https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹) Da sunan Allah me rahama mejinkai 🙏 Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen 🥰🤎 Masha Allah mundawo hutu da izinin Allah. Book two 📚📚📚📚📚 ꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂ &_____________________________________& Page 3️⃣1️⃣ Dagowa fanan tayi dasauri tana kallon me martaba dan San gasgata wani azaad din yake nufi, gyada mata kai me martaba yayi domin tabbatarwa tunani tafarayi taya hakan ze kasance Mr azaad din da bawai sona yakeyi ba zasuce sun mana aure innalillahi wainna ilaijiraji unnn yah Allah Ina rokon ka daka bani iKon cinye wannan jarabawan. Ummi tarasa farin ciki zatayi ko akasin hakan tayi matukar jin dadin wannan labarin domin dama burinta bewuce fanan tazamo surkantan taba gashi Allah ya amsa adduah ta, amma abin tambayan anan shin fanan zata amince da wannan auren kuwa . Mama kam ji takeyi lamarin kamar amafarki cikin awowin dabasu wuce uku zuwa biyu ba har an tabbatar da fanan amatsayin matar aure lallai baa mamaki da iKon Allah me kowa me komai mai tsara komai ayanda yaso kallon fanan kawai takeyi tana tuna zata koma wani gida tayi rayuwa nan take taji wani irin kewarta yakamata, ganin tayi shuru kanta akasa tana wasa da yatsun hannunta ne yasa baba cewa " Fatima nasani ke yace me biyayya ga iyayenta bakya taba sabama umarninmu shisa akoda yaushe nake matukar alfahari na kasancewarki ya agaremu , wannan auren da akayi bawai anyishi bane dan kuntatawa daya daga cikinku bane ah ah! Anyi wannan auren ne domin kare mutunci da martabanku dakuma namu gaba daya, zaku iya fitowa duniya kununa musu kudin ma'aurata ne hakan shikadai ne ze wanke sunanku a idon duniya! Kuma iname tabbatar muku da sesun nemi afuwarku, auren nan da akayi yana daga cikin kaddarar rayuwarku Allah yariga daya kaddara azaad shine mijinki kema kece matarsa kiyi hakuri ki rungumi wannan auren in sha Allah zakiga alkharin dake cikinsa Allah yamuku albarka " She's speechless gaba daya kalaman baba sun gama kashe mata jiki tama rasa takamemmen mezatace innalillahi wainna ilaijiraji unnn kawai take iya furtawa acikin ranta ahankali tafara samun nutsuwa. Gaba daya tausayinta yakamasu Abba ne yace " Fatima kifada mana shin kin amince da hakan dan bazaa taba miki dole ba munsan dole zakiji wannan lamarin awani iri amma munyi hakan ne saboda wanke sunanku" kanta akasa tana wasa da kyawawan yatsunta dasuka kasance chocolate color with her sweet voice tace " na amince " basuyi tsammanin hakan ba amma dasukayi laakari da fanan yarinya ce me biyayya ko da batasan abu bazata taba musawa ba kokuma taki bin umarninsu ba, alhamdulillah sukace atare yaseer ne yace " yanzu abinda zefaru asamu ashawo kan azaad inyaso zuwa gobe se ashirya hira dasu agidan tv " jinjina kai sukayi alamar gamsuwa da maganarshi , cigaba da magana yaseer yayi yana kallon faisal" kashirya appointment da BBC news dakuma NTA domin sun dade sunason hira dashi Allah beyi ba seyanzu da dalili yazo nasan zasuji dadin wannan maganar " " to shikenan zanyi hakan yanzu base anjuma ba " aikuwa yana gama magana ya lalubo wayarsa yayi dialing number customer service na BBC news macece ta daga tace " hi, am Jenifer thank you for contacting BBC news how can I help you?" Maida mata da amsa yayi " by the way my name is Faisal adamu I am azaad the billionaire official secretary luckily I want to inform you that your appointment has been approved " wani irin ihun farin ciki tasa tana " heyyy thank you jesus " bama ita kadai ba hatta sauran ma'aikatan dasukaji labarin murna kawai sukeyi dan abinda suka dade suna jira kenan yin hira dashi bakaramin daraja zedagawa gidan tv suba domin he's the most famous person da kowan ne suke bukatar tattaunawa dashi. Haka faisal yakara kiran NTA yasanar dasu kafin yakashe wayarsa. Duk shuru sukayi suna jiran suji abinda me martaba zece ____ " alhamdulillah abu nagaba danakeso infada duk da kunsani kuma shine! duk yarinyar da aka daura aurenta tana tarewane agidan mijinta a ranar inbawai akwai wani kwakwaran dalili bane zehanata tarewa" yajuwa ga su ummi yacigaba" Aysha yau base gobe ba ku fara shirin daukan amarya banyan sallah isha " daf!daf!daf gaban fanan yatsinke ta shiga uku yanzu ana nufin bazata kwana agidansu ba wani irin rayuwa zatayi atare da Mr azaad. Abinda baba yake tunani yazo daya da abinda mama da su ya Usman suke tunani taya zaayi amarya ta tare batare da iyayenta sun mata kayan daki daduk wani abinda ake bukata ba, suna bukatar abasu ko nan da gobe ne saboda bawai basu dashi bane Allah ya hore musu abinda zasu mata irin na yar gata ma kuwa. Baba ne ya nisa kafin yace " me martaba agafarceni, banqi ta taka ba domin kai amarya aranar da aka daura aurenta izuwa dakin mijinta bakaramin lada zata samu ba da albarkan aure saboda hakan shine ka'ida ! amma abamu daga yau zuwa gobe wannan auren yazo mana baa kan shiri ba bamu tanadi komai ba in sha Allah daga yau zuwa gobe inyaso se azo adauketa" murmushi irin tasu ta manya me martaba yayi yana kallon yan falon gaba dayansu sannan yace " shin awani ayah ko hadisi kukaji ance kayan dakin mace dakuma duk wani abinda zata bukata agidan aurenta yarataya aka wuyan iyayenta ? To bari kuji abinda kuka manta a musulunce muddin mutum ya auro mata komai yanakanshi daga abinda yakama gida wato muhalli, kayan amfanin gida, tufafinta, shanta da ciyar da ita duk ya tattara akan wuyanka amatsayinka na shugaba agareta! Yanzu ne da zamani yake juyawa yakoma juyi_juyi iyaye suka fara kai yayansu da kayan su gado su setin daki dasauransu amma badole bane wannan kuma yin hakan shike Kara sangarta mazan sukeyin duk abinda suka gadama gadaransu yanzu shine kawai sadaki zasu bada da kayan lefe se gida shikenan amma da su sukeyin komai da komai dakansu bazasu taba kuskuren sakin matansu ba dan haka babu abinda fatima zata tafi dashi gidan mijinta koda kuwa cokali ne " babu yanda su baba suka iya tabbas maganar me martaba gaskiya yafada amma yanzu anawa mata hakane domin gudun reni ko kana nan maganganu. Abba da ummi kuwa sunji dadin maganar da me martaba yafada domin suma abinda zasu fada kenan yarigasu domin sune da matukar godiya da baba yabasu auren fanan yarinya me hankali da tarbiya babu gidan da bazaayi farin cikin samun yah Kamar taba . Karfe 5:00 saura Adduah me martaba yayi sosai taro yakare, mikewa yayi rike da sandar shi yana musu sallama su fulani da galadima suma sukabi bayanshi suka tafi, su abba ma fitowa sukayi zasu tafi suka rako su har bakin gate suna musu se anjuma insunzo daukan amarya tare da musu godiya sosai ahaka sukayi sallama . Komawa cikin gida sukayi suna jinjina iKon Allah babu wanda yayi zaton haka awannan lokacin zama sukayi suna dan maida magana mikewa fanan tayi tabarsu afalon bin bayanta sukayi da kallo gaba daya jikinsu babu laka bin bayanta suhaima da amira sukayi dakin akwance suka sameta kanta na kallon saman celling kamar wata me tunani zama sukayi akusa da ita. Baba ma dakinshi yashiga bayanshi mama tabi dan tanason jin yanda sukayi dangane da fanan. via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & Written by.. MRS 🌹 ISHAM 🌹 Page 3️⃣2️⃣ _____ " babansu yakamata kafada musu komai dangane da fanan kar azo daga baya abu yazo yacabe " cewar mama dake zaune tana facing din baba , Maida hankali baba yayi gunta yace " haba sumayya ta taya kike tunanin zan boye musu wani abu dangane da yarmu nafada musu komai domin me martaba Shima ashe yanada labarin amma besan wacece takamemmen sarauniya ba " yafadi hakan ayayin da yake bude wata locker dake jikin wardrobe dinshi kudi yafito dasu akalla sun kai dubu dari hudu " Kinga wannan kudin ki kira firdausi kibatasu taje kasuwa tasiyowa fanan kayan sawa dakuma akwatin da zaa sasu amma banda atamfa shi innaje shago zabayar wa tela yamata dinki " yamika matasu ahannunta karba tayi tana jujjuya kudin ahannunta hawayen dake kokarin zubowa a idonta ta mayar dasu tana fadin " yanzu kenan fanan ayau zatabar gidan nan tun kafin ta tafi nafara kewarta bansan wace irin rayuwa yata zatayi atare da wanda bayason taba " shikanshi baba abin yadameshi amma hakan shine ze samo musu sauki , girgiza kai yayi kafin yace " karki fadi haka aure anriga da anyishi amatsayinki ta mahaifiyarta adduah kawai zaki mata na zaman lafiya agidanta " jiki asanyaye mama tace" hakane Allah yabasu zaman lafiya " ameen. ____ " haba azaad sekace baka da tausayi dan saboda kaine fah wannan abun yafaru da yarinyar nan Yakamata da akayi maganar auren nan kabada goyon bayanka dari bisa dari amma ko kunyar iyayenta bakaji ba afili kace bakason yarsu " cewar yaseer da dawuwansu kenan yashigo part din Azaad, duk wannan maganganu dayakeyi azaad najinshi kalla bece mishi ba shikadai yasan abinda yake damunshi duk bazasu fahimmce shi bane, tashi yayi yazauna yana kwabe fuska yace " yaseer nasani nasan saboda nine sunan yarinyar yabaci kuma am willing to do anything daduk karfina wajan ganin nawanke sunanta amma aiba dole seta hanyar aurenta ba ! Can you imagine wai kamar ni azaad muhammad mainasara the billionaire nizaawa auren dole unbelievable, bana sonta kwata_kwata kuma banajin zan iya sonta saboda she's still kid to me akwai sauran yarinta akanta and tamin karama , duk inda aka ambaci aure yashiga tsakani to andauki amanarta ne anbaka kulawa da ita, lafiyanta rashin lafiyanta dakuma tarbiyanta se adalci nikuma yanda banasanta banajin zan iyayin daya daka cikin wayan nan abubuwan shisa bazan iya zama da ita ba " tabbas abinda azaad yafada haka shin ze iya kula da fanan ne ko baze iyaba mutumin da ko kadan mata basa gabanshi be masan tayanda zekula dasu ba wani irin tausayin fanan ne yakamashi amma yasa aranshi in sha Allah seyayi iyayinshi naganin ya dedeta tsakaninsu da iKon Allah. _____ " to yanzu de ba wannan ba kashirya ayau zaa kawo maka amaryaka kazama cikin shiri dan acikin daren nan Yakamata ka angonce " cike da shakiyanci yaseer yake maganar dan yasan yanzu ze fusata azaad, uhmmm kawai azaad yafada yana aiyanawa aranshi inya kusanci wannan jaririyar aiseta kusan mutuwa, Yaseer de tashi yayi yabarshi adakin dan yaga azaad inya fusata zasuyi dauki ba dadi. Anty firdausi ce da mama, suhaima,Amira,auta afalon suna zaune sunata bubbude kayan da anty firdausi tasiyo da kudin da baba yabada kayane nagani nafada akwati biyu masu kyau abaya ne da akalla zasu kai guda ashirin se wasu fitinan nun kana nan kaya nahutawa dakuma liffaya suma sunkai 20 da takalma da jaka se jewelries nagani nafada kaya de masu matukar kyau suna zaune suna kallon kaya ya usman da ya al ameen suka shigo suma hannunsu niki_niki rike da manyan ledoji na kayan cosmetics daga abinda yayi kan turare, kayan make up, lotion,soaps shower gel, shower perfume etc. Shirya kayan akayi duka a akwatu nan se aka fitar mata da wanda zatasa yau suka gama shiryasu tsaf. Ana kiraye_kirayen sallah mangrib mama tace " firdausi yakamata kitashi kuje ki shiryata kinga lokaci natafiya kar babansu yashigo yasamu baa kammala ba" Daukan kayan dazata sa anty firdausi tayi takai dakin tasameta tana kwance tabawa kofa baya zagayowa tayi gabanta idonta biyu ba bacci takeyi ba , hannu anty firdausi tasa tadagota tazauna murya asanyaye tace kitashi kije kiyi wanka tare da alwala inkikayi sallah sena shiryaki " babu musu tamike tashiga wanka, tayi wankan tadauro alwala tafito daure da towel amma ta rame fuskanta fayau dogon rigar jallabiyarta tasa tadau hijab ta tada sallah seda tayi adduah sosai kamin tadan jabaya tajinginu da jikin gadon . Matsowa kusa da ita anty firdausi tayi tarike kafadarta sannan tace " fanan kidena sawa kanki wasu irin tunani ki karbi komai ayanda yazo miki kuma kikara da godewa Ubangiji yasa hakan shine mafi alkhari domin duk abinda kikaga yasamu bawa to muqaddarine daga Allah , nasan tunaninki ya karkata akan wani irin zama zakiyi da mijinki da bayasonki to kisani wannan abu ne me sauki inkika kara mika lamuranki ga Allah sannan ahankali hankali zakike cusawa mijinki sonki azuciyarshi mu mata inde mukaso babu tayanda bama bi da namiji duk yanda kikaso zaki iya lankwasashi domin namiji zumane seda wuta kisa aranki zakuyi rayuwar farin ciki kedashi ko bakuyi ayanzu ba zakuyi nan gaba zanyi duk iya kokarina wajan tallafa miki kina dani kidenajin wani kunya kinji ko " gyada mata kai tayi domin kalamanta sun kwantar mata da hankali tadanji relief, karajin kwarin guiwa tayi. Jin datayi anshiga sallan isha ne yasa ta tashi ta tada kabbarah bayan ta idar ne anty firdausi tace mata tazauna agaban mirror zama tayi kamar yanda tabukata miko mata wasu mayuka masu bala'in dadi tayi dan tashafa shafawa tayi tana jin kamshin har tsakiyar kanta light make up anty firdausi tamata karkuso kuga fanan yanda tayi kyau da make up din nan, Mika mata wando na jeans dakuma yellow din body hook me dogon hannu tayi karba tayi tasa bakaramin kamata sukayi ba tab sukamata sunzauna ajikinta sosai hips din nan kamar zasu faso wandon sufito , liffaya anty firdausi tadauko fari sol medan touch din yellow ajiki nada matashi tayi mekyau ajikinta ta mata dauri da dolface yellow gashin kanta kuwa dauresu tayi seya zama kamar gammo dan kunne da sarka tasa mata se awarwaro da abin hanci me dan karamin stone rufa mata liffayan tayi ajikinta tako Ina harda fuskanta sannan tafesheta da wasu mayun turare masu kamshi sosai tabata takalmi white color se hand bag dinta,shiryata tsaff tayi wani irin kyau da fanan tayi mara misaltuwa tafito sakk amarya , rikota anty firdausi tayi tazauna akan gadon tana kokarin rufe mata fuska kenan segasu amira, suhaima sunshigo suma sun gama shiryawa cikin atamfa sunyi kyau sosai zama sukayi akusa da ita suna yaba irin kyaun datayi kamar su saceta sugudu duk yanda takai da basar dasu seda suka dan sata dariya, dan dazunma dasuka shigo dakin dataga zasu dameta kawai tasharesu tajuya musu baya. Anty amina, anty shayida anty Zainab se zeenat ne zasuje dauko amarya su yaseer da fawwaz ne zasu kaisu duk sunci ado abunsu suka nufi anguwarsu fanan motar uku kawai suka dauka dan baason ayi yawanda zaa gane,bayan su isone suka shigo falon mama suka zauna suna Kara gaisawa mikewa anty firdausi tayi tashige dakin tariko hannun fanan da fuskanta yake arufe dakin baba sukayi domin yamata nasiha via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story Written by... MRS 🌹 ISHAM 🌹 Page 3️⃣3️⃣ & 3️⃣4️⃣ Dakin baba suka shiga tazauna akan sallaya fuskanto ta baba yayi kafin yafara magana " Fatima ni nafi kowa sanin halinki kin kasance me hakuri da juriya dakuma sadaukarwa , to ayanzu ne wayan nan halayen zemiki amfani ke yanzu ke bakamar sauran yan mata bace karki dinga hada kanki dasu domin ke yanzu kinzama babba tunda kika zama matar aure kikama mutuncinki amatsayinki ta matar aure , wani shiga shirgin daba naki ba babu ruwanki! Sannan aure yar hakuri ce duk wasu ma'aurata dakika gani dukkansu hakuri suke da juna domin anriga da anzama daya, yazama dolene se anyi hakuri da juna kiga misali da mahaifiyarki yau shekara ashirin da biyar da aurenmu amma dede da musu wannan bata tabamin ba balle bakar magana mara dadi hakurinta yazarce misali itadin matace tagari to zanso kiyi koyi da ita kiyi hakuri da mijinki ako wani irin hali kikasance meyi mishi biyayya kibishi sau da kafa nan ne zakiga ribar auren dakuma hakuri rashin kunya ba naki bane, inyace kiyi , kiyi inyace bari kibari karki tsaya yana fada kina maida masa magana , sannan mudin kika fita zuwa wani wajen batare da izinin mijinki ba duk taku daya mala'ikun Allah tsine miki zasu dingayi ! Wannan gidan bekai gidan mijinki ba domin mace da gidan mijinta take tunkaho duk abinda ze hadaki da mijinki kizama mace me sirri karki yarda sirrin mijinki yafita sede in abinda yakeyi yazarce ka'idan addinin musulunci nan ne zaki kai kara domin neman solution, Karki manta aljannarki na karkashin kafarsa seya daga zaki shiga dan haka kiwa mijinki biyayya karki saba mishi Allah yamuku albarka yabaku zaman lfy zaku iya tafiya" tunda baba yafara magana taketa sheshekar kuka gaba daya maganganunshi ya ratsata sosai rarrafawa tayi har gabanshi tarungumeshi tana kuka bubbuga bayanta yakeyi yana shafa kanta tare da samata albarka . Haka anty firdausi tafito da ita falo tana kuka mikewa su anty Amina sukayi da niyyar tafiya fitowa mama tayi hannunta rike da wata yar karamar box riko hannayen fanan tayi tabude box din awarwaro ne guda hudu aciki na zinari alamun sundade ba design din zamanin nan bane se sheki sukeyi zurawa fanan tayi ahannun kafin tace " wannan awarwaron dakike gani gadon alhalinmu ne kakar kakatace tabawa kakata lokacin datayi aure itakuma kakata tabawa mama na dazatayi aure nima sanda zanyi aure mamana tabani kinsan metace min " dago manyan idonta dasukayi jaa tayi takalli mama ta girgiza Kai, yar murmushin yake mama tayi tacigaba" cemin tayi duk sanda nahaifi yata tayi aure itama inbatasu, ki kula dasu sosai kinji? Kizauna da mijinki lafiya fanan kimishi biyayya kizauna dashi da akwai da babu Allah yamiki albarka yabaku zaman lafiya " fashewa da kuka fanan tayi ta rungume mama kam_kam kamar zata koma cikinta kuka takeyi kamar ranta zefita, na mijin kokari mama tayi bata bari hawaye yafita a idonta ba sosai sukaji tausayin fanan amma dolene wannan akan kowace ya mace dole tabar gidan iyayenta , kokarin raba jikinsu takeyi amma fanan taki saketa ganin takine yasa su anty shayida sukazo suna kokarin rabasu suna bata hakuri Abu kamar wasa sunfi 30mint ahaka karasowa gunsu ya usman yayi yamata magana akunnenta sake maman tayi tarungumeshi shida kanshi yafara tafiya da ita zuwa motar bayansu sukabi zama mama tayi hawayen rabuwa da yarta dakuma farin ciki na kwarara daga idonta. Motarshi yashigar da ita back seat anty firdausi da anty amina suma suka shiga tana kuka suna rarrashinta su amira dasu anty shayida suka shiga motar suhaima natsaye tama rasa ina zata shiga fawwaz lura da hakan ne yabude matar gaban motarshi yamata alama da hannu yace " princess let's go" cike da kunya tashiga anty zainab dake motar dariya tayi kasa_kasa aranta tana fadin "ohhh wato su fawwaz ma ankamu kenan " tada motocin sukayi sukahau titi tafiya sukeyi ahankali harsuka iso gidan wangale musu tangamemen gate din akayi suka shigo fitowa sukayi dukansu suka tsaya suna jiran afito da fanan rungume da ita anty Amina tafito suka nufi part din ummi abakin kofa anty Amina tatsaya tace mata tayi adduah sannan tashiga da kafar dama haka kuwa akayi afalo suka samu abba, ummi da areef mikewa ummi tayi tazo ta rungumeta tana mata lale marhaban zaunar da ita tayi akan lutsa_lutsan kujerun falon abba se murmushi yakeyi yaso ace azaad na gida daya mishi tsiya dazun yafita da car key ahannunshi ko inazeje oho . Budewa fanan fuska ummi tana Masha Allah dukda tabata kwalliyar da kukan datasha fuskan nan yadan kumbura zama sukayi afalon gaba daya suna hira duk dan susamu fanan tasaki jikinta ya usman ne yashigo falon yana rike da akwatin kayan fanan dayan kuma wani security narike dashi anty Amina ce tamike tacewa security yabiyota da akwatu nan part din Azaad tanufa security nabiye da ita abaya shiga tayi falon nashi dakuna ne manya guda biyu banda na azaad se babban falonshi da dinner table da kitchen komai akwai a part din se corridor sunji furnitures dakin dake manne dana azaad painting dakin fari ne se makeken gado da wardrobe me girman gaske ga mirror da aka cikashi da kayan shafa and kayan make up,dade sauransu , bude wardrobe tayi wanda yake shake da kaya nagani nafada babu abinda babu komai ansaka matasu aciki kaya kala_kala bangaren takalma da jaka daban bangaren kana nan kayama haka se bangaren dogayen ruguna su hijab pants and bra sleeping dress, atamfofi, waje tasamu ta ajiye akwatu nan tarufe wardrobe din layin ummi takira tace su anty firdausi da suhaima suzo da fanan part din Azaad aikuwa haka akayi shigowa sukayi dakin datake toilet ta nunawa fanan tashiga tayi wanka tana mika mata doguwar rigar abaya da gyalensa karba tayi tashiga toilet din tayi wanka tasa abayar milk color ta yafa gyalen tafito tasamu anty Amina da anty firdausi basa dakin zeenat tashigo tana masu suhaima masifa " wato shine zaku taho bazaku kirani bako" hararan wasa suhaima tamata " to aigaki kinzo " magana zeenat zata kara fanan dake gaban mirror tana shafa lotion tace " to anty masifatu Allah karku dameni tam" Zama zeenat tayi tace " wace ni rufamin asiri amaryar yaya guda nina isa indameki matarmu" dariya sukayi kara bata fuska fanan tayi tacigaba da abinda takeyi tana gamawa kuwa batace musu komai ba ta tadawo main falo tazauna ganin hakane yasa suma suka fito . abu me aikice ta sanar da ummi angama shirya komai a dinning " to kutashi dukkanku food is ready ko " mikewa sukayi dukansu suka zauna akayi serving dinsu fried rice da kaji se farfesu , masa da Miyan kifi. Yaseer ne yafara gamawa yamike yakoma falo yana kiran layin azaad seda yamishi almost 5miss called kafin yadaga " haba ango wannan wani irin iskancine akawo maka amarya kawani fita kayi sauri kadawo" yana jiran abinda azaad din zece yaji dogon tsaki Mr azaad yaja yakashe wayar dariya yayi dan yasan zaa rina bayan sun gamacin abincin suka dawo falo wayar suhaima ce tafara ringing dubawa tayi taga number yaya inlaw ne murmushi tayi kafin tamike tafita a falon taje compound tadaga wayar " hello yaya Ina wuni " adayan bangaren aka amsa " lafiya da nayi fushi dake bansan ya akayi nakiraki ba babynmu ne takeson jin muryanki shine mimi tace inkiraki " dariya yabata wai babynsu ce takeson jin muryanta kai ya amir sarkin zolaya " uhmmm kuda kuka manta dani ma aini yakamata inyi fushi bakuba" tafada tana murguda baki " yanzu bawa mimin " amir mikawa matarshi mimi yayi sunkusan 10mint suna waya kafin sukayi sallama yakashe, juyawa tayi zata koma ciki kawai taga mutum atsaye abayanta yaharde da hannunshi tadan tsorata ganin fawwaz ne tace " laaaaah ya fawwaz wannan aisekasa inzura da gudu " murmushin gefen baki yayi yace " hmmm ai hankalina ne yakasa kwanciya shisa nabiyoki a tunanina ma wanine yakeson min kwace ashe yayanmu ne " daure mata kai yayi da kalamansa " bangane mekake nufi ba ya fawwaz" daga mata giran sama yayi kafin yace " lokacin da wayarki tayi ringing ganin irin murmushin dakikayi yasa zuciyata tsinkewa dan nadauka wani ne yakesonmin kafa agun matar danake buri tazama uwa ga yayana " sosai tazaro kyawawan idonta tana kallonshi wura mata iska yayi a ido kauda kanta gefe tayi hannunshi yasa yakarbi wayarta yayi dialing din number sa ya mika mata murmushi yayi yace" naji kinyi shuru kifada mini namiki ne ko ko banyi ba ?" Dariya tayi jin yanda yake magana da wakar dan musa tafiya sukeyi suna yar hira harsukazo falo ja tayi tatsaya tace" ya fawwaz kabarni infara shiga " gyada mata kai yayi tashige tazauna sedaga baya yashigo yazauna akan kujera dake facing dinta daga sun hada ido se yasakar mata murmushi itama tamayar mishi babu wanda yalura dasu se fanan wani irin dariya tafashe dashi wanda rabon datayi irinshi tun ranar agida itada suhaima seyau kuma dariya takeyi ba qaqqautawa harda rike ciki zuba mata ido sukayi suna kallon iKon Allah suna mamakin meye yasata irin wannan dariya haka sedata kai kusan 5mint kafin ta dakata ganin suna kallonta ne yasa taboye fuskanta ajikin ummi tana yar dariya basu kawo komai aransu ba su a tunaninsu wani abun ne yasata farin ciki amma yawan da dariyar yayine yabasu tsoro . ___ Abba ne yace " fanan daga yanzu kidaukemu kamar iyayenki bawai surakanu ba domin ke yace awajanmu matsayinki daya da zeenat so dan haka kisake jikinki nanma gida ne kinji ko ?" Fitowa tayi daga jikin ummi tace " in sha Allah abba nagode " mikewa anty firdausi tayi tace " kutashi muyi shirin tafiya " tashi sukayi suna musu sallama fanan jitayi kamar tayi kuka rungumeta suhaima da amira sukayi atare kasa_kasa amira tace " to besty azage akula da miji abashi kulawa atarerayeshi kamar kwai nan da 5 months muzo sunan yan hudu" tsaki fanan taja " kefa iskancin kine yake hadani dake kifita a eyes dina tam" kafin tajuya kan suhaima " kekuma dama kin iya kallon love haka inyaah " amira de batasan akanme take magana ba suhaima kuwa hararanta tayi tace " to ina ruwanki yarsa ido kawai " jarare jikinta fanan tayi tana " uhmm jeki can da yawar soyayyarki ni karkimin rashin kunya" cewar fanan ahaka suka dingayi harsuka je bakin motar suka shiga daga musu hannu tayi tana musu bye_ bye tafiya sukayi suma suka koma ciki Abba kam already yawuce part dinshi su fawwaz ma haka anty shayida da anty zainab kuwa ko wacce mijinta yaturo driver sun maidasu gida, yazamana daga ummi, zeenat,anty amina se fanan din ne afalon ummi ce tayi magana " fanan kitashi kije ki kwanta kihuta kinga gobe kunada program zaku fita karfe 10:00am nasafe ! Sannan a part dinku duk wani abinda zaku bukata akwai aciki kayan girki kidingawa mijinki girki koda bazeci ba kimishi de yasan kinyi kinji ko " "to ummi" cewar fanan dake mikewa zata wuce part dinsu seda safe tamusu tashige atare ummi da zeenat suka sauke ajiyar zuciya dan yau burinsu na fanan tazama sirka agidan yacika sunyi farin ciki sosai. Ita atunaninta yadawo gida dan dazun taji su fawwaz sunce baya nan dakinta tawuce cire rigar tayi tadaura towel tashiga toilet tayi wanka da ruwan zafi tayi alwala tafito goge jikinta tayi da towel din tashafa turare masu dadin kamshi wardrobe din tabude kayan baccin tazubawa ido ganinsu da yawa wani me riga da wando black silky tadauko tasaka tasa hula akanta takwanta taja blanket tana adduah bacci aikuwa bacci barawo yayi awun gaba da ita. Se karfe kusan 12:00 nadare tukun yadawo gidan kowa ya kwanta yashiga part dinshi toilet yafada yayi wanka yafito towel daure a kugunshi shafa lotion yayi ajikinshi yafeshe jikinshi da perfume kayan bacci yasa ajikinshi yakwanta. Washe gari 5:30am Tana zaune akan sallaya ta idar da sallah tana azkar se karfe 6:30 ta tashi takoma kan gado takwanta dan bacci be isheta ba, se karfe 10 ta farka ta shiga toilet tayi brush tawanke fuskanta fitowa tayi tana shafa cikinta dake kukan yunwa falo tafito jikinta nasanye da kayan baccin dube_dube takeyi tana neman kitchen wata kofa tagani akusa da inda dinning area yake wajan taje tabude kofar katon kitchen ne irin nayan gayu komai akwai aciki kamar wanda tundama mace na ciki tunani tafarayi to dama Mr azaad na girkine karewa kitchen din kallo takeyi yaburgeta sosai wani kofa tagani tabudeshi store ne kayan abinci ne aciki iri_iri kwalin idomie tabude tadauki guda daya se kwai biyu da gesher tafito standing gas takunna tadaura tukunya akai tahada indomie ta jollof da gesher kwai din ta dafashi daban kamshine kawai yaketashi a kitchen din tana gamawa tazuye a plate tasa cokali tafito falo tazauna kure A.C tayi dan tasamu yahuce dawuri seda tafaraci ne talura da basket din dake kan dinning ashe ankawo musu abinci cigaba tayi da cin indomie ta se shishitan yaji takeyi sekace wani ne yasata sawa dayawa ahaka tacinye abincinta , fitowa yayi daga bedroom dinshi babu riga ajikinshi dagashi se short din three quarter kokadan beyi tunanin zesameta ba bema kawo apart dinshi zaa ajiyetaba zama yayi akan kujera yana amsa kiran Faisal dake sanar dashi komai ready su kadai kawai BBC news suke jira okay kawai yace jin muryanshine yasa tadago tace " Ina kwana Mr azaad" kamar bejitaba yacigaba da danna wayarsa tabe baki tayi aranta tana fadin " kaika sani karka amsa din " haka suka zauna a falon kamar wasu kurame can yamike haryakai bakin kofar bedroom dinshi yace " kishirya yanzu zamu tafi and banason jira" yashige bin bayanshi da harara tayi tana kwaikwayan yanda yayi magana sannan tamike tayi wanka tafito da atamfa super wax me touches din pitch da sky blue riga da skirt dinki yayi kyau sosai duk pattern yasha stones ajiyesu tayi tadauko gyale da takalmi half cover se jaka masu matukar tsada zama tayi agaban mirror tadanyi light make up tayi kyau sosai ta gyara gashinta tayi packing dinshi se kyalli yake kayan tasaka sun zauna mata ajiki kamar dama sundauki measurements dinta das das da ita dawuwa gaban mirror tayi da dankwali ahannunta dauri tayi mekyau me shigen ture kaga tsiya wanda akesa mishi kwali aciki amma ita batasa komai ba tayi abunta daurin yazauna sosai akanta akasan daurin kuma gashinta ne wanda tayi packing dinshi feshe jikinta tayi da daddadan turare masu masifar kamshi, gyale tayafa yanada dan girma yarufe mata jiki tadau jakanta tasa takalmi tayi masifar kyau dan karamin bakin nan seyayi kamar tasa janbaki kasancewar libs dinta ja ne gashi tasa mishi libs gloss se shinny yake. fitowa falon tayi tazauna zaman jiranshi seda takusa 10mint tana jiranshi se gashi yafito, yana sanye da tsadadden yard milk color half jumfa gashin nan yasha gyara yayi matukar kyau , wuceta yayi abinshi bece mata ci kanki ba ganin haka yasa tamike tabi bayanshi suka gangaro main falo su Abba da ummi da kowa suna zaune afalon jin takun takalminsu ne yasasu juyawa suna kallonsu bakaramin burgesu sukayi ba sunyi making perfect match zama Mr azaad yayi, tsungunawa fanan tayi har kasa tana gaishesu suka amsa fuska asake zama tayi akusa da zeenat " kai anty fanan wallahi kinyi kyau sosai dama wai kin iya kwalliya shine bakyayi wallahi baki ganki bane " hararanta tayi jin takirata da anty tace " bansan wani iyayi dazaki wani cemin anty tam " batagama magana ba taji areef nafadin " antynmu Ina kwana " waro ido tayi cikeda mamaki qin amsawa tayi kara nanatawa yayi " anty ina kwana" kwabe fuska tayi da shagwaba tace " Abba kanajin su ko kace musu subari banaso " takarashe maganar kamar zatayi kuka dariya sukasa banda azaad daya wurga mata harara , Abba yace " to ai fatima dole suce miki anty tunda yanzu ke matar yayarsu ce " Kara daure fuska azaad yayi jin abinda abba yace karsusa ta renashi mikewa yayi yace " ke tashi mutafi " yayi gaba tashi tayi tace " to muntafi semun dawo " Allah kiyaye hanya suka musu tabi bayanshi ganin motoci har guda goma sunyi shirin fitane ga securities da Sojoji suna fitowa suka dinga kwasar gaisuwa ganin ogansu da wata macen dake jikin hotunansu da aka yada yasa suka fara tunani bude musu motar tsakiya akayi yashiga tsayawa tayi bata shiga ba dagowa yayi yace " dallah malama kishigo mutafi karki batamin lokaci mana" bashiri tashige tazauna nesa dashi fita motocin sukayi agidan suka hau kan titi. Tunda suka fara tafiya babu wanda yakula dan uwanshi harsuka iso bude musu motar akayi suka fito kusan atare shiga ciki sukayi manager jikinshi na rawa yamusu sannu da zuwa yakaisu har inda zaayi hira dasu. Photographer's masu shooting videos duk sun hallara suna jiran afara saboda direct live zaayi kowa zega shirin alokacin da akeyinsa , wanda ze gabatar da shirin ne yace start nan da nan suka fara shooting. Gyara zama yayi yafara da " assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum jamaa kamar yanda kuka sani nine naku me suna jamilu abubakar wanda yau nazo muku da manyan baki wato bakowa bane bace wannan shahararren dan kasuwan damuka dade muna jiran opportunity samun hira dashi Allah beyi ba seyau wanda ayanzu ake zargin kancewa shidin womanizer ne ahausance manemin mata zakuji komai de daga bakinshi wannan kuma itace Fatima muhammad Umar mahaddaciyar Al qur'ani wacce ta taciyo kyaututuka da dama saboda kwazonta itama zamuji komai daga bakinta " Seda azaad yayi kusan 5min fuska adaure kamar wanda akawa wani abu cike da izza yace " kamar yanda kuka sani am azaad muhammad mainasara sauran labarina kuma beshafe ku ba dan bawan nan ne yakawo niba nazo ne akan qazafin dakukamin nida wife dina kuka bata mana suna saboda kawai biyan bukatarku saboda kawai kusamu kudi kuke watsa abinda ze taba rayuwar mutane batare da bincike ko wani abu ba acikin abinda befi 20 mint ba kuka bata mana suna" mamaki dauke akan fuskar jamilu yace " shin kana nufin kace mana hafeza fatima matarka ce? Amma tayaya? yaushe ? Kayi aure ba tare da sanin duniya ba Mr azaad? Zamuso Karin bayani " azaad kamar bazeyi magana ba yace " itadin matatace anyi aurenmu nida ita a lokacin da saukanta saura 1week aka bari se anyi sauka tukun nan ayi biki nasan jamaa da dama sunganni awajan walimar to bari kuji infada muku nayi shuru ne saboda wasu yan dalilai narabu daku amma ayau din nan banfito ba seda natsayar da matakin dazan dauka akanku kukuma al umman duniya wayanda basawa yan uwansu musulmai kyakyawan zato hakkinmu nakanku irin mugayen alkaba'in dakuka dinga binmu dashi ku kuka sani da Allah " bakaramin sanyi jikin duk wani wanda yake kallon gidan tv yayi ba dasu kansu BBC news seyanzu sukasan sun tabka babban kuskure . Sallama tayi da muryanta me dadin sauraro sannan tace " Kun batamin suna dukda ni matar aure ce amma haka yayi matukar taba darajata abisa kalaman dakuka rubuta ko tsoron Allah bakuji ba kuka kirani da dadiro harda cewa wai nasha zubar da ciki innalillahi wainna ilaijiraji unnn karku manta kuma kunada yaya mata in baku dashi kuma kunada kanne mata ko kun mantane khamatu dhinu tudanu kunjefa ni ama wuyacin hali saboda bakowa bane sukasan munyi aure ba bakomai nayafe muku amma kusani inkunwa wasu sun yafe wasu fah sede ku hadu agaban Allah tunda ku kwata_kwata bakwabin yan uwanku da kyakyawan alkhari se sharri " sosai jikin jamilu yayi sanyi saboda shi yayi editing da printing din labarin. Murya asanyaye yace " to jamaa ansamu babban kuskure domin labarin nan ba gaskiya bane duk masu bukatar karin bayani ko tambaya zasu iya kiranmu awannan layin wayanmu ayanzu " aikuwa yana gama fadin haka telephone din dasuke amsa kira dashi tayi ringing dannawa yayi yadaga wanda duk maganar dazaayi acikin duniya zataji . " Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum sunana sheikh Sulaiman Ahmad gombe nakirane domin bada shedan ido! Aranar da malama fatima tayi sauka nida kaina naje nasamu malama fatima domin nayaba da dabi'un ta nabukaci tabani daman insamu iyayenta da maganar aure amma taban hakuri ta shaida min ita matar aure ce agaskiya musulman duniya muji tsoron Allah muguji yada karya da jita_jita kokuma sharri " jamilu ne yace" to masu gani da sauraranmu fatan kunji abinda sheikh Sulaiman Ahmad gombe yace muna gdy da shaida sheikh Allah yakara girma " yakatse kiran yaci gaba" agaskiya mun tabka kuskure... via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by MRS 🌹 ISHAM 🌹 Page 3️⃣5️⃣ & 3️⃣6️⃣ " Batare da hujja ba munyi abinda be kamataba a madadina da tashar BBC news muna me matukar bawa Mr and Mrs azaad mainasara hakuri akan laifin da muka musu " shigowa manager da chairman sukayi suname basu hakuri akan kuskuren da akayi domin sunsan muddin Mr azaad yabar wajan nan batare daya hakuraba to kashinsu yabushe. Kafin nan da abinda be wuce 1hr ba labari yabaza duniya kota ina se sakon bada hakuri ne yake shigo TikTok, YouTube, Facebook, Twitter, Instagram, mikewa Mr azaad yayi yace " Nina gama abinda yakoni nan dan haka banda lokacin batawa " yafada yana rike hannun fanan suka fara tafiya se hotuna da video ake musu har suka fita bin bayansu masu tsaronshi sukayi suna bude musu marfin motar shiga yayi yana rike da hannunta zama tayi tana kallon fuskanshi sake hannunta yayi haka sukaci gaba zamansu kamar kurame harsuka iso gida ana bude motar tayi gaba dan sotakeyj taje tabawa su ummi labari , aharzuke ta hango aneesa ta nufota, tana isowa gurinta ta wanketa da mari ta shaketa " wallahi yau sena kasheki ko ni ko ke " kakari fanan tafara saboda shakan da aneesa tayi mata bana wasa bane cikin sauri azaad yakaraso yafisge aneesa daga jikin fanan rike wuyanta fanan tayi tana kuka mari azaad yawanka mata yana fadin " bakida hankali ne kasheta kikeson kiyine " kuka tafashe mishi dashi " baby you betrayed me nizaka yaudara kaje kayi aure a munafurce bayan anmana baiko dama kai munafiki ne bansaniba " ji yayi tabashi tausayi yasan baa kyauta mataba riko hannunta yayi yace" calm down muje ciki " wuce fanan sukayi dake tsaye tana kuka kallonta aneesa tayi tana mata gwalo, goge fuskanta tayi tashiga falo babu kowa aciki haurawa tayi part dinsu afalo tasamesu aneesa nakwance akan kafadarshi shikuma yana aiki a laptop ko kallonsu bata sakeyi ba tashiga bedroom dinta tarage kayan jikinta zuwa wata dogon riga me hannun vest mara nauyi yakamata sosai duk shape dinta yafito tasa hula fitowa falon tayi still suna zaune suna kallon labaran da akeyi akan sharrin da akamusu an wanke sunansu tare dabasu hakuri tanajin sanda Mr azaad yayi kiran waya yana cewa adakatar da su dukda batasan dawaye yake magana ba Amma tafahimci BBC news yabada umarnin adakatar . Jin haka yasa fanan tashiga matsanancin farin ciki jitayi duk bacin rai dinda take ciki ya yaye kitchen tashiga tayi jallof din macaroni da beef yasha vegetables se tashin kamshi yakeyi tadawo falon dan nesa dasu tanacin abincinta gaba daya kamshin yacika musu ciki sedataji ta koshi ta ajiye plate din gefe kasa hakuri aneesa tayi tamike tashiga kitchen din bude tukunyan da fanan tayi girki tayi kozata samu sauran macaroni babu komai aciki dan iya cikinta tadafa dawuwa falon tayi " baby yunwa nakeji kuma abinci kadan tayi basaura kace mata tamin wani kaji" shuru yamata be kulata ba sake nanata maganar tayi ganin zata dameshi ne yasa ya kalli fanan dake zaune tana kallon tv tanashan drinks hankalinta kwance yace " Meye dalilin dazesa kiyi abincin dan kadan tunda yakare seki dafa mata wani " dariyar renin hankali tayi ta kalli aneesar cike da tsiwa tace " ohhh really indafa abinci wata katuwa taci ? To ni baa kawoni gidan nan dan indafawa wata katuwar banza abinci taci ba" cike da mamaki azaad ke binta da kallo with his sexy voice yace " me aka kawo ki kiyi?" Ko ajikinta tace bautar aure da kula da miji dan haka kar wata takara cemin inmata abinci yauwa" mamakin yanda take zaro zance yakeyi yar yarinya da ita wato hartasan wani bautan aure . Akule aneesa tace " to dakike maganar wani kinzo bautar aure nasan komai baby yafadamin dalilin auren naku kuma yanzu da sunanshi yawanku zesake ki ya aureni kinzo kina wani iyayi " magana fanan tayi azuciyarta yazama dole in koya mata hankali , fari tayi da manya_manyan idonta tadaura kafa daya kan daya, Mr azaad de da ido kawai yakebinta . Sa idonta tayi cikin na aneesa tana fadin" kalleni dakyau namiki kama da wacce zaa aura asaka? To shi saurayin naki daya fada miki hakan yafadane dan kawai yakwantar miki da hankali amma inbanda haka meye zeyi dake nifa yarinya ce me kananan shekaru shisa yakyasa yatakura, hankalinshi be kwanta ba seda yaga nazama matarshi kuma yana bani kulawa sosai ko bahaka bane honey sugar ?" Tafada tana kashewa Mr azaad ido daya, yama rasa mezece mata kullum iyayin yarinyar nan da yarintar ta karuwa yakeyi cize libs dinshi nakasa yayi. Kuka aneesa tasa tafita da gudu zuwa part din mommy tana kudurta aniyar ganin bayan fanan domin yau ta wulakanta ta setadau mataki . Seyanzu tafara danasanin abubuwan data fada meya kaita nema, mikewa tayi simi_simi tashige dakinta takwanta tana dariya inta tuna abinda tawa aneesa , kamar amafarki taganshi atsaye akanta tashi tayi tazauna tana narai_narai da ido dukufowa yayi, ja baya tayi, rumfa yamata da faffadar kirjinshi da hannayenshi guda biyu , kallon cikin idon juna sukeyi without a blink sa hannu yayi yazame hulan dake kanta gashinta yazubo akan bed din hannunsa yasa yadamki kan da karfinshi ihu tasa jin azaba rike hannunshi tayi da duk hannayenta biyu tana kuka dagota yayi tsaye still yana rike da gashin. dayan hannunshi yasa yamatse dan karamin bakinta yace " banason inga ina hurting din mutum amma kinja dole sena hukuntaki abinda nakeso dake stay in your limits don't try to cross it inba haka ba sekinyi dana sanin sanina! Bantaba sonki ba kuma har abada bazansoki ba dan ke yarinyace dakanta ke cike da yarinta impact ke bakima kai girman dazan yi rayuwar aure dakeba kinmin yarinya kikarewa kanki kallo dakyau reason din dayasa akayi auren nan shine saboda awanke sunanmu and komai yanzu is steady zansake ki kije kiyi rayuwarki freely kwaila kawai " duk maganar dayakeyi besaketaba yana damke da gashin kanta da kuma bakinta daya matse seda yagama magana tukun yayi wurgi da ita kan gadon yafice. Kukanta tasha mecin rai ahaka bacci yadauketa. " Mommy wallahi sena kasheta inbahaka ba hankalina baze taba kwanciya ba " cewar aneesa dake magana tana kuka tsaki mommy tayi tace " yanzu ke ko kunya bakiji ba kanwar bayanki zaki tsaya kina mata kuka baki kamata ba kin manta jakin duka ! Wallahi shame on you" sake fashewa tayi da kuka tazo tafada mata instead of sunemi solution tahau ta da fada lura da hakan ne yasa mommy takwantar da murya " is okay my angel karki damu yau yau din nan zandau mataki setayi danasanin abinda ta aikata miki karki kara shiga part din se gobe kinji ko angel din dadi" sake fuska tayi tana murmushi seyanzu hankalinta yakwanta jin mommy tace zatadau mataki akanta. Har seda time din sallah yayi ta farka taje tayi sallah har time din tana tuna bakaken maganganun da Mr azaad yamata haka tazura dogon hijab dinta tayi falon ummi samun zeenat tayi afalo tana shan rufaida yogurt zama tayi tana karban roban yogurt din tafara sha sake baki zeenat tayi dan batasan da shigowarta ba tace " ikon Allah anty fanan yaushe kika shigo " tana Shan yogurt din tace mata " sanda kike kwadayi mana" dariya zeenat tayi tace" to naji ya kike ya program munganku a tv alhamdulillah komai yatafi successful yanda akeso" " hmmm kede bari kawai nikadai nasan irin farin cikin danake ciki " hira sukeyi har anty Amina tafito tasamesu kallon fuskan fanan tayi taga alamar tayi kuka kiranta tayi wajanta fanan taje tazauna waigawa tayi ga zeenat tace " to anty kwadayis kidan bamu waje zamuyi magana " tashi tayi tayi dakinta maida kallonta tayi kan fanan sannan tace " my fanan meke damunki wani abu azaad yamiki " dasauri ta girgiza mata kai alamar ah ah ta fahimmci tanason boye mata ne yasa tace " karkimin kallon sirka kidaukeni amatsayin antynki firdausi duk wata damuwarki karki boyemin dakuma tsakaninki da azaad semu samo solutions kinji" sosai hankalinta yakwanta dan dama tarasa wazata fadawa damuwarta , bata labarin tun daga dawuwarsu da shaketa da aneesa tayi har izuwa abinda Mr azaad yamata dakuma maganganu daya fada mata. Jinjina kai tayi dan tasan zaa rina kuma bakomai yasa yakula aneesa ba sedon taji haushi amma yanzu dole tadaura fanan akan hanya dazata gyarawa azaad zama dakuma ita kanta aneesa datakeson takurawa rayuwarsu. ____" kinaji abinda kikayi yau kinmin dede domin inkika sake kika kyale aneesa tsaf zata renaki sannan inason kinunawa azaad ke ba yarinya bace kamar yanda yafada shida kanshi zedawo yana baki hakuri da lallabaki ! Tunda harya ce miki kwaila yayi mukuma zamuyi iya kokarinmu dan muyi proving dinshi wrong " zare ido tayi tana kallon anty Amina kamar amafarki " yanzu Mr azaad dinne zewani lallaba mutum har yabada hakuri tabb " sosai anty Amina ta dinga bata shawarwari tayanda zatajawo hankalin Mr azaad duk da fanan tanajin kunyan wasu Abubuwa amma haka tanutsu tana sauraran anty Amina dan tadau aniyar nunawa Mr azaad ita ba yarinya bace. Farin ciki anty Amina tayi ganin fanan tadauki shawararta dakuma wayon data mata yayi tasiri dan ita tayi hakan ne da tasamu su dede ta kansu dan tasan yanda Mr azaad baya son fanan, haka itama fanan bata sanshi auren kawai Allah yayi de zaayi shine . Duk sunyi sallah isha suna zaune akan dinning zasuyi dinner kowa ya hallara harta Mr azaad yafito serving dinsu akayi suka faracin abinci kwarewa fanan tayi tana yar tari kadan_kadan suna mata sannu abu kamar wasa tari yayi karfi hartana biga kanta da table din gaba daya rudewa sukayi suna mata sannu anty Amina da ummi suna bubbuga bayanta. Nan take kuma tarin yatsaya suka bata ruwa tasha idonta yayi ja dan wahala , rike wuyanshi yayi dayaji kamar anshake shi jin shakewan yayi yawane yasa yamike rike da wuyanshi yana kakari kamar wanda zemutu tashi sukayi arude suna nufo wajanshi sosai aka shakeshi amma su basa kallon kowa se rike wuyanshi dayayi babu yanda basuyi ba dan su cire hannunshi akan wuyanshi amma sun kasa. lokaci daya jikinta yayi wani irin kaduwa akayi walkiya da karfi farin haske yarufe ko ina tashin hankali baasa mata rana gaba daya yau sunga abinda basu taba gani ba hasken seda yakai 5mint kafin yawashe duk sundukufa akan Mr azaad dake kakarin mutuwa se adduah sukeyi mishi ga farin hasken daya tsorata su mikewa azaad yayi yazauna yana sake wuyanshi jin ansakeshi , Karan sarkan kafa sukaji duk taku daya idan tayi se yayi kara juyawa sukayi domin ganin ta idan karan kefitowa tozali idonsu yayi da SARAUNIYAR nasminaya cikin shiga ta jarumar sarauniya dakuma sadaukiya wacce ta amsa sunan ta jaruma farin wando ne me fadi kamar wandu nan Pakistan kafan wando kamar ansa mishi roba se riganshi me hannun vest tsayinshi har kusada guiwanta farin kayane sol anmishi kwalliya da zinari domin kayan da sarki da sarauniya suke sawa ma daban ne asaman kayan kuma ga irin rigunan nan kamar nakarfe da akesawa idan zaa fita yaki bayanta nadauke da kwari da baka dasuke cikin gidansu akillace suna jiran kota kwana. se kugunta dake dauke da wukane dogo na sarauta awajan , kunnent,wuyanta duk suna sanye da sarka da dankunne harta dantsen hannunta nadauke da wasu irin saraquna , kafanta tana sanye da sarkokin kafa na zinari dawo da kallona na iya izuwa fuskanta da kanta gashinta nagani yakara tsayi amma bawani sosai ba yayi curly anzubasu agefen wuyanta nadama dana hagu sauran kuma suna gadon bayanta anmusu kwalliya da sarkan kai ( head band chain) ga crown 👑 akanta me matukar kyau fuskanta kamar wacce akayiwa kwalliya ( umm to aidole ma aga fuskar sarauniyar aljanu da kwalliya ) dan karamin bakin nan yasha dark maroon janbaki idonta na sheki sosai . Fuskanta ahade kamar hadari gaba daya ta tashi daga fanan din dasuka sani se takoma ainihin sarauniya babu abinda takeyi daya wuce yalki saboda gwala gwalan dake jikinta gaba daya gakuma daddadar kamshin dake fitowa ajikinta wani irin masifar kyau takara . Suman tsaye sukayi suna kallonta tunani suka farayi kode yaune ranar komawarta masarauta gaba daya sukaji tayi musu gwarjini jikinsu yayi sanyi, tafiya tafara kamar wacce take lankwasa jiki da gangan takaraso wajansu ko kallon direction din dasuke batayiba tasa hannu tashake iska tunani suka farayi meye to tashake dansu basu ga komai ba. Cikin wata murya me zaki da amo tayi magana tana karkata kanta gefe kamar wata robot " ki bayyana kanki " seda falon ya amsa da muryanta aikuwa tana gama fadin haka wata halitta tabayyana cikin bakaken kaya mara kyaun gani seda sukaja baya banda azaad. Dagata tayi suka fara tafiya a sararin iska acikin falo seda suka kusa roof din falon suka bace batt. Sunshiga cikin damuwa yanzu shikenan bazasu sake ganin fanan bah kenan zeenat se kuka takeyi, iyayenta zasuji zafin tafiyanta batare da sunyi bankwana ba, Mr azaad ne yace " Amma ai waadin tafiyanta beyi ba bekamata ace tunyanzu harta tafi ba " abbane yace " Kuma hakane waadin tafiyanta beyi ba taya zaayi ta tafi yanzu kila abinda yafaru harin da aka kawone yasa jaaazana bayyana ajikinta da sauri " jimami suke tayi har sha Daya nadare basu kwantaba wani security ne yashigo falon da gudu haryana kokarin faduwa zuba mishi ido sukayi suna kokarin tambaynshi lafiya yayi saurin fadin " ranka yadade naje zanrufe kofan garden ne naga mutum akwance awajan jin haka yasa Mr azaad fita da sauri yafice yanufi gadin din suma suka rufa mishi baya tundaga nesa daya hango hijabin jikinta tana kwance plat bata motsi yaganeta sa hannunshi yayi yadagota kamar yar babyn roba yayi ciki da ita ahanya yahadu dasu ummi duk sunfito sunbi bayanshi ganinshi dauke da itane yasa suma suka koma ciki haurawa yayi da ita part dinsu dakatawa sukayi afalon suna alhamdulillah sannan abba yacewa kowa yaje yakwanta se gobe haka kowa jiki amace suka tafi. Direct bedroom dinshi yayi da ita yakwantar da ita akan bed hannu yasa yacire mata dogon hijab din jikinta da kayanta yarufeta da blanket yashiga bedroom dinta yabude wardrobe yadauko sleeping dress white color me guntun wando yadawo yasa mata kallon kirjinta dake cike da dukiyar fulani yayi nan take yaruntse ido yanajin haushin kanshi naganin dayayi mata yagyara mata kwanciya, yayi toilet bayan kamar 15mint yafito yayi wanka yasa sleeping dress dinshi yahau bed din dan nesa da ita kadan yaje yakwanta yana rufe jikinshi da blanket yayi musu adduah yakashe wutan dakin yabar bedside lamp. ____ cikin dare tafarka da zazzabi jikinta rau zafi cikin bacci yaji kamar sheshekar kuka tashi yayi zedubata yagansu manne da juna yana rungume da ita ajikinshi kokarin raba jikinsu yakeyi tasake rikeshi tana " uhmm uhmm sanyi nakeji karka tashi" tafada ashagwabe kallon fuskanta yayi da hasken dake gefen bed din idonta arufe ga hawayen datakeyi gashin idonta sunyi zara_zara seturo baki takeyi duk abinda take fada acikin baccine da zafin zazzabi kallon cute face dinta yayi yasamu cikin dabara yatashi toilet yaje yadibo ruwa a bowl medan fadi yafito da karamar towel ahannunshi zama yayi akan bed din yatallafo ta jikinshi so yakeyi yadan goge mata jikinta da ruwan sanyi saboda zafin da jikinta gashi dole seya cire yacire mata riga amma yana tunanin karta tashi tayi tunanin wani abu tazo ta renashi he has no choice hakan yayi yacire rigan yafara goge mata jikinta da towel din jin hannunshi na gogan kirjinta ne yasa yahakura yamaida mata rigan yakwantar da ita locker dayake ajiye magunguna shi yabude yadauko mata magani tashinta yayi , kallon fuskanshi tayi tace " miye! miye ? katasheni nikam bacci zanyi " sa mata magani yayi ahannunta yace tasha bata fuska tayi ganin kwayan magani fashewa dakuka tayi nikam " bazan shaba " tafada tana make kafada ganin inya biye mata dagasken bazata shadin ba, yasa yawatsa kwayoyin maganin cikin glass cup suka jiga dan kwantar da ita yyi ajikinshi yasa hannu yamatse bakinta yadùra mata kakarin amai takeyi yahade bakinsu waje daya seda yatabbatar aman ya koma kafin yakwantar da ita shima yakwanta manne da ita ajikinshi Karfe 5 dede tafarka jinta ajikinshi yasa tayi saurin tashi sosai abin yadaure mata kai metakeyi ajikin Mr azaad akuma dakinshi duk abinda yafaru adaren jiya ta manta kallon jikinta tayi taga kayan datake sanye dasu waro ido waje tayi data tuna ai ita dogon riga ne da hijab ajikinta taya akayi suka dawo kayan bacci kuma gata a dakin Mr azaad zuciyarta ce tace " waye kike tunani zeyi haka Mr azaad ne mana" cikin sauri takalleshi bacci yakeyi abinshi hankali kwance sadaf _ sadaf ta tashi tabar dakin tashiga nata dakin wanka takesonyi dan kwata_kwata batajin jikinta da karfi. To bari muleka bangaren mommy. Awurge a tsakiyar falonta nahangota acikin mawuyacin hali se numfashi takeyi dakyar kamar zata mutu kayan jikinta duk ya yayyage ga jikinta nafitar da jini kamar wata al majira. Abinda yafaru shine bayan tayiwa aneesa alkawarin gamawa da babin fanan atime din dasuke dinner taje da niyar kasheta tayi iyayinta ana haka taji anbuga ta da kasa kallon wacce tamata hakan tayi taga ashe khairatyyy ce ganin mission dinta na kashe fanan beyi bane yasa takoma kan azaad kokadan khairat batayi yunkurin hanata ba domin ita umarnin kula da sarauniya kawai jakadiya tabata. Ganin zaayi kisane yasa wani bangaren jaaazana yamotsa shisa fanan ta bayyana a ainihinta ta sarauniya domin takareshi cike da jindadi ganin sarauniya tabayyana khairaty ta duka kasa cikin girmamawa, lokacin da sarauniya ta rike mommy suka bace sararin samaniya takaita tamata mugun duka kokarin ramawa mommy tayi amma ina ko kadan karfinta beze iya da sarauniya ba haka tanaji tana gani taji mata mugun raunika ajiki sannan tasaketa tafado kasa dakyar mommy ta iya lallabawa takoma gida. ___ wasu irin sambatu tayi nan take tanzarzar yabayyana yana wannan dan iskan dariya nashi mara dadinji kafin yafara magana " hafsat nadade da fada miki da ki nisanta kanki da ita gashi yanzu kinjawa kanki ina matsayin shugabanki amma kikasa bin umarni na wannan shine hukuncnki babu abinda zanmiki kije kiyi jinyar jikinki taurin kai yanzu yamiki rana ai" ya karashe maganar yana dariya me karfin gaske kafin yabace bat. Masha Allah masoyana inata ganin ruwan comments da adduah ina godiya sosai Allah yabar kauna love you Lodi lodi 🌹🫂🥰🥰🥰🥰 via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by MRS 🌹 ISHAM 🌹 Page 3️⃣7️⃣ & 3️⃣8️⃣ Haka tanzarzar yabace yabarta batare dawani taimako ba , fitowa Mansoor yayi daga bedroom dinshi rikeda shisha pot idonshi ne yasauka akan mommy dake kwance tana fitar da numfashin wahala arazane yanufeta yana " mommy meya sameki haka? Waye yamiki wannan abu?" Ahankali ta iya cemai yakaita dakinta ciccibarta yayi yakaita yana mata sannu. _____ tana zaune agaban mirror tayi light make up tana sanye da dakakkiyar lace me tsada dinkin dogon riga fitted gown wuyanta yasha sarka da dan kunne na gold tayi kyau sosai takafa dauri , Allah Allah takeyi tagama shiryawa taje ta gaida su abba dan rana harya dan fito karfe 10:30 gama shiryawan tayi tadau gyale tasa da takalmi hill tana tafiya kamar wata me tsoron taka kasa shigowa falo tayi tanajan kofan bedroom dinta jin muryan aneesa tayi se zuba surutu takeyi mamakine yakamata wai ita wannan bata da aikinyi se makalewa mutane, karasowa falon tayi taganta tana zaune atare da Mr azaad jikinsu amanne yakwantar da kanshi ajikin kujeran dasuke zaune idonshi alumshe kamar wani me bacci dan gaba daya surutun aneesa ya isheshi, cike da neman magana taje kusa dasu tatsaya akansu tana rike kugu " ke kam aneesa wace irin mayyace mara zuciya ban rabaki da mijina ba? Kinzo da sassafe zaki hanashi hutawa to baki isaba ki tattara kibarmin part ko kuma inyi maganinki " tana magana ta jijjiga jiki kamar dagaske in anbarta da aneesa din iya dukanta zatayi . Slowly yabude idonshi akan kyakyawar fuskanta shide yagaji da lamarin fanan ciwon kai takesashi dan yalura bajin magana takeyi ba inya biye mata ze iya karyata abanza a wofi. Sake shigewa jikin azaad aneesa tayi tana fadin " to badole inzo ba keda kwata_kwata bakya bashi kulawa baki masan yanda zakiyi da miji ba so he needs me by his side ! Kinga ni zan mishi abinda bazaki iyaba tunda haryanzu baki gama girma ba" dan zare ido fanan tayi tama rasa mezata fada mata wanda ranta zeyi mugun baci, samun kanta tayi dafadin " aneesa shiyafada miki haka ? To bari kiji jiya kwana mukayi bamuyi bacci ba gabaki daya yanzu haka agajiye nake kawai karfin hali nayi zanfita gaba daya yasa jikina se ciwo yakeyi abinki da yarinya nasan dakece goggiyar yar duniya nasan Koda wasa bazakiji kingaji ba to nina tafi se anjumanku ! Honey sugar bye" tana fadin haka kuwa tayi waje batare da jira amsar da aneesa zata miyar mata ba. Mr azaad kam he's totally out of words lamarin fanan goge mishi hadda takeyi yarinya karama da zaro manyan maganganu kwafa yayi yana fadin " zaki dawo kisameni" ya shige bedroom dinshi yabar aneesa afalon ta cika tayi bam kamar zata fashe. Ahankali take taka staircase din gaba dayansu sun hallara afalon daga gani abu me mahimmanci suke tattaunawa, tsugunawa tayi tagaida abba da ummi,anty Zainab dasu anty Amina gaba dayansu seda tabisu tana gaidasu, suka amsa da murmushi akan fuskansu areef ne yace " Ina kwana anty ? " Hararan wasa tawurga mishi tana " Allah ya areef banaso kabari " zeenat ma tace " anty fanan ina kwana" banza tayi da ita, dariya sukayi duka , anty shayida tace " yauwa kingama maganarki akeyi segaki nan " murmushi tayi tace " to anty gani " fawwaz ne yace " daman maganar bikinku akeyi kinga kwata_kwata baayi komai ba, so nan da 1 week ko 2 weeks zaayi event din bikin dinner ne da kamu se walima " shuru tayi tana tunanin itada zasu rabu da Mr azaad meye kuma na wani shagalin biki, tana jinsu se tsara yanda bikin ze kasance sukeyi. Abba ne yace " Fatima gobe dukanmu zamuyi tafiya zamu tafi dubai yiwa kakansu zeenat yajiki kwana biyu bayida lafiya bazamu dade ba munso tafiya dake amma kinga ke bakida visa inmun dawo zaku tafi tare da mijinki daga yanzu zuwa lokacin komai dinki zezama ready" cike da kunya tace " to Abba Allah yakaimu" Suna haka se gashi yasauko cikin shirinshi nazuwa office yasha kyau suffarshi ta larabawa yakara fitowa, sakai yayi zefita abba yace " azaad zo nan" dawuwa yayi yazauna kusada abban . __" yauwa namanta banfada maka ba next week inmun dawo in sha Allah zaayi event din aurenka " kaff dinsu zuba mishi ido sukayi dan sonjin mezece. Yau tunda yatashi bayajin yin wata dogon magana ciki_ciki yace " auren waye din ake magana?" Ganin yamanna musu haukane yasa ummi cewa " son auran kai da fanan mana kuma bawai shawaranka muke nema ba! Ah ah munriga da munzartar seka fara shiri zaka iya tafiya" mikewa yayi besake ce musu komai ba dan shibawai ya iya musu bane kuma yasan insukayi magana ba canzawa zasuyi ba. 8:00pm tana zaune afalo tana kallon series din India atashan zee word me suna the promise, jikinta nasanye da guntun wando jeans boom short da wata yar ficikar riga iya cibiya batasa bra ba rabin dukiyar fulaninta awaje wandon yadámeta tam tayi donot da gashinta sosai tayi kyau kamar wata bakar balarabiya, duk da kana nan kayane amma haka taji sundame ta haka tadaure taci gaba da kallon. ___ bashi yashigo gida ba har 9:00 part dinshi yanufa hannu yakai kan handle din ze murda yaji kamar karan tv shiga yayi yahangeta tana zaune tana kallo se shan fruit takeyi batama san da shigowanshi ba, zama yayi akan kujeran dake facing dinta se anan ne taganshi " barka da dawuwa Mr azaad" bece mata kalaba yacire socks din kafarshi yafincike necktie din , tunda tagaidashi be amsa ba bata kara kallon inda yake ba . " Ke tashi kikawo min tea " tashi tayi tashiga kitchen tahada mishi tea tadawo falo bata sameshi ba yasa tawuce bedroom dinshi nanma baya ciki ajiyewa tayi akan center table tana kokarin juyawa taga yafito daga toilet yana daure da towel akugunshi, runtse idonta tayi gam dan tunda take bata taba kallon namiji ahaka ba , karasowa wajanta yayi yasa dukka hannunshi yatallafo fuskanta Murya anarke yace " miyasa kike rufe idonki bayan kina gaban mijinkine ! Ohhh namanta ashe yanzu lokacin dazaki bani kyakyawar kulawa ne oyah Start" gabanta ne taji yana duka da karfi tuna abinda tamusu da safe shine yanzu yake dauko mata maganar, dasauri tajuya da niyar tafiya fincikota yayi tafado akan faffadar kirjinshi dayake dauke da kwantaccen gashi jikinshi gashi ajike da ruwan dayayi wanka gashin kanshi se diga yakeyi mannata yayi da jikinshi hannunshi daya narike da waist dinta. Wani kalan kunyarshine yarufeta tarasa yazatayi tabar dakin. Ganin haryanzu taki bude idanunta ne yasashi sake matseta ajikinshi ba shiri tabude ido, Kallon fuskanshi tayi taga kalan kallon dayake mata nan take tasunkuyar dakai kasa dan bazata juri kallon kwayar idonshi ba , sa hannu yayi ya dauketa kamar yar baby besauketa a ko inaba sekan bed dinshi . kokarin tashi takeyi yasa hannu yamaida ita yamata rumfa kwanciya yayi ajikinta yasake mata nauyinshi duka nan take tafara nishin wahala dan jitayi kamar wanda aka dorawa buhun cement ajiki tureshi takeyi amma ko motsawa beyiba zatayi magana yadaura yatsanshi a libs dinta " shhhh don't say a word ! Kikace jiya bamuyi bacci ba saboda kinbani hakkina? Tom bari inbaki yanzu tunda haka kikeso , aibansan kinaso ba da tun ranar da aka kawoki gidan nan nabaki " fanan ido yarena fata inbanda danasani babu abinda takeyi nan take hawaye yafara wanke mata fuska dan talura Mr azaad babu wasa alamarinshi. Slowly yafara zame mata rigan jikinta harya kawoshi zuwa cikinta sa hannunta duka biyu tayi tarufe kirjinta tana kuka " please Mr azaad don't do this to me" dede kunnenta yafurta " I will! abinda kikeso kenan tunda har kika iyayin shela na gajiyar dake bari ayi na gaskiyan karki damu it won't be hurt" daduk karfinta take dukan kirjinshi tana kuka da rokonshi daya kyaleta bazata karaba. Hade bakinsu yayi waje daya yafara bata hot kiss harda na mugunta na cizon libs dinta da karfi sosai take kuka tana tureshi amma ko motsawa bayayi seda yatabbatar da ta mugun galabaita kafin yadakata yadago yakalleta yana wannan killer smile din nashi dayake kara mishi kyau, shafa libs dinta yakeyi da yayi jajir yadan kumbura dan bakar wahalar dayasha yace " tom yanzu saura inbaki hakkinki ko?" Hawaye na gangarowa daga idonta tace " kayiwa Allah daya halicceka Mr azaad kayi hakuri kabarni" watsa mata harara yayi yace " stupid girl bakince ke mara kunya ba naso yau inga karshen inda rashin kunyan zetsaya yarinya tunbaki tafasa ba kina kokarin konewa harkinsan kicewa wata mijinki ya gajiyar dake saboda taji haushi ko? " Girgiza kai tayi alamar ah ah matse libs din yayi seda tayi kara" ni kurmane dazaki girgizamin kai kokuma ke kurma ce? common open your mouth and talk joo" cikin muryan kuka tace " ah ah " kwafa yayi " I warned you several times amma naga kamar kwata_kwata taurin kanki yahanaki saurarata to muzuba nidake agidan nan kedajin dadi kuma se randa narubuta miki sakinki as from today you're my maid duk wani aikace_aikacen part din nan ke zaki dingayi inkuma ba hakaba " ya kyasta yatsunshi afuskanta, yatashi daga jikinta kifa kanta tayi akan pillow tana kuka daga baya ta tashi tashige bedroom dinta ahaka tacigaba da kuka daga baya bacci yasaceta. Karfe 5:00am tana kwance tana bacci yana tsaye akanta hannunshi rike da karamin bucket cike da ruwa ahannunshi dagawa yayi ya kwarara mata daga sama har kasa afirgice ta tashi tana salati four eyes sukayi " kitashi aibakiga ta bacci ba kiyi sallah kisameni a bedroom dina" to kawai tace mishi ta tashi tacire bedsheet din da suka jike da ruwa takai toilet ta tasasu a drying machine itama tayi wanka tayi alwala tacanza kaya. Bayan ta idar da sallah tanufi bedroom dinshi samunshi tayi yana zaune yana pressing din system idonshi sanye da farin glass daga gani wani aiki yakeyi me mahimmanci muryanta ahankali tace " Mr azaad gani" batare da yakalli inda takeba yace kishiga kiwanke toilet dina da jikin toilet din sannan akwai kaya acikin washing machine kifito dasu ki wanke su tass inkin gama kuma banason inga dirty ko kwallin zarrah acikin part din nan and try to finish it before 9" batace komai ba tashiga toilet din tabude washing machine ganin tulin kaya aciki kuma dukkansu wankakkune agoge wasuma baa taba sasu ba sunfi set 50 haka tafito dasu tafara wankewa tuntanayi ta dadin rai hartaji gaba daya tagaji bayanta har rikewa yakeyi. Ba ita tagama komai ba se wajajen 11:30am ko ina tayi kall dashi jiri take gani saboda gajiyan datayi ga yunwa bataci komai ba. Lallabawa tayi tashiga kitchen tadafa indomie da tea tagama ci kenan tadan mike akan kujera har baccin wahala yafara daukanta yadawo tsayawa yayi akanta yana binta da eyes fridge yaje yadauko bottle water yabude yazuba mata afuska dasauri ta mike ganin shine tafashe da kuka " shhhhh yimin shuru dukanki nayi ko zaginki nayi kitashi yanzu muje " yafadin haka yayi gaba babu yanda ta iya haka tabi bayanshi wata kofa taga yashiga bata taba sanin akwai wani bedroom aciki ba seyau shiga ciki sukayi. Sake baki tayi ganin wani room and falon ne aciki sede alamu yanuna kamar yadade duk yayi mugun kura sosai wanda ko mutane uku ne sesunsha wahala kafin sugama gyarawa , tana cikin wannan tunanin taji yace " oya ki gyara side din nan dan zuwa gobe nan zandawo " fita yayi yabarta aciki tunani tafarayi shin ta ina zata fara gyara nan ,neman tsintsiya tayi tashare ko Ina sannan tafara mopping haka tabirkice kamar ba itaba babu abinda yake tsayar da ita se sallah. Har karfe 9 nadare bata gama ba. Hango jakadiya abashiyya nayi da khairatyyy suna tsaye duk wani movement dinta suna wajan gabaki daya ransu abace yanzu sarauniyarsu ake aizabtarwa haka . Khairatyyy tace " shugaba meze hana mudauki mataki akanshi " girgiza kai abashiyya tayi tace " ah ah khairatyyy wannan bangaren rayuwar sarauniya ne shidin mijinta ne mukuma babu ruwanmu da shiga tsakaninsu, domin tsakanin mata da miji se Allah amma abu daya ne nasani shine zeyi matukar dana sani arayuwarshi seyaji yatsani kanshi jizeyi komai na duniya bayamai dadi" Yinin yau curr su ummi basuji dúriyan fanan ba harsun fara tunanin ko wani abune yasameta , fitowan Mr azaad zasuje masallaci ne yasa suka tambayeshi lafiya kuwa fanan shuru sece musu yayi tana nan lafiya kawai yau batajin fitowane zeenat ne tace " to bari inje intayata hira" mugun kallo yawatsa mata yace koda wasa kar wanda yashigamin part yayi gaba abinshi. Shigowa yayi bedroom dinta yasamu bata nan side din dayace tagyara yashiga anan yasameta akwance akan tiles ta dukun kune waje daya tana baccin wahala duk tagama aikin dayasata sa hannu yayi yadauketa yanufi bedroom dinshi da ita ajiyeta agan bed tashi tayi tana murza ido kallon ta yakeyi sosai can yace " bace min da gani " atsorace tabar dakin nashi dan ita yanzu tafarajin tsoronshi , batare data cire kayan jikinta ba ta fada toilet tasakarwa kanta shower warm water seda tadau 30mint kafin tafito daure da towel ajikinta duk tagaji batare data shirya cikin sleeping dress ba takwanta dakyar ta iyayin adduah tasamu tayi bacci, haka takwanta batare dataci komai ba. Yau tun 5:00 ta tashi tafara nafila kafin aka kira asuba tanajin motsinshi lokacin daya tafi masallaci, yau ko komawa bacci batayi ba tafara aikace_aikace koda yadawo yasameta tanayi bece mata komai ba yashiga bedroom dinshi yakwanta , haka tasha aiki se 8:30 tagama komai tahada breakfast taci sannan tashiga tayi wanka tasa riga da wando tazura hijab dinta sadaf_sadaf take tafiya tanason taje gunsu ummi suyi sallama dantasan tsaff zece ze hanata fita tunda yanzu yasata agaba, kamar daga sama taji daddadar muryanshi yana fadin " karki yarda kifita a part din nan kijira tukun " ko waigowa batayi ba haka bata koma tazauna ba fitowa yayi yana sanye da farar jallabiya yabude suka fita. Kowa ya hallara suka dai kawai ake jira sufito jinsu shuru ne yasa ummi tacewa zeenat taje ta kirasu kila basu tashi bane har zeenat tafara tafiya se gasu nan sun sauko sunkuyawa tayi tagaidasu, suka amsa suna tambayarta ko lafiya jiya bata fito ba satan kallon Mr azaad tayi ganin yakafeta da ido yanason yaji mezatace yasa tace " ummi jiyan ne nadan tashi bana wani jin dadi sosai shine Mr azaad yasamomin magani" sannu suka dinga mata. Ahaka suka fito motoci guda 10 ne yakejiransu banda na securities, rungumeta zeenat tayi tana " anty zanyi missing dinki" " zanyi missing dinki nima sosai zee" cewar fanan, zuwa fanan tayi tarungume ummi, murmushi ummi tayi tace" my feena ba dadewa zamuyi ba kinji take care of yourself in son yamiki wani abu kifadamin" tom ummina, haka abba yasake jawa Mr azaad kunne akan yakula da fanan kamar gaske yace " to" sosai tamusu adduah Allah yakiyaye hanya yakaisu lafiya yadawo dasu lafiya, sunjidadin addu'arta sosai. Haka suka shiga motar zuwa airport suna musu bye-bye fanan kam jitayi kamar tayi kuka antafi anbarta da Mr azaad dakyar inzasu dawo susameta araye cewarta. Haka yafinciki hannunta suka koma cikin gidan. Tundaga wannan ranar fanan bata Kara sanin meye farin ciki ba duk wani hanyar dazata huta taji dadi Mr azaad yadatseshi gaba daya tafita ahayyacinta azabtar da ita kawai yakeyi da aiyuka masu matukar wahala duk tabi tarame tadanyi duhu abun tausayi ko kyakyawar bacci batayi yayi nasarar jefa mata tsoronshi aranta ko muryanshi taji jikinta daukan rawa yakeyi , kuma duk wahalar daze bata baya barinta da yunwa. Yauma kamar kullum tunda garin Allah yawaye take faman wanke mishi wankakkun kaya da lafiyarsu kalau babu abinda yasamesu haka take tawanki kamar baiwa kwala mata kira yayi da " keee " naman jikinta ne yafara bari tsabajin tsoro haka tafito atsorace tace " Mr azaad gani" cike da izza da gadara yace hadamin black tea " dasauri tafice tashiga kitchen 3mint yadauke tagama tafito dashi hannunta narawa taza mika mishi yadan zuba ajikinshi wani gigitaccen mari yazabga mata a kumatu wanda seda tadena ganin komai nakusan minti uku kawai jinshi tayi yana" ke wacce irin mahaukaciya ce dazaki kona ni da hot tea" hawayen daya wanke mata fuska tagoge tana bashi hakuri dan tasan inya fusata yanzu ze kara mata wani marin daukan cup din tayi takai dustbin dan yadan fashe, tagoge wajan tana danne kukan daya ciyota kiranshi yaseer yayi yasanar mai yana falo. Hira sukeyi da yaseer tashigo hannunta dauke dasu drinks takawo mishi tunda tashigo yaseer yake kallonta da mamaki ganin lokaci daya tayi wani rama kamar wacce tayi jinya fuskanta asake tace " ya yaseer ina wuni " amsawa yayi yana kare mata kallo dole akwai abinda yake faruwa , harzata juya cikin tsawa azaad yace " ke zonan " jikinta har bari yakeyi itaduk a tunaninta wani laifin takarayi nan da nan hawaye yafara zuba a idonta, kallonta yayi kafin yace " meye nafada miki dangane da falon nan ?" Tana share hawaye tace " kace karna kara shigowa " " okay yanzun renine yasa kika shigo " cewar Mr azaad ja da baya tayi tana" kayi hakuri Mr azaad bazan sake ba" Inbanda salati babu abinda yaseer yakeyi aranshi dama abinda azaad yake aikatawa yarinyar nan kenan tabbas yasan azaad ze aikata haka koma abinda yafi haka amma dayaji shuru yayi tunanin yarungumi matarshi ne suna zaman lafiya ashe bahaka bane, kallon fanan yaseer yayi yace " zeki abinki" dagudu tashige cikin bedroom dinta dan gani takeyi kamar zebiyota yadaketa. _____ Maida kallonsa kan Mr azaad yayi dake danna wayarsa ko ajikinshi gyara zama yayi yace " yanzu dude abinda kake aikatawa dedene? dan Allah wallahi baka rike amana ba wannan karamar yarinyar inka azabtar da ita meye ribarka " kallon yaseer yayi yace" dama aina nace nakarbi amanarta? Laifi tamin shisa nake hukuntata tana gama karban punishment dinta kuma zan saketa " girgiza kai yaseer yayi yace" karkayi haka azaad wallahi fanan ba kamar sauran mata bace ! Koma me take maka kamata yayi kayi hakuri ko kamanta lokaci kadan yarage mata dazatama barmana duniyarmu takoma inda ake bukatarta haba dude kaji tausayinta mana zata tafi tabar kowa nata amma dukda haka kana wulakanta ta wallahi insu ummi sukaji bazasuji dadi ba" daga kafada sama yayi alamar I don't care kafin yace" tafiyanta dakuma rashin tafiyanta nifa duk bedameni ba tatafi har yaumu takumu karta dawo dan nima ba kaunar ganinta nakeyi ba cos she's like a burden to me! Abinda nasani shine intamin laifi zan hukuntata " yaseer gani yayi inya biyewa azaad yanzu zasu iyayin fada yasa yatashi yatafi abinshi. Yau Kwanan su Abba 5 da tafiya kullum insuka cewa Mr azaad yabawa fanan waya sugaisa ceyata basu uzuri, ummi de tanaji ajikinta kamar akwai abinda yake faruwa gashi wayarta yana hannunshi. " Mr azaad dan Allah kabarni yau inje gidanmu ko kuma kayi hakuri kakiramin mama awaya " idonshi alumshe kamar bayajinta tunani tafarayi kode bacci yakeyi sake nanatawa tayi nanma yayi banza da ita haka taci gaba da mishi magana harta gaji be kulataba yasa takoma bedroom dinta takwanta tana kukan halin data shiga , daga hannunta sama tayi tana adduah " yah Allah ina rokonka kakawo karshen zamana da wannan bawan naka dayake kuntatawa rayuwata ! Allah kabashi ikon rubutamin takardar saki yau zuwa gobe " haka tadinga adduah tana kuka...... Tom se mun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏 Masu comment damin adduah nagode sosai Allah yasaka da alkhari, kukuma da sede ku karanta kuyi shuru ba sannu bare Allah ya isa🤔 kallonku kawai nakeyi kowa yayi dede yasani . via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & Written by MRS 🌹 ISHAM 🌹 Page 3️⃣9️⃣ & 4️⃣0️⃣ Haka sukaci gaba da rayuwa acikin gidan daga ita seshi se yan aiki wahala babu irin wanda baya bata haka kurum zesata wankin manya_manyan bedsheets da blanket ga fada da tsawa gakuma maruka. Ana gobe su ummi zasu dawo taje tasameshi yagama shiryawa zefita office " Mr azaad inaso muyi magana " okay kawai yace , tadaura da " Mr azaad badanni ba kayiwa Allah daya halicceka kayi hakuri kasakeni bana kaunar zama dakai dede da dakika biyu banajin zanci gaba da zama dakai yanda ka tsaneni na tsaneka yanda baka sona haka nima bantaba sonka ba duk abubuwan dakamin na yafe maka ka sauwakemin intafi wajan iyayena sukadai ne nazama musu dole " ko kadan kalamanta basu bata mishi rai ba, hasalima tunda tafara magana yake kallonta babu ko kyaftawa yakafeta da wayan nan mayun idon nashi , gyara tsayuwarshi yayi ajikin kofa hannayenshi na harde akirjinshi yana kallonta murmushin gefen baki yayi yace " saurin mekikeyi haka base kinsake tunamin ba am aware kawai Jiran lokaci nakeyi " besake sauraranta ba yafice zama tayi akan kujera tana tunanin rayuwa anrabata da gidansu yan uwanta da kowa nata gashi farin ciki yakaurace mata, haka ta yini jiki asanyaye jitakeyi kamar bata da wani lafiya, sosai takejin sanyi nan take jikinta yabara barin sanyi bedroom tasamu tashiga takwanta taja bargo tarufe jikinta. Zazzabi me zafin gaske ne yariketa ko kwakwaran motsi bata iyayi tana kwance tun safe daya fita yabarta be dawo ba balle yasan halin datake ciki ko aikin dayasata bata samu tayi ba. Kwance take adaki se sakin murmushi kawai takeyi waya na manne akunnenta lumshe ido tayi giyar soyayya na dibanta murya anarke tace " hubby wallahi nayi missing dinka!katafi kabarni uhmm uhmm Allah inbaka dawo dawuri ba zanyita kuka kuma bazanci abinci ba haka zanbar kaina da yunwa" ajiyar zuciya fawwaz yasauke yana karajin tsananin kaunar suhaima nakara shiga ranshi besan wani irin so yake mata ba tariga da tazama wani bari na rayuwarshi yanzu sunriga dasun kamu da son juna, kara rungume pillow yayi yana fadin " am sorry baby nima nayi missing dinki fiyeda yanda bakya zato gobe zamu dawo" ihu tasa seda yacire wayar akunnenshi " hubby are you serious? " Dariya yayi dan suhaima itama ba laifi akwai dan sauran yarinta yace " in sha Allah baby gobe zamu dawo just pray for us kinji " nutsuwa tayi ta shagwabe fuska kamar yana gabanta tace " hubby kamin alkawarin kana dawuwa zakazo inganka " murmushi yayi yace " I promise Ina dawuwa ko gida bazan shigaba zanzo inga babynah " rufe fuska tayi tana kyalkyalewa da dariya " baby tsarabar me kikeso in kawo Miki?" Shuno baki tayi tace " hubby i want nothing than you kai kadai kawai nakeso " haka suka dinga zubawa junansu kalaman soyayya masu dadin gaske ( nida ba soyayya nakeyi ba gajiya nayi da hirar nayi gaba abuna karsusa in fusata) Yana zaune a office dinshi yana duba wasu files dinda sakatariya jamila takawo mai na sabobbin ma aikatan dazaa dauka ga faisal shima azaune yadukufa yana aiki a system, ringing wayarshi yayi yayi picking yasa akunne yana fadin " my sweet mom kuna lafiya ?" Abangaren ummi ta amsa mai " da lafiya Lau son yakuke ina fanan tunda mukazo kullum senace kahadamu amma abu yagagara! Kasiya mata waya kabata kasan badadi yan uwanta nason magana da ita sujita shuru" harga Allah seda ummi ta ambaci sunanta tukun yama tuna da ita dan kwata_kwata yamanta da lamarinta okay yacewa ummi sukaci gaba da hira kafin tayi hangup, system dinshi yakunna yashiga footage din gidan na CCTv camera, tun daga sa'ilin dayake gida be fitaba yashiga harzuwa lokacin datashiga daki takwanta around 10:00 besake ganin ta motsaba haryanzu duba time yayi yaga 4:00pm mamakine yakamashi ganin harzuwa time din tana kwance tunani yakeyi ko bacci takeyi sekuma yatuna duk baccin dazatayi seta tashi tayi sallah amma yau shuru ko breakfast batayi ba. Basarwa yayi yaci gaba da aikinshi can kuma yamike yayi switching din system din daukan jacket din suit dinshi yayi. faisal ganin oganshi yatashi yasa yamike yadau briefcase dinshi suka fice tada motar driver yayi dayaga sunfito shiga sukayi suka nufi gida , direct bedroom dinta yashiga yasameta kudundune acikin bargo numfashinta nafita sama_sama batama san yaye blanket din yayi yasa hannu taba jikinta dasauri yacire jin zafin daya dauka daukanta yayi yakaita bedroom dinshi , lalubo wayarsa yayi yakira doctor ammar, within 20mnt doctor ammar yashigo shikanshi yasha mamaki ganin fanan awannan yanayin ga ciwo datake fama dashi , kallon Mr azaad yayi yace " amma tadade tana ciwo ne Koh?" Amsa yabashi da " I don't know" jin haka yasa besake mishi magana ba yafara bata taimakon gaggawa yadaura mata drip yayi mata allurai " ga magungu nanta tana farkawa tasamu tasha abu me dumi like tea setaci abinci kafin tasha magani Allah yabata lafiya " yatabi yabarshi zama yayi agefenta yana kallon beauty face dinta dayayi fayau sa hannu yayi yana shafa gashin kanta daga bisani yakoma kan cusion yazauna. ______ karfe 8 ruwan yakare cire mata drip din yayi yana kokarin cire calular , ahankali tafara bude idonta dasuka mata nauyi dishi_dishi take kallon fuskanshi harta fara ganin komai clearly fisge hannunta tayi daga nashi takoma can kuryan gadon ta dukunkune awaje daya tana " Mr azaad kayi hakuri dan Allah karka dakeni kaina ne yakemin ciwo amma yanzu zanyi aikin kayi hakuri kamin rai bazan sakeba" haka tadinga sambatu tana bashi hakuri, jikinshi ne yadanyi sanyi hawa gadon yayi yanufeta ganin tunkarota yakeyi duk tunaninta dukanta zeyi ko yamata tsawa yasa ba shiri tasauka akan gadon zata gudu jirine yafara dibanta tayi tangal_tangal zata fadi yatarota tafado jikinshi muryanta dabaya fita tace " Mr azaad kabarni intafi dakina" tana magana manyan idonta na lumshewa dagata yayi yamaida ita kan bed din sannan yadanna line din gidan wanda in aka kira masu aiki zasu daga , dagawa abu me aiki tayi umarni yabata data shirya abinci da tea yanzu takawo part dinshi aikuwa haka akayi , bata jima ba tazo tayi sallama jin muryanta yasa yaje yakarbo tana zaune atsakiyar gado tana binshi da ido ita haryanzu gani take kamar ze mata wani abun dan batayi abinda yasata ba . Sa tea yayi acikin cup yamika mata karba tayi tafara sha kadan_kadan hartasha fiyeda rabi taji dadin shan tea din sosai ajiye cup din tayi akan bedside table , food flask yabude jallof din arish potato ne dayasha kifi banda da vegetables diba yayi yadawo gabanta , zefara bata kai mata spoon din yayi zebata abaki taki bude bakin se kawai kallon mamaki datake binshi dashi tafara tunani aranta anya Mr azaad ba poison yasa mata acikin abincin ba kuwa abinda betaba mataba yau shiyake mata. Ganin taki bude bakin yasashi kara tamke fuska yana watsa mata uwar harara bashiri tabude bakin haka yadinga feeding dinta hartace ta koshi maganinta yamiqa mata tasha nan take tabara bata fuska zatayi kuka , lura yayi da kwata_kwata bata kaunar magani hakan yasa yajika maganin a cup yamatseta kamar wata yar jaririya yamata dúre dakyar tasha kokarin amayar da maganin take fuska ahade yace kina amar dashi adaren nan zanbaki hakkinki , aikuwa ba shiri tamaidashi. Kara daukanta yayi yashiga toilet da ita yadireta akasa yafice ,cire rigar jikinta tayi tana kokarin hanging dinshi yafada acikin jacuzzi cireshi tayi ta ajiyeshi a gefe wanka tayi tare da alwala rasa yazatayi tafito tayi iya towel ne a toilet din gashi kayanta din ruwa yajiqashi tafi mint goma tana tunanin mafita daura towel din tayi tafito, godewa Allah tayi dataga baya dakin hanyar fita tanema, harta kusa bakin kofa yafito daga dressing room hannunshi narike da jallabiya. Idonshi ne yasauka akan kyakyawar surar da Allah yamata , kasa motsawa yayi sebin shape dinta da kallo yake musamman hips dinta dasuke acike masha Allah mamaki yafarayi dama wannan yarinyar haka ainihinta surarta yake ga brest dinta da rabinsu suka fito waje aranshi yace" how could that be possible yarinya da jikin manya?" Ganin irin mayen kallon dayakebin jikinta dashine yasa tayi saurin murda handle din dakin tafice tafada bedroom dinta tasamu tasa doguwar riga da hijab ta tada sallah , duk sallolin da akebinta seda tayisu kafin tasa kayan bacci jikinta bawani karfi sosai ta kwanta. Shikuwa gogan naku gaba daya kasala ce tarufeshi lokaci daya barinma inya rufe idonshi yahasko mishi hoton surarta ,haushin kanshi yafaraji taya zetsaya yana tunanin wannan karamar yarinyar da ko cikekken hankali bata gamayi ba. Karfe 1:00 na rana jirgin su abba yayi landing,Mr azaad damasu tsaransu ne sukazo tarbansu fawwaz de car key kawai yakarba dan beda burin daya wuce yaje yacika alkawarin daya daukawa babynshi . Duka suna zaune afalo ummi tace " son ina feena ?" Yana danna waya yace " tana bedroom " "okay jeka kirata " tashi yayi tahaura upstairs din afalo yasameta tana yar goge_goge, kallonta yayi up and down kafin yace " ummi nakiranki afalo " cike da Al ajabi take bin bayanshi da kallo wato su ummin sundawo shine baze fada mata ba lallai Mr azaad. Dama doguwar rigar abayace goldin color ajikinta komawa bedroom tayi tasa gyale me girma tasauko. Tun kafin ta iso gaba ki daya mutanen falon hankalinsu yakoma kanta ganin yanda lokaci daya tayi uwar rama sosai suke kallonta, tashi zeenat tayi suka rungume juna cike da murna tukun suka karasa falon duqawa tayi tagaishesu amsawa sukayi suna kallonta, zama tayi abinta akan lallausan carpet din falon , Abba ne yakalli Mr azaad yace " meyake damun fatima? datayi wannan ramar haka azaad?" Kallonta shima yayi yana neman ramar da akace tayi bayan ko ina najikinta acike bulbul. Shuru yamusu dan besan amsan daze bayarba tunda shide bega wata rama ajikinta ba, girgiza Kai abba yayi yakalli fanan " Fatima meyake damunki kika rame haka kode azaad yana miki wani abune bayan tafiyarmu?" Satan kallonshi tayi taga ko ajikinshi wayarsa ma yake latsawa abunshi , murmushin yaqe tayi tace " Abba babu abinda yakemin kawai de kwana biyu ne nayi rashin lafiya " ran ummi yabaci dajin haka domin kullum sesunyi waya da Mr azaad kuma seta tambayeshi ya fanan take yace mata" lafiyanta Klau" ashe baiwar Allah tana nan tana fama da ciwo amma dan bakin hali irin nashi yaki sanar da kowa. Dago kai yayi suka hada ido da ummi dake doka mishi harara sunkuyar dakai yayi dan yasan dalili. ______ Rai abaci abba yafara magana " yanzu kai azaad ka kyauta kenan matarka bata da lafiya kusan kwana biyu amma baka taba fadawa kowa ba! Sannan kabata wayarta ko kasiya mata wani abu yagagara kullum semun ce kahadamu da ita amma ka kasa to ka kiyayeni kaduba yarinya duk tabi ta lalace kamar ba itaba " shide ko uffan bece musu ba saboda shibega abinda suke magana akai ba daga karshema tashi yayi yabar musu gidan , aranar kam fanan tahuta se lallabata sukeyi kamar kwai da dadin baki ummi take samu tama fanan wayo tasha magani har goma suna hira , jitayi kamar ta cewa ummi zata kwana apart dinta amma inta fadi haka zasuyi zargin wani abu tanaji tana gani sukayi sallama tawuce nasu part din. Bari muleka Romeo and Juliet Girki suhaima tayi mishi me ji da lafiya taci ado suna zaune suna sunashan hiran love Yanacin abinci se shagwaba takeyi mishi , bakaramin gigitashi takeyiba intana wannan shagwabar haka sukasha love dinsu ya ajiye mata tsarabanta tarakashi har bakin motar shi yatafi. Komawa gida tayi tadauki fashion bag din daya ajiye mata tashiga dakin mama tanuna mata budewa tayi dogayen ruguna ne masu shegen kyau yan dubai da sarka da dankunne na gold se zobe, murmushi mama tayi tace " ohhh su suhaima anyi saurayi " kunya taji yarufeta tarufe ido suna dariya , " tun jiya babanku yace inbada miki ki mishi magana inde da gaske yake auren zeyi yafito" cike da kunya tace " to mama zan fada mishi". Haka rayuwa taci gaba da tafiya yau yakama 1 month dayin auren fanan da Mr azaad, yana nan yana mata abinda yagadama wata rana yasata aiki wata rana kuma kota kanta bayabi, tun su ummi basu farga ba har suka fara fahimtan wani abu wani lokacin fanan setafi kwana biyu bata sauko downstairs ba kuma baya taba yarda wani yaje ciki ,sanda ze barta kuma se inzaayi dinner gaba daya tacanza, kuma komin tambayar dazasu mata amsa daya take basu shine " bakomai bayamin komai" ummi ce ta siya waya iphone 14 pro max tabawa fanan da sim taloda mata kati da data aciki,tacewa Mr azaad saura kuma kar inganshi ahannunta, tanan ne fanan tafara samun saukin wasu kayan bakin cikin kullum setayi waya da yan gidansu, suhaima da amira,auta sunzo wajanta harso biyu suma sunyi mamakin yanda takoma wata shuru_shuru da ita . Alhamdulillah su Abba da yan uwansu sunje sun tambayawa fawwaz auren suhaima kuma anbasu ansa date nan da wata hudu zaayi ( tom Romeo and Juliet ankusa angoncewa kenan Allah yakaimu musha biki) Ayau ne ranar asabar akatashi da wani irin gagarumin tashin hankali agarin gombe sakamakon ganin gawawwakin yara da manya , maza da mata ancire wasu sassa najikinsu anyi ritual dashi( tsafi) ansamu gawawwaki kusan 30 lamarin yadagawa mutane hankali kowa yanutsu da iyalanshi agida , jami'an tsaro se bincike sukeyi akan case din daga zaran yaro yafita haka zaa daukeshi baze dawoba sede aji labarin antsinci gawanshi. Wannan aikin bana kowa bane face kungiyar SATANIC and BAPHOMET dasuke ritual domin yakar junansu domin duk wanda yayi nasara akan daya shize kwaci jaaazana haka suka dinga tsafi da mutane da basuji ba basu gani ba ,babu ruwansu dakoma waye yafita kana yin waje zaa daukeka cakk shikenan kuma katafi, wannan dalilin yasa akasa lockdown agombe. Duk suna gida suna jin abinda yake faruwa Abba yace karwanda yafita, dukkansu suna zaune afalo sunata kallon labaran da akeyi . Bangaren mommy kuwa tun ana kwana biyu zaa fara ritual din abin duniya yadámeta gashi bahalin zuwa ayi da ita dan haryanzu bata warke ba tanata kan jinya dan tasan dataje anyi da ita tasan dole tanzarzar yakara mata matsayi. Jikin fanan ne yafara wani irin kadawa kamar wacce akasawa shocking , nufanta sukayi cikin tashin hankali ,riqeta gam azaad yayi duk jijigan datakeyi tana jikinshi yaki saketa can kuma seta dawo normal, kallonsu tayi gabaki dayansu tana zubda kwalla tace " shin akwai abinda ake boyemin ne daban sani ba? Kufadamin jinake kamar zanmutu yanzu inbanji ba wayyo Allah na" takarashe maganar da karfi tana rike kanta da yasara mata tabbas abu takeso ta tuno amma takasa sede yadinga mata flash, duk shuru sukayi sun rasa abin fada shin yau ne fanan zatasan ko ita wacece? Kokuma yau ne zatabar duniyarsu? gaba daya tambayar dasukewa kansu kenan. Areef ne sukaga yaje gabanta yazube akan guiwowinshi kanshi akasa , nan ne jikinsu yasakeyin sanyi domin sunsan tabbas wannan ba areef bane. Cike da mamaki takalleshi ganin yadúrkusa agabanta goge hawayen fuskanta tayi tace" ya areef Meye haka ?" Girgiza kai yayi cikin muryan daya manyanta " yace sarauniya ba areef bane! Sunana abdud Shakur nine galadiman masarautar nasminaya! Nazo ne domin in amsa miki tambayoyinki sannan insanar dake ko kedin wacece....... Hakikanin gaskiya inajin dadin adduah dakukemin dakuma comments dinku it means alot to me, wallahi ina matukar kaunar ku sosai Allah yabarmu tare daga nan har gidan aljanna 🙏😘😍, ku Kuma masu karantawa kuyi shuru ba sannu balle Allah ya isa kallonku nakeyi kawai kowa yayi dede yasani amma zaazo time dinda mutum in yaganshi awaje karyaga laifina domin nima mutum ce ba engine ba. Se munhadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏. via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & Written by MRS 🌹 ISHAM 🌹 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION ✍️✍️ Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum iname mika sakon taaziyata ga alhalin anty hadiza salisu sharif dakuma marubuta da kowa gabaki daya, Allah Ubangiji yajikanta da rahama, Allah yasa tahuta , Allah yakai haske kabarinta ya yafe mata 🙏🥺 Allah yasa innamu yazo mucika da imani da kalman shahada , Allah yagafarta mata 🙏🙏 Ameen ya hayyu ya qayyum. ꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁ Page 4️⃣1️⃣ & 4️⃣2️⃣ Fa ra bata labarin tun daga lokacin da take ciki har zuwa haihuwarta da kuma abinda take dauke dashi a jikinta da yakar kungiyoyin kaff seda ya fada mata sannan yakara da " labari mara dadinji shine! gaskiya sarauniya a ko wani irin lokaci za ki iya tafiya domin yawan rashin adalcin da akeyi yana kusantoki! Jaaazana nakara bayyana a jikinki , duk inda aka samu irin wannan bar nan ya afku sau uku nan take zaki koma masarautar ki , ko da kuwa kin shirya ko baki shirya ba yanzu de anyi biyu ina tunanin saura daya". Takasa cewa komai se hawaye da kuma murmushin datakeyi atare lokaci daya , Tabbas masarautar take gani yana mata flash dakuma sarki abdud daar ashe itadin shugaba ce dazata kawo gyara . Se yanzu take jinta cikakkiya amma dà se ta dinga jinta kamar akwai abinda ta rasa ,kamar ta rasa wani bàri a tare da ita amma yanzu da tasan ita wacece se taji duk wani gurbi yacike, Duk suna jira suka reaction dinta ya zataji intaji wannan labarin, abinda basu taba zata ba tayi sujjada tayi ta daga hannunta sama tana yiwa Allah godiya " Allah nagode maka dakasa nazama zabàbbiya ! tabbas zanyi aiki da duk wani wani karfi danake dauke dashi domin kare rayukan al'umma daga jinsin bil adama harzuwa jinni koda kuwa zezama sanadiyar rai ne , Allah kasa ta dalilin haka in zama me rabo a aljanna " amma data tuna za tabar iyayenta da duk wayanda ta sani se taji gaba daya duniya bata mata dadi. Kallon Abdud Shakur tayi dake jikin areef tace " inson magana da kai sirri" dago kai kawai yayi ya wuro iska a bakinshi yace " sarauniya za ki iya maganarki ayanzu babu wanda zeji me muka tattauna " kallon yan falon takeyi dan ta tabbatar yasa tace " zeenat kinaji ?" Shuru zeenat bata mata reply ba sede ta bita da ido . Su kuwa su abba kallonsu kawai suke suna magana amma basajin abinda suke fada azaad de ya kafe bakinta da ido dansan gane abinda zata fada, gam yarike yanda bakinta yake motsi amma yagagara seta kalmomin. Suna gama maganar abdud Shakur ya fita daga jikin areef, tashi areef yayi dan besan meyafaru yace " antynmu yanaga kamar hawaye kikeyi wani abu yafaru ne?" Girgiza mishi kai tayi tace " babu abinda yafaru ya areef" "okay" yace tare da wucewa part dinsu . murmushi kawai takeyi da gaba dayansu sun rasa gane na miye , tabbas samun irinsu fanan acikin al'umma abune dazeyi matukar wahala awannan duniyar koda kuwa akwaisu zasuyi wahalan samu sannan basuda yawa , ta yarda zata sadaukar da rayuwarta akan yakar azzalumai bata damu ta mutu ko ta rayu ba farin ciki ma takeyi da hakan akan shahadar da zatayi . Jikinsu ya mutu sosai nan take tun kafin lokacin tafiyar ta yayi harsun fara kewarta , shikanshi Mr azaad seda yaji ba dadi part dinshi yatafi yabarsu afalon, lura fanan tayi baya falon yasa itama tabi bayanshi, zama sukayi duk basa cikin dadin yanayi kiran baba abba yayi ya sanar mai da fatima tariga da tasan ita wacece , murmushin takaici kawai baba yayi ranshi na kuna yace " alh nariga da nasan wannar ranar na nan zuwa na sawa zuciyata dangana kullum kokarina in kwantar wa mahaifiyarta hankali ! Nasan yau inde taji labarin abinda yafaru hana kanta sukuni zatayi" haka sukata jinjina lamarin cikin rashin jin dadi amma babu yanda zasuyi sede sumata adduah Allah yabata saa a abinda zatayi yakareta daga sharrin wayan nan mugayen azzaluman. bedroom dinta tashiga takwanta tana tunanin tafiyarta nan take ta tuna wani abu tasa zuruf ta mike. Toilet tashiga tayi wanka ta wanke gashinta da shampoo's masu dadin kamshi, koda tafito she didn't bother to dry it gogeshi kawai da towel tayi , tunawa da shawarwarin da anty amina tabata tayi , killer smile ta sake daya fito mata da kyaunta ta bude tankamemen wardrobe dinta , one by one take bin kayan dake lode aciki da kallo ,sauka idonta yayi akan bangaren wasu tsinannun kana nan kaya, tun kafin ta dagosu kunya yakamata taya zatasa wayan nan kayan taje gabanshi , dubawa takeyi hartazo kan wani yar iskar riga da ita da babu duk daya daukoshi tayi ta dagashi sama tana kare mai kallo daga sama har kasa , gallawa kayan harara tayi sekace shi yace ta dauko shi . tafi minti 5 tana tsaye tana juyashi rigar kalanshi sak da wayanda karuwai suke sawa, wurgashi kan bed tayi tadau wayarta tayi dialing number anty amina dagawa tayi tana " assalamualaikum my feena kina lafiya?" Zama tayi a gefen mirror ta amsa sallaman tana tambayarta yasuke da junior kafin tadaura da " am! am anty amina dama maganar da mukayi kwanaki ne to yanzu kuma.....uhmmm " kasa karasawa tayi jin kunya yakamata, anty amina ta rigada tasan inda maganar ta dosa ,kunya ya hanata fada , yar dariya tayi jin yanda fanan take in da in da takasa fadar taka memen abinda yasa takirata " calm down my feena kidena jin kunyata kifadamin duk abinda kikeson fada se munsan yazaayi ko?" Sosa wuyanta tayi tarufe idonta kamar anty aminar na gabanta tace " dama zanje wajan Mr azaad ne tom kamar yanda kikace inde inaso muja hankalinshi da wuri dole se inasa kana nan kaya dakuma sauran abinda kikace" sosai anty amina taka sa kunne tana sauraranta cike da jindadin yanda fanan ta shirya karban shawaranta sannan tace " ci gaba ina jin ki " sake runtse ido tayi ta daura da " tom nayi wanka na dauko wata riga wallahi anty amina baki gantaba kamar irin wayanda karuwai sukewa rigar fah yar iska ce sosai" ta karishe maganar tana dan fito da dara_daran idonta . Dariya anty amina ta keyi sosai jin abinda fanan ta fada wai rigar fa yar iska ce sosai hhhhhh, tsaqaitawa tayi da dariyar tukun tace " wallahi my feena za ki kashe mutum da dariya ! duk yanda rigar take karki damu kisata ahaka sannan kuma................." tasake fada mata wasu abubuwan da nikaina banji ba . bayan sungama wayan ne taje gaban mirror tazauna ta shafa lotion masu tsada da dadi , tayi usual make up dinta, daukar rigar tayi tsaban yanda yake da yanka_yankan tsagu ajikinshi ta rasa ma ta ina zata sashi haka tafara gwadawa dakyar tasamo kan rigar . Kallon kanta tayi a mirror zaro ido waje tayi ganin yanda rigar tamata , guntuwar rigace roba yana yalki red color du ka tsayin rigar da kadan yawuce Santala_santalan cinyoyinta da suke glowing gefen hagu na rigar tundaga hannu har inda rigar ta tsaya tsagu_tsagu ne manya ana kallon fatarta awaje yana da dogon hannu se wuyan rigar daya kasance me fadi sosai open shoulder kenan dukiyar fulaninta duk suna waje rabi ne aciki ya matseta sosai duk wani structure dinta seda yafito fili , ga lallausan chocolate fatarta awaje , inde tayi kwakwaran motsi jikinta seya motsa , seyanzu nikaina na sake mata kallo sune ainihin matan da ake kira masu shape din coca-cola, juyawa tayi tasake kallon kanta a mirror slice smile tayi tace " Allah yashiryeni" hills black color tasa tafeshe jikinta da wasu irin daddadar tururuka masu sanyin kamshi , gashin kanta be gama bushewa ba sunyi wara_wara nan ne takara fitowa very sexy, tsayawa fadar kyaun datayi bata bakine , wani taku takeyi step by step cike da nutsuwa take tafiyarta , yanda body ta ke juyawa dakanshi wani zeyi tunanin da gangan ne amma ita kanta batasan sunayi ba . ___ kitchen ta nufa ta hada mishi coffee ta daura cup din akan plate dinshi. Tsayawa tayi abakin bedroom dinshi tare dayin knocking "come in " kawai yace shigowa tayi hannunta na rike da plate din coffee din , tun bayan shigowarshi part din yazauna kenan faisal yakirashi bayan sungama wayar ne yashiga toilet yayi wanka yafito daure da towel akugunshi yana digar ruwa yasamu waje yazauna zeduba sakon da faisal yace yatura mishi a email kenan tashigo , batare da ya dago ya kalleta ba yace " how can I help you?" Shuru tayi bata bashi amsa ba tana bin surar jikinshi da kallo babban abinda yake daukan hankalinta kenan atattare dashi murdadden jikinshi da kuma faffadar kirjinshi dake dauke da kwantaccen suma. Jin shuru ba amsa ne yasa yadago yakalleta lokaci daya yayi suman zaune sanadiyar cin karo dayayi da yarinya me jikin manya lolx, tun daga yatsun kafarta yake binta da wani slow motion look har zuwa fuskar ta , koda kwakwaran motsi yakasayi inbanda kafeta da sexy eyes dinshi dayayi nan take idanuwanshi suka canza kala har lumshewa sukeyi , murmushin cin nasara takeyi domin babban burinta shine tayi galaba akanshi dan tacinma burinta da takeson cimma in harde Mr azaad yafada wannan tarkon komai zezo da sauki, karasawa tayi gabanshi ta duqa ta ajiye mishi coffee din ,hango dukiyar fulaninta yayi suna mishi kwalele dake batasa bra ba , sosai ya rude yana binta da mayen kallo juyawa tayi zata tafi yasa hannu yafisgota tafado jikinshi, bin cute face dinta yakeyi da kallo babu ko kyaftawa . Shafa fuskanta yayi kafin yace " so bakiji warning din da na miki bako ? Shine kika dawo da wannan salon right? tunda naga abinda kikeso kenan yasa kika kawo kanki well bari in taimakeki " cike da kissa tayi farí da ido tace " to ai abinda nakeso din kenan shisa nakawo kaina " yanayin yanda ta kashe murya take magana bakaramin tafiya tayi da imanin shi ba, maida gashinta yayi gefe daya yasa kanshi a wuyanta yana shakar kamshin dake tashi a jikinta , se shinshinta yakeyi turaren da tasa yadada tada mishi da hankali tallafo habarta yayi ya hade bakinsu waje daya yafara bata hot kiss, kashe wutar dakin yayi yabar iya bedside lamp shima me multi color dakin yagaurayi da different colors of light se yakara kayatarwa , mayar mishi da martani takeyi sosai hakan yakara susu tashi ,zame rigar jikintan yayi yafara shafa dukiyar fulaninta dasuke birkita mishi lissafi ita kuma ta cusa hannunta atsakiyar gashin kanshi tana shafawa hade da mishi tafiyar tsutsa so take kawai yaje inda take jira dukda tana dar_dar amma she has no choice dolene hakan yafaru. Sosai Mr azaad yayi wasa da ita seda yaji hankalinshi yadawo jikinshi sannan ya kyaleta koda wasa beyi gigin yin sex da itaba saboda yasan abune mawuyaci ta daukeshi, tana kwance ajikinshi suna cikin bargo tana baccin wahala jikinta gaba daya ciwo yake mata dan ya jagulata ne son ranshi musamman ma dukiyar fulaninta yafi ko ina shan wahala , amma hakan be dameta ba saboda kudirinta aranta yanzu shine tasamu ta cimma abinda tasa agaba burinta seya kawar daduk wani tsoro atare da ita. Mannata yayi ajikinshi yana kallon sleeping beauty face dinta intana bacci kara kyau takeyi ganin ta turo bakine yasa yayi murmushi ahankali yafurta " stubborn girl" tunani yafara yanda fanan take tsoronshi yau shine takawo kanta batare data nuna wani fargaba ko tsoro ba tabarshi yayi yanda yaso da ita tabbas akwai abinda take shiryawa amma koma menene seya gano , tashi yayi yashiga toilet yayi wanka yafito yasa kayan baccinshi daukanta yayi yadireta acikin jacuzzi ware idonta tayi da bacci ke cike aciki ganin sa tsaye akantane yana kare mata kallo yasa tayi saurin kallon jikinta ganin bakomai ajikinta ne yasa takare kirjinta da du ka hannunta murya a shagwabe tace" wayyo nikam kafita inyi wanka " fita yayi yabarta tayi wanka tafito daure da towel, yana tsaye yaga fitowar ta duk tunaninshi bedroom dinta zata tafi with his surprise yaga ta dàle gado ta kwanta ko kaya batabi takanshi ba taci gaba da baccinta girgiza kai yayi shima yahau gadon ya kashe light din dakin yabar bedside lamp jan bargo yayi yarufesu......... Semun hadu ran Monday inme duka yakaimu da Rai da lfy masuyin comment Allah ya suburbuda muku albarka🙏🙏🌹 I love you so much. via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 🔔 📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚 Page 4️⃣3️⃣ & 4️⃣4️⃣ Tunda sukayi sallar asuba suka koma bacci karfe 10 fanan ta tashi daga bacci tsareshi da ido tayi tana kallon yanda yake bacci he looks innocent kamar ba ruwanshi sosai ta shagala da kallonshi murmushi ne ya subuce daga fuskanta hannu takai zata shafa fuskanshi ya dan motsa da sauri ta janye hannun baya ahankali ta furta " Mr azaad zanso ka cikamin burina a yan kwanakin nan amma naga you're very arrogant dole senayi sena cusa maka hakan a ranka " ta karishe magana tana kallon body packs dinshi bargon da yake rufe dashi ya yaye time din data tashi sexy body dinshi awaje ,sauka idonta ya yi akan nipples dinshi dasuke ja sosai ga wasu kana_kanan gashi sun zaga nipples din murmushi tayi tace" kana da kyaun fuska kyaun jiki da sura tako ina ka hadu amma de kyaun hali ya maka wuya " sulalewa tayi ahankali daga dakin dan karta tasheshi daga bacci tashiga nata bedroom din wanka tayi hade da kwalliya tasaka wando pencil crazy blue color tasa riga fara da kadan yarufe mata cibiya me guntun hannu gaban rigan akwai hoton teddy , lallausan gashinta kuma ta rabasu gida biyu ko wanne tasa mishi ribbon ta tubke , seta fito kamar slay queen , takalmi me yar tudu tasaka kallon kanta a mirror tayi taga tayi kyau sosai wayarta dake bedside drower tadauka tafara selfie , tayi sunfi kala goma kafin tabari zama tayi tana kallon hotunan, murmushin dake kara mata kyau tayi dan duk hotunan sun mata kyau , tunawa tayi da Mr azaad a ko wani lokaci ze iya tashi daga bacci yasa tayi saurin ajiye wayar tanufi kitchen. Simple breakfast ta hada musu ta jera a dinning table, aranta tace " anya wannan Mr arrogant din ze yarda yaci ma kuwa?" da wannan tunanin tashiga bedroom dinshi har time din yana bacci be farka ba , zama tayi a bed din ta sunkuyar da kanta har kumatun shi ta sake mishi fresh kiss a kumatu , ahankali ya fara bude wayan nan rikitattun idanunshi dake rikita mata da kuma razana abokan gaba, kallonta yayi yana mamakin sudden change din datayi jin kiss din data mishi wanda yaji tundaga tafin kafarshi har tsakiyar kanshi. _____ sunkuyar dakai kasa tayi dan bazata iya kallon cikin idonshi ba dan yanzu zasu rikitata , yasa tayi kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Se yanzu ya kalli dressing din jikinta, kyau tayi mishi aranshi yana fadin " yarinya me jikin manya komai tasa yana fitting dinta" kafin afili yace " me yakawo ki bedroom dina?" langwabe kai tayi tana yatsina fuska tace " Mr azaad I made some breakfast shine nazo tashinka muje muyi" tana magana tana jujjuya kai gefe da gefe kamar wata karamar yarinya, yanayin yanda tayi yaso bashi dariya se yabasar, tsareta da mayun idonshi sannan yace " dama tare mukeyi ne! Ko duk cikin shirin kine?" Satan kallonshi tayi jin abinda yafada tunani tafara anya wannan ba aljani bane kuwa daburcewa tayi ta rasa amsar da zata bashi , hakan datayi ne yasake tabbatar mishi da zarginshi ya tabbata, tabbas akwai abinda take shiryawa wanda ita kadai tabarwa kanta sani se Allah. tashi yayi ya zauna riko hannunta duka biyu yayi yana matsawa kadan kadan " ki kalli cikin idona fanannnn " cike da al ajabi da mamaki take kallon nashi jin yafadi sunanta , bata taba jiba ko da yaushe sede yace mata kee amma baya kiran sunanta duk tunaninta besan sunan bane, se taji yanda yafadi sunan da wani irin style ya burgeta jitayi shikadai ne ya iya fadan sunan , kyasta mata yatsunshi yayi afuska ganin ta tafi duniyar tunani, kallonshi tayi hade da sakin murmushi me tafiya da zuciya , "ya salam" yafurta aranshi yarasa meyake damunshi da yarinyar nan kwanan nan ya lura inbeyi a hankali tabbas zata iya galaba akanshi dukda yanada yakini abinda take shiryawa bawai mugun abu bane . Matsa hannunta yayi kadan yar kara tayi hade da turo dan bakinta gaba tana kunkuni , zaro ido yayi yace " ni kike zagi ?" Tashi tayi zata gudu dan taga sharri yakeson mata wai ta zageshi , maida ita yayi tazauna hade fuska yayi yace " ina zakije kuma?" ganin fuskanshi yakoma na ainihin Mr azaad ne yasa murya asanyaye tace " babu " " fanannnn ! meyasa kikeson sa rayuwata a cikin hadari? ko dan saboda abinda na mikine yasa kikeson ramawa ta wannan hanyar ? shin kina ganin hakan zesa ki huce ne? Kinsan tafiya zakiyi shine kikeson azabtar da rayuwata? kinason nasha wahalar inkin tuna kinsani awannan halin zakiji dadi ko? " Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara zubowa daga idonta dama tasan dole se yayi tunanin hakan kancewa ramuwa takeyi bayan babu hakan aranta , tashi tayi da gudu tafita a dakin tana kuka , ajiyar zuciya ya sauke shi kadai yasan yanda yakeji toilet yashiga yayi wanka. fadawa kan gado tayi tana kuka me ratsa zuciya afili take fadin " Mr azaad wallahi bantaba rikeka azuciyata ba balle inyi tunanin rama abinda kamin taya mutum ze cutar da abinda yakeso Mr azaad ina sanka bazan taba barin wani ya cutar dakai ba balle ni dakaina ya Allah ka kawomin sauki cikin raina " . Yana tsaye abakin kofan bedroom dinta duk wani abinda tafada akan kunnen shi idonshi sun rine sosai yayi ja da karfi zuciyarshi yake bugawa be bari tasan da yana wajen ba yakoma bedroom dinshi zama yayi akan kujera jikinshi duk ya mutu dafa kanshi yayi da ke sarawa kamar ze fita babu abinda yake furtawa aranshi in banda " innalillahi wainna ilaijiraji unnn na cutar da baiwar Allah da take sona! bansan menene so ba amma zanyi iya kokarina in kyautata mata kafin tabar duniyarmu " haka yata saqe_saqe aranshi cikin kankanin lokaci ciwon kai yasauka mishi . Haka suka kai har azhar batare da sunci komai ba ita tayi zatan baya nan yafita ne tayi sallah ,ta canza kaya izuwa riga wanda tsayinshi ya wuce guiwanta yanada fa di light green, falo tafito ta gyara ko ina tasa burner yana fitar da kamshi me dadi bedroom dinshi tashiga saboda tagama gyara ko ina saura nashi , akan kujeran tasa meshi yana zaune idonshi alumshe kauda kallonta tayi daga kallonshi tafara gyara bedroom din ya saura kan kujeran tsayawa tayi nesa dashi tace " Mr azaad zangyara kujeran" shuru yamata bece mata ka la ba tayi magana yafi baki biyar amma shuru tunani tafara kode bacci yakeyi , har zata juya tafita saboda karta tasheshi daga bacci taga ya miko mata hannu alamun takama, batare da tayi tunanin wani abu ba tarike hannun tana kokarin janshi yatashi, tadage se janshi takeyi ko motsawa beyiba bare yatashi haki takeyi kamar wacce tayi gudun tsere harda hada zufa. Jawota yayi tafado jikinshi ya rungumeta muryanshi baya fita yace " patient dinki yana bukatar special care bayida lafiya" sa hannu tayi ta taba jikinshi tabbas bayajin dadi kamar zazzabi ne yakeson rufeshi jikinshi yayi zafi, amma dazun kuma lafiyarshi kalau , kokarin tashi takeyi dan ta dubashi yasake rungumeta sosai kamar wani zekwaceta murya anarke yace " karki tashi ina bukatar dumin jikinki atare dani" yanda yake maganar kamar yana mata rada. Tausayi yabata kamar ba Mr azaad ba hakan yasa tasake jikinta dashi shishigewa jikinta yakeyi sanadiyar warm temperature nata se yaji yana jindadin kasantuwar su a haka , ta takura sosai ayanda suke kujeran ya musu kadan gashi runguman daya mata ba karamin runguma bane , dede kunnan shi tace " Mr azaad kirjina ze balle " saketa yayi yana kallonta da sexy eyes dinshi yace " yunwa nakeji " kyaf_kyafta ido takeyi tana kallonshi dan yamata bazata batayi tunanin haka awajanshi dan so take ta tabbatar ko mafarki takeyi ko kuma da gaske ne, yasan mamakine yahanata magana yasa yasake maimaita " yunwa nakeji" tashi tayi da hanzari tashiga kitchen tayi fast food noddles ta dafa ta soya kwai tajuye a plate kaiwa bedroom din tayi ta ajiye saman center table ta koma kitchen tadauko drinks da ruwa , yanda ta tafi ta barshi haka tasameshi bata zauna ba se tadauko mishi magani ta ajiye komai akan table kafin tace " Mr azaad katashi nadafa maka noddles saboda yafi wuri" " okay" yace tare da mikewa ya zauna nuna mata kusa dashi tazo ta zauna, faracin abincin yayi seda yaci kusan rabi kafin yakai bakinta ze bata dan yasan itama bataci abincin ba make kafada tayi tana " uhmm uhmm " tamke fuska yayi yace " Ina wasa dake ne ?" ba shiri ta bude bakinta yafara feeding dinta har yakare yabata ruwa , fanan de yau gaba daya Mr azaad gani takeyi kamar ancanza shi sewani lallabata yakeyi sau daya kawai ya kalleta yadau magani yasha dan yasan abinda ke ranta. Toilet yashiga yadauro alwala ya shinfida sallaya adaki yayi sallah azhar yau kam yayi missing jam'i . tana zaune akan kujeran babu abinda takeyi banda binshi da kallo duk abinda yayi kyau yake masa takasa janye idonta akanshi dago kai yayi suka hada ido yar harara yawurga mata yace " banason yawan kallo gudun kar acinyeni " dariya tayi jin wai gudun kar acinyeshi , shagala yayi yana kallon yanda dariyan yakara mata kyau , ganin irin kallon dayake mata ne yasa ta tsagaita da dariyan " Mr azaad dan Allah in nemi wata alfarma awajanka ?" ta karishe maganar tana komawa kalar abin tausayi, murmushi kawai yayi yace " kishirya yau zamuje gida karfe 7 karki batamin lokaci " da gudu ta tashi tafada jikinshi cike da murna se dariya takeyi yau zataje gida ,rabonta da gida tunda tayi aure rungumeshi tayi gam tace " nagode sosai Mr azaad" yayi farin ciki da ganin irin murnan data shiga yau de yayi sanadiyar farin cikinta "asshhh" yafurta da dan karfi dagashi tayi tana tambayarshi meyafaru amsa yabata da " kinmanta bana jin dadi kinwani zo kin daddan ne ni" tunawa tayi da hakan dan tsaban murna ne yasa ta shaafa kunya ne yarufeta yasa tafara sosa kai tana turo baki . Hannu yasa yarike laben kasan yace " zaki fara rashin kunyar takine" girgiza kai tayi gudun karta ja yace yafasa " am sorry bari inje gun ummina ka kwanta kasamu kayi bacci kafin la'asar" ko jiran amsarshi batayi ba tafice yau de yasata murna se murmushi takeyi ita kadai, sake nanata abinda tafada yayi " ummina" hakan yamishi dadi saboda yana matukar son dakuma daraja meson umminshi. " My feena nikam yau naga se farin ciki kikeyi meye sirrin ?" rufe fuska tayi tana dariya sannan tace " ummi Mr azaad ne yace yau zamuje gida " ummi kanta taji dadin labarin dama tanada niyar mishi magana saboda yakamata ace taje taga gida murmushi ummi tayi tace " ahhh to lallai wannan Mr azaad din yakyauta! Feena fatan de babu wani abinda yake miki na rashin jin dadi? " Kwantar da kanta tayi akan kafadar ummi tace " ummi babu abinda yake mini" ko kadan ummi bata yarda da abinda fanan tafada mata ba , domin kuwa yanayin yanda suke ganinta a yan sattitikan sunsan dole akwai abinda ke faruwa kuma ko sun tambayeta sede tace musu bakomai saboda fanan yarinya ce me hankali taki fa dane gudun fadan dazaa mishi bayan haka kuma bazata iya kai karanshi ba, amma yau ganin yanda take murna yasa ummi tafara tunanin Allah yafara hada kansu, hakan yayima ummi dadi sosai takara jin fanan aranta tare da alfahari da ita. " Nikam ummi wai ina zeenat da su ya fawwaz ne gidan shuru sun tafi sun barki ke kadai" shafa kanta ummi tayi tace " ai tun sha daya suka fita sunje gidan daughter! Shine zeenat wai sede taje ta kiraki kutafi tare fawwaz yace shide ba ruwanshi dan yasan son na nan jin haka zeenat dinma tafasa zuwa kiranki " dariya sukayi atare aranta tana fadin" wato Mr azaad de kowa be bari ba " haka tayini agun ummi suna hira nan ne ummi ke sanar da ita yaran kannenta nazuwa daga dubai gobe, ba ita tabar part din ummi ba se dataji ana kiran sallah mangrib yasa ta tafi part dinta tayi wanka hade da alwala tazo ta gabatar da sallah. Shadda lace brown and golding color tasaka Riga da skirt dinkin rigar bubu ne yakawo har guiwa skirt din kuma pencil skirt gashi ta kafa dauri haka tagama shiryawa tsaff bakaramin kyau tayi ba bedroom dinshi tashiga tana adduah Allah yasa ya shirya agaban mirror ta sameshi ya shirya cikin wata hadadden yard white color, " tsarki yatabbata ga Allah Ubangijin talikai dayayi wannan halittan" abinda ko wannen su yake fada aranshi kenan ta cikin madubi yake kallonta yakasa dauke idonshi akanta juyowa yayi suna facing juna tafiya yakeyi cikin takunshi na jaruman maza ya isa gabanta jan dogon karan hancinta yayi "aucchh Mr azaad hancina " sake hancin yayi yana cewa " bana hanaki kallona ba " murguda mishi dan karamin bakinta tayi tace " to aini bakai nake kallo ba kaina nake kallo a madubi" kwaikwayan yanda tayi maganar yayi dariya yabata ganin yanda ya kwaikwayeta in tana magana, tambayar sa tayi " to yanzu ya kakajin jikin naka ?" Amsa yabata" da sauki" . harsuka fito daga part dinsu inta tuna kwaikwayonta dayayi setayi dariya, girgiza kai yayi dan yaga inta fara dariya batasan bari ba . Ahankali suke taka staircase din yana rike da hannunta, jin karan takalmi ne yasa dukkansu suka juyo suna kallonsu, hakan ba karamin dadi ya musu ba barinma yanda suka dace sosai tun kafin su karaso fawwaz yafara musu hoto tare da videos batare da sun sani ba, mutsu_mutsu tafarayi da hannunta tana son kwacewa sake rike hannun yayi kam yaki sakewa kunya ne ya cikata kamar ta nitse akasa haka takeji su abba,ummi , fawwaz,areef duk suna falon banda zeenat da zata kwana a gidan anty amina. Dukkansu murmushi ne dauke akan fuskokinsu yanda fanan ke kokarin kwace hannunta gashi Mr azaad yake sakin hannun abin yaso basu dariya sesuka danne, sallama suka musu suka fita tasowa securities sukayi dan rakashi hannu yadaga musu kawai packing space yaje yafito da motar kirar BMW baka, shiga tayi me gadi yabude musu gate harsuka iso babu wanda yayiwa dan uwansa magana. Yana yin packing akofar gidan tafito da gudu tundaga bakin gate take kwala kiran " mama!mama!mama" duk suna zaune afalo suna hira kamar daga sama sukaji muryanta ya karade gidan tagumi baba yayi Yana kallon mama yace " ohhh mamansu nikam yaushe fanan zata girmane" duka dariya sukasa fitowa ya Usman,ya al ameen sukayi , ya Usman ne yafara fitowa aikuwa tana ganinshi taje da gudu ta rungumeshi tana dariya, dariyar shima yakeyi na farin cikin ganin yar kanwar tashi. Mr azaad na tsaye abakin gate yashigo yana harde da hannunshi akirji yazuba musu ido fuskan nan ahade kamar wanda akawa mutuwa hada ido sukayi da ya usman dake rungume da fanan ganin yanayin Mr azaad abin yabashi dariya domin babu abinda yake hangowa a kwayar idon Mr azaad daya wuce wutan kishi , kamar ancewa fanan ta kalli bakin gate aikuwa karaff suka hada ido dashi mugun kallo kawai yake watsa mata ba shiri ta raba jikinta dana ya usman, kwafa yayi yawucesu yashiga falon suka gaisa da mama da baba cikin girmamawa sosai suke alfaharin kasancewar Mr azaad a sirkinsu da suna tunanin wani rayuwa yarsu zatayi tare dashi saboda ko fuskanshi kadai mutum ya kalla yasan mutum ne me tsatsauran raayi da rashin magana amma bayan aurensu da kwana biyu yazo gidan kusan duk bayan kwana biyu se yazo gidan gaishesu amma betaba fadawa fanan yaje gidansu ba. Rungume auta tayi sosai , haka ya al ameen ma sosai yayi murna da ganinta yana tsokananta " yar kanwa wato seyau kikayi niyar zuwa ko ?" " Ah ah fah ya al ameen" dariya kawai yayi, sake auta tayi ta cigaba da kwalawa mama kira harta shiga falon fadawa jikin mama tayi ta rungumeta sosai tana fadin " mama na nayi missing dinki sosai" " kai!kai fanan kede bazaki taba girma ba mutum kullum ace baya girma dagani karki karya ni" shagwabe fuska tayi ta daga maman tana " yanzu mama bakiyi kewata ba " ganin yanzu seta farawa mutane kuka yasa mama tace " ah nikuwa nayi kewarki shagwababbiyata" dariya tayi ta sake rungumeta yau wani irin annashuwa take cikj na ganin iyayenta, haka taje gun baba tagama mishi shagwaba dariya kawai yaitayi yana kallonta yana jin wani irin daci aranshi babu yanda suka iya dolene seta tafi inde bata tafi ba sede wani ikon Allah shafa kanta yayi yace" Allah yamiki albarka ya kare mana ke da karewarsa " duka suka amsa da abin. haka suketa hiransu dukda Mr azaad ba wani gwanin magana bane amma yau yadan sake wani yabada amsa wani kuma yayi shuru tashi tayi tashige dakinta dan tasan suhaima na ciki tana wayar jaraba kilama batasan tazo ba , aikuwa kamar yanda tayi hasashe tana ciki tashige bargo ta kashe murya tana waya da masoyinta , tsalle tayi tadira akanta afirgice suhaima tamike ganin fanan yasa tasa ihu suka rungume juna. cire wayar fawwaz yayi daga kunnenshi dan yaji muryan fanan murmushi yayi kasa_kasa yace " kai matar babban yaya da baby se adduah" lura da yayi suhaima tamanta da suna waya sun baje da hira yasa yakatse kiran. Shuru_shuru fanan bata fito ba se zuba ido yakeyi yana jiran tafito duk cikin abubuwan tabawa da mama ta kawo mishi drinks da fruit kawai yataba, suma yar hira sukeyi sama_sama da ya usman da ya al ameen kirane yashigo wayar ya usman ya mike yayi waje , picking yayi yanata hello hello bayajin me maganar network ya hana bude gate yayi yafita waje . Magana yakeyi da yaron shagonshi idonshi ne ya sauka akan khairatyyy dake tsaye ta bashi baya iska se kada kayan jikinta yakeyi da dogon gashinta dayake sharan kasa, yanayin de abin tsoro in bil adama yagani amma ya usman de kara burgeshi tayi babu wani fargaba ko tsoro ya nufeta yatsaya abayanta tun fitowarshi a gida take sane dashi awajen amma batayi tsammanin har yanada karfin guiwan tunkaranta ba domin duk wani bil adama dayayi gamo da ita mugun firgita yakeyi amma shi meya taka haka , batare da ta juyo da gangan jikinta ba tajuyo da kanta kadai fuskanta ba alamun dariya ko wasa idon nan manya_manya dasu tace " meya kawo ka nan kazo ka tsareni da ido babu ko tsoro a tattare dakai " dariya ya usman yayi ganin tadage ita adole seta tsoratar dashi bata san son dayake mata ya kore duk wani tsoro da firgici ba , ganin yaki ce mata komai yakafeta da ido yana murmushi ne yasa ta murguda mishi baki tace " kabari banaso kadena kallona kokuma in hukuntaka" shi komai tayi kyau take mishi dakara burgeshi " kin taba kallon wanda yaji tsoron abinda yakeso ?" yamata tambayar yana kallon cikin manyan idonta dasuka zarce na bil adama, kara zaro su waje tayi tajuya ta kalli gaba daya arean dan tabbatar da babu wani jinni kana nan yaran aljanune kawai suke wajan suna wasa , kasa kasa tayi da murya tace " baka da hankali ne? kokayi hauka ne? kode bakasan nidin wacece bace kakemin irin wannan banzan maganar to koda wasa kar kasake insake jin irin wannan maganar abakinka in bahaka kuwa ze iya yuwa inyi ajalinka " tunda tafara magana yake kallonta sake matsowa daff da ita yayi yace" to aini hakan zezamo abin alfahari agareni ace wacce nakeso ce ta kasheni! balle ma nasan ke ba muguwa me cutarwa bace khairatyyy kiji tausayina kisoni kamar yanda nake sanki dan Allah " yafada yana hade hannunshi duka biyu yana rokonta , dafe kai khairaty tayi yau taga takanta duk iya yanda zatayi ta fahimtar da ya usman kancewa babu maganar soyayya tsakaninsu saboda sudin ba jinsi daya bane amma yaki fahimtarta . Sosai yabata tausayi tabbas ta yarda da irin son da yake mata amma dolene tunkafin yayi nisar da bazeji kira ba ta dakatar dashi , godiyarta daya tasan duk abinda suka tattauna sarauniya taji. _____ zuruf fanan dake hira da suhaima tamike domin duk maganganun da ya usman da khairaty suka tattauna akan kunnenta tana jinsu fitowa tayi daga dakin ganin haka yasa suhaima tabi bayanta ,suna zaune afalo sukaga tafito da mugun sauri kamar zata tashi sama hannu daya Mr azaad yasa yariko ta dan sun lura ba lafiya ba irin yanda tafiton nan duk tunanin su wani abunne yake faruwa, Mr azaad ne yafara magana " lafiya fanannnn ina zakije kike wannan saurin haka?" Ajiyar zuciya tasauke seyanzu ta lura a irin yanayin da tafito ko dankwali babu akanta gashi sun fara tunanin wani abu rike hannunshi tayi suka zauna akan kujera batare da tace musu komai ba ta daga kai ta kalli sama tace " khairat kizo keda ya usman yanzun nan " gaba daya lamarin yadaure mata kai taya akayi har ya usman yafada soyayya da jinsin daba tashi ba, ana haka yayi sallama yashigo yazauna kallonshi kawai fanan takeyi tama rasa mezata ce mishi " kallon bakin kofa tayi tace" kishigo kema " bayyana khairaty tayi taxube akan guiwowinta tagaida sarauniya,umarni fanan tabata data zauna itama, zama khairaty tayi tana satan kallon sarauniya sude da basu san meke faruwa ba sun kasa kunne da sunji abinda fanan zata fada. Gyara murya tayi kafin tace " khairat meye hadinki da ya usman danaji zancen soyayya natashi " dafe kirji mama tayi tace " so me? Kamar de kunne na ne beji dede bako?" alama baba yamata da tayi shuru su gama jin me fanan zata fada sukansu abinda yabasu mamaki amma banda ya al ameen daya san dama zaa rina. ______ kanta na kallon kasa tace" yake sarauniya bantaba sanin da wannan labarin ba se dazun yake sanar dani babu irin fahimtar dashi da banyi ba amma yakasa fahimtar babu wani soyayya atsakanin mu saboda mun kasance jinsi daban daban" sun gamsu da maganar khairatyyy . maida kallonta fanan tayi kan ya usman da har time din idonshi na akan habibiyarshi khairaty " ya usman kabar wannan maganar saboda babu aure tsakaninka da khairaty kai bil adama ne itakuma jinnu ce hakan baze taba yiwuwa ba " hararanta yayi yace" fanan wallahi inasonta ni ahakan na amince zan aureta " daka mishi tsawa baba yayi kafin yadaura da " usman ina maka kallon me hankali ashe babu taya zaka fara tunanin fara son abinda kasan bazaka taba samuba ko so kake ka lalata rayuwarka yar uwarka tafada maka illan hakan amma kai har kana wani cewa zaka aureta ahaka " " nooooo bazeyuba ba Ina san khairaty babu abinda ze rabani da ita se mutuwa! wallahi ba ni na daurawa kaina son taba Allah ne yadaura min bazan iya rayuwa ba in babu ita aciki dan Allah kutaimakamin ku auramin ita " ............ Tofa ana wata ga wata.😨😨 Masu comment Allah yabar kauna ina godiya sosai Allah yamuku albarka. Semun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏. via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚 Page 4️⃣5️⃣ Abinda be taba faruwa ba a tarihin agidan yau shine yafaru , ko da wasa basa yiwa iyayensu musu akan duk abinda zasu zartar amma yau ya usman ne da kanshi baba yayi magana yana cewa bazeyuba tabbas yayi nisan da bazeji kira ba soyayya yariga da yarufe mishi ido,yanzu duk abinda zasu fada baze taba sauraran su ba , babban abinda fanan take tsoro kenan dan tasan so mugun abune in mutum ya fada tarkon so tofa komin munin abu baze taba gani ba gaba daya tausayinshi ne yakamasu dan sun san ya daukowa kanshi dala ba gammo ne hakan baze taba faruwa ba bil adama da jinni. Mama kam tsaban takaicin daya cikata ma ka sa magana tayi da wanne zataji, da tafiyar fanan zataji ko kuma da abinda ya usman ya jajibo musu . Cikin kwantar da murya baba yace " usman yanzu zaka fara bijire min kenan saboda so ya rufe maka ido ? Kasan bazan taba hanaka duk wani abu ba sede inde yakauce hanya hakan kuma bazan taba lamunta ba daga yau kama fara tunanin cireta aranka dan ba samunta zakayi ba nagama magana " ya usman dafe setin zuciyarshi yayi da yakeji kamar ana watsa mishi wuta dan bala'in zafin da yake mishi murya na rawa yace " baba bana fatan ranar da zezo inzama mara biyayya ga iyayena! Amma zanso kuji abinda nakeji wallahi baba in ban samu khairat ba mutuwa zanyi, ku taimakeni kumin wannan alfarman" ya matukar bawa Mr azaad tausayi bama shi kadai ba duk wani wanda yake falon seda ya kashe musu jiki mikewa Mr azaad yayi yarike hannun ya usman suka fita waje. Sallamar khairatyyy fanan tayi nan take ta bace azuciyar fanan kuwa tana tunanin abinda yakamata tayi dan ceto dan uwanta. Auta kam duk abinda akeyi se binsu da ido takeyi kasancewar takan fahimmci wata maganar wata kuma bata fahimta saboda kananun shekarunta ,ta riga da tagane duk wannan maganar akan khairaty ce da ya usman inde ta ita zaabi khairaty tayi mata kyau sosai, ( kuji auta fah ahhh lallai yaro yarone) fanan da ya al ameen ne suka kwantar wa su mama hankali akan zasuyi iya kokarinsu domin ganin ya usman yacire khairaty a ranshi, kirane yashigo wayar suhaima ganin sunan "my hubby" yabayyana akan screen din ne yasa tabar falon tashige daki. Haka a bangaren Mr azaad duk da yakasance mara son magana haka yabawa ya usman shawara sosai har yasamu yadawo normal suka dawo falo ko zama ya usman beyi ba ya shiga dakin shi , zama Mr azaad yayi yana shafa lallausan sumar kanshi kafin yace " baba kuyi hakuri ku mishi uzuri yariga da yayi nisa na lura usman yana matukar sonta , dole muyi kokarinmu domin ganin ya cireta aranshi " sake baki da hanci fanan tayi tana kare mai kallo jin maganganunshi tunani tafara yaushe Mr azaad yafara damuwa da damuwar mutane amma hakan yamata dadi ganin ya damu da damuwar ahalinta sonshi ne takaraji yashiga cikin zuciyarta, duk maganar nan da Mr azaad yakeyi auta na kwance ajikinshi tayi lamo kamar wata me bacci can kuma ta mike zaune ta kalli Mr azaad tace " Yaya balarabe kasanme ? " Kallon fuskanta yayi me kama da na fanan se an nutsu sosai zaa gane kamar tasu saboda skin color dinsu ba daya bane auta farace sol kamar tsada fanan kuma chocolate color ce ,ita kadaice me color skin din agidan , girgiza kai yayi tare da cewa " cutie bansaniba sekin fada " cigaba tayi da " nikam budurwan ya usman tamin kyau sosai especially her eyes that are so big like ball tayi kyau sosai kaima tamaka kyau ko?" Basu taba tsammanin abinda auta zata fada ba kenan amma se sukayi laakari da wayon datake dashi domin basuyi tsammanin harzata fahimci akan abinda ake magana ba kenan , shisa bakowani magana akeso adinga yi agaban yara ba saboda yaran yanzu sun wuce duk yanda kuke tunani , satan kallon fanan yayi yaga se aikin gallawa auta harara takeyi jin tana tambayarsa shima tamasa kyau, murmushi yayi dan yasan akan abinda yasa take hararan auta , lakatar hancin auta yayi yace " karki kara magana akan abinda manya suke tattaunawa bakyau this is improper" gyada Kai tayi takoma jikinshi ta kwanta . Sun dan taba hira kafin Mr azaad yakalli agogon diamond dake daure a hannunshi sannan yace " baba mu zamu wuce dare yayi seda safe " sallama sukayi ya fita shida ya al ameen fanan ji tayi kamar karta tafi dakinta tashiga ta canza kayan jikinta zuwa riga da wando falazo tasa hijab dinta har kasa dama kayanta duk suna cikin wardrobe dinta, Haka tanaji tana gani tayiwa su mama sallama, suka fito ita da suhaima tana rike da hannun auta ajikin motar suka samu Mr azaad da ya al ameen suna tattaunawa game da yanda zaa shawo lamarin ya usman bude motar yayi ya dauko fashion bag dake cike da chocolate kala_kala yaba auta karba tayi tana fadin " thank you yaya balarabe god bless you" murmushi kawai yayi azuciya ya amsa da Ameen motar suka shiga fanan na musu bye-bye. Sun danyi nisa da tafiya se taga yacanza hanya kallonshi tayi tace " Mr azaad ina zamuje naga nan de ba hanyar gida bane" batare da ya kalleta ba yace " namanta ban fada miki ba dazun nagama cinikin kanki to yanzu zamuje a fille ne" iya tsorata fanan ta tsorata saboda ko kadan bataga alamar wasa a fuskanshi ba he sounds very serious mazgewa tayi tana turo baki tace " da ka siyawa kanka rashin kwanciyar hankali dan wallahi nadinga maka fatalwa kenan" tuntsirewa yayi da dariya tare da taka birki motar gudun kar asamu matsala sosai yake dariya kamar ba Mr azaad ba, ya salam wani irin kyau yakara da yake dariyar kyawawan fararen hakoranshi su kansu abin kallo ne zuba mishi ido kawai fanan tayi yayi masifar mata kyau tun daga saninta dashi izuwa yanzu bata taba ganin yayi dariya irin haka ba se yau seta ga ma dariyar yafi mishi kyau ,koda shekara dari zasukai ahaka da wannan dariyar dauke akan fuskanshi bazata taba gajiya da kallonshi ba. hura mata iska yayi a fuska sauke idonta kasa tayi tana wasa da yatsunta jan motar yayi sukaci gaba da tafiya beyi packing a ko ina ba se a ice cream planet zallan ice cream ake siyarwa awajen wajan ya hadu sosai kaff gombe inde wajan da ake siyar da ice cream ne to yafisu kyau da tsaruwa, se fitar da hasken wuta kala_kala yakeyi tunda suka iso gun wajan yadauki hankalin fanan se kallon wajan takeyi tana sakin lallausan murmushi, " muje " kawai yace mata ya bude motar ya fito fitowa itama tayi suka shiga ciki , ice cream yazaba yafi kala biyar masu tsada mika mata ledar yayi yabada atm card suka cire kudinsu motar suka koma tun kafin yatada motar fanan tabude roba daya tafara sha se lashe baki takeyi ice cream din yamata dadi bata taba shan ice cream me dadi irin wannan ba , ahaka harta sha roba uku ta bude na hudu kenan zata fara sha yayi karaf yarike hannunta yakarbe ya ajiye kafin yace " yanzu ke in anbarki se ki tazubasu a cikin ki ko ? Keda yakamata ki hana wani shine ke kikeyi to wayan nan se gobe" yatsina fuska tayi idon nan nata dasuke manya dasu yayi rau_rau kamar me shirin kuka tace " ayyah Mr azaad kabarni in shanye Allah yanzu in bansha ba kwadayina ze tashi " kallonta yayi ta gefen ido yaga yanda takoma abin tausayi aranshi yace " wani abu se yarinta in bahaka ba mutum yata durawa cikin shi sanyi" afili Kuma yace " idan kwadayin yatashi inada abinda zan bashi " ganin ya manna mata hauka ne yasa tayi shuru tana bin ledar ice cream din da ido ahaka har suka iso gida. Gyara packing yakeyi ta faki idonshi tadau roba daya tasa a hijab dinta tafito daga motar da gudu tayi ciki , murmushi kawai yayi dan yaga abinda tayi wato shi zatayiwa wayo , bin bayanta yayi yanda tasamu falon ba kowa shima haka yasamu duk sunshiga sun kwanta dakinshi yashiga yayi wanka ya sauya kaya izuwa sleeping dress ya kwanta. Tana zaune a tsakiyar titi misalin karfe 2 nadare kafa yadauke babu kowa ba alamar koda kafar mutum se haushin karnukan dake tashi , zaman yan bori tayi gashi duk yarufe mata fuska ga mutum kwance agabanta cikin jini dake malala ajikinshi sanadiyar yaga cikinshi datayi kayan cikin duk suna waje itakuma se aikin cin namanshi takeyi zaro dogon hanji tayi tasa abakinta dake dauke da dogayen hakwara duk sun rine da jini , tana janshi kamar yanda akecin indomie harta gama cinyewa tass bata kyaleshi ba seda ta cinye duk wani nama ajikinshi yarage qashi bakinta ta kafa adede wuyanshi tana zuqan jini seda ta tsotse jinin kaff kafin ta dago kanta bakinta yayi dama_dama da jini zaro dogon harshenta tayi ta sude baki hade dayin gyatsa mikewa tayi tsaye tamaida gashinta baya nan take fuskanta ya bayyana ba kowa bace face zeenat Muhammad mainasara...... Kuyi hakuri da yanayin read more din yau wallahi yau nidince se a slow. ~Semun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏~ via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚 Page 4️⃣6️⃣ & 4️⃣7️⃣ Duk abinda takeyi suna kallonta a madubin tsafi sun san yanzu zasu samu abinda sukeso tunda yar family sunsamu sun jawota cikin kungiyarsu bako wani kungiya bane wannan da yawuce vampires union, kungiya ce da suke shan jini da kuma cin naman mutane da dabbobi sunada matukar hadari Kuma sun bawa zeenat maita ne dan su rama abinda mommy ta aikata musu. Taya akayi zeenat tazama daya daga cikin kungiyar vampires union, yau fitansu da safe ita da ya fawwaz and areef zasuje gidan anty amina daga nesa ta hango wata yarinya na tallan guiva setaji ya shiga ranta magana tayiwa fawwaz yatsayar da motar tasiya tafara sha acikine tasha maitar batare data sani ba . Bayan sunzo gidan anty amina ne tafara jin wani irin sauyi ajikinta setaji kamar abu na mata tafiya hade da magana akunne. dakin su aslam da islam tashiga tadan kwanta ciwon Kai ne yafara damunta shisa dasu fawwaz sukace zasu tafi tace suje kawai ita se gobe zata dawo aikuwa tafiyar sukayi abinsu, anty amina data lura da yanayinta kamar bata da lafiya yasa ta tambayeta amma se kawai tace mata bakomai. Around 10 duk sun kwanta ita kam takasa bacci wani azabebben yunwa ne yafara ciyota ,kitchen tashiga har lokacin ciwon Kai din besauka ba bude food flask din tayi dan ta dibi abinci toshe hanci tayi jin abincin namata wari kamshin danyen nama ne yadaki hancinta bin direction din da takejin kamshin tayi har izuwa fridge dauko namar tayi duka tana kallon shi , tunani" tafara taya zanci danyen nama " jitayi andaka mata tsawa akunne cike da umarni taji murya nafadi " ki tabbatar da kincinye naman nan " tun kafin yagama magana tahau cin naman haka tacinye namar da yafi kilo goma , wani sabon yunwa tafaraji jitayi naman dataci yatayar mata da kwadayi kamar wata mahaukaciya haka ta birkita kitchen din tana neman nama amma babu daki takoma kamshin su aslam da islam ne yacika mata hanci shinshinasu tayi tana ajiyar zuciya tasamu nama hankali kwance bude baki tayi nan take dogayen hakwara suka fito , jitayi namar aslam yayi tauri sosai kamar dutse haka ma Islam duk yanda takai da son cinyesu to abin yagagara badan komai ba sedan adduah da mamansu da babansu sukeyi musu afusace ta tashi tabar dakin jikin bango ta shige fitowa tayi abakin titi kwance taga mutum da sauri ta karasa wajan ta farka cikinshi tafara cin naman dama su suka ajiye mata ganin abin yafara aiki ajikinta yasa sukayi murna sunada ya kinin se ta cinye yan gidansu kaff. Washe gari. "Mr azaad ! bansan meke faruwa ba amma yau natashi da faduwar gaba Allah shine masanin dede" cewar fanan dago Kai Mr azaad yayi yadan kalleta shikanshi inya tuna zata tafi seyaji wani irin aranshi amma babu yanda suka iya, kwantar da kanta yayi a cinyarshi sannan yace " inkin ji faduwar gaba kidinga karanta innalillahi wainna ilaijiraji unnn in sha Allah ze dena, " murmushi tayi ta sakeyin lamo ajikinshi , tunda sukayi breakfast suke zaune afalo yana duba wasu files, yaseer ne ya kirashi awaya ya sanar mai yana falon ummi okay kawai yace mishi kallon fanan yayi yace " dauko hijab dinki muje falon ummi" tashi tayi dan ta dauko hijab din jikinta na sanye da Riga da skirt na kanti ,fitowa tayi tasamu ita yake jira rike hannunta yayi suka nufa falon ummi, duk suna zaune afalon banda abba da ya fita meetings ummi, yaseer, fawwaz,areef tsungunawa tayi ta gaidasu sannan ta zauna , yaseer ne kasa_kasa kamar wani munafiki yace " dude two days kayi wuyan gani ina kashiga " hararanshi Mr azaad yayi shida yadena nemanshi tun zuwan dayayi last harsuka so yin fada akan fanan amma yanzu yana ce mai ya buya , dariya yayi da yaga hararanshi kawai Mr azaad yayi bece mai komai ba , sallamar zeenat ne yasasu kallon bakin kofar tun kafin ta iso cike da tsokana yaseer yace " yanzu haka ake bakunta zeenat daga zuwa kin kwana shine za ki dawo da sassafe kamar wacce aka koro " turo baki tayi tace" ya yaseer kaiko ni nayi missing din ummina ne shisa na dawo " itade ummi batace musu komai ba suna yar hira da fanan da gudu zeenat tafada jikin fanan tana rungumeta, ummi ne tace " nikam zee kina da hankali kuwa karyata zakiyi" kafin takarasa maganar sukaga fanan tasa iya karfinta ta ture zeenat ajikinta seda ta kusa faduwa yaseer yariko ta dukkansu kallon mamaki suke binta dashi meye dalilin dazesa tayiwa zeenat haka ganin yanda suke shiri sosai kuma ko fada sukayi fanan bazata mata haka ba. Tashi fanan tayi taje har gaban zeenat dake wur_wurga ido irin namasu rashin gaskiya bata taba tunanin fanan zata ganota ba . Kamar wata tsohuwar mayya haka fanan take shinshina zeenat, Mr azaad dasu ummi sunzuba ido suna kallon ikon Allah,kallon cikin idon zeenat fanan tayi kafin tafara fadin " zeenat meyasa kike Karnin jini?" Inda_inda zeenat tafarayi tarasa karyan dazata mata daka mata tsawa fanan tayi tana " nace aina kika samo jini meye hadinki dashi karki bari in kara tambayarki zeenat" kansu yadaure sun rasa ina maganar fanan yadosa me take nufi da zeenat na karnin jini. Zazzare ido kawai zeenat takeyi can kuma tace " ayyah anty fanan dazun ne dazan dawo daga gidan anty amina se naga motar ya bige wata yarinya karama shine naje na dauketa jikinta duk jini to kuma dole jikina nima yabaci da jini, nakaita asibiti to kinji dalili" ajiyar zuciya duka sukayi harta Mr azaad danshi kanshi yafara zargin wani abu saboda yasan haka kurum fanan bazatayi irin wannan maganar ba,domin ita ba kamar sauran mutane bace shisa ita kadai taji karnin jinin su basu ji ba , ko kadan fanan bawai ta yarda da abinda zeenat tafada bane kawai ta kalleta ne dan tasan tabbas akwai wani bakon lamari adangane da ita , wucewa part dinsu tayi tabarsu agun dan har tsakiyar kanta takejin karnin jinin na damunta kallon zeenat ummi tayi tace " sekije kiyi wanka kinde ji abinda antyn ki tace " okay ummi itama tashige bedroom dinta wata nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tasamu tasha da kyar da asirinta yatonu magana ta fara hawaye nabin fuskanta " nashiga uku ni zeenat wannan wani irin mugun rayuwa na tsinci kaina bazeyu ba dole in fadawa anty fanan gaskiyar abinda ke faruwa nasan dole zata taimakamin" murya mara dadinji taji yana fadin " karki kuskura ki aikata aikin da nasani domin yin hakan dede yake da salwantar da rayuwar ahalinki in kunne yaji jiki ya tsira sannan adaren yau ki tabbatar da kin cinye yaron hafsat " cike da umarni ake mata magana babu abinda takeyi inbanda aikin girgiza kai. Zaune suke a garden Mr azaad da yaseer , yaseer ne yake magana " mutumina naga kamar yanzu kadan fara saukowa " ajiye wayar da yake dannawa yayi sannan yace " dude bansan meyake faruwa dani ba yanzu kwata_ kwata bana iya mata abinda nake mata da and the worst thing shine komai tayi burgeni yakeyi haka kawai nakeson kasancewa da ita I don't know why" yaseer saboda farin ciki kamar yazuba ruwa akasa yasha haka yakeji yasan abokinshi yafada tarkon soyayya amma besani ba saboda be tabayin soyayya ba arayuwarshi yanzu bema san yana son fanan ba," dude inna fada maka wani abu zaka yarda?" Ya tambayeshi yana kallonshi gyada masa kai Mr azaad yayi cigaba da magana yaseer yayi " ka fara son fanan ne shisa ka kakejin wayan nan ba qin yanayin " sosai Mr azaad yake kallonshi dan san gasgata abinda yafada gaskiya ne ko karya tayama shi yafada soyayya batare da yasani ba. sassauta murya yayi yace " dude ba santa nakeyi ba kawai maybe kewanta nafara amma ka ajiye maganar soyayya agefe hakan baze faru ba" yar dariya yaseer yayi daya tuna wata magana da Mr azaad yataba gaya mishi " ina ruwana da tafiyanta" kafin yace " dude ba maganar kana kewanta da fa kafin kabara sonta ka tuna abinda kafadamin cewa fa kayi babu ruwanka da tafiyanta ko kamanta " shuru Mr azaad yayi. daurawa yaseer yayi da " kanason kasancewa da ita ko ?" gyada mishi kai Mr azaad yayi kamar karamin yaro yana son jin abinda yaseer ze fada. " dude wallahi kana sonta it will be better kayarda da hakan tun kafin time ya kure maka kafada mata kana sonta kaji dude" shikanshi yanzu ya yarda da tabbas yana sonta shafa lallausan sumar kanshi yayi yace" dude bazan iya fada mata ba saboda zata iya raina ni nikuma banason raini yashigo tsakanina da ita kasan mata haka suke " fashewa da dariya yaseer yayi Jin abinda Mr azaad yafada " haba dude wallahi fanan bahaka take ba duk wanda ya santa yasan bata da wannan rashin kunyar da kake magana akai mutumina kawai just go and confess to her shine kawai " murmushi ne ya subuce akan fuskar Mr azaad se yanzu ne yakejin sonta na kara shigewa zuciyarshi amma yana tsoron wani abu, yasan dole very soon zata tafi tabarshi karyazo yasabar wa kanshi da ita tazo tabarshi haka sukaci gaba da hira kafin suka bar gidan zuwa gidansu yaseer din afalo suka samu hajiyarsu yaseer tanawa kaninshi fada akan yawan yawon da yakeyi tunda suka shigo anwar yasha jinin jikinshi yasake nutsuwa ganin yaseer tare da Mr azaad dan yasan halinshi sarai hakuri yake bawa hajiyar gudun karta fada musu abinda ke faruwa watsa mishi harara Mr azaad yayi kafin yace " hajiyarmu meyayi " aikuwa kamar jira takeyi ya tambayeta tafara fada mishi, daura hannu akai anwar yayi aranshi yana fadin " nashiga uku hajiya ta kasheni wallahi yau nashiga hannun ya azaad nawa ta takare" pointing dinshi da hannu Mr azaad yayi akan yazo jikinshi duk yayi la'asar haka yazo wajanshi hannu Mr azaad yasa ya damki kunnen anwar da karfi ,kara anwar yasa yana yarfa hannu dan bakaramin damke kunnen yayi ba, magana Mr azaad yafara " wato ku yanzu kunyi girman da zaku dinga gantali ko ? Last time ya mukayi dakai ?" Kamar anwar zeyi kuka yace " alkawari namaka bazan kara ba ! dan Allah ya azaad kayi hakuri in sha Allah daga yau natuba wallahi bazan sake ba" frog jump Mr azaad yasashi haka yafarayi yana zagaye falon, juyawa yayi yakalli hajiya ya gaisheta fuska asake ta amsa tana fadin " wato son se yau kayi niyar zuwa ko ? nadauka ma da matarka zakazo min " murmushin gefen baki yayi yace " kiyi hakuri hajiya in sha Allah zan kawo miki ita very soon" dariya tayi dan tasan halin Mr azaad yanzu setafi watanni ma bazata kara sashi a ido ba , part din yaseer suka shiga anwar de yana nan yana famanyin frog jump. Haka yau fanan ta wuni wata sukuku da ita saboda lamarin zeenat ya tsaya mata arai dan tasan karya kawai zeenat tayi mata dan ta kaucewa zarginta , har tara Mr azaad be dawo daga gidansu yaseer ba abincinta taci tayi wanka tasa sleeping dress dinta ta kwanta. Packing din motarshi yayi a packing lot tafiya yakeyi kawai yaga kamar gilmawar mutum wul ta gabanshi dakatawa yayi da tafiyar yana kallon the whole house, masu gadine kawai suke zaune suna jin radio sekuma securities da suma hiransu sukeyi , cigaba yayi da tafiyar harya shigo part dinshi har ze shiga bedroom dinshi se yajuya zuwa nata bedroom din wutan dakin a kashe flashlight din wayarshi ya kunna ya haskata akwance take tana bacci takawa yayi har izuwa bed dinta shafa cutie face dinta yayi daga bisani kuma ya manna mata kiss a forehead (goshi) komawa bedroom dinshi yayi shima wanka yayi ya kwanta. Sanyayyar murmushi fanan tasake lokacin da ya manna mata kiss tun shigowarshi ta tashi adduah takeyi aranta Allah yasa Mr azaad yafara sonta kamar yanda itama take sonshi. To fa wato akace in zaka tona ramin mugunta ka tona dede kai yanzu de tsakanin mommy da zeenat nide narasa wazan kira mugu acikinsu. Mommy tasamu lafiya sumul da ita tashirya fita dan taje itama tasamo yara 8 da suka rage zaayi sacrifice dinsu, itakuma zeenat tashiga part mommy har bedroom din Mansoor domin aiwatar da abinda a kasata ga shi dan banzan yunwa takeji tana bukatar jini ko nama kwance tasamu Mansoor yayi dai dai akan gado yana bacci bayan yagama shaye shayenshi dalewa kan gadon tayi tasa dogayen yatsunta tafara tsaga cikinshi , shuri daya Mansoor yayi rai yayi halinsa tass zeenat ta cinye namanshi da jininshi Tana gamawa kuwa ta bace ta tafi dakinta tayi kwanciyarta cikinta a cike. Karfe 3 mommy ta dawo gidan ta kashe yara biyar 5 takai kungiya, tana shigowa part dinta tafara jin karnin jini mamaki ne yakamata bin direction din inda karnin jinin ke tashi tayi tafiya takeyi har dakin Mansoor dake kwance babu rai ajikinshi babu koda tsokan nama sede kashi uwar ihu da kururuwa tayi wanda yacika gidan yayi sanadiyar tashin kowa daga bacci har rige_rige sukeyi suka fito kaff dinsu afalon ummi suka hadu suna tambayar junansu meyafaru tsaban rudewa dukkansu da kayan bacci suka fito buga kofar falon akeyi kamar zaa ballata babu ko tsoro Mr azaad yaje ya bude bangaje shi mommy tayi ta nufi abba ta rikeshi kam tana kuka kamar ranta zefita, duk ta daburtar dasu sun rasa gane abinda yake faruwa jijigata abba yayi saboda ta dawo cikin nutsuwarta cikin tashin hankali tace " muhammad sun kasheshi sun kashe Mansoor sun kashemin dana Mansoor" innalillahi wainna ilaijiraji unnn zufa ne yafara yanko musu jin kalamanta saketa abba yayi yawuce part dinta yau ne rana ta farko da yasanya kafa a part dinta tun bayan shekara 12 saboda ya dade da sanin wacece mommy har dakin mansoor din yashiga runtse ido yayi lokacin da yayi arba da gawar mansoor ko kuma in ce gwarangwal din mansoor bakyaun gani, shigowa su ummi sukayi suma duk kallo daya sukawa gawar suka kauda kai, yau kam sun shiga matsanancinyar tashin hankali , babu abinda kirjin fanan yakeyi fa ce bugawa da karfi_karfi tsoronta daya shine kar zargin da takeyi yazama gaskiya akan zeenat saboda yanzu tasake samun hujja ganin dan kunnenta yashe akasan gadon sa kafa tayi ta bigeshi yashige can kasan gadon batare da kowa ya gani ba. bedsheet Mr azaad yasa ya rufe mansoor dashi duk karfin zuciyarshi da taurin zuciya seda yaji tsigan jikinshi yatashi barinma da yaga fuskan mansoor kaf an kwakule komai harta ido an cire , fita sukayi daga dakin zuciyarsu a karye sosai tausayin mommy yakamasu . haka suka kwana a part din mommy batare da sun runtsu ba yanda sukaga dare haka suka ga rana . Sallah suka tafi a masallaci Abba yafadawa liman akwai jana'iza agidanshi dan shi ya rasu , liman yayi sanarwa a masallaci mutane suka tayi musu taaziya. haka akayi jana'izar mansoor aka kaishi gidanshi na gaskiya kowa na binshi da adduah Allah yaji kanshi , mommy kam yar karamar hauka ne kawai batayi saboda duk duniyar nan babu dan adam din da takeso sama da danta mansoor saboda halinsu yazo daya duk wani mugun nufinta bata taba tunkarar shi ba , ko magana bata iya yi balle ta karbi gaisuwar , su anty shayida da anty zainab da anty amina duk sunzo , me martaba da duk jamaar masarauta sunzo, haka su mama suma sunzo sun musu taaziya sun koma sosai mutuwar mansoor ya taba su fawwaz dukda bawani shiga harkanshi sukeyi ba saboda rashin kunyar dayake musu baya ganin kowa da mutunci kuma ko sun dakeshi hakan baze hana yakara musu wani rashin kunyar ba , haka zeje yafadawa mommy ita kuma tashigo part dinsu ta musu rashin mutunci tayi gaba . duk wannan gaisuwan da akeyi da zaman makoki ko idon zeenat baa gani ba ko lekasu batayi ba tana can ta kulle kanta adaki tana kukan nadaman halin dataga kanta aciki abin na mugun damunta gashi kuma bata isa tafadawa kowa ba kugin yunwa cikinta yafara nan take halittar jikinta yafara sauyawa dogayen hakwara da yatsunta sun fito idonta yarine yayi jaa kuka takeyi da dan karfi dan yau kam tayi niyya sede in mutuwa zatayi sede tayi amma bazata karacin naman kowa ba tun tana iya jurewa harta kasa , fanan tana zaune a main falo dan batason yawan hayaniya sosai tabar wajan zaman makokin ita daya a falo , tana nan tana tunanin yanda zata shawo kan lamarin zeenat kenan taganta ta diro daga can upstairs ta dira a gabanta kamar wata yar biri tashi fanan tayi tana ja da baya zeenat na binta harsuka kai dungun gini yanzu kam fanan tagama tabbatarwa kanta zeenat mayyace , kafa mata hakwara tayi awuya zata fara shan jininta yaseer ya cafketa ta baya gam yariketa yaki sakinta . kokarin fin karfinshi takeyi dan girgizan da takeyi yawuce iya karfin zeenat da akasani , fashe musu da kuka zeenat tayi tana " wallahi mutuwa zanyi in bansha jini ba dan Allah ku taimakeni kubani in kuma ba haka ba zan iya mutu " hawayene yakebin fuskan fanan dan jitayi duniyar ta dena mata dadi tama kasa karasa wajan yaseer da yake kokuwa da zeenat, son da yake mata ne yasa lokaci daya tausayinta yayi tasiri aranshi hannunshi yamika mata aikuwa karaff ta damki hannun yaseer din tasa abaki ta fara tsotsan jinin shi cike da tausayi suke kallonta shigowar Mr azaad kenan yayi karo da mugun gani da wani irin speed ya isa inda suke ya fincike zeenat dake shan jinin yaseer da takeyi cikin daka tsawa yace musu " dama dukkan ku biyu baku da hankali bansani ba yaseer taya zaka bata hannunka tasha jininka " gam yarike wuyan zeenat yasa idonta cikin nashi aikuwa nan take ta sume bin Mr azaad sukeyi da kallon tuhuma meye abinda ya aikata yanzun nan meye dalilin dazesa daga kallon idonshi zeenat zata suma, bebi ta kansu ba yadauketa cakk yanufi part din ummi da ita yakwantar da ita afalo . Su ukun duk suna zaune a falon ummin babu wanda yacema dan uwansa kala, fanan tana yiwa yaseer dressing din hannunshi da zeenat tasha jini, daga waya Mr azaad yayi ya kira layin ummi yace mata tazo ita da abba it's urgent, shigowa sukayi su biyar Abba,ummi, fawwaz,areef se anty amina ganin zeenat akwance bakinta da jini_jini Abba da ummi har suna hada baki wajan tambayar Mr azaad meya sameta , fada musu abinda ya gani yayi ,juyawa ummi tayi ta kalli fanan hawaye na fita a idonta jin halin da yarta ke ciki tace mata " my feena meya sameta " girgiza kai fanan tayi murya asanyaye tace " ummi tun dawuwarta jiya nace naji tana karnin jini seta min karya dawani abun daban amma dukda haka ban yarda da itaba seyau na kara tabbatarwa" dama suma tunda sukaga fanan tayi hakan sunsan da walakin goro a miya amma se basu wani bawa abin mahimmanci ba. tashi fanan tayi taje ta durkusa agaban zeenat tasa hannunta akan goshinta sannan ta rufe ido nan take tafara ganin tun lokacin da vampires union suka fara shirin bawa daya daga cikin ahalin mainasara maita harzuwa time din da daya daga cikinsu yazama karamar yarinya me tallan guiva da siyan da zeenat tayi takoma maiya da cin naman da tayi da komai da komai seda fanan tagani kamar wacce ta kunna film tana kallo . dasauri ta bude idonta ta kalli yan falon da suma ita suke kallo musamman ma Mr azaad duk abinda tagani seda ta fada musu salati kawai sukeyi zufa na keto musu ta ko ta ina duk da sun rasa abinda yahada su da vampires union, ana haka zeenat ta tashi daga suman da tayi sauka idonta yayi akan areef dake tsayi akusa da ita , hannu takai zata rarumeshi ta ciza yayi baya , damkar gashin kanta fanan tayi suna facing din juna kafin tasa mata hannunta abaki aikuwa nan da nan tafara shan jinin fanan dakatar da ita suke kokarinyi ta daga musu hannu haka sunaji suna gani zeenat tadinga zukan jinin fanan seda suka kai almost 30mint a haka kafin dukkansu biyu suka zube a sume. Se mun hadu gobe inme duka yakaim. Masu comment na gode Sosai Allah yamuku albarka.🥰🥰🥰 via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚 Page 4️⃣8️⃣ Zeenat ce ta fara farfadowa tana wani irin amai me dauke da jini da nama_nama seda ta amayar daduk wani abinda ke cikinta tsaban yanda aman yaci karfinta seda kaff kuzarinta yakare riketa sosai anty amina tayi tana kiran abu tazo ta gyara wajan daki takai zeenat ta kwanta bacci , fanan na kwance akan kujera har time din bata farfado ba kusan an hour shuru , tun suna san ran tashin fanan nan kusa har tsoro yafara kamasu jinta shuru duk wani abinda zasuyi danta tashi sunyi amma fa shuru , da karfin gaske Mr azaad ke jijjigata duk da haka bata tashi ba lamarin yabasu tsoro seyanzu suka kara danasanin barin zeenat tasha mata jini gashi yanzu taki farfadowa daukanta Mr azaad yayi yakaita bedroom dinshi yakwantar da ita akan bed sannan yarufeta da blanket.zama yayi agefenta hannunsu rike dana juna . ba abinda yake matsar dashi daga gefenta fa ce sallah gudun karta farfado ba kowa akanta har dare fanan shuru ba labari, haka ya gyara musu kwanciya suka kwanta. Asuba ta gari. tashi tayi ta zauna tana murza idonta kallonta tayi a dakin Mr azaad kuma babu shi aciki tuna abinda yafaru tayi danna wayarshi da ta gani a kasan pillow tayi karfe 5:40am ta gani batayi mamakin ganin haka ba tashi tayi tashiga toilet tayi wanka da alwala dressing room dinshi ta shiga bangaren jallabiya taje ta dau arche color tasaka yawa yamata ganin hijab dinta tayi akan kujera dauka tayi, tayi sallah tana zaune tana azkar ya shigo ya zauna akan kujera yazuba mata ido harta idar, juyawa tayi ta kalleshi kafin tace " Ina kwana Mr azaad" batayi tsammanin ze amsa ba taji yace " lafiya ! tashi kizo" tashi tayi taje ta tsaya a jikin kujeran da yake zaune , " malama ki zauna mana kin tsaya min akai" zama tayi dan tasan halinshi yanzu se ya fara , bayan ta zauna ne yake tambayarta " ko zan iya sanin fa'idan shan jininki da kika bar zeenat tayi?" bashi amsa tayi da " Mr azaad ka rigada kasan nidin wacece , dakuma abinda nake dauke dashi ina da ya kinin shan jinina da tayi ze iya fitar da maitar ajikinta" cike da gamsuwa da maganarta hadi da kaunarta yace " Allah yasa " ta amsa mishi da " ameen " satan kallonshi tayi suka hada ido itama ita yake kallo gyara zama yayi yace" to miye na kallon kuma " girgiza kai tayi . Kwantar da kanta tayi a kafadarshi ta lumshe ido kamar tana bacci tana shakar daddadar kamshin turarenshi , " fanannnn!" batare da ta Bude ido ko ta tashi ba tace " naam" shafa kumatunta yayi ya dan jashi kadan runtse ido tayi saboda yamata zafi ," fanannnn meyasa kike boyemin abinda ke ranki ?" cewar Mr azaad da har lokacin yana shafa mata kumatu , tashi tayi daga jikinshi ta zauna suna kallon juna tace " Mr azaad miye nake boyewa din ?" kwantar da kanshi yayi a jikin kujeran be sake ce mata komai ba ganin haka yasa fanan mikewa zata tafi bedroom dinta rike hannunta yayi yace " karki tafi please" kaman wani bako haka take kallonshi wai yau Mr azaad ne yake ce mata please anya ba mafarki takeyi ba kuwa, janyo hannunta yayi tafado jikinshi sunfi 5mint kafin ya sauke ajiyar zuciya yace " fanannnn am sorry for all mistakes nasan na miki Abubuwa da dama kiyi hakuri na miki alkawari hakan baze sake faruwa ba " sosai idonta ke fitar da ruwan hawaye tun tana hawaye harta fara shesheka azuciyarta tana godewa Allah da yasa Mr azaad ya gane abinda yake mata ba dede bane dukda bata taba rikeshi arai ba son da take mishi yasa bata ganin laifinshi . rungumota yayi ajikinshi yana rarrashinta dede kunnenta yakawo pink libs dinshi wura mata iska yayi acikin kunne da yasa taji tsigan jikinta ya tashi kafin ahankali cikin rada yace " baby be with me for the rest of my life! I love you " cak duk wata ma gudanar jinin jikinta seda yatsaya yadena aiki na wasu lokuta jin abinda ko da amafarkin wasa bata taba tsammanin ji ba hawayen farin ciki ne yafara saukowa daga idonta runtse idon tayi sosai tana rokon Allah yasa koda a mafarki nake Allah karkasa in tashi , haka ya dinga fada mata daddan kalamai dashi kanshi besan ya akayi ya iya su ba kawai abinda yasani duk abinda yafada mata daga cikin zuciyarshi yafito, rungumeshi tayi gam muryanta na shake tana kuka hade da dariya tace " I love you too Mr azaad inasanka sosai" raba jikinsu yayi ya manna mata kiss a goshi tare da fadin " Allah ya miki albarka my wifey" kallon cikin idon juna sukeyi babu ko kyaftawa hawaye me zafine ya gangaro kuncinta hannu yasa ya share matashi yana girgiza mata kai sannan yace" hawaye bashida gurbi a cikin rayuwarki har inde ina tare dake ! adah nabari kinyi amma banda yanzu domin kuwa inya sake saukowa zan hukuntashi " dariya tayi tana kwanciya ajikinshi tayi lamo . ______ bacci suka koma se 11 suka tashi komawa bedroom dinta tayi sakeyin wanka tayi ta shirya cikin atampa super Holland me purple color se touch din maroon da fari, dinkin doguwar rigace pencil gown me dogon hannu kasan hannun an mishi play wuyan rigar kuma adan bude yake batayi kwalliya sosai ba kawai powder tashafa se kwalli da libstick , dankunne da sarka tasa na gold tayi dauri me v feshe jikinta tayi da turarurruka masu dadi dakuma sanyayyar kamshi hills tasaka a kafarta maroon sak tafito a amarya tayi kyau sosai kamar wacce zataje gasar kyau gashi kayan sun matseta nafitan hankali duk wani shape dinta seda yafito fili . yau fess takejin ranta ji takeyi babu wanda yakaita farin ciki a irin wannar rana saboda wanda take matukar so shima yana santa, kallon kanta tayi a mirror ta kashe ido daya tare da fadin " excellent" knocking tayi yabata izinin shigowa, samunshi tayi yayi wanka ya shirya cikin kana nan kaya three quarter dark blue yasa da kuma riga armless baka waya yakeyi da yaseer dake tambayar shi jikin zeenat kamshin turarenta ne ya sanar dashi isowarta kallonta yayi da narkakkun idonshi kasa magana yayi kawai yayi hanging din kiran murmushi dauke a fuskanta, tafiya takeyi ahankali kamar wata me tausayin kasan, har izuwa lokacin be kawar da idonshi akanta ba cike da kissa ta zauna agefenshi ta shagwabe fuska tace " Mr azaad wannan kallon fah?" cize libs dinshi yayi kafin yace " to laifine dan na kalli matata?" rufe fuskanta tayi ajikinshi tana dariya dagota yayi yatsurawa libs dinta ido dayasha man baki matso da fuskanshi yayi daff danata ahankali ta lumshe manyan idanunta,hade bakinsu yayi waje daya yasakar mata hot kiss sannan yadago yana kallonta yace " baby kinyi kyau sosai" dadi ne taji yarufeta jin yabon daya mata tana kokarin yin magana sukaji anyi knocking tare da fadin " sir your food is ready" beyi magana ba sukaji alamar wanda yakawo abinci ya fita tashi sukayi sukaje falon sukayi breakfast. Haka suka kasance cikin farin ciki a wannan rana har dare suna part dinsu suna soyewa ( ohhhhh su Mr azaad an fada tarkon love) wanka tafito tana daure da towel daya tsaya mata a cinya zama tayi agaban mirror shi , lotion dinshi me dadi tashafa tare da perfumes dinshi yana kwance akan bed ya zuba mata ido duk wani motsinta akan idonshi yana binta da mayun idonshi duk inda tayi idonsa na kanta surar jikinta yana matukar daukan hankalinshi, tashi tayi ta nufi hanyar barin bedroom din kasa_kasa yace " ina zakije " waigowa tayi tana murmushi tace " Mr azaad zansa kayane sannan in hada mana dinner" gyada Kai kawai yayi ta fita a dakin , sleeping dress tasa rigar doguwa ce har kasa white color silky gown , hula tasa akanta dan bako yaushe takeson farin gashinta awaje ba ( matan aure da yan mata kudena barin kanku abude saboda shedanu kuma haramun ne inma bazaki iya daura dankwali ba ga hula nan sekisaka akanki barin kai abude bashida kyau ko kadan wasu kam ma ahakan suke shiga bandaki batare da hula ba to ku kiyaye Allah yakyauta) kitchen tashiga tama rasa me zata musu fast food fridge tabude gashashiya ta dauka tayi musu peppe chicken se ta soya chips data gama ta jerasu akan tray da su drinks , knocking tayi " come in" kawai yace mata , ajiye tray din tayi akan center table tayi saving dinsu batare da ta kalleshi ba tace " Mr azaad food is ready" tasowa yayi yazauna, cin abincin takeyi cikin nutsuwa ji tayi kamar ana kallonta yasa tajuya suka hada ido kayittaciyar murmushi ya sakar mata mayar mishi da murmushin itama tayi sannan tace " Mr azaad meyasa bakacin abincin ?" kallon abinci yayi ya kalleta kafin yace " to ki gama ci sekiyi feeding dina" dariya yaso bata yanda yayi kamar dan karamin yaro ajiye spoon din tayi tadawo gabanshi tazauna sa hannu tayi acikin plate din kazan ta gutsura takai mishi baki,karba yayi tare da hadawa da yatsanta daya " wayyo Mr azaad zaka cinye min hannu" murmushi kawai yayi bece mata komai ba,haka tadinga bashi abaki yana hadawa da hannunta har ya koshi yasha drinks itakuma ta tattara komai takai kitchen bata dawo ba seda ta wanke komai tukun ta maidasu wajan zamansu , bedroom taje tadau dogon hijab kasancewar kayan bacci ne ajikinta tasa slippers tashiga bedroom dinshi ganinta da hijab ne yasa Shima ya mike dukda besan ina zata ba riko hannunta yayi suka bar part dinsu, part din ummi suka shiga bakowa direct bedroom din zeenat suka shiga . _____ a can kuryan gadon suka sameta ta dukunkune awaje daya ta hada kanta da guiwa waje daya tayi shuru hawa gadon fanan tayi ta dafata a firgice ta dago tana kallonta rungumeta tayi tana kuka " nagode sosai anty fanan Allah ya biyaki da gidan aljanna kimin abinda bazan taba mantawa dake ba " shafa bayanta fanan takeyi tana fada mata kalaman da suke kwantar mata da hankali raba jikinsu tayi tazauna suna kallon juna fara magana fanan tayi " zeenat ki saki jikinki kinji kidena boye kanki yanzu fadamin yaushe kika tashi ?sannan kuma kinajin akwai alamar wani abu ajikinki?" girgiza mata kai zeenat tayi tace " yanzu ina jina kamar wata yantattiyar baiwa da aka yanta,banajin komai atare dani yanzu ! dazun natashi daga bacci yanzu kusan awa 3 kenan" shafa fuskanta fanan tayi tace " in sha Allah kin rabu dasu kenan da izinin Allah" Mr azaad tunda suka shigo yazauna akan kujera yake binsu da ido bece musu komai ba se godiya yakewa Allah aransa da yasa be rabu da fanan ba itadin seyanzu yagane ita din mahadin rayuwarsa ce tundaga lokacin da tafara haduwa dashi taimakon shi da family dinshi takeyi tabbas su masu saa ne da suka samu yar baiwa atare dasu kuma me daraja wacce tasan daraja , bashi da bakin da ze mata godiya shisa a kowani awa, a ko wani minti , a kowani dakika santa kara karuwa yakeyi azuciyarshi ,san rayuwa da ita na har abada yakeyi sede kuma kash hakan ba me faruwa bane. zeenat da batasan tare suka shigo da Mr azaad ba cikin yar zolaya tace " anty fanan ina heartbeat dinki kika baroshi kikazo nan?" hannu fanan tasa tana nuna mata inda Mr azaad yake ware ido tayi tana " yaya yaushe kashigo?" yar dariya yayi dan yanda ta zare idon kamar wacce taga abin tsoro be bata amsar data tambayeshi ba yace " yanzu kam babu abinda kikeji ko?" gyada Kai tayi watsa mata harara yayi nan take ta bashi amsa da " eh ya azaad babu abinda nakeji" " good ". Se munhadu Monday inda rai da lafiya. Masuyin comment na gode Sosai wayanda Kuma sukeyin comment da yanzu haka kurum suka dena ko sun karanta bame cewa kala bayan Kuma da suna comment Kuma sannunku da kokari kunji nace sannunku 🤔 yanzu kunzama daya da wayanda basayi. via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚 Page 4️⃣9️⃣ & 5️⃣0️⃣ suna kokarin barin dakin zeenat Abba da ummi suka shigo dubata , ganin su adakin ne abba yace " Kuna nan kenan ? fatima ya kikejin ki yanzu fatan ba wata matsala ko?" amsawa fanan tayi da " eh abba bakomai" kanta a kasa zama ummi tayi akan gadon tana magana da zeenat kafin ta juyo gun fanan fuskanta da dan damuwa tace " my feena Allah ya miki albarka, tabbas ke alkhari ce acikin rayuwarmu bamuda bakin da zamu gode miki kedin ya ta garice " wasa kawai fanan takeyi da yatsunta tana sakin murmushi dan taji dadin adduah ummi, Mr azaad yana zaune yana binsu da ido seyaji sun matukar burgeshi haka zalika abba ganin irin kaunan dake tsakanin ummi da fanan duk da sudin sirkanun juna ne . ( Yanada kyau ya kasance tsakanin ki da uwar mijinki ko matar danki akwai kyakyawar mu'amula , bakomai yake kawo hakan ba fa ce kyautatawa Koda uwar mijinki bata wani sonki ke yakamata kisamo hanyar da zata fara kaunarki domin kyakyawar mu'amula da ita ze kara miki mutunci da kima a idon mijinki barinma yaga yanda kike kyautata mata ,girmamata, koda yaushe kidinga bata girmanta yanda zakiwa mijinki biyayya itama kiyi mata tunda ita ta haifeshi har ya auroki to kinga kuwa bazeji dadi yazama bakya mutunta uwarshi ba , rashin kunya banaki bane barinma da uwar miji wasu ko kadan basa ganin mutuncin surkan su a zo a ta kana nan maganganu , yanda bazakiso a rena mahaifiyarki ba karki rena mahaifiyar wasu Kuma hakan shizesa batare da bata lokaci ba ki fara fita aran mijinki da kuma family shi har azo ana maganar zaa hadashi da wata ya aura tunda ke kin renasu. Abinda zakiyi domin siye zuciyar dangin miji shine yawan kyauta inde kinada hali kidinga musu kyauta ko bama na wani abu ba wata rana de kiyi girkinki me dadi ki tura musu, sannan kowa kidinga bashi respect yanda yakamata, babu ruwanki da sa kanki a kana nan maganganunsu koda kinji kowa na tofa albarkacin bakinshi kija naki bakin kiyi shuru dan yanzu abin magana baya kadan abinda zaki tofa daban abinda zaa canza kince daban tsakaninki dasu Allah yakyauta bawai kuma hakan na nufin ba ruwanki da damuwar family bane ah ah. Se abu na gaba ziyara musamman ma mahaifiyarshi , wannan de sune kadan daga ciki. Se kuma uwar miji in danki nada mata babu ruwanki dasu babu sa ido dakuma korafe_korafe kikama girmanki yanda sirkanki bazata samu hanyar renaki ba , karda kidinga nuna mata kyara hakan zesa taja baya dake dakuma family.) Sallama suka musu suka koma part dinsu hanyar bedroom dinta tayi yariko hijab dinta har cikin bedroom dinshi dariya takeyi ganin yanda ya kwabe fuska barinta yayi yashiga toilet yayi wanka fitowa yayi yasamu bata dakin shiryawa yayi ya hau gadon ya kwanta batare da ya kashe light din ba . dauke da sallama a bakinta tashigo hannunta rike da cup din coffee yana tiriri tana sanye da hijabi dogo ajiyewa tayi tazauna agefenshi tace " Mr azaad ga coffee" bece mata komai ba yadauka yafarasha da ya gama yakoma ya kwanta lura tayi da yan maganan basa kusa cire dogon hijab din tayi wasu sexy outfit ne ajikinta wayanda da su da babu duk daya mini skirt take sanye dashi na roba daya tamketa tam se rigarshi yar karama kamar vest gashinta tayi donot dashi atsakiyar kai jikinta se tashin kamshi yakeyi , arba yayi da kyakyawan surarta yana daga kwancen be mike ba yamata alama da ta kwanta ajikinshi hakan tayi , tayi lamo ajikinshi idonsu alumshe rike kugunta yayi dakyau sannan ya sa hannu ya warware donot din datayi da gashinta dan yafison su ahaka zubowa gashin yayi yarufe musu fuska mirginawa yayi da ita takoma kasa shikuma yamata rumfa da faffadar kirjinshi kare mata kallo yayi daga sama har kasa lokaci daya yaji kasala yarufe shi murya a shake yace " baby irin wannan kwalliya haka za ki barni kuwa ?" Yar murmushi tayi daya kara mata kyau tace " Mr azaad......" Yatsanshi daya ya daura akan libs dinta hadiye abinda zata fada tayi girgiza mata kai yayi yana fadin " shiiiish ! daga rana kamar ta yau karki kara kirana da wannan sunan banaso" " tom Mr azaad mezan kira ka dashi ?" dafe goshi yayi yana " oh my God" kunshe dariyar da yake kokarin fitowa tayi dan tasan metayi , rike habarta yayi yace " nace miki banason wannan Mr azaad din " tsayawa tayi tana kyafkyafta mishi ido kamar bata gane me yake fada ba kafin tace " Mr azaad na gane me kake nufi amma ai bansan dame zan kiraka ba" tsura mata mayun idonshi yayi lumshe idonta tayi dan bazata iya kallon cikin nashi idon ba sake daga habarta yayi yace " ki kalli cikin idona fanannnn" kamar wata qadangaruwa tafara girgiza mishi kai magana yakara mata " meyasa bazaki kalla ba? in harde na isa dake ki kalli cikin idona " babu yanda ta iya haka ta dago ta kalleshi ido cikin ido , jitayi jikinta yayi sanyi sosai kallon cikin kwayar idonshi ya kashe mata jiki lumshe idanu tayi kamar wata me jin bacci tace " na kalla habiby" , manna mata kiss yayi a kumatu jin sunan data kirashi dashi, sunce igiyoyin rigar yafarayi ta baya yafara shafata shuru tayi tana jin abinda yake mata, cire mata rigar yayi ya zubawa dukiyar fulaninta ido sa hannunta tayi ta rufe ido dan kunyanshi takeji musamman yanda taga yazubawa kirjinta ido, rufe su yayi da bargo yana wasa da ita, fanan so takeyi yayi sex da ita amma taga bedama alamar hakan kasa shuru tayi kasa_kasa muryanta a narke tace " Mr azaad kaban hakkina yau ina bukatarka" dakatawa da romancing dinta da yakeyi yayi yazubawa kyakyawar fuskanta ido jin maganar da ya fito daga bakinta yamutsa fuska yayi kamar bazeyi magana ba kuma can yace " baby you're to young bazaki iya daukana ba ki bari nan gaba inkin kara girma kinji" sosai kalamansa suka batawa fanan rai jin wai she's very young, mikewa tayi ta lullube jikinta da blanket din tabar mishi dakin , bedroom dinta tashiga tasa key ta rufe toilet tashiga tayi wanka tasa wani kayan baccin ta hau gado tayi adduah bacci takwanta duk ranta a dagule . Rike kai yayi ganin babyn nashi tayi fushi ta tafi , ita bazata gane me yake guje mata ba tayi yarinya sosai tausayinta yakeyi yafiso ko da zeyi wani abu da ita seta kara girma tunani yakeyi taya ze lallasheta sannan ya fahimtar da ita, yanda yake sonta bazeyi abinda ze sa tasha bakar wahala ba, haka jiki asanyaye yatashi yayi wanka yanufi bedroom dinta knocking yayi tana jinshi taki tashi balle ta bude mai haka har ya gaji ya koma nashi bedroom din gaba daya yayi abin tausayi. Tun datayi sallah asuba bata koma bacci ba seda ta gyara musu part dinsu ko ina yana daukan ido da kuma kamshi dawuwa yayi daga masallaci yasameta tana kunna burner tsayawa yayi akanta yayi shuru , dagowa tayi fuska ba yabo ba fallasa tace " Ina kwana Mr azaad?" be taba ganin ta canza fuska ba sede in kuka ne tayi amma ganin yanayinta nayau yasake tabbatar mishi da jiya kwana tayi da bacin rai kuma shi bawai yafadi maganar dan yabata mata rai bane, numfashi yaja sannan ya furzar yace " wifey fushi kikeyi da ni ne?" cigaba da abinda takeyi tayi batare da ta kalli inda yake ba tace " ah ah" " to in ba fushi kikeyi dani ba meyasa jiya kika tafi kika barni gashi yau mood dinki ba kamar yanda nasani ba?" cewar Mr azaad dake zama a gefenta gama kunna burner tayi bata tsaya bashi amsa ba ta wuce bedroom dinta ta kwanta dan maida baccin safe , yau de Mr azaad ji yayi kamar yasa ihu dan yarasa yanda zeyi ya shawo kan fanan ta hakura duk wani abu dakuma hakuri yayi amma daga bayama dena mishi magana tayi sede tadinga binshi da ido kamar batasan abinda yake fada ba. badan komai fanan ta mishi haka ba se dan tasan inde bayasan bacin ranta ze mata abinda take bukata domin hakan shine babban abinda takeso ta aiwatar kafin ta tafi amma shi baze gane bane hakan ba karamin taimaka musu zeyi ba . After one month. yau wata daya da rasuwan mansoor,haka kuma saura wata biyu da sati uku auren fawwaz da suhaima. Mr azaad yanzu duk ya susuce kwata_kwata fanan ta dena kulashi dan bayan abinda yafaru a wannan ranar ta yafe mishi sunci gaba da mu'amularsu ranar da ta nuna tana bukatar shi nan ma yasake fada mata abinda ya fada mata kwanaki tunda ga wannan ranar ta canza mishi , haka ya koma kamar wani mara lafiya ita kanta daurewa takeyi ji tayi bazata iya cigaba da shareshi ba saboda bashi take horarwa ba kanta take horarwa. Fanan ,zeenat, fawwaz ,areef, Mr azaad yau weekend suna zaune afalo suna hira Mr azaad kuma yana gabatar da online meeting aneesa ta shigo da trolley a hannunta gaba daya kallonta sukeyi suna jiran suga inda zatayi wajan Mr azaad tayi ta ajiye trolley din agefen kujera ta zauna ajikinshi,satan kallon fanan yayi dan yaga reaction dinta, ko kallon inda suke batayi ba taci gaba da bawa su fawwaz labari sukansu mamaki sukayi ganin ko ajikinta, zagayowa da hannunta tayi ta wuyanshi ta kwantar da kanta a kirjinshi tana zuba mishi shagwaba, tana cikin basu labari sukaji tayi shuru ta tsurawa Mr azaad da aneesa ido ganin bece ta tashi ajikinshi bane yasa ranta yakara baci dazun ma dannewa tayi dan tayi zaton Mr azaad zece ta tashi sekuma taga bece mata komai ba yaci gaba da abinda yakeyi. Shikuma badan komai yaki cewa aneesa ta tashi ba sedan bata mishi rai da fanan tayi wato ko ajikinta ta nunawa kowa bata kishinsa shisa yabar aneesar be kulata ba. Afusace fanan ta mike babu abinda zaka gani a idonta daya wuce wutan kishi fisgan trolley din aneesa tayi, tayi waje dashi ta cillar a compound din gidan sannan ta dawo kanta hannunta tasa ta jawota daga jikin Mr azaad kokarin faduwa aneesa tayi ta tsayar da ita kafin rai amatukar bace tace " aneesa wallahi kidena shiga gonata daga yau inna sake ko da ganin inuwar ki a part din nan na lahira seyafi ki jin dadi amma inkin musu ki gwada " cike da masifa take mata magana har haki takeyi tsabar yanda ranta ya baci , galla mata harara aneesa tayi sannan tace " ko! to bismillah duk sanda na shigo gidan nan senazo part din nan kuma ba wajan kowa zanzo ni ba fa ce baby , and baki da right din da zaki hanani zuwa gun my husband to be , kina zaune a gida kikasan ko yayi ajiyar baby a jikina" wata irin zafafan mari guda hudu fanan ta dauketa dasu kafin tajata da karfin gaske tayi waje da ita duk suna tsaye sunyi carko_carko ganin yau daya sunga fushin fanan abinda basu taba gani ba , Mr azaad kuwa yatafi duniyar tunanin yanda ze mugun hukunta aneesa saboda tanason tashiga tsakanin shi da matarshi yanzunma ya akare fushi takeyi dashi bata gama wucewa ba azo da wannar maganar . wucesu tayi ko kallon inda Mr azaad yake batayi ba tayi part dinsu shima bin bayanta yayi yasameta tana safa da marwa, tsayawa yayi abakin kofan ya harde hannunshi akirji yazuba mata ido ganin yanda ita kadai take cika tana batsewa " Mr azaad banta ba tunanin haka daga wajanka ba wato kayi hakan ne dan kaci min fuska agaban budurwanka ! har zatace min ko kayi ajiyar baby ajikinta ni ina matarka bakayi ajiyar ajikina ba se ajikin wata daba muharramarka ba" ta karishe maganar idonta tabb da hawaye , betaba tsammanin haka daga wajanta ba shi tunaninshi Koda kowa baze fahimce shi ba ita yakamata ta fahimce shi dakyar ya iya bude baki yace mata " fanannnn ni kike zargin aikata alfasha da wata ?" Yagama maganar yana nuna kanshi da yatsa " ni ba alamusuru bace dazan san hakan balle inyi shaida kuma aiba tare muke fita ba dazansan abinda kake aikatawa awaje nasani ko....." dauketa da mari wanda yasa tayi shuru tadena gane komai ta dafe setin inda ya mareta nan take hawaye yafara kwarara daga idonta " fanan haryakai ki yarda da abinda wata zata fada miki akaina kizo zakimin rashin kunya amatsayina na mijinki kin ban mamaki wannan shine irin son da kikemin ?" cewar Mr azaad da lokaci daya ciwon kai yarufeshi yadade beshiga cikin matsanancin bacin rai irin na yau ba tabbas fanan ta bashi mamaki dukda yasan shima yanada laifi amma ita meyasa zatayi saurin yanke mishi hukunci batare da tasan gaskiya ba , bacin ranshi da kowa yake gudun ganin shine yau yamotsa badan kowa ba sedan fanan jikinshi babu abinda yakeyi in banda aikin rawa da tsuma, share hawayen fuskanta tayi taci gaba da fadin " eh nafada din Mr azaad aiba karya bane ni ina matsayin matarka ka taba kusanta na ne nasha binka da maganar hakan amma seka tsaya kanamin wasu maganganu da hankali baze Kama ba kana cemin yarinya! Ita ai ba yarinya bace ta girmeni nesa ba kusa ba se kaje ku daura daga inda kuka tsaya" batare da yace mata komai ba yadauketa cakk dan baya cikin hayyacinsa saboda yau tagama tunzurashi , bedroom dinshi yanufa da ita ya wurgata akan bed cire rigan jikinshi yayi yahau bed din ya fincike hijab din jikinta yasa hannu ya yage rigarta gida biyu , komai da zafi yake mata shi saboda baya cikin nutsuwarshi daze tuna itadin virgin ce , jin yana kokarin ratsata ne yasa tayi kara me karfi tsaban azaban da taji dukanshi takeyi da iya karfinta da yakushi amma ko kadan bayajin yarigada yayi nisa bayajin kira kukan da takeyi bayaji balle yamata rangwami hakuri take bashi tana kuka kamar ranta zefita, tun tana iya kukan har numfashinta yadauke cak bata motsi ta suma , seda yasamu gamsuwa tukun yasauka ajikinta nan ne hankalinshi yadawo jikinshi kallonta yayi yaga babu alamar tana numfashi kai idonshi kan bed din yayi yaga yanda yayi dama_dama da jini ko ina yabaci da jini yamata kaca_kaca betabajin tsoron wani abuba arayuwarshi seyau rike kanshi yayi dayaji yana neman fita danasanin ne yacikashi tabbas bacin ranshi be mishi rana ba babban abinda yake guje mata kenan amma ita bata gani gashi abinda yaje yadawo, tana kwance bata numfashi gashin kanta duk ya barbaje fuskanta ya kumbura musamman wajan libs dinta tausayinta ne yakamashi yama rasa mezeyi mata yanzu gashi shiba likita ba tunanin kiran doctor ammar yayi se kuma ya fasa kishinsa baze bar namiji ya kalle mishi mata ba tunawa yayi da anty amina na gida layinta yakira bugu biyu yayi ta daga muryanshi dabaya cikin nutsuwa taji yasauka mata a kunne " big anty kiyi sauri kizo wifey ba lafiya " kitt yakashe kiran tanajin hakan ta mike dasauri dan bata raba dayan biyu na yau fanan tazama cikakkiyar mace , toilet yashiga yayi wanka shaf_shaf yazura jallabiya baka ajikinshi dawuwa inda take kwance yayi da dabara yacire bedsheet din daya baci yakaishi cikin washing machine underwear dinta dasuke kasane ya kwashesu yakaisu toilet yadawo yarufeta da blanket yazauna yarike hannunta yayi tagumi. _____ knocking anty amina tayi cikin sauri yabude mata kofa ganinshi acikin wannan halin ya tabbatar mata da fanan tasha bakar azaba wuceshi tayi tabarshi a bakin kofa tashiga ciki kwance tasameta yanda yabarta seda gaban anty amina ya fadi da ta kalli fanan a wannan yanayin, kallonshi tayi tace " kadan bamu waje kaji" gyada mata kai kawai yayi yafita yazauna afalo. Toilet tashiga ta hada ruwan zafi acikin jacuzzi taje ta dauki fanan din dan bawani nauyine da ita ba tasata acikin jacuzzi,nauyayyar ajiyar zuciya tasauke dukda haka tana asume bata farfado ba , seda ta tabbatar da ruwan zafin ya ratsata sosai kafin ta canza wani daya dan fishi zafi , sosai ta gasa mata jiki dan Mr azaad yayi mata barna da take tunanin dole se an mata dinki , kwantar da ita tayi akan bed tasa mata jallabiyar Mr azaad data dauko a dressing room dinshi layin kawarta ta kira doctor safiya, bayanta dagane tamata bayani kafin ta kashe , Bayan 40mint doctor safiya tazo gidan kiran layin anty amina tayi ta sanar mata ta iso fitowa tayi tashigo da ita, Mr azaad na falon yakasa fita a part din ganin doctor da anty amina ta kira ne yasa hankalinshi kara tashi , dubata doctor safiya tayi kafin ta kalli anty amina tace " kawata yarinyar nan baa mata shigan sauki ba sekace fyade gaskiya tasha wahala se an mata dinki " gyada Kai kawai anty amina tayi dan itakanta fanan tabata tausayi . dinki doctor safiya tayi mata hade da allurai ta daura mata drip da fadawa anty amina abinda yakamata adinga mata suka fito ta rakata har inda tayi packing din motar ta, tana dawuwa falo ta iske ummi na zaune tana jiran dawuwarta " nikam daughter waye ba lafiya danaga kamar doctor safiya tazo gidan nan?" cewar ummi datake jiran amsar anty amina ajiyar zuciya anty amina ta sauke kafin tace" ummi feena ce ba lafiya shine azaad ya fadamin nikuma na kira doctor safiya" tunda ummi taji hakan tagane inda maganar ta dosa ta wani bangaren tana farin ciki wani bangaren kuma tana tausayin fanan dan tunda harda doctor tasan tasha wahala Allah yakara sauki ummi ta mata anty amina ta koma part din, ganin sun fitane yasa yashiga dakin dakyar yake iya daga kafarshi jin shima kamar beda wani ishashen lafiya durkusawa yayi agabanta yariko hannunta daya, ciki_ciki yake fadin " am sorry wifey !am so sorry ki yafemin nasan ni me laifine agareki " yafada yana kifa kanshi akan bed din , hannunta dake dauke da drip din tasa akanshi tana shafa gashinshi dagowa yayi yana kallonta idonta dayayi ja ya kumbura yana kanshi tana sakin murmushi da fuskanta daya dan kumbura dakyar ta iya bude baki tace " thank you Mr azaad" mamaki ta bashi ganin bataji haushin abinda yafaru ba sema murmushin da ta mishi hadi da godiya shafa kumatunta yayi yace " am sorry wifey nagode sosai Allah yamiki albarka narasa wani irin godiya zan miki kimin kyautan da bazan taba mantawa dashi ba har iya karshen rayuwata" murmushi kawai takeyi suna rike da hannun juna dan yamutsa fuska tayi dasauri yace " meyafaru baby ?" a shagwabe tace" habiby yunwa nakeji" tashi yayi dan sauri haryana kokarin yin tuntube ze fita kenan anty amina tashigo riko hannunshi tayi tana " wannan saurin fa ?" Sosa wuyanshi yayi yace" wifey ce tace tanajin yunwa " kai kallonta tayi kan gadon da fanan din take kwance tayi taga ta farka sannan ta maida kallonta kanshi tana " ka samu waje kazauna zan hada mata yanzu kai dinma kamar baka da lafiya naga " tafada tana taba wuyanshi jikinshi akwai dan zafi zama yayi akan kujera itakuma taje wajan fanan da take binsu da ido tace mata " sannu ko my feena" sauke idonta tayi tanajin kunyar anty amina shikenan yanzu kenan anty amina tasan abinda yafaru tsakaninta da Mr azaad yar murmushi anty amina tayi dan tasan kunyar fanan baze barta su hada ido ba yasa tafita a falon tashiga kitchen dinsu ta hada mata farfesun naman rago yaji kayan hadi da yaji ta samata sannan tasawa Mr azaad dakin ta koma ta ajiye mishi nashi agabanshi tace" oya kaci kaima " sa pillow tayi ta gyarawa fanan din tadan zauna kadan ta fara bata abaki harta koshi , shima Mr azaad yaci amma bawani sosai ba duk hankalinshi na kan fanan da takeci kadan kadan tana yamutsa fuska magani anty amina ta bare ta mika mata kin kallonsu tayi dama tunda yaga an balla magani yasan zaa rina tasowa yayi daga inda yake zaune yazo yakarbi maganin a hannunta yasasu a cikin glass cup ya jiqasu suka narke yabata tasha dakyar tana qaqarin amai lallabata yayi harta dena yunkurin amai din anty amina komawa gefe tayi tana kallonsu sunyi matukar burgeta bugu da kari sun dace da juna musamman yanda Mr azaad yake tarerayan fanan . drip din karfe 7 nadare ya kare shi yacire mata yadauketa yakaita toilet yamata wanka yakara gasa mata jiki da ruwan zafi tayi alwala,ya nadota a towel kamar wata jaririya kayan bacci yasamata sannan yabata doguwar hijab ya shinfida mata sallaya daga zaune ta rama sallalolin da ake binta . zeenat ce tayi knocking yabata izinin shigowa basket ne a hannunta hade da flask zama tayi akan kujera tace " anty fanan sannu ya jikin ?" " da sauki zeenat ya ummi yau kwata_kwata banje wajanta ba " cewar fanan tana zaune akan sallayar bata tashi ba bude flask din yayi dake dauke da lafiyayyar kunun gyada ummi ce ta hada mata shi da kanta mika mata cup yayi takarba ta kai baki dadi ne yaratsata batasan lokacin da ta shanye ta mika mishi cup ya kara mata ba, zuba mata yayi yabata zeenat ce tace " anty fanan ashe kema kinason kunu ? ummi ce ta miki da kanta" " laah da gaske ummi ce tamin?" cewar fanan dake shan kunun , shide Mr azaad surutun zeenat ya isheshi, fanan seda ta shanye kofi uku kafin taji ta koshi , gyara zama zeenat tayi tace " anty fanan amma meye yake damunki ?" daka mata tsawa Mr azaad yayi yace " tashi ki fita ina ruwanki da abinda yake damunta " tun kafin yagama magana zeenat ta fita da gudu , kunshe dariya fanan tayi tana girgiza kai hararan wasa Mr azaad yamata yace " ke ko ?" Kokarin tashi tayi zata hau kan gado tasa kara zata fadi ya riketa dan ita tamanta akwai ciwo ajikinta kwantar da ita yayi akan bed din yana mata sannu , turo baki gaba tayi tace " nide bazanyi hakurin ba se kamin tausa " nade hannun jallabiyarsa yayi yace " ni awa ai dolena inyi abinda baby takeso " mammatsa mata jiki yafara yana mata tausan tailan hhhh tsabar dadin tausan har tayi bacci. Bakin hayaki ne yake tashi acikin wata kungurum din kogo da girmanshi baze misaltu ba duk suna sanye da bakaken kaya jikinsu duk gashi yan kungiyar satanic kenan , tanzarzar na zaune akan kujeran mulkinsa su kuma yan kungiyar sunyi circle ga yara da manya dasuke kwance amace kusan rai goma an sare musu kawunan su jini nata zuba a acikin manyan kwarya seda yacikasu dam tukun, na hannun daman tanzarzar yamike yaje gaban jinin yafara wasu surkullenshi da sambatu irin nasu na matsafa walkiya ne ya bayyana akan kwaryar jinin , yasa wata karamar kwarya ya dibo jinin aciki yakai bakinsu yafara sha kamar Wanda yasamu ruwa , mommy ce second haka suka shanye jinin duka tanzarzar na zaune akan kujera yana sakin yar iskar murmushi da wannan muryar tashi mara dadin ji yafara magana " sadaukarwa ya kammala kowa yafadi bukatar shi da yakeso ayi mishi " matsowa kusa mommy tayi tace " ya shugaba nasan kasan abinda akamin an kashemin dana! da yardar ka ina bukatar daukar fansa akanta " bushewa da mugun dariya tanzarzar yayi yace " nasan da hakan amma kisani ke kika fara takalar yaki tsakaninmu da vampires union, duk hurdar mu bama shiga harkan wayanda ba yan kungiyar mu ba amma ke kika kashe musu har mutane uku. yanzu gashi seda sukayi sanadiyar rayuwar danki sannan wacce zaki dau fansar akanta tana dauke da jinin sarauniyar nasminaya duk abinda zaki mata baze tabayin aiki ba ki bari nan gaba inmun shafe tarihin ita sarauniyar tasu semu dawo kansu " durkusawa tayi kafin ta koma wajan tsayuwarta , alh Ibrahim tijjani mahaifin aneesa ne yafito yace " ya shugaba nikuma so nakeyi in kashe azaad muhammad mainasara bayan ya auri yata aneesa " sake bushewa da wata dariyar tanzarzar yayi yace " kar wanda ya sakemin maganan da yashafi wayanda suke tare da sarauniya domin muddin tana raye bazata bari a cutar da wani nata ba so nakeyi in kwace jaaazana atare da ita sannan in aureta ! muddin mukayi nasara akansu dole sena maida ita baiwata sannan in aureta in kashe mijin nata hhhhhhhhhhh" ya gama maganar yana wata muguwar dariya , cikin tsawa dayasa kogon girgiza yace " duk ku bace kuban waje " jinjina mishi sukayi kafin dukkansu suka koma jemage suka fire sama . Adamawa Yola agidan alh badamasi me ruwa. Duk ya tara iyalanshi a falo yana zaune yana girgiza kafa ga nusaiba a zaune akasa kan carpet bude taro yayi da adduah yafara da " nusaiba nasan kinsan dan ke na shirya wannan zaman kinason ki nuna min ni ban isa dake ba ! Kin na ce akan azaad mainasara ya nuna baya raayinki amma ke kinqi fahimta na hadaki da dan uwanki dayake sonki nanma kinqi to bari kiji kar insake jin kinje mainasara family kin tayar musu da rigima tunda yanzu yariga da yayi auranshi kuma magana ta karshe nariga da na miki miji ko kinaso ko bakyaso dan uwanki lukman zaki aura" tashi tsaye madina tayi ta tsaya tana rike kugu " baa isa ba! Baa isa ayiwa yata auran dole ba , bazaku kashemin itaba ku cuceni yauwa " taja hannun nusaiba fuuuu suka bar falon girgiza kai alh nasir yayi mahaifin lukman din , hajiya Hussaina de bata da bakin magana tunda alh yagama fadar abinda ze fada, haka zalika alh me ruwa be sake cewa komai ba abinda yasani de shine muddin madina tayi kokarin tarwatsa wannan auren ze dau mummunar mataki akanta . " auta zoki kaiwa yayanku abincinshi daki nasan yana nan yana bacci be tashi ba " cewar mama da ta gama zubawa kowa abinci tunda akayi wannar case din na tsakanin ya usman da khairaty yadena shiga cikin mutane ko kasuwa ba wani zuwa yakeyi ba yarame yayi baki kamar ba ya usman ba babu yanda basuyi dan ya sake amma abu yaci tura harsuka gaji suka zuba mishi ido koda ya al ameen yaje dan yamishi hira haka zeyi shuru ya barshi harya gaji yayi shuru haka suka zubamai ido kawai kuma tundaga wannan ranar be sake ganin koda me kama da khairaty ba , shigowa dakin auta tayi hannunta na rike da kulan abincin shi wata razananniyar kara tasa da gudun gaske suka shigo dakin nashi cikin tashin hankali dan karan da auta tayi ta firgitasu kwance suka samu ya usman acikin aman jinin da yayi asume innalillahi wainna ilaijiraji unnn kawai suke iya furtawa daukanshi ya al ameen yayi yasashi a mota shida suhaima da auta baba kuma shida mama basu tsaya ako ina ba se a medical center na cikin garin gombe admitting dinshi sukayi a emergency , taimakon gaggawa suka fara bashi kusan bayan 1 hour suka fito suna goge zufa tasowa sukayi suna tambayarsu ya jikin nashi kallon baba da ya al ameen doctor yayi yace " ku biyoni office" yayi gaba suka bi bayanshi duk sun matsu suji me ze fada zama sukayi doctor yacire glass din idonshi yafara magana " am ranka yadade kuyi hakuri da abinda zan fada muku! dan ku gaskiya yana cikin wani halin rayuwa ko mutuwa duk da ranshi baa hannunmu yake ba amma a halin dayake ciki yanzu tabbas inbe samu abinda yakeso ba zaa iya rasa shi domin yakamu da ciwon zuciya kuma saura kadan ya buga , a shawarce kafin nan da awa 2 ku gaggawar samo mishi abinda yakeso saboda inya tashi yayi arba dashi ko hakan ze taimaka amma in ba haka ba yana cikin danger" tunda doctor yafara magana baba da ya al ameen suke zufa kamar wanda aka watsawa ruwa sun jike tashin hankali da baa sa mishi rana yanzu tayaya zasu fara wannan kwamachalan hada aljan da mutum . via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚 ( J. W. A 📚📚📚) PAGE 5️⃣1️⃣ & 5️⃣2️⃣ Damuwa iya damuwa su baba sun shiga fadawa su mama yayi suma hankalinsu inyayi million seda yatashi duk sun shiga tashin hankali sun kasa tsaye sun kasa zaune yanzu me sukasan zasuyiwa ya usman ko giyar wake suka sha de babu yanda zaa hada aljan da bil adama, matsawa suhaima tayi awajansu ta kira layin fanan , fanan na manne ajikin mijinta suna bacci kadan kadan takejin kamar ringing din wayarta idonta arufe ta dauka tasa akunne tace " assalamualaikum" amsawa suhaima tayi tana " fanan ya usman ba lafiya yanzu muka kawo shi asibiti yana aman jini" duk baccin dake idonta lokaci daya ya kaurace mata ta zauna cikin damuwa tace " innalillahi wainna ilaijiraji unnn! suhaima meyake damun ya Usman din ?" Abangaren suhaima ta bata amsa da " doctor's sunce yanada ciwon zuciya kuma daf yake da bugawa inde baa samo mishi abinda yakeso ba " da karfin gaske kirjin fanan yake bugawa taya sukasan zasu fara wannan kwamachalan , jin maganar ta ne yatashi Mr azaad daga bacci kallo daya yamata ya gane akwai abinda yake faruwa sa hannu yayi ya karbi wayar yasa akunne yaji muryan suhaima tambayar ta yayi meyake faruwa suhaima kamar wata yar jarida ko hadiye yawo batayi se jero mishi jawabi takeyi , sosai lamarin ya girgiza shi jin usman harda aman jini katse Kiran yayi yatashi yasa jallabiya yadau car key dinshi kallonshi fanan tayi kafin tace " habiby ina zakaje da wannan tsohon daren?" dawuwa yayi inda take ya manna mata kiss a kumatu yace " asibitin zanje zanturo miki zeenat ta tayaki bacci" langwabe kai tayi tace " ayyah habiby am zan bika" girgiza mata kai yayi kawai yafice adakin part din ummi yaje ya ma zeenat knocking tasowa tayi tabude dakin tana mustsuka idonta, waro ido tayi ganin mr azaad a bakin bedroom dinta a irin wannan lokacin 12:58am nadare " kije ki taya antynki kwana zanje asibiti " abinda yace mata kenan yafice securities biyu ne suka rakashi har asibitin a zaune yasamesu duk sunyi cirko_cirko suna neman mafita gaishesu yayi ya zauna akusa da baba sukaci gaba da maganar lallai gaskiya lamarin usman akwai rudarwa yanzu mafita kawai suke nema haka suka kwana bakin ward din auta ce kawai tayi bacci sukam sun gagarayin bacci sakamakon jikin ya usman daya tashi numfashinshi yana sama yana kasa idonshi ya sauya kala duk sunyi tsammanin fitan rai ne dan abinda yakeyi kamar wanda zewuce lokaci dayane duk suna waje suna ta mishi adduah likitoci kusan shida sun hadu akanshi domin ceto rayuwarshi , family mainasara ne suka shigo asibitin securities na rike da basket na abinci, ciki kuwa harda fanan da ta nace se ta bisu taga jikin dan uwanta dan yanda take tafiya ma mutum ya lura yasan something is fishy haka de anty amina ce take rike da ita kuma ta daure sosai tana tafiya dede dakyar saboda batason kowa ya fahimci wani abu, anty amina tana rike da ita suka shigo zaunar da ita anty amina tayi suka gaisa da mama da mutanen wajen , Mr azaad beji dadin zuwan da akayi da itaba dan yasan wahala kawai takesha daurewa takeyi saboda irin karfin halinta , ummi na tare da maman tana kwantar mata da hankali, fitowa likitocin sukayi dukansu sukayo kansu suna tambayarsu ko anyi dace daya daga cikin likitocin ne yace " a yanzu de munyi nasarar dedeta numfashinsa da bugun zuciyarshi amma zuwa anjuma kuma duk abinda ya biyo baya muqaddarine daga Allah"jikinsu yayi sanyi sosai babu abinda sukeyi se adduah samun sauki dasuke yiwa ya usman, fanan tayi tagumi tana cikin tsaka me wuya yanzu bata da wani solution inde tayi sanya akan al amarin zata iya rasa dan uwanta na jini mafi soyuwa agareta , wani tunani tayi na meze hana ta mantar dashi komai wata zuciyar tace mata" hakan bazeyuba inde ya manta komai zezama yamanta da kowa dake cikin rayuwarshi hatta shikanshi se yamanta dashi wanene" kallon su mama tayi taga yanda duk suka shiga cikin damuwa aranta tace" yah Allah kadubi wannan bawan naka ka sassauta mishi abinda yake damunshi ka kawo mishi mafita kabashi lafiya" wayar Mr azaad ne yayi ringing yaduba yaga abba ne picking yayi yace " hello abba" abangaren abba ne yake tambayarshi ya jikin usman din yabashi amsa dasauki mikawa baba wayar Mr azaad yayi suka fara magana . Suna ahaka aka fito da ya usman dake kwance rai a hannun Allah akan gadon marasa lafiya nurse's suna turawa zuwa resting room, wani ward babba shi kadai aka kaishi sannan nurse tace musu " zaku iya shiga " duk shiga sukayi, sukayi shuru , ahankali yabude bakinshi yafara magana jini na fitowa abakinshi yace " khairat karki barni kinji wallahi inasonki" sa tissue ya al ameen yayi ya goge jinin dake fita abakinshi, duk tagumi sukayi sun rasa abinyi , ware idonshi yayi yafara bin yan dakin da kallo kokarin tashi yafara dasauri ya al ameen ya gyara mishi pillow ya zaunar dashi , duk se ya jiki suke mai baya iya ce musu uhmmm balle uhmm uhmmm , se kawai kallonsu yakeyi kamar be sansu din suwaye ba doctor ne yadawo yana mishi preking din drip din . Dukan kofar dakin ward din akeyi kamar zaa fasa shi dan tsaki doctor yayi yace" ko su waye haka oho kilama wasu daga cikin yan sakatiri ne " mikewa fawwaz yayi ya bude kofar wata matashiyar budurwa ce wacce bazata wuce shekara 16 ba a duniya kayan jikinta duk ya kode yafita a hayyacin sa kodadden hijab dinta har kasa tasa hannu da hijab dinta ta kare fuskarta tana kuka tashigo dakin duk juyowa sukayi suna kallonta , cikin siririyar muryanta tace " doctor dan Allah kazo ka dubamin Yayana karya mutu ya barni " ji yayi kirjinshi na bugawa da mugun karfi muryanta seda yaratsa dukkan wani sassar jikinsa zabura ya usman yayi jin muryan da be taba tunanin jiba ganin ya zabura ne yasa suka rirriko shi sunyi tunanin wani abunne yasa meshi ko kuma ciwon ne , dirkowa yayi daga kan gadon ya tsaya agaban yarinyar hannunshi yasa ya cire hijab din da ta rufe fuskanta dashi ja baya yayi yana furta "khairatyyy" da karfi , kallonsu suka maida kan ita yarinyar bakaramin girgiza sukayi ba ganin sak me kama da khairaty babu abinda ya rabasu sede ita komai nata normal ne saboda ita bil adama ce itakuma khairatyyy komai nata over mikewa sukayi tsaye suna al ajabin wannan iKon Allah , bata ko kalle ya usman da yake mata magana ba taje ta zube guiwanta akasa ta kama kafar doctor tana " doctor dan Allah ! dan annabi kamar yanda Allah yarufa maka asiri ka taimakemu mudin narayu ne, ka cece rayuwan yayana ze mutu wallahi duk duniya shi kadai ne gata na bamuda kowa kayi hakuri kaje ka dubashi" ta gama magana tana sheshekar kuka sude kawai ido suka zuba mata tausayinta ya darsu aransu ganin yar karamar yarinya da ita me kananun shekaru tana irin wannan rokon tabbas suna cikin mawuyacin hali, without thinking twice ya usman ya dagota yana kallon cikin manyan idonta da suka kasance brown masu daukan hankali yace " fadamin meya sami yayan naki ?" Share hawayen fuskanta tayi tace" bashida lafiya ne yanzu kuma dakyar yake numfashi dan Allah ku taimakamin kucewa likitocin nan su dubashi, in yayana ya mutu nima mutuwa zanyi " girgiza kai ya usman yayi yace " my girl bazaki mutu ba babu abinda ze sameki da shidin ! In kika mutu nima mutuwa zanyi" gyada mishi kai kawai yarinyar tayi dan bata gane inda zancen nashi ya dosaba , riko hannunta yayi suka fita a dakin shida ita sukayi dakin da yayan nata yake. Duk zuru sukayi suna kallon ikon god daga su har doctor bin bayansu sukayi da kallo ganin lokaci daya ya usman ya watsake kamar bashine bashi da lafiya ba yana kwance harda su aman jini amma lokaci daya yakoma rass dashi harda jan hannunta sukayi waje , kallonsu doctor yayi yace " dama itace abinda yakeso kenan ?" Yar dariya sukayi suka amsa mishi da "ehh " kawai dan basusan amsar da zasu bashi ba , dariya yayi yace " soyayya kenan to Allah yabasu zaman lafiya" Ameen suka amsa shikuma yafita yabi bayan ya usman da yarinyar, sude ganin abun sukeyi kamar almara duk da ance dama kowa yanada me kama dashi guda bakwai amma ai khairaty ba mutum bace taya akayi sukayi kama da wannar yarinyar to basuda me basu amsa yasa suma sukayi dakin da yayan nata yake kwance, tunda wanda suke jinyar yayi waje ya barsu suma suka fito, suhaima ce tace " ohhh su ya usman abin nema yasamu " dariya zeenat da fanan sukayi harara fawwaz yamusu na wasa yace " kude Allah yashiryeku ! ke Kuma baby danyi maganinki tunda kowa tsokanan shi kikeyi " nanma dariya su fanan sukayi dan dama sudin ne suka rage abaya su ummi da mama,baba Mr azaad,anty amina,duk sunyi gaba sun barsu abaya. Ya al ameen ne yace " nikam bazan iya shirmenku ba nayi nan kaide da zaka iya sekata fama " yafada yana nuna fawwaz sannan ya shige ciki suma rufa mishi baya sukayi wannan karon zeenat ce take rike da fanan kuma sosai ta daure tana takawa . A tsaye suka samu ya usman da yarinyar akan yayantan doctor kuma yana dubashi shima kanshi yaro ne matashi da be wuce shekara 19 ba fari kyakyawa suna kama sosai da kanwar tashi yana kwance yana baccin wahala zama sukayi akan kujerun dakin kallon yarinyar doctor yayi yace " Yan mata ki kwantar da hankalinki yayanki ze samu sauki da izinin Allah kinji" murmushin yaqe tayi shikuma ya fita , mama ce tace " zo nan yata " ita se yanzu ma ta lura dasu dan dazun da tashiga tsaban hankalinta baya jikinta bata wani lura dasu ba jiki asanyaye taje wajan mama ta tsuguna har kasa da siririyar muryanta tace " mama gani" wani irin dadi mama taji jin yarinyar ta kirata da mama lokaci daya taji hankalinta ya kwanta da yarinyar gyara murya mama tayi tace " meye sunanki ? Su waye ku?Kuma sannan ina iyayenku?" Share kwalla yarinyar tayi tace " sunana hairah ! Yayana kuma sunanshi hafiz mu yan garin gombe ne iyayenmu sun rasu wata 9 dasuka wuce, kuma tunkafin su rasu dama bamuda kowa tom dama babanmu ne yakeyin sanaar dako yake siya mana abinda muke sawa cikinmu se yazo yarasu bayan ya rasu da sati daya mamanmu ma tarasu , tundaga lokacin komai ya canza mana bama samun abinda zamuci se nayi mana bara tukun wata rana mu samu wata rana kuma mu kwana haka shine yayana yashiga kasuwa shima yafara yin dakon inya samu kudi se ya siya mana waina ko kuma rogo ko garin kwaki shine yazo yafara ciwo wani mutum dayake hayan will bairon agurinshi ya kawo shi asibiti tunda yazo sau daya be sake dawuwa ba babu kudin dazaa dubashi shisa likitocin babu wanda yakebin ta kanmu " ta gama magana tana kuka me tsuma zuciya sun matukar tausayawa rayuwarsu domin yaran sunga rayuwa ba uwa ba uba dole su wulakanta tunda babu dangin iyayen , ga ta mace kuma karamar yarinya riko hannunta mama tayi ta zaunar da ita a gefenta tana lallashinta fanan dake gefensu ta zubawa hairah ido tana kallon tsantsan kamarsu da khairaty amma tayi murna da faruwan hakan , ya usman de ya kame akan kujera se faraa yakeyi kamar wanda aka mishi kyauta da kujeran makka yanata kallon hairah ,Mr azaad shi abun ya usman ma dariya yaso bashi ganin irin murmushin dayake sakewa tsaban abinda yake nema yasamu. Baba ne yace" mamansu kuje gida mazan zasu zauna da shi ku dauketa kaima usman tashi ka bisu tunda kaji lafiyar dole ja'iri kawai " tunkafin yagama magana ya usman ya mike riko hannunta suhaima tayi duk suka fito dasu ummin sukayi gidansu fanan din a falo suka yada zango fanan kuma takai kanta dakinta tana yar dingisa kafa binta da kallo mama tayi dan tun zuwansu ta lura da tafiyarta murmushi ta sake kawai , nunawa hairah bathroom suhaima tayi ta shiga tayi wanka sosai, tafito sanye da dogon kodadden hijab dinta na roba ,masha Allah itama ba laifi dukda yanzu ta fara tasowa amma tana da sura me kyau, riga da skirt din atamfa suhaima ta bata sabo dal dan tunda ta karbosu agun dinki kala biyar taga duk sun mata kadan ta ajiyesu shine yanzu ta bawa hairah daya ta ajiye mata sauran , das kayan suka zauna mata ajiki be kamata ba tayi kyau sosai shafa mai tayi kawai ta zauna can nesa dasu duk a takure take se dar_dar take ganin haka yasa fanan ce mata " hairah ki saki jikinki damu kinji kidauke mu kamar yan uwanki na jini karki dinga dar dar daga yanzu kinzama yar gidan nan saboda haka feel free " godiya tayiwa fanan sosai harda kwalla , shigowa dakin zeenat tayi hannunta rike da plate din abinci tuwon shinkafa da miyar kubewa bushashshe yaji kifi banda hade da nama se kamshin man shanu yake, lokaci daya fanan taji yawonta ya tsinke mikawa hairah plate din zeenat tayi da ruwa , tana kokarin zama fanan tace " yau naga wariyar launin fata zee nizakiwa haka ?" Cike da mamaki suke kallonta musamman ma zeenat duk tunaninta tayi mata wani laifin ne tace " anty fanan mena miki?" Bata fuska fanan tayi tace" ni shine bazaki dibo min abincin ba ko " kallon juna suhaima da zeenat sukayi kafin suka fashe da dariya harda tafawa hada baki sukayi wajan fadin " kice mun samu karuwa " dalla musu harara fanan tayi da dara_daran idanunta tace " banason iskanci kun fara ko ?" Haka sukata tsokanata tayi banza dasu kiran layin Amira tayi ta tambayeta ko tana gida , daka tsalle amira tayi tace " besty kinzo gida kenan ?" eh kawai fanan tace mata ta kashe wayar aikuwa kafin kiftawa kawai sukaji yo sallamar amira shigowa tayi tazauna tana kallon besty nata da suka kwana biyu basu hadu ba tun rasuwan mansoor dasuka je musu taaziya " ohhh besty kina nan abun ki gaskiya bakida kirki " cewar fanan " sorry besty kinsan yanda abu suka hade min se a hankali ga school ga asibiti abin ba sauki" bude baki tayi zatayi magana wayarta yafara ringing miko mata wayar hairah tayi se anan ne amira ta ganta tace " woww suhaima aina kuka samo wannan beautyn ko de su zeenat ne suka zo da ita?" tayi maganar tana sake kallon hairah da kanta akasa ta gaisheta takoma ta zauna suhaima ce tace " bakisanta bane itama kanwar muce" kin daga kiran fanan tayi ganin bakuwar special number batasan nawaye ba , five 5 digit din last number ya kare da 99999 seda aka kira kusan sau uku kafin ta daga tasa akunne tayi shuru daddadar muryanshi me tafiya da Kuma ratsa mata jijiyoyin jikine taji ya sauka mata akunne yana " hello " nauyayyar ajiyar zuciya tasauke wanda yasa suka dago suka kalleta tace " assalamualaikum habiby " suhaima, zeenat,amira tsaban shakiyanci har suna hada baki wajen cewa " awwwwwwwwn ! Habiby" hade da shewa pillow fanan ta wurga musu hade da harara sannan tayi kwafa shagwabewa tayi tace " habiby ka gansu suna tsokanata ko ?" Jan numfashi yayi kamar wanda yaci yaji lokaci daya yaji ta tayar mishi da hankali idan tana mishi wannan shagwabar kawai daurewa yakeyi dan shi kadai yasan yanda yakeji katse kiran yayi , tabe baki tayi tace " Allah zanyi maganinku kafin in tafi " kiran hairah tayi ta zauna akusa da ita tadinga janta da labari dan tasamu tasaki jiki , Bayan 30mint har lokacin basu fito ba suna dakin suna hira gani sukayi an yaye labuyen bedroom din , Mr azaad ne tsaye ajikin kofa fuskan nan adaure tamau duk seda sukasha jinin jikinsu lokaci daya suka nutsu suka shiga taitayinsu hatta ita fanan din . " Wato matar tawace kuke tsokana ko?" Kamar zasuyi kuka suka girgiza kai alamar ah ah watsa musu harara yayi kafin yayi kwafa inda fanan take yaje yasa hannu yadauketa cak yayi hanyar fita falo mutsu_mutsu tafara ganin abinda yake shirin aikatawa tasan akwai mutane a falon yazataji in suka gansu haka ahankali tace " habiby kayi hakuri ka saukeni kasa zan iya tafiya da kaina" ko sauraranta beyi ba suka fito falo babu kowa afalon duk sun watse mama da ummi suna daki suna hira, gauron numfashi ta sauke tana godewa Allah . Be sauketa ako ina ba se a motar yaja suka hau kan titi , cikin nutsuwa yake driving zubawa kyawawan fuskanshi ido tayi tana kallonshi cike da so da kauna, batare da ya kalleta ba yace " baby wannan kallo haka ?" tace " to ai bana gajiya da kallon kane " cize libs dinshi nakasa yayi jiyayi magana ma kadai idan tayi kara ingizashi take bece mata komai ba ya nufi migration office barinta yayi a motar yashiga ciki after some few minutes yafito hannunshi dauke da envelope daura mata yayi akan cinya ya tada motar suka dau hanya bata ko dauki envelope din ba saboda bece mata komai ba yanda yadaurashi hakan tabarshi kallonta yayi yace " open it" sa zara_zara chocolate color yatsunta tayi ta bude passport da visa ta gani nata daduk wani abu da mutum yake bukata inzashi abroad duk akwai jujjuyasu tayi a hannunta kafin ta kalleshi tace " habiby to sukuma wannan fah tafiya zamuyi ?" driving dinshi kawai yakeyi be kalli direction dinta ba ya gyada mata kai, bata sake cewa komai ba ta maidasu ta rufe , cikin makay shawarma suka shiga yayi packing motar fita yazoyi tarike hannunshi tace " habiby nide bazaka barni nidaya anan ba " matso da kanshi yayi ya manna mata kiss a libs dinta yace " bazaki iya tafiya ba kibari inje in fito" kwabe fuska tayi tana kokarin yi mishi kuka bayanson ta tayar mishi da rigima yasa yafito yazo yabude mata itama tafito duk idon jamaa yadawo kansu se kallon akeyi saboda sun burge jamaa sosai musamman ma wayanda suka ganesu , rikota sosai yayi ajikinshi yanda bazataji zafi sosai ba intana tafiya dukda tanajin zafin ba sosai ba haka ta sake daurewa tana hada tafiyanta. makay shawarma babban joint ne a gombe yana da girma dakuma kyau sosai babu abinda babu a ciki , rike hannunta yayi suka fara tafiya har ciki wajan shopping tsayawa yayi yace ta dauki abubuwan da take bukata side din su perfumes taje ta diba masu kamshi da dadi hade da lotion's se shower gel, body spray, mouthwash, sannan takoma kan kayan kwalama ta dibe chocolate sosai da ice cream security wajan ne yariko keken kayan yatura har wajan yin bills ATM ya bada suka cire kudinsu suka hada musu komai a leda karba security yayi akasa a bayan motar suka shiga suka tafi duk tunaninta daga nan gida zasuyi setaga ya sakeyin packing a yahuza suya yafita ya karbo nama da yogurt dinsu masu matukar dadi . Agajiye de suka dawo gida fanan duk ta gaji jira kawai takeyi taganta akan gado , bude motar yayi yadauketa cakk yama daya daga cikin securities dinsu alama da ido ya kwaso kayan cikin motar yabisu dashi har part din su direta yayi akan bed dinshi ya koma falo ya karbi ledojin ya ajiye akan kujera, cire rigar jikinshi yayi wannan hadaddiyar surar nashi ya bayyana especially his 6packs and muscles amurde suke bathroom yashiga ya sakarwa kanshi shower yafito daure da karamin towel a kugunshi se dingan ruwa yakeyi tana zaune akan gadon yanda yafita yabarta haka yasameta sede ta cire hijab din jikinta ta ajiye a gefe jin yanda ya dameta wajanta yanufa yahau kan gadon ya kwantar da kanshi akan cinyarta ya lumshe ido kamar mejin bacci sa hannunta tayi ta cusa cikin gashinshi tana yamutsawa hade da shafawa burgeta gashin yayi musamman da ruwa yajika shi se yayi wara_wara gwanin burgewa, duk abinda takeyi yana jinta beyi yunkurin mikewa ba ahankali hankali reaction dinshi yafara canzawa , rike hannunta dake kanshi yayi yadawo da hannun kan faffadar kirjinshi dake dauke da kwantaccen suma baki me laushi yakwanta luf , batayi tunanin wani abu ba tafara shafa kirjin nashi musamman inda gashin yafi yawa kasa hakuri yayi yadaura hannunshi akan dukiyar fulaninta yafara yawo dasu da sauri ta cire hannunta akirjinshi tana kokarin mikewa dan bata shiryawa hakan ba a irin wannan halin da take ciki bata manta da bakar azaban datasha jiya ba qin dagata yayi yasa hannu yamaida ita ta kwanta ya mata rumfa dede kunnenta yakawo face dinshi yace " wifey where are you going to? karki tafi ina bukatarki akusa dani" sake tsorata fanan tayi jin yanda muryanshi one time ya canza ga idonshi dasuka rine suka canza kala mutsu _ mutsu tafara mishi hade da kuka runtse ido yayi dan bayason jin kukanta har cikin ranshi yakejin hakan dagata yayi yace " am sorry wifey bawai wani abu zan miki kawai bacci zamuyi " ba ta yarda da maganarshi ba ,gani takeyi kamar ze sake mata abinda yamata jiya , yasa ta maqe kafada, dafe goshi yayi ahankali yafurta " oh my goodness" tashi tayi tafara tafiya tana bin bango taje wajan kujeran tadubo ledar naman daya siya hade da yogurt dan yunwa_yunwa tafaraji dawuwa tayi inda yake tabude ledar kamshin gashashiyar naman kaza dayasha kayan hadi ne yadaki hancinta ,cike da nutsuwa tafaraci tana hadawa da yogurt din harta koshi zuba mata ruwa yayi a glass cup yayi yabata tasha tayi hamdala ta koshi qat. Mikewa tayi dan tanason tayi wanka , dakyar takai kanta bathroom dinshi tashiga tayi wanka tafito sanye da rigar towel fari kal samunshi tayi ya kishingida da pillow kanshi na kallon sama damuwa karara ya bayyana akan kyakyawan fuskanshi ganin yana kokarin sauke kanshi ne yasa ta dauke kanta daga gareshi tazauna a gaban mirror tashafa lotion dinshi da perfume ta shiga dressing room dinshi , dubawa takeyi ko zataga wani kana nan kayanshi dazata samu su mata dede dan qiwiyan komawa nata dakin takeji, idonta ne yasauka akan wata trolley me kyau sosai pink color burgeta yayi taji tanason ganin meye aciki durkusawa tayi tasa hannu ta bude akwatin kayan bacci ne kala kala aciki sunfi set 30 masu kyau da daukan hankalin duk wani da na miji daukan na farkon tayi ta bareshi a ledarshi , wata yalolon rigace me tsantsi da kuma raga_raga rigar transparent ne onion color tsayinshi iya guiwanta yatsaya hade yake da pant dinshi aciki shima onion color sunyi kyau sosai dauka tayi tasaka ajikinta babu abinda baa gani komai yana waje muraran harta pant din datasaka , rufe akwatin tayi tamaidashi inda yake tasa slippers tafito gaban mirror taje tasake feshe jikinta da different perfumes masu dadi dakuma sanyayyar kamshi ta gyara gashinta. Karfin hali tayi tasamu tahau kan gadon tana ciccije libs dinta yana nan a kishingiden taje ta kwanta akan kirjinshi da har lokacin besa kayaba dagashi se towel , tun kafin ta iso inda yake kamshin turarenshi sun sanar dashi zuwanta bude sexy eyes dinshi dasuka canza kala su da kansu suke lumshewa tsabar wutar shaawar dake damunshi yazuba mata na mujiya dagowa yayi yazauna yana bin jikinta da kallo daukewa numfashinsa yayi na wasu yan dakiku ganin dressing din datayi ta matukar tafiya da duk imaninshi kallon hips dinta dake da fadi da tudu yayi yana kallonsu duka awaje gana shanunta dasuke gaisheshi , hannu yasa yazagayo dashi a kugunta yakai kanshi kan wuyanta yana shakar kamshin jikinta dake sake birkitashi , fanan duk a tsorace take . kamar zeyi kuka yace " baby please I need you karki cemin ah ah" dukda yabata tausayi amma bazatayi gangancin barinshi ba muryanta na rawa tace " Mr azaad akwai stitches ajikina fah " tunawa yayi da anmata dinki yasa jikinshi mutuwa janta yayi ajikinshi suka kwanta yaja musu blanket yana manne da ita yanata tabe_tabe bata hanashi ba. Su ummi basu tashi ankara da fanan bata gidan ba se bayan isha tukun nan ,anzo zasuci abinci suka ga duk sunfito mama ce ta tambayi hairah " Ina antynki " amsa mata hairah tayi da " bata nan dazun yaya yazo yadauketa " dake bayan fitar Mr azaad da fanan seta tambayesu waye shi sukace mata ai mijinta ne, jinjina rashin kunya irin na Mr azaad ummi da anty amina sukayi itakam ma anty amina duk tsoronta daya kar Mr azaad yace ze kusanci fanan da dinki ajikinta Allah_Allah takeyi sugama cin abinci su koma gida kafin me afkuwa ta afku. se wajajen 9:00 su ya Usman,ya al ameen, fawwaz, areef suka dawo gida tare da hafiz da yaji sauki sosai suna sallama hairah ta mike da gudu taje ta rungumeshi tana tsallen murna ganin yayanta jikinshi yayi sauki zama sukayi shida ita a kujera daya baba ma yana falon , kasa hafiz ya durkusa yana musu godiya sosai na taimakonshi da kanwarshi da sukayi murmushi kawai sukayi suna yabawa da hankalin yaran baba ne yace " hafiz tunda baku da kowa zaku zauna atare damu kunzama yayanmu da yardan Allah! kanwarka zata zauna a gidan nan zan maida ita makaranta! Kai kuma dazun kafin azaad yabar asibitin yamin magana kancewa tunda ni nadauki hairah shikuma yadaukeka zaka koma gidansu da zama ze mayar dakai makaranta duk sanda kakeso zakazo kaga kanwarka haka itama sanda ba makaranta zatazo ta ganka, kun zama jininmu yanzu in sha Allah bazaku sake kukan maraici ba kusaki jikinku munzama daya" tsabar farin ciki hafiz da hairah har hawaye sukeyi basuyi tunanin akwai irin wayan nan mutanen a doron duniya ba dan duk inda sukaje neman taimako sede abisu da kyara da tsangwama. Ummi tace " bari mu gudu dare na yi hafiz mutafi ko ?" Gyada mata kai yayi ya mike shida su fawwaz rike hannun hairah yayi har waje yana ce mata " hairah kinga yanzu munsamu wayanda zasu taimakemu tsakani da Allah dukda nasan halinki bakida kiriniya da neman fada duk da haka dole insake fada miki kinji banda rashin kunya dukda shima ba halinki bane kimusu biyayya kamar appu da amma Allah yajikansu karki zama me manta halacci " ya karisa magana yana shafa kanta gyada mishi kai tayi tace " in sha Allah yaya zanyi yanda kace " ummi dake bayansu basu sani ba tajiyo duk abinda suke fada tayi murmushi tasakejin yaran sun kwanta mata arai. Sallama suka musu suka tafi hairah se bye-bye takeyiwa yayanta hafiz , rike hannunta suhaima tayi zasu koma ciki yar gyaran murya ya usman yayi yama suhaima alama da ido tashiga ciki tagane abinda yake nufi , yasa tasaki hannun hairah tashiga ciki tabarsu a compound din gidan su biyu , kallonshi tayi da manyan idanunta tace " laaah ya usman kaine ?" Yace " eh khai.... "Sekuma yacanza tunawa da yayi ba khairaty bace yace " hairah yayanta nine zo kitayani hira " zama sukayi akan plastic chairs dasuke cikin compound din, haka yadinga janta da labari harta sake itama tadinga zuba mishi hira nan yagane itama gwanar surutuce gashi ko magana tayi se angane akwai tsantsan yarinta a tattare da ita haka yabiye mata suka dinga hira har karfe goma yace mata taje ta kwanta dare yayi gobe zasu karasa tashi tayi tashige dakinsu shima yashiga daki ranshi fess komai normal yakeji yana tafiya mishi yasan yau zeyi bacci me dadi. Karfe 2:30 nadare fanan tafarka sakamakon Kiran sunanta da taji akeyi cikin sigan bada umarni dakuma girmamawa tashi tayi taga Mr azaad na baccinshi hankali kwance sauka tayi akan gadon tabude kofar ahankali yanda bazeji karan ba fitowa falo tayi tana sanye da kayan baccin jikinta falon ne yasauya daga falo zuwa wani irin hadaddiyar daji me dauke da shuke_shuke gwanin ban shaawa ga kamshi hade da dusan kankara sama kuma sararin samaniya ne , batayi mamakin hakan ba ji tayi an kara kiran sunan nata acan saman sararin samaniya yasa tabude hannayenta duka biyu tafiya tafarayi akan iska tana firewa sama inda sautin muryan ke fitowa seda ta kusa isowa wajan tukun kayan jikin yacanza zuwa doguwar riga fara sol komai din jikinta seda yacanza yazama hadadde hatta gashin kanta style dinshi canzawa yayi takoma sarauniya sak, isa wajan tayi taga bakowa babu alamar mutum ko tsuntsu kallon kudu da yamma tayi can ta hango jaaazana shi kadanshi akan iska yana daukar ido hular mulkin da yake ran kowa daga mutane har aljanu kowa burinshi ya mallakeshi , shine yayi wannan kira ga fanan wajanshi taje ta tsaya tanajin sanyi na ratsata , jitayi magana na fitowa daga jikin jaaazana " sarauniya fadima shin kinsan da lokacin ki yakusa karewa a duniyar bil adama? lokaci kalilan ne yarage miki da ki fara gabatar da abinda yakamata" To semun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏. Masu comment Allah yasaka muku da aljanna ina godiya sosai matuka. via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚 ( J. W. A 📚📚📚) PAGE 5️⃣3️⃣ Shuru kawai sarauniya fanan tayi tana sauraran jaaazana har ya gama fadin abinda ze fada ya narke ya shige cikin jikinta , bangarewa tayi idonta suka fifito sosai hasken su da sheki yakara fitowa kulle idonta tayi ta sake budewa ta ganta a tsakiyar falonsu ajiyar zuciya tayi tanufi bedroom din Mr azaad slowly ta bude kofar dan gudun kar ya tashi yahau tambayarta ina taje shigowa tayi tamaida kofar ta rufe , juyawa tayi zata je ta kwanta kawai taga Mr azaad a tsaye a gabanta idonshi akanta kallon tuhuma yake binta dashi kafin yace" wifey daga ina?" tace nadanje kitchen na sha ruwa ne" ta karishe maganar tana inda_inda " karya be dace dake ba domin baki iyashi ba karki fara ! sannan naga ga can bottle water akan center table ko me sanyi kikaje sha?" cewar Mr azaad da haryanzu ya tsura mata mayun idonshi da yasa takasa nutsuwa duk ta birkice se sosa wuya takeyi bazata iya sanar dashi lokacin tafiyarta ya qarato ba dan batason ya shiga wani halin damuwa, canza maganar tayi da " habiby kazo muje mu kwanta bacci nakeji" be sake dauko mata wata tambayar ba ganin bataso taki bashi amsa se kauce_kauce takeyi yasa yakoma kan bed yakwanta hawa gadon tayi itama ta shige jikinshi rungumota yayi kamar wani ze kwace mishi ita. Washe gari 5:20am Tashinta yayi daga bacci " baby time for prayer" tashi tayi tazauna tana mika da salati bin kirjinta yayi da kallo, kallon setin da yake kallo tayi taga yazubawa kirjinta ido kashe mata ido yayi kafin yafita zuwa masallaci . Sallah itama tayi yau alhamdulillah ta tashi tana iya takawa ba laifi kuma baya mata zafi tana zaune akan sallayar tana azkar shuru_shuru Mr azaad be dawo daga masallaci ba har 7 tashi tayi ta share bedroom dinshi tagyara kan bed, tayi mopping ta wanke toilet komawa falo tayi tagyara ko ina hade da bedroom dinta ta kunna turaren wuta ko ina yayi fess yana kamshi kitchen tashiga nan ma ta gyara ko ina sannan tafara tunanin me yakamata ta musu na breakfast. Cikin store tashiga ta dauko doya madedeci tasa ruwa acikin bowl tadauki wuka ta fareshi tsaff ta yankashi acikin bowl dake dauke da ruwa , kunna gas tayi ta daura ruwa acikin tukunya yafara zafi tasa doyan da gishiri ta rufe , bayan doyan yadafu tasashi a basket yadan sha iska eggs ta dibo guda shida ta fasa acikin separate kwano tasa magi,albasa se ginger kadan saboda karni kwai ta kadashi yakadú,daura frypan tayi akan gas din tasa oil tasa albasa sannan tafara sa doyan acikin kwai tana soyawa harta gama daga ido ma kadai mutum ya kalla yasan zeyi dadi ba dan kadan ba, cabinet taje ta bude tadauko dinner set food flask masu kyau dukda sabbine seda tasake wankesu tagogesu da dry towel tazuye soyeyen doya da kwan aciki tarufe ta ajiye agefe. Fridge din ingredients (kayan miya) ta bude takwaso abubuwan bukata saboda miyar kwai takesonyi kamar su attarugu,albasa,Karas, green pepper , green beans ta gyarasu, tayi blanding attarugu . fasa eggs din datasan zeyi mata miyan tayi tayanka albasa acikin kwan ta ajiye agefe , ruwan zafi ta dibo tafasheshe a heater tasaka karas din da green beans da baking powder kadan rufe bowl din tayi ta barshi few minutes, budewa tayi ta tsameshi, sake wankewa tayi sannan shidinma ta ajiye agefe , Daura tukunya tayi akan gas tasa butter ta narka shi tasa albasa yasoyu sama sama . attarugun datayi blanding dinshi tasa aciki da curry, thyme, tasa ruwan zafi kadan aciki tajuyashi tarufe da marfi , can tabude tasa kwanta data fasa acikin tukunyan tarage wutan tasake rufe tukunyan tabarshi nawasu mintuna tasa mishi karas da green beans tajuya ahankali tabarshi ruwan yatsotse ta tabbatar da yayi ta kashe gas din tajuye miyar kwan acikin food flask ta kaisu dinning ta jera tadawo tadafa tea dayaji kayan kamshi shima takaishi dinning, wanke duk wani abinda tayi amfani dashi tayi tanufi bedroom dinta tacire kayan jikinta tadaura towel tashiga bathroom tashiga jacuzzi dake dauke da zuwan zafi ta gasa jikinta sosai sannan tayi wanka tafito tana tsane jikin da dogon gashinta da tsayinshi yakai kugunta zama tayi agaban mirror tadauki hand dryer ta busar da gashin ta shafa mayukan gashi ta tajeshi tayi packing da ribbon fari, lotion tashafa tayi light make up ta fesa turare kaya tadauko Pakistan riga da wandonshi fari da pink hade da gyalenshi ,wandon pencil ne rigar kuma yanada tsayi yakawo mata har guiwa gefe da gefenshi a tsage yanada dogon pencil hand yasha stones, yafa gyalen tayi akanta da bashida wani girma sosai tasa farin plate shoe, tayi kyau sosai kasancewarta chocolate color,se color kayan suka karbeta white and pink sake feshe jikinta tayi da body spray tafito falo ta tsaya tana jiranshi ta bawa kofar falon baya, shigowa yayi shakar kamshin dayaji yake tashi apart din hade dana jikinta yayi ahankali ya hada jikinshi da nata ya rungumeta ta baya ya saukar da kanshi awuyanta yana shakar kamshin turarenta hannunshi duka biyu ya daura akan kugunta seda suka kai almost 5mint ahaka , rike kafadunta yayi ya juyo da ita suna facing juna , manna mata light kiss yayi a libs yace " morning kiss ! Kinyi kyau baby kullum Kara kyau kikeyi " sa hannunta tayi tazagayo dashi awuyanshi tana shafawa kadan kadan tace " morning habiby " be amsa ba kawai yamata murmushi tsayar da ita yayi yana binta da kallo from toe to head, godewa Allah yayi daya bashi mata me hankali dakuma sonshi tsakani da Allah, me tsafta kamarshi dukda akwai masu aiki a gidan amma ita take komai da kanta ta iya kula da jikinta. ( to mata gareku , kurike tsafta! kurike tsafta maza sunason mace me tsafta da tattalin kanta ,karki kasance ballagaza da bata damu da jikinta ba bare tayi tunanin gyara muhalli . Babu na mijin da bayason mace me tsafta Koda shi yakasance kazami bayida tsafta amma ke inkina da tsafta zakiga shikanshi ze rage , zekuma jidadi duk sanda yadawo gida yasamu ko Ina tsaff dakuma ke kanki kinyi wanka da kwalliya kin feshe jikinki da turare kina tashin kamshi , tsafta na daya daga cikin abinda yake kara soyayyarki azuciyar miji dan bakowa bane zeyi toleranting kazanta ba , mata da yawa aurensu ya mutu ta dalilin rashin tsafta . To adage adinga tsafta dan faranta ran oga ,bama dan oga ba kema kanki inkina tsafta sekinfi jindadin jikinki da rayuwarki,a shigo gidanki ma aganshi tsaf ai da dadi bazakiji kunya ba . ) rike hannunshi tayi ta langwabar da kai hade da turo dan karamin bakinta me red libs tace " habiby aina ka tsaya haka inata jiranka baka dawo da wuri ba" tsurawa dan karamin red libs dinta ido yayi dake fitar da kalma daddaya kamar bata iya magana ba tsaban shagwaba, ji yayi kamar yakama libs din yata tsotsa , tallafo habarta yayi yasa idonshi cikin nata yace " am sorry baby ! na tsaya a falon ummi ne " sake turo bakin tayi takoma kamar wata teddy tace " to yanzu muje kayi wanka sekazo muyi breakfast nafara jin yunwa " ta fada tana kai hannunshi kan cikinta ,shafa shamulallen cikinta yayi dayake plate kamar batacin abinci kai hannunshi yayi kan maranta yadan shafa yace " baby yanzu baya miki zafi sosai ko" ganin yana kokarin zarcer da hannunshi kasa ne yasa tayi saurin rikewa kam tace " muje kayi wanka" dariya taso tabashi ganin lokaci daya tadan tsorata jan hannunta yayi zuwa bedroom dinshi yana " yau ke zakimin wankan " zaro ido waje tayi tafara zazzaresu gasu dama masha Allah manya_manya dasu tace " nide ah ah". Sake hannunshi tayi yashiga toilet din, fitowa yayi daure da towel akugunshi karami kuma ahannunshi yana goge kanshi dake digar ruwa, karban towel din tayi ta goge mishi jiki zama yayi akan kujera ta shafa mishi lotion se kallonta yakeyi especially her cute face satan kallonshi tayi taga ita yake kallo. tana gama shafa mishi man tabarshi awajen tashiga dressing room dinshi tana tafiya ahankali tadauko mishi kaya kana na marasa nauyi takawo mishi tana tsaye agefenshi yasaka riga murmushin mugunta yayi kafin ya kunce towel din dake kugunshi ya fadi kasa, kara tasa tarufe idonta tazuya baya batayi tunanin ze iya hakan agabanta ba zuciyarta se bugawa yakeyi da karfi ita kadai tasan me tagani , Mr azaad kuwa se dariyar mugunta yakeyi harda dan rike ciki dan abinda yayi tsammanin haka kuwa yafaru tsoron fanan yayi yawa saka kaya yayi kafin ya rungumeta ajikinshi yanaci gaba da dariyar , kukan shagwaba tasa mishi tana dukan kirjinshi da duka hannunta rike hannayen yayi yana dariya yace " Meye abin tsoro baby ?" murguda mishi dan karamin bakinta tayi tace " nide munyi fada tam " rike kunnenshi yayi yace " afuwan wifey " make kafada tayi, daukarta yayi cak be zarce ko ina ba se a dinning table yazaunar da ita akan kujera shima yazauna, bude warmers din tayi nan take kamshin abincin yadaki hancinshi seda yarufe ido sannan yabude ya kalli abincin dake cikin kulolin seda ya hadiye yawo, burinshi kawai yakai abincin bakinshi , serving dinsu doya da kwan tayi a one plate sannan ta zuba musu lafiyayyar miyan kwan tarufe warmers din, hada musu tea tayi sannan ta ajiye mishi plate agabanshi tace " inde kanason inci sede kayi feeding dina" girgiza kai yayi yace " abu me sauki " dagata yayi yadaura akan cinyarshi yafara feeding dinta harta koshi sannan shima yaci dadin abincin ne yake ratsashi har kwakwalwarshi bayan girkin umminshi yadade beci abinci me dadi irin wannan ba haka suka gama breakfast dinsu yanata santin girkin ,tazo zata kwace kayan ya hanata dan bayaso tadinga shan wahala shida kanshi yakai komai kitchen din sannan yatayata wanke abinda suka bata..... Bari muleka kungiyar BAPHOMET. suna can duniyar su shugabansu daya kansance katon bakin aljani mara imani me mugun halitta mara kyaun gani rabinshi mutum rabinshi dabba kuma wata halitta daban ga katon qaho akanshi, yana zaune akan kujeran mulkinsa suna tattaunawa da wasu mugayen halittu marasa kyaun fasali inda sukema kadai duk bil adaman daya shiga inde yaje tofa fitowa se wani iKon Allah, wata bakar mujiyace daga zama tafado kasa kamar wanda aka wurgo tana fadowa gabansu takoma rabinta mutum rabinta mujiya tsirara ba kaya ajikinta duk jikinta gashi gashi ga qaho agaban goshinta, afusace shugaban nasu da murya me amo mara dadinji yace " keeeeeeeee! Abinda yafi miki sauki shine ki sanar dani abinda naturaki kinemo min domin shi kadaine ze taimaka mana wajan mallakar sarauniyar nasminaya" muryanta kamar yanda kukan mujiya yake fita haka yake tace " yakai shugabana SHUBUMBUM na samoshi ! shidin cikekken dan baiwane dayazo duniya besan shiwaye bane kuma babu wanda yasan da hakan se wata halitta kwali daya dake tare dashi wato tsuntsun arnass , shidin yakasance dan babban gida acikin bil adama shidin babban dan kasuwane da akeji dashi" murmushi kawai shubumbum yakeyi jin bayanan da aka kawo mishi duba madubin tsafi yayi ko ze ganshi domin yanzu shi kadaine ze iya sasu suyi nasara akan kungiyar satanic kuma harsuci galaba akan sarauniyar nasminaya, wasu surkullenshi yayi a hannu sannan ya watsawa madubin tsafin, hoton kafanshine yafara bayyana nan take kuma madubin tsafin yatarwatse kaca_kaca yana fitar da hayaki, seda suka ja baya suna jinjina karfin baiwan da yake tare dashi...... Tom duka duka anan nakawo karshen rubutun yau se mun hade tomorrow in sha Allah. via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&rehttps://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 Wannan labarin qageggen labarine ban yarda wata ko wani yajuyamin labari ta kowani tsiga ba , bana bukatar ajuyamin labari ko ayi wani Abu batare da izinina ba😐🤔 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚 ( J. W. A 📚📚📚) PAGE 5️⃣4️⃣ Hajiyarsu amira ce zaune afalo tagama list din abubuwan da zata aiki amira kasuwa , fitowa amira tayi daga dakinta sanye da riga da wando ta daura after dress baki akai tayi rolling din gyale akanta tayi kyau sosai,se turo baki takeyi, kama baki hajiya tayi tana kallon amira dake turo baki gaba tace " to ba baki za ki turo ba ! Ko wuya zaki turo sekinje kasuwar nan yauwa" kamar amira zatayi kuka tace " hajiya yanzu da yamman nan zakice min inje kasuwa kibari gobe da safe" " to ban bari ba ga kudin nan da list, in kin gadama kije " cewar hajiya . Daukar kudin tayi tasaka ajaka da paper tafito , tana tsaye abakin titi tana jiran masu napep se ga motar ya al ameen ya tsaya agabanta yasauke glass , kallonta yayi yace" yar kanwa ina zuwa haka ?" turo baki tayi tace" hajiya ce ta aikeni kasuwa " ganin yanda take ta babbata rai ne ya bashi dariya yace mata " shigo muje " bude murfin motar tayi ta shiga tace " ya al ameen ina wuni ?" amsawa yayi da fara'a akan fuskarshi yace " wata kasuwa kenan ?" " Main market " okay yabata amsa kafin yace" nikam yar kanwa yaushe ne zamusha bikinki ne ?" dariya tayi sosai dan tambayar yabata dariya tukun tace " ya al ameen Allah kaban dariya ! Tom ba yanzu ba tukun dan yaron abokin daddy da muke soyayya dashi mun rabo dan bashida dabi'a me kyau , shisa ni yanzu bazan sake bawa ko wani na miji dama ba tukun gudun kar abatamin lokaci , se na gama karatu tukun " jinjina kai kawai ya al ameen yakeyi dan ya gamsu da maganar ta yace " tofa yar kanwa kina nufin bazaki bawa ko wani namiji dama ba kenan harda yayanki da ya dade da dakon sonki aranshi ? " Kamar saukar aradu haka taji maganarshi cak taji ruwan jikinta ya shanye ta gagara ko da kwakkwaran motsi , tabbas ya shammaceta batayi tunanin haka ze fada mata ba kunya ne yarufeta, nunawa tayi kamar bata gane me yake nufi ba tace " ya al ameen wani yayana din kenan?" Murmushi ya al ameen yayi yace " yayanki da kuke tare acikin motar yanzu kuna tafiya zuwa kasuwa " yabata amsa cike da barkwanci , sa gyale tayi ta rufe fuskanta takasa magana har suka isa main market yayi packing , Bude motar tayi tasa kafafunta waje sannan tace " se anjuma ya al ameen nagode" " noo my mirah baki ban amsa ba za ki tafi?" daburcewa tayi dan tarasa amsar da zata bashi yasa tace " ayyah ya al ameen mu karisa magana a waya " ta fada tana shagwaba fuska . gyada mata kai yayi tafice ko juyawa batayi ba taci gaba da tafiya amma tanaso tajuya ta sake kallonshi ko da sau daya ne, juyowa tayi suka hada ido yana tsaye ajikin motar yazuba mata manyan idonshi irin na fanan , seda taji meyasa tajuyo gudu_gudu , sauri_sauri takeyi saboda ta bacewa ganin shi seda ya tabbatar da tashiga kasuwar sannan yashiga motar , yana murmushin nasara dan yadade yanason amira kawai be taba fada mata bane . Bayan sati biyu soyayya ya kankama sosai tsakanin ya al ameen da amira kuma har manya sunshiga ciki an yanke zaa hada rana daya dana fawwaz,ya al ameen sekuma na yaseer da zeenat dasuma yanzu suke shan soyayya ruwa_ruwa, ya usman kuwa yanzu ne suka fara shakuwa da hairah ahankali yake samata sonshi a zuciyarta duk da she's just 16yrs , kuma an komar da ita school tana jss 1 haka hafiz ma an sashi a school yana ss 1 , suna samun gata sosai kamar yan gida sun saki jiki gashi alhamdulillah suna fahimta a makarantan dan brain dinsu naja. Nusaiba anyi aurenta da yayanta lukman dukda madina takawo tashin hankali sosai amma hakan be hana auren ba saboda alh me ruwa ya sanar mata muddin ta hana auren a bakin aurenta shisa ta zubar da makaman yakinta bawai dan tanason auren ba. Yau ne su suhaima da ya al ameen suka fara shiryawa domin komawa bauchi state gobe zasu wuce da sassafe zasu dau hanya shiryawa suhaima da auta sukayi ya al ameen ze kaisu gidansu Mr azaad suyiwa fanan sallama , sun fito har sun shiga motar amira tazo itama zata bisu komawa baya zeenat tayi tazauna tabata front site hakan kuwa yayiwa ya al ameen dadi, haka suke tafiya suna hira shida mirah shi . bayan isarsu gidan duk afalo suka samesu suna zaune banda Mr azaad da fawwaz da suka fita office, anty amina tun sati daya da ya wuce takoma, fanan ta warke sumul tana tafiyanta dede kamar da, takara fresh da kyau sosai suna falo ita da ummi da zeenat,areef . shigowa falon sukayi suka zauna suna gaida ummi . Amsawa tayi fuskanta cike da farin cikin ganin su , auta kuwa rungume fanan tayi tana dariya tayi luf ajikinta , zeenat ce tace" ohhh su auta akwai son jiki kamar mage " dago kai auta tayi tace" ummi ina wuni ? Anty zeenat Ina wuni? Anty fanan ina wuni" ya alif Ina wuni ?" Amsawa sukayi suna dariya jin bata iya kiran sunan areef ba sede tace alif, areef ne yace" baby auta dan Allah kibarni karki batamin suna " dariya sukayi dan auta da areef insun hadu haka zasuta drama yana biye mata. gaida ya al ameen zeenat da fanan, areef sukayi ya amsa yana tambayar areef " Ina fawwaz?" " Fawwaz ya fita office" cewar areef gyada kai ya al ameen yayi . Shigowa abu me aiki tayi da su drinks da fruits hade da snacks ta ajiye musu. Amira ce tace " besty kinji suhaima ko? wai gobe zasu koma bauchi " da sauri fanan ta kalli ya al ameen tace " ya al ameen wai dagaske dama tafiyar taku gobe na nan ?" kafin ya al ameen yabude baki yayi magana suhaima ta rigashi da " ahhh lallai matar nan da kin dauka wasa ne ko yanzu ma sallama mukazo miki " har ran fanan taji ba dadi tafiyarsu da zasuyi dan tunda suke basu taba zuwa sun dade sosai ba irin wannan setaji dama kar su tafi dukda ma suhaima kam gombe zata dawo kuma a gidan amma taji ba dadi , kwabe fuska tayi tace" ayyah sweet sis karki tafi kinji ? , Ya al ameen ku kara wata 1 " dariya taso bawa ummi ganin yanda lokaci daya walwalarta ya dauke yasa tace " karki damu feena kafin lokacin bikin ai zakije in kun dawo daga dubai zaku tsaya acan kinji ?" " tom ummina " fanan tafada tana kwantar da kanta akan cinyar ummin . yanda ummi take da fanan kamar ita ta haifeta ,matar batada matsala ko kadan hakan ya faranta ran ya al ameen da suhaima hatta amira taji sun burgeta adduah takeyi Allah yasa itama nata surkan suzama haka dukda bata san cikekken halin umma rahina ba , dan duk zuwan da sukeyi gaisawa ne kamai yake hada su. Haka suka ta hira har 4:30pm , tunda me gadi yabude musu gate yakejin maganganunsu da hiran da sukeyi duk a kunnenshi dukda nisan dake tsakanin packing lot da compound din gidan sannan a shiga part din ummi har izuwa main falo akwai tafiya me yar rata amma duk yanajin hiran , packing driver yayi security ya bude mishi murfin motar zuro hadaddiyar farar kafarshi guda daya yayi waje seda yakusan 5mint sannan yafito securities na biye dashi da system dinshi da wayarsa hade da jacket din suit dinshi, da kyakyawar fuskarta ya faracin karo tana kwance akan cinyar ummi se hira sukeyi da su suhaima da zeenat duk basu ga shirgowar shi ba , tsinkayar muryanshi me dadi sukayi yana " barka da hutawa ummina " duk maida kallonsu sukayi kanshi " yauwa!son yau ka dawo da wuri kenan ?" " Uhmmm" kawai yace dan yanda Abubuwa suke neman dagula mishi lissafi a yan kwanakin nan yasa bayason wani dogon magana, haurawa upstairs yayi yawuce part dinsu securities na binshi , kallon fuskan fanan tayi taga bata da ma niyar tashi tace " feena tashi kije part dinku " mikewa tayi batace komai ba tahaura , a falo ta sameshi yana zaune ko takalman kafafunshi be cire ba ya kwantar da kanshi ajikin kujeran ya rike kanshi da hannu daya duk wanda ya mishi kallo daya ze gane yana cikin matsanancin damuwa , ita kanta fanan taga sauyi daga wajan shi , ako da yaushe se taga kamar yana cikin damuwa amma yana iya kokarin shi wajan boyewa. Zama tayi akan carpet ta daura kafarshi daya kan cinyoyinta ta cire mishi takalmi da safa haka dayar kafarma tayi sannan ta mike ta balla botil din rigarshi zuba mata ido yayi , ita dinma shi take kallo tace " sannu da dawuwa habiby yau naga ka gaji sosai " " yeap" bude fridge tayi ta dauko ruwa me sanyi tasa mishi a glass cup tabashi karba yayi yasha ya ajiye cup din mika mata hannunshi yayi ta kama ya jawota jikinshi kwantar da kanta tayi akan faffadar kirjinshi ji tayi zuciyarshi na bugawa da sauri da sauri " habiby meyasa kake boyemin abinda yake damunka ne , ni matarka ce bazanso inganka a cikin wani hali ba dan Allah kafadamin kaji " kiss yamata a goshi yace " baby karki damu is not necessary kawai de wasu irin abubuwa strange ne suka shigo rayuwata " bude baki tayi zata sake magana ya girgiza mata kai hade da daura yatsanshi akan libs dinta ba yanda ta iya haka tayi shuru , can kuma yace " gobe su al ameen zasu koma kenan ?" kallonshi tayi tace " amma ya akayi kasani ko ya usman ne yafada maka?" Itama ta wurga mishi tambaya batare da ta bashi amsar tambayar da yamata ba " no ba wanda yafadamin kune naji kuna hiran ai" tashi tayi daga jikinshi tazauna tana kallonshi sosai cikeda al ajabi dan itade tasan tunkafin ya yashigo falon suka dade da dena maganar amma taya akayi har yaji ganin kallon tuhumar da take mishi ne yasashi mikewa yayi bedroom dinshi dan yayi wanka , har yayi wanka yadawo falon anan ya sameta yanda yabarta tana nan tanata tunanin abinda Mr azaad yafada mata , kallonta yayi ta kasan ido yace " wifey in kin gama tunanin I need food" tashi tayi tawuce dinning yana biye da ita abaya zama sukayi tayi serving dinshi tuwon semonvita da miyar egusi yau favorite food dinta ta dafa dukda batasan ko yanaci ko bayaci ba , yanacin abincin tana kallonshi tanaso taji mezece taga harya kusan gamawa bece komai ba yasa tadan bata rai tace " habiby bakace yayi dadi ba " murmushi yayi yace " yayi dadi sosai wifey dadin abincin nema ya hanani magana ai" seyanzu taji hankalinta yakwanta . Barinshi tayi a dinning din tashiga bedroom dinta ta bude babban make up kit dinta tadauki fashion bag tazubawa su suhaima da amira kayan make up dinta dasu perfume ta dau wata ledar ta zuba chocolate sosai aciki ta fito dasu falo samunshi tayi yana zaune ya gama cin abinci " habiby bari inje downstairs inkaiwa su suhaima " mikewa yayi ya karbi bag din hannun nata yace " kawo in tayaki " fitowa sukayi daga part dinsu suna kokarin fara taka staircase din yaji ummi na waya da abba ita datake can part dinta amma yana iya jiyota, haka suka gangaro duk maganar da akeyi afalon tun kafin su karaso duk yaji . ji yayi kamar ya koma inda yafito be sake girgiza da lamarin ba seda yaji muryan anty shayida da shigowarta gidan kenan taje part din mommy, tana gaishe da mommy , mommy tace mata " ke uban me yakawoki gidan nan nace ina bukatarki ne ? To ki tattara kikoma part din uwarki aysha tunda kunfi fifitata akaina " hakuri anty shayida tabata , dafa kanshi yayi dan baze iya daukan wannan sabon al amarin ba ji yakeyi kamar zeyi hauka karasowa falon sukayi suhaima suka gaida Mr azaad amsawa yayi yana zama akan kujeran da fanan take yace " ashe gobe zaku koma ?" "Eh in sha Allah " suhaima tabashi amsa auta dake buga game a wayar zeenat batasan da shigowarshi ba seda taji muryanshi tasowa tayi takoma kusa dashi ta zauna tace " Yaya balarabe good afternoon " dan jan kumatunta yayi yace" afternoon cutie kina lfy?" " Lfy Lau yaya balarabe kalli game din dana keyi " kallon wayar yayi yace " good ashe kin iya" dariya auta tayi jin yace ta iya yasa ta gyara zama taci gaba dayi abinta , areef da ya al ameen kuwa sun fita suna garden . Daff da mangriba suka musu sallama zasu tafi sosai ummi ta musu sha tara na arziki haka Mr azaad ma , basu kayan make up din fanan tayi tabawa auta chocolate dinta sannan suka rakasu har packing lot inda ya al ameen yayi packing sosai suka musu godiya sannan sukayi ban kwana hade da adduah Allah yatsare hanya suka tafi ,sukuma suka koma ciki suna shiga ciki kuwa anty shayida tazo suka tafi part din ummi ta zauna abinta acan tunda zuwa kusada nata mahaifiyar ya gagara . Haka dare yayi Mr azaad yakasa bacci har fanan tayi bacci tabarshi , se ya rufe ido se yadingajin kana nan maganganu kasa_kasa na aljanun dasuke gidan shiya hanashi baccin yasa kawai yatashi yayi alwala yazo yafara nafilfilu har hudu na dare kafin yaji yafarajin bacci yakoma kan gadon yakwanta . Washe gari Gidan yayiwa su mama girma dan su ya al ameen da suhaima sun tafi sun dau hanya tun 7:00am suka tafi sosai sukayi kewarsu wannan karon sun jima musu dayasa suka zo tafiya sukaji kamar karsu tafi mama yanzu ne tasakejin kewa gashi ba fanan din ba suhaima daga ita se hairah da auta sukuma duk makaranta suke zuwa in suka tafi 7:30 se 5:00 suke dawuwa . Karfe 10:00 dede suka shiga garin bauchi direct hanyar gidansu sukayi dake cikin gra horn ya al ameen yayi me gadi yabude musu washe baki buzu me gadi yayi da hausarshi dabe gama fita ba yana " ah ! ah ! ah ! al ameenu kune yau agarin ah sannunku da hanya " amsa mishi ya al meen yayi "yauwa baba sannu da aiki" haka yashigo yayi packing ganin motar uncle kabir ne ya tabbatar musu da yana gida yau be fita ba rike da trolley dinsu suka shiga falo aikuwa uncle kabir da umma rahina suna zaune afalo suna kallon labarai sukaji sallamar su dagudu suhaima tafada jikin umma rahina tana " umma nayi missing dinki" dariya uncle kabir da umma sukayi lokaci daya tace " sannunku da hanya amarya " rufe fuska suhaima tayi tace " umma banaso kibari " ya al ameen ne yace " Allah ko amaryar hubby " uncle kabir yafara magana" ka ganka al ameen? zan saba maka akan amarya haba yarinya takusa aure amma kadameta zo nan autar daddy " me umma da ya al ameen zasuyi in ba dariya ba, haka sukata nishadi su hudu ne abunsu a gidan se me aiki da me gadi , uncle kabir sosai suke kama da baba komai dinsu kusan iri daya harta muryansu iri dayane , umma rahina mace ce wacce tasan yakamata bata da matsala ko kadan halinsu daya da mama kamar ciki daya suka fito sede mama in aka kureta tanada dan zafi amma umma rahina kam batada son tashin hankali sannan dukansu yaran duk suna kama da iyayensu ne kasancewar su fulani sunada farar fata fanan ce kawai tafita daban ita chocolate color ce. In Allah yaban iko da dama in sha Allah gobe ma zanyi posting Allah yakaimu darai da lfy 👍🙏. via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DDferrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚 PAGE 5️⃣5️⃣ Gombe state....... " Hairah zo ki je min gidan su amira kikaiwa hajiyarsu kayan nan " cewar mama dake zaune a tsakiyar gida tana gyara zogale hairah Kuma sun dawo daga makaranta kasancewar yau Friday sun dawo da wuri tun 12:30pm suke gida, wanke_wanke takeyi auta na mata dauraya mama ta kirata tashi tayi taje ta sako hijab ta karbi kayan ta fita , tana gab da karasawa gidansu amira taji an mata sallama daga bayanta , juyawa tayi ta kalleshi dan matashi dashi irin yaran anguwa ne . Amsawa tayi tana daure fuska, yace " sorry sister kiyi hakuri na tareki akan titi, sunana anwar ni abokin yayanki ne hafiz " dan sake fuska tayi tace" ayyah amma ya akayi ban sanka ba " shafa wuyanshi yayi yace " makarantan mu daya ai classmate dina ne a matrix" ganin ze bata mata lokaci bataje aikan da mama ta mata ba yasa tace mishi " to se anjuma kaga yanzu an aikeni ne gidan nan " tafada tana nuna mishi gidansu amira , kallon gidan anwar yayi yace" to in badamuwa bari in jiraki ko?" Bayanda ta iya haka tace mishi " to " shiga gidan tayi tabawa hajiyarsu amira kayan tafito bata samu amiran a gida ba ta tafi asibiti. Yana nan a kofar gate din yana jiran fitowarta , jerawa sukayi suna tafiya yana bata labarai tun bata sake ba harta sake tana dariya dan anwar akwai barkwanci shima balaifi sunkusa karasowa gida kenan ta hango ya usman yana tsaye a jikin motarshi ya harde hannunshi akirji yazuba musu ido, fuskanshi babu alamun sauki harwani girgiza kai yakeyi tsabar yanda ranshi yabaci idon nan sun jawur, ji tayi bazata iya ci gaba da tafiya ba kafafunta sun rike sun kasa motsawa bata taba ganin ya usman awannan yanayin ba tabbas yau ran yan maza yabaci dama mutum mara saurin fushi ance aguji ranar da ranshi ze baci , kallonta anwar yayi yace " sister yanaga kin tsaya ?" bakinta kasa buduwa yayi se hannunta datayi amfani wajan nuna mishi inda ya usman yake, shi kanshi seda yandan sha jinin jikinshi duk da besan meye laifin da ta aikata ba amma dagashi har ita sun kasa motsawa , ya usman kuwa ganin sunki karasowa ne yasa shi ya karasa wajansu , yana karasowa ya kalli anwar da kakkausar murya yace " inason wannan yazama gargadi na farko da na karshe agareka indan na kuskura nasake ganinka near my wife ! Se ranka yayi mugun baci " ya karishe maganar yana maida kallonshi kan hairah da kamar ruwa yacinyeta yace " ke kuma zakiyi mini bayanine tunda har kin manta da abinda nafada miki " ya rike hannunta yajata zuwa gida suka bar anwar a tsaye a wajan tunani yafara to taya akayi yazamana tayi aure shi da ma bawai soyayya yake nema suyi ba kawai de ganin ita kanwar abokinshi ce . ya usman be tsaya ako ina ba se a falo ya kalleta yace " wato magana ta tazama ta banza agareki ko hairah ?, saboda ni ban Isa dakeba shine yau kika nuna min matsayina kenan ?" Kuka takeyi tana girgiza mishi kai ,kanta akasa hawaye na zuba akan yatsunta da take wasa dasu da kyar ta iyacewa " ya usman kayi hakuri bazan sake ba" zuba mata ido yayi ganin yanda take zubar da hawaye abin ya sosa mishi rai amma yakamata yanuna mata sanin darajan alkawari sannan yace " okay ya mukayi dake?" tana sheshekar kuka tace " alkawari na maka da babu ruwana da wasu mazan da ba yan family ba " jinjina kai yayi yace " sekuma yau kika karyamin alkawari ko?" dago manya_manyan idanunta tayi ta sauke a cikin nashi idon , lumshesu tayi ayayinda ruwan hawaye ya zubo akan kuncinta, runtse ido yayi dan baze juri kallon kukanta ba . sa hannu yayi ya share mata hawayen kafin yace " kidena kukan nan ya isa haka, alkawari ne de kin rigada kin karya dan haka karki damu kanki kije kiyi yanda kika gadama kinada right din kula duk wanda ya miki i won't force you again" yana gama fadin haka ya shiga dakinshi , kalamanshi na karshe sun gigitata sunkuma sa tayi danasani jitayi dama bata tsaya kula anwar ba daduk haka bata faru ba tabbas ya usman mutum ne me saukin kai dakuma kirki sosai bata taba ganinshi ranshi yabaci ko kuma yayi fushi ba seyau , zamanta datayi agidan ta fahimci rayuwarsa sosai tun batasan menene so ba ahankali hankali yayi nasarar jefa mata sonshi acikin zuciyarta , yanzu gashi tayi abinda ya bata mishi rai harya furta mata " he won't force her again " zama tayi akan kujera taci gaba dayin kukanta kasa_kasa , fitowa mama tayi daga dakinta dan bayan fitan ta , mama tahada miya tashiga wanka tana dakine taji kamar magana yasa ta fito tasamu hairah zaune tana kuka . Tabata mama tayi tace " lafiya me yake damunki ?" dago kai hairah tayi ta kalli mama da mamaki mama ta kalleta ganin kuka takeyi yasa abin yabata mamaki zama tayi kusa da ita ta kwantar da kanta akan cinyarta tace " hairah mama fadamin meyasa meki keda waye?" cikin muryan kuka tace" ya usman ne" tunani mama tashigayi to meya hadota da ya usman din kuma suda baajin kansu tace " yau kuma keda ya usman din naki me ya hadaku haka ?" Kwashe komai hairah tayi ta fadawa mama bata boye mata ba , share mata hawayen fuskanta mama tayi tace" karki damu inde yayanki ne bashida matsala kibashi dan lokaci kadan zakiga yasauko , sannan kema ki kiyaye yayanki nada kishi sosai , sannan inde kinsan alkawari bazaki iya rikeshi ba to maganin bari kar afara karma kifara daukanshi domin alkawari kayane yanzu kibari anjuma sekije kibashi hakuri kinji? " hairah taji dadi sosai da tafadawa mama kuma mama ta kwantar mata da hankali tace " to mama " dagata tayi tace " to yanzu dena kukan ! Kin kaiwa hajiyarsu kayan?" gyada Kai tayi tace " eh na kai mata tace zakuyi wayama " murmushi mama tayi tana mamakin har yaushe itama hairah tafara son usman din kuma tayi nisa sosai, hakan yamata dadi dan dama burinta su samu su dedeta kansu suma asa musu rana dan bakaramin so takewa hairah ba yanda takejin auta azuciyarta haka takejin hairah tare da dan uwanta hafiz da asati yana zuwa gidan sau biyu yaran sunada shiga rai sosai ga ladabi da biyayya. Spider ne agaban alh Ibrahim tijjani dake daure tamau ajikin kujeran karfe sun mishi daurin hoho kamar wani katon barawo dukan da suka mishi kam baa cewa komai dan yaji jiki baa magana ko magana baya iyayi kamar zasu kasheshi haka suke dukanshi tun randa suka sato shi suke gana mishi azaba abisa umarnin boss dinsu azaad, hatta numfashi alh Ibrahim tijjani dakyar yake iya futarwa ko ina na jikinshi se diga yakeyi da jini fuskanshi yacanza kamanni kamar ba shiba duk yawani tsomare se katon tumbi kamar wani me cikin wata goma lol. Daga waya spider yayi yasa a kunne yace " boss munyi yanda kace shin mukara cin ubanshine ko kuwa ?" abangaren Mr azaad dake zaune a makeken office dinshi kamar na shugaban kasa yayi killer smile yace " no spider allow him to rest idan ya huta seku daura daga idan kuka tsaya , tunda yace dani ze gwada zesan ni da matata yayiwa sharri ! He will have to pay for it, ku nakasa minshi " kitt yakashe be tsaya jin abinda spider zece ba , yana zaune akan kujeranshi se juyawa yakeyi musamman idan ya kunna video da spider yaturo mishi lokacin da suke nadawa alh Ibrahim tijjani duka , wani irin nishadi ne yake kamashi yau yana cikin good mood dama dalilin da yasa yayi shuru yazubawa alh Ibrahim tijjani ido be dau mataki akanshi ba kawai yanason yaga iya gudun ruwanshi ne dan yasan aduk lokacin daya ritseshi baze mishi ta dadi ba . murmushi kawai yakeyi daga waya yayi yayi dialing number "my heart in human form " , fanan dake bacci da yanzu ta samu na ba gaira ba dalili taji karan wayarta lalubo wayar tayi tasa akunne murya duk bacci tace " hello" yace " wifey bacci da wannan yamman please kitashi haka " mikewa tayi tazauna tana gyara towel din jikinta daya fita yakoma gefe dan dama fitowarta wanka keda wuya taji bacci takwanta batare da tasa kayaba tace " habiby natashi " murmushi yayi da seda taji sautin shi yace " 8 zan dawo gida prefer something good and nice for me" bata wani fahimci me yake nufi ba yasa tace " tom habiby na me kakeson indafa maka?" dafe goshi yayi yace " nothing just prefer yourself for me !yau zaki karbeni hannu bibbiyu ,be ready put on something sexier da baze ban wahala ba " kitt fanan ta kashe kiran tana bin wayar da kallo sekace shine Mr azaad din da yayi maganar, itade ta rasa yaushe Mr azaad zesan wani abu waishi nan kunya , kamar tasa kuka ta mike ta danna kiran layin anty amina tana dagawa ko sallama batayi ba tafara da " wayyo anty amina am scared haryanzu ban fa gama warkewa ba and!and ! Mr azaad yace uhmm ....." tama rasa ta ina zatawa anty amina bayani yanda zata gane , anty amina dake gidanta kwance ajikin mijinta tace " my feena wannan kunyar taki ko tam gwarama kicireshi , yanzu zanbawa driver na sako ze kawo miki dan miki bayani inya kawo din " murmushi tayi tace" uhmmm thank you antyna love you " tace " love you to feena" sukayi sallama , aikuwa tashi tayi tafara gyara bedroom dinta dan yau tun safe babu abinda tayi a part din , two days din nan gan'da da lalaci takeji sosai bata iyayin komai se aikin bacci rabonta da part din ummi ma tun daren jiya da taje ta tayata yin kunun gyada. Ko ina ta gyarashi sosai yana fitar da kamshi me dadin gaske tana kokarin shiga bathroom dan yin wanka taji anyi knocking tace ashigo , abu me aiki ce tashigo fanan ta gaisheta mika mata wani fansy bag tayi me dan girma ta karba tamata godiya komawa daki tayi ta baje a kasa ta zazzage duk abinda ke ciki akan carpet wani galon madedeci tafaracin karo dashi dake dauke da wani hadi kamar zuma tarasa gane meyeshi yasa tabude ta diba a murfinshi takai baki jin za ki da dadi ne yasata lumshe ido , batasan tsumi bane haka tasha sosai tsaban kwadayi dakyar ta lallashi kanta ta ajiyeshi agefe bawai dan ya isheta bane . Bude daya ledar tayi taga abu kamar gunba haka mayar dashi tayi ta rufe tadau wata ledar nan kuma gorun nan wasu humran ne masu tashin kai lokaci daya batasan lokacin data sauke ajiyar zuciya da lumshe ido ba tsaban kamshin da humran yamata haka tabi ta bude kayan tass sannan ta kira anty amina dan neman karin bayani, sosai anty amina ta fada mata yanda zatayi dasu har suka gama wayar tana gode mata , jin kiran sallah ne yasa ta kwashesu ta sama musu mazauni a cikin locker tarufe , sallah tayi tana zaune akan sallayar bata tashi ba har aka kira isha , ana shiga itama ta gabatar da nata sallah. Yanda anty amina ta fada mata kuwa haka tayi turaren wankan da anty amina tasako mata aciki tasa acikin jacuzzi seda tayi wanka a shower sannan tashiga cikin jacuzzi din ta dade aciki tukun tafito lungu da sakon jikinta na fitar da wani shu'umin kamshi me fisgar mutum , yake tashi ajikinta ita kanta kasala ce ya fara rufeta gashi yahadu da tsumin da ta narkawa kanta wani yam_yam tafaraji , fito da wata riga pjama dress white color me tsantsin gaske tsayin rigar a cinyarta ta tsaya budedden rigane me botil irin na Tshirt yanada dagon hannu sannan wuyan rigar bashida botile , shafa lotion tayi ajikinta tabi jikinta tasake shafa mishi humra tana cikin shiryawa taji yabude kofar bedroom dinshi alamun yadawo kuma tasan yana dawuwa a gajiyen nan firstly abinda ze farayi shine wanka , hakan ne yabata daman cigaba da shiryawar ta hankali kwance. gyara gashinta tayi ta zubashi agadon bayanta dan ta lura Mr azaad yafison su ahaka bude akwatin jewelries dinta tayi tana dubawa taci karo da leg chain ( sarkan kafa) yamata kyau sosai gasu na gold sun sha ado basuda wani nauyi kamar single chain haka suke se kwalliyar da aka musu , daurawa tayi akafarta tana kallon kafar yayi kyau sosai aranta tace " a lallai zan fara sawa indingawa habiby kwalliya dashi nasan zesoshi " bata kara daukan komai aciki ba tarufe jewelry box din ta rufe , saka rigar tayi taga yabi jikinta yakwanta luf saboda silk ne gashi botil din wuyan rigar babu haka yabawa dukiyar fulaninta da batasa musu bra ba daman lekowa duk rabinsu awaje suke gama shiryawa tayi ta dauki cin gum center fruit na strawberry tasa abakinta tafara taunawa kallon kanta tayi a madubi tayi kyau harda na fitina she looks so sexy and hot ga mayen kamshin da takeyi har zatasa ta takalmi kuma se ta fasa santala_santalan kafafunta dasuke shining da glowing duk suna waje cikin rangwada take tafiya harta isa bakin bedroom dinshi , cike da yanga tayi knocking yace " come in" dan fitowarshi a wanka kenan yasa boxer ajikinshi yana tsaye yanashan yogurt yaji knock , shigowa tayi tana tafiya kamar wata me tausayin kasa tsayawa tayi abakin kofar tana wani jujjuyawa hade dayin kwai da cin gum din bakinta kamar wata yar tasha ( ohhhh ni ISHAM yau fah fanan na ban mamaki ) tunda tashigo yaji wani kamshi me daga hankali da kashe jiki ya ziyarceshi zuba mata ido yayi yana kare mata kallo tun daga tafin kafa tsayawa idonshi yayi akan santala_santalan cinyoyinta ,har izuwa kan kugunta kai idonshi yayi kan dukiyar fulaninta da kusan duka suna waje lokaci daya fah Mr azaad yashiga cikin matsananciyar bukatuwa musamman inyaga yanda fanan take wani irin jujjuyawa kamar wata macijiya , rausayawa tayi har gabanshi ta tsaya tayi kwai da cin gum ta fasa shi yayi kara tauuu, shide kamar wani mutun mutumi haka yadawo se kallo kawai dan yau fanan ganinta yakeyi kamar ancanza mishi ita , murmushi tayi with a sexy voice tace " habiby welcome home" be iyabata amsa ba inbanda kallon dukiyar fulaninta da yakeyi dan sun tsole mishi ido ganin hakane yasa fanan sa hannunta guda daya akan kirjinshi tadan turashi baya yafadi akan lallausan gadonshi bin bayanshi tayi tazauna akan cikinshi sannan tasa hannunta daya ta kwashe gashinta tamaidasu gefe daya , tadawo da dayar hannun tazame wuyan rigarta yanda yabawa breast dinta daman fitowa waje , daukan hannunshi tayi tadaura akan dukiyar fulaninta nata , wani irin shocking ne yaziyarcesu dukkansu biyu, aikuwa kamar wanda yake jira yafara wasa dasu , sa hannunshi yayi yariko kugunta sannan yazame rigar yafara bata sakonni hade bakinsu tayi suna aikawa da junansu hot kiss , zame bakinshi yayi acikin nata yasa fuskanshi akan wuyanta kamar wani maye haka yafara shinshinanta yana lumshe ido sannan yadawo da kanshi tsakiyar twins dinta yana wasa dakanshi awajan gaba dayan su sun rikice se maidawa junansu martani sukeyi , seda yakai kusan 40 suna romancing din junansu kafin yamaida ita kasanshi yafara kokarin kashe boss , bataji zafi ba saboda tsumin data narka gaba daya ya kara wutan shaawarta, seda yashiga tukun nan fa hajiya fanan ido yafara rena fata , sosai yake having sex da ita duk dauriyar datakeyi seda tayi hawaye dan jitayi ba marabar ranar farko da kuma yau Mr azaad yafita a hayyacinshi , hawaye kawai yakeyi yana sambada mata albarka tsaban yanda tayi mishi chakwai ( nide sadaf_sadaf na lalaba nafito naja musu kofa ,dan bazeyu wajan dauko muku rahoto Mr azaad yalura dani yamin koran damisa ba inje abanza ya karyamin kafa in shiga uku tom gwara maganin bari kar afara yasa nafito nabar musu part din nazauna awaje Ina jiran su kammala 😂😂😂 kamar wata marainiya ) Yaseer da zeenat suna main falo suna hira irin nasu na masoya labari zeenat take bashi shikuma yabiye mata , can ta kalleshi tace " ya yaseer kasanme?" Girgiza kai yayi yace " honey bansaniba sekin fada" tace " kasan meyake burgeni idan zaayiwa mata aure ?" Nan ma sake girgiza kai yayi batare da yace komai ba tacigaba da " ai amare sunacin dadi wata kaza aike dafa musu me shegen dadi amma akwai wani abu aciki kamar magani nina manta yanda ake kiran kazan ma katunamin " tafada tana kallonshi,tunda zeenat tafara magana yaseer yatsura mata ido yana mamakin aina tasan hakan yace " honey aina kika taba gani ?" gyara zama zeenat tayi tace " akwai wata kawarmu datayi aure last month tom inmunje gidansu ne semuga ankawo mata kazan mukuma semu tayata ci semu dingajin jikinmu na mana zummmmm! zummmmm haka " zataci gaba da magana yaseer yasa hannu yatoshe mata baki kafin yadafa kanshi aranshi yana" ohhh ni zeenat de irin matan nan ne da babu ruwansu komai fada suke ko a ina , fadi baa tambayeta ba kuma har cikin ranta batasan amfanin kazan ba bare tasan dalilin da yasa ake bayarwa " mikewa yayi yace" honey kije ki kwanta dare yayi zamuyi waya kinji ?" Tace " tom ya yaseer bye-bye senazo maka amafarki " tafada tana haurawa upstairs shikuma yafita Yana girgiza Kai. via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚 ( J. W. A 📚📚) Gargadi Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowaci siga, ko akaranta min shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ,ko a hadamun document ko amin edit ,idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutum zebimin hakkina Kuma yasakamin. PAGE 5️⃣6️⃣ MR AZAAD & SARAUNIYA FANAN suna kwance acikin bargo idon su biyu har sha 11:20 nadare basuyi bacci ba tana kwance akan kirjinshi tayi luff tanajin yanda zuciyarshi yake bugawa , Mr azaad yadade be tsinci kanshi cikin yanayin farin ciki da annashuwa irin yau ba fanan ta mishi komai yarasa wani irin so ze nuna mata wanda ze gamsu , yau tajiyar dashi dadin da ya wuce za'kin zuma shafa fuskanta yayi ya ce " baby ! Allah ya miki albarka kedin ta dabance kinshayar dani zumar daban taba dandanawa ba " kayittaciyar murmushi tayi ta ce" ameen habiby inasanka sosai aduk halin da zaa shiga inason kamin alkawarin bazaka taba rabuwa dani ba koda na tafi karka manta dani sannan kasan me nakeso kamin dan Allah?" she sounds very serious hakan yasa ya maida ilahirin hankalinshi kanta ya ce " inajinki " ta ce" dan Allah koda na tafi I didn't survive kayi aure kanemi mace me hankali ka aura kaji ?" wani irin kallo yake mata ranshi lokaci daya yabaci ya ce " banason insake jin wannan kalmar abakinki! In sha Allah zakije kiyi abinda yakaiki sannan harma ki dawo muci gaba da rayuwarmu " jinshi kawai takeyi amma deep down her heart tasan bazata taba dawuwa ba , shisa takeson tunyanzu tafara mishi maganar yayi aure , shafa dogon lallausan gashinta yayi ya ce " baby banason indinga jin irin wayannan maganganun daga bakinki ! Inada full confidence akanki za'ki yaqesu sannan kidawo" gyada Kai kawai fanan tayi kafin tasake shigewa jikinshi, body contact din da suka samu ne yasake saukarwa Mr azaad wata sabuwar shaawar amma yayi kokarin dannewa dan yasan fanan yau tayi namijin kokari saboda tasha bakar wahala da azaba amma inbanda iya hawaye babu abinda tayi kafafunta duk rikewa sukayi danshi yakaita bathroom yamata wanka yanadota a towel kamar yar jaririya se zuba mishi shagwaba takeyi . haka yamusu adduah suka kwanta. Washe gari shida kanshi yakaita toilet ya gasa mata jiki tayi alwala yadawo da ita, ta gabatar da sallah shima yafita zuwa masallaci yau duk wanda yaga Mr azaad yasan yana cikin matsanancin farin ciki fuskanshi ma kadai ya isa ya nuna hakan dan yau fuskar asake yake bakamar kullum ba . Suna dawuwa daga masallaci yashiga wajan ummi , tana kwance alamun ba ta dade da idar da sallah ba ta kwanta hannunta rike da carbi , zama yayi yadaura kafafunta akan cinyarshi yafara mata tausa , ummi tunda taji hakan tasan wayene bude ido tayi akan Mr azaad ta ce " son!" Ya ce " barka da safiya farin ciki na " dariya ummi tayi ta ce " katashi lfy , yau kazo yiwa umminka tausa kenan dama ka dade bakamin ba " murmushi kawai yayi bece mata komai ba yaci gaba da yi mata tausan . " Ummi ! jibi zanyi tafiya inada meeting a USA kuma zan iya kaiwa wata daya ko biyu " jin haka yasa ummi cewa " tom amma kasan auren fawwaz da zeenat saura wata biyu de ko? " ya ce " nasani ummi zandawo kafin lokacin " ci gaba da magana ummi tayi" tom yanzu feena fah yakamata kutafi tare saboda inason kutsaya a dubai kuyi ko da one week ne , kaga basu san ta ba , itama ba ta san su ba! ko jiya da nayi waya da abbu seda yamin maganar. kasamu kuje " motsa leben bakinshi yayi kawai ba dan tana kallon fuskanshi ba bazatayi tunanin ya amsa ba , haka yadinga mata tausa har bakwai nasafe kafin yakoma part din su , tana kwance tana bacci tarufe duk ilahirin jikinta da blanket iya cute face dinta ne a waje , Kiran layin masu aikin gidan yayi yasanar a zo part dinshi agyara dan dama tunda fanan ta dakatar dasu take gyarawa da kanta bata sake barin sunzo mata gyara ba komai ita takeyi , shigowa wata mata tayi ta gyara ko ina fess ta tafi har time din baccinta takeyi , ganin tara yakusa ne yasa ya kwabe kayan jikinshi yarage daga shi se singlet da boxers farare , murdaddiyar jikinshi nan awaje masha Allah ga gashin jikinshi sun sake qa'wata jikin , kitchen yashiga yarike kugu yanabin ko ina da kallo yama rasa mezeyi kusan 10mint yana tsaye be gama yanke abinda ze mata na breakfast ba,wani tunani yayi yasa ya dauko frypan yadibo kwai ya kada yasa albasa da maggi kadan ya soya kwan , yasashi acikin plate ya hada mata tea me kauri da kuma slice bread din white light. Ya hada komai akan tray madedeci yafito a kitchen din se zufa yakeyi idon nan yayi jawur saboda yankan albasar da yayi yanada zafi , ajiye tray din yayi akan table sannan yahau gadon yaje dede kunnenta cikin rada ya ce " baby ki tashi kiyi breakfast na miki da kaina " tanajinshi amma baccin be sake taba yasa ta ki tashi , dagata yayi yazaunar da ita a tsakiyar gadon , kukan shagwaba tasa mishi tana dukan kirjinshi hade da turo baki rike hannayenta yayi yasa idonshi cikin nata ya ce " muje kiyi brush " daukan yar baby yamata ya sabà ta a kafadarshi sukayi bathroom, can suka fito nanma yana dauke da ita , zaunar da ita yayi akan bed ya dauko tray breakfast din ya ajiye akan bed . Kallonshi takeyi ba ko kyaftawa mamaki da tausayinshi ne yakamata ganin yanda idonshi yayi jawur tasan wannan aikin albasa ne , tayi mamaki jin shi ya mata breakfast lallai arayuwan nan nothing is permanent komai me wucewa ne in bahaka ba wai yau ita ce Mr azaad yayiwa breakfast mutumin da ko magana ma wahala yake bashi , lura da mamaki takeyi yasa ya ce " baby bari kiji ko nima na iya girkin " ya fa da yana yanko hadaddiyar kwai din yasa akan sliced bread din yakai mata baki, gutsura tayi ta ci , ba yabo ba fallasa kwai din yayi dadi balaifi, babban yatsanta tadaga alamar jinjina sannan ta ce " wow ! habiby aina ka koyi girki ?" Ya ce " zan fada miki amma ba yanzu ba" haka yadinga bata egg and bread da tea harta koshi shima yaci yakai tray din kitchen. Yadawo yana mustsuka ido kamar zeyi kuka dan seyanzu ne yakejin zafi a idonshi, kwantar da kanshi yayi akan cinyarta yana ci gaba da murza idon , ganin haka ne yasa fanan sa kyawawan hannunta akan fuskanshi ta bude dara_daran sexy eyes dinshi ta matso da bakinta setin idon tafara wura mishi iska me dadi kusan minti biyar sannan ta tsaya Ta ce " yanzu ya denayi ko yanayi ?" Gyara kwanciyarshi yayi kanshi na kan cinyar nata ya ce " yadena ! and na manta ban fada miki ba ,jibi zamu tafi USA daga nan kuma zamuje dubai " shafa lallausan sumar kanshi tayi tana murmushi ta ce " Allah yakaimu". daga waya yayi yasa akunne yafara magana " okay ganin zuwa " daga kanshi yayi a cinyarta ya ce " baby inazuwa " gyada mishi kai tayi yafice yabar mata wayarshi tana buga game. tana kwance tana game yashigo bedroom din hannunshi da wata yar siririyar qyalle fari me kyau daga dan bakin kofa yatsaya ya ce " baby zaki iya tafiya ?" ajiye wayar tayi ta sauko akan gadon , dagashi har ita basuyi tsammanin zata iya taka kafar ba saboda jiya har kuka tayi mishi kafarta yarike bazata iya tafiya ba amma yau da ikon Allah taji yasake , ahankali take tafiya jikinta sanye da jallabiyarsa daya mata tsayi da girma sosai kanta kuma da pink din gyale ta daurashi , ta iso gabanshi murmushi yayi yasa wannan yar qyallen ya daure mata ido dashi sannan ya dafa kafadarta suna tafiya ahankali hankali suna zuwa wajan staircase yadagata har suka sauko main falo areef ne da zeenat kawai suke zaune sukaga fitowarsu , direta yayi akan kafafunta acikin falon sukaci gaba da tafiya suna tunkarar kofan barin part din. _______ ta ce " wayyo habiby bamu iso ba har yanzu ?" ya ce " yes saura kadan " haka har suka iso cikin compound din, sa hannunshi yayi acikin aljihu yafito da wata hadaddiyar car key yadamka mata a hannunta rikesu tayi dukda batasan meye bane idonta arufe , warware mata dauren qyallen yayi daga idonta ya koma gefe yatsaya ya harde hannunshi ya ce " surprise" Slowly tabude manyan idonta tafara ganin dishi_dishi sauke idonta tayi akan . Brand_new Range Rover SV version white color wanda kudinshi yakai kimanin $234,000 dollars akudin Nigeria kuwa yakai kimanin naira million dari biyu da hamsin ( 250 million) , motar ce da ta amsa sunanta se wanda ya isa manyan masu kudine kawai suke iya hawar wannar motar, jikin motar an mata kwalliya da jan balloons( balon balon) da flowers jajaye , kallon motar takeyi ba qaqqautawa sannan ta kalli car key hannunta. kallonshi tayi tana neman karin bayani juyawa tayi tana kallonshi murya na rawa ta ce " habiby....." girgiza mata kai yayi alamun kartace komai yana me nuna mata jikin motar da akabar envelope me kyau sosai kamar IV , dasauri ta isa jikin motar ta sa hannu ta ciro envelope din hannunta har rawa yakeyi wajan bude wa paper ne ajiki anyi rubutu da jan alkalami an rubuta " MY FEELINGS FOR YOU ARE VERY STRONG! YOU HOLD A SPECIAL PLACE IN MY HEART BABY, I love you so much . Here is a small gift for you, hope you liked it " karantawa takeyi ayayinda ruwan hawaye ke gangarowa daga kwayar idonta na farin ciki yar ihu tayi kafin taje da gudu ta fada jikinshi ta rungumeshi sosai tana tsalle na murna hade da kuka duk ta kasa bude baki ma tayi magana in banda kukan da takeyi, rungumeta yayi shima yana shafa bayanta fuskanshi dauke da kayittaciyar murmushi, ihu datayi ne yasa zeenat da areef dasuke falo fitowa da gudu dan su tunaninsu wani abune yafaru dakatawa sukayi ganin dankararriyar motar range Rover SV version a fa ke agaban Mr azaad da fanan dasuke rungume da juna , yasa suka gane Mr azaad ne yabawa fanan amatsayin gift sosai sukayi farin ciki motar yamusu kyau sosai, daka tsalle zeenat tayi dan farin ciki kamar ita aka siyawa motar tayi part din ummi da gudu fadowa dakin tayi seda ta tsorata ummi ganin yanda tashigo da gudun gaske ta ce " ke lafiya meyafaru?" dariya zeenat tayi tariko hannun ummi tana janta sede ta tashi , mikewa ummi tayi tabiyota tana rike da hannunta. seda suka kusa falo kafin cikin zumudi ta ce " ummi kinsan meyafaru? " ba ta jira abinda ummi zatace ba ta daura da " guess what! ya azaad ne ya siyawa anty fanan motar brand new range Rover SV version, oh my God motar nan ta hadu ummi gaskiya ya azaad yana son anty fanan" magana takeyi babu ko hadiye yawu kamar wata yar jarida, ummi tunda taji haka tayi yar dariya ta ce " wallahi zee Allah ya shiryaminke " tafada tana raba hannunta da nata tayi gaba tabar zeenat din abaya a compound din gidan ta samesu motar na fa ke har lokacin fanan tana jikin Mr azaad, kallon ummi fanan tayi ta raba jikinta dana Mr azaad taje da gudu ta rungume ummi gam ta ce " ummi kalle motar da Mr azaad yaban " murmushi ummi tayi ta ce " wow my feena congratulations ! natayaki murna yanzu sauran koyan driving, jeki kalli motar ki dakyau " ta raba jikinsu har rige_rige sukeyi ita da zeenat suka karasa wajan motar suna tattaba balon balon da flowers din sannan fanan ta bude murfin kofar motar tashiga ciki da shima duk an cikashi da furanni da balon balon anyi decorations din cikin motar kamar wasu yara ita da zeenat se fasa balon balon din sukeyi suna dariya , su ummi da Mr azaad suna tsaye suna musu dariyar fa sa balloons din dasukeyi kamar wasu kana nan yara. komai na motar abin kallon ne haka suka gama kallo motar zeenat da fanan suka rungume juna zeenat na fadin " congratulations anty fanan a kashe lafiya " ta ce " ameen darling sis " sannan suka fito , wajan Mr azaad fanan taje ta riko hannunshi duka biyu murmushi kwance akan fuskanta ta kalli cikin idonshi ta ce " nagode! nagode! nagode habiby banida bakin dazan iya maka godiya wallahi am out of words bansan wani kalan godiya zan maka ba , Ubangiji Allah yakara arziki da budi , ya kareka daga sharrin makiya da mahassada , ya tsareka daga sharrin mutum, aljani, karfe , yadauwamar da farin ciki arayuwarka yasa kagama da duniya lafiya . Yabiya maka dukan bukatunka na alheri , ya Allah yasa ka gama da iyayenka lafiya " haka tadinga kwararo mishi adduo'i shi kuma shida ummi da zeenat, areef suna amsawa da " Ameen " fuskansu dauke da murmushi. Jawota jikinshi yayi ya rungumeta, ummi ce ta ce " wato ni kun manta dani ko " ta fada tana bude musu hannayenta duka biyu, rungumeta Mr azaad da fanan sukayi ta rungumesu itama cike da farin ciki haka zeenat da areef suka rungumesu gwanin burgewa happy family. Duk abinda sukeyi akan idon mommy dake tsaye ta window falonta tana kallonsu tana hucin bakín ciki tana fadin " wato ni kun tarwatsamin nawa farin cikin, ku kuna farin ciki lallai! tabbas ni ce ajalinku gaba dayanku bazan barku da rai ba sena kasheku" tana magana tana huci kamar wata zakanya idonta ya canza launi zuwa jajir kamar jini hancinta da kunnenta nafitar da bakin hayaki. " baby let's go highway driving" cewar Mr azaad yana mika mata hannunshi takama suka shiga cikin motar tanawa su ummi bye_bye su ma byebye suka mata , ya tada motar masu gadi suka wangale musu tangamemen gate suka fita suka hau kan titi yana driving da hannu daya itakuma tana rike da hannun guda daya airport suka nufa , babban filin koyan driving din airport sukaje yayi horn me gadi yabude musu gate babu kowa acikin gaba daya filin, suna shiga ciki yayi packing yabude yafito itama tafito zama yayi a seat din data zauna yace mata tazauna a driver seat din , zama tayi tarufo kofar motar , yafara koya mata tuki a hankali_hankali, tun 11 yake koya mata har kusan karfe 1 , sannan yace yanzu baze nuna mata ba ta tuka da kanta yagani , kwakwalwarta nada saurin daukan abu aikuwa haka tafara driving dinsu acikin wannan filin beyi mamaki ba dan yasanta da kaifin basira , tana cikin driving din kawai taja birki ta tsaya kallonta yayi ya ce " meyasa kika tsaya kuma?" kashe mishi ido tayi sannan ta je kan seat din da yake zaune ta zauna akan cinyarshi suna kallon fuskan juna , matso da fuskanta tayi daff danashi har suna shakar numfashin juna , hancinsu na gogan juna sannan ta hade bakinsu waje daya tafara zuba mishi zafafan hot kiss me gigitarwa , Mr azaad dayake a hannu aikuwa nan take shima ya karbi sako yafara juya harshenshi cikin bakinta yana wasa dashi , sunkai kusan 20 mint ahaka kafin tacire libs dinta acikin nashi tana kokarin sauka akan cinyarshi yariko kugunta ya ce " please no baby let's make sunna here " idonshi jawur tadanno mishi da wutar shaawar dake damunshi har mararshi yafara mishi ciwo , kallon yanda yakoma ne yasa taki tashin dan bazata iya barinshi awannan halin yanda yake sata farin ciki itama dole tasashi , yasa hannu ya balle botil din jikin jallabiyar , yayi ka sa dashi ya manna bakinshi akan dukiyar fulaninta yafara sha kamar wanda yasamu sweet , shafa kanshi kawai takeyi tana lumshe ido dan salon da yake mata tana ji har tsakiyar kanta ganin suna atakure ahakan ne yasa ya kwantar da kujeran yakwanta , yadawo da ita kasanshi, cikin so da kauna yake having romantic and gentle sex da ita cikin nutsuwa dakuma binta a hankali yanda yasan bazataji zafi ba , lumshe ido tayi tana cize libs dinta bata wani jin zafi sedan abinda bazaa rasa ba wannan karon zata iya cewa tasamu sassauci , almost an hour kafin yasamu gamsuwa sosai yacire jikinshi daga nata yakoma gefe ya kwanta yaname rungumeta hade da manna mata kiss a goshi. Seda suka huta tukun nan suka gyara jikinsu cike da farin ciki da kaunar juna suke hira , ya tada motar dan komawa gida tafiya sukeyi akan hanya sunzo dede junction din anguwar bagadaza da karfi ta ce " habiby dakata " wani irin wawan birki yataka daya kusa causing din accident kafin yakoma gefen titi ya ce " baby meyafaru wani abu ne yasameki ?" turo baki tayi ta ce " habiby kaga wancan yalon nakeson ci " ta fada tana nuna mishi inda me bairon yalon yake tsaye yana saida yalo , sake baki Mr azaad yayi ciki da mamaki da al ajabi yake kallon fanan yanzu dama saboda wannan abun ne ma ta tsayar dasu har suna kokarin yin accident, ya ce " yanzu baby akan wancan abun kika kusan samuyin accident? Ya salam " yafurta yana rike habarshi , ko ajikinta ta ce " habiby kaje kasiyomin ka ji ?" tafada kamar zatayi kuka shide yana ganin iKon Allah yau kuma fanan rigima takeji dashi kallon yalon dake cikin bairon yayi sosai danshi kwata_kwata besan wannan abun ba kaf iya rayuwarshi be taba ganinshi ba . babu yanda ya iya haka ya sauko daga motar ya tsallaka titi yaje gun me yalon yabashi 20k yace abashi wannan abun aikuwa me yalo jikinshi har ba'ri yakeyi ganin yau ka karshi ta yanke saqa duk yalon dake wajan yadinga juye mishi su acikin manya_manyan ledoji kusan biyar , shide Mr azaad ido kawai yazuba mishi yanasonjin waye yake hadawa wannan tarkancen , gama zubawa mutumin yayi sannan ya washe baki ya ce " yauwa yallabai nagama bari insa yara sukai maka motar " hade fuska Mr azaad yayi ya ce " wa din ? duk karikesu leda daya kawai zaka bani " daukan leda daya yayi yawuce abinshi yabar me yalo se godiya yake mishi. Shigowa motar yayi ya ajiye ledar akasan motar bedewa tayi ta dauki gudu uku tafara duba cikin motar ko zataga ruwa can back seat ta hango bottle water da Mr azaad yayi amfani dashi dazun dauka tayi tabude motar tazuro hannunta waje ta wankesu bata damu da ajike suke ba ta daurasu akan jallabiyarta ta dibo wasu tasake wankewa, shide Mr azaad ido kawai yazuba mata, rufewa tayi yaja motar suka tafi , cin yalon takeyi harda lumshe ido taci yakai goma , se kallonta yakeyi can wata tunani yafado ranshi " anya wifey ba ciki take dashi ba " jinjina kai yayi yana tabbatarwa kanshi hakan dukda be tabbatar ba. Packing yayi suka shiga cikin part dinsu , bedroom dinta zata shiga ya ce " muje muyi wanka " batayi musu ba tabishi , rage kayan jikinsu sukayi tadaura towel tazauna akan bed ta jirashi yafito lura da jiranshi takeyi yashiga yafito yasa yazo bece mata komai ba yadauketa yayi toilet da ita ya sauketa acikin jacuzzi dake cike da warm water, cire towel din jikinsu yayi dasuka jiqe wasan ruwa suka tsaya sukeyi kamar yara Sannan sukayi wanka hade da wankan tsarki, bayan sun fito ne yasata ta shirya tasa doguwar riga na roba tasa hijab jalbab suka fito wannan karon cikin packing lot dinshi yashiga ya dauko motar kirar Maserati baki suka shiga . suna zaune shida ita a office din doctor ammar andibi jininta zaayi gwaji , angama suna jiran result yafito . shigowa doctor ammar yayi hannunshi rike da result din yazauna ya mikawa Mr azaad ya ce " ango babu komai tukun , Allah ya kawo babban rabo " suka amsa da ameen ita fanan ma se yanzu taji kancewa test din ciki aka mata kuma babu, ko ajikinta, Mr azaad shi yayi tunanin he's going to be a father harya fara murna amma hakanma yana rokon Allah yakawo me albarka haka suka koma gida shiya ajiyeta ya wuce company itakuma tashiga ciki ganin ummi a kitchen ne yasa ta tsaya ta tayata aiki. Areef yana zaune a garden yana video call da abokanshi yafara ganin duk wani haske ahankali hankali yana gushewa , har ko ina yazama dulum ba haske koda digo ne mamakine da tsoro lokaci daya yakama areef domin yasan yanzu de time baze wuce irin karfe 5:30 haka ba amma one time ace ko ina yayi duhu , yanata lalube dan yasamu yafita a garden din dan amatukar tsorace yake, kawai yaji ya lalubo mutum tsayawa yayi cak waje daya yafara kallon wanda yataban daga kasa fararen kayane ajikinshi dagowa yayi yakalli fuskanshi , wani irin kerma jikinshi yadauka ba qaqqautawa hannunshi na matukar rawa yanuna inda wanda ya da fan murya na vibrating ya ce " mansooooooor " seda yaja sunan.... Tom sekuma munhadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏. Kar a manta yin comment.. https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 Gargadi.... Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashi na book din nan ba takowani siga, ko akaranta min shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a hadamun document ko amin edit , idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutum zebimin hakkina Kuma yasakamin. Page 5️⃣7️⃣ kerma kawai jikin areef yakeyi ganin dan uwanshi mansoor zahiri agabanshi hakan ya matukar girgizashi dakuma daga mishi hankali dan kowa yasan de mansoor ya mutu. Magana mansoor yafara mishi da murya me matukar sanyi ya ce " ya areef ni ne fa! kanin ka mansoor, nayi kewarku sosai , kunsan waye sanadiyar mutuwa ta kuwa ?" har wannan lokacin jikin areef be bar kerma ba bin Mansoor da kallo kawai yakeyi dan bawani gane abinda yake fada yakeyi ba kawai ganin bakinshi yayi yana motsawa amma tsaban a rude yake bayajinshi . Mansoor yasake cewa " mommy ce fah tayi sanadiyar mutuwa ta ita ce musabbabin komai wallahi itadin muguwa ce ku kare kanku daga sharrinta" duk wannan bayanin da fatalwar Mansoor keyiwa areef baya jinshi dan hankalinshi baya jikinshi yana razane. areef ji yayi an fincikoshi qara yayi yana" Mansoor ne wallahi Mansoor ne na ganshi da ido na" girgiza shi da karfi fawwaz yayi ganin yafita a hankalinshi yana wasu sambatu dago kai areef yayi yaga fawwaz ne ya ce " fawwaz wallahi naga Mansoor yanzun nan yana nan wajan har yanamin magana " yana magana yana fisge jikinshi daga rikon da fawwaz ya mishi, sosai fawwaz yasake rikeshi yana tunanin kode kwakwalwarwashi ne yafara samun matsala saboda shigowarshi garden din ne ya ganshi yana tsaye shikadai yakafe waje daya da ido ga jikinshi da ya ke rawa kamar wanda aka jonawa shocking shisa yazo ya rikeshi. dakyar ya iya jan areef har cikin falo ya zaunar dashi , duk ya rude dakyar fawwaz yashawo kanshi ya nutsu sannan ya tambayeshi " meyafaru?" bayani yafara mishi dalla_dalla akan ganin Mansoor da yayi cikin sigan kwantar da hankali fawwaz ya ce " areef ka kwantar da hankalinka kawai is just imagination amma katabajin wanda ya mutu yadawo ne , Mansoor is gone kadinga mishi adduah". " hmmmm " kawai areef ya ce dan shi kadai yasan me yagani tabbas ganin Mansoor da yayi bawai mafarki bane kokuma gizo dagaske ya ganshi amma hankalinshi yakwanta jin kalaman fawwaz, haka fawwaz yadinga kwantar mishi da hankali har time din sallah yayi suka tafi masallaci gabatar da sallah mangrib. Hairah tagama shigo da food flask din abincin dare da zaaci tazauna agefen auta dake faman yiwa Mama surutu wai ita ahakan labari take bayarwa tun mama na amsa mata harta fara bata amsa da "uhmmm, eh, hmmm" hairah se dariyansu takeyi ganin mama de adole take amsawa auta , dan auta in tana bawa mutum labari yayi shuru ya shareta seta fashe da kuka shisa inde tana bada labarai gudun rigimarta suke amsawa dukda wani lokacin bagane abinda take fada sukeyi ba . Baba da ya usman ne suka dawo daga masallaci sunyi sallah isha suka zauna a falon dan cin abincin dare , gaishe da baba hairah tayi ya amsa fuskanshi asake , satan kallon ya usman tayi dake zaune yana danna waya ta ce " ya usman barka da dawuwa?" batare da ya kalli inda take ba ya ce " yawwa hairah barka de " fuskanshi ba yabo ba fallasa sabanin da inde ze amsa gaisuwanta fuskanshi dauke da murmushi kuma se ya kalleta kafin ya amsa gaisuwan amma tunda wannan abin yafaru daga ranar da ya furta mata kalmar " I won't force you again" ya canza mata sosai he totally changed hakan baya mata dadi, se lokacin da tace zataje bashi hakuri sekuma ta fasa . Sawa kowa abinci mama tayi tuwon cus_cus ne da miyar stew dayaji namomi aciki, suna cikin ci sukaji muryan hafiz . cire hannunta tayi acikin abincin dasukeci ita da auta ta mike da gudu taje ta rungume yayanta sannan ya tsuguna ya gaishe da kowa suka amsa da fara'a akan fuskokinsu zama yayi hairah ta gaisheshi, kallon auta yayi ya ce " abokiyar yau ba magana ne " cike da iyayi ta ce " ni ai babu ruwana dakai ya hafiz dakai da ya areef no me no you" dariya duka sukayi dan sunsan abinda yasa ta fadi hakan , saboda ranar da areef da hafiz sukazo gidan ta na ce seta bisu wajan anty fanan dinta sukuma ba gida zasuyi ba , ta tayar musu da rigima aikuwa sukayi wayo suka gudu shine yau da hafiz yazo taki kulashi, kama kunne hafiz yayi ya ce " sorry yar autanmu " batako kalleshi ba ita adole tana fushi ta ce " ina wuni " kunshe dariya hafiz yayi ya ce " lafiya lau yar auta" cikin zolaya ya usman ya ce " hafiz kayiwa Allah karka daga mana rigimarta da wannan daren" nanma dariyar sukayi baba yamusu alama dasuyi shuru dan kuwa auta ta cika tayi bam kamar zata fashe kafin su gama dariyar tasu ta bare baki ta fashe da kuka kamar wacce akawa wani abun. Lallashinta sukeyi amma takiyin shuru mama ce tadauki wayan wuta ta ce " kifa kiyayeni yarinyar nan ko in miki dan banzan duka tam" mit auta tayi kamar bata falon, dama kukan ba hawaye tayi shuru taci gaba da cin abinta tana turo baki , karawa su ya usman abinci tayi dan su biyu ne shida hafiz . sun gama cin abinci hairah da auta sunkai komai kitchen suna zaune suna hira baba mikewa yayi ya ce " tom nide na shige seda safen ku" suka mishi seda safe yashige bedroom dinshi haka ma mama ita da auta suka tafi yarage daga hairah,hafiz se ya usman. Hafiz ganin dare yayi ne har karfe 9 yasa yamike ya ce " ya usman bari inwuce dare nayi ! hairah seda safe " rakashi har bakin gate sukayi inda driver ke jiranshi ya tafi , wuceta yayi zeshiga falo yasa hairah tayi saurin riko hannunshi, dakatawa yayi yajuya ya ce " lafiya? " narai_narai tayi da fuska tasake rike hannun gam ta ce " ya usman dan Allah kayi hakuri natuba kayafemin " raba hannunshi da nata yayi zesake wuceta tasha gabanshi ta tare mishi hanya , ba'ta fuska ya usman yayi ya ce " malama kiban hanya in wuce bacci nakeji " cika idonta yayi tab da kwalla suna kokarin zubowa ta ce " ya usman wallahi bazan iya jure wannan baqar horon da kakemin ba ! Kasan yanda nakeji kuwa ? kasan yanda raina yake kuna kuwa ji nakeyi kamar in mutu bazan iya jurewa ba zuciyata nada rauni sosai kayi hakuri" ta karishe maganar tana sheshekar kuka hade da sunkuyawa kasa tana kuka , shikanshi dama kawai jurewa kawai yakeyi amma rashin kulata da bayayi yafi kowa shiga damuwa amma yau dole ya hakura dan baze iya jure wahalar da zuciyoyinsu ba , sa hannu yayi ya riko kafadunta yadago ta tsaye ya kalli cikin idonta cikin tsokana ya ce " to dear yakikeso in miki ? nabarki ne kawai kisamu irin freedom din da kikeso, za ki iya auren wanda kikeso " sake fashewa tayi da wani kukan tana " banaso ! banaso ! banaso kadena fadamin haka ko in hadaka da mama " dariya yayi ya ce" to shikenan kinyarda muyi aure wata daya me zuwa ?" dasauri ta gyada mishi kai alamar amincewa , murmushi yayi ya ce " to shikenan gobe zanwa baba magana anema min aurenki " murmushi ne ya subuce mata tafara blushing murmushi shidinma yayi ya ce" ki shirya go be zankaiku yawo keda auta " nanma gyada mishi kai tayi kafin ya mata seda safe suka shiga ciki ko wanne ya shiga bedroom dinshi hankalinsu kwance zuciyarsu fes dauke da farin ciki. Khairatyyy dake gefensu tana kallonsu tayi murmushi ta ce" alhamdulillah Allah nagode maka daka bani iKon sasanta wannan lamarin cikin sanyi " tafada tana murmushi sannan tafara tunanin ayanda tahada su. Wata rana tanata shawaginta aduniyar bil adama tazo dede anguwar pantami kawai Allah ya nuna mata hairah da ta fito a firgice ko takalmi babu a kafanta tana rike da wata tsohuwar naira ashirin (20 naira) ta tsaya abakin kofar wani karamin chemist ta ce abata paracetamol mugun kaman da sukeyi ne yaba khairaty mamaki dayasa seda tasa hannunta ta shafa nata fuskan , karban maganin hairah tayi tashiga yar karamar gidansu da ginin yafara daddarewa , bakin randar kasa taje tadibi ruwa a kofi tashige daki bin bayanta khairaty tayi domin ganin ina zataje , acikin dakin kuwa tasamu hairah zaune da wani kyakyawan yayanta da suke matsanancin kama . barewa hafiz maganin tayi tabashi hade da ruwa ya karba yasha yakwanta ta lulubeshi da tsohuwar bargo da taji jiki, wani tunani ne yafado ran khairaty yasa taje tadaura hannunta akan goshin hafiz nan take jikinshi yayi zafi yafara rawan sanyi tsorata hairah tayi nan take tafashe da kuka tafita a gidan da gudu inda tasan zata samu me gidan hafiz da yake hayan bairon dayakeyin dako tayi , aikuwa tayi saa ta sameshi a bakin kasuwar waya ta badaru , suna zaune acikin majalisa tazo tana kuka take fadamishi yayanta ba lafiya yataimaka ya kaishi asibiti, me gidan hafiz kuwa ganin idon mutane akanshi ne kowa najiran yaji mezece yasa badan, yayi niya ba yace muje gidan naku , ya tari napep suka shiga gidan aka dauki hafiz zuwa asibitin medical center zuwansu yayi dede da kawo ya usman da akayi yana aman jini , gado akabawa hafiz aka rubuta musu magani na kusan dubu bakwai me gidan yatafi da sunan siyan maganin daga nan ya gudu, har gari ya waye babu wani likitan dayazo kan hafiz da sunan dubashi hakan yasa hairah fitowa tana kuka ga tashin hankali ga yunwa , office din likita take nema , shafe duk wasu kofofi khairaty tayi yarage hairah kofa daya kawai tagani inda ya usman yake kwance kenan , tashiga dakin domin yin magana da likita anan ne ya usman yaganta dakowa dake wajan . Hakan yasanya khairaty farin ciki sosai saboda bataso ace saboda ita wani ya cutu nan take ta bace. Wannan kenan. 9:40pm hafiz suka dawo gida bayan driver yayi packing yafita yana kokarin shiga part dinsu kawai ya hango matashin saurayi sanye da fararen kaya har daukan ido sukeyi yana tsaye daga dan nesa yana kallonshi , mamakine yakama hafiz yafara tunanin dama bayansu ya fawwaz da ya areef akwai wani na miji agidan ne betaba ganinshi ba kuwa , ko ajikinshi yakarasa inda fatalwar Mansoor yake tsaye yana kallonshi, mika mishi hannu yayi dan suyi musabaha, girgiza kai fatalwar Mansoor yayi ya ce " ni bakamar kowa bane hafiz ! nasan bakasanni ba sunana Mansoor yaron mommy kuma nima ada ni kanin su ya azaad ne " wasu maganganu dayakeyi ne ya daurewa hafiz kai dan maganar abaibai yayisu yakasa fahimta ya ce " ban gane me kake nufi da kai kanin su ya azaad bane ada ? to ayanzu kenan kai ba kanin su bane ? amma meyasa to? sannan ya akayi kasan sunana dan ni nasan bamu taba haduwa ba ? " ya jero mishi tambayoyi atare , girgiza kai kawai fatalwar yayi ya ce" bazaka gane ba hafiz se anjuma kacewa kowa ina gaishesu inka shiga ciki " yagama magana yajuya yafara tafiya , hafiz afili ya ce " to ai hikenan" yashiga falo duk suna zaune abinsu harta ummi da Mr azaad fanan ce kawai bata falon taje dakin ummi neman dabino, zama shima yayi kusa da areef ya gaishesu ummi ta ce " hafiz harka dawo kenan ni na daukama ai tare kuka tafi da areef ashe yana nan shi " ya ce " eh ummi nadawo ! nace mai ai yazo mutafi yacemin shi tsoron rigimar auta yakeyi yasa ya ki bina dan yasan haduwarsu " dariya ummi da zeenat da fawwaz sukayi zeenat ta ce " lallai ya areef wato kai karasa ma wacce zaka tsokano se auta rigima " nanma dariya sukayi , hafiz ya ce " ummi dazan shigo na hadu da wani wai yacemin sunanshi Mansoor sannan Kuma yacemin in gaisheku sosai , ashe shima kanin su ya fawwaz ne " duk dagowa sukayi har suna rige_rige wajan kallon hafiz dake magana yasa lamarin basu mamaki da daure musu kai dan kuwa sunsan de tabbas hafiz be san Mansoor ba balle yayi irin wannan maganar, jikin areef ne yadauki rawa ya mike yana kallon fawwaz ya ce " fawwaz bana fada maka ba wallahi Mansoor na gani dazun amma kacemin sam bashi bane to gashi hafiz ma yaganshi " riko areef Mr azaad yayi ya ce " calm down areef " zama sukayi amma har lokacin jikin areef be bar kerma dayakeyi ba. shiko hafiz mamaki ne yakamashi ganin yanda firgici da tashin hankali ya bayyana akan fuskokinsu lokaci daya dan kawai ya fada musu yanda sukayi shida Mansoor din . Mr azaad ne yakalli hafiz ya ce " hafiz aina ka kalli shi Mansoor din ?" fada mishi hafiz yayi sannan Mr azaad yasake maida kallonshi kan areef ya ce " ka kwantar da hankalinka kafadamin aina kaga Mansoor din ?" duk abinda yafaru a garden din areef ya fada mishi sannan yakara da " yayi tamin magana wanda nakasa gane me yake nufi amma naji yafadi wata kalma 'ku kare kanku daga sharrinta ' wannan kalmar ce kawai zan iyacewa naji " zeenat kam uwar tsoro tunda taji aka ambaci sunan mansoor ta kankame fawwaz kam ta ki sakinshi. girgiza kai ummi tayi ta ce " karku daga hankulanku akan wannan mansoor yariga da ya mutu kawai sharrin shedanu ne da jinnu amma kun tabajin wanda ya mutu ya dawo ne " zaro ido hafiz yayi shima lokaci daya jikinshi yafara rawa jin wai Mansoor din da ya hadu dashi har sukayi magana wai matacce ne ya rigada ya mutu babban tashin hankalinshi shine inya tuna yar maganar da sukayi na wasu yan mintuna , da mugun karfi zuciyarshi yake bugawa sakamakon jin maganar yayi kamar saukar aradu hakan yasa yadafe kirjinshi da karfi sauka yayi akan kujera yaduqa kasa yana rike da setin zuciyarshi dagashi Mr azaad yayi yadan rungumeshi dan dama yasan hakan seya faru muddin hafiz yaji dan bakowane yake da wannan karfin guiwan tunkarar magana makamancin wannan ba ace kayi magana da wanda yarigada ya mutu baka sani ba daga baya inkaji hakan dole hankalinka yatashi , kokarin zaunar da hafiz Mr azaad yakeyi yaji yakara nauyi nan yagane suma yayi yasa ya kwantar dashi akan kujeran dauko ruwa fawwaz yayi yamikawa Mr azaad ya yayyafawa hafiz shuru be farfado ba , zama ummi tayi kusa dasu ta daura kan hafiz akan cinyar ta tarike hannunshi tana murzawa da dan karfi ko hakan ze temaka duk suna tsaye akanshi , saukowa fanan tayi tana murna tasamo dabinon dataje nema, ta samesu duk sunyi cirko_cirko sannan ga hafiz dake kwance dasauri takaraso falon , tambayar fawwaz tayi meyasa meshi karya yamata yafada mata kancewa sunga yarike kirjinshi ne daga bisani kuma yasuma zama tayi agefen kujeran ta rike hannunshi dede wajan pause dinshi taji yana harbawa da wuri tasake sa hannunta akan kirjinshi nan taji wani irin lugude da zuciyarsa yakeyi hakan ne ya tabbatar mata da tabbas wani abune yagani ya razanashi ko kuma wani abun yaji daya firgitashi kallon ummi tayi ta ce " yadan shigo yar doguwar suma amma zuwa nan da 4hours ze iya farfadowa amma kuma in muka bari ya farfado ahaka tabbas akwai matsala , ze iya samun matsalar brain kokuma yashiga firgici har nan da sati daya " tagama musu bayani tana karasawa kan center table tadauki pen and paper data gani ta rubuta allurai da magunguna ta mikawa fawwaz karba yayi yafice dasauri dukda darene zeyi wuya susamu pharmacy abude sede yadangana asibiti, duk suna zaune fanan ta kalli Mr azaad ta ce " Mr azaad meyasa meshi " bayason yafada mata yasa kawai ya ce mata " baby we don't know kawai ganinshi mukayi ahaka yarike kirjinshi" ta ce " Allah sarki inna mishi alluran nan in sha Allah zeji dama dama dan zesamu baccin 12 to 14 hours kuma baze tashi da wannan firgicin ba " jinjina kai yayi ummi ta ce "zeenat tashi kije ki kwanta dare yayi ko " make kafada tayi alamar ah ah dan duk atsorace take bazata iya kwana ita kadai ba , taso basu dariya areef kuwa shuru yayi yana binsu da ido , haka fawwaz ya dawo da allurai da magunguna , allurai fanan tayi mishi sannan Mr azaad yadaukeshi cak kamar wani yaro karami yayi part din su fawwaz dashi yakaishi dakinshi yakwantar dashi hade da rufeshi da blanket sukafito . Ummi tabasu umarni da kowa yaje ya kwanta haka suka shige part dinsu , Mr azaad maganar mansoor ya tsaya mishi arai amma zesan yanda ze bullowa lamarin . Duk wannan wainar da ake toyawa mommy bata da masaniya akai tana nan tana neman hanyar da zata kashe kaf yan gidan hatta yayanta suma seta kashesu bazata bar kowa ba dan dukkansu ta tsanesu mansoor ne kadai takeso shikuma yarigada ya mutu, tamafi tsanan anty shayida shisa aduk sanda anty shayida tasamu karamin ciki , tunkafin sunsan da cikin mommy take cinye dan tun a mahaifa, kusan sau takwas anty shayida nasamun ciki mommy tana cinyewa tunkafin yazama hallita take cinyewa. Haka tasoyiwa anty zainab amma dake mijinta atsaye yake gashi babban dan siyasa kuma malami. Bauchi state Fitowa suhaima tayi daga bedroom dinta tana rike da waya tana video call da fawwaz har karfe 11:30 nadare ta farajin yunwa tafito tashiga kitchen din ta ajiye wayar yanda yana kallonta ta daura indomie akan wuta yadafu taje falo tazauna tanaci fawwaz ya ce " ba bismillah kenan? " Yar dariya suhaima tayi ta ce " hubby tom ai kona maka bismillah bazeyu kaci ba sede inci mana ka ji " tafada tana ci gaba da cin indomie fawwaz ya ce " to babynah kici mana din " haka suka dinga hira kafin ya kashe kiran dan dare yayi suka sauka a online din . fanan ta dade dayin bacci while Mr azaad idonshi biyu beyi bacci ba dan so yakeyi adaren nan yayi clearing issues din dasuke faruwa acikin gidan sulalewa yayi yafice adakin yasauko ya bude kofar part din gaba daya yaje garden din shikadai kamar wani maye ko ina yayi tsit se kananun maganganun dayakeji kasa_kasa which is yasan nasu wayene haka yazauna yana girgiza kafa. Mommy na kwance akan makeken gadonta fatalwar mansoor yabayyana atsaye agefen gadonta, murya da dan karfi yafara kiran " mommy! mommy! mommy! Ki tashi kina bacci wato kin barni inata garari Koh?" adan firgice mommy ta tashi daga bacci tana mustsuka idonta rass ta waresu akan Mansoor dake tsaye yana sanye da fararen kaya tashi tayi tazauna dakyau tana kiran " Mansoor dina kaine? dana nayi kewarka" daka mata tsawa yayi ya ce " karki sake kirana da danki muguwa azzaluma, ke ba uwa ta gari bace annamimiya kawai . hankalinki yakwanta dakikayi sanadiyar barina duniya?" ya daka mata wani gigitacciyar tsawa " nace hankalinki yakwanta yanzu? bazan taba samun salama ba harse asirinki ya tono senayi hanyar dazan fadawa kowa ke matsafiyace yar kungiyar BAPHOMET masu shan jini da shirka , yanzu wato babban burinki shine ki kashesu ko ?" hawayene yake zuba akan kumatun mommy taduqa akasa ta ce " my son kayafemin yanda nakesonka bazan taba barin komai yasameka ba bare har inyi sanadiyar rayuwarka sannan magana akan daukan fansana dole sena kashesu kaf dinsu Koda shugaba tanzarzar be amince min ba sena aiwatar da hakan , daga zaran munyi nasarar gamawa da shafin sarauniyar nasminaya sesune target dina " girgiza kai kawai fatalwar mansoor kafin lokaci daya yabace bat . Inbanda tsuma da jijjiga babu abinda jikin Mr azaad yakeyi tsabar bacin rai da bakin ciki idon nan yajuya yazama mugun jajir da karfi yake cizan libs dinshi na kasa da har gurin yayi ja sosai yafara tsastsafo da jini . yau bayajin ze iya barin mommy ta kwana daranta seya kasheta dan daga inda yake zaune a garden yana yana jiyo duk wani maganar dasukayi da ita da fatalwar mansoor tabbas mommy ta cucesu ta ha'incesu yanzu dama all this while suna tare da munafuka matsafiya agida daya basu saniba tom tabbas shi zedau mumunar mataki akanta tunkafin abba yadawo daga marley sede yadawo yaji labarin kawai ya kasheta. yana cikin wannan mugun bacin ran fatalwar mansoor yabayyana agabanshi fuskanshi dauke da murmushi ya ce " yayana yanzu nayi farin ciki dakasan gaskiya akan mommy zansamu salama yanzu bazaku kara ganina ba se adarul salam nabarka lafiya " yafada yana me bacewa yanawa Mr azaad bye-bye shima bye-bye din ya mishi duk da yana cikin matsanancin bacin rai, hakan be hanashi maida mishi da martanin murmushin daya mishi ba, domin yafayyace musu komai dangane da mommy. Tofa ana wata ga wata yaude alhamdulillah asirin mommy yatonu shikenan. Ina jiran ruwan comments dinku duk wanda yasan ina binshi bashin comment yafito yamin abuna tam. Se munhadu ranar laraba jibi kenan inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏. https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚 Gargadi ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba takowani siga ko akaranta min shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutum zebimin hakkina Kuma yasakamin. Three pages in one . Page 5️⃣8️⃣ Yana barin garden din part din mommy yanufa kofofin part din arufe knocking yayi , mommy dake kuka taji ana knocking yasata goge fuskanta tazo ta bude kofar ganin Mr azaad ne yasa tadaure fuska tamau ta ce " kai lafiya zakazo kana bugamin kofa da wannar uwar Daren?" miskilin murmushi Mr azaad yayi yadan hadiye bacin ranshi ya ce " ehhh to lafiya ba lafiya ba zan iya shigowa ?" shima yajefa mata tambaya ganin taki motsawa daga inda take tsaye ne yasa ya kutsa kai cikin part din nata direct kan kujera yaje yazauna yana ciro wayarsa yakira layin abba, " hello abba sorry natasheka abacci banason kadawo ka ji labarin na kashe maka mata shisa nace bari in sanar dakai tukun" tunda abba yaji abinda Mr azaad yafada yagane kancewa yagano komai hamdala yayi dominshi yasan komai akanta amma shi sun rufe mishi baki Koda yayi kokarin sanar da wasu seya gagara , gyara murya abba yayi ya ce " karka mata komai tukun 4:00am zan biyo flight din safe just make sure bata gudu ba " jinjina kai Mr azaad yayi ya datse kiran. ganin ya shige mata falo ne yabarta tsaye acan bakin kofa , shigowa falon itama tayi taga ya zauna be da niyar tafiya kuma shi be fada mata abinda yakawoshi wajanta ba ya sa ta ce " katashi ka fita kabani guri " afusace yatashi dan dama haushinta yakeji kamar yakasheta lokaci daya kowa ya huta , ya mata mugun shaqa fiffitowa idon mommy yayi waje taji damkar maza kakari tafarayi idonta yajuya jaa tana kokarin shekewa domin shaqar da Mr azaad yamata bana wasa bane ya daka mata tsawa lokaci da ya yacanza fuskan nan tayi ja tsaban bacin rai " kimin shuru ko kuma kiyi dana sani" mit mommy tayi ganin ya hayayyako gashi yaki sakinta cillar da ita yayi ta kifu akasa tana rike wuyanta hade da nishin wahala ga idonta yayi ja , dakyar ta rarrafa tazauna akan kujera tana tunani iri_iri shi meyasa Mr azaad zeyi mata haka yaron da ma zata iya kirga sau nawa magana yataba hadasu tunda aka haifeshi be taba shiga part dinta ba sede in yanason hira da anty zainab da anty shayida ya kirasu suzo part din ummi ko a garden. Tanzarzar na kallon abinda yake faruwa ta mudubin tsafi nan yagane asirin mommy yatonu kuma inde taji bakar azaba zata iya tonawa sauran yan kungiya asiri hakan yasa yamata magana ta cikin madubin " hafsat kisan hanyar dazakiyi ki tsere musu domin yarigada yasan komai akanki " jin abinda tanzarzar yafada mata yasa taji wani irin fargaba yakamata bawai dan na asirinta yatonu ba sedan tasan muddin ta fadi wata kalma dangane da yan kungiya to tabbas nata yakare, dago kai mommy tayi ta kalli Mr azaad dashima firgitattun idonshi na kanta , wuff tamike zata da ki kasa domin ta bace kenan , sarauniya ta damki dantsen hannunta ta baya , wurgi da ita kasa sarauniya tayi tana binta da muguwar kallo da idanunta masu firgita abokan gaba fuskan nan babu alamun sassauci ko rangwama atare da ita. Mamaki ne yakama Mr azaad ya akayi fanan tasan da yana nan Kuma ga abinda yakawoshi, laakari da irin shigar dake jikinta dayayine yagane ba fanan bace sarauniya fadima ce , sarauniyar nasminaya, hakan yasa yamike yatsaya yana kallonta ganin ko inda yake tsaye bata kallaba bare yasa ran zatamai magana. abinda yayi laakari dashi shine duk sanda ta bayyana a asalin sarauniyarta tofa wasu dabi'un ta kamar bata sansu ba wata zuciyar ta ce mai " karfin jaaazana ne yasa hakan domin inta bayyana, sarauniya ce bawai fanan ba " gabanshi ne yatsinke lokaci daya, da ya tuna kenan fanan intabar nasu duniyar mantawa zatayi dasu gabaki daya kenan bazama tasan da zamansu ba balle tayi tunanin dawuwa wajan ahalinta, dafe kai yayi dayaji yana juyawa. daga inda sarauniya take tsaye ta daga hannunta tayi pointing mommy dake yashe akasa , kyasta yatsunta guda biyu tayi nan take igiyoyi suka fara daure mommy dauri bana wasa ba suka mata tamau yanda ko numfashi dakyar take iya fitarwa. tana gama daure mommy kuwa ta bace tabarshi tsaye awajan. barin part din Mr azaad yayi yasa securities su tsaya akanta kar subarta tayi koda motsine dukda adaure take . yakoma garden yazauna yana kada kafa har asuba , yayi alwala duk a garden din yanufi hanyar fita a gidan dan zuwa masallaci yaga su fawwaz da areef sunfito su ma. jerawa sukayi sukaje suka gabatar da sallah suka dawo be fadawa kowa abinda ke faruwa ba haka zalika be fada musu abba yataso ba yawuce part dinshi samun fanan yayi tana zaune tana azkar zama yayi akan kujera yana facing dinta harta idar ya ce " morning wifey" ta ce " habiby katashi lafiya ?" ya lumshe idanu kawai. ta ce " habiby ina kaje daren jiya natashi naga baka nan amma naganka amarfakina a part din mommy" " eh naje part dinta ne " daga haka yakawar da zancen ta hanyan dauko wata maganar daban ya ce " gobe zamu tafi yau zankaiki kije kiyiwa su mama sallama yau " cike da murna taji zataje gida ya ce " to Allah yakaimu" bata koma bacci ba ta cire babban hijab din jikinta yarage daga ita se wandon falazo da vest ajikinta tafara gyaran part dinsu tayata shima yayi suka gama , atare suka shiga kitchen sukayi breakfast dan wake tamusu tunda tafara kwaba dan waken da digawa Mr azaad yaketa yamutsa fuska yana " nide bazanci wannan abun ba abu kamar wani kwallo_kwallo " dariya tayi tasan be taba ci ba gashi itakuma shi takeson ci yau din nan gama danwaken tayi ta dafa kwai ta baresu sannan tayanka vegetables salad , tomato, ta yanyanka kwai din a bowl daban taki saka albasa aciki saboda yanzu seyasa bakin mutum yafara warin albasa, plate ta dauko tazuba danwaken dayawa sannan tasaka mai din data soya yaji albasa ta zambada yaji zaro ido waje Mr azaad yayi ya ce " yanzu da wannan pepper zakici baby" murmushi tayi ta ce " kadingayin jam'i zamuci zakace yau zan koya maka yanda akecin danwake" haka taci gaba da saka salad da tomato din da ta yanka tasa kwai din. ( bakaramin daukan hankalina danwaken nan yayi ba lokaci daya naji yawuna ya tsinke, kunsan ni , akwai ni akwai kaunar dan wake sosai. gashi ban Isa ince zanci ba yanzu se Mr azaad yayi kasa_kasa dani ) haka ta dauko plate din taje tsakiyar falo ta ajiyeshi akan carpet takoma taje tadauko bottle water da glass cup ta ajiye ta zauna zama shima yayi dan yaga yau tayi niyar kumburar mishi da ciki ne . sa hannunta tayi tafaraci tana santi babu yanda ya iya haka shima yasa hannu yayi yanda tayi yakai baki, ai ba arziki yafurzar dashi waje idonshi harseda ya kadà murya na rawa ya ce " is to spicy kiban ruwa " zuba ruwa tayi a glass cup ta mika mishi yasha yanata shishitan yaji, sannu tamishi sannan tasa hannu dede ta gabanshi ta kwashe yajin yarage dan kadan takara maggi ta gauraya mishi ta ce " to nacire yajin kaci ka ji " make kafada yayi kamar yanda take mishi a shagwabe ya ce " nide bazan iya cin wannan abun ba is to spicy" dariya tayi ganin yanda yake mata shagwaba hakan ya kayatar . diba tayi ta bashi abaki dakyar ya iya cinyewa dukda babu yajin sosai wannan karan, haka suka cinye danwaken tas daga ya ce yakoshi setace ah ah yakara kadan de haka ta mishi wayo tadinga feeding dinshi harsuka cinye ,sunaci suna shishitan yaji kamar wayanda akama dole, sukasha ruwa hancinshi har wani ja yayi dan wahala gaba daya yazama wani kala dukda yaji dadin danwaken amma ya ji ya azabtar dashi . Karfe 10:00am dede abba yashigo gombe yasauka agida part dinshi yayi , wanka yayi ya kimtsa babu wanda yasan da zuwanshi saboda babu wanda yasani se Mr azaad . Kiran yayanshi yayi awaya yasanar musu yanason ganinsu yanzu yanzu batare da bata lokaci ba , wannan kiran gaggawan da abba yamusu ya tayar musu da hankali yasa babu wacce tabata lokaci kowa suka hallara a main falo harta su Mr azaad da fanan duk babu wanda bezo ba duk suna zaune ,m afalo sukaji sallamarshi , zama yayi akan kujera fuska babu yabo ba fallasa. shan jinin jikinsu sukayi kowa yasake shiga rigar nutsuwa, suka fara gaisheshi. bude taro yayi da adduah sannan yafara magana " na taraku anan ne bandan komai ba sedan fayyace muku gaskiya" zuba mishi ido sukayi sunason suji meye ze fada , bin kowannesu yayi da kallo. ya ce " kamar yanda dukkanku kuka sani hafsat itace matata ta farko ! yar wazirin gombe ce tun kafin in kammala karatuna muka fara soyayya da hafsat , amma mahaifiyata wato marigayiya ammi , bata bada goyon baya ba saboda hafsat batada kunya bata son mutane kullum ako da yaushe adaki ake samun hafsat bata mu'amula da kowa seni sekuma yan gidansu ga ta da tsiwa ga shegen rashin kunya, amma dukda wannan dabi'ar nata take sona kuma nima inasanta, me martaba da waziri sunyi farin ciki sosai da kasantuwar wannan al amarin bayan na kammala karatu aka mana aure , me martaba yace tunda yanzu na kammala karatuna kuma nayi aure ni zan karbi sarautar gombe , hankalina yatashi domin ni bantaba kaunar zama sarki ba hasalima abubuwan sarauta baya burgeni ni babban burina shine inzama business man, shisa na ki kuma fulani ta goyamin baya , haka me martaba yakyaleni nayi abinda nakeso . dede da rana daya ammi bata ta ba son hafsat ba in an tambayeta dalili setace jikinta nabata akwai wani mugun abu atare da hafsat tana ganinta amafarkinta. babu wanda yataba daukan maganar ammi serious kowa gani yakeyi kawai dan ta tsaneta ne yasa take fadar haka. bayan aurenmu da wata daya ammi ta rasu sanadiyar bugawar zuciya haka akayi zaman makoki aka watse tundaga nan ne hafsat ta fara nunamin mugayen dabi'un ta, bata sallah , ba karatun addini ko adduah bantabaji tayi ba,bata kaunar kowa ya rabeni , sannan kullum tana daki yanda na fita nabarta haka zandawo in sameta bata, bantaba sanin ya kalar test din girkin hafsat ba har yau danake muku wannan maganar sede masu aiki suyi mana abinci. bata rayuwarta da kowa tun ina mata fada harna hakura nazuba mata ido domin daga zaran nafarayi mata fada itama zata hayayyakomin kamar zata dakeni nikuma bazan iya sa'in sa da mace ba yasa se inbar mata part din se dare in dawo haka har tasamu cikin zainab ta haifeta, tunda nake arayuwata bantaba ganin macen da ta tsani abinda tahaifa ba se akan hafsat ta tsani zainab har kamata natabayi tashaqe ta tana kokarin kasheta dakyar nakarbi zainab ahannunta jaririya dabatasan komai ba se zabga kuka takeyi . daukan zainab nayi nakaiwa fulani nafada mata abinda yake faruwa hannu biyu ta karbeta renon zainab yakoma gun fulani. mukaci gaba da zaman doya da manja nida hafsat yau lafiya gobe kuma fada da tashin hankali ahaka harta fara fita araina dan nagaji da mugayen dabi'un ta. zainab nada shekara uku hafsat tasake samun wani cikin bata nuna bataso ba wannan karon har ina murna gata iya gata na nuna mata amma tana haihuwar shayida komai yasake dagulewa tsantsan tsana shayida tagani kamar ba ita tasha wahala tahaifeta ba harta abinci bata ba ta haka zata wuni da yunwa se na dawo gida tunku mukecin abinci abin nata da ya isheni ne yasa nafada mata muddin taci gaba da gallazawa shayida to nikuma zan saketa hakan ne yasa tayi sanyi domin tanasona sosai , akan abinda takewa shayida tarage kashi 20 acikin 100 gashi Zainab bata isa tazo part dinta ba seta mata mugun duka , lamarin ya isheni yasa nasaketa saki daya ta tafi gida nikuma nadauki shayida itama namikata gun fulani. zuwana dubai gabatar da wani meeting da babban Company na A.A AZAAD, bayan mungama meeting kanin sarki azaad me suna arash ya gayyaceni gidansu cin abincin dare dukda inada wani uzuri haka na amsa gayyatarshi naje babban gidan sarautar dubai sunada matukar mutunci da karrama bako yanda suke haba_haba dani hakan yamin dukda nima dan sarki ne . muna zaune munacin abinci sarki azaad ya gabatar min da ahalinshi da matar kannenshi , matar arash dakuma matar asaad, sekuma matarshi wato mahaifiyar umminku aysha kenan se yaransu dasuka kasance dukkansu maza rai 9 jinjina kai nayi nace " Masha Allah,Allah ya azurtaku da yara maza Allah yarayasu" suka amsa da ameen sarki azaad ya ce" ai sunada kanwa guda daya rak ita kadaice mace agidan nan " murmushi kawai nayi bance komai ba , kiran sunanta sarki azaad yayi " Aysha" fitowa tayi tana tafiya cikin nutsuwa yarinyace dabazata wuce shekara 15 ba aduniya kyakyawar balarabiya sanye da doguwar riga baka kanta rufe da mayafi tunda tafito idona akanta yake lokaci daya naji nakamu da santa, gabatar min da ita sarki azaad yayi, fuskanta dauke da murmushi tagaisheni amsawa nayi iname yaba hankalinta komawa ciki tayi duk matan wajan suka bamu waje , harga Allah tunda naga aysha naji inasonta kuma so na aure bazan iya barin dubai batare danayiwa iyayenta magana ba , ban boye musu komai ba na fayyace musu abinda ke raina nahada da fada musu inada mata da yaya biyu. banyi tsammanin zasu amincemin ba cikin ruwan sanyi ba kawai naga sun amince domin ba kowani balarabe ko farin fata bane yakeson hada jini da bakar fata ba sukace in turo iyayena da full confidence dina nabar masarautar zuwa masaukina dukda sunyi sunyi inzauna na ki. haka nadawo nigeria da farin ciki naje nasamu me martaba nasanar mishi shima ya amince da lamarin saboda suna shiri sosai da sarki azaad haka suka nemamin auren aysha, tunda hafsat taji labarin zan kara aure ta dami waziri da sede yanemeni zata koma gidanta haka waziri yanemeni yarokeni da inmaida auren haka kuwa akayi namayar da auren . hafsat takoma gidanta mukaci gaba da rayuwa balaifi dukda bakamar da ba , har a wannan lokacin bansake haduwa da aysha ba saboda a al adarsu inde yarinya zatayi aure bazata sake ganin mijin ba ko jin muryanshi ba se randa aka daura musu aure. Bayan nagama gina wannan gidan ne aka daura aurena da aysha saboda nafison zama awajen masarauta, hafsat itace uwar gidana yasa nabata zabi tazabi part din da takeso haka tazaba , aka kawomin aysha gidana yan uwanta mutane hudu ne suka rakota bayan anyi shagalin biki anwatse , natarasu a part dina dan musu nasiha dukda aysha batajin hausa daga larabci se turanci haka namusu fada sannan naraba musu kwana , hafsat bata nunamin komai ba ta tashi ta tafi abunta , haka rayuwa taci gaba da tafiya nan ne nafara samun kwanciyar hankali. takuramin aysha tayi akan lallai sede indawo da shayida da zainab wajanta haka nakarbosu daga wajan fulani na damka mata su aikuwa suna ganin gata sosai kamar ita ta haifesu ana haka aysha tasamu ciki tayi laulayi sosai fulani na yawan zuwa dubata kuma kullum ita take mata abinda takeso ta bada akawo mata. bayan wata tara tahaifi ya mace akasamata suna amina wato sunan kakarku ammi kenan ,haka tahada yaran dukkansu uku taci gaba da kula dasu tunda aysha ta haihu har akayi suna tayi arba'in ko kafa hafsat bata taka a part dinta ba nayi maganar harna gaji , amina nada shekara hudu aysha tasake haihuwa ta haifi da namiji yaci sunan kakanshi wato azaad sosai yaro yaga gata nan ne kadai hafsat tazo suna daga nan batakara zuwa ba amma aysha tana zuwa mata ta gaisheta lokaci zuwa lokaci , daga nan ne hafsat ta tayar da bori sede abata yayanta gudun masifarta yasa na kwashi yaran nakai matasu duk tunanina tacanza halayenta ashe bahaka bane ta karbesu ne dan ta kashesu , bazan taba mantawa wata rana inazaune a office meyi mata aiki takirani aboye tana sanar dani hafsat ta bawa shayida da zainab guba ba shiri nadawo gida tare da motar ambulance aka kwashesu akayi asibiti dasu dakyar aka ceto rayuwarsu saboda guban bedau lokaci ajikinsu ba , haushi kamar ya kashe hafsat raina abace nadawo idona yarufe bansan lokacin da na dinga zabga mata maruka ba tsabar taurin rai irin na hafsat ta kalli idona tacemin inde yaran nan ne seta kashesu domin bazata taba sonsu ba har duniya ta nade, banyi mamaki ba dan yanzu nasan hafsat bata sansu haka naje wajan aysha dabatasan abinda yake faruwa ba nace ta shirya muje asibiti duba su zainab hankalinta yatashi jin abinda hafsat ta aikata musu anan ne tasan bata sansu tayi kuka sosai dakyar na iya lallashinta, tadauki azaad da ake goyo muka tafi asibitin satin su biyu aka sallamesu ko da wasa banyi gigin kaisu part dinta ba nabarsu awajan aysha tacigaba da kula dasu . Haka shekaru sukata ja sosai aysha tasake haihuwa ta haifi fawwaz dakuma areef a time din duk suna makaranta duk sun girma , hafsat bata sake haihuwa ba. su shayida da sungama karatu har akayi auren zainab daga baya akayi na shayida , Allah yabawa zainab haihuwa ta haifi dan ta namiji akamin takwara Muhammad wanda yanzu yake Russian yana karatu, nan ne hafsat tasake samun ciki zuba ido nayi inason inga wannan karon ma zata tsani abinda zata haifane da iKon Allah tahaifi namiji aka samishi Mansoor soyayya, gata, kulawa babu wanda mansoor be gani ba tasoshi sosai kamar ranta , Mansoor nada shekara daya Aysha tahaifi zeenat kusan atare suka taso Wanda nasan kunsan hakan yanzu bari infada muku ainihin dalilin dayasa nataraku anan. Ranar wata lahadi yakasance kwanar hafsat ne nadawo daga dubai sena sauka a part dinta, nashiga har bedroom dinta bansameta ba senayi tunanin ko tana toilet haka nazauna nayita jiranta shuru_shuru bata fito ba sena je jikin toilet din nayi knock naji ba alamar mutum yasa nabude naga wayam tunani nafara to ina ta shiga saukowa downstairs nayi naduba dakin mansoor nasameshi yana bacci , fitowa nayi har nazo zanfita naji kamar ana magana awani dakin saukan ba ki da hafsat ta hana kowa shiga acewarta intayi ba ki anan suke sauka kuma ni bana ganin kowa yana zuwa wajanta hatta danginta tamusu iyaka da gidan kuma bata zuwa se ta bushi iska , tsayawa nayi ajikin kofar na kasa kunne na dakyau wasu irin sambatu ne ke tashi wanda baze fadu ba kuma bana mutum daya ba . ahankali nabude kofar natsaya abakin kofar mummunar gani idona yayi da har yau inna kulle idona inaganin wannan bakar ranar , sauka idona yayi akan hafsat da wasu mutane kusan mutum uku da ita na hudu cikin wata suffa nadaban me ban tsoro jikinsu duk gashi babu kaya ajikinsu tsirara haihuwar uwarsu , sun sa namomin mutane agaba sunaci hade da shan jini hankalina yakai kololuwar tashi narasa meyakamata inyi in fitane ko in tsaya , yanda nake kallon su haka su ma suke kallona. bacewa sauran sukayi yarage daga ni se hafsat adakin nan take takoma ainihin suffar mutane, matsowa kusa dani tayi ta ce kai mijina ne kuma inasonka amma yanzu yazama dole in kasheka kokuma kahaukace amma kafin nan bari indan baka takaitaccen labarina tafada tana yar murmushi tafara magana , nakasance tun ina yar karama dani nake shaawar son cin naman mutane domin ko a labarai haka ake fada wai naman mutum yafi kowace nama gardi dakuma dadi hakan yasa nadauki son duniya na daurawa naman mutum, wata rana naje makaranta ina primary 5 naje toilet yin fitsari naga yarinya karama yar nursery 3 tafito daga toilet din tanata wasanta dubawa nayi naga babu kowa awajan ganin wannan babban damane agareni inna barshi subucemin zeyi yasa nakirata na mata wayo nakaita toilet din dukda banida wani isheshen karfi haka nayita kokarin murde mata wuya harnayi nasara na kasheta zama nayi dirshen akasan toilet din nasa hakori nafara fincikar namanta inaci senaji wani bankwarakwai saboda shine karo na nafarko amma hakan nadingaci seda nayi nisa acin naman sannan nafarajin dadi nakaimin har tsakiyar kaina haka nacinye yarinyar nan tas yayi saura kasusuwanta, tarkatasu nayi nazuba acikin dustbin nawanke toilet din yanda babu wanda zeyi zargin wani abu daga nan nakoma aji nadauki jakata nakoma gida kwanciya nayi cike da nishadi nafara bacci , abaccin ne naganni awani dokan daji me matukar girma sosai ga mutane sanye da bakaken kaya fuskokinsu arufe, sunatamin barka da zuwa cikinsu banji wani tsoro ba lokacin da suka sanar dani nazama daya daga cikin yan kungiya kuma zansamu duk abinda nakeso daga kudi duk wani abun duniya ga cin nama da shan jini sosai nayi farin ciki shisa duk wayanda sukace inkawo ayi sadaukarwa nake kaiwa , ganin mutane danakeyi ne yasa koda yaushe nake shiga cikin bukatuwa da cin nama idan kuma haka yaci gaba da faruwa to tabbas zaa ganoni shisa nake kebe kaina ni kadai bana shiga harkan kowa wanda kuwa yayi kuskuren takalata senaga bayanshi hankalina yake kwanciya , ana haka Allah yadoramin sanka kuma naji bazan iya cutar dakai ba harmukayi aure dalilin dayasa natsani shayida da zainab kuwa tunda nasamu cikinsu nabayar dasu ga kungiya akan insunzo duniya zaayi sadaukarwa dasu amma kwata_kwata hakan ya gagara akwai tsari ajikinsu domin me martaba yanason jikokinshi shisa tun ranar da sukazo duniya yake basu maganin tsari daga dukan sharrin mugaye acikin ruwan zam_zam , shisa na tsanesu tunda sungagara biyamin bukata , sekuma kadaukesu ka kaiwa matarka su wacce duk duniya babu wayanda natsana sama da ita da yayanta kuma nice nan ajalinsu sena kashesu musamman wannan dan nata azaad. haka tadinga fadamin asalin kalarta kwakwaran motsi nakasa ji nayi duk duniya babu wacce natsana sama da ita dakyar na iya bude bakina nace mata sena tona miki asiri kowa seyasan kedin wacece muguwa azzaluma macuciya kawai bari kiji na sakeki saki uku babu ni babu ke har abada , anan ne tayi kokarin kasheni da tsafi nadinga adduo'i bakina yaki shuru , hakan yasa tayi kokarin haukatani nan ma Allah bebasu saa akaina ba umarni shugabansu yabata kawai suka rubemin baki koda inasan infadawa mutane halin da ake ciki amma se inkasa , na matukar shiga damuwa seda nadanyi rashin lafiya aysha koda yaushe tanakan tambayata meyake damuna sede ince mata babu komai haka rayuwa taci gaba har lokacin da azaad yahadu da muguwar hatsari wanda ita da alh Ibrahim tijjani suka hada hannu dan kasheshi duk nasani amma ba halinyin magana , wato abinda yafaru jiya shine jiya harna fara bacci azaad yakirani yake shaidamin zekasheta kafin indawo inajin hakan nagano yasan komai hakan yamin dadi shisa nazo na warware muku komai " in banda koke_koke ba abinda ke tashi afalon musamman na anty shayida da anty zainab jin wacece uwarsu dakuma irin tsanar da ta musu sosai ummi take kuka lamarin ya girgiza duk wani wanda yake cikin falon domin mommy ta gurbata rayuwarta dakuma cutar da rayuka mara adadi wayanda hakkinsu kadai sun isheta saboda tazabi duniya tayi son kai da son zuciya , kifa kai fanan tayi ajikin Mr azaad tana kuka domin al amarin kamar a film , dukda kasancewar ita tun farkon haduwarta da mommy tasan akwai wani abu ashe macijiyar sari ka noke ce , haka zeenat ma tana rungume da ummi tana kuka , mazan kuwa idanunsu yayi ja jijiyoyin kansu yatashi jisukeyi kamar su kamo mommy su kasheta kowa yahuta musamman Mr azaad barinma inya tuna yanda ta tsani yan uwanshi da ita tahaifesu shuru kawai yayi dan inya bude baki zeyi magana yasan kawai kalmar kashe mommy ne kawai ze fito daga bakinshi, kuma muddin yatashi tom nan ma seya kasheta shisa kawai yayi shuru dan yaga shi yafi alkhari yana lallashin fanan dake kuka . Abba ne yadaga waya yakira securities yace su kunce mommy sukawo ta , shigowa sukayi da ita duk tafita a hayyacinta domin igiyar da sarauniya ta daureta dasu kamar na dalma ne azaba kadai takeji ga shi duk wani karfin tsafinta yabar jikinta dungurata sukayi a tsakiyar falon ta fadi da kallo kawai suke binta anty shayida ce ta ce " mommy Meye zesa ? Mommy me muka Miki ? Meyasa kika jefa rayuwarki a irin mugun halin me kika nema kika rasa? Mommy bakya tuna haduwarki da Ubangijinki ? meye ribarki yanzu meyasa za ki mana haka bakya tunanin ya rayuwarmu zata kasance ?" muryanta dake fita dakyar ta ce " tsanar dana muku baze taba canzawa ba kuma yanda na kudurta aniyar ganin bayanku tofa sena aiwatar, tsabar tsanar dana miki shisa daga zaran kinsamu ciki nake cinyewa tunkafin kusan da hakan tunda ke kinfi karfin kungiya ai abinda ke cikin be fi karfi ba sau takwas kina samun ciki ina cinyewa haka kema zainab naso in miki se kuma banyi nasara ba kai kuma " tafada tana kallon abba" tunda na fuskanci ammi ta tsaneni yasa nakasheta domin yanda ta tsaneni nima haka na tsaneta, se kai azaad dan iskan yaro duk wata hanyar da zanbi wajan kasheka nabi amma hakan beyuba amma sena kasheka din " daura hannu akai anty shayida tayi tamike tana kuka tana maganganu kamar wata mahaukaciya Jin abinda uwar da ta haifeta tayi mata ashe ita ba juya bace, mahaifiyartace take cinye mata ciki ganin zata iya zaucewane yasa abba yarikota yarungumeta yana lallashinta yana jin ciwon abinda hafsat ta aikata mishi wato ita takashe ammi tabbas dole yadau mataki akan mommy domin ta cutar dasu da yawa , tsananin tashin hankali kam yau sunjishi ,yau itace bakar rana agaresu haka mommy tadinga confessing abubuwan datayi , tsuma kawai da rawa jikin Mr azaad yakeyi mikewa yayi da niyar damko mommy abba yamishi alama da ido komawa yayi yazauna barin falon areef da fawwaz sukayi dan insuna kallon mommy jisukeyi kamar su mata mummunar kisa hakan yasa suka wuce part dinsu zuciyarsu na tafasa. Ana cikin wannan mugun yanayin mommy ta fashe da wata muguwar dariya tana sambatu da kuma fade_fade nan take tafara fincike gashin kanta tana zubarwa akasa lokaci daya ta haukace, hauka tuburan babu wanda ya kalli inda take domin itadin baabin atausayawa bace mikewa tayi da gudu tafita afalon baba me gadi na bandaki tabude yar karamar kofar gate din tayi waje bin bayanta securities din gidan sukayi , Ina tariga da ta musu nisa tahaukan titi wata katuwar tankan ruwa ne yabi takanta ya takata haka namanta yayi piecing akan titi harta kanta seda yatarwatse kwakwalwarwa awaje haka mommy tayi mutuwar wulakanci atozarce gaba daya jikin securities din yayi sanyi haka wasu daga cikinsu yashiga gida yasamesu afalon yasanar dasu abinda yafaru haka Abba,ummi, zeenat,anty zainab,anty amina dakuma anty shayida dake atare da abba tana kuka suka fita Mr azaad kuwa ko ajikinshi yadauki fanan suka haura part dinshi . Tunda suka kusa isowa inda tanka yayi kaca_kaca da mommy suka fara ganin namar jikinta daya tarwatse ga dandazon al'umma dake tsaye awajen, sa hand gloves securities din sukayi suka fara hada naman mommy waje daya aka samo leda zasu kwashe kenan wuta yatashi akan namar haka wuta yacinye naman nan tas yayi saura toka kowa nata tofa albarkacin bakinshi da yin tir da mommy haka suka diba tokar akasa aledar. jiri ummi tafara ganin tana kokarin faduwa anty zainab da anty amina suka riketa suka koma cikin gida suka zauna suna jimamin wannan bakar rayuwar duk sunyi shuru lokaci daya sabon tsoron Allah yasake shigansu ganin irin mutuwar wulakanci da mommy tayi daga fitarta da zuwa fada musu da securities sukayi befi minti biyar ba amma har rai yayi halinshi sosai sukeyi mata adduah samun rahaman Allah . dakyar aka samu siraran mutane dabasu fi 10 ba suka sallaci mommy ciki kuwa harda Abba shikadai domin daya kira waziri yasanar dashi ma kawai cewa yayi baze samu zuwaba Allah yajikanta yakatse kiran, yakirasu fawwaz da areef suma kin fitowa sukayi haka Mr azaad dayaga Kiran Abba ma kashe wayarshi yayi gaba daya haka aka je aka binne tokar nata a makabarta suna mata adduah. zaayi zaman makoki abba ya ce baa gidanshi ba haka sukaci gaba da zama kowa jikinshi lakwas ba karfi anty shayida kuwa zazzabi ne me zafi yarufeta anty amina takira doctor safiya tazo tasamata drip abun tausayi . tunda Mr azaad da fanan suka koma part dinsu basu sake fitowa ba se karfe 3 , suka fito cikin shiri nazuwa anguwa babu yanda fanan batayi dashi akan abar maganar tafiyar gobe ba amma yaki haka dole yasata tashirya zuwa gida tasanya hijab dinta shima yasha half jumfa sunyi matukar kyau haka suka fito ba kowa afalon se zeenat kallonta fanan tayi ta ce " zee hafiz ya farka ne ?" amsa zeenat tabata " eh yafarka Kuma cikin nutsuwa babu wani damuwa atare dashi yayi wanka ummi tabashi abinci yaci yanzu hakama bacci yakoma " murmushi sukayi atare ita da Mr azaad daman jiran farkawarshi sukeyi suga reaction dinshi Kuma ga shi alhamdulillah. zeenat ta ce " anty fanan ina zakuje?" ta ce " zamuje gida ne yi musu sallama gobe zamu tafi " dama zeenat yau setaji gidan badadi bawani annashuwa kowa yana cikin damuwa saboda abinda yafaru hakan yasa tacewa fanan " zan biku bari indauko gyale " tafada tana haurawa part din ummi dasauri dan tasan halin Mr azaad inde tabata mishi lokaci yanzu zata dawo tasamu baya nan , tafito tasamesu a packing space duk suna cikin motar shiga back seat tayi ya tada motar suka tafi . Kamar wasu kurame tunda suka fara tafiya babu wanda yace wani abu har suka isa yayi packing abakin gate , fitowa sukayi daga motar suka shiga gidan bakinsu dauke da sallama mama ce kadai agida kuma tana bacci adakinta, auta da hairah da ya usman sunfita dan yace zekaisu yawo ,zama sukayi akan kujera fanan takawo musu drinks da ruwa hade da snacks dan mama batayi girki ba saboda batasan da zuwansu ba kuma ita dayace agida dakin mama fanan tashiga tasameta tana bacci tashinta tayi ta hanyar kwanciya ajikinta tashi mama tayi ta ce " dama nasan seke din ai tunda auta bata nan ! yaushe kukazo?" Mama ta tambaya tana daura dankwali akanta , ta ce " bamu dade da zuwa ba suna falo " daukan hijabi mama tayi tasa tafito tabar fanan a dakin. murmushi tayi ta ce " sannunku da zuwa ?" gaisheta Mr azaad yayi sannan zeenat tagaisheta ta amsa zama tayi tana tambayarsu mutanen gida suka amsa da kowa lafiya haka suke hira sama_sama dan mama najin kunyar Mr azaad amatsayinshi na sirkinta , fitowa fanan tayi da liffaya ahannunta ta ce " mama wannan na waye ?" kallonta mama tayi ta girgiza Kai ta ce " na wa ne jiya babanku yakawomin meyafaru" yar murmushi fanan tayi ta ce" bakomai naganshi acikin leda ne shine nace bari intambayeki " dariya mama tayi dan tagano fanan wato yamata kyau shine taketa wannan kauce_kaucen ta ce" to kuma seki mayar ko " turo baki tayi ta ce" tom " dariya taso bawa Mr azaad danshima ya harbo jirgin nata . Dawuwa falon tayi tazauna sukaci gaba da hira ganin kamar su Mr azaad basu sanarwa mama anyi rasuwa bane yasa ta ce " mama anyi rasuwa a gida " ta kasan ido Mr azaad yawatsa mata harara dauke ido tayi kamar bata ganshi ba , mama ta ce " Allah sarki waye yarasu " ta ce " mamansu anty shayida ce " sosai mama tayi musu taaziya dukda Mr azaad bece komai ba se jinjina kai da yakeyi zeenat da fanan kawai suka amsa , ya ce " mama dama munzo muku sallama ne zamu tafi USA gobe in sha Allah " adduah Allah yatsare hanya mama tayi musu bata sake cewa komai ba . tashiga kitchen domin hada musu abinci bin bayanta fanan tayi ta tayata sukayi komai tare jollof din dankalin turawa sukayi dayasha vegetables da nama ta shirya musu a food flask tajera a tray ta bawa fanan takawo falo . Daki mama tashiga dan tabarsu suci abinci , , serving din Mr azaad tayi a plate hade da sa mishi ruwa a glass cup da drinks din ta jera mishi komai agabanshi sannan tasa musu nasu itada zeenat tamike takai musu dakinta da ruwa ta ce zeenat muje ciki , shiga dakin zeenat tayi fanan na kokarin tafiya Mr azaad yariko hannunta yajawota kan kujeran ya ce " inazakije kuma?" " zamuci abinci ne nida zeenat " cewar fanan, rike habarta yayi yana kallon cikin idonta ya ce " nikuma dawa zanci abinci in kika tafi " zaro ido waje tayi ta ce" ka lan mama tafito taganni ina cin abinci tare da kai ah ah gaskiya " bata fuska yayi" to shikenan tashi kije kici keda zeenat din nibazanci abincin ba hakan yamiki ina " ya karishe maganar yana kwantar da kanshi ajikin kujeran ya lumshe ido haka bayanda ta iya ganin ranshi yabaci dantace zasuci tare da zeenat yasa tadibo hadaddiyar jallof din dankalin takai mishi baki, bude ido yayi yasaukesu akanta bece mata komai taci gaba da bashi abinci se lumshe sexy eyes dinshi yakeyi tsabar yanda girkin ya mishi dadi , takawo mishi spoon dede bakinshi kenan yasa hannu yarike spoon din yakarba yakai mata baki , haka sukata feeding din juna har suka koshi sukasha ruwa da drinks. abangaren zeenat kuma gajiya tayi da jiran fanan yasa tafito dan kiranta taga sunacin abinci ita da Mr azaad, komawa ciki tayi ta zauna tana "lallai matar nan shine zata sani jiranta tasan da mijinta zataci nima de Kwanan nan zanyi mijin yauwa " ita kadai take wayan nan magana tanacin abincin . Kwashe komai fanan tayi takai kitchen tadawo gun Mr azaad din bata dade dazama ba sega auta tashigo da gudu tayo wajan Mr azaad, ganin tanufo wajanshi yasa yabude mata hannu tarungumeshi tana " oyoyo Yaya balarabe, ai ina ganin car awaje nace it must be you ashe kaine " tafada tana haki dan dama gashi sun gaji ga gudun datayi ya ce " cutie Ina kikaje haka ?" ta ce " ya usman ne yakaimu yawo nida anty hairah kasan ina da ina mukaje ?" girgiza kai kawai yayi tacigaba " munje ice cream planet bayan mungama shan ice cream mukaje makay shawarma daga nan ya usman yakaimu shaf'an sekuma yakaimu G_connect nayi lilo " fanan kam bin auta kawai takeyi da ido ganin yanda intana magana bata tsayawa kamar suhaima ta ce" sannu fa auta tunda ba magana ko ganina ne bakiyi ba ?" " Laaah anty fanan kece nadauka ai Yaya balarabe ne kawai yazo " yanda take fitar da magana kamar wata uwar mata , shuru kawai fanan tamata . dariya Mr azaad yayi ya ce" ah gaskiya kunsha Lilo kam " yana rufe bakinshi ya usman suka shigo shida hairah tsugunawa hairah tayi ta gaishesu suka amsa fuska asake, musabaha ya usman da Mr azaad sukayi nanma fanan tafadawa ya usman anyi rasuwa, taaziya yayi musu . Seda sukayi sallar la'asar fanan da hairah suka dawo falo suka zauna tana tambayarta ya karatu , Zeenat dake daki fitowa tayi ta gaishe da ya usman da basu dade da shigowa ba daga masallaci shida Mr azaad. kallon fanan tayi ta ce" bari in shiga gidansu amira! hairah zoki rakani " tashi hairah ta ce " tom " dakin mama tashiga tafada mata zata raka zeenat gidansu amira mama tace sekun dawo fitowa tayi tasamu zeenat najiranta ta ce" anty zeenat muje " harsun kusa bakin kofa fanan ta ce" ku tsaya " sannan ta kalli Mr azaad murya kasa_kasa ta ce" habiby ayyah inje gidansu amira?" " Eh " yace aikuwa dasauri ta mike tayi gaba tabarsu abaya, dariya ya usman yayi ya ce " to sannu iyah ! sun jiraki shine ke kina zuwa kikayi gaba kika barsu " dariya kawai tayi batace komai ba , tafiya sukeyi suna har hira harsuka isa gidansu amiran afalo suka sameta tana waya da ya al ameen se zuba mishi shagwaba takeyi tana ganinsu ta taso tarungume fanan " oyoyo my bestie" " oyoyo bestyna kuma antyna " cewar fanan ya al ameen yanajinsu yayi dariya kawai yakashe wayar. dakin Amira suka shiga suka yada zangon hira hairah de jinsu kawai takeyi batace komai ba saboda duk sun girmeta babu yanda zatayi tasa musu baki a magana basu sa ko ta ba aciki , lura da hakan dasukayi ne yasa suke hiran harda ita , takuwa sake jiki dasu sunata hira drinks Amira takawo musu sukaci gaba da hira. Agidan sukayi sallar mangrib sannan suka fito suka shiga dakin hajiyarsu suka gaisheta da fara'a ta amsa musu fanan tafada mata anyi musu rasuwa hade da gobe zasuyi tafiya tazo musu sallama taaziya hajiya tayi musu da adduah Allah yakiyaye hanya , sannan suka wuce gida sunko dawo adede baba yadawo yana gida gaidashi sukayi yayi musu taaziya domin mama da ya usman sun sanar dashi kuma sun sanar mishi da gobe zasuyi tafiya hakan yasa yabukaci ganin su , su biyun adakinshi , shinfida sallaya fanan tayi akan carpet din suka zauna adakin baba , ganin yanzu sun dedeta kansu ne yayi wa baba dadi nasiha me ratsa zuciya da kashe jiki yamusu yahada da musu fada , daga karshe yamusu Allah yatsare hanya,suka fito akunne Mr azaad ya rada mata ku shirya kuzo mutafi saboda zamu tsaya agidan maman junior tace mai to tasanar da zeenat kintsawa sukayi . Suka fito zasu tafi mama ce tafito hannunta rike da fashion bags guda uku tabawa fanan daya tabawa zeenat daya sannan tabawa amira daya godiya suka mata takoma ciki duk suka rakasu har bakin mota suka tafi hade da kewarsu Amira ta wuce gidansu tana me musu seda safe . Shiga gida ya usman, hairah da auta sukayi dakin baba ya usman yayi sallama izinin shigowa baba yabashi zama ya usman yayi akan sallayar yana sunnar dakai kasa, tunda yashigo baba ya lura dashi yasan akwai magana abakinshi ya ce " kazo kamin shuru kode babu abinda zaka fada ne usman?" Ya tambayeshi yana kallonshi sosa wuyanshi ya usman yayi ya ce " am dama baba maganar hairah ne" sekuma yayi shuru , murmushinsu irin na manya baba yayi domin kuwa ya ganoshi seya nuna kamar besan meyake nufi ba ya ce " tofa! meyasami ita hairah ?" yasake jefo mishi wata tambayar. Ya usman ganin baba yakasa gano inda ya dosa ne ya ce " dama inason a tambayamin aurenta ne " gyara zama baba yayi ya ce " to shikenan tunda naga kazo da wannar maganar nasan kun gama dedeta kanku kai da ita hairah in sha Allah zaa tambaya maka aurenta inyaso se a hada auren nakun dana sauran yan uwan naka ! se anjuma tashi ka tafi bacci zanyi " dariya ya usman yayi dan ya lura yau baba naji da barkwanci ya ce " nagode sosai baba Allah yakara girma " ya amsa da" ameen" sannan yafita da farin ciki aranshi kamar yazuba ruwa akasa yasha dan jindadi . Kiran Abba baba yayi yamishi taaziya. Wasa takeyi da junior dake kan cinyarta se dariya yakeyi ga anty firdausi akusa da ita daddyn junior Kuma sunje sallah masallaci shida Mr azaad basu dawo ba. Ina jiran comments dinku. Se munhadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏 . https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 (* Yar lelen Jarumai*) 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚 ⚜️📚 J. W.A 📚 🖋️ Gargadi..... Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba takowani siga ko akaranta min shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutum zebimin hakkina Kuma yasakamin. Page 5️⃣9️⃣ zeenat ta ce " anty firdausi nide kibarmin junior dinkin nan wallahi kyau yakemin " hararanta fanan tayi ta ce " narigaki malama tun Yana ciki nace inaso " sa hannu zeenat tayi tadauki junior akan cinyar fanan tadaurashi akan nata cinyar ta ce " junior kace mata ni kakeso kaji" kamar wata me magana da babba , shide junior se dariya yake mata fanan ta ce " Allah yashiryeki zeenat yanzu junior kikewa magana?" gyada kai tayi dariya anty firdausi tayi ganin drama zeenat da fanan akan junior , kallon fanan anty firdausi tayi ta ce" muje zamuyi magana " tayi gaba fanan tabita abaya zama sukayi akan gadonta ta kalli fanan dakyau ta ce " fatan de yanzu komai normal keda mijinki babu wata damuwa ko?" ta ce " eh anty firdausi komai alhamdulillah " hakan yayiwa anty firdausi dadi , ta bata shawarwari da koya mata wasu abubuwan bude wata karamar wardrobe tayi tafito mata da magunguna dakuma mayukan gyaran jiki, dasu turarurruka masu yawa ta saka mata su a yar jaka me kyau sannan ta fada mata yanda zatayi amfani dasu godiya fanan tayi mata suna cikin hira taga Kiran Mr azaad dagawa tayi , ya ce" dare yayi kuzo mutafi " yana gama fadin haka yakatse kiran, fitowa sukayi tare ita da anty firdausi suka samesu a falo sundawo ga zeenat dake wasa da junior, mikawa anty firdausi junior tayi tana " senazo karbanshi ya yini awajena " daddyn junior ya ce " to shikenan sekinzo" haka suka rakasu packing space daddy junior nayi musu godiya sosai domin ya matukar jin dadin ziyarar da suka kawo mishi , sukayi musu adduah Allah yakiyaye hanya, suna tafiya akan hanya daga can nesa zeenat ta hango me soya awara murya asanyaye ta ce " ayyah ya azaad dan Allah katsaya agun me awaran can " juyowa yayi yawatsa mata banza kallo ya ce " wato harkin mata da abinda yafaru dake ko ? baki daddara bako ? kisakemin maganar wani abun akan titi kiga iKon Allah" yafada yana kara wurga mata harara shuru bata sake cewa komai ba jikinta yayi sanyi , amma harga Allah kwadayin awaran take , tunkafin zeenat tahango me tuyar awarar fanan ta ganta tana kokarin yi mishi magana se zeenat tarigata jin amsar dayabawa zeenat ne yasa tayi shuru takama bakinta amma ita yanzu hakama ji takeyi in bataci awara ba bazata iya bacci ba , haka suka wuce masu suyar awaran sunaji suna gani Mr azaad ya hanasu siya . 8:12pm dede suka shigo gida zeenat ce tafara fita a motar tashiga gida fita yayi harya fara tafiya yajuya ze riko hannunta yaga wayam batama fito ba tana cikin motar komawa yayi yabude mata murfin motar still bata fito ba kanta akasa tana wasa da yatsunta, sa hannu yayi yadago fuskanta zaro ido yayi ganin yanda fuskanta yayi jaga_jaga da hawaye , mamaki yafara meye aka mata take irin wannan kukan riko hannunta yayi ya ce " baby meyafaru kike irin wannan kukar" kamar wacce take jira yayi magana takara volume din kukanta harda shesheka, tsugunawa yayi agabanta yana rike da hannun nata yazubawa sarautar Allah ido kuka takeyi bil hakki kamar wacce akawa mutuwa tambayarta yayi ko wani abun akamata tayi mishi shuru lallashinta yakeyi Amma kamar zugata yakeyi, haryama rasa me zece mata kawai yazuba mata idanunshi, seda tayi kukanta son ranta sannan tayi shuru da kanta har lokacin Mr azaad yana tsugune agabanta rike da hannunta, ganin tayi shuru ne yasa ya ce " sorry wifey fadamin meye mekikeso " ajiyar zuciya tasauke tagoge fuskanta da hijab murya ashagwabe ta ce " bakai bane ba" nuna kanshi yayi da yatsa ya ce " nikuma menayi miki?" turo baki tayi ta ce " bakai bane ba kace bazaa siya awara ba bayan inason ci" sake hannunta yayi yadafe kanshi aranshi yana" ya salam yanzu dama akan wannan abun tatsaya tana kuka lallai mata rigimammune " tsaban yanda yake cike da mamaki hade da al ajabi gagara cewa komai yayi se binta da kallo dayakeyi sake fashewa da kuka tayi ganin yazuba mata ido kuma shi bece mata komai ba , zaro wayarsa yayi ya kira layin faisal bugu biyu yadaga abangaren faisal yagaishe shi be ko amsa gaisuwar ba ya ce " akwai wani abu ana siyarwa akan titi please kasiyowa wifey yanzu " daurewa faisal kai yayi domin shi besan tankamemen abinda zaa siyoba tunda bawai yafada mishi sunan abun bane ya ce " sir to meye sunan abinda zaa siyo din ?" shuru fanan tayi tana aika mishi da harara jin yatsaya yanawa faisal kwantancen abinda shikanshi be sani ba bekuma fadi sunan ba , yafi tsawon minti 10 yanawa faisal kwantancen amma be gane ba gashi Mr azaad ya manta sunan abun Kuma be tambayi fanan ba, iya cika fanan ta cika tazo har wuya takaici kamar ta tashi tabar mishi wajan shi besan abu ba Kuma baze tambaya afada mishi sunan ba gashi dare karayi yakeyi , sa hannunta tayi ta zare wayar akunnenshi tasa a handsfree, sallama tayi jin muryanta yasa faisal gaisheta, " faisal awara ne zaka siyo , amma danye wanda baa soya ba dan Allah" tafada tana murgudawa Mr azaad baki murmushi yayi dan yasan acike take jira takeyi yace wani abun ta taso mishi da sabon rigima . faisal ya ce " madam eh zaa samu dan kanwata ma tanayi na order yanzu haka bari in karbo miki " yafada yana kunshe dariya wato mace de babu yanda bata juya namiji gashi oganshi lokaci daya matarshi tajuya mishi lissafi mutumin da maganar mint 2 ma bayi yakeyi ba amma yau dake tanason abu yatsaya yana bayani kusan na 10mint mata mutanen mu. godiya tayi mishi takatse kiran tana mika mishi wayarshi karba yayi yana kallon fuskanta da ta daureshi ita dole fushi takeyi bata kalli inda yake ba tadauki jakar da mama tabata dana wanda anty firdausi tabata tayi gaba ta barshi abaya , tafiya takeyi batako juyo takalleshi ba balle tasan yana binta abaya hannu daya yasa yadagata sama kamar wata yar tsana , mutsu_mutsu tafarayi na sede ya ajiyeta akasa ta tafi da kafarta be saurareta ba seda suka kusan isowa falo sannan yasauketa yarike hannunta suka shiga falon ba kowa aciki, kowa na part dinshi , part dinsu suka shiga zama fanan tayi akan kujeran falo tana " washh nagaji " tafada tana bude fashion bag din da mama tabasu ciro hadaddiyar liffaya tayi me matukar kyau multi color jikin liffayan yasha manyan stones bakaramin kyau yayiwa Mr azaad ba, har imagine kayan yakeyi ajikin fanan intasa ,shafa liffayan yayi ya ce " wifey kayan nan zasuyi miki kyau sosai" har ranta taji dadi yanda ya yabi kayan dukda inde tayi kwalliya seya yabi kayan dakuma irin kyaun da tayi. maida kayan cikin gidanshi tayi ta ajiye agefe kallonta yayi ya ce " wifey amma ai nima zaa ban tsumin in sha ko ?" Kallonshi takeyi bako kyaftawar ido mamaki ne yakusa sumar da ita aina yaji maganar tsumi kuma saboda tasan itade bata mishi ba sannan bawai bude jakar da anty firdausi tabata tayi ba , cikin inda_inda ta ce " habiby tsumi kuma?" dariya taso bashi amma yafuske ya ce " yes up course tsumi kuma inzakisha kimin magana musha tare " kunya kamar fanan ta nutse kasa tama rasa mezatace mishi , dariya kasa_kasa Mr azaad yakeyi dan tun dawuwarsu daga masallaci suna kokarin shiga falon gidan anty firdausi yaji duk hiran da sukeyi murmushi yayi aranshi ya ce " Allah de ya biyaki maman junior" knocking sukaji Mr azaad yace ashigo Faisal ne yashigo hannunshi rike da food flask me girma ya gaishesu hade da ajiyewa akan table ya musu sallama ze tafi fanan ta ce " ah ah katsaya agama soya awaran " dadi sosai faisal yaji yana kara yabon matar oganshi nashi da irin kirkinta fita yayi zuwa main falo dan shigowarshi yabar zeenat da yaseer suna hira se fawwaz da areef sukuma suna kallon ball zama yayi ya jonasu shima. daukan kulan tayi zuwa kitchen taname jin dadin samun danyen awaran da akayi gyarashi tayi sosai ta soyashi sannan tayi sauce din hanta me dadin gaske, ta dafa kwai . ba ita tagama ba se karfe tara saura kuloli madedeta ta dibo tasawa ummi nata tasawa abba nashi sannan se nata da Mr azaad, tasan su anty Amina suna tare dasu anty shayida tasa musu , se su fawwaz da areef da zeenat se kuma tasawa faisal dakuma hafiz nashi duk da haka awaran yarage nan ta sawa masu gadi da securities din gidan zuba kulolin tayi acikin basket taga basu shiga duka ba dauko wani basket din tayi tasa sauran kulan tafito rike da basket duka biyu a hannunta se nishi takeyi, tunda tafito daga kitchen Mr azaad yake kallonta yanayin ka zar _ ka zar dinta batada gandan aiki she's not that lazy yana burgeshi amma bayason tadinga shan wahala. tunkafin takaraso yamike yakarbi basket daya ahannunta ajiyar zuciya tayi saboda daukan basket din datayi setaji duk ta gaji sosai kamar wacce tadau buhun cement ta ce " thanks habiby dama downstairs zanyi amma mufara zuwa part din ummi " bece komai ba yariko hannunta dan yaga kamar agajiye take sunje sunyi ziyara sannan tana dawuwa tashiga kitchen yanzu kuma zata kai musu . tausayi tabashi dan seyanzu yake ganin laifin kanshi dan da tun farko ya tsaya an siya awaran da yanzu awuce layin amma shi yaji tsoron hakan ne saboda abinda yataba faruwa da zeenat, part din ummi suka shiga nan ma ba kowa bedroom dinta sukayi sallama ta amsa hade da cewa " ku shigo " shigowa sukayi har a lokacin hannunsu na sarke dana juna murmushi ummi tayi ganin sune zama sukayi akan kujera fanan ta gaisheta hade da mata taaziya amsawa ummi tayi ta ce " ya kika baro gidan naku fatan kowa lafiya? " " lafiya lau ummi " fanan ta fada tana fito da food flask madedeci dake dauke da awara da sauce din hanta da dafaffen kwai ta ce " ummi ga awara " ta karishe maganar tana ajiyewa akan center table murmushi ummi tayi " ahh lallai my feena sannu da kokari yanzu awannan daren kika tsaya yin awara kindebo gajiya sannu ko kidena wahala kinji " ummi ta fada tana kallon fanan din da ta sunkuyar dakai kasa tana murmushi zatayi magana kenan Mr azaad yarigata da fadin " ai yau ita da zeenat sekinga yanda suka dameni akan awaran nikuma naki saya akan titi gudun abinda yafaru yasake faruwa amma wannan feenan naki wallahi sekinga kukan datakeyi min akai " yagama magana yana jan kumatun fanan dake muntsininshi , dariya sosai ummi tayi dantaga muntsin da fanan takeyiwa Mr azaad sake kallon fanan din tayi dakyau taga tayi fresh sosai tayi kiba tunani tafarayi kode fanan nada ciki saboda wasu sign din datagani amma bari zatayiwa Mr azaad magana yakaita asibiti agwada Allah yasa cikin ne dasunyi matukar murna , mikewa sukayi zasu tafi ummi ta ce " nagode miki sosai daughter dama nadade banci awara ba Allah yamiki albarka" amsawa fanan tayi da " ameen ameen ummina" suka tafi harsuka fita tana binsu da kallo taname godewa Allah daya nuna mata matar Mr azaad dan babu wanda yayi tunanin zeyi aure nan kusa kafin ya auri fanan ko andago maganar aneesa seya nemi hanyar da yasa se an kwantar da maganar finally gashi yanzu yayi aure kuma alhamdulillah suna farin ciki da matarshi bude kulan awaran ummi tayi kamshi yabugi hancinta faracin awaran tayi tana jinjina kai dan bata tabacin awara me dadin wannan ba haka tagama se Santi takeyi tana sawa fanan albarka. Suna fitowa daga bedroom din ummi suka shiga na anty amina suka same anty amina da anty zainab suna hira sama_sama akan kujera anty shayida kuma tana kishingide akan gado ta rufe idonta kamar bacci takeyi amma idonta biyu takoma abin tausayi dan tagama waya da mijinta da baya Nigeria yatafi Egypt kenan ta kwanta tana jin duk hiran dasukeyi , gaishesu fanan tayi hade da musu taaziya zama tayi kusa da anty shayida datake jinsu hannunta fanan tarike murya asanyaye ta ce " anty shayida" bude idonta tayi akan fanan tayi mata murmushin yaqe ta ce " naam feena " gyara zama fanan tayi ta ce " anty shayida dan Allah kidena sawa kanki damuwa haka karki kamu da wata cutar daban tabbas abin da ciwo amma kiyi hakuri kimika lamarinki ga Allah komai zewuce in sha Allah mommy kuma muta binta da adduah" siraran hawaye ne yake fita daga idon anty shayida tasa hannu ta goge sosai kalaman fanan ya kwantar mata da hankali ta ce " nagode sosai feena samun yarinya me irin hankalinki awannan zamanin se antona! bawai nadamu da mutuwar mommy bane wallahi ah ah bandamu ba domin kuwa kowa ze mutu duk zamu koma ga ma haliccinmu amma ina tuna irin mugun tabon datamin wai ace mahaifiyata ce tamayar dani juya karfi da yaji , feena sau takwas fa inasamun ciki yanzu kila bazan taba samun wani cikin ba " duk ta kashe musu jiki mugun tausayinta ne ya kamasu mommy ba karamin illa tayiwa rayuwar anty shayida ba, anty amina da anty zainab duk idonsu ya taru da hawaye sun kuma ji dadin zuwan fanan domin kuwa yanzu anty shayida ta amayar da abinda yake damunta tunda akasa mata drip tayi bacci ta tashi babu wanda takeyiwa magana sede ta girgiza kai tsoro sukaji kar tashiga depression amma zuwan fanan yasa tayi magana ta amayar da abinda yake zuciyarta, mikewa Mr azaad yayi yazauna akusa dasu shima yarike dayan hannun anty shayida ya ce " meyasa zakice bazaki kara haihuwa ba ? baa cire rai daga rahamar Ubangiji kidena irin wannan maganar kinji komai yayi farko zeyi karshe " ajiyar zuciya tasauke tana fadin " nagode muku sosai kannena Allah yabarmu tare kuma in sha Allah zanyi amfani da abinda kuka fadamin " duk murmushi nadauke akan fuskansu ganin ta sa ki ranta har ana hira da ita mikewa fanan tayi tadauki kulansu ta ce " ga awara dazun nayi " jinjina mata sukayi suna yar dariya anty amina ta ce " ahh lallai feena sannunki da kokari da wannan daren yin awara kode munsamu karuwa ne ?" ta fada cike da zolaya kallon juna Mr azaad da fanan sukayi ya kashe mata ido daya itade kunya takeji se rufe ido takeyi tana buya ajikin anty shayida sosai anty shayida take dariyar fanan da take buya ajikinta dan anyi maganar ciki , bude kular anty amina tayi tana " wow irin wannan liyafar haka godiya muke " tunkafin takarasa abinda zata fada sukaga anty shayida ta toshe hancinta sannan daga baya ta tashi da gudu tafada toilet tana sheka amai kamar zata amayar da hanjin cikinta rufa mata baya sukayi banda Mr azaad daya fita a bedroom din yana kayittaciyar murmushi, taimaka mata sukayi ta gyara jikinta suka riketa suka fito aka zaunar da ita akan bed , muryanta kamar zatayi kuka ta ce " dan Allah ku rufe awaran nan please" rufewa sukayi sunayi mata sannu duk basuyi tunanin wani abu ba duk gani sukeyi kamar zazzabin da takeyi ne hakan yasa anty amina kara kiran layin doctor safiya ta sanar da ita abinda yafaru abangaren doctor safiya ta ce " Kinga dare yayi dana dawo amma yanzu kinsan me dazun nayi mantuwa adakinki kiduba zakiga handbag dina akwai PT aciki seku gwada fitsarinta " tunda doctor safiya tafara jawabi jikin anty amina yake tsuma jira kawai takeyi tagama jin abinda take fada ta aiwatar cikin sauri tadubo handbag din aikuwa taci karo da PT dauka tayi taje kusa da anty shayida ta ce " anty shayida tashi muje toilet mugwada yin abinda doctor tafada " batare da musu ba anty shayida ta mike anty Zainab ta kamata suka kaita toilet suka barta tayi fitsarin acikin wata yar container tabawa anty amina suka barta a toilet din tayi pt din bayan wasu mintuna baro_baro jan layi guda biyu suka bayyana da karfin gaske anty amina tafurta " alllahuuuuuuuu akhabarrrrrrr " dasauri tafito rike da PT strip din ahannunta, jin yanda taja kabbarah ne yasa suka taso zasu shiga toilet din sukaci karo abakin kofar toilet din sa hannu anty zainab tayi ta karba tana kallo farin ciki ne mara misiltuwa yakamata tafara " alhamdulillah! alhamdulillah! alhamdulillah! alhamdulillah ! Allah mungode maka daka nuna mana wannar rana me albarka tabbas wannan kalmar gaskiya ce da akace wani hanin ga Allah baiwa ne , Allah me yanda yaso , Allah mungode maka da sa muna cikin rayayyu dazamu sheda wannar rana me cike da albarka " rungume juna anty amina da anty zainab sukayi suna murna haka fanan ta rungumi anty amina da anty zainab, tayi matukar jin dadi sosai dakuma taya anty shayida murna . Zuba musu ido kawai anty shayida tayi dan ita gani takeyi kamar mafarki takeyi jin wai ita akace take dauke da ciki acikin mahaifarta , hawaye masu zafine suke sauka akan kuncinta adduah takeyi Allah de yasa ba mafarki takeyi ba domin tasha yin ire_iren wayan nan mafarkan amma nayau kam fatan ta daya inma mafarkin ne Allah yasa karta tashi ta tabbata ahaka . Rike kafadunta anty Zainab tayi itama tana hawaye ta na fadin " Allah ya amsa adduo'in mu shayida! Allah yadubeki da idon rahama bayan shekara goma sha takwas yau gashi kema kinadauke da da ajikinki kinkusa zama uwa alhamdulillah" tabbas yanzu tasake tabbatarwa ba mafarki bane zahirine yasa ta rike hannun anty zainab da dan karfi kafin ta rungumeta sosai tana adduo'in acikin zuciyarta , raba jikinsu tayi , tayi sujjada taname godewa Allah daga hannunta sama tayi hawaye na kwarara a idonta ta ce " tabbas baa cire rai da rahamar Ubangiji, nadade da dena tunanin nima zanga jinina wacce na haifa banyi tsammanin bayan wayan nan shekarun zan zama uwa ba se yau Allah nagode maka, ya Allah ka karemin abinda ke cikina daga sharrin masu sharri kasa yafito lafiya " haka taci gaba da adduah suna amsa mata da Ameen lalubo wayarta tayi tana me dialing din number mijinta kusan missed call biyu tayi mishi be daga ba se daga baya yakirata hannunta na rawa tasa ta daga tana " alhaji albishirinka ?" yanayin yanda yaji muryanta adashe gakuma yaji ta ambaci albishir ne yasa ya ce " hajiyata meyake damunki naji muryarki haka ?" bata bashi amsar tambayar da ya mata ba tasake maimaita mishi " albishirinka?" amsawa yayi da " goro " dan yaga inbawai amsar tambayar yabata ba tofa shima bazata bashi tashi amsar ba cike da zumudi ta ce " Allah ya amsa kukanmu alhaji ni da kai nanda watanni tara masu zuwa inda rai da lafiya zamu zama iyaye " alhaji auwal aiki yakeyi a laptop yana shigar da wayansu bayanai jin wannan maganar da anty shayida ta furta mishi yasa ya tsayar da komai yaname cire wayar akunnenshi yakalli wayar dakyau sannan yamaidashi kunnenshi murya a sarkaqe ya ce " hajiyata banji me kikace ba ko Zaki iya maimaitamin ?" Duk murmushi sukayi na farin ciki sunajin abinda alhaji auwal yake fada saboda anty shayida tasa wayar a handsfree maimaita mishi tasakeyi kabbarah alh auwal yayi hade dayin sujjada yana mika godiyarshi ga Allah madaukakin sarki me kowa me komai meyin yanda yaso a lokacin da yaso . kasa magana ma yayi ji yayi yafi kowa murna awannan daren tunda ya karbi sako me matukar girma da daraja sosai sukayi waya dashi sannan yakashe . daukan basket din duka biyu fanan tayi dan Mr azaad yatafi bedau dayan ba , taya anty shayida murna tayi sannan tayi musu seda safe ta tafi , har yanzu su fawwaz basu bar falon ba dan tun da ta tunkaro downstairs takeji muryansu suna musun ball hangota sukayi rike da basket har guda biyu tasowa areef yayi ya karbi dayar ya ajiye akan table zama tayi ta gaishesu suka amsa suma suka gaisheta kin amsawa tayi yaseer ne ya ce " antynmu barka da dare " kallon shi tayi batace komai ba dan tasan tsokana ne kawai can kuma ta ce " ayyah ya yaseer dan Allah kudena banaso " kwaikwayonta zeenat tayi tana " ayyah antynmu kema kidena kin amsawa " dariya sukayi harda ita fanan din tajefawa zeenat pillow tana " kekuma zanyi maganinki " fiitowa kowa kulan awaran shi tayi tabasu suka karba suna godiya Faisal kam ana bashi nashi ya ce " tom nikam natafi seda safenku madam nagode" yatafi . Fawwaz ne yabude nasu kulan yaga awara ne ya ce " yau akwai cin dadi irin wannan zazzafar liyafa haka antynmu" murmushi kawai tayi zeenat jin an ambaci sunan awara ne yasa tabude nata kulan ido biyu sukayi da awara ihu tayi " yessssssss wallahi awara ne" toshe kunne sukayi saboda ihun zeenat datakeyi na farin cikin ganin awara dan tunda suka dawo ta sallamar ba samu zatayi ba harta cireshi arai , kallon fanan tayi ta ce " gaskiya anty fanan kedin ta musamman ce wallahi Allah ya suburbuda miki albarka muah" takareshi tana yi mata blowing din kiss dariya kawai fanan tayi ta ce " tom yanzu de gaki ga awara amma kafin ki faraci tashi ki rakani wajan abba inkai mishi nashi " jikin zeenat har rawa yakeyi dan so takeyi sukaiwa abba sannan ta dawo tacinye nata takuma hada danasu ya fawwaz dan plan din data shirya kenan. kallon areef fanan tayi ta ce " nikam ya areef hafiz ya farka ne ?" " Eh yatashi yayi sallah yasake komawa bacci bayan yaci abinci " areef ya sanar mata ta ce " tom ganashi nan inkun shiga ku bashi please". " to shikenan antynmu " tun kafin subar falon ma fawwaz da areef, yaseer sun faracin nasu se santin girkin sukeyi . Securities kowa nakan aikinshi su fanan sunzo dede inda suke suka gaishesu mika musu nasu kulan tayi ta ce " bansaniba ko kunacin awara gashi " sa hannu sukayi suka karba suna " munaci madam mungode sosai " wucesu sukayi suka nufi part din abba .yana zaune afalo yashiga duniyar tunani bemasan da shigowarsu ba sakeyin sallama sukayi se anan ne yajisu ya kallesu da fara'a ya ce " fatima yau kinkawo min ziyara kenan ?" Kan fanan akasa ta ce " abban barka da dare! ya Karin hakurinmu Allah yajikanta da rahama" nuna musu wajan zama yayi suka zauna , amsawa yayi da " ameen ameen Fatima ,naji azaad yace gobe zaku tafi ko ? " " Eh abba haka yace " jinjina kai abba ya ce " masha Allah , Allah yakaiku lafiya " ita da zeenat suka amsa da " ameen" ajiye mishi kular awara tayi ta ce " Abba ga awara " sa hannu yayi yadauki kular awaran yabude cikin barkwanci ya ce " gaskiya Allah yataimakeni da yasa banyi bacci yanzu ba da yanzu awaras ta wuceni " sosai fanan da zeenat suke dariya dan Abba yabasu dariya shima darawa yayi ya ce " to nagode sosai kuwa Allah yayi albarka" ta amsa da ameen, zeenat ce ta marairaice ta ce " abbana nakaina dan Allah in tayaka ci?" hararan wasa yamata ya ce " iyeeeh yau naga abin al ajabi wato baƙin kine yasan dadi nawa besani ba, to aikuwa ko budewa ma bazanyi ba sekin tafi " yayi maganar yaname rufe kular , dariya fanan takeyi na drama abba da zeenat itade ji tayi babu wacce takaita saa saboda Allah yahaɗata da sirkan nai nagari masu kuma sonta kamar yarsu kowa na gidan yana matukar kaunar fanan dakuma girmamata, kullum addu'ar ta shine Allah ya bata iKon kawo farin ciki akan fuskokinsu wannan al kawarine da ta daukawa kanta bazata taba barin wannin su da bakin ciki ba inde har akwai yanda zatayi na ganin farin cikinsu yanda take kaunar familyn ta haka take kaunar su . sallama sukawa Abba suka koma part din ummi shigowa falon sukayi suka samu su fawwaz sun gama cinye nasu awaran yaseer yana ganin shigowarsu ya ce " alhamdulillah my girl gwara da Allah yadawo daku yanzu wallahi Allah ne kawai yasa kinada rabon cin wannan daddadar awaran , saboda dakyar na iya kwace kular ahannun su fawwaz wai tunda bakya nan zasuci rabin naki " yafada yana hararan su fawwaz dasuke kunshe dariya hade fuska zeenat tayi ta ce" Allah ya fawwaz da ya areef da kuncinye min awarata yau da se anyi yakin basasa " dariya fawwaz da areef sukayi Sannan suka tafa sake fusata zeenat sukayi yasa tadauki kular takoma kusa da yaseer tazauna tanaci . fanan de seda safe tayi musu domin kuwa tasan yanzu haka Mr azaad yanacan yana jiranta harta haura upstairs setayi wani tunani ganin yanda suketa hiransu kamar basu ji labarin anty shayida nada ciki ba hakan yasa tajuyo cikin yar daga murya ta ce " albishirinku ?" dukkansu suka bata amsa da " goro " gyara tsayuwa tayi ta ce " Kuma dole sekun bani goron albirshir dina! Anty shayida tanada ciki takusa haihuwa kusata a adduah Allah yasauketa lafiya " kabbarah sukayi cike da farin ciki suka godewa Allah yanzu darabon zasuga jinin anty shayida zeenat kam harda rawa girgiza kai fanan tayi tabarsu abinta tashige nasu part din tana murmushi itama , haka sukata nishadinsu part din ummi zeenat tafada domin sanar da ita wannan labarin , har ummi tafara bacci zeenat ta tasheta tafada mata jitayi baccin ya yaye babu abinda take furtawa se kalmar alhamdulillah tashiga bedroom din anty amina nan tasamesu rungume anty shayida ummi tayi dukkansu suna farin ciki sosai ummi tadinga mata adduah sannan tabar dakin tashiga nata takira abba ta sanar shima yayi matukar murna sosai haka suka kwanta kowa na cike da farin ciki. Samunshi tayi adaki yana kwance abinshi yayi shirin bacci cire kayan jikinta tayi tadaura towel tashiga bathroom tayi wanka tafito ta shirya jikinta sannan taje kitchen tazuba musu nasu awaran a plate tashigo hannunta dauke da plate da ruwa zama tayi ta ce " habiby kazo muci awara " yana daga kwance ya ce" wifey kici kawai ni bazan iya ci ba " yanda yayi maganar tasan kota matsa mishi ma bacin zeyi ba yasa taci abunta harta koshi tasha ruwa ta maida komai kitchen ta gyara musu zama . Dawuwa tayi tahau gadon tashige jikinshi ta kwanta matseta yayi ajikinshi ya ce " se yanzu kenan ?" " uhmm yeap kasanme anty shayida takusa zama mother" ta sanar mishi tana sakin murmushi bata amsa yayi da sexy voice dinshi ya ce " nasani Allah yasauketa lafiya! Saura ke nakusayin ajiya anan wajan " yafada yana shafa shamulallen cikinta murmushi kawai tayi manna mata kiss a goshi yayi, ya kashe light din dakin yabar bedside lamp yaja musu bargo , duk shuru sukayi kuma basuyi baccin ba dago fuskanta dake kirjinshi yayi yakalli cute face dinta ya ce " gobe 8:30am flight dinmu ze tashi " kamar me rada ta ce" Allah yakaimu habiby " ya ce " ameen " adduah yayi musu sannan kowa yayi niyar bacci suna manne da junansu. Washe gari Sungama shirin tafiya yar karamar trolley fanan tadauka dakyar Mr azaad yabarta tadauka nan ma yana tsaye akanta tadauki abubuwan bukata hijabs ne se abayas da kuma jallabiya nayin sallah sekuma abubuwan da anty amina da anty firdausi suka bata daukan trolley din security yayi yakai boot suka fito suma kowa ya hallara afalo fanan na sanye da doguwar rigar abaya dark blue da mayafinshi se Mr azaad dake sanye da kana nan kaya jeans da riga sunyi kyau sosai . Har kasa fanan ta gaida kowa hade da taaziya, suka amsa cike da so da kauna mikewa sukayi domin yi musu rakiya airport amma banda ummi,abba,anty shayida,anty amina,anty zainab, masu yi musu rakiya iyakacin yaseer, zeenat, fawwaz, areef se hafiz da yau yajishi klau alhamdulillah. motoci goma ne ke fa ke a compound din gidan suna jiransu, shiga sukayi su ummi nayi musu adduo'in tsare hanya har suka bar gidan komawa cikin gidan sukayi kowa jikinshi asanyaye yau de sunsan zasuyi kewar fanan sosai . daga ita se habibynta Mr azaad amotar se driver dake driving dinsu tana kwance ajikinshi Mr azaad shikuma yana shafa bayanta tana bashi labari taji ringing din wayarta cirota tayi a handbag dinta ganin my dad tayi yasa tayi murmushi dama sukadai ne basuyi waya da safen ba tayi waya da su baba da mama ya usman da auta Amira ma ta kirata duk sun musu Allah yakiyaye hanya, dagawa tayi da sallama abakinta ta gaisheshi amsawa uncle kabir yayi suka gaisa yamusu adduah shima sannan yamikawa umma rahina itama suka gaisa tamusu Allah yatsare haka suhaima da ya al ameen seda suka gaisa duka sannan sukayi sallama tana kokarin ajiye wayar kiran anty firdausi yashigo itama tayi musu adduah sannan tabawa daddyn junior bayan sun kammala ta kashe kiran. dede kunnenta Mr azaad ya ce " wow gaskiya wifey ke yar gatace kowa na sonki " fari tayi da ido ta ce " ehh mana shisa yanzu nafika fans " murmushin gefen baki kawai yayi, yasa hannu ya matse libs dinta yamatso da fuskanshi daff da nata har suna shakar daddadar kamshin turaren jikinsu da ya hade yabada kamshi me dadi da tafiya da zuciya yace " baby ai ke din ta dabance dole kifini" yagama maganar yana manna mata kiss a libs din sannan yasake ta gyara kwanciyarta tayi ajikinshi tana shakar kamshin jikinshi hade da lumshe ido, har aka iso airport basu sani ba seda sukaji tsayuwar motar , seda kowa yafito kafin yafito yabudewa fanan murfin motar tafito yarike hannunta suka fara tafiya seyanzu Mr azaad yalura da yan jaridun dasuke wajan tun fitowarsu akeyi musu videos da hotuna hankalin al'ummar airport din duk yadawo kansu ganin wannan shahararren dan kasuwan nan ne tare da matarshi bakaramin burge jamaa sukayi ba kowa se fatan alkhari suke musu wasu na burin Allah yabasu masoya irin Mr azaad, duk yanda sukaso suyi magana da Mr azaad bayuba ko kallon su beyiba jin anfara kiran sunaye yasa suka rungumi juna shida yaseer akunne yaseer ya ce " dude karka yarda ku dawo baku samo mana baby ba " dukan kirjin yaseer Mr azaad yayi Yana fadin" seka hanamu dawuwa ai dan iska " dariya yaseer yayi yace"waneni " haka sukayi bankwana dasu gaba daya suka fara hawa matattakalar jirgin suna daga musu hannu harsuka shige , direct Vip Mr azaad da fanan suka shiga sukadai ne awajan bakowa a vip zama fanan tayi Mr azaad yadaura mata belt , fara tafiya jirgi yayi yana kokarin tashi runtse ido fanan tayi sosai Mr azaad yariketa dan yaga yanda ta tsorata saboda wannan shine karonta na farko hawan jirgi shisa duk tabi ta rikice . duk ta galabaita harwani jin tashin zuciya takeyi kamar zatayi amai yana rungume da ita ajikinshi ahaka hartayi bacci. 19:00pm dede jirginsu yayi landing a Denver international airport , wato karfe 7 nadare kenan alokacin Nigeria duk dacewa akwai tazaran 7hours tsakanin Nigeria da USA . kallon fanan yayi da take bacci duk tayi laushi sau biyu tana amai ƙunce mata seat belt dinta yayi sannan yadauketa cak yafara taka staircase din jirgin hasken da airport din ke dashi tako ina yatashi fanan daga bacci tabude idonta tana karewa airport din kallo , kamar rana kowa se sabgar gabanshi yakeyi airport din kanshi abin kallo ne komai nawajan medaukan hankali. Wasu jibga_jingar motoci guda hudu sukazo daukar Mr azaad and Mrs azaad kuma dukkansu turawa ne sanye da bakaken suits , har suka sauko daga jirgin fanan bata sani ba hankalinta na kan airport dan ya burgeta sosai , cikin girmamawa turawan nan suke gaishesu beko kallesu ba daya daga cikinsu yabude musu murfin motar tsakiya Mr azaad yashiga dauke da fanan a hannunshi kwantar da ita yayi akan seat yadaura kanta akan cinyar shi shafa fuskanta yayi ya ce " sannu ko wifey munkusa isa gida " da muryanta da baya fita ta ce " to habiby" tafiya sukeyi akan titi slowly kamar wayanda suka dauko sarki ko shugaban kasa har suka iso wani hadedden waje me matukar girman gaske wani katon sign bot kamar tv yana fitar da rubutu da colors kala_kala yana rubuta ' welcome to las Vegas ' babban birnin las Vegas kenan dake cikin kasar america . Horn sukayi a tangamemen gida masu gadi suka bude aljannar duniyar gidan daya kasance daya daga cikin manyan gidaje a las Vegas komai na more rayuwa akwaishi awannan gidan akashe masa daula iya daula,gidan da ya yakasance mallakin Mr azaad, bude musu gate akayi suka shiga fanan kamar bakauyiya haka takoma domin gidansu Mr azaad na Nigeria bekai wannan kyau ba dukda cewa shima dankararriyar gida amma wannan ya hadu iya haduwa aikunsan banbancin gidajen turai dana gida Najeriya, tsayawa fada muku kyaun gidan ɓa ta ɓaki ne buɗe musu motar akayi yafito dauke da ita ahannunshi, turawa dake aiki a gidan se ɗiban gaisuwa sukeyi haka yashiga da ita cikin gidan kai tsaye wani ƙayitatciyar bedroom yashiga ya kwantar da ita akan makeken gado, luf tayi tana kallonshi daga mata gira yayi alamar tambaya girgiza kai tayi , dukunkune jikinta tayi waje daya saboda sanyi da takeji ganin haka yasa Mr azaad kashe ac sannan ya rufa mata bargo , kayan jikinshi ya cire yashiga toilet yayi wanka da alwala,yafito yasamu harta fara bacci batare da yasa kaya ba yana ɗaure da towel yahau kan makekiyar gadon , yaye bargon yayi yaɗagota yafara cire mata kayan jikinta , bacci ne a idonta duk abinda yakeyi tanajinshi amma takasa koda bude idonta ne haka yadauketa yashiga toilet da ita yamata wanka da ruwan zafi tayi alwala sannan yanaɗota a towel yakwantar da ita akan gadon sosai taji dadin jikinta. Kitchen din dake cikin part din yashiga ya haɗa mata cornflakes yakawo mata hartayi nisa abacci babu yanda ya iya dole seya tasheta tasa wani abu acikinta baze barta ta kwanta haka ba zama yayi agefenta ya ce " wifey kitashi kisha cornflakes seki koma baccin " tana jinshi sama_sama hakan yasa ta make kafada tare da turo mishi dan karamin baƙinta , murmushi yayi yasa hannu yadagota zama tayi tana marairaicewa kamar wacce tasha maganin bacci dakyar ta iya cewa " habiiiiibyyyyy kabarrrrni inyiiiiiii bacciiiii " yanda take jan maganar nata seda yaji tsigan jikinshi yatashi musamman yanda takira shi se dayaji har cikin ranshi , fa ra bata yayi abaki harta shanye duka batama san tashanye ba kwanciya take kokarin yi yarikota ya ce " ki bari muyi sallah seki kwanta" dressing room yashiga yadauko mata wandon da riga na bacci masu kauri se katon jacket din rigar sanyi domin ana sanyi sosai bude trolley dinta yayi yafito mata da hijab , shima jallabiya yasaka , sannan yadawo bedroom din, sa mata kayan yayi ya shimfida musu sallaya jansu yayi sukayi sallolin da ake binsu bayan sun idar tayi addu'a ta haye gado ta kwanta se bacci murmushi kawai Mr azaad yayi shima agajiyen yake hakan yasa yakashe wutar dakin yabar bedside lamp yaja musu bargo hade da musu addu'a bacci . To sekuma gobe inme duka yakaimu da rai da lafiya . Waiting for your comments and share fisabilillahi 🙏. https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 ( Yar lelen Jarumai) 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚 ⚜️📚 J. W. A 📚🖋️ Gargadi.... Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowani siga ko a karanta minshi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira koda Allah nabar mutum ze sakamin kuma yabimin hakkina. PAGE 6️⃣0️⃣ NIGERIA Adamawa Yola Shigowa lukman yayi yadawo daga office yasamu nusaiba zaune tana chatting dinta hankali kwance tanajin shigowar shi amma ko dago kai batayi ta kalleshi ba balle yasa ran zatace mishi sannu da dawuwa girgiza kai yayi kawai yana mata fatan shiriya domin tunda akayi aurensu yake fuskantar bacin rai daga wajan nusaiba betaba ce mata uffan ba balle yabiye mata haka zata tsaya ta mishi rashin kunya iya isarta ko kadan bata ganin girmanshi ta renashi ga tsanar datayi mishi tunda akayi auren wani abu be taba shiga tsakaninsu ba a matsayin miji da mata , bata daga tsinke bata da aikinyi se chatting da kawayenta ko girki bata tabayi mishi ba kullum a restaurant yakecin abinci duk da akwai me aiki agidan amma nusaiba tahanata shiga mata kitchen bakomai ne yayi tasiri awajan nusaiba ba fa ce huɗubar da mahaifiyarta madina tayi mata. wanka yayi yafito yazauna afalon har lokacin tana nan a inda yabarta bata motsa ba se hira takeyi da kawayenta a whatsApp, zuba mata ido yayi yana kallonta kamar wani me nazarin wani abu wata uwar harara nusaiba ta watsa mishi lokacin da ta ankara yana kallonta sannan ta ce " meye haka ? Kazo kawani sani agaba kana kallo mtsssw " ta gama maganar hade da jan doguwar tsaki kamar wacce take magana da sa'anta, ran lukman yabaci sosai da tsakin dataja mishi ya ce " nusaiba ni kika jawa tsaki?" Kallon tara saura takwas tayi mishi tana ƙaɗa kafa ta ce" ehh kai nayiwa wannan tsakin lukman! nace kai nayiwa kadau mataki , inka isa cikekken namiji ka sakeni mara zuciya kawai " murmushi me ciwo lukman yayi kafin ya ce" nusaiba kenan kice gaba da barin duniya tana ruɗarki da kuma hure miki kunne duk abinda zakiyi sede kiyi amma bazan taba sakin kiba wannan alkawarine nadaukawa kawu , amma kisani nikaina bawai kaunarki nakeyi ba kawai de so ne na yan uwantaka bayanshi babu komai araina , tun yanzu Yakamata kizubar da mukaman yakinki ki karbi wannan auren namu hannu bibbiyu tun kafin lokaci yakure miki " duk maganar dayakeyi mata nan cikin sanyin murya yakeyinsa dukda kuwa ranshi abace yake lukman yana da sanyin hali sosai , haka yatashi yabarta a falon tana cika tana batsewa , gani takeyi babu wanda aka cuta sama da ita za'a aura mata lukman ita ai ba sanshi takeyi ba kuma dole taci gaba da yi mishi abinda Madina take fada mata domin ta wannan Hanyar ce kadai zasu samu ya saketa. Yau de Allah yayi dare gari ya waye se yau Mr azaad yabawa su spider umarnin ƙyale alh Ibrahim tijjani su da kansu suka fitar dashi wajan gari suka hankaɗoshi waje yafadi aƙasa timm kamar wani kayan wanki, duk yabi ya yamutse yafita a hayyacinshi ya canza kamanin wannan tumbin nan nashi duk seda ya sa ce dan baƙar azaban dayasha tabbas yaji jiki bana wasa ba, dede da yatsun hannunshi dakyar yake iya dagawa fuskan nan ya kumbura sumtum ya tara jini musamman idonshi , yana yashe akan hanya motar ambulance yazo suka dauke shi suka wuce asibiti dashi . _____ jikinta na matukar rawa take magana tana nunashi da yar yatsa ta ce " bazeyuba ! baze taba yiwuwa ba ka cuceni ! in kyaleka? baka isaba kayi kadan amjad" wanda takira da suna amjad yana zaune yazuba mata ido hankalinshi kwance ya ce " keee aneesa karki yarda kice zaki nunamin akuyanci koɗan kinga nayi shuru na ƙyaleki ne ? Ni bance kin cuceni ba se kece zakice na cuceki" aneesa dake tsaye a kanshi tana huce idonta yayi ja sosai duk alamu sun nuna kuka tasha ta koshi ta nunashi da yatsa tana fadin " kayi kaɗan ka shafamin cuta sannan ka hanani magana HIV positive fah nagani toma dakake cewa bakai ka shafamin ba agidan ubanwa nasamu to? iyeeh nace agidan ubanwa nasamu inbakai kasamun ba?" murmushi yayi irin nasu na gogaggun yan duniya yabata amsa da " ai badani kadai kike yawon tazubar ɗinki ba , waye besan ke karuwa bace zaki zo ki dameni kina cemin nina shafa miki HIV kije can kinemo sauran abokan holewarki " kukan kura aneesa tayi ta cukumi kwalar rigar amjad afusace ta ce " amjad nikake fadawa haka halaccin dazakamin kenan , kaine na mijin daya fara amfani dani a matsayin virgin , kyautar budurcina fah nayi maka amma yau kaine kake cewa wai ai bakai kadai kake amfani dani ba , to naji bakai kadai bane amma ai kasani kai da ya ne kake sex dani batare da condom ba kaga kuwa dole kaine ka shafamin HIV " fincike hannunta daga kan rigarshi yayi ya ce " karamar yar iska kema yanzu da kanki kinfada ai bani daya kike sex ba to wallahi nasakejin kince nine nashafa miki HIV ranki se yayi mugun ɓaci " Azafafe tadau handbag dinta da wayoyinta tafita a hotel room din tana me danasanin sanin amjad a rayuwar ta. SATANIC Duk suna tsaye sunyi shuru suna jiran suji abinda shugabansu tanzarzar zece shikuwa yana hakimce akan kujeran mulkinsa cikin murya me amo ya soma magana " hafsat ta kasance daya daga cikin mu, babba me muƙami ce , amma mutuwar nata shine dede agareku domin zata iya tona muku asiri yanzu amanta da babinta, lokaci kara kurewa yakeyi inason yanzu nan da wani lokaci ƙalilan zamuyi sacrifice (sadaukarwa)mata masu ciki da kuma jarirai sekuma mata masu jego duk wani asibiti dayake cikin wannan gari dole ashiga akashesu wannan shine babban sadaukarwar dazamuyi wanda tun bayan shekara ɗari ba'a ƙara yi ba , idan muka yi shi ze taimaka mana wajan samun sarauniyar nasminaya, nan da yan watanni zaayishi . Akalla muna bukatar masu ciki guda dari se jarirai maza da mata guda hamsin se masu jego hamsin doleeeeee ayi wannan sadaukarwar " yagama magana cikin sake tabbatar musu da hakan ze faru bayan sun gama tattaunawa yabawa kowa izinin tafiya nan da nan suka zama jemage suka ɓace. U S A LAS VEGAS ✈️ Gjiyar da sukayi ne yasa tunda sukayi sallah asuba suka koma bacci basu tashi ba har se wuraren karfe 11 na safe kafin suka tashi sukayi wanka, sukayi breakfast sannan suka fito ze nuna mata gidan suna sanye da riga iri daya tshirt se wando jeans tasa hula akanta suna rike da hannun juna suke ta zagaye gidan duk inda suka wuce se ma'aikatan gidan sun gaishe su ita ce ma take amsawa amma Mr azaad ba amsa musu yakeyi ba babban garden din gidan suka shiga dayasha furanni kala da iri wajan ya matukar kayatarwa fito da wayarsa yayi yafara daukanta hotuna sannan yamusu selfie sunyi kyau sosai sun dan jima a garden din suna hiransu gwanin sha'awa kafin suka bar garden sukaje swimming pool yana da girma shima ya haɗu sosai yanda ruwan yake blue in color ne ya burge fanan yasa ta ɗan sunkuya tasa hannunta acikin ruwan tana wasa dashi tana dariya , Mr azaad na gefe yana mata video batare da tasani ba kiran sunanta yayi tadago ta kalleshi ya ce " baby ko zaki shigane " girgiza kai tayi ta ce " noo habiby ai ban iyaba " " yau zanfita meeting dana koya miki amma zan koya miki ko wani lokaci" cewar Mr azaad daya iso inda take yasa hannu yadagota suka koma kan kujerun da suke wajan swimming pool din suka zauna call ne yashigo wayarshi sunan Abba ne yabayyana picking yayi sukayi waya yamusu ya gajiya sannan ya ce yabawa fanan karba tayi sukayi waya da Abba dake falo tare da duk wani dan gidan haka seda suka gaisa dakowa cike da farin ciki sannan sukayi sallama , kiran layin baba Mr azaad yayi yagaisheshi sosai baba yamusu sannu da hanya nan ma seda suka gaisa da duk yan gidan , sun jima awajan suna hira kafin suka koma cikin gida. Haka rayuwar su taci gaba cike da soyayyar juna da jindadi , haka yan gida Nijeriya kullum sesunyi waya dasu harda video call, ranar da ummi takira Mr azaad yana office sukayi waya dama tun zuwansu takeson fada mishi magana ɗan gane da fanan ta ce " son please ka kula da feena sosai sannan la kaita asibiti amata pregnancy test domin ni naga kamar akwai ciki atare da ita " murmushi Mr azaad yayi shima yayi experiencing hakan amma da sukaje asibiti se yazama ba haka bane ya ce " ummina nima nayi tunanin hakan amma kafin muzo seda mukaje hospital aka mata test babu ciki ajikinta" jinjina kai ummi tayi sannan ta ce " to Allah yakawo babban rabo " ya amsa mata da ameen sannan sukayi sallama. AFTER TWO MONTHS yau watan su fanan biyu dazuwa USA kuma haka zalika watansu biyar dayin aure , Shakuwa me karfin gaske yasake shiga tsakani Mr azaad da fanan wani irin narƙekkiyar da kuma zazzafar soyayya suke nunawa junansu hankalinsu kwance duk sanda yadawo daga office haka ze dauketa sufita yawa wajaje daban_daban , alhamdulillah Mr azaad ya gama meeting dakuma aikin daya kawoshi , sannan ummi tafara mishi maganar dawuwarsu saboda auren amare da angwaye saura sati uku anata shirye-shiryen biki sannan tasake tuna mishi maganar tsayawar da zasuyi a dubai kamar yanda tafada mishi kafin su tafi . Bacci yake son yi amma fanan ta hana shi tana zaune akan cikinshi ta cusa hannunta acikin gashin kanshi tana mishi tafiyar tsutsa ranƙwafo da kanta tayi dede kunne shi kamar raɗa zata mishi da karfi ta ce " habibyyyyyy ! Katashi muje shan ice cream din" runtse ido Mr azaad dan sautin muryanta data ɗaga seda yakusa kashe mishi dodon kunne yau tunda ta tashi take mishi rigima akan ice cream kuma ya ce zeyi order akawo mata har gida ta ce ah ah sede suje su siyo . Juyawa yayi da ita tadawo ƙasanshi ya mata rumfa da faffadar kirjinshi daɓe sanya riga ba ga kwantaccen gashin kirjinshi dasuke ƙara mishi kyau kallonta yayi da rinannun idonshi da suke cike da bacci a cikinsu ya ce " haba wifey yanzu baccin ma bazanyi in peace ba " fiki_fiki tayi da ido kamar wacce batada gaskiya ta ce " nide Allah barakayi baccin nan ba semunje mundawo " zuba mata ido yayi yana kallon yanda take motsa dan karamin baƙinta dayasha libstick se sheƙi yakeyi dawo da kalloshi kan dara_daran fararen idonta yayi dasuka kasance oily eyes suna dauke da zara_zaran gashin ido , hannunshi daya yasa yana shafa kyakkyawar fuskantar , turo mishi baki tayi cike da wani iriyar shagwaba ta ce" katashi mutafi ko in maka kuka " yanayin yanda tayi maganar da yanda ta shagwabe mishi ne yasake narƙar da zuciyar Mr azaad besan lokacin da ya hade baƙin su waje daya ba , daura hannunta daya tayi akanshi tana shafa mishi kai sannan dayan tafara shafa mishi kirjinshi musamman wajan nipples dinshi da kwantaccen gashin kirjinshi, kara ingiza Mr azaad tayi da irin wannan salon nata sa hannunshi yayi ya fincike yar ficiciyar rigar da ke jikinta yadaura hannunshi akan dukiyar fulaninta yafara wasa dasu sannan ya gangaro da hannunshi izuwa private part dinta ya soma wasa da wajan dogon numfashi fanan taja tasake cusa hannunta cikin sumarshi seda sukayi romancing juna sosai kafin suka fara sex tsabar yanda Mr azaad yakejinshi awata duniya har hawaye yakeyi ɗan dadin dayakeji daura bakinshi yayi akan dukiyar fulaninta yafara sha kamar yasamu sweet kokuma lolipop , abangaren fanan ma ba'a barta a baya ba duk wani salo datasan ze gigita Mr azaad seda tayi shi maida mishi da martani gaba daya sunfita hayyacinsu , ganin sunyi nisa ne sunfita anamu duniyar yasa na lallabo nafito naja musu kofar dakin. Bayan one hour nakoma dakin bakowa aciki suna bathroom suna wanka , fitowa sukayi atare jikinsu sanye da rigar towel , hand dryer fanan tadauka ta busar da gashinta tashafa mishi mayuka ta taje daukan ribbon tayi taje wajen Mr azaad dake zaune akan kujera yana danna wayarshi ta mika mishi kallon ribbon din yayi kafin yasa hannu yakarba ɗurƙusawa tayi agabanshi tabashi baya haɗe gashin yayi yamata fakin dinshi sannan ya manna mata kiss a tsakiyar bayanta da wuyanta yana kokarin sa hannunshi acikin rigar ne tayi saurin mikewa dan tasanshi yanzu se yayi loosing control dinshi kuma hakan zesa zuwa shan ice cream din yakai anjuma , kallonta yayi ganin yanda ta mike da wuri ya jefa mata tambaya " kin gaji ko ?" dasauri ta girgiza mishi killer smile yayi ya ce " bari mudawo zakiyi bayani ne " komawa gaban mirror tayi ta shafa lotion hade da fesa body spray dan kadan yanda kamshin baze tashi ba , dressing room tashiga tana sake kallon bangaren da kayanta suke yawancin kayan jeans ne da riguna se rober jeans da kayan bacci se kana nan kayan sawa agida se dogayen riguna wa'yanda ko kaɗan basu da nauyi kuma masu hannun vest, ko falazo datake sawa ta saƙe babu aciki tasan wannan aikin Mr azaad ne , gasu nan ɓirjik rasa mezata sa tayi kawai ta fito da wandon jeans da kuma riga body hook Black color jacket me tsayi datasan ze rufe mata jiki tadauka wanda tsayinshi zekai guiwanta. Saka riga da wandon tayi tasa takalmi shau ciki tadauki gyale da jacket din tariko su a hannunta tafito yanda ta barshi haka tasameshi , sauke sexy eyes dinshi yayi akan hips dinta dasuke acike tam sun cika wandon kamar zasu fito ga body hook din dayabi jikinta yakwanta boobs dinta sun kara cika sosai da kugunta , kasa dauke idonshi daga kanta yayi kamar wanda ya samu tv tacikin mirror ta lura da irin mayen kallon da yaƙe binta dashi yasa tafito da harshe tanayi mishi gwalo hade da juya mishi hips dinta dasuke tsone mishi ido, lumshe idonshi yayi kafin da murya irin wanda yake cike da sha'awa ya ce " baby kici gaba da tsokanoni kika bari nazo wajan nan Allah se na sake round two " ai kafin ma ya iddasa abinda ze fada fanan tadauki jacket dinta daya kasance white color tasaka , tahaɗe botil din jacket din sannan tadaura belt din rigar sosai kayan yazauna ajikinta tayi kyau sosai kamar asace daukan baƙin gyalen tayi rolling dinshi , irin kyau datayi ba'a cewa komai tsaff tagama shiryawanta Mr azaad kawai take jira yana zaune har lokacin be cire towel din ba bekuma tashi daga inda yake ba , ɓata fuska tayi ta ce " habiby katashi kashirya ni nagama fa " yanda tayi maganar yaso bashi dariya amma yafuske, mikewa yayi yazauna agaban mirror daukan lotion tayi ta shafa mishi sannan tafesa mishi body spray ta gyara mishi sumar kanshi tashiga dressing room tafito mishi da kaya da takalmi sannan taje jerin da inda facemask yake tadauko tafito , tayashi tayi yasa kayan sannan ta bashi facemask da alamar tambaya ya kalleta ta ce " ehh kasa ni banason mata su kalle minkai ne ai" sawa yayi batare da yace komai ba, yagama shiryawa ya kamo hannunta suka fito dauko wata ɗanƙararriyar motar driver yayi securites suka bude musu motar suka shiga masu gadi suka bude musu gate suka dau hanya. Tunda suka dau hanya inbanda shagwaba babu abinda take mishi shikuma ya biye mata baturen driver se kallonsu yakeyi tacikin madubin motar yana murmushi domin sun burgeshi . Packing yayi a ƙayitatciyar wajan shan ice cream a saman wurin an rubuta 'lappert's ice cream ' gurin ya haɗu sosai bude musu motar driver yayi suka fito , tun kafin sukaraso wajan ma'aikatan dake aiki awajen sukazo suna gaishesu hade da nuna musu hadeden wajan zama suka basu list ɗin ice cream din karba fanan tayi taga sunaye kala_kala tama rasa wanne zata zaba , can tayanke decision ta zabi kusan guda uku tanuna musu hade da mika musu list ɗin karba sukayi cikin girmamawa, maida hankalinta tayi kan Mr azaad dake pressing phone ta ce " habiby to in mungama anan zamuje neman wainar masa ko?" Hade hannaye biyu Mr azaad yayi alamar roko ya ce" wifey kiyiwa Allah kiyi hakuri karki ma sa waina aranki dan aƙasan nan ba samu zamuyi ba Please and please " kunshe dariyar dayaso kufce mata tayi yanda yake rokon ta ne yabata dariya ita kanta tasan basamu za'ayi ba kawai tsokanarshi takeyi tanaso taga reaction dinshi hararan wasa yamata ya ɗan ja kumatunta saboda yagane tsokana ce ya ce " zanyi maganinki " suna haka waiters suka kawo mata ice cream kala ukun data zaba akan tray me kyau suka ajiye hade da fadin "enjoy your day ma'am" yatafi daukan na farko tayi daya kasance vanilla flavor ta fara sha, tanasha tana lum_lumshe ido ɗiba tayi zata kaiwa Mr azaad baƙi ya ce " no baby just enjoy banason shan sanyi " gyada mishi kai tayi taci gaba da shan ice cream dinta. Bayan tagama ne ya kira waiter din ya ce mishi yamusu fakejin din wasu komawa waiter yayi can yadawo suna ahannunshi anyi packing dinsu aguri daya karban acct no su yayi yamusu transfer sannan suka tafi , se yamma liris suka dawo gida, tana tsaye agaban mirror ta sauya kaya zuwa riga yar yalo_yalo mara hannu dede cinya tana cire ribbon din kanta , yashigo yasameta, ta cikin mirror taga shigowar shi rungumeta yayi ta baya yakwantar da kanshi akan wuyanta yana shaƙar kamshin jikinta, kallon kansu sukeyi acikin madubin suna sakarwa junansu sanyayyar murmushi, cire mata ribbon din yayi yasa kanshi acikin gashin nata yana shaƙar kamshi mayukan gashin datake amfani dasu , juyo da ita yayi suna facing din juna kafin yasa hannu yaɗagata yaɗaura ta akan mirror din hannunshi kan cikin gashinta yana yamutsawa , dan ɗuƙowa yayi yamatso da fuskanta daf danashi , bude dan karamin pink libs dinshi yayi yafito da harshenshi waje tana ganin haka yasa tahaɗe bakinsu waje daya suna aikawa juna hot kiss sosai sukasha soyayyar su suka koshi. Bayan kwana biyu sun kammala shirin su na tafiya ya yanka musu tickets din dubai washe gari suka wuce airport , lokacin da jirginsu yatashi wannan karon bata tsorata sosai ba tayi luff ajikin Mr azaad. Yan masarautar dubai duk sun hallara a airport din suna jiran Flight dinsu yayi landing. befi 20mint da zuwansu ba jirgin yayi landing a Dubai international airport, fitowa sukayi hannunsu na cikin na juna hango yan familyn nasu yayi, dukkanin su fuskokinsu dauke da murmushi, shimfida musu royal carpet akayi daga bakin matattakalar jirgin har izuwa bakin motocin dasuke wajan wa'yanda aƙalla zasu kai guda goma sha biyar, tafiya suka farayi akan carpet din wanda ajikinshi aka rubuta welcome home , ƙuyangu se watsa musu flowers sukeyi , acikin wa'yanda sukazo tarbansu harda kawunsu asaad da matarshi da kuma yayanshi se kuma ƴayyun ummi rungume Mr azaad sukayi suna farin ciki ganin su fanan na gefe tana kallon su tana murmushi, matar uncle asaad ce tazo gabanta tasa hannu tadago fuskantar tana mata murmushi sannan ta rungumeta haka yan matan da sukazo suma suka rungumeta suna yaba kyanta dukda ita chocolate color ce amma hakan be hana tsantsan kyanta fitowa ba shiga cikin motar sukayi suka dau hanya babban Masarautar Dubai. Wangale musu gate din masarautar akayi suka shigo , fitowa sukayi fadar sarki suka nufa domin se sunje sun fara gaisheshi kafin su shiga cikin gida , a kishingide suka samu sarki azaad yatsufa sosai farin balarabe yana sanye da kayan sarauta yana ganinsu yafara musu marhaban duƙawa sukayi agabanshi suna gaisheshi ɗagosu yayi ya rungumesu ajikinshi yana sa musu albarka, sun jima sosai a fada tare da sarki azaad sannan suka koma cikin gida , an shirya musu kwarya_kwaryan liyafa kowa na murna da ganin matar Mr azaad manya maza da mata kowa se yabon halinta yakeyi dakuma kyanta , yanda aka martabata dakuma nuna mata zallar soyayya hakan yayiwa fanan da Mr azaad dadi duk da yasan halin dangin umminshi suna da matukar karrama mutane basa kyaran mutum duk yanda yake duk halinsu daya kuma tarbiyan da su ummi suka taso akai kenan kuma haka yaran masarautar suka taso , hakan yasa ummi ma ta gina yaranta akan tarbiyyar gidansu. Ammu mahaifiyar ummi ce ta ce fanan bazata kwana ako inaba se awajanta, bayan sunyi Sallah isha suka hadu s babban dinning table na ahali kowa ya hallara anacin abinci cikin nishadi da jin dadi bayan an gama kuma suka koma falo ana hira, fanan tanajin larabci sosai hakan yasa takejin duk abinda suke fada kuma ake hiran da ita video call fawwaz yakira Jamal yaron kanin ummi connecting yayi ta system, ummi tayi matukar farin ciki ganin fanan acikin danginta kuma kowa na haba_haba da ita da hausa ta ce " my feena kinga danginki ko ?" Murmushi tayi ta ce " naga kowa ummi kuma sun karbeni hannu biyu nayi matuƙar jin dadi da hakan , naji dadin kasance acikin wannan ahalin " haka sukasha hira kafin sukayi sallama. Darene yafarayi aka fara watsewa , har kowa suka tafi yayi saura ammu da fanan , Mr azaad se layla matar uncle asaad mikewa Mr azaad yayi ya ce " wifey muje mu kwanta dare yayi" ƙin motsawa tayi dan kunya takeji bazata iya binshi ba agabansu kuma dama ammu tace tare zasu kwana , duk da basa jin hausa amma sun fahimci abinda Mr azaad ya ke nufi , hararanshi ammu tayi cikin harshen larabci ta ce " katafi kabani wuri , gwara kaje kayi baccinka ita anan zata kwana" daure fuska yayi ya harari ammu shima cikin harshen larabci yabata amsa " ammu banason haka babu ruwanki dani da matata tunda ke na sakeki saki uku " dariya layla da fanan sukayi wato wasan kaka da jika ne ahakan kowa na hararan kowa musamman ma fanan jin Mr azaad yace yasaketa ne abin yasake bata dariya , haka suka dingayi tun sunayi kamar faɗa har yakoma lallashinta amma sam taƙi yarda tace fanan awajanta zata kwana haka yafita daga falon rai abace dan yasan ba lallai ne ya iya bacci batare da yaji fanan ajikinshi ba yariga da yasaba da ɗumin jikinta amma yau yanaji yana gani ammu tahana. Ita kanta fanan bataso haka ba amma koda ammu batace awajanta zata kwana ba , bazata bishi ba . Dakyar Mr azaad ya iya bacci batare da yaji fanan akusa dashi ba , washe gari haka yafarka ranshi amatukar bace domin shi yafi ganin laifin fanan da ammu tace seta kwana awajanta aida setacewa ammu ni awajan mijina zan kwana amma tayi shuru daga baya ma se tadinga dariya ( iyeeeh lallai Mr azaad din nan wato kai bakasan kunya ba shisa kake fadar haka .) Bayan sun gama breakfast ne aka yiwa fanan wanka da ruwan madara aka shiryata acikin alkyabbah domin za'a gudanar da al'adun da mutanen masarautar da akeyiwa surkanai , fitowa tayi a sarauniyarta sak dukda basusan itadin wacece ba amma sunyi matukar mamaki ganin yanda kayan ya amsheta ga wani irin kwarjinin da lokaci daya ta kara , manyan matan mutane masu muƙami a Dubai duk sunzo domin gabatar da al'adar saboda iya matane sukeyi . Zaunar da fanan akayi akan kujera me kyau da ado , addu'a aka farayi da gabatar musu da surkarsu Fatima kafin daga bisani aka fara gudanar da al'adun kasancewar ammu ce babba ita tafara gudanarwa, daukan sweet tayi ta bawa fanan a baki sannan ta fesa mata turare miƙa hannu ammu tayi wata kuyanga ta miko mata wani hadaddiyar box ta karba bude shi tayi , sarƙa da ɗan kunnen zinari ne me mugun tsada se daukan ido yake ta daurawa fanan akan cinya sannan ta manna mata kiss agoshi ta koma gefe , bayan ammu ta gama se matar uncle arash itama tazo tayi nata ta bata kyautan sarƙa ɗan kunne na zinari, haka akatayi har aka tashi fanan tasamu kyaututtuka sosai agajiye takoma part din ammu kuƴangu suka taimaka mata wajen cire kayan domin jinta takeyi kamar akan ƙaya aikuwa tana cire su tashiga bathroom tayi wanka hade da alwala tafito tasa abaya da hijab tayi sallah azhar ta kwanta dan tagaji sosai. Yana fada shida sarki azaad suna hira da sauran kawunan shi , kiran sunanshi yaji anyi hakan yasa yaɗago saboda yayi tsammanin daya daga cikinsu ne ya kirashi din , kallon fuskokinsu yayi yaga hirama sukeyi babu wanda yakirashi daga cikinsu karajin kiran yayi ana fadin " azaaad kafito ina waje " mikewa yayi yace musu yana ɗan zuwa tafiya yakeyi bega ko alamun wanda ke kiran nashi ba acikin masarautar hakan yasa yanufi gate fadawan dasuke wajan suka bude mishi gate suna kokarin yi mishi rakiya ya ɗaga musu hannu alamar baya bukata yayi waje , titin masarautar shuru babu kowa tafiya yakeyi har lokacin bega kowa ba wani dattijo yagani yana zaune aƙasa kayan jikinshi duk ya koɗe yarufe jikinshi da yar bargo ga kwanon baranshi agabanshi wuce shi Mr azaad yayi, sekuma zuciyarshi ta raya mishi wani abu dawuwa yayi wajan wannan dattijon yazauna kusa dashi bedamu da ya jikinshi zeyi datti kokuma wani abu ba ya ce " kaine ka ƙirani ?" batare da dattijon yaɗago kai ya kalleshi ba yabashi amsa da " nine nayi ƙira agareka " kallonshi dakyau Mr azaad yayi kafin ya ce " shin ko zan iya sanin dalilin wannan kiran " gyara bargon da yarufe jikinshi dashi dattijon yayi yafara magana " nasan kanata tambayar kanka menene abinda yake shirin faruwa dakai abisa sabon al'amarin daka tsinci kanka a ciki na jiye_jiyen maganar mutane harta da wa'yanda ba mutane ba , abinda bakasani ba shine kaidin ɗan baiwane , kana dauke da baiwar jin magana duk nisar dakuwa akayi ta zaka iyaji . Awannan ƙarnin ku uku ne kaɗai masu irin wannan baiwa kune akewa laƙabi da ' majiya ' azaad kaiɗin majiyine yau na amsa maka wannan tambayar taka" cike da zallar mamaki Mr azaad yake kallon wannan dattijon dayake mishi wa'yannan bayanan domin tabbas wani sabon al'amarin daya tsinci kanshi aciki yana damunshi sannan kullum cikin tambayar kansa yake yi menene dalilin faruwar hakan, tambayar dattijon yayi ya ce " to kaiɗin wanene? " yaye bargon daya rufe jikinshi dashi dattijon yayi fuskanshi ya bayyana fara ni ƙal ga gashi ne ajikinshi kwantacce tako ina hatta fuskantar shi akwai suma kallon cikin idon Mr azaad yayi da idonshi da ya kasance kwayar idon jane da fari ba kalar na bil adama bane ya ce " sunana tsuntsu arnass me baku bayanai akan wasu lamuranku dasukeson sarƙe muku, yanzu babban abinda yakawoni wajan ka shine magana akan sarauniyar nasminaya, wato cikekkiyar yar baiwa me dauke da karfin ikon jaaazana atare da ita. ta kasance yar baiwa ce me bada abubuwa guda biyu a rayuwar dan adam , tana dauke da baiwar taimako dakuma baiwar yaɗa farin ciki a duk inda ta zauna wannan dalilin yasa setafi kowa iya sarrafa karfin ikon jaaazana ajikinta saboda shi jaaazana baya bayan mugunta hakan ne ya sanya ya zabeta a domin baiwar da Allah yayi mata atare da ita , sarauniya fadima inharde tana waje farin ciki yana bayyana awannan waje sannan tana taimako da iya iyawarta. Abu nagaba da baka sani ba shine kungiyar BAPHOMET sun shirya ganin bayanta adoron ƙasa domin cikar muradinsu hakan yasa suka nemo wanda yakasance dan baiwa domin suyi amfani dashi wajan tarwatsata sannan su mallaki jaaazana , daga zaran sun mallaki jaaazana kuwa komai ze dagule babu me iya ceton al'ummar duniya fa ce Allah SAW, shin kokasan dawa zasuyi amfani domin cikar muradinsu?" Ya wurgawa Mr azaad tambaya idonshi cikin nasa , jikin Mr azaad yayi sanyi sosai dakyar ya iya furta kalmar" ah ah bansaniba " Murmushi arnass yayi ya ce " kaine nan " arazane Mr azaad yake kallonshi ya nuna kanshi da yatsarshi ya ce " arnass nikuma ? Me dalilin hakan ? " Cigaba da magana arnass yayi " tabbas dakai zasuyi amfani ko kana so , ko bakaso dole dakai zasuyi amfani suna nan suna shirya yanda zasu jefa maka wutar kiyayyar sarauniya acikin zuciyarka wanda hakan ne zesa duk wani sirrin abinda yake wakanan zaka dinga sanar dasu , sukuma zasu shirya yanda zasubi su sameta harsu cire narƙekken jaaazana ajikinta wanda anacireshi ta karfin tsiya dole sarauniya zata mutu su kuma zasu samu abinda suke nema bayan bukatar su ta biya zasu kashe duk yan masarautar nasminaya kasan da sa hannun waye za'a kashe sarauniya? da sa hannunka za'a kashe ta . daga bayan bukatar su ta biya zasu tarwatsa kungiyar SATANIC sekuma abu nagaba zasu kashe ka domin ka gama musu amfani sesu dawo kan al'ummar duniya su fara yaɗa zalunci su . Wannan abun da nake fada maka du ka nanda yan watanni nan zasu faruwa kuma yanzu kaine sa ransu kaine makaminsu azaaad majiyi " idon Mr azaad ya rine yakoma jaa jin irin wannan tashin hankalin dake tunkarosu babban abinda yafi daga mishi hankali shine jin dasa hannunshi za'a tarwatsa sarauniya sannan akasheta shikuma yayi alƙawarin baze taba basu wannan dama hakan yasa riko dukka hannayen arnass dasuke kamar ƙankara tsabar sanyi ya ce" arnass shin babu wani hanya da zaabi domin ganin wannan mummunar ƙudirin nasu be faru ba ? Wallahi da inbada wannan gudunmawan ganin bayan wacce nake so gwara in rasa raina " jinjina kai arnass yayi yana kara girmama wannan girman soyayyar tasu domin sudin an haifesu ne saboda junansu hakan yasa daya ze iya bada ranshi ga dan uwanshi , shafa kan Mr azaad arnass yayi ya ce" akwai hanya daya dazaabi amma hakan ze iya sawa ka rasa naka baiwar jin , se bayan shekara hudu zedawo gareka " a gaggauce Mr azaad ya ce" na amince koma miye inhar hakan zesa bazasuyi amfani da ni ba" " hakan yayi kyau azaaad inkayi hakan shine Kacika babban masoyi, yanzu anan wajan zan zare maka baiwar jinka dakake dauke dashi zantafi dashi inje in ɓoye , zaka koma yanda kake ɗa , zaka dena jin wa'yannan maganganun , hakan ze ɓata musu nasu shirin zasu dena bibiyarka domin abinda kake dauke dashi din babu. Wannan kadai ze hana faruwar wannan lamarin, amma kasani nan da yan watanni za'a tabka babban zaluncin da ze farkar da jaaazana dake jikin sarauniya awannan ranar kuma zata tafi tafiya kuma kusan na har abada " tunda Mr azaad yake arayuwarshi betaba shiga irin wannan tashin hankalin ba seyau yanayin yanda kirjinshi yake bugawa kadai mutum yaji yasan akwai babban tashin hankalin dake damunshi wasu irin zafafan hawayene suke saukowa daga idonshi , tabbas abinda zesaka jajirtacce kuma jarumin namiji kamar azaad zubar da hawaye tabbas ba karamin abu bane . Dafa kafadarshi arnass yayi ya ce " kayi hakuri azaaad kasani koda ace tafiyarta bata rabaku ba to tabbas mutuwa dake kan kowa ze rabaku " yafada mishi yana sa hannunshi atafin hannun Mr azaad ya fara magana , wani irin kananun taurarine suke fitowa daga jikin Mr azaad suna shiga cikin kwanon baran arnass , har suka shige gabaki daya cikin kwanon sake mishi hannu yayi yarufe kwanon yamike tsaye , mikewa Mr azaad yayi shima arnass ya ce mishi " daga rana irin nayau bazaka sake jin wani magana dake nesa ba nafitar da majiyi ajikinka se nan da shekaru hudu zasu dawo gareka ni zan tafi ka isarmin da sakon gaisuwana awajan jaruma , sadaukiya sarauniya, duk sanda kakeson ganina kawai ka kira sunana da izinin Allah zan bayyana nabarka lafiya " kallonshi Mr azaad kawai yakeyi saboda baya cikin yanayi najin ze iyayin magana da kowa ba , murmushi arnass yayi mishi sannan yakoma wani irin tsuntsu me ban sha'awa yafire sama. Shigowa cikin masarauta yayi duk wa'yanda suka haɗu dashi sesunyi mishi magana amma shi ina hankalinshi baya kan kowa babban burinshi shine yaje yaga fanan domin ji yakeyi kamar inyashiga zaace mishi bata nan annemeta an rasa, direct yanufi part din ammu mutane cike afalon kowa se magana sukeyi mishi amma babu wanda yakula yashiga dakin ammu akan makeken gadon ammu yasamu fanan kwance tana baccinta cikin kwanciyar hankali, hawa gadon yayi ya kwantar da kanshi akirjinta yasa hannu yarungumota tsam ajikinshi kamar za'a kwace mishi ita hawaye nazuba a idonshi , cikin baccinta datakeyi taji kamar tana jikin mutum farkawa tayi cin karo tayi da kamshin turaren shi hakan yasa tayi murmushi murya cike da bacci ta ce " habiby katashi kar ammu tazo ta ganmu ahaka" shuru yamata bece komai ba magana tasake yi mishi taga yasaketa yamike yazauna yabata baya ,tashi zaune tayi tana mutsutsuka idonunta saukowa tayi daga kan gadon tadawo gabanshi ta tsaya , tana mishi magana nan ma shuru ba amsa kanshi aƙasa, sa hannunta tayi tadago dakan nashi , bakaramin girgiza tayi ba ganin hawaye afuskanshi tallabo fuskanshi tayi hankali a tashe ta ce " habibyna menene yake faruwa dana ga hawaye akan fuskar jarumin mijina daya kasance gwarzo" nan ma shuru bece mata komai ba nan hankalinta yasake tashi nan take itama ta fara kuka tana tambayar shi abinda yake faruwa, jawota yayi yarungumeta gam kanshi akan shamulallen cikinta rungumeshi itama tayi tana kuka , dakyar Mr azaad ya iya bude bakinshi murya a kausashe ya ce " baby bazan iya rabuwa dake ba! zanshiga mugun hali inkika tafi kika barni bazan iya rayuwa batare dake aciki ba , duniyar zatamin kunci inbakya a cikin rayuwata , wifey kina tunanin zanci gaba da rayuwa mejin dadi ne idan bake ? narigada nasaba da komai naki kedin kece jigon rayuwata , duniya juyamin baya zatayi bayan tafiyarki " jin wa'yannan kalaman daga bakin Mr azaad ne yasake dagawa fanan hankali musamman idan ta tuna sun kusa rabuwa fashewa tayi da kuka na tausayin kansu , an rasa samun wanda ze lallashi wani acikinsu dago rinannun idonshi yayi yakalleta ya ce " wifey yau zamu koma Nigeria zanfi samun sauki acan kishirya yanzu zamu tafi bari inyi booking din ticket" takasa magana tsabar yanda kuka yaci karfinta se gyada mishi kai tayi raba jikinsu yayi yana kokarin barin dakin wani haske ya bayyana abdud Shakur ne da jakadiya abashiyya zubewa sukayi akan guiwowinsu suka gaida sarauniya sannan suka mike , abashiyya ce ta soma magana " kuyi mana afuwa abisa ganinmu dakukayi kai tsaye , sarauniya yakamata ayau din nan kikoma gida domin hana wani al'amari faruwa kuma bin jirgi da zakuyi ze ɓata mana lokaci kuyi musu sallama kawai mutafi " ta karishe magana kanta na kallon ƙasa, dama abinda Mr azaad yake jira kenan baya bukatar koda kara awa daya agarin yafito da waya yakira layin uncle arash yace mishi yabawa mutanen gida hakuri komawar gaggawa yakamasu suyi musu afuwa sun rigada sun tafi dukda hakan beyiwa uncle arash dadi ba amma haka yamusu addu'a Allah yatsare hanya . Bayan yakshene yake sanar da sarki azaad dakuma mutanen fada . Abdud Shakur ne yace musu su rufe idanunsu , yanda yafada haka sukayi suka rufe idonsu bayan wasu mintunan dabasu fi minti uku ba suka bude idonsu atare ganinsu sukayi acikin tsakiyar bedroom din Mr azaad, basuyi wani mamaki ba toilet fanan tashiga tayi wanka tafito kallon Mr azaad tayi dake kwance kanshi na kallon celling kaya tasaka ajikinta taya fa gyale ta ce " habiby bari inje gun ummi " Kai kawai ya gyada mata ta tafi , duk suna falo suna zaune suna yar hira motsi sukaji upstairs yasa suka maida kallonsu wajan mamaki ne yakamasu ganin fanan ce take saukowa tambayar kansu suka farayi yaushe suka dawo harta shigo falon da kallo suke binta fadawa jikin ummi tayi ta rungumeta tana fadin " nayi missing dinki sosai ummina " ummi ta ce " my feena yaushe kuka dawo?" lalubo karyan dazatawa ummi tayarda tayi ta ce " ummi dazun mukadawo dama munce surprising dinku zamuyi " sunyi farin ciki da ganinsu dama sunyi kewarsu sosai musamman fanan, rungumeta zeenat tayi tana " highly welcome anty fanan dama wallahi jinayi gidan ba dadi dabake" murmushi fanan tayi ta ce " to yanzu gani nan nadawo ai" sukayi dariya gaishe dasu anty amina da dazun zuwanta gidan saboda maganar biki itada anty shayida anty zainab bata samu zuwa ba tace se gobe zatazo , suka amsa suna mata ya hanya daga nan ta juya tagaishe dasu areef da fawwaz maido mata da gaisuwarta sukayi taƙi amsawa , kamar daga sama taji wata bakuwar murya na fadin " inayini ya hanya ?" Kallon inda maganar yafito fanan tayi wata budurwa tagani rakube awaje daya bata saki jikinta ba tana sanye da kayan zeenat se sunnar dakai ƙasa takeyi , kafeta da ido sosai fanan tayi kafin ta amsa kallon zeenat tayi ta ce " zeee aina aka samo wannan baiwar Allah" taɓe baki zeenat tayi ta ce " dazun ne Abba ya kawota wai zata zauna tare damu yatsinceta ne wasu ne sukayi kidnapping dinta daga kauyensu yanzu de yace gobe ko jibi za'a maida ita kauyensu " jinjina kai kawai fanan tayi tana sake kallon yarinyar gaba daya hankalinta be kwanta da itaba tsigan jikinta ne taji yana tashi , tambayar ta tayi "meye sunanki ?" ta ce " sunana maryama" tunda ga nan fanan tasamu waje tazauna bata sake cewa komai ba amma hankalinta na akan maryam din domin tanajin wani abu dangane da ita . Anty shayida ce ta ce " mash Allah mutanen turai, feena gaskiya turai ya karbeki kinyi fresh sosai " dariya sukayi sannan suka fara hira , saukowa Mr azaad yayi yana zuwa ya rungume umminshi kawai bece mata komai ba tunda taganshi haka ummi tasan akwai wani abinda yake damunshi shafa kanshi ummi tayi yazagayo yazauna kusa da ita , gaisheshi sukayi babu wanda yacewa ƙala acikinsu suma ganin haka suka san yau he's not in a good mood gaisheshi Maryam tayi jin bakuwar murya yasa Mr azaad yakalleta nan take yaji hankalinshi be kwanta da itaba yadaka mata tsawa " ke daga gidan ubanwa " rawa jikin Maryam ya soma tafara hawaye ummi ce ta ce" haba son meyasa kake haka " kwantar da kanshi yayi akan kujera besake tanka musu ba . Anty amina ce ta ce " yawwa anty shayida nunamin hotunan dake wayar naki na akwatunan " anty shayida ta ce " bari indauko wayar tana daki " tafada tana kokarin mikewa fanan ta ce " anty shayida zauna bari indauko miki " " to feena" harta kusa barin falon Mr azaad yaɗago ya kalleta ya ce " ina zakije?" langwabar da kai tayi ta ce " waya zandaukowa anty shayida" kamar zece mata tadawo tazauna zeje da kanshi sekuma ya gyada mata kai , bin bayanta Maryam tayi da kallo seda takusa hayewa stairs din karshe Maryam ta motsa bakinta yanda babu wanda yalura da ita, tsantsine yakwashe fanan ta sake karfen stairs din tafara gangarowa tundaga can stairs din farko ƙara tasaka wanda yajawo hankalinsu, tashi tsaye sukayi gabaki dayansu suka nufa wajanta ganin yanda take gangarowa daga bene da mugun gudu Mr azaad ya isa kan benen tana kokarin fadowa daga na karshe yasa hannu ya tallafota , hankalinsu yayi mugun tashi , kanta yafashe yana fitar da jini , rufewa idonta yake kokarin yi Mr azaad yasa hannu yana jijigata dakyar ta iya bude idonta ta ce " habiby zan mutu " tundaga wannan kalmar tadauke wuta cak tadena numfashi kuka zeenat tafashe dashi ta daura hannunta akai jawota fawwaz yayi yarungumeta da shima hawayene yake zuba a idonshi ummi kam ɗurƙusawa tayi agaban fanan takasa koda motsine anty amina da anty shayida duk kuka sukeyi harda areef kuka sukeyi yau sunshiga matsanancin tashin hankali, ummi ce ta ankara da jinin dake bin ƙafan fanan kamar wanda aka kunna famfo, da karfi ta ce " fawwaz dauko motar tana zubar da jini " duk kallon inda ummi take kallo sukayi jini ne bana wasa ba yakebin ƙafan fanan, daukanta cak Mr azaad yayi bedamu da jinin dake ɓata mishi jiki ba, be jira kowa ba yasata a back seat yatada motar, horn kawai yake dannawa da gudu baba me gadi yabude gate yafisgi motar kamar zasu fire sama , bin bayanshi su ummi sukayi , anty shayida da anty amina suna motar areef ,ummi da zeenat kuma suna motar fawwaz, gudu kawai Mr azaad yake yi akan titi motoci duk wa'yanda suka ganshi yanufo su hanya suke bashi , hakama fawwaz bin bayanshi sukeyi saboda karya ɓacewa ganinsu , horn yake dokawa abakin gate din medical center, ko kyawawan packing beyi ba yafito yadauketa , nurses naganinshi suka nufoshi da gadon daura mara lafiya kwantar da ita yayi , ya tayasu turawa manyan doctors ne suka rufa musu baya domin tun shigowar su suka ga Mr azaad ne shisa ba wasa suka shiga da ita emergency room yana kokarin shiga dakin suka bashi hakuri akan yajirasu awaje suka rufe kofar emergency room din suka rufu akan fanan domin bata taimakon gaggawa, jikinshi duk yabaci da jini amma bata shi yake ba ta matarshi yakeyi jirine yaji yana kokarin yada shi fawwaz da shigowarsu yanzu kenan yarikoshi suka zauna akan kujerun dake wajan , yau abubuwa sun hadu sunyiwa Mr azaad yawa ji yakeyi duniyar baya mishi dadi yanzu damuwarshi shine fanan tafito daga cikin hatsari. duk jugum_jugum sukayi kowa addu'a yakeyi aranshi zama ummi tayi kusa da Mr azaad, kwantar da kanshi yayi akan kafadarta murya na rawa ya ce" ummi duk wannan laifina ne daban barta taje ba da hakan be faru da itaba am at fault ! laifina ne" anty shayida dake kuka ta ce" azaad wannan ba laifinka bane ,laifin ne danaje nadauko wayata da kaina " shafa kanshi ummi takeyi takasa lallashin sa itakanta tana cikin tashin hankalin da zataso a lallasheta , kirane yashigo wayar zeenat tsabar tashin hankalin datake ciki up side down ta manna wayar akunnenta murya Abba taji yana tambayar ta suna ina dan yadawo gida ake sanar dashi abinda yafaru , goge hawayen da yazubo mata yayi ta ce " muna medical center" katse Kiran yayi . Layin suhaima zeenat takira tasanar da ita abinda yake faruwa cikin tashin hankali suhaima takira ya ya usman tafada mishi , suhaima tayi kuka sosai babban takaicinta shine bata Gombe tana Bauchi. Kusan atare Abba,baba,mama,anty firdausi,anty zainab,ya usman da hairah , yaseer , Amira da hajiyarsu suka shigo asibitin ko wannensu hankali atashe ko nutsuwar gaisawa basu samuyi ba duk zama sukayi kowa na jiran fitowar doctors. Bude kofar doctors din sukayi suka fito suna goge gumin fuskansu tasowa sukayi sukayo kan doctors din suka fara tambayar su ya fanan din take, shuru sukayi , tunzura Mr azaad sukayi afusace yashake wuyan dayan doctor din da karfi ya ce " kafadamin meye yasamu matata ?" Ganin Mr azaad na kokarin yin kisan kai ne yasa duka mazan wajan suka fara kokarin raba Mr azaad da doctor din, dakyar suka ɓanɓare hannun Mr azaad awuyan doctor din , rike wuyarshi doctor yayi yana fitar da numfashi da kyar zillewa yayi yabar wajan dan yaga Mr azaad ze iya hallaka mutum . Wani doctor ne ya ce " ku kwantar da hankalinku ! tafito daga cikin hatsari tana cikin koshin lafiya se abu nagaba babyn dake cikinta ma lafiyarshi klau babu abinda yasameshi....... Comments and share fisabilillahi 🙏 Read more 10 to 11 is not easy 😢 inajiran comments dinku. Se gobe inme duka yakaimu da rai da lafiya. https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 ( Yar lelen Jarumai) 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚 ⚜️📚J. W. A 📚🖋️ Gargadi Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe daga cikin book din nan ba ta kowani siga ko a karanta minshi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira koda Allah nabar mutum ze sakamin yabimin hakkina. Three paged in one PAGE 6️⃣1️⃣ Godiya sukayi wa Allah jin daddadar labari biyu a lokaci daya,ga labarin tana tafiya tafito daga hantsari ga kuma labarin cikin da take dashi kuma alhamdulillah abinda ke cikin na lafiya , sujjada Mr azaad yayi yana godewa Allah , mika mishi hannu doctor yayi ya ce " congratulations natayaka murna sosai" dayan hannunshi Mr azaad yasa a aljihun wandonshi daduk riga da wandon sun ɓaci da jini yafito da key din motar da sukazo dashi sabuwar Benz yau yafara amfani da ita daze kawo fanan asibiti ya ce " ga goron albirshir dinka dakamin " karban key din doctor yayi murna kamar ya kashe shi yama rasa ina zesa ranshi godiya kawai yake kwararawa Mr azaad, kowa awajan nan yana cikin farin ciki dangane da abinda sukaji doctor yafada yanzu jira sukeyi afito da fanan din , se anan ne suka samu nutsuwar gaisawa , Abba ne yakalli Mr azaad ya ce " azaad Yakamata kaje gida kayi wanka ka canza kayan nan kaga yanda yabaci da jini " " no abba bazan tafi yanzu ba se anfito da wifey" yafada yana zama , gaba daya tausayinshi ne yakamasu, saboda yana fuskantar kalubale musamman ma idan fanan ta tafi , se bayan 20mint aka fito da fanan dake kwance tana sanye da rigar asibiti kanta daure da bandeji hannunta an daura mata ruwa , fuskanta yayi fayau za'a kaita resting room mikewa Mr azaad yayi yabi bayansu zuwa room din, jawo kujera yayi ya ajiye agaban gadon nata , yarike hannunta yana kallon fuskanta murya adashe ya ce " am sorry wifey! kiyafemin laifina ne wannan" jakadiya abashiyya dake kallonsu ta dafa kafadarshi dagowa ya kalleta murmushi tayi mishi kafin ta ce " azaad wannan dalilin ne yasa nace kuyi gaggawan dawuwa gida saboda badan fanan ta tashi ba to wannan abun akan shayida ze faru , daga nan kuma zata rasa yaran dake cikin cikinta idan hakan yafaru Allah ne kaɗai yasan halin da shayida zata shiga, sarauniyarmu akoda yaushe ita tana taimako, abinda yafaru yau Allah yariga da ya rubuta haka daga kai har shayida kudena bawa kanku laifi " idonshi yayi ja sosai girgiza mata kai yayi kafin ya ce" abashiyya amma yanda tarasa jini sosai nayi tunanin zaace ana bukatar jini amma ga shi da ikon Allah ta dawo hayyacinta " abashiyya ta ce" eh tabbas tarasa jini sosai amma kasani sarauniya ba kamar sauran mutane ba ce , nan da anjuma zata farka gobe kuma zasu sallameku " sosai abashiyya tadinga kwantarwa Mr azaad hankali haryaji wani ɗan damuwar dake damunshi yadan ragu suna cikin tattaunawa, su ummi duk suka shigo ciki har a lokacin abashiyya na tare da Mr azaad amma babu wanda yake kallonta se shi kadai kawai,duk zama sukayi ummi tazauna agefen gadon fanan ummi ta ce " yaseer kadauki son kuje gida yayi wanka " " to ummi" yafada yarike hannun Mr azaad tashi Mr azaad yayi badan yaso ba , bayaso yayi nisa da ita fita sukayi shida yaseer din duk bayanshi sukabi da kallo ganin yanda yake tafiya cikin sanyin yanayi . Ahanzarce yayi wanka yashirya yafito yasamu yaseer afalo ya ce " dude mutafi nagama " riko hannunshi yaseer yayi ya zaunar da shi ya ce " dude calm down please ka kwantar da hankalinka fanan yanzu na cikin koshin lafiya, yanzu ka tsaya ka sa wani abu a cikinka " ajiyar zuciya Mr azaad yasauke ya ce " banida lokacin wani cin abinci yanzu kawai mutafi karka ɓata min rai" yanda yaga ya haƙiƙice sesun tafi yasa cikin sauri ya shiga kitchen ya dauko mishi yogurt yabashi ya ce " dude ɗan Allah kayi hakuri kasha wannan se mu tafi kaga kai kanka yanzu baka cikin yanayi me kyau kamar fah zaka fadi " ganin yaseer baze barshi su tafi ahaka bane yasa ya karbi yogurt din yabude yakafa abakinshi seda yashanye tas yayi cilli da goran sannan ya ce " yanzu zamu iya tafiya ?" Yar murmushin yaseer yayi at least yasamu Mr azaad yasa wani abu a cikinshi ya ce " to muje " gaba Mr azaad yayi yabarshi abaya saukowa sukayi dede zasu fita a falon ya hangi maryam rakube abayan kujera , " keeee" yafurta yana tsaye yariƙe kugu yaseer kuma na gefenashi yanason ganin wayake ƙira fitowa tayi daga lungu kujerun jikinta na rawa ta ce " naaam" watsa mata harara yayi ya ce " karki yarda in dawo gidan nan in sameki " yana gama fadin haka yafice kare mata kallo yaseer yayi fuskanshi adan hade yabi bayan Mr azaad motar suka shiga yaseer yafara driving hankalinshi nakan titi ya ce " dude wancan yarinyar daga ina ? wallahi kallo daya na mata naji hankalina be kwanta da itaba, kamar wata mara gaskiya" kwantar da kanshi Mr azaad yayi akan seat din motar ya ce " nima haka dazun bayan dawuwarmu naganta agidan kallo daya na mata naji na tsaneta , banason ganinta jikina na bani kamar akwai abinda yakawota gidanmu " dukan siterin motar yaseer yayi ya ce" exactly wallahi dude dole abinciki yarinyar nan kasan yanzu duniya ba yarda ,bakowa ne zaka yarda dashi ba daga baya seka taimaki mutum yazo ya cutar dakai " sake maimaita maganar yaseer Mr azaad yakeyi acikin ranshi se yanzu ne ma yafara zargin wannan yarinyar tabbas akwai abinda yakawota gidan, zarginta yafara abisa abinda yafaru da fanan tuna maganar abashiyya yayi na kancewa abin akan anty shayida yaso faruwa sekuma fanan taje amaimakonta tabbas akwai wani abinda ba dede ba , haka yadinga tunani har suka iso asibitin, shiga cikin resting room din sukayi suka samu abba da baba basa nan , da sallama dauke abakinsu suka shigo mikewa Amira tayi ta bashi kujeran gaban gadon fanan zama yayi yariƙe hannunta yana kallon fuskanta, mama kam kunya ne ya kamata se kawar da kanta gefe takeyi saboda rike hannun fanan da Mr azaad yayi,ummi ta lura da haka murmushi tayi aranta ta ce " kunyan fanan ashe ga do tayi " karban wayarta tayi ahannun zeenat dake zaune waje daya tayi tagumi tazubawa fanan ido , kiran layin gida ummi tayi abu me aiki tadauka sanar da ita tayi girki sukawo itada driver asibiti tayi sannan ta katse kiran. Kiran sallah la'asar akayi mazan suka tafi masallaci matan kuma sukayi acikin dakin bayan sun idar suka zauna a lokacin mazan duk sun dawo . Kusan atare anty firdausi tadawo hannunta rike da katon basket na abinci daddyn junior kuma na rike da junior haka abu me aiki itama hannunta rike da basket din abinci gaishesu abu me aiki tayi tana tambayar yame jiki suka bata amsa da sauki sannan ta zauna . Kowa sa mishi abinci akayi yanaci amma banda mama da Mr azaad dake zaune yana rike da hannun fanan. Bayan kamar awa daya lokacin har biyar yayi hannunta dake cikin nashine yaji yana motsawa maida hankalinshi yayi kan hannun yaga yana motsi , ahankali tafara ware idanunta da tajisu sunyi mata nauyi kamar ba nata ba hasken dataci karo da shine yasa tamaida idon ta rufe sake jarraba bude su tayi nan tafara gani dishi_dishi , akan kyakkyawar fuskar Mr azaad tafara bude idonta da shima itadin yake kallo murmushi yamata itama tamayar mishi tana kokarin mikewa rungumeta yayi ajikinshi sannan yazaunar da ita , ya sa hannu yashafa gashinta ya ce " alhamdulillah wifey thank god you're awake" yagama magana yana manna mata kiss agoshinta , ganin ta farka ne yasa sukayi hamdala suna godewa Allah rike hannunta ummi tayi ta ce " my feena ya jikin naki ?" Muryanta da dan karfi saboda ta tashi taji jikinta da karfi kamar babu abinda yake damunta sedan ciwon kai kadan ta ce " da sauki sosai ummina " haka suka dinga mata ya jiki hairah da zeenat Amira duk dawuwa kusa da ita sukayi suka zauna kallon mama fanan tayi ta ce" mamaana " murmushi kawai mama tayi ta ce" na'am fanan ya jikin naki ?" " Dasauki mama " motsa hannunta dake cikin na Mr azaad tayi amma yaƙi sakinta shi babu ruwan shi bedamu da mutanen da suke cikin dakin ba . Hairah ce ta kalli zeenat ta ce" anty zeenat ina ya hafiz ?" Kafin zeenat tayi magana ma areef ya rigata da" hafiz na makaranta yanzu hakama maybe ko sun tashi kokuma sun kusa tashi " jin ya'yan nata na makaranta yasa bata sake cewa komai ba. Kamar ba mara lafiya ba haka ta sake anata hira da ita duk sunyi farin ciki da ganin condition din nata is not critical, shide Mr azaad ƙala bece ba se aikin kallon yanda fanan take hira yakeyi yana jin dadi aranshi ɗan dawani abu yasameta besan yazeyi da ranshi ba . Se yamma liris hafiz yadawo gida driver nayin packing yafita rike da school bag dinshi da laptop yashiga cikin main falo babu kowa gidan shuru beyi tunanin babu kowa ba yawuce part dinsu yashiga bedroom dinshi ya ajiye school bag din da laptop akan table yashiga toilet wanka yayi yafito yashirya yadau wayarshi acikin locker dan inze tafi makaranta ajiyeta yakeyi dukda makarantarsu makarantar masu kudine yara suna abinda suka gadama amma shi barin waya yakeyi agida saboda karatu ne yakaishi beze yi abinda wa'yanda suka taimaki rayuwarshi zasuji ba dadi ba. Part din ummi yashiga ze gaisheta yayi ta sallama a bedroom yaji shuru ba amsa se ya dawo main falo kawai yazauna yana danna waya , motsi yafaraji abayan kujera beyi tunanin komai ba yatashi ya leka bayan kujeran ganin mutum yayi tana zaune ta rakube mamaki ne yakama hafiz dan yasan shide be santa ba amma daga ina take to ya ce " sannunki" kallonshi Maryam tayi ta ce " inayini " be bata amsa ba se tambayar ta dayayi " me kikeyi anan ?" Inda_inda ta fara " uhmm ina zaune ne " "okay to kifito abayan kujera wani inya ganki ahaka zeyi tunanin bakida gaskiya ne " yafada yakoma inda yake yazauna besake bin ta kanta ba yaci gaba da danna wayarshi. Alamun mutum yaji tsaye akanshi hakan yasa yaɗago kai , kallonta yayi tsaye akanshi tana kallonshi haɗe fuska hafiz yayi dan ta bashi haushi ya ce" ke meye haka zaki tsayamin akai bakisan babu kyau ba " wani irin munafikin murmushi maryam tayi batace mishi komai ba , kuma bata tashi mishi akai ba ganin hakane yasa yatashi akan kujeran dayake ya koma wani yaci gaba da abinda yake yi sake tsayawa tayi akanshi , kallonta kawai yayi bece komai ba yadauki wayarshi yabar falon yahaura upstairs kamar daga sama yaganta agabanshi ja da baya yayi ɗan yadan tsorata saboda yasan afalo yabarta maida kallonshi yayi fallon yaga tana nan a inda yabarta sannan yakalli wacce take gabanshi addu'a yafarayi acikin zuciyarshi kafin ya ce " meye kike bukata awajena ? Meya kawoki wannan gida?" Murmushi tayi mishi kafin ta ce " abinda nake buƙata awajanka shine ranka , abinda yakawo gidan nan kuma shine kashe duk wani wanda yake cikin wannan ahalin " duk adan tsorace hafiz yake amma afusace ya ce " Allah baze taba baki nasara ba , kuma nima bazan bar hakan yafaru ba sede koke koni! Koki kasheni ko ni in kasheki" dariyar bosawa tayi harda rike ciki ganin yanda yake da karfin hali kyasta yatsunta tayi nan take kayan jikinta da ita kanta ta sauya, fara ce sol tana sanye da bakaken kaya ,matsetsen riga da wando baƙi jikin riga da wandon akwai chains , ga uban hills shima baƙi , gashin kanta brown color ne curly bakinta yasha baƙin janbaki , shiganta da komai nata na yan America ne , ja baya yakeyi tana biye dashi ta ce " zamu gani yau kaiɗin jarumine ko kuma ragone " juyawa hafiz yayi yana neman abinda ze buga mata mopper ya hango yadauko ya buga mata akanta nan take mopper ya karye sake ja da baya hafiz yayi ya ce " to ke din wacece ? meye mugun nufin ki akan mu?" Hannunta ta mika nan take yayi tsayi tashaƙo wuyar hafiz ta dagashi sama kafin ta ce" okay tunda abinda kake so ka ji kafin ka mutu , sunana Jessica kelvin " tana fadar haka ta kara shaƙe mishi wuya sannan taje can saman upstairs tana shirin wurgoshi ƙasa, kallon ƙasa hafiz yayi yaga irin mugun nisa dayake dashi da ƙasa yasan tabbas ta wurgoshi mutuwa zeyi hakan yasa muryarshi da baya fita sosai saboda shaƙeshin datayi ya ce " hairahhhhhhhhhh" dariya tayi ta ce " itakuma wacece haka shin kana ganin zata ceceka ne ?" . Suna zaune suna hira lokacin su Abba da baba ma sun dawo suna cikin dakin , zuruf sukaga hairah ta mike jikinta ne yadau rawa , ko wannensu da al ajabi akan fuskokinsu suke kallonta, zubewa tayi aƙasa jikinta na ci gaba da rawa mikewa dukkansu sukayi suna tambayarta meya faruwa amma ba ta basu amsa ba ya Usman yasa hannu yadagota yazaunar da ita akan gadon fanan yana mata magana " hairah meyake damunki ?" hawaye takeyi jikinta na tsuma , fanan ce ta ce" kowa yanda yi shuru na wasu lokuta " mikawa hairah hannunta tayi duka biyu , daura hannayen hairah tayi da nata hannun lokaci daya jikinta yadena rawan dakyar ta iya cewa " yayana ! Zata kashemin yayana " fanan ta ce "ki fadamin meye kike kallo " ta ce " na naganta itadin makira ce kuma mara imani " sake matse hannun fanan tayi ta cigaba da magana " ta shaƙe yaya hafiz zata wurgoshi ƙasa daga upstairs" jin abinda tafada ya tsorata su de yanzu suka tuna da babu kowa agidan dasauri fanan ta ce " su waye agidan bayan hafiz din sannan akan waye kike magana?" Hairah ta ce " babu kowa agidan securites ne dasuke cikin compound babu wanda yasan abinda yake faruwa , yayana kuma ita da shine acikin falo yanzu haka tana gab da wurgoshi ƙasa" tana gama fadin haka Abba dasauri yazaro wayarshi yakira number securites din gidan nan take suka daga yasanar dasu abinda yake faruwa , kusan su ashirin suka shiga cikin falon lokacin da Jessica ta gansu dariyar mugunta tayi sannan ta ajiye hafiz a ƙasa shafa wuyanshi yayi yana tari ganin tana gangarawa downstairs ne yasa yafara rarrafawa yasulale yashiga part din Mr azaad daga nan ya bullo ta garden sannan yafito compound baba me gadi ne kaɗai se driver suka rage acikin gidan dakyar ya iya kwalawa driver kira suka shiga motar yace mishi yakaishi gun ummi da gudu driver yafisgi motar . Gangarowa ƙasa Jessica tayi ta tsaya a tsakiyarsu wani daga cikinsu ne yafara tunkaronta duka daya ta mishi yazube aƙasa yasuma , dukansu takeyi baji ba gani kaff dinsu kaff seda ta sumar dasu da muguwar duka , sannan ta fito compound tunda baba me gadi yaganta yaji tabashi tsoro tunkafin ta ce yabude mata kofa yabude . fita tayi tana kallon titin daya kasu gida uku nan take tagano hanyar da su hafiz sukafi ,gudu tafarayi tana ɓacewa kamar walkiya tana bin bayansu . Hairah dake rike da hannun fanan tana kallon duk abinda ke faruwa a falon ta ce " dukkansu tamusu duka sannan ta sumar dasu , yayana kuma yanzu haka yashigo asibitin nan tana binshi abaya " tana karishe maganar da takeyi tasake hannun fanan, ta mike tsaye , tana magana da hafiz dake gudun ceton ranshi domin har cikin asibitin ta biyoshi mutane se kallonta sukeyi kamar sun samu tv , yana gudu itakuma tana tafiya cikin kwanciyar hankali. Gudu yakeyi yana hakki yana jin kwantaccen da hairah takeyi mishi can yace " hairah naga wasu kofofi gudu biyu wanne zanshiga wanne ne kuke ciki ga ta nan abayana" tsayawa hairah tayi abakin kofa ta ce " na farko zaka shigo yaya " sude al'amarin ya matuƙar girgizasu tunani suka farayi suna tambayar kansu shin hafiz da hairah sudin su waye ?. Da karfin gaske ya turo kofar yarungume hairah dake tsaye abakin kofa, fashewa tayi da kuka tana " yayana " suna a haka Jessica tashigo dakin ja da baya sukayi dagudu hairah taje ta buya abayan mama shikuma hafiz ya boye a bayan Mr azaad harde hannunta tayi akirjinta tana kallonsu kamar yanda suma ita suke kallo seyanzu suka gane ashe Maryam din da Abba yatsinto ce innalillahi wainna ilaijiraji unnn lallai duniya babu yadda aciki se ka taimaki mutum yazo ya cuceka shisaka yanzu taimako yayi karanci , zuciyar Abba se kuna yakeyi yana kallon Maryam yama kasa magana amma har cikin ranshi beyi danasanin taimaka mata da yayi ba domin shi tsakani da Allah yataimaka mata , kallon Mr azaad tayi ta ce " ka turo yaron bayanka ko kuma ta sanadiyyar shi kowa na dakin nan ya rasa rayuwarshi , mugun kallo fanan da Mr azaad suke watsa mata, ganin beze miko mata shi bane yasa taje gaban Mr azaad din tasa hannu zata jawoshi Mr azaad yakai mata damka a wuya sannan ya dagata sama ya hade kanta da jikin bangon dakin ta zube aƙasa, daman haushinta yakeji domin yanzu yasake tabbatarwa Ita ce nan ummul aba isin abinda yafaru da fanan tana kokarin mikewa daga bugun datasha Mr azaad ya taka ruwan cikinta so yakeyi kawai yaga ta mutu ko hakan ze rage mishi raradin abinda yakeji , sa hannu yayi ya sake damko gashin kanta , ɓacewa tayi ta dawo bayanshi ta ce " kana tunanin zaka gwada min kai jarumine hahaaa" tafada tana dariya nuna anty shayida ta yi da hairah da hafiz ta ce " dake , dake dakuma kai duk sena kasheku ayau din nan " a tsorace anty shayida ta je taboye akusa da Abba . Baba ne ya ce " baiwar Allah menene hadinki damu ? wani laifin mukayi miki ne ?" Abba ya kalli baba yace " ni ne nan nakawota gida da niyar taimaka mata ashe annoba nadauko bansaniba" Maida kallonta kan baba tayi ta ce " babu abinda kukayi mini nidin yar saƙoce nazo gudanar da abinda aka aiko nine " ummi ta ce " to waye ya aiko ki wajen mu " fanan da ranta yayi matuƙar ɓaci ne ta ce " yi shuru ummina kar wanda yasake ce mata ƙala yanzu zatayi da nasanin zuwa aikan da aka mata " tana magana tana zuro ƙafafuwan ta kasa mikewa tayi tsaye tana bin Jessica da kallo dama tun farkon ganin da ta mata taji tsanarta lokaci daya ashe akwai dalilin haka, tunkaro fanan tayi tana kallonta daga sama har kasa cikin shakiyanci ta ce" oho nagane wato ke ce sarauniya? Amma yanaga bakiyi kama da sarauniyar da kowa yake shakka ba yanda ake labarin ki se naga ba haka kike ba , kinmin kama da matsoraciya sede balaifi kinada kyau kam, dukda bake nazo kashewa ba wancar me cikin nazo kashewa sekuma kema kina da ciki sekiyi kokarin taimaka mata ta hanyar zuwa a madadin ta , hakanma ba laifi tunda kema kinada cikin " tayi magana tana kallon anty shayida dake bayan Abba ,murmushi fanan tayi ta ce" kwantar da hankali, ai gane asali ba daga fuska take ba se angwada ake ganewa . shin kinason ganin asalina? amma fa kisani in kika gani ba lallai ba kici gaba da rayuwa ba " cewar fanan da idonta yakoma kalar fari tayi magana tana damkar wuyan Jessica kokarin kwatar kanta Jessica tafara tana fisge_fisge amma takasa kwatar kanta a hannun fanan, matso da fuskanta fanan tayi daff dana Jessica,sannan ta zaro idonta da suka koma fari tass babu digon baƙi aciki , hasken cikin idonta ne yafara shiga cikin idon Jessica nan take tafara konewa ta ciki ihu tafarayi . Fanan ta ce" nasan zaki bawa wa'yanda suka aiko ki labari inkun hadu a lahira " tana gama fadin haka tasake Jessica ta fadi ƙasa nan take jikinta yafara karkarwa kamar wacce aka jonawa shocking jikinta nafitar da hayaƙi me tururi haka tadingayi har ta koma kwarangwal daga nan kuma takoma toka tabace. Dukkansu ajiyar zuciya suka sauke ganin sun rabu da ita , jinjina mata zeenat dake ɓoye abayan mama tayi ta ce " aikin ki na kyau anty fanan" hararanta fanan tayi ta ce " kema naki nakyau saboda kin iya ɓuya kam " dariya sukayi . Kallon hafiz fanan tayi ta ce " lallai hafiz kaiɗin jarumine kayi na mijin kokari " hafiz da se yanzu hankalin shi yakwanta ganin fanan ta gabama da Jessica yayi murmushi kawai yaje bayan mama yariko hannun hairah suka zauna akusa da ya usman ya ce" fatan babu abinda yake damunki " kai ta gyada mishi sannan ta kwantar da kanta akan kafadarshi , sude yanzu tunda sun samu sun rabu da Jessica damuwar su susan su hairah sudin menene suke dauke dashi koɗe karya sukayi musu adangane da asalinsu. Babane ya ce " hafiz shin ya akayi kuke iya magana da junanku batare da waya ba kuma hairah take iya ganinka aduk inda kake ? " Ajiyar zuciya hairah da hafiz suka sauke atare domin sun san dama dole sesunyi zargin wani abu , hafiz ya ce " mahaifinmu yakasance babban wanzami ne dake taimako sosai kuma yana bada magani , yana aiki da aljanu to tun muna yara wata rana yadawo gida da daddare muna bacci yasa mamanmu ta tashemu , zama mukayi agabanshi ya ce " hafiz ga hairah kanwarka ce ko bayan ranmu nasan zaka iya kula da ita " sannan ya yafito da wasu abubuwa acikin leda wanda nida hairah bamu san meye aciki ba, sunce ledar yayi nan take mukaga wasu abubuwa guda uku biyu masu zubi da kunne daya kuma kamar ido , miƙa min kunnen yayi yace in rike shi da karfi sannan yabawa hairah ido da hannu ya ce itama tarike, bamufi mintuna 30 da rikewa ba muka nemi abubuwan mukarasa domin ji mukayi babu su ahannun namu ashe cikin jikinmu yashige , se babanmu yace mana wannan abinda yabamu shine zezama garkuwa garemu duk nisar duniyar damuke zamu iya magana da junanmu sannan hairah zata na kallona inde wani mugun abu ze faru ne kaɗai hakan ze kasance, tundaga wannan lokacin in waninmu yana cikin hatsari mukan iya jiyowa har musamu wa'yanda zasu taimaka , wannan shine " shuru sukayi suna jinjina wannan lamarin ta wani bangaren za'a iya cewa hakan ze taimakawa yaran amma ta tawani bangaren hakan tsubbu ne tunda bawai dashi aka haife su ba rana tsaka yasaka musu shi ajikinsu , abba ne ya ce" Allah yajikansu da rahama " suka amsa da ameen. Washe gari doctors din ganin jikin fanan da sauki sosai yasa ya rubuta mata sallama , sungama kimtsawa mazan suke jira su shigo su tafi wa'yanda suka kwana da fanan ummi ce se anty shayida , su mama tun jiya bayan mangrib suka koma gida zeenat kuma Abba ne yacewa Mr azaad da fawwaz su maida su gida , Mr azaad da yaseer suka shigo cikin asibitin ga securites suna binsu abayana rike da manyan kwalaye yaɗuwa yayi da doctor din yabashi result din fanan, shiga cikin resting room din sukayi suka bar securites din suna rabawa majinyata da kuma nurses din asibitin kudi kamar yanda Mr azaad ya sanar da su , duk wani wanda yake cikin asibitin seda yasamu dubu dari dari , haka suka dinga kwararowa Mr azaad da family shi adduo'i , saboda awannan lokacin kafi karfin abinda zakaci arana daya ma ka godewa Allah gashi yau sun samu wani bawan Allah yaraba musu kyautar dubu ɗari _ɗari babu abinda zasu gode masa dashi sama da addu'a. Tana zaune akan gadon ta sanya doguwar rigar atamfa kanta ba dankwali saboda bandejin dake kanta ummi ce tahaɗe mata gashin tadaure mata da ribbon zama yayi akusa da ita yasa hannu yana ɗan taba kan nata kaɗan gaisheshi tayi shida yaseer, amsawa yaseer yayi sannan yamata yajiki , Mr azaad be amsa mata gaisuwar da ta mishi ba ya ce " wifey ya jikin naki " kallon ummi tayi taga hankalinta ba'a kansu yake ba tana magana ne da yaseer, ta ce " jiki alhamdulillah" tashi sukayi da niyyar tafiya rike hannunta yayi ya mikar da ita tsaye sannan yadau gyalen da ya gani akan gadon ya rufe mata ajikinta, gaba su ummi sukayi shikuma yana rike da ita suna baya , duk inda suka wuce se jama'ar asibitin sun mishi godiya tare da sa mishi albarka haka suka shiga motoci suka dau hanyar gida , bayan sun isa ne , duk afalo suka samu su zeenat suna zaune suna zaman jiransu tashi sunayiwa fanan ya jiki ta amsa musu fuska asake wucewa da ita Mr azaad yayi zuwa part dinshi basu tsaya a ko ina ba se a bedroom dinshi zaunar da ita yayi akan gadon ya zauna akusa da kwantar da kanta tayi akan kirjinshi tana shaƙar kamshin turarensa , " habiby inasanka sosai" kallonta yayi da sexy eyes dinshi yace " wifey! inasanki bantaba tunanin aduniyar nan akwai macen da zanso har inyi rayuwar aure da ita ba se akanki Allah yadoramin sanki banajin zan iya rayuwa batare dake ba, inasonki sosai da ke dakuma unborn baby mu " dagowa tayi dasauri ta kalleshi da alamar tambaya ta ce" habiby bangane abin kake son fadamin ba ! what do you mean by our unborn baby?" daura hannunshi yayi akan shamulallen cikinta da babu alamun akwai ɗa aciki ya ce" yes up course baby kina dauke da ciki , kinadauke da jinina acikin ki munkusa zama parents, bazan iya misalta irin farin ciki da nake ciki ba " hawaye ne yafara wanke mata fuska da mamaki yake kallonta ganin daga fada mata tana dauke da ciki tafara hawaye gabanshi ne yafadi tsoronshi daya kar fanan ta ce batason cikin dake jikinta, riko hannayen ta yayi suna fuskantar juna ya ce" baby why are you crying?" rungumeshi tayi gam cikin muryan kuka ta ce" habiby kukan farin ciki nakeyi , nima yau ina dauke da baby acikina alhamdulillah zanji abinda iyaye sukeji insuna da juna biyu. habiby babban farin cikina shine zantafi in bar muku abinda zaku kalla kuji sanyi aranku , ko bayan raina nasan nabar iri aɗoron ƙasa " shi yanzu babu abinda ya tsana sama da yadinga jin maganar tafiyanta hakan daga mishi hankali yakeyi se yaji kamar shima yabita kome ze faru ya faru shafa bayanta yakeyi ya ce" kidena fadar haka ko so kike kidinga dagamin hankaline , yanzu lokacin farin ciki ne ba lokacin bakin ciki ba Please ki bari " raba jikinta da nashi tayi ta aro murmushi ta yaɓa wa fuskanta ta ce" am sorry my love bazan sake ba , yanzu fadamin wata nawa ne babyn ?" fito da result din da doctor yabashi yayi ya bude duk sun nutsu shida ita suna karantawa sosai sukayi mamaki ganin cikin wata hudu ne dede, su duk tunanin su karamin cikine da be wuce one month ba ganin yanda cikin nata yake a shamule babu alamar akwai ɗa acikinsa " laah habiby cikin wai wata hudu amma kalli cikina " tafada tana daukan hannunshi ta daura cikinta shafa cikin yayi yaduƙo da kanshi dede cikin ya mannawa cikin nata kiss shafa kanshi tayi tana murmushi ta ce " father to be " yar dariya yayi ya ce " yes yakamata ko da yaushe mahaifi yadinga jin lafiyar ɗan sa " cike da so da kaunar juna suke ta hira . Bayan kwana biyar da sallamota anty amina ta kawo me gyaran amaren part din mommy da ba kowa aciki aka gyara aka fitar da kayan tsafinta aka konasu, aka bar musu part din anan zasuyi komai dinsu aciki zeenat ce ta fara dawuwa aka fara mata ta , anty amina tace fanan ma itama amaryace harda ita tare aka fara musu ita da zeenat. Suhaima tadawo gombe saboda baba ne ze aurar da ita , anty amina ce tazo har gidan ta roƙi alfarma awajen mama akan ta bata aron suhaima da hairah tadauko me gyaran da zata yiwa du ka amaren gyara , dakyar mama tayarda ita gani takeyi za'a daura musu dawainiya ahaka anty amina ta lallabata ta ɗauki suhaima da hairah daga nan bayan sun fito tashiga gidansu Amira ta taroki hajiyar Amira itama duka direct part din mommy tashiga dasu . Suna ganin juna sukasa ihu suna murna harda tsalle girgiza kai anty amina tayi ta ce " yaran nan Allah yashiryeku , my feena dan Allah kidena biye musu kinga ke bake kadai bace" " tom anty amina" cewar fanan. gyara akeyi musu na gani na fada lokaci daya suka canza acikin sati biyu sunyi kyau sosai fatar su ta kara glowing se sheƙi yayi luwai_luwai, fatar su kamar ataba jini ya fito bugu da kari ga shi ba shiga rana sukeyi basa fita ko nan da kofar falo duk abinsu acikin part din sukeyi ga kamshin da jikinsu yakeyi duk inda suka zauna sesun bar kamshin su awajan . ga tsumin da ake basu suke sha , burin zeenat de yashika abin nema yasamu ci da kaza da take magana akai ,yanzu itama lokacinta yazo tanaci. Abun duniya ya dami Mr azaad shi gani yakeyi baayi mishi adalci ba ace sati biyu cur ahanashi ganin matarshi dakuma jin ɗuminta dana ɗanshi. Duk laifin anty amina yafi gani taya zata daukar mishi mata bayan tasan yana bukatar matarshi akusa dashi, rabon da yasata a ido tun ranar da tazo tadauketa da sunan za'a musu gyaran jiki , haka yayi hakuri ya kyalesu amma kullum suna manne awaya arana zasuyi waya sau uku sau hudu harda video call. Haka bangaren sauran angwayen ma suma basu sake saka amaren a idonsu ba sede suyita waya. Ana daurin aure saura kwana uku , Yan beauty saloon's sukazo domin yi ma amare lallai da wankin kai , lalle da dayis akayi musu me rai da lafiya ja da baƙi hannu da ƙafa sannan aka yi musu saloon duk kansu kitso akayi musu amma banda fanan da ta ce ita kawai a gyara mata kan . sun sha gyara kam na fitan hankali . Washe gari ana jibi daurin aure Hajiya ta turo da motar yadau Amira da suhaima dakuma hairah . Masha Allah abangaren gidajen amare da angwayen komai yayi ready ranar daurin aure kawai ake jira domin abba da baba sunce bazaayi wata bidi'a ba saboda albarkan aure ake nema . Yan uwa na nesa da na kusa duk sun samu hallara yan Dubai sun iso haka su umma rahina da uncle kabir duk sunzo . gidan da komai seda aka canza mishi komai sabo , babu abinda ba'a canza yazama sabo ba anyi ƙayitatciyar decorations, part din Mr azaad anzuba sabbin furniture haka part din fawwaz da areef ma anzuba furniture da duk wani abinda ake bukata, areef da Hafiz kuma sundawo part din downstairs na karban ba ki . Shirye shiryen biki akeyi ba kama hannun yaro duk sun shiga busy , anty amina da anty shayida da anty zainab sune gaba akan komai . Safiyar jumma'at ranar daurin aure, da safe anty amina tashigo da masu aiki rike da kayayyakin da zeenat da fanan zasu saka. misalin ƙarfe sha biyu , wanka aka sasu sukayi da ruwan madara dake dauke da sinadaren kamshi, sannan aka sake hada musu ruwan wanka da ruwan turare sukayi bayan sun fito ne aka basu kayan atamfa riga da zani rigar ɗinkin bubu ba'a musu kwalliya ba babu abinda aka shafa musu dangi nata shigowa cikin part din suna kallon amare ana jiran lokacin daurin aure , haka aka ta daukansu hotuna , ga fans din NIDA PATIENT DINA duk sun samu hallara se daukan hoto da fanan sukeyi saboda kowannesu yasamu nayin posting a status , karfe daya kuma aka sake sasu sukayi sabon wanka aka shirya su cikin hadaddun dogayen riguna na amare ,na fanan milk color na zeenat kuma white color aka musu make up sannan aka daura musu dankwali , sunyi masifar kyau . Bangaren amare suhaima da hairah kuwa suma misalin ƙarfe sha biyu atamfa suka saka akayi ta musu hotona karfe daya aka sasu sukayi sabon wanka aka shirya su cikin breathing taking gown masu masifar kyau ga shi sun sha make up kyau kam ba'a magana kusan amare babu wanda yake kaisu kyau. Manyan mutane daga ƙasa daban daban sunzo domin halartar daurin auren jikokin sarkin gombe da kuma Sarkin Dubai sannan ya'ya ga shahararren dan kasuwan nan, ga kuma azaad babban dan kasuwan da ake tunkaho dashi , sarakuna, gomnoni, manya masu faɗa aji aƙasar Nijeriya da kuma ketare duk sunzo , haka manyan abokan baba da uncle kabir da dangi ga abokan nan angwaye duk a masallacin sarkin gombe za'a daura auren nasu . Bayan an sauko daga salar jumma'at aka daura auren. (Usman Muhammad umar & Hairah Aminu ) da ( yaseer Yakubu sani & zeenat Muhammad mainasara) da ( Fawwaz Muhammad mainasara & Suhaima Kabir Umar ) da ( Umar Kabir Umar & Aysha Abubakar Wada ) akan sadaki naira dubu dari da hamsin hamsin lakadan ba ajalan ba , bayan angama daura aure suka tashi suna taya junansu murna , sosai aka taya angwaye murna da se washe baƙi sukeyi suma yanzu sunzama mazajen aure , duk sunsha manyan dakakkun shadda farare sunsha aiki , rungume juna yaseer da Mr azaad sukayi , Mr azaad ya ce " congratulations dude " yaseer ya ce " thank you dude" haka Fawwaz suka rungume babban yaya sukayi wato Mr azaad, taya fawwaz murna Mr azaad yayi sannan ya rungumi ya al ameen da ya usman yau suna cikin farin ciki sosai wanda baƙi baze iya faɗa ba haka baba da Abba da uncle kabir sukayi musabaha. Fadawa se kirari sukeyiwa angwayen anata bushe_bushen sarewa haka suka tafi akayi reception sannan suka wuce gida. suna shigowa gidan mata suka fara guɗa ana cigaba da busa sarewa murmushi ummi tayi tana hamdala yaranta sunyi aure . Duk yanda zeenat takeson yaseer amma ana fadan an daura aure taji gabanta ya fadi . Mr azaad, yaseer fawwaz areef da sauran abokansu sun je part din ummi sun gaisheta da kuma sauran yan uwa sannan suka biyo anty amina zuwa part din mommy dan ganin matansu , zama sukayi a falo anty amina da anty zainab suka shiga ciki , anty amina tariko fanan anty zainab kuma tariko zeenat tafito dasu. Karan hills din takalman sune yajawo hankalinsu zuwa upstairs, suman zaune Mr azaad yayi ganin irin kyau da canzawan da fanan tayi tun kafin su iso Mr azaad yakarasa wajan nasu sannan ya mikawa fanan hannunshi satan kallon anty amina tayi , saketa anty amina tayi takoma gefe tazauna, daura hannunta fanan tayi akan nashi , shafa hannun yakeyi yakafeshi da ido yana kallon zanen lallen da aka mata kissing din hannun yayi ya jawota jikinshi yarungumeta fanan duk kunya yarufeta ganin duk mutane dake wajan su suke kallo sunayi musu video da hotuna. Ga zeenat zaune agefen yaseer se kallon kauna suke jefawa juna fawwaz ne ya ce " wallahi bazan yarda ba " maida kallonsu kanshi sukayi jamal ne ya ce " hey bro what happened?" dan shi bayajin hausa Fawwaz ya ce " babban yaya kuzo mutafi dan Allah " dariya sukayi harda Mr azaad shima seda ya murmusa dan yasan dalilin dayasa yayi maganar. Duk fitowa sukayi zasu tafi gidan surkansu wato gidan su fanan tundazun suke jiran Mr azaad yafito yana can shida fanan afalo , kallonta yakeyi babu ko kyaftawa ji yakeyi kamar kar yamatsa daga inda take, sa hannunshi yayi ya zame daurin dankwalin da aka mata , ribbon din da akayi packing gashin yacire , daura kanshi yayi akan wuyanta yana shaƙar daddadar kamshin dake tashi ajikinta shafa cikinta yayi ya ce " baby kwanakin nan danayisu batare da ke ba , it has been very difficult for me! kinyi kyau sosai jinakeyi yanzu kamar induba ɗanmu anan " shafa jikinta dayakeyi ne yasa tafarajin wani irin yamm tsigan jikinta natashi jin wai zeduba babynsu anan ne yasa tafara kokarin raba jikinta da nashi ɗan tasan halinshi tsaf ze aikata abinda yafada. yana kokarin sa bakinshi cikin nata kira yashigo wayarshi tsaki yayi yadaga ganin yaseer ne abangaren yaseer ya ce " dude wannan wani irin iskanci ne ,muna jiranka kaƙi fitowa ka mannewa yarinya mudin anfada maka mudin ba mata bane damu " tsaki Mr azaad yaja yakashe wayarshi kiss ya mata a libs din ta sannan ya ce bari muje gida " ta ce " to habiby adawo lafiya " ya amsa da ameen yafice bin bayanshi tayi da kallo tana murmushi sannan tahaura upstairs tashiga daki tasamu zeenat zaune. Tunda yafito yake watsawa yaseer harara yaseer ya ce " oho de tunda kafito " dariya sauran sukayi kafin kowa yashiga motar shi suka nufi gidan su fanan. A canma ana nan anata daukar hotuna da sauran hidimomin biki ya usman se washe baƙi akeyi shigowa gidan tawagar su Mr azaad sukayi nan take aka sa musu guɗa anata tayasu murna , falo suka shiga suka zazzauna suna gaishe da iyaye kafin anty firdausi tafito da suhaima fawwaz ji yayi kamar yatashi yaje ya rungumeta yana jin dadi yanzu shikenan baby tazama mallakinshi. Gaishesu hairah da suhaima sukayi kafin suka fito waje aka fara dauka amare da ango hotuna da dangi , suna gamawa suka ɗuƙunzuma zuwa gidansu Amira nanma hotuna sukayi sukayi gaisuwa sannan suka watse suka koma hotel saboda kaf abokanayensu a hotel din suka sauka saboda abokansu a international hotel suka sauka . Bayan sallar mangrib an shirya du ka amaren ɗan kaisu gidajensu , aciki kuwa harda fanan , duk shiryasu akayi cikin liffaya aka rufe musu fuska aka kaisu part din Abba yamusu faɗa sosai sannan aka kaisu part din ummi ita tayi musu fada dasauran yan uwa , dangin yaseer sunzo daukan amarya nan fa zeenat ta tuɓure tace bata san zancen ba tana rungume da ummi tana kuka , ummi kanta dauriya kawai tayi dakyar aka raba zeenat ajikin ummi har anfara tafiya da ita tafisge tazo da gudu ta rungume fanan tana kuka, itama fanan seda tayi hawaye da ta tuna itama lokacin da za'a kawota seda tayi kukan rabuwa da mama, haka aka tafi da zeenat su anty shayida da anty zainab sukayi musu rakiya har gidansu yaseer sun samu kyakkyawar tarba a gidan suka miƙa amanar zeenat awajan hajiyarsu nan suka koma gida danzuwa dauko amarya suhaima. Bayan sundawo ne aka kai fanan part din Mr azaad, sannan suka wuce dauko suhaima . Yan uwa su mama ne da anty firdausi suka kai hairah ɗanƙararriyar gidan da baba ya ginawa ya usman komai anyiwa hairah irin na yan gata an ƙawata mata gidan ta gwanin kyau komai an mata shi itama seda tayi kuka da akazo tafiya da ita ta rungume mama tana kuka autama na kuka ,sosai sukayi musu godiya sosai ita da Hafiz , hardashi aka kaita gidanta amatsayinshi na yayanta kamar uba ya ke , seda yazubar da hawaye dayaga aljannar duniyar da aka kawo kanwarshi sosai shima yamata nasiha akan wanda mama da baba suka mata duk da bashida wani shekaru , basu jima ba aka barta ita daya agidan tana kuka haka suka tafi suka barta . Zuwa su anty amina sukayi dan tafiya da suhaima itama tasha kukanta sosai dakyar aka raba ta da mama da umma rahina aka tafi da ita harda auta , duka amaren seda aka kai kowacce gidan ta, Amira kuma ita se bayan kwana biyu zasu wuce bauchi gida aka kawota , aka kaita dakin fanan. Duk adaren angwayen suka angwance banda ya al ameen , zeenat ansha azaba angane shayi ruwane babu sunan wanda bata kira ba musamman ummi tasha kira kamar ba gobe , haka suhaima ma seda ta gommace kiɗa da karatu roko babu irin wanda batayiwa Fawwaz ba tun tana kiranshi da habiby har takoma kiranshi da sunanshi tana dukanshi shikam ko jinta beyi ba. Ya Usman ma ya angwance amma sanin hairah karamace shisa yabita ahankali sosai , duk da haka seda hairah tasha azaba tayi kuka harseda ta gaji ɗan kanta . LOVE BIRDS Seda yaraka yaseer tukun nan yadawo, fanan na part dinta tasha wanka tasa wasu arnayen kayan bacci ta watsa gashinta a tsakiyar bayanta yasauko har kugunta ga fatarta ta dake daukan ido jikinta na fitar da kamshi ga zanen lallen da aka musu tagama duk abinda zatayi tana zaune agaban mirror tana jiran dawuwar Mr azaad taƙagu yadawo domin tayi kewarsa sosai , toilet yashiga yayi wanka yafito daure da towel a kugunshi shafa lotion yayi ya fesa perfumes jin har lokacin fanan bata shigo ba yasa yanufi bedroom dinta yamurda handle din dakin dago kai tayi jin an bude kofar sauke idonsu sukayi acikin na juna atare suka sakarwa kansu tsadadden murmushi, shigowa yayi yaje gabanta yadagota tsaye yanabin kayan jikinta da kallo hadiye yawu yayi domin tashin farko yaji hankalinshi yatashi ga fitinannen kamshin turarenta dake dukanshi , zuba mishi oily eyes dinta tayi tana kallon murdeden jikinshi da ke tafiya da hankalinta ,ganin irin kallon da take mishi ne da sexy voice dinshi ya ce " what are you looking at ?" Matsowa tayi kusa dashi tadaura hannunta akan kirjinshi tana shafawa ta ce " am looking at this " tafada tana daga mishi gira kamar yanda yake yi mata , killer smile yayi ya ce " yau zaki biya bashin sati ukun da kika dauka tunda guduna kikayi " murmushi kawai tayi batace mishi komai ba,ɗurgusawa kasa yayi yasa hannunshi du ka biyu ya riƙo kugunta yadaura kanshi akan shamulallen cikinta sannan ya manna mata kiss, mikewa yayi yajuyar da ita yarungumeta ta baya suna kallon kansu amadubi maida gashinta gefe daya yayi , ya manna mata kiss agefen wuyan lumshe ido fanan tayi saboda wani irin shocking din datakeji , haka yadinga manna mata kiss ajiki kafin ya dauketa cak suka koma kan gado ya kashe wutar dakin yau tsabar za'a sa ke sabon angwancewa ma ko bedside lamp din be bari ba dan kar indauko muku bayani nima araina nace to dama so nakeyi in ganku ne nafito waje abuna. Asuba ta gari Yaseer dakyar ya iya shawo kan zeenat tayi shuru yakaita toilet ya gasa mata jiki yanaɗota a towel yasa mata kaya da hijab sukayi sallah , turo musu da breakfast hajiyarsu tayi , yayi feeding dinta sannan yabata pain relief , samu yayi ya rarrasheta tayi bacci shima yaja musu bargo suka koma bacci yana jin farin ciki mara misiltuwa. Ya Usman ma yasha rarrashi kam awajan hairah dakyar ta bari yasata acikin ruwan zafi ya gasata se zuba mishi shagwaba takeyi , bayan sunyi Sallah naji ana yin knocking fita yayi yaduba yaga driver anty firdausi ne, turo musu breakfast anty firdausi tayi , sukayi breakfast yabata magani sannan yajata suka koma bacci . Abangaren suhaima kuwa lallashin duniyar nan fawwaz babu irin wanda beyiwa suhaima ba amma har lokacin kuka takeyi ta na " hubby ashe dama ba sona kakeyi ba ? Jiya banyi tunanin zaka barni da raina ba rabani gida biyu fa kayi ko tausayina bakaji ba! yanzu nasan irin zaman da zanyi dakai " kokarin riketa yakeyi yakaita toilet yamata wanka amma fir taƙi ya tabata ganin takeyi kamar sakeyi zeyi , daga zaran yanufeta zata zabga mishi uwar harara , haka tamike tana dafa bango takai kanta toilet tahada ruwan zafi a jacuzzi tashiga ciki, ruwan na ratsata ta runtse ido hade da cize libs dinta tana kuka, seda tafarajin dama_dama tukun tacanza ruwa tasake komawa sau uku tana sa ke ruwa kafin tayi wanka tsarki tadaura towel tafito tana ɗingisa ƙafa, shide fawwaz yama rasa yazeyi da suhaima gashi yanason yataimaka mata amma ta tsayar mishi da rigima nufarta yayi ze dauketa ta ce " Allah hubby karka sake ka tabani" haɗe fuska yayi ya koma kamar bashi ba, nan ne tsananin kamar dasukeyi da Mr azaad yafito nan take tashiga rigar nutsuwa ya ce" in kika sakeyi mini musu sena sake round two " tundaga nan yasamu lafiya da suhaima tadena mishi gardama shiryata yayi yadauketa yadaura akan gado kamar karamar yarinya , sukayi sallah asuba , ji sukayi ana knocking yaje yabude abu me aiki yagani gaisheta yayi ta amsa tana mishi yagajiyar biki mika mishi basket din breakfast dinsu tayi ta nufi part din su Mr azaad, koma ciki fawwaz yayi ya serving dinsu sukayi breakfast suka koma bacci . Suna kwance manne da junansu suna bacci hankali kwance dan tun bayan su idar da sallah suka koma bacci jin knocking yasa suka farka Mr azaad ya ce bari yaje yaduba , abu me aiki ce ta gaisheshi sannan tabashi basket din breakfast dinsu. Ajiyewa yayi a dinning yakoma suka ci gaba da baccin su. Haka suka yini a shashin suna soyewa se bayan isha ne suka shirya cikin wankan atamfa suka tafi part din ummi saboda an shirya cin abinci dare , anaci abinci anata shan hira ummi se nan_nan takeyi da suirkan nata fanan da suhaima saboda sonsu takeyi sosai auta na gidan tun daren jiya da aka kawo suhaima sunzo tafiya ummi ta ce abarta anan aikuwa sukayi ta wasansu itada aslam da islam saboda dukkansu shekarunsu daya ne kansu daya , areef ne yazo yajasu zuwa part dinsu sukaje suka dinga biye musu shida hafiz dare yayi suka koma part din su kowa yaje ya kwanta. Washe gari kuwa baki suka watse kowa yakoma garinsu, haka ya rage iya sune kadai agidan su anty amina duk sun koma gidajensu, haka su umma rahina ma sun koma Bauchi tare da suhaima bayan sun isa sun huta gajiya ya al ameen yadauki matarshi zuwa part dinshi dake cikin gidan komai akwai aciki na more rayuwa, shima aranar ya angwance. Rayuwa me dadi sukeyi hankalinsu kwance agidan mazajensu , suhaima da fanan suna samun kulawa sosai awajen ummi musamman ma fanan dake da ciki haka suma kullum suna part dinta tayata hira dakuma yi mata girki , ga kulawar da suke samu agun mazajensu, cikin fanan yafara girma yanzu yakai wata shida Mr sosai yamaida attention dinshi wajan kula da fanan da abinda ke cikinta sosai take samun kulawa agidan . Hairah anzama manyan mata soyayya suke sha ita da yaya usman dinta kamar bazaa mutu ba , abubuwa haka sukata faruwa lokaci nata tafiya , laulayin ciki hairah da zeenat suka fara aikuwa gwajin farko aka gano ciki ne dasu na wata daya Hajiya sosai take kulawa da zeenat, haka mama tasa ya Usman ya dawo da hairah gida saboda cikin na bata wahala tana laulayi sosai duk abinda tace takeso mama nayi mata shi . Yanzu cikin fanan watanshi bakwai da sati biyu ayan kwanakin nan ciwon mara da ciwon baya yasata agaba amma haka take daurewa bata nunawa . Adamawa Yola Nusaiba ce da wata kawarta me suna ruma sa'u data kawo mata ziyara suna cikin hira ruma sa'u ta ce " ƙawata dama tun bayau ba nakeson infada miki wata magana amma bansan ya za ki dauki maganar ba " nusaiba ta ce " karki damu ƙawata faɗa kawai inajinki" Ruma ta ce " ƙawata yanzu Yakamata ace kin kwantar da wuya ki karbi aurenki , wallahi karki tsaya kallon ruwa gwaɗo yamiki ƙafa, kindega yanda duniyar nan yake yanzu kisamu wanda ze soka ya yi hakuri daduk wani halinka shima kyau ne daga Ubangiji , ya lukman wallahi namijine da ko wace ya mace zatayi fatan samu amatsayin miji , yana da hakuri sosai ga ka war da kai bashida matsala ko kadan amma ke kinsame shi se ranshi kunya da wulakanci kike mishi amma duk da haka yaci gaba da hakuri dake . Kina tunanin da wani na mijin ne zeyi toleranting wannan abinda kikeyi ne ? In za ki farka daga wannan rashin hankalin dakikeyi gwara ki farka , wallahi yana samun wata matar ze ƙyaleki yayi aurenshi kinga daga nan kuma kinyi biyu babu ke baƙi samu ya sakekin ba kuma ke awannan lokacin zaki rasa hankalinshi, wannan shawara ce nake baƙi tun kafin lokaci yakure miki " maganganun Ruma yayi matukar ratsa nusaiba lokaci daya taji danasani ya kamata se yanzu take ganin wautarta dukda wani lokacin tanayi mishi wasu abubuwan ne bawai da son ranta ba sosai tayiwa Ruma godiya domin ta nusar da ita inbadan itaba da yanzu bata gane gaskiya ba , bayan tafiyan Ruma nusaiba ta tashi ta gyara gidan tas tashiga dakinshi ta gyarashi sosai ,ta shiga kitchen tayi girki me rai da lafiya bayan tagama tajera a dinning ta kunna turaren wuta dama me aikinta ta tafi saboda ta ce bazata iya da halinta ba. Wanka tayi taci kwalliya tasa lace ɗinkin riga da skirt ya kamata sosai tasha dauri tazauna afalo tana zaman jiranshi , tunda lukman ya tunkaro falon yaji kamshi na tashi shiga ciki yayi yaga ko ina tsaff tana , sauke idonshi yayi akanta tana zaune akan kujera, mikewa tayi ta nufeshi tana sakar mishi murmushi tasa hannu ta karbi brief case din hannunshi ta ce " sannu da dawuwa ya lukman" shide kallonta kawai yakeyi ɗan gani yakeyi kamar amarfaki ganin yana binta da kallon mamaki ne yasa tariko hannunshi zuwa bedroom dinshi shide binta yakeyi kamar raƙumi da akala taimaka mishi tayi yarage kayan jikinshi yashiga toilet yayi wanka yafito har lokacin mamakin nusaiba ya hana shi bude baki yayi magana , fito mishi da kayan shan iska tayi yasaka taja hannunshi zuwa dinning table tayi serving dinshi girkin da tayi mishi , dakyar lukman ya ce " nusaiba yau wani irin mafarki nakeyi haka " murmushi tayi ta ce " yayana ba mafarki kakeyi ba, kayi hakuri nasan nayi maka abubuwa da dama na bacin rai nasan na kuntata maka amma baka taba daga min murya ba Kaci gaba da hakuri dani tabbas kaiɗin mutum ne na gari ,kuma miji nagari da ya cancanci soyayya daga gun matarshi ,sannan kuma uba nagari dan Allah kayi hakuri kayafemin natuba " tafada tana ɗurgusawa agabanshi tana hade hannayenta waje daya, yasan maganar datayi dakuma tuban datayi na tsakani da Allah ne domin nusaiba bata da fuska biyu kuma bata iya karya ba dan ta farantawa mutum komi munin magana inde yazo bakinta zata fada maka shi kuma har cikin ranta amma yau jin wa'yannan kalaman nata yasa yagane gaskiyar ta kenan dagota yayi yadaurata akan cinyarsa ya ce" alhamdulillah my nusee nagodewa Allah dayasa kika gane gaskiya, Allah yabamu ikon farantawa junanmu " yafada yana manna mata kiss a kumatu rungume juna sukayi kowanne yanajin farin ciki aranshi. Tanzarzar yabawa yan kungiyar shi umarni dasu fara aiwatar da abinda yasa su na kashe duk wani jarirai dasuke asibiti dakuma mata masu ciki da masu jego acikin dare kuwa misalin ƙarfe goma sha daya suka fara kashe mutane acikin asibitoci sunyi shiga cikin bakaken kaya. Karfe sha biyun dare fanan na bacci ajikin Mr azaad naƙuda yatashi mata ranga_ranga hankali atashe yatashi yaje ya bugawa ummi yasanar da ita abinda ke faruwa dasauri tabiyo bayanshi aikuwa tana duba fanan taga naƙuda ne jinjina ikon Allah tayi wato bakwaini itama zata haifa , ita bakwaini sannan zata haifi bakwaini , tasanar da Mr azaad haihuwa ne,dauko motar yayi yazo yadauketa Fawwaz jin an tada motar ne cikin dare yasashi lekawa ta window yaga Mr azaad dauke da fanan dake murkususun azabar naƙuda ga ummi da ta fito da kayan haihuwa acikin jaka suka shiga motar aka bude musu gate , da sauri Fawwaz ya tashi suhaima ta shirya suka bi bayansu suma , da gaggawa aka karbi fanan aka shiga da ita labour room tare suka shiga da Mr azaad yana rike da hannunta se faman nishi takeyi ga gumin datakeyi , Mr azaad is very speechless ganin irin azaban da mata suke sha wajan haihuwa jiyayi kamar yamayar da ciwon kanshi tana kuka hade da addu'a shima yana hawaye tun sha biyu ake fama amma har karfe hudu na asuba bata haihu ba har karfinta ya kare tama gagara yin nishin se wasiyya take barwa Mr azaad sosai yake kuka gani yakeyi kamar tafiya zatayi tabarshi , su ummi duk suna waje suna mata addu'ar sauka lafiya duk yan uwan sun hallara a asibitin harta su mama sunzo da abba su ya usman duka sunzo . duk se safa da marwa sukeyi abakin dakin labour din ganin har shida tayi babu labarin ta haihu. Yau garin Gombe an tashi da munanan labarai na kashe kashen da akayi kuma ake kanyi ansa tsaro ba shiga ba fita sojoji da polisawa se dirƙa sukeyi acikin duk wani asibitin dake jahar gombe saboda kisan gilan da akeyiwa masu ciki da yara jarirai ankashe mutane sun fi ɗari lamarin ba kyan gani kowa a tsorace suke ko ina labaren ne ke tashi , gashi masu aikata kisan ba'a ganinsu , wannan shine tashin hankalin da aka wayi gari dashi a jahar gombe kenan. Shigowa sukayi cikin asibitin medical center suka fara ɓarna sunshiga dakin da ake ajiye jarirai suka fara kashe su . Shirye shiryen yiwa fanan operation sukeyi saboda ta ƙasa haihuwa da kanta har Mr azaad da baba sunyi sign za'a shiga da ita , karfinta yadawo tafara nishi da karfi ahaka harta haihu . Ta haifi ya mace kyakkyawar gaske me matukar kama da ita kamar tayi kaki ta tofar sede farin fatan Mr azaad tadauko fara ce sol gyarasu akayi ita da babyn sannan aka bata ita tana kallonta tana murmushi hade da hawaye manna mata kiss tayi ta ce " am sorry my angel zaki taso bazakiga mahaifiyarki akusa dake ba Allah ya miki albarka nasan babanki ze kula dake sosai " sude doctors binta suke da kallo dukda basu san ina zancen nata ya dosa ba amma tabasu tausayi , bude kofar labour room din sukayi suka fito hannunsu nadauke da baby girl din dasauri suka taso suna alhamdulillah mikawa mr azaad jaririyar sukayi karbanta yayi , nan take yaji wasu irin zafafan hawaye sun sauko daga idanunshi jiyayi kamar ayau din nan ze rasa wani barin bangare na jikinshi mannata yayi ajikinshi ya manna mata kiss a goshi, yayi mata huduba a kunne, karbanta doctor yayi yace " congratulations Mr azaad tasauka lafiya kuma itama Madam na lafiya yanzu ita babyn zamu sa ta acikin kwalba ne" sunaji suna gani aka tafi da ita suna jira suga an fito da fanan kenan sukaji ihun jama'a a asibitin suna neman taimako , mutane mata da maza se guduwa sukeyi suna ɓuya sude suna zaune kansu yadaure basu san abinda yake faruwa ba , ganin fanan sukayi tafito da gudu daga ita se rigar asibiti hannunta na zubar da jini saboda fincike calular da tayi , dasauri Mr azaad yarikota ganin bata cikin hankalinta yarikota ya na " wifey meyafaru Ina zakije ?" abirkice ta ce " yata zasu kashemin yata habiby " duk ta rudar dasu suna kokarin yin magana sukaga doctor dayatafi da babyn ya shawo kwana da mugun gudu hannunshi dauke da jaririyar gudu yakeyi kamar ranshi zefita ga jikinshi dake zubda jini duk anji mishi rauni , dasauri Mr azaad yasake fanan anty amina tariketa yaje yakarbi jaririyar ahannun doctor din yana tambayar shi meyake faruwa , doctor dake kokarin mutuwa ya ce" wasu azzalumai ne suka shigo wannan asibitin suna kashe mana mutane daga mata masu ciki zuwa kan jarirai dakuma masu shayarwa " yana gama fadin haka yafadi awajan rai yayi halinshi . Iya tashin hankali sun shiga sunma rasa ɓuya zasuyi ne kokuma komawa gida zasuyi ga shi jama'a ne shaƙee abakin gate din asibitin jami'an tsaron sun hana kowa fita , suma da sauri suka fito compound din asibitin Mr azaad na rike da jaririyar Anty amina tarike fanan baba nadauke da auta akan kafadarshi haka Abba ma yadauki aslam, Fawwaz narike da hannun suhaima da Islam, babu yanda basuyi ba amma jami'an tsaron sunce bazeyu subar kowa yafita ba saboda awajenma ana fuskantar tashin hankalin da yafi na cikin asibitin ko ina se zubar da jini akeyi. Kuka takeyi kamar ranta ze fita se kallon ahalin nata takeyi ita tasan yau ne ranar tafiyarta domin ayanzu ne zata fara tunkaran wa'yannan azzaluman , Mr azaad ya ce " kuzo muje mu ɓuya awani awajan" dugunzuma sukayi suka fara binshi juyawa yayi yaga fanan na tsaye , abayan su batako daga ƙafarta ba dakatawa yayi ya ce "wifey kizo muje hurry up" duk juyowa sukayi suna kallon fanan da itama su take kallo tana kuka , Abba ma sake mata magana yayi girgiza musu kai tayi tana kuka me tsuma zuciya ta ce " am sorry amma bazan biku ba ni yau ne ranar tawa tafiyar " duk jan burki sukayi lokaci daya zuciyoyinsu yafara bugawa da karfin gaske musamman ma Mr azaad da mama , se yanzu suka tuna da cewa akwai wani babban zaluncin da za'ayi da aranar fanan zata tafi , da gudu Mr azaad yaje gabanta yatsaya ya ce " common on wifey don't be so childish kizo mutafi kinji " girgiza mishi kai tayi ta ce " am sorry habiby amma yau bazaku koma gida tare dani ba " da karfi Mr azaad ya ce " noooo! hakan bazeyuba baby please karki min haka dan Allah karki tafi look at our daughter please kitsaya mu kula da ita tare dan Allah rayuwa zatayi mana zafi dani da ita in bake " yagama magana yana zubewa akan guiwansa agabanta yana kuka ga baby a hannunshi " riko hannunshi tayi ta mikar dashi ta ce" habiby inada full confidence akanka nasan zaka bawa twinkle dinmu dukkan kulawa daya kamata kayafemin inna tabayi maka wani abu sannan in twinkle ta girma ka ce mata ta yafewa mommynta, ta dinga min addu'a" girgiza kai Mr azaad kawai yake yi yana kuka shida ita ta rungume shi. Kuka su mama sukeyi mama ji tayi zuciyarta na mata zafi sosai kamar ze fito waje ummi na kuka kowa na wajen kuka yakeyi musamman suhaima da zeenat Anty amina mazan ne kawai sukayi dauriya suna me matukar tausayawa Mr azaad, baba kam idonshi yayi ja yakasa cewa komai domin shi kullum dama da haka yake kwana aranshi saboda yasan ko ba jima ko ba ɗa ɗi yasan wannan lokacin na zuwa , Abba hawaye yataru a idonshi. Fuskantar su fanan tayi tana share hawaye tayi folding hannayenta waje daya ta ce " mamana inasonki sosai amma haka zan tafi in barki kiyafemin sannan kitamin addu'a zantafi yaƙin da bazan dawo ba har abada , baba dan Allah kaima ka yafemin inasanka sosai, ummi kiyafemin kinji ? Abba ka yafemin zanyi kewar kyakkyawar ahalinku kudinga sani a addu'a, ya usman kaima kayafemin zeenat forgive, suhaima kiyafemin sannan ga twinkle nan karki barta tayi kukan maraicin uwa , Anty amina nagode sosai, " haka tadinga bin su tana nemar yafiyar su sannan ta koma kan yaseer ta ce" ya yaseer dan Allah karka bar habiby yashiga wani hali dan Allah ku kulamin dashi sosai karku barshi yayi kewa na sannan ku aura mishi mace ta gari wacce zata mayar mishi da gurbina sannan tazamowa twinkle uwa " dakyar take iya magana saboda kukan da yaci karfinta, sukkansu yanzu mazan sun kasa jurewa kuka kawai suke yi hatta jama'ar cikin asibitin da suka fito domin ceton rayuwarsu hankalinsu yakoma kansu sosai suka basu tausayi . Mr azaad da ido kawai yake binta ji yayi dama Allah yadauki ranshi ayanzu ko zefi ji raradin dayakeji ya ragu . Komawa tsakiyar asibitin tayi tana kallonsu suma suna kallonta suna kuka tana kuka , idonta na cikin na Mr azaad da yake kallonta yana girgiza mata kai alamar karta tafi lumshe idanunta tayi hawaye suka biyo baya , bude hannayenta tayi du ka biyu nan take garin yafara hada gagarumin haɗari bana wasa ba, ruwa yafara zubowa a iya inda take tsaye , sabon kuka ne Yakamata dagudu ta nufi Mr azaad dake tsaye hawaye nafita a idonshi dasuka rine tsabar kukan da yayi yakoma kamar Mutum mutumi ƙwakwaran motsi ma yakasa zuciyarshi na mishi tururin zafi, tsayawa tayi agabanshi jikinta na digar ruwa , ɗage ƙafarta tayi ta isoshi a tsaye tasa hannunta duka biyu ta riƙe kanshi idonsu na sarke acikin na juna suna zubar da hawaye bata damu da yawan jama'ar dake wajan ba bata da mu da iyayensu da idonsu ke kansu ba tahaɗe bakinsu waje daya ta fara bashi unforgettable kisses masu zafi , duk wani wanda yake wajen sunkuyar da kansu ƙasa sukayi ganin fanan na mishi kissed din ban kwana , seda tadau minti 20 tana kissing dinshi kafin tasake shi, suna kallon idon juna murya a dashe Mr azaad ya ce " kin tafi kinbar min abu biyu arana daya wanda duk sanda nagani kuma natuna zan tuna ki , kinbar min twinkle dakuma kiss dinki ! baby zan iya mutuwa idan kika tafi daga nan kuma twinkle zata taso a marainiya mara uwa da uba " hawaye na kwarara a idonta ta ce " inka tafi kabar twinkle kuma zafin zemata biyu ka kula mana da ita idan ta girma ta tambaya ina mamarta kace mata ta tafi yakar azzalumai, kafada mata mahaifiyarta jaruma ce data sadaukar da rayuwarta wajan ceton al'ummar Musulmai sannan kullum kafin tayi bacci ka sanar da ita da ina matukar kaunar ta tadingamin addu'a " tana gama fadin haka bata jira abinda ze fada ba ta manna wa twinkle kiss agoshi sannan tasake komawa inda ta haɗa hadarin ruwa yaci gaba da dukanta , daga musu hannu tayi tana musu bye-bye du ka suma hannun suka daga mata suna mata bankwana suna kuka banda Mr azaad da mama da sude kallonta kawai suke iyayi basa iya motsa jikinsu . Wani irin walkiya akayi me hasken gaske da tsawa nan take ta koma asalin sarauniyarta cikin shiga na yaƙi fuskan nan babu annuri ko rahama ko kadan aciki. Hannunta na rike da bulalar wuta tana jujjuyashi nan take taba ce yazama babu wanda yake ganinta tashiga cikin asibitin ta kashe duk wa'yanda sukazo suna aikata kashe _kashen seda ta kashe su sannan ta bar asibitin ta je sauran asibitocin tana ka kashesu , seda takashe duk wa'yanda tanzarzar ya aiko takuma gyara duk abinda suka bata wadanda suka raunata tayi musu magani suka warke sunayi mata godiya domin bayyanar ta yayi dede domin ta dakatar da zaluncin dasuke aikatawa, komawa medical center tayi sannan tayiwa wa'yanda suka raunata magani , suna nan a tsaye a inda ta barsu ko da ta dawo taimakon mutane tayi bata ko kalli inda suke ba , drygon ne ya sauko ƙasa acikin asibitin nan take jakadiya abashiyya da abdud Shakur suka bayyana suma wajan su mama sukaje suna basu hakuri sannan sukaje wajan sarauniyarsu suka dibi gaisuwa hawa kan drygon ( jegare ) sarauniya tayi yafara firewa da ita akai, duk daga kansu sukayi suna ganin yanda suke tafiya a sararin samaniya tun suna iya hango su har suka ɓacewa ganinsu nan take su jakadiya ma suka ɓace . sake fashewa sukayi da kuka lokacin da suka tabbatar eh dagaske fanan ta tafi tabarsu na har abada yanke jiki mama tayi tafadi cikin tashin hankali suka dagata nurses suka shiga da ita shiga dan dubata . Mr azaad yana nan awajen da fanan tabarshi beko ƙara koda taku daya ba kanshi na kallon sama kamar wanda yake kallon fanan din Abba ne yazo ya ce " son muje ciki " shuru ba amsa Abba yayi magana yafi baƙi biyar amma ba amsa du ka damuwa sukayi kusa dashi suna mishi magana amma ba wanda yabawa amsa sake fashewa da kuka ummi da zeenat sukayi . " Wifey karki tafi kinga twinkle ma na miki dariya ko tana cewa ina sanki sosai mommyna kalleta kigani " yayi maganar Kamar wani yaro karami yana kallon sama yana kuma kallon twinkle dake hannunshi, Abba ne yasake mishi magana amma amaimakon yabashi amsar maganar dayayi mishi seya sake maimaita " wifey karki tafi kinga twinkle ma na miki dariya ko tana cewa ina sanki sosai mommyna kalleta kigani" tashin hankali suka shiga ganin abinda yake shirin faruwa duk wanda yamishi magana awajan abinda yake maimaita musu kenan , ya nanata wannan maganar yafi sau goma . Dakyar suka iya kwace twinkle ah hannunshi, suka rirrikeshi suka shiga dashi cikin asibitin doctor ƙwaƙwalwa ne yayi mishi hoton kwakwalwar shi nan take result yafito dayake nunawa kancewa yasamu brain problem wato ( Broca's aphasia ) shi wannan matsalar kwakwalwar duk sanda mutum yakamu dashi nanata kalma daya kawai zedingayi ...... 🥺😭😭😭 Am typing and also shading tears in pain , nakasa jurewa. Please 🥺 comments and share fisabilillahi wannan pages din was very heart touching. 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 (Yar lelen Jarumai) 🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚 ⚜️📚J. A. W📚🖋️ Gargadi Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe daga cikin book din nan ba ta kowani siga ko a karanta a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira koda Allah nabar mutum ze sakamin yabimin hakkina. PAGE 6️⃣2️⃣ Abba cire hular kanshi yayi dan ji yakeyi komai zafi yake mai suna cikin tashin hankalin da Allah ne kaɗai ze kawo musu mafita dakuma sa musu hakuri azuciyoyinsu amma kuwa sunyi Babban rashi arayuwarsu basaji da akwai wata yarinya dazata iya maida musu gurbin fanan. Yaseer ne ya ce " doctor yanzu menene mafita ? Kuma tsawon wani lokaci zedauka kafin ya warke?" Doctor ya ce " ya danganta daga yanayin treatment din da majinyacin yasamu ne , mutum ze iya warkewa daga wata uku zuwa wata shidda , amma shi Broca's aphasia cikin biyu ne inhar yadade ajikin mutum be warke ba so , wannan majinyacin ze iya rasa ranshi , yanzu de inhar ana bukatar abashi kulawa na musamman sede kufitar dashi abroad acan ne suke da manyan psychologist cikin yardar Allah Mr azaad ze warke " jinjina kai sukayi cikin gamsuwa da bayanin da doctor ya musu Abba ya ce" mun gode sosai doctor " murmushi yayi ya ce" bakomai akwai doctor dazan hadaku dashi a India babban psychologist ne sunanshi doctor Shankhar " Kiran number doctor Shankhar doctor yayi ya mishi bayanin komai sannan yabawa Abba number nashi , yaseer na rike da little twinkle se kallonta yakeyi wata doctor ce ta shigo tace " yallabai kabani ita angama preparing NICU ( neonatal intensive care unit" din " miƙa mata twinkle yayi yanajin wani irin abu na sukanshi aranshi, haka doctor tashiga da twinkle akasata acikin NICU. Fawwaz areef dasu ummi na zaune da Mr azaad da kanshi ke kallon ƙasa yayi shuru yazubawa waje daya ido kamar me nazartan wani abu, shigowa Abba da yaseer sukayi tare da doctor din Abba yazauna kusa da Mr azaad ya ce " son katashi mu tafi gida ko " " duk fa maganar da zakuyi bajinku yakeyi ba balle yamaido muku da amsa " cewar doctor,duk zubawa Mr azaad ido sukayi cikin tausayawa ummi ta ce " barin inje wajan mamansu " tafada tana mikewa ɗan bazata iya cigaba da kallon halin da Mr azaad yake ciki ba , bin bayanta zeenat da anty amina sukayi izuwa dakin da aka kwantar da mama, tana zaune akan gadon ta farfaɗo baba,ya usman, hairah, auta, suhaima,hafiz duk suna dakin sunyi ta gumi babu wanda yake iya magana acikin su , shigowa sukayi ummi ta zauna kusa da mama , rike hannun mama ummi tayi ta ce " mamansu hakuri zamuyi saboda me faruwa yarigada yafaru , babu abinda feena take bukata agurinmu sama da addu'a, duk da rabuwa babu dadi amma mu abin alfaharinmu ne yau a ce yarmu tazama jarumar datayi nasara akan azzalumai harkuma takawo ƙarshensu , kuma koda wannan tafiyar nata be rabamu ba to tabbas mutuwa zata rabamu hakuri da tawakƙali shine abinda yakamacemu , itakuma muyi mata addu'ar nasara in kuma munada rabo da sake ganin ta Allah yatabbatar da ikon sa" maganganun Ummu sun ratsa mama sosai ajiyar zuciya tayi kafin ta ce" ina Azaad ?" ummi ta ce" son yasamu matsalar kwakwalwa yanzu haka anfara shirye shiryen fita dashi India twinkle kuma ansata acikin kwalba " wani hawayene me zafi yazubo a idon mama jin Mr azaad yasamu matsala a brain dinshi, jikarta kuma tana cikin kwalba. Haka wa'yannan ahali biyun suka tashi daga happy family izuwa sad and broken family, haka gidaje biyun nan suka rasa duk wani walwalarsu da farin cikin su , cikin kwana biyu aka gama shirya tafiyar Mr azaad , Abba da Fawwaz se yaseer ne zasu tafi dashi mama ma an sallameta sun koma gida , kusan kullum ummi da zeenat suna zuwa gidan . Suhaima kuma ta roki Fawwaz akan yabarta tadanyi kwana biyu agida tare da su mama , kuma ya amince da hakan. Suna zaune a falo kowa yayi shuru ko wannensu da abinda yake saƙawa a zuciyarshi , Mr azaad na kwance akan kujera kanshi akan cinyar ummi , da gudu Hafiz yasauko downstairs Abba ya ce " Hafiz lafiya kuwa" sa hannu yayi ya dauki remote kafin ya ce " bakuga labaran yau ba? Ko ina maganar anty fanan akeyi " ya karishe maganar yana kamo tashar BBC Hausa duk mayar da hankalinsu kan tv sukayi banda Mr azaad dabemasan meye sukeyi ba balle yasan me suke fada. Video ne da CCTV Camera yadauketa na duka asibitocin da taje ta taimaka musu da kuma short video lokacin da suka rungume juna itada Mr azaad ga kuma twinkle dake hannun Mr azaad, se playing din videos din akeyi again and again aƙasa a rubuta 'the warrior ' wani journalist yafara kwararo bayanai " wannan dakuke gani ita ce Jarumar da ta cece rayuka bila adadi, kwana biyu dasuka wuce wanda a wannan ranar ne muka tashi da tashin hankali mara misiltuwa , kamar yanda kuka gani a wannan dauka na CCTv camera ita ce ta cece jarirai da ake kokarin kashewa da kuma mata masu ciki da masu jego, dama ako ina Allah baya taba goyon bayan zalunci shisa yaturo mana da wannan baiwar Allah. Allah yashiga tsakanin mu da mugaye azzalumai yayi mana tsari dasu itakuma Allah yabiya mata bukatunta na alheri yabata Sa'a akan abinda tasa gaba, ya Allah ya kare ta aduk inda take , ƙasa Nijeriya dakuma ƙetare we're very proud of her she's our superstar warrior. Yanzu zakuji daga bakin wa'yanda suka kasance sheda na gani da ido, sune wa'yanda suke cikin asibiti abin yafaru " magana wani magidanci yafara " sunana Abubakar lawan . wato abinda yafaru shekaranjiya tabbas ni ganau ne ba jiyau ba domin nakai matata haihuwa ne wannan lamarin ya rufta damu a asibitin wannan baiwar Allah ita ta cece jaririnmu dakuma matata bazan taba mantawa da ita ba kuma , itadin matace ga azaad the billionaire sannan sirka ga ahalin mainasara, yanda ta taimaka mana Allah ya taimaka mata ya shige mata gaba aduk lamuranta " haka sauran da aka gayyato suka dinga fadar irin aiyukan da fanan tayi da taimakonsu datayi, haka aka dinga hasko hotunan fanan ta ko Ina yazamana labarinta akeyi , ko ina aka waiga jama'a se addu'a sukeyiwa fanan manya da yara, kowa se bashi dama akeyi yana fadan ra'ayinsa dangane da fanan kowa alkharinta kawai suke magana . Duk jikinsu yayi sanyi ganin irin yanda al'umma tun yanzu sunfara alfahari da fanan ko ina yabonta akeyi , guntun hawayen da yazubowa ummi ne tasa hannu ta share , Abba ya ce " Allah mungode maka " tashi yake kokarin yi idonshi yasauka akan video fanan da ake nunawa a tv asukwane yakarasa tashi yanufi tv da gudu yasa hannu yana shafa " wifey kalleni , ki kalleni wifey kizo mu tafi gida kinji " dasauri suka bi bayanshi zuwa wajan tv ganin yanason birkicewa lokaci daya, dukan tv yakeyi da iya karfinshi wai anashi tunanin yanason yafito da fanan din ne dake cikin tv ,dunkule hannunshi yayi ya bugawa tv wanda seda yayi sanadiyar wargajewarsa raga_raga rikoshi Abba da Fawwaz sukayi yanata sambatu yana kiran sunan fanan, su biyu suke rike dashi amma sun gagara mishi rikon da baze kubce ba ,fisgewa yayi yahaura upstairs da gudu yashiga part dinshi yarufe yasa key . Yaseer ko magana ya kasayi yana zaune yayi tagumi abin duniya yadameshi ganin yanda babban amininsa da bayida kamarshi yana cikin wani hali, hawaye yataru a idonshi. Ummi kam izuwa yanzu bata iya controlling din hawayenta idonta sunyi ja sosai, daga ranar da fanan ta tafi izuwa yanzu kullum a cikin kuka suke da damuwa. Haka abangaren su mama duk suna kallon labarai da suke yawo a gidajen rediyo da kuma social media, murmushin takaici kawai mama tayi aranta tanayiwa fanan addu'a. Yau Flight dinsu Mr azaad yatashi zuwa kaishi India suka sauka a asibitin Narayana superspeciality hospital babban asibitine a India da babu kamarshi komai nasu na musamman ne , babban part aka bawa Mr azaad acikin asibitin aranar da sukazo a ranar doctor Shankhar yafara dubashi . Bayan kwana uku Abba ya koma Nigeria, Fawwaz da yaseer ne zasu zauna tare dashi. Acikin wata daya duk sun rame amma damuwar dasuke ciki yadan ragu dukda bawai yafita azuciyoyinsu bane kawai suna dannewa ne domin sunyi tawakƙali. Duk bayan sati daya se sunkaiwa little twinkle visit a asibiti suna kallonta acikin kwalba haka ma suna kaiwa Mr azaad visit duk sanda sukaje sesunyi kuka , acikin dakin dayake ko ina yayi bi bangon yazana hoton fuskan fanan da yana kallo shi kadai za'a ga yana magana, amma yanzu abun da sauki. NASMINAYA. Tafiya takeyi cikin izza da mulki hade da jarumta, tana sanye da doguwar riga yellow color kanta dauke da crown ( hular sarauta) din sarauta, rigar yanaja abaya kuƴangu suna rike mata da bayan rigar domin yana da tsayi sosai , jikinta tako ina tasha ado da zinari, fatar jikinta se yalki yakeyi da idanunta , gashin kanta yana abaje shima an mishi kwalliya da gold sosai tayi kyau , fuskanta babu ko da alamar murmushi. Tunda suka nufo hanyar fa da ake mata bushen sarewa duk inda ta wuce se an sunkuya an gaisheta sannan bazasu tashi ba seta wuce tukun zasu iya mikewa , tana shigowa fa da duk suka zube akan guiwowinsu suna ɗiɓan gaisuwa agun babban sarauniya, zama tayi akan kujeran mulkin da aka ƙawa tashi da lu'ulu'u ta ɗaura ƙafarta daya kan daya daga musu hannu tayi alamar ta karbi gaisuwar sannan suka koma suka zauna , manyan sarakunan aljanu ne takowa ni bangare sunzo ne domin yi mata barka da zuwa , agefenta kuwa akwai kujeran gimbiya afroza da na yarima ahil se kuma na manya masu muƙami a nasminaya irinsu galadima abdud Shakur da jakadiya da sauransu , tashi sukayi suna gabatar mata da kansu , haka ranar sukayi shagali sosai domin farin cikin dawuwar sarauniyarsu abin sonsu. AFTER THREE MONTHS Gangarowa zeenat tayi daga upstairs tadan rame ga cikinta da yafara fitowa tana " ya areef wai kai da Hafiz baku gama bane nifa nashirya dan Allah kuzo mu tafi kunga su Abba sun riga da sun tafi " tayi maganar tana saukowa daga staircase din , areef ya ce " muje mungama muma" fitowa sukayi zuwa packing lot suka shiga motar areef yayi driving dinsu zuwa medical center. Ciki suka shiga ɗan karasawa inda su ummi suke , samunsu sukayi suna rike da baby a hannunsu se wasa sukeyi mata tasha hadaddun kayan baby Pink color , suna cikin farin ciki da sauri zeenat ta isa inda suke tsaye din ta ba ta fuska ta ce " amma ai bahaka mukayi ba , Ni ce fa nace aduk sanda akazo daukan twinkle I will be the first person to carry her amma yanzu kun bata min Abinda nake matukar jira" du ka dariya sukayi jin maganar da zeenat tayi Abba ya ce " to zee yanzu ma ai gata nan " miƙa mata twinkle ummi tayi ta karbeta tana washe fuska se kallonta takeyi, fuskar fanan sakk take gani ana twinkle tsabar yanda kamanninsu yaɓaci sede fatar Mr azaad ne da ita , idonta arufe hannunta na cikin bakinta tana tsotsa hawayen da yazubo daga idon zeenat ne yasauka akan kumatun twinkle mutsu_mutsu tafarayi kamar zatayi kuka taname bude idonta kadan sannan ta rufe , zaro ido waje zeenat tayi lokacin dataga kalar idon twinkle da karfi ta ce " laaah kuga ikon Allah idonta brown color ne irin na kaka me martaba " zubawa twinkle ido sukayi suna jiran suga ta bude idon nata aikuwa tasake budesu , tabbas idonta iri daya dana me martaba shi ta gado a kwayar halittar ido kenan sannan natama yafi nashi nata brown ne sosai , haka suka koma gida cike da farin ciki bayan awa daya zuwa biyu su suhaima sukazo ganin baby amma banda mama da baba . Baby girl gata nan yar lukuta da ita ga farin fata se karbanta sukeyi suna santin jaririyar sunayi mata photos suna turawa Fawwaz da yaseer da suke India su kansu sunyi farin ciki , adaren ranar me martaba da Fulani sukazo ganin jaririya aka tsayar da ranar suna nan da sati daya. Tun bayan tafiyar fanan basu sake tsinkayar kansu acikin farin ciki ba se zuwan twinkle ita kadaima insuka gani ransu nayi musu sanyi domin suna kallon fanan atattare da ita, har yau daya kasance gobe suna baba da mama basu sa twinkle a ido ba sede a hoto ne suhaima da ya usman suke nuna musu ita , su umma rahina da amira da ya al ameen sunzo saboda suna da za'ayi. INDIA NARAYANA SUPERSPECIALITY HOSPITAL Yau tunda suka tashi doctor yazo ɗan ganin ya yanayin condition din Mr azaad yake saboda yanzu ne yacika wata uku da sati biyu inhar de be samu lafiya a wannan lokacin ba to fa sede afara mishi shirye shiryen treatment din wata shida, yaseer da Fawwaz suna zaune akan kujera suna ganin yanda doctor din yake kokarin yin conversation da Mr azaad amma yakiyin magana ,yau haka suka tashi dashi ko irin dan sambatun da yake yi ma beyi ba yana zaune yabasu baya yana kallon waje daya, doctor Shankhar ya ce " Mr azaad don't you want to speak to me today?" Ko kallon inda yake Mr azaad beyiba doctor Shankhar yasake cewa " alright is okay, but do you know that you're a father now ?" kamar daga sama batare da sun taba tsammanin hakan ba kokuma tunanin haka ze faru ba , sukaji Mr azaad yabawa doctor Shankhar amsa da" Yes i know " shikanshi doctor Shankhar seda yaji kamar kunnen shine ya mishi gizo yasashi sake cewa " okay do you know you're a father right?" murya adaƙile kamar wanda ake takurawa cikin rashin sonyin magana ya ce" Yes i know and please don't disturb me " atare Fawwaz da yaseer suka ɗaga hannu sama suna godewa Allah matsanancin farin ciki suka shiga wanda baƙi baze iya faɗa ba zama sukayi kusa da Mr azaad fuskokinsu dana doctor duk na dauke da murmushi, congratulations doctor yayi musu sannan ya ce nanda One week za'a sallameshi , kafin doctor Shankhar ya rufe baki Mr azaad ya ce ko kwana ɗaya baze ƙara a asibitin ba , yanayin yanda yake magana kaɗai ma mutum yaji yasan ya canza sosai domin inyana magana ko ɗago kai ba yayi balle ya kalli me mishi magana miskilanci yaƙaru fiye da na da . Sallama doctor yayi musu yafita, yaseer ya ce " dude nayi farin ciki sosai da Allah yabaka lafiya" banza yayi dashi kamar be jishi ba se bayan minti goma ya ce " ina twinkle?" Fawwaz ya ce " an karbota a asibiti,gobe za'ayi sunanta" tundaga nan besake ce musu komai ba ya mike yashiga toilet bin bayanshi sukayi da kallo , ganin a ƙashi ɗari na halinshi nada yanzu ƙashi 90% yadawo, saboda dama shigowar fanan rayuwarsa ne yasa yarage amma yanzu sundawo fiye dana da dinma , suna magana yafito daure da towel a kugunshi kallonsu yayi be ce musu komai ba dan maganar ma wahala yake bashi , fahimtar abinda yake nufi da sukayi ne yasa Fawwaz mikewa yabude wardrobe a bangaren da kayanshi yaje ya fito mishi da jallabiya fa ra , karba yayi ya koma toilet din yasaka yafito fuskan nan adaure kamar wanda besan menene kalmar dariya ba arayuwarsa. Sude se aikin binshi da sukeyi da ido , Dan sunsan ko sunyi mishi magana ma ba kulasu zeyi ba hakan yasa suka zuba mishi ido kawai, kira ne yashigo wayar yaseer number Abba ne dagawa yayi suka gaisa sannan ya tambaye shi Mr azaad , girgiza mishi kai Mr azaad yayi alamar kar ya ce musu komai. Kamar yanda ya buƙata haka yaseer yayi yace mishi yana nan lafiya haka suka gama magana sannan ya katse kiran. " Fawwaz kayi mana booking flight ayau din nan zamu koma Nigeria". " okay " Fawwaz ya amsa sannan yayi musu booking flight s online karfe 6:00mp jirginsu ze tashi. https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8 🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺 Story & written by ✍️ MRS 🌹 ISHAM 🌹 ( Yar lelen Jarumai) *🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚* ⚜️📚J. A. W🖋️📚 THE END . *Wato Hausawa sunyi gaskiya dasukace komai yayi farko zeyi karshe haka zalika laifin daɗi karewa,ya Allah ka yafemin kura kuran da nayi acikin wannan littafin😭🙏 duk wanda na batawa rai yayimin afuwa ya yafemin dan ɗan Adam ajizine . Masu min addu'a da fatan alkhari ina godiya bazan taba mantawa daku ba, masu karfafamin guiwa Kuma ina godiya bazan taba mantawa daku ba domin kun ban babban gudunmawa nagode sosai Allah yabar zumunci* PAGE 6️⃣3️⃣ Batare da yan Nigeria sun san da zuwan nasu ba karfe shida nayi suka wuce airport jirginsu yatashi zuwa gida Nigeria, karfe hudu na asuba jirginsu yayi landing a gombe lawanti international airport, taxi suka shiga zuwa gida tunda suka taho a cikin jirgin babu wanda Mr azaad yayiwa magana acikin su har suka shiga taxi zuwa gida se hiransu sukeyi uffan be ce musu ba daga karshema surutun nasu ma ya fara damunshi yaja dogon tsaki suna jin haka sukayi shuru da bakinsu . *Horn me taxi yayi , fitowa baba me gadi yayi dan ganin su waye , ganin Mr azaad ne dasu Fawwaz yasa ya wangale musu gate yaname murnan ganin Mr azaad* Fitowa yayi yabarsu suna sallamar me taxi , shigowa cikin part din yayi jin motsi a kitchen yasashi ya tsaya daga bakin kofa ya ce " ƴata na wajen waye ?" Dasauri abu ta juyo jin muryan da batayi zato ba , cikin farin ciki ta washe baƙi " yallabai Azaad kaine alhamdulillah sannu da hanya , tunkwal na wajan ummi" yar harara ya watsa mata jin yanda takira sunan twinkle da tunkwal barin kitchen din yayi ya shige part din ummi dake bathroom taje dauro alwala zatayi nafila. Hawa kan gadon yayi yadauki twinkle dake baccinta peacefully yana kallon fuskanta da bashida maraba dana fanan yanajin tsananin kaunar twinkle aranshi ,ahankali yafurta " sleeping beauty" ya mannata ajikinshi tashi yayi dauke da ita ahannunshi yafice a bedroom din ummi ya nufi nashi bedroom din, kwantar da ita yayi akan makeken gadonshi yasake rufeta da blanket sannan ya shiga toilet yayi wanka da alwala yazo yafara nafilfilu yana addu'a Allah ya kare mishi fanan yakuma sa tadawo rayuwarsu be tashi na har seda aka kira asuba yayi Sallah sannan yahau gadon yashiga blanket din yajawo jaririyar shi kusa da shi yana kallon fuskanta,ahaka bacci yayi awon gaba da shi . Fitowar ummi daga toilet tadauro alwala kenan ta kalli kan gadonta fuskantar dauke da murmushi, gabanta ne yafadi lokacin dataga babu twinkle akai dasauri ta karasa izuwa gadon kamar wasa bataga twinkle ba hankalinta yayi matuƙar tashi ba shiri ta fice a part dinta saukowa downstairs tayi taga abu , abirkice ta ce " abu dan Allah akwai wanda kika gani yashiga part dina ne?" Murmushi abu tayi ta ce " eh ummi! Yallabai Azaad ne yashiga kuma naga fitowar shi da tunkwal a hannu " shuru ummi tayi jin abu ta ambaci sunan Mr azaad tunani tafara yaushe suka dawo to kenan hakan na nufin yasamu lafiya murna ne yakamata da sauri_sauri ta nufi part din nashi, bedroom tasamesu suna bacci zama tayi akan gadon tana shafa kanshi tanajin matsanancin farin ciki yana ratsata , ahankali yafurta " ummiii" batare da yabude idanunsa ba , " na'am son , fatan kundawo lafiya ?" tashi yayi yazauna ya ce " uhmmm" tundaga jin amsar daya bata ummi tasan he has changed completely ganin gaba daya fuskar shi ba walwala, riko hannunshi tayi ta ce " son kaga our little feena ko , babu abinda yarabasu da my feena, aduk sanda na kalli fuskar ta inaga ganin my feena atattare da ita, son yakamata yanzu kayi move on ko dan amanar twinkle da feena tabaka kazama uba na kwarai inkana cikin wannan yanayin taya ne zaka kula da twinkle? Hakuri shine Yakamata muyi ,mudauki dangana da juriyar rashin feena nasan is not easy for you my son, but you have to for the seak of twinkle ka ji " gyada mata kai yayi kawai batare da ya iya cewa komai ba yaname kwantar da kanshi akan kafadarta slowly ya ce" thanks ummi " ummi ta ce " son yaune sunan twinkle wani suna Yakamata asa mata " ajiyar zuciya Mr azaad yayi ya ce " Fatima za'a samata sunan wifey tun ranar da aka haifeta nayi mata huduba da Fatima " murmushi kawai ummi tayi tanajin dadi aranta a part din tayi Sallah. Karfe 7:00am aka raɗawa twinkle suna da sunan mahaifiyarta fanan, kafin gari yagama wayewa duk family kowa yasan Mr azaad yadawo cikin koshin lafiya , anty shayida tazo da yaranta yan biyu mata ta haihu satin da yawuce sukayi arba'in sunansu adeema da adeena ,haka anty zainab tazo tare da yaronta daya dawo daga egypt ya kammala karatu , yan uwa duk anzo suna su hairah da auta da amira tun karfe 8 suka zo gidan , haka mahaifiyar yaseer ma tazo , shigowa gidan baba da Abba sukayi suna part din Abba da wasu abokan abba suna hira Mr azaad yashigo da twinkle ahannunshi tana sanye da kayan jarirai me matukar tsada , zama yayi akan kujera rike da ita ya gaidasu suka amsa fuska asake Abba ne ya ce " to kabamu ita mu ganta mana" kamar baze bada twinkle din ba se kuma ya miƙawa baba ita , murmushi baba yayi yace " Fatima na biyu kenan , Allahu Akbar Fatima ta tafi Fatima ta dawo Allah yarayaki ya albarkaci rayuwarki" haka baba yadinga mata addu'a sannan yamikawa Abba ita shima karbanta yayi yana yi mata addu'a, yana zaune yana jiran su gama su bashi yarshi yayi tafiyarsa , karbanta yayi a hannun Abba . yafice abinshi ya nufi part dinshi afalo ya tsaya yana kallon katon hoton enlargement din hotonshi shi da fanan fuskantar dauke da ƙayitatciyar murmushi ta riƙe hannunshi tana kallon fuskanshi , shikuma yazagayo da hannunshi yana rike da kugunta fuskanshi asake dayan hannun kuma yakama kumatunta . Murmushi yayi lokacin daya tuna sanda akayi hoton , ranar da suka dawo daga shopping ne suka tsaya a garden suna hiransu gwanin sha'awa tashi sukayi zasu tafi yajawota jikinshi yayi yadaura hannunshi akan waist dinta dayan kuma kuma yariƙe kumatunta itakuma tana sakar mishi tsadadden murmushinta dake kara mata kyau , suna ahaka basu sani ba Fawwaz dabesan suna cikin garden din ba yashigo burgeshi sukayi sosai yasa yafito da wayarshi yafara daukansu hotuna,yayi musu hoto yafi guda goma ankara dashi Mr azaad yayi yagalla mishi harara ganin inda yake kallo ne yasa fanan juyawa tana ganin Fawwaz ne awajen dasauri taraba jikinta da na Mr azaad cike da jin kunya tabar garden din da gudu, da karfi Fawwaz ya ce " haba antynmu kiyi hakuri kidawo bari in baku guri " damkar kunnenshi Mr azaad yayi ya ce " wato labe kakeyi mana nida matata ko ? " Kara Fawwaz yasa yana " sorry Babban ya'ya wallahi kun burgeni ne yasa nake muku hoto" hararanshi Mr azaad yayi ya ce " kafin awa daya kazo min da enlargement din hoton in kuma beyi kyau ba zakayi bayani " yasakeshi yabi bayan fanan. Dariya fawwaz yayi ya ce " salon soyayyar ku na daban ne ya azaad da anty fanan Allah yabarku tare " ya ida maganar yaciro waya yakira layin wani photographer yatura mishi hotunan ya ce yanaso ya mishi katon enlargement nan da anjuma akawo. Haka yazauna a garden har aka kawo enlargement din da akayi rapping dinshi shiga part din Mr azaad sukayi da shi basa falo suna cikin bedroom dinshi , manna enlargement din akayi ajikin bangon falo yazauna sosai yanda suka fito sukayi kyau ajikin hoton Kamar a kirasu su amsa. Fitowa Mr azaad yayi yaga harsun manna enlargement din ya ce " Allah yataimake ka " murmushi Fawwaz yayi suka fita shida wanda yakawo hoton , jin sunfice ne yasa ta fito " habiby kazo ka nunamin wanne zansa" tayi maganar batare da ta lura da enlargement din jikin bangon ba , nuna mata yayi da hannu zaro manyan fararen idonta waje tayi sosai ta rufe baƙinta ta karaso gaban hoton tasa hannu ta shafa ta ce " yaushe akayi wannan hoton , wallahi yayi matukar kyau sosai" tafada tana rungumeshi. Murmushi yayi bayan ya gama tunawa yasa hannu yashafa hoton dede fuskar ta ya ce " i missed you so much baby rayuwa yamin zafi sosai da babuke aciki, ki kalli our little twinkle , na miki takwara sunanta Fatima ina fatan itama tazama jajirtacciya irinki me kyawawan halaye. Bazan taba cire rai da dawuwar ki ba ina nan ina zaman jiranki " Kuka twinkle tafarayi jijjigata yayi yana murmushi ya ce" karfa kidauko min rigimar mommynki " kamar tasan me yafada tayi shuru yana tsaye agaban hotonsu zeenat tashigo kallo daya tayiwa hoton bata sake kallo ba saboda tasan intaci gaba da kallo tasan yanzu zata fara kuka ɗan ji takeyi tafi kowa missing din fanan " ya azaad ummi ta ce kabada twinkle " ya ce" kifice ki bani waje bazan bada ita din ba" da sauri tafita mishi a part din shi tsaki yaja yashiga bedroom yazauna abakin gado har time din yana rike da ita, fadawa ummi yanda sukayi da Mr azaad zeenat tayi,ummi dama tasan zaarina mikewa tayi dakanta ta tafi part din nashi tace yabata twinkle be mu sa ba ya mika mata ita takoma falo tabawa umma rahina da sukazo da mama, mama ta dade bata shiga farin ciki irin na yau ba jitakeyi kamar tana rike da fanan ne , haka akayi suna nagani nafada baby twinkle tasamu kyaututtuka me tarin yawa ,an yanka manyan shanaye guda biyar da raguna anyi sadaka dasu komai anyi awadace karfe hudu na yamma aka watse kowa ya koma gidajensu, dare yayi yagama komai yazo ze kwanta zasuyi bacci twinkle tafara kuka rarrashin duniya yayi mata amma takiyin shuru daukarta yayi yanufi part din ummi tunkafin ya karaso ummi tajiyo kukan twinkle dama abinda take jira kenan saboda bataci abincin dare ba haɗa mata madaranta tayi a feda yana shigowa ta ce " dama nasan zaku dawo ai ta fada tana karban ta tafara bata madaran shuru tayi tanasha , gama sha tayi yakarbeta sannan yasa hannu ya kwashi kayan madaran nata ummi de binshi da ido tayi harya fice . Tunda twinkle tayi arba'in yafara fita da ita duk inda zashi yana rike da ita ummi da Abba sunyi mishi magana harsun gaji akan yadena fita da twinkle amma hakan be hanashi daukar yarshi ba duk inda zashi a gida ma sosai twinkle take samun kulawa kullum tana tare da ummi ko Abba ko suhaima da sauran yan gidan haka zeenat da yaseer suma suke zuwa gida akai_akai ɗan ganin twinkle haka su ya usman ma suna zuwa , haka duk sanda Mr azaad yatashi daga office yana biyawa gida da twinkle yakaiwa su mama ziyara . irin kulawar da take samu awajen familyn ta guda biyu na musamman ne takara girma kowa sonta yakeyi duk abinda suka gani na jarirai zasu siya mata shi musamman me gayya me aiki daddynta duk sati se yayi mata shopping din lafiyayyun kayan madaranta da kayan sawa daduk wani abinda yaro yake bukata ga dakin da aka ware mata anzuba mata kayayyakin wasa aciki , sau daya twinkle takesa kaya bata sake maimaitawa duk kayan data saka baa kara samata shi komai nata special ne kuma masu mugun tsada ,hatta kayan da zatasaka komai dinta. gata iya gata twinkle na ganinshi . Sosai ummi tayiwa Mr azaad fada kafin nan suka samu yadena fita tare da twinkle, tana da wayo sosai gashi bata da ƙiwiya saboda kowa tasan fuskarsu musamman yanzu da tafara zama daga zaran taga daddynta yadawo zata fara bude baki tana dariya hade da miko hannu yadauketa haka zedauketa yana dariya haka take tabasu nishadi agidan , safiyar yau zeenat ta tashi da naƙuda aka kaita asibiti ta haifi namiji kyakkyawa me kama da babanshi yaseer, seda suka dawo gida tukun suka kira family suka sanar dasu aikuwa sunyi farin ciki da jin labarin haka sukaje yi mata barka , bayan sati daya akayi suna aka yiwa baban yaseer takwara yakubu suka mishi inkiya da ashraff. bayan ta haihu da sati biyu hairah ta haihu amma bata iya haihuwa da kanta ba seda aka mata operation ta haifi ya mace taci sunan mama wato sumayya akayi mata inkiya da samha gida aka dawo da hairah saboda kulawa da ita kuma mama na iya kokarinta wajen kulawa da ita yanda Yakamata su ya usman anzama baba , Amira ce take ta ja da nata tsohon cikin haihuwa ko yau ko gobe , suhaima haryanzu shuru kuma daga ita har Fawwaz din hakan be damesu ba . Duk sanda Mr azaad yatafi da twinkle Company ma'aikata sun dinga yi mata wasa kenan saboda tana da farin jini ga rashin ƙiwiya , duk da Mr azaad baya basu ita saboda be yarda da kowa ba se Faisal, shi kadai ne duk sanda Mr azaad yazo da ita suke tare dama tun faɗan da ummi tayi mishi akan fita da ita yadena se de duk ranar Friday yana fita da ita . Amira ma ta haihu ta haifi na miji anyiwa baba takwara suna ce mishi musin duk anje suna Bauchi bayan angama suna kuma suka dawo . haka rayuwa yaci gaba da tafiya abubuwa nata faruwa aciki me dadi da akasin haka Mr azaad de yana bawa twinkle datayi wayo sosai kulawa shida yan gidan suna nuna mata gata , areef yafara zuwa aiki a kamfanin Abba , hafiz kuma ya zana papper anfara nema mishi addimission a gombe state University , kuma yasamu yafara zuwa. Allah yayiwa Alh Ibrahim tijjani rasuwa kuma yayi ta tonawa kanshi asiri daga karshe ya haukace sannan ya mutu , ga aneesa da ciwo yafara cin jikinta tadawo gida ta nutsu duk irin rashin kunya da wulakancin data dingayiwa mahaifiyarta Hajiya Zainab daga karshe ita ce, take kula da ita saboda uwa ce ita bazata iya kauda kai akan yarta ba dukda kuwa abubuwan datayi mata haka taci gaba da kulawa da ita sukaje asibiti aka daurata akan magani , alhamdulillah maganin yanadanyi mata aiki amma ba sosai ba saboda HIV yarigada yayi tsanani ajikinta yafara kashe duk wani garkuwar jikinta. Abangaren nusaiba da lukman suma suna nan suna rayuwar farin ciki da yaronsu namiji da ta haifa wata biyu dasuka wuce . __________________________________________ NASMINAYA. " Sarauniya kar muce zamu biyewa zuciya, kar ayi wannan yakin yanzu koda kuwa za'ayi muma mu rama irin abinda sukayi mana mu farmakesu a lokacin da basu sani ba nan ne zamu iyacin galaba akansu amma wannan sakon dasuka turo yanuna kancewa sun rigada sun shiryawa yakin kafin suka turo mana da saƙo" cewar wazirin nasminaya .daka mishi razanannen tsawa sarauniya tayi, a harzuke ta ce " yanda suka bukaci ayi wannan yakin dole za'ayi shi mudin ba matsorata bane , ai wannan nuna tsorone bamu cika ainihin jarumai ba inhar de bamu taresu gaba da gaba ba dole ne ayi kare jini biri jini , amma maganar kai musu hari batare da sun sani ba duk shirme ne "tafada tana kallon fuskokin ko wannensu kafin taci gaba da fadin " muma zamu nuna musu mudin masu nasara ne , hankalina baze taba kwanciya ba senaga bayan wa'yannan azzaluman dan haka kufara shirin yaƙi, sannan ku maida musu da saƙon cewa na amince da wannan gwabzawar da za'ayi , abashiyya ke kuma kitafi masarautar kusfah ki fadawa sarki habar muna bukatar dakaru saboda yaƙin dazamuyi . Dole wannan ƙaron ayi dayan biyu ko mu ko su " gimbiya afroza ce ta ce " yake sarauniyata tabbas iname goyon bayanki dari bisa dari amma muna bukatar dakaru masu matukar yawa, saboda wa'yanda zamu fuskanta kungiyoyi biyu ne kuma shu'umai ne marasa tsoron Allah " yarima ahil yace " nayarda da Maganar ki gimbiya amma fa kisani, masarautar nasminaya yafi karfin duk wasu kungiyoyi munada karfi dakuma kwarjini , kar ɗan sun kasance kungiya biyu ne su daga mana hankali da yardar Ubangiji munfi karfinsu" murmushi sarauniya tayi wanda tunda tazo masarautar ba ta tabayi ba ta ce " wannan gaskiya ne yarima ahil " suna cikin wannan tattaunawa wani tsohon dattijo yashigo fa da hannunshi rike da wasu abubuwa masu tsayi yarufesu da farin tufafi , dakatar da shi fadawa sukayi suka hanashi shiga yayi yayi subarshi domin yanada magana da sarauniya amma suka hanashi da karfi yayi magana " yake shugaba me adalci zasu kibawa wannan bawan naki daman yin muhimmiyar magana dake dan Allah dan Annabi" daga musu hannu sarauniya tayi suka barshi yashigo nuna mishi wajan zama jakadiya tayi , yazauna ya ce " shugabata zanso abamu waje" kallon su tayi suka ɓace yarage daga ita se gimbiya afroza da yarima ahil se jakadiya, galadima abdud Shakur,se waziri iya sune sukayi saura a fa da. Sarauniya ta ce " dattijo zanso kafadamin dalilin dayasa kakeson yin magana dani" mikewa dattijon yayi ya ajiye abun hannun nashi akasa yabude tufafin da ya rufe su dashi nan take wukake guda biyu suka bayyana, wukane da akayi domin yaƙi anyi shine da baƙin narƙekken dalma se yalki da daukar ido sukeyi, duk kallonshi sukeyi suna jiran ƙarin bayani daga wajan shi . " Ya shugabana wannan wukar ni na hadashi da hannuna domin bada nawa gudunmawan , a iya karfafa bincike na danayi shubumbum da tanzarzar zallar wuka babu abinda zeyi musu , shisa naje har birnin sin wajan uban gidana shine yafadamin abinda ze kashesu , bayan nadawo ne nahada wa'yannan makaman domin baki su nasan ze taimaka dan Allah shugabata ki karbi nawa gudunmawan " yafada yana zubewa akan guiwansa jinjina kai sarauniya tayi itada su jakadiya ta ce" na karbi wannan kyautar taka amma kafadamin amfaninsa me kyau , saura mara kyau din " zama yayi ya ce" shugaba ko min yaya kar ki bari wannan wukar ya yankeki domin yanda zeyi miki illa haka suma zeyi musu illa " murmushi tayi ta ce" Masha Allah " galadima abdud Shakur ya ce" tabbas sarauniya da yan fa da sunyi matukar godiya da kuma jinjinawa wannan gudunmawan naka " sosai dattijon yayi murna yayi musu sallama yatafi. Sarki habar yaturo musu da dakaru masu matukar yawan gaske haka masarautar nasminaya sungama shirya duk dakarun su domin fita yaƙi, masu kai saƙo wa kungiyar SATANIC da BAPHOMET duk sunje sunkai. Fitowa sarauniya tayi cikin azabebben shiga na yaƙi ga khairaty na hannun daman ta dakuma dakaru mata dasuke biye da ita, haka gimbiya afroza tafito itama cikin shigar yaki da yarima ahil ga shufan da shufaina yaran jakadiya da ita kanta jakadiyar duk sunyi shiga cikin kayan yaƙi. tsofaffi dakuma yara na masarautar sunatayi musu adduo'in samun nasara dakuma dawuwa lafiya . Hawa kan dawakai sukayi suka fara firewa akan dokunansu har suka dira a babban filin dazaa gabatar da yaƙin . Tanzarzar yazo da mugayen aljanun dakarun shi haka shima shubumbum yazo da nashi dakarun masu yawan gaske , yaƙi aka fara yi baji ba gani kowa burinsa yaga yayi nasara yakashe makiyinshi , anyi kashe_kashen da bazasu san adadin su ba , inka duba bangaren sarauniya kisa kawai takeyi idonta yarufe burinta kawai takawo bayan wa'yannan azzaluman dasuka addafi ƙasa, jikinta duk yayi gaja_gaja da jini duk wanda ya shiga hannunta kisan wulakanci takeyi musu ga drygon dinta dake feso musu aman wuta , haka abangaren gimbiya afroza itama kisa takeyi bana wasa ba , harta khairaty ba'a barta abaya ba duk da ankashe musu mutane dayawan gaske amma hakan besa sun sare ba acikin faɗane aka kashe yaron jakadiya abashiyya wato shufan, sannan ankashe galadima abdud Shakur sauran kuma anji musu mugun raunin da bazasu iyayin yaƙi ba duk sun jigata musamman abashiyya da khairaty sunji rauni sosai, sarauniya ganin haka ne yasa ta kara kaimi , isowa gabanta tanzarzar yayi yana fadin " sarauniya karkiyi zaton keda mutanen ki zaku bar nan araye , kiduba munci galaba akanku , dake da jaaazana duk nawane hhhhhhhhhhh" yakarasa maganar nashi yana muguwar dariya ,dirowa shubumbum yayi gabansu ya ce " karya kuke yi nine kadai zan mallaki jaaazana dan haka inkun isa mu gwabza mugani " yafada yana zaro sharɓebiyar wuka, duk su biyun sun mata kewaye ga ta yar karama agaban su , gwabzawa suka farayi suna kaiwa junansu hari cikin zafin nama sarauniya tafito da wa'yannan wukaken da aka bata , tayi wani irin tsalle da seda tayi sama tana ihu me karfin sannan tadawo ƙasa tana caka musu dukkansu biyu lokaci daya nan take shubumbum yazube awajan babu rai duk wasu mutanen shi nan suka fara marmashewa izuwa toka suna mutuwa , karfin hali tanzarzar yayi yazaro wukar acikinshi kafin sarauniya ta ankara ya caka mata acikin ta ya ce " dole sede dukkanmu mu mutu , tunda kikayi nasarar ka war dani abangon duniya dole kema ki mutu " yana karishe maganarsa yazube ƙasa jikinshi yakama da wuta ya marmashe yazama toka yabi iska , haka duk wasu mutanen shi haka suka dinga marmashewa suna komawa toka duk seda suka mutu yayi saura iya yan masarautar nasminaya kadai afilin dagan , ganin halin da sarauniyarsu take cikine yasa yarima ahil da gimbiya afroza da sauran dakaru suka nufota da gudu kamin su iso tafadi aƙasa babu rai atattare da ita zare mata wukar cikinta yarima ahil yayi kafin yadauketa yasabata a kafadarshi suka ɓace , duk wa'yanda suka jigata suma ɓacewa sukayi zuwa masarauta , duk wanda suka gansu sunsan cewa sunyi matukar shan gwagwarmaya a yaƙin da akayi suna shigowa aka fara buga kararrawar nasara nan take kuma lokaci daya masarautar nasminaya ta tashi da labarai guda biyu daya na farin ciki daya na bakin ciki, wato na kashe musu mutane da akayi gakuma sarauniyarsu da aka dawo da ita itama babu rai sekuma na nasarar dasuka samu . AFTER THREE YEARS ( bayan shekara uku) Misalin ƙarfe 6:30am na safiya _____ " twinkle ki tsaya kidena wannan gudun zaki fadi Please kitsaya " suhaima ce tayi maganar dake bin twinkle abaya itakuma tana gudu tana dariya , ashe ba iya suhaima ce take binta ba harda Fawwaz da Hafiz duk iya yinsu sunkasa samun nasarar kamata dan taki tsayawa gudu kawai takeyi , karasawa tsakiyar falon nayi dan nide sunan twinkle kadai naji suna kira amma ban gantaba seda nadawo cikin falon sannan nasamu ganin ta , yarinya ce yar kimanin shekara uku fara tas kamar baturiya yar duma_duma da ita jikinta tsabar yanda hutu yazauna ajikinta ko alamar ƙashi babu tana sanye da kayan baccin pjmas orange color kafarta sanye da takalmi slippers irin nasu na yara gashin kanta brown color ne an raba mata shi gida biyu an yi fakin dinsu idonta brown color fuskanta na dauke da manyan ido ga dogon hancinta tanada zara_zara eyelash , dan mitsintsilin baƙinta nadauke da red libs , babu inda twinkle tabaro fanan akama kamar fanan sanda take karama sede ita fanan gashinta baƙi ne sannan idonta ba brown bane , juyowa tayi tanayi musu gwalo da muryanta irin na yara ta ce " you can't catch me bazaku iyabaaaaa" tafada tana jan maganar kokarin cafke ta Fawwaz yayi ta zille ta bugi Center table dake dauke da glass flower nan take kwalbar flowers din yafado ƙasa ya fashe ganin tayi ɓarna ne yasa tazaro idanunta waje tasa hannu ta rufe baƙinta aikuwa da gudu tashige cikin kitchen tasamu abu na shirya mata breakfast dinta abu tana ganin shigowarta ta ce " tunkwal bazakije school yau bane ?" Cike da iyayi tarike kugu harda gyara tsayuwa kamar wata babbar mace ta ce " well anty Abu kinsan next week is my birthday so teachers dinmu sunbani hutun wata biyar " sa ke baƙi Abu tayi tana kallon twinkle jin abinda ta fada tana kokarin yin magana Hafiz yashigo yana haki ya ce " haba my baby twinkle kiyi hakuri ki tsaya kinga time fa na tafiya zakiyi letting a school" make mishi kafada tayi ta ce " am not going anywhere se bayan birthday party dina" dafe goshi Hafiz yayi sannan yayi kokarin kamota garin guduwa ta tunkude bowl din dake dauke da sauran fulawar da aka mata sandwich dashi yazube aƙasa sannan bowl dinma yafashe , tafi ce da gudu haka suka dinga wasan tsere_tsere da twinkle amma sun gagara kamata. Bacci yakeyi akan makeken gadonshi jin ƙarar fashewar glass dakuma hayaniya yasa shi gane da waye ake rikici bude sexy eyes dinshi yayi yazauna ya ce " my sturbon baby twinkle ta tashi kenan , wifey your daughter is very stubborn as you , kidawo kiganta yanda ta girma ga surutu kamar wata yar shekara biyar " yasan yanzu duk rigimar da akeyi da ita be wuce akan zuwa school ba , dan kusan kullum haka ake fama da ita akan maganar makaranta duk da batafi wata uku da akasata ba tana nursery one ,amma kwata_kwata twinkle batason zuwa makaranta tafiso tazauna agida tayi ta wasa da kannenta minal yarinyar suhaima se yaron zeenat ashraff da yake gidan wajan ummi . Tashi yayi fuskanshi ahade yasauko downstairs sanye da jallabiya hango twinkle yayi zaune akan kujera sukuma masu bin nata sunyi saronda suna zaune akan kujeran suna maida numfashi, tana ganin shi ta tashi da gudu tana " daddy ! daddy" daukanta yayi sama yanayi mata cakulkuli tana dariya juyawa yayi da ita zuwa part dinsu suna shiga ya ce " meyasa twinkle din daddy tafiye rigima ne? " cuno baƙi tayi ta ce " sorry daddy" toilet yashiga da ita yayi mata wanka yashafa mata lotion dinta sannan ya gyara mata gashinta yashiryata cikin uniform dinta ya sa mata sandal sannan yadauki school bag dinta ya ce " wow twinkle din mom and dad, yanzu se muje kiyi breakfast" ta ce " okay daddy " fitowa sukayi falo yana rike da hannunta tayi kyau gwanin sha'awa tsayawa sukayi agaban hoton fanan yaɗago ta sama kan kafadarshi ya ce " oya talk to mommy before leaving " hoton fanan ta mannawa kiss dede kumatunta da muryanta da maganarta be gama ƙwari ba ta ce" good morning mommy , i missed you , nida daddy muna jiranki bye zantafi school wish me all the best " ta fada tana kara mannawa hoton kiss murmushi kawai Mr azaad yakeyi , shima kiss din ya mannawa hoton sannan ya ce " wifey Ina matukar kewarki sosai ban cire rai da zaki dawo gareni ba muna jiranki nida little fanan " twinkle dake dauke akan kafadarshi da karfi ta ce " yessssssss daddy mommy takusa dawuwa daga tafiya , daddy kafada mata birthday party dina next week ne ?" Barin falon sukayi suka sauko upstairs nan ne ya bata amsa " twinkle shiiii surutunki is too much darling, mommynki tasan birthday dinki yazo , ta ce bazata samu zuwa ba se next month" Jin abinda yafada ne yasa ta ɓare ba'ki zatayi kuka jin wai mommynta bazata zo birthday party dinta ba , ummi da tasauko downstairs ne taji maganar dasukeyi yasa ta girgiza kai ta ce " my twinkle waye yafada miki mommynki bazata zo ba , zatazo kinji don't cry kinji kishiyata" da gudu taje ta rungume ummi tana dariya ta ce " Yes i know mommy na zatazo kuma sannan bazan yanka cake ba harse tazo zamu yanka tare " murmushin yaƙe ummi kawai tayi dan tafadawa twinkle hakane ɗan ta kwantar mata da hankali daukanta ummi tayi suka zauna akan kujera ta kira Abu takawo mata breakfast din twinkle anan tayi feeding dinta sandwich dinta da tea ga lunchbox dinta da aka shirya mata ɗan ita bata cin abinci makarantar da ake bawa student shisa akeyi mata nata kullum inzata tafi , tagama ummi tagoge mata bakinta da tissue, ta ce" grandma Ina my grandpa ?" dariya ummi tayi ta ce" grandpa yayi tafiya amma zedawo before birthday dinki " suhaima ce tafito hannunta rike da minal ta ce " ummi yau kinsan irin exercise din data samu sekinji tausayinmu , gashi yarinya nan narasa ya akayi ta iya gudu kamar wata yar tsere" tazauna tana magana hade da murmushi tana kallon twinkle dake kan cinyar ummi ga Mr azaad agefensu, dariya ummi tayi dan tanajinsu ta ce " to bagashi yanzu tasaku kunyi exercise ba " dariya ummi da suhaima sukayi gaishe da Mr azaad suhaima tayi ya amsa da " lafiya " daukanta yayi ya ce " muntafi " harsuka fita tanayi musu bye-bye suma sunayi mata fuskokinsu dauke da murmushi. Dropping dinta yayi a school har cikin class dinsu yakaita sannan ya koma gida yakoma bacci . Karfe 11:30 Faisal yakirashi yasanar dashi ankawo order furniture na company da sukayi a London" okay " kawai yace yakashe wayarsa yatashi yayi wanka yashirya cikin suit yafita zuwa Company dan ganin kayan da aka kawo. Ya Usman da hairah suna zaune afalon gidansu ga yarinyarsu samha tana wasanta akan keken yara ya usman ya kalli hairah ya ce " honey ki kalli samha da kyau " juyawa hairah tayi ta kalli samha din bataga komai ba ta ce " meye ajikin samha din ya usman?" ganin bata fahimci abinda yake nufi bane ya ce " bakomai kawai de naga Yakamata ace tasamu kanwa ko kanine yanzu fa two years take " lokaci daya hairah ta ɓata rai wanda shima seda ya fahimci haka ta ce " ya usman Ni fa daga kan samha bazan sake haihu ba saboda azaban danasha a haihuwar ta kaɗai ya isheni" calmly ya usman ya ce " Yes Honey nasani amma ko da daya ne semu sake haihuwa planning din ya isa haka in yaso kika kara daya se abar haihuwar haka kinji Please" " ah ah ya usman bakasan wahalar danasha ba ni kadai nasha wahala ta ɗan haka nide gaskiya bazan iya haihuwa ba shine kawai " tafada tana haɗe fuska , ran ya usman yayi matuƙar ɓaci ganin yana lallabata amma tana tuɓurewa sekace akanta aka fara haihuwa mata nawane suka sha bakar wahala wajan haihuwa bayan sun haihu din kuma suka sake dauka wasu cikin amma ita tace daga yarinya daya bazata sake haihuwa ba rai abace ya ce" hairah planning ko kinaso ko bakyaso se an tsayar dashi saboda ni inason yara inke bakyaso nagama magana ta " zuciya da shedan suna zuga hairah gakuma tarin yarinta ta ce" to kuwa sede kanemi wacce zata haifa maka yara amma nikam nagama " girgiza kai yayi ya ce" haka kikace ko? Shi kenan karki damu basekince innema ba zannemo kuma zan aurota zata haifa min adadin yaran danakeso " yana gama fadin haka yadauka car key dinshi yafita yabar mata gidan , kuka tafashe dashi jin wai ze sake aure kukanta tasha ma'ishi sannan ta wanke fuskanta tazo tadau samha suka shiga daki . " Ya yaseer Please inason zuwa gida kusan kwana na uku banga twinkle ba kuma nayi missing su ummi" dariya yaseer yayi ya ce " beb yanda kikace haka za'ayi anjuma da dare zamuje ! nagama ko tambayar ashraff bakyayi ko shi bakiyi missing dishi bane? " gyara kwanciyarta tayi ajikinshi ta ce" to ai nayi missing din shi shima in mukaje yau aiduk zan gansu " ya ce" okay,mubina tayi bacci ne?" Ya tambayeta karamar yarsu kanwar ashraff da take da shekara daya ta bashi amsa da" tayi bacci fah tun dazun " " bari inje office" mikewa sukayi atare tarakashi ya hau motar yafita. Yau auta bataje makaranta ba wai kanta na ciwo suna zaune suna hira da mama , areef da yatashi a office ne yabiyo gidan , yayi sallama mama ta amsa mishi ya shigo gaisheta yayi yazauna kallonshi auta tayi ta ce " ya areef ina wuni ?" shima kallonta yayi kafin ya ce " lafiya lau auta ya akayi yau bakije makaranta ba?" rike kanta tayi da hannu ta ce " yau da ciwon kai natashi se inji kaina yanason faɗowa " mama ta ce " ko kuma yau bakiyi niyar zuwa ba kawai " dariya areef yayi ɗan yasan bawani ciwon kai din da auta takeyi tafadi hakane ɗan kartaje makaranta ya ce " wai gaskiya ciwon kai be kyautaba sannu kinji " narai_narai tayi da ido ta ce " yawwa ya areef! Ina twinkle sarkin rigima da iyayi " yanda tayi maganar yayi matukar basu dariya mama kam girgiza kai tayi kawai ɗan ita tafi yarda da duk wani hali irin na auta shi twinkle ta gaɗo ga iyayi ga manyance da surutu , ga shi twinkle din tayi saurin magana Shisa insuka haɗu ga auta ga twinkle sede kawai tazuba musu ido , tsagaitawa da dariya areef yayi yace " mama kiji min ikon Allah wai kura ne zecewa kare maye , ke yanzu auta dan Allah har zakicewa wani yanada surutu da iyayi ?" ɓata fuska auta tayi ta ce" ya areef banaso kaga kai kullum seka tsokaneni, nide nasan banida surutu " sa ke tuntsirewa da dariya areef yayi ya ce" eh hakane kam bakida surutu mamar twinkle, birthday din twinkle ranar Friday ne zanje indauki aslam da kawarki Islam se inzo indauke ki daga nan se mu biya mu dauki samha da kuma yan biyun anty shayida adeema da adeena " yar dariya mama tayi ta ce" lallai sannunka da kokari areef" dariya shima yayi daga kai sama auta tayi tana yar tunani ta ce" oh my god ! inata nazarin gift din da zanbawa my twinkle as a birthday gift " mama kam mikewa tayi dan iyayin auta ya isheta dama bacci takeji ta shige dakinta tabarsu a falo se surutu take zubawa areef shikuma ya tsaya biye mata yanacin dariya. Karfe 5:00pm Mr azaad daga office dinshi shida Faisal suka wuce matrix dauko auta dan yasan sun tashi , suna isowa gida tafara kokarin bude kofar motar zata fito ɗan ta hango suhaima da ashraff da minal a gefen part din suna zaune akan lallausan carpet ga fruit dake wajen ga kuma kayan madaran minal damko hannunta Mr azaad yayi ya ce" twinkle inazakije?" nuna mishi su ashraff tayi ya ce" yanzu kibari kiyi wanka sekije kuyi wasan " to ta ce suka nufi part dinsu Faisal yabi bayansu da school bag dinta da lunchbox din , wanka yayi mata yasa mata riga da wandon jeans yasa mata hula yana gamawa ta manna mishi kiss a kumatu ta ce" bye-bye daddy " tafita da gudu hafiz na zaune afalo yaga wucewar ta ya ce" to anty twinkle se ina? " saurin da takeyi ne yasa bata tsaya mishi magana ba kawai tanuna mishi kofa tayi waje abinta suna zaune suka hango ta rungume suhaima tayi ta ce " i missed you mom one " dake haka take kiran suhaima zeenat kuma ta ce mata mom two shafa kanta suhaima tayi ta ce " missed you too my baby twinkle" bata fruit tayi dasuke a slice tafara sha hartace ta koshi sannan ta hau wasa da ashraff da minal, kan mangrib suka tattara suka koma Ciki ɗan yin Sallah. Bayan sallar isha yaseer, zeenat da mubina sukazo seda suka kai goma kafin suka koma gida. Ana gobe birthday party din twinkle Abba yadawo tunda yadawo ta koma part dinshi ita da sauran jikokin shi sauran da basa gidan kuma gobe za'a kawosu, Abba idan yakallesu sanyi yakeji har ranshi ganin shima yanzu yatara jikoki masu yawa alhamdulillah, kuma kaff cikinsu babu mafi soyuwa agareshi irin twinkle yana matukar sonta ko kuka tayi in yana nan tofa seyaji dalili son dayakeyiwa mamanta fanan ne yaƙaru yakoma kanta . Washe gari da safe bayan sunyi breakfast aka dauko kwararren me decoration yazo yayi decoration me masifar kyau a main falo white and pink color falon bakaramin kyau yayi ba , kamar yanda areef yafada haka kuwa yayi gidan anty amina yaje yakwaso aslam da islam anty amina ta ce se bayan sallar juma'a zatazo sannan yabiya yadauko auta ilham nan suka bude sabon fagen iyayi da surutu ita da islam ɗan itama ba baya ba wajan surutu areef de ta cikin madubi yake kallonsu shida aslam dasuke gaba daga nan yaje yadauki samha se sukaje gidan anty shayida yadau adeema da adeena , gidan anty firdausi sukaje suka dau junior sukayi gida , yau jikoki sun cika gidan hayaniya tako ina se barna dasukeyi acikinsu mubina ce kawai baazo da itaba itama se anjuma zasuzo itada zeenat da yaseer din . Bayan ansauko daga jumma'at ne anty amina da anty shayida sukazo atare , se yaseer da zeenat kowa ya hallara agida suna nan amma banda anty zainab ita sunyi tafiya garin dangin mijinta, anty amina ita da kanta tayiwa twinkle birthday cake pink color and white babba me three steps yasha decoration a saman an rubuta' happy birthday twinkle ' ga snacks da sweet din da akayi ga drinks da rago an gasa shi komai yazama ready afalon bayan sallar la'asar, anty shayida da zeenat sukayi musu wanka suka shiryasu cikin hadaddun kaya sukaje main falo suka zauna kowa ya hallara a falon harta Abba da kowa suna zaune ana jiran fitowar birthday girl, wanka akayiwa twinkle anty shayida ta shafa mata lotion hade mata gashinta tayi waje daya tayi fakin dinsu tabar mata wasu agaba suka zubo tayi mata light make up kayan barbie girl da ummi tayi mata order daga Dubai tasa mata gown din pink color rigar kansa abin kallo ne dauko mata wasu mayun takalma tayi masu kama da sandals amma yanadan hill kadan white color ta samata , tasamata dankunne dakuma chain din gold da bangules tasa mata crown silver color ta fesheta da perfumes, twinkle tayi matukar kyau bana wasa ba ta hadu iya haduwa , ta daurata asaman mirror kallon kanta twinkle tayi ta zaro brown eyes dinta ta ce " haaaaaa! Haka nayi kyau " tafada tana juyawa tana kallon kanta dariya kawai anty shayida takeyi mata sannan tadinga mata hotuna kala_kala sannan ta dauketa a kafadarta suka fito tunda suka fito suke kallon twinkle suna sakin murmushi musamman Mr azaad sauketa ƙasa anty shayida tayi nan take suka fara "woww baby twinkle kyau kenan " dariya itakuma takeyi wajanta auta taje tace " wow my twinkle you so gorgeous" tafada gyara mata zaman crown din kanta da maganarta na yara ta ce " thank you anty" wani abu ne yasoki Mr azaad azuciya sedayaji kamar yazubar da hawaye saboda zafin rashin fanan gaba daya jikinshi sanyi yakeyi aduk sanda twinkle ta tambayeshi yaushe mommynta zata dawo daga tafiya wani lokacin ya mata karya wani lokacin yama rasa meze fada mata . Mikewa sukayi dukka aka daura twinkle akan kujera yanda tsayinta ze iso cake din nata suka fara mata wakar " happy birthday to you! Happy birthday to you! happy birthday dear twinkle happy birthday to you" haka suka dinga mata wakar itakuma tana dariya, zeenat tace mata ta wure wutar candle din aikuwa haka tayi ta sunkuyo da karamin baƙinta tawure wutar candles din suka mutu nan sukayi tafi mika mata wuka Mr azaad yayi ya ce" now cut the cake " karba tayi harta daura wukar akan cake din seta fasa ta ce" aini nace bazan yanka cake ba se mommyna tazo " dam seda sukaji kirjinsu yabuga jin sabon rigimar da twinkle takeson daukowa Mr azaad ne ya ce" baby your mom is coming kiyanka cake din" turo baƙi tayi ta ce" nooo i won't cut it se mommy tazo" ummi kam shuru tayi takasa magana domin twinkle ta fama mata inda yake mata ciwo Abba ne ya ce" haba amaryata ki yanka cake din mommynki na hanya" " nooo grandpa" ta fadin haka ta fashe da kuka rarrashin duniyar nan sunyi mata takiyin shuru kuka takeyi harda ajiyar zuciya da shesheka tana kiran " mommy please come " duk jikinsu yayi sanyi tausayinta yakamasu run rasa mezasuyi mata tayi shuru, muryar Mr azaad na rawa dakyar ya iya cewa " twinkle kidena kuka , in angama birthday party zan kaiki wajen mommynki kinji " yanda yake maganar kadai duk wanda yaji yasan akwai babban ciwon dake damunshi acikin zuciyarshi yau kuma anfame mishi , twinkle na kuka ta ce " noooooooo" dafa kafadarshi yaseer yayi da shima jikinshi yayi mugun sanyi , suhaima da zeenat se hawaye suke yi . Cire crown din kanta tayi ta yardashi aƙasa tana cigaba da kukanta. Unexpected sukaga wutar gidan yadauke sannan falon yayi dubu dishi_dishi kawai suke iya gani tunani suka farayi meyake faruwa suda wuta steady ne baya ta ba dauke musu , zazzakar muryanta ne yakatse musu zancen zucin dasukeyi muryanta me dadi da amo yana rera wakar " happy birthday to you! Happy birthday to you, happy birthday dear my daughter happy birthday to you" ko amarfaki sukaji wannan muryar bazasu taba mantawa dame itaba koda kuwa shekara ɗari aka dauka bazasu taba mantawa da wannan muryar ba arayuwarsu ,yau gashi sunji muryanta shin amafarki ne kokuma gizo ne , rabon da su ji muryanta shekara uku da watanni kenan. Wutar gidan ne yadawo suna tsaye awaje daya sunkasa motsawa zuciyoyinsu nacike da al ajabi da mamakin abinda sukaji , daga kai twinkle tayi ta kalli upstairs da karfi ta ce " yeeeeeeeh my mommy is here" tafada tana saukowa daga kan kujeran tanufi upstairs da gudu , maida kallonsu sukayi upstairs din da twinkle tanufa , idanunsu ne yayi arba da fanan dake saukowa ta tunkaro twinkle itama tana sanye da abaya fara sol tayi rolling din gyale akanta , suman tsaye sukayi suna binta da kallo kamar a film musamman Mr azaad da idanunshi suka ƙada sukayi jaa. Da gudu tanufi twinkle da take kokarin haurowa upstairs din suka rungume juna fanan ta fashe da marayan kuka tana furta kalmar " am so sorry my baby girl ! am sorry mommynki yanzu ta dawo bazata sake barinki ba " ta fada tanayi mata kiss tanata kallonta tana kuka , yan dugul_dugul ɗin hannayenta tasa ta riƙe fuskar fanan tana girgiza mata kai sannan tasa hannu tana share mata hawayen fuskanta sake fashewa da kuka fanan tayi ta mayar da twinkle jikinta ta rungumeta gam tana jin dumin jikin yarta da tun ranar da ta haifeta batasake ganinta ba ko jin muryanta amatsayinta na uwa , wani irin sanyi ne taji yana ratsata yana shiga dukkan sassan jikinta maida kallonta tayi kan Mr azaad da ya kafeta da rinannun idonshi yana kallonta kamar a mafarki, twinkle dake manne ajikinta ne ta ce " mommy dama nasan yau zakizo birthday dina, I love you mommy" murmushi fanan tayi da muryan kuka ta ce " i love you too mommy's angel " raba jikinta da na twinkle tayi tana kallonta da itama ita take kallon da gudu auta ta rungumeta itama ta rungumeta atare zeenat da suhaima suka rungumesu suna kuka , hada baƙi sukayi wajan fadin " anty fanan kece dagaske kokuma gizo kikeyi mana dan Allah karki sake tafiya kibarmu " tana kuka itama ta ce " ba kizo bane zahirine nice ba wata ba" tabbas yanzu sun sake tabbatarwa da gaske ne fanan dince bawai gizo ba dagaske ita ce ta dawo rayuwarsu addu'a dasuka dade sunayi yau ga shi Allah ya amsa musu roƙonsu matsanancin farin cikin dasuka shiga baze taba misiltuwa ba duk wani bakin ciki dake zuciyarsu lokaci daya sukaji yatafi farin ciki yamaye gurbinsa, raba jikinta tayi danasu tanufi ummi dake zubda hawayen farin ciki ta rungumeta ummi ta ce " my feena nayi kewarki sosai" " nima haka ummina " tafada tana yar murmushinta dake kara mata kyau. Shafa kanta Abba yayi ya ce " alhamdulillah Fatima munyi matukar farin ciki da dawuwarki cikin rayuwarmu " ta ce" nima haka Abba " cikin tafiyarta kamar mahauniya ta nufi inda Mr azaad yake tsaye kamar wanda aka shuka a wajen , dukkansu ido suka zuba musu suna kallon wa'yannan masoyan na haƙiƙa da labarin soyayyarsu yakai matsayin a rubuta shi a tarihin duniya , kallon cikin kwayar idon juna suke yi bako kyaftawa idonta daya cika da hawayene ya gangaro ta ce" habiby ko de bakayi farin cikin ganina bane ?" sa hannunshi yayi yajawota jikinshi ya rungumeta gam kamar ze maida ita ciki yana mayar da hawayen dasuke kokarin zubowa daga idonshi ya ce" nafi kowa farin cikin ganin ki wifey dama inada yaƙinin za ki dawo gareni bantaba loosing hope ba " murmushi tayi ta ce" karfin son da nake maka ne yadawo dani gareka dakuma son danakeyi ƴata da ahalina Allah nagode maka dayasa ban mutu ba kasake bani dama na biyu domin yin rayuwa da wa'yanda sukafi soyuwa agareni " sake rungume juna sukayi suna fadawa junansu kalamai masu dadin gaske , yaseer da Fawwaz, areef se video sukeyi musu da hotuna gwanin burgewa sosai suka burgesu kuma sunyi matukar farin cikin ganin wannan ranar arayuwarsu, ganin sun manta da suna tsaye awajen ne yasa Abba cikin zolaya yayi gyaran murya dasauri fanan taraba jikinta dana Mr azaad kunya yakamata sosai dan tsabar wutar soyayya yasa ta manta dasu Abba na tsaye awajen sunkuyar da kanta ƙasa tayi sukuwa dariya sukayi kawai Mr azaad yariko hannunta yana kallonta kwata_kwata yakasa janye idonshi akanta gani yakeyi inya dena kallonta zata sake tafiya tabarshi , Hafiz ne ya ce " yeeeeh what are we waiting for let's celebrate" aikuwa dukkansu suka sa dariya harda Mr azaad,anty amina ta ce " ahh lallai yau kam Azaad na cikin matsanancin farin ciki rabon da muga dariya akan wannan fuskantar taka tun bayan tafiyar feena" murmushi kawai yayi yana sake matse hannunta cikin nashi daukan twinkle Fawwaz yayi ya mayar da ita kan kujeran. aka bata wukar daura hannunsu Mr azaad da fanan sukayi akan nata aka yanka cake din ta yanka tabawa fanan abaki tasake yanka tabawa Mr azaad abaki duk wa'yanda ke falon seda tabawa kowa abaki haka akasha birthday party sosai suka dinga mata hotuna da bata gifts masu masifar tsada , har kan mangrib sannan suka samu aka gama ana kiran sallah mazan suka tafi masallaci matan kuma kowa yayi , fanan a bedroom din ummi tayi sallah . Bayan sun dawo ne aka shirya dinner table sukaci abinci dare sannan suka dawo falo suka zauna , sallaman ya usman sukaji tare da na mama, baba da hairah suka shigo amsawa sukayi tundaga bakin kofa mama take kallon fanan kamar a mafarki jin muryan mama ne yasa fanan ta tashi dasauri tanufi mama ta rungumeta, mama da ke hawaye ta ce " dama nasan zaki dawo gareni fanan ga shi Allah yadawomin dake nayi matuƙar kewarki sosai" ta ce " nima haka mamana ,nayi farin cikin dawuwata" karasawa cikin falon sukayi suka zauna suka gaggaisa suna taya junansu murna dawuwar fanan, suna tsaka da farin ciki sukaji sallamar me martaba da waziri se galadima ga kuma Fulani zama sukayi aka sake sabon gaisuwa , dama suhaima ita takira ya usman ta sanar dashi fanan ta dawo sannan takira yan Bauchi nan ma ta sanar dasu , Fawwaz kuma yakira me martaba yafada mishi. Bude taro da addu'a Abba yayi , me martaba yayi ya kalli fanan dake zaune aƙasa akan carpet kanta a ƙasa ya ce " Allahu Akbar lallai babu abin bautawa da gaskiya se Allah shi kadai ,me kowa kuma me komai meyin yanda yaso ah lokacin dayaso , muna me gode mishi da yadawo mana da yarmu Fatima cikin rayuwarmu. Munyi matukar godiya da hakan kuma munyi murnar dawuwarki Fatima , kuma alhamdulillah kinje kin isar da sakonki wajan ganin bayan wa'yannan azzaluman kin ƙa war dasu adaron ƙasa Allah ne kaɗai ze biyaki domin kinyi na mijin kokarin kin taimaki rayuka da dama , lallai ke din cikakkiyar yar baiwa ce medauke da abubuwan mamaki Allah yayi miki albarka ya albarkaci rayuwarki da zuri'arki " du ka suka amsa da" Ameen ya Allah " sannan me martaba yadaura daga inda ya tsaya " Fatima zamuso ki fada mana yanda Allah yayi kika dawo domin mun san ke din kinrigada kinzama shugaba a masarautar nasminaya " duk ka sa kunne sukayi ɗan sunason suji ya akayi wannan lamari yakasance,gyara zama fanan tayi tafara basu labarin yanda akayi ta dawo " aranar da muka fita yaƙi nayi nasarar kashe su dukkansu biyu na tarwatsa kungiyar nasu , sede tanzarzar yayi galaba akaina yasokamin wukar danayi amfani dashi wajen kasheshi wannan wukar kuwa bakamar sauran wuƙaƙe yake ba yana fitarwa mutum duk wani karfi dayake jikinshi sannan seyasa maka guba ajikinka sekuma mutuwa , dasauri suka daukeni suka maidani fada aka kira ainihin wanda ya ƙirƙiri wannan wukar, shi yadingamin magani har na tsawon shekaru uku da ikon Allah se nasamu lafiya amma sede jaaazana dake cikina ya gurɓace adalilin wannan gubar dake jikin wukar , seyazamana babu wani karfin iko atare dani , ganin hakane yasa natarasu gaba dayansu afada nasanar dasu kan cewa ni yanzu babu wani irin taimako da zan iya basu amatsayina na sarauniyarsu domin narigada narasa karfina dan haka nace zanbawa yarima ahil mulkin nasminaya amma duk se suka nuna sude ahaka sunason inci gaba da mulkarsu dakyar de nasamu na nusar da su illar haka , sannan na naɗa yarima ahil amatsayin sabon sarkin nasminaya. sannan nayi musu bankwana nadawo duniyar bil'adama " Jinjinawa wannan lamarin sukayi sude tunda abinda tajeyi ta aiwatar, su sunyi murna da dawuwarta . Baba ya ce" tabbas baa cire rai da rahamar Allah ga shi da yardar shi kindawo garemu " haka sukayi ta murna awannan rana sun dade suna hira sannan kowa ya koma gida cike da tarin farin ciki. Dare yayi Mr azaad yafita ɗan,tana kwance ta sa twinkle dake bacci akan makeken gadon bedroom dinta agaba tana kallonta duk suna sanye da kayan bacci, taji anbude handle din bedroom Mr azaad ne yashigo hawa gadon yayi ya ce" kina kallon twinkle din mune ?" Murmushi tayi ta ce" ehh bana gajiya da kallonta habiby " shima murmushin yayi ya ce" komai nata irin naki fuskanta, yanayin maganar ki rigimarta everything, sede surutunku ba iri daya bane na mommynta auta ta dauko " dariya sukayi atare ta ce" habiby ban taba tunanin zan dawo inci gaba da rayuwa daku ba ashe inada rabo da kasancewa da mijina da kowa nawa" sa hannu yayi yatallafo habarta ya ce" nikuma bantaba cire tsammani da damuwarki ba kullum zuciyata rayamin take komin daren dadewa kina nan zuwa gareni " yagama maganar yana ɗaukarta kamar yar baby ya ce" ina bukatarki shekaru uku ba wasa ba " dariya tayi sukafito yana dauke da ita yajawa twinkle kofa yarufe yanufi bedroom dinshi kwantar da ita yayi akan bed yayi mata rumfa da faffadar kirjinshi sannan ya hade bakinsu waje daya , wani irin hot romance suke yiwa junansu kowa na kewar dan uwansa burinsu awannan daren su gamsar da kansu domin kewar dasukayi yanada matukar yawa , cire mata kayan jikinta yayi ya cire nashi yafara sex da ita itama tana mayar mishi da martani, ina yar goge kwallar tausayinsu danaga abin nasu yanason wuce gona da iri kawai nafito narufo kofar ahankali dan kar in dakatar dasu nashige bedroom din twinkle nayi kwanciyata anan. Rayuwa me dadi Ako wani ɓangare sukeyi cikin farin ciki da jin dadi twinkle me mommy's dayawa ga ainihin mommynta ga kuma su suhaima da zeenat, Mr azaad da fanan da twinkle, Fawwaz da suhaima da yarsu sukaje Bauchi kai musu ziyara sunyi murna sosai da ganinsu satinsu daya suka dawo domin Ramadan yakawo kai saura kwana hudu . Haka suka gabatar da ibadar Ramadan sallah yazo akayi bikin sallah cikin nishadi da tarin farin ciki, lokacin zuwa aikin hajji nayi kuwa Mr azaad yabiyawa kowa harda su mama suka tafi suka je sukayi ibadarsu . Bayan sundawo ne aka rabawa dangi da abokan arziki da mabukata tsara ba. Wata rana Mr nazaune a office dinshi sakatariya jamila tashigo ta ce wata ta ce tanason magana dashi da kamar zece ah ah sekuma yace " abarta ta shigo " bayan ta shigo ne yaga aneesa ce duk tabi ta rame kamar ba itaba ta koma saliha,shi inbama yanzu da yaganta ba mantawa yayi da ita , neman yafiyarshi tayi akan takurawa rayuwarsu da tayi sannan ta ce yabawa fanan itama hakuri , sannan ta sanar dashi itama tayi aure ta auri amjad, yatayata farin ciki sannan yace mata bakomai yayi musu addu'a samun zaman lafiya. Babban private hospital Mr azaad ya ginawa fanan ga doctors din dayasa mata, akasa mishi suna ' fanan hospital' yabatashi kyauta sannan ya bata manyan motoci guda biyu , bakaramin murna tayi ba tayi mishi godiya sosai family's sunje sungani harda doctor ammar da matarshi sunje sungani kowa se Allah sanya alkhari yakeyi mata . Hairah tayarda zata sake haihuwa dan tanason ya usman tana kuma son abinda yakeso ga kuma tsoron kishiya datakeyi hakan yasa suka dakatar da planning suka cigaba da kulawa da yarsu samha gwanin burgewa suna nunawa junansu so da kauna. Haka Amira da ya al ameen da suke da yara biyu musin da hamnat suke rayuwarsu cikin jin dadi suna nunawa junansu soyayya. Abangaren nusaiba da lukman ma suma sede Muce Masha Allah. Zeenat da yaseer ma soyayya suke sha kamar ba gobe ga kuma yaransu ashraff da mubina. Haka suhaima da Fawwaz suna nunawa junansu kulawa da soyayya ga minal se son barka. Abangaren love bird kuwa nasu kankat ne ruwan soyayya kawai suke sha basa iyayin awannin batare da sunga junansu ba ko kuma sun jin muryan junansu ba soyayyar su na matukar burge kowa zazzafar soyayya Mr azaad da fanan sukeyi sunayiwa junansu tsabtacciyar soyayya. Hafiz da areef ne sukaje suka samu abba suka sanar dashi suna son anema musu auren auta da Islam Abba yace bakomai kar su damu bayan tafiyarsu ne Abba yakira baba yasanar dashi areef ya ce yanason anema mishi auren auta baba yace yabashi ita nan gaba kadan inta kara girma se ayi auren nasu. Bayan sungama waya yakira sirkinshi wato mijin anty amina yasanar dashi dan wajen shi Hafiz yanaso anema mishi auren Islam daddyn twins ya ce yabashi ita. Abba yasanar dasu yanda sukayi bakaramin farin ciki sukayi ba. Wata rana Mr azaad yana driving da kanshi ,ya wuce wasu samari masu faskaren itace daya daga cikinsu ne yayi murmushi ya ce " Allah yaci gaba da kareka yallabai azaadu " dayan yace tofa kaikuma aina ƙasanshi dariya saurayin yayi ya ce "shine wanda nabaka labarin yayi hatsari na taimake shi din nan " dayan ya ce " Allah sarki Allah yarabashi da makiya" haka sukaci gaba da hiransu sunabin bayan motar da kallo ,duk maganar dasukeyi Mr azaad yajisu dukda nisan dasuke dashi domin ya wucesu sosai nan ne ya tabbatar da baiwarsa na ji yadawo, reverse yayi yakoma wajansu yayi packing yafito babu kyama yamika musu hannu sukayi musabaha ya ce " naji hiranku da kukayi kaikuma nagode sosai na ceton rayuwarta da kayi " dukda sunyi mamakin ya akayi yajisu amma sunyi farin cikin rashin nuna kyamar dabeyi ba agaresu dukda suna talakawa, cikin mota Mr azaad yashiga yafito da bandir_bandir din kudade dasukafi million daya yabasu yace gashi ku raba sannan yabasu katin shi yace gobe suzo Company shi yadaukesu aiki , tsabar murna harda kuka sukayi suna gode mishi murmushi yayi kawai yatafi. Bayan ta tashi daga asibiti ne taje gida suka sha hira da mama da baba dan ta samu be fita ko ina ba yau sundade kafin taje makarantar su twinkle ta daukosu ita da ashraff da minal suka koma gida dukkansu apart din suhaima tabarsu ta wuce part dinsu tayi wanka tana daure da towel tashiga bedroom din Mr azaad akwance ta sameshi dagashi se boxers alamun be dade da fitowa daga wanka ba jin kamshin turarenta ne yasanar mishi da shigowarta , batare da ya dago kai ba ya ce " naji kun shigo gidan nan keda su twinkle shine kika barta agurin suhaima " dariya tayi tana hawa kan gadon tayi ta kwanta ajikinshi ta ce" to mijina dan baiwa majiyi abin alfahari na inasanka sosai" sa hannu yayi yazame towel din jikinta yana binta da mayen kallo " wifey gaskiya kedin na dabance komai naki na daban ne musamman ma wannan breast din naki suna burgeni sosai " yafada yana shafasu fari tayi da ido ta ce " habiby kaima ai na dabanne shisa kullum nake sake sonka mijina " salon yanda take mishi maganar yasa sha'awar ta dayakeyi yasake tashi ya ce " wifey yau din nan zanyi ajiyar kanwa ko kanin twinkle acikin wannan shamulallen cikin naki" yafada yana shafa cikinta ya gangarar da hannunshi zuwa mararta yana shafawa , lumshe idanunta tayi tana cize libs dinta romancing juna su sukeyi sosai " baby you're very sweet my wifey , please fadamin meye sirrin gaskiya dole inyiwa anty amina kyauta, inason kamshin jikinki wifey I love you so much " yayi maganar da wata iriyar murya wanda dakajita kasan yana cikin matsananciyar sha'awa, ita kanta wutar sha'awa ya hanata yin magana , suka fara shayar da junansu dadi suna gabatar da sunna. Haka rayuwa taci gaba da tafiya soyayya da kulawa suke nunawa junansu me ban sha'awa dakuma tafiya da zuciya, twinkle kullum tana tare da mommynta da daddynta , rayuwa me dadi suke gaba daya familyn suna cikin matsanancin farin ciki da annashuwa tare da kaunar junansu. *To Alhamdulillah Alhamdulillah ala kulli halin nan nakawo karshen wannan littafin nawa NIDA PATIENT DINA sai mun hadu daku acikin sabon book dina me suna ASHE ZAMUGA JUNA karku bari abaku labari ɗan wannan littafin zezo muku da salo kala_kala* *Ɗinbin godiya da tarin jinjina a gareku yan NIDA PATIENT DINA gaisuwar ban girma da tarin jinjina da fatan alkhari yan NIDA PATIENT DINA comments section group, Ina matukar godiya da comments dinku dasuke karamin karfin guiwa sosai da sosai Allah yabar zumunci da qauna* *Sakon jinjinawa agareku manya_manyan members na masu karamin karfin guiwa ta hanyar min ruwan hot comments dinku kullum bakwa gajiya tabbas bazan manta daku ba* 1. Maman shurem 2. Eysher raj 3. Maman afra 4. Maman widad 5. Maman junior 6. Esha kitchen 7. Rabi b bello 8. Oum Maryam 9. Umamah Abbas 10.bilkisu Billy 11.baby maimuna 12. Aysha kwaishe 13. Anty rukkaya 14. Mum basma 15.mhizz dejeer 16.hauwa 17. Halima zinder 18.snacka craving 19. Jermy 20.ninarh malle 21.ummu shaheed *Da sauran wa'yanda bansamu kiran sunan su ba wallahi You really means alot to me in harde kasan kanamin comments tom Ina matukar sonku sosai nagode da karfin guiwa Allah yabar zumunci* Jinjina agareku admins na masu kokari ina matukar godiya Allah yabar zumunci. Duk wa'yanda nayi wa laifi atarayanmu a NIDA PATIENT DINA yamin afuwa.