[13/2 07:11] 💕Ummieekhaleel 💕: 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 1✨✨✨ Bismillahi Rahmanin Rahim On the authority of Abu Hurairah, who said : The messenger of Allah said : "Part of someone's being a good Muslim is his leaving alone that which does not concern him." fine Hadith narrated by Termithi and others Abu Hurairah  (May Allah be pleased with him) reported: The Prophet (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "He who believes in Allah and the Last Day, let him show hospitality to his guest; and he who believes in Allah and the Last Day, let him maintain good relation with kins; and he who believes in Allah and the Last Day, let him speak good or remain silent."[Al-Bukhari and Muslim **************************** Buckingham Palace, City of Westminster... 3 years ago.... A hankali ya bude idanun shi sai kuma ya sake rufewa da sauri. Haka yayita kifkifta ido har idunsa suka kai agogon bango dake cikin karamin Cubical dinsa. Zumbur!!  Ya mike tsaye tareda tangal tangal alamun zai faɗi kasa. Innalillahi wa inna ilayhi rajiun yayita nanatawa, “Shikenan na gama yin latti” ya faɗa tareda wucewa bayi. A gurguje yayi wanka tareda saka kaya, Dukda bala’in lattin dayayi saida ya sha Coffee saboda baya wasa da breakfast. Acewarsa breakfast is the most important meal of the day. Haka yayi ta sintiri cikin cubical dinsa har ya gama shirinsa tsaf sai ya rufu kofa ya fita zuwa inda za shi. “Good Morning Miss Beckinsale?” ya faɗa ma next door neighbour dinshi Wanda zata kai shekara saba’in a duniya amma bata taɓa aure ba. “Good Morning sunshine, How are you?” ta faɗa tana fari da ido. Dama haka take tsokanar sa wai  batayi aure ba saboda dama tana jiransa ne yazo ya aureta. Tanada bala’in fara’a kuma sau da dama yana rakata irin su cocktail ko Fund raising haka. “I’m fine” ya faɗa tareda danna elevator ya shiga cikin azama sanadiyar lattin daya riskeshi yau. Dama yadan kishingida ne bayan yayi sallar asuba domin yayi 5mins sleep to shine bai farka ba sai 8:45am. Gudu yakeyi akan sidewalk babu k'akk'autawa, yana yi yana bige mutane tareda fadin "Sorry please"  haka har ya kai wajen traffic, tsayawa yayi yana ganin yanda motoci ke wucewa da gudu. Daya lura basuda alamun tsayawa sai kawai ya kutsa dukda ba'a nuna alaman Pedestrian su wuce ba. Kuuuu kake ji wani mota ya kusan kadeshi, haka yayi kokarin komawa baya amma sai ya zame ya fadi wanwar a kasa, tsaki yayi tareda mikewa, shi kuma mai motan ya fito da sauri don yaga yanayin shi. Sai ya fada ma mai motan, "Sorry please, I'm in a hurry" shi kuma mai motan yace, "Damn you Man, you can get urself killed with these attitude"  sai yayi kwafi ya koma motarshi. Ko ajikinsa tuni ya cigaba da gudu, yana yi yana duba agogo. "09:24 Insha Allah I won't miss the train" ya fada a fili. Har ya kai subway yana gudu tareda tsallake stairs uku ko hudu. Ikon Allah train din bai tashi ba mutane sunata shiga tunda tafiya ta Subway yafi idan mutum yayi latti bcs babu traffic yasa baima fita da motarsa ba.         💦💦💦 Sanye take da wani multi coloured long chiffon gown mai guntun hannu, saita hadashi da karamin Blazer Silver mai stones wanda bazai kai cikinta ba, k’afanta kuwa Gucci hightop ne mai spikes kuma yana daukar idanu. Headphones din Beat By Dre ke kunneta kuma ta rataye dogon Vintage jaka a gefen damanta. Hannunta kuwa wayar handset ne tana latsawa tareda yin murmushi. A hankali take tafiya zata shiga speed train din, a sanya sanya take komai sai gashi yazo da gudu yana so ya shiga bcs in a minute train zai tashi. "Hello Miss can you hold the door for me please"  ya fada mata. Ita kuma Wanda tuni tana sauraron wani abu daga wayarta bata ma San yana yi ba, koda ta shiga kofa yana kokarin rufewa sai ya hada da jakarta. Shi yaji dadin abin saboda zai iya kustawa amma bata nuna tana so tayi hanzarin cire jakarta ba balle ya wuce. A hankali take abinta har ta samu ta cire sai kofan yayi karap ya rufe jirgi ya tashi. Da gudu yabi jirgin yana fadin" Nooo no no no no" sai kuma ya tsaya ya soma boxing da iska tareda dukan k’arfen dake wurin da hannunshi, zafi yaji mara misaltuwa  saiya soma ihu yana tsalle, daga bisani ya lura kowa kallonshi yakeyi, kwafa yayi sai ya kame a gefe. "Dama idan za'a hada abu da mata sai rai ya baci" ya fada ma kansa. Abin haushi baiga fuskarta ba saboda tayi wrapping irin na Arabs, at least koba komai zai saka ta a list din mak'iyan sa bcs wannan hassada ce k'arara. Haka yayita zama har 10mins later inda wani train din yazo suka ware. Victoria Tube Station ya sauka saboda shine nearest station to Palace din Queen Elizabeth II, tafiyan mintuna 7 yayi ya kai main entrance. Tsaye take a queue din Palace din, dama dream dinta ne taga inda Queen Elizabeth take, Daddy ya fada mata idan CGP dinta yakai 4.80 zai kaita country of her choice for summer kuma ikon Allah ta buga 4.82 Tabi duk wani protocol din security saboda yau akwai wani gagarumin taro dat is significant to yan England, yaune Her Majesty zata bada yabon girmamawa ga best students din kowane University din country dinta. Tana shiga ciki idonta ya hangi royal standard flag din wajen a sama, murmushi tayi tareda fadin "yes the Queen is around"  saita shiga ta fara kalle kallen su statue din wajen masu bala’in kyau. Shi kuma yana isa ya gyara kayan jikinsa, grey suit ya saka tareda farin riga sai kuma  purple tie, yayi adjusting dakyau tareda mak’ala links din hannun rigarsa sai ya soma taku daya daya kamar bashi ke gudu dazu ba. "Da zuwa da wur wuri gwara zuwa da wuri" ya fada yana murmushi. Sai yaje inda security yafi yawa zaiyi signing in. Mika masu babban yastan shi yayi suka daura akan na'uran su saiga sunan shi ya fito. NAUFAL HUSSAIN BELI  representing Oxford University, "that's correct" ya amsa masu. Gaba ki daya suka ce "Congratulations Mr Hussain, welcome to the Great Buckingham Palace" Tun dayake karatu bai taba zuwa wajen ba kuma bai taba tunanin zaije ba, yana tafe yana kare ma wajen kallo sosai. Furanni irin su hydrangeas, tulips, lily da kuma Roses tako ina ga kuma wasu anyi customizing sunar Elizabeth dashi. Security din wajen sun saka Bearskin hat, riga mai Ja da ratsan blue sai kuma bakin wando.  Da MI6 gasu birjik, suma FBI da CIA ba'a barsu a baya ba saboda John Kerry na America da dignitaries din England sun hallara.          💦💦💦 A cikin fadan  kowa yana tsaye za'a fara taro, masu karban yabo na daga gefe, kid’a na tashi a hankali mai dadin ji irin na al’adar yan England. Duke and Duchess sun fara saukowa daga wani katafaren stairs mai dumbin tarihi. Yaransu biyu suma ana saukowa tare. Kida ne ya chanza alamar a natsu Her Majesty zata fito. Ta sauko an fara taro anata bada awards har an kai turn din Naufal, "For Oxford University we present the brilliant Naufal Hussain Beli from Bauchi State Nigeria" Raf Raf Raf suka rinka tafa masa, shi kuma cikin natsuwa yaje wajen Her Majesty yayi bowing head dinshi tareda shaking hannunta "Thank you so much your Majesty, I'm really honoured"  ya fada ita kuma tace, "The pleasure is mine Mr Hussain" saita yi murmushi wanda ya bayyana mata hokararta. Ya juya zai koma wajen tsayuwarsa saiga wata  yarinya idon shi ya hango mai, ya lura tafi kowa tafi a cikin audience. Murmushi ya soma yi yana tafiya tareda kara kallonta. Yana wajen tsayuwarsa ne ya lura da headphones din dake wuyanta, a hankali ya rinka ware ido dan yaga ko zai ina gano kayan jikinta. Zuciyarshi ta soma aiki da sauri sauri tana kokarin kawo mashi wasu tunani marasa amfani, wani siririn murya ta raya mai "kila fah yarinyar dazu ce..." da sauri ya kawar da tunanin tareda korar shedan saiya sake kallon bangaren ta. Kaddara ta riga fata saboda anan yaga Multi coloured kayanta tareda jacket mai stones wanda keta walkiya. anan take bakin cikin mara misaltuwa ya riske shi. Kwafa yayi tareda juya kansa, "Bad luck! har nan kika biyo ni?" ya tambaya kansa rhetorically. *Special shout out to my best friend turned sister, Aisha Sulaiman aka Momyn Jawahir. Allah ya kara dankwan zumunci* *All rights reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [13/2 07:12] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 2✨✨✨ Abu Hurairah (May Allah be pleased with him) said: The Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "Do you know what is backbiting?" The Companions said: "Allah and His Messenger know better." Thereupon he said, "Backbiting is talking about your (Muslim) brother in a manner which he dislikes." It was said to him: "What if my (Muslim) brother is as I say." He said, "If he is actually as you say, then that is backbiting; but if that is not in him, that is slandering."[Muslim]. ************************* Haɗa girar sama dana k’asa yayi bai k’ara kallon inda take ba, Jira kawai yake a gama taro yaje ya sameta su gwangwanje. Bcs irin sanya sanya data keyi ba k’aramin wahala zata shaba musamman idan ta aure namiji mai gajen hakuri. Ita kuma bawai tana wani concentrating bane, abu takeji a headphone dinta which she is addicted to Kuma shine wanda ya dauke mata hankali, idan taga ana tafi sai itama tayi. Sam bata lura da cewa nata yafi na kowa k'ara ba. Ana gama taro kowa yana kokarin tafiya sai ta sidada ta wuce upstairs da sauri kafin a ganta, dama she is obsessed with paintings da kayan art works tunda  Fine Arts take karantawa a Jami’a Paintings din Van Dyck da Reubens ta fara gani a wani corridor, a hankali taje ta rinka kallonsu tana yabawa da structures ɗinsu. Yanda aka k'erasu ya bala'in burgeta. “I wish I can paint like this” ta fada ma kanta. Daga nan sai ta soma touring cikin Palace din sai ga na Vermeer, poussin da kuma Claude. Ta tsaya a gaban painting ɗin tayi su selfie tareda bude snapchat dinta. “HI Snapchat, I'm in the Buckingham Palace, look at these amazing priceless paintings” saita nuna paintings ɗin, haka ta rinka having fun abinta hankali kwance. Bata bar wajen ba saida tayi su Instagram videos kuma tayi posting hotuna a whatsapp da sauran chats haka. Yanda take abinta a hankali kai zaka zaci yanga takeyi amma yanayinta ne kawai. Komai a sanya sanya takeyi kuma abinda Naufal ya tsana kenan wajen mutane. He prefers swift individuals. Ta hange wani daki wanda akwai sculpture ɗin Canova zata je gurin sai security masu Bearskin hat suka dakatar da ita tareda faɗin, “Sorry ma'am, restricted area” Locacin yayi daidai da k’arar wayanta, ta saka hannu zata dauka “ahn ahn Ma'am, please no calls allowed”  suka k’ara fadi. Kwafa tayi tareda murguda masu baki, tana tafe tana turo baki tareda Jan kafanta karap karap duk ta ishe kowa. Kafin ta isa wajen building ɗin sai wayar ya tsinke, tsaki tayi ta fara neman signal tareda returning call ɗin. Har ya shiga an fara magana, “kiyi sauri ki bar wajen nan ki sameni a…..” bata k’arasa jiba sai ga yara sunzo da gudu da kites suna wasa, tureta sukayi komai ya tarwatse saida ta ɗuka tabi ta roro battery ɗinta da Sim card. Shi kuma Naufal ware ido yayi yana kokarin yaga inda take a cikin hargitsin mutanen, amma bai ganta ba. Shifa bai dandara ba saboda ya riga ya sakata a black list ɗinshi. 1- Ya tsana mutum mai nawa. 2- Sai wani tafi take tana zak’ewa da aka kirashi sai kace ya santa. “Shifa shishigi ne baya so”ya faɗa a ranshi. idonshi ya mayar Kan Electric door amma babu ‘Bad luck’ babu dalilinta. “Dama nasan cewa tana nan tana nawa ta wani bangaren bazan ganta ba” Tsaki yayi ya koma wajen sauran awardees sunata raha tareda fadin zasu hadu a after party din da akayi don karrama su. Amma dukabinda sukeyi hankalin shi baya jikinshi. Ya fito daga building ɗin zaiyi answering call, sai ya hangota daga nesa sai faman zuba sauri takeyi, daga alama zata tafi ne. “Ashe kin iya aiki da jiki”  ya fada ma kansa. Sassarfa ya soma yi yana kokarin zuwa inda take. “Excuse me Ma'am, you just dropped this” Wani security ne ya dakatar da ita yayinda ta zubar da passport dinta a kasa wajen fito da wallet ɗinta. Murmushi tayi tareda cire headphone ɗinta don taji mai zai fada da kyau. “FADEELA ABBAS BELLO” abinda ya fada kenan bayan ya bude ciki, “Thanks so much, but I need to go”  ta faɗa mishi tareda nuni da hannunta alamar ya bata. Bai bata nan take ba ya tsaya yana wasu dube dube, haushi ya kamata saboda bataga dalilin da zai yi mata bincike ba. “Have a nice day Ma'am” ya fada sai ya mika mata tareda daga mata gira, ita  kuma, “Thanks, you too” tace tareda murguda masa baki, mayar da Headphone dinta mazaunin shi tayi saita cigaba da tafiya cikin sauri wannan karon harda Sassarfa. Dayaga security mai Bearskin hat ya tsayar da ita ba k’aramin jin dadi yayi ba, amma kuma sai ga ta yanzu ta soma gudu. “Excuse me Please”  ya faɗa yayinda yake binta amma headphone ɗin kanta bazai barta taji ba. “kila ma ba wani abun Kirki take ji ba” ya faɗa ma kanshi. Ita kuma tana isa bakin titi ta tare Cab ta shiga abinta, suka soma tafiya. "Hello!  hello!!!" yayita nanatawa amma bata jiba. Text din Momy ta gani "Na hada miki kayanki, ki same ni a airport" sai tayi murmushi  tareda mayar da wayan jakarta. Shi kuma Naufal dayake bai iya ɓoye frustration dinshi ba, “Nooooooo no no”  ya rinka faɗi saboda yana isa titi cab ɗinta yana tafiya. Sai kawai yayi kwallo da wani empty cup din coffee tareda naushin iska. Hannunshi yana Kan waist ɗinshi yana fuzgar iska mai zafi kamar mayunwaci zaki yana kallon yanda motar ke tafiya. “Ma’am I think that guy was talking to you” Cab driver ya faɗa. Ita kuma ta juya don ganin wanene amma yana mata dishi dishi still bata San ko waye ba.  “Don't worry I don't know him” ta faɗa tareda gyara zamanta. “where I'm I taking you to?” ya tambayeta. “Home” ta amsa mashi. Kallonta yayi cikin rashin fahimta tareda faɗin, “And where is home?”  murmushi tayi saita ce “Nigeria, sorry please. I meant to say Heathrow Airport” *Hankali baiwa ce kuman idan Allah ya baka ka gode masa. Special shoutout to my triplets, Ummiee Rilwan (Fatimah), Ummiee Jafar(Faizah) and Ummiee Khaleel (Aisha)* *All rights reserved* [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 3 ✨✨✨ On the authority of Abu Hurairah, who said : the messenger of Allah said : "Do not envy one another; do not inflate prices one to another; do not hate one another; do not turn away from one another; and do not undercut one another, but be you, O servants of Allah, brothers. A muslim is the brother of a muslim: he neither oppresses him nor does he fail him, he neither lies to him nor does he hold him in contempt. Piety is right here-and he pointed to his breast three times. It is evil enough for a man to hold his brother muslim in contempt. The whole of a muslim for another muslim is inviolable: his blood, his property, and his honor." Related by Muslim. ************************ *Bauchi....* *Present day....* Conference hall ne mai madaidaicin girma irin wanda kujeru zaici mutane akalla 24 sai wani katafaren brown table a tsakiya. Babu abinda ke mosti sai TV dake manne a bango kuma shima yana mute ne. Sanyin AC yana sirara kuma ga kamshin room freshener tako ina. Mutane bakwai ne zaune, fararen fata guda uku sai sauran bak’ake. Zaman mintuna 54 cifkenan da sukayi. Babu wanda yace komai, daga mai haɗa girar sama dana k’asa sai mai latsa wayar handset. Tsaki ya buga a Karo na uku, “Please we need to get started” wani bature ya fad'a yayinda ya k'ara kallon Rolex wrist watch dake manne a hannunsa na hagu. Sai wani bak’in fata ya chapke tareda faɗin, “Please be patient Mr Pearson, I'm sure Mr Hussain is on his way. He is not usually dis late” Wani bature daban yace, ‘Mr Jibrin call him again bcs our flight is for today” sai yayi kwafa yana tattara takardunsa. Aminu Jibrin yace, “Excuse me please”  sai ya tashi ya fita tareda wayarsa a hanunshi. Ya fita chan wajen balcony yayi facing Kan titi yana danna wayarsa tareda ware ido ko zaiga zuwan Naufal. Sanye take da wani Indian attire, wani shararren designer dinsu na chan mai suna 'Gaurang' yayi. Ta fito daga wurin Tailor dinta mai Suna Ismail a kasuwan Wunti. Ranta a ɓace take tafiya cikin yanayinta na sanyi, tunani kala kala ke zuwa mata saboda ta dau alwashin idan suka haɗu sai tayi mashi rashin mutunci, Ankon course mate ɗinta da bakinta ya gabato nanda 8days amma yana mata hide and seek saboda bai ɗinka ba.  Tana tafe tana turo baki saboda ta bala'in jin haushi, yanda yan shagon Ismail sukeyi tasan cewa yana ciki kila ya ɓoye a cikin shargi ne. Wak’ar ‘The weeknd’ na Starboy ke tashi kuma shine ringtone ɗin Naufal, yasan sarai wake kiransa amma bai dauka ba. Haka wayar ya gama rero wak’a ya tsinke. Gudu yakeyi babu k'akk'autawa, baisan dalilin daya sa yayi muguwan latti ba, ko sallar asuba sai 9:30am yayi. Kunya abinma yaji dukda babu wanda ya ganshi sai mahillicin shi. Koh tie baiyi knotting ba kasancewar zasuyi meeting da turawa akan Merger kuma he is suppose to look smart and collected. Haka gashin kanshi kacha kacha bai taje ba, a birkice yake yin komai saboda ko kwallan rigarsa tana mak'ale a cikin wuyarsa. K'arar wayarsa yaji, da gefen ido ya kalla yaga still Aminu ke kiransa, "idan kai maye ne, toh fah saidai Kaci yan gidan ku"  ya fada, sai da wayar ta kusa tsinkewa kafin ya dauka, "Guy I dey road, no disturb me abeg" ya fada yana dariya. Shikuma Aminu ya k'ulu sosai saboda baiga abin barkwanci akai ba bcs wanna shine biggest contract da kamfanin su suka samu tun buɗewarsa. Tsaki yayi saiya kashe wayan. Bai koma cikin conference room dinba yana tsaye yana haki kamar wanda yayi gudu. Tana kokarin tsallaka titi shi kuma Naufal ya kauda kanshi for less than 3 secs don ajiye wayar shi. Kuuuuuuu ya taka barki yayin daya kusan kad'e wata baiwar Allah. Ita kuma dama taga hanya babu kowa cikin yanayinta na Sanya Sanya ta shiga zata tsallaka. Earpiece ɗinta na fama yana kunnen ta yasa bataji zuwan mota ba. Kawai wani faduwan gaba taji tareda juyawa, "dam" gabanta ya fadi data lura baifi taku uku mota ya nik'ata ba. Salati ya rinka jerowa tareda addu'oi kala kala wanda ya dace da wanda bai dace ba, dama shi yanada tausayi sosai. Earpiece dinta ta cire daga kunnen ta tana kokarin mayar wa cikin jakarta. “Bad luck” abinda ya fada kenan tareda tsaki, dukda three years ago ya ganta last amma bai mance da fuskarta ba. “Bazata bar saka wannan abun a kunnen taba koh?”  a fusace yayi parking motarshi da kyau tareda fitowa. Dama ita ta koma baya inda ta fito bayan abin ya auko. Jikinta yanata rawa zufa sai keto mata yakeyi, hannu na karkarwa duk ta fita hayacinta. Dama akwaita da bala’in tsoro kamar farar kura. “Ke jakar ina ne?” abinda ya faɗa kenan yana nuna mata yatsa kamar zai tsokane mata ido, bata amsa shiba illa hawaye daya soma malalo mata daga fuska. A duniya tashin hankali ne abinda yafi ɗaga mata rai. Dama tun yau tanata samun mood swings kamar mugun abu zai faru da ita, “Dake nake, nace ke wace irin gara ce da zaki saka Earpiece akan titi?”   Ita bataga abinda yasa ya hasala haka ba yana wani tsuma, accident do occur besides da gangan bazata shiga ba. “Ni jakar garin ubanka ne” ta amsa idonta kur a nashi. A fusace ya ɗaga hannu zai mareta. “kada ka kuskura ka taɓa ta idan ba haka ba zamu taru muyi maka shegen duka da sai ka raina kanka yanzu yanzu”  wasu masu saida fruits suka fada. Yanda yaga babu wasa a tareda su saiya mayar da hanunshi kasa, “ku dama masu kuɗi sai ku rinka tink'aho da titi kuna cewa kada kowa ya hau, toh bari kaji titi na gwamnati ne saboda haka dole muyi amfani dashi” K’arar wayarsa yaji sai yayi tsaki ya koma wajen motarsa, 10 missed calls ya gani. Gabanshi yayi mummunan faduwa saboda ya shafa'a ya mance da conference ɗin yana nan yana so yayi faɗa da Bad luck. Wani call din ya shigo sai ya ɗauka da hanzari, “I’m sorry man, abu ya tsayar dani but......”  Aminu  bai bari ya karasa magana ba yace, "Calm down, ka cigaba da abinda kakeyi saboda Mr Sutter yace ka raina shi kuma ya wuce Abuja”  din din din abinda Naufal yaji kenan a kunnen sa. Cilla wayar yayi cikin mota sai ya fara dukan motar da hannu da kafa, sai ya kuma kifa kanshi akan motar yana mayar da numfashi da sauri sauri. “Bad luck” ya faɗa da karfi daya tuna itace sila. A guje ya koma wurin daya barta saboda yanzu babu mai kwatanta a hannunsa, sai yayi kas kas da ita. Idan ya gama sai sauran mutanen suma su dake shi. Yana isa wajen babu ita babu dalilinta, “Bad Luck” ya faɗa da karfi saboda gaskiya ko wacece yarinyar nan duk inda taje saita jawo annoba..... Jiki babu kwari ya koma motarsa, bai tada ba illa kifa kai dayayi akan steering yana tunani kuma zuciyarshi yana mai k'una. "wannan wani irin tashin hankali ne? Yanzu meye abin yi? Allah ya shirya ki idan zaki shiryu" “Sam Sam baiwar Allah bakiji dadin halinki ba..... At all” *All rights reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 4✨✨✨ It was narrated that Abu Usaid, Malik bin Rabi'ah, said "While we were with the Prophet(), a man from the Banu Salamah came to him and said: " O messenger of Allah, is there anyway of honoring my parents that I can still do for them after they die?' He said: "Yes offering the funeral prayer for them, praying for forgiveness for them, fulfilling their promises after their death, honoring their freinds and upholding the ties of kinship which you would not have were it nor for them.'" (Hasan) ***************** Wani na annabi ne ya taimaka ma Fadeela ya samo mata keke napep ta hau bayan Naufal yaje wajen motarshi. Tana tafe tanata kuka, still jikinta bai bar rawa ba, dukta susuce. Ita abinda yafi ɓata mata rai bai wuce wai ita ce zatayi faɗa da namiji wanda ko mata bata gama yi dasu ba. Dama daga shagon Ismail, Yelwa zan wuce inda makaranta mu yake watau ATBU, amma yanzu gida zan koma dukda inada test amma bazani ba bcs I'm too angry to write. Muna isa GRA inda gidan mu yake nayi kuka har murya na ya fara dishewa, “Allah ya isa” na rinka faɗi a raina saboda bazan yafe mashi ba. A daddafe na fito duk jiri na ɗibana saboda bana ko ganin gabana, “nawa ne kudin?” Ki barshi kawai Hajia ai naga abinda ya faru, Allah ya kiyaye na gaba. "Amin" na faɗa mashi kawai na wuce saboda banida energy ɗin wani magana. “Assalamu Alaikum” na faɗa saina wuce upstairs, ko tsayawa na gaida Momy banyi ba, which ba d’abiana bane. “Wa'alaikumus Salam” ta amsa sai ta bini da ido tana karantan yanayi na. Har na kusan kaiwa karshen stairs saita ce, “Yaki dawo nan, lafia bakije school ba kuma kin shigo kina wani kumbure kumbure?” Ban amsata ba saboda hawaye dake fito min, haka na tsaya kuma ban yuja ba. “Bada ke nake magana ba?” kafin na amsata saiga Daddy ya fito daga ɗakin shi cikin black suit and grey tie daga alamun yanada court case Kasancewarshi na Judge. “Ni matsa min daga hanya, mahaifiyarki tana miki magana kin wani kyaleta. Uwa dai ba abin wulakantawa bane!” Daddy ya faɗa yayinda yake saukowa. Saura kaɗan daya hankaɗe ni saida naja baya, nan take na fashe da kuka saboda duk laifin azzalumin mutumin nanne wannan abu ya faru dani. Wucewa ɗaki nayi da gudu na kwanta a gado na dauko wani babin kukan. Sai ga momy ta shigo ta zauna akan gadon, janyoni tayi jikinta saita ce, "Auta waya taɓa min ke? Na hana shi sukuni a garin Bauchi” Sarai nasan halin Momy kuma tanada connections, k'akalo murmushi nayi saina ce, “ Momy fault dina ne, naje tsallaka titi sai mota ya kusan bigeni” dariya momy tayi sosai kafin tace, “ Ho sarkin shagwaba, ni banga abin kuka ba. Anyway tunda kin dawo zo na aike ki gidan Jawahir kinsan Jiya mijinta ya dawo akwai sak'ona a wajen shi. Momy kallon Fadeela takeyi saboda sam bata iya fushi ba, most of the time tana abu kamar goyon kaka aside rashin kunyar, “Allah ya bata mijin wanda zai rinka tausayinta”momy ta fada a ranta yayinda take fita. 💦💦💦💦 Shikuma Naufal wani dabara ya fad'o mashi, gwara yabi Mr Sutter Abuja ya basu hakuri. Haka kuwa yayi, zura gudu yakeyi akan titi yayi hanyar Abuja. Dama idan wajen gudu ne to fah ya kware saboda zaka sha drifting din motoci ne. Yana isa Nicon hotel ya fito daga parking lot, tunani kala kala yakeyi tareda neman mai zai fada masu, yana so ya shiga reception din kenan saiya hango Mr Sutter, Mr Pearson da Mr Targeyan sun fito da kayansu zasu tafi. Da sauri yaje ya sha gabansu, "Please I'm very sorry for my actions, I take full responsibility, please just consider this merger with my firm and I promise you will never regret it" hannun shi biyu yana rok'on su. Fuskarshi tsantsan nadama ke nunawa. Mr Pearson yaji tausayinshi amma Mr Targeyan yafi zafin kai, juyar da fuskarshi yayi kamar baima san Naufal na wajen ba, dama tun farko baiso ayi abu da bak'in fata, a cewarsa basuda rike alkawari. Mr Sutter ya kalle Mr Targeyan which har yanzu yaki murmushi, "since he owned up to his mistakes, I think we should consider him but this time around we will reevaluate the first contract. We will give you 6months trial bfr signing the agreed documents" Murna mara misaltuwa a wajen Naufal, “wow dats what I’m talking about” ya fada yana shaking hannu su, kwata kwata baisan me zai faru dashi ba idan yayi losing deal din saboda anyi relying dashi a firm dinsu gashi uwa uba shine Bread earner(Mai tallafi) ɗin gidansu... Okay let’s go inside and talk, Mr Targeyan ya fada wannan karon yana murmushi harda dafa shoulder ɗin Naufal. Bayan sunyi meeting ɗinsu suka had’a da lashe lashe, daga bisani kowa yayi hanyar sa. Su suka wuce airport inda zasu tafi Newyork, shi kuma ya dauki hanyar Bauchin Yakubu saboda shi baisan kwana a wani waje idan ba gida ba. Daukar wayarsa yayi ya kira Miemie kanwarsa suka sha hira dukda shirme take zuba masa sanadiyar tanada psychotic disorder(Ciwon Hauka) but a duniya bashida kamar Miemie. Farin cikin sa kenan, kuma duk wani zafin nema dayake yi saboda health dinta ne yasa ma bashida sha’awan aure. Acewarsa baya so mace tayi distracting dinsa while sister dinshi batada lafiya. Ko yanzu ba maganar kirki sukeyi ba, babbaka dariya takeyi saboda tun shigowar wannan makon yan dariya suka motsa. Dama turn by turn ne, akwai yan dariya, yan shiru, da kuma idan ta samu lafiya kadan. Jira yake ya koma Bauchi gobe su wuce Psychiatric Hospital na Kaduna. Dama idan deal ɗin baiyi working ba dole su canza mata asibiti. Bayan ya kashe wayan sai ya kira Aminu amma har ya gama k’ara bai dauka ba. Murmushi yayi saboda yasan fushi yayi dashi. Text ya aika mashi na, “Calm down please, I know na ɓata maka rai but don’t worry everything is going to be alright. Ka mance nine Naufal?” saiya tura mai. *Wanene Naufal?* *Birthday shout out to my dearest Kawa Aysha kirya. Allah ya baki more meaningful years yasa muje har Isiala Ngwá(lol) musha biki..... Amin. Calm down everyone it's her birthday* #NiDaDiyata *All rights reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 5✨✨✨ Abu Barzah Al-Aslami narrated that the Messenger of Allah (s.a.w) said "The feet of the slave of Allah shall not move [on the Day of Judgement] until he is asked about five things: about his life and what he did with it, about his knowledge and what he did with it, about his wealth and how he earned it and where he spent it on, about his body and for what did he wear it out." (Da'if) ************* Naufal Hussain Beli matashi ne mai jini a jiki ɗan shekaru Ashirin da tara a duniya, kuma ɗan asalin Bauchi ne a wani gari da ake kira Shira. RTD Engr Hussain Beli shine mahaifin Naufal kuma yanada mata biyu. Hajia Sarai wanda ake cema ‘Mama’ sai kuma Hajia Saudatu suna ce mata ‘Anty Saudah’. Mama tanada yara biyar a duniya, Nabil ɗan kimanin shekara 32years kuma yana aiki a Airtel Networks a Abuja. Yanzu haka yana auren Safeena yar garin Katsina ne amma a Abuja take zama, sun haɗu sanadiyar supervising wani promo da akeyi a University of Abuja which a locacin ita student ɗin school dinne. Sunada yaro ɗaya mai suna “Mohammad Eemaad” Daga nan kuma sai Naufal, sai kuma “Amatullah” yar kimanin 25yrs kuma tana aure a Gombe da yaronta guda daya “Abdulrahman” Amatullah tanada bala’in zafi bata daukan raini at all, kuma itama tanada raini sosai, ga kuma kyaman talaka musamman yanzu data aure mai k’unban susa. Daga ita sai kuma Abla yar 22 years wanda yanzu take serving a NEPA, itace dai mai sauk’in kan ɗakinsu. Batada matsala at all saboda tanada daɗin sha’ani. Sai kuma autan mama wato yan matan 100l ‘Bilqees’ itama footstep ɗin Abla take bi amma bata kai Abla kirki ba. Anty Saudah tanada yarinya guda d’aya mai suna “Laurat” amma suna kiranta “Miemie” saboda sunan maman babane. Bayan haihuwar Miemie da wasu shekaru sai suka lura tayi developing wasu strange ɗabi’u, an kaita asibiti shine akayi masu confirming tanada ciwon Hauka watau Psychotic disorder. Ansha wuya wajen neman mata magani, sunyi zirya a Psychiatric Hospital Kakuri, Kaduna. Kuɗaɗe masu ɗunbim yawa ake kashe mata kuma still bata warke ba. Jefi jefi yake yi mata tuburan. Hajia Sarai watau Mama ta tada bala’I akan bazata zauna gida d’aya da Mahaukaciya ba, dayake locacin Abba yanada k’umba susa, saiya siya wani gidan gona haka mai dan girma. Duka yaran Mama basu ji daɗin abin ba saboda Miemie yarinya ce mai shiga rai, musamman Naufal da Abla, shi saida ya koma gidan da zama, jefi jefi yake zuwa gurin Mama. Yanzu haka Miemie tanada shekaru goma sha hudu a duniya, kamar yanda bature ke fad’in first impression matters, to haka rayuwar Miemie yake. Idan kuka hadu for the first time ta nuna bata sanka, toh fa saidai kayi hakuri. Amma idan tayi maka fara’a zaku shirya sosai. Ana cikin yi mata magani sai Abba yayi retire daga wajen aiki. Ko karatun Naufal bashi ya ɗauki nauyin sa ba, Gwamnatin jihar Bauchi ta bada scholarship ga yara masu hazaka, kuma cikin sa’a Naufal ya samu wannan damar. Shine yaje Oxford University inda ya karanta Architecture kuma yanzu haka yana cikin best Architects a Nigeria. Kasancewar Naufal ya shaku da Miemie yasa ya dauki nauyin Medical bills dinta. A duniya yanzu bashida wani buri face yaga ta samu sauki bata tuburan ko doke doke, bcs idan lafiya ya ɗan zo mata har special school ana kaita domin tayi karatu. Yanzu haka duk sati biyu sai an kashe mata 70k, yasa da ya kusan losing deal ɗinshi dasu Mr Sutter ranshi ya bala’in bace bcs baisan ya zaiyi bill din Miemie ba tunda sun samu ta rage hauka tuburan, saidai kawai tayita kyalkyala dariya ba gaira ba dalili. Naufal tun fil azal yanada tausayin ɗan Adam, baya so yaga mutum cikin pain. Ko bai sanka ba ka rokeshi alfarma zaiyi maka koba duka ba. Abinda baya so a rayuwarshi shine “Nawa” da Sanya Sanya saboda a cewarshi “Time is money” He is very swift Idan zaiyi abụ yasa ake ji dashi wajen aiki, kuma idan yanayi bawai rawar kai yakeyi ba. Bashida surutu sosai musamman idan bai sanka ba toh bazai ce uffan ba, daga eh saidai ah ah Har ku gama magana, gashi yasan addini daidai gwargwado kuma yana kokarin kare hakkin shari’a. Bak’I ne sosai mara misaltuwa, amma bak’inshi yanada kyau kuma skin dinshi is fluffy. Yanada tsawo daidai misali ba jankala kok’I ba, gashin kansa yayi curly a matsayinshi na Fulde. Yanada Emerald eyes which is very rare ma yan Africa, kuma idanun are not that bulging, sunje daidai da dogon fuskarshi. Bashida saje ko kaɗan saboda bai taba yiba, fuskarshi haka yake payau. One good thing about him shine ya iya dressing thou mostly suits and tie ne na week days sai kuma T-shirts haka ma weekends. Idan kuma traditional wears ne toh fah saidai ya saka farin kaya da hula, baya sa wani colour at all. Idan yayi kwalliyar nan kuma Miemie tana daidai tana mishi lak’abi da “Yaya bak’i da fari” wai gashi baki amma yasa farin kaya. Kuma he is very neat, koda yaushe yana fadin “Al naxafatu shaɗaral iman” Wannan kenan!!! 1 week later... Yaune bikin k’awata kuma aminiyata Hadiza, tun jiya muka fara su kunshi, Hajia Sumayya Gaya wanda aka fi sani da “India” tazo tun daga kano domin yi mana, Hadiza ta fito sosai sai san barka, nima ba tayar baya ba. D’inkin da Isma’il yayi min ya fito da duk wani bangaren jikina har kunya nakeji, “gaskiya saina yafa gyale” na faɗa ma kaina tareda kara kallon madubi. Haka na tsala ma kaina kwalliya tunda ni ma’abociyar shine kuma ina shiga YouTube da Instagram na kalle videos haka, mune ake kira da “Internet Makeup Artist” Shi kuma Naufal tun yau yakejin Mood swings, gabanshi faduwa yaketa yi. Innalillahi wa inna ilayhi rajiun ya rinka maimaita wa. Komai sukuku yakeyi, saiga Miemie ta shigo. Dama bata fiye magana ba tunda yanzu ‘yan maganar basa nan, hawa kan gadansa tayi ta kura mashi ido, “Ya Naufal bakada lafia ne?” shima karin kansa baisan meke damunsa ba. “Halan baki iya gaisuwa bane?” “Na iya mana, but please answer me” Juya kanshi yayi gefe saboda bai san me zaice ba, gashi in an hour zai wuce wani dinner na friend ɗinshi Sadeeq. A hankali ya tashi ya wuce bayi yayi wanka tareda dauro alwala. Ya gama ya fito kenan saiyaji kamar bai kulle shower da kyau ba, ya koma ciki sai yaga komai lafiya lau, juyawa yayi sai kawai yayi missing steps dinshi yana kokarin faɗuwa. Sink, bango da k’arfen shower duk yayi kokarin kamawa but still saida ya zube a kasa, “tim” kakeji kawai. Shiru yayi a k’asa zafin ya gama barin jikinshi, da tangal tangal ya samu ya koma wajen gado. Tsaki yayi kafin ya soma dressing, farar Boyel ya saka as expected. Saiya murza hular k’ube wanda ake kira kwalba a kanshi. Fashe turaran Christian Dior yayi dana Ralph Lauren ko ina sai kamshi. Ya juya zai tafi saiya lura Miemie tana kallonsa, “ashe baki tafi ba?” “Ya Naufal zaka kashe arna yau, yan mata zasu rinka rububinka” ta faɗa tareda zurawa a guje. Dama haka takeyi idanta faɗa abinda yafi karfin bakinta saita gudu shima ya bita ayita wasa. Amma Sam yau bazai iya ba saboda har yanzu bayan shi yana mashi ciwo. Baiji haushin abinda ta fada ba saboda it’s true, ya saba yaje biki yan mata suyi masa cha a kai suna k’arairaya, shi kawai yasan cewa bai haɗu da soul mate ɗinshi ba har yanzu. Yanada feeling duk randa ya ganta he will know! *All rights reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 6 ✨✨✨ Narrated `Abdullah bin `Umar, Allah's Messenger (pbuh) said, "A Muslim is a brother of another Muslim, so he should not oppress him, nor should he hand him over to an oppressor. Whoever fulfilled the needs of his brother, Allah will fulfill his needs; whoever brought his (Muslim) brother out of a discomfort, Allah will bring him out of the discomforts of the Day of Resurrection, and whoever screened a Muslim, Allah will screen him on the Day of Resurrection . " ******************** Saboda yanda kayana ya matse ni, da ban na shiga hall ɗin batare da zugan amarya ba. Na samu wani seat a gaba na zauna tareda sauran friends ɗina tunda high table is just for bride and groom. Kowa ya hallara da wanda aka gayyata da wanda ba’a gayyata ba, kowa yazo rangem yaci shinkafa. Yana isa Zaranda hotel inda za’ayi dinner din, yawan mototin wajen ya bashi mamaki. Hall ya cika sosai kuma rabin gurin yan mata ne “Sunzo tallan kai” ya fada a ransa yana taku cikin k’asaita. A wani table guda ɗaya dattawa uku ke zaune kuma duka aminan Alhaji Sulaiman ne(Baban ango). “Ai ina gaya maku na rasa dalilin sa na kin yin aure gashi ba yaro ba” Engr Hussain ya faɗa fuskarshi duk takaici. Alhaji Musa ya dauki samosa guda ya gatsa saiya buɗe roban Swam ya sha, “Kuma kace ya gama karatu koh?” ya tamabaye su. “Yaron kirki mai taimakon iyayen shi, wallahi tun sanda Engr Yayi retire ya rinka daukar ɗawainiyan k’anansa, amma sam baya maganar aure” Alhaji Sulaiman ya chapke. Saiya k’ara da cewa “ko dayake tare suka tashi da Sadeeq duk halinsu ɗaya na rashin san aure amma shi Sadeeq baida aikin yi sai 8 Months ago ya samu. Amma shi kuma gogan ya kusan shekara 3 dafara aiki kuma yanzu yana chaɓawa sosai a garin Bauchi” Shi dai Alhaji Musa shiru yayi yana sauraron hirar da abokinsa yakeyi da amininsa. Kuma yaji ance yanada da halin rik’e mace ga kuma yaji ance yanada hankali da tausayi. “wow!!! dude ɗin chan ya hadu, sai dai baki ne” Mansura ta faɗa. Ita kuma Sadiya tace, “wanga green eyes haka, naji ance idan dare ya tsala masu irin idon suna komawa mage” sai gabaki ɗayansu suka kyalkyale da dariya. Ni ko jin abinda suke banayi saboda ina sana’ata na shan wak’a, Mansura ta fizge earpiece din “wai dalla meye haka? Inace Momy ta hana ki?” juyawa nayi na kalli left and right cikin isgilanci kafin nace, “banga momy anan ba, so bani abuna” saina fizga abina. “Amma bansan guy ɗin, saboda yasan ya haɗu shine yake wani salo” Sadiya ta faɗa. Ni kuma na juya inda suke kallo naga waye amma naganshi a duke yana gaida wasu. “Ashe yanada tarbiya” Mansura ta faɗa, har cikin raina ina so naga fuskarshi saboda yanda suke kod’ashi yayi yawa, inaso naga if he is worth kwace min earpiece ɗina. Naufal ya cika yayi fam, tun shigowarsa yan mata ke kallonsa but nasu yafi bak’anta mashi rai. Mutum ɗaya ta kalleshi tayi magana sai sauran su kwashe da dariya ba karamin haushi ya bashi ba. Fatan shi ɗaya, wata tayi mashi ba daidai ba ya daketa tunda yanada saurin hannu. Dama yazo wucewa ne yaga Abbanshi da baban Sadeeq, toh shine suke gaisawa while yan matan two table away sunata giggling suna kallon shi “Nifa raini ne banso” ya faɗa a ransa. Su Mansura kuwa sai magana suke a hankali suna kallon Naufal, ni kuma tuni na fizge earpiece dina na mayar mazauninshi. Daukar Pepsi nayi na buɗe sai abin ya fara zuba. Da sauri na mike ina kokarin juyawa sai na bige mutum. Shi kuma yazo wucewa ta gefen su sai wata daga cikin su ta bigeshi tareda watsa mashi Pepsi. “D’ankari” ya faɗa a ranshi. Ni kuma Dimples nace abin nema ya samu wai matar makaɗi ta haifi ganga. Tasss ya watsa mata mari, sai ya k’ara dauketa da wani ta ɗaya bangaren, marin daya yanka mata mai sa fitsari a jiki ne kuma dole kaga taurari. Ni kuma a razane naja da baya dana lura azzalumin mutumin dana haɗu dashi kwanaki ne, “dole a rina wai an sace zanin Mahaukaciya” Dama suna bashi haushi sai ya lura “Bad Luck” ne a gabansa kuma ga earpiece a kunnenta yasa ko tunani baiyi ba ya watsa mata frustration dinsa. Tabbas sukuku da mood swings dayake ta samu yau sanadiyar zaiyi gamo da ita ne, bcs duk wanda ya hadu da ita yayi gamo. Idanunshi suka kad’a bcs Bad Luck din dake binta yasa ya fadi ɗazu a bayi. Karkarwa na somayi bakina sai rawa yakeyi, gumi nake tayi duk na jik’e hawaye sai malalo min yake kamar bakin teku. Baya na rinka ja ina kallon mai zai biyo baya, daɗin abin hankali mutane baya kanmu sabida sunata cin abinci. “Yanzu dai na tabbatar a jakunan duniya, kinfi kowa jakanci” ya faɗa a hasalce. Tsuru tsuru nayi bance komai ba. Mansura ce tazo da sauri “Kayi hakuri Mallam, Fadeela is very clumsy” “Kambu” na faɗa a raina Word ɗin clumsy data fada ya bani haushi, bata ganin ya mareni ne? Kuma shine zata bini da zagi “toh saime idan na watsa mashi drink? Yafi karfi ne” Na fada ina turo baki tareda juya idanu duk salon marasa kunya. “kefa na lura karaman mara kunya ne, kuma samarinki masu fruits basa nan balle su tare maki” ya faɗa sai kuma ya cigaba da sababi “kisan me zaki rinka faɗa kafin ki yaba ma aya zakinta” Wasu yara suna guje guje sai suka tureni na sake watsa mashi, tasssssss ya sake dauke nida mari saida naja baya. “Dama bakisan ina raga maki bane saboda ke sa’ar k’anwata ce, amma bari na koya maki darasi” “Daga yau kin gama rashin kunya, ko a mafarki kikaga wasu zasuyi zaki kwaɓe su” Idanun kowa a kanmu, kafin kace ‘Jack Robinson’ Kowa ya dauki wayar shi anata video. Anata posting a snapchat da Instagram, dama Mallam Bahaushe yace idan ba’a yi faɗa a biki ba baya armashi. Koba komai an samu abin tseguntawa. Ja da baya na rinka yi hannu na biyu a kunci na, Shi kuma Naufal ya dauki alwashin sai ya shiga jikinta da duka sosai saboda saita yaba ma aya zakin tareda bambance zare da abawa. Abinda yafi bashi haushi ko Ango bai gani ba balle kawai ace ya juya gida. Damkarta yayi ya k’ara watsa mata mari, “Idan ka kasheta sai ka bani gawarta na mayar ma iyayenta” Abba ya faɗa ranshi a bace. Sai a locacin ya tuna dasu Abba, sakinta yayi ta faɗi kasa wanwar tana kuka. Hall anata kallonsa ana tsegumi, Sadeeq ya sauko daga high table rai a bace. Kallon up and down yayi ma Naufal sai yayi nuni ma Amaryarsa da hannu alamar tazo su tafi. Ko k’ara kallon Naufal baiyi ba suke wuce. Abba hannunshi harɗe akan kirjinsa ya k’ura ma Naufal ido, wannan ɗebo ruwa dame yayi kama. shikuma yana kallon k’asa cikin nadama. Baban Sadeeq yaketa kallon Fadeela, ajiyar zuciya yayi kafin yace, “Naufal ka ɗebo ruwan dafa kanka saboda if I’m not mistaking wannan yarinyar Grand Kadi ce na Bauchi” Jikin Engr Hussain yayi la’asar “Dan Kuka mai jawo ma uwarsa jifa” ya ayyana a ransa. Bashi ba har Naufal cikinsa yanata kaɗawa saboda kowa yasan cewa ba’a taɓa yaran manyan mutane a zauna lafiya, uwa uba yarinyar Grand Kadi gaba ɗaya. Yanzu yanzu within minutes zasu iya mayar da life dinka miserable. #NiDaDiyata *Xeemee you are appreciated, Allah ya bar zumunci* *All rights reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 7 ✨✨✨ Abdullah It was narrated that 'Abdullah said: "The Messenger of Allah said to us: 'O young men, whoever among you can afford it, let him get married, for it is more effective in lowering the gaze and guarding chastity, and whoever cannot then he should fast, for it will be a restraint (wija') for him.'" ******************** Sheshek’ar kukanta da sukaji ya dawo dasu hayacinsu, Abba ne ya matsa dab da ita ya fara magana kasa kasa, “kiyi hakuri diyata, insha Allah sai anbin miki hakkinki, nine mahaifinsa” A hankali na daga ido na kalle dattijon dake magana, kammanninsu ɗaya babu bambanci. Bance komai ba illa rage sautin kukana ina Jan magina a hankali. Alhaji Sulaiman (mahaifin Sadeeq) wanda yayi shiru kamar wanda ruwa yaci, a sanyaye yaje wajen tubur dinsu inda suka bar Alhaji Musa, shi dama baisan abinda ya faru ba sanadiyar yana waje yana waya. “Ranka ya daɗe dama wani ɗan matsala ta taso” shikuma Alhaji Musa yace, “Injin dai lafiya?” tare suka koma inda su Naufal suke. Gaban Egnr faɗuwa yayi daya lura da Fuskarshi yayi kama dana Fadeela. Nan kowa yayi tsuru tsuru ana inda inda. A gurguje mahaifin Sadeeq yayi mashi bayanin abinda ya faru, shiru yayi kafin yace, “Yarinya tashi ki faɗa sunan ki dana gidan ku?” ita kuma Fadeela tana daga ido ta ganshi saita barke da sabon kuka kai zaka zata locacin ake marinta. “Big Daddy kasheni yakeso yayi wallahi” ta faɗa cikin sigar kuka. “yi min shiru please, ni shiririta ne bana so” ya fada mata. Tsit tayi bata kara cewa komai ba, “Ai abin yazo da sauki tunda na gida ne kuma ba matsala sai mu tafi gidan Grand Kadi, though ni banga abin tashin hankali anan ba, tayi rashin kunya kuma ya hukunta ta” “ Ah ah gwara aje ayi abu cikin mutunci”, shi Abba abinda yasa ya nace su tafi a warware komai baifi akan iyayen Fadeela ba bcs yanzu sai a hana mutum sakat. Yanzu yanzu yaji tace kasheta akeso ayi. Fadeela ta shiga motar Daddy babba(Alhaji Musa) shi kuma Abba da baban sadeeq suna mota daya, sai Naufal dake baya yana bin su. Yana tafe zuciyar shi yana mashi k’una, wai fisabilillah gidan Bad Luck zaije ya bada hakuri, tun dayake bai taba jiba. Daddy babba yana tuk’i murna fal a zuciyarshi, shi kaɗai yasan dalilin haka. Sun isa gidansu Fadeela wanda ke GRA, katon gidan wanda komai akwai. Daga su Garden, swimming pool da kuma karamin basket ball court wanda yake da double function as tennis saboda Grand Kadi yana san motsa jiki. Daga Naufal, baban Sadeeq da kuma Abba saida suka jinjina tsarin gidan, sum sum suka bi bayan Alhaji Sani. Ita kuma Fadeela tun kafin mai gadi ya buɗe kofa ta fito daga cikin mota tabi k’aramin gate ta shiga “Ho sarkin shagwaba” Daddy babba ya faɗa. Bata iske kowa a falo ba sai motsi dataji a kitchen, da sauri ta haye upstairs kafin a risketa a fara mata tambaya. Su kuma su Naufal da Abbanshi sannu a hankali suka rinka bin Daddy babba har cikin Main parlour. Suna isa ciki sunyi Sallama sau wajen uku saiga Mommy ta fito tana gyara zaman gyalenta tareda amsawa. “Abbansu Fadeela Kaine tafe?” ta fada fuskanta dauke da fara’a. Shi kuma ya murmusa sai yace, “Eh nine Hajia, kuma tafe da manyan baki nake” sai a lokacin ta mayar da hankalinta wajen su Naufal, fuskanta a sake tace masu sannu da zuwa. Wucewa tayi kitchen ta jero abinci akan tray saita kawo masu suci. “Bismillah mana” Daddy babba ya faɗa, su kuma Naufal mutuwar zaune sukayi saboda sun tuna idan mutum zai cuce ka saiya bari kun sake kafin ya ɗana maka tarko. Upstairs mommy ta wuce domin ta kira Daddy, basuyi minti 5 ba sai gashi sun dawo tare. Zama yayi akayi gaisuwan mutunci, shi dai Daddy babba baice komai ba, gabzan abinci ya rinka yi yana santi tareda jinjina ma girkin mommy tunda ta iya sosai a matsayin ta na professional Chef. Daga bisani yace, “Ai tare muke da Diyata” Grand Kadi(Alkalin Alkalai) ne yace, “wanne daga ciki?” “Auta nake nufi, sarkin shagwaba” yana kaiwa nan ya fara dariya. “Ban masan ta dawo daga bikin ba” Mommy ta fada. Shi dai Big Daddy saida ya cika Gizzard dinshi kafin yayi gyaran murya, gaban Naufal ne yayi mummuna faduwa. Dama tun yau abinda yake samu kenan but na yanzu ya ninka sau dubu. Gyara babban rigarsa yayi, falo yayi tsit kowa naso yaji mai zai faɗa, “Da Alheri nazo” murmushi yayi wanda shi kadai yasan ma’ana shi, kowa kawai kallonsa yakeyi. Naufal duk ya k’agu yaji mai zai faɗa, “Dama batun auren ɗiyata ne da mijinta gashi kuna kallon shi” ba su Daddy ba har Abban Naufal saida suka mayar da idonsu kanshi. Shi kuma zare ido yayi yana nuna kansa da ɗan yatsa, da kyar ya iya bude baki yace, “Da ni kuma?” kwarai da gaske, kai muke nufi Alhaji Sulaiman ya chapke. Shi dai Alhaji Hussain baice komai ba, ya bar ma Allah komai. Idan auren zai zame mashi rufin asiri ba’a tozarta shiba to gwara ayi. “Yanzu dama akwai wanda aka ajiye ma Fadeela ta aura amma shine ba’a sanar dani ba? Kun kyauta min kenan? NI DA DIYATA amma sai ayi abu ba’a shawarce niba. Idanun Mommy fal da hawaye take magana cikin k’aramin murya. Grand Kadi zaiyi magana sai Big Daddy yace, “bazan canza magana taba, dole ayi bikin nan. Badun ina san Fadeela ba da nasa ayi bikin nanda 6 weeks but zan k’ara mata wani 6 weeks din kunga ya kasance 3 months kenan sai ayi proper gaisuwan iyaye da kuma biyan sadaki” Shi dai Naufal tunda yake bai taba ganin something that is absurd ba Kamar yau, “ya mare yarinya, maimakon a hukunta shi sai aka bashi ita a matsayin mata. Bai taba ganin inda aka ɓare gyaɗa aka tsinci mota ba. Daga alamu sun gaji da annoban data ke jawo masu ne shi ne ake so a mak’ala mashi, amma bazai yiwu asha fate ranar sallah ba” Ranshi a bace ya ɗaga green eyes dinshi wanda idan ranshi ya baci yana glimmering, zaiyi magana sai ga Fadeela ta fito tana kuka. A kasa ta zauna gefen Daddy tana facing Big Daddy, muryanta k’asa k’asa ta soma magana, sai kayi da kyar kafin kaji abinda take faɗi. “Please alfarma nake nema gurin ku, kunsan cewa tun dana ke ban taɓa saɓa maku ba? Ina kokarin fulfilling all righteousness a matsayina na yarinyar ku. Banida kamar ku a fadin duniya, dama daga Allah, Manzaninsa tareda sahabbai kune next danake bi.” Gyara zamanta tayi tare da durk’usawa, hannunta biyu a harɗe saita sunkuyar da kanta k’asa, “please kada kuce na aure……” Tas…. Mommy ta dauketa da wawan mari, “halan nan gurin sa’anki ne ke zaune? don raini ina kokarin k’wato maki hakkin ki shine zaki watsa min k’asa a ido wai ga zance ga magana, dan ace nike sangartar dake” Ya isa haka Hajia, “ai gwara ta faɗi ra’ayinta amma bazai canza komai ba saboda sai anyi” Big Daddy ya chapke. Ita kuma Mommy ranta ya baci saboda da Fadeela bata fito ba data san yanda zatayi ta ruguza abin, amma yanzu tana cewa kule za’a ce sun haɗa baki ne. Amma tabbas yau saita shiga jikinta da duka, tunda ta ruguza mata plan dinta bcs of her stupidity. Fadeela tana Sheshek’ar kuka ta koma ɗakinta, shi kuma suka mayar da idan su kan shi, wanda baka ganin komai sai green eyes kawai, “Kanada ja ne?” Alhaji Sulaiman ya faɗa. “Gaskiya kuyi min afuwa, ni inada wanda zan aura kuma alamomin munafiki ne idan yayi alkawari ya saɓa” Mallam rufe mana baki, Abba yayi magana a karo na farko tun bayan sun gaisa. “Nifa bazan aureta ba” ya fada tareda mikewa, kallonsa kowa keyi “Grand Kadi kayi hakuri akan abinda nayi ma yarka which nasan Baka sani ba, but bazan aureta ba saboda wasu dalili nawa” wucewa yayi ya nufe hanyar kofa, “Naufal karka bar gidan nan batare da na baka izini ba” Abba ya faɗa mashi amma yayi kunnen uwar shegu yayi ficewarsa. Yana tafe yana haki, “wai Bad luck za’a haɗa ni da ita! Ta kashe ni kenan da bak’in jininta. Sam Sam bazai yiwu ba” yana tafe yana faɗa ma kansa har ya kai wajen motarsa. Haka ya fito daga cikin gidan su Fadeela sai yayi shawara yaje gurin Mamansa ya shawo kanta ta mara masa baya dukda tana fushi dashi akan yawan zuwa wajen Anty Saudah tareda daukar ɗawainiyan Miemie. Ya hau babban titi yana tsugaga gudu baji ba gani, kuuuu yayi kokarin taka birki yayin daya lura da ɗan ga ruwa yana tura amalanken sa. left Naufal yayi kokarin zuwa cikin tashin hankali tareda rankamo salati but ashe masu Fruits da kuma balangu suna wajen wanda shi baima lura dasu ba. Saisaita steering dinsa yayi a firgice but sai da yayi Karon rago dasu. Nan take ya sume sanadiyar buga kanshi daya yi..... Su kuma mutanen wajen salati suka rinka jerowa, daɗin abin kowa ya kauce. Gaggawa aka je bashi, anata dambe da mota da kyar aka fito dashi. Tun sanda aka fara cincibarsa ya farka amma baice komai ba saida aka ajiye shi. A hankali ya ware idonsa ya rinka kallon wanda suka ceceshi. “Ina fatan babu wanda yaji ciwo?” “Alhamdulillah babu kowa ya kauce” wani dattijo ya amsa shi. “Amma Mallam kai ɗan rainin wayo ne, dan wulakanci zaka hau titi kayi ta zura gudu kamar na ubanka” Wani matashi ya faɗa “Toh wallahi ba zanyi asara ba, ko a bayani kuɗin Fruits ɗina kona tada zaune tsaye yanzu yanzu” ya faɗa yana zaro ido tareda lakwansa baki. Shiru Naufal yayi saboda yasan duk me ya faru dashi laifin shi ne, iyaye ba abin wasa bane. Bazai disrespecting dinsu hankali kwance ba. Gaskiyar Mallam Bahaushe ne daya ce “Rashin bin maganar iyaye hatsari ne” gashi abin ya zama mai hatsari physically ba a baki kawai ba. Su kuma su Abban Naufal shiru sukayi kunya sai ɗawainiya dasu takeyi. Mommy ce tace, “naji yayi maganar wani abu ya faru, halan lafiya?” Nan Abban Naufal da kanshi ya labarta masu daki daki abinda ya faru. Mommy shiru tayi kada ta tozarta Daddy ace matarsa batada kintsi yasa bata k’ara cewa komai ba. Amma bazata yarda ayi auren nan ba, bata taɓa jin inda aka ɓare gyaɗa aka tsinci mota ba. Su Engr bada hakuri suka kara yi kuma fuskar Grand Kadi a sake. Shi kuma Alhaji Musa yace hakuri ɗaya zaiyi idan aka sa Naufal yayi auren nan. “Kar ka damu, nima auren nake so yayi tuntuni amma yaki. Aiko gawarsa ne sai an daura” Engr ya jaddada. Grand Kadi har mota ya rakasu ana raha. Shi dai bashida abin cewa, duk abinda Big Daddy yace shi za’ayi. Saboda matsayin shi yafi karfin haka a wajen shi, yayi mai hallaci sosai a baya saboda haka bazai watsa mashi k’asa a ido ba. Ita kuma Mommy idanta ya cika fal da hawaye, kullum addu’a take Allah ya ba Fadeela miji mai tausayinta amma gashi za’a haɗata da wannan gwaskar. Haka Naufal ya wuce wajen motarshi domin ya dauko masu kudi. Dama yayi withdrawing kuɗin dazai lik’i ne. Dubu goma sha biyar yaba mai Fruits su rage asara, sai yaba mai nama dubu goma. Shi kuma mai ga ruwa aka bashi dubu ɗaya da ɗari biyar, sauran mutanen wajen su uku ya basu dubu ɗaya ɗaya. Haka ya koma motarshi datayi damaging, glass sun farfashe handle din kofa ya lankwashe. Komai dai babu kyan gani, ya shiga ya fara tuk’awa sai motar tanata hayaki tareda k’ara kamar Vespa. Tafiya yakeyi kamar bayayi saboda bashida maraba da kunkuru. Kowa kallonsa yakeyi yana kwafa bcs duk ya ishesu. Abban Naufal ya kira Anty Saudah a waya yaji ko Naufal na wajenta amma tace rabonta dashi tun kafin yaje dinner. Abba ya rasa a inda Naufal ya koya mugun ɗabi’a amma ya dauki alwashin anyi na farko anyi na karshe. Zuwa gida yayi ya wuce bayi kai tsaye yayi wanka, daya fito saiya saka wani Ash jallabiya haka. Daukar jaridar Daily Trust yayi ya wuce Varenda yana jiran shigowar Naufal, zama yayi a kujerun wajen saiya ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya. Baya ma gane jaridar kawai k’afarshi yana karkarwa. Sannu a hankali Naufal ya rinka gungura motarsa har gidansu, k’aran ɓararan motan ya sanar dakowa gashi nan zuwa, ga kuma hayaki kamar ana gobara. Yana zuwa mai gadi saida ya leka ta karamin gate yaga waye kafin yagane Naufal ne. Shikuma Naufal tunanin shi ɗaya yazai yi da annoban ta, wai ace daga zuwa gidansu har ya kusa mutuwa, ina ace inuwar su ɗaya. Yana isa parking lot ya ajiye motarsa zai wuce BQ inda ɗakinsa yake. Sam baiyi tunanin zaiga kowa war haka daren nan. “Mallam zo nan” Abba ya faɗa fuskarshi babu wasa. Sum sum Naufal yaje waje, tun yau abubuwa mara misaltuwa ke faruwa dashi, yanzu a gajiye yake yayi likis. Yana isa ya ɗuka kasa alamar girmamawa. Abba baiyi wata wata ba ya wanka mashi mari kyawawa guda biyu. “Faɗa min daga inda kake ka shigo min gida cikin dare kamar ɓarawo?” kanshi duk’e baice komai ba, shiru kawai yayi yana tunanin irin marin da zai rinka dauke Fadeela dashi. Saboda aurenshi zai zamo mata bak’in canji a rayuwarta. #NiDaDiyata *All rights reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 8 ✨✨✨ *A LESSON* The Holy Prophet(SAW) said, "Stop doing everything during the ADHAAN(calling of prayer), even reading the Holy Quran, the person who talks during the Adhan shall be deprived of saying the KALIMATUSH-SHAHADA when he or she is about to die! May Allah guide us... ********* “Dama na danyi wani  k’aramin hatsari ne” Naufal ya amsa ma Abba still yana ɗuk’e a kasa. Shiru Abba yayi na wajen 5 minutes yana tunani irin halin Naufal. Ajiyar zuciya yayi abin duniya ya isheshi sai yace “Wato sabon alkawarin daka dauka ma kanka kenan koh?’’ “Yanzu bazaka  barni na sha ruwa a garin Bauchi ba koh?  Idan an hanaka mutuwa sai ka suma. Shi kenan yanzu dan na haife ka banida sauran kwanciyar hankali a tareda ni kuma. Kana abu kamar k’aramin yaro.” “Wai tsakani da Allah Naufal mena rageka dashi da kake so bakin cikin ka ya kasheni. Haba mana! Bafa kai kaɗai na haifa ba balle kamin haka, idan ka gaji ne sai kayi min bayani na yafeka a cikin yarana then we can call it a day” “Kayi hakuri dan Allah Abba Wallahi bai kai zafin haka ba, tsautsayi ne kawai aka samu. Kuma wanda nayi hatsari a gefen su ko qurjewa basuyi ba” Naufal ya faɗa yana tunanin yayi abin arziki. “Ai bakayi gwaninta ba, daka kashesu ne saina san ka cika namiji” Abba ya amsa. Ita kuma Bilqees ta tashi karatun TDB saboda tanada test saita ji hayaniya a varenda. A hankali taje taga ta lek’a sai idonta yayi arba dana Abba. “Zo nan” ya faɗa ita kuma ta fara jan k’afa duk takaici tace a hankali “I don dieooo.... Meya kawoni wajen nan” haka taje wajen Abba ta durkusa “Gani Abba” Kallon sama da kasa yayi mata saiya ce, “kije ki tada Abla da Maman ku sai kuzo ku sameni gabaki ɗayan ku a falo” ya faɗa tareda kallon Naufal alamar harda shi. 20 mins later.... Duk suna zaune a falon Engr, Mama da Naufal ke kan one one seater, su Abla ana k’asa ana turo baki. Mama tana ɗan jijiga kafarta ta cika tayi fam. Ita bata ga dalilin da za’a tasheta cikin tsakar dare ba?  Wani zuciya ya raya mata ai aikin Anty Saudah ne. Tsaki tayi a ranta sannan ta faɗa “Nayi maki nisa mahaifiyar mahaukaciya” “Abba gamu mun zo” Abla ta sake maimaitawa a karo na biyu. “Ai na ganku since niba makaho bane” shiru ya k’ara yi wanda Fallon baka jin komai sai motsin jaridar dake hannunsa. Kafarsa ɗaya akan ɗaya yana karkaɗasu, shikuma Naufal bai taɓa gajiya kamar na yauba. Kwakwalwarsa sai chaji yake yi a hankali don komai yayi masa zafi. “Hajia Sarai” Na’am Alhaji ta amsa tana kallon gefe. “Naufal” Na’am Abba “Abla” Abba Na’am “Bilqees” Na’am Ya kira sunan su ko kallonsu baiyi ba still yana duba jarida. Ajiyar zuciya yayi saiya ajiye akan centre table kafin ya mayar da hankalin shi kansu. “Wannan gidana ne bana wani ba! Saboda haka dole abi dokoki na. My house my rules” “Bazai yiwu akawo min raini under my roof ba, akan me? Bari kuji daga yau an daina tozarta ni. Ban ɓata ma iyayena suna ba bazaku ɓata min nawa sunan ba, haba!” “Hajia Sarai daga yau kin gama Kishi da Hajia Saudah, shekararmu wajen sha shida da aure amma kinki saka ma zuciyar ki salama. Daga yau sai yau bana so na kara jin kin takaleta ko wani abu makamancin haka. You are going to be nice to her and her daughter, Zaki rinka zuwa kina dubasu kuma zaki bar yaranki suje” yana kaiwa nan ya numfasa. “Naufal! Dole ka aure Fadeela, kuma you will treat her nicely. Gobe zakaje kabama iyayenta hakuri da ita kanta. Zakayi auren nan cikin daɗin rai, yar mutunci zaka aura dole ka mutunta ta. Batun Miemie kuma banida abin cewa sai Allah ya saka da alheri” shiru Naufal yayi baice komai ba saboda duk gabobin sa yana mashi ciwo. “Abla da Bilqees ku fito da mijin aure tun kafin nakai hoton ku masallaci, musamman ke Abla tunda kece babba. Kuma zaku rinka zuwa wajen Miemie kuna dubata” Yana kaiwa nan ya dauko jaridar sa tareda fadin “Duk wanda yaga bazai iya bin abinda nace ba sai yayi hanyar gate yanzun nan or else kowa yaje ya kwanta” Naufal ya fara tashi tsaye tareda faɗin “Saida safe Abba” saiyayi hanyar BQ. Sai mama ta tashi tayi hanyar ɗakinta. Su Abla suma saida safe sukace sakayi hanyar ɗakinsu. Murmushi Engr yayi saboda ya fara dawo da tarbiyan gidansa hanya madaidaciya. “Nifa ban gane me ake nufi da Ya Naufal zai yi aure ba?” Bilqees ta faɗa. “Shine nima naji gashi kin sanshi yanada bala’in taste” Abla ta amsa Bilqees tayi ajiyar zuciya kafin tace, “Fadeela! Ko wacece ita?” WACECE FADEELA ? Marigayi Mallam Bello ya haifa yara biyu tal a duniya. Musa da Abbas, ya rasu babban yaronshi yanada shekara 21 duniya. Dukda k’arancin shekarunsa bai hanashi rike mahaifiyarsa tareda kaninsa ba. Shiyayi jjigilarsa harya zama lawyer gashi yanzu shine Grand Kadi, yanzu Sam bazai iya musa masa ba akan alfarma saboda shine mahaifinshi. Alhaji Musa wanda ake kira Big Daddy yanada yara biyar, Maimuna, Zainab, Hafsat, Safiya sai auta Mubarak. Sunar matarshi Hajia Rabi.Yanzu haka duka yaranshi mata na zaune lafiya lau gidan mazajen su thou Zainab aurenta na biyu kenan. Jikoki 14 Big Daddy yakeda. Shikuma Grand Kadi Abbas yanada yara uku, Jawahir, Muhsin sai auta Fadeela. Jawahir tanada yara uku, Yanbiyu Abdulrahman da Abdulrazak sai Fauziya. Shi kuma Muhsin yana Masters a Dubai tareda Mubarak shi kuma degree yakeyi . Ita kuma Fadeela tana 400l a ATBU Bauchi tana karanta fine arts. Fadeela dai yarinya ce mai natsuwa ga dadin zama, ta san ya kamata saboda ba’a yi masu wasa da tarbiya ba. Fara ce daidai misali, bazaka cemata kyakyawa ba amma babu muni a fuskarta, daidai gwargwado take Tabarakta mashaAllah. Siririya ce kuma tanada ɗan tsawo. Gashin kanta yanada santsi amma bashida tsawo bai wuce cikin cokali ba. One good about her shine she is very classy, ta haɗu iya haɗuwa. Dressing A1 take ci saboda tasan fashion trends. A duniya tanada bala’in san yara, domin ko a bus saita murmusa masu. Burinta ɗaya ta haifinata but gashi yanzu an haɗa ta da wanda ya tsaneta. AllahuMusta’an kawai take faɗi. Matsalarta guda biyu ne. 1.Tana san shan waka kamar ibada. 2.Ta fiye sanya sanya da nawa ko wajen magana. But dama dan Adam ajizine,  dukda wannan bata san raini at all. Bataga dalilin da bazaku mutunta juna ba. Wannan kenan! ********* Daga ɗayen bangaren Fadeela ta koma ɗaki ta shiga cikin bargo ta duk’unkune sai kyarma takeyi, duk zazzabi na farad ɗaya yayi awon gaba da ita. Momy kai tsaye ɗakin Fadeela ta nufa saboda saita cin mata. Tana tura kofa taji abuɗe but wuta a kashe. “Gwara da baki rufe ba” momy ta faɗa da karfi. “Dan rashin hankali uban waye sa’anki? Muna magana zaki shigo mana da zancen banza” sai Momy ta fizge blanket dinta. Yanayin dataga Fadeela ya bata tausayi sai ta mayar da duk wani abu data je dashi. Dama ita Fadeela bata iya fushi ba, abu kadan sai ta hau zazzabi. Zama tayi akan gadon ta jawo ta jikinta, rau taji zafi kamar ana shirin soya kwai. A hankali ta soma magana “Yi hakuri auta, komai ya faru da mutum daga Allah ne. Kwantar da hankalinki. Gobe zani wajen Big Daddy na rok’esa alfarma, but idan bai yarda ba Please im begging you in kina gidansa I want you to show him how well trained you are.” “Please Karki bani kunya, ki nuna masa ke yar halas ce kuma yar mutunci” haka Momy tayita rarrashinta tana mata nasiha har barci ya kwashe ta. Washegari, 4:56am….. Abba ne yake tafiya zuwa ɗakin Naufal domin tadashi su wuce masallaci sallar asuba, dama ɗabi’ansu ne muddin Naufal ya kwana a gidan. Ya mika hannu zai kwankwasa kofa sai ga Naufal ya buɗe zai fito, “Alhamdulillah ai ka hutar sheni” Abba ya faɗa yana murmushi. Shi kuma Naufal murmushi ya mayar masa sai suka jera suka yi hanyar masjid. Bayan sun idar suna dawowa sai Naufal ya koma ɗakin shi, shi kuma Abba ɗakinsu Abla ya wuce direct yaga yanda suke. Bilqees ya gani tana karatun Al Quran sai Abla tana zura hijab da alamun sallah zatayi, baice komai ba ya wuce ɗakin Mama. Itama tana bayi da alamu alwala takeyi. Tunani ya soma yi bcs iyalinshi na kokarin kare hakkin addini, kwata kwata baisan idan Naufal ya debo halinshi na jiya ba. “Maybe he is the black sheep of the family” wani zuciya ta raya mai. “Allah dai ya shirya shi” ya fada a fili. TV ya kunna ya kalle sunna TV inda ake hira da Bn Uthman sai wajen 6am ya koma NTA inda zai kalle AM Express. 6:30am… Locacin ne Fadeela ta tashi, kasancewar bata sallah yasa ta ɗan kara barci. Da kyar take tafiya bata ko ganin gabarta sanadiyar kukan data ci which ya haifar mata da azabataccen ciwon kai mai sara kamar na gatari. Tana tafe tana tangal tangal kamar yar k’waya, ruwan zafi ta watsa a jikinta saita soma samun kanta. A daddafe ta wuce ta haɗa ma kanta Espresso a PS Gucci Nespresso machine dinta dake dakin tunda ita ma’abociyar shan coffee ne. A yanayinta na sanya sanya ta wuce bedside drawer dinta ta dauki Paracetamol, Boska da Panadol extra duk ta hadiye. Saita jingina akan gado tana ajiyar zuciya. Hawaye ke gangaro mata data tuna sabon rayuwar da zata shiga, within minutes life dinta yayi shredding into pieces. Dogon ajiyar zuciya ta yi saita ce “Alhamdulillah ala kullu halin” a fili saita mike tsam ta saka kaya. Wani valvet overall ne kuma yana cikin kayan zaman gidanta. Dakin Daddy ta soma zuwa, a kan couch ta ganshi yana duba Alqur’ani da wasu takardu a gefensa da alamu yanada court case. “Assalamu Alaikum Daddy” ta faɗa a sanyaye tareda da zuwa gefensa ta zauna. “Wa’alaikumus Salam, Auta kin tashi lafiya” “lafia lau, hope kaima haka?” Kallonta ya tsaya yi yanda bata nuna wani damuwa akan batun jiya ba, abinda yasa tafi burgeshi kenan a yaransa saboda batada riko kwata kwata. “Daddy wat are you working on?” ta fada tareda daukar ɗaya daga cikin papers din kan table. “kul ki ajiye” ya faɗa yana dariya “Wannan aikin na manya ne” Murmushi tayi saita ce, “me zan haɗa maka na breakfast?” “Na hutarshe ki, matana chef ne so zata yi min gangariya” ya faɗa yana dariya. Ita ma dariya ta soma yi bcs a duniya parents dinta su ne relationship crush dinta. Yanda suke abinsu cikin mutunci da girmamawa yana burgeta sosai. Kullum fatan ta itama ta samu koda rabine, idanunta suka ciko da kwalla data tuna Naufal, da sauri ta mike kada Daddy yaga yana yinta. “Daddy ayi aiki lafia, bari na duba Mommy” bata bari ya amsa ba tayi gaba abinta. Share k’aramin kwalla daya soma gangaro mata tayi, ɗakin Mommy ta shiga which is adjacent to na Daddy. Tana tura ɗakin sai taga duhu alamun momy ta koma barci, itama zuwa tayi ta shiga bargon ta kwanta. Ido ta kafa ma Mommy kur, “kaza mai ‘ya’ya bata mai” Mommy tace tareda murmushi. “watau baza’a barni nayi barci hankali kwance ba?” “Mommy ina kwana?” “lafia lau auta ya hakuri damu?” Dariya Fadeela tayi sosai saita canza topic din, “Daddy yace zakiyi masa gangariya” “Na sani Malama ba sai kin faɗa ba” sai Mommy ta kalle silver and black agogon bangon dake manne. “Innalillahi bari na tashi kaɗa na makara, today I’ve a lot of things da zanyi” Ita Fadeela tana so ta tambaya Mommy ko abubuwan data keso tayi ya jiɓance zuwa gurin Big Daddy but ta kasa magana. “Mommy please kada Kije wajen big Daddy kafin yace mun raina shi” ta faɗa idonta fal da hawaye. Kallonta Mommy tayi tana nazarinta kafin tace, “akan me Auta?  Kin taba ganin inda mutum ya bude gyaɗa ya tsinci mota?” “marinki fa yayi shine za’a aura miki shi ya kashe ki gaba daya” “Mommy ba abinda nake nufi ba kenan, idan Allah ya kaddara auren babu abinda zamu iya and vice versa. Kawai bana so muyi forcing komai ne muyi ma Allah shishigi kafin muji kunya” “Besides dan ya mareni is not the worst scenario that people meet their spouse, Wasu fah a social media suke haɗuwa” Mommy shiru tayi tana kallon ɗiyarta, “Gaskiya hankali baiwa ne kuma idan Allah ya baka sai kawai ka gode masa” jawota tayi jikinta tana jin dumin ta. A hankali tace, “Nagode Fadeela” which is rare ake kiranta, anfi ce mata Auta har masu gadi da makwabta. 4:38pm… Jallabiya ya dauko sabuwa fara sol ya saka, sai ya haɗa da bakin wando tareda bakin hula. Fashe kanshi yayi da turaren Yes Saint Laurent yana tafe yana shan kamshi, gashi kuma rana ya fara sauka so emerald eyes dinshi yana ɗan glimmering. “wannan wanka haka? Ya Naufal sai ina?” Bilqees ta faɗa daga gani ta dawo daga School ne. “Kinsan niba sa’anki bane?” abinda yasa yayi mata magana in a rude way baifi haushin zuwa wajen Bad Luck da zai yi, wanda har yanzu bai taba faɗin sunanta ba. “Yi hakuri but please jirani na dauko kayana saika ajiye ni wajen Anty Saudah anan zan kwana yau” Kallonta yayi baice komai ba, mamaki karara a fuskarshi sai kuma ya tuna Bilqees batada matsala probably Mama ke zugata, mai zafin kan gidansu bai wuce Amatullah ba kuma tana chan ta karata da mijinta. “Karki bata min locaci” ya faɗa yayi hanyar motan Abba tunda ya kai nashi gyara. Ya ajiye Bilqees a gidan gona saiga Miemie tazo da gudu, “Ya Naufal wai da gaske zakayi aure?” ta faɗa tana haki. Shi kuma yace “bakya so ne?” “Ina so mana sosai ma kuwa, na gaji da Mommy kaga sai na dawo wajenta” ta faɗa tana waige waige. Shi yaso tace Ah ah amma ta bashi haushi kawai. Kwafa yayi “dama wayace na tambaya mahaukaciya abu?” ya faɗa a ransa. Tun kafin ya kai gidansu Fadeela yake addu’o’I, shifa ya riga ya chamfa duk randa ya ganta sai wani mugun abu ya same shi. “La ila inna anta subhanaka inni kuntu minnal zalumin” yaketa maimaitawa while driving har ya isa cikin gidan….. #NiDaDiyata I'm really sorry for my silence, buki mukayi. Uncle Usman Allah ya baka zaman lafiya da amaryar ka Rahama. *All rights reserved * 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 9 ✨✨✨ It was narrated from Hakim bin Muawiyah, from his father, that a man asked the Prophet(): "What are the right of the woman over her husband?" He said: "That he should feed her as he feeds himself and clothe her as he clothes himself; he should not strike her on the face nor disfigure her, and he should not abandon her except in the house (as a form of discipline)." (Hassan) ********* Ina kwance akan sallaya bayan na idar da sallar Asr, lazimi nake tayi harna gaji. Dama ni kaɗai ke gidan Mommy taje supervising wani catering services haka. Anty Husna ce ta shigo wai ana sallama da dani. Shiru nayi bance komai ba, sai kuma na Mike zaune ina fuskantar ta tareda wani irin kallo. Saboda ni kwata kwata I’m not expecting any male visitor, though I don’t have plenty of them. “Wanene?” “Ina ganin yana cikin bak’in jiya” ta amsa mani. “Oh!” Na faɗa saina yi kwanciya na, nifa tukura ne banso. Watau shi har yana san auren kenan da har zaizo zance wajena. “mts” naja tsaki mai bala’in k’ara. Ita kuma Anty Husna har takai stairs sai wani zuciya ya raya mata kamar fah Fadeela bazata fito ba. Juyawa tayi nan take ta koma ɗakin. Inda ta barta nan ta same ta. “Auta kinyi bak’o shine kike kwance? Babu kyau wulakanci! Kije kiji mai zai ce mana, koba komai su Hajia basu ji dadi ba idan kika raina sa, kuma bakya tsoro kada ya rama idan an kai ki?” Mai aikin mu Anty Husna ta faɗa, ni kuma shiru nayi sai daga bisani nace, “Haba Anty wani irin wulakanci kuma! Wallahi bansan me nayi masa ba. Kwata kwata ya tsane ni, kamar ya sanni a wani waje. I just can’t figure it out. Kina ganin Idonshi zakiga tsanata a ciki karara” Na faɗa idona fal da hawaye, kallona ta tsaya yi saita ce, “Kiyi hakuri, wata rana sai labari. Kinsan cewa mai hakuri yana dafa dutse harya sha romonta” miko min hannunta tayi saina kama tareda mikewa tsaye. Drawer na wuce na dauki Swiss lace orange mai ratsan purple da silver. Saina dauki purple gyale wanda ake ce masa Aisha Buhari na saka tareda takalmin Zara. Fuskana payau babu makeup sai pink lip gloss wanda ya kara ma pink lips ɗina armashi kafin yace ina sanshi yasa nayi masa kwalliya. Shi kuma Naufal bayan yayi parking motarshi sai yaje wajen mai gadi akan yayi mashi iso da mai gidan, to anan ne aka faɗa mashi babu kowa a gidan illa Fadeela. Shiru yayi kafin yace to ayi mashi iso da ita. “karshen wahala bai fi mutuwa ba, kila yau zata kasheni kowa ma ya huta” ya faɗa a ranshi. Haka yayita zaman jiranta tareda latsa wayarshi tunda shi ma’abocin Instagram ne. Yana cikin motarshi ya shafa’a ya mance da komai sai yaji kamshin turaren da bazai mance dashi ba. “Chanel No 5” ya faɗa a fili yayin da ya ɗago green eyes dinshi. “Assalamu Alaikum” na faɗa da murya kasa kasa tareda tsayawa gefen motan. “Wa’alaikumus Salam” ya amsa mani sai ya mayar da hankali shi akan wayar shi. Ni firgitani yayi, bashida maraba da mage. Ga Green eyes ga bakin fata, sunkuyar da kaina kasa nayi ina wasa da yastuna. Bayan 45 mins…… Haka na cigaba da wasa da yatsuna ina regretting rashin fita da banyi da wayana ba, koba komai zan buga Candy Crush. Shikuma Naufal kwata kwata ta birkitar dashi da kamshinta, turaren data saka irinshi Ex Gf dinshi Anastacia take sawa. Sunyi soyayya sosai a London sai daga baya ta guje shi wai bazata aure Musulmi ba. Acewarta Muslims are terrorist. Yayi kokarin wayer mata da kanta about Islam amma ta kafe. Abin ya ɗaga mashi hankali sosai har ya kusan shiga wani hali da bai dace ba. Bayan aukuwan abin da 2 weeks sai yagane ashe Anastacia aure zatayi da Mayor din district dinsu. Zuciyar shi ya fara mai zafi sanadiyar tuna Anastacia daya yi, duk wani assignments shi ke mata kuma har exams yayi mata amma ta guje shi. “Birds of the same feathers” ya faɗa tareda kwafa. Shi yanzu tsanar Fadeela ya karu a zuciyar shi, dukda tanada kyau kuma she is hot but tana firgita shi gata kuma da bala’in nawa. Deep down yasan champi haramun ne a musulunci but he can’t help himself to blame her for all the bad stuff in his life. Yasa ya basar da ita baice mata komai ba thou yana ankare da every move dinta, ya lura sai kwafa takeyi tana girgiza kafanta. “kaɗan ma kika gani” ya faɗa yana kallonta ta gefen ido. Haushi ya kamani sosai amma nayi kokarin controlling kaina. Insha Allah bazan nuna mashi I’m weak ba, saidai yayi ya gaji. Muna cikin haka ne saiga Daddy yazo. Da sauri Naufal ya fito daga motarshi, nima naje wajen Daddy ina shagwaba. “Ashe Daddy’s gal ce…. Tabdi!” ya fada a ranshi. Mikama Daddy hannu yayi suka gaisa tareda risinawa. Daddy da fara’arsa ya amsa. “wannan wani irin mutane ne da ake masu abu basa nunawa” Naufal ya sake faɗa a ransa. “Ah ah Mallam Naufal kaine tafe haka?” sai kuma ya mayar da fuskarshi kan Fadeela “ya baki kai shi cikin ɗaki ba” “Daddy tun fa dazu yazo yanzu ma tafiya zaiyi sai gaka ka dawo” “oh! Allah sarki toh mu shiga mu kara gaisawa” haka suka wuce cikin falon Grand Kadi suka zauna. Naufal sai inda inda yakeyi. Grand Kadi ya lura akwai magana bakinshi, saiya canza topic din tareda mashi tambayoyi akan aiki da sauran al’amura. Daidai gwargwado Naufal ya bashi amsa saboda ya lura audition Daddy yake yi akan auren ‘yarsa, shi kuma Daddy ya yaba da ɗabi’un sa, murna fal ransa saboda koba komai in sha Allah ba zasuyi zaɓen tumun dare ba, wannan shi Mallam Bahaushe ke cewa ‘wai faɗuwa ne yazo daidai da zama’. Har wajen 30 mins sunata zantawa sai Naufal ya mike zai tafi. “okay sai Fadeela ta raka ka mota”Daddy ya faɗa. Daga Deela har Naufal babu wanda yaji dadin abin amma haka suka hakura. Rakiyar da nayi ma Naufal was the longest journey of my life, shuru mukayi bamu ce uffan ba har muka kai parking lot. Motar mommy ya danno kai, tsayawa yayi da fara’arsa na munafunci yana jiran ta iso. Bayan ta fito daga motar ta saiya risina ya gaishe ta yana wani kunya kunya. Sai kuma yace, “Mommy nazo bada hakuri jiya, nasan ban kyauta ba” “Allah sarki ai babu komai, dama zo mu zauna zo mu saɓa ne” numfasawa tayi kafin ta ce “Allah yayi maka albarka” “Amin Mommy” ya amsa dashi. Sai Mommy ta wuce cikin gida tana yabawa da halin surikin ta. Shi kuma motarshi ya shiga saiya mika ma Fadeela bandir din 500 naira. “ka bar abin ka bana so” na amsa mashi. Kallon up and down yayi min, duk ya firgitani saboda Magrib yayi gashi idansa yana glimmering. Ban ankara ba sai naji ya tada motarshi, har ya fara tafiya saiya cilla min kudin a fuskata. Saiya faɗa “Kece matsiyaci ya amma badai niba” Sororo na tsaya kallonshi har ya ɓace daga haraban gidan mu. Tunda nake ban taɓa ganin makirci irin nasa ba. Oh ni Fadeela ! Meke shirin Faruwa dani? Dukawa kasa nayi na dauke kudin tareda wucewa daki. Akan mirror na ajiye sai na kwanta akan gado na dauko sabuwar babin kuka. #NiDaDiyata *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 10 ✨✨✨ Malik relate from Nafi that when Abdullah ibn Umar sneezed and someone said to him, "May Allah have mercy on you," (Yarhamuka'llah), he said, "May Allah have mercy on us and you, and forgive us and you." (Yarhamuna'llah wa yaghfirlana wa lakum) *************** 17 days later..... MIEMIE Tafiya takeyi cikin sauri sauri, kallabinta tamke akan qugun ta. Dayake tanada tsawon gashi haka wasu suka bazu a fuskarta har yana tsone mata ido. Bata cireba haka ta barshi tana tafiya abinta. Ta kai babban titi near Bauchi club dake kusada makarantar su na Special school. Tana kokarin tsallake titi amma dataga mota ya danno kai koda ta kai rabi ne kuma motar yayi nesa da ita zata pella baya. Tsaye yake gefen mai gasa masara yana kokarin ya siya, baima lura da wasu halitta ba a wajen balle ita. “Amma anyi wawiya” mai gashin masara ta faɗa. Juyawa yayi tareda cire tabaransa ya kalli abin ake magana akai. Wata yarinya ya gani wanda bazata kai 15 yrs ba tana guje guje a titi. Tsaki yayi ya mayar da tabaransa ido saiya mika ma mai gashin masara dari biyu “Keep change” ya faɗa sai yayi hanyar motarsa. Ta kara komawa baya da gudu a karo na uku kuma duk a Idonsa. Tsaki ya karayi ya soma danna wayarsa ko ajikin sa. Wasu samari su uku sukaje wajen ta suna mata surutai, Ita kuma bata kula suba. “Bada ke nake magana ba?” ɗaya daga cikinsu ya faɗa tareda chapke mata gashin kanta. Kara ta saka wanda ya mayar da attention ɗin kowa kansu. Kwafa yayi saiya fito daga motarshi da saurin gaske, “Kai meye haka Mallam, kanwata ce fah” ya faɗa tareda janyo ta zuwa inda motarsa yake. Buɗe kofar gaba yayi saiya turata ciki. Shima ya zagaya ɓangaren driver ya zauna saiya kunna motar tareda fadin “Inane gidan ku na kaiki” Bata amsa mashi ba illa kuka data keyi, tana jin alamar ciwonta zai tashi ne yasa ta gudu daga school ta fara gantali akan titi. Duk a hargitse take kamar bible din hausa. Daya lura batada niyar amsashi saiya kira babanshi which shine IG din yan sanda. Bayan wayan da wajen 45mins haka saiga babanshi ya iso tareda escorts dinshi. Kallo ɗaya yayi ma Miemie yasan cewa akwai alamar tambayan hankali a tareda ita. Tag dinta na suna dake rataye akan Wuyanta wanda shi guy din baima lura ba babanshi ya ɗaga ya karanta. “Bauchi Special School” ya karanta. Sai ya mayar da attention dinshi kan yaronshi tareda faɗin “Khattab ai ga komai a rubuce don ruɗewa shine ka kirani, gashi an rubuta Laurat Hussain Beli” sosa k’eya Khattab yayi tareda dariya saboda yasan he wasn’t really paying attention to her. Nan take IG yasa wasu police suzo su tafi da ita station ayi documenting komai cikin protocol. Nanfa ta soma dambe dasu wai bazata bar motan Khattab ba, shure shure takeyi tana hambarin police din idan kuma fatan ka ya kusa da bakinta saita ganna maka cizo. Haka tayi biji biji dasu tayi masu jina jina, su kuma suna raga mata ne saboda ba lafia ga yarinta. Daddyn Khattab yace su kyaleta. “Bakyaso ki bisu ne?” Gyada kai tayi alamar eh “Ina ne gidan ku?” “Ni tareda YaNaufal Zan tafi” “Waye YaNaufal?” ɗaga idonta tayi saita nuna Khattab. Sai IG yayi murmushi tareda faɗin, “Ai sunan shi ba Naufal ba, bakiji Khattab nake kiransa dashi ba.” “Na sani amma idan mutum yanada kirki toh YaNaufal zan kirashi” tafada tana Sheshek’ar kukanta. Khattab ne yace mai zai hana aje school dinta tunda gashi rubuce maybe aga family member dinta. Daga ɗayan bangaren Anty Saudah take zaune dirshan a gaban school din Miemie wai sai an fito mata da ɗiyarta. Tun sanda driver ya koma gida wai babu Miemie babu dalilinta saita saɓa gyale tawuce makarantan tanata kuka. Su kuma school din Naufal suka kira a matsayin Next of kin dinta. Duk an taro hankali a tashe kowa yayi charko charko, Naufal tunanin shi ɗaya ya zaiyi idan ya rasa Lil sister dinshi. Duk zufa yakeyi ya rasa meke masa dadi, har police station yaje yayi reporting babu wani kyakyawan labari. Su Abla da Bilqees suma sun samu labari hankalin su a tashe, sai Abba yace suje gidan gona incase Miemie ta gane hanyar gida. Ita ma Mama bataji dadin abin ba sanda ta samu labarin, tasan cewa babu daɗi babba yayi ɓatan hanya balle yaro. Kawai addu’a takeyi Allah yasa a ganta. Su Khattab sun nufa hanyar makaranta Miemie za’a mayar da ita. Shi dai baice komai ba illa tuk’a mota, ita kuma kuka take rusawa. A hankali ya furta “Sunana Khattab ba Naufal ba” ta gefen ido ta kalle shi saita watsar. “Na sani amma banga dama bane” ta faɗa tana fyace magina da kwallar riganta. Nan take abin yaba Khattab kyama saida yayi kakarin amai, dama shi abu kadan saiya saka shi amai. Waigawa yayi don yayimata magana sai ya hange tasono mak’ale a hancinta, da sauri ya buɗe window ya tsida miyau. Ita kuma Fadeela tana cikin kitchen ta dafa abinci, Danbun shinkafa tayi wanda yasha zogale da gyada ga kuma nama k’anana a ciki. Sai kuma tayi juice ɗin garin kuka wanda yasha pineapple da cucumbers sai ta haɗashi da Sambousah. Ta jera a wasu fararen Italian coolers komai yayi tsaf sai san barka. Bayi ta wuce tayi wanka tareda jero alwala, tayi nafilfilon ta saita haɗa da sallar Asr. Ita kadai tasan meke damunta saboda a duniya rainin wayau ne ta tsana. Tsaki ta doka tareda faɗin “Karma kazo mana tunda dama ban gayyace kaba” tana cikin haka ne saiga Mommy tazo, “Har yanzu Naufal ɗin bai zoba?” “Eh shine nima na gani” “To kira wayansa mana kiji ko lafiya” Shiru Fadeela tayi bata san mezata ce ba, saboda rabonta da shi tun ranar daya watsa mata kudi, itama Mommy a Pharmacy suka haɗu shine sukayi exchanging number. Toh a bakinta ne Fadeela taji zaizo sai Mommy ta tursasa ta akan saita mashi girki. Maza ki saka wannan kafin yazo baki shirya ba Kinga babu daɗi, ita kawai kallon Mommy takeyi yanda take rawar kai akan Naufal, “Da kinsan true colors dinshi da kin daina haka” ta faɗa a ranta. Tsam ta mike ta dauki kayan, Sky blue cord lace da akayi mashi ɗinkin kimono. Batayi makeup ba saboda acewarta kanayi ne wajen burge mutum kuma ita tsakani da Allah bata sanshi kawai tasan cewa dole ta mutunta shi. Su Khattab sannu a hankali suka isa school din Miemie, suna gaba su IG da escorts na baya. Kashe engines dinshi yayi saiya ce, “Okay sauka muje wajen Principal” bata kulashiba kuma bata nuna tanada alamar motsawa ba. Sauka yayi saiya zaga ta ɗayen bangaren. Dayake motarsa Range rover ne kuma it’s somehow high sai Khattab ya mika mata hannun sa ta kama ta sauko. Aiko a idan Naufal akayi haka, da sauri ya karasa tareda cin kwallarsa “Ubanwa ya baka dama ka dauki k’anwata? Da harzaka sakata a cikin akwalan motar ka salan whitlow ya kamata” Kafin Khattab ya amsa Abba yace, “Meye haka kake yi sai kace dage? Dalla sake shi” bai so ba saiya sake shi. Ita kuma Miemie kallon kowa tayi saita ruga motar Khattab ta dauke Masara a ciki ta fara gabza. Naufal ranshi yayi bala’in baci, “Zo nan Mallama bana hanaki barin school ba? Hawan jini kike so ya kamani na mutu koh? Shikenan na tafi naje na mutu” sai yayi hanyar motarshi. A guje taje tana bashi hakuri saboda a duniya ta tsani wasan mutuwa. Su kuma su Abban Khattab yayi Introducing kanshi a matsayin Inspector General Hamza Aminu Danbatta. Anan sukayi gaisuwan mutunci shine ya zayyana masu yanda Khattab ya tsinci Miemie. Nan take Abba yasa Naufal ya ba Khattab hakuri, musabaka sukayi sai yace, “I’m sorry man, I don’t know what my life will be Idan babu ita” “Dont worry komai ya wuce bcs I don’t hold grudges.” Ita Anty Saudah saida ta rankwashe Miemie akai, ita kuma Miemie tayi dariya wai da gangan ta gudu wai saboda YaNaufal yace bazashi wajen amaryar sa da ita shine tace gwara kowa ya rasa. Sai a lokacin ya tunada zancen wani Bad Luck, gefe yayi ya kira Mommy tareda bata hakuri akan rashin zuwan shi, yayi mata explaining Miemie ta ɓata ne but yanzu an ganta, in sha Allah within the week Zai duba ta. Jaje tayi masa tareda aika regards dinta wajen Miemie da Mamanta. Wata sabuwa wai inji yan cha cha! Miemie ta kafe bazata shiga motar kowa ba saina Khattab, shi kuma Naufal yace bata isa ba, nan aka rinka Jani in jaka da ita saida Khattab ya durkusa gabanta yayi mata magana cikin raɗa kafin ta tashi ta shiga motar Naufal. “Everything yayi daidai yanzu” ya faɗa saiya nufa hanyar motarsa. Naufal dabai iya boye abin mamaki ba saida yayi magana “Mai kace mata data hakura?” Murmushi yayi tareda faɗin “It’s our secret” Nikuma Dimples nace Iyye su Miemie yan mata. Ita kuma Fadeela ana gaya mata bazai zoba tayi kwafa saita kwashe abincin kaf takai ma mai gadi tace masa yaci sauran ya bama almajirai. “Daga yau na gama maka girki” ta faɗa yayin da take hayewa upstairs. *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 11 ✨✨✨ Jaber bin Abdullah Al-Ansari narrated that : A man asked the messenger of Allah : "Do you think that if I perform the obligatory prayers, fast in Ramadan, treat as lawful that which is lawful and treat as forbidden that which is forbidden, and do nothing further, I shall enter Paradise ?" He said: "Yes." Related by Muslim. ********  Kwance tashi ba wuya wajen Allah, shakuwa ne mara misaltuwa ya kullu tsakanin Khattab da Miemie. Tun yana fushi idan ta kirashi da ‘YaNaufal’ Har ya hakura. An raba routine dinta, Naufal ke kaita makaranta sai Khattab ya dauko ta. Shi dai Naufal bai sake jiki da Khattab ba. Baiga dalilin da wani katon banza zai rinka sintiri gidansu ba. Thou a ranshi deep down yana jin dadi atleast someone yana appreciating sister dinshi without discrimination. A chan gidansu Khattab kuwa an lura ya fiye fita kuma he is distracted, but ba’a San me yakeyi ba. Kawai ana tunanin zaman kadaici ne baya so. Shi kuma koda wasa bai taɓa tunanin ya faɗa masu ba saboda yasan za ayi tashin hankali. Haka rayuwar shida miemie ya kasance, kullum shakuwa sukeyi. Kwata kwata baya son damuwarta, abinda taga dama takeyi, sangarta ta yakeyi sosai har saida Naufal ya taka mashi birki kafin ya ɓata mata tarbiyya. Shi Khattab komai na Miemie burgeshi yakeyi, deep down a ranshi Idan ta soma hauka kadan kadan baya yarda, kawai k’uruciya yake daukan abin saboda tun haɗuwan su batayi tuburan ba saboda tana shan magani akai akai. Naufal yana nan yana aiki tareda su Mr Sutter, yaro mai hazaka suna jin daɗin aiki dashi. Basu ɓoye mamakin suba saida suka cemasa basu taɓa ganin bakin fata mai rik’on amana kamar shiba. Sunyi alkawari suma zasu saka mashi nan bada daɗewa ba. Ta ɓangaren aurenshi da Fadeela kuwa, babu abinda ya canza both families anata hada hada aga an kece tsara. Sau ɗaya Naufal ya tada maganar wajen Abba amma bai samu fuskar karasawa ba saboda wanki babban bargo yayi mashi, kuma da yaje wajen Mama itama bata sake mashi fuska ba saboda tun ranar da Abba ya tarasu da daddare yayi masu tas ta hankalta dashi. Zancen sadaki kuwa an biya dubu ɗari cash da kuma Ningi(shanu) guda biyar. Alhaji Musa ne watau Big Daddy ya jagoranci komai saboda a gidansa akayi komai tunda shine zai bada aurenta. Shi kuwa Alhaji Sulaiman ya bada kudin sadaki saboda shine zai karba auren Fadeela. Anyi komai cikin mutunci tareda tanɗe tanɗe, zumunci sosai ya kullu tsakanin iyayen kai zaka zaci sun san juna da daɗewa kuma ba surikai bane. Ko Mommy takan kira Anty Saudah domin taji lafiyan Miemie, jefi jefi tana kiran Mama itama. Saidai su kaɗai ke abinsu, Daga Naufal har Fadeela kowa harkan gabansa yakeyi kamar ba zancen aure nan kusa. Kuma rabon dasu haɗu tunbayan yaje bada hakuri gidansu. Zuwan bazata yakeyi kuma cikin ikon Allah bai taɓa riske taba. Mommy yake gani sai sau ɗaya yaga Grand Kadi. Kullum Mommy adduar daidaituwan tsakanin Su takeyi saboda bata san Fadeela tasha wahala zaman aure. Aure dace ne kuma idan kayi sa’a kaji daɗi. Siyayya babu kama hannu yaro Mommy kema Fadeela, kullum tana ziryan zuwa Kanti kwari dake Kano. Ita bataga bambanci tsakanin kayan dake Nigeria da kuma Kasar waje ba, acewarta yan Nijeriya ke zuwa Kasar waje siyowa saboda haka sun hutarshe ta. Kana ganin abinda aka siyan mata kasan cewa ‘yar so akema wannan siyayya. ******** Ita kuma Amatullah ba’a san ranta tayi siyayyan lefe ba. Data siyo na farkon saida ran Mama ya baci. Karanci k’arara ta nuna kamar lefen matsiyata. Nan take Mama ta sakata ta mayar dakomai. Dukda itama ba wai tana wani san auren bane amma za'a zageta a mak’ota saboda ace wai duk kuɗin Naufal tsiyan da ya iyayi kenan. A karo na biyu tareda Anty Uwani k’anwar mama akaje. Wannan Karon komai yayi sai san barka, akwatuna set 2 akayi mai gudu hudu making eight boxes altogether. Komai yaji duk yanda Amatullah taso tayi k’arancin Anty Uwani bata fuska ba, dole ta hakura da duk wani mugunta data soyi babu hali. Dama akwaita da san Duniya taso ta siya fake abubuwa saita ci sauran kudin. Itama Anty Saudah akwati set guda tayi purple Calvin Klein mai guda shida. Saboda ita ta dauki Naufal a matsayin yaronta bana kishiya ba. Gabaki daya set din akwatuna uku akayi wanda za’a kaima Fadeela. ******** Kwance yake akan three seater yana kallon JSC sport, favorite sports ɗinshi ake nunawa watau Badminton but baya ganewa. Tunani yakeyi kala kala ranshi duk ya jagule. Mommyn shine ta shigo ta soma magana, “Kaiko Khattab tun dazu Lili ke ɗakin ka tana jiranka amma kazo falon Daddyn ka. Halan ka daina san Lili din ne?” sai kuma ta fashe da dariya tareda faɗin, “Khattab na Lili babu mai raba ku. Nasan kaima baka ji dadi da akace saita gama school kafin ayi bikin ku, but karka damu yau da gobe duk ɗaya ne wajen Allah.” Yak’e kawai yake mata saboda yanzu kwata kwata baya son zancen Lili, dama bawai Santa yakeyi kawai yanuwan taka ne sai aka kai baikonsa dana Lili. Toh dayake ta haɗu iya haɗuwa yasa baiyi gardama ba. Amma yanzu komai zai faru saidai ya faru saboda shi k’anwar Naufal yakeso. Dukda yasan cewa yarinya ce kuma gata da taɓun hankali amma shifa yaga matar aure saboda ko Naufal bai isa ya hana shiba. “Yaya Khattab nan dama kake shine ka barni Inata kewarka” Lili ta Faɗa tana shagwaba tareda yauki kamar kuɓewa. “Eh” ya amsa mata dashi saiya mayar da hankalin shi kan Plasma dake bango. “Yanaga kayi shiru?  Ko yunwa kake ji?” “Eh” “Na dafa maka Indomie ne?” “Eh” shifa abinda yasa yake amsa mata da eh kawai bai wuce baiso ya bata fuska takama mashi surutu ba. Domin idan ta fara tana jin kanta kamar ta haɗiye radio. Amma ya lura Sam bata ganewa, ko ka bata fuska ko baka bata ba saita yi. Harta kai kofa ya dakatarda ita, “A haka zan aureki kina dafa min Indomie?” murmushi tayi tareda dawowa kujera ta zauna daf dashi tareda rik’o hannunsa, “Yaya kada ka bari k’aramin abu kamar girki ya shiga tsakanin mu.” “But kinsan farinciki na shine naga kwanan abinci koh?” Shiru tayi na wasu seconds haka saita ce, “Akwai masu aiki ai, kokuma muje restaurant muyi ordering abinci irin mai yawa wanda ake stocking a fridge kaga da munji yunwa sai dai muyi micro waving” “Lallai” ya iya faɗi kawai domin abar maganar. 25 mins later...... Lili ne ta dawo tareda tray ɗin abinci a hannun ta, Indomie ne wanda yasha kayan haɗi, daga su carrots, peas, sweet corn da baked beans duk ta kwaɓa. Amma yana sakawa a baki ya shak’e ya kasa haɗewa. Idanun shiya firfito duk yayi ruwa. Da sauri Lili ta tallafa mashi kafaɗan shi, “Yaya Lafia?” “Na kware ne” Roban chi exotic dake wajen ya kurɓa, bai barsha ba saida ya shanye. Tunanin shi ɗaya bai wuce ina zaije da sauran abincin. Bcs yasan cewa mata basa so idan sunyi girki ak’i ci. Rashin dadin Indomie ɗin baya misaltuwa, closest da zai iya faɗi shine kamar an wanke kan tsohuwa ko mahaukaciya k’azama. Haka ya sake tura wani loma tareda taimakon ruwa. “jeki dauko min wani exotic kinga bai isheni ba” Da fara’arta ta mik’e tayi downstairs hanyar kitchen. Yana ganin tayi nisa ya tashi da gudu yayi hanyar bayi domin yayi flushing din abinci ciki. Ya dawo ya zauna kenan yana haki sanadiyar gudun dayayi saita dawo. Kallo ɗaya tayima kwanon saita sakar mashi wani lallausar murmushi tareda fari da idanu. Shima murmushi yayi tareda sosa k’eya. “Narrow escape” ya faɗa a ranshi. Ita kuma ta mik’a mashi exotic ya hau kyankyama. Yana gamawa saiya dauki mukullin motarsa yayi hanyar k’ofa, “Bari naje wajen Sambo” bai jira amsa dinta ba ya ficewarsa. Abokinsa Kabir Sambo shine suke haɗa baki dashi idan zashi wajen Miemie incase an tambaya. Yana tafeyana tunanin irin artabu da za’a sha idan ya kuskura ya furta Soyayyar Miemie but he can’t help it. Dama in life you don’t chose who you fall in love with. Yana isa gidan gonar Anty Saudah maigadi ya buɗe mashi saboda sun saba. Kai tsaye Babban falo ya wuce, Anty Saudah kawai ya riske a falo tana kallon Sunna TV. Rinsinawa yayi ya gaishe ta saiya zauna akan One seater, ya shafa’a ya mance da komai yana danna waya saiya ji kamshin turare ya dake hancin sa. A hankali ya ɗaga ido yaga ko waye, Saida ya k’ara murje Idonshi da kyau kafin ya ganeta. Sanye  take cikin wani peach Da viva wanda yasha ɗinkin shoki. Dayake kwanan biyu Bilqees tana gidan ita tayi mata daurin gwargwaro saboda ta lura Khattab baa matsayin k’anwa ya dauketa ba fyace masoyiyarsa, shine tace bari tayi surprising ɗinsa. Light makeup tayi mata na nude lips sai light smoky eyes. Saida ta kwaɓeta akan tayi tafiya a hankali kuma karta faɗa jikinsa. Dayake kanta yana ɗan daidai kwanaki biyu haka tayi duk abinda akace tayi. Sallama tayi a hankali cikin siririn murya saita kame a one seater. Shi kuma bai samu daman amsawa saboda ya shagala yana tunani. Gabaki daya ta canza ba Miemie yar 14 yrs ba, ta zama cikarkiyan mace san kowa k’in wanda ya rasa. Naufal ne ya shigo saiya lura da meke faruwa, snapping fingers dinshi a iska yayi tareda cewa “ me kake kallo haka?” Dariya yayi tareda cewa, “Haskena” #NiDaDiyata *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 12 ✨✨✨ It was narrated from Aws bin Aws that The Prophet (pbuh) said: "One of the best of your days is Friday. On this day, Adam was created and on this day he died, on this day the Trumpet will be blown, and on this day all creatures will swoon. So send a great deal of salah upon me on this day, for your salah will be presented to me." They said: "O Messenger of Allah (), how will our salah be presented to you when you have decomposed (after death)?" He said: "Allah (SWT), the Mighty and Sublime, has forbidden the earth to consume the bodies of the prophets, peace be upon them." (Da'if) *********** Kallon up and down Naufal yayi mashi sai yayi kwafa ya zauna shima a falon. Abin baiyi ma Khattab daɗi ba amma babu yanda zaiyi tunda gidansu ne. Shi dama yaso a hankali da lallaɓi da wayau ya rinka cusa mata sanshi a zuciyarta but ga wanta yazo yayi masu k’erere. Miemie ta riga ta faɗa mashi yayanta yana fushi da ita idan tayi mashi maganar sabuwar amaryarsa, so daga dukkan alamu baya san auren da za’a yi mashi. Shi dai abinda ya sani cewa soyayya gamon jini ne kuma dashi aka haife mu, kuma yana saka ran ya haihu dashi saboda haka idan Naufal bayayi toh shi yana yi. Hankalin kowa yana kan TV a Nickelodeon channel inda ake nuna Sponge Bob Square Pants. Wannan shine favorite program ɗin Miemie Kuma idan kana Santa dole ka kalla. Ni dai Khattab bana gane abinda ake nunawa, jefi jefi saina kalli inda Miemie take. Sau da dama idan nayi haka muna haɗa ido da Naufal sai ya haɗa girar sama dana k’asa. Dama tun kafin shigowar Miemie Anty Saudah ta koma ɗaki, haka na gaji da zama na tashi zan tafi. “Lil sis Haskena, goodbye and see you tmr” Sai na ɗaga mata gira. Shi kuma sai na bashi hannu muka gaisa. Ashe abin ya bala’in bashi haushi har na buɗe murfin mota zan shiga, “Khattab ji mana” ya faɗa. “Lafia dai koh?” na tambaya. “me kakeso wajen k’anwata? I mean Wats ur end game?” “Ban gane question ɗin ba” “Okay! Bari nayi maka dalla-dalla, kasan cewa kanwata batada lafiya kuma she is young. So Karka ce mun duk kuɗin ka da aji itace yarinyar da kake so which kasan bazan yarda ba. Nasan cewa kawai kanaso kayi taking advantage ɗinta kuma bazan iya bari haka ya furu ba.” “So tun kafin ranka ya ɓaci gwara ka nisance duk wani plan ɗinka bcs Miemie tayi maka nisa kamar sararin samaniya.” Shiru Khattab yayi na wasu ‘yan mintuna sai yayi ajiyar zuciya kafin yace, “Wallahi banida wani manufa daya wuce alheri tsakanina da ita. Thou nasan tayi k’arama kuma bai kamata na furta mata komai. But ni zan iya jiranta harta k’ara wayau. Please YaNaufal kar ka rabani da ita saboda bansan halin da zan shiga ba” Yana kaiwa nan sai wayar shi tayi k’ara, Suna ɓaro ɓaro ya fito akan screen wanda aka rubuta ‘Bae’. Harara Naufal ya watsa mashi saboda shima ya karanta, kai tsaye wajen mai gadi ya wuce, “Karka k’ara barin wancan ya shigo mana gida” “An gama Oga daga yau ya gama” Mallam Bello mai gadi ya amsa. Har ya soma tafiya ya hau benen dake varenda saiya juyo ya kalli Khattab tareda faɗin, “For thelast time baka babu ita” saiya garke kofa. Shikuma Khattab ya rasa mai zaice bcs tabbas Naufal yaga daidai but locacin suna ɗasawa da Lili shine yayi saving ɗin sunanta as ‘Bae’ amma number ɗin Yafi six months da ɓacewa so bata amfani da shi gashi ya mance yayi deleting. Jiki babu kwari ya shiga motarsa zai tafi saiga Miemie tazo da sauri, “Yaya Khattab tsaya kaji wani abu” Mamaki k’arara a fuskarshi saboda tun dayake da ita Naufal take cemasa. “Kaga ɗazu nayi shiru koh? Toh wlh Anty Bilqees tace wai na daina magana a gaban ka, duk mekace min kawai nayi murmushi ne. Sai kuma me ta ce min......” ta ɗaura yatsan ta akanta tana tunani. Tun da yake da ita sai yau ya tabbatar da ciwon na gaske ne bcs anyi abu a sirri tazo tana faɗa mashi. Murmushi kawai ya rinkayi bcs Dis is the least of his problem. “Sai kuma me tace?” ya tamabayeta Shiru tayi kafin tayi ihu tareda daka tsalle, “Yauwa na tuna.... Wai na rinka kiranka da Yaya Khattab” “Toh kice ma Bilqees nagode sosai, bye Haskena be a good gal kinji koh” Gyada kai tayi alamar Okay, shikuma ya tafi. A mota yana tuk’i yana tunanin wani matsala zai fara magancewa, Naufal ko Lili? ****** “Wa’anan Sune last set koh?” Mommy ke tambayan Fadeela. “Eh Mommy, kinsan tun jiya na fara kaiwa” Shiga mota sukayi suka bar haraban gidansu, tafe suke zasu Larema inda Fadeela zata yi exhibiting Art works ɗinta. Su paintings ne daya jiɓanci k’orama, sararin samaniya, ciyayi da gonaki, fituwan rana da saukar shi, hasken taurari, al’adun Mallam bahaushe da sauran k’abilu. Akwai kuma laka data k’era abubuwa daban daban kai duk dai kayan Arts. An gyara hall an gayyaci manyan ɓaki kuma duk sun hallara. Grand Kadi ne ya buɗe taron da addu’a sai aka bama Fadeela dama tayi bayani akan abinda ta zana. Yarinya mai hazaka tayi komai gashi turanci ya zauna mata a baki. Bayan ta gama sai mutane suka shiga siye, wakilin Commissioner of Culture and Tourism ya siya guda uku wanda za’a kai gallery ɗin ma’aikatan su. Su Jawahir da Mijinta suma sun dauki ɗai-ɗai, an siye komai saura guda ɗaya kuma shi ne wanda Fadeela tafi so, wanine ya shigo da saurinsa ya ɗauka tareda biyan kudin. Bayan komai ya daidaitu sai Fadeela da k’awayenta suka keɓe ana hira tareda tanɗe-tanɗe. “Oh yanzu baza mu k’ara taruwa haka ba sai bikin Deela” Samɗa ta faɗa “Aikuwa dai” Mansura ta chapke. Ita dai Deela bata ce komai ba illa wasa da Ihsan yarinyar Samɗa. Kawai a ranta tana sha’awan dama ɗiyarta ce. Batada wani buri a duniya daya wuce ta haihu amma tasan cewa indai da Naufal ne to zata bushe! “Saura kwana nawa yanzu?” Samɗa tayi tambaya tana kallon Deela, taɓe baki tayi tareda faɗin, “Ni ina na sani, kya tambaya kaza hanyar rafi ai agwagwa zaki tambaya Kisha labari. Sai kije ki tambaya wanda zasu min auren” ta faɗa tana matse kwalla. “Babban magana!” Mansura ta faɗa sai sukayi shiru. Mommy ne tazo wajen zamansu tareda Baby Fauziya yarinyar Jawahir, “Halan baki gayyaci Naufal bane naga bangan shiba?” Tsuru tsuru Deela tayi saboda tabbas Mommy ta gargaɗeta akan lallai saita gayyaci shi toh amma bata san yanda zata fara cewa batada number ɗinsa ba kuma koda ta ɗauka a wayar Mommy bata san me zata ce masa ba. Da Mommy taga Fadeela batada gaskiya sai tayi kwafa tareda Faɗin, “Kin kyauta tunda ke bakya jin magana” saita juya ta bar wajen. “Wai meye haka kike yi ne?” Samɗa ta faɗa. “Inace duk cikin mu kinfi hankali amma shi ne kike so ki nuna ba’a yaban ɗan kuturu saiya girma da yatsa” “Wai tsakani da Allah meye aibun Naufal? Ga kuɗi ga kyau dream ɗin yanmata amma shine kike misbehaving” “Please Karki basu mommy kunya kinga dai yanda suke ɗawainiya dake,” Buɗen bakin Fadeela saita ce “Nifa ban masa komai ba ya tsane ni tun kafin a kaini gidansa kenan! Shikenan dan mutum baya magana sai a taka sa?” “Toh ai kece mace saboda haka dole ke zaki rage girman kai kiyi masa biyayya. Wai shin wani irin zama kike so kuyi idan an kaiki? Doya da manya? Wallahi yarinya ko mak’iyina bana ma wannan fatan” “Ya isa haka ni bari naje na samu ma Ihsan Bobo ta sha” Deela ta faɗa tareda barin wajen. Dariya Samɗa kawai tayi tareda faɗin “Wasa kike yarinya, baki san aure ba wallahi! ” Daga ɗayen ɓangaren bayan Khattab ya tafi, Naufal yazo wucewa wajen Larema saiya ga Flyers na Art exhibitions haka, a cikin hoton saiya hangi akwai paintings ɗin fitowa da saukar rana shine yaje siya. Yanda gurin ya cika sai kawai yayi parking ɗin motarsa a waje tareda bama Secretary ɗinsa kuɗi ya siyo mashi kuma cikin ikon Allah the last one that was remaining shine choice ɗin Naufal. Shidama tun fil azal ya saba suje su kalle sunset da sunrise tareda Anastacia, yasa daya ga paintings ɗin ya kwallafa saiya siya. Thou yanada paintings shigan haka a ɗakin shi but their is smtin unique about dis one. Ya gama duk wani harkar gabansa na ranar ya koma gida, ya kai painting ɗin dakinsa yanata neman inda zai ajiye. Duk ɓangaren daya saka sai yaga baiyi ba, a karshe awards ɗinshi dake manne a bango ya cire ya saka. “Perfectly placed” ya furta a fili. Hannayenshi yana harɗe akan kirjinsa yana kallon painting ɗin yana murmushi sai idanshi ya hange wani rubutu a ciki ta gefe, “Deela” aka rubuta da style ɗin calligraphy. Murmushi ya sakeyi tareda faɗin “koma waye Deela, you’re talented and unique” hayewa gadonsa yayi tareda dai-dai har barci ɓarawo yayi awon gaba da shi. 10:45pm..... Locacin ne Khattab ya bar gidan Sambo ya koma gida. Yana isa cikin gidan sai ya risk’e wutan falo a kashe, jindadi mara misaltuwa ya kamashi saboda kwata kwata baya son ya haɗu da Lili. Yana isa wajen stairs sai yayi karo da wani abu tim ya kusan faɗi. Karon rago yayi da Lili wanda ta kefa kanta akan gwiwoyinta tana sharban kuka. Da hasken waya ya haska mata fuska saiya lura idanunta sunyi luhu luhu. “Daga ina kake?” Kallon up and down yayi mata baice komai ba saiya ratsa ta ya haye sama abinsa. “Da Kai nake Yaya Khattab, ina kaje ka daɗe haka? A haka zan aure ka kana kaiwa tsakar dare? Wallahi da sake wai anba mai kaza kai” “Toh uwata jirani nazo nayi maki bayani” ya faɗa mata still bai waiga ba. “Gaskiya Yaya I won’t tolerate it, saboda haka dole ka bani kwakwaran dalili idan bahaka ba......” “..... Idan ba haka ba me zai faru?” ya juya a fusace yana kallon ta, ido cikin ido yana haki duk ranshi ya baci. Ita kuma jikinta ya soma rawa duk ta tsorata. Hannunshi guda ya daura akan shoulder ɗinta sai ya soma magana cikin raɗa raɗa, “Daga yau sai yau, Karki k’ara min tambaya daya wuce gona da iri. Babu ruwanki da al’amura na,....” sai ya cize leɓansa tareda saketa. Dakinsa ya wuce direct, ji kake Dam ya banko k’ofa. Ita kuma da sauri taje ta rinka bugawa. Sababi takeyi babu kama hannun yaro wai bazata bar wajen ba saiya buɗe. Shikuma direct bayi ya wuce yayi wanka, yana dawowa ya saka green three quarter da farin singlet. Still yana jin mostin ta a kofa tana kuka. Wayanshi ya dauko ya shiga YouTube ya fara kallon video. Bubbuga k’ofa ta k’ara yi wannan karon harda kafafuwanta, Mommy ce ta fito tayi mata magana amma tayi kunnen uwar shegu da ita. “Badake nakeyi ba, nace ki bari ya isa haka” Tsandara ihu tayi tareda faɗin, “Mommy ni bansan meyasa yake min wulakanci ba for no reason” “Ki bari gobe zan ci masa but go and sleep yanzu” saita jawo Lili jikinta tana bubbuga mata baya har suka bar wajen. Yana jin duk abinda sukeyi amma bai sa ma su baki ba, Sam bai ji daɗin yanda Lili take treating Mahaifiyarsa ba but duk laifin Mommy ne. Itace tace ta dawo gidansu da zama, yanzu shekara ɗaya kenan. Kuma ita ce ta cusa ma Lili idea taso shi, gashi idan tayi magana anyhow bata kwaɓan ta. Saidai bazai dauki iskanci ba, tana mashi yake mata ko sanda yake santa balle da yanzu komai salam. Kawai yasan cewa akwai ranar k’in dillanci, wai randa babban rigan Maigari ya ɓace. #NiDaDiyata *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 13 ✨✨✨ On the authority of Anas, who said: I heard the messenger of Allah say: Allah the Almighty has said: "O son of Adam, so long as you call upon Me and ask of Me, I shall forgive you for what you have done, and I shall not mind. O son of Adam, were your sins to reach the clouds of the sky and were you then to ask forgiveness of Me, I would forgive you. O son of Adam, were you to come to Me with sins nearly as great as the earth and were you then to face Me, ascribing no partner to Me, I would bring you forgiveness nearly as great as its." Related by Al-Tirmithi, who said that it was a good and sound Hadith. ****** Muddin an tsayar da lokacin abu toh inda rai da lafiya sai anyi. Yau Asabar kuma yazo daidai da ranar tarban lefen Fadeela. Lefe yana daga cikin al’ada na Mallam Bahaushe idan zaayi aure, ya jiɓanci kawo kayan sawa dana amfani daga dangin miji zuwa ga amaryarsa. A al’adan daya gabata ana kaiwa a cikin kwalla ko makamancin haka, amma yanzu zamani yazo da su akwati seti seti. Toh dayake Fadeela yar zamani ce itama akwati aka kai mata, akwatuna guda goma sha huɗu watau seti kala uku wasu ‘yan huɗu wani mai shida. Kamar yanda al’ada ya nuna, ana taruwa a gidan Amarya tareda yanuwa, makwabta da abokan arziki. Ana tanajin su kayan motsa baki kamarsu Sambousah(Samosa), Meatpie, spring rolls, peppered chicken or meat etc Wanda za’a bama dangin miji as tukwici. Mommy itama ta tsaya a tsaye saida taga an tanaji komai na bak’in. Anty Saudah itace a gaba wajen ganin komai ya kankama daga ɓangaren su, mota uku sukayi aka dunguma GRA inda gidansu Fadeela yake. Kowa ya hallara a babban falon Grand Kadi ana zaune, Anty Uwani ta buɗe taro da addu’a sai aka fara. Gwaggo Mahaifiyar Grand Kadi aka mik’a ma trinket box. Ran Anty Saudah fari sol saboda bataji kunya ba, itama Mommy ta yaba da kaya saboda komai yaji Tabarakta Masha Allah. “Wai banga Amaryar bane?” Anty Saudah ta Faɗa “Eh nima inaso na ganta” Miemie ta chapke. “Kunsan ta da kunya, wallahi tun jiya ta dawo gidana kada ku riske ta” Hajia Rabi matar big Daddy ta amsa. “Babu komai muda zata dawo cikin mu da zama” Anty Saudah ta faɗa tana dariya. “Allah ya Kaimu lokacin, yasa ɗakinta ne ya kuma basu zuri’a ɗaiyiba” Maman Humairah makwabciyar su Fadeela ta faɗa. “Amin summa Amin” kowa ya faɗa. Daga nan sai aka basu tukwicin kuɗi tareda na abinci aka watse. In ran Miemie yayi dubu to ya ɓaci, taso taga amaryar amma bata samu dama ba. Dayake da Abla akaje sai tayi mata raɗa ko suje gidan Hajia Rabi don suga Fadeela. Harara ta daka mata wanda ya natsar da ita. Ita kuma Fadeela tun jiya take kuka data lura abin da gaske ne. Yanzu saura sati biyu cur a daura mata aure da wanda baya santa. Ko sau ɗaya bata taɓa tunanin haka zai faru ba. Ita irin Telemundo gal ce, batada wani buri daya wuce tayi zaman soyayya da mijinta thou bawai ta taɓa yin shi Soyayyar bane, but still! Kuka tayi babu k’akkautawa tana k’okarin ta tattara tunaninta waje ɗaya ta gano dalilin da Naufal ya tsaneta amma ta kasa ganewa, ita dai ba wai ta sanshi bane daga wani waje balle ace wani abu. Kawai dai ta lura idan ya ganta har wani jijjiga yake saboda bala’i. Tashi tayi tsam ta wuce bayi ta daura alwala, sallah raka’a biyu tayi tareda mayar ma Allah komai. Tasan cewa nata jarabawar kenan kuma tana fatan taci da flying colours. Bayan la’asar sakaliya Hajia ta dawo daga wajen tarban lefe, washe baki kawai takeyi tana murna. “Amma ‘yannan kinyi tagomashi. Lefe sai kace na yaran sarakuna kokuma masu gwamnati” Hajia Rabi ta faɗa Murmushi kawai Fadeela tayi ta cigaba da kallon wani reality program a ‘E’ mai suna The Rich Kids of Beverly Hills. Hajia Babba sai kawo mata maganar lefen takeyi amma bata sakar mata fuska ba, dolenta ta hakura da hirar. ****** Kullum sai Khattab yaje k’ofar gidansu Naufal sau biyu ko uku amma baya samun damar yaga Miemie. Sau biyu yana riske Naufal amma baya bashi dama ya shiga. Babu irin magiyan da rok’o da bai yiba amma ko kulashi baiyi ba. Ita kuma Miemie tafiya Naufal ya faɗa mata Khattab yayi, harda karyan cewa ai randa yazo sallama yayi mata saidai bata lura ba. “Allah ya dawo dashi lafiya” abinda kawai ta iya faɗi kenan saboda tasani sarai k’arya yakeyi. Sau da dama Khattab yana zuwa makaranta Miemie amma Naufal har cikin school yake shiga da motarsa ya dauko ta. Da abin ya isheshi saiya mayar da ita gidansu wajen Mama wai tayi mata hutu tunda yasan Khattab baisan wajen ba. Shi kuma Khattab abubuwa sun cunkushe mashi, na farko an hanashi ganin Miemie. Na biyu kuma jarabar Lili, tariga ta raina shi kamar mijinta ko sa’anta. Kullum suna cikin bala’i kamar kaji kuma koda yaushe Mommy tana mara mata baya. Fatan shi ɗaya next week Mommy Zata tafi Ummarah kuma gashi Daddy ba mai zama bane, Lili tana mashi yayi mata ɗan iskan duka da saita raina kanta. Ya ɗauki alwashin saiya saisaita mata duk wani rawar kan datake tak’ama dashi kuma gashi mai cecenta bata nan. Sam Khattab bai iya tashin hankali ba sai sanda ya dawo gida bayan yayi graduating Masters ɗinshi a Almadina University dake Shah Alam Malaysia. Ya karanta Information Technology kuma yanzu haka yana serving a wani ICT center haka Thou ba kullum yake zuwa ba. Khattab dai fari dogo ne, yanada cikar halitta kuma fuskar shi akwai saje wanda ya kara k’awata wajen. Shi cikakken bakano ne a wani gari da ake kira Danbatta. Mahaifin shi IG Hamza Aminu Danbatta ya aure mahaifiyarsa Hajia Shatu kumaAllah ya albarka cesu da yaro ɗaya tilo watau Khattab. Bayan wasu shekaru sai k’anin IG watau Alhaji Ibrahim ya aure k’anwar Hajia Shatu. Sun haifi yara uku, Usman, Halima wanda ake cema Lili sai auta Lubna. Lili shekarunta 19 a duniya kuma tana School of Nursing and midwifery dake ATBU a garin Bauchi. Yanzu haka tana 3rd year ɗinta. Kyakyawan yarinya san kowa k’in wanda ya rasa saboda Allah bai rageta da komai ba wajen fannin halitta, in hasken ne tana dashi, tsawon gashin shima kazo wajen, shape kamar an zana number ‘8’, zak’in murya ka samu.... In fact everything. Saidai dama ɗan adam tara yake bai kai goma ba, kyau kawai gareta babu halin kirki. Yanda kasan empty vessel ko fanko to haka take. Kwata kwata batada daɗin sha’ani. Bata iya magana ba at all, duk abinda ya fito daga bakinta zata yaɓa maka kuma ko taji kunya saidai na gefenta su ji. Ga tsiwa ga rashin kunya ga kuma bala’i koda yaushe kamar dage. Tun kafin Khattab ya dawo daga school Mommy ta dauko Lili ta dawo da ita gidan saboda yana dawowa yayi arba da ita su fara soyayya. Duk mugun halin Lili Mommy bata gani, ko tana mayar da abin yarinta ne ko kuma menene dalilinta Oho? Sau da dama Lili na chaba ma Mommy magana amma sai Mommy ta kauda kanta. Sanda Khattab ya dawo yaga Lili yayi Na’am da batun Soyayyar su saboda yar gaban mota ne, but daga baya daya lura da halinta saiya fara ja da baya da ita but yanzu dai it’s too late saboda Har Iyaye maza sun shiga maganar. Shi Khattab mutum ne mai san girma kamar gyambo ita kuma Lili akwai k’ask’anci, yasa idan suka fara gardama basa tsayawa. Tun yana kyaleta amma yanzu ya dauki alwashin tana mashi zai rama, when it comes to Lili to bayada hakuri kamar zawo. Shidai ya gwammace ya zauna da wanda rashin hankalinta ciwo ne kuma idan sauki yazo mata tanada daɗin sha’ani da yazauna da Lili, Wannan kenan! #NiDaDiyata *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 14 ✨✨✨ On the authority of Sahl bin Saad Al-Saedi, who said : A man came to the prophet and said: "O Messenger of Allah, direct me to an act which, if I do it, [will cause] Allah to love me and people to love me." He said: "Renounce the world and Allah will love you, and renounce what people possess and people will love you." A fine Hadith related by Ibn Majah and others with good chains of authorities ********* Yanda yaga rana haka yaga dare, tsaye yake gaban agogon bango. Kallon kur yayi mashi yana kallon sauran awanni nawa a daura mashi aure da ‘Bad luck’ wanda shi bai taɓa kiranta da sunan taba. Duk jijiyoyin fuskarshi ya mimik’e, idanunshi sunyi jazur daga bacin rai da kuma rashin barci. “Wai tsakani da Allah a ina aka taɓa yima namiji auren dole?” ya faɗa da karfin gaske tareda naushin bango. Hura iska ya rinka yi ta baki da hanci. Rabon daya kwana a gidansu kwana huɗu kenan tun kafin zuwan ‘yan biki. Da akayi mashi magana saiya wayance wai bai so ya takura ma mutane ne. Mama taji daɗin abin sosai saboda ya nuna yanada hangen nesa. Shi kuma abinda yasa ya bar gidan baifi rashin san yaga yanda ake shige da fice kuma daya ci karo da mutum zai iya sanya alheri a lamarin kuma abinda baya so kenan. Baisan gaibu ba amma baya jin akwai alheri a tareda lamarin. 11:09am abinda ke rubuce akan agogo, “Saura awa uku a kaini makisa na” Bayi ya shiga yayi wanka saboda ya mance rabon dasu haɗu da ruwa saboda tashin hankali, yana fitowa ya nema inda wayarsa na handset yake. “20 missed calls” ya gani. Shiru yayi daya lura da wanda yayi Most Call ɗin. Abbanshi ne tareda Anty Saudah kuma indai abu daya jiɓance bukin ne toh basa raga mashi, yanzu yanzu sai suyi balangu da namanshi. Shi abinda yafi bak’anta mashi rai bai wuce yanda Fadeela ta saka soyayya ɗinta a zukanta yan uwanshi. Wai tun ma kafin ta shiga kenan! Mutum ɗaya ce ya lura bata san abin, watau Amatullah amma tana aure a Gombe balle su taru su musguna ma Fadeela. Daga ɗayan ɓangaren Fadeela ta saka bala’i baza ayi mata kowane gyaran amare ba. Tun ana binta da lallami da ɗadin baki saida Mommy ta shiga jikinta da duka, farfasa mata jiki tayi sosai saboda hanger ta ciro a drawer ta rinka auna mata. Hajia Rabi matar big Daddy ta shiga tsakaninSu, Mommy ta rinka sababi duk takaici ya isheta. “Ke bahun ubanki, yar tselan uwa! ” mommy tayi ashar bata masan tayi ba. Ita dai Fadeela kuka takeyi kamar ranta zai fita, wai akan Naufal aka taɓa lafiya jikinta. Abinka da farar mace duk ta kumbura tayi jazur, kana ganinta saita baka tausayi. Idanunta sunyi k’anana saboda kuka da rashin isharshen barci. Ta hakura za ayi mata auren dole amma babu wanda zai mata wani gyaran jiki, ko kitso bata so kawai a  kyale ta. A daki Hajia Rabi ke mata nasiha akan rashin bin maganar iyaye amma abin baya shigan Fadeela, sai kawai tace mata, “Wannan rashin kunyan da fitsara da kikeyi halan wani yace ki kashe auren ki ne zai aure ki?” Sai a locacin abin ya dake ta, Sam bata so tayi zawarta da wuri kuma ita batada wanda ke jiran ta. Nan take tayi ma kanta karatun ta natsu, bcs ga yanmata birjik a gari babu mazajen aure ita ta samu tana yanga. Tun daga lokacin aka samu kanta, har kitso da kunshi ta yarda anyi mata. Da aka yi mata maganar tsimi da maganin mata sai kawai ta taɓe baki tareda kawar da fuska. Nan aka kyaleta ba’a kuma takura mata ba. Ta ɗanyi fara’a sosai ba kamar jiya ba, Mommy itama taji daɗin yanda ta sauya tana harka cikin ‘yan uwanta. Koda Mommy tayima Naufal magana ko yanada events ne dayake so Fadeela tayi attending, sai yace mata shi bazai yi komai ba. Amma kuma ya tambayeta idan akwai wani abu daga nasu ɓangaren, uku uku zuciyar shi ke bugawa saboda baiso wani abu ya haɗashi da ita. Gaskiya bazai iya zama waje ɗaya da ita ba, ai saiya rasu! Kaddara ta riga fata saboda Mommy tayi assuring dinshi suma ba zasuyi komai ba. Kuɗi sosai ya aika ma Fadeela wai kada tayi lacking saboda sha’anin biki. Har cikin ran Mommy taji daɗin abin, ita kuma Fadeela da farko taso tak’i amfani da kuɗin amma sai ta tuna bahaushe yace ‘Raba mugu da makami ibada ne’ nan take ta soma fachaka tana spending anyhow. 2:30pm...... Hausawa sunce ranar wanka ba’a ɓoye cibi, an daura auren Naufal Hussain Beli tareda Amaryarsa Fadeela Abbas Bello akan sadaki naira na gugan naira har Dubu dari ɗaya. Mutane daga kowane ɓangaren Bauchi har Nigeria baki ɗaya duk sun hallara. Kowa yazo ya tayasu murnar wannan haɗin tunda duk gidan mutunci ne aka haɗa. Walima mai rai da lafiya akayi wajen ɗaurin auren, kowa ya goge wuyansa da abinci yanda ya dace. Suma daga cikin gida kawai shige da fice na abinci akeyi, kowa fuskarshi a washe kamar gonar auduga anata raha. Mommy ranta fari sol ta aurad da yarta. Ita Fadeela fuskantar babu yabo babu fallasa take abinta. Kowa ya yaba da yanda ta sake jiki tana komai. Su Samɗa, Sadiya da Mansura sune kan gaba a k’awayenta. Dayake Sadiya taje Makeup school ita ta tsala ma Fadeela kwalliya mai rikitarwa. Tayi kyau sosai babu kama hannun yaro, ko Fadeela tayi mamakin yanda kimanin ta ya sauya farad daya. Ta tabbata idan Naufal ya ganta sai zuciyar shi ya sosu ya rage tsanarta, dama itama saboda ya tsaneta shine take mayar mashi da martani. Basai ta faɗa ba amma kowa yasan zaman doya da manja zasuyi dashi, ita kawai adduar daidaituwan tsakanin Su zatayi saboda Sam bata saba da faɗa ba kokuma a zauna a gida ɗaya ba’a ma mutum magana ba. Tarbiyan da akayi masu shine bayan ka faɗa ma mutum laifin shi toh komai ya wuce an rufe babin amma ba wai ayita jan magana ana haɗuwa ana banka ma juna harara ba. Shikuma Naufal ya saka wani dakarkiyar farin shadda wanda akayi mashi dinkin zaren hannu kuma babban rigane tareda yar ciki da wando. Farin hula da agogo duk ya haɗa dashi. Thou yana san saka fararen kaya but still Abba ya gargaɗe shi akan kada ya kuskura yazo wajen ɗaurin auren kamar rainbow. Fara’ar dole ya rinka yi yana shan hannu dasu, ana sanya mashi alheri shikuma yana amsawa ciki ciki. Haka yayi tayi har taro ya watse. 8:30pm.... Kuka babu kama hannu yaro Fadeela keyi a yayin da ake mata nasiha. Duk ‘yanuwa an taru anyi mata nasiha mai tsuma rai. Mommy kasa cewa komai tayi tanata sharban kuka, fyace majina take da haɓan zaninta. Kowa tausaya masu yakeyi saboda an san yana yin shakuwan su. Duk inda akaga Fadeela zaaga Mommy, barci kawai ke rabasu kamar k’awaye. Ajiyar zuciya Mommy tayi tareda gyaran murya “ Dan Allah idan ankai ki inaso ki nuna mashi cewa daga gidan mutunci kike. Yi nayi, bari na bari a koda yaushe” “Ba yau aka fara karatun zaman aure ba, ke mai ilimi ce kuma kinsan right and wrong. Please show him how well trained you are, kada Kiyi abinda za’a ce waye mahaifiyar ki da batayi maki tarbiyya ba.” “Kinsan cewa aure ibada ne kuma idan kikayi da kyau zai iya sanadin shigar ki aljanna, nima nan da kika ganni nawa ibadar nakeyi kuma bana fatan denawa sai ranar mutuwa na” Haka Mommy tayi ta mata nasiha daga nan tace, “Duk abinda kikayi min wanda na sani da wanda bansani ba duk na yafe maki da fatan Allah Mahaliccin ya yafe mana baki daya. A haka Fadeela ta faɗa jikin Mommy tana kuka wiwi kamar wanda za’a kai makisa. Dakyar aka rabasu, Anty Saudah da sauran yanuwan Naufal sunji tausayinta ainun saboda rabuwa da mahaifa bashida dadi. Haka aka kaita gidanta wanda daga ita sai halinta da zai kwaceta. Anty Saudah ta sallami duk k’awayen amarya wai babu wanda zai kwana a gidan saboda dole ta fara neman aljannarta from the first day. An sake fashe gidan dasu turaren wuta da room freshener komai sai san barka. As expected, babu Naufal babu dalilinsa. Tun Fadeela na kallon wucewar agogo daga 11, 12pm, 1am. Hakura tayi taje tayi azkar ta rufe Ko’ina tareda kwantawa. Dan tsoro da kayanta na lace da alkyabba ta kwana bcs bata san stories that touch. Shi kuma gogan jin kansa yayi kamar ɗan tasha, bayan su ABBA da Mama sunyi mashi nasiha mai shiga jiki, sumi sumi yayi kamar komai ya shige shi ashe banan gizo ke sak’a ba. Shi ya riga yayi planning ɗin zaman aurenshi. Bayan isha’i sai yayi hanyar Club domin ya huce takaicin shi, ya ɗauki alwashin gwara ya kwana a club daya kwana gida ɗaya da Bad luck. Dayake baya shan Barasa ko wani kayan maye, VIP table ya kama aka kawo mashi fresh peppersoup na kifi ya fara bi takai. Daga bisani aka kawo mashi zafafan tsire yana taci yana shan Smoove hankali kwance, shi dama idan yana  matsakancin ɓacin rai to kawai yaci abinci komai zaizo mashi da sauki. Bayan nan ya rinka kallon masu rawa kafin barci ɓarawo ya sace shi, “Abeg Oga wake up its 4:30 am and we want to close”  Wata mai aiki a club ɗin da kayanta iya cinya take tadashi taga barci. “Innalillahi wa inna ilayhi rajiun!”  ya faɗa a  tsorace tareda ja da baya saboda ta firgita shi da kamininta. ‘yan kunnaye wajen shida shak’e a  kunnuwanta, ga kuma ta huda k’asan bakinta wajen gemunta kuma shima ta bishi da ɗan kunne round babba. Eye shadow ne blue ɗampare a idonta ga green jan baki ta mulka a baki, sai kuma gashin kanta ɗan guntu, shiba dreadlocks ba.... Wani k’azamin abu haka babu fasali. Tsaki yayi, “Amma dai bariki bai yiba Wallahi!” ya wuce motarshi. Wani waje chan nesa da gidan shi yayi parking motarsa, baya ya koma ya hau barci, da kyar wajen 6:30am ya samu yayi sallah a wani masjid saiya koma barci. 7:45am.... Locacin ne aka kawo ma Fadeela abinci, Abla aka tura tareda Miemie. Ba k’aramin jin daɗin ganin Fadeela Miemie tayiba, kuma wai ance idan sun huta da buki zata koma wajen su da zama. Itama Fadeela taso Miemie, nan take Sister’s ɗin Naufal suka burgeta. Bata barsu suka tafi ba saida ta basu kyautar underskirt, vest, eye shadow, body spray tareda lipstick. Bayan tafiyar su tayi wanka tareda fesu kwalliyar kamar zata buki, duk wani kusurwa na gidan inda akwai switch sai ta saka burner ɗin turaren wuta, kafin 10mins gidan ya gane Amaryar ba kuchaka bace. Abba ne ya shigo cikin falon yanata sallama tareda Alhaji Sulaiman, Shi kuma Naufal bai shiga da motarsa cikin gidan ba, yazo ne kawai a gurguje don ya canza kaya saiya ware. Baima lura da motarsu a parking lot ba hankalin shi yana abinda ya kawo shi. Fadeela ta sauko daga upstairs kuma idonta ya kumbura saboda kukan data kwana tana yi, saiga Naufal ya shigo cikin falon tareda turesu Abba saboda labule ya ɓoye su. Charko Charko Naufal yayi saboda ga babban rigar shi a hannu duk ta chukurkuɗe kamar ya fito daga bakin kada sannan yasan meAbba yace akan aurenshi da Fadeela. Tsuru tsuru yayi yana adduar daya dace da wanda bai dace ba. Abba ne ya kalle Fadeela saiya kalle Naufal kafin yace, “Daga ina kake?” #NiDaDiyata *Shout-out to my Tawan khadeejerh Abubakar, Allah ya bar so da kauna*        *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 15 ✨✨✨ On the authority of Abu Malik Al-Harith bin Asim Al-Ashari said that the messenger of Allah said: "Purity is half of faith. alhamdu-lillah [Praise be to Allah] fills the scales, and subhana-Allah [How far is Allah from every imperfection] and alhamdu-lillah [Praise be to Allah] fill that which is between heaven and earth. Prayer is light; charity is a proof; patience is illumination; and the Quran is an argument for or against you. Everyone starts his day and is a vendor of his soul, either freeing it or bringing about its ruin." Related by Muslim. ******* Naufal ɓarin laɓe ya soma yi ya rasa mai zaice, kawai kallon Fadeela yayi, irin kallon Please help me. But ya tuna da yanda dake da nawa bata abu da jiki, yasan baza tayi saurin taimakon saba. Ita kuma dayake yar gari ce saita kakalo murmushi tareda faɗin, “Laaaa Abba yaje ɗauko babbar rigarsa ne a hotel ɗin dayake kwana kafin yan room service su kwashe” “Ai gwara daka je da wuri, nima sun taɓa yimin gaba da agogo na” Alhaji Sulaiman ya chapke. Dukda Abba yasan karya ne, but irin matan dayake son yaronshi ya zauna da ita kenan, mai rufawa mijinta asiri a koda yaushe itace mace. “Okay ba matsala dama nazo naga yanda kuka kwana ne, kuma ku sani zuwan bazata zan rinka maku, so ku kiyaye!” Naufal har k’asa ya ɗuka ya gaishe dasu Abbansa, Fadeela ma haka. Babu yanda basuyi dasu akan su tsaya karin kumallo amma suka k’i. Bayan tafiyar su Abba, Naufal ya tsaya yana kallon Fadeela. Ita har ta fara murmushi a ranta ta samu lambar sa, shi kuma sai yanzu ya kalleta da kyau a rayuwarshi ‘Za’a je da babe ɗin nan fah’ wani siririn murya ya a ranshi ya faɗa. Kawar da tunanin yayi da sauri,taku daya daya ya soma cikin k’asaita rai a bace har yakai wajen matakalan bene inda Fadeela ke tsaye. Bai waiga ba kawai magana yayi a bayyane, “Iska na wahalar da mai kayan kara” sai yayi gaba abinsa. Ita kuma abin dariya ya bata saboda bata taɓa irin rayuwar nan ba. Zuwa tayi ta fara touring cikin gidan, gaskiya iyayenta sunyi kokari babu abinda zata  faɗa sai Allah ya saka masu da alheri. Shi kuma kai tsaye ya wuce master bedroom a zatonsa nanne ɗakin sa, yanda yaga komai Orange daga jere, curtains and rug Kuma ba color dinsa bane. Haushi ya kamashi wai ace shida gidansa amma bashi ke cikin babban ɗaki ba. Rufewa yayi ya koma wani ɗaki wanda ke biye da master room din, shikuma purple ne kayan ciki. A fusace ya fito yana masifa “Wai tsakani da Allah ina ne ɗakina?” Yayi maganar lokacin Fadeela ta gama taka matakalan bene na karshe. Tsayawa tayi tana kallonshi cikin Tuhuma irin me akayi maka saboda taga yana wani zazzare idanu. “Ke ina ne ɗakina? Infact dan kin rainani watau ke zaki zauna a master bedroom koh?” Shiru tayi tana kallon ikon Allah, “Kayi hakuri dama ina son Katon daki ne dats y, but bari na koma wancan” sai tayi ciki zata kwashe kayanta. “Wa zai zauna a cikin ɗakin chan mai kalar yan secret society, salan a cinye min kuruwa na. Yi zaman ki ni saina zauna a falo” taji muryanshi. Fitowa tayi tana nazarin shi bcs ta rasa meke damunsa, “Ga wani daki chan fari, idan kuma baiyi maka ba saina saka Mommy su kawo color of ur taste” saita nuna wani daki mai girma madaidai ci. Kwafa yayi sai ya tafi hanyar dakin, kamshin turaren wuta ya fara mashi welcome. Dakin fari sol daga bedsheets, curtains etc. Cire takalmi yayi saiya taka carpet, wani laushi yaji mai daɗin gaske. Lumshe ido yayi yana murmushi wanda bai masan hakan ya faru ba. Ya mike tsaye zaiyi wanka sai kuma ya tsaya yana tunani, tsaki yayi tareda naushin iska “Wallahi banso haka ba” shi yaso suyi Jani in jaka da ita ne kuma yaso batada farin daki yayi sanadiyar mata dukan tsiya. Sai yanzu ya lura batada hayaniya at all Kuma tashin hankali bai dameta ba, Ranshi yayi mummunar baci bcs bazata bashi reason to beat her ba, kuma haka kurum bazai kama dukanta babu gaira babu dalili tunda shiba mahaukaci bane. Ita kuma sororo ta tsaya tana ganin ikon Allah, wai zaka ga abu muddin kana raye. Ita dama farin ɗakin ta shirya mashi kuma koda aka kawo kayensa nan aka ajiye. Cikin orange room ɗin ta shiga tayi ɗai-ɗai akan gado tareda ajiyar numfashi a hankali, sai kuma tayi zumbur ta tashi da sauri. Dakin Naufal ta wuce, a hankali ta tura kofa tareda sallama, babu wanda ya amsa Still ta shiga. K’arar ruwa taji a bayi da alamun yana ciki. Shikuma ya fito daga shi sai boxers da hand towel a hannu sai kawai ya ganta tsaye tayi zurfi cikin tunani. “ke meye haka? Meya kawoki ɗakina?” Rasa me zatace tayi sai kawai ta kafa mashi ido. “Badake nake ba? Wayace ki shigo” “Dama abincin Kane nake so na tambaya inda zan jera maka” Kallonta yayi baice komai ba ya wuce mirror ya fara shafa man Nivea, yana gamawa fashe spray din same Nivea for men sai ya haɗa da Hugo boss. Yana yi yana takama Still Fadeela tana wajen baice komai ba. “Ina kayana yake?” ya tambaya amma ko kallonta baiyi ba. “Yana cikin wardrobe” Bai kalleta ba yaje ya buɗe, a yatsine ya kalle ciki saiya fito da wani milk jallabiya ya zura. Hawa gado yayi ya dauki wayar shi ya kunna wakar 2pac. “Ki kawo min abincin nan” ya faɗa yana wasa da wayar shi. Ita kuma fita tayi waje tareda rufo kofa, “ina da aiki a gabana” ta faɗa yayin datake sauka stairs tayi hanyar dinning area. Abincine mai rai da lafiya Anty Saudah ta aiko masu dashi. A cikin cooler ɗin farko Appetizer ne na minced chicken wanda yasha kayan lambu kamar su carrots da green beans Sai kuma kayan kamshi da barkono. A cooler na biyu aka soya dankali da plantain sai kuma wainar kwai. Sai kuma pancakes mai vanilla flavor. Daga nan sai Fruits salad wanda aka kwaba madara a ciki. Daidai gwargwado ta zuba mashi akan tray saita kai mashi cikin ɗakin. Harta ajiye ta juya ta fara tafiya sai kawai yace, “OMG! I’ve change my mind. Biyo ni downstairs dashi” Bai tsaya jin mai zata faɗa ba sai ya wuce abinshi. Wani kololon bakin ciki ya tokareta, tunda take bata taba ganin k’askanci irin wannan ba, wai dan wulakanci up and down Zai rinka mata, hakuri kawai tayi saboda zaman aure takeyi kuma ya jiɓanci haka. Cikin yanayinta na sanya sanya ta karasa wajen dinning area ta ajiye abincin. Ta fara tafiya saiya kirata, “keh meye haka? Dalla zokiyi serving ɗina” Cak ta tsaya na wasu seconds kafin ta juya taje tanayi, ranta duk ya jagule. Shi kuma haushi ya kamashi saboda yanda take abu kamar babu jini a jikinta, ji yake kamar ya kwace chukalin yayi da kanshi amma da yake mugunta na cin sa saiya barta da abinta. Dayake Mommy chef ce, Fadeela tasan yanda ake decorating plate yayi kyan gani. Koshi abin yayi mashi kyau saidai bai nuna ba. “Saura ccoffee” ya faɗa tareda kai spoon din abinci baki. Ta haɗa mashi cappuccino a Nespresso machine dake kan coffee table ɗin wajen. Ta ɗaura akan saucer tareda teaspoon ta kai mashi. Tas kake ji alamun cup ɗin ya faɗi ya fashe. Data mika mashi cup ɗin saiyaga cappuccino kuma shi Latte yake so yasa bai amsa ba komai ya zube a jikinta tareda faɗi kasa. “Kefa bakida hankali!  Wannan wani irin busy body ne? Waye ce maki ina shan Cappuccino? I only take latte” “Yi maza ki haɗa min yanzu kafin na tara maki gajiya...... Mts” Kananan hawaye suka soma malala a fuskarta sai tayi sauri ta goge, ta lura yanaso ya bakanta mata raine amma bazata bashi damar ba. She will always be happy. Latte ta mashi a wani cup tunda na farkon ya fashe, little sugar ta saka daidai misali. Koshi sanda ya saka a baki saida yayi mamakin to his own taste ne. Kitchen ta wuce ta dauko vacuum cleaner saboda wajen yayi kacha kacha, tsaf ta gyara wajen tunda ta iya aiki ba’a sangartar da  ita ba. Bayan nan daki ta wuce ta rufe kanta. Kwanciya tayi rub da ciki tareda dauko babin kuka, wiwi takeyi mai tsuma rai kamar ranta zai fita, kana ganinta saita baka tausayi. A duniya rainin hankali tafi tsana amma gashi anayi mata kamar pure water. Datayi kukanta ma ishi saita mirgina tareda rungumo pillow tayi  barci abinta. 1:15pm....... Locacin ne su Bilqees suka kawo lunch, hayaniya dinsu ya tada ta. Da fara’arta ta karramasu kamar kannenta na jini. Tana zuwa wajen dinning taga komai yayi normal saboda sunyi mata wanke wanke Thou tanada dish washer, but still! Miemie ne taje ɗakin Naufal amma bata riske shiba daga alama ya tafi Masjid ne. Horn sukaji a waje driver yana masu alamar su fito. “Anty yar gayu mun tafi, sai kuma mun Kawo dinner” Miemie tace tana dariya. “Sai anjima Anty” Bilqees tace tana murmushi. Har kofa ta rakasu ana raha. Ta koma daki tayi alwala tareda sallah itama. Bayan nan ta sake gyara make up ɗinta da kyau tareda daurin ture kaga tsiya. Tayi matukar kyau tunda her skin is fluffy Kuma she is fair. Gashi dama fitted gown ta saka komai nata aziman. Tana tafe tana feleke kamar rashen bishiya, tako daidai yarinya yar kwalisa Amaryar Naufal. A falo ta riske shi yana kallon CNN inda ake Inauguration ɗin Donald Trump sabon shugaban k’asan USA. Tsaki yayi tareda canza channel daga alamu abin bai kai mashi karo, BBC ya koma still suma abinda suke nunawa kenan. Kwafa yayi tareda rufe idanun sa.  Sai kawa yaji kamshin dake firgitar dashi, “Chanel No 5” ya faɗa saiya bude idonsa. Nan take suka haɗa ido saiya banka mata harara. Sinna kai kasa tayi saboda idonsa yana firgita ta musamman idan ya zare. “Yaya ina wuni?” Bai amsataba kuma bashida niyar amsawa. “Dama nazo na tambaya ne ina zan kai maka abinci” Nanma kamar bazai ce komai ba saiya ce, “Set the table, Yanzu zan ci” “Please idan Kinga dama ki rinka yin busy body idan kina abu, mutum sai shegen nawa kamar kunkuru” Ya faɗa yana wani yatsine fuska. Tana tafe tana gunguni tareda magana ciki ciki, “Bani bace kunkuru saidai......” kafin ta karasa maganar saiga shi agabanta yana huci kamar mayunwacin zaki. “Saidai wa?.......”  ya tambayeta. #NiDaDiyata *Corpers wee! Shout-out to all corpers I know the struggle is hard esp now that dey have not paid our allowee, we will still survive biko! Special shout-out to 2016 Batch B stream 1 most esp Ummunah Bende corpers. If you are reading this you are wrong! Is that clear!* *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 16 ✨✨✨ Abdullah bin 'Amr bin Al-'as (May Allah be pleased with them) reported: A man asked the Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam): "Which act in Islam is the best?" He (Sallallahu 'alaihi wa sallam) replied, "To give food, and to greet everyone, whether you know or you do not."[Al-Bukhari and Muslim]. ******** Rufe ido tayi ta kasa haɗawa dashi tareda karkarwa, ji kawai tayi an damk’eta. Ihu ta tsandara saboda rik’on dayayi mata babu sassauci kuma abinka da farar mace babu makawa hannunsa saiya nuna. Still bata buɗe ido ba kawai hawaye suka soma fitowa kamar a bakin teku. “Bada ke nake ba? Nace karasa maganar mana. Ashe ke karamar mara kunya ne. Tun ba yau ba nace ki hankaltu dani.” “Idan nace zan rinka dukan kine kawai kasheki zanyi saboda bakida wani abun duka tunda bakifi loma ɗaya da rabi a haɗiye kiba. Kuchaka kawai!” “Sai shegen iya rashin kunya ga kuma shegen tsoro kamar farin kura. Da an riskeki sai ki fara kukan munafunci kamar ana kashe ki..... Mts” Saiya wurga ta k’asa ta faɗi wanwar. Baka jin komai sai Sheshek’ar kukanta kawai tana jan majina a hankali. “Idan kinso gobe ki kara, Karkiga yanzu na kyale ki” ya cigabada sababi har ya koma wajen couch ya zauna. Kafa ɗaya kan ɗaya ya daura yana kallon TV dake aiki. Wannan karon ESPN ya saka. Ita kuma a hankali ta tashi jiki babu kwari rai a jagule tayi hanyar dining, karap karap kake ji karar takalmi ta isheshi kuma da gangan takeyi. Ko cooler da karfin gaske take buɗewa kamar zata karya murfin, haka take amfani da chokali karap karap ita kanta ta damu balle shi. She was just acting clumsy Sai ɓari takeyi ta ishe kowa. Tsaki yakeyi saboda duk ta cika mashi kunne, a fusace ya juyo rai a bace yana nuna mata ɗan yatsa. “Ke dalla meye haka ba zakiyi abu a natse ba kin cika min kunne” Puppy eyes tayi mashi tareda cewa, “Kayi hakuri yaya bansan yana damunka ba” “Okay yanzu kin sani gwara ki bari kafin na damk’eki” Bata ce komai ba illa sinna kai tana dariya, tabbas taji daɗin abinda tayi tunda da gangan ne. Cikin ruwan sanyi zata rinka frustrating ɗinshi. Ta jera mashi abinci wanda multi-colored rice ne da stew ɗin Cat fish. Sai kuma Coslow wanda yasha Macaroni da hanta. Drink kuma coconut ne aka markaɗa da shinkafa na tuwo tareda pineapple. Karap karap ɗin slippers ya sanar dashi gatanan zuwa, dab dashi taje ta tsaya kamar zata auka mai. “Yaya ga abincin na zuba maka” Harda bazai amsata ba sai kuma ya canza ra’ayinsa. “Sai kin fado jikina zan san kina min magana?” ya tambaya yana mata kallon raini. “oh sorry!” saita matsa baya Shiru sukayi for some seconds saitace, “Akwai abinda zanyi maka kuma?” Bai tanka taba saiya mike tsaye, yanda dunkaro ta idan da batayi saurin matsawa ba daya banke banza. Hawa yayi dinning ya zauna, yanda ta jera ya k’ara burgeshi. Ita kuma dama ta ɗiba nata yana kitchen. Karap karap takeyi harta wuce ta shiga kitchen, wannan Karon harda juya mai jiki. Shiru yayi saboda ya shaka matuk’a, “indai jiki ne toh I’ve seen better” ya faɗa a ranshi. Sannu a hankali ya gama cin abinci saiya tashi ya wanke hannu, sink ɗin wajen yayi hooking yaki budewa so dole yaje wani wajen. Nearest to the dinning area kitchen ne, ranshi baiso ba amma haka ya hakura ya tafi. Ita kuma ta gama cin abinci har ta fara wanke wanke sai Naufal ya faɗo mata a rai. Dariya ta tuntsire dashi tareda magana a fili, “Wai ace mutum bashida sana’a sai faɗa, dage yafi shi hakuri.... Haba kullum faɗa kamar a Syria aka haife shi” “Ina jinki” Ya faɗa. A tsorace ta juyo tareda sakin plate ɗin hannunta, tas kakeji ya fashe. Neman wajen guduwa taso yi amma shike hanya. Tabbas yau kashinta ya bushe saboda saita daku. Narai narai tayi da ido bakinta na rawa amma babu abinda ke fita. Zufa ya soma yanko mata duk ta fita hayacinta. Takowa ya somayi tareda smug face, kana ganin shi kasan yana shirin mugunta. Sannu a hankali har ya kai wajen datake ya tsaya. Da hannu yayi alamar ta matsa mashi, wucewa yayi ya wanke hannunsa saiya bar kitchen ɗin. Shi abinda yasa baice komai ba saboda yanda ta tsorata, ihu yayi mata zata iya haɗiye ranta ta mutu ta jawo mashi bala’i babu gaira babu dalili. Amma tabbas maganar datayi ya taɓa shi, wai yau shi ake ce ma dage da kuma yana faɗa kamar haihuwar Syria, lallai! Ita kuma sororo ta tsaya tana tunanin abinda ya faru few seconds ago, gaskiya ya bata mamaki matuka saboda bata sanshi da hakuri ba, wani zuciya ya raya mata kila tayi Azkar da kyau ne. “Gaskiya ba mamaki!” ta faɗa a fili saita ɗuka kasa ta fara gyara ɓarnar datayi. Dama wayanta yana gefe sai kawai ta dauka ta kunna wakar Nazeefi Asnanic mai taken Ga Amarya, Haka ta rinka rero wakar kamar ita ta rubuta mashi. Dakinshi ya koma ya zauna akan gado yana tunani, faɗa Sam sam ba ɗabi’arsa bane kuma kowa ya shedeshi. But tun haɗuwarsu yake wasu shikashikan rashin mutunci babi babi. “Ka manta Bad luck ɗin dake binta ne ya canza ka” wani zuciya ya raya masa. “Hakane fah” ya faɗa a fili. Tashi tsaye yayi saiya canza kaya. Farin Boyel ya saka wanda aka ɗinka jumper da wando. Sai ya haɗashi da coffee Brown hula da takalmi. Turaren Ralph Lauren ya fashe jikinsa dashi har ya fara choking saboda yawansa. Yaci kwalliya kuma yayi kyau sosai a matsayin shi na kyakyawa, wannan green eyes ɗin yana glimmering. fine guy san kowa, ko makiyan sa basa kushewa. Ni kuma Dimples nace “ Na Fadeela bada kanka a sare!” Yana tafe taku dai-dai zashi gidansu Fadeela yayi godiya akan karamcin da suka yi mashi. Abba ya gargaɗe shi akan dole saiya je ya gode masu, kuma shima yana so ya daki tsuntsu biyu da dutse daya. Tunda ya lura Mommy tana sanshi gwara yayi mata shishigi saboda koda ta kai k’ara babu mai gasgata ta. ******** A chan gidan lambu kuwa, Miemie ce ke gyara flowers ɗin datayi planting da kanta. Sun flower ne kuma kullum saita duba su, ta dauki wani flower pot sai kuma ta sake shi k’asa ya faɗi ya fashe. Bata ko damu ba saima takashi da tayi kurmus. Kana ganinta kasan ‘yan kanta sun motsa. Tunda baya Naufal ya bar gida take jin kanta wayam, tunanin Khattab kawai takeyi. Ya diran mata kamar kibiya batada wani katabus sai shi. “Ba Ya Naufal, ba Ya Khattab.... Toh wallahi bazai yiwu ba” Komawa cikin gida tayi wanda ‘yan biki sun ragu yanzu. Abla ta gani a hanya saita ce mata, “Kinga Yaya Khattab kuwa?" Harara ta watsa mata kafin tace, “Eh yana buje na” sai tayi wucewarta. Miemie bata ce komai ba illa wucewa ɗakin Mamanta watau Anty Saudah, “mama ki kaini wajen Yaya Khattab dan Allah” Shiru Anty Saudah tayi kafin ta fara magana a hankali, “Mamana yau Kinsha magani kuwa?” “Ni wajen Yaya Khattab zaki kaini....” “idan Kinsha magani sai muje koh” “Wallahi ban yarda ba, nasan bazaki kaini ba” Sai kawai ta fashe da kuka. Anty Saudah da sauri ta ɗauko magani domin ta bata atleast su samu saukinta. Fizgewa tayi daga hannun Mamanta ta zubar dashi ta rinka takawa da kafarta tana yi tana kuka tayi kacha kacha da wajen. “Bazan shaba” ta faɗa tana rusa kuka a ɗuk’e. Nan take ran Anty Saudah tashi. Number ɗin Naufal ta soma nema, bugu ɗaya, biyu, uku saiya ɗauka. A gurguje tayi mashi bayanin komai. Nan take ya yi hanyar gidan saboda yabar gidansu Mommy kenan zai koma nashi. Yana tafe yana tunanin condition ɗin Miemie bcs sun ɗade batayi tuburan ba. Bai rufe k’ofan motarshi ba da sauri yayi cikin gida, yana isa wajen yagasu Abla anyi charko charko a waje saboda Miemie tace bata san taga kowa. Tana zaune ko Mommy ɗinta ta kasa zuwa wajenta kafin ta mauje ta, Kiran sunar Miemie yayi a hankali tareda tura kofa. “karka matso kusa dani” “Calm down Lil sis,nine fah” “I hate you” ta faɗa tareda kuka sosai. “Kace min Yaya Khattab yayi min sallama ne, saboda ka maida ni mahaukaciya koh?” Shiru Naufal yayi ya rasa me zaice kafin ya faɗa wrong thing tayi losing mind ɗinta hauka yazo gadan gadan. Ita kuma ta kifa kai akan gwiwa sai kuka takeyi mai tsuma rai. Kawai saita mike tsaye tace, “Muje ka kaini wajen Yaya Khattab” Zuwa yayi dab da ita ya ce babu inda zata. Wani irin kukan ta somayi kawai saita ruga window ta fara buga kanta dashi, duk da glass ɗin wajen ya fashe sai karfe Still bata daina ba. Yaya Khattab ta rinka maimaita wa. Duk yanda Naufal yayi kokarin kwanceta yana so ya gaza mashi. Tausayinta yake matuka saboda yasan zafin so. Fincikarta yayi ya watsar a Kasa, jini ke fito mata ta hanci ta baki gashi kuma daga kanta yana gangaro wa. Kuka takeyi sosai tana kiran Khattab da muryanta daya fara dishewa, idanunta sunyi jazur kamar garwashi saboda wahala, duk ta galabaita a hankali takeyi. “Kashe kanki kike so ki yi?” Ko kallon shi batayi ba kawai tana kuka ne, duk abinda akeyi su Anty Saudah da Abla ana gefe ana kuka. Gashi Abba ya tafi Kano. Kawai Miemie ta ankara da inda take saita soma sabon aiki. Daukar kwalba tayi a k’asa ta soma chachaka ma hannun ta, tana kaiwa wajen jijiyanta saita kwala ihu tareda sakin komai. Nan take ta fita hayacinta tareda sumewa. Anty Saudah ta rusa ihu tareda rugawa wajen ta, Abla ma haka. Shi kuma Naufal mutuwar tsaye yayi saboda duk laifin shi ne. Saida wasu seconds suka wuce kafin ya dawo hayacinsa, kukan zuci yake wanda yafi na baiyane ciwo. Daukarta yayi kamar ‘yar tsana yayi waje cikin ruɗewa, ko mota bai shiga ba kawai ya nufa titi yana gudu da ita. Dadin abin Anty Saudah ta iya mota Saita tuka na Naufal ta riske shi a hanya. “Saika shigo muje tunda ba’a kafa za’a ba” yaji kunya sosai daya lura da abinda yayi amma babu time for that. Suna kaiwa Asibiti ER aka wuce da ita direct saboda tayi losing jini babu adadi. Kacha Kacha sukayi da jini kuma asibiti ɗin saida yasan da zuwansu. Anje za’a kara mata jini amma babu match ɗinta saboda haka sai anje blood bank. Dauke Doctor ɗin da mari Naufal yayi tareda cin kwallarsa, “Dan ubanka meyasa tuntuni baku nema ba dan sakarci sai yanzu?” Sai kawai ya sake shi ya koma gefe yana kuka, ya tabbata idan suka rasa Miemie shiya kasheta. Suna zaune aka kawo jinin, nan take aka soma yi mata aiki gadan gadan cikin awa biyu an gama komai. 10:45pm...... Fadeela tana zaune akan Couch tana jiran other half ɗinta babu shi babu dalilinsa kuma su Miemie basu kawo dinner ba, kawai komai yana mata wani iri amma bataso ta kawo mugun zato a ranta. Har wajen 11:30 bai dawo ba, idanunta ya cika da hawaye tun tana matsewa har saida ta barke da kuka wiwi. Akan 3 seater ta kwanta tayi ma’ishi har barci ya dauketa. Ita kuma Miemie tana buɗe ido a hankali ta soma magana. Kamar kowane mara Lafiya ruwa yake nema amma banda Miemie, “Khattab” ta furta tana hawaye. Naufal yaji sarai sai ya kyaleta, kwakwal warsa baya aiki abin duniya yayi mashi chunkoso. Kana ganinta saita baka tausayi, ga jikinta duk bandage ko fuskarta an rufe wajen rabi dashi. Gashi kuma an saka mata oxygen ta hanci saboda numfashi. Shi baisan yanda zai fara faɗa mata Khattab ya bar Nigeria ba, tunda ya rasa Miemie saiya gudu yabar gidansu, yanzu haka baada tabbacin ga inda yake. Wasu Doctors su uku suka shigo tareda Nurse guda ɗaya. “gaskiya zakuyi hakuri bcs alamarinta sai addu’a, yanzu kawai for safety shine za’a rinka k’ulleta saboda idan hannayenta is free saita rinka kokarin nakasa kanta.” Sai suka fito da handcuff guda biyu, sun gark’e mata hannu ta kowane ɓangaren tareda gado. Itadai kallon kowa takeyi bata masan sunayi ba, “Yaya Khattab” tayita nanatawa. “Wannan wani irin sone?” Naufal ya tambaya kansa. #NiDaDiyata *Fatan alkairi zuwa ga yan group din DIMPLΣS, Allah ya bar zumunci* *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 17 ✨✨✨ Jabir bin 'Abdullah, may Allah be pleased with them, narrated that Allah's Messenger said: "The key to Paradise is Salat, and the key to Salat is Wudu'." (Hasan) It was narrated from Abu Hurairah that The Messenger of Allah said: "When it is very hot, then wait for it to cool down before you pray, for intense heat is from the flaring up of the Hell-fire." (Sahih) ********** Six months later..... Hakuri shine gishirin zaman duniya, kuma ainun Fadeela tayi exhibiting ɗin wannan abu. Babu abinda Naufal baiyi mata ba na cin zarafi kuma duk ta shanye. Ko sau ɗaya bata taɓa tunanin zata faɗa ma Mommy ba ko Jawahir, ita kawai tasan nata jarabtan kenan. Sau biyu taje gidansu kuma shima sallah babba da karama ne. Saidai kuma bai takura mata akan karatu, ya kyaleta ta cigaba amma koda wasa bai taɓa rage mata hanya ba. Idan kuma tanada 8am class toh tun wajen 4am take tashi tayi breakfast and lunch duk ta saka a cooler. Azumi kuwa na Monday and Thursday baya wuceta Muddin tana cikin lafiya, ma’ana idan tana sallah. Daga ɗayan ɓangaren ana nan ana fafutukan neman ma Miemie magani, Shidai Khattab har yanzu babu zancensa babu dalilin sa. Sau da dama idan ciwon Miemie ya tashi Naufal ya rasa tudun dafawa sai kawai yaje gidansu Khattab ko office ɗin babansa ya zauna yayita rusa kuka. The last time dayaje Sai Abban Khattab ya rantse mashi da girman Alkuran akan baisan inda yaronshi yake ba, shima rabon dasu haɗu tun text msg daya aika mashi akan ya tafi kuma daga nan yayi disconnecting layin, koda akayi tracing ɗakin Khattab ne last location. Anan fa hankalin Naufal ya tashi sosai saboda ciwon Miemie sai gaba yakeyi. Akwai wani rana haka, Anty Saudah takaita bayan gida domin ta zaga, unfortunately ta cire mata hand cuff sai kawai Miemie ta naushe window da hannunta. Nan take jini ya soma gangaro wa kuma sai ta dauki broken glass tayi slitting wrist ɗinta. Tashin hankali Anty Saudah ta gani mara misaltuwa saboda nan take Miemie ta sume, sau dama Miemie tayi abubuwa da zai janyo mata asarar ranta. Akwai wani lokaci tafi One week bata kira sunar Khattab ba, kowa hamdala yakeyi ta fara samun sauki sai Naufal ya cire mata hand cuff ɗinta. Aiko basu suka ganta ba sai bayan kwana biyu. Shima wajen data fara haduwada Khattab ne, ta zauna a gefen da ake gasa masara tanata rusa kuka, babu wanda yabi ta kanta saboda kana ganinta kasan babu hankali, gashi batada takalmi ga kai a tsefe yayi sama duk kacha kacha. Tunda daga lokacin sukayi taka tsantsan da ita, yanzu dai basu saka mata Handcuffs akwai wani igiya haka mai yanayin beat. Shi ake saka mata kuma tana wani ɗaki ne wanda babu komai ciki sai carpet. Wata rana tayita ihu tana buga kanta a kasa amma saboda laushin carpet bata jin ciwo. Wata rana kuma tayita kiran sunan shi a hankali tana hawaye, haka rayuwa ya kasance mata! Duk Safe da yamma sai Naufal yaje ya dubata, da farko bata san ganinsa. Dayazo ta window inda ake lak’enta saita rinka ihu tana rufe idonta. Kullum kalmar “Ka cuce ni take furtawa” Ba karamin tashin hankali ya shiga ba, ya kan rufe kanshi sau da dama a ɗaki yayita rusa kuka, tabbas yasan shine sila but yanzu da zai iya maida hannun agogo baya daya yi. Amma yanzu ta rage mishi haka, tana zuwa har wajen window ta tsaya, Thou bata cewa komai but tana murmushi jefi jefi. Idan kuma time ɗin abinci da magani yayi yana shiga yayi feeding ɗinta. Ita kuma Fadeela bata wuce One week bataje ta duba taba, abin yana burgeshi sosai amma baya nunawa, kuma ko sau ɗaya bai taɓa tunanin yabar ɗiban albarkan dayake mata ba. Shi dama yace aurenshi zai zame mata ɓakin canji a rayuwarta, kuma daidai gwargwado yana kokarin ya nuna haka. Dukta susuce tayi fari kamar fatalwa, yasa bataso taje gidansu kafin hankalin Mommy ya tashi. Ko Jawahir baifi sau biyar taje nata gidan ba kuma shima a gurguje ne. Kullum tana cikin waya da Mommy, “babu abinda kike nema? Lafiyan ki kalau? Me za’a yi maki?” shine tambayar datake mata kuma ko sau ɗaya bata taɓa furta abinda zai jawo ma mijinta kaskanci ba ko bakin jini. Idan ta gama aikace aikace ɗinta saita je wani empty room haka wanda kayan art work ɗinta suke tayita painting hankali kwance. Shi kaɗai ne abinda takeyi mai kawo mata solace, idan tana yi saita mance da bakin cikin gidan aure. ****** Yau Juma’a kuma kamar kowane sati inada 8am class. Tun wajen 4am alarm ɗina ya tashe ni but ban samu daman saukowa daga kan gado ba sai wajen 4:30am. A daddafe na sauko inayi ina murje ido bcs barci bai isheni ba. Wajen karfe sha biyu da rabi na kwanta sanadiyar projet dana farayi kasancewar mune final year student. Kitchen naje na fara kama aiki watau breakfast kuma shima Soyayyar dankali ne wanda tun jiya da daddare na fere na ajiye abina a fridge domin na samu sauki yau. Daga nan sai nayi jollof Rice na saka ma Naufal abinsa na rana a cooler saboda bazan samu daman dawowa da wuri ba bcs ina Missing Miemie. Kafin na gama aiki Asbah ta danno kai gadan gadan tunda sai karfe shida akeyi. Pausing girkin nayi na mayar da komai on low heat saina wuce ɗaki. Alwala na dauro tareda nafilar raka’atanil fijr, ina cikin azkar sai aka kira sallar karshe which nima na tashi nayi. Adduar safe nayi wanda kowane ɗan Adam ya kamata yayi sai kuma na haɗa da neman ma kaina, mijina,iyayena da al’umma baki daya tsari daga sharrin masharranta watau mutum ko aljani. Kai tsaye kitchen na koma na cigaba daga inda na tsaya, ina ciki naji Ya Naufal ya dawo daga masallaci, murmushi nayi k’arara saboda My other half yasan darajan sallah, at all Baya wasa dashi. Saboda haka ni bana cire ran wata rana zai soni. Nasan cewa wata rana zai gane nice other half ɗinsa Kuma nasan zaiyi alfahari dani kamar yadda nakeyi dashi. Kwata kwata yanzu bana jin haushin cin kashin dayake mun, I’m not making excuses for his actions but nasan cewa yana cikin damuwa akan ciwon Miemie, fatana kullum Allah ya bata lafiya kila nima na samu lambar zuciyar sa. 12 pm..... Locacin ne na gama lectures ɗina, kasancewar yau Friday kuma short working day so banyi tunanin zuwa wajen project supervisor ɗina ba. Tafe nake da Samɗa,Jumaimah da kuma Mansura k’awayena. Muna tafe muna hira hankali kwance. Samɗa ce tayi hanyar parking lot inda motarta yake. Ihsan Baby ɗin Samɗa na dauka wanda ke tareda mai aikin ta, wasa nakeyi sosai tunda ina san yara, kallona samɗa tayi cikin tuhuma kuma kana ganinta kasan da magana a bakin ta. “Faɗa karya kasheki” nace ita kuma dariya tayi kafin tace, “Kinsan cewa ke zaki rinka nuna masa salo da zai janyo maki hankalin shi? ” “Wallahi kin bani dariya, meye banyi ma bawan Allah ɗinnan ba amma banza yake dauka na. Ke ni na gaji wlh” “Ah ah Karki ce Haka, da lallami da kissa zaki sameshi. Dama Wayace maki shiga Aljanna cin tuwo ne, ai sai kin nuna juriya da hakuri tukun” “Allah dai yasa mu dace” nace sai mukayi shiru. A al’ada yanda ake gane matar aure a cikin makaranta mu shi ne ta hanyar mota, sau da dama idan mijinki yanada k’umban susa zai siyan miki mota amma dai banda nawa mijin. Idan na shiga motarshi to naje gaida Miemie kuma yamma yayi kuma shima ya gargaɗe ni da na daina kaiwa dare tunda shi ba driver ɗina bane. Samɗa kawai kallon kawarta takeyi, yanda abin duniya bai dameta ba. At all bata jin kunyar hawa bus ko napep Thou kana ganinta kasan babban mace ce, idan ba wai kayi mata sanin da bane toh bazaka gane ta lalace ba. Naufal yafi mijin Samɗa arziki nesa ba kusa ba, bazama ka haɗa ba esp yanzu dasu Mr Sutter suke ji dashi sosai. Kudi mara misaltuwa suke sakin mashi sosai yasa indai batun maganin Miemie ne to baya damuwa, but dama sauki na Allah ne! As usual wajen roundabout ɗin Yelwa Samɗa take ajiye Deela sai kowa ya kama gabansa. Direct gidan gona na wuce tareda tsaraban masara a hannuna bcs of Miemie. “Assalamu Alaikum” Na faɗa yayin dana shiga cikin falo, Anty Saudah Nagani da kuma Abba harda Mama duk ana zaune. Nan take fara’arsu ta karo sosai which dama haka sukeyi idan sun ganni. “Ina wuni? Ina gajiya?” na Faɗa tareda duk’awa kasa. “Lafiya lau, ya kike?” Suka amsa “Lafiya lau” nace. “Bari na shiga daga cikin wajen Miemie” Ba Abba ba har Mama akwai tuhuma a yanayin Fadeela, indai ba ciki gareta toh tabbas ana musguna mata ne, shi dai Abba saiya tsareta Thou yasan bazata ce komai ba but he wants to assure her yana side ɗinta. Ita dama Anty Saudah tayi tambayar harta gaji but Deela batace komai ba. Tana ankare da yanda Naufal ke mata wani mugun kallo. Sau da dama tana tsare shi akan yaji tsoron Allah, “Inba dai ita tace ina mata wani abu ba, toh ni ba wani abu dake hadani da ita” abinda yake faɗa kenan. “Hello Miemie!” Deela ta faɗa tareda shiga cikin ɗakin. Ita kadai Miemie takeso ta rinka shiga unless abinci zaka bata, toh kayi tsayuwar ka a waje. Murmushi Miemie tayi batace komai ba, Fadeela ta karasa inda take zaune chan kurya saita zauna kusa da ita. Riko hannunta tayi tana mata murmushi tareda murzawa a hankali. Magana tayi ciki ciki saika saka Mind ɗinka da kunnuwa kafin kaji. “My Miemie please come back, Ya Naufal really needs you” ta faɗa tana kuka. Miemie na jinta batace komai ba sai daga bisani tace, “NI kin cika min kunne" “Oh sorry!” ta faɗa tareda share hawayenta. Kakalo murmushi tayi saita mika ma Miemie masara, nan take ta karba ta soma cabza. “Kema zaki biye masu ne bazaki kaini wajen Ya Khattab ba?” “kina tunanin banida hankali ne koh?” Fadeela batace komai ba illa kallonta, ita kuma ta cigaba da cin masara bata ɗaga idonta ba. “Idan an kai ki wajen Khattab ɗin mai zakiyi masa?” “Kawai ina son ganinsa ne bcs I have a bad feeling” “Dan kina son ganinsa sai kin kashe kanki ?” “Eh, har saina samu abin nakeso” ta faɗa kana ganin fuskantar babu wasa. Shiru sukayi for some minutes Har Miemie ta cinye masara guda uku, Magana Miemie ta somayi. “Ya Yaya Naufal yake? Nasan he is not alright but Kema haka. Yana miki wani abu ne?” Ta tambaya tareda kama mata haɓan fuskanta. Hawaye kawai ya soma gangaro ma Fadeela saboda ko Miemie da bata da lafiya ta gane komai balle sauran mutane. Da sauri ta goge tareda cewa, “Just try and be alright Naufal Shima zai zama daidai” ta faɗa cikin muryar kuka. Tashi Fadeela tayi tsaye zata tafi sai kawai Miemie itama ta mik’e wai zata bita, “Please Anty Karki tafi ki barni, bakiga yanda suke treating ɗina ba. Please don’t leave me here” “Miemie dont worry, zan dawo next week kinji koh!” “Please ki tafi dani, Anty kada kiyi min haka. I promise to behave myself. Insha Allah Bazan k’ara jima kaina ciwo ba” Hawaye ke malala a fuskar Fadeela, karasa wa tayi dab da ita tana shafa mata kumatu tareda da share mata nata hawayen. “My sweet Miemie I’m sorry but ban yarda ba, jibe hannunki da bandage ga wani a cinyar ki. Tuntuni kike min alkawari kin daina amma last week kikayi wannan. Ko totuwan masara da zai illanta ki da kinyi dashi” “Anty bazan kara ba Please” Murmushi Fadeela tayi na takaici tareda sumbatar goshinta saita juya tana kuka ta tafi, muryan Miemie kawai take ji yana echoing. “Dan Allah Anty Karki tafi ki barni, wallahi na tuba. Bazan kara ba, please kiyi min rai” Haka ta rinka maimaitawa tana fizge fizge ta karfin tsiya, rusa kuka takeyi gwanin ban tausayi but babu yanda Fadeela zatayi. Haka Miemie ta rinka fizgo hannunta tana kokarin kwance kanta saita kasa. Kawai zubewa tayi a kasa ta fara ihu, “Yaya Khattab kana ina ne” ta faɗa sai kuma ta fara buga kanta akan carpet tana kuka, Anty Saudah tana falo tareda Fadeela suna rusa kuka. Itama Mama tana matse hawaye saboda Miemie abin ban tausayi ne, shiko Abba tuni ya tafi Masallaci kafin yayi missing huɗuba. Sallah Fadeela tayi saita wuce gida, hankalin duk ya tashi. Tana isa gida saida tayi kuka ma’ishi saboda yanzu kuka shine latest hobby dinta bcs bata 3 days bata yiba. 6:30pm.... Wani dabara ya faɗo min akan nabi shawarar samɗa, bayi na shiga nayi wanka tareda ɗauro alwala. Akan dressing mirror na zauna na Fara shafa mai, Saida na lura ina kyali sosai tukun. Body spray ɗin Victoria secrets na saka tareda turaren J’adore sai nayi light make up almost nude a fuskata. Jumpsuit ɗin Naeem Khan nasa sai na saka wani Gladiators na Giuseppe Zanotti. Nayi kyau ainun kamar zani Red carpet, kitchen naje na haɗa ma other half ɗina White Macaroni da sauce ɗin kwai. Na sake gyara falo tareda kunna turaren wuta da kuma spraying room freshner, tafiya nakeyi ina rangwaɗa duk practice yanda zanyi idan ya dawo. Shikuma Naufal bayan ya tashi daga aiki as usual wajen Miemie yaje, kuka takeyi haryanzu amma bata burgima, a hankali takeyi saboda duk ta galabaita. Sunar Khattab take faɗi kawai repeatedly, bai samu yayi mata mata ba bcs baya so yaje gabanta ya barke da kuka, ko yau a office bayan sun gama conference call dasu Mr Sutter Sai kuma sukaje wani site tareda Aminu. Yana komawa office ɗinshi ya garke yana hawaye, duk ya gaji komai yayi masa yawa. Gashi duk abinda yakema Fadeela amma maiyar yarinya tak’i zuciya ta tafi gidansu. Ita a dole ta samu wajen zama, shi yaso ya wulakanta ta to the extend da zata tafi gidansu saiya koma wajen Miemie full time. Saida yayi sallar isha ya koma gida, yana tafe yana tunanin salon cin fuskar da zaiyi mata yau kowama ya huta. Shiga falo yayi tareda sallama a matsayinshi na musulmi, but to his surprise Sai yaga wutan falo a kashe amma TV yana aikinsa. Haushi ya kamashi saiya fara sababi, “Meye aka kashe wuta salan na faɗi” saiya kunna. Zaune ya ganta akan 3 seater ta daura kafa ɗaya kan ɗaya tana mashi murmushi. “I’m sorry! Bansan Yanzu zaka dawo ba yasa na kashe” yanda ta faɗa cikin siririn murya da kissa dole saika sosu. Da sauri ta tashi zataje ta karba briefcase ɗinsa kuma tana tafe tana rangwaɗa. “Sannu da zuwa” ta faɗa data karasa dab dashi. Ja da baya yayi saiya ce a fusace, “keh meye haka” saiya ratsata ya wuce abinshi. Ko kaɗan bataji haushin abinda yayi ba, Infact tanaji yanzu ta fara. Daki ya wuce domin ya kimtsa kafin yaci abinci, jallabiya ya zura bayan yayi wanka. A kan dinning table ya ganta zaune tana jiran shi fuskanta dauke da annuri. Rai a bace ya haɗa girar sama dana kasa yana wani mazurai ya zauna akan kujera Which tun kafin ya iso ta jawo mashi, harara ya doka mata amma ta mayar masa da murmushi. Haushi yaji sosai saboda ya lura ta bala’in rainashi bata jin tsoron sa again. Tanayi tanata baɗa mashi kamshin turarenta harta gama serving, maimakon ta tafi kamar yadda ta saba sai ta zuba ma kanta itama tana ci. A cikin yanayinta na sanya sanya ta rinka ci kamar bata so taci, shikuma jefi daya, biyu yakan kalle ɓangaren ta. Haka har suka gama cin abinci ta kwashe ta kai kitchen shi kuma ya wuce kan couch domin ya kalle 9 o clock news na NTA. Itama taje ta zauna akan One seater, baice komai shiru yayi mata kamar baisan tana wajen ba. Yana ankare da ita sai gyangyaɗi takeyi kanta yana rawa amma dan jaraba tana forcing kanta a wajen. Dariya abin ya bashi kuma yau ne rana na farko da wani abu nata yasashi dariya. Data gaji dan kanta ta tashi tana tangal tangal kamar yar k’waya. “Yaya saida safe” ta faɗa muryanta yayi kasa saboda barci. “uhm” yace yana kallonta ta gefen ido. Sannu a hankali ta rinka layi harta kai cikin ɗakinta, takalmi kawai ta cire ta shiga bayi domin ta kama ruwa, ta fito tana cikin tafiya sai raguwan ruwa tareda santsi na tiles ya ɗibe ta. Tim ta faɗi a kasa, salati ta somayi kuma idonta yanzu yayi ras saboda barcin ya tafi. A hankali ta dafa gado tareda mikewa tsaye, amma sai me? Kafa yace tsaya mugani mana..... Ashe ta turguɗe ne. #NiDaDiYata *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 18 ✨✨✨ On the authority of Abu Hurairah, who said : The messenger of Allah said : "Part of someone's being a good Muslim is his leaving alone that which does not concern him." fine Hadith narrated by Termithi and others. On the authority of Abu Dhar Jundub bin Junadah, and Muadh bin Jabal that the messenger of Allah said : "Fear Allah wherever you are, and follow up a bad deed with a good one and it will wipe it out, and behave well towards people." Tirmithi narrated the Hadith and said it was fine, and in another version, said ture and fine. ******* K’ara kokarin daura kafar tayi a kasa amma ta kasa. Wani azabataccen zafi taji har cikin birnin kwakwalwarta. Nan take zafafan hawaye suka fara malalo mata. Changala kafarta tayi har cikin bayi ta kunna mashi ruwan zafi but still babu wani improvement. Haka ta koma cikin ɗaki ta hau kan gado tana tunanin duk yanda zata rinka ma ‘Other half’ ɗinta hidima. Bata gano answer ɗinba har barci ya fara fizgarta, gashi bata kashe wuta ba amma bazata iya tashi ba saboda azaba. Shikuma Other Half ɗin Fadeela Kawai tunanin abinda ya faru tsakanin shida ita Few minutes ago yake. ‘Kardai ace yarinyar nan ta fara sona ne?’ wani zuciya ya raya masa. ‘No no no... Allah ya kiyaye, it’s not even possible. Haba duk wulakanci danake mata!’ wani zuciyar ta sake raya mashi. ‘Maybe kuma kuɗi takeso’ ‘Yes I’m very sure, dama mata idan suna san kuɗinka sai su ta maka iyayi’ Yayi concluding Kudi takeso sai yayi tunanin ajiye mata check ɗin 50k kafin ta takura masa. Haka ya gama kallonsa saiya kashe kayan kallon tareda lantarki sanda zai tafi. 3 days.... Ciwon Fadeela sai gaba yakeyi saboda ko Makaranta ta daina zuwa. Dakyar take komai gashi ko kauɗin girki kala kala ta daina, dayake tanada stew dayawa a fridge sai ta rinka dafa white rice or Macaroni ta ajiye mashi. Drink kuma saita ajiye mashi Fanta ko Pepsi kawai, idan kuma breakfast ne Tea and bread Zata ajiye. Kuma rabon daya ganta tun ranar data turguɗe. ‘Dingisa kafarta from upstairs to downstairs and vice versa Yana bata wahala saboda tana tafe tana kwalla gashi ya kumbura sintim kamar Doya. Shikuma Other Half abin ya fara damunsa, ya lura check ɗin daya ajiye bata ɗauka ba kuma next day yayi withdrawing cash ya ajiye mata amma bata bi takai ba. Ya rasa menene matsalar ta gashi ko abinci anyhow takeyi. Kuma rabon daya ganta tun sanda tayi wani hot kwalliya. Shi Bawai Santa yake ba but atleast.... Sai kawai ya kasa Karasa tunanin. Zama yayi a falo daga safe har wajen azahar yaki zuwa aiki yana son yaga kozata wulkita amma Sam. Kwafa yayi saiya dauki key ɗin motarsa ya tafi gidansu, gwara yaje yaga Miemie yafi kafin Bad luck ɗinta ya jaza mai! À wajen Miemie babu yabo babu fallasa tanata fara’a kuma sunsha hira. “ina Anty yar gayu?” ta tambaya. Dadi sosai ya kamashi saboda an taɓo mashi inda yake mai k’aik’ayi. “Ban sani ba amma bari na ara wayar Momyn ki sai mu kirata. Zulumi a ranshi yana tunanin mai zai ce ma Anty Saudah bcs kwata kwata bayada number ɗinta. Aiko wayar ya gani akan centre table kuma Anty Saudah tana kitchen, a guje ya sure wayar yana jin ɗadi. Bugu ɗaya, biyu sai ta dauka. “Assalamu Alaikum, Anty ina wuni?” ta faɗa. Shi kuma yana jin muryanta sai ya kauda da sauri tareda kara ma Miemie a kunnenta. “Anty yar gayu yaushe zaki zo?” “Ah ah Miemie Kece ?” “Eh please yaushe zaki zo?” “Gaskiya ban sani ba saboda banida lafiya” Kallon Naufal Miemie tayi tareda faɗin “Ya Naufal dama Anty batada lafiya shine baka faɗa min ba?” Tsuru tsuru yayi saboda baiso Fadeela taji yana wajen ba, harara ya watsa ma Miemie tareda juyar da kansa. “Anty kiyi hakuri kinsan halinsu koda nace zanzo dubaki bazasu barni ba” ta cigaba da wayarta. Hira sosai sukayi daga bisani aka kashe. Burin Naufal ya cika yasan meke faruwa but still baisan meke damunta in particular ba. Anty Saudah tazo tana tambayar Naufal koyaga wayanta data ajiye a falo. “Eh dama nine na dauka saboda Miemie tanaso tayi waya da Anty ɗinta” “bakada wayane? Innalillahi kodai bakada number ɗinta ne?” Kana ganin yanda yayi kasan cewa bashida gaskiya, kallonsa Anty Saudah tayi kafin tace, “Allah zai saka mata koma menene” Anan ta barshi tsuru tsuru ta koma ɗaki saboda haushin takeji ainun, ita tasan basa jituwa amma batayi tunanin haka bane. Baiji daɗin yanda ran Anty Saudah ya ɓaci ba, kawai saiya yanke shawara ya bita ya bata hakuri tunda a matsayin uwa ya ɗauketa ba step mom ba, Thou bazata haife shiba. A bakin gado ya ganta tana matse kwalla, kakalo murmushi tayi data ganshi. Yasan sarai shi takema kuka. A kasa ya zauna dab da ita saiya daura hannunsa akan cinyarta. Nadama karara saiya soma magana kasa kasa. “Dan Allah Anty kiyi hakuri, Karki min haka, bana so kiyi kuka a kaina. Insha Allah I will do better.” “Allah yasa” kawai ta iya faɗa bcs zata iya barkewa da kuka wiwi. Sallama yayi mata kuma tashi mai da albarka saiya koma wajen Miemie sukayi sallama sannan ya tafi. A hanya tunani kawai yakeyi bcs ya ɗebo ruwan dafa kansa tunda yayi ma Anty Saudah alkawari amma baya tunanin zai cika mata ba. ***** Ita kuma tana jin tashin motarsa saita ɗingisa kafarta har kitchen, Feldin ɗinta ya kare saura Paracetamol gashi tana shan wuya. Abinda yasa take gudun Naufal baifi sanin halinshi na mugunta data yiba, tabbas muddin yaga tana pain zai kara inflicting mata more bcs burinsa kenan yaganta ta su suce. Nan take ta yanke shawara akan tayi Cous Cous saboda it’s very easy. Ta gama saita je dauko Fanta a fridge amma to her surprise ya kare. Dama tasan ya kusa gashi bazata iya zuwa kasuwa ba. Ruwa na sachet ta ajiye mashi kawai saita koma ɗaki. Zaman ɗirshan tayi a kasa tana numfashi sama sama, fisge ɗankwalin kanta tayi ta jefar. Ji tayi kamar ana tsikarinta a kafan gashi yayi nauyin. Ko numfashi ta lura yana kara mata zafi. Dukta fita hayacinta ta rasa meke mata daɗi, kwalla kawai takeyi gashi bata iya cin abinci sai shayi. “Wayyo ni Fadeela na shiga uku!” Shi kuma yana shiga falo ya lura har tayi abinci, kwafa yayi a ranshi tareda faɗin “ke kika sani” Haka yaci abincin kamar maɗaci saboda ya kwaɓe. Daya gama saiya kora ruwa yayi ɗakinsa, daya kai kofar Fadeela saida yaɗan tsaya koh zaiji motsi amma shiru kawai. 8:30 pm... Yaune nake ina tunani tareda kallon TV, ko ganewa banayi saboda tunanin yarinyar chan nakeyi, “karfa ta mutu” na faɗa da sauri tareda mikewa saboda nasan Abba zaiyi balangu dani muddin haka ya faru. A hankali na haye sama saboda banso taji karar zuwana. Safa da Marwa na rinka yi wajen ɗakinta na kasa shiga. Ni dai ban iya amai ba na lashe, Sam idan na shiga zata iya raina ni. Shiru nayi na rasa TUDUN DAFAWA(littafin my awesome UmmieeJafar) Kawai na yanke shawara na shiga tareda zare mata ido kamar mugu. Idea ɗin yayi min daɗi bcs haka nayi. Banka kofa nayi da k’arfin gaske tareda shiga, ina jin ta yanda tayi salati a razane. Ta bani tausayi ainun amma no time for weakness yanzu. “Ke dan raini zaki dafa min wani abinci babu kyan gani? Waye sa’anki?” sanda na faɗa ina jin ciwo a raina but a haka na cigaba. Narai narai tayi da ido tana kuka batace komai ba, jan magina kawai takeyi. Tausayinta ya kamani sosai saboda nasan tana kokari but it’s not enough bcs Itace dai Bad luck. Bance mata komai ba kawai na tsaya ina kollonta, data lura ita nake jira ta bani amsa saita fara share hawayenta, “Kayi hakuri Yaya wlh bada gangan nayi ba, banida lafia ne” ta faɗa cikin muryan kuka. “But Bari naje na dafa maka wani” saita fara Kokarin tashi. Duk rashin imaninka saika sosu. A hankali nace, “Dont worry” saina fita daga ɗakin, nawa na koma saina zauna akan gado. Hannaye biyu na daura akan kumatu na ina tunani, gaskiya ya kamata na taimaka mata koba dan halinta ba sai dan Allah. Ban koma cikin ɗakin ba but haka na rinka zirya wajen, idan naje sai na saka kunne na akan kofarta. Kukanta nakeji a hankali yana tashi. Gabaki daya ranar dagani har ita bamuyi barci ba. Sau biyu ko uku a cikin awa daya ina bakin ɗakin, sai wajen asuba naji tayi shiru da alamun barci tayi. Ban kwanta ba illa nafila danayi, na rok’on ma Miemie lafiya tareda ita bcs dey need it. 7:30am... Ta fito tana ɗingisa kafa which sai a locacin na lura da mai ke damunta, dukta kumbura ta susuce. Ji nayi kamar naje na daukota tsam daga stairs bcs ta dade bata sauko ba balle dama akwaita da nawa. Sannu a hankali harta isa inda nake, “Ina kwana yaya?” ta faɗa murya kasa kasa. “Lafia lau, ya jikinki?” ashe na sosa mata inda yake mata k’aik’ayi. Nan take ta barke sosai da kuka babu kama hannun yaro. Tanayi tana Sheshek’ar, bata tafi illa tsayawa a wajen. A hankali na karasa wajen datake, har zan saka hannuna nayi patting bayanta saina fasa kafin ya zama wani abu. “Kinaso akaiki asibiti ne?” Bata amsani ba kuma nima naji haushin tambayan bcs yanda take tana ɓukatar medical attention. Key ɗin mota ɗina na zura saidai kash......... Bazan iya bari ta fita haka ba, wani armless chiffon gown ta saka kuma bazan yarda wani Katon banza ya ganta ba, thou bawai ina Santa bane, but still! “Bakida wani kaya dazaki haɗa da wannan kinsan akwai maza a wajen?” Kallon kanta tayi saita sinna kai kafin tace, “bari naje na dauko abaya ɗina” Juyawa tayi ta fara tafiya, idan na biye mata zamu kwana a wajen. “just wait! Yana Ina ne idan na biye maki zaki ɓata min lokaci” Kallona tayi kafin tace, “Cikin drawer ɗina third shelf” Haka naje na dauko mata na bata abinta. Tana ɗingishi kamar raina zai fita saboda ni ko ban san mutum banaso naga ciwonsa . Wani private mukaje nan kusa damu, cikin sa’a Doctor yana nan. Tambayoyi ya rinka watso min wanda na kasa amsawa, wani irin kallo yayi min wanda kaida matarka amma bakasan komai a kanta ba. Kunyar duniya naji shi ranar saboda mutumin yana mutuntani sosai saboda unguwar mu ɗaya but daga alamu ya daina. Fadeela ne ta rinka shigan min tana amsawa, gaskiya yarinyar is very smart Kuma nagode mata cikin raina. Anzo za’a ja mata k’afa shi kuma Naufal zai fita kawai ta chapke masa hannu ”please stay with me Yaya, Karka tafi ka barni. Im very scared” Ta faɗa da puppy face idonta yana kwalla. #NiDaDiYata *My Lil sis, Amigo, Mon Amie, Te amo, Habibtee, Noor, Pyar........ I’ve no words to appreciate ur Respect, loyalty, kindness, compassion, honesty and support. I love you to the moon and back(NoHomo), Allah ya albarkace rayuwar ki. Ur enemies will never find peace, may they suffer till they perish.... Amin. Calm down her name is UmmieeJafar aka Pha’eexah, the author of My marriage series, My Greatest Weakness,Tudun Dafawa etc* *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 19✨✨✨ It was narrated from Aishah that the Messenger of Allah said: "Marriage is part of my sunnah, and whoever does not follow my sunnah has nothing to do with me. Get married, for I will boast of your great numbers before the nations. Whoever has the means, let him get married, and whoever does not, then he should fast for it will diminish his desire." (Hasan) ********** Hannunta na mak’ale da nawa ta rike tsam, kawai wani iri nakeji. Juyawa nayi bance komai ba kuma ban kwace hannuna ba. Tsaya nayi dab da ita, ita kuma ta rufe ido tana hawaye. Mamaki kawai take bani yanda bata gajiya da kuka. Shikuma Doctor yazo ya fara matsa mata kafa, ihu ta tsala tareda mirganawa kamar zata faɗi, da sauri na tarbo ta tareda daka mata harara. "Ni raki ne da rashin juriya ne banso”na faɗa mata. Narai narai tayi da ido tareda saka hannunta ta matse bakinta. Doctor Yanata complain akan sakacin damu kayi bamu zo da wuri ba. “Afuwan doctor wlh bansan abin zai kai haka bane dana kawota da wuri” Naufal ya faɗa mashi Shidai Doctor baice komai ba illa cigaba da aikinsa, yana kawai kallon Naufal as complete idiot ne bcs gaskiya kafan Fadeela ya lalace. Ita kuma Fadeela sai matse baki takeyi tana share hawaye, wata sa’in ta faɗa jikina idan an murɗa mata kafan but da sauri take bari idan taji daidai. Bawai zance bana jin daɗin abin bane idan ta taɓa ni, kawai I’m just neutral. Kafin a gama mata tasha kuka sosai duk ta galabaita. Daga nan aka bata magunguna da allurai, dole aka kwantar da ita saboda akwai na barci da sauransu. “Toh Alhaji saika je gida ka kawo mata abinci da sauran kayan amfani” Doctor ya faɗa mani. Toh kawai nace mashi na tafi, motana na wuce kai tsaya, ina ciki nafi 20mins banyi komai ba. Bansan me zanyi ba. Na farko dai ban iya girki ba, na biyu kuma bazai kyautu na siyo abinci daga restaurant ba tunda bazai taɓa Kamada na gida ba. Balle yanda Doctor ke mun kallon mugu, yana lura da abincin zai gama concluding banida saura imani. Kawai wani dabara ya faɗo min akan naje wajen Mommy bcs tana sona, ita kaɗai ne zata mara min baya. Nan take na tada motar nayi hanyar gidansu, Grand Kadi na gani a parking lot da suit and tie daga gani zashi court case ne. Har k’asa na ɗuka na gaishe shi kafin na zayyana mashi komai. Salati yayi cikin damuna tareda alkawarin zaije direct bayan ya fito daga kotu. Tun daga lokacin jikina yayi la’asar yanda naga ya razana, tabbas yanzu na fara sanin gatan Fadeela. K’afa babu kwari na shiga cikin gida, Mommy na riske a falo tana kallon Manara TV. Itama har k’asa na gaisheta which dama ɗabi’a na ne. Tashi tayi wai tana zuwa, dawowanta keda wuya sai gata tareda mai aiki shak’e da kayan breakfast. Nan take kunya ya fara ɗawainiya dani, wai ace tsakani na da mutanen nan banda mutunci da arziki babu abinda ke shiga tsakanin mu. Ni kuma banda tsiya bana masu komai. “Ga abinci kaci, nasan bazaka rasa guntun yunwa ba” Mommy ta faɗa. Sinna kai nayi bcs kunyar ta nakeji, “Mommy bazan iya ba, dama Fadeela ce ke asibiti” “Innalillahi wa inna ilayhi rajiun, meya sameta? Tun yaushe?” Yanda naga ta ruɗe sai na fara jin nauyin faɗa mata yarinyar ta tafi kwana uku ba lafiya sai yau na kaita asibiti. Ina cikin tunani ashe har Mommy ta zura hijabi tana tsaye kaina. “Mu tafi koh” tace “Dama abinci nazo karɓa saboda idan ta tashi saita ci” Bata kulani ba kawai ta wuce kitchen, bayan 30 mins haka sai gata ta fito da Katon flask ɗin ruwan zafi dasu kofuna tareda kayan shayi. “Sai mu siyan mata bread a hanya kuma na saka Husna (Mai aiki) ta dafa abinci, anjima zaka dawo ka karba” “Nagode sosai Mommy, Allah ya saka da alheri” Muna tafe a cikin mota zulumi fal raina, kawai yanda Fadeela ta susuce nake tunani. Da akwai yanda zanyi mata makeup karda a gane danayi. Dadin abin su Abba da Anty Saudah basu sani ba aiko cinye nama ɗina zasuyi bcs na lura dis days sunfi Santa akaina. Mun isa cikin asibiti lokacin Fadeela ta farka, tana ganin Mommy ta barke da kuka. “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel” na rinka nanatawa kafin Fadeela ta tona min asiri. Kawai Mommy patting bayanta takeyi ciki so da kulawa, “Yi hakuri My baby, Kowa da jarabtan shi. Karki damu an kankare maki zunnuban ki ne... Daddyn ki shima ya kusan zuwa” Haka Mommy ta rinka shafa mata baya tana bata baki. “Ka kira Hajia Saudatu kuwa dasu Hajia Sarai?” Mommy ta tambaye ni, yak’e nayi kafin nace, “Yanzu zan kira su” A gabansu na kira Anty Saudah da Mama harda Abba akan an kwantar da Fadeela, yanda hankalin su ya tashi yafi na iyayen Fadeela.Nidai bazan iya barin ɗakin ba bcs ina tsoron kada ta fayyace ma Mamanta komai. 1 hr 45 mins later..... Motar Anty Saudah ya fara isowa cikin haraban asibitin. Tazo tareda cooler ɗin abinci dasu fruits da kayan shayi. Tana shiga tayi ido da Fadeela ba tace komai ba, kawai ajiye kayan tayi suka gaisa da Mommy har tana tambayar ta jikin Miemie shine take cewa gaskiya yanzu yayi sauki sosai. Bayan nan ta matsa wajen Fadeela tana mata kallon tuhuma, “Sannu kinji! Tun yaushe kikaji ciwon?” Ita Fadeela bata gane abinda akeyi ba saita faɗa ranar. “Shine dan mugunta yau kaga damar kawo ta asibiti” ta juya tanama Naufal sababi. “Dan wulakanci an gaya maka jaka aka kai maka, salan ta mutu ko ta nak’asa?” Mommy ne ta chapke, “Yi hakuri Hajia Aiba laifin shi bane” “Karki ce haka, nasan halinshi sarai kuma nasan abinda zai iya aikatawa” Suna cikin haka ne saiga Mama da Abba da Bilqees. Mama kallona tayi ta juyar da kanta kuma koda na gaisheta bata amsa mani ba. Shikuma Abba da nace mashi “Ina kwana” da kai ya amsa min. Chan gefe na koma na tsaya kamar bare saboda kowa fuskarshi yana ɗauke da irin kallon da kake ma mugu. Abba ya soma magana k’asa k’asa, “Yanzu Naufal me muka yi a duniya da kake so ka hana mu sakat?” sai kuma ya kafa min ido. Kunyar duniya ya kamani kamar kasa ta buɗe na shiga. Bance komai ba nayi shiru. “Gwara dai ka tambaye shi sai mu bashi hakuri?” Mama tace. Ita kuma Anty tace, “Ai kuwa dai, saboda wannan ɗebo ruwa dame yayi kama?” Abba yayi ajiyar zuciya saiya kalle Fadeela sannan ya sake kallona, “Dube yarinyar nan fisabilillahi, halan kana tunanin jaka aka kai maka? Dafa gatan ta da komai ka k’askantar da ita.... Kalleta da kyau kamar an hak’ota a rami” “Ai idan rami ne da sauki, ji yanda tayi kamar ita ce k’asan da aka hau sanda ake yin Badar” Mama tace. Mommy ne tace,”Kuyi hakuri bafa laifin shi bane yasa ta faɗi, ai tsautsayi baya wuce ranar shi” “Toh sai akace kada ya kawo ta asibiti??” Anty Saudah ta faɗa. “Ina dasu Paracetamol a ɗaki yasa nace kada ya damu bari mu gani ko zanji sauki” Fadeela ta tare min. Mama ce a hasalce tace, “Idan kika kara saka baki saina mauje ki. Watau ke mai miji koh? Kina tsoron kada ya rama abinda mukayi mashi akan ki koh?” Saita juyo tana fuskantana, “Kana ji na koh?” Bance komai ba sai Abba yace “bada kai ake magana ba, you’re Very stupid” Ba shiri na amsa Mama saboda na lura da girmana sunaso su tara min gajiya. “Ciwon kai naji labarin yarinyar chan tayi sai anjimu a gari, dama ɓata min suna kake so kayi na kasa shiga makwabta, ina tafe ana nunani ga Maman Mugu.” Sai kawai tayi kwafa ta juyar da fuskanta. Dama Hausawa sunce abinda ka suka shi zaka girba, idan alheri ne to, idan kuma tsiya toh shima haka saboda babu wanda zai shuka shinkafa yaga rake. Tas bayin Allah ɗinnan suka min, wanki babban bargo suka min la’ada waje saboda su uku ba wanda ya raga min. Mommy babu magiyan duniya da batayi su bari ba amma ina, sai mita sukeyi.Kamar kwallo suka mayar da abin, sai attacking ɗina sukeyi tareda passing ma junar su. Harda cewa Abba yayi, “Toh Hajia Sarai Kinga abinda yaronki yayi” Da sauri ta chapke, “Ba yarona bane, yaron Saudatu ne” “Nima banaso gaskiya, Hajia kinaso?” sai Anty Saudah ta kalli Mommy tana dariya tareda tambayar ta. “Sosai ma kuwa tunda kun haɗe mashi kai” Dama tun zuwansu Bilqees ta fara ba Fadeela abinci bcs tun tea ɗin da Mommy ta bata babu komai a cikin ta. A baki ake bata ana lallashinta gwanin ban sha’awa. Anty Saudah ta ɗauki kankana da abarba ta fara ferewa, kallo nayi tareda shiru bcs cikina ya fara kiran ciroma tunda banci abinci kwata kwata yauba. Mommy daga baya ta zuba min abinci tareda bani Fanta, Motana na wuce naci nayi gyatsa tareda guntun gyangyaɗi bcs na galabaita daga sintiri danayi ɗakin Fadeela jiya. Bayan kwana uku...... Babu wanda baizo gaishe da Fadeela ba including Miemie, saboda tana jin Anty yar gayu batada lafia sai kan ya fara motsawa. Dole aka kawo ta kuma cikin ikon Allah babu handcuffs kuma batayi anything funny ba. Ita tayi ɗawainiya bata abinci da ruwa, ita abin dariya ya bata saboda ciwon K’afa takeyi ba na hannu ba, kuma ta fara taka kafan kaɗan kaɗan. Kana ganin ta cikin kwanakin nan kasan cewa yar so ce kuma ba abin wulakanta wa bane. Hatta Big Daddy da iyalansa Ba’a barsu a baya ba, ko Alhaji Sulaiman baban Sadeeq yaje dashi kanshi Sadeeq da matarshi. Abinci kuwa mai aikin Anty Saudah ke kawo three square meal tareda Mai aikin Mommy. Itama Jawahir duk sanda taje saita kai masu wani abu. Kwata kwata Naufal baya jin daɗin asibitin idan Anty Saudah da Mama nanan, yafi son idan sun tafi gida ya zauna da Mommy Asha hira. Bilqees ke kwana da Fadeela thru out. Ni Naufal wajen 6am na isa asibitin kafin su Mama su rigani zuwa asibitin su kama kirana ‘Mugu’ bcs na tsana sunan har cikin raina. 5pm.... An haɗa kayan Fadeela komai da komai ana jiran Doctor ya gama prescribing magani ya sallame su. Itama ta ɗan warware tayi ɗan armashi abinta ba kamar yadda aka kaita ba. Mama ce tace saidai Fadeela ta wuce wajenta ta k’ara murmurewa saboda tasan halin Wa’e saita kalleshi ta gefen ido. Idan ana sabo da tozarci ya riga ya saba dashi dis past few days saboda sun mayar dashi laughing stuff, mocking ɗinsa anyhow kawai sukeyi. Saidai ba fault ɗinsu bane, dama komai kayi akwai reckoning ko a duniya ko lahira baki ɗaya. Da bai zubar da girman da Allah ya bashi ba yayi abin tsiya da haka bai faru ba. But he promised to do better. “Nifa ba inda za’a je min da mata” ya faɗa masu. Mama ta dubeshi a kaikaice, irin duban hadarin kaji “Toh mara kunya hanamu” ta hayayyakoshi. “Ai dama da bakice haka ba, wajena zata zauna kinsan sun saba da Miemie” Anty Saudah ta faɗa. Haka suka rinka jani in jaka shi babu wanda zai tafi mashi da matarsa wani wajen. Fadeela na daga kwance tana jinsu duk rai a jagule, tsakani da Allah tunda yace he will do better gwara a barta ta koma ɗakin ta. Sai wani zuciya yace mata “Karya yakeyi kawai bauta yake so ta koma tana yimashi” Kauda tunanin tayi bcs aure ibada ne kuma ladanta yana sama wajen Allah. Indai da aure tsakanin su gwara tayi masa koma menene muddin bazai kare hakkin addini ba. Kowa yasani Allah yana tareda masu hakuri Besides Hausawa sunce mai hakuri shike dafa dutse har yasha romonta. Anty Saudah ta dafa mata kafaɗa “ ‘yata! Zaki bini muje gidan gona?” Bata ce mata komai ba illa Sinna kai kasa tana wasada hannunta. “Sauraron ki nakeyi” Daga ido tayi saita lura kowa kallonta yakeyi, musamman shi gwaskar ya kafa mata ido babu kiftawa. Sunkuyar da kai tayi tareda cewa, “Anty duk abinda kuka ce shi za’a yi” Kwafa yayi ranshi ya bala’in ɓaci bcs tunda suna Santa idan tace zata zauna dashi babu mai hanata. “Ko kai bazaka zauna da kanka ba idan an barka” wani siririn murya ya raya mashi. Ita kuma koda wasa bazata iya cewa tana son zama da mijinta ba bcs rashin kunyarta bai kai haka ba besides suna kwatan mata yancin tane. Daidai lokacin su Grand Kadi da Mommy suka shigo, Naufal bai bari sun natsa ba ya fara masu k’orafi akan za’a rabashi da matarsa. Murmushi Grand Kadi yayi, “ karka damu babu mai hanaka tafiya da matarka, kai ka shigo da ita kuma kai zaka fita da ita” “Woooow!” ya faɗa tareda naushin iska. Ko kunyar kowa baiji ba ya nuna murnarsa a fili. Harda shaking hannun Grand Kadi yana godiya. Dariya yake masu Anty Saudah domin yaci argument ɗin, ita kuma takaimai dukan wasa a kafaɗa sai shikuma ya kauce tareda saurin barin ɗakin. Fadeela sinna kai tayi ba tace komai ba but murna fal ranta zata koma wajen Other Half ɗinta. An tarasu su biyu an masu nasiha akan aure mai shiga jiki, idan kayi shi da kyau ka kuɓuta, if not Zai kaika ga hallaka. Aure ba abin wasa bane kuma yana cikon manyan sunnonin Manzan Allah SAW. Zo mu zauna dama zo mu saɓa ne, kuma mistakes are what makes you human but Yanda Kayi handling ɗinshi makes u a better person. Wajen 30 mins kowa na tofa albarkacin bakinsa kafin aka shi masu albarka suka wuce. Dama da safe Bilqees, Abla harda Miemie sunje gidanta sun gyara mata tsap. Ita Miemie tun sanda ta fara fita wajen Anty yar gayu aka fara gane kanta, tana shan magani akai akai kuma bata gardama. Thou ba’a barinta alone, sun shirya ma Fadeela komai hardasu laundry aka tayata. Shikuma ya tsaya Vanilla joints ya siyan masu kayan lashe lashe sai kuma ya siyan masu kaji gasarshe na kan titi. Shi Bawai Santa yakeyi ba but kawai after everything he put her through, tayi deserving something sweet. Ita tana mota tana mamakin yanda yakeyi kamar ba shiba. #NiDaDiyata *Big shout-out to all the fans of this book, Nagode sosai Allah ya bar zumunci. Especially those dana keda direct contact dasu kamar su UmmieeJafar Novels, Xarah Novels, The Queen Bee, Deyart Novels, Hamagee Novels, Billy Galadanci Novels, Marubuci, Rash Kardam Novels, Xoubhie Novels etc* #TeamNiDaDiyata #TeamFadeela #TeamNaufal #TeamMiemie #TeamKhattab *Ni dai TEAM NAUFAL ce* *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 20 ✨✨✨ *Lesson* ‪Patience is when you're able to conquer that angry voice in your head which wants to take revenge on others who hurt you or are mean to you!‬‬‬‬‬‬ Mufti Ismail Menk Ibn Mas'ud (May Allah be pleased with him) said: The Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "He who says: 'Astaghfir ullah-alladhi la ilaha illa Huwal-Haiyul-Qayyumu, wa atubu ilaihi (I seek the forgiveness of Allah, there is no true god except Allah, the Ever-Living, the Self- Subsisting, and I turn to Him in repentance),' his sins will be forgiven even if he should have run away from the battlefield (while he was engaged in fighting for the Cause of Allah)."[Abu Dawud, At-Tirmidhi and Al-Hakim ********** CYPRUS A East ɗin Mediterranean akwai wani Island da ake kira Cyprus, chan daga wajen Arewan garin akwai wani k’aramin gidan gona wanda ya k’unsa ɗakuna biyu da bayi uku tareda da kitchen daya. A cikin falon akwai dinning area, drinks cabinet da kuma chimney. Wani matashi ne wanda bazai kai shekara 25 a duniya ba ya shiga cikin gidan, hannunsa shak’e yake da itatuwa kuma ya nufa hanyar fireplace ɗin falon, yana zuwa wajen saiya dire tareda ajiyar zuciya. Kayan sanyin dake jikinsa ya fara k’okarin ragewa, safar hannu ya cire sai kuma maufler tareda head warmer. Yanzu fuskarshi ya bayyana sosai wanda da baka ganin komai sai k’wayar idanu. Jacket ɗinsa ya cire tareda ajiye wa akan couch sai ya rige daga shi sai sweat pants tareda T-shirt. Kai tsaye dinning area ya wuce ya haɗa ma kanshi shayi a wasu fararen Chinese wears. Yana sha yana lumshe ido,Saida ya zuba ma kansa kofi biyu na ruwan bunu kuma ya shanye tas. Tsam ya mik’e tsaye ya wuce wajen wani calendar haka wanda yayi kacha kacha da rubutu. “Day 190” ya rubuta a bangon saiya wuce hanyar bedroom ɗinsa ya shiga bayi direct. Kallon kansa ya tsaya yi a mirror ɗin bayin, duk ya canza kamanni ya susuce. Rabon daya aske gashin kansa kona gemunsa tun yana Nigeria. Yanzu Afro yayi tsawo kamar jirgi ya doso gari ga kuma fuskarshi jaɓa jaɓa da gashi. Mutane biyu kawai yake tausaya mawa, na farko dai Mahaifiyarsa wanda yasan tana cikin matsananci tashin hankali akan rashinsa. Na biyu kuma Haskensa Miemie, rashinta yayi sanadiyar gudunsa. Shifa bazai iya zama gari ɗaya babu ita yasa kawai ya tafi. Wanta yayi making ɗinshi clear bazai taɓa bashi ita ba saboda wasu dalilai nashi. Shikuma idan ba Miemie bazai zauna da wata mace a inuwar aure ba. Babu makawa idan yana gidansu za’a tursasa shi akan ya aure Lili which bazai iya buɗe idonsa ya ganta ba. Wanka yayi sannan ya shirya cikin Long sleeve da jens wando, ɗayan ɗakin opposite nashi ya wuce tareda shiga. Maidaidacin ɗaki shake da kayan computer kala kala tareda sauran abubuwa daya jibanci haka. Zama yayi akan wani kujera dayake gaban babban computer. Kunnawa yayi sai wani rubutu ya fito inda aka rubuta NTI TELECOMMUNICATIONS. Nan ya saka password ya soma aiki gadan gadan, kana ganin yanda yake aiki cikin kwarewa kasan cewa ba sabon hannun bane. NIGERIA “Inspector mun samu leads akan shi” wani Sergent ya Shiga office ɗin IG tareda mashi salute. Ajiye takarda yayi dake hannunsa sannan ya gyara zama tabaransa. “A Ina ne wajen?” “Sir Chan Cyprus ne, akwai wani ICT company dayake ma aiki. Toh wani ɗan department ɗinmu dayayi tracking hotonsa a cikin database ɗinsu” “Innalillahi, tuntuni muna nemasa amma yana chan Cyprus. How true is this information?” IG ya tambaya. “Anyi kowane bincike kuma an gane Khattab ne” “Kuma kun tabbata anan yake aiki ba scam bane?” “Affirmative Sir” “Okay ku shirya mana Visa muje Cyprus muga gari” 2 days later.... Khattab ne ke cikin Garden ɗinsa yana gyarawa, dayake Miemie ta koya mashi yanda zaiyi shuka da sauran su so bashida matsala wajen yi yanzu. Saboda yana Missing Miemie in the first place Yasa ya siya gida mai yanayin gidansu watau na gona. Yana cikin gyara sunflowers da kuma Hydrangeas sai kawai yaji an shigo mashi gida, bai yi kokarin dubawa ba saboda mutum ɗaya ya sani watau makwabcin sa Mr Kareem. Tafiya yaji ta wajen ɓangaren dayake Kuma yasan Mr Kareem bazai zo wajen ba. A hankali ya ɗaga tareda juyawa, fuskar da bazai taɓa manta wa ya gani. IG ne yake tafiya wajen dayake. Nan take gabansa yayi mumunar faduwa, da sauri ya mike tsaye tareda da sakin shovel ɗin hannunsa. Jikinsa rawa ya somayi baisan mai zaice ba. Shikuma Daddy ɗin Khattab zuwa company ɗin Khattab yayi sai akace mashi Khattab a gida yake masu aiki wai baya san cuɗanya da mutane, toh dayake he is good babu Yanda zasuyi. IG yana nuna masu clearance ɗinshi a matsayin jama’an tsoro kuma ana neman Khattab dead or alive a Nigeria. Nan take suka haɗashi da wani officer domin ya jagoranci shi zuwa gidan. Yana isa saiya ji motsi ta wajen garden yasa yaje ya duba. Ido cikin ido yake kallon Khattab shi wanda ya maza ya sauke nasa saboda kwarjini. “Ka kyauta kenan Khattab?” Mahaifinsa yace. ********* Motar shiru babu abinda ke tashi sai tafsir ɗin Sheik Aminu Ibrahim Daurawa akan aure. Sannu a hankali har suka isa gidansu, horn sau ɗaya yayi Maigadi ya buɗe masu. Suna cikin parking lot sun fito sai Maigadi Mallam Idi yazo wajen su. “Ina wuni Hajia ya jiki?” “Lafia lau ya aiki? “Alhamdulillah” Daga nan saiya ɗaukan masu jakar su, har cikin falon ya ajiye masu sannan ya masu saida safe. Fadeela a hankali ta ɗingisa kafarta har ɗakinta domin tayi sallah, shima Naufal ya wuce Masallaci. Bayan ta idar saita sauka ta sake microwaving kazan saita haɗa mashi da snacks ɗin da suka siya. Ta ɗeba nata tana kokarin wucewa saiya shigo falon, kallon ta yayi sau ɗaya saiya kawar da fuskarshi. Kan Dinning ya kalla sai yaga komai is set. Murmushi yayi a ranshi yana tafe fuskarshi kuma babu yabo babu fallasa. “Saida safe Yaya” ta faɗa sannan ta haye sama. “Toh” ya amsa mata dashi. Tana ɓacewa saiya tsaya cak, haushin kanshi ya fara ji sosai bcs yanda ya amsata bai dace ba. Besides shida yake neman sulhu. Amma zai gyara abin, yayi assuring kansa. Next Day.... Ya kasance Weekend so Naufal bazashi aiki ba, kuma koba haka ba babu inda zashi bcs ya barma Aminu komai a hannunsa tunda shi yana jinya. Wajen asuba ta farka tana mitsike idanu, tana cikin bargo tana ajiyar zuciya a hankali. Karar kofan Naufal taji da alamu zashi Masjid ne. Murmushi tayi mai bayyana hakora saboda Other half ɗinta akwai ibada. “Allah ya daidaita tsakanin mu” ta faɗa tareda yin mik’a, salati tayi saita wuce bayi. Shikuma Naufal yaso ya tsaya ɗakinta domin ya tasheta amma wani zuciya yace masa “Meye ruwanka da ita salan raini ya shiga tsakani, halan da kai kake tashin ta?” Bayan an Idar da sallah saiya tsaya lazimi kafin gari ya k’ara haske, yanayi sai kuma Fadeela ta faɗo masa a rai. Da sauri yake kawar da tunanin but still ya kasa bari, haushin abin yakeyi matuka but babu yanda zaiyi. Da gari yayi haske saiya wuce gida abinsa, a hanya ya haɗu da Doctor daga gani asibiti zashi. Sun tsaya sukayi gaisuwan mutunci but still Doctor ɗin Bai wani sake jiki dashi ba kamar da. Ya tambaye shi lafiyan Fadeela kuma ya jaddada mashi amfanin magani da kuma tayi kokarin taka kafanta. “Karka damu Doctor” Naufal yayi assuring ɗin sa. “Toh” yace saboda yana bala’in jin haushin Naufal. So da dama ya saba ganin couples wanda basa shiri amma ba kamar yanda nasu yake ba. Ya lura matar batada matsala kawai mijinta ne mai zafin kai yasa ya dena sake mashi fuska. Bayan ta idar da sallah saita mirgina gefe ta kama barci, ba ita ta farka ba sai wajen 7:30 am. Wanka ta somayi saita shafa ma kafarta wani magani haka mai suna ‘Power Heat’ Zama tayi akan mirror ta rasa wani irin kwalliya zatayi, sai kawai tayi smoking eyes da purple lips. Wardrobe ɗinta ta wuce ta ciro wani bakin dogon pencil gown saita dauki wani peach kimono ta haɗa dashi. ‘Daurin turban tayi wanda ya kara k’awata mata fuskarta. Su humra da turaren Chanel No 5 ta fashe kanta dashi. Tayi kyau ainun ita kanta ta yaba balle wani, takalmin soso baki ta saka mai dunlop. Kitchen ta wuce kai tsaye ta auno wake ta fara wankewa saboda kosai zatayi masu da kunun gyaɗa. Dayake blender ɗinta na zamani ne saita markaɗa abinta. Shikuma koda ya dawo bai ganta ba sai ya wuce kai tsaye ɗakinsa, baiyi 5mins ba barci mai kyau yayi awon gaba dashi. Wajen 9 am ya tashi kuma kamshin abinci ya cika mai hanci. Shima wankar yayi saiya saka 3 quater camouflage da sleeveless riga fari. Koda ya shiga falo bai ganta ba kuma babu abinci akan dinning kawai kamshi ne yacika Ko’ina. Zama yayi akan Couch ya fara kallo, Keeping Up with the Kardashian ya gani yana aiki kuma Yasan ita ta Saka bcs koda yaushe abinda yake riskewa kenan, dariya yayi saboda baiga amfanin kallon mutanen da basuda sana’a sai shopping. JSC sport ya saka ana nuna Basketball kuma favorite player ɗinshi Kobe Byrant ke wasa, nan ya shagala Yanata kallo. Ita kuma ta fito zata ajiye cooler sai taga ya shafa’a yana kallo. Bayan ta gama jere komai yayi tsaf saita taka sannu a hankali har wajen dayake, wannan Karon babu karap karap ɗin takalmi. Kamshin Chanel No 5 yaji but bai hasala ba kamar da yanda yakeyi, wannan Karon jindaɗin kamshin yayi. A gefen sa ta tsaya ta rasa me zata ce bcs ya kura mata ido Which baisan ma yanayi ba. “yaya ina kwana?” ta faɗa tana wasa da yatsunta. “lafia lau, ya jikinki?” ya faɗa fuskarshi babu yabo babu fallasa. “I’m much better, thanks” sai sukayi Shiru basu ce komai ba, kana ganin su kasan akwai tension a tsakanin su. Da wani siririn murya tace masa, “Dama yaya nazo na faɗa maka na gama abinci ne” “Okay sai muje kiyi serving ɗina” Tana tafe yana binta da ido kawai kallon ta yakeyi, tanaji à jikinta ya kafa mata ido saboda duk ta birkice. Dadin abin kayanta bai nuna matsewa saboda Kimono data saka if not tasan Zata kara turguɗewa. Kamar yadda ta saba ita ke jawo masa kujera saiya zauna, wannan karon yace mata, “Thanks” Gyada kai kawai tayi saita soma zuba mashi, yanda yake abin har mamaki yake bata bcs he was very polite. Ta gama zuba masa kunun saita saka masa madara a ciki yanda akeyi, ashe shi bai taɓa gani ba. “Toh fah!” ya faɗa a ranshi bcs da bfr ne saiya watsa mata a jiki koya haska mata mari bcs baya san shishigi. Ita kuma ta shafa’a cikin tunani ta mance kofinshi ne saita saka madara, koda ta ankara salati kawai takeyi bcs tasan shi. Tayi mamaki sosai da baiyi magana ba. Hanyar ɗaki ta nufa saita ji muryan shi, “Ke bazaki ci abinci bane?” Cak ta tsaya saita juyo a hankali, bata yarda sun haɗa ido ba bcs idanunsa yana making ɗinta uncomfortable sosai. “Banajin yunwa” ta faɗa tana murza ido tareda tura baki. Kawar da fuskarshi yayi saiya ce, “Maganin fah?” Bata ce komai ba illa wasa da yan yatsun hannunta, tanayi tana kallon kasa. “Please kici abinci saboda Kisha magani” ya faɗa kasa kasa. Babu yanda zata yi dole ta hakura ta koma, komai a hankali takeyi bcs duk ya takura mata da Idonshi. Da a kaikaice yakeyi amma daga baya saiya fito ɓaro ɓaro yana kallon ta, ko sun haɗa ido saidai taji kunya ta cire nata amma bazai cire nashi ba. Shi kawai yanda take yin komai yake mashi kyau, komai a hankali kamar batada jini. Gashi ta tsantsara kwalliya kamar yanmatan TV. Haka suka gama cin abincin ta kwashe komai ta gyara tas. Ita tunda take zaman gidan bata taɓa takura ba kamar yau, duk inda taje kanshi yana kanta. Ya mayar da ita abin kallo dukta tsargu. Tunanin yanda zai nemo sulhu tsakanin su yakeyi amma ya rasa. Gashi ko number ɗinta bashida shi balle ya aika mata text. Kiran Bilqees yayi a waya akan ta tura mashi number ɗin Fadeela, within Minutes tayi mashi sending. Murna yayi sosai kuma yayi mata alkawarin waya dama tuntuni tana rok’on sa amma yaki sai yanzu. Komawa ɗakinsa yayi bcs tuntuni Fadeela ta barshi shi kadai. Zama yayi akan bedside drawer ya daura kafa ɗaya kan ɗaya fuskarshi dauke da annuri. A hankali ya soma composing mata msg ya tura mata. Yayi rubutu sosai saiya tsaya kafin ya cikata da surutu kuma still wani zuciya yana raya mashi zata raina shi amma wannan karon ko ajikin sa, indai zata amsa batunsa bai damu ba. Ita kuma data koma ɗaki hawa kan gado tayi ta rungume pillow, kawai yanda Naufal yakeyi ke bata mamaki bcs farad ɗaya ya canza from the mean husband ɗinta to someone sweet and gentle. Blushing Kawai takeyi bcs idan ya fara santa batasan irin daɗin da zataji ba. Tana kwance tana tunani tareda kallon ceiling, wani msg ya shigo mata, ta karanta yafi sau uku tana mitsike idanu amma still abu ɗaya tagani. “Nasan cewa we didn’t start on the right foot, but fate ya kawo mu tare. I feel wrong but I’m human Kuma dan Adam ajizine, I Can’t help it but you reflect in my heart. You blossom in my heart and I’m going to cherish it till my last breath. You are my sound of redemption, the faith that I’ve lost, the answer that I’m seeking no matter the cost. You taught me forgiveness by giving your love back to me even when I don’t deserve it. I see truth somewhere in your eyes, I can’t ever change without you bcs you reflect Me and I love that about you. No matter how I dodge trying to be careful, going round in circles still my feelings grew more for you. What I’m trying to say is that, I just wish for us to be like other couples.” Kallon msg ɗin take wai ita Fadeela ya tura ma wannan abu, gyara zamanta tayi saita kalle kanta ta madubi ta kalle waya bakinta a buɗe tana mamaki. #NiDaDiyata #TeamNiDaDiyata *Awwwn I'm so sad, Wai yanzu ace TEAM FADEELA su suka lashe gasar. Ya akayi kuka zabeta bayan idon Naufal yana glimmering.* *And before I forget this page belongs to you Zeenaseer author of AMAL and MARAICI Allah ya albarkace rayuwar ki, Amin* *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 21 ✨✨✨ Abu Umamah Al-Harithi narrated that he heard the Messenger of Allah (pbuh) say "No man seizes the wealth of a Muslim unlawfully by means of his (false) oath, but Allah will deny Paradise to him and will doom him to Hell." A man among the people said: "O Messenger of Allah, even if it is something small?" He said: "Even if it is a twig of an Arak tree." (Sahih) ******** Dama bahaushe yace mai hakuri zai dafa duste kuma yasha romonta, a yau naga fa’idan hakurin danayi a gidan Naufal, duk wulakanci da yayi min na shanye shi. Wannan shine wanka ya biya kuɗin sabulu. Dama kaso, kuma a soka shine ribar aure. Burin ma’aurata kenan su zauna da spouse masu kaunarsu kuma nima yanzu na shiga sahun su. Haka na rinka bin gado ina mirginawa daga bangare ɗaya zuwa wani. Karanta msg din nakeyi saida na haddace, na shafa’a na mance da ya kamata na amsa mashi. A haka har barci ɓarawo yayi gaba dani. Shikuma Naufal ya rasa meke masa dadi, jira yakeyi tayi masa reply tunda ta IMessage ne yaga ta karanta amma kuma batayi reply. Nan take ya fara over reacting, safa da Marwa kawai yakeyi cikin ɗakin from bango ɗaya zuwa wani. Kwakwalwarsa ta fara rage aiki saboda abubuwa sun cunkushe masa, “Shikenan na cuce kaina, nayi sanadiyar da ta tsane ni” Haka yayita nanatawa tareda dafa kanshi. A yau yayi dana sanin duk abinda yayi mata, dama shi zuciya ba’a kwabarsa. Idan yace yana san abu to dole a bashi. Yayi hanyar bayi kenan zai kama ruwa, wani kara yaji alamar msg ya shigan masa waya. Da gudu yaje domin ya buɗe kuma fuskarshi dauke da annuri. Ashe MTN ne sukayi mashi msg ɗinsu na fama akan How to learn English. Ranshi yayi mumunan ɓaci saboda yaso ya kirasu yayi masu tas. Bayi ya koma yayi abinda zaiyi ya fito, a hankali yaje wajen ɗakin ta tareda kafa kunne akan kofa amma baiji komai. Haka ya hakura ya koma ɗakinsa saboda ko zaman falo ya isheshi musamman yanzo data tsane shi. 1 pm..... Locacin yana zaune akan mirror yayi tagumi, tunani kala kala kawai yakeyi. Jin an kira sallah yayi saiya wuce masallaci. Koda aka idar baiga amfanin shiga ciki ba kawai saiya zauna tareda Maigadi. Ni kuma koda na tashi sallah nayi kafin na makara, bayan na idar wayana na dauka sai na kira Yaya amma bai dauka ba. Nan take na canza zama bcs shine kaga samu kaga rashi. Kara kiransa nayi amma bawan Allah nan bai dauka ba, a kalla nayi masa 5 missed calls but still babu response. Nan na soma zufa, “Ko dai wasan April fool yayi min” saidai ba watan April muke ba, muna January ne. Ni dama ban iya firgita ba, da sauri naje dakin Yaya saina kwankwasa amma shiru. Dole na tafi bcs tuntuni yayi min iyaka da ɗakinsa. Hawa nayi kan mirror na kifa kaina, sana’a ta na kuka na somayi. Saida nayi ma’ishe naje bayi na fyace magina tareda dauraye fuskana. Ko makeup banyi ba kawai kitchen na wuce domin na shafa ma cikina lafia saboda naji yana kuka. Jollof ɗin shinkafa da wake nayi tareda Fish Nugget, sai na haɗa da ginger drink wanda yasha kayan kamshi. Still Koda na gama na jera komai banga yaya ba. Zama nayi ina kallo, daga 3 seater sai 1 seater sai kuma kasa na rinka bi. Har wajen uku da rabi bai dawo ba, haka na koma upstairs na cigaba da zama a wajen. An kira sallah na tashi nayi tareda nafilfilo, as usual daidaituwan tsakanin mu na roke Allah. Nifa a duniya Ban iya zama ba’a min magana ba yasa duk kamanni na ya canza. Kimono ɗin duk ya isheni sai nace bari na cire sai nayi maza naje na ɗebo ma kaina abinci. Wayana yana hannuna ina tafe ina sana’ata na shan waka. Wakar su Taylor Swift da Zayn Malik Mai suna ‘I don’t wanna live forever’ na saka akan repeat. Shikuma Naufal bai bar dakalin gate ba saida aka kira sallah, masallaci yaje daga nan ya koma gida. Duk baya jin dadin jikinsa, a hankali yake tafiya sanya sanya kamar Fadeela. Yana isa falo yayi sallama ciki ciki saikana kusa zaka ji, karar wakar yaji saiya mayar da hankalin sa wajen dinning area inda yaga Fadeela. Tana bin wakar ta a hankali tareda ɗiban abinci kana gani bata san yana wajen ba. Kafa mata ido yayi sosai babu kiftawa, “Every disappointment is a blessing in disguise” a yau yasan ma’anar abinda babba ya hango yaro koya hau Kufena bazai gani ba. Yau ya gode ma iyayensa da basu bari wawancin sa ya kai shi ga losing ɗinta. Kuma ya godema iyayen Fadeela dasuka kara bashi second chance ba’a wuce da ita ba. Tana bin wakar dai dai wani baiti saita kara murya, “I'm sittin' eyes wide open and I got one thing stuck in my mind. Wondering if I dodged a bullet or just lost the love of my life Baby, baby, I feel crazy Up all night, all night and every day I gave you something, but you gave me nothing What is happening to me?” Haka ta rinka bin wakar shi kuma kawai kallon ta yakeyi bcs kara shigan masa rai takeyi by the minute. An kai wani baiti shima ta fara yi wannan Karon kamar performance takeyi bcs harda motsa hannunta. Gashi muryanta shigan masa rai yakeyi. “I just wanna keep callin' your name Until you come back home I just wanna keep callin' your name Until you come back home I just wanna keep callin' your name Until you come back home” Wani zuciya yace masa waye take jira? ya dawo kamar wakar da gayya takeyi. Kawai ya yanke shawara yaje yayi mata magana koma mai zai faru shikenan. Karar tafiyar shi taji, bazata ce bataji daɗin ganinsa ba but gaskiya bataso ya ganta cikin kayanta ba, kunyar sa takeyi tunda ta lura ya fiye kallo. Da sauri ta bar diban abinci zata bar wurin, kasa magana tayi zata ratsa ta wuce sai kawai yasha gabanta. Bata ɗago ta kalleshi ba bcs bazata iya ba. Kara kokarin ratsawa tayi ta wani ɓangaren shima ya tareta. A hankali ta soma magana kamar zatayi kuka bcs duk ta birkice, “Yaya please bari na kai abincin ɗaki saina dawo na saka maka naka” Shiru yayi baice komai ba, kawai a ranshi yake ayyana shikenan ta gama tsanar sa saboda ko kallonsa ta kasa yi. “Kin tsane ni koh?” ya faɗa cikin raɗa. Da sauri ta dago ta kalleshi ashe shima kallonta yakeyi, suna haɗa ido saita sauke nata. “Bazaki amsani ba? Nace kin tsane ni koh?” Daga kai tayi masa alamar ta ‘ah ah’ “Toh idan baki tsane niba menene? Bakiga text ɗina bane?” Daga ido tayi suka kara hadawa saita sauke, gashi abinci yana hannunta yana kona ta. “Yaya bari naje ɗaki na dawo?” “Au yanzu ma bazaki iya cin abinci tareda niba sai a daki koh?” “wlh ba haka bane, Hijab ɗina zan dauko” Wani kallo ya watsa mata tareda janyo hannunta zuwa dinning, kamar yadda ta saba mashi ta janyo mashi kujera haka shima yayi mata. Abincin dake hannunta ya amsa ya ajiye saiya dauko cokali. Mamaki kawai takeyi amma bata ce komai ba, kawai kallon gefe takeyi tana wasa da yatsan ta. Kana ganin yanayinta kasan she is intimidated by him. Shi kuma daɗi yakeji yanda ta natsu ta kasa sakat, abinci ya deba zai bata a baki, “Na lura bakya shiri da abinci, fisabilillahi ji wanda kika diba!” Kallonsa tayi yana kokarin bata a baki saita kauda fuskarta tana kokarin magana a shagwabance, “Yaya Please da zafi kalle yanda yake tiriri” “Shhhhh, bana san surutu” Haka dan dole tayi shiru ya rinka bata, ita kuma sai zuba mashi shagwaba takeyi wai yana cika cokali. Dariya take basa sosai saboda yanda take abinta, Komai cikin sanya sanya. A yau yaga fa’idan sanya sanya ba garaje ba. Bayan ya gama bata dukda ba sosai taci ba shima ya ninke hannu saita bashi. Kunya sosai ya kamata bcs Naufal ya sauya sosai kamar bashi ba. K’ememe yayi wai bazai iya ci da kanshi ba. Dole ta rinka bashi yana ci kamar zai tauna harda hannunta, shagwaba sosai ya rinka zuba mata kamar yaro karami, ko abinci ya taɓa masa gefen fuska zai tabe baki wai sai an goge masa. Dariya ya rinka bata ita kuma tayita yi, NI kuma DIMPLΣS bakina kamar gonar auduga saboda taya Fadeela murna akan ta samu other half ɗinta. #NiDaDiyata *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨ ✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 22 ✨✨✨ Yahya related to me from Malik from Sumayy, the mawla of Abu Bakr ibn Abd ar-Rahman, from Abu Hurayra that the Messenger of Allah, may Allah bless him and grant him peace, said, "If people knew what was in the adhan and the first row of the prayer and could only draw lots for it, they would draw lots. And if they knew what was in doing dhuhr early, they would race each other to it. And if they knew what was in Isha and subh they will go to them even if they had to crawl” ********** Cyprus Tsuru tsuru yayi ya rasa meke masa dadi, baice komai illa kallon kasa cikin nadama. Tunanin shi bai wuce yanda suka san inda yake ba bcs yayi covering tracks ɗinshi daidai gwargwado. “Da Kai nakeyi, abinda kayi ka kyauta kenan?” IG ya faɗa. Daga Idonshi yayi suka haɗa da mahaifinsa amma saiya mayar kasa bcs kunyar kansa yakeyi. “Nifa bawai nazo nace maka ka bini bane, kawai nazo naga lafianka ne. Tunda dai bakasan ka zauna damu, saboda mahaifiyarka ta samu natsuwa akan ba saceka akayi ba kuma ba mutuwa kayi ba.” Yana kaiwa nan saiya juya ya tafi. Da sauri Khattab yaje gaban Daddyn sa yana rok’on sa hannu biyu, IG ko kallonsa baiyi ba ya ture shi tareda cigaba da tafiya. “Dan Allah Daddy kayi hakuri, wallahi k’uruciya ne. Please karka kyale ni.... Im really sorry” Sekeke IG ya kalli Khattab tareda kwafa, “Kuruciya koh? Ka raina kanka bani ba. Wannan tozarci dame yayi kama? Wai ace dan ɓata suna shi ne kayi gaba abinka saboda ka tozarta ni akan ban isa ba” “Kaga duk bincike ɗinnan danakeyi Bawai saboda kai nayi ba, kaji ni da kyau saboda Matata nakeyi bcs dukta birkice kullum kuka. Mutane suka zauna babu yara balle ni don kace ka gaji dani” IG yake magana muryanshi zallan ɓacin rai ke tashi, shi kuma Khattab yana ɗuk’e a kasa yana kuka tareda rike masa k’afa. Haka yayita rok’on sa Shi kuma IG yayita sababi yana mita, don kansa yayi shiru saboda Khattab yayi alkawarin binsa gida. IG a gidan Khattab suka yada zango shida Boys ɗinsa, shi ya kwana a ɗakin Khattab while boys ɗinsa su biyu tareda Khattab suka kwana a falo. Next day around 10am....... Khattab ne a airport tareda mahaifinsa tareda escorts suna jiran lokacin tashin su saboda shi IG baya san garin at all. Saidai Khattab ya kasa sukuni,tun jiya bai rutsa ba, tunani ɗaya ya sark’e masa zuciya. Gashi kuma Daddy dinsa bai sake masa fuska ba balle ya tambaye shi anything about her. Kawai shiru yayi zuciyar sa yana masa kuna, fatan shi ɗaya ace tana sanshi har yanzu kamar yadda yake son ta. Amma cikas ɗinshi ɗaya yayanta amma zai nema yanda zaiyi maganinshi. Haka yaketa tunani harya shiga jirgi suka ɗaga zuwa gida. Jirgin su ya sauka a Murtala Muhammad Airport dake Lagos. Daga nan wani jirgin suka shiga direct sai Bauchin Yakubu. Suna fitowa daga jirgi motoci na tarbasu yana jiransu kuma harda Lili. Tana ganin shi ta ruga da gudu tareda shigewa cikin jikinsa, babu kunyar idanu balle tsoron Allah. “Yaya Khattab I miss you so much, please don’t ever leave me again” ta faɗa tana wani k’ank’ameshi. A hankali ya zame jikinsa tareda shiga mota ya barta a wajen. Bata ko damuba illa binsa cikin motar, dayaga ta shiga ɓangaren baya inda yake wani haushi ya kamashi yana dana sanin abinda yasa bai shiga gaba ba. Kara hawa kan kafadarsa tayi ta kwanta, harda bazai kulata ba sai kuma wani zuciya ya raya masa gwara ya kwaɓeta. “Ke! Wai Meye haka? Baki lura tafiya nayi ba kuma duk na gaji”ya faɗa a hasalce. A hankali ta ɗago tana shagwaba kamar zatayi kuka “Haba yaya nayi missn ɗinka ne, baka san irin kukan danayi sanadiyar rashin ka ba” Sai kuma ta fara matse karamin kwalla ta cigabada magana “Yaya ni na gaji Wallahi, kawai gwara ayi mana aure haka kowa ma huta” Wani haushine ya turnuke shi, gyara zama yayi tareda ingijeta. “Ashe bakida hankali! Na dawo ko hutawa banyi ba, ko gida bankai ba kin kawo min shirme” kwafa yayi ya soma kallon window “Yaya Maganar auren mu ne shirme? Ka daina so na ne?” ta watso mashi tambaya. Juyawa yayi ya kalleta saiya watsar, bashida locacinta balle na cha chan baki da ita. Sun isa cikin gidansu mutane cike sunzo ganin shi kuma duk yan uwa da abokan arziki ne, duk inda ya ratsa abu ɗaya suke tseguntawa. “Laaa ga Khattab, ya canza kamar bashi ba” Baiko kula suba ya wuce falon Mommy ɗinsa, zaune take kuma gefenta Maman Lili ne. Har kasa ya duka ya gaishe su, Mommy muryanta duk kuka ta amsa, ita kuma Maman Lili kallon rainin arziki tayi ta watsar tareda amsawa à wulakance. Inda sabo yaci ace ya saba da halinta bcs halinta Lili tayi biyo na empty vessel kyau babu hali. Rike hannun mahaifiyarsa yayi yana murzawa a hankali, magana ya somayi cikin natsuwa. “Mommy ki yafe min, nasan cewa na sakaki cikin zulumi da fargaba” Bata amsa shiba illa kukanta a hankali, haka ya rinka mata magana sai daga baya ta ɗago tayi murmushi tareda cewa, “Allah ya yafe mana baki daya” Zuwa yayi sai yayi patting bayanta sannan yace, “bari naje na kimtsa” ko kallon Maman Lili baiyi ba ya wuce abinsa dama basa shiri. Yana shiga ɗaki sai yaga Lili kwance tana jiransa, a fusace yace, “Ke Meye haka? Oya oya zo ki fita kafin raina ya baci” “Ni ban san me nayi maka ba duk ka tsaneni” saita fashe da kuka. Indawani ya yi kukan zaiyi wani iri amma yanzu kamar tana busa sarewa a kunnen bebe ne. Zuwa yayi wajen data ke ya finciketa kamar yar tsana har waje sannan ya banko kofar ɗakinsa. “Damn!” ya faɗa tareda daura hannu akan waist yana tunanin irin rashin kamun kai nata. Ita kuma as expected ta tsaya tana buga kofar tareda watsa kalamai na rashin kunya. Mommy ne tazo ta taka mata birki tareda Faɗi, “Meye haka kikeyi kamar wanda zamu kai turu? Gwara ki natsu kisan me kikeyi, shifa namiji yana son space ɗinshi baya son takura. Idan yace ki tafi ai saiki tafi tunda ba’a ma mutum dole. Ace ko 12hrs da dawowa baiyi ba kin soma tada mashi hankali. Nifa kada kisa yarona ya kara gudu” Tana kaiwa nan saita bar Lili à wajen à ruɗe, shi kuma yana daga ɗaki yana jin su. “Woooow! Allah ya barmin ke Mommy” ya faɗa saiya shiga bayi. ******* Bayan 3 days.... Haka rayuwa ya cigaba da kasance ma Naufal da Fadeela cikin tsantsar so da kulawa. Koda yaushe ana tare ana hira, girki ko cin abinci. Sam Sam yaki zuwa aiki yabarma Aminu komai, abu ɗaya ke fitar dashi daga cikin gidan watau sallah. Sai kuma sau ɗaya dayaje stores domin ya siyo masu kayan abinci da ba’a rasa ba. Tun jiya Aminu ke kiran Naufal akan ana bukatarsa cikin office bcs su Mr Sutter sunyi zuwan bazata. Ranshi yayi mumunan baci bcs baya son abinda zai nisance shida da ita. Tun da daddare yaketa mita, “Haba banda bakin ciki karara wannan dame yayi kama? Shikenan ba’a bari mutum ya zauna da matarsa lafiya” Fadeela na daga kwance tana murmushin k’eta, sai kawai ya ganta. Daga gira yayi kafin yace, “Au you will not sympathise with me shine kike min dariya koh” “No Other half ba haka baneba, I want to be with you but kasan cewa nima zani school” Saita mike daga kwance tana kokarin tashi, “Bari naje na haɗa mana breakfast kafin ka makara” Harta kai wajen kofa saita ji muryanshi “A me zaki” “A me na saba zuwa? Motar haya mana” ta amsa bata ko juya ba. Shiru yayi yana jin haushin kanshi akan duk abubuwan dayayi mata, bcs ya kaskantar da ita ba kadan ba. Dadin abin bata dauki duniya da zafi ba. Ita kuma taje kitchen ta fara fere masu doya zatayi yam balls, tagama ta daura akan gas kenan sai kawai taji ya riketa ta baya. Bata ce komai ba shima haka kawai shiru sukayi for some minutes. Itace tayi masa magana cikin raɗa “Other half” Bai amsata ba illa kara kamkameta kamar wani zai kwace mashi ita. “Other half please kasan zamu fita yau koh?” “Na sani mana” Daga nan saiya saketa. “Okay wat can I help you wit?” ya tambayeta Murmushi tayi tareda jan masa kumatu cikin wasa saita ce, “Dont worry dear, na hutarshe ka” Lagwaɓe kai yayi waishi bai yarda ba, da sauri ta rike masa hannu sannan ta matsa dab dashi har suna shakar numfashin juna. “Bana son ka wahala ne, but If you insist dauko min sardine a cikin shelf. Daga nan saika fasa min kwai” Ita kuma ta dauko kayan miya tayi jajjage saboda yafi tunda babu ruwa ko kadan. Haka suka rinka abinsu gwanin ban sha’awa. Koda doyan ya nuna tare sukayi mulmula. Dama tun yau yake mata salon shagwaba kala kala, indai wannan ne ta saba da halinshi dis past few days Kuma yana burgeta ainun. Latte ta haɗa mashi ita kuma ta haɗa ma kanta cappuccino. Zaune take akan kujera dab dashi tana bashi. Yaci sosai a matsayinshi na ma’abocin doya. Daga nan daki sukaje ya shiga wanka ita tana wajen drawer ɗinshi zata ciro masa kaya. Blue suit ta dauko mashi tareda grey tie da kuma farin riga. Bayan ya gama shiri ita tayi mashi knotting tie, to his surprise ta kuma iya sosai. Ta lura yana mamaki saita ce, “nike ma Daddy knotting idan zai fita” Daga gira yayi alaman ya gane, ita ta rike masa jakarsa sannan tana makale dashi har suka kai kofar falo, bata rakashi mota ba saboda kayan jikinta bai kyautu maigadi ya ganta. Yatsunta biyu ta saka akan bakinta sannan ta daura akan nasa. Da sauri ta koma cikin gida tana dariya bcs tasan me tayi. Shikuma cikin dariya yace “Zanyi maganin ki ai” Saiya juya ya tafi, yana cikin tafiya yaji maganar ta, “eh din” juyawa yayi sai ya ganta a window tana murguɗa masa baki. Dariya yayi yana nuna mata yatsa saiya tafi bcs idan ya biye mata babu inda za shi. Ita kuma ɗakinsa taje zata gyara, rigan daya cire ta dauka ta rungume, ji takeyi kamar shine ke wajen. Kawai ta rufe idonta tana shakar kamshin. Tunawa tayi zata fita saita tashi da sauri ta gama aikinta, har lunch saida tayi kafin ta bar gidan. Ta rufe kofa tareda faɗin “Bismillaahi, tawakkaltu 'alallaahi, wa laa hawla wa laa quwwata ‘ illaa billaah.” tafe tana nishaɗi bcs she is in her perfect neighborhood, with her perfect husband, tanayin rayuwar data ke sha’awa.... Wat could possibly go wrong? #NiDaDiyata      *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 23 ✨✨✨ Abu Hurariah said; 'The Messenger of Allah said 'When it is Ramadan, the gates of Paradise are opened, the gates of Hell are closed, and the devils are chained up."' It was narrated by Ibn Ishaq from Az-Zuhri. (Sahih) ******* Bayan wata haɗu....   Rayuwar Naufal da Fadeela ya kasance rayuwa ne mai ban sha’awa, kowane ma’auraci idan ya gansu saiya ji sun burgeshi. Yanzu Fadeela takanje gidansu kuma Mommy na yabawa da yanayinta, kosu Anty Saudah sunji daɗin yanda suka daidaita kansu. Gashi tayi bala’in murmurewa kuma tayi armashi, ko fatar jikinta abin kallone, ta kile abinta kuma dukwanda ya ganta will wish he was her and guys zasuyi wishing matarsu ne. Daga kowane ɓangaren shi masu da albarka akeyi tareda fatan masu akan su samu zuri’a ɗayyiba. Dama Fadeela ma’abociyar san yara ne, duk inda ta haɗu da yaro saita murmusa masa. Ko yaran Jawahir ana kawo mata daga safe har yamma. Yanzu burinta ɗaya ta samu nata na kanta, wata huɗu da shiryawa da Naufal amma har yanzu babu labarin ciki. Tun suna wata ɗaya ta kwallafa ranta akan batada juna biyu,dariya Naufal yakeyi sosai wata sa in har yana shakewa idan yaga tana mita akan abin. Kullum tana cikin zulumi da fargaba bcs sau da dama wasu suna aure suke daukar ciki kamar yana jiransu bcs ko Jawahir abinda ya faru da ita ne amma banda Deela. Da Naufal ya gaji da mitan ta gashi kuma wata hadu, suna kwance wajen sha ɗayan dare saita soma magana a hankali, “Other half” “Uhmm” ya amsa mata saboda barci ya soma daukar sa. Jijigashi ta farayi tana magana cikin shagwaba, “nika tashi Wallahi magana zamuyi” A hankali ya buɗe emerald eyes ɗinshi ya sauke akanta yana mata wani kallo cike da so da kauna. Cizan leɓansa yayi wanda ya soma bushewa. Thou yasan labarin Gizo bai wuce na Koki ba. “Baka ganin ya kamata muje asibiti kila something is wrong” Murmushi yayi wanda ya bayyana masa hakorarsa, gyara kwanciya yayi saiya jawota jikinsa sosai. “Talk to me Baby, what’s ur problem?” Shiru tayi batace komai ba tana wasa da yatsunta, “Duk kin dame kanki akan rashin haihuwa Wen I’m not even complaining. Bakya Jin daɗin zama dani ne?” Da sauri ta ɗago ta kalleshi tana girgiza kai kamar zata yi kuka, “Ba abinda nike nufi ba kenan, kawai ina jin akwai wani matsala ne a raina” Kallonta yakeyi yana tunanin irin wannan san yara data keyi, amma dole yayi reasoning da ita bcs halitta ne saboda haka take. Tallabo mata gemu yayi sai yace, “Okay Baby, menene? Wat do you want?” “Asibiti zamu” “Asibiti dai zaki bcs ni babu inda zani” “Okay fine, Nagode sosai. You’re the best husband anyone can have” Daga nan suka soma hira thou Deela keyi, sai surutu kawai takeyi kamar ta haɗiye radio. Tana bashi labarin project supervisor ɗinta da rashin mutuncin dayake ma wasu but baya mata probably bcs tanada aure. Shi banda “uhm” sai “uhm uhm” yake amsawa kuma Idonshi a rufe bcs duk ya gaji saboda sunje wani construction site ne. Daga baya ya daina amsawa kawai sai numfashi taji kaɗan kaɗan alamun yana barci. Dariya tayi saita gyara mashi pillow sannan saita rufeshi dakyau da Duvet, itama ta kishingiɗa da kyau ta kwanta. The next day..... Zaune suke a motar Naufal zasu asibiti thou shi rakata zaiyi amma bazai shiga ba. Babu magiyan da batayi masa ba amma yayi kememe, “Sorry Baby, kinsan zan iya ciro zuciya na in baki but I can’t grant you this wish” Dole ta hakura ta kyaleshi tunda yace baya so kafin yazama masu jidali. Ta shiga ciki tabi duk wani protocol daya kamata saura ganin Doctor, an kaita wajen Dr Hadiza Pate akan ta dubata. Tana zaune cikin wani katafaren office na Doctor ɗin saboda tana wajen wani patients daya bukace attention ɗinta. Sallama Doctor ɗin tayi tareda shiga ciki. A hankali Deela ta juyo ta kalli Doctor ɗin, Mace kyakyawa mai kyan halitta. Bayan sunyi gaisuwan mutunci sai Deela ta bayyana ma Doctor komai. Dariya Doctor tayi tareda gyara zaman tabaran ta. “kiyi hakuri mana wasa suna kai shekara da shekaru kafin suzo test” Deela batace komai illa jiran doctor ta gama surutan ta sannan ta fara duba ta. Murmushi tayi saita tashi ta fara dubata cikin kwarewa kuma tana mata tambayoyi. Anan ta gane cewa Fadeela nada matsalar daukan ciki bcs tanada excessive menstrual pains. Nan take Fadeela ta ruɗe, Haba tasan a rina wai an sace zanin mahaukaciya. Nan take ta ruɗe tareda barkewa da kuka, wayanta ta dauka ta kira Naufal amma bai dauka ba. Wani tashin hankalin ta shiga. Doctor tayita bata hakuri sannan tayi mata prescribing drugs kuma aka sakata a 3 months observation. Daga ɗayan ɓangaren kuwa, ko sau ɗaya Khattab bai nema Miemie ba. Mahaifinsa ya samo masa aikine a wani ICT company inda yake aiki babu kama hannu yaro. Bawai ya mance da Miemie bane, kawai baya so yaje ya tada mata hankali ne bcs yaji irin ciwon datayi akan rashinsa kuma yanzu ta samu sauki sosai. Sau dama  yana zuwa ta wajen School dinta amma nesa sosai. Ya lura da yadda tayi kyau sosai gashi ta zama budurwa. Gashi yaga tana walwala sosai, kawai tsoron kada yanzu ta daina sansa bcs It’s really a long time. Ita kuma Miemie tana al’amuranta kamar every normal teenage girl. Sauki yazo mata sosai har ana tunanin kaita makaranta masu lafia. Gameda Soyayyar ta da Khattab kuwa, yananan dirshan babu inda yaje. Akwai wani rana haka dataga kamar shi a gefen School dinsu but dayake tasan baya gari bata saka Mind dinta ba. Kawai ta mayar da abin maybe ciwonta yake so ya tashi. Ita dai kullum idan tayi sallah rok’on Allah takeyi ya bayyana mata shi duk inda yake, idan kuma akwai alheri tsakanin Su Allah ya tabbata idan kuma babu Allah ya cire mata shi daga ranta. Ita kuma Lili banda jaraba babu abinda ta saka a gaba, yanda takeyi wani idan ya ganta zai zata mijinta ne. Kullum matsala daban take complain about. Kuma it’s mostly about girkinta da baya ci, tun yana mata kara tareda bata flimsy excuse har saida takai shi bango ya sauke mata komai. Still bata hakura ba, kullum saita girka masa kwamachala wai kuma saiya ci. Wata sa’in har office take kai masa don rashin hankali. Itafa irin matan nanne da basuda kintsi at all. Zata iyama saurayi komai, acewarta tunda zata aureka gwara ta fara sabawa da maka ɗawainiya tun kafin ta shiga. Kuma gashi bata iya komai sai rawar kai, daka bari tayi maka abu gwara kayi da kanka bcs it’s useles. Ko wanke wanke tayi saika sake, balle shara kamar ta karo kurane a wajen. Kuma kamar ta saka ma dakin Khattab ido, kullum sai taje ta tada mashi kura ta fice. Idan tanayi ko kallonta bayayi saidai yayi dariya a ranshi tareda faɗin, “Iska na wahalar da me kayan kara” Tashi yayi ya tsala wanka tareda fesa kwalliya kamar sabon ango. Yau ya dau ma kansa alwashin komai zai faru saidai ya faru. Yana tafe yana addu’a saboda baisan me zai biyu baya ba, daidai Office ɗin Naufal ya faka. Ya fito yana zulumi wani zuciya yana cemasa ya koma bcs he is not ready amma ya dake ya cigaba da tafiya. Sanda ya kai Naufal yana conference hall amma aka umurceshi daya jira shi. Haka ya zauna duk fargaba yanata addu’a. Cikin ikon Allah ya jira for less than an hour saiga Naufal yazo. Kallon kallo sukayi ma juna kowa da abinda ke ransa. A hankali Naufal yayi magana, “Me kake yi anan?” Da sauri Khattab ya tashi tsaye sai yaje wajen Naufal ya rike masa riga, “Please ka bari mu fahimci juna” “Mallam Meye haka? Sake ni mana” Naufal ya faɗa a hasalce kuma fuskarshi babu wasa. “Dan Allah kayi hakuri ni bazan taɓa cutar Miemie ba, idan na cuceta kamar kaina nayi mawa bcs ita ce rayuwata” “Cuta na nawa kuma? Ka saka ma yarinya Soyayyar ka sai kuma ta tafi ka barta you were no where to be found dukda kasan condition ɗinta” Kallon mamaki Khattab yayi ma Naufal,ji yanda ya juya abin kamar bashi ya kore shi ba, kawai yanzu ba locacin daura ma wani laifi bane. “Eh naji na dauki laifi kawai amincewarka nake nema” Shiru Naufal yayi kafin ya kalle Khattab cikin ido irin man to man yana nuni da hannunsa. “Okay na yarda, but idan kayi wani abu na cutarwa akanta babu mai rabani da kai sai Allah” tun kafin ya karasa ya rungume sa yana murna. Da sauri Naufal ya turesa sannan ya haɗe girar sama dana kasa, “Nace maka bana san ana rike ni koh!” Sannu a hankali Naufal da Khattab suka tafi gidan gona, dukansu zulumi sukeyi bcs basu san yanda zatayi reacting ba. Sanda suka isa falon babu kowa a ciki, Naufal ya shiga dakinta amma bai ganta ba. Sai ya wuce ɗakin Anty Saudah, kwance ya ganta tayi daidai tana kallon ceiling. “Ke saka Hijab ki biyoni falo” Yanda ya umurceta tayi, tana shiga cikin ciki sai tayi ido da Khattab wanda shi bai ganta ba bcs ya rufa ido kuma yayi Zurfi cikin tunani. Ihu kawai ta kwala tareda rike kanta. “Yaya Khattab ka cuce ni, meyasa ka tafi ka barni” abinda taketa nanatawa kenan. Da sauri Khattab yaje wajenta, “Haskena I’m really sorry. Gani na dawo kuma in shaAllah bazan sake tafiya ba. Please control yourself” Hawaye ta rinka yi hannunta yana dafe da kanta, “Please control urself” yayita nanatawa. A hankali ta rage sautin kukanta saita sake kanta, hannu tasa tana Share hawayenta. “ Ina so kayi min alkawarin bazaka sake guduna ba” Murmushi yayi tareda cizon leɓensa, “Ni Da Ke mutuwa zata rabamu in sha Allah” Shiru sukayi babu wanda yace komai, shine yace “okay Haskena smile for me Ko zan samu sauki cikin raina” Nan ta somayi saiga Naufal ya fito, “Oya zo ka tafi ya isa haka, remember yarinya ce so akwai abubuwa da dama da bazan lamunta ba. Misali zance ko taɗi.... Koma me ake kiran abun, banaso kuma baza ayi ba.” “kawai zaka shigo  har falo ne ku gaisa sannan ka kara gaba” Murmushi Khattab yayi sannan yace shima nagode sosai Allah ya saka da alheri. Daga nan sukayi sallama da Miemie duk suka bar gidan, Khattab na murnar samun Haskensa sannan Naufal na ɗokin zuwa wajen nasa Hasken tauraruwan mata. #NiDaDiyata *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 24 ✨✨✨ Narrated Abu Hurairah reported the Prophet (pbuh) as saying "Women may be married for four reasons, for her property, her ranks, her beauty and her religiosity. So get the one who is religious and prosper (lit. may your hands cleave to the dust)." ********** Haka rayuwar Khattab da Miemie ya kasance, kusan kullum sai yazo yaga Miemie amma a falon su. Idan ta shiga motarsa to Naufal ne da kansa ya kira shi akan ya taimaka masa wajen daukanta daga School bcs bazai samu time ba. A duniya Khattab yana san irin wannan locacin bcs yana samun daman zance sosai, ya kan biya da ita wajen su Vanilla joints haka da sauran su, ya siyo mata su shawarma da sauran kayan lashe lashe. Shake da Leda take komawa gida idan yazo. Tsalla soyayya sukeyi mai tsafta, saidai shi kullum zulumin ya zaiyi da maganar auren shi da Lili yakeyi. Bcs an riga an kai baikonsu tun kafin ya gudu. Yanzu abinta sai girma yakeyi bcs yanzu kayan aure take siya, bata da aiki sai Online shopping gashi kuma ta shiga whatsapp groups na business ɗin kayan aure bila adadin. Haka take saving hoto ta ajiye mashi idan ya dawo saita rinka nuna masa. “Yaya wannan colour ɗin yayi? Wanne yafi tsakanin wa’annan” haka take damunsa da tambayoyi. “kiyi abinda kike so” abinda yake amsa mata dashi kenan kuma bazai kara ce mata kala ba. Wata rana tayi zuciya ta tafi wata rana kuma ta zauna tayita tambaryasa a haka dukda baya amsawa. Shikuma abinda yasa baya amsawa bcs bashi zai zauna da ita ba saidai ya sake guduwa, kuma koda ta aureshi saidai gangar jikinsa amma ba ruhinsa ba yasa gudun ba’a cigaba ba gwara ba’a soma ba. On the other hand Lili kallonsa kawai takeyi, ana nan ana mata haɗin mata gangariya yar Maiduguri. Duk abinda Khattab ke mata tana ankare dashi, auren nan dole ayishi koda yana suma ne, jira kawai takeyi ya santa a matsayin ‘ya mace sannan maganin ta yana aiki. Idan yayi mata wani abu dariya takeyi a ranta saita ce, “zaka shigo hannu ne, bakasan halina bane” Ni kuma Dimples nace hali na Wanne kuma? ******* Fadeela tana shan maganinta daidai yanda akayi mata prescribing, gashi idan ta fara shagwaɓan ta na fama tana kuka, Naufal yana gefenta yana petting ɗinta. At all Baya San yaga hawayenta, duk randa taje school taga yaran samɗa saita mashi jidali, gashi Hadiza matar sadeeq haihuwa yau ko gobe. Shiyana tunanin hanata zuwa makaranta bcs zuwanta baya kara masa komai sai tashin hankali. Sannu a hankali harta kai 2 months tana shan magani. Kawai saita tsira shan fanta mai kankara, Itafa ba ma’abociyar shan abin bane, tafi san Coke but kawai saita fara marmarin shan Fanta kuma shima fanta ɗin saiya fara kankara ko alamar haka. Wata rana idan zata dawo daga School take siyo abinta, wata rana kuma Other half ɗinta zai siyan mata. Haka tayi stuffing ɗinsu a cikin fridge abinta, daganan sai kwaɗayin ya girma. Daga fanta ta kara da agwaluma da gasharshen masara, Naufal tun baya complain har ya soma yi bcs shike siyowa saboda ta daina zuwa makaranta bcs sunyi exams, rana daya ko biyu take zuwa wajen supervisor dinta. Abin ya fara damunsa sosai, bata da lalaci bcs tana duk wani aiki daya kamata mata but saidai ta sauya masu yanayin girkinsu. Kwata kwata bata san warin stew so batayi. Saidai kullum sai sunci tuwo miyan kuka bcs shine yanzu best food ɗinta. Gashi tayi dundumemiya abaya kawai ke shigan ta sai kuma kimono tunda duk kayanta fitted ne. Ita dai kawai ta lura tayi ɓatan wata ne amma bata gaya ma kowa ba har Naufal. Wata rana taje school suna zaune a garden chairs dasu samɗa da Mansura, kallonta sukeyi cikin tuhuma. Bata ko kallesu ba bcs kananan tsegumi ne bata so. Saiga mai masara dafaffe tazo wucewa. “mai masara! Kawo mana, ina tsammani akwai canji cikin jakana” Fadeela ta faɗa tana duba jakarta. Samɗa ne ta jungure Mansura tana mata kyas da ido alaman su kalle Deela. “Gulma ajali !” Fadeela ta faɗa bata kallesu ba. Mansura ta gyara zama saita dafata sannan tace, “Baki lura kin fiye kiba bane halan? Gashi sai cin tsiya. Idan bakiyi hankali ba sai Naufal ya sake aure” Dariya Fadeela tayi sosai kafin ta ce, “ wai wani Naufal ɗin? Badai nawa ba bcs baki lura yanda muke soyayya bane” “Mun lura mana gashi ya bayyana a jikin ki” Samɗa ta chapke. Sekeke  Fadeela ta kallesu sannan ta juya kai. Da sauri Mansura ta zaga ta duka gabanta, “Bakya jin wani motsi a cikin ki?”   “Banaji Rabu dani” “Amma kina amai da ganin jiri?”   “ka nace maki babu abinda ke damuna, ah ahn kyaleni mana” “Mansura tace lafianta lau ki kyaleta mana” Samɗa ta faɗa. “Malama babu ruwanki, kana ganin Fadeela kasan akwai wani abu cikin jikinta, ga shegen kwaɗayi yanzu bata wuce tayi kwata kwata” Shiru Fadeela tayi for some minutes Sai ta soma magana kasa kasa “Nima abin ya fara isana, gashi rabon danaga period dina tun kafin na fara shan magani” “Oya bani kudina” Mansura ta faɗa ma Samɗa tareda mika mata hannu. Sai kawai Samɗa ta zuge cikin jakarta ta fito da 500 naira guda 4 ta bama Mansura. Itadai Deela bata gane me sukeyi ba, sai bayan sun natsa Mansura ta soma magana, “Dama nace ma Samɗa ciki gareki shine tace wai baki gaman shan maganin kiba. Kawai wai kiba ne bcs kinajin daɗin aure” “Shine nace idan cikine zata bani dubu biyu idan kuma ba shi bane zan bata dubu biyar” Dariya suka kwashe dashi su duka suna shewa harda shan hannu, “Kunada kudin banza shine bazaku bani na kara na cin masara ba da fanta” Deela tace. “Karki damu muje na siyo maki da kuɗin nan” Mansura tace. “Amma fah kina wuta ” Samɗa ta faɗa tareda zungurinta. “Toh dafa! Nina wasa ne” Deela ta faɗa tana ɗaga kafaɗa. Haka suka gama hirar suka tashi kowa ya kama hanyar gidansu, yau Deela tayi alkawarin fada ma Other half ɗinta good news. Gyara gidanta tayi tas ta bishi da turaren wuta dasu room freshener. Rissotto ta kirka wanda yasha Ugwu da albasa mai lawashi. Sai tayi ginger drink mai garlic a ciki. Tayi setting table gwanin ban sha’awa bcs wasu sabbin coolers peach ta dauko yau. Upstairs ta wuce domin tayi wanka saboda tasan zashi gidansu kafin ya dawo. Ta lura tunda Miemie tayi saurayi bashida katabus kullum saiya je shi a dole yaya babba. Leggings ta saka baki sai crop top wanda bayan duk an yanka, jiran sa takeyi à falo dukta kagu ta faɗa masa sun kusan zama parents. 8:15pm..... Locacin na ya dawo daga gidansu, sallama yayi sai ya ganta kwance akan couch tana jiransa. Ga kuma kamshin abinci da turare ta Ko’ina. Murmushi suke sakar ma juna harya isa wajenta. Shafa mata kai yayi yana kashe mata ido. A hankali yace “How is my baby dis evening?” “we are fine” Kallonta yayi bai gane ba, “Me kike nufi da ‘We’?” Dariya tayi saita daura hannunsa akan cikinta tana murmushi, nan take ya ɗago abinda take nufi. Da sauri ya rungume ta don murna. Ita kuma sai dariya takeyi. A hankali ya soma magana, “koba komai na huta da kukan dare” Dukan wasa  takai masa sai ta ce, “Dawa kake yi?” “Nifa bance dake nakeyi ba Malama” “Gwara dai” saita kara makale shi. Daga nan kuma ta raka shi yayi wanka tareda shiryawa kana sukaje wajen cin abinci. Yaji daɗi sosai daba tuwo miyan kuka bane bcs ya tsane abincin amma bazai iya magana ba. Yanzu yasan ba laifin ta bane, cikin ne yake mata haka. Saidai fatanshi Allah ya rabasu lafia kawai kowa ma ya huta. 3 days later... Wajen karfe goma na safe ya shirya zashi office, panke tayi mashi wanda yasha ayaba. Saita yi masu oats suka haɗa dashi saida bata saka madara a nata ba. Sun gamaci saita rike mashi brief case ɗinshi sannan hular sa duk yana hannunta. As usual kofa ta tsaya saboda kayan jikinta. A hankali ta daura masa hulan a kanshi saita kara gyara masa button ɗin dabai gama makala wa ba. Ta juyo zata koma saiya jawota ya kaima bakinta kiss, da sauri tayi kokarin tureshi amma yafi karfinta, don kanshi ya kyaleta yana ɗaga mata gira. “Idan Kinsan bazaki min proper bankwana ba ki daina raka ni” Dariya tayi kafin tace, “NI banason mai gadi ya ganni Wallahi” juyawa yayi ya kalle inda maigadi yake amma baya wajen, “Kwantar da hankalinki duba baima wajen” “Okay” tace saita kara jawoshi sannan ta manna mashi wani, ya shagala  kenan ta sake shi sannan ta rufe kofa karab. Dariyar ta kawai yakeji bcs tasan ta nema tsokana. “Ai zan dawo nayi maganin rashin kunyar ki” “Eh din ai bana tsoro” ta faɗa ta window. “Zakiyi bayani ne yarinya” Saiya tafi motarsa, yana tafe yana tunanin yanda san matarsa yayi tasiri cikin jikinsa, ashe dama haka aure keda dadi idan kanada right spouse. Yanke shawara yayi gwara yaje ya fara siyan kayan yara kafin ya wuce Office, Mumtaza Stores ya tsaya bcs akwai girma sosai, ya shiga ya siyo kayan yara kala kala daga na maza da mata duk ya haɗa, saida ya siya san ranshi kafin ya biya kudi ya tafi. Ya gama sakawa a boot yana zaune cikin motarsa, tunanin Fadeela yakeyi da sabon rayuwar da zasu gina. Dayake baiyi winning glass ɗin motarsa ba, yana jin hayaniyan jama’a. Wata ya gani tana tafiya da sauri sauri ta fito daga store ɗin kuma wani namiji yana mata magana amma bata kulashi ba. Sanye take da riga pink iya cinya da wando jens wanda aka yayyanka sai tayi daurin turban. Jakarta na bouquin Blue yana gefen hagunta. Tazo  inda Naufal yake zata shiga motarta. “Haba Yasmeenah, ji ina maki magana kin wani Share ni” a fusace ta juyo ta yi magana cikin harshen Hausa wanda kafin nan bazaka zata ta iya ba saboda ma yanayin shigarta da siffanta. “sai me dan kasan sunana?” “Haba Yasmeenah Nifa dan uwanki ne amma kike wulakanta ni for no reason” Guy ɗin ya faɗa. Harara ta watsa mashi sannan ta zura hannu cikin jakarta ta fito da mukullin mota. Shi Naufal yana daga cikin mota yana jin su bai fito ba. Ita kuma Yasmeenah ta buɗe motarta zata shiga ciki sai guy ɗin ya jawota waje, “Haba Meenah” bai karasa ba ta sharara mashi kyakkyawan mari. “are you stupid Yaya Huzaifah? How  dare you ka saka kazamin hannunka a jikina? Rainin harya kai haka eyee? Tana masifa jikinta yana ɓari. Shikuma Huzaifah idonsa yayi ja sosai saboda bacin rai, “Dan ubanki ni kika mara koh? Don kin samu ina kallon ki har zaki raina ni haka?” “An mareka Yaya Huzaifah ko bari nace Huzaifah..... Kayi abinda zakayi. Kuma ka sake saka filthy hands ɗinka a jikina saina kara maka” Ta fada tana zare masa ido tareda taunar chewing gum. Gadan gadan Huzaifah ya nufota saita saka hannu kerere akan kugun ta tana jiransa babu tsoro a tareda ita. Da sauri Naufal ya fito bcs yaki suke shirin yi. “ya isa mana” ya faɗa tareda janye Huzaifah. “ Karyan iskanci yakeyi, aida ka kyaleshi na koya mashi hankali tunda yana jin kanshi kamar jaki” ta faɗa tana jijiga. “Ba Kinga an shiga tsakanin muba  ai dole kiyi kumfan baki. Banza asarrariya” Huzaifah yace sai ya nufa hanyar motarsa. “eh ɗin, soko kawai” ta mayar masa. Ikon Allah Naufal ya tsaya gani bcs gaba ɗayansu basuda tarbiya. Karar wayarsa yaji saiya bar wajen yaje motarsa, ita kuma nan ta bisa da kallo tana yaba kyansa da kuma kamalan sa. “woow dis Guy is so marriage material ta faɗa a ranta” Shikuma kamar yadda ya saba idan ya dauki business phone ɗinsa saiya faɗi sunar sa, “Hello ! Naufal Hussain Beli speaking, how may I help you” Anan Yasmeenah taji sunar shi, murmushi ta somayi saita gyara tsayuwanta tana yauki. Bayan Naufal ya gama wayanshi baima koma inda take ba saiya ce “Sai anjima Allah  ya kiyaye na gaba” Nan take ya shiga motarsa ya fice, cizon yatsa Meenah ta soma yi bcs taso ta karba number ɗinsa amma ya tafi. But ta dauki Alwashin saita binciko shi duk inda yaje tunda tayi mai Wuyan tasan sunar shi. Wayanta ya soma ringing, kawarta Laila ke kiranta a waya. Da fara’arta ta dauka sai tace, “Sorry my dear gani nan zuwa, I just met Mr right. Nanda 3 months Idan banyi aure ba zan baki dubu hamsin” “Yayi daidai aminiya ta, faran mace hasken tsakar gida. Kura mai kallabin kitse, karya gwafa shahon karfe, Mace daya tamkar dubu, dukan matan duniya a bayanki suke.....” laila tace Dariya Yasmeenah tayi bcs idan ta kyale Laila zasu kwana ana kirari. “okay naji tawan, thanks but Ina so daga yau ki rinka kirana Mrs Naufal Hussain saboda tunda na ganshi to fah saina mallake shi” #NiDaDiyata *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 25 ✨✨✨ Ibn 'Abbas said, "If any Muslim obeys Allah regarding his parents, Allah will open two gates of the Garden for him. If there is only one parent, then one gate will be . If one of them is angry, then Allah will not be pleased with him until that parent is pleased with him." He was asked, "Even if they wrong him?" "Even if they wrong him" he replied. ********** Haka Yasmeenah ta tada motarta tana tafe tana kewar Naufal, tunaninsa ya saukar mata cikin rai. Komai akanshi ya burgeta daga siffansa har shigan sa. Gashi yanda yake magana cikin kamala lafuza yariyari. Murmushi takeyi kawai tama rasa ta inda zata fara, abinda kawai ta sani koma waye shi saita aureshi. Haka tayita tunani harta kai gidansu Lubna inda zasu haɗu harda Laila. Daga nan suka soma hirarakin su na yau da kullum. Shikuma Naufal yana isa office ya rufe kofa ya hau kiran Fadeela, ita harta soya kifi Catfish ta barbaɗa mashi yaji ta hauci. Daga ita sai vest da Under wear tayi daidai ta zauna a kasa tana ci. Kallo takeyi wani American film 'live by Night' a laptop ɗinta wanda Ben Aflek da kuma Zoey Salderna. Ta shafa'a tana kallo sai wayanta yayi kara. Da fara'arta ta kara a kunne sai ta soma magana tana kashe murya. "My other half inata kewar ka" "Nima kewarki nakeyi yasa nace bari na duba ki, yanzu dai ya kuke?" Dariya tayi saita shafa cikinta sannan tace, "Lafian mu kalau, har mun soya kifi muna girba" Murmushi yayi ta ɓangaren sa yana cizon laɓe kamar mai shirin barci kana ya lumshe idanu. A haka suka cigaba da hira hankali kwance suna watsa ma juna kalamai masu rikitarwa har wajen minti arba'in da rabi kafin sukayi sallama. Yanzu tunda yayi magana da babyn sa hankalinsa ya dawo jikinsa, bakin aiki ya koma gadan gadan dama yanada zanen da zaiyi na wani plaza haka. Ita kuma tana gama cin kifi saita sha kankaran fanta sannan taji daidai. Tashi tayi tsam ta soma aikin gida, kafin awa biyu da rabi harta gama duk wani aikace aikace ɗinta tanayi tana hutawa. Su kuma su Abba tunda sukaji Fadeela na dauke da juna biyu suka rinka jindadi, wani idan yaga yanda suke murna zaka zata ba'a taɓa jika cikin gidan ba. Mama da kanta tasa aka tsinko kuka sannan aka busar tareda dakawa Fadeela, kuma ta haɗa dasu kayan yaji da kuma na kamshi. Harda su Na'a Na'a duk ta haɗa mata. Itama Anty Saudah kullum tana cikin mata aiken abinda ba'a rasa kuma Miemie ke zuwa wata rana da driver wata rana kuma da Khattab. Idan taje bata bari Anty Yar gayu tayi aikin komai, wala tayi ita kadai kokuma Deela ta rinka nuna mata. Wata sa'in har mamakin yanda suke mata takeyi, kuma gashi dai dangin mijinta. Kawai tana rayawa wannan shi ne fa'idar hakuri. Daga wajen yan uwanta kuwa kullum Mommy nasiha take mata akan tsabta, saboda wasu matan suna daukar ciki zasu tara shargi har sai sun haihu. Kuma idan akaci abu sai dai idan miji ya gaji da wari ya kawar. Kullum tana cikin mata nasiha akan hakkin aure, kamarsu girki, tsabta, kwanciyar da sauran su. Daidai gwargwado kuma ta dauki abinda ake faɗa mata. Bayan mako ɗaya......... Yasmeenah tana kwance ɗaki tayi daidai kaman ɗakin mijinta. Sanye take da wani gajeren riga iya cinya kuma bata haɗa shi da komai ba. Kafa a harɗe tana amfani da IPad ɗinta sannan tana shan wakar Falz the Bad Guy Mai taken Bad Baddo Baddest. Tana bin wakar tana rausaya kanta cikin rangaji, tunanin Naufal ya faɗo mata. Duk wani hanya da zata bi ta neme shi tayi amma bata samu ba. Abin yana daure mata kai sosai saboda farad ɗaya babu shi babu dalilinsa. Kawai wani tunani ya faɗo mata ta nemeshi ta Facebook. Nantake tayi downloading abun dalilin bata taɓa yiba saboda baya burgeta, saidai taji su Laila suna magana akan abun wai kusan kowa nayi. Naufal Hussain ta soma rubutawa sai gashi masu irin sunar sunfi ɗari, shiru tayi tana tunaninta inda zata fara. Dabara ya faɗo mata akan ta kara Beli a cikin sunar, kaddara ta riga fata saiga shi ya fito shi kaɗai. Da sauri ta gyara zama saboda ruɗewa, hotansa ne akai yana murmushi ga idanun nan kore dasu gwanin ban sha'awa. Bincike ta farayi ciki harta gano inda yake aiki, tasan wajen saboda sun shahara wajen zana gidaje. Kallon agogon bango tayi saita ga karfe sha ɗaya da rabi. Da sauri ta tashi tayi wanka, wani jumpsuit mai kalar hoda ɗin Ellie Saab ta saka saita ɗaura blazer mai kalar karfe. Purple jan baki ta damp'ara saita zane girarta kamar fuka fukai zasu tashi, tamke gashinta tayi baya sai wani yayi jela ta gaba. Ita yau tafa dauki alwashin saita gyarota da Naufal, zungureriyan takalmi inchi shida ta kwama mai rufewa. Tana tafe tana kwas kwas da kafa sai layi takeyi kamar zata faɗi. "Mommy saina dawo" ta faɗa ma Hajia Hindu mahaifiyar Huzaifah. "okay baby Sai kin dawo" ta amsa mata. Su dama haka suke rayuwarsu cikin gidan, kwata kwata babu tarbiya kuma duk me kayi ba'a tsawata maka. Tana cikin tafiya wajen motarta saiga Hilal mai binma Huzaifa ya fito daga motarsa. Dama yafi kowa rashin ji cikin gidan, sune ake cema sheɗanun mutane. Kallon Yasmeenah yayi yana lashe baki saboda wankarta yakai mashi karo. "kanwata sai ina da wannan wankar?" ya faɗa yana lashe baki tareda shafa gemu duk alamun yan iska. Zuwa yayi ya tsaya dab da ita saiya soma magana kasa kasa. Yanayi yana numfashi a jikinta, duk ta tsorata amma saita dake. "kinsan halina amma kike wannan shigar? Kar kiga tun kina yawo da pant kike gidan nan, wallahi zan mance ne nayi maki abinda naga dama" ya faɗi saiya shafa kumatun ta ya wuce. Batace komai ba saboda ba Huzaifah bane mai saukin kai da sunyi cha chan baki. Wannan kanshi na motsawa, yanzu yanzu zai iya rabata da mutuncinta na 'ya mace a cikin parking lot dinnan. Ya daɗe da shiga cikin gida kafin ta dawo daidai, ɗabiun yaran gidan yana cikin dalilin data keso tayi aure ta bar musu gidansu tun kafin su far mata, dama sun saba amma basa samun nasara. Gashi maza har biyar ita kadai ce mace sai Mommy, gwara tun wuri tasan nayi saboda Mommy bata tsawata ma yaro at all. Shiga tayi ta soma tuki, dabara take nema na yanda zata ma Naufal magana. Kawai saita yanke shawara taje kai tsaye wajen daga nan tayi yauki da sauran dabarun mata harta cimma burinta. Shikuma Hilal ya shiga cikin ɗaki zai kunna sigarinsa amma baiga abun kyastawa ba, yana kyautata zaton ya barshi cikin motarsa yanzu. Kiwiyan komawa yaji saiya ce bari ya shiga ɗakin Haisam kaninsa wanda yake kusa da nasa ɗakin. Yana tura kofa ya shiga ciki sai Haisam da Huzaifah suka fara kokarin ɓoye Wiwi da suke busa. Dariya Hilal yayi sai yace "Matsorata kawai" "Tsoron me? Kana ganin Mommy ta fara biye ma zigin kawayenta wai bamu jin magana, shine waccan satin Ina bakin varenda ina busa sigari sai kwastam wai karna kara sha a cikin gidanta" Huzaifah ya faɗa duk ranshi a bace, daga nan saiya zuka Wiwi ya hura ta hanci da baki cikin kwarewa. "Dama nazo na ara lighter ne amma tunda kuma sana'a kukeyi bari na zauna muyi tare" Hilal ya faɗa yana kanne ido. Haisam ne ya tashi ya saka sakata a kofa, yana juyawa suka kwashe da dariya su uku. Sai Hilal ya fito da hodar iblis. Tsaki Huzaifah yayi sai yace, "Dalla Meye haka? Sai ka rinka bata kudinka akan wannan abu" "Mallam ina ruwanka? Kudinka ko nawa? Baka san daɗin abinnan bane saboda idan ka fara baka iya denawa. Ko gidan ka zaka iya sayarwa akan ka siye shi" ya amsa mashi. "Nidai bazan iya cire kudina in siya wannan yar hodar ba, gwara nayi ta amfani da Wiwi cikin sauki" Haisam yace. "Shine ai Danuwa" Huzaifah ya amsa yana dariya saiya mika ma Haisam hannu suka sha. "Ku kuka sani, ni dai yanzu na fara" Hilal ya faɗa tareda buɗe hodar sa. A kasa ya barbaɗa kan tiles ya soma sinsina yanayi yana jan numfashi da karfin tsiya ga idansa jazur. Saida yayi wajen sau uku sannan ya kishingida yana hutawa kamar wanda yayi aikin karfi. Sai ya soma jero magana mara kan gado. "Yanzu naga Babe ɗinnan, sa'a taci yau juma'a kuma bana iskanci ranar danayi maganinta" "wace yarinya?" Haisam yace "Wanda ta mare Huzaifah mana" saiya faɗa yana babbaka dariya, ihu ya kwarara kafin ya cigaba da magana, "Ba'a haife macen da zata mareni ba, idan na fara dukanta kamar Allah ya aikeni in kasheta" Daga nan saiya sake ɗukawa ya sinsina hodarsa sau ɗaya kana ya dago kuma akwai wani a hancinsa amma bai goge ba. "Wallahi gaskiya ake faɗi kafi hankali cikin mu, saboda yanda bakayi mata komai ba" Hilal ya faɗa. "Ai da nine ta mara wallahi ɗakinta zanje nayi yanda nakeso a jikinta, gobe bazata sake" Haisam ya faɗa. "Allah yayi maka albarka, nima abinda na faɗa kenan... Amma wancan ya tsaya kamar wani soko" Hilal ya chapke. Saidai Huzaifah baice komai ba yanata busar Wiwi, Saida ya gama kana ya dauko Shisha ya fara dashi, ahankali ya soma magana, "Gwara ku daina tunanin ta saboda Daddy yace zan aureta" Ciza yatsa Hilal yayi saboda baiso daya ji labarin ba, dama cikin yan kwanakin nan yakeso ya far mata tareda gwangwaje wa a jikinta saboda indai haduwa ne to tayi. Dariya Huzaifah yayi yana nuna Hilal kana ya soma magana, "Musamman kai nasan ka iya maita tun wuri nayi maka iyaka da matana" Sosa k'eya yayi saiya manne tafin hannunsa biyu kana yace, "It's all good, ba matsala na kyaleta. Amma ba haka rai yaso ba, gaskiya anfi sanka à gidan nan" Haisam ne yace, "toh amma babu tastin?" ya kalle su yana warware idanu. Pillow guda biyu Huzaifah ya wurga mashi suna dariya. Yasmeenah ta isa wajen aikinsu Naufal ta rasa me zatayi, babban gini ne mai bene da yawa kuma akwai office daban daban. Ta fito daga motarta ta rufe harta soma tafiya ɗaya ɗaya cikin kasaita. Naufal ta gani yazo wucewa shi baima lura da ita ba, da sauri ta tsayar dashi. "Hello! Baka gane ni bane?" Saida ya ware ido da kyau kana ya tuna, baiyi murmushi ba kawai ya soma magana. "Ohh! Allah sarki! Sannu" Murmushi tayi saita taka taje gabansa, "Ina wuni ina gajiya?" "lafia" ya amsa. "OMG! Locacin lunch yayi Muje na siyan maka mana saboda na biya taimakon daka min." "Karki damu dan Allah nayi badan komai ba" "Noo ni ban yarda ba, I insist please. Karka yi turning ɗina down mana. Just lunch ne Fah" ta faɗa tana kanne ido. Haka kawai ya hakura yace suje. Ita kuma Fadeela tayi tuwon shinkafa da miyan egusi wanda yasha ganda da busharshen kifi. Wani mai masu wanki ta kira kana ta bashi dari biyar akan ya kaima Naufal abinci office. Yana zuwa baiga Naufal ba haka ya maida abincin gida, sai ta gwada wayarsa amma ringing sau uku bai ɗauka ba. Shiru tayi tana tunanin inda yaje, kiran wayar Miemie tayi kuma akace mata baya wajen. Abinda yake daure mata kai shi ne yau yanada aiki da ko fita daga office bazai iya ba shine tace bari tayi surprising ɗinsa da abinci gashi kuma babu shi babu dalilin sa, wani zuciya ya raya mata kila ya fita da Aminu ne, tabbas taba kanta amsa. Su Yasmeenah an samu abin so, rufe motarta tayi ta shiga motar Naufal wani Benz yar yayi GLK 350. Sai yauki take masa suna tafiya, shi haushin sa ɗaya abu yazo dauka motarsa gashi wayarsa yana office. Sun isa Larema zasu ci abinci, shi shinkafa yace akawo mashi duk ya kagu ya bar wajen, ita kuma sai zuba turanci takeyi tana salo. Daga karshe saita ce akawo mata chips da kebab. Har waiter ɗin ta tafi sai Yasmeenah ta kirawo ta " I like my chips the way I like my men, hot and brown" saita kanne mashi ido. Wayancewa yayi ya kawar da fuska. Bayan an kawo masu abinci suka ci sukayi nat, Naufal ya tashi ya biya sai Yasmeenah ta fara kukan shagwaba wai ita zata biya gashi yayi mata wayo. Hakuri ya soma bata amma ta kafe sai buga takalmi takeyi a kasa, ji kakeyi kwas kwas tana taramasa jama'a. Daga nan tace saidai wata rana su sake zuwa ta biya. Dole ya yarda, daga nan juya mashi bayanta ta tafi hanyar mota cikin salon rausaya. Sun koma office ɗinsa saita ce "Yanzu yaushe zan kara ganinka" "Yaushe kike so?" "ko anjima bai dameni ba" "No saidai within the week" "Toh babu damuwa, Im Yasmeenah by the way" Daga nan su kayi exchanging number kana kowa ya tafi, da sauri ya shiga domin yaga wayarsa. Missed call ɗin Fadeela ya gani dama yana kyautata zaton haka. Da sauri ya bar office yayi hanyar gida, yana isa Fadeela ya gani kwance a kan 3 seater sanye da A shaped atampha ɗinkin gown. A hankali ya tadata saboda barci ya soma dibanta. Murmushi tayi saita ja masa kumatu, "Baby harka dawo?" "Eh nayi missing ɗinki yasa na dawo da wuri" Murmushi tayi tana kokarin tashi, "Muje kaci abinci" "Sorry baby Yanzu Aminu ya Kaimu muka ci shinkafa" "Ni gaskiya zan kira Aminu na bashi warning ya daina kai mun miji yawon cin abinci, toh yanzu ya zanyi da wanda na dafa?" "Baby sai muci anjima bazai baci ba" Murguda baki tayi ranta baiso ba, suna makale da juna suna tafe zasu ɗaki sai tace "Other half akwai abinda ya faru yau ne?" Gabansa faduwa yayi, miyan bakinsa ya bushe, da kyar ya saita kansa kafin yace , " Babu abinda ya faru, kinsan bazan ɓoye maki komai ba" "Other half na sani mana, dama kawai jikina yana min wani iri ne" "Karki damu Baby babu abinda ya faru kuma babu abinda zai faru. Jira yakeyi sukai daki domin yayi deleting number ɗin Yasmeenah da komai daya jibance ta. #NiDaDiyata *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 26 ✨✨✨ Narrated Ibn 'Umar, The Messenger of Allah (pbuh) found 'Umar al-Khattab in a caravan while he was swearing by his father. So he said: Allah forbids you to swear by forefathers. If anyone swears, he must swear by Allah or keep silence. ********** Same day wajen 9:45pm....... Su Fadeela suna zaune a falo suna kallon 9 O clock news na NTA, shi ya zauna akan 3 seater ita kuma ta kwanta akan cinyarsa anayi ana hira. Saiga wayarsa ya fara ruri alamun an kirashi, da sauri ya saka silent saboda ya gane wanda ya kirashi. Ita Fadeela bata ma lura da abinda yake ciki ba, duk hankalin ta yana wajen TV dake aikinsa. Haka wayar ya cigaba da kara a karo na biyu shima ya kuma sakawa a silent, a hankali ya zame kan Fadeela dake jikinsa ya Mike tsaye. “Baby bari inje bayi na dawo” Ya faɗa kana ya soma tafiya. Hanyan upstairs ya nufa zuciyarshi yana duka saboda bashida gaskiya. “Ah ahn Other half baga bayi a kasa ba saika je wani upstairs” Ta mashi magana yayin dayake tafiya. Cak ya tsaya tareda juyawa rai baiso ba, bakinsa yana rawa ya soma magana, “Kanin wanka fa zanyi” “Ohhh kace babban Harka ne, gwara kaje chan kafin naji wari” Murmushi yayi saiya juya ya tafi, yana tafe yana rarrabe ido alamun rashin gaskiya. Yana isa ɗaki saiga wayar Yasmeenah ya sake shigowa. Da zumuɗi ya dauka tareda karawa a kunnen sa, “Hello!” Ita kuma gyara kwanciya tayi saita makale murya chan kasa, “Hi Mine, ya kake?” shiru yayi dayaji tace mashi mine amma saiya basar ya cigaba da magana. “Lafia lau, kefa?” “Ni gaskiya I’m not fine, Wai ace baka kira kaji yana kai gida ba koh? Bcs I’m not important to you” “Ba haka bane, kinsan ina aiki da yawa but I’m sorry” sake mirginawa tayi daga kan gado sannan ta harde kafafu. “Okay naji Mine, Kaci dinner kuwa? ko nazo na dauke ka mu fita mu ci?” “Ai ni da wuri nake ci Wallahi” “Ni gaskiya ban yarda ba, kawai rowa kayi min but It’s all good nima zan rama” ta faɗa muryanta à shagwaɓance. Daga nan suka cigaba da hira kala kala har sunfi minti talatin suna zantawa. Ita kuma Fadeela tasan Other half ɗinta Baya daɗewa a bayi, saita bishi taji ko lafiya? Yana kwance yana hira saiya ji zuwan Deela, da sauri ya tashi harda tuntuɓe zai shiga bayi, kafin ta buɗe kofan harya kunna famfo domin taji karar ruwa. Ajiyar zuciya ya rinka yi duk zufa yana keto masa. Text yayi ma Yasmeenah akan he is busy zasuyi Waya gobe. Saiya dauraye fuskarshi da ruwa sannan ya fito. Deela yagani zaune tana jiran shi, “Other half lafiya ka dad’e a bayi?” “Mts gaskiya kamar cikina ba lafiya ne” saiya zauna yana ajiyar zuciya. Dukda yanda jikinta ke mata ciwo bai hanata sauka downstairs ba wajen First Aid box domin ta dauko masa Lemotin. Tana taka matakalan karshe saida ta huta, a hankali ta karasa ɗakinsa domin ta bashi. Inda ta barshi anan ta iske shi, bare masa tayi kana taje bedside fridge ta dauko masa ruwa. “Ungo karbi ko zaka ji dama dama” Amsa yayi saiya yi kamar ya saka a baki amma ɓoyewa yayi a tsakiyar hannunsa, ruwan kawai yasha sai yayi wayo ya saka a aljihun wandon sa. Ita kuma shafa masa kai take tayi tana masa sannu, ranar kwana tayi tana jinyarsa, ta kwantar dashi saita rufe shi da duvet. Saida ta tabbata yayi barci kana ta koma downstairs dukda tana ganin jiri Idan ta fiye bin wajen. Kayan kallo ta kashe tareda kulle kofa da kyau, komawa tayi wajen Other half ɗinta duk tausayinshi ya mamaye ta. Ji takeyi kamar ta dauki ciwon ta daura ma kanta, fatan ta daya shine gobe kada ya farka dashi. Nima dai DIMPLΣS nace Amin ya rabb. Washe gari misalin biyar da rabi na asuba suka tashi, sannu tayi mashi sannan ta koma dakinta. Shi kuma bayan ta tafi saiya dauki wayarsa wanda ke cikin bedside drawer. Text msg ɗin Yasmeenah ya gani tayi mashi reply kamar haka, “Okay Mine, can’t wait to see you. Goodnight and chocolate dreams” Murmushi yayi wanda baisan yanayi ba. Nan take yayi saving sunarta as ‘Aminu Office’ saboda kada Deela ta zarge shi dukda bawani abu yakeyi ba. Ita kuma Deela tana idar da sallah ta wuce kitchen kasancewa yau talata kuma zata awo asibiti. Strawberry pancake tayi masa mai honey saita haɗa da sap ɗin Acha. Yau da ciwon kai ta tashi saboda a daddafe take aiki ko ganin gabarta batayi, shiru tayi bata faɗa ma Naufal ba kasancewar shima yanaji da jikinsa. Wajen karfe takwas ya ajiyeta a haraban asibitin Al madina saiya koma office idan ta gama saiya je ya dauketa. Tana cikin asibiti tabi layin ganin Doctor, Dr Hadiza Pate tana ganin Deela saita mata murmushi. “Bagashi Allah ya nufa fah” ta faɗa yayin da Deela take kokarin zama. Daga nan aka duba yadda take tareda kwanakin cikin a jikinta. Anan ne aka gano satinshi goma sha daya. Duk wani protocol daya kamata masu ciki subi duk tayi, ba ita ta gama ba sai wajen 11 ɗaya da wasu kananan mintuna. Ta bala’in gajiya saita kira Naufal amma taji call waiting alamun Yana waya. Kashewa tayi tana jiran ya gama saiya kirata. Shikuma daga ɗayan ɓangaren waya yakeyi da Yasmeenah sai Deela ta kira. Dayake ear piece yake amfani yana kallo yake ringing amma baiyi gigin dauka ba harya tsinke. Shi yana so ya gama da Yasmeenah ne kafin ya kira Deela saboda yana kyautata zaton ta gama daga asibiti ne. Ita kuma Yasmeenah sai zuba takeyi wai bata karya kumallo ba tana so ya raka ta. Yanata nokewa amma taki yarda wai saiya rakata koda baci zaiyi ba. Suna cikin gardama saiga Aminu yazo da wani drawing yana so Naufal ya duba masa. Da hannu yayi masa alama ya kashe wayar, sallama yake ma Yasmeenah saiya ajiye. Anan ya soma dubawa shaf ya mance zai kira Deela. Suna cikin haka 30 mins later sai Yasmeenah ta kira wai tana Larema tana jiran sa. Nan take yayi ma Aminu sallama saiya tafi, Aminu shikuma ya ɗaga masa k’afa ne saboda yaji yace, “okay gani nan zuwa” duk zatonsa Deela ce ke ɗayan ɓangaren. Sanye take da Swiss Lace mint green Wanda akayi mashi ɗinkin peplum. Ya ɗameta dakyar take numfashi balle tafiya. Gwawaro style ta daura kawai amma bata saka mayafi ba kasancewa ita ba ma’abociyar sa bane. Chewing gum ta saka a bakinta tana tauna kas kas tareda wulla idanu. Sannan gashi ta fashe kanta da turaren Unbreakable Bond. Tana cikin motarta kirar kia picanto tana jiran isowar Naufal. Tunanin irin salon da zatayi mashi ne yau saboda ta lura yanada zafin kai. Shikuma yana isa Larema ya fito daga cikin motarsa, harya kulle saiya tunada Fadeela. Nan take yaji babu daɗi tareda haushin kansa. Wayarsa ya dauko domin ya kirata, itakuma ta kulu tayi fam kamar ta fashe, a parking lot zaune take duk rana ita kaɗai kamar mayya. Taso tayi zuciya ta tafi amma kawai ta hakura kila yana wani abune, saisaita kanta tayi tana faɗin Allah yana tareda mai hakuri. Sunansa tagani baro baro ‘other half’ murmushi tayi saita dauka, shikuma bugu ɗaya, biyu, na uku yaji ta dauka tareda faɗin, “ My Other half” Bai kai ga amsa mata ba sai Yasmeenah tayi karab ta kwace wayan tareda kashewa. Kallonta yayi a fusace ya rasa me zaice, “Meye haka? Bani wayana mana” Ya faɗa a sanyaye. Murguɗa masa baki tayi cikin wasa tana jijiga jikinta komai nata yana rawa, “Bazan bada ba, lunch zamuci so no phones allowed” saita fara rausaya ta tafi ciki. “idan kana so kazo ka karba” ta nuna masa wayan sannan ta zura cikin jakarta. Ranshi a bace ya bita ciki duk fargaban yanda Fadeela zatayi yake. Ita kuma ta rinka Hello! Hello!! Amma taji Shiru. Sake kira tayi sai kawai taji an kashe, “kambu” ta ce saboda bata san sanda tayi ashar ba. Da karfin tsiya ta fige jakarta, dama gidansu Anty Saudah zata saboda rana ya bigeta gashi jiri yana fizgarta. Napep ta tare tayi gidanta tunda bata tambaye shiba, tana isa locacin azahar yayi. Bayi ta shiga ta watsa ma kanta ruwan zafi sai tayi alwala. Sallolinta tayi tareda addu’a, bata bar kan sallaya ɗinba mirginawa kawai tayi ta soma barci. Gashi yunwa ya soma addabarta amma bazata iya tashiba saita huta. Yasmeenah ta zauna wannan Karon a wajen VIP tana jiran Naufal, sannu a hankali ya taka wajen datake zaune. Murmushi ta sakar masa Shikuma fuskarshi babu yabo babu fallasa. Duk ya kagu daya bar wajen saboda ya lura da abin iya shege ne. Kawai ordering jollof yayi baima ciba tsakura yayi. Ita kuma Shawarma aka kawo mata da Non alcoholic wine. Tana Ci tana mashi salon turanci kamar zata karya harshe, bai biye mata ba illa uhm da kuma uhm uhm dayake amsawa. Jira yakeyi su gama ci ya karɓi wayarsa domin ya kira Fadeela saboda yasan tana jiransa. Bayan nan saita ce wai suje Vanilla joints shan Ice cream, wani mugun kallo ya watsa mata kana yace, “Halan bakisan inada aikin yi bane?” “Oh na mance, muje na rakaka office I promise bazan dame kaba” saita ɗaga hannunta sama alamar rantsuwa. Baiko kalleta ba ya buɗe motarsa. “Maybe some other time” Yace sannan ya shiga ciki. “Okay ba matsala” tace saita ɗaga masa hannu. Yana tafe yana Zura gudu saboda yasan bai kyauta ma Fadeela ba, duk tausayinta ya kamashi kuma yayi mata alkawarin bazai sake ba. Yana isa asibiti babu alamar Fadeela babu dalilinta, masu gadi ya tambaya sai suka ce masa ta kusa awa daya da tafiya. Dafa kansa yayi yana salati saboda yasan yanzu hankalinta ya tashi. Wayanta ya kira amma bata ɗauka ba, dama yana kyautata zaton zatayi haka. Ita kuma wayar ta barshi cikin jakarta kuma yana downstairs saboda bazata iya jigilarsa ba. Yasmeenah gidansu Laila ta wuce kai tsaye domin ta bata labarin abinda tayi kwana biyu. Anan ne Laila ke fada mata indai Architect Naufal ne to fah yanada mata, Amatullah kawar cousin dinta itace kanwarsa. Cizon yatsa tayi tana jin haushin labarin, sai kuma kawai tayi fuska. Ita zata aureshi koda mata ɗari gareshi ballantana kwara ɗaya karamin alhaki. Zata zama amarya sa uwar gida hauka tareda maida uwar gida ta zama bora. Koma waye matarsa kawai tayi hakuri ta bar mata Naufal salin alin kafin ta samata bakin ciki ya kasheta. Kowa yasan Yasmeenah bata iya kishi ba, ba’a cin nasara akanta. Kawai a ganta a kyaleta! Yana isa gida yaga jakar Deela a falo amma bata wajen, hankalin sa ya ɗan kwanta saboda ya buɗe yaga Wayanta ciki. Dakinta ya nufa saiya ganta kwance a kasa, yayi nadaman abinda yayi mata ainun. A hankali yaje inda take saiya tallabota. Mistike ido tayi sai tayi murmushi kamar babu abinda ya faru, dama ita bata iya mita ba. Shine domin borin kunya ya fara jero mata zance. “Babyna kiyi hakuri, dazu da kika kirani muna conference call dasu Mr Sutter, muna gamawa shine na kiraki saiga wani ogan mu yazo yasa na kashe wayar” “please I’m really sorry my love, in sha Allah bazan kara ba” kakalo murmushi tayi saita sumbace kumatunsa, “Babu komai, ya wuce saboda nasan baza kayi da gangan ba” Daga nan ta tashi zata wuce kitchen, rakata yayi domin suyi tare Thou kawai mika mata abu yakeyi. Jollof din Cous Cous ne sukayi sai suka wuce dinning domin yunwa yana damun Deela, shi kuma karfin hali kawai yakeyi saboda ya riga yayi nat tareda Yasmeenah. #NiDaDiyata *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 27 ✨✨✨ On the authority of Al-Numan bin Basheer, who said : I heared the messenger of Allah say : "That which is lawful is plain and that which is unlawful is plain and between the two of them are doubtful matters about which not many people know. Thus he who avoids doubtful matters clears himself in regard to his religion and his honor, but he who falls into doubtful matters falls into that which is unlawful, like the shepherd who pastures around a sanctuary, all but grazing therein. Truly every king has a sanctuary, and truly Allah's sanctuary is His prohibitions. Truly in the body there is a morsel of flesh which, if it be whole, all the body is whole and which, if it be diseased, all of it is diseased. Truly it is the heart." Narrated by Bukhari and Muslim. ********* Yasmeenah Yusuf(YY) kokuma Meenah yanda friends ɗinta suke ce mata. Ita bafillatana ce yar asalin garin Shandam dake jihar Jos. Mahaifinta Marigayi Alhaji Yusuf ya rasu tareda matarsa Hajia Jidda à car accident tun tana shekara biyar. Daga nan saita koma zama wajen wan mahaifinta Alhaji Abdulrahman. Shi yana zaune locacin a Las Vegas da matarshi Hajia Hindu tareda yaransa guda biyar. Babban yaronsu mai suna Huzaifah yanada shekaru 28, sai Hilal 27yrs, Haisam yanada 25yrs, Hashim 23yrs, sai dan auta 20 yrs. Ita kuma Yasmeenah tanada shekaru 22 a duniya. Shekarar daya gabata suka dawo Nigeria sanadiyar Daddy yayi retire a aikinsa. Yara rainan turai Sam basuda tarbiyya kwata kwata, gaba d’ayansu karka cire kowa duk jakai ne. Dama dama Hashim, shi duk rinsti yana sallah kuma bai kwana da mace, shisha ne dasu codine. Ko auta Habeeb yana shan Wiwi, balle ayi maganar gwaska Hilal. Shi wannan tsakanin shi da sallah sai ranar Eid, shima saboda ana taruwa aje baki ɗaya. Ga Cha Chan bala’i, Bin mata kamar bunsuru, shaye shaye kamar salansa. Dab da zasu dawo Nigeria da zama ya koyi shan Hodar iblis. Sannan yanada bala’in zafi, baya daukan rainin at all. Yanzu saiya tara maka gajiya. Dukkansu babu mai aikin yi daga Huzaifah sai Hashim kasancewar duk sun gama. Tun suna yara Daddy ya siyan masu Shares mai yawan gaske, kowa da nashi har Yasmeenah yasa suke fachaka babu kama hannun yaro. A cikin su tarbiyan Yasmeenah ne yafi dama dama, at all bata shaye shaye kuma bata bin maza suyi fasikanci. Kawai dai ka barta da shigan banza saboda takan fita ma babu kallabi. Sannan takan saka gashin gira, kumba da kuma gashin kanti dukda nata yanada tsawo. Itace ma taci Prom queen a makaranta saboda tana cikin kin yadda. Gashi tanada kokari babu laifi saboda bata faɗi jarabawa. Tunda Yasmeenah takai shekara sha shida a duniya kyanta ya fara bayyana a mastayinta na ‘Ya mace. Tun daga nan suka fara far mata, tana tafiya yayyinta zasu shafa mata jiki. Tada bala’i tayi sosai saida Mommy ta shiga tsakanin su. Tun daga nan ta raina su saboda girma ya faɗi, suna ce mata kule zata ce masu chas. Wata rana idan Mommy bata gidan haka zasu zauna suyita hirar yanda suka kwana da mace. Komai suke faɗi kuma basa damuwa idan Yasmeenah tana wajen. Saidai taji kunya ta tashi, idan kuma ta bar wajen sai su bita da zagi, “Shegiya munafuka kamar bakiyi” Tasan cewa tarbiyanta akwai gyara sosai amma ita Manzo ne a gaban su. A sanda taji kishin kishin wai za’a haɗata da ɗaya daga cikin yaran gidan, kuka ta kwana tanayi. Ta ɗanji dama dama da taji Huzaifah ne saboda shi solobiyo ne, juyashi zata yi kamar waina. Amma dai dukda haka bata so, sam bazata iya haɗa zuri’a da yaran gidan ba. Yasa tun dataga Naufal ta birkice akansa, duk wani aji data ke dashi a matsayinta na ‘ya mace ta ajiye gefe. Dama Hausawa sunce da zafi zafi akan daki karfe, ta dauki alwashin bazata hakura dashi ba harta sameshi. Zatabi kowane hanya daya dace daga kissa, yauki, iyayi kai har Malaman zaure zata iya bi domin Naufal. Abinda yake mata daɗi shine tun kafin aje Ko’ina ta fara samun lambar zuciyarshi dukda bawai sun wani sake bane yanda takeso amma tana kyautata zaton cewa ya kusan zama nata baki daya. ******** A kwana a tashi babu wuya wajen Allah, yanzu a kalla cikin Fadeela ya kai wata biyar a duniya. Tayi katuwa sosai kuma kafanta ya soma kumbura, komai a wahalce takeyi amma bata fasa aikin gida ba. Ko Defence na project tayi kawai yanzu zaman gida takeyi tana rainon cikinta. Saidai  bata jin daɗin yanda aiki ya kacame ma Naufal, tun safe idan ya fita sai goman dare yake komawa gida. Tun tana complain akan abin saboda yana damunta sosai gashi ko waya sau ɗaya sukeyi shima sai idan ta kirashi. Flimsy excuse yake bata koda yaushe akan yana conference call da su Mr Sutter, wata rana kuma yace yana construction site ne. Hakuri takeyi koda yaushe tayi masa uzuri, koba ta faɗa ba tasan Allah yana tareda mai hakuri. Sam bata nuna masa ɓacin ranta saboda tasan cewa duk zafin neman dayake yi akan itane da abinda zasu haifa. Shikuma yana zuwa aiki karfe 2 yake tashi daga nan zai tafi yawo da Yasmeenah. Basu Ice cream joints Ko wajen shawarma duk dai wurare marasa kan gado kuma baya komawa sai sunci dinner tukun. Shakuwa mara misaltuwa ke tsakin su, soyayya mai karfi ya shiga tsakanin su. Tun yana ɗari ɗari da ita har yake sake sosai. Weekends kawai Fadeela ke ganin sa sosai saboda shima bazai iya karyan aiki ba, amma wata rana idan Yasmeenah ta nace dole yace zashi dauko wasu takardu office. Yanzu jin kansa yakeyi kamar tubabban sarki don karya, tun yana ɗari ɗari idan yanayi kuma yana jin wani iri ajikinsa har yazo ya saba. Yin karya yakeyi kamar yana faɗin gaskiya. Akwai wani rana haka da asuban fari Abba ya kirashi akan yana san ganinsa. Yana isa ya rufe shi da faɗa akan dalilin da bai siyan ma matarsa mota ba, nan take yi charap yace ai Birthday ɗinta ya kusa ya kuma order akawo mata. Kuma alhali karya yakeyi, dayake baya zaman gidan ya mance Fadeela Keke Napep take hawa duk kuɗin mijinta. Shi yanzu duk girman mutum zai iya mashi karya yasa ko tunani baiyi ba yayi ma mahaifinsa. Babu mamaki idan aka bashi ministan kula da lafiyar karya. Yanzu ne zaisa akaima Fadeela Mota. Koda yake ya ɗanji tausayinta, ga ciki ga kuma rashin abin hawa but he promised to do better. Last week ya kashema Yasmeenah dubu dari da hamsin akan motarta, ita bawai ta tambayeshi bane saboda tanada kudinta. Shine don raayinsa ya bada wai ‘Meye amfanin zama tare’ Tun daga nan bata sake masa musu ba wajen kudi, haka yake siyan mata su designer bags dasu takalma. Sauda dama yakan mance daya kamata ya siyan ma Fadeela. Sai daga baya ya tuna, daga nan saiya rinka siyan komai guda biyu. Leda ɗaya Yasmeenah ɗayan kuma Fadeela. Idan yakai gida wajen Deela, ta rinka shi masa da albarka kenan tana jindadi. Shi karin kansa yana jindadin addu’o’inta unlike Yasmeenah dake cewa ‘Thanks’ sai a wuce wurin. Gashi kuma wayarsa ya saka password, shima idan ka bude akwai wani a Whatsap, msg, phone book etc. Kuma idan ya dawo goman dare zaita danna waya, idan Deela tayi masa complain zai ce tayi hakuri Email yake aika masu Mr Targeyen. Wata rana tana jiransa wata rana kuma tana kwanciya ta kyalesa, kawai daɗin abin su Miemie da Bilqees sukanje sukai har Magrib sai Khattab yaje ya daukesu. Wani alhamis haka bayan sun gama karin kumallo kafin ya fita, saita tambayeshi izinin tafiya kasuwan Muda lawal domin tayi masu cefane. Ya bata izinin ta tafi tareda cika mata jakarta da kudi. As expected shi masa da albarka tayi sannan ta rakashi wajen motarsa saiya tafi... 11 am....... Locacin ta gama aikace-aikace daya kamata tayi sai tayi wanka domin ta tafi  kasuwa. Tana gaban mirror saita lura da gashin kanta yayi datti ya chukurkuɗe, anan ta yanke shawaran gwara taje saloon tunda duk hanyar ne. Ita kuma Yasmeenah jindadi takeyi sosai saboda zata fita date da Mine ɗinta. Zumuɗi Kawai takeyi, wani bakin leather wando na Victoria Beckham ta saka saita haɗashi da riga na chiffon white and black Mai guntun hannu. Takalmin Jimmy Choo silver ta saka saita dauki Bouquin din Marc Jacobs. Fuskanta shake da makeup kamar mannequin. Sai kuma wani munafikin gyale data dauka. Tafe take cikin motarta zata salon ayi mata gyaran gashi dasu kafa kafin yamma yayi. Taje har an fara mata sai ta kira Laila kawarta akan tazo ta tafi da motarta saboda Naufal zata kira banyan nan. Suna zaune a cikin dryer suna hira saiga Fadeela ta shiga itama, kafin a gama wanke ma Fadeela ayi mata setting har nasu yayi sai suka fito suna yauki kana suka zauna dab da ita. Kana ganin Fadeela kasan babban mace ce, iPhone 7 ke hannunta ga kuma tasha qwala qwalai daga kunnenta har yatsun ta. Sannan atamphan Super wax ke jikinta kuma anyi mashi ɗinkin masu hannu da shuni. Gashi dama jikinta ya murmure, dole ta birge ka. Su Yasmeenah saida suka kasa hakuri sukayi mata magana. “Halan ke amarya ce?” Yasmeenah ta tambaya Deela. Murmushi Deela  ta sakar mata saita amsa da eh. “Wallahi kin burgeni ne kawai, ina so nayi kama dake idan nayi aure” dariya Deela tayi bata cekomai ba. “Ki tayani addu’a, inada wanda nakeso na aura da fatan Allah ya tabbatar da alheri” “Aminsumma Amin” Deela ta amsa. Daga nan ta tashi zata shiga dryer, anan ne sukaga tanada ciki. Laila ce tace ‘Lahhhh ciki gareta! Wallahi ina son yara sosai kamar raina” “Kai nayi maki murna, Allah ya saukeki lafiya” Yasmeenah ta ce. “Amin summa Amin” ta amsa mata dashi. Daga nan sukayi sallama saboda anzo daukar su. Ita Deela kawai tana amsasu ne amma sam basu burgeta ba. Duk sunyi shigar arna ga gashin Kanti da kuma gashin ido. Da basuyi hausa ba bazata zata musulmai bane, kawai tana tunanin wanda zai auresu a haka. Wayanta ya soma ruri saita tashi taje ta dauka. Ta window ta hange shigan motar Naufal yana barin parking lots, bayan tagani kuma yayi nesa da ita. Kauda tunanin tayi ta koma aka gyara mata gashin kanta. Bayan ta gama sai tayi chatan Napep taje kasuwa tayi Siyayyanta. Data koma gida ta daura masu dinner saboda Naufal ya daina cin lunch a gida, ko office ta tura masa bata samunsa kila ya tafi construction site. Tuwan alkama tayi da miyan karkashi, saita fasa kwakwa da pineapple ta markaɗa masu. As usual ta kanyi kwalliyar tarban miji, yau kawai daɗi takeji saita saka wani bakin guntun free gown. Gashi kanta yasha gyara so bata daura kallabi ba, dama wajen goma yake dawowa amma wannan Karon har wajen minti arba’in da biyar. Sam batayi fushi ba saboda hakuri shine zaman aure, koba komai saboda ita yake neman kuɗi. Yana shiga falo ta tashi da sauri ta karasa wajensa tayi hugging ɗinsa. “My Other half, Finally ka dawo.... Yau na rasa dalilin dayasa nayi missn dinka sosai” Manna mata kiss yayi sai yace, “Toh gani me kika ajiye min” “Muje kayi wanka sai kazo kaci abinci, yau favorite dinka na girka” Daga kanshi yayi sannan ya soma magana kasa kasa, “Afuwan babyna Wallahi Aminu ya isheni da yana jin yunwa shi ne na kaishi daga nan saina ci” Shiru tayi batace komai saboda ta bala’in shaka, gashi har konewa tayi wajen wrapping tuwon. Idanta Saida ya canza kala saboda bacin rai, ba wannan karon bane take abinci yaki ci, yayi yafi a girga amma na yau ya ɓakanta mata rai. “other half Ko drink ɗin bazaka shaba” ta faɗa cikin muryan kuka. Shafa bayanta yayi saiya ce, “Ki ajiye min a fridge gobe sai na sha” “Allah ya kaimu lafiya” “Amin babyna” Sun tafi ɗaki har yayi wanka tana goge jikinsa da hand towel, “Other half yau Kaje wannan sabon plaza ɗin ne wanda ke kusa da Apple clinic?” Datana kallon fuskarshi dataga rashin gaskiya karara ya bayyana. Dakewa yayi saiya amsa mata da, ‘Ah ah, menene ?” “Babu komai kawai naga kamar motarka ne a wajen” “NI dama yanzu zan faɗa maki a Gombe na wuni, Zaayi renovating Government house shine mukaje meeting” tabbas akwai zance kamar haka amma meeting ɗin saura sati biyu. “Oh Allah sarki other half dina nayi maka murna sosai, Allah ya sanya alheri” “Amin, amma  kema meya kaiki wajen? Inace kasuwa zaki amma shine kika biya wani wajen? A duniya karya yana cikin abinda na tsana Wallahi. Idan kika tambayeni ai bazan hanaki ba, amma dan nuna ban isa ba shi ne kikayi abinda kikaga dama koh?” Nan take ta firgice yanda taga karamar magana ya zama babba, saukowa gabansa tayi ta rike masa hannu, “Other half Kayi hakuri dan Allah, ka mance na saba biyawa saloon idan zani kasuwa saboda banso nayi fita biyu” “Toh donkin saba sai akace banajin haushi ko me? Ni dai Karki saki saboda bana san karya” “In sha Allah Other half bazan kara ba” Daga nan ta hau gado tana shafa masa bayan shi tana watsa mashi kalamai masu dadi. Dolenshi ya sauko ya biye mata suka fara soyayyar su, suna haka har barci ya kwashe su. #NiDaDiyata #TeamFadeela #TeamNaufal #TeamYasmeenah I'm proudly Team Fadeela this time around. *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs[9/2 15:52] Dimples: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 28 ✨✨✨ *Lesson* Beware the liar. He lies so much that he forgets the truth. He even finds it hard to accept the truth & ends up believing in his own lies. MUFTI ISMAIL MENK Abu Ayub narrated that the Messenger of Allah said: "Whoever fasts Ramadan, then follows it with six from Shawwal, then that is (equal in reward) to fasting everyday." (Sahih) *********** Washe gari.......... Tun sanda Fadeela ta tashi daga barci bata koma ba, kitchen ta wuce ta fara wanke wake saboda tana sha’awan cin kosai da kunun tsamiya. Ta gama wankewa saita markaɗa à blender, shima ruwan zafin yana cikin Kettle amma yaki tausa. Wucewa tayi upstairs domin ta kira Naufal ya taimaketa ya duba mata. Tana isa taji karar wayarsa amma kafin ta karasa ya tsinke,, kuma waya da password balle ta duba. Shikuma yana cikin bayi yana wanka. Tana zaune a bakin gado tana jiransa saiga wayan ya sake shigowa, da hanzari ta dauka kuma cikin ikon Allah wanda takeso tayi magana dashi ya kira, watau Aminu office. Ta kara a kunnenta kafin tayi magana sai taji muryan mace tana magana cikin yauki, “Mine tun dazu nake kiranka amma baka dauka ba” Mamaki karara ya kama Deela saita cire wayar daga kunnenta ta sake kallo da kyau kuma tabbas Aminu ne. Mayarwa tayi kunnenta sai taji, “Mine baka jina ne? Hello Naufal!” nan take gaban Fadeela ya faɗi sai tayi maza ta kashe wayar. Jikinta ya soma bari, tabbas ba wrong number bane tunda ance ‘Naufal’ amma yaushe Aminu Office ya koma mace. Gashi harda kiran mijinta Mine. Shiru tayi tana jiran shi ya fito daga bayi, yana fitowa sai yaganta zaune. Murmushi ya sakar mata kana yace, “Babyna yadai?”     Fuskarta babu yabo babu fallasa ta soma magana, “Other half Aminu ya kiraka kuma na dauka amma naji muryan mace saina kashe. Probably wrong number ne” “Probably” ya amsa saiya soma shafan mai. Dayake yanzu ya kware a iya shararo karya yasa baya girgiza idan yana yi. Tabbas yasan Yasmeenah ne kuma yayi warning ɗinta data daina kiransa idan yana gida amma bataji. Kallon rainin arziki tayi masa sannan tayi kwafa, dama ta saba dauko masa kaya amma wannan Karon tayi kememe. A duniya rainin wayo yana cikin abinda ta tsana. Ji yanda yayi pretending bayan harga Allah tasan ba wrong number bane. Ita abinda bata sani ba shi ne ko amsar wayan Aminu tayi ta kira Naufal kokuma itace Aminu ɗin da ake magana kullum. Suna cikin haka sai wayarshi ya sake kara, toh dama yana hannunta, kallo ɗaya tayi saita lura da Aminu Office ke kira. Cilla mashi wayar tayi kamar zai faɗi sannan tace, “Gashi ya sake kiranka” Kallo ɗaya shima yayi saiya yastina fuska kana yace, “bazan dauka ba tunda yanzu zani office” Ita tasan yanada aboki Aminu amma kawai yanzu komai ya chunkuse mata ne. Kawar da tunanin tayi yanzu kafin zuciyar ta ya buga. Ya lura tayi shiru saiya je gabanta ya ɗuka tareda kama mata hannu. “Babyna meke damunki? Murmushi tayi wanda bai kai ciki ba sannan tace, “Kaina ke ciwo” shafa mata goshi yayi tareda kumatu “Allah sarki babyna, ko na zauna ne nayi jinya” “Na hutarshe ka” saita mike tayi hanyar kofa harta kusan ficewa saita tsaya tace “Bari naje kitchen” Saboda bacin rai bata fada mashi kettle ya baci ba, kawai zataje ta daura akan gas. Shikuma dama gaste yake mata saboda koda tace ya zauna awa daya zai kara yace mata ana nemashi maza maza a office. Dama yau zai raka Yasmeenah Kano karban dinki wajen wani tailor ɗinta. Ita kuma Fadeela tana aiki a kitchen duk ranta yana mata zafi, bata ma lurada suyan data keyi dukta kona. Haka sukaci ita kokon kawai ta tsakura. Daya lura da yanayinta saida ya tambaye ta matsalarta saita ce masa kanne. Shi kwata kwata baiyi tsammanin ta ɗago sa bane saboda yasanta da nawa a al’amura ta, kafin ta ɗago locacin kila ta haihu kuma dama abinda yake jira kenan. Harda cewa ta dauko mayafi ya ajiye ta a asibiti amma taki, ce masa tayi idan ta kwanta zataji daidai. Harya kai kofa bata tashi domin ta rakashi ba, juyowa yayi saiya fara magana, “Baby tunda bakida lafiya ba sai kinyi girki dani ba” “Zaku fita Kuci da Aminu koh?” tayi charab ta tari numfashin sa. Murmushi yayi yana sosa k’eya saiya ce “Eh baby zamu koma Gombe kuma” “Allah ya dawo daku lafiya” ta faɗa tana mashi kallon tuhuma. Dama ance kukan kurciya jawabi ne kuma sai mai hankali ke ganewa, amma sam bai saka a ranshi ta gane komai ba. Inshut yau ya kara jindadin yanda yayi mata karya dazu kuma bai girgiza ba, kanne ido ɗaya yayi saiya furta a fili “Kai Naufal bakada dama” yana tafe hanyar gidansu Yasmeenah yana Nishaɗi tareda sauraron wakar Young Alhaji na Nomis G. Ita kuma Deela kifa kanta tayi a kan dinning tayi kuka san ranta, wai yaushe yaushe da shiryawa da shi harta  gundureshi ya soma kallon wata. Upstairs ta wuce dakinta domin ta dauki wayarta, kawarta da suka tashi tare Jumaimah ta kira a waya akan tazo gidanta yanzu yanzu. Within hour ɗaya ta iso. A falo ta riske Deela ido yayi sutu sutu ya kumbura. Bata iya karasa sallama ba ta wulla jakarta kasa tareda rugawa wajen Deela. Rungumota tayi saita soma magana da sauri sauri “Deela meya faru? Dukanki yayi?” Rushewa da kuka Deela tayi dama abin nema ya samo wai matar falke ta haifi jaki. Jijigata Jumy tayi saida taga ta rage kuka sannan ta kuma tambayarta “Deela my dear kin ruda ni, kiyi wa Allah ki faɗa min saboda hankalina ya huta” Cikin muryan kuka ta soma magana gwanin ban tausayi, “Tunda nake ba’a taɓa min rainin hankalin da Yaya Naufal yake minba” Daga nan tana kuka ta fayyace mata komai da komai duk abinda Naufal yakeyi wanda duk bata lura ba sai yanzu. “ni nama rasa me zance Wallahi” Jumy ta faɗa tana jinjina ma kokarin Fadeela. Daga nan saita ce, “Toh yanzu me zakiyi? Zaki tambayesa ne ko me?” “In tambayesa? Wallahi karya zai shirgo min. Aini tun karyan dayayi min dazu  na firgita dashi” “Okay ki bani nanda awa biyu Deela, zan nemo maki waye asalin Aminu. Office ɗin su zani nayi masu hadarin kudi dole su faɗa min wake zuwa wajen mijinki” Murmushi Deela tayi saboda taji daɗin shawarar. A kwance Jumaimah ta bar Deela kana ta wuce bank ta ciro dubu hamsin. Kai tsaye office ɗin Naufal ta wuce. Masu gadi suka tareta suna mata magana akan inda zata da sauransu. Murmushi tayi saita yi parking motarta daga gefe saboda hanya ne. Sannu a hankali ta fito daga cikin motarta taje inda suke, murmushi ta sakar masu kana ta gaishe su. “Da alheri nazo wajen nan bayin Allah” saita zuge jakarta ta kyallara masu kuɗi su gani. Dama su biyar ne, hudu suka soma washe baki daya kuma fuskarshi babu yabo babu fallasa. “Dama tambaya nakeyi” “yarinya Allah ya sa mun sani” “Kunsan Arc Naufal Hussain” Noke noke suka farayi basaso suyi magana, data lura da yanayin su sai tayi murmushi kana ta kara matsawa kusa dasu, “Kar kuji tsorona, niba muguwa bace kawai wasu abu ke faruwa a office ɗinnan shine nake so na sani” “eh mun sanshi, lafiya koh?” “Bansani ba ko akwai wata wanda ke yawan zuwa wajen shi ?” “kice mai shigar arna” Daya daga cikin su ya chapke. Daga nan suka soma magana akanta, kowa na faɗin magana marasa daɗin ji akanta. Jumy taji dadi sosai koba komai Fadeela ta kace mata tsara tunda ita  ba mutumiyar arziki bane. “Toh kun san sunanta ko wani abu game da ita” ta tambaya. Wani daga cikin su yaje ya dauki wani takarda daya kunsa sunarta da address dinta. Acewarsa tazo cikin motarta shine zasu fita a motar Oga sai aka bashi address ya mayar mata nata. Jumy taji dadi sosai saita dauki dubu talatin ta basu zasu raba akan dubu shida shida. Dama aikin dubu ashirin ne a wata toh gashi sun sami kwantan shi, nan suka rinka godiya suna shi mata da albarka. Dadin zance suka faɗa mata yau Naufal baizo aiki ba jiya ma tun goma daya fita bai koma ba. Tana zuwa ta fayyace ma Deela komai daya faru, kuma tace mata tanada wani uzuri a gabanta amma gobe bayan Naufal ya fita sai tazo suje suci kaniyar karuwarsa. Deela taji dadi sosai kuma tayi Na’am da shawarar. Batayi girki ba saboda tasan bazai ciba, sauran kokon ta take ta sha sai wajen yamma tayi Indomie da sardine. Wajen yamma su Naufal ana Kano Anje shoprite da Yasmeenah ana kallon wani sabon American film ‘XXX return of xender cage’ anayi ana shan ice cream da popcorn. Dama tun safe suka karba ɗinkin kawai ana holewa ne. Siyayya ba kadan ba tayi saida kuɗi sukace Allah ya isa kudaina kasheni haka. Waya akayi ma Naufal wai an kawo motar Deela daga Cotonou, dayake baya garin sai yace kawai a kaimata dukda birthday ɗin shigarta 21 saura kwana uku. Shi a dole yayi abin arziki ya bata early birthday present, da farko har zata mayar masa da abinshi amma saita tuna raba mugu da makami ibada ne. Shikuma sai kallon waya yakeyi yana jiran yaga ta kirashi ta fara kwarara mashi addu’a amma sai yaga wayam. Haka ya hakura da tunanin kira sai ya mayar kila batada kati ne, yanzu yana kyautata zaton ta saka English wear mai rikitarwa tareda saka turaren wuta tana jiran sa. As expected wajen goman dare ya koma gida, Deela tana jin karar motarsa ta kashe wutan ɗakinta tareda kwanciya abinta. Yana shigowa bai ganta ba sai tausayinta ya kamashi sosai saboda yasan ciwon ne ya sakata a gaba. Yana zuwa ɗakinta yaga harta kwanta, zuwa yayi yana shafa fuskantar amma ta rinka mashi magagin karya. Dole yaje ɗakinsa ya barta, basuyi wani Chatting sosai da Yasmeenah ba saboda ya gaji sosai gashi kuma ranshi baya mashi daɗi Deela babu lafiya. Washe gari..... Dankali da kwai ta soya mashi, dukda yana hanata akan batada lafiya amma taki ji. Ita kawai badan shi takeyi ba sai dan Allah. Batayi mashi maganar motar ba shine ya gaji da shirun ya tambaya. “Eh dama naga an kawo mota amma bansan na menene ba?” Kanne mata ido yayi yana dariya,”Babyna zatayi birthday dole na fito da ita” “Ai ashe zaka tuna?” “Meyasa bazan tuna ba?” “Naga yanda kuke fita sosai aiki da Aminu ne yasa banyi tsamanin zaka tuna ba?” Shiru yayi ya cigaba da shan Coffee ɗinsa saboda kamar magana ta gaya mashi. Har mota ta raka shi daganan ta sake kallon nata. Venza ce 2016 model kuma kana gani kasan tasha kuɗi. Wajen 10am Jumy tazo tana zuwa sai taga mota a parking lot. Cikin mamaki ta tambaya Deela kona waye shine tace ai shiya turo jiya. “Dauko mayafinki mu shiga ciki muje muci ubanta” dama Deela ta iya tuki saboda takan tuka motar Mommy. A hanya suka dauke Mansura aka wuce da ita, suna isa kofar gidansu Yasmeenah sai suka tsaya a bakin gate wai ayi masu iso da ita. Daya tambayesu sunar su sai Jumy tace ace mata Naufal ne. Yasmeenah tana zaune tana kallon wani tsohon Comedy The big bang Theory Sai akace Wai Naufal yana jiranta. Dayake bata expecting ɗinsa sai bayan la’asar saboda yanada aiki sosai. Daga ita sai leggings da t-shirt kai babu kallabi ta ruga a waje saboda dama tana missing ɗinshi. Tana fita gate bata ganshi ba sai wasu mata uku. Tambayar maigadi tayi sai yace ai sune suke nemanta. Tana karasawa tareda magana, “Bayin Allah daga ina haka..?” bata karasa ba Fadeela ta dauketa da mari, zatayi magana saita sake kai mata wani. Hannunta biyu a kunci tana mamakin meya faru da ita, sai a locacin suka kalle juna kuma sun gane cewa sun haɗu a saloon. “me na maki da zaki mareni?” Ta tambaya. “ni bazan ce ki daina kula mijina ba, kawai nazo nayi maki bushara ne bcs kin kawo kanki gidan wahala. Saina nuna maki iskanci ba karuwai irinki kawai suka iya ba.” Anan Yasmeenah ta hasala, “Dama akan Naufal kika mareni shine na tsaya kallonki, wallahi zaki san wa kika mara?” Saita nufa Deela. Jumy ce ta mauje mata baki da jakarta. Nan take jini ya barke, kukan kura ta sakeyi saita koma kuma anan Mansura ta samu nata rabon tareda wanka mata mari. Da gudu maigadi ya shiga tsakani tareda korar su Deela. Sun tafi murna fal Ransu koba komai sun girgizata, sun koma gidan Deela a inda Jumy da Mansura sukayi mata sallama suka tafi. Ita kuma Yasmeenah kiran Naufal tayi a waya tana masa kuka akan matarsa tazo da gayya sun fasa mata baki. Yayi mamakin yanda ta sani amma wannan bashi ke gabansa ba. Zuwa yayi gida ko shiga da motarsa baiyi ba kawai yayi parking a waje saiya shiga ciki, motsi yaji a kitchen da alamu tana ciki. Zuwa yayi wajen baiyi wata wata ba saiya haska mata mari, “Wayece ki dake matar da zan aura?” yana huci kamar mayunwacin zaki. Hannunta akan kumatu tana hawaye, cikin muryan kuka ta soma magana “Nika mara? Wallahi ka mari aurenka” #NiDaDiyata *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [10/2 18:21] Dimples: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 29 ✨✨✨ *Lesson* "FASBIR SABRAN JAMILAH". Patience is one of d most beautiful attributes one can ever have, It makes one listen, understand, forgive, forget, endure and move on in life. May Almighty Allah in His Infinite Mercy and wisdom uphold our faith in Him and may HE grant us d best of this world & d best of hereafter. Ameen ******** Sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa, jikinsa yayi la’asar sosai. Dama yasan saurin hannunsa wata rana zai kaishi ya baro, daɗin abin Fadeela tanada hakuri kuma yasan zata yafe masa. Magana ta cigaba cikin kuka, “Duk Meka min à duniya bazanga laifin ka ba! Don ka ganni cikin gidanka ne” saita kashe gas dama ta daura ruwan miya ne. Zuwa tayi zata rastashi ta wuce, sai yayi kokarin kama hannunta. Da sauri ta kwace tareda nuna masa yatsa tana hawaye, “This is the last time da zaka mareni” sai tayi hanyar upstairs abinta. Shikuma yasan ya tabo ta saboda bai taɓa ganin tayi haka, koda yaci zalinta bata nunawa, burinta bai wuce ta kyautata masa ba. Haushin kansa yayi saboda ya bar shedan yayi tasiri a rayuwarsa. Barin gidan yayi saboda ya bata dama ta sauko, idan yaso anjima zai bata hakuri yadda zasu fahimce juna. Wayarsa yayita kara kuma Yasmeenah take kiransa. Kashe wayarsa yayi gabaki daya saboda yasanta da raki, yanzu hankalinsa baya jikinsa gwara yayi dealing da mace ɗaya tukun idan yaso gobe zaije wajenta. Deela tana hawa upstairs ta dauko wani zungureriyan akwati tareda buɗe drawer ɗinta. Zuba kaya kawai takeyi tareda tunanin zuci. Saida ta gama saita fara tunanin inda zata. Tasan cewa Mommy bazata barta ba sai kawai ta yanke shawaran zuwa gidan gona. Nan take ta ɗebo takalma da duk wani abinda zatayi amfani. Rufe gidan tayi saita bama Maigadi key idan Naufal ya dawo saiya bashi. Cikin sabon motarta ta shiga saboda bazata bar masa ba. Tana isa gidan gona taga Miemie a garden chairs da Khattab, su da farko basu ganeta ba saida ta sauko tayi hanyar boot tukun. Da hanzari suka tashi domin su taimake ta, “Anty kin dawo nan da zama ne?” “Eh Miemie” “Ke kuma babu gaisuwa babu komai kin rufeta da tambaya” inji Khattab. Daga nan suka wuce cikin gida. Sun isa cikin falon sai aka gaisa yadda ya dace, locacin Anty Saudah tana daki sai Miemie taje ta kirata. Bayan tazo an gaisa, sai kuma Khattab ya tashi wai shi zai tafi kuma Miemie tazo ta rakashi. Daga nan Anty Saudah ta soma mata kallon tuhuma. Kallon kasa ta somayi kana tace, “Aiki yayi mashi yawa sai goman dare yake dawowa tun safe, kuma ganida ciki. Yasa nace bari na dawo nan har na haihu” Shiru Anty Saudah tayi saboda tasan bashi bane kaɗai dalilin, sai dai kawai taji daɗin yanda bata koma gidansu ba ko wajen Mama da abin ya tabarbare. Mai aikinta ta kira taje ta gyara mata wani daki tareda canza zanin gado. Fadeela taji daɗi sosai yadda Anty batayi mata binkice ba dukda tasan karyan takeyi. Bayan an gama gyaran ɗakin saita wuce domin ta huta, daɗi taji sosai saboda yanzu bata da wani aiki sai bin gado ko hira. Sam bata kewar Naufal asalima haushin sa takeji. Wayarta ta dauka ta kira Mommy da Jawahir sai ta faɗa masu Exactly abinda ta faɗa ma Anty. Mommy tayi faɗa sosai akan dalilin da bata dawo da rainon gidanta, ita dai bata hakuri tayi. Tasan yadda Mommy ke san Naufal, yana zuwa sau ɗaya zata ce ta bishi. 8:30 pm.... Biyawa yayi Vanilla joints tareda Oasis ya siyo kaya shak’e da leda, yana isa gida yayita bugawa amma ba’a amsa ba. Komawa yayi wajen mai gadi ya tambayesa koba mutum ne. Anan ne ya mika masa key wai an bashi dazu ya mance bai bashi ba. Shiru yayi ya rasa me yayi zafi da ta tafi gida amma ya dauki alwashin Ko’ina taje saiya dawo da ita. Haka ya shiga cikin gidan gwiwa babu kwari. Washe gari Fadeela bata tashiba sai wajen 9am saboda ta kara barci bayan tayi sallah. Tana fitowa su Anty na kan dinning suna karin kumallo saita zauna itama tareda dasu. Ana cikin haka saiga Naufal ya shigo, kallo ɗaya tayi masa ta watsar saita bar dinning ɗin gaba ɗaya. Shikuma yazo ya dauki Anty Saudah aje bikon Fadeela sai yaga motar Fadeela a parking lot. Yaji dadi sosai saboda da kanshi zaiyi bikon abinsa, ba fariya ba amma yasan ya kware a watsa kalamai. Abin ya daure mashi kai dayaga har yanzu bata sauko ba. Shidai Fadeela daya sani batada riko amma yanda wannan ke kumbure kumbure. Zama yayi akayi gaisuwa da Anty Saudah, koda aka kai masa breakfast shayi kadan ya kurba. Anty ta lura yana inda inda saita mashi magana, “Lafiya dai koh?” “Dama bansan ko meta faɗa miki bane?” “Ban gane me kake nufi ba?” “Ina nufin ta faɗa maki dalilin zuwanta ne” “Eh tace yanzu bakada wani sana’a sai gantali yasa ta dawo nan har Allah ya sauketa lafiya” Shiru yayi, sai dai kuma yaji daɗi data rufa mashi asiri. Koba komai ta kara nuna masa ita mace ta gari ce. Tashi yayi ya bar Anty wajen zaune saiya tafi ɗakin da Fadeela take. Ita kuma bayan ta bar falon laptop ɗinta ta kunna tana kallon wani horror film mai suna Rings. Tanayi tana matse ido tareda rungumar pillow saiga Naufal yazo, ko sallamarsa a ciki ta amsa saita cigaba da kallonta. Mamaki ya kamashi sosai saboda ko gaida shi bata yi ba, asalima haɗa girar sama dana kasa tayi tamau tareda tsuke bakinta. Yana tsaye a bakin kofa yaga batada niyyar mashi magana. Shine ya soma magana kasa kasa cikin lallami da lumana, “Kinki kallona kuma ko gaishe ni bakiyi ba kin kyauta kenan, koma mene maki bai kamata ki dauki zafi dani........” Bata bari ya karasa maganar ba tayi pausing film ɗin saita figi wayanta ta shige bayi tareda banko kofa ‘dam’ Abinda yasa ta wuce ta kyaleshi baifi yanda ranta ya ɓaci sosai ba, saboda tayi alkawarin randa zata bashi amsa sai yayi mamakinta but yanzu gasu Anty bata so suji. Shikuma sororo ya tsaya shake da mamaki daya lura babu wasa a abinda takeyi, asalima kamar soyayyarsa ya fice mata a rai farad ɗaya. Haka ya rinka kallon hannun daya mareta dashi yana jin haushin kanshi saboda gashi yanzu ya kaishi ya baro. Ranshi na mashi kuna saboda baisan yadda zai yi da ita ba, dayake bata taɓa daukar zafi dashi ba so baima san me zaiyi ya wanke kanshi ba. Haka yayita tsayuwa gefen kofa ya jinjina da bango tareda daura hannu daya akan kwankwaso, ɗayan kuma ya dafe kai dashi. daya lura batada niyyar fitowa saiya fita, yana komawa falo saiya tarad da Yasmeenah tayi masa Missed calls kamar zata rusa mashi waya. Haka ya tashi yaje with the aim Zai dawo anjima ya dauki Fadeela su tafi gida. Ita kuma saida ta tabbatar ya tafi kafin ta fito tareda komawa ta kammala kollonta. Murguɗa baki tayi tareda magana a fili, "Babu inda zani, zama daram dam" Koda taji dawowarsa da daddare saita garke kofanta, yana turawa yaji karfi. Yafi minti uku tsaye yana tattara tunanin sa waje guda, “Abin yarinyar nan da gaske nefa!” ya faɗa cikin ransa. Gwiwa babu kwari yayi hira kadan tareda cin abinci saiya wuce gida, yanzu babu mai kwabarsa yayi waya da Yasmeenah sosai. Ita kuma murna fal ranta duk tsammanin ta agaban Deela yake wayan. Sai wani rangaji da kafa takeyi tanata mashi shagwaba, Sam Shikuma bai faɗa mata Deela ta gujeshi ba saboda yasan halinta na rashin hankali zata rinka ziyarar sa tayi making situation ɗinsa ya tabarbare. Kawai yace yayi handling komai bazata sake ba. Ita kuma harda samun waje wai sai Deela ta bata hakuri, wani irin kallo ya watsa mata kana ya soma magana a hasalce. “Halan bakida hankali ne? Matana mother of my child kike so ta kiraki? Better watch ur tongue” Kwafa tayi tana zumbure zumbure, dama kofar gidansu ne saita fita daga cikin mota tareda banging kofa. Tsaki yayi kana yace “Allah ya raka taki gona” Da daddare ta kirashi tana neman sulhu saboda ta lura ya fita iya shege. Kwana sunata tafiya babu alamar komawar Deela babu dalilin sa, kwance tashi yanzu satin ta biyu da barin gidan Naufal, tana jin zuwanshi zata bar duk inda take ta koma ɗaki ta rufe kofa. Haka tana sallar isha’i take kwanciya, babu mai takura mata daga Abba har Anty kullum cikin mata hidima suke. Gashi ta murmure ta kara fresh abinta hankali kwance. Yau Asabar tun takwas Miemie da Anty Saudah suka tafi islamiyya. Dama Abba a gidan Mama yake, Deela na zaune a falo sai gyangyaɗi ya ɗebeta. Muryan Naufal taji a kanta, a hankali ta buɗe sannan ta sake rufewa. Murmushi yayi saiya cigaba da magana. “Fadeela sarauniyar mata, babyna Matana na kaina, kece shugaba a cikin Matana a aljanna..... Haba babyna I’m sorry please” “Nagane laifina please kizo mu tafi gidan mu, wallahi nayi missing dinki, your smile, jokes, care in fact everything about my sweet Other half” Buɗe ido tayi domin ta kalleshi, green eyes dinnan Sai sheki sukayi. Kuma kana kallonsa kasan cewa yana cikin damuwa. Idan baka sanshi ba zakaji tausayinsa amma banda ita, ita yanzu zuciyar indai akan shine toh a bushe yake kamar stock fish, aslima haushin sa takeyi. Dayake mata magana muryanshi kamar narkarkiyan dalma ne a cikin zuciyarta. Zama tayi sosai ta gyara daga kishingiɗin, kallon up and down tayi ta watsar kana ta cigaba da kollonta. Shikuma yaje dab ta ita zai zauna tareda rike mata hannu. Da sauri ta mik’e dukda cikin jikinta, yanda tayi kamar an soka mata mashi, a fusace ta soma magana muryanta yana rawa. “Menene haka zaka taɓa ni? Baka burgeni ba! da sai kaje wajen matar da zaka aura saika taɓa ta” “Haba babyna ki daina faɗin haka mana, nace am sorry fah” “ Mai I’m sorry dinka zai kara min a jiki? Bazai kareni da komai ba kuma bazai rage niba. So I don’t need it” “Nika mara akan wata karuwa da batasan darajar kanta ba balle na wani koh? ai duniyar nan babu wanda yayi min abinda kayi min” “All the lies, deciet, betrayal for what? Haba Naufal! ban chanchanci haka ba a wajen ka. I thought I meant more than this to you” Kuka kawai yaci karfinta, shikuma jikinsa yayi sanyi tareda la'asar, saiya matsa wajenta zai taɓa ta, da sauri daja baya harda tuntube. Cikin kuka ta soma magana a hasalce, “karka kuskura ka taɓani, you’re done touching me” Cak ya tsaya bai iya motsi ba, yasan cewa yayi gaggawan ɗaukan hukunci but ya kamata subar komai a past tunda abin yafi two weeks da faruwa. Rufe ido tayi tanata masa bala'i babu kakkautawa, yanda kasan ta haɗiye tabarya haka take jin kanta a tsartsaye. “Wallahi  ban taɓa tunanin haka zai faru dani ba so soon, kaci amanar soyayya Naufal. Idan haka ake soyayya to I don’t want to have anything to do with it” “Baby please kiyi hakuri nasan na bata maki rai, but I promise to do better” “Don’t you dare lie to me kana so kace kasan yanda nakeji, you have no idea how I went through all the Loneliness, Kawai ka baka damu ba. Duk abinda nake maka baka taba gani ba” “Duk rashin mutuncin da kake min ban taɓa nuna bacin raina ba, kullum hakuri nakeyi. Ko ance maka banida zuciya soso ke wajen. Amma na shanye komai saboda hakuri shine zaman aure” "Shine zaka mareni akan......" Anan kuka yaci karfinta tayi shiru da magana saidai rasgar kukanta, muryanta ya soma dishewa gashi karfin jikinta yana raguwa. A hankali ya soma magana cikin nadamar halinsa, “please baby I’m sorry, kizo mukoma gidanmu, our home mu haife babyn mu” Dagowa tayi cikin masifa, “ Home! Wat home? Gidan da bakasan komai a kaiba saboda baka zama kun tafi gantali da Aminu office” Daga nan ta juya ta wuce tareda barin shi a wajen, da sauri ya sha gabanta. “Wallahi ka matsa min If not duk me nayi maka kaika ja ma kanka” saita kalle wani golf stick dake gefe, shima yana kallo saiya matsa mata kafin ta illanta shi. Kawai tunanin gwara yaje ya faɗa ma Mommy gaskiya, a dawo mashi da matarsa. Ita kuma rastashi tayi ta wuce hanyar ɗakinta. Binta ya cigaba dayi amma tayi burus dashi, tana tafe tana hawaye sanadiyar tuna irin rainin dayayi mata. Buɗe kofa tayi ta shiga daki, ta juya zata rufe kofa saita ganshi tsaye gaban wajen, fuskarta babu annuri ta harɗe gira kana ta fara magana confidently, “Ni da kai, we are done” Karab ta rufe kofar ɗakinta tareda saka key. #NiDaDiyata *I’m Dedicating this page solely to all the fans of NI Da Diyata, I really appreciate your love and support. Your awesome comments keep me going all the time. Allah ya barmu tare har mugama lafiya Amin* *Ya kamata Fadeela ta koma, kokuma ta zauna har saita haihu?* *Waiting for your answers* *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥 [13/2 07:02] Dimples: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 30 ✨✨✨ On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said that the Messenger of Allah (peace be upon him) said: When Allah decreed the Creation He pledged Himself by writing in His book which is laid down with Him: My mercy prevails over my wrath. It was related by Muslim (also by al-Bukhari, an-Nasa'i and Ibn Majah). ********** Kwanaki sai wucewa sukeyi babu alamar komawanta, da kanshi ya tafi gidan Grand Kadi ya faɗa masu abinda ke faruwa. Mommy ta kirata tayi mata faɗa sosai kuma tace she is disappointed in her, duk tarbiyan da sukayi mata saida ta watsa masu kasa a cikin idanu. Grand Kadi ne yace ayi mata uzuri  gwara ajita bakinta. Washe gari suka tafi gidan gona inda Fadeela take, Naufal yaci shadda dakarkiya fari ɗinkin babban riga. Yana tafe yana raha tareda full confidence yau zai tafi da matarsa. Kowa ya taru a falo, Big Daddy, Grand Kadi, Abba, Mommy, Mama sai kuma Anty Saudah. Sannan saisu Deela da Naufal. Grand Kadi ya buɗe taro da addu’a sannan ya fara faɗin fa’idojin aure. Daga nan sai Big Daddy ya fara magana akan batun auren su, Fadeela aka tambaya menene ainihin abinda ya faru tsakanin su. Bata ɓoye komai ta fayyace musu komai, kowa salati ya rinka jerowa bayan ta gama wanda ita a lokacin kuka takeyi. Mama ce ta soma magana “Amma baki kyauta minba, aida kin faɗa min da ban rinka bashi abinci ba idan yazo” Big Daddy yace yanzu babu wani sauran magana kawai Fadeela zata koma ɗakinta ta haihu a chan. Nan take Deela ta barke da kuka tana sheshek’a. Kuka takeyi babu kakkatawa kamar zata haɗiye ranta. Abba ne yace bai kamata Abi sarai ba, ayi mata hakuri tunda yanzu baifi saura wata ɗaya ta haihu ba. Dagowa Naufal yayi zaiyi magana sai Anty ta kasteshi akan ya rufe masu baki, dole yayi shiru tunda babu sa’anshi a wajen. Mommy ranta yayi bala’in baci saboda kawai ana sangartar da Deela ne, sau da dama mazajen wasu suna dukansu amma suke zaune ras, kawai dan an mare Deela za’a ce bazata zauna ba. Ita tana ganin ana bama Fadeela dama ta raina shi ne. Haka dai aka kyale Fadeela ta cigaba da zama gidan Anty har Allah ya rabata da cikin lafiya. Naufal ya nuna bacin ranshi a fili saboda ba’a gama magana ba ya fita daga falon ya koma cikin motarsa ya kifa Kanshi. Kuka ya soma rizga wiwi saboda ya gaji, gashi yanzu Yasmeenah ta sakashi a gaba wai saidai ya aureta kuma bazai soma zancen wani aureba tunda Deela bata gidan. Ita kuma Deela murna fal ranta ta samu nasara, Mommy magana sama  sama take mata bayan abin ya faru saboda takaici. Koda suka kebe a ɗakin Deela karfin jikinta kawai ta tambaya sai sukayi shiru. Kuka Fadeela ta somayi kana ta soma magana, “Mommy ki yafe min. Nasan na bata maki rai kuma zakice na watsa maki kasa a ido, but I promise you tarbiyan da kika min shiyasa yake kwaɗayin zama dani, please kiyi hakuri harna haihu tukun kafin ku mayar dani” Mommy kawai kallon Deela takeyi yadda ta kafe, ba k’aramin abu zai mayar da ita haka, duk cikin yaran family itace batada riko ko naci akan abu, tunda ta nace akan haka to gaskiya ita kadai tasan ukuban datake fuskanta. Murmushi ta sakar ma Deela saita matsa inda take ta soma bubbuga mata baya, babu komai baby, Allah ya sauke ki lafia” “Amin summa Amin” Bayan kwana biyu...... Naufal yana kwance a office ɗinshi abin duniya yayi mashi chunkoso, saiga Secretary ɗinshi ya shigo ya bashi wasu takardu. Nan take ya haushi da faɗa wai baza’a barshi ya huta ba, daga  nan yayi tsaki ya dauki jakarsa zai koma gida. Yana isa yayi horn sau ɗaya, biyu, uku kafin mai gadi ya buɗe masa. Aiko nan ya soma masa masifa yana mai barazanar kora idan bai dauki hankali ba. Yanzu yana Missing Fadeela to the extend daya zama very aggressive, kana kallonsa zai iya gaya maka magana  san rai, idan kai mai hayaniya ne sai faɗa ta kaure maku. Dakin Deela ya wuce wanda ya mayar nasa tun kwanaki, kwanciya yayi akan gado yana tunaninta ga kamshin turarenta ta Ko’ina. Abin bai isheshi ba dauko Chanel No 5 yayi ya fesa akan pillow kana ya runguma kamar ita ke wajen. Turaren da idan ta saka da yakeji kamar ya kasheta yanzu shine abin so wajen shi. Yana kwance sai cikinsa ya fara kiran ciroma alamun yunwa, babu kidan da bayayi daga yori yori sai bumper to bumper. Murmushi yayi mai kuna a rai kana yace a fili “Allah ya jikan Fadeela badan bata mutu ba, da yanzu tazo tana rok’ona naje naci abinci” Saida ya huta gajiyarsa yayi sallah tukun kana ya wuce kitchen yana kallon me zai dafa, Indomie ya yanke shawaran ya dafa tunda yafi sauki. Ya daura Indomie akan gas saiya fara kokarin buɗe Geisha. Cikin Kaudi ya karya karamin handle din abun dole yayi amfani da wuka. Ya dukufa yana wannan ashe ya mance bai saka seasoning ba, maganar albasa da kayan miya bai taso ba saboda baima yi niyyar sakawa ba. Kaurin konewa yaji gashi ko Geisha bai gama fafewa ba, yana zuwa da sauri ya taba zai sauke dama wajen electric ne. Nan take wuta ta fizgeshi, da sauri ya bar wajen saboda har cikin zuciyarshi yaji kamar za’a cire mashirai. Gashi bai cire ba, ga shocking ga kone hannu dayayi, saida yadan huta kafin ya koma gashi yana gani Indomie ɗin yayi kurmus yayi bakin kirin. Ko’ina kauri kamar ana gobara, kashe socket yayi saiya bar cikin kitchen ɗin bcs shi karin kanshi abin ya dame shi. Buɗe fridge yayi zai dauki koda lemu ne amma wayam saboda ya cinye komai tas kuma bai siya wani ba, koda yaushe Deela tana hanyar kasuwa idan ta lura abincin su yayi kasa. Haka ya sake hawa sama yaje bayi ya saka hannusa a cikin ruwa saboda yana masa zugi, gashi masu restaurant ɗin layinsu sun fara mashi sheda har sun daina cewa ‘Welcome Oga’ sai ‘Customer welcome’ Yanda yake sintiri gidan abinci ba kimansa bane a matsayinshi na namijin aure, daidai gwargwado Deela ta kare masa wannan hakkin saidai idan shine bayaso yaci. Shikuma yanzu baya son yana haduwa da Yasmeenah saboda tana stressing ɗinshi akan ya nuna soyayyarsa yace zai aureta. Shikuma ya bata uzuri akan tabari matarsa ta haihu tukun. Shi a locacin yanada tabbacin dole Deela ta dawo saboda batada wani excuse, sai yayi aurensa hankali kwance. Kuma abu na biyu dayasa yake gudun ta face karta gane cewa Fadeela bata gidan a irin cikin zance haka kafin ta raina shi akan ya kasa rike gidansa. Haka ya hakura yaje ya siyo kayan shayi wanda dama ya kare da bread, yana shiga kitchen zai daura ruwan zafi saiya tuna haɗuwarsu da rana, girgiza kai yayi ya bar wajen. Bayi ya wuce ya ɗebo ruwan zafi kana ya soma dakan bread ɗinsa. Yaci yafi rabin babban leda amma cikinsa kamar an shafa ne. Wani matsananci yunwa yakeji saboda rabon dasu haɗu da abinci tun jiya da suka fita lunch da Yasmeenah. Coke yayita sha sai yanzu, mukullin mota ya dauka yace gwara yaje gidansu kafin yunwa ya kashe shi. Yana isa parking lot yaga Miemie da Khattab suna cikin mota ana dariya. Haushi ya kamashi ya nufesu gadan gadan, su basu ma sani ba kawai suka ganshi a gabansu yana haki. Su kuma abinda suke ma dariya shine Khattab yana bata labarin Lili, yanzu baya ɓoye mata komai tun wani rana da Lili ta kira a gaban Miemie har yayi sanadiyar dena masa magana na kwana biyu. Yanzu baya ɓoye mata komai, duk shirmen data ke masa yake faɗa mata sai suyita dariya. Ita Miemie murna take ta samu wanda ta fita hauka. Muryan Naufal sukaji wanda shiya saka suka bar dariya tareda tsayawa cak. “Bana hanaku zance cikin mota ba?” Khattab ne ya fito yana kokarin mika ma Naufal hannu su gaisa amma yaki bashi, mayar dasu cikin aljihu yayi kafin ya cigaba da magana cikin faɗa. “Wannan wani irin abune? Idan kanwarka akema haka zakaji dadi? Koda yake bakada kanwa you wouldn’t know” Juyawa yayi ya kalle inda Miemie take tsaye tana tura baki, “wuce ciki, ta ɗin an fasa” Tura baki tayi tareda makale kafada tana bubbuga kafa a kasa, “Haba Yaya yanzu yazo fah!” “Ni kike gaya ma haka, Karyan iskanci! Ni sa’anki ne ?Wallahi na sameki a wajen saina karya ki” Saiya cire takalminsa ya nufa inda take, Khattab yana ganin za’a nakasa mashi Haskensa saiya ce mata ta tafi kafin taci dukan banza. Anan ta ruga tana faɗin “saina gaya ma Anty abinda kamin” ta faɗa tana kuka. Yaji haushin da za’a kai kararsa wajen Deela amma babu yanda zaiyi. Juyawa yayi ya kalle Khattab, da sauri ya shige motarsa kafin Naufal yayi masa magana tareda mashi saida safe. Shikuma saiya tafi cikin gida, yana shiga tareda sallama ya tarar da kowa a falo, as expected Deela a ciki ta amsa mashi. Murmushi yayi saboda komai zatayi bai zai koreshi daga rayuwarta ba. Miemie ta soma korafi akan masifan da yayi mata. Anty Saudah ce ta zungureta da kafa akan tayi masu shiru. Deela na daga gefe tana fere kankana da abarba. Zama yayi akan kujera harda canza masu chanel daga ZeeTv zuwa CNN, “Ya  haka Mallam?” Anty Saudah tace. Itama Deela taji haushin abin amma ta danne, dariya ya soma kafin yace, “news ne fah” “Maza ka canza mana, kaje gidanka chan amma nan gidana ne” Baiso ba ya canza masu, yana lura da yadda Deela taki kallonsa, yama mance yaushe rabon dayaga idonta. Kullum tana cikin kallon kasa kafin tabar wajen baki ɗaya. “Miemie jeki dauko min plate matana ta saka min kankana” ya faɗa yana kallon Deela yaga yanayinta. Babu musu tayi yadda yace, itama Deela ta zuba masa sosai yasha ya nare. Daga nan ta soma kokarin tashi tsaye, yanda takeyi komai da kyar gata da nawa asalinta. Gashi ciki komai a hankali zakayi, sannan kafarta sun kumbura sunyi narka narka kamar doyar Benue. Duk tausayinta ya kamashi. A hankali ta soma tafiya tayi hanyar ɗakinta saboda idanunsa yana takura mata. Bayan ta tashi Anty ta tambaye shi ko a kawo masa abinci, baiyi musu yace mata eh. “Daka rike matarka da kyau ai bazaka rinka bin gida je kwaɗayi ba” Anty Saudah ta faɗa sai tayi hanyar kitchen. Wani tunani ya faɗo mashi a rai ko ya auri Yasmeenah kurum koba komai zai rinka samun abinci a sauki. Wayarsa yayi kara kuma wanda yakeso yayi magana da ita ne. Yana dauka yaji kukanta sosai daga ɗayan ɓangaren, “da kyar nasha wajen Yaya Huzaifah” taketa nanatawa tana kuka. “calm down meya faru? Talk to me please” Cikin kuka ta fayyace masa abinda Huzaifah yayi mata, hankalin Naufal yayi mumunan baci. Hankalinsa ya kasa daukar abinda ya faru, ya kasa saisaita tunanin sa waje ɗaya. Wai ace wanda zai aura akeso a lalata, gwara yayi gaggawa ya aureta kafin suyi mata mai gaba ɗaya, besides jiran meya keyi! #NiDaDiyata *All Rights Reserved* 💥∂ιмρℓεs💥[15/2 19:52] DIMPLES: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 31 ✨✨✨ It was narrated that Wathilah bin Asqa' said "The Messenger of Allah (pbuh) offered the funeral prayer for a man among the Muslims and I heard him say: 'O Allah, so-and-so the son of so-and-so is in Your case and under Your protection. Protect him from the trial of the grave and the torment of the Fire, for You are the One Who keeps the promise and You are the Truth. Forgive him and have mercy on him, for You are the Oft-Forgiving, Most Merciful." ******** Bayan  ya gama cin abinci saiya yi masu sallama kana ya tafi gidan Mama inda Abba yake. A varenda ya iske Abba yana sauraron BBC hausa. Sallama yayi mashi sannan sukayi gaisuwan mutunci. Shima zama yayi gefe suka cigaba daji tare. Bayan minti akalla ashirin ya wuce basuce komai ba. Naufal shi addu’a yakeyi saboda yanaso Abba ya amsa batunsa babu gargada. Gyara murya yayi sai yayi adjusting zamansa, idonsa na kallon k’asa ya soma magana cikin ɗa’a. “Dama nazo muyi magana ne” Ya faɗa. Shikuma Abba rage karar radio sa yayi ya mayar da hankalinsa wajen Naufal, baiyi magana ba illa kallonsa yana jiransa. “Dama batun Yasmeenah ne nakeso aje gidansu domin ayi magana”da kyar ya karasa maganar muryanshi sai rawa yakeyi saboda yanda Abba ke kallonsa kur. “Bangane ba?” “Ina Nufin maganar auren mu” ya amsa. Ashe Mama tana jinsu sai tayi karab ta chapke. “Ban gane ba?Kamar ya kana so ka kara aure? Yaushe yaushe kayi aure ne? Ni duk daukana shiririta ne naku na yaran zamani ashe abin yakai haka. Ko mace ɗaya ka kasa rikewa balle biyu” ta faɗa, kara fitowa tayi varenda ta jingina da bango saita soma magana. “tuntuni ake fama dakai akan kayi aure amma kakiyi shine kake so a cikin shekara biyu kayi mata biyu koh? Bazai yiwu ba asha fate ranar sallah” ta cigaba da sababi. Abba ne ya tsinke ta tareda faɗin, “Inbaa aure shine za’a aure ki?” “Ai tunda shi yake son abinsa gwara a kyaleshi, tunda yanada halin da zai rike su. Kawai addu’a za’a bisu dashi Allah ya kauda tsautsayi da fitina” “Amin summa Amin” Mama tace daganan sai tayi shiru. Naufal yaji daɗi sosai saboda zai shiga sahun manyan mutane watau masu mata biyu. Abba ya umurce shi akan a gayama iyayen Yasmeenah gobe zasu kai gaisuwan iyaye kuma da sadaki duk za’a haɗa. Godiya yayi saiya bar gidan ya tafi hanyar gidansu Meenah, murna sosai tayi harda rungumarsa. Daga nan ta soma zuba mashi sabon shagwaba. Bai bar kofar gidansu sai wajen sha daya saura kadan. Washe gari anyi komai an bada sadakinta a dubu dari biyu, sai kudin gaisuwa dubu hamsin. An sanya biki da tarewa nanda sati shida watau ana kyautata zaton idan Deela ta haihu da sati biyu. Da Anty Saudah taji maganar ta rasa ta inda zata fara gayama Deela, zaunar da ita tayi ta fara mata nasiha akan hakuri. Ita dai Deela batasan meke faruwa ba amma tasha jinin jikinta. Da Anty Saudah ta gaya mata an saka auren Naufal ne, wani bakin ciki taji sosai wanda idan tana tsaye ne zata iya faduwa don takaici. Saisaita kanta tayi saita sunkuyar da kanta kasa saboda hawaye sun fara mamalo mata, “Anty Allah ya sanya alheri” abinda ta iya furtawa kenan. A hankali ta tashi da niyyar zuwa kitchen saboda danwake take so taci amma yanzu ya fita daga ranta, kawai su Anty zatayi mawa. Tafe take tana tunanin rashin alkawari irin na ɗa namiji. Sai dai in zama da kishiya ne baya damunta saboda kowa halinsa zai kwaceshi. Haka taje tayi abinci duk ranta a jagule, tana gamawa ta wuce daki tareda rufe kanta ta soma kuka. Lallai duniya budurwar wawa ne, idan ka saka shi a ranka zai kaika ya baro. Duk jindadin da kake ciki within seconds idan Allah yaso saiya mayar maka da tashin hankali. Ita dai tasan cewa kowa da nasa jarabawar kuma tana rok’on Allah ya bata Ikon cin nata. Fatan ta baifi Allah yasa ta sauka lafia ba babu wani complications. Yasa duk wani abu da Dr tace ta kiyaye daidai gwargwado tanayi. Dadin ta ɗaya shine tayi scanning taga gender ɗin abinda zata haifa. Yadda take da san gayu haka take son ta haifi mace domin ta rinka mata. Cikin ikon Allah abinda ke cikin cikinta kenan, yanzu duk siyayyar da zatayi ko Naufal ɗin kalar pink ake siyowa kokuma white. Sun siya su cradle, drawer, kaya daban daban komai dai na tanajin haihuwa. Mama ta saka an sak’a mata showel masu kyan gaske da kuma rigar sanyi na yara. Ita kuma Anty super ta dinka mata  na fitar suna, su kuma su Bilqees, Abla da Amatullah da Miemie anko sukayi wani material purple mai ratsan lemon green. Shikuma Naufal yayi ma Deela kala uku na fitar suna, sai kuma seti biyu na akwati da kit na faɗar kishiya. Sannan yayi ma kannasa kala ɗaya tareda iyayen sa duka. Ita kuma Yasmeenah ce masa tayi ya bata kudi ta siya lefenta da kanta tunda ita zata saka abinta, dama zataje Dubai siyan ma kanta kayan dakine. Tana chan tana Siyayya saita rinka kiransa akan kuɗi ya kare ya gaggauta aiko mata. Idan yayi mata korafi saita soma sababi tana cewa, ‘To keep a classy woman like her is not easy’ idan ta fada irin wannan abu yana mamakin ta sosai kamar ba ita ke rok’on sa ya aureta ba. Kuma zancen classy da take magana, da zata ga matarshi da batace komai ba. Tun kafin aje Ko’ina  har ya fara gajiya da yawan korafin ta. Ita kuma murna fal ranta ta samu mai kuɗi gashi kyakyawa zata aura. Siyayya takeyi son ranta saboda tanaso bikinta ya jijiga Instagram. Events kala shida zatayi, za’a buɗe da Fulani day, Korean Day saboda tana bala’in san film dinsu, sannan Kamu, Mother’s Day, Bridal shower da kuma Dinner. Duk dinkinta a chan tayi, wedding gown dinta fari wanda zata saka ranar dinner Donatella Versace ta ɗinka mata. Burinta ya cika saboda komai yana zuwa mata yadda take so. Yanzu matsalar ta ɗaya shine yadda zata fitar da matarshi daga cikin gidan. Wani abin takaici shine ankai mata kaya jere cikin gida sai akace ɗakinta yana downstairs saboda duk na upstairs an cika shi. Abin yayi mata ciwo sosai amma ta kwantar da hankalinta saboda Hostile take over zatayi wa matarsa. Dole ayi juyin mulki, duk wani abu datake controlling zata daina ne, Karyan iskanci takeyi! Shikuma Mama ta gargade shi akan kada ya kuskura ya tada Deela daga cikin ɗakunan ta. Dama dakuna uku ke sama, kuma Deela na cikin 2 sai Naufal ɗaya. A kasa kuma akwai ɗakuna biyu anan Yasmeenah zata zauna, kawai dai dakunan manya ne ba laifi kuma sunada bayinsu. Batun kitchen kuwa lundary room aka kira carpenter yayi mata su shelves sannan aka kira plumber yayi sink da sauran su. Dayake d’akin karami ne bazata ji dadin kitchen ɗinba, Komai a marmaste zatayi. Bazata wata ya kamar yadda Deela zata baza tabarma a kasa ba taji dadi. Dama komai idan ba’a yi dakai ba bazaka ji daɗin abin ba. Dama shi Naufal ya tsara rayuwarsa da mace ɗaya ne yasa zuwan Meenah kamar takura masa ne. Yasmeenah ta dawo daga Dubai shake da kaya zata kaima dangin mijinta, fitted gown material ta saka Ja da rastin silver wanda ya dame ta. sai tayi wrapping kanta da karamin gyale irin na Arabs. Hannayenta kuwa wasu kwabɗa kwabɗan zabbai ne da warwazo. Takalmin nan dai mai tsawo tareda igiyoyi ke kafarta zata gaida In-laws. Su sun saba a turai, soyayya kawai yaro yakeyi da yarinya zai kaita gidansu ta gaishe da iyayen shi amma sam Naufal yaki. Ita kawai bataso tayi bakin jini wajen su yasa ta siyo masu turare zata kai masu. Bata sha wani wuya wajen gane gidan ba saboda kowa yasan architect. Ta fara zuwa wajen Mama kafin taje taga Miemie saboda yadda yake maganar ta. Koda akayi mata iso wajen Mama akan tayi bakuwa, mamaki ya kamata da taga yarinya zaune tana jiran ta. Gaisuwan yan bariki tayi ma Mama  Irin,”Sannu Mama, ya kike?” mamaki ya bayyana a fuskar Mama karara wanda ya hanata amsawa. “Yarinya daga ina?” Murmushi Meenah tayi kana ta fara magana cikin salo, “Baki ganeni ba koh?” “Ina zan ganeki baiwar Allah bayan ban sanki ba” Sosa gemu tayi tana dariya harda makela kafada, ita kuma Mama haushi ya kamata saboda bata Santa ba gashi tazo falon ta tana mata salo. “Mama nice fah Yasmeenah” ta faɗa tana dariya. Kallon hadarin kaji Mama tayi mata sai tace, “lafiya kika zo min gida” jikin Meenah yayi sanyi amma ta dake ta soma  magana, “Dama nace bari nazo na gaishe Kine, dama nayi tafiya ne shine nace bari na kawo maki wannan” “toh fah!”Mama tace tana mata wani kallo, irin kallon you’re not welcome. Gyara zama tayi da kyau tana fuskantar saita soma magana idanunta babu wasa a cikin su. “Mu fah a al’ada tun kaka da kakanni bamu saba budurwa taje gidan saurayi ba gaisuwa. Asali sai an kaita gidanta dangin miji zasu san fuskarta.” Kara gyara zama tayi ta kalle Meenah da kyau kana ta cigaba da magana fuska a murtuke “koh matar Naufal watau Fadeela bamu sakata a ido ba, bata bi gida gida tana neman fada. Amma kince tsaraba kika kawo min koh? Toh ajiye kan table” Daga nan sai Mama ta mayar da hankalinta kan SunnaTV dake aiki. Gwiwa babu kwari ta aikata abinda akace saita ce ma Mama “sai anjima” “Yauwa mu jima da yawa” ta amsa ko kallon gefenta batayi ba. Tunda Yasmeenah take ba’a taba mata wani abu daya taɓa taba kamar yau. Ranta a jagule ta shiga motarta tayi hanyar gidansu kafin taje wajen Anty Saudah ayi mata wanda yafi wannan. Ita kuma Mama ganin Ikon Allah ta tsaya yi wai budurwar da zai auro kenan, duk fake lashes da fake hair. Gashi sai yauki takeyi kamar danyen kuɓewa. Naufal ta kira tayi mashi tas, shidai bata hakuri ya rinka yi kuma yayi mata alkawarin Yasmeenah zata canza yanayin shigar ta. ********* Kwance tashi an kai satin haihuwar Deela, kullum cikin tambayarta akeyi ko tana jin wani ciwo amma sai tace masu ah ah. Ita kuma sam bata jin komai saidai kafarta daya daɗe da kumbura, sau ɗaya bayanta yayi mata ciwo kuma cikin darene kafin safe ya daina yasa bata faɗi ba. Dayake kitchen ɗin Anty akwai kananan kwari da kyankyasai, sai Deela ta saka maganin kashe su daga nan ta fita da duk wani kayan kitchen da Anty ta mallaka zata wanke. Babu yanda Mai aikin Anty da ita kanta Anty ɗin basu hanata ba amma ta kafe, acewarta ai akan kujera zata zauna kuma hannunta suna aiki sosai. Da taimakon Miemie sukayi tas tareda mopping kitchen komai yayi charasras. Bayan  nan sai Deela ta haɗa masu dambun tsaki wanda yasha alayyahu, yakuwa, gyada, kashi, nama da sauran su. Kowa yaji daɗin abin saboda a babban paranti aka zuba masu, Abba da Naufal aka zuba masu tare tun dayake ya zo kawo masu katin daurin aurene saiya taras an gama, shine yace bari yaci mai dadi kafin ya tafi. Su kuma su Anty da Deela tareda Miemie a round tray Babba suka saka nasu, sannan ga kakiɗi a gefe suna aunawa ciki. Bayan kowa yayi nat ya nare, Naufal ya tafi itama Deela ta kwanta. Wajen sha ɗayan dare sai bayanta ya rike yana mata wani irin zafi. Zufa ya rinka yankomata ta ko’ina, dolenta ta sauko daga kan gado tana addu’a tareda safa da marwa cikin tsakar ɗaki tareda bankare baya. Zafi sai karuwa yakeyi wata sa’in kamar ana tsikarinta. Saidai kawai ta tafa hannunta tareda rankamo salati tanayi tana sukurkurta gashin kanta. Hawaye takeyi tana kokarin matse bakinta saboda bataso ta tashi kowa, wajen ɗaya da rabi sai ruwa ya fara fitowa ta kasanta. Aikuwa duk wani dauriya datake yi ta daina, kwala ma Anty Saudah kira tayi. Dayake ɗakin Miemie yafi kusa so ita ta riga zuwa. Abinka da tiles koina santsi yake gashi ɗakin sharkap. Nan take Anty ta haɗo mata kayan haihuwa kamar su zannuwa, auduga, detol, glucose, kayan jariri, pampers, feeding bottle etc. Ita kuma Miemie tana daga gefenta ta riketa tana kuka, Abba yanada bakin kofa ya haɗe hannu a kirji yana tausayinta. Sai ya tuna da Naufal, zuwa yayi ya dauko wayarsa domin ya kirasa amma yaji switch off. Ranshi yayi matukar baci amma babu yanda zaiyi, shikuma Naufal daya kaima Yasmeenah katin aure sai Aminu ya kirashi, karban wayar tayi ta kashe. Acewarta idan suna tare dole yayi respecting ɗinta ya kashe wayarsa, toh tun daga lokacin bai tuna ya kunna ba. Abba ya tuka motar da aka kai Deela wanda a locacin kuka kawai takeyi, Anty Saudah na yin mata sannu ita kuma Miemie na tayata da kuka tareda fiffita. Nurses sun karbeta an wuce da ita maternity ward, saidai ba yanzu zata haihu ba zata iya kai 7 ko 8 na safe. Abba bai kira kowa ba yana jiran asuba tayi tukun. Anty Saudah alwala ta dauro tayi sallah tareda neman mata easy delivery, ita kuma Miemie addu’o’i kawai take to fah mata. Cikin awa kadan ta canza kaminta sai fizge fizge takeyi tana jefa hannu gashi kuma bayanta kamar zai balle. 4:53am..... Har locacin bata haihu ba illa bakin azabar data kesha, ta kama bakin gado da jikin Miemie harta gaji. Gabaki daya babu wanda ya runsta a cikinsu. Kowa tausayinta yakeyi ga uwa uba mijinta baya wajen. Bayan sunyi sallah sai Abba ya kira su Grand Kadi ya sanar dasu halin da ake ciki. Cikin minti talatin suka garzayo tunda safe ne babu hold-up. Mommy na ganin halinda Deela take ciki ta fashe da kuka, Daddy ne ya kwaɓeta akan Fadeela tafi bukatar adduarta akan kukanta. Nan ta shiga mata sannu tana hadawa addu’a. Har wajen bakwai saura wayar Naufal baya shiga, Abba ne da kansa ya tafi gidansa yaji ko lafia. Kwance  ya riske Naufal a falo yana sharara barci. Daga alamu tun daya dawo daga masallaci yakeyi. Zungurinsa yayi saiya soma masa magana , “Kai haka zaka bar gidan kayi ta barci sai an shigo anyi maku sata” Naufal a firgice ya tashi dayaji muryan Abbanshi da safe haka cikin gidansa. Waige-waige ya somayi yana kokarin tantance ko mafarki yakeyi. Murje idonsa yayi saiya ga Abbanshi da gaske ke kallonsa, “Dama matarka muka kai asibiti wajen ɗayan dare, amma dayake ka kashi wayarka bazaka sani ba” Abba yana faɗi ya nufa hanyar kofa. A fusace ya figi mukullin motarsa wanda ke kan centre table yabi sahun Abba. Three quater baki ke jikinsa da riga mai guntun hannu amma bai dameshi ba. Haka ya soma tuki yana tunanin irin pain ɗin datake ciki. Yana isa gaban asibiti yaga su Anty Saudah da Miemie anyi charko charko ana kuka. #NiDaDiyata      *All Rights Reserved* #YarinyaMaiDimples [15/2 22:30] DIMPLES: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 32 ✨✨✨ It was narrated from Hakim bin Muawiyah, from his father, that a man asked the Prophet(): "What are the right of the woman over her husband?" He said: "That he should feed her as he feeds himself and clothe her as he clothes himself; he should not strike her on the face nor disfigure her, and he should not abandon her except in the house (as a form of discipline)." (Hassan) ************ Karasawa yayi da gudu tareda damkar Miemie yana tambayarta koh lafia. Cikin kuka ta faɗa mashi cewa Fadeela tana cikin labour gadan gadan yanzu. Anan fa hankalin sa yadan kwanta saboda duk zatonsa mutuwa tayi. Sakin Miemie yayi saiya karasa cikin asibiti, kukan Deela yaji tun kafin ya karasa wajen. Nurse Anisa take karban haihuwar, middle age woman mai akalla shekaru 35 a duniya. Shekarun ta wajen goma da aure amma bata taɓa koda ɓatan wata ba. Yasa idan aka kawo mai naguda take jagora tayi, cikin ikon Allah idan tana wajen akan samu Successful delivery. Da karfin tsiya ya tura kofan har saida ya buɗe, nurses ne suka zo da sauri akan ya fita amma ya kafe babu inda zashi. An kawo mashi sanitizer dasu hand gloves sai aka barshi a wajen, zuwa yayi da sauri kan gadon datake ya soma mata sannu. Tausayinta ya kamashi sosai saboda bazai iya kwatanta irin ciwon dake ciba, rike mata hannu yayi yana mata addu’a. Suna cikin haka tareda taimakon Doctor saita haifa baby girl ɗinta wajen 7:45am. Da sauri ya karba babyn ya runguma tun kafin a gogeta. Karin sallah ya soma yi mata tareda addu’a. Ita kuma Deela tana daga kwance tana numfashi kadan kadan, an karba babyn akayi mata abinda ya dace sai aka bashi ya fita domin ya nuna masu. Babyn kyakyawa fara sol kamar Deela saidai fuskarta sak irin na Naufal harda kalan idanun. Yana tafe inda su Mama suke fuskarshi zallan annuri yana walwala. Mai aikin Mommy watau Anty Husna ta soma guda tana faɗin anyi mata kishiya. Kowa yaso ɗiyar kuma ɗaya bayan daya suketa dauka ana mata addu’a. Koda aka bama Miemie tace su gama dauka saboda itace karshe, duk sun dauka daga ABBA da Grand Kadi kuma tasha addu’a daidai gwargwado. Daga nan sai Miemie ta dauka ta fara kallon ta, har ranta take jin san yarinyar komai about her is so innocent and fresh. Shima Naufal yanada ga gefe yana wasa da ita, baiji kunyar surikansa ko irin kunyar ɗiyar fari. Mama ce tace a kawo ta za’a bata glucose tasha. Daga shi har Miemie basu so ba amma babu yanda za ayi. Ana cikin haka saiga Deela an fito da ita tana taka kafa da kyar, ji yake kamar yaje ya dauketa amma kawai ya barshi. Kowa sannu yake mata har aka kaita ɗakin da zata huta kafin a sallame su. Anje an kwantar da ita tareda kara mata ruwa, su Doctor saida suka jinjina kokarin ta. Tana kwance kowa yana cikin dakin, Anty Saudah ta haɗa mata ruwan shayi cikin Katon kofi wanda yasha madara. Kamar madaci taji amma dole tasha, ita har locacin bata kalli meta haifa ba saboda kunyar iyaye. Tadai san kawai mace ne ɗiyarta, gashi babyn sai barci takeyi balle tayi kuka ta sake jin muryanta. Tana kwance a haka barci mai dadi ya dauketa, bata farka ba sai wajen sha ɗaya lokacin ruwan da ake kara mata ya kare. A hankali ta buɗe idonta taga yan barka birjik cikin ɗakin saboda baima isa mutane ba. Su Jawahir ana rike  da babyn lokacin, “Malama saiki tashi ki bata Nono tun dazu sai wani barci kikeyi kamar wanda tayi aikin wahala” ta faɗa tana dariya. Sinna kanta kasa tayi batace mata komai ba saboda tana bala’in kunyar su Mama da Anty Saudah, “Woow Maman Baby” Jawahir tayi exclaiming saita koma gadon inda Deela take domin su gana. Su kuma su Naufal  sunci Abinci sunyi nat saboda Bilqees da Abla sun kawo breakfast daya isa kowa. Doctor ta kira Naufal yayi signing takardun sallama. Nurse Anisa tayi masu sallama kuma tace zata rinka zuwa duba su bcs little one tanada shiga rai sosai. Ya basu kudi sosai fiye da bills ɗin haihuwa kuma an umarce Deela ta dawo nanda kwana biyu saboda aga lafiyan jikinta. Ita kuma Mai aikin Anty ta daura garwan ruwan zafi ana jiran Deela ta dawo tayi wanka. Darbejiya masu kyau da kwari  aka tsinko kuma saida ruwan ya tausa sau uku kafin aka juye a wani katon baho. Hajia Rabi matar Big Daddy tayi mata wankar da kanta. Tun Deela na ihu don azaba harta hakura ta daina. Nishi sama sama kawai takeyi, ita kuma Mama tayima baby wanka sau bakwai tareda gyarata tsaf ta saka mata kaya. Deela na fitowa daga wanka Jawahir ta taimaka mata ta shirya tsaf cikin wani atampha kore dinkin a shape na riga da zani. Tayi ras abinta sai kamshi takeyi sabuwar mai jego. Ta kowane bangare nuna mata kulawa akeyi, ko su samɗa da Jumaymah sun zo. Ita kuma Mansura bata samu daman zuwa ba saboda tana Abuja. An gama abincin rana inda akan dafa tuwan semovita da miyan karkashi wanda aka barbaɗa yaji da kuma man shanu. Ga nama jaɓa jaɓa saboda kowane loma saika hada dashi. Ga kuma peppersoup din kayan ciki a gefe yana jiranta, sai kuma kunun kanwa mai zafin gaske wanda yasha kayan kamshi. Kafewa tayi wai yayi mata yawa saboda idan taci zatayi katon ciki. Mommy ta zare mata ido dolenta taci tana tura baki, shima Naufal yana daga wajen garden yan cin nashi abinci. Jefi jefi yake aikawa akai masa ɗiyar sa. Son duniya ya daura mata da Mamanta. Shi ya tabbata yanzu Deela itace soulmate dinshi, burinsa bai wuce Deela ta yarda ta koma suyi rainon babyn tare cikin kwanciyar hankali babu mai takura masu. Kuma gashi har yanzu baiyi mata magana ido da ido ba, Waya ne ya kira kuma batayi wani cooperating ba. Bayan ya tambaye ta karfin jikinta saita amsa bata sake ce abinda yafi ‘uhm ko uhm uhm ba’ Shi dai yaketa watsa mata kalamai yana faɗin irin kewarta dayake yi. Da taga zancen sa bashida niyyar karewa sai tace yan barka sunzo zatayi attending masu, daga nan saita kashe wayar. Ita kuma Yasmeenah ya kirata ya gaya mata sau ɗaya zasu rinka waya kuma da daddare ne saboda yanzu his family needs him. Abin yayi mata ciwo sosai amma saita danne. Congratulations tayi mashi tace ya tura mata pictures,ko sau ɗaya baiyi crossing ranta akan taje barka ba. Laila kawarta ta kitsa mata akan taje kafin Deela ta kullaceta. Tunda bikinsu bai wuce saura sati biyu ba so itama family ce, ita Laila abinda yasa tace haka bai fi yanda take mutuwar san yara ba. Yasmeenah taje stores ta ciko leda wajen uku da kaya na yara da niyyar kaiwa ranar suna. ******** Nurse Anisa takan zo duk safe kafin ta wuce aiki domin ta duba lafiyan Deela dana baby. Ko ranar daya kamata ayi ma jaririya allura ita tazo ta dauketa sukaje tareda Miemie suka dawo. Matar mutunci kowa na yaba yadda takeda halin kwarai, yanzu kawance ya kullu sosai tsakaninta da Deela. Wajen taran dare jajibarin suna, gida ya cika da yan suna daga Ko’ina duk anzo tayasu murna. Ga raguna manya manya wanda suka amsa sunarsu guda biyu sai kuka sukeyi. Abinci kuwa, Mommy ta dauki nauyin girka komai daga catering company ɗinta. Shi tuntuni ya saka ma yarinya suna saboda masu printing su Memo da paper bags. Saidai bai faɗi ba. Ita kuma Deela ta goge sosai tayi fresh kamar ta rinka haihuwa koda yaushe. Tana wanka da ruwan zafi sau biyu yadda ya dace kuma an fara koya mata yanda zata rinka ma kanta. A nesa yake ganinta kuma yana kallon ta yana hadiye miyau, ya lura hankalinta kwance bata ko missn ɗinshi, ba kamar yadda yake kwad’ayi su zauna tare ba. Gashi tana shan kunun kanwa sosai yasa kirjinta ya cika da dukiyar fulani. yarinyar ta bata rasa abinci,  ci takeyi sosai saita ture. Itama tayi murmur tayi yar kiba, very chubby ga kuma fara’a. Sannan dimples dinta waje biyu sun lotsa sosai, gata kuma da gashi tunda ta biyo babanta. Tana zaune a bakin gado tana shayar da yarinyar ta, yanda yarinyar keshan Mama yana karasa ma Deela taji sonta cikin ranta. Murmushi kawai take yi saboda soyayyarta ya mamaye mata rai. Ita yanzu batada wani farin ciki daya wuce ɗiyarta, duk wani san duniya ta daura mata. Tana ganin tafi Maman sharukhan a Kabbi Khushi Kabbi Gham san yaro. Dukda ita wancan daga gate tana jin alamar shigowarsa. Tana cikin haka sai ga Naufal ya shigo, sallama yayi tareda saukar mata murmushi. Fuskanta babu yabo babu fallasa ta amsa mashi. Jawo kujerar mirror yayi saiya zauna dab da ita ya watsa mata ido kur. Sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da ɗiyarta. “Baby Yanzu kin dena kallona” ya faɗa. Ita kuma bata amsa ba saboda bama tada niyyar magana. Mika mata hannu alamar ta mik’a masa yarsa. Babu musu ta bashi, ita jaririyar harta soma barci dama abinda takeyi kenan all the time. “Yarinya mai kamada the gorgeous Fadeela” ya faɗa yana kallon ta. Murmushi tayi kadan saita kauda fuskarta.shima murmushi yayi wanda ya bayyana kwarjininsa da kyau. Riko hannun Deela yayi sai tayi kokarin kwacewa amma ta kasa, “Baby kiyi hakuri da abinda nayi maki, nasan ban kyauta ba amma inaso ki yafe min. Rabon kwado baya wuce cikin ruwa, Allah ya kaddara min auren nan tun kafin nazo duniya, please inaso mu runguma kaddara mu mance da  differences dinmu” Gyara zama yayi sosai saiya tallabo ma Deela gemu kana ya cigaba da magana. “Haba uwargidan Naufal, uwar gida zuciyar miji, uwar gida sarautar mata,uwar gida lantarkin gida, uwar gida babu kamar ki” “I know you are a strong woman, Koda yaushe kina kokarin ki ɓoye damuwar ki koda yana cin maki rai. Kuma nasan cewa deep down you don’t hate me, kawai you miss me ne.” “Nima wallahi i miss you, gashi yanzu babyn mu tazo. Ko ba zakiyi don ni ba Please kiyi saboda Pha’eexah” Daga ido tayi tareda murmushi saboda yanzu taji sunar yarinyar, Daga mata gira yayi yana dariya. “Eh na saka mata Pha’eexah, please ki dawo mu raineta tare cikin gidan mu, Baby i love you so much” Matse mata hannu yayi cikin kulawa yana mata wani irin kallo mai rikitarwa, gashi idanunsa sun canza kamanni, kana gani kasan yana cikin tashin hankali ne, “Baby Karki Bari kishi ya raba mu, kinsan cewa kece kika fara nuna min asalin soyayya, kece farkon matana a duniya kuma in sha Allah harda aljanna” “Gashi kuma kin haifar min wannan Beautiful Angel mai kamada ke, please i need my family back. Baki lura you are my first everything bane, Komai dazai faru dani second ne saboda kin riga kinyi min komai and I will forever cherish you for that. Baby bakiga Allah ya riga ya karrama kiba tareda baki girma, girma fah baiwa ce! Please i will do anything Dan Allah ki yarda kawai ki dawo wajena” “Banaso kuyi min nisa keda Pha’eexah, kinason na canza maki motane ko kayan daki? Just name it baby please” Ita kuma a dikilce tace, “I like my furnitures and my car, thanks” saita juya fuskanta. Dukawa kasa yayi saiya daura kanshi akan cinyarta, “Baby please ki dawo wajena, ina shan wahalar rashin ki, please gobe ko jibi sai ki dawo koh?” saiya duba yaga yanayinta. “Okay zan yi tunani” ta faɗa Da sauri ya dago tareda rungumota, ingijeshi tayi saita ce, “Sakeni Mallam, baka lura jego nakeyi ba halan” Suna cikin haka sai ga Miemie tazo rike da pillow tana hamma daga alamu barci takeso tayi. Dama tun haihuwar Pha’eexah take kwana tareda su. Patting bayan Deela yayi saiya sumbace yarsa a goshi kana ya tafi, yana tafe yana annashuwa bcs he is hopeful nanda Kwana biyu zata dawo. Ita kuma Deela tana tunani gwara ta koma, ko babu komai yanzu akwai rabo tsakanin Su. Bazata yarda wata yar bariki ba ta rainan mata yarinya. Kuma bazata  bari azo a kwace Naufal haka kurum ba, ta gama taming dinshi, ta nuna mashi yadda ake Soyayya shine za’a rabata dashi. Zata koma ɗakinta kuma zata zauna, zata nuna mashi ta fita daban cikin sauran mata. #NiDaDiyata *All Rights Reserved*     ~Yarinya Mai Dimples~©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 33 ✨✨✨ ~LESSON~ Life comes with both happiness and sadness. Learn to be patient when sad and be grateful when happy. Allah will reward you and elevate your status. It was narrated from Hafsah, the wife of the Prophet (pbuh) that The Prophet (pbuh) said: "Going to jumu'ah is obligatory for everyone who has reached the age of puberty.'" (Sahih) ********** Ranar Suna... Tun wajen karfe hudu na asuba as usual aka daura garwan ruwan wanka, wajen biyar da yankai ruwan yayi tausa uku aka sauke ma Deela. Anty Saudah ta tada ta locacin data tashi sallar asuba, as usual Miemie ne mai rike Pha’eexah idan Deela ta shiga wanka har saita fito. Yau da kanta tayi wanka yasa saida  ta dauki lokaci, abinda akeyi na minti talatin saida tayi wajen awa daya, tana fitowa little one tayi kuka ta gaji tanaso taci abinci. Zama tayi gefen gado ta soma shayar da ita, tana tunanin sun kusa komawa inda ya dace watau asalin gidansu. Jawahir kawai take jira ta iso saita faɗa mata cewa gobe takeson komawa tunda Mommy bazata zo gidan suna ba irin yadda al’adan Mallam Bahaushe yake. Shikuma yayi radin sunar Pha’eexah a masallaci tareda gayyata walima karfe biyun rana. Kowa yayi masa fatan alheri tareda addu’a, yaji daɗi sosai yanda aka nuna masa kulawa saboda limamin masjid ɗin yayi alkawarin zuwa. Wasu tun daga nan suka soma kiransa da Abu_Pha’eexah kuma  yaji daɗin abin sosai. Kiran Deela yayi after that ya faɗa mata, itama sanya alheri tayi kana suka cigaba da magana. Yau tayi mashi magana daidai gwargwado, kuma shima abin ya burgeshi sosai domin har cemata yayi suyi breakfast tare. Babu musu  wajen 7am ta saka aka kai kayan abinci ɗakin Abba saita kirashi a waya yazo suci. Kunun kanwa ta zuba masu da kosai, shi bawai yana san abin bane amma tunda Deela tanaci kuma bata mutu ba toh shima zai sha. Bata wani sha sosai ba dama batasan cin abinci tun asalinta. Yayi mata magana saita ce masa ta koshi ne, wasa da hannun Pha’eexah takeyi while ita tana tsotso. Wayar Anty Saudah suka gani akan ya saka Deela taci abinci kokuma Deelan ta fito haka an fasa breakfast ɗin tare. Mika ma Deela kokon yayi amma taki karba. Asalima murguda masa baki tayi saita kawar da fuskanta gefe, rok’o yakeyi amma ta kafe akan bazata shaba. Haka ya hakura saiya sha harda nata kason saboda idan Anty ta riske abinci cikin kwano zata saɓa masu. Shi bai damu idan anyi mashi faɗa ba, kawai ya daukin ma kansa alkawari ne akan Fadeela ta daina zubar da hawayen takaici saina farin ciki. Yanaci yana zaro ido gashi ko rabi bai shanye ba, tun Deela tana matse dariya bata san sanda ta bushe tayi a bayyane ba. Kallon ta yakeyi yana jin dadin yadda take nishaɗi. Murna fal ransa saboda koba komai shine yasata dariya, “this is beginning of a new era, Yanzu zaki rinka samun farin ciki sosai” shi duk zatonsa tunanin zuci yayi ashe ya faɗa a fili kuma taji. Gimste dariyar tayi ta cigaba da kallon yadda yake shan kokon cikin wahala, sam batayi tunanin taimakonshi ba saboda dama tana so tayi watching weight ɗinta amma babu dama. Ya gama kenan saiga Anty ta shigo kamar an aiko ta, tana ganin kwanon empty sai tayi murmushi kana ta tafi. Deela still murguda masa baki tayi tana masa gwalo. “baby kin koya rashin kunya koh?” Ya faɗa tareda janyo ta jikinsa. Tureshi tayi saita matsa baya kana tace, “Sake ni mana, jego nakeyi” “Shikenan bazan rike matana ba domin tana wani jego” “Eh” saita wulla masa idanu. “Oh really! Ni da matana.... Okay bari naga wanda zai hanani” saiya nufota gadan gadan. Jan baya takeyi shikuma yana mata smug face yana matsawa kusa da ita. Dataga babu sarki sai Allah saita mintsili Pha’eexah dake kwance tana jin daɗin barcin ta. Tsandara ihu tayi sai yayi sanadiyar kaste mashi hanzari, kallon babyn dake kuka ido rufe sukeyi. Daga na sai babyn ta buɗe ido tana kokarin ganin waya tada ta, bushewa da dariya sukayi saboda it was funny. “Allah ya soki, yau danayi maganin rashin kunyarki. Ki gode ma Pha’eexah” “Allah dai ya soka saboda nidai bani tsoron ka” tana maganar ta sunguma diyarta suka bar ɗakin a guje. “Ai da kin tsaya mana” ya faɗa yana dariya. 12pm....... Mutane sun fara hallara, Mommy ta aiko da duk wani abinci da za ayi amfani dashi. Daga su White rice, coconut rice, fried rice, tuwan shinkafa, sakwara, alale, samosa, spring rolls, doughnuts, salad da coslow etc. Drinks Kuma akwai na gargajiya kamarsu xobo rodo, ginger, kunun aya dana zaki, sai kuma anyi Punch, milk shake Gasu katon katon ɗin Coke dasu fanta. Su Miemie anci kwalliya kamar za’a fashe domin kyau, ankon da suka ɗinka suka saka yanzu kafin anjima kowa ta canza zuwa personal ɗinsa. Fadeela cikin atamphan da Anty ta ɗinka mata take, ɗinkin yasha aiki da stones kowa yabawa yakeyi. Baby Pha’eexah kuma mai green eyes ta saka riga da skirt fari sol. Daga ita har Mamanta sun saka gwalagwalai na yan kunne, sarka da abin hannu. Su Samɗa anzo ana tayata murna. Sosai kawayen Deela  sunyi mata kara, kusan kullum suna tafe cikin so su duba lafianta. Itama Anty Anisa ma haka saidai yau bata iso da wuri saboda tanada wani uzuri. Samɗa baby clothes masu tsadar gaske ta kawo mata guda uku, sai sinkin sabulun wanka dakuma na wanki biyu biyu. Itakuma jumaimah Dankunnen gold ta kawo ma baby,Mansura kuwa dayake ta iya ɗinka su duvet da throw pillows. Shi ta ɗinka ma baby Pha’eexah na yara. Sauran kawayen Deela duk sunzo kuma sunyi mata kara, yau taga amfanin mutunci. Wulla ma Mansura waya tayi saita ce, “Kashe mana hotuna masu kyau sosai NI Da Diyata” “Wooooo! Masu yara, badai dani kikeyi ba” Samɗa ta faɗi tana dariya. Deela bata amsa ba illa mayar da hankalinta kan hoton da ake mata. Ita kuma Yasmeenah saura sati ɗaya ta mallake Naufal, tasha gyaran amare harta koshi. So take idan Naufal yaji yadda take saiya manta da tsohuwar matansa. Gashi fatanta yasha coiling saboda yayi farin gaske, dama Deela ta fita haske amma yanzu ina ai wutsiyar ragumi yayi nesa da kasa. Wani pink lace ta dauko wanda akayi mashi ɗinkin gown fitted, saita haɗashi da blue fashion earrings da Kuma su abin hannu. Hajjoe Makeovers ta kira suyi mata saboda bata so ‘yan suna su rainata. Komai nata is ready kawai tana jira la’asar yayine sai Lubna da Laila su rakata. Ta kira Naufal taji inda yake saiya ce mata yana gidansu saboda anan za ayi taron suna. Toh anan taji inda Deela take dama tanata zulumi saboda bai taɓa faɗa mata location ba. Yanzu sai dai kawai yaji taje saboda bata faɗa mashi ba. Tana so ta nuna mashi ita mace ta gari ne tunda ta ajiye kishinta zata ganin yarsa. Shiko Khattab yaci kwalliya kamar shine uban jaririya, program ɗin wajen biyu za’a fara amma shi tun ɗaya yazo saboda ya samu su zanta da Haskensa. Yanzu yana jira a gama taro sai ya tambaya Naufal auren kanwarsa. Ya riga ya gaya ma Mommy ɗinsa komai akan Miemie kuma tayi naam da batun sa. Ita yanzu komai na Lili ya isheta, fitsari sosai takeyi mata yasa itama ta mara ma Khattab baya ya auro wanda yake so. Kuma cikin ruwan sanyi zata canza ma Daddyn Khattab ra’ayinsa. By the time idon Lili zai buɗe lokacin it will be too late. 2 pm... Su yan uwan Fadeela sun iso, wasu daga chan kauyen su watau shira wasu kuma daga cikin Bauchi da sauran garuruwa. Anata walwala da annashuwa saboda yafi daurin auren Deela armashi. Amarya ta canza zuwa shadda blue dayasha aiki gaba da baya kuma daga sama har kasa. Gashi Mansura ta tsala mata kwalliya da kuma gwargwaro style, kowa burgeshi takeyi saboda kana ganinta kaga yar gata. Mitsi Mitsi kadan Naufal zai kirata yaji lafiyarta, an kawo abinci taci. Wannan Karon babu Naufal da zai tayata, haka ta rinka tura sakwara da miyan agushi wanda yasha stock fish, dry fish da kuma ganda. Idon Hajia Rabi kur a kanta tana jiran taki ci ta mazgeta. Taci rabi saita ɗaga ido taga ko Hajia ta daina kallonta saita ajiye. Lokacin kuwa Hajia  tana waya, da sauri Deela ta cire hannu tana lashewa. “Idan baki cigaba daci ba saina ballaki na balla banza” Hajia ta faɗa tana zare ido. Kashe wayar data keyi tayi saita cigaba da sababi. “Wai ace kamar yarinya karama kullum sai anyi k’aramin badar dake akan cin abinci. Ke baki ciba mai kike so Pha’eexah taci?” “Nifa bansan nayi katon ciki ne” ta faɗa tana matse kwalla. “Lallai yaran zamani da shiririta, toh gwara kici abinci kiyi dundumemiya ba kamar yadda kike da a bushe ba” wata kakar su dake gefe ta amsa. “Eh din, ai haka mijina ke sona” Deela ta amsa tana mata gwallo. “Toh daman wannan mai idon Mayun ai baisan kyau ba. In ba haka ba wazai aure mata a bushe kamar kara” “Ni wallahi ba a bushe nake ba” ta faɗa tana murguda ma tsohuwar baki. Ita Hajia na daga gefe tana jin daɗin drama ɗinsu. “Ni dama da biyu nazo suna, samun Naufal zanyi anjima na faɗa mashi nayi masa mata chan kauye yar duma duma” “Ai saiki aura mashi mu gani, wake tsoro. Kafan daya shigo da ita shi zai mayar da ita” sai tayi kwafa tana cin abinci. Haushin tsohuwar sosai taji yasa bata sake kulata ba. “Jikalle,haba Uwar gidan Naufal. Kishin ya motsa ne” Yake Deela tayi bata kuma cewa komai ba, suna cikin haka sai ga Miemie ta shigo zatayi sallah saita canza kaya saboda Sheik Kabiru Gombe yazo. Dama abokin Grand Kadi ne so shine yazo yayi huduba akan Tarbiyar yara a Musulunci. Mutane da dama sun hallara,kowa yazo ya kara ilimin sa. Mata an saka masu canopy cikin gida da fararen kujerun roba. Maza kuma suna daga waje an saka loudspeaker yanda kowa zaiji harda mutanen unguwa. Ita dai Deela bata fita ba saboda iska, tana zaune a daka tana ji, sudai su samɗa an tafi gaba gaba, gidan ya washe tas banda Deela. Shikuma Naufal yaci babban riga yayi kyau abinsa. Ya shiga ciki ya duba Fadeela, anan take faɗa masa gobe zata koma ɗakinta, yayi murna sosai saboda yayi mata alkawarin kujerar Makka as present ɗin haihuwa. Taji daɗin abin sosai dukda ta taɓa zuwa, nan ta rinka jero masa addu’a tana godiya. Jawota jikinsa yayi yana patting bayanta. Yau yasan cewa Hausawa sunyi gaskiya da suka ce, “Siya na gari maida kuɗi gida” Mace na gari daban take cikin sauran mata. Abinda bai taɓa haɗashi da ita Yasmeenah kenan, Addu’a bai taɓa shiga tsakanin suba. Shidai abinda yasani kawai sha’awarta yakeyi amma nothing else bayan wannan. Bata kuɗi sosai yayi akan aje ayo Siyayya abinda zata koma dashi, daga nan zai faɗa ma Bilqees da Miemie suje gobe su wanke mata abinda ya dace a wanke. Tareda gyara gidan tsab. Yau yaji daɗi sosai saboda mood ɗin Deela ya canza, murmushi kawai takeyi batada wani matsala. Daukar yarsa yayi ya tafi da ita wajen taron tareda kewar matarsa. 4 pm... Lokacin an gama tafsir an kuma ci sosai an sha, daga nan aka raba so souvenir. Maza daga waje an basu jaka wanda akwai hankachief, key holder, memo da biro, mug da kuma husnul Muslim. Mata sukuma nasu akwai Mascara da powder,sai memo da Husnul Muslim. Daga nan kowa yayi alwala aka fito da tabarma akayi sallah kafin kowa ya watse. Naufal ya tafi gidanshi ya dauko sauran souvenir saboda ya kusan karewa  na wajen. Su kuma cikin gida kowa hira akan wa’azi da akayi sukeyi . Kowa yana gasganta abinda akace akan sakacin da iyaye keyi akan tarbiyan yaransu, iyaye sun dauki ɗabi’un turawa da wasu al’ada masu gurbanar da tarbiya. Yara zasu girma basu san idan matsala yana damunsu suyi azkar ko sallah ba, ah ah zasu dauki waya da ear piece su saka wakar Lil Wayne ko Wizkid suna cashewa. Idan suka dauki rawar shoki daga sama sai sun kai kasa zasu dire, da kuma rashin girmama na gaba dasu. Saboda baka haifa mutum ba bazaka faɗa mashi gaskiya ba if not zai zageka tas babu ruwanshi. Deela addu’a takeyi Allah ya bata Ikon kare hakkin addini wajen tarbiyar da Yarta. Mai aikin Anty ta daura ruwan wankar dare, dariya Deela tayi saboda harta fara gajiya tun kafin a kai Ko’ina. Anty Anisa tazo tana basu hakuri akan rashin zuwa da wuri da batayi ba. “Haba  Anty babu komai tunda mun zama ɗaya” “Gaskiya ne, amma kuma aiki zai kai mijina Port Harcourt kuma gobe da asuba zani tafi.” Har cikin ran Deela bataji daɗin ba amma babu yadda zatayi, kawai fatan alheri tayi mata sai aka kawo mata abincin ta dasu souvenir. Itama ta kawo mata atampha na Da viva da kuma kayan baby. 5:30pm..... Taro ya kusan watsewa, mutane sun soma tafiya. An kawo gara daga gidanmu, akwatuna uku da kit akayi mani daga wajen dangina. Kayan abinci shake kamar su shinkafa, semovita, taliya dasu mangyaɗa. Wani mota ne ya shigo cikin gidan. Miemie locacin tana haɗa kujerun da akayi amfani dasu. Wani mota ne ya shigo sai taga yan mata su uku sun fito suna feleke. Sannu a hankali taje ta gaida su. A yatsine Meenah ta amsa, Laila ne da Lubna suka amsa da kyau. Daga nan suka tambayeta inda mai jego take, “Ku biyoni” tace masu. Sannu a hankali suka bita har inda nake, ni kuma na fito daga wankar dare har na saka Lace wanda akayi zani da riga simple dinki. Fuskana babu komai sai natural beauty ɗina, su Mansura kuwa anata kwalliya zasu tafi saboda saurayinta zai zo daukar ta. Su Laila suka shiga suka tsaya a bakin kofa, sallama sukayi tareda gaisuwa a tsartsaye. Ina ganin su na gane su, itama Mansura ma haka. Nan take muka haɗa girar sama dana kasa. Mika ma Miemie katon sallaya nayi akan ta shimfiɗa masu. “Miemie jeki kawo ma amaryan Yayanki abinci koh?” Mansura ta faɗa rai a haɗe. “OMG keh ce Miemie? wallahi MINE yana bani labarin ki all the time” Yasmeenah ta faɗa tana washe hakora. “Allah sarki” kawai tace tareda balla mata harara. Haushi ne ya kamata wai ace yanzu YaNaufal wannan yar iskan zai auro. Laila ce cikin fara’a tace a mika mata jaririya su gani, daga nan ta tambaya sunar ɗiyar. Yarinyar tanata ma Laila  murmushi har dimples ɗinta yana nunawa. Nan take Yasmeenah taji sha’awar ta, har cikin ranta taji soyayyarta. Gata tana kama sosai da Mine ɗinta, fuskar da kuma idanun. Itama mika hannu tayi a mika mata, tana karba ta fara mata wasa saita ta fashe da kuka maimakon dariya. Tanata jijigata a hankali amma taki shiru, Lubna ne ta karba domin ta gwada. Itama batayi shiru ba, ina daga kwance akan gado na hakince ni a dole matar gida. Anty Saudah ce ta shigo sai suka mika mata Pha’eexah “Jikata,kunyarsu kikeyi?” Anty tace. “She is not comfortable ne kawai around strangers” nace ina gimtse baki. Yasmeenah tasan magana ta gaya mata amma babu komai, nanda Next week Zata zama matarshi. An kawo abinci Meenah ko kallo batayi ba, kawai latsa wayar ta takeyi tana murmushi. Su Laila ne suke cin samosa da cake. Miemie ce ta shigo da sauri tareda wayana a hannunta wai YaNaufal yana kirana. Saidai kafin na dauka ya tsinke, Daga nan saita soma wasa ni. “ Anty yar gayu uwar gida sarautan mata, kece ta farko kuma kece ta karshe a zuciyar Yaya. You bring out the best in him” guɗa tayi kana ta cigaba da wasani. “ ke kura ce kuma dole karnuka suji tsoron ki, walkiya mai haskaka gari, ɗawisu adon tafiya.....” Zata cigaba saina tsinke ta. Ina dariya nace, “Ya isa haka mana, It’s getting lame” Itama Miemie dariya takeyi harda Mansura da Sadiya, “Anty ai gaskiya na faɗa” Su Yasmeenah haushi sukaji sosai, mikewa tsaye tayi wai zasu tafi, Laila ce tace Uwar gida bazaki raka muba, harda bazan kula maganar ba sai Mansura ta tashi wai itama zata tafi. Mika ma min kayan gaisuwan su sukayi kuma na gode masu sosai. An ajiye Pha’eexah cikin Craddle ɗinta saboda ta fara barci. Miemie ce ta zauna da ita saboda ɗakin babu kowa. Nikuma ina rike da  souvenir ɗinsu Meenah a hannuna har wajen motarsu kana na mik’a masu. Basu tafi ba nan take wai suna jiran friend ɗinsu dake unguwar ta zo ta samesu, sallama nayi masu kana na karasa wajen Motana inda Mansura take. Munata hira abinmu sai mukaji ihu daga cikin gida anayi ana salati. Da sauri muka karasa wajen shine akace wuta ne ya kama a dakin mai jego. Da gudu muka ruga domin baby Pha’eexah tana ciki, muna karasawa mukaga wuta yana ci fal fal fal kuma kamar chinnawa akayi. Kuka na barke dashi inayi ina kururuwa. Gashi kuma kofa a rufe gam babu daman shiga. Bubbugawa nakeyi ina kiran sunar yarinya na. Mutane anyi charko charko ana kuka,gashi an kasa shiga ciki. Duk abinda akeyi babu Miemie babu dalilinta. Wani cousin ɗin Naufal mai suna Hadi yazo ya rinka dukan kofar, daga bisani sai gashi ya buɗe. Da gudu naje zan shiga amma wuta ya korani baya. Ruwa aka watsa mashi amma kamar ana karawa ne, ina kuka duk na fita hayacina gashi kuma saura kadan ya karasa Craddle din Pha’eexah. Omo aka saka cikin bokatin ruwa sai aka watsa ma wutan sai ya fara lafawa, ina shiga na soma gudu kenan sai nayi tuntube da abu. Kallon da zanyi saina ga Miemie ce kwance a sume jini yana malalo mata daga fuska da alamun ta bige ne. Gashi wuta ya soma cin wajen cikinta. Kuka na sake fashewa da shi saboda ban taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba. Da sauri na tashi domin naje na dauko Pha’eexah tunda ya kusa karasawa inda take. Nan naga babu yarinya, gashi kuma wutan bai fara cin wajen ba. Dama yafi karfi a bakin kofa. Waige waige na samoyi ina kuka. Wata sabuwa kuma inji yan cha cha! Wayam kawai saboda babu alamar yarinyar nan a cikin ɗakin. Da gudu aka janye Miemie waje aka soma watsa mata ruwa amma hayaki yayi yawa a lungs ɗinta. Ko motsawa batayi ba kuma da kyar in akwai rai a tareda ita. kuka nakeyi sosai saboda tashin hankali baya misaltuwa, babu Pha'eexah gashi kuma Miemie rai yana hannun Allah. Duk na sukurkuce na kasa saisaita tunanina a waje guda. Wani tunani nayi saina ruga parking lot nayi ko zan ga Yasmeenah da ayarinta amma babu su a wajen. Nan take na yanke jiki na faɗi sumammiya. #NiDaDiyata ~Yarinya Mai Dimples~©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 34 ✨✨✨ It was narrated form Anas that the Messenger of Allah said "None of you should wish for death because of some harm that befalls him, rather he should say: 'Allahumma ahini ma kanatil-hayatu khairanli wa tawaffani idha kanatil-wafatu khairanli (O Allah, keep me alive so alive so long as life is good for me, and cause me to die when death is good for me.)"' (Sahih) *********** Nan take mutane sukayo kan Fadeela tareda kwanon ruwa, watsa mata akayi ana mata fifita.Tana farfaɗowa taga mutane charko-charko akanta tasan cewa ba mafarki takeyi ba da gaske ne. Nanta sake barkewa da kuka mai tsuma rai, ita kuma Anty Saudah tana chan tana ganin tashin hankali saboda Miemie bata motsi har locacin. Hadi ne ya sungumeta ya tafi da ita cikin Mota saboda zasu asibiti. Haka Anty tabi sahun shi a ruɗe ko mayafi babu, a hanya ne wajen parking lot wata ta mik’a mata hijabi. Deela na ganinsu ta mik’e wai zata bi su, anyi anyi a hanata tareda cewa ta zauna a gida kila Babyn an fita da ita unguwa ne. Nan Deela ta fashe da kuka, zama tayi dirshan a parking lot sai rizgar kuka takeyi. Kana ganinta gwanin ban tausayi, Hajia Rabi tazo ta janyeta daga wajen saboda maraice ne kafin sanyi ya shigeta. Bilqees ne ta kira Naufal ta faɗa mashi abinda ake ciki, dama locacin yana hanyar layinsu. Juyawa yayi ya nufa hanyar asibiti. Abinda yasa bai fara zuwa wajen Deela ba yasan cewa she is a strong woman unlike Anty Saudah. Yana isa locacin an shigar da ita ER, Hadi ne yayimasa bayani a gurguje. Ita lokacin Anty Saudah tana kan kujera tanata kuka a hankali. Tunani ɗaya  yake mata yawo a kai, ya zata yi idan ta rasa yarta ɗaya tilo. Nan ta soma kuka a bayyane, Naufal duk zafin dayake ji a ranshi ya shanye yana bata hakuri. Itakuma Fadeela tanata kuka kamar ranta zai fita, bata san Wanne yafi mata ciwo ba. K'onewan da Miemie tayi kokuma ɓacewan da Pha’eexah tayi? Idanta yayi jazur kamar garwashi domin kuka kuma kanta sai sara yakeyi. Ji takeyi  kamar Allah ya dauki ranta ta huta da wannan tashin hankali. Suma su Mommy sunajin abinda ya faru tazo gidan gona, anan kuma Fadeela ta soma sabon kuka, Mommy bata hanata ba illa tayata. Haka suka runguma juna sunayi gwanin ban tausayi, kowa a wajen tausaya masu yakeyi. Gashi Fadeela tayi trying wayar Naufal bai dauka ba. Sabon kuka ta somayi  saboda duk a zaton ta yana wajen Yasmeenah ne. Cema Mommy tayi bari taje asibiti wajen Miemie da Anty tunda anyi ransacking gidan ba’a ga Pha’eexah ba. Zamanta anan baxai fito da ita ba. Mommy bata hanata ba saboda ita ta tuka ma motar da suka tafi. Shikuma cikin ruɗewa ya bar wayar a cikin motarsa. Yasa bazai san wanda ke kiran sa ba. Su Grand Kadi da Abba sun tafi police station dasu gidan radio. A wajen police station ɗinne sukaga IG watau babban Khattab yazo duba abu wajen DPO. Nan take ya saka kwararrun yan sanda akan case ɗin kuma yayi masu alkawarin basu huta ba sai anga duk wanda akwai saka hannunsa a cikin abun. IG da kanshi ya kira Khattab ya faɗa mashi halinda ake ciki, anan fah Khattab ya ruɗe. Mukullin motarsa ya figa ya soma gudu babu ji ba gani. Sau biyu yana kusan aukawa ma trailer amma yana kaucewa da wuri. Haka yaketa yi harya kai asibitin. Ko rufe motarsa baiyi da kyau ba ya soma gudu ciki, lokacin kuma yayi daidai da isarsu Fadeela. Suna tsaye a bakin Emergency Room babu wanda ya fito daga ciki, likitoci ne keta aikinsu. Anty Saudah tana ganin Fadeela saita sake barkewa da wani sabon kuka, nan suka rinka yi su biyu. Duk cikin family suna cikin wanda sukafi shakuwa da ita. Shima Khattab yana ganin yadda suke kuka saiya kame chan kurya yana kuka. Hankalin Deela ya kwanta dataga Naufal a wajen. Tsagaita kukanta tayi taje inda yake ya dafa kumatu yana tunani ta zauna, riko masa hannu tayi ta soma magana cikin kuka, “Pha’eexah ta.........” saita barke da kuka, kwantawa tayi akan kafadarsa tana kuka wiwi. A hankali ta soma magana, “Shikenan an tafi da ita, na shiga uku na lalace” tana kuka sosai wannan karon kamar ranta zai fita daga jikinta. Lokacin yayi daidai da fitowan wani doctor, da sauri suka tashi kowa yana so yaji me ake ciki. Shikuma Dr din baice komai ba zai ratsa su ya wuce. Khattab ne finkico shi yana masa masifa “Meye haka Doctor kana ganin mu tsaye zaka wani ratsa mu ka wuce” “Mallam sakeni mana” Doctor yace “Basan sake ba ɗin, dan rainin wayo” ya amsa Naufal ne ya shiga tsakanin su, shima yaji haushin abinda Dr din yayi kuma yaji daɗin yadda Khattab ya saisaita shi. Kawai baya jin daɗin jikinsa ne da sai yayi ma Doctor ɗin dukan tsiya. Doctor ɗin ya soma tafiya abinsa tareda nuna Khattab da yatsa yana hararar shi, Mommy tayi magana daga zaune. “Doctor Haba mana ya zaka wuce mu baka ce mana komai ba” “Kiyi hakuri Mama, jini zani store in dauko” saiya tafi. Yaje ya dauko zai shiga ciki sai Naufal ya tambayeshi “Doctor please ta farfardo kuwa?” “Kuyi hakuri shi muke kokarin yi” nan take Khattab ya fashe da kuka, wai ace kusan awanta uku a ciki amma an kasa tada ta. Shima baya maso ya kawo wani mugun tunani waiko bazata farka ba. Daddyn shine ya shigo tareda Grand Kadi da sauran jama’a. “Meye haka kake yi kamar mara tawakkali? Maimakon kayi mata addu’a” Daddyn shi ya faɗa. Mikewa yayi ya tafi kurya inda yake kukanshi babu mai kwaɓansa. 9:30 pm...... Locacin wasu Doctors su huɗu suka fito duk suna zufa, ga kuma leberori suma suna fitowa da Miemie akan gadon da ake turawa. Da sauri yan uwan Miemie sukayi wajen ta, kana ganinta saita baka tausayi matuka. Duk bandage a jikinta manya manya, daga fuskanta, cikinta haɗe da bayanta, kafar dama da kuma hannun damanta. Ga wani an zagaye goshinta dashi, sannan an saka mata Oxygen domin shakar numfashi. Da sauri suka rinka bin gadon dakin da aka ware masu. Daga nan wani Doctor mai suna Abdullahi ya soma magana, “Bincike ya nuna cewa ba bigewa tayi ba, an buga mata kanta da sledgehammer ne. Kafin wutan ya soma ci” Salati kowa ya somayi, masu matse kwalla kuma kamar su Fadeela da Anty suka soma. Kowa Mamaki yakeyi wai da gangan akaso kashe Miemie. Dr ne ya cigaba magana. “Munyi kokari munga munyi stabilizing ɗinta amma gaskiyar magana shine sai anyi addu’a saboda har yanzu jini yana fitowa daga cikin kanta kadan kadan” “Kuma hayaki yayi yawa a cikin lungs ɗinta, yanzu dai idonta biyu kuma tana jinku. Amma bansan ko zata iya magana ba ko buɗe idonta” Daga nan sai Naufal ya tambaya asalin meya faru, Fadeela ta labarta masu komai daga zuwan  su Yasmeenah har batan Pha’eexah da kuma konewan Miemie. Kuka takeyi sosai saboda tana tunanin yau zata rasa mutane biyu da sukeda mahimmanci a rayuwarta. Duk juriyar da Khattab yake kokarin Nunawa saida wani hawaye na takaici ya gangaro daga idanunsa. Shiko Naufal abin duniya yayi masa chunkoso, ‘yarsa ta ɓace ga kuma k’anwarsa rai yana hannun Allah. Zuciyar shi sai zafi yakeyi yana tafasa, shiko kuka ya samu yayi ko zaiji sanyi amma ya kasa. Idanunsa a kafe sai zallan ɓacin rai dake bayyana, tausayin kowa yake a wajen musamman wanda abin yafi shafa kamar Khattab, Anty da kuma Fadeela. Doctor yace su Abba su biyoshi office zai masu magana, duk sun watse sai Khattab yaje inda Miemie ke kwance. Rike mata hannu yayi yana rero kuka, ko ajikinsa baya jin kunyarsu Anty ko Deela. Baice komai ba haka ya kafa ma fuskanta da baka ganin komai daga bandage da Oxygen. Saida yayi ma’ishi sai ya fara magana still hawaye yana malalo mashi daga idanu. Abinda yasa yaketa kuka baifi yadda yau da rana Miemie ke masa maganar mutuwa. “Yaya Khattab idan na mutu ya zakayi?” “Miemie meye haka?” “Please just answer me” “Bazaki mutu ba sai munyi aure kin haifan min yara masu kalan ‘yan  gidan ku” dariya tayi kafin tace “You never know......” Kuka ya sakeyi sosai daya tuna abinda ya wakana tsakanin shida Miemie da azahar dazu. Cikin kuka yace, “Please Haskena ki tashi karki mutu. Nasan anso a kasheki ne amma ina so ki basu kunya by staying alive” “Kuma i promise you duk wanda yayi ɗanyen aikin nan za’a kamashi duk inda yake.....” saiya cigaba da kuka. Rike mata hannu yayi yana matsawa a hankali, itama ta rike masa hannu amma idanun ta a rufe. Suna cikin haka sai su Naufal da Abba suka dawo. Yanda suka ga Khattab jaɓe jaɓe da hawaye gwanin ban tausayi, ita Anty tana tausayin shi saboda yama fita damuwa. “Meye haka kake kuka? Wayace maka mutuwa zatayi?” Naufal ya faɗa a takaice. Mikewa Khattab yayi yana jan manjina saiya bar ɗakin gaba daya. Motarsa ya koma kai tsaye, sai a lokacin ya lura baima kulle ba. Kifa kai yayi akan steering yana sheshek’ar kuka. Itakuma Deela zuwa tayi tana shafa mata goshinta wanda akwai bandage akai, hawaye itama takeyi saita soma magana da dishenshen muryanta. “Please Miemie ki tashi kinji, kinga an tafi da little one. Im sure zaki san wanda yayi wannan abun....” kuka ta barke dashi mai kara, su Mommy da Anty sunata matse kwalla saboda tausayin Deela. Tabbas zata shiga wani yanayi idan ta rasa Miemie kuma bayan ta rasa ‘yarta. Ciwon Miemie yanzu ya hanata kukan rashin yarta. Naufal ne ya janyo Kujera ya zauna dab da ita, bubbuga mata baya yayi ya kwantar da ita akan kafaɗarsa. “Kiyi hakuri kinji, in sha Allah komai zai daidaita” “Allah yasa” ta amsa. Suna haka kowa yana addu’a a ranshi. Abba ne yace masu Fadeela su tafi da Anty. Akwai nurses da aka ware zasu rinka dubata kafin gari ya waye. Kuka Deela ta barke dashi wai baza’a bar Miemie ta kwana ita kadai da bare ba. Hakuri  aka rinka bata amma taki shiru. Naufal ne yace zaije ya dauko Abla ta kwana  da ita. Anan ta rage kukanta sai tace yaje ya dawo zata zauna da ita tukun kafin yazo ya mayar da ita gida idan an dauko Abla ɗin. Kowa ya tafi tareda mata addu’a. Naufal ya tafi ya dauko Abla, yana parking lot dasu Anty da Abba za’a tafi sai suka ga Khattab cikin motarsa yana kuka. Tadashi aka yi ya tafi gida sai yace ba yanzu ba tukun. Abba ne yace ya shiga ciki ya zauna kafin Naufal yaje ya dawo saiya tafi. Shiga yayi ciki jiki babu kwari duk ya gaji. Ga wani matsananci ciwon kai da kuka da haifar masa. Zuwa yayi cikin ɗakin saiya tarar da Deela ta shingiɗa, zama daga chan bakin kofa amma ta ciki. Tagumi yayi saiya soma gyangyaɗi saboda gajiya. Itama barci yana daukarta amma tana buɗe idonta ta. Suna cikin haka sai barci ya dauke su duka. Basu suka farka ba sai sanda Naufal ya dawo da Abla. “Ya akayi wanchan abin ya daina motsi? Naufal ne ya tambaya sanda ya shigo kana ya nufa hanyar ECG da aka haɗa da jikin Miemie. A firgice suka tashi, Deela tana mitsike ido Shikuma Khattab ya zura da gudu wajen gadon. Saka kunnen shi akan kirjinta yayi amma baya jin alamun bugun zuciya. “Why is she not breathing?” Deela ta faɗa hankali a tashe. Da sauri ya mayar da kunnen sa wajen hanncinta tareda cire Oxygen tube ko zaiji alamun shakar numfashi amma wayam. Innalillahi wa inna ilayhi rajiun ra rinka maimaitawa yana yi yana jijigata amma bata motsa ba, asalima jikinta a kankame. Fadeela ce ta tsandara ihu saita sulale kasa, da sauri Naufal ya tarbota. Bata hakuri ya somayi yace kila wani abune daban. Ko ba’a faɗa mashi ba yasan Miemie ta koma gidanta na gaskiya. The worst part shine an kasheta ne bawai hakanan bane, tunanin sa ɗaya how can someone be this cruel? Abla zuwa tayi ta rungume Deela sunata  kuka  tare, Fadeela ne ke magana cikin kuka a hankali, “Innalillahi wa inna ilayhi rajiun, shikenan Miemie ta tafi barmu” Shikuma Khattab gefe yake ya zauna a kasa zaman dirshan, kwakwalwarsa sai tafasa yakeyi. Shi tunda yaji labarin accident ɗin yasan za’a yi haka. Yau gaba ɗaya sai maganar mutuwa takeyi da kuma rok’on sa gafara. Har haushi yaji yayi mata magana, ce masa tayi “you never know when you’ll die, gwara ka shirya kafin lokacin ka” Duk kalamanta yanzu yawo yake masa a kai, saidai yanzu Idonshi ya kafe. Yama kasa kuka, salati kawai yake cikin ransa. Kirjinsa zafi yakeyi ga gudu da sauri kamar zai fashe. Ji yayi kamar an daura mashi katon dutse cikin kirjinsa, ga kuma miyau na bakinsa ya kafe k'ab. Karkarwa kawai yakeyi kamar yana jin sanyi. Shikuma Naufal komawa yayi bakin Varenda yayi tagumi, abin daure masa kai yayi wai dazu ya ganta  yanzu kuma ta rasu. Daukar wayarsa yayi domin ya kira ABBA. “Assalamu Alaikum, ya akayi  ne Naufal” Abba yace ta ɗayan ɓangaren. Naufal bai iya amsa sallamar ba, kawai  magana ya soma. “Abba shikenan Miemie ta tafi ta barmu. Abba Miemie ta rasu, ta koma gidanta na gaskiya” “Innalillahi wa inna ilayhi rajiun” abinda Abba ya iya faɗi kenan. Shikuma Naufal wasu zafafan hawaye suka soma gangarowa daga idanunsa, da farko kadan kadan sai kuma suka fara gudu. #NiDaDiyata ~Yarinya Mai DIMPLΣS~©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 35 ✨✨✨ 'Imran bin Husain (May Allah be pleased with them) reported: Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "Shyness does not bring anything except good."[Al-Bukhari and Muslim].In a narration of Muslim: Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "All of shyness is good." *********** Kullu Nafsin Za’katul maut. Valar Morghulis. Kowane mai rai mamaci ne, sai dai zamuyi fatan mu cika da kyau da imani. Fadeela da Abla suna cikin ɗakin suna hawaye, jiki babu kwari Abla ta mik’e tsaye taje inda gadon yake ta rufe mata jiki da mayafi. Mamakin mutuwar Miemie takeyi, abin yayi mata zuwan ba zata. Addu’a yanzu kawai zata ya Allah yakai haske kabarinta, ya kuma basu hakurin jure rashinta. Gaba daya babu wanda yayi barcin kirki, Naufal yakan shigo akai akai ya duba su. Saidai kuma Fadeela tayi shiru  bata ma cewa komai, kana ganinta kasan cewa kukan zuci takeyi  wanda  yafi na bayyane ciwo. Hawaye neke gangaro mata ɗaya bayan ɗaya. Haka har gari ya waye, suka fara shirin komawa gida. Khattab yanata tunanin dogon suma tayi, Naufal ma haka. Amma Doctors sun masu confirming lallai babu rai a tareda ita. Anyi making preparations na tafiya da ita gida, shikuma Naufal ya tukasu zuwa gida saboda Deela tana jego kuma sanyi ya fara shigarta. Cikin gida kuma anata koke koke, Anty Saudah ce tace duk wanda ke kaunar Miemie yayi mata addu’a instead. Daga nan aka rage hayaniya sai masu hawaye kawai. Shiko Khattab dakyar ya iya tuka kansa zuwa gida. Yana shiga falo babu sallama ya tarar da Daddynshi da Mommy akan dinning suna kalaci. Ko kallonsu baiyi ba ya haye sama inda ɗakinsa, yana shiga ya banko kofa Karab. Hayewa gadonsa yayi ya kwanta rub da ciki. Anan ya soma sabon kuka, yanayi yana shesheka gashi muryanshi ya dishe. Mommy ce ta bishi domin ba ɗabi’arsa bane, kofa taji a garke saita firgita. Komawa tayi wajen IG ta gaya mashi, nan take ya dauke  wayarsa dake gefe ya kira Abba. Anan ne ake sanar dashi rasuwar kuma jana’iza karfe 9 na safe. Yana soma salati Mommy ta gane cewa rasuwa Miemie tayi, nan take tansoma gumi. Kawai tunanin irin halin da Khattab zai shiga  take, Allahu Musta’an ta faɗa a fili. Su Fadeela tana komawa gida sukayi ido da Anty, hawaye ya soma malalo ma Deela amma batace komai ba. Dama ruwan zafi yana jiranta, Hajia Rabi ta chuɗa ta da kanta. Tayi ɗan kan gado, an kuma kawo mata abinci amma ci takeyi kamar magani. Fuskanta a cunkushe babu annuri kwata kwata gashi ta daina magana. Suma Forensic tun kafin isowar su Naufal gidan suka zo suka fara aiki gadan gadan. Kokari sukeyi suga wani trace da zaiyi leading ɗinsu wajen gane wanda yayi wannan ɗanyan aikin. Dama mutane sunfi bada karfi idan Miemie ta tashi zata faɗa koma waye amma kuma ta rasu. Tabbas kuma Miemie taga wanda yayi mata haka saboda bincike ya nuna a jikinta tayi dambe da mutumin kafin aka buga mata karfe. 9am..... Mutane sun hallara za’ayi ma Laurat Hussain Beli watau Miemie sallah. Shi Khattab kulle kanshi yayi cikin ɗaki yaki zuwa, yana cikin kwance saiga Lili tazo da shiririta wai tana so suyi magana. Bai kulata ba haka ta gama tsayuwa ta tafi tareda watsa ashar. Ita kuma Yasmeenah tayi kiran duniya Naufal bai ɗauka ba, shi yana kyautata zaton da saka hannunta wajen wannan aika aikan. Jira yakeyi agama jana’iza ya raka ‘yan sanda har gidansu suyi gaba da ita. Idan yaso bayan sun kulleta su saka ɗanmakullin cikin rafi. Mommy ɗinta ne ke kallon NTA ita kuma tazo wucewa sai taga hoton Pha’eexah ɓaro ɓaro wai ta ɓata. Tashin hankali ta shiga sosai saboda ta ganta kafinta jiya. Daga nana kuma sai taga sanarwa akan rasuwar Miemie, anan tayi mutuwan tsaye saboda abin yayi yawa. Sai alocacin ta gane abinda yasa Naufal baya daukar wayanta. Shiryawa tayi tsab da niyyar zuwa tayi mashi ta’aziyya. Ita kuma Mommy Khattab ta shirya zata gidan gona ta’aziyya, lili ta tambayeta ina zata saita ce “Wanda Khattab yakeso dazu ta rasu” Taɓe baki Lili tayi sai tayi Magana ciki ciki, “To ni ina ruwana” ashe Mommy taji. “Babu ruwanki Halima, amma bari nayi maki albishir ko bayan raina ban yarda Khattab ya aureki ba. Na gwammace ya zauna babu aure” “Babu ruwanki koh?” Mommy tayita nanatawa tana tafiya saboda taji haushi sosai. Ita kuma Lili kuka takeyi saboda bata san meyasa uwar mijinta ta tsaneta haka for no reason. Gaskiya yanzu bataga lafin da wasu matan ke fada “Idan Uwar mijina nada kirki Allah ka barmin ita, if not Allah ka kasheta tun kafin in shiga” ****** Anyi sallah kuma an kai Miemie gidanta na gaskiya, mutane sunzo sosai saboda kyawawan ɗabiun ta dukda ma tanada taɓun hankali. Kowa fatan hasken kabari yake mata, Naufal shi ya jagoranci sakata a rami kuma ya tabbatar babu wani guri daya buɗe. Bayan nan police station ya wuce kai tsaye saboda yaji labarin bincike amma basu bashi wani labari mai daɗi ba. Shi yanzu hankalinsa ya rabu kashi uku. Na farko mutuwar Miemie, sai kuma ɓatan yarsa ga kuma matarsa ta shiga wani yanayi. Haka suka zauna a gidan gona anata karban gaisuwa. Baiyi mamakin rashin gainin Khattab ba saboda yasan zaifi kowa missing ɗinta. Sun gaisa da mahaifiyarsa da kuma Mahafinsa kuma shima anjima yayi alkawarin zuwa duba shi. Ita kuma Deela ɗakin Miemie ta koma zama. Hawaye takeyi bata cewa komai gashi nonota sai ruwa yakeyi saboda rashin tsotso. Duk sai jika mata riga yayi, gashi tana jin alamun kukan Pha’eexah a ranta. Ita tasan ɗiyar ta tanada rai amma kuma babu ita babu dalilinta. Haka ake zuwa mata gaisuwa, binsu da ido kawai takeyi bata cewa komai. Koda Yan sanda suka zo karban statement wajenta kallonsu kawai taketa yi, Mansura ce ta faɗa abinda ya faru. Wajen azahar saiga Yasmeenah tazo sanye cikin purple After dress tayi wrapping kanta irin na Arabs. Tana parking a waje saboda kowa nan ya ajiye nasa. Naufal yana hangota daga nesa saiya tashi da sauri ya nufa inda take. Ita kuma tana tafiya sannu a hankali saita hange shi. Wajen dayake ta nufa tana kokarin masa magana kenan, shikuma baiyi wata wata ba ya dauketa da mari. Kafin ta ankara ya kara mata guda ɗaya sannan ya hambareta da kafarsa a cikinta. Rike ciki tayi ta faɗi kasa tana kuka, a hasalce ya fara mata masifa. “ke dan Ubanki ina yarinya na?” kallonsa cikin rashin fahimta tayi tana kokarin gane meyasa yake mata irin tambayar. Fincikarta yayi ya shake, “Ina yarinya na nace dan ubanki? Ki gaggauta fito da ita ko ki yabama aya zakinta.” “Halan kishi hauka ne? Zaki zo ki daukan min yarinya kuma ki kashe min k’anwa.” “Infact Uban wa yace kizo gidan suna, shishigi da shiga sharo ba shanu” “Naufal meye haka? Sai kace bakada tawakkali?” Anty Saudah tace. Sakin Yasmeenah yayi saita ɗurkusa tana kuka, ita yau abin al’ajabi take gani. Wai daga zuwa gidan rasuwa ance ita tayi kisan. Jiki babu kwari ta shiga cikin gida, tana tafe  kowa yana mata kallon muguwa. Haka har takai ɗakin da Deela take, Fadeela tana ganinta ta rufe ido bata sake buɗewa. Hawaye kawai taketa yi, haka Yasmeenah ta gama zamanta ta tafi. A wajen fita sai tayi kicibis da Naufal, ja da baya tayi saboda ta tsorata dashi. Zai buɗe baki yayi  magana saiga Yan sanda sunzo mata tambayoyi as protocol. Ana mata tambaya tana kuma amsawa kuma kana ganinta Kasan akwai alamar gaskiya a tareda ita. Shi karin kanshi Naufal ya karaya amma bai nuna ba. Abba ne yace tace ma iyayenta biki nanda kwana biyar ne babu ɗagawa. Dama Daddyn ta ya kirashi a waya yayi mashi ta’aziyya kasancewa yana Lagos. Naufal ya fara korafi akan a ɗaga bikin amma Abba ya dakatar dashi. “Bana son karanci da shiririta Mallam! Kai kace kana so kuma dole ayi babu fashi” Yasmeenah taji daɗi sosai saboda har kasa ta ɗuka tayi godiya which dama godiya ba ɗabi’anta bane. Harga Allah idan ba’ayi bikin ba zata shiga tashin hankali saboda magunguna na mata daketa dirka. Da yamma...... Naufal ne yaje da kanshi ya ba Fadeela abinci bayan ta fito daga wanka. Ita yanzu ta daina magana ko musu, yin komai takeyi sannu a hankali amma bata cewa uffan. Haka ya ciyar da ita harta koshi, yana isarta saita kawar da fuskanta. Magana yayi  mata na duniya amma taki amsa shi, daya takura mata saita soma hawaye, dole ya hakura rai baiso ba yabar ɗikin. Hanyar  gidansu Khattab ya nufa tunda dama ya taɓa zuwa sanda Miemie tayi ciwo akanshi. A falo ya tarar da Mommy da Lili. Dukawa yayi suka sake gaisuwan mutunci da Mommy tunda dama sun haɗu dazu. Ita kuma Lili ‘sannu’ tace ta cigaba da ɓare gyada tana murzawa cikin bakinta. “kaje upstairs, first room on your left shine ɗakinsa” Mommy tace “Nagode sosai” ya amsa Zuwa yayi yana buga kofa a hankali amma babu wanda ya amsa shi, lokacin Khattab shikuma ya soma barci sai yaji bugun kofa. Duk zatonsa Lili ne, tsaki yayi saiya ɗaura pillow a kanshi saboda  ya rage noise. “buɗe mana, nine fah!” murya yaji kamar na Naufal, kasa kunne yayi ko  kizo ne amma ya sake jin muryan Naufal. Da sauri ya tashi ya buɗe, yana ganin fuskar Naufal saiya fashe da kuka.”Dalla Mallam meye haka? Kashe kanka kake so kayi kamar baka yarda da kaddara ba” “YaNaufal kasheta fah akayi, i can’t imagine the pain she went through” ya faɗa cikin Muryar kuka. Patting bayansa Naufal yayi saboda shima yana dab da hawaye. “Kaci abinci kuwa?” “Yanzu  zan ci” “Haba Khattab tun jiya  fah” kallonsa Naufal yayi yana tunani saiya tashi  ya fita. Downstairs yaje saiya gaya ma Mommy abinci yakeso na Khattab. Alamun zata tashi saiya dakatar da ita, “tashi ki samu ma Khattab abinci” ya faɗa ma Lili. Watsa mashi harara tayi saita basar. Mommy ce kunya ya soma ɗawainiyan da ita, “bari kawai naje” Mommy tace. “Ita wancan meyasa bazata ba?” ya tambaya yana kallon Lili. Sai kuma ya soma masifa tunda dama yanzu ya koya gashi yana neman inda zaiyi pouring frustration ɗinshi. “Bada ke nakeyi ba? Better hurry up Kije ki kawo min abinci kafin na saɓa maki. Niba ɗan nan gidan bane yanzu zan saɓa maki” “Bakida hankali ne Mommy tana maki magana kin kyaleta, waye sa’anki? You have lost your goddamn mind, idiot kawai” Mamaki ya kamata yanda yazo yana mata masifa, amma kuma ta mik’e saboda ta lura kanshi yana motsawa kafin ya jibgeta. Tana jan kafa tana tura baki har taje dinning ta dauko cooler. “maza ki kai mashi sai ki dawo ki dauko mashi ruwa.”  Haka tayi abinda yace, Mommy ce ta fara kuka. “wai da yanzu wannan akeso a lika ma Khattab, munzo mun samu Miemie shine rai yayi halinsa” “Yi hakuri Mommy, dangana kawai zamuyi” Dakin Khattab ya koma, bai bar gidan ba saida ya tabbatar yaci ya koshi kuma yayi wanka tareda sallah. Shi yanzu yana tausayinshi sosai, kawai yana tunanin yanda zai taimake shine! #NiDaDiyata ~Yarinya Mai DIMPLΣS~©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 36 ✨✨✨ Abu Sa'id Al-Khudri (May Allah be pleased with him) reported: Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "The most evil of the people to Allah on the Day of Resurrection will be the man who consorts with his wife and then publicizes her secret."[Muslim]. ******** Ranar daurin aure....... Ta ɓangaren Naufal kamar ba yau bane bikinsa, babu wani kuzari a tareda shi. Komai sanya sanya yakeyi kamar auren dole. Kawai ɗaci yakeji a ranshi gashi baiji haka ba sanda akayi masa auren dole da Fadeela, duk abinda yaji locacin wancan biki na wannan ya ninka. Ji kawai yakeyi kamar ya gudu, haka yaje daurin aure ya dawo. Kiran Fadeela yayi, tana kallo bata ɗauka ba. Abla ke zaune a wajen saita dauka ta kara mata a kunne. "Yaya tana jinka" Abla ta faɗa da karfi. Kwata kwata yanzu Deela ta daina magana. An kira Doctor sunce tana suffering from emotional and psychological stress. yana cikin abinda yasa hankalin Naufal ya tashi sosai saboda baya son yayi nesa da ita in her time of need. Anty Saudah tace abar mata ita tayi jinyarta harta samu sauki. Baiso haka ba amma babu yanda zaiyi. Haka ya soma ma Deela magana ta waya, as expected jinsa kawai takeyi amma batace uffan ba. "Baby Kiyi hakuri kinji, har an ɗaura auren" a sanyaye ya faɗa, duk yana jin haushin kansa. Ita kuma Fadeela hawaye ta soma yi. Kawar da wayar tayi ta haye chan kurya ta kwanta,,wani kishi kawai takeji. Tama rasa inda zatayi focusing anger ɗinta. Ga mutuwar Miemie, ga ɓatan Pha'eexah gashi kuma yanzu anyi mata kishiya. Duk a ciki yanzu abu ɗaya tafi ɓukatan daidaituwan shi watau fitowan Pha'eexah duk inda ta shiga. Ita kuma Yasmeenah tayi buki yanda takeso saidai babu ango, anyi raye raye da sauran su babu kama hannun yaro. Yanda Instagram suka dauka bikin ta taji dadi sosai. Yan Uwan Mama sukaje daukota tunda Anty Saudah bazata iya ba. An kaita ɗakinta an barta daga ita sai halinta wanda shi zai kwaceta ba kyauba. Wajen 10 na dare ta soma kiran Naufal domin ya dawo gida, amma dayake wayar yana silent yasa baiji ba. Abun ya kuwa bata haushi sosai ta cika tayi fam kamar zata fashe. Huci takeyi tana jiran isowar Naufal, aiko kaddara ya riga fata saboda wajen 11 na dare ya shigo. Shi tun wajen 8 yayi ma Deela sallama saidai bai je gida ba sai yanzu. Yana shiga cikin falo yayi sallama, sauraren wakar Psquare takeyi mai taken Away cikin dare, tayi connecting da Aux spot na home theater. Ko kallonsa batayi ba balle ta amsa mashi, shima yaji daɗin abin sosai saiya haye sama. Da sauri ta boye shi tana kokarin chapke masa riga. "Naufal meye haka halan ka mance yau kana cikin dakina ne?" "toh idan ɗakin kine me zan maki? Ke bazaki biyoni ba" tafiya ya cigaba dayi saboda bashida lokacin ta. Haka ta rinka binsa tana masifa, baice mata komai ba saboda baya cikin mood din tashin hankali, yau kwanan Miemie shida da rasuwa. Yana tafe tana binsa tana surutai, a cikin ɗakin Deela orange colour ya shiga dama nan yake kwana kuma duka kayansa yana wajen. Ita kuma duk zatonta ɗakinsa ne balle ta gani kato, daidai tayi kan gado tana jiran sa. Shikuma bayi ya shiga yayi wanka tukun saiya fito. "Ke tashi mu tafi" ya faɗa kana ya soma tafiya, gyara kwanciya tayi ta mirgina sosai saita soma magana cikin shagwaba. "mine please Barci nakeji" "Eh yasa nace tashi mu tafi, kokuma a ɗakin matana kikeso ki kwanta" zumbur ta mik'e da sauri tana kyankyamin gadon. "Dama dan Wulakanci ɗakin wancan ka shigo dani?" "Nine nake maki wulakanci? Besides wayace ki biyoni kinga ina tafiya" Nan ya barta ya fice abinsa. Da sauri tabi bayansa tana sababin zuwan ɗakin Deela datayi, baiko kulata ba ya shige nashi dakin. Kerere ta tsaya mashi akai tana wani yatsine fuska, "Jekiyi alwala kuma ki dauko hijab" harda bazata ba saita soma tafiya. Ta daɗe kafin ta dawo Kai da zaka zata an aiki baiwa garinsu ne. Data dawo akwai alamun wanka a tareda ita kuma sanye take Lingerie mai bala'in fitsara. Ko kunyar kanta bataji ba irin yau aka daura masu aure bari ta saba tukun, kuma ga overall a hannunta amma bata daura a kai ba. Yauki takeyi kamar ɗanyen kuɓewa, saita auka jikinsa tana magana cikin shagwaba, "Mine nayi missing ɗinka amma sai wani basarwa kake yi" "Malama sallah zamuyi tukun" saiya tureta ya mike saboda yanzu saita ɓata masa lissafi. "Idan kana tunanin banyi Isha'i bane toh wallahi nayi tun around 9, kallonta yayi yana mamakin cewa batasan ma'aurata suna nafila tareda addu'a domin kariya against all odds ba. "nafila zamuyi" "Ohhh bari nayi alwala" "Tun dazu me kika tsaya yi?" "Wanka nayi ko baka lura bane?" "Na lura mana" ya faɗa yana sake kallonta tareda hadiye miyau me zafi. Ta fito saita koma downstairs domin ta dauko Hijab, haushi yaji sosai saboda datayi abinda yace babu busy body da haka bai faru ba. Yanzu yana tuna abinda yake cema Fadeela lokacin akan ta cika busy body, ashe bai aura busy body wancan lokacin ba sai yanzu. Data dawoda wani zungureriyan Hijab har kasa, tada sallah yayi saiya ja masu raka'a biyu. Daga nan saiya rinka jero addu'a. Ya lura sai kwafa takeyi tana murje ido wai ita a dole barci takeji. Bai bariba saida yayi san ranshi kana ya shafa, tana mikewa bata ninke hijab ɗinba yadda ya dace illa chukurkuɗe wa kamar shargi ta cilla chan gefe. Zuwa tayi ta rugumesa tana mashi shagwaba, "Inace yanzu kika gama mitsike ido kina tura baki" "Hahaha" ta bushe da dariya "Mine nikake jama aji koh" bayasan wani dogon zance saiya kashe wutan ɗaki suka kwanta. 4:30 am.... Ya tashi yayi wanka sannan ya dauro alwala, zama da Fadeela ya koya masa irin extra salloli bayan sallan wajibi. Tada Yasmeenah yayi a hankali domin ta tashi tayi wanka koda rakatanil Fijr ta samu. A fusace ta dago jajayen idanta, "Meye haka kake tadani sai kace mara imani, duk rashin barcin daka hanani bai isheka ba sai kuma na samu hutu kake min hassada" Dogon tsaki taja kana ta fizge bargo ta mirgina da kyau. Shikuma ya tsaya sororo yana kokarin gane abinda tace, "Wai yana mata hassada, yanzu meye abin hassada a barci" yake faɗa cikin ransa. Wucewa Masjid yayi abinsa, bai dawo ba sai wajen bakwai saura. Koda ya dawo ɗakin Deela ya shiga ya kwanta a kan gadon ta, yanzu wani santa yana mamaye masa zuciya. Gashi yanzu tayi masa nesa, yanzu yasan ma'anar 'Appreciate the little things that you have' amma babu komai. Nashi jarabawar kenan. Kiranta yayi a waya, tana kallo amma bata ɗauka ba. A fizge tayi barci jiya, Naufal Kawai take tunawa yana chan da wata wanda ba ita bane. Haka Naufal ya gama kwakwan so yayi magana da ita amma babu hali. Dama wanka zata yi, wucewa tayi taje wanka yadda ya dace. Kirjinta zafi yakeyi kamar me saboda abincin little one. Ita har yanzu tana jin alamun little one a ranta, tana wanka tana kuka. Koda ta dawo Abla ta gani gefen gado tana mata murmushi. A fizge Abla tana yanayi da Miemie sosai, bambanci tsakanin su shi ne kalar fata da kuma shekaru. Sai bayan mutuwar Miemie duk inda Abla taje sai ayita kuka harta koma zaman ɗaki. Ita Abla daidai shiru shiru ce kamar Fadeela Unlike Miemie dake magana da fara'a sosai. Naufal yana kwance a ɗakin Deela yasan cewa zuciya tayi, ta saba daukar wayan dukda bata cewa uffan, shi kadai yake surutan sa. Sake kira yayi sai Abla ta dauko, "Hello Yaya ina kwana" "lafia lau ina Momyn Pha'eexah?" Gata bari na bata" ta mik'a ma Deela amma ko kallon wayar batayi ba. Asali ma haɗe rai tayi. "Yaya tana abune ka bari anjima" Abla tace. Murmushin takaici yayi ta ɗayan ɓangaren saboda yasani sarai taki karban wayan ne Abla ta kasa gaya mashi. Bayan ya kashe wayar, yaso yaje ya duba Yasmeenah amma ya lura ta iya masifa gashi shi yanzu tashin hankali ne bayaso. Kawai kwanciyarsa yayi barci ɓarawo yayi gaba dashi. Bai farka ba sai wajen tara da rabi, da salati a bakinsa ya mike yana hamma. Bayi ya wuce ya gasa jikinsa da ruwan zafi, kayansa da tuni ya dawo dashi nan ɗakin ya dauki sweatpants da t-shirt ya saka. Ita Yasmeenah wajen goma saura ta tashi, tana zaune akan gado ta soma mitsike ido tana mika. Murmushi takeyi sosai saboda daren aurenta ya kai mata karo. Yanzu kawai hanyar da zata malleke shi ita kaɗai zatabi. Gaskiya bazata iya sharing mijinta da kowa ba, figigiyan kayanta ta mayar jikinta tayi hanyar ɗakinta, sam bazata iya shiga bayinshi ba tayi wanka saboda yayi kura. Tana isa downstairs bataga Naufal ba duk zatonta breakfast yaje siyo masu, murmushi tayi ta shige bayi. Ta fito daga wanka ta chaba kwalliya kamar me shirin zuwa biki, daga nan ta saka wani crop top wanda hoton Taylor Swift take saita haɗashi da pink leggings. Zura Hijab dinta tayi zatayi sallah kuma lokacin karfe 11. Shikuma Naufal rarraba ido yakeyi ko zai ganta amma shiru. Zaune yake akan Couch yana kallon BBC lifestyle, kamshin turare yaji saiya ɗaga ya ganta. Babu karya tayi kyau ainun, murmushi suka sakar ma juna. Zuwa tayi ta zauna dab dashi, a hankali ya soma magana, "kin tashi lafiya?" "Lafiya lau" "Ya jikin ki?" "I'm fine, har kaci breakfast ɗinka ne?" "Bangane ba, wani breakfast kuma? Ke nake jira ki tashi kiyi mana" Kallon takaici tayi masa bcs ta rasa me zata ce, "Nine zan dafa abinci daga kawoni jiya sai kace wata bazawara" "Yanzu don kin girka ma cikin ki abinci ya zama zawarci? " "Eh" saita murguda masa baki tana ware ido alamun marasa kunya. "Kinsan cewa Fadeela batada karfin jikin da zata yi maki girki, kuma anyi rasuwa balle su Anty ko Abla suyi. Please why can't you be understanding mana" "Kasan Allah bazan yiba, besides idan baka lura ba barina fahimtar dakai. Bafa yar aiki ka auro ba, nifa matarka ce" "Yanzu danke matana ne saiki barni da yunwa" Ko kallonsa batayi ba, asalima daukan remote tayi ta canza channel which abinda Deela bata masa. Sam babu raini tsakanin shida ita, amma wannan tun jiya take gasa masa magana san ranta. Big Brother ta kunna, wani dan gidan aka nuna saita daka tsalle tana murna, "Kai TTT kana burgeni" Kwafa Naufal yayi yaje ɗaki ya dauko wallet ɗinshi, daga nan wani Kiosk dake bakin anguwan su yaje. Kayan shayi ya siyo da kwai da sardine. Inda ya barta nan ya sameta sai kallo takeyi, "Bisola meye haka?" Yasmeenah ta faɗa tana ɓata rai. Dire ledan yayi akan centre table. "Okay ga kayan shayi na kawo, Latte zaki haɗa min sai kuma ki soya kwai tareda sardine. Ba wani aikin wuya bane" Bata ko kalleshi ba, asalima haɗa rai tayi. "Tunda ba wuya saika yi da kanka mana" "Sannu me wayo! Kai ka hakince akan Couch zata takura min" baiso tankawa ba amma yace gwara ya kwaɓeta kafin raini ya shiga tsakanin su. "Meye haka kikeyi tun dazu? Don ina kyaleki shine kike so ki raina ni" "Ni dai ka daina min ihu tunda bakai ka haifeni ba" ta faɗa ciki ciki, Mikewa yayi ya shiga kitchen ɗin Deela ya dauko Mug, hawa sama yayi ya shiga bayi ya ɗebo ruwan zafi. Daukar kayan shayin yayi ya nufa dinning, komawa kitchen yayi ya dauko cokali da plate. Zuba sardine din yayi saiya haɗa coffee mara madara ya soma sha. Yanayi yana haɗa bread da kifi, ya tabbata idan ya biye ma Meenah yunwa zai iya kaishi lahira. Yana cikin ci sai itama tazo domin ta saka wani abu cikin bakinta, ko kallonsa batayi ba ta fara gabza bread da sauran sardine ɗin. Bata sha shayi dama bata sha. Baice mata komai ba har suka gama brunch (Breakfast /lunch). Komawa yayi kan couch ya canza channel. Zuciyar shi sai zafi yakeyi yana tafasa, baima san yadda zasuyi ba wajen abincin rana. Lallai hankali baiwa ne kuma ba'a shekaru suke ba, Yasmeenah ta girma Fadeela da kusan shekara biyu amma Deela ta fita hankali. Suna zaune suna kallo saiga Huzaifah ya shigo da Haisam. Ba Naufal ba har Meenah sai da tayi mamakin ganin su, musamman Huzaifah. Haushin Meenah Naufal yakeji saboda bata wani gaggawa ta rufe jikinta. Ita kuma ba yau suka saba ganinta haka ba. Haka shigarta yake ko cikin gidansu, kayanta kenan su leggings da bom shorts. Mikewa tsaye tayi domin ta kawo masu ruwa. Tana tafe tana juya jiki which yana yinta ne. Gashi duk jikinta rawa yakeyi kamar ka saka ruwa cikin leda. Huzaifah ya kalleta sosai kuma yaji daɗi har cikin ranshi. Ta dawo da chi exotic da kuma dubulan da alkaki which dama tazo da abinta na tarban baki. Su Huzaifah sunci sunata hira, itama sama sama takeyi saboda sun daina shiri da daɗewa. Bayan almost 40 mins saiya tashi wai su tafi, dama yazo yaga lafianta ne a matsayin sa na babban Wanta. Zata mike ta rakasu sai Naufal ya fincike ta. Dole ta zauna sai shi ya rakasu. "Wancan Huzaifah meye matsalar sa?" Naufal yake tambayar Meenah bayan ya dawo daga rakiya. Dariya Meenah tayi tana rausaya kai saita soma magana cikin yauki, "haba Mine kar kace kishi kake yi?" "Ba maganar kishi bane kawai i dont Like him ne, koko im not allowed to say my mind. Besides Bakiga yadda yake kallon ki bane" "Haka yake idan ma yadda ya kalleni ne, i think nature dinsa ne. Kosu Lubna da Laila haka yake kallon su." "besides munyi faɗa i think ya gane kuresa yasa yakeso yayi squashing ɗin komai. Everything ya zama past tense tunda yanzu nayi aure" "Koba wannan ba he is my brother for heaven sake ai bazan iya hanashi zuwa wajena ba. Its just kamar nace Abla karta zo ko Bilqees.. Kaga ai its not even making sense mana" "He is not Abla ko Bilqees, kuma Nidai i hate him" Ya faɗa sai yayi hanyar upstairs, "better learn to like him saboda bazan rabu da family ɗina ba wai a dole nayi aure" ta mayar masa. Dama haka take, duk me kace saita baka amsa. 4:30pm.... Naufal ya idar da sallah saiya saka manyan kaya saboda suje su gaishe da yan gidansu. Baici komai ba banda cikinsa da ke wakar yori yori. Ita kuma Yasmeenah Big Brother Nigeria take Kallo abinta a falo, da yunwa ya soma ɗibarta saita dauko bread ta ajiye gefe tana tsakura. Ko azahar batayi ba balle wani la'asar. Ga kuma sauran exotic wanda su Huzaifah suka sha bata kawar ba. Shita rinka gyangyama. Yana saukowa ya ganta tana kallo, "jeki shirya zamu gidan gona" "Meyasa?" tace tana wani kallonsa. "Bcs i say so" ya faɗa saiya fice ya wuce chan bakin gate domin yasha iska kuma ya jirata. Rai a jagule taje ta soma shiri, lace ta saka mai ɗan karan tsada, ɗinkin kimono akayi saita dauki mayafi. Fuskanta shake da makeup, yana ganinta yayi fuska kamar bai ganta ba. Data gaji da tsayuwa saita fara sababi, "Haba kace zamu fita kuma ka shanya ni kamar kayan wanki, idan bazaka ba saika min bayani na koma daki. A duniya wulakanci ne bana so" Yaji kunya sosai saboda dukda Maigadi yana nesa da inda suke dole yaji saboda yadda ta ɗaga muryanta chan kurya. Wai yau matarsa ke daka mashi tsawa kamar ɗanta. Idan baiyi wasa ba Yasmeenah tana dab da mayar dashi mijin Hajia. "da makeup zaki gidan mutuwa" "Toh ba saika faɗa minba,sai ka shanyani kamar wata shargi" soma tafiya tayi tana gogewa da haɓan gyalenta. Shima tasowa yayi suka shiga mota, babu wanda yace komai sai tafiya akeyi, itace tayi connecting wayar ta da Aux ta kunna wakar Wizkid mai suna Daddy Yo. Haka ta rinka yi har suka isa ciki. Sama sama tayi ma kowa, ita yanzu bata damuda kallon dasuke mata ba saboda bakin alkalami ya bushe yanzu Naufal nata ne. Koda aka haɗasu ana masu nasiha akan hakuri da sauran al'amura na rayuwa, attention ɗinta yafi karkata akan TV while ita Deela kanta yana kasa. Bayan nan aka kawo masu abinci suci, daga ita har Naufal sunci sosai saboda yunwa yana addabar su, tuwan shinkafa ne da miyan taushe sai kuma kunun aya. Abba ne ya shigo yana neman Abla ta kaima Khattab abinci saboda rabonsa da gidan tun Miemie na raye. Dama Naufal ya gama ci saiya tashi domin su gaisa, a garden ya iske Khattab yana wasa da Sunflowers. Tausayin shi yake sosai saboda Miemie ta shuka da hannunta. Khattab yana ganin Naufal ya mike da fara'arsa, hakuri ya soma bashi akan rashin zuwa bikinsa da baiyi ba. Acewarsa kwanan sa huɗu a asibiti sai dazu aka sallame shi. Jaje Naufal yayi mashi sai yace su koma falon baki ya zauna, Naufal saiya koma ciki domin ya faɗa ma Abla inda zata kai abinci. Yana zaune ya kifa kansa akan cinyarsa, baisan da zuwanta ba saiya ganta a gabansa. Baya ya matsa a firgice har saida ta tsorata. "Haskena kin dawo ne?" ya faɗa a tsorace. Sai kuma ya fara mika hannunsa dake rawa yana so ya taɓa fuskarta yaji ko itace ɗin. #NiDaDiyata *Dedicated to all the family of this book, because yanzu mun zama yan uwa* ~Yarinya Mai DIMPLΣS~©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 37 ✨✨✨ On the authority of Abu Dhar Jundub bin Junadah, and Muadh bin Jabal that the messenger of Allah said : "Fear Allah wherever you are, and follow up a bad deed with a good one and it will wipe it out, and behave well towards people." Tirmithi narrated the Hadith and said it was fine, and in another version, said ture and fine. ********** Ikon Allah Abla ta tsaya gani, duk ya ruɗe babu gaira babu dalili, though ranta yana bata cewa kila shima yana ganin gizon da akace tanayida Miemie. Sai dai ba wani big deal bane dazai rude haka kamar yayi gamo. Bata hanashi taɓa fuskarta ba saida itama ta kafa mashi ido kamar yadda ya kafa mata. Yana taɓata yaji mutum ne saiya sake baya ya rufe idonsa. Rufa ke keto masa duk ya firgita, saiga Naufal ya shigo. “Yauwa Abla dama ke nake nema” Kallon Khattab yayi yaga ya sukurkuce, Cikin damuwa ya soma masa magana. “Lafiya kake zufa duk Ac dakin cikin nan?” “I think shima yana ganin Miemie a fuskata ne” ta amsa a sanyaye “Ohhh! Of course Abla ne, yes im not running mad” Khattab ya faɗa yana ajiyar zuciya a hankali, handkerchief fari ya ciro daga cikin aljihunsa ya share zufan Fuskarsa. Da farko ya dauka yayi gamo ne, sai kuma ya sha hauka ya somayi. Zuwan Naufal ba karamin relief ya bashi ba. Ita kuma mikewa tayi ta bar wajen tana matse kwalla. Abin ya fara isanta, hala mutane basu lura itama tana missn Miemie bane, duk inda taje sai an firgita kuma ba’a lura itama tana jin ciwon abun cikin ranta. Shi kuma fasa cin abincin yayi saiya tafi gida kawai, kwanciyar rub da ciki yayi akan gadonsa. Kawai tunanin yanda Abla batada bambanci da Miemie ne yakeyi. Magrib aka kira saiya tashi ya wuce masjid. A hanyar gate ya haɗu da Lili tana dawowa daga anguwa, da gudu ta karasa inda yake ta rungume sa. Dama rabon data haɗu dashi tun shekaran jiya. “YaKhattab naji daɗin ganinka Wallahi” “Na hanaki rikeni, wai meyasa bakya jine?” “Toh fah ji wani sanabe, wallahi iyayi da kakeyi kamar baka jin dadi idan na rike ka bani mamaki yakeyi” “Eh naji nidai sakeni kawai kinga masallaci zani kafin na makara” “Anaso ana kaiwa kasuwa” tace saita sake shi. Harya soma tafiya wajen taku biyar haka saiya juya, “Lili” ya kirata. Itama waigowa tayi tana rarraba idanu, “ya akayi ne Yaya?” “Am mani mutuwa amma bakiyi min gaisuwa ba, mutuwa fa ba abin wasa ne!” “Toh ni ina ruwana dan budurwa ka ta mutu? Wallahi banki ba duk wanda ta ganka tace tana so ko cikin ranta ne toh ta gangara lahira” ta faɗa tana hura hanci. Murmushi yayi mai bayyana bakin ciki, cikin gadara ya bata amsa. “toh saiki zauna gadin duniya idan kina tunanin bazaki mutu ba, kuma mutuwar nan yana kan kowa balle kice banda ke” “chan ta matse maka” saita barshi wajen ta nufa cikin gida. Shikuma girgiza kai yayi yana murmushi, nan ya tuna da Miemie daya kirata a waya sunsha dariya. “Allahu Musta’an” ya furta a fili saiya nufa Masjid. ***** Yasmeenah ta rinka hura ma Naufal wuta akan su tafi, ko sallar Magrib da kyar ta bari sukayi. Ita bama zata yiba saboda ana binta bashin azahar da la’asar kuma da kunya kaje gidan mutane kana jero salloli. Yana dawowa ta mike wai a dole sai ta tafi, kamar kyamar gidansu takeyi taki sakin jikinta, bata lura cewa Deela bata haɗa komai dashi ba amma ta mayar da gidansu kamar nata. Yaune ake sadakan bakwai amma Abba ya umarce shi akan yayi zamansa, da wata matar arziki ne da tun safe ta tilasta suje. Haka sukayi sallama da yan gida suka tafi, tun bayan da akayi masu nasiha bai sake ganin Deela ba. Koda ya aika Bilqees ta kirata bata ko kalleta ba. A Vanilla joints suka tsaya ya siyan masu shawarma, burger da milkshake. Daga nan ya tsaya a Chuchu Stores ya siya bread, milo, Madara, Indomie, sardines da sauran su. Ita hakima ta hakince cikin mota tana duba Instagram, hotunan celebrities take kallo musamman ma maza tana jindadi hankali kwance. Ya dawo shake da kaya amma ko ta taimaka masa, asalima yi tayi kamar bata san yana jiran ta tayashi buɗe kujerar baya ba. Haka ya ajiye kayan a kasa saiya buɗe da kansa kana ya sake dauka daya bayan daya ya rinka sakawa ciki. Bayan na saiya zaga ya shiga ya soma tuki. Ko irin ‘Sannu da kokari Maigida’ bata ce ba. Tuki ya soma yana tunainin ko ta daina sanshi ne kokuma kawai iya shege ne... “Bazaki taimaka min bane kin ganni sai wahala nakeyi” tana yatsina fuska ta dauki ledar Shawarma da burger kawai tayi shegiwarta ciki. Daki ta shiga ta ajiye, saita buɗe shawarma tana ci. Tanayi tana kallo ko bin kan Naufal batayi ba. Shima ya watsar da zancenta ya nufa Masjid domin yayi sallah isha. Saida taci tayi nat kana ta wuce hanyar ɗakinta, a locacin tayi wanka tareda daura alwala.Jero train ɗin sallolinta ta soma yi. Ita bata kwana batayi sallah ba amma bata fiye sallah akan lokaci ba, duk dare zatayi abinta. Wani pink nightgown mai laushin gaske gashida sansti ta saka. Saita saka palms din barci ta nufa hanyar ɗakinsa. Shikuma ya dawo daga Masjid yaga falo duk burbushin abinci wanda taci ta bari, daukan nasa yayi ya tafi ɗakinsa. Baici ba saida ya kintsa. Ya gama ci yana shan ruwa daga bedside fridge ɗinsa saita shigon tana masa murmushi, dakewa yayi amma bata damu ba. Shagwaba ta soma masa, daya mata maganar behaviour ɗinta na ranar saita bashi hakuri wai kawai she is overwhelmed by everything ne. Ba laifi ya sauko daga fushin sa daga nan sukayi kwanta. After six weeks... Fadeela ta soma samun sauki sosai, har yanzu bata magana amma ta rage yawan kuka kamar yanda ta mayar ibada. Kuma tana ɗan murmushi koda sau ɗaya ne a rana. Kullum cikin addu’a take a zuciyarta Allah ya bayyana mata ɗiyarta. Har tayi arba’in ta soma sallah da kanta tana rok’on fita daga cikin matsalan. Naufal da kanshi ya dauko mata donkey, paints dasu sauran kayan masu painting. Taji daɗin abin sosai saboda yanzu batada wani sana’a sai shi. Kowa yana murna yadda ta fara mayar ma Allah komai ta dauki dangana. Yakan zo dubata sau biyu, da safe idan zashi office sai kuma da yamma idan ya dawo kafin ya wuce gida. Ta ɓangaren aurenshi da Yasmeenah kuwa babu abinda ya canza. True colour dinta ya bayyana sosai, samsam bata da kunya ko kadan. Gatada tsiwa yana cewa kule zata ce chas. Abinda ke bashi haushi shine rashin iya girkinta. Kwata kwata bata san yadda ake sarrafa ɗanyen abinci a mayar daffafe ba. Kawai managing yakeyi saboda bayaso ya tsinka ta wajen iyayen shi ya rinka cin abincinsu har su gane. Sau da dama yakan kira Abla ko Bilqees suzo tayata aiki duk a zatonsa hannunka mai sanda yake mata, ita kuma bata san wannan ba suna zuwa take naɗe kafa ta fara kallon Korean series ta barsu su kadai cikin kitchen din. Gajiya yayi da ɗabiarta ya hanasu zuwa , dama suma basa santa at all. Ta rinka daka masu ihu kenan kamar yaranta, abin yafi bama Abla haushi ita dake sa’a da ita. Ita Abla ta gama Nysc ta soma aiki a Ministry for Women affairs, ita kuma Bilqees za'a shiga 300l. ****** Shikuma Huzaifah baya kwana uku cikarkiya baije ya duba Yasmeenah ba, shakuwa ne sosai ya shiga tsakanin su. Kullum cikin tambayarta yake ko tanada wani matsala wala na kuɗi kona Naufal. Tun tana ɗari-ɗari dashi harta sake mashi sosai. Musamman yanda idan zaizo yakan kawo su shawarma da chocolate wata rana harda ice cream da kasarshiyar kaza. Sukan sha hira sosai tana jin daɗin company ɗinsa, Hilal dai bai taɓa zuwa ba amma sauran yan uwanta duk sunje wasu sau daya wasu kuma biyu. Naufal ya nuna bacij ransa a fili amma bataji ba, sau da dama abin ya jawo masu tashin hankali amma tace bazata daina sake mashi ba. Thou bai taɓa shiga ɗakinta ba amma bata kiba idan tayi wanka sanye da towel tazo falo suna hira tayi shafa da kwalliya... Sau da dama tana ba shi kanshi Huzaifah labarin irin faɗan da sukayi da Naufal akanshi, ‘sis kina wuta fah, wallahi bakida dama’ yake cewa. Wata rana suna cikin hira ya ce, ‘yanzu kina samun ciki kika haihu kema za’a maki kishiya’ “Akan me za’a min kishiya” “Konine matana ta dauki ciki cikin early years ɗin auren mu to zan mata kishiya dole” “Kai daban mijina daban!”” “We are all guys, kuma tunanin mu daya ne. Idan zan baki shawara ki dauka toh ki bari nan gaba saiki haihu” Ajiyar zuciya yayi yana kallonta,yana ganin kamar maganar shi ya fara tasiri cikin ranta saiya soma magana da full confidence babu inda inda, “nifa dan uwanki ne bazan cutar dake ba, mufa maza bama son takura kuma kinsan tara yara ba karamin takura bane” “Shikenan zanyi tunani” ta faɗa a sanyaye. “Da yafi maki Lil Sis” Murna fal cikin ranshi saboda hakkunsa ya kusan fara cinma ruwa, wani smug kallo kawai yake mata ta gefen ido kuma yana kara ma jikinta kallo. Yau sanye take da blue crazy jens wanda yasha yanka ta wurin cinya da gwiwa, saita haɗashi da chiffon top mara hannu. Yana kallonta yana haɗiye miyau saboda kwanan nan bashida wani katabus sai tunanin ta. Ko barci yanzu gagaranshi yakeyi saboda yanda take masa yawo cikin rai. Yasa saiya zo ya ganta yake jin daɗi, saidai inda abin yake zuwa mashi da sauke tana bashi free show din jikinta koba duka ba amma yana samun banza. A hankali zai koya mata sanshi harta rabu da mijinta ta koma mashi. Ita kuma abinda Huzaifah ya faɗa mata ya soma mata yawo a cikin kanta, tabbas akwai kamshin gaskiya a tareda zancen saboda gashi Fadeela bata gida kuma ta lura tun kanta haihu take chan gidan. Ita yanzu duk wani hanya da zata bi ta malleke Naufal take nema, idan rashin haihuwa zai zame mata mafi saukin toh shi zata bi. Yanzu idan Naufal ya dawo zata faɗa mashi suyi tsarin iyali, sai wani zuciya ya raya mata cewa gwara tayi abinta ita kaɗai babu wanda ya sani. Chuchu Stores and Pharmacy taje ta siyo contraceptives kala kala na kamfani daban daban. Haka ta rinka shan abinta bada sanin Naufal ba. Three months later........ Koda Naufal yaga batada ciki bai damu ba saboda Fadeela itama haka tayi kafin komai ya daidaitu mata. Bashida wani buri daya wuce ya tara iyali sosai, gashi har yanzu ba’a ga Pha’eexah ba. Saidai IG baban Khattab yace har yanzu suna kan case din baza’a huta ba sai anga karshen abin. Shikuma Khattab ya koma bakin aikinsa yanayi sosai. Sunyi kacha kacha da Lili har yayi sanadiyar barinta gidan su, yaji dadi sosai saboda yanzu yana samun ya wataya. Saidai har yanzu zancen wata budurwa kuma baiyi ba. Bayada lokacin kallon wata ‘yamace kuma. Soyayyar Miemie yana nan fal cikin ransa kamar basu rabu ba, ya rasa inda zaiyi da irin abun. Wata rana yana zaune cikin office ɗinsa, wayarsa ya dauka yana kallon screensaver ɗinsa wanda hoton Miemie ne bai cire ba. Kawai daukar mukullin motarsa yayi saiya nufa gidan gona. Ya shiga anyi gaisuwan mutunci da Anty da kuma Deela, yanzu ta murmure ta soma magana sama sama tunda dama surutu ba ɗabi’arta bane. Shiru yayi baice komai ba, ya rasa Dalilin zuwan shi gidan. “Lafiya dai koda wani matsala ne?” “Lafia lau Mommy” ya amma yana inda inda. Suna cikin haka saiga Abla ta shigo cikin falon tareda sallama. Deela da fara’arta ta daga ta kalleta “Wata sabon gani, Abla kin share ni” “Ba haka bane Momyn Pha’eexah, Boss dina tayi tafiya zuwa Abuja yasa nike komai a office. Wallhi Yanzu banida wani isarshen time” Zama tayi akan Couch na 2 seater Kusa da Fadeela, “Ina wuni Anty?” “ina gajiya Abla ya aiki?” “lafiya ya gida?” “Alhamdulillah, yasu Mamanki?” “Duk kalau suke” Suna gaisuwa amma attention ɗin Khattab yana kanta, tabbas itace ke masa sukuku cikin rai kuma dalilinta yazo gidan nan. Soyayyarsa da Miemie yayi zurfi yanda bazai iya maye gurbinta da wata mace ba amma ya rasa gane dalilin da yana jin wani iri idan yayi tunanin Abla. “Ina wuni Khattab” Abla tace, dayake yayi zurfi wajen tunani saida ta sake maimaitawa kafin ya amsa. “Lafia lau” ya iya cewa saboda yadda zuciyar sa yake gudu da sauri. Mikewa yayi ya tafi. Kai tsaye ɗakinsa ya wuce, kanshi ya soma mashi zafi gashi zuciyar sa yana mashi wani irin barazana. Sam baya so ya yarda cewa yana san ta ne, amma ya kasa daina tunaninsa. Saida ya ganta ya lura ba Miemie yake tunawa ba illa ita. Tirkashi! Yanzu ya zaiyi? Haka yake tunanin yadda zaiyi over coming problem ɗinsa. Ya yanke shawarar yaje ya sameta saboda zuciyarsa yana mashi barazana bugawa idan bai samu abinda yake so ba. Bayan Isha ya tafi gidan gona, a bakin gate Mai gadi ya faɗa mashi cewa ta tafi gidansu. Dayake ya taba kai Miemie gidan sanda take raye so bai wahala ba. Ya aika ayi mashi iso da ita, shikuma yana zaune cikin motarsa yana addu’a saboda gabansa yanata faɗi na rashin dalili. Ita kuma tana kwance akan gado ta gama rubuta wani proposal haka. Whatsapp ta shiga tana ɗan karance karance littafin hausa mai suna “A Dalilin Mene” wanda UmmieeJafar ta rubuta. Maigadi yayi sallama wai ana nemanta a bakin kofa. Koda ta tambaya wanene yace gaskiya cikin dare ne kuma baiga fuskarshi ba,saidai ya ce ai mashi iso da Abla. Dayake ta riga tayi shirin kwanciya, saita daura dogon riga da kuma Hijab wanda ya wuce gwiwanta da kadan. Sallama tayi data isa wajen motarsa, ya fito yana jingine. Saida ya amsa ta gane Khattab. Nan taji gabanta ya faɗi saboda idan abinda take tunani yake so yayi zata tsayar dashi tun kafin komai yayi nisa. Na farko dai ita ba Miemie bace, saboda haka babu gurbin dazata maye mashi. Bayan sunyi gaisuwa sai sukayi shuru na kusan minti biyar , kana ganinsu kasan akwai tension tsakanin su. Kawai nazarinta yakey, tabbas wannan ba Miemie bace, koh ɗabi’un su ya bambanta sosai. Miemie bazata taɓa ganinsa tayi shiru ba, saidai kuma Miemie tana sanshi, wannan babu wani abu datake ji mashi a ranta. Haka suka gama tsayuwa ya kasa cewa komai sai kawai yayi mata sallama ya tafi. Itama sallama tayi ta wuce cikin ɗaki. Abla irin matan nanne masu kwarjini da ba kasafai zaka iya gaya masu aininhin abinda ke ranka ba. Ita ma taji dadi bai kawo mata wani shirmeba. Bawai tanada wani tsayayye bane amma bata tunanin zata iya soyayya dashi, ita tana ganin cin amana ne wajen mai rasuwa Miemie.Babu abinda bata sani na Khattab daga abincinsa, kayansa, colors da sauran abinda ya dace wani ya sani akan ka. Miemie idan ta dawo daga taɗi takan bata labarin shi sosai. So wannan amanar yasa bazata iya betraying trust ɗinta ba even in death. Kawai Khattab ya dauki na damu ya nema wata chan daban. Shikuma yanzu duk bayan kwana biyu sai yaje dubata, sometimes ya kanyi siyayya ya kai mata. Bai taɓa faɗa mata dalilinsa na zuwa ba, asalima basa hira daga gaisuwa sai bayan wajen 20mins haka ko 30 sai ya tafi shikenan kuma sai gobe ko jibi. Infact ko number dinta bashida shi itama haka batada nasa. Duk sanda ya zo ya tafi abu ɗaya take faɗi a ranta, ‘Iska na wahalar da me kayan kara” Shikuma yasan cewa every disappointment is a blessing in disguise, baisan abinda zai faru nan gaba but he is optimistic about everything. Yasan cewa Allah baya baka abinda bazaka iya handling ba. Komai rabo ne da kuma lokaci, idan babu rabonka a cikin abu duk yanda kaso bazaka samu ba, dama zabin Allah yake nema a koda yaushe. #NiDaDiyata _Yarinya Mai DIMPLΣS_©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 38 ✨✨✨ Abu Hurairah (May Allah be pleased with him) reported: The Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "There are two statements that are light for the tongue to remember, heavy in the Scales and are dear to the Merciful: 'Subhan-Allahi wa bihamdihi, Subhan-Allahil-Azim [Glory be to Allah and His is the praise, (and) Allah, the Greatest is free from imperfection]'."[Al-Bukhari and Muslim]. ******** Wani Laraba haka wajen sha biyun rana, ina zaune cikin Office dina saiga Sadeeq ya shigo. Bayan munyi sallama sai yayi min korafin yunwa. Nan take gabana ya faɗi saboda gidana ba inda za’a kai bako bane, Aminu shima ya shigo wai a dole sai sunje gidana cin abinci. Babu noke noke da banyi ba amma sukayi burus dani. Haka na tashi ina Hasbunallahu wa ni’imal wakeel inatayi har muka kai gidana. A parking lot mukaga Motar Huzaifa, nan jikina yayi la’asar. Yanzu Huzaifa bashida timetable na zuwa gidana, baisan safe balle rana. Koda yaushe zuwa yakeyi. Su kuma su Huzaifa da Yasmeenah sun zama besty 5 and 6. Suna jin daɗin company ɗin junarsu. Babu tashin hankali da batayi dani akan abin kuma na nuna mata bacin raina amma tayi kunnen uwar shegu. Suna zaune a falo suna kallon sabon India mai suna ‘Dilwale’ wanda Kajol da Sharukhan sukayi acting. An kai wajen wani waka haka sai Yasmeenah tayi rewinding ɗinsa daga farko. Toh dama laptop din Huzaifa suke kallo dashi. Nan ta soma babbaka rawa, su crip walking takeyi saita haɗa da azonto daga nan sai tayi ending dinshi da dab. Su kuma su Naufal ana cikin tafiya akaji karar waka, nan take raina ya ɓaci. Gashi kuma nazo da baki. Yau tabbas sai na ji kunya. Dama duk wanda baiji bari yaji hoho! Fatana ɗaya kada na risketa tana zabga rawa tunda karamin aikinta ne. Aikuwa kaddara ta riga fata saboda babbaka rawa take yi abinta. Sororo muka tsaya bakin kofa muna kallonta. Huzaifa yana daga kwance ya hakince a 3 seater kai zaka ranste shine mijinta. Amshi yake mata “Go Meenah! Go Meenah!! Go go go Meenah !!!” ita kuma sai dancewa take yi. Dariya ya bushe dashi sannan ya naushi iska tareda tafa hannayensa sai yace “Tirrrrrr yarinyar nan bakida dama wallahi” Itama dariya tayi saita juya ta ganni tsaye bakin kofa da baki. Da gudu tazo inda nake ta sumbace bakina babu kunyar mutanen dake wajen. “Mine ka bani mamaki bansan yanzu zaka dawo ba” “Nida gidana saina tambaya izininki kafin na shigo?” “No bahaka bane im not expecting you, at least ko waya da kayi min amma bawai kawai ka fado min ba without a warning” ban kulata ba saboda ina dab da marin ta, karyan iskanci takeyi nazo na iske ta tana rawa gaban wannan gwaskar shine zata wayanace. Sai kuma ta juya ta gaida su Aminu kana tayi introducing Huzaifa as Big bro dinta. Shikuma Huzaifa ya mika masu hannu suka gaisa, nidai ban mika masa ba saboda na tsane shi. Da baki muka gaisa saiya tafi, har yakai bakin kofa saiya juyo yace, “Lil sis gobe da safe zanzo na karɓa laptop dina saboda munada board meeting” “okay Yaya Huzzy dont worry yau ba zanyi barci ba zan kwana ina kallo har saina gama”Daga gira yayi daga nan sai ya tafi. Ni yanda yake behaving ban taba zaton yana anything for a living ba saboda baya zuwa aiki at all, kullum yana gidana. Wata rana har Saturday and Sunday. Shigowa falon muka yi gashi kacha kacha babu gyara, su ledan Oasis ne birjik dasu gwangwani na maltina da pepsi wanda aka sha aka rage. Ga kuma burbushin cake daga kan kujera har kasan carpet. Da sauri taje ta fara tattara wa, gashi rigar ta doguwa ce amma ya matseta tsam. Duk wani haushi da kunya ya kamani kawai bance komai ba. Itace ta fara magana, “Please kuyi hakuri dama inaso na gama kallo ne tukun kafin nayi shara” “Karki damu amarya lantarkin gida, ai bakya lefi koda kin kashe dan masu gida” Aminu yace yana kallon fuskar Naufal. Ni kuma haɗa rai nayi saboda nasan iskanci yake min. Wucewa tayi ta dauko ragowar cake dasu shawarma ta kawo mana, nidai banci ba saboda yadda na tsane Huzaifa bana iya cin abinda ya kawo. Su dai su Sadeeq sunci. Ta kwashe tarkacen da zata iya tsincewa saita ce, “Kuyi hakuri banyi abinci ba, yanzu sharp sharp zan maku taliya” “Au bama ki daura ba kenan?” Aminu yace yana dariya. “Wallahi kuwa, nifa house chores is not my calling, i really hate it... Kawai saboda ina san Mine ne yasa nakeyi” “Toh fah!” Aminu yace “Mazaaa kaji ance saboda ana sanka ne ake yi a haka” Sadeeq yace. Ni kawai ban kula suba banda chanza channel zuwa Aljazeera na soma kallon labarai. Wucewa tayi kitchen domin ta daura sanwa, wanke wanke ne shake a wajen. Gashi batazo da Dish washer ɗinta saboda kitchen dinta is too small. Wasu daga cikin sun fara yauki saboda tun na jiya dana shekaranjiya ne. Haka ta matsar da wanda zata iya saita dauraye tukunya ɗaya. Saita daura ruwa akan gas, manja ta saka bata ko soya ba saita saka tomato paste. Bata saka albasa ba saboda bata so hannunta yayi wari sai kuma ta zambada barkono. Dauko kifi tayi daga fridge mai kankara, dayake akwai sanyi dayawa, da kyar ta wanke. Ko scales din bata cire ba, haka kashin dake ciki ba duka suka samu daman fita ba. Cikin ruwan dake tafasa ta tsumbula saita saka spaghetti ɗaya ma gardawa uku. Maggi kuwa ta saka kusan goma ma taliya leda daya. Babu kamshin dake tashi bazaka zata ana girki cikin gidan ba, ko su Naufal mamaki sukeyi har yanzu bata daura ba saiga abinci a cooler ta fito dashi. Ta ajiye masu akan dinning table saita koma ta cigaba da kallonta. Ta hada masu Ginger drink mai dan karan zafi, Aminu yana sakawa a baki saida ya fito dashi. Hawaye ya soma gangaro masa saboda zafin dayaji. Sun buɗe cikin cooler sai sukaga taliya kitub ya chabe, gashi mai isheshi ba. Kawai addu’a sukayi kada yayi rashin daɗi. Sun zuba ma kansu amma bazai ishesu ba saidai managing. Naufal ya fara kaiwa baki, zare ido yayi saiya toshe bakinsa da hannunsa. Da sauri ya dauki zuwa yakai baki tunda bazai iya shan ginger dinba. Tauna yakeyi amma abincin yaki wucewa, saida ya sake korawa da ruwa tukun. Gaban Sadeeq ya faɗi sosai saboda a duniya abinci mara daɗi ne baya so. Haka suka ci abincin suna zare ido tareda shan ruwa, kuma kowane cokali saika kora da ruwa saboda babu inda zai wuce da kansa. Kwata kwata bashida dadi kamar an wanke kan mahaukaciya! Sun gamaci sai nishi sukeyi kamar sunyi aikin karfi, “Amarya mun gofe fah, Allah ya saka maki da alheri da duk abinda kikayi mana” Sadeeq yayi mata ba’a. “Haba dont mention, it’s my pleasure” ta amsa tana yauki, dayake bata ciba so bata san how horrible abincin yake ba. Ba Aminu kawai ba har Naufal saida ya bushe da dariya saboda sun san abinda Sadeeq yayi. “Amaryar Naufal kina sha’aninki, Allah ya barku tare” Aminu yace yana kyallara ido ma Naufal. “Amin summa Amin” ta amsa. A hanyar rakasu sai mashi iskanci sukeyi, “Ashe dama haka kake kwasan dadi, yasa naga kayi fari fat kamar fatalwa. wannan shine kaikayi ya koma kan mashekiya”Sadeeq yace. “Aikuwa dai, kaso musguna ma Deela babu gaira babu dalili shi ne Allah ya kama ka” Aminu yace. “Nifa kasan har daina magana yayi min, don kawai ina bashi shawara akan ya bar zancen auren nan. Amma yanzu me gari ya waya ka dawo gida ga wani katon banza ya hakince yana kallon matar ka tana mashi rawa” Sadeeq yace yana kwafa. “Wallahi na rasa yadda zanyi da ita ne, kamar ta raina nine” Naufal yace a sanyaye. “Ai babu tantama ta gama rainaka, if not bazata yi haka ba, but ai duk tsuntsun daya kirawo ruwa shi yake duka”Aminu yace. “Allah dai ya kare” Sadeeq yace. Daga nan suka yi sallama suka wuce. ********** Soyayyar Abla sai kara zama yake a zuciyar khattab, bata bashi fuska at all. Kullum saidai yazo yayita inda inda baya iya cewa komai. Gashi har yanzu bashida number ɗinta. Wata rana yana zaune a cikin Office dinsa saiya dauki alwashin yau zai gaya mata abinda ke cikin ransa. Ya tashi bayan yayi Maghreb saiya tafi gidan su Abla. Maigadi ya fada mashi cewa Abla bata dawowa, dafa kansa yayi yana tunanin inda take sai kawai ya yanke shawara ya tafi gidan gona ya dubata tunda bashida number ɗinta balle ya kira ya tambayeta. Ita kuma Deela ta samu sauki sosai, ta mayar ma Allah komai saboda yanzu har magana takeyi. Ta murmure sosai har Naufal yana tunanin yayi mata maganar komawa ɗakinta koba komai zai samu abinci sosai. Tunda yanzu bawai yana samun abinci isarshe bane, Yasmeenah da kanta tace mashi ya rinka cin lunch dinsa a waje saboda bazata dauki nauyi ba. Missing fadeela yakeyi sosai saboda ko kadan bazata mashi haka ba, dama Hausawa sunce idan baka gode ma alherin da Allah ya baka ba zaka gode ma azabarsa. Ita Abla daga wajen aiki kai tsaye gidan gona ta wuce saboda Deela tanata mata korafi akan ta watsar da ita. Suna zaune akan gado suna shan fruits salad suna hira cikin dakin Miemie wanda yanzu ya zama na Fadeela. Fadeela tace mata ta kwana ita kuma tace batada su brush da kayan sawa. “Indai wannan ne matsalar ki karki damu zan baki” “Allah ya barmin ke matar Yaya” Wayan Fadeela ya soma ringing sai taga sunar Khattab baro baro akan screen. “Assallamu alaikum” “Waalaikumus salam Khattab ya kake ya aiki?” “Alhamdulillahi” sai kuma sukayi shiru na wasu dakikai kadan. “Dama Anty ina kofar gidane bansan ko Abla na kusa ba kice mata ta fito” “Eh gata gefena, babu damuwa” daga nan suka kashe wayar. Deela da fara’arta ta soma magana, “Khattab huh! Gaskiya naji dadi sosai” Hada rai Abla tayi sosai, bata kula Deela ba kuma batada niyyar fita waje yau saboda zuwansa ba karamin takura bane a wajenta. “Tashi mana ki fita kin barshi a waje, wulakanci bashida kyau dai” “Saurayin Miemie ne fah!” “Wani Miemie kuma? Wanda ta rasu ko wata daban, yarinya na ciki kabari kina lakata da wani saurayi. Koko shi Khattab din katako ne da bazai sake aure ba?” “Nifa bawai wulakanci nakeso nayi masa bane, kawai banaso mutane su ce na kashe sister dina domin in aure saurayinta” Deela bushewa da dariya tayi sosai. Ashe Anty tana jinsu, a hasalce ta fara magana, “Bada bakinsu zasuyi magana ba, sufa suke kiɗansu kuma suke rawar su. Fatan Alheri kawai zakiyi ki mance da komai” “Kuma idan zan baki shawara kiji tofa kiba yaron nan haɗin kai, haba sai kace shi kadai yazo duniya, ya gama wahala da Miemie yanzu kema zaki saka mashi ciwon kai” “Ai kuwa dai, yana kokarin sosai ga shida kamala” Deela tace. Ita dai Abla bata ce komai ba kawai zata yi nazarin abinda suka ce ne. Anty ne ta cigaba da magana, “Sau nawa kuma sai kiga Miemie bata rasu ba an fasa da ita ayi dake... Idan fa shine mijinki babu yadda zakiyi gwara kisan me kikeyi” Haka ta tashi rai bai so ba ta saka mayafi ta wuce wajenshi, sallama tayi mashi sai suka gaisa. Daga nan tace masa su wuce cikin Falo amma yace ta barshi cikin motar sa. Sunyi shiru for like 45mins, ita tana wasa da yatsunta shikuma ya kafa mata ido. Dama yaso ya kureta ne yaga ko zatace wani abu amma batayi ba. Tun dayake zuwa wajenta basa kai 30mins, mostly 20mins saiya tafi. “Saidai na kashe ki amma bazaki ce komai ba” bata amsa ba kawai kanta yana sunkuye da kasa. “Abla” “Na’am” “Inaso idan zaki min magana ki rinka kallona” “Toh” saidai kuma bata kalleshi ba. “Abla me kike min haka? banida wani tunani yanzu banda naki.... Please Abla answer me ko zanji saukin radadin danake ji. “Ni babu abinda nake maka” ta fada a sanyaye, shikuma kaima steering duka yayi. “Haba Abla ji yanda kike treating dina kamar nayi maki wani laifi, bafa ni na saka ma kaina ba. Allah ya daura min. Though nasan kina tunanin zanyi replacing Miemie dake ne but Wlh komai dana ke jin maki its different” Shiru tayi kawai tana nazarin abinda yake faɗi, “Abla tunanin me kike yi? Kin tsane ni koh... Meyasa kike min haka? “Nifa ban maka komai ba tun dazu kace nayi maka wani abu” “Kamar ya bakiyi min komai ba, shirun nan is killing me. Nafiso ki saki jiki ki rinka mini magana please” “Toh ai kaima baka magana” Dariya ya soma, “Haba baiwar Allah ta ina kikeso nayi magana bayan kin haɗa rai....salan ki wanka min mari. Please oooo i like life” Murmushi kawai tayi daga nan saita soma hamma alamun barci. Wayarshi ya fitoda akan ta karanta mashi lambarta, ita kuma sai ta amsa zata saka da kanta amma yaki, dole ta rinka kiran masa yana yi da kanshi. Saidai kuma idan tace 7 sai yace 5, haka taketa gyara masa har suka gama. Da gangan yayi mata haka duk salon bata lokaci da ita kuma tace wani abu ko babu dadi. Yayi alkawarin kiranta anjima yaji amsar da zata bashi akan batun su. Nan yayi flashing number dinsa sai yace tayi saving ya gani, Khattab ta rubuta mashi. “Haba mana, Khattab kawai zaki rubuta. Babu dan Baby ko Sweetie yanda yan mata keyi” dariya kawai tayi tana mamakin yanda he is free and very fun. “Okay ni bari nayi saving ki ga naki” ‘Haskena’ yayi storing dashi. Nan fuskanta ya canza saboda kowa yasan Miemie ce Haskensa. Dariya yayi saiya ce, “Allah ya bani Haske da farko sai kuma ya dauke mani ita. Nayi dangana shine ya sake bani wata” Daga masa kai tayi alamun ta gane. Itadai kawai tana tunanin irin amsar dazata bashi anjima ne. Tana isa daki taga Deela tana gyara drawer, kayan suna ne take sake jerawa da kyau. Daga nan sai suka ga Cd plate da aka yi video covering amma basu kalla ba. Fadeela nata ninke kaya daga gefe ita kuma Abla ta dukufa tana kallo a laptop. An nuna Miemie sosai saboda ko ina tana wajen kamar MTN, ga shi little One itama sai dariya takeyi. Video din yana kunshe da happy moments sosai. Ita kuma Deela cin karo da kayan Anty Anisa tayi, “Allah sarki baiwar Allah tana chan port Harcourt” Deela tace cikin ranta. Haka ta gama ninke kayan ta ajiye cikin drawer. Saidai kuma wani abin mamaki bazata tuna sanda sukayi sallama da itaba. Though kuma dai akwai jama’a gashi kuma ya dade da faruwa saboda kusan wata shida kenan idan baima fiba. Abla na cikin kallo saita tsandara ihu saboda sledgehammer din da akayi amfani wajen kashe Miemie ta gani cikin video. ‘Haba Abla meye na ihu kamar ba musulma ba, ni duk kin firgita ni” Hawaye na gangaro mata tace, “Nasan wanda ya kashe Miemie” Da gudu Fadeela ta karasa wajen domin ta gani itama, Abla tayi rewinding amma Deela bayan mutum take kallo. Gashi kuma bata gane ko wacece ba. “Abla nifa bangane ba.... Wai waye wannan? Kin ganta ranar suna ne?” “Eh mana Anty, baki gane.......” #NiDaDiyata *Shout out to Lubna Sufyan, Hussaina Ubandiya, Sumy Gaya, Jidda, Feeyah Galadanchi, Taatuh, Rukky Mt, Kharriya, Mrs Chubado, Asiya Ahmad, Basira Sabo, Fulani, Asmeebae etc, Thank you from me to you* #AinauMardiyah[2/3 11:00] DIMPLES: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 39 ✨✨✨ An-Nawwas bin Sam'an (May Allah be pleased with him) reported: I heard the Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) saying, "The Qur'an and its people who applied it, will be brought on the Day of Resurrection preceded with Surat Al-Baqarah and Surat Al-'Imran arguing on behalf of those who applied them."[Muslim]. ******* Kuka Abla ta fashe dashi ta kasa magana, “Ki fada min wacece mana tunda ke kin ganeta” “Anty ki kalla da kyau mana, yanzu baki gane wannan Anty Anisa bace?” Ras! Gaban Deela ya faɗi, kara kallon video din tayi kuma lallai babu makawa wannan Anty Anisa ce. Kuka ta barke dashi wiwi saboda bata taɓa tunanin Anty Anisa zatayi haka ba. Anty Anisa ta kasance mace ce mai mutunci, batada kyashi ko kadan. Duk cikin asibitin anfison ayi mu’amala da ita. Gata da bala’in fara da tausayi. Ko sanda Fadeela ta haihu haka tayita ɗawainiya da ita. Kowane safe kafin ta tafi aiki saita duba ta. Sun zama kamar yan uwa cikin kwanaki kalilan. Video din na cikin playing kanshi sai aka kyallara Anty Anisa da goyo a bayanta. Anan kuma kallo ya koma sama wajen Deela. Kuka tayita rizgawa saboda kowa yasan Anty Anisa shekarar ta goma da aure amma bata taɓa batan wata ba. Anty Saudah ne ta shigo domin taji dalilin kukansu, anan Abla ta nuna mata itama. Nan kafarta ya soma rawa saboda tashin hankali. Bakin gado ta samu ta zauna tana jimamin wannan abu. Wai yanzu ace mutum bashida tawakkali, idan zata dauki Pha’eexah meye na kashe Miemie kuma. Saidai kuma tasan cewa Miemie bazata bari a dauki Pha’eexah hakanan ba babu wani dambe. Fadeela nata kuka bata ma iya cewa komai, babu mamaki idan ciwonta ya tashi ne. Anty ce ta kira Naufal da Abba a waya wai suzo yanzu yanzu. Naufal a rude ya tashi duk zaton sa Fadeela ta rasu ne, Yasmeenah tana tambayarsa amma bai kula ta ba. Addu’a yakeyi kawai kada worst nightmare ɗinsa ya zama gaskiya. Shima Abba tunaninsa kenan. Nan aka zayyana masu tareda nuna masu video, cikin kuka murya kasa kasa Deela tace bata tuna sanda Anty ta tafi ba saboda kwata kwata basuyi sallama ba. “Dama ni na tsaneta wallahi” Naufal yace Anan aka kira baban Khattab aka gaya mashi. Nan take ya kira ma’aikatan shi wanda suke wakiltan case din domin su soma aiki gadan gadan. Haka aka kwana ranar cikin kunci sabida bakin ciki sabo fal kamar ranar akayi mutuwar. Naufal bai koma gida sai wajen shadayan dare. Haka Yasmeenah tayita zumbure zumbure kamar zata fashe. Washe gari wajen karfe 8, Yan sanda Uku ne a bakin Asibitin. Nan aka soma masu tambaya daya bayan daya akan al’amuran Anty Anisa. Kowa ya shaideta akan kyawawan ɗabi’unta. Kuma gashi ba’a faɗa masu dalilin tambayar ba. An tambaya sabon address ɗinta Kokuma number ɗinta amma babu wanda ya sani. An kuma tambaya inda mijinta ke aiki amma shima wayam saboda ya canza aiki dab da tafiyarta. Anje tsohon inda yake aiki amma ba’ayi dace ba saidai number ɗinsa. Nan take akaje Company ɗin Airtel tareda police report direct wanda IG ya rubuta masu. Daga nan sai akayi tracing number ɗin. Anan aka gane ba Port Harcourt takeba kamar yadda tace. Tana cikin Abia state ne a wani gari da ake kira Isiala Ngwa. Anan aka kira police din state ɗin suje su duba asalin zancen. Motaci uku ne shake da yan sanda da kuma mobile police akan babura suka nufa hanyar garin. Sun isa sai babban cikin su yayi knocking a kofar gidan. Da kanta ta bude saiya fara mata bayanin yana so ya bincika cikin gidan saboda wani case dayake aiki akai. Da sauri tayi kokarin rufewa saboda tasan zancen dayake yin magana akai. Nan take ya hankade kofar kafin ya rufe. Wawan mari ya wanka mata kana wasu yan sanda da bindigogi suka sauko daga cikin Hilux dinsu. Wata yar sanda ta hamɓareta da kafa kana tace, “Yeye woman see how you fine reach but you go dey steal pesin child, Ewu(akuya)” Anan yar sandan ta saka mata handcuffs sai sauran suka shiga cikin gidan gadan gadan. Mijin Anty Anisa yana kan dinning yana karin kumallo sai kawai yaga yan sanda sun dunkareshi, wani sergent ya wanke fuskar shi da mari. “Kaine kake ajiye yar sata koh?” “Ranka ya dade yar sata kuma?” “Ina yarinyar take?” kafin su karasa magana saiga Pha’eexah tana rarrafe ta shigo falo. Wasu yan sanda suka maza suka dauke ta. Nan take ta tsandara ihu, “Yi shiru Ihsaan ba abinda zai faru dake” Anan aka tasa keyar Anisa da Mijinta Aysar zuwa office din yan sanda. Su kuma su Naufal sun hau private plane din office din babban Khattab zasu Abia domin ayi dasu. A cikin jirgin akwai Naufal, Abba, IG, Grand Kadi sai Khattab. Ita Deela tace zata amma aka hanata zuwa, dole ta hakura ta zauna a gida. Daren ranar ta kwana tana sallah saboda bataso taji wani labari ko Pha’eexah ta mutu ko wani abu. Su Anisa da Aysar suna nan tamke a bayan canta, An kwace ma Anisa dan kwalinta da takalmi haka kanta bude, shima Aysar babu hula kansa da kuma takalmi. Su kuma yan sanda nan suka bude chapter dinsu, ashar suketa watsa masu kowa naji. Har sauran wanda ke cikin cell tareda Anisa saida suka zageta. “Aboki naso u wicked reach, ahhha i no fit kill pesin as u see me so. Na fight i fight with my madam na him i enter here.... I swear you are wicked” saita mauje ma Anisa baki kuma tace idan tayi kuka saita kusan karya ta. Shikuma Aysar abin mamaki yake gani wai ance sunyi sata, su dai Ihsaan dinsu watace tayi cikin shege a asibitin su Anisa shine ta basu kyauta. Su Naufal an ajiye su a cikin conference hall zaa fara maganar case gadan gadan. Su Anisa an shigo dasu daure da handcuffs saboda ga Grand kadi basai an shiga Court ba. An kawo baby Pha’eexah ta girma sosai tayi wayo. Tun kafin a soma Magana DPO ɗin wajen yasan cewa yarinyar Naufal ce. Ga kalan idanun ga kuma yanayin fuskar. Shima Aysar yana haɗa ido da Naufal yaji kunya saboda yasan shine babban Ihsaan dinsu. Shi aka fara tambaya yayi bayani. Nan ya zayyana masu cewa Anisa da dadewa tace zatayi masu adopting yaro. Toh sai kuma akayi transferring dinshi. Kiran shi tayi wai ta samu kuma ita zata bar aiki sabida tanaso ta raine yarsu da kyau. Shi bai zirgi komai ba saboda har magana yayi da uwar yarinyar sanda aka haifeta, kuma suna waya akai akai. Dukda bayanin da yayi saida aka zazzage shi tas kuma aka bashi daurin shekara ɗaya da rabi a gidan yari. Shiru akayi sabida anzo wajen gwaskar watau Anisa. Su Naufal basu ce komai ba, shi ko Khattab wasu hawaye suka taru masa cikin ido. Tabbas yasan Anisa saboda sun haɗu a asibiti kuma suna shiri da Miemie sosai. Domin har tana cema Miemie bazata bari tayi aure ba sai tayi masters. Ita kuma Miemie tayita zumbure zumbure daga nan. “Ke kuma Anisa fara bayanin ainihin abinda ya faru?” “Ranka ya dade babu abinda zance saidai kuyi hakuri” “Waye sa’anki anan... Ki fara bayani nace” IG ya zare mata ido. Kuka ta fashe dashi wanda tun dazu takeyi saita ce, “Kuyi hakuri bada gangan naso na kashe ta ba, dama naso na firgitata ne amma saita kamani da dambe wai bazata bani Pha’eexah ba” “Ba abinda muka tambaya ba kenan, daga farko zaki fara bayani” Shiru tayi batace komai ba, wata Yar Sanda taje ta wanketa da mari, nan take jini ya barke mata ta hanci. Yar sandar tace, “Oga Abeg give me 5mins make i handle dis idiot” Wani Dan sanda daban ya nufota tareda hamɓarinta, sai kuma ya shaketa kamar zai cire mata rai. Bata ma iya ihu saboda azaba, hawaye kawai takeyi. Da hannu tayi alama ya daina zatayi magana. Yanka mata mari yayi guda biyu tukun saiya sake ta. Kallon dayan yar sandan yayi kana yace, “see how it is done” Dariya tayi saita ce, “you try small” kallon Anisa tayi dake zaune a kasa, harara ta watsa mata saita mike da sauri. Cikin kuka ta soma magana. “Banyi niyyar cutar da Fadeela ba, kamar Kanwata na dauketa amma kafin taga Pha’eexah na rigata. A hannuna ta fito. Nan take soyayyarta ya shiga raina. Bana wani tunani sai nata” “Toh dama nayi ma mijina magana zanyi adopting amma ban samu ba, shine nace bari na tafi da Pha’eexah garin nan babu wanda ya sani. Toh wata mata makwabciyar mu nake ba kudi ta kira a matsayin mahaifiyar Pha’eexah” “Shikuma Aysar nace masa watace tayi cikin shege kuma batada wadata yasa ta bani ita, sai muka ce zamu rinka kiranta Ihsaan.” “Saidai kuma Miemie tana bani matsala, koda yaushe tana tareda ita, har labari naji tare ma suke kwana, kwata kwata bata bari ta huta suna tare” daga nan sai Anty Anisa ta fara magana cikin faɗa faɗa tana zare ido kamar yar daba. “Shine kawai nace zanyi maganinta, banyi niyyar kashe ta ba saboda ban iya kisa ba, kawai naso nayi mata shegan dukane kuma naɗan karya mata wani sashe na jikinta” Salati kowa keyi saboda idanun Anisa bashida maraba da yan ta’adda. Itama magana takeyi tana zare ido kamar ba mutumiyar kirki mai shakenken murya da suka sani ba. “To sai nayi gurizin sledgehammer daga kasuwa abina, na fada ma Deela zan bar gari saboda bana so a zargeni. Naji dadi da Amaryar Naufal tazo sai hankali Fadeela ta fita daga kaina” “Sun fita zasu rakata sai naga Miemie zaune da Pha’eexah kamar yarta, shine na sidada na shiga anan muka soma kokawa. Nayi mata alkawari idan bata matsa min zan kwada mata amma taki” “Shine na auna mata, amma ba akai naso auna mata ba. Tsautsayi ne wannan. Ina ganin yadda jini ya fara fita daga kanta. Tana rokona nayi hakuri na taimaketa, amma lokacin bana jin kira na kyaleta bansan ko ta mutu ba” “Wajen cradle din Pha’eexah naje, kyakkyawa mai shiga rai. Nan take na dauke Diyata na goya a baya. Sai kuma nayi tunanin idan forensic suka shigo zasu ga prints dina a wajen. Saina goge inda na taba, cradle, jikin Miemie etc. Saina fasa turare tareda kyasta ashana” “Daga nan saina rufe kofa na tafi da key” kuka ta fashe dashi saita durkusa kasa. “Dan Allah karku rabani da Ihsaan dina, itace farin cikina. I deserve to be a mother, please kada ku raba NI DA DIYATA... Bani na haifeta ba but she is mine” Naufal ne yaje ya wanketa da mari, “Bakida hankali, Allah ya isa tsakanin mu dake bazamu taba yafe maki ba. Kuma Allah saiya binma Miemie hakkinta.... Shashasha muguwa azzaluma” Saiya dauki Pha’eexah amma taki sakewa dashi, kuka ta fashe dashi saboda bata san shi ba. Kallon Anisa takeyi tana mika mata hannu alamar tazo ta dauketa. Dariya Anisa tayi sosai saita ce, “Kuna ganin kun raba Ni Da Diyata amma abinda baku sani ba shine bazata sake daku ba saboda ni ta sani, kuma sai kun shiga kuncin da kuka saka ni” Kallonta ake yi saboda kamar tanada tabun hankali, if not ga iyayen yarinya amma tana kiranta Diyarta. Grand kadi ne yanke mata life in prison, abinda yasa yayi haka bai bata ɗaurin rai da rai ba saboda idan akayi mata wannan nan take zaa wanke mata laifinta wajen Allah, amma idan aka bata wahala a duniya kuma taje lahira ta hadu da Mahaliccinta. An kuma barta a Prison din Abia saboda koba komai kabilu zasu ci ubanta sosai, shikuma Aysar Bauchi aka mayar dashi. Nan take yayi ma Anisa Allah ya isa tareda saki uku kyawawa. ******** Ita ko Fadeela Naufal na gaya mata anga Pha’eexah gatama a hannu sa, kukanta taji ta waya, abin yayi mata ciwo amma tasan idan suka ba yarinyar lokaci zata saba dasu itama. Tun daga waya Naufal ya soma ma Fadeela maganar komawa, “Baby we have been through alot, kawai ina tunanin ki dawo dakinki mu raina Pha’eexah tare please” “Okay in sha Allah” dama itama abinda suka gama magana da Anty Saudah kenan. Yanzu an saka one week saita koma. Sun dawo garin Bauchi kowa sai murna yakeyi, saidai kana ganin Pha’eexah kasan tana jin dadi saboda jikinta yayi fluffy yayi kyau. Deela bata damuba da Pha’eexah bata sake da ita ba, tasan cewa komai lokaci ne. Yarinyar tafi sakewa da Mommyn Deela, ita ke bata abinci da goyata. Shikuma Naufal yaje Chuchu Stores ta ɓangaren furnitures yace suzo su canza ma Deela kayan ɗakinta duka. Komai aka canza saidai the same colour ne. Yasmeenah ta shiga tashin hankali sosai saboda yanda Naufal yake rawar kai anga Pha’eexah gashi kuma Fadeela zata dawo. Tunaninta daya, saboda bazata iya zamada kishiya ba wallahi musamman yanda ta saba wataya wa ita kadai. Dole ta nema yanda zata ruguza abin as soon as possible. #NiDaDiyata *Kawayena ban mance daku ba, soyayyarku yana cikin raina. Nana Haruna, Xobeaderh, Khadija Tawan, Xee Harun, Aisha Kirya, Maman Jawahir, Hadiza Pate, Rabie Saeed, Faiza Adamawa and of course not forgetting Maman Eemad* #AinauMardiyah [2/3 22:59] DIMPLES: ©Exquisite Online Writers ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 💦 Ni Da Diyata 💦 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Written by DIMPLΣS Wattpad @Aynarh_dimples 💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦 ✨✨✨Page 40 ✨✨✨ Season Finale ******** It was narrated from Abu Bakr Siddiq that he said to the Messenger of Allah (saas): "Teach me a supplication which I can say during my prayer." He said: "Say: Allahumma inni zalamtu nafsi zulman kathiran wa la yaghfirudh-dhunub illa Anta, faghfirli maghfiratan min 'indika warhamni, innaka Antal-Ghafurur-Rahim (O Allah, I have wronged myself greatly and no one forgives sins but You, so grant me forgiveness from You and have mercy on me, for You are the Oft-Forgiving, Most Merciful)." ********* Yanzu saura kwana biyu Deela ta dawo gidan aurenta, babu irin shirin da ba’a yi mata ba kai zaka zata yanzu zatayi auren fari. An kaita wani Saloon mai suna Loobnerh spa and make over. Anan aka gyara mata gashinta, k’umba, dilke da kuma kunshi. Tayi kyau tayi fresh sosai saboda harda Snail and charcoal spa anyi mata. Sai sheki takeyi itama tana feeling kanta, Anty Saudah ta saka aka daka mata su kuka, yaji, kuɓewa busarsa sannan ta saka aka nika mata su garin danwake da kuma gero. An siyo mata kayan cefane dayawa wanda zatayi stocking a fridge da zai dade mata. Komai chas ana jiran kawai ranar komawanta watau Friday yayi ne kawai. Ita kuma Abla da Khattab shakuwa ne sosai ya kullu ya tsakanin su. Ta sake mashi sosai though shi baya ganin haka amma yana mata uzuri saboda hayaniya da surutu ba yanayinta bane. Mommyn shi tazo tayi ma Fadeela murna kuma daga nan taga Abla, ta yaba sosai da zabin dayayi. Fatan Allah ya kara daidaita tsakanin su takeyi saboda ita yanzu ta samu sirika. Shima Khattab yana jiran a dan kwana biyu ne saboda yayi ma Daddyn sa maganar zuwa gaisuwa wajen su Abba. Yasmeenah hankali a tashe ta kira Laila ta fada mata abinda yake faruwa. Laila tace mata ta kwantar da hankalinta itama ai zata haihu kuma zaiyi rawar kai akanta . Anan Yasmeenah take fayyace mata cewa ta kusan wata uku tana shan contraceptives. Salati Laila tayi tana fada mata ta cuce kanta gwara ta daina. Fada ta hauta dashi tana mata mita akan wani iskanci ne da aurenta batayi haihuwar fari ba zata sha abin. Besides bata lura Naufal is a Family man bane, tun wuri gwara ta daina kafin Fadeela ta kwace Naufal gaba daya. Nan tayi tunanin zuwa asibiti ta duba lafiyar mahaifanta taji ko zata iya daukar ciki. Washe gari ta shirya ta tafi asibiti akayi mata test wanda zata karɓa gobe. Dama bawai tana tambayar Naufal bane idan zata fita. Daga nan saita biya gidansu Lubna ta dauke ta suka wace Saloon ayi mata makeover kafin kishiyarta ta raina ta. Gyaran gashi tayi dasu kunshi, daga nan ta wuce boutique ta siya English wears masu yawa saboda tana so tayita ma Deela feleke sosai. Ita tasan cewa Fadeela batasan yadda ake saka irin kayan ba, ta tabbata koda yaushe tana cikin manya manya kaya marasa shape. Koda ta dawo bata girka masa abinci ba wai tana fushi dashi, shima bai damu ba saboda kwata kwata gobene Deela zata dawo. Tea and bread yasha ya kwanta abin shi. Kiran Fadeela yayi suka sha hirar soyayya kafin suka kwanta, yanzu Pha’eexah ta sake dasu ba kamar da ba, sun siyan mata kayan wasa masu yawa saboda ta samu ta saki jikinta. Next day around 9:30 am.... Yasmeenah ne ke zaune a gaban Dr tana jiran ya kawo mata results ɗinta. Kallonta yakeyi ya kasa gaya mata sakamakon ta. “Malama Yasmeenah, kinada aure ne?” “Eh Doctor” “Yaranki nawa?” “Banida shi Doctor” “Toh meya kaiki shan maganin hana haihuwa, koko mijinki ne yace kiyi haka?” “Lafia Doctor kake min bincike haka? A ina aka taɓa haka? Mallam dalla bani results dina in wuce... Aikin banza aikin hofi daga zuwa asibiti sai kuma akace na gaya maka sirrina” kallonta yayi cikin mamaki kana ya mike mata results ɗinta. Fizgewa tayi ta balla masa harara kana ta mike tsaye, ta soma tafiya harta kai kofa sai yace, “Results dinki yana reading bazaki iya haihuwa ba saboda mahaifarki ya lalace sanadiyar contraceptives kala kala da kike ta dirka” “Karya kake munafuki bokan bature... Mts” tace saita wuce. Ta tafi motarta ta shiga saita kara dubawa. Nan take ta rude tareda fashewa da kuka. Ta dauki wayarta zata kira Naufal saita tuna sanda tayi abinta bai sani ba, lambar Huzaifa ta kira, bugu daya ya dauka. Kuka ta fashe mashi dashi nan take ya rude. Ce mata yayi ta tafi gida gashinan zuwa ya sameta. Shikuma yau ya dauki alwashin kashe k’ishinsa a jikinta, ya lura ta raina masa wayo ta mayar katako. Amma yau zai bata mamaki, duk wannan rawar da take keyi gabansa tareda saka bom short zaiyi maganinta. Ya dauki alwashin saiya gwangwaje a jikinta son ran shi, idan yaso ta gaya ma Naufal ya sakota daga nan yama aureta baki daya. Dama leggings da yar top ke jikinta saita daura abaya dazata fita, yanzu ta cire tana zaune akan one seater tana kuka. Huzaifa ne ya shigo da wani smug face yana wani kallonta. Gashi dama tayi gyaran jiki sai sheki takeyi, nan take ya kara jinta cikin birinin ransa. Nan yaje dab da ita ya rike mata hannu yana murzawa a hankali. Magana ya soma da muryansa na yaudara, “Toh menene dan bazaki haihu ba? Ai ba kowane namiji ke son yara ba, besides idan yana sanki bazai dameshi ba” Da jajayen idanta ta watsa mashi harara, wata rana idan yayi magana saika zata mahaukaci ne. “Kamar ya ba kowane namiji keson yara bah? Bora kake so na zama akan bana haihuwa?” “Ni kinga idan ina son mace zan so komai akanta” “Look mallam bana san shiririta anan, haba ina serious talk kana kawo min zancen ka... Aurenka zanyi da kake gaya min haka!” “Sorry my dear, ba haka nake nufi ba, come close and give big bro a hug.... Everything will be alright in sha Allah” Tashi yayi yana kokarin jawota jikinsa, ita kuma saita noke, “C’mon lil sis im just trying to cheer you up” Babu wani gardama ta yarda, ita tasan bata san shi kuma babu yadda zata kashe aurenta akan shi. Besides bayau suka saba hugging ba a matsayin au na yan uwa. Tana makale a jikinsa tana kuka a hankali, kirjinsa ne ya soma bugu da karfi, gaskiya soyayyarta yayi zurfi cikin ransa. Ya yanke shawara akan ya samu rabonsa wajenta kafin ya mutu. Shikuma Naufal yaje ya dauko Family ɗinsa, Abba ya zaunar dasu yayi masu nasiha sosai akan aure. Daga nan sai suka wuce gidansu Deela suma su Grand kadi suyi masu nasu, shi masu albarka akayi sai Mommy tace bata yafe ma Fadeela ba idan ta bar gidanta da sunar yaji. Murna fal zuciyar Naufal, bai taba daukinta ba kamar yau, baya ma behaving kamar yanada wani mata a duniya. Gashi soyayyar Pha’eexah sai kara dasuwa yake cikin ranshi. Yana tuki hannunsa daya yana makele dana Fadeela kamar wani zai kwace mashi ita. Anan ne Deela tayi masa maganar Abla da Khattab. Mara misaltuwa ya nuna saboda tuntuni Khattab ya nuna shi mutumin arziki ne kuma he will be honored ace shi sirikinsa ne. Sun isa gidansu sai yaga motar Huzaifa, tsaki yayi cikin ranshi tareda faɗin, ‘Aikin kenan’ Shikuma Huzaifa a hankali ya soma shafa Meenah, yanayi kamar yana petting ɗinta ne amma tsantsan iskanci ke ranshi. Daga nan saiya kaima bakinta chapka da nashi, tureshi tayi tana mashi kallon mamaki, “Meye haka yaya?” “Nifa munafunci ne bana so, kamar ya meye haka... Baki lura da abinda ke shirin faruwa bane” “Look Huzaifa bana san iskanci, dama manufan ka kenan koh? Oya maza maza ka barmin gidana kafin ranka ya baci” “Dama zan tafi amma saina yi abinda ya kawo ni wajen ki, dayake kin raina ni koh.... Kiyi ta seducing dina kamar bakisan me kike yi ba. Ke jahilar ina ne? Bamu hada uwa da uba dake ba amma ki rinka abinda kika dama a gabana all in the name of civilization.... Well okay dear nima im going to be civil on your body” Nan ya finciko ta ya matse da jikinsa, tana kokarin tureshi amma ta kasa. Kissing dinta yayi kokarin yi saita yanka mashi cizo. “La la la la dan ubanki ni kika ciza? Yau sai na nuna maki baki iya bariki ba” Nan ya fige rigarta saida ya yaga tas, jikinta ya bayyana ita kuma ta fashe da kuka tana kokarin rufe kirjinta da hannayenta amma duk a banza. Wani ja’irin dariya yayi saiya fito da wani kwaya daga aljihunsa ya saka a baki ya haɗiye. Nan idansa ya canza kala babu alamar wasa a tareda shi, tana kokarin dambe dashi ya yanka mata mari, amma bata hakura ba sabida bazata iya barin wani wawa yaci amanar Naufal ba. Nan ta cigaba da kici kici dashi amma kwayar daya sha ya soma aiki a jikinsa, kuka takeyi tana naiman taimako amma babu wanda zai taimaka mata. Tsine mashi takeyi da iyayensa da kakaninsa amma duk a banza. Yakushi takeyi amma ina, daya ga tana bata mashi lokaci saiya nakada mata duka wanda ya sakata likis ko numfashi zafi yake mata idan tayi. Ta zama abin tausayi sosai saidai kuma ita ta jawo ma kanta. Nan ya fashe da dariya, baiyi wata wata ba ya keta mata haddi a cikin falonta, hawaye kawai ke gangarowa daya bayan daya, sukuma su Fadeela sun shiga falo saiga Huzaifa yana kokarin mayar da kayansa. Salati suka somayi saboda kowa yasan abinda ya faru, nan gaban Huzaifa ya faɗi. Gadan gadan Naufal ya nufa inda yake ya soma auna mashi naushi. Dukansa yakeyi kamar Muhammad Ali wani shahararen boxer a Amerika. “Dan ubanka da matana zaka yi iskanci a cikin falona dan bakada hankali” ya farfasa mashi baki da hanci duk ya kumbura mashi fuska. Nan yayi mashi las kana ya ingiza shi waje da ragowar kayansa a hannusa. Ita Deela nadaga gefe rike da yarta suna kuka. Dama ita ta fara sai Pha’eexah ta chapka. Ita kuma Meenah wanda zuciyar ta yana mata radadi, kawai mamakin cin amanar da Huzaifa yayi mata take. Maganar taji daga sama kamar saukar mashi. “Ba iskanci ba koh? Jeki dan ubanki nayi maki saki uku. Sai ki goma gidanku kuci gaba” nan ta rinka kokarin tashi tana so ta roke Naufal amma ya fizge hannun Deela sunyi hanyar upstairs. “Mine karkayi min haka, na ranste da Allah raping dina yayi” “Kanki kika raina amma bani ba, kuma ke kika san wannan saboda ni na riga sake ki.... Kuma Allah ya isa cin amata da kikayi” Wajen 9pm..... Naufal yana kwance akan gado, ya gama gaya masu Abba abinda ya faru da Yasmeenah. Kuma ya kira Abban Huzaifa ya gaya mashi komai. Yaba Naufal hakuri sosai tareda mashi fatan alheri, shi karin kanshi shedancin yaransa ya fara kaishi bango. Ita kuma Yasmeenah akwati daya ta dauka ta tafi gidansu ta gayama Mommy abinda ya faru kuma ta roketa taje ta bama Naufal hakuri. Zagin ta tas tayi sannan tace mata sanda take barin Huzaifa koda yaushe cikin gidanta bayan tasan halinshi bata san da zancen ba, saboda haka yanzu ma babu ruwanta. Duniya yayi mata zafi tana kaico da hali irin nata, tabbas Huzaifa ya cuceta kuma bazata yafe mashi ba. Sai wani karamin murya cikin ranta yace Huzaifa bai cuceta ba ita ta cuce kanta. Fadeela tana kwance jikin mijinta tana tuna irin obstacles din dasu kayi over coming, lallai duniya akwai abubuwa kala kala. Ko sau daya bata taɓa tunanin Anty Anisa zata iya abinda tayi ba, wai ace mutum babu tawakkali samsam cikin al’amuran sa. Kome Allah ya baka koya hanaka duk yanada kyau ka gode masa, bakasan alherin dake gaba ba. Sai kuma Yasmeenah da wani gardi a dakin aurenta. Koda yake tsautsayi babu yadda baya giftawa kuma Allah ya rabamu da irin wannan. Shiko Naufal yana makale da matarsa da kuma yarsa, Hamdalah yakeyi yau he has his complete family with him. Wani tunani ya faɗo mashi cikin rai. Tuntuni dayake kiran Deela bad luck but asalin Bad luck din itace Meenah. Na farko yana haduwa da ita aurenshi ya lalace da Deela, a lokacin ya koya karya kamar tubabben sarki. Na biyu yarsa ta bace bayan haduwarsu, na uku kuma ga mutuwar Miemie. Sannan kuma anyi kwartanci a falonsa. Yasan chamfi haramun ne but Yasmeenah is really a bad luck. Yanzu babu abinda zaice face Allah ya raka taki gona. Six months later...... Rayuwar Meenah yazama darasi ga mutane dayawa, ko ina taje zunɗenta akeyi. Tayi kuka harta gode Allah. Gashi duk samarinta na da sun gudu suna tsoron kada su aureta ta rinka kawo masu kwarto cikin daki. Shidai Huzaifa yace idan tanaso zai aureta, da farko bataso ba asalima restraining order tayi placing tsakanin su. Amma daga baya tayi ma kanta karatun ta natsu, yanzu batada mahaifa so gwara ta rufa ma kanta asiri tunda yace yaji ya gani. Fadeela kuwa ana kaiwa da komawa saboda yaune bikin Abla da Khattab. Kowa ya taru ana masu fatan alheri. Khattab burinsa ya cika saboda zai aure Haakensa mai haska mashi zuciya. Itama Abla ana rawar kai za a zama amarya. Gaba daya kowa bakinsa kamar gonar auduga domin murna. Baby phaexah an fara tafiya so cute kuma yanzu ta saba da iyayenta na asali. Naufal kuma an murmure sai sheki yakeyi saboda Deela tana kula dashi yadda ya dace. Komai nasu gwanin ban sha’awa kuma suna fahimtar junansu yadda ya dace. Ko sunyi fada basa kwantawa da junansu a cikin rai. Ya bude mata katon art studio inda ake exhibiting paintings kuma suna tallafa ma young talented artist. Gashi kuma su Mr Sutter suna kokarin bashi head din branch dinsu ya wakilci Nigeria gaba daya. Komai yana zuwa masu da sauki tabarakta masha Allah. Idan Deela ta zauna ta tuna abinda ya faru da ita a baya babu abinda take jin dadi sai irin hakuri da mayar ma Allah komai da tayi. Tasan cewa hakuri yanada fa’ida a musulunci kuma ko Hausawa sunce mai hakuri zai dafa dutse ya kuma sha romonta. Gashi yanzu tana ganin fa’idan hak’urin sosai. An daura aure ankai Abla Gidanta a GRA bashida nisa da gidan iyayen Deela. Naufal ya kira Deela domin yaji Lafianta, “Hello baby nayi missing dinki fah, wannan bikin ya kware ni dayawa” “Other half karka damu gamu nan zuwa” “gaku nan zuwa dawa?” “NI DA DIYATA mana, who else?” “Iyye masu yarinya, please ya kamata ayi mata kani koh babyna?” dariya Fadeela tayi sosai sai tace “Soon.... In sha Allah very Soon” “Okay babyna saikun zo, dont forget to remember i love you so much kinji koh?” “I love you too, sai mun iso” ALHAMDULILLAH RABBIL ALAMIN, anan na kawo karshen wannan littafi mai suna Ni Da Diyata. Allah ka bamu ikon amfani da darusan ciki.... Amin Wannan littafi na sadakar dashi zuwa kawata Xaynarb B Idreez (Maman Eemaad), ke ce Ni da diyata saboda without you babu shi. Allah ya albarkace Muhammad Eemad... Amin. Sannan best friend dina Nanah Fatima, Allah ya albarkace kawancen dake tsakanin mu. Ga yabon girma ga sauran Kawayena kamar su Xee Haruna,Aisha Sulaiman, Xobeaderh, Xeemee, Khadija, Aisha Kirya, Hadiza Pate, Rabie Saeed thanks from me to you. Idan kuna tunanin kunsan DIMPLΣS kuma bakusan cewa inada kannen kamar su Ummiejafar(Pha’eexah) da kuma UmmieKhaleel (Aysha) then you have no idea of who i am. I don’t know the correct word to explain how amazing you cuties are. I really appreciate everything you do towards me...Allah kuma ya albarkace rubutun da kukeyi ya kuma kareku daga sharrin mashanranta... Thanks so much cuties. Ban mance daku ba, Ummie Rilwan(Fatima), Sumy gaya, Jidda, Asmeebae, Red Butterfly etc. Kuna raina writers kamarsu Lubna Sufyan, ZeeNaseer, Sadnaf, Cute Zarah, Lemmcy, Fulani, Rash Kardam, Hamagee, Fiyya Galadanchi, Fatty Azland, Xoubie, Mjay, Hussaina Ubandiya, Momyn Sultan, Badiya Yusuf, Zainnundeen, Kdeey, Ayusher, Natty Gal, CwtJidda, Mmn Shukra, Ummul khairi etc. Fatan Alheri ga wattpad fans dina, thanks so much cupcakes, i love you guys so much, you’re comments was superb and it kept me going... You guys made Ni Da Diyata the number one story under Spiritual for weeks #OneLoveSweethearts Facebook groups kamarsu Ummu Maryaem Novels and Deyart Yusuf Novels. WhatsApp groups kuma kamar DIMPLΣS, Ummiejafar Novels, Xarah Bukar Novels 1, Hamagee Novels, Marubuci, Matan Arewa, kema ki Girka, Hausa Novels, Rash Kardam Novels, Gidan Buki etc.... Thanks so much. Naku daban ne, Exquisite Online Writers saboda daku nake tinkaho, Allah ya sake hada kanmu kuma ya karemu daga sharrin mashanranta. Kada ku mance you can only reach me on Wattpad @Aynarh_dimples for any comments or recommendations. Also check my new book dat will be posted there titled ‘Yan Gidan Gwaiba. Da fatan shima za’a amfana dashi. Subhanakallahuma wa bi hamdika, Ashadu Allah ilaha ilallah, Astagarifullah wa atubu ilayhi. Ainau Mardiya also known as yarinya Mai DIMPLΣS