MATSATSUBI 2 Lokacin da su Jafar suka fada cikin shafi na goma sha shida KUNDIN TSATSUBA, wato bayan iskar cikin KUNDIN ta zuƙe su, sai suka tsinci kansu a cikin sararin samaniyar wata sabuwar duniyar, kuma a ƙudundune cikin wata irin gagarumar guguwa mai tsananin ƙarfi. Saboda ƙarfin guguwar sai da ya zamana cewa ta tale hannayensu da ƙafafuwansu. Gashin kansu ya tsefe sama kamar taron tsintsiya. Idanuwansu suka gwale, ƙofofin hancinsu da bakunansu suka ƙara girma, banda ihun azaba babu abinda suke yi. Kwatsam sai suka ga wata surar fuskar bil'adama a samansu wacce ta saje da kalar gajimare. Bakin surar ya wangame yana mai ƙyaƙyata musu dariya. Al'amarin da ya ƙara jefa su cikin razana da fargaba kenan. Mazalish ta fara ƙoƙarin haɗe hannayenta biyu waje guda don tayi tsafi, amma sai abu ya gagara, domin ta kasa haɗe hannayen nata, saboda tsananin ƙarfin guguwar. Fuskar ta sake wangame baki a karo na biyu ta ɓarke da mahaukaciyar dariya mai tsananin firgitarwa, sannan ta ce, "Nice GUGUWAR MASIFA, kuma nice GUGUWAR BALA'I, duk wanda ya ziyarceni sai na kai shi cikin mahallaka dubu. Kaicon ku waɗannan baƙi masu karambani, yau za ku san cewa karambaninku ya janyo kun tsokano tsuliyar tashin hankali irin wanda baku taɓa gani ba,kuma ba ku taɓa jiba." Kafin wani daga cikin su Jafar ya iya buɗe bakinsa yace wani abu tuni wannan fuska ta bi jikin guguwar sun zama iri daya. Kawai sai Guguwar ta kanannaɗe su ta riƙe to da su ƙasa, daga sararin samaniya, cikin tsananin gudu saida suka zo tsakiyar wata ƙatuwar teku, sannan Guguwar nan ta saki su Jafar ta ɓace. Koda Jafar, Yelisa, Gulzum, Mashrila da Mazalish suka ga an sake su za su faɗa cikin tsakiyar teku mai tsananin girma da faɗin da ba'a iya ganin ƙarshen tsawonta da faɗin ta sai duk suka rafka ihu. Kafin su tsunduma cikin tekun sai wani ƙaton, jibgegen kifi ya wangame bakinsa suka faɗa ciki. Kawai sai kifin ya rufe bakinsa ya yi nutso izuwa ƙarƙashin ruwa ya ci gaba da tafiya abinsa. Lokacin da su Jafar suka faɗa cikin bakin kifi suka biyo ta cikin maƙogwaronsa, sannan suka ratsa ta cikin hanji, tuni gaba ɗayansu sun fita daga hayyacinsu, basu isa cikin kifin ba sai bayan tafiyar daƙiƙa ɗari uku da arba'in. A matuƙar galaɓaice suka faɗo ƙasan cikin kifin suka zube shararaf kamar tulin tsummokara, da ƙyar suka miƙe zaune sannan suka fara kalle-kalle cikin firgici da mamaki. Jafar ya ƙare nazarin kayan cikin kifin tsaf sannan ya ce, "Yau kuma a tsakiyar shuke-shuken teku aka watsomu, yanzu ta ya ya zamu iya fita daga wajen nan nikam banga alamar akwai wata hanya ba." Koda jin wannan batu sai aljani Gulzum ya bushe da dariyar ƙarfin hali sannan ya ce, "Amma dai ka cika daƙiƙi kuma kidahumi(lallai ma Gulzum anyi ɗan iska😂😂😂ku ji pah,wai Jafar mutumin nawa yake kira daƙiƙi🙄🙄🙄,toh in akwai daƙiƙi a cikin su ai bai wuce Gulzum ba,ko ya kuka ce😂😂), wa ya gaya maka cewa nan acikin shuke-shuken ƙarƙashin ruwa muke? To ka duba da kyau ka gani. Nan a cikin cikin kifi muke, tabbas rayuwarmu na cikin mugun hali domin ko zafin dake cikin kifin nan bai kashemu to kuwa yunwa da ƙishirwa sa kashemu, nan da kwanaki da baza su gaza biyu ba." Koda jin wannan batu sai gaba ɗayansu hankalinsu ya dugunzuma kowa ya rasa abin da ke masa dadi. Daga can sai Yelisa ta dubi Mazalish ta ce, "Wai ke ina taƙamarki ta tsafi take? Me yasa baza ki cece mu ba daga cikin wannan masifar da muke ciki?" Mazalish ta ce, "Ai kin san cewa gaba da gabanta ko? Inda tsafina zai iya cetonmu da tun kafin guguwar nan ta jefomu cikin tekun zamu kuɓuta." Jafar ya mike tsaye ya duba gaba da baya ya jinjina kai ya ce, "Kai amma fa Ubangijin da ya halicci wannan kifi ya cika abin tsoro, ku duba fa ku gani sam-sam ban iya hango ƙarshensa. Wai shin yanzu mene ne abin yi?" Mashirila ta miƙe tsaye daf da Jafar suka fuskanci juna sannan ta ce, "Ni ina ganin babu abinyi face muje ƙarshen bindin kifin nan baza mu kasa riskar ƙofar da yake fitar da abin da ya ci ba, sai mu fita ta wajen." Gaba ɗayansu suka yarda da wannan shawara don haka sai suka kama tafiya acikin cikin kifin suka nufi inda jelar kifin take a sahu guda. Gulzum ne akan gaba sannan Jafar, Mazalish,Yelisa da Mashrila, sai da suka yi tafiyar sa'a guda sannan suka iso bindin kifin inda suka ga ƙofar da suke nema, nan take Gulzum ya zura kansa ta cikin ƙofar da niyyar fita. Koda kifin ya ji wani irin raɗaɗi a bindinsa sai ya yi ta juyi yana mai ƙaraji. Gaba ɗayansu suka rikito suka hau tsinawa a cikin kifin, a haka suka yi ta ƙoƙarin fita amma abu ya gagara. Ƙoƙarin nasu ne ya gigita kifin yai ta juye-juye har ma ya fita da gudu sai daya iso gaɓar tekun sannan ya yi kakarin amai ya amayar da su gaba ɗaya don ya huta da azabar abin da ke kartarsa aciki, ai kuwa yana gama amayar da su ne ya koma cikin tekun ya nutse, kafin daya daga cikinsu ya sake dawowa haiyacinsa tuni guguwar nan tazo ta kanannaɗesu tayi sama da su tana mai ƙyalƙyala dariyar mugunta. Guguwar ta ci gaba da gudu ɗauke da su Jafar a sararin samaniya har tsawon lokaci sannan ta sauko ƙasa ta watsar da su a tsakiyar wani makeken jeji. Jeji ne mai yawan bishiyoyi, duwatsu, tsaunika da ƙoramai abin gwanin sha'awa sai wanda ya gani. Koda su Jafar suka tsinci kansu a wannan wuri sai suka cika da farin ciki don tsammanin cewa sun shigo wuri mai ni'ima wanda babu abubuwan tashin hankali a cikinsa. Abin da basu sani ba shine sunyi gudun gara sun faɗa gidan zago domin bala'in da ke cikin wannan jeji ya ninka na faɗawarsu cikin cikin kifin sau arba'in. Nan fa su Jafar suka mimmiƙe tsaye suka isa bakin wata ƙorama kowa ya tsuguna ya jiƙa makoshinsa, sannan suka fara zuba ruwan ajikinsu don su ji ɗan sanyi, sakamakon ɗumamewar da jikinsu yayi a cikin kifi. Ai kuwa suna gama yin hakan kenan suka ga waɗansu abubuwa kamar manyan duwatsu sun kewaye jejin gaba ɗaya. Abubuwan suka rinƙa matsowa a hankali, ashe waɗannan abubuwa ba duwatsu ba ne wadansu irin maridai ne masu tsananin girma, tsawo da faɗinsu ya wuce ƙima. Ƙaramin cikinsu shine wanda tsawonsa ya kai kamu ɗari, faɗin ƙirjinsa kuwa ya kai arba'in. Koda ganinsu sai hankalin su Jafar ya dugunzuma suka rasa abin yi, kawai sai Gulzum yayi tsalle sama ya kama reshen bishiya ya fara tsalle-tsalle da nufin guduwa, caraf ɗaya daga cikin maridan ya kamo Gulzum a cikin tafin hannunsa, maridin ya ɗago hannunsa ya saita Gulzum dai-dai fuskarsa ya ƙare masa kallo sannan ya ƙyalƙyale da dariya. A lokacin ne maridan gaba ɗaya suka tsaya ƙyam a waje ɗaya, wannan wanda ya kama Gulzum dama shine mafi girma sai ya sauko da Gulzum ƙasa ya ajiyeshi kusa da su Jafar suma ya ƙare musu kallo sannan ya sake bushewa da dariya. Daga can kuma sai ya waiga ya dubi 'yan'uwansa ya ce, "Ya ku ahalil Bauzuls yau fa mun fito farauta a sa'a domin munyi tsintuwar abin da muka daɗe muna nema shekara da shekaru wato jinsin aljan da mutum." Ko da jin haka sai Jafar ya sha gaban Gulzum ya ɗaga kai sama ya dubi wannan maridi mai magana ya ce, "Ya kai wannan basamudan maridi me yasa kuke neman jinsin mutum da aljan har tsawon lokaci, amma baku samu ba sai yau. Shin kana nufin mutane da aljanu basa shigowa dajin nan ne?" Sa'adda Jafar yazo nan a zancensa sai maridin yasa dan yatsansa guda a cikin kunnensa na hagu tamkar ansa guga a rijiya yayi susa. Sannan ya sosa kunnen dama ya dubi Jafar ya ce, "Ya kai wannan karamar halitta me kake cewa ne wanda ban ji ba? Ina son ka sake maimaitawa." Koda jin haka sai daya daga cikin maridan ya zaro wani ƙaho dake saƙale a ƙugunsa ya ajiye shi a gaban Jafar tamkar ya ajiye ƙaton kwale-kwale. Ya ce da Jafar yasa bakinsa a bakin bututun ƙahon sannan yai magana. In ba haka ba kuwa sarki ba zai ji muryar sa ba. Koda Jafar ya doshi wannan ƙaho sai ya fuskanci cewar ai ƙofar dake bakin ƙahon ma takai faɗin ƙatuwar rijiya. Kawai sai ya zura kansa gaba ɗaya a cikin ƙahon ya maimaita maganar daya faɗi ɗazu. Ai kuwa sai nan take muryar Jafar tayi kauri kuma ta cika jejin gaba ɗaya da amsa kuwwa. Al'amarin da ya janyo tarwatsewar namun dajin dake wajen kenan, gaba ɗaya duk suka kama gabansu. Sarkin maridan ya yi murmushi mai kama da kukan jaki ya ce, "Ba komai ba ne yasa muke neman jinsin aljan da na mutum face maganin wata masifa data addabe mu shekara da shekaru, ya ku waɗannan ƙananan halittu kuyi sani cewa dani da jama'ata mun fi shekara dubu sittin acikin wannan daji kuma tunda muke zaune a nan bamu taɓa ganin jinsin mutum da aljan ba, sai sau ɗaya tsawon waɗannan shekaru. A halin yanzu akwai wata cuta da take addabarmu kuma mun kasa samun maganinta, wannan cuta itace ta rashin haihuwa, matanmu ko sun sami ciki baya zama,kai koda ya tsufa sai dai rana guda aga ya ɓace. Gaba ɗayanmu nan mu dubu ɗari bakwai ne da saba'in da bakwai. Tsawon waɗannan shekaru dubu sittin bama haihuwa kuma bama mutuwa, wato dai bama raguwa kuma bama ƙaruwa, kimanin shekaru ashirin da biyu baya wani hatsabibin aljani yazo nan neman wasu abubuwa na sirrikan tsafi. Sunan wannan aljani SHAMHARU, lokacin da yazo mana mun rufar masa gaba ɗaya don mu hallakashi amma muka kasa. Bayan ya tilasta mu mun samo masa abubuwa biyar da yake da buƙata sai muka roƙe shi da ya taimaka mana bisa cutar data addabemu ta rashin haihuwa. Nan take ya sanar damu cewa ba zamu fara haihuwa ba har sai mun samo jinin bil'adama kimanin cikin kwanson kabewa babba guda uku da kuma jinin aljan cikin ƙaramin kwanson kabewa. Idan muka haɗa wannan jini guda biyar waɗanda muka samo masa, mu da masu gaba ɗaya, kowa daga cikinmu sai ya lakaci wannan tsumi ɗan kaɗan ya lashe,tabbas idan muka yi haka zamu rinka haihuwa amma kuma zamu rinƙa mutuwa. Da yawanmu tsufa ya fara zame mana cuta don haka muna bukatar mutuwa,babu yadda ba muyi ba akan mu rage yawanmu ta hanyar kashe junanmu amma abu ya gagara domin duka,yakushi,sara da suka basa tasiri a jikinmu. Yau gashi mun tsinci dami a kala wato mun sameku don haka yanzu, yanzu bada wani ɓata lokaci ba zamu kama ku mu tafi daku izuwa gidajenmu inda zamu yankaku mu tara jininku acikin kasko guda don hada wannan magani. Mukam wahalar mu da baƙin cikinmu ya ƙare daga yau." Kafin ɗaya daga cikin su Jafar yace wani abu tuni an damdamƙesu an tafi da su. Nan take maridan nan suka kama kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe suka nufi wani katon dutse mai tsananin girman gaske. Su dai su Jafar tuni sun sallama rayuwarsu don sun tabbatar da cewa babu mai cewa yanzu mu shi kenan haka ƙarshenmu zai kasance. Ai kuwa mun sha wahalar duniya a banza kenan,mu ba muyi suna ba kuma bamu sami matsayin komai ba." Ita kuwa Mashrila sai tace, "Ni kam inda nasan hakane zata faru a gareni da nayi zamana acan garinmu na mutu acikin irin masifar da ta addabe mu." Mazalish tace, "Ni kam mutuwata anan ta fiye mini alheri akan na rayu a matsayin mayya mai shan jinin bil'adama." Jafar ya share hawayensa yace, "Ni kam babban abin baƙin cikina shine zan mutu banga abin dake cikin shafin karshe na KUNDIN TSATSUBA ba."(😲😲😲😬😬😬😬😬ho Jafarun mu🤣🤣🤣🤣🤣j jama'a kunji halin mutumin naku ko🤣🤣🤣.) Ko da jin haka sai Gulzum ya yi tsaki yace, "Amma dai kai Jafar ka cika banza mara tunani,in banda rashin hankali da hauka irin naka wane ne zai yi fatan ya karance wannan tsinannen littafin. Kaga mu bala'in da muka sha a baya ma ya ishemu. Ai gwarama waɗannan maridan su kashe mu huta da fargabar sauran masifun dake jiranmu." Haka dai su Jafar suka ci gaba da surutai na tausayawa kansu har maridan nan suka iso gaban wannan tafkeken dutse. Da zuwa sai su Jafar suka ga ashe a jikin wannan dutse maridan suka gina gidanjensu. Ba wai gini aka yi akan dutsen ba,a'a dutsen aka ƙwaƙule akayi ɗakuna. Abin mamakin shine,gaskiyar al'amarin shine da kaifin faratan hannaye maridan akayi wannan gagarumin aiki. Da zuwa sai aka sauke su Jafar aka ɗaɗɗauresu tamau da igiyoyi ajikin wasu turaku na dutse,daga nan gaba ɗayan maridan suka kewaye wani ƙaton kasko wanda girmansa ya kai a sanya bil'adama dubu a cikinsa. Nan take aka cigaba da kiɗa ana rera wata irin waƙa mai daɗin sauraro kai kace mutane ne masu nutsuwa suke waƙar. Jafar ya dubi Yelisa yace, "Ya ke Yelisa haƙiƙa ina mai matuƙar baƙin ciki da ya zamana zamu mutu ba tare da kun cika burin zuciyarmu ba,amma ina jin daɗi cewa zamu bar duniya a tare muna masu kallon junanmu,in ba don nasan mutuwa zan yi ba da nace wannan kiɗan da waƙar sun isa su gusar mana da takaicin duk irin wahalar da muka sha a baya." Mashrila tace, "Ya kai abin begena ni kam indai dai ace kai ne ka rigani mutuwa da tabbas haɗiyar zuciya zanyi na mutu,amma tun da dai tare zamu mutu ba zanyi takaici da nadamar komai ba. Kuma babu mamaki mu sake haɗuwa a wata duniyar dabam muyi sabuwar rayuwa." Koda jin haka sai kishi ya turnuƙe Yelisa suka fara kace nace. (Kutttttt😳😳😳 lallai yaran nan a gaishe su,suna gaf da mutuwa amma ta kishi suke😂🤣🤣) Mazalish ta dubesu ta bushe da dariya tace, "Haƙiƙa kukan daɗi kuke yi kawai saboda ganin masoyinku a kusa daku yanzu ni da ban san a inda nawa yake ba kuma ban san a inda zan riske shi ba,ai sai dai naci gaba da kuka tunda gashi ma yau zan bar duniyar gaba ɗaya." A dai-dai wannan lokacin ne suka ga an ɗebo wani garin magani kala biyar an zazzagesu duk a cikin ƙaton kaskon nan. Daga nan kuma sai wani ƙaton maridi ya dubi sarkin maridan yana mai tambayar wanda za'a fara kashewa daga cikin su. Sarkin maridai yai nuni ga aljani Gulzum. Koda ganin hakan sai Gulzum ya fashe da kuka yana baiwa Yelisa wasiya cewar, "Idan ta koma duniyarsu ta nemi iyayensa ta sanar dasu yadda ya kasance kuma ta nema masa gafararsu domin ba'a son ransu ya bar gida ba,ya shiga duniya." Yelisa ta zubar da ƙwalla don tausayi da sabo tace, "Ya kai Gulzum ai abin da ya same ka shine zai same ni sai dai muyi hakuri gaba daya." (😂🤣🤣🤣🤣. Su Gulzum anga mutuwa🤣) Kafin wani daga cikinsu Jafar yace wani abu tuni ƙaton maridin nan ya suro Gulzum,igiyar da ta ɗaure shi ta tsitstsinke,da hannu ɗaya maridin ya aza Gulzum a saman ƙoƙon sannan ya ɗaga ɗaya hannunsa ya kaiwa maƙoshin Gulzum suka da tsinin farcen babban ɗan yatsansa. Ba zato ba tsammani sai aka ga wata runɗumemiyar macijiya mai kawuna dubu arba'in ta zuro bakinta guda ta gutsure hannun wannan maridi ta haɗiye. Damar da bai samu ba kenan ta sukar makoshin Gulzum. Maridin ya kwarara ihu sa'adda jini ke bulbula ta jikin dungulmin hannun nasa. Ihun maridin ya haɗe da gurnanin macijiyar a lokaci guda. Nan fa maridan nan suka firgice kowannensu ya fara neman hanyar gudu amma tuni macijiyar mai kawuna dubu arba'in ta fara yi musu ɗauki ɗai ɗai,sai dai kaga kawunanta na saukowa ƙasa suna wangame bakuna suna yin loma ɗaya da maridan. Shi kansa sarkin maridan bai san sa'adda ya kama rarrafe ba a ƙasa, sai da ya isa ƙofar ɗakinsa dake kan dutsen har ya tura kansa cikin dakin, sai macijiyar ta finciko shi da ƙarfin tsiya,ta lanƙwame shi. Cikin tsananin zafin nama macijiyar nan ta ci gaba da cinye maridan nan ɗaya da ɗaya,sai da ta cinye su gaba ɗaya,a cikin abin da bai wuce daƙiƙa ɗari uku da sittin ba. Koda ta gama cinyesu sai ta zube ƙasa rikica! Tana ta numfashi da ƙyar. Kawai sai ta fara shiga cikin wani ƙaton rami dake ƙarƙashin wannan dutse,wanda maridan suka yi gidajensu akai. Sai da aka shafe sa'a guda cur sannan doguwar jelar macijiyar ta gama ƙulewa a cikin ramin,ta ɓace bat,tamkar bata taɓa wanzuwa ba a wajen. Nan fa wajen yayi tsit ya zamana ba kowa face Gulzum,Jafar,Yelisa,Mashrila da Mazalish. Koda Gulzum ya ga ya tsira sai ya daka tsalle ya kama rawa don murna. Cikin sauri ya sauko daga cikin ƙaton ƙoƙon nan yaje ya kwance su Jafar yace, "Maza ku zo mu bar wajen nan da sauri don bamu san abin da zai biyo baya ba,babu mamaki macijiyar nan ta sake dawowa idan abin da ta haɗiya ya gama narkewa a cikin ta." Ba tare da gardamar komai ba su duka suka runtuma cikin jeji da gudu ba tare da sanin inda suka dosa ba,sai da suka yi nisa sosai suka gaji sannan suka tsaya a wani wuri mai tarin rairayi suka zauna suna haki,har suka sami 'yar nutsuwa. Jafar ya dubi Gulzum yace, "To kai in banda abinka me wannan macijiya za ta ji idan ta haɗiye mu nan duka? Ka duba fa yadda ta rinƙa loma ɗaya da manyan maridan nan tamkar mutum ya jefa ƙwayar hatsi a bakinsa." Gulzum ya murtuke fuska yace, "To ban da abinka ai mai kwaɗayi bashi da ramuwa. Komai ƙanƙantar abin lasawa baya bari." Mazalish ta yi ajiyar zuciya tace, "Kai jama'a wanda bai yi yawo a duniya ba bai sha kallo ba. Ni kam tun da uwata ta haifeni ko a labari ban taɓa jin labaran macijiya irin wannan ba mai tsananin girma,kuma mai duban kawuna haka barkatai ba. Tabbas in muka sami nutsuwa sai na roƙi Mashrila ta zana mini taswirarta. Kun ga ku tashi mu kama gabanmu don an ce zama waje daya tsautsayi ne,inji kifi." Koda jin haka sai Jafar ya bushe da dariya yace, "Wannan shi ne abun mamaki kare da tallar tsire,wai ya za'a yi a ce aljani yafi bil'adama tsoro. Gaskiya Gulzum kana bani haushi saboda raguwar zuciyarka." Cikin tsananin fushi Gulzum ya yunƙura don ya make Jafaru in yaso komai ta fanjama-fanjam,amma haka ba ta yiyu ba, sakamakon ganin wata irin ƙatuwar inuwa da ta lullube su gaba ɗaya daga sama. Cikin firgici suka ɗaga kawunansu sama don su ga abin da ya yi musu inuwar,kwatsam suka yi arba da wannan ƙatuwar macijiyar nan wadda ta cinye maridan nan ta zubo kawunanta kas reras, barkatai ba kyan gani suna fesar dafi. Kafin daya daga cikin su Jafar ya yi wani yunƙuri tuni ta lankwame su gaba ɗaya. Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar yayin da suka fuskanci kaɗan daga cikin azabobin muguwar guguwa da ke cikin shafi na goma sha shida a KUNDIN TSATSUBA. *************** A can fadar sarki Dujalu kuwa bai ci gaba da baiwa su Ruziyal labarin Hikayar jarumi Nazmir da gimbiya Luzaiya ba,sai bayan an zo da kan wannan bawa mai kula da damisar sarki wanda tsautsayi ya sashi ya manta bai kulle kofar kejin damisar ba a jiya da daddare har ya zamana damisar ta yi fitar burgu ta shigo fada,kuma har ta nemi hallaka mai gidanta. Nan take sarki Dujalu ya bada umarnin a yi waje da kan bawan a hada da mushen damisar aje a binne a jeji. Bayan tafiyar masu cika umarni ne sai Dujalu ya yi gyaran murya yace, "To sai ku shirya don zan ci gaba. Lallai ina son na kai ƙarshen wannan doguwar hikaya ko ma shiga ta gaba,don na sallame ku a cikin kwanaki goma daidai,ku kama gabanku." Koda jin haka sai boka Hajarul Mukurus ya sunkuyar da kansa ƙasa sakamakon ƙwallar dake shirin zubowa daga idanunsa, sannan yace, "Ya kai wannan sarki haƙiƙa duk a cikin hikayoyin da ka bamu babu mai tausayi kamar wannan,na roƙe ka da ka hanzarta sanar da mu ƙarshenta don mu ji yadda za ta wakana." Sarki Dujalu ya yi murmushi yace, "Ai da sauran abin tausayi ma a gaba. Ku dai ku bani aran kunnanku idan na gama sai ku yi muhawara." Nan take sarki Dujalu ya ci gaba da bayani kamar haka............. "Lokacin da jarimi Nazmir ya saɓa gimbiya Luzaiya a kafaɗarsa yana laluben hanyar da zai bi ya koma wajen 'yan uwansa su Bagwan. Sai Luzaiya tayi ta zulle-zulle tana ihu gami da dukan bayansa da hannu biyu,don ya sauketa ƙasa,shi kuwa sai ya yi biris da ita tamkar wanda ya goya kaza. Haka dai ta yi ta wutsil-wutsil a bayansa shi kuwa ya ci gaba da tafiya ta cikin kwazazzabai,duwatsu da ruwa yana dube-dube da ƙwalawa abokansa kira,amma shiru bai ji komai ba,a jejin face amsa kuwwar muryarsa. Sai da ya jima a cikin wannan hali har ya zamana gimbiya Luzaiya ta gaji da ihu muryarta ta dashe kuma ko hannayen tama ba ta iya daga su. Bisa dole ta rungumi ƙaddara ta daina motsi. Saboda gajiya sai barci ya kwashe ta akan kafaɗar jarumi Nazmir. A wannan lokaci duhu ya soma, kuma jarumi Nazmir ya gaji sosai. Koda ya fuskanci cewa Luzaiya tayi bacci sai ya isa gaban wata bishiya ya sauketa a hankali. Har ya miƙe zai tafi neman itatuwan da zai kunna su ji ɗumi sakamakon hunturun sanyin dake kaɗawa a jejin,sai ya tsaya yayi gajeran tunani,don haka sai ya fiddo wata igiya daga cikin jakarsa ya ɗaure ƙafafun Luzaiya sannan ya kwantar da ita ta yi rub da ciki, ya ɗaure hannayenta ta baya don kar ta gudu. Sannan ya tafi neman itatuwan. Bayan kamar daƙiƙa dari da ashirin da tafiyar jarumi Nazmir sai sanyi ya bugi gimbiya Luzaiya ta farka daga barcin. Ai kuwa tana buɗe idanunta,sai tayi arba da wata mayunwaciyar kura nesa can daga inda take. Ita dai wannan kura wannan rana ta yini da yunwa domin ta gaji da neman abin da zata ci ta rasa. Koda suka yi ido-da-ido sai kuran nan ta taso a guje haikan don rashin haƙuri ma har tsalle take sama tana kara dirga gaba don gani take gudun bai isheta ba. Koda Luzaiya ta yunƙura don ga miƙe tsaye ta gudu sai ta ji ƙafafunta da hannayenta a ɗaure. Nan take hankalinta ya dugunzuma jikinta ya kama karkarwa don tsananin tsoro ba ta san sa'adda ta ƙwala uban ihu ba. A wannan lokaci jarumi Nazmir ya deɓo kayan itatuwa niƙi-niƙi. Koda ya jiyo ihun gimbiya Luzaiya sai ya yi watsi da itatuwan ya kece da tsananin gudu ya nufi inda ya baro ta. Gudu yake iya ƙarfinsa kuma irin wanda bai taɓa yi ba a rayuwarsa. Har yanzu bai daina jiyo ihun gimbiya Luzaiya ba,al'amarin daya ƙara fusata shi kenan ya ƙara ƙaimi. Kafin ya iso tuni kuran nan tayi tsalle sama ta dira gaban Luzaiya. Nan take kuwa ta kaiwa gadon bayanta cafka da hakoran bakinta. Cikin zafin nama Luzaiya ta mirgina baya amma duk da haka sai da haƙoran kurar suka yage rigar Luzaiya kuma suka karce fatarta jini ya tsatstsafo. Kurar ta sake kai mata cafka a karo na biyu bisa rashin sa'a sai ta faɗa hannun jarumi Nazmir ya shaƙe wuyanta,suka kama kokawa, su faɗi nan su tashi can. A lokacin ne gimbiya Luzaiya ta zuba musu idanu kawai zuciyarta cike da tunani kuma hawaye na zuba a idanunta tace a ranta, "Wai shin mene ne ma dalilin da ya sa na tsorata da wannan kura? Ashe bani ce wadda ke neman mutuwa ba? Ya akai na kasance mai ƙoƙarin neman tsira? Haba Luzaiya me kike so ki yi a duniya alhalin baki da kowa,ba ki da komai. Haƙiƙa kin yi kuskure da kika yi ihu har jarumi Nazmir ya kawo miki ɗauki da wuri. In da kin yi shiru da yanzu haka kin mutu kin huta da takaicin duniya.' Tun da jarumi Nazmir yake bai taba haɗuwa da ƙatuwar kura irin wannan ba,a duk lokutan da ya sha arangama a jeji a yayin farautarsa. Ita dai wannan kura ta kasance mai taurin kai,ƙarfi da jajircewa. Sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna gumurzu ya zamana tayi masa rauni sosai da faratan hannunta amma da zarar ta kawo masa cizo sai ya goce ya naushi bakin nata. Saboda ƙarfin naushin nasa sai kaga ta zube ƙasa rikica amma kuma sai ta sake miƙewa cikin zafin nama,ta afka masa. Yayin da jarumi Nazmir ya ga kurar nan tana so ta galabaitar dashi sai ya harzuƙa zuciyarsa ta yi baƙinƙirin kawai sai ya suri ƙafafunta biyu na baya ya dagata sama ya rinka haji-jiya da ita tamkar wanda yake wasa da majajjawa. Bayan ya wulwulata kamar sau arba'in a sama sai ya rinka rotsa kanta akan wani dutse har saida ya ga kan ya dagwargwaje sannan ya yi jifa da gawar kurar,shima ya tsugunna ƙasa yana haki da numfashi. A sannan ne suka haɗa idanu shi da gimbiya Luzaiya. Koda ya ga raunin da kurar nan ta yi mata a gadon baya sai tausayinta ya kama shi. Cikin sauri ya miƙe ya je ya buɗe jakarsa ya ɗauko magani ya shashshafa mata a raunin,sannan ya kwance igiyar da ya ɗaure mata hannaye da ƙafafu,ya jinginar da ita a jikin bishiya. Kawai sai ya juya mata baya yace, "Idan kin so kina iya yin ƙoƙarin guduwa amma ki sani ba za ki iya tsere mini ba,a cikin jejin nan,duk inda kika shiga kika ɓuya sai na laluboki." Yana gama faɗin hakan ya tafi ya barta a wajen cikin tunani. "Me kike jira ne ga dama ta samu? Walau ki gudu ko kuma ki sami wani icen ki tsire cikinki ki mutu. Ko kya huta da baƙin cikin rayuwa." Zuciyar Luzaiya ce ta saƙa mata waɗannan maganganu. "Me yasa na rayu har na kawo i yanzu? Lallai akwai wani dalili a ƙarƙashin wannan sanadi. Zai fi kyau na tsahirta dan naga wannan dalili da idanuna tunda dai nayi iyakar ƙoƙarina akan na ga na halaka kaina,amma abu ya faskara. Duk da kasancewar ban yi imani da ɗaya daga cikin irin addinan zamani ba babu mamaki wani Ubangijin ne yake tsara rayuwata saboda wani ɓoyayyen dalilin." Luzaiya na cikin wannan tunani ne jarumi Nazmir ya dawo ɗauke da itatuwa. Shi kansa yayi mamaki da ya iske ta har yanzu a zaune a inda ya barta,kuma hawaye bai daina zuba a idanunta ba. Ban da karkarwar ɗari babu abinda take yi. Nan da nan ya zube icen a gabanta ya kunna musu wuta,sannan ya sake buɗe jakarsa ya fiddo wata riga wadda aka yi ta fatar damisa ya lulluɓawa gimbiya Luzaiya. Shi kuwa dogon wando ne kaɗai a jikinsa na fatar zaki. Nazmir ya zauna tsallaken wutar suna masu fuskantar juna. Tsawon daƙiƙa biyar wurin yayi tsit baka jin komai face kukan tsuntsaye da kuma kukan manyan namun dawa,da ke can nesa. Nazmir ya katse shirun da cewa, "Me yasa ba ki yi ƙoƙarin guduwa ba sa'adda na kwance ki na tafi nemo itatuwa?" Ba tare da ta ɗago kai ta dube shi ba,tace, "Guduwa ta ba ta da wani amfani ko tasiri,domin na rigaya nayi kusure tunda har na yi ihu ka kawo mini agaji sa'adda kura ta afka mini." Nazmir ya yi ɗan guntun murmushi sannan ya janyo maganin nan da ya shafa mata a rauni ya fara shafawa a nasa raunikan. "Bai kamata ki yi ƙoƙarin kashe kanki ba,saboda baƙin cikin rashin mahaifinki,mulkinki da danginki,ki tuna cewa mai rai baya fitar da rabo,za ki iya sake saduwa da mahaifiyarki nan gaba,shin ba kya tunanin irin ɓacin ran da mahaifiyarki zata shiga idan ta sami labarin mutuwarki,ki sani cewa idan na kai ki ga sarkina ya aureki zaki ci gaba da rayuwa ne cikin tsananin jin daɗi da walwala." Koda jin haka sai ta dubi jarumi Nazmir cikin ƙunar zuci tace, "Shin jin daɗi da walwala zasu iya maishe da gurbin abokanka waɗanda ka rasa a wannan yaki da ka yi?" Koda jin wannan tambaya sai idanun Nazmir suka ciko da ƙwalla,jikinsa yayi sanyi gaba ɗaya ya kasa cewa komai. Luzaiya ta ci gaba da cewa, "Babu wani farin ciki da zai iya gusar mini da đacin zuciyar da nake ji sakamakon kisan gillar da kuka yiwa mahaifina. Ka yi sani cewa a duk sa'adda na dubi abokinka na kan ji kamar ana sukan zuciyata da tsinin masu. Inda zan kashe shi na yi gunduwa-gunduwa da sassan jikinsa izuwa sala-sala,mini-mini yadda tsuntsun kanari zai iya tsinta da bakinsa ya ci ba zan huce takaicin zuciyata ba. Bani da wani masoyi a duniya wanda yafi ubana. Na rayu a cikin ƙaunarsa,da begensa dare da rana,kuma cikinta zan mutu." Sa'adda Luzaiya tazo nan a zancenta sai ta fashe da kuka. Tausayi ya kara turnuke Nazmir yace, "Na san har abada ba za ki iya yi mana afuwa ba,wato ni da abokaina amma ki sani bamu kashe mahaifinki don buƙatar kanmu ba sai don mu ceto rayuwarmu da kuma farin cikin iyayenmu. Kowanne 'ɗa' na gari ba shi da wani buri wanda yafi na nunawa iyayensa tsantsar ƙauna kamar yadda suka nuna masa tun yana ƙarami kawo izuwa girmansa. Tsantsar ƙaunar da nake yiwa mahaifina ce tasa na fito wannan yaƙi,amma ba wai don tsoro da bin umarnin sarkina ba. Hasalima a duniya babu mutumin dana tsana fiye da sarkin garinmu saboda zaluncinsa da rashin tausayinsa ga talakawa." Koda gimbiya Luzaiya ta ji wannan batu daga bakin jarumi Nazmir sai ta cika da mamaki tayi shiru ba ta ce komai ba. Daga can kuma sai ta dube shi tace, "Ya kai wannan jarumi ina son nayi maka wata tambaya idan har ba za ka sami damuwa ba?" Nazmir yace, "Faɗi tambayarki in dai ina da amsarta zan sanar da ke." "Shin za ka iya gaya mini dalilin da ya sa mahaifina yace idan ya bari aka kashe ku ya ci amana? Mene ne dalilin da ya sa ya kawo kansa gareku har ya umarce ka da ka sare kansa kuma ka kamani ka tafi da ni? Kayi sani cewa zuciyata ta daɗe tana damuwar akan wannan al'amari,kuma ta shiga cikin bakin duhu babu mai fito da ita izuwa cikin hasken fahimta face kai." Sa'adda gimbiya Luzaiya ta zo nan a zancenta sai jarumi Nazmir ya yi ajiyar zuciya yace, "Ba komai ne ya sa mahaifinki ya yi haka ba sai don ya sakawa mahaifina abin da alherin da ya taɓa yi masa a baya kimanin shekaru da suka gabata." Nan take jarumi Nazmir ya kwashe labarin abinda ya faru tsakanin sadauki Halufa da sarki Fahalul Bahafus ya zaiyane mata. Koda ya ƙare labarin sai ta fashe da kuka tana mai cewa, "Haƙiƙa mahaifinka masoyi ne a gareni da mahaifina lallai kai ba abokin gabata bane,domin ba don darajar mahaifinka ba da na girma a cikin maraici. Haƙiƙa mahaifina ya riƙe amana kuma ya tabbatar da alƙawari. Ya kai Nazmir kayi sani cewa daga yau na rungumi ƙaddara,kuma zan kasance mai bin umarninka har mu isa ƙasarku ka danƙani a hannun sarkinku,domin yin hakan a gareni shi ne cikar riƙe amanar da ke tsakanin mahaifina da mahaifinka. Lallai kun yi halacci a garemu,lokaci yayi da zamu saka muku,ina mai roƙonka da ka yafe mini kura-kuran da na yi maka a baya." Nazmir yayi murmushi yace, "Ai duk abin da kika yi mini banga laifin ki ba,domin kin yi ne don sanin martabar mahaifinki." Haka dai Nazmir da gimbiya Luzaiya suka ci gaba da hira har dare ya raba sosai,ya umarce ta da yin barci,shi kuma yayi gadin lafiyarsu. Koda jin haka sai ta miƙe tsam ta dawo inda yake ta kwanta tana mai ɗora kanta akan cinyarsa tace, "Yanzu hankalina ya kwanta da kai na san cewa har abada ba zaka cutar da ni ba,domin kai masoyi ne ba maƙiyi ba." A iya rayuwar jarumi Nazmir mace ba ta taɓa kusantar sa ba,irin yau sai dai a larura ko a wajen yaƙi. Don haka lokacin da gimbiya Luzaiya ta ɗora kanta akan cinyarsa,sai gaba ɗayan tsigar jikinsa ta tashi,ya ji kamar ya ture ta,amma da ya tuna cewar 'yar sarki ce fa mai mulki,kuma wadda ke cikin baƙin cikin rayuwa mai matuƙar buƙatar nutsuwa da kwanciyar hankali sai ya ƙyaleta. Yayin da asuba ta fara gabatowa sai Luzaiya ta farka daga barci ta roƙi Nazmir da ya kwanta don shi ma ya dan rintsa. Nazmir yace, "Ai gari ya kusan wayewa don haka kaima sai ka kwanta ba." Nan fa gardama ta ƙarke a tsakaninsu da ƙyar ta shawo kansa ya amince ya kwanta,ita kuma ta ci gaba da tsaron lafiyarsu. Luzaiya bata tashi Nazmir daga bacci ba sai da ta gari ya waye sosai,rana ta ƙwale. Koda farkawarsa kuwa yaga ashe gari ya daɗe da wayewa sai ya dubi Luzaiya yace, "Ya gimbiya me ya sa kika barni ina ta barci har tsawon lokaci haka?" Yayin da Luzaiya ta ji wannan tambaya sai tayi murmushi tace, "Saboda kaima ka bani dama na samu isasshen barci,kuma nasan cewa akwai bashin barci mai yawa a tare da kai,idan ba ka yi ba zaka iya samun matsala a lafiyar ka." Wannan batu ba ƙaramin bashi mamaki ya yi ba,domin shi a tunaninsa bai ga dalilin da zai sa ta damu da lafiyarsa ba. Nazmir ya miƙe tsaye ya ɗauki kwari da bakansa da kuma takobinsa ya gyara musu zama a jikinsa. Koda ganin haka sai Luzaiya ta dube shi cikin damuwa tace, "Ina kuma zaka je?" Nazmir ya maida mata murmushi yace, "Zan je ne nayi farautar abin kalaci." "Ai kuwa sai dai mu tafi tare, don ba zan yarda ka barni ni kaɗai ba a wannan mugun dajin." Wannan batu ba ƙaramin mamaki ya baiwa jarumi Nazmir ba,domin a tunaninsa Luzaiya bata kasance matsoraciya ba,in da kuwa matsoraciya ce ai ba za ta hau doki ba,ta yiwa mayaƙa jagora a lokacin nan da ake gumurzun yaƙi tsakanin su Nazmir da baraden mahaifinta. Jarumi Nazmir ya dubi gimbiya Luzaiya ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Haba ranki ya daɗe ai ni zatona ke jaruma ce daga cikin mata,ya kuma kike nuna gazawarki a fili haka?" Luzaiya tayi murmushi tace, "Ai ido ba mudu bane,amma ya san ƙima. Tabbas ko kaɗan ban yi kama da jaruma ba,haka kuma ba ni da sura irinta jarumai." Ba tare da ɓata wani lokaci ba jarumi Nazmir ya nausa cikin jeji yana mai sauri-sauri, gudu-gudu. Luzaiya ta bishi a baya duk in da ya ɗauke sawunsa sai tasa na ta,ko kaɗan bata yarda ya bata tazara ba. Suna cikin dube-dube ne a jejin Nazmir ya hango wata barewa. Ai kuwa yana ganinta ya ɗana baka akan kwari ya sai tata. Koda ya saki bakar sai barewar ta ruga cikin dawa,kibiyar ta wuce ta saman kanta. Koda ganin haka sai Nazmir ya bi barewar da gudu,itama Luzaiya sai ta bi shi a guje iya ƙarfinta,don kada ya ɓace mata. Sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna wannan gudu basu cimma barewar ba,ita kuma barewar bata ɓace musu ba. Ya zamana Luzaiya ta jigata ainun sai haki take,kuma tana sassarfa kamar za ta fadi ƙasa,amma sai ta jure. Koda suka iso kan wani ƙaton dutse sai barewar nan ta fara ƙoƙarin isa karshen dutsen. Anan ne jarumi Nazmir ya tsaya ya zaro kibiya guda ɗaya daga cikin kuttun kibbau ya aza akan bakar, sannan ya ja ya taɓe yana mai saita barewar nan. Yayin da ya gama taɓewa da saitawa iya ƙarfinsa da iyawarsa sai ya saki kibiyar. Cikin tsananin gudu da ƙarfi kibiyar ta tafi ta caki gadon bayan barewar ta faso ta cikinta ta ɓulla waje. Take barewar nan ta fadi ƙasa matacciya. A sannan ne Nazmir ya waiga bayansa ya yi arba da gimbiya Luzaiya wacce ta zauna dirshan tana kallon abin da ke faruwa cikin nuna al'ajabi. Nazmir yayi murmushi a gareta, itama ta yi masa fuskarta na nuna yabawa bisa jarumtakarsa. Kawai sai Nazmir ya nufi inda wannan barewa ke kwance da nufin ya ɗaukota. Ba zato ba tsammani sai ya gansu suna saukowa ƙasa daga saman wannan dutse. Ba wasu ba ne face Bardil,Bagwan da kuma sauran baradan nan abokan tafiyarsa. Koda su Bardil suka yi arba da jarumi Nazmir,kuma suka ga gimbiya Luzaiya a bayansa sai suka cika da tsananin farin ciki. Nan take suka rugo gare shi shima ya ruga garesu take aka rungume juna,cikin murna mara misaltuwa. Ba tare da ɓata wani lokaci ba aka ɗauko barewar nan aka sauko daga kan dutsen. Nan dai aka gasa barewa kowa ya yi kalaci,sannan aka shiga hira inda jarumi Nazmir ya baiwa su Bardil labarin abubuwan da suka faru bayan rabuwarsu. Al'amarin da ya ƙara jefa su cikin matuƙar al'ajabi kenan. Bayan nan sai Bagwan ya yi gyaran murya yace, "Yakai abokina kayi sani cewa bayan rabuwarmu daku muma mun sha baƙar wahala sakamakon gamuwa da muggan namun jeji da kuma nau'i-nau'in 'yan fashi,amma duk sai da muka fatattake su muka tarwatsa su. A haƙiƙanin gaskiya bamu taɓa tsammanin zamu sake saduwa da ku ba,domin mun zata kai da ita duk kun hallaka a lokacin da kuka faɗo ƙarƙashin tsaunin nan mai kwazazzabo. Tuni mun yankewa kanmu hukunci cewar ba zamu koma can ƙasar mu ba,muddin bamu ganku ba sai dai mu ci gaba da rayuwa a cikin jejin nan har ajalin mu ya riskemu, domin mun san cewa idan muka koma ba tare da biyan buƙatar sarki ba gaba ɗayanmu mun zama gawa." Koda jarumi Nazmir ya ji wannan jawabi sai yayi ajiyar zuciya,sannan ya dubi Bardil da Bagwan yace, "Ya ku abokaina ku yi sani cewa tabbas na ji a jikina cewa ɗayanmu ba zai sake mutuwa ba,har sai mun isa gida lafiya,tare da biyan buƙatar sarki sai dai baƙin cikin rabuwa da abokanmu shi ne babban abin damuwarmu." Yayin da jarumi Nazmir ya fadi haka sai idanun Bardil da Bagwan suka ciko da ƙwalla suka kama kuka,shima sai ya taya su. Al'amarin da ya sa gimbiya Luzaiya ma ta tuno da mahaifinta,mahaifiyarta da kuma ƙasarsu kenan. Itama dai bata san sa'adda ta fara zubar da hawaye ba,don haka sai ta miƙe ta koma gefe guda ta zauna ta ci gaba da kukanta. Su kuwa sauran barada sai suka kamu da tausayi suka yi shiru da zugum cikin juyayi. Nazmir ya kama hannun Bardil da Bagwan ya jasu izuwa gefe guda suka keɓe,sannan ya dube su ɗaya bayan ɗaya sa'adda yake goge hawayen idanunsa, yace, "Yaku abokaina ku yi sani cewa jikina yayi sanyi,haka kuma zuciyata na bugawa ma'ana ina jin tsoro da faɗuwar gaba bisa abin da zai faru garemu bayan mun isa gida. Jikina yana bani cewar akwai wani mugun abu da zai faru a garemu dangane da sakaiyar azzalumin sarkinmu zai yi mana domin halinsa ne ya cutar da talakawansa waɗanda suka kyautata a gare shi." Yayin da Bardil da Bagwan suka ji wannan batu sai duk hankalinsu ya tashi suka shiga tunani. Nazmir ya katse tunanin nasu da cewa, ni kam a yanzu tausayin gimbiya Luzaiya ya shigeni har ina jin cewa kamar bazan iya danƙata ba a hannun azzalumin sarkinmu, to amma fa idan nayi tunani sai na ga cewa ba mu wata mafita don haka dole ne na miƙata in ba haka ba kuwa rayuwarmu da ta iyayenmu na cikin haɗari. Yanzu ku mece ce shawararku bisa abin da kuke ganin zai fishshe mu?" Lokacin da Bardil da Bagwan suka ji wannan tambaya sai hankalinsu ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe duk suka yi shiru suna juya al'amarin cikin zukatansu. Bayan dogon nazari sai Bardil ya ɗago kai ya dubi jarumi Nazmir yace, "Ya kai abokina haƙiƙa maganarka abin dubawa ce matuƙa,to amma ka yi sani cewa yanke hukunci a garemu yanzu yafi komai haɗari. Ni a tunanina zai fi kyau mu bari mu isa gida in ya so sai mu yanke shawara bayan mun miƙa gimbiya ga sarki." Koda jin haka sai Bagwan yace, "Ƙwarai kuwa wannan shine abin da yafi cancanta a garemu." Da wannan shawara aka yi amfani. Wato daga wannan rana su jarumi Nazmir suka ci gaba da tafiya ba dare ba rana,sai dai kawai idan sun gaji su yada zango. Bayan wata da watanni ne suka iso ƙasarsu. Yayin da suka iso bayan gari dare ya raba,don haka sai suka tsaya suna shawarwari akan shiga gari yanzu ko kuwa su bari sai gari ya waye? Koda mahawara tayi yawa a tsakaninsu sai jarumi Nazmir yace, "Wai shin wane ne shugaba a cikin tafiyar nan tamu?" Bardil da Bagwan suka ce, "Kai ne shugaba ya jarumin jarumai." Nazmir yayi murmushi yace, "Tunda haka ne ni yanzu nake son mu shiga cikin garin,kuma ba zamu shiga ba sai mun ɓatar da kamanninmu domin mu san sirrin abin da gari ke ciki,don kada mu faɗa cikin tarkon sarki. Kamar yadda kuka sani cewar marigayi mahaifin gimbiya Luzaiya ya roƙeni da na fara nuna kansa ga mahaifina tare da yi masa bayanin cewar ya sallama rayuwarsa don ceto tawa. Don haka idan muka shiga cikin gari babu inda zamu fara zuwa face gidanmu don riskar mahaifina. In yaso da safe sai mu tafi gidan sarki mu miƙa masa gimbiya Luzaiya." Yayin da jarumi Nazmir ya zo nan a zancensa sai gimbiya Luzaiya ta dube shi idanunta cike da hawaye tace, "Yanzu da hannunka zaka danƙani a hannun azzalumin sarki wanda ya zamo sanadiyar mutuwar abokanku,waɗanda kuka shaƙu ainun tun yarinta? Ka tuna fa cewa a sanadin wannan azzalumin sarki ne mahaifina ya mutu,kuma a sanadinsa ne aka yi asarar dubannan rayuka, kuma a sanadinsa ne kuka rabu da iyayenku da danginku tsawon lokaci,kuka jefa kanku cikin muguwar rayuwa mai mugun haɗari. Nikam da dai na zama matar wannan sarki gwara na mutu tsuntsaye su cinye gawata,ya zamana an mance da tarihina a duniya har abada." Lokacin da gimbiya Luzaiya tazo nan a zancenta sai hankalin su jarumi Nazmir ya tashi,suka yi shiru cikin matuƙar damuwa da kokwanto. Bayan ɗan gajeran tunani,sai jarumi Nazmir ya dafa kafaɗunta a karo na farko tun haɗuwarsu,suka tsurawa juna ido yace, "Yake gimbiya,sarauniyar kyawawan duniya ki kwantar da hankalinki ki sani cewa ni jarumi Nazmir na yi miki alƙawari cewar har abada ba zan bar rayuwarki ba a cikin ƙunci da baƙin ciki,lallai zan kuɓutar dake,kuma na mayar da ke kasarku don ki sadu da mahaifiyarki ki ci gaba da rayuwarki ta sarauta,kamar da a cikin ƙasarki ta haihuwa." Koda jin haka sai gimbiya Luzaiya tayi murmushin yaƙe sannan tace, "Duk wannan ba zai burgeni ba face ka hana faruwar aure a tsakanina da azzalumin sarkinku." Nazmir ya yi shiru bai ce komai ba, domin ya san cewa shi kam bai isa ya hana wannan aure ba. Yayin da Luzaiya ta ga jarumi Nazmir ya yi shiru bai ce komai ba sai zuciyarta ta karaya ta cigaba da zubar da hawaye tace, "Shi kenan kuyi duk yadda kuka so, amma ku sani cewa na gama yanke shawara cewa lallai a ranar da aka ɗaura aurena da sarki zan kashe kaina." Daga wannan furuci Luzaiya ta tsuke bakinta bata ƙara cewa komai ba. Kawai sai ta koma gefe guda ta ci gaba da kuka abinta. Nan fa su jarumi Nazmir suka shiga cikin sabon tsahon hankali da matuƙar damuwa,sai da suka shafe rabin sa'a suna masu tunanin mafita,amma babu. Kawai sai jarumi Nazmir ya bada umarnin kowa ya sauya kamaninsa. Nan take aka bi umarnin. Ita kanta gimbiya Luzaiya sai da aka ɓatar da kamanninta duk da tsananin kyawun nan nata ya dishashe aka mai da ita mummunar gaske. Bayan an gama wannan shiri ne suka hawa dawakansu suka nufi ƙofar gari. Da zuwa suka ƙwanƙwasa ƙofar,maigadi ya leƙo ta cikin wata mitsitsiyar taga ya dube su yace, "Su waye ku?kuma daga ina kuka fito,har da kuke ƙoƙarin shigowar a tsakiyar dare haka?" Jarumi Nazmir ya make muryarsa yace, "Mu manzanni ne daga ƙasar Maskur mun zo da saƙo na musamman ga sarki daga hannun sarkinmu." Koda jin haka sai maigadin ya rufe wannan mitsitsiyar taga. Jim kaɗan sai suka ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar gaba ɗaya. Ita dai wannan kofar shiga gari ta kasance ƙatuwar gaske,domin tsawonta ya kai kamu ɗari shida haka kuma faɗinta ya kai kamu ɗari bakwai. An yi ta ne da zunzurutun ƙarfe mai kauri da nauyin tsiya. Mutum arba'in ne ke buɗe ƙofar waɗanda suka kasance ƙarti majiya ƙarfi. Bayan an gama buɗe ƙofar sai su jarumi Nazmir suka ga dakaru sama da mutum dubu ɗari a tsaitsaye bisa dawakai sun yi sahu a gabansu,kuma gaba ɗayansu cikin shirin yaƙi suke. Ba a bar jarumi Nazmir sun wuce ba sai da aka kawo fitila aka haske fuskokinsu aka yi nazarinsu sosai. Bayan hakan ma sai aka haɗa su da wasu dakarun mutum hamsin don su wuce dasu kai tsaye izuwa gidan sarki. Yayin tafiya gidan sarki ne zuciyar jarumi Nazmir da ta abokan tafiyarsa ta cika da mamaki domin ba su san dalilin wannan tsatstsauran matakin tsaro ba da aka ɗauka a garin. Haka kuma sai suka kasance cikin fargaba,domin idan suka bari aka kai su gidan sarki kai tsaye an tarwatsa shirinsu gaba ɗaya. Nan fa suka fara tunani da saƙe-saƙen zuci. Dabara dai bata faɗo musu ba,har suka shigo wata siririyar hanya matsatstsiya. Sai da suka zo tsakiyar hanyar sannan jarumi Nazmir ya dubi Bardil da Bagwan ya yi musu wata irin inkiya,suma sai suka yiwa sauran baradensu. Cikin gaggawa Nazmir,Bardil, Bagwan da baradensu suka zare takubba suka afkawa waɗannan barade hamsin masu yi musu rakiya izuwa gidan sarki. Cikin abinda bai wuce daƙiƙa ɗari da ashirin ba,suka karkashe su gaba ɗayansu ba wanda ya tsira. Nan da nan suka kwashe gawarwakin suka jefa cikin wata tsohuwar rijiya wacce babu ruwa a cikinta suka rufe,sannan suka sauya hanya suka nufi gidan mahaifin jarumi Nazmir wato sadauki Halufa. Abin ka da 'yan gari duk inda suka bullo suka ga dakarun tsaro sai su sauya hanya. Haka dai suka ta kauce-kauce da raɓe-raɓe har suka iso gidan sadauki Halufa ba tare da wani ya gansu ba. Koda suka hango gidan a kulle kuma suka ga dakarun sarki a kofar gidan a tsaitsaye suna kai-komo sai suka laɓe suka tsaya suna mamaki. Jarumi Nazmir ya dubi su Bardil yace, "Yaku abokaina ku yi sani cewa ruwa baya tsami banza. Lallai akwai wani mugun abun da wannan azzalumin sarki namu ya shirya a kanmu. Yanzu mene ne abin yi?" Bardil yayi gajeran tunani,sannan yace, "Bai kamata mu yi komai ba face mun gano abin da aka shirya a kanmu,ina ganin zai fi kyau mu je gidana da kuma gidan Bagwan don muga halin da suke ciki tun da mun ga halin da gidanku ke ciki. Ba tare da wata gardama ba suka tafi gidajen biyu. Abin da suka gani a gidan su jarumi Nazmir shi suka gani a gidan su Bardil da Bagwan. Nan fa hankalinsu ya dugunzuma ainun suka rasa abin da zasu yi. Daga can sai dabara ta faɗo musu suka haura gidan wani maƙocin Bagwan wanda ya kasance tsoho ɗan shekara tamanin da huɗu ana kiransa Hamlabi. Lokacin da suka shiga,Hamlabi na ta sharar barci har da munshari kai ka ce wata dabbar ce ke gurnani. Sai da suka zo kansa suka tsaya bai sani ba. Nan take Bagwan ya bugi tulelen cikin Hamlabi mai kama da kwarya. Hamlabi ya farka a firgice. Koda yaga zarata a gaban sa riƙe da takubba tsirara,sai ya taƙarƙare zai ƙwalla ihu. Cikin sauri Bagwan ya toshe masa baki da hannu yace, "Kada kayi ihu ya kai Hamlabi kayi sani cewa nine Bagwan maƙocinka, waɗannan kuwa su jarumi Nazmir ne abokaina da kuma sauran dakarun nan waɗanda sarki ya haɗamu da su don zuwa dauko gimbiya Luzaiya a can ƙasarsu." Koda jin wannan batu sai jikin Hamlabi ya kama karkarwa alamun tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarsa. Cikin sanyin jiki Hamlabi ya miƙe tsaye ya je ya dauko fitila,sannan ya zauna ya dubi Bagwan yace, "Yakai maƙocina ya ya akai kamanninka suka sauya haka gaba ɗaya? Na rantse da darajar tsufana ko kaɗan fuskarka ba ta yi kama da ta makocina Bagwan ba,haka kuma suma waɗannan abokan tafiyar taka basu yi kama da su jarumi Nazmir ba,amma kuma gaskiya na ji cewar muryarka na nan kamar yadda na santa." Koda jin wannan batu sai Bagwan ya yi murmushi,nan take ya ɗebi ruwa ya wanke fuskar tasa,sai ga kamanninsa sun bayyana ƙarara. Al'amarin da ya jefa tsoho Hamlabi cikin matuƙar mamaki kenan,ya buɗe baki galala yana kallonsa. Daga can kuma sai yayi ajiyar zuciya ya dubi Bagwan ya ce, "Haƙiƙa kun yi babbar hikima,in ba don kun ɓatar da kamaninku ba da tuni yanzu kun daɗe da zama gawarwaki." Koda jin haka sai mamaki ya kama su Bagwan. Nazmir yace, "Yakai wannan tsoho wai shin meke faruwa ne? Ka sani cewa mun je gidajenmu mun iske su a kulle,kuma dakarun sarki na gadinsu." Yayin da tsoho Hamlabi ya ji wannan tambaya sai ya gyara zama gami da gyaran murya,kuma ya saita muryarsa tasa ƙasa-ƙasa yace, "Bayan tafiyar ku izuwa birnin su gimbiya Luzaiya wani hatsabibin boka ya bayyana a ƙasar nan, kuma ya nunawa sarki duk abin da ya faru gareku a cikin wani madubin tsafi. Duk yaƙin da kuka yi har da yadda mahaifin gimbiya Luzaiya ya sallama kansa gareku,ku ka sare kansa,ku ka taho mun gani a wannan madubin tsafin. Kai na taƙaice muku labari dai har lokacin da gimbiya ta faɗa ƙasan tsaunin nan don kashe kanta jarumi Nazmir ya bita kawo izuwa haɗuwarku akan dutsen nan inda Nazmir ya harbe barewa duk kowa a garin nan ya gani a cikin madubin tsafin can a fadar sarki. Bayan an gama ganin hakan ne boka Sharmadu ya sanar da sarki cewa kada ya kuskura ya bar iyayenku daku a raye. Muddin yayi haka kuwa har abada ba zai auri gimbiya Luzaiya ba, kuma ku ne zaku zama sanadiyar ajalinsa. A dalilin haka ne sarki ya sa aka kamo iyayenku gaba ɗaya aka kai su cikin turakarsa aka ɗaɗɗauresu da sarƙoƙi,yanzu haka ana jira ne ku iso a kamaku a hada da su a kashe ku lokaci guda dan haka dokar boka Sharmadu ta kasance. Bisa wannan dalili ne na yi mamaki matuƙa da na ganku a cikin gidana don nasan cewa an saka matakan tsaro masu tsauri akanku,wai shin ma ya akai kuka shigo nan ba tare da an kama ku ba? Ina mai yi muku ta'aziya bisa rashin abokanan ku,kuma masoyanku waɗanda kuka taso tare tun yarinta." Sa'adda tsoho Hamlabi ya zo nan a zancensa sai idanunsa suka ciko da ƙwalla,domin tausayin su jarumi Nazmir ne ya turnuke shi. Jarumi Nazmir ya dafa kafaɗar tsoho Hamlabi yace, "Yakai wannan tsoho haƙiƙa ka taimakemu da ka sanar damu halin da ake ciki. Yanzu wacce irin shawara zaka bamu domin mu tsira da rayuwarmu da kuma rayuwar danginmu?" Tsoho Hamlabi yayi shiru bai ce komai ba yana tunani. Nan take Bagwan ya shiga tunanin matarsa Muslaiya,wacce ya tafi ya bari da tsohon ciki wadda a halin yanzu bai san halin da take ciki ba. Shi kuwa Bardil sai ya shiga nasa tunani. Jarumi Nazmir ya katse musu tunani da cewa, "Ba mu da isasshen lokaci na tunani mai zurfi. Ya kai tsoho Hamlabi me zaka iya cewa damu yanzu?" Hamlabi ya yi ajiyar zuciya yace, "Shawarar da zan ba ku guda daya ce kacal. Lallai kada ku je gidan sarki sai kun tabbata kun fara zuwa ɗakin bauta inda boka Sharmadu yake kun riske shi kun kashe shi. Muddin yana raye ba za ku iya kuɓutar da iyayenku da danginku ba daga gidan sarki. Ku yi sani cewa kashe boka Sharmadu daidai yake da neman jaki mai ƙaho. Babu wani abu da zan iya sake fada muku face na yi muku fatan samun nasara,kuma ina roƙo a gareku daku hanzarta barin gidana don kada ku shafa mini kashin kaji." Yayin da tsoho Hamlabi ya zo nan a zancensa,sai su jarumi Nazmir suka yi tsuru-tsuru suka hau duban juna. Bardil ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Haƙiƙa anan nahiyar bamu san irin ƙarfin bokaye ba,amma ga yadda nake samun labarinsu sun kasance ababan tsoro. Kai an ce ma idan boka ya bunkasa yana zama ubangijin mutanensa,saboda tsananin tsoro da girmamawa a gare shi. Ashe kuwa faɗa irin waɗannan mutane ba ƙaramin bala'i ba ne." Koda jin haka sai jarumi Nazmir yace, "Ai kuwa komai bala'insa ba zamu kasa tunkararsa ba. Ai dama yanzu haka rayuwarmu na cikin ɗaya-biyu. Kodai mu mutu ko kuma mu rayu. Tsakaninmu da sarki sai gaba,sai yaƙi. Ko dai yaga bayanmu ko mu ga bayansa. Ku tashi mu tafi ɗakin bauta don mu riski wannan shegen,tsinannen boka mu fara ƙaddamar dashi, sannan mu tunkari gidan sarki. Gimbiya Luzaiya kuma ba zamu bayar da ita ba face ɗayanmu baya numfashi a doron kasa." Jarumi Nazmir ya ɗaga takobinsa sama ya ce, "Waye zai bi bayana?" Take Bagwan da Bardil suka ɗaga nasu takubban suka kara a jikin takobin Nazmir. Cikin haɗin baki suka ce, "Muna tare da kai,komai wuya, komai dadi,mutuwa ce kaɗai zata raba mu." Sa'adda sauran baradan suka ga haka sai suma suka ɗaga nasu takubban suka yi iƙirarin abinda su Bardil suka yi. Nan take jarumi Nazmir ya wuce gaba ya kama katanga ya haura. Bardil,Bagwan,Luzaiya da sauran baradan suka yi yadda ya yi. Sannu a hankali su jarumi Nazmir suka yi ta kutsawa cikin gari,suna masu laɓe-laɓe su shiga nan,su fita can,har suka sami nasarar shiga cikin ɗakin bauta inda boka Sharmadu yake. Da shigarsu suka hau yin sanɗa da laɓe-laɓe,suna duddubawa don su yi masa kwaf ɗaya. Sai da suka duba ko'ina a cikin ɗakin bautar,amma ko ƙuda ba su gani ba. Al'amarin da ya fusata su kenan, kuma hankalinsu ya yi mummunan tashi. Ba zato,ba tsammani kuma sai suka ji an bushe da dariya. Dariyar ta cika ɗakin bautar gaba daya, babu dadin ji. Cikin fushi da kakkausar zuciya jarumi Nazmir yayi tsawa yace, "Yakai baƙin la'ananne in ka isa namiji ka fito fili mu yi gaba da gaba. Ai ba a san maza da ɓuya ba. Na rantse da darajar iyayena muddin za mu yi fito na fito sai na kai ka kushewa." Koda gama faɗin hakan sai aka sake bushewa da dariya. Lokaci guda kuma dariyar ta ɗauke,sai ga boka Sharmadu ya bayyana a tsakiyarsu jarumi Nazmir riƙe da wata isgar tsafi wadda aka yi da jelar zaki. Boka Sharmadu ya kasance matashi,ɗan kimanin shekara talatin da bakwai. Garjejen ƙato ne,mai ƙirar sadauki. Hannayensa biyu a cike suke da layu. A ƙugunsa akwai wani gurun tsafi ja,babu takalmi a ƙafarsa. A kansa babu gashi ko sili da ɗaya, kuma a aske yake ban da sheƙin salsal babu abin da kan ke yi. Idanunsa manya-manya ne,kuma ƙwala-ƙwala ababan tsoro. Bashi da gemu ko saje sai wani murtukeken gashin baki tamkar tsumma aka nannada masa. Yana da ƙaton hanci,mai faɗin ƙofofi. Bakinsa kuwa wangameme ne, cike da wargatsatstsun haƙora marasa kyan gani. Kai duk inda ake neman mummuna da an ga boka Sharmadu an gama neman,don shi ne ƙarshen muhawara. Sharmadu ya dubi jarumi Nazmir yace, "Kai samari iya bakinka kada kuruciya ta dubeka,ta ɗebe ka,ta jefa ka cikin bakin kura ka halaka a banza. Ka yi sani cewa nine boka Sharmadu shiryayyen da ya shirya tun masu neman shiri basu farka daga barci ba. Nine dodan mazajen duniya,kuma nine sa gudu maganu ƙi gudu. Nine ɗaya tamkar dubu." Nazmir ya sake daka masa tsawa yace, "Ƙarya kake ƙaramin barde yau ka hadu da gwarzo,ɗaya maganin gwarzaye dubu. Yau sai takobina ta sha jininka sannan ta je ta sha jinin mai gidanka,wannan azzalumin sarkin wanda ya daɗe yana cutar da iyayenmu da sauran talakawa." Koda jin wannan batu sai boka Sharmadu ya turɓune fuska, muninsa ya ƙaru kamar an shaƙe alade. Kafin wani daga cikin su Nazmir ya yi wani yunƙuri tuni Sharmadu ya nuna jarumi Nazmir da wannan isgar tsafi da ke hannunsa,kawai sai wata irin iska mai ƙarfi ta ɗaga Nazmir sama ta rinƙa makashi a jikin ginin ɗakin. Koda ganin haka sai Bardil,Bagwan da sauran barade suka ruga kan boka Sharmadu da nufin gididdiba shi. Kawai sai ya juyo ya dube su. Take wani haske ya fito daga cikin idanunsa ya buge su duk suka ƙame,suka zama gumaka. Sharmadu ya ci gaba da ƙyalƙyala dariya. Har a yanzu iskar nan bata daina gwara jarumi Nazmir ba a jikin ginin dakin. A wannan lokaci gimbiya Luzaiya na daga gefe guda a tsaye ita kaɗai tana ganin abinda ke faruwa. Koda ta ga halin da Nazmir ya shiga ya zamana kansa ya fashe jini na zuba kuma ya ji raunika a sassan jikinsa,harma hankalinsa ya fara gushewa sai hankalinta ya dugunzuma,bata san sa'adda idanunta suka cika da ƙwalla ba,ta fara kuka. Nan take ta tuna lokacin da jarumi Nazmir ya sallama rayuwarsa ya bita cikin ramin nan mai tsananin zurfi. Haka kuma ta tuna sa'adda ya ceci rayuwarta sa'adda kura ta kawo mata farmaki. Ta tuna da irin kulawar da yayi mata yayin zamansu a cikin jeji. Nan take gimbiya Luzaiya ta ji cewa duk duniya babu abin da take so sama da jarumi Nazmir. Cikin zafin nama ta daka tsalle ta dirga a gadon bayan boka Sharmadu ta ɗane wuyansa. Kawai sai ta kama isgar tsafin dake hannunsa ta matseta. Ba zato sai taga boka Sharmadu ya kurma ihu. Gaba ɗaya sassan jikinsa suka kama karkarwa ya hau layi kamar wanda ya sha gida ya bugu. Ba shiri ya ƙwalawa aljaninsa kira. Kawai sai Luzaiya taji an figeta daga kan wuyan Sharmadu an jifa da ita,tamkar tsakuwa aka wurgar. Luzaiya ta faɗi can gefe ɗaya sumammiya. Wani gabjejen aljani ya bayyana mai kama da goggon biri,jikinsa gaba ɗaya gashi ne mai kauri da tsini tamkar ƙayar bushiya. Kuma ya kasance baƙı wuluk,muninsa ya linka na boka Sharmadu sau ɗari. Boka Sharmadu ya miƙe tsaye da ƙyar yana tangaɗi,sannan ya dubi aljanin yace, "Yakai Dumudulmus na umarce ka da ka kwashe mu nan gaba ɗaya ka kaimu fadar sarki yanzu-yanzu." Dumudulmu yayi sujjada ga boka Sharmadu yace, "An gama sarkin bokaye." Kamar ƙiftawar ido,ya kwashe su gaba đaya ya ɓace tare da su. Bai bayyana a ko'ina ba sai a fadar sarki Fahalul Bahafus inda suka iske fada ta cika maƙil ana fadanci. Boka Sharmadu ya risina a gaban sarki ya kuwashi gaisuwa sannan yace, "Ya sarkin duniya ga masoyiyarka gimbiya Luzaiya,kuma ga manyan abokan gabarka na kawo maka kamar yadda na ɗauki alƙawari. Don haka sai ka gaggauta hallakar da su ta hanyar da na sanar maka." Koda jin haka sai farin ciki ya lulluɓe sarki Fahalul Bahafus. Nan take ya sa aka je aka fito da su sadauki Halufa,a cikinsu harda Muslaiya matar Bagwan da kuna Lamiz da sauran iyayen abokan nan su jarumi Nazmir. Koda Lamiz ta ga ƙyallenta a goshin jarumi Nazmir sai ta fashe da kuka don ta san cewa yayanta ya mutu. Shi kuwa Bagwan yaga wani kyakkyawan yaro a hannun matarsa Musalaiya. Da shi da yaron kamanninsu ɗaya tamkar an tsaga kara. Nan take farin ciki ya kama Bagwan ya yunƙura da nufin ya ruga wajen su amma damar hakan bata samu ba,don boka Sharmadu ne ya nuna shi da isgar tsafi. Take wata baƙar sarƙa murtukekiya ta ɗaure hannayensa da kafafunsa. Suma sauran iyayen abokanan su Nazmir da basu ga 'ya'yansu ba,sai suka fashe da kuka. Nan take aka tusa ƙeyar su jarumi Nazmir izuwa tsakiyar fada aka tsaida su gaban wasu manyan turakan gini inda aka saba kashe mutane waɗanda suka yi laifi ga sarki. Yayin da sadauki Halufa da jarumi Nazmir suka dubi juna sai Halufa ya murtuke fuska. Lokaci guda idanunsa suka ciko da ƙwalla ya dubi jarumi Nazmir cikin fushi yace, "Ya kai ɗana haƙiƙa kaci amana ta da kaje ka kashe mahaifin gimbiya Luzaiya don kawai ka biya buƙatar wannan azzalumin sarki namu. Kayi sani cewa har abada ba zan yafe maka ba,face ka hana auren sarki da Luzaiya,kuma ka kuɓutar da rayuwar mu nan gaba ɗaya." Yayin da jarumi Nazmir ya ji wannan batu daga bakin mahaifinsa sai ya durƙusa ƙasa da ƙyar bisa gwiwoyinsa sakamakon raunikan da ke jikinsa kuma har yanzu jini na zuba a kansa,kuma jiri na ɗibarsa. Cikin ƙarfin hali ya dubi sadauki Halufa a lokacin da idanunsa ke rufewa da buɗewa tamkar mai jin barci yace, "Yakai Abbana ka yi mini aikin gafara,ka sani cewa ban aikata wannan mummunan aiki ba bisa sani da son zuciyata. Lallai wannan sarki namu yayi mana dole ne kamar yadda ka sani idan kuwa muka saɓawa umarninsa rayuwarmu da taku na iya salwanta. To yanzu ma dai ga shi kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba,tunda dai mun sha wahala mun biya buƙatar tasa,amma kuma sakamakonnu shi ne kisa. Haƙiƙa wannan sarki ya cika azzalumi." Gama faɗin hakan ke da wuya sai ga sarki ya fito. A ɓangaren hannunsa na dama gimbiya Luzaiya ce a tafe ta sha kwalliya,kuyangi na biye da ita. A wannan lokaci duk 'ɗa' namijin da ya ƙyallara ido ya ga gimbiya Luzaiya dole ne ya ruɗe,ya ɗimauce saboda tsananin kyawunta da ya bayyana a fili ƙarara. Fuskarta na ta sheƙi da annuri,amma cikin zuciyarta baƙin ciki ne a lulluɓe, kamar zata fashe. Hawayen takaici yayi sintiri bisa kyawawan kumatunta,ta hanga, ta dubi inda jarumi yake ta ganshi cikin mawuyacin hali,kuma cikin sarƙa a ɗaɗɗaure. Kawai sai ta fashe da kuka. Nan da nan sarki ya sa aka zaunar da ita,shima ya zauna akan karagarsa,sannan yasa aka fara shirye-shiryen ɗaura aurensu. Su kuwa su jarumi Nazmir sai aka jera su a gaban wani ƙaton basamuden bawa baƙin fata wanda ya riƙe wata zabgegiyar adda. Shirin da aka yi shine da zarar an gama ɗaura auren sarki da gimbiya Luzaiya sai wannan baƙin bawa ya sare kawunansu jarumi Nazmir ta yadda jininsu zai zuba cikin wata ƙatuwar tukunyar tsafin boka Shamradu. A kowanne ɓangare na fadar gabas da yamma,kudu da arewa dakaru ne birjik tsaitsaye cikin shirin yaƙi,shi kuwa boka Shamradu na tsaye a tsakanin karagar sarki da ta gimbiya Luzaiya yana murmushin farin ciki, don ya san cewa saura ƙiris buƙatarsa ta duniya ta cika. Tsakanin boka Shamradu da sarki akwai wata yarjejeniya ta cewar idan ya taimaka masa yaga bayan maƙiyansa,shi kuma zai bashi kyautar babban gari daga cikin ƙasarsa ya mulke su,kuma zai zama makusanci a fadar sarki. Lokacin da aka ci gaba da harkokin ɗaurin aure, sai gimbiya Luzaiya ta dulmiya a cikin kogon tunani, inda take cewa da kanta,tabbas idan ta kuskura ta auri wannan sarki rayuwarta ta gama gurbata gaba daya. Babu wani abu da zai sata farin ciki a duniya face ta auri Jarumi Nazmnir masoyin da shi kadai ne zai iya mayar da ita kasarsu ta sadu da mahaifiyarta, kuma ta hau kan karagar mulkin da ta gada. Ta ya ya za ta sami wannan nasara? Babu wata dama face ta tsaida wannan daurin aure, kuma ta ceci rayuwar su jarumi Nazmir. To wai shin me za ta yi ta tsaida ɗaurin auran, kuma me za ta yi ta iya ceton rayuwarsu Nazmir din? Wannan tanbaya ce wadda gimbiya Luzaiya ta yiwa kanta, kuma ta kasa gano amnsarta. Tana cikin haka ne ta tuno da abin da ya faru dazu a dakin bauta tsakaninta da boka Sharmradu. Koda ta tuno wannan al'amari sai ta mike zumbur cikin zafin nama ta shammaci boka Shamradu ta fisge isgar tsafinsa daga hannusa ta cauɗa masa ita a wuyansa. Kawai sai aka ga boka Shamradu ya kankance ya zama ƙanƙanin dutse. Nan fa sarki ya zabura ya faɗa bayan karagarsa ya ɓoye dakaru suka yi ca kan gimbiya ita kuwa ta nunu su da isgar tsafin nan suma sai suka kuma suka zama gumaka. Nan fa fada ta hargitse aka hau guje-guje da iface-iface. Gimbiya Luzaiya ta ruga inda su jarumi Nazmir suke ta nuna sarkar da ta ɗaure su da isgar tsafi, take sarkar ta narke ta zama ruwa. Koda ta ga sun kuɓuta sai ta miƙawa jarumi Nazmir isgar tsafin, ta ce rike wannan ta zama makaminka, kai ne namiji ni kuwa macece ban saba da gumurzu ba. Cikin hanzari Nazmir ya karbi isgar. A daidai wannan lokaci ne sarki ya fito daga maboyarsa koda ya hango iskar tsafi a hannun jarumi Nazrnir sai ya dakawa dakarunsa tsawa ya ce, "Maza ku raba shi da wannan isgar tsafin ku kawo mini ita nan." Gaba daya dakarun wajen suka yi caa kansa, shi kuwa ya rinka nuna su da ita sai dai ka ga tsawa na dira kansu, suna zubewa kasa matattu. Wani lokacin kuma wuta ce jikinsu su kone kurmus. Wani lokacin kuma dai kawai aji wuyansu na karyewa rakakas, ko kuma a ga kibiyoyin tsafi na jukunansu. Anan fa yaki ya yi yaki, Nazmir zubar da maza, amma sai ka waɗansu na daɗa shigowa cikin fadar kamar ba za su kare ba. A wannan yaki sadauki Halufa ya taimakawa jarumi Nazmir matuka, domin shi ma tsohuwar jarumtarsa ce ta motsa, ya dunga girbar maza kamar yana sassabe a gona. Haka ma su Bagwan sun taka muhimmiyar rawa a wannan yaki. Yayin da aka shafe sa'a uku ana wannan yaƙi amma ya ki karewa sai hankalin su jarumi Naznir ya tashi. Don haka sai sadauki Halufa ya bada shawarar a bude hanya da ƙarfin tsiya a fice daga cikin fadar don a fita daga garin gaba daya. Ai kuwa haka aka yi, ámma duk da haka sai da sarki ya ja tawagar miliyoyin mayaka aka bi bayansu Nazmir har aka riske su a daji,sannan aka ci gaba da yaƙi. Yayin da gumurzu ya yi gumurzu,bala'i ya yi bala'i sai isgar tsafin nan ta subuce daga hannun jarumi Nazmir ta fadi ƙasa. Ai kuwa tana faduwa sai kasa ta tsage ta fada ciki. Take kasar ta rufe kanta tamkar an binne gawa a kabari. Koda sarki da dakarunsa suka ga babu isgar tsafi a hannun jarumi Nazmir sai suka yi kukan kura suka afka musu. Nan fa aka buɗe sabon lale,aka ruguntsume da mummunan yaƙi. Wannan yaƙi dai ba'a gama shi ba,sai bayan wata shida. Ma'ana bisa dole aka rinką tsayawa ana ja da baya musamman idan dare yayi. Da safe kuwa sai a sake gamuwa a filin daga a ci gaba da rubdugu. Tsakanin mutanen sarki da mutanan su jarumni Nazmir. A wannan yaƙi ne sadauki Halufa da dukkanin iyayen abokan Nazmir suka rasu,Bagwan ma a wannan yaki ne ya rasa rayuwarsa ya zamana jarumi Nazmir,gimbiya Luzaiya, da Bardil ne kaɗai suka rayu, suma ba su tsira ba sai da taimako ya zo musu daga birnin gimbiya Luzaiya na dakaru miliyan dubu huɗu. Jarumi Nazmir ne ya kama azzalumin sarkin garinsu da ƙarfin tsiya ya đaga sama ya fyaɗa da ƙasa. Take sarki ya sume. Kafin ya farfaɗo Nazmir ya kama wuyansa ya karya ya yar da gawarsa anan ƙasa. Bayan an gama yaƙi ne aka koma birnin gimbiya Luzaiya inda aka ɗaura auren jarumi Nazmir da gimbiya Luzaiyà ya zauna tare da ita a ƙasarta. Mutanensa suka so ya koma gida ya zama sarki,amma ya ƙi yace ya bar gida har abada,tun da ba shi da iyaye a garin bashi da kowa sai Bardil. Don haka sai aka baiwa Bardil sarautar ƙasar." Lokacin da sarki Dujalu ya zo nan labarinsa sai ya yi shiru ya dubi boka Hajurul Mukurus,tsoho Rafkanagu da Ruziyal yace, "yanzu ya ya kuka ji wannan hikayar ina fatan dai kun ji daɗinta?" Ruziyal yace, "Ƙwarai kuwa ai na ji daɗinta,musamman yadda na ji ƙarshen wannan azzalumin sarki sai dai kuma na ji tausayi matuƙa da ya zamana iyayen jarumi Nazmir sun mutu har da sauran abokansa ya rage mutum ɗaya jal daga cikin su, wanda hakan ne ya sa ya ji garin nasu ya fita daga ransa." Tsoho Rafkanagu yace, "Ƙwarai kuwa nima haka na ji a raina, amma fa gaskiya wannan hikayar ta cika tsawo ina fatan ta gaba ba ta kai wannan yawa ba?" Sarki Dujalu ya bushe da dariya yace, "Ai hikayar da zan ba ku nan gaba ta ninka wannan sau biyu a tsawo,kuma akwai abubuwan al'ajabi da yawa a cikinta,sai ku gyara zama ku kasa kunnuwanku don ku ji ta." Caraf sai boka Hajarul Mukursu yace, "Ranka ya daɗe zai fi kyau dai kasa a sake kawo mana sihirtaccen shayin nan naka mu sha, don mu ƙara kimtsawa tun da dai ka ce hikaya ce mai tsawo." Sarki Dujalu ya sake bushewa da dariya yace, "Wannan babu laifi." Nan take ya ce, aje a gayawa kuyanga mai shayi ta kawo. Cikin hanzari wani bafade ya miƙe ya shiga cikin gida. Wannan shi ne abin ya faru a fadar sarki Dujalu bayan ya gama basu labarin hikiyar jarumi Nazmir da gimbiya Luzaiya. ********* Al'amarin su jarumi Hubairu kuwa,bayan sarki Lu'umanu ya sace gimbiya Sima ya ɓace da ita a cikin sararin samaniya,sun neme shi sun rasa, sai hankalin Hubairu ya ƙara dugunzuma, ya rasa abin da ke masa dadi, a duniya. Koda ganin halin da ya shiga sai sai aljani Abtarul Hudes ya shiga rarrashinsa yana mai kwantar masa da hankali cikin daɗaɗan kalami, da nuna masa mubimmancin rungunar ƙaddara. Hubairu ya yi shiru bai ce komai ba. Daga bisani sai ya dubi Abtarul Hudes yace, "ya kai Abtarul Hudes ka yi sani cewa shi SO cuta ce,wadda in dai ta shigi mutum har abada ba zai warke ba,face ya sadu da masoyinsa. Ka yi sani cewa sarki Lu'umanu va zama babban maƙiyi na a duniya, tun da yana son ya raba ni da masoyiyata, kuma yana son ya abin da nake so kuma yana son daƙile addinina. Abinda nake so da kai kawai shine ka ƙara azama don mu isa birnin Teheren da wuri kafin Mushrikin nan ya samu damar aurar masoyiyata. Idan hakan ta faru zan kasance cikin baƙin ciki. Da yardar Alah zamu sami nasara akansa,kuma tsafinsa ba zai sami tasiri akan mu ba." Yayin da aljani Abtarul Hudes ya ƙara ƙarfin kaɗawar fukafukansa, ya zamana suna masu tsananin gudu sai keta gajimare suke tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya. A can birnin Teheren kuwa tuni sarki Lu'umanu ya sauka da gimbiya Sima har ma ya tashe ta daga wannan barci da ta daɗe ta na yi,amma bai tashe tan ba, sai bayan ya tsafanceta ya juyar da tunanin ƙwaƙwalwarta ya zamana ta mance da duk abubuwan da suka faru gareta a baya. Wato ƙwaƙwalwar ta zama sabuwa tamkar ta jaririyar da aka haifa yau babu komai a cikinta face abin da za'a sa mata. A cikin turakar sarki Lu'umanu bisa wani ƙasaitaccen gado na alfarma. Gimbiya Sima ce a zaune fuskarta cike da murmushi da annuri,kuyangi na ta shige da fice a ɗakin ɗauke da kayan marmari iri-iri da kuma sauran nau'in abinci da abin sha. Duk suna kaiwa gimbiya Sima ne don ta zaɓi abin da za ta ci amma har yanzu ba ta zaɓi komai ba. Daga ƙarshe dai naman ɗawisu ta ci,sannan ta sha ruwan inibi. Bayan ta gama kimtsa cikin ta ne,kowa ya fita ya barta,sannan sarki Lu'umanu ya shiga ciki ya risketa,da shigarsa ya ƙare mata kallo sama da ƙasa ya ga irin tsananin kyawunta sai farin ciki ya turnuƙe shi ya ji kamar an bashi duniyar nan gaba ɗaya. Sarki Lu'umanu ya zauna a gefen gadon kusa da gimbiya Sima suka dubi juna suna masu murmushi,mai nuna tsantsar so da bege. Lư'umanu yace, "Yake masoyiyata ki yi sani cewa gobe i yanzu kin zama matata,ina nufin an ɗaura mana aure,yanzu me kike so a cikin faɗin duniyar nan na baki shi,koda kuwa yana ajiye a can bangon ƙarshen duniya?" Gimbiya Sima ta ƙyalƙyale da dariya tace, "Bana son komai daga gareka ya masoyina face ka yawata dani ko'ina da ina acikin gidan sarauta don na marewa idanuna da kallo." Koda jin wannan batu sai sarki Lu'umanu ya bushe da dariya sannan yace ai wannan bukata taki a komai sauƙi ce a wajena. Nan take Lu'umanu ya nuna tagar ɗakin da hannunsa kawai sai tagar ta buɗe daddumar tsafinsa ta shigo ta cikin tagar. Daddumar ta sauko ƙasa ta dira a gabansa kawai sai ya kama hannun Gimbiya suka hau kan daddumar suka zauna. Zaman su ke da wuya daddumar ta tashi dasu sama ta ringa shiga dasu saƙo saƙo lungu lungu na gidan sarautar kai har cikin kurkukun nan na ƙarƙashin ƙasa inda aka taɓa tsare aljani Markahul sabus sai da suka shiga. Anan né suka riski waziri kuddaru a ɗaure cikin sarƙa an ajiye abinci a gabansa ya zubawa abincin idanu yana kuka,koda ya ɗago kai yaga Gimbiya Sima tare da sarki Lu'umano bisa daddumar tsafi saiya miƙe zumbur ya dubeta yana mai cewa ranki ya daɗe ki ceceni kisa a fitar dani daga cikin wannan mugun wuri,ki tuna cewa ni ne waziri Kuddaru babban wazirinki. Koda jin haka sai Gimbiya Sima ta dubi Kuddaru tace, "Waye kai,a ina kasanni? Waishin ma a ina muka taɓa haɗuwa har da zakace ka sanni?" Yayin da Kuddaru yaji wannan batu sai ya cika da mamaki baisan sa'adda ya fashe da kukaba yana mai cewa, "Yanzu har daɗin daula yasa kin manta dani. Ranki ya daɗe kiji tsoran Ubangijin da kikayi imani da shi ki ceci rayuwata." Girnbiya Sima ta dubi sarki Lu'umanu tace, "Wannan kuma wane wawan mutum ne haka kamar mahaukaci?" Lu'umanu ya bushe da dariya yace, "Ai kuwa mahaukacine na ƙwarai,asalinsa bawana ne mai kula da bargar dawaki. Rana ɗaya ya sani taɓin hankali ya rínga kashe mini đewakai. Ni kuma da naji haushin abin daya aikata sai nasa aka kamo shi nan aka ɗaure. Bazan yi masa komaiba har sai na kama babban maƙiyina da'ake kira Hubairu sannan zan haɗasu tare nayi musu kisan gilla." Sima ta sake duban sarki Lu'umanu tace, "Waye kuma Hubairu,kuma menene ya haddasa muguwar gaba a tsakaninku?" Lu'umanu ya numfasa yace, "Hubairu wani hatsabibin yarone mai taurin kai da ƙarfin sihiri bashi đa burin da yafi ya rabani dake kuma ya hallakani." Koda jin haka sai gimbiya Sima a dafe ƙirji cikin alamun razana tace, "Ya kai masoyina duk wanda ya nemi shiga tsakanina da kai sai naga bayansa. Domin duk duniya babu abinda nake so sama da kai. Duk ranar da ka kama Hubairu ka bani dama na tsireshi da mashi da hannuna don hankalina ya kwanta na tabbatar da cewa na kashe maƙiyinmu." Koda jin haka sai sarki Lu'umanu ya bushe da dariya yana mai cewa tabbas nayi miki alkawarin wannan dama kece zaki kashe maƙiyinmu da hannun ki. Lu'umanu yaci gaba da rusa dariyar ƙeta har suka bar wannan wuri inda kuddaru ke zaune yana ta faman kuka da mamakin abin da ya faru tsakaninsa da Gimbiya Sima. Kashe gari da sassafe fadar sarki Lu'urnanu ta cika ta batse da jama'a. Baƙin sarakuna kuwa suka hallara daga manyan ƙasashe don amsa gaiyatar sarki Lu'umanu bisa ɗaurin aurensa da gimbiya Sima. Nan take aka fara kaɗe kaɗe da bushe bushe,kayan ciye ciye dana shaye shaye kuma suka yawaita a fadar fiye da buƙatar Jama'a. Sarki Lu'umanu da Gimbiya Sima suka fito daga cikin gidan sarauta suka zo suka zauna akan karaga mai ɗaura aure ya fara aikinsa. Ana cikin wannan haline aka ga aljani Abtarul hudes ya baiyana a sararin sama ɗauke da jarumi Hubairu. Koda sarki Lu'umanu ya ɗaga kai yayi arba dasu sai ya hura musu wata irin iska mai sanyi daga cikin bakinsa,take suka faɗo ƙasa sumammu. Sarki Lu'umnu ya bushe da dariya yasa aka ɗauki jarumi Hubairu aka banƙareshi a jikin dirka sannan aka ɗaukeshi da igiya nan take yasa aka dauko kuddaru daga cikin kurkuku aka daureshi kusa da Jarumi Hubairu. Kuddaru ya dubi jarumi Hubairu yaji daɗi a ransa yace tunda mun sake saduwa babu mamaki wannan karon ka ceci rayuwata. Maimakon yaji Hubairu yace wani abu sai yaji yayi shiru. Koda ya dube shi da kyau sai ya fuskanci cewar ai ko motsi ba yayi bare ya taɓuka wani abu. Nan fa Kuddaru ya rikice ya kuma firgice ya ƙaddarawa kansa mutuwa. Adai dai wannan lokaci sarki Lu'umanu ya baiwa Gimbiya Sima mashi yace, "Ungo kije ki tsire wancan saurayin shine babban maƙiyinmu a duniya." Take ta karɓi mashin ta nufi inda Hubairu ke ɗauke fuskarta a murtuke ba tausayi. Wannan shine abin da ya faru a fadar sarki Lu'umanu na birnin teheren bayan ya sami nasarär tsafance zuciyar Gimbiya Sima ta soshi fiye da komai a duniya kuma yayi sa'ar kama jarumi Hubairu da aljani Abtarul Hudes. Al'amarin su Boka Durfus kowa bayan sun gama tattaunawa dangane da yadda zasu sami nasara akan Boka Shamharu Shahararre sai sukayi shiri suka nufi garin da sarkin ɓarayin Aljanu yake. Suna cikin tafiya a sararin samaniya su biyar kawai sai suka gawani abu mai kama da bakan Gizo yasha gabansu kuma abin na fitar da tartsatsin wutane tamkar batoyi ita kuwa wutar ta kasance mai hucin zafi kana doso ta sai kaji kamar ana dafa naman jikinka, cikin tsananin tsoro su duka biyar din suka ja da baya a sararin samaniya. Markahul sabus,bokanya Samaratu,boka Jinshan,boka Sulbaini da boka Durfus su kayi tsuru tsuru kamar jiƙaƙƙen tsumma a rüwa suna masu duban juna Kowannansu ka duba kasan a matuƙar tsorece suke dan jikinsu ma karkarwa yake yi cikin ƙarfin hali Markahul Sabus ya dubi aljani Durfus yace, "Yakai sabon boka mai abin al'ajabi mene ne wannan abun da ya sha gabanmu?" Durfus ya haɗiyi miyau da ƙyar yace, "Ashsha,kallonmu yake gaba ɗaya. Haƙiƙa daga yanzu tamu ta ƙare,duk wani buri da muke da shi cewa wannan abin da kuke gani a gabamu ba komai ba ne face boka Shamharu shahararre." Durfus na gama faɗin hakan suka ji an ƙyalƙyale da mahaukaciyar dariya. Nan take bakan gizon nan ya rikiɗe ya zama aljani Shamharu yana mai ƙyalƙyala dariyarsa,har wani irin tururin masifa ne ke fita daga bakinsa. Nan take tsoro ya ƙara baibaye su Markahul Sabus suka ruɗe, suka rasa abin yi. Shamharu ya daka musu tsawa yace, "Ku ƙananan ƙwari ku sani cewa kun yi sake na rigaku kwana don haka dole ne na rigaku tashi. Ina sanar muku cewa a yau ne na fito daga halwar tsafina kuma na gano hanyar da zan bi na zama MATSATSUBI a cikin wasu 'yan shekaru. Duk wani shiri da kuke yi a kaina na san da shi. To ku sani cewa na gaba yayi gaba na baya kuwa sai labari. Ni Shamharu shahararre na gama da duniya, don na san gaba dayan sirrin cikinta. Da sannu zan mallaki komai da da kowa. Ku kuwa ba zan hallaka ku ba, yanzu zan tafi da ku ne izuwa kurkukun fadata da ke can tsibirin Baharzus na ajiye ku a matsayin fursonini. Ba zan sake ku ba har sai na zama MATSATSUBI nan da shekara goma sha tara da wata shida masu zuwa." Koda jin wannan batu sai su Markahul Sabus suka yunƙura suka juya da baya don su gudu, amma sai suka ji wata irin iska mai ƙarfin tsiya ta tsaida su a waje daya,sun kasa yin gaba ko baya. Shamharu ya dube su ya sake ƙyalƙyalewa da dariya,kawai sai ya buɗe tafin hannunsa guda. Take su Markahul Sabus suka zama 'yan ƙanana,mini mini suka faɗa tafin hannun Shamharu,shi kuwa sai ya buɗe aljihun rigarsa ya watsa su ciki. Suka ji kamar an jefa su cikin rijiya gaba dubu. Take Shamharu ya rikiɗe ya zama bakan gizo sannu a hankali bakan gizon ya ɓace ɓat a sararin samaniya. Wannan shi ne abin da ya faru ga su boka Jinshan bayan sun yi mugun gamo da boka Shamharu a sararin samaniya yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin sarkin ɓarayin aljanu. Aljanin dashi kaɗai ne zai iya zuwa fadar boka Shamharu ta tsibirin Bahar Zus ya sato addar tsafi. A can fadar sarki Dujalu kuwa, jim kaɗan da aika bafade cikin gida,sai ga kuyanga ta fito ɗauke da butar sihirtaccen shayi. Koda shigowarta cikin fadar sai sarki Dujalu ya dubeta yace, "Maza ki zuzzuba mana shayin nan mu sha har kowa ya gamsu." Cikin sauri kuyanga ta cika aikinta. Tana gamawa ta shige cikin gida riƙe da butar shayin wacce babu ko digo guda a ciki. Sarki Dujalu yayi murmushi gami da gyaran murya yace, "Shin akwai mai buƙatar ƙarin shayin ne?" Gaba ɗayansu suka ce, "A'a." Sarki Dujalu ya sake yin murmushi a karo na biyu,yace, "To sai ku nutsu da kyau domin yanzu zan baku labarin Hikayar wata azzalumar boka da ake kira Tazibul Luhucul da manyan sarakunan duniya guda shida. Wannan al'amari ya faru ne a birnin Sin. ldan kuka nutsu sosai zaku ji abubuwan al'ajabi da kuma tsabar tuggu da kisisina waɗanda za su amfani rayuwarku wajen kare kanku daga sharrin maƙiya da mahassada...... A wani zamani mai tsawo da ya shuɗe a cikin ƙasar Sin an yi wata gagarumar bokanya mai suna Tazibul Luhucul. Masu harsashe a wannan zamani na ta babu wata 'ya mace mai yawan shekarunta a duniya,domin a ƙallah bata bar duniya ba sai da ta shekara ɗari da saba'in. Har ta mutu ba ta taɓa yin aure ba,kuma ba ta taɓa haihuwa ba. Tazibul Luhucul ta fara bokanci ne tun tana da shekara bakwai sa'adda ta yi ƙawa da wata aljana 'yar sarkin birnin Sin wadda ake kira Saubatul Azwas. An haifi Tazibul Luhucul da Saubatul Azwas shekara ɗaya, rana ɗaya,kuma lokaci guda. Tun sa'adda sarkin aljanun ya fuskanci baka sai ya ƙudure a ransa cewa sai ya haɗa ƙawance tsakanin 'yarsa da wannan bil'adama wadda aka haife su rana guda. Saboda haka tun Tazibul Luhucul ba tafi shekara biyu a duniya ba ya zamana ya buɗe mata idanu tana iya ganin kowanne irin aljani ba tare da ta tsorata ba. Kuma kullum sai ya kawo mata Saubatul Azwas sun yini suna wasa tare. Tun mahaifiyar Tazibul Luhucul ba ta fuskanci abin da ke faruwa ga 'yar ta har ta fara ganin abubuwan al'ajabi a tare da ita. Sau tari sai ta ga Tazibul Luhucul ta ɗauki abu mai nauyi wanda sai ƙarti arba'in sun taru za su iya ɗaukarsa. Haka kuma duk maganar da za ta yi sai ka ji cewar magana ce ta babbar mace mai hankali da nutsuwa. Daga nan kuma sai ta fara faɗin abubuwan da zasu faru a gaba a birnin Sin. Duk abin data faɗa kuwa sai a ga ya tabbata. Haka ma duk irin cutar da mutum ke yi in dai aka ɗauko shi aka kawo shi gaban Tazibul Luhucul a bashi magani take zai warke. Yayin da jama'ar birnin Sin suka ga baiwar Tazibul Luhucul ta yi yawa sai suka shiga girmamata ainun,har ta kai cewa ma ana bauta mata,kuma duk dokar da ta kafa kowa na binta,har shi kansa sarki Alyasil buhus wanda ke mulkin jama'ar kasar Sin gaba ɗaya a wannan lokaci. Lokacin da sarki Alyasil Buhus ya ga irin girmamawar da akewa Tazibul Luhucul ya zamana an bata matsayin abin dogaro sai hankalinsa ya dugunzuma ya fara tunanin cewa lallai da sannu wannan bokanya za ta raba shi da karagar mulkinsa. A bisa wannan dalili ne ya tara 'yan majalisarsa a ɓoye don su tattauna wannan matsala a keɓaɓɓen wuri. Bayan dukkanin 'yan majalisar sun hallara sai sarki ya miƙe ya gaishe su sannan yace, "Yaku 'yan majalisata kun sani cewa a halin yanzu wannan sarauta tamu ta shiga wani mugun hali na rashin ɗorewa domin kuwa yanzu talakawan mu basa jin maganar kowa face ta bokanya Tazibul Luhucul. Tabbas al'amarin wannan bokanya da ban tsoro yake,kun sani cewa ba zamu iya yin yaƙi da ita ba,kuma ba zamu iya korarta ba daga cikin ƙasar, yanzu mene ne abin yi? Ban tara ku anan ba dan komai sai don mu yanke shawarar da za ta fishshe mu don mu tsira da mutuncin mu,kuma mu tsira da mulkinmu." Yayin da sarki Alyasil Buhus ya zo nan a zancensa sai gaba dayan 'yan majalisar suka ruɗe, hankalinsu ya dugunzuma. Tsawon daƙiƙa ɗari da sittin ɗayansu bai ce uffan ba. Daga can sai waziri yayi gyaran murya yace, "Ya shugabana ka yi sani cewa idan har muna so mu tsira da mutuncinmu da mulkinmu dole ne mu cire tsoro daga zuƙatanmu,walau dai mu je mu zauna tare da wannan bokanya mu nemi sulhu ta fita daga ƙasar nan ko kuma mu yi tarar aradu mu koreta da ƙarfin tsiya,tun da dai bamu jarraba yin hakan ba mun kasa. Kasan ance a rashin tayi ake barin araha." Caraf sai Galadima ya tari numfashin waziri yace, "Haba waziri ya za'a yi mu yi irin wannan gangancin. Ai shi yaƙi ɗan zamba ne,idan har muna son haƙanmu ya cimma ruwa dole haɗa da yaudara. Tabbas za mu yi nadama idan muka ce za mu yi fito na fito da bokanya Tazibul Lubucul." Koda galadima ya faɗi haka sai sarki Alyasil Buhus yayi ajiyar zuciya,sannan ya dubi kowa yace, "Haƙiƙa kai ma ka zo da uzuri babba. To wai shin me zai hana mu je mu nemi sulhu da ita?" Kamar haɗin baki sai gaba ɗayan 'yan majalisar suka amince da wannan shawara ta sarki Alyasil Buhus,kuma aka tsaida magana akan cewa gobe da safe za su ɗunguma gaba ɗaya su je kogon tsafin bokanya Tazibul Luhucul don warware wannan matsala. Kash rashin sani yafi dare duhu. In da sarki Alyasil buhus da 'yan mjaitsarsa sun san abin da zai biyo baya da basu yanke wannan shawara ba. Kashe gari da hantsi sarki Alyasil Buhus da 'yan majalisarsa gaba ɗaya suka yi hawa suka tafi izuwa kogon tsafin bokanya Tazibul Luhucul. A wannan lokaci Tazibul Luhucul ba tafi shekara tamanin ba a duniya. Koda zuwan su sarki Alyasil Buhus bakin kogon sai suka ja dunga,suka yi crko-cirko,suna masu kallon kogon wanda ya kasance a rufe ruf babu wata ƙofa ko kafar shiga. Nan fa suka yi tsuru-tsuru suna kallon juna,suka rasa abin yi. Suna cikin wannan hali ne suka ji wata irin mahaukaciyar dariya ta cika jejin gaba daya cikin amo da amsa kuwa. Ba zato kuma ba tsammani sai ga wani murgujejen aljani mai ɗan ƙanƙanin kai da tsawo kamar shantu ya bayyana. Yana da faffaɗan ƙirji cike da gashi,mai faɗin kamu ɗari. Hannayensa dogaye ne zanƙala zanƙala,kuma sirara tamkar wuyan zalɓe. Ƙafafunsa kuwa guda huɗu ne murtuka-murtuka kamar bishiyar kuka. Saboda tsananin ƙarar dariyar wannan aljani sai da su Alyasil Buhus suka ji kamar kunnuwansu za su toshe. Ba shiri suka faɗo daga kan dawakansu suna masu tohe kunnuwansu da hannuwansu. Iskar bakin aljanin kuwa ta tashi hankalin komai da ke wajen hatta duwatsun wajen sai da suka kama girgiza. Lokaci guda aljanin yayi tsit, komai ya tsaya cak. Kafin su sarki Alyasil Buhus su buɗi baki su ce wani abu tuni aljanin ya feso musu iskar bakinsa,take suka rikida suka zama guguwa. Aljanin ya cire wata battar fata dake ɗaure a ƙugunsa ya buɗe sai guguwar ta shige ciki,sannan ya rufe. Kawai sai ya ɓace ɓat,bai bayyana a ko'ina ba saí a tsakiyar cikin kogon bokanya Tazibul Luhucul. Babu yadda za'a yi mutum ya tsinci kansa cikin wannan wuri ya yarda cewa a cikin kogo yake,domin kuwa gaba ɗayan wajen a gine yake da dutsen lu'u-lu'u. Kayan ƙawa kuwa gasu nan iri-iri birjik iyakar ganin mutum. Zaune akan wata karagar zinariya kuma riƙe da gajeriyar sandar tsafi tsohuwa Tazibul Luhucul ce. Tazibul Luhul ta kasance 'yar tsarmurmura kamar a hureta ta faɗi,duk da ta kasance tsohuwa tana da kyawun fuska,kuma babu wani abun muni a jikinta. Ko yaushe fuskarta a cikin annuri take kamar ta mai tausayi da imani,amma kuwa al'amarin ba haka ba ne,domin zuciyarta baƙinƙirin ce cike da mugun nufi da rashin tausayi. Koda bayyanar aljanin sai ya yi sujjada a gareta ya miƙa mata battar tsafin. Ita kuwa sai ta miƙe zumbur ta karɓi battar ta ɗaga ta sama,sannan ta kece da dariyar mugunta. Sai da ta jima tana dariyar sannan ta dubi aljanin tace, "Gaishe ka Haddagul Gubur. Haƙiƙa yau kayi mini kyakkyawan aiki." Haddagul Gubur yayi murmushi yace, "Godiya nake uwar bokaye." Ba tare da ta ce komai ba sai ta sake buɗe battar fatar nan. Tana buɗe wa guguwar ciki tayi fitar burgu ta zuba ƙas ta rinƙa katantanwa waje ɗaya. Tazibul Lubucul tayi nuni ga guguwar da sandarta ta tsafi,tana mai cewa, "Gaa ɗayanku ku zama naƙasssu masu mutuwar ɓarin jiki." Rufe bakinta keda wuya sarki Alyasil Buhus da 'yan majalisarsa suka bayyana gaba ɗayan su a kwankwance kowannansu rabin jikinsa a shanye. Koda suka dubi jukunansu suka ga halin da suka kasance,sai duk suka fashe da kuka suna masu tuba ga bokanya Tazibul Luhucul. Ita kuwa sai ta ƙyalƙyale da dariya lokacin da suke ta roƙonta. Lokaci guda kuma ta daka musu tsawa ta murtuke fuska tace, "Kaicon ku waɗannan sarakuna. Lallai ba zan taɓa yafe muku ba,domin kun kawo matuƙar raini a gareni. Shin kuna tsammanin har akwai wani abu da za ku ƙulla a sirrance wanda ban sani ba? Duk abin da kuka shirya a majalisa jiya na gani,kuma na ji. Ina tabbatar muku da cewa sai na nuna muku cewa ni Tazibul Luhucul nafi gaban raini. Kai bama ku ba gaba ɗayan manyan sarakunan duniyar nan kun jawo musu bala'i. Na rantse da darajar ƙarfin tsafina,duk waní sarki mai ji da kansa dake cikin duniyar nan da 'yan majalisarsa gaba ɗaya sai na maishe su Naƙasssu kamar yadda na maida ku yanzu. Yayin da Tazibul Luhucul ta zo nan a zancen ta sai sarki Alyasil Buhus ya yunƙura da ƙyar ya jingina kafaɗarsa jikin wata kujera yana mai fuskantar Tazibul Luhucul yace, "Yake wannan matsafiya naji duk abin da kika faɗi,kuma na tabbatar da cewa ba za ki yafe mana ba,amna ina son na nemi alfarma guda biyu a wajenki saboda albarkar darajar ɗaukakarki da girmanki a wajen al'ummar ƙasar nan,ina son duk abin da za kiyi mana kada laifinmu ya shafi zuri'armu. Alfarma ta biyu ita ce ina son ki sanar damu yadda zamu samo maganin da zamu warke daga wannan cuta,don ya zamana koda ba kya raye a doron ƙasa zamu iya ƙoƙarin nemo maganin,duk da cewar kuwa mun san cewa ba za mu iya samo maganin ba,amma ai mai rai baya fitar da rai da samun rabo." Koda jin wannan batu sai bokanya Tazibul Luhucul ta ƙyalƙyale da dariya har sau uku sannan tace, "Yakai wannan sarki ka yi sani cewa ba'a taɓa neman alfarma ba a wajena na ƙi yi,face abin da dama na yi rantsuwa akan ƙin yinsa. Bisa wannan dalili na rantse da darajar tsafi ba zan taɓa cutar da iyalanku ba,kuma zan sanar da ku yadda za'a samo maganin da zaku sha ku warke daga wannan cuta gobe daddare,ku yi sani cewa bayann zai riskeku cikin gidajenku." Tana gama faɗin hakan ta dubi aljani Haddagul Gubur tace, "Maza ka kwashe su ka maida kowa gidansa,domin iyalinsu su cigaba da yin jinyarsu bisa wannan cuta ta ajali domin kuwa ita ce sanadiyar mutuwarsu. Tabbas babu wanda zai ƙara shafe sama da shekara uku nan gaba a rayuwarsa. Kuma kayi sauri ka dawo nan domin ina son ka kirawo min gaba ɗayan hadimaina domin muyi shirin zagaye duniyar nan a cikin kwana arba'in don yaɗa wannan cuta ga dukkanin manyan sarakunan duniya da 'yan majalisarsu." Kafin Tazibul Luhucul ta gama rufe bakinta tuni aljani Haddagul Gulbur ya kwashe su sarki Alyasil buhus su goma sha ɗaya ya kai su cikin gidajensu ɗaya bayan daya cikin abin da bai wuce daƙiƙa biyar ba. Yayin da iyalan sarki da iyalan 'yan majalisarsa suka ga abin da ya faru sai hankalinsu ya dungunzuma,gari ya ruɗe, ko'ina ka gifta babu zancen da ake yi sai na wannan annobar cuta data samu sarakan gari. Nan fa jama'a suka yi ta shawarwari iri-iri har ma aka haɗa kai aka ƙudiri niyyar zuwa kogon Tazibul Lubucul don a roƙeta gafara. Bayan jama'ar gari sun yi dandazo da niyyar tafiya sai kawai aka ga aljani Haddagul Gubur ya bayyana a sararin sama. Nan take tsoro ya baibaye kowa. Jama'a suka firgice suka kama iface-iface da guje-guje. Cikin kakkausar murya Haddagul Gubur ya daka tsawa yana mai cewa, "Yaku jama'ar birnin Sin na umarce ku daku tsaya waje guda ku saurari saƙo daga mai girma uwar bokaye ko kuma yanzun nan nayi fishi da fishinta." Koda jin wannan batu sai kowa ya tsaya cak a inda yake. Gaba ɗaya garin ya yi sit tamkar babu wani mai rai. In ka ɗauke kukan ƙwari dana tsuntsaye da kuma sautin iska dake kaɗawa ba ka jin komai. Haddagul Gubur yayi gyaran murya yace, "Mai girma uwar bokaye tace a gaya muku cewa ba ta da buƙatar ganin ɗayanku don neman gafarar ta bisa abin da ta yiwa sarki da 'yan majalisarsa. Kuma tace tana mai yi muku gargaɗi cewar duk wanda duk ya kuskura yaje gareta akan wannan batu abin da ya sami sarki da 'yan majalisarsa shine zai same shi." Koda Haddagul Gubur ya zo nan zancensa,sai ya bace ɓat. Nan fa gari ya ruɗe masu kuka na yi masu faɗin albarkacin bakin su na yi. A can cikin gidan sarki kuwa,gaba ɗayan iyalansa sun taru a cikin turakarsa sun kewaye shi,yana kwance bisa gado sai kuka suke gaba ɗaya. Babban ɗansa kuwa a tsaye yake gefe guda ya yi jugum fuskarsa a murtuke babu annuri,haka kuma zuciyarsa cike take da tsananin baƙin ciki. Idanunsa sun kaɗa sun yi jawur, amma ba sa zubar da hawaye. Shi kaɗai sai huci yake kamar macijin da ya fasa kai zai yi sara. Kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da cewa jarumi ne na gaske,domin yana da ƙirar ƙarfi. Ya kasance saurayi ɗan kimanin shekaru ashirin da biyar,kuma ana kiransa da suna Sammaru. Sammaru kyakkyawan saurayi ne,kuma mai kyawun hali,domin yana da tausayi da taimako ga talakawa,to amma ta yana da matuƙar fushi,domin ba wuya ya zare takobi ya ƙaddamar da mutum musamman mazalunci. A rayuwar Sammaru babu abin da ya tsana sama da zalunci. Sarki Alyasil buhus ya ɗaga kai yana duban iyalansa ɗaya bayan ɗaya,sa'adda hawaye ke zuba a idanunsa,amma bai ga Sammaru ba sai yace, "Ina yarima yake?" Mahaifiyar yarima Alfisa tace, "Ai gashi can a gefe guda." Sarki ya kira Sammaru yace, "Yakai ɗana zo nan gareni mu gana." Sammaru ya tako ƙafafunsa cikin karayar zuciya,ya iso gaban gadon ya durƙusa,sannan ya kama hannun mahaifin nasa ya sumbata kawai sai hawaye ya zubo masa yace, "Yakai Abbana ina so ka sani cewa zuciyata na faman zogi da raɗaɗin baƙin ciki bisa wannan hali da ka shiga. Ina son ka yi mini izini yanzu na tafi kogon uwar matsafa na sare kanta." Koda jin wannan batu sai gaba ɗayan iyalan sarki suka firgice suka faɗi ƙasa suna masu dunƙule jukunansu cikin tsananin tsoro don gani suke tamkar hallakarsu ta zo. Shi kuwa Sammaru ko gizau bai yi ba. Kawai sai sai ya zare takobinsa yayi tsayuwar shirin ko ta kwana. Sarki Alyasil Buhus ya ɗaga hannunsa na dama wanda bai shanye ba,ya kamo hannun Sammaru yace, "Yakai ɗana ka yi haƙuri ka sanyawa zuciyarka ruwan sanyi, ka sani cewa ba za ka iya ba da uwar matsafa,domin tafi ƙarfin ka. In ba don ta ɗauki alƙawari cewar ba za ta taɓa iyalannmu ba,da tuni wannan farucin da kayi ya zamo ajalinka. Ina roƙonka a bisa ƙaunar da ke tsananina da kai da ka janye nufinka na son yaƙar uwar matsafa,abin da nake so da kai shine ka saurari bayanin da zai zo mana akan yadda za'a samo maganin da zamu sha mu warke daga wannan cuta. Yakai ɗana na sani kai jarumi ne mai dakakkiyar zuciya da tsagwaron ƙarfi da jarumta. Bana shakkarka bisa kowanne irin hali da za ka tsinci kanka a ciki. Na sani cewa komai nisan wuri da kuma masifun dake kan hanya za ka iya ke tasu ka kai ga biyan buƙata. Ina son ka jajirce a ranka cewa za ka iya zuwa inda wannan maganı yake ka samo shi." Yayin da yarima Sammaru ya ji wannan jawabi daga bakin mahaifinsa,sai ya ji wani sabon ƙarfi ya zo masa tamkar zai iya y yaƙar duniya shi kaɗai. Cikin zafin nama ya miƙe zumbur ya juyawa mahaifin nasa baya sannan lashi takobinsa yace, "Yakai Abbana ka yi sani cewa na rantse da darajarka da kuma kaifin wannan takobi tawa duk inda wannan magani yake sai na je na nemoshi. Haka kuma komai daren daɗewa sai na tsinke kan Tazibul Luhucul da wannan takobi,domin kuwa ta kasance azzaluma. Lallai ba ni da abokin gaba a doron ƙasa wanda yafi azzalumi." Koda Sammaru ya zo nan a zancensa,sai suka ji ɗakin ya cika da dariyar Tazibul Luhucul. Al'amarin da ya firgita sarki da sauran iyalansa kenan. Shi kuwa Sammaru sai ya gyara tsayuwa gami da ƙara riƙe takobin sa hannu biyu. Dariyar ta ci gaba kamar ba za ta daina ba. Daga can kuma sai wani irin haske ya fara bayyana dishi-dishi a cikin siffar bil'adama. A hankali surar ta haɗu gaba ɗaya sai ga Tazibul Luhucul tsaye a gaban Sammaru riƙe da sandarta ta tsafi,kuma fuskarta a murtuke. Koda Sammaru ya yi arba da ita sai ya kai mata wawan sara a tsakiyar kafaɗarta da niyar tsargeta gida biyu,kawai sai yaji takobin tasa ta sari iska. Sammaru ya ci gaba da saranta amma iska yake sara. Tazibul Luhucul ta ƙyalƙyale da dariya a karo na biyu al'amarin da ya sa Sammaru ya ja da baya kenan ya sauke takobinsa ƙas. Tazibul Luhucul ta nuna shí da ɗaya hannun nata mara sanda tace, "Kai yaro tsaya iya matsayinka domin na gaba ya yi gaba,na baya sai labari. Ina so ka sani cewa duk duniyar nan babu wani mahaluƙi da zai iya kashe ni. Ba don na yi rantsuwa ba akan cewa ba zan taɓa iyalan sarakan garin nan ba da tuni ka daɗe da zama gawa. Ban zo nan dan komai ba sai don na tabbatar maka da cewa ni walki ce daidai da gindin kowa. Matsayina ya wuce yadda kake tsammani. Shawara ɗaya zan baka ka cire batun yaƙi da ni a ranka ka sanya tunanin nemo maganin cutar mahaifinka,domin kuna da ƙanƙanin lokaci. Tabbas indai ba ka samo maganin ba kafin shekara uku daidai sai dai ka dawo ka iske gawarsa." Cikin fushi Sammaru ya dubi Tazibul Luhucul yace, "Ina ne inda wannan magani yake? Na rantse da darajar mahaifina komai nisan wajen,komai masifar dake wajen sai naje na deɓo wannan magani." Tazibul Luhucul ta sake ƙyalƙyalewa da dariya, tace, "Yaüwa haka 'näke sön naji furucin namiji mai zuciyar maza. Kada ka damu nayi alƙawari zan faɗa sai ka jira zuwa tsakiyar daren yau cikakken bayani zai zo ya riske ka har nan." Tana gama faɗin hakan ta rikiɗe ta zama wannan haske. A hankali hasken ya rinƙa disashewa har ya ɓace ɓat. Wannan shine abinda ya faru tsakanin yarima Sammaru da uwar matsafa Tazibul Luhucul a can birnin Sin. A sauran manyan ƙasashen duniya kuwa labari ya iske sarakuna cewa ga wata annobar nan na shirin afko musu,wato gaba ɗayansu zasu zama naƙasssu. Sun sami wannan labari ne daga bakin aljanun da suke bautawa. Nan da nan hankalin sarakunan duniya ya dugunzuma,suka shiga ganawa da aljanun nasu don neman tsari daga wannan masifa mai shirin afkowa. Kowa ya tuntuɓi aljaninsa nasa sai aljanin ya ce da shi ai wannan al'amari yafi ƙarfin sa domin kuwa ba kowane zai haddasar dashi ba face bokanya Tazibul Luhucul uwar matsafa,ita kuwa wannan boka a halin yanzu duk duniya babu wani matsafi ko matsafiya mai tarin sirrikan tsafi kamarta. An ce tana da sirrin tsafi guda miliyan dubu tara da casa'in da tara guda ɗaya ne kacal ya rage mata ta mallaka,kuma duk ran da ta mallake shi za ta iya mayar da duniya tamkar ƙwan kaza a gaban ta. Waɗannan sirrikan tsafi data mallaka guda miliyan dubu tara da casa'in data tara ta ɓoye su ne a cikin wata taska,ita kuwa an ajiye tana a cikin wani kogon dutse. Shi kuwa kogon yana tsakanin duniya ta bakwai da ta takwas daga cikin duniyoyin ƙarƙashin ƙasa. Babu wani abu mai rai da ya taɓa zuwa wannan wuri,kuma ba za'a samu wanda zai iya zuwa ba. Lokacin da sarakuna suka ji wannan jawabi sai duk suka ɗimauce suka firgice, wasu ma dalilin rikirkicewar al'amuransu kenan. Wasu suka kama kuka,wasu kuma suka kama ciwo don tsananin fargabar wannan baƙin labari. Su kuwa aljanun na su sai suka rinƙa kwantar musu da hankali suna cewa su yi haƙuri su saurari jawabin da uwar matsafa za ta yi dangane da inda maganin wannan cuta yake,lallai zasu samo musu shi. A wannan lokaci manya ƙasahen duniya mafi girma guda shida ne,ƙasa ta farko ita ce birnin Sin,sai kuma birnin Hindu sai Rum,Ƙisra,Misra da kuma Farisa. Ƙasar da ake ganin za ta iya biyo bayan waɗannan ƙasashe ita ce Askandariya. A can fadar bokanya Tazibul Luhucul kuwa wato cikin kogonta na tsafi gaba ɗaya hadimanta sun taru sun durƙusa a gabanta yayin da take zaune bisa karagarta ta mulki. Amma bisa mamaki sai suka ga tayi shiru ba ta ce da su uffan ba,kuma ta sunkuyar da kai ƙasa ta nutsu ainun kamar mai jiran umarni. Jim kaɗan sai suka ga wani haske mai launin ɗorawa ya bayyana a tsakiyar fadar yana katantanwa a waje guda. Koda ganin hasken sai Tazibul Lubucul ta miƙe zumbur cikin farin ciki ta nufe shi. Kafin ta isa gaban hasken tuni ya rikiɗe ya zama wata kyakkyawar aljana wadda ke riƙe da sandar tsafi iri ɗaya da ta Tazibul Luhucul. Nan take wannan aljana ta rungume Tazibul Luhucul suka sumbaci junansu,cikin tsananin farin ciki. Aljanar ta dubi Tazibul Luhucul cikin murmushi tace, "Gaishe ki ƙawata,haƙiƙa duk abubuwan da na umarce ki da yi kin yi su daidai. Ina mai yi miki bushara cewa burin mu ya kusa cika. Tabbas idan muka sanya wannan cuta a jikin manyan sarakunan duniya na bil'adama zamu gano inda wannan sirrin tsafi guda ɗaya yake wanda ya gagaremu samu." Tazibul Luhucul ta yi murmushi gami da ƙyalƙyalewa da dariya, sannan tace, "Yake Saubatul Azwas ki yi sani cewa raina cike yake da farin ciki bisa wannan bushara da kika zo mini da ita,kuma dama ke nake jira ki iso,domin na tara dukkanin hadimaina gasu suna jira sai ki faɗa mana yadda zamu kai ga gaci. Koda yake kin san cewa hadiman nan nawa basu san ki ba ya kamata na gabatar dake a gare su ko kuma ki gabatar da kanki don ance waƙa a bakin mai ita tafi daɗi." Saubatul Azwas ta yì murnushi,sannan ta dubi hadiman Tazibul Luhucul waɗanda gaba ɗayansu sun kasance aljanu ne,kuma su talatin da bakwai ne. Guda talatin mata ne zallah, guda bakwai ne maza. Saubatul Azwas ta fuskance su tace, "Ni fitacciya ce a cikin al'ummar aljanu amma ba a sanni ba a fuska,domin ban yarda na bayyana kaina ba,tun ina ƙarama kawo iyanzu saboda wani buri dake cikin zuciyata. Yaku waɗannan hadimai ku sani cewa ni ce SAUBATUL AZWAS 'ya' guda ɗaya ga sarki Kalimul Ifwan." Koda jin wnanan batu sai gaba ɗayan hadiman nan suka yi sujjada ga Saubatul Azwas cikin girmamawa,ba su yadda sun sake haɗa idanu da ita ba,kuma take jikinsu ya kama ƙyarma,kamar a ce ƙyat su tashi su ruga. Ba wani abu ba ne ya sa waɗannan hadimai firgita face sanin cewa sarki Kalimul Ifwan shi ne sarkin da ya zamo abin tsoro ga dukkanin aljanun duniya a zamaninsa,domin ya kasance ƙasurgumin matsafi. Saboda tsananin ƙarfin tsafinsa idan zai yi yaƙi da wata ƙasar yana daga zaune yake yaƙin,kuma yana iya maishe da garı guda turɓaya har da komai na cikin sa,wato yana iya maishe da aljanu,dabbobi da komai na su ya zama turɓaya. Kuma wannan turɓaya zata cigaba da wanzuwa abadan-abidina. Har wannan sarki ya gama zamaninsa ba a taɓa samun wanda ya sami galaba akan sa ba. An sani cewa yana da 'ya' guda ɗaya kacal a duniya kuma kafin ya mutu ya bata gaba ɗayan sirrikan tsafinsa. Bayan ya mutu sai aka nemi wannan 'ya' tasa sama da ƙasa aka rasa. Yayin da Saubatul Azwas ta fuskanci cewar waɗannan hadimai sun tsora ta da ganinta sai ta daka musu tsawa tace, "Na umarce ku da ku iya bakinku,kada ku kuskura ku sanar da wasu cewar ina nan a cikin duniyar nan. Ku sani cewa a duk inda kuke ina tare da ku,kuma ina ganinku ina jin ku,koda kuwa kuna ƙarshen bangon duniya ne,ko cikin kuratandu. Ina son ku nutsu ku tattara hankalinku waje guda ku saurari jawabin da zan muku bisa gagarumin aikin da ke gabanmu. Idan har muka yi nasara gaba ɗayanku ku talatin da bakwan nan zaku zama manyan sarakai a cikin ƙasashen aljanu,kuma za mu ba ku dukiya irin wacce baku taɓa ganin mai yawan taba. Ina so ku sani cewa ni da ƙawata Tazibul Luhucul bamu da wani buri wanda yafi na mallakar duniya gaba ɗaya. Ni ina son na mallaki ƙasashen aljanu,ita kuma tana son ta mallake ƙasashen bil'adama. Lallai mu biyu kacal ba zamu iya wannan aiki ba,sai da taimakonku. Zan kasa ku gida biyu,kaso guda zai bini,ɗaya kason kuma zai bi ƙawata Tazibul Luhucul. Mataki na farko shi ne nan da kwana bakwai zamu tafi izuwa ƙasashen sarakan duniya mu zuba musu wanna cuta ta mutuwar ɓarin jiki. Wannan ciwo zai zame musu ajali,amma sai sun yi shekara uku suna jinya. Da zarar sun mutu zamu sace gawarwakin su mu zuba a cikin wani sunduƙi gaba ɗaya. Ina nufin gawar sarakunan aljanu da gawar sarakunan bil'adama za mu gwamutsa duka a cikin wannan sunduƙi ba zamu buɗe sunduƙin ba sai bayan shekara uku,idan muka buɗe zamu tarar ƙasusuwansu,naman jikinsu kuma ya gama ruɓewa ya zama tsutsa. Haka kuma zamu đebi ƙasusuwan da tsutsotsin mu zuba a cikin wata hodar tsafi mu dama,sannan mu zuba a cikin wata ƙatuwar tukunyar tsafi mu yi ta dafawa har tsawon shekara uku. Lallai dole ne ku yi ta gadin wannan tukunya tsawon shekara uku,don kada ɗigo ɗaya na abin dake ciki ya salwanta. Idan shekara ukun ta cika zamu buɗe tukunyar mu iske abinda ke ciki ya zama salalan tsafi. Zamu ɗauki wannan salala mu tafi da shi izuwa taskar tsafina. A can ne zamu haska madubin tsafina a jikinsa ya nuna mana inda sirrin tsafi guda ɗaya yake, wanda shi ne kaɗai sirrin da ban mallaka ba a duniya. Da zarar na je na ɗauko wannan sirri burinmu gaba ɗaya ya cika." Koda Saubatul Azwas ta zo nan a zancenta sai gaba ɗayan hadiman nan suka cika da mamaki. Ɗaya daga cikinsu wata mace mai ƙarancin shekaru ta dubi Saubatul Azwas tace, "Ya shugabata shin za ki iya sanar damu a inda taskar tsafinki take?" Koda jin wannan tambaya sai Saubatul Azwas ta murtuke fuska,sannan ta dakawa mai tambayar harara tace, "Wannan kuma wace irin banzar tambaya ce? Mene ne amfanin sanin wajen da za ki shige shi da ƙafarki idan har buƙatar mu ta biya." Mai tambayar ta duƙar da kai ƙasa tace, "Tuba na ke ranki ya daɗe ki gafarce ni." Wata tsohuwa ta ɗaga hannu tace, "Ranki ya daɗe a cikin bayaninki na fuskanci cewar sai mun yi shekara tara muna yin wannan aiki,kuma na ji kin ce dole ne mu yi gadin wannan tukunya don kada ɗigo ɗaya na abin da a ke ciki ya salwanta, idan ɗigo ɗaya ya salwanta me zai faru?" Saubatul Azwas ta yi ajiyar numfashi tace, "Ke dakata ki ji bama ɗigo ɗaya ba,idan muka bari ƙuda ya tsotsi ƙwayar zarra daga cikin wannan abu da muke dafawa a tukunyar,gaba ɗayanmu shirinmu ya wargatse sai dai mu dawo da baya mu fara sabon shiri,wato mu samo gawarwakin sababbin sarakunan duniya,mu sake ɓata wasu shekaru taran,muna haɗa wannan sinadari." Saubatul Azwas ta a cigaba da cewa, "Yanzu dai abin da nake so ku fahimta shine,dole ne ku kiyaye wasu abubuwa yayin da zamu je waɗannan manyan ƙasashen duniya guda biyar don yaɗa cutar mutuwar rabin jiki ga sarakunansu da 'yan majalisarsu. Ƙasashen nan dai da za mu je sune,Hindu,Rum,Ƙisra,Misra da Farisa. Ni ce zan je birnin Hindu,Rum da Ƙisra. Ita kuwa Tazibul Luhucul za ta je Rum,Ƙisra,Misra da Farisa. Kamar yadda na fada muku ɗazu,ku kuwa zamu rabaku kaso biyu. Kaso guda su bini,đaya kason su bi ƙawata Tazibul Luhucul. Ni da ita mune zamu je gidajen sakaruna,ku kuma kuje gidajen 'yan majalisarsu. Gaba ɗayan ku zaku tafi da wani bututun tsafi ne,wanda shi za ku hura iskar cikinsa ta zuba kan 'yan majalisar da zarar kun yi hakan take cutar mutuwar rabin jiki za ta kama su. Ni da Tazibul Luhucul kuwa zamu je ne da sandar tsafinmu kawai da zarar mun nuna su da ita za su kamu da cutar. Ku yi sani cewa babu inda zamu je sai da tsakar dare. Duk inda muka je muka tarar da cewar Sarakunan suna yin wani abu daya danganci tsafi ko bauta kada mu kuskura mu yi musu komai. Wanda kuwa ya bijirewa wannan doka take zai zama gunki. Ku sani cewa bai zamo lallai sai suna yin barci ba,amma babu lokacin da yafi kyau face lokacin da suke tarawa da iyalansu. Ina daɗa tunasar da ku cewa wanda duk ya manta ya kusance su a lokacin da suke aikin tsafi ko bauta zai zama gunki,idan kuwa ya zama gunkin ni kaina ba zan iya dawo da shi ainihin halittar sa ba. Da wannan batu nake muku sallama zan tafi ba zan dawo na ba sai bayan kwana bakwai,don mu ɗunguma mu tafi aikatar da wannan babban aiki." Koda Saubatul Azwas ta zo nan zancenta,sai ta juya ta fuskanci Tazibul Luhucul suka rungume juna đa sumbatar goshinsu suka yi sallama. Nan take Saubatul Azwas ta rikiɗe ta zama haske mai launin đorawa. Hasken ya disashe ya ɓace ɓat. Ba tare da ɓata lokaci ba Tazibul Luhucul ta ware aljanu goma sha đaya daga cikin waɗannan hadimai nata ta rarraba musu wasiƙa tace maza su je su kai gidan sarki Alyasil Buhus da 'yan majalisarsa a cikin wannan dare. Nan take hadiman suka tafi aiwatar da wannan umarni. Wannan shi ne abin da ya faru a fadar bokanya Tazibul Luhucul bayan ƙawarta aljana Saubatul Azwas ta kawo ziyarar bazata. A can gidan sarki Alyasil Buhus kuwa da kuma gidajen 'yan majalisarsa har yanzu hankali bai kwanta ba,domin yadda iyalansu suka ga rana haka suka ga dare,wato har dare ya raba basu rintsa ba. Ba zato,ba zammani sai su rinƙa ganin wasiƙu na dira,kuma ba'a ga wanda ya kawo ba. Lokacin da wasiƙar gidan sarki Alyasil Buhus ta faɗo a tsakiyar turakarsa iyalansa gaba ɗaya na zaune sun yi tagumi. Wasu suna kuka,wasu kuma suna juyayin wannan hali da sarki ya shiga rana tsaka. Cikin sauri da zafin nama yarima Sammaru ya yunƙura ya ɗauki wannan wasiƙa ya warware ta ya fara karantawa kamar haka:- "Daga uwar matsatan duniya Tazibul Luhucul zuwa ga sarkin birnin Sin Alyasil Buhus. Bayan gaisuwa a gareka gami da jajen wannan masifa da ta same ka ina mai farin cikin sanar da kai cewa idan har kana son ka warke daga wannan cuta dole ne aje taskar tsafina a deɓo ruwan tsumin tsafin da nake sha a baka ka sha. Da zarar ka sha wannan tsumi take za ka warke. Ka yi sani cewa taskar tsafina na cikin wannan kogon da ake kira MADDARUL IKISINA,shí kuwa Maddarul Ikisina na nan tsakanin duniya ta bakwai da ta takwas daga cikin duniyoyin ƙarƙashin ƙasa. Sa'a na ga mai rabo. Lallai me nema yana tare da samu,amma abin da kamar wuya tsohuwa da tauna ƙwallon goruba." Ko da Sammaru ya zo nan a cikin karatun wasiƙar,sai yayi jifa da wasiƙar. Cikin matsanancin fushi ya zare takobinsa ya nufi ƙofar fita daga cikin turakar sarki Alyasil Buhus,cikin sauri yan'uwansa maza suka ruga suka sha gabansa suna masu bashi baki da lallaminsa,da ƙyar ya haƙura ya dawo ya zauna sannan ya dubi sarki Alyasil buhus yace, "Ya kai Abbana kayi sani cewa haƙiƙa wannan matsafiya ta raina mana hankali. Shin a ina aka taɓa jin cewar wani mahaluƙi ya taba zuwa cikin wata duniya dake ƙarƙashin ƙasa." Sarki Alyasil Buhus ya muskuto da fuskarsa da ƙyar ya dubi yarima Sammaru yace, "Ya kai ɗana haƙiƙa akwai wasu duniyoyin a cikin ƙarƙashin ƙasa kuma na sami wannan labarine daga bakin bokana Hulumul makahur. Na umarceka da kayi shiri gobe da safe ka tafi izuwa jejin Dulmas ka riski boka Hulumul Makahur ka bashi wannan wasiƙar wacce uwar matsafa ta kawo kuma ka buƙaci taimakonsa a bisa wannan al'amari. Tabbas zai taimaka muddin akwai halin taimakawar." Koda jin haka sai Sammaru ya miƙe tsaye ya dubi Alyasil Buhus yace, "Ya kai Abbana kayi sani cewa bazan iya bari sai gari ya waye ba,tabbas a yanzu zanje nayi shiri na tafi jejin Dulmas kuma na rantse da darajarka ko boka Hulumul Makahur ya taimakeni ko bai taimakeni ba,ba zan dawo ba sai da tsumin tsafim uwar matsafa. In kuwa ban samo shi ba kar kuyi sallama gaba ɗaya sai wata rana. Idan da rabon zamu sake saduwa zan dawo." Ko da jin haka sai mahaifiyar Sammaru ta rungumeshi kuma ta fashe da kuka,suma sauran 'yan'uwan na sa duk sai suka matso gareshi suka rungumeshi suna kukan gaba ɗaya. Sarki Alyasil bubus ya share hawaye a idanunsa yace, "Ya kai ɗana ka sani cewa kaine babba a gidan nan don haka kaine mai jiran karagata. Mai zaisa ka yanke wa kanka wannan ɗanyen hukunci yanzu idan baka nan waye zai gaje ni?" Sammaru ya saki yan'uwansa ya dawo ga mahaifin nasu ya durƙusa a gabansa ya kama hannusa na dama ya sumbata a lokacin da gaba ɗayansu suna zub da hawaye. Sammaru yace, "Ya kai Abbana kayi sani cewa ko bana nan akwai ƙanne na don haka sai a zaɓi wanda ya fi dacewa daga cikinsu a bashi sarauta." Alyasil Buhus yace, "Ai kaine kafisu dacewa domin ka gajeni a komai." Sammaru yayi shiru tsawon 'yan daƙiƙu sännan yace, "Na yarda haka ne amma ina so ka sani cewa nine kuma nafi dacewa da tsayawa tsayin daka don kare darajarka da ƙimarka. In dai ina numfashi a doron ƙasa bazan taɓa barin rayuwarka a cikin tozarta ba,lallai sai nazo da maganin wannan cuta taka kafin cikar shekara uku,sai na dawo." Sammaru na gama faɗin haka ya miƙe da sauri ya fice daga cikin turakar. Da yake dama Sarmmaru bai taɓa yin aure ba kai hasalima bai taɓa son wata 'ya mace ba kuma a gaba ɗayan birninsu bashi da aboki ko guda ɗaya don haka bai sake neman kowa ba don yin sallama nan da nan yasa aka shirya masa guzuri sannan yayi shigar yaƙi ya hau wani baƙin ingarmar doki ya kama hanya ya nufi dajin dulmas acikin wannan dare. Wannan shine abinda ya faru tsakanin sarki Alyasil Buhus na birnin Sin tare da ɗansa jarumi Sammaru bayan wasiƙar bokanya Tazibul Luhucul ta riskesu. A can birnin Hindu kuwa sarki Bahacal da 'yan majalisarsa sun kasance cikin tsananin tashin hankali tun sa'adda boka Kirish ya sanar dasu cewa nan da kwana bakwai annobar ciwon mutuwar rabin jiki zata same su kuma sai sun shekara uku suna wannan cuta sannan zasu mutu. Tun a lokacin ne suka tambaye shi,shin babu wata hanya da zasu iya bi su kare kansu daga afkuwar wannan masifa? Boka Kirish yace ai ba wani bane zai aiko da wannan masifa ba face uwar matsafan duniya bokanya Tazibul Luhucul wadda ke zaune a birnin Sin. Tabbas wannan bokanya tafi ƙarfin dukkanin matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da ita. Abin da za'a iya yi shine kawai a saurara aji hanyar da za'a bi a samo maganin wannan cuta domin Tazibul Luhucul tayi alƙawarin baiyana hakan. A ranar da wasiƙar Tazibul Luhucul ta riski sarki Alyasil buhus da 'yan majalisar boka Kirish yaje fadar sarki Bahacal inda ya iskeshi tare da 'yan majalisarsa gaba ɗaya da kuma sauran fadawa da matanen garı a zaune cikin matuƙar ga zulumi da fargaba. Da zuwa sai boka Kirish yayi gaisuwa ga sarki sannan ya zaiyana musu batun zuwa kogon maddarul ikisina don đebo tsumin tsafin bokanya Tazibul Luhucul kuma ya sanar dasu a inda wannan kogo yake. Koda jin wanan batu fiye da kowa ne lokaci,take wasunsu suka kama kuka wasu kuwa suka rinƙa nadamar kasancewarsu a cikin wannan masarauta. Ana cikin wannan hali ne gimbiya Ashwarya ta shigo cikin fadar bisa wani farin ingarman doki sanye da kayan yaƙi kuma ta ɗora gawar wani murgujejen zaki akan wuyan dokin. Dawowarta kenan daga farauta sai ta samu labarin cewa ga boka Kirish can a fada zai yi ƙarin bayani dangane da masifar da akace zata zo ta riski mahaifinta da 'yan majalisarsa. Tun sa'adda labarin al'amarin ya fara zuwa kunnenta ta ɗauki abin tamkar tatsuniya don ma har sai da ta yiwa boka Kirish rashin kunya tace taga alama ya fara zautuwa tunda ya fara zuwa da labaru masu kama da almara. A lokacin da ta faɗi hakan boka Kirish baiyi fishi ba sai yace da ita ta zuba ido izuwa lokacin da abin zai faru lallai zata gasgata shi ta tabbatar da gaskiyar al'amarin. Gimbiya Ashwarya kyakkyawar budurwa ce ta kwatance wadda shekarunta baza su fi sha tara ba. Tun tana ƙarama ta taso da jarumtaka,rashin tsoro da kuma iya yaƙi,tana da matuƙar iya jure wahala,yunwa da ƙishirwa kuma idan ta kece da gudu ko barewa albarka,tana da matuƙar zafin nama kuma ita kaɗai tana iya fasa taron mayaƙa. Haka kuma tana da yawan shige da fice wajen matsafa don haka ta sami sirrikan tsafi da ɗan dama waɗanda suke taimaka mata sosai wajen fuskantar abubuwan haɗari. Bisa wannan daliline take shiga daji ita kaɗai tayi farauta sannan ta dawo gida. Lokacin da gimbiya Ashwarya ta shigo cikin fada ta iske mabaifinta sarki Bahacal da 'yan majalisarsa a cikin halin firgita da damuwa sai ta dubi boka Kirish tace yau kuma da wane labarin ƙanzon kuregen kazo mana dashi. Boka Kirish ya dubeta cikin fishi ya maimaita abinda ya faɗi gasu sarki. Ashwarya ta ƙyalƙyale da dariya tace bazan yarda da wannan labarin ba har sai idan abin da ka faɗi ya tabbata wato sai na gani da idona cewar sarki da 'yan majalisa sun kamu da wannan cuta nan da kwana bakwai,idan kuwa al'amarin ya kasance na rantse da darajar karagar sarki sai na nemo maganin da zasu sha su warke kafin shekaru ukun su cika." Gimbiya Ashwarya na gama faɗin hakan ta kaɗa linzamin dokinta ta wuce izuwa cikin gidan sarautar tana mai tunƙaho da matsayinta. Gaba ɗayan mutanen fadar suka bita da kallo. Yana zaune acikin turakar tsafinsa ya runtse idanu,ƙafafunsa a tanƙwashe suke kamar lauje yana mai fuskantar wani ƙaton kaskon wuta wanda aka cika shi da ƙiraren tsafi kala-kala har guda ɗari ba daya. Gashi babu garwashin wuta a cikin kaskon amma sai wani shuɗin hayaƙine ke ɓulɓula yana tashi sama daga jikin ƙiraren kuma basa ƙonewa. A dai dai wannan lokacine sarki Jamshul tare da 'yan majalisarsa suka banko ƙofar shigowa wannan turaka suka faɗo ciki,a fusace boka Karluz ya waigo ya dubesu a tsanake ba tare da wata fargaba ba sannan ya kau da kai yaci gaba da yin abin da yake. Su kuwa sai suka tsaya suka yi cirko-cirko kamar masu jiran umarni su ƙaddamar. Boka karluz bai sake waigawa gare su ba sai bayan daƙiƙa ɗari biyu da arba'in,cikin girmamawa ya risina ya gaida sarki Jamshul yace, "Ya sarkin sarakai lafiya kazo har nan turakana tare da 'yan majalisarka yanzu alhalin mun rabu akan cewa yau da yamma zan zo fada na riske ku?" Koda jın wannan tambaya sai sarki Jamshul yace, "Tun sa'adda ka labarta mana batun bokanya Tazibul Luhucul da kuma masifar da zata jeho mana muka kasance cikin matuƙar tashin hankali,mun kasa zaune mun kasa tsaye haka kuma mun kasa ci mun kasa sha,barci ya ƙauracewa idanunmu don hakane muka kasa jurewa har yamma tayi kazo fada,wannan shine dalilin da yasa kaga mun kawo maka ziyarar bazata,lallai muna son musan hanyar da zamu bi mu kuɓuta daga wannan masifa." Yayin da boka karluz ya ji wannan jawabi daga bakin sarki Jamshul sai ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubesu ɗaya bayan daya cikin alamun karayar zuciya yace, "Ya shugabana kayi sani cewa bincikena ya tabbatar mini da cewar ba makawa wannan masifa sai ta sameku acikin waɗannan kwanaki bakwai,dama ɗaya ce a gare ku kuma ba komai bace face tafiya neman maganin wannan cuta bayan kun kamu da ita kafin shekara uku,ku sani cewa shi dai wannan magani wanda zaku sha ku warke ba komai bane face tsumin tsafin bokanya Tazibul Luhucul wanda ke ajiye acikin taskar tsafinta. Ita wannan taskar tana can cikin wani kogone da ake kira Maddarul Ikisina. Maddarul Ikisina kuwa na nan tsakanin duniya ta bakwai data takwas daga cikin duniyoyin ƙarƙashin ƙasa." Koda boka Karluz ya zo nan a zancen sa,sai sarki Jamshul da 'yan majalisarsa suka firgice suka rasa abin dake musu daɗi nan duniya,gaba ɗayansu suka yi tagumi suna masu juyayin al'amarin cikin zukatansu. Ba zato ba tsammani sai suka ga yarima Yauhana ya fito daga cikin wani saƙo na wannan turaka shi kansa boka Karluz bai san sa'adda Yauhana ya shigo ba har ya ɓuya a cikin wannan saƙo don haka sai da yayi matuƙar mamaki. Yauhana ya dubi mahaifinsa sarki Jamshul yace, "Ya kai mahaifina ina son ku kwantar da hankalinku bisa wannan al'amari domin in dai akwai wannan kogo na Maddarul ikisina nayi alƙawarin sai na riskeshi a duk inda yake na deɓo muku wannan tsumin tsafi kafin cikar shekara uku." Ko da jin haka sai sarki Jamshul ya fashe da kuka sannan yace, "Ya kai ɗana ka sani cewa duk faɗin ƙasarnan ta Rum babu wani abu da nake so sama da kai,kai ne ɗana a duniya don haka bazan yarda ka tafi neman wannan abu mai haɗarin ba a sanadıyar hakan rayuwarka ta salwanta. Ina son ka rungumi ƙaddara daga yau har izuwa ranar da zamu kamu da wannan cuta izuwa lokacin da rai zai yi halinsa domin ka gajeni ka zama sarkin Rum." Yarima Yauhana ya dubi mahaifinsa cikin dakakkiyar zuciya yace, "Ni kam na gama zartar da wannan hukunci kuma babu abin da zai hanani zartar da shi face mnutuwa,ba zan cika ɗa a gareka ba har sai na sami nasara bisa wannan buƙata. Ya kai boka Karluz ina son ka sani akan turba yadda zan iya zuwa wannan wuri inda kogon Maddarul ikisina yake." Sa'adda yarima Yauhana yazo nan a zancesa sai boka Karluz yace, "Ni kam nayi iyakar bincikena ban gano yadda za'a iya zuwa wannan wuri ba,amma a cikin binciken nawa na gano wani boka guda ɗaya wanda shi kaɗai ne zai iya faɗar hanyar da za'a bi aje wannan wuri. Shi dai wannan boka sunansa Hulumul Makahur,yanzu haka yana nan zaune cikin wani jeji da ake kira Dulmas a yankin kasar Sin kuma yarima Sammaru ɗan sarki Alyasil Buhus mai mulkin ƙasar Sin ya tafi izuwa gareshi don ya sa shi akan turbar zuwa kogon Maddarul ikisina." Koda yarima Yauhana yaji wannan batu na boka Karluz cikin zaƙuwa yace "Na umarce ka da kasa ɗaya daga cikin aljanunka ya ɗaukeni da gaggawa ya kaini wajen wannan boka a cikin ƙanƙanin lokaci." Karluz yayi murmushi yace, "Zanyi duk yadda kace amma nima ina rokon alfarma guda ɗaya a wajenka. Ina son kayi wannan tafiya tare da ni domin idan na sadu da boka Hulumul Makahur zan sami ƙaruwa mai yawa a cikin ilimin tsafi bare kuma ace an sami nasarar shiga kogon Maddarul ikisina tare dani." Yarima Yauhana yayi murmushi yace, "Na amsa wannan buƙata taka." Ba tare da ɓata wani lokaci ba boka Karluz ya kimtsa nan take ya kira wani basamuden aljani waishi Labagaza ya baiyana gabansa. Bayyanar Labagaza keda wuya sarki da 'yan majalisarsa suka zube kasa sumamnmu saboda tsananin razana. Boka Karluz da yarima Yauhana kaɗai suka rage a tsaye ƙiƙam su kansu zuciyoyinsu na rawa. Aljani Labagaza ya kasance ƙatoton gaske kuma mummuna ne na kwatance. Faɗin tafin hannusa guda yakai zira'i ɗari,hancinsa kuwa wawakekene tamkar ƙofar gari,idanunsa manya- manya ne kuma ɓalo ɓalo kamar za su faɗo ƙasa. Idan ya wangame bakinsa sai kaga harshensa ya zazzago ƙasa har yana shafar ƙasa saboda tsawonsa,girman haƙorinsa guda ya ninka ɓauren giwa uku. Yana da fukafukai guda ɗari,hamsin a kuiɓin dama,hamsin a kuiɓinhagu,idan ya bushe da dariya sai kaga ƙasa ta kama girgiza tamkar za'a kifar da duniyar. Labagaza risina gaban boka Karluz yace, "Ya shubana gani gareka me kake buƙata daga gareni? Ina mai tunasar dakai cewa a halin yanzu saura aiki uku kacal tsakanina da kai,idan nayi na ukun shi kenan mun rabu har abada bazan sake yin bauta a garcka ba." Boka Karluz yayi murmushi yace, "Zancen ka dutsene,ya kai Labagaza kayi sani cewa ban kiraka nan ba sai don ka ɗaukemu ni da yarima Yauhana ka kaimu dajin dulmas inda boka Hulumul makahus yake a cikin abin da bai wuce sa'a huɗu ba wato kafin yarima Sammaru đan sarki Alyasil Bubus ya isa gareshi." Koda jin wannan batu sai aljani Labagaza ya ƙyalƙyale da dariyar mugunta al'amarin da ya janyo rugujewar turakar kenan ƙasa ta kama girgiza,gaba ɗaya birnin na Rum ya kama tambal tambal. Ba don aljani Labagaza yayi sauri ya ɗauke su boka Karluz dasu sarki Jamshul ba da tuni sun rufta cikin ƙasa ta binnesu. Koda ganin wanna ɓarna ta aljani Labagaza yayi. Boka Karluz ya daka masa tsawa yace, "Ashe bana haneka da yin dariya a nan ba?" Labagaza ya sunkui da kansa ƙasa yace, "Tuba nake ya shugabana,haƙiƙa na sha'afane saboda jin bautar da na yiwa Bil'adama a doron ƙasa zan iya kai ku gaban boka Hulumul lakahur a cikin abin da bai wice sa'a daya da rabi ba." Boka Karluz ya sake yin murmushi a karo na biyu sannan ya watsawa su sarki Jamshul ruwa suka farfaɗo daga dogon suman da sukayi,kafin ɗayansu ya buɗi baki yace wani abu tuni boka Karluz da yarima Yauhana sun kama hawa kan aljani Labagaza tamkar masu hawa gini mai matattakala dubu,cikin gudu suka isa tsakiyar gadon bayansa suka zauna. Zamansu ke da wuya aljani Labagaza ya buɗe fukafukansa gaba daya đarin ya tashi da su sama. Yarima Yauhana ya rinƙa ɗagawa sarki Jamshul hannu har suka ƙule a cikin gajimare. Kamar yadda al'amura suka kasance a birnin Rum haka suka kasance a birnin Ƙisra da Farisa tamkar haɗin baki,sarkin Ƙisra na da ɗa guda kuma Jarumin gaske sunansa Lubaika. Yanzu haka Lubaika ya nufi dajin Dalmus don riskar boka Hulumul Makahur bisa kan wani aljani wai shi Karakainu. Shi kuwa sarkin farisa yana da 'ɗa' mai suna Larbuz wanda ya kasance gwarzon shekara acikin birnin Farisa domin shi kaɗai ya fatattaki waɗansu dodanni da suka addabi ƙasar da kawo sumamen bazato suna đauki ɗai ɗai cikin dare. Ance yawan dodannin ya kai dubu ashirin da bakwai kuma suna da matuƙar girma da ƙarfi amma da yake yarima Larbuz ya kasance sadauki mai tsananin zafin nama koda ya tarbasu cikin daji inda suka yi sansani sai ya zame musu alaƙaƙai yayi ta ragargazarsu,sai da ya kashe guda ɗari tara da saba'in da bakwai daga cikinsu. Koda sukaga yayi musu wannan ɓarna kuma sun kasa cimma masa sau suka ranta a ana kare amma duk da haka bai ƙyalesu ba sai da ya bisu ya rinƙa kifar dasu,da ƙyar guda ɗari biyar suka tsira da rayuwarsu. Wannan jarumtaka da yarima Larbuz yayi ba ƙaramar ɗaukaka ta jawo masa ba a wajen mutanen ƙasar Farisa. Sai da ya zamana kowa na ƙaunarsa maza da mata yara da manya,kai duk wata budurwa da ta isa da kanta a fagen kyau bata da burin da ya fi ta auri yarima Larbuz. A ranar da aka shirya gagarumin taro a fadar birnin Farisa don zaɓar budurwar da yarima Larbuz zai aura sai bokan ƙasar ya bayyana wanda a kewa laƙabi da Sharudul Bahabul. Nan boka Sharudul Sababul ya sanar da sarkin Farisa labarin masifar da zata faɗo kansa da kuma 'yan majalisarsa. Haka kuma ya zaiyana musu yadda zasu kuɓuta ta hanyar samo wannan tsumin tsafin dake can taskar tsafin bokanya Tazibul Luhucul. Bugu da ƙari yayi bayanin cewa babu wani boka da zai iya faɗin hanyar da za'abi aje wannan wuri face boka Hulumul Makahur. Duk wannan bayani boka Sharudul Bahabul yayi shine acikin bainar jama'a. Koda ya ƙare jawabi sai gaba ɗaya wajen ya ruɗe da iface iface,masu kuka nayi masu surutai nayi. Sarkin Farisa kuwa da 'yan majalisarsa tuni sun fita haiyacinsu tamkar wađanda suka shekara suna cutar ajali. Koda ganin abin dake faruwa sai yarima Larbuz ya daka tsawa cikin kakkausar murya. Take wajen yayi tsit kai kace mutuwa ce ta gifta. Yarima Larbuz ya hau kan wani mumbari dake ajiye a tsakiyar fadar ya waiga gabas da yamma,kudu da arewa yaga ko'ina jama'ane rututu babu masakar tsinke amma kowa ka dubi fuskarsa sai kaji tamkar ka fashe masa da kuka domin alamun tsorone da fargaba ƙarara zaiyane a fuskarsa. Yarima Larbuz yayi gyaran murya yace, "Yaku mutanen bimin Farisa kuyi sani cewa ni yarima zan tafi Larbuz na rantse da martabarku zan tafi wannan wuri inda tsumin bokanya Tazibul Luhucul yake ba kuma zan dawo ba sai da shi. Lallai na yi alƙawarin kare lafiyar sarki data 'yan majalisarsa,kamar yadda na kare rayuwar jama'ar ƙasar nan daga harin muggan dodannin nan." Koda yarima Larbuz ya zo nan a zancensa sai wajen ya cika da shewa ana yi masa jinjina. Ba tare da ɓata lokaci ba boka Sharudul Bahadul ya ajiye sandar tsafinsa a ƙasa sai ta rikiɗe ta zama wani ƙaton shaho mại girman gaske,wanda idan ya kaɗa fukafukansa sai ka ga iska na neman kwantar da jama'a. Sharudul Bahabul ya dubị shahon yace, "Ya kai wannan tsuntsu na umarce ka da ka duƙa ƙasa domin yarima ya hau bayanka ka ɗauke shi ka kại shi dajin Dalmus inda boka Hulumul Makahur yake." Ai kuwa tamkar da mutum yayi magana,sai shahon nan ya durƙushe ƙafafunsa ƙasa. Cikin hanzari yarima ya haye bayansa ya zauna. Kafin tsuntusn ya tashi sama sai boka Sharudul Bahabul ya matsa gaban yarima Larbuz yayi masa raɗa a kunne yace, "Da zarar kun dira a can wannan tsuntsu zai rikiɗa ya zama sandata ta tsafi sai kaɗauka ka riƙe ta har ku je taskar tsafi ku dawo. Lallai ka dawo tare da wannan sanda tawa." Yarima Larbuz yace, "Tabbas zan kasance mai cika alƙawari zan dawo maka da sandarka." Boka Sharudul Bahabul ya bugi bayan shahon kawai sai ya buɗe fukafukansa ya yi sama. Shahon ya yi ta lulaƙawa cikin gajimare,tun jama'a na iya hangensa har ya ɓace ɓat. Su kuwa 'yan matan da suka zo wannan gagarumin taro don a zaɓi ɗaya daga cikinsu a matsayin wacce yarimna Larbuz zai aura sai suka fashe da kuka,suka kamu da tsananin baƙin cikin rabuwa da abin begensu dare da rana. Wannan shine abinda ya faru a birnin Farisa. A can birnin Misra kuwa sarki Usman ne ke mulkí. A wannan lokaci mutanen birnin Misra gaba ɗayansu ma'abota addinin Musulunci ne. Sarki Usman na da kyakkyawar 'ya' guda ɗaya wacce saboda tsananin kyawunta ba a bari ga fuskarta,koda yaushe fuskar ta ta a rufe take da baƙin kyalle mai shara-shara. Ita dai wannan 'yar' sarki sunanta Fauwaza. Fauwaza ta kasance budurwa 'yar shekara goma sha takwas mai cikakkiyar sura tamka ita ƙera kanta. Haka kuma ta taso da kaifin basira da kuma ilimin addini ma yawa. Wata baiwa wadda Allah yayi mata shi ne tana da ilimin fassarar mafarki. Duk irin mafarkin da mutum yayi in dai ya faɗa mata take zata fassara shi,kuma duk abin da ta faɗa sai an ga faruwarsa walau na farin ciki ne ko na baƙin ciki. Yayin da sarki Usman ya ga mutane na girmama Fauwaza bisa lamarinta na fassarar mafarki har na suna neman su maishe da ita abin dogaronsu sai ya hanata fassara mafarkin kowa face na sa,don gudun kada mutane su kauce hanyar Allah su shiga saɓo. A wani dare sarki Usman na kwance yana barci sai yayi mafarki da wäsu irin baƙaƙen tsuntsaye guda talatin da bakwai suna shawagi a sararin samaniya,amma kuma wasu halittu biyu ne ke yi musu jagora. Halittun kuwa ɗaya mutum ce đaya kuma aljana ce. Tsutsayen da halittun suka rinƙa zuwa kan wasu manyan turakan gini guda shida suna watsa wata guba. Nan take turakan ginin suka rinƙa rugujewa suna faɗuwa ƙasa. Al'amarin da ya janyo rugujewar gaba ɗayan gidajen shida waɗanda ke ƙarƙashin manyan turakan nan har ma wuta ta kama gidajen zasu ƙone ƙurmus. Kawai sai sarki Usman ya tsinci kansa a gidajen guda shida. Koda yaga wuta na ƙoƙarin ƙone su gaba ɗaya sai ya fara ƙoƙarin kashe wutar dake cikin gida na ƙarshe,kuma yana kiran taimako cikin ihu da ƙaraji. Haka dai ya yi ta ƙoƙari bai samu mataimaki ba,har ya zamana wutar ta kama gefen rigarsa kafin ya ankara gaba ɗayan rabin rigar ɓangaren hagu ya cinye gaba ɗaya,amma wani abin mamaki shine ko kaɗan fatar jikinsa ba ta ƙone ba. Yana cikin wannan hali ne wata ƙanƙanuwar tsuntsuwa fara sol ta bayyana gare shi tace, "Ya kại adalin sarki na san cewa daga cikin abubuwan daka mallaka a duniya babu abin da ka fiso sama da wata kurciya guda ɗaya wadda ka keɓeta,ka hana kowa kusantarta,inda zaka saki wannan kurciya da ta zo nan ta kashe wannan wutar gaba ɗaya wadda ke shirin ƙone gidajen nan guda talatin da bakwai,sannan ta yaƙi masu yi musu jagora wajen aiwatar da wannan mummunan ɓarna ya zamana labarin suma ya gushe har abada." Farar tsuntsuwar na gama faɗin haka sai sarki Usman ya farka daga wannan mummunan mafarki mara kan gado,da wuyar fahimta. Gaba đaya jikinsa ƙyarma yake haka kuma fuskar sa cike take da zufa. Haƙiƙa sarki Usman ya razana da wannan mafarki. Nan dai ya karanta waɗansu addu'o'i ya koma ya kwanta da niyyar cewa da safe zai kira 'yarsa Fauwaza ya sanar da ita wannan mafarki don ta fassara masa shi. Kashe gari kuwa sarki ya aika a gayawa Fauzawa cewar yana gaiyatarta kalaci turakarsa. Al'amarin da ya matuƙar baiwa Fauwaza mamaki kenan,domin rabonta da barin ɓangaren da take an kai shekara huɗu. Kullum a tsare take kamar 'yar fursuna sai dai sarki da mahaifiyarta su kawo mata ziyara da kan su. Babu mai shiga inda take face barori da kuyangi masu yi mata hidima. Fauwaza ta fara saƙe-saƙe a ranta cewar anya kuwa ba batun aure sarki zai yi mata ba. Ai kuwa idan har bayar da ita za'a yi ga wani wanda bata taɓa gani ba zata kasance cikin tsananin baƙin ciki. Haka dai ta yi ta saƙe-saƙe a ranta,ta ƙulla wannan,ta kwance wannan,har aka turo 'yan rakiya suka shige gaba don kaita turakar sarki. Sarki Usman na zaune shi kaɗai a ƙasa, bisa wata ƙatuwar dadduma an ajiye kalaci a gabansa,irin wanda kowanne talaka zai iya ci a gidansa,sai ga gimbiya Fauwaza ta shigo cikin ɗakin da sallama. Cikin fara'a da murmushi ya ɗago kai ya dube ta yana mai amsa sallamar. Cikin ɗari-ɗari Fauwaza ta zauna tana mai fuskantarsa. Sarki Usman ya dubeta cikin nutsuwa yace, "Haba 'yata,ki saki jikinki mana ki tuna fa cewa nine mahaifinki,kuma babu abin da nake so a duniyar nan sama dake. Na unmarce ki da cin wannan abin tare da ni." Koda jin haka sai farin ciki ya lulluɓe Fauwaza domin tana jin daɗin kasancewa tare da mahaifinta,a kowanne lokaci. Nan take ta yaye ƙyallan da ya rufe mata fuska,kuma ta saki jiki suka fara cin abincin cikin kwanciyar hankali. Sai da suka sha ruwa,a sannan ne sarki Usman yayi gyaran murya yace, "Yake 'yata ki yi sani cewa ban kiraki ba nan domin komai sai don na labarta miki wani mafarki wanda nayi,ya firgitani kuma ya jefani cikin rashin fahimta da ruɗani. Ina son ki fassara mini wannan mafarki don na gane ma'anarsa." Ba tare da ɓata wani lokaci ba,ya zayyana mata wannan mugun mafarki da yayi. Bayan ya gama sai yaga gimbiya Fauwaza ta shiga yanayin damuwa cikin alamun karayar zuciya tace da shi, "Yakai Abbana ina son ka sani cewar fassarar wannan mafarki naka a bayyana take. Waɗannan baƙaƙen tsuntsaye guda talatin da bakwai daka gani ba komai bane face hadiman wata ibilishiyar bokanya,waɗanda duk sun kasance baƙaƙen aljanu,kuma kafirai marasa tausayi da imani. Waɗannan halittu biyu dake wa baƙaƙen aljanun jagora kuwa bokanyar ce da uwargidanta,wata aljana muguwar gaske. Wannan mafarki naka yana bushara ne da cewar waɗannan kafirai zasu jehowa manyan sarakunan duniya wata irin muguwar cuta. Sarakunan guda shida ne,kuma sune waɗannan turakan gini daka gani a cikin mafarkinka. Wannan guba wacce tsuntsayen ke zubowa akan turakan gini ita ce nuguwar cutar. Rugujewar turakan ginin da faɗuwarsu ƙasa na nufin cewa waɗannan sarakuna guda shida zasu kamu da ciwon ajali har ya kaisu ga kushewa,idan baka manta ba akwai gidaje guda shida ƙarƙashin turakan,waɗannan gidaje sune manyan ƙasashen duniya dake ƙarƙashin manyan sarakuna. Waɗannan ƙasashe sun haɗa birnin Sin,Hindu,Rum,Ƙisra,Misra da Farisa. A cikin mafarkin an nuna maka cewa gidajen shida sun ƙone ƙurmus,sakamakon rugujewár turakan ginin guda shida. Wannan yana nufin cewa da zarar cutar ajalin ta gama kashe sarakunan waɗannan ƙasashe shida za'a cisu da yaƙi gaba ɗaya. Kà tuna cewa wutar data kama gidajen ta kama rigarka har ta ƙone rabinta ɓangaren hagu,amma ko kađan bata ƙona fatar jikinka ba,wannàn yana nufin cewa babu makawa kaima sai kamu da cutar mutuwar ɓarin jiki,amna ba zai taɓá imaninka da addininka ba. Wannan farar tsuntsuwa kuwa data zo maka da bushara ba komai ba ce face Addinin Musulunci. A cikin wannan mafarkin naka farar tsuntsuwar data gaya maka cewa inda za ka saki wata kurciya guda ɗaya wadda ka keɓeta ka hana kowa kusantarta da fa kashe wutar dake ƙoƙarin ƙone gidajen shida kuma ta káshe baƙaƙen aljanun nan guda talatin da bakwai da iyayen gidansu. Wannan kurciya ba komai bace face ni ɗin nan gimbiya Fauwaza." Koda gimbiya Fauwaza tazo nan a zancenta sai sarki Usman ya cika da tsananin mamaki. Hankalin sa ya dugunzuma fiye da kowanne lokaci. Kawai sai yayi ajiyar zuciya ya dubi gimbiya Fauwaza cikin alamun karayar zuciya da sallamawa yace, "Yake 'yata haƙiƙa fassarar wannan mafarki ta tayar mini da hankali. Na sani cewa ba ki taɓa yin ƙarya ba,kuma duk abin da kika faɗi yana faruwa a zahiri. Lallai ni da sauran waɗannan sarakuna muna cikin mummunan tashin hankali. Tabbas ya zama wajibi in baki dama ki fita yin jihadi a doron ƙasa,domin kawar da maƙiya addinin Allah,kuma ki kawar da zalunci ki shimfiɗa adalci. To amma abin tambayar anan shine ke ba jaruma bace,kuma baki taba yin yaƙi ba,ta yaya zaki iya fuskantar waɗannan manyan azzalumai masu tsananin karfin damtse da ƙarfin tsafi?" Yayin da gimbiya Fauwza ta ji wannan batu na mabaifinta sai tayi murmushi tace, "Yakai Abbana ina son na tuna maka cewa wanda duk yayi dogaro da Allah,haƙiƙa Allah zai iya masa bisa dukkanin abin da yasa a gabansa. Abin da nake so da kai shi ne kasa a shirya mini runduna ta mayaƙa kimanin mutum dubu saba'in,ni kuwa nayi musu jagora izuwa cikin waɗannan manyan ƙasashen duniya,duk inda muka je za mu yi musu wa'azi bisa addinin Allah cikin masalaha da nasiha,idan sun karɓa hannu shikenan Alhamdulillah,idan kuwa suka bijire sai na yaƙe su da ƙarfin tsiya na kafa tutar Musulunci a ƙasar. Tabbas in dai ka lamince mini hakan Musulunci zai rinjayi kafirci kuma cutar da zata kamaku sai na zamo sanadiyar warkewarku." Lokacin da gimbiya Fauwaza tazo nan a zancenta sai hawaye ya zubowa sarki Usman. Koda ganin haka sai hankalinta ya tashi ta matsa gare shi ta riƙe hannayensa biyu tana mai cewa, "Yakai Abbana ina dalilin zubar wannan hawaye a idanunka? Ka yi mini gafara idan har maganganuna sun ɓata maka rai,don kada na shiga cikin fushin Allah." Cikin alamun tausayawa dana nuna tsantsar kauna,sarki Usman ya kama kafaɗun gimbiya Fauwaza yace, "Yake 'yata na rantse da sarki makaɗaici wanda bashi da abokin taraiya baki taɓa faɗin wata kalma ba guda ɗaya wadda ta ɓata mini rai,tun haihuwarki kawo iyanzu,ki yi sani cewa ba komai ba ne ya haddasa zubar hawaye a idanuna ba face sanin cewa lokaci ya zo wanda zamu rabu tsawon lokaci alhalin kin sani cewa a duk duniya babu abin da nake so sama da ke. Daidai da rana guda ban son rabuwa dake,saboda tsananin so da nake yi miki ne na hana kowa kusantarkı,na hanaki yin aure,kuma na ɓoye kyawun nan da Allah ya yi miki. Yau gashi za ki tafi ki barni,kyawunki zai bayyana a duniya kowa ya gani." Sa'adda sarki Usman ya zo nan a zancensa sai jikin gimbiya yayi sanyi. Tausayi da ƙaunar sarki Usman suka baibaye zuciyarta. Kawai sai ta rungumeshi,ta fashe da kuka tana mai cewa, "Da yardar Allah duk inda na je zan dawo gida lafiya. Albarkacin wanda aka yi duniya da lahira dominsa,ajali ba zai zamo sanadin rashin sake saduwar mu ba. Zan cigaba da roƙon Allah da yasa mu yi tsawon kwana har ka ga ranar aurena kuma kaga jikanka da idanu ka." Sarki Usman ya janye jikinsa daga na gimbiya Fauwaza suka fuskanci juna sosai,yana mai share hawayen idanunsa yace, "Yake 'ya ta,ki dube ni da kyau ki gani fa haƙiƙa tsufa ya riske ni domin a ƙallah shekaruna sun haura casa'in,anya kuwa zan iya kai wannan lokacin?" Cikin sauri ta tari numfashinsa tace, "Kada ka ƙara faɗin haka ya Abbana domin kuwa rai da mutuwa duk a hannun Allah suke,kuma babu wanda ya san gawar gobe." Cikin yanayin nadama sarki Usman yace, "Allah na tuba ka yafeni,kuma na roƙe ka daka sakawa wannan 'ya tawa da lada mai yawa,domin ta kasance mai sani akan tafarkin shiriya. Allah na roƙeka da kayi mata jagora bisa wannan gagarumin aiki da zata yi dominka. Ka kareta daga dukkan tsautsayi,asara,mugun ji da mugun gani,ka bata nasara bisa maƙiyanka. Ka ɗaukaka ta,ɗaukaka irin wacce ka yiwa bayinka na gari magabatanmu." Haka dai sarki Usman yayi ta yiwa gimbiya Fauwaza addu'o'in alheri. Bai gushe ba yana yi har sai da itama ta karɓa,tana mai yi masa fatan alheri. Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin sarki Usman da 'yarsa gimbiya Fauwaza kyakkyawar budurwar da babu kamarta a duk faɗin duniya a wannan zamani a cikin birnin Misra. Al'amarin bokanya Tazibul Luhucul,aljana Saubatu Azwas da hadimai talatin da bakwai kuwa kafin su rabu kaso biyu don tafiya aiwatar da wannan mummunan aiki dake gabansu saida süka tsaya suka tattauna gami da yin shawara bisa inda ya kamata su fara zuwa. Tazibul Luhucul ce ta fara magana yayin data dubi Saubatul Azwas tace, "Yake ƙawata ina son ki sani cewa sarkin Misra da sarkin Hindu dana Farisa sune mafiya jajurcewa akan yawaita bauta da ibada,don gudun kada su ɓata mana lokaci zai fi kyau mu fara zuwa kasar Rum da Ƙisra don aiwatar da wannan aiki in yaso daga baya sai mu je Misra,Hindu da Farisan." Koda jin haka sai Saubatul Azwas ta ƙyalƙyale da dariya tace, "Yake ƙawata haƙiƙa maganarki gaskiya ce,don haka ni yanzu zan kwashi rabin hadimanki mu tafi kasar Rum ke kuma sai ki kwashi rabin ku tafi kasar Ƙisra." Tazibul Luhucul tace, "Ƙwarai kuwa wannan shawara tayi kyau,kuma koda na haɗu da wata matsala zan neme ki a cikin madubin tsafina na sanar dake don ki kawo mini đauki." Saubatul Azwas ta sake ƙyalƙyalewa da dariya a karo na biyu tace, "Wannan ba matsala ba ce." Ba tare da ɓata wani lokaci ba Saubatul Azwas da bokanya Tazibul Lubucul,suka kwashi hadiman nan suka kasu gida biyu. Saubatul Azwas ta nufî ƙasar Rum,ita kuwa Tazibul Luhucul ta nufi kasar Ƙisra. Lokacin da bokanya Tazibul Luhucul tare da rabin hadiman ta suka nufi ƙasar Ƙisra basu fi sa'a uku da rabi ba suna tafiyarsu suka iso bayan birnin. A daidai wannan lokaci ne rana ta faɗi,wato Magariba ta doso kai. Tazibul Luhucul ta ciji yatsanta,sannan ta dubi hadimanta cikin alamun takaici tace, "Kash babu damar mu shiga cikin wannan birni yanzu dole ne mu tsaya anan har dare ya raba." Koda jin haka sai wata hadima mai suna Lulaija tace, "Ya shugabata mene ne hikimar hakan?" Cikin fushi da harara Tazibul Luhucul ta dubi Lulaija tace, "Amma dai duk yadda aka yi ƙwaƙwalwar ki ta kifi ce,mara basira da mantuwar tsiya. Ashe har kin manta da bayanin da mai girma Saubatul Azwas ta yi mana kenan cewar lallai ba zamu ziyarci sarakunan nan ba sai da tsakar dare,kuma kada mu kusance su yayin da suke aikin bauta ko tsafi." Lulaija ta duƙar da kai tace, "Ki gafarce ni ya shugabata haƙiƙa zancenki dutse ne,lallai na sha'afa." Kafin Lulaija ta gama faɗin haka tuni Tazibul Luhucul ta nuna gaba ɗayan hadiman da sandar tsafinta har dama ita kanta. Ai kuwa nan take suka bace ɓat,a lokaci guda tamkar dama can babu su a wurin. Bayan kamar rabin sa'a sai Tazibul Luhucul ta murza sandar tsafin nata suka sake bayyana gaba ɗaya a wajen. Bayyanarsu ke da wuya Lulaija ta rusina a gaban Tazibul Luhucul cikin alamun girmamawa tace, "Ya shugabata mene ne ya faru kika ɓoyemu gaba daya?" Tazibul Luhucul tayi murmushi, tace, "Ba komai ba ne ya sa na ɓatar damu ba face na jiyo ƙamshin aikin bokayen garin nan suna son su san da zuwanmu. Abin da ba su fahimta ba shine wanda duk ya riga ka kwana,dole ne ya riga ka tashi." Cikin alamun mamaki Lulaija tace, "To saboda me suke son su san zuwanmu?" Tazibul Luhucul tace, "Saboda su san matakin da zasu ɗauka wajen hanamu aiwatar da abin da ya kawo mu. Na rantse da ƙarfin tsafina yanzu ba su isa su ganmu ba,ko su ji muryarmu,domin na tsafance mu mu da ƙarfin sihirin tsafina. Kowannen ku ya zauna cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,da zarar dare ya raba zan baku izini ku tafi izuwa gidajen 'yan majalisar garin nan ku barbaɗa musu hodar tsafin nan wacce zamo sanadiyar kamuwarsu da cutar ajali." Kamar yadda Tazibul Luhucul tayi wannan batu haka al'amarin ya kasance,wato basu shiga cikin birnin Ƙisra ba,sai da dare ya raba tsakiya. Hadiman na ta suka kasu gida goma,suka tafi izuwa gidajen 'yan majalisar. Cikin sa'a kuwa duk gidan da suka je sai su iske maigidan na kwance yana ta sharar barci. Nan take sai su watsa masa wannan hodar tsafi,su wuce gaba. Gida ɗaya ne suka sami matsala,wannan gida kuwa na wazirin garin ne,shi dai wannan waziri ya kasance yayan bokan birnin wanda ake kira Garfas. Boka Garfas ya sanar da waziri cewa idan har ya daina barci a cikin dareren wannan shekara to tabbas wannan sihiri na cutar ajali ba zai hau kansa ba. A bisa wannan dalili ne ya sauya lokacin barcinsa gaba ɗaya,ma'ana ya daina yin barci da daddare sai dai da rana. Lokacin da hadimai suka zo gidan waziri sai suka iske shi a zaune yana ta aikin bautar gunkin da suke bautawa mai suna Gulmakuru. Koda suka riskeshi a cikin wannan hali sai suka ja da baya da sauri suka koma bayan katangar gidan suka zauna,suna haki da dafe ƙirazansu,cikin yanayin tsoro da tashin hankali. Daga can sai Lulaija tace, "Kai amma fa wannan shegen waziri da nacin tsiya yake,lallai ku sani cewa mun tsallake rijiya da baya,ba don mun yi sauri mun koma da baya ba da tuni gaba dayanmu mun zama gumaka. In kuwa muka zama gumakan babu wanda ya isa ya dawo damu ainihin halittarmu,shi kenan tamu ta ƙare." Yayin da Lulaija ta zo nan a zancenta,sai wata hadimar mai suna Kamtura tace, "Tabɗijam ai kuwa in dai haka ne babu wawaye a duniyar nan kamarmu yanzu saboda tsananin kwaɗayin abin duniya muka jefa kanmu cikin irin wannan mugun aiki,mai mugun haɗari?" Lulaija tace, "Eh, to haka ne,amma ai kin san cewa faɗan da yafi ƙarfinka dole ne ka mayar da shi wasa. Duk mun sani cewa ko muna so,ko bama so dole ne mu zama bayin Tazibul Luhucul,in kuwa muka ƙi bin umarninta hallaka mu za ta yi." "Kunga yanzu dai ba hira ce mafitarmu bà yaya zamu ɓullowa wannan shegen wazirin mai naci. Kun sani cewa idan fa lokacin da aka ɗiba mana ya cika dole ne mu bar wajen nan,kuma idan muka tafi ba tare da samun biyan buƙata ba gawa ma sai ta fi mu jin daɗi da kwanciyar hankali." Wata hadima ce mai suna Faltu,tayi wannan furuci. Gaba ɗayansu suka yi shiru suna tunani aka rasa wanda zai ce wani abu tsawon daƙiƙa sittin. Gaba ɗayan waɗannan hadimai su goma sha bakwai ne,amma namiji ɗaya ne tak a cikinsu,ana kiransa da suna Murkubalu. Cikin alamun mamaki Murkubalu ya dubi waɗannan hadimai 'yan uwansa ɗaya bayan ɗaya yayi tsaki,sannan yace, "Amma dai kun bani mamaki a matsayinku na mata iyayen kaidi a ce kun kasa tunano hanyar da zamu hallakar da wannan mutum. To idan kun sallama mini ni zan faɗi abu ɗaya da za'a yi mu sami nasara." Koda jin haka sai Faltuz tace, "Ai dama ku maza kaidin ku yafi namu masifa,kawai dai ƙaurin suna muka fiku. Maza sanar damu dabarar da zamu yi don mu hallakar da wannan basarake cikin ƙanƙanin lokaci." Murkubalu ya yi murmushi, sannan kuma ya ƙyalƙyale da dariya har da doka ƙafarsa guda ƙasa,yana mai yiwa kansa kirari da cewar, "Nine Murkubulu tsuliyar dodo, kuna nine baƙin annamimi uban munafukai. Nine sharri kayan kwalba,kakan mugayen aljanu,masu baƙar zuciya da mugun nufi da baƙin tanadi." Murkubalu ya ci gaba da cewa, "Abin da za'a yi shi ne,wace ce tafi kowa rashin tsoro a cikinku?" Nan da nan su duka suka nuna Lulaija suka ce, "Gata nan kuma ita ce wawiya don an bata sandar girma akan hakan,kuma an tabbatar da cewa a cikin gaba ɗayan al'ummar aljanun garinsu babu mai iya sai da rai kamarta." Murkubalu yayi murmushi,a karo na uku yace, "Yauwa ke nake so ki juye kamanninki izuwa na matar wannan waziri,ki kasance cikin suturu mai shara-shara wato wadda ke nuna surar jikinki sai ki gifta ta gabansa,yayin da yake wannan aikin bauta na gunkinsa. Tabbas yana ganinki sha'awarsa zata motsa ya tashi ya bar bautar ya bi bayanki. Mu kuma sai mu yi amfani da wannan damar mu cim masa." Koda jin wannan batu sai Lulaija tace, "Tabɗijam amma kun zo mini da rainin hankali,to ku tsaya ku ji don fa an ce ni wawiya ce kuma bani da tsoro baya nufin cewa bana son na cigaba da rayuwa a duniya,shin ka mantane cewa an ce kada mu kusance su yayin da suke aikin bauta ko tsafi? Ko kuwa kana so ne na halaka a banza." Murkubalu yace, "Ai ba so nake ki halaka ba,kuma bana ce ki kusance shi ba,nesa da shi zaki gifta,buƙata dai kawai ya ga giftawar taki cikin wannan yanayi." Yayin da Lulaija ta ji haka sai tayi murmushi tace, "An gama." Kafin wani daga cikinsu ya ƙara cewa wani abu tuni ta ɓace ɓat,bata sake bayyana a ko'ina ba sai akan tagar turakar wannan waziri a matsayin tsuntsun kanari. A wannan lokaci waziri,ya tsugunna gaban gunkinsa bisa gwiwoyinsa yana bauta. Cikin hanzari tsuntsun kanarin ya sauko ƙasa ya tsaya ya zamana tsakaninsa da waziri ya kai taku arba'in. Kawai sai tsuntsun kanarin ya rikiɗa ya zama matar waziri wadda ta kasance ɗanyar budurwa mai tsananin kyawun fuska da kyawun surar jiki. Sanye take cikin wata irin doguwar riga mai launin shuɗi kuma shara-shara. Daga ƙasanta an yi mata beza da adon dutwatsen lu'ulu'u. Koda ta yi tafiya taku biyu sai ƙarar duwatsun lu'u lu'un suka janyo hankalin waziri ya ɗago da kansa da sauri don yaga komene ne. Ai kuwa sai ya yi arba da kyakkyawar matarsa tana mai bayyanar da surar jikinta kuma ta faɗa cikin ɗakin da sauri. Cikin kiɗemawa waziri ya miƙe zumbur har ma yana dungure gunkin nasa,wato abin bautar tasa. Gunkin ya tuntsure ya faɗi ƙasa,amma san bai lura ba. Kawai sai ya ɗaga ƙafarsa ya shallake gunkin ya nufi ƙofar ɗakin da matar tasa ta shiga. Har ya jefa ƙafarsa ta dama cikin ɗakin ya ɗago ta hagun kenan sai yaji wani irin abu ya shiga jikinsa gaba ɗaya,wanda ya haddasa sandarewar jijiyoyin jikinsa na tsagin ɓangaren hagu. Kawai sai ji yayi komai na rabin jikinsa ya daina aiki. Take ya yanke jiki ya faɗi ƙasa,yana mai kurma ihu. Al'amarin da ya janyo farkawar gaba ɗayan mutunen gidan kenan,suka rugo inda yake a firgice. Koda suka zo suka ga halin da yake ciki sai duk suka kama kuka suna cewa, "Shi kenan ta faru ta ƙare,annobar da ake faɗi ta sauka." A can gidan sarkin Kisra kuwa lokacin da Tazibul Luhucul ta sauka a tsakiyar harabar gidan sai ta iske sarki a kishingiɗe yana gyangyaɗi,amma hannunsa guda na kan irin wannan gunki wanda wazirinsa ke bautawa. Koda ganin haka sai hankalin Tazibul Luhucul ya dugunzuma don ta san cewa ba zata iya yi masa komai ba,muddn hannunsa na kan gunkin. Nan fa ta tsaya tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta da tunanin mafita. Sai daya zamana alfijir ya kusan ketowa anma bata sami mafita ba. Ta ɗauko mudubin tsafinta ta shafe shi da hannun hagu,take taga duk abin da ya faru tsakanin hadimanta da 'yan mnajalisar wannan birni wato taga cewar gaba ɗaya sun sami nasara akan 'yan majalisar birnin cikin sauƙi,waziri ne kawai ya basu wahala amma shima ɗin a ƙarshe sun gama dashi. Kuma taga cewa tuni hadiman nata sun koma can bayan gari sun tsaya ita kawai suke jira. Gashi kuma saura baifi daƙiƙa ɗari uku da sittin ba lokacin tafiya yayi. Nan fa Tazibul Luhucul ta ji zuciyarta ta cika da mugun baƙin ciki tace a ranta, "Haƙiƙa abin kunya ne ace hadimaina sun sami nasara amma ni na kasa. Ya zama dole nima nayi tunanin dabara kafin ƙarewar ƙanƙanin lokacin da nake da shi." Tana gama aiyana hakan ne,wata kyanwa ta zo giftawa ta gabanta. Cikin fushi Tazibul Luhucul ta kaiwa kyanwar duka da hannunta na dama,ai kuwa kyanwar nan sai ta tsorata tayi tsalle ta faɗa kan sarki. Ba shiri sarki ya farka a firgice,ya miƙe tsaye gami da zare takobinsa ya kama leƙe-leƙe da dube-dube. Ba zato,ba tsammani,sai ya ji komai na tsagin rabin jikinsa ya daina aiki. Take ya faɗi ƙasa,kawai sai jin dariyar Tazibul Luhucul yayi tana mai cewa na gama dashi,na gama da shi. Ƙiri ƙiri ta baiyana a gabansa tana ta yin wannan furuci. Shi kuwa sai ya kurma ihu yana mai kiran sunan ɗansa jarumi yarima Lubaika wanda tuntuni yayi nisa akan hanyarsa ta zuwa dajin dulmus don saduwa da boka Hulumul Makahur. Kafin mutanen gidan sarautar su kawo wani ɗauki tuni Tazibul Luhucul ta ɓace ɓat sai zuwa akayi aka iske sarki a kwance ya zama naƙasasshe. Kamar yadda Tazibul Luhucul tare da hadimanta suka sami nasara a birnin Ƙisra haka ma Saubatul Azwas da nata hadiman suka sami nasara a birnin Rum wato dai suma sun mai da sarkin garin da 'yan majalisarsa naƙasssu masu mutuwar jiki. Bayan wannan gagarumar nasarane suka sake haɗuwa a wata mahaɗa dake tsakanin biranen biyu,nan take suka ƙyalƙyale da dariyar farin ciki. Saubatul Azwas tace, "Yauwa yanzu mun gama da ƙasa biyu saura guda huɗu. Yake ƙawata yanzu sai ki tafi ƙasar Hindu da Farisa ni kuma ki barni da Misra domin itace ƙasa mafi haɗari tunda sun kasance ma'abota addinin musulunci,waɗannan mutane suna iya hallakar da aljanu ta hanyar ƙonesu da wuta irin sihirtacciyar wuta yayin da suke kiran sunayen Ubangijinsu wato abin bautarsu. Koda jin haka sai Tazibul Luhucul tace ai dama babban kaya sai amale,dole ne na barki dabirnin Misra,babu abinda zance dake sai fatan sa'a." Saubatul Azwas ta fashe da mahaukaciyar dariya tana mai buɗe fukafukanta ta tashi sama cikin sauri hadiman dake tare da ita suka bi bayanta,nan da nan suka cilla izuwa ƙololuwar sararin samaniya suka nufi birnin Misra. Tazibul Luhucul da nata hadiman ma suka tashi sama suka nufi ƙasar Hindu da Farisa. Wannan shine abinda ya faru gasu Tazibul Luhucul bayan sun fara samun nasara bisa gagarumar buƙatarsu ta duniya wacce itace mallakar mutane da aljanu dakuma haɗa sinadarin gano inda wani sirin tsafiwanda shine kacal ya rage musu su mallaka a taskarsu ta tsafi. Al'amarin yarima Sammaru kuwa lokacin daya kama hanya ya nufi dajin Dulmas saida yayi tafiyar sa'a bakwai cif ba tare da ya yada zango ba,kuma bai haɗu da wani tsautsayi ba ko mugun abu face namun daji iri-iri waɗanda ko guda ɗaya bata tare shi ba ko afka masa. Yayin da rana ta take sai zafi ya yawaita a jejin,duk da cewa akan doki yake tafiyar sai daya jiƙe sharƙaf da gumi. Da yake zuciyarsa a harzuƙe take ko kaɗan bashi da niyyar tsayawa a ko'ina har sai ya riski kogon da boka Hulumul Makahur yake,dama ya sani cewar tafiyar sa'a goma sha huɗu ce zata kaishi wannan wuri daga cikin birnin Sin. Wato a ƙa'ida in dai mutum ya taso da sassafe tabbas zai isa bayan magariba. Babu zancen yunwa,ƙishirwa ko gajiya a tare yarima Sammaru domin yayi watsi da su a ransa burinsa kawai ya ganshi a gaban kogon tsafin boka Hulumul Makahur. Bisa rashin sa'a sai yaga dokinsa ya fara nuna alamun sarewa domin baya iya sauri sosai kamar da farko,sannu a hankali kuma sai dokin ya fara tafiyar sassarfa,wannan al'amari ya fusata shi amma daya fuskanci cewar dokin ya gaji ne kuma yana buƙatar ruwa da abinci sai ya rungumi ƙaddara ya tsaya ya sauka. Sammaru ya duba gabas da yamma,kudu da arewa don ya hango inda za'a sami fadama. Ai kuwa sai ya hango wata ƙorama wadda ke kwaranya bisa wasu ƙananan duwatsu. A gefenta wasu ciyayine masu tsawo da duhuwa,koda ganin wannan wuri sai murna ta kama shi cikin sauri yaja dokin ya nufi inda wannan ƙorama take. Abin da bai sani ba shine wannan wuri wata mafakace ta waɗansu gungun muggan 'yan fashi. Adadin waɗannan 'yan fashi ya kai dubu biyar,duk suna nan a kwance cikin ciyawa mai duhuwa sunyi lamɓo. Tun sa'adda yarima Sammaru yazo wajen suna ganinsa amma shi bai gansu ba kuma bai ji motsin komai ba a wajen,kai ko kaɗan ma bai taɓa zaton wani mai rai zai iya zama a cikin wannan duhuwa ba in dai kasance ire-iren su kifi,kwaɗo da makamantansu ba. Sammaru ya kai dokin nasa cikin ƙoramar,dokin yasa bakinsa ya sha ruwa ya ƙoshi sannan ya nufi cikin duhuwar nan inda doguwar ciyawa take ya kama cin ciyawar,shi kuwa yarima Sammaru sai ya cire takobinsa da sauran kayan yaƙinsa ya ajiye a gefe guda sannan ya tuɓe kayan jikinsa gaba ɗaya ya ajiye,ya faɗa cikin ƙoramar ya kama wanka. Faruwar hakan keda wuya 'yan fashin nan suka yi fitar burtu gaba ɗayansu suka kewaye ƙoramar duka. Waɗannan 'yan fashi sun kasance gabza-gabza masu ƙirar samudawa kuma suna ɗauke da muggan makaman yaƙi,komai rashin tsoron mutum in yayi arba dasu sai zuciyarsa ta harba,cikin tsananin mamaki Sammaru ya ɗaga kai sama ya dubesu,to amma shi dai yasan duk bala'in da za'ayi sai dai ayi amma ba zai yarda su kämashi ba su wulaƙantashi bare su ɓata masa lokaci bisa saurin daya keyi na isa kogon tsafin boka Hulumul Makahur. Wani garjeje daga cikin 'yan fashin wanda shine mafi girma,kwarjini da ban tsoro ya matsa kusa da Sammaru yace ɗan nema samamme fito kayi gaisuwa gaban sarkin ɓarayin jejin Dulmas tun gabanin banyi fishi da kai ba,ka ware ido kana kallon mu kamar mutum đa mutum. Wannan kalma ta ƙarshe ba ƙaramin ciwo ta yiwa yarima Sammaru ba domin shi a ganinsa anyi matuƙar muzantashi,wai shin ma me wannan ɗan fashi yake nufi da kamar mutum da mutum,lallai akwai raini a cikin wannan batu,wato yana nufin su sune mutane shi kuwa ba mutum bane,cikin tsananin fushi Sammaru ya dubi sarkin ɓarayin ya daka masa harara gami da tsawa yace, "Kai ƙaton banza,la'anannen wofi,shin bakusan ko ni waye ba,kake bani umarnı,kuma har kake ƙasƙantani. To kasani cewa idan kana yi mini kallon jaki ne ni kuma ina yi maka na harawa ne. Babu wani đan da ya isa ya ɗaga hannu a gabana ba tare da na ladabtar da shi ba,nine yarima Sammaru ɗa ga sarki Alyasil Buhus na birnin Sin,duk wani abu daya kwana ya tashi acikin jejin nan ƙarƙashin mulkina da iko na yake." Koda jin wannan batu sai sarkin ɓarayin ya bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da gogen tsumma. Nan fa sauran yaransa suka karɓa,ma'ana suka taya shi yin dariyar. Lokaci guda kuma ya tsuke bakinsa ya sake murtuke mummunar fuskarsa mai kama da tatsilallan man shanu yace, "Kai yaro sarauta acikin gari ake yinta banda cikin daji,babu sarki a jeji sai mai ƙarfi,mune sarakan dawa maganin 'yan' dawa da baƙindawa,babu mai shiga dajin nan ya fita lafiya face mun tatseshi ya zama talaka fitik,koda kuwa shine ya fi kowa dukiya,sai mun kwankwashe shi ya zama tamkar ƙwaryar molo kuma sai mun ragarjeje shi ya fatattake tamkar yayin iska." Sammaru yace, "Ai kuwa ƙaryarku tasha ƙarya daga yau kun dena wannan ƙazamar sana'a ta zalunci domin na kasance mala'ikan azzalumai mai mai dasu turɓaya a doron ƙasa." Kafin Sammaru ya gama rufe bakinsa sarkin ɓarayin ya bada izinin a ragargaza shi. A guje mutum hamsin sukayi caaa a kansa da nufin su daddatsashi suyi gunduwa gunduwa dashi a cikin ƙoramar. Kash,rashin sani yafi dare duhu inda waɗannan barade hamsim sun san abin da zai biyo baya da basu haiyakewa Sammaru ba farat ɗaya. Lokacin da baraden hamsin suka yi caa kansa kowa ya kai sara da mugun nufi sai Sammaru ya yi nutso izuwa ƙarƙashin ƙoramar ya lume a cikinta suka nemeshi suka rasa. Cikin ƙaraji sarkin ɓarayin yace dasu suma suyi nutso ƙasa,nan take suka bi umarni. Ai kuwa tunda suka nutse,đayansu bai ɗago ba sai bayan gajeren lokaci sannan aka ga gawarwakinsu na tasowa sama kuma ko kaɗan babu alamar yanka ko tsini ko kaifi a sassan jikinsu. Al'amarin da ya ƙara harzuƙa sarkin ɓarayi da yaransa kenan. Kafin ɗayansu yayi wani yunƙuri sai ga Sammaru ya taso sama daga cikin ƙarƙashin ƙoramar riƙe da takobin ɗaya daga cikin 'yan fashin yana mai ƙaraji. Nan fa 'yan fashin nan suka yi caa kansa gaba ɗaya wuri ya yamutse ya shiga saransu suma suna mai da martani. Sai gashi Sammaru yana kutsawa ta cikinsu,in yaso yayi gabas ko yamma,wani lokacin kuma yayi kudu da arewa. Amma yin hakan baisa ya sami nasaran kai guda ɗayansu ƙas ba suma kuma ɗayansu bai samu damar saransa ko sukarsa ba,nan fa aka ci gaba da artabu da ɗauki ba daɗi. Shi dai Sammaru ya kasance mai tsananin zafin nama da jarumta su luma sun kasance masu juriya da ƙarfin damtse. Duk da cewar yana saransu a sassan jiki jinı na zuba basu kai ƙasa ba kuma amma suma sun kasa kai shi ƙasan. Nan fa ya zame masu alaƙaƙai suma suka zame masa alaƙaƙai. Tofa! yau ga ƙarfi ya haɗu da naci,juriya ta haɗu da dakakkiyar zuciya kuma zafin nama ya haɗu da yawan aiki. Abin dai da yarima Sammaru ke gudu sai da ya faru domin sai da rana ta faɗi duhu ya soma ana wannan masifafen faɗa. Ana cikin haka ne wata ƙatuwar inuwa ta lulluɓe filin fafatawar gaba ɗaya suka ɗaga sama,cikin kaɗuwa 'yan fashin nan suka ɗaga kawunan su sama gaba ɗaya,ai kuwa sai suka yi arba da wata ƙatuwar halitta,wannan halitta dai ba komai bace face aljani Labagaza,zaune akansa yarima Yauhana ne da boka Karluz. Nan take aljani Labagaza ya sauka gefe guda,Yauhana da Karluz suka sauka daga kansa. Koda 'yan fashin nan su kaga cewar aljani Labagaza bai taso kansu ba sai kawai suka ci gaba da kaiwa Sammaru farmaki,cikin hanzari yarima Yauhana ya kai masa ɗauki aka ci gaba da fafatawa. Aljani Labagaza kuwa da boka Karluz sai suka zama 'yan kallo,yaƙi yayi yaƙi,gumu yai gumu kuma wahala tai wahala ya zamana gumurzun ya zama kare jini biri jini. Ko da ganin haka sai ran boka Karluz ya ɓaci,kawai sai ya dubi aljani Labagaza yace gama mini da waɗannan 'yan fashi domin suna nema su ɓata mana lokaci. Kafin Karluz ya gama rufe bakin sa Labagaza yasa yatsunsa biyar ya tsince 'yan fashin gaba ɗayansu su dubu biyar ya mutsitsikesu cikin tafin hannunsa. Kawai sai ya yarfe hannun ya zubar dasu ƙasa a rugurguje tamkar an dakesu a cikin turmi. A dai dai wannan lokacine yarima Sammaru ya dubi Yauhana da Karluz cikin ɗumbin mamaki sannan kuma ya dubi aljani Labagaza wanda babu abin da ya burgeshi da shi face tsananin girmansa da fadin tafin hannunsa,cikin yanayin mamaki Sammaru ya dubi Yauhana da kyau yayi nazarin suturar dake jikinsa ya tabbatar da cewa ɗan sarkine sai yace, "Yakai wannan ɗan sarki wane ne kai kuma ina dalilin taimakonku a gareni? Kafin Yauhana ya buɗe baki yace wani abu sai boka Karluz ya tari numfashinsa gami da shan gabansa sannan ya risina a gaban Sammaru ya kwashi gaisuwa yace, "Gaisuwa a gareka ya kai yarima Sammaru 'đa' ga sarki Alyasil Buhus na birnin Sin,kayi sani cewa wannan ɗan sarkin dake gabanka yarima Yauhana kenan 'đa' ga sarki Jamshul na birnin Rum. Ya kai Sammaru ka sani cewa bamu taimake ka don komai ba sai domin muna kan tafarki guda na buƙatar riskar boka Hulumul Makahur wanda zai samu akan turbar zuwa kogon Muddarul ikisina inda taskar tsafi take don deɓo tsumin tsafin da sarakunanmu zasu sha su warke daga muguwar cutar mutuwar rabin jiki. Ni da nake maka wannan bayani sunana boka Karluz,hadimi ga mutanen Rum." Yayin da yarima Sammaru ya jı wannan jawabi sai murna ta kamashi nan take ya miƙa musu hannu suka yi musabiha yace, "Ina murnar haɗuwa da abokan tafiya kuma abokan share hawaye tare,lallai ina mai yi muku bushara da cewar muna daf da isa wajen boka Hulumul Bakahur." Koda jin haka sai boka Karluz yayi murmushi yace, "Nasan da haka. Yakai wannan ɗan sarki zaifi kyau ka rabu da dokinka anan domin mu tafi tare akan bawanmu aljani Labagaza gashi tsaye yana jiranmu." Sammaru ya ƙarewa Labagaza kallo sama da ƙasa yace, "Haƙiƙa kaci sunanka don tun da nake ban taba ji ko ganin aljani mai girmanka ba sai yau." Labagaza ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Haba yaro ai duniyar nan da faɗi take inda kasan aljani Shamharu shahararre da baka faɗi haka ba." Cikin mamaki Sammaru yace, "Wane ne kuma Shamharu shahararre?" Labagaza yace, "Ai wannan labarine mai tsawo sai dại ka nemi littafin tarihi mai suna KUNDIN TSATSUBA a cikin sane zaka sha labarin Shamharu shaharare. A taƙaice dai wani taƙadirin aljanine da ya gallabi duniya a zamaninsa ya zama alaƙaƙai ga komai da kowa." Yayin da aljani Labagaza yazo nan a zancensa sai boka Karluz ya daka masa tsawa yace, "Kai malam ba hira muka zo yi ba,maza ka đaukemu ka kaimu fadar boka Hulumur Makahur." Cikin abin da bai wuce daƙiƙa ɗaya ba aljani Labagaza ya suri Sammaru,Yauhana da Karluz ya azasu a gadon bayansa har ma yayi tafiyar zango biyu,sai gasu sun iso kofar kogon tsafin boka Hulumul Makahur. A hankali kuma a tsanake aljani Labagaza ya sauke su ƙasa. Koda suka dubi kogon sai suka ga ashe siffar mutumce dashi,wato mutum ne a zaune ya tanƙwashe ƙafafunsa kuma ya buɗe tafin hannayensa. Akan tafin hannunsa na dama wata farar kwatanniyace. Akan tafin hannun hagu kuwa jar kwatanniyace. Boka Karluz,Sammaru da Yauhana suka ɗaga kai sama suna kallon wannan gunki cikin al'ajabi da rashin gane ma'anarsa. Yauhana ya dubi Karluz yace, "Shin kuwa kasan ma'anar wannan kwatanniya guda biyu?" Karluz yai ajiyar zuciya yace, "Haba yarıma ya za'ai na sani ai munzo inda sanina bai kai ba. Kasan ance Baba da Babansa,haka kuma malam da malaminsa,ni kam almajirine anan,neman sani nazo biɗa." Karluz na gama faɗin hakan suka ji an bushe da dariya. Dariyar ta cigaba tsawon ɗan lokaci daga bisani ta ɗauke ɗif,kawai sai hannun daman mutum mutumin mai siffar kogon ya sauko ƙasa gabansu. Bakin mutum mutumin kuma ya buɗe yace, "Lale marhaban daku 'ya'yan sarakai ku sanya hannayenku a cikin wannan kwatanniya." Koda jin haka sai boka Karluz ya fara kai hannunsa zai sa acikin kwatanniyar,cikin tsawa mutum mutumin yace, "A kul kasa hannunka idan baso kake ya ruɓurɓushe ba. Domin wannan kwatanniyace ta 'ya'yan sarakai kawai." Cikin tsoro boka Karluz ya janye hannunsa jikinsa na karkarwa yaja da baya Yauhana da Sammaru suka sa hannayensu acikin kwantanniyar kawai sai suka zama farin haske suka ɓace. Mutum mutumin ya sake sauko da ɗaya hannun nasa na hagu mai jar kwatanniya yace, "Saka hannunka aciki ya kai Karluz domin wannan kwatanniya ta bokaye ce kaɗai. Lallai babu mai shiga wannan kogo face sarakai da bokaye." Cikin azama Karluz ya sanya hannunsa a cikin kwatanniyar take ya zama jan haske ya ɓace. A cikin wata ƙasaitacciyar fada mai ginin dutsen jauhar ruwan ɗorawa suka tsinci kansu. Komai dake cikin fadar akan iska yake yawo babu wani abu dake ajiye a ƙasa. Kai irin iskar dake kaɗawa a cikin kogon ma ba irin wacce mutum ya saba shaƙa da ji bace. Abubuwan al'ajabi kuwa gasu nan birjik kaka-kala irin wanda idanu basu taɓa gani ba ne. Nan fa Karluz,Yauhana da Sammaru suka zama cikakkun 'yan ƙauye kuma suka cika da al'ajabi domin su kansu yawo suke yi akan iska kuma tafiya ake yi dasu a cikin kogon ana ƙara nutsawa da su ba akai madakata ba. Har yanzu kuma basu ga mutum ko aljan ba. Babu komai face dabbobi iri iri daga irin halittun ruwa da kuma na jeji masu siffofin al'ajabi. Wani lokacin sai kaga mitsitsin kifi da ƙaton kai mai girman tsauni ko kuma kaga kazar ruwa mai kawuna dubu da silin ƙafa đaya. Haka dai suka yi ta ganin abubuwan mamaki har suka gaji da ganinsu. Ba zato ba tsammani sai gasu acikin wata fadar dabam wacce tafi ta baya kyau da tsaruwa sau dubu. A cikinta aljanu barkatai suna ta aiyuka iri iri na hidimar tsafi. Komai a wannan fadar ma akan iska yake yawo har su kan su aljanun masu hidima. Haka kuma abubuwan al'ajabin dake wajen sun ninka waɗanda ke fadar farko. A cikin wannan fadar ne boka Karluz ya cire rawaninsa ya sake shi don ya ga abin da zai faru Shin rawanin zai faɗo ƙasa ne,ko kuwa zai tsaya a cikin iska? Ai kuwa yana sakin rawanin sai ya tsaya a cikin iska,kuma yayi sama ya naɗa kansa akan boka Karluz. Take boka Hulumul Makahur ya bayyana a gabansu bisa wata karagar mulki. A kansa akwai hular sarki ta zinariya. Hannunsa na hagu na riƙe da farar sandar tsafi. Karagar zinariyar tana tafiya ne akan iska. Yana sanye da wata doguwar jar riga. A wuyansa akwai murjanai kimanin guda arba'in da bakwai,kuma kowanne đaya an yi shine daga abu dama,daga dangin zinare,sai lu'u'lu'u,jauhar, zubarjadi,demon,yaƙutu da dai sauransu. Wani abin ma ko sunansa mutum bai taɓa ji ba. Boka Hulumul Makahur ya dubi boka Karluz yace, "Iskar dake cikin fadar nan tamu ba irin iskar duniyar ku bace. Wannan iska mun samo tane daga duniyar wata." Hulumul Makahur ya waiga ya dubi yarima Sammaru da yarima Yauhana yace, "Ina yi muku barka da zuwa fadar sarkin bokaye. Haƙiƙa kun zo inda za'a share muku hawaye bisa babbar buƙatar dake gabanku,amma ku sani cewa za ku yi shirin nada gammo don đaukar abin da yafi duniyar nan da abin dake cikinta nauyi." Yayin da su Yauhana suka ji wannan batu sai hankalinsu ya tashi,gaba ɗayansu suka ƙurawa boka Hulumul Bakahur idanu,shima sai ya zuba musu ƙwala-ƙwalan idanunsa masu kama dana mujiya. Bisa mamaki sai suka ga ya tuntsire da dariya. Lokaci guda ya haɗe fuska,kuma sai ga hawaye daga cikin idònsa guda. Al'amarin da ya ƙara jefa su cikin fargaba da ruɗewa kenan. Yarima Sammaru ya dube shi cikin nutsuwa yace, "Ya kai wannan boka ina dalilin yin dariyarka,kuma ina dalilin yin kukanka?" Boka Hulumul Makabur yai ajiyar zuciya yace, "Ya kai wannan ɗan sarki kayi sani cewa yau shekarata casa'in da tara a cikin wannan kogo. A cikin nan uwata da ubana suka yi rayuwa,ina da 'yan uwa guda bakwai dukkaninsu mata ne,nine kaɗai namiji. Mahaifina gawurtaccen matsafi ne,ba wani abu bane ya zama sanadin aljalin mahaifina da mahaifiyata da kuma 'yan uwana face bincike akan yadda za su mallaki sirrikan tsafi guda miliyan dubu tara da casa'in da tara,irin wanda bokanya Tazibul Luhucul ta mallaka,kuma ta ɓoye su a cikin taskar tsafinta,wadda ke kogon Maddarul ikisina. Sun sha ƙoƙarin zuwa kogon Muddaril ikisina,amma da sunje gaban ƙofar kogon sai shiga ta gagarasu. Dawowa da baya ta gagara,anan suke rasa rayuwarsu. Ɗaya bayan ɗaya da haka 'yan uwan nawa bakwai suka rasa rayukansu. Ni kaɗai ne yanzu nayi saura. Daga tsawon lokacin mutuwar 'yar uwata ta ƙarshe,kawo iyanzu shekara arba'in kenan. Tsawon wannan lokaci bana komai face bincike da gano yadda zan iya shiga cikin kogon Muddaril Ikisina na sato waɗannan sirikan tsafi kuma na fito lafiya har na dawo nan cikin kogona. Har yau kawo yanzu maganar nan da nake muku ban gano mafita ba,kuma na rantse da darajar rayukan iyayena da 'yan uwana ba zan fasa wannan aiki ba,har ajalina ya riskeni. Wannan shine dalilin da ya sa nace daku kun naɗa gammo don shirin ɗaukar abinda yafi duniya da abinda abin cikinta nauyi domin abu ne wanda ya gagari dukkanin matsafan duniya." Sa'adda boka Hulumul Bakahur yazo nan a zancensa,sai su yarima Sammaru suka yi ajiyar zuciya,cikin zulumi da juyayi yarima Yauhana yace, "Ya kai wannan boka yanzu mun gamsu cewar wannan aiki dake gabanmu gagarumine,to amma ka sani cewa har abada mai rai baya fitar da rai ga samun rabo. Tuni mun sallama rayuwarmu bisa wannan al'amari,don haka babu gudu,babu ja da baya,walau mu dace,walau ba mu dace ba. Yanzu muna so ka sanar damu hanyar da za mu bi mu je wannan kogo na Muddaril Ikisina,inda taskar tsafi take don ceto rayuwar iyayenmu." Boka Hulumul Makahur yayi murmushi yace, "Yaro man kaza,lallai inda ka san bala'in dake cikin wannan al'amari daka rungumi ƙaddara amma koda yake ance ba'a ƙwacewa yaro garma. Zan faɗa muku matakan da za ku bi ku je wannan wuri,amma sai abokan tafiyarku sun iso." Cikin yanayin namaki yarima Sammaru yace, "Su wanene kuma abokan tafiyarmu?" Boka Hulumul Makahur yace, "Abokan tafiyarku mutum uku ne. Akwai gimbiya Ashwarya 'yar sarki Bahacal na birmin Hindu,wadda ta kasance gagarumar jaruma mace,mai dakawa maza gumba a hannu. Akwai yarima Lubaika 'dan' sarki Marluzil Hauras na birnin Ƙisra,sai kuma yarima Larbuz ɗan sarki Katimul Barhul na birnin Farisa,wanda shima gwarzon mayaƙi ne,wanda yayi gagarumar bajinta a nahiyarsu." Gaba ɗayansu sun taho nan don na sanar dasu hanyar da zasu bi suje kogon Muddaril Ikisina. Lallai gobe iyanzu sun iso,sai ku yi haƙurin zuwan goben,domin nayi muku jawabi tare dasu a lokaci guda,kuma na sallameku ku tafi izuwa wannan gagarumar tafiya." Take wata kuyangar aljana ta bayyana gabansa ta duƙa cikin biyayya da gimamawa. Hulumul Makahur ya dubeta yace, "Yake Ikilis na umarce ki daki kai manyan baƙinmu izuwa ga masaukinsu a basu kyakkyawar kulawa domin su sami hutu da nutsuwa. Gobe iwar haka a dawo mini da su nan." Ikilis ta ɗago kai tace, "An gama ya shugabana." Kafin su yarima Sammaru suce wani abu tuni Ikilis ta shafe su da fukafukanta guda ɗaya wanda ya lulluɓe su tamkar an jefa su cikin rijiya. Kawai sai suka ɓace,gaba ɗaya tare da Ikilis ɗin. Cikin abinda bai wuce daƙiƙa uku ba suka tsinci kansu a cikin wani ƙasaitaccen gida mai kyawun gini da abubuwan ƙasaita irin na sarakunan duniya. Barori da kuyangi na bil'adama kyawawa,kuma tsala-tsala nata kai komo,suna ta hidima. Cikin matuƙar mamaki yarima Yauhana ya dubi Ikilis yace, "Nan kuma a ina muke?" Koda jin wannan tambaya sai Ikilis ta bushe da dariya tace, "Ai nan masaukin baƙi ne irin ku sarakai. Daga can fadar mai girma Hulumul Makahur inda na ɗauko ku zuwa nan tafiyar wata uku ce,amma na gajarce ta izuwa daƙiƙa talatin. Ga gadaje nan da kujeru,masu taushi,kuma ga abinci nan da abin sha iri-iri,haka kuma ga matanan kyawawa sai kun zaɓi waɗanda kuke so,ku zauna ku huta sai gobe zan dawo na kwasheku na mai da ku can fadar mai girma." Ikilis na gama faɗin hakan ta ɓace musu ɓat. Cikin farin ciki Sammaru,Yauhana da boka Karluz suka hau ciye-ciye da shaye-shaye har sai da suka sha giya suka bugu,kuyangi kuwa suka rinƙa yin kiɗa da rawa don ɗebe musu kewa. Kai a taƙaice dai anan suka shagala da more jin daɗin rayuwa tamkar sun manta da abin da yasa suka baro gida. Washe gari kuwa Ikilis ta dawo masaukin su yarima Sammaru a daidai lokacin da tayi alƙawarin dawowa. Koda zuwa sai ta riskesu a kwance su duka suna ta sharar barci. Cikin mamaki ta dubi shugabar kuyangin gidan tace, "Me ya faru naga baƙina suna ta yin barci tun jiya,kawo i yanzu?" Shugabar kuyangi ta risina tace, "Ranki ya daɗe ai tun da kika tafi kika bar su suka shagala da ciye-ciye da shaye-shaye,kuma suka far mana basu gushe ba suna more rayuwarsu har dare ya shuɗe kuma alfijir ya keto. Daga sannan ne suka kama aikin rago har yanzu kuma basu farka ba." Koda jin wannan batu sai Ikilis ta ƙyalƙyale da dariya,tana mai cewa, "Tabɗijam yanzu a haka ne waɗannan ragwagen zasu je kogon Muddaril Ikisina. Ai kuwa da ganan ma sun faɗi jarrabawa. A yi dai mu gani,kallo ne namu kawai." Tana gama faɗin hakan ta lulluɓe su da fukafukinta guda. Take ta ɓace tare dasu bata bayyana a ko'ina ba sai a tsakiyar fadar boka Hulumul Makahur. Da zuwa ta yarɓar dasu a ƙasa tamkar wadda ta deɓo gawarwaki. A wannan lokaci gimbiya Ashwarya,yarima Lubaika da yarima Larbuz na zaune a cikin fadar sun harɗe akan kujeru na alfarma suna masu sauraron bayani daga bakin boka Hulumul Makahur bayan ya gama yi musu barka da zuwa. Bayan Ikilis ta ajiye su yarima Sammaru,sai Hulumul Makahur ya dubi su gimbiya Ashwarya ya nuna su Sammaru yace, "Yauwa ga abokan tafiyar taku waɗanda naba ku labarin cewa suna can masaukin baƙi." Gimbiya Ashwarya ta dube su tace, "Me ya faru gare su suke barci,mai nauyi haka?" Hulumul Makahur ya bushe da dariya,sannan yace, "Ai sun sha giya ne mai yawa jiya,kuma sun hole sosai bari na tashe su daga barcin." Nan take boka Hulumul Makahur ya nuna su da đanyatsansa guda na hagu. Take wata irin iska mai ɗan karan sanyi ta fito daga cikin ɗanyatsan ta buge su suka miƙe zumbur a firgice,suka hau kalle-kalle tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni. Koda yarima Sammaru da yarima Yauhana suka yi arba da gimbiya Ashwarya sai suka ruđe,suka kiɗime saboda ganin tsananin kyawunta da kwarjininta. Yarima Lubaika da yarima Larbuz suka dubi juna suka yi murmushi. Lubaika ya yiwa Larbuz raɗa a kunne yace, "Ya kai abokina dubi fa yadda suma suka ruđe,lallaı muma ba mu yi laifi ba,da har muka yi faɗa da juna akan gimbiya domin kyawunta ya kai matuƙa." Larbuz yayi dariya ya lce, "Ƙwarai kuwa zancenka dutse ne abokina." Boka Hulumul Makahur ya dubi su yarima Sammaru yace, "Ya ku waɗannan 'ya'yan sarakai ku nutsu ku dawo cikin hayyacinku ku sani cewa in dai kyawun gimbiya Ashwarya ne ke ɗibarku to ku sani zan nuna muku wadda ta fita kyau sau dubu nan ba da daɗewa ba." Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuƙe 'ya'yan sarakunan nan su duka huɗun. Ita kuwa gimbiya Ashwarya sai kishi ya kamata tace a ranta, "Yanzu a cikin duniyar nan har akwai wata mace wadda ta fini kyau? Lallai zan so na ganta a duk inda take." Hulumul Makahur yayi gyaran murya yace, "Kamar yadda nayi alƙawari cewar yau zanyi muku bayanin hanyar da za ku bi ku je kogon Muddaril Ikisina to yanzu zan cika wannan alƙawari,don haka sai ku nutsu da kyau,ku saurareni,kuma ku kiyaye dokokin da zan faɗa muku,domin idan kuka kuskure guda ɗaya ku duka ne za ku hallaka. Abu na farko shi ne daga nan zaku yi tafiyar shekara bakwai idan akan dawakai ne,zuwa inda tsakiyar wannan duniya tamu take idan kuwa akan hadiman aljanuna ne kwana bakwai kacal za ku yi. Zaku keta ta cikin manyan dazuzzuka guda uku masu mugun haɗari kafin ku je wannan wuri. Daji na farko ana kiransa da suna Baluzul Mahaful. Babu komai a cikin wannan jeji face tarin dodanni ƙabila-ƙabila har kala bakwai. Waɗannan dodanni basu da abinci face naman bil'adama. Lallai a cikin wannan daji sai kun yi tafiyar kwana uku cir in dai akan hadimaina ne,tsafi ba zai ƙwaci rayuwarku ba,a wannan daji face tsagwaron ƙarfinku da kuma iya yaƙinku,lallai anan ne zaku jarraba iyakar jarumtakarku. Daji na biyu kuwa shi ne wanda ake kira Zamutul Makatul. Babu komai a cikinsa face mugayen namun dawa,kuma sihirtattu. Dole ne ku yi amfani da tsafi da kuma ƙarfin damtse a wannan wuri. Ga wanda ya san sirrin daji daga cikinku zai samu sauƙin kuɓuta a jejin Zamutul Makatul. Shi ma sai kun shafe kwana uku cur a cikinsa. Daji na uku kuwa wanda shine na ƙarshe ana kiransa da suna Halalil Masur. Shi kuwa wannan jeji babu komai a cikinsa face wata gagarumar wuta mai ci a ko'ina sama da ƙasa. A tsakiyar sararin sama ne kaɗai babu wutar,kuma dole sai dai ku bi ta kan wata doguwar gada a ko yaushe harshen wuta na lasota. Wani karon sai tayi girgiza kamar zata faɗo ƙasa cikin wutar ko kuma ka ga iska na majajjawa da ita,kamar zata yi sama da ita,cikin wutar dake sama. Dole ne ku yi tafiyar kwana guda akanwannan gada. Yayin da kuka je ƙarshen gadar zaku fita daga jejin Halalil Masur ku tsinci kanku a tsakiyar wani tafkeken jeji wanda babu komai a cikinsa face wata doguwar bishiyar gwanda guda daya cal,wadda tsawonta ya kai zira'i ɗari uku. A ƙarshen wannan bishiya ne hanyar zuwa duniyar ƙasa take. Zan baku wani icen tsafi wanda shine zai huda muku ƙasa ku shige cikinta ku yi ta tafiya har sai kun iso tsakanin duniyar bakwai da duniyar takwas,inda kogon Maddarul Ikisina yake. To fa daga wannan wuri ban san yadda za ku yi ku iya shiga cikin kogon Maddarul Ikisina ba. Iyayena da 'yan uwana ma a wannan wuri suka hallaka. Bayanina na ƙarshe a gareku shi ne a cikin bincikena na gano cewa duk duniyar nan babu wani mahaluƙi da zai iya shiga cikin wannan kogon dutse na Maddarul ikisina a sauƙaƙe face gimbiya Fauwaza 'yar sarki Usman na birnin Misra,wadda ita ce macen da tafi gaba ɗayan matan duniya kyawu a wannan zamani. A halin yanzu ta baro ƙasar ta tare da waɗansu dakarun yaƙi,don yaɗa addininsu wanda akewa laƙabi da Addinin Musulunci. Duk ƙasar da ta je sai ta cisu da yaƙi,ta kuma hana su yin addinin da suka gada tun iyaye da kakanni ta ɗora su bisa tafarkin nata addinin. Haƙiƙa gimbiya Fauwaza na da tarin baiwa da sirrikan nasara,ba zamu iya ja da ita ba,gaba ɗayanmu nan face mun mallaki sirrikan tsafi adadin wanda Tazibul Luhucul ta mallaka." Boka Hulumul Makahur na gama wannan jawabi ya yi nuni da hannunsa izuwa ga allon tsafi sai ga gimbiya Fauwaza tare da dakarunta suna gwabza yaƙi da kafirai a cikin birnin Askandariya. Koda su yarima Sammaru suka ƙyallara ido suka ga gimbiya Fauwaza sai kyawunta ya ruɗe su suka shiga sumbatu da koke-koke tamkar waɗanda suka shekara cikin cutar begenta. Ita kanta gimbiya Ashwarya saida ta raina kanta ta tabbatar da cewa ita kam ba kyakkyawa bace,kyau na wajen gimbiya Fauwaza domin ita ce ƙurunƙus. ******** Lokacin da sarki Dujalu ya zo daidai nan a labarinsa sai wata baƙar kyanwa ta shigo cikin fadar a guje ta nufi inda karagar sarki take. Koda ganin kyanwar sai sarki Dujalu ya miƙe zumbur cikin firgita,saura ƙiris yayi abin kunya ya ruga da gudu. Kawai sai tsoho Rafkanagu ya cafke magen ya jefa ta cikin bakinsa ya tauneta da ranta ya haɗiye. Al'amarin da yayi matuƙar razana sarki da sauran 'yan majalisarsa kenan,domin basu taɓa ganin mutumin da ya cinye mage da ranta ba,sai yau. Nan fa kowa ya sha jinin jikinsa aka fara tunanin anya kuwa wannan tsohon mutum ne. Rafkanagu yayi gyatsa sannan ya dubi sarki Dujalu cikin murmusi yace, "Ranka ya daɗe ai sai ka cigaba da bamu wannan labari don mu ji yadda ƙarshen wannan Hikaya ta bokanya Tazibul Luhucul zata kasance." Cikin alamun rashin yadda sarki Dujalu ya dubi tsoho Rafkanagu yace, "Kai ba za ta yiyu ba. Kowa ya tashi ya bani wuri,ba zan cigaba da wannan labari ba har sai na yi bincike akan wannan baƙuwar mage data shigo cikin fadata tana ƙoƙarin hallakani,kuma sai na yi bincike akan ka kai wannantsohon,tabbas kaima ban yarda da kaiba." Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin su Ruziyal da sarki Dujalu yayin da yake basu labarin Hikaya ta huɗu wacce itace ta ƙarshe sai dai su tafi wani garin neman sauran labarai don hada rubutun sabon KUNDIN TSATSUBA. Al'amarin su Jafar kuwa bayan ƙatuwar macijiyar nan ta haɗiye su sai kawai suka ga an jefo su cikin ainihin ta su duniyar ta cikin KUNDIN TSATSUBA aka watsar da su a gaban littafin kundi,har yanzu shafi na goma sha shida ne a buɗe. Mazalish ta dubi Jafar,Gulzum, Yelisa da Mashrila tace, "To fa mun gamu da bala'i mara sauƙi da ƙarshe zai fi kyau mu hanzarta ganin ƙarshen sa don mu huta da tararrabi." Cikin fushi da tsawa Yelisa tace, "Amma dai ke kin cika mahaukaciya. Ai da mu kai kanmu cikin bala'i gwara shi bala'in yazo ya same mu da kansa." Caraf Jafar ya ansa yace, "Haba Yelisa ai Mashrila ta fiki gaskiya me zamu tsaya jira kawai a cigaba da karɓar sakamako tunda dai mu da kanmu muka ɓaro wannan aiki." Gulzum ya dakawa Jafar harara yace, "Tabbas ka cika wawa,sususu. To bamu yarda wani ya buɗe shafin gaba ba. Kawai bari ya buɗe kansa." Nan fa aka hargitse da kace-nace. Ba su ankara ba har lokaci yayi kundi ya buɗe kansa, izuwa shafi na sha bakwai,sai ga hoton ƙatuwar macijiyar nan,kuma babu rubutun komai a jikin shafin. Nan take iskar kundi ta zuƙe su suka faɗa ciki. Sai tsintar kansu suka yi gaban macijiyar a wata duniya dabam,kafin su yi wani yunƙuri tuni macijiyar ta wangame ƙaton bakinta ta haɗiye su gaba ɗaya. Haka dai su Jafar suka dunga shiga cikin masifu iri-iri har guda dubu,kuma duk guguwar nan ce ta rinƙa kai su cikin masifun. A cikin shafi na ashirin ne na KUNDIN TSATSUBA suka rabu da wannan guguwar bala'i bata sake ɗaukar su ta kai su wani wuri ba. Bayan an watso su cikin duniyar su ne suka sami hutun daƙiƙa ɗari da ashirin,sannan KUNDIN TSATSUBA ya buɗe kansa izuwa shafi na ashirin da ɗaya suka yi arba da hoton wata duniyar da ke sararin samaniya. SHIN GIMBIYA SIMA ZATA TSIRE JARUMI HUBAIRU DA WANNAN MASHI WANDA SARKI LU'UMANU YA BATA? SHIN SARKI DUJALU ZAI ƘARASA LABARIN HIKAYAR BOKANYA TAZIBUL LUHUCUL? YAUSHE NE SHAMHARU ZAI ZAMA MATSATSUBI? INA LABARIN SU MARKAHUL SABUS WAƊANDA SHAMHARU YA MAIDA SU 'YAN MINI-MINI YA JEFA A ALJIHUN RIGARSA? ME SU JAFAR ZA SU GANI A CIKIN WANNAN DUNIYA DAKE SARARIN SAMANIYA? Mu haɗu a MATSATSUBI 3.