da'din sa ba ko kuma na cutarwa bazan 6oye mata ba...tace in kwantar da hankali na insha Allahu bazata ta6a bari ya cutar da ni ba matu'kar numfashin ta na aiki...ni dai kawai in masa biyayya matsayin sa na miji na kar na raina shi...saboda shine tsanin aljannah ta daga yanzu....tace aure na dashi ya riga ya zama rubutaccen 'kaddara ne baya ga da ko ita da kanta bazata ta6a bari hakan ta kasance ba...sai dai yanzu kam babu yadda zatayi tunda ba'a jayayya da yin ubangiji kuma shi yasan dalilin faruwar komai...tace min idan na kwantar da hankali na na zauna dakanta zata sa ya siya min waya mai kyau wanda zan na 'kiranta kullum muna gaisawa.." Jin hakan da ta fa'di ne ma ya 'dan sanyayar min da hankali na har na kwantar da kaina kan cinyar ta ina maida numfashi yayin da ta ringa shafa min kaina tana sake lalla6a ni. " Ammi" na 'kira sunan ta a hankali. Sai ta amsani tare da bada hankalin ta gare ni.. Nace " Banga su Saif ba Ammi.." Tace " Kar ki damu zaki gansu ai uwata har gidan ki zasu je su gaida ki kinji?" " To"..nace 'kasan ma'koshi na ina sake tunanin rabuwar mu da Saif ta jiya. 'Karfe tara da 'yan mintina aka tafi dani gidan Yah Deen da sunan gidan aure na, bansan me yasa ba amma sai na kasa tsaida hawaye na...sanda za'a shigar dani gidan kuwa fargaba ce ta shige ni mai tsanani musamman saboda sanin halin sa da nayi hakan yasa kuka na ya tsananta. Gashi babu wanda zai kwana tare dani dan haka koda suka kawo nin ma basu zauna ba shiga suka yi suka lalle'ka cikin gidan sannan daga bisani suka dawo nan kuma suka fara niyyar tafiya, nan kuka kuwa naji hankali na ya tashi sosai...tunanina ta yanda zan iya zama tare da shi a gida 'daya. Addah ta Maryam na rungume ina ro'kon ta kar ta tafi ta barni tsoro nake ji..haka ta dinga yimin nasiha tana sake tuna min kalaman Baban mu da Ummah ta...still ban sake ta ba na cigaba da kuka na..wayo tamin tace in bari ta tafi tunda dare yayi yanzu amma gobe insha Allahu da sassafe zata dawo mu yini. Nace mata ni tsoro nake ji ni ka'dai dan Allah kar ta barni..sai tace min to bari ta dubo Mu'een idan baya nan sai ta kulle 'kofa ta dawo...da jin haka sai na sake ta ina share hawaye na. Daga haka ban kuma jin motsin ta ba. Allah ma ta taimake ni dan tamkar ha'din baki da fitar su basu jima ba sai ga shi shima ya shigo gidan da farko ma da naji motsin 'kofa nayi tunanin ko Addah Maryam 'din ce..but jin sallamar sa da nayi wanda yayi ta daga bakin parlour 'kasa-'kasa tamkar ma bazaiyi ba hakan ne ya sani fahimtar shine. Ai kuwa ban ko amsa ba na cigaba da kuka na..sai ma ganin san ya sake tada tsimin kukan nawa na fara yi tamkar an doke ni ne. 'Karamin tsaki yaja da jin irin kukan da nake yi...ko kulani bai yi ba balle in saka ran ya san da zama na, abin hannun sa ya ajiye kan center table dake tsakiyar parlourn daga haka ya sa kai ya wucewar sa ciki. Tsawon mintina kusan biyar sannan na sake jin muryar sa daga baya na a tsawace yace " Ki min shiru...". Yi nayi kamar banji ba na cigaba da kuka na ina share hawaye...'dan takowa yayi ka'dan yana sake ha'de fuska yace " Wallahi 6allaki zanyi idan kika dame ni banson hauka ni". Ji da ganin hakan ne yasani saurin mi'kewa tsaye ina yarfa hannuwa na cikin kukan nake fa'din" Ni dai Ammi na.." Tsakani na da Allah nake bu'katar komawa wurin Ammi har zuciya ta...yaushe zan zauna da mutumin da ko dariyar kirki ma zan iya irga sau nawa naga yayi ta tsawon zama na a gidan su..kwatsam kawai ace yau gani ga shi matsayin ma'aurata. Da wani tsawan naji ya sake fa'din " Dan ubanki na 'daure ki ne ko ni ne na kawo ki gidan da zaki dame ni?" Dalili guda biyu kacal ne suka hana ni nufan hanyan fita saboda nasan already ya rufe 'kofar bayan da ya shigo, sannan kuma nasan a lokacin dare yayi, wa'dannan dalilan ne suka sanya ni cigaba da rera kuka na kawai batare da na nufi hanyar waje ba. Tsaki yaja sannan ya sake komawa ciki...da shigar shi sai ya rage kayan jikin sa cikin hanzari dan duk ji yayi ransa ya 6aci, bayi ya shiga sai dai bai jima ba ya sake fitowa. Da yake lokacin da za'a kawo kaya na kaf aka fitar da kayan sa a gidan aka kai gidan Alhaji Baba  so bashi da ko da kayan bacci ne yanzu anan dan haka kawai sai ya zauna da boxern dake jikin sa da nufin bacci da shi. A hakan kuma ya dawo parlour inda nake da yake ya saba da zama hakan tun asali. 'Bangare na kuwa a lokacin na daina kuka sai dai ajiyan numfashi zaune nake kan gwiwoyina nake a 'kasan parlour sai faman murzan idanu kawai nake yi...a haka naga ya fito ya nufo inda nake. Da ganin sa hakan sai nayi 'kasa da kaina tare da  saurin rintse idanu na cuz ni baya ga shi ban ta6a ganin wani namiji cikin irin wannan yanayin ba...cikin raina nake mitar halin sa. Yanda zuciya ta ke harbawa ya sanya nake jin wani sabon tsoron sa na sake kamani da ban na menene ba...daga nesa dani ka'dan ya zauna yana sake ha'de ransa cikin ba'kin hali ya ce..." Kin yi sallah ne?" Da sauri na 'dage masa kaina alamar " Erh" ...sai yace " Abinci fa?" Nace " Naci" Still idanu na a rufe. " To maza ki tashi ki je ki kwanta banson sake jin wata rigima kuma in ba haka ba zane ki zanyi...". Daga fa'din hakan ya tashi ya koma ciki ya bar ni zaune a wurin kamar yadda ya samo ni. Sai da na tabbatar ya fita sannan na bu'de idanu na ina sake kallon inda ya tashi. Baki na ta6e na kawar da kaina gefe...na 'dauki a'kalla kimanin mintina sha uku kafin na mi'ke na cire mayafi da 'dan kwalin kaina nayi kwanciya ta kan doguwar kujera Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *60* Baki na ta6e na na kawar da kaina gefe....na 'dauki a 'kalla kimanin kusan mintina sha uku kafin na mi'ke, mayafi da 'dankwalin da ke kaina na cire daga nan nayi kwanciya ta kan doguwar kujera. Take kuwa bacci yayi awon gaba da ni....Yah Deen ma bai sake bi ta kaina ba har sai da gari ya waye bayan ya 'dauro alwala sannan yazo ya tashe ni inda ya bubbuba 'kafafuna yana fa'din" Ke..." Firgigi na tashi na zauna ina ha'de raina cuz ni ban saba da irin wannan tashin ba..Ammi na ba haka take tashi na daga bacci ba. Tuno cewa wai yanzu da shi zan zauna a gidan ya sani na sake jin wani iri har cikin zuciya ta..bansan ranar da zan saba da Yah Deen ba ni.kam a rayuwa ta. " Ta shi kije kiyi sallah?" Abinda kawai yace dani kenan sannan ya juya ya koma ciki. Ko motsawa ban yi ba daga inda ya bar ni har ya idar da tasa sallar ya kuma fitowa ina nan na takure wuri guda tamkar almajira abin a tausaya min. Ga shi fitsari nake ji sosai kuma na kasa zuwa inyi saboda fargaba...tamkar daga sama naji muryar sa akaina yana sake fa'din" Har kinyi sallar ne?" Saurin girgiza kaina nayi ina sake matse fitsarin da ke damuna. " Lokacin kuma jiran ki yake yi ko?.." Ya sake fa'da daga inda yake tsaye. Ban san me zan ce da shi ba dan haka sai na 'dan waigo ka'dan na kalle shi, tsaye yake ya ri'ke labile a hannun sa daga bakin 'kofar shiga cikin, fuskar sa ba yabo ba fallasa amma ban wani tsaya na 'kare  masa kallo ba na kawar da kaina cikin raina nake 'kun'kunin" ta ina zan wuce to bayan ka tare hanyar".. Tsaye na mi'ke hannu na ri'ke da shirgin kaya na mayafi da 'dan kwali na...shahada kawai nayi  na nufi bakin 'kofan bedroom 'din cikin sanyin jiki kaina a 'kasa...nasan duk tsiya ai idan anzo zai matsa in shiga. Tsaki ya ja guntu sannan ya saki labilen ganin na tunkaro sa...nasan bai wuci yayi tunanin zamana da shi zqi takura masa ba shiyasa naga ya wuce ni a 'dan fusace ya 'karasa shiga cikin parlourn batare da ya ko sake kallon inda nake ba. Yayin da ni kuwa hakan shi yafi komai yimin da'di cuz dan da ganin ya bar bakin 'kofan nayi saurin shigewa ciki, da yake dama ri'ke nake da fitsari...ai su mayafin ma duk watsasu nayi kan bed nayi saurin shigewa bathroom. Ko da na fito rasa yadda zanyi nayi sallar nayi, gashi sai da na tsaya na watsa ruwa ban kuma son maida kayan da na cire cuz suna da nauyi, gashi ba wasu ban san kayan da zan saka ba a wannan lokacin. Tsaye nayi ina tunani gami da kalle-kalle cikin 'dakin tamkar zanyi kuka 'kasa-'kasa nace" Waiyo Ammi na dan Allah kizo ki tafi dani...wardrobe na nufa duk da banda tabbacin samun abinda zai min amma sai naji raina ya kwanta da in bu'de 'din, kamar wasa kuwa da na duba sai naga kaya ne jere aciki. Duk da bansan na wanene ba amma take sai naji farin ciki ya lullu6e ni, abaya ba'ka na ciro na sanya tare da Hijab babba pitch colour da na gani shima cikin kayan rigar kuwa daidai tsayi na tayi min dai-dai, daga haka na wuce kn dadduma na tada sallah ta. Har na idar na zauna kan daddumar ina karanto Azkar 'din da muka saba yi da Ammi har a lokacin kuma Yah Deen bai dawo 'dakin ba...sai dai banyi mamaki ba cuz daga inda nake zaune ina iya jiyo sautin T.V na tashi nasan babu mamaki abinda ya 'dauki hankalin sa kenan. Na 'dauki a'kalla kusan mintina ashirin zaune a wurin kafin na mi'ke izuwa parlourn dan na gaida shi. Kishingi'de na same shi 'kafafun sar'ke da juna 'daya kan 'daya yayin da ya 'dago su saman kujeran yayi musu masau'ki, hannun sa 'daya ri'ke da remote yayin da gaba 'daya ya bada hankalin sa kan T.V 'din yana kallo. Ko sallamar da nayi ma da 'kyar in yaji ta ni dai ban damu ba saboda sanin halin sa da nayi. A hankali na 'karaso nesa ka'dan da shi na zauna na takuru cikin hijabi na...da rawar murya nace " Ina kwana Yayah". Cikin sa'a kuwawannan karon ya jini duk da yake ma ba da 'karfi sosai nayi maganar ba, amma hakan nai hana shi jin abinda na fa'di ba, na fahimci yajin ne ta dalilin waigowa da naga yayi ya kallo ni, sai dai bai amsa ba gani kawai nayi ya sau'ko da 'kafafun sa ya dire su a 'kasa still kuma suna sar'ke da juna, sai a lokacin ma na lura ashe rigar Jumpan sa na jiya ce a jikin sa har yanzun, sai dai bai saka dogon wandon kayan ba...'dauke idanuna nayi da sauri na mayar da shi 'kasa ina kallon tiles dake 'kasan 'dakin zuciya ta na dokawa, a hankali na sake maimaita gaisuwar da nayi... Yayin da ya amsa ni da fa'din" Lafiya lau". Inda ayi maganar ne batare da ya 'dago ya dube ni ba. Muryar T.V naji ya rage sannan ya dube ni a lokacin yana wani cin magani yace" Ya ma sunan ki?" " Hudah" Na bashi amsa a ta'kaice kaina a 'kasa...a 6oye nake ta6e baki cikin raina nake ayyana wannan shi baya ri'ke sunan mutane ne?" Cuz ni dai nasan tuntuni yasan sunana. Ko da yake ma ai ban ta6a ji ya 'kira ni da sunan ba 'kilan ya manta ne" Ni ka'dai nayi magana ta kuma na warware ta, har a lokacin kuwa zuciya ta bai bar bugu ba. " Wani irin suna ne kuma Hudah?" Shima naji ya tambaya da alamun rainin hankali cikin maganar tasa, idan ka gansa a lokacin zaka yi zaton ko wani abin da bai so aka ambata masa ko kuma irin bai ta6a jin ko da kalar sunan ba. Baki na na 6ari na amsa shi da fa'din cikakken sunana wato" *NOORUL HUDAH* ..." " What ever.." ya fa'di yana wani kawar da kansa...." Ni dai ki  saurare ni da kyau kiji..kin san waye ni ai ko baki sanni ba?" " Na sani" Na bashi amsa a ta'kaice Yace " Gud...kar kiga an ha'da ni zama gida 'daya dake kiga kamar kin samu hanyar raina ni ko wani abu, sanin kanki me bazan ta6a 'daukan wannan ba kinsanni... wallahi 6a66ala ki zanyi matu'kar kika ce zaki tsiro min da wani hali, ko kuma kika yi saken da har na ci karo da wani abinda bai game ni ba kin san sauran ba sai na miki bayani ba...Ina nan da hali na da kika sanni da shi wannan Deenin ne har yanzu ban canza ba, dan haka be careful...kar inji kuma kar in gani cewa kin 'dauki magana daga gidan nan kin kai wani wuri dan nasan irin ku 'din nan ba 'kananun munafukai bane...so ki kiyaye ni...ban ce ki samin idanu cikin rayuwa ta ba balle har kiyi tunanin shiga gona ta..bana ma tunanin ba saboda sa idanu aka ha'dani zama da ke ba dan banga abin da zai sa ayimin aure da ke ba in ba haka ba...wallahi kika kuskura naji sunana ya fita daga gidan nan ta 6angaren ki ki kuka da kanki...sannan bansan 'kazanta kina jina ko?..zaman ki anan ma na 'dan lokaci ne da an gama gyaran gidan gaba 'daya zaki koma wani 6angaren daban amma kafin hakan ban son takura sam...dan haka ki kiyaye..kinji ko baki ji ba?" Da sauri na 'dage kaina sama tare da bu'dan baki nace" Naji.." " Gud". Kawai yace tare da sake maida hankalin sa kan kallon da yake yi bai sake bi ta kaina ba. A hankali na tashi na fita zuwa harabar gidan ganin cewa gari ya riga yayi haske. Tausayin kaina nake ji sosai yanzu...wai yau gani ga Yah Deen matsayin ma'aurata...sauran sahashin gidan da ba'a kammala 'din ba na tsaya ina kallo..ji nake da ma ayi a kammala gyaran ayau-ayau dan kawai in bar zama tare da shi. Ban koma ciki ba nayi zama na a waje har lokacin da naji an turo 'kofar gida...da sauri na 'daga kaina sai naga Zaidu kamar daga sama. Bana shiri da shi amma har ga Allah da na ganshi sai da naji wani sanyin farin ciki ya lullu6e ni...take na washe ha'kora na nufe shi ina fa'din" Zaid". Fuskar sa ba yabo ba fallasa ya amsa ni ban damu ba na taho da sauri na kar6i bakset 'din dake hannun sa ina fa'din" Ya su Ammi..?" " Lafiyan su" Ya bani amsa ata'kaice sai na sake fa'din" Yah Saif bai zo ba to sai kai ka'dai". Yace " Nima 'din Ammi ce ta tilastani wai sai na kawo muku abinci". Daga haka naga ya fara alamun juyawa sai nayi saurin fa'din " Yayah fa na ciki Zaidu...bazaka gaida shi bane.." Na fa'di hakan ne kawai dan bani son ya tafi tun yanzu. Waigo yayi ya 'dan ha'de goshi sannan naga ya dawo da baya ya nufi hanyar parlourn, abaya na bishi hannu na duka biyu ri'ke da basket 'din saboda akwai 'dan nawi..kallo 'daya zaka min ka fahimci fara'ar da nake 'kunshe da shi. Sallama yayi bakin parlourn yayin da Yah Deen ya amsa masa 'kasa-'kasa kamar yadda ya saba. 'Karasawa yayi ya zauna saman kujera sannan ya gaida shi tare da yi masa bayanin abinda ya kawo shi. Yah Deen jinjina kai yayi kawai...mintina biyu masu kyau Zaidu bai 'kara ba ya mi'ke da niyar komawa. Yah Deen na daga inda yake yace da shi" Zaid da mota ka zo ne?" " Erh" Zaidu ya bashi amsa yana kallon fuskar sa...Yah Deen sai yace da shi" idan kaje ka tambayi Ammi key 'din 'daki na akwai kayana aciki ka kawo min su gaba 'daya..." " To" Zaidu yace sannan ya juya har ya kusa barin 'dakin sannan Yah Deen ya sake fa'din" Zaid kar ka da'de fa ina jiran ka yanzu please". Jin cewa zai je ya dawo ne ya sani saurin dakatar da shi da fa'din" Zaid in zo in raka ka?" Bai tanka ni ba sai ya waigo ya dube ni sannan ya dubi Yah Deen yayin da shi kuma yayi kamar bai san me muke tattaunawa ba. Fita Zaidu yayi daga 'dakin yana 'ko'karin saka takalman sa nima na bishi abaya kaina har yanzu da Hijabi na...tsakani na da Allah nake so in bishi ni kam...so nake na koma gida...inga Ammi na da Ummah ta. Ina gab da barin 'dakin najiyo muryar sa yana fa'din" Bani san rawar kai da hauka fa". Cak na tsaya amma ban waigo ba...sarai nasan da ni yake yi wanda hakan ya sa na fara jin hawaye na taruwa cikin idanu na. Daga hakan kuma bai sake furta komai ba ina ji ina gani daga inda nake ina hango Zaidu ta cikin labile har ya fice a gidan batare da na bishi ba, abu na 'karshe da naji shine dirin motar sa daga haka na lumshe idanu na take sai hawaye na ya gangaro a hankali..." _Kar ki yadda magana ta iso kunnena cewa kina fita ba da izinin mijin ki ba...koma ni ban ji ba kar ki manta Allah yana kallon ki..kuma baya son mace ballagaza marar kamun kai...duk macen da bata yin abu bisa tsari da koyarwar Annabin mu to azahiri za'a iya 'kiranta da suna ballagaza...kuma banda girman kai Hudah ki riga gaida shi kina yi masa biyayya kar ki yadda ki tsiri mugun hali da rashin kunya cikin zamantakewar ku, idan ma kika yi kece da asara domin darajar martabar ki kike ragewa_ ....." Kalaman Ummah ta na tuna da tayi min irin su kusan sau uku a 'dan sati biyu da na zauna dasu kafin akawo ni gidan Yah Deen. Hawaye na naji ya 'kara gudu ban iya na 'daga ko hannu na ba kuwa domin sharewa ba...kuma har a lokacin ban juya na kalle shi ba...kenan wannan shine auren? Na gaida shi da safe shima garga'di kawaicya sake yi min, haka zan 'kare kullum cikin garga'di...badan kalaman Ummah ta da na tunobba da babu abinda zai hana ni fita da gudu in bar gidan nan. Bai damu da yanayin da nake ciki ba sai naji yana fa'din" 'Dauko plates a kitchen ki kawo min". Tamkar dama jiran maganr tasa nake yi sai kawai na yi waje da sauri na da yake nasan kitchen 'din a varanda yake...sai a lokacin ma na tuna da shi cuz ko 'dazu da na fito ban tuna na le'ka ba. Tura 'kofar nayi na shiga ciki..ban yi abinda ya kawo ni ba kawai na tsaya na shar6i kuka na son raina sannan na tari ruwa a tap 'din saman sink na wanke fuska ta. Plates 'din na 'dauko da spoon na 'dauraye sannan kawo masa..da fitowa ta sai na tarar da shi ya sauko saman carpet 'din tsakiyar 'dakin da kulolin abincin agaban sa, nima gaban sa nazo na zo na ajiye plates 'din tare da mi'kewa, idanun sa na hannu na har ajiye bai kalle ni ba naji yace" Je ki 'karo wani". Kitchen 'din na koma na 'dauko wani plates 'din na dawo..zan ajiye yace" Zauna". Dole na zauna..ina sake share hawaye na. Da kansa ya zuba abincin cikin duka plates 'din..abinda ban ta6a gani yayi da kansa ba kenan shine serving abinci. Gaba na ya tura min batare da yayi magana ba. Ban kula ba har sai da yayi kusan spoon uku a nashi sannan ganin ban da niyya ne kafin ya kalle ni umarni ya min da fa'din maza in daina wannan kukan in cire hijabin kaina inci abinci...da nutsatstsiyar murya yaci gaba da fa'din" ke baki da wayo ne? Kin ta6a ganin inda mace ta fita washegarin auren ta ne ko kuwa so kike ke ki bar abin fa'di a gari?" Shiru nayi kawai nayi 'kasa da kaina batare da na cire hijabin ba a hankali na kai hannu na 'dauki spoon na fara wasa da abincin kamar zanci nan kuwa ni koka'dan banji zan iya cin abinci a gaban sa ba. Shima 'din kuwa bai sake kulani ba har ya kammala ya tashi ya shige bathroom...shirun da naji ne ya sani tunanin cewa bazai kuma fitowa ba. Tattare kayan nayi kaf na mayar kitchen wanda zuwa lokacin na daina kukan tuntuni musamman ma da naji ya min magana cikin natsuwa sai na 'dan ji damuwata ta ragu. A lokacin ne kuma na tsaya ina kallon 'kauye a kitchen 'din da ya amsa suna nawa...ni Noorul Hudah wai matar Yah Deen abin fa na matu'kar bani mamaki sosai, wannan 'dan 'kwalisan nan shine wai yau mijina...murmushi nayi mai sanyi har cikin zuciya ta naji da'di ganin komai da nasan ana amfani da shi a cikin kitchen to akwai shi a wannan kitchen 'din Ammi bata rage komai ba..yayin da aka sanya kalolin komai iri 'daya wato kalar lemon green da fari, 'dazu da nazo sam ban kula da kyau ba. Sosai kitchen 'din ya haska yayi wani kyau da shi duk wani abin da ya kasance cikin kalolin sa babu lemon green to sai aka sanya fari...sosai komai ya 'dauki hankali na na rin'ka jin da'di...nasan ko bama ni ba duk wanda zai ga kitchen 'din dole zai birge shi... _harda su hajiya Nusee ma_. Farin cikin da na shiga har ya kasa 6oyuwa a saman fuska ta... Hijabin dake kaina na cire na ajiye shi saman counter na cigaba da sha'ani na....sai bu'de-bu'de nake yi ina sake kallon kayan dake kitchen 'din...duk babu wanda zai ban wahala wurin amfani da shi saboda duk nasan kaf kayan elctronics a gidan Ammi. Duk yadda akayi 'ko'kari wajen tsara parlourn gidan amma sam banji ya birge ni kamar yadda kitchen ya shiga raina ba. Ina nan ban sani ba na shagala a kitchen ashe har Zaidu ya kawo aikan da aka yi masa ya sake komawa. Sai da na gama iya shirme na na fito da hijab 'dina a hannu na kafin muka ci karo da Yah Deen da jikin sa ke faman tashin 'kamshi. Yasha kwalliya cikin manyan kaya da hula...hanya na bashi ya wuce abinsa cuz naga alamar fita zaiyi. Ciki na shiga nan na tadda jakunkunan kayan sa a cikin bedroom wanda na tabbatar sune wanda yace Zaidu ya kawo masa. Sosai naji haushi da har Zaidu ya iya zuwa gidan har ya tafi bai min sallama ba, na tabbata da Saif ne bazai ta6a yi min hakan ba cike da jin haushi nace" Banza mai ba'kin hali".  Ranar rasa abinda zanyi nayi wallahi gidan duk babu da'di, gashi Yah Deen ma bai dawo ba har sai bayan la'asar sannan ya dawo wannan 'din ma yana zuwa yayi shirin fita ball ya sake ficewa daga ruwa babu abinda ya sha agidan. Haka na yi ta zama ni ka'dai kewar su Ammi sosai ya dame ni, na kanji sanyi idan naga Ammi ta aiko mana da abinci hakan na tabbatar min da cewa bata manta da ni ba, abin haushin kawai shine da ake aiko wannan 'dan ra'ayin wato Zaidu, maganar arzi'ki ma bata shiga tsakani na da shi kuma da yazo yake komawa...ban san me yake hana Saif zuwa ba..in shi 'din ne kuwa nasan zama zai yi musha hirar mu da shi. Ummah ta ma sosai nayi kewar ta sai da nasan in ba wani ikon Allah ba zan jima ban ganta ba cuz a tun zama na da ita ban ta6a ganin ta fita zuwa gidn 'ya'yan ta ba sai dai in da wani dalili 'kwa'k'kwara..so na kuwa san a kaina bazata fara ba, gashi nima banga alamun fita ta kwana kusa ba. Tsakani na da Yah Deen gaisuwa ce kawai dan yanzu ko abinci bamu ci tare, tunda ya fahimci ban sakewa a gaban sa sai ya daina takura ni, a kullum sai ya gama nasa cin abincin sannan nake zuwa inci nawa, sau da dama kuwa cikin kitchen nake cin nawa kamar wata munafuka. Ni ke yin aikin gidan kaf babu mai tayani, gashi shi sam bai san ganin koda 'dis 'din stain ne a muhallin sa...kullum kazo zaka samu ko'ina tsaf sai 'kamshi da ke tashi a koda yaushe. Haka kuma bamu ta6a ha'da wurin bacci da shi ba, kullun kan kujera nake kwana shi kuwa yana cikin bedroom abinsa...sallah wannan bai ta6a janmu tare ba kuma gida yake yin har sallahr asubah amma bai ta6a tunanin tashi na in bishi sallah ba, nashi yake yi inyi nawa daban. Duk da banjin da'din gidan amma rashin kyara da yake min ya sanya hankali na kwantawa...balle yanzu ni da kaina nake yi mana abinci...da farko ma idan nayi baya ko kulawa amma tun ranar da muka yi brekafast tare shikenan daga baya da kansa ma yake zama yace in zuba masa yaci. Inaso in je gida wurin su Ummah ta da Ammi amma tsoron fa'di nake yi gashi banda waya balle in tambayi Ammi. Zamana shirun ne yasa na fara jin matsanancin son ri'ke waya ya a hannu na ya kamani..sai dai dole na ha'kura saboda bansan ya zanyi in samu ba ban manta ba da Ammi tace min idan na kwantar da hankali na da kanta zata sa ya siya min waya...to gashi na kwantar da hankalin nawa amma bansan ta yadda zan yi in sanar da Ammi ba. Abin haushi har su Saif suka koma makaranta ban sani ba...ranar wata laraba lokacin satina biyu agidan sa muka je da shi wai zan kwaso kayan makaranta ta anan na samu labarin tafiyar su Saif makaranta. Ai kuwa na ringa yiwa Ammi kuka harda shahshe'ka...sosai naji haushin tafiyar tasu batare da mun sake ha'duwa da Saif ba. Cikin lallashi Ammi ke bani bakin cewa ai Saif kam 'kin zuwa yayi amma ko ita tace da shi suje suyi min sallama kafin tafiyar su amma ya 'ki Zaidu kam dama shi ba damuwar sa bane...Saif kuwa cewa yayi ba yanzu zai je ba bata kuma san dalilin sa na yanke wannan hukuncin ba. Haka muka 'debo kayan makarantar tawa muka kamo hanyar gida still ina share hawaye na...tun a hanya kuwa na daina kukan da Yah Deen ya banka min wata uwar  harara. Abinda ya 'kara kwantar min da hankali na shine komawa ta makaranta, tunda na samu ina fita school shikenan na 'dan samu natsuwa...walwala ta ta 'dan dawo. Sai dai komawa ta makarantar sai batun Ma'u ya dawo sabo, kullum sai anyi gulmar ta musamman ma ni da ake tunanin agidan su Yahvm Deen nake maganrctake zuwa akai-akai, sai wasu na tambaya ta wai dagaske ne 'dan gidan mu ne yayiwa Ma'u ciki?. Wannan tambayar na matu'kar 'kona min raina amma haka nake daurewa na bada amsa da fa'din" nima ban sani ba.." Tausayin Ma'u nake ji sosai musamman idan kana jin labarin irin halin da take ciki. Nasan koma menene ita kanta cikin 'kunci take a yanzu, gashi ina so inje in ganta amma babu dama. Abakin mutane nake jin labarin wai cikin yazo mata ne da matsala kullum bata da lafiya ta rame sai haske da tayi. Ji nayi kamar in zubda hawaye na...jikina sanyi 'kalau ranar na koma gida inda na tadda shi a palour yana bacci...da shiga ta ya farka sai na gida shi. Idanun sa ya sake rufewa bayan ya amsa, ban wuce ba sai nace " Yayah". Hannun san ya 'dage ya kalle ni sai nayi 'kasa da idanu na a hankali nace " 'kawata ce bata da lafiya dan Allah inaso in je in gaida ta". " Wacece 'kawar ta ki?" " Ma'u" Na bashi amsa"..me yasa meta?" Ya sake tambaya ta yana sake ruef fuskar sa da hannun sa. Shiru nayi na rasa abinda zan ce da shi...sai naga ya juya zai gyara kwanciyar sa ganin da yayi bani da niyyar magana, ai da sauri na furta" 'kawata fa Ma'u na gidan Malam Barau". Fasa juyawan yayi ya tsaya kallon idanu na yana wani tattare goshin sa. " Bazaki ba". Haka kawai ya fa'di atakaice sannan ya juya ya gyara kwanciyar sa ya juya min baya. Ni kam jiki na sanyi 'kalau na shige ciki, da uniform 'din na fa'da kan gado ina hawaye..bana so ya ji 'karan kukan nawa ballantana ya daka min tsawa...danbhaka sai.kawai ma ringa hawaye ina sjare abina. Sam zama cikin gidan nan ya ishe ni sosai, ban kuma san yaushe zan gama ba, ban san amfanin kawo ni nan da akayi ba aka hanani zuwa ko ina, bansan laifin da nayi da yasa hukuncin takunkumi irin wannan ya hau kaina ba....gani nake yanzu kowa ya daina so na ne ma shiyasa suka share ni. Hatta Baban mu inaso inyi magana da shi amma duk babu dama. Bacci ne ya yi agaba dani a hakan cike da 'kuncin zuciya. *****      *Bayan wasu kwanaki* Tun da muke da Yah Deen bai ta6a ko kwatanta nema na da wani abu ba balle yaga 'kwazo na ko kuma lalaci na ba...amma abin takaici ina cikin barci ranar wata Lahadi tsakanin sallar azahar da la'asar kamar ance da ni in farka sai ji nayi yana fa'din"....No karki damu gidan ai akwai mace yanzu, babu wanda zai zarge ki". Ban san me akace dashi daga 'daya 6angaren ba haka kuma bansan farkon maganar tasu ba sai ji nayi kawai ya ajiye wayar. Ban wani sa maganar tasa aka ba balle inyi tunani akai, ina nan ina kwancen kafin nayi wani yun'kuri sai naji motsin sa har ya shigo bedroom 'din. Maida idanu na nayi na lumshe kamar mai bacci...ban bu'de ba kuwa har ya gama abinda zaiyi ya fita. Sai da na tabbatar ya fita sannan na tashi nima na cire kaya na na fa'da bayi dan 'dauro alwala. Sai da na sallaci La'asar da naji ana 'kira kafin na nufi kitchen dan neman abinda zan sawa ciki na cuz na fara jin yunwa a lokacin... maganar da naji yana yi 'din bai kuma zuwa kaina ba. *****     Yah Deen sai yamma ya dawo gidan lokacin ina 'ko'karin ha'da mana abincin dare...daga sannu babu abinda ya sake ha'da ni da shi ya wuce ciki. Daf Maghrib sai muka ji sallama daga 'kofar gida. Jin muryar kamar ta manya ne ya sani saurin fitowa ina amsawa yayin da Yah Deen dake parlour ma ya fito da sauri jin muryar abokin sa Imrana dan sam bai sanar da shi cewa zai zo ayau 'din ba. Da ganin Yah Deen Imrana sai ya saki dariya sannan ya waiga ya kallo wa'danda ke tsaye gefe da gefen sa...sannan ya kalle ni...kan YahcDeen ya maida idanun sa daga 'karshe. Ni dai bance da su komai ba ganin ba ni da ala'ka da su ya sani kowa cikin kitchen na cigaba da aikin dake gaba na. Yah Deen na shirin 'karasawa gaban su dan su gaisa sai Imrana da rikitacciyar muryar sa irin ta 'yan wiwi yace" Bahba ashe fa sa'a ce da mu...ya akayivhakan ta faru banda labari?...kasan da jimawa labari ya iske ni cewa an kawo gara gidan ka..shab sai na manta da batun, ko munyi waya da kai ban tunawa, haka kaima baka yi min zancen ba, yau da dawowa ta su shadow ke sake tunamin maganar al'kawarin da muka yi da kai kasan harda su na yiwa magana a lokacin da kace in gayyato abokaina, ashe su sun saka rai sosai shine fa suka saka ni gaba wai sai munzo yau ashe kuwa gaskiya ne da zuwan mu sai gata...." Ya 'karashe maganar yana 'yar dariya. Turus Yah Deen yaja ya tsaya yana wani 6ata ransa...ji yayi tamkar ya hau Imrana da duka saboda takaici, take yaji ransa ya 6aci har canza launi idanun sa suka yi. Cike da takaici yace" Ban son hauka ni Imran, hala ka manta ne ko? ba ni da kai muka samu labarin an fasa auren bane...ko tsabar ka raina min hankali ne ya sanya ka 'debo min wannan shirgin kuka zo min gida dan ka tabbatar min da cewa baka da hankali ko?..idan auren zanyi zan 6oye maka ne...dallah ku fice ku bar min gida...". Zaiyi magana Yah Deen yayi saurin 'daga hannu ya dakatar da shi" Wannan 'din ce baka gane ta ba ko me? yarinyar Ammi ce fa kuma amanar ta Alhaji ya bani".. " Kenan kai 'din darasi kake 'daura mata ko?" 'Daya daga cikin su ya fa'di wanda ganin sa ka'dai ya isa ya tabbatar ma da cewa a bige yake 'dif bada wasa ba. " Ban sani ba mahaukatan banza kawai". Wannan karan a fusace ya bada amsa. Imran ma zai sake magana yana nuna kitchen 'din da nake ciki kafin fitowar maganar tasa Yah Deen sai ya cusa hannun sa 'daya cikin aljihu tare da dakatar da shi cikin tsarewa da fa'din" Ku bar min gida". " Gaskiya Deeni ka iya yawa...wallahi wannan yawane". Fa'din shadow da tunda suka zo bai furta komai ba sai yanzun. Juya wa sukayi duk suka fice suna tanga'di tare da buga 'kofar gidan da 'karfin gaske. Yah Deen ya 'dauki a 'kalla kusan mintina goma yana tsaye idanun sa tun 'dazun na kan 'kofar da suka fita, ko a kwatance baya so ya 'kiyasta Hudah da wa'dannan 'yan iskan...dama Husnah ce ya tabbata ko kwana zasuyi zai iya bar musu ita amma wannan yasan da ya ta6a ta iyayen sa zasu ci uban sa...shi duk a kan haka ya bar maganar wai dan saboda gudun 6acin ran iyayen sa shiyasa bai basu ni ba, nan kuwa ba haka bane dan da 'kyar ya samu nastuwar zuciya, kusan sati guda abinvna cin sa arai, da ya tuna sai dai kiji ya saki tsaki, sai dai shi kansa bai san dalilin da ke sashi yin hakan ba, haushi yake ji sosai kawai amma ya rasa takamamman dalilin shin zuwan su Imarana yake jiwa haushin ko kuwa dalilin zuwan su?" 🌷 ~Happy Ramadan in advance~ 🌷 Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 🕌🌙 ~RAMADAN MUBARAKH~ 🌙🕌 _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *61* Nima ina kitchen duk ina jin tattaunawar tasu amma sam ban fahimci inda maganar tasu ta dosa ba, hakan yasa ban wani sa zancen aka ba. 'Kiran sallahr Maghrib da akayi ne ya sa Yah Deen lumshe idanu ya kuma bu'de su nan take...da 'kyar ya iya motsi daga inda yake tsayen ya juya ya koma ciki, zuciyar sa ba'ki'kirin haka yake jin ta, alwala ya 'dauro duk na zaci zai tafi masallaci ne ma amma ga mamaki na sai banga fitowar sa ba. Shiga nayi nima dan inyi tawa sallar nan na tarar da kan dadduma a parlour har ya idar da sallar sa agida, abu 'daya da zan shaidi halin Yah Deen da shi shine rashin wasa da lokutan sallah,  koda wasa baya wasa da 6angaren ibadar sa. Ganin yana parlour ne ya sanyi ni shimfi'da nawa abin sallar a ciki na gabar da abina. Haka ranar ko abinci ban ga ya ci ba...na kan ji dai time to time yana sakin tsaki da bansan dalilin yin sa ba...sai dai kawai in ta6e baki na...domin har a lokacin ko hira bama zama muyi da shi balle har in samu daman tambayar sa damuwar sa. Har bacci ya 'dauke ni kan kujerer da nake bacci shi kuma yana cik amma bai daina zirga-zirga tsakanin parlour da bedroom ba kamar wanda allurar sa ta 6ace masa yake faman nema..ban da'de da fara baccin ba naji yana tashi na, firgigi nayi na farka take na mi'ke zaune ina micik-micik da idanuna, sai yace min in tashi in koma ciki in kwanta. Da muryar bacci nace da shi" Anan fa nake kwan..." " Shut up dallah...ni bansan me nake yi ba kenan ko?" A tsawace ya fa'di hakan tamkar zai doke ni. Ai kam da sauri na tashi ina 'kun'kuni na shiga cikin na kwanta...yayin da ya bi bayana da mugun kallo. Ban kuma jin motsin sa ba cuz da shiga ta nayi bacci abi na. Sai da na tashi da safe ne ma sai naga alamun a parlour ya kwana ranar. Da safen kuwa da nagama ha'da masa breakfast 'din sa naci nawa sai na hau shirin  makaranta  sai da na kammala komai na fito kafin yace wai bazani makarantar ba sai gobe, kamar zanyi kuka na koma ciki ina tura baki na, haushi sosai ya kama ni, musamman da na tuno Ammi bata ta6a hana ni zuwa makaranta ba koda ta rana 'daya ce...haushin da ya bani.ne ya sanya ni shigewa ciki ban kuma fitowa ba shiyasa ban san ko yaci abinci ko kuma akasin haka ba. Sai da rana dana fito nemawa ciki na abin ta6awa nan na tarar da nasa abincin Tea kawai yasha. Baki.na ta6e ban wani damu ba kuma...haushin da ya bani ma a ranar ya sanya ko inda yake bana kalla, haka na yi ta sha'ani na. Sai bayan kwana biyu kafin da 'kyar ya barni na tafi makarantar sai da yaga alamun zanyi masa kuka ma kafin ya amince inje, ni kam kwata-kwata sai na rasa dalilin wannan 'ketar... bacin ya san ba yau na fara fita school 'din ba me yasa sai yanzu zai tsiri yi min hali kuma. Muna tashi daga makarantar ma gida na wuto cuz an hanani zuwa ko'ina, Ammi ta min warning tun ba yau ba haka shima ko yau ma kafin ya bar ni fitowa sai da yayi min garga'di sosai, shiyasa da an tashi a school nake kamo hanyar gida bana tsayuwa ko'ina. Wataran ma ina tafiya ina jimamin hanya ta ta da da nake bi in tafi gidan Ammi yau gani ina yankan wani hanyan daban ba wanda nasaba bi ba. Inajin kewar kowa da kowa gashi babu wanda ya ta6a zuwa gidan nasa dan dubani, bansan laifin da nayi musu ba sam...sau tari idan ina hanyar makaranta share hawaye nake yi na ba'kin ciki da takaicin zama na tare da shi. Ko yanzun ma zuciya ta cunkushe nake tafiya ina sake jin wani 6acin rai da fargaba suna sake shiga ta, har na shigo gidan ban daina jin hakan ba, dalilin ma kenan da ya sanya ko sallama ban iya tunawa nayi na. Da yake mafi yawan ranaku idan na dawo bacci zan tarar yake yi wasu ranakun kuwa ban samun sa agida so ban cika samun amsar sallama ta daga bakin sa ba...sai dai duk ranar da yasan zai fita yakance da ni in tafi da key holder saboda bai san lokacin dawowar sa ba. Ko takalman 'kafata ban tsaya na cire ba kawai na 'daga curtain na parlourn sannan na sa kaina na shiga ciki. Ciki-ciki nayi sallamar kamar wa kaina nayi ta kaina a 'kasa nake tafiya, nasan in ba ganin ahali na nayi ba bazan ta6a iya daina kewar su ba, kullum sune cikin raina safe rana da dare. Sam ban lura da inda na saba ganin sa kwance ba cuz damuwa ce fal zuciya ta hakan yasa na cigaba da tafiya har na isa tsakiyan parlourn sannan na yi tunanin dubawa ko yana nan...nan take nayi gamo da mugun gani, abinda har 'karshen rayuwa ta bazan ta6a iya daina ganin sa cikin idanu na ba. Ji nayi kawai kaina na juyawa jakar makarantar dake hannu na ma ban san lokacin da ya bar jiki na ba ya fa'di 'kasa...kafin kice miye hawaye ya wanke min fuska ta....duk da 'karancin shekaru na amma hakan bai hanani fahimtar mummunan abu suke aikatawa ba. Fa'duwar jakar tawa ne ya fargar da su, da sauri Yah Deen ya mi'ke yana dafe goshin sa da hannun sa... Ni kam da 'karfi na rintse idanu na amma sai na kasa barin su a hakan saboda ko na rufe ban daina ganin abinda na gani ba. Hakan yasa na sake bu'de wa nan na sau'ke su akan fuskar budurwar sa Husnah wacce na sani tun ba yau ba, ita kanta fuskar ta babu alamun walwala sannan ta wani takure wuri guda siraran hawaye na bin kuncin ta. Ko ka'dan banji tabani tausayi ba illah haushin ta da ya cika min zuciya, gani nayi yana 'ko'karin nufo inda nake hankalin sa a matu'kar tashe...sam ban son ya zo kusa da ni, haka kawai sai naji ina 'kyamar sa, wata tsanar sa naji ta shiga zuciya ta fiye da tsanar da nayi masa abaya, da sauri na fara yin baya-baya ina shashshe'kan kuka idanu na na kansa. Ganin da yayi fita nake da niyyar yi ya sanya shi fara 'kiran sunana cikin sanyin murya" Noor"! Yace tare da yimin alamu da hannu akan inzo. Da jin hakan sai na juya na fita da gudu ina kuka..." OMG... Ke Noor"! Ya sake 'kira na da 'karfi cikin tashin hankali. Ko kallon gabana ban yi na ringa sauri sai da na tabbatar nayi nisa da gidan kafin na 'dan saita tafiya ta, ban zame ko'ina ba sai gidan Ammi. Na same ta a 'daki idar da sallar ta kenan ko tashi daga kan daddumar ma bata yi ba na same ta. Sallama ta da shigowa ta duk lokaci guda....jikin ta na fa'da na rungume ta sannan na saki uban kuka wanda da kajishi zaka fahimci cewa cike yake da 'dacin zuciya. Ammi kam hankalin ta tashi yayi matu'ka, rikicewa tayi tana tambaya ta abinda ya faru amma ban iya nace da ita komai ba illah kukan da na cigaba da yi mai cin zuciya. Ammi tayi lallashin tayi tambayar ina Yayan nawa, in gaya mata abinda ya same ni amma duk abanza har lokacin bance da ita komai ba...balle tasan ainahin damuwa ta. Gajiya tayi da tambayar tawa, gashi itama zuwa lokacin hankalin ta ba 'karamin tashi yayi ba, dan haka sai ta barni ta tafi ta 'dauko wayar ta ta 'kira layin Yah Deen, jin layin sa ya shiga ya bata daman sauraren sa da kyau domin taji yanayin sa, domin tayi tunanin ko wani abu ne ya same shi. Ai kuwa jin sautin muryar sa da yayi mata sallama cikin sassanyar murya yasa ta adake tace da shi" Kana ina ne?" Yace " Ina gida Ammi". " To kazo ina neman ka". Shi kam " _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ " kawai ya iya furtawa cikin zuciyar sa, yasan dama dole yarinyar nan sai ta fa'da, abinda ya tsana kenan shine tonuwar asirin sa musamman wurin iyayen sa. Sai ga shi dan iya shege yarinyar ta rasa inda zata nufa da maganar nan sai gurin Ammi... Ai da kunya ma ace duk abubuwan da suka faru tsakanin sa da iyayen sa ace kuma tun ba'aje ko'ina ba ya watsar da duk maganar su ya aikata same laifin da suka hane shi da aikatawa..wanda dalilin hakan ma suka ha'da shi zama da ita, yanzu kuma me ze je ya ce da Ammi fisabilillahi, da wani idanu zai dube ta?" Ji yake tamkara ya shirya kawai ya bar garin batare da kowa ya sani ba, amma yasan yin hakan tamkar yayi prooving laifin sa ne...sam ya rasa mafita, takaicin zaman sa da ita ne ya shige shi, yasan da badan ita, ba da babu abinda zai tona masa wannan sirrin a yanzu..sai gashi ita ta tona, sha'afa ma yayi da lokacin dawowar tan da bazai bari ta samo shi yana aikata wannan abin ba, ita da ba amfanin komai take yi masa ba sai ma haifar masa da tashin hankali koda yaushe. Tun 'dazu yake zaune dafe da kansa ya kasa tsinanawa kansa komai, Husnah ta wuce tuntuni amma shi har yanzu bai iya yin koda wanka bane saboda damuwar da ta cika masa zuciya...." Mtheww" ya ja tsaki afili gami da mi'kewa...da tashin sa sai ga shigowan 'kiran Ammi wayar sa. Koda ya ga 'kiran Ammi fargabar sa 'karuwa tayi akan na baya, da farko kamar ba zai 'dauka ba amma yasan yin hakan ma 'karin wani laifin ne. Sai da ya koma ya zauna kafin ya 'daga wayar gami da sallama. Tashi jikin sa sanyi 'kalau ya ta shi ya shiga wanka bayan sun gama waya da Ammin... yasan yau kam ta faru ne ta 'kare kankat,  bai kuma san mai su Ammi zasu ce da shi ba bayan duk nasiha da warning 'din da suka yi masa amma ya watsar...shi kansa kunyar kansa ma ya fara ji yanzu. Wata zuciyar tasa ne tace da shi" ai ba laifin ka bane taya za'a ha'da ka da 'yar yarinyar nan matsayin mata kuma ayi tunanin zaka iya kame kanka bacin ansan yanayin ka?...yasan wannan ba hujja bace da ya kamata ace ya ri'ke amma ta wani 6angaren zancen yayi masa aganin sa ai hakan 'dinne ba shivda laifi. Sharp-sharp ya shirya ya fita zuwa gidan Ammi...inda yaje ya tarar da Ammi zaune a parlour ranta ya kai 'kololuwa wurin 6aci tana zaune kurum ta rafka uban tagumi, yayin da ni kuma nake cikin 'dakin ta na daina kukan a lokacin illah ajiyan zuciya...tun 'dazun.kuma Ammi.bata sake tambaya ta wani abu ba, haka kawai taji aranta cewa shine bashi da gaskiya...'kilan duka na ma yayi. Hakan ka'dai da tasa cikin zuciyar ta ya sanya 6acin ranta ninkuwa akan na baya da yake tasan halin sa bashi da sau'ki wurin hukunci. Yana shiga tun kafin ya rufe bakin sa daga sallamar da yayi Ammi ta fara jero masa tambayoyin tuhuma game da ni. Marairaice murya yayi jin tambayar sa Ammi take ba nuna masa laifin da ya aikata ba, hakan ne yasa shi fahimtar itama labarin bai shiga kunnan ta ba tukunna. Wani sanyi yaji cikin zuciyar sa shiyasa ma ya samu 'karfin gwiwar 'karasowa kan kujera yana shirin zama ya ba Ammi amsa a tsare da fa'din" Ammi ni kuma me zan mata kawai fa rigima ce ke damun yarinyar nan?" Da yaren su ta fara yi mai masifa saboda bata so inji abinda zata fa'da masa, yayin da ya Yah Deen ya zauna dafe da kansa yayi shiru yana sauraren ta duk da ya fahimci bata san komai ba amma still ya kasa sanya idanun sa cikin nata. Ammi kam ta inda take shiga bata nan take fita ba masifa ta ringa yi masa akan sam baya bani kulawa shiyasa zai zo yace da ita bai san me ya same ni, in ba haka ba dubi yarinya ko uniform bata cire ba ta taho tana wannan uban kukan kuma yace bai san komai ba?" Daga 'karshe Ammi  'kwalla min 'kira tayi, sai nayi banza da ita kamar banji ba, sai da ta sake 'kira na kafin na taso na fito idanu na jajazur. Yah Deen kam ko 'daga kai ya kalle ni ma bai yi ba saboda tsananin kunya da ta cika shi...nima 'din kuma ban kalli inda yake ba dan ysananin haushin sa nake ji yanzu. Cikin fa'dan Ammi kaf baiji abinda ya 'daga masa hankali kamar ganin yanayi na ba, saboda a maganar Ammin bai ji abinda ya danganci lamarin ba...sai dai ganin yanda duk na fita hayyaci na ya matu'kar 'daga masa hankali. Ta wani 6angaren godiya yake ga Allah da yasa ban riga na gaya mata ba yana kuma fatan fa'dan nata ya tsaya iya nan kar Alhaji Baba yaji, ni 'din kuma kar na fa'di komai. Gefen Ammi nazo na zauna tare da kwantar da kaina a jikin ta na 6oye fuska ta..." Ta shi ki sanar da ni Abinda ya miki banaso ki 6oyemin komai kinji mama na". Ammi tayi maganar tana 'ko'karin tallafata. A hankali da rawar murya nace. " Bakomai Ammi". Kwafa tayi gami da sake 6ata ranta tace. " Ina wasa da ke ne?" Sai na yi saurin fa'din " Ammi dagaske ba abinda ya min..ni gida kawai nake so nake so in dawo". Yah Deen bai iya ya bayyana farin cikin sa da jin hakan daga bakin Noor ba amma idan kana fuskantar sa zaka ga yanda ya lumshe idanu yana 6oyayyan murmushi na farin ciki. Cikin ransa ya furta" Allah yayi miki albarka Nuree". A fili kuwa yana nan a zaunen sa bai ko motsa daga yanda yake ba. Ammi kam sam tace bata yaddada abinda na fa'di ba, yayin da na cigaba da kuka na  ahankali ina sake fa'din ni gida nake so Ammi dan Allah kice kar na koma can..idan na koma mutuwa zanyi". " Kiyi min shiru ni "Ammi ta daka min tsawa jin ina ambatar mutuwa. Ga Yah deen ta dawo da kallon ta tace" Ka gaya min gaskiya Mu'een...wallahi idan na bincika na tarar da laifin ka wannan lamarin ka tabbatar ba zakaji da'di ba ko?" Da seriousness yace " Haba Ammi ni kenan bazaki ta6a yadda da ni ba, gata fa agaban ki da bakin ta kuma ta gaya miki ba komai...fisabilillahi ni me zan mata da har zan 6oye miki?...in dai zaman gidan take so a barta mana ta yi zaman ta tunda har yanzu takasa sabawa da can in, ni 'din ma ai next week zan koma school insha Allahu kinga ba wata matsala ai". Tun zuwan sa sai yanzu ya iya yin dogon bayani wa Ammi saboda ya samu 'kwarin gwiwa. Ammi hararar sa tayi kana tace" Dama ai ba son zaman nata kake ba shiyasa kayi saurin yanke wannan hukuncin". Yace" Ammi za6in ranta ne fa..yanzu idan nace a a bazata zauna anan 'din bama laifi na zaki gani". Tace" Ko.ma miye ne ai da laifin ka, am sure that da kana mata adalci agidan bazata ce nan take so ba...amma kai babu abinda ka sani sai mugun hali da ba'kar zuciya". 'Kasa yayi da kansa yana fa'din" Sorry Ammi..insha Allahu zan gyara". " Ya rage maka ai..yanzu kam sai ka kawo mata kayan ta dan bazata sake komawan bama balle ka 6ata ranta...gashivsai wani.kakkauda kai kake yi na munafurci..ai.nasan dole baka da gaskiya Mu'een kawai kun 6oye min ne". Sai da ya sosa kansa da hannun sa 'daya yana 'dan murmushi kafin yace" Zan kawo mata kayan Ammi...amma please idan Alhaji yayi magana kice da shi itace kanta tace gida zata dawo kar yaga kaifi na". A takaice Ammi tace " Naji". Murmushi ya sake yi yana jin da'di har cikin zuciyar sa, fatan sa Allah ubangiji ya sa kamar yadda na 6oye yanzun ya cigaba da 6oyuwa cikin zuciya ta kar na bayyana lamarin ga kowa... Tashi yayi yana fa'din barin je inyi sallah zanzo inci abinci idan nayi sallahr. Ko 'kala Ammi ba tace da shi ba har ya fita daga 'dakin. Daga haka ya Ammi  tace da ni" Tashi to ki ha'da muku abinci a dinning kafin ya dawo ko dan kema banga alamun kinci abinci ba.." Kafa'da na no'ke tare da fa'din" Ni na 'koshi". Ammi saurin cire ni tayi daga jikin ta da mamaki tace" Hudah ban san rashin ji fa, dama ko agidan naki haka kuke zama da yunwa ko?" Girgiza kai nayi alamar a a. " To yanzun fa? ko so kike ince ki koma can 'din". Sake girgiza kaina nayi harda fa'din " a a" " Oya to go and serve ur lunch now". Da hanzari na 'daga kai sannan na mi'ke tsaye. Har na fara tafiya sai Ammi ta 'kira ni da sanyin murya tace min zo nan Hudah.." gefen ta na dawo na zauna..nifa hatta Ammin kunyar ta nake ji yanzu har zuciya ta...amma ita bata san hakan ba. Cikin kwantar da murya tace dani " Wani abin ya miki kuke 6oye min ke da shi ko?" Kaina 'kasa nace" Bakomai Ammi kawai fa nayi kewar ku ne". A 'dan fusace tace " Akan kawai kinyi kewar mu shine kike irin wannan kukan Hudah? Meyasa bazaki ce ya kawo ki ki gan mu ba?..kinsan yanda kukan kinnan ya 'daga hankali na kuwa?". Da sanyin murya nace da  ita" Kiyi ha'kuri Ammi bazan sake ba". Hmm kawai tace daga haka tayi shiru...yayin da ni kam na wuce dinning na ha'da masa abincin iya bakin sa na sake komawa 'dakin Ammi na yi kwanciya ta. Koda ya dawo Ammi tayi 'kirana kan batun abincin, sai cewa da ita nayi ni kam na 'koshi. Ammi bata matsamin ba ta bar ni har ya kammala cin abincin sa ya tafi kuwa ban kuma ganin sa ba...dama ni yanzu ba 'kaunar ganin sa nake sake yi ba balle yasa ni yawan tuna abinda naga yana aikatawa...wanda ko giyar wake nasha bazan ta6a iya furta shi ga wani daban ba... Sam ban yi mamakin ganin san da macen da na jima ina ganin su tare ba wato Husnah, nasan kuma ba yau suka fara aikata irin hakan ba, bambamcin kawai shine  na yau 'din yafi 'kona min zuciya ban kuma san dalili ba...sai dai nasan babu mamaki dalilin bazai wuce igiyar aure dake tsakanin ni da shi ba.             Dan sam bansan miye kishi ba balle nasan dililin da yasa ake yinsa...wannan abinda na ganin nan kuwa cikin sallah ta ne ka'dai bana tunawa da shi, sosai abin ya tsaye min a raina, shi yasa a kullum yake 'karamin tsoro da tsanar sa a zuciya ta...a yanzu ko 'kaunar ganin fuskar sa banyi...ko sunan sa banso inji an 'kira. Sai dare ya kawo min kayana akwati 'daya kawai ya kawo min da sauran abubuwan da yasan zan bu'kata. Ammi ce me ce da shi tunda basake komawa gidan zanyi kwana kusa ba ai da ya kawo min kayan nawa gaba 'daya. Sai yace" Ammi tace ta kwaso da kanta idan ta bu'kace su". Ko da Alhaji Baba ma ya dawo abinda Ammi ta sani shi ta fa'da masa...bai damu ba shima illah cewa da yayi dama ina zata iya zama da wannan mai ba'kin halin". Bai ce in koma ba haka kuma bai damu da ya 'kira Yah Deen kan maganar ba...daya ke wannan karan labarin zuwan Husnah bai isa gare shi ba shiyasa tunanin sa ma bai yi zurfi ta can 'din ba..balle da yasan cewa Yah Deen 'din ya kusa komawa shikenan shima ya barni a gidan kawai na cigaba da zuwa makaranta ta. Haka na cigaba da rayuwa gidan Ammi hankali na ya 'dan fi kwanciya acan sai dai a duk lokacin da naji muryar sa ya zo na kan ji tsananin fargaba na shiga ta da bugun zuciya. Gaisuwa wannan badan gudun fa'dan Ammi ba da bazan 'kara gaida shi ba, balle yaga ko fuskata, amma Ammi a kullum tana 'ko'kari sosai wajen nuna darajar da miji ke da shi a wurin iyalin sa. Hakan yasa nake daure zuciya ta ina zuwa inda yake, daga gaisuwar kuwa babu abinda ke sake ha'da ni da shi zan dawo 'daki...hakan da me faruwa tsakani na dashi sai yake 'kara 'daure kan Ammi ranar har ta tambaye ni dama ko can gidan ma irin zaman da muke yi kenan?" Shiru nayi ban bata amsa ba cuz a yanayin da tayi tambayar nasan duk amsar da na bata wata tambayar ce zata sake biyo baya dangin son jin dalili...cuz idan nace nasan zata ce to me yasa yanzu kuma nake yi masa haka?" Ni kuwa sam bani da amsar bata kan irin wa'dannan tambayoyin. Ana gobe zai koma ne Ammi tace in tambaye shi zuwa gidan Ummah ta, raina baya so ma amma daya ke tace dole mace ta tambayi iznin mijin ta kafin ta fita ya sanya ni tilastawa kaina dauriyar tambayar sa..musamnan da yake naji gidan mu zani..dama da wani wurin daban ne da wallahi sai dai in yafe fitar amma bazan ta6a tambayar sa ba. Sai da ya shiga ya gaida Alhaji Baba kafin ya fito wurin Ammi itama ya gaida ta..da yake bayan maghrib ne so shima Alhajin dawowar kenan gidan bai da'de ba, suna gaisawa da ita daga nan kuwa Ammi sai ta wuce side 'din Alhaji Baba bayan ta sanar dani cewa in tambaye shi kar na manta. Ina son zuwa in tambaye shin amma sai nake jin nauyin ta shi in fita, gani nake kamar bazan iya harha'do dogon kalaman da zan iya furtawa ga Yah Deen ba..hakan yasa na cigaba da zama na kan dadduma ina lazimi na da tunanin ta ina zan fara, ban tashi ba tunda na idar da sallar maghrib ina zaune a wuri guda...duk da ina jin haushin sa yanzu amma tun faruwar lamarin nake addu'ar Allah ubangiji ya shiryar da shi ban ta6a tsallake ko rana guda ba. Ina zaune a wurin na ji motsin mutun ya shigo..zato na Ammi ce dan nasan ita ka'dai ke shigowa a duk lokacin da ra ga dama, hakan yasa na fara harha'da 'karyar da zan gaya mata idan ta tambaye ni batun zuwa gun nasa...ban gama tunanin da nake yi ba naji  'kamshin turaren da na tabbatar ba na Ammi bane ta baya. Da sauri na waiga da yake nasan ba 'kamshin da na saba ji ba ne wurin Ammi, sai naji ya zame min ba'ko. Bazata kawai naga Yah Deen na shirin zama kan side drawern gefen gadon Ammi. Komawa nayi na gyara zama na ina ta6e baki tare da cigaba da abinda nakeyi duk dama dai na daina fahimtar komai amma still ban daina yi ba...ban ma san me dame kuma nake anbata ba a lokacin. " Noorul Hudah"! Ya 'kira sunana yana wani jan sunan kamar dole aka sanya shi 'kira,  ban amsa ba haka kuma ban motsa daga yanda nake bai. Bayan wasu sakannivya sake fa'din" Noor". Instead na amsa shi a a sai nace" Ina yini"? Murmushi yayi mai sauti  kafin ya amsa da" Lafiya lau". Shiru ya 'dan biyo baya sai can yace da ni" Gobe zan koma". Tun kan ya rufe baki nace " Allah ya bada sa'a". " Ameen". Yace yana shafa kansa. Tare da kallon 6angaren da nake. Ya so ya ban ha'kuri kan maganar can amma sam baya so ya sake tunowa da shi, shi kansa yanzu haushin kansa yake ji da ya sa Husnah tazo har gidan sa a 'dakin matar sa yayi fasi'kanci da ita...da kansa ya zauna yayi tunani tare da kwatanta abin cikin ransa, ya 'kiyasta yanda yaji ranar da su Imrana suka zo da niyyar ya basu kyautan matar sa kamar yanda yayi musu al'kawari, duk da bai ji cewa hqr cikin zuciayr sa yana son Noor ba amma yanda yaji lokacin ya san da hakan zai faru dagaske da mutuwa ce ka'dai bazai yi ba, 'kilan ma mutuwar ta iya riskar sa saboda ba'kin ciki bai sani ba kuma ko dan saboda Noor ne yaji hakan ba, bai sani ba ko har akan Husnah zai ji hakan....idan hakane kuwa dole Noor ma zata ji ciwon ganin sa gani mafi muni yana aikata zina a gidan da yake na auren ta ne, cikin 'dakin ta da wata macen daban,  duk da 'karancin shekarun ta amma yasan dole zata ji ciwo cuz shi kishi bai san 'kan'kanta ba...dan yanayin tan alamun kishi 'karara ne ya bayyana tattare da ita. Cikin zuciyar sa yayi al'kawari insha Allahu bazai sake neman Husnah ba, bazai sake cin mutnucin auren ta ba, wanda yayi abaya ma yana fatan ubangiji Allah ya yafe masa, daya je kuma zai nemi gafarar ta cuz shivya tilastata zuwa da barazanar zai tona ta wurin mahaifiyar ta, yana jin Husnah navkuka tana ro'kan sa akan yayi ha'kuri ya bar ta ta fuskanci ubangijin ta amma yayi biris ya kashe wayar sa, dole hakan ya tilasta ta sake 'kiran shi ta tambaye shi cewa matar sa fa dacyake tana da labarin an 'daura masa aure shima...sai yace kar ta damu babu komai yarinya ce matar gidan. Cewa ta sake yi kar a ganta kuma a sake zuwa a sanar da iyayen sa..amsar da ya bata shine wanda Hudah taji ranar da ta farka a bacci...idan ya tuna wannan abin ya kan sake jin haushin kansa da kansa akoda yaushe. Ba zai gaya wa Noor a zahiri ba amma insha Allahu saboda ita zai yi 'ko'karin ganin ya kame kansa daga aikata abinda yake yi. Cuz idan har wannan yarinyar ta iya ganin abu makamanci wannan kuma ta iya 6oye wa yasan shima barin zina abu ne mai sau'ki a wurin sa...wannan abin ka'dai da ta aikata ya ja mata wani babban matsayi cikin zuciyar sa da shi kansa bazai iya misaltawa ba. Bakin sa na son furta _kiyafe min_ amma harshen sa sai yayi masa nauyi wurin furta shi, sai ma yake jin gaba 'daya Noor 'din tayi masa kwarjini a idanun sa. Tsaye ya mi'ke da niyyar tafiya...bai kuma niyyan sake furta komai ba, nima ban ko yi motsin kirki daga inda nake ba har ya isa bakin 'kofa zai bu'de sai a sannan nace da shi" Ammi tace in tambaye ka kayi min izni inje gida". Take ya waigo yana fa'din " Wani gida kuma?" Inda yayi tambayar yana kallon bayana dan ko juyowa banyi ba, shi kansa yana mamakin wai 6eran yarinyar nan ce ke yi masa irin wannan abin...hmmm Allah mai sanadi...sai yayi 'dan ta'kaitaccen murmushi. Amsa na bashi da fa'din" Gidan mu zani da wurin dangi na". Wannan karan murmushin mai sauti yayi jin yanayin maganar tawa kamar da gaba.... Sai da ya juya yana bu'de 'kofan kafin yace" Toh ki je mana sai kin tamabaye ni ne?" Shiru nayi ban ce masa komai ba...har ya sa kai zai fita kuma sai dakata sannan yace" Amma fa family kawai na miki izni ki ziyarta ban yarda da shiga ko'ina ba". Ko yanzun ma shiru nayi sai dai bai damu ba cuz yasan sarai na jishi.. daga haka kuma ya fita daga 'dakin yana fa'din"  Sai da safe"...cuz daga masallaci wai bazai dawo gidan ba saboda yau 'din bai jin cin dinner shiyasa. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 🕌🌙 ~RAMADAN MUBARAKH~ 🕌🌙 _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *62* Washe gari kuwa da safe ya koma Jigawa, wanda kafin tafiyar tasa sai da yazo gidan Ammi ya musu sallama ni kuma ya ciro ku'di ya ban masan nawa bane ya ajiye min yayi tafiyar sa, daga" na tafi" babu abinda ya sake ha'da ni da shi, kuma ko da yace ya min hakn ma baki n ta6e ban furta masa komai ba illah harara da na bi ku'din nasa da shi. Ban ko saka 'dan yatsana na ta6a ku'din.ba na bar su nan inda ya ajiye su na cigaba da harkoki na. Sai bayan tafiyar sane ne ma da 'dan jimawa kafin Ammi tazo ta ga ku'din da kanta sannan tactambaye ni sai nace mata" Yayah ne ya ajiye". Ammi da ku'din a hannun ta tace " Shine kuma kika bar su nan?" Inda tayi maganar tana kallo na. 'Dan marairaicecfuska nayi nace " Ammi to ni ina zan kaisu? shine fa da kansa ya ajiye a wurin". "Da ya ajiye 'din ce miki yayi ki ta kallon su ko kuma ki barshi a nan, i thought ke ya ajiye ko?" A hankali nace" Ammi to ki ri'ke a gunki". Kai ta girgiza kawai ta tafi ta bar ni a wurin.   Nima ban jima ba bayan hakan na gama shiri na dan zuwa gidan mu wurin Ummah ta...lokacin da zan tafi Ammi sai ta ce in tafi da ku'din zan yi magana ta hanani...dole ta 'dauko tasamin cikin jakata tare da ha'da ni da tsaraba tace in kai wa Ummah ta. Ranar Allah ka'dai ya san irin farin cikin da nake ciki musamman da naga Ummah ta...'kin zuwa ko'ina nayi saboda so nake na 'dan kwana biyu agidan Ummah ban san komawa can gidan a yau 'din. Sosai naji da'din zuwa gidan kuwa inda nan take na sake cikin gidan mu walwalata duk tacdawo sabuwa har ma 'dan manta damuwar da ke ci na arai. Ammi data ga dare yayi sai ta 'kira Umman mu awaya bayan sun gaisa tace ta ha'da mu...nan nayi mata bayanin ba yau zan dawo ba...Ammi bata damu ba haka bata ce dani komai ba illa sai da safe kawai da tai min. Nan na sake sakan jiki na a gidan ganin Ammi bata hana ni ba. Ko Ummah ta ma da na bata ku'din 'kin kar6a tayi abin sai ya bani haushi sosai, sai da ta ga na fara hawaye kafin ta kar6i 5k ta bar min 15k wai in ajiye a wuri na...nace mata Ammi ce fa tace in zo da shi..ni me ma zanyi da ku'din to?" Ummah ta yi tayi tamkar bata jini ba, kukan da taga na dage da yi ne ma yasa ta ciran 5k 'din wanda ni kuwa kukan nawa har da tunowa da sirrin da na 6oyewa zuciya ta wanda ganin ku'din da ya bani da kansa a hannu na ne ya sani tunowa da shi da halayyar sa..ha'kika wani lokacin furta abu ma yakan sa ya yi ma sau'ki a zuciya yayin da ri'ke abu sam baida wani amfani inba yazama dole ba, nasan da ace na samu wanda zamu tattauna batun da shi na fahimta da zanji sau'ki cikin raina amma bazan ta6a iya yin hirar ga kowa ba, ciki kuwa harda mahaifiya ta...yanzu kam na fahimci akwai sirrin da 6oye shi ya fiye wa kowa alkhairi fiye da furta shi, balle ma ni da ya kasance sirrin mijina ne, ban manta garga'din da akayi min kan ri'ke sirri ba...nasan zan iya ri'ke shi har abada duk da na san bazan iya manta shi cikin raina ba. Na bari dai akan sanin da nayi cewa rufin asiri ga wani tamkar ka rufa naka asirin ne...al'kawari 'daya da na 'daukan ma kaina game da Yah Deen shine zan nayi masa addu'ah ubangiji Allah ya shiryar da shi Allah yasa ya gane hakan da yake aikatawa babban laifi ne a wurin Ubangiji. Sai washegeri muka je gidan su Addah ta saudah ni da Ummie, har  gidan Yaya Usman da sauran 'yan uwan mu dake kusa duk munje yayin da wasu daga cikin su ke min zolayar wai har na canza amarcin ya kar6e ni, ni dai kawai sai dai inyi murmushi cuz' ni ka 'dai na san damuwa zuciya ta. Kamar yadda ya umarceni kuwa banje gidan kowa da yakansace ba ahali na ba, duk iya ziyarar da nayi ban 'ketare maganar sa ba, daga nan kuwa na dawo gidan Umma ta. Kowa ya ganni sukan ce kyauna ya 'karu haka shiru-shiru na ma, hatta ma'kwabtan gidan mu sai da suka yabi tsari na...ni kam murmushi kawai nake yi ban bada amsar komai. A duk lokaciin da na ke6e na a mafiya yawan lokauta na kan tsinci kaina ian mai zubda hawaye wanda duk baya rasa nasaba da Yah Deen, sam ban san dalilin damuwa ta akan rayuwar da na ga yake yi ba, kuma nayi-nayi in manta da lamarin amma na kasa a kullum yana nan sabo cikin zuciya ta. Ban ta6a bari kuma Ummahn mu ta fahimci halin da nake ciki ba, sosai nayi 'ko'kari wajen 6oye mata, ni da kaina nasan nayi wannan 'ko'karin ko da wani bai fa'da ba. Kwana na biyu sannan na koma gidan Ammi na cigaba da zama na,  hankali na a 'dan kwance saboda ko waya bama yi da shi, ina dai gaisawa da su Saif akai akai amma shi kam ban da shi, sai dai inji suna waya da Ammi lokuta da dama ina gefen ta amma ban ta6a ji ya ko gwada ambatan sunana ba balle yace a bani wayar. 'Bangarena nima hakn yafi min da'di dan idan akec zan yi magana da shi nasan kuka ne kawai zai rinjaye ni bazan iya maganar ba...in kuwa hakan yacfaru nasan zuciyar Ammi zai cika ne da tarin tambayoyi. Ashe Ammi ma da kanta hakan da yake yi 'din na bata haushi, kawai ta 'kyale shi ne dan tana so taga iya gudun ruwan sa akaina. Haka take amsa masa gaisauwa faram-faram su kuma sha hirar su amma ko da wasa bata ta6a sako sunana a cikin zancen su. Zancen waya ma nake so in tunawa Ammi zancen  da tace zata sa a siya min amma ina tsoron kar tace ai ban kwantar da hanakalin nawa ba tunda nace ni gida zan dawo, ita kuwa ina ganin kamar ta manta ma da batun, hakan yasa nima 'din dole nayi shiru na barwa lokaci kawai inda rabo na nasan wataran da kanta ma zata sai min in dai Ammi ce ba ma sai na tambaya ba. *****      Bayan tafiyar Yah Deen da Sati uku wani tashin hankalin ya sake faruwa, domin kawai wayan gari akayi Ma'u bata raye Allah ubangij ya amshi abin sa bayan tasha uwar rashin lafiya, tunda ta samu cikin nan bata samu nutsuwar kanta ba...ranar nasha da naji labarin mutuwar nasha kuka sosai,  kuka kamar raina zai fita, bazan manta ba yanda nayi ta damuwa da son zuwa dubata amma aka hana ni, bacin ina jin labarin wahalar jinyar da take sha a bakin mutane 'yan makarantar mu. A kullum tausayin ta 'kara kamani yake yi, bayan uban gorin da ake binta da shi agida cewa ta bi ku'di ta lalata rayuwar ta, haka ma duk ranar da Alhaji Baba ya aika mata da kayan marmari da kaji ko 'yan ku'di ta kan yini cikin bakin ciki na gori akan ta,  gashi ko iya cin abincin ma bata yi bata iya cin komai da ta ci zata harar...maltina ka'dai ne ke iya zama acikin ta shima 'din babu wanda yake siya mata cuz ko Alhaji ya aiko ku'di bata ganin idanun su, babu wanda ya damu da lafiyar ta balle yunwar cikin ta, ga tsananin wahalar laulayi ga zazza6in typhoid da ya sako ta a gaba...a kullum kuka ne aikin ta, yau gashi ta bar mana duniyar ta koma ga mahallicin ta. Alhaji Baba yayi namijin 'ko'kari wajen ganin ya kula da lafiyar Ma'u, saboda yasan koma menene ya same ta 'dan sa ne sanadi. Akwai ranar da ya kawo mota ma da kansa yace akai ta asbiti dan lokacin bata da lafiya amma daga ranar ba'a 'kara sanar da shi rashin lafiyar ta ba. Shi 'din kuma yanzu baya zuwa gidan nasu sai dai kawai yayi aike koda, ya Deen yazo ma bai damu ya sashi zuwa wajen ta ba dan ya bari ne akan idan ta haihu dole maganar auren su ta taso. Allah cikin ikon sa sai lokaci 'daya kawai ya amshi ran baiwar sa. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _🎑🎆🌙Barka da sallah to d all Ummah...Taqaballahu minna min kum...ubangiji Allah ya maimaita mana shi da Alkhairi_ 🙏 _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *63* Tsanar da naji ta Yah Deen cikin zuciya ta a lokacin ni kaina ban san iya adadin ta ba...ban ta6a jin na tsani mutun sama da yanda nake jin haushin sa a lokacin ba. Ji nake tamkar duk duniya baza'a ta6a samun mai mugun hali irin nasa ba, saboda duk lokacin da tunanin sa zaizo raina baya ta6a zuwa min da Alkhairi,  shiyasa nake gani kamar nasa halin na musamman ne. Yau gashi sanadin sa Ma'u ta ta rasa ranta, ta tafi tafiya irin ta har abada, ta tafi ta bar duniyar cikin 'kuncin zuciya..ni da kaina a lokacin na yi fatan Allah ya saka mata zaluncin da aka yi mata sau babu adadi...ban sani ba ashe sakayyar har da ni ma da nake tare  da shi zata shafa...Hafsat dubi abinda aka yiwa yarinya ta dalilin mugun halin sa, Jasmine 'di na....bata iya ta 'karasa maganar ba kawai ta sunkuyar da kanta ta sanya kuka mai matu'kar tsuma zuciya. Hafsat kanta sai da ta share hawaye amma gudun kar a rasa mai lallashin wani a cikin su ya sanya itan ta daure ta shanye nata kukan ta bawa Noor ha'kuri cikin nuna mata ai komai dake faruwa da bawa 'kaddara ne, duk abinda ya samu bawa to rubutacce ne tun kafin ya zo duniya 'kaddarar sa ta zanu..shiyasa ake so bawa yai imani da ko wace irin 'kaddara idan ta same shi mai kyau ce ko kuma akasin haka, wannan shine cikar imani da Allah da kuma Manzo. " Hakane...". Noor tace tana me share hawayen ta da suka kasa tsaya mata, tana goge wa amma wani na sake gangarowa...amma a hakan ta daure ta furta..." Allah ubangiji ya ji'kan Ma'u, Allah yasa ta ta huta, Allah ya ji'kan duk wa'danda suka mutu ya kyautata makwancin su, muma da muke raye Ubangiji Allah ya sa namu 'karshn yayi kyau,  Allah yasa mu mutu muna masu aikata Alkhairi ba sharri ba.." " Ameen Thumma Ameen" Hafsat tace cikin sanyin murya, yayin da Noor ta cigaba da labarin ta kamar haka" Babban abin tausayi ma shine  Malam Barau, dattijon kuka ya ringa yi da hawaye yana sharewa, Alhaji Baba kam komai tsaya masa yayi cak, musamman da yake yana ganin cewa 'dan sa ne sanadin komai, abin ya tsaya masa arai sosai har ya hana shi sukuni. Da shi akayi komai har aka sada Ma'u da makwancin ta na gaskiya, hatta abincin da za'a bu'kata gidan rasuwar Alhaji Baba duk shi ya 'dauki nawin komai har aka 'kare kar6an gaisuwa, bayan bakwai jama'ah kowa ya koma harkokin gaban sa amma banda Alhaji Baba. A kullum zaka same shi ne cikin tunani, yana so ya sanar da Yah Deen batun rasuwar amma idan ya tuno shi sai yaji takaici ya kama shi haka ya sa ya kasa sanar da shi da kuma nuna masa muhimmancin sa a wurin. Alhaji baya ta6a yin kwanaki biyu batare da ya ziyarci mahaifin Ma'un ba saboda zuciyar sa ta kasa nutsuwa wuri guda. Ko gidan gonar sa badan mutane masu amana ne akai ba da komai lalace masa zaiyi dan baya tuna zuwa can kwata-kwata illah waya da suke yi, hakan ma sai dai yace da su suyi duk abinda ya dace kawai kar su damu. Ammi ce ta sanar da  Yah Deen batun rasuwar inda yaji abin har zuciyar sa saboda mutuwar ta masa bazata, sosai jikin sa yayi sanyi...amma ko da Ammi ta nuna masa dacewar zuwan sa dan gaida mahaifin ta take ya kawo wani excuse cuz baya son zuwa cikin irin wannan taron musamman ma da yasan cewa sai an ta nuna shi idan yazo wurin, shi kuwa ba ha'kuri ne da shi rayuka sai su 6aci a banza. Da gama wayar su da Ammi take sai ya 'kira Imrana da tun baya zuwan su gidan sa basu sake wata gaisuwar kirki ba, ko rasuwar Ma'u Imran bai 'kira shi akai ba, nan suka nunawa juna alhini cuz shi Imrana bai ma san da batun ba ashe tuni yana Kano sai da Yah Deen 'din ya sanar da shi kafin nan daga nan kuwa suka yi sallama kowa ya ajiye wayar. Cikin sati na biyu da rasuwar Ma'u sannan Yah Deen yazo gida bisa umarnin Alhaji Baba da yake ma a lokacin duk an watse babu kowa sai mutanen gari. Lokacin da Alhaji ya umarce shi da zuwan ma sosai hankalin sa ya tashi, zaton sa ko magana ce akaina ko kuma abinda ya faru abaya kafin tafiyar sa, hakan ya sa natsuwar sa tayi masa 'kaura dan Alhaji bai kawo batun Ma'u cikin maganar tasa ba. Da niyyar sa yace su taho da Ishaq amma sai yayi tunanin kar Ishaq yaji wannan uban abin kunyar da ya tafka wanda basu da masaniya sam akanta, hakan yasa ya shirya kawai ya taho dan ba zai iya yiwa Alhaji musu bane ma baya ga haka da babu abinda zai sashi tahowa. Sai da ya iso ne ma kafin ya 'dan ji natsuwa da yaji dalilin zuwan nasa ashe ba abinda yake zato bane gaisuwar gidan Malam Barau ne kawai. Bai wani damu ba cuz can cikin zuciyar sa ma wani kwantaccen farin ciki yake ji wanda daga baya bayan jin labarin rasuwar Ma'un yayi tunani, a ganin sa Allah ya so shine ma shiyasa ya kar6i ranta bayaga haka da ina zaije da ita da abinda zata haifa a duniyan nan...ba'a farin ciki da mutuwa saboda kowa mutuwar zaiyi amma shi kam sai dai yace Alhamdulillah...duk da haka zuciyar sa na 'dan jin abin a sirrance saboda shi kansa yasan ya zalunce ta ya ci mutuncin 'kuruciyar ta  da wayo. A fili kuwa sosai yake nuna alhinin sa ga Alhaji Baba da duk wanda zancen ya ha'da su. Washegari da sassafe Alhaji Baba ya sa shi gaba suka wuce gidan Malam Barau ya gaida shi ya kuma nemi gafarar sa bisa abubuwan da suka faru, inda Malam Barau ya nuna masa ba komai ai 'kaddara rubutacciya ce sai dai fatan a kiyaye gaba, Allah kuma ya shirya, yace karamcin da mahaifin sa yayi masa ma ka'dai ya ishe sa..Ma'u kuwa addu'ah ce kawai tsakanin su a yanzu, Ubangiji Allah yajiqan ta da Rahama ya kyuatata makwancin ta. Nasiha ya yiwa Yah Deen sosai game da rayuwa sannan suka taho gida bayan sun yi masa goma ta arzi'ki. Kwanan sa biyu ya sake komawa Jigawa wanda a kwanaki biyun nima sau uku ka'dai na ga fuskar sa, tsanar sa ce ta ke sake girma a zuciya ta yanzu, musamman da na san cewa shine sanadin mutuwar Ma'u...haka abin yake kuwa ko a bakin mutane 'yan kaiwa da kawowa ma abinda suke yawo da shi kenan...hatta Ammi a lokacin na lura abin ya dame ta sosai sai dai ban san takamamman dalilin damuwar tata ba dan bamu tattauna batun da ita ba. Ina dai da tabbacin itama 'kilan taji ra'de-ra'den da jama'ah ke yi ne game da rasuwar, kawai sai naga ta 'kara jana a jiki ta jan yawaita bani ha'kuri da nasiha mai kwantar da hankali wanda a hankali na fahimci duk ta nayin hakan ne saboda ta rage min damuwa, cuz tasan dole yanda taji nima zanji koma fiye da hakan. Ni kuwa da na fahimce ta sai na dinga 6oye damuwa ta agaban ta, sosai nake nuna mata babu komai ni cikin zuciya ta hakan kuwa ya matu'kar faranta ranta a yanda na lura. A gidan Ammi Yah Deen yayi kwanaki biyun nasa har ya koma, sai bayan tafiyar tasa ne ma nake jin Ammi na labarin irin gyaran da za'a yiwa 6angaren sa na gidan saboda yace yanzu anan gida zai na zaman hutun sa har sai an kammala aikin wancen gidan gaba 'daya. Nikam baki na ta6e cikin raina na furta damuwar sa ai ni me ruwa na..shi yasani da ba'kin halin nasa. *****        *Bayan watanni biyu* Su saif suka dawo hutu, sosai zuciya ta ta cika da farin cikin dawowar su saboda sune dama abokan hira ta. Har Ammi na min dariya lokacin da nake ta sauri da zumu'di wajen ganin na shirya musu lafiyayyen abinci. Ammi ce ke gyara min ta na nuna min abinda ban yi dai-dai ba yayin da na zage na nuna mata 'ko'kari na sosai..ita kanta ta yaba min da 'ko'karin da nayi wajen saurin koyan kalolin girki sosai kuma ta bayyana min farin cikin ta kan haka matu'ka...tace tana so ranar da miji na ma zai dawo in yi masa fin na yau wanda zai manta inda kansa yake idan ya 'dan'dana..ta 'karashe maganar tana murmushi. Ni kam da jin ta ambace shi sai na ta6e baki na a 6oye a fili kuwa shiru nayi, ganinbhakan yasa fa'din" Baki ce komai ba kuma". Da sanyin murya nace" Ammi shi kam sai dai ke ki yi masa ni bazan iya ba kin san..." Murmushin ta ta 'kara fa'da'dawa sannan tace" Ai tunda yayi aure nima na watsar da shi, ga matar sa na me zan sake dinga yi masa wahalar kuma ke de ki shirya kawai ranar da duk zai zo a kitchen zaki yini". Ban kalle ta ba na shagwa6e murya nace" Ni dai Ammi a a". " Toh shikenan naji". Ta fa'di tana 'yar dariya. *****      Kamar de kullum Saif ne ka'dai me min fara'a acikin su banda Zaidu, shima Saif 'din yanzu sai naga duk ya canza min, duk da haka sai da nayi ta jera masa 'korafin share nin da yayi lokacin da nake wancen gidan da tafiyar da suka yi batare da sun min sallama ba. Ha'kuri kawai ya bani yana fa'di kin san yanzu kin zama Miss Yaya sai a hankali, dole sai mun iya takun mu...yayi maganar yana 'yar murmushi daga haka kuwa bai sake fa'din komai ba har suka nufi wajen cin abinci. Ko wajen cin abincin ma da suka fara yabawa take Ammi ta sanar da su ai duk nice nayi, bu'dan bakin Saif sai cewa yayi" Ashe yaya ya huta shi kam ya ji da'di". Zaidu kam bai ce komai ba, Ammi kam murmushi kawai tayi yayin da ni kuma na kawar da kaina, na tsani wannan ha'din sam, ace komai nawa sai an dangana ni da shi. Wani abu guda da na lura game da su yanzu shine kamun kai, ba kamar baya da muke zama muyi wasa da karatu cin abinci duk tare ba, yanzu kam hira ka'dai ke ha'da mu, hirar ma sai an ha'du a parlour lokaci zuwa lokaci. Ammi ma taja kunne na game da zama da su ta garga'de ni da kame kaina matsayi na 'ya mace inda ta sake yi min tuni da igiyar Auren da ke kaina. Nice na basu labarin mutuwar Ma'u inda duk suka nuna alhinin su sosai sai dai sam ban iya na fa'di musu asalin sanadin mutuwar tata ba na barwa zuciya ta..na kuma san ko Ammi ma da 'kyar ne ta sanar da su ainahin labarin. Zuwan su Saif sosai ya 'debe kaso mafi girma daga cikin damuwa ta, yayin da farin ciki ya lullu6e ni gaba 'daya, sam na manta da batun Yah Deen na watsar da lamarin sa, sau tari sai dai idan cikin hira ake tuno min da shi ko kuma idan naje bacci wasu lokutan yake zuwa raina  har nayi bacci. Satin su biyu da dawowa shima ya zo gida kuma gidan Ammi ya sau'ka dagaske...shiyasa naga an 'kara gyare 6angaren nasa an canza tsarin komai. Sosai naga ya canza min ya sake zama babban mutum da shi ga kyau da ya 'kara komin sa tsaf, gashin kansa sai shai'ki yake yi sosai naji ya birge ni amma ban nuna a fili ba na cigaba da sha'a ni na. Shima bai damu da ni ba duk da kuwa cikin ransa ba haka bane, amma ya basar...ko bayan isowar sa ban yi niyyan gaida shi ba amma da yake muna zaune ne da Ammi a lokacin dole na daure ba'kin hali na na gaida shi, sau 'daya ya kalle ni ya amsa da" Lafiya" A ta'kaice. Sanye nake da ba'kin Hijab akaina 'dan madaidaici cikin wa'danda nake zaman gida da su, hannaye na duk na daga ciki illah 'kafata, da yake ma ba'ki ne hijab 'din sai ya 'kara fito min da haske na sosai, da yake ma kwanaki biyu kenan da Ammi ta sa aka zo akayi min kitso har gida tace ayi min harda jan lalle ma mai zanen flower ya kuwa yi kyau sosai ni kaina ya birge ni...a lokacin ban san dalilin da yasa akayi min lallen ba, kawai dai ji nayi Ammi nata 'korafin wai na da'de banyi lalle ba sai kace ba mace ba, ni idan ba'a inyi ba da kaina bazan yi tunanin inyi ba...zato na ko haka kawai ne ta sa akayi min sai daga baya na fahimci ashe dan zuwan Yah Deen ne. Tashin hankali na ya fara ne lokacin da Ammi ta zo da batun na daina kwana anan 'dakin daga yau lokacin ina shirin bacci na tace da ni in shirya in wuce wurin mijina ba anan zan kwana ba. Take na marairaice fuska na fara yi mata kuka amma Ammi ko kula ni bata yi ba, sai ma zaman jiran in kammala shiryawar da tayi...tana fa'din ai Alhaji Baba ne yace ba ita ba idan kuma zanja da maganar sa ne to sai taje ta sanar da shi. Jin sunan Alhaji cikin maganar ne ya sani yin shirin dole ba dan naso ba ina yi ina share hawaye na. Duk yanda naso in nuna mata ni banson zuwa wajen sa amma Ammi fir ta'ki yadda a gaba ta tisani har parlour ta zauna tace maza in wuce tana kallo na, na kuskura na yi wani abin kuma ita da ni ne kuma sai ta gayawa Alhaji Baba. Nasan zaman Ammi nan wurin babbar alama ce ta bayyana kafiyar ta akan zuwa na wurin nasa hakan yasa dole na wuce raina ba'ki 'kirin ina share hawaye. Ammi kam murmushi kawai tayi da taga na wuce cikin ranta ta furta" Ja'ira abubuwa nata faruwa amma still hankalin ta bai kai ko'ina ba, haka kawai ta jefa sunan Alhaji cikin maganar saboda tasan shi 'din ina jin nauyin sa sosai ba kamar ita ba. Lokacin kusan 'karfe goma ne na dare dan tara ra wuce tuntuni, zato na zan samu ma yayi bacci shiyasa da na isa sai da na tura 'kofar kafin nayi sallama ta ciki-ciki...ina saka 'kafata sai hoton sa da Husna ya dawo raina da sauri na tsaya cak sannan na 'daga idanu na kallo shi. Zaune yake daga bakin bed yana duba cikin system 'din sa inda ya bada dukjan hankalin sa akai,  ban ji ya amsa sallamar da nayi ba sai dai kawai naga ya 'dago ya kalle ni, fuskar sa ba yabo ba fallasa haka muka tsaya kallon kallo inayi ina ha'de gira ta dan abinda ke cikin raina daban yake. 'Kasa yayi da kansa bayan ya gama 'kare min kallo sama da 'kasa, cigaba da abinda yake yi yayi batare da ya furta min komai ba. Ganin hakan yasa ni jin wani sabon takaicin ya sake kamani, kawai sai na saki kuka harda sheshshe'ka. 'Dago kansa da kuma rufe system 'din nasa duk lokaci guda yayi su sannan ya mi'ke tsaye a fusace yana tambayar" na miki wani abu ne? Ko cewa nayi kizo ki dame ni?" Ganin yana nufo inda nake ya sanya ni jan baya ka'dan tare da girgiza kaina alamar a a. Cak ya tsaya, hannun sa 'daya ya shafo gashin kansa da shi sannan ya dube ni, zaiyi magana nai saurin taran sa da fa'din" Ammi ce tace in zo in yi bacci anan.." " To kukan fa?" Yayai tambayar yana kallo na. " Ni banso". Nace cikin muryar kuka. Sai yace " To na ri'ke ki ne? ki koma abinki mana". Nace " Ammi ai ta hana ni". Yatsan 'daya ya 'daga ya nuna bed 'din sa dashi sannan yace" Wuce to ki kwanta bance ki dame ni da kuka da wannan daren ba". 'Kin motsawa nayi na cigaba da tsayuwa ta a wurin ina murza idanu, tsaki ya tsaki na takaici gami da 'kun'kunin yarinya kullum sai shirme. Juyawa yayi ya shige bayi abin sa wanda ganin hakan yasa ni saurin 'karasawa gadon na haye na du'kun'kuna cikin hijabi na. Kafin ya fito kuwa har nayi bacci, sau 'daya kawai ya dube ni sai ya 'dauke idanun sa haka ya gama shirin baccin sa ya kwanta gefe na ban ma sani ba. Ko da safe kafin in tashi har ya tashi bama zaka ga wata alamar da zata bayyana maka cewa a gefe na ya kwana ba. Inayin sallah kuwa na fice daga 'dakin nasa kamar wata marar gaskiya. Kamar wasa tun daga ranar Ammi bata 'kara bari na na kwana a wani 'dakin ba sai a wurin sa, tun bana sakin jiki na har na zo na saba abin ya daina damuna. Da nazo idan na gaida shi sai nayi kwanciya ta ko hira bata ha'da ni da shi. 'Bangaren Yah Deen kuwa shima 'din da farko bai wani damu da zuwan nawa ba, amma yau da gobe sai yake jin wani sabon yanayi na 'darsuwa masa a zuciya  game da ni. Ya kan yi 'ko'kari wajen ganin ya kaucewa hakan kamar yanda ya kaucewa  Husnah abaya amma abin ya faskara, sosai yake jin wani abu na fisgar sa izuwa gare ni da ya jima bai tsinci kansa cikin irin yanayin ba. Kamar yanda yayiwa kansa al'kawarin rabuwa da Husnah hakan ne ya faru, duk dama ya daina ganin ta a school bai kuma san dalili ba, amma koda wasa bai ta6a gwada 'kiran layin ta ba balle yaji meke faruwa, shi da kansa yana so ya nemi yafiyar ta bisa abubawan da suka ta faruwa abaya, amma ya san koda ya 'kira ta yanzu bazata ta6a yadda da duk abinda zai fa'da mata ba shiyasa kawai ya 'kyale ta. Kuma bai iya ya tattauna batun ko da Ishaq bane haka ya bar lamarin cikin ransa, sannan yayi 'ko'karin tsare zuciyar sa daga fa'dawa tarkon wata macen bai bari ko wacce mace ta birge shi ba balle yayi wani tunani akanta tunda ya koma karatun sa kawai ya sa agaba. ***** Ranar da na cika kwanaki na na takwas da fara kwana wurin sa ranar cikin farin ciki nake jin zuciya ta saboda nayi waya da Baban mu da daren ranar har ma yayi min albishir 'din ya kusan zuwa Shuwarin domin yanzu jikin sa Alhmdulillah da sauqi, jinin ya 'dan sauqa, da yake tunda jimawa baya jin da'di har Alhaji Baba ma yaje can Jos 'din ya dubo shi haka ma Yah Usman yaje. Alhaji Baba ne da kansa ya ha'da ni da shi a wayar ko yau 'din ma, inda bayan mun gama waya da Baban mun yace dani insha Allahu zai siya min waya ta nima in huta da ta aro tunda mijin nawa bai san yayi abinda ya kamata ba. Farin cikin nawa sai suka zama tagwaye, sosai naji murna ta kamani, take kuwa naje nayi wa su Ammi albishir da su Saif ina murna ta. Alhaji Baba kam murmushi kawai yayi ya girgiza kansa. Haka har na tafi 'dakin nasa fuska ta da walwala, yau sallama ta ma da 'dan sauti nayi ta, yana kwance akan gadon yana daddana wayar sa. Sallama ta tace ta sa shi ya mi'ke zaune da mamaki yana kallo na. " Ina yini " nace da shi, sai amsa da lafiya a takaice. A hankali na 'karasa bakin gadon 6angaren da nake kwana ina shirin kwanciya ya dakatar da ni da fa'din sunana " Noor" yace madadin Hudah da kowa ke 'kira na da shi. " Na'am" na amsa shi tare da waigowa na dube shi. " Je kawo min ruwa na sha". Yace cikin natsuwa. Bance komai ba kawai na mi'ke na yi waje kaina da hijabi na kamar kullum, tun lokacin da naga yanayin halitta ta ya 'kara canzawa shikenan na 'kullawa hijab kamar wawiya, musamman ma da yanzu nake zuwa wurin sa bacci haka nake kwana in tashi da abu na a kaina. Yanzun ma da idanu kawai ya raka ni har na 'karasa fita daga 'dakin, haka na dawo na same shi kamar yanda na barshi a zaune. Wajen sa na nufa da sassanyan ruwan faro da na 'dauko na mi'ka masa. A hankali ya 'dago hannun sa na dama ya dam'ki ruwan tare da lumshe idanun sa duk biyu...bansan me yasa ba nima karo na farko tunda na fara kwana a 'dakin sai yau naji inaso inga fuskar sa da kyau musamman da yanzu yake kusa da ni, a hankali na 'dago idanu na na sau'ke su akan nasa lumsassun idanun" Masha Allah". Naji zuciya ta na fa'di a sirran ce...motsin da bakin sa ya fara ne sani maida idanu na wajen bakin na sa.." Yayi sanyi sosai..'dauko min wani please". Ya fa'di tare da bu'de idanun sa dake lumshe take sai muka yi 4 eyse dashi...bazata kawai naji harbi a 'kirji na da ya sa 'kafafu na yin sanyi 'kalau nan take sandaiyyan sanya 'kwayar idanu na cikin nasa. 'Kasa nayi saurin yi da nawa idanun sannan can ciki na amsa shi da fa'din" to"...ina shirin juyawa sai naga ya ajiye ruwan da na kawo masan kan side drawer, sannan da hannun sa mai sanyin naji ya kamo hannu na, da sauri na 'dago na kalle shi da mamaki 'karara kan fuskata, ina 'ko'karin fizge hannun nawa daga nashi naji yace" Me ya faru kuma?" Banyi magana ba kawai na kalli hannun san inda ya ri'ke ni, shima sai yayi 'kasa da idanun sa zuwa wurin, murmushi 'kayatacce yayi sannan yace" ba kyaso?" Nayi shiru. " Me yasa to?" Still ban bashi amsa ba illah 'ko'karin cire hannu na daga cikin nasa da nake ta faman yi amma na kasa. Da 'dayan hannun sa ya 'dauko ruwan daya ajiye 'din sannan ya bu'de hannu na ya samin na ri'ke" Ki tafi da shi". Still bai sake min hannun ba ya 'dago ya kalli idanu na yana murmushi yace da ni" Kije in kin dawo zaki fa'da min me yasa kike son zama da hijab 'din nan akanki". Da fa'din haka ya saki hannu na...sai naja baya da sauri ina sake kallon sa, idanu ya lumshe take ya kuma bu'dewa yana murmushi, sai na juya na fita daga 'dakin zuciya ta na dokawa. Ina tafiya har sar'kewa 'kafafuna suke yi saboda ru'danin da na shiga, zuciya ta ta kasa tantance min abinda ke damin Yah Deen a yau 'din gaba 'daya. Yana yin abu ne tamkar ba shi ba. *Fatan Anyi Sallah lafiya.....Allah ubangiji yasa ibadun mu su kasance kar6a66u* 🙏 _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmerh ce*😍 https://www.facebook.com/106273870926057/posts/149762286577215/?app=fbl 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *64* Yanzu Ammi ta daina damuwa da ni saboda taga na 'dan saki jiki na, kuma ko na shiga wurin san bana sake fitowa. Abu 'daya dai da kullum baya raba ni da ita shine kafin in shirya in tafin sai ta tisa 'keya ta nake tafiya wanda burin ta kawai a kullum yanzu shine taga tafiyar na tafin matu'kar na riga na shiga 6nagaren nasa shikenan itama sai ta wuce shiyasa ma ko da ya aiko nin 'dauko masa ruwan tun fitowa ta na farko ban tadda ta a parlour ba. Yanzun kuwa da na fito jin yanda 'kafafu na ke sar'kewa da yanda 'kirji na ke dokawa ne ya sanya ni samun wuri na zauna akan kujera na 'dan maida numafshi na. Sai da na tabbatar na samu natsuwa kafin na tashi na canzo masa ruwan, ko da na shiga 'dakin kuma sai ban gan shi ba. Da'di naji har cikin raina, da sauri na 'karasa dan inyi in ajiye masa inyi baccin 'karya kafin ya tuhume ni amma tun kafin in 'karasa tsakiyan 'dakin na gansa ya fito daga bayi kamar dama jiran shigowa ta yake yi, take wata fargabar ta sake kamani mai tsanani. Jikina sanyi 'kalau na 'karasa na ajiye masa ruwan gefen da na same shi 'dazu ko iya sake kallon inda yake ban yi ba...'dagowa nayi da niyyar isa nawa 6angaren in kwanta sai naji nayi karo da mutun ta baya na, da sauri na waigo cike da firgici da ya bayyana har kan fuska ta. Kafin nayi wani yun'kuri sai naji hijab 'di na ya bar jiki na gaba 'daya. 'Kan'kame jiki na nayi zan saki kuka sai yayi saurin dakatar da ni da tsare ni da idanu tare da tsaida yatsan sa saman bakin  sa. Taimako 'daya Allah yayi min kayan bacci na masu yalwa ne riga mai botila da kuma dogon wando farare ne masu zanen flowers maroon amma duk da haka sai naji na kasa sake wa a gaban sa. " Miye matsayi na a wajen ki?" Naji ya tambaye ni bayan ya cire hannun sa daga bakin nasa. Ban bashi amsa ba sai nayi baya ka'dan ina dama fuska ta amsar da zan bashin sam banji ta cikin brain 'dina ba. Biyo ni yayi da taku 'daya zan sake matsawa baya kawai sai naji ni jikin bed na...take hawaye ya gangaro min tsoro ya kamani cuz ba wurin guduwa kuma. Yanda naga yake kallo na ya sani sake yun'kurin neman hanya inda na sake yin baya zuciya ta cike fal da tsoron sa, cikin rashin sa'a sai na fa'di da baya na kan bed 'din ina neman hanyar zamewa sai naga ya matso daf da ni, fuskar sa kusa da tawa, kallo na ya tsaya yi daga idanu na zuwa dukkan ilhirin fuska ta...yayin da zuciya ta ta cigaba da dokawa da sauri da sauri jiki na ya fara kakkarwa sosai. Da hannun sa naga ya shafo kansa tare da juya idanu..." Ba ance ni mijinki ba ne?" Naji ya sake fa'di cikin jan maganar kamar dole aka sanya shi. Saboda ina so ya 'kyale ni nayi saurin 'daga masa kaina sama alamar " Erh" Sai yace" To daga yau banson wannan abin a inda nake.. kinji ko?" Yayi maganar tare da 'dago hannun da ya ri'ke Hijab 'dina da shi dayake har a lokacin yana na'de a hannun sa. Kaina na sake 'dagewa ina bin hannun san da idanu kuma har a lokacin jiki na bai daina rawa ba, buri na kawai inji ya bar kusa da ni...shiru ya 'dan biyu baya na sakanni, yayin da ya cigaba da 'karewa fuska ta kallo batarecda ya 'karacfa'din komai ba idan na yun'kura sai ya tsare ni da idanun sa dole na ha'kura illah hawaye. Sa ban fahimci komai daga yanayin da yake ciki ba a lokacin ko ka'dan, ni dai damuwa ta ya 'kyale ni ne kawai, hakan yasa hawaye na ya kasa tsayawa. Da yatsa 'daya ya shafo hawaye na dake gangarowa, a hankali cikin sanyin murya yace dani" Kukan fa na menene?" Ban bashi amsa ba na yi shiru saboda ni agani na tambayar tasa bata da amsa a waje na... cikin idanu na ya kalla na tsawon sakanni uku kafin a hankali naga ya mi'ke tsaye tare da juya min baya sannan yace" Je ki kwanta". A tsarge na mi'ke zaune ina share hawaye na gangara 'daya gefen bed 'din na kwanta can daga nesa sosai da inda yake kwanciya, haka na du'kun'kuna wuri guda kamar marainiya ina share hawayen da bansan dalilin fitar su ba har bacci 6arawo ya sace ni ban kuma kallon inda yake ba balle in san me ke faruwa. ***** Washegari kuwa da sassafe na fice daga 'dakin tun da asuba da ya tafi Masjid na gudu 'dakin Ammi na 'karasa bacci na acan, ko da ya dawo daga sallah ma da bai ganni ba murmushi kawai yayi ya san ba mamaki guduwa nayi dan naga ya fita masallaci. Wunin ranar kaf bai ga idanu na ba, ko da wasa banyi gigin fitowa parlour ba dan ko su Saif ma sai bayan da na tabbatar baya gidan kafin na fito muka 'dn yi hira da su.   Matu'kar na tabbatar yqna gidan to.bana fitowa har dare yayi, lokacin kuma sai naji hankali na ya fara tashi dan nasan dole sai na je inda yake dan Ammi ba bari na zata yi ba. Sallar Maghrib da isha'i duk cikin rashin kuzari nayi su...ko da na idar kuwa sai na mi'ke nayi kwanciya ta akan daddumar har bacci ya fara 'dauka ta sai naji Ammi na tashi na kamar dai kullum... Ban san yadda zanyi da Ammi.ba na tabbata da da ne babu abinda zai hana ni sanar da ita damuwa ta amma yanzu ban iyawa, jin Ammin nawa nake yi kamar wata daban. Raina ba'ki 'kirin na tashi na shiga bayi na barta a wurin, na shafe a 'kalla kusan mintina sha biyar da gangan kafin na fito ai kuwa na sami Ammi zaune tana jira na. Ban yi mamaki ba dan nasan indai Ammi ce fiye da hakan ma zata jira ni dan kawai taga iya gudun ruwa na, bata ce min 'kala ba ko da na fito in...haka nima ban yi mata magana ba so nake da kanta ta fahimci cewa har yanzu ni fa ba son zuwa can 'din nake ba...amma ga mamaki na Ammi kam ko a jikin ta. Tsaye naga ta mi'ke sannan tace" Ina zuwa". Da fitan ta sai na nemi kayan bacci na kamar yanda na saba kullum riga da dogon wando dan ni da irin su nafi sabo sai dai na yau 'din zallar pink ne...turare ka'dan na fesa a jiki na hakan ma ina yi ina tura baki na ina 'ko'karin sanya hijab 'dina sai ga Ammi ta dawo. Murmushi tayi da gani na cikin nuna yabawar ta tace" Masha Allah yarinta ba dai kyau ba". Shiru nayi kawai na sunkuyar da kaina 'kasa, nayi tunanin Ammi zata cecinyi zama na ne idan taga ina hakan amma ga ga mamaki.na sai sa6anin hakan na gani domin ko kula ni ta wancan 6angaren Ammi ba ta yi ba. " My dear dare yayi sai da safe ko". Ta fa'di tana min murmushi wanda ke fita tun daga zuciyar ta. Da jin haka sai na kasa ha'kura kawai na shagwa6e fuska ta kamar zanyi kuka nace" Ammi please yau in kwana anan mana wai ni dole sai naje can in ne?" " Ni ai ban hana ki ba...amma kije ki tambayi mijin ki first in ya yarda sai ki dawo nan da kwana abinki ni ba ruwa na..but for now kama hanya ki wuce sai da safe". A fusace na 'daga 'kafafu na bar 'dakin.raina duk ba'ki'kirin...ciki-ciki nayi sallama na shiga inada na same shi zaune da system 'din sa agaba kamar dai rannan. 'Dauke kaina nayi daga kallon sa na sunkuyar da kaina 'kasa inda na 'karaso cikin rshin.kuzari. " Yaya ina yini". Nace da shi lokacin da na isa gefen bed 'din...ban jira jin amsar shi ba kawai na haye na yi kwanciya ta ina sake share hawaye na. Ko kula ni kuwa bai yi ba ya cigaba da abinda yake yi ban san tsawon lokacin da ya 'dauka zaune a wurin ba saboda baccin da ya 'dauke ni. Cikin baccin naji kamar ana ta6a jiki na, ko da na bu'de idanu na sai na ci karo da shi a kusa dani...a 'dan firgice na yun'kura zan tashi sai naji hannun sa saman jiki na...juyo da fuska ta nayi na kalle shi ina daga kwancen sai ya sakin min murmushi 'kayatacce. " Matsoraciya.." ya furta 'kasa-'kasa, inda yana maganar ni kuma ina jin yanda hannun sa ke yawo min a jiki. Kasa jurewa nayi na sake yun'kurawa da niyyar tashi take na ji sau'kan sautin muryar sa cikin kunnuwa na inda ya daka min tsawan" Mai miye hakan wai?" Luf nayi ban sake motsin kirki ba illa hawaye da ke gangaro min ta gefe da gefen idanu na. Tsawon mintina uku muka 'dauka a haka sannan ya cire hannun sa daga saman jiki na ya sake rungumo ni cikin jikin sa bai ce da ni uffan ba har bacci yayi gaba da shi...ni kam da na kasance a matau'kar takure sai baccin ya kasa 'dauka ta...shi kuwa baccin sa yayi cikin kwanciyar hankali batare da wata damuwa ba. Motsin kirki idan nayi sai inji ya sake janyo ni jikin sa sosai...haka dole na ha'kura na zubawa sarautar Allah idanu wanda daga 'karshe hawayen nawa daina fita suka yi ma a hakan nima har baccin ya 'dauke ni rungume a jikin sa. Tun daga ranar salon kwanciyar mu da shi ya canza zuwa yanda ya ga dama...haka kullum inaji ina gani zai rungumo ni jikin sa har muyi bacci  tun bana sakin jiki na har nazo na saba da hakan na ma daina damuwa. Alhaji Baba ma ya cika al'kawarin sa kamar yadda ya fa'da ya kawo min wayata sabuwa dal akwalin ta 'yar yayi harda sim 'dina...ranar murna kamar zan tashi sama, Saif yayi ta min dariya yayin da Zaidu ya ta6e baki yayi gaba abin sa. A wajen Ammi na kar6i numbern Ummah ta na 'kira ta nayi mata albishir 'din an sai min waya nima...daga ita sai Baban mu amma bai 'dauka ba...sai bayan kusan awa guda kafin ya zo ya 'kira ni shima ina murna na sanar da shi bayan mun gaisa..da fara'ar sa ya sanya min albarka tare da min garga'din sai inbi a hankali, in kula da mutuncin aure na. Ammi ce da kanta ta ta sanar da Yah Deen wayar da Alhaji Baba ya sai min, Yah Deen bai ce komai ba sai" Allah ya sanya Alkhairi" kawai da ya furta ba yabo ba fallasa fuskar sa. A ranar da dare da naje kwanciya ya tambaye ni wayar wai zai gani sai nace na bari a 'dakin Ammi yace inje in 'dauko. Zuciya ta fes naje na kawo masa wayar dan duk zato na ganin.kawai zai yi, ko da ya kar6a kuwa sai naga ya ajiye gefen bed yayi shirin bacci abinsa. Hakan bai bani mamaki ba dan a tunani na ko dan saboda dare ne shiyasa. Washe gari da na tashi da yake dama hankali na akan wayar ne so sai na duba inda naga ya ajiye jiya sai kuma ban ganta ba, haka na ha'kura na wuce cikin gida batare da ita ba. Gashi bai dawo daga masallaci ba har a lokacin balle in tambaye sa.       Zuciya ta fal tunanin inda ya kaimin waya ta, tsoro na kar yace bazan kuma bani ita ba. Ko bayan da gari ya 'karasa wayewa ma ban iya na naje inda yake musamman saboda wayar ba ni dai na zauna inajiran ko zai bani da kansa.       A duk kuwa lokacin da naji muryar sa ya shigo hankali gaba 'daya nake tattara wurin sa wai ko zanga ya ciro ya bani amma ko alamun hakan ban gani daga gare sa ba. Kamar wasa kuwa Yah Deen bai bani wayar ba har yamma, sosai na damu da kewan wayata dan kuwa na fara sabawa da ita, ko da na yiwa Ammi maganar ma sai tace min tsakanin mu ai ita babu ruwan ta. Abinda ta fa'da 'din sosai ya 'kara min haushi dan nasan indai ya Deen ne idan ya ga dama ba zai bani ba in ba Ammin ta sa baki ba, shiru nayi kawai na zuba wa sarautar Allah idanu...ni ka'dai sai ina mita cikin zuciya ta, mutun baka siya min abu ba kuma an siya min kana ba'kin cikin da shi. Ko da dare kuwa ban samu damar tambayar sa ba dan naga kamar ba'a dai-dai yake ba ransa 6ace yake wanda har kan fuskar sa zaka fahimta halin da zuciyar sa take ciki, tsoron ma yi masa magana naji dan bansan dalilin canzawar tasa ba. Ranar a 6angaren sa nayi sallar Asubah na jira har ya dawo daga Masjid, shi kansa yayi mamaki da ya dawo ya tarar da ni amma bai ce da ni 'kala ba, sau 'daya kawai ya dube ni ya kau da kansa. Gai she ni nayi a 'darare da tsoron ko bazai amsa ba, amma daga yanayin da naji muryar sa na fahimci da 'dan sau'ki. " Yaya ba ka ban wayar tawa ba fa har yanzu". Na fa'di cikin rawar murya da marairaita kamar mai neman gafaran wani babban laifi. Shiru yayi ya zuba min idanu...cikin natsuwa yace" Ni me kike yi da wayar ne?" " Ina 'kiran Ummah ta, kuma zan 'kira Baban mu ne". Na bashi amsa cikin sauri. Murmushi naga yayi na gefen baki sannan yace min" Su ka'dai kawai kike 'kira?" Sama na 'dage kain alamar " Erh" da hannun sa ya nuna min drawer inda ya ajiye wayar yace min je ki 'dauka amma ki kula kinji?" Nace to ina murna har cikin zuciya ta. Ina 'daukan wayata kuwa na ficewa ta daga 6angaren sa, dama abinda ya zaunar da ni kenan. Ammi naje na nunawa nace ai ya bani wayar tace" Kin huta ai". A takaice ta fa'di hakan tana 'yar murmushi. Baban mu shine mutun na farko da na fara 'kira amma still yau ma bai 'daga ba. Ban damu ba dan nasan yau 'din ma idan yazo yaga missedcall 'dina zai 'kira ni...dan haka sai na 'kira Ummah ta muka gaisa amma muryar ta sanyi 'kalau naji, koda na tambaye ta kuma sai tace da ni bakomai. Daga su ban kuma 'kiran kowa ba kawai na saka wayar tawa acaji...ban kuma bi ta kanta ba na tafi sha'ani na har bayan kusan 2hrs kafin nazo na cire ta a charge nan naci karo da missedcall 'din Baban mu guda 'daya wanda aka 'kira 57 mins back...ina shirin sake 'kiran sa sai naji Ammi na zuba salati daga parlour a 'dimauce nan hankali na ya kasu gida biyu. Da sauri na mi'ke na nufi parlourn na sami Ammi tsaye da hannu dafe da 'kirji tana fa'din" Alhaji yaushe hakan ya faru?" Daga wannan maganar na fahimci da Alhaji Baba take wayar. Tunawa nayi da lokacin da ya bar gidan nan bai wani jima ba..." to me kuma ya faru?" Na tambayi zuciya ta. Ban ji amsan da aka bata daga 'dayan 6angaren ba sai gani nayi kawai ta koma ta zauna bisa kujera tana girgiza kanta tare da fa'din _Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un_ 'karasawa nayi gaban ta da sauri na tambaye ta" Ammi me ya faru?" " Bakomai" Shine amsar da ta bani sai kuma naga hawaye na gangaro mata sirara, haka da na gani sai ya sake 'dage hankali na sosai take nima na saki kuka ni kam har da sheshsheka dan ganin Ammi na da kanta tana kuka...ina yi ina sake tambayar ta abinda ya faru. " Haba Ammi da kanki...?" Naji muryar sa kamar daga sama yana fa'din haka daga bakin parlour. Ammi bata kula shi ba haka nima a hankali ya 'karaso ya zauna gefen Ammi sai kuma ya dafe kansa..." Ni da nake kuka ina tambayar Ammin ni dakawa tsawar inyiwa mutane shiru sannan yace in tashi maza inje in shirya in fito zamu wani wuri". Haka yace dani yana kallo na. Duk da nayi mamakin maganar tasa amma sam koka'dan banga fuskar da zan tambayi inda za'a je ba. A hankali na tashi ban bar kukan ba haka kuma ban fasa mamakin shirin da yace inje inyi ba. Sharp-sharp na shirya na fito haka ma Ammi, tare muka fito dashi babu mai cewa 'kala cikin mu duka, Yah Deen ne da kansa ya sau'ke mu a 'kofar gidan Ummah ta nan na tarar da wajen gidan duk mutane, take zuciya ta ta tsinke haka kawai naji tsoro ya shige ni sosai. Ammi na kalla na je fa mata tambayar abinda ke faruwa anan 'din cikin ki'dima sai tace min bakomai. Banji amsar Ammi ya gamsar da ni ba dan haka sai na bu'de motar cikin sauri nayi gaba inda na tunkari mashigar gidan mu. Abinda kunnuwa na suka  fara cin karo da shi shine sautin koke-koke.       Da mamaki na 'karasa cikin gidan nan tarar da Addah ta kamar ranta zai fita saboda yanda ta fita hayyacin ta tana kuka..kukan nima na fara a ki'dime na isa gare ta na zube kan gwiwoyi na" Addah.." Nace cikin kuka..Abinda ta fara furtawa shine" Baban mu...Baban mu Hudah, Allah ya kar6i ran Baban mu da safiyar yau 'din nan". Cak kuka na ya tsaya na bu'de baki ina kallon ta da mamaki har da 'kan'kance idanu na...lokaci guda sai kuma na jijjiga kaina nace" Kai Addah ba shi ba dai, sai dai wani, 'dazun nan fa naga 'kiran sa cikin waya ta ina ma shirin 'kiran sa ne sai wani abin ya 'dauki hankali na ta ya kuma za'a ce Allah ya kar6i ransa". " Shine mana Hudah a asbiti fa suka kwana...." Ta sake bani amsa da alamun tabbatarwa. " Nayi waya da Ummah amma bata sanar da ni ba kuma..." Ban 'karasa maganar ba nayi shiru sakamakon tuno yanayin yanda naji muryar Ummah da safennan da na 'kira ta. " Ke nan dagaske Baban mu ne ya rasu?" Na sake tambayar zuciya ta.    Wani kukan ne ya 'kwace min mai tsuma zuciya... Allah sarki rayuwa, ashe duniyar bakomai bace ga 'dan Adam...Allah ya ji'kan Ban mu da Rahama Allah yasa aljannar Firdaus ta kasance makomar sa ta har abada. Ha'ki'ka munyi rashi babba.. A can Jos akayi jana'izar sa aka kaishi gidan sa na gaskiya da kyakkyawar shaida a bayan sa. Su Alhaji Baba da su Yah Deen da sauran 'yan uwa duk can Jos 'din suka je sannan washegari suka dawo. Su Zaidu ma sun zo gaisuwa inda suka shigo hatmr cikin gida suka gaida Ummah ta da sauran 'yan uwa. Ammi kuwa dama kullum muna tare, ta kan zo da safe da yamma ta koma gida sai wata goben kuma. Kwana na biyu a gidan mu da wata safiya da Ammi zata zo sai ta taho min da waya ta. Ina kar6a sai naji hawaye na gangaro min a hankali musamman da na tuna 'kiran da na gani na mahaifi na na 'karshe. Shiga nayi cikin wayar na sake dubawa wani hawayen na sake zubo min ina tuna mahaifi na da karamcin sa...Ammi ko da taga haka sai ta ce da ni da wayar zata koma ai in dai haka zan riga yi...". Kife wayar nayi kan 'kirji na na juya mata baya na cigaba da share hawaye na. 11 da 'yan mintina na safiya lokacin ina can cikin 'dakin Ummahn mu ina kwance ina tunani, gefe na wasu ne daga cikin dangin mu yawancin su matasan 'yan mata ne kamar ni suna 'yar hira...Vibration naji waya ta nayi na neman agaji lokaci guda sai naji zuciya ta ta tsinke sanadiyan tuno Baban mu da nayi saboda da jin dirin wayar shi ya fara zuwa raina amma koda na duba sai naga ba'kuwar number ce ba ta shi ba. Ban 'daga ba har ta tsinke ina kallon ta zuciya na dokawa, take wani 'kiran ya sake shigowa wannan ma ban 'daga sai da ya kusan yankewa kafin na 'daga. Shiru nayi bayan na sada wayar da kunne na. " Ya dai" Da naji an fa'di daga 'dayan 6angaren ne ya sanyani saurin fahimtar wanda ke 'kiran nawa. " Bakomai" nima na bashi amsa a ta'kaice ina murza idanu. " Kina lafiya ko?" " Umm" na bashi amsa 'kasan ma'koshi. " Ya ha'kuri kuma?" " Alhamdulillahi". " Har yanzu kina kuka ko?" " A a" " ance min kuka kike yi kullum".. Shiru nayi ina sake jin idanu na na tsatstsafo da hawaye..taya bazan yi kukan rashin Mahaifi na ba...na ayyana cikin zuciya ta. " Kina yi masa addu'a kuwa". Naji ya sake tambaya ta. Da" Umm" na bashi amsa 'kasan ma'koshi. Sai yace " Yauwa abinda zaki na yi masa kenan yanzu ba yawan kuka ba kinji?" " Uhum" " Allah ya ji'kan sa da Rahama" " Ameen" Nace a hankali. " Ina Ammi?" Ya tambaye ni sai nace " Tana waje..bari in kai mata" Saurin dakatar da ni yayi da fa'din " a a barta anjima zan 'kira ki kinji". " Uhum" Daga haka ya yanke wayar...ni kam ri'ke ta nayi a hannu na ina binta da idanu na" _Yah Deen_ ". Na furta cikin zuciya ta, ji nake tamkar wani ne daban ba shi ba. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *65* Mamakin sa be 'kara kamani ba sai ranar da aka cika 7days da rasuwar Baban mu ranar kamar daga sama naji ana fa'din wai ga Deeni mijin Hudah sun shigo cikin gida gaisuwa. Ina 'dakin Baban mu ni da wasu 'yan uwan mu da basu wuce sa'anni na ba, su biyun su ma suke hirar su ban fiya saka baki cikin maganar su ba, da jin abinda aka fa'din kuwa haka kawai sai naji na mi'ke tsaye ta kafan labile na le'ka nan na hango su dur'kushe suna gaisuwa shi da abokan sa guda uku, ni kam ma ban tsaya na lurako da su waye yake taren ba akan sa ka'dai na tsaida idanu na. Tun ranar da ya 'kira ni a waya bai sake 'kira na ba, na kan yawaita tsammanin ganin 'kiran sa ya shigo cikin wayata amma shiru  kwana hudu kenan rabo na da ko jin muryar sa, ban ta6a tsammanin cewa nayi kewar sa ba sai yanzun. Kaina na jingine daga jikin bangon gefen 'kofan na bar kallon su, ko 'yan matan da nake tare su da a 'dakin ma babu wacce ta bi ta kaina da yake dama ba wani hira sosai ke shiga tsakanin mu ba, hakan yasa suka cigaba da hirar su batare da sun kula da yanayin da nake ciki ba... ban san cewa na shiga dogon tunani tsaye a wurin ba har sai da naji ana 'ko'karin shigowa ciki daga waje sannan na dawo hayyaci na...Addah ta Maryam ce ta shigo" Yauwa ashe kina nan ma...". Ta fa'di tana 'kare min kallo" Me ya sameki kuma Hudah?" Ta 'kara tambaya ta da alamun mamaki 'karara kan fuskar ta. 'Kasa nayi da idanu na sannan na bata amsa da fa'din" Bakomai Addah". Bata ce dani 'kala ba sai kawai ta bi ta 'kare min kallo sama zuwa 'kasa sannan ta saki ajiyan numfashi mai sanyi" Mijin ki yazo zasu shigo, abokan sa ne inajin suke son gaida ki". Bata tsaya ta saurari jin amsa ta ba kawai ta juya ga sauran dake 'dakin tace" Biba ku kintsa ba'ki zasu shigo yanzu". " Toh". Suka bata amsa da shi cikin ha'din baki daga haka naga ta juya da niyyan barin 'dakin,  yayin da naji 'kirji na ya ri'ke ni haka kawai ban san dalili ba, tsintan kaina nayi da tambayar" Wai da gaske ne zasu shigo 'din?" Fat fat fat naji zuciya ta ta harbawa lokaci guda, ban iya nace da Addah ta komai ba har ta 'karasa barin 'dakin, a hankali na lumshe idanu na sannan na bi 'dakin da kallo a tsanake. Ba laifi 'dakin nasan koma waye za'a iya kar6ar sa a ciki batare da damuwar komai ba, balle Yah Deen da abokan sa ka'dai. A hankali na koma na zauna gefen su Biba tare da gyara zaman mayafin na...ba bu'katar sai na sanar da wa'danda muke tare a 'dakin domin nasan ta riga tayi musu bayanin komai dan haka ban kuma ce da su 'kala ba kawai nayi shiru. 'Dayar mai suna Fati itace ta ta jefa min tambayar" wai su mijin nawa ne zasu shigo?" Da kai na bata amsa alamar" Erh "sai tace ita dama tana so ta ganshi dan bata ta6a ganin sa ba kuma taji ana fa'din wai 'dan gayu ne". 'Dan murmushi kawai nayi mata sai ta 'kara da fa'din" Dan Allah idan yazo ki nuna min shi kinji..juyawa tayi ga Biba tace kema Biba ba kina so ki gansa ba?" Duka Biban ta kai mata tana fa'din" Allah ya shirye ki ke kam". Zabura tayi gefe tace" ba wani ai gaskiya ne". Duk yanda nake jin zuciya ta na harbawa amma hakan bai hana ni yin murmushi da jin irin maganganun nasu ba. A fili cewa nayi da su " Kar ku damu insha Allahu zaku ganshi". nace dasu ina mai yin 'kasa da kaina. Kafin ta 'kara yin wata magana sai muka ji sallama daga bakin 'kofar shigowa 'dakin. Imam ne kan gaba sai Ishaq sannan Yah Deen da wani a bayan sa da bansan sunan sa ba. Jan Hijab 'dina na 'karayi ya rufe min rabin fuska ta yayin da su Biba suka gyara zaman su da kyau tamkar wasu manya...gaisuwa da ta'aziyar Baban mu su Ishaq suka yi min wanda cikin muryoyin nasu ko ka'dan banji tashin muryar sa ciki ba. Duk yanda su Biba suka 'kagu da su ganshi amma kasa sakin jikin su suka yi balle su fahimci waye Mu'een 'din a cikin su, daga gaisuwar kawai naga sun mi'ke tsaye duk suka yi waje ya rage daga ni sai su Yah Deen. Su Ishaq ke 'dan labarin sanin da suka yiwa Baban mu musamman lokacin da ya bada aure na ga Yah Deen wanda tun a lokacin kusan dukkan su suka yabawa karamci da dattakon sa,  ashe kwanaki 'kalilan suka rage masa...yanzu sai dai Fatan ubangiji Allah yayi masa Rahama yasa Aljannar firdausi ta kansace makoma agare sa...muma ya kyautata namu tafiyan...Ameen   Daga 'karshe Ishaq ne ya 'dan 'kara yi min nasihar ha'kuri da kuma yadda da 'kaddara inda ya nuna min cewa irin su Baban mu ba iyalan su ka'dai ne ke damuwa da rashin su ba..yace kusan duk wanda ke tare da shi dole yayi alhinin rashin sa, gata 'daya da yakamata mu yi masa a yanzu itace addu'ah ka'dai...da kansa yayi masa addu'ah muka shafa wanda daga haka duk suka mi'ke tsaye suka nufi hanyar fita. Suna masu sake maimaita Allah ya ji'kan Baba da Rahama. Kaina 'kasa nake amsawa da" Ameen Ameen" ina wasa da yatsun hannu na yayin da nake jin siraran hawaye na gangaro min saman kunci na a hankali. Ban yi ta6a tunanin har haka Baban mu zai samu yabo daga abokan Yah Deen ba musamman akan auran mu, ji nayi duk jiki na yayi sanyi 'kalau, cikin raina na ayyana" in dai har haka ne kuwa da iznin Allah zan yi ha'kurin zama da shi cikin kowace irin hali, in dai har akan aure na da shi mahaifi na zai ri'ka samun kya'kkyawar Addu'ah to kuwa zan 'daura 'damarar zaman aure na, Yah Allah ka mantar da ni komai, Yah Allah ka sanya fahimta tsakani na da shi. Ban yi tsammanin akwai wanda yayi saura cikin 'dakin ba da yake naji shiru, amma haka kawai sai naji ni a tsarge tamkar ana kallo na, a  hankali na 'dan 'dago kaina ka'dan nan naci karo da shi zaune shiru ya zuba min idanu. 'Kasa na sake yi da kaina batare da na furta komai ba illah tunanin abinda ya zaunar da shi a anan 'din da na fa'da, nan na tsinkayi muryar sa yana fa'din" Har yanzu kukan kike yi ko?" Girgiza kaina nayi a hankali sannan na fara goge hawayen dake fuska ta da hannu na 'daya. Tsaye ya mi'ke ya sanya hannun sa 'daya cikin aljihun wandon jikin sa sannan ya kalle ni yace" Anjima zamu koma Jigawa da su Ishaq fatan ba wani abu ko?" Da kai na bashi amsa alamun a a...sai yace" Toh Saif zai kawo miki sa'ko anjima ko zuwa gobe, in kuma akwai wata matsala ma ai ga  Ammi ko kuma ki 'ki 'kirani a waya kawai ki sanar da ni kinji". Ya 'karashe maganar yana duban agogon dake 'daure a tsinysiyar hannun sa. " Uhum" Na bashi amsa da fa'din hakan batare da na kalle shi ba. " Na tafi" Ya sake fa'di yana me nufan bakin 'kofa cikin tafiyar sa mai birgewa....da farko rasa abinda zance da shi nayi dan haka nayi shiru ina bin bayan sa da idanu kawai...dai-dai ya isa bakin 'kofa zai fita sai na tsinci baki na da furta" Allah ya tsare". Take kuma na sake yin 'kasa da kaina. Cak ya tsaya sannan ya waigo ya dube ni, fuskar sa ba yabo ba fallasa ban kuma ji ya amsa addu'ar da nayi masan ba balle insan matsayin ta kawai sai naga ya sa kai ya fice daga 'dakin abin sa. Zugum nayi kamar kurma idanun 'kyam wuri guda ina bin hanyar da yabi da kallo...ni kaina ban san me yasa nayi masa addu'ar ba, kamar yadda yanzun ma ban san me nake tunawa ba haka kuma na kasa fahimtar matsayin da zuciya ta take a yanzun da naji cewa zai tafi Jigawa ba. *****        Ko bayan tafiyar sa ban koma gidan Ammi ba, zama na a gidan mu nake jin ya fiye min kwanciyar hankali domin ina ganin Ummah ta da sauran 'yan uwa na sai nake jin bani da damuwar komai. A hankali duk jama'ah na nesa da na kusa suka watse ya rage saura mu ka'dai, ko gaisuwan ma yanzu an rage zuwa sosai hatta Ammi ta kan 'dauki lokaci bata zo ba...haka ma 'kawata Binta ta kan yawaita zuwa tana tayani hira, wani lokaci har yini mukan yi tare yayin da wasu lokutan bara jimawa take komawa. Sa'ar da naci ma 'daya ne domin duk cikin su babu wanda ya matsamin da batun cewa in koma gidan Ammi. Baba Alhaji da kansa ya kan yawaita yin aike na ku'di ko wani abu yace akawo min bayan ko wanda Saif ya kawo min bayan tafiyar Yah Deen ma har yau ban ta6a ko sisi a ciki ba. Waya kuwa bana 'kiran kowa daga Anty Zainab yayye na sai Ammi, ita ma idan na 'kira ta bata 'dauka sai dai ta yanke ta 'kirani daga baya...ko Yah Deen 'din ban ta6a 'kira ba ban ta6a ko tunanin 'kiran sa ba, hasalima ni ko saving number shi cikin wayar ban yi ba,  haka kuma shima banga ya sake 'kira na ko sau 'daya ba. Har akayi 40 days 'din Baban mu aka gama ina gida..wanda tun kafin ranar su Saif suka koma school da yake hutu ya 'kare, ni kam ma ban san me yasa yanzu naji bana son zuwa makarantar ba sam naji ta fice min aka. Ammi ce ma da kanta ta fara yi min maganar makarantar har ta tattaro min shirgin uniforms 'dina ta kawo min amma ko sau 'daya ban iya naje ba. Lokacin da Addah Maryam zata koma ne nace zan bita Ummah ta ta hanani, nan na fara yi mata kuka sosai na 'daga hankali na kan batun tafiyar har Ammi sai da ta sani nan ta ro'ki Ummah ta da fa'din abar ni man naje tunda ba 'dadewa zanyi ba Ummah ta tace " a a ba inda zani tace hala kun manta ne cewar matar aure take yanzu ba kamar da ba". Murmushi Ammi tayi domin sai yanzu ta fahimci Ummah da manufar hana ni tafiyan duk da bata fito fili ta bayyana ba amma hakan bai hana Ammi fahimtar ta ba.   Cikin ranta ta bari akan cewar da ta koma gida zata 'kira Yah Deen ta gaya masa taji shi kuma me ze ce. Hakan kuwa akayi, Ammi bata ta6a tunanin bama waya da shi ba, so a yanda tayi maganar sai ta nuna masa cewa idan munyi waya ko da na tambaye shi batun tafiya dan Allah kar ya 'ki amincewa, tanaso taje mahaifiyar ta kuma ta hana ta wai saboda tana da aure". Yace" Gaskiya ne ai Ammi matan aure na yawo ne dama?" " Ba yawo bane fa Mu'een sistern ta take so tabi...". Tun kan ta rufe baki ma ya tare ta da fa'din" Sistern ta har ina kenan?" " Ban sani ba...kana min irin wannan tambayar nice fa na haife ka ba kai ka haife ni ba". Ta yi masa maganar a 'dan masifance. Kansa ya sosa sannan yace" Sorry Ammi amma ai naga anyi resuming school shine kuma zata wani wuri saboda me?" " Ka tambaye ta mana zata gaya maka ai, shikenan saboda makaranta bazata yi ziyara ba?" Sai yace " To Ammi taje abinda ni ba ruwa na...Allah ya bada sa'a". Daga haka ya yanke wayar yana mai jin haushi cikin ransa amma ya danne bai bayyana ba. Bayan tafiyar Ammi da muka ke6e da Addah Maryam sai take shan cikina akan yanayin zama na da Yah Deen dan tunda take bata ta6a ganin ko waya ma muna yi ba, tace bata ga wani alamun kulawa tattare da 'dayan mu ba...tace da alamu ma har yanzu baki san me manufar auren da akayi miki ba". Ni kam ban 6oye mata komai ba na sanar da ita yanayin zama na da shi, abu 'daya ne ban bayyana mata ba shine ganin sa da nayi da Husnah, haka kuma ban sanar da ita cewa dalilin kenan da yasa da na dawo gidan Ammi da zama ba...na riga na yiwa kaina al'kawarin bazan ta6a sanar da kowa wannan abin ba, duk da nasan bani da ranar mantawa da shi, a kullum idan har zan zurfafa tunani na to dole sai  wannan mummunan photon ya zo raina. Duk da hakan ma sosai naga ta nuna alamun mamaki 'karara kan fuskar ta, a fili ta furta dama ai irin wannan auren galibi haka yake kasancewa sai dai in mutun ya dage sannan yake samun kwanciyar hankali, amma kafin hakan sau an kai ruwa rana, tace shiyasa sam baku damu da junan ku ba, nan ta fara yi min fa'dan wai ai nima da laifi na, wannan ganganci ne ne na aikata, me yasa ni idan zaman ya 'daure minbaki bazan nemi shawarar kowa ba, tace mu miye amfanin mu matsayin mu na yayyanki ai dole ne muyi iya 'ko'karin.mu wajen ganin daidaituwar farin cikin gidan ki, amma kika 6oyewa kowa, nasan ko Ummah bata san komai ba game da zaman kun nan ba ko?" Na girgiza kaina tace" Ammi fa?" Sai nayi shiru..masifa ta hau ni da shi me yasa tunda ya tafi ni ban 'kira sa ko a waya ba? haka kika ga ake yi ne?" Shiru na sake yi mata cuz ni kaina ban san dalilin ba. Sai da ta daka min tsawa kafin na 6ata rai nace" Addah shima fa bai 'kira ni ko sau 'daya ba tunda ya tafi". " 'Kaniyar ki....wallahi Hudah tun wuri ki dawo hankalin ki ki san me kike yi..tun ranar da aka 'daura miki aure fa ya kamata ace kin bar wannan shirmen a baya". Tace dani cike da 6acin rai tana nuna ni da yatsa. Shagwa6e fuska nayi kamar zanyi kuka nace" Addah dan Allah ni toh me zan masa?" Shiru tayi ta zuba min idanu tana kallo na, sau'kar da murya tayi sannan ta 'kara da fa'din" Ina fatan dai ke da kanki kin san halin mijin naki ba sai an fa'da miki ba?, me kike tunanin zai yi dake shi da yake hul'da da 'yan mata da suka take ki a komai? Wannan yarinyar Ma'u ka'dai ma in kina da tunani ta isheki babbar misali Hudah, ke kina tunanin a hakan da kike yi har miji zai iya dawo da hankalin sa gare ki?" Idanu na hawaye kawai suka fara tuno asalin halayen Yah Deen da nayi cikin zuciya ta, ni ka'dai na san me nake ji a duk lokacin da na tuno irin abinda idanu na suka gane min yana aikatawa..a gani na Yah Deen ko me zan aikata a duniyan nan hankalin sa ba zai ta6a juyowa zuwa gare ni ba, saboda naga irin matan da yake mu'amala da su, ni da kaina nasan ko cikin mafarki ban isa in kamo 'kafan Husnah a komai ba, toh dan me yasa zan dami kaina bacin nasan abu ne mai wahalar gaske ganin faruwar hakan. Cikin muryar kuka nace da ita" Addah toh ni nace ina son hankalin sa ya dawo gare ni ne....?" Tun kan na rufe baki na ta tare ni da fa'din" Ki min shiru 'yar 'kauye kawai, wallahi ke dai wannan karatun naki sam ban san amfanin sa ba..jibe ki kamar zaki yi abin kirki idan angan ki nan kuwa ba haka ba, Hudah ke baki san cewa kin girma ba ko? sa'annin ki nawa aka yi musu auren suka je suka zauna lafiya a 'dakin mijin su ke kin tsaya wani banzan shirme dan kin samu da ma ko?" " Nima ai ba fa'da muke yi ba Addah". Na bata amsa ina share hawayen idanu na. Idanu ta zaro sannan tace" Ikon Allah! anya Hudah kina da wayo kuwa? da alamu 'kauyen cin ki ba mai 'karewa bane har abada, tun wuri fa wallahi  ki natsu ki ja mijin ki a jiki tun kafin lokaci ya 'kure miki...yanzu ina wayar ki?" " Tana nan". Na bata amsa ina mai tura baki na jin tace da ni 'yar 'kauye. Sani tayi na 'dauko wayar wanda bayan na kawo wayar ta kar6a ta ajiye gefen ta. Maganganu tayi min cikin natsuwa inda ta ringa nuna min muhimmanci da darajar da miji ke da shi a gun matar sa...manufar aure da kuma asalin dalilin da yasa ake yin sa duk sai da ta sanar da ni cikin natsuwa. Wasu maganganun nata ma ni kunya suka bani sosai amma ganin ita bata damu ba yasa kawai nayi 'kasa da kaina na cigaba da sauraran ta. Ta 'dauki tsawon lokaci tana yi min bayani sannan daga 'karshe tace in kwantar da hankali na indai ina son in bita can Darazo to dole sai nayi abinda zata saniyi yanzu. Tace ke kanki kin sani ko Ummah ma bazata ta6a barin ki ki tafi ba har sai ta tabbatar da yardar Deen kafin nan dan haka ki 'kira shi yanzu ki gaishe shi sannan ki ro'ke shi batun tafiyar.      Tace duk da tasan 'kiran da zanyi masa a yanzun bazai 'dauke shi da muhimmanci ba saboda dan kaina nayi shi ba wai dan inji ya yake acan ba amma dai still yana da kyua in 'kira shin kuma zai iya jinsa daban ta 6angaren sa. Duk wannan bayanan da tayin kaina 'kasa ban kalle ta ba har sai da ta kai aya kafin na 'dago kaina nace da ita" Addah ai ni bani da numbern sa a wayar?" " Kamar ya kuma bki da numbern sa Hudah?..baku ta6a waya da shi bane dama?" " Mun ta6a yi sau 'daya". " To ki duba cikin wayar mana...." Tayi maganar tana mi'ka min wayar tawa. Ansa nayi na shiga inda ya nasan zan samu numbern na tafi can 'kasa ina dubawa, ni da kaina nasan babu numbern da banyi saving ba sai ta shi ka'dai, hatta Zaidu nayi saving numbern shi duk wanda na ta6a yin waya da shi to bana ajiye wayar har sai nayi saving numbern, ta Yah Deen ce ka'dai ban bata wajen zama cikin waya ta ba. Ban wani sha wahala wurin nemo numbern ba domin ita ka'dai ce babu suna, na riga na samu amma sai na kasa sanar da Addah Maryam cewa na samu, shiru nayi na zubawa wayar idanu kamar me neman wani abu ina tunanin ta yadda zan fara magana da shi idan na 'kira shi. Bansan lokqcin da na cika iska cikin baki na na furzar ba tare da 'dan 'dage kaina sama ka'dan. Ganin hakan yasa Addah Maryam jefa min tambayar" Wai har yanzu baki samu bane?" Sai nace " A a ban gani ba, ga dai wata number amma ban sani ba ko ta shin ce". Nayi maganar ina mi'ka mata wayar tawa, bata kar6a ba sai tace da ni" Ni kuma me zan yi da ita kina mi'ko min, ki gwada 'kira mana kiji ko shi 'din ne". Fa'dan hakan ke da wuya take sai naji zuciya ta ta fara harbawa da sauri-sauri...marairaicewa nayi nace" Addah ni inna 'kira toh me zance masa dan Allah...shi fa kullum masifa ce da shi?" " Ikon Allah ke da a tunanin ki haka zaku cigaba da zama ne? Ke da mijin ki amma kike irin wannan maganar?" Nace" Ni wallahi Addah tsoro nake ji". Sai kiyi ai, idan kin gama tsoron sai ki 'kirasa ina nan ina jiran ki..." Mita ta cigaba da yi ina da take fa'din" Ashe dama ma kinsan numbern ta shi shine dan kin raina min wayo kike wani ce min baki sani ba ko?" Yi nayi.tamkar zanyi kuka ina 'kif-'kif da idanu ina kallon ta. Cike da masifa tace" Sai fa kin 'kira, ke bari kiji ko ma ba dan batun tafiyar ba a yau 'din nan in kinga baki 'kira yaron nan ba to 'kaddara numfashi na ne ya tsaya cak wallahi, shashancin banza kawai, idan haka ake yi ai bazaki ga kowa na zaune lafiya a gidan sa ba, maza kira shi yanzu ki gaida shi ki tambaye shi ya karatu sannan kice dashi kina so za ki bi Addar ki Darazo muji me ze ce". " Toh Addah in ya'ki amincewa zaki ro'ka min shi?" " Allah ya kiyaye ai in ke baki da wayon ki tambayi mijin ki abu da kanki sai dai kawai kawai ki ha'kura zuwa wani lokacin idan wayo ya ratsaki". Ta fa'di haka ne a fili amma cikin zuciyar ta cewa tayi wannan 'dan rainin hankalin yaron ina zanje ina wani kwantar masa da murya a banza salon.ya ha'da ni da ke in duk ya raina mu". Ta 'karashe da ta6e bakin ta. Hannu na har rawa yake yi lokacin da nake 'ko'karin yin dialling numbern shi,  sai na tsaya kallon wayar kamar wawuya. Yanda nake jin wayar ke 'kara nuna alamun 'kiran ya shiga haka nima nake jin zuciya ta na harbawa...daf da zai yanke sannan ya 'daga amma sai naji yayi shiru...nima kuma sai.na rasa me zan ce da shi dan haka shirun nima nayi. Satan kallon Addah Maryam nayi sam ban san me zance da shi ba a dai-dai wannan lokacin da ni da kaina fama nake da zuciya ta. Da idanu Addah Maryam tayi min alamun inyi magana mana sai nace"  Hel...lo" Da rawar murya har nawi naji baki na yayi min...sai Shima yace" Hi" a hankali tamkar dole aka sanya shi yin maganar. " Ina yi...ni" na sake fa'di ina yin 'kasa da idanu na. Bai amsa ba sai yace " Yau kin tuna dani kenan". Ina kan tunanin yanda akayi ya gane ni na bashi amsa da fa'din" A a" Inda nayi maganar ina mai satan kallon Addah ta. Daga inda yake sai yayi saurin gyara kwanciyar sa sannan cike da mamakin amsar da na bashi yace" Indai ba tunawa dani kika yi ba toh me yasa kika 'kira ni...tell me". ..." _ki 'kira shi ki gaida shi ki tamabaye shi ya karatu sannan...._ maganar Addah Maryam na tuna dan haka sai nayi saurin bashi amsa da fa'din" Yah Makaranta?" Ajiyan zuciya naji ya sau'ke sannan yana shafo kansa daga 'daya 6angaren ya bani amsa da fa'din" Alhamdulillah...karatu ya 'kare ai saura ka'dan mu kammala insha Allahu..". " Allah ya bada sa'a". Na fa'di ina kamo wayar da duka hannuwa na biyu kamar wani kayan nauyi ne na ri'ke. Shiru ya 'dan biyo baya na 'tan sakanni.. daya ke wayar ba'a speaker yake ba so Addah Maryam sai ta zaci ko shirun da nayin sauraran maganar sa nake yi dan haka bata ce da ni komai ba...yayin da ni kuma cikin zuciya ta aikin harha'do maganganun da zan furta agare sa nake yi ko zan yi sa'a ya bar ni in bi Addah ta. Kafin nayi magana sai ya rigani da fa'din" Ba wata matsala ko ?" Girgiza kaina nayi kamar yana kallo na sai daga baya kuma nace" a a bakomai". " Ok...Ya su Mama". " Lafiyan su qalau". " Da kyau". yace sai kuma ya 'kara yin shiru. Jin yayi shirun ne ya sani nayi niyyan yi mai magana take kuma sai naji jiki na yana 'kai'kayi tamkar marar gaskiya, 6ata raina nayi nace..." Ya..yah". Yace " Ina jinki...ya akayi?" "....Addah Maryam zata koma Darazau gobe...". Batare da wata damuwa ba yace " Owk Allah ya kaimu goben akwai matsala ne?" Sai nace " a a...ni dai ina so in bita ne..." " Ki bita kuma? Me zakiyi acan 'din?". " Bakomai ni dai ina so inje ne kawai". " Shine aka ce sai kin gaya min?" " Ummah bazata barni ba inje ba wai sai ka yarda shiyasa". Shiru yayi na 'dan lokaci sannan yace" Kwana nawa zakiyi?" " 2months kawai". " Ban yadda ba...1 week zakiyi ki dawo kinji?" "Uhum". Nace a hankali ba dan na amince da hakan ba. Shiru ya 'dan biyo sai can yace " Dan haka kika 'kira ni ko?" Shiru nayi masa ban bashi amsa ba dan ni 1week 'din da yace 'din sam bai game ni ba sai ma naji ya 6atan raina gaba 'daya duk da bawai zancen ya hau kaina bane. Jin nayi masa shiru ne ya sa shi fa'din " Toh bye..sai na dawo ko?". Bance 'kala ba har ya kashe wayar tasa.      Kallon Addah ta nayi da ta zuba min idanu tana kallo na...ina 'dan ha'de rai nace da ita yace inje". " Yauwa ko ke fa...ai dama nasan ba zai hanaki ba, kawai ke 'din ce dai wata iri...daga haka ta 'kara 'dora min wasu lectures 'din cikin 'kwa'kwalwa ta. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *66* Bayan mun rabu da Addah Maryam sai na 'kira Ammi...ko yau 'din ma bata 'daga ba sai da nawa 'kiran ya yanke kafin ta 'kirani daga baya, gaida ta nayi sannan na sanar da ita cewa na tambaye sa kuma ya amince wai inje.." " Owk...yayi kyau..ni na fiso ki tafin ma ai kije ki huta abin ki Mama na". Cewar Ammi...yayin da na 'dan yi murmushi daga 6angaren da nake. Tambaya ta tayi" yaushe ne ma dama ranar tafiyar ?" sai na bata amsa da fa'din" Gobe ne fa Ammi". Tace" To shikenan Allah ya kaimu" Da" Ameen" na amsa ta a ta'kaice...daga hakan bata ce da ni komai ba kawai sai sallama da muka yi. Da yamma ban zataba kawai naga Ammi ta aiko min ku'di har 10k da tsarabar da zan tafi da shi wai, take kuwa na 'kira ta na sanar da ita cewa ai akwai ku'di a guri na tun wanda Yah Deen ya aiko min farkon tafiyar sa ma suna nan ban yi komai da su ba harda wanda ake aiko min ma". Tace" Wancan ai naki ne Mamana wannan kuma ni na baki kuyi ku'din mota". " Ammi ai zasu yi yawa to..." Ban 'karasa rufe baki na ba ta tare ni da fa'din wai na koyi musu yanzu..." Jin haka ya sa na bata ha'kuri gami da godiya daga haka ta yanke 'kiran daga 6angaren ta. Ummah ta kam tunda taji cewar Yah Deen ya bar ni yin tafiyar bata ce da ni komai ba, ashe ita dama damuwar ta shi 'din ce kawai, bata fito fili ta bayyana hakan bane saboda ita tunanin ta babu hanyar da zan sanar da shi cuz bata ta6a ji ko ganin ina waya da shi ba shiyasa kawai ta yanke shawarar hana ni tafiya saboda babu bakin mijina. .....Ummah ta kullum tausayi na take ji cikin ranta musamman da ta fahimci cewa babu wata sha'kuwa ta kirki tsakani na da Yah Deen, tasan dama zama na dashi zai matu'kar bani wahala cuz ni ba kamar su Addah Maryam nike ba, kaf cikin 'ya'yanta babu wacce ta gado halayyar ta sama da ni, sanyin hali da kuma rashin sawa rai abu. Shiyasa take ganin da 'kyar ne zaman mu yayi saiti saboda shima 'din bai wani nuna alamun son auren ba koka'dan, a 'dan zaman da nayi agidan ta fahimci auren na mu suna kawai ya tara ba muhimmanci ke gare shi wajen mijin nawa ba balle tayi tunanin ko watarana zai yi kyau...shiyasa a kullum take sani cikin addu'ar ta akan Allah ya daidaita tsakanin mu in har kasancewar mu taren alkhairi ne in kuma ba alkhairi bane ta kance Allah kai kasan yanda zakayi da auren nan Yah Allah babu wanda ya isa yace maka ga yanda zaka yi..Allah kayi mana jagora cikin al'amuran mu ka bawa yarinyar nan kariya. Addu'ar da Ummah ta ke yawan yi min kenan kusan koda wani lokaci cikin sallar ta. Kaya na da nake amfani da su wanda aka kawo min daga gidan Ammi da su ka'dai na shirya tafiyar, dan musamman ma Ammi ta 'kira ni tace ya kamata in zo in duba wasu kaya wa'danda yakamata inyi tafiyar da su sai nace mata a a wanda nake tare da su ma ka'dai sun isa..ta so ta nuna 'kin amincewar ta da hakan saboda a fa'dar wai ai sun sha ruwa sai na nuna mata ai ba abinda ya same su ni ban ma fiya amfani da su ba sai dogayen riguna ka'dai, haka dolen Ammi ta 'kyale ni ba dan ta so ba. Washegari kuwa ni da Addah Maryam muka wuce Darazau cikin kariyar ubangiji muka isa lafiya lau batare da matsalar komai ba. *****        Tun tafiya ta ban yi waya da shi ba har na kwana biyar a can, bai 'kira ni ba sam ganin hakan yasa nima kuma ban yi 'kiran sa ba, na kanyi da waya da Ummah, Anty Zainab da kuma Ammi na kusan kullum amma banda shi...ko Addah Maryam sau biyu take tambaya ta cewar mun yi waya da shi ne?" Sai nayi saurin bata amsa da fa'din" Erh" saboda bana so ta sake sani a gaba tace sai na 'kira shi. Haka nayi ta faman 6oye mata gaskiyar lamarin ina kaucewa duk dalilin da zai sa ta fahimci tsakani na da shi. Sau tari idan saif ko Ammi sun 'kira ni matu'kar tare muke da ita na kan yi basaja na tashi daga inda take tamkar shine ya 'kira ni sai na koma can cikin 'daki na amsa wayata cikin kwanciyar hankali, hakan da nake yi kuma sai ya 'dan kwantar da hankalin Addah ta har sai ta ma daina tambaya ko munyi waya domin a tunanin ta shine ke 'kira na. Sosai Addah Maryam ta zage dantse wurin fahimtar da ni sirrin da ke cikin aure, wasu lokutan nibkam har mamaki take bani yanda ko 'dar bata ji ballantana taji kunya ta, a mafi yawan lokuta idan ta gama tsara min karatun nata nan nake bar mata su saboda nawin da suke wa 'kwa'kwalwata sai inji sam wannan ba hurumi na bane bama zan iya ko abu 'daya daga cikin su ba. *****               Ranar dana cika mako guda acan aranar Yah Deen ya 'kira Anty Zainab yake tambayar ta wai yaushe rabon da muyi waya da ita?" Dagangan tace da shi" Ai ko yau ma bamu da'de da yin waya ba, wani abu ne ya faru?" Ta 'karasa da tambayar sa sai yace a a ba komai kawai ya tambaya ne.. Shiru ya 'dan biyo Anty kam so kawai take yi taga iya gudun ruwan sa, yayin da shi'din kuma sai yakasa ha'kuri da maganar saboda yanda yake jin abun na tawo cikin ransa sai yace" Anty wallahi wannan yarinyar ta ba 'karamin raina ni tayi ba" " Me kuma ya faru Mu'een kai kullum ba'a rabaka da masifa me yasa ne?". " Haba Anty! tun tafiyar ta fa ko 'kira na bata ta6a yi ba, ba dan Allah ma yasa kuna waya da ita da kuma Ammi ba ma ai da ko halin da take ciki bazan sani ba, fisabilillahi hakan ya dace kenan...?" Anty sai tace masa " To kai me yasa baka 'kira ta ba?..ai idan.ita bata 'kiraka ba kai da kake matsayin sama da ita kai 'din sai ka 'kira ta kaji halin da take ciki, kuma ma fa kai da kanka kasan yarinya ce Hudah har yanzu me ta sani har yanzu da sauran ta..." " Yarinya ce Anty amma ai ansan hakan kuma akayi mata aure". Ya tari bakin ta da fa'din hakan a masifance. 'Dan.murmushi Anty Zainab tayi sannan tace" to ni kam Mu'een miye laifi na yanzu cikin maganar nan? matar ka ce fa yanzu she is your responsibility kai ke da alhakin kulawa da ita lafiyar ta da komai, balle gashi yarinyace 'karama abubuwa da yawa kaine zaka fahimtar da ita...". " Anty ai shiyasa tun farko ni banso auren ba..lokuta da dama idan na tuna wai wannan yarinyar ce aka 'daura min aure da ita Allah kar kiga yanda nake ji a raina, yaushe zan iya da ita? yarinya 'karama ta maida ni tamkar ni tsaranta?..." "...kana son girma sosai kaima, kuma tunda kasan yarinya ce me yasa kai baka yi 'kiran ta ba kaci girman?" " Hmm" kawai yace da ita..sannan ya 'dan sau'kar da murya yace..." Ai yau zata dawo ko..zata gamu da ni ne..". Anty kuwa sai tace " Ba dai yau ba kam dan bata ce da ni yau zata koma ba". " Wai sai yaushe?" " Ba rana dai inajin?" " Kuma uban wa zai je mata makarantar?" Ya fa'di a hassale. Zaro idanu Anty Zainab tayi sannan tace " 'Kaniyar ka Mu'een da ni fa kake magana.." 'Dan sosa kansa yayi yana fa'din " Sorry Anty...amma please kice mata ta dawo ko dan saboda makarantar ma". " Kai me ze hana ka gaya mata da kanka?" " Ok Anty zan gaya mata.." Daga haka suka yi sallama da shi. Ammi ya 'kira itama yayi mata maganar tace da shi ba yanzu zan dawo ba. Ai kuwa sosai ransa ya 6aci da jin amsar da Ammi ta bashi. Shi laifin ma ba nawa ka'dai yake gani ba har da na sauran saboda ai kowa yasan an yi resuming school, tunda kuwa sun san zan 'dau lokaci to dan me yasa za'a barni na tafi kuma? Kuma tsabar na raina shi ma yace da ni 1 week shine na yi banza da zancen sa nayi zama na...haushi na da yaji cikin zuciyar sa hatta su Ammi basu tsira ba, bai sani ba ashe ni ban sanar da kowa batun 1 week 'din da yace min ba. Ko da Ammi ta 'kira ni tambaya ta tayi cewa wai dama bama waya da Mu'een ne?" Sai nace da ita" a a Ammi muna yi fa kwana biyun nan ne kawai be 'kirani ba". " Me yasa to?" Ta tambaye ni sai nace nima bansani ba Ammi ni dai kawai be 'kira ni ba". " 'Kyale shi..na san wataran ko ance yayi miki hakan ma da kansa zai ce a a..." Cewar Ammi kenan cike da jin haushi sai nayi 'yar dariya kawai musamman tuno cewa ko Anty Zainab ma irin abinda take yawan fa'da min kenan...takan ce da ni _watarana da kansa zai godewa wanda ya ha'da auren mu da shi, tace raina 'yar Ammin nan yayi ni kuma nasan bakowa ke sa'an samun irin ta ba..._ " Anty Zainab kan yawan fa'da min haka ne musamman saboda ta kwantar min da hankali na...kuma har raina nake jin maganganun ta idan tana yi min shiyasa nake jin da'din mu'amala da ita. Duk da nasan ni ba komai bace, kuma mawuyacin abu ne abinda Anty ke fa'da ya faru ni agani na amma duk da haka nakan ji da'di idan ta fa'di hakan har cikin raina. Ko yanda muka yi kan batun tafiyar ma dana gaya mata cewa 1 week wai yace zanyi dariya kawai tayi tace rabu da shi ki huta abinki...Bai san cewa ke matar sa bace sai wurin bada umarni ka'dai sannan yasan da haka..." Ban kai 'karshen tunanin ba na tsinkayi muryar Ammi na fa'din" Amma yaushe kika shirya dawowa ne?" Ammi ta tambaye ni. Wanda da jin hakan take  sai na 'dan shagwa6e murya ta sannan na bata amsa da fa'din" Ammi ni fa gaskiya ba yanzu zan dawo ba garin akwai da'di wallahi". Murmushi Ammi tayi tace" Nasani Mama na...amma ai kinga karatu na ta wuce ki a school ya kamata ki zama a kusa, ko shi ma Mu'een 'din complaint 'din da yayi 'dazu kenan". Sake shagwa6ewa nayi nace" Ni dai dan Allah ba yanzu zan dawo ba Ammi..." " Sai yaushe kenan?" "May be nextweek". " Kai Mama na har da may be kuma?" 'Yar dariya nayi ka'dan tare da fa'din" To nextweek zan dawo Ammi na". Murmushi tayi daga 'dayan 6angaren sannan tace " Shikenan to Allah ya kaimu...amma ki gaya masa fa dan kar ya ishe ni da mita kinji". Da" to" kawai na amsa ta ba wai dan zan sanar da shi 'din dagaske ba. Haka na cigaba da zama na gidan Addah Maryam hankali kwance batare da damuwar komai ba, ban damu sam da lamarin sa ba, ni lokuta da dama ma in ba zancen sa akayi min ba sam ban tunawa da shi. Har gara ma in Addah Maryam ta sani gaba da darussan ta na kan zurfafa tunani akan sa cikin raina na kance Addah kenan, ita har yanzu bata san waye Yah Deen ba. Na kan yawaita fa'din hakan ne idan naji tana ikirarin wai maza ba komai suke ba wajen matayen su matu'kar mace ta san kanta to namiji bai isa ya raina ta ba balle wani abu makamancin tsawa ya shiga tsakanin su..." Har dariya take bani idan ta fa'di hakan, domin.ni ban hango faruwar hakan ga nawa mijin.ba sam, gani nake ba ranar faruwar hakan. Tambaya nake jefa mata da fa'din" Addah kuma har da Yah Deen shima?" Kwafa Addah Maryam take yi sannan ta bani amsa tace" hadda shi mana shi 'din ba namiji ba ne...wallahi in kika tsaya lusaranci haka har abada zaku cigaba da rayuwa bazai ta6a baki kima ba balle ya daraji ki, amma idan kika tsaya kika nuna masa ai kema mace ce mai aji da kanki sai kinyi mamakin biyayyar da zai miki". Yawancin idan irin wanna n maganar ta zaunar da mu to da dariya muke tashi awurin domin ni kam gani nake Addah Maryam son ranta kawai take fa'di bakomai ba. *****              Ko bayan yin wayar mu da Ammi ban 'kira shin ba kamar yanda ta fa'da, haka kawai ni sai banji son 'kiran nashin ba har cikin zuciya ta, balle ma da na samu Anty Zee na 'kara 'dora ni akan wai in cigaba da share shi, tace yanda ya raina ajina 'din nan idan ina shishshige masa watarana abinda zai min har sai ya girmi tunani na. Shawarwari da maganganu da yawa nake ji game da shi daga mabanbantan baku na wa'danda kuma duk nake da tabbacin baza su cutar da ni ba. Nasani kowa yana bani shawarar ne bisa la'akari da halayen sa amma bansan meyasa ba haka kawai duk sai nafi jin na Anty Zainab yafi kwanta min a raina saboda nata babu tsanani a ciki, babu abinda zai gagareni aikatawa domin bata sani yin abinda ban da ra'ayin sa. Addah ta kuwa a kullum  ilimin zaman aure gaba 'dayan sa take 'ko'karin ganin ta koya min, na kan zauna in saurare ta tas wasu lokutan ma har kunya maganganun ta ke bani musamman idan ta fara canza 6nagare wannan kam bana yi mata musu ko jayayya ko nuna 'kin amincewa ta shiru nake in saurare ta,  amma har cikin raina gani nake babu ranar da irin hakan zai faru da ni. Duk 'ko'karin Addah ta bai wuce nuna min hanyoyin da zanbi in ja hankalin miji na ba..musamman da yake kowa yasan halin sa, kowa yasan cewa shi 'din  manemin mata ne, duk da bata fito fili ko sau 'daya ta furta hakan.ba amma a yadda take karkata zantukanta da kaina fahimci kallon da ake yi masa, wanda ni kaina ma shaida ce ta gani da ido akan halayayr sa..'kilan dalilin kenan da yasa take 'ko'karin wayar min da kai ta 6angaren zamankewar aure. Ban 'kira Yah Deen ba haka shima bai 'kira ni ba har na cika kwana goma sha 'daya a Darazau, sai a ranar ne ma da 'karfe tara saura na dare naga waya ta na haske, da yake silent take shiyasa bata yi 'kara ba, kwance muke na gama shirin bacci na, duk ma yaran Addah ta sunyi bacci saura ni ka'dai na rage ni 'din ma bacci ne cike a idanu na hasken da wayar ta fara ne yasa na 'dan bu'de idanu na lalu6o ta. 'Dago wayar nayi batare da na ko duba ko waye me 'kiran ba na sada wayar da kunnuwa na tare da fa'din" Hello". cikin muryar bacci. " Shiru naji ba'a amsa ni ba, sai na sake fa'din" Hello!! Ina ha'de raina jin ba'a amsa ni da farkon ba. " Kin dawo ne?" Abinda naji ya tambaya kenan da ya sani saurin gwalo idanu na, ciro wayar nayi daga kunne na na sake dubawa tamkar wanda aka ce min zan ga photon sa a ciki. Maida wayar nayi jikin kunnen nawa sannan da rawar murya nace" Na'am...Yayah..." Tuni baccin nawa ya kama gaban sa. " Nace kin dawo ne?" Ya saki fa'di a 'dan tsawace. Sai na girgiza kaina tamkar ina gaban sa kafin na 'kara da fa'din" a a". Sai yace " Saboda kin raina ni ko?" Nayi saurin bashi amsa da" a a". " Yaushe nace ki dawo dama?". Shiru ina 'kif-'kif da idanu na'ki yin magana. " Wallahi 2days kika yadda kika 'kara a wancen garin zaki ha'du da ni, in ba hauka ba baki san ana zuwa school bane da zaki je kiyi zaman ki a can 'din?" " Na sani.." " Owk u just want to proof ur mentality ne ko?" " um- um". " Ki yi yadda kika ga dama amma wallahi if kika kuskura kika tsallake ranar dana gaya miki ke da kanki kin san sauran..." Yana shirin datse wayar sai kuma ya dakata yace"  da zaran kin koma ki gida ki sanar da ni kinji ko baki ji ba?...". " Naji?" Nace ina tura baki na sai yace " Aha" Daga haka ya yanke 'kiran...jiki na duk sai naji wani iri a lokacin, sakamakon rasa tunanin da ya kamata inyi ne ya sanya ni mitar " Ni me ruwan ka da ni to.." Tun lokacin nayi niyyan sanar da Anty Zainab saboda a tunani na itan zata ce dani inyi zama na ne kar in tafi cuz ita a kullum abinda yafi kwanta min itama shi take so, amma ganin kamar dare yayi ne ya sanya ni fasa 'kiran nata na bari zuwa safiya. Ai kuwa washegari sassafe ina idar da sallah na 'kira ta na gaya mata cewa Yah Deen ya 'kira ni jiya da dare. Dariya Anty Zainab tayi tace" 'Dan duniya yaga dama kenan?" 'Dan ha'de raina nayi nace" Masifa fa yai min Anty". Dariya sosai Anty tayi tace" Me kika yi masa to?". Nace" Bakomai fa kawai wai dan ban koma ba shine ya ce wai dole in tafi gobe". Nayi maganar kamar zanyi kuka. Anty takaita dariyar ta ta tayi sannan cikin kwantar da murya tace" Ai to ba abin damuwa bane, ki kwantar da hankalin ki kinji?, kinsan koma miye ne yake faruwa Allah bai 'dauke matsayin sa akanki ba ko da 'kwayar zarra still shine dai mijin ki, dole ne kuma kiyi masa biyayya kinsan shine aljannar ki ko?" 'Kasan ma'koshi na amsa da" Umm". Sai tace" Yauwa kin gani...ai ni hakan ma da yayin ba 'karamin birge ni yayi ba, ko ba komai yanzu nasan ya damu da ke, kin san ya za'ayi?" Nace" a a?" Anty sai tace" Yanzu ki gayawa Addan ki cewa yace ki koma gobe ai bazata hana ki ba nasani sai ki shirya ki taho zamu yi waya daga baya kinji..?" " Uhum" nace da ita sannan na ajiye wayar raina ba'ki'kirin, ni ba haka naso ba sam. Ko da na sanar da Addah ta ma da mamaki ta tambaye ni cewa da kansa kuma yace ki koma?" Nace mata" Erh shi ne ya 'kira ni jiya ya fa'da min". Ina maganar kamar zan fasa ihu saboda haushi. Sai naji tace " To ai shikenan tafiya ta kama ki". " Ni wallahi Addah banso.in tafi yanzu". Na yi maganar kamar zan saki kuka sai tace" Dolen ki ai, kinsan ni ba goya miki baya zanyi ki aikata son ranki ba". Da fa'din.hakan.sai ta fice ta barni cikin 'dakin. Haka ina ji ina gani Addah ta shirya min kaya na na taho ba dan raina ya so ba. Ai kuwa gidan Ummah ta na sau'ka waya kawai nayi da Ammi na sanar da ita dawowa ta, ko Anty Zainab ban 'kira ba dan haushin yau bata goyi baya na ba. Shi 'din kuwa 'kin 'kiran sa nayi duk da kuwa yace da ni idan na dawo in 'kirasa amma na share shi har sai can bayan sallahr Isha'i kafin na 'kira sa lokacin ma har na gama shirin bacci zan kwanta. Da ganin ya 'dauka na gaida shi tare da fa'din" Na dawo". A ta'kaice. " Dan baki da sence kuma sai kika jira har dare sannan zaki taho?" Take sai nace " a a fa ni tun 'dazu na dawo". Yace " Kuma shine yanzu zaki gaya min?" Nace " Mantawa nayi ne..." Tsaki yaja sannan ya kashe wayar sa.   Ni kam baki na ta6e a fili na furta" _Almasifatu_ " A hakan ne Addah take tunanin watarana zaka canza? Hmm so take in mutu kawai a hannun sa wannan me kai biyun kam ba canzawa zai yi ba...cikin zuciya ta nayi wannan tunanin a fili kuwa baki kawai na ta6e. Washe gari kuwa na shirya naje na gaida Ammi na da Alhaji Baba. Yini nayi da Ammi sannan da yamma na koma gida. Sai da na kwana biyu da dawowa kafin na fara zuwa makarantar har ranar kuwa ban kuma waya da shi ba...ai kuwa karatu ya barni sosai a makaranta balle gashi SS class muke yanzu abin ba sau'ki dole na na dukufa da karatu dan kar abar ni abaya...gefe guda kuma Ammi na yawan cewa da ni na 'ki ta yanzu, wanda ni kaina bansan me yasa yanzu na fi jin da'din zama a gidan mu ba..gidan Ammin ne yazama shiru yanzu ba da'di ba su Saif gidan shiru ita ka'dai take yini abin kuma ya fara isanta. Da kaina na fara jin tausayin ta kuma sai na yi tunanin dawowa gidan kawai, banyi maganar da kowa ba na dai bar shi cikin raina, kafin in sanar da Ummah ta kuma sai Ammi ta riga ni, ai kuwa Ummah ta tace maza in shirya in koma gidan miji na, dama ai rasuwa ce kuma ta jima da shu'dewa, tace zaman mace 'dakin mijin ta shine darajar ta. Ni dai bance da Ummah ta komai ba, tunani nake cikin rina, cewar indai wancan 'dakin da yaci sunan nawan ne ma take tunanin zan koma ni kam har abada na yafe shi, bana jin zan iya sake rayuwa cikin wannan gidan da ya kasance wurin aikata masha' a tun kafin zuwa na..ina.babkashevkaina nake son yi ba bazan koma can ba cuz ni ka'dai nasan me nake ji cikin zuciya ta game da gidan, to tuno shi nayi ballnatana ace in sake rayuwa cikin sa, abu ne da har yau banga alamun zan iya mantawa da shi ba. Duk da yake ita ma Ummahn nasan ba can 'din take nufi ba amma cewa da tayi gidan mijina ya sa ni zurfafa tunani akai tunda nasan can 'din shine gidan mijin nawa, kuma nasan Ummah ta baza ta6a cewa dani in koma wancan gidan ni  ka'dai ba dan haka ko da na shirya kaya na sai na koma gidan Ammi muka cigaba da zaman mu. Ko guda daga cikin kulan da take min kuwa bata daina ba, sai abinda ma ya 'karu...Alhaji Baba ma kan yawaita yi min kyauta ta musamman ni da kaina nasan iyayen Yah Deen na 'kauna ta sosai. Kwanaki na goma sha uku da dawowa gidan Ammi sai ga Yah Deen ma ya dawo wai ya kammala karatun sa gaba 'daya. Ni dai bazan ce ga yanayin da na shiga da dawowar tasa ba amma har zuciya ta na taya shi farin cikin kammala makarantar da yayi. Tun dawowar sa kuwa maganar kirki bata ha'da ni da shi ba, saboda bai ma wani zauna ba, ya kan yawaita yin 'kananun tafiye-tafiye amma duk da hakan ranar da akace yana gari kuwa ranar bana yin yinin farin ciki, na kan tsinci kaina cikin rashin sukuni musamman saboda wani salon tsareni da ya fara wanda ban san dalilin sa ba, Allah ma ya taimaka ni 'din ma ba gwanar shiga sabgar da bata shafe ni ba ce shiyasa ba kasafai lamari ke ha'da mu ba. A yanda na fahimta ma sai naga tamkar ni ka'dai yake wa hakan, tamkar mai jin haushi na, duk dama ko a wurin Ammi yake ba kasafai zaki ga suna hira kamar da ba amma da sau'ki akan innice tare da shi sai na rasa dalilin wannan canjin. Gani na abin farin ciki ne ya same shi daya kamata ace yafi kowa nuna farin ciki amma 6angaren sa kam abin ba haka bane. Sai nake tunanin ta6 ashe kuwa zamu da'de mafarkin Addah bai tabbata ba in dai Yah Deen ne, mutun da kullum halayen sa canzawa suke yi gaba 'daya sai ka kasa gane inda ya dosa. Ban sani ba ashe hakan na faruwa ne sanadiyyan tsintan kansa da yayi dumu-dumu cikin so da 'kauna ta, sai yake ganin in ba haka yake min ba tamkar abin zai girmama ne a zuciyar sa shi kuma baya so kowa ya fahimce shi domin ayanda yake ji 'din idan yace zai bayyana soyayyar da yake min kowa dariya zai masa musamman su Anty Zainab hatta Ammi yasan sai ta masa dariya bayan duk iyayin da yai ta musu akaina. Kafin cikar 3weeks da dadowar sa kuwa wai sai  ji muka yi har zai fara aiki da wani abokin Uncle Ja'afar cikin garin Bauchi. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *67* Sosai nayi farin ciki da samun wannan aikin nasa dan ko ba komai zan huta da ganin sa, nima in sake kamar kowa ma. Abin mamaki da lokacin tafiyar tasa tayi kuma sai  Alhaji yace wai dole tare da matar sa zai tafi jin wannan labarin sosai ya 'daga hankali na bada wasa ba. Kamar wasa sai gani nayi Ammi ta fara shiri gadan-gadan, ragowar akwatina na da kayayyaki na dake can gidan tasa wai akwaso, da tace ma wai da ni za'a je can 'din amma tun daga lokacin kuka na ya 6alle ina fa'din ni bazani gidan ba, duk yadda Ammi ta so aje da ni wai ko zan duba wani abin amfani na 'kin zuwa nayi sai turawa tayi akwai aka 'debo mata kayan bisa jagorancin Yah Deen. Shi kam da yake yana zargin kansa ne bisa  dalili na na 'kin zuwa sai bai damu da shiga maganar ba gudun kar allura ta tono garma. Ni kuwa sam kuka na sai ya kasa tsayawa yinin ranar kuwa kaf haka na sa Ammi gaba da kuka ina fa'din ni ba matar sa bace bazan bisa ba. Ammi ko kula ni ba tayi ba har sai yamma sannan ta zaunar da ni tayi ta lallashi na da ban baki harda al'kwarurruka tayi min akan wai da kanta watarana ma zataje ta duba ni in tana raye...tace kuma koda wasa naga abinda bai min ba ko kuma ya aikata wani abin wanda raina bai kwanta da shi ba in 'kira in gaya mata uban sa zata ci...taceckovwaya naga yana yi da wata macen in sanar da ita sai taji dalili. Ni kam bance da ita komai ba, damuwa ta ni kawai a yanzu shine inji ance bazan bishi ba. Abakin Ammin ma nake jin wai za'a kwashe kayan kitchen 'din mu na wancen gidan a tafi mana da shi can Bauchin, ni kam baki na ta6e na kauda kaina. Ko ranar da za'a 'dibi kayan ma ba yadda Ammi bata yi da ni akan muje ba sam na'ki, Yah Deen ne ya sau'ke ta gidan dama lokacin da Ammi zata tafin da na'ki binta sai naga ya sa kai yayi gaba inda ya jira ta a waje har ta fito. Yana sau'ke ta ba'ajima ba ya dawo gidan, da shigowar sa kuwa bai zame ko'ina ba sai cikin 'dakin Ammi da yake bai ganni a parlour ba. Lokacin da ya shigo ina bayi ban san ya shigo 'dakin ba dan haka skirt 'di na a sama na fito ban sau'ke shi ba, da fitowa ta ne sai na ganshi tsaye ya wani cika iska cikin bakin sa take kuwa na sau'ke skirt 'din nawa cikin sauri har da jan shi sosai zuwa 'kasa. Yana daga tsayen ya furzo da iskan bakin sa sannan ya ta6e baki gami da buga min wata  harara da ban ta mecece ba. Kawar da kaina gefe nayi ina tunanin me kuma ya kawo shi, me yake nema. 'Ko'karin fita na fara daga 'dakin inda na tunkari hanyar fita. Sai ji nayi ya ri'ko hannu na gami da fa'din" Zonan". Take na waigo a 'dan firgice na kalle inda ya ri'ke hannu na kafin na ankara sai ji nayi ya janyo jikin sa kusa da shi sosai ya ha'da bayana da jikin sa still yana ri'ke da hannaye na, cikin kunne ya ra'da min" Kin raina ni ko?" Sai nayi saurin girgiza kaina. Yah Deen sai yace " Erh mana kin raina ni..yau ma ko gaida ni ma 'kin yi kika yi". " mancewa nayi". Yace" Me yasa to kullum kike wa Ammi gardamar zuwa gidan can?" Shiru nayi na nayi narai-narai da idanu kamar zan yi kuka. Jin nayi shiru ya sanya shi juyo da ni na fuskance shi take nayi 'kasa da idanu na sai ga hawaye ya gangaro saman kuncina. Kaina ya 'dago da hannayen sa amma ban iya duban sa ba.." Har yanzu baki mance wancen abin ba ko?" Shiru nayi sai ma nayi 'ko'karin cire kaina daga hannun sa amma bai sake ni ba sai ya maida min kannawa saman 'kirjin sa ya rungume ni...ni kam sai na cigaba da kuka na. Bayan kamar sakan sha biyar sai naji yana fa'din suna na" Noor!" Ya fa'di cikin sanyin murya mai hankali. Ban amsa shi ba illah hawaye na da na cagaba da gogewa. " Kina jin kishi na dama sosai har haka ne?" Girgiza kai nayi da sauri alamar" a a.." " To menene yake damun ki ki gaya min kinji?" " Ni bakomai kawai ban son zuwa ne". " Kin tabbatar bakomai?" Nace" Umm". 'Kasan ma'koshi. Sai yace" Zan tafi Bauchi yanzu kimin addu'ah..." " Allah ya tsare hanya". "Murmushi yayi sanna yace" Ameen" A takaice. Cire ni yayi daga jikin sa amma bai saki hannu na 'daya daya ri'ke ba yace" Barin je sai na dawo ko?" " Uhumm". Na bashi amsa da shi Daga haka ya sake min hannu yayi waje. Ko bayan fitar sa ma kuka na nasha na na 'koshi sannan nayi shiru. Lokacin da Ammi ta dawo kuwa bacci nake yi ban ma sani ba sai da na farka kusan Azahar sannan na ganta. Washe gari Yah Deen ya dawo Bauchin ko damuwa da kamarin sa ma banyi ba, shima 'din kuma bai damu da shiga sabga ta ba. Bayan kwana biyu kuwa sai ya kasance gidan Ummah ta zan yini da sunan wai muyi sallama da su, Yah Deen ma Ammi tasa ya sau'ke ni, haka kuwa tunda ya 'dauko ni har ya sau'ke ni babu wata kalmar da ta shiga tsakani na da shi domin haushin sa yanzu nake ji sosai, musamman saboda tafiyar nan, baya ga haka ma gashi jiya ya 'kara tunatar dani batun sa da Husnah sai haushin sa ya 'karu sosai cikin zuciya ta. Har na fita cikin motar na rufo ta bance da shi 'kala ba kawai na juya na yi cikin gida, da shiga ta na cire mayafi na na shige 'dakin Ummah ta na kwanta na cigaba da zubda hawaye na. Ummah ta data ga yanda na shiga sai bata kula ni ba ta cigaba da sabgogin gaban ta domin ba yau tasan da batun tafiyar ba kuma tasan babu mamaki akai ne nake kukan. Ina daga cikin 'daki kamar daga sama najiyo sallamar sa, Ummah ce ta amsa shi tare da yi masa iso sannan ta umarci Ummie da ta shinfi'da masa abin zama..inda ta 'kara da fa'din" Ke kuma Hudah kinsan bake ka'dai bace shine kuma kika wucewar ki ciki dan shegantaka ko?" Ina daga inda nake kwancen nake gungunin" Ni nasan zai shigo ne, mutun kullum yanayin sa daban-daban ina zan gane masa" Bazan manta masifar da ya zabga min lokacin da naje Darazau ba...amma ji shi kamar ba shi ba a 'yan kwanakin nan, sai daga baya ma nayi mamakin me yasa be tada zancen ba musamman yanda naga ya 'dauki zafi a lokacin har tsoro ya sani. Murmushi kawai Yah Deen yayi da jin furucin Ummah ta..haka ya zuna fuskar sa wasai tamkar wanda dama can yayi sabo da gidan sosai...in kinji yadda ya nutsar da murya yake gaida Ummah ta bazaki ta6a zaton yana da wani hali daban ba. Da kansa ya 'kara yi mata bayanin tafiyar ayanda tazo Ummah tace" Ai bakomai Allah ubangiji ya tsare ya bada sa'a" Yace" Ameen-Ameen". Bai wani da'de ba ya tashi ya fita bayan ya ajiyewa Ummah ta ku'di, duk yanda tayi da shi ya tafi da ku'din nan 'ki yayi, da yake shima yasan ba fitowa zan yi ba yasa da fitowar sa yaja motar sa yayi gaba abin sa. Ina daga cikin 'daki nake mita da zagin sa cikin raina..mutun sai munafurci da fuska biyu, idan ka ganshi bazaka ta6a zaton zai iya aikata abinda yake aikatawa ba, kuma Allah sai ya sakawa Ma'u kashe ta da kayi..tuno Husnah da nayi yasa ni fa'din 'yan iskan banza kawai". Cikin 'dacin rai nake tuno duk 6oyayyun halin nasa na ina kuma jin ciwon su cikin zuciya ta. Ummah ko ka'dan bata yi niyyan tanka ni ba har sai da na gama zaman 'dakin da kaina na fito sannan gani na haka a hargitse ya sa ta tambaya ta abinda ya same ni, take kuwa na bata labarin tafiyar tare da nuna mata rashin amincewa ta ina fa'da ina kuka, dan ni harga Allah bana son inbisa wani gari mutun cikin garin iyayen sa ma bai ji shakkan kawo mata gidan sa ba inaga inya ke6e gefe kuma?" Cikin zuciya ta na 'karasa wannan tunanin ni ka'dai. Ummah kam shiru tayi ta gama saurara ta sai da na dasa aya sannan tace" Yanzu Uwata akan wannan tafiyar kike faman 'daga hankalin ki har haka? Miye abin damuwa aciki to?" Shiru nayi mata bance da ita 'kala ba...cikin zuciya ta na ayyana" Ai Ummah bazaki ta6a ganewa ba, 'kilan nima sai an kawo miki gawata ya kashe nima kafin zaki fahimci abinda ke damu na a lokaci na da kuma dalilin 'kin binsa da naso yi". Ummah kam tsura min idanu tayi tamkar mai tunani daga 'karshe tashi tayi ta barni a wurin,m zaune, da kaina na gaji da kukan na watsar da batun na cigaba da harkoki na. Sai can har bayan azahar ma da taga na nutsu sannan ta zaunar da ni tayi min Nasiha, garga'di, ban ha'kuri da kuma jan kunne game da aure na, sosai ta nuna min cewa irin nawa auren natsuwa yake bu'kata dole in bada hankali na, in kula da hakkokin aure na kar inje inbiye wa shirme har wata 6araka ta sake 6ullowa, tace" kowa da kike gani a duniyan nan Hudah da aure ya ginu, aure ne nasarar kowa, da yawan mutane kuma auren na riskan su ne cikin rashin amincewar su amma sai suka yi ha'kuri gagarumar nasara kuma ta cimma su sanadin ha'kurin su, dalilin hakan ma sai kiga sun dace ranar gobe alkiyama, kema ina miki kwa'dayin wannan nasara matsayina na mahaifiyar ki Uwata, ko kukan da kike yi a yanzu da kanki kinsan ba amfani ne da shi ba, domin ba tun yau aka 'daura auren ki ba, bani da ikon sawa ko hanawa a yanzu kinsan yanzu ke mallakin su ce, su ke da iko akanki bani ba, ni kuma bazan ta6a saki ki bijirewa auren ki ba har abada sai dai in wani abin na nagani wanda ya sa6awa shari'a sannan, amma yanzu kam sai dai ince kiyi ha'kuri ki bi mijin ki, kuma ki sani yanzu ne rayuwar aure na sali ya tunkaro ki ba shirmen da kika kusan shekara kina yi ba, domin zaki jene inda babu kowa naki sai ke sai Allahn ki sannan mijin ki abu na uku da zai kasance tare da ke shine halayyar ki, dan haka ki yi 'ko'kari ki tsarkake zuciyar ki ki zauna da kowa lafiya ki yiwa mijin ki biyayya ki kuma ri'ke sirrin ki, mijin ki ka'dai ne abokin hirar sirrin ki da ya shafi auren ki, Hudah har yanzu nasan da sauran ki amma watarana da kanki zaki fahimci cewa ba 'kinki muke yiba inma kinsa hakan cikin zuciyar ki, sannan ki daure ki koyawa zuciyar ki kar6an 'kaddara kowace iri ce kinji? ki cigaba da yiwa mijin ki addu'ah Allah ya nutsar da hankalin sa wuri guda insha Allahu watarana komai zai zam tarihi kamar ba'a yi ba,  abinda kuma ya riga ya faru ya wuce kar ki yadda ki barshi cikin zuciyar ki balle ya dame ki, domin Allah shi ka'dai yasan dalilin ha'da auren ku, tace bazan 6oye miki ba Hudah ni kaina raina ba son wannan auren yake yi ba amma ba yadda zanyi dan ban isa inja da yin Allah ba, sai dai fatan Allah ya baku zaman lafiya mai 'dorewa, idan ancutar dake Allah yana gani kuma zai miki sakayya amma dan Allah kiyi min al'kawari bazaki ta6a cutar da kowa ba". " Insha Allahu Ummah na" Na yi maganar siraran hawaye na gangaro min. Ta sake fa'din" Kiyi min al'kawarin zaki zauna da mijin ki lafiya kiyi masa biyayya da ha'kuri cikin ko wani irin hali". Wannan karan ina share hawaye nace" Insha Allahu Ummah na". " Yauwa Uwata kuma banda zargi kinji? domin Zargi na da matu'kar muhimmanci wajen lalata darajar aure, komai da yafaru ya wuce kar ki saka cikin ranki balle ki tuno da shi har ya gur6ata miki tunani, kowa da kike gani.yana da nasan mugun.halin a 6oye bambancinnkawai na wani yafi na wani.ne shiyasa ba'a fiya gane wa ba". Nace " Hakane Ummah". Sai ta cigaba da fa'din" Ma'u kam 'kaddara ya riga ya hau kanta sai dai muyi fatan Allah ya ji'kan ta da Rahama Allah ya tsare 'yan baya..ke ma kici gaba da Addu'ah ubangiji Allah ya kawo miki shiriya cikin gidan ki..wannan karon kam matu'kar naga da cutar wa bazan bari a salwantar min da rayuwar ki ba da kaina zan 'dau mataki, Ke de ki kwantar da hankalin ki, ki nutsu ki bi mijin ki kinji Uwata?". Kuka na rushe da shi sosai tuno Ma'u da nayi, yanzu har abada wannan ba'kin fentin bazai barni ba, a kulluma za'a dinga kallona ne matsayin matar Deen wanda yayi sanadin ciki ga Ma'u daga 'karshe ma ta rasa ranta gaba 'daya..bana so in dinga yawan tuno wannan incidence 'din domin.gaba 'daya yake tunamin da dukkan rayuwar Yah Deen da na sani tun abaya har zuwa zama na da shi agidan sa, ji nake tamkar idan na 'kara cin karo da irin hakan daga gare shi mutuwa zanyi...cikin kukan na bawa Ummah ta tabbacin" Insha Allahu bazan bata kunya ba". Sarai nasan gaskiya itama take fa'da min, amma Ummah bata san ni abinda na gani da idanu na ba cikin halayyar Yah Deen da na tabbata ba kowa ke da irin ta ba, ita kanta Ummah da tasani nasan da bazata fa'di wasu abubuwan ba, to ma ta ina zan fara gaya mata sam bazan iya ba..hakan yasa na 'kara sunkuyar da kaina kawai na cigaba da kuka na...rayuwar Yah Deen kacokam 'din ta wata iri ce, a yanda nake.jin zuciya ta ji.nake da ba Ammi bace ta haifi Yah Deen da ko Soyayyar shi zata yi ajali na ne da kuwa zan sadaukar da zuciya ta in mutu da in amince yin zaman aure da shi..amma ina Ammi da Alhaji Baba sunfi 'karfin hakan awaje na. Jikin ummah na kwantar da kaina sai ta 'dago hannun ta ta 'dora saman kaina sannan tace" Allah ubangiji ya albarkaci rayuwar ki Uwata, Allah ya baki zaman lafiya da mijin ki, ya ha'de kanku ya kawar da shai'dan tsakanin ku". Ban iya na amsa ta koda da kalma ba kawai na cigaba da aikin kuka na. Ummah kam daga haka bata 'kara fa'din komai ba shiru muka zauna na tsawon lokaci, tana sake lallashi na ganin Ummie ta dawo daga gidan Yayah Usman da ta je ne ya sata fa'din maza inyi shiru in shiga ciki in huta kafin anjima dan kar Ummie ta fahimci yanayin da nake ciki. Da yamma kafin azo 'dauka ta Ummah ta bani wani magani ha'di da kindirmo tace inshanye, haka na 'daga na sha ina 6ata raina na goge baki na. Wata 'yar roba ta bani mai 'dauke da ha'din zuma tace insa cikin jaka ta sai mun tafi can Bauchin sai in ringa sha ka'dan-ka'dan nace to. Ba'a jima ba sai aka zo 'dauka ta daga nan muka yi sallama da Ummah ta na tafi, banje gidan kowa bama hatta Addah Saudah banje nayi mata sallama ba haka ma gidan Yah Usman...duk na bari ajan zan 'kira su daga baya. Wannan karan kam" ina yini" Nace da shi jin ya amsa sai na kawar da kaina, sau 'daya tak na kalle shi ban sake kallan inda yake ba, jikin sa rigar Jessy ce ja cikin wa'danda yake zuwa wasan ball da su sai ba'kin dogon wandon jeans da ya sanya, kansa sai tarin kwantacciyar suma da ya saba tarawa. Gefen hanya na maida idanu na ina bi da kallo yayin da yake tu'kin cikin hankali tamkar ba shi da niyyan jan motar. Kamar daga sama na tsinci muryar yana fa'din" Kinje kin ta yiwa Ummah kukan naki ko?" Kallon sa nayi saurin yi batare da nayi niyyan bashi amsa ba, sai yace" Dubi yanda idanun ki suka yi ja dan Allah..baki son mu tafi taren ne?" Jin tamabayar da yai min daga 'karshe yasa da sauri na 'dage kaina alamar" Erh" zato na ko zai ce to inyi zama na ne, ga mamaki na kuwa sai ji nayi yace" Toh ai sai ki kashe kanki kafin ranar tafiyar tunda ni cinye ki zanyi idan kin bini". Shiru nayi ban ce da shi komai ba, cikin zuciya ta nake jinjina ba'kin hali irin na Yah Deen, shi dai a kullum bai canzawa halin sa na nan tare da shi sai mugun hali da ba'kar magana kawai ya iya tsarawa. Kaina gefe nace" Ni dai kam bazan je ko'ina da kai ba". " Wai saboda mene...ni in ba mutun bane da baza'a bini ba?" Yayi maganar cike da murmushin mugunta. Cikin shagwa6e murya nace dashi" Ai wasu mata kake kawowa gidan ka kullum kuma ance babu kyau". Na fa'di hakan ne saboda abinda ke cikin raina yake cimin zuciya kenan. Dariya ma maganar tawa ta bashi a yanayin da na yita tamkar yara 'yan goye, amma sai yayi murmushi madadin dariyar, bai kalle ni ba tunda na fa'di hakan, dama yasan dole har yanzu hakan na nan cikin raina bn manta ba, kallo na yayi sau 'daya sai kuma akayi sa'a nima 'din bashi nake kallo ba so ban ma san ya kalle nin ba, sai da ya maida idanun sa kan hanya sannan yace" Kar ki damu yanzu ke ka'dai ce bazan 'kara kawo kowa ba kinji". Fuskar sa ba yabo ba fallasa yayi maganar amma shi ka'dai yasan yanda yaji furucin nawa cikin zuciyar sa, abu ne wanda ya matu'kar girmi lissafin koma waye idan yaci karo da shi, wanda ko shi da kansa ma ba iya jura zai yi ba misali ace ya kama abokiyar zaman sa dumu-dumu cikin wancan halin, yasan Allah ne ka'dai yasan me ze faru da shi alokacin dan yana ga har kisa zai iya yi in ba Allah ya tsare shi ba, amma yarinyar nan ta gansa da idanun ta kuma tayivshiru ta rufe masa wannan sirrin duk da 'karancin shekaratun amma sosai ya jinjinawa bajintar da tayi. Bazai 'karya ta zuciyar sa ba ya sani faruwar hakan shine babban dalilin da yasa shi tsintan kansa cikin zazzafan soyayyar ta da yayi, sau da dama ko yana school idan ya tuna sai ya dafe kansa, ko da shika'dai ne zaune amma haka kawai sai yaji ya tsinci kansa cikin matsanancin jin kunya haka kawai karma ace ya tuno da Hudah wannan kam sosai tunota yake tsuma zuciyar sa. Bance da shi 'kala ba kawai na kawar da kaina gefe... Sai can naji ya sake fa'din" In tambaye ki?" Kallon sa nayi sai na kawar da kaina tamkar abokan gaba, cigaba yayi da fa'din" Kin gayawa Ummah ne cewa wata ta tazo gidan mu kwanaki?". Kaina na girgiza masa alamar a a, sai yace" Ammi fa?" Nan ma kaina na sake girgizawa sai naga yayi murmushi harda lumshe idanun sa sannan ya bu'de bai kalle ni ba yace" In ma kin fa'da cewa zanyi mafarki kika yi ba gaskiya bane". Tunani yake cikin zuciyar sa cewa ai dama yasan matu'kar ban bada labari a lokacin da abin ya faru ba da 'kyar in sake iya furta galibi 'dan adam nada wannan halayyar. Baki na ta6e ni kam 'kasa-'kasa nace" Ai Allah ya gani". Ko da na fa'di hakan ma sau 'daya kawai ya kalle ni daga haka kuma bai sake kallo na kamar yadda bai 'kara fa'din komai ba har muka isa gida. Da shigan mu gida kuwa ina yin arba da Ammi sai ta kama bakin ta tace" Ikon Allah..haba Mama na yanzu zuwa kika yi kika yini kuka wa Ummahn naki ko? Dan Allah dubi yanda idanun ki duk suka 'kan'kance kuma nasan duk kuka ne ya kawo hakan". Shiru nayi bance da ita komai ba sai ta jijjiga kanta kawai ta shige ciki. Washegari Ammi ta tura ni yin kitso da lalle tamkar wata sabuwar amarya..ma'kudan ku'da'de ta kashe wajen ganin an tsara ni yanda ya kamata, nikam ma anayi ina tura baki na har raina bana so. Tun ranar da muka rabu bayan ya sau'ke ni daya 'dauko gidan Ummah shikenan babu abinda ya sake shiga tsakanin mu, baya shiga sabgata haka nima ban kuma da shi ba sam...mu kan gaisa dai idan mun ha'du da safe ko rana ko yamma sai in gaishe shi. Ranar da yashigo bayan sallar azahar ya tarar ina waya da su Saif tsayawa yayi ya 'kare min kallo yanda nake fama walwala da sakin fuska baki ya ta6e ya shige ciki ni ban ma kula da shi ba, sai bayan kamar mintina sha biyar sai naji wayata na ringing sunan sa ya bayyana kan fuskar wayar kamar yanda nayi saving" YAH DEEN". Sosai zuciya ta ta tsinke da ganin 'kiran cuz na jima banga hakan cikin wayata ba. 'Dauak nayi na kai wayar kunne na sai naji yace min" Kawo min wayar ki zan duba abu". Baki na tura sannan na yanke 'kiran. Ko da na kai masa wayar kar6a yayi yace inje zai kawo min. Haka na fita ina 'kukkuni cikin zuciya ta. Kamar wasa ranar wata laraba Ni da Yah Deen muka bar Shuwarin zuwa cikin garin Bauchi, da kansa yayi driven motar cikin 'daya daga cikin motocin gidan Alhaji Baba...tunda kuwa ya fara tafiyar babu ko kalma da ta ha'da mu, lokaci zuwa lokaci na kan goge hawaye na a haka har bacci yayi awan gaba dani. Da yake ma baya bin mota da wasa hakan yasa bamu wani da'de ba muka isa. Kafin lokacin ma na jima da farkawa domin baccin nawa bai wani yi nisa ba, sai da muka shigo cikin garin kafin ya tambayi me nake so nace da shi bakomai, bai tsaya ko'ina ba direct gida muka wuce. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *68* Gida ne 'dan madaidaici mai kyau da kyan tsari, da shiga ta ma naji ya birge ni har 'kasan zuciya ta, gidan Yah Deen dake Jigawa aka siyar sai aka sayi wannan 'din da ku'din ashe wai. Already ma an zuba funitures da komai na amfani a ciki wanda duk ragowar kayan cikin suka kasance sababbi ne a idanu na, kitchen ne ka'dai na riga na san da zaman kayan, sai dai yanayin tsarin kitchen 'din nan ya tsere na Shuwarin nesa ba kusa ba. Da isowan mu Yah Deen  ya sake fita ya barni ni ka'dai a gidan, gajiya ce ta hana ni lalle'kawa amma na so in yi gulma  har bayan kamar 1hr sannan ya dawo da ordern abinci masu rai da lafiya. *****      Rayuwar aure na da Yah Deen ya fara ne tun washe garin komawar mu garin Bauchi, a lokacin ne Yah Deen ya fara 'dora ni kan asalin nufin kasancewar mu tare da shi, sai dai bai fito fili ya bayyana bu'katar sa gare ni ba yakan yawaita yi min wayo idan yana so ya ra6i jiki na da fa'din wai size 'din boobs 'dina kawai yake so gwada saboda ya sani wai ko na girma. Shekaru na goma shida ne a lokacin amma ba laifi ni da kaina nasan inada albarkatun 'kirji dai-dai da yanayin jiki na masha Allah wanda ko marar idanu ya ta6ani sau 'daya amsar sa ta isar masa ba sai ya 'kara ba. Sau da dama na kan yi mamakin irin auna size 'din da yace yake min cuz yakan 'dan shafe 'yan mintina bai cire hannun sa daga jiki na ba, wani sa'in har bacci na 'dauka ta da hannun sa ajiki na, wani lokacin ma har sai na nuna banso ko kafin yake bari na dan haushi sosai hakan ke bani banda ma tsananin kunyar sa dake kamani, ayanda na fahimta kuwa 6angagren sa ko ajikin sa bai damu ba sam. Ya 'dauki a'kalla kusan kwanaki biyar yana min wannan gwajin da bansan ma'anar ta ba, tun ina jin nauyin sa har nazo na fara sabawa dan dole na, da yake ma duk Addah ta karantar dani cewa dole akwai faruwar irin hakan cikin zaman aure amma ban san cewa haka abin zai zo min cikin lokaci 'kan'kani ba, du da haka nayi 'ko'kari sosai wajen ganin na 'dan saki jiki na bisa la'akari da maganar Addar Maryam, wannan dalilin ne yasa ko lokacin da naji ya zarce da kissing baki na zuwa wuyana ma ban wani 'daga hankali na ba balle in yi yun'kurin hanashi, balle lokacin da na tsinci la66an sa saman boobs 'dina ranar da kaina sai da na shiga wani yanayi. Wasa-wasa abubuwan da Yah Deen ke min suka fara zarce tunani na, a time 'din ne kuma na fara  'kin amince masa da gwajin da yake min, da yaga hakan kuwa sai ya  daina sassauta min zafafan romance ya fara yimin mai tsayawa a zuci, bansan yanayi da hakan ke shigar dani ba ni dai kawai sai in jini ina kuka sosai, da sannu naga yafara haukace min yana 'ko'karin raba ni da sittarar dake jiki na, ganin haka yasa nayi saurin ri'ke masa hannu ina girgiza kaina ina hawaye. Hannun nawa ya ri'ke cikin nasa sannan ya rufe baki na da nashi...tsawon wasu da'ki'kai yana kissing baki na sannan ya barni, kansa ya kwantar gefen fuska ta hannaun sa na yawo min a baki idanun sa rufe naji yace min" A gida ba'a ce miki ki kula da hakki na ba?" Shiru nayi hawaye na gangaro min ta gefe da gefen fuska ta, cikin raina nake tunanin abinda Addah ta da Ummah ta suka gaya min, Ammi ce ka'dai wannan kalmar bata shiga tsakanin mu ba. Jin hucin numfashin sa gefen kunne na ya sani dawowa daga tuanin da na tafi, take na matsara da kaina, ai kuwa sai ya sake dawo dani kusa da shi hakan ne ya sani sakin wani kukan amma ko bi ta kai na bai yi ba sai da yaga dagaske nake kukan kafin ya 'kyale ni badan ransa ya so ba, bai kuma iya yace dani komai ba kawai ya shigar dani cikin jikin sa ya rungume, hakan bai dame ni ba cuz a yanda ya saba caku'da min jiki na a ganina runguma is normal dan haka bacci 'dauka ta yayi cikin kwanciyar hankali. Ban san halin da yake ciki ba balle hakan ya dame ni, ban sani ba ashe shi kam daban yake,  sassaucin sa ka'dan ne ta wannan fannin. Cikin bacci na ji ana sake bin jiki na, lokacin da na farka ma ya riga da ya yi nisa, duk wasu 'kananun koke-koke ne bai bi ta kansu ba, wani azaban zafi da naji ya ratsa ni ne ya sani sakin ihu mai 'dan 'kara tare da dam'kan hannun sa da 'karfin gaske tamkar zan cire mishi naman wurin, shi kam ma bai wani damu ba illah saurin toshe min baki dayayi da nasa dole kuka na ya tsaya illah hawaye ban kuma saki hannun san ba har a lokacin saboda koka'dan ban ta6a sanin akwai irin zafin nan a duniya ba tamkar ana yankan naman jiki na haka naji. Ranar Ammi na ta sha 'kiran neman ceto, duk da hakan bai barni ba har sai da ya cimma burin sa kafin nan. Duk kuwa da cewa cikin tsananin tashin hankali nake amma hakan bai hana ni jin albarkar da ya dinga sanya min ba dan da naji ya fa'da nima zance" Ni bana so ka 'kyale ni". Sai yayi murmushi kawai, ranar kam na ga sauyi sosai domin da kansa ya rakani bayi nayi wanka inayi ina banka masa masa harara, in zai kamani kuma ince bana so sai ma na saki wani kukan dan ni harga Allah tsoro yake bani yanzu. Da yaga haka sai yace" Ai ramawa nayi, nima kusan cire min fata kika yi ashe ba da'di" Ban kula shi ba na kawar da kaina gefe, sai ya kamo hannun nawa a 'ko'karin sa na ganin faratana, saurin fisge hannu nayi na cusa su 'kar'kashi na ina tura baki. Ganin hakan ya sa shi sakin murmushi kawai ya dawo baya na ya kwanta, saurin jan jiki na zan matsa sai yace min" Kul...dan kinga ban rama yakushi na ba ko? kina matsawa sai na rama kuma irin na 'dazu zanyi ni...". Luf nayi da jin abinda ya fa'di ban kuma yin wani yun'kuri ba illa hawaye dake gangaro min zuciya ta cike fal da tsoro. A kunne na ya ra'da min" Matsoraciya kawai... kiyi baccin ki bazan sake ba kinji?". Shiru nayi masa kawai na rintse idanu na yayin da ya cigaba da bin fuskata da kallo a hankali ciki-ciki ya furta" Kin sani farin ciki sosai, ubangiji Allah ya biya ki da aljannah" Yana 'dan shafa kaina yay i maganar ni kam sai na ta6e baki na na ma manta da abinda ya fa'da da farko take na matsa gefe na karkata kaina hannun sa ya bar jiki na...haushin sa nake ji ni kam, dama halin sa duk basu yi min ba, gashi yazo ya 'kara min da mugunta irin ta marasa imani na raya hakan a zuciya ta. 'Bangaren sa kuwa kasa sakewa yayi da na bar jikin san sai ya tsaya bin bayana da kallo, a hankali ya sake matsawa kusa da ni 'kafafaun sa ya 'daga ya 'dora saman nawa wai dan kar in sake zamewa sannan ya ran'kwafo da kansa saman nawa. Inajin sa nayi shiru dan ni ka'dai nasan kalar azabar da nasha, nake kuma jin gurbin sa har yanzu shiyasa ma hawayena suka kasa tsayawa. " Me kike so?" naji ya tambaye ni cikin murya mai sanyi kamar ba Yah Deen ba, shiru nayi ban kula shi ba sai da ya sake maimaitawa kafin nace" Ni bakomai". Da muryar kuka nayi maganar. Sai yace" Owk in shikenan..so kike in sake ko?" Da jin haka sai nayi saurin girgiza kaina gami da fa'din" a a". " Fa'da min to me kike so?" " Ni bacci nake so in yi". ' Yar dariya yayi wanda da ji kasan daga cikin zuciyar sa ta fito" Kiyi baccin ki to...shikenan?" Na 'dage kaina. " Akwai ciwo ne?" Kai na sake 'dagawa alamar ehh sai yace" Very sorry dear Ki yafe min Kinji?" Shiru nayi na 'ki kulasa. Shima bai sake ce da ni komai ba har bacci yayi gaba dani. Ko da asubah dana farka ban gansa cikin 'dakin ba, sai nayi zaton ko masjid ya tafi, shaf na mance da abinda ya faru, 'ko'karin mi'kewa tsaye na fara nan naji 'kafafuna sun ri'ke ni, komawa nayi na zauna da sauri hawaye na kuwa tamkar an 6alle su sai na dafe kaina a hankali na fara tariyo abinda ya faru, cikin hakan tunani na ya gangara can Shuwarin ganin da nayi masa da Husnah a can...sai na rasa ma dalilin da yasa nake jin haushin lamarin, ashe irin azaban da itama take sha a wurin sa kenan, Allah sarki shiyasa ranar naga tana zubda hawaye, gaskiya Yah Deen mugu ne shi na gaske. Na fa'da cikin raina, zuciya ta cike da fal da tausayin mu gaba 'daya. A daddafe na taka na 'karasa bakin bayin ina 'ko'karin saka silifas sai na gansa ya shigo jikin sa da farar jallabiya..da gani na tsaye awurin sai yayi saurin jefa min tambayar" zaki iya ne?" Cike da kulawa. Kawar da kaina nayi sannan na bashi amsa da fa'din umm hannu na dafe da bango. Sai yace" Kiyi amfani to da ruwan 'dumi kinji?" " Uhum"  nace tare da 'karasa shigewa na rufo bayin. Yinin ranar kam ba laifi na yi tane cikin kulawar sa da yake ma bai fara fita aiki ba tukunna, hakan yasa muka yini a gida tare da shi, sau 'daya kawai ya fita ya mana odern abinci sai kuma masallaci da yaje. Lokacin da ya sanya 'karamar riga ne naga inda na yakushe shi ashe  wurin har ciwo yayi kau da kaina nayi sai kuma naji ba da'di har cikin raina. 'Kilan hakan ne yasa idan zai fita sai ya canza riga zuwa mai dogon mai hannu dan ya rufe wurin. Yah Deen kam da ya fahimci.bana sakewa da shi sai ya ke barin idan nake dan kar ya takura ni, suna dai yana gida ne amma ba inda nake ba, ya kan shigo dai akai kai duba ni dan ko abincin ma da kansa ya zo ya 'diba min duk da ina cikin ciwo amma bai hana ni mamakin sa ba, ni dai sai naga bai canza min daga Yah Deen dana sani tun farko ba, fuskar sa dai wasai ba yabo ba fallasa amma bazaki ta6a iya fassara yanayin sa ba, tunani na kuma bai bani cewar a yau 'din ina matu'kar bu'katan kulawar sa ba, dan ni ko shigowa da yake yi ma takurani yake yi, saboda har a lokacin tsananin kunyar sa da haushin sa ne suka yi min ca. Hankali na ya 'kara tashi ne da lokacin bacci na yayi, fargaba yabi ya cika min zuciya, duk yanda naso in kawar da tunanin abinda ya faru tsakani na da shi jiya kasawa nayi saboda yanda tsoro ya mamaye ni. Haka na kwanta luf amma motsin kirki idan naji sai zuciya ta ta harba take sai in shiga firgici. Lokacin da naji ya janyo jikin sa kuwa kusan sumewa nayi jiki na ya fara kakkarwa sosai..yi nayi tamkar ina bacci da tunanin 'kila hakan zai sa ya 'kyale ni duk dama nasan jiya ina cikin baccin amma ya tada ni bai kuma sassauta min ba. Cikin sa'a ma sai bai yi min komai ba ashe shi da kansa ya fahimci halin da nake ciki na tsorata da nayi da shi, da kansa ma kuma bai yi niyyan yi min komai ba,  ina rungume cikin jikin sa naji yana sau'ke numfashi da alamu bacci ne yayi gaba da shi. A fili na sau'ke ajiyan zuciya sannan na bu'de idanu na, hannun san da ya rungumo ni da shi nabi da kallo a hankali na 'daga nawa hannun na 'dora kan nasa kamar ance dani inyi hakan. Ban san lokacin da bacci ya tafi da ni ba, yayin da nayi bacci na cikin kwanciyar hankali. Kwanan mu biyu da shi amma bai sake yi min komai ba, haka kuma har a lokacin shike siyo mana abinci rana da da na dare, haka kuma ako da wani lokaci ya kan tabbatar da cewa nayi amfani da ruwan 'dumi, nima kuma da yake na fahimci idan nayi amfani da shi 'din ina jin da'di shikenan da kaina ma ko bai tuna min ba na kanyi anfani na da shi. Sosai na fara sakan jiki na ganin irin waccan abin bai sake faruwa ba, gashi ba laifi yanzu na 'dan samu samu lafiya da yake da kansa ya duba ni,  bana so amma bazan iya yi masa gardama ba dole inaji ina gani ya gane min jiki na da sunan wai duba lafiya ta...ranar haka na yini ina tura baki na, ga shi kunya sosai ya kama ni fiye da na ranan can...ko lokacin da ya gama duba nin ma kifa kaina na yi na kasa 'dagowa in kalle shi..ga haushi ga kunya haka suka taru suka hanani sakat...shi kam sai naga ko ajikin sa bai damu ba...cikin zuciya ta na raya ai dama Yah Deen ba shi da kunya sam. Ranar kwana na uku da jinyan nawa ne na sake raina kaina, domin Yah Deen mantar da zuciyar sa yayi wace ni, ya manta da batun tsorona ya kuma kawar da kai ga 'kan'kantar shekaru na, tun kafin yayi nisa na raina kaina, domin ji nayi ko na farkon ma ba komai bane  akan yau, azabar na danaci ranar sam bazan iya misaltawa ba. Nayi kuka kamar raina zai fita ko tausayi na bai ji ba yau kam bai min sassauci ko na 'kwayar zarra ba, ba 'karamar wuya nasha a hannun sa ba. Tun daga ranar ya maida ni abincin ruhin sa, duk lokacin da yaga dama baya ko bi takan hawaye na...watarana da abin ya isheni ne ina kuka nake ce da shi ya 'kyale ni ya tafi wurin 'yam matan sa, ni banaso yaje inda ya saba wurin Husnah ya 'kyale ni. Da jin na ambaci sunan Husnah sai ya bige min baki na take kuwa nayi shiru ina hawaye cike da takaici. Sam ni banason abin nan da yake yimin, sa'a ta ma 'daya yanzu yakan fita asbiti bakin aikin sa baya yini a gida, hakan yasa nake 'dan samun sararin da zan zauna ni ka'dai, a haukana gani nake zama tare da shi 'din takura ne babba. Abu 'daya da yake tilastawa kansa shine lalla6a ni a duk lokacin da yaso ra6a ta, amma idan zaki gan mu da shi haka bazaki ta6a zaton muna zaman kirki a gidan ba, saboda babu wata sha'kuwa ta zahiri a tsakanin mu rayuwar sa yake yi nima nake yin tawa, musamman ma da ya fahimci ba nason zama da shi shikenan ya sawa zuciyar sa gudun takurani, tunda ya fahimci bana samun walwala a inda yake sai yake taka tsantsan da duk abinda zai takurani balle ya shiga rayuwa ta,  lokacin baccin ne kawai rayuwar mu take zama wuri guda wanda hakan ma dan yasan ba zai iya bane. He was da so kind to me that koka'dan ban ta6a zata ba, ban ta6a tunanin zai saki ransa mu zauna har haka da shi ba hantara ba, cuz a zato na zan fuskanci abu fiye da hakan a zama tare da shi. Ni sam  hakan sai ta6a damu na ba dan banga aibun sa ba ballantana in hango illar sa, abu 'daya da na sani shine kawai Yah Deen mijina ne na aure wanda idan nayi masa biyayya wata'kil Allah ya ha'da ni da rahamar sa, ko shawarwarin da akayi ta 'dura min cikin kaina har yanzu suna nan a brain 'dina ban manta ba, sai dai har yanzu ban ta6a tunanin akwai ranar da zan iya amfani da wasun su ba, saboda a gani na a gun Yah Deen ba aiki zasu yi ba da ma ace wani daban ne, ban kuma ta6a yin tunanin zamantakewar mu da sha'kuwar mu zai iya saurin dai-daita ba idan nayi amfani da damar da nake da shi musamman da nasan cewa yakan sau'kar min da kansa aduk lokacin da yake son ra6ata ba. Na bar hakan ne matsayin dole akai na ne kawai matsayi na na matar sa shiyasa a kullum yanayin zama na da shi bai ta6a damuna ba. Da kaina na fahimci 6oyayyen halin sa na sanyin hali, kyautatawa da kuma sanin hakkin wanda ke tare da shi, sai dai idan baki zauna da shi sosai ba bazaki ta6a gane hakan ba, 6angare na kuwa duk da na fahimci duk wannan amma sam nakasa yin wani yun'kuri dan yin amfani da damammakin da na samu. Ko dogon hira ban ta6a zama nayi da shi ba, gani nake kamar komai da Addah ta ta koyar dani idan nace zan yi a wannan gidan tamkar wahal da raina ne kawai,  shiyasa na share na watsar da komai hakan ma da muke rayuwa ni anawa ganin ya ishe mu. Na kan yi waya da duk makusanta na, Ammi na, Ummah ta, Anty Zainab, Addah na Maryam Saif da sauran su, Yah Usman ma sau 'daya na ta6a 'kiran sa muka gaisa ya tambaye ni akwai matsala ne nace da shi bakomai yace to shikenan idan da wani abin in sanar da shi nace to, tun ranar ban sake 'kiran sa ba haka kuma shima bai 'kira ni ba, Addah Saudah kam ba waya a hannun ta shiyasa ban ta6a samun daman magana da ita ba tunda na zo garin Bauchi. Addah Maryam ma kan yawaita tambaya ta yanayin zaman mu sai ince da ita ai bakomai yanzu lafiya lau muke zaune, a kullum ta kanyi 'ko'karin ganin ta 'dora ni a kan hanya amma ni kam a wautata sai dai inji ta inyi murmushi kawai a 6oye..ko da wasa ban ajiye akwai ranar faruwan irin zaman da Addah Maryam take tunanin muna yi ba. Anty Zainab ma yanzu bana gaya mata komai dake tsakani na da shi, kullum idan ta tambaye ni sai ince da ita ai ya canza yanzu ba kamar da ba...duk da haka Anty idan tayi waya da shi akullum sai ta yi masa fa'dan cewa dan Allah kar ya yawan yi min masifar sannan sai yayi dariya yace" Itace ta ta gaya miki ina mata masifa ko Anty?" " a a haba dai, ai nasan  halin kane Mu'een shiyasa". Yace " To ki kwantar da hankalin ki Anty, ni da ma ba zama nake yi agidan sosai ba yaushe zan ganta ma har nayi mata masifa.." " Bangane baka zama ba, ba ka ganin ta? Kamar yaya? wai kana nufin a haka kuke zaman auren Mu'een?" " Kai Anty ba yanda kika 'dauka nake nufi ba". Tace " To yaya ne?" Yana sosa kansa ya bata amsa da fa'din " Ina ganin ta mana Anty,  amma ai kinsan abubuwa sun min yawa yanzu sai ahankali bana  samun zama ne sosai". Anty kawai sai tace "  Hmm.. Allah dai ya shirya min kai". " Ameen Anty na". Ya 'karasa maganar da 'yar dariya Duk da hakan a kullum Anty bata gajiya da tunasar da shi yaji tsoron Allah ya gujewa sharrin duniya, ta kan kuma ce da shi dan Allah ya ringa sassauta min da yake tasan ni da masifar tsoron sa. Ko Ammi ma ta kan yawaita tambaya ta abinda ke damu na acewar ta wai sanyi na yayi yawa, sai dai inyi murmushi ince da ita bakomai, dan ni yanzu nawin Ammi nake ji sosai...yanzu nasan asalin matsayin ta waje na. Ko bayan gama wayar ta mu da ita ma murmushi  kasa barin fuska ta yayi saboda jin da'din yanda suke bani kulawa, ni kaina yanzu bazan iya ce ga matsala ta ba, cuz ban san ta ba, na kan samu kaina cikin matsananciyar nisha'di idan ina game da waya ta, in 'dauki pics in yi duk yanda nake so da ita, zan yi wanka na in sanya duk irin sittirar da nake so babu mai takura ni, ko shi Yah Deen 'din ba shiga sabgata yake yi ba, ko da kwalliya nayi baya yabamin a zahiri, baya nuna hakan ya birge shi cuz' gudun 6ata min rai yake yi, gani yake kamar idan ya nuna jin da'din sa zan daina sakewa ina abinda raina ke so cikin gidan, banda ma garga'din da Ammi take masa shi da kansa ma baya da burin takura ni ballantana ya hanani sukuni, duk irin dressing 'din da zanyi baya min kallo sau biyu yi yake tamkar hakan baya gaban sa, nima 'din kuwa ba dan shi nake yi ba, ina yin abu na ne kawai saboda nisha'din kaina, babu kowa da ke kawo min ziyara haka nima babu inda nake zuwa, to da wa ma zan zauna balle har inyi hira? ko shi mai gidan ma ba zama yake dani yayi hira ba balle wani daban. Zama na ni ka'dai da na saba da shi 'din nan shine ya sa sanyi na ya 'karu sosai, har Ammi suke ganin kamar da wani abu da ke damuna. Duk cikin su kuwa babu wanda bai 'kira yayi masa tambaya a kaina ba, shima 'din ce musu yake yi ba komai, Ammi kam kullum bata gajiya da sake garga'din sa akai na, takance wallahi matu'kar ya zalunce ni Allahn ta nan, yasan me hakan yake nufi dai-dai yake da Allah ya isan ta akansa, har mamakin su yake yi ma wani sa'in, shi a ganin sa ai tun asali haka halayyata take me yasa yanzun kuma ake neman 'dora alhakin akansa dan kawai zama ya ha'da mu? Shifa shiyasa bai ta6a ba'kin ciki da irin zaman namu ba, yanda banaso ya shiga harkata 'dina na hakan yafi masa sosai, aganin sa yawan zama ke kawo sa6ani har asamu matsala ta kunno, in kuwa irin zaman nan ne yasan zamu da'de bamu samu matsala da shi ba, zamu kwana tare mu tashi shikenan ba abinda zai sake ha'da mu har sai ya dawo, idan ya dawo 'din ma baya bu'katar inyi masa komai, zai yi wankan sa ya shiray sannan ya fito yaci abincin da already na ajiye masa, ko da wasa bama ha'da lokacin cin abinci, bai san me zai ha'da ni da shi da har zai zalunce ni ba aganin sa, kuma yaga duk wasu dokoki da ya kafa min tun da aka kawo ni gidan sa acan Shuwarin har yau su nake bi, tsafta ce matsalar sa kuma ba laifi bai ta6a kamani da kuskure kan tsafta ba daga 6angarorin tsaftar jiki da muhalli duk ina kulawa so bashi da matsala dani har abada matu'kar zan kiyaye hakan. Da abin ya ishi Ammi ne sai tace da shi yayi hanzarin nema min makarantar da zan 'karasa secondary na bata son zama shirun nan. Bai 'ki ta Ammi ba dan shima 'din kansa abin yana ransa kawai bai 'karasa nutsuwa bane shiyasa bai 'dago zancen ba. *****        Sannu-sannu lokaci ya 'dan tafi ka'dan, domin mun doshi makwanni shida da dawowa garin Bauchi, nima yanzu ba laifi na riga na tilastawa zuciya ta da jiki na sabo da komai da ya shafi Yah Deen na daina damun kaina, balle ma da yake ba kullum ne yake neman hakkin sa wuri na ba, yakan yawaita tsallake ranaku hakan kuwa ko nima yafi min har a zuciya ta. Abu 'daya dake tsaye min rai a yanzu shine ganin da nayi masa da Husnah, bansan me yasa wannan mugun abin ya ke yawan dawo min cikin tunani na ba, na rasa me yasa na kasa mancewa da shi. Ko abinda ya faru da Ma'u baya damina kamar na Husnah, duk da yake cewa ta dalilin sa Ma'u ta rasa rayuwar ta amma nata bai dame ni sosai ba, a kullum 'kara zirfafawa nake yi cikin tunanin waye miji na? Mecece kuma asalin halayyar sa?" A yanzu kam na riga na samo wa'dannan amsoshin domin babu makawa dole ne yaci sunan da nasan ko shivkansa ba zai so a 'kira shi da shi ba, babu batun kuskure idan ma nace zan 'kira ala'karsa da Husnah matsayin kuskure yayi amma da'dewan da nayi ina ganin su tarecya zarce a 'kira hakan da kuskure, in haka ne kuwa kenan sun da'de suna aikata son ransu, sannan yazo ya 'kara ribatan Ma'u ya yaudare ta da soyayya 'karshe ya barta ta mutu cikin 'kuncin zuciya...Allah sarki. Kwata-kwata yanzu na daina tausayin Husnah na daina tausayawa ala'kar ta da shi domin na fahimci harda amincewar ta wannan hawayen da na gani 'kila na wani abin ne daban ba   na irin azabar da naci a wurin sa ba. Kalmar da ya kamata a 'kira shi da shi koka'dan bana so ko cikin raina in ayyana ta saboda ciwon da hakan ke min, amma ya zanyi...nasani ko da ni ban 'kira shi da sunan ba dole ne da yawan mutane da hakan zasu ganshi, ni kuma aganni matsayin matar sa. Rintse idanu nayi a hankali hawaye ya gangaro min..a cikin raina na furta 'kaddara kenan...Allah kai ka'dai kasan dalilin ha'da ni da shi, Yah Allah ka shirye shi ya daina duk abinda yake aikatawa marasa kyau, Yah Allah kayi mana gafara gaba 'dayan mu, Ubangiji Allah ka raba mijina da neman mata"....karo na farko kenan da na ambaci Yah Deen da wannan kalmar wato Miji na, ada ko da zanyi masa addu'ah sai dai ince in ro'ka masa gafara da shiriya matsayin Yah Deen, amma yanzu kam nasan babu makawa miji yake agare ni kamar kowa...Ko na 'ki ko naso hakan take ako ina, ciwon da hallayar sa yake min azuciya ni ka'dai nasan abu na. Gashi bani da abokin hira, ko da ma inada shi ba lalle in iya tattauna batun da kowa ba, shima Yah Deen 'din da farko idan ya ganni wata iri yakan so yaji damuwa ta amma sai in nuna masa ni bani da matsalar komai babu abinda ke damuna. A kullum baya jin abinda ya banbanta da wannan kalmar duk kuwa 'ko'karin da yake yi wajen ganin ya magance min damuwa ta ko da ban furta ba amma wannan kam ya kasa ganewa balle ya taushe ni...haka na bar abin cikin zuciya ta amma da shi nake ganin sa ko da wani lokaci. A kullum kuwa zaki ganni babu wargi, ina nan ne haka shiru har abin yabi jiki na, hatta Ummah ta ban iya yi mata dogon surutu yanzu haka ma Ammi...6angaren Ummah ta kuwa ita ka'dai tasan yanda hakan ya dame ta, gani take kamar ina cikin 'kunci ne amma ban gaya mata ba. Addu'ah kawai take bina da shi a kullum kamar yanda ta min al'kawari kafin na taho. Cikin hakan akayi min register na makaranta amma wai sai dai in yi full Ss3 har zuwa lokacin da za'a yi SSCE . Ni kam sai naji hakan yafi min, dan ko ba komai zan huta da zama shirun nan. Gashi ma Allah ya taimake ni anzo 'karshen semester dole sai next semseter zan cigaba da zuwa so yanzun zan na zuwa ne kawai ina 'dan revising abubuwan da na manta. _Afuwan please kun jin shiru...._ _Comment_ _Vote_ _Share_ *Salmern ku ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *69* Hakan kuwa akayi domin sai da na sake cin wata guda a gida kafin nan da hutu ya 'kare muka fuskanci karatu. Fara fita ta makarantar ne nayi sabo da wasu 'dalibai 'kalilan classmate 'dina, sai dai ha'duwa ta da su bai sa komai daga gareni ya canza ba ina nan a yanda nake da halayya ta...sai dai ba laifi sukan ta 6angaren su domin sosai suke 'debe min kewa da surutan su, dan sun iya hira. Cikin hirarrakin nasu ma nake sake fahimtar wasu abubuwan rayuwa, ni dai ban ta6a fa'di wa ko 'daya daga cikin su komai da ya shafe rayuwa ta ba amma duk da hakan yawan kawo hirarraki yasa har na fahimci ashe akwai wasu dake fama da irin tawa damuwar, a hankali nake 'kara fahimtar cewa irin su Yah Deen na da yawa a fa'din duniya, wa'danda sam ba da tarbiyyar da mahaifan su suka 'dora su akai suke amfani ba. *****      Babu yabo babu fallasa nake karatu na, ban kasance daga cikin 'dalibai masu haza'ka da bu'da'd'diyar 'kwa'kwalwa ba, haka kuma bana daga cikin wa'danda za'a 'kira su da marasa 'ko'kari, karatu na dai-dai iyawa ta nake yin ta...a hankali kuma nake 'kara fahimtar salo da hikimar dake cikin rayuwa cikin natsuwa. Jigon zaman aure, biyayya da kuma kawar da kai duk yanzu na 'kara fahimtar su a 'dan zaman da nake yi da classmate 'dina, duk dama nasan wasun amma ada nakanga kamar Addah Maryam son ranta kawai take gaya min, ko kuma ni 'din sai inga kamar ba iri na ke yin hakan ba, ko kuma tunani na ya tafi akan cewa ni 'din nawa mijin ba nasara zanyi akan sa ba ko da na aikata hakan. Yanzu me na fahimci ashe yanda nake tunanin Yah Deen 'din ba haka yake ba wanda a yanzu nake ganin kamar ko nima zan iya dawo da hankalin mijina izuwa gareni ni ka'dai, matsalar kawai shine ban san ta inda zan fara ba, inaso inyi hakan amma ban san ta ina zan fara shigan ta ba, hakan yasa na cigaba da bibiyan abin cikin raina. Tun ba yau ba Addah ta ta gaya min cewa duk wacce Allah ya jarabce ta da miji irin nawa mai kula wasu matan a waje,  wallahi zama bai ganta ba sam, dole ne matu'kar tana son dai-daita al'amuran gidan ta sai ta tashi tsaye ta hana idanun ta bacci, ta ro'ki ubangijin ta ta kuma dagewa wajen kula da dukkan al'amuran sa, kula da hakko'kin sa da sauran su, a wancen lokacin ganin abin nake tamkar wasa, gani nake tamkar ni ban kai matsayin ba tukunna, da yake kallon wasa nakewa auren namu, sai gashi yanzu na fara sanin muhimmancin aure na, ina jin zafi cikin raina idan na tuna halayyar miji na. Addu'ah kam ba laifi ina 'ko'karin yinta amma sauran abubuwa kam har yanzu ban ga ranar yin su ba...(agani na kenan). Haka na cigaba da zuwa makaranta ta hankali na rabe bibbiyu, sai dai ban bari 'dayan 6angaren ya rinjaye ni ba kawai nafi bada hankali ga karatu na. Shima Yah Deen duk wasu abubuwa da ya kamata yayi su bayan gama makarantar sa anan garin Bauchi yayi su, a asbitin ya ha'du da sabon abokin sa mai suna Safwan wanda ko makarantar da nake yi ma tare da shi suka yi min komai. *****         Watanni biyu da sati uku kenan da zuwan mu garin Bauchi wanda yake dai-dai da cikar shekara guda yanzu da auren mu. Bazan ce ga abinda Yah Deen yayi min na rashin jin da'di ba tun zuwan mu Bauchi haka kuma bazan iya furta shin tsakani na da shi wake son wani cikin zuciyar sa ba, har yau na kasa fahimtar hakan. Ni dai ta 6angare na nasan bana jin soyayyar sa cikin raina, amma na kanji kewar sa a duk lokacin da baya tare dani, na kanji tsananin son ganin sa matu'kar na yini  ban gansa ba, sannan na kan yawaita tsintan kaina da son faranta masa duk dama ba yaba min yake yi a zahiri ba amma bana damuwa, uwa uba kuma kishin sa da na fahimci yake damu na, da kaina na fahimci kishin sa ne ke sani yawaita tuna wancan al'amarin da har ya kasance wani lokacin idan na kasa controlling zuciya ta har kuka inayi da hawaye na saboda ciwon sanin halayyar sa da nayi tun abaya, da kansa kuma zaki ga ya rarrashe ni idan yana gida dan ya rsani ganin hawaye a idanu na, in kuwa baya nan sai inci kuka na in 'koshi har inyi shiru, ko da ya dawo kuwa tambaya 'daya yake min akan me ya same ni har nayi kuka?" Idan yaji ban bashi wata gamsashshiyar amsa ba sai ya 'kyale ni baya sake kula ni akan hakan. Sau da dama irin hakan na faruwa tsakanin mu amma ban ta6a sanar dashi ainahin abinda ke damina ba sai dai ince masa ni kawai Ammi na nake missing. Wani sa'in zaunar da ni zama yake yi atake ya 'kira Ammi sai kiji ya 'kira Ammi ya gaya mata, idan ya ha'da mu awayar tayi ta bani ha'kuri tana lalla6a ta. Duk hakan kuwa ni a gani na basu isa hujjar da zan ri'ke su matsayin so ba, kawai na bar shine akan matsayin da yake da shi na miji agare ni shike sa ni jin wa'dannan abubuwan. Ko daga 6angaren sa kuwa haka na fahimta, Yah Deen baya sona a gani na dan bai ta6a furta min kalmar so ba ko da wasa, duk yadda yake shiga shau'ki idan munatare da shi amma hakan bai ta6a sawa yayi ko kuskuren ambata min kalmar so ba. Abinda nasan yake bayyane daga 6angaren sa shine yana matu'kar kula da duk al'amura na, baya son ganin kuka na a yanda na fahimce dan ko kusantata yaso yi idan na yaga ina kuka bari na yake yi, ni kuwa tsananin takaicin halin sa idan na tuna shike sani wannan kukan ba komai ba, amma zaki ga ya 'kyale ni ya koma lallashi na har muyi bacci, na kuma fahimci yana matu'kar jin da'din ganin walwata, domin a duk sanda na yi dariya har ha'kora na suka bayyana ko da bada shi nake ba zaki ga  shima yayi murmushi mai sanyi kuma ta'kaitacce. Tsananin kishin da yake da shi akaina ma ban kasa fahimta daga gare shi ba, shiyasa duk abinda zan yi na kan yi 'ko'kari sosai wajen ganin ban aikata abinda zai motsa kishin sa ba. Sosai ya garga'de ni lokacin da zan fara fita makaranta, a lokacin bai 6oye min ba yace min" matu'kar ina son Ammi da farin ciki to in kiyaye maganganun sa, yace min in kula da darajar aure na a ko'ina, rantsuwa yayi min akan cewar matu'kar na kuskura ya kamani da laifi ko kuma yaji ko yaga ina mu'amala da wasu mazan to in sani daga ranar batun makaranta ya 'kare kenan a rayuwa ta, idan kuma ina son farin cikin Ammi to dole ne in bi maganar sa dan baya tunanin zai iya sake rayuwa idan har wani labari daban ya riski dangin biyewa wasu mazan dan yana da tsananin kishi wanda yake tunanin har lahira zai iya kaishi idan har akan iyalin sa ne, kuma mutuwar sa dai-dai yake da tashin hankalin Ammi da Alhaji harda Anty Zainab..ya 'karashe da fa'din..." Ko kina so kiga hankalin su Ammin ki a tashe?" Da sauri nace da shi  a a gami da girgiza kaina. Sai yace" to dan Allah ki kiyaye kinji?" Ya hane ni da shiga motar haya, hawa lift ko wani abu yace sam bai amince min ba, yace matu'kar inada bu'katan zuwa gida lokacin tashi ne a school ko wani abu daban idan bangan sa ba to in 'kira shi a waya kawai zai zo ya same ni. 'Banagaren abokan sa ma duk yana taka tsantsan da duk wata ala'kar da zata ha'da mu, bama ya kawo kowa gidan sa, Safwan ka'dai ne Yah Deen ya sakewa fuskan zuwa gidan sa,  shima 'din kamilalliyar sutura ya hore ni da sawa ko da yazo. Duk wannan kuwa agani na ba so bane tunda bai furta da bakin sa ba, kishi ne da kuma son kula da maratabar auren sa ya ke sa shi yin hakan, balle ma da nasan lamarin da ya faru tsakanin sa da su Imrana shikenan na bar dalilin  akan hakan, dan tun lokacin ya ke gudun abota da kowa, Ishaq ka'dai ya yarda da nagartar sa sai kuma Safwan mutun na biyu. A yanda tunani na ya bani a hakan na 'dauka kuma naji araina gaskiyar kenan, wato babu wata soyayya tsakani na da shi, haian yasa ban ta6a bawa kaina 'kwarin gwiwar gyara mu'amalar mu saboda a gani na tunda baya sona ai babu amfani yin hakan, dalilin kenan da yasa muka cigaba da zama cikin gidan auren mu amma babu wata sha'kuwa tsawon lokaci. *****     Shirye- shiryen bikin Safwan aka fara gadan- gadan (bikin ku kenan) ta 'dago ta kalli Hafsat, sannan ta cigaba da fa'din sai kuma ya kasance Yah Deen sune a gaba da komai har aka 'kare bikin wanda nima sai lokacin ne ya kaini gidan su Safwan wajen mahaifiyar sa, ko ranar bikin ma can na yini da su, 'kannen sa kyawawa da su fulanin Bauchi, sosai Allah ya ha'da jinina da su, dan ma biyu daga cikin su daga wasu garuruwa suka zo ba anan suke aure ba, 'daya ce ka'dai ke aure a Bauchin amma duk da haka sosai sha'kuwar mu tayi 'karfi. Duk matsayin 'kanwa suka 'dauke ni da yake duk sun girme min. Ba 'karamin da'din zama da su nayi ba dan kuwa basu da mugun hali, kafin 'karewar bikin kuwa har ji nake dama Yah Deen ya barni in zauna agidan tare da su in huta abina, ni da kaina ma nasan hakan ba mai yiyuwa bane, domin kusan 3days muna zirga-zirga zai kaini zai kuma koma ya 'dakkoni da kansa baya gajiya amma ba zai ta6a bari na in kwana ba. Su kuma 'kannan Safwan ganin hakan da suka yi sai suke tsammanin sosai wai miji na yake ji da ni shiyasa ma ba ya bari na kwana a waje. 'Daya daga cikin su ce tana dariya tace" ai kuwa ba laifi Noor akwai kyua ga tsafta 'kila sune suka sa tayi nasaran siye zuciyar shi". Dariya suka sanya harda nima ina sunkuyar da kaina dayake nasan ba hakan bane, tana cikin dariyar ta 'kara da fa'din amma fa kin birge ni wallahi, gaki 'karamar yarinya amma Allah ya baki baiwa, mutum kamar Dr. samun kansu abu ne mai wahalar gaske, na jinjina miki 'kanwata". Murmushi na ne ya 'karu still ina 'kara sunkuyar da kaina cuz sosai kunyar su ta kamani. Wannan shine _kallon kitse ake yiwa rogo_ dan duk yanda suka 'dau ki abin ba haka yake ba. Ban 'kara tsinkewa da al'amarin su ba ma sai lokacin da 'daya daga cikin su ta bani wani turare akwalba 'dan 'karami mai shegen 'kamshi tace wai sai zan kwanta zan yi amfani da shi, inshafe a jiki na har zuwa wuya na..tana murmushi tace wannan kam da kanki zaki zo ki bani labari 'kanwa ta". Murmushin nima nayi cikin raina nake jinjinawa karkataccen tunanin su, nan wai su a dole sun ga masoya...hmm Wani sa'in idan na tuna maganganun su har dariya kamani take yi ni ka'dai, sam koka'dan banji haushi ba, ji ma nake da ace yanda suke tunani 'din zai faru ai da sai nafi kowa farin ciki da samun natsuwa, nima da kaina yanzu ina so inji kalmar so daga bakin miji na sai dai ga dukkan alamu bani da wannan matsayin agare shi...hakan yasa na bar abin a zuciya ta. Lokacin da na koma gida kamar yadda Anty Fiddausi 'kanwar Safwan ta gaya min haka nayi da turaren da yake bata fito fili ta bayyana min ainahin amfanin sa ba hakan yasa nima ban yi wani dogon tunani akai ba. Zato na ko kawai turare ne na bacci shiyasa nayi amfani da shi, ai kuwa ranar na gane kure na wajen Yah Deen, dan ko kukan da na keyi ma ranar bai bi ta kai ba sam...anjima ka'dan ya kuma dawowa kamar zan mutu haka naji. Da kansa da asubah yake tambaya ta wai a ina na samu turare mai 'kamshi haka, 'kamshin ya masa da'di" Ban 6oye ba na fa'da masa cewa sistern Abokin sa ce ta bani. Sai yace to ince mata ta kawo zai siya min". Da yake na fahimci 'kamshin ne ya ja ra'ayin sa har jiya ya takura ni sosai shiyasa take na juya kaina 'dayan 6angaren sannan nace ai ya 'kare na wajen tan". Yace " To bari zamu nemo ba'a akwai aurin ki ba?" Girgiza kaina nayi sannan cike da 'kosawa nace" Ni a a, babu dama ba yawa kuma san min tayi a wani kwalba 'karami". Nayi.maganar ne ina tura baki na, baya kallon idanu na amma daga yanda nayi maganar yasan 'dayan biyu ne, inma raina baya son maganar da yake min 'din ne ko kuma zancen turaren ne ban so. Hakan yasa yayi shiru bai sake yi min zancen ba. Ni kuwa gari na wayewa bayan na bashi.breakfast sai na koma cikin 'daki, turaren na 'dauka na tsiyanye shi a bayi na kora ruwa, kwalbar kuma na jefa a dustbin ina ta6e baki cikin raina nace" Bazan mutu akaron banza ba ni kam".  Ban kuma komawa gidan ba da yake biki ya 'kare so a waya ta tambaye ni batun turaren sai nace mata ai nayi amfani da shi har ma ya 'kare.. Sai tace min" Ya to kina son 'kari?" Da sauri na girgiza kaina sannan na nace a a please Anty Fiddausi ba irin shi ba ni kam". Dariya ta sanya sannan tace" Matsoraciya...kafin in koma ai zaki zo muyi sallama ko?" Nace" Erh zanzo". " Ok shikenan.." Tace daga haka kuwa ta yanke 'kiran tana min dariya. Shi da kansa Yah Deen da aka kwana biyu bai kuma jin 'kamshin ba sai da ya tambaye ni amma ban bashi amsar komai ba...hakan yasa bai kuma tambaya ta ba. Abinda baki sani ba Hafsat ko a bikin ku sai da Yah Deen yayi wata budurwa mai suna Yusrah inajin 'yar sistern Mummy ce mahaifiyar Dr Safwan. Yah Deen da kansa ya nemi ha'da ala'ka da ita batare da sanin Safwan ba har suka 'kulla soyayya, ko bayan bikin ku sun 'dan da'de suna tare da shi, har ala'kar tasu ta juye ta koma wani abu daban kamar yanda ya saba. (" Yah Deen kenan, inajin mantawa yayi da girman al'kawarin da ya 'daukan ma kansa na cewar ya daina neman wasu matan saboda Huda, musamman saboda girman abinda ta aikata masa na rufa masa asirin da tayi ban fa'dawa kowa sirrin sa ba, da kansa yayi al'kawarin yanzu kuma hala har ya mance...ka'dan kenan daga halayyar 'dan Adam...shine saurin mantuwa musamman ma abinda ya dace). Ni dai gani kawai nayi ya daina yawan nemana a shimfi'dar sa, duk da yake ma nasan ko ada 'din ba kullum yake ra6ar jiki ba amma na yanzun sai yayi yawa, ya kan shafe kwanaki bai nemi ha'da shimfi'da da ni ba, ban kuma san dalilin ba a lokacin, amma koka'dan bai canza min fuska ba da yake ya iya takun sa, ni kuwa hakan dama bai dame ni ba, ban damu ya nemi hakkin sa ko a a ba balle in sa abin cikin raina har in kuma kawo wani tunani daban. Da idanu kuma na nasha cin karo da 'kiran mace cikin wayar sa, na kanga suna Yusrah ta 'kira shi kamar yadda yayi saving. Dan a duk lokacin data ga dama 'kiran sa 'kira take yi 'kilan bai sanar da ita yana da mata bane oho, sassafe wataran zaki ga 'kiran ta, wani lokaci kuma yana wanka in ta 'kira idan na duba sai in ga sunan ta ko da yazo yagani kuwa baya ta6a 'kiran ta acikin gidan sai ya fita, cikin dare kuwa idan ta 'kirasa kashe wayar yake yi gaba 'daya yayi baccin sa, duk hakan da ke faruwa ina lura da shi ni kam sai dai in ta6e baki na kawai domin bani da damar da zan tunkare shi da maganar shiyasa na zuba idanu kawai ina ganin sarautar Allah. Hatta gidan Safwan ma da 'kyar yazo ya samu lokaci muka je bayan da Safwan yai ta masa gorin cewa kamata yayi ace shine ba'ko na farko da zai fara ziyar tar gidan sa  amma sai gashi ya nuna masa halin ko inkula, ko ranar da muka je 'din ma Safwan sai da ya maimaita hakan aka maida shi wasa, bai sani ba ashe Yah Deen kam wata ce ke 'dauke masa hankali da ya tashi daga aiki bashi da wani cikakken lokacin kansa sai nata. Ni dai ban sa cikin raina cewar akwai irin wancan ala'kar tsakanin su ba duk da yawan ganin 'kiran ta da nake yi, ina dai tsintan zuciya ta wani sa'in da matsanancin jin haushin 'kiran nata. Tsawon wata guda hakan na faruwa tsakanin su, acikin wata gudan kuwa kaf bai fi sau biyu ya nemi kusantata ba, duk hakan bai wani dame ni ba dayake yanayin rayuwar mu bata canza daga yanda take farko ba, duk wani da yasan zan bu'kata tun.kafin in nema yake kawo min shi, abu 'daya ne kawai nasan ya ishe ni shine yawan ganin 'kiran Yusrah da nake yi cikin wayar sa. Ranar ma lokacin bayan Isha'i yana zaune kan dinning ina serving masa abinci sai wayar shi ta fara ringing, wayar kuma tana can kan center table dake tsakiyar parlourn mu. " 'Dauko min wayar". Yace yana me kar6an serving spoon dake hannu na. Zuwa nayi na 'dakko masa wayar nan naga sunan mayyar nan" Yusrah. Nan take naji wani 'kululun ba'kin ciki ya taso min har zuciya na canza salon harbawan ta. Baki na ta6e ina mai 'karfafawa zuciya ta gwiwa da fa'din" Ina ruwan ki ke kuma Hudah?" Wata zuciyar tace dani" Ai mijin ki ne ba nata ba". Cikin raina nace" Jarababbiya kawai". Zuwa nayi na mi'ka masa still ina jin yanayin yanda heat beat 'dina ke saurin harbawa. Cikin idamun sa nake kallo domin inga reaction 'din sa amma ban ga komai ba. Kar6an wayar sa kawai yayi dai-dai lokacin da 'kiran ya yanke sai ya danna flight mode ya ajiye ta, sai a lokacin kuma ya kalle ni muka ha'da idanu. Saurin kawar da kaina nayi jiki na sanyi 'kalau na bar inda yake da yake dama batare muka saba cin abinci ba shima sai bai kula ni ba kawai ya bini da idanu. A fili ya fahimci kishin da ya taso min, shi da kansa bai ji da'din faruwar hakan ba har cikin ransa amma sai yaji ya kasa tantance abinda ya kamata ya aikata, tunanin sa ya kasa bashi abinda ya kamata ya aikata. Hakan yasa ya sunkuyar da kansa kawai ya fara cin abincin sa. Sati 'guda bayan faruwar hakan naje gidan mahaifiyar Safwan domin yin sallama da Anty Fiddausi zata koma Katsina garin da take aure, nan na samu ma har Mimah tazo 'karamar 'kanwar su dake aure a nan cikin garin Bauchi, itace ma na samu duk ranta a 6ace sai naji wani iri, lokaci-lokaci takan saki tsaki, har bayan zuwa na muka gaisa still naga fuskan ta bai canza ba, na samu Mummy bata nan tana wurin aikin ta suka ka'dai a gida dana tambaye su ita ne shine Anty Fiddausi ta gaya min. Na kan lura da su idan Mimah tayi wani 'dan reaction ko kuma tayi tsaki sai kiga Anty Fiddausi ta harare ta ni kuma muna hirar mu da ita cikin kwanciyar hankali. Da ta gaji da yanayin Miman a zuciye sai tace da ita" Wai ke ka'dai akace miki kika ji haushin abin ne? Ko kuwa son ta kika fi kowa aaka gaya miki? Bana son iskanci idan zaki dame ni anan maza ki shirya ki koma gidan ki na yafe miki zuwan, ai ma munyi sallaman ko..to maza ki tashi tafi gidan ki kije can ki kai 6acin ranki can kin ishe ni". Mimah sai cewa tayi" Wallahi abin ne da haushi wallahi Anty bazaki gane bane, ji bi 'yar yarinyar nan dan Allah amma ace tun yanzu har an fara raba mata hankali fisabilillahi". A zafafe Anty Fiddausi ta nuna ta da yatsa tana fa'din" Zanci mutuncin ki anan Mimah idan baki min shiru ba, baki da hankali ne?" Matsawa tayi nesa ka'dan sannan ta cigaba da fa'din" A a fa Anty ki barni in fa'di abinda yake cikin raina, wallahi abin ne da haushi sosai, yarinya tana ganin mutuncin mu kuma ace ga abinda ya fito ta 6angaren mu ai babu da'di, kuma in ba abin Anty Yusrah bama ina zata je da irin wannan rayuwar?.... Sunan Yusrah ka'dai da naji Mimah ta ambata sai da zuciya ta ta tsinke. Yayin da ta cigaba da fa'din"....Da gani ma fa bai wuci sa'an ta ba wallahi, amma tsabar duniyanci tabi ta nace masa bacin yana da matar sa a gida". " Ce miki akayi ita ta nace masa ne..ka fa fita ido na Mimah". " Anty ai cikin maganganun ta zaki fahimta, koma dai shiyace yana son ta amma ai ita ke damun sa yanzu kam, bakiji complaint 'din ta bane wani wai baya 'daga 'kiran ta idan yana gidan sa harda yi mata warning akan 'kiran sa idan yana gida, wai fa da gangan take yin 'kiran taji mai zai faru wai dan ya hanata.. shima 'din fa da alama saboda matar sa ne yake gudun 'kiran tan amma dan iskanci ta nace masa, ke bakiyi auren ba wa'danda suka yi kuma ki bi ki uzzura musu ki hana su zama da mazajen su lafiya...mtheww ni fa shiyasa tun farko jini na da nata sam bai ha'du ba wallahi, ko kunya ma bata ji wai tazo tana hirar abinda saurayi yake yi mata, fiye da haka ma ya kamata ta gani ai tunda ita bata san abinda ya dace da ita ba...duniyar ai gata nan ta ishi kowa, sa'o'in ta duk sunyi aure ita tana nan tana bin mazan wasu, amma tunda mutumiyar ki ce Anty dan Allah ki bata shawara ta barwa yarinya mijin ta in ba haka ba wallahi sai na gayawa Mummy abinda ke faruwa ba ruwa na...". Idanu kawai Anty Fiddausi ta zuba mata haka nima har ta dasa ayan maganar sannan Anty Fiddausi ta sau'ke numfashi tare da fa'din" To naji Mimah zan bata, amma please tashi ki ban waje dan Allah kinji?" Tashi Mimah tayi ta bar 'dakin tana fa'din" ai gaskiya ne Anty, mutune babu abinda suka iya sai biye-biyen maza ko'ina, sai sun je sun kwaso cuta kuma su cuci wacce bata ji ba bata gani ba a 'dauki hakkin ta a banza tana zaune a gida zaman bauta da biyayya...duk sai Allah ya saka musu wallahi". " Allah ya shiryeki Mimah...Fitinanniya kawai". Haka kawai Anty Fiddausi tace bayan fitan Mimah sannan ta dawo da kallon ta gare ni tace" Kiyi ha'kuri dan Allah Noor, Mimah duk ta hana mu hira da hayaniyar ta". 'Dan murmushi nayi murya ta har na kakkarwa nace da ita" Lah haba bakomai Anty" Na 'karashe maganar da sunkuyar da kaina na wasa da yatsun hannu na. Jiki na duk yayi sanyi da maganganun Mimah, ina tsoron kar wannan Yusrahn ta kasance itace da ke 'kiran Yah Deen, in kuwa itace nasan labarin ya riga yasha bambam, ayanda na fahimci aka bayyana halin Yusran to kuwa babu tantama biyu ne suka ha'du dan shima 'din ba baya bane wajen iya bin mace matu'kar tayi masa...Idanu na lumshe da kaina a 'kasa cikin zuciya ta na fara jero Addu'ar" Allah ka rufa min asiri, Yah Allah kasa ba mijina bane, Yah Allah kar ka jiyar dani abinda yafi 'karfin kunnuwa na wanda na gani da idanu na ma sun ishe ni, Yah Allah ka shiryar min da miji na ka raba shi da matan banza". Hawaye nake jin na son gangaro min amma na matse su 'karfi da yaji kan dole nake tilastawa zuciya ta kawar da tunanin ina maimaita Allah yasa ba shi 'din bane Allah yasa maganganun Mimah basu ha'da ala'ka da Yah Deen ba". Ina wannan tunanin ne kawai, mma ni da kaina nasan yaudarar kaina kawai nake yi domin ko da bani da hankali a yanda naga Anty Fiddausi ke 'ko'karin kawar da zancen tana kakkarewa nasan akwai dalili, 'kilan bata so ne ni inji shiyasa take 'ko'karin Mimah ma ta 6oye min kamar yanda ita tayi, sai akayi rashin sa'a ita kuma Mimah da yake fushin ta a kusa yake sai ta kasa jurewa. Anty Fiddausin kanta yau bamu wani yi dogon hira da ita ba, duk sai naga bata sakin jikin ta da ni wanda ni kaina ma a daddafe nayi yinin duk na 'kosa in koma gida. Koda Mummy ta dawo kuwa sosai ta nuna farin ciki da zuwa na, har kyuatan turaren wuta tayi min mai shegen 'kamshi. Mimah kam dama bata iya zaman ba ta tattara ta koma gidan saboda haushi. Da lokacin tafiya ta tayi kuwa sai Anty Fiddausi  ta 'dan bani shawarar ina 'ko'karin yiwa kaina da miji na Addu'ah saboda yanzu duniya agur6ace take". Nace" to Anty Insha Allahu zan ringa yi". Addu'ah kam ai ba ba'ko na bane, inda sabo ma na riga na saba bazan kuma gaji ba insha Allahu, da kaina nasan akwai ranar da Allah zai amsa min, ko ba yanzu ba wataran Allah zai amsa addu'ah ta zai kuma canza min ba'kin ciki na ya koma farin ciki insha Allahu. Yah Deen kansa da ya ganni sai da ya tambaye ni" Lafiyar ki kuwa?" Saboda gani na da yayi wata iri sai nace da shi lafiya ta lau". Daga haka na maida kaina gefen titi ina kallon.hanya har muka iso gida. Wannan abin sosai ya dame ni a zuciya gashi bani da wanda zan zauna inyi hirar da shi, sa'a ta ma 'daya yanzu ba sosai nake ganin 'kiran Yusrahn ya shigo wayar sa ba, amma duka da haka a yanayin yanda yake rayuwar sa na fahimci tare suke har yanzu. Bani da yanda zanyi da shi saboda rayuwar shi, kuma ban isa in sa ko hana shi aikata abinda ya ga dama ba, hakan yasa kawai na cigaba da bibiyan abin cikin raina. Wani lokacin haushin kaina sosai nake ji ganin yanda duk na damu kaina bacin abin bai shafe ni ba, amma idan na tuna ai miji na ne sai kuma inji erh ai da gaskiya ta. Idan kinga yanda nacrame har zaki yi mamaki amma ko da wasa ban iya na yi masa magana akai ba ko kuma in nuna masa cewa na san yana tare da wata ba. Shi kan sa ramar tawa na matu'kar 'daure masa kai amma bai san yanda zai yi da ni ba, idan tambaya ta yace zai yi yasan babu wata amsa gamsashhsiya da zai samu sanin hakan da yai yasa ya cigaba da zuba min idanu kawai. Sanadin rashin sakewar tawa ya sanya ya fasa zuwa Shuwarin da ni da dama ya ayyana cikin ransa cewar idan zashi wannan karon tare zamu tafi..ta ina zai 'dauke ni a haka ya tunkari Ammi da ni? da kansa ya san ko wurin Alhaji Baba sai ya amsa tambayoyi, sanadin hakan yasa bai ko sanar da ni ba ya fasa abinda ya shirya. Wasa-wasa sai da suka shafe a'kalla  kusan watanni uku suka suna tare da Yusrah, sannan Allah ya taimake ni labarin ya isa kunnan Safwan bayan haka ma da kansa ya sa idanu ya fahimci irin ala'kar da ke tsakanin sun. Sam bai ji da'di ba dan haka sai yayi saurin datseta da yake yasan asalin halayyar Yusrah ba mai kyau bane dama ta saba biye-biye. Kuma acewar sa ma yaushe Yah Deen 'din yayi aure harda zai fara raba hankalin sa kashi-kashi, da 'kuruciyar ka ka tsaya kana gur6ata rayuwar ka Mu'een, yace yarinya 'karama da ko haihuwar fari bata yi ba shine zakayi mata kishiya a waje? kishiyar ma irin Yusrah, yace matu'kar Yah Deen bai rabu da ita ba ya 'daukan ma kansa al'kawari har Shuwarin zai je ya gayawa Alhaji Baba in yaso.sai ya san mai zai ce da shi. Jin hakan ne ya sa Yah Deen rabuwa da Yusraj badan yaso ba, har kuma sai yaga ma wautar sa na 'daure kansa da kansa da yayi, domin kuwa Safwan shine mutun na farko da Yah Deen ya zauna ya bawa tarihin rayuwar sa kaf, har girman matsayin da nake da shi azuciyar sa sai da ya fa'da masa da dalilin hakan, a lokacin bai ta6a zaton akwai irin wannan ala'kar da zata sake ha'da sa da wata ba kwatsam sai yaga Yusrah, ya kuma ji son kasancewa da ita bisa tursawan Shai'dan y kuwa yi galaba akansa har ya leading 'din sa izuwa cimma manufar sa duk da yasan cewa Yusrahn matsayin 'kanwa take ga Safwan, ya 'kara basar da hakn ne ma lokacin da ya fahimci ba shine farkon da ta fara bada kanta ba, ga dukkan alamu ta riga ta saba da hakan. Safwan kam da yaji asalin halin Yah Deen daga bakin sa sosai abin ya bashi mamaki alokacin, dan yasan bazai ta6a yiwa kansa sharri ba, in hakane kuwa babu 'karya koka'dan cikin kalaman sa, tun lokacin shima ya 'kara jinjina min yake kuma 'kara bani daraja har a zuciyar sa, ya kuma bashi shawaran to ya ri'ke ni da kyau da amana dan bakowa ke sa'an samun irin hakan ba, da 'kyar ka samu wacce zata iya irin hakan ma cikin mata,( ko ita Salmerhn ba iyawa zata yi ba kuwa har ga Allah..lolz Allah ma ya tsare faruwan hakan) Cikin labarin da Yah Deen ya bashi ne ya fahimci har yanzu yana shakkan Alhaji Baba indai kan wancan batun ne shiyasa yayi saurin yi masa barazana da sunan sa ya kuwa yi sa'a Yah Deen ya janye dan gani yake tamkar Safwan zai iya aikata abinda ya fa'da musamman yanda yaga ya nuna 6acin ransa a fili shi kuwa ba zai sake kuskuren da Alhaji Baba zai zarge shi kan irin wancan rayuwar ba har abada, tsoron sake fuskantar fushin sa yake yi. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *70* Tun zuwan mu kuwa har yau ban ta6a zuwa Shuwarin ba, Yah Deen shi ka'dai yake zuwa ya dawo abin sa, duk yanda nake nuna damuwa ta  akan son tafiyar amma baya kulani ya kan je ya kwana 'daya tak ya dawo. Duk bayan tafiyar ta sa kuwa kuka nake yi sosai abu na saboda tsananin son zuwan da nake yi. Gashi abin haushin ko yaje ya dawo bana samun jin wani labari daga bakin sa abinda yake gaban sa kawai yake cigaba da yi... Duk yadda nake 'kaguwa inji yace min su Ammi sunce kaza, ko kuma Ummah tayi kaza...haka nake ha'kura domin Yah Deen baya bani labarin komai, ni kuma bana iya tamtayar sa. *****         Watannin mu takwas a garin Bauchi a lokacin mun yi nisa da fara zana SSCE, cikin 'dan hutun dake tsakanin Waec da Neco acikin sa  na fara fuskantan wasu sauyi tattare da lafiya ta. Zazza6in dare, da kuma yawu da baki na ya fara yawan tarawa, abin sosai yake bani haushi har cikin zuciya ta...gashi bansan dalilin ba sam. Da farko nayi tunanin Maleria ce ke damuna amm sai naga inba daren ba ba na sake jin alamun zazza6i ko wani abu sai dai ko yawun da yake 'dan takura ni wasu lokutan. Da yake ba gida yake yini ba hakan yasa bai da labarin halin da nake ciki. Ranar wata Juma'ah zai fita aiki da safe bayan har ya min sallama yana daf da fita daga parlour na 'kira sunan shi. Cak ya tsaya sannan ya waigo, sai nace" Dan Allah idan zaka dawo ka siyomin magani kullum yawu damuna yake yi sai na nasa abu a baki na. Kallo na ya tsaya yi batare da ya furta komai ba, yayin da cikin zuciya ta nake ayyana" Allah yasa dai ba 'kin siyomin zai yi ba". Kawar da kansa yayi ka'dan daga kallona tamkar wani tunani a hankali kuma naga ya tako izuwa gaba na. Fuska ta ya tsaya kallo kamar mai karantar wani abu.." Me ke damun ki?" Ya sake tambaya ta as if bai ji me na fa'da da farkon ba. Ban damu ba na sake maimaita masa cuz sosai nake so inga na daina wannan yawun. " Bayan shi fa ba wani abu?" Saurin girgiza kaina nayi. Sai yace min" In 'dauko mayafina mutafi tare idan an duba ni sai in dawo gida". Shi da kansa ma daman ya fahimci wani sauyi tattare da ni musamman na rashin sukuni a 'yan kwanakin kawai shiru yayi da tunanin in damuwa ce ke damuna ai da kaina zan fa'di.                Sai kuma gashi hakan akayi, Yah Deen da kansa ya gwada ni bayan isarmu asbitin nasu. Bayarwa yayi aka akai Lab shi kuma ya zauna tare da ni, kwata-kwata ma sai ya kasa yin aikin komai, har 'kiyastawa yake cikin ransa yanda zai ji idan hasashen ya zama gaskiya. Ai kuwa sosai nayi mamakin sa, dan kuwa hauka ne ka'dai be yi ba ganin sakamakon gwajin da akayi min da abinda ke 'kunshe a ciki. Wai ni Hudah ce ke 'dauke da ciki a jiki na. Dama tunda yaji abinda na gaya masa da sukayi kama da symptoms in masu ciki sai zuciyar sa ta kasa natsuwa. Lokacin da ya tabbatar cikin ne dagaske kuwa murna tamkar zai cinye ni, haka ya dinga bin jiki na kisses yana samin albarka da fara'ar sa...Alhamdulillah kawai yake ta faman maimaitawa cikin zuciyar sa. Haka kawai bazata ya tsinci kansa cikin matsanancin son cikin jini da zuciyar sa. A asbitin ne aka tabbatar mana da cewa cikin na watanni biyu ne kacal da 'yan kwanaki..godiya wa Allah ya ringa zubawa yana jin soyayyar cikin na 'kara ratsa shi. Ni kaina naji da'di sosai duk dama ban ta6a kawowa a kaina cewar nima zan haihu cikin lokaci 'kan'kani irin haka ba, amma yanzu da ya kasance na samu cikin sai nake jin da'di har cikin jini na, a gani na ai ko ba komai zan samu abokin hira a gida. *****         Samun cikin da nayi shine nasara na farko da na fara samu cikin zama na da shi, da kaina wani lokacin na kanji farin ciki matsananci, har ma sai inyi tunanin ai da na san hakan zai canza min zaman 'kuncin da nake yi da shi da tun farkon dawowar mu garin Bauchi zan ringa ro'kon Allah ya bani kyautar ciki ko dan in samu farin ciki ma, amma ko yanzun ma Alhamdulillah kawai zance domin a yanzu ne na fahimci 6oyayyiyar soyayyar da Yah Deen ya da'de ya ke min wanda bani da masaniya akai koka'dan sai ta dalilin cikin, duk dama wasu lokutan na kanyi tunanin cewa Yah Deen cikin sa kawai yake wa son bani ba amma wasu lokutan da kaina nake sake 'karyata tunani na, domin a yanda nake ganin yanayin sa sai kuma inga kamar abin yafi 'karfin cikin dake jiki na ka'dai. Kulawa ta musamman yake bani da ko a mafarki ban ta6a zaton samu daga gareshi ba. Yah Deen har kitchen yana shiga da kansa musamman da safe lokacin breakfast abinda ban ta6a ganin yayi ba kenan a kaf 'din rayuwa ta. Zallar soyayya da 'kauna mai sanyi gami da kulawa yake nuna min, sha'kuwa ce sosai ta shiga tsakani na da shi amma ta ba'dini, tun zaman mu da shi ko da wasa bai ta6a bayyana min abinda yake so game da ni ba, amma sai gashi yanzu da bakin sa yake irga min, yace babban abinda yafi 'kauna cikin halayya ta shine sanyi na...taurin kai na kuma baya 'kaunar sa sam. Da bakin sa yake zayyano min 'dumbin 'kaunar da ya jima yake min cikin zuciyar sa wanda kafuwar hakan ya samo asali tun daga ranar da ya fahimci na rufe masa sirrin sa wurin Ammi. Yace tun daga ranar ya ware min wani matsayi  daga cikin zuciyar sa wanda babu wanda ya kai gurin har gobe, ya bani muhimmanci fiye da kowa a zuciyar sa baya ga ahalin sa. Ban yi mamaki ba ko da naji hakan daga bakin sa, duba da yanda ya jima yana sanya ni cikin tunani ya 'daure min 'kwa'kwalwa ta na kasa fahimtar takamamme ko shi 'din waye ne da kuma matsayin da nake da shi a wurin sa. Da kaina yanzu idan na zauna na kanji natsuwa na ratsani, wasu lokutan ni ka'dai idan na zauna sai in ringa murmushi musamman idan na tuno kulawar da yake bani. Yau ina Addah Maryam, ina Anty Zainab kuzo kuga yanda a rayuwa ta ta canza a gidan aure na, ni ma da kaina nasan ina son miji na, so kuwa mai tsananin gaske. Yanzu ne na gane cewa miskilanci kawai a jinin Yah Deen yake, bawai yana min bane dan ya tsane ni ni ka'dai ko kuma wani abu daban. Sai dai kuma duk da hakan har a lokacin ban iya na saki jiki da shi ba, gani nake kamar watarana zai 'kara yi min irin wancan abin, 'kila sai bayan yaga na saki raina da shi sai ya sake kawo wata macen kuma, bazata inzo inci karo da abinda zai iya yin sanadin rayauwa ta, cuz na tabbata a halin da nake ciki na tabbatar da 'kaunar da nasan nake yi masa, nasan matu'kar na sake cin karo da irin wancan abin 'kilan sai dai a 'dauki gawa ta. Hakan yasa naji ban yadda da soyayyar da yace yake min ba, sai kuma na dawo da tunani na baya, da yake nasan yanzun ma dalili ne ya sanya shi furtawa ada bai ko ta6a nuna min ba, sai na barwa cikin da ke jiki na duk soyayyar da ya nuna min wanda na tabbatar har gobe bazai daina ba matu'kar cikin na nan kwance a jiki na...'kila da ba cikin ba zan ji komai daga gare shi da ya danganci so ba har abada. Haka na maida kaina kamar na'ura wurin tunani, duk wani abu da ya faru tsakanin mu sai dai in bishi da idanu, amma cikin zuciya ta kuwa tamkar zata fashe saboda yawan tunane-tunane. Batun kishi ma da kansa yace min shi tun asali ma yakanji matsanancin kishi na tun ma kafin batun aure tsakani na da shi ya gifta, yace ko da dasu Saif yaga muna mu'amala har cikin jinin sa yake jin haushin hakan amma a lokacin sai ya rasa dalilin sa na jin haushin mu gaba 'daya matu'kar ya gammu tare muna walwalar mu, sai daga baya a hankali ya fahimci halin da yake ciki. Duk kuwa 'yar sha'kuwar da ta gifta tsakanin mu da shi still ba koda yaushe ne zaki gan mu tare cikin farin ciki ba, da yake ma sha'kuwar bata zahiri bace hakan yasa duk kowa ke kama kansa wani sa'in, surutun Yah Deen na zuwa ne lokacin da ya ga dama har ma kiji yana bayyana abinda ke ransa, wanda nima cikin hakan nake 'dan tsintan wasu abubuwa da suka shafe ni, amma da yake wani lokacin yana 'dan canzawa ya koma asalin Mu'een 'din sa sai hakan ya 'kara sawa nake jan jiki na daga gare shi har sai in shi ya nemi zama tare da ni. Idan na zauna kuwa banda tunanin 'yan matan sa dake yawan min zirga-zirga cikin brain 'dina babu komai, duk wani abu idan kinga ya tsaya min arai to idan kika bincika ya shafi Yah Deen komenene kuwa abin, tun ban dangana  batun da su ba har dai nazo salon tunani na ya fara canzawa akai, sai nake ganin ai da dagaske yana so na 'din kamar yadda ya fa'di da ba zai 'kara neman wasu matan ba bayan ni. Wannan dalilin ne abu na 'karshe da yasa ni na kasa amincewa da cewa erh dagaske Yah Deen na 'kauna ta kamar yadda ya fa'di da bakin sa, a kullum sai na kasance cikin tunani da kokwanton maganar sa..abin kullum shine cikin raina ina jjujjuya shi, lokuta da dama ko da Yah Deen yazo min da sakin fuska ko da wata 'yar zolaya response 'din da yake lura da shi ta 6angare na shike sakan mai gwiwa da ni, dan ko abin dariya ne ban fiya taya shi yi ba, in hira ce kuwa sai dai in ta kallon sa duk da shima 'din ba wai gwani bane wajen hirar amma sosai yake 'ko'karin yaga ya faranta min yayin da ni a kullum nake nuna masa halin ko in kula batare da damuwar komai ba. Tun yana 'ko'kari yana danne rashin jin da'din sa game da yanda nake nuna masan har dai ya zo ya watsar da komai, muka koma irin zaman mu na baya, abu 'daya kawai ne bai bari ba shine kula dani da kuma cikin da nake 'dauke da shi. Gashi ta ko wani 6angare banda abokin shawara 'daya, in familyn Safwan ne ai suma Yusrah ta su ce, nasan da wuya ne su za6e ni su 'kyale ta akan koma menene, tunda ga ma misali 'daya yanzu kusan 5weeks bamu koyi waya da Fiddausi ba, ni agani na duk akan maganar Yusrah ne, duk da kuwa Mimah ta fito fili ta nuna 6acin ranta amma ai nasan naka nake ne. Ban sani ba ashe yanzu Fiddausi kunya ta wai take ji ne shiyasa haka ma Mimah su aganin su wai zanga kamar su munafukai ne shiyasa suka 'dan rage shiga jiki na, Mummyn su kuwa dama bata da labarin komai. *****          Ciki na 6months muka je Shuwarin ni da shi bayan tsawon lokacin da na 'dauka ban je ba, domin kuwa wannan shine zuwa na karo na biyu kenan tun bayan komawar mu Bauchi da zama, Ammi na murna sosai tayi da ganina,  bakin ta sai ya kasa rufuwa, yayin da ni kuma tsananin kunyar su ya rufe min zuciya ta, sai dai nayi ta sunkuyar da kaina ina murmushi kawai. Kunyar su nake ji tamkar bada su na taso ba, Yah Deen ma murmushi yayi ganin yanda nake yi 'din sai dai bai ce da ni komai ba. Ammi tamkar zata goyani data ga ciki ajiki na, cikin gidan babu wanda ya 6oye farin cikin sa game da cikin balle ma da yake su Saif na gida sai nake jin wani iri. Har ma sai naji dama ban biyo shi munzo ba. Gashi har 1week yace zamu yi kafin mu koma, ni yanzu kowa ma sai inji kunyar sa Yah Deen ka'dai ne ban jin nawin sa a wannan lokacin. Su Zaid angama makaranta duk sun 'kara girma shekara 'dayan da ban gansu ba sai naga sun canza min sosai. Ganin cewa yanzu da da da banbanci yasa kowa yanzu 'dakin sa daban ne, 'dakin su na da shi Zaidu ya cigaba da zama a ciki yayin da sabon 'dakin Saif yake facing da na Yah Deen inda muka sau'ka kenan. Washe gari da yamma ya kaini gidan Ummah ta, sai naji can 'din na 'dan fi sakewa da yake daga ita sai Ummie ne agidan na ukun sai ni da nazo. Bana aikin komai kuwa dan ko Ammi bata bari na in tayata aiki haka ma Ummah ta, ni kam har dariya suke bani ince hala manatawa suka yi cewar aure nake da shi yanzu, ko da banyi musu aiki anan ba dan cikin ai idan ina Bauchi ni ke yin duka aiyuka na. Abin mamaki inje gidan su Addah Saudah ma dana tambaye shi Yah Deen hanani yayi wai yanzu banda lafiya in bari sai wani lokacin ko kuma in 'kira in sanar da su nazo sai suzo mu gaisa. Haushi ma sosai ya bani a lokacin 'kin kulasa nayi, dan banga hujja ko manufar yin hakan ba, har ya kashe wayar bance da shi komai ba. Ace inzo har cikin garin amma zuwa gidajen su ne za'a ce bazani ba?" Sai daga baya bayan kusan awa guda na sake 'kiran sa kamar zan yi kuka nace da shi" Ai zan iya tafiya ni babu abinda yake damuna, amma ai in banje ba bazasu ji da'di ba". Sai yace" To ki bari zanzo in kaiki". Da sauri nace" Ni kam a a". Jikin sa sanyi yayi cikin natsuwa yace " Saboda me?" Nace" Haka kawai". dan nasan in shine ya kaini atsatstsaye  zai ce mu dawo kamar yadda yake min idan kuma je gidan Safwan ko gidan Mummyn sa, kuma gashi yau 'din har gidan Yah Usman da Binta 'kawata nake son naje. Jin amsar da na bashi ne ya sashi fa'din" To shikenam.Allah ya tsare". Na amsa da" Ameen" Ni da Ummie muka tafi, in kinga yanda nake tafiyar ma da 'kyar dan ba laifi cikin na min nawi ka'dan ga kuma 'kafafuna da suke min ciwo amma a hakan na dage dole sai na fita. Kowa idan ya ganni sai yayi farin ciki da zuwa na,   kowa na murna da yanayin da suka ganni, yayye na ka'dai ne amma ke jajanta min halayyar miji na sai inyi dariya in 'kara da yi musu 'karyar ai yanzu da sau'ki komai ya wuce, kuma muna cigaba da addu'ah har kullum. Kwana na biyu agidan Ummah ta Yah Deen yazo muka koma gida, ban tashi sanin manufar dawo da ni ayau 'din da yayi ba sai da naga yana neman ra6ar jiki na, nan kuwa nace bansan zancen ba, duk da nasan tun kafin zuwan mu Shuwarin ya 'daga min 'kafa kusan kwanaki goma kenan yanzu amma still na kauda kaina na'ki amince masa nace ni kunya nake ji agidan Ammi, ganin cewa gidan Ammi muke sai na fake da hakan, kuma har ga Allah ni banaso irin haka ya shiga tsakani na da shi a irin wajen nan bana iya sakin jiki na. Duk yadda yaso ya fahimtar da ni halin da yake ciki kuwa 'kin sauraran sa nayi na kawar da kaina, Yah Deen baya ta6a matsamin kan bu'katar sa matu'kar na nuna 'kin amincewa ta, dan haka sai ya 'kyale ni yayi kwanciyar sa. Da kaina nasan zunubi babba nake 'dibarwa kaina matu'kar na'ki yadda da bu'katar san hakan yasa da gari ya waye idan nayi sallah na gaishe shi sai kiga na marairaice fuska nace da shi" Ka yafe min ko?" Da yake ya saba ba sai ya tambayi dalilin yafiyar ba zaki ga yayi murmushi  shi kenan abin ya wuce nima sai in saki raina, ko da wasa bai ta6a fitowa fili ya nuna min 6acin ransa kan haka ba, kuma ko a gidan mu can Bauchi haka nake yi masa a duk ranar da nasan ya kwana da 6acin raina da yayi murmushin nan kuwa nasan me yake nufi. Washe gari da misalin 'karfe goma na safe yace wai in shirya in raka shi wancan gidan zamu dubo wasu kaya, duk da a tsare da fuskar sa ta asali ya min maganar amma hakan bai sa naji ko 'dar cikin zuciya ta ba, shiru nayi ina tunani sai da ya sake maimaitawa sannan na bashi amsa da fa'din" Ni dai bazani ba sai Saif ko Zaidu wani raka ka". Da mamaki ya kalle ni yana 'kan'kance idanu, taurin kanki 'karuwa yake yi kullum Nuree, yanzun duk kina yin hakan ne dan ki guje min ko me?" Girgiza kaina nayi idanu na na tara ruwa. Sai yace" To menene?" Nace " Ni kawai banson zuwa gidan ne, ko sunan unguwar banaso inji raina 6aci yake yi idan naje kuwa mutuwa zanyi...". Shiru yayi yana kallo na cike da mamaki, sannan yace min wai saboda me?" Nace "Kai ne ai...". Sai na kasa 'karasawa kuka ya 'kwace min. Idanu ya lumshe ya dafe kansa cike da damuwa, shi kansa baya so in yawaita tunawa amma ya zaiyi da bu'katar sa, da kansa yasan bai kyauta ba amma zuwa yanzu ai kamata yayi ace na manta na kuma yafe masa...tunda ko giya cecruwan shansa a yanzu bazai ta6a iya sake kawo wata macen cikin gidan auren sa ba indai ba aure ya 'kara ba. A hankali ya tako ya iso inda nake, kaina ya ya kwantar kan 'kirjin sa batare da ya furta komai ba idanun sa a lumshe, sosai yake danasanin wancan scene 'din, shi kansa bai san me kaishi har yayi haukan 'kiran Husnah gidan ba bayan ya tabbatar ba shi ka'dai ke rayuwa cikin gidan ba. Ada kam yayi hul'da da Husnah sunyivrayuwa mafi muni kuma yasan duk laifin sa ne shi ka'dai amma yanzu bazai raba 'daya 'dayan biyu ba cewa ko da ya kuma neman wata to laifin har da na Noor aciki, ko neman Yusrah da yayi yasan harda nata laifin ma domin ba kullum take yadda da bu'katun sa ba. Shi kuwa har kullum al'kawarin da yayiwa Ammi akan Noor shi yake son cikawa, shiyasa tun zaman su da ita baya ta6a matsa mata akan komai, koda kuwa abin zai iya cutar da shi ne yakan mata yanda take so. Amma yana ganin wannan tafiyar tana cutar da shi ka'dan-ka'dan dole saj yayi wani yun'kuri bawai dan ya sa6a al'kawarin Ammi ba, a a sai dan kawai ya gyara rayuwar gidan sa. Ko ita kanta Noor in kamata yayi ace bai karya al'kawarin da 'daukan ma kansa na rabuwa da Kowa ba dalililn ta, alokacin da ta yi masa halacci, amma sai gashi tun ba'aje ko'ina ba ya rusa komai, yayi 'ko'karin koyar da ita zama da shi yavwatsar da komai da na rayuwar sa na baya musamman da yake yanzu yana da iyali ba kamar da ba,  amma sai yaaka rashin sa'a domin da kansa ya fahimci itan she is not ready at all hakan yasa ya 'kyale ta kawai. Hudah yarinyace mai ha'kuri, kawaici da kuma sanyin hali, amma a 6oye taurin kai ne da ita matsananci, ga kuma nuna halin ko in kula akan komai, sau da dama yana gudun tunkaran ta ma da wasu bu'katun nasa saboda sanin halin ta da yayi yanzu sai ta nuna bata so kuma shi bazai iya tilastata ba musamman ma saboda kashedin da Ammi tayi masa akan 6ata mata rai da suka yi babu wanda ya sani daga shi sai ita Ammin. Hakan yasa ko cikin gidan sa ba sosai yake sakin jikin sa ba saboda ance yawan zama shike yawan kawo sa6ani har ya kai ga 6acin rai, Ammi kuwa cewa tayi matu'kar hawaye ya sau'ko a idanun Noor sanadin.6acin rai wallahi bata yafe masa ba, shiyasa yake binta da duk yanda yaga take ra'ayi a kullum 'ko'karin sa bai wuce yaga ya faranta mata ba ko da ka'dan ne duk da itan bata bayyana jin da'din ta afili. A mafi yawancin lokuta idan yayi mata abu godiya ka'dai ke raba su bata ta6a nuna jin da'din ta har shima ya fahimci irin abinda yafi zama mata arai, wannan halayya ta Noor yasan ba kowa ya sanshi ba, sai ma yake ganin kamar shi ka'dai take yiwa hakan cuz da ba haka take ba, yasan ko da ya fa'dawa Ammi ba yadda zatayi da shi ba dalilin kenan da ya sanya shima ya fita harkar ta, duk yadda take ha'da masa zafi amma baya damuwa da duk wani abinda zatayi masa kuma baya ta6a nuna mata cewa abin na damin sa. Shiyasa ma ko lokacin da yaga Yusrah batare da 6ata lokaci ba ta shiga ransa har ya nemi ha'da ala'ka da ita, da kansa yasan da wuya ne ya iya daina kula wasu matan matu'kar zaman nasu ya mi'ke a haka da ita...... Bai ce da ni 'kala ba nima ban damu ba dayake dama a haka ya saba lallashi na lokuta da dama idan ina kuka. Ko yanzun ma da na gaji da kuka na da kaina nayi shiru ni dai abu 'daya da na sani kawai shine bani ba wancan gidan har abada al'kawarin da na 'daukar wa kaina kenan tun abaya. Tun daga ranar kuwa Yah Deen bai sake tada batun zuwa wancan gidan da ni ba har muka koma Bauchi...wanda sai bayan komawar mu ne kafin ya samu damar kasancewa dani sai da kuwa ya tabbatar min da cewa duk rigimar da na tayi masa abaya bashi na 'daukam ma kaina. Haka na cigaba da rainon ciki na har ya shiga wata tara...Yah Deen ma koka'dan bai rage 'kalilan daga cikin lokacin sa da yake bani ba, zuwa yanzun kuwa da sau'ki ba laifi dan har muna zama muyi hira da shi, wani sa'in ma har ina bacci da kaina bisa 'kafafun sa. Idan ya dawo aiki kuma da kansa yake mammatsa min 'kafafu na wani sa'in kuma mu fita zagawa batare da mota ba...wai exercise amma da nace na gaji zai ce to ya isa mu kom gida. *****       Wata tafiya ce ta taso masa zuwa aiki a wani 'kauye dake 'kar'kashin jahar Bauchi domin, bai so tafiyar ba saboda ganin na shiga watan haihuwa ta amma sai ya kasance dole sai da shi tafiyar. Ko kafin ya tafi yayi da ni akan in shirya ya kaini gidan Mummyn Safwan amma na 'ki amincewa,  duk yadda ya nuna damuwar sa 'ki nayi nace masa ai bakomai da naji wani abu zan 'kira ta. Ai kuwa tunda ya tafi hankalin sa bai kwanta ba, wani iri yake jin ransa ya kasa sakewa, a koda yaushe 'kiran sa zaki gani yana shigowa wayata" Yah Deen". Kamar yadda yake arubuce. Da yaji lafiya ta kuma shikenan, anjima ka'dan zaki sake ganin 'kiran sa, idan da wasu nake tare a gidan har haushi zasu ji a yanda yake damuwa da jin lafiya ta 'din. Bayan tafiyar sa da kwana hu'du lokacin ma waya muke yi da shi sai na fara jina cikin wani yanayi baya na na suka na, ban ma zaci wani abu  babba ba ne amma kuma sai ban 6oye masa ba kamar wasa na gaya masa. Ai kuwa take naga ya 'daga hankalin sa, ya ringa tambaya ta bayan hakan kuma me nake ji nace bakomai, duk da hakan ransa ya kasa sakewa yace bari ya 'kira Safwan gara inje asbiti aga halin da nake ciki ko kuma ya turo wata Nurse ta duba ni. Kashe wayar da muka yi abin sai ya 'karu min kamar jira yake yi dama. Nan na fara cije lips ina kwafa fuska ta, nan take kafin kice miye wallahi har na raina kaina, shi kuwa bayan 'kiran da yayi ya fa'dawa Safwan in sai ya sake 'kiran waya ta  amma ina ji na kasa 'dagawa, sai da ya sake 'kira kafin na 'daure na 'dauka wanda sai a lokacin naji ciwon ya 'dan lafa min ka'dan. Yace " Ya dai" Nace masa " Babu". Sai yace" Na 'kira baki 'daga ba.." Katse shi nayi da fa'din" Wayar ce ai ta fa'di ni kuma na kasa 'dagowa". Murmushi yayi kawai sai ya tambaye ni yace min" har yanzu kina jin ciwon ko?" Da sauri na bashi amsa da fa'din " a a ka'dan-ka'dan ne". Sai yace" 'karya..ai naji muryar ki ta canza ba kamar 'dazu ba". Shiru nayi masa hannu na 'daya kan marata ina cize la66ana, jin.nayi shirun ne ya shi fa'din" Yanzun nan Hibbah zata zo ta duba ki, kar ki yi mata rigima kinji". " Uhum". Na amsa masa 'kasan ma'koshi na. Sai yace" Yauwa Nuree na, kar fa ki 'daga hankalin ki idan kinji ciwo sosai sai kina addu'ah kinji". " Uhum". Na sake fa'di akaro na biyu. Sai yace" barin in 'kira inji ko ta taho". Ban ce komai ba yanzun kam har ya yanke 'kiran. Ba'a 'dauki wani dogon lokaci ba da yin wayar tasa kuwa sai wata Nurse Hibbah ta zo gidan ta duba ni kamar yadda ya saba yi min idan naji wani canji ajiki na. Nan tace ai wai haihuwa zanyi, ina jin haka na fara kuka ina 'kiran Ammi na. Ganin yanda na rikice 'din ne yasa ta faki idanu na ta sanya wayata a silent wai dan kar hankali na ya tafi ga wayar ko da an 'kira ni. Ina kukan 'kiran Ammi sai naji ciwo gadan-gadan ya taso min, take akalan kukan nawa ya canza na fara na gaskiya, Allah cikin ikon sa kuwa cikin 'kan 'kanin lokaci na haifo yarinya ta 'yar cukul da ita sai dai ace Masha Allah. Nurse Hibbah ita tayi min komai ta gyara babyn tsaf yarinya sam barka mai kama da Yah Deen abinta. Sai da ta kammala komai kafin ta ciro wayar ta nan taga tarin missed calls da yake natan ma silent ta saka shi, ni kam ma babu labarin tawa. Yah Deen ne yayi ta 'kiran ta da dani da yaga duk bamu 'daga ba sai ya 'kira Safwan, shima yayi ta 'kiran Hibban amma ba response hakan yasa ya fito da niyyan zuwa gidan namu da kansa  musamman jin yanda hankalin abokin sa yake a tashe. Har kuwa ya shiga mota sai yaga Hibbah ta 'kira shi yana 'dagawa kunnuwan sa suka cika  da albishir 'din haihuwa ta tana dariya. Safwan "Alhamdulillah" ya furta a fili. Suna gama wayar ya 'kira layin Yah Deen ya samba'da masa labarin shima, ai farin cikin Yah Deen kam abin ba'a cewa komai domin sam bazan iya misalta shi ba. Hibbah na shirin 'kiran sa sai taga ya 'kira ta shima,  tana 'dagawa ya hau yi mata godiya da fa'din" Nagode Hibbah...Allah ya baki abinda kike so, yaya iyalai na hope duk suna lafiya ko?" " Lafiya lau". Nurse Hibbah tace da shi. " Alhamdulillah" ya sake furtawa a fili sannan ya 'kara da fa'din wai Hibbah ta kula masa da mu kafin ya iso dan Allah. Tace" Bakomai Dr. Jiyake Tamkar yayi tsalle saboda murna, a ranar kowa da suke tare sai da suka san yana cikin farin ciki. Kafin cikar awa biyu da rabi kuwa har ya iso gida, a lokacin ma Mummyn Safwan tazo itama tun zuwanta kuwa Hibbah ta koma asbiti, inda ta taho min abinci daga gidan ta har da kunun tsamiya. Abincin kam ban iya naci ba saboda baki na babu da'di amma kunun tsamiyan na shashi ba laifi yayi min da'di ga  'kamshin kayan yaji da yaja hankali na. Tashi na daga bacci kenan ina zaune bakin gado yayin da Baby ke ri'ke a hannun Mummy tana shirin kwantar da ita gefe na....jiki na ciwo yake min ina ta 'da'ddaure fuska ta Mummy kuma na tsaye tana min sannu sai muka ji sallamar sa. Ko 'daga kaina ban yi ba ina wasa da yatsun hannu na, Mummy ce ta amsa sallamar tasa gami da yi masa barka da isowa, gaida ta yayi idanun sa na kaina, Mummy na amsa gaisuwar tasa take mi'ka masa Babyn, suna gama gaisuwar kuwa ta fita can palour ta zauna abinta. Yah Deen kam a hankali ya 'karasa bakin bed 'din, gefe na ya zauna tare da mi'ka min hannun sa 'daya, hannun dama na na 'daga na sanya cikin nashi, sai yayi sama da  hannun zuwa bakin sa ya sumbaci hannu na sannan yace" Thank u so much Nuree Ubangiji Allah yayi miki albarka". Daga yanayin muryar sa zaka fahimci tsananin farin cikin da yake 'dauke da shi. Ni kam bance da shi komai ba, a hankali ya kwantar da kansa saman kafa'da ta, ya lumshe idanu sannan yace" Kin gama min komai Nuree, yau kin bani farin ciki, kin sada ni da sanyin idaniya ta..ubangiji Allah ya bamu ikon tarbiyantar da ita cikin muslunci bisa sunnar ma'aiki (S A W).." Da" Ameeen" na amsa 'kasan ma'koshi na dan ni ka'dai nasan abinda nake ji a lokacin. 'Daga kansa yayi daga jikina sai yasa hannun sa 'daya ya bu'de fuskan babyn" Masha Allah"! Ya furta a fili. Sannan ya sake fa'din " Allah nagode maka, yau gani ga jini na.." 'Dagowa yayi ya kalle ni yace" Kinsan sunan ta?" Girgiza kaina nayi ina kallon sa, sai yace min" Sunan ta Aishatul Amin, my Jasmine.." Murmushi nayi masa cikin jin da'di nace" Allah ya raya ta". Raina fari 'kal dan nasan sunan Ammi na yake son sanyawa Babyn. Motsi tayi tana 'dan mimmi'kewa cikin kayan ta Pink da aka sanya mata, Yah Deen yatsan sa yayi saurin sanyawa cikin hannun ta ai kuwa take ta ri'ke gagam kamar an ce mata ta aiakata hakan ne. Comment Vote Share *Salmerhn ku ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _This page is specially dedicated to my luvly sis...Zainab Kabir Ingawa_ 😍 _Godiya nake 'kwarai da gaske._ _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *71* A fili ya bayyana murmshin sa cike da jin da'di ya 'dagota ya sumbaci goshin ta" I luv u ". Ya furta a hankali. Wayar sa ya ciro ya 'dauke ta pics kala-kala sannan ya maida wayar cikin aljihun sa, ni kam kallon sa kawai nake yi, da gama 'daukan pics 'din sai ya kwantar da ita a hankali kamar 'kwai ya sake lullu6e ta. Gareni ya dawo ya sumbaci goshi na..fuskar sa daf da tawa ya tsaya kallon cikin idanu na. Yi nayi kamar zanyi kuka sai yayi saurin tambaya ta" Me kike so?" " Ni bakomai". Na bashi cike da shagwa6a in kwa6a fuska ta. Girgiza min kai yayi yace"  Ban yadda ba". Shiru nayi ni kam nayi 'kasa da idanu na zuwa kan hannu na. Shima nan ya maida idanun nasa, batare da 6ata lokaci ba ya kai hannun sa kan nawa. Yatsu na ya sanya cikin nashi ya sarke su, a hankali ta yadda ni ka'dai zan jishi yace" Ji nake kamar dukkanin farin cikin rayuwa ta yana tare da ke ne Nuree please tell me what u want". Ban bashi amsa ba sai na girgiza mai kaina. Hannun nawa ya sake ya dube ni da kyau sannan yace" To bazaki kwanta ki huta ba zaman yafi miki?" Da yake dama na gaji da zaman, da jin abinda ya fa'di sai na sake mi'ka masa hannu na 'daya, shine ya gyara min kwanciya ta yanda zan dinga hango babyn, kusa da kaina ta yadda ni.ka'dai yanzun ma ya kawo kansa a hankali ya furta" Nuree bacci ki huta kinji?" Da kai na amsa shi. Sai ya sake fa'din" Zan fita amma bazan da'de ba...Mummy ma na nan in kina bu'katan wani abu ki gaya mata kinji?". " To" nace da shi murya ta 'kasa-'kasa. Sai da ya shafi fuska ta sannan daga haka ya fice daga 'dakin. Anty Zainab, Ishaq, Saif da kuma Zaidu su yayiwa  forwarding photon Babyn kowa 'da'd'daya...yana gama turawa kuwa ya danna flight mode a wayar sa. Saif na kan WhatsApp a lokacin so shi a take ya ga sa'ko daga Yah Deen, ko da ya bu'de kuwa photon Baby ya gani 'kasan an rubuta _My Diamond_ ai da sauri ya mi'ke ya nufi 'dakin 'dan uwan sa, Zaid na baccin sa kawai yaji an 'daka masa duka gami da fa'din" Zaid tashi kaga ikon Allah....". Saif ya fa'di cike da 'kaguwa. Tsaki Zaidu yaja ya juya 'daya 6angaren yana 'kun'kunin Saif zai dame shi da wannan lokacin. Ganin hakan yasa Saif bar masa 'dakin ya ja 'kofan, direct wurin Ammi ya tafi, yana isa wajen ta kawai ya mi'ka mata wayar sa yana murmushi yace" Ammi guess what?" Kallan wayar tayi tace" Me ya faru? Kamar Baby nake gani ko?" Tayi maganar tana mai kar6ana wayar daga hannun sa. Hannu Saif ya 'daga yana murmushi yace" Ammi Yaya ne ya tura min yanzun nan, ina jin mun samu little pumpkin ne a gidan nan". Ya 'karashe maganar da tsananin farin ciki kan fuskar sa. Ammi da mamaki ta kalle shi sannan tace" Kar dai 'yata ce har ta haihu? shine Mu'een ko.sanar da ni bazai yi ba? me ta haifa kuma ikon Allah" Saif cewa yayi" Nima ban sani ba Ammi kawai 'kira mana Yayan muji daga bakin sa". Mi'ka min wayata a can ta fa'di tana me 'kara kallon wayar Saif 'din tana murmushin jin da'di. Cikin rashin sa'a kuma ko da ta 'kira sai wayar tasa bata shiga ba, duk layukan sa ma a rufe suke abin sai ya 'daure mata kai gaba 'daya. Tama cikin Jimantawa sai ga 'kiran Anty Zee ya shigo wayar ta wanda itama complain 'din ta kenan cewa taga pic 'din Baby but bata samun sa a waya kuma. Ammi baki ta kama tace" Ikon Allah! Wallahi Mu'een Ja'iri ne, wannan wani irin abu ne haka? Muma nan kinga abinda muke kai kenan duk layukan sa basa tafiya..." " Allah dai yasa lafiya". Cewar Anty Zainab, yayin da Ammi ta 'kara da fa'din" Ni lafiyan yarinya ta ma nake son ji duk hankali na ya kasa kwanciya..." Tana cikin fa'din hakan sai ga Zaidu ya shigo cikin 'daurewar fuska, gefen Ammi ya isa ya zauna yana fa'din" Me ke faruwa ne wai yau a gidan..? ina bacci na fa Saif yaje ya tada ni har da buga min mari a hannu na... sai kace nace ya dame ni...mtheew". Ya 'karashe da jan tsaki. Ammi ce ta bashi amsa da fa'din" Photon Baby yayan ku ya turo shine muke zaton ko matar sa ce ta haihu". Duk mugun halin Zaidu a lokacin washe baki yayi shima take ya nemi ba'kin cikin sa ya rasa. Da fara'ar sa yace" Haba dai Ammi dagaske?" " Gashi muma haka muka gani, kuma kowa na ta 'kiran sa baya tafiya, yanzu ma muka gama waya da Antyn ku". Kar6an wayar yayi yana dubawa hadda zooming pic 'din yana murmushi yace" Ammi wannan kam da gani jinin gidan mu ne, baki ga kamar da suke yi da Yaya ba?" Ammi sai tace" Ni ina zan gane wani kama anan abu cikin waya". Zaidu kam ko 'dagowa bai yi ba still yana kallon Babyn yace" Kai Masha Allah...wannan Allah yasa tayi kyan Yayah wallahi....". Saif ne yayi saurin taran sa da fa'din" Ka jishi kamar ance da shi macece har yana wani lissafi". Ya 'karashe yana 'dan hararan sa. Zaid kuwa cewa yayi" Sai kayi ai 'dan 'kauye kai baka ganin yanayin dressing 'din ne, the Baby with pink mostly are baby girl while blue kuma for boys, mutane 'kalilan ke caku'da colours 'din" Saif saurin kar6a yayi yana sake dubawa yake fa'din" Haba dai ai ni ban ma sani ba". Ammi kam da idanu kawai take bin su tana murmushi da shirmen nasu...cikin ranta tace" Zaid sarkin tsari". Zaidu ne ya tashi shima yaje ya 'dauko wayar sa, ai kuwa yana dubawa yaga an tura masa shima. Nan take ya danna pic 'din a status da kalamai masu da'di a 'kasan na nuna tsananin 'kauna farin ciki....Ni kaina sai da Zaidu ya bani mamaki. Wayar Yah Deen bata tashi shiga ba har sai kusan la'asar, Kafin lokacin kuwa Ammi tuni ta fara shirin ta na tafiya duk dama bata ji daga bakin sa ba har a lokacin bata tabbatar ba amma dai hakan bai sa ta fasa shirin tafiyar ba. Haka ta yini neman layin sa amma baya tafiya, da la'asar bayan ya fito daga Sallah sannan ya bu'de wayar sa yana murmushin mugunta dan yasan duk ya 'daga musu hankali zuwa lokacin. Ishaq ne mutun na farko da 'kiran sa ya fara shigowa da yake shima akai-akai yake fama gwada layin nasa. Ai kuwa sai da yayi masa masifan kashe wayar kafin nan yayi masa sam barka da samun 'karuwar da yayi, yana cikin magana da Ishaq 'kiran Ammi ya shigo ganin hakan yasa ya sanar da Ishaq sannan ya 'kira Ammin bayan sun yi sallama da shi. Ammi na 'dagawa ta 'kundumawa Uban sa zagi da yaren su, sannan ta 'kara da fa'din" Ina wasa da kai ko Mu'een?" Dariya yayi mata yace" Sorry Ammi kaina 'kasa...". Tace " Where is my daughter?" Yace" Ammi yarinyar ki ta haihu lafiya ta sami Baby girl". Ammi sai tace" Shine kuma ka kasa sanar dani ko Mu'een, 'karshe ma kashe wayar ka kayi...ai kasan dole hankali na zai tashi..kuma hadda na ta duk baya tafiya". Cikin ladabi yace " Afuwan Ammi wallahi abubuwa ne suka yi min yawa shiyasa na kashe wayar saboda in samu natsuwa". Ammi bata bi ta kan maganar tasa sai tace" Bani ita to inji ya jikin nata?" " Ammi ai bana gida yanzu amma idan na koma zan 'kira ki". Sai tace " Ita da waye ka barta?..ka san fa..." Tun ma kafin ta kai aya yayi saurin taranta da fa'din" Karki damu Ammi, Mummyn Safwan na tare da su". Hankalin Ammi kwantawa yayi take ta 'dan ji sanyi cikin ranta, " Ok shikenan idan ka koma karka manta ka 'kira ni". Abinda kawai tace da shi kenan kuma shine 'karshen maganar su, daga haka suka yanke 'kiran yana mai bata tabbacin cewa da ya isa gida zai ha'da su. Ammi bata ajiye wayar ba sai da ta 'kira Anty Zainab ta gaya mata cewar sunyi waya da shi yanzu tace Baby girl ta samu...kuma duk suna lafiya. Murnar Anty Zee ninkuwa yayi akan na baya saboda yanzu ne ta tabbatar Babyn ko na waye, Mu'een 'din ta ne yau yake matsayin uba, Allah sarki rayuwa.. ubangiji Allah ya raya mana Baby. Ammi har Umman mu ta 'kira ta fa'dawa, shirin tafiyar ta kuwa sai ya tashi gadan-gadan, Alhaji Baba tun kafin ya shigo gida 'yan biyun Ammi suka yi masa albishir bayan sun fito daga masallaci. Ai kuwa shima Alhajin koka'dan be 6oye farin cikin sa ba, a fili ya ringa godiya wa Allah. Koda Ammi tace da shi ita har ta kammala shirin ta ma Allah ya kaimu goben yace da ita yana yi mata dariyar zumu'din da take. Sai bayan sallar Isha'i sannan Anty Zainab ta samu daman 'kiran sa, yana zaune gefen mu gama waya ta da Ammi kenan sai gashi itama ta 'kira. Mi'ka masa wayar nayi ganin an 'kira sa, sai ya 'dauka tare da yin sallama. Fuskar sa cike da annuri ya gaishe ta. Tace" Alhaji Mu'een kenan manya Baban Baby, kawai sai na samu labarin wai 6eran Ammi ta haihu". Dariya ne sosai ya kama shi wanda ya jima be yi irin ta ba dan yasan me Anty ke nufi da fa'din hakan yana dariyar yace" Ni dai kawai asamin albarka Anty...ai komai ya wuce". Tace" Silly u, kamar ba kai ba Mu'een duk murnar new Babyn ne yau 'din haka?...to Allah raya mana ita da Albarka". " Ameen Ameen". Ya amsa ta yana murmushi sai tace" Bani 6eran Ammin to mu gaisa". 'Yar dariya yayi yace" Kai Anty". " To ba abakin ka naji sunan ba?" " Ta girma ai yanzu wancan tsohon suna ne". Ya fa'di hakan yana mi'ka min wayar...gaisawa muka yi da ita, ta ringa yi min sannu tana min fatan Alkhairi sannan muka yi sallama. Wallahi Yah Deen sosai yake bani mamaki yanda farat 'daya ya canza, tunda nake da shi ban ta6a ganin fara'ar sa kamar wannan lokacin ba. Daren ranar kuwa Babyn ta ringa kuka, Yah Deen ne yayi ta 'dawainiya da ita har tausayi ya a daren, dan be wani yi baccin kirki ba, gashi ni ban san me zan mata ba kuma daga ni sai shine cikin gidan Mummyn Safwan bayan maghrib ta koma gida. Da kansa yayi ta rainon abin sa har kusan asubah sannan suka yi bacci ya kwantar da ita kan cikin sa hatta sallah sai da ya makara ranar be yi kan lokaci ba. Washe gari kuwa sassafe driver ya sau'ke Mummy kafin 8 na safiya ta kammala yi mana duk abinda ya dace. Ni dai raina tas dan Ammi na tace dani yau zata iso insha Allahu, koba komai zan ga wani daga gida cuz ba 'karamin kewar su nayi ba, balle ma Ammi na da nake da tabbacin tana matu'kar 'kauna ta. Yah Deen kuwa har mamaki yake bani irin kashe ku'di da yake yi, duk fitan sa in zai dawo gida sai ya dawo da kaya ni'ki-ni'ki koda ba'a ce da shi ana bu'kata ba, hakan ma fa kusan duk siyayyan ya kammala shi tun kafin ranar haihuwan amma duk da hakan be fasa ba kamar akan sa aka fara haihuwa. Matar Safwan sunzo da Mimah suma muka kusan yini tare da su dan sai da suka yi sallan la'asar kafin suka koma gida suka barmu da Mummy. Da tafiyar su basu da'de ba sai ga Ammi ta iso,  take naji farin ciki ya lullu6e ni marar misali, har hawaye nayi dana ganta saboda farin ciki, domin tunda na haihu banga kowa daga 6angare na ba bayaga shi. Ammi ce ta cigaba da kulawa da mu shima tun zuwan ta ya huta da rainon dare Ammi ta fanshe shi. *****      Ranar suna yarinya taci suna Aishatu, sosai Ammi tayi farin ciki jin cewa sunan ta aka sanyawa Babyn, da kanta ta yiwa Alhaji Baba albishir 'din sunan ta da aka sanya shima yayi san barka. Saif ne ya 'kira ni Video call wai yana son ganin Little mummyn sa, na nuna masa ita tana jujjuya hannuwa, yayi ta yabawa da sa mata albarka, shine yace min wai Zaidu Jasmine yake 'kiran ta da shi, 'yar dariya nayi nace masa ai shima Yayan naji haka ya 'kira ta dashi tun ranar da aka haife ta. Murmushi Saif yayi yace Allah ya raya mana ita, nace Ameen thumma Ameen. Ranar sunan da rana Anty ta 'kira Yah Deen  suka gaisa, sai yace mata ?" Sunan Babyn Aishatu.." Tace da shi Ammi ta gaya min tun safe, ubangiji Allah ya sa mata albarka, tunda yanzu kai ka guje ni zaka bani ita ai ko?" Da sauri yace" Anty wannan in? Gaskiya ki bari sai an samu wani". Dariya tayi tace" wasa nake maka ma Mu'een ai yanda naji kake wannan fara'ar da ji nasan akwai 'kauna tsakanin ku". Yace" Wallahi kuwa kamar kinsani Anty, ji nake tamkar in dinga yawo da ita...". Dariya sosai ya bawa Anty kafin suka yi sallama. Da Yah Deen cewa yayi wai sai dai mu cigaba da zama da Ammi a Bauchin Ammi kuwa ta'ki Amincewa, duk yanda yaso ya nuna mata baya so muyi nisa da shi Ammi 'kin yarda tayi da batun sa. Da yaga ta dage kuma sai ya 6ullo da batun wai taya za'a yi tafiya mai 'dan nisa da Baby kwana biyu bayan suna ai wahala za'a bawa babyn. Ammi tace" Idan zamu tafi sai ka hana kaji tunda ka isa". Daga lokacin tafara yi mana shirin tafiya Shuwarin dolen sa kuwa ya kaimu da kansa har gida. A gidan Ammi muka sau'ka ni dai ban damu ba dan ni ko ina ma gida ne a wuri na. 'Yan biyu kam kasa ganewa nayi shin cikin su waye yafi son Baby, dan kowa be 6oye soyayyar da yake yi mata, da an mata wanka zaki ga kowa na rubibin 'daukan ta photo. Duk iskanci da girman kan Zaidu kawar da shi yayi ya daina yi min, sai dai inga yana yiwa wasu musamman da ya kasance yanzu ana 'dan zuwa gaida mu jin mun dawo, har masifa ranar yayi wa Saif wai yana kashe mata idanu da flash light 'din wayar sa me yasa ba zai 'dauke hasken ba idan zai mata oic 'din, su Zaidu manya  dan wai yaga idan wayar tayi haske sai tayi saurin lumshe idanu shine yake masifar. Dole yayi kane-kane ya hana Saif yin yanda yake so akan 'daukan Baby photo. Ammi tayi ta musu dariya tana fa'din ni dai kar a takurawa takwara ta. Akwai lokacin da har hana Baby yake yi idan anzo ganin ta in ya kasance tana wurin sa akaje kar6o ta sai yace bacci take yi, musamman idan yaji ance ba'ki ne suka zo dan shi asalin sa ya tsani yaga ana shige da fice a gidan su. Ko ranar da su Ummah ta suka zo ma haka yayi musu, da yake bai san su bane suka zo a lokacin, sai da Ammi ta tashi da kanta taje ta anso Babyn tana masifar" Ka bari idan ka haifi naka sai ka yiwa mutane abinda ranka ke so amma yanzu bazaka ringa yiwa mutane iya shege akanta ba, ai ko wacce ta haife ta ma tana cikin hankalin ta balle kai". Sai yace" Allah damunta ake yi, bakya ganin da dare bata fiya bacci bane kuma duk saboda jagwalgwalatan da ake yawan yi ne". Tsaki Ammi tayi ta taho da Babyn. Da ta dawo ne take basu labarin irin bakin halin da Zaidu yake nunawa akan Babyn tace ko mahaifin ta iyaka abinda zai yi kenan. Abin sosai ya bawa su  Ummah ta dariya. Addah Maryam ma musamman tazo daga Darazau suka zo da matan Yaya Usman, matar Baban mu ma ta zo har gidan Ammi ta kawo mana Turmin zani da riga wa Baby, da yake ta dawo gida da jimawa har tana shirin yin wani auren ma yanzu. Satin mu uku a gida sannan Anty Zee ta iso, a lokacin ma Baby harta fara wayo, _Jasmine_ mafi yawan mutane ke 'kiran ta da shi, amma 'yan biyu kan 'kira ta da Baby Jas, little Mummy, Angel, ko kuma Daddy's girl, ko wani suna suka ga dama 'kiran ta suke yi da shi...Alhaji Baba ka'dai ne kan 'kira ta da _amarya ta_ . 'Bangaren Yah Deen ma kusan duk weekend a Shuwarin yake yin ta, ko gajiya da tafiyar baya yi sa6anin da da yake 'daukan tsawon watanni bai zo ba. Kowa yanzu ya saki ransa da shi, ana ganin kamar halayyar sa ta canza ne, yayin da mahaifan sa suka fi kowa farin ciki gami da 'kara gode wa Mahallici,  dan aganin su yanzu Mu'een ya nutsu ba kamar baya ba, ni kam bana cewa komai koda kuwa hirar ta ha'da dani,  domin a gani na babu amfanin fa'din wani abu bayan wanda su suke gani a zahiri, ko ada ma dan ban san menene so ba ban iya tona asirin sa ba balle yanzu da na san ina matu'kar son miji na ne zan fa'di aibun sa?hakan yasa sai in bisu ayanda suka 'dauki maganar har ta wuce gaba 'daya...addu'ar ce dai nima insha Allahu bazan daina ba. Wani zuwa da Yah Deen yayi ne su Ishaq ma suka zo dole kuwa sai da aka gyara musu gidan mu dake bayan makaranta  aka yi musu masau'ki acan. Washegarin zuwan su Ishaq sai ga Anas ma yazo shi da wani abokin sa, amma su basu kwana ba suka koma aranar,  duk yanzu sun zama manyan mutane kowa ya kama aikin sa aure ka'dai ne ya rage musu...Imran kam.ma already an sanya rana lokaci kawai ake jira yayin da Ishaq ke shirin sanya manya cikin tasa maganar auren, Anas ne dai yace shi ba yanzu ba tukunna. Ku'dade kowa ya bayar wai asiyawa Baby riga abin ba'a cewa komai..suma da Babyn suka fita harabar gida duk suka yi photuna cikin nuna farin cikin su. Ishaq ne yake zolayan Yah Deen wai gaskiya za'kewar tasa tayi yawa kan Babyn, ganin cewa  duk sati sai yazo Shuwarin. Yah Deen yana dariya ya bashi amsa da fa'din" Iyalai wasa ne angaya maka? yaro bazaka san dad'in su ba sai ka ajiye naka sannan..wallahi ganin su ka'dai yana sani natsuwa inji kaina nima wani ne a rayuwa, shiyasa kaga bana iya 'daukan lokqci banzo gare su ba". Dukkan su dariya suka sanya cike da jin da'din yanda abokin su ya fara canzawa har ana jin abinda ke cikin ransa game da wani. Kafin tafiyar su kuwa Ishaq kamar da wasa yake yiwa Yah Deen maganar" Wai tunda yanzu an girma kamata yayi arage wasu abubuwan ko dan saboda 'yan baya ma". Ko be tambaya shi da kansa ya fahimci me Ishaq ke nufi da fa'din hakan, kuma shi da kansa ma dama burin sa kenan, dan haka sai ya bawa Ishaq tabbaci da fa'din" Insha Allah komai ya wuce aboki na". Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *72* Watan mu uku a gida kafin muka koma Bauchi, nan Yah Deen ya 'dora daga inda ya tsaya, soyayyar sa ga 'yar sa sai abinda yayi gaba, lokuta da dama ni sai dai in zame musu 'yar kallo dan matu'kar yana gida to kuwa Jasmine bata zama da ni har sai dai in shayar da ita zanyi. Sha'kuwar sa da ita sosai ya ninka nawa, yarinya ce 'karama amma har zakiyi mamakin irin wayon da take da shi, ba 'karamin farin sani ta yiwa mahaifin ta ba, tun kafin ta cika shekara guda ya fara fita da ita unguwa da yake ma tayi tafiya tun tana 9months ne. In kinga shirgin kayan wasan da ya tarawa Baby abin har zai baki dariya m, dan kuwa wasun sam bata da wayon da zata gane amfanin su a lokacin sai daia kawai ta lalata su, shi kam duk ya ha'da ya tara mata. Ni dai bazan iya ce ga takamammen matsayi na a wurin sa ba cuz tunda ya samu Jasmine shikenan na kasa gane masa kuma, hankalin sa da tunanin sa gami da kulawar sa duk gareta ya mayar. Akan Jamsine har masifa yake yi min wani lokacin, wanda da kansa kuma daga baya zaki ga ya dawo ya ban ha'kuri da yake yasan be kyauta ba, sai yace dani kawai ransa ne ya 6aci a lokacin shiyasa har yamin masifan amma nima indai na yawan saka ta kuka.        Domin yakan yawaita yi min fa'dan ne musamman idan ya ji tana kuka. Ni kam bana ta6a tanka shi kan hakan saboda ban ma san me zance da shi ba kwata-kwata da zai iya yadda dani indai akan Jasmine, domin yarinyar akwai shegen son kuka, ko abu be kai na kuka bane ita kam sai tayi, shi kuma kar yaji hakan take zaki ga ya 'dorawa mutun laifi, kuma fa da kansa ma yasan halin kayan sa amma baya ta6a ganin laifin ta ko me kuwa zata aikata. Yah Deen sam baya 'kaunar yaji muryar 'yar sa da sunan kuka, ko wanka zan mata idan bana so tayi kuka sai dai muyi ta wasa a haka har wankan ya kammala kuma zaki ga sai mun 6ata lokaci sosai, randa kuma naga bani da wannan lokacin to wankan kawai nake yi mata ranar kuwa kuka zata tayi kamar wacce aka doka. Idan yaji hakan sai kiga ya fara yi min masifa wai bana binta a hankali ne shiyasa har take kuka, take zaki ga ya kar6i abinsa ya shirya ta sai dai inji muryar su suna dariya. Sallah ce ka'dai yake 'daga min 'kafa idan ya tarar ina yi while Baby na kuka, baya ga haka kam ko ni kaina bazan iya gaya miki so nawa nasha masifa akan 'yar da na haifa da ciki na ba. A kullum kuma sai dai bata ga na sa hijab ina sallah ba kuka zakiga tana yi tana jan hijabin nawa har na idar ko kuma kiga ta shige gaba na ta rungumo 'kafafu na ita adole sai dai in 'daga ta, da 'kyar da dabara nake samu in idar da sallar tawa, tana idar kuma sai in 'dauke ta in rungumi ajiki na wani sa'in rikita ni ma take yi in kasa yin azkar 'di na, idan ta ban haushi kuwa share ta nake yi dan ban laifi Baby akwai rigima gaskiya sau da dama ma.zaki ga ko na idar da sallan na 'dauke ta bata daina kukan, gata bata jin lallami sai dai in Yah Deen na kusa, idan ta ban haushi sai in share ta in cigba da yin abinda ke gaba na. Shikuwa kar yaga hakan ttake zakiga ya nuna miki 6acin ransa a fili. Abin sosai ya ke min suya a zuci amma bani da yadda zanyi tunda ni na haifi kaya na. Sau da dama wankan ma idan ta fitine ni 'kyale ta nake yi da ruwan tayi ta wasan ta domin ita Allah ya zuba mata masifan son wasan ruwa kamar kifi, tafi so idan na sata a ruwa kar a cire ta kuma kar ace za'a goga mata abu ajiki nan ne bazaku shirya ba...idan na 'kyale tan baya damuwa sai kiga ya zo ya 'karasa yi mata wankan yana jan ta da wasa har ya shirya ta...wani lokaci har ficewa suke yi daga gidan ma ni ban sani ba. Gashi dama ba wani damuwa tayi da shan mama ba sai su yini a waje bata damu ba. Abu 'daya da har yau bai canza min ba shine suna" _Nuree_ " da yake 'kira na da shi ko da wasa bai ta6a canzawa ba. Yah Deen da ya zauna da ni a gida yayi hira ya 'kwammaci ya 'dauki 'yar sa su fita harabar gida ko kuma su wuce yawon su cikin gari. Babban amfani na yana zuwa masa ne idan bu'katar sa ta taso, wannan kam baya min iyayi akai zaki ga ya kwantar da kansa domin cimma burin sa. Ni kuwa duk ranar da ya 6atan rai 'kin amince masa nake yi dan a gani na wannan ne ka'dai hanyar da zanbi in rama abinda yake yi min. Sosai kuwa ransa ke 6aci amma baya takura ni kamar yadda baya sake kula ni kan maganar balle ya ro'ke ni sai dai kawai kiga ya juya min baya yayi baccin sa. Irin hakan ya sha faruwa tsakani na da shi dan bazan iya lissafa adadin ranakun ba.         Ban ta6a yin tunanin  ko wannan dalilin ne ya sanya baya shayin yi min masifa a duk lokacin da ya ga dama ba musamman ma idan abin ya ha'da da 'yar sa, dan da ba haka yake min ba. Tun a lokacin na so fara karatu, a lokacin Watannin Baby Goma Sha biyar amma ya hana ni wai sai ta 'kara girma...idan na fara fita yanzu wa ye zai dinga kula masa da Baby, dole na na ha'kura na cigaba da zama a gida badan raina ya so ba. Bazan manta ba akwai watarana lokacin kaina ciwo sosai yake min da 'kyar nake iya 'daga kaina, mura ce ke damuna kuma abin kamar na neman baki kan nawa bai fara ciwon ba sai da ya fita, ni kuma ban 'kira na gaya masa ba saboda a gani na da nasha paracetamol shikenan, ko da na sha 'din ma kuwa sai bai daina ba, ko idanu na bana iya bu'dewa da kyau saboda tsananin ciwon kan, a hakan Baby tazo tana ta yimin rigima wai sai na goya ta. Janyo ta nayi jiki na na rungume ta ina llalshi amma a banza na bata mama ta'ki ansa sai kuka, bakin ta har ja ya yi saboda yanda da dami kanta da kuka, dole na daure na bu'di baki na nace" Ki bari idan Daddy ya dawo ya goya ki ko Mama na?" Take ta 'daga kafa'da ita wai a a ta cigaba da kukan ta. Allah ya sani ni abinda zan iya yi mata kenan a lokacin amma duk ta 'ki...duk nima sai ta 'kara hautsina min hankali na, na ratsa me ma ya kamata inyi. Hawaye kawai naji yana gangaro min saman kunci na, duk yadda nayi da Baby 'kin amincewa tayi ta cigaba da rigimar ta, sau'ke ta nayi daga jiki na ina sake share hawayen da ya gangaro min. Kinsan rigimar yara yanda take da cin rai sosai. Jamsine kuwa sai ta sake dawowa jiki na tana 'kara sakin wani kukan, kaina naji tamkar zai rabe gida biyu bansan lokacin da na matsar da ita ba azuciye ina fa'din" wallahi mari zan miki idan kika 'kara damuna..." ban.kai ga rufe baki ba sai na hango shi kamar an daga sama ya shigo...wallahi sai da zuciya ta ta tsinke take ciwon kan nawa ya 'karu...saboda sanin hali, ga shi da turewan da na mata da tsawan duk akan idanun sa suka faru. Take nayi 'kasa da idanu na ina goge hawayen fuska ta. 'Bangaren Yah Deen kuwa sosai 6acin rai ya bayyana kan fuskar sa, a hankali ya 'karaso kusa da ita ya rungume abin sa batare da ya furta komai agare ni ba. Sai da ya tabbatar ta yi shiru tana sau'ke ajiyan zuciya sannan ya 'dago jajayen idanun sa ya dube ni, koka'dan ba bu ko alamun fara'a tattare da fuskar sa...ban damu ba cuz dama nasan yau kam dole sai yamin masifa. Bai yi min magana ba sai ya kai hannu bayan rigar Baby yana bu'de zip 'din bayan rigar ta ta yace" Har abada Nuree bazaki canza ba, wallahi da ace ba ke kika haifi yarinyar nan da ban san kuma me ze faru bayan wanda na sani ba...amma ki sani ko da wasa bazan lamunci irin hakan ba". Da muryar kuka nace da shi" Damuna fa tayi da kuka kuma ni kaina ciwo yake yi sosai". A fusace yace " Shine dan baki da tunani zaki doke ta? Yarinyar nan fisabilillahi me ta sani da har zaki yi mata irin wannan hukuncin? Kuma ma lokacin da zan fita kin sanar da ni cewa baki jin dad'i ne da har zaki zo kina dukan min yarinya akai, ke kullum baki iya kiyi abu irin na masu tunani ba sai yaushe zaki girma to?" Kuka na na cigaba da yi har ya 'kara shi masifar sa yayi shiru 'karshe 'daukan abinsa yayi suka yi ciki. Wanka yayi mata yana yi kuma yana yi mata fa'dan" Baby na Mummyn ki bata jin da'di kuma kina da mun ta da rigima ko? Baki ga har kuka take yi ba ne?..ko so kike Daddy yayi miki bulala?" Da sauri ta girgiza kanta alamar" a a". Sai yace" To kar ki sake kinji Mama na, ki daina yiwa Mummy rigima in ba haka ba zan zane ki kuma mummy ma zata daina goya ki kinji?". Da sauri ta sake 'dage kanta sama jin zancen bulala, babu wanda ya ta6a zane ta amma tsoro gare ta sosai. Sai gani nayi sun sake fitowa, abinki da uwa da gudu kuma ta iso gaba na tana dariya take gaya min da gwarancin maganar ta wai Daddy yayi mata wanka. Dole na nayi murmushi ina shafa kanta...har cikin jini na nake jin 'ya ta. Zama yayi kan kujera mai  facing da mu yana kallon mu...kamar ba ya so kuma yace" Me ke damun ki?" Sai nace masa" Headache". A ta'kaice dan masifar da yamin yasa ni jin haushin sa. Kamar yasan me ke cikin raina sai be ko sake tanka ni ba kawai yace" Baby mu tafi ko?" Da gudu ta tafi inda yake ya 'daga ta sama yana fa'din" Yauwa Mama na". Bai ko sake kallon inda nake ba yayi waje abin sa. Asbiti suka koma yaje ya kawo min magani, da yake yasan da batun muran da nake yi shiyasa bai sha wahala wajen gano abinda ya haddasa min ciwon kan ba. Ranar kam da kaina na bashi ha'kuri da dare ganin har a lokacin kama min kai yake yi..cikin natsuwa yace min" Ai ke ke tilastani yin wasu abubuwan Nuree ko da ban yi ba, please ki ringa bin Baby a hankali kinsan ita yarinya ce abinda ubanta ya jure ita bazata iya ba...wataran da kanta ma idan akace tayi irin hakan bazata yi ba so ki na ha'kuri da yarintar ta kema kinji?" Da kaina na amsa shi alamar naji. Ai kuwa ranar ya samu daman rabar jiki na cikin kwanciyar hankali da yake nasan nayi masa laifi shiyasa ban yi masa gardama ba. *****          Abu ko wani iri ne idan Baby ta nuna ra'ayin ta akai ko da kuwa iyaka abinda yake da shi kenan zaki ga ya cire ya siya mata. Ciwo idan Baby nayi to shikenan shima walwalar sa ta 'kare kenan har sai yaga ta samu lafiya, balle lokacin da ta fara zazza6in ha'kori wallahi Yah Deen hutu ya 'dauka musamman a wurin aikin sa dan ya kula da ita ban sani ba ko raina nawa kulan yayi oho masa, domin azahiri ya nuna ni 'din bazan iya kula masa da ita kamar shi ba, Yah Deen sosai yake raina 'ko'kari na akan Jasmine. Shiyasa nima yanzu na rage damun kaina, abu in dai naga ya fini za'kewa akai game da Baby to bar masa nake yi na hutawa raina. Bai kasance ma'abocin kula da lamuran yara ba amma akan Jasmine sai da ya koyi duk wani abu da ya shafi 6angaren yara.        Su Saif ma musamman suka zo shi da Zaidu wai ganin Baby Jas, suna ma fa shirye-shiryen tafiya makaranta ne amma wai su sai sun zo sun ganta kafin su tafi. Tun zuwan mu Bauchi wannan shine karo na farko da suka ziyar ce mu, wannan 'din ma nasan saboda Baby ne. In kinga kayan wasa da suka kawo mata abin ba'a cewa komai, haka ma sutura da Ammi da kanta ta sissiya mata ta bayar akawo mata ni kuma abaya ta siya min kala uku da takalmi. Ni duk sai ma rasa wani irin so suke wa yarinyar nan, dan ko Alhaji Baba ba'a bar shi abaya ba, haka yake biye shirmen ta a waya har video call suna yi da ita, sai kiga tana ta shashshafa kan watar tana dariya tana fa'din _Baba_ ....da irin maganar ta. Lokacin da ta isa yaye na yaye ta, sai ya kasance boobs 'dina na damu na sosai da zogi, har zazza6i yasa min dan nayi amfani da ha'din 'danyar shinkafan nan da ake yi. Ni da kaina nasan Yah Deen na 'ko'kari wajen 'daga min 'kafa a duk lokacin da na'ki amince masa wurin kusantata, amma a cikin kwanakin sai na rasa me ya shiga kansa da yasa ya kasa ha'kura duk da yake cewa bana jin da'di. A zahiri nasan yana matu'kar tausaya min amma da yazo min da bu'katar sa a lokacin da nake 'dan fama da zogin boobs 'din sai na'ki amincewa, nima 'din nasan ban kyauta ba saboda harga Allah a ranar bana jin zugin sosai, amma duk da haka sai na sanya masa kuka ina fa'din" sam baya tausayi na ai yana ganin halin da nake ciki amma zai 6ullo min da wani abu". Na fa'di hakan ne kawai badan komai ba sai dan bana jin zan iya da shi alokacin dan nasan halin sa ba shi da sau'ki in dai ya samu kaina ba 'karamin caku'da min boobs yake ba...da jin na fara yi masa kuwa sai ya 'kyale ni da kansa ya lalla6ani gami da ban ha'kuri har nayi bacci na a jikin sa batare da na damu da halin da yake ciki ba. Ni kaina yanzu bansan me yasa wasu lokutan nake 'kin amince masa ba, koma ba yau 'din ba lokuta da dama ma haoan nake yi masa, Yah Deen ya kasance 'daya daga cikin irin mazan nan da suka iya bi da mace wajen kwanciya ni da kaina nasani dan sosai salon sa ke tsaye min a zuci bazan yi 'karya ba, baya ga haka ma sosai nasan yanayin sa ta fannin bu'kata amma na banzatar cikin raina..a fili nake nuna bandamu da lamarin sa ba har hakan ya zauna min a zuciya. Ada nakan 'ki amince masa ne da yake akwai haushin sa araina na bibiyan mata da yake yi, amma yanzu Alhamdulillah na fara mantawa da komai, kuma ina da tabbacin baya tare da ko wace mace a yanzu, amma duk da haka sai na rasa dalilin da yasa nake gudun sa, har sai nazo kuma na fara dangana hakan da 6atan rai da yake yi akan Baby sai inga hakan matsayin hukunci musamman da nasan shike fara lalu6a ta kowani lokaci..idan ya biye ni sai muyi 2weeeks ko ma fi batare da na amince masa ba. Ban sani ba ko sabawa da nayi da 'kin amince masan ne yasa har yanzu ban daina yi masa gardamar ba. Ranar lafiya lau muka kwana bai sake kula ni ba, a lokacin kwana biyar kenan da yayen Baby dan ita kam ma ta 6angaren ta babu wata matsala, ko irin kukan yayen nan bata yi sosai ba. Washegari kawai naga ya hau shiri bai tanka ni ba har kayan Baby ya shirya da kansa batare da ya nemi taimako na ba, ina zaune parlour sai ganin sa nayi da jaka Jas kuma a hannun sa, waro idanu nayi kafin nayi magana yace min" Zamu tafi gida..Baby say Bye to ur mum". Ai kuwa ta 'dago hannu tana min bye-bye. Hanyar fita yayi yana fa'din" Ayi mana addu'ah". batare da ya min ko.kallon arzi'ki ba. Kaina sosai ya sara min, saboda tsananin tashin hankali, a fili na fahimci fushin da Yah Deen ke yi da ni, yau kam.nasan na 'kure shi, domin ada ko ba komai idan zasu tafi mukan yi sallama mai kyau har sumbata ta yana yi kafin ya wuce amma na yau 'din yasha banbam. Inaji ina gani suka yi tafiyar su ban iya na ko yi musu addau'ar da ya bu'kata ba. Da rana sai ga Hibbah tazo duba ni, wai inji shi ne ta ringa zuwa tana duba lafiya ta kafin ya dawo. ni kuwa cike da haushi nace ni lafiya ta 'kalau ba abinda ke damuna, duk yadda taso ta nuna min cewa Dr.Mu'een ne ya turo ta amma na'ki sauraran ta, haka ta tattara tarkacen ta tayi gaba. Ina jin ita ta sanar da shi cewa na'ki amincewa da yamma sai ga 'kiran sa kamar bazan 'dauka ba sai na 'dauka, take kuma sai naji kuka ya kubce min, shiru yayi yana sauraran kukan nawa daga inda yake harda lumshe idanu, yana jina har na 'dan tsagaita sannan naji muryar sa na fa'din" Jikin naki ne?" Nace" a a". " To menene kuma na kuka bayan naturo Hibbah ta duba ki kika 'ki amincewa?" Shiru nayi ban ce dashi komai ba, shine ya cigaba da fa'din" Ki daina nuna kowa cewa ke mai taurin kai ce..kinga Hibbah daban ni daban amma sai da kika sa ta gane taurin kanki". Da shagwa6a nace dashi " Ai na warke ne shiyasa". Ajiyan zuciya ya sau'ke tare da fa'din " Haka ake so ai" Sannan ya sake fa'din" mun iso lafiya su Ammi ma na gaida ki". Da jin sunan Ammi sai wani kukan ya taso min. Kashe wayar nayi na kifa kaina na cigaba da kuka na, shi kuwa 6angaren sa murmushin mugunta ya saki harda cije gefen baki. Ashe ko da suka je ma Ammi sai da tayi masa fa'dan wai me yasa bamu taho gaba 'dayan mu ba, miye amfanin tahowar su su biyu su barni acan 'din. Yah Deen ko tsoron Allah babu yace da ita wai ai nice na'ki binsu, wai banda lafiya yanzu sai dai wani lokaci, yace in ya bar Baby kuma damu na zata yi tayi shiyasa ya taho da ita" Ya fa'di hakan ne da tabbacin 'karyar sa ta shiga domin yasan ni bazan ta6a musawa ba koda Ammi ta tuhume ni akai. Wasa-wasa sai da suka shafe kwanaki takwas acan, duk zaman gidan ya ishe ni, ya kan 'kira na kullum sau uku mu gaisa yaji lafiya ta shikenan,  wani lokaci sai ya ha'da ni da Baby tayi ta min shirme. Har gajiya nake yi da nata surutun sosai nake so ya bani ishshshen lokacin sa amma sam ya 'ki kamar yasan me ke cikin raina. Ba 'karamin gajiya nayi da zama ni ka'dai a gidan ba, kewar su nake ji sosai musamman ma shi, domin yanzu na warke sumul kamar ba ni ba, da kaina kuma na zauna nayi tunanin abubuwan da nake yi masa da rashin dacewar su, ko ba komai ai yanzu ya kamata ace na girmi hakan shekaru kusan uku da auren mu. Duk fa wasu dabarun zama da miji na sansu amma ban san me yake hana ni sakin jiki da su ba, ina matu'kar 'kaunar miji na da ya kamata ace zuwa yanzu yasan hakan musamman da nake da tabbacin cewa baya tare da kowa a yanzun sai ni. Ganin kamar basu da niyyan dawowa ne ranan kwanan su na goma da ya 'kira ni da safe muka gaisa yana shirin datse 'kiran nayi saurin dakatar da shi da ambatan sunan sa. Sai yace" Ya akayi?" Marairaice murya nayi nace" Dan Allah yaya ku dawo gida i missed u all, ko tausayi na ma bakwa ji ni ka'dai ce a gidan Yayah". A dake ya bani amsa da fa'din" 'kilan bamu da tausayin ne shiyasa Nuree". " am serious Yah Deen dan Allah ku dawo haka nan, wallahi sosai nayi kewar ku, bana jin da'din zama ni ka'dai 'din nan..". Sai ce min yayi" Bamu gama hutun mu ba ai sai nan da 1 week kafin mu dawo". Yace " Yah Deen aikin ka fa?" " Wannan matsala ta ce ai ba taki ba". Sosai na lan'kwasa murya ta kalar tausayi nace " Yanzu Yah Deen ko dan ni bazaka dawo ba?" Yace " Ai baki damu da ni ba balle in dawo saboda ke, nima ki barni in huta a inda ba'a sani ba'kin ciki". " Yah Deen...". Rasa me zan sake ce da shi nayi, nan take sai hawaye ya fara tsiyayowa daga idanu na. Bansan ta ya zai fahimci halin da nake ciki ba, dagsake kenan saboda ni yayi wannan doguwar tafiyar? hankali na duk ya tashi sai nake jin tankar in bu'di idanu in ganni gaban sa, ashe haka yake ji idan nayi masa abin 6acin rai?...in kuwa hakane ya zame min dole in bashi ha'kuri, amma yanzu damuwa ta bai wuci ta yanda zan shawo kansa ya dawo Bauchi ba, ban san yadda zan yi ba sam. Bance da shi komai ba kawai na yanke 'kiran, take ya 'kira ni amma ban 'daga ba, kuka na ci son raina ranar sosai nayi nadaman halayyar da nake yi masa, domin a 'yan kwanakin wallahi da kaina nake jin kewar sa a kusa dani, kewar tarairaiyar da yake min touches 'din sa da sauran su, abinda tun zama na da shi ban ta6a ji ba kenan...yinin ranar haka wayata ta yini akashe. Ashe Yah Deen yayi ta gwadawa bai samu ba har zuwa dare, shima kuwa zuwa lokacin hankalin sa sosai ya tashi, ba nufin sa ya 6ata min ba, burin sa ya bani sarari ne tunda ya fahimci bana bu'katan su kusa da ni. Alhamdulillah domin yanzu ya fahimci hakan da yayin ya taimaka sosai tunda gashi da kaina na 'kira shi da irin kalaman da be ta6a ji daga baki na ba koda wasa...ya kuma fahimci babu 'karya a ciki direct daga zuciya ta suka fito..amma me yasa zan kashe waya ta kuma. Har megadin gidan mu ya 'kira wai yaji ko gidan lafiya me gadi yace masa lafiya 'kalau, yanzun ma ya 'dakko abincin sa. Hankalin sa sam duk da haka bai kwanta ba domin ya fahimci abin da shi nake yi, fatan sa Allah yasa Nuree da gaske take yi, Allah yasa ta gane rashin dacewar abinda take yi masa su gyara rayuwar auren su kamar kowa, yayi al'kawarin nuna min so na zahiri duk soyayya ta da yake ri'ke da ita cikin zuciyar sa sanadiyyan abubuwan da nake yi masa duk zai bayyana min matu'kar ya tabbatar da gaske nake yi nayi kewar sa. Be iya ya sake kwana acan ba domin washegari da sassafe suka kamo hanya tafiya ba ko shiri, Ammi na fa'da tayi masa har tace su bari mana ko zuwa gobe ma amma irin wannan tafiyar ai ba'a son ta, Yah Deen sai cewa yayi ai wurin aiki ne  aka neme shi. 'Bangare na ni kuwa ban sake kula wayar tawa, cikin raina na yanke shawarar bazan sake 'kiran sa haka kuma bazan kunna wayar ba balle nashi 'kiran ya samu daman shigowa in yaso idan ya gama iya hutun da zaiyi ya dawo sai in basho ha'kurin. Washegari da na rasa abin yi kawai sai na fara  aiki a gidan, tun safe ban zauna ba, na gyara ko'ina tsaf-tsaf lungu da sa'ko cikin gidan na tsaftace kaya na. Kana isowa sai 'kamshi kawai zaka ji yana tashi, bayan na kammala nima nayi wanka na na shirya cikin doguwar riga na yane kaina da mayafi. Ko ba komai ni ma zanji nutsuwa tunda sun guje ni, haka na ayyana cikin raina badan Mai gadi bama da ko girki bazan yi ba saboda gajiyar da na yi, amma dole na sai da nayi girki na ajiye masa nasan a inda nasan ya saba 'dauka. Ragowar kuwa juye ta cikin foodflask 'daya. Bacci ne sosai yake damu na dan haka sai na kashe komai na wuce bedroom, rigar jiki na kawai na iya cirewa ya saura min saura under wear da bra a hakan nayi kwanciya ta sanin da nayi cewa ni ka'dai ce cikin gidan babu mai shigo min 'daki. Tun jiyan kuma har yau ban kunna wayata ba, nima haka kawai naji in barta akashen 'kilan ta hakan zai fahimci irin damuwar da na yi da rashin su kusa da ni. Cikin bacci naji ana shafa min fuska ta tamkar cikin mafarki, ko da na bu'de idanu na sai na ganshi kwance gefe na ya 'dora kansa gefen kafa'da ta. Da idanun bacci nake duban sa batare da nayi motsin kirki ba dan duk zato na mafarki nake yi...tashin farko na lura da 'yar ramar da yayi wanda ba kowa ne zai fahimci hakan ba sai wanda ya san shi sosai...ko.motsin kirki bana so inyi saboda kar mafarki na ya yanke so nake in ta kallan sa a haka batare da na tashi abaccin ba. Hakan yasa na zuba masa idanu ina kallon fuskar sa yayin da shima ta 6angaren sa hakan ne ya kasance. Ganin kamar bazan ce komai bane ya sa shi fa'din" Nuree na". Yayi magamar cike da shau'ki yana 'dan murmushi   Idanu na na lumshe sanadiyyan yanda muryar sa ya ratsa min har cikin zuciya ta, take  na kuma bu'de na sau'ke su kan fuskar sa...Alhamdulillah na fa'di cikin zuciya ta bayan fahimtar da nayi cewa ba mafarki nake ba...dagaske shine kusa da ni. " Yah Deen". Nace a hankali ta yadda la66ana ne ka'dai suka yi motsi in ma ba kallo na kake ba bazaka da na ambaci sunan mutun ba. Amsa ni naji yayi da fa'din" Na'am Nureen Deen". Tambaya na sake jefa masa ina duban sa nace " Ka daina fushi da ni yanzu?" Sai yace " Dole na ai Nuree, ke ma kinsan bazan iya fushi dake ba har na tsawon lokaci ba, amma kullum sai kin 6ata raina sam baki damu da damuwa ta ba Nuree...idan nace zan cigaba da zama kusa dake watarana 'kirji na fashewa zaiyi zuciya ta fa'do...'kilan ma mutuwa ta riske ni batare da kin fahimci halin da na shiga a dalilin ki ba...." Saurin yun'kura nayi na rufe mai baki da hannu na wanda hakan dole ya tilasta masa yin shiru, kallon cikin idanu na ya tsaya yi wanda a hankali hawaye ya fara gangaro min saman kunci na yana 'diga a kan fuskar sa. Sai da ya lumshe idanun sa sannan ya 'dago hannayen sa duk biyu ya sa ya rungumo ni da shi yana jin wani shau'ki na 'diban sa, nima 'din kaina na kwantar bisa 'kirjin sa na cigaba da zubda hawaye na. Gaba 'daya jina nayi na karaya da maganganun sa, ha'ki'ka ban yiwa kaina da miji na adalci ba, ban yiwa rayuwar aure na kyakkyawar runguma ba shiyasa a kullum nake cikin rashin natsuwa, a kullum damuwa ta 'kara yawaita take yi amma taurin kaina ya hana ni tsayawa in fuskanci gaskiya. Kuka na cigaba da yi wanda ke fitowa tun daga cikin zuciya ta, da kaina nasan bana kyauta masa  sam azaman auren mu da shi gashi har na kai shi ambatan mutuwa duk ta dalili na.... Da muryar kuka batare da na 'dago kaina ba nace da shi" Dan Allah Yayah Ka yafe min bazan sake 6ata maka rai ba...." Ban kai ga 'karasa maganar tawa ba ya dakatar da ni da fa'din"  Shiii...Ya isa haka kiyi shiru kinji...?". Shirun nayi kaina bisa bisa 'kirjin sa ina jin yanda zuciyar sa ke harbawa...Yah deen kam wani natsuwa yake jin yana ratsa shi, bai ta6a zaton akwai irin wannan ranar ba da Noor zata yi nadaman irin zaman da suke yi da shi, tayi nadaman abubuwan da take aikata masa duk dama yasan da laifin sa amma sosai ya gaji da irin zaman da suke yi a gidan, ba 'karamin 'kosawa yayi da yanda har yau ta kasa sakin jiki sosai da shi ba, abin na matu'kar ba'kanta ransa musamman idan ya ci karo da ma'auratan da ke rayuwa kushiyar ta gidan sa, Safwan ka'dai ma babban misali ne amma haka ya basarwa baya bayyana sirrin nashi gidan, Allah ne ka'dai yasan yanda abin ke yi masa suya a zuci. Bai ta6a tsammanin ranar zata zo haka kwana kusa ba,...yau 'din sai yake jin sa kamar ba shi ba, ji yake yau tamkar ya zama wani mutun ne cikakke wanda ya jima yana rayuwa da 6arin jiki..wani 6angaren kuwa tamkar basarake yake jin kansa saboda tsananin farin cikin da zuciyar sa ta shiga. " _Alhamdulillah_ " Ya furta cikin zuciyar sa while a zahiri kuma yana murmushi. Ni da kai na ma sai da naji wani natsuwa ya shige ni, sabon yanayi na tsinci kaina a ciki farat 'daya, ha'ki'ka babu abinda ya kai masoyi sanya farin ciki a rayuwa...tunawa nayi da doguwar tafiya da suka yi kuma ban bashi komai ba haka kuma banga Baby Jas ba, 'dagowa nayi na dube shi har alokacin idanun sa alumshe kuma bai 'dauke hannun sa da ya zagaye ni da shi ba" Yah Deen". Na fa'da kamar ban san yin maganar. Take sai ya bu'de lumsassun idanun sa ya sau'ke su akan fuska ta...murmushi naga yake yi mai 'dauke da wani sirri mai ma'anoni da dama. A hankali nace " Yah Deen banga Baby ba". Yana murmushin ya bani amsa da fa'din" Na barta wurin Ammi". Maida kaina nayi na kwantar, jiki na naji yayi sanyi 'kalau kamar zanyi kuka nace da shi" Ai baka gaya min cewa zaka barta acan ba". Yace" Ai naga babu amfanin sanar da ke in ne shiyasa". Kaina nayi saurin 'dagowa na sake duban sa da alamun mamaki sai jinjina min kansa sannan ya cigaba da fa'din" Saboda naga baki damu da mu ba daga ni har ita shiyasa kawai na barta wurin Ammi dan nasan zata kula da ita, ina fargaban kar ya kasance dukkan mu cutu da halin ko'in kula da ake nuna mana ne, ko Ammi ma da na gaya mata bata ji da'di ba shiyasa kawai tace in bar mata Baby awajen ta 'kilan.hakan zai fi miki farin ciki...". Bai gama rufe baki ba na gangara na bar jikin sa wani hawayen na sake biyo kunci na...suya naji zuciya ke min sosai, duk da nasan da wuya ne ya iya fa'da wa Ammi hakan amma tunda har ya bar Baby acan nasan dole akwai wani abu ne daban, babu mamaki yaudaran kaina nayi da tuanin bazai iya fa'da matan ba bacin tsakani na 'da da uwa Allah ne ka'dai ke iya ratsawa...domin shi da kansa ma idan haka kawai ne nasan abu ne mai wahalar gaske wani yace ya bar Baby acan kuma ya amince. Raina ba'ki 'kirin na zari hijab na sanya ajiki na wanda yake iya gwiwa ta, bathroom na shiga dan ha'da masa ruwan wanka still hawaye na bai daina tsiyaya ba, tsoro nake ji idan Ummah ta taji wannan batun nasan Ammi bazata min fa'da ba amma Ummah ta bazata barni ba. Ina ha'da ruwan nake wannan tunanin. Yayin da shi kuma Yah Deen ya 'kara fa'da'da murmushin sa yayi ya bi baya na kawai da idanu cikin ransa ya furta " sarkin kuka". Da kammala ha'da ruwan na fito sai na tarar da shi yana rage kayan jikin sa, ya 'daura towel, zuwa nayi na 'dibi kayan da ya cire a hannu na da niyyan ajiye a inda ya kamata...ko ban fa'da masa cewa ruwan wanka na jiran sa ba nasan daga hakan bayi ya nufa, dalilin kenan da ya sanya ban ko ce da shi komai ba kawai na juya da niyyan barin wajen sai naji ya sarke min hannu da nashi, saurin waigowa nayi na kalle shi wanda shi kuma bai damu da hakan ba sai matsowa ma da yayi kusa da ni, fuskar sa ya kawo dab da tawa ina shirin kawar da nawa fuskar sai ya'ki bani daman aiwatar da hakan, bakin sa kawai na tsinta saman nawa ya fara kissing 'dina.. Hakan bai sa hawaye na ya tsaya ba domin sosai zuciya ta ta shiga ru'du...tun jin cewa ya kai 'karata wurin Ammi har ma ya bar Baby a can. Tsawon mintina biyu ya 'dauka sannan ya raba connections 'din ya tallafi kaina da hannayen sa biyu, fuska ta daf da shi yake kallo na.." Wai menene na kukan?" Ya tambaye ni. Shiru nayi masa ban ce da shi komai ba illah yin 'kasa da nayi da nawa idanun" Bazaki gaya min ba?" Ya sake tambaya ta. Sai lokacin na bu'di baki na da muryar kuka nace " Ai kaine..." " Me nayi miki daga dawowa ta yanzun?" Ya sake tambaya ta yana 6oyayyen murmushi. Ban damu ba sai nace da shi"... Ammi nake jin tsoro kar ta yi min fa'da kuma ina missing Baby". Murmushi yayi sannan yace" Shine sai kin yi kuka akan hakan? To oyah share hawayen ki idan na fito daga wanka zan miki wani albishir...kinji?" Kaina na 'dage sama alamar naji. Sai da ya shafi fuska ta kafin ya wuce bayin. Riga ta na 'dauka na sanya bayan na cire hijabin dake kaina, sannan na wuce parlour da niyyan zuwa kitchen domin ha'da masa abinda zai ci nan idanu na suka sau'ka kan Baby dake kwance tana Bacci akan kujera. Wani sanyin da'di ne naji ya ratsa ni nan take da na ganta, fara'a ce ta cika fuska ta nan take, inda Baby take na isa na sumbaci goshin ta ina murmushi...ita kam babu ruwan ta ko 'dis banga alamun rama tattare da ita ba ba kamar Yah Deen ba. Kitchen 'din na wuce na ha'da masa komai a dinning da yake dama abincin da na dafa 'din bai 'kare ba...so shi na ajiye masa. Kasa ha'kura nayi sai da na tada Baby a baccin na rungume abina a 'kirji na ina jin wani farin ciki na ratsa min dukkan ga6o6i na. Da fitowar sa kuwa na banka masa harara sai yayi murmushi sannan ya tako zuwa inda muke ..." Da alamu ciki kike son maida ta ko?" Ya fa'di lokacin da yake zama gefen mu. Wata hararar na 'kara yi masa tare da fa'din" Da zanfi son hakan ai kaga shikenan ka rasa ta". 'Yar dariya yayi yace" Yarinya kenan shikenan duk kukan sun tafi?..." Tun kan ya rufe bakin sa nace da shi " Gaskiya Yayah ka shammace ni". Yace "Maganin ki kenan ai". Nace " Zan rama ai nima". Sai yace " Ni kuma in ta gayawa Ammi ba". Baki na 'dan tura navkalle shi sai ya 'dage min gira. Ban kuma cewa komai ba kawai mi'ke tare da 'daukan Baby nayi nai ciki da ita. Yah Deen kam dariya ma na bashi ya kwantar da bayan sa jikin kujera ya bini da idanu har na 6acewa ganin sa. Wanka na yiwa Baby na canza mata kaya da marasa nauyi, har a lokacin kuwa bata ce da ni komai ba saboda baccin da tayi har yanzu bata gama warware ba. Dawowa muka yi ina ri'ke da hannun ta bamu zauna ba na nufi hanayn dinning ina fa'din" Yah Deen abinci da alamu Baby ma yunwa take ji, kuma nima ina jiran albishir 'dina dan haka..." na 'karashe da nuna masa dinning in. Yana mi'kewa yake fa'din " Wani albishir kuma bayan wannan?" Yayi maganar da nuna Baby, sai nace" Ammin fa ?" Na tambaye shi cikin son jin ko dagaske ne ya sanar da ita wani abu. Sai yace " Ammi sa'ko ta bani kawai tace idan baki canza ba in ringa zane ki ba ruwan ta". Take murmushi ya cika fuksa ta nace masa " Ai nasan Ammi na bazata fa'di haka ba". " Yarinya kenan...munan nan da ke ai zaki sha mamaki". Yayi maganar dai dai ya iso yana jan kujera ya zauna. Muna cikin cin abincin ne nace" Hmm...da fa  marainiyar 'karfi da yaji kuka maida ni a gidan nan...kullum inji kamar bani da gata". Da saman idanu ya kalle ni bai ce dani 'kala ba kawai ya cigaba da cin abincin sa. Daren ranar kuwa sosai muka faranta ran junan mu, domin ban masa shamaki da komai na jiki na ba...sosai kuwa ya nuna min irin kewata da yayi tsawon kwanaki. Sai daga baya ne na kwantar da murya ta na nemi yafiyar sa ya kuma yafe min.... Tun daga lokacin na 'dauri aniyar gyara rayuwar aure na, duk wasu abubuwa da suka shafe shi na daina nuna halin ko in kula da su, sosai nake kulawa da rayuwar 'yata da miji na. Ko bayan dawowar su ma munyi waya da Ummah ta har hiran  zuwan su baby ya shigo zancen namu, nan nake tambayar ta cewa ai an kai mata Baby ko?" Tace" Erh sunje da Baban ta mun gaisa amma ma tare suka koma gida da ita... Ko hakan ma da naji sosai naji babu da'di, musamman dana fahimci a duk zaman nasu Ummah ta ma sau 'daya tak kawai taga Baby, sauran 'yan uwana kam ma babu ko wanda ya ganta balle asan da zuwan su kuma nasan duk laifin Yah Deen ne dan Ammi bazata hana akai Baby gidan Ummah ba sai dai in shine zai yi iyawar sa. Ko hakan ma dana ji sosai ya 6ata raina amma ban bari cikin zuciya ta balle ya dame ni..duk na ha'da al'amuran na watsar  kawai na bari akan ai hakan ma arzi'ki ne, ka haifa aso yafi ka haifa a nuna 'kiyayya. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *73* Shekarar baby uku Yah Deen ya kaita makaranta amma a kullum hankalin sa na wurinta, da yake ma kuka take yawan yi idan an barta, watarana har 'kiran sa ake ya baro office ya tafi makarantar ta su saboda tsananin rikicin da ta ke yi musu...ni kam sau tari sai dai idan sun dawo gida ya bani labari. Yah Deen dole ya tilastawa kansa 'daukan hutu, da yake ma yana da burin ya koya min mota saboda tafiya makaranta ta ga kuma baby ma, hutun da ya 'daukan ne ya sa shi samun isashshen lokacin yin hakan, cuz duk bayan ya ajiye Jasmine sai ya dawo nima ya fara aikin koya min motor, da zaran lokacin break in su Baby yayi sai ya sake komawa makarantar ya duba ta sannan ya dawo gida, mu kan fita ne duk safiya da kuma yammaci idan an kaita Islamiya. Cikin lokaci 'kan'kani kuwa na koya dan ban wani sha wahala wajen fahimtar komai ba, hutun 3weeks yayi sannan ya koma bakin aikin sa, kafin hakan kuwa sai da ya tabbatar ya nemawa Jasmine Special Nanny wacce ke kula da ita a makarantar ita ka'dai yana biyan ta. Da sun yi break kuwa zata 'kira shi suyi hira da baby yaji muryan ta yayi ta jan ta da hira har sai yaji tana dariya kafin yake hanging 'kiran, aikin ta kenan kulawa da Jamsine har a tashi a school sannan ta wuce bayan ta sada ta da wanda yazo 'daukan ta. A lokacin kuwa asbiti har biyu Yah Deen ke aiki da su abin sai ya zame masa ba hutu sam, wani sa'in har tausaya masa nake yi, dan duk yadda ya so ya ringa samun isashshen lokaci yana zama da iyalin sa hakan ya kasa samuwa, Baby kanta sosai take damuwa da rashin sa kusa dan ta sha'ku da shi ba laifi...motsin ta ka'dan zakiji ta ambaci sunan sa, ko wasa ta ke yi" Daddy ta fiye ambato. Da farko shi ya cigaba da sau'ke Baby a school amma daga baya da abubuwa suka yi masa yawa sai na nemi ya bar Baby Jas in rin ka kaita makarantar amma ya'ki amincewa sam. Da 'kyar na samu ya amince ya bani ragamar kaita makarantar da 'dayan motar sa wanda sanadin hakan yasa ya 'dan samu natsuwa ya rage fita sassafe, yakan yi shirin sa cikin tsanaki ya gama komin sa a nutse sannan ya fita office. Banfi 2months da fara jigilar makarantar Baby ba nima na fara tawa makarantar. Lokacin fitar mu da Baby ba 'daya ba haka ma lokacin tashin mu amma duk da haka sosai nake 'ko'kartawa wajen ganin kowa ya isa tasa makarantar akan lokaci. *****      Bazan manta ba ranar wata talata Yah Deen yazo min da batun wai ya ha'du da wani matashi dake son yin aiki kuma wai ya iya tu'ki ba laifi, yace sunyi magana da shi kuma ya fahimci yaron na da natsuwa dan haka zai ringa sau'ke ni da Baby a school yana 'dauko ta in yaso nima idan na futa a lectures sai ya koma ya 'dauko ni cuz shi har yanzu ransa bai kwanta da nawa tu'kin ba. Wallahi tun lokacin ban ji da'din 6ulluwar yaron nan ba, haka sam banji batun  Yah Deen in ya kwanta min arai ba haka kawai sai na tsinci kaina cikin rashin natsuwa. Sai ma na tsaya da mamaki ina duban sa, domin da bakin sa ya furta wannan maganar kamar yanda ya ta6a furta min garga'di abaya akan shiga mota da wani, baki na ta6e cikin raina nake ayyana ina kuma kishin ya tafi oho? Ko da yake yace ya yaba da natsuwar yaron 'kila shiyasa ma bai damu 'din ba. " Baki ce komai ba" Ya sake fa'di yana duba na. Kaina na kawar gefe sannan nace" Toh ni Yayah me zance?" " Akwai mana ai naga kamar ranki bai so hakan ba". " A a ba haka bane kawai nayi mamaki ne...dan Allah Yah Deen yanzu miye abin sai ka 'dauki driver bacin ba shiga hakkin karatun kowa cikin mu akayi ba..". " Shi ai namiji ne Nuree kuma sosai na yaba da hankalin sa, nima 'din zanfi samun natsuwa idan ya kasance na 'dora wani a bayan ku in ba haka ina office amma kullum hankali na a rarrabe, tunanin halin da kuke ciki nake koda yaushe tunda nasan ba wai sosai kike 'kware a tu'kin ba". " Ni dai please a barshi Yaya, ka nema masa wani aikin". " Haba Nuree..zaki fara ko?" Yayi maganar yana janyo ni jikin sa. 'Dan 6ata rai nayi nace" ni bana san damuwa ne kawai Yayah..." Bai bari na idasa maganar ba ya rufe min baki da nashi wanda hakan ya tilasta min yin shirun dole. Duk da hakan daga baya sai da na so nuna masa 'kin amincewa ta dan sam lamarin bai min ba har cikin raina amma ya dakatar da ni ta hanyar fa'da min cewa" Hakan zai fi mana gaba 'daya saboda babu wanda zai shiga hakkin wani...ya kuma ce dan Allah baya son musu...taurin kanki kullum 'kara hauhawa yake yi Nuree". Ya 'karasa maganar da 'dan alamun 6acin rai akan fuskar sa. Dole na watsar da zancen musamman ma saboda yanda naga Yah Deen ya fara 6ata ransa kan batun yasa kawai na zuba idanu na ba wai dan raina ya so ba. Haka driver mai suna Sani ya fara aikin sa wanda cikin gidan yake kwana tare da maigadi. Idan ya fara sau'ke Baby nima sai ya ajiye ni a tawa makarantar, tun farkon zuwan sa maganar kirki bata ha'da ni da shi, daga gaisuwa shikenan musamman ma da na lura yaron surutacce ne hakan yasa na ke kama kaina dan kar ya samu fuskan cika ni da surutu. A bakin Nannyn Jasmine yake jin wasu labarin rigimar da take yi farkon sata makarantar da yake idan yaje 'dauko Baby sukan 'dan yi hira da Nannyn dan Sani gwani ne ko baka yi ra'ayin magana ba sai ya saka yin magana na kan fahimci hakan ne idan suna tare da Yah Deen. Kuma ma da yake watarana Nannyn ma shi ke sau'ke ta idan sun tashi, aikin ta kuma dama a iya school ne kawai da zarar su Baby sun tashi shikenan aikin ta ya 'kare sai kuma gobe...idan kinga su da Sani suna sururtu har zakiyi mamaki, za ma ki zaci cewa sun shekara biyar tare da yake duk irin su 'daya ne surutattu ne na masifa...ni kuwa a rayuwa ta na tsani mutun mai yawan magana. Ai kuwa tunda Sani yaji labarin rigimar Baby a abkin Nanny shikenan sai yake yawan tsokanar ta akan hakan, yakan ce da ita cry-cry mai kukan Daddy...idan yaga ta 6ata ranta tana fushi sa kiga yana ta yi mata dariya yana sake maimaitawa while ita kuma tana tura baki tayi tamkar zata yi kuka, da yake yanzu ba laifi ta saba sosai da makarantar ta kuma saki jikin ta so sam bata so ace mata mai kuka a school. A kullum idan ta dawo sai ta min 'karar Sani wai yana yi mata dariya wai tana kuka sai tace min kuma Mummy ai yanzu na daina" Haka take ce min tana nuna alamun rashin jin da'din ta afili. Tun ina bata lalla6a ta akan maganar har nazo na gaji na daina kula ta sai ta koma gayawa Daddyn ta wanda shima akwai ranar ta dawo yana gida ne yana ganin ta sai yayai turus yace" Maman Daddy ya da fushi haka?" Sai ta nufe tana dama fuska tace" Ai Sani ne yake ce min wai cry-cry kuma fa Daddy yanzu bana kukan". Dariya sosai ta bashi amma ya danne yana cire mata uniform yake ce mata rabu da Sani zane shi zanyi shima yayi kukan sai kiyi masa dariyar kema ko?" Hakan da ya fa'da mata ne ya sata jin da''di shiyasa ta maida kaiwa 'karar wurin sa, a duk ranar da Sani ya takale ta  to Yah Deen take sanar ma wa. Shi ma da 'marar ta ishe shi ranar yana dariya ya 'kira Sani yace masa" Sani gaskiya kana takurawa Mama na da yawa, kai baka ganin yanzun ta girma ne? kuma ai ma bata kukan yanzu ko?" Ya 'karasa yana duban ta Saurin 'dage kanta tayi tana ta6o kunnen ta, sai yace" Sani to ka kiyaye ni...idan baka daina ba kaima zane ka zanyi kayi kuka Mama na ta rama dariyar ta..." Sani na jin haka ya bushe da dariya dan yasan Deen wasa yake yi masa dan ya kwantar da hankalin Jasmine, yana cikin dariyar yake fa'din" Hajiya maman Daddy wato 'karata aka yi?" " Ni dai na gaya maka". Yah Deen ya fa'di tare da hanging call in. Lalla6a ta yayi har ta saki ranta da taji cewa anjima zasu je yawo. Daga lokacin kuwa sai Sani ya 'dan rage tsokanar ta 'din a hankali ma sai yazo ya daina gaba 'daya sai jifa-jifa. A cikin wannan lokacin aka haifi Afrah, wanda tun zuwan gidan na farko  da muka dawo Baby ta fara yi min rigimar ita ma wai asiyo mata Baby..Yah Deen kam dariyar ya ringa yi duk dama shi kansa yana so yaga ya tara iyali amma shiru har yau babu komai, babu abinda na sha ko muka yi amfani da shi amma tun haihuwar Jasmine har yau ban 'kara ko 6atan wata ba. Lalla6a ta ya ringa yi yana taro mata Babys in wasa kala-kala sannan ta huce. Ranar da shima zai je gidan Safwan in kuwa dukkan mu muka je har da ni muka gaishe su sannan muka dawo. Kamar wasa sai abin ya fara damun sa, duk dama ya san ba yin kan mu bane amma shekara hu'du ya kamata ace ya sake ajiye wani Babyn. Kwance muke hannayen sa dabaibaye cikin jiki na, yayin da ya kwantar da kansa bayan wuya na yana sau'ke min numfashin sa a hankali ya 'kira suna na ban amsa ba amma da yake yasan na jishi kawai sai ya cigaba da maganar sa" Nuree yaushe zan sake samun wani Babyn ne, ina son inga na tara yara da yawa". Hannun sa ya 'daura saman hanci na yana ja a hankali tare da dawo da bakin sa saitin kunne na sannan ya cigaba da fa'din" Ina so in haifi mai irin hancin ki Nuree, da mai irin wannan bakin..." Murmushi nayi masa dan sosai nake jin wani shock a jiki na ga kuma yanayin maganar tasa har cikin zuciya ta take ratsawa. Jin bance komai ba sai yayi saurin birkito ni ya koma saman jiki na..." fuskar sa ya kai dai-dai da tawa ni kam tuni na lumshe idanu na ina sakin murmushin jin da'di. A hankali ya kai bakin sa saman la66a na ya sumbace ni sannan ya 'daga kansa" Baki bani amsa ba Nuree..na ga alama ke babu ruwan ki ko..ni kam na koma bayan Baby..." Bayan sa na sau'ke hannu na ina yawo da shi a hankali sannan na bu'de idanu na yanda shi ka'dai zai ji nace" Allah ya kawo masu albarka". " Ameen Nuree" Ya amsa ni da sauri. Sumbata ta ya 'kara yi hannayen sa na gefe da gefen wuyana yayin da ya tsare da idanu yace " Allah yasa ma har na ajiye.." 'Yar dariya nayi nace" A a kam" " Wai me kike nufi ne Nuree". " Ni ba komai". " To naji..insha Allahu anjima ka'dan zan ajiye ko baki so?" " Ina so mana daga yanzu har zuwa 5yrs duk sanda Allah ya kawo Alhamdulillah". Cizo na yayi ka'dan nace" Ash ina mai rintse idanu na. " me yasa kika ce har 5yrs wayo zaki min ko..ok saboda school ne zaki ki haifa min Babys". " Nifa ba 'ki nayi ba Yah Deen Allah ne bai kawo ba kawai mu cigaba da Addu'ah har Allah ya bamu ". Shiru yayi yana duban cikin idanu na, a hankali ya sau'ke bakin sa saman wuya na yayi kissing tare da furta" I love u Nuree". Lumshe idanu na nayi ina jin sanyi cikin zuciya ta, ba yau na fara jin wannan kalmar daga bakin sa ba amma a duk lokacin da ya fa'da min sai naji natsuwa ta shige ni, sosai yake 'kara min nawin soyayyar sa dake zuciya ta. Bance da shi komai illah ajiyan numafshi da na sau'ke yayin da ya cigaba da bin ilahirin jiki na yana sau'ke min numfashin sa sai da ya zo dai-dai saitin Boobs 'dina kafin ya sau'ke bakin sa wurin. Gaba 'daya naji jiki na ya saki, Yah Deen ya yau bai canza ba, sosai ya iya bi da mace, duk yadda yasan zai illah ta zuciyar ki da touchs 'din sa nan zaki ga yafi bawa muhimman ci, hakan yasa a kullum nake 'kara jin soyayyar sa na shiga ta, abaya idan akace min zan yi masa irin wannan soyayyar wallahi da akina zan 'karya ta maganar, sai gashi dumu-dumu na tsinci kaina cikin tsananin 'kaunar sa. *****     Shekarar Nannyn Baby guda da fara yi masa aiki sai tayi aure da yake dama bazawara ce, so Yah Deen bai nemi wata Nanny 'din ba ganin cewa Baby tayi wayo yanzu kuma ko a makarantar ma ta daina rigima har ma da 'kawayen ta su Afreen yda Siyama. A cikin lokacin kuma sai Uncle Ja'afar ya siyawa Yah Deen mota mai masifan kyau da tsada kuma 'yar yayi, a fa'dan sa wai tukuicin sa ne na haihuwar Baby dan bai yi komai ba tun da aka haife ta. Ranar Yah Deen shigowa yayi yana murmushi yana karka'da key 'din da wata yammaci ranar juma'ah, ni da Jas muke zaune wai tana koya min karatun Islamiyar su. Dukkan mu idanu muka zuba masa da shigowar sa. Shi kam bai damu ba duk da akllon a bamu labari da muke yi masa, zama yayi gefe na ya kama kuncin Baby ya jijjiga yana murmushi yace" Baby na kin ciyo mana mota"...Murmushi ita ma tayi duk da bata san manufar maganar tasa ba. 'Dagowa yayi ya kalle ni sannan ya aki hannu yaja hanci na yace" 'Kila da kin 'kara da jirgi za'a bamu". 'Yar dariya nayi ina kallon sa, dan har yanzu ban fahimci inda zancen sa ya dosa ba, sai da ya gama ja mana rai kafin ya bamu labari cewa Uncle J ne ya aiko masa wai na tukuicin haihuwar Baby. Murmushi nayi cike da jin da'di nace" Ashe ma motar tawa ce" " Dalili?! " Ai ni haife ta ba kai ba". " Yarinya kenan, da yake ya san 'ko'kari na ne yasa ai shiyasa yace tawa ce ba taki ba...ke de ki yita fama da wancan na bar miki gado kafin al'amura su canza sai a san yanda za'a yi". Yayi maganar yana mi'ko min key 'din motar sa da yake hawa. Wasa ma ni nake yi masa in ba haka ba ma ina ni ina mota, ban tashi mamaki ba ma sai da muka fita naga motar sosai na yaba da karamcin Uncle Ja'afar, harga Allah naji da'di sosai har cikin raina amma sai nace da shi amma dai ba wai dan Baby kawai bane may be dama yayi niyyan siya maka motar". Murmushi yayi ya 'daga Baby sama yana dariya yace" Yarinya ta mai albarka, ke zan fara sawa cikin ta". Kamar wasa itan kuwa ya fara sawa suka shige Baby na dariya sai da suka fito sannan yace kizo ki duba". Sai na tsaya na karya wuya na alamun nayi fushi. Ga mamaki na sai cewa yayi" To ke ma je ki 'da na taki". Hararan sa nayi nace" Ai na santa". " To zo ki shiga ba dan halin ki ba". Idan na biye Yah Deen kullum gani zan ke yi kamar shishshigi nake yiwa rayuwar sa, wani lokaci idan yayi abu har zakiyi mamaki, duk da nasan wasa yake yi min amma sai inke jin wani iri a raina. Murmushi nayi na matsa kusa, har a lokacin kuma Baby na hannun sa, ciki muka shiga duka, mota kam masha Allah sai fatan Allah ya sanya Alkhairi. Daga wurin muka nufi wajen tashi motar wacce ya saba hawa da yace daga yanzu nice zan cigaba da hawan ta. Itan ma nasan ba laifi dan lokacin siyan ta taci ku'di kuma tana nan garau babu abinda ya same ta daya ke tana samun kulawa sosai,  idan kin ganta ma zaki ce bata fi 3months a hannun sa ba. Yanda naga yake farin ciki da wannan motar ya yasa nima naji ni cikin farin ciki, sosai na ringa sanya albarka cikin zuciya ta nakewa yiwa iyayen mu fatan Alkhairi, wani sa'in sai in ga  tamkar Yah Deen shine ka'dai farin cikin Uncle Ja'afar dan wallahi motar sai masha Allah kawai dan ko shi Uncle J in bai hau kamar ta ba sosai ya 'dagawa Yah Deen ajin sa ya 'kara masa akan nada. Tun ranar yake fa'din" Yarinyar Daddy kema dole in canza miki motar zirgarzirga makarantar ki tunda kin ciyo min mai daraja". Baki na ta6e gefe ina murmushi na jinjina masa dan nasan zai iya indai akan Baby ne, fiye da mota ma in ku'din sa zai kai zai sai mata...amma wannan kam ai sai dai yace zai canzawa Sani tunda shi ke hawa ba ita ba. Abun fa kamar me domin cikin sa'a wata uku ba'a cika da kawo sabuwar motar Yah Deen ba sai ga wani sabon labari domin aikin da ya jima yana nema a Abuja ya fito kuma ya samu da matsayin consultant. Wannan labarin yafi komai yi masa da'di a rayuwar sa, ni kaina na ji da'di domin kuwa gaba akaci ba baya ba, duk da bana son yayi nesa damu amma hakan bai hanani bayyana farin ciki na a fili ba. Cikin lokacin sai ya ringa zirga-zirga tsakanin Bauchi da Abuja har komai ya kammala ya tattara ya tafi...zuciya ta babu da'di amma ya zanyi, nasan ba dan makarantar da nake yi ba da babu abinda zai sa mu cigaba da zama a Bauchi while shi yana can Abuja dan ko shi da kansa ma ba son shi bane amma babu yadda zamuyi dole haka muka ha'kura muka bishi da fatan Alkhairi. Babban matsala ta Jasmine ne domin da 'kyar ta saba da yin  cikakken wata guda kafin taga mahaifin ta, a hankali ma da zaman yayi zama sai ya fara rage satikan yana dawowa weekend duk bayan 2 weeks amma ko da yaushe zaki same shi ma'kale da waya suna waya da Baby. Zakiyi mamaki Hafsat domin tun ranar zuwan Yah Deen Bauchi weekend na farko na fahimci cewa wata mace ta shiga rayuwar sa, amma sam ban nuna masa damuwa ta ba kamar yadda na saba dannewa haka na danne. 'Karfin addu'ah ta kawai na 'kara domin na 'dan fara shagala ganin abubuwa sun daidaita min, gani da nayi kamar ya daina ne ya sani sakin jiki har na rage yin Addu'ar, musamman da na ga zama mu da shi a lokacin sai dai ince Alhamdulillahi, domin bana tare da wata damuwa, yana kulawa da ni ya bani lokacin sa ya ji damuwa ta, in zai iya ya magance min, 'kauna ta musamman yake nuna min. Watan sa biyu da komawa aiki Abuja ya canza motar da ake kai makaranta kamar yanda yayiwa kansa al'kawari, a hannun ta ya dam'ka key 'din yana dariya yace" Maman Daddy kema ga taki tunda kin ciyowa Daddy mota ko?" Dariya tayi kawai tana ri'ke da key 'din tace" Daddy nima zan fara driving irin na Mummy ko?" Kuncin ta ya kama yace" A a Diamond 'din Dady bata driving, ai ita ta musamman ce sai ta kai 20yrs zata fara driving..yanzu Sani ne zai ringa driving 'din ki a sabuwar motar ki ko Baby na?" Kai ta 'dage masa tare da fa'din" Thank u Daddy". Murmushi muka yi har ni dake gefe ina kallon su, Yah Deen shafa kanta yayi yace" Baby na sai kuma me kike so yanzu?"  baki ta washe tace" Daddy saura ka kaimu Makka da Madina da kai da Mummy". Murmushi yayi mata yace " Ki kwantar da hankalin ki yarinyar Daddy, Insha Allahu zaki je Makkah kinji..ki rinag Addu'ar Allah ya bawa Daddy ku'di". Kai ta 'daga masa tana murmushin ta mai sanyi da kuma 'kawata fuskar ta. Sosai hankalin mu ya kwanta yanzu domin komai normal yake tafiya, Yah Deen ya kan dawo weekend duk bayan wata guda ko 'kasa da haka, har Shuwarin munje a wani weekend da ya dawo amma kwanan mu biyu muka dawo cuz bashi da lokaci. Kwatsam rana tsaka sai na fara cin karo da sa'k'konin wata mai suna Jiddah cikin sha'anin sa musamman wayar sa...wani abu guda da ni ni kuma arayuwa ta bana iya danne zuciya ta a lokacin, idan naga 'kira ko kuma sa'ko ya shigo masa daga wata daban na kan ji ni cikin tsananin tashin hankali musamman idan abin ya shafi 6angaren soyayya ne, tsoro nake kar rayuwar farin cikin mu ya sake samun gi6i...ina tsoron.kar wata ta 'kwace min shi, ban manta ba lokacin da yake neman Yusrah sosai rayuwar da shi ta canza, ina tsoron kar wata ta sake shiga tsakanin mu dan a yanzun bazan iya jurewa ba. Tsoro nake ji sosai kar ya kasance wancan rayuwar da yayi abaya da Husnah ita yake sake maimaitwa da Jiddah, tsoro da fargaba sosai suke ri'ke zuciya ta har yana barazanar hana ni sukuni.        Ina son miji na irin soyayyar da duk wata mace da ta cika mace take yiwa mijin ta, Hafsat koka'dan na tsani inga wata mace ta ra6e shi duk da nasan yaudarar kaina kawai nake yi domin yana da daman auro uku baya na amma na kasa jure hakan. Ko abaya ma dalilin  kenan da ya sanya nake sake mai jiki na a duk lokacin da ya bu'kaci hakkin sa aguna koda ni bana ra'ayi na kan sawa raina dole, ba dan komai ba sai dan kawai inga na faranta masa, inga cewa ban barshi cikin 'kuncin da har zai iya sha'awan wata macen daban bayan ni ba... ban sani ba ashe hauka ta kawai nake yi.   Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *74* Da kaina kuma na fahimci jin da'din da yayi da wannan canjin nawa ya kuma bani wani babban muhimman cin da har yau 'din nan nasan ina da shi a wurin sa. Domin ko yanzu Yah Deen kusance ni sai yayi min sumbatu, ya yaba min, ya samin albarka, ya kuma nuna min cewa ni ta dabance, Hafsat yanzu har na saba, inajin kaina ne tamkar Zahra cikin taurari saboda irin riritawar da yake yimin, saboda shi nake duk wasu abubuwan da mata ke yi dan kula da jikin su dan jin da'din mazajen su, babu abinda bansa kaina na koya ba sabo shi da soyayyar sa, duk wani abu da zai kawo mana farin ciki indai bai sa6awa addini ba Hafsat a hankali na sawa raina shi na koya duk dan saboda Yah Deen. Da kaina na ringa neman ilimi kan zamantakewa, ha'kuri juriya da biyayya hatta kwanciyar aure duk sai da na nemi 'karin ilimi akan su, duk wani styles na kwanciyar aure na koya dan kawai in faranta masa. Na kan ji kaina kamar zai fashe idan Yah Deen ya yaba min bisa wani abin da na yimasa musamman a shimfi'dar mu, zuciya ta duka na bashi yake sarrafawa, na bashi rayuwa ta na bashi duk wani abu da ya shafe ni, yayin da shi kuma ya dinga cika ni da 'karyar yana so na yana 'kauna ta, ashe duk 'karya ne, Yah Deen ba zai ta6a so na ni ka'dai ba, ban san ya zanyi da shi ba, wallahi na 'kwammaci da auren sa yayi ya cika gidan sa da mata da zai fi min akan a ringa yiwa yara na kallon 'ya'yan Mazina ci mai neman mata.      Allah be yoni mai tsananin san a kusance ni ba amma dole nasawa raina tun ban saba ba har nazo na saba kawai saboda shi da farin cikin sa...duk da hakan fa Yah Deen ya raina 'ko'kari na Hafsat ya zanyi masa...ya zanyi masa ya fahimci ciwon da yake 'ko'karin yi min cikin zuciya ta? Sosai abin nan yake damuna a zuci wanda ni ka'dai na na ri'ke ban sanar da kowa ba ciki kuwa har Ammi na da kullum take cikin tuna min cewar matu'kar naga abinda bai game ni ba tare da shi in sanar da ita, amma bazan iya ba Hafsat ina matu'kar son shi, ina 'kaunar sa, sosai nake tausayin ranar da 6acin ran iyayen sa zai sau'ka kansa, shiyasa ma na kasa sanar da kowa hatta ke da kike matar abokin sa ban ta6a sanar miki ba kin sani, Ummah ta, Anty Zainab da Addah na Maryam duk babu wanda ya sani. Duk yanda na so zama na da shi yayi kyau amma da zarar mun fara 'daukan hanya sai kiga ya sako wani al'amarin sa daban ya gusar mana farin cikin mu, domin harga Allah ni 'kwa'kwalta 'karama ce, ban iya ha'da abu biyu lokaci guda ba, bazan iya danne kishi na akan sa ba balle in rayu cikin walwala kamar yadda na saba while nasan zahiri ga halin da ya cusa kansa. Nakan zurfafa tunani wani lokacin sai kuma inga ai kyautata zato ya kamata inyi masa ba munanawa ba, domin ban tabbatar da wacce irin ala'ka bace tsakanin sa da Jiddah...dole na kawar da kaina da sunan basarwa ko ince gudun zato haka na cigaba da rayuwa ta ni da yarinya ta...amma bazan miki 'karya ba Hafsat na dai danne ne kawai amma sanin asalin halin sa yasa na kasa cire batun cikin raina, haka muka koma rayuwar mu kamar baya bana iya wani sakin jiki da shi, duk yadda yaso yaji abinda ke damuna kuma ban iya sanar masa. *****     Tun bayan tafiyar sa sai muka raba hanya da su Baby domin nima na fara tafiya makaranta da kaina yanzu nake driving, yayin da Sani kuma yake sau'ke baby ita ka'dai yake yake kuma 'dakkota. Tun a lokacin abubuwa suka fara ta6ar6arewa ta 6angaren Jamsine, domin ganin ya samu ishshen damar da zai ke6e da Jas ne shai'dan ya fara yi wa Sani muguwar sa'ka azuci, cikin lumana ya fara lalata min tarbiyar yarinya batare da na farga da hakan ba, sau da dama Baby na so ta gaya min wani abu amma sam bana bata hankali na domin asali ni ba gwanar zama in saurari surutan Baby ba ce, baya ga haka ma kuma nima 'din a kullum ina tafe ne da tawa damuwar. Kwata-kwata sai Allah ya toshe min kwakwalwa ta ya kawar min da tunanin wani abu a raina...sam ban ta6a sa hankali na ga canjin da rayuwar Baby ya shiga ba, dan duk yanda naga ta canza sai in ga kamar damuwar rashin mahaifin ta ne kawai ba komai ba. Daga baya ma sai bata ko gwada kawo min wata magana, sau tari kuma sai dai in ga ta dawo fuskar ta wata iri ba fara'a sam..cikin raina sai ince" Gado". Nufi na ta gaji halin ubanta ne wurin rashin fara'a, ban sani ba ashe Jasmine cikin tsananin damuwa take, a hakan ma sosai Sani yake garga'din ta akan kar ta fa'dawa kowa, duk ranar da ya san yayi kissing 'din ta ko wani abu ya kan yi mata garga'di sosai akan kar ta sanar da kowa...hakan kuwa yake faruwa domin bata gaya min, amma duk da haka nasan da ace tana samun damar yin hira da ni da wani lokacin dole zan 'dan ji hint daga bakin ta, amma da kaina na toshe wannan damar. Kuma Allah da ikon sa sai kiga duk ranar da ta yi su6ul da baka ma tayi niyyan sanar da ni sai kiga wani abin yazo ya shiga tsakanin maganar  dole maganar ta yanke ko kuma kiga ni 'din na kasa sauraran ta har batun ya wuce...kinsan idan Allah yaso jarabtan bawa gaba 'daya 'dauke hankalin sa yake yi akan abin shiyasa koda wasa ban ta6a tunanin wani abu makamancin hakan ba game da Baby. Da kaina kuma sai na fara experiencing wani abu, bakin Baby jan sa ya 'karu gashi sai ya zama wani iri ba kamar baya ba da yake 'dan cukul amma yanzu ya fito sosai kullum sai kiga kamar a kumbure, duk da nasan bakin dama asali ja ne saboda hasken ta amma sosai ya 'karu a lokacin. Ranar ma ina mata wanka ne nake tambayar ta ina shafa bakin nace" Wai meke damun ki ne baby abakin ki?" Rau-rau naga tayi da idanu tamkar zata yi min kuka tana kallon cikin idanu na. Sai nace" Yana ciwo ne yanzu?" Kai ta girgiza min alamar a a still tana kallon cikin idanu na. Sai nace" Shikenan to..na 'karasa da fa'din" Kallon fa? Bana hanaki yi min irin kallon nan ba Baby...yana sa rashin kunya ki daina kinji Ammi na?" Kai ta 'dage min kawai alamar to. Allah sarki baiwar Allah ashe zuciyar ta magana ce a 'kunshe amma tana tsoron fa'di saboda garga'din Sani da kuma tsoron hantarar da zan mata akai...wallahi yau ka'dai nayi dana sanin tsangwamar da nake yi mata yafi sau hamsin cikin zuciya ta...wanda na tabbatar da na yi ta ne a kurarran lokaci. Ranar Baby bata iya tace da ni komai ba nima kuma ban sa komai aka ba har na kammala yi mata wankan... Damuwar halin da ubanta ke neman shigar da mu ne duk ya dame ni. Shima 'din da kansa yazo ya fara fahimtar rashin walwala daga Jasmine, dan idan ya dawo yanzu ba kamar da take walwala ba, amma sai yace ai dama yasan rashin kulawar da nake yi matan nan dole zai yi mata illah watarana, a fa'dar sa wai ai dan bana jan ta ajiki ne shiyasa take 'dan shiga damuwa kuma gashi shi baya nan, a lokacin har zama yayi yai min nasiha akan hakkin yaro da Allah ya 'dora akan iyaye...yace min kin hana kanki farin ciki kuma kin.kasa sanar dani abinda ke damun ki Nuree gashi kuma abin naki har ya shafi Baby, idan haka kika ce zaki cigaba da rayuwa Nuree dukkan mu hakan zai cutar mu ne". Cikin raina nace" Ai kaine ka ja mana". Kwantar da kansa yayi yai min nasiha wanda daga 'karshe ya 'kara da fa'din idan ban saki raina ba da Ammi zai ha'da ni ta min bulala. Dariya ma ya bani dan haka sai nayi murmushi kawai. Sosai na gamsu da baya nan sa amma ina damuwar dake cikin zuciyata ta ishe ni ta hana ni bada hankali na akan 'ya ta, ni kaina yanzu ba walwalar nake da ita ba balle in iya dawo da farin cikin Baby da take neman rasawa. Bazan manta ba wani hutu da su Baby suka yi a lokacin na so in dawo da jigilar Baby hannu na saboda na fahimci Sani ba mutunci ne da shi ba musamman da naga yanda yake yawan takurawa yarinyar da ke taya ni aikace-aikace abin sosai yake bani haushi, ga kuma baya dawo min da Baby gida akan lokaci 'karshe ma wai sai ya fara bata kyautar ku'di, wa'dannan dalilan su suka 'kara cire min shi a raina har na sanar da Yah Deen bayan wata tafiya da yayi Jos jinyar mahaifin sa, amma Yah Deen ya 'ki ya goya min baya dole Sani ya cigaba da aikin sa badan raina ya so ba. Haka muka cigaba da rayuwar mu kowa baida  walwalar kirki, har a lokacin Addu'ah ta be wuce Allah yasa 'karamar ala'ka ce tsakanin miji na da wannan Jiddahn ba, kuma na sani ko ba'a fa'da min ba nasan acan Abuja suka ha'du, kuma ai ina jin yanda ake labarin 'yam matan Abuja shiyasa tsoro da fargaba kullum 'kara hauhawa suke min cikin zuciya ta. Kwatsam watarana ina zaune sai gashi an 'kira ni da wata new number kamar bazan 'dauka ba ma sai kuma na 'daga, sallamar kirki bata yi min ba kawai ta hau yi min tuhuma akan miji na, wai sai na gaya mata dalilin da ya sa Mu'een yake ikirarin ni ka'dai na ishesa rayuwa har mutuwar sa, tace wani irin ri'ko nayi masa har haka da ko bayan idanu na ma baya iya kushe ni". Sosai naji haushin wannan rainin hankalin nata dan haka sai na nace da ita ta tambaye sa mana tunda saurayin ta ne ai zai gaya mata dalilin. Daga haka na yanke 'kiran ban 'kara sauraren komai ba daga gare ta. Allah ya sani naji babu da'di har raina dan har na fara tunanin bakin su 'day ne da shi, amma yanda ta bayyana min irin yanda nake da muhimmanci a wurin Yah Deen shi yafi komai yi min da'di har ma sai ya wanki takaicin 'kiran da ta yi min..kusan kowacce mace naso ta samu irin wannan matsayi wurin mijin ta, abu 'daya ne ni 'din na rasa shine cikakkiyar 'kaunar sa daya kasa bani ni ka'dai, sannan kafar da ya bari har wasu matan ke samun daman shiga tsakani na da shi shima yana bani haushi. Duk da haka ban bar 'kiran da Jiddah ta yimin ya zauna cikin raina ba dan ko da wasa ma ban sanar da shi ba, da kansa ya dawo yake bani ha'kuri akan maganar tare da yimin bayanin ala'kar dake tsakanin su, ban gamsu ba da bayanan sa ba sam domin nasan indai ba tana da wani marsayi a wurin sa ba da bazata ta6a samun daman ta6a wayar sa ba balle har ta bincika ta 'dauki pin 'dina ta kuma samu guts 'din 'kira na ta tuhume ni akan sa ba,  dole akwai wani abu da nasan ba zai iya sanar da ni ba... amma dole na sawa raina yadda da miji na na watsar da waccen batun. Cikin sa'a sai na ga duk ya dawo da hankalin sa wurin mu, ya kan 6ata lokaci sosai fiye da baya yana hira da ni, ya kan kuma dawo akai-akai ba kamar baya ba da yake 'daukan wata guda be zo ba, kuma ma sai na daina ganin 'kiran Jiddahn ko da yazo gida, sosai na saki raina na watsar da komai kawai na ri'ki karatu na kullum cikin raina da kuma salloli na nake addu'ar Allah ya kare min miji na ya shirya min shi ya dawo da hankalin sa gare ni. Sai gashi kwatsam rana tsaka ban zata ba ban yi tsammani ba kawai naci karo da wani mummunan abu cikin waya ta, Hafsat mijina yana aikata zina da wata macen da ban ma santa ba kuma aka 'dauka aka tura min dan na gani. Ya kike ganin zan 'dauki wannan lamarin Hafsat? Yah Deen da na 'dauki soyayyar duniya na 'dora masa na 'dauki duk wata kulawa ta na bashi amma da abinda ya saka min kenan ya munafurce ni ya 'dauki hankali na da kalaman sa 'karya ya kautar da tunani na akan halayyar sa ta hanyar nuna min zallar soyayya. Lokaci guda na fahimci Yah Deen ba zai ta6a canzawa ba, banga alamun zai iya canza halayyar sa ba, hakan yasa na yanke shawarar tafiya in barshi tafiya ta har abada, na riga na gama ji cikin raina cewar bazan ta6a samun cikakken farin ciki tare da shi ba illah ba'kin ciki a koda wani lokaci, yaushe zan rayu a kullum  idanuwa na na cin karo da abinda hankali na ba zai iya 'dauka ba kuma akan mijina, wallahi koda ace bana jin 'kaunar sa cikin raina dole zanji zafi ballantana Hafsat ina matu'kar son shi, ni da kaina bazan iya misalta miki irin 'kaunar sa dake raina ba. Na gama yanke shawaran rabuwa da shi,  tun a jiyan na so inyi tafiya ta domin lokaci yayi da zan fuskanci rayuwa ta in daina yaudarar kaina da sunan ina zaman soyayya da miji na, ko da rabuwa da shi zai illah tani na gwammaci hakan da acecin zauna hallayar sa ta yi sanadin kumburin zuciya ta,  amma sai aka samu akasi Baby bata dawo gida da wuri ba, hankali na gida-gida ya kasu, wanda ganin lokaci ya tafi sosai ne na nemi mayafi na na tafi har makarnatar neman ta amma babu labari, na yi tafiyar da tunda mahaifiya ta ta haife ban ta6a yin irin ta ba, nayi kuka kukan da ko lokacin mutuwar mahaifina ban yi irin ta ba Hafsat, da wanne zanji, na rasa farin ciki na tako wani fanni, bayan 'kuncin dake zuciya ta akan Yah Deen sai gashi wani babban al'amarin ya sake faruwa na rasa inda zanga Baby. Tamkar wata mahaukaciya haka nake jin kaina a lokacin, ta ya zan iya rayuwa babu Yah Deen babu Baby, Jasmine itace sanyin idaniya ta, na gama shirya mana yanda zamu rayu bayan bashi amma ko'ina naje bana samun cikakken bayanin inda zanga 'ya ta. Hankali na sosai ya tashi fiye da zaton ki Hafsat, ban ta6a sanin yanda ake jin zafin 'da a zuci ba sai jiya da na ga alamun rasa Baby zan yi,  domin kaf na bincika amma ba Sani ba labarin su shi da Jasmine...babu tunanin da bai zo raina ba dan gani nake tamkar Sani saida min yarinya yaje yayi. Daga 'karshe da wannan mummunan labarin naci karo Baby kwance wai ba lafiya a gadon asbiti. Hankali na ya 'dan kwanta da na ganta, saboda bata ji wani mummunan rauni ba kuma ganin nata koda cikin wani hali ne yafiye min ace ban ganta ba kwata-kwata. Abin takaici abin ba'kin ciki wai sai Safwan ke sanar da mu abinda ya so waka na koma ince ya faru, Sani ya raping min yarinya... Kuka sosai ta fashe da shi a wannan ga6ar yayin da tausayin ta duk ya mamayi zuciyar Hafsat. Hafsat bata ce da ita komai ba, domin abin kuka ne ya same ta da ya kamata ace ta zubda hawayen ta, ko case 'din Jiddah ka'dai ma ya kamata abarta tayi kuka akai ballantana abinda aka yiwa 'yar ta kuma Allah da ikon sa abin duk sai yazo mata cikin rana guda, ha'ki'ka wannan ba 'karamin tada hankalin ta zai yi ba. Da 'dauki tsawon mintina uku tana kukan kafin ta fara magana. " Zuciya ta tafasa take yi Hafsat duk da nasan da kaina ina da laifi cikin lamarin cuz da na bawa Jas cikakakken lokaci da natsuwar da zan zauna inji damuwar ta nasan da baza'a kawo wannan lokacin ba za'ayiwa tufkar hanci, amma duk da hakan nasan nawa laifin ragagge when it comes to halin Yah Deen, zato na komai ya wuce abaya, duk da nasan yana tare da Jiddah ahalin yanzun amma ban sawa raina cewar mummunan ala'ka ke tsakanin su ba sau da dama koran wannan tunanin nake yi cikin raina, ashe yaudaran kaina kawai nake yi, yau gashi da kansu suka tabbatar min da abinda suke aikatawa wanda nake da ya'kinin shine ya so faruwa da Baby. 'Kwalla ne masu zafi suka sake gangaro mata...ta sa hannu ta share su da wuri sannan ta cigaba da fa'din" Da kaina nake jin cewar rayuwa ta tazo 'karshe dan bazan iya da halin sa ba Hafsat, yaushe zan cigaba da rayuwa while ina ganin Baby da wani mummunan tabon da na tabbatar sakayyar halin mahaifin ta ce? Bazan iya ba sam, bani da hakkin kowa, in akwai ma sai dai ta Baby ka'dai amma rayuwar Yah Deen cike take da tarin abubuwan Allah wadai wanda nasan a duk lokacin da na kalli Baby sai na tuno da su, duk 'yammatan sa sai da yayi lalata da su daga 'karshe kuma ya guje su...Na tabbata da Yah Deen bai lalata rayuwar 'ya'yan wasu ba da 'kila Allah zai ji 'kaina ba zai 'dora min wannan abin ba, wata 'kil da Allah zai bawa Baby kariya amma kinga da yake alhaki ne sai da aka lalata ta aka 'daura mata wannan mummunar 'kaddarar...taya kike tuanin bazan yanke ala'kar da ke tsakanin sa da Baby ba? ta ya kike tuanin zan bar Baby ta cigaba da kallon sa matsayin mahaifin ta? Idan na yi hakan sam ban yiwa rayuwar Baby adalci ba...ta 'karashe da shashshe'ka mai cin zuciya. Cikin kukan tace" Dana sani nake ji masu yawan gaske Hafsat, dana sanin yadda da auren sa da nayi tun farko, da nasanin rayuwa da shi, haihuwar da nayi da shi da kuma cigaba da barin sa yana kusanatata bayan nasan halin sa.        Ji nake dama rayuwa ta bata kawo i yanzu ba nasan da duk hakan basu faru ba, 'kila da ko haihuwa da shi ma bazan yi ba, wallahi da nasan hakane da ranar da su Imrana suka zo da da kaina zan ro'ke shi ya barsu su aikata abinda ya kawo su koda kuwa hakan zai yi sanadin raina ne tunda dama burin sa kenan 'kila da yanzu labarin bai iso nan ba da duk hakan bai faru ba. " Da ya zama 'kaddarar ki kuma fa Noor? Haba dan Allah, kar ki bari tashin hankali ya gusar miki da tunanin ki mana, ina ilimin ki ina ha'kurin ki? Haba Noor ya zaki rin'ka fa'din maganganu tamkar baki san ciwon kanki ba? kar ki manta fa abar halitta ce ke, kinfi 'karfin Allah ya jarabce ki ne ko me? Hala kin manta cewa Allah yana tsarawa bawa rayuwar sa ne tun kafin zuwan sa duniya.." "Nasa ni Hafsat ban manta ba, amma har abada ni nasan wannan sakayya ce ba 'kaddara ba ce, Allah ne ka'dai yasan yawan rayukan da banzan halin Yah Deen ya cutar ya lalata kuma yayi dumping in su, wanda gashi kina gani 'karshe ya 'kare ne akan Jasmine, kuma wallahi har abada bazan ta6a yafe masa ba, kuma baby ma bazata yafe masa ba koda kuwa abu ka'dai da ya rage masa da zai sa asashi a aljanna kenan baza mu ta6a yafe masa cutar da zuciyoyin mu da yayi ba". Hafsat goshi ta dafe cike da damuwa da 'kuncin zuciya, sam bata san me zata sake fa'diwa Noor ba da zai kwantar mata da hankali...cikin hakan taji Noor 'din na fa'din" Babu yadda Alhaji Baba bai yi da shi ba, haka ma Ammi hadda Uncle Ja'afar amma duk ya watsar, an nuna masa illolin aikata zina, an gaya masa sakamakon mai yin ta, an kwatanta masa zabar da Allah yake yiwa mai aikata ta amma duk abanza after all ma da kansa yasan komai tunda yayi karatu dai-dai gwargwado amma ya take, ni dai nasan ban ta6a yi masa magana akai ba saboda banga fuskar hakan ba, amma ai nasan Ammi sun yi masa fa'da da kansa kuma shima 'din ya sani, kuma yasan dalilin hakan ne ya hana auren mu 'daukan hanya har yau amma ya share, ko Sani ma na sha nuna masa cewa halin Sani bai min ba amma yayi banza da magana ta ya cigaba da nunanwa Sani 'kauna ya bashi muhimman ci ya 'daukaka darajar sa sama da mai gadin gidan sa da tun zuwan mu Bauchi muke tare da shi...'karshe suka cutar min da yarinya, suka lalata min rayuwar yarinya...insha Allahu duk sai sunga sakayya domin Allah bazai bar su ba, zama da Yah Deen kam daga yanzu ya 'kare, mun bar rayuwar sa kenan har abada..zanje in rayu da yarinya ta in kula da ita da tarbiyar ta, zanyi 'ko'kari wajen ganin na goge duk wasu munanan tabo da yayi mata...ko babu shi tana da Alhaji Baba, tana da Saif ga Zaidu sannan ga ni ga Ummah ta da 'yan uwana mu ka'dai mun ishe ta ba sai da shi ba...daga yau matsayin _babu_ yake a wurin Baby insha Allahu...sai na mantar da ita shi da duk wani abu da ya shafe shi. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *75* Ha'kika Mu'een ya aikata son ransa a duniya ya manta cewar Allah yana hukunta mutum ne dai-dai da abinda ya aikata a duk lokacin da yaso, ya manta cewar tun a duniya Allah yake sakayya musamman irin wannan zunubin, Mu'een yaci mutuncin 'kauna, ya ci mutuncin yarda da kuma amana, ya zarafin aure 'karshe ya 6ige da yaudarar mahaifan sa ya 6oye musu asalin waye shi. Allah da kansa ya toni asirin sa wajen mahaifan sa amma duk da haka bai watsar da banzan halin sa ba...'karshe wa gari ya waya?..rayuwa sau'ki ne da ita sosai matu'kar ka tsarkake zuciyar ka ka sanya tsoron Allah a cikin ta, sa6anin hakan kuwa a kullum bazaka ta6a ganin dai-dai ba...Allah ka rufa mana asiri ka yafe mana zunuban mu badan halin mu ba". Hafsat ce ke wannan tunanin cikin zuciyar ta tana mai jin zafin abin, ga kuma Noor da ke kuka a gefen ta wanda tasan ko ita ce haka ya faru da ita abinda yafi kuka ma zata yishi domin wannan abin kuka ne, abin ba'kin ciki ne sosai, bata da bakin da zata furta wata kalma da take ganin zai taushi zuciyar Noor ko kuma ya hana ta zubda hawaye, to koma ta daina hawayen ai bata isa ta kankare tabon abin cikin zuciyar ta ba, domin kuwa a zahiri an zalunce ta iya zalunci, an ci mata fuska an kuma 'kunsa mata ba'kin cikin da har 'karshen rayuwar ta bazata iya mantawa da shi ba, ina ma laifin ace aure yayi ya cika gidan sa da mataye ta tabbata da sai yafi ma Noor sau'ki fiye da ji da ganin irin wannan lamarin. Sosai Yah Deen yaci amanar masu son shi, yayi wasa da tunanin su, yayi amfani da 'karfin soyayya duk ya yaudare su da ita ya lalata musu rayuwar su. Farko rayuwar *Rahma* yaso ya 6atawa tun tana cikin 'kuruciyar ta, sai Allah ya taimake ta ya bata kariya ta hanyar sako yayan ta cikin lamarin 'karshe Allah ya ha'data da miji mai so da 'kaunar ta duk da yasan cewa ga abinda ya so faruwa amma ya kawar da kansa ya aure ta ya zauna da ita da amana...yanzu haka tana nan da yaran ta biyu mace da namiji. 'Kaddara ce ta sake ha'da shi da *Husnah* na biyu wacce ta so shi da dukkan zuciyar ta, ta nuna masa 'kauna, amma shi koda wasa bai ta6a jin soyayyar ta cikin zuciyar sa ba, amfani yayi da hakan yayi rayuwa da ita irin wacce yake so ya maida ita tamkar matar sa batare da yayi tunanin makomar sa ba. Abu mafi muni da Allah wadai shine zubar da cikin da yayi mata wanda azabar Allah ce ke jiran duk mai aikata irin hakan, ya sani amma ya kawar da kansa. Mahaifin sa yaso aura masa ita amma Allah bai 'kaddara aure tsakanin su ba sai iyayen ta suka zo da batun aura mata 'dan uwan ta Hisham shi kuma 'kaddara ta ha'da auren sa da Noor batare da neman amincewar ta ba. Mu'een hakan duk bai ishe shi misali ba sai ma ya 'kara da cin mutuncin auren Husnah bayan iyayen ta sun aurar da ita, duk daraja irin ta aure amma hakan bai hana Mu'een sake shiga rayuwar Husnah ba tana kuka amma sam ya kawar da kai ga hawayen idanun ta, ya kasa fuskantar haukan da yake aikatawa saboda son zuciyar sa ya riga ya rinjaye shi..abin takaici ma cikin gidan da yake zama da matar sa ta sunnah nan ya kawo Husnah da sunan fasi'kanci batare da ko jin tsoron abinda zai biyo baya ba. Hakan bai ishe shi ba ya sake yin amfani da soyayyar da *Ma'u* take yi masa ya ya yaudare ta da soyayya ya 6oye manufar sa abayan rashin wayewar ta, 'karshe ya barta da guzurin cikin sa batare da ya nuna kulawar sa gareta ba har ta rasa rayuwar ta sanadin cikin da kuma tasku da 'kuncin rayuwa da ya jeta ciki. Duk yadda iyayen sa suka nuna masa 6acin ransu akan hakan amma ya basar ya rufe kunnuwan sa ya mantar da zuciyar sa nasiha da garga'din da suka 'dauki tsawon lokaci suna yi masa, abin mamaki da zuwan sa Bauchi ma sai da ya nemi *Yusrah* wacce ita ka'dai ce ya nuna ra'ayin sa gareta da karin kansa har suka 'kulla ala'ka irin ta soyayya, 'karshe suka 6ige da aikata zina a hotel a duk lokacin da bu'kaci hakan...itama rabuwa suka yi bisa tursasawar Safwan in badan shi bama 'kila da har yanzu suna tare da ita tunda gata can auren ya kasa yiyuwa har yanzun kuma still tana son shi ta kasa mantawa da shi. Hankalin Noor har ya kwanta bayan rabuwar sa da Yusrah kwatsam sai kuma ga *Jiddah* ta 6ullo bayan komawar sa Abuja...itama kuma duk abin 'daya ne....abubuwan Allah wadai da Mu'een ya aikata gaskiya suna da yawa sai dai fatan Allah ya yafe mu gaba 'daya...Har ga Allah Noor ba 'karamin ha'kuri tayi ba da cigaba da zama da shi ahakan bayan tasan duk 6oyayyan halin sa, sosai Hafsat ta jinjina mata, ita aganin ta koma me Noor tace zata aikata yanzu bazata hanata ba domin ya cancanci ko wani irin hukunci, Mu'een mutun ne da bai san bambancin hagun sa da daman sa ba, bai san halak da haram nada bambanci ba sam, bata ga alamun ya sawacransa akwai ranqr nadama ba sam baya hangen gaba baya tuna makomar sa wurin mahalicci, rayuwar duniya da jin'da'din ta kawai yasa agaba, in ba haka ba ace kana da mace kamar Noor a gida me zakayi da 'yammatan layi 'kazamai marasa kamun kai in ba son zuciya da neman 6atawa kanka daraja ba. A labarin da Noor ta bata ta fahimci Nanne ce ka'dai wacce ya so ta so na gaskiya, so mai tsananin gaske, domin ya so ta ne da dukkan zuciyar sa da tunanin zai aure ta watarana dalilin ta ya tafi karatun likitanci, amma da yake Allah baya barin wani dan wani sai bai barta da ranta ba ya kar6i abin sa tun kafin Mu'een ya kai ga cika burikan sa akanta...daga ita bai 'kara jin soyayyar wata cikin ransa ba sai Noor da a yanzu take kyautata zaton yana yi mata soyayya mai masifar zafi, ga dukkan alamu yana tsananin so da 'kaunar ta a yanzun, domin sosai yake respecting feelings 'din sa ta 6angaren ta, duk wanda yake tare da shi dole sai ya fahimci game da shi kuma ma ko shi da kansa baya 6oyewa. Amma idan tayi tunanin sai taga kamar gaskiyan Noor ne da tace Mu'een ba zai ta6a son ta ita ka'dai ba, cuz ko ni na kasa fahimtar dalilin da yasa ya kasa bibiyan wasu matan ya kasa barin mummunan halin sa duk da yake yana ikirarin Noor ka'dai ta ishe shi rayuwa, ako'ina baya 6oye tsananin soyayyar da yake yi mata?... A hankali Hafsat ta 'dago kanta ta dube ta cike da tausayawa da sanyin murya tace" Kiyi ha'kuri Noor, dan Allah ki fawwalawa Allah komai, nasan babu da'di, dole akwai ciwo sosai, faruwar irin hakan yana da mugun 'kuna amma tawakkali shi zamu sanya cikin rayukan mu saboda Allah na ganin komai. Ha'ki'ka Dr. bai kyauta ba, bai kyautawa ahalin sa dake 'kar'kashin inuwar sa ba, ya za6i son zuciyar sa ya manta da girman darajar da yake da ita, ya manta girman nasabar ba, ya manta cewa babban zunubi yake aikatawa 'karshe ya cutar da zuciyar ki mafi tsananin cutar wa...kiyi ha'kuri, kiyi ha'kuri Noor duk nima nasani ba'a kyuata miki ba amma kisani wannan ba shine cikakkiyar hujjar da ya kamata mu ri'ke bisa faruwar hakan ba balle har kice zaki tuhume shi da shi matsayin sa na uba mahaifi ga Jasmine, baki kyauta masa ba Noor, shi da kansa kinsan bazai ta6a son ganin faruwar hakan ga Baby ba. Idan kinji cikin zuciyar ki cewa an miki ba dai-dai ba fine zaki iya barwa Allah ki jira ha'duwar mu a madaka ta ki 'kara ninka ha'kurin ki akan na baya wanda kika da'de kina aikatawa, da kaina ma na baki lambar yabo kan ha'kurin ki Noor, amma a yanzun har ga Allah bazan 6oye miki ba kin tsawwala masa da yawa, 'karamin misali ma ki duba kiga halin da ya shiga wallahi sosai Dr. ya bani tausayi yau ka'dai, da wanne kike so yaji? shima fa abinda ya faru ga Baby yaji ciwon sa sosai musamman idan kika yi duba da yanayin da aka fita da shi daga 'dakin nan, da kanki kinsan shima 'din abin ya ta6a shi ba sai an gaya miki ba..tunda kinsan Jasmine 'yar sa ce 'ya kuma mafi soyuwa cikin zuciyar sa... Numfashi Hafsat taja dan ita kanta dauriya kawai take yi take neman kwantar da zuciyan Nuree ba wai dan tana goyon bayan Yah Deen ba, tana yin.hakan ne kawai dan sau'ke hakkin zamantakewa bai kamata ace ta bada nata gudunmawan wajen rushe musu farin cikin su ba...a hankali ta 'karasa maganar tata da fa'din" kuma kar ki manta fa Noor ko wani bawa yana da tashi 'kaddarar a zane, so me ze hana wannan in ma ki 'dauke shi a matsayin taki 'kaddarar?" Wani kallo Noor ta jefe mata sannan ta kawar da kanta gefe" Hafsat kar kiyi tunanin zaki tursasa ni in yafewa Yah Deen koka'dan banji zan iya yafe masa ba, kuma batun yanda aka fita da shi wannan duk ba damuwa ta bace matsalar sa ce, inyaso daga yanzu ya ha'diyi zuciayr sa ya ha'kura da numfashin ma ba ta yanda hakan zai shafe ni, inda yasan hakan ai da ya jima da tuba ya daina abubuwan da yake aikatawa da har kike ni zan 'dauke alhakin zunuban sa matsayin 'kaddara, hakkin wa na shiga a rayuwa ta? In ma akwai akwai wata 'kaddara da zan 'dauka ai babu wacce ta wuce na auren Yah Deen da nayi a duniyan nan? In ma akwai ni banganta ba sam, kuma har abada bazan ta6a daina danganta abinda ya faru da baby da shi ba domin shine sanadi". Tana fa'din hakan ta mi'ke cikin sanyin jiki ta nufi inda Baby take kwance...har a lokacin baccin ta take yi cikin kwanciyar hankali, yayin da Noor ke jin kanta tamkar zai zage biyu dauriya kawai take yi dayake tasan musabbabin sa a yanzu, burin ta bai wuce taga ta 'dauke 'yar ta daga garin Bauchi ba...wannan kawai shine Burin ta, taga ta nesanta Jasmine da Mu'een da duk wani abinda ya shafe shi. Safwan dake tsaye bakin 'kofa ne yayi gyaran murya gami da yin sallama ya 'karaso ciki, shima 'din wajen Baby ya nufa kansa 'kasa yake sake maimaita kalaman da yaji Noor na furtawa da zuwan sa kenan yaji tana tana magana shine ya 'dan tsaya yaji. Sosai yaji da'di da bai tarar da matar sa na zuga da sake aibanta Muceen a gaban ta ba, wanda ya tabbatar da ace wasu matan ne da sai sun fita za'kewa akan nuna rashin jin da'din su game da faruwar wannan lamarin. Erh yasan cewa tana da daman da zata aikata duk yadda taga dama ko dan ta samu sassauci ma a zuciyar ta saboda an cutar da ita an ci zarafin ta a zahiri, amma kai da kake tare da ita bai kamata ace ka 'kara hura mata wutar abin ba koda kuwa kasan cewa itace da gaskiya a lamarin in bazaka taushe ta ba kawai yi shiru yafi. Sam babu halacci cikin abinda akayi mata amma ya zama dole ka taushi zuciyar ta ko dan sau'ke hakkin zaman takewa ma. Ganin ya nufi wurin Baby ne ya sa Hafsat ma tayi saurin tasowa, duba ta yayi sannan ya waigo gare su wanda har alokacin babu wanda yace uffan tsakanin su, sai da ya juyo garesun ne kafin yayi magana Hafsat ta riga shi da jefa masa tambayar" Ya jikin nata?" Yace" Alhamdulillah ba laifi gaskiya". Yayi maganar yana sake juyawa ya Kalli Baby. Noor kam kallon sa kawai take yi tana so taji yace Babyn ta warke amma bata ji ya furta hakan ba. Idanun sa kan Hafsat yace" Har yanzu baku rintsa ba dare yayi sosai fa". Inda ya 'karasa maganar yana duba agogon dake 'daure a tsintsiyar hannun sa. Babu wanda yace da shi uffan a cikin su, sai ya 'dago ya maida kallon sa ga Noor cikin natsuwa yace" Madam kiyi ha'kuri fa dan Allah, ki sawa ranki cewar komai da ya faru ga bawa daga Allah ne, ki daina ganin kamar wai ko Mu'een shine sanadin hakan ta dalilin halayyar sa, ko kuma dalilin aminta da kuma yadda da yayi da drivern sa ne hakan ya faru duk ba wannan bane, duk mumini da kika gani idan mummunan abu ya faru da shi Allah ka'dai yake fara kawowa cikin ransa sanadin haka sai kiga ya samu damar furta kalmar _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ , dukkanin mu bayin Allah ne, ababen halitta ne mu, kuma bauta muka zo yi a duniyan nan, so kinga bamu fi 'karfin Allah ya jarrabe mu da duk abinda yayi niyya ba, ya kan iya 'daukan rai ma kuma dole a zauna ayi ha'kuri, Noor yanzu ina mahaifin ki? kin isa kice me yasa Allah ya kar6i ransa ne? Kin isa ki 'daurawa wani laifin barin sa duniya ne ko kuwa kin kasa rayuwa bayan bashi? Me yasa? Saboda ba ki da ikon yin hakan domin mutuwa da rayuwa duk daga Allah ne, lafiya da rashin sa ma duk nasa ne, amma me yasa kuma da ya gwada imanin ki ya jarrabe ki ta hanyar Baby sai kike jayayya kina nuna kamar imanin ki ya samu rauni Noor...yanzu inda ace Jasmine mutuwa tayi ta barki ya zakiyi? shima zaki ce Mu'een ne sanadi kenan? Na sani cewa akwai abubuwa da dama da muke aikatawa marasa kyau kuma Allah ya 'kyale mu ya dube mu da su har 'karshen rayuwar mu, amma Noor kisani bayin Allah masu sa'a ne ka'dai Allah kan waiwaye su ya fahimtar da su laifikan su tun anan duniya yayi musu hukunci in anyi dace sai kiga mutun ya nutsu ya gyara rayuwar sa ya koma ga Allah kafin wa'adin rayuwa ta tsaya musu...wannan masu sa'a kenan, wasun koda wasa basa samun damar yin hakan, Allah baya basu daman shiriya har wa'adin su ya tsaya 'karshe suyi mummunan 'karshe abin Allah shi kyauta. Dan haka ki gode Allah kawai Noor domin da rahamar sa ya dube ki ya dubi ahalin ki, kiyi tawassuli, ki kai kukan ki ga mahalicci, ki ro'ke shi da dukkan zuciyar ki inaga hakan ka'dai shine mafita, wanda 'kilan sanadin yadda da zakiyi da 'kaddarar da ta same kin sai kiga Allah ya sada ki da rahamar sa, amma yawan 'dorawa Mu'een laifin da kike yi sai kiga har ya jijjiga zaman imanin ki cikin rashin sani, domin zai zamane tamkar baki yadda cewa Allah buwayi bane kuma yanda yaso yake aikatawa ga bayin sa. Dan Allah Noor kiyi ha'kuri, nasan da ciwo, da zafi da 'kuna kuma wallahi dukkan mu mun jishi cikin jikin mu, duk da nasan bazai kai naki ba matsayin ki na uwa dole ne ki fimu nuna damuwar ki amma ya zamuyi? Fatan mu kawai shine Ubangiji Allah ya kiyaye mana gaba abinda ya faru kuma ya zame mana izna a gaba...akwai darasi babba da Allah ya 6oye kan hakan dan haka kiyi ha'kuri kinji? Ki kwantar da hankalin ki insha Allahu Baby zata samu sau'ki zata warke ta koma kamar baya ta rayu cikin farin ciki kamar kowacce yarinya". Jikin Noor sanyi yayi sosai bata iya ta furta komai ba illah hawayen da ta cigaba da sharewa a hankali ta koma ta zauna gefen Baby ta kafe fuskar ta da idanu. Ko tantama babu tasan tsagwaron gaskiya Safwan suke gaya mata amma taya zata iya sake duban Yah Deen da wata fuska mai nuna alamun bata jin haushin sa cikin zuciyar ta, how can i? Ta tambayi kanta, ta yadda yanzu kam ta barwa Allah, ta sawa ranta cewar abinda ya samu Baby 'kaddarar ta ce amma tsakanin ta da Yah Deen kam sam bazata iya ba, wannan 6angaren tana jin daga yau ya 'kare tsakanin su, idan ma tace zata iya sake amincewa zama da shi to tayi 'karya ta riga ta yanke shawaran rabuwa da shi, rabuwa kuma ta har abada...bazata sake rayuwa cikin 'kuncin zuciya 'kar'kashin inuwar auren wanda bai san kawaici da halacci ba, wanda baya iya bambance tsakanin masoyin sa da ma'kiyin sa, tunda biye biyen mata ya zabar wa kansa shikenan, rayuwar sa ce shika'dai amma bazata sake bari hakan ya illata mata zuciya ba, tun tana da 'kananun shekaru halin sa ya fara gasa mata zuciya har yanzun ta da ya kamata ace ta zauna ta rayu cikin farin ciki da mijin ta amma hakan ya gagare ta duk da tsananin so da take yi masa dole ta barshi, dole in barka kayi rayuwar ka yadda kake so Yah Deen..ni bani da kowa Kai kuwa kana da gata ta ko ina a rayuwar ka. Duk yanda Hafsat tayi fama da ita akan ta 'dan mi'ke ta huta amma Noor 'ki tayi, idanun ta 'kyam akan Baby tana kallon ta tana tunani cikin ranta. Tananan zaune har aka 'kira assalatu akayi sallah basu rintsa ba, Hafsat kanta ta kasa natsuwa, tausayin Noor takeyi sosai, dududu bazata wuce 22yrs ba amma abubuwa sun yiwa rayuwar ta 'kawanya, abubuwa masu girma kuma mafi muni cikin zu'kata. Shida saura Safwan ya fita da su Hafsat da Afrah ya kaisu gida, shima 'din yana so ne ya kimtsa ne ya sake fitowa dan baya so case 'din baby ya shiga hannun kowa saboda gudun ya'duwar maganar, kuma ma gashi yau ne yake sa ran za'ayi aikin cire hannun sani tunda an riga angama komai, Mu'een kam dama wannan ba layin sa bane wani likita ne daban ke kula da shi, kuma shima jikin nasa Alhamdulillah cuz kafin ya fito sai da yabi ya duba shi ya kuma ji da'di ya samu labarin numfashin sa ya dawo dai-dai saura kawai ya bu'de idanun sa ne, sosai Safwan yake so wannan ya kasance sirri a tsakanin su su ka'dai...wannan dalilin ne yasa shi jan kunnan Hafsat akan kar yaji labarin ta fa'da ko kuma yaji ance daga bakin ta akaji, har abada idan wannan maganar ya fito daga bakinta bai yafe mata ba. Dama ma ko bai fa'da ba itama batayi niyyan fitarwa ba, kuma yanda ya nuna damuwar sa kan Jasmine 'din sosai ya birge ta, domin in tace tasan kanta da zuciyar ta ai bata san wani ba, 'kila da wata dabance matar sa da maganar nan sai inda mai ya tsaya musamman dangin ta idan ta riga ta furta kuma zakiga cikin lokaci 'kan'kani maganan ya bazu ko'ina 'karshe azo anayi ma gorin da zai gigita tunanin ka watarana, wasu ma sai sunga yarinya zatayi aure sannan ake fara tone-tone ana nemo abinda za'a kushe ta dashi 'karshe a tono sirrin ka da kai kanka kama ka jima da mantawa da shi, ko kuma ace kai baka san shi ba, musamman ma sirri irin wannan da tasan cewa in anyi dace zuwa gaba Baby na iya mantawa da shi sai dai iyayen ta ne abin zai kasance cikin rayukan su har abada. Da fitar su sai Noor ta koma wajen Baby Jas ganin tana 'dan motsawa, gefen ta ta kashingi'da, a hankali ta sa hannu tana shafa kanta tana tunanin rayuwar ta gaba 'daya, siraran hawaye ne ke zubo mata suna sau'ka kan hannun ta da ta tallafi kanta da shi, kallo 'daya zaka yi mata ka fahimci cewa cikin mawuyacin hali take a lokacin. Yanzu Jasmine ka'dai ke bata tausayi, tasan bazata ta6a iya duban ta bataji zuciyar ta ya karye ba, saboda a kullum kallon wacce aka zalinta zata yi mata...Allah sarki rayuwa, jiya ka'dai duk wani farin cikin su yayi musu 'kaura, har abada bazata ta6a iya manta ranar ba kamar yadda ta kasa manta ranar da idanun ta suka gane mata Yah Deen kwance da wata.... " Mummy"! Taji sassanyan muryar Baby ya yanke mata tunanin ta wanda tayi maganar tamkar ba itace ake jinya ba, da sauri Noor ta kalle ta ta sakan mata murmushi tare da gyara zaman ta da kyau wasu 'kwallan na sake kwaranyo mata amma bata damu ba, cike da kulawa ta amsawa Baby da fa'din" Na'am Ammi na...ya jikin naki? kina jin wani ciwo ne yanzu?" Instead Jas ta bata amsa sai tace da ita" Mummy ina Daddy na? waye ya saki kuka mummy? Anjima zan gayawa Daddy ya rama miki kinji?". Murmushi ta sake yi ta shafo kanta idanun ta cike da 'kwalla tace" Baby ai Daddyn ki bai damu da kuka na ba...kuma kar ki damu zan daina kukan yanzu kinji? Buri na in ga kin sami lafiya kin warke sumul Mama na..." Baby kam idanu ta zuba mata har ta gama maganan da take yi sannan ta sake fa'din" Mummy ki daina kuka...". Tsigar jikin ta taji.ya tashi sosai da jin muryar Babyn har ma bata san lokacin da ta kam bakin mayafin ta ta share hawayen da shi ba, tanajin wani nason zubo mata amma ta ri'ke cikin idanun ta ta hanshi zubowa. Sake rankwafowa tayi ta ha'da kanta da na Jasmine sannan tace" Kina so mutafi gida ko Baby na?" Kai Baby ta girgiza mata alamar a a sannan a hankali da sanyin murya tace" Ni ba da ke zanje ba.." Idanu ta 'dan gwalo tana duban ta tana murmushi tace" Dagaske baza ki je da ni ba Mamana?" dage sama tana 'dan tura baki tace" Erh Mummy ni wajen Daddy nake so inje". " A a Daddy ai baya nan, can fa zamu tafi, can wurin Maman Daddy da Baba Alhaji ko baki so?" " Inaso Mummy". Ta bata amsa tana murmushi. Noor ma murmushin ta 'kara yi sannan tace " Yauwa yarinta, sai in dinga kaiki makaranta acan da kaina ko?" Jasmine kanta ta 'dage sama alamar Erh. Goshin ta Noor ta sumbata tana mai fatan Allah ya bata lafiya cikin gaggawa su tattara su bar garin Bauchi bari na har abada. Tayiwa kanta al'kawari daga ranar da aka sallame su da tabbacin baby ta samu lafiya to daga ranar bazata sake yadda ta kwana cikin garin ba balle gidan sa..." Mummy fitsari zanyi". Taji muryar Baby ta fa'di hakan tana 'dan motsa hannaun ta. Dum zuciyan Noor ya tsinke da 'karfin gaske, musamman da ta tuno abinda ya faru da Baby...tun jiyan kuma Allah da ikon sa batayi fitsari ba ko dan bata sa komai acikin ta ba ne oho. Ta shi tayi ta cicci6e ta tana yi tana kulawa dan kar ta ta6a mata 'kananun ciwukan dake jikin ta wanda aka lullu6e da farin bandage. Haka ta kaita bayin ita kanta tunani take yi cikin ranta, da girman ta ma ranar first night 'din ta ta ci azaba musamman in zatayi fitsari ballantana Baby dake 'yar 'karama bata san komai ba, she wish ana transfer na ciwo da wallahi tuni ta janye wannan azabar daga Babyn ta. Kawar da tunanin tayi cikin ranta afili ta furta " Baby zaki iya fitsarin kuwa ?" Ai kuwa Jasmine da ke rungume da 'kafar Noor kasa tsaguno tayi dama tsayuwar ma da 'kyar ta taka da Noor da kawo ta bayin haka ma yanzun kuka kawai ta sanya tana fa'din" Mummy ciwo 'kafa na". Dole yasa Noor rungumanta sosai jikin ta tana jin wani 'daci na taso mata a zuciya, Allah ya isa kam har 'karshen rayuwar ta bazata daina ja musu ba. Rigar ta ta tattare zuwa sama a tana tallafe da ita, a haka daga tsayen tace da Jas tayi fitsarin..ai kuwa ta kasa, dama ga ta sam bata so abu ya ta6a lafiyar ta amma da yake sosai take jin fitsarin haka tayi shi tanayi tana kuka tana fa'din" Zafi, mummy zafi ki samin ruwa fitsarin ciwo mummy..". Jasmine na kuka itama Noor 'din na hawayen tausayin ta har ta gama fitsarin nata. Tunani tayi da kanta taga dacewan yi mata amfani da ruwan 'dumi, da yake private hospital ne so suna da komai, heater ta kunna ruwan yayi 'dumi ka'dan da dabara ta samu ta sata ciki har tayi mata tsarkin suka fito har a lokacin Baby kuka takeyi sosai gwanin tausayi. Kwantar ta Noor ta soyi amma Jasmine ta'ki kwanciya, 'kam'kame Noor tayi tana mai cigaba da kukan ta. Sun 'dauki tsawon lokaci a hakan kafin ta sami damar kwantar da ita cikin natsuwa ganin cewa ta daina kuka a lokacin illah ajiyan zuciya. Sam ba ta son ganin cikin idanun Baby a yanzun hakan yasa ta ringa kawar da kanta saboda tsananin yanda take tausayin Baby cikin ranta. Wiper dake gefen ta ta mi'ka hannu ta 'dauko ta fara goge jikin Baby da shi domin ba damar ta watsa mata ruwa saboda bandages 'din dake wasu sassa na jikin ta, lokacin da tazo dai-dai cinyar ta kuwa tsayawa tayi tana sake kallon gaban Jasmine 'din, yanda ya kumbura har yanzun bai sa6e ba gashi yayi ja ka'dan, wani abu taji yana taso mata dangin ba'kin ciki da takaici take ta girgiza kanta kawai ta cigaba da abinda take yi zuciyar ta na harbawa. Sai da ta kammala goge mata jikin kafin ta sake dawo da hankalin ta wurin, hannu ta kai a hankali ta ta6a sai baby tace" Ish...Mummy zafi yake min fa...Sani ne ya min tsarki mai zafi shai ya jimin ciwo a wurin... Mummy ki rama min kinji?" Sabbin hawaye taji suna gangaro mata, a hankali tace da ita" Kiyi ha'kuri Mama na ni bani da ikon rama miki amma nasan Allah da kansa zai miki sakayya akan duk wanda ya zalunce ki kinji Baby na?" Jasmine kanta ta 'dage sama alamar" Erh". Noor sai a lokacin ta iya sakin jikin ta, tana shafa kanta tace" Baby..." Kallon ta Jasmine tayi batare da ta amsa ba. Itama bata damu ba kawai ta cigaba da fa'din" Dama Sani ya ta6a yi miki irin tsarkin nan shine baki ta6a gaya min ba ko?". Kai ta girgiza mata sannan tace" A a Mummy..yau ne kawai ya min tsarkin kuma ai Mummy ban yi fitsari a school ba". " Bai ta6a saka miki hannu a wandon ki ba?" " Erh Mummy...kullum baki na kawai yake cinye min idan ya 'dauke ni a cinyan sa sai ya 'dora ni akan wani abu, kuma yace kar in fa'da ma kowa hadda Daddy ma". Tana jin ciwon abin cikin zuciyar ta amma dole ta danne saboda tana taji komai, tana so tasan ta inda ya kamata ta fara dawo da tunanin Jasmine ya zam dai-dai irin ta yara. Dan haka sai ta ha'diye duk abinda takeji. Rufe mata jikin ta tayi zuwa cikin ta da abinda ake lullu6e ta da shi sannan ta sake dawo da hannun ta kan Baby tana shafawa tace" Baby na...kullum kuma Sanin yake 'dora ki a cinyar tasa?" Kai ta 'dage sama. " Kuma har yake cinye miki bakin naki kullum?". Da yake bata da wayo sai ta 'dage kanta sama alamar Erh tana mai turo baki gaba. Noor sai tace " Shiyasa ashe nake ganin bakin naki wani iri amma ai Baby idan na tambaye ki 'kin gaya min kike yi". Shiru Jasmine tayi tana kallon idanun mahaifiyar tata...ganin.hakan yasa Noor fa'din" Ko tsoro kike ji idan kin fa'da min kar in do ke ki.." A a Mummy ai Sani yace kar in fa'da miki da Daddy, kuma ai Mummy kin hanani surutu ko..." Rintse idanu Noor tayi wani mahaukacin suka taji cikin zuciyar ta, ha'ki'ka ita da kanta tasan ta aikata hakan, a lokacin da take tsaka da damuwar Yah Deen, sosai ta tsani wata damuwar kuma shiyasa take hana Baby yawan yi mata surutu, amma bata ta6a sanin cewa babban kuskure ta aikata ba sai yanzun da lokaci ya riga ya 'kure mata bayan anyia rayuwar 'yar ta Babbar illah. Ha'kika tayi babban asara tayi sake a rayuwar ta ta tafka kuskure, kuskure mafi muni da ya kaita ya baro, bata ja Baby ajikin ta ba saboda rashin natsuwa gashi wanda take abin domin san ma bai san tana yi ba, bata ci wata riba face 'karin takaici tunda gashi abinda idanun ta ya sake gane mata a karo na biyu. Bata ta6a jin dana sani irin na yau, ji taka da tasan wannan 'kaddarar na tafe cikin rayuwar su da wallahi mantawa zatayi da soyayyar Yah Deen ya tayi jifa da batun makarantar ta ta dan kawai ta bawa Baby kulawar da ta dace, amma ina ba dama, da kanta ta hana kanta sauraran surutan Baby, ta 'ki.janta ajiki balle taji damuwar ta, ta 'ki warewa kanta lokacin da ya kamat su zauna da Baby su sha'ku ganin cewa ta samu soyayyar mahaifin ta a dili shikenan tayi watsi da nata 6angaren, ba ta wani damu ba tunda aganin ta ai tana son.abin ta tunda ta haifa so ba sai ta nuna mata kulawar zahiri ba, a ganin ta yanda suke rayuwa a hakan ya wadatar bata san ashe abubuwa da dama ke cikin zuciyar yarinyar ba, da ya ha'du da garga'din sani kuma sai ya kasance ko Yah Deen 'din ma bata iya sakewa ta sanar da shi halin da take ciki ba. Bu'de idanun ta tayi akan fuskan Babyn a fili ta furta" Yah Allah ka yafe min, ka yafe min cin amanar da na yiwa rayuwar Jasmine. Ha'da idanu suka yi da Baby sai ta 'danyi mata murmushi sannan ta tataro dauriya ta sanyawa muryar ta a hankali" Daga yau Duk wanda ya sake yi miki abu ko wani iri ne ko zagin ki mutum yayi kizo ki fa'da min kinji Baby..bana sake fatan faruwar wani abu amma ko hannun ki mutun ya gwada kamawa kizo ki gaya min kinji Mama na". " Sani yace zai yanka min ciki na da wu'ka idan na fa'dawa Daddy". " Kar ki damu ba ruwan ki da su Sani yanzu, bama ganin ki zai sake yi ba insha Allahu, ni zaki na gayawa duk abinda akayi miki kinji ko?" " Toh Mummy...amma kice kar ya yanka min ciki na nima". Murmushin 'karfin hali tayi mata gami da jinjina mata kai tana shafo fuskar ta. Tana nan tana jan Baby da surutu har gari yayi haske ma'aikata suka shigo suka yi aikin su bayan sun yi mata ya jiki tsaf suka gyare wurin kafin suka fita. ***** 'Bangaren Safwan kuwa bai dawo da wuri ba dan ko daya gama abinda yake ma sai da ya jira Hafsat ta ha'dawa su abin kari kafin ya fito a gidan, daga nan kuma sai ya biya gidan Mummy (mahaifiyar sa) ya sanar da ita abinda yake faruwa kafin ya 'karaso asibitin. Mummy kam hankalin ta tashi yayi sosai, duk abubuwan da ke faruwa ko 'daya bata da labarin su sai yanzu da Safwan ya biya ya gaya mata...haka suka rabu da al'kawarin itama yanzu tana tahowa, Allah sarki Safwan duk da take matsayin mahaifiyar sa amma bai fito fili ya sanar da ita ainahin abinda ya faru ba, ya dai ce mata ne kawai Jasmine na asbiti sun samu accident jiya ita da drivern ta amma bai gaya mata abinda Sani yayi mata ba. 'Karfe takwas da mintina kafin Safwan ya dawo asbitin inda yazo musu da sa'kon Hafsat kan cewa itama anjima ko zuwa yamma zata dawo. Sai da ya duba Baby yayi mata abinda ya dace kafin ya fita bayan ya sanar da Noor abinda zatai mata, warm wata yace ta sanya ta ciki na 'yan mintina saboda kumburin jikin tan, sai Noor tace da shi ai ta sanya ta ma tun 'dazun har tayi fitsari ma. Take ya nuna farin cikin sa gami da godewa Allah cikin ransa da irin kulawan da Noor tayi da Baby, shaf ya mance ne kafin ya tafi bai sanar da ita hakan ba, da yake ma bai shige ta ba so ba bu'katan sai anyi mata aiki a hankali in ankula komai zai daidaita. Da gama wannan tunanin ya fita ya basu wuri dan su samu daman sanya abu a cikin su. Tea mai kyau Noor ta ha'da musu sai da ta bawa Baby sannan itama ta sha, dukkan su bawani abun kirki kuwa suka shaba cuz cup 'daya da ta ha'da musun ma sai da ya rage basu shanye ba. Comment Vote Share *Salmern ku ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *76* Safwan da barin inda suke 'din sai ya nufi 'dakin da aka kwantar da Deen, shi ka'dai ne 'dakin sai na'ura da aka sanya masa a hancin sa, hannun sa kuwa canular ne da tun jiya aka cire drip 'din da aka jona masa bayan ya 'kare. Ko motsi baya yi amma kuma idanun sa gefe da gefe hawaye ne ke bi a hankali, hakan ne ya tabbatar masa da cewa Mu'een ya farka daga suman da yayi... _Alhamdulillah_ ya furta a fili yana me 'karasawa bakin gadon. Hannu yasa ya cire masa abin hancin tare da zama gefen sa yana 'kiran sunan sa cikin natsuwa, bai amsa ba haka kuma bai bu'de idanun sa ya dubi Safwan ba illah hawayen sa da suka cigaba da tsiyaya sai dan wannan karon cikin turereniya wani ke bin wani. Ko ba'a fa'da masa ba ya san zuwa yanzun kowa ya tsane sa, kowa ya riga ya san mugun halin sa da ke 6oye...kunyar Safwan yake ji mafi tsananin kunya, domin Safwan ba sau 'daya ba ba sau biyu ba yake yawan yi masa tuni akan illar Zina, Safwan sosai ya so yaga rayuwar gidan sa ta daidaita ko dan yadda da yayi da natsuwar Nuree yake kuma bata wata daraja ta daban, amma duk ya watsar da shawarwarin Safwan ya cigaba da rayuwar sa yanda yaga dama. Ganin bai tanka shi ba sai aikin hawaye da ke bin gefen idanun sa ya sanya Safwan furta" Haba Mu'een manta ko kai waye kayi ne, me yasa zaka dinga zubda hawayen ka har haka? Cuta ai ba mutuwa bace Insha Allahu ba abinda zai sami Jasmine...bu'de idanun ka inyi maka wani albishir.." Ya 'karashe maganar yana murmushi. A hankali Mu'een ya bu'de lumsassun idanun sa ya sau'ke su kan Safwan dake zaune gefen sa, yun'kurawa yayi da niyyan tashi Safwan sai yayi saurin taimaka masa ya zauna da 'kyar yana dafe 'kirjin sa da hannun daman sa. Bai iya ya kalli Safwan cikin idanu ba, fuskar sa gefe cikin muryar da daka ji zaka fahimci cewa yana jin jiki yace "...Safwan Allah yasa albishir 'din Nuree ta yafe min zaka yi min...kuma kace min Baby na tana lafiya". Hannun sa 'dayan Safwan ya kamo cikin nasa da alamun rarrashi yace da shi" Ka kwantar da hankalin ka please, kai fa namiji ne, 'karfafa musu gwiwa zakayi Mu'een ba wai kaima ka tashi hankalin ka ba". " Dole hankali na ya tashi Safwan, da kanka kasan ni ne silar komai, ni na jawa Baby wannan abin, 'kila da ban kasance mahaifinta ba da hakan ba zai faru da ita ba.. gaskiyan Noor ne, gaskiyan ta ne da take neman cire ni daga rayuwar su, ha'ki'ka ban kasance abin alfahari a gare su ba...i wish mutuwa nayi Safwan da ace Baby ta taso da wannan tabon agaba na ina ganin ta da shi zuciya ta bazata iya 'dauka ba Safwan..." Ya 'karashe da sakin kuka mai tsuma rai irin wanda bai ta6a yin irin sa ba..kansa ya kwantar bisa hannun Safwan ya cigaba da kukan sa. Safwan kam shiru yayi shi kansa idan ka ganshi duba na farko zaka fahimci a matu'kar tashe hankalin sa yake. Hannun sa 'daya ya 'daga ya 'dora a kan Yah Deen tamkar wani yaro 'karami da ake shirin lallashi, a hankali yace da shi" Kayi ha'kuri, abin ba da'di kam amma babu yanda zamu yi, u have to bear that pain Mu'een, ko ba komai yanzu nasan zaka fahimci abinda na da'de ina nuna maka a baya game da rayuwa, nd ka kwantar da hankalin ka Baby na nan lafiya haka Noor ma..yanzu haka ma na baro su ne zaune Baby zata ci abinci". Murmushi yayi mai ciwo yana jin zafi cikin ransa, ko shi da kansa ya tsani kansa tunda ya kasance silar rugujewar farin cikin gidan sa..kuma ko Safwan bai fa'da ba yanzu kam ya san irin ciwon da ake ji idan aka lalata rayuwar wani naka, Hayat ya tuno, yanda hankalin sa ya kasa kwanciya bayan ganin da ya yi masa da Rahma 'kanwar sa, hankalin Hayatu bai kwanta ba sai da ya tabbatar da ya aurar da Rahma tukunna. Ma'u Malam Barau kam da kansa ya san ba 'karamin 'kunci iyayen ta suka shiga ba musamman mahaifin ta, dan sosai yayi 'ko'kari wajen ganin ya kula da tarbiyar ta amma duk ya 6ata masa shirin sa, abu mafi muni da mahaifinta ya fara cin karo da shi shine cikin da take 'dauke da shi, yasan wannan ba 'karamin tada hankalin sa yayi ba. While a lokacin shi bai wani damu ba, da yake bai san yanda ake cin abin ba haka yayi watsi da Ma'u Alhaji Baba ka'dai ne ke kulawa da rayuwar ta har ta rasa rayuwar ta sanadin cikin. Sai gashi Allah cikin ikon sa shima ya bashi haihuwa, haihuwa kuma ta 'ya mace wacce ta kasance mafi soyuwa cikin zuciyar sa fiye da komai, daga 'karshe ya jarrabe shi da abu makamancin wanda ya jima yana aikatawa akan 'yar sa, yasan Allah yayi hakan ne badan komai ba sai dan kawai ya nuna masa nasa ikon ya kuma sawa shima ya 'dan'dani 'dacin da ake ji akan duk yarinyar da aka 6atawa Rayuwa, Yah Allah ka yafe min.... 'Dago kansa yayi a hankali da jajayen idanun sa yace " ...Ina so inga iyali na Safwan, inaso inga Baby, ina so in ro'ke ta ta yafe min alhakin ta da ke kaina, amma tsoron Nuree nake yi tace ta tsane ni bata son gani na, tace in fita daga rayuwar su, please Safwan help me..." " Is okay...ya isa haka nan Mu'een be a man mana, ka daina yin abu tamkar mace please, Baby ma ta yafe maka ka daina damun kanka dan Allah". " Ni dai ina so in gansu, inaso in rungumi Baby a jiki na.." " To shikenan ka kwantar da hankalin ka zaka gansu amma ka bari sai zuwa anjima ka'dan idan ka samu 'karfi sai in kaika wurin su kaji, Nuree ma ta sakko yanzu kuma inada ya'kinin zata yafe maka itama insha Allahu ". Kallon Safwan yake yi har ya dasa aya a maganar sa, sai da ya lumshe idanu ya bu'de kafin ya tambaye shi " Sau nawa Nuree tazo ta dubani anan Safwan?" Shiru yayi bai kamar mai tunani cuz rasa amsan da zai bashi yayi, bai san zai tambaye sa hakan ba kwata-kwata, dole dan ya sake kwantar masa da hankali ya 'kirk'iro 'karya yace masa tazo sau 'daya amma a lokacin bai farka ba". Komawa yayi da bayan sa ya kishingi'da yana murmushin takaici a hankali yace..." Nasan halin Nuree sosai Safwan, Nuree na da taurin kai da kafiya, nasan ko mutuwa nayi da 'kyar ne ta min.duban Rahama bazata ko kula gawa ta ba tunda ta tsane ni sosai yanzu..." Idanun sa ya mayar ya rufe su tare da cije la66an sa daga gefe" 'Kirji na zafi yake min Safwan ina jin tamkar rayuwa ta 'kare ne, farin ciki na yazo 'karshe, 'kilan ma bazan sake kallon Baby ba, bazan sake kallon Nuree na ba har abada..." Safwan hannun sa ya sanya cikin nashi zai yi magana sai Yah Deen ya riga shi da cigaba da fa'din" Alhaji Baba, Ammi na dan Allah Safwan kace su yafe min nasan suma idan suka ji labarin abinda ya samu Baby tsanata zasuyi hadda Uncle Ja'afar, Safwan dan Allah ka kula min da iyalina ka basu farin ciki...ka...". Kasa 'karasawa yayi saboda wani suka da yaji a 'kirjin sa, hannun sa dake cikin na Safwan ya dam'ke da 'karfi while 'dayan hannun san still na nan saman 'kirjin.sa saitin zuciyar sa. Numfashi mai 'dumi ya furzar yayin da Safwan ke faman jera masa sannu cuz ya fahimci sosai yake jin jiki.." bari in 'kira Dr." Safwan ya fa'di cike da kulawa. Dauriya yayi ya 'dan bu'de idanun sa tare da cire hannun sa daga cikin na Safwan a hankali ya yun'kura ya kwantar da kansa da kyau...Da kansa ya tsani rayuwar sa yanzu, shi kansa baya so ace ya cigaba da rayuwa saboda bai san da wani idanu zai sake kallon Baby ba matsayin sa na mahaifin ta da ya kasa bata kulawar da ta dace ya kasa tanadar mata kyakkyawan 'kaddara yayi silan rushewar farin cikin ta dana mahaifiyar ta mafi tsananin takaici cikin zuciya. Fita Safwan yayi ya 'kira likitan dake kulawa da shi, ko da suka dawo kuma sai suka tarar baya 'dakin kansu duk ya kulle yayin da hankalin Safwan yayi mummunan tashi, kafin ya dai-daita tunanin sa suka gansa ya fito daga bayi, wani ajiyen zuciya Safwan ya sau'ke, bai tanka su ba ya wuce ya zauna bakin gadon sannan ya kalli Safwan yace masa" Zanyi Sallah". " Ok" Safwan yace tare da fita ya tafi sauri-sauri gudu-gudu ya 'dakko masa dadduma daga office 'din sa. Suna nan zaune har ya idar da dukkan sallolin dake kansa tun na jiya har na yau, ya jima yana addu'ah sannan ya shafa. Duk yadda likitan yaso sake duba shi Yah Deen 'kin amincewa yayi yace shi kam ya bar shi ya riga ya warke...key 'din sa da wayar sa yace su bashi Safwan ya 'dakko ya mi'ka masa ya kar6a amma bai kunna wayar ba saboda baya son a dame shi a halin yanzun. Dole haka suka ba dan sun so ba suka barshi ya nufi hanyar fita bako takardar sallama.😀 Safwan ne ya bishi abaya yana ro'kon sa akan kar yayi driving, yace ko yasa a sau'ke shi a gida ya girgiza masa kai, da 'kyar yake tafiya daka gansa zaka fahimci yana jin jiki amma a hakan ya cigaba da tafiya, 'dakin da su Noor suke ya nufa ga mamakin Safwan sai yaga bai yi gigin shiga ciki ba ta window ya tsaya yana 'kare musu kallo yana murmushi ganin kamar bakin baby na motsi tana yiwa Noor magana, yayin da ta kwantar da kanta gefen na Babyn tana shafa kanta. Sanyi yaji har cikin zuciyar sa, tare da godewa Ubangiji...haka kawai ya tsinci kansa da son ganin su, yaso wannan hirar ta kasance da shi amma ba dama ya riga ya yiwa kansa babban katanga tsakanin su, sam bai ga laifin Noor bisa hukuncin da ta yanke masa ba, fiye da hakan ma yasan ya cancanci ayi masa. Yana daga wurin ko jin abinda suke fa'di baya yi amma sai sakin murmushi yake yi lokaci zuwa lokaci kuma yana share hawayen tausayin su. Cikin ransa ya ayyana indai hakan shine farin cikin ku Nuree har abada bazan 'kara takura muku ba, ni kece farin cikina haske na da walwala ta amma tunda kin za6i rayuwa ba ni, kin za6i in barki in fita daga rayuwar ku, nayi al'kawarin bazan sake takura muku ba bazan sake shiga rayuwar ki ba Nuree...". Girgiza kai Safwan yayi ganin yanda Mu'een ke uban zubda hawaye, sosai yake jinjinawa wannan lamarin da har ya isa sa mutun irin Mu'eenuddeen zubda hawaye, abu mai girma ne zai iya sa hawayen sa sau'ka... dai-dai lokacin da wayar sa ta 'dauki ringing yana dubawa sai yaga mahaifiyar sa ce, 'dauka yayi yace" Kar dai har kin iso Mummy?". Deen baiji mai aka fa'da daga 'daya 6angagaren ba sai gani yayi Safwan ya fara faciya yana fa'din" Gani nan nan zuwa yanzu". Saurin barin window in Yah Deen yayi ya ha'da bayan sa da jikin bango yana sakin numfashi, sosai ya gaji da tsayuwan numfashin sa har sama-sama yake yi amma saboda jin da'din ganin su da yake yi a hakan.ya daure ya cigaba da tsayuwa. Ahankali ya bar wurin ya fara tafiya hanyar da yasan bazata ha'da shi da Safwan ba yabi ya koma parking space na asbitin ya bu'de motar sa da tun jiya take a wurin ya shiga ya 'dage duk gilasan motar ya kwantar da kansa idanun sa a lumshe. Idan baka sani ba bazaka ta6a tunanin da mutun acikin motar ba, duk yayi hakan ne kuma dan kawai ya kaucewa ha'duwa da Mummy, sosai yake jin kunyar ta, nawin ha'da idanu yake yi da ita..zaton sa ko itama tasan abinda ya faru ne shiyasa yayi hakan, dan yasan babu wanda zai goya masa baya, shi da kansa ma yasan shi mai laifi ne, bai ta6a sanin akwai ranar da zaiji da kansa ya tsani kansa kamar yau 'din nan ba. Safwan ne yayiwa Mummy jagora har zuwa 'dakin da suke, sosai ta tausayawa baby ganin halin da take ciki tare da fatan Allah ya basu lafiya gaba 'dayan su, koda ta nemi duba Sani driver sai akace mata ai shirin shiga thearter room ake yi da shi sai dai in sun fito, sosai Mummy ta tausayawa lamarin nan ta zauna suna 'dan ta6a hira da Noor. Koda wasa kuwa bata yi gigin sanar da ita gaskiyan lamarin ba tunda tasan babu maganin da fa'dan zai yi mata. Mu'een kam kwantar da kujera yayi ya mi'ke ganin kamar hakan zaifi masa, jira kawai yake yi wa'adin sa ya cika, dan gani yake tamkar ba shi da wani amfani yanzu, so ma yake mutuwa ta riske shi kafin ha'duwar sa da mahaifan sa cuz ya san 'kwayar zarra na sassauci ba zai samu daga wurin su ba, kwatankwacin tsanar da yayiwa kansa haka yake tsanar Jiddah ma, domin itama.ta bada babban gudunmawa wurin tunzira zuciyar sa Nureen sa. 'Kirjin sa ya dafe a hankali ya fara tariyo tun farkon ha'duwar sa da Jiddah.... _Comment_ _Share_ _Vote_ *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *77*              Wata shida kenan yanzu da fara aikin sa a Abuja amma tun ranar zuwan sa na farko 'kaddara ta ha'da shi da Jiddah, motocin su ne suka yi sanadin ala'kar su. Tafe yake yana 'dan hanzari ya isa inda ke gaban sa yayin da ita kuma ta taho da zafin kanta na 'yan matan ci ta wani 'kwama tabarau a fuskan ta kana ganin ta kallon farko zaka san cewa sosai Naira ta zauna a jikin ta ga kuma wani ji da kai cikin yanayin ta. Cikin rashin sani ya gogi jikin motar ta a kan Junction da zai shigar da shi cikin unguwa while ita kuma tana fitowa. Nan take kuwa ta fito cike da masifa tana wani huhhura hanci ta tunkaro shi, saurin dakatar da ita yayi da fa'din" kiyi ha'kuri please kuskure ne". Yayi hakan ne dan ya gaji a lokacin sam baya san gajiya ga shi ga dukkan alamu kuma ba ha'kuri ne yarinyar ba, ba ya so abin yayi tsayi sam. Harara ta banka masa sannan ta juya cikin takun ta na isa ga kuma 'daukan hankali tana tafe take mitan" Mutane sai su dinga abu kamar basu da idanu..." Baiji mai tace ba dan shi daga cikin motar yake bai fito ba amma duk da hakan bai sha wahalar fahimtar 'kananun mitan da take yi ba. Sai da ya bi bayan ta da kallo sama har 'kasa ya ta6e baki kafin ya juya gami da mi'ka hannun sa ya ciro wasu ku'da'de dai-dai tana shirin bu'de nata motan ta shiga yace" Baki ji ba...". Waigowa tayi ta dube shi hannun sa 'daya na kan stairy shima ya zuba mata lumsassun idanun sa sannan yace" Idan da matsalar babba ce ga wannan Please ki kai a duba miki motar..." Yayi maganan tare da  mi'ka mata ku'din da ke hannun sa wanda zasu kai kimanin 20k. Fasa bu'de motan tayi ta zuba mishi idanu harda har'de hannuwa a 'kirji zuciyar ta cike da takaicin wannan rainin hankalin, gani tayi kamar tunda take ba'a ta6a ci mata mutunci irin wannan ba, sai ta rasa me yake ji da shi da har yake tunanin ita Jiddah zata ansa ku'din hannun sa saboda wannan dalilin. Tana daga tsayen bata ko motsa ba illa 'kan'kance idanu da tayi, kwata-kwata ma bata san ma amsar da ya kamata ta bashi a zahiri ba. Da kansa ya fahimci ya bata haushi musamman yanda yaga ta tsaya tana yi masa kallon _ka rena min hankali_...gira ya 'dan 'dage sama tare da duban hanya yace" Ga dukkan alamu baki bu'kata...ko? Anyway kiyi maza ki bar kan hanya ni sauri nake yi akwai abubuwa agaba na". Yayi maganar yana maida ku'din sa inda ya ciro su tare da yiwa motar sa key yaja yayi gaba abin sa batare da ya ko sake duban inda take ba. Jiddah kam binsa tayi da idanu har yayi nisa sosai ya 6acewa ganin ta, cikin ranta ta ayyana" Ni kuma ga maras abin yi mana dan ka raina min hankali.." Sosai ya 'kunsa mata ba'kin ciki cikin zuciyar ta, yayin da a wani 6angaren kuma taji ya matu'kar birge ta sosai ya tafi da imanin ta...haka itama taja motar ta tama fasa fitan kawai ta koma gida. Lokaci zuwa lokaci take sakin tsaki da 'kyar ta samu ta manta da lamarin cikin ranta. Ha'duwan su na biyu a shopping mall suka ha'du, wanda ya kasance kwanaki takwas bayan ha'duwar su na farko, itace ta fara gane shi ai kuwa sai ta matsa kusa da shi ta tari gaban sa. Idanu ya waro yana duban ta da mamaki sam ya kasa yuno inda ya santa but her face looks familiar to him. Murmushi tayi sannan ta tace" Seems like baka gane ni ba". Kansa ya girgiza mata alamar " Yes". Sai tace" Last week mun ha'du a junction...".bata 'karasa ba yayi murmushi   tare da fa'din" Awwn..waccen mai masifan ko?". Murmushi ta sake yi masa sannan suka gaisa  tamkar sun san juna, tare suka zagaya suka yi shopping 'din su yazo ya biya suka fito, kafin su rabu sai da suka yi exchanging number shikenan tun daga ranar suka 'kulla abota. Ta kan yawaita 'kiran sa taji lafiyar sa haka shima tun ba ya tuna 'kiran ta har ya fara 'kiran ta da kansa suna gaisawa. Sau tari ta kanje har asbitin da yake aiki musamman saboda ta ziyar ce shi, amma Mu'een bai ta6a zuwa gidan su ba, bai ta6a binta wani wuri dan kawai gana ba...in kuwa ya taho Bauchi hankalin ta sam baya kwanciya ta ringa damun sa da 'kira kenan tana tambayar yaushe zai dawo. Wasu lokutan har haushin ta ke kama shi amma baya nuna mata, sau tari idan ta 'kira shi sanda yake gida sharewa yake yi sai ya bari idan ya   fita masallaci ya tsaya yayi 'kiran ta...baya ta6a yadda yayi waya da mace cikin gidan sa matu'kar yana Bauchi. Wasa-wasa abu makamanciyar soyayya ta fara 'kulluwa tsakanin su, sai ya zama na ma Jiddah har gidan sa take zuwa masa ziyara batare da wata damuwa ba. Takan yawaita zuwa masa musamman a weekend ko kuma idan ya tashi daga aiki har girki tana yi masa watarana sai tace yau ya huta bazai yi take away ba. Shi kam bai damu ba idan tayi cin abincin sa yake yi ya bishi da ruwa. Ya kan lura da ita idan yana yin waya da iyalin sa fuskar ta na 'dan canzawa, bai ta6a furta mata kalmar so ba shiyasa shima baya sa fushin nata aka duk kuwa da cewa ya gama fahimtar inda ta dosa amma shi matsayin abota ya ajiye ta har a lokacin bai canza ba. Sakewan da tayi da shi ya sa bata ko shayin yin wasu abubuwan agaban sa, da yake ma bai ta6a bayyana mata asalin waye shi ba, shiyasa bata san halin sa ba bata san cewa yanda ta saki jiki da shi 'din ya fara canza masa tunani akanta ba. Musamman ranar duk da tazo har tayi masa girki kafin ta bar gidan sai ta watsa ruwa, sannan ta sake shiryawa ta tafi. Sosai yayi 'ko'karin kawar da zuciyan sa agare ta amma ya kasa, shai'dan ya riga ya mamayi zuciyar sa tunda da da'dewa, to wanda ma basu saki jiki da shi ba yana iya neman su balle wacce ta kawo.kanta har muhallin sa...ni dai nace Allah ya kyauta. Jiddah bata ta6a sanin kuksure take aikatawa ba sai watara rana da tazo tayi masa girki, girkin ma mai sau'ki tayi cuous-cous ne da sauce 'din kifi, yayi yayi da ita ma akan ta huta abinta kar tayi amma ta dage tace sai da tayi...a fa'dan ta wai tausayin sa take ji ai tasan bai ci komai ba cuz ranar tasowan sa daga aiki kenan shine tazo. Ai kuwa ta shiga wanka ta fito tana 'daure da towel a jikin ta ta zauna gyara make-up 'din ta bata ankara ba kawai sai ganin shi tayi ya shigo yana binta da mayatattun idanun sa idanun sa masa rikita zuciyar mai rauni. Wani shu'umin kallo yake binta da shi wanda yasa ita da kanta ta fahimci cewa ba lafiya yake ba, take ta rikice jikin ta ya fara rawa bayan fahimtar dalilin kallon nasa tasan bai wuci dan ya ganta cikin wannan yanayin bane tunda tasan bai taba shigo mata a irin wannan yanayin ba, bama ya ta6a kallon ta a hakan ba sai yau, domin kullun idan zatayi shirin ta a palour yake zama kuma baya shigowa har ta kammala ta fita, yau 'din ma bata san mai ya shigo da shi ba. Barin kwalliyar tayi ta taho da sauri da niyyar 'diban kayan ta ta sitirce jikin ta amma ga mamakin ta sai taji shi a bayan ta har tana iya jiyo hucin numfashin sa kusa da ita. Kafin tayi wani yun'kuri har ya kamo waist 'din ta ya matsa kusa da ita tare da juyo da ita ta fuskance shi. Jikin Jiddah rawa ya fara take ta fara 'ko'karin jan jikin ta daga nashi dan sosai ta rikice da yanayin nasa a lokacin amma sai ya 'ki sakin ta. Tana shirin yi masa magana yayi saurin dakatar da ita ta hanyar sau'ke bakin sa saman nata ya fara kissing 'din ta kamar ta sa shi...dole hakan ya tilasta mata yin shiru illah mutsu-mutsu da take yi amma ta kasa 'kwatan kanta dan ya riga ya kewaye ta da hannayen sa biyu. Tunda take a rayuwar ta babu wanda ya ta6a ko kwatanta yi mata irin hakan ko da wasa..shiyasa lokaci guda tsoro ya mamayi zuciyar ta ta fara hawaye tana tsoron mai kuma yau Allah ya ha'da ta da shi. Jiddah na da kyau tana kuma da kyawun jiki dai-dai misali, ga ta da iya tsara kwalliya amma bata ta6a ganin irin wancan rayuwar matsayin abin birgewa ba...ta gama.tsara rayuwar ta ne dai-dai da tunanin ta, bata ta6a kawo faruwar irin hakan tsakanin ta wani wanda ya kasance ba mijin ta ba sai gashi yau 'din ta kawo kanta da 'kafar ta wurin wanda bama ta da tabbacin da soyayyar ta cikin ransa. Jiddah na da rashin ji da rashin kunya amma iya nan ta tsaya bata da wani hali na daban da za'a iya kushe ta da shi, duk kuwa da yake a shekarun ta na ashirin da uku ne a lokacin amma sosai abinda yake yi matan ya zame mata ba'kon lamari. Dalilin kenan da ya sa ta 'kara rikicewa domin yana kissing 'dinta ne yana kuma yawo da hannun sa saman bom bom in ta. Jiddah kam bata san lokacin da kayan dake hannun ta suka kai 'kasa ba, da 'karfi ta samu ta 'kwaci jikin ta daga gare shi ta ja baya ta juya daga barin kallon sa tana sau'ke numfashi sama-sama kamar wacce tayi tseren gudu. Cikin zuciyar ta take ja masa Allah ya isa...A fili kuwa da rawar murya batare da ta dube shi ba tace" Mu'een Please...kar sake yi min wannan abin ban so ni.." Da yake baya ta juya masa sai bata san har ya sake zuwa kusa da ita ba kawai sai ji tayi ya rungumo ta baya tare da kwantar da kansa saman kafa'dar ta. Matsawa tayi da sauri cike da firgici take duban sa idanun ta duk sun canza launi saboda tsoron abinda yake shirin yi mata, matsawa ta sake yi sai ta ji bayan ta ya ha'du da bango, cak ta tsaya tana duban sa tana girgiza kanta a hankali hawaye ya fara bin kuncin ta gwanin tausayi. Shi kam takowa yayi ya dawo gaban ta ya tsaya tare da sata tsakankanin hannayen sa biyu ya matsar da kansa kusa da nata har a lokacin bai furta mata komai ba. Jiddah kam mamakin sa ma sai ya hana ta motsi, musamman yanda taga idanun sa duk sun canza sun koma wani abu daban, cikin ranta take mamakin halin sa, ashe dama haka yake bata sani ba...ha'ki'ka tayi kuskuren yadda da shi tun farko, ba ko wani mutun bane abin yadda a wannan zamanin. Duk duk kyautatawan ka a gare shi baya ta6a shayin ya cutar da kai. Bata ankara ba tana cikin tunanin sai ji tayi ya sake 'dora bakin sa saman nata, a lokacin kam bata hana shi ba cuz shai'dan ya 'dan shiga zuciyar ta ka'dan sai tayi tunanin ko a iya hakan zai tsaya wata'kila iya abinda zai mata kenan, dan har a lokacin tana ji cikin ranta cewar shi 'din ba haka yake ba bazai iya cutar da ita ba dan sosai ta yadda da halin sa na zahiri. Bata 'karashe tunanin ba taji hannun sa ya sau'ka akan saman shafaffen cikin ta bata ma san lokacin da towel 'din ya sau'ka 'kasa ba tsabar ru'danin da ta shiga. Kusan zaucewa tayi sakamakon hannun sa da taji cikin pant 'din ta harma bata san lokacin da ta sau'ke ajiyan numfashi ba, shi kam jin hakan sai ya 'kara masa 'kwarin gwiwa yayin da ya kai hannun sa sosai a 'kasanta yana yawo da shi. Jiddah kam komai ya tsaya mata yayi cak, da kanta tasan kuskure ne ta bar shi da jikin ta amma duk da haka sai take sawa ranta tunanin 'kila daga wannan shi kenan zai barta bazai zarce 'ka'ida ba, duk abinda taji yayi mata sai ta rin'ka sake masa jikin ta da tunanin may be iya nan zai tsaya bazai zarce ba. Da hakan ta ta yaudaran kanta har  bata san lokacin da ta sake masa jikin ta gaba 'daya ba, shi kam shagalin sa yake yi batare da damuwar komai ba. Yanayin yanda yaga take bu'de mai 'kafafu ya sa shi raba bakin su dan a ganin sa ya riga ya samu dama daga gareta ne,  sau'kar da kansa yayi saman shoulder 'din ta zuwa wuyan ta yana sau'ke mata hucin numfashin sa har ya kai zuwa boobs 'din ta ya fara wasa da shi da bakin sa. Jiddah kasa motsawa tayi saboda yanda taji ya zautar da ita, da kanta ta 'kara ban'kara masa 'kirjin ta hadda lumshe idanu, the next inda ta tsinci kanta shine kan bed 'din sa ya cigaba da aika mata sa'konnin sa masu shiga jiki sosai ta sake masa jikin ta gaba 'daya dan duk ya fitar da ita a hayyacin ta ta manta wace ita, ta manta cewa ba kalmar soyayya ko guda tsakanin sa da ita balle batun aure, ta manta tsawon lokacin da ta 'dauka tana killace kanta batare da ta bawa wani damar ra6an ta, ta manta cewa haramun suke aikatawa wanda yake fishi da masu aikata shi. Bata tashi dawowa hayyacin ta ba sai lokacin da taji masifaffen azaba daga 'kasanta na zafin shigan ta da yayi, a lokacin ne tafara kuka tana regretting tana tsinewa begen da yasa ta zuwa gidan sa tun ranar farko. Kuka sosai take yi tana ro'kon sa ya ya 'kyale ta amma bai ko kula ta ba, ko ajikin sa bai damu da kukan nata ba balle hakan yasa shi sarara mata har sai da ya biya bu'katar sa tukunna kafin ya barta. Har a lokacin kuka take yi, tana kuma sau'ke numfashin azaba tare da ja masa Allah ya isa, tana kuma tuno asalin dalilin ma da yake kawo ta inda yake tun farko, ga shi ya kaita ya baro, ya cuce ta ya gama da rayuwar ta ya 6ata mata tsarin da ta yiwa rayuwar ta tsawon shekaru, ashe mugu ne shi mazinaci mai cutan 'ya'yan mutane mayaudari mai fuska biyu. Duk cikin ranta take wannan tunanin yayin da take Allah wadai da ranar da ta fara ha'duwa da shi. Sa'a 'daya da ta yi a ranar ya kula da ita, ya kuma bata pain relief dan kar ciwon ya dame ta har ma da injection ya mata na flushing mahaifa, da yake ya fahimci cewa shine ya fara shigan ta shiyasa ya lalla6a ta amma ko da wasa bai ji 'dar cikin ransa ba. Ranar da 'kyar ya samu Jiddah tayi shiru ta daina kuka bayan ya cika ta da za'kin bakin ai babu komai babu ma wanda zai gane in dai ba ita ta fa'da ba. Har mota ya rakata inda ya 'kara da fa'din idan bata so agane ta daina kukan da take yi, Jiddah tana kuka ta tafi gidan su, tayi sa'a kuwa babu wanda ya fahimci halin da take ciki, dan sosai ta daidaita yanayin tafiyar ta ta nutsar da fuskar ta hatta mahaifiyar ta bata fahimci halin da take ciki ba domin babu abinda ya canza daga yanayin ta illah muryar ta, shima 'din sai tace ai ta gaji ne sosai shiyasa kuma sun je asbiti da wata 'kawarta taga marasa lafiya abin tausayi shiyasa tayi kuka. Mahaifiyar ta kam bata 'karyata ta ba dayake tasan halin Jiddah da tausayi. 'Bangaren zuciyar Jiddah kuwa abin mamaki duk abinda Mu'een yayi mata bai sa ta ji haushin sa ba koka'dan illah ma tsayuwa a ranta da ya sake yi, hatta abubuwan da yayi mata ranar ta kasa mantawa da su, da kanta sai ta ringa sakin murmushi sosai kuwa hakan ya 'kara rura mata wutar 'kaunar sa a zuciyar ta. Ko daga baya da ya 'kira ta dan jin ya yanayin jikin ta ma sai yaji ta 'dauka kuma bata yi masa wani complain ba, da ya tambaye ta halin da take ciki tace da shi bata jin komai. Sai yace" Da kyau ai dama nasan ke 'din da musamman ce". Murmushi kawai tayi masa bata ce komai ba. Kwanan ta uku kafin ta warware sosai amma she is there telling him that bata jin komai. Bata dai sake gigin  komawa gidan sa ba amma kullum yana cikin ranta kuma suna ba laifi. Sai da aka kusan yin sati biyu yaga shiru bata zo ba kuma.bai ji ta saka ranar zuwa ba kafin ya fara yi mata 'korafi. Jiddah ko da wasa bata nuna masa 6acin ranta shiyasa ma har ya samu damar da zai sake bayyana mata wata bu'katar tasa inda ace ta nuna masa kukskuren sa na tabbata da sai yaji shakkan sake tunkaran ta da wani banzan zance. A hakan da 'kyar ya sake lalla6a ta ya samu tazo dan wai ita tsoro ta ke ji shiyasa...tun daga lokacin kuwa ya maida Jiddah tamkar matar sa duk lokacin da ya bu'kaci ganin ta da ya 'kira ta zata zo ta same shi. Zuwa yanzun ta riga ta saba da shi da irin  rayuwar da suke yi. Burin ta 'daya ne kawai a yanzu shine taji ya amince da batun auren ta amma ya'ki sam, duk yanda ta fito fili ta nuna masa ra'ayin ta akan son auren sa amma ya'ki bata ha'din kai a kullum muhimmancin matar sa yake nuna mata shiyasa ta 'kullaci Noor sosai a zuciyar ta gashi bata iya yin fishi da shi...maimakon ma taga laifin sa kan batun a a da haukar ta sai ta 'dauki laifin kacokam ta 'dora akan matar sa, tsanar ta sosai take ji cikin zuciyar ta dan ita aganin ta itace ka'dai ta kasance shamaki a tsakanin su baya ga haka da tasan babu abinda zai hana shi auren ta. Bata san cewa shi bai ta6a saka rai da auren duk yarinya ya nema a waje ba, gani yake har abada bazai iya auren macen da yasan ta kafin aure ba. _Yah Allah, Yah Rahman, Ya Ubangiji ka tsare mana imanin mu kasa mufi 'karfin zu'katan mu, Yah Allah ka raba mu da sharrin masu rusa tarbiyya masu lalatawa iyayen mu farin cikin su da suka gina shi tsawon shekaru" Ameen Yah Rabbal Alameen🙏..._ Yasan cewa ba komai ne yasa Jiddah 'kiran Noor a waya ba face rashin amincewa da batun auren ta da yayi, amma ko anan ma ya matu'kar jinjinawa Nuree, jinjina mai girman gaske, domin ko alama bata nuna masa ba na cewar wata ta 'kira ta saboda shi ba, balle akai ga ta furta masa da bakin ta, shiyasa a kullum yake 'kara bata wani babban matsayi na da muhimmanci na daban cikin zuciyar sa,  soyayyar ta a kullum sake ratsa shi yake yi, ba zai ta6a iya ha'da soyayyan Nuree da kowa ba a fa'din duniyan nan, shi dai barshi ya hole yaji da'din rayuwa in a waje ne amma babu batun aure kam ya gama sawa cikin ransa cewar Nuree ta ishe sa rayuwa, ko shayin fa'dar hakan ba ya yi ga kowa wanda yake kyautata zaton dan hakane Jiddah ta tanadi wannan Videon dan kawai ta tunzura zuciyar Nuree akan sa, ta muzanta soyayyar dake tsakanin su, ta wargaza tubalin ginin 'kaunar sa dake cikin.zuciyar Noor. Zaton Jiddah ko Noor bata san asalin halin sa ba, ta 'dauka duk a munafurce yake komai...bata san Noor mace ce da ko wani namiji yake burin samun irin ta ba, da kansa yasan ba wayon sa bane ya bashi Noor matsayin mata face ya bashi ita ne kawai saboda yaji 'kansa, Noor mata ce ta rufin asiri abin so ga kowa. Shi kansa ma bai san mai yasa ya nemi Jiddah ba tun farko, yasan lokacin da ya nemi Yusrah laifin Nuree ne bayan ya yiwa kansa al'kawarin zama da ita ita ka'dai cikin ko wani irin hali amma daga baya Nuree sai ta fara gudun sa tana gudun bu'katun sa, shikuwa mutun ne da baya da juriya ta wannan fannin hakan yasa ya karyawa kansa al'kawari,  amma Jiddah kam yasan son zuciyar sa ne kawai ya kaisa gare ta ba komai ba, sharrin shai'dan ya ja shi ga kusantar ta, gashi ta kai shi ta baro shi, ta kunna masa wutan da yasan kashe shi zai matu'kar wahal da rayuwar sa, tunda har yau Nuee ta iya duban tsaban idanun sa ta gaya masa magana son ranta yasan cewa ha'kurin ta ya 'kare ne, sosai ya kaita bango ta yadda shawo kanta zai yi masa wahalar gaske...sosai yake jin haushin Jiddah da ma shi kansa gaba 'daya. A ganin sa Jiddah hauka tayi ba komai ba, dan shi ko ma mai zai faru bai ga abinda zai sa ya aure ta ba, abu mafi muni da ta aikata masa shine ba'kanta zuciyar Noor da tayi, hakan matu'kar ta6a shi, bata san cewa Nuree itace mutun na farko da zata iya bada shaida akan 6oyayyan halin sa da ba kowa ne ya san shi da shi ba amma ta ruaf masa asiri, itace mutun na farko da ta ganshi da mace ra'ayil ain kuma ta rufe maganar duk da hakan ma kuma ta 'kara ha'kurin zama da shi har ta haifa masa Baby sanyin ransa. Wa'dannan dalilan ka'dai aganin sa sun isa susa ya ji tafi kowacce muhimmanci agare sa, bazai ita6a iya ha'da ta da kowa ba dan ta cancan fiye da hakan ma...matar sa mai ha'kuri ce, kawaici da sanin.ya kamata, baya tunanin har abada zai sake yin sa'an samun irin ta cikin mata...'kaunar da yake mata shi da kansa bazai iya misalta shi ba, a yanzu bashi da burin da ya wuce ya faranta mata koda kuwa hakan na nufin 'karshen rayuwar sa ne. Cikin ramsa yake jin cewa matu'kar ta za6i rayuwa babu shi a yanzu  yayi al'kwarin barin ta, ba zai matsa mata ba, ba zai sake tilastata zama da shi ba koda kuwa shi 'din hakan na nufin cutar wa agare shi..koda zai rasa rayuwar sa yayi wannan al'kawarin for the first time zai sata farin ciki madadin farin cikin da ta sashi abaya, zai barta da Baby kamar yanda ta bu'kata amma kafin hakan yana so ya sake ganin Babyn sa, yana so ya sake neman yafiyar Nuree ko zai yi sa'a ta yafe masa.     Yana so ya gaya mata cewar ba da yaddan shi Jiddah ta tura mata wancan Videon ba, sam bai isa ya 'karya ta batun  kusantar Jiddah da yayi ba dan yasan Nuree tasan halin sa zai aikata fiye da hakan ma dan haka ba zai sake yi mata 'karya ba...amma ta sani cewa ba da sanin sa Jiddah ta tura mata ba. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *78* Zaune ya tashi yana kallon 'dai'daikun mutane da ke wucewa lokaci zuwa lokaci wasu na shiga yayin da wasu ke fita, kowa fuskokin shi na tafiya ne da yanayin sa, idan yaga mutun na farin ciki sai yaga kamar shi bashi da damuwar komai ne, ji yake dama ace shine yake wannan farin cikin, yayi Allah wadai da rayuwar sa yafi a 'kirga, idan ya tuno Baby kawai sai ya rintse idanu, tausayin yarinyar yake ji sosai. Yasan da ace tasan halin sa zai iya ja mata wannan abin da ko abaya ma bazai samu ko quartern 'kauna daga gare ta ba, amma yarinyar sosai take ji da shi matsayin sa na mahaifi agare ta amma bai yi wa rayuwar ta adalici ba sam...Allah sarki Mama na, ki yi ha'kuri, ki yafewa Daddyn ki ba dan ya na da wanna matsayin sa ba.         Dishi-dishi yake gani idanun nasa zogi sosai suke yi masa, kansa ciwo ga kuma 'kirjin sa dake barazanar tarwatsewa...shi ka'dai yasan me yake ji a jikin sa...banda yafiyar Ubangiji babu abinda yake iya furtawa. A duk lokacin da ya tuno ta'asar da ya tafka a fili zakiji ya furta _Astaghfirullah_ ...lokaci- lokaci yake furta hakan tamkar zautacce. Ya 'dauki tsawon lokaci a ahakan kafin ya koma da kansa ya kwantar...ya cigaba da danasanin rayuwar sa kaf. *****       Misalin 'karfe sha 'daya da rabi su Alhaji Baba suka iso, duk neman da Safwan yayi wa Mu'een cikin asbitin amma bai gansa ba, yayin da hankalin mahaifan sa ya 'kara tashi sosai fiye da ganin Jasmine da suka yi da halin da take ciki. Tsoron su kar wani abin ya same shi a inda babu wanda ya sani dan tun jiyan Safwan ya sanar da su halin da shima yake ciki..shiyasa hankalin su ya kasa kwanciya. Yayin da Safwan kuma ke fargabar kar mahaifan nasa suga kamar bai ri'ke musu amana bane cuz Jiyan a hannun sa Alhaji Baba ya mi'ka ragamar komai a fa'dan sa wai kafin su iso. Sai gashi sunzo in kuma babu Mu'een babu alamar sa. Ammi kam kuka sosai take yi dan harga Allah hankalin ta bai kwanta ba, gashi sunzo kuma suna tarar da jikin Baby yayi tsanani, ko ganin ta da kyau ma basu samu daman yi ba aka fito da su waje likitoci biyu Safwan da wata Nurse suka tsaya akanta...shikansa hankalin rabe yake gida biyu ciz yasan duk inda Mu'een yake to cikin wani matsanancin hali yake. Jikin Baby sai rawa yake yi ga wani zazzafan zazza6i da ya taso mata lokaci guda, takan 'dan fizgi jikin ta lokaci zuwa lokaci kamar mai razana da wani abu. Noor ma kuka kamar ranta zai fita, haka ma Ammi da abin ya zame mata biyu ga rashin ganin Mu'een ga kuma jikin Baby da yayi tsanani, tasan jinyan Baby ne ya tashi hankalin Mu'een shiyasa yayi nesa da inda suke, dayake tasan irin 'kaunar da yake mata, duk wanda yasan Mu'een to yasan irin soyyayar dake tsakanin sa da Jasmine ba na wasa bane, wanda ko wani irin hali ya shiga saboda ita ba abin ayi mamaki bane, gashi tasan yanda yake fama da ciwon sa idan ya motsa masa sosai hankalin ta ya tashi ta kasa natsuwa, Alhaji Baba ka'dai da Mummyn Safwan sune masu 'dan natsuwa har ma suke iya basu ha'kuri...Noor ma ba'a cewa komai. Safwan na gamawa da Baby ya fito ya 'kara kwantar musu da hankali da tabbacin komai zai daidaita da iznin Allah sannan yayi gaba dan shima zuwa lokacin hankalin sa ya tashi sosai, har gida yaje ya duba amma bai tarar da Yah Deen ba, sam ya rasa ina ya tafi a ina zai same shi, gashi kuma motar na nacan a Parking space cikin asbitin inda ya ajiye tun jiya anan take bata motsa ba. Hanyar office 'din sa ya nufa yana tunanin a ina ya kamata ya neme shi, da shigan sa sai ya 'dago wayar sa ya gwada 'kiran layin Yah Deen Amma shiru bata shiga. Tunowa yayi da lokacin da Yah Deen ya kar6i wayar sa da key 'din motar da safe a wurin sa. Fita ya sake yi cikin sauri da wani tunani a ransa...Addu'ar sa Allah yasa hasashen sa ya kasance gaskiya. Yana zuwa jikin motar Yah Deen 'din sai ya tsaya yana duban motar ko.zai ga alamun mutun a ciki amma baiga wani alama ba saboda tinyed glass in dake lullu6e da motar. Motar da ya siyawa Baby na zuwa makaranta ce dan tashi na Abuja yayin da ta Noor kuma na can ta zama wani abu sanadiyyan accident 'din da akayi da ita jiya. Gwada bu'dewa yayi amma yaji a kulle, dum.zuciyar sa ta tsinke tsoro y kama shi, in dai akace Mu'een ba yanan to ina ya shiga? Ya tambayi kansa. Bashi da tabbacin yana ciki amma sai ya 'kwan'kwasa da fatan Allah yasa yaga an bu'de masa. Yah Deen tsayawa yayi yana 'kare masa kallo daga cikin da yake, bai so zuwan sa a wannan lokacin ba sam. Safwan cigaba yayi da 'kwan'kwasaw yayin da Yah Deen yayi luf ko motsin kirki bai yi ba balle asaka ran zai tashi ya bu'fe masa. Safwan kam cire rai yayi da tunanin yana cikin motar har ya juya ya fara tafiya inda yake 'daga 'kafar tasa da 'kyar. Jasmine ce ta fa'do ransa sai yayi saurin yun'kurawa ya kaiwan hannu da fatan zai samu jin da'd'dan labari daga bakin Safwan game da iyalan sa. A hankali ya bu'de motar wanda yayi dai-dai da waigowan Safwan sai yayi arba da shi yana duban sa da lumsassun idanu, kallo 'daya zaka yi masa ka tabbatar ba lafiya yake ba. Wani ajiyan zuciya Safwan ya sau'ke cike da farin ciki ya dawo baya yana furta _Alhamdulillah_ a fili, gaban sa yazo ya tsaya yana duban sa yace" Haba Mu'een me yasa kake haka ne wai? Baka tunanin halin da iyalanka.zasu shiga saboda rashin ka? wallahi ka tashi hankalin mu sosai babu inda ban nemeka ba amma na rasa ka har gidan ka naje..ga can su Alhaji ma sunzo Ammi duk damu kasa tana can tana ta kuka a banza..." Jin sunan iyayen sa cikin maganganun Safwan 'din ne ya sashi saurin sako 'kafafun sa waje ya fito tare da kulle motar. Bai jira Safwan ba kawai yayi gaba yana tafiyar sa cikin natsuwa, 'karfi da yaji ya danne ciwon da yake ji dan kar suyi tunanin kwantar da shi suce a duba shi. A baya Safwan ya bisa har bakin ward 'din da Baby take kwance...yana tafiyar yana yi masa mitan 6acewan da yayi. Har a lokacin kuwa Yah Deen bai furta masa komai ba har suka isa. Yana fara hango su Ammi sai yaji 'kafafun sa sunyi masa nauyi a hankali ya 'karasa kusa da su wanda Alhaji Baba ma da hango shi ya yi saurin isa gaban sa suka rungume juna. Kuka Mu'een ya sanya masa yana fa'din" Dan Allah Alhaji ka yafe min, bansan haka rayuwa ta zata juye min ba..." Alhaji Baba zaton shi ko duk kan rashin lafiyan Babyn ne dan haka sai ya ringa kwanatr masa da hankali amma Yah Deen ya'ki yin shiru..fa'di yake"  Noor tace nine sanadin komai, ni ne na jawa Baby duk abinda ya same ta kuma na yarda nima Alhaji, wallahi nayi nadamar rayuwa ta na zalunci Baby na 6ata mata future in ta tun kafin zuwan ta duniya batare da na farga da hakan ba...". Saurin cire shi Alhaji Baba yayi daga jikin sa yana duban sa cike da mamakin kalaman sa, yayin da Ammi da ta matso da farin cikin ganin sa ita ma ta kafe shi da idanu tana duban sa cike da tausawa. Hawayen dake zubo masa Alhaji Baba ya fara share shi masa, duk tunanin bai ja shi wani wuri ba, yayi zaton ko duk zafin so da tausayin Jasmine ya sa shi furta wa'dannan kalaman. Ganin Ammi gefen sa ne ya sanya shi waigowa ya tafi gaban ta itama ya rungume ta tana bubbuga bayan sa cike da tausayawa. Zaiyi magana ta dakatar da shi da fa'din" Shi...ya isa haka nan Mu'een kar jinyan yarinyacya zautar min da kai..ka manta cewar Allah ne ya 'dora mata ko?". Murmushi yayi tare da cire jikin sa daga jikin Ammin, hannun sa 'daya yasa ya share hawayen fuskar sa, cak idanun sa suka sau'ka kan Noor suka ha'da idanu, itama hawaye ne kan fuskar ta sha6e-sha6e, take kuwa tayi saurin kawar da kanta gefe ta daina kallon sa, bai damu ba sai ya dawo da kallon sa wurin Ammi. Dur'kuswa yayi ya zuba gwiwoyin sa a 'kasa, sannan ya kamo hannun Ammi yace" Ammi..ku iyaye na ne masu matu'kar 'kauna ta, kun bani tarbiya kun bani ilimi, kun bani farin ciki da gatan rayuwa, kunyi 'ko'kari sosai wajen ganin kun bani duk wani abu da yake hakkin ku, kuka 'kaunace ni kuka koya min son Allah da mazon sa, kuka koya min bauta da kuma bautawa Ubangiji na, kun nuna min haramci da duk abubuwan halal dake cikin rayuwa amma nayi watsi da shi. Ammi ku yafe min dan Allah, badan hali na, ban ta6a sanin cewa da gaske halayya ta kan iya dawowa ga ahali na ba sai yanzu Ammi, ace da ciwo, na 'dauki abin.wasa ne shiyasa duk na mance da hakan sai gashi yanzu ya faru akan yarinya ta..." Ammi saurin fizge hannun sa tayi daga nata ta wani zuba masa idanu cikinbalamar tambaya kan batun da yayi, yayin da Alhaji Baba ma daga inda yake tsayen yake duban sa duk alamun tambayoyi ne kan fuskokin su. Noor kam kuka ta sanya tare da kwantar da kanta bisa cinyoyin ta, koda wasa bata son taji ana sake maimaita wannan batun..'konabmata zuciya yake yi sosai. Mummyn Safwan ne tayi saurin 'karasawa kusa da ita ta fara rarrashin ta amma ina, kukan ya riga ya zauna cikin zuciyar ta bazata iya daina shi ba. " Alhaji..Ammi ku yafe min, amma a yau shirya sanar da ku ko way ni, a yau zan bayyana muku 'dayan 6angare na da bakowa me ya sanshi ba..." Dukkan su kallon shi suke yi suna jiran jin abinda zai fa'da musu, tun farkon maganar tasa suka fahimci cewa akwai lauje cikin na'di, a fili suka fahimci cewa wani mummunan lamari ne ya faru da Jasmine, domin ko su idan ance su fa'di wani hali Mu'een halayya 'daya zasu iya fa'da wanda yake da munin da zai iya illata wa mutun zuri'ah.." Ammi idanu ta lumshe bata fatan taji wani makamancin hakan ga Baby, ahse dama haka ne ko da mutun ya tuba ya koma ga Allah fa'dar sa sai ya faru ga nakan.ahse dagaske ne? Abinda tun farko Alhaji Baba yayi ta masa gudu kenan amma ya 'ke'kashe idanun sa ya yi kamar bai san da hakan ba. Yah Deen bai damu da irin kallon da suke masa ba a hankali ya bu'di baki kaf ya basu labarin halin sa wanda suka sani da wanda ma basu san da shi ba..wanda ya jima yana 6oye musu da wanda Noor ma ta rufa masa asiri, hatta cikin da ya zubarwa Husnah bai 6oye musu ba...dan ganin sa ba bu'katan wani rufin asiri kuma yanzu bai cancanci hakan ba sam...a hankali har ya gangaro kan abinda ya sami Baby, yanda tuncfarko Noor tayi ta nuna masa rashin dacewar Sani amma ya yi banza da ita, ko ka'dan jinin ta bai 'dauki na Sani ba, da sonta ne da tuni Sani ya bar gidan su amma yayi banza da ita, Allah ya kawar da zuciyar sa ya toshe masa tunanin sa akan komai, hatta 'karan Sani da Baby take yawan kawo masa da yanda take fa'din yana cinye mata baki duk ya tuna su, kuma sai yanzu yasan manufar su wanda abaya bai ta6a fahimtar mai Baby take nufi ba, dayke Allah yaso kama shi, shiyasa ya rufe masa idanu yasa masa yadda da aminta da Sani, jinsa yake tamkar su Saif ne shiyasa bai ta6a ko gwada yi masa fa'da akan wani abu ba, ko zai yi ma sai dai suyi maganar kamar da wasa ta a wuce hakan...bai sani ashe Sani na tafe ne da mummunan 'kaddarar sa da Allah ya tamadar masa, wanda da ace ya sani da tun farko ma ko magana ba zai yadda ta ha'da shi da Sani ba babble har ya bashi masau'ki cikin gidan sa...ayu nayi danasanin rayuwa ta Amma, nayi nadamar komai dana aikata, dan Allah ku yafe min Ammi....Alhaji..." Sai kuka yaci 'karfin sa ya kasa 'karasa abinda yayi niyyan fa'da. Alhaji Baba kam kansa ya dafe cikin tsananin tashin hankali, ashe duk yanda ya 'dauki abin Mu'een 'din abin ya zarta hakan sosai, bai ta6a zaton yayi nisa har haka fiye da tunanin sa ba, da Husnah ka'dai ya sanshi kuma bai yi tunanin cewa muhallin su 'daya a makaranta ba, ashe har da zubar da ciki yayi, banda wanda ya 'dirkawa 'yar gidan Malam Barau hallau yazo ya dinag bibiyan Husanh bayan yasan da aure akanta...Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Yah Allah me na haifa? Ada yayi zaton ko tunda yayi aure shikenan da yake bai sake ji ko ganin wani abu makamancin wancan da yafaru abaya ba ashe yaudaran kansa yayi da wannan tunanin, ko bayan.auren sa ma Hudah ta kamashi da Husnah kuma ta rufa masa asiri..bazai ta6a mantawa da lokacin da ta dawo gida ta'ki komawa ba wanda 'karshe dole sai.kayanta aka kawo mata ta cigaba da zama agida, ashe duk saboda banzan halin sa ne, a lokacin baya zurfafa bincike akansa dayake yana tunanin komai ya wuce..Mu'een Allah ya wadaran rayuwar ka wallahi, banda tarin abin kunyar daka 'kunsa min a Shuwarin, mutun mai mutunci amma ka ha'da ni da shi ka ha'da 'yar sa da kayan cikin 'karshe ma ta rasa rayuwar ta Mu'een ashe wannan ma bai ishe ka ba,.har gobe tsananin kunya da nauyin Malam bai barshi ba banda ma jama'ar gari kawai dannewa yake yana mu'amalar sa dan kar aga fuskan da za'a gaya masa magana amma shi ka'dai yasan yanda yake ji cikin zuciyar sa. ...Alhaji Baba jiri ya fara ji na 'diban sa Safwan ne yayi saurin tare shi suka zauna kan kujerar dake wurin yana bashi ha'kuri. Sam Safwan bai yi mamakin jin labarin Mu'een ba cuz da kansa ma ya sanar da shi a lokacin giyan son Nuree na 'diban sa so bai 6oye masa komai ba illah batun Jiddah da ya faru daga baya, shiyasa ko yanzun ma bai yi wani mamaki ba. Ammi kam tsaye ta mi'ke ta wafce hannun ta daga cikin nashi, babban abinda ya 'daga mata hankali shine jin asalin abinda aka yiwa Jasmine ga haushin Noor na rufa masa siri da tayi tun abaya har ta cigaba da zama da shi, wanda da tasan hakan da ko hauka take yi bazata ta6a barin ta ta zauna da shi ba,  wajen ta tayi niyyan zuwa ta sau'ke mata 6acin ranta amma sai taji Yah Deen ya sake ri'ke hannun ta yana ro'kon.ta yafe masa yayi al'kawarin ba zai sake ba... Wani mahaukacin mari ta sau'ke masa ta sake 'karawa akaro na biyu har bakin sa na jini, kafin tayi na uku Noor bata san lokacin da ta taso da gudu ta shiga tsakanin su ba, duk yanda take jin tsanar sa cikin ranta amma bazata ta6a juran ganin irin hakan tsakanin sa da iyayen sa ba, sosai taji tausayin sa da Ammin ke dukan sa, kuka take tana ro'kon Ammi akan tayi ha'kuri ta bar shi, tavyafe masa, shi da kansa yayi mamakin ta sosai duk kuwa cikin matsanancin tashin hankali yake. Jikin Ammin ta shige tana kuka tana bata ha'kuri, sosai jikin Ammi yayi sanyi, ta rasa wani irin.zuciya ce ke ga Hudah, duk wanda yaji wanna labarin yasan sosai aka shiga hakkin ta amma duk da hakan alamun tausayi take nuna agare shi. Yarinyar nan dama na jima ina tunanin bata cikin walwala, tunda na bashi auren ta yarinyar nan bata canza ba, hakan nan take kullum kamar wacce bata cin abinci ashe ita ka'dai tasan me ta 6oye cikin ranta.." Ammi ce ke wannan tunanin cike da matsancin tausayin ta. Ita ka'dai ce agaban ta yanzu, Jasmine ai 'yar sa ce, sai yaje can yaji da da ita tunda shine ya lalata mata rayuwa, duk tausayin Baby da Ammi ke ji awanni biyu da suka gabata duk sun tashi sun dawo kan Noor, yayin da haushin Yah Deen ya mamaye mata zuciya. Mummyn Safwan ha'kuri itama take bawa Ammi at same time kuma tana bata misalai da manyan-manyan 'kaddarorin dake faruwa a wannan duniyar, tace tunda har ya kasance halin sa ya zayyano da bakin sa bai kamata kuma tayi masa irin wannan hukuncin ba, ga dukkan alamu nadama ce mai girma ta shige shi dan haka.nasiha ya kamata tayi masa ba duka ba. Huci ammi ta sau'ke dan sosai ranta ya 6aci da su, Allah wadai take yi cikin zuciyar ta da rayuwar Mu'een, sam bakin ta ya kasa furta komai, illah nuna shi da take yi da yatsa idanun ta jajazir...da 'kyar ta fizgi magana tace" Allah ya sauwa'ke in sake 6ata yawun baki na dan.kawai in yiwa wannan banzan nasiha, idan har wanda akayi masa abaya bai shiga kansa ba to banga alamar shiryuwa tattare da shi ba, yaje can shi yasa ni rayuwar sa ce ai...banza marar hankali wanda bai san ciwon kansa ba.." Ta 'karasa fa'da da yaren su na Igbo. Shi kam sai hawaye kawai yake yi hannun sa dafe da kuncin sa, yacriga ya shiryawa duk hukuncin da za'a yi masa a yau 'din, cuz aganin sa ya cancanci koma wani irin hukunci ne. Safwan gefe yake da Alhaji Baba yana bashi ha'kuri da kwantar masa da hankali. Abinda bakin Ammi ya iya sake fa'di kawai shine" Wallahi...ka yi asaran rayuwar ka Mu'een..." Kafin ta sake yin wata magana Mummyn Safwan tayi saurin rufe mata baki..tana bata ha'kuri. Gaban ta Yah Deen ya jawo gwiwan sa ya dawo gaban ta yana hawaye yake fa'din" Ammi dan Allah idan duka na zai sa zuciyar ki tayi sanyi ki min komai, ki dake ni ki min duk abinda zaki min indai ranki zai yi sanyi, ni da kaina ma na tsani kaina Ammi, wallahi bana so in sake rayuwa a duniya saboda ban iya faranta wa masoya na rai ba...Mummy ki bar min Ammi tayi ta bugu na son ranta koda kuwa zai yi sanadin rayuwa ta ne bazan ji ciwon sa ba, kaico na da na kasance mujiya cikin ahali na, kaico na da na za6i kazamar rayuwa na sa ta zamto wani 6angare cikin rayuwa ta ....." Bai kai ga rufe bakin sa ba sai ya fara tari akai-akai yana dafe 'kirjin sa da duk hannuwan sa biyu...wani jini ne ya sake fitowa ta bakin sa take sai ya 'dur'kusar da kansa 'kasa cike da azaba ko hawayen ma tsayawa suka yi. Da sauri Safwan ya bar Alhaji Baba yayo kansa ya ri'ke shi haka ma Mummy dake yi masa sannu a rikice take bawa Safwan umarnin yayi wani abu mana. Shi kam da 'kyr yake fizgan kalmar" Ku...bar ni na mutu Safwan...bani da amfani yanzu.....". Mummy cike da ausayawa take girgiza kanta gaba 'daya jikin ta yayi sanyi 'kalau. ...Safwan ne yayi 'kira wanda ba'a fi mintina biyar ba sai ga shi anzo da gadon tura marasa lafiya za'a tafi da shi inda ya kamata aduba shi. Har a lokacin Alhaji Baba bai motsa daga inda yake ba, gaba 'daya jin halayen Mu'een daga bakin sa ya matu'kar sanyatar masa da jiki, ya tattabata ko 'karya babu a cikin zancen sa tunda yasan bazai yiwa kansa 'karya ba. Ammi kuwa rungume take da Noor dukkan sau suna hawaye gwanin tausayi, da dubara ta kautar da fuskan Noor ta yanda bazata hango Yah Deen ba balle har taji tausayin sa. 'Bangaren Yah Deen kuwa fir ya'ki amincewa da a tafi da shi 'din da ka gansa kasan yana jin jiki amma ya'ki.bada daman da za'a taimaka masa wai shi sai yaga  Jasmine tukunna, duk yanda suka zo su yi hanzarin tafiya aduba shi 'kin amincewa yayi, dole yasa Safwan fa'din abar shi ya ganta kawai 'din.   Da Safwan in suka shiga yana ri'ke da kafa'dar sa...bakin gadon da Jasmine ke kwance yaje ya tsaya sai yaga kuma an jona mata wani sabon drip a hannun ta bacin yasan tun jiya aka gama da wannan. Haske sosai yaga ta 'kara yi masa a idanun sa. Da mamaki natare da ya kalli inda Safwan yake ba da yana duban ta ya tambayi Safwan me kuma ya sake faruwa da Jasmine?" Yayi maganar ne yana barin jikin Safwan daga ri'kon da yai masa a hankali ya isa gaban ta, hannun sa 'dayan ya 'daga ya ta6a jikin ta da shi sai yaji zafi rau a hankali ya shafa fuskar ta...yana jin tsananin tausayin ta na ratsa shi...ga wani masiffafen 'kaunar ta da yake ji kamar ya ha'diye abin sa ta huta da wannan wahalar. Sai dai ya san koma me ze mata a yanzu ba zai saka ta farin ciki ba, musamman ranar da ta fahimci cewa shine ya ja mata wannan abin yasan duk daren da'dewa Baby tsanar sa zata yi kamar yadda mahaifiyar ta ta tsane shi yanzu. Shafa fuskan ta da yayin ne ya sanya ta 'dan bu'de idanu, bata iya ta bu'de idanun duka ba saboda zazzafan zazza6in dake jikin ta a lokacin, banda cikin jikin ta dake gudu ko iya 'daga hannun ta bata yi. Tana ha'da idanu da mahaifin ta sai ta saki murmushi irin na 'karfin hali da murnar ganin mahaifinta. Bakin ta ka'dai ya iya motsawa tace" Daddy"..Wanda in ba idanu ka na kanta bane bazaka ta6a fahimtar tayi magana ba cuz bata yi shi da wani sauti ba amma a hakan Yah Deen ya fahimci abinda ta fa'di. Shima murmushin yayi mata tare da 'dora hannun sa 'dayan saman goshin ta yana kallon cikin idanun ta, yayin da 'dayan hannun nasa ke dafe da 'kirjin sa har a lokacin. Duk ya fita hayyacin sa kamar ba shi ba...amma zaman sa gaban Baby ya 'dan sanyatar masa da wani 6angare daga cikin halin da yake ciki. Da 'kyar yake magana saboda numafshin sa dake fita akai-akai hannun san dafe da kanta yace"...Allah ya baki lafiya Maman Daddy...Allah tashi kafa'dun ki, Allah ya ta'kaita miki...ciwon nan ki warke cikin...'kan...'kanin lokaci, ko ba na raye Saif zai cika miki burin ki kinji Mama na, Uncles 'din ki da Mummyn ki zasu kaiki Makkah da Madinan ki ko?" Jasmine bata yi magana ba illah idanu da ta zuba masa tana kallon fuksar sa. Bai damu ba sai yayi murmushi bayan fahimtar abinda take kallo saman fuskar sa in. Yasan yanda yarinyar shi take da tausayi, musamman kuma yasan.yanda take 'kaunar sa da rashin son.ganin damuwa tattare da shi, Jasmine yarinya ce 'karama amma sossai yake alfahari da ita wurin tausayi da 'kaunar mahaifanta, yasan badan  itama fama take da kanta ba da babu abinda zai.hana ta tambayar abinda yake yiwa hawaye. Hannu yakai ya share hawayen dake kan fuskar sa sannan ya sake maida hannun sa da hankalin sa gareta. Safwan.kam tsaye yayi a gefe yana ganin ikon Allah..gaba 'daya gani yake Mu'een ya canza ya zama kamar ba shi ba, bai sanshi da yawan surutu sai gashi yau in surutun sa har na neman zarta iyaka a gaban yarinya 'karama. A hankali ya cigaba da fa'din" Inajin kamar rayuwa ta ta 'kare ne Baby, ina ina ganin tankar bazan sake ganin ki ba, na so in canza muku.rayuwa ke da Mummyn ki amma bani da damar hakan yanzu , dan Allah Baby..ki yafe min kinji? Ki yafe wa Daddyn ki da yayi sanadin da aka cutar da rayuwar ki Baby, wallahi ji nake kamar in raba kaina da rayuwa saboda yanda nake tsananin jin tsanar kaina, da kaina na cutar da ke na cutar da mahaifiyar ki... Idanun sa ya lumshe sannan ya cigaba da fa'din" Ki gafar ce ni Maman Daddy..ki yafe min, Insha Allahu daga yau bazaku 'kara yin ba'kin ciki saboda ni ba....". Kallon sa kawai Jasmine take yi tana kallon bakin sa inda taga jini ba ma ta fahimtar abubuwan da yake fa'di dan maganganun nasa sun girmi shekarun ta sosai, hakan yasa tayi shiru kawai tana duban sa batare da ta fahimci ko.kalma 'daya daga cikin zantukan nasa ba. "...ki yafe min duk abubuwan da suka faru badan hali na ba, nasan nine na ja miki gashi ya faru a lokacin da bani da ikon hana faruwar sa wallahi kunyar in 'kira kaina matsayin mahaifi agare ki nake yi a yanzu Baby dan Allah ki yafe min kinji, ke da Mummyn ki ku yafe min, idan Allah ya kar6i raina kiyi min addu'ah, idan kin girma ki tuna cewa mahaifin ki mai 'kaunar ki ne dan Allah kar ki tuna munanan laifuka na, ban ta6a yin wani abu dan na 'kuntatawa rayuwar ki ba sai dan farin cikin ki, ko wannan ma da ace nasan da faruwar hakan da wallahi har abada bazan ta6a ko fara kwatanta aikata alfasha ba, Baby...". Saurin dakatar da shi Safwan yayi ganin cewa da 'kyar yake 'kwa'kulo maganan yana 'kara ran'kwafawa saboda ciwon dake cinsa a zuciyar sa... kafa'dun duk biyun Safwan ya taklafo sannan yace " Please ka daina irin wannan maganganun  Mu'een, Jasmine ce fa a gaban ka, nd she is just 5yrs yarinya ce 'karama ba fahimtar ka take yi ba sam, baya ga haka ma da wanne kake so taji? Kaima in wahal da kanka kawai kake yi...ka bari aje a duba ka in ka 'dan warware sai kazo kayi mata hiran kaji..". Safwan yayi maganar ne yana 'ko'karin tada shi amma ya turje ya gyara zaman sa da kyau, da Safwan ya matsa sai Yah Deen yace sai dai azo a duba shi anan amma shi babu inda zai je yana nan tare da 'yar sa, yace"..idan na tafi na bar Baby hankali na bazai kwanta ba Safwan...". Safwan fita yayi yana jan 'kafafu, duk kansa ya kulle da wannan lamarin, san ya rasa ta ina zai fara ma, da fitar sa sai ya tarar da su tsaye cirko-cirko daga waje, banda Alhaji Baba da har yanzu yake can zaune inda ya bar shi ya zuba uban tagumi shi ka'dai yasan me yake ji.a zuciyar sa game da Yah Deen..lokaci lokaci yakan furta" Ahamdulillah ala kulli halin, ha'ki'ka Allah ya jarabce shi, jarrabawa mafi girma daya bashi 'da irin Mu'een, bai san me zai ce ba face ya godewa Allah kawai. Ammi ma har yanzu tare take da Noor tana aikin lallashi, ita kam a yanzu Noor ka'dai ke gaban ta, domin ita ka'dai ke bata tausayi sai kuma Jasmine dake can kwance cikin mawuyacin hali...Yah Deen kam koka'dan bata jin sa a zuciyar ta, gaba 'daya taji ya fice cikin ranta, banda tsanar sa babu abinda take ji a yanzu. Da fitowar sa sai ya sanar da su abinda Mu'een 'din yace, kowa sai ya bu'de baki da alamun mamaki kan fuskokin su, domin sun san idan aka biye a  haka cikin wannan halin.ba zaibkai labari ba.   Alhaji Baba kam wani wani 'katutun ba'kin ciki yaji ya tokare shi a 'kirji, duk yanda yake jin babu da'di a jikin sa amma hakan bai hana shi mi'kewa ba, cikin 'dakin ya shige direct da ka ga fukar sa kasan yau 'din akwai bambamci da kullum, tsananin 6acin ransa a bayyane yake a fili. Yana zuwa ya sau'kewa Yah Deen wani mari mai cike da da jin haushin sa atake ya 'kara masa wani bai ko damu da halin da ya gansa ciki ba, ya sake sau'ke mishi wani yana huci..sannan ya nuna.shi da 'dan yatsa. Shi kam bai ko iya 'daga idanu ya dube shi ba illah Baby da yake kallo, ya riga ya sawa ransa cewar ko wani irin abu iyayen san su masa matu'kar hakan zai sa zuciyar su tayi sanyi shi bazai damu ba...ya san idan a musulunce ne ma hukuncin jefewa ne akansa wanda zai kai shi har mutuwa, so dan sun mareshi hakan ba zai sa yaji haushin su ba..ya cancanci komai daga garesu domin bai yiwa rayuwar su adalci ba. Tunda yake da mahaifin sa karo na biyu kenan da ya ta6a sau'ke hannun sa saman jikin sa da sunan  mari, kuma duk shine yake jawa kansa. Alhaji Baba bai bar shi ba sai da ya sau'ke masa maruka har guda biyar a zuciye sannan ya 'kara da finciko hannun sa ya jashi ya tura shi waje yana fa'din" Maza kaje can da banzan halin ka da ba'a maka nasiha kaji,  bazan yi maka baki.ba Mu'een amma kaje indai rayuwar duniya ce gaka ga ita, bacin ka lalata mata rayuwa kuma yanzu me kazo ka zauna kayi mata, ko kake sai kaga bayan ta tukunna hankalin ka zai kwanta? banza wawa marar hankali, wallahi nayi dana sanin baka auren yarinya ta, sam bata dace da mutun irin ka ba,  baka cancanci zama miji agare ta ba balle mahaifi ga Aishatu...har abada bazan daina danasanin haihuwar ka ba domin baka 'kare ni da komai ba sai abin Allah wadai, tun baka kai hakan ba nake fama da kai, tunda da yarintar ka kake dasa min ba'kin ciki a zuciya wanda cikin 'kannan duk babu wanda ya ta6a ko kwatanta yi min irin hakan sai kai ka'dai 'dan iska marar tunani mai halin gwaraye...". Wannan karon kam numfashin Yah Deen kafewa yayi, daga inda yake dur'kushen ko motsin kirki kasawa yayi...bai masan su wa  da waye bane ke tsaye a wurin har aka 'dauke shi akayi gaba da shi bai san inda kansa yake ba. Taimakon gaggawa aka fara bashi da 'kyar aka samu numfashin sa ya daidaita amma har a lokacin bai farfa'do ba...numfashin sa yaja sosai. Baby kam da idanu ta ringa kallon Alhaji Baba ganin dukan da yayiwa mahaifinta a idanun ta, ba ta iya tace da shi komai ba illa idanun ta da ta maida ta ta rufe su a hankali. Noor kukan ta 'karuwa yayi jin irin mugayen kalaman da Alhaji Baba ya furta akan Yah Deen, sam bata so hakan ya faru ba, sai ma take ganin laifin sa da ya bada labarin rayuwar sa kaf da bakin sa, mai yasa bai bar shi sun cigaba da rufewa tsakanin su ba? Ita koda zata rabu da shi ne tayiwa kanta al'kawarin bazata fa'diwa kowa abinda ta gani ba, sai gashi da kansa ya bayyana komai ga iayen sa. Kuka take tana 'karawa, tausayin dukkan su take har zuciyar ta. Tasan kowa bazai ji da'din wannan abin ba sam. Da yake Ammi tasan halin 'yar ta jin kukan da take sake yi yasa ta 'dago kanta tace" Karki ce min dan wannan banzan kike kuka..?" Girgiza kai Noor tayi tace" Ammi baki ji maganganun Alhajin ba? sun yi tsauri da yawa fa". " Ina ruwan ki to..ni banason shirme, lokacin da yake yin son ransa ya tausayawa kansa ne, sai kece yanzu uwar tsausayi ko, to ba shiryawa zamuyi dake ba matu'kar kika ce kuka zaki dinga yimin saboda shi, ki bar shi can ai shi ya sani ba rayuwar sa bace..." Mummyn Safwan ce ta sako.bakin ta da fa'din" Hajiya ayi ha'kuri dai, in.kika lura zaki ga tsananin nadama ce tattare da shi yanzu, me yasa bazaku bashi dama ba?" Murmushin takaici Ammi tayi sannan tace" Ki bar shi ba wani nadama da yayi in dai wannan yaron ne, idan fushin da Alhaji Baba yayi da shi abaya bai sa ya nutsu ba wallahi bana tunanin akwai abinda zai nutsar da shi cikin sau'ki haka..munafurci kawai ke damun sa ba komai ba". Shiru Mummy tayi kawai tana tunani cikin zuciyar ta, ita kam gaba 'daya tausayin sa take ji, ai kowa da yanda Allah yake tsara masa rayuwa, kuma dan ka tsinci kanka ko wani naka matsayin shiryayye bawai dabarar ka bace tasa hakan kawai Allah ne ya so ganin ka da wannan matsayin, to ko shima Mu'een 'din bawai rashin wayon sa bane ya kai shi ga fara wannan rayuwar face 'kaddarar dake zane cikin rayuwar sa wanda Allah ne ka'dai yasan nufin sa da shi. Babu wanda ya saje wata magana tsakanin su kawai suka cigaba da zaman alhinin faruwar lamarin. *****        'Bangaren Sani kuwa tuni anyi nisa cikin thearter room sai fatan Allah yasa afito lafiya ya kuma sa a dace da aikin da za'a yi masa. Sun 'dauki kimanin awa guda da rabi a zaune, lokacin har anyi sallar Azahar, bayan sun idar sai mummyn Safwan tace zata tafi gida zuwa yamma zata dawo ko kuma gobe, ro'kon ta Ammi tayi akan dan Allah ta sau'ke mata Noor a gida ta 'dan watsa ruwa ta kintsa in yaso sai ta dawo dan taga alamar tun jiyan bata samu nutsauwa ba. Noor da farko 'kin amincewa tayi da tafiyar amma Ammi ta matsa dole suka tafi tare da Mummy ta sau'ke ta, ko a motan ma ha'kuri take sake bata saboda yanzu kam da kunnuwan ta taji komai da ya faru, ta kuma fahimci irin ha'kurin da Noor tayi da shi, sai dai duk da hakan tasuayin sa bai gaza zama cikin ranta ba, amma ya zama dole ta.bawa Noor ha'kuri dan ta cancanci yabo, ba kowace mace bace ke da irin zuciyar ta, ko ita nan da take da jikoki ma idan akace ta ga mijin ta da wata macen daban ganin idanun ta tasan Allah ka'dai ne zai gyara lamarin balle Noor da take yarinya mai 'karancin shekaru, ha'ki'ka tayi ha'kuri, ta nuna masa halacci ta kuma rufa masa asiri matu'ka, babban abinda yafi tsaya mata arai ma shine sunan Yusrah da taji cikin labarin, kenan ita aka rufe ba'a gayawa ba tun farko, tunda gashi yace Safwan ne ma ya raba su, kenan shima ya sani amma ya 6oye mata...ta riga ta sa cikin ranta cewar uban Yusrah zataci idan har ta tabbatar da wannan labarin gaskiya ne. Ai ba yau ta fara yi musu nasiha ita da mahaifiyar ba akan yawacen-yawacen banza  da Yusran ke yi, shine har abin ya zago ya dawo kan abokin Safwan...hmm" Har suka isa gida tausan Noor take yi kuma ba laifi yanzu kam hankalin ta ya 'dan kwanta tunda da taga Ammin ta sai taji 'kwarin gwiwa ya shige ta sosai, hukuncin da ta riga ta yanke ne dai bata jin zata iya janyewa saboda bata bu'katar sake rayuwar aure da shi, ta 'kwammaci ta mutu ba aure da ta cigaba da rayuwa da mutun maci amana irin Yah Deen da ba ya ta6a hangen gaba, baya da kyakkyawan zuciyar da zai fahimci kuskuren da yake aikatawa balle yayi tuba na gaskiya. Watarana idan yayi wani abin sai taga kamar ya daina ne amma da kanta take 'karya ta kanta kuma idan halin san ya sake bayyana mata. Hakan ne ma yasa ta fahimci cewa daidaiton hankalin sa zaiyi wahala, baza ta ta6a amincewa da nadamar sa ba. Kullum raba mata hankali yake yi da salon da ke nan iri daban daban, ko kaga alamun nadama tattare da shi kwana kusa kuma zaka sake 'karya ta tunanin ka, domin a fili yake bayyana cewa bazai iya barin harkar neman mata ba. Videon sa da Jiddah ka'dai ma ya ishe ta gane hakan, shiyasa itama ta yanke shawaran da ta ga yafi kwanciya mata a zuci. Addu'ar ta kawai shine Allah ya bawa Baby lafiya su yi tafiyar su su bar shi yaje can da 'yam matan sa sa da ya fi son yin rayuwa da su. Cikin gidan ta shiga tana jin sa wani iri duk babu da'di...fili sosai taga yayi mata, da idanu ta kalli inda suka rabu da Baby jiya lokacin da Sani zai tafi da ita makaranta.. _Allah Sarki_ ta furta cikin ranta sannan ta 'dauke idanun ta. Sai da ta tsaya suka gaisa da Bala maigadi kafin ta shige ciki, shima bayan ta yabi da kallon tausayi yana girgiza kansa dan duba na farko idan kayi mata zaka fahimci hankalin ta ba a jikin ta yake ba, duk ta fige ta rame cikin yini guda da kwana 'daya kacal...A fili ya furta Allah ya rufa asiri. Da fitar su Noor daga asbitin sai Hafsat ta 'kira ta sanar da shi cewa yanzu zata taho ta gama abincin rana. Nan ya sanar da ita cewa ai Noor in ma yanzu ta wuce da Mummy, amma tabiya ta can dan ta ringa 'dan 'debe mata kewa kar ta rin'ka yawan tunanin in yaso in ta gama shiryawa sai su taho tare da ita. Hakan kuwa akayi domin Hafsat can ta wuce aka sau'ke ta ta biya 'dan sahu ku'din sa yayi gaba ita kuma ta shiga ciki. Kayan abincin dake hannun ta ajiye a bakin parlour ta ciki tare da sau'ke Afrah suka 'karasa ciki..dan duk salkamar da take ko 'daya bataji an amsa ta ba. Noor mamaki sosai ne ya kamata lokacin da ta shiga ciki ta tarar da kayan ta da ta shirya babu su duk an sake jere su, tayi mamakin lokacin da hakan ya faru, kuma tasan ba kowa ne zai yi hakan ba sai Yah Deen, baki ta ta6e kawai bata wani sa aka ba dan damuwar kanta ma ta ishe ta a yanzun. Wanka ta shiga yi wanda a lokacin ne Hafsat ta iso shiyasa bata samu an amsa sallamar ta da tata yi ba. Noor kam wankan ta tayi ha'di da wankan tsarki dan yanzu kam tasan kwanakin hailar ta ya cika jiya ma mantawa tayi har tayi gaggawan yin wanka tayi sallah batare da ta tuna ba. Sallahr azahar ta gabatar bayan ta saka dogon riga a jikinta. Sai da ta idar sannan ta fito nan ta tarar da Hafsat zaune, sabon  gaisuwa suka sake Hafsat ta tambayi jikin su Baby Noor ta amsa ta fa'din" Alhamdulillah.. da sau'ki. Hafsat sai tace" Ashe shima Mu'een 'din jikin ya 'kara motsawa, 'dazun Safwan ke sanar dani". Da" Umm" kawai Noor ta masa ta tana yin 'kasa da idanun ta. " Ga abinci ki ci to dan nasan idan muka je can ba iya ci zakiyi ba.." Cewar Hafsat dake 'ko'karin mi'kewa dan 'dauko mata abincin. Saurin dakatar da ita tayi da fa'din" A a kam ki bari mu isa can 'din..Ammi na fa ta zo tana can da Alhaji Baba..". Washe baki Hafsat tayi cike da farin cikin zuwan su Ammin tasan dama abin zai yiwa Noor yawa ita ka'dai. Fuskar ta cike da murmushi tace" Duk da hakan dai kamata yayi kici agida nake ganin zai fi can in ko?". Kawar da kai tayi gefe tace " a a ki barshi Hafsat ban jin ci ma yanzun wallahi". Komawa tayi ta zauna tana duban ta tace " Ke dai bakya ji Noor, Baby ba lafiya, ga Dr. Ma can rai a hannun Ubangiji, kema kuma so kike Ulcer ta kwantar da ke ko...?" Murmushi tayi mata tana kamo hannun Afrah tace" Bani da Ulcer ai ni.…bana so ne inyi nisa da Baby shiyasa nafi so mu koma can in da sauri.... ." Kafin Hafsat tayi wata magana sai wayar ta ta 'dauki ringing ko da ta 'dauko sallama tayi ganin sunan Safwan ne ya 'kira. " Hafsat kuna tare da Noor ne?" Ya tambaye ta da sanyin murya sai ta amsa da " Erh ina tare da ita". Yace " Okay..ba sai kun taho ba ku jira mu muma gamu nan zuwa yanzu...". Yayi maganar ne cikin sanyin murya, da ka ji kasan zuciyar sa a karye take. Hafsat ma jikin ta sanyi yayi da jin yayanyin nasa amma sai tayi tuanin ko jikin su Mu'een 'din ne ya sashi canzawa. Noor kam idanu ta zuba mata fuskar ta tallafe cikin hannun ta 'daya har ta kammala wayar sannan ta tambaye ta" wai ya akayi?" " Yace kar mu koma..suma suna zuwa yanzu..'kila am sallamo su ne". Goshi Noor ta tattare da alamun mamaki tace" Sallama kuma? naga 'dazun nan jikin Baby yayi  tsanani fa..ko de su Ammi zai kawo gida?" Hafsat tace " May be..kin gama sai kici abincin ki kafin su iso". " Sako mana to inga ko zan iya ci...amma zuciya ta na tsinkewa". Tashi Hafsat tayi ta ta nufi kitchen tana fa'din" Shai'dan ne ki dinga maimaita _Innalilliahi Wa Inna Ilaihi raji'un..._ Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *79* Hakan kuwa akayi domin  Noor cikin zuciyar ta ta ringa maimaiata _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ har Hafsat ta dawo ta zuba musu abincin, a hankali ta fara ci amma sam sai nemi  natsuwar ta ta rasa, bugun da zuciyar ta ke yi sai 'kara yawaita mata yake yi, bata fi spoon biyar ba taji abincin ya ishe ta gaba 'daya, ruwa mai sanyi ta 'dauka ta sha sannan ta kwantar da kanta tare da lumshe idanu. Ta 'dauki tsawon lokaci  a hakan Hafsat kanta bata iya fa'din komai cuz a yanda ta san Safwan da dukkan yanayin sa tasan da wani abu musamman yanda taji sauyi cikin muryar sa..amma da yake bata san ko menene ba shiyasa tayi shiru..fatan dai Allah yasa ba jikin Baby da mahaifin ta ne ya tsananta ba...tuno Sani da tayi ne yasa ta ta6e baki ashe har shima ba lafiya... Wasa-wasa kusan mintina hamsin da uku suka 'dauka bayan wayar da Safwan ya 'kira sannan suka ji tsayuwar motoci kimanin uku daga harabar gida.     Hafsat ne mai 'dan 'karfin hali dan haka ita ta fara mi'kewa tsaye yayin da zuciyar Noor ya amsa da 'karfi...'kafafun ta har na sar'kewa tabi bayan Hafsat Little Afrah kam tuni tayi baccin ta. Ganin yanayin da su Ammi suka firfito daga motar yasa ta kasa motsawa daga inda take tsaye, bata san me yasa ta tsorata ba, a hankali idanun ta ya sau'ka kan  Bala Mai gadi da hannun sa duk biyu ke kansa yana kuma girgiza kan da alamun alhini. Hakan ne ya 'kara tabbatar mata da cewa ba lafiya ba, gani tayi su Alhaji Baba, Safwan da wasu da bata ma gane ba sun tattaru wurin mota guda 'daya. Dole cikin uku tasan akwai 'daya cikin Yah Deen, Jasmine ko Sani...Ammi ce ta taho wajen ta da sauri ta kamata tayi ciki da ita, da ka ganta kuwa zaka san cike take da damuwa, Noor dai kawai ta bita ne amma ba wai dan ranta yaso.ba, taso taga menene ya faru acan wajen, me su Alhaji suka taruwa gaban motar can. Ji tayi kawai hawaye na gangaro mata yayin da zuciyar ta ya gama cika da waswasi..Ammi bata ce da ita komai ba har suka isa 'dakin ta da Ammi. Anan ne Ammi ta fara bata ha'kuri da alamun kwantar da hankali  amma bata san dalilin ha'kurin ba..burinta kawai taji menene ya faru kuma. Da 'kyar ta iya bu'dan baki tana hawaye ta tambayi Ammi" Me ya faru ne wai Ammi...?" Kafin ta rufe bakin ta sai ji tayi murya kamar ta Hafsat tana Salati daga waje. Ai bata san lokacin da ta zabura ta mi'ke da sauri ta fita ba, Ammi na 'ko'karin tarota amma ina ta riga tayi gaba. .....turus taja ta tsaya sakamakon ganin abinda ke kwance a parlourn ta, gwiwoyin ta ta zuba a 'kasa kamar wacce hankalin ta ya bar jikin ta tana nuna abinda ta gani. Da 'dayan hannun ta ta rufe bakin ta tana fatan Allah yasa zargin ta kar ya kasance gaskiya...Da muryar kuka batare da ta dubi fuskar Alhaji ba tace " Alhaji Baba waye aka na'de haka?...Innalillahi...wa inna Ilaihi raji'un...Yah Allah kasa mafarki nake ba gaskiya ba..Hafsat waye wannan dan Allah?" Da kuka ta rushe tana rufe bakin ta da dukkan hannuwan ta biyu, Ammi ce tazo ta kamata itama 'din hawaye take zubdawa...rungume kanta tayi a 'kirjin ta tana bubbuga bayan ta a hankali..tana fa'din" Kiyi ha'kuri Uwata...Kullu nafsin za'i'qatul maut...kinsan mutuwa dama dole ce..." Bata jira ta 'karasa jin abinda Ammin ke fa'di ba tayi saurin barin jikin ta ta mi'ke ta tafi..jin cewa da gaske mutuwa akayi, kuma bata raba'dayan biyu 'yar ta ce domin duk cikin marasa lafiyan itace 'karama kamar yanda taga wannan abin. Zuwa tayi gaban inda aka kwantar da gawan ta sa hannu ta bu'de...take sai tayi saurin rintse idanu..." _Na shiga uku na ..Ammi Jasmine ce, wallahi Ammi yarinya ta ce dagaske, waiyo Allah ne, Ammi itama ta tafi ta barni? Dan Allah kice min ba gaskiya bane Ammi, Alhaji kace min zolaya ta take takeyi, dan Allah kuce mata ta dawo wallahi nayi rantsuwa zan kula da ita, bazan sake bari a cutar da ita ba.."_ Kan fuskar Jasmine ta dawo da kallon ta, fuskar ta ta tallafa tana kuka hawayen ta na 'diga kan jikin Babyn tace" Baby na..dan Allah ki tashi kinji, kin manta nayi miki al'kawarin zamu bar rayuwar su, kin manta nace miki zamu bar inda suke bari na har abada, amana ce ke awaje na Baby amma ban ri'ke amanar da Allah ya bani da kyau ba, dan Allah Maman Daddy ki tashi, ki tashi ki bani wata damar da zan wanke dukkan kuskure na, me zan gayawa mahallici na Baby idan kika tafi batare da na sau'ke hakkin ki dake kaina ba....Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un...Ya Allah ka farkar da ni daga wannan baccin...." Tayi maganar tana dafe goshin ta da hannun ta 'daya...at same time tana kuka gwanin ban tausayi. ...Wata ma'kwabciyar su da ta shigo tun 'dazun itama kuka take yi sosai na tausayin Noor haka Hafsat ma, Ammi kanta bata iya ri'ke kukan ta ba. Cikin su babu wanda ya iya zuwa kusa da ita balle ya bata ha'kurin kukan da take yi. Dai-dai shigowan wata Hajiya dake bayan gidan su fuksar ta cike da Alhini amma ahakan bai hana ta ja ta tsaya ba ganin.kukan da Nnor ke yi, a hankali tabi sauran dake 'dakin da idanu taga duk suma yanayin da suke ciki babu alamun zasu iya iya lallashin wani. A hankali ta 'karaso kusa da Noor ta kama ta ...tana fa'din"Haba- Haba Maman Baby, sai kace kin manta matsayin musulma kike, ba kuka ya kamata kiyi mata ba..Addu'ah zakiyi mata kinji.." Jikin matar ta fa'da tana fa'din " Innalillahi Wa inna ilaihi raji'un..." Sai da maimaita ya kai sau biyar sannan ta fara fa'din" Ammi na! Ammi na..Ammi na.." Da sauri ta bar jikin hajiyan ta nufi inda Ammi take taje ta fa'da jikin ta ta sake sakin wani kukan. Ammi rungumar tayi da kyau tana 'ko'karin goge mata hawayen fuskar ta sam tarsa me ma ya kamata ta ce da ita...sosai Noor ke bata tausayi fiye da tunanin mai karatu. "... shikenan Ammi yanzu bani da kowa?" Hajiyan nan ce tayi saurin amsa ta da fa'din" Kina da Allah Maman Baby". " Wallahi ina son 'ya ta kice da ita ta dawo min, zan kula da rayuwar ta kamar 'kwai Ammi, har makaranta ta ma zan bari saboda ita, wallahi ina son 'yata, Baby dan Allah kar ki tafi ki barni, ban ri'ke amanar ki da Allah ya bani ba, waiyo rayuwa ta...". Kuka take yi sosai tana maganganu. Yayin da Hajiyan nan ke 'ko'karin tausan ta da maganganu masu sanyi, a hankali.take nuna mata cewar" Ai duk soyayyar da take yi mata bai kai wanda Allah ke mata ba, shi ya bata Baby kuma shine ya kar6i abin sa dan haka tayi ha'kuri tayi Addu'ah, tace duk mu ma mutuwar muke jira a kullum Maman Baby, bamu san yanzu ne, anjima ko kuma gobe ba...ki daina tuhumar Allah akan abinda ya riga ya aiwatar...". Duk maganganun da Hajiyan ke yi be hana Noor kuka ba, yayin da sauran ke faman tsiyayar da hawaye kawai Hafsat rungume da Afrah duk ta ji'ka su da ruwan hawaye. Alhaji Baba dake harabar gidan shine yayi saurin shigowa jin kukan Noor da ya kasa 'karewa, shi kansa jikin sa yayi sanyi sosai, domin Jasmine akwai shiga rai yarinyar bata da hayaniya, sosai mutuwar ta shige shi shi kansa....Cikin natsuwa ya fara fa'din" Haba Hudallah... ke da nake yabon ki kuma, kukan amfanin me zai yi? kar ki manata fa idan an tafi ba'a dawowa, kukan ba zai dawo miki da ita ba... Kiyi mata addu'ah kawai kiyi fatan Allah yayi mata  Rahama, Allah yasa mai ceto ce kinji...nasiha ya ringa mata mai ratsa jiki har ta yi shiru ta daina ihun sai dai hawaye.... Sai da yaga ta nutsu kafin ya juya ya fita yana tuno lokacin da yarinyar ta rasu a hannun sa. Mintina goma kafin ranta ya bar jikin ta tana kallon idanun sa a lokacin bakin ta ya bu'du..yanda take 'kaerwa idanun sa kallo ne ya sa shi tambayar ta" Lafiya kuwa Aishatu kike kallo na haka?" 'Dan bakin ta ta tura sannan tace" Ai kaine ka mari Daddy na..." Murmushi ya 'ka'kalo sannan yace mata " Daddyn ki baya ji Aishatu..shiyasa na dokesa". " Ai shi babba ne kuma ba'a dukan Babba...". Yace" To kiyi ha'kuri bazan sake ba...". Tun kafin ya rufe baki tace" Baba Alhaji..." Ta 'kira sunan sa tana lulllumshe idanu. Sai yace" Na'am Uwata ya akayi?" Idanun ta rufe tace " Mummy na...!..ai Daddy na yace da Mummy da Uncle Saif zamu tafi Madina da Makkah..." Sai tayi murmushi, daga hakan bata sake wata magana ba tayi shiru, ba'a da'de ba sai yaga jikin ta ya hau kakkarwar sanyi, har alokacin kuwa fuksar ta da murmushin zasu je Makkah..sha'kuwa ta fara tana jan jiki, sai yayi saurin 'kiran Safwan a waya da ya tafi duba Sani bayan an fito dashi daga thearter room. Sha'kuwan ta cigaba da yi wanda kafin Safwan ya iso ma har ranta ya bar jikin ta. Shi kansa tsayawa yayi yana kallon ta a lokacin, jiyake kamar wasa, amma da yake shi babba ne kuma yasan mutuwa ya kuma san tana kan kowa hakan yasa shi shafa fuksar ka da fatan Ubangiji Allah yayi mata Rahama....kwana idan ya 'kare babu wanda ya isa ya hana mutum tafiya ko da kuwa babu ciwo dole ne atafi, a zahiri ciwon baby ba mai tsanani bane wanda har zaka kawo mata mutuwa kusa, domin Sani ya fi ta jikkata amma shi yanan nan lafiya kamasa aikin sa aka fito shi, ga kuma Deen da kenan shikam ma bai san inda kansa yake ba amma yana raye yayin da Baby take nan har hira tana yi amma dayake Allah ya riga ya rubuta iya rayuwar ta na duniya kenan haka anaji ana gani ta tafi...Allah kayi mana 'karshe kyakkyawa". *****         Noor tana nan har aka gama yiwa Baby suttura tana aikin kuka. Addu'ah aka bu'kaci tayi mata amma bata iya tayin ba, bakin ta kaf kaf yake yi tana yi kamar zata rungume ta, idan dai kana wurin ko baka yi niyyan yin kuka ba ganin Noor ahakan ma sai ya saka kuka saboda tsananin tausayin ta..dan mata da dama cikin parlourn sai da suka zubda 'kwalla. Ammi ce tayi 'karfin halin cewa..." Ki daure ko cikin zuciyar ki kiyi mata addu'ar kinji.." Tace" To Ammi zanyi". Sai ga wani sabon hawaye. Wata mata tace" Kiyi ha'kuri dan Allah ki rage kukan maman Baby..". Tace" Zan bari...zan bari Insha Allahu.." Da rawar murya take basu amsoshin maganar su tamkar zautacciya. Lokacin da akazo fita da Baby kuwa kamar zata shi'de saboda kuka a hankali cikin shashshe'ka take fa'din...shikenan yarinya ta, shikenan Baby na...Allah ya ji'kan ki mama na, Ubangiji Allah ya miki Rahama, Allah yasa haske ne ke jiran ki cikin qabarin ki...". Duk kowa da ke wurin da Ameen ya amsa addu'ar tata, tausayin ta sosai ya kama su, saboda suna da labarin cewa mijin ta ma na can kwance a asbiti bai ma san da batun rasuwar ba...dole abin ya zame mata ba da'di ga rashin 'ya ga kuma jinyar miji...duk rashin tausayin ka sai ka tausayawa Noor idan ka ganta a wannan lokacin. Jikin Ammi ta fa'da ta cigaba da rero kuka. Kamar wasa wai Baby Jas ta tafi, tafiya kuma ta har abada, shikenan bazata sake ganin ta ba kenan..kamar yanda ta rasa Nannen su, ta rasa Mahaifinta...Allahu Akbar...Allah ka ji'kan mu ka bamu ikon bauta maka muna masu tsorin ka, kasa mana imani da yadda da 'kaddarar ka kowacce iri ce..." Idanun ta sun kasa tsaida hawayen da suke yi  saboda tausayin kanta da take yi, gani take kamar Allah ma bazai yafe mata sakaci da tayi da rayuwar Baby ba gashi ya kar6e abin sa batare da ta cije gurbin kuskuren ta ba...tana makale jikin Ammi...bata ko iya amsar gaisuwa sai dai su Ammi. Ba laifi kuwa dan duk da yake mahaifin ta baya nan amma sosai Jasmine tayi mutane an taru sosai wurin jana'izar Baby haka aka kaita makwancin ta na gaskiya...zuciyoyin mutane cike da alhini. Mummyn Safwan da Mimah ma tuni sun zo gidan rasuwar Kowa yaji sai jikin sa yayi sanyi, jiya-jiya yarinya na nan amma da yake ba a gayawa Allah yanda zaiyi sai gashi yau an yini babu ita...rayuwa kenan...Allah ka bamu ikon gyara kurakurakanmu kafin cikar wa'adin mu...Ameen" Su Saif ma Alhaji bai sanar da su ba da yake sun riga sun sanar da shi cewa gobe zasu iso, yaso ya hanasu ma tun safen da suka yi waya amma sam sun kafe sai sun zo sunga jikin princess 'din su..Allah sarki basu sani ba ashe Baby kam ta amsa 'kiran Ubangijin ta. Uncle Ja'afar ka'dai Alhaji Baba ya fa'dawa wanda shima sosai jikin sa yayi sanyi, lokacin da ya sanar da Anty Zainab kuwa har sai da yayi da na sanin sanar da ita cuz sosai ta tashi hankalin ta ta 'kara tashin nasa ma, kukan da tayi tunda yake da ita bai ta6a ganin tayi irin sa ba, tausayin su Deen takeyi sosai, domin tasan yanda ya 'kwallafa Jasmine a ransa...tun ranar ta gama shirin ta tace gobe zata taho Bauchi. Uncle Ja'afar bai hanata ba cuz shi da kansa ma badan aikin Bank yake ba da tare zasu taho, amma dole ne sai ya nemi izini tukunna. Hakan yasa da kansa ya shirya mata komai na tafiya zuciyar sa cike da tunani, shikan sa yana tausayin 'dan nasa, tunowa da irin yawan Pic 'din sa da na Jasmine dake wayar sa wanda kusan kullum sai yayi musu pic masu kayu ya tura musu wai su ga jikar su. Ko motar da Uncle Ja'afar ya siya masa ma sai da 'dora Baby akai tana zaune ta sha wata jar riga mai kyan gaske ya yi mata pic ya kuma sawa aka 'dauke su tare da shi ya turawa Uncle J da emojin dariya 'kasan Pic 'din yasa hope watarana jirgi Baby zata ciyo mana. Ranar Uncle Ja'afar yasha dariya a fili ya furta shai'danin yaro kawai...kar kayi fatan Allah ya azurta ka ka siya ka tsaya maula a 'kar'kashin yarinya, nan gaba ai idan kaga na siyi abu to ita da kanta zata anfanu da shi ba kai ba. Dariya shima Yah Deen 'din yayi masa...Allah sarki, ashe zaman ta tare da mu na 'dan lokaci ne. Yau gashi babu ita. Hankalin Noor bai tashi ba sai da dare yayi ta kasa bacci...idan ta rufe idanu Baby kawai take gani sai tayi saurin bu'de idanu tamkar zata ganta gaban ta amma shau babu ita, hawaye ta ringa yi tana daga kwancen take tuno maganganun da suka yi da ita da safiyar yau 'din inda tace"...Mummy ina Daddy na? Waye ya saki kuka Mummy? Anjima zan gayawa Daddy na ya rama miki kinji?...'kwalla ta share tana sake tuno lokacin da Baby tace mata" Mummy ki daina kuka..." A lokacin sosai tsigar jikin ta taji ya tashi ashe daga lokacin Baby bazata sake rarrashin ta ba, shiyasa ma ta yi ta kallon idanun ta amma bata gane komai ba duk da kallon da baby ke ta binta da shi...Ashe amsar tambayar da ta bata bata yi kuskure ba lokacin da ta tambaye ta cewa tana so su koma gida ne Baby sai tace da ita" Ni ba dake zanje ba...". Allah sarki rayuwa gashi ta dawo gidan kuma bata dawo da ni ba...shikenan bazan sake kallon ki ba  Mama na? Shikenan kema kin tafi?" "... _ban yi Pupu ba a school kuma ko fitsari ma banyi ba amma ya min tsarki mai zafi_ ..." Wannan maganar da ta tuno ne ya toni asirin kukan ta, sosai take jin ciwon wannan abin, gani take har abada babu wanda zai 'kara yi mata cutar da zata kai mata wannan abin, Sani da Ubangidan sa sun cuceta, cuce mafi tsananin ciwi a zuci, gashi sanadin su ta rasa Baby, rashi na har abada...".. Kuka sosai take yi sahf ta mance da cewar dare ne ba rana ba. Ammi ce ta ta shi ta cigaba da kwantar mata da hankali ha'de da nasiha mai ratsa jiki. Wanda tun faruwar lamarinbsai yanzu ta iya yi mata magana mai tsayi har ma da Nasiha mai sanyi. Kwana tayi tana tunane-tunane batare da ta iya rintsawa ba, ko gaisuwa idan anzo sai dai su Hafsat su amsa da su Ammi amma ita kam bata iya fa'din komai. Cikin Alhaji Baba da Ammi kuwa babu wanda ya sake waiwayen inda Yah Deen yake ko su damu da halin da yake ciki, tausayin sa ko misqala zarratin babu shi a zuciyoyin su. Da yamman ranar su  Zaidu suka iso, a bakin Safwan suka ji halin da yake ciki take kuwa sai hankalin su ya 'kara tashi, sosai suka ji mutuwar Baby har cikin jinin su, dan kuwa babu wanda be zubda 'kwalla ba, ganin basu ga 'dan uwan su bane ya sa suka tambayi Alhaji Baba sai yace da su shima be sani ba. Safwan ne ya girgiza kansa sannan yayi musu bayanin komai ganin kamar hankalin su ya tatshi da rashin ganin san, zaton sa ko sanar da su in zai sa su samu natsuwa. Ai kuwa take ya 'karya ta batun sa dan kuwa kuka suka ringa yi kamar 'kananun yara, abin duk ya musu bazata, da yake su sun taho ne kawai jin cewa Jasmine tayi accident amma har suka iso basu san cewa already ta rasu ba, basu gama wancan jimamin ba kuma ak 'kara musu da wani sai kuma 'dan uwan su na can jikin na'urori bai ma san da batun rasuwar Baby ba. Zaid kam bai iya ya motsa zuwa ko ina ba,  ya zauna a wurin karban gaisuwa, cikin ransa yake ro'kon Allah akan ya tausayawa Yah Deen ya sassauta masa wannan abin, gani yake tamkar sun yi masa yawa damuwan dole zai illata shi, tun ma bai san da batun jinyar baby ba gashi ya shiga coma ina ga yasan cewa Precious Babyn sa ta tafi ta bar shi...tausayin sa sosai Zaid yake ji yayin da wani 6angare na zuciyar da ke  jin haushin Yayan nasa da ya 'dauki drivern da be iya tu'ki sosai ba gashi ya salwantar musu da rayuwar Yarinya a banza...a ganin Zaid kamar rashin iya tu'ki ne ya kawo accident in. Saif kam kasa natsuwa yayi domin dauriya yasawa zuciyar sa ya danne komai ya danne damuwar rashin Baby musamman da yasan cewa ko ya damu kansa ma Jasmine ba dawowa zatayi ba so da me rai ake yi dan haka hankalin sa duk ya tattara ya dawo da shi kan 'dan uwan sa...cikin zuciyar sa yake juya amsan da Alhaji Baba ya basu game da Yah Deen in, dole yasan akwai wani abu amma haka kawai Alhaji Babab bazai ce bai san inda yake ba bacin zaman kar6an gaisuwan 'yar sa ake yi, babu ammaki akwai laifin da yai masa shiyasa har ya fa'di hakan game da shi. Abin sosai ya dame shi, Zaid kam ma ko aka bai sa ba, balle yayi wani tunani akai. Saif ne ka'dai yaje har asbitin ya dubo shi a daren ranar batarecda ya bari ya kwana ba, wanda har a lokacin ma ya tarar da shi ne bai san waye akan sa ba...duk yanda ya so ya danne batun rashin Baby amma ya kasa, sosai yake ji da Jasmine yake sonta fiye da yanda yake son kansa, hakan yasa tunanin ta kan yawaita zuwa brain 'dinsa lokaci kan lokaci zaki ga yana share hawaye da fatan Allah ya ji'kan ta, ashe haka rayuwa take?" Sani ma tuni ya farfa'do yayin da Dr.Felix ya cigaba da bashi kulawa,  cikin sa'a akayi aikin kuma anyi nasara sai fatan Allah ya kiyaye na gaba...sani.ya zama mai hannu 'daya, sa'an sa 'daya ma hannun hagun aka cire aka bar shi da dama. Tunda ya farka kuwa hawaye yake zubdawa,.nadama sosai ya shige shi matsannanci, da kansa yake Allah wadai da halayyar sa, yasan idan Umman sa taji abinda ya aikata ma da 'kyar ne idan zata yafe masa...kaico na...na bi son zuciya gashi ta kaini ta baro ni...sai gashi tun a duniya naga sakamako na ..Yah Allah ka yafe min, Yah Allah ka ji 'kaina, ka bani lafiya ka kuma bani 'kwarin gwiwar da zan iya dur'kusawa gaban oga Deeni in nemi yafiyar sa bisa cin amanar da nayi masa, in ce Maman Baby ta yafe min raina mata hankali da nayi, In ro'ki Jasmine tai min afuwa badan hali na ba, nayi al'kawarin zame mata bawa har 'karshen.rayuwa ta matu'kar zata yi min afuwa ta yafe min abinda na yi mata.." Kuka yake yi sosai wanda ya rasa mai lallashin sa, bashi da kowa da zai ce masa kayi ha'kuri daga shi zai tarin nadamar sa a zuci. Washe gari Sai ga Su Ishaq tun daga Maiduguri inda sun taho dan Alhaji Baba da kansa ya sanar da Ishaq rasuwar Jasmine cus duk cikin abokan Deen Ishaq yafi kwanta masa sosai. Tare suka taho da su Imam, Anas da wasu daga cikin abokan su na makaranta da duk ya sanar mawa. Kowa yaji labarin rasuwar Baby da kuma rashin lafiyan Mu'een Noor ake fara tausayi,  saboda dole ansan sai ta shiga wani hali sakamakon rashin 'yar ta ga kuma ga Miji can kwance shima rai a hannun Allah. Kwanan sa biyu kafin ya dawo hayyacin sa..da salati abakin sa, abu na biyu da ya ambata shine sunan Noor followed by 'yar sa Jasmine... Safwan aka yi saurin nemowa yazo lokacin da ya iso hannun Yah Deen dafe kansa yana yayyamutsa fuska duk jikin sa wani iri yake jin sa...yana jin muryar Safwan sai yace"...Kaina Safwan ciwo". Matsawa Safwan yayi kusa da shi yana yi mar sannu tare da nema masa sau'ki daga wurin Ubangiji. Bai jima da farkawan ba sai ga Saif ma yazo dam baya iya yin awa biyar masu kyau batare da yazo yaga halin da 'dan uwan sa yake ciki ba. Sosai yake bashi tausayi dan yasan a zahiri Yah Deen sai yafi kowa jin ciwon mutuwar Baby Jasmine. Tausayin 'dan uwan nasa ne ya sanya shi kuka yana tsaye daga bakin 'kofa yake share hawaye, Yah Deen sai tsura masa idanu yana kallon sa da lumsassun idanun sa amma bai furta masa komai ba. Ganin hakan ne yasa a hankali Saif ya 'karaso ya matso kusa da shi sannu yayi masa cikin tausayawa yana me kawar da kai dan baya so ya fahimci halin da ake ciki tun yanzu. Baya jin ciwin komai sai 'kirjin sa ka'dai da yayi masa nawi sai kuma kansa jikin sa dake ciwo kuwa yasan ba komai bane face gajiya da kwanciya wuri guda da yayi, dan haka da kansa ya yun'kura ya tashi ya zauna, cire zcannular dake hannun sa yayi...Likitan sa da Safwan na yi masa fa'dan baya bin ka'ida kamar be san dokar aiki ba. Ko tanka su bai yi ba, a fa'dar su ma wai ya tsaya tukunna a gama tabbatar da sau'kan ciwon kafin ya tashi..." Kaina ka'dai ke min ciwo..". Daga fa'din hakan bai damu ba kawai ya tambayi Safwab iya kwanakin da yayi a kwance Safwan yayi masa bayani sai ya jinjina kai tare da mi'kewa tsaye ya nufi bayi da dubara ya 'dauro alwala ya fito. Haka yayi sallolin sa batare da jan dogin surori ba dan jiri baya barin sa 'kafar sa ma rawa take yi masa sosai...idan yayi sai ya tsaya ya huta kafin yake cigaba da jerowa. Saif ne ya tsiyaya masa fresh milk mai 'dan sanyi ka'dan amma ya 'ki sha shi wai Coffee zai sha, duk yanda Safwan yayi 'ko'karin nuna masa muhimmancin shan fresh milk in ammaYah Deen 'kin amincewa yayi..sai da yaga Saif na hawaye kafin ya ansa ya 'dan sha yana kawar da kansa. Dole tasa Safwan ya aika  aka kawo masa Coffee 'din dan ya lura Mu'een taurin kai ne da shi da kafiya, yanayin abinsa kamar Noor, itama haka bata jin magana wani lokacin, wanda duk bai san hakan ba sai yanzu da zama ya ha'da su a asbiti yasa ya 'dan fahimci wasu halayyan ta, sosai take da taurin kai irin na Mu'een, gashi ba ta jin lallami idan ranta ya 6aci. Cikin sa'a kuma ma ba'a jima ba sai gashi an kawo masa kafin hakan kuwa 'karasar da jerin sallolin dake kasan yayi. Sai da ya idar kafin Saif ya gabatar masa da Coffee 'din ya kar6a ya sha abin sa cikin kwanciyar hankali, banda 'yar rama da yayi babu abinda zaka gani ajikin sa kace shine marar lafiyan..domin ya 'dan warware. A hankali yake sipping yana tunanin halin da iyalan sa ke ciki, Saif kam ba 'karamin farin ciki yayi da farkawar 'dan uwan nasa ba sai dai ta wani 6angaren tausayin sa yake ji matu'ka, yasan jin labarin mutuwar Baby shine zai zame masa wani babban illar kuma idan ba ayi sa'a ba...gashi Safwan ya garga'de shi da cewa kar ya sanar da shi tun yanzu su bari tukunna sai ya 'kara samun natsuwa. Yana cikin sipping Coffee 'din ya dubi Safwan yace" Ya jikin Baby ne..Allah yasa dai ta warware yanzu...". Shiru Safwan yayi yama rasa ta inda zai fara yi masa bayani. Saif kam 'kasa yayi da idanun sa kafin Safwan yayi magana kuma sai ga su Ishaq sun shigo da sallamar su. Cikin natsuwa duk yake duban su, har cikin ransa ya ji da'din zuwan su. Yayin da suma sukai matu'kar farin ciki da ganin sa a zaune cus jiya bayan isowan su sun zo amma a lokacin bai tashi ba sai gashi kuma yanzu cikin sa'a yana zaune had da cup a hannun sa da alamu jiki yayi sau'ki. Hannu suka zo suka bashi suna yi masa ya jiki tare da gaisawa da Safwan. Deen yana murmushi yace" Lalle Maman Daddy 'yar gata ce, kardai duk saboda duba jikin Baby kawai kuka zo all the way from Borno State?..". Murmushi Ishaq yayi tare da zama gefen sa yana cire hular kansa. Ganin yana shirin zama ne ya sanya Yah Deen saurin fa'din" A a ku tashi muje Please nima nan da kuke gani ba 'karamin 'kaguwa nayi da ganin su ba...". Hakan da ya fa'da ne ya sanya Ishaq saurin fahimtar cewa har yanzun bai san halin da ake ciki ba kenan... Fuskar sa ya kalla sannan yace" Kar ka damu ai zamu...amma gama cin abincin naka tukunna". Yamutsa fuska Deen yayi yana fa'din" Ai na gama..ya ishe ni fa dama, tun 'dazun su Saif ke 'duramin madara kamar wani 'karamin yaro..." Yayi maganar yana murmushi tare da ajiye cup in hannun sa a gefen sa. Maganin sa Safwan ya 6allo ya bashi inda shi kuma yana murmushin yace" Safwan sarkin dubara so dai kake sai na 'kara sha kenan..?". Da haka ya kar6i maganin ya sa abaki sannan yabi bayan sa da Coffee 'din, dire cup 'din yayi yana sau'ke ajiyan zuciya...yana duban hannun sa inda aka 'daura masa canular ya shafa a hankali cuz 'kai'kayi wurin ke masa. Yun'kuri yayi yana shirin mi'kewa amma sai Ishaq ya dakatar da shi...da fa'din" Magana fa nazo muyi da kai". Koma wa yayi ya zauna yana fa'din" Okay ka hanzar ta, na 'kagu inga iyali na..". Cikin ransa ya ayyana ba mamaki shima yaji labarin abinda ya faru ne, nasan kowa ma tsana ta zai yi yanzu". Nasiha Ishaq ya fara yi masa cikin natsuwa har ya gangaro kan batun rasuwar Baby...Yah Deen kam tsura masa idanu yayi ganin kamar da gaske yake yi bada wasa ba ya sanya Yah Deen juyawa ya ringa binsu da kallo 'daya bayan 'daya. Kansa yaji yana juya masa sai ya lumshe idanu" Ishaq kasan bama irin wannan wasan da kai ko?" " Ana wasa da mutuwa ne Mu'een?" Imam ya bashi amsar tambayar sa da wata tambayar. Bai damu ba da wata raunanniyar murya yana dafe da kansa yace" Safwan dagaske Jasmine ta rasu? Dagaske Baby ta tafi ta barni?" Safwan matsowa yayi daf dashi dan yayi masa bayani cikin natsuwa yace" Jasmine ta rasu Mu'een, tun ranar da su Ammi suka zo bata 'kara kwana da rai ba, idan baka manta ba ranar shine kaima aka kwantar da kai anan 2days kenan yanzu...". Jajayen idanun sa ya bu'de ya sau'ke su kan fuskar Safwan yayin da ya cigaba da fa'din" ha'kuri zaka yi Mu'een ha'ki'ka rasa Jasmine babban rashi ne mai ta6a zuciya amma babu wani abinda zamu iya aikatawa tunda muma 'din duk shi muke jira..." A fizge ya furta Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...kansa ya fara girgizawa a hankali da sanyin murya yace" Ishaq...Nuree fa wani hali take ciki? Ku tashi ku kaini gida please..zan je in duba ta, nasan hankalin ta tashe yake sosai yanzu, kuma ina so in ro'ki Ammi ta yafe min Alhaji ma yayi fushi da ni..yace babu shi babu ni.." Kuka Saif ya fara a hankali dama yasan dole akwai wani abin tsakanin sa da mahaifin su, Yah Deen duban sa yayi da riannanun idanun sa yace" Saif dagaske ne Jasmine ta rasu..?" Bai iya ya bashi amsa ba dan kuka da yaci 'karfin sa. Yayin da Yah Deen ya maida idanun sa ya rufe..ko ina jikin sa ji yayai yana masa gudu, yayin da bugun zuciyar sa ya tsananta ya sosai...amma duk da hakan fa'di yake su kaishi wurin ahalin sa, yana so yaga iyalan sa. Basu yadda sun tafi ba har sai da liktan sa ya basu dama domin yace ciwon nasa tashi yake yi idan ya riga ya sau'ka kuma shikenan dan haka discharging nasu yayi ya 'kara da fa'din idan akwai wata matsala suyi saurin tuntu6ar sa. Godiya suka yi tare da kamo hanyar gida dukkan su hadda Safwan dan shima tun lokacin da aka kwantar da Jasmine har zuwa yau 'din bai huta ba. Cikin motar yake gayawa Ishaq cewa" Nuree tace wai har abada bazata yafe masa ba, ka taimake ni Ishaq wallahi bazan iya rayuwa babu ita ba..itace farin ciki na bana so in rasa ta kamar yadda na rasa Baby Ishaq". "Kar ka 'daga hankalin ka please Mu'een, Noor mai ha'kuri ce na tabbata zata yafe maka duk abinda kayi mata Insha Allahu". Abinda kawai Ishaq yace kenan har suka isa gida, yayin da Saif ke share hawaye a 6oye, tausayin 'dan uwan sa yake ji sosai...aganin sa abubuwan sun yi masa yawa ma. Da isar su 'kofan gidan nasa sai jikin sa yayi sanyi 'kalau bai iya ya sake furta komai ba har suka fiffito daga motan, a hankali ya ringa bin mutanen dake zaune da idanu, hadda abokin Uncle Ja'afar ya gani a wurin zaune wanda ya bashi aiki anan asbitin da ya bari a bauchi, Babban mutun ne mai fa'da aji amma gashi zaune 'kofar gifan sa tare da mahaifin sa wurin kar6an gaisuwar 'yar sa Jasmine, da 'kyar yake 'daga 'kafafun sa amma ya daure suka 'karasa wurin jama'ar, da yawa sun yi farin ciki da ganin ya taho da 'kafafun sa domin duk sun san halin da yake ciki a gadon asbitin...cuz Safwan na kawo musu labarin halin da ake ciki dan su kwantar da hankalin su. Kowa gaisuwa ya ringa mi'ka masa yayin da shima ya mi'ka gaisuwa ga manyan sa su Alhaji da sauran su, Alhaji Baba a takaice ya amsa masa gaisuwar batare da yako nuna kulawa ba, shi da kansa ya sani shi mai laifi ne a wurin Alhajin dan haka bai damu ba, so yake su ke6e ya samu daman da zai 'kara neman afuwar su. Bai samu ya shiga cikin gida ba sai da yamma lis wannan ma Safwan ne ya matsa masa akan su shiga ya watsa ruwa ya canza kaya, haka ya shiga ya watsa ya canza wasu kayan sannan ya fito suka yi sallar maghrib da Isha'i...fuksar sa fayau jin kansa yake yi kamar bashi ba, sam baya jin wani nauyi tattare da jikin sa, illah 'kafafun sa dake yi mai nauyi. Cikin gida suka koma wanda sai a lokacin ya shiga ya gaida su Ammi, itama 'din babu yabo babu fallasa ta amsa shi, haka ma Nuree, abin kuma sai ya fara sashi yana jin wani iri, me yasa bazasu tausaya masa ba ko dan rasa Baby da yayi? Antyn sa Zainab ita ka'dai ce ta amsa masa gaisuwa da tausa sashshiyar murya har ta 'kara da kwanatr masa da hankali... haka ya tashi sum-sum ya fita yana jin babu da'di cikin ransa, itama Anty Zainab in may be da tasan halin da ake ciki yasan da 'kyar ne idan zata kula shi.. Wahshegari akayi sadakan uku da bakwai aranar kuma Alhaji Baba suka koma gida shi da wa'danda suka zo daga Shuwarin gaisuwa..wanda kafin tafiyar sa sai da ya bawa Ammi umarnin ta tafi masa da 'yar sa bai amince Noor ta 'kara ko da kwana guda ba ne  tare yake so su koma gida. Ammi jinjina kai kawai tayi bata sanar da kowa batun Alhajin ba kawai ta ri'ke cikin ranta, dama ko be fa'da ba bata da niyyan sake barin Noor zama tare da Deen yanzu. Duk mazan sun tafi Illah 'yan biyun Ammi suka rage. Gidan sai ya zama daga ni, Ammi, Anty Zainab, Ummah ta sai Addah Maryam da suka daga baya. 'Yan biyun Ammi ma washegari suka koma dayake suna makaranta ne dama daga can suka taho...Ummah ta ma ranar da su 'yan biyu suka tafi a ranar su Ummah ta ma suka koma wanda da kuka muka rabu rabu da su, Ummah ta na ta yi min nasiha akan tawakkali, ita kanta cikin idanun ta idan ka kalla damuwa ce fal, tausayi na take ji sosai.     Dan ma har suk koma basu ji labarin abinda ya faru ba, an dai sanar da su gaskiyan case in Baby  wanda hakan ne yasa Ummah ta tsanannin tausayi na, shiyasa ma take min nasiha da tawakkali a ganin ta Allah ya jarabce mi da auren mutun irin Yah Deen, dan kowa idan yaji abinda ya samu Baby ya kuma san asalin waye Mu'een cewa yake yi sakayya ce kawai Allah ya nuna masa ba komai ba. Shiyasa da dama ke tausayi na. Anty ma da farko bata san ainahin abinda ya faru ba ita dai kawai jimamin rasa Baby ne yafi damun ta dan sosai rasuwar Baby ya ta6a ta. Kuma Ammi bata sanar da ita saboda taga hankalin ta atashe yake sosai, duk sai ranar da ta sanar da su Ummah ta kafin itama taji abinda ya faru. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *80* Rungume ni tayi tana hawaye, Anty yanzu ko dogon magana bata iya yi, ko ina ka ganta shiru zaka ganta a zaune tana tunani, sosai take jin mutuwar Baby cikin ranta. Sati guda naji Ammi na fa'din zasu yi kafin su koma, dan haka tun daga lokacin nima na fara kimtsa kaya na a 6oye batare da na bari sun sani sani ba, tunani idan su ka san niyyata 'kila su dakatar da ni d wannan kalmar ta ha'kuri, ni kuwa a yanzun sam bazan iya ba na riga na yanke abinda nake ganin ya fimin.   Ana gobe su Ammi zasu tafi na je na bu'de akwati guda ina jera kaya na,  'ko'karin zugewa nake yi sai ga Anty Zainab ta shigo ta same ni. Da mamaki ta tsura min idanu tana kallo na dan ita bata san dalilin da zai sani shirya kaya ba. Tambaya ta tayi" Me zakiyi da kaya har haka kuma?" Ina tayi maganar da alamun mamaki 'karara kan fuskar ta. Tun lokacin da naji motsin shigowan ta sau 'daya tak na 'daga idanu na na kalle ta daga hakan ban sake ba, sai ma na fara jin hawaye na taruwa min. Ko yanzun ma da tayi min tambayar ban 'daga kaina na dube ta ba nace" Gida zan koma Anty...tare zamu tafi da ku...". Na 'karasa maganar da muryar kuka. Shiru Anty Zainab tayi tana duba na jikin ta sanyi 'kalau a hankali ta mi'ke ta fita, bansan me taje ta gayawa Ammi ba sai ganin ta nayi ta shigo bayan fitan Anty Zainab bada jimawa ba. Lokacin har na gama harha'da kayan ina tattare kayan dake kan mirror na. Sunana Ammi ta 'kira da raunanniyar murya sai na waigo na dube ta batare da na amsa ba, 'lasa nayi da idanu na kawai wanda take naji zuciya ya fara dukan uku-uku, Addu'a nake a raina Allah yasa Ammi kar ta hanani barin wannan gidan, a hankali na 'karasa gaban ta na dur'kusa tuni idanu na sun cika da hawaye, 'kasa nayi da kaina batarexda iya duban fuskar ta ba, hawayen da suka taru min ne suka yi saurin gangarowa na kai hannu na share su, duk abinda nake yi Ammi bina kawai take da idanu bata cecda ni 'kala ba. Hawaye na ne suka dinga gudu akai-akai ina share su na fara ro'kon ta" Dan girman Allah kar ki hanani tafiya tare da ku, Ammi ban jin zan iya sake rayuwa a garin nan  kar ki dakatar da ni dan Allah. Ammi ban ta6a neman wani abu na rasa ba tun tasowa ta saboda baki rage ni da komai ba girma na har kuwa yau 'din nan Ammi nasan kin wadata ni da komai, amma yau ka'dai ina neman alfarmar ki Ammi, yau ka'dai ina ro'kon ki  ba wai dan kin kasa ba sai dan ki cika min buri na kawai dan Allah ki barni in tafi. Wallahi Ammi bazan iya sake rayuwa inyi farin ciki ba matu'kar ina tare da Yah Deen...ban tsane shi ba amma na tsani rayuwa ta tare da shi, na tsani in sake gani na 'kar'kashin inuwar gidan sa, idan nace zanci gaba da zama anan wata'kila nima gawata zaki zo ki tarar Ammi...dan girman Allah badan ni ba ba dan bana son Yah Deen ba ki ce ya sake ni..Ammi". Kuka sosai ne ya ci 'karfin ta ta kwantar da kanta kan 'kafafun Ammin tana kuka sosai. Ita kanta Ammin ji tayi zuciyar ta ya karye sosai, ha'kika ha'kurin ta ya kai ma'kura tunda har ta iya bu'dan baki ta sanar da ita abinda ke ranta, a hankali Ammi ta dur'kusa sannan ta 'dagota ta rungume ta ajikin ta tana bata ha'kuri tace" Daina kuka kina damun kanki...da kaina ma ko baki ro'ke ni ba ba iya tafiya zan yi in sake barin ki tare da shi ba, shakka nake ji kar ki 'ki amincewa shiyasa na kasa fa'da miki amma ni na riga na yanke hukuncin raba shi da ke....domin hankali na zai fi kwanciya idan nasan cewa baki tare da auren sa, ha'kurin da kika yi masa abaya ma ka'dai ya isa bana fatan ki sake kwatanta irin wannan zaman har abada, tsananin tausayin ki ke hana ni magana 'yata shekarun ki sunyi ka'dan da wa'dannan abubuwan..." Da haka ta ringa lallashi na har ta samu nayi shiru yayin da tsananin farin ciki ya lullu6e ni jin cewar Ammi na ma ta amince da tafiya ta. Har sallar Isha'i a 'daki na muka yi shi ni da Ammi, da kanta ta nemo Biro da Memo ta ajiye akan side drawer sannan ta 'daga wayar ta ta 'kira Yah Deen..fuskar ta ka'dai idan ka kalla zaka san ranta 6ace yake da shi. Daga can 6angaren da yake ba 'karamin da'di yaji ba da ganin 'kiran Ammi a wayar sa, zaton sa ko itan ta sau'ko ne dan Alhaji Baba ko sauraran sa be yi ba kafin ya tafi da suka je da Ishaq bashi ha'kuri. Da farin cikin sa yayi sallama bayanvya 'daga 'kiran Ammi ko amsa shi bata yi ba kawai ta tsuke fuska tace" Meet me..". Wani ras zuciyan sa ya tsinke tun daga kansa har tafin.'kafan sa yaji wani yir saboda gudun da jinin sa yayi a lokacin, ko daga jin yanayin muryar Ammi ka'dai ya san da akwai matsala babba. Shi ka'dai ne kwance a 'dakin sa, cuz duk ba'kin sa da suka zo sun koma garuruwan su, dama kwance yake yana tunanin ta inda zai fara shawo kan iyayen sa su yafe masa, a ganin sa 6angaren Noor da sau'ki baya jin ta ita kamqr yanda yaga su Alhaji sun 'dau zafi kan maganar, shi ka'dai ya san me yake ji a zuciyar sa dan har a lokacin babu abinda ya canza daga ciwon dake damun sa a 'kirji gashi kuma ya'ki komawa asbiti balle ya samu kulawa, magungunan sa kawai ya cigaba da sha batare da ya koma an sake duba matsayar lafiyar tasa ba. Tafiya ma ba ya iya mi'kewa idan zai yi ta kawai wani sa'in daurewa yake yi yana yi tamkar bai jin komai. 'Kiran da Ammin tayi masa sai ya sa shi jin wani ras a zuciyar sa da ya haddasa sabon yanayi, har jiri yake ji na kwasan sa dan yasan dole there must be something da shi bai sani ba. A hankali ya mi'ke amma ganin idanun sa na barazanar daina gani ne ya sashi komawa da sauri ya zauna yana dafe kansa dake barazanar tarwatsewa, sara yake yi masa tamkar wanda ake buga abu akai idanun sa duk sunyi laushi ga jiri dake kwasan sa idan ya mi'ke. Ya 'dauki tsawon sakanni a hakan kafin ya sake yun'kurawa ya tashi yana waro idanun sa da 'kyar, da dubara da bin bango ya samu ya isa parlour yana tanga'di tamkar 'dan maye. Antyn sa Zainab na ganin sa tayi saurin mi'kewa cike da kulawa take tambayar sa me kuma ya same shi. Batare da ya dubi fuskar ta ba yace" Kar ki damu Anty Bakomai, Ammi ce tayi 'kira na..." Tun ma kafin ya rufe baki ta nuna masa 'dakin da Ammin ke ciki. A hankali ya taka ya shiga 'dakin da sallamar sa, yayain da Anty Zee ta bishi da kallon tausayi, a 'dakin babu wanda ya amsa shi illah Ammi da ta amsa sallamar ciki-ciki ko sautin muryar ta ma bai ji sosai ba. Idanun sa da su gani sosai in ya tsurawa Noor ganin yanda duk ta rame cikin sati guda kacal, koma me ya same ta yasan laifin sa ne, da idanu yake nuna alamun tausaya agare ta har da karkata wuyan sa gefe yana duban ta, amma Noor bata jira ganin hakan ba tayi saurin kawar da kanta gefe tana share siraran 'kwalla dake bin kuncin ta. Mu'een be wani damu da hakan da tayin ba cuz yasan itama fushi take yi da shi, fatan sa Allah yasa Ammi sulhu zatai musu tunda yaga Noor zaune tana kuka 'kila ba'a son rqnta bane. A hankali ya 'karasa gaban Ammi ya dur'kusa ya gaida ta muryar sa na sar'kewa, haka Ammi amsa shi a ta'kaice a fili zaka fahimci ba har zuciyqr ta take yi masa maganan ba saboda yanayin da take nunawa. Hannu ta 'kai ta dauko memo da biro 'din da ta ajiye ta mi'ka masa batare da ta furta masa komai ba. Deen da bai san manufar hakan ba sai bai yi musu ba yasa hannu ya kar6a yana mai duban fuskar ta da alamun neman 'karin bayani sam bai kawo faruwar wani abu mummuna cikin ransa ba. Idanu Ammi ta lumshe cike da 'dacin zuciya, sosai take son Mu'een take ji da shi, take kuma 'kaunar ganin farin cikin sa akoda yaushe har a zuciyan ta take jin da'di a duk lokacin da ta fahimci yana tare da walwala, amma babu yadda zata yi halayyar sa yasa dole ne tayi abinda ya dace da shi ko da hakan na nufin tashin hankalin sa ne, ko  tilasta shi ne dole tayi ko dan gudun 'daukan alhaki ma. Fes ta bu'de idanun ta akansa suka ha'da idanu a hankali cikin muryar natsuwa tace da shi"...Ina fatan da kanka ka shiryawa wannan ranar Mu'een? hope ka riga kasan mai zai biyo bayan cin amanar da ka jima kana yi mana...?" Kallon Ammi yayi kawai yana mai jin nauyin abubuwan da suka ta yaudaran sa wurin mata har ya kasa tsaida hankalin sa wuri guda, ya kasa tsaida zuciyar sa da gangan jikin sa wurin matar da Allah da kansa ya za6a masa isa batare da wayo ko dabarar sa ba, sai dai har yanzu bai fahimci me Ammi take nufi da dam'ka masa littafi da al'kalami ba, bai san me zai yi da su ba sam.        Sannan shi bai shiryawa faruwar komai ba hasali ma shi bai ta6a kawo faruwar wani abu makamancin hakan da ya riga ya faru cikin ahalin sa ba...sai dai maganganun Ammi sun masa karan tsaye, sosai hankalin sa ya kasu kashi-kashi ya shiga nemo ma'anar su, kuma har lokacin batun saki sam bai zo kansa ba...illah zuciyar sa dake faman lugude na tashin hankali. Yanzu kam bai ga wani alamar sulhu da yake tunanin Ammi zata yi tsakanin sa da Noor ba... A hankali ya sau'ke idanun sa kan littafin dake ri'ke a hannun sa yayin da Ammi ta cigaba da fa'din"...'Kauna da mutuntaka yasa aka 'dauki auren Hudah aka baka kasani Mu'een ba wai dan ka isa ba, amma kayi watsi da komai, ka bi son zuciyar ka baka damu da halin da na kusa da kai zai iya tsintan kansa ciki saboda damuwar ka ba, musamman ma iyalin ka, bansani ba ko dan kana ganin baka sha wahala kafin ka same ta bane shiyasa oho..cuz na tabbata da da kanka ka nemi auren ta bazaka dinga yi mata hakan ba, if zan tuna lokacin da ka fara jin.soyayyar Amina a zuciayr ka a lokacin kusan zaucewa kayi, ba mamaki da itama Noor in ka wahala wajen neman auren ta da bazaka yi mata irin wannan cin zarafin ba...sai dai ka sani idan baka son ta ni ina son kaya na, Mahaifiyar ta da dangin ta duk na son ta ba zai yiwu mu zuba maka idanu kana azabtar mana da zuciyar ta ba while tana da gatan ta, dubi yanda duk ta lalace kuma na tabbata duk damuwar ka ce ba komai ba, ni kaina nasan yarinyar nan tayi ha'kuri da kai matu'ka, tunda kuwa har aka zo wannan gandun nasani mai iya zama da kai sai yayi ha'kurin ya kai a buga misali da shi, a kulumm idan na tambayi yarinyar nuna min take babu matsalar komqi duk wai dan ta rufa maka asiri, ba'kin halin ka da rashin wayo bai sa ka fahimci rashin walwala da yarinyar nan ke ciki ba saboda ka 'dauki hankalin ka gaba 'daya ka dam'ka a hannun matan banza, da aure ka ce zaka yi Mu'een wallahi ko ni bazan hana ka ba, amma madadin.hakan bige da biye-biyen mata sai kace wani.bunsuru, kai ko.kunyar Allah ma baka ji? yarinyar nan koda wasa bata ta6a kawo min 'karar ka ba bata ta6a nuna min ko alama cewa bata jin da'din zama da kai ba, ta rufa maka asiri Mu'een wanda ko mu iyayen ka da muka haife ka iya ka rufin asirin da zamu iya yi maka kenan a wannan duniyan,  amma duk ka san hakan ka kuma yi watsi da shi ka cigaba da cutar da ita saboda son zuciyar ka. Bazan hanaka ba, rayuwar ka ce, iya ka ta da kai a kullum in nuna maka cewa sa6on Allah kake yi ba bakomai ba, sai dai ko yanzun nasan ka fahimci cewa ba'a aikata Zina ya kuma tafi abanza, kayi ne kaina ka jira ranar faruwan naka..ai kaga misali 'daya, idan kuwa kace ba zaka bar 6ata yaran mutane ba haka kaina.zaka yi ta haifa ana  lalatawa...". Da sauri ya 'dago ya dubi Ammi zuciyar sa cike da rauni...a ganin sa bai kamata Ammi ta fa'di hakan ba saboda ita Uwa ce agare shi...me yasa bazata banbance tuban sa na da da na yanzu ba, ji yake da ana iya bu'de zuciya da ya bu'de mysu yanda yake game da rayuwar sa na baya, sosai yayi nadama ta gaskiya baya jin akwai ranar da zai sake komawa wancan rayuwar har abada..yana cikin tunanin ya fara jin hawaye na tauruwa masa kuma still bai daina kallon Ammi..gani yake kamar zata iya karantar zuciyar sa a fuskar sa. Idanun su sar'ke da juna Ammi ta cigaba da fa'din" Yes..i mean it..fa'dar Allah ce ba ni ba, kuma ko yanzun sai dai ince Alhamdulillah cuz i know zuwa yanzun da kanka kasani ba sai an sake maimaita maka ba, in da akwai dattako ma kai ne ya kamata ka zaunar da mutane kana yi musu nasiha akan irin hakan amma tunda ka za6i rayuwar jind'adi fiye da tsoron Allahn ka shikenan, kaje kayi tayi, ni nasan akwai ranar nadama tana tafe, domin ina da ya'kinin cewa har yanzun baka 'dauki darasi cikin abubuwan da suka faru ba, yau gashi kana ji kana gani babu Baby ta koma ga Ubangijin ta inda ta tafi da mummunan tabon da halayyar ka ya ja mata...akan hakan ka'dai ma bana jin har abada zan iya yafe maka Mu'een sam naji ka fice min arai na...nd bazan iya barin yarinya ta ta mutu da ciwon zuciya ta sanadin ka ba...ha'kurin ta ya riga ya kai ma'kura ta yanda ko ita da kanta ta nemi sake zama da kai ma bazan amince ba bazan barta tana gida zaman bautar aure kaje can gantalin ka ka kwaso mata wata cutar ba....i just want u to open this book now ka rubuta min sakin 'ya ta...". Wani ras yaji a dukkan ilahirin jikin sa ya amsa, lumshe idanu yayi da 'karfi hawayen sa suka gangaro a fili ya furta Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un... tunda Ammi ta fara magana sai yanzun hawayen sa ya gangaro. Idanun sa ya bu'de ya zuba akan fuskar Ammi suka ha'da idanu...wanda ganin hawayen nasan bai sa ta fasa niyyar ta ba sai ma cigaba da tayi da fa'din" Ka sakar min.'yata sai ka je kayi ta jin da'din.rayuwar ka kai ka'dai, duk ranar ka tabbatar nadama ta shige ta gaskiya sai ka zo ka tabbatar min in gani.may be a lokacin zan iya yafe maka...but for now banda case da kai da kai bama na jin ka matsayin 'dan da ni na haifa..." Zaro idanun sa yayi da kayu yana duban Ammi, harshen sa yaji yayi masa nauyi sosai, wai shi Ammi ke wa irirn wa'dannan mugun kalaman? Ga Noor ya maida kallon sa sai yaga kanta ma kife yake kan cinyoyin ta  kuka take yi sosai har da sheshshe'ka.... Yun'kuri yayi da niyyan tashi ya isa gare ta sai Ammi ta dakatar da shi a tsawace. Kallon fuskar ta yayi yana girgiza kansa wasu siraran hawaye na bin kuncin sa yayin da hannun sa 'daya ke dafe kan 'kirjin sa da yake jin tamkar zuciyar san fa'dowa zata yi bisa hannun sa. Bai san me ze ce da Ammi ta yadda da shi ba, Noir ce ka'dai yake da tabbacin zata fahimce shi but yaga itama tana kuka. Kallon Ammi ya sake yi 'kwalla na zubo masa masu zafi sosai...a hankali ya fara takawa ya  'karasa wurin ta wannan karon Ammi bata hana shi ba. Kafa'dar ta yayi niyyan kamawa da niyyan ro'kon ta ta taya shi yiwa Ammi bayani ko zata fahimce shi da kyau fatan sa Allah yasa itama ta yafe masa su sake shimfi'da sabuwar rayuwa..." Cikin zuciyar sa yake wannan tunanin but bakin sa ya kasa furta komai..ji yake tamkar an tokare shine daga 'kirjin sa numfashin sa ma da 'kyar yake fita. Ga mamakin sa sai yaga yana ta6a jikin Noor ta firgita tamkar an tsikare ta ta mike tsaye tana banka masa hararan ta6a mata jiki da yayi. Murmushi Ammi tayi domin ba'karamin birge ta Noor tayi ba dama tasan hakan na iyq faruwa tunda ita ce da kanta ta nemi rabuwa da shi, shiyasa ma Ammi ta barshi ya isa garetan dan ya tabbatar wa kansa da kansa. Shi kam cikin zuciyar sa yake furta" Ki yadda dani Nuree wallahi ni mai 'kaunar ki ne, bazan ta6a ha'da ki da wata cuta ba, soyayyar ki daban take a zuciya ta, ban ta kwatanta 'kaunar da nake yi miki da wata macen daban ba kuma har abada bana jin zan iya ha'da ki da wata, Deen 'din ki ne Yayan ki dan Allah ki bu'di ki wakilce ni wurin Ammi ki fahimtar da ita cewa nadamar gaskiya nayi, tayi ha'kuri kar ta raba ni dake na rasa Baby bana so.kema in rasa ki Nuree, ki ce min ta yafe min laifuka na Insha Allahu bazan sake 6ata mata rai ba har 'karshen rayuwa ta..." He wish a fili ya iya furat hakan amma harshen ya kasa yi mai motsi duban ta kawai yake da idanu zafin zuciyar sa na 'karuwa. ..Gaban sa Ammi ta tako ta tsay nesa ka'dan da shi, hannun Noor ta ru'ko cikin nata ganin kallon da yake yiwa Noir ne ya sa Ammi nuna shi da 'dayan hannun tan sannan ta nuna inda littafin ke ajiye tace" Kai nake sauraro...". Bisa gwiwoyin sa ya sulale yana hawaye ya dafe kansa da dukkan hannuwan sa biyu kuka yake yi mai matu'kar tsuma zuciya da 'kyar ya samu bakin sa ya bu'du ya furta" Haba Ammi!...ke xe fa kika haife ni, me yasa bazaki tausaya min ba, 'yata fa na rasa Ammi.kuma sannan.ki sake raba ni Noor ina zan sa kaina?". " Inda ka saba sawa mana...". Ta bashi amsa a hassale. Bai damu ba ya cigaba da fa'din" Please! please ba dan ni ba, dan Ubangijin mu Ammi ki ji 'kaina ki bani wani chance, i promise u bazan sake yin wannan kuskiren ba, zan canza wallahi zan zame mata d best husband ever morethan u can imaging, nasan ban kyauta ba nasan nayi kuskure amma dan Allah ku yafe min Ammi i promise u bazan sake maimaita irin wancan rayuwar ba...Ammi ki tausaya min ki yadda da tuba na, believe me bazan miki 'karya ba.. wallahi ina son Matata, i luv Noor with all my heart that rabamu zai iya zame mana matsala Ammi, ki tambaye ta kiji ita kanta nasan..." Hannu Ammi tayi saurin 'daga masa alamun ya isheta haka nan sannan tace" Kalaman kan nan 'kona ni suke yi Mu'een sam basu da amfani yanzu lokacin da ya kamata ka basu muhimmanci.watsi kayi da su, i don't care weather son mutuwa kake yi mata is alla useless tun da kayi wasa da damamma kin ka abaya...now komai ya wuce buri na kawai inga babu wata ala'ka tsakanin ka da 'yata, buri na inga bata tare da mutun irin ka, ka rubuta min abinda na bu'kata kawai yanzun nan..." " Ammi ta ya kike tunanin zan iya rubuta wa Nuree saki da hannu na, matar da nasan idan na rasa ta tamkar rasa farin cikin rayuwa ta ne, Ammi Noor itace rufin asiri na, itace Hasken rayuwa ta, ada da kaina nayi al'kawarin zan bar rayuwan su saboda ta bu'kaci in daina zuwa inda take, nd nayi i promise zan bar su saboda su sami farin cikin rayuwa ita da Baby, but Ammi yanzu babu Baby, ta tafi...ina jin tausayin Noor sosai, sam bazan iya rabuwa da ita ba a wannan halin bacin nasan cikin 'kunci take ayanzu, Ammi ki fahimce ni ki bani daman gyara kuskire na, ta ya Noor zata samu wani  farin ciki bacin babu kowa tare da ita...?" " Dan ubanka kuma sai akace maka kaine ka'dai farin cikin ta?.. Ammi ta jefa masa tambaya a hassale cike da 'kosawa da maganganun sa. 'Kasa yayi da idanun sa yana mai share hawayen fuskar sa da hannun sa 'daya tamkar yaro 'karami. Ammi kam bata damu ba ta cigaba da fa'din" Ai koka'dan banga alamun tausayi tattare da kai ba, shekaru nawa kake tare da ita? kwanaki nawa ka 'dauka kana cutar min da ita? ko angaya ma bana damuwa da rashin ganin walwala a fuskar ta da banayi ne...ko dan kaga ban ta6a tuhumar ka akai ba ko? Idan soyayyar da kake ikirarin kana yi mata na gaskiya ne to ka sakar min ita domin na tabbata rayuwa babu kai shine farin cikin Hudah na har abada...." Zai yi magana tayi saurin taran sa da fa'din" Matu'kar kana so ka cigaba da rayuwa matsayin haifaffen 'dan halak to ka je ka 'dauki pen ka rubuta min sakin 'yata..." Noor na jin Ammi ta fa'di hakan tayi saurin.matse hannun ta dake cikin.na Ammi, hawaye ne sosai yake zubo mata kan kuncin ta, bata so irin hakan ya dinga shiga tsakanin sa da iyayen sa amma ya zatayi? harga Allah bata jin zata sake jin da'din rayuwa tare da shi...burin ta ayanzu kawai shine taga bata 'karkashin inuwar auren sa. A hankali Deen ya mi'ke  ya isa inda pen in yake ya dur'kusa hannun sa na rawa yana share hawaye yayi rubutu layi 'daya tak daga hakan ya mi'ke ya fice yana share hawaye bai ko sake kallon inda Ammi take ba balle Noor in. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *81* Bin bayan sa da idanu Ammi tayi har ya 6acewa ganin ta, sannan ta dawo da hankalin ta ga rubutun da yayi, a hankali ta 'dago takaddan ta sada shi da idanun ta... Wani tu'kukin bakin ciki taji ya mamaye mata zuciya...sakamakon ganin rubutun da yayi. Saman la66a ta furta" Mu'een ya raina ni da yawa". Abinda ya rubuta 'din yawo ya dinga yi mata aka, sake 'dago wa tayi ta karanta karo na biyu tana mai cize le6en ta na 'kasa. Noor da bata san abinda ya rubuta ba a hankali ta 'karaso gaban Ammi ta dur'kusa tana kuka take ro'kan Ammi akan ta yafe masa kar tayi fushi da shi, tace ita ba nufin ta tsakanin su ya 6aci ba da shi bane, rayuwa da shine ka'dai bata so ayanzu... Amma bata ce da ita 'kala ba kawai ta saki takkadan ya fa'do 'kasa dai-dai 'kafafun Noor, a hankali Ammi ta 'daga kafar ta tayi waje tana mai jin wani abu na taso mata, tausayin Noor gami da Danasanin bawa Mu'een auren ta da suka yi, ba kowa ce mace ba zata iya irin hakan, ace duk irin abinda yayi mata amma still burinta taga bai samu sa6ani da mahaifan saba, sa6anin matan yanzu da wasun su da kansu ma suke raba tsakanin mijin su da iyayen sa saboda son zuciyar su. Kuka sosai Noor ta sha har kanta nayi mata ciwo mai tsanani, tana hawaye ta 'dago takkadan da Ammi ta jefar da niyyan ganin yawan sakin da yayi mata amma abinda idanun suka gani sosai ya bata mamaki take kakan ta ya tsaya cak, 'kurawa rubutun idanu tayi tana karamtawa tana 'karawa" _Kiyi ha'kuri.. bazan iya sakin ta ba Ammi_ ". Abinda kawai ya rubuta kenan...cikin zuciyar ta ta furta _Allahumma ajirni fi musibati_ ...yayin da a fili ta furta" Wallahi ko babu saki tafiya ta zanyi bazan sake zama da kai ba". Haka ta 'karashi kukan ta tayi shiru...zuciyar ta cike da haushin Yah Deen ji take tamkar ta sha'kesa. Deen kuwa tunda da barin sa wurun Ammi direct 'dakin sa ya wuce ya 'dauki key kawai yayi waje. Can wani gida can wani gidan sa da yake ginawa bai 'karasa aikin ba ya tafi da yake babu wani nisa sosai da gidan nasa na asali. Babu komai a gidan na amfani, amma haka yake tahowa yayi zaman a duk lokacin da yaji abubuwa sun sha mai kai. Safwan ka'dai ne kuma yasan da cewa yana ke6e kansa a wannan gidan. Kuka ya dinga rizga kamar yaro 'karami gashi babu mai lallashi, tausayin Noor yake ji sosai, mai yasa Ammi bazata fahimce shi ba? tayaya zai iya rabuwa da Noor cikin wannan halin bacin yasan cewa komai da ya faru sanadin sa ne, meyasa bazasu bashi dama ya cika al'kawarin da ya 'dauka ba?...yasan sakin Noor a wannan ga6ar na iya haddasa mata wani matsananciyar damuwa ne saboda yasan dole tunanin Baby zai dame ta sosai ga kuma ace shima ya sake ta da wanne da zataji? " Ammi ki yafe min amma bazan iya rabutawa Noor saki ba sam, nasan ni mai laifi ne sosai na sani, kuma ban cancanci afuwar Noor ba, bama ni da idanun.da zan iya duban ta in nemi afuwar ta. Amma ya zanyi Ammi? Rabuwar mu da Noor bazai gyara komai ba, al'kawari nayi yanzu Ammi zan bar dukakkn abubuwan da nake aikatawa, wallahi ko garin Bauchi Noor tace mu bari zan bari saboda ita ina son sake ganin farin cikin ta..ina son matata ina 'kaunar zama da ita, iyace farin ciki na hasken raina...". Haka yayi ta sumbatu kamar mahaukaci, duk ya fita hayyacin sa gaba 'daya, gashi yana jin ciwo amma ya basar saboda tsananin damuwar da ke cinsa...a hakan har bacci ya yi gaba da shi. Sai cikin dare ya tashi ya alwala ya 'dauro sai da ya koma motar sa ya 'dauko dadduma sannan yazo ya sallaci sallar da bai yi ba. Sai da ya 'kara da nafilfili haka ya dinga istighfari yana ro'kon yafiyar ubangijin sa da fatan ya daidaita masa rayuwar gidan sa yasa mahaifan sa su yafe masa fusgin da suka yi da shi. Akan daddumar ya koma ya kwanta wani baccin ya sake 'daukan sa. ***** Washegari su Ammi suka firfito da kayan su gaba 'daya har da na Noor dake ta faman share hawaye lokaci zuwa lokaci, Ammi sam bata damu da 'kin sakin Noor da Mu'een yayi ba ta riga tasa cikin ranta cewar ko bai sake ta ba bazata barta tare da shi ba. Tun jiya Safwan ke ta 'kiran layin sa amma baya 'dagawa, abin ya 'daure masa kai sosai dan ko da safiyar yau ma sai da ya 'kira amma still bai 'daga ba, sanin da yayi cewa lafiya bata ishe shi bane yasa shi kamo hanyar gidan nasa da sassafe da zummar jin ko lafiya. Yana zuwa sai ya tarar da kayan su Ammi a harabar gida, shiga yayi suka gaisa da su ganin su cikin shirin kuwa bai sashi mamaki ba cuz yasan da batun tafiyar, fahimtar da yayi harda Noor a tafiyan ne yaso sashi mamaki har ma ya kasa yin shiru sai da ya tambayi Ammi cewa tafiyar harda Noor ne?" Kallon sa Ammi tayi tana 'dan ha'de rai tace da shi" Umm da ita zan tafi Safwan..ko so kake in barta ku 'karasa min ita a banza?" Kai ya 'dab sosa sannan yace" kiyi ha'kuri Ammi naga ai mijin nata ba lafiya sosai gare shi ba..." " Ya mutu mana shi ya sani ai...ita ma lafiyar bata ishe ta ba jinyar ta zanje inyi bazan iya barin ta ku 'karasar min da ita ba...". " Ammi kiyi ha'kuri dan Allah kar ki yanke wannan hukuncin wallahi Mu'een na bu'katan kulawa yanzu kuma na tabbata zai canza tunda ga abubuwan da suka yi ta faruwa nasan sazu zame masa izna, ga dukkan alamu ma already yayi nadama ai Ammi..." Baki Ammi ta ta6e cikin nuna halin ko'in kula ta kawar da kanta. Ga Noor ya dawo da kallon sa yace" Please Noor ki yafewa mijin ki kuma ki taya ni bawa Ammi ha'kuri...." Noor tun bata kai ga jin 'karshen furucin nasa bama kuka ya 'kwace mata. Ganin hakan yasa Ammi saurin fa'din" Baruwan ka da ita Safwan, ku bar min yarinya ta yi numfashi mai kyau dan Allah, ba ita ta aiki mutun aikata abinda yaso ba so bata da alhakin jinyar sa, sam bashi da alamar gyaruwa, ba yau ya fara irin munafurcin nan ba daga baya kuma sai kaga ya koma ruwa dan haka ka barshi...yaje shiya sani nasan akwai ranar da duniya zata juya mai baya, idan ta'kamar shi kyau da Allah yayi masa ne ai mai gushewa ne, kuma kansa yake yiwa mummunan tabo ba wani ba...Jasmine kam sai dai muyi fatan Allah ta mata Rahama kuma ya jira sakayyar ta wurin Ubangiji...idan yace bazai bari ba ma shiyasa ni, yaje can yayi ta haifa ana lalatawa amma kam ba da 'ya ta ba...." Ha'kuri Safwan ya cigaba da bata amma Ammi kam sai ta 'ki sauraron sa fa'di take ka gaya masa, kar ya kuskura ya tako inda nake matu'kar ba tafe yake da sakin Noor ba, akan wannan sakin har kotu zan iya kaisa, dan bazata sake zaman aure da shi ba..." Safwan kam wannan karan shiru yayi yana jinjina kansa...ya lura Ammi da gaske take bata sassauta musu ba, d kansa yasan Noor tayi ha'kuri amma ai ba gajiyawa da ha'kuri tunda ba'a san mai gaba zai haifar ba, ha'kuri baya yawa ko da wasa, idan kayi shi da ikhlasi ma sai kaga Allah ya dubi zuciyar ka ya sada ka Rahamar sa. Ita kanta Noor in ga dukkan alamu rabuwar dole ta zame mata amma ba wai haka ta so ba. Ya fahimci hakan ne sanadiyyan kukan Noor da ya kasa tsaya wa. Cuz lokaci-lokaci take share hawaye. Yana so ya tambayi inda Deen 'din yake amma tsoron Ammi yasa yayi shiru...sai dai ganin har sun kulle gidan ya sashi fahimtar baya ciki kuma babu motar sa agidan koda ya shigo bai gani ba. Shine ya kaisu tasha da motar sa bayan sun damka makullin gidan hannun Bala mai gadi. Bai yi wani dogon nazari ba bayan ya sau'ke su sai ya nufi sabon gidan sa da tabbacin yana can cuz cikin kwanakin acan yafiye zama. Ruf da ciki Safwan ya same shi kan dadduma da alamun tashin hankali, duk ya galabaita numfashin sa na fita da 'kyar. " Subhanallahi.." Safwan yayi saurin furtawa tare da 'karasowa kusa dashi. Da ganin Safwan sai yayi 'ko'karin mi'kewa zaune yana duban sa da jajayen idanun sa da suka 'kan'kance. " Me ke faruwa ne Mu'een? Me yasa ka taho nan kuma?" Safwan ya tambaye shi yana duban sa da kulawa. " Bakomai...kaina ke ciwo". " Ayyah sannu, na ta 'kiran ka baka 'dagawa hankali na ya tashi sosai..I thought wani abin ne ya faru..". Cikin galabaita ya bashi amsa da fa'din" wayar na can gidan ne .." " Ohh..yanzun nan na sau'ke su Ammi me yasa baka je kunyi sallama ba har suka wuce? Naga ma har da Noor suka tafi...". Rintse idanun sa yayi da 'karfi yana jin ciwon tafiyan da Noor tayi ta bar shi... Idanun sa a lumshen muryar sa na rawa ya furta"...Ammi bata..so..na yanzu Safwan, Ammi na...da kanta tace in...sakar mata Noor, Ammi tace bazata sake..ba..rin ta zama tare dani ba, Safwan zan cinye ta ne? Ban san ya zanyi da Ammi su gane cewa nayi nadamar gaskiya ba, wallahi da kaina Allah wadai nake da rayuwa ta ta baya, me yasa suke tunanin zan sake maimaitawa? Ina son Noor sosai, i can't let her go just like that batare da na bata farin cikin da ta rasa atare dani abaya ba, Safwan wannan ma laifi ne please?" Kai Safwan ya girgiza tare da fa'din" Ka kwantar da hankalin ka komai zai wuce insha Allah.." " Ni dai ka taimake ni ka dawo min da ita Safwan, ka bawa Ammi ha'kuri ta dawo min da Mata ta....". Kasa 'karasa maganar yayi kawai ya dafe kansa da yake jin yana sara masa sosai, Safwan kam duban sa yake yi cike da tausayawa, shi al'amuran Deen 'din yanzu duk sun fi 'karfin tunanin sa, ha'kika yasan a yanda Ammi ta ji labarin halin sa daga bakin sa ya kuma ga yanayin ta 'dazun ya tabbatar abu ne mai wahala ta sake barin Noor zama da shi tunda har kotu yaji take ambata, sai dai bazai fa'di wa Deen hakan ba saboda gudun kar ya 'kara masa wani ciwon akan wanda yake ciki. Sam bai ga laifin Ammi ba, domin ba ita ka'dai ba duk iyaye idan suka tsinci hakan cikin rayuwar 'yar su dole ne yasan sai sunyi wani yun'kuri...sai dai ai shima Deen in a yanzu yana bu'katar agaji kuma iyayen sa su ya kamata ace sun tsaya masa wajen ganin lafiyar sa ta samu me yasa duk zasu guje shi akan kuskuren da ya aikata?" A fili kuwa" Allah ya kyauta" ka'dai ya furta tare da sakin ajiyan numafashi. Tare suka fito da Safwan inda ya sauqe shi a 'kofar gidan sa tare da kwantar masa da hankali cikin nutsatstsiyar murya da kalamai masu sanyi inda ya tabbatar masa da cewa ya bari ya 'dan basu chance zuciyar su tayi sanyi nan da 2weeks zasu je da shi su 'kara basu ha'kuri. Girgiza kai Yah Deen yayi yana duban fuskar sa yace" Bazan iya ba Safwan, 2weeks yayi min yawa mu tafi gobe..". " Kayi ha'kuri dai, komai cikin natsuwa yafi, kuma nafi son ka warware da kyau tukunna don kaga yanzun halin da kake ciki kaima kana bu'katan hutu". Shiru kawai yayi masa yana jin sa ba wai dan zancen nasa ya shige shi ba sai dai kawai ba yanda zaiyi da Safwan Maganar ma 'karfin halin yin ta yake yi amma sosai yake jin babu da'di...kuma ga alama kowa ba fahimtar halin da yake ciki suke yi ba, ga dukkan alamu shi ka'dai yasan ciwin da ke zuciyar sa, sam gani yake komai ya yi masa duhu musamman da yasan a yanzu Noor bata tare da shi. Daga 'karshe Safwan tabbaci ya bashi na cewa Insha Allahu zuwa dare zai zo ya sake duba shi, da haka suka rabu Safwan ya wuce inda zashi. Mai gadi na ganin sa ya taho wurin sa da sauri-sauri yana gaida shi, key 'din da su Ammi suka bashi ya bawa Yah Deen cike da girmamawa. Hannu ya sa ya kar6a sannan ya nufi ciki da tuanin da gaske kenan ta tafi... 'kafafuwan sa ma da 'kyar yake iya 'daga su, dishi-dishi yake gani sosai, ya san koma menene ya faru ga rayuwar sa shine sanadin komai, yau gashi gidan sa babu kowa sai shi ka'dai, bai ta6a tunanin irin wannan ranar na zuwa masa bazata kuma kwana kusa irin haka ba. Baby ta rasu ta tafi ta barshi yayin da Noor ta guje shi batare da ta tsaya ta saurari amincewar sa ba.... Haka ya bu'de 'kofan parlourn ya shiga yana rarraba idanu, kwanaki 'kalilan da suka gabata idan ya shigo gidan da gudu Jasmine ke zuwa wurin sa tana dariya take yi mai oyoyo Daddy..inda yake 'daga ta sama yana dariya haka itama...idanu ya lumshe ya kuma bu'de su nan take...lokacin yana 'ko'karin zama kan kujera...ya furta Allah ya ji'kan ki Mama na, Allah yasa ki kasance me ceton mu, duk da nasan ban cancanci hakan daga gareki ba. Bayan sa ya kwantar tare da 'dago 'kafafun sa ya mi'ke yana lumshe idanu. Tunani ne fal aransa amma duk ya rasa wanda zai sanyayar masa da zuciya... Haka ya yini shi ka'dai agidan batare da ya ko iya saka ruwa abakin sa ba, kusan la'asar ya fara jin zazza6i sosai ya rufe shi jikin sa na ta kakkarwar sanyi, motsin kirki ya kasa ballantana ya samu damar jan abincrufa ya rufe jikin sa da shi, tunda ya kwanta bai sake ko motsin kirki ba har yanzun da fever ya ratsa shi. Fat-fat yake jin 'kirjin sa na bugawa ji yake tamkar dutsi aka aza masa akan zuciyar sa, ga ciwon kai ga zazza6i...cikin hakan ya fara amai kamar zai amayar da hanjin cikin sa, dayake cikin sa babu komai sai hakan ya 'kara galabaitar da shi..jikin sa babu 'karfi ko ka'dan. 'Kasa ya dawo ya kwanta yana maida numfashi sama-sama gwanin tausayi. Gashi gidan babu mai taimakon sa, mai gadi ne ka'dai a harabar gidan shima in kuma bai san abinda ke faruwa da shi ba balle ya taimaka masa. Da 'kyar ya samu numfashin sa ya daidaita sannan ya mi'ke ganin jiri na 'diban sa yasa ya fara dafe bango da hakan ya samu ya isa bathroom. Sai da yatsaya ya dinga sau'ke numfashi anan in ma sannan ya samu ya tsaftace jikin shi, ya 'dauki tsawon lokaci a hakan kafin ya samu ya fito boxer da rigar jallabiya kawai ya iya sanyawa ya sallaci La'asar ko azkar bai iya jerowa ba ya cire jallabiyan saboda ji yake tana takura sa haka ya koma ya kwanta tare da jan abin rufa ya lullu6e jikin sa da shi har zuwa kansa gaba 'daya. Saman abin rufan idan ka ta6a zaka iya jin 'dumin daya 'dauka sanadiyan zazzafan zazza6in dake jikin sa a lokacin, rawar sanyi kawai yake yi ha'koran sa na karo da juna. Safwan bai dawo gidan ba sai 'karfe biyar, koda ya shigo ma haka ya dinga doka sallama amma babu wanda ya amsa shi. Sosai yayi mamaki don kuwa kafin ya shigo sai da ya tambayi Bala mai gadi ya tabbatar masa da cewa yana ciki kafin ya iso. Jim ya tsaya da tunanin ko yana bayi ne shiyasa yaji shiru, parlourn babu wadataccen haske sosai duk da haka sai ya fara bin ko'ina da kallo yana daga tsayen bai motsa ba. Can gefen doguwar kujera ya hango abu a zube sai ya 'dan tsuke fuska da tunanin me kuma ya zubar a wajen. 'Karasawa wurin yayi a hankali ya tsaya yana duban abin da ya gani, komawa yayi ya lalu6i switch ya kunna haske ya grawaye parlourn gaba 'daya nan idanun sa suka tabbatar masa da abinda ke 'kasan tiles in. A firgice ya furta _subhanallahi_ , take ya fara duba shi cuz yasan koma ina yake yanzu cikin mawuyacin hali yake, 'dakin sa ya fara le'kawa sai dai nan ma da ya tura sai yaga duhu ba'kiri'kirin nan yayi tunanin ko baya nan 'dakin, har ya juya da nufin duba sauran 'dakunan sai ya jiyo nishin sa dake fita da 'kyar. Komawa yayi da sauri, bai ma tsaya ya kunna wutan 'dakin ba ganin kamar zai 6ata mai lokaci kawai ya ciro wayar sa ya kunna hasken ta wanda a lokacin tsaye yake a bakin bed 'din yana kunna hasken ya ganshi lullu6e cikin bargo. Yanda yake jiyo yanayin fitar numfashin sa ka'dai ma already ya rikitar da shi. Da 'dayan hannun sa ya yaye mayafin nan yayi arba da fuskar sa idanuwan sa a lumshe yana fitar da numfashi da 'kyar....ba bu'katar sai ya sake ta6a jikin sa cuz jikin mayafin ka'dai ma ya tabbatar masa da yanayin da jikin sa ke ciki. Sunan sa Safwan ya 'kira yana ji amma bai iya ya amsa ba, sake 'kira yayi amma still ya kasa bu'dan baki ya masa shi cuz sosai ya galabaita gwanin tausayi...hankalin Safwan gaba 'daya ya tafu ne ga zafin da yaji jikin sa yayi sosai ya rikitar da shi. Hannun sa na dama na dafe da kan 'kirjin sa saitin zuciyar sa yana numfashi da 'kyar...idanun sa a lumshe. Ko ba'a fa'da wa Safwan ba yasan sosai Mu'een ke jin jiki domin shi mutun ne mai matu'kar jarumta, ya kan iya daure ciwo yayi ta tafiya da shi indai ba fin 'karfin sa yayi ba. Ko ciwon zuciyar sa ma ba ko wani lokaci bane yake bari a kwantar da shi, ahakan zai ta tafiya da shi har ya sau'ka da kansa sa6anin 'yan kwanakin da dauriyar sa ta kasa yin amfani, duk ya fita hayyacin sa gaba 'daya. Fita yayi da sauri ji yake tamkar ya zubda hawaye, ya rasa da me ya kamata ya kwatanta wannan abin,.kansa ya fara kullewa. Mai gadi ya yiwa magana yazo suka kama shi, sai da suka sanya masa kaya jeans da tshirt sannan suka fitar da shi. A motar sa suka sanya sa sannan ya sanar da Mai gadin cewa asviti zai kaisa dan Allah ya kula da gidan 'kilan ba yau zasu dawo ba. Jinjina kai Bala yayi zuciyar sa cike da tausayin ogan nasa, domin yasan abubuwa ne kawai suka yi masa yawa ba komai ba. Da fitan su sai Bala ya koma ya tsaftace parlourn yana yi yana girgiza kansa...lokaci 'kalilan gida ya zama wani iri kamar ba gidan da suka saba walwala ba. Hauwa kam tunda Jasmine ta rasu ya lura itama bata saki jikin ta ba, da farko da mahaifyar ta suka zo ta'aziyan Hauwa na kuka sosai dan Jasmine mutumiyar ce, ko daga baya ma kusan kullum sai tazo ta gaida Noor jiya da yau ne ka'dai bai ganta ba...bai sani ba ashe Noor ce tayi mata bayani a 6oye cewa zasu bar garin ne. Da yake asbitin nasu ne so suna zuwa aka hau bashi taimakon gaggawa, Safwan sai da aka tabbatar masa da cewa yayi bacci kafin hankalin sa ya 'dan kwanta. Sai lokacin kuma ya iya ciro wayar sa ya 'kira Hafsat dan tun 'dazun take ta 'kiran sa amma bai iya ya 'daga ba. Nan yayi mata bayanin abinda ke faruwa tare da tabbatar mata da cewa anjima ka'dan zai dawo gida tunda ya samu bacci... itama Hafsat cike da tausayawa ta nuna alhinin ta a bayyane, duk abubuwan da suka faru abaya amma sosai take tausayawa Dr. Mu'een domin kuwa ga dukkan alamu yayi nadamar komai. Da gama wayar ta da Safwan ta 'kira Noor, nan ta fara yi mata nasiha tana nuna mata rashin kyautawar ta, ita ce ta bayyana mata halin da yake ciki a lokacin...Noor kam bata ce da ita komai illah kuwa da take yi hadda sheshshe'ka, da hannun ta 'daya ta toshe bakin ta tana kukan tausayin su gaba 'daya. Hafsat kam jin Noor bata tanka ta illah kuka ya sata fa'din" Ki dai nutsu ki sake tunani Noor kar ki biyewa zuciyar ki please.." Daga haka ta yanke 'kiran ta bar Noor da aikin kuka. Ita sam ta rasa inda zata sa ranta. Cikin wannan halin Ammi tazo ta same ta ai kuwa masifa ta hau ta da shi wanda dole daga 'karshe lallashi ta koma dan Noor ta kasa yin shiru. Tun lokacin da Safwan ya sanar da ita cewa Noor sun wuce da su Ammi hankalin ta ya kasa kwanciya, balle da ta 'kira ta ji kukan da take yi sai hankalin ta ya 'kara tashi. Bayan isha'i ta sake 'kiran ta amma sai taji baya tafiya akashe, sosai taso ta sake yi mata nasiha taja hankalin ta cikin natsuwa akan tafiyar da tayin cuz aganin ta ba mafita bace kwata-kwata, da ha'kura tayi kawai suka rungumi juna suka gyara dukkan kurakura su da zai fi...ga shi da alama itan ma ranta bai sake da tafiyar ba tunda kuka take yi. Sai dai rashin samun nata bai bari ta fitar da abin ranta ba. ***** 'Bangaren Safwan kuwa kafin ya tafi sai da ya bi ya duba Sani, a koda yaushe idan kaje zaka same shi ne cikin wani mawuyacin hali, har yau 'din cikin dangin sa babu wanda ya san halin da yake ciki, shi da ya fito da niyyan neman abin yi sai gashi zai koma musu gida da hannu guda sanadiyyan son zuciyar sa. Kuka sosai yake yi yana tausayin kansa, dan yasan dole Allah sai ya hukunta shi, gani yake wannan bakomai bane akan tanadin da Allah yayi masa, kullum cikin zuciyar sa istighfari yake jerowa yana kuka, yana kunyar ranar da zai ha'du da mahaifiyar sa yaba ta labarin abubuwan da ya ai kata cuz tabbas dole ya bata labarin da bakin sa, ayanzu ba shi da za6i illah ya maida hankalin sa ga neman gafara wurin ubangijin sa. Tunda yaji labarin mutuwar Jasmine daga bakin Safwan shikenan ya rasa natsuwa. Kuka yake yi yana fa'din" Ban nemi yafiyar ta ba, gashi ta rasu...ya Allah ka yafe min kasa Baby ma ta yafe min, Kaico na, dana kasance mai son zuciya ta, kaico na da na sake har Shai'dan yayi min illah a zuciya ta ya sani aikata abinda zai jani ga dana sani na har abada. Allah sarki Jasmine, yarinya mai tsananin tausayi da sanyin hali, bazai manta ba ko ranar da abin ya faru da ta ganshi wani iri sosai ta nuna tausayawa agare shi koda ta tambaye shi abinda ya same shi kuwa sai yace mata zazza6i ke damun sa. Jasmine cikin tausayawa tace" _Sorry kar kayi kuka kaji, idan Daddy na yazo zai baka magani amma kace kar ya maka allura akwai zafi_ ..." Hawayen sa ya share da 'dayan hannun san mai lafiyan, kana yace" Allah ya ji'kan ki Aishatu, Allah yasa kiyi ceto Allah ya bawa iyayen ki madadin ki...wallahi nayi hasarar rayuwa ta, Yah Allah ka yafe min, ka yafe min Yah Allah...da wani idanu zan dubi Oga Deeni ince masa yayafe min, ga shi nayi sanadin da yarinya ta rasa rayuwar ta... Kuka yake sosai ahakan Safwan ya shigo ya same shi. Sosai yayi mamaki da ganin halin da Sani ke ciki..." Innalillahi haba Sani me ke damun ka kuma? Dan Allah ka daina 'daga hankalin ka ciwo ai ba mutuwa bace, kuma tana iya samun kowa, kar kaga kamar Allah bai son ka ne da ya jarrabe ka da hakan, kuma ai dama ba'a gama wa bawa halitta har sai ranar da ransa ya bar jikin sa, duk cikin 'kaddarorin Ubangiji ne kar kace zaka tambaye sa dalili kuma domin shine masanin komai shine yasan mai yasa ya jarrabe ka da hakan...." Sani bai jira yaji 'karshen maganar Safwan in ba yace"...Dr...ya zanyi? Ya zanyi da rayuwa ta? Ta ya zan iya sakin raina bacin nasan Jasmine bata yafe min abinda nayi mata ba gashi tabar min duniyan, ina zan shiga inji da'di, wallahi ciwon nan baya damu na kamar yadda nake jin ciwon rasa Baby, nasan yanzu haka iyayen ta na cikin wani hali ta ya zan iya zuwa gaban su in ce su yafe min, kunya nake ji soaai Dr...wallahi tir nake yi da halayya ta, har abada nasan da wannan abin za'a yi ta kallo na...ina ma da nine na mutu..ina ma da nine na bar duniyan ba Baby ba....". " Kar kace haka, yanzu fa na gama gaya ma ba'a yiwa Allah tambaya, ko ka manta kai muslumi ne, duk abinda ya dame ka kawai ka juya ga Allah, in batun Baby ne kuma kawai kayi ta istighfari ka tabbatar kayi tuba na gaskiya, ko da wasa kar ka sake kwatanta irin wancan abin har abada ina da ya'kinin Allah zai yafe maka idan kayi hakan...." " Nagode, nagode sosai Dr. Insha Allahu zan nemi garafa wajen mahalllici na, zan ro'ke shi ya yafe min..." Daga haka bai sake furta komai ba kawai ya cigaba da kukan sa. Safwan tashi yayi ya bar 'dakin yana jin tausayin su a zuciyar sa. Kafin ya fita sai da yabi ya sake duba Mu'een yaga baccin sa yake yi, cikin zuciyar sa yayi masa fatan Allah ya bashi lafiya kafin ya nufi inda motar sa take ya kama hanyar gidan sa. Ya riga ya gama komai da Sani zai bu'kata ya ajiye me kula da shi, da wanda zai na jigilar abincin sa da duk abinda zai bu'kata har zuwa ranar da za'a sallame shi wanda ba kowa ne ya 'dau nawin hakan ba face Mu'een. Da dukiyar sa ya 'dau nawin komai game da Sani, wanda Safwan ya jagoranci abin ta hanyar nemo wa'danda zasu yi musu aikin. **** Wasa-wasa sai da Yah Deen ya 'dauki sati guda a asbiti kafin ya 'dan fara warware wa... Comment Vote Share *Salmerh* 😍 💕 *NOORUL* 💕       (Haske nah) By *Salmerh MD*   *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *82*          Rama sosai yayi kamar ba shi ba duk idanuwan sa sun firfito, wanda cikin lokacin kuwa duk Safwan ne ke kansa, shi ke kula da komai na shi, har Alhaji Baba Safwan ya 'kira ya fa'diwa batun rashin lafiyar tasa ganin kamar abin na neman yayi tsanani ga mamakin sa kuwa sai ji yayi Alhaji Baba yace" To ni mai zan masa Safwan...Allah ya bashi lafiya". Daga haka ya hanging call 'din ya jefa wayar sa cikin aljihu, Safwan sosai yayi mamakin sa anan kuwa ya 'kara tabbatar da irin fushin da iyayen sa suka yi da shi, bai bari Yah Deen ya san hakan ba soboda gudun sake 'daga mai hankali kawai ya bari cikin ransa. 'Bangaren Sani ma _Alhamdulillahi_ jiki yayi sau'ki babu abinda ke damun sa yanzu illah gurbin ciwon hannun sa inda aka cire. Shima 'din baya damun sa sosai, yana iya yiwa kansa wasu abubuwan yanzu saboda baya jin wani ciwo, jira kawai yake a sallame shi yasan inda dare yai masa. Yah Deen duk da yana cikin wani hali amma a kullum damuwar sa iyayen sa ne da kuma matar sa, burin sa bai wuce yaje inda suke ba, da yaga ya 'dan fara samun sau'ki sai ya fara batun tafiyar amma Safwan ya ce da shi ba yanzu ba tukunna sai ya warware gaba 'daya. *****     'Bangaren Noor kuwa tunda ta koma gida sai tunani suka yi mata yawa, domin babu inda take zuwa daga aikin gida shikenan sai zama dole badan tana so ba tunanin suka cika mata kwanya. A kullum bata iya bacci da wuri saboda tunanin rayuwar ta, idan ta tuna Baby kuwa sai dai kawai tayi ta hawaye, tana jin babu da'di a zuciyar ta, dagaske ne ashe Allah dama yake bawa bayin sa, idan ka'ki yin amfani da damar ka ta wuce ka shikenan, kamar ita... Allah ya bata amanar Baby matsayin 'ya dan ta kula da ita amma tayi watsi da amanar Allah, ta 'ki bawa Baby kulawan da ta dace gashi ya kar6e abinsa batare da ya sake bata wata damar ba...kuka take yi sosai tana ro'kon Allah akan ya yafe mata, kar yaga laifin ta akan hakan, tace Allah kasan halin da nake ciki, damuwa ce nima tai min yawa Yah Allah kar ka tuhume ni akan hakan Yah Allah ka sani ina damuwa ne akan abinda bani da damar canza shi shiyasa hankali na ya kasa natsuwa. A kullum bata da aiki sai kuka amma bata ta6a bari Ammi ta fahimta ba, maganar kirki yanzu bata yi tafi so ta yi zamanta ita ka'dai yafi mata komai. Sai da ta kusan kwana biyar da dawowa kafin ta sake kunna wayar ta, wanda shine ya 'dan fara 'debe mata kewa, ta kan yi game ta kuma chat da wasu friend nata na makaranta. Idan sun tambaye ta batun makaranta kiwa takan ce da su ta bari ne kawai tana so zata canza wata. Su kan yi mamaki sosai wasu har na mata nasiha akan cewa ai dan 'yar ta ta rasa ranta ba ya nufin komai nata na rayuwa ya tsaya ne...da yake suna da labarin rasuwar Baby har ma sun zo mata ta'aziya a lokacin...sai suke ganin kamar dan hakan ne. Amsa take bayar wa da fa'din" Nasani, kawai na bar makarantar ne dan munbar garin Bauchi mun koma gida so nafi so in nutsar da hankali na wuri guda..amma ba wai dan Jasmine ta rasu bane.". Ita kam cikin zuciyar ta take jin komai ma dake cikin garin Bauchi ya fice mata aka, bata 'kaunar abinda zai sake sata shiga garin balle har zama ya kamata talk more of attending lectures.         Duk take jin ta yafe...tunda har ta iya ha'kura da Yah Deen a rayuwar ta menene ma ba zata iya ha'kura da shi ba?. Alhaji Baba ne ma yayi mata batun makarantar inda ya tambaye ta ko zata koma cikin school ta cigaba da makaranatar, take ta nuna masa a a bata so inda rabon ta wataran zata yi.. Da yake yasan dalilin ta sai ya jinjina kansa da burin canza mata wata, ko BUK ma tunda Saif ma acan yake duk dama shekarar 'karshe yake amma zata fi jin da'din zama a can. *****      Satin Mu'een biyu a asbiti sannan aka yi discharging na sa washegari kuma aka sallami Sani dan shima ya warware sosai...shi kam sai share hawaye kawai yake yi yana tunanin ta inda zai fara. Da 'kafar sa yake ta takawa domin bai yadda ya 'dauki komai da yake nasa bane a asbitin duk yace mai kula da shi 'din ya tattare ya bar masa, duk irin kayayyakin da Safwan ke sayo masa duk ya bar wa wanda yayi ta kula da shi in. Ko sisi babu ajikin sa shiyasa yake takawa abin sa da 'kafa, Safwan yasan da batun Sallamar amma yayi zaton sai zuwa yamma za'a sallame shi irin na Mu'een sai kuma akayi rashin sa'a suka yi sa6ani. Da 'kafar sa yake takawa a hankali har ya iso gidan Ogan sa Deen. Wanda tunda ya dumfari gate in gidan zuciyar sa ke luguden bugu yana jin babu da'di amma bashi da wata mafita da ta wuce hakan burin sa bai wuce yayi arba da mahaifan Baby ya nemi gafarar su ba.          Daga hakan kuwa Insha Allah garin zai bari gaba 'daya ya koma mahaifar sa tunda fitan nasa bai masa amfani ba. Hatta Bala mai gadi ma kunyar hada ido yake yi da shi domin shine ya san komai cikin halayyar sa...ai kuwa yana zuwa ya tura gate in yasa 'kafar sa ya shigo cak ya tsaya yana duban mai gadi dake zaune gefen gate in wanda shima turo 'kofan da akayin ya sanya shi 'dagowa. Tsaye ya mi'ke da mamaki yake duban Sani ganin hannun sa 'daya, tausayin sa ne ya kama shi sosai cuz yana da labarin komai amma sam yau in ganin da yaiwa Sani sai yasa zuciyar sa karyewa. Gaban shi ya fara takowa Sani sai ya kauda kansa gefe yana share hawaye. Bala maigadi na zuwa sai ya rungume shi shima in kukan yake yi. Dauriya Sani yayi yana murmushi yace" Sannu Bala, ya aikin? Bala bai tanka ba illa sake kallon fuskar sa da yake yi. Murmushi Sani yayi fuskar sa da hawaye yace" Kaga abinda Allah ya maida ni ko Bala?" "..Na gani sani, ba komi bane kar ka damu wannan 'kaddarar Ubangijin mu ce.." " Hakane..ya ha'kurin mu kuma..Jasmine Allah yayi mata rasuwa?". Girgiza kai Bala mai gadi yayi yana jin mutuwar Baby har ransa...a fili furta" Ai yarinyar nan ta tafi da zu'katan mutane da dama, wallahi har yau ban daina alhinin rashin ta ba, mahaifin ta kansa ya kasa cire ta aransa, inajin kusan satin sa biyu kwance a asbiti sai jiya ya dawo..." " Allah sarki...Allah ya ji'kan Jasmine". Cewar Sani da fuskar ke cike da nadama marar misaltuwa, shi ka'dai yasan yanda yake jin abin a zuciyar sa. Sai da ya ja numfashi sannan yana duban gefe yace" Ina so mu gana da yalla6ai domin yau nake so in wuce Plateau.." " Ai kuwa yana ciki ka shiga ka same shi". Bala ya bashi amsa yana mai matsawa daga gaban sa.      A hankali Sani ya fara takawa kansa 'kasa yake tunanin ko kashe ni zasuyi ma ya zame min dole in nemi gafarar ku Oga Deeni babu yanda zanyi saboda ni na jawa kaina da wannan tunanin  ya nufi cikin gida. Sallama yayi a parlour yana jin zuciyar sa kamar zata faso waje...Yah Deen kansa da yaji muryar Sani sai da Zuciyar sa ta tsinke, sosai aka hane shi da yawan firgici amma babu yanda zai yi ya zame masa dole ne. Ciki-ciki ya bu'di baki ya amsa sallamar tasa, wanda ya matu'kar bawa Sani mamaki domin a yanda yaga Oga Deen yai masa ranar bai zaci zai samu amsar sallamar sa daga gare su ba,..." To ko dai bai gane Murya ta bane?" Sani ya tambayi kansa while yana nan tsaye sam ya kasa 'daga 'kafafun sa balle ya shiga. " Sani shigo ma na". shine abinda kunnuwan sa suka jiyo masa daga ciki wanda ya sashi 'karya ta tunanin sa na cewa bai gane shi ba. A hankali ya shigo yana yin 'kasa da idanun sa saboda kunya...gaban sa ya 'karaso nesa ka'dan da shi ya dur'kusa sau 'daya tak ya kalle shi daga haka yayi kasa da idanun sa duk da hakan sai da  ya fahimci muguwar ramar da yayi. Gaishe shi yayi ha'di da tambayar sa jikin sa..Yah Deen yana murmushi yace" Jiki Alhamdulillah ai sai dai in tambaye ka...yaushe aka sallame ka?" Sani yace" Yanzun nan bai da'de ba.." " Toh masha Allah, Ubangiji Allah ya 'kara sau'ki". " Ameen Yah Allah". Cewar Sani wanda daga hakan kuma sai ya rasa mai zai 'kara fa'di. Yah Deen tashi yayi ya zauna da kyau shima 'din bai sake fa'din komai ba. Bakin Sani har na rawa ya furta" Yalla6ai... ya ha...'kuri kuma..?" Inda Yah Deen ya amsa da fa'din" Ha'kuri Alhamdulillah...Jasmine kam an tafi..sai fatan Allah ya ji'kanta yai mata Rahama...". 'Kwalla Sani ya fara kamar ba namiji ba, take ya Deen ya zaro idanu yana duban sa yace" haba Sani...ba fa yau ne akayi mutuwar ba common share hawayen ka addu'ah kawai zamu yi mata ba kuka ba..." Shima 'din 'karfin halin maganar yake domin har yanzun bai gama samun sau'ki ba...kuma baya jin zai iya cire Baby a ransa kwanan kusa, ko yanzun ma kafin shigowar Sani pics din Baby yake dubawa yana tuno duk moments din da suka yi tare. Shine kawai ya matsa akan gida zai dawo shi yasa aka sallame shi baya ga har yanzun kirjin sa bai bar yi masa ciwo ba. Girgiza kai Sani yake yi a hankali cikin kuka yake fa'din" Yalla6ai wallahi na rasa ta ina zan fara neman afuwar ku, dan Allah ku yafe min..ku yafe min abubuwan da suka faru, ban ta6a dana sanin abinda nake aikatawa ba sai yanzun...ha'ki'ka na ci amanar ku na yaudari zuciyar ku na zalunci yarinyar da bata ji ba bata gani ba..ban san da wane idanu zan dube ku ba, kunya nake ji sosai, gani nake kamar Allah bazai ta6a yafe min ba...amma nasan idan kun yafe min wata'kila in samu sassauci...ka ro'ka min Hajiya ta yafe min dan Allah nasan tafi kowa shiga tashin hankali.." Cike da karfin hali Deen yace " Kar ka damu Sani, 'kaddara ce ai kuma dama azane yake, hakan ya zama ne tamkar Iznah agare mu gaba 'daya, ba mamaki ya kasance silan shiryuwan wasu daga cikin mu...ban ri'ke ka cikin zuciya ba saboda nasan baka da laifi Allah ne ya tsara saboda wasu dalilai da shi ka'dai ya sansu..fata na kawai ya kasance kayi nadama ne ta gaskiya kuma kayi min al'kawarin daga Jasmine bazaka sake 6ata 'yar wani ba...". " Insha Allahu ranka shi da'de..wallahi zan yi fatan mutuwa ta 'dauke ni fiye da sake ganin faruwar irin hakan a rayuwa ta, tsakani na da Allah nayi nadama.." " Very gud...zan so hakan ya kasance ko ba komai zaka taimaki ahalin ka ne, ba mamaki kana da 'kanne ko yayye mata, sannan dole wataran zakayi aure indai har ana raye, kuma zaka haihu...ka tsarkake tuban ka ta yanda zaka iya fansar ahalin ga fa'dawa cikin irin wannan halin". " Nagode sosai Allah ya 'kara girma Insha Allahu zan kiyaye..nagode daka yi saurin fahimta ta..Allah ya 'kara 'daukaka yalla6ai Allah ya baku madadin JASMINE, Allah ya yiwa rayuwa albarka ya ji'kan mahaifa...nagode sosai.." " Kar ka damu Sani..sai dai wani hanzari...inaso wannan abin da ya farun ya kasance sirri tsakanin mu, yanda ya faru anan bana so maganar taje ko'ina..Sani kayi min lakawarin bazaka fa'diwa kowa ba...." Ba haka yaso ba amma he had no choice than ya amsawa Yah Deen ko dan halaccin da yai masa ma..." Insha Allahu zan kiyaye yalla6ai kar kaji komai". Kai yah Deen ya jinjina cike da gamsuwa. Sani kam ba haka ya so ba, da niyyar sa idan yaje zai fadawa mahaifiyar sa komai ne amma tunda haka ya za6a shikenan..." zaka iya tafiya". Abinda ya tsinkayi muryar Deen ya fa'da kenan. Sai yace " To yalla6ai godiya nake...amma dama ina so ne yau in wuce gida saboda babu amfanin sake zamana anan..". " Saboda me yasa kuma zaka tafi?". " Hakan dai naga yafi min shiyasa na yanke shawara...". Tun kan ya rufe baki Yah Deen yace da shi" Aikin naka kuma fa...". " Yalla6ai bar batun aikin nan, da me zan yi aikin ni da ke da hannu guda, ko dama ace hannun nawa na nan yalla6ai ba zan iya aikin ba yanzu..gara kawai in koma gida...zai fi". Tausayin sa sosai Yah Deen yaji shi aganin sa ai shine yayi masa silar da har aka yanke mai hannun sa, duk da Sani yayi masa ba daidai ba amma sosai yake tausaya masa cikin zuciyar sa. A hankali ya sau'ke idanun sa kan Sani sannan yace" Ka bari amma ba yau ba ko zuwa gobe ka wuce, yanzun rana tayi idan ka 'dan huta kaga sai ka yi tafiyar bazan hana ka ba ". Sani ba haka yaso ba amma baya son yin doguwar musu da Ogan nasa, domin ya fahimci dauriyar maganar kawai yake yi ba jin da'din ta yake yi ba. Tashi yayi ya fita yana zuba godiya, domin da kansa yasan Deen yayi masa halacci, halaccin da bakowa ne zai iya ba, yasan komai da akayi masa a hospital Deen ne ya 'dau nawi, sannan kuma duk da yasan abinda ya faru amma ya 6oye bai ha'da shi da hukuma ba dan a hukunta shi sai ma ya bishi da nasiha, fatan Alkhairi kawai yake yi masa cikin zuciyar sa...yayin da Yah Deen ya lumshe idanun sa yana tunanin irin sallamar da ya kamata yayi da Sani. Safwan da yazo duba shi adaren yake gaya mai yanda suka yi da Sani..cike da jimami Safwan ya furta Allah sarki...rayuwa kenan, naje ai Dr.Felix ke gaya min ai already anyi discarging nashi ashe nan ya dawo". Sai da Sani ya kwana biyu kafin Yah Deen ya sallame shi da 50k yace yaje yayi jari da shi. Da farko Sani 'kin kar6a yayi amma Yah Deen ya tsare shi dole ya ansa yana godiya ya fita bayan yayi masa sallama ya tafi. Tun jiya abakin mai gadi yake jin labarin ai Hajiyar gidan sun tafi da su Ammi tun bayan rasuwar Jas, sosai ya tausaya mata wanda ya ku'durta cikin ransa cewar komai da'dewa sai ya dawo ya nemi yafiyar ta itama. Bai ko 'kara awa guda cikin gidan ba ya shirya ya tafi bayan yayi sallama da kowa haka suka rabu da Bala mai gadi kowa na jin babu da'di, rayuwa kenan ta ha'da ta kuma raba aduk lokacin da ta ga dama. *****      Tunda Yah Deen ya dawo gida yake damun Safwan da batun tafiya Shuwarin amma yana kakkaucewa domin shi yafi son sai ya 'kara warwewa while shi kam yana ganin kamar 6ata masa lokaci yake yi. Batun aikin sa kam ba'a magana..Safwan ne ya tura report can Abujan ta email bisa ga abinda yake faruwa da neman iznin hutu mai 'dan tsayi an kuwa amince masa..dan haka basu takura shi ba. Ransa ne ya fara 6aci da yanda Safwa ke jan ransa dan haka yace masa Zuwa tursday shi kam ya shirya tafiya kuma bazai fasa ba. Jin hakan yasa Safwan amincewa cuz yaga ya damu sosai, a lissafin sa kenan nan da kwana biyu zasu yi tafiyar. Adaren ranar ya kasa ha'kuri, sosai yaji zuciyar sa na son jin muryar ta, tun tafiyar ta basu sake ganawa ba..babu ma wanda ya 'kira shi hatta Anty Zainab tayi fushi da shi. Banda 'yan biyun Ammi babu wanda ya damu da shi yanzu. Relaxing yayi yana kan dialling numbern ta, cikin sa'a kuwa ya shiga, lokacin kwance take tana game in Candy Crush 'kiran ya shigo mata bazata kawai ta ja recieve wanda shigowan 'kiran kenan sai ya zama kamar jira take yi tayi recieve. Sai ma da ta 'dauka sannan ta fahimci abinda ta aikata ganin sunan shi rubuce kan fuskar wayar tata ga kuma sekanni da ke faman irguwa. Cike da haushi ta runtse idanun ta lokacin da ta tsinkayi muryar sa yana fa'din sunan ta. Taso tayi hangin call in amma bata so ya san cewa da gangan tayi dan haka sai ta ajiye wayar ta juyar da kanta 'daya gefen tayi shiru. Hawaye ne suka fara taruwa mata jin yanda yake maganar ko daga muryar sa zaka fahimci halin da yake ciki. "...mutuwa na kusan yi da kika tafi kika barni Nuree yaushe zaki dawo min?...baki ko yi tunanin halin da zan shiga ba kika tsallake kika bar ni bacin kinsan kece rayuwa ta?...". Cikin zuciyar tace" 'karya kake yi ni ba rayuwar ka ba ce Yah Deen..". Ta 'karasa fa'da hawayen ta na 'kara kwaranyowa. Wayar ba'a speaker take ba amma tana iya jiyo abinda yake fa'da. "...ni dai ki yafe min, ki dawo mu yi rayuwar mu dan Allah, Nayi miki al'kawarin canzawa, wannan karon dagaske nake yi bazan sake kwatanta ha'da wata macen da ke ba, ban ta6a tsammanin soyayyar da nake yi miki ta kai hakan ba sai da na wayi gari naga bakya gida na..please Nuree talk to me ko pim kice da ni insan cewa u ar with me...". Da sauri ta rarumi wayar ta kashe 'kiran tare da kashe wayar ma gaba 'daya. Kuka sosai take yi harda sheshsheka, taimako 'daya Allah yayi mata Ammi bata kusa da tasan dole ne sai ta tuhume ta. Da kanta ta lallashi kanta tayi shiru, har yau har gobe tana son mijin ta sosai amma bata jin zata iya sake rayuwar aure da shi, burin ta kawai ya bata sakin ta ta samu damar da zata yi rayuwar ta ba 'kar'kashin inuwar auren sa ba...abu 'daya da ke damun ta kuma yake sata tausayin sa shine fushin da iyayen sa ke yi da shi, duk bata jin dadin hakan kwata-kwata, zaton ta ma ko zai biyo bayan su da wuri bayan tahowar sun, bawai dan dan ita ba tunanin zai biyo bayan iyayen sa ne amma ga mamakin ta sai taga shiru. Koka'dan batajin tana son zuwan nasa dan jin da'din kanta face dan burin ta na ganin daidaito tsakanin sa da su Alhaji Baba. Domin ita nata ta riga ta gama lissafi bama ta damuwa da kanta ji take koda bai rubuta mata saki ba a hakan zata cigaba da rayuwar ta amma bazata ta6a komawa gidan sa ba. Indai igiyar auren ne zata iya tsare su batare da ta keta iyaka ba. Sai da ta idar da sallahr Isha'i sannan ta sake 'dauko wayar ta ta kunna, tasan in ba wani dalili ba abu ne mai wahala ya sake 'kiran ta cuz tasan halin sa sarai...dan haka ranta sake ta kunna wayar, wurin text ta shiga ta rubuta masa message ta tura masa sannan ta sake ajiye wayar ta. Yana zaune a parlour lokacin ya 6alli drugs 'din sa zai sha sai yaga wayar sa tayi haske alaman sa'ko ya shigo sai da ya kammala da shan maganin kafin ya 'dago wayar..ganin sunan Nureen sa ya sa jikin sa har na rawa ya bu'de text in... _Ka daina jinkirin neman yafiyan iyayen ka musamman idan suna fushi da kai, kar ka manta aljannar ka 'kar'kashin 'kafar su take...._ ". Abinda kawai ta rubuta kenan amma wani sanyi  da farin ciki ya ji ya ratsa shi har sai da ya lumshe idanu, wani zazzafan 'kaunar ta yake jin yana sake shigan sa, kife wayar yayi saman 'kirjin sa yana murmushi" how can i divorce u Nuree, ina son ki, ina kaunar ki Haske na...kyakkyawar zuciya gareki ba irin tawa ba, manufar ki kyakkayawa ce...wallahi farin cikina tare dake yake na sani... dan Allah ki dawo gida na..". Cikin zuciyar sa yake wannan maganar yana sakin murmush 'kayatacce. 'Dago wayar yayi ya rubuta mata reply da fa'din" _Zan zo Nuree na, dole zanzo, kema ki shirya tare mu zamu dawo..bazan iya rabuwa dake ba...luv u_ ". Yana gama rubutawa ya tura mata batare da ya saka ran ganin reply ba dan yasan ba sake kulashi zata yi ba. Ai kuwa Noor baki ta ta6e da ganin abinda ya tura mata daga hakan bata sake tura masa komai ba haka kuma shima 'din bai tura mata ba har kusan 'karfe goma sannan taga ya tura mata" _Ke ta dabance Nuree na, i luv u_ ". " Kai ka sani ai". Ta furta a fili sannan ta danna flight mode wa wayar ta cigaba da harkokin dake gaban ta. Babu wanda ya sake tura ma 'dan uwan sa komai har akaci kwanaki uku kwatsam rana tsaka sai gashi sun iso Shuwarin shi da Safwan abokin sa su biyu..... Comment Vote Share *_Salmerh_* 😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *83* Noor kam dama tun washegarin 'kiran da yayi mata tace da Ammi zata gidan Ummah ta kwana biyu, tayi hakan ne dan gujewa ha'duwar su musamnan ma da yake bata san actual ranar da zai zo 'din ba. Cikin sa'a kuwa Ammi bata hana ta ba cuz duk abinda take so shi Ammi ke yi mata bata takura ta. Dan ita Ammi gani take tamkar duk masu laifi suke agare ta tunda su suka aura mata 'dan su. So wannan dalilin ne yasa ko da suka zo ma basu ha'du ba, Ammi gaisuwan Safwan ka'dai ta amsa daga haka ta tashi ta shike ciki kamar wacce taje 'dauko abu amma suka ga shiru kusan mintina talatin bata ba labarin ta bata kuma le'kowa ba. Yah Deen kam bai yi mamakin hakan ba yayin da Safwan ke tunanin 'kila Ammi ta manta da su ne ma. Deen kam har zuciyar sa yake jin babu da'di dalilin ma kenan da yasa tun tahowar su bai 'kira su a waya ba cus yana da ya'kinin ba sauraran sa zasu yi ba....jikin sa sanyi 'kalau ya tashi ya shiga 'dakin ta..har zuciyan sa baya ganin laifin su cuz yasan koma menene shi ne ya jawa kansa. Zaune a bakin gado ya same ta hannun ta Qur'ani ne take karanta shi, tayi hakan ne kuma dan ta samu sau'kin abinda take ji a zuciyar ta musamman game da shi. Tana jin yana sallama amma bata ko 'dago ba balle ya sa ran samun amsawar ta. Ammi kam ganin ya shigo 'din bai sa ta fasa karatun ta ba. Tsayuwa ya cigaba da yi yana tunanin ta inda ya kamata ya fara. Ammi kam sai da ta dire suratul Rahaman 'din da ta fara sannan ta rufe Al-qur'anin tare da kawar da kanta gefe, batare da ta dube shi ba cikin sanyin murya tace da shi" Sakin 'yar tawa kazo ka kawo min ko kuwa rainin hankali ya kawo ka...?" 'Karasowa yayi gaban ta ya dur'kusa yana shirin kwantar da kansa saman 'kafarta tayi saurin mi'kewa tsaye tana duban sa kamar ba ta sanshi ba. Sam bai yi mamaki ba dan ya shiryawa fiye da hakan ma idan zasu mishi matu'kar za'a bashi matar sa bazai ji ciwon komai ba. Da raunin murya sosai yace " Ammi na..am ur Mu'een fa...". " Ai bani da idanu...". " Ammi dan Allah ki yi ha'kuri ki yafe min, Ammi ni kaina ban ji da'din faruwar wasu abubuwan ba amma sun riga sun faru kuma wallahi nayi regretting komai, Ammi ki fahimce ni dan Allah, nayi miki al'kawarin hakan bazai sake faruwa ba..sam bana jin da'din wannan fushin da kuke yi da ni Ammi...da wanne zanji? Ammi duk kun guje ni har Uncle Ja'afar baya 'daga 'kira na, Anty Zainab haka, Alhaji Baba kam bama zan fara ba, Ammi idan kowa ya guje min ai ke bai kamata ace kin goya musu baya ba...nayi ciwo kamar zan mutu amma babu kowa nawa da ya nuna min tausayawa Saif ne ka'dai, hakan ba 'karamin damuna yayi ba duk nasan shima Saif 'din kawai ne, Safwan ka'dai ke 'dawainiya da ni..wallahi da kaina kunya nake ji sosai idan na tuna ni na jawa kaina...kamata yayi ace zuwa yanzun kinfi kowa fahimtar nadama ta Ammi, ke kika haife ni kinfi kowa sanin ciwo na...Ammi fushin ku sosai yake hanani sukuni duk wayewar gari da damuwa nake sake yini ina jin babu da'di, tsoron ta yanda zan sake tunkarar ku shi ya hanani zuwa gare ku da wuri, dan Allah Ammi ku tausaya min ku yafe min laifukana.....". Ya karashe maganar hawaye na taruwa cikin idanun sa sai ya sunkura da kansa. Ammi kam bazata ce bata tausayin 'dan ta ba, tana son 'dan ta kuma tana son farin cikin sa, sannan raunin dake tare da shi sosai ya bayyana nadamar sa a fili, amma bata jin zata iya biye masa gudun kar ta shiga hakkin Noor bayan wanda aka yi mata abaya. Dole ta tilasta ma kanta zafafa kalaman ta tace da shi" Sam banga alamun nadamar gaskiya tattare da kai ba, sannan idan kana so ma ni na yafe maka toh ka tabbatar ka dan'ka min takaddar sakin 'ya ta ne, bazan iya sake juran ganin ta cikin mayuwacin hali ba".. " Ammi...nifa? bakya tauasaya min ko?" " Ka rubuto min takaddar sakin Hudah ka damka min then a lokacin zan iya tantance shin ina jin tausayin ka ne ko a a ". Hawayen da ya taru masa ne suka gangaro sai yayi saurin share su, gefe ya kawar da kansa yace" Ni dai Ammi kiyi ha'kuri, amma bazan iya sakin Noor ba sam...". " Then leave my room..." Ta daka masa tsawa. Zai yi magana ta yi saurin dakatar da shi da wani tsawan da ya zarta na baya, da yaren su ta fara mai masifar da ni kaina ma banji me take fa'di ba. Sum-sum naga ya tashi ya fita yana jin babu da'di, bai ko saurari Safwan dake kai komo a palour ba yayi waje kawai..bin sa Safwan yayi da sauri wanda direct wurin motar sa ya nufa Safwan ma ya bishi abaya. Jijiyoyin kansa duk sun firfirto, idanun sa jajaye, sosai yake jin ciwon wannan sakin da Ammi ke son yayi wa Noor, shi dai yana son Matar sa nd bazai ta6a iya sakin ta ba. Shiga suka yi dukkan su Safwan yaja motar, Yah Deen kam idanun sa ya lumshe a hankali yana jin zuciyar sa na mai suya. Be ce da Safwan komai ba har suka bar gidan...shima ganin halin da yake ciki yasa be furta masa komai ba. 'Kar'kashin wata bishiya yayi parking sannan ya dubeshi, kallon 'yan sakanni yayi masa yana mai tsananin tausayin sa na ratsa sa, sunan sa ya 'kira a hankali, Deen bai bu'de idanu ba yace da shi" Please muje wurin Alhaji..." Safwan bai tanka ba kawai yayi wa motar key, shine ke kwatanta masa gidan lambun Alhaji Baba har suka isa. Sai ma ya kasance abinda Ammi tayi masa mai sau'ki ne akan na Alhaji Baban, cuz shi har sai da ya mareshi ma yana huci yake sau'ke masa ruwan bala'in wai ya damesa da surutan sa na 'karya. Duk da hakan Yah Deen bai daina ro'kon sa ba, haka ma Safwan dake ta faman bawa Alhajin ha'kuri. Daya ga kamar zasu takura shi kawai sai ya wuce yana gyara zaman babbar rigar jikin sa yayi gaba ransa a matu'kar 6ace ya bar a wurin. Basu yi kasa agwiwa ba suka koma motar su suka bi shi abaya. Gida ya dawo ya wuce masallaci suma 'din masallacin suka nufa sai bayan an idar da sallah sannan suka nufo gida suna bin sa abaya har parlour...har alokacin kuma bai kara tanka su ba...hakan ma Allah ya taimake shi tare suke da Safwan wanda albarkacin sa yasa bai yi musu rashin mutunci son ransa ba. Ganin da suka yi ya shige 6angaren ya turo 'kofan ya sasu fahimtar dagaske fa Alhaji baya da alamun sake sauraron su. Haka suka koma 6angaren Yah Deen hankalin sa kashi-kashi, da ya ji motsi sai ya le'ka da tunanin Noor zai gani amma shiru har yanzun bai ganta ba, ko motsin mota yaji sai ya tashi ya le'ka amma ba ita yake gani ba, da daren asa rintsawa yayi, tun lokacin da yaga Alhaji yayi aike da mota yayi tunanin ko ita za'a 'dauko dan haka ya yi ta duban window amma koda aka dawo da motar mutum 'daya kawai ya gani babu ita, ko da safennan na ma haka ya dinga duban waje amma babu alamhn Noor 'din sa...har kitchen ya saci hanya da sassafe yaje ya duba wai ko zai ganta can da yake yasan halin ta da wuri take shiga kitchen ita, amma ko alamu bai gani da zai nuna masa cewa Noor 'din sa na kusa ba. Alhaji Baba bai sake tanka su ba har washegari wanda da safe bayan sunje gaida shi ya amsa sai ya 'kira sunan Safwan yace" Naga kamar kai in ka fishi hankali, dan Allah Safwan ka tattara abokin ka ku koma can inda kuka fito, daga yanzu zuwa 8:00 idan na ganku agida na ku tabbatar hukuma ce zata raba mu..banson damuwa sam dan Allah ku tattara ku tafi...". Shiru Safwan yayi yama kasa fa'din komai, hankalin Yah Deen sosai ya tashi, dan ga dukkan alamu bazai samu abinda yake so ba, Ammi ta kore shi ga Alhaji ma haka, sannan da alamu ganin Noor ma wahala zai bashi, ina ta shiga ne? Ya tambayi kansa. Tuno gidan Ummah da yayi ya sa ya 'dan ji sanyi aran sa da tunanin babu mamaki indai tana can zai iya ganin ta cuz yasan halin Ummah da kawaici bazata hana shi ganin ta ba....cikin ransa ya bari akan sai ya gama da 6angaren mahaifan sa kafin zai je gareta itama. Alhaji Baba na gama bayanin sa ya tashi ya fice ya bar su a 'dakin. Jim suka yi gaba 'daya, sun 'dauki tsawon lokaci ahaka bayan fitar Alhajin sannan suka tashi suka fita batare da kowa ya furta komai ba. Safwan kam kansa ya kulle ne gaba 'daya jikin sa ya mutu, yana so yayi wani abin amma sai ya rasa ta ina zai fara, Ammi zai fara tunkara ko Alhaji Baba? Dukkan su bai san suna da tsaurin ra'ayi irin haka ba...dalilin ma kenan da ya hana shi ta6uka komai kawai ya tsaya tunani. 'Bangaren Deen ma hakn ne domin kwata-kwata ya kasa sanin inda zai dosa, har tanga'di yake yi idanun sa na ganin bibbiyu, gani yake kamar rayuwar sa ne ta gangaro tazo 'karshe..." Ganin ya nufi waje ya sanya Safwan bin sa abaya, wajen mota ya shiga ya kishingi'da yana tunani, sun 'dauki tsawon lokaci ahakan sannan yace sutafi gidan su Noor...ko yanayin maganar sa kadai ma sai yabaka tausayi domin duk ya saduda yayi sanyi gaba 'daya. Koda suka je can kuwa basu samu kowa a gidan ba sai Ummie, Ummah bata nan sai Ummi ka'dai itace kuma ta sanar da su cewa ai Hudah tayi tafiya yau in nan da safe har da akwatin ta ma ta tafi. Deen kansa yaji ya sara masa da 'karfi dai-dai da bugun da zuciyar sa. Da mamaki ya kalli Ummie sai ma ya kasa fa'din komai. Safwan ne ya tambaye ta sunan garin da taje Ummie tace ita kam ta manta. " Ana wata ga wata"! Safwan ya furta a fili yana shafo kansa. Juyawa kawai Mu'een yayi ya fita yana jin tamkar ya zubda hawaye...Ko cikin motar Safwan ka'dai ne ke iya magana yana bashi baki. Da kalamai masau sanyi. *Darazau...* shine sunan gari na farko da ya fara zuwa cikin ransa saboda ta ta6a zuwa garin da jimawa kuma bai manta ba, amma kuma ko yaje in ma ai be san ta ina zai fara ba tunda shi ba sanin gidan da taje yayi ba, ya gwada 'kiran layin Noor yafi sau ashirin amma ko guda bai tafi ba _is not reachable_ ake ce da shi. Yanzu kam yasan Allah ne ka'dai gatan sa...cuz bai san ta inda zai tunkari wa'danann abubuwan ba, wani bin.sai yaji tamkar ya sjare kowa kawai ya koma yayi zaman sa har lokacin da zasu sa'kko sai dai bazai iya ba, ya riga ya yiwa Noor al'kawarin zai zo ya bawa su Ammi hakuri so baya son ya sa6a alkawarin sa. Sosai yayi danasanin rashin ajiye numbers in 'yan uwan ta cikin wayar sa, numbern Yah Usman ka'dai yake da shi wanda shima 'din ko da ya 'kira bai samu ta shiga ba. Haka ya dinga gwadawa lokaci zuwa lokaci, duk ya fice hayyacin sa ganin kamar rayuwa na shirin juya mai baya. Bai samu numbern Yah Usman ya shiga ba har sai kusan sha biyu na rana sannan, nan kuwa yayi 'karfin halin nutsar da muryar sa gudun kar ya fahimci abinda ke faruwa. Numbern Addah Maryam ya nema kawai batare da yayi mai wani dogon bayani ba. Yah Usman kam batare da wani tunanin ba ya tura masa numbern yana mai sake yi masa taazitan Baby cuz bai samu zuwa ba yayi wata doguwar tafiya ne zuwa 'kasar yarbawa, zuciyan sa cike da jin da'din yau Mu'een ya tuna da su. Sai da ma ya kira Addah Maryam din jin layin nata na tafiya sannan ya tura masa...shima atake batare da 6ata lokaci ba ya 'kira ta jikin sa har rawa saboda farin cikin da ya lullu6e shi, ya'ki yin magana ne gudun kar ta san shine itama ta kashe wayar ta ko kuma ta hana shi ganin matar sa idan yaje, yafi son yayi musu bazata a ganin sa hakan shi zai sa ya samu sau'kin ganin ta. Ajiyan numfashi Safwan ya sau'ke yana dawo da zaman kafafun sa dai-dai yace" Ina muka nufa yanzu?" " Safwan Darazau zamu je, inaga can Noor ta tafi". Kai kawai ya jinjina tare da yiwa motar key, cike da farin ciki suka kama hanyar Darazau da tambaya har suka isa. Sai da suka je in kafin ya sake 'kiran Addah Maryam da wani layin daban wanda ya san ba kowa ne ya sanshi da shi ba. Safwan ya bawa wayar gudun kar ta 'dago sautin muryar sa bayan ya shirga masa 'karyar da zai yi mata. Murmushi kawai Safwan yayi cikin ransa yace" Rayuwa kenan". Koda ta 'daga suka gaisa sai yace da ita 'dan aike ne shi daga Shuwarin amma bai gane kwatancen gidan ta da aka yi masa ba shiyasa ya 'kira. Addah Maryam da mamaki tace" 'Dan aike kuma? waye ya aiko ka?" Kallon Yah Deen yayi sai yayi saurin ha'da la66an sa yace" Ummah..Ummah" Batare da sauti ya fito ba. Safwan da bai gane ba sai kawai yace mata" Mama ce.." " Mama kuma? bangane ta ba, Mamar waye kenan". " mamar ki mana..ina sauri ne please kiyi min kwatance da wuri". ya bata amsa da alamun 'kosawa. Ranta bai so ba amma haka dai ta kwatanta masa, sam bata ji batun ya kwanta mata ba dan Ummah bazata yi aike batare da ta sanar da ita ba. Gashi wayar ta ba kati a lokacin balle ta kira Umman taji. Ko data kwatanta musun ma da 'kyar suka gane gidan hakan ma sai da suka ha'da da tambaya tukunna. Sun sha wuya sosai ga zafin rana amma Yah Deen duk bai damu ba matu'kar zai ga Matar sa bashi da damuwar komai. Yasan ganin ta ka'dai can heal what he is feeling a zuciyar sa, dawo da Noor rayuwar sa kuwa yasan dai-dai yake da shiryuwar sa da iyayen sa, yasan zata shige masa gaba dan tana da kyakykyawar zuciya, bata biyewa son zuciyar ta ta 'kuntata wani. Tarba mai kyau Addah Maryam tayi musu bayan fahimtar cewa Mijin 'kanwar ta ne yazo ashe". Sai da ta sake yi mai gaisuwan Baby cike da nuna tausaya suka jimanta lamarin kafin ta tambaye shi lafiyar 'kanwar ta. Sosai suka yi mamaki da jin abinda ta ce dan ko ka'dan babu alamun wasa tattare da maganar ta...duk da hakan cikin zuciyoyin sai suke ganin kamar wasa da hankalin su kawai take so tayi. Ta fahimci sauyin yanayi tattare da su wanda ta lura tambayar Noor da tayi sai da yasa suka dubi juna amma bata wani sa akanta ba kawai ta 'karasa da tambayar su aiken da suka ce an turo su. Sam Addah Maryam bata san abinda yake faruwa ba, tun bayan da suka dawo daga Bauchi gaisuwar Jasmine gidan ta taho saboda ta bar yara kuma tun daga ranar bata sake jin komai ba, ko Noor ma sukan yi waya da ita lokaci zuwa lokaci amma bata ta6a sanar da ita komai ba game da ita ba. Safwan ne ya gyara zama da kyau yana duban ta yace" Antyn mu afuwa muka zo nema, dan Allah ayafe mana abinda ya riga ya faru...Anty ki taimaka ki ha'da mu da Noor ko na mintina uku ne dan Allah badan mu ba...".. Zaro idanu Addah Maryam tayi tace" Noor kuma? Rabo na da ita tun bayan bari na Bauchi sati kusan hu'du kenan yanzu ban 'kara sanya ta a idanu na ba sai dai awaya". " Ya salam!..." Yah Deen ya furta gami da dafe kansa dake sara masa, zugum ya zauna yayi 'kasa da kansa yayin da Safwan ya furta Innalillahi wa innah ilaihi raji'un...ayanda suka ga yananin da ta shiga ka'dai ma ya ishe su fahimtar iya gaskiyar ta kenan. " Wai me ke faruwa da ita ne ku gaya min?" Ta sake tambayar su cike da damuwa dan ta fara fahimtar akwai wani abin daban da ita bata da masaniya akai. " Kina nufin ba nan ta zo ba? Yau in nan fa akace tayi tafiya ta bar Shuwarin ina taje to? munyi tunanin nan tazo shiyasa muka biyo sahunta..." Safwan ne ya fa'di hakan yana duban Addah me Maryam dan sake karantar yanayin ta. tace " Ikon Allah..bata iso nan ba wallahi...kuma mun kwan biyu bamu koyi waya da ita ba Ina Hudah ta shiga ni Maryamu...". Ta 'karasa maganar cike da alamun rikicewa. Wayar ta ba kati amma haka ta gwada layin nata kuma bai shiga ba...itama 'din rikicewa tayi sosai kuma sai bata yi tunanin ayi 'kiran Ummah ba... Yah Deen ta shi yayi Safwan na shirin ce da ita ta tambaya musu Ummah ko ta sani...amma sai ya ga yacrike kai sosai yana shirin zubewa...da sauri Safwan ya mike ya rike shi suka fita. Direct mota suka koma ko sallama babu wanda yayi mata suka kama hanyar Bauchi...numfashin Mu'een na fita sama-sama saboda tashin hankali. Ko tsakanin su ma babu mai ce da wani 'kala domin duk tunani ne fal cikin rayukan su, Deen tunanin inda Noor ta shiga yake yi yayin da Safwan ke tausayawa halin da abokin nashi yake ciki. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *84* 'Bangaren Noor kuwa tun lokacin da taga an kawo mata kayan ta jiya da dare da ku'di wai daga Alhaji Baba sai taji hankalin ta ya kasa kwanciya cuz bata san dalilin hakan ba. Tana cikin tunani taga 'kiran Ammi ya shigo mata, take zuciyar ta ta tsinke sai ta fara tunanin ko Yah Deen ya sake ta in ne kamar yanda ta bu'kata. Da rawar murya tayi wa Ammi sallama tare da gaida ta nan Ammi ke shaida mata sa'kon Alhaji Baba cewa ta shirya gobe da sassafe driver zai zo ya kaita Azare daga nan ta wuce Taraba gidan Anty Zainab". Bata yi musu ba duk kuwa da cewa abin ya mata bazata amma sam baza ta iya ja da Ammi ba balle Alhaji Baba da kansa...Ammi 'karasawa tayi da bata ha'kuri gami da kwantar mata da hankali. Murmushi tayi tace" Haba Ammi bakomai ai..". Suna gama wayar ta yiwa Ummah bayani...Ummah kam dama tasan bakomai zata ce ba, ai kuwa kawai cewa tayi" Allah ya kaimu goben". Daga haka shikenan bata 'kara fa'din komai ba, ita kam bata san ranar da rayuwa zai daidaita wa Noor ba, tausayin yarinyar a kullum 'kara ratsa ta yake yi, yarinya ce 'karama amma abubuwa na neman fin 'karfin shekarun ta...sau tari shiru kawai take yi ta bisu da idanu ba wai dan bazata iya sanya baki cikin maganar su ba a a..haka kawai wani bin sai taga shirun yafi mata koda kuwa abin ya ta6a zuciyar ta ne. Kamar dai wannan, tafi so taji inda matsayar auren Noor yake amma kuma sai aka 6ullo da batun tura ta wani.garin daban, bata so hakan ba dan tasan still da aure akan Noor kuma bazata so a keta haddin Allah ba amma dayake suke da ita yanzun hakan yasa kawai tayi shiru da bakin ta. Tun cikin daren Noor ta gama shirin ta tsaf washe gari kuwa 'karfe shida Alhaji Baba ya aiko mota aka kaita inda ta hau mota. Batasan dalilin tafiyar ba amma cikin zuciyar ta take jin kamar ba haka kawai bane aka ce ta tafin, ko gwada 'kiran da su Safwan ke tayi mata ma ba wai ta kashe wayar ta bane a a kawai dan tana kan hanya ne shiyasa ba' a samun ta. Bata sani ba ashe Alhaji Baba yayi gudun ha'duwar ta da Deen ne, ya sani matu'kar tana gidan Ummah toh Mu'een ba zai sha wahalar shawo kanta ba da yake yasan mata da rauni shiyasa yayi tunanin tura can in. Tun adaren ma ya sanar da Uncle Ja'afar isowan ta da kuma garga'din kar su yadda su sanar da kowa cewa tana nan. Alhaji da kansa ya fa'di hakan kuma Anty Zainab ma da kunnan ta taji dan haka sosai ta kame bakin ta cuz ko da wasa bazata yadda ta yiwa Alhaji kuskure bisa hukuncin sa ba. Tana isa Taraba aka taho da ita gida dayake already Uncle Ja'afar ya tura a 'dauko ta. Anty Zainab kam murna ta samu abokiyar hira a gidan dama ka'daici ya dame ta sosai, murnar ta kasa 6oyuwa tayi ita da kanta ta 'kira Ammi ta sanar da ita cewa Noor in ta iso. Ammi kam cewa tayi" To dan Allah ki kula min da ita har zuwa lokacin da yaron nan zai sakar min ita, naji ma Alhaji na zancen makarantar ma 'kila acan zatayi dan Allah amanar 'yata Zainab, marainiya ce, ga kuma maraicin 'ya data ke ciki banda damuwar dake 'kunshe cikin zuciyar ta dan Allah ki bata kulawa kinji... " Insha Allah kar ki wani damu". "Kuma kar ki yadda Mu'een yasan cewa tana wajen ki takura ku zai yi sakin ta nake so yayi bazan kuma barin ta zama da shi ba..". " Bazai sani ba Insha Allah ki kwanatr da hankalin ki" Anty cecda fa'di hakan da tunanin.kuskuren da Mu'een ya aikata, sam bata son zancen rabuwa tsakanin su, bata do taji Ammi na wannan ikirarin amma ga dukkan alamu haian ka'dai Ammi ke muradu har cikin zuciyar ta a yanzu, bata damu ba indai za'a hora shi koda na shekara nawane amma bata so sam taji wai rana auren su za'a yi.... Tana cikin tunanin taji Ammi na fa'din" Yauwa bani Hudahn mu gaisa..". Mi'ka mata wayar Anty Zainab tayi tana sakin ajiyan zuciya gami da murmushin 'karfin hali. " Ki saki jikin ki wurin Antyn ki kinji, bata da matsala ni kaina nasani, kuma ki rage yawan damun kanki with time komai zai wuce kinji?" " Toh Ammi". Noor ta bata amsa cike da girmamawa yayin da Ammi ta cigaba da fa'din " Kuma ko ya 'kira ki kar ki yadda ki sanar da shi inda kike Alhaji da kansa ya hana asanar da shi, bama shi ba duk wanda zai 'kira ya tambaye ki garin da kike plz Hudah kar ki fa'diwa kowa kinji?" " Toh Ammi insha Allahu zan kiyaye...nagode sosai..". " Bakomai". " Ubangiji Allah ya 'kara girma.." Daga haka suka yi sallama da Ammi. Anty Zainab kam.kanta ta tallafa da hannu tana binta da idanu zuciyar ta cike da tunani...har gobe ladabin.Hudah na birge ta, yarinyar nada hankali sosai, me yasa su Ammi zasu yanke wannan hukuncin da wuri haka? A ganin ta raba shi da Noor sam bazai kawo gyara ba..kamata yayi a zauna a sake tunani..ita kam Noor da Mu'een duk cikin.zuciyar ta take jin su, bata sani ba ko dan Allah bai ta6a bata haihuwa bane shiyasa hakan oho, ko da wasa bata so taga 'dayan su cikin 'kunci in ba ya zama dole ba, ko 'kiran sa da bata 'dauka a yanzun ita ka'dai tasan yadda abin ke cin ta cikin zuciya, sai dai babu yadda zata yi ne kawai tunda ance dole sai an hora shi shiyasa take biye musu dan dole ba wai dan tana so ba. Cikin zuciyar ta ta bar batun bayan ta yanke shawaran da take ganin yafi mata. ***** Anty Zainab kam ba ya ita, Noor har kasa ganewa take yi cikin ita da Ammi waye yafi sonta, ha'ki'ka ba 'karamin dace tayi da iyayen miji masu tsananin 'kaunar ta ba, sai da kash 6angaren mijin ne aka samu babbar matsala domin sai a hankali. Rayuwar ta take yi cikin kwanciyar hankali bata tare da damuwar komai yanzu, gidan Anty Zainab babu aikin komai dan duk house maid 'din ta keyi kuma haka suka saba abin su. Girki ka'dai ne take yi shima 'din Anty Zee bata ta6a barin Noor tayi ita ka'dai. Da yake dama sun jima da yin sabo da Anty Zainab so ba wani ba'kunta, Anty Zainab kam sai da nutsu ta fahimcevta sosai, da kanta ta gane Noor ma yanzu.bata 'kaunar sake zama da Mu'een hakan yasa ta ringa binta a yanda take so amma a kullum burin ta ba wuce taga ta gyara wannan auren ba sai da; ta lura cewa sai tabi a sannu. Cewa tayi tun bayan rasuwar Baby ta lura Noor bata gyara jikin ta sosai, da yake Anty Zainab 'yar gayu ce ta gaske bata wasa da gyaran jikin ta, hakan yasa ta ja Noor suka je suka yi mata siyyaya na kayan gyaran jiki da mayuka masu kyau da tsada wanda zai dace da fatar jikin ta itama ta rara amfani da su. Duk kuwa fitan da suke yi sosai Noor take 'ko'karin ganin ta kare martabar auren ta, bata ta6a barin kafar da za'a yi tunanin babu aure akanta da yake tasan har yanzun Mu'een bai sake tan ba. Ammi kam na cana.mam sam hankalin ta ya kasa kwanciya musamman da yake tasan Mu'een 'dan gaban goshin Anty zainab ce, tasan a kullum abinda yake so shi take yi masa, hakan sai yasa take ganin kamar zata iya bashi daman ganawa da Noor batare da sun sani ba. Saboda gudun kuskure ko kuma abinda kan iya zuwa ya dawo yasa ta bawa Noor shawaran kwashe numbobin ta dake kan Layin ta sai ta canza sabon Sim ta fara amfani da shi kafin zuwa wani lokaci. Ai kuwa Noor bata yi musu ba tashin farko tayi na'am da wannan shawaran musamman da ta tuno 'kiran da yayi mata kafin tahowar ta Taraba. Hakan ya sa batarecda 6ata lokaci ba ta ajiye sim 'din ta sauya wani, sai daga baya take yiwa Anty Zainab bayani da msmaki tace" To meyasa sai anyi hakan kuma..ko duk gujewa 'dan nawa haka Noor?" Noor murmushi tayi tana sunkuyarcda kai tace" A a fa Anty...Ammi ce tacecin sauya ba wai dan shi bane.." " Ita Ammin fa? Ai na lura itama yanzu duk a tsarge take...bansan meyasa hakan ba wallahi, ai abin zai masa yawa, ni nan gashi an hanani waya da shi 'karfi da yaji, Uncle Ja'afar har mamaki yake bani yanda ya hau dokin fushi da shi sai inga kamar ya manta waye Mu'een ne..kuskure kam ai kowa nayi haka ma laifi amma nashin sai aka tsaurara sosai wallahi bana jin da'di sam...sosai nake tausayin sa, yaro ba'a da'de ba ya rasa 'yar sa wacce kowa yasan irin 'kaunar da yake yi mata kuma sai a sake sashi agaba cewa ya rabu da matar sa ba ko tausayawa fisabilillahi akwai adalci anan kenan....fushin da suka 'dauka da shima ai wani tashin hankalin ne a gareshi...haba dan Allah, kema kuma sai kika biye musu ko?". Shiru Hudah tayi ta sunkuyar da kanta. Anty ne ta cigaba da fa'din" Harda canza layin ki bayan kinsan dole zai nemeki ko min da'dewa...". " Ayyah Anty nifa haka kawai ne na canza ba dan wani abu ba..kawai na gaji da wancan 'din ne". "..hmm ke de ki bi a hankali..kar ki biyewa zuciya Noor mijinki na 'kaunar ki ke kanki kinsani wallahi ko yanzun ma da aka jishi shirun nan nasan ba cikin natsuwa yake ba..Allah ne ka'dai yasan halin da yake ciki amma kowa ya kasa tausaya masa...kun ha'de mai baki kuna azabtar da shi abanza bacin duka abubuwan da aya aikata 'din ba akansa aka fara ba, kuma ma inada ya'kinin zai nutsu ko dan abinda ya faru ma...me yasa sai kun 'kara mai da wani...?." Sosai zuciyar Noor ta karye sosai jikin yayi sanyi 'kalau. Mi'kewa tayi ta koma 'dakin ta cuz tasan idan ta cigaba da zama anan kuka ne zai 'kwace mata. Ko bayan fitan ta Anty kam surutu ta ringa yi dan harga Allah ita kam bata jin da'din wannan hukuncin. Tayi 'ko'kari sosai wajen ganin ta manta da komai, ta manta rayuwar ta na baya, musamman dacyake Anty bata sake tada maganar atsakanin su ba, Addu'a kawai take yiwa Mahaifin ta su Nanne da kuma Jasmine fatan ta a kullum shine Allah Ubangiji ya ji'kan su da Rahma ya kyautata zuwan na baya. Cikin lokaci 'kan'kani ta murje jikin ta ya dawo, tayi wani fresh da ita, yayin da Yah Deen ke can kwance rai a hannun Allah zuciyar sa tayi mummunan bugun da likitan sa ma sai da ya tsorata da shi. Tun da ya gwada 'kiran ta yaji baya shiga sai hankalin sa ya tashi sosai. Shi tsoron sa ma kar ace wani abin ne ya same ta batare da ya sani ba. Cikin rashin sa'a kuma duk 'kiran da yake gwada yi mata sai yake zuwa da sa6ani da farko kafin ta canza layin baya 'kira sosai amma tunda ta canza a lokacin kuma sai yafi jin damuwa da ita a kullum sai ya gwada 'kiran layin nata fin sau biyar amma yaji baya samu. Hankalin sa sosai yake tashi, ranar sai ya 'kira Ammi bai ma zaci zata 'dauka ba ga mamakin sa sai yaji ta 'daga.. Jikin sa har na rawa saboda jin da'di yace "...Ina yini Ammi.." Tace " Lafiya". A takaice. " Ya wajen su Alhaji..?" shima 'din" Lafiya" ta sake fa'di. ji yayi kamar ya rushe da kuka saboda takaici, wai yau shi Ammin sa ke yiwa irin wannan abin, me za'ayi da banzar rayuwa...kwantar da murya yayi tamkar gaban ta yake da kaji muryar zaka san cikin matsanancin halin da za'a tausaya masa yake ciki a hankali cikin raunin murya ya fara magana... " ...Ammi kiyi ha'kuri badan hali na ba, Ammi ku yafe min, wallahi ji nake kamar zan mutu saboda rashin sukuni bansan inda zan saka rayuwa ta ba, abubuwa dayawa nayi nadamar su Ammi..ko ban fa'da ba da kanki ma nasan kin fahimce ni, ko kowa ya guje ni Ammi ke be kamata ace kin guje ni ba, ki tausaya min Ammi ba dan hali na ba, gashi inata 'kiran Noor kullum ba ya shiga please Ammi ke uwata ce wacce ta haife ni nasan baza'a rasa birbishin 'kaunata a zuciyar ki ba, Ammi ko dan saboda nawin ciki na da kika 'dauka na tsawon watanni..dan Allah ki yafe min Ammi...ki yafe min ko zan samu sassauci daga wani 6angaren cikin abubuwan da ke damu na, Ammi ki yafe min kuma ki tausaya min ki ceci zuciya ta ki gaya min inda Noor take Ammi hankali na ya kasa kwanciya...". " Ta mutu". Shine amsar da Ammi ta bashi ata'kaice,.amsar da ya doki zuciyar sa take ya haddasawa jikin sa karkkarwa. Da rawan muray murya yace" Ammi Noor fa nake nufi Nuree...na...my wife..". " I said ta mutu, kasa aranka bata raye kawai dan bazaka sake ganin ta ba..". Tana kaiwa nan ta cire wayar a kunnan ta gami da hanging call in. Ita kanta ba 'dadi take ji ba, sai take jin wani tashin hankali game da shi musamman da yake tasan ba lafiya cikakka gare sa ba, gashi a kwanakin takan yawaita mafarki da shi marasa kan gado duk tana ankare da hakan amma babu yanda zatayi..so take yasan muhimmancin Noor ya kuma san muhimmancin zama mutum nagari, so take da kansa ya fahimci illar rayuwar da ya za6a ma kansa...so take yayi tuba na gaskiya, can cikin zuciyar ta ba son rabuwar su take ba sam, domin tasan kafin ya sake samun madadain Noor zai matu'kar wahala sosai, ko kalan ha'kurin da tayi ma da wuya kasamu mai ma irin sa balle kuma hankali da natsuwar ta, amma aganin ta hakan ka'dai shine mafita tunda ma Noor da kanta ta nemi sakin, kuma tasan tayi ha'kuri da shi abaya baya ga haka da bazata ta6a saka baki 6angaren sakin ba sai dai kawai ta hora shi. Shiru tayi tana tunani jikin ta sanyi 'kalau. 'Bangaren Yah Deen kuwa bai ma san lokacin da wayar ta bar hannun sa ta fa'di 'kasa ba, ji yayi ya kasa tantance tsakanin sama da 'kasa ina yake rayuwa, idanun duk sun cika da wasu kalan 'kwalla masu matu'kar numama zuciyaya, 'kirjin sa tafarfasa ya fara....danganta Noor da mutuwa daidai yake da fitan nashi numfashin ya haka yake ji kamar...da wanne zai ji? da alhinin rashin Jasmine zai ji ko da fushin da suke yi da shi ko kuwa da rashin Noor da ya dame shi. Idan kana daga kusa da shi a fili zaka dinga ganin yanda 'kirjin sa ke hawa da sau'ka, wanda cike da matsanciyar azaba ya dafe saitin zuciyar sa, hawaten sa suka gangaro har tsawon wani lokaci zai 'dauka yana azabtuwa da rashin makusantan sa, masoyan sa masu matu'kar daraja agare shi? mai yasa bazasu fahimci halin da yake ciki ba? Da 'kyar numfashin sa yake fita yana komawa. 'kiran Ushaq ne ya shigo masa a daidai lokacin..sai ya lumshe idanu kawai baya son.Isahqvya fahimci halin da yake ciki danbhaka bai 'daga wayar ba har ta tsinke wani 'kiran ya sake shigowa. 'Karfin.halin 'dagwacyayi bayan yayi 'ko'karin daidaita murya muryar sa. Ishaq na ganin an 'daga sai yayi sallama amma ya kasa amsawa. " Hello! Ishaq ya sake fa'di Mu'een sai ya 'kira sunan shi cike da 'karfin hali. Duk 'ko'karin da yayin kuwa hakan bai hana Isahq fahimtar yanayin da yake ciki ba. " Me ke faruwa ne?" ya tambaye shi daga dayan 6angaren yana mai bada hankalin sa gare shi. " Bakomai". Yah Deen ya amsa a takaice yana mai juya kansa. " Ja gaya min plz..I heard ur voice wani iri like akwai abinda ke damun ka...please tell me...dama na jika shiru 2days shiyasa na 'kira...hope ba wani abu bane?" " Bakomai Ishaq kar ka damu...". Saurin taran sa yayi da fa'din" Nasan akwai... please Mu'een tell me kar ka 6oye min hankali na ya tashi sosai". " Ishaq...mutuwa zanyi ku yafe ni...dan Allah..". Yayi maganar muryar sa na rawa. " Subhanallah...me ke faruwa kuma..?" Ishaq ya tambaya cike da kulawa yana jin tamkar ya gansa agaban sa a wannan lokacin. " Ammi..! Kasa karasawa yayi sakamakon ciwon da ya sake haura masa. A hankali ya saki wayar ta sulale Isahq nata Hello! Hello!! amma yaji shiru. Ko da ya sake kira kuma ba'a amsa ba. Sosai hankalin sa ya tashi...ya fara 'kiran Safwan shi kuma bai ma ji ba wayar tasa na silent so bai san ma da 'kiran ba. Haka yayi ta gwadawa amma baya 'dagawa haka ma Mu'een. Kansa ya dafe daga inda yake tsayen cuz tuni zama ya gagare shi. Sai ma ya rasa wa ya kamata ya 'kira. Addu'a ya ringa yi da fatan Allah ya ta'kaita masa. Tuni ya yanke shawaran tafiya gobe-gobe idan ya tashi cikin masu rai dole sai ya je ya duba halin da abokin nasa ke ciki kafin zai samu natsuwa...sosai yake tausaya masa duk dama yasan wani abin har da laifin sa a ciki amma a yanzu abin tausayi yake matu'ka. .....Deen ya 'dauki tsawon lokaci ahakan kafin Allah ya taimake shi ya kawo masa Safwan wanda tasowan sa kenan daga aiki ya nufo gidan cuz baya iya jimawa batare da yazo ya duba shi ba saboda yasan lafiya tayi masa 'karanci a yanzu, kusan ma za'a ce tare suke yini agidan dan akoda yaushe idan kaga anfita to Safwan ne, idan an shiga ma shi 'din zaka gani. Da ganin halin da yake ciki arikice yayi kansa yana salati. Yau ma Bala mai gadi ne ya taya shi suka kaishi mota, shikan sa Bala tausayin Ubangidan nasa yake yi sosai, yau lafiya gobe akasin haka...duk ya lalace ya zama kamar ba shi ba. Tun rasuwar Baby Jas gidan bai 'kara zama dai-dai ba, sai dai takamammai idan za'a yi masa tambaya bazai iya fa'di ga dalilin da ya kawo rushewar farin cikin gidan ba. Amma abin na damun sa sosai...ko ranar da suka yi bankwana da Sani ma sai da yayi 'kwallah saboda tausayin sa, ganin yanda rayuwa duk ta juya mai cikin kwanaki kalilan. ***** Sosai likitoci suka fara bashi taimako wanda kamar jira yake da shigar su asbitin ta fara tari mai azabtar wa, yi yake yi Safwan na goge masa bakin sa, idon sa guda ne ke hawaye saboda azaba, daka ganshi zaka san cikin matsanancib hali yake kuma har a lokacin hannun sa na dafe da 'kirjin sa ne. Yana tarin idanun sa suka fara kakkafewa nan take ya yi 'dif komai ya tsaya masa. Safwan kam rikicewa yayi sosai take ya 'daga wa likitocin hankali kan su ceto rayuwar sa dan Allah. Sai da ya tabbatar an bashi taimakon da ta dace kafin ya nutsu ya fita daga 'dakin yana share gumi a goshin sa. Da fitar sa sai ya ciro wayar sa sai a lokacin ma ya ci karo da tarin missedcalls in da Ishaq yayi masa, Alhaji Baba ya fara 'kira yau in yana kuka yake bawa Alhaji ha'kuri akan ya taimaka ba dan halin sa ba ya yafe masa Yace wallahi Mu'een na matu'kar bu'katan taimako, yace ba fata ba amma a irin halin nan da yake ciki gab yake da ya rasa rayuwar sa, to me zeje ya gayawa ubangijin sa idan ya koma gare shi yana 'dauke da fushin iyayen sa, Alhaji u need to see his condition bai ta6a irin hakan ba..dan..Allah kuzo ku duba shi Alhaji..kuyi masa albishir in..kun yafe masa...". Alhaji Baba kam sai da ya gama jin bayanan Safwan sannan ya bashi amsa da fa'din" Bani da lokacin zuwa ko'ina Safwan, abubuwa da yawa ne akai na...." " Innalillahi wa inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, haba Alhaji, 'dan ka ne fa..? Wallahi Mu'een yayi nadama Alhaji, na tabbata bazai sake kwatanta waccen rayuwar ba..dan Allah Alhaji ka yafe masa...". Murmushin takaici Alhaji Baba yayi sannan yace" In dai ka biyewa Mu'een kunya zai baka Safwan, kawai ka share shi, bana masa fatan abu mummuna a rayuwar sa amma sam ban ga alamun nadama tattare da shi ba". " Alhaji ni na tabbata yayi kuma daka ga halin da yake ciki a yanzun kaima zaka fahimta da kanka...dan Allah ku tausaya masa Alhaji..nasan bazai sake kuskuren maimaita irin hakan ba". " To ka bari zanyi tunani akai, ka kwanatr da hankalin ka kaji". " Owk Allah bada iko..godiya muke Alhaji Ubangiji Allah ya 'kara girma". Sai bayan gama wayar sa da Alhaji Baba kafin ya 'kira Ishaq, ha'kuri ya bashi game da rashin 'daga wayar sa da be yi ba. Ishaq kam wannan be dame sa ba fiye da 'kaguwa da yayi yaji halin da Mu'een ke ciki. Nan kuwa Safwan yayi masa bayani a takaice cikin nuna tsananin tausayawar sa. Fatan samun sau'ki yayi masa sannan suka yi sallama. Washegari Ishaq ya kama hanya, sai da ya tsaya a Shuwarin wurin iyayen Mu'een ya 'kara basu hakuri cikin lafazi mai sanyi kafin ya wuce garin Bauchi. Shi kansa Alhaji Baban bayan tafiyar sa ya jima yana tuananin, sosai ya yaba da hankalin Ishaq, sai ma yake kara gode Allah da ya hada Mu'een abota da irin su ba dan hakan da be san inda zai javrayuwar sa ba, cuz abokai na da matukar tasiri a rayuwar mutum. Maganganun Ishaq ne ke tayi masa yawo akan sa ya kasa manata su, shi kadai sai yayi murmushi dan sosai Ishaq ya karya masa zuciya har ma yasa shi bayyana sirrin.dake ransa game da Mu'een batare da ya farga ba wanda yasan bakomai.ne yasa hakan ba face kamalar da Ishaq ke da ita, mutun ne shi da ganin sa na farko idan.kayi zaka fahimci nutsuwar da ke tattare da shi. Murmyshi ya sake yi cike da tsananin jin da'di yake tuno kalaman Ishaq in...." Alhaji Baba ka dube ni matsayin 'dan ka daka haifa karka yi min duba irin na abokin 'dan ka, wallahi har cikin zuciya ta nake jin ka Alhaji, ka yi min duba irin duban da kake yiwa Saif da Zaidullahi..yau ina gaban ka ne matsayin dan ka Alhaji, da wannan matsayin nake barar alfarma ta farko a wurin ka kayi ha'kuri alfarmar Annabi Muhammad (SAW) ka yafewa 'dan uwa na, kar ka dubi girman kuskuren sa Alhaji..falalar yafiya kawai zaka duba, wallahi bana samun natsuwa a duk lokacin da na tuna halin da Mu'een ke ciki, bana jin da'di, ni ban tashi da mahaifiya da mahaifi ba amma ina jin ciwon hakan har yanzu, sai dai da yake nasan ikon Allah ne shiyasa bana damuwa sosai, duk da yake naso in taso tare da su amma Allah ya riga ya kar6i rayukan su tun kafin girma na dan ya fini son su, hakan ya sa na tsani inga ko 'karamin sa6ani ya faru tsakanin 'da da iyayen sa, balle Mu'een da nake jin sa tamkar 6arin jiki na, Alhaji idan kana fushi da Mu'een tamkar da mu duka kake yi domin duk rashin walwala ke ziyartar mu, ka ji 'kan mu Alhaji ka yafe mana ko farin cikin mu zai cigaba da wanzuwa, da kanka nasan bazaka ji da'di ba ace duk yaran ka na cikin 'kunci dalilin mutum 'daya tak... da kaina nasan Mu'een yayi kuksure amma Alhaji dogon fushin nan sake 6ata lamari zaiyi ba ze gyara ba, Alhaji idan har ka yadda cewa nima 'da nake a wurin ka dan Allah a karon farko ka yi min wannan alfarman ka yafewa 'dan uwa na laifukan da yai maka, hakan ka'dai ya ishe ni yadda cewa mahifina nanan a raye bai mutu ba...". Idanu Alhaji Baba ya lumshe sannan ya bu'de su akan fuskar Ishaq, tausayin sa ne sosai ya kama shi, ha'ki'ka maraici abu ne mai ciwo sosai, bai ta6a sanin Ishaq maraya bane ba sai yau da ya furta masa. Yana cikin tunanin yaji Ishaq na sake fa'din" Dan Allah Alhaji kayi ha'kuri kace ka yafewa Mu'een..nayi maka al'kawarin bazai sake maimaita irin wancan kuskuren ba, idan ma ya sake faruwa ka tuhume ni..." Ajiyan numfashi Alhaji Baba ya sau'ke yana jin wani sanyi da farin ciki na ratsa masa zuciya..duban Ishaq ya tsaya yi na tsawon sakanni sannan yace da shi" Matso nan Ishaq zo kusa da ni". Matsawa Ishaq yayi kamar yadda Alhaji Baba ya umarce shi. Kansa Alhaji ya shafa yana jin 'kaunar sa na ratsa masa zuciya. Ishaq 'kasa yayi da kansa cikin girmamawa, Addu'a yake a zuciya Allah yasa Alhaji Baba kar ya 'ki amincewa. Yana cikin wannan tunanin yaji Alhajin na ce da shi" Kasa naji da'di sosai Ishaq, ka dasa min sabon hpoe a zuciya ta, yanzu ina jin kaina ne matsayin mahaifin 'ya'ya har guda biyar...rabon da naji ni cikin irin wannan farin cikin har na manta, Allah yai maka albarka Ishaq, Allah ya ji 'kan mahaifan ka. Naji da'di sosai da ya kasance kana daga cikin makusantan Mu'een kasancewar ka abin ayaba a kuma yi alfahari da shi, hakan ka'dai ma baiwa ce..kuma ngd wa Allah kan hakan..." " ko ban fa'da ba nasan kaima kasan laifin da Mu'een ya aikata ko?" " nasa ni Alhaji, babban laifi ne ko a wurin Allah Zina na da 'dumbin zunubi..amma please ka yafe masa insha Allahu bazai sake aikata irin wannan laifin ba". Murmushi Alhaji Baba yayi sannan yace " Ni ban ri'ke shi a zuciya ba, laifin sa tsakanin sa da ubangijin sa ne ni ba ruwa na, na riga na sau'ke nawa hakkin, tun abaya nata nuna masa rashin dacewar hakan, na kawo masa misalai da ayoyin qur'ani kala-kala hoping that zai ji tsoron Allah ya canza halayyar sa amma Mu'een ya watsar da batu na, bana fushi da 'dan uwan ka amma bazan 6oye maka ba cutarwa da yayi wa Noor shine abinda yafi tsaya min, buri na kawai ya sakam min ita ne yaje can da rayuwar sa ina so zan aura mata wanda zai bata farin cikin rayuwa, someone that ll lead her to jannah ba irin shi da ke sata cikin 'kunci ba, da ya bata takadda shikenan ba wani fushi tsakani na da shi...ka daina damun kanka kaji ko?" " To Alhaji..thank u so much...Ubangiji Allah ya 'kara nisan kwana". Kai Alhaji Baba ya jinjina masa yana murmushi mai 'kayatarwa. Bai da'de tare da shi ba yayi masa sallama yace zai je gida wurin Ammi daga nan zai wuce dan yana kan hanya ne. Alhaji Baba yace bakomai duk lokacin da yake son ganin sa zai sanar da shi. Sallama suka yi bayan ya ciro ku'di masu 'dan nawi ya mi'ka mai. Ishaq 'kin amsa yayi sai da yaga ran Alhaji Baba na shirin 6aci kafin yasa hannu ya amsa yana godiya ya tafi gida wurin Ammi. Itan ma Ammi duk batun ta kusan 'daya ne da Alhaji Baba burin su kawai wai ya saki Noor. Shi kam Ishaq sam bai ga laifin su ba, amma sai yake jin fargaban tunkaran Mu'een da wannan zancen. Haka dai itama yayi mata godiya ya kama hanyar garin Bauchi, bai isa da wuri ba kuwa sai da yayi dare sosai a hanya, ko da yaje ma bai samu ganin Mu'een ba sai washegari. Kwanan sa biyar tare da shi kafin ya koma Borno ganin kamar jikin da 'dan sau'ki amma har ya tafin ya kasa sanar da shi batun da suka tattauna da iyayen sa. Gani yake kamar abin zai 'kara sashi cikin mawuyacin hali ne shiyasa yayi shiru kawai. Da kansa yayi ta neman layin Noor da tunanin bata baki akan tayi ha'kuri ta ce da su Alhaji kar su raba su amma ya kasa samun ta sam, dole ya ha'kura da 'kiran nata ya sake tunanin wata mafitar. Tausayin Mu'een kuwa daram ya dasu a zuciyar sa, dan kullum idan ya bu'di baki zancen iyayen sa zai yi maka, sai su Uncle Ja'afar da Noor matar sa. Sai da ya shafe a 'kalla sati uku yana kwance ba lafiya kafin ya samu sau'ki sosai, kuma still Safwan ne ka'dai akansa, shike yi masa komai...Isahq kansa ba 'karamin.jinjinawa Safwan yake yi ba, kusan kullum sai sun yi waya da shi yana sake jin halin da Mu'een 'din ke ciki. Alhaji Baba kam shiru 'kila har yanzun bai kammala tunanin da yace da Safwan zai yi ba ne, Safwan ba 'karamin rashin jin da'din haushin nuna halin ko'in kula da suka yi da Mu'een 'din yake yi ba hakan yasa bai kuma 'kiran su kan batun sa ba har yanzu. Last week ma abokan sa suka zo duba shi su Anas wanda Isahq ya sasu zuwa duba shi dan shi baya kusa, sosai suka tausayawa halin da yake ciki. Siahq na 'ko'kari sosai wajen.'kiran.Alhaki yana sake ro'kon alfarma ko Alhajin zai sassauta amma ga mamakin sa a kullum kalaman Alhajin basu canzawa. Sake maimaita masa yake cewa shi bai wani ri'ke shi a zuciya ba, abinda yake aikatawa ai rayuwar sa zata ta illatawa ba wani ba, iyaka kawai ace 'dan wane ne so shi bai dame sa ba, abinda yake so da shi yanzu kawai shine takaddar 'yar sa da ya'ki bayar wa, yace matu'kar ya sakam masa 'yar sa shikenan komai ya wuce bashi da wata damuwa da shi. Har zuwa ya sake yi musamman kan maganar amma still Alhaji na nan kan bakan sa bai canza ba. Duk yanda ya so yasan inda Noor take daga bakin su kuwa 'kin sanar da shi suka yi, daga gidan sai ya wuce gidan Umman Noor, nan ma 'din duk bata sauya zani ba tamkar ha'din baki itama bata sanar da shi ba. Layin Noor da yake da shi kuwa sam baya gaijayawa da gwada 'kiran ta, a ranar ma ya 'kira yafi sau hamsin amma baya shiga abin ya 'daure masa kai sosai. Burin sa dama da ace ya same ta da nasiha zai mata sosai, bai kamata ace ta guji mijin ta ta bar shi cikin wannan halin ba..ita ce ya kamata ta fara tausaya masa ba wani ba, kuma ai abinda ya riga ya faru ya riga ya wuce so babu amfanin dawo da shi musamman da yake ya nuna nadamar sa a ganin sa in dai ba 'karshen sa suke son gani ba kam ai abin ya isa haka nan. Safwan ya 'kira yayi masa bayanin komai inda ya 'kara da fa'din" Idan zai yiwu dan Allah ka fahimtar da shi, fushin iyayen sa a kullum baya zai rin'ka maida shi ta fannin rayuwa abin na damu na sosai Safwan bai kamata ya ja tsawon lokaci mahaifan sa na fushi da shi ba, tunda sun ce sakin Noor suke bu'kata kawai ya daure ya sake ta, may be dama Allah bai tsara musu 'karshen rayuwar su tare ba dan haka kawai ya ha'kura da ita ya nemi albarkar iyayen sa. Shi kansa Safwan ya jima da yin wannan tunanin amma fargaban yanda Mu'een zai 'dauki abin ya sa shi kasa furtawa. Wannan karon kam Ishaq 'kwarin gwiwa ya bashi yace idan kuma ba zai iya gaya masa ba kawai ya ha'da su awaya shi zai masa bayani. Hakan kuwa akayi, Ishaq ne cikin natsuwa ya fahimtar da shi komai, a fili ya bayyana masa muhimmancin da iyayen sa ke da shi a wurin sa, ya tuna masa cewa su ne aljannar sa, ya kuma nuna masa illar biyewa son zuciya, yace idan Noor matar kace babu wanda ya isa ya raba ka da ita Mu'een, amma ayanzu ka bi iyayen ka ka aikata abinda suke so insha Allahu bazaka yi hasara ba, Alhaji ya nuna yafiyan on condition zai maka, sakin Noor ne zai sa ka samu yafiyar sa dan haka dan Allah Mu'een ka sake ta ko ma saki nawa suka bu'kata kayi mata, kaga idan suka yafe ka sai ka koma ga Ubangijin ka kuma ro'ki abinda yake alkhairi ne, tsakanin Hudah ko wata daban..ina ganin hakan zai fi maka, da ka zauna da fushin iyayen ka akan ka gwamma ka rayu babu Noor a kaf in rayuwar ka wallahi ko awurin Allah bazaka yi laifi ba...." Idanu ya rintse da 'karfi yana jin zafi cikin zuciyar sa a hankali ya furta" Insha Allah zan yi yanda kace Ishaq, na gode sosai, nagode da 'ko'karin.da kuka yi a kaina Ubangiji Allah ya bar zumunci". Tun kafin ya 'kara samun sau'ki ma ya matsa wa Safwan ya fitar da shi daga asbitin..wanda sosai ya 'kagara yaga ya shirya da mahaifan sa har ji yake tamkar basu ta6a shiri da su mai kyau ba...ya riga ya saduda a yanzun a ganin sa Noor tayi masa nisan da be san ta ina zai fara lalu6o ta ba...ya sawa ransa dangana ba dan ransa na so ba a ganin sa rabuwa da itan dole ta zame masa kawai. Washe gari ya shirya ya taho Shuwarin, wannan karon shi ka'dai ya tafi, Safwan ma yayi-yayi da shi akan ya bari sai ya 'dan natsu jikin sa ya 'kara 'karfi kafin yayi tafiyar amma Mu'een ya'ki, haka ya tafi bai ko 'dauki kaya bama daga su Atm 'din sa da Magungunan sai 'dan abinda ba'a rasa ba, ku'di masu nawi ya bawa mai gadin sa dan shi kansa bai san ranar daowar sa ba, ko da ya sake ta baze bar Shuwarin ba har sai ya samu labarin inda take...domin a ganin sa har yanzun akwai nawin ta akansa cuz bai nemi yafiyar ta ba, haka ya bi motar kasuwa kamar ba shi ba ya kama hanyan gida. Cikin mota kuwa da ya rufe idanu sai yaga Jasmine 'din sa tana yi mai murmushi, in ya bu'de idanu kuma sai bazai ganta ba. Sake lumshe idanu yayi Cikin ransa yake ayyana hala dai kin zo tuna min da batun zuwa makka da Madinan ki ne Mama na...na riga nayi al'kawari amma Allah bai nufi zaki je ba...sai dai insha Allahu nayi maki al'kawarin Mummyn ki zata je zata cika miki burin ki..ko da bama tare...Mummyn ki ta guje ni tace bata so na yanzu". Murmushi kawai take yi masa amma bata fa'din komai...i missed u Maman Daddy..". Ya sake furtawa 'kasan ma'koshin...yana jin tamkar hawaye zai zubo masa. Allah ma ya taimake sa ba sosai yake maganar ba da ba babu abinda zai hana sauran fasinjojin jiyo abinda yake fa'di. May be suyi tunanin ko ba lafiya yake ba ganin.shi ka'dai yana surutai. Da wannan tunanin har ya kai gida tunanin Baby fal a ransa..Allah ya ji 'kanki mama na..". Shine abu na 'karshe da ya furta bayan ya shigo garin Shuwarin...domin tunanin Jasmine ne ya dawo masa sabo fil. Tun daren ranar da ya iso ya 'dauki takadda ya rubuta sakin Noor kamar haka..." _Assalamu alaikum ...ni Muhammad Mu'inuddeen na saki mata ta Noorul Hudah Mamman Jaji saki 'daya tak batare da tai min laifin komai ba.._ ." Ninke wa yayi yana jin suka azuciyar sa har ruwa ruwa idanun sa ke yi saboda tsananin damuwar da yake ciki...wai yau shine da kansa da hannun sa ya saki Noor 'din sa? Jin abin yake tamkar cikin mafarki. Bai sake fita daga 'dakin sa ba ya zauna yana alhinin sakin Noor da yayi, da yake tun maghrib suka ha'du da Alhaji so ba bu'katan komawa wurin sa ayanzu. Yana zaune akan kujera hannun sa ri'ke da takaddan sakin Noor in sai yaga wayar sa na haske alamun 'kira ya shigo masa wanda a yanzu sosai ya tsani yaji 'karan abu ma kusa da shi, shiyasa ko wayar sa ma silent take koda yaushe. Sunan Jiddah da yaga yana yawo kan fuskar wayar ne ya sashi jin wani tukukin bakin ciki ya kamashi...'dan 'karamin tsaki ya sake yana mai sake maida idanun sa ya lumshe. 'Kiran na yankewa a take wani ya sake biyo baya. A zuciye Mu'een ya kai hannu ya 'daga wayar ya kai kunnan sa, bai ko jira yaji abinda zata ce da shi ba yace mata"...Idan kika sake kuskuren 'kiran wayata wallahi Uban ki zanci, useless kawai marar hankali..." Daga haka ya yanke 'kiran yana huci kamar dole aka sanya shi. Ni dai nace an kwan biyu ba ayi ba yau kuma kan Jiddah aka rage wutan masifar. Jiddah kam daga can 6angaren kuka ta sanya, sosai Allah ya jarrabi zuciyar ta da 'kaunar sa fiye da zaton mai karatu, gani take kamar in ba shi bazata iya rayuwa ba, hakan yasa yanzun ma da ya zage ta har bata san lokacin da ta saki kuka ba saboda takaici, tun ba yau ba tayi danasanin turawa Noor wa'dancan Video da pic in, domin tun ranar har yau bata sake samun kansa ba, bata sake samun magana mai da'di daga gare shi ba...abin na damun ta sosai. Da tasan abin kanta zai dawo ma da tun farko bazata fara ba, tana son shi sosai ta yadda ta tsani komai da zai iya shiga tsakanin ta da shi...zuwa yanzun kuwa ta fahimci tsananin soyayyar da yake yiwa matar sa, cuz a tunanin ta tun case 'din wancan Videon da ta tura in ne ya sa har yanzu bai dawo Abuja ba, kusan 3months kenan yanzu, sannan wayoyin sa ma ba a ko wani lokaci take samu ba, sau tari kuma ko ta 'kira ma ba 'dagawa ake yi ba, yau ne ta samu ya 'daga shima 'din sai ya bita da hargagi batare da ya ko saurari abinda ke tafe da ita ba. Mummyn tane tayi saurin shigowa 'dakin jin tashin kukan ta lokaci guda wanda take yin sa cike da takaici. Ko da ta jefa mata tambaya kuwa Jiddah bata 6oye ba ta sanar da ita domin hankalin ta ya riga ya tashi mafita take nema, hakan yasa bata ma san lokacin da ta furta" Mummy ni shi nake so amma yace wai kar in sake 'kiran sa...". Salati mummyn Jiddah tayi tana tafa hannuwa tace" Yanzu wai duk akan namiji kike wannan uban kukan Jiddah?" " Mummy zagi na fa yayi wai kar na sake 'kiran sa". " Dama an gaya miki ana 'kiran saurayi ne haka sakaka? Ai in kina so ki 'kira namiji batare da wulakanci ya shigo ba to ki bari sai magana ta zauna tsakanin ki da shi". " Ni dai Mummy ki taimake ni, ki ce Abbah ya ro'ka min shi dan Allah mummy wallahi idan ya guje ni mutuwa zanyi". Abbahn ta dake tsaye bakin 'kofar 'dakin nata taji yace" Waye shi?" Zabura tayi ta maida kallon ta gare shi da rawan jiki tace " Abbah wani ne...sunan shi Muhammad..ni shi nake so Abbah please ka taimake ni.." " 'Dan waye ne haka?" " Ni ban sani ba Abbah, amman dai garin su ne jihar Bauchi..mahaifan sa na zaune a wata 'karamar hukuma Shuwarin.." " Ki bari to gobe da safe ki kawo min photon sa in gani.." " To Abbah Allah ya kaimu, nagode Allah ya 'kara girma". Juyawa yayi ya koma inda ya taso zuciyar sa cike da tunanin wannan abin, Jidfah ka'dai ya mallaka ba zai so 'kunci yayai wa rayuwar ta 'kawanya ba, dama tare suke zaune da Mummyn Jiddah a palourn wanda jiyo kukan Jiddan yasa ta ta shi shima kuwa take yabi bayan ta dan jin meke faruwa da tilon 'yar sa da yake matu'kar so da 'kauna. Ashe ma batun soyayya ne, sai dai shi a ganin sa babu 'dan wani ko wata a 'kasar nan da zai yi wasa da zuciyar 'yar sa, koma waye shi dole ya nemo sa yasan matakin da ya kamata ya 'dauka akansa. Washegari Jiddah da sassafe tana idar da Sallah ta nufi 6angaren Abban ta fuskan ta cike da murmsushi cuz tasan tunda yasa baki to kamar anyi an gama ne ta zama matar Mu'een. Gaida shi tayi tare da fa'din Abbah ga shi nan. Comment Vote Share *Salmerh ce*😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy, smile, educate nd to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *85* Abban Jiddah murmushi yayi yana kar6an wayar yace" Ga dukkan alamu wannan muhimmacin sa na musamman ne, rabo na da ganin ki sassafe haka har na manta Jiddah". Kunya taji sosai sai tayi 'kasa da kanta tana murmushi. Kallo sosai ya 'kare wa Yah Deen, domin kuwa ya fahimci shima 'din yana mai ji da kansa ne, sittirar dake jikin sa ka'dai ma ta ishe sa amsa baya ga yanayin sa, domin kuwa ba'kin suit ne ajikin sa mai shegen kyau da tsada, ya rataye farar rigar sa ta aikin likitan ci bisa wuyan sa, yayin da 'dayan hannun kuma ya sanya shi cikin aljihun wandon sa yana murmushi aka 'dauki pic 'din. Duba 'daya zaka yi masa ka tabbatar bai taso cikin babu ba domin bai gani a yanayin sa ba, motar dake bayan sa ma yasan taji ku'di ba na wasa ba. Idanun sa kan wayar ya furta" Wannan ba mamaki babban aiki kika samo min Jiddah, takamar dama Naira ne kuma ga dukkan alamu shima 'din cikin ta yake, to da me zamu yi masa barazana kenan?" Ya 'karasa maganar da kallon fuskar ta. " Abbah ka ro'ke shi kawai 'kilan zai amince idan yaga kaine dan taurin kai ne da shi sosai, nuna ku'di bazai sashi ya amince da ni ba Abbah..". Mi'ka mata wayar yayi yana fa'din" Yanzun dai ki bari zuwa next week muga abinda hali zai yi...". Cike da shagwa6a tace " Abbah gobe Allah yafi ai tambaya ne kawai..." Idanu ya zaro yana duban ta da tsananin mamakin ta" Kina nufin tambayar auren ki zamu je a wurin mijin?" Sai yanzu ma maganar tata ya sata kunya jin kunya, 'kasa tayi da idanun ta tana dan kwa6a fuska tace" a a Abbah I thought...maganar fahimta za'ayi...kaga sai asa ranar da za'a fara shirin tar6ar su..." Cikin ransa yace ikon Allah..zama ni. A fili kuwa cewa yayi " Kar ki damu zan yi tunani akai tukunna inga ta inda ya kamata a fara" Tuni farin ciki ya mamaye ta, fara'a ne sosai ya bayyana kan fuskar ta, tana murmushi ta furta" Thank u Abbah na, Allah ya bar min kai har 'karshen rayuwa ta". ***** Washe garin zuwan sa da safe lokacin da zai je gaida Alhaji Baba sai ya tafi da takaddar sakin Noor da ya rubuta yana gaida shi ya amsa a tsanake batare da ya wani bada hankalin sa gare shi ba..Yah Deen sam bai jin da'din yanda iyayen sa suka 'dauki abin da zafi har hakan, a yanzu burin sa bai wuce yaga sun dawo kamar baya ba, rabon da yaga fara'a kan fuskar iyayen nasa har ya manta, 'kara ma idan suna tare da 'yan biyu ko kuma idan suna waya da su a lokacin ne zaka tsinci fara'ar ya'ke akan fuskokin su. Kan ninkakkiyar takaddar dake hannun sa ya sau'ke idanu, sai yaji ya karaya sosai, yau ga takaddar sakin Hudah ri'ke a hannun sa, abinda ko cikin mafarki bai ta6a tunanin faruwar sa ba..." Allah ka bani ikon jurewa". Cikin zuciyar sa ya furta hakan yana me sakin numfashi. Ta shi yayi daga inda yake zaunen ya matsa kusa da Alhaji Baba da hankalin sa ke wani wurin daban, hannu biyu yasa ya ri'ke takaddar da shi sannan ya mi'ka masa yana sunkuyar da kansa yace" Alhaji gashi na rubuta"..batare da wani dogon bayani ba kawai yayi shiru daga hakan. Alhaji Baba bai yi musu ba ya sa hannu ya kar6a yana sake duban fuskar sa lura da sauyin yananyin dake tattare da shi a lokacin. " Takaddar mecece wannan kuma?" Tambayar da yayi masa kenan yana yatsina fuskar sa kamar be san abinda takaddar take nufi ba. Sai yanzun ya 'dago ya dubi Alhaji Baba, da raunin murya ya bashi amsa da fa'din" Takadda ce Alhaji...takaddar sakin...mata..ta". Baki Alhaji Baba baki ta6e yanavmurmushin gefen baki, sai a wannan lokacin kuma ya fara warware takaddar yana fa'din" Kayi kyan kai ai...Allah ya ha'da kowa da rabon sa". Daga haka yayi shiru idanun sa kan papern da alamu karanta abin ciki yake yi. Baki ya sake ta6ewa yana ninke papern bai 'dago ya sake duban Yah Deen ba kawai ya mi'ke tsaye wanda ganin hakan yasa shi niyyan magana. Kansa ya sosa sannan ya 'dan 'dago kansa" ...am dama Alhaji nace..." sai kuma yayi shiru. Waigowa Alhaji Baba yayi yana duban sa da 'daurarriyar fuska yace" Me kace?" " Alhaji dan Allah kayi ha'kuri ka yafe min 6ata ma da nayi, wallahi ni kaina nasan ban kyauta ba amma na tuba Alhaji dan Allah ka yafe min, bazan iya juran dogon fushi daga gare ku ba....". Alhaji Baba bai ma bari ya 'karasa maganar ba ya dakatar dashi da fa'din" Ai dama ni ban ri'ke ka a raina ba...me ma yasa zanyi hakan? rayuwa ce kuma kowa shi ke za6ar ma kansa irin wacce ya ga dama..so waye ni da zan ce ga yanda nake kayi taka rayuwar..." Yasan magana Alhaji Baba ya fa'da masa, duba da yadda yake fitar da maganar 'dauke da 'dacin zuciya, yana jin ciwon hakan cikin ransa amma ya daure ya basar.." Alhaji idan kace haka tamkar ka ware ni cikin 'ya'yanka ne..idan kace kai baka kai matsayin da zaka canza min rayuwa ba Alhaji to waye zai maye gurbin ka...na riga na gane kuskure na Alhaji kuma tsakani na da Allah na tuba, insha Allahu bazan sake baka kunya ba, da iznin Allah abubuwan da suka faru abaya bazasu sake faruwa ba..Ka dubi girman Allah Alhaji ka yafe min..ka ji 'kaina ka bani daman da zan gyara lahira ta tun yanzu..." " Allah ya yafe mu gaba 'daya". Abinda kawai Alhaji Baba yace kenan amma Yah Deen ya dinga zuba masa godiya yana yi masa addu'ar Allah ya 'kara girma da 'daukaka...cike da jinda'di. Haka ya tashi ya fita yana jin wani sashe na 'kullin dake cikinvzuciyar sa na kwancewa, wani farin ciki yake ji marar misltuwa. A lokacin Ammi na kitchen ne dan haka 'dakin sa kawai ya koma ya kishingi'da yana jin wani iri cikin jikin sa, godiya yake ga Allah daya nuna masa wannan rana, ranar da mahaifin sa ya sassauto fushin da yake yi da shi...a hankali tunanin sa ya gangara wajen Noor...lumshe idanu yayi yana tuno ta da yanayin ta, sanyin jikin ta, sanyin halin ta, komai nata mai sanyi ne ita, sosai yake jin wani sabon babin 'kaunar ta na sake bu'duwa masa...baya jin zai iya sake rayuwa da wata macen in ba Noor in sa ba.... Tuno cewa ashe fa yanzu ita ba matar sa bace ya sanya shi jin wani fargaba da tashin hankali. Cikin ransa ya ayyana" Da hannu na na datse igiyar aure na da Nuree...yanzu ba matsayin.mijin ta nake ba." Ya 'karashe maganar yana mai 'dago hannun sa na dama yana dubawa kansa ya 'dora hannun ya us cikin gashin kansa yana lumshe idanu..yayin da bugun zuciyar sa ke 'kara hauhawa fiye da baya. Shiru yayi yana sake tunanin makomar rayuwar sa idan akace babu Noor a ciki. Bai ta6a sanin girman 'kaunar da yake mata har ya kai hakan ba sai yanzu da yaga take neman kubce masa, yanzu ne yasan girman muhimmancin da take da shi cikin zuciyar sa. Erh da kansa yasan yana son Noor da jimawa tun ba yanzu ba amma bai yi tunanin abin nasa ya girmama har haka ba, ashe ganin ta da yake yi kusa da shi ne ya sa ya kasa gane muhimmancin ta na asali da ke zuciyar sa. Yana jin lokacin da Alhaji Baba ya fita, sai a lokacin shima ya tashi ya isa parlour wurin Ammi. Zaune take akan kujera mai zaman mutun biyu idanun ta na kan wayar ta ne tana dubawa. Sallamar da yayin ma ko 'dagowa batayi ba a hakan ta amsa shi. Gaban ta ya 'karaso ya zauna tare da kwantar da kansa bisa 'kafar ta, haka kawai sai yaji kuka ya kubce masa na tausayin kansa da yake yi. Ammi barin abinda take yi tayi ta zuba masa idanu da alamun mamaki. Daga bisa ni baya tayi ta jingina tana duban suman kansa har zuwa fuskar sa gaba 'daya. Yanda duk suka yi wani iri da su, basu samun gyara yanzu sosai kamar baya, tamkar ba Mu'een ta ba 'dan 'kwalisan nan wanda akoda yaushe zaka ga kansa na 'kyal'kyali da sheki fuskar fayau gwanin birgewa, gashi da son barin gashi akansa ya tara shi ba'ki'kirin...a hankali ta maida idanun ta wajen wuyan sa duban farko idan kayi masa zaka fahimci uwar ramar da yayi musamman idan ya kasance ka sanshi watanni biyar da suka gabata. Har cikin zuciyar ta take jin tausayin sa amma ta danne bata nuna ba..she have to purnish him saboda yasan ba haka kawai suka haife shi suka barwa duniya shi ba, so take yasan illa da aibun rayuwar da yata aikatawa. Alhaji ya riga ya sanar da ita batun takaddar Noor da ya kai masa bata ji da'di ba kam amma ta wani 6angaren tana ganin shine dai-dai...hankalin ta be tashi bane ma ganin cewa saki 'daya ya rubuta mata, har yanzu akwai possibilityn da Noor zata koma masa amma sai ta tabbatar da daidaiton hankalin sa tukunna...duk dama taga Alhajin kamar shi baya da wannan ra'ayin kuma. Cikin kukan ya fara fa'din" Ammi yanzu..kwata-kwata kin daina sona, Ammi baki 'kauna ta kamar baya, nayi kuskure kuma na gane kure na amma Ammi kin kasa fahimta ta balle ki ce kin yafe ni, 'karshe sai kika ce sai na rabu da matata kafin zaki yafe min. Ammi yau gashi na rabu da Noor, ba matsayin iyali na take ba Ammi na sakar miki 'yar ki da kika fi kauna kamar yadda kika bu'ka ta, a yanzu na fahimci soyayyar da kike min koka'dan bata kama 'kafar wanda kike wa Noor ba tunda kika za6i raba ni da ita bayan kinsan itace rayuwa ta, raba ni da ita tamkar raba ni da farin ciki na ne Ammi, bazan iya cigaba da walwala ba matu'kar Noor bata tare dani....nasan nayi mata laifi Ammi amma me yasa baku barni na wanke mata ba'kin cikin da na jima ina sanya ta ciki ba...wallahi ina so in wanke laifi na Ammi..ina so in dawo da farin cikin Noor da ta rasa abaya..amma kun hanani wannan damar Ammi..." Ammi bata san lokacin da ta kai hannu kansa ba saboda tsananin tausayin sa da taji. A hankali ta furta" Kar ka ga laifi na Mu'een komai da ya faru laifin ka ne...kuma ko yanzun ma laifin ka ne, da kanka kasan bazai ta6a yiyuwa na nuna 'kiyayya ga 'dan da ni na haifi abu na ba, 'kiyayya ta ga halin kane, basu yi ba, kuma bazan ta6a goyon bayan ka kan sa6on Allah ba ka sani, Mu'een aure fa? Ace duk daraja irin ta aure amma ka rasa matar da zaka nema sai me aure wallahi wannan yafi komai yi min ciwo sai inga kamar ba dan dama na haifa ba, 'karin takaici ma kuma har gidan daka tabbatar matar ka na zama agidan kake kawo.mata wannan wani irin 'karamin tunanin ne Mu'een?" "..Kiyi hakuri Ammi na ni da kina nasan ban kyauta ba...". " Ni na ha'kura kar ka damu amma ka nemi gafarar mahallici dan shi ka yiwa laifi.." " Ina yi kuma Insha Allahu zan 'kara neman gafara a wurin sa.." "..Gud...ka 6ata raina sosai Mu'een, ka zalunci matar ka ka maida ita tamkar bata san abinda take yi ba kawai dan kaga tana hakurin zama da kai ko?" " Ba haka bane Ammi...ni dai ki yafe min dan Allah". Ajiyan zuciya ta sau'ke sannan ta ce "... komai ya wuce..sai dai kuma nadamar ka tazo ne a 'kurarren lokaci, na riga na yanke shawara so kaga saboda ni na haife ka bazai yiwu in shiga hakkin wata ba, baya ga haka ma ga shi Alhaji ne ya fara jagorantan rabuwar ta ku, ita kanta ma ta bu'kaci sakin ta tun kafin mu baro Bauchi, kaga kenan ita ma da kanta taji bazata iya sake rayuwa da kai kamar yanda tayi abay ba, finally yanzu ka sake ta kuma naji da'din hakan dalilin ma kenan da ya sani cika al'kawarin dana 'daukam maka na cewa zan yafe ma da zarar ka bani takaddar Noor..Alhamdulillah yanzu babu nawin kowa akaina, kaima sai kaje ka huta wa ranka domin baka da daman gyara kuskuren da ke tsakanin ka da ita cuz ta fita daga cikin igiyoyin auren ka..sai dai kawai ka tsaya ka gyara tsakanin ka da ubangijin ka...6angare na kuwa baka da matsala komai ya wuce buri na shine ka tabbatar min da cewa ka rabu da wancan rayuwar ne rabuwa ta har abada....". "..Insha Allah Ammi I promise u ban sake wa har abada....". Murmushi Ammi tayi tana duban sa tace" Not this way, cikin actions din ka nake so na fahimta". Zai yi magana Ammi tayi saurin dakatar da shi da fa'din" ya isa hakan nan...ga breakfast can je ka sanyawa cikin ka wani abin idan basu yi maka ba let me know sai in sama maka wani". Mi'kewa kawai yayi batare da ya sake duban table in ba kawai ya nufi 6angaren sa. Har jin kansa yake yi babu nawi saboda tsabar rashin sukuni, dagaske kenan yanzu komai ya 'kare tsakanin sa da Noor, bai san me yasa ma yake jin sabuwar 'kaunar ta na sake ratsa shi ba...ina take? Cikin wani hali take? Duk bai sani ba. Burin sa kawai shine ya ganta ko da sau 'daya ne amma ya rasa ta ina hakan zai faru...yana so ya ganta ya bata ha'kurin abinda ya faru da Baby amma da alamu tayi masa nisa. Da kansa ya 'kira Ishaq da Safwan yayi musu albishir 'din yafiyar da iyayen sa suka yi masa bayan sakin Noor da yayi, inda ya 'kara da yi musu godiya sosai akan jajircewa da suka yi akan sa, ha'ki'ka sun kasance mutane da bazai ta6a iya mantawa da suba cikin rayuwar sa. Su Ishaq basu 6oye masa farin cikin da suka shiga ba da jin wannan labari...a yanzu duk hankalin su ya kwanta nan suka yi mai nasiha akan rabuwar sa da Noor 'din, suka ce kar ya damu haka Allah ke ikon sa, idan da rabon zama watarana zata dawo masa da iznin Allah...idan kuma babu Allah ya musanya masa da wata mafi Alkhairi.. Kai ya girgiza yace" Bana tunanin akwai wata Ishaq, babu wacce zata kai min Noor". " Kar kace haka man, ai duniya nada fa'di Allah ka'dai yasan iyakar abin alkhairi dake cikin ta mu ne dai bamu san hakan ba balle mu san ta inda alkhairin zai zo mana...samu da rashi ma duk na Allah ne, dan ka rasa Noor kuma ba yana nufin ka rasa farin ciki bane...may be wani tanadin yayi maka wanda yafi wannan 'din...yace nima ba gashi ba lastweek mahaifin yarinyar da zan aura yazo daga Niger ya tafi da 'yar sa, kasan dama wurin mahaifiyar ra take mijin mahaifiyar shi ya bada auren ta, anyi mai batun auren ta da ya kusa ma sai cewa yayi wai a janye batun kawai shi bazai aurar da ita anan ba haka yasa yarinyar agaba suka tafi tana kuka..kaga shikenan batun ya tashi, so na isa in cewa Allah meyasa ne? Ina jin son yarinyar amma dole na hakura na barwa Allah komai..sau tari abinda ka sawa ranka sai kaga ba shine alkhairin rayuwar ka ba". " Hakane Ishaq, Ubangiji Allah yasa mu dace, Allah ya ka wata wacce tafi wancan..." " Ameen Mu'een tare da kaima". Cewar Ishaq yana murmushi, shima 'din Murmushin yayi kawai batare da ya furta komai ba. Duk yanda yaso ya 'dauki hankalin sa da tunanin Noor kasawa yayi, sosai yake zurfafawa zuciyar sa wajen hasko inda Noor in sa take har yanzu ya kasa ganowa. Alhamdulillah yanzu kaso mafi rinjaye daga cikin damuwar sa sun kau domin iyayen sa sun yafe shi duk kansu suna amsa gaisuwar sa duk dama babu wani sakin fuska sosai amma da sau'ki...damuwar sa a yanzu kashi biyu ne kacal, rashin kulashi da Uncle Ja'afar basuyi sai kuma tsananin tunanin Noor da ya addabe shi. A kullum ji yake tamkar 'kara masa wutan 'kaunar ta ake yi cikin zuciyar sa shiyasa takasa barin ransa, a kullum tunanin sa ita ne ka'dai...sai Jasmine da yake yawan tuna memories 'din ta. Wa'dannan abubuwan ne ka'dai yanzu damuwar sa kuma su suka hana shi sukuni. Tsakanin sa da Uncle Ja'afar kam ya riga ya shirya yanda zai yi, jira kawai yake ya 'dan 'kara 'karfin ala'kar sa da iyayen sa ya kuma sake samun karfin jiki kfin ya tafi, ya yanke shawara can Taraban kawai zai je su sasanta da su in yaso ma sai ya 'dan huta can kafin ya dawo. Hakan yasa ya 'dan saki ransa cuz yasan idan yaje gare su kamar anyi an gama ne..d fact that ya saki matar sa ka'dai ne ke damun sa yanzu. Idan ya gaji da zaman gida har gidan gona yake bin Alhaji Baba ya taya shi ayyuka, kuma fitan na 'debe masa kewa sosai yake rage masa yawan tunani. Abinda yasa shi ya daina fita 'din shine watarana da ya fita da yake yana tafiyar sa ne da 'kafa kullum idan zashi, ranar ma haka ya fito jikin sa dogon wandon jeans ne, sai farar singlate daga ciki, longslip riga ya sanya ja mai ratsin ba'ki-ba'ki, bottles na 'kasan rigar kawai ya sanya saman 'kirjin sa abu'de kana iya hango farar singlate in nasa. Tafiya yake iskan hantsi na hura shi, tafiyar sa yake cikin natsuwa tamkar wanda ake irga takun sa, ji yake kamar iskan zai tafi da shi saboda rashin 'karfin jiki, rama sosai yayi wanda duban farko idan kayi masa zaka tabbatar da cewa cikin tsananin damuwa yake. wata majalisa ya wuce ta samari wanda tun lokacin da ya doso su yaji sunyi tsit amma bai san dalili ba...da shigewar sa sai yaji sun fara musu a tsakanin su, dayake kowa na son a saurari nashi ne sai abin ya zame musu tamkar hayaniya, daga inda yake tafiyan ma har yana iya jiyo wasu daga cikin maganganun nasu. Abinda kunnuwan sa suka fara jiyowa shine"... _Dallah can kai idan baka san abu ba kawai ka yiwa mutane shiru..."_ Wani yace" _Ya zaka ce haka bacin ni farin sani nayi masa, ai ko lokacin da cikin Ma'u ya bayyana ma kowa yasan shine ya aikata..._ " " _Da wannan fa suke tafiya Imrana wanda kwanaki 'yan drugs suka kama innan..'yan iska ne na gaske...shima wannan in sa'a yaci da hadda shi za'a kama, yanzu ma haka ance 'yar wani babba yaje ya ta6o shine kuka ga ya dawo gida gudun kar a ka mashi_ ". Wani daga cikin su yace" _Munafiki ai ni wallahi da nasan ko waye sai naje na tona masa asiri...banzaye 'yan iska marasa tsoron Allah kawai..kuma duk iyayen su ke 'daure musu gindi..._ ." Daga haka ya rage jin abinda suke fa'di dan sun koma yi 'kasa-kasa ne. Idanu ya rintse yana jin babu da'di cikin zuciyar sa, ko da ya bude idanun nasa ma dishi-dishi yake gani,fat-fat zuciyar sa ke bugawa da sauri, Allah wadai yake da rayuwar sa ta baya, ashe kowa yasan halin sa babu kyau, har ma gashi anan neman juya masa abin ta yadda ba haka bane, har mahaifan sa basu tsira kan harshen jama'a ba, da kansa da hankalin sa ya aikata abinda ya jawa iyayen sa zagi a gari, haushin kansa sosai yake ji yanzu, koma menene za'a fa'da yasan basu da laifi... yanayin fahimtar su suke bayyanawa...kuma da be bi mata ba da babu wanda ya isa ya dangana shi da hakan balle har a shigar da iyayen sa ciki...ji yake kamar ya koma ga samarin nan amma ya san zuwan nasa ba zai haifar da Alkhairi ba...Allah ka kaji 'kaina ka yafe min laifuka na." Abinda yace ka'dai kenan yana me cigaba da tafiya har ya 'karasa lambu. Ko daya tashi dawowa ranar kuwa bai dawo da wuri ba har Alhaji Baba ya baro shi a can, sai da ya yayi maghrib acan wurin sauran ma'aikatan kafin ya dawo gida gudun kar wasu su 'kara ganin sa su ma suyi maganar sa. Tun daga ranar bai sake komawa lambu ba...haka kuma bai sanar da ko Ammi abinda ya faru ba. Sai dai ya fita can harabar gidan ta baya wajen garden yayi zaman sa nan yana tunanin rayuwar sa, bai kwanta jinya ba kam amma a kullum rama ce ke saka shiga jikin sa saboda damuwa, idan yafar jin kirjin sa na ciwo sai ya dukufa shan magungunan sa har yaji dama-dama. Sukan yi waya da su Ishaq Safwan da sauran su, Jiddah ce ka'dai baya 'daukan wayar ta, yayin da a kullun baya gajiya da 'kiran Uncle Ja'afar Anty Zainab da kuma Noorul Hudan sa, rashin ji daga garesun a kullum 'karamar jinya yake haifar masa mai shiga jiki. Da kansa yasan ya yiwa rayuwar sa babbar illar da kowa zai ta ganin sa da shi. Uncle J tuni ya sa numbern sa a divert yayin da Anty zainab kuma 'kiran ke shiga amma ko a kuskure bata ta6a 'dagawa ba...layin Noor kuwa kullum akashe yake samu abin na bashi haushi sosai...text marasa adadi yake tura musu Noor da Anty Zainab, duk da kullum layin Noor akashe amma baya gajiya da tura mata sa'ko...wani bin sai yaga kamar ko dagaske ne da Ammi tace da shi ta mutu kwanaki da kansa kuma sai ya girgiza kansa ya 'karyata batun sa sai ma ya 6ige da tunanin ai da ace ta mutu dagasken da bazasu sake 'daga batun saki tsakanin sa da ita ba, kuma ma yanda yasan Ammi ke ji da ita baiga alamar rasuwar ta tattare da ita ba...hakan yasan shima baya gajiya da tura mata sa'konni da tunanin ai wataran in da rai zata gani. Tun bayan sakin da yayi mata Uncle Ja'afar ya tura su Malesia ita da Anty Zainab inda Noor zatayi karatun ta acan 2yrs programme ne dan haka babu batun dawowa, shine dai da kansa yake zuwa duba su idan ya samu lokaci. Duk kuwa abin nan da ke faruwa Yah Deen bai ma san Noor bata Nigeria ba, ya dai san Anty Zainab na waje amma bai san cewa da Noor in sa suka tafi ba. Anty Zainab kam 'kiran ne ka'dai bata 'dagawa amma ita ka'dai tasan yanda take jin tausayin sa a zuciyar ta, da ya 'kira ta sai ta tsaya har 'kaguwa take yi taga text in sa ya shigo cuz tasan a kullum bai gajiya da turawa. Ita kam ba fushi take yi da shi ba dan tuntuni ta watsar da komai balle da taji labarin sakin da yayiwa Noor sai tausayin sa ya nunku mata a zuci, ko cikin text in da yake tura mata da kansa ya sanar da ita cewa ya saki Noor, tun yana yi mata text 'din ban ha'kuri har ya dawo gaya mata halin da yake ciki game da rashin matar sa, shi ne da kansa yake bata labarin komai idan ya faru da shi a ata'kaice...wani sa'in har kuka take 6uya tayi saboda tausayin Mu'een idan ya cika ta, abu 'daya ke hana ta 'daga 'kiran sa a yanzu dan gudun sa6awa Alhaji Baba maganar sa da kuma warning in Uncle Ja'afar, ta sani matu'kar kunnuwan ta suka yi arba da muryar Mu'een bazata juri ja masa rai akan Noor ba, da kanta zata fallasa komai saboda tausayin sa...kuma bata san me ze biyo bayana hakan ba shiyasa take tsoro. Shima ya sani tana ganin text in sa dan haka sai yake tura mata da. Ya'kinin tana karantawa. Wanda hakan ne kuwa, duk lokacin daya tura text in sai ta rufe layukanta ta rubuta masa reply dai-dai da abinda ya rubuta amma baya tafiya da yake layukan ta akashe sai ta ta tabbatar yayi error kafin take bu'de layin ta. Duk wani text nasa dayake yi mata suna da reply awayar ta batare da ya sani ba. Sosai Anty Zainab ke tausayin sa tana jin babu da'di da rashin sa. Ko da wasa bata bari zancen sa ya shiga tsakanin ta Noor mai tsayi domin bazata juri gani da jin 'kiyayyar sa daga gareta ba. Taka tsantsan take yi sosai akan hakan wani sa'in takan jajanta batun da Ammi idan ya dameta...yayin da Ammi ke ce da ita ta barshi kawai wannan ka'dan kenan daga sharrin aikata son zuciya.." ***** Yah Deen duk ya zama wani abu daban, ya fita hayyacin sa, shiru-shiru ya zama na gaske. Ko iyayen sa ma ba wani maganar kirki dake shiga tsakanin su daga gaisuwa shikenan. In kinga wani uban gashi da ya tara akansa da fuskar sa abin har zai baki tsoro...yayi fayau ya rame siririn 'karfi da yaji ya zama...gashi duk Ammi ta san halin da yake ciki amma bata nuna damuwar ta akan sa. Ko waya zatayi da Noor bata yi inda ta tabbatar zaiji..shi dai kawai bai ta6a ganin alamun kewar Noor tattare da ita ba. Har su Saif sukayi hutu suka dawo gida, a lokacin dukkan su jikin su sanyi 'kalau yayi da ganin sa hakan da suka yi. Saif sosai yaji tausayin 'dan uwan sa fiye da zaton mai karatu, Noor kuwa na can ta saki ranta bata da damuwar komai yanzu. 'Karfi da yaji ta yi 'ko'karin cire shi cikin zuciyar ta ta fuskanci sabuwar rayuwar ta da ke gaban ta gami da karatun da ta sa agaba...ta murje tayi 6ul-6ul da ita, kewar Ummah da Ammi kawai ke damun ta. Comment Vote Share *_Salmerh ce_* 😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *86* Tun kafin zuwa su Saif akwai watarana ya shigo parlour sai ya ci karo da wayar Ammi na haske alamun shigowan 'kira while Ammi na kitchen bama ta sani ba. ko daya ya 'dago wayar bai gane wanda yayi 'kiran *ba...Jewel* yaga an rubuta..yana ri'ke da wayar har 'kiran ya yanke yana tunanin inda Ammi ta sami me irin wannan sunan, wani 'kiran yaga ya sake shigowa, sai ya zauna yana duban wayar da tunanin waye haka...kuma bai yi tunanin mi'ka ma Ammi wayar ba sam. Bai san meyasa ba kuma sai yaji zuciyar sa na bashi shawaran amsa 'kiran...haka kawai sai yaji yanan so yasan wace Jewel 'din kuma Ammi ta samo. Kunnan sa yakai wayar yayi shiru yayin da daga 'dayan 6angaren ta sake dubanbwayar ganin.yau Ammi ta 'dauki 'kiran da tayi mata...bata bari ta 'kira ta kamar yadda ta saba mata ba. Murmushi tayi ta ha'da wayar da kunnan ta, kamar a mafarki yajiyo muryar ta na fa'din" Ammi na har na fara tsoro tun 'dazun nake 'kira baki 'daga ba....". Baya ya jingine bayan sa da jikin kujerar yana sake manne wayar da kunnan sa tare da folding hannun sa 'dayan bisa 'kirjin sa...shin da gaske itan ce ko kuwa kama ce ta muryoyi?. Jin shiru Ammi batayi magana ba yasa ta fara cewa" Hello!..Hello Ammi!.." Kamar zatayi kuka ta sake fa'din" Ammi baki ji na ne?" Saurin gyara zaman yayi bayan tabbatar da cewa itan ce da yayi, da rawar murya ya furta" Nu..ree..!" Goshi tayi saurin tattarewa jin wata murya ba ta Ammi ba...wayar ta cire ta duba waiko ba Ammin ta 'kira bane? ganin sunan Ammi yasa ta sake maida wayar kunnan ta...dai dai yana fa'din"...Ina kika shiga a duniyan nan Nuree?...kin san..." Bata bari ta kai ga jin 'karshen maganar ta sa ba tayi saurin datse wayar ta ma kashe ta gaba 'daya. Ranar yinin kuka tayi domin ya fama mata tsohon ciwon ta, bata yadda ta sake kunna wayar ba har sai da ta tabbatar ta musanya layin ta da na 'kasar tukunna. Dama tun farko itace taki amincewa ta canza amma tuni Anty Zainab ta canza nata ta fara amfani da na can. Yah Deen kam komawa yayi ya jingina da kujerar dake kusa dashi yana jin kansa na sarawa da 'karfi..dafe kan yayi yana lumshe idanu lokacin da ya sake 'kira yaji wayar akashe... Gudun kar Ammi ta fito ta tarar da shine ya sanya shi saurin 'dago wayar ya sake dubawa. Kallon sakanni 'kalilan yayiwa numbern take ya haddace su. Fita yayi daga wajen 'kiran ya ijiyewa Ammi wayar ta sannan ya tashi ya koma 6angaren sa. Da shigan sa 'dakin sa ya nufivwayar sa, sunan Ishaq ya nema ya turawa numbern sannan ya 'kira shi daga baya ya bashi bayanin abinda zai yi masa. Ishaq bai wani 6ata lokaci ba ya fito cikin gari ya nemi inda ake tracing number ya bada wanda Deen ya tura mai da tunanin ko ta waye oho dan bai masa dogon bayani ba shi dai ro'kon sa kawai yayi akan yabi masa diddigin layin ya ga location 'din da yake. Kafin sau'kar rana kuwa Ishaq ya 'kira shi ya sanar da shi cewa ba'a 'kasannan ma ake amfani da layin ba. Deen shiru yayi kawai ya rintse idanu, koka'dan bai yi tunanin cewa Noor nada ala'ka da Anty Zainab ba, illah ru'din da ya shiga na damuwar abinda ya fitar da ita wata 'kasa. Ko daga baya ma bai yiwa Ishaq bayanin ba duk kuwa tambayar da yayi ta jera masa amma sai cewa yayi da shi bakomai. Cikin lokacin har akayi bikin Imam amma bai samu ya je ba saboda damuwar da yake ciki. Cigaba yayi da gwada 'kiran layin nata a koda wani lokaci amma cikin rashin sa'a a kullum baya samun ta. Abin sosai yake 'daure masa kai, zuwa yanzun a fili ya fahimci cewa ba 'karamin tsana Noor tayi masa ba. In har zata iya kashe wayar ta na tsawon lokaci ko kuma canza layin ta saboda shi ka'dai to kuwa yasan abin ya girmama sosai. Sai dai hakan ba dame shi sosai ba fiye da rashin sanin takamamme me ya fitar da ita waje da be yi ba..kenan tunda auren sa akanta tayi tafiyar ko kuwa? me ma ya kaita wajen 'kasar nan sam ya kasa haskowa. Bai sake yiwa kowa maganar ba kawai ya bari cikin zuciyar sa akullum kuma baya gajiya da sake gwada 'kiran sabuwar layin nata da ya samu hoping that zai same ta watarana, bai sani ba ashe ta canza wani layin. Safwan ma har Shuwarin yazo ya duba shi ya kuma tausaya masa matu'ka, ace mutum kamar Mu'een amma kullum zaune cikin gida sai kwanciya sai zama a 'daki duk rayuwa ta canza shi ya koma wani abu daban kamar bashi ba. Da kansa yaje ya sake bawa su Ammi ha'kuri domin ya fahimci ayanzun damuwar Mu'een abu 'dayane kawai, amma sai suka nuna masa cewa su babu ruwan su indai akan Noor ne, tana da 'yan cinta a yanzu babu wanda zai takura ta, ko ada in ma ita da kanta ta nemi rabuwa da shi indai hakane kuwa su basu da dalilin takura ta dole ta zauna da shi, tawakkali kawai zai yi ya koma rayuwar sa ya daidaita ta, in yayi sa'a yayi dacen samun wata matar kuma shikenan su basu da matsala da shi. Safwan bai yi mamaki ba domin kuwa yasan _sakayyar Allah_ idan ta tashi fa'dawa kanka fiye da hakan ma zaka iya gani. Shawara ya bashi akan ya daure ya koma bakin aikin sa zai fi samun natsuwa wala Allah ma damuwar ta sa ta 'dan ragu. Baya son wata damuwa balle batun wani aiki a yanzu, shi aganin sa wa zai yiwa aikin yanzun, wa zai nemawa farin cikin rayuwa tunda bashi da kowa, babu Jasmine babu Noor aikin me ze yi kuma.. amma ta wani 6angaren kuma da kansa sai yaga dacewan komawa aikin cus zama gu 'dayan nan sosai yake illata shi...da kansa ya fara jin babu da'di, koda wani lokaci inba tunani ba baya aikin komai. Gashi da alamu ciwon sa na son motsa shi a 'yan kwanakin, 'kirjin sa na yawan yi masa zafi da nawi..ga wani masifaffen ciwon kai dake yawan addaban sa ko motsin kirki wani sa'in be isa yayi ba. Haka suka rabu da Safwan da al'kawarin zai yi tunani akan batun tukunna. Be gama yanke shawarar bane har su Saif suka zo gida. ***** Tun dawowar su Saif sai abin 'dan uwan sa ya dame sa sosai, sai yaje ya samu Ammi kan batun domin shi harga Allah tausayin sa yake ji matu'ka, mutum tun safe idan ka ganshi waje to gaida su Ammi ya fito yi bayan haka kuma bazaka sake ganin sa ba, ko abinci ma 'dakin nasa aka koma kaima masa wanda shima 'din sau tari yanda aka shigar haka ake fitar da shi. Ammi yaje ya samu da maganar tace to ni ya zan yi da shi Saif? Shi fa ya saka kansa duk abinda kaga ya same shi ba wanine ya sashi ba. " Duk da hakan Ammi ya kamata ai zuwan yanzun a tausaya masa..kuyi ha'kuri Ammi ku duba lamarin nan..kuma cikin wannan yanayin bai kamata ace itama Noor tayi nisa da shi ba, na rasa ma me yake damun ta yanzu duk ta canza wallahi....tausayin ta yayi 'karanci..na tabbata damuwar sa harda ta guje masa da tayi a ciki...mtheww". Ya 'karashe da jan tsaki cike da jin haushi. " Kai de kasa ni, kai kaga me 'dan uwa ko? Ni dai abar min yarinya ta huta yanzu dan babu wani ala'ka tsakanin ta da shi, da jimawa ya rubuta mata takadda..". " Takddar me kuma Ammi?" Yayi saurin tare da tambaya tun kafin ta 'karasa. Sai ta bashi amsa da fa'din " Saki mana...he divorced her tun ba yau ba yanzu haka ma karatu take yi abinta...gaka ba wada ala'ka yanzu". Wani banbara'kwai yaji abin har ma bai san lokacin da ya mi'ke tsaye ba ransa a matu'kar 6ace yace" haba Ammi..me yasa zaki jagoranci abinda kinsn illah zai yiwa 6angare 'daya, na tabbata bakomai ke barazana ga rayuwar Yayah ba illah rashin matar sa kusa da shi, Ammi koma wace iriyar nadama ake bu'kata ai duba 'daya zaki masa kisan itace tare da shi, me yasa kuma za'a raba shi da matar sa bacin kunsan yana son ta har zuciyar sa Ammi..harga Allah ni ban ji da'din hakan ba". Ammi kawar da kanta tayi gefe bata ce da shi komai ba. Zai sake magana tayi saurin dakatar da shi da fa'din" Wai Saif so kake ka nuna min kai me 'kaunar 'dan uwan ka ne ko me? har zaka zo kaina ka tsaya nagging at me for what?...uban ka ne shi? Ko kuwa da shawarar ka yayi rayuwar sa?" Sau'kar da murya Saif yayi jin ranta ya fara 6aci yace" ba haka bane Ammi...ki tausaya masa please..ki duba... " Waje tayi saurin nuna masa fuskar ta a sha'ke. Yi yayi jamar be fahimta ba zai sake magana ta daka masa tsawan" Kayi min waje". Da yaren su tayi maganar cikin tsananin 6acin rai. Saif kai ya girgiza kawai yayi waje...zuciyar sa babu da'di. Abin sosai ya tsaya masa arai..gani yake kamar ba ayiwa 'dan uwan sa adalci ba. ***** 'Bangaren Jiddah kuwa hankalin ta sosai ya tashi da wannan shariyar da Mu'een yayi da ita tsawon watanni, tun da jimawa tayi dana sanin abinda ta aikata domin aganin ta dalilin kenan. Gashi yanzu yana ganin 'kiran ta amma baya 'dagawa, whatsapp ma ko tayi masa magana baya dubawa, taje asbitin da yake aiki yafi sau goma amma duk babu labarin sa. Gidan su kuwa dake Abujan kusan kullum sai taje amman duk matsalar iri 'daya, dan ko alamun an ta6a rayuwa a wurin ma bata gani kullum gidan datse yake da padlock babba, abin na 'daure mata kai sosai. Tun tana damuwar ita ka'dai a 'daki har ta fara bayyanawa, kowa dake gidan su sai da yasan abinda ke damun ta, tana son Mu'een ra yadda take tunanin bazata ta6a iya rayuwa babu shi ba. Abban ta kam shi yafi kowa shiga tashin hankali sam ya rasa ta ina zai fara, gashi gunsa tafi zuwa tayi masa kuka ganin cewa bashi da niyyan cika mata al'kawarin da ya 'daukam mata kwanaki, sam bataga alamun zai cika mata burin ta ba. Mummyn ta ma bata barin sa, domin hankalin ta tashi yake a duk lokacin da ci karo da tilon 'yar ta a gaban ta tana kuka kan wani dalili wai shi soyayya, tasan mahaifin ta nada ku'din da ko a wata 'kasar ne zai iya siya mata soyayya da ku'din sa in bu'katar hakan ta taso, me yasa yanzun kuma da abin ma yake kusa da shi zai yi watsi da ita. Shi kam har ga Allah abin ya masa wani iri ne, bai kamata ace shi mai 'ya mace shi zai kai batun auren 'yar sa gidan maza ba amma yanda Jiddahn ta matsa dole ya sanyawa zuciyar sa amincewa. Da kansa ya sanya rana shi da P.A 'din sa sai kuma drivern sa suka tafi, dan a ganin sa wannan abin kamar sirri ne, bai kamata wasu suji labari ba hakan yasa bai gayyaci kowa ba..saboda gudun zubewar mutuncin sa, ace mutum kamar shi amma yake nemawa 'yar sa soyayya matsayin ta na 'ya mace mutum mai daraja cikin al'umma Tun kafin ya tafi ya sa ta tura masa pic 'din gayen da numbern sa in case ko bai same shi a waya ba sai su nuna pic in tunda 'karamin gari ne babu mamaki asan shi ko baya garin zaiyi magana da iyayen sa inyaso kawai su san matsaya. Tun a hanya ya fara gwada 'kiran sa domin yaji ko yana ina. Yah Deen da yanzu a ankare yake da sabbin numbers so yana ganin 'kira da sabon number yake gaggawan 'dauka da tunanin ko Noor in sa ce. A wannan ga6ar kam sabbin numbobi ka'dai ne ke da gatan da zai daga 'kiran su batare da sun samu jinkirin ganawa da shi ba, baya ga haka kuwa indai har yana da number saving a wayar sa kuma ya sanka to kuwa sai ya gadama yake 'dagawa, a ganin sa babu abinda zasu rage masa daga damuwa illah shirme...wayar Ishaq da Safwan ka'dai yake 'dagawa. Ko yau 'din ma 'kiran Abban Jiddah na shigowa wayar sa ringing 'daya na biyu ya 'daga wayar. 'Daga 'dayan 6angaren akayi masa sallama ciki-ciki ya amsa jin muryar namiji ne. " Hope da Muhammad nake magana...". " who ar u?". Shine tambayar da Yah Deen yayi masa cikin dakewa. " Kwantar da hankalin ka man soon zaka sanni, wurin ka na tunkaro fatan kana da chance 'din ganawa da mutane...". "...Banda shi...zaka iya yi min bayani yanzu..ina jin ka.". Yayi maganar yana me gyara zaman da kyau. Shiru Abvan Jiddah yayi yana mamaki, tuni zuciyar sa ta cika da wasiwasi, yanda yake zaton yaron ma ashe abin ba haka yake ba. Gudun kar ya bada kansa gaban yaran sa ne ya sanya shi datse wayar kawai yana jinjina kansa...Yaro 'karami na nenan raina masa hankali.."Jiddah baki kyauta min ba..." Shine abinda ya fa'di cikin ransa yana jin babu da'di. Tun ma kafin su isa garin ya fara jin zuciyar sa na tsinkewa, har haushin kansa ya fara ji domin gani yake kamar zuciyar sa na fargaban ha'duwa da Mu'een. Yaron da ma yake tunanin tashin 'kauye ne shine har zai sashi fargaba...lumshe idanu yayi tuno pic 'din Mu'een da yayi. Da kansa kuma sai ya 'karyata kansa, domin sosai ya fahimci Izzs dake tattare da shi cikin maganar sa..may be ba anan shi in ya tashi ba, ko dai iyayen sa ka'dai ke rayuwa a 'kauyen.. Shi sai ma ya rasa me ya kai Jiddah fa'dawa tarkon irin wannan 'dan iskan yaron, daga ji ba hankali gare sa ba. Ko da suka isa Shuwarin tun daga bakin hanya Dad in Jiddah yace su fara tambaya ko an sanshi cikin ransa yake ayyana bazan kuma 'kiran sa ya raina min hankali abanza ba. Tambaya suke da pic 'din sa suna 'kara shiga cikin garin...wasu sun sanshi wasu kuwa basu sanshi ba. Yayin da wasu ke cewa wannan ai 'dan Alhaji ne..masu ambatan sunan mahaifin sa suke kwatanta musu gidan gonar Alhaji Baba. Amma da yake takamamme basu san wurin ba sai suke sake tanbaya...da 'kyar suka samu wani ya shiga motar ya kaisu har lambun Alhaji Baba dan kowa tsoron su yake yi da ganin.'katuwar mota haka nan, musamman ma yanda Abban Jiddah ya hakimce cikin motar sai yake bawa mutane tsoro...kunsam duniyar mu ta yanzu sai a hankali. *Happy sallah to all Ummah..Aci nama lfy..😎* Comment Vote Share *_Salmerh ce_* 😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *87* Bai fito daga motar ba sai da ya tabbatar basu yi kuskure ba tukunna...sai da aka yi musu iso wurin Alhajin ya bada Umarnin su shigo kafin ya fito daga motar. Zama suka yi suna jiran zuwan sa dan a lokacin yana tare ne da wasu costumers 'din sa, zaman jiran sa suka yi a inda aka tanadar musamman saboda saboda ba'ki...P.A in sa na tsaye ne daga gefen sa wanda ganin hakan yasa Abban Jiddah bashi umarnin su jira shi wurin mota dan wannan personal issue ne. Hakan kuwa akayi P.A komawa yayi ya bu'de mota ya shiga yana jiran fitowar Ubangidan nasa. Gyara zaman Abban Jiddah yayi ha'di da murmushi tuno yawan 'kiran da Jiddah tayi masa daga lokacin da ya bar gida zuwa yanzu..ko bayan shigowar su garin nan ma sai da ta yi 'kiran sa burin ta kawai shine taji cewa an amince da batun aura mata shi. Yana murmushin yake bin cikin wurin da idanu... sosai lambun ya birge shi saboda akwai ni'ima sosai, 'kasan wajen luf-luf yake da korayen ciyayi masu birgewa awani 'bangaren ma har design aka cire da shi ya kuma bada ma'ana mai kyau abin sai wanda ya gani. Murmushi maahifin Jiddah ya sake yi, cikin ransa yake tuno rigima irin ta Jiddah" 'Dan gidan mai lambu...". Ya furta a fili inda ya 'karasa da murmushin mugunta. Gyara zaman sa yayi yana sake bin ko'ina da idanu. Wannan karan cikin ransa ya furta" Da alamu Naira zata yi amfani tunda naga akwai 'dan kashi..." Ya 'karashe da jinjina kansa. Cigaba yayi da sa'ka abubuwa cikin ransa yana me sake bin lambun da idanu. "Jin sa kawai yafi ganin sa, 'kila da hakan ya yaudari zuciyar Jiddah har ta fa'da tarkon sa... gashi nima yasa na taso ba shiri saboda fitinar ta...ai da nasan hakane da aike kawai zanyi a gama komai ba sai nazo ba". Ya 'karashe wannan tunanin da canza yanayin zaman sa ya karkace gefe guda, 'kafar sa 'daya ya mi'kar bayan ya cire takalmin sa ya maida 'kafar akai yayin da ya 'dayar ke tan'kwashe. Hannun sa 'daya ya 'dago ya tallafi gefen fuskar sa da shi..a hakan sai yafi jin da'din 'karewa lambun kallo da kyau. Baki ya ta6e lokacin da yaga manyan motoci guda biyu dake 'ko'karin fita daga lambun da alamu muhimmin abu ke gaban su duba da yanayin da yaga suka figi motocin. Sam bai kula da tahowar Alhaji Baba ba dake tahowa kansa 'kasa yana gyara zaman babbar rigar dake jikin sa...Sanye yake da shadda wagambari mai kalar madara wanda duban.farko zaka fahimci maku'dan ku'daden da aka kashe kafin samuwar kayan. Idanun sa na wani wuri can da ya 'dauki hankalin sa ga kuma haushin.6ata lokacin sa da yayi wurin zuwa wannan garin da yayi... har Alhaji Baba ya 'karaso kusa da shi har ma yayi masa sallama amma bai ji sa ba. Sai da Alhaji Baba yayi gyaran murya kafin Abban Jiddah yayi saurin ankarewa. Waigowa yayi domin.ganin.wanda ke masa sallamar nan take sai suka ha'da idanu da juna. Cak Alhaji Baba ya tsaya yana duban sa cikin idanu yayin da mahaifin Jiddah yayi saurin mi'kewa tsaye har yana 'ko'karin fa'duwa amma ya yi sa'a be fa'din ba. Alhaji Baba duban sa yake yi da tunanin in da ya sanshi, domin fuskar sa sosai tayi masa kama da wanda ya sani amma ya kasa tunawa. Mahaifin Jiddah jikin sa rawa ya fara da tunanin Allah yasa mafarki yake ba gaskiya ba, gaba 'daya ya rikice ya rikita zuciyar sa, kallon da Alhaji Baba ke yi masa na a ina ya sanshi ne..yayin da shi kuma da ke tsarge yake sai yake ganin tamkar kallon tuhuna yake yi masa. Da rawan baki ya furta sunan" Ta...heer". Da disashshiyar muryar sa da ko fita da kyau bata yi ba. Mamaki sake kama Alhaji Baba yayi wanda hakan ya shi 'dan waro idanun sa, domin kuwa yanzun ya fahimci zuciyar sa ba 'karya take yi masa akan wannan mutumin ba, tunda gashi da kansa ma ya sanshi hadda sunan sa ya 'kira, duk yadda akayi sun san juna ne da jimawa...amma shi ya manta. Nuna shi da yatsa Abban Jiddah yayi muryar sa na rarrabewa ya furta " Ta..heer..kaine nan da gaske... dama kana raye Taheer?" Wani bugu zuciyar Alhaji Baba tayi mai mugun firgitarwa sakamakon wani abu da ya fara fahimta game da wannan ba'kon nasa...kallon.'kurilla da suke yiwa juna shi ya sake bashi babban gudummuwa wajen.saurin.fahimtar waye wannan agaban sa. Ko daga bacci ya tashi ba zai kasa gane wannan halittar ba, ballantana muryar sa..da farkon yanayin girma da ya kama shi ne ya hana shi saurin fahimtar waye shi... Alhaji Baba duban sa kawai yake yana tariyo muguwar cin amanar da yayi musu abaya...sosai yaji tashin hankali a zuciyar sa gami da tunanin.yau kuma me ke tafe da shi wa ma ya sanar da shi inda muhallin sa yake sai Allah. Basarwa Alhaji Baba yayi ya sawa zuciyar sa dauriya duk kuwa da cewa ganin mutumin ya ka'da shi, a hankali ya 'karaso ya zauna bisa kujerar dake kuma har a lokacin bai furta komai gare shi ba. Cikin dakiya irin ta Alhaji Baba harda 'daura 'kafa 'daya kan 'daya, murmushi mai sanyi mai nuna alamun rashin damuwa ita ya sanyawa fuskar sa sannan ya dube shi da muryar sa mai cike da dattako ya furta" Bismillah..ranka ya 'dade...". Yayi maganar yana nuna masa kujerar da ya tashi. abban Jiddah komawa yayi ya zauna a 'darare dai-dai shigowan 'kira cikin wayar sa, duk ya rikice ya kuma rikita kansa, 'dagowa yayi da rawan jiki ya duba sai ya jefa wayar cikin aljihun saman rigar sa...yana rarraba idanu. Alhaji Baba kam duk na binsa da idanu yana karantar yanayin sa, ganin ya kasa natsuwa ne ya sa shi fa'din" Barka da zuwa...". Tun ma kafin Alhaji Baba ya rufe baki Abban Jidda yayi saurin amsawa gumi na karyo masa ta ko ina a jikin sa. Banda danasanin zuwan sa tShuwarin babu abinda yake yi, bai ta6a zaton wannan tafiyar ga Taheer zata kawo shi ba..da ya san hakane da tuni zai bawa Jidda ha'kuri ta ha'kura da zancen yaron nan ta nemi wani. Sam ya kasa sake duban Alhaji Baba sai gefe yake kalla yana 'kif-'kif da idanu...ashe har yanzu yana raye?. Abinda zuciyar sa ke ta maimaita masa kenan. Alhaji Baba ne ya yanke shirun dake tsakanin su da fara mi'ka masa masa gaisuwa. Haka Abban Jiddah ya amsa a ta'kaice batare da ya iya duban sa ba. Ruwa mai sanyi Alhaji Baba ya bu'kaci a akawo masa dan yaga kamar yana da bu'katan hakan amma ko da aka kawo Abban Jiddah kasa sha yayi. Zuwa lokacin kuwa ji yake tamkar ya nutse cikin 'kasa saboda tsananin kunyar da ta kama shi...gefe guda ga 'kiran da Jiddah ke mai daya sake takura shi..karo na 'karshe da ta 'kira sai ya ciro wayar a 'dan hassale yace da ita" Jiddah plz zan 'kira ki an jima". Wannan maganar da yayi matan ne ya sanya 'kiran da take yi masan ya kasance na 'karshe cuz ta fahimci yana bu'katan natsuwa ne. Wanda shima Abban Jiddah da gama fa'din hakan sai ya maida wayar cikin aljihu yana sake jin babu da'di..wannan wace iriyar 'kaddarace haka? ace duk yanda yake ji da kansa ya tara dukiya masu 'dumbin yawan nan, yana rayuwar sa yadda ya ga dama lokaci guda 'kaddara ta 'dauko shi da 'kafafun sa ya tako ya zo ga tashin hankalin sa...kuma ma wai shi ke tafe da batun aure, shi mahaifin 'ya mace wanda shi yakamata azo gareshi neman aure sai gashi abin ya juye masa, gashi ma a yanda yasan Taheer yasan waye shi yana da ya'kinin ko da ace Jiddah ce mace ka'dai da ta rage a duniya yasan Taheer ba ze ta6a yadda ya ha'da jini da shi ba...in dai har ya gano waye shi cuz yasan abu me mai wahala ya manta wancan lamarin. Cikin zuciyar sa ya fara tunanin mafita, a ganin sa gara kawai ya tashi ya tafi tun kafin asirin sa ya 'karasa tonuwa in yaso sai yaje yasan me ze ce da Jiddah... Tunanin sa ya yanke ne lokacin da ya tuno irin tashin hankalin da Jiddah ta shiga kafin tahowar sa, me kuma ze iya faruwa idan ya koma mata da batun da ba shi take tsammani ba....Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...hakan ya furta a fili batare da ya farga ba...goshin sa ya dafe da yake jin kamar kansa na juyawa. Amsa kuwwa sunan Taheer yake masa cikin 'kwa'kwalwa, yasan Taheer ya kuma san irin kafiyar sa, yasan taurin rai da yake da shi, ya kuma san muddin Taheer ya gama fahimtar waye shi ba zai bar shi ya tafi haka nan ba..me ya kamata inyi? ya tambayi kansa. Duk yadda yake ji da kansa da dukiyar sa yau gashi gaban Taheer komai ya kunce masa, ji yake kamar ba shi ne wannan me fa'da ajin ba. Sosai kwarjinin Taheer ya cika masa idanu, tsoro da fargaba duk sun mamaye shi...sai dai duk wannan ba damuwa bane kamar idan yayi kuskuren da Taheer ya 'dago waye shi dole yasan abinyi kafin faruwar hakan, Cikin zuciyar sa ya gama yanke shawarar da yake ganin itace mafita agare shi. Duk wannan abin da ke faruwa Alhaji Baba bai ce da shi 'kala ba, tsawon lokaci yana zaune yana jira ne yaji abinda ke tafe dashi amma hakan ya kasa faruwa, fuskar Alhaji wasai banda bayyananniyar murmushi dake kwance a fuskar bakaka fahimci komai daga 6angaren sa ba.... Duban.sa yake yana 'karawa cike da mamakin sa, yanda yaga ya rikice in sosai yake bashi mamaki, har zuwa lokacin da yaga ya 'dan sawa zuciyar sa natsuwa..duban Alhaji Baba yayi cikin dakiya da nuna alamun kuskure yace" Alhaji afuwa dan Allah..wallahi ina jin kuskuren fahimta muka yi muka zo gare ka....sai yanzun na fahimci ba kai in nake nema ba...". Yana gama fa'din hakan ya mi'ke tsaye gami da bawa Alhaji Baba hannu. Mi'ka masa nasa hannun yayi yana murmushi me 'kayatar wa suka yi musabahar bankwana. Abban Jiddah be jira komai ba kawai ya sa kai yayi gaba abinsa cikin sauri da fatan Allah yasa kar Taheer ya gane sa...shaf ya manta da cewar tun farkon ganin Alhaji Baba da yayi ya ambaci sunan sa, zaton sa ko duk cikin zuciyar sa ne yayi hakan. Tsaye Alhaji Baba ya mi'ke yana duban bayan sa da mamakin sa, maganar sa 'karshe 'din sam bata gamshi Alhaji ba, sam sai yaji bai yadda da shi ba, 'kila wani shirin zai koma yi akansa tun da har ya gano inda yake rayuwa, mamakin sa Alhaji Baba ke yi domin ya fahimci Barrister tamkar mara hankali ya 'dauke shi, me yasa yake tunanin shi ba zai gane sa ba, in har shi da yayi abin ma bai manta kammanin sa ba me yasa kuma shi zai iya mantawa da nashi kamannin. Taku biyar yayi ana shidan Alhaji Baba dake kallon bayan sa bai bari ya 'karasa ba ya furta" _Barrister Kido_ ...!" Yana murmushi ya fa'di hakan da muryar da ya tabbatar zai ji sa. Cak Abban Jiddah ya tsaya dai-dai da harbawan da zuciyar sa tayi, salati ya maimaita atake kusan sau uku da be masan yayi su ba. Takowa Alhaji Baba yayi ya dawo gaban sa hannuwan sa duk na cikin babbar rigar jikin sa yayin da Abban Jiddah ya sake rikicewa jikin sa na rawa ya kauda idanun sa gefe abinka da marar gaskiya. Alhaji Baba kam be damu ba bayan kallon 'yan da'ki'ku da yayi masa sai yace da shi yace da shi" Barrister kenan...bayan tsawon lokaci da rabuwar mu sai gashi kallon farko da kayi min ka fahimci waye ni me yasa kake zaton ni bazan iya gane kamannin ka ba..? U thought haka kawai zan iya mantawa da kai ne bayan duk abubuwan da suka faru abaya?" Shiru Abban Jiddah yayi ya kasa furta komai, 'kafafun sa yake jin tamkar baza su iya 'daukan sa ba. Alhaji Baba ne ya cigaba da fa'din" Ai in har zaka iya fahimtar ko ni waye tsawon wannan shekarun nima kasan bazan gaza fahimtar waye kai ba...amma yanzu duk ba wannan ba i know wani abin muhimmi ne ya kawo ka gare ni kuma bamu kai ga tattaunawa ba ka tashi...dan Allah ka manta da baya mu koma mu 'karashe maganar da ta kawo ka". Zai yi magana Alhaji Baba yayi saurin dakatar da shi da fa'din" Please Barrister...". Inda yayi maganar tare da nuna mai hanya fuskar sa ba yabo ba fallasa bazaka ta6a tunanin ganin Barrister ya ka'da shi ba. Haka badan yaso ba Abban Jiddah ya juya suka koma suka sake zama, shiru ya 'dan biyo baya kowa tunanin da yake sa'kawa daban ne, sai da Alhaji Baba ya sake ce mai ina jin ka kafin ya bu'di baki, madadin ya fa'di abinda ke tafe da shi a a sai ya fara ro'kon Alhaji Baba gafara kamar zai yi kuka...sosai nadamar bazata ta kama shi, yanzu ne ya fahimci cin amana bata da rana sam. Gashi tun ba'a je ko'ina ba Allah ya kama shi da dasawa 'yar sa 'kaunar yaron da yaci amanar mahaifan sa da da'dewa...bai 6oye komai ba duk ya sanar da Alhaji Baba hadda batun da ya kawo shi, nan ma ya 'karashe da ha'dawa da neman afuwar su. Duk abubuwan da ya fa'di 'din babu ba'ko wurin Alhaji Baba, amma batun Jiddah sosai ya ka'da shi. Cikin.zuciyar sa ya furta ' _karshen zamani_ sosai yayi mamakin wannan lamari, yasan a haife Barrister ya girme masa dan ko lokacin da ya sanshi ma ya san yafi shekaru talatin a lokacin kawai haihuwa ce Allah bai bashi da wuri ba amma sam bai ji da'din jin wannan labarin ba. Zurfafa tunani yayi a lokacin, a zahiri shiru Abban Jiddah yaga yayi har sai ya fara tabbatar da tunanin sa na cewa Taheer ba zai amince da wannan batun ba. Alhaji Baba kam can cikin rayuwar Deen ya tafi da tunanin sa, idan bai manta ba akwai sunan Jiddah cikin labarin sa da ya basu, kenan itama tana 'daya ne daga cikin irin 'yan matan da yayi abaya. Murmushin gefen baki Alhaji yayi, sai kuma yaji tausayin iyayen nata ya kama shi, abin takaici ne ace ga abinda 'dan ka ko 'yar ka suke aikatawa musamman abu dangin Zina sa6on mahalicci shi ya san ciwon hakan ya kuma yasan Abban Jiddah ba zai so jin wannan batun ba, baya ga haka ma a idanun sa zaka fahimci zallar 'kaunar da yake yiwa 'yar sa, babu mamaki itace mafi soyuwa a zuciyar sa cikin 'ya'yan sa shiyasa ma har ya iya amince mata kan wannan batun da yazo masa da shi wanda ya tabbatar ba kowa ne zai iya irin hakan ba. Muhammad 'dansa ne na cikin sa amma zai iya rantsuwa akan bai bar Jiddah haka nan ba, matu'kar ya ta6a neman ta to kuwa babu mamaki itama tabi sahun su Husnah ne...kuma abu ne me wahala ya amince da auren ta.... Bai kai ga 'karasa tunanin ba ya jiyo muryar Barrister na sake ro'kon sa, wannan karon kam mamakin sa 'karuwa yayi akan na baya musamman saboda ganin gwiwoyin Barrister da yayi zube a 'kasa, fuskar da muryar da muryar sa duk sunyi rauni da alamun ro'ko yake fa'din" Taheer dan Allah kar ka tuna abinda na aikata muku abaya..kaji 'kaina ka amince da wannan ha'din, wallahi Jiddah ba hali ne da ita ba halin mahaifiyar ta tayi..kuma basu san komai game da hakan ba a yanzu idan ka 'ki amincewa bansan yadda zanyi da ita ba, tsoro nake ji kar na rasa ta Taheer ita ka'dai Allah ya bani bani da kowa sai ita..idan dukiyar ku ne i promise u zan dawo maka da ita gaba 'daya ni dai ka amince kawai shine damuwa ta...". Alhaji Baba bai yi mamakin jin hakan daga bakin Barrister ba, domin da kanshi ma ya zargi hakan bayaga haka me ze sashi biyewa batun yara har ya iya yada girman sa haka nan. Ro'kon sa yayi akan ya tashi ya koma ya zauna amma Barrister ya'ki cuz shi a ganin sa ai bashi da sauran girma kuma tunda har ya kasance maciyin amana, ko da kwanciya ne zai iya yi a wannan lokacin matu'kar zasu yafe masa su kar6i batun Jiddah. Da 'kyar Alhaji yasa shi ya koma ya zauna sannan ya tabbatar masa da cewa shi bashi da matsala ta 6angaren shi kar ya damu in har Muhammad ya amince bakomai. comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *88* Alhaji Baba zuciyar sa 'daya ya 'dauke shi ya kai gidan sa wanda kafin hakan sai da ya 'kira Ammi ya sanar da ita cewa suna ba'ki dan ta shirya musu wani abin kafin isan su. Sai da suka tsaya suka sallaci la'asar a masallaci kafin su isa cikin gidan da su Zaidu da suma suka je masallacin. Cikin girmamawa kuwa suka gaida ba'kin Alhajin a tare suka isa gidan har parlour Alhaji ya shigar da shi da yake sauran 'yan tafiyan nasa daga wajen gidan suka tsaya suna daga harabara gida, sukan sosai suke jin da'din komai da ya shafi wannan bawan Allah, gashi da sanyin hali, komai nasa ma mai sanyi ne, gidan sa ma ni'ima sosai sassanyar iska ke ka'dawa ta ko'ina. Parlourn babu kowa dan haka Alhaji Baba yayi mai iso sannan ya umarci Saif da ya 'kira Ammin su yayin da ya tura Zaid 'kiran Mu'een a 6angaren sa. Koda yaje kuwa Sallah ya same shi yana yi cuz baccin da yayi ya makarar da shi zuwa masjid. Zama yayi ya jira shi ya idar kafin ya bashi sa'kon Alhajin. Mu'een kai ya jinjina masa da tunanin me ya kawo Alhaji gida kuma da wannan yammacin?..wanda sai bayan da ya gama addu'o'in sa kaf kafin ya tashi ya fito. Already Saif ya cika gaban Barrister da duk abubuwan da yaga Ammi ta ha'da na tarar ba'kin so ko da Zaidu ya dawo ma ba wani sauran abu kawai sanar da Alhajin yayi cewa Yayan yana sallah ne amma yana fitowa. Kai Alhaji ya jinjina sannan ya sallame su dan aganin sa abin bai wani shafe su ba. Saif kam sam hankalin sa bai kwanta da ba'kon Alhajin ba, musamman ma daya ga yana wani sussunkuyar da kai 'kasa kamar marar gaskiya. Ko da suka fitan Saif 'kin tafiya yayi ya tsaya daga jikin 'kofa dan ya saka cikin ransa cewar sai yaji abinda ke faruwa. Ammi ce ta fara fitowa jikin ta lullu6e da mayafin ta, murmushi tayi ganin yaran nata sun hutar da ita sun gama mata komai da ya dace tayi. Zuwa kawai tayi ta zauna gefen Alhaji Baba sannan ta gaida Barrister, sau 'daya tak ya iya duban ta har suka 'kare gaisuwan bai sake ba kallon fuskarta ta ba. Ammi kam sam bata gane shi ba..dan haka sai ta dubi Alhaji Baba tana murmushi..ganin hakan ya sashi murmushin shima...gyara zaman sa yayi gami da fa'din" Sirkin ki ne fa..". Idanu Ammi ta 'dan zaro zaton ta ko sirkin ta ta 6angaren Hudah ne, da yake tasan yanzu ba matar kowa bace tana da damar kula duk wanda taso. " Alhaji kar dai Hudah ta..?" Ta tambaya da mamaki. Sai ya girgiza kansa sannan yace" Mu'een dai". Tsuke fuska tayi nan take fuskar ta ta nuna alamun tambaya. Alhaji Baba bai damu ba sai ya dubi Barrister sannan ya dubi Ammi sannan yace" Wai baki gane shi ba ne har yanzu?" Kai ta girgiza masa duk kanta ya 'daure ma. Deen ne tafe a hankali kamar yanda ya saba tafiyar sa, yana zuwa sai yaci karo da Saif nan tsaye da mamaki ya dube sa da alamun tambayar me kake anan kuma. Saif kunya yaji dan haka sai ya sosa kansa yana murmushi yayi gaba. Gyara zama Alhaji Baba yayi sannan ya furta" Daga Abuja yake tafe kan batun auren 'yar sa... Dai-dai nan Mu'een yayi sallama ya shigo wanda ya dakatar da Alhaji Baba daga maganar da yake yi. Wuri ya zo ya samu ya zauna daga 'kasa sannan ya gaida su Alhaji Baba da ba'kon na sa daya gani zaune. Cigaba Alhaji Baba yayi da bayanin sa wanda ya fara da yi musu bayanin farkon abinda ya kawo Barrister wajen sa...Mu'een na jin batun ya 'daure fuska tamau dan shi har ga Allah baya son wata damuwa yanzu balle Jiddah da yake ganin itace farkon tubalin rushe masa farin cikin rayuwar sa. Ammi kam ba'ki ta ta6e jin abin sam bai yi wani tsari ba. Daga hakan Alhaji Baba ya gangara da yi musu bayanin waye asalin Barrister. Atare Ammi da Mu'een suka mi'ke tsaye suna duban Barrister da idanun su kamar zasu cinye shi 'danye. Ammi kam mamakin kanta ma tayi da har ta kasa gane shi tun farkon shigowar ta, sai da ma Alhaji yayi bayanin kafin ta gane shi sarai. Idanun ta ne suka cika da 'kwalla hannu ta 'dago ta nuna shi da yatsa amma ta kasa fa'din komai, tsoron ta kar ya sake dawowa cikin rayuwar su da niyyan sake tarwatsa musu farin cikin su, hawaye ne ya fara gangaro mata tana share su.... " Aishatu ki yafe min dan Allah ha'ki'ka ban kyautawa rayuwar ku ba dana kasance mai son zuciya ta..." Ciki kawai Ammi ta wuce batare da ta kai ga jin 'karshen maganar tasa ba, 'dakin ta ta shiga ta kullo 'kofan ta dinga kuka, bata son abinda zai sake 'daga mata hankalin iyalan ta sam, bata son dawo da abinda ya wuce, me yasa Barrister zai dawo cikin rayuwar su a wannan lokacin..me kuma ya rage musu da zai dawo dan sake mallakewa? Hankalin Ammi sosai ya tashi da ganin Abban Jiddah, bazata ta6a manta rashin imanin da ya gwadawa rayuwar su abaya ba wanda dalilin sa suka guji zama cikin gari suka ha'kura da duk wani jin da'di, don su tseratar da rayuwar su yasa suka dawo nan da zama sai gashi da 'kafafun sa ya sake biyo su da wani batun kuma. Ammi na shigewa Mu'een ma ya kama hanyar barin 'dakin shima a fusace batare da ya furta ko kalma ba, ji yake badan Alhaji Baba ne ya kawo shi gidan ba da babu abinda zai hana shi tara masa mutane...Alhaji Baba na ganin cewa shima barin su zai yi yasa shi saurin ambatan sunan sa. Cak ya tsaya sannan ya waigo ransa a matu'kar 6ace fuskar sa babu alamun fara'a ko ka'dan..yace" Alhaji ni bazan auri 'yar sa ba..kawai ya koma inda ya fito". Yayi maganar ne batare da ya ko kalli inda Abban Jiddah yake ba, a ganin sa bashi da ko arzi'kin da zai samu kallo mai kyau daga gare shi. Yana shirin juyawa yajiyo muryar sa na fa'din" Haba Muhammad ka dubi girman Allah kayi ha'kuri, kai fa musulmi ne..." " Kai kuma kafiri kake ai a lokacin da ka zalunci iyaye na ko..." ya furta hakan ne a matu'kar fusace wanda yasa Barrister saurin 'kasa da kansa.. cigaba yayi da fa'din. " Kai har kana da bakin magana ne? ka ro'ke ni, ni in auri 'yar ka? in ba ma rasar kunya ba har ka isa ka zo gaban mahaifi na ka ce wani kana so ka ha'da jini da shi bayan duk zaluncin dakayi masa? bani da wayo fa a lokacin amma har yau 'din nan ban ta6a mantawa da kwanan cell da ka sa mahaifi na ba na tsawon kwanaki bacin babu abinda ya aikata..ciwon hakan nake ji sosai..haushin kaina nake ji da ban canza ma kamanni ba..." Abban Jiddah kam duk yayi laushi da raunin murya ya fara fa'din" Kayi ha'kuri...." " Bazan yi ba..." Mu'een sam baya bari ya kai ga jin 'karshen furucin Abban Jiddah sai ya yanke maganar tasa. A zafafe har jijiyoyin kan sa na nunawa yayin da idanuwan sa suka fito sosai suka yi ja. "...bazan yi ha'kurin ba.." Ya sake maimaitwa...har ya juya sai Alhaji Baba ya sake 'kiran sunan sa. Wannan karon bai waigo ba cike da dakiya yace da Alhajin" Ni bazan auri 'yar sa ba har abada Alhaji, idan Jiddah ta kasance mace 'daya da ta rage ne a duniya ni bazan ta6a auren ta ba...". " Kana so ka nuna cewa ni ban isa da kai ba ne ko?" Da jin hakan sai yavjuyo yacdawo gaban Alhaji Baba ya dur'kusa kansa 'kasa yace" Kayi min afuwa Alhaji amma harga Allah bazan iya auran 'yar sa ba...Alhaji kai mahaifi na ne kuma ka isa da ni kana da damar da zaka za6a min kowace irin mace kuma ni me biyayya ne agare ka zan aure ta in zauna da ita amma dan Allah Alhaji kar ka tilastawa kanka ha'da jini da wannan tsohon azzalumin domin har abada bazan ta6a iya yafe masa cutarwar da yayi wa rayuwar ku ba...". Shiru Alhaji yayi ya lumshe idanu yana sauraran sa. Da gama fa'din hakan sai ya tashi bai sake bi takan Alhaji ba kawai ya wuce gaban Abban Jiddah ya tsaya ido cikin ido yake duban sa kafin yace" Fatan ka fahimce ni?...ni bana ha'da jini da maciya amana masu zalunci irin ka...kasan halin da muka shiga ta dalilin ka ne abaya? ko kuwa kasan 'kuncin da ka jefa mahaifa na aciki saboda son zuciyar ka? dalilin ka muke rayuwa a wannan garin ba dan muna so ba duk kasan hakan ne? sanadin ka mahaifa ne ke rayuwa a 6oye kamar basu da 'yancin kai basu shiga mutane, ka haramta mana rayuwa a inda muke so ka rufe mana duk wani hanyar jin da'din mu, lokacin da ka zalunci iyayena kayi tunanin yadda rayuwa zata kasance musu ne baka yi ba...kayi tunanin halin rashi da zasu fa'da ne? d answer is no..duk baka yi wannan tunanin ba saboda son dukiya ya riga ya rufe maka idanu ka manta da farin cikin wasu sai naka..mutum ya gina gidan sa baka san ta yadda aka yi ya samu hakan ba amma kasa an 'kone shi, baka yi tunanin abubuwan sa muhimmi dake gidan da zai iya rasawa ba duk ka sa an 'kone su gaba 'daya, zaton ka ma ko duk muna gidan, sai Allah ya nuna maka gazawar ka ya tseratar da mu,...duk a lokacin baka yi tunanin rashin imanin da ka aikata ba, baka yi tunanin farin cikin wasu da ka da'kile ba sai yanzun da kake farautan naka farin cikin shine zaka kwaso 'kafafun ka ka zo mana gida? hadda kwantar da kai na munafurci ko?" Baya ya 'dan ja ka'dan ya bar gaban Barrister sannan ya cigaba da fa'din"...as u can see Allah na son mu ya kuma rufa mana asiri ya sake bamu wani farin cikin kwatankwacin wanda ka zalunce mu akansa, bamu rasa komai na rayuwa ba duk da nasan ba haka ka so ba...dukiya kuma kaje da ita ai wanda ya tara ta ma tafiya yayi ya barta bansani ba ko kai 'din har kabarin ka za'a kaika da shi..wannan duk matsalar ka ce ba damuwa ta ba ce amma malam ka sani wancan farin cikin daban yake da wanda kake barar sa a yanzu nd in har ni 'dan halak ne bazaka ta6a samun sa daga gare ni ba idan arzi'kin ka zai iya siya maka kuma bismillah... in kuwa zuwa kasake yi musamman dan ka zalunce mu ne bismillah mu zuba ni da kai.. amma for now mintina biyar bana bu'katan ka sake yi cikin gidan nan ko gurbin 'kafafun ka bana so in sake in sake gani ka fice ka bar mana gida kafin inci maka maka mutunci, in kuma baka yadda ba try me..". Yana gama fa'din hakan ya juya ya kama hanyar 6angaren sa. Barrister bin bayan yayi da kallo har ya 6acewa ganin sa, ha'ki'ka duk abinda yaron ya fa'di kan hanya suke, lokacin da yayi nasan zaluncin bai yi tunanin halin da su zasu shiga ba, yayi ne dan farin cikin kansa da kansa sai gashi kuma yanzu a gaban su yana neman taimakon su da kansa yasan bai kyauta ba cuz har attempting na kashe su yayi Allah ne tseratar da su amma duk da haka sanadin sun ya sa an kashe mutane kusan guda uku kafin ya samu natsuwa dan yana ganin kamar asirin sa ya gama rufuwa ne a lokacin. A yanzu kam bashi da wata kalma da zai iya sake ce da su, ha'kurin ma yana ganin sam bai cancanci ro'ka daga wajen su ba..amma ya zanyi da Jiddah? ya tambayi kansa. Ya sani a yanzu Jiddah bata da wani farin cikin da ya wuci ta ga ta mallaki Mu'een, burin ta ka'dai kenan a yanzu nd yayi al'kawarin sama mata farin ciki ta kowani irin hali saboda soyayyar da yake yi mata ashe yaudaran kansa yake... Sum sum ya 'daga 'kafafun sa ya kama hanyar barin 'dakin...Alhaji Baba ne ya sha gaban sa zai yi magana Barrister ya dakatar da shi tare da girgiza kansa..." yaron ka gaskiya ya fa'da Taheer kuma na gamsu da shi...ban cancanci a yafe min haka cikin sau'ki ba ni kaina na sani, Jiddah ma zan bata ha'kuri ta ha'kura da shi amma nayi al'kawarin next week zan dawo, kuma Insha Allahu zanzo muku da dukkan dukiyar ku ba wai dan inaso Muhammad ya auri Jiddah ba a a, karamcin da kayi min ma na gode sosoi Taheer..ha'ki'ka kai 'dan halak ne...abaya nabi son zuciya ta na yaudari kaina da kwa'dayin dukiyar da take mallakin ku ne....na ji babu da'di Taheer har a zuciya ta naji haushin kaina domin gashi a zahiri son zuciya ta na barazanar hana 'yata farin cikin rayuwar ta...". Kasa 'karasa maganar tasa yayi illah kafa'dar Alhaji Baba da ya dafa sannan yayi gaba yana share hawayen da suka gangaro mai... Fita yayi direct ya nufi wajen motar su ya shiga tare da basu umarnin tafiya. Alhaji Baba kam shiru yayi jim a tsaye duk komai ya kwance masa...yana jin dirin tashin motar su wanda har ya daina jin dirin motar amma bai motsa daga inda yake tsaye ba. Ajiyan numfashi ya sau'ke bayan tsawon wani lokaci sannan ya nufi 'dakin Ammi da 'kyar ya shawo kanta tayi shiru ta daina kukan da take yi, wanda tana kukan ne hadda tunawa da tayi da mahaifin ta da 'kannan ta. Nasiha sosai Alhaji yayi mata sannan ya baro inda take bai sake bi takan Mu'een ba dan yasan shi baya sa'k'kowa da wuri idan yayi fushi.... 'Bangaren sa ya koma ya lulu6o layin Uncle J yayi masa bayanin komai, shi kansa da yaji abinda ke faruwa hankalin sa tashi yayi sosai abinda shima ya furta shine" Mu'een ba zai auri 'yar sa ba har abada, yaje ya nema mata wani mijin..." Jin da yayi cewa yace next week zai dawo yasa Uncle Jafar ma 'daura aniyar zuwa kafin satin dan ayi komai akan idanun sa. ***** Barrister da komawan sa gida batare da 6ata lokaci ba ya tara iyalan sa ya sanar da su komai dake faruwa, hatta mahaifiyar Jiddah bata san wannan labarin ba sai yau, gata mace mai hankali da natsuwa sosai take gujewa duk abinda wani abinda zai ja ta izuwa sa6on Allah, kuka ma ta sanya ita kam tana jimamin tsawon lokacin da ta 'dauka tana 'durawa cikin ta haramun, ta sha haramun ta sitirta jikin ta da haramun. Wannan abin shi yafi komai tsayawa a ranta, hankalin ta ya tashi sosai ta ja masa Allah ya isa fin cikin kwando. Bata sake yadda ta 'kara shan koda ruwan gidan bane ta tattara kayan ta bar gidan sa tana kuka. Jidda ma binta tayi tana kukan itama dan ita aganin ta halin mahaifinta ne yayi mata katanga da samun farin cikin ta, shine ya hanata mallakar zuciyar masoyin ta na dindindin...sam bata ga laifin Mu'een ba. Domin tasan koma waye aka mai irin wannan da 'kyar ne ya iya amincewa da batun aure kuma tsakani, sa'an sa 'daya da suka barshi ma dawo basu ha'da shi da hukuma ba. Haka suka tattara suka bar masa gidan sa gaba 'daya sai shi sai halin sa. Hankalin sa sake tashi yayi amma yafi bada kai wurin ganin ya tattara duk dukiyan Ammi daya mallake ya bata abinta shima ya raba kansa da haramun, kafin satin yake so ya harha'da komai ya sada su da abinsu in ma hukuma zasu ha'da shi da shi duk bai damu ba, da ace ya mutu yana cikin haramun gwamma ace ya mutu a hannun hukuma yafi masa. Maganganun Mu'een ne a kullum ke ta mar yawo aka, kuma ya 'kara fargar da shi, ha'ki'ka gaskiyan sa ne da ya ce wanda ya tara dukiyar ma ya barta, kuma haka aka kaishi makwancin sa daga shi sai farin yadin da aka mai sutura da shi shi kansa shaida ne akan hakan, balle shi da 'karfi da yaji ya kwace ta ma amfanin me kuma zata yi masa, bacin yasan mutuwa na iya 'daukan sa a duk lokacin da ta ga dama...me ze je yace da ubangijin sa? Tun da yake a rayuwa bai ta6a danasanin aikata abu irin wannan ba, yayi danasani fin yawan shekarun sa, yayi nadama fin laifukan da ya aikata gaba 'daya yayi nadamar komai. ***** Basu sake zama sun tattauna batun ba har kusan kwana biyar da tafiyar Barrister, duk a kwanakin kuwa gidan wani iri ya dawo tamkar lokacin da aka ta6a kulle Alhaji a shekarun baya can. Gidan sam babu mai walwalar kirki kowa tunanin da ke cinsa daban. Noor ma a lokacin ta 'kira Ammi amma sai taji muryar ta wani iri ba kamar yadda suka saba ba, koda ta tambaya kuma Ammi sai tace da ita ba komai. Hankalin ta sam ya kasa kwanciya sai take jin kamar wani abin ne daban ke faruwa. Anty Zainab ta samu da maganar itama sai taji wani iri amma bata nuna mata ba kawai ta kwantar mata da hankali. Sai daga baya kuma Uncle J ke fa'da mata wai zai yi tafiya zuwa Bauchi. Tambayar sa tayi cikin natsuwa abinda ke faruwa dan ta fara zargin kamar jikin Mu'een ne ya motsa sai da yayi mata bayani ata'kaice kafin ta samu natsuwa. Itace tayiwa Noor bayanin amma still Noor ta kasa hankalin ta dan tana da tarihin abinda ya faru abaya can, tsoron ta kar labari ya sake maimaita kansa ne. Hakan yasa ta kasa kwantar da hankalin ta. ***** Sati na cika Barrister ya dawo wanda kafin zuwan sa ma already Uncle Ja'afar ya iso shine ya 'kara tausan Ammi ya kuma yi magana da jam'ian tsaro in ma wani abin zai biyo baya ya zama na suna da masaniya akai. Shima Barristern da yake ya riga yayi niyyan dam'ka musu dukiyar su ne da kansa ya taho da wasu Jam'ian tsaro wanda ganin hakan yasa Uncle Jafar 'kin amincewa da su, Ja'mian tsaron da yai magana da su tun farko ya 'kira aka zo duk suka 'dunguma da su can garin Bauchi Ammi kam sam bata so tafiyar ba tana kuka take fa'din ita bata son dukiyar...ya koma da abinsa bazata kar6a ba tace yaje har abada ta yafe masa ita dai ya barta da iyalan ta su zauna lafiya. Lokacin da zasu tafi ma kuka ta ringa yi sosai ga shi daga Alhaji, Mu'een sai Uncle Ja'far suka tafi ta 6angaren su sai kuma Jami'an tsaro ita kam 'kin binsu tayi... Saif da Zaid ne ka'dai suke tare da ita suke kuma bata baki akan ta kwantar da hankalin ta babu abinda zai sake faruwa da iznin Allah. A kotu suka 'karashe maganar bayan ya 'dauke su kusan kwanaki uku, domin sun 6oye ainahin abinda ke faruwa kuma basu so a tona shi saboda Alhaji yace baya so ace za'a hukunta Barrister, Uncle Ja'afar ne ma da Mu'een suka 'dan so su nuna tirjiya amma daga bisani suka amince da hukuncin Alhajin inda daga 'karshe Mu'een ya sa hannu aka dawo wa da Ammi dukkan dukiyar ta hannun ta duk wani hannun jari da sanya a kampanoni duk ya dawo da shi harda ribar da yake samu ma, a adalcin sa sai yaga hakan ka'dai ne idan yayai zai sashi wanke kansa, sai ya zamana kamar juya mata dukiyar kawai yaje yi ya dawo mata da abinta. Bai barwa kansa komai ba illah gidan da yake ciki da kuma 'yan ku'dade da basu haura 5ml ba..yayi hakanne kuma dan yasan komai da ya mallaka daga dukiyar Ammi ya same shi, cuz ya jima da ajiye aikin sa tun awancan shekarun kawai ya kama harkar kasuwanci. Ganin cewa dukiyar ta sake ninkuwa ne ya sanya Alhaji Baba neman 'karin bayani nan Barrister ya sanar da shi be 6oye masa ba, sosai Alhaji ya yadda da gaskiyar sa nan take ya yi 'ko'karin ware wani abu daga ciki ya bashi da tunanin idan ya koma zai yiwa mai dukiyar bayani amma 'kememe Abban Jidda ya 'ki amsar komai yace wanda suka rayu a ciki ma yana neman afuwa akanta su yafe mai amma ba zai sake yadda yaci dukiyar su ba koda kuwa da amincewar su ne. Hakan ma yasan sun mai halacci domin yasan da wasu daban ne da babu abinda zai hana shi cin prison baya ga haka ma gashi dokar aikin sa ya karya. Amma duk suka rufa mai asiri kawai aka yi maganar akan cewa mahaifin Ammi ya rasu ne ya bar dukiyar sa a hannun Barristern sai yanzun ya dawo mata da shi bayan ya samu labarin inda suke...daga 'karshe Uncle Ja'afar ya sake yi masa babban kashedi kan cewa duk abinda ya samu 'daya daga cikin familyn sa to kuwa ya kuka da kansa yace ya amince indai ta 6angaren sa ne bashi da matsala. Da haka suka rabu da Barrister yana ta zuba musu godiya. Duk wannan hada-hadan da aka tayi babu abinda ya ha'da Uncle Ja'afar da Mu'een magana, duk yadda yaso ya ga ya shiga jikin sa Uncle Ja'afar kawar da kai ya ringa yi sam Mu'een bai ji da'di ba, ga shi ana gama case 'din ya koma Taraba abinsa. Wannan dalilin ya tabbatarwa Mu'een da cewa sosai Uncle 'din nasa ke fushi dashi. Abin tsaye masa arai yayi sosai. Ga shi a kullum Ishaq na sake bashi shawaran komawa bakin aikin sa shima 'din zuwa yanzun yayi na'am da wannan shawaran..Sati biyu bayan case 'din su Jiddah ya tattara ya koma Abuja...kafin hakan kuwa sosai Alhaji ya zaunar da shi yayi masa nasiha cikin natsuwa ta yadda zai fi fahimtar sa, shi kam ma yana jin yanzu ai ko hauka yake bazai sake ra6ar 'yar wani ba..Burin sa kawai ya dawo da Noor 'din sa cikin rayuwar sa ne yanzu. Noor ma yanzu hankalin ta ya 'dan kwanta cuz Ammi duk ta yi mata bayanin komai da ya faru sai alokacin ta 'dan ji natsuwa amma still kewar su Ammin na dumun ta. Gefe guda shima Yah Deen a kullum baya gajiya da gwada 'kiran layin ta amma baya samun ta...haka ma Anty Zainab ya daina samun layin ta sam hakan dai ya daure ya cigaba da aikin sa yana lalla6awa, idan yace lafiyar sa 'kalau ma yayi 'karya ne, cuz tun rasuwar Jasmine har yau 'din nan bazai ce ga ranar da yaji shi garau ba, sai dai Alhamdulillah ba laifi gaskiya. Da ciwon sa yake tafiya sai dai ramar da ke yi har yanzun sake bayyana take yi, yana kuma 'kiran sa mahaifan sa akai akai suna gaisawa inda a kullum nasiha ce ke 'kara ha'da su..basu gajiya da yi masa. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *89* Baya yin cikakken wata biyu bai zo gida ba..haka zai zo yayi weekend 'din sa ya koma lafiya lau, duk yanda zai ji ciwon sa na damun sa baya bari kowa ya fahimta sai dai in abin yafi 'karfin sa ne. Sai dai ko a fahimta ta yanayin 'karfin jikin sa ko kuma rashin walwalar sa amma da kansa kam baya furtawa ga kowa cuz gani yake kamar shine ya jawa kansa da kansa... 'Bangaren Jiddah kuwa ta riga ta sanyawa ranta ha'kuri yanzu, tayi kuka, kuka sosai fiye da zaton mai karatu har sai da ta raaa mai lallashin ta ma, da 'kyar ta daure ta fara rage damuwar dake cikin zuciyar ta akan Mu'een. 'Ko'kari sosai tayi wajen ganin ta cire shi cikin zuciyar ta domin ta fahimci tana son wanda ba zai ta6a zama mallakin ta bane, 'kila 'kaddarar ta kenan shine 'dumbin 'kaunar sa da tayi tasan har abada bazata iya ta6a son wani kamar yadda ta so shi ba, amma ya zama ta ha'kura da shi, badan komai ba sai dan labarin da mahaifin ta ya bata, abu guda 'daya tak ne ya taka mata birki ya kuma yi mata katanga tsakanin ta da shi baya ga da babu abinda zai sa ta janyewa har sai inda 'karfin ta ya 'kare domin tana son shi sosai, amma kunyar abinda mahaifin ta ya aikata musu ka'dai ma ba zai barta ta sake kusantar inda Mu'een yake ba har abada. Sam ta'ki mahaifin ta ta 'ki komawa inda yake kamar yadda mahaifiyar ta ma ta'ki...duk da cewa tana da masaniya akan irin 'kaunar da yake mata amma hakan bai hana ta jin haushin sa ba. Mahaifin Jiddah lokuta da dama ya kan zauna ne yayi kuka da hawayen sa kamar yaro 'karami ganin cewa duk ahalin sa sun gushe shi ne saboda mugun halin da ya shuka tun abaya, ji yake dama lokacin ya dawo baya ya kasance bai aikata hakan ba, yasan da yanzu yana zaman sa cikin farin ciki da iyalan sa kamar kowa...tsananin tausayin Jiddah yake ji a koda wani lokaci, dan ya san abin ita zai fi ta6awa, gashi bata kusa da shi balle ya san halin da take ciki har ya samu daman tausan ta yana bata ha'kuri. Cikin cousins 'din ta ta samu wani Bilal ke son ta..da farko 'kin bawa kowa fuska tayi wanda daga baya da kanta tayi tunani taga dacewar bawa wani dama ko dan ta rage ra'da'din damuwar da ke cin ta ma a kullum game da Mu'een hakan yasa ta amince da shi sai dai ba sosai take bashi fuska ba sai lokacin da ta ga dama...a hakan har manya suka sanya baki cikin maganar ta su. Tambayar auren tane ya kai wasu daga cikin dangin mahaifiyar ta wajen Barrister nan suka tarar da shi ya koma abin tausayi, ciwon diabetes yake fama da shi gashi babu wani da ke kula da shi. Koda suka tambayi auren batare da 6ata lokaci ba ya basu ya kuma ce da su duk lokacin da suka ga ya dace kawai su sanya ba sai sun sake dawowa wurin sa ba. Shikam ma farin ciki yayi da jin batun auren Jiddah ya taso cikin 'kan'kanin lokaci haka kuma Allah ya nufe shi da bada auren da kansa. Ko da suka koma gida hankalin su kasa kwanciya yayi haka suka dinga yiwa Mummyn Jiddah nasiha da yake manyan yayun tane da kuma kawunan ta bazata iya yi musu gardama ba dole haka ba dan taso ba ta dawo gidan mijin ta amma Jidda 'ki tayi tayi zaman ta can wurin dangin mahaifiyar ta. ***** _Bayan wasu watanni_ Lokaci ya 'dan ja sosai dan 'yan biyun Ammi duk sun kammala makarantar su yanzu saura bautar 'kasa...sun girma sun zama manyan samari dasu. Ishaq kuwa na nan har a lokacin bai kuma 'dago zancen aure ba tun da aka raba shi da wancan yarinyar shikenan ya fawwalawa Allah komai, da farko ma gani yake kamar zata dawo watarana amma da yaga har anci shekara guda shiru shikenan ya saki ransa ya manta da ita, ya kanzo Shuwarin ya gaida su Alhaji Baba duk lokacin da ya samu dama, kuma ba 'karamin da'di yake ji ba da yanda suka 'dauke shi kamar 'dan su na cikin su...abu da ke tsaya masa arai a kullum kan rashin matar Deen ne, gaba 'daya ya rasa har ina su Ammi ke son jan maganar dan har ga Allah shi ba 'kaunar rabuwar sun yake ba, gefe guda kuma da kansa ya 'daukan ma Alhaji Baba cewa idan yayi masa kyauta yayi al'kawarin baze mayar masa da kyautar sa ba, duk da be san miye ba amma ya amince masa yanzu kuma abin na damun sa bayan fahimtar da yayi cewa kyautan da Alhajin ke fa'di na aure ne bana komai ba nd be san wace ba. Alhaji Baba da kansa ya bashi labarin dukiyar Ammi da aka dawo da ita sosai yayi murna 'kwarai da gaske ya kuma sanya albarkar sa a ciki... Sani ma yazo Shuwarin kamar yadda yayi al'kawari, abin tausayi yanzu hannun sa 'daya sai hannun riga 'daga dake lilo amma babu hannu ciki, sosai ya sake neman afuwar su Ammi sun kuwa yafe masa, rashin sa'ar da yayi shine duk be tarar da Deen da Noor a gida ba balle ya 'kara basu ha'kuri, haka ya koma zuciyar sa babu da'di, kyautar 10k Alhaji Baba ya bashi yayin da su Zaidu ke ta banka masa uwar harara, ji suke kamar su sha'ko banza...haushin sa suke ji sosai. Yah Deen kam jiki ya'ki yin da'di sai dai ace Alhamdulillah kawai, tun yana dannewa har ta kai shi ga kwanciya a asbiti, wanda zuwa lokacin hatta Saif yafi shi kaurin jiki, tausayin sa sosai Saif yake ji kamar ya 'dauke masa ciwon..shine ma ya tafi Abujan lokacin da labarin rashin lafiyar tasa ya iso kunnuwan su. Hankalin sa 'kara tashi yake yi idan yaga Yayan nasa na aman jini, kuka yake yi yana share masa, duk sai ya galabaita ya fita a hayyacin sa gaba 'daya, Saif sai yake ganin tamkar kowa baya tausayin Yayan nasa ne...ya kan yawan ambatan sunan Uncle Ja'afar da Noor wanda da kanshi ya fahimci cewa sune ka'dai damuwar zuciyar sa a yanzu shiyasa baya iya 6oyewa. Uncle Ja'afar ya 'kira ya sanarmawa yana kuka, hankalin sa sai yaji ya tashi nan take, duk da baya kula shi har yanzun amma sosai yake jin sa aransa, kuma shima yasan be kyauta ba da yaja tsawon wannan lokacin yana fushi da shi. Lokacin ko maganar kirki Mu'een baya iyawa, da idanu kawai yake bin komai. Bayan 'kiran da Saif yayiwa Uncle da kwana biyu sai ga shi ya dira Abuja dan hankalin sa ya kasa kwanciya, a zihiri lokacin da Saif 'din ya 'kira shi bai ce da shi uffan ba but daga baya abin sai ya dame shi sosai domin ya fahimci akwai abinda ke faruwa dole sai da ya yanke shawarar tahowa. Lokacin da ya iso ma Mu'een bacci yake yi, ba'a barin kowa zuwa inda yake saboda ciwon san ba mai son hayaniya sosai bane hatta Saif 'din ma ba koda yaushe ake barin sa shiga inda yake ba, amma yanda Uncle Ja'far in ya matsa dole sai da suka barshi ya shiga wajen sa. Gaba ya sashi ya na kallo, tausayin sa duk ya mamaye masa zuciya duk yayi ba'ki ya rame daga inda yake yana iya hango 'kasusuwan dake 'kirjin sa da wuyan sa in ma irgawa akace masa yayi tsaf zai uya irga su, uwar rama yayi fiye da zaton mai karatu, ji yayi tamkar ya zubda mai hawaye, gaba 'daya jikin sa sai yayi sanyi, wannan idan ba dan farin sani da yayiwa Mu'een ba idan akace masa shine sam ba zai yadda ba. Ido kawai ya tsura masa yana sake 'kare masa kallo. ......Alhaji Baba ma sau biyu yana zuwa duba shi amma baya wani 'daga hankali da ciwon nasa sosai, gara ma wani lokaci da yayi wata doguwar suma Saif duk sai ya rirkice he thought mutuwa Yayan nasa zaiyi, sai da ya 'dauki sa'oi ashirin da bakwai kafin ya farfa'do wannan lokacin ne me Alhaji Baba ya nuna damuwa sosai cuz hadda Ammi suka zo suka duba shi, itama kuka ta ringa yi tana 'karawa, bata san ina zata sanya tausayin 'dan nata ba. A hakan bata ta6a kuskuren sanar da Hudah abinda ke faruwa ba, ko waya zatayi da ita tana 'ko'kari sosai wajen ganin ta daidaita muryar ta...ko da Anty Zainab ma sai dai taji labarin ciwon.nasa a wani wuri amma Ammi bata ta6a sanar da su saboda tasan tare suke koda wanai lokaci dole idan 'daya yaji 'dayan zai ji. Hikimar ta anan kuwa shine wai m kar Noor taga tamkar tana son dawo da ita cikin rayuwar Mu'een ne shiyasa bata yadda ko zancen sa ya ha'da su. Shima Uncle Ja'afar in sai yanzu da yake zaune gaban sa sannan ya ke jin haushin kansa ma, ai kuskure ya kan zama kuskure ne idan mai aikata shi ya kasa canzawa, yanada ya'kinin yanzu Mu'een ya canza rayuwar sa gaba 'daya, ha'ki'ka bai ji da'din abinda Deen 'din ya aikata ba shiysa ransa ya 6aci sosai cuz ko a mafarki be ta6a tunanin har Mu'een na iya 6ata rayuwar sa ta hanyar biyewa matan banza ba, shiyasa ya kasa bashi fuskan da zasu fahimci juna... Yanzun kuwa da yake jin 'kaunar yaron sa gami da tausayin sa na sake ratsa shi hannun sa ya kamo cikin nashi yana shafawa a hankali zuciyar sa duk tayi rauni ya karaya gaba 'daya. A hankali Mu'een ya bu'de idanun sa, jin hannun sa cikin na mutun sam bai sashi mamaki ba dan yasan Saif na nan tare da shi...bai bu'de idanun sa ba dan ra'dadi suke yi masa sosai...sai da ya 'dauki tsawon lokaci kafin ya bu'de idanun a hankali. Dishi-dishin da yake gani ne ya sashi sake maida idanun ya rufe amma a hankalin sa sai ya tafi kan wanda ya gani zaune kusa da shi, sam girman jikin sa ba irin na Saif bane. Bayan wasu da'ki'ku ya sake bu'de idanun tare da 'dan motsa hannun sa dake cikin na mutumin...nan take ya 'dago kansa, ha'da ido yayi da Uncle 'din sa da ya jima bai ganshi kusa da shi kamar hakan ba, ido ya tsura masa tsawon lokaci yana duban sa, sai yake ganin tamkar a mafarki...kasa gaskata idanun sa yayi dan haka sai ya maida su ya kuma kullewa siraran hawaye suka gangaro masa ta gefe da gefen fuskar sa. Uncle J goge masa hawayen ya fara da sauri yana yi masa magana cin murya mai kwantar da hankali.." Kayi ha'kuri Baba na insha Allahu bazan sake yin fushi da kai ba..ni da kaina nasan nayi kuskure may be ma fin wanda kayi...na dawo gare ka yanzu kaji ka kwantar da hankalin ka insha Allahu farin cikin ka zai dawo soon..." Gefe yayi da kansa batare da ya sake kallon inda Uncle in yake ba yayin da hawayen sa ke cigaba da gangarawa...Uncle bai damu da hakan da Mu'een yayi masa ba dan yasan shima sam bai kyauta masa ba...wayar sa ya ciro ya 'kira Matar sa wanda tana 'dauka yayi saurin fa'din" Meet ur Mu'een.." Bai jira jin komai daga gare ta ba ya sanya wayar a speaker ya kai kuda sa da shi. Anty Zainab tsabar farin ciki bata san lokacin da ta zauna daga tsayen da take ba...'kirjin ta ta dafe ta wani sau'ke ajiyan zuciya tana murmushin jin da'di, bayan wani tsawon lokaci yau ga Mu'een da Uncle 'din sa zaune wuri guda ga dukkan alamu komai ya daidaita tsakanin su kenan abinda ta jima tana fatan faruwar sa sai yau Allah ya cika mata burin ta. ....a hankali take jin hucin numfashin sa na sau'ka ta cikin wayar amma bai ce da ita komai ba... Sunan sa ta 'kira da sanyin murya amma bai amsa ta ba...." Talk to me pls Mu'een kar kayi fushi da ni, kasan haka kawai bazan share ka tsawon wannan lokacin ba ko/ dan Allah kace min wani abu...". Noor da ke cikin 'daki fitowar ta kenan sai taji Anty na ro'ko a waya ido ta 'dan zaro tace" Anty ke da waye haka?" Tayi maganar tana nufo inda Anty Zainab take ganiana yanda ta tattara dukkan hankalin ta kan wayar harda hannu biyu ma ta ri'ke wayar tamkar wacce akace mata za'a 'kwace ne. Anty Zainab kam ma hankalin ta sam bai je ga maganar Noor ba, dagsken duk ta bada hankalin ta wajen sa amma still ya'ki cewa komai. Shi kam jin murya kamar ta Noor 'din sa cikin wayar ne ya sanya shi nutsar da zuciyar sa wuri guda, ido ya 'dan zaro ya kalli wayar sannan ya kalli Uncle Ja'afar da lumsassun idanun nasa. Uncle Ja'afar da ya san abinda ya sashi hakan kawai sai yayi masa murmushi cuz wayar a speaker take kuma shima yana jin dukkan motsin da aka yi daga wancan 6angaren ballantana muryar Noor da ya fito tarwai. Kunne ya sake kafewa amma bai ji muryar ta 'kara magana ba illah muryar Anty Zainab ka'dai. Idon sa ya sake lumshewa yayi shiru yanayin fitar numfashin sa na 'kara hauhauwa yana canza salo. Ganin hakan ya sa Uncle Ja'afar 'daukan wayar ya cire a speaker sannan ya kai kunnan sa domin ya fahimci Mu'een sam bai da niyyan cewa komai...." Ba shi da lafiya ne shiyasa bai yi miki magana ba but anjima zan 'kira ki". Haka kawai yacecda Anty Zee wanda da gama fa'din hakan sai ya kashe wayar tasa ya sanya ta cikin aljihu. Cigaba yayi da lalla6an Mu'een wanda har a lokacin ya'ki sake bu'de idanun sa ballantana ya bu'di bakin sa ya furta wani abu, cikin zuciyar sa yake ta ayyana" Uncle...kaima ka daina so na...ba ka tausayi na....ji nake kamar in mutu idan na tuna fushin da kake yi da ni Uncle..me yasa ka kasa fahimta ta? me yasa kuka 6oye Noor daga idanu na, me yasa kuka 'ki bayyanar min da ita bayan kunsan ina matu'kar son mata ta?..." Haka har likatan sa ya dawo Uncle Jafar ya fita magana guda bata ha'da su ba. Shi kam abin yawa suka yi masa, muryar Noor da yaji cikin wayar yafi komai 'daga masa hankali...ga kuma Uncle 'din sa da ya kama da laifin 6oye ta navtsawon lokaci, da wanne zai ji, da murnar dawowar Uncle rayuwar sa ko kuwa da ba'kin cikin rashin Noor zai ji. Uncle Ja'afar na fita daga ward 'din sai yaci karo da Saif sai suka koma suka zaune tare. Shiru na 'yan sakanni kowa na jimami cikin ransa, nan ma wayar Uncle Ja'afar ce ta fara ruri ko da ya ciro ya duba sai yaga sunan Anty Zainab ne...dama yasan sai ita, yasan tunda taji batun yaron ta ai babu sau'ki. 'Daukan wayar yayi ya kai kunnan sa..." Nextweek zan dawo". Shine abinda ta fara furtawa cike da 'dauki wanda yake fita tun daga cikin zuciyar ta. Goshin sa ya 'dan tattare sannan ya tambaye ta dalili. Instead ta bashi amsa a a sai tace" Dan Allah kar ka hana ni...ina so in ga jikin Yaro vna.." " Toh ita kuma Hudahn da wa zaki barta?" " Tare zamu zo zan mata bayani ai". " Toh shikenan Allah ya kaimu". Da gama fa'din hakan sai ya cire wayar a kunnan sa daidai lokacin da Saif ya jefa masa tambayar" Unlce wace Hudah kake magana akai kuma? kar dai Noor 'in Yaya?" Kallon sa kawai Uncle Ja'afar yayi yai shiru Saif kam haushi kamar yayi kuka, dama duk wannan abin baki suka ha'dewa Mu'een, dama sun san inda matar sa take shine suka bar shi yake faman kokuwa da rayuwar sa?". " Hmm.." kawai ya iya furtawa a fili gami da sunkuyar da kansa, ji yake badan kawun sa bane Uncle Ja'afar da sai ya tara masa mutane anan wurin, wannan ai rashin tausayi ne a ganin sa. Zuwan Uncle Ja'afar sosai ya bada himma wajen ganin an tsananta kulawa da lafiyar Mu'een yadda ta dace, maku'dan ku'da'de ya dire kafin ya samu aka 'dauko wani likita na musamman domin ya duba shi. Kwanan Uncle Ja'afar biyu ya koma kafin hakan kuwa sai da ya sanar da Mu'een cewa Antyn sa ma zata zo kwanan nan ta duba shi, har lokacin tafiyar tasa kuwa basu yi wani maganar kirki ba da idanu kawai Yah Deen ke kallon sa cikin zuciyar sa yake ayyana irin rashin kyautawar da yayi masa. Shi kam fatan sa Allah yasa idan Anty tazo in ta taho masa da Noor 'din sa cuz tunda yaji muryar ta awayar Anty yasan tare suke da ita, sai ma yanzu yake jin haushin kansa da tuntuni bai yi tunanin hakan ba bayan dukkan alamu sun bayyana a fili, bai ta6a zaton Noor na wurin Anty Zainab ba da tuni ya tafi Taraban yama rasa dalilin da ke hana shi zuwan kwata-kwata. Komawar Uncle Ja'afar da kwana uku sai ga Ishaq ma yazo duba shi wanda washegari aka disacharging 'din su ya koma gida dan ciwon da 'dan sau'ki ba laifi kuma likitan nasa yayi al'kawarin bashi kulawar da ta dace koma a ina yake. Tare duk suka koma gida da Ishaq wanda har a lokacin maganar bakin sa take 'yar 'kalilan, baya ta6a yin maganar da tafi uku zuwa hu'du a kowace rana. Shuwarin suka koma gaba 'dayan su sai washe gari kafin Ishaq yayi musu sallama ya koma Maiduguri. Ammi ce ta cigaba da kulawa da 'danta tana nan-nan da shi, gaba 'daya ta sau'ko tayi sanyi, banda tausayin sa babu abinda take ji yanzu. Ji take da tana da dama da babu abinda zai hana ta dawo masa da matar sa amma taga alamun Alhaji ba niyyar sa kenan ba, da kansa ya sanar da ita shirin sa akan Noor in 'din wanda hakan sai yasa wani sa'in take ganin kamar shi 'din bai damu da rayuwar Mu'een 'din bane bai damu da farin cikin sa ko ba'kin cikin sa ba. Ranar da su Zainab suka sau'ka aranar ma zazza6i ne sosai ya rufe shi..ko sanin wanda ke kansa baya yi, dayake ma likita dake kula da shi yana nan kusa kuma yana zuwa duba shi akai-akai shine ke yi masa duk abinda ya dace kafin ya tafi...jikin sa kam Alhamdulillah yanzu dan illah zazza6in da ke yawan kama shi kuma sosai yake galabaitar da shi. Shima likitan yayi wa su Alhaji bayani cewa abinda ya sa cikin ransa da be samu ba shike hana shi warwarewa kuma a kullum tunanin sa a kai ne shine kuma ke haddasa masa yawan zazza6in... Saif kam kallon su kawai yake yi dan haushi ma ko batun Noor da yaji Uncle yayi be iya zancen da kowa ba cuz yasan duk suna da masaniya kuma suka bar shi yake shan wahala suna ta 'karar da ku'daden su abanza, to tunda kam sun sani shime ze sake cewa da su. Ko ranar da za'a sallamo su ma batun da likitan yayi musu shine dai guda 'daya na cewa a rin'ka 'ko'karin kwantar masa da hankali ta hanyar sada shi da duk abinda yake so...tunda basu da niyyan ganin kwanciyar hankalin sa ai shikenan shikam ido zai zuba musu duk ranar da 'dan uwan sa ya rasa ransa kuwa a lokacin zai karantar da su babban kuskuren da suka aikata, a lokacin zai bayyana musu babbar illan da suka yiwa rayuwar 'dan uwan sa sanadin sakacin su da son zuciya. Duk wani kulawa da Ammi ke bashi a yanzun Saif duk ba yabawa yake yi ba, gani yake duk na banza ne tunda ga can inda matsalar take kuma sun sani suke basarwa. Anty Zainab da sau'kan ta ko ruwa bata sha ba ta ce ita kam yaron ta take son gani... Ammi ce ta sanar da ita cewa yana 'dakin sa. Noor kam shiru tayi tana danna wayar ta hankalin ta kwance. Ta yi kyau shar abinta tamkar wacce bata ta6a zaman aure ba. Ammi kan ta tayi mamakin canzawar Noor ga wani salo da wula'kanci da ta koyo. Noor 'din ta duk ta canza ba kamar Hudahn ta me tsananin kunyan tan nan abaya ba. Ammi bata yi mata batun zuwa duba Mu'een 'din ba ganin kamar bata da niyya sai kawai itama ta mi'ke tabi sahun Anty. Noor tashi tayi ta koma 'dakin Ammi ta kwanta dan ba 'karamar gajiya tayi ba, ga tafiyar jirgi ga ta mota duk ga6o6in ta sun gaji sosai, hakan ma sai da suka kwana a Azare gidan su Anty Zainab suka 'dan huta kafin suka 'karaso. Vibration wayar ta ta fara..ni kaina nayi mamaki da ganin sunan dake kai ha'di da jan symbol na heart na yawo akan fuskar wayar...'dauka tayi tana murmushi murya can 'kasa take magana ni kaina banji komai da tace ba. Sai dai mamaki ya kasa bari na na ganin wannan lamari. Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *90* Basu samu daman gaisawa da Saif ba har kusan la'asar gwamma Zaidu ma shi kam sun ha'du sun gaisa da shi sama-sama. Shi kansa Saif da ya ganta sosai mamakin ta ya kama shi ta zama wata 'yar gayu sosai ta murmure da alamu bata da damuwar komai..." Hudahn Ammi wai kece haka?" Tambayar da yayi mata kenan da alamun mamaki 'karara kan fuskar sa. Murmushi tayi masa sannan ta bashi amsa da fa'din" Ni ce mana Saif hala har ka manta da ni ne?" " Ko nayi hakan ma aganin ki inada laifi ne? how many months ban gan ki ba, baki neman mutum kuma ko a waya ne.." Murmushi kawai kawai tayi masa. Sai yace " Allah fushi ma nake da ke.." Ido ta 'dan zaro tana murmushi sai yace" Erh mana sam baki kyauta mana ba, ban ta6a zaton zakiyi irin hakan ba wallahi". Tana duban sa still tana murmushin tace da shi" Hala wani laifin nayi mai girma..." " Sosai kuwa, haushi ma naji shiyasa ban ta6a tambayar ki wajen Ammi ba, amma Noor ace ki tafi tsawon watanni ko irin ki neme mu awayar nan, ba sa'ko ba gaisuwa ba komai...ai ke kanki kinsan baki kyauta ba..kin bar mu kawai da kewar ki gida ya kasa samun natsuwa". Murmushi kawai tayi tana maida idanun ta kan wayar hannun ta tace" Saif kenan...ya karatu kuma?" " Karatu ya 'kare sauran wata kuma Insha Allah". "To Allah ya taimaka..har kun 'kare service kenan?" " Soon zamu fara.." " Owk Allah ya bada sa'a" " Ameen" Ya amsa yana mai gyara zaman sa. Shiru ya 'dan biyo baya can.sai Saif ya mi'ke yana fa'din" Bari in duba Yaya anjima mu ha'du pls kinji". " OK bakomai" Haka kawai tace masa ta maida idanun ta kan chat da take yi. Saif kam girgiza kansa yayi sannan yayi gaba abin sa. Ya fa'di duba Yaya ne da tunanin ko itama zata ji kunya tace suje tare amma ga mamakin sa sai tayi kamar ma bata ji abinda ya fa'di ba. Ita kam ji take kamar zaman gidan zai takura ta, cuz Yah Deen na gidan kuma bazata iya denying zuwa duba shi ba a koda yaushe ba ko dan saboda Ammi ma and bata son ganin sa balle ta tuna wani abu da yata6a ha'da ala'kar ta da shi...cikin zuciyar ta take yi masa fatan samun lafiya amma duk da hakan tasan idan har bata je ta duba shi ba Ammi cikin ranta bazata ji da'di ba sam dan hakan gwamma ta 'dan yi nesa ka'dan da su...zai fi mata. Cikin ranta ta yanke shawaran komawa gidan Ummahn ta ayau in amma bayan sallar maghrib. Hakan kuwa akayi sai dai kafin tafiyar tata ta samu ta bi Ammi 6angaren nasa badan ranta na so ba ma, haka dai kawai dan kar ammi taga kamar ko bata damu da lafiyar sa bane. Allah ya taimake ta kuma lokacin ma bacci yake yi, har cikin zuciyar ta taji sanyi...hakan yasa tayi masa fatan samun lafiya sannan ta fito tana karanto yanayin sa da ta gani cikin zuciyar ta. Sosai ta fahimci ramar da yayi duk kuwa da cewa ba wani sosai ta kalle shi ba, tasan babu mamaki ba 'karamar jinya yake yi ba dan tasan kalar ciwon sa..amma wata zuciyar ta sai ta kwa6e ta akan zurfafa tunani akan sa bata son ta fame tsohon ciwon da ta jima da binne shi hakan yasa ta tsagaita tunanin da cusawa zuciyar ta tsanar sa kamar yadda ta saba kullum. Bata tafi ba sai da ta jira Alhaji Baba ya dawo gida suka gaisa kafin ta sanar da su cewa tana so zata gidan Ummah ne. Babu wanda ya hana ta sai ma Saif Alhaji ya sa ya sau'ke ta dayake yasan tasu tafi zuwa 'daya. Haka suka tafi suna 'yar hira ka'dan-ka'dan nan yake tambayar ta makaranta tace ai 3months kacal ya rage mata ta kammala gaba 'daya. Murna sosai yayi mata da fatan Alkhairi sannan suka rabu. Su Ummah kam ba 'karamin da'di suka ji ba da ganin ta bayan tsawon wani lokaci, sun jima suna hira ranar dan Ummah har mamaki ta bawa Noor, cikin hirar Ummah ke bata labarin duk wahalhalun da Mu'een ke sha da bata nan, tace tausayin yaron take ji sosai dama so take tayi mata maganar amma tabari akan sai sun ha'du saboda ta fahimce ta da kyau. Jin Ummah ta fara maganar Yah Deen ne ya sata yin shiru kamar tana bacci...Jin shirun yasa Ummah ta 'kyale ta da tunanin ko baccin tayi da gaske. Nan kuwa itama duniyar tunani ta fa'da...sam bata so ta sake komawa rayuwar Mu'een shiyasa ma ta yadda da soyayyar Abdulhakeem da ya nace mata, ba wai dan tana son shi ba sai dai dan kawai ya 'dauki hankalin ta, kuma ko batun aure ne ya tashi a shirye take ta aure sa tunda ta yadda da soyayyar da yake yi mata tsawon lokaci. Ko ja masa rai da ta tayi ma tasan da ba dagaske yake son ta ba da tuni ya janye amma haka ya jajirce akanta ya nuna tsantsar juriya da ha'kuri duk kuwa da cewa yasan labarin komai akan ta amma bai janye ba. Ita kam da kanta bata sanar da shi komai game da ita ba, bazata manta ba ranar yazo gidan su while ta tafi school Anty ce ka'dai a gida nan tayi masa iso suka zauna a parlour suka gaisa ya sanar da ita cewa shi ne me son Noor amma ta'ki bashi ha'din kai har yanzu. Anty bata yi mamaki ba dan tasan dama Noor bata bawa kowa hankalin ta, nan ta fara yi masa bayanin wace Noor da kuma dalilin da yasa bata son kula kowa, Anty kam ma nuna masa tayi kamar har yanzun son Mu'een ke hanata kula wasu. kuma tayi hakan ne dan bata son shima 'din ya cigaba da ra6ar Noor tafi son ta komawa Deen su 'karashe rayuwar tare, dan Anty Zainab tasha kamata tana kuka idan ta tambaye ta dalilin kukan kuma ta kance da ita bakomai wani sa'in bathroom take shigewa ta sha kukan ta son ranta sannan ta fito duk Anty Zee ta san hakan amma bata ta6a tanka mata ba..kuma ta fahimci duk akan rabuwar ta da mijin ta ne, daga baya ma sai ta daina bari Anty na ganin alamun kukan tattare da ita. ...A tunanin Anty ko idan Hakeem yaji cewa Noor 'din ta ta6a aure har da 'ya ko zai janye ne. Amma ga mamakin ta Hakeem kam sai ma 'kara bada himma da yayi, gashi da 'dan banzan surutun da ko bakayi niyyan tanka shi ba ma dolen kane matu'kar kun zauna da shi. Hakan yasa ya shiga jikin Noor sosai tun ma bata sakin jiki har zo ta saki jiki da shi, hatta sunan sa dake wayar ta ma da kansa yayi saving kayan sa, a yanzu idan tace bata 'kaunar sa to kuwa tayi 'karya sai dai har yanzun bai ko taka 'kafar 'kaunar da ta yiwa Yah Deen abaya ba. ***** Lokacin da zazza6in ya sake shi ya fahimci cewa Anty Zainab tazo hankalin sa kasuwa yayi kashi-kashi, burin sa yaga Noor in sa tazo inda yake amma shiru, shi kuma bai tambayi kowa game da ita ba dan shi yanzu abu mai yi masa wahala shine magana, ya tsana sam. Ko motsi yaji zaki ga ya dubi wurin da sauri da tunanin ko zai ganta, yana ji cikin ransa cewar wannan karon me raba shi da Noor koma waye shi to babban ma'kiyin sa ne. Itama Antyn har yanzu bata ga wani sakin fuskar sa ba, dan ya sanya cikin zuciyar sa cewa itace ta raba shi da Noor 'din sa ta janye ta daga kusa da shi bacin tasan halin da yake ciki kuma ta share shi, da kansa ya sha rubuta mata abinda ke damun sa game da rashin Noor amma Anty Zainab bata ta6a tanka shi ba balle ta nuna masa alamun ta san inda Noor take, while tsawon lokacin tana nan tare da ita. Washe gari Saif ya sake dawowa gidan Ummah dan sosai yake so su gana da Noor su fahimci juna. Da Ummah suka gaisa dake harabar gidan tana 'yan aikace aikacen ta nan take tambayar sa jikin yayan nasa, tace taji da jimawa ance ya koma bakin aikin sa. Saif Amsa ta yayi da fa'din" Erh Ummah ya koma amma yanzun haka ma yana gida jikin har yanzu babu da'di.." Subhanallah..kai Allah dai ya sauwaka.." Ameen Ummah" Tace" A ini ban ma sani ba". " Erh ai cikin kwanakin nan aka kawo shi shiyasa ba kowa ya sani ba.." " Allah sarki..." Ummah ta fa'di tana duban Hudah dake tsaye bakin 'kofa tana sauraran hirar ta su...kawar da kai tayi tamkar bata ga Ummah na kallon ta ba. Iso ta yiwa Saif zuwa 'dakin nan ya cire takalman sa ya shiga. Tana daga gefe jikin ta wata duguwar riga ce mai kyan gaske ta yane kanta da mayafin rigar, yayin da Saif ke zaune shima daga can gefe guda suna fuskantar juna. Gaisuwa suka sake yi me 'dauke da kewar juna..." Yah Me jiki fa?" Ta tambaya tana sunkuyar da idanu. Sai da ya furzar da numfashi kafin yace" Jiki Alhamdulillahi da sau'ki...i thought zaki zo da safe ai ki duba shi shiyasa ma banzo da wuri ba.." " Murmushi tayi tace da shi" Erh wallahi nayi niyyan zuwa kuma sai wani uzuri ya ri'ke ni..". " Ke de kice baki damu da shi ba yanzu dan ba mijin ki bane shiyasa". " Haba dai ya zaka ce haka kuma Saif? mutum ai mutum ne...balle jinin.Ammi kasan bazan ta6a wula'kantawa ba." Kai ya girgiza tare da fa'din " Kar ki wani yaudare ni da wannan kalmar dan sam bazan yadda da ke ba, alamun ki kwata-kwata basu nuna cewa kin damu da jinyar sa ba, ganki fa kyau ma kika yi abinki hadda 'kiba kamar ba me karatu ba..." 'Yar dariya tayi sannan tace " Hala so kake ka ganni na 'kwanjame na zama 'kashi ko?" Ta karashe maganar tana murmushi. Girgiza kai yayi yace ba nufi na kenan ba Noor...kawai wani sa'in ina mamaki ne, a dalilin ki fa Yaya kamar zai rasa ransa, wallahi tun rabuwar ku bai sake yin 1 week mai kyau cikin natsuwa ba, kullum shine a gadon asbiti kamar wani mai fama da ciwuka 'dari ta ya bazan tausaya masa ba...kowa ya kasa fahimtar sa hadda kema kika share sa da Ammi ka'dai kike waya itama kuma ta hana kowa damar da zai gana da ke...ban ta6a sanin ana rabuwa irin wannan ba sai akan ki Noor...wallahi koma miye Yayah ya miki zuwa yanzun ya kamata ace kun tausaya masa ke da su Ammi, ku duba halin da yake ciki fa, laifin sa tsakanin sa da mahalacci ne amma duk kun juya masa baya, nasan kema be kyauta miki ba amma Noor me yasa bazaki kalli abin matsayin 'kalubalen dake cikin rayuwar auren ki ba? kina da tabbacin ko wani daban kika aura zaki rayu babu wasu 'kalubalen ne? Ba ina yi miki magana matsayin 'dan uwan Mu'een ka'dai bane Noor ina miki magana ne matsayin 'dan uwan ku gaba 'daya, dan Allah ki zauna kiyi tunani da kanki ki san abinda ya dace da ke, Allah ma kansa idan bawa yayi masa laifi ya kuma tuba tuba ta gaskiya Allah yana yafe mai ya kuma karrama shi balle mu 'yan Adam da dukkan mu ma muka kasance masu laifi, ki yafe masa dan Allah koma bazaki komawa auren sa ba Noor ki dubi girman Allah kije ki duba shi..? kar ki kasance mai son kanki wacce bata damu da damuwar wanin ta ba...rayuwa ko wani 6angare ha'kuri ake da ita balle shima Yayan na tabbata ko giyar wake yake ko wani sa'a bazai yadda ya sake maimata abinda ya wuce ba..dan Allah ki nutsu kiyi tunani kinji...?" Kallon Saif take yi ta kasa fa'din komai gaba 'daya ya sanyatar mata da jiki...shi kam da gama fa'din hakan sai ya mi'ke tsaye bai jira jin ko kalma daga bakin ba cuz maganganun sa basu bu'katar amsa ko 'daya, tsaye ya mi'ke yana jin babu da'di cikin ransa. Hanyar fita ya nufa yana fa'din " Ni na wuce sai anjima ko ince watarana..." Bata tanka shi ba sai itama ta mi'ke tsaye tana duban bayan sa da raunannun idanun ta wanda tuni har sun fara tara ruwa...yana shirin 'daga labile ta 'kira sunan shi da sanyin muryar ta da baya ta6a canzawa. Waigowa yayi ya dube ta take sai ta kawar da kanta gefe sannan a hankali tace..." Bayan Maghrib kazo ka kaini in duba shi...". Cike da jin da'di yayi murmushi gami da jinjina mata kansa kafin ya 'karasa fita. Ko bayan fitan sa ma zama tayi kawai ta 'kure wuri guda da idanu tunanin da zatayi takamamme ma kwata-kwata ta rasa shi, haka kawai take jin ta wata iri zuciyar ta duk ta dagule, abubuwa da da dama ke mata yawo cikin brain 'din ta amma ta rasa wanda ya kamata ta cafka. Ana idar da sallar maghrib kuwa Saif yayi parking 'kofar gidan su, zuciyar sa wasai yake jin ta. Da yake ta riga ta sanar da Ummah batun zuwa duba Mu'een in ya sanya tun da wuri Ummah ta uzzura mata ta gama shiryawa tana idar da Sallah kuwa sai gashi yazo da jin sallamar sa ta 'dauko mayafin ta fito suka wa Ummah sallama suka fita. Ko cikin motar bata fa'din komai Saif ne ka'dai ke janta da hira..amma a ta'kaice take amsa shi, yanzun zuciyar ta bugawa take yi sosai tamkar wanda bata ta6a ganin sa bane a rayuwar ta sai a wannan lokacin. Ko da suka isa gidan ma sai da ta zauna wurin su Ammi suka gaisa sannan ita da Saif suk shiga wurin Alhaji Baba nan ma suka gaishe da shi yake tambayar ta yaushe ne zata 'kare makarantar tace da shi" wata uku ya rage". Cike da jin da'di yace" to Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a 'ya ta." Da " Ameen" ta amsa shi tana mai yin 'kasa da kanta. Daga wurin sa sai suka wuce 6angaren Yah Deen...zuciyar ta har harbawa, duban 6angaren take yi kamar bata ta6a rayuwa a wurin ba, yanzu komai ya canza an canza sabo da ya ci 'kaniyar wanda ta sani a kyau. Saif ne ya fara shiga bedroom 'din nasa, wanda ko sallamar da yayi ma bai amsa shi ba, gaban gadon yaje ya tsaya yayi masa sannu ya amsa shi ma be yi ba illah kansa da ya girgiza masa haka ya fito yana jin tsananin tausayin sa a zuciyar sa, sosai yake jinjinawa halin rayuwa, yau ga Yah Deen mai cike da Izzar nan mai kwarjini da haiba, mai nuna isa da tsananin jin kai amma yau gashi maganar da zai furta da bakin sa ma wahala take bashi..Allah kenan Sarki gwanin sarrafa al'amura a duk yadda ya so. Ganin Saif ya fito ne ya sanya ta saurin fa'din" Bacci yake ko?" " A a idanun sa biyu..ki shiga ina zuwa ya aike ni ne yanzun zan dawo". Ya bata amsa yana mai nufar 'kofan da zata fitar da shi daga 6angaren. Tsayuwa Noor tayi jim kamar bazata shiga ba. A hankali ta 'daga 'kafafun ta ta bedroom 'din nasa...bakin ta nawi yayi mata sosai ko sallama bata iya ta yi ta yanda za'a ji ta ba, daga bakin 'kofa ta tsaya tana tunanin abinda zata ce da shi, daga inda take tana iya hango shi, baya ya juya ma 'kofan so baima san da tsayuwan ta wurin ba...jikin sa farin singlete ne sai abin rufa da ya lullu6e daga 'kafafun sa zuwa 'kugunsa..tana iya hango gefen fuskar sa da uban 'kasumbar da ya tara wanda ada ba hakan yake bari ba. Bata ko yi motsin kirki ba balle ta furta wani abu har lokacin da ta 'dan ji motsin shigowa, zaton ta ko Saif ne dan yace da ita zai dawo hakan yasa ta waigowa amma sai taga Ammi ce ta shigo...take taji kunya ta lallu6e ta..sai ta 'kara yin gefe ta bawa Ammi hanya ta shigo. Ammi da mamaki ta dube ta sannan tace" A a Hudah..dama kun baro wajen Alhajin ne?" Sam Ammi bata ta6a zaton Noor zata yi tunanin zuwa duba shi ba. " Erh" tace a hankali tana mai 'kara sunkuyar da kanta. " Bacci yake ko?" Ammi ta sake tambayar ta tana duban inda yake. Noor shiru tayi dan bata san me zata ce da Ammi ba kuma. Abincin da ke hannun Ammi ta ansa ta 'karasa ta ajiye kan drawern gefen gado..Ammi sai kawai ta 'karasa kusa da shi tana 'kiran sunan sa. Shi kam tunda yaji an ambaci sunan Noor 'din sa ya kuma ji sassanyar muryar ta kusa da shi sai ya lumshe idanu, fatan sa Allah yasa ba mafarki yake yi kamar yadda ya saba ba, ko cikin Ramadan 'din da ta gaba ta ma ya ro'ki Allah sosai akanta, ya ro'ki Allah ya dawo masa da ita idan har itan ta kasance Alkhairin sa ne, sosai kuma ya du'kufa wurin neman yafiyar ubangijin sa bisa ga abubuwan da ya aikata, fatan sa Allah yasa Addu'ar sa ce ta kar6u Allah yasa ba wani mafarkin yake yi ba...bai yi ko motsin kirki ba amma da kansa ya gaskata kunnuwan sa musamman da yaji yanda yanayin bugun zuciyar sa ya canza nan take, har sanda Ammi ta iso kusa da shi ta fara 'kiran sunan sa amma ya kasa amsa ta. Yun'kuri kawai yayi ya tashi zaune...a hankali idanun sa suka kai gare ta daga can gefe tana tsaye. Kallo 'daya yayi mata sai ya kauda kansa gefe yana jin wani irin sanyi na ratsa masa cikin zuciya. " Sannu ya jikin ?" Ammi ta tambaye shi. Saman la66a ya amsa mata da" Alhamdulillah". " Bari in kawo ruwa ina zuwa" Shine abinda Ammi ta fa'da kafin ta bar 'dakin zuwa waje. Idanun sa da suka 'kara fitowa sosai ya 'kura mata yana kallon fuskar ta, itama 'din shi take kallo, zuciyoyin kowannen su da magana amma babu wanda ya iya furtawa... Ita kam dake saurin kuka gareta har yanzun tuni hawaye ya wanke mata fuskar ta, a hankali tayi 'kasa da idanun ta ta tana share hawayen tausayin sa ne sosai ya cika mata zuciya. Sai da ta share hawayen kafin tayi dauriyan bu'de baki ta tambaye shi" Ya jiki?" Bai amsa mata ba sai ma kawar da kansa da yayi ya daina kallon ta, hannun sa ya koma mammatsawa a hankali haka kuma bai sake 'dagowa ya dube ta ba balle ta san ran yana da niyyan amsa ta. Itama sai bata sake magana ba ta ja bakin ta tayi shiru.... Ammi na dawowa ta yi mata sallama gudun kar dare yayi mata tace zata koma gida..Allah ya 'kara sau'ki". Ammi amsawa tayi da fa'din" Amin Hudah..sai gobe ko ki gaida Ummahn ta ki dan Allah". " Zata ji Insha Allahu". Duk muryar ta da sanyi tayi wannan maganar har Ammi taso ta fahimci sauyin yanayi tattare da ita ma amma sam bata bari sun ha'da idanu da Ammin ba dan haka kawai sai ta bita da idanu har ta yi waje. Sallama taje yiwa Anty Zainab sai ta tarar da ita tana Sallah sai da ta jira ta idar kafin tayi mata sallaman ta fito, a harabar gida ta ha'du da Saif nan ta sanar da shi ta gama ya maida ta gida. A fili take fahimtar farin cikin dake fuskan Saif wanda ba na komai bane face na zuwa kawai da tayi ta duba Yah Deen...tana lura dashi sosai farin cikin nasa na fita tun daga cikin zuciyar sa ne. Hakan ne ya 'kara fahimtar da ita 'dumbin 'kaunar da suke yiwa 'dan uwan su. 'Bangaren Yah Deen kuwa bakin sa nawi yayi masa sosai, banda ma haushin dayake ji yana cin sa arai, ganin ta ka'dai da yayi ya rage masa kaso dayawa na abinda yake ji yanzu, ba gaisuwar ta yake bu'kata ba burin sa kawai yaji an sake mallaka masa ita ne, burin sa ta sake kasancewa matar shi ta har abada...a lokacin ne yake da duk wasu kalmomi da zai iya fahimtar da ita yawan 'kaunar da yake yi mata. Washe gari Alhaji Baba da ya fita lambu sai ya samu lokaci ya 'kira 'kanin sa Ja'afar nan yake yi masa bayanin 'kudurin dake cikin ransa na son bada auren Noor da yake da buri wa Ishaq. Uncle Ja'afar kam take ya nuna 'kin amincewra sa da fa'din.." a a ai hakan zai zama ne tamkar an shiga hakkin su gaba 'daya musamman ma shi Ishaq 'din, tunda kam ba aure ne da shi ba, kuma ma Noor matar abokin sa ace za'a bashi ai sai ya ziya ama sanadin rabuwar abotan su kenan..dan yasan Mu'een bazai juri hakan ba, kuma ma Alhaji kai baka tunanin halin da shi Mu'een 'din zai sake shiga ne? zuwa yanzun fa ya kamata ace an watsar da komai...yana son matar shi kawai a maida auren su idan ta amince da hakan shine ka'dai mafita in yaso sai a sanya idanu sosai akansa shima Ishaq 'din ayi masa fatan Alkhairi Allah ya bashi wata ta gari". Shiru Alhaji Baba yayi yana tunani. Uncle Jafar jin shirun yasa shi fa'din" Baka ce komai ba Alhaji?" " Ka bari zanyi tunani". Cewar Alhaji Baba wanda daga hakan suka yi sallama kowa ya ajiye tasa wayar. 'Bangaren Noor kuwa ganin tana gida ya sanya Abdulhakeem matsawa akan yana so kafin ta koma manyan sa suzo ayi magana in yaso data 'kare karatun sai a 'daura auren su kawai ta tare a gidan sa. Duk yanda ta so ta kauce masa abin gagarar ta yayi domin ya matsa sosai, shi har ya yi magana ma da mahaifiyar sa akanta ta dai nuna 'kin amincewar ta amma yasan da zaran mahaifin sa ya amince shikenan. Yanda ya matsa 'din ya sanya dole ta yiwa Ummah maganar cewa iyayen wanda ke neman auren ta naso su zo daga Kano wai. Ummah kam shiru tayi tana duban ta da mamaki tace" Kina nufin wani auren daban zaki yi ne wai?" Tuni ta marairaice tace" Ummah toni ya zanyi? ya matsa min kullum na rasa yadda zanyi da shi..". Ummah baki ta ta6e gami da kawar da kanta gefe sannan tace" Sai kije ki sanar da iyayen naki ai kinsan suke da zancen auren ki ni ba ruwa na". Koda ta shiga 'daki kuka ta ringa yi sosai, haushin kan ta ma take ji da danasanin biyo Anty Zainab da tayi, tasan ba dan ta zo 'din ba da duk hakan bazai faru ba. Saif yace da ita Yayan sa na rashin lafiya ne saboda ita toh taya zata iya tunkarar su Ammi da batun wani daban kuma, ai sai suga kamar bata da tausayi ne shiyasa, ita kuma har ga Allah bata jin zata sake iya zaman aure da shi, a yanzu banda tausayin sa babu komai a zuciyar ta game da shi. _Wai ina labarin Husnah ne?_ Comment Vote Share *Salmerh ce*😍💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *91* Waya ta 'kira Anty Zainab da niyyan ta nemi shawarar ta amma sai ta kasa fa'din komai sai kuka, hankalin Anty Zainab tashi yayi sosai da jin hakan nan ta kwantar mata da hankali da al'kawarin gobe zata zo ta same ta, dama ta 'kira ne akan ga6a domin itama Anty Zainab in tana cikin tunanin ta ta 'kira, bata da'de da gama waya da Uncle Ja'afar ba tana cikin tunanin ta inda zata fuskanci abin sai gashi ta 'kira ta. Washegari ta sa Saif ya sau'ke ta bayan tace da Ammi zataje gaida Ummahn Hudah ne. Koda taje suka gaisa da Ummah suka 'dan ta6a hira ka'dan sai Ummah ta basu wuri kamar dama tasan da maganar da zasu yi sai ta tafi cikin gida gun ayyukan ta. Nan Hudah ta samu sararin bayyanawa Anty abinda ke damunta...tace ita bata san ta ina zata fara tunkarar Alhaji Baba da batun auren Hakeem ba. Anty Zainab shiru tayi tana nanata abin cikin ranta. Wannan shine ana wata ga wata. Ajiyan numfashi ta sau'ke sannan ta kalle ta tace" Ni har ma na rasa abinda zan ce da ke wallahi...kina nufin wai dagaske bakya tunanin sake zama da Mu'een ne yanzu?" Shiru Noor tayi ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannun ta...kowa irin tambayar da yake yi mata kenan, to ita me zata ce da su? amsar wannan tambayar tuntuni ta bayyanar musu da shi me yasa kuma suke son sake maida maganar baya? Anty Zainab rage sautin muryar ta tayi sosai ta sake matsowa kusa da ita tace" Hudah kin san mun 'dauki tsawon lokaci tare da ke ko haka ne ko ba haka ba?" Da sanyin murya ta amsa ta da fa'din" Hakane Anty". " A iya zaman mu dake na ta6a tilasta ki yin abinda ranki bai so ne?" Nan ma kai ta girgiza mata. " Na ta6a cusa miki ra'ayin son Mu'een ko kuma na ta6a nuna miki rashin jin da'di na game da 'kiyayyar da kike yi masa?" " A a Anty baki ta6a ba". " Kin san dalili?" " a a". " Toh saboda naga ra'ayin ki ne hakan shiyasa na biye ki, kuma na fuskan ci ciwon da kike ji a lokacin cikin zuciyar ki shiyasa ban ta6a takuraki akan sa ba, nasan duk wacce irin hakan ya same ta dole ne taji babu da'di amma Noor bazan 6oye miki ba, dai-dai da rana guda ban ta6a farin ciki da rabuwar ki da Mu'een ba, idan kuwa naga irin 'kiyayyar da kike yi masa har cikin zuciya ta nake jin babu da'di kinsan dalili?" Kai ta girgizawa Antyn. Yayin da ta cigaba da fa'din" Saboda 'kaunar da nake yi masa ne matsayin sa na 'dana, Mu'een tun yana da shekaru shida a duniya ri'kon sa ya dawo hannu na bai kuma bar gaba na har sai lokacin da ya shiga Jami'ah a lokacin kuwa kinsan ya riga ya mallaki dukkan hankalin sa ya san me ya kamata yayi da rayuwar sa, Noor ki kwatanta yanda ni nake ji matsayi na na uwar ri'kon sa da yanda Ammin sa zata ji ita datake matsayin mahaifiya agare shi wacce ta haifi abinta da kanta, kinsan dole nata fin nawa ne ko?...wallahi ko ala'kar dake tsakanin ki da Hakeem ban son ta, amma babu yanda zanyi, inaso inga auren ku ya gyaru da shi amma na rasa ta ina zan fara, ina ganin ki agaba na amma ban isa nayi yanda nake so ba saboda gudun kar inci amanar da Ammin ki ta bani, domin an kawo ki wuri na ne da niyyar shiga tsakanin ki da Mu'een..kinga babu yadda zanyi in nuna miki muhimmancin dayake da shi agare ki tunda ga dalilin zuwan ki waje na, shiyasa kika ga ban ta6a furta komai agare ki ba, amma wallahi nasan hatta Ammi kawai dauriya take yi tana biye miki ne saboda farin cikin ki, ko lokacin da kuka ha'da baki da ita kika canza layi ma ba 'karamin takaici naji ba haushi sosai hakan ya bani har ya sani furta wasu 'yan maganganu idan baki manta ba... amma ba wai nayi ne saboda wani abu ba kawai dai raina ne ya 6aci da ganin 'kyamar da kuke nunawa duk wani abinda ya shafe shi...dukkan ku ina son ku Noor ina kuma son farin cikin ku, yanzu da kike gaban iyayen ki kika bar hannu na a yanzu ne nake da damar da zan iya bayyana miki komai da ke raina...Ke da kanki kinsan Mu'een na 'kaunar ki kuma nasan kema kina son shi Noor me yasa zaki da'kile muku farin cikin ku ta hanyar shigowa da wani cikin rayuwar ku? me yasa bazaki koma 'dkin mijin ki na asali ba? kar kiyi zaton auren wani da zakiyi mafita ce agare ku domin shima baki da tabbacin nagartar halayyar sa, may be idan kika bincika ki samu nashi halin ninkin na Mu'een ne ta iya yiwuwa kuma ki kasa fahimta har sai bayan auren ku a lokacin ya zakiyi da shi to?..ko shikenan kin ringa yin aure kina fitowa kenan saboda mazajen nada wasu halayya?, na tabbata bazaki yadda da hakan ba, me ze hana ki daure ranki ki koma ga mijin ki tunda shi kin riga kin san halayyar sa kuma gashi nan da kanki kinsan yayi nadama sai ku rungumi rayuwar ku ku rufa asirin junan ku, dan Allah zakiyi badan komai ba nd na tabbata Ammin ki kanta zata fi farin ciki da hakan, kar kiga wai su suka raba auren ku da shi, ina da tabbacin har gobe suna son sake ganin ku tare kawai farin cikin ki suke son gani da kuma gudun danne miki hakki shiyasa suka basar...yanzu ki zauna kiyi tunani da kanki ki ga me yafi dacewa da ke, koma bazaki tausaya wa halin da yake ciki ba dan Allah ki zauna kiyi nazari ki bi dacewa ba wai dan nayi miki maganar ba a a, kiyi abinki saboda Allah, ni ban miki magana dan ki takura kanki ko kuma dan in tilasta ki koma masa ba face dan ki fahimci gaskiyar da ta kasa bayyana miki. Horo ko wani irin horo kun hora min yaro Hudah sauran kuma sai dai in bayan sa kuke son gani...". Ta 'karasa tana murmushi sannan ta 'dora da fa'din" Kinga ko Uncle J ma jiya muka gama magana da shi kuma ban sanar da kowa ba wannan tsakanin ni dake ne, yace Alhaji Baba na shirin bada auren ki ne ga wani abokin Mu'een amma ya dakatar da shi saboda yafi so ki koma ga mijin ki ya ma ce idan ya samu amincewar ki zuwa nextweek yake so amaida auren kun kafin tafiyar ki in yaso sai ki 'karasa karatun da auren ki..ke ya kk gani jira kawai yake yaji daga gare ki yanzu dan ke ke da linzamin komai". Kuka sosai Noor ta sanya ta kife kanta tsawon lokaci babu wanda ya sake furta komai tsakanin su Anty ma shiru tayi tana jimamin wannan lamari, tasan duk laifin sa ne koma menene da ace bai aikata abinda ya aikata ba da duk hakan bazai faru ba, da yanzu suna can zaune a gidan su cikin farin ciki da iyalan sa. Ganin kamar kukan Noor 'din bashi da alamun tsagaitawa ne ya sanya Anty Zainab fara rarrashin ta tana neman afuwan magangun da tayi tace idan na 6ata miki raine kiyi ha'kuri Noor ko ka'dan ban fa'di abu guda da niyyan 6ata miki ko cin zarafin ki ba, abinda ke raina kawai na gaya miki saboda ganin kamar na isa in fa'da 'din ne, nasan dole zakiji babu da'di amma please kiyi ha'kuri on behalf of dukkan iyalan Taheer Manga nake baki ha'kuri, Noor kar kiga laifin mu kuma kar kiga kamar son zuciya muka nuna, dukkan wanda irin hakan ya faru da 'dansa dole ne yayi wani yun'kuri dole zai aikata abinda yaga yafi dacewa ne shiyasa kika ga mun dawo miki da maganar baya kuma ba wai dan kema bamu son ki bane a a kawai dai dacewa muka duba sai dai nasan a yanzu bazaki ta6a fahimtar hakan ba, inaso kiyi mana afuwa dan Allah idan kinji 'kudurin mu ya 6ata zuciyar ki..ni zan tafi amma ina so ki zauna ki nutsu kiyi nazari kafin wani lokaci ina so in san abinda kika yanke.." Anty ta shi tayi tai mata sallama ta fita nan taje ta samu Ummah ma suka yi magana..a nan ta sake fahimtar Ummah ma ba da'din hakan take ji ba, tunda taji cewa akan ta lafiya tayi masa 'karanci duk sai take tausayin sa, Ummah tace su fita harkar ta kawai duk abinda suke ganin ya dace suje suyi. Anty Zainab ne tace a a kam ba za'a yi haka ba, Umman Saudah ai hakkin ta ne yanzu dole sai an nemi amincewar ta kafin a zartar da wani hukunci". " Hakane kam..to Allah ya za6ar mana mafi Alkhairi". " Ameen Ameen" Anty Zainab ta amsa ta da shi sannan ta yiwa Ummah sallama ta fita daga gidan gaba 'daya. Nasiha Ummah tayi wa sosai akan hakan ta kuma bata wasu addu'o'i tace ta ringa yi ta kuma ro'ki Allah akan yayi mata za6i mafi alkhairi...kar ta wani ru'dar da kanta domin dukkan mafita yana wurin Ubangiji ne..". Anty Zainab da 'kafan ta ta koma gida kuma tun a hanya ta 'kira Uncle Ja'afar tayi masa bayanin abinda ke faruwa bai damu ba sai yace a barta ta samu lokaci tukunna. Anty bata ko tattauna batun da Ammi ba dan tasan hanawa zatayi zata ga kamar za'a takurawa Hudah ne hakan yasa Anty Zainab taja bakin ta tayi shiru sai dai a kullum bata fasa Addu'a akan Allah ya daidaita lamarin ba. A ko wani da'ki'ka rashin natsuwa ke sake ziyartar ta haka take yini ba ko walwala domin kuwa sosai Hakeem ya matsa mata a hakan ma bata fasa Addu'ahn da take yi kullum ba, wani sa'in yini take yi da wayar ta akashe saboda Hakeem ka'dai, gefe guda kuma maganganun Saif da Anty ke mata yawo aka, banda wanda Ummah ke shigar mata cikin brain 'din ta kusan kowace rana tana sake nuna mata ribar da mai ha'kuri ke da shi, ta kan ce ita kanta lokacin da labarin ainahin waye Muhammad ya iso gareta ba 'karamin ba'kin ciki taji da auren da ke tsakanin su ba dan a ganin ta bai cancanci a ha'da jini da shi ba, amma tunda taji cewa ya bada sakin Noor shikenan kuma sai jikin ta yayi sanyi, bata tsinke da lamarin ba sai da taga ya kasa samun cikakken lafiya tun rabuwar sa da matar sa tace da 'kafafun ta ma ta sha zuwa duba shi idan an dawo da shi gida da yake zuciyar tausayi ne da ita tuni ta zubar da makaman ta ta fara tausaya masa..." Bani da tabbacin ga dalilin ciwon sa amma ina ji ajikina kina da ala'ka da ita, kuma naji wasu ma na fa'de cikin gari...bazan yi son kai ba domin bamu san inda rana zata fa'di ba...haka nasan idan har ya kasance kece matar sa na san mu bamu isa mu hana ku rayuwa tare ba..kinga anan dole ne ke ki danne naki burin kibi za6in da Allah yayi miki..idan kika cigaba da ha'kuri sai kiga Allah ya dubi zuciyar ki sanadin biyayyar auren ki sai ya saki a aljannar sa ma'daukakiya kinga idan hakan ya faru ai bakiyi hasarar rayuwar duniyar ki ba ko?" " Hakane Ummah". " Toh ki yi ha'kuri ni dai a kullum shawarar da zan baki kenan shine ki sawa ranki ha'kuri ki rungumi 'kaddarar ki kinji?". " Insha Allah Ummah..nagode sosai..". " Yauwa Uwa ta..idan kin kunna wayar ki ma ki 'kira Addar ki, 'dazun take gaya min wai a kwanakin nan bata samun ki sai ki neme ta kinji..". " Uhum" Tace gami da tashi ta bar inda Ummahn ke zaune. Cikin 'daki ta koma ta rizgi kukan ta son ranta kafin daga bisani ta nemi layin Addar tata. Ko Addah maryam ma shawarar da ta bata kenan duk kalan na Ummah ne wanda zuwa wannan lokacin ita kanta ta fara jin wani 6angare na zuciyar ta na yin na'am da batun amma mafi rinjaye na zuciyar tan yana garga'din ta ne yana kuma tuno mata da can abinda ya wuce abaya..ji take kamar ace an canza ta ba ita bace yafi mata, wani sa'in har ji take dama Allah ya 'dauke ranta 'kila hakan zai fi mata sau'ki..har ga Allah ita bata son komawa auren sa amma ya zatayi? abu ne mai mai matu'kara wahala agare ta ta iya duban idanun su Ammi tace da su wani daban zata aura ba 'dan su ba, aganin ta sam Ammi bata cancanci hakan daga gareta ba bayan duk 'kaunar da ta nuna mata arayuwa. Tun ba yau ba ta za6i ta farantawa Ammi fiye da kanta wanda hakan ke nuni da cewa ta amince da sake zaman aure da Mu'een ne, amma inda matsalar take yanzu shine ita sam bata san ta ina zata fara furtawa ba, a zuciyar ta take jin ta amince saboda Allah da kuma Ammin ta amma bakin ta yayi mata nawi da furtawa. Addar ta Saudah ka'dai ce bata yi na'am da batun ba cuz ita cikin gari take tana kuma yawan jin maganganu akansa musamman da yake rayuwar babban gidan take yi shiyasa a kullum aibun Mu'een baya ta6a barin kunnuwan ta. Hatta Yah Usman ma bai nuna rashin amincewar sa ba lokacin da Ummah ke bashi labari sai yace Allah dai ya shige mana gaba. Abinda kawai ya iya fa'di kenan da yake shi ba gwanin jan magana bane hakan yasa bai sake sanya bakin sa ba..dama ace Saudah ce ko Maryam da a matsayin sa na babban wan su dole ne zai yi wani yun'kuri amma Noor kam yasan ko ya fa'di wani abin ma aikin banza zai yi domin ita tun mahaifin su na raye aka bawa Alhaji Baba ri'kon ta so yanzu su ke da iko da ita ba shi ba...gashi sanadin su har waje ta samu daman fita dan yin karatu wanda ko cikin 'ya'yan Alhajin ma ya tabbata babu wanda ya fita karatu a waje ita ka'dai suka bawa wannan gatan...da ace kuwa suna da son kansu da nasu 'ya'yan ka'dai da ya tabbata Noor ko kusa da jikin 'dan su ma bata isa taje ba balle har batun aure ya ha'da su...talk more of fita malesia karatu. Wannan tunanin yayi shi ne cikin zuciyar sa kawai amma a fili bai wani yi dogon magana ba. ***** Cikin satin kuma jikin Yah Deen ya matsa sosai hatta Uncle Ja'afar sai da yazo Bauchi, idan yana tari har ta hancin sa jini ke fita duk ya galabaita baya iya ko yin numfashi mai kyau dole aka tafi da shi asbitin koyarwa dake garin Zaria. Tuni Uncle Ja'afar ya fara shawarar fitar da shi waje ma amma sai likitocin suka nemi abar shi tukunna akwai possibilitin sabon dashe da zuciyar sa ke so ayi dan gab zuciyar tasa take da daina yi masa amfani kuma koda anje can 'din ma duk zancen 'daya ne..so idan ance za'a ja lokaci kuma yana iya rasa ransa ma gaba 'daya duk da ba lallai ne sai anyi dashen ba amma dai hakan na da matu'kar muhimman ci..sai dai kuma hakan zai iya zama tarihi idan zasu iya wani abu..likita yace su tanadi abinda suka tabbatar zai sanya shi farin ciki da farkawar sa idan anyi sa'a ma yin hakan zai iya sau'kar da kaso mafi girma daga cikin ciwon nasa. Dole ba dan suna so ba suka ha'kura suka zubawa sarautar Allah idanu sai dai zu'katan su cike da yake tunanin abinda ya kamata su tanada kowa ya rasa mafita yayin da dukkan su suka zurfafa tunani wajen gano abinda ya dace suyi, kowa tunanin sa kan Noor ya fa'da dan sun san itace ka'dai matsalar sa a yanzu sai dai ta ya zasu iya sanya shi farin ciki da batun ta wannan me har yanzun sun kasa ganowa..Duk 'ko'karin da ya kamata ace likitocin sunyi sun yi shi akan sa kafin su samo kan matsalar tasa. Kwanaki na sake 'karatowa lokacin tafiyar Noor na sake matsowa domin kwanaki hu'du ya rage mata ta tafi..sam bata san cewa ankai Mu'een Zaria ba saboda babu wanda ya sanar da ita, Saif kuwa da shi aka tafi balkanatan taji labarin daga wajen sa, Zaidu kuwa dama tuni ya tattara ya koma Taraba wurin Uncle Ja'afar so baya gida yanzu. Kan batun tafiyar tata taje gidan Alhajin domin su tattauna da Anty hadda Ammi ma, nan ta tarar da su kowa jigum-jigum gashi dama tun ranar da suka yi magana da Antyn basu 'kara ha'duwa ba ko awaya basu gaisa ba yau kusan kwana shida kenan rabon su da juna shiyasa ma ta raso ta zo. Hankalin ta tashi yayi da ganin yanayin su Ammin gashi da alamu hankalin su duk ba wuri guda yake ba. A bakin Anty Zainab take jin labarin abinda ke faruwa..wanda nan take taji gaba 'daya tsigar jikin ta ya tashi. Bata kai ga dai-dai ta natsuwar ta ba taji wayar Ammi na ringing nan duk suka maida hankalin su kai..Saif ne ke yiwa Ammi bayanin duk abinda likitocin suka ce..harda lokacin da suka nemi abasu dan shawo kan abin suga ko dashen ne ya dace ko kuma zasu dace su shawo kan matsalar tunda da saura zuciyar tasa bata daina amfani ba har yanzu. Ammi kawai hawaye ne ya fara gangaro mata wayar ma sulalewa tayi ta fa'di kan cinyar ta batare da ta kula ba..." Allah ka jarabce ni, Yah Allah ka bani ikon cinye wannan jarrabawar..". Haka ta fa'di cikin kuka wanda da sauri ni da Anty Zainab muka zo kusa da ita ni kam ban iya magana ba illah kukan da yaci 'karfi na ganin halin da Ammi ta shiga. Anty Zainab ma hawaye take yi tana kuma bawa Ammi baki..Ammi sai girgiza kanta take yi tana jin zuciyar ta babu da'di...idanun ta lumshe tace" Zainab Mu'een na shan wahala sosai, ban san inda ya samo ciwon zuciyar nan ba gashi tana neman halaka min shi, wallahi ji nake da ina da damar da zan bashi farin cikin da yake so da na bashi Zainab bana so in rasa shi...'kalubale da yawa ya fuskan ta a rayuwar sa kuma ya jura wannan kam ina jin ba zai iya jurewa ba...". Ban da shashshe'ka babu abinda ke tashi cikin parloun idan ka gammu sai kayi zaton ko labarin mutuwa ce ta riske mu a lokacin. Ni da Anty Zainab ko magana ma bama iyawa Ammi ce ka'dai ta cigaba da fa'din"...yaro ne shi mai matu'kar 'kauna da tausayin iyayen sa, 6angare 'daya kawai ya samu mummunar shaida..." Bu'de idanun tayi tace" Zo Noor zo kusa da ni..." Da sauri na matso jikin ta na kwantar da kaina a jikin ta na cigaba da kuka na..tana shafa kaina tace" Zainab ku yafe masa dan Allah duk abinda yayi muku ku yafe masa...Noor please ki yafewa yayan ki kinji..kar ki ri'ke shi a zuciyar ki kinga ma rayuwar sa gaba 'daya tana neman 'karewa...kar ya mutu da fushin ku akan sa..." 'Dago kai Noor tayi tana toshe bakin ta da hannun ta 'daya take duban Ammi, idanun ta cike taf da hawaye wasu na gangarowa yayin da idanun ke sake cikowa. Girgiza kanta kanta take yi a hankali tace" Ni bana jin haushin sa Ammi...tuntuni na yafe masa..ban rayu da haushin sa cikin zuciya ta ba..kuma na riga na yanke shawaran sake auren sa kice masa kar ya tafi ya barni Ammi dan Allah kice masa ya yafe min...". Kuka sosai ne ya ci 'karfin ta yayin da taji 'dumin hannayen Ammi ya sau'ka abayan ta. Runguma Ammi tayi mata mai nuna tsantsar farin ciki da jinda'din ta a fili..." Allah yayi miki albarka Noor dama nasan ke 'yar halak ce..Ubangiji Allah ya faranta miki ya baki 'ya'yan da zasu ji 'kanki su faranta miki fiye da wanda kika yiwa manyan ki...". Anty Zainab kanta murmushi take yi agefe tana kuma zubda hawaye na jin da'din furuci na. Ammi na sake ni Anty Zainab ta kama hannu na muka bar 'dakin. Itama rungume ni tayi cike da farin ciki tace" Baki ta6a sanya ni jin cewa Mu'een yayi dacen mace fiye da yau 'din ba Noor...nagode! Nagode!!..Allah ya biyaki da Alkhairi..a yau 'din na zan sanar da Uncle Ja'afar a maida muku auren ku domin babu wani abinda za'a jira tunda kin riga kin amince...sai dai fa kiyi ha'kuri da kalan auren naki 'kilan haka Allah ya 'kaddaro miki dukkan taron 'daurin auren ki na zuwa ne cikin rashin shiri". " Zan koma gida Anty dama nazo ne batun komawa ta school inji yaushe ya kamata mu sa rana..." Karki damu ki bari zamu yi magana daga baya duk abinda ake ciki zan sanar dake...yanzun muje ki yiwa Ammi sallama kafin ki wuce". Comment Vote Share *Salmerh ce*😍💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *92* Fita suka sake yi dukkan su zuwa wajen Ammi sun same t ne idanun ta kan waya tana faman dubawa, ko da tayi mata sallamn ma kai kawai Ammi ta jinjina mata cike da jinda'di, ita kam fuskar ta ba yabo ba fallasa ta fita. Sai bayan fitar ta sannan Ammi ta kalli Anty Zainab tace" Zainab kinga fa ni nama rasa wanda zan 'kira in sanar mawa saboda farin ciki kaina ya kulle kuma". Murmushi Anty Zainab tayi idan ka gansu bazaka yi zaton sune ke shar6an kuka lokaci 'kalilan da suka gabata ba. " Bari zan gayawa Baffan su". Shine abinda Anty Zainab ta fa'di tana mi'kewa tsaye. Wayar ta taje ta 'dauka ta 'kira shi sai dai cikin rashin sa'a ko 'kira guda daga cikin missed call uku da tayi masa bai 'daga ba. Text ta tura masa kamar haka.." _Mun yi magana da Noor kuma ta amince da auren ka sanar da Alhaji please_ ". Tana gama rubutawa sai ta tura masa sannan ta 'kira Saif ta tambaye shi ya jikin Mu'een 'din yace " Anty da sau'ki dai za'a ce amma har yanzu akwai damuwa..ance sai an tare shi da labarin da aka san zai kwantar masa da hankali ya sa shi farin ciki kuma duk mun rasa yadda zamu yi tsoron kar ya farka ma muke yi a halin yanzu...." Murmushi Anty Zainab tayi gami da fa'din" ka kwantar da hankalin ka be jima ba muka rabu da Noor kuma ta amince da batun maida auren su..ina jin kawai ku jarraba wannan labarin 'kila ze yi amfani". Cike da farin ciki Saif yace" Alhamdulillah...ai kamar anyi an gama ne ma Anty...bari in sanar da Alhaji Yanzu". Ko jiran jin ta bakin ta ba yi ba ya yanke wayar. Alhaji Baba be wani bayyana farin cikin sa a fili ba ko bayan da ya ji labarin dan ciwon Mu'een 'din ya riga ya 'daure masa kai ya zarta tunanin sa gaba 'daya, gani yake kamar ba rayuwa zai sake yi ba kawai likitocin na yaudaran su ne, yau kusan kwanan su biyu kenan da zuwa Zaria amma ko motsi da yatsun sa be yi ba..yau ne ma ake saka ran farfa'dowar sa amma shiru har yanzu gashi har la'asar ta shige maghrib ta gabato. Gani yake ma kamar wannan auren banda tauye hakkin Noor babu abinda za'a yi, mutun kullum yana kwance ba lafiya ina za'a yadda da aura masa mace irin Noor kuma...yaushe ma ake da tabbacin zai tashi, shi ya fara tunanin ma kawai gara su amince a ayi masa dashen indai har akan zai fi kawo masa sassauci sai dai dashen ance babban risky ne likitocin da kansu suka fa'da...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...a zuci yake tunanin amma be san lokacin da wannan kalmar ta kubce daga bakin sa ba, goshin sa ya dafe da shima yake jin yana sara masa. Ganin hakan ya sanya Uncle Ja'afar kallon.sa, cikin 'yan da'kiku ya karanci yanayin da yake ciki, fara kwantar masa da hankali yayi domin duk yasan akan ciwon Mu'een ne yace masa su gwada batun auren dai tukunna su gani, yace shi inda hali ma tunda ta amince me zai hana kawai a 'daura auren ayau 'din aganin sa hakan zai fi kawo musu sau'ki fiye sanar da shi labarin amincewar tan kawai. Alhaji Baba yaso ya nuna 'kin amincewar sa amma Uncle Ja'afar ya kafe dole sai da ya amince. Saif ya tura ya ciro masa ku'di a bank sannan ya tura shi nemo dabino domin ya tura anemo masa goro ba'a samu ba. Ai kuwa bayan sallar Isha'i aka gabatar da 'daurin auren Deen da Noor bisa sadaki 50k da Uncle Ja'afar ya bayar. Alhaji Baba me ya bada auren kamar yadda ya ta6a bayar wa abaya dan haka a hannun sa aka bada sadakin nata karo na biyu...shi dai fuskar sa ba yabo ba fallasa haka yayi ta binsu da idanu har aka 'kare komai. A daren Ja'afar ya ke6e da saif ya tsara masa duk yadda yake so ayi, Alhaji Baba kam bai ma san sunayi ba, kuma ma ko ya sani 'din ba baki zai sanya musu ba. Saif ne ke kwana tare da shi su Alhaji Baba da Uncle Ja'afar Hotel suke kwana inda suka yi masau'ki tun farkon zuwan su. Dama ya gama tsara masa cewar a duk lokacin da yaga alamun zai farka sai yayi kamar waya yake yi bayan ya gama shirya masa abinda zai fa'da. Daren ranar kaf haka Saif ya gama gadin Mu'een amma bai farka ba, har washe gari shiru har sun fara cire rai ma da ganin farkawar tasa domin magashiyan yake kwance sai uban na'urori da aka jona mai..tunda suka kawo shi bai motsa ba yau kwana hu'du kenan..abin ya fara 'daure musu kai sosai gashi Uncle na so ya koma bakin aikin sa amma ya kasa dauriyar yin hakan sam ba ze iya tafiya ya bar Mu'een cikin wannan mawuyacin halin ba, gani yake kamar da ya tafi za'a sanar da shi mutuwar sa shi yasa yafi so yaga anyi komai a gama kan idanun sa. Noor kuwa tun lokaci da ta tabbatarwa da Ammi amincewar ta bata 'kara kunna wayar ta ba, ko 'daura auren ma da akayi sai Ummah aka 'kira aka sanar mawa wanda itama abakin Ummhan taji. Kuka kuwa kamar wacce aka ce an sai da ita ga wani ma'kiyin ta ne haka take ji..duk ta hana kanta sukuni da kuka..Ummah na 'ko'kari sosai wajen kwantar da mata da hankali amma a banza. Haka Saif suka rabu da yammacin ranar ma duk jikin su sanyi 'kalau suka koma masu'kin su..Saif kansa har 'yar rama yayi, yana matu'kar tausayawa yayan nasa, bai san wace iriyar taimako ya kamata yayi masa ba... Likitoci na zuwa akai-akai suna duba shi kuma kullum abin numfashi da bugun zuciyar sa na reading yadda ya kamata amma har yau farfa'dowa ta gagare shi. Ko yau in ma Saif duk jikin sa da sanyi, gaba 'daya ya tsinke da lamarin Yayan nasa 'karfe tara likita ya bar 'dakin wanda hakan ya bawa Saif damar shiga wajen sa da yake tare suke kwana. Baccin ma yanzu ko damun sa baya yi da yayi da bai yi ba duk baya jin komai ba, har ya saba da zama yana 'karewa Yah Deen kallo...sosai ya fahimci rayuwa ba'a bakin komai take ba..yana zaune sai dai ya duba wayar sa ko kuma idan uzurin shiga bayi ya kama shi ya tashi ya shiga ya fito, tunani kala-kala babu irin wanda bai zo ransa ba... Kwana yayi idanun sa biyu amma babu wani canji da yagani tattare da shi. Har gari yayi haske ma'aikata suka zosuka gama aikin su suka tafi amma shiru, haka likitocin ma suka shigo suka duba shi suka sake fita, su Alhaji Baba ma duk sun zo inda Saif ke ro'kon su akan suje su huta abinsu tunda shi yana nan duk abinda ake ciki yayi al'kawarin sanar da su, Saif yayi hakan ne saboda tausayin mahaifan nasa, tun zuwan su Zaria ba su huta ba kullum suna cikin zirga-zirga, aganin sa gara shi domin da 'karfin.sa inda sabo ma ya riga ya saba da hada-hada...sosai suka ji da'din furucin Saif in dan 'karara ya nuna tausayawar sa gare su....kafin su koma sai da suka sake ganawa da likitan anan Alhaji Baba ya fa'di nashi ra'ayin amma likitan yace har yanzun dai da saura su 'kara basu lokaci. Haka suka fita suna baza babbar riga kowa jikin sa yayi laushi. Fita suka yi suka koma masau'kin su suka bar shi da Saif 'din kamar yadda ya bu'kata. 'karfe tara da 'yan mintina na safiya lokacin Saif yaje yin breakfast ma, ko da ya dawo kuwa kamar ba zai shiga duba shi ba kuma sai wata zuciyar tace ka duba dai. Tura 'kofan yayi da niyyan le'kawa sai cak idanun sa suka sau'ka kan yatsar 'kafan sa guda dake motsi. Saurin 'karasowa yayi ciki yazo kusa da shi...saman idanun sa yaga yana motsi ka'dan-ka'dan yana jujjuyawa amma bai bu'de idanun ba. Da farko tsaban farin ciki Saif rikicewa yayi har ma sai ya rasa mi ya kamata yayi tuno abinda Uncle Ja'afar ya sashi yi ne ya sanya shi saurin ciro wayar sa daga aljihu idanun sa kan fuskar Mu'een. 'Kira ya dannawa Uncle 'din wanda daga 'dagawa ya furta" Hello..Hello Uncle" " Erh gani nan tare da shi" " Ohh har kun dawo daga wajen 'daurin auren ne?" " Kai..masha Allah..Ubangiji Allah ya sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya...nayi matu'kar farin ciki sosai". Shi ka'dai yayi ta maganar sa amma bazaka ta6a gane hakan ba. Shima Uncle Ja'afar hakan da yaji Saif na fa'di ne ya sanya shi saurin fahimtar halin da ake ciki, yana da tabbacin Mu'een ya farka ne shiyasa Saif ya 'kira shi domin shine da kansa ya tsara masa komai da zai ce. Albishir 'din da yayiwa Alhaji Baba kenan nan suka shirya a hanzarce suka fito. Saif cikin farin ciki yayi wayar tamkar babu wata damuwa tattare da shi...yana sau'ke wayar daga kunnan sa sai ya suka ha'da idanu da Mu'een domin tuni ya bu'de nasan lumsassun idanun ya zubawa Saif tunda yaji muryar sa kusa da shi. Cike da murmushi yace" Yaya albishirin ka..! yanzun Uncle ke ce min an maida muku auren ku da Noor...gaskiya ka bani tukuici na..." Idanu ya zubawa Saif na tsawon lokaci sannan a hankali ya maida idanun sa ya lumshe gami da juya kansa...hawaye Saif yaga yana tsiyaya daga gefe da gefen idanun sa..take kuma na'urar dake irga bugun zuciyar sa ta fara 'kara yana 'dan sau'ka a hankali...fisga jikin sa ya fara ka'dan-ka'dan...kana iya ganin hawa da sau'kan da 'kirjin sa ke yi. Rikicewa Saif yayi da ganin hakan take ya fara 'kiran sunan sa, hannu ya sa aka yana ji tamkar ya 'kwala ihu saboda tausayin Yayan nasa, a rikice ya fara ja da baya da niyyan fita 'kiran likita, sai dai kafin ya kai ga isa jikin 'kofan ma sai suka riga shi turowa. Da sauri suka yi kansa bayan sun bawa SAIF umarnin fita sai suka datse 'kofan ko ta glass in window Saif ba ya iya hango shi haka duk sai yaji hankalin sa ya tashi sosai. Bei iya ya ko 'kira su Alhaji ba tsaye yake yana safa da marwa da ka gansa zaka san cewa hankalin sa duk a tashe yake, wanda ba'a 'dauki tsawon lokaci ba sai ga su Alhaji ma sun iso nan yayi musu bayani a takaice yana nuna damuwar sa a fili 'karara. Innalillahi kawai suke ta maimaitawa yayin da Alhaji ya samu wuri kawai ya zauna ya dafe kansa. Kimanin awa guda da rabi kafin likitocin suka fito su kansu ba'a nutse suke ba..domin da 'kyar Allah ya taimake su suka ceto rayuwar sa cuz bugun zuciyar san 'kasa sosai ya sau'ka. Albishiri suka musu akan cewa ba wani matsala su kwantar da hankalin su nan da wani lokaci komai zai daidaita da iznin Allah...nan Alhaji Baba ya saki wani ajiyan zuciya Uncle Ja'afar kam godiya ya ringa zubawa mahalicci. Cike da farin ciki suka samu wuri suka zauna gaba 'daya...tsabar sauri ma duk wayoyin su basu taho da shi ba, a masau'kin sun suka baro shi. Allah cikin ikon sa kuwa kafin sati guda har yana iya shiga bayi da kansa...sai dai har yanzun baya magana da kowa...sai da ido kawai. Uncle Ja'afar ma jiya ya koma ganin jikin nasa da sau'ki kuma likita yace ba sai anyi masa dashen ba ma insha Allahu komai zai wuce. Fatan su dai Allah ya 'kara lafiya ne ingantacciya. Sai da Alhaji Baba ya dawo ne kafin su Ammi ma da Anty Zainab suka shirya zuwa can Zarian, sai dai Alhaji yace bai yadda su kwana ba a ranar zasu dawo dan haka sassafe suka shirya tafiya. Tun dare Anty Zainab tace da Noor ta shirya zata raka ta wani wuri gobe kuma da sassafe zasu zo su 'dauke ta, da yake da motar gida ne so basu da matsalar komai. Noor kam toh kawai tace da ita ba wai dan ranta na so ba..sai da ma suka fito kafin take sanar da Ammi cewa tafiyar fa wai harda Noor ne tun jiya na gayyace ta amma ban sanar da ita Zaria zamu ba. " Ammi jim tayi kafin tace kar kuma taga kamar an takura ta fa?" Anty cewa tayi " A a ita da mijinta wani takura kuma yanzu, idan kika biye ta Noor fa har abada baza'a yi abinda ya dace ba". Haka driver ya jasu zuwa 'kofar gidan Ummahn Saudah..shiga suka yi suka gaggaisa kafin suka fito dukkan su, Noor kam tun da taga harda Ammi sai taji hankalin ta bai kwanta da tafiyar ba, ai kuwa kamar wasa sai taga sun 'dauki hanyar Zaria ta kuma san can Mu'een ke kwance...shiru kawai tayi tana jin faragabar ganin sa a zuciyan ta. Sosai su Ammi suka yi farin ciki da ganin sa zaune, magana ce ka'dai baya yin ta sai ya ga dama, haka ya dinga bin Noor da kallo bai iya yace da ita ko uffan ba, ko gaisuwa akayi masa baya amsawa sai dai ya lumshe idanu kawai. Banda murmushin farin cikin ganin su Ammi babu abinda zaka gani kan fuskar sa. Haka har suka baro Zaria magana bata ha'da su da ita ba..ita kam ko a hanyar komawar su ma jikin mota ta kwantar da kanta tana share hawaye a 6oye. Tana jin yanda su Ammi ke bayyana tsananin farin cikin su a fili da ganin yanayin jikin nasa, amma ita bata iya sanya musu baki ba. Tunanin ta ma tafiyar da ke gaban ta ne, dama tun lastweek ya kamata ta koma amma Anty Zainab ta dakatar da ita, yanzun wai zuwa jibi zasu koma har da ita Antyn. Koda aka sau'ke su ita kam bata fita daga motar ba tace a wuce can gida da ita tana so zata 'karasa shirin ta ne... Bayan kwana biyu da zuwan su Zaria suka bar Shuwarin ita da Anty Zainab amma sai da suka kwana kusan uku a Zaria kafin suka wuce dama ashe haka Anty ta tsara tafiyar shiyasa ta dakatar da ita. Tunda suka koma kuwa sam ta kasa barin ta ta ci abinda ranta ke so, ci wannan sha wannan duk ta ishe ta da su, a 'yan kwanaki biyu zuwa uku da suka yi a Azare 'din ba 'karamin ha'da abubuwa Anty Zee tayi ba shiyasa a kullum bata zama a gida har sai ranar da suka taho. Wani sa'in har mamakin ta Noor ke yi domin sarai tasan dan me Antyn ke sa ta gaba da shashayen abubuwan ita kuwa ranta ba so yake yi ba, a ganin ta duk 6ata lokaci suke yi abanza da wannan auren nasu bashi da darajar da har za'a yi masa shiri irin haka. Bata manta lokacin da ta kunna wayar ta ta 'kira AbdulHakeem ba..lokacin da kanta tasan ta sanyawa Zuciyar ta dauriya, amma duk da haka sai da tayi kuka daga 'karshe kasa ma magana tayi sai text ta tura masa akan cewa an riga an 'daura mata aure. Da farko 'kin amincewa yayi sai daga baya ya yadda dan yasan Noor bata yi masa 'karya. Ya ji haushi sosai kam amma hakan bai hana shi yi mata fatan Alkhairi a auran ta ba...Abin mamaki sai ga shi harda kyautar ku'di yayi mata masu 'dan nawi a fa'darsa wai tashi gudummuwar kenan, sam be nuna alamun yaji 6acin rai ko wani abu ba duk da tasan dole abin sai ya dame shi amma yanda yayin sosai taji ya 'kara birge ta. Sai take jin dama shine ta aura da babu abinda zai hana ta shan duk wani abinda ake sha da ku'din ta ma zata siya amma Mu'een kam wannan ba damuwar ta bane shi domin ko duniya zata ha'da ta shanye saboda shi tasan ba kwarjini zata yi a idanun sa ba, tunda hakan ba zai hana shi ya tsallake ta ya tafi wurin wasu matan ba. ***** _Wai ya labarin Husnah ne?_ Husnah na can yanzu duniya tayi mata da'di domin babu mai takurawa rayuwar ta, tun rabuwan ta da Mu'een bata 'kara sashi a idanun ta ba, da yake ma ha'kura tazo tayi da makarantar ta koma Abuja wurin mijin ta ta cigaba da bautawa auren ta. Duk yanda Hisham yaso yaji dalilin barin makarantar Husnah 'kin sanar da shi tayi, ta kuma canza layi ta daina amfani da tsohon layin ta abin duk sai yake bashi mamaki matu'ka. Da farko abin damunta yake sosai a zuci, haushin yanda ta ringa biye masa tana yadda da bacin da auren wani namijin akanta. Sam ta rasa me ya toshe mata 'kwa'kwalne ma da bata 'dauki mataki akansa ba, tasan hadda sakacin ta ma baya ga haka da be isa ya 'keta mata haddin auren ta ba. Haushin sa sosai yanzun take ji ko tunawa da shi bata so tayi, Allah ma ya taimake ta tun ranar da Noor da gansu bata sake sanya shi a idanun ta ba. Wani sa'in idan abin ya ishe ta sai taji kamar ta sanar da Hisham gaskiyar abinda ya faru amma wani 6angare na zuciyar ta sai yake yawan garga'din ta akan kar ta fa'di ma kowa domin idan kasan farkon fitina baka san 'karshen ta ba. Sai daga baya duk ta watsar da komai ta cigaba da rayuwar ta kamar kowa sai dai har yau 'din nan bata daina istighfari da neman gafarar mahalicci ba. Hisham mutun ne mai tsananin ha'kuri da kawar da kai, ga sanin ya kamata ga shi sam baya 'dagawa kansa hankali a kan komai. Zaman su lafiya suke da ita yana kuma kulawa da duk wani abu da yake hakkin ta ne. Alhaji Maman mahaifin sa kuwa tun lokacin da wani hatsari ya rufta da shi jinya ya kasa 'karewa sai amaryar sa ta wawashi iya abinda taga zata iya sannan ta je har asbitin da yake jinya ta tsaya akansa wai ya sai ya bata sakin ta. Ai kuwa sai da ya sake tan kafin tayi gaba tana ta6e baki gami da taunar chewingum tace bazata iya zama da miskini ba domin daga 'kugun sa zuwa 'kafafun sa duk sun yi damage basa amfani. Haka tana yatsina fuska tayi gaba kowa dake wurin sai da yayi mamakin ta domin kaf cikin matan Alhaji Mamman ita yafi fifitawa sai gashi itace ta fara guje masa a lokacin da yake tsananin bu'katan kulawa. Tun lokacin ya fara danasanin abubuwan da ya ta aikatawa dama kuma duk abinda ba'a shirya shi ta hanyar da ta dace ba 'karshen sa ba kyau yake yi ba. Taimakon da Allah yayi masa ma shine be kai ga wula'kanta ba Allah ya kar6i ransa...domin dududu bai fi 3months da jinyar ba ya koma ga mahalicci. Yanzu Mummyn Husnah da Hajiya Kareemah mahaifiyar Hisham suna rayuwa ne tamkar 'yan uwa babu ruwan su da wani batun dukiya ko kishi da junan su, sun ha'de kansu suna kasuwan cin su a tare balle ma da yake Hajiya Kareema ma'aikaciyar gwamnati ce shikenan sai Mummyn Husnah ke yi musu jagoranci haka komai yake tafiya musu dai-dai. Babban damuwan Husnah a yanzu bakomai bane face rashin haihuwa..daga ita har Hisham 'din duk sun damu, banda ma iyayen su da kullum ke taya su addu'a ko za'a dace. Ita kam Husnah wasu lokutan sai dai ta zauna tayi ta shar6an kuka, domin tasan musabbabin da yakawo mata hakan bakomai bane illah alluran da ta tayi lokacin da take tare da Mu'een shiyasa har yau bata yadda taje asbiti tare da Hisham ba gudun kar asirin ta ya tonu a idanun sa...sau da dama shike sake bata baki akan tayi tawakkali, haihuwa da rashi duk na Allah ne, kuma idan bai nufe su da samu ba ko ma me zasu aikata haka zasu ta wahalar da kansu bazai basu ba, idan kuwa ya nufe su da samu haka nan ma zasu tsinci kansu sun zama iyaye batare da sun wahalar da rayuwar su ko dukiyar su ba. Sosai take jin da'din halayyar Hisham tana kuma godewa Allah daya ha'da ta da mutun irin sa..taje Umrah taje Hajji kusan sau uku tana ro'kon Allah akan haihuwa amma har yanzu shiru babu labarin komai. Da kanta ta fara bawa Hisham shawaran yayi aure amma ya'ki, itan ma ba wai tana so yayi auren bane amma a ganin ta rashin adalci ne tayi idan tace da shi bazai yi aure ba tun da tasan matsalar daga gare ta ne. Hisham 'kin amincewa yayi yace ai a wurin Allah suke nema ba mutun ba, idan kuma ya 6ata lokacin sa yayi auren kuma itama matar bata zo ta haihu ba fa me akayi kenan. Cike da marairaita Husnah tace " Duk da hakan dai ka gwada dan Allah, Familyn mu ya yi shiru da yawa Hisham ya kamata kayi wani abin kaima.". Sai ce mata yayi" Ai ban isa inyi abinda Allah be nufa ba dan haka kima daina 6ata lokacin ki, ni babu wani aure da zanyi". Da ta ga dagaske yake bazai amince ba sai ta kai 'karar sa wajen iyayen su. Mummyn tace tafi 'karfafa zancen dan haka dole ta tilastawa Hisham fara neman aure...cikin kwanciyar hankali kuwa ya samu wata yarinya anan Azare ya aura, yarinya ce 'karama dan sacondary school kawai ta kammala aka bashi ita. Sai a lokacin da kusanci yarinyar sannan ya fahimci akwai bambam mai tarin yawa tsakanin Husnah da yarinyar sai dai hakan bai yasa ya canzawa Husnah fuska ko kuma cin zarafin ta ba, balle ma shi ba gwanin dawo da abinda ya riga ya wuce bane. Ya dai yi 'ko'kari wajen ganin ya daidaita tsakanin Husnah dayarinyar be yadda ya tauyewa kowa hakki ba kasancewar kowaccen su nada nata kalan muhimmancin a zuciyar sa. Allah cikin ikon sa kuwa shekarar farko da auren su ta cika shi ne da 'dan ta namiji da Allah ya azurta ta da samun sa, yaro mai kama da ita...murna a wurin wannan familyn ba'a cewa komai...Husnah sam bata yi ba'kin ciki da haihuwar ba amma haka take shiga 'daki ta risgi kuka son ranta dan tasan itace ta cuci kanta abaya, da ace bata biyewa Mu'een ba da duk hakan bai faru ba...kusan kullum sai ta tuna lokacin da ya zubar mata da ciki ashe da rabon bazata sake ganin 'kwanta a duniya ba. Hakan ka'dai idan ta tuna shi yafi komai 'kona mata zuciya haka ya dinga sawa ana 'dirka mata allurai ba bisa 'ka'ida ba. Ta kanyi dana sani fin a irga a kullum gashi Allah ya ha'da ta zama da yarinya fitsararriya, duk ta raina ta bata kuma san dalili ba, takan yawaita yi mata habaicin marar haihuwa ko kuma komai a gida sai ta nuna tamkar mallakin 'dan ta ne shi ka'dai, Husnah bata ta6a biye mata ba amma Hisham kansa ya gaji da halin yarinyar. Duk yadda yaso ta bawa Husnah girman ta abin ya faskara..gani take kamar dan ita ta haihu to bazai ta6a iya yi mata abinda ba shine ba. Abin ma ya 'kara nin kuwa ne lokacin da aka sake yi mata gwajin ciki akaro na biyu, 'dan ta na da wata takwas ta 'kara samun wani cikin, iskanci, fi'ili da rainin hankali kuwa sai abinda yayi gaba..shab ta manta da cewa Allah ne ke bada haihuwa ba dabara ko kuma isar mutum ba. Shekaran sa 'daya da wata biyar ta haifi wata yarinyar kyakkyawa da ita mai kama da Hisham sak, yarinyar ne ma Hisham ya so su dam'kata a hannun Husnah amma uwar ta'ki sam, tace bata isa ita da shan bugu gardiya da cin moriya ba. Akan wannan kalmar Hisham har sakin yarinyar yayi dan sosai ta tayar masa da rigima cikin gida, Husnah ce ma ta 'kara tilasta shi ya dawo da ita 'dakin ta..amma zaman ya kasa yiyuwa dan tana yawan ciwa Husnah fuska shi kuma ya kasa jure hakan kwata-kwata...Bambam cin yarinyar da Husnah kenan dan ita Husnah sam ba ta iya hayaniya ba..tun zaman sa da ita bata ta6a yi masa abinda ya sosa zuciya kamar na Ikilimah amaryar sa ba. Daga 'karshe auren ya raba gaba 'daya ta hanyar sauwa'ke mata ya cike sakin uku gaba 'daya dan baya so su sake takura shi akan ya maido da ita...dan fitinan yarinyar duk ya ishesa a gidan sam bata 'kaunar a zauna lafiya da ita ba zai iya kullum yana cikin kwantar da murya yana mata nasiha amma a banza ba. Shi ba me son a 'daga masa hankali bane, zuwan tane duk tasa shi yawan surutai kullum cikin yi mata fa'da yake amma a banza. 'Ya'yan sa duk ya amshe ya bawa Husnah ta kuwa ri'ke su hannu bibbiyu, sosai take kula da su tamkar ita ta haifa, gefe guda kuma tana Addu'ar itama Allah ya ji'kan ta ya bata nata 'dan kafin mutuwar ta, Hisham ne a kullum yake saka mata ran cewa itama da iznin Allah zata haifa masa 'ya'ya hakan yasa itama ta 'dora ranta akan hakan sosai. ***** Safwan ma yaran sa uku ne yanzu dan Hafsat ta sake haifa masa 'yan biyu mace da namiji suna rayuwar cikin kwanciyar hankali da 'kaunar juna. 'Bangaren Sani kuwa aure ya kasa yiwuwa masa 'yan matan garin su duk gudun sa suke yi suna nuna masa 'kyama, hakan yasa ya ha'kura shima kawai ya cigaba da 'yan sana'oin sa yana kulawa da mahaifiyar sa, sam baya ganin laifin su, a hakan ma yana da ya'kinin basu san abinda ya aikata bane da ko kallon arziki bazai samu daga wurin kowa ba. Ya dai riga ya sa aransa cewar duk lokacin da Allah ya nufe shi da yin aure ya kuma azurta shi da samun 'yarsa sai ya sa mata suna Aisha..dan Jasmine bata ta6a barin ransa ba..murmushin ta kullum yana nan zane a allon kansa baya mantawa da ita...Addu'ar sa kullum ga iyayen ta shine Allah ubangiji ya basu madadin ta badan halin mu na yan Adam ba sai dan cikar mulkin sa. ***** Mu'een kam jiki yanzu Alhamdulillahi dan komai yayi sau'ki..watan sa guda a asbitin aka sallame shi wanda kafin hakan sosai idanun sa suka 'kagu da sake son ganin Noor amma shiru shi kuma bai bu'di baki ya tambayi kowa ba, duk da yanzu ya riga ya tabbatar da cewa matsayin miji yake agare ta dagaske amma sam bai nuna za'kewar ba...hakan ma ka'dai idan ya tuna sosai yake jin natsuwa na ratsa shi, yasan Allah ne kawai ya sake bashi wannan damar ba kowa ba, ya kuma yi al'kawarin cika rayuwar Noor da duk wani farin cikin da ta rasa abaya saboda shi. Yanzu babu abinda ke damun sa illah rashin 'karfin jiki da kuma ciwon da yake ji zuciyar sa nayi masa lokaci zuwa lokaci wannan kuwa inda sabo ya riga ya saba da hakan tun da jimawa so baya damun sa sosai. Lokacin da suka koma gida Alhaji Baba sai ya tara su ya nemi shawarar yanda ya kamata ayi da sdkiyar Ammi cos har yau 'din ba'a ta6a komai daga cikin ta ba. Ita Ammi already ma ta sanar da Alhaji cewa ya kakkasa ya warewa kowa nashi kowa yasan kalar sana'ar da zai yi da shi. Koda Alhaji Baba ya sake neman shawarar ta su ma still Ammi abinda ta sake maimaitawa kenan tace bata so abari wuri guda saboda gudun wani ibtila'in kuma duk dama ba za'a yi fatan hakamn b.. ...sauran kam shiru suka yi koda Alhaji Baba ya nemi shawarar Uncle Ja'afar kuwa shi cewa yayi kawai a bu'de gidan mai da shi in yaso abinda ya rage sai asaka jari da shi da izinin Allah babu abinda zai faru. Da jin hakan kowa yayi na'am da wannan shawaran dan haka Alhaji Baba ya fara shirye-shirye. Safwan da iyalan sa musamnan suka zo tun daga Bauchi dukkan su dan duba jikin Mu'een kwanan su biyu kafin suka koma da uban tsarabar da su Ammi suka ha'da su da shi dan ba 'karamin da'di take ji ba idan taga mutane na nunawa yaranta 'kauna, haka ta dinga nan -nan da yaran Safwan musamman 'yan biyun nan tana tunawa da lokacin da ta raini nata itama. 'Bangaren Ishaq ma Alhamdulillah yanzu komai normal yake tafiya masa domin ya sake samun wata matar ma nan cikin Maiduguri ya kuma kawo wa Alhaji Baba invitation 'din auren inda yayi murna da faruwan hakan 'kwarai da gaske fatan samun nasara ya bishi da shi. comment Vote Share *Salmerh ce* 😍💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *93* Satikai da dama suka shu'de har ya kasance yanzu wata guda kacal ya rage wa Noor ta kammala makaranta, yayin da Yah Deen har yanzu ke hutu be koma bakin aikin sa ba. Sosai ya 'kagu ya gansa gaban matar shi amma abu ya gagara gashi ko waya basa yi da ita. Anty ma ke yawan 'kiran sa shima yana 'kiran ta amma ko ta ha'da shi da Noor bata cewa komai..Anty duk bata san hakan ba dan da ta ha'da su take barin wurin ta tafi sabgar ta, shima 'din yanzu ba magana sosai yake yi ba dan haka duk shiru suke yi babu me ce da wani uffan. Sau tari ita ke gajiya ta kashe wayar ko kuma ku'din dake wayar ya 'kare abanza sannan 'kiran ya yanke. Idan yaga haka sai yayi murmushi kawai, wani sa'in yace" Zan kama ki ai yarinya bari kizo hannu na". Barin Shuwarin yayi ranar wata litinin da sunan zashi Abuja duba wurin aikin sa daga nan kuwa daya kammala abinda yake yi sai ya nemi ticket ya wuce malesia ko Anty bata san zai zo ba sai 'kiran ta yayi ya sanar da ita cewa ya shigo. Anty kam mamakin sa ne ya kamata dan bata ta6a zaton zai zo a wannan lokacin ba...bata san cewa ya samu 'karfin jiki har da zai iya doguwar tafiya irin haka ba. Sai bayan ya iso kafin ya 'kira ya sanar da su Ammi yana dariya. Ammi ma dariyar tayi tace" Kaji kunya ai...sai kace wacce bazata dawo ba Mu'een?" 'Yar dariya yayi yana sosa kansa. Ammi sai tace" Antyn ka dawo to itama ta huta wa ranta da yi ma gadin mata tunda ka wanki 'kafa kaje..". Dariya kawai yayi yana cire wayar a kunnan sa yace" Anty kinji Ammi wai ai sai ki koma gida tunda nazo". Murmushi Anty Zee tace. " Dama fa Umrah zamu wuce wai da ita da ta 'kare karatun .." Take ya yatsina fuska gami da fa'din" A a Anty ni dai ban yadda ba kawai kiyi tafiyar ki, bacin ni nawa Jasmine al'kawari da kaina kuma sai ariga ni ki bari kawai zamu biki daga baya...Yau she ma akayi shawaran tafiyar ni ban sani ba, wato da banzo ba sai dai kawai inji kun tafi..ai kuwa ba da ita za'a yi wannan tafiyar ba". " To ai shikenan zan yi magana da Baffan ku inji me ze ce shi kuma, kasan tafiyar daga wajen sa ne..". Zama ya gyara yana duban Anty yace" Kice masa wurin wani likita na nazo kuma sai an yi 2months ana duba ni kafin in koma kar yace taho bada sanin sa ba..kuma kinga idan yaji cewa zan 'dan jima 'kila ya yadda bada Noor za'a Umran ba". Dariya Anty Zee tace " Ba wani ni nan..ni dai bazan yi 'karya haka kawai ba". " Haba my one nd only Aunt dan Allah kiyi ha'kuri..ni ne fa?" " Kai 'din dai". " Anty please ki taimake ni kinsan halin sa fa yanzu sai kiji yace ban gama warkewa ba ina yawo bana son surutai wallahi". " Toh dama me yasa ka tahowa gashi ma ko su Ammi basu san da batun ba". " Ganin matata nazo Anty kuma ma ai na sanar da da su yanzu..". " Amma yaushe zaka koma..?" " Gaskiya ba rana". Idanu Anty ta zaro tana duban sa sai yace" Erh mana...dan nifa gaskiya Anty 'kafa ta 'kafar mata ta haka kawai zama ya'ki 'karewa da banzo bama da shikenan anyi da ni tunda gashi shirin tafiya wata 'kasar ma kuke yi abin ku da Allah ne ka'dai yasan ranar da zan ganku..ni bawan Allah". Ya 'karashe da karkata kansa. " Kai kasa ni ai, dududu wata nawa ne, kayi shekaru biyu ma baka ganta balle watanni biyu kacal?" " Su 'din Anty sai kiga sun fi yi min tsawo..". " Hmm" kawai Anty tace tana murmushi. Noor na school lokacin da ya iso so koda ta dawo ma bata san cewa gidan da ba'ko ba haka kuma Anty ma bata sanar da ita ba...har suka gama zaman su a parlour sai da ta shiga ciki dan kimtsa jikin ta kafin taga jaka a 'dakin ta. Zaro idanu tayi da mamaki ta sake fitowa tace" Anty waye yazo kuma naga ja'ka a 'daki na?" Fuskar Anty Zainab da murmushi tace" Mijin ki"!. Tattare goshi tayi take ta ha'de ranta ta cike da salon shagwa6a tace..." Sai a 'daki na kuma Anty dan Allah?" " Ina kike so ya sau'ka to Noor? 'dakin naki ai shine ya dace da shi". " Anty dama me yasa sai nan gidan zai sau'ka ga kala-kalan hotels meyasa be sau'ka can ba?" " Ki bari idan ya dawo kya tambaye shi..amma ni banda wannan amsar tambayar taki". " Ni dai Anty 'dakin ki zan koma wallahi bazan zauna dashi a 'daki ba". Tayi maganar ne tana juyawa ciki ranta a matu'kar 6ace. Haka Anty na gani ta dinga kwaso kayan ta da duk wani abinda tasan zata bu'kata tana maida shi 'dakin Anty Zainab kamar wata me juju. Anty Zainab kam binta kawai take da kallo tana murmushi cikin ranta ta ayyana" bari kuma in bar muku gidan sai inga inda zaki shiga". Bata tanka ta ba har ta gama kwaso dukkan kayayyakin ta ta mayar 'dakin Anty. Gefen ta tazo ta zauna tana sau'ke numfashin gajiya" Sannu". Anty Zainab ta ce da ita tana 'karewa fuskar ta kallo. Sai tayi murmushi ta kawar da kanta. Ko da ya dawo kuwa bai yi mamakin ganin yanda 'dakin ya 'kara fili ba fiye da 'dazun yasan wannan ka'dan ne ga aikin Noor, be wani damu ba tunda yasan gida guda suke dan ta raba musu 'daki wannan ba zai zama damuwa ba. Bai ga ko idanun ta ba har sai da dare lokacin suna zaune da Anty Zainab suna hira ya shigo. Ha'de rai tayi sosai ita mantawa ma tayi da wani batun sa, da yake baya zama sosai a gidan yau 'in nan ya iso amma fitar sa ta kai sau uku. Gaida Anty Zainab yayi yana zama gami da sau'ke numfashi yace" Wallahi Anty na gaji sosai..abani ruwa". Shima ko kallon inda take be yi ba tunda ya shigo haka kuma itama, kanta 'kasa tana kan harha'do kalaman bakin ta wanda zata gaida shi da su. " Aba ni ruwa Please". Ya sake maimaitawa. " Noor kawo masa ruwa" Anty Zainab ta umarce ta. Tsaye cak ta mi'ke bata ko dubi inda yake ba ta nufi kitchen tana 'kun'kuni..shi kam dama kawai so yake ya ganta da kyau shiyasa ya nemi ruwan dan yasan dole itace zata kawo. Da idanu ya bita har ta lume sannan ya 'dan waigo nan yaga Anty Zainab kanta 'kasa ma ko kula da shi bata yi ba...ita gani take ma kamar zata takura musu gashi gidan ba asake yake ba hakan yasa ta fara tunanin komawa can gida in yaso ta taho Umrar daga can. Dawowa tayi da ruwan ta mi'ka masa wanda yana kar6a ta furta" Ina yini?" Bai amsa ba illa kallon fuskar ta da yake yi ita kuwa sam taki yadda ta ha'da ido da shi. Yana amsan ruwan ta 'dauki wayar ta ta shige ciki. Da shigan ta sai ta bu'de system 'din ta ta fara karatu wai dan kar tunani ya dame ta dan har ga Allah haushin zuwan nan nashi taji sosai..kafin Anty ta shigo kuwa har bacci yayi gaba da ita. Washegari bayan tafiyar ta shima sai ya fita..nan Anty Zainab ta samu daman ganawa da Uncle Ja'afar ya kuma fahimce ta yace nan da jibi ta dawo gida toh. Gadan-gadan ta hau shirin ta Noor da ta fahimci hakan ai sai kuka gashi ita da sauran kusan 10 days ya rage mata kafin ta 'kare exams gaba 'daya, haka har ranar tafiyar Antyn bata nutsu ta kwantar da hankalin ta ba. Tana jin tamkar za'a barta da makashin ta ne agidan. Tun tafiyar Anty kuwa sai ta daina ganin sa sosai domin bata zaman palour, idan ta shiga 'daki kuma datsewa take yi daga ciki. Wataran yini take yi ta kwana ma bata sashi a idanun ta ba, lokaci-lokaci take ganin sa wataran da safe wataran kuwa sai Azahar take ganin sa. Gaisuwa ka'dai ke ha'da su, gaisuwar ma sai ya ga dama yake amsata, domin sama-sama yake amsawa tamkar baya son gaisuwar tata ne. Idan taga haka sai ta yatsina fuskar ta tayi gaba tana ta6e baki. Sam Yah Deen bai takura ta ba musamman da ya san cewa exams take yi a lokacin haka zaman su ya kasance har lokacin da ta 'kare karatun..nan ta fara shiri cuz dama abinda ya ajiye ta kenan. Lokacin da ya fahimci shirin da take yi nan ya dakatar da ita yace babu inda zata je sai ya kammala abinda ya kawo shi kafin su koma tare...dukkan abubuwan amfanin ta ya tattare a wurin sa bata san lokacin ba sai gani tayi kawai babu su..ba ATM 'din babu ticket da su I.D card 'din ta duk ya tattare. Bata son jan magana tsakanin su hakan yasa taja baki tayi shiru bata tanka ba. Wasa-wasa sai da suka shafe sati guda cur amma shiru bata ga alamun yana da niyyan tafiya ba kullum sai dai ya fita yawon sa ya dawo sai aukin kawo mata kayan ciye-ciye tun bata kulawa har ta fara dubawa idan ya kawo sai 'dauki abinda taga zata yi ci ta bar sauran anan..idan taga bai kula ba kuma da kanta zata koma ta canza musu wurin ajiya. Gashi dole ya tilasta mata yin abinci da shi haka badan taso ba take yi ta ajiye masa..sai kuma yazo ma yace baya so tana ajiye masa a parlour ta ringa kai masa ciki. Lokacin da ya gama fa'din hakan ya juya harara ta bankawa bayan sa tana tura baki..sai wani tsatstsare ta yake yi ga uban bada umarni. Yanzu abincin nasa cikin 'daki take ajiye masa kusan kullum ma idan ta 'dauko sai taga ba sosai yake ciki ba amma tasan idan bata kai ba jan maganar zai yi. Watarana da ta kai masa breakfast 'dakin sai ta tarar da shi yana ta nishi da 'kyar yana dafe 'kirji...zuciyan ta tsinkewa yayi sosai bata san lokacin da ajiye abin hannun ta tayi kansa ba, shikuwa dama da yake shirya abinsa yayi jin ta kusa da shi ya sanya shi sake narkewa yana canza salon numfashin sa. Ai tuni ta fara kuka tana ambatan sunan sa a ki'dime. Waje tayi da sauri ta lalu6o wayar ta ta 'kira Ammi tana kuka take gaya mata halin da yake ciki. Ammi ma da jin hakan sai ta rikice take ta fara salallami. Da 'kyar ta kwantar wa Noor hankali ta tsagaita kukan da take yi. Komawa tayi 'dakin nasa nan ta tarar da shi kamar yadda ta barshi...sai di zuwa yanzun numfashin sa ya daidaita amma idanun sa a lumshe suke. Fargaban ta ita bata san yadda zatayi da shi ba koa da da suka yi zaman aure ma bata ta6a yi masa jinya irin haka ba..da muryar kuka tace da" Sannu.. ko na 'kira azo atafi da kai asbiti?" Kai ya girgiza mata a hankali batare da ya bu'de idanun ba, cike da galabaita ya nuna mata inda magungunan sa suke yace ta 'dakko masa. 'Balla masa tayi sannan ta 'dauko cup 'din tea da ta kawo masa sai kuma taga ai a kwance yake. Mayar da cup in tayi ta ajiye sannan ta dawo ta wurin kanshi ta 'dan 'dago shi ka'dan da 'kyar ta iya jingina kan sa da 'kirjin ta ta mi'ka hannu ta 'dago cup 'in ta sanya masa abaki sai da ya 'dan kurba kafin ta bashi maganin ya sha. Ajiye Cup in tayi sannan ta matsa baya a hankali ta fita daga inda take nan ta maida kansan ta kuma kwantarwa a hankali. Sannu ta ringa jera masa shi kuwa ya lumshe idanu sai sau'ke numfashi yake a hankali..ganin yanzu baya fizgan numfashin yasa ta jinjinawa 'karfin magungunan nasa da ingancin su. Shi kam haka yayi luf kamar wani mai ciwo dagaske...da ta juya sai ya faki idanun ta ya 'kyallara ido guda yana murmushi da ya ga zata waigo sai ya komar da idanun ya rufe kamar bashi ba. Sai daya tabbatar ta fita daga 'dakin kafin ya 'dauki wayar sa ya turawa Ammi text akan cewa kar ta wani 'daga hankali zazza6i ne kawai ke damun sa kuma ma ya sau'ka. Yayi hakan ne kasancewar yaji lokacin da take waya a palour kuma yasan da Ammi tayi wayar...gudun kar suma su 'daga hankalin su. Tun daga ranar ita ke 'dawainiya da shi..ita zata kawo masa abinci ta zauna ta dinga bashi abaki wanda ka'dan yake ci ya girgiza mata kai alamar ya ishe shi...kullum hannun sa dafe da 'kirjin sa yana nuna mata alamun yana jin jiki, tayi tayi da shi kuma suje asbiti ya'ki...idan ta 'kira gida ta sanar da su kuma sai dai suce mata" Allah zai kawo sau'ki ta kwantar da hankalin ta" Bata san meyasa yanzu basa damuwa da ciwon nasa ba. Hatta brush ita ke yi masa ta kuma taya shi wanka...bacci ma yanzu wani sa'in a wurin.sa take yi domin idan tazo gayara masa kwanciya hana ta barin jikin sa yake yi dole sai ta kwana kusa da shi..duk ta gaji ta fara fita hayyacin ta har 'yar rama tayi..shi kam fakon idanun ta yake yi lokuta da dama yana yiin murmushin mugunta...ko da wasa be taa kuskuren da zata fahimci cewa ciwon 'karya yake yi ba. Sai in ya tabbatar bata kusa tana kitchen ko kuma 'dakin ta sannan sai ya 'kira su Ammi su sha hirar su lafiya lau, guarantee sun san babu abinda ke damun sa...shiyasa ko Noor ta fa'da musu ba basu wani 'daga hankalin su domin kusan kullum sai sunyi waya da shi. Anty Zainab ce ma taja masa kunne akan rikitar da Noor da yake yai yace " Rabu da ita Anty yarinyar nan ta raina ni da yawa, itama ta ta6a wahalar da na tayi akanta taji abinda ake ji". Kwafa Anty tace" abin ya ishe ni kuwa kasan gaskiya zan gaya mata ko?" " Sorry Anty ki barni da ita dan Allah bata gama yin hankali bane har yanzu...". Daya ji motsin ta sai yayi saurin kife wayar ya koma luf kamar mai bacci. Ko da wasa baya bari taga wani wargi tattare da shi...haka zasu shiga bayi suyi wanka tare tayi masa su fito amma baya ko nuna alamun yaji sha'awar ta ma balle ya kuskurewa shirin sa. Ita kam ta 6angaren ta wani lokacin sosai yakan bata mamaki, sau da dama ta kan lura da shi kamar yana iya yiwa kansa wani abin musamman idan bata kusa, ta kan yawaita tarar da shi ya canza kaya ko kuma ta tarar da shi yana sallah lafiya lau amma da zaran ya idar shikenan zaki ga ya sake narkewa babu abinda zai sake aikatawa matu'kar tana nan. Sai ta fara tunanin ko dai sallar ne ka'dai Allah ke bashi 'karfin yin ta...ita fa duk tausayin sa ya gama cika mata zuciya. Har 'yar rama tayi dan kusan kwanaki goma kenan suna abu 'daya da shi 'karfi da yaji ya sanya ta sabawa da jikin sa da zama kusa da shi badan tana so ba. Da abin yayi yawa kuma sai ta fara lura da wasu abu, domin ko bata yi masa abu ba da kansa ma zaiyi abin sa hakan yasa ta rage damuwa domin ta fahimci kamar sau'ki ya fara zuwa masa ne. Ita dai Addu'ar ta a kullum be wuci Allah ya bashi lafiya su koma gida bane, burin ta kawai kenan shiyasa bata yi masa wasa da shan magungunan sa. Da abin ya ishe ta wata rana agaba ta sa shi ta dinga kuka kamar ranta zai fita domin idan taga kamar sau'ki na samuwa sai kuma ta ga abu ya sake dagulewa. Kanta 'kasa tana ta kuka gwanin ban tausayi, shi kansa dake kwancen tausayin ta ya gama cika shi idan bata kallon sa sai ya bu'de idanu 'kir yana duban ta yana ganin yanda take kukan yana ji kamar ya rungumo ta ya lallashi abin sa amma bai gama hora ta ba tukunna. Sosai taci kukan ta ta gaji gashi Anty Zainab ma kusan kullum ha'kuri take bata tace da ita ta daina damun kanta ai zai warke ne...ita kam zancen Antyn sam baya shiga kanta ma, tana ganin Yah Deen na kwance rai a hannun Allah ta ya hankalin ta zai kwanta...rashin nuna damuwa da suke yi yanzu akan sa ya sanya itama ta rage sanar da su...domin bata ga amfanin hakan ba. Tana cikin kukan taji wayar ta na ruri amma ta kasa 'dagawa. Sai da ta yi missedcall biyu kafin taji ta Yah Deen ma na 'kara...shima 'din har ta gama ringing ba'a 'daga ba dan kwance yake yana jinyar kansa na 'karya.🤪 Akaro na uku nata wayar ya sake 'kara da sauri ta kai hannu ta 'daga ko tsayawa taga waye ma bata yi ba ta rushe da kuka, Ammi ce amma bata kula ba kawai ta fara fa'din" Anty dan Allah ki taimake bansan ya zanyi da shi ba, Anty dan Allah ki dawo wallahi kullum 'kirjin Yayah ciwo yake yi masa ban san yanda zan yi ba, Anty tausayin shi nake ji sosai dan Allah ku taimake ni in samu a kai shi asbiti ni nayi-nayi da shi ko anan ne ma amma ya'ki, idan wani abin ya faru da shi ban san yanda zan yi ba...". Tashi tayi ta fita ta koma palour wai dan kar ta dame shi...Still da wayar a kunnen ta tana me cigaba da ro'kon Anty. Ammi kam shiru tayi sai da ta gama jin abinda Noor 'din ke fa'di kafin ta 'kira sunan ta da raunin murya...dan duk jikin ta yayi sanyi da jin abinda Noor 'din ta fa'da. Noor na jin muryar Ammi cikin wayar sai kukan ta ya 'karu tana yi tana kai 'dayan hannun ta saman la66anta tana rufe bakin da shi..hawaye duk sun wanke mata fuskar ta tas. Shi kansa Yah Deen tun fitar ta ya tashi zaune, daga inda yake yana iya jiyo duk maganganun ta yasan kuma duk saboda shine take kukan bai ta6a jin tausayin ta irin na yau ba, ya riga ya sanyawa ransa cewar daga yau wasan nasu zai 'kare ba zai sake wahalar da ita ba. Tambayar ta Ammi tayi abinda ke damun sa nan ta fara fa'da mata tana kuka tace" Ammi dan Allah kar kice min bakya son shi yanzu kullum idan na gaya muku bakwa nuna damuwa a kansa Ammi 'dan ki ne fa shi, kin manta wancan lokacin da na ga kin damu akan sa..Ammi yanzun ma fa ko motsi baya iyawa da kyau...baya iya yiwa kansa komai me yasa bazaku tausaya masa ba....?". Da 'kyar Ammi ta lallashe ta tayi ta yi shiru da fa'din ta kwantar da hankalin ta za'a san abinyi..ba wai son shi ne suka daina ba.. ita dai Ammi tasan babu abinda ke damun sa amma ta rasa dalilin da yasa Mu'een yake wahalar mata yarinya. Murmushi yayi bayan gama.jin abinda ta fa'di yanzun ga Ammi..hannun sa yake 'dan mammatsawa yana murmushi, shi kansa fa ya gaji da kwanciyar nan kawai 'karfin hali yake yi...ba'a jima ba sai yaji wayar sa ta 'dauki 'kara. Hannu ya kai ya 'dago wayar sai ya saki wani sabon murmushin ganin sunan Ammi..gyara muryar sa yayi tarwai sannan yayi mata sallama daka ji muryar sa zaka san lafiya cikakka gare shi ba wani alamun jinya tattare da shi, abinda yasa kullum Ammi bata damuwa kenan domin haka kullum take jin sa idan suna waya da shi. A lokacin Noor ta tsagaita da kukan ta illah ajiyan numfashi dan haka itama taji 'karan wayar tasa. Tana amsa sallamar yace" Ammi na..!" " Kayi min shiru! me ke damun ka tell me?" " Ni bakomai Ammi". Ya bata amsa yana murmushi. " Yanzun nan fa matar ka ke ce min ko motsi baka iyawa shine nake jin muryar ka haka nd u ar still telling me bakomai...wai meke faruwa ne dan Allah Mu'een?" " Lafiya ta qalau Ammi..kawai fa wasa nake yi mata". " Baka da hankali!.." " Thank u Madame" Ya bata amsa yana murmushi. Tace " Idan ka sake rikita min yarinya Allah ni da kai Mu'een zaka zo ka same ni ne" Yana 'yar dariya yace " Sorry Ammi..yarinyar taki ne bata ji shiyasa" " Haka ma kace ko to wallahi ka yadda ta sake 'kira na kan hakan ka gani..kasan hali naai ba sai na sake gaya ma ba, this time around idan na dawo da ita gaba na har abada tsakanin ka da ita sai dai hange..ai kasan wace ni". " Ai kuwa da mutuwa zan yi Ammi...itace bugun numfashi na fa..". " Ka gwada ka gani kana wasa da ni ne..." Dariya sosai yayi sannan yace " Kiyi ha'kuri Ammi insha Allahu baza'a sake ba...daga yau na daina". Noor dake parlour jin muryar sa yana waya garau ya sanya ta tahowa da sauri dan ta ganewa idanun ta shin kunnuwan ta 'karya suke yi mata ko kuwa dagske shi 'dinne har da dariya. Zaune ta hange shi kunnan sa ma'kale da waya yana dariya. Mutuwar tsaye tayi tana duban sa da tsananin mamaki take cigaba da sauraran surutun da yake yi. Mutum da ko hannun sa ma baya iya 'dagawa shine kuma yanzu take gani zaune har yake wannan uban surutun? Comment Vote Share *Salmerh ce* 😍 💕 *NOORUL* 💕 (Haske nah) By *Salmerh MD* *Wattpad @* *Serlmerh-md* 💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION* 💫 We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all..... *DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* _*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_ *Last Page* 💯 *Bismillahir* *Rahmanir Raheem* 🅿 *94* Mamaki 'karara ya bayyana kan fuskar ta, sai ta rasa shin kuka zata yi ne ko kuma dariya...yana cire wayan daga kunnan sa suka ha'da idanu da ita. Murmushi kawai yayi gami da cire duvet daga saman jikin sa ya tashi ya nufi bayi tsab kamar bashi babu wani dafe 'kirji da ri'ke bango bai ko sake kallon inda take ba ma. Tana ganin ya shige bathroom da kansa taji wani 'kululun takaici ya kamata ashe dama lafiyar sa 'kalau shine yake ta wahal da ita. Komawa tayi jikin window ta dafe 'karfen windown tana hawaye..babu tunanin da bai zo ranta ba, sam ta rasa dalilin da yasa yayi mata hakan. Fitowar sa daga bayin sai yaga bata inda take tsaye..bai tsaya ba sai ya bi bayan ta inda ya hango ta jikin window tana kuka mayafin dake kanta ya 'dan zamo yana iya hango tsefaffen gashin kanta dake nan 'daure cikin ribbom guda. A hankali.ya tako zuwa inda take ya matso daf da ita da kansa yasan be kyauta mata ba dan wahala sosai ya bata ya ringa yi mata wasa da hankali. .. ..kusa da kanta ya kawo fuskar sa yana sha'kan 'kamshin da kanta ke fitar wa...a hankli ya maida idanun sa ya lumshe tare da matsawa jikin ta sosai. Tana jin motsin sa kusa da ita kawai sai ta juya gami da sar'ke hannun ta a wuyan sa bai wani 6ata lokaci ba ya ha'de musu baki ya fara kissing 'din ta irin wanda ta manta a rayuwar ta cewa ana yin irin sa...lumshe idanu tayi tana kar6an sa'kon nasa gami da jin zuciyar ta wasai musamman da yake yanzu ta fahimci cewa mijin ta lafiya 'kalau yake babu abinda ke damun sa. Tsawon lokaci kafin ya rabu da ita wanda kamar jira take kuma sai tayi saurin juya masa baya tana fuskantar windown. Murmushi mai 'kayatarwa yayi gami da kai hannun sa gefen wuyan yana yi mata tafiyar tsutsa yace" What kuma?...bayan kin gama cinye min baki shine kuma zaki juya min baya?" Ya 'karasa maganar da sau'kar da kansa saman wuyan ta. Kafa'da ta no'ke tana lumshe idanu amma bata ce da shi komai ba. Abubuwan da taji yana fa'dawa Ammi cikin waya sune suke dawowa 'kwa'kwalwar ta...murmushi tayi tana jin 'kaunar mijin ta na ratsa mata zuciya. Ganin baza ta juyo ba ya sanya shi cire hannun sa daga jikin ta ya 'dan matsa baya ka'dan yana murmushi...'kirjin sa ya dafe gami da fa'din" Wash..!" Ai da sauri ta waigo tana zare idanu har ta ma manta da cewa ciwon 'karya yake yi. Da ganin ta juyo 'din sai ya tuntsire dariya yana nuna ta...kicin-kicin tayi da fuska tamkar zatayi kuka.." Ba gashi kin juyo ba yanzu ai na gano maganin masu taurin kai cikin sau'ki". Shagwa6e fuska tayi ta taho da sauri zata gifta gefen sa ta wuce sai yayi saurin kamo hannun ta fa'da jikin sa ya rungume ta. Dukkan su ajiyan zuciya suka sau'ke mai cike da ma'anoni da dama. ***** Cikin lokaci 'kan'kani suka daidaita zaman auren su har ma sun fara shirye-shiryen komawa gida inda Deen yace da zarar sun koma zasu wuce Umrah dan cika burin Jasmine 'din su kamar yadda yayi al'kawari. Yanayin 'kaunar da yake nuna mata ita kanta yanzu tasan ba irin na baya bane...sannan ko ita kanta ma bata yadda ta sake yin wani sakaci kamar yadda ta aikata abaya ba. Sosai ta ri'ke mijin ta hannu bibbiyu ta jashi a jiki. Sam yanzu bata kuskuren hana shi hakkin sa dake kanta dan ta fahimci ko abubuwan da suka ta faruwa abaya ma ciki harda laifukan ta. Darasin rayuwa kala-kala yanzu ta koya. Wani sa'in har ji take kamar yanzu ne suka yi sabon aure da shi domin sai yanzun ne suka yi sha'kuwar da ya kamata ace sun yi ta tun a baya amma sai suka kasa fahimtar junan su wancan lokacin. Ko lokacin da suka koma gida ma ba 'karamin farin ciki Ammi tayi da ganin su ba, jikin Deen ya 'dan koma sai dai har yanzun ba kamar baya can da yake rayuwar sa cikin farin ciki ba. Sai dai da yake har yanzun bai daina kar6ar magunguna ba ya sanya basu wani damu ba domin sun san with time komai zai daidaita ne, balle ma sun san yanzu ya riga ya samu abinda yake so in ba wani ikon Allah kam tafiya mai nisa ciwon zai yi. Yana zuwa kuma ana sake duba shi a duk lokacin da bu'katar hakan ta taso...sannan baya sa6a dokar shan maganin sa bisa 'ka'ida yake shan su, da ya 'dan kuskure lokaci ma Noor zata tunatar da shi. Ummah kanta ji tayi kamar ta goya su saboda farin ciki sai dai kunya bai barta ta bayyana hakan a fili ba...Albarka ta ringa sa musu tana yi musu fatan Alkhairi cikin rayuwar su da samun zuri'a 'dayyiba. Satin su biyu da dawowa suka wuce Umrah...Yah Deen da ya gansa gaban ka'abah sosai jikin sa yayi sanyi...Noor kuwa kasa jurewa tayi sai da ta zubda hawaye, bata ta6a manta kalaman Jasmine da kuma burin ta na son zuwa Makkah da Madinah taga 'dakin Allah ba, yau gashi Allah ya nufe su da zuwa amma babu ita. Addu'ah sosai suka yi kafin su dawo...ko a Madinah sai da suka 6ata lokaci sosai dan kusan satin su uku kafin suka juyo gida. Ginin da ake yi na gidan mai 'din Ammi ma ba'a jima da kammala shi ba... *T. Manga and sons* aka sanya wa gidan man. ...Ishaq Alhaji Baba ya 'dora matsayin manager na gidan mai 'din dama a kullum burin sa bai wuce yaga yayi wa Ishaq wani abin da zai taimaki rayuwar sa ba domin yanda Ishaq ke son zuri'ar sa ka'dai ya sa yake birge shi balle tuni ya koma yi masa kallon 'da kamar su Muhammad, har cikin zuciyar sa yake jin sa. Sosai Ishaq ya nuna tsantsan farin cikin sa da wannan karramawa da Alhaji yayi masa dama aikin da yake yi ba wani ku'din kirki ake biyan sa ba 40k ne duk 'karshen wata ake bashi, sai ga shi tashin farko matsayin manager ya fito inda za'a biya shi maku'dan ku'dade...amfanin zama da mutane masu karamci kenan. Hatta Sani da ke can jihar Plateau Alhaji Baba sai da ya nemo shi shima ya bashi aiki agidan man, cikin sa'a kuwa albarkar Allah tuni ta sau'ka akan sa...sosai suke samun 'karuwa abin ba'a cewa komai. Saif ma anan yake aiki sai dai bai kai Ishaq matsayi ba Sani kuwa dama dake be yi wani karatun kirki ba a matsa mai kawai ya tsaya...Zaidu kuwa na can wurin Uncle Ja'afar shima a shekarar nan yayi retire daga aikin sa sai dai babu ranar dawowa gida, dan kuwa acan ya samawa Zaidu aiki shima a wani bankin daban mai suna Gt ba wanda yayi nasa aikin ba. Tuni anyi bikin Ishaq ya tare da amaryar sa anan Azare, nuna mata matsayin da gidan Alhaji Taheer Manga ke da shi a wurin sa yayi koda wasa baya nuna mata wani bambamcin da zai sa taji ta raina wani daga cikin familyn, matsayin iyaye ya basu ita ma kuma kan hakan ya 'dora ta. Imrana kam na can tun da 'yan drugs suka tafi da shi ba'a sake jin 'duriyar sa ba...ashe wai sai da 'kwayoyi yake yi da manyan abubuwan maye shiyasa har yanzun ba'a sake shi ba. Mu'een duk ya manta da shi sai ranar yana wucewa ya hango wasu 'yan shaye-shaye shine Imrana ya fa'do ransa da yake ya jima da sanin cewa inda Imrana yafi kauri kenan amma duk da hakan yake abota da shi da kansa ya sha bashi ku'da'de yana zuwa yana sayen kayan mayen sa da shi, tun lokacin da suka zo gidan sa ne shikenan yaji ya fita ransa bai kuma neman sa ko shiga harkar sa ba. Sake kallon su yayi sai ya girgiza kansa, yara 'kanana ne amma duk sun lalata rayuwar su da shaye-shaye. Cikin zuciyar sa ya furta Allah ya sauwa'ka ya shirya mu baki 'daya...Allah ya baku baki amma 'karfi da yaji kun maida shi salansa kuna ta 'karawa duniya hazo...manyan ku ma basu ci nasara ba balle ku... *_Allah Ubangiji ka raba mu da aikin dana sani da mu da Zuri'ar mu da ma Al'ummar Musulmai baki 'daya_ .* Anan gidan man Sani ya samu wata me sai da goro suka daidaita ta kuma amince da shi duk da yake tasan yana da matsalar hannu 'daya amma bata 'ki shi kamar yadda 'yan can garin su suka guje shi ba. Sai dai bai tashi sanin wace ya aura ba sai bayan auren nasu nan ya fahimci sauran gardawan ya kwasa...bai ce da ita komai ba domin yasan duk cikin hukuncin sa ne da Allah ya tanadar masa badan hakan ba ba zai ta6a ha'da shi da ita ba balle har yaji tayi masa cikin zuciya. Yasan alhakin Jasmine bazai ta6a barin sa ba, kuma da yake yasan ba'a yiwa Allah wayo shiyasa be wani damu kansa ba domin yasan komai na tafiya ne bisa tsarin mahalicci, koda yace zai rabu da ita be kuma san wace kala zai sake karo da ita ba...hakan yasa dole ya watsar da komai ya ja matar sa ajiki suka yi zaman su lafiya lau dan biyayya ne da ita sosai. *_Allah ka raba mu da kusantar Zina balle har mu aikata shi_* Kusan lokaci guda matar Ishaq da matar Sani suka sau'ka dan tsakanin su bai fi 3weeks ba...Matar Ishaq ce ta fara haihuwa inda ta haifi 'yar ta mace mai kyan gaske...sunan Ammi Ishaq ya sanyawa Babyn inda suke 'kiran ta da Nana. Matar Sani ma mace ta haifa shima kuma ya sanyawa Babyn sa suna Aisha amma bai sanar da kowa sunan da ya sanya ba, kunya yake ji ya furta cewa sunan Jasmine ya sanya, hakan yasa ya bar abin sa aran sa shika'dai...Baby ake ce da yarinyar Sani. Noor ce dai shiru har yanzu..Deen tuni ya koma bakin aikin sa shima sun koma Abujan gaba 'daya da zama..zaman su suke mai cike da so da 'kaunar juna basu yadda su 6ata lokaci wajen tuno abinda ya riga ya wuce musu. Husnah sai da ta shekara goma da aure kafin a shekarar Allah ya nufe ta da samun ciki, murna kamar zata ha'diye kanta, Hisham ma kamar ya goya ta, Husnah kam banda godiya ga Allah babu abinda take yi ga yaran Hisham duk sun yi wayo suna makaranta...Mummyn ta tafi kowa farin ciki dan abinda ta jima tana jira ne yau Allah ya bata, daga Husnah bata da kowa sai yanzu da Allah ya nufe ta da samun rabo...itama yanzu da'di take ji zata zama kaka na asali. Koda lokacin haihuwa tayi sai ta sam6alo 'danta namiji 'katoto da shi. Sunan mahaifin ta aka sanya wato Hamza amma Daddy suke 'kiran sa...Husnah sau da dama agaba take sa yaron tayi ta kallo tana murmushi. *Ashe in da rai da rabo...Bai kamata 'dan Adam ya cire rai da rahamar Allah ba.* ***** Zaune yake yayin da Noor ke kwance tayi matashi da 'kafar sa...yanzun nan ya gama cire waya a kunnan sa Anas ya 'kira shi da Albishir 'din matar sa ta haifa masa Baby girl karo na biyu...da farin ciki ya sa albarka gami da fa'din sai munzo suna yana dariya ya cire wayar a kunnan sa. Duban ta yayi ta wani lumshe idanu...sai ya kai hannu jikin ta a 'ko'karin sa na son 'dago ta amma ta sake narkewa..." Tashi mana albishir zan yi miki fa..?" " Na riga naji ai..Allah ya raya mana ita.." Ta bashi amsa da idanun ta a lumshe. " To tashi muyi magana please...nifa na fara 'kosawa...3yrs fa yanzu da dawowar ki amma shiru har yanzu..gaskiya dole ne na duba ki in san abinda ke faruwa...". " Ni dai a a...". " Ni kuma nace Erh...so nake nima na fara raino...kin ganin yarinyar Ishaq har ta fara 'kiran Daddy fa..gaskiya da sake dole in san abin yi...". Har yanzun idanun ta a lumshe tace" Ka kar6o mana aron ta kawai mu zauna da ita shikenan ka samu abin rainon ka...ni kaga dama ba so nake in sake haihuwa ba..". 'Bata rai yayi nan take..da 6acin rai yace" Baki da hankali...". " Dagaske ban so ni". " Nuree ban son shirme..." Zatayi magana yayi saurin dakatar da ita. 'Karfi yasa ya 'dago ta zaune sai gata daf da dashi sosai, ta firgita ma she thought marin ta zai yi sai kuma taji shiru hannun sa taji yakai 'kasan marar ta yana yawo da shi wanda hakan yasa tayi saurin bu'de idanun ta ta sau'ke su akan fuskar sa. Murmushi taga yana yi memakon 6acin rai da taji cikin muryar sa, da mamaki sai tsaya duban sa..bakin sa ya sau'ke saman la66an ta ya sumbata gami da matsa marar tata da 'dan 'karfi sai ta saki 'kara. A kunne ya ra'da mata" Naki albishir 'din kenan...". " Me hakan ke nufi wai?" Ta tambayi kanta mamaki 'karara kan fuskar ta...hannun ta ta kai kan nasa itama ta shafo cikin sai yace mata" Kinga ikon Allah ko..dama mugunta kike so kiyi min baki san Allah na so na ba...ba tun yau na fahimci kina 'dauke da ciki ba kawai gudun ruwan ki nake son gani dan naga alamar baki da mu da rashin cikin ba ke ashe ban sani ba dagaske baki 'kauna ta..". Shiru tayi tana jin tsananin fargaba na kamata, ita fa ba wai bata son haihuwa bane kawai tsoro take ji kar labari ya sake maimaita kansa akan abinda zata kuma haifa, shiyasa ta tilastawa kanta ha'kura da haihuwa gaba 'daya. Allah ma sai ya dubi zuciyar ta ya ja mata lokaci har cikin eanta take jin ta ha'kura da haihuwa indai zasu yi rayuwar su a hakan dashi bazata ta6a damuwa ba koda kuwa basu da 'da ko 'ya agaban su har abada..shiyasa tun yanzu take jin tausayin abinda ke cikin cikin ta. Hawaye ne da bata shirya musu ba taji sun gangaro saman kuncin ta..Yah Deen kam tsayawa kallon ta ma yayi sosai take bashi mamaki. Wasa-wasa Noor sosai ta 'daga hankalin ta akan cikin duk ta tashi hankalin ta ta hana shi natsuwa, sosai yake kwantar da murya ya mata nasihar amma abanza, tsakanin ta da Allah take nuna rashin son cikin, har sai ma ya rasa yadda zai yi da ita. Ya fahimci so take ta rabu da cikin cikin ko wani irin hali, sai da ya fito a Mu'een 'din sa ya nuna mata cewa hauka zai mata idan ta kuskura ta salwantar masa da cikin sa...kafin ta 'dan rage haukan da take yi. Amma kullum tana cikin kuka, tunda labarin cikin ya bayyana mata basu 'kara walwala a gidan ba. Daga 'karshe sai da batun ya kaisu har wajen iyayen su, da 'kyar Noor ta ha'kura akan zata haifi cikin bayan Anty tayi mata nasiha sosai da al'kawarin da ta haifa zata 'dauke a wurin ta...misalai da dama Antyn ta bata inda tace" Ni kaina ma babban misali nake Noor idan kin bada hankali, rana guda aka 'daura auren mu da Ammin ku amma Allah cikin ikon sa har yau bai ta6a bani haihuwa ba, nayi kuka munyi Addu'ah 'karshe dole muka ha'kura muka fawwala Allah komai, yanzu haka na riga na cire raina da samun rabo shiyasa kika ga ina ruyuwa ta cike da walwala domin ban isa in ce da Allah miye dalili ba....amma ke gashi kin samu cikin sau'ki amma kina wasa da damar ki ta hanyar ki maidawa Allah babban kyautar da yayi miki, a kaf 'din rayuwa babu abinda yakai kyautar 'da da kuma lafiya da Allah yake yi mana domin duk dukiyar ka baka isa ka siya ba har sai yaga dama, godiya ya kamata kiyi baki nuna ba fushin ki ba Noor. Banda kuka babu abinda Noor ke yi dan a ganin ta har yanzu basu fahimce ta bane shiyasa, ita da kanta tana son taga 'ya'yan ta amma bazata juri ganin ba'ka'ken ta6o ajikin su saboda uban su ba shiyasa ta ha'kura kawai, hala sun manta da abinda ya faru da Baby ne. Ganin ta kasa kwantar da hankalin ta ne ya sanya Ammi ta hana ta komawa Abujan ta zauna da ita tana bata kulawar da ta dace...shi kansa ma hakan yafi masa dan 'daga masa hankali take yi idan tana kusa da shi. Kwanaki na ta tafiya cikin Noor na sake girma, sai dai zuwa yanzun Alhamdulillah ta kwantar da hankalin ta sosai saboda yawan nasihar da ake yi mata, ita kanta yanzu tasan cewa kuskure ta aikata domin kuwa duk abinda Allah ya tsara kai baka isa ka canza shi ba, wayon ta bai isa ya kawar da shirin Allah ba matu'kar ya riga yace sai ya faru. Bayan wata tara da 'yan satikai ta haifo yaranta kyawawa guda biyu mace da namiji...inda yaron yaci sunan Alhaji Baba amma ana 'kiran sa da _Affan_ macen kuma sunan Anty Zainab aka sanya mata se ake 'kiran ta da suna _Farrah_ . Tunda ta haife su kuma saj taji 'kaunar abinta ya sake kamata, haka ta cigaba da rainon abinta bata 'kara nuna musu 'kyama ba Addu'ar ta ayanzu kawai shine Allah ubangiji ya raya mata su ya kuma basu kariya a duk inda suke... ***** _Bayan shekaru biyu_ Tsaye take a kitchen da tu'ke'ken cikin ta hannun ta wu'ka ne tana slizing green beans a hankali dan kar ta kuskure. Gidan shiru cuz yaranta duk basu nan, Affan na can wurin Ammi yayin da Farrah aka yi can gaba da ita wurin Anty Zainab tuni an tattara mata kayan ta can, hakan yasa banda 'karar T.v dake aiki a parlour baka jin komai sai ko kuma idan kayo hanyar kitchen kaji kwarabniyar da take yi. Tana daga kitchen 'din tajiyo muryar sa yana 'kiran sunan ta kamar wanda akace masa bata gidan ne. " *Nureen-Deen* !" Ya sake anbata a karo na uku. Noor bata amsa ba illah murmushin da take yi daga inda take tsaye tana mai cigaba da aikin ta. Yanzun fa ya fita zuwa masallaci kuma yasan aiki take a kitchen amma yake ta fama 'kwala 'kiran sunan ta. Kitchen 'din ya nufo sai ya tsaya daga bakin 'kofa ya wani kama kunkumi..gira ya 'dage da alamun 'kosawa yace" Ya ina ta 'kiran Nureen-Deen amma bata amsa ni ba?" Tana murmushi ta bashi amsa da fa'din" May be bata ji ka ba ne shiyasa ". Tayi maganar ne batare da ta waigo ta dube shi ba. Gaba tayi zuwa wajen sink tana wanke hannu yayin da ya 'karaso ta bayan ta ya sarke hannuwan sa a wuyan ta yana sau'ke numfashi. " *_Nuree na_* "! Ya ra'da mata a kunne gami da sumbatar bayan wuyan ta. Fuskar ta 'dauke da murmushi ta sake fa'din" _Ni ban ji ba_ ". " *Hasken Deen* ". Ya 'kara fa'da yana mai gangarawa da hannun sa zuwa saman cikin ta. " _Har yanzun ni banji ba_ ". Ta sake fa'da tana mai 'ko'karin kwatan kanta daga jikin sa tayi gaba zuwa gaban Gasscooker ta sa hannu tana juya ha'din kayan miya da take soyawa...fuskar ta cike da murmushi. Sosai ya sake matso ta ya rungume ta a jikin sa ta baya tsam sannan ya sake ra'da mata" *Ciwon zuciyar Deen* ". Cikin kunne. Wannan karan dariya ya bata sosai ai kuwa tana fara dariyar shima ya taya ta yana jan baya yace" Ai gaskiya ne...." *Nuree na itace ciwon zuciya ta...*". Kai ta girgiza masa sannan ta cigaba da abinda take yi murmushi ya kasa bariñ fuskar ta. _They live happily ever after....._ *_Tammat bi hamdil-lah_* *Me na manta?* 🤔 *Idan ma akwai kuma kuka tuna to ku jefa shi nan inda ya dace da shi...sai kuma ayi min afuwa domin ba laifi na bane laifin Brain 'dina ne* 🤗 *Alhamdulillah!!!...*🖊️ _Anan na kawo 'karshen wannan labari mai suna *NOORUL (Haske nah)...* wannan duk abubuwan dake cikin sa yake 'kir'kira ta ce ba da sunan wani ko wata nayi shi bs, in ma yayi kama da labarin ki/ka ayi min afuwa kuskuren al'kalami na ne bada niyya na aikata ba, ina ro'kon Allah ya yafe min dukkan kura-kuran dake cikin sa ya kuma sa a fahimci sa'kon da labarin ya 'kunsa...(Ameeen Yah Allah)_ _Duk Abinda aka tsinta ciki na kuskure kuma ayi min afuwa ba dan ni ba, duk abinda be yi miki ko maka cikin labarin ba shima dan Allah a watsar da shi kawai kunsan 'dan Adam Ajizi ne ba lallai ne in iya farantawa kowa dake bin labarin ba._ _Masoya na dake wattpad da whatsapp ina gaisuwa ina kuma mi'ka 'dumbin godiya ta, bazan iya lissafo sunayen ku anan ba amma ku sani wallahi ina 'kaunar ku irin unlimited 'din nan._ _Musamman 'yan group 'din_ *DA BAZARMU WRITTERS ASSOCITAION.* *SALMERH MD PALACE.* *NOORUL FANS GROUP* *UNIQUE ONLINE HAUSA NOVELS* _....Alherin Allah ya cimmaku a duk inda kuke 'yan uwa na...Allah ya kare ku daga sharrin CORONA, cututtukan zamani da ma dukkan wani abin 'ki._ 🙏 ~*Salmern ku nayi muku fatan Alkhairi*~ 😍 _Sai wani lokacin kuma idan Allah ya kaimu in ma zan iya kenan kun san sai a hankali rubutun ba sauqi wahala yake bani sosai_.🤗 🔚🔚🔚🔚🔚 *Taku har kullum Miss Salmerh MD*. ©️ *2020*