[1/29, 16:19] +10 7812: *NI BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *NA* __Zee_ _MD_ ✍🏻 *Hamdala* *Writer's* *Association*💪 https://www.facebook.com/14371046 ✨✨ *{{* *H.W.A* *}}* ✨✨ *Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim* _Inayiwa_ _'Daukacin_ _Masoyana_ _Fatan_ _Alkairi_ _wanda_ _Nasani_ _dawanda_ _Bansaniba_ , *Wannan* *littafi* *Nawa* *Mesuna* _Ni_ *BORA* _Ce_ _Banrubuta_ _dan_ _Rayuwar_ _wata_ _kowaniba_ _Narubutane_ _kawai_ _dan_ _nishad'i_ _kuma_ _k'agaggene_ , _Duk_ _wanda_ _yayi_ _Daidai_ _darayuwar_ _sa_ _toyayi_ _hak'uri_ *Allah* *yasa* *mu* *Amfana* *da* *darusan* *Dake* *ciki* _Ameen_ *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Mesan* *karantawa* *tabiya* _200_ *Kacal* _Zaki_ _Tsinci_ _Abinda_ _ko_ _Dubu_ _Dari_ _Biyu_ _Bazata_ _Siyamiki_ _Shiba_ _Bokomai_ _Bane_ _Face_ *Darasin* *Rayuwa* ✍🏻 🆓 page. 1 Zaune nake abakin gado inbanda kuka babu abinda nakeyi , wannan wanne irin aure nayi ni Hanan ? tambayar dana fara yiwa kaina kenan , tunda aka kawoni gidan Alhaji Nasir yau kwana na uku amman bantab'a tsintar farin ciki ko sau d'aya ba , Tabbas Nasan da Ammi tasan wanne irin miji Kawu Idi ya auramin da bata amince ba , Ashe haka gidan Alhaji Nasir yake ? Ashe daman matan sa Uku 'Ya'yansa Ashirin da Bakwai , Wayyo ni Hanan naga takaina Kawu Idi ka cuceni , Kuka take iya k'arfinta tamkar ranta zai fita , Shigowar Alhaji Nasir yasa ta sassauta da Kukanta , Dan wani mugun tsoronsa takeji , gakuma wata irin tsanar sa datakeji , yana k'arasowa ya Zauna kusa da ita tamkar zai shige jikinta , dasauri taja da baya tare da mik'ewa tsaye , dubanta yayi Ransa a b'ace yace " wai ke meye hakan da kikeyi ? nifa mijinki ne ba kwarto ba , sadaki na biya sannan kowa yasheda hakan, tunda aka kawoki cikin gidan nan nake fama dake , a yau inaso kisani wallahi ko kiso ko ki k'i jikinki saina mallakesa yazama nawa , sannan inaso kisani gidana duk matar da na aura bana rabuwa da ita sai dai in mutuwa tayi , mik'ewa tsaye yayi da hanzarinsa kafin ta motsa ya cafko ta , tuni ya wurgata kan gado yayi mata rumfa , ihu take tana kaimasa duka amman baisan tanayi ba , Sai dai me ? Maimakon taji ya kusance ta ta gaba sai jin Sab'anin hakan tayi , Dan jitayi yana tura gabansa ta wajen datake Bayan gida wato bayanta , Turk'ashi ai tuni wata azaba ta ziyarci duburar Hanan ta kwallah k'ara kafin ta sume ...... Shikuwa ko ajikinsa asalima wani irin gurnani yake tamkar mafaraucin zaki , ga wani miyau yana fitowa ta bakinsa tamkar wani k'aramun yaro , wani irin ihu yake yana sambatu har yajuye mata ruwan mararsa , d'agata yayi batare da yabi takanta ba yafice abinsa..... Hanan tafi awa d'aya ahaka kafin 'yar gidan Alhaji Nasir tashigo d'akin , tana shigowa tayi tozali da Hanan da sauri ta k'araso wajen ta tana kiran sunanta , ruwa ta d'ebo tazo ta watsawa Hanan d'in a fuska , wata ajiyar zuciya tayi tare da bud'e ido , aikuwa tayi ido biyu da Nasma wacce ta kafeta da idanu tamkar mayya , dasauri ta yunk'ura zata mik'e sai dai wata Azaba data ratsata ta k'asanta tuni ta koma ta zauna , Kuka tasaka tare da cewa Nasma "Dan Allah ki d'aukeni kikaini gidan mu gurin Ammina wayyo zan mutu , Nasma wacce zasuyi sa'anni da Hanan ko tagirmi Hanan d'in ma taruk'o hannun Hannan tana cewa "Haba Matar Abba kema kinsan haka first Nirth yake sai hak'uri , Bari nahad'a miki Ruwan zafi zakiji dai dai , Daman Alhaji Nasir d'in ne yaturo ta dan tagyara Hanan d'in , Mik'ewa tayi ta nufi Toilet dan had'awa Hanan Ruwan wanka , ita kuwa Hanan Kuka take tana cewa "Allah ya isa tsakanina da Kawu Idi , wannan wacce irin rayuwa ce ta dabbobi ? ita ko alabari bata tabajin ana kusantar mace tabaya ba saikace wacce Dabba sai ita , tabbas dole tasan abinyi tun kafin Alhaji Nasir yakasheta, Maganar da Nasma tayi ita tadawo da ita daga tunanin datakeyi , K'arasowa tayi har kan gadon ta d'agota tana fad'in " muje ga ruwan can na had'a miki inkikayi wankan zakiji k'arfin jikin naki sosai , Hanan bata musa ba ta yin k'ura zata tashi sai dai me ? jitayi wani abu nafitowa ta k'asanta babu birki ga wani irin wari lokaci d'aya ya ziyarci cikin d'akin , da Sauri Nasma taja baya tare da toshe hancinta......... *Tofah* *Yakukaji* *Salon* _wannan_ _littafi Yayi_ _Daban_ *Akwai* *Turka* *Turka* _kuyi_ _K'ok'arin_ _Mallakar_ _Naku_ _Akan_ *200* _Kacal_ _kukaranta_ _Cikin_ _Aminci_ 🥰 *Taku* *'Yar* *Mutan* *Kanawa*😍🌹 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Na* _Zee_ _MD_✍🏻 *Hamdala* *Writer's* *Association* 💪 https://www.facebook.com/111403834371046 ✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨ *Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim* *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *tayimin* *Magana* *ta* *wannan* *Number* , 07046107812 *kuyi* *k'ok'arin* *Mallakar* *Naku* _karkubari_ _Abaku_ _labari 🤝🏻🤝🏻 kusiya_ _kukaranta_ _cikin _Aminci_ 🆓 page . 2 Dubawar da zatayi sai ganin kashi tayi yanata zubowa , wani tsoro ne ya ziyarce ta lokaci guda , nana take tafara Kuka tana fad'in " shikenan Alhaji kacucune wayyo Allah ni Hanan yazanyi da rayuwata , Nasma tana jin hakan tafara mamakin taya za'ace kashi na zubowa haka, mai makon ma taga jini kamar yadda tasaba ji a first nigth d'in Amare suna gani ? nan take tsoro yakama ta , to meye yake shirin faruwa da Hanan d'in ne ? Hancin ta na toshe ta taimaka wa Hanan sukayi cikin toilet , da k'yar tasamu kashin ya tsaya tafara k'ok'arin gyara jikinta , Nasma tunda aka kawo Hanan gidan su taji jininsu ya had'u , dan duk aure auren da Daddyn su yakeyi bata shiga sabgar matansa , dan duk wacce ya auro ta hud'u to ita yake saka yakuma auro wata , sauran mata ukun ne dai suka zamar masa cingum , shiyasa tunda taga Hanan taji ta shiga ranta kuma take tausayinta , yanzuma bataji k'yank'yamin kashin da Hanan d'in tayi ba ta nad'o zanin gadon tafara gyara mata d'akin , Hanan ta dad'e tana gyara jikinta tana gasa k'asanta wanda takejinsa kamar ana tsatstsaga mata shi , a hankali ta lek'o tana cewa Nasma "dan Allah kibude wodrop d'ina ki mik'omin kayana zansa , Nasma ta juya ta d'auko mata kayan ta mik'a mata .... A can cikin gida kuwa Hajiya Hajjo ita ce uwar gidan Alhaji Nasir , ta kasa ta tsare tana jiran Hanan tazo tayi musu girki , tunda itace da miji dan haka ba wanda zai mata girki , tana nan zaune tana k'wafa ta cika ta batse , dan duk cikin gidan bawacce takai Hajiya Hajjo masifa kowa shakkar ta yake , Ganin Yamma nayi yasa Hajiya Hajjo nufo d'akin Hanan d'in ido rufe da masifa har tuntub'e take , tana zuwa ta buga k'ofar d'akin da k'arfinta na gaske , tafara k'walawa Hanan kira tamkar wacce tayi mata wani mugun abu , Hanan dake taka k'afa a hankali tamkar 'yar kaciya saboda azaba , tanajin kiran da Hajiya Hajjo takeyi mata sai da taji k'irjinta ya buga saboda tsoro , ita a yanzu kowa ma tsoronsa takeji a cikin gidan , shurun datayi ne bata amsa ba yasa Hajiya Hajjo shigowa cikin d'akin , lokacin Nasma tagama wanke komai ta fito , Hajiya Hajjo ta dubi Nasma tace " Munafika daman kina cikin d'akin kenan , to inaso ki zaunar da ita kigaya mata dukkan sharud'an cikin gidan, sannan inaso kisanar da ita wacece ni a cikin gidan sannan ya halina yake , kafin sannan yanzu yanzu inaso kifad'a mata tatashi taje ta d'ora mana girki dan muna da buk'ata , juyawa tayi tafice daga cikin d'akin tamkar kububuwa , Nasma taja ajiyar zuciya tana jinjina kai , saboda tafi kowa sanin wacece Hajiya Hajjo , kallan Hanan tayi tace "tashi kiyi sauri kije kiyi abinda Hajiya Hajjo tasaki , rashin yin wannan girkin zai jawo miki abinda yafi wanda kike cikin yazu , kiyi hak'uri ki daure kije kiyi insha Allah komai zaiyi sauk'i , Hanan ta goge Hawayen dasuke gangaro mata tace " Nagode sosai 'Yar uwa , indai kinsamu lokaci inaso kizo kigayamin k'a'idojin cikin gidan , sannan kuma inaso insan sunanki dan indinga kiranki dashi , Nasma tagaya mata sunan ta sannan tace " in anjima da daddare nasan Abban mu baya dawowa da wuri zanzo dan nabaki labarin cikin gidan nan namu dakuma dokokin , suka mik'e dukansu suka fita daga daga cikin d'akin gudun jarabar Hajiya Hajjo...... Kuyi maneji😜 *Littafina* *Na* *Kud'ine* *kisiya* *kikaranta* *cikin* *Aminci* 🤝🏻🤝🏻🥰 *Taku* *'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 🥰🌹 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Na* _Zee_ _MD_ ✍🏻 *Hamdala* *Writer's* *Association* 💪 https://www.facebook.com/111403834371046 ✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨ *Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim* *Littafina* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *kuyi* *k'ok'arin* *Mallakarsa* _kukaranta_ _cikin_ _Aminci_ *Sai* *Najiku* *Masoya* 🤝🏻😍 🆓 page. 3 Hanan na k'arasawa wajen dataga Hajiya Hajjo a zaune ta durk'usa tana fad'in " gani Hajiya wanne aikin zanyi ? Hajiya Hajjo ta watsa mata Harara ta nuna mata cikin kitchen tace " kishiga ciki ki d'ora tukunya sannan ki kizo nan , cike da girma mawa Hanan tace to sannan ta mik'e ta nufi kitchen d'in , tana shiga tayi tozali da wata Babbar Tukunya tamkar a gidan biki , gawasu k'atun k'atun d'in dutsuna na wuta dakuma tarin ice a gefe , Nan take Hanan taji wani irin kuka yazo mata , wannan wacce irin Rayuwace zatayi ? yanzu ita taya zata iya had'a wuta a wannan murhu kuma har ta iya d'ora wannan tukunya ? tun tasowar ta a gidan su bata tab'a kunna ice ba , saboda daga ita sai Ammin ta suke rayuwa , girkinsu bashi da yawa dan watara na ma basayin girkin sai dai suyi d'an ciye ciyensu su kwanta , tana tsaye tana tunanin yadda zata iya had'a wuta har ta d'ora tukunya taji anshigo cikin kitchen d'in , juyowa tayi sukayi ido biyu da Nasma , wani sanyi taji aranta dan tasan zata taimaka mata , Nasma batace komai ba tahau saka ice cikin murhu kafin ta kunna ashana , Nan danan wuta taka ma Nasma ta ciccib'i tukunya ta d'ora akan murhu , duban Hanan tayi tace " kije kicewa Hajiya Hajjo me za'adafa , kuma karki nuna muna tare a cikin kitchen d'in nan , dan intasani wallahi kashin mu ya bushe nidake , kinga kitchen d'in nan duhu ne dashi koda tazo bazata ganni ba , Hanan tace " to Aunty Nasma nagode Sosai tafice cike da d'an saurinta ..... Nasma ta girmewa Hanan da kad'an shiyasa tafita wayo , Hanan tana zuwa gun Hajiya Hajjo ta sheda mata ta d'ora tukunya me za'a dafa ? saida Hajiya Hajjo ta bushi iska kamar bazatayi magana ba sannan tace " kice ki tsayar da ruwa sannan kizo ki anshi abinda zaki dafa , Hanan tace " to sannan ta mik'e ta nufi kitchen d'in.... Gayawa Nasma tayi yadda sukayi da Hajiyar , dama akwai diron ruwa a cikin kitchen d'in nan suka d'iba suka zuba , Nasma tana nunawa Hanan adadin Ruwan dazata dunga zubawa intatashi girkin , sannan tacewa Hanan " abinda yasa nake nuna miki yadda zakiyi saboda innakoma sch nasan ke kadai zaki dunga aikin nan , kuma kinsan yanzu kece zaki dunga aikin komai a cikin gidan nan bawanda zai tayaki , haka tsarinsu yake duk wacce Abbanmu ya aura to komai ita zata koma yi , Hanan idon ta yayi raurau tace " yaushe zaki koma sch d'in kuma ? Nasma ta matso ta dafa kafad'ar Hanan tace " saura sati biyu nakoma , amman ai in nadawo da wuri zandunga tayaki aikin , Hanan ta goge hawayenta tace " Nagode sosai Aunty Nasma , Nasma tayi saurin saka yatsa a baki tana cewa " karki k'ara cemin Aunty saboda nice yakamata Nace miki tunda ked'in Matar Baba nace , koda na girmeki ai kinriga da kinzama Auntyna kinji ko , Hanan tace " Dan Allah nidai kibarni nace miki Aunty kawai , Nasma tace " to shikenan na amince dukan mu mu girmama junan mu , Murmushi Hanan tayi tace "to nima na amince , Nasma tace " jeki ki anso abinda za'adafa kidawo , Hanan tafita fuskar ta a d'an sake dan Nasma tagama faranta mata rai..... Tana zuwa Wajen Hajiya Hajjo ta tarar da shinkafa dawaya cikin wata roba , sai kuma wasu kayan miya 'yan kad'an a leda , sai maggi da mai dukansu bawani na arzik'iba , duba dayawan shinkafar da za'a dafa amman kayan had'inta 'Yan kad'an , Hajiya Hajjo ko dubanta batayi ba tace "d'auki kibani waje malama kin tsareni da idanuwa tamkar mayya , da sauri Hanan ta sunkuya ta d'auki kayan tabar gurin... Nasma ce ta taimaka wa Hanan har suka kammala girkin , bayan sun kammala Nasma tadubi Hanan tace " Aunty Hanan yanzu kinsan yadda za'ayi ? Hanan tace a'a , to yanzu tashi zakiyi kije kigaya mata kin kammala girkin , nikuma zanyi k'ok'arin barin kitchen d'in tunkafin tazo rabo ..... Hanan tace " to Aunty Nasma , bari naduba naga tsakar gidan in babu kowa sai kifita , lek'owa Hanan tayi a hankali tsakar gidan wayam taganshi babu kowa , ta koma tayiwa Nasma nuni data fito babu kowa , Nasma a hankali tafito batare da kowa yaganta ba ..... Hanan taje har cikin d'akin Hajiya Hajjo ta sheda mata ta kammala abinci , Hajiya Hajjo ta dubeta shek'ek'e tace " zaki iya tafiya inna raba kyazo ki anshi naki , Hanan ta mik'e tafice tana Hamdalar tafita daga tarko na farko ... Hanan komawa d'akinta tayi ta zauna tana tunanin rayuwar dazatayi a cikin wannan gida , Tayi Nisa a tunaninta taji andafa kafad'arta , a zabure ta juyo sukayi ido biyu da Nasma tana mata murmushi , Kwanukan Abincin dake d'aya hannun nata ta ajiye sannan tace " yakamata fa Kirage tunani karki kamu da hawan jini , Sauko ga abincinmu nan muci kibani labarinki da kuma yadda kika auri Abban mu , nima zanbaki labarin duk abinda gidanan yake ciki , Hanan ta sauko k'asa suka zauna akan capet suna duban juna , Murmushi Hanan tayi sannan tace " Tabbas zanbaki labarina da yadda akayi nashigo cikin gidannan aure.... Kuyi manegi Anyi mun rasuwa yanzu ina barar adduarku👏🏻👏🏻👏🏻 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Na* _Zee_ _MD_ ✍🏻 *Hamdala* *Writer's* *Association* 💪 https://www.facebook.com/111403834371046 ✨✨ *{{* *H.W.A* *}}* ✨✨ *Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim* *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *k'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *kukaranta* _Cikin_ _Aminci_ *Saina* *jiku* *Masoyana* 🤝🏻😍 🆓 page. 4 *Asalin* *Labarin* *Hanan* Ni Hanan Haifaffiyar garin Jos ce , Mahaifina d'an asalin garin Numaiy ne can birnin Niger , acan iyayensa suke , su biyu iyayensa suka haifa a duniya dagashi sai K'aninsa , iyayensu sun rasu dukansu , hakan yasa Baffa wato Mahaifina ya d'auko k'aninsa suka baro garinsu , Sun sauka a garin Jos suka fara sana'ar saida kayan lambu , Allah yasawa sana'ar tasu Albarka suna samun kud'i ba laifi , lokacin Baffa na ya yanke shawar yasaka Kawu Idi wato k'aninsa Makaranta , Kawu Idi bayajin Magana sosai tun yana yaro , dan haka Baffa na yasakashi a Makaranta wacce in yatafi sai yamma yake dawowa , Akwana a tashi Baffa na yafara neman Aure , ita kuma Ammi ta Gidan dasuke haya anan Shagon Baffa na suke kwana , tunda Baffa yaga Ammi hankalinsa ya kwanta da ita , ahaka har shak'uwa me k'arfi tashiga tsakaninsu , Mahaifin Ammi na bashi da wani k'arfi , Matar sa d'aya itace Mahaifiyar su Ammi , su Uku iyayensu suka haifa suma , biyun duk maza ne sai kuma Ammi ita kad'ai ce mace a cikinsu , Baffa da Mahaifin Ammi jininsu yahad'u sosai , kusan kullum in sundawo daga wajen kasuwancin su zasu zauna k'ofar gidan suna hira , lokacin da Baffa ya nuna yanason Ammi bai sha wata wuyaba Mahaifinta ya amince dashi , dan tuntuni yake mata sha'awar auren sa ...... Ba'a d'au lokaci me tsayiba aka saka ranar auren Ammi da Baffa , Kawu Idi lokacin yanuna farin cikinsa amman bawani shiri suke da Ammi ba , Baffa yana ta k'ok'ari sosai wajen shirin Auren su da kuma neman wajen zama , Allah yasa kasuwa ta bud'a masa sosai yasamu kud'i yasai musu k'aramin gida me d'aki Biyu da shago , Bayan anyi aurensa da Ammi suka tare a gidan nan nasa daya siya , lokacin yacewa Kawu Idi yadawo shagon gidan yadunga kwana aikuwa haka akayi yadawo shagon gidan yana kwana ..... Bayan Bikin Ammi da Baffa na dakusan wata hud'u akatashi da rigima a cikin garin Jos , a lokacin aka kashe Iyayen Ammi dukansu da Yayanta guda d'aya , shikuma dama d'aya Babban Yayan nata yana lagos yana sana'ar sa acan , lokacin Ammi tayi kuka tamkar ranta zai fita , dayake su gidan da Baffa na yasiya ba a'cikin gari yakeba , shiyasa fad'an mesa mesuba , Haka Baffa yai ta rarrashin Ammi tare da bata baki harta hak'ura tayi shuru ta fawwala wa Allah ...... Haka Rayuwa ta cigaba da tafiya har Allah yabawa Ammi na ciki , Baffa sosai yayi murna da samun cikin Ammi na , haka suka cigaba da rainon cikin jikinta har Allah ya sauketa lafiya , tasamu 'Yarta Mace kyakkyawa tamkar kasace ta , Kowa yaga jaririyar saiyayi santinta , Kawu Idi lokacin yana neman aure shima , haka sukazo da Budurwar sa sukayi wa Ammi Barka , Baffa kullum yana d'auke dani a hannunsa , dan yana fad'ar cewa nida Mahaifiyar sa kamar mu d'aya , Ranar Suna aka samun Suna Hannatu wato sunan Mahaifiyar Baffa na , shine ake cemin Hanan , ansha suna sosai sannan kowa ya watse , Bayan wata hud'u da haihuwa ta Kawu Idi yayi aure , inda yatare shima acikin gidan mu , farkon zamansu lafiya k'alau da Ammi da Safara'u , dan itace ma take raino na koda yaushe , Bayan shekara biyu Safara 'u ko b'atan wata batayiba , sai hankalinta yatashi tafara shiga Malamai , Anan ne ake cemata wai Ammi ce tayi mata Asiri shiyasa bata haihuba , tundaga nan Safara'u ta canza halinta takoma rashin mutunci a cikin gidan , lokacin Innazo gunta saita tureni ko ta dokeni , Abinka da Yaro gobe ma haka zan koma bazan gajiba , Da abinci ma tare sukeyi da Ammi amman tace sai anraba , Ammi tayi mata tambayar duniya akan wanne laifi sukati mata Amman ko kallon ta batayi ba , Ammi tafad'awa Baffa duk yadda Safara'u ta koma , yayi jim kad'an yana nazari sannan yace Allah ya kyauta...... Bayan wani lokaci Safara 'u Abin nata ya k'ara girmama dan kusan kullum saita yadawa Ammi magana , tun Ammi na k'yaleta har wata rana ta tanka mata suka hau fad'a .... Lokacin ne Baffa da Kawu Idi suka shiga tsakaninsu , tundaga lokacin kowa yadaina kula kowa , nikuwa kullum cikin shiga d'akin Safara'u nake tana koroni , lokacin ina da shekara Hud'u a duniya kuma har lokacin Safara'u bata haihuba itama kuma Ammi bata k'ara Haihuwa ba , wani daren Alhamis Baffa na yatashi da Amai da gudawa , Kafin aje Asibiti Allah ya amshi Abinsa , Bak'aramin tashin Hankali Ammi na tashiga ba , dan suma tayi saida aka kaita asibiti , Kawu Idi shima Mutuwar ta dokeshi sosai , Bayan angama zaman Makoki Ammi taci gaba da zama dan yin takabar ta a d'akin mijinta , tun daga nan Ammi takamu da hawan jini , nan rayuwar ta ta koma shuru batason yawan magana , Nikuma Kawu Idi yasani a makaranta , lokacin Safara'u tasamu ciki zokuga iyayi da gwalli , aikima hanata yi Kawu yayi wai sai dai Ammi tafito tadunga yin aikin , haka Ammi ke fitowa tana shan aiki Safara'u tana mata rashin mutuncinta.... *Littafina Na Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* ta *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *k'ok'arin* *Mallakarsa* _kukaranta_ _cikin_ _Aminci_ *Saina* *jiku* *Masoyana* 🤝🏻😍 *'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 😍🌹 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Na* _Zee_ _MD_ ✍🏻 *Hamdala* *Writer's* *Association* 💪 https://www.facebook.com/111403834371046 ✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨ *Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim* *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* *Naira* 200 *Kacal* *Kukaranta* _cikin_ _Aminci_ 🤝🏻 *Saina* *jiku* *Masoyana* 🥰😍 🆓 page. 6 Bakowa bane face Zunnur , gyaran muryar da mukaji a saman kanmu yasa ka dukan nin mu mik'ewa cike da jin kunya , Abban sune shida Haidar suka shigo , sai kuma Afrah dake binsu a baya d'auke da jakar kayan su , duban Haidar nayi ina cewa " sannu da zuwa Abokina , Haidar yayi murmushi yace " wai daman kinanan shine ko neman mu bakyayi ? ai nayi fushi dake yanzu bama Abotar , Abban su yasamu gu ya zauna yana Murmushi yace " Abotar ku tana nan ba inda zataje kar kusa su Afrah suyi muku dariya , kowa waje yasamu ya zauna sannan aka fara gaisawa ana musu ya hanya ...... Saida suka gama gaisawa sannan Umman su tace " ga Abinci can yana jiranku inkun gama gaisawar , Ammi tace " kamata yayi sufara yin wanka suhuta sai su zo suci Abincin , Nan suka mik'e sukace "shawar Ammi zamubi bari muyi wankan sai mufito..... Bayan sunyi wanka sunfito dukan mu muka had'u akan Dinning table , dancin Abinci , nida Afrah aka ce mutashi muyi savening d'in kowa dake gun , Afrah tace nidai zanzubawa Ammi da Ya Haidar , kekuma sai kizubawa Abban mu da Ya Zunnur , ita kuma Umma daman ta k'oshi da k'amshi tun d'azu , Dariya suka saka dukansu Amman banda Zunnur wanda Murmushi kawai yayi yana duba wayar sa , mik'ewa nayi na janyo kulolin Abincin nafara zubawa kowa dake gun , Bayan na kammala kowa na tura masa gabansa sannan nazuba nawa nima nazauna , fara cin Abincin mukayi kowa sai santi yake tamkar muna Resturen , nikuwa nakasa sakin jiki naci Abincin saboda duk d'agowar dazanyi sai munyi ido biyu da Zunnur , duk ilahirin jikina banda rawa babu abinda yakeyi , cikin Zuciya ta nafara tambayar Kaina " wai meyasa nakejin haka game dashi ? meyasa saishi kad'ai nakejin hakan akansa ? ina ta wasa da cokali a cikin Abincin nakasa ci , Muryar Umma naji tana cemun " Hanan lafiya kuwa naga tun d'azu kink'i cin Abinci sai wasa kike da Cokali ? Murmushi nayi nace " Umma banajin yunwa ne saboda bandad'e da karyawa ba , Afrah tayi tsagal tace " Bawani Umma kawai inajin kunyar Ya Zunnur takeji , tunda naga shikad'ai ne baya magana a wajen nan , Hararar Afrah nayi sannan nace " Kunyar sa kuma saikace sirikina , Abban su yace " Kwaji dashi dai keda Afrah , mik'ewa yayi yana fad'in Alhmd nidai na k'oshi yabar wajen , Umma su ma tashi tayi tabi Bayansa , Ammi daman tuni tagama ta mik'e tabar wajen , yarage dagani sai Afrah da Haidar da Zunnur , sai da aka kwashi minty kusan goma sannan Haidar ma ya mik'e yana fad'in " tonidai nagaji dayawa , zanje nayi Bacci zuwa k'arfe biyar , Hanan innatashi zanzo muyi hira sosai dake , Nayi Murmushi nace " Afito lafiya Aboki , Haidar ya wuce 'Dakinsu yabar mu a gurin , Afrah mik'ewa tayi tafara kwashe kwanunkan da akayi Amfani dasu tana Nufar kitchen dasu , Zunnur yana Zaune sai latsa wayar sa yake tamkar baisan Ina wajen a , Mik'ewa nima nayi da zummar barin wajen kamar daga sama naji ance " Dawo ki zauna inason muyi magana , juyowa nayi na dubesa tamkar bashi ne yayi maganar ba , Mamakine yakamani Nadawo na zauna ina wasa da yatsun Hannuna , d'agowa yayi ya dubeni yace " Yaushe kukazo keda Ammi ? cikin sanyi nace " Munyi sati biyu yanzu haka , cike da isa irin tasa yace "kuma kwana nawa zakuyi kafin ku tafi ? Nan a nace masa Sati Uku daman zamuyi saboda munkusa komawa hutun Makaranta , kuma mun komawa zamu fara pepar ta kammala SSCE , dubana yakuma yi sannan yace " Inafatan dai bakya wasa da karatunki dan yana da mutuk'ar Amfani ga 'Ya mace kodan 'Ya'yanta Nangaba , amsa nabashi da " Ae bana wasa da karatuna , jefomin wat tambayar yayi yace " Ina fatan bakya kula Samari dan ked'innan ba isa kikayiba ? wannan Tambayar ce nakasa bada amsar ta , dan indai kula samarina yariga da ya makara , shurun dayaji nayi yasa ya d'ago sosai yana dubana , cikin alamar yaji rashin dad'i da shirun danayi masa yace " ko kurma kika koma kinaji ina miki magana kinyi min shuru , jikina tuni yafara rawa nace " Bana kula kowa ni , kallo na yayi yace kintabbata ? Nace E . Zai sake magana kenan saiga Umman su tataho , wani dad'i naji ya rufeni dan daman akan k'aya nake , irin wannan Tambaya tamkar d'an jarida , Umma na k'arasowa tace " Hanan ina Afrah take kuzo in aikeku yanzu , Mik'ewa nayi ina fad'in Bari nadubata nagani tuni nabar wajen.... Afrah naje nagayawa Umman su zata aikemu , cike da zumud'i tace " wallahi daman Hanyar fita nake nema tund'azu , saboda Anas yanason muhad'u amman yanzu bani ba had'uwa dashi a cikin gidan nan tunda du Ya Zunnur suka dawo , kallanta nayi nace " aikuwa indai muka fita kika kulashi tabbas saina fad'awa Ya Zunnur ya caskala ki , dariya tayi tana had'e hannuwan ta alamar ban hak'uri , fitowa mukayi wajen Umman su tabamu aiken datace zamuyi mata , har mun ansa munyi haryar tafiya mukaji Muryar Ya Zunnur yana cewa " Ke Hanan ahaka zaki fita ne kamar wata yarinya ? tsayawa nayi tsam ina duban jikina , Doguwar rigace sai mayafinta danayi Rollyn dashi , Umman su ce naji tana ce masa " To me kayan jikin nata yayi dazaka dakatar da ita ? cike da jin badad'i yace " nidai nafad'a mata mutuk'ar bata d'auki Babban gyale tayafa ba to tadawo ta Zauna , da sauri Afrah tace " Bari naje na d'auko mata tasa sai mutafi , nikam abin nasa ma mamaki yabani , duba da yadda yake b'ata rai tamkar wani mijina , Umma kuwa cewa tayi "Allah ya kyauta maka da wannan halin naka , Matar ka zaka dinga yiwa wannan ikon ba yaran mu ba ta wuce tayi cikin 'Dakinta ... Afrah tana kawomin gyalen na ansa na yafashi , tunda na yafa gyalen yake satar kallo na Haka muka saka kai muka fice daga cikin gidan...... Saida mukaje aiken da Umman tayi mana sannan muka biya wajen wani Garden , Afrah takira Saurayinta Anas tafad'a masa inda muke , Muna Zaune na dubi Afrah nace " kinsan Allah tsoron Ya Zunnur nakeji sosai , kwata kwata baya dariya tamkar ba 'Dan gidankuba , Afrah tayi murmushi tace " wallahi haka yake da wannan miskilancin , magana ma saiya ga dama yakeyinta , Sannan ga fad'an tsiya shiyasa insuka dawo hutu wallahi duk ata kure nake , Suna cikin hira saiga Anas ya k'araso , Nan muka gaisa yasa mu guri shima ya zauna , Hira suka fara shida Afrah nikuma na mik'e nabar musu gurin , Samun wani guri nayi na zauna ina kallon yadda masu kud'i suke shigowa su da 'Yan matansu wasu kuma Matansu da yaransu , Ina Zaune naji ance min Aminci agareki Tauraruwa ta , da sauri na kalli wajen bakowa bane face " Muktar yana mun murmushi , Mamakine yakamani taya yasan ina nan gurin ? kamar yasan tambayar danakewa Zuciya ta kenan yace " Afrah ta turamin test tace kuna cikin Garden nazo intayaki hira tana da bak'o itama , Cikin Zuciya ta nace " Afrah akwai rashin mutunci , a fili kuwa nace " Sannu da zuwa yakake ya hanya , Zama yayi kusa dani tamkar zai shige jikina har sai da na matsa , shi kuwa ko ajikinsa ya fara k'okarin rik'emin Hannu , 'Bata Rai nayi ina cewa " Kasan banason irin wannan Abun haka , Muktar yayi Murmushi yana fad'in " Am sorry my luv bazan k'ara ba , d'agowar da zanyi mukayi Ido biyu da Zunnur yana nufo wajen mu a fusace , take naji wani fitsari ya ziyarci marata , tuni na mik'e tsaye jikina inbanda rawar Banjo babu abinda yakeyi , yana k'arasowa ya damk'i wuyan Muktar ya haushi da duka tamkar wanda yakamashi da Matarsa , ai tuni na nufi wajen da Afrah take da gudu bansan inada gudu ba ma sai ranar........ *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* 200 _karku_ _Bari_ _Abaku_ _labari_ _Kusiya_ _Kukaranta_ _Cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰 *'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 😍🌹 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Na* _Zee_ _MD_✍🏻 *Hamdala* *Writer's* *Association* 💪 https://www.facebook.com/111403834371046 ✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨ *Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim* *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *k'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Kukaranta* _Cikin_ _Aminci_ *Saina jiku* *Masoyana* 🤝🏻🥰😍 🆓 page. 5 A haka har Safara'u ta haihu d'anta Namiji , Ranar suna aka saka masa sunan Baffa na wato Mahmud , Bayan wasu watannin Ammi na taga zama haka bazai mata ba , fara saro kayan miya tana saidawa , Koda Safara'u taga Ammi nasamun Alkairi da Kayan miya sai tashiga tafita tafara sai dawa itama , Ammi tanaji tana gani tadaina saida kayan miya , sai tasamu kud'in tafara sana'ar soya k'osai a k'ofar gida , Alhmd nan ma Allah yasa mata Albarka tana cikini Sosai , da wannan sana'ar Ammi taci gaba da rik'e mu , lokacin Kawu tuni yadaina biyamin kud'in sch , Ammi itace komai nawa har na fara girma .... Zawarawa dayawa sun fito neman auran Ammi amman tak'i Saboda ni , lokacin Safara'u tana da yara biyar , dan tunda tafara haihuwa take kwanika , kullum cikin yiwa Ammi hassada take gashi ta tsaneni Sosai tamkar takasheni , kuma har lokacin Kawu Idi yak'i ya kammala gidansa bare sukoma subar mana namu , Ina aji k'arshe a primary saiga Yayan Ammi yazo daga Lagos , shida Matar sa da Yaransa guda uku , Ammi tayi murna Sosai daganin d'an uwan nata , Sunyi hirar Yaushe gamo sannan suka shiga hirar Rayuwa , Inadawo wa daga sch naga bak'in damukayi wanda Ammi tadad'e tana bani labarinsu , aikuwa naita murnar ganin 'Yan uwa , Babban 'Dan Yayan Ammi ya girmeni sosai , sai Mai bimasa shima yad'an girmeni sai kuma K'anwarsu wacce zamuyi sa'anni da ita , Sunan Babban Usman suke ce masa Zunnur , saboda sunan Baban su Ammi ne , me binsa kuwa sunan sa Haidar , sai k'aramar su Afra , Maman su tana da kirki sosai , tasaki jiki da Ammi sai hira suke tamkar daman sun san juna , nima nida Afrah tuni muka saba dan kusan kanmu d'aya da ita , Zunnur bashi da yawan Magana kaganinsa kaga miskili , shikuwa Haidar yana da sakin fuska sosai , kwanan su Biyu sukace zasu tafi saboda sch . Ammi tayi tayi suk'ara kwana Amman yace tabari in sunsamu hutu zaikawo su suyi anan , Yayan Ammi yayi mata fad'an tayi Aure zaman haka babu dad'i , kokuma takoma gabansa can lagos d'in ta zauna , Ammi tace zatayi Shawara akan hakan duk abinda ta yanke zata gaya masa , lokacin da zasu tafi sosai nasha Kuka sai nabisu nima , Afrah itama kukan take tana rok'on Ataimaka ataho dani , da k'yar Maman su ta lallab'amu akan zasu dawo nan badadad'ewa ba , Yayan Ammi yabata dubu talatin yace tak'ara ajarin nata , sannan yabawa Kawu Idi dubu goma , sai kuma yabawa Safara 'u dubu biyar , sunyi godiya Kawu Idi yabasu tsarabar kayan Gwari , lokacin da muka rakosu waje Na kalli Zunnur nace " Ya Zunnur sai wata rana tunda kai murna kake zaku tafi , daman tunda kuka zo kake jin Haushi to yau saika saki ranka , kowa a wajen sai dayayi dariya , shikuma murmushi yayi bai ce komai ba har suka tafi.... Bayan wasu shekaru. Lokacin Na zama 'Yan mata ina Ss 2 a secondry sch , duk wata hailtta ta jikina ta bayyana , nakasan ce Doguwa Fara me d'auke da doguwar fuska , ina da Hanci har baka ga bakina k'arami dashi , idanuwana dara dara dasu cikinsu fari fat sai k'wayar idon bak'a k'irin , ina da siririyar wushirya a tsakiyar hak'ora na , sannan ina da Dimple a gefen kumatuna , Bani da jiki amman kuma ina da k'ugu sosai , Banda cikar K'irji dai dai suke abina , tunda nazama Budurwa Samari suka fara kawomin hari , kuma har lokacin Ammi na tana suyar k'osai a k'ofar gida , Tunda lokacin Kawu Idi yasakoni gaba saboda madu zuwa ta wajen sa, Wata ranar Friday na dawo daga Sch ina tafiya naji ana min magana , dak'yar na tsaya saboda cikamin idanuwan da yayi mutumin , mungai sa yace min dan Allah inbashi kwatancen gidan mu , yanaso yazo dan tsayuwa a hanya ba mutunci bane , Nan na daure nagaya masa kwatancen gidan mu , ya fad'amin sunan sa Kamal nan muka rabu akan zaizo gida..... Bayan kwana biyu ina zaune nida Ammi muna hirar tafiyar mu Lagos da zamuyi inna samu hutu , kawai sai ga yaro yashigo wai ana sallama da Hanan a waje , Nan nacewa yaron yace Bananan , Ammi tace ace ina nan , turo baki nayi ina fad'in "Nifah Ammi bazanje ko inah ba , kallo na tayi sannan tace " yanzu Hanan inbaki fita ba taya zaki samu mijim da zakiyi aure ? kinsan dai nafad'a miki cewa iya secondry sch zaki gama in aurar dake Hanan , yakamata kifara kula samari ko zaki samu wanda zakuyi daidai , kalaman Ammi sun shigeni sosai dan haka na mik'e nasaka hijan d'ina na fice , Nasan Ammi bata da k'arfin dazata biyamin kud'i nayi karatu sosai , dan haka nima na amince da zancenta ...... Ina fitowa naga Kamal a tsaye , yana ganina yafara sakarmin Murmushi yana cewa " Gimbiya sarauniya gaskiya nazama sarki acikin masoya tunda har aka fito wajena , murmushi nayi sannan na gaidashi cike dajin kunya , Nan ya amsa yafara gabatarmin da kansa , Sosai nasaki jiki da Kamal , kodan yana da Abin dariya ne oho , haka mukaita hira haryamin sallama yatafi , tunda ganan Soyayya ta k'ullu tsakanin mu nidashi , har muka samu hutun Sch muka tafi Lagos da Ammi ..... Zuwana Lagos shine yafara canzamin Rayuwata tafarko , Muna zuwa gidan Yayan Ammi , Sosai muka samu tarba ta musamman , karkuga murnar da Afrah tayi taganina , nima nayi murna sosai da ganinta , tazama Babba sosai dan harta fini girman jiki , lokacin da mukaje su Haidar da Zunnur suna Sch amman suna shirin dawowa gida , dukansu suna karatu a B.U.K a can kano , dagani sai Afrah kullum sai munfita ganin gari , watara rana munje wani Shopping mukayi karo da wani Saurayi , duk abinda muka siya saida ya biyamana kud'in , bayan munfito ya biyomu ya gabayar mana da kansa sannan ya nuna yana sona , Afrah tabasa Addrees d'in gidan su muka wuce muka tafi..... Tunda ganan Muktar yafara zuwa guna , tun ina sharesa Afrah tasa ni gaba saida nafara kulasa , Muktar irin samari nan wayayyu , wani lokacin in muna hira sai yanemi tab'amin jikina , sai da nanuna b'acin raina Sosai sannan muka dai daita , Ranar dasu Zunnur zadu dawo tun safe muka gyara musu d'akinsu , sannan muka shiga kitchen muka fara shirya musu Abinci lafiyayyau , kafin k'arfe biyu mun kammala komai , dayake a jirgi suka taho lokacin Abbansu har yatafi tahowa dasu , wanka nashiga dana fito na shirya cikin wata doguwar riga da mukaje Shopping Abbansu Afrah yasiyamin ita , nikaina nasan nayi mugun yin kyau Sosai , da haka nafito palor ina k'walawa Afrah kira , hanyar k'ofa nataho zan bud'e shikuma dai dai lokacin zai shigo , aikuwa mukayi karo dashi har wayar hannunsa ta fad'i muka sunkuya atare dan d'aukar ta , Idanuwan mu ne suka had'u waje guda take kowannen mu zuciyar sa ta buga....... *littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *ta* *Wannan* *Layin* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* _Karkubari_ _Abaku_ _Labari_ _kusiya_ _kukaranta_ _Cikin_ _Aminci_ 🥰🤝🏻 . *'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 🌹😘 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Na* _Zee_ _MD_ ✍🏻 *Hamdala* *Writer's* *Association* 💪 https://www.facebook.com/111403834371046 ✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨ *Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim* *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* *Naira* 200 *Kacal* *kukaranta* _Cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰 🆓 page. 7 Ina zuwa naga Afrah sai hirarsu suke hankali kwance , ganina datayi a firgice yasa ta zabura itama ta mik'e , cike da tsoro tace min " lafiya kuwa Hanan naganki hakan ? Muryata har sark'ewa take nace mata " Ya Zunnur ne yazo , tuni Afrah ta firgice tana cewa Anas " Maza kabar wajen nan wallahi inyazo yaganmu tare zai maka rashin mutunci , kafin Anas yayi wani yunk'uri saijin shak'a yayi ta wuya , kafin kace me tuni yaji saukar Naushi , Kafin Anas yadawo Daidai yakuma jin wani Naushin , nida Afrah duk ilahirin jikinmu Rawa yake , tuni munfara Hawaye saboda tsoro , da k'yar mutane suka kwaci Anas a hannun Zunnur , yadda kasan wani mayunwacin zaki haka jijiyoyin jikinsa suka tashi , kallon mu yayi kawai ya nufi wajen da yayi parking d'in mota , sai abakin mutanen dasuka k'waci Anas naji suna cewa " wanda yafara rik'ewa yana dukansa da k'yar yasamu ya turesa ya gudu Muktar kenan , jikin mu a sanyaye muka nufi hanyar fita daga cikin Garden d'in , wani wawan burki da'aka ja a gabanmu take muka had'e jikinmu waje d'aya muna karkarwa , bamu gama dawowa dai dai ba mukaji an finciki Hannuwan mu an bud'e motar ansaka mu , muna bud'e ido mukayi ido biyu da Zunnur tamkar mayun wacin zaki , shiga motar yayi ya figeta a miliyan yabar wajen...... Yanayin gudun da Zunnur yake yasa muka tsure kowacce cikin mu addu'ar cikawa da imani take , bud'e gate kawai mukaji anyi sannan mukaji ya kashe motar , muna cikin Motar dukan mu harshi daya had'a kai da sitiyarin d'in mota , sai da aka kwashi Minty 20 sannan ya juyo ya dubemu yace " daman Abinda kukeyi kenan ? Yaushe kuka zama 'Yan matan dazaku ringa had'uwa da Samari a wani wajen ? tunda naga yadda Afrahbke rawar kai akan tafiya aiken nan nasan da abinda kuke k'ullawa , wato kunyi da samarin ku zaku had'u a wani wajen kenan ? shuru mukayi inbada rawar jiki babu abinda jikinmu keyi , wata tsawa ya daka mana wanda fitsarin danake rik'ewa tuni saiga shi nasakeshi , aikuwa Afrah tace " Dan Allah Ya Zunnur kayi hak'uri wallahi bamu tab'ayin hakan ba sai yau , wani Mari ya d'auketa dashi har saida tayi wata k'ara , yace " ai kece mara mutuncin dakika d'auketa kuja tafi , inaso insanar muku wallahi wannan ne na k'arshe fita ma bazaku k'araba bare ku had'u da wasu 'Yan iska , kufice min daga cikin Motar tun ban zaneku ba wallahi , ya dubi Afrah yace " Bani wayar hannunki ke kuma ki tsaya ki wankemin motata saboda fitsarin dakikamin , wata kunya ce naji ta rufeni tamkar na nutse a wajen , Afrah kuwa tana bashi wayar ta fice da tana Kuka , nikam kasa motsawa nayi saboda Kunyar danakeji gashi jikina a jik'e yake da fitsari , Ruwa ya mik'omin a robar Faro sannan ya bud'e motar ya fice , yana fita nasaki ajiyar zuciya sannan nasaka ruwa a cikin jikina nafice daga cikin motar ..... Koda na shiga palor nayi sa'a babu kowa , dasauri na nufi d'akin Afrah na shiga , ina shiga toilet na fad'a nafara wanka , Bayan nagama na fito d'aure da tawul na nufi wordrup na d'auki wasu riga da siket na Atamfa nasaka , dawowa nayi na zauna kan Mudubi nafara shafa mai , ina cikin shafawa naji anturo k'ofar d'akin anshigo , ta cikin Madubi naga Zunnur tsaye ya goya hannuwansa a k'irji sai kallona yake , tuni na mik'e tsaye ina juyawa dukana ina kallonsa nima , dan wani tsoronsa nakeji tamkar dodo yazamar min , ganin tsoronsa k'irik'iri a idonta yasa yad'an saki fuska yace " kinyi wanka kenan to ita kuma motar tawa waye zai yimata wankan ? k'asa nayi da kaina sannan nace " sallah zanyi yanzu inna idar zanzo na wanke mska ita , Murmushi yayi sannam yace " inajiranki karki k'i zuwa kuma kinji , kai na gyad'a masa tamkar k'adangare ya juya yafice..... Yana fita nabi Bayansa da Harara ina fad'in " mugu azzalimi kawai , wallahi bari naje nasamu Ammi kawai tashirya gobe mukoma gida , dan bazan iya zama da wannan mugun ba , ina cikin zancen zuci saiga Afrah tashigo fuskar ta tayi ja alamar tasha Kuka , dubanta nayi nace " kiyi hak'uri Sister gaskiya wannan Zunnur d'in mugune sosai , Ni wallahi har nafara jin tafiya zamuyi gobe mubar garin nan saboda shi , Afrah ta dubi Hanan tace "Dan Allah karkice zaku tafi saboda Zunnur , nasan hutun nan nasu badadewa zasuyi ba zasu tafi , duban ta nayi nace " to ko sudad'e ko kar su dad'e ai saura sati mukoma gida , Afrah tasamu waje ta zauna tana fad'in " wallahi shiyasa banason du dawo , musamman Ya Zunnur akwaishi da mugunta sosai , Nace " ai koni yau na tabbatar dahakan , yanzuma yafita daga d'akin nan wai yana jiran inje in wanke masa motar , dariya Afrah tafara tana fad'in " wai ke ya akayi kikayi fitsari ? kinsan kad'an yarage nayi dariya kawai sai naji ya mareni , Nima dariyar nayi nace " ke kuwa wannan Uwar tsawar dayake daka mana ai dole nayi fitsari , gaskiya Matar Ya Zunnur tashiga Uku da Muguntar sa , Afrah tace " irinsu ai basa yiwa matansu haka sai dai tarairaya da nuna Soyayya , Nan mukaci gaba da hirar mu wacce rabi duk akan Ya Zunnur ce....... Kuyi maneji 😔 *'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 🌹😍 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Na* _Zee_ _MD_ ✍🏻 *Hamdala* *Writer's* *Association* 💪 https://www.facebook.com/111403834371046 ✨✨ *{{* *H.W.A* *}}* ✨✨ *Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim* *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Tawannan* *Number* 07046107812 *kuyi* *k'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* 200 *Kacal* *Kukaranta* _Cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰 🆓 page. 9 Dasauri Ya Haidar ya bud'e dan ganin waye meyi musu wannan bugu , nikuwa nida Afrah daman munsan kwanan zancen , tuni Afrah ta kama Hannu na tace " inkin shirya kibuyoni dan wallahi da gudu zanfita ba tsayawa , nima kai na gyad'a mata alamar na shirya , aikuwa muka bud'e murfin k'ofa ta b'angaren da ba anan Ya Zunnur yake ba , tuni muka kwasa da gudu cikin gida muka bar Ya Haidar da Ya Zunnur suna cacar baki...... Muna shiga maka tarar da Umma da Ammi suna hira , suna ganinmu sukace " kukuma meye hakan kuke wannan gudu tamkar wasu k'ananun Yara ? Afrah tace " wallahi Umma muda Ya Zunnur ne wai dan munje unguwa da Ya Haidar , Ammi tace " ai kunyi laifi tunda baku gaya masa zaku fita ba yana matsayin Babba a cikin gidannan nan , mudai bamu tsaya ba muka nufi cikin d'aki muka saka key abinmu ...... Wanka kowaccen mu tayi sannan muka saka kaya marasa nauyi , sai lokacin muka fara jin cikinmu na kiran chiroma , Afrah tadubeni tace " Hanan kije ki d'ebo mana Abinci dan wallahi ni tsoron fita nake nahad'u da Boss , duban Afrah nayi nace "Tabd'ijam wato nikuma inje ya ritsani a hanya yamin dukan tsiya , muna zaune muna ta jayayya mukaji ana buga k'ofah , da sauri na haye saman gado ina duban Afrah , dariya tahau yimin tana cewa " Sannu farar kura irin wannan gudu haka , k'ofar d'akin taje ta tsaya tana tambayar waye ? muryar Umma taji tana cewa " bansaniba yau ku bakwajin yunwa ne tund'azu kun k'ule a d'aki kunk'i fitowa ? da sauri Afrah ta bud'e d'akin tana fad'in " Wallahi muna ji Umma , tsoron Ya Zunnur yahamu fitowa , tasowa nayi muka fito palor dan cin Abinci , aikuwa Ya Zunnur suna tare da Ammi sai hira sukeyi tamkar bashi ba , wucewa mukayi sai sinsik'e kai muke tamkar muna fukai , shikuwa gogan ko kallon mu baiyi har muka wuce kan Dinning...... Bayan wasu kwanaki har munwuce lokacin da zamu koma gida , lokacin Su Ya Zunnur hutunsu ya k'are suna shirin komawa Sch , A lokacin Daddynsu tafiya ta taso masa zuwa Dubai , har an samar min komai da komai zanfara zuwa sch d'insu Afrah , Duk da ina kewar Garin Jos da kuma k'awayena , Ya Zunnur tunda ga randa mukaje wannan party da Ya Haidar bai k'ara shiga sabgar muba , muma kuma duk abinda zai had'amu dashi bama nema , Ana Gobe zasu tafi muna zaune nida Afrah a cikin kitchen tana ta bani labarin yadda sch d'in su take , ganin mutum mukayi a tsaye kofar kitchen rungume da hannunsa a k'irji sai kallona yake , Tuni na dabarbar ce nakama 'Yan kame kame , Afrah kuwa yankan salad d'inta taci gaba dayi batare da tak'ara magana ba , sai da ya dad'e a haka sannan yace " Hanan kizo yanzu inason ganinki , saura kuma injiki kink'i zuwa kiga yadda zanyi dake , a hankali na furta masa to ganinan zuwa , shigewa yayi yafita yabar mu , Afrah tana ganin ya fita tafara doka tsalle tana murna wai yau zataji kukana , Hararar ta nayi ina fad'in " ai dayake yace miki dukana zaiyi , Tace " kikama hanya kije wallahi karki janyo wa kanki wani laifin , ficewa nayi batare da nayi magana ba ...... 'Bangaren su Ya Zunnur na nufa ina sand'a tamkar muna fika , ina zuwa k'ofar d'akin nayi sallama cikin murya me sanyi , shuru naji ba'a amsa minba , sake wata sallamar nayi akaro na biyu ina d'an d'aga murya , daga ciki naji ance Yes Coming . Bud'e k'ofar nayi a hankali mukayi ido biyu dashi zaune kan d'aya daga cikin kujerun d'akin nasa , ina shiga nasamu kan Cafet na zauna ina fad'in " Ganin Yaya , kallo na yayi nawasu mintyna sannan yace " intaso in zauna kan kujera , mik'ewa nayi na zauna kan kujera ina sunkuyar da kaina , dan ni ko idanun Ya Zunnur tsoron su nakeji , sai da aka kwashe mintyna sama da biyar sannan yace " Inaso inja hankalinki sosai dan naga kanku yana rawa keda wannan yarinyar , Abinda nakeso dake zaki fara zuwa Sch d'insu Ranar Monday , duk da bahaka nasoba naso ace arraba muku Sch kowacce da tata Amman Daddy yak'i , inaso kisani karatu aka turaku ba kula samarin banza dana wofi ba , inhar naka maku da wannan halin wallahi dukan ku jikinku sai yafad'a muku , dan karkuga bana gari kuji dad'in sakewa kuna rashin hankali wallahi zuwan bazata zandunga yi muku yadda zanfi ganin me kukeyi , Fad'a sosai Ya Zunnur yayi min akan na maida hankali nayi karatu , a k'arshe yace min Akwai wata magana yanaso ya fad'amin Amman sai yakuma da wowa , Nan yaduba hannuna yace " naga hannunki ko a zurfa babu dan haka ki shirya muje yanzu insiya miki , nace masa to sannan na mik'e nafito..... 'Daki nashigo dan shiryawa kamar yadda yace min , Afrah na ganina tace " meyace miki kuma ? na harareta nace " meyahana ki kibiyoni kiji , nafara shiryawa batare da nace mata komai ba , sai da nagama nace mata mudai munwuce nida Ya Zunnur sai Allah yayi mana dawowa , Dariya Afrah tasa tana fad'in " Ah lallai had'in naku yayi Allah yabar k'auna , niko lokacin ban fahimci maganar ta ba nafice Abina..... A gidan gaba na zauna har mukaje shagon saida sark'ok'i da zobunan azurfa da gwal , Fitowa mukayi nidashi muka jera har cikin wajen , kowa dake wajen idansa akanmu , harda wad'an da basa iya shuru sai sun taka suka fara fad'in " wannan had'in yayi kyau sosai Allah yabaku zaman lafiya , nifah duk abinda suke fad'i ba ganewa nakeyiba shiyasa banwani damuba , wani glass Ya Zunnur ya bud'e yana d'auko wani Zobe me shegen kyau har wani d'aukar ido yake , Hannu na naji ya rik'o yana k'ok'arin sakamun , yana samun kuwa zoben ya zauna daram tamkar danni akayishi , Abinka da fararen yatsu dogaye dasu take suka d'auki wani kyau sosai , Ya Zunnur wani murmushi yayi yana duban hannun , sai wata a zurfa daya d'auko me farkon Sunan Z ajiki yasamun a hannu , sai kuma yasa wata me farkon sunan H yacemin " in ansa insaka masa , ina ansa ya mik'omin hannu nasaka masa , take 'Yan wajen suka fara tafa mana suna fad'in " wannan Abu yayi Allah yabar Soyayya , duk jinayi kunya takamani nayo waje da sauri ina Murmushi , Kud'in zobunan ya biya sannan yafito muka tafi..... Washe gari tun sassafe suka shirya muka rakasu har filin jirgi suka tafi , duk yadda muke murna da tafiyar su musamman ma Ya Zunnur saida mukaji rashin dad'i lokacin da mukaga sunhau jirgin suntafi , muna dawowa gida nakoma duk wata mara sukuni , Afrah sai tsokana ta takeyi wai ina kewar Masoyina , samun kaina nayi da duban zobuna na wanda yasaka min su musamman me farkon sunan Z d'in..... Bayan kwana biyu da tafiyar su Ya Zunnur katsam saiga Kawu Idi yazo , da kwatance yazo gidan su Ya Zunnur , lokacin har nafara zuwa sch nida Afrah , Bayan sun gaisa da Ammi yafara yi mata fad'an yayi shuru shuru munk'i dawowa shiyasa yazo yaga ko lafiya ? Nan Ammi take gaya masa ai Yayan ta yace bazasu koma ba anan zata zauna , Nan Kawu yayi tsalle yace sai dai ita ta zauna ita kad'ai tunda itace tazama dolen sa , Amman nikuwa k'afata k'afarsa bazai bar 'yar gidan 'Dan uwan sa ta taso a wani garin ba , Nan yadung sababi Ammi ita kuwa banda kuka ba abinda takeyi , tabbas tasan za'ayi hakan , shiyasa kullum cikin zulumi take tana tunanin Yadda rayuwar Hanan zata kasance gidan Kawun nata , da k'yar Kawu Idi yayi kwana biyu a gidan nan yace in shirya zamu wuce....... *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Ne* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *k'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* 200 *Kacal* _kusiya_ _kukaranta_ _Cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰 *Nagode* *Masoya* *'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 😍🌹 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Na* _Zee_ _MD_ ✍🏻 *Hamdala* *Writer's* *Association* 💪 https://www.facebook.com/111403834371046 ✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨ *Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim* *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* *Naira* 200 *kacal* *kukaranta* _Cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰 🆓 page. 8 Washe gari duk Hanyar danasan zata had'ani da Ya Zunnur nak'i binta , yini guda ina cikin d'aki sai k'arya nayi nace ciwon Kai nakeyi , har magani Umma takawomin tasani agaba sai dana sha , Ammi na tana can d'akin da aka sauke ta , ko lek'owq batayi taganni ba danagaji da zaman d'akin dole na fito nashiga d'akin Da Ammina take , sai dai me ina shiga naga wanda nake gudun had'uwa dashi a zaune suna hira da Ammi , har zan juya naji Ammi tace " Hanan ina zakije kuma ? bakiga nida Yayan ku bane ai bawani bak'o bane kinsan shi , shigowa nayi jiki a sanyaye nasamu guri na zauna , Dubansa nayi nace " Ina yini Ya Zunnur ? tamkar gonar auduga haka ya bud'e baki yana dariya ya amsa min , ni abinma mamaki yabani natsaya ina dubansa , mutumin da ko murmushi bayayi amman shine da wannan fara'a , na dubi Ammi nace " shine ko kizo dubani Kinjini shuru ko ? murmushi tayi tace " ai gaki yanzu kinzo ke kuma nasan lafiyarki k'alau , turo baki nayi ina cewa " nidai Ammi dan Allah gobe muhad'a kayanmu mutafi nifah nafara gajiya da garinnan , tuni naga fuskar Zunnur ta canza tamkar anyi mishi albishir dawani mugun Abun, jinayi yana cewa " Ammi indai ita tagaji ahad'a mata kayanta gobe Haidar yaje yakaita , sannan ya dubeni yace " ita kuma Ammi tadawo kenan dan baza mubarta ta koma Jos ba , daman shirin tafiya taho da ita muke kuma yanzu tazo kenan , shuru nayi masa batare da nace komai ba .... Bayan Zunnur yafita nadubi Ammi wacce naga tayi nisa a dogon tunani nace " wai lafiya kuwa Ammi ? yaufa kwata kwata naga bakya cikin walwala ko wani Abunne ? Murmushi Ammi tayi sannan tace " Hanan d'azu dasafe munyi magana da Yaya wato Abban su Zunnur kenan , yace bazan koma Jos ba , dole sai dai nazauna a gidan nashi har Allah yakawomin miji nayi aure , babu irin rok'on danayi masa Akan ya hak'ura yabarni sai na aurar dake nadawo yace "bazai yadda ba , kuma kema yace makarantar da Afrah ke zuwa ita za'a samar miki kidinga zuwanta , shuru nayi ina sauraran Ammi , Taci gaba da magana " ni bada muwata zaman dazanyi ba a'a kawai ina tuna Kawun ki inyaga munk'i komawa dole zaizo yace saiya d'aukeki , tunda akwai lokacin da Yayan yace sai nadawo nan d'in dazama wallahi dana gayawa Kawun ki cewa zamu tafi da Yaya cewa yayi " wai inna tashi tafiya inbar masa ke a wajensa , kece kad'ai wacce yake kallah yaji dad'i saboda rashin d'an uwan sa , Tuni idanun Ammi suka kad'a sukayi Ja tamkar zatasa kuka , nima cikin zuciyata tuni nafara jin babu dad'i , tabbas zanso zaman garin nan Amman mutuk'ar Zunnur yana gidannan nikam bazanyi walwala ba , kuma banajin zanbi Kawu nabar Ammi na anan garin bazan iyaba , shurun da Ammi taga nayi yasa ta dafamin kafad'a tace " tun muna yara indai Yaya yayi magana ba'a musa masa , dan haka nasan zaiyi wuya na koma Jos dazama , addu'a ta d'aya yanzu itace " Allah yasa Idi ya amince kiyi zamanki a nan wajena , Dubanta nima nayi sannan nace " Ammi kece fa kika haifeni kinfi kowa iko dani a halin yanzu , taya za'ace wani zai miki iko da abinda kika haifesa ? Ammi tace " karki k'ara kiran kawunki wani Hanan , kinsan duk tak'amar mutum dole da dangin Uba zaiyi ado , a yanzu in aka tashi aurenki bawanda za'asamu sai shi , inhar kinga mun aurar dake to kitabbatar da Babu ran Kawunki , yana da iko akanki tamkar 'Yar cikinsa , saboda bakida kamarsa a dangin Mahaifinki cikinsu d'aya da Mahaifinki , Shuru nayi dan jikina ya riga dayayi sanyi , tabbas Nasan abu me wuya ne ace kawu ya yadda na zauna a gun Ammi na , Amman zamuga yadda Allah zaiyi damu nida ita...... Kwana biyu wasan b'uya mukeyi da Ya Zunnur , duk inda zanbi nagansa yanzu banabi , Afrah kuwa duk gidan yamata rashin dad'i , saboda Ya Zunnur yakasa ya tsare ko k'ofar gate bata zuwa , Yauma muna Zaune nida ita tana ta mitar wayar ta da Ya Zunnur ya k'wace saiga Ya Haidar ya shigo , kallon mu yayi yace " Hy 'Yan mata ya kuke ? Murmushi nayi nace " Ya Haidar abin harda tsokana kuma ? shima Murmushin yayi yace " kutashi kushirya kurakani ganin gari tare da partyn Abokina , aikuwa da sauri Afrah ta mik'e tana fad'in " da gaske Ya haidar damu zakaje ? ya kalle ta yace " kefa har yau bakya girma sai na jiki , da wasa nake muku kenan ? tuni muka mik'e dan canza kaya daman munyi wankan mu , fita yayi yace musa mesa cikin motarsa ...... Dukan mu shiryawa mukayi cikin wani Less me mugun kyau , Abban su ne ya d'inka mana shi iri d'aya nida Afrah tamkar 'Yan biyu , Abinda nafita shine haske da tsayi , ita kuma ba fara bace choculate kala ce , tana da jiki amman ba sosai ba , kayan sunyi mana kyau sosai d'inkin riga da siket ne kowacce ya zauna a jikinta zam , takalma masu tsini mukayi amfani dasu , sai maya fai kalar takalmin mu ba k'aramin kyau mukayi ba , muna fitowa ya dube mu yace " wow kyawawan k'anne na tabbas zaku fito dani bari muyi pic , wayar sa ya d'auko k'irar Samsung yafara yimana pic , fukan mu sai da muka d'auka tare dashi sannan yayi mana dani da Afrah muka tafi...... Sosai muka zaga gari tamkar kar mudawo dan dad'i , Ya Haidar yayi mana siye siye dayawa sannan muka nufi gun partyn Abokin nasa , muna zuwa wajen duk idanuwa sukayo caa. Akan mu tamkar a lashe mu , Nan Abokan Ya Haidar suka fara fad'in " Wow Aboki wad'an zafafan Babys d'in kuma fa ? had'e rai Ya Haidar yayi yana fad'in " Banson iskanci k'anne na fa , shewa suka fara suna fad'in " wallahi daga yau munkoma cema Yaya Zaki , da sunan da suke kiransa dashi kenan , dariya yasa sannan muka samu guri muka zauna , ba laifi Partyn Birthday d'in nasa yayi kyau sosai , Ya Haidar suna filin rawa yabamu wayarsa muna kallo kawai saiga kiran Ya Zunnur , duban Afrah nayi nace " kid'aga kice masa baya nan , dubana tayi tace " tabb wallahi sai dai ke kid'aga , muna haka har kiran ya katse bamu d'agaba , sai da yayi kira Uku sannan nad'aga , jinayi yana cewa " gidan Uban wa kuka tafi kaida yaran nan ? shuru nayi nakasa magana , dan har jikina yafara rawa tamkar mazari , k'ara maimaita tambayar yayi cike da zafinsa nace " Ba Ya Haidar bane wayar tana hannun mu shi yana gurin Rawa , wata uwar Ashar naji Ya Zunnur yayi yace " wajen Rawa fa tabbas Haidar bashida hankali , shine ya d'aukeku har gun Rawa inane wajen ? tuni Afrah ta karb'e wayar ta kashe , da sauri na dubeta nace " yakika kashe wayar kinsan bala'in dazai mana akan kashe wayar nan kuwa ? Afrah tace " ai wanda yayi mana bala'in munkashe waye akan yaji wajen da muke yazo ya kunya tamu , Ya Haidar muka gani ya nufo wajen mu yana murmushi , muma kawai bamu nuna masa komai ba mukace " yakamata kazo mutafi gida fa kar dare yayi dayawa , lakacewa Afrah hanci yayi yace " daman tafiya nazo muyi dan nima inason in huta , mik'ewa mukayi sannan mukayi musu sallama muka tafi gida..... Muna isa harabar cikin gidan mukayi tozali da Ya Zunnur tsaye yana safa da Marwa , take naji cikina ya karta tamkar zanyi gudawa , dan gaskiya ina bala'in tsoron Ya Zunnur , ita kuwa Afrah gani nayi ko ajikinta , bare kuma Ya Haidar da baisan wainar da ake toya waba , hutunan mu Ya Haidar yafara nuna mana yana cewa tunda nayi posting d'inku a IG.Da Tiktok nake samun followers , dariya Afrah tayi tana fad'in " ai mud'in bana wasa bane ko Sister ? duk jikina bawani kuzari nayi yak'en dole kawai nace Ae, ai bank'arasa had'e bakina ba naji an bugo k'ofar Motar da k'arfi tamkar za'a ballata....... *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *kuyi* *k'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* 200 *Kacal* _Kusiya_ _kukaranta_ _cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰 *Nagode* *Masoya* *'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 😍🌹 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 ✍🏻 *MD*. 11. Nasma zata k'arayin magana kenan taji shigowar Daddyn su , mik'ewa tayi tadu besa tace "Daddy sannu da zuwa , batare da tajira ya amsa ba tafice abinta da kwanon da sukaci Abinci ita da Hanan , Alhaji Nasir duban Hanan yayi yana wani murmushi ganin tayi wanka tayi kyau abinta , kallon ta yayi sannan yace " Amarya ba magana naga nashigo ko sannu da zuwa bakiyi min ba bare insamu tarba ta musamman , Hanan cike da jin haushi tare da wata irin tsanar Alhajin tace " sannu da zuwa taja bakinta daga haka tayi shuru , shikuwa Alhaji Nasir ko ajikinsa haka ya hau cire babbar rigar sa yana ajewa , daga nan ya cire ta ciki itama da wando , daga shi sai singlet da gajeran wando yazauna dab da Hanan , d'an matsawa tayi dataji jikinsa yana gugan jikinta , had'e fuska yayi sannan yace " naga kina matsawa daga kusa dani saikace kinga wani dodo , sadaki na biya sannan aka bani ke dan haka dole nayi yadda nakeso dake batare da wani yatakamin birki ba, Hanan mik'ewa tayi tsaye tana fad'in " Gaskiya Alhaji bazan iya jurewa wannan Abin naka ba , koda sadaki kabiya ai bata hanyar data dace kake nemana ba , sannan farin saninka ne niba sonka nake ba kawai dai anfi k'arfina ne , Alhaji Nasir tuni ya mik'e ya doshi Hanan ya matseta a bango yana fad'in "sake mai matamin maganar dakika fad'a , inaso kisani ko kina so na ko bakya sona tunda har nariga dana aureki dole ki zauna dani , maganar kice bana kusantar ki ta yadda yadace wannan kuma ra'ayina ne hakan , tunda harna biya sadaki haka zaki cigaba dayimin biyayya , janyota yayi tamkar d'azu ya jefata kan gado kafin tayi yunk'urin tashi ya danneta , dayake Alhajin k'arfaffane gashi da jiki shiyasa bazata iya k'watar kanta ba , tanaji tana gani yakuma kusantar ta kuma yanxu ma ta baya yayi , Kuka sosai Hanan take tana kiran sunan Amminta tazo ta ceceta , bai d'agata ba har saida yabiya buk'atar sa sannan ya d'agata..... Bayan yayi wanka ya fice da k'yar Hanan ta iya rarrafawa tashiga band'aki ta gasa jikinta sannan tafito , kuka tashiga yi sosai har zazzab'i ya rufeta , wannan wacce irin masiface haka , saikace wani dabba ace yana kusantar ta ta baya , anya ba guduwa zatayi ba takoma can wajen Ammin ta , wata zuciyar ta tuno mata da maganar Nasma datace " duk wacce Alhaji yasa keta bata dad'ewa take mutuwa , tsoro ne yakuma kama Hanan ta fashe da wani kuka me tab'a zuciya a haka har bacci ya d'auketa..... A can Lagos.. Tunda Kawu Idi yace yataho da Hanan Ammi tashiga damuwa , dan tafi kowa sanin halin Kawu Idi dakuma Matarsa Safara'u , tabbas tasan Hanan saita shiga damuwa avwajen su sosai , kullum cikin yiwa 'yarta addu'a take Allah yatsareta duk inda take , Afrah kuwa kullum cikin zancen Hanan take , koda Abban su Afrah yadawo sosai yayiwa Ammi fad'a akan tacire damuwa akan Hanan d'in tunda da wayonta ai bak'aramar yarinya bace , Ammi taso ace yabata goyon baya ta anso 'yarta tarik'eta amman taga hakan baiyu ba , saima turo mata zawarawa dayakeyi akan tazab'i guda a ciki tayi aure tunda bata wuce aure ba ...... Tunda su Ya Zunnur suka koma Sch karatun ma wani lokacin gagararsa yake , kullum cikin tunanin Hanan yake , xoben dake hannunsa me farkon sunanta shi yake murzawa yana sumbata , yanxuma idonsa a rufe sai murmushi yake yana tuna yadda yarik'e mata hannu yana saka mata zoben , a hankali ya furta Ina Sonki Hanan Beauty , wata zuciyar tace " meyasa baka gaya mata kana sonta ba ? yanzu idan wani yaje ya tusa mata soyayyar sa a zuciyarta fa kai kuma azakayi ? tuni yayi saurin dakatar da zuciyar sa yana fad'in " Hanan tawace nikad'ai , duk wanda yayi gigin saka santa aransa to saidai yayi dakon asara , wayar sa ya d'auka yakira Number Ummansa , saida takusa yankewa yaji and'aga muryar Afrah yaji tana fad'in " Ya Zunnur Umman bata nan tafita tabar wayar a gida , cikin isarsa da ginshira irin tasa yace " wato sai ke kenan kina d'aukar mata waya kina kiran samari ko ? Afrah ta shagwab'e tace "nifah banida wani saurayi Ya Zunnur , kawai nima ring d'in naji nashigo d'akin d'aukar kayana , Zunnur yace " to intadawo kice nakira ina gaidata , sannan inaso kigayawa Ammi kice " nakira wayyar ta bata d'agawa lafiya kuwa ? Afrah tace " wallahi tunda wannan Kawun yazo ya d'auki Hanan yatafi da ita shikenan Ammi tadaina sukuni , wata irin zabura Zunnur yayi tare da fad'in " what , kina nufin kice Hanan ankomar da ita Jos wannan gidan ? Afrah tace ae. Kusan wata biyar ma kenan , nifah sanake Abban mu yasanar daku shiyasa , kuma kaga nibani da waya Umma kuma sai yanzu tayi waya itama , haka Ammi itama , Zunnur salati yashiga yi sannan yace taje takaiwa Ammi waya..... Lokacin da Afrah takaiwa Ammi waya samunta tayi tana goge hawaye , tana ganin Afrah tayi saurin k'ak'alo murmushin dole tana fad'in " oyoyo 'yata har antaso daga Sch d'in ? Afrah jitayi tausayin Ammin yakamata , tabbas tasan tunanin Hanan takeyi , mik'a mata wayar tayi tace " ga Ya Zunnur zakuyi magana ta juya ta fice ... Ammi ta kara wayar a kunnenta suka fara gaisawa , sannan yace "Ammi dama Bayan tafiyar mu babu dad'ewa Akazo akatafi da Hanan amman bamu sani ba ? shuru Ammi tayi batare da tace dashi komai ba , cigaba da Magana yayi yace " a gaskiya banji dad'in komawar Hanan Jos ba , saboda kwata kwata nidai bana k'aunar zamanta agidan wannan Kawun nata , Amman Allah yasa hakan yazame mata Alkairi , kuma insha Allah indai munsamu hutu zanje Jos d'in naganta , Ammi sosai taji dad'in kalaman Zunnur d'in , dan yana da Hankali sosai yafi Mahaifinsa tsayawa yayi hangen nesa , sai da suka d'an tab'a hira har saida yaji tasaki ranta sannan yayi mata sallama .... Ita kuwa Ammi daman lokacin ma Bacci takeyi tayi wani mugun mafarki akan Hanan , shine tana tashi taji hawaye na zuba aidanunta har Afrah tazo tasameta a haka...... Hanan Sosai tayi Bacci har saida akayi isha'i , lokacin Hajiya Hajjo ta aiko kiranta akan tazo ta d'ora musu Abincin dare , Hanan ganin anyi sallar isha'i duk a tunaninta ai har angama abincin dare amman saiga aiken kiran ta nan yazo , mik'ewa tayi ta nufi wajen kiran Hajiya Hajjon , dan Nasma ta gaya mata duk lokacin da Hajiya Hajjo ta kiraka to kome kakeyi kayi k'ok'arin barinsa kaje , dan hakan shine samun sauk'in ka a wajenta , Hanan na isa gurin Hajiya Hajjo tasamu tana tsaye tana jiranta , rissinawa tayi tace " gani Hajiya , Hajiya Hajjo tace " ga garinan maza kije ki tankad'e ki d'ora mana tuwo , inkingama saikizo ki anshi kayan miya ki d'ora miya , da sauri Hanan ta anshi garin ta wuce cikin kithen d'in , tunda tashiga kitchen d'in tafara tunanin ta inah zata fara , gashi bataga ko giftawar Nasma ba bare ta taimaka mata , shuru tayi tana tunani taji alamar shigowar Mutum ta bayanta , waigowa tayi da sauri sukayi ido biyu da Nasma tana mata murmushi , zatayi magana Nasma tayi mata alamar tayi shuru , Nan take Nasma tafara had'a wuta suka d'ora tukunya sannan suka hau tankad'e gari , Nan ma Hanan bata b'oyewa Nasma komai ba gameda Abinda Daddynsu yakuma yimata d'azu , duk da a hankali sukeyin maganar gudun kar wani ya lek'o yaga Nasma a ciki , Nasma ta tausaya wa Hanan d'in sosai , fara tunanin yadda zasu samu mafita yadaina kusantar ta ma kwata kwata suka shiga yi , a haka har suka kammala tuwo suka d'ora miya , Hanan tace " gaskiya Aunty Nasma bazan kuma kwana a d'akina ba , inajin wajenki zantaho mudunga kwana tare saboda banason Abinda Daddyn ku keyi dani , Nasma tace " aa Aunty Hanan zuwanki d'akina akwai damuwa dosai , kicigaba da hak'uri har allah yasa mugama samo mafita , yanzu haka naji labarin wacce Wata Suwaiba da Daddyn mu yasaketa ya aureki tana nan bata mutu ba amman bata da lafiya , inaso naje gurinta kozan samo mana wani k'arin haske game da abinda zamusa gaba , Hanan tace " yauwa Allah yasa dai karta mutu ni wallahi tsoro ma nakeji sosai , Nasma tace " nace miki kisaki jiki kidaina nuna tsoro yin hakan zaisa yarage saka miki ido har yafara barinki fita daga haka zamu b'illo da shirinmu , cikin hikima Nasma tadunga tsarawa Hanan yadda zata saki jiki da Daddyn nasu har susamu sugama shirinsu , sosai Hankalin Hanan ya kwanta dan tana jin maganar Nasma sosai tunda ta girmeta , motsin tahowa sukaji alamar antaho cikin kitchen d'in da sauri Nasma ta b'oye bayan wasu shirgin kaya....... [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Na* _Zee_ _MD_✍🏻 *Hamdala* *Writer's* *Association* 💪 https://www.facebook.com/111403834371046 ✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨ *Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim* *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta* *Wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* 200 *Kacal* *kusiya* *Kukaranta* _Cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰 *Last* 🆓 page. 10 Kuka babu irin wanda banyiba akan Rabuwa da Ammi , Koda aka kira Number Yayan Ammi aka gaya masa Kawu yazo zai tafi dani Cewa yayi " Abawa Kawun wayar , komai yace masa Amman Kawu yak'i Amincewa , haka Abban su Afrah yace da Ammi " tabari yatafi dani kawai inyadawo zasu san yadda za'ayi , haka muka rabu da Afrah tana kuka tamkar zata shid'e..... Ammi kuwa kasa magana tayi har muka fice daga gidan nida Kawu , Tunda muka fita yaketa min fad'a akan nadameshi da Kukan Munafinci , harda cemin ai shine dole na duk inda akaje , cikinsu d'aya da Mahaifina dan haka bazai bari 'Yar Yayansa tarayu a wani guri daban ba , ahaka har muka isa tasha motar mu takama Hanyar Jos...... Tunda muka sauka garin Jos duk wani farin ciki bana cikinsa , Ammina kawai nake tunani da halin datake ciki yanzu , duk danasan Ammi tana cikin gidan da ko tari tayi sai antambaye ta lafiya , nice yanzu Abar tausayi..... Muna isowa cikin gidan mu nafara karo da muryar Aunty Safara'u wato matar Kawu , fad'a takeyiwa 'Danta Mahmud wanda yaci sunan Baffa na wai yazubar mata da tsakin tuwo , tana ganin mu mun shigo ta dubeni shek'ek'e tana tab'e baki , Sallama Kawu yayi yashigo cikin gidan dayake yatsaya gaisawa da Abokinsa a waje , amsawa tayi tana fad'in " wato zuwa kayi ashe kadawo dasu saboda Jaraba irin taka , dubanta yayi yace " Nine Jarabar Kenan Safara'u ? nadawo gida ko sannu da zuwa bakiyimin ba nayi tafiyar kwana biyu sai kitareni da rashin mutunci kin kyauta , shigewa cikin d'akin yayi , nikuma na durk'usa ina gaida ta , Amsa min tayi ciki ciki sannan tace "Ina ita Uwar taki take ? Nace batare muka taho da itaba , sai Sannan naga tasaki fara'a tana yashar baki tamkar anyi mata albishir me dad'i , dubana tayi tace "kice ita bazata dawoba kenan? wannan karon haushi ne yakamani na mik'e tsaye nace " Nima bansaniba na wuce na nufi d'akin mu....... Tunda nadawo gidan mu bank'ara samun kwanciyar hankali ba , kullum nice nake aiki acikin gidan tamkar zan mutu saboda wuya , ga Abincin da Aunty Safara'u kebani d'an kad'an ne , wani zubin ma k'anzo take bani saboda mugunta , duk nabi na rame na lalace , Tunda aka koma Sch banje ko sau d'aya ba sun hanani zuwa , Wai Inna tafi waye zai dunga yimata aikin cikin gidan ...... Tun ina damuwa inshiga d'aki insha Kuka harnazo nafara dangana , dan yanzu *NI* *BORA* _Ce_ acikin gidan nan , kowa ya kwaso shirginsa niza ace nayi masa wanki , gashi duk arrabani da k'awayena wanda nake dasu wai suna zugani .... Kamal kuwa Saurayina wanda yakesona tun kafin mutafi Lagos Kawu ya dakatar dashi wai bashida sana'ar arzik'i.. A haka har nayi wata Hud'u da dawowa nasaba da wahalar cikin gidan Kawu , inada masoya sosai masu zuwa suce suna sona Amman kawu daga yaga babu na lasawa sai yace " Yayimin miji , indai kaga Kawu na rawar jiki da Saurayi inyazo gurina to tabbas zai moreshi ne , ana haka Har Allah yakawo Alhaji Nasir " wato Mahaifinki Nasma , lokacin dayazo sosai Kawu yayi Murna , Dan tashin farko Alhaji Nasir yasiyawa Kawu Abin Hawa wato Machine , Sannan yabashi jari metsoka , tuni Kawu yacewa Alhaji Nasir yabashi ni kawai yaturo a d'aura aure , Alhaji Nasir bai b'ata lokaci ba yaturo da kud'in Aurena , Sati Uku Aka saka tamkar angaji dani , lokacin da Alhaji Nasir yazo wajena nagansa bantab'a jin inason sa ba ko sau d'aya , duk zuwan dazai yi inna fito bana cemasa cikanka , sai dai shi yak'araci surutunsa yagama yatafi , Aunty Safara'u tamkar itace Amarya haka tashiga gyara d'akinta harda canza funutures , kud'in da Alhaji Nasir ke bawa Kawu haryaso yayi yawa , dan tuni aka gyara gidan mu tas harda saka k'aramin gate , Kawu har wani tumbi yayi saboda kud'i ..... Kullum ina cikin d'aki ina Kuka tamkar zanyi hauka , gashi banida wayar dazan nemi Ammi na in gaya mata damuwata , bani dawata k'awa wacce muke tare kowacce Kawu ya koreta , A haka Biki yak'araso Saura sati d'aya .. Ranar ina Zaune naji Aunty Safara'u nacewa Kawu "wai kagayawa Uwar waccen yarinyar Bikin kuwa ? jinayi Kawu yana cewa " Banfad'a musu ba haryanzu , kinsan haushina sukeji dan naje nataho da ita , dana barta ina zansamu wannan Abin Arzik'in , wallahi sai dai su mutu dan Haushi , Shewa Aunty Safara'u tasaka tana fad'in " ai inajin ma Hajjin Bana in Allah yaci damu kaga ya biya mana , da sauri Kawu yace " Yaci dani dai , ke yanzu in anbiya miki Hajji a dalilin wa kenan? Cike da rashin kunya tace "au Abin harda gori kenan ? Kawu yace " ba gori ba ko goruba zakice nayi , tunda bikin nan yataho banga kina yiwa yarinyar nan gyara naku irin na mata ba , kuma na tabbata da 'Yarki ce saikin gyarata , a hakan kike jiran a biya miki aikin Hajjin yajita ba gyara , Safara'u ta tab'e baki tace "Kaima inka gyarata ai ba fad'uwa kayi ba ...... Haka akayi Bikina Nida Alhaji Nasir batare da Ammina tasani ba ita da 'Dan uwanta , dan Kawu yace bazai gaya musu ba tunda suma basu nemeni ba , Haka aka kawo ni gidan nan naku gashi yanzu nafara ganin wata rayuwar bacin waccd nabaro...... *K'arshen* *Labarin* *Hanan* datake bawa Nasma , *Cigaban* *Labari* Nasma ajiyar Zuciya tayi sannan tace " tabbas kinga rayuwa a zaman ki na gidan Kawu , sannan nan gidan ma akwai tarin k'alubale wanda zaki fuskanta , dan nan d'inma bawani gidan zama bane , Hanan ta goge Hawayen dake fuskar ta tace " wallahi Babu abinda yabani tsoro game da cikin gidan nan tamkar yadda Alhaji ya kusanceni ta baya , Bantab'a sanin Namiji ba amman nasan Ance haramun ne kusantar mace tabaya , Nasma a tsorace ta dubi Hanan tace " ta baya fa Aunty Hanan ? Kai Hanan ta d'agawa Nasma Alamar Ae dagaske , Salati Nasma tafarayi tana tafa hannu , can tace " kenan wannan dalilin ne yasa duk Matan da Abba yake aure suke ficewa , Tabbas ina mamakin Yadda akayi duk wacce Abba zai aura a ta hud'u saita fita , ashe wanna ce take faruwa dasu , Lallai Yau na tabbata Abba bashida Imani da tausayi , sannan bashida cikakken ilimi akansa , da sauri Hanan ta toshewa Nasma baki tana fad'in "kidaina wannan furucin ga Mahaifinki , duk lalacewar Uba dole za'a kirasa da Uba , addu'a yakamata ace kinayi mishi Allah ya shiryashi yaganar dashi , Nasma Hawayene ke zuba ta cikin Idanunta tana ayyana wa a zuciyar ta " Inama bashine Mahaifinta ba , inama ba agidan aka haifeta ba tabbas wannan ba Mahaifin k'warai bane , Hanan tace " Inaso insan labarin cikin gidan nan wanda kikace zaki gayamin Shi .... Nasma ta goge hawaye tace " yanzu zanfad'a miki yadda cikin gidan nan yake , sai dai akwai wani abinda yake bani tsoro Aunty Hanan, Hanan tace "Kamar me kenan ? duk wad'anda Abbana yake aura yana saka to tabbas zakiga basa dadewa suke Mutuwa , take Hanan taji hanjin cikinta ya Juya wani zawo taji yana neman zubo mata , ta dubi Nasma tace "Shikenan nashiga Uku ni Hanan , yanzu banida ranar dazan fita daga gidan nan kenan ? in kuma nafita Mutuwa zanyi kenan ? Kuka ta fashe dashi tana fad'in "Wayyo Ammina shikenan bazan k'ara ganinkiba , shikenan Afrah dasu Ya Zunnur kowa bazan sake ganinsaba , Zoben da Ya Zunnur yasa mata a hannuwanta tafara dubawa tamkar shi take gani , murzasa take tana zubar da hawaye tabbas sai yanzu tagane San Ya Zunnur takeyi , dan kullum kafin ayi mata aure intashiga damuwa tana duba Zoben takejin sanyi , Nasma ce ta dafata tace " Inaso ki nutsu ki daina damuwa ki cire komai aranki , insha Allah saikin bar wannan gidan cikin k'oshin lafiya batare da kin Mutu ba , nayi miki Alk'awarin zanfitar dake daga gidan nan namu batare da kindad'e ba......... *Last* *Page* ✍🏻 *Littafina* *Na* *Kud'ine* *Duk* *Meso* *Yamin* *Magana* *Ta wannan* *Number* 07046107812 *Kuyi* *K'ok'arin* *Mallakar* *Naku* *Akan* 200 *Kacal* _Kusiya_ _Kukaranta_ _Cikin_ _Aminci_ 🤝🏻🥰 *'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_😍🌹 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 ✍🏻 *MD.* 12. Hajiya Hajjo ce tashigo cikin kitchen d'in , duban Hanan tayi wacce tashiga tura ice cikin Murhu tana goge gumin dake zubo mata na tsoro , ta dad'e a tsaye a gurin tana k'arewa kitchen d'in kallo kafin tajuya ta fita batare da tacewa Hanan ci kanki ba , tana fita Hanan ta sauke wata ajiyar zuciya tana Hamdala da godiya ga Allah dayasa Hajiya Hajjo bataga Nasma ba , Nasma itama fitowa tayi sannn ta lek'a taga ba kowa tadawo suka ci gaba da aikin , Hanan tace " nifah kawai ina ganin yakamata Aunty Nasma kibar aikin nan haka ki fita kar Hajiya Hajjo tadawo , Nasma tace " to bari na kad'a miki miyar sai nafita inyaso saiki sauketa , tuni Nasma ta mik'e ta hau kad'a miya tana gamawa ta lek'a taga ba kowa ta fice da saurin ta ..... Nasma tana fita ba dad'ewa Hanan taje tafad'awa Hajiya Hajjo ta kammala girkin , Hajiya Hajjo tace " kije palor cikin gida ganinan zuwa yanzu , Hanan tace to sannan tafita daga cikin d'akin Hajiya Hajjo d'in , d'akin Nasma Hanan ta nufa , tana zuwa taga Nasma na zaune tana karatun Alkur'ani , zama tayi har saida Nasma takai aya sannan tadubi Hanan tace " ina fatan bawanda yaganki lokacin dazaki shigo d'akina ? Hanan tace gaskiya babu kowa a tsakar gida , nima yanzu zuwa nayi kirakani palor cikin gida dan bansan ina ne ba , Nasma tace " Hajiya Hajjo ce tace kije can kenan ? Hanan tace ae itace inafatan dai lafiya bawani laifin nayi ba , Murmushi Nasma tayi sannan tace " ba laifin da kikayi sai dai yau zaki fara cin Abinci cikin Jama'ar gidan nan , Hanan tayi jugum tana kallon Nasma , Nasma ta mik'e taje tayiwa kur'anin ta wajen zama sannan tace " tashi muje karta rigamu zuwa , Hanan ta mik'e suka fito suka yi hanyar Babban palor cikin gida..... Suna shiga cikin palor Kowa na cikin palor yafara kallon Hanan , dayawa wasu yaran dake cikin gidan basusan Daddyn nasu yakuma wani auren ba sai yau , yarane k'ananu zasuyi su Ashirin a zune kufi kufi dasu , kana kallon sai sunbaka tausayi saboda yadda suke , kayan arzik'i babu ajikinsu kowanne yana zaune yayi jigum ko walwala basu da ita irin ta sauran yara , Nasma tasamu guri ta zauna sannan ta dubi Hanan tace " ki zauna kema , palor babu komai a cikinsa sai capet da aka shimfid'a dukansa , sai wata Tv 'yar k'arama da ita kuma irin ta dacan , Hanan zama tayi itama tana kallon yaran tamkar wad'anda suke a gidan birsin , cikin zuciyarta take fad'in " Anya Alhaji Nasir zaiga Rahamar Allah kuwa cikin lamarinsa ? wannan zalincin har ina kalli yara wad'an da yadace ace suna tare da iyayen su Mata suna basu kulawa amman ji yadda suke rayuwa , tabbas da wannan rayuwar wanda ace a gidan marayu suke watak'ila zasu samu gata fiye da nan , tunda ta zauna bata k'ara cewa komai ba , can sai ga Hajiya Hajjo d'auke da k'atuwar Roba a hannu , tana shigowa ta dubi Nasma tace " kije kicewa su Alawiyya da Hindatu suzo , Nasma tace to ta mik'e tafita .... Hajiya Hajjo tashi tayi takuma fita , Hanan hawaye taji yana zubowa a kan kuncinta , tabbas wannan ba gidan zama bane , a gaskiya Kawu ka cuceni da ka auramin wannan mugun mutumin , ganin wata yarinya tayi wacce bazata wuce shekara uku ba tazo wajenta tana gwarancin " Ummata kibani abinci naci da kanki karsu Habibu sucinye , Hanan wani kuka taji yazo mata ta rungume yarinyar tafara kuka , kana ganin yarinyar kasan wanka ma bayi mata akeba gashin kanta yayi duk'u duk'u , Nasma ce tashigo cikin palor , tana hango Hanan rungume da yarinya tayi sauri ta k'araso ta janyeta daga jikinta , komar da ita tayi cikin sauran yaran sannan tacewa Hanan " meyasa zakiyi hakan ? kinsan hakan zai iya janyo miki matsala me girma a wajen Daddy da Hajiya Hajjo , duk wani tausayin su da zakiji a yanzu ki adana shi bayanzu ba , kibari musamu mafita sai musan yadda za'ayi , Hajiya Hajjo ce tashigo shine yasaka Hanan da Nasma yin shuru , Hajiya Hajko tace " ke Nasma baki gaya musu nace suzoba ne najisu shuru ? Nasma tace nafad'awa kowa kina kiransu ... shigowar su tasa Nasma yin shuru , Hajiya Hajjo tadubesu tana hararar su tace " saikun ga dama zakuzo kenan ? Alawiyya tace " to ke wacece da za'ace kina kiran mutum saiya taho , Hajiya Hajjo tanajin hakan tasan yau Alawiyya ta gaji sotakeyi tayi abinda Alhaji zai saketa , batabi ta kanta ba ta hau zubawa yara Abinci , duka wannan bataliyar yaran ahad'e sukecin Abinci , sannan ta zubowa wa 'Yan matan ciki tare da Nasma suma tabasu , saikuma ta zubo musu ita da Hindatu da Alawiyya sai kuma Hanan , tuni kowa yafara cin Abincin sukayi tsit dasu ..... Kafin kace meye tuni yaran nan suncinye nasu tuwon, sai faman sid'e hannu suke suna zare ido alamar basu k'oshiba , wamnan Yarinyar datazo gun Hanan itace take kuka tana duban Hanan tana cewa Umma ban k'oshi ba suncinye , Hanan hawaye ya ciko idanunta tasaci kallon Nasma wacce keyi mata nuni da karta kula yarinyar nan , Hanan kwata kwata kasa cin Abincin tayi tana duban yarinyar , tuni su Hajiya Hajjo sunkusa cinyewa dan ko sau d'aya basu kulataba , Suna gama cinyewa Alawiyya ta mik'e tana harare harare tafice abinta , itama dai Hindatun tashi tayi ta fice Abinta , saida Hajiya Hajjo tagama sid'e kwano sannan ta mik'e tacewa su Nasma kufito da kwanuka inkungama tasa kai ta fice...... Hanan ko kallon wajen da Nasma take batayi ba ta mik'e tafita , d'akinta ta nufa prizer d'inta ta bud'e ta d'auko wata leda da Alhaji taga yashigo mata da ita yasaka a ciki , tana bud'ewa taga Balangu ne da biredi , sai kuma damammiyar fura da nono a roba , tuni ta d'auko furar tare da gutsiro biredi da kuma d'ebo nama takuma fita , tana zuwa wajen k'ofar Babban palor taga Nasma zata fito , tarar ta tayi sannan tace " Aunty Nasma inaso kisan yadda zaki d'aukomin yarinyar nan zan bata fura da biredi taci , Nasma ta zare ido tana fad'in " wai meyasa bakyajin magana Hanan wallahi wannan Abun dakike k'ok'arin yi Babbar kasadace , kuma inhar aka ganoki wallahi Daddy zaiyi miki hukunci me tsauri , Hanan tace " wallahi koda kasheni zaiyi sai nabata , bazan tab'a iya bacci ba ina ganin yarinya k'arama tanajin yunwa , inbanda mugunta taya za'ace adunga had'awa manya da yara abinci , kuma abincin ma bawanda mutum zai k'oshi ba , Nasma tace " Meye naki nadamuwa Hanan kawai kikoma d'akin ki kiyi musu addu'a Allah yakawo mafita , Hanan tuni ta shige cikin palor Nasma na ta k'wala mata kira amman tak'i dawowa , tana zuwa ciki tasamu yaran kowanne ya kwanta yayi lamo alamar dai basu k'oshiba , can tahango Yarinyar tana tsotar hannunta tana rufe da idonta alamar bacci zatayi , Hanan na zuwa ta lallab'a ta d'aukota ta fito da ita bayan d'akin sannan tafara bata Fura da biredi tana ansa , wani irin ci yarinyar takeyiwa biredin da fura tamkar tsohuwar mayya , kafin kace me harta tada furar da biredin , Naman tabata shima ta cinyeshi tas , Hanan tace kin k'oshi yanzu ? kai ta d'aga alamar ta k'oshi sannan Hanan tace " muje ki kwanta kinji Saikuma dasafe , cikin hausar ta ta gwaranci tace " zaki kuma kawomin wani da safe Ummata ? Hawaye Hanan taji yana zuba a kuncinta sannan tace " ae zankawo miki , maidat cikin 'Yan uwanta tayi sannan tafito taga Nasma a inda tabarta , dubanta Nasma tayi tace " kinbata taci kinji dad'i , inaso kisani karkisaba mata da abinda kikasan ba d'orewa zaiyiba , dakin barta a haka zata saba tamkar yadda muka saba kuma gashi har muka rayu ahaka , Hanan tace " Nasan koda bazai d'oreba nidai zancigaba da kulawa da ita , dan duk cikin yaran ai ita tafisu k'ank'anta dole a tausaya mata.... [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 ✍🏻 *MD*. 13. Bayan kwana biyu tuni Hanan tasaba da aikin wahalar gidan Alhaji Nasir , Sosai Hanan take kula da wannan k'aramar yarinyar me suna Aisha , koda yaushe sai sungama cin Abinci a had'e da sauran 'Yan uwanta sun kwanta sannan Hanan zata lallab'o tazo takuma bata , tuni Aysha tasaba da Hanan wacce take kira da Umma , duk wannan Abin da Hanan keyi sauran matan gidan bawacce tasani sai Nasma kad'ai , Hanan tana zaune a cikin d'akinta tana tsefe kanta saiga Nasma tashigo cikin d'akin d'auke da Sallama , amsa Hanan tayi Nasma tasamu guri ta zauna , duban Hanan tayi tace " yau tsifar kai kikeyi kenan ? Hanan tace "ae wallahi kan nawa yayi datti dayawa shiyasa na tsefeshi kuma gashi bansan waye zaiyi min kitsoba , Nasma tace " wannan ma wata dama ce daza musamu dan muje gurin Matar da Daddy yasaka , Hanan ta dubi Nasma cike da son jin k'arin bayani , Nasma tace "kin manta nagaya miki cewa wacce Daddy ya saketa sannan ya aureki tana nan yanzu haka ita bata mutu ba , Hanan da sauri tace " ea na tuna wacce kikace sunanta Suwaiba ko ? Nasma tace ea "ita nake nufi yanzu kinsan yadda za'ayi ? Hanan ta girgiza kanta alamar A'a . Nasma tace " yanzu tashi zakiyi kije d'akin Hajiya Hajjo tunda Daddy baya gari kice mata zakije kitso , Nasan bazata hanakiba saboda tanason taga ana fita in Daddy bay nan saboda tasamu shedar ce masa mace nafita yawo in baya nan , kinsan a kullum ajin haushin auren da Daddy yakeyi take , intaji yayi saki har murna take sosai ranar saboda jin dad'i , Hanan tace " ni wallahi mamaki ma take bani akan wannan kishin nata da takeyi , yanzu inbanda Abinta meye abin kishi a wajen Alhaji Nasir ? Mutumin dayake mu'amalar aure da mace ta baya sannan cikin gidan sa bawani kwanciyar hankali , irin wannan rayuwar ta gidan nan yanzu har wata abar so ce , Nasma tayi d'an Murmushi dan tanajin ciwon halin Mahaifin nata dayakeyi , sai lokacin Hanan ta tuna da cewa Alhaji Nasir fa Mahaifin Nasma ne kuma duk lalacewar sa dole zata kirasa da sunan Uba , cike da jin Nauyin Nasman tace " kiyi hak'uri Aunty Nasma dan Allah akan abinda na fad'a game da Mahaifinki , Nasma tayi Murmushi sannan tadafa kafad'ar Hanan tace " babu komai ai halinsa ne kuma nima na tsani halin nasa , yanzu dai tashi kije kitambayi Hajiya Hajjo d'in sai kisameni a k'ofar gate ina jiranki ....... Koda Hanan ta tambayi Hajiya Hajjo bata samu wata matsala ba ta amince mata , Hanan ta shirya tasaka Hijab d'in ta tafita , tunda aka kawota gidan Alhaji Nasir yau tafara zuwa k'ofar gate d'in gidan , tana fita ta hangi Nasma a tsaye sanye da Hijab itama , tana k'arasawa suka fita titi suka hau Napep suka nufi gidan su Suwaiba , dayake Nasma tasan gidan ta sanadiyyar Zuwan datayi lokacin da Baban Suwaibar yarasu , suna tafe Hanan tacewa Nasma "yanzu yazamuyi da kitso kuma ? kar mu koma gida Hajiya Hajjo taga banyi kitsoba fa , Nasma tace " in munfito daga gidan sai muje gidansu wata k'awata ta iya kitso sosai sai tayi miki , Suna zuwa suka sauka Nasma tabiya kud'in sannan suka shiga lungun gidan su Suwaiba..... Zunnur tunda yaji labarin Hanan ta koma Jos hankalinsa duk yabi yatashi, Allah Allah yake suyi exams. Su samu hutu yanufi Jos dan ganin halin da Hanan ke ciki , Haidar so dayawa zai saka Zunnur a gaba yana tambayar sa ko lafiya ganin Yadda ya canza gaba d'aya , amman kwata kwata yak'i fad'a masa sai dai yace ba komai , a haka har suka fara Exams. Suka kammala , koda suka kammala Zunnur yayi shirin zuwa garin Jos batare da yafad'awa Haidar ba , kawai yace zaije gurin wani Abokinsa amman kwana biyu zaiyi yadawo , a haka sukayi sallama ya nufi Hanyar Jos...... Lokacin da Zunnur ya iso Jos dak'yar yagane Unguwar su Hanan , yana zuwa gaya gidan duk ya canza tamkar ba gidan ba , tsayawa yayi a k'ofar gidan yana neman yaron da zai aika cikin gidan , yana tsaye saiga wani yaro yazo wucewa . da sauri Zunnur ya tsayar dashi sannan yace Ya shiga cikin gidan yace ana kiran Hanan inji Yayanta , yaron yashiga cikin gidan ya sanar da sak'on Zunnur , lokacin Kawu Idi yana zaune yana cin Abinci , duban yaron yayi yace " wacce Hanan kuma kake nema ? ai Hanan d'ayace a gidan nan kuma anyi mata aure , Yaro yanajin haka ya fito waje dan sanar da Zunnur , Kawu ya dubi Safara'u yace " kiji wani tsohon zance wai ana kiran Hanan , ai yanzu Hanan sai dai mufara maganar zuwan 'Danta , Safara'u ta tab'e baki sannan tace " to katashi ka lek'a kagani ko wani d'an uwan naku ne tunda naji ance Yayanta , Kawu tuni ya mik'e dan fita yaga waye ke neman Hanan d'in ...... Lokacin da Yaron da Zunnur ya aika yadawo masa da zancen wai ance ta dad'e dayin aure sai da yaji k'irjinsa ya buga , sake tambayar Yaron yayi yace " Hanan kace kuwa ? saiga Kawu Idi ya fito yana duban Zunnur d'in sannan yace " Sannu da zuwa d'an samari amman bangane daga inah ba , Zunnur ya gaida Kawu cikin girmamawa , shima amsawa yayi cike da sakin fuska , Zunnur yace " ni d'an gidan Yayan Ammin Hanan ne daga Lagos , nazo ne inga lafiyar ta shine abinda yakawoni , Kawu najin hakan ya canza Fuska sannan yace " au to dan na d'aukota shine aka ce muku bata cikin k'oshin lafiya ? To kasani nafi kowa iko da Hanan shiyasa naje na d'aukota kuma na Aurar da , wata irin zabura Zunnur yayi yana duban Kawun , cikin wata murya yace " wanne irin aure kuma ? Hanan d'in nawa take da zaayi mata Aure fisabililkahi , Kawu yadubi Zunnur yace " sokake saita janyo abin kunya za'ayi mata kenan , to kasani banshirya d'aukar rainon shege ba a gidana , inaso inka koma ka shedawa Uwar tata cewa na aurar da Hanan , kuma dama ai nine ma d'aurin aurenta ba wani ba , Zunnur wanda yakejin zuciyar sa nawani irin tafasa saboda Takaici , jiyake tamkar ya shak'o wuyan Kawun Hanan d'in ya haushi da duka saboda abinda yayi , taya zai aurar da Hanan alhalin Mahaifiyarta ma bata saniba , Yanzu yazaiyi da soyayyar Hanan wacce a kullum takeyi masa Barazana tamkar zata haukatashi , tabbas yasan wannan auren ba inda zaije mutuk'ar yana Numfashi , dan bazai tab'a barin Hanan tayi rayuwar Aure da wani ba indai ba mutuwa yayi ba , kallon Kawun yayi yace " inaso arakani gidan Hanan d'in dan inganta , Kawu Idi yadubi Zunnur yace " kasan bazan tab'a d'aukar k'afa na raka ka gidan Hanan ba , taya ma zakaje musu gida kana k'ato dakai ko sokake ka kashe mata auren ne ? Zunnur yace "aa taya zan kashe mata aure daga zuwa ganinta kawai , Kawu Idi k'eme me yak'i yace baza a raka Zunnur gidan Hanan ba , dole haka Zunnur ya hak'ura yabar k'ofar gidan , cikin gari yashiga dan yasamu Abinci yaci yasan Abinda zaiyi ...... Su Hanan suna shiga cikin gidan su Suwaiba suka sameta a zaune jingine da pilo a bayanta, duk ta rame ta koma wata kala tamkar me cutar Hiv. Sallama sukayi ka yi musu iso sannan suka gaisa da Mahaifiyar ta suka zauna kan shimfid'ar datake kai , Bayan sungaisheta sukayi mata yajiki , dubansu Suwaiba tayi tana son sanin fuskokinsu sai Nasma tace " Aunty Suwaiba nice Nasma fa ko kin manta dani ne ? Suwaiba tanajin muryar Nasma tagane ta take ta tuno da Alhaji Nasir hawaye suka fara fitowa daga idonta , magana tafara cikin wata irin Murya wacce take nuni da tanajin jiki sosai , cewa tayi " Nasma yakike ya sauran 'Yan uwanki kuma ? Nasma tace " lafiyalau kowa yake Aunty Nasma , sannan ta cigaba da magana , daman zuwa nayi dubaki nida k'awata kuma Auntyna , Suwaiba ta dubi Hanan tace " Nagode kinji baiwar Allah , Hanan tayi d'an Murmushi tace "bakomi ai yiwa kaine , Nasma ta gyara zama tace " Aunty Suwaiba wannan d'in da kike gani matar Daddy ce , ya aurota ne bayan yarabu dake , ita auren k'iyayya akayi mata da Daddy dan basonshi takeyi ba , ke kuma naga kamar kedashi ba auren k'iyayya kukayiba , Dan Allah munason sanin meye yarabaku da Daddy harya sakeki kuma meyasa kema kika kamu da rashin lafiya tamkar sauran matan dayake saka kafin zuwanki , Suwaiba take tafara hawaye tana tuno irin zaman da sukayi da Alhaji , kallon Hanan tayi tace " tabbas kina cikin tashin hankali ba d'an kad'an ba , duk da nace bawanda zaiji sirrin Alhaji amman yau naji araina inason sanar daku waye Alhaji , duk cikin Matan Alhaji bawacce tasan me Alhaji yake yi kamar yadda nasani , Amman kafin nafara gaya miku inaso inyi miki tambaya ta kalli Hanan , Hanan data gama tsorata tace " inajinki . Suwaiba tace " Alhaji Nasir yana kusantar ki ta Baya ko ? tuni wata zufa ta karyowa Hanan tace ea yanayi , Murmushin takaici Suwaiba tayi sannan tace " wannan yana d'aya daga cikin Abinda Yarabani da Alhaji Nasir , kuma kema tabbas zairabaku dashi mutuk'ar zaki d'auki Shawarata ..... Dafarko dai Alhaji Nasir yaganni ya nuna yana sona , nima kuma na soshi tamkar yadda yasoni , sosai yakemin b'arin kud'i tamkar bayajin ciwon nemansu , a haka har mukayi aure nidashi , matsalar dana fara fahimta da Alhaji Nasir itace " duk lokacin da zaizomin kwanciyar aure to da tsakar rana zaizo , kuma sai yace ta baya yakeso muyi bata inda Allah ya halatta musu ba , tun ina bijirewa har nafara sakin jiki dashi , ganin nabashi had'in kai batare da ina gaddama ba hakan yasa yake sakarmin kud'i sosai , kuma duk wani aikin cikin gidan nan yahana abani ko d'aya , sannan kullum muna hanyar fita cin Abinci dan banacin girkin cikin gidan ... Ana haka wata rana Alhaji yayi bak'i wato wasu Abokansa sukazo daga Kaduna , ranar girke girke masu dad'i akayi a cikin gidan dan kowa saida yaci ya k'oshi ina fatan kintuna da ranar ta dubi Nasma , Nasma ta d'aga kai alamar ta tuna , Suwaiba ta cigaba da magana " awannan ranar kamar a mintsineni natashi na nufi b'angaren Alhaji wanda duk yadda yakeson mace baya bari taje b'angarensa , kuma yasha gayamin cewa duk matan dayake saka saboda suna zuwa b'angarensa yake sakinsu , a lokacin na tambayesa meyasa bayason aje b'angaren nasa ?sai yacemin wata rana zai fad'amin , to a wannan ranar dayayi bak'i yasa na nufi b'angaren Alhaji cikin sand'a batare da kowa yaganni ba , ina zuwa nashige palor nasa naji alamar basa ciki shida bak'in nasa , ta cikin labule nake bi har nazl k'ofar bedroom d'insa , anan naji wani irin nishi yana fitowa tamkar na yanka wani Abu , a hankali na tura k'ofar batare da naji tsoroba , ina shiga na lab'e bayan labule ina lek'o kaina , a lokacin idanuwana sukayi arba da wani mugun gani , Alhaji Nasir ne shida Abokansa tsirara haihuwar Uwarsu da Ubansu sai Amfani sukeyi da junan su ta 'Duwawu , wato ta inda yake amfani dani , a gabansu kuma wata k'warya ce wacce wani gari yake acikinta , ina tsaye k'afata sai rawa take jikina sai kyarma yakeyi , nakasa daina kallonsu kuma nakasa ficewa daga d'akin ... .. lokacin da Maniy d'insu yazo zuba nan naga sun zubashi cikin wannan k'waryar ta gabansu , anan take wannan garin yarikid'e wata irin halitta suka fara wasu surutai , tunda naga haka nayi saurin fitowa daga cikin d'akin batare da sun kula dani ba , tunda nadawo d'akina zazzab'i me zafi ya rufeni nadunga kyarma tamkar mazari , Bayan wasu a wanni saiga Alhaji ya shigo d'akina inajin muryar sa naji fad'uwar gaba , nan ya nuna yana buk'ata ta kuma ta bayan yakeso yayi , tuni nace sam bansan wannan zance ba tundaga wannan rana muka fara samun matsala sosai da Alhaji , dan fir nahanashi jikina saboda abinda nagani , kwata kwata cikin gidan Alhaji Nasir ya fice min akaina har saida yasakeni sannan naji sauk'i , sai dai kuma tunda nadawo gidan mu wasu irin tsutsotsi ke fitowa ta k'asana , gashi kullum cikin zazzab'i me zafi nake , ba kalar asibitin da bamuje ba amman sunkasa ganin cutar dake damuna , wannan kuma yasamo asaline daga Alhaji Nasir dan nasan bawanda zai sakamin wannan cutar sai shi , to kunji dalilina na fitowa daga gidan Alhaji Nasir ........... [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 ✍🏻 *MD*. 15. Fitowa sukayi da gudu dan ganin meyake faruwa , ashe Hindatu itama ta Mutu tana cikin d'akinta a kwance , kamar yadda mutuwar Yaran Alhaji ta kasance haka ita tata takasance , Alawaiyya ce tashiga d'akin dan ganin me yahana Hindatun fitowa anyi mutuwa a cikin gidan , tana zuwa taga ashe ita rai yai halinsa shine tasaki Uban ihu , Nanfa kuka ya kuma zama sabo musamman yaranta , aikuwa nan danan aka kira Alhaji a waya amman shuru baya d'agawa har aka kira 'Yan uwanta aka fara had'ata , sai gab daza akai su gidan su na gaskiya sai ga Alhajin yazo ..... Nunawa yayi yafi kowa jin mutuwar dan harda kukansa wiwi , musamman dayazo kan gawar Hinda tu , tuni aka tafi aka kaisu gidan su na gaskiya akabar makusan tansu da jimami , Hanan tunda takaga Hindatu ta mutu kuma takaga irin mutuwar datayi tuni hankalin ta yakuma tashi , tabbas tasan wannan mutuwar da sukayi wallahi akwai lauje , Nan ta k'udurta a cikin ranta tabbas saita shiga d'akin Alhaji taga irin aikin dayake aikatawa , kuma wannan zuwan da zatayi ko Nasma bazata sanar waba , dan inajin ma su Hindatun ba mutuwa sukayi ba tsafi yayi dasu... Ranar sadaka gida ya cika taf da 'Yan uwa sai zuwa gaisuwa akeyi , Alhaji yana Harabar cikin gida shida Abokansa sai karb'ar gaisuwa yake , Kawu Idi sunzo shida Aunty Safara'u suma , Aunty Safara 'u tana zaune a d'akin Hanan ta dubi Hanan d'in tace " gaskiya gidan Alhaji yana da kyau sosai ga kud'i ga cima me kyau , inama nina samu gidan nan wallahi lafiya lau dani , Hanan yanzu duk wannan kayan d'ad'in da akeci a mutuwar nan haka kukecin wanda yafishi ko ? Hanan duban ta tayi cikin Ranta tana fad'in " dama ace baki da aure ki gwada auren Alhajin wallahi dasai kinyi bayani , zama cikin rufin Asiri yafi zama cikin daula , dan wani kud'in wallahi bana kwanciyar hankali bane , shurun da Hanan d'in tayi ne yasa Safara'u jin haushi " wato nizakiyiwa Banza ina magana ? ba shakka Hanan kin k'aro wulak'anci , dan kina auren me kud'i shine zaki fara wulak'an tamu to wallahi kiyi a hankali dan wallahi insaka yasakeki ba k'aramin aikina bane , Hanan da sauri ta dubi Aunty Safara'u tace " Dagaske zakisa yasakeni ? wallahi ni inaso yasakeni dan Allah Aunty kisaka yasakeni , Safara'u ta d'auka raina mata hankali Hanan takeyi tuni ta mik'e ta fice Fuuu daga cikin d'akin..... Hanan ta biyota tana fad'in " dan Allah Aunty kisaka yasakeni , Safara'u k'ara fusata tayi wato ita hanan zata tozarta dan tazo gidan ta ? to tabbas tayi da 'Yar halak dan saita nuna mata ta rigata shak'ar iskar duniya....... Nasma ce ta fahimci Hanan bata cikin hayyacinta tayi saurin tareta tana jan Hannunta ta komar da ita cikin d'aki ..... Zunnur tunda yashiga cikin Hotel yake tunanin Hanan , inama bai saka face mark ba yasan dasai taganesa , itace kenan tasaka Nik'af ta zauna a kusa dashi ? tabbas jininka duk inda yake saikaji acikin jikinka , lokacin da duka tsayar da Napep d'in har zaiyiwa me Napep fad'an meyasa zai d'auki wasu alhalin Drop d'insa yayi ? bai kai dayin magana ba yaga sun shigo da alamar sauri ma sukeyi , tana zama kusa dashi saida yaji zuciyarsa ta harba ashe Hanan ce , Tabbas gobe da safe sai yakuma komawa inda aka ajiyesu ko zai sake ganinta...... Washe gari ma saida ya koma unguwar su Hanan amman ko mai kama da ita baigani ba , haka ya gaji da zaman jira tamkar wanda aka ajiyeshi , lokacin daya mik'e zai tafi lokacin aka wuce da gawar su Hindatu har addu'a yayi musu sannan yabar Unguwar , Yana komawa Hotel ya shirya yafito dan komawa Sch da niyyar nan da sati biyu zai kuma dawowa Neman Hanan d"in kuma dole Kawun ya nuna masa ita.... Gidan Alhaji Nasir yanzu yadawo shuru sosai , dan kowa bayason magana bare hayaniya mussam Hanan , Nasma lokacin ta koma Sch amman hankalinta duk baya kan karatu yana ga matsalar dake cikin gidan su ... Yanzu Alhaji ya koma basu Abinci me dad'i dan andaina yin tuwo a gidan yanzu , kullum cefane yakeyi me rai da lafiya tare da sakin kud'i wanda har gyara gidan aka kumayi , dai dai da funutures d'in gidan duka saida ya canza musu shi , yara kuma ya yi musi d'inkuna kala kala tare da d'auko malami yana koya musu karatun boko da islamiyya , kud'in da Alhaji yakuma samu cikin satuttukan yana da Uban yawa , a nan Hanan ta kuma tsorata sosai , dan ko baka da hankali inkaga yadda Alhaji ke facaka da kud'i wallahi saika rik'e baki , kusan kullum saiyazowa da Hanan buk'atarsa ta inda yasaba yi , kullum cikin kokawa suke ita dashi dan yanzu tayi mugun tsanarsa , amman dayake k'arfinsu ba d'aya ba haka zai danneta har saiya gamsu...... Safara'u kuwa tunda ta koma gida take k'ulla yadda zata kashe auren ta da Kawu taje ta auri Alhaji ta koro Hanan , Har ita Hanan zata wulak'anta ? tabbas saita yi dana sani yi mata abinda tayi mata , dan inta shiga cikin gidan Alhajin saita kori kowacce mace ta maida Hanan 'Yar aikinta sannan ta dunga juya Alhajin shima kansa , tundaga ranar tafara yiwa Kawu Idi tujara iri iri tamkar me iska , shikuwa tunda yaga haka sai yarage dawowa gida da wuri saitayi bacci...... Yau gidan su Hanan tsit tamkar ba d'an adam , hakan yabawa Hanan damar fitowa daga cikin d'akinta sadaf sadaf , Nasma wacce ta taho zata gun Hanan d'in tana ganin Hanan d'in nayin sand'a sai itama ta b'oye kar Hanan d'in taganta , dan tanaso taga me Hanan d'in zatayi take sand'a haka ? Hanyar d'akin Daddyn su taga tayi , tunda take bata tab'a ganin anshiga d'akin Babansu ba sai sanda Suwaiba tafad'a musu tashiga , itama samun kanta tayi dabin bayan Hanan d'in har tashe b'angaren nasa , a hankali Hanan take tafiya harta shiga palor sa , tsaruwar da palor yayi tsayawa ma fad'a b'ata bakine , haka tagama kalle kallenta kafin ta fara dube dube tamkar wacce tayi ajiya tazo d'auka , ganin bata samu komaiba yasa tayi gaba zuwa wani d'aki data gani cikin palor , a hankali ta tura k'yauren d'akin sannan tasaka kai , hango wani k'aton gado tayi yasha gyara tamkar ba'a tab'a kwanciya a kansa ba , can tajiyo motsi tawani lungu a cikin d'aki , tsoro ne ya kamata amman ta dake ta tunkari gurin , tana lek'awa taga wata k'atuwar k'warya me zurfin samun kanta tayi da lek'awa aikuwa tayi karo da abinda ya furgitata , da sauri taja da baya zata fasa k'ara , jitayi anyi maza anrufe mata bak'i , take takuma tsorata tana fad'in " shikenan nakawo kaina wajen mutuwata........ [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 ✍🏻 *MD*. 14. Dukansu sai da labarin ya firgitasu sosai dan Hanan har wata irin zufa ce ke karyo mata , Suwaiba ta share hawayen idanunta tace " wallahi nayi dana sanin auran Alhaji Nasir ba iyaka , ta dubi Hanan tace " kitashi tsaye da ibada dakaiwa Allah kukanki dan kina cikin babban tashin hankali , ni ajikina inajin nakusa mutuwa saboda irin azabar danakeji a cikin jikina , sosai su Nasma suka tausayawa Suwaiba nan sukayi mata addu'ar samun lafiya , mik'ewa sukayi sukayi mata sallama Nasma ta bata dubu biyu tace tasai magani , sosai taji dad'i tare da yi mata godiya suka tafi...... Zunnur tunda yabaro gidan Kawun Hanan yasamu wani Resturen yaci Abinci , yana gamawa yabiya kud'in tare da nufar Hotel dan yakama d'aki ya kwana kafin gobe ya wuce ..... Hanan da Nasma tunda suka fito daga gidan su Suwaiba kowacce takasa magana , suna tafe tamkar kurame Hanan tace " wai yanzu inane gidan k'awar taki dakikace zatayi min kitson ? naga munyi yamma dayawa , Nasma tace " munkusa zuwa dan nima haka wallahi nafison muyi sauri muje tagama miki mu wuce gida , Hanan sauri tayi ta bud'e jaka ta d'auko Nik'af tasaka saboda tanaganin tamkar zasuyi karo da Alhaji Nasir , dan yanzu wani mugun tsoronsa takeji tamkar karta koma , suna tafe har suka iso gidansu k'awar Nasma sunyi sa'a kuwa tana nan , ba wata wata Nana tahau yiwa Hanan kitso , tana gama mata sukayi sallama suka fito....... Napep suka tare sai dai sun tadda akwai mutum d'aya a ciki , ganin Magriba tayi yasa suka hau batare da b'ata lokaci ba , Zunnur dake cikin Napep yana d'auke da face mark a fuska yad'an b'ata rai ganin anhad'ashi da mata , Hanan ce kusa dashi sai Nasma a k'arshe , Hanan itama Nik'af ne a fuskar ta shiyasa ba wanda yagane d'an uwansa , a haka har suka sauka daga cikin Napep d'in , anan Hanan ta manta da jakarta saboda Sauri kar Alhaji yadawo...... Sai da sukayi nisa da sauka sannan Zunnur yaga jakar tasu , da sauri yacewa me Napep " kaga matan da suka sauka sun manta jakar su , Me Napep yace " sunyiwa kansu ai dan bazan koma neman suba , inka bibiya babu komai a ciki sai kayan kwalliya , Zunnur samun kansa yayi da son ganin meye a cikin jakar , hannu yasa ya d'auka ya zugeta kud'i yagani aciki dubu uku , sai d'ank'aramin mudubi dakuma wani hoto wanda fuskar sa yake a kife , jiyayi yanason ganin hoton hannu yasaka ya d'auko shi yana dubawa yaci karo da hotonsa a bayan hoton an tubuta *ILUV* *U* *YAYA* *ZUNNUR* 🌹 Saikuma a k'asan Rubutun aka saka *By* *Hanan*, wata k'ara Zunnur yayi wacce sai da me Napep yataka burki ya tsaya , da sauri ya juyo yana duban Zunnur sannan yace " lafiya kuwa Malam irin wannan k'ara ? Zunnur yace " Plss dan Allah ka juya mu koma wajen da ka'ajiye Matan nan wallahi Ko nawa kakeso zan k'ara maka , Me Napep ya dubi Zunnur yace "saboda me me gida zan koma ? Zunnur ya nuna masa pic d'in sannan yayi masa bayani a cikin jakar yagani tabbas yasan wacce yake nema ce , tuni me Napep ya gamsu da hujjar Zunnur ya juya zai koma wajen da ya'ajiye su Hanan........ Hanan itace tafara shiga cikin gida , tayi sa'a batasamu kowa a tsakar gidan ba har ta shige d'aki , tana shiga d'aki tacire hijab d'inta a nan ta tuna da jakar ta , take gabanta ya fad'i Allah yasa dai ba a Napep ta manto jakar nan ba ? Babbar damuwarta itace hoton ya Zunnur datake ajiye dashi tuntuni , kullum dashi take kwana a kan k'irjinta ta riga tasaba indai a Napep tabaroshi shikenan tadaina bacci me dad'i , fitowa tayi ko Allah zaisa ace jakar na gurin Nasma ta d'auko mata , tana fitowa sukayi kicib'us da Hajiya Hajjo . Dubanta Hajiya Hajjo tayi sannan tace " kindawo shine bakije kinfad'amin kindawo ba ? Hanan cike da jin tsoro tace "yanzun nan nadawo kuma dama fitowa nayi nazo nafad'a miki nadawo , Hajiya Hajjo ta zubawa Hanan ido tana nazarin ta kafin tace " kije kitchen ki kad'a mana miya dan itace ba'ayi ba , Hanan tace " to cike da girma mawa sannan ta juya ta tafi ..... Zunnur suna k'arasowa wajen da suka ajiye su Hanan yafito , dubasu ya shiga yi lungu lungu amman babu ko masu kama dasu , dayake unguwar duk manyan gidaje ce dan haka bata da yawan Jama'a , haka suka gama dube dubensu batare da sunga me kama dasu Hanan ba ma bare su , hak'ura Zunnur yayi tunda dare yayi ya nufi Hotel dan kama d'aki saidai Jakar tana gunsa dan bazai iya rabuwa da itaba....... Hanan harta k'arasa kad'a musu miya amman duk yanayin ta babu dad'i , gashi tunda tashigo bataga Nasma ba haka tagama ta nufi d'akinta tashiga wanka , tana fitowa tanemi wata riga marar Nauyi tasaka sannan ta kwanta , tunane tunane tunane tashiga yi akan zamanta a gidan Alhaji Nasir , tabbas ta tausaya wa Suwaiba mutuk'a Amman yanzu itama abar tausayice , yau kwata kwata bataje gurin da suke had'uwa suci Abinci ba dan ko yunwar bataji , tunaninta guda d'ayane shine Aysha dan tasan zata dunga nemanta taga bata ganta ba .... Washe gari suka tashi dawata annoba a cikin gidan nasu , guda biyu daga cikin yaran Alhaji antashi dasu duk sun sank'ame ga wani jini nafita ta k'asansu da kuma bakinsu , kafin kace me tuni sunce ga garinku nan , tuni gida ya cika da koke koken mutuwa , sauran yaran gidan sai kuka sukeyi na rashin 'Yan uwansu , tashin Hankalin da Hanan tashiga ita da Nasma yayi yawa , tuni suka keb'e waje guda suka fara tattaunawa akan Mutuwar yaran.... Hanan datake sharar hawaye tace " wallahi nafarajin tsoron zama a cikin gidan nan , cikin mutuwar wannan yaran wallahi akwai lauje cikin nad'i , Nasma taja Numfashi tadubi Hanan sannan tace "Nikaina al'amarin Daddy yafara bani tsoro , tunda aka haifeni a cikin gidan Nan Ummata ta ajiye ta fice daga cikin gidan nan har yanzu bansan a inda take ba , a gurin Hajiya Hajjo nataso tun ina k'arama na saba da wahalhalun cikin gidan nan har na girma , ba kalar matar da bangani a cikin gidan nan Daddy ya aura ba , nasha ganin tashin hankali kala kala amman bantab'a cin karo dana yau ba , tabbas Mutuwar Abbas da Faruq akwai lauje cikin nad'i , kuka itama takeyi dan tana son k'annan nata duk daba uwa d'ayace ta haifesuba , Suna zaune suna tunanin yadda zasu b'illowa lamarin cikin gidan sukaji ana ihu....... [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Zee* *MD* ✍🏻 17. 'Daukota Alhaji Nasir yayi cak a kafad'arsa yafito , karo sukaci da Hajiya Hajjo yadubeta yace " ki k'arasa aikin batajin dad'i , baijira amsar taba ya juya ya nufi d'akin Hanan d'in . ..... Wata harara Hajiya Hajjo ta rakasu da ita tare da furta " lallai wannan yarinyar wato ni zakiyiwa kissa , wallahi zakiyi bayanine ai Alhajin zai fita yabarmu cikin gidan sai kingane baki da wayo mtsss tashige kitchen d'in ....... Yana shiga d'akin ya shimfid'eta a kan gado tare da d'auko ruwa ya yayyafa mata , wata ajiyar zuciya tasaki tare da mik'ewa zaune , koda taga Alhaji Nasir sai gabanta yakuma fad'uwa tafara ja da baya , dubanta yayi na wasu Minty na sannan yace " meyasa kike matsawa baya saboda kinganni ? sannan kuma fasa k'arar da kikayi itama saboda meye ? Hanan jitayi hanjin cikinta ya ya mutsa wata gudawa taji tana niyyar zubo mata tuni ta matse k'afarta , wata dabara ce ta fad'o mata tacewa Alhaji Nasir " dan Allah karka ce zaka kwanta dani wallahi jini nakeyi kuma banajin dad'in jikina ga aiki inayi , share hawayen fuskar ta tayi tana sunkuyar da kai k'asa , Alhaji tsayawa yayi sosai yana nazarin maganganunta sannan yace " saboda kar na kusance ki shine kina ganina kika fasa k'ara ? Hanan ta had'iyi wani muyau k'ut sannan tace " badan hakan bane saboda kaina yana min ciwone sosai kuma lokacin daka shigo tsoro naji sanake Hajiya Hajjo ce , take Alhaji Nasir ya gamsu da maganar Hanan yace " inbaki da lafiya basai kifad'iba akai ki asibiti kya zauna da ciwo , kuma zanyiwa Hajiya Hajjo magana kwata kwata tadaina sakaki aiki anemo meyin aiki inyaso na dunga biya , tashi tsaye yayi yadubeta sannan yace " kishirya yanxu Nasma tazo ta rakaki ki ga likita yasa kai ya fita..... Hanan bin bayansa tayi da kallo tana furta " Allah yafitar dani daga wannan bak'in gidan naka me tarin hatsari , kuka taci gaba dayi marar sauti tana Allah ya isa tsakaninta da Kawu Idi .... Alhaji Nasir yana fita ya tsaya yana nazari sosai akan waye ya shigar masa d'aki , ganin Nasma yayi tazo zata wuce ya kirata , tana zuwa ta rissina tace " gani Daddy , dubanta yayi yace " kije d'akin Hanan tashirya ki kaita wajen Likitana yabata magani batajin dad'i , Nasma tace to sannan ta mik'e ta nufi d'akin Hanan d'in... Nasma na shiga ta tarar da Hanan na zaune sai goge hawaye takeyi , Hanan naganinta ta mik'e ta rik'o hannun Nasma suka zauna nan tashiga gaya mata komai daya faru tsakaninta da Alhaji , Nasma tace " yakamata ki nutsu Hanan karya fuskanci mune muka shigar masa d'aki , wallahi yanzu mukayi waya da Aunty Suwaiba ita saida tasake gayamin akan inja kunnenki karki kuskura yagane munsan labarinsa , Hanan tace " wallahi a mugun tsorace nake a cikin gidan nan , gani nake tamkar Alhaji zai maidamu irin yadda yamaida su Aunty Hindatu , kuka tasaka sosai tana fad'awa jikin Nasma , ita Nasma Hawaye tashiga yi sosai tabbas tasan Hanan tafita shiga tashin hankali , domin ita taga abinda yake cikin k'waryar tsafin Daddyn nata dole zata fita shiga damuwa ...... Rarrashin ta tayi tace " kuka bazai zamo mana mafita ba Hanan , kawai dagewa zamuyi da addu'a Allah yakaremu da kariyar sa , Yanzu tashi zamuyi muje kiga likitan karya shigo yasamemu a hakan..... Safara'u sosai ta canzawa Kawu Idi , kullum cikin neman rigima take dashi saboda yasaketa , tariga ta k'udurta a ranta mutuk'ar tana numfashi sai tayi rayuwa a gidan Alhaji Nasir ko tahalin k'ak'a , yauma tunda tatashi take cika tana batsewa , can wata dabara ta fad'o mata akan tasan yadda zatayi tasamu Number Alhaji Nasir , lokacin Kawu Idi na kwance cikin d'aki Safara'u ta shiga , wani murmushi ta k'ak'alo na kissa ta nufi wajensa , tuni Kawu Idi yafara murna cikin ransa sayake Safara'u ta sauko yanzu , da jikinta ta rud'esa har saida ya gamsu da ita sannan ya mik'e ya nufi toilet yin wanka , yana fita tayi sauri ta d'au wayarsa ta nemo Number Alhaji Nasir ta kwafa , tana gama kwafa ta ajiye sannan ta tashi tafita daga cikin d'akin..... A b'angaren Ammin Hanan kuwa tunda ta tare gidan Alhaji Murtala bata da wata matsala , kawai dai kullum cikin tunanin Hanan take da yawan mafarkinta , zaman su lafiya lau da Abokiyar zamanta da kuma mijinsu , Hajiya Asma'u bata da damuwa ta d'auki Ammi tamkar 'yar uwarta sun had'e kansu , 'Ya'yan Hajiya Asma'u hud'u dukansu bawasu Manya bane , kamar kullum yauma suna zaune su uku a palor suna hira Alhaji Murtala yace " wai Hadiza yaushe zamuje Jos muga 'Yar tamu ne ? Ammi itace Hadiza , k'asa tayi da kanta tana murmushi batare da tabawa Alhaji Murtala amsa ba , Hajiya Asma'u jin an ambaci Jos saida k'irjinta ya buga , ko kad'an batason sunan garin bare wata k'addarar ta maidata , kallon Alhajin tayi sannan tace " wai dama Hanan A jos ake rik'onta ? Alhaji yace " a can ake rik'onta wajen k'anin Babanta , Hajiya Asma'u tace " yakamata ace kuje kuganta daga nan kunga kwataho manada ita muma muganta , wani dad'i Ammi taji cikin ranta yadda taga suna son 'Yar tata wacce ko ganinta basu tab'ayi ba , Nan Alhaji Murtala ya tsaida maganar k'arshen sabon wata zasuje suganta , sosai Ammi taji dad'i har saida tayi murmushi , nan suka shiga tsokanar ta kafin Alhajin yatashi ya fita ....... Hajiya Asma'u take zuciyarta tafara tunano mata rayuwar datayi a jos , haka kawai taji zuciyarta duk ta dagule mik'ewa tayi tacewa Ammi zataje ta kwanta.... Bayan Hanan sunje Asibiti Likita yadubata sannan yabata Magani , bayan sunfito daga asibiti a hanya Hanan ta dubi Nasma tace " Nifah inajin bazan koma gidan kuba , daga nan zanwuce duk inda Allah yakaini , dubanta Nasma tayi a tsorace sannan tace "haba Aunty Hanan wanne irin maganace wannan haka ? kinsan abinda kikeson yi kuwa ? ko kinmanta waye Daddy tsafi fa yakeyi kinga kuwa duk inda kikaje saiya dawo dake garesa , ko kinmanta da labarin da Aunty Suwaiba ta bamu , ko kuma kinaso kikamu da ciwo irin na Aunty Suwaiba ne ? dan Allah kiyi hak'uri mukoma gida inyaso sai musan ta inda zamu b'illo wa lamarin , Hanan ta tsaya tana duban Nasma sannan tace " Nasma kinaso muma a waye gari damu munkoma tamkar su Aunty Hindatu ? koda yake banga laifinki na rashin damuwa da halin da muke cikiba , ke kinsan bazai tab'a yi miki komai ba , sannan kina sane da ta inda Daddyn naki yake kusanta ta , inhar zanci gaba da zama wallahi sai narasa raina koda azabar mu'amala dani ta baya , Nasma tace " karki manta da cewa 'Yayansa ma Alhaji ba k'yalesu yayi ba , ko kinmanta su Abbas daya badasu suma , inaso kisani guduwar da zakiyi itace zata janyo yayi miki wani mugun abun , kinga kenan wanda ki zauna muci gaba da addu'ar neman mafita ....... Da wannan shawarwari Nasma ta shawo kan Hanan suka koma gida ..... Alhaji Nasir yana tare da wani Abokinsa suna aikata tsafinsu kiran wayar Safara' u ya shigo , baid'aga ba har saida aka bashi umarni dodon tsafinsu sannan ya d'aga , Kashe murya Safara'u tafara tare da shedawa Alhaji tanason magana dashi , Alhaji Nasir yace " kiyi hak'uri ina aiki zankira zuwa wani lokacin , katse wayar yayi batare da yajira amsar tana , nan dodon tsafinsu ya kawo hoton Safara'u tare da cewa Alhaji Nasir ya amince mata dan suna son amfani da jinin mace irinta......... [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 ✍🏻 *MD*. 16. Muryar Nasma taji tana cewa " me ya kawoki Hanan kinsan irin hatsarin da muke ciki kuwa ? sai sannan Hanan tayi ajiyar Zuciya tare da fitar da wani gauron numfashi , jiyowa tayi ta dubi Nasma tare da fad'awa jikinta tasaka wani kuka marar sauti , cikin kukan take cewa " Aunty Nasma dan Allah kifitar dani daga wannan gidan , kinsan meye acikin k'waryar can kuwa ? to wallahi kawunan su Aunty Hindu ne a ciki dukansu jini nafitowa ta idanunsu , da sauri Nasma tad'ago da Hanan tana fad'in " dagaske kike Hanan su Hindatu ne cikin waccan k'warya ? kai Hanan ta gyad'a mata batare datayi magana ba , wani tsoro ne yakama Nasma a hankali ta nufi wajen zata lek'a , motsin shigowa sukaji da alamar anshigo cikin d'akin , da sauri Nasma tayo baya tare da jan hannun Hanan wacce tuni tafara sakin fitsari saboda tsoro , Bayan labule suka shige tare da d'auke numfashinsu..... Alhaji Nasir ne ya shigo tare da wani Matashin saurayi wanda bazai wuce 25 year ba , suna shigowa Alhaji yafara cire kaya shima saurayin haka , Nan sukayi wannan d'an lungun suka fara aikata Mad'igo abinsu , su Hanan mutuwar tsaye sukayi dan komai akan idonsu akeyi , Hanan kuwa hawaye tuni ya kuma wanke mata fuska , wata k'ara Saurayin nan yasaki shida Alhaji sannan suka juye Abinsu cikin k'warya , Sake komawa sukayi suna surutai tare da fara wani zance , Nasma tuni tarik'e Hannun Hanan suka dunga bin labule harsuka k'araso k'ofah , dasauri suka bud'e zasu fita a dai dai lokacin Alhaji ya kallo wajen jin ana motsi , giftawar mutane yagani sunfita da gudu aikuwa tuni hankalinsa ya tashi yad'aga wannan saurayin sai dai lokacin da yataho k'ofar tuni su Hanan sun fice daga ciki ..... Alhaji cikin ransa yake fad'in " wato daman ana shigo masa d'aki har ana ganin sirrinsa , to suwaye da irin wannan k'ok'arin ? tabbas saiya nemo ko suwaye dan dole a cikin gidan nan suke....... Hanan da Nasma suna fitowa da sand'a suka shige d'akin Hanan , Kowacce kanta ya kulle sunkasa furta komai , can Nasma ta nisa tace " tabbas lokacin barin gidan mu yayi Hanan , nikaina da bansan dangina ba na wajen Uwa dole nabar gidan nan, bazan iya zama anaci dani da haram ba kuma kud'in tsafi , Hanan tace " kema kenan dayake mahaifinki inah gani kuma tabbas da da hali yau zanbar gidan nan na gudu wajen Ammina , Nasma ta dubi Hanan tace " a wajen fitowar mu Daddy yaganmu dan naga lokacin daya juyo , sai dai baiga jikinmu ba motsin fitar mu kawai yagani , dan haka barin gidan mu adai dai lokacin nan bazai yuwuba , yanzuma haka tashi nakeso nayi na wuce d'akina dan karya fito yayo nan d'akin yaganmu , Hanan tuni taji wani tsoro ya kamata tace " dan Allah inbiyoki d'akinki Aunty Nasma wallahi tsoro nakeji , Nasma tace " zaman mu waje d'aya yanzu hatsarine kiyi hak'uri ki zauna a d'akin ki , kawai abinda nakeso dake kiyawaita addu'a , ji sukayi anyi sallama muryar Islam d'aya daga cikin 'Yayan Alhajin tace " Aunty Hanan kizo inji Hajiya Hajjo zaki d'ora girki , Nasma ta dubi Islam tace " kice gatan zuwa kuma karki nuna kinganni cikin d'akin nan kinji , kai Islam ta d'aga alamar taji sannan tafita , Hanan ta dubi Nasma tace " wallahi bazan iya girkiba banajin dad'in jikina , dafa kafad'ar ta Nasma tayi sannan tace mata " ki daure kije kiyi zamanki cikin d'akin shima hatsari ne , kuma indai naga bakowa ai zanzo intayaki , tashi kije nima yanzu zantaho , Nasma sai da ta lek'a taga babu kowa sannan tafice daga d'akin...... A can Lagos kuwa tuni Abban su Zunnur ya d'aurawa Ammi aure da wani Abokinsa , Ammi kwata kwata batason auren dan ita haryanzu bata cikin nutsuwar ta , tuntafiyar Hanan haryanzu bata k'arajin muryar 'Yar ta ko kuma ganinta ba , tabbas tasan Hanan duk inda take tana buk'atar taimako ajikinta taji hakan , Haka tatare da k'udurin bayan kwana biyu zata tambayi mijinta taje Jos tagano 'Yarta ........ Alhaji yana fitowa daga b'angarensa ya shiga zagaye cikin gida dan gane waye yake shigar masa d'aki , Hajiya Hajjo yaci karo da ita tana zaune tana yanke farce , dubanta yayi yace " Hajiya niko bakiga wasu sun gilma ta nan ba ? Hajiya Hajjo ta d'ago ta dubesa sannan tace " wasu kuma Alhaji to kamar suwa ? wucewa yayi yana fad'in " barsu kawai bari naje ..... Kitchen ya nufo ganin hayak'i yasan girki akeyi , Hanan ta sunkuya tana gyara wuta taji anrik'eta ta baya , yadda taji rik'on tagane ba Nasma bace Wannan dagaji Namiji ne , da sauri ta juyo sukayi ido biyu da Alhaji aikuwa sai taga tamkar shima jinin fitowa yake daga cikin idonsa , wata k'ara tasaki tare da jan baya zata fad'i da sauri Alhaji ya rik'ota tayo jikinsa a Sume , Take Alhaji Nasir yasaka ayar tambaya akanta , meyasa dan tagansa zata yi irin wannan k'ara ? ............ [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Zee* *MD* ✍🏻 18. Bayan Alhaji Nasir yagama ganawa da dodon tsafinsu fitowa yayi daga cikin dak'insa , darak d'akin Hanan ya nufa dan tabiya masa buk'ata , Yana shiga yasa meta a takure a jikin gado ta had'a kai da guwa tana goge hawayen idonta , motsin shigowa d'akin da akayi yasa ta d'ago kanta a muk'ar tsorace , ganin Alhaji Nasir ba k'aramin fad'uwar gaba tayi ba , da sauri ta mik'e tsaye tamkar zata zura da gudu , yana k'arasowa tana matsawa a haka har ta k'urewa bango , dab da ita ya k'araso numfashinsu na dukan juna yace " meyasa kwana biyun nan kike guduna ne ? cikin zuciyar Hanan tace " kaid'in matsafine mugu azzalumi , a fili kuma shuru tayi batare da ta tanka masa ba , ganin hakan yasa Alhaji Nasir fincikota a zuciye ya jefata kan gado tare da danneta da duka k'arfinsa , ai tuni Hanan tafara kuka tana fad'in " dan Allah kad'agani karka kusance ni , wallahi bazan iyaba nagaji da aurenka kasakeni mugu azzalumi kawai ....... Alhaji Nasir tuni yaji ransa yayi mugun b'aci , Wato itama tafara shirin komawa tamkar sauran matan dayasaka , to tabbas zata yabawa aya zak'inta , dole zaiyi bincike a kanta ko tasan wani abu a game dashi , a haka ya danneta sai daya biya buk'atar sa ta inda yasaba wato bayanta ....... Bayan ya kammala ya mik'e tare da dubanta tamkar ta suma haka ya maida kayansa ya gice , daman indai Alhaji Nasir ya kusanci matansa to baya wani tsarki , a haka yake maida kayansa sannan yanufi d'akinsa yaje yayi tsarkin akan k'waryar tsafi ...... Hanan ta dad'e a hakan kafin ta mik'e k'afarta tace batasan zancen nan ba , kuka takeyi sosai tana fad'in " wayyo Allah Ammi na dan Allah kizo ki ceceni zasu kasheni , Kuka take sosai har muryar ta tadashe ta daina fita .... A hankali ta lallab'a ta sauko tashiga toilet d'in dake cikin d'akin ta gyara jikinta , wanka tayi tagasa jikinta da ruwan zafi sosai , k'atarta tak'i takuwa sosai ta rik'e . Haka ta dunga d'ingisawa har tafito daga toilet d'in , saka kayanta tayi sannan ta kwanta saboda wani zazzab'i dake barazanar kamata , lullub'a tayi cikin barko tana tunanin yadda za'ayi ta gudu daga cikin gidan...... Zunnur tunda yakoma Sch yakasa kwanciyar hankali , kullum tunanin Hanan ga yawan mafarkinta dayakeyi tana kuka , tabbas duk inda Hanan take bata cikin kwanciyar hankali , Haidar har saida ya fahimci d'an uwan nasa yana cikin damuwa , haka yasashi a gaba da tambaya amman fir Zunnur yace bakomai kawai bayajin dad'i ne ... Hanan tana ta tunane tunanenta har bacci yayi awon gaba da ita , Nasma so biyu tana shigowa cikin d'akin tana ganin Hanan nayin Bacci , ana biyun ne ta zauna tana jiran ko Allah zaisa ta farka , Ihu Nasma taji an kurma a tsakar gida , da sauri ta mik'e ta fito dan taga menene , ihun da aka cigaba dayi yasa Hanan ta farka a tsorace , da sauri ta mik'e daga kan gadonta tana d'ingisa k'afa tayo hanyar waje , Lokacin duka yaran gida sunfito sai kuka sukeyi , Hanan naganin Haka taji gabanta ya yanke ya fad'i tuni tafara Kukan itama tana tambayar meye , Yarinyar da Hanan d'in ke mutuk'ar so wato Aysha itace ta mutu , kuma itama mutuwar ta tamkar yadda sauran 'Yan uwanta sukayi haka tayi , Hanan yanke jiki tayi tafad'i tuni Nasma tayo kanta da gudu , Nan tashiga yayyafa mata ruwa amman shuru ko motsi , Nasma kuka tashiga yi sosai tana fad'in " dan Allah Aunty Hanan kitashi karki tafi kibarni plss , nariga na saba dake kece nake gani nasamu farin ciki ki taimaka plss , shuru Hanan ta daina motsi Yaran gida tuni sunzagaye ta sai kuka sukeyi suma , Nasma takuma zubawa Hanan Ruwa tana jijjigata tana fad'in " kitashi Hanan karki mutu bakiga mutuwar Daddy ba , tabbas nasan bazaki mutu yanxu ba har sai munga irin mutuwar wulak'ancin da Daddy zaiyi , kitashi dan Allah mucika burin mu kar mubari sauran yaran ma su Mutu , kwata kwata Nasma ta fita a hayyacin ta batasan Alhaji Nasir yazo wajen ba tuni ...... Hankalin Ammi kwata kwata ba a kwance yake ba , dan kwana biyun nan mafarkin datakeyi na Hanan yayi yawa , koyaushe sai taga anbiyo Hanan d'in wasu jibga jibgan maza , kuma koyaushe tana ihu tana fad'in " Ammi na kizo ki ceceni karsukasheni , shiyasa yau da tatashi ta k'udurta aranta tabbas gobe zata tafi Jos dan gano halin da 'Yar ta take ciki ........ A b'angaren Zunnur ma tuni ya shirya tsaf dan k'ara dawowa Jos , dan wannan karan bazai k'yale Kawun Hanan ba duk inda take saiya kaisa yagaji da rainin hankali , batare da yakuma gayawa Haidar ba ya kuma shiryawa dan yana so gobe da sassafe ya wuce garin Jos...... Safara'u tuni anshirya Had'uwa da Alhaji Nasir , dan ta k'udurta a ranta ko ta halin k'ak'a saita shiga cikin gidansa , in ma yace bazai aureta ba to tabbas zatasan yadda tayi yadunga kusantar ta harta samu rabonta itama , ai tunda Hanan ta wulak'an tata tabbas saita d'au fansa itama..... Alhaji Nasir duk irin maganganun da Nasma tayi yajisu , amman dayake d'an duniya ne saiya share ya k'araso wajen tamkar baijiba , lokacin Hanan ta farfad'o Nasma na rik'e da Hannunta , duban Nasma Hanan tayi sannan cikin muryar Kuka tafara magana " Aysha itama ta Rasu irin yadda su Abbas sukayi ? meyasa Alhaji yake kashe Yaransa da Matansa ? Alhaji Nasir dayake tsaye yana jinsu cikin ransa yace " tunda har kuka riga kuka ganeni to tabbas kuma taku tazo k'arshe , daman kune wad'an da kuka shigarmin d'aki to tabbas saikun bisu kuma , dan barinku a raye barazana ne ga dukkan wani burina danake dashi , a fili kuwa tuni yabar wajen dan kar su ganshi ma bare su fahimci yaji abinda suke fad'i....... Sosai mutuwar Aysha ta kuma hargitsa Hanan , nan tak'arajin tsoron Alhaji mutuk'a Koda yaushe tana tare da Nasma , yanzu kwata kwata ma tadaina kwana a d'akinta ta koma d'akin Nasma , ita yanzu Nasma ta daina tsoron komai ga wata muguwar tsana datayiwa Mahaifin nata , tabbas tayi danasanin zuwa duniya ta tsatson azzalumin Mahaifi irin Alhaji Nasir.... Bayan anyi sadakar Ukun Aysha komai ya lafa , amman duk wanda zaka gani a cikin gidan Alhaji Nasir a tsorace yake , walau Babba walau yaro kowa yatsorata da gidan , Yauma kamar kullum dare yayi kowa ya koma bacci da ido d'aya , yaran ne masuyin bacci saboda yarinta , Hanan da Nasma suna kwance amman ko wanne a cikinsu tunani yakeyi , dan rabonsu da bacci tun randa Aysha ta Rasu , wajen k'arfe d'ayan dare sukaji anbud'e k'ofar d'akin dasuke ciki , tuni suka mik'e tare da kashe k'wan d'akin , da sauri Hanan tace " Nasma shikenan muma kashemu zaiyi wallahi Alhaji ne , Nasma ta toshewa Hanan baki a hankali tace " bazai kashemu ba insha Allah zo mushiga toilet mufita ta windor ciki , a hankali suka sauko daga kan gado rik'e da Hannun juna suka shige toilet d'in , suna shiga sukayi maza suka saka masa sakata sannan suka nufi wajen windon ciki , Hanan tace " wannan windon yanzu kina ganin zamu iya fita ta cikinsa ? Nasma tuni ta taka kan tudun abin wanka tafara k'ok'arin b'allo glass d'in , Hanan itama takowa tayi tahawo wajen tafara taimakawa Nasman , aikuwa dai dai lokacin glass d'in ya yanki Hanan tayi wata k'ara da sauri Nasma ta toshe mata baki gudun kar aji suna ciki , aikuwa sai ji sukayi anfara girgiza k'ofar Toilet d'in .......... *Juma'at Kareeem Mutanena* 🤝🏻🥰 *Karku Manta da Karanta Suratul Khafi Aya Gomar Farko* *Yin Salati Ga Shugaban Halitta Annabi Muhammad S.A.W*🙏🏻🙏🏻 *'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ 🌹😍 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Zee* *MD* ✍🏻 20. Da sauri Nasma ta dubi Hanan tace " meye hakan ke kuma kodai bakya gani ne ? sai a lokacin Hanan ta dawo dai dai tana maida numfashi , maganar Direbance ta katsesu yace musu " Bayin Allah ku kuwa me kukayiwa wad'an can garadan mazan suke binku ? Nasma tace " wallahi babu abinda mukayi musu kawai 'yan iska ne , Dayake gari bai fara haske ba shiyasa har suka shigo cikin tasha Hanan bata kula da wanda ta fad'a jikinsa ba , suna iso ciki kowa ya fito daga cikin motar Hanan tadubi Nasma tace " kinsan a koda yaushe Alhaji zai iya sakawa a kuma biyomu, wallahi da da kud'i a hannun mu da Lagos zamu tafi wajen Ammi , Nasma tace " yanzu yadda za'ayi muje gidan Kawun ki sai mugaya masa komai kozai samo mana mafita , Dasauri Hanan ta dubi Nasma tace " anan gurin dai baki kawo shawara wacce zata yiwuba , ai zuwan mu gidan Kawu tamkar komawace gidan Alhaji Nasir , dan ko me zamuce wallahi Kawu bazai yadda ba...... Shuru sukayi suna nazari dan basu san ta yadda za'ayi suje Lagos ba , can Hanan taga giftawar wani Saurayi ta kusa dasu zai wuce , da sauri ta mik'e tana nufar wajensa tana fad'in " Dan Allah bawan Allah muna neman taimakon ka , juyowa yayi saboda jin muryar wacce a ko yaushe yake mafarkinta , aikuwa Idanunsu suka had'e waje d'aya , da sauru Zunnur yace " Hanan kece haka ? Hanan batasan sanda tafad'a jikinsa ba tare da fashewa da kuka wanda batasan na meye ba...... Yaran Alhaji Nasir tuni suka kirasa a waya suka gaya masa komai daya faru , cikin fusata yadunga yi musu fad'a akan sakacin dasukayi har su Hanan suka gudu , Anan suka yi masa Alk'awarin zasu duba kaf cikin gari dan nemo masa su , kashe wayar yayi batare da yace komai ba tabbas yayi mugun sake da har yabari su Hanan suka san sirrinsa , dole zai nemosu duk inda suke a fad'in Nageria jininsu ya riga dayayiwa dodonsu Alk'awarinsa.......... Da k'yar Hanan ta saki Zunnur tana share hawayen murna , dan yazo musu a lokacin dasuke da buk'atarsa , Nan yajasu gefe yana dubansu yace " dama kune aka biyoku kuka shigo cikin motar mu ? Nasma tace " mune . Zunnur yace " me kukayi musu haka suke binku kuma ke Hanan ai ance anyi miki aure ina mijin naki yake ? Nasma tace " wannan zancen ba na nan bane yanzu dai dan Allah ka kaimu wani gurin ka b'oyemu , da sauri yadu besu yaga jikinsu duk yabaci gashi kowacce da ciwo a jikinta , cikin zuciyar sa yafara tunanin yanzu ina zai kaisu Kano ko kuma Lagos ? wata zuciyar tace inka kaisu kano a inah zaka ajiyesu kawai ku nufi Lagos , da sauri yadubesu yace " kujirani Anan ina zuwa yanzu zandawo , da sauri ya juya yanufi cikin tasha lokacin har mutane sunfafa fitowa , wani P.O.S na cikin Tasha yashiga Nan ya kira wani Abokinsa yagaya masa ya turo masa kud'i , Baijima ma ya turo masa kud'in nan ya ansa tare da nufar wani guri yasiya musu Hijabai manya dan kayan jikinsu ma duk sun yage , koda yadawo samunsu yayi cikin wani lungu wanda ba yawan mutane , basu Hijab d'in yayi yace susaka sai su tafi , ansa sukayi suka saka sannan yabasu face mark shima suka saka nan suka bar cikin Tashar , a hanyarsu ta fita daga cikin tashar sukayi karo da Yaran Alhaji sukuma zasu shigo...... Ta gaban su Hanan suka wuce batare da sun gansu ba , su Hanan suka kuma tsorata sosai Zunnur yace " ku nutsu kar kuyi abinda zaisa aganeku , haka suka hau motar yace akaisu airpot dan Lagos yakeso su nufah..... A can b'angaren Ammin Hanan kuwa tashi tayi da zazzab'i da Amai , dan haka ta d'aga tafiya zuwa gobe ko jibi intaji sauk'i , sai dai tunda tatashi gabanta yake mutuk'ar fad'uwa , kwata kwata batajin dad'in komai , Hajiya Asma'u tana ganinta hakan ta anshi aikin girki tace mata taje ta kwanta ta huta ...... Tafiyar Awa d'aya da Rabi sukayi a jirgi suka isa Lagos , sosai Nasma take mamakin garin Lagos d'in , mutane sutacewa akwai cunkoso a lagos babu gidaje masu kyau to itadai bata cunkoso ba sai kyau da kuma tsaruwa, Tunani Zunnur ya shiga akan inah zai kai su yanzu gidansu ko kuma gidan Ammi , kawai ya yanke ya kaisu gidan Ammi tunda yasan gidan daman , hawa motar da zata kaisu gidan Ammi sukayi suka nufi can , Hanan batasan inah zasuje ba tunda basanin gari tayi ba kawai dai jitake kamar ta mik'e ta hau taka rawa saboda farin cikin zataga Ammin ta , duk wata fargaba da suka taho da ita kwata kwata babu a gun Hanan dan har wani murmushi takeyi da jin dad'in zataga Ammin ta yau..... Alhaji Nasir tuni ya hau motar sa ya nufi gidan Kawu Idi , tunani yakeyi ko su Hanan suje can su gaya masa abinda yafaru dasu.... Yana zuwa yasamu Kawu Idi yana k'ok'arin fita , yana ganin motar Alhaji ta tsaya yafara fara'a ya nufi wajen motar , Alhaji Nasir ya fito fuskar sa kadaran kadahan ya mik'awa Kawu hannu sukayi musabiha , Kawu yace " ina fatan dai lafiya ba Wannan ja'irar yarinyar ce tayi ma wani Abunba ? Alhaji Nasir najin haka yasan Hanan basuzo gidan Kawu ba , wata zuciyar tace " kodai sunzo sunfad'a masa shine yakeso ya raina masa hankali , gyara murya Alhaji Nasir yayi sannan yace " daman neman su nazoyi ita da yarinyar wajena , dan tuntuni suka gudo daga gidan ba inda ba'a duba ba amman ba'a gansuba shine nayi tunanin ko sunzo Nan , salati Kawu Idi ya shiga yi yana duban Alhaji sannan yace " wallahi basu zoba amman lafiya kuwa suka gudu ko wani laifin suka aikata ? Alhaji Nasir yashiga shirgawa Kawu k'arya ganin baisan komai ba yace " wallahi sunyiwa Uwargidana duka akan rabon Abinci , kuma ni ba dukan da sukayi bane damuwa a'a ba'asan inah suka nufa ba shine damuwar , ko kuna da wasu 'Yan uwan a nan ko can sukaje ? Kawu yana salati yace " tabbas wannan aikin Hanan ne itace zata kawo wannan banzar shawara ta dukan Hajiyar , Maganar 'Yan uwa kuwa bamu da kowa sai dai gidan su Safara'u me d'akina , dan ko ita Uwar Hanan d'in kasan na fad'a maka cewa tana can Lagos wajen d'an uwanta , kuma bana tunanin zasu gudu can d'in , sai dai ko ita yarinyar wajen naka ko tajata sunje danginka , Alhaji Nasir yace " gaskiya ba wasu dangina da Nasma ta sani bare suje , amman kakira min me d'akin naka kozata yiwa 'yan gidan nasu waya muji , da sauri Kawu Idi ya nufi cikin gida dan yiwa Safara'u magana........ Suna zuwa gidan su Ammi Hanan tadunga kallon gidan , cikin ranta tafara tunani tabbas tasan gidan su Zunnur yafi haka kyau sosai , to nan suka daso kuma duk da wannan d'in ma yana da kyau , suna k'arasawa palor gidan sukayi sallama daga ciki aka basu umarni su shigo , suna shiga suka samu Hajiya Asma'u da Alhaji Murtala a zaune suna hira , koda sukaga Zannur suka tareshi da fara'a dan sunsan shi sosai tunkafin Alhaji ya auri Ammi , gaishesu yayi cike da girma mawa amsawa sukayi suna nuna musu wajen zama , Hajiya Asma'u ta dubi su Hanan wad'an da suke sanye da face mark har lokacin tace " sannunku da zuwa 'Yan mata , sai lokacin suka cire Face mark d'in suna gaida su Hajiyar , Hajiya Asma'u tana kallon Nasma taji gabanta ya fad'i take taji lokaci d'aya yarinyar ta shiga cikin ranta , gaisuwar da suke mata kwata kwata takasa amsawa saboda kallon da takeyiwa Nasma , A dai dai lokacin Ammi tafito daga cikin d'akinta tasha wanka cikin wata Atamfa me kyan gaske gashi tayi wani kyau da ita kana ganinta kaga me yaron ciki , Hanan tana ganin Ammi ta tafi da gudu tana fad'in " Ammi na I miss u so Much ta fad'a jikinta , sai kuma ta saki kuka tana kuma k'ank'ame Ammin nata tamkar za'arabasu , A take su Hajiya Asma'u suka gane Hanan , nan suka shiga murna suna fad'in " kace yau gidan namu muna da manyan bak'in Jasawa sannun ku da zuwa , Ammi itama ta rik'e Hanan kam tamkar zata maidata cikinta dan murnar ganinta , samun waje sukayi suka zauna sannan Ammi tafara k'arewa Hanan kallo , gani tayi duk tarame ta lalace gashi kwata kwata tamkar ba a Hayyacinta ta tahoba duba da yanayin kayan jikinta , Nasma kuwa tana ganin yadda Hanan ta rungume Ammin ta tana murnar ganinta tuni zuciyar ta ta karye tafara hawaye , cikin Ranta take fad'in " inama itama taga Mamanta , wacece Mamanta ma ita tunda ta taso batason kowa ba sai Hajiya Hajjo kuma itama daga baya ta tsaneta bata maidata 'Ya ba , Hajiya Asma'u ta dubi Nasma tace " samu guri kema ki zauna , Nasma tayi saurin goge hawayen idonta tana zama , Ammi ganin yadda jikinsu yake tasan ba zuwan dad'i sukayi nan tace su tashi suje suyi wanka suzo suci Abinci inyaso sai suzo a kuma gaisawa........ koda Kawi Idi yashiga cikin gida yasamu Safara'u da maganar da Alhaji Nasir yazo masa da ita , tuni ta mik'e tanajin wani dad'i na ratsa ta , cikin ranta ta fara furta " Allah yasa baza aga Hanan d'in ba daga can tayi can dan dama baso takeyi tayi gogayyar miji da itaba , dan tuni tagama yanke hukuncin shiga cikin gidan Alhaji ko tahalin k'ak'a , duban Kawu tayi tace "yanzu ina shi Alhajin yake ? Kawu Idi yace " gashican a waje yana jirana gaskiya Yarinyar nan bata kyauta ba tagama zubar min da mutuncina , Safara'u ta dubi Kawu Idi ta tab'e baki sannan tace " daman kai har wani mutunci gareka a gunsa ? yana baka abin duniya kana saka hannu ka karb'e kana rawar jiki har wani mutunci zakayi , ta turesa da duwawu tana fad'in ni gafara naje wajensa muyi magana , ko mayafi bafa rufa ba daga ita sai waya yololuwar rigar bacci duk jikinta a waje , da sauri Kawu ya bita yana kiranta tare da fad'in " ahaka zaki fita titi bakida Hankaline ? ko kallonsa batayi ba ta lek'a a haka tana sakarwa Alhaji Murmushi , Alhaji Nasir kallonta yashiga yi yana maida wani mugun miyau k'ut , dan iya mace Safara'u mace ce ita tanada dirin jiki , koda Kawu Idi yaga irin kallon da Alhaji Nasir keyiwa Sarafa' tuni ransa yayi mugun b'aci baisan sanda ya tsinka mata mari ba , aikuwa ta saki wata k'ara tana nufo Alhaji Nasir ta fad'a jikinsa duk dan taja hankalinsa , aikuwa Kawu Idi yashiga zaginta yana tsinemata shikuma Alhaji Nasir sai k'ok'arin tureta yakeyi daga jikinsa ita kuma sai k'ara shigewa takeyi tana goga masa na shanunta wanda suke tsaye tamkar bata shayar ba...... [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Zee* *MD* ✍🏻 19. Hanan cike da sarewa da rayuwa tace " shikenan Yau mungama Rayuwa a duniya , A dai dai lokacin Nasma tagama cire glass d'in k'ofar dukansa , rik'o Hannun Hanan tayi ta ciccib'ata tace " kizo ki fita tanan Hanan inaso ace koni bantsira ba to ke kitsira kodan Amminki da Yaya Zunnur , Rayuwarki tafi tawa Amfani Hanan , bani da Uwa banida 'Yan uwa damuke ciki d'aya banida Dangi dan gaka bani da wani amfani , Hanan tarik'e Hannun Nasma tace " kina da Amfani sosai Nasma sannan duk abinda kika lissafa kema kina dashi , bazan iya tafiya nabarki a wannan halin ba , bugu k'ofar da k'arfi da aka sakeyi shine yasa dukansu suka Razana , da sauri Nasma ta tura Hanan tace " to fara dira nima saina diro daga baya , Hanan ta tahau sannan ta lek'e wajen , duhu tagani sai hasken farin wata k'adan , direwa tayi aikuwa ta fad'a kan kwalba , wata k'ara tasaki datasa Nasma saurin d'ane wa itama zata haura , a dai dai lokacin Alhaji Nasir ya karye k'yauren tare da shigowa cikin Toilet d'in , Nasma ta juyo ta kallesa rik'e da wata k'warya sanye da wani Jan yadi a jikinsa , suna had'a ido yayi saurin nufu wajen da niyyar janyota tuni ta dire waje itama , dasauri ta mik'e tare da rik'e Hannun Hanan tace " tashi Hanan mutafi wallahi Daddy ya ganni , da sauri Hanan ta mik'e k'afarta sai zubar da jini take suka fara gudu....... Alhaji Nasir tuni yayo waje tare da nufar k'ofar gate , kwata kwata ya manta a yadda ya fito yana zuwa ya fara k'ok'arin bud'e gate ya fita , megadin gidan tuni ya mik'e ya d'au sandar sa yanufi Alhaji Nasir ya buga masa , shi a tunaninsa 'Barawone yashigo cikin gidan , wata k'ara Alhaji yasaki tare da sakin k'waryar hannunsa , wani ruwa ne dayake ciki ya zube a k'asar wajen , haske fuskar Alhaji megadi yayi aikuwa yaga Alhaji Nasir tuni jikinsa yafara rawa yana bashi hak'uri , ko kallonsa Alhaji baiyiba saboda jin zafin Abinda yayi masa , da sauri yadaka masa tsawa yace " kayi sauri ka zagaya bayan gida ka kamomin su Nasma yanzu yanzu , karka barsu su b'acemaka , da sauri megadi ya bud'e gate tare da ficewa da mugun gudu ....... Sosai su Hanan suke gudu har suka iso bakin titi , lokacin suka hango Garba me gadi ya nufosu da mugun gudu , ai tuni suka ci gaba da gudu iya k'arfinsu , Hanan k'afarta sai Jini ne yake fita saboda azaba , wani lungu suka shiga a nan suka samu wani k'ofar gida a bud'e tuni suka shige cikin gidan , suna shiga suka maida k'ofar gidan suka rufe tare da neman wajen b'uya , Bayan wani d'aki sukayi tare da shigewa cikin kayan wanki da suka gani shirgi guda , koda Garba me gadi ya shigo lungu rasa inda su Hanan sukayi yayi , take yafara wasuwasi wanne gida suka shiga a cikin gidaje biyun daya gani ? kowacce k'ofa turasu yayi yajisu duk a kulle , yadad'e a tsaye a wajen kafin ya juya yatafi..... Alhaji Nasir tuni yakoma d'akinsa ya canzo kayansa tare da fitowa , nan Garba me gadi yake gaya masa baigansu ba amman yaga lungun dasuka shiga , take Alhaji Nasir ya d'auke Garba dawani mahaukacin mari sannan yace " Banza k'aton banza , yanzu ace wad'annan yaran sungagara kamuwa a wajenka , kashige muje karakani wajen dasukayi barinsu bankama suba hargari ya waye da matsala....... Hanan da Nasma suna cikin kaya wanki Sai kuka Hanan takeyi , Nasma cike da k'asa da murya tace " kiyi shuru Hanan a yanzu addu'a itace zata zamar mana mafita , Hanan ta janyo wani zani a cikin kayan wankin ta yagashi ta d'aure ciwonta dashi , Nasma tace " ina ganinfa tashi zamuyi mubar wannan gidan shima dan da Alama ba gida bane na matan aure , Da sauri Hanan ta dubi Nasma tare da fad'in " gaskiya nidai babu inda zani kina kallon yadda k'afata takemin wani mugun zafi kuma in muka fita ina kike tunanin zamuje ? motsi sukaji tare da magana , kasa kunne sukayi tare da yin shuru suka daina motsi , Nasma ta lek'o da kanta dan ganin ko Daddyn nasune yakuma zuwa wajen nasu kawai sai ganin wasu maza tayi suna shaye shaye tare da wasu mata , cikin hirar da suke Nasma taji suna fad'in " gaskiya yau dawa batayi Nama ba kuna ganin da k'yar muka sha a wannan gidan , 'Daya daga cikin matan tace " ai saboda yana da kayan aiki shi megidan shiyasa amman akwai gaba dole sai munci rabonmu , fahimtar da Nasma tayi anan 'Barayine kenan , nan suka gama bushe bushensu sannan suka fara aikata iskanci da matan , ahaka suka gama sannan suka shige wani d'aki...... Nasma tacewa Hanan " yanzu kinfahimci gidan da muka shigo ko ? to kitashi mubar gidan nan tun kan gari ya waye mana , Hanan tace " idan muka fita yanzu bamu san inda zamu fad'a ba , kibari asuba tayi sai mufita tunda ba ganinmu zasuyi ba lokacin , da wannan shawarar Nasma ta yadda suka yi shuru suna addu'oinsu ....... Alhaji Nasir tunda suka shigo lungu shida Garba yake nazari , tabbas indai wannan lungun ne ai yasan akwai yaransa dayake nema a cikinsa , wayar sa yazaro ya kira wani yaransa har ta katse bai d'agaba , sake kira yayi harta kusa katsewa sannan aka d'aga , cikin muryar Bacci yaron Alhaji Nasir yafara magana " sai megida wanne me k'aran kwanan ne yatab'a mana kai ? Alhaji Nasir yace" inada Wasu tsuntsaye ne da suka shigo cakwalinku , da sauri ya mik'e daga kwancen dayake yace " kace akwai Nama tare da Zuma bari intashi sauran mufito , Cikin k'ank'anin lokaci duk suka tashi tare da fitowa wajen Alhaji Nasir , su Nasma k'arajin motsi sukayi dan haka suka kuma tsorata , Nasma tacewa Hanan bari naje nagano mana ko dai wani Abin ne , Hanan ta rik'e hannun Nasma tana girgiza mata kai alamun kartaje , Nasma tace " badad'ewa zanyiba fa a hankali zan lek'a naga ko meye yanzu zandawo , a hankali Hanan ta saki Hannunta ta juya tafara tafiya a hankali...... Zunnur mafarkin dayayi shine yayi bala'in tsoratashi da sauri ya farka , tunani ya shiga yi yadda yaga Hanan tana kuka wasu maza na binta tana gudu , wai sai kiran sunan sa takeyi da sunan Ammin ta , tashi yayi yayo arwala tare dayin sallah raka'a biyu sannan yashiga yiwa Hanan addu'ar kariya a duk inda take , Cikin zuciyar sa yana fad'in duk inda kike Hanan gobe sainayi tozali dake , dan tun yanzu zanfita zuwa tasha nasan duk inda akayi sallar asuba dole motoci zasu fara tafiya ..... Nasma na lek'awa taga Daddyn ta tare da wad'an nan 'Yan fashin yana fad'a musu yadda zasu nemo su , Nan yace sufito su zauna cikin lungun da gefen lungu tabbas baza su wuce gurinba , Nan suka zazzauna tare da busa sigari suna cewa " ka kwantar da hankalinka indai suna cikin lungun nan to tabbas kamar sunzo hannunka , dan wancan gidan na Maman Iyabo innan suka shiga da asuba zata korosu da bala'i , Nan Alhaji yace " zaije gida duk abinda ake ciki suyi masa waya , sannan lallai karsu bari yaran nan su tsere...... Nasma da gudu tadawo wajen Hanan tana fad'in " kinga irinta ko Hanan , sai da nace miki tund'azu mubar wannan gidan ni hankalina bai kwanta dashi ba , gashinan Daddy yazo ashe yasan masu gidan nan , wata irin zabura Hanan tayi tana duban Nasma cike da tsoro sannan tace " shikenan kashin mu ya bushe dama bamu fito munsha wannan wahalar ba gashi yanzu abinda muke gudu shine dai zai afku , Nasma tayi jugum dan ita kanta yanzu batasan mafitar suba , ta inah zasu fita daga wannan gidan ? sannan insunce sai gari ya waye nan ma basu tsiraba , tabbas suna cikin tashin hankali , Hanan tuni tafara shashshekar kuka tare da cewa " kiyi magana Nasma kece me nemo mana mafita , Nasma tace dole muzama jarume a wannan lokacin inba haka ba bazamu tsira da ranmu ba tunda har Daddy yasaka a nemo mu har haka , yanzu dole kiyi d'amara dan gudu ne zamuyi sa sosai in anjima kad'an , kinsan dole wad'an nan zasuyi bacci tunda a bige suke to a wannan lokacin zamu samu mufice daga wannan gidan....... Tun kiran farko Zunnur ya fito ya nufi tasha , Allah yataimakesa yasamu abin hawa , yana zuwa yasamu wata motar me gudu wacce zataje Jos , haka ya hau me motar yace mutum biyu zasu jira sannan sutafi , Nan Zunnur yace " zai biya kud'in Mutum biyun kawai su shige sutafi , take yabiya kud'in Direba ya d'au hanyar Jos..... Ana kiran sallah Nasma ta zunguri Hanan wacce take gyangyad'in wahala , firgigit ta mik'e tana duban Nasma , a hankali Nasma tace mata " ki shirya Hanan lokacin fitarmu yayi , a hankali suka fito daga inda suka b'uya hanyar waje sukayo a hankali suna sand'a , dayake k'ofar gidan a bud'e take shiyasa basu sha wuya ba wajen zura k'afafunsu suka fita , suna fita sukaga Yaran da Alhaji yasa su kawosu dukansu idonsu biyu , sai dai da alama basu da wani kuzari saboda a buge suke da k'waya , suna ganin su Nasma sunfito aka fara kallon kallo , d'aya daga ciki yace " daman kuna cikin gidan mu kuka wahalar damu haka ? su Nasma suka tattare zani suka ranta ana kare , suma Yaran Alhaji tuni suka mik'e tare da rufa musu baya.... Gudu suke baji ba gani tamkar su tuntsira , suma kuma binsu suke iya k'arfinsu , dayake titi na da nisa da wajen ga duwatsuna shiyasa su Hanan suka fara gajiya , dan tuni tafama ciwonta da ta d'aure sai jini ne yake zuba , Nasma itama a lokacin tayi tuntub'e da wani dutse aikuwa ta fad'i tim a k'asa , take goshinta ya fashe jini ya wanke mata fuska , da sauri Hanan taje tana k'ok'arin tashinta , lokacin Yaran Alhaji tuni sunkusa k'arasowa , a hankali Nasma ta yunk'ura ta mik'e tare da taimakon Hanan suka ci gaba da gudun su , suna fara hango titi suka ga Yaran Alhaji sai k'ara k'aimi sukeyi suka masu , suma k'ara gudu sukayi har suka iso titi , da gudu suka ga wata motar ta taho hannu Nasma ta shiga d'agawa alamar ta tsaya , sunayi suna waiwayen Yaran Alhaji wanda shuka kusa k'arasowa , aikuwa Direban motar da kamar bazai tsayaba sai kuma wata zuciyar tace ka tsaya ko cetonsu zakayi , da sauri yataka burki su Hanan suka tafi da gudu suma Yaran Alhaji suka rufa musu baya , suna zuwa suka ga anbud'e musu k'ofah da gudu suk shige suna rufowa Direban yatasheta da gudu dan yagane biyosu akayi....... Yaran Alhaji cizon yatsun su sukayi tare da zubewa wajen suna zage zage , Hanan tunda ta fad'a cikin motar tajita ta fad'a jikin wani mutum , samun kanta tayi da kuma kwanciya tana maida numfashi , shima wanda tafad'a jikinsa jitayi dai dai saitin zuciyar sa yana bugawa da sauri da sauri........ [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Zee* *MD* ✍🏻 23. Bayan wasu watanni Matan nan biyu kowacce tasamu ciki a cikinsu , Alhaji kullum cikin yi musu rashin mutunci yake , ina ganin hakan nagama yadda Alhaji bason haihuwa yakeba , a dole naje asibiti sukamin allura na tsaida haihuwa , dan tuni Alhaji yasaki wad'annan matan yarage dagani sai Hajjo , Kuma har wannan lokacin Alhaji baya kulani , gashi yahanani naje naga iyayena , duk nabi nadamu kaina dan haka nafara rama , Nasma na da shekara d'aya da rabi na Yayeta , lokacin Mahaifina yazo garin jos dan ganina tunda ni nak'i zuwa a cewar su , koda yazo sosai Alhaji Nasir yayi masa tarba ta musamman , a nan ne muka shirya dan Mahaifina kwana biyu yayi , randa zai tafi shatara ta arzik'i Alhaji Nasir yayi masa sannan yasa Direba ya maida shi , sosai naji dad'in yadda Alhaji Nasir ya girmama Mahaifina har hawaye nayi lokacin dazai tafi , Bayan tafiyar Babana da kwana biyu Alhaji ya shigo d'akina , Nan yana nuna yana buk'atar mu kwanta amman ta baya yakeso , Nan ma na bijire masa Amman da k'arfi da yaji sai da yayi hakan dani , sosai nayi kuka tamkar raina zai fita gawani rad'ad'i danakeji ta k'asana , Haka nasha kuka na lokocin dayake da Rana ne Nasma tadunga min gwaranci tana gogemin hawaye .... Tunda ganan nadaina kula Alhaji Nasir nasamu kaina da mugun tsanar sa , ana haka aka kawo masa yaran sa wad'an da matansa suka haifa masa , yana ansar su yabawa Hajjo dan itace yake shiri da ita sosai , Ba'ad'auki lokaci me tsayiba saiga shi Alhaji Nasir yakuma yin aure wasu matan biyu , tunda ganan nashiga tsoron lamarin Alhaji Nasir sosai ...... Wata rana da daddare natashi ba wanda yasani na nufi b'angaren Alhaji Nasir , ina zuwa nasamu a bud'e sad'af sad'af nadunga tafiya har zuwa cikin bedroom d'insa , Anan naga abin Al'ajabi dan Alhaji Nasir nagani zindir haihuwar Uwar sa yana shan wani Abu a cikin k'warya , lab'ewa nayi nashiga lek'owa ina ganin Abinda yakeyi kawai sai gani nayi wani Saurayi ya fito daga toilet d'in d'akin , Shima tsira yake tamkar yadda Alhaji Nasir yake , yana fitowa suka fara aikata Luwad'i shida saurayin , sai wata k'ara suke suna gurnani tamkar wasu zakuna kafin sukawo , ina ganin haka najiyo nabar d'akin ina tafe inah kuka , tundagan nafara neman hanyar barin gidan Alhaji Nasir , kwata kwata nadaina jin dad'in komai a gidan , Komai ya siyo mana bana amfani dashi saboda natsani kud'insa dan nagama ganewa idona tsafi yakeyi , tuni nashiga nadama ta aurensa tare dayin dana sani , gashi haryau bansan asalin Alhaji Nasir ba , wad'anda yasamu ya turosu gidan mu lokacin aurena suma hayarsu yayi , danayi bincike akansa aka tabbatar min bad'an garin Jos bane kawai zuwa yayi cirani ...... Suma sauran matan da ya aura saigasu da ciki , Nan yashiga Jaraba yasasu a gaba yana zagi akan cewa harkud'i yabasu tunkafin suyi aure akan suje ayi musu allura ta hana d'aukar ciki ...... Kaisu yayi akan azubar da cikin amman fir ciki yak'i zubuwa , haka yaraka kowacce gidansu da saki , yana dawowa Nima nadunga rashin mutunci Akan sainaje garin mu naga iyayena , shikuma ya tubure bazanjeba haka na rufe ido naita gayamasa maganganu , aikuwa ya tunzira yafara dukana nikuma ina masa Allah ya isa , muna haka akazo masa da labarin matan da yasaka na farko sukansu sun mutu , da sauri nashiga tsoro ina fad'uwar gaba dan mutuwarsu ta dokeni sosai , Murmushi naga Alhaji Nasir yayi tare da cewa " duk macen data sake tasan sirrina to tabbas bazatayi tsayin rai A duniya ba , yana fad'ar hakan yashige yabar wajen , tuni hankalina yatashi sosai wato Alhaji Nasir yana nufin shine yakashesu ? tambayar dana shiga yiwa kaina kenan , Bayan kwana biyu yakuma zuwar min da buk'atarsa wacce yasaba , nak'i yarda inda yazo zaiyi da k'arfinsa nima na tattaro k'arfina na buga mada murfin sif , tuni goshinsa ya fashe amman bai hak'ura ba haka ya danne ni saida yabiya buk'atarsa ina faman cizonsa ...... Washe gari da sassafe tuni na had'a kayana na gudu , Tare da Nasma nataho gidan dan yadda nakeji bazan iya barinta ba , lokacin danazo gida iyayena sunyi mamakin ganina , nan na sheda musu irin abinda Alhaji Nasir yakeyi , suma sosai sukayi mamaki tare da yimasa addu'ar shiriya..... Bayan kwana biyu da zuwana Saiga Alhaji Nasir yazo , sosai yabada hak'uri amman nace bazan koma ba , tunda yaji nace bazan koma ba yashiga yin rashin mutunci sannan ya kwace Nasma yace da ita zai tafi , ba yadda ban yiba akan yabarmin 'Yata amman yak'i , cewa yayi indai inason yarinya ta sai dai mukoma gidansa , Mahaifina yace bazan koma ba yaje da 'Yar nima nahak'ura , haka inaji ina gani ya d'auki Nasma yatafi da ita..... Tundaga nan bank'ara ganinta ba kuma sannan bank'ara zuwa jos ba , nasha jinya tun bayan da yaturomin da takardar sakina , sosai nasha ciwo tamkar bazanyiba har saida aka fidda raina , Allah cikin ikonsa nasamu wani mutun yabani magani na warke , daga nan nafara zawarci har Allah yahad'ani da Alhaji Murtala , sosai yanuna min soyayya , dayake tamkar Yaya yake a guna tuni aka d'aura mana aure , a Lagos yake aikinsa dan haka yataho dani , saida na shekara biyu sannan nahaihu a gidan sa , 'Yan biyu na haifa duk maza sannan na haifi Aminatu da kuma Hafsa , *kunji Labarina*...... ina fatan kungamsu da nice Mahaifiyar Nasma , inbaku gamsuba ma akwai wani d'igo a gefen wuyanta wanda nake dashi nima a duba , a take Ammi ta duba gefen wuyan Hajiya Asma'u aikuwa taga tabon , sannan ta duba gefen wuyan Nasma itama take taga nata , Cike da godiya ga Allah Ammi tace " Allahu Akbar Alhamdulillah tabbas Nasma Yarinyar kice , dan ko yanzu nakuma tabbar dahakan nima ta yadda kuke kama , Nasma take tasaka kukan wanda tarasa nameye na dad'ine ko na meye oho jikin Hajiya Asma'u tafad'a tana kuka , Hajiya Asma'u ta ringumeta sosai tanajin k'aunar 'Yarta na ratsa duk wata gab'a ta jikinta , Bayan sun nutsu Ammi ta dubi Zunnur tace " Yanzu bawanda yaganka sanda kashigo garin nan dasu ? Zunnur yace " a gaskiya bawanda yaganmu dan ko gida bamujeba bare aganmu , Ammi taja numfashi sannan tace "Inaso ka kwana d'aya gobe saika wuce Sch d'in , zasu zauna anan banason ko Abban ku yasani dan bayanzu nakeso yasaniba , sannan ina gudun shi wannan Alhaji Nasir d'in karsuzo nan nemansu tunda kaga dole Idi zaikawosa nan , kaga indai sukaje gidan Yaya ai zaice musu Hanan batazo ba , tunda sunsan batasan nayi aureba dole intazo garin zasuce gidan Yaya zata sauka , da wannan shawara ta Ammi sukayi Na'am dukansu , Hajiya Asma'u tace " dole zamu samu Alhaji Murtala muyi magana , dan sai annemo musu maganin tsari sosai , nan suka shiga tattauna yadda zasu b'illowa lamarin Yaran nasu...... *Bayan kwana biyu* Tuni And'aura auren Alhaji Nasir da Safara'u sosai akasha bidiri a gidan su Safara'u , shikuwa Alhaji Nasir kwata kwata baya cikin nutsuwarsa kawai dan dai dodon tsafi ya nuna ya auri Safara'u shiyasa ya aureta , amman shi yanzu soyake yaga Hanan da Nasma , gashi Kawu Idi yazo har gidansa yayi masa rashin mutunci da ya lallab'ashi yayi masa kwatancen inda Mahaifiyar Hanan take , amman zaije ya jik'ashi da kud'i watak'ila ya kulashi inyaga ruwan nera..... Ankawo Safara'u gidan mijinta , sai faman hura hanci takeyi tana cika tana batsewa ita ala dole ta auri me kud'i , lokacin da Alhaji Nasir yazowa Safara'u ta Baya ya nuna mata zai kusance ta , nuna masa tayi sam batasan wannan batuba , kud'i ya d'auko ya zube mata dayake yaga daren farko ne tuni Safara'u ta amince masa yayi yadda yakeso da ita , sosai tasha azaba tamkar kayan cikinta zasu fito amman data tuna kud'inta kwata kwata sai zafin yatafi...... Hanan kwana biyun dasukayi har sun murmure , Alhaji Murtala sosai ya tausaya musu dayaji labarin tare dayin Allah wadai da Alhaji Nasir , Nasma kuwa koda yaushe tana manne da Hajiya Asma'u dan jitake tamkar yanzu tazo duniya , lalle Uwa akwai dad'i sai lallab'asu akeyi tamkar wasu k'ananan yara ...... Zunnur tunda yakoma yasamu nutsuwa dan kullum suna tare da Hanan a wayar Ammi , yanzu abinda yarage masa shine yasan yadda zaiyi yakoma Jos yasa Alhaji Nasir yasaki Hanan tunda da aurensa akanta haryanzu.......... [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Zee* *MD* ✍🏻 22. Hajiya Asma'u tafara basu labari kamar haka..... Ni 'Yar asalin garin Kano ce iyayen mu mu biyar suka haifa , mu hud'u mata sai Namiji guda d'aya wand Shine autan mu , duka Yayyena sunyi aure saini dana rage inah karatu , lokacin ina zuwa F.C.E kano a lokacin na had'u da Nasir muka k'ullah soyayyah , Nasir d'an garin Jos ne yazo kano karatune , Bayan ya kammala karatunsa ya koma Garinsu amman ko da yaushe muna waya dashi , soyayyar mu tayi k'arfi sosai kwata kwata Mahaifina baya k'aunar Nasir ko kad'an , niko kwata kwata idanuna sun rufe banaji bana gani akan Nasir , da Mahaifina yagaji da halina na korar samari yaga banida niyyar kula kowa indai ba Nasir ba , samuna yayi da maganar incewa Nasir d'in ya turo mutuk'ar da gaske yakeyi , ranar murna a wajena ba'a magana tuni nakira Nasir nasanar mai da wannan sak'on , shima murna yayi sosai tare da yimin alk'awari zaituro iyayen sa cikin satin...... Hakan kuwa akayi cikin sati iyayen Nasir sukazo daga jos , Nan aka tsaida lokacin bikinmu wata biyu masu zuwa , karkiga murna a wajena duk da inajin zanyi kewar iyayena , dan duk cikin Yayyena bawacce aka kaita nesa .. Akwana a tashi ba wuya saigashi lokacin biki yazo , sosai Nasir yayimin lefe d'an Ubansu ga kaya kamar me dan yawa , nayi mamakin ganin irin kayan da Nasir yasakomin a lefe , tunda nidai yadda yake cemin kullum wai aikin koyarwa yake , saikuma yana d'an tab'a kasuwanci , amman lefena kowa yagani a lokacin saiya k'ara gani saboda yawansu , Anyi biki lafiya angama washe gari aka wuce dani jos , sosai nayi kukan rabuwa da iyayena da kuma 'yan uwana , haka aka kawoni gidan Nasir me kyau dashi aka ajiyeni... Bayan kwana biyu dangina suka yimin sallama tare da tarin nasihohi akan rayuwar aure sannan suka wuce... Sosai Nasir yake tattalina tare faranta raina , kullum cikin yimin hidima yake tamkar ya maidani ciki , matsala ta farko dana fara fuskanta shine rashin ganin kowa nashi yazo , kullum cikin tambayar sa nake banga 'Yan uwansa ba amman saiyace min " wai sunsamu matsala tun lokacin bikina da sukace dole saiya auri 'Yar uwarsa ya had'amu mu biyu , haka nagaji da tambaya na k'yalesa har na cika wata uku ..... Matsala ta biyu dana k'ara fuskanta kwata kwata Nasir baya fita ko inah , kullum yana gida daga bacci sai cin Abinci da kallo , gashi koda yashe cikin kashe kud'i yake sababbi tamkar me aikin Bank , Nan ma nayi masa magana yace mun bayason yawan bincike a lamarinsa dan haka ido ne nawa , koda nashiga wata na hud'u a lokacin Allah yabani ciki sosai nakeshan wahala saboda laulayi , kwata kwata yadda na fahimci Nasir baya murna da wannan ciki , kuma a lokacin yabiya kud'in tafiya Hajji , yana ta shirin tafiya na rok'esa a kan ya maidani garin mu can gidan mu inyadawo sai nadawo nima , fir Nasir yak'i yace bayason a nuna gazawarsa dan haka zai kawomin 'Yar uwa wacce zamu zauna tare , duk bankawo komai ba ana saura kwana hud'u yatafi nafa ana gyara d'aya d'akin dake jikin nawa , akazo akayi jere dare nayi naji gud'a ankawomin Amarya ..... Sosai nayi mamakin Abinda Nasir yayimin naci kuka nagode Allah batare da nafad'awa kowa ba , haka ya shigo gidan yahad'amu nida Amaryar sa yayi mana fad'an zama lafiya , Amarya wacce naji yakira da suna Hajjo tace " insha Allah daga gurinta babu matsala nima hakan nace tare da mik'ewa nabar d'akin..... Ranar Tafiyar sa haka yatafi Saudi'a Abinsa yabarmu da tarin kud'i me yawa , Yadda na fahimci Hajjo tana da son Abin duniya , gata da bak'in kishi tamkar itace uwargida , Anan nakejin wai bazawara ce ita aurenta hud'u duk bata haihuwa shiyasa Nasir ya aurota , Anan nagane maganar ta inda ta nufa wato ni tunda nayi ciki bayaso bari ya auro wacce bata haihuwa , watan Alhaji Nasir Biyu yadawo gida lokacin cikina yafara girma ..... Koda yadawo bamu dad'e a wannan gidan ba muka tashi ya gina mana wani babban gida , gidan yahad'u sosai tamkar gidan wani gwamna , kullum cikin raina mamakin irin kud'in Alhaji Nasir nake , dan kullum yawa suke k'arayi tamkar ana turo masa su , gashi nayi nayi yasanar dani irin sana'ar dayakeyi fir yak'i yafad'an , dan har cewa yayi indai nakuma damunsa to wallahi abakin aurena , haka na hak'ura na k'yalesa har Allah yasaukeni lafiya nasamu 'Ya mace , ba laifi yayi murna amman bai d'auketa ba tunda aka haifeta , Ranar suna Yarinya taci Sunan Ummana Halimatu muke cemata *Nasma* 'yan uwana duk sunzo suna , sun nuna suna so sutafi dani wanka amman fir Alhaji Nasir yahana dole aka k'yaleni.. Bayan wata biyu da haihuwar Nasma nafara ganin sauyi a tare da Alhaji , kullum inyazo min kwanciyar aure sai yace ta Bayana zai kusance ni , nikuma nak'i yadda fir tunda ganan muka fara samun matsala , domin kwata kwata ya fita daga sabgata , gashi yahanani zuwa ganin gida firr , akwana atashi saiga Alhaji Nasir ya auro mata biyu rana d'aya , Nayi mamaki dabai gayamin zaiyi aureba amman haka nakuma dannewa batare da nanuna damuwa ta ba , a kullum banida burin sai son sanin ta ina Alhaji Nasir yake samun kud'i , dan kullum Abin yana bani tsoro sosai , kuma gashi har na haihu dashi amman bantab'a ganin danginsa ko d'ayaba........... *Kumin Afuwa yau Posting d'in Ni bora ce kad'ai zaku samu* *Shid'inma kuma kuyi hak'uri bayawa*✍🏻✍🏻 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Zee* *MD* ✍🏻 21. Tuni mutane suka fara cika a wajen ana bawa Kawu Idi hak'uri , amman ko takansu baibiba ya shige gidansa tare da rufowa , Alhaji Nasir shima nufar motar sa yayi zai shige yatafi Safara'u tayi tsagal tace " Alhaji dan Allah kataimaka min ka kaini gidan mu , ko jiyowa Alhaji Nasir baiyiba yace tashiga motar kawai...... Bayan su Hanan sunyi wanka Ammi ta d'auko musu dogayen riguna a cikin kayanta , mik'a musu tayi tace " gashinan kowacce tasaka sai kuzo palor kuci Abinci , Hannu biyu suka saka suka ansa tare da cema to , Bayan fitar ta Nasma ta dubi Hanan tace " gaskiya Hanan kinyi sa'ar Uwa tagari gata me fara'a dason mutane , nifah dana ganta wallahi saikace bata haifeki ba gashi tafiki kyauma , Hanan tayi murmushin jin dad'i tace " kedai kawai kice kinkoma Bayan Ammi yanzu nikuma an zubar dani , itama Nasma Murmushin tayi tace " in ma hakan ne ai ba laifi nayi ba dan kinsan Ina ganinta naji tamkar naga Ummata duk da bansan taba , Hanan tace " insha Allah zaki santa nan bada dad'ewa ba , Nasma tace " Allah yasa hakan dan inaso ko yayane nima naji d'uminta atare dani ...... Bayan sunsaka kaya suka fito daga cikin d'akin suka nufo palor , Zunnur tunda suka taho idonsa yake kan Hanan , gani yayi tarame sosai dai dai ta k'ara haske sosai ga idanunta sunkuma fitowa masu shek'i dasu , suna k'arasowa ya d'auke idonsa daga kallonta , samun guri sukayi suka zauna Hajiya Asma'u tuni ta kawo musu Abinci , jollof d'in shinkafa ce data wadatu da kayan lambu sai kuma Naman rago soyayye akai , gefe d'aya kuma ruwan roba ne da lemo , Zunnur shima anzuba masa nasa daban , nan sukayi bisimillah tare da fara cin Abincin su....... Safara'u tana zaune cikin motar Alhaji tamkar ba itace tasha duka ba , ta dubi Alhaji Nasir tawani kashe murya tace " Alhaji nidama naga baka dace da wannan yarinyar ba kwata kwata , kasan Hanan bata da wayewa ko kad'an mezai hana ka hak'ura da neman ta kawai kamaye gurbinta dani , tawani kashe masa ido ta mirro d'in motar tana wani k'ara turo k'irji , Alhaji Nasir yayi wani guntun murmushi sannan yace " ai duk wannan me sauk'ine , tunda har kinga nayi miki to kije gida kigama idda sai inzo muyi magana , Safara'u wani dad'ine ya rufeta tamkar tamik'e tafara tsalle tace " wacce Idda Alhaji ni ko gobe ka fito da wuri zantaho gareka , ko ka manta bari ya wuce shine ke kawo rabon wani , Alhaji yace " Amman kina ganin mijinki bazai zargin dama hakan ce takawoni ba harna kashe miki aure ? tab'e baki tayi sannan tace " k'yale wannan mara zuciyar ai ko inah gidansa kanuna kana sona dole zai hak'ura yabarmaka ni , bare yanzu yariga da yasakeni agaban mutane , Alhaji tunowa yayi da maganar dodon su dayake cewa " jinin Safara'u zaiyi musu Amfani , take Alhaji Ya Amincewa Safara'u tare da cemata Nan da kwana biyu zaizo neman auren ta , Murna a wajen Safara'u ba kama hannun yaro tuni tafara hango kanta a gidan Alhaji Nasir tana baza mulkinta..... Kawu Idi ransa ba k'aramin b'aci yayi ba , dama yadad'e yana zargin Safara'u tana son Alhaji Nasir saboda taga yana da kud'i , yau yaga gaskiya da kansa dan haka taje gata ga shinan , Abin kunya be dai ace Hanan na gidansa da aure itama tashiga gidan , tabbas zaisan yadda zaiyi ya hana Alhajin Hana kula Safara'un..... Bayan su Hanan sungama cin Abinci Nan suka kuma gaisawa da tambayar bayan saduwa , Alhaji Murtala yatashi yafita saboda kiran da akayi masa a wajen aikinsu , Hajiya Asma'u kuma k'anwarta tazo itama ta mik'e suka shiga ciki , yarage sai su Hanan da Nasma da Zunnur da Ammi , Ammi ta dubi Zunnut tace " yaushe kadawo gida banida labari ? Zunnur ya gyara zama sannan yace " Akwai muhimmiyar magana a game da Hanan Ammi , Ammi tace "tunda nagansu haka ita da wacce suka zo nasan ba zuwan dad'ine ba , Nan tace " inajinka kasanar dani komai banaso ko kad'an a boyemin wani Abu , Nan Zunnur ya shiga gayawa Ammi tun randa yaje gidan Kawu Idi da yadda sukayi dashi har takawo zuwansa gidanta shida su Hanan bai b'oye komai ba ....... Ammi tuni taji wani gumi yana karyo mata wato duk mafarkin datake akan Hanan ashe da walakin , Mik'ewa tsaye tayi tashiga yin safa da marwa a cikin Palor , tabbas Idi yaci Amanar zumunci wato shine ya aurar da 'Yar ta batare da tasaniba , ta dad'e ahaka sannan tadawo ta zauna ta dubi Hanan tace "waye mijin naki kuma a ina yake inaso nasan waye wanda ya aura miki ? Dai dai lokacin Hajiya Asma'u tafito ta nufi cikin kitchen , Abincinci ta zubowa K'anwar ta ta fito kuma a dai dai lokacin Hanan ta furta Ya aurar dani ga wani me kud'i wanda ake sakawa a lissafin masu kud'in Jos wato Alhaji Nasir , Tuni farantin Abincin da Hajiya Asma'u ta d'ebo ya sub'uce daga hannunta , jitayi gabanta ya yanke ya fad'i lokaci d'aya jikinta yafara rawa , dukansu juyowa suna kallonta kafin suce " Lafiya kuwa ? sauri tayi ta dawo dai dai tare da cewa " wallahi sub'ucewa yayi daga hannuna , Nasma da sauri ta mik'e ta nufeta tana fad'in " bai dai fad'o miki a k'afa ba ko ? duban Nasman tayi tana murmushi tace " bai fad'oba 'Yata koma ki zauna zangyara da kaina , sunan da takira Nasma dashi ba k'aramin dad'i yayiwa Nasman ba , sunkuyawa tayi tana kwashewa da hannunta tana xubawa cikin filet d'in , Hajiya Asma'u sai k'ok'arin Hanata takeyi Amman tak'i , saida ta gyara wajen tsaf sannan ta koma ta zauna , nan Hajiya Asma'u ta shiga sa mata Albarka ...... Lab'ewa Hajiya Asma'u tayi dan tanaso taji labarin Hanan d'in , tabbas tanaji a jikinta tamkar Alhaji Nasir d'in data sanine za'abada labarinsa ..... Nan Hanan tashiga bawa Ammi da Zunnur labarin Rayuwar datayi tundaga lokacin da Kawu yazo ya d'auketa , har Auranta da Alhaji Nasir da irin wahalar datasha agidansa da kuma yadda Nasma ke taimaka mata tare da yadda yadunga mu'amalar aure da ita bata b'oye musu komai ba , Kuka sosai Ammi takeyi ita kanta Hanan d'in Kuka takeyi Nasma kuwa hawayene ke zuba a idanunta , Zunnu kuwa tuni idonsa ya kad'a yayi jajir , tabbas da yanzu zaiga Alhaji Nasir baiga abinda zai hana bai kaishi lahiraba , wata muguwar tsanar Kawu Idi yaji ta kamashi duban Ammi yayi wacce take kuka har wannan lokaci yace " kishare hawayenki Ammi , Yanzu ba lokocin kuka bane tabbas nayi Alk'awari sai na d'aukarwa Hanan fansar Abinda Sukayi mata , Hanan ta share hawayenta sannan tace " Abinda ya gudo damu yanzu daga gidan Alhaji Nasir yanzu kuma shine yana tsafi yakeyi da shan jini , kuma yanzuma haka neman mu yakeyi yayi tsafin damu , Ammi ta Hanan tace "Itama wannan d'in Matarsa ce ? Hanan tace " 'Yarsa ce ta cikinsa kuma itama harda ita yakeson Halakamu , duban Nasma Ammi tayi sannan tace " Tabbas ke 'Ya tagari amman baki sa'ar Uba nagari ba , Mahaifiyarki tana ganin tashin hankali dan zama da irin wannan mijin tamkar zama a kabarine , Hanan tace " Batasan Mahaifiyar ta ba tun tana yarinya suka rabu da shi , Hajiya Asma'u duk labarin da Hanan takeyi a cikin kunnenta taji komai , Kuka takeyi me cike da murna dan tabbas tasan ko ba'a fad'a mata ba tasan Nasma 'Yar tace wacce tabar gidan Babanta tana 'Yar shekara biyu , da sauri ta fito daga cikin kitchen ta nufi wajen Nasma ta rungumeta tana kuka tana fad'in " tun shigowarki cikin gidan nan naji ajikina tabbas ked'in jininace , ashe kuwa hakan ce Nasma ked'in 'Yatace wacce na haifa da cikina , duk labarin da Hanan takeyi inajinku kugafarce ni bana lab'e dan wani abubu sai dan fitowa ta danayi naji Hanan ta ambaci sunan Alhaji Nasir Jos , to daga nan naji inaso insan labarin dazata bayar , tabbas Alhaji Nasir yadad'e yana aikata zunubi a cikin duniya , Dukansu sakin baki sukayi suna duban Hajiya Asma'u tare da tarin tambayoyi da mamaki a bakunansu , tabbas zasu so jin taya akayi Nasma tazamo 'Yarta ? taya tasan Alhaji Nasir ? .... Dubansu tayi dukansu tace " nasan zakuso jin taya nakasance Mahaifiyar Nasma ko ? to kafin kusani inaso dan Allah ku nutsu sosai ku dubeta sannan kudubeni nasan ko a hakan zaku gamsu da wani Abun , dukansu kafawa Hajiya Asma'u idanu sukayi sannan suka fara duban Nasma itama.... Safara' u koda taje gida Iyayenta basu damu ba , dan suma sarakan san kud'ine gado itama tayi , nan suka karb'i maganar Alhaji Nasir tare da tsaida rana sati d'aya yazo a d'aura masa aurd da ita , tuni Alhaji Nasir ya jik'asu da kud'i dan yaga suna buk'ata dayawa , yana tafiya suka fara murna suna suma kwanan nan zasu faso gari , Nan Safara'u tafara hura hanci tana wani jan Aji ita a dole zata auri me kud'i.......... [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Zee* *MD* ✍🏻 25. Kawu Idi yadubi Hajiya Hajjo yace " dan Allah ina Hanan take ? tab'e baki tayi sannan tace " ai sunfi sati biyu basa gidan nan ita da yarinyar wajen Alhaji , kuma yadda yace mana wai sun gudu ne saboda sunyi masa sata shima neman su yake , sosai Kawu Idi yashiga mamakin maganar Hajiya Hajjo , sallama yayi mata ya fice cikin ransa yana fad'in dole ya shirya yaje Lagos ko Hanan taje can ......... Alhaji Nasir nashiga cikin d'akin sa tuni yayi zindir yafara kiran dodon tsafinsa , suna fara ganawa kenan saiga Safara'u tashigo cikin d'akin dai dai lokacin da Alhaji yake shan jini yana wanka dashi a cikin wata k'warya , yanayi yana zagaye yana fad'in " Safara'u ! Safara'u !! aikauwa tuni Safara'u k'irjinta ya buga tafara ja da baya tana ganin wani k'warangwal d'in kai yana zubar da kud'i kuma fuskar kamar ta matar Alhaji Nasir d'in data mutu , juyowa Alhaji Nasir yayi sukayi ido biyu da Safara'u tuni yayo kanta da sharb'ebiyar wuk'arsa , ai tuni Safara'u tajuya tafice da gudu tana neman matsera , Hajiya Hajjo taganta da gudu tana ihu tana fad'in " Alhaji zai kasheni wallahi shan jini yakeyi , Hajiya Hajjo batagama jin Maganar Safara'u ba taga Alhaji Nasir zindir shima yataho da gudunsa , tuni itama ta juya da gudu tana neman matsera , Alhaji Nasir yana ganin haka yatuna a yadda yafito tuni ya juya yana cizon yatsa na rashin kama Safara'u dan wallahi yau dasai dai wata ba itaba , amman yanzu ma tunda har tagansa wallahi saita mutu dan bazata tona masa asiri ba ...... Safara'u tuni tafice daga cikin gidan sai gudu take tamkar zata ci da baka , duk nisan dake tsakanin gidansu da gidan Alhaji bata ganiba tuni takawo gida , da gudu tashigo tana ihu ba gyale ba d'ankwali bare takalmi kuma , tana shigowa ahaka suma suka mik'e suna neman matsera , dan cewa take gashinan da wuk'a zai yankani yasha jinina..... Hanan ansamu Nassarar yi mata aiki , Alhaji Murtala shine ya biya kud'in da akayi mata aikin , lokacin Ammi ta yanke shawarar zuwa tasamu Abban su Zunnur tagaya masa duk abinda ke faruwa , waya ta kira ta tambayi Umman Zunnur tace mata yana gari , dan haka tashirya daga asibitin ta wuce tabar Nasma a wajen Hanan d'in , dama da ita da Nasma suke kwana a gunta Hajiya Asma'u kuma kullum sai tazo takawo musu Abinci... Lokacin dataje gidan tasamu Yayan nata da maganar Hanan d'in , sosai yayi mata fad'an rashin gayamasa dabatayi ba , sannan yayi Alk'awarin zuwa Kano wajen Kawu Idi yaji dalilin dayasa yayi wa Hanan d'in hakan , kuma sosai ya jinjinawa Zunnur da irin k'ok'arin dayayi wajen kawo su Hanan d'in Nan , Afrah najin ance Hanan tazo tana asibiti tuni tafara shirin bin Ammi dan tace saitaje taga Hanan d'inta.... Zunnur tunda yaji Ance Hanan ba lafiya dama gashi sunsami hutun sati Uku , tuni suka had'o kayansu suka nufo Lagos.... Afrah tana ganin Hanan tasaka kuka ganin yadda Hanan d'in takoma, dak'yar Ammi ta lallab'ata Nasma ma tasa baki sannan tayi shuru , Hanan kuwa haryanzu bawani gane mutane take ba saboda wuyar datasha sosai , dan likitan dayayi mata aiki cewa yayi data k'ara wasu watannin da tsutsotsi ne zasu fara fitowa ta gabanta , gashi dole zata koma tana neman maza ko mata kuma ta baya , lokacin daya fad'i wannan maganar sosai su Hajiya Asma'u da Ammi sukayi kuka , Abban su Zunnur shima sunzu shida Umman Zunnur sosai suka tausayawa Hanan , sosai yayiwa Alhaji Murtala godiya ganin yadda yanuna damuwa akan Hanan d'in tamkar shine ya haifeta , kullum daga gidan Su Afrah sai ankai musu Abinci nan ma...... Su Zunnur suna da wowa ko hutawa baiyiba yashirya ya nufi Asibiti , yana zuwa lokacin Hanan tana bacci su Ammi da Afrah da Nasma suna zaune a reception sai hira suke , shima zama yayi yana d'an tayasu kafin Hanan d'in tatashi ..... Safara'u tuni tazama k'aramar Mahaukaciya , dan kullum cikin zabura take tana ihun fad'in gashin yazo da wuk'a zai yankata , lokacin da Alhaji Nasir yazo guduwa tayi d'aki tasa sakata tafara ihu , Babanta yace ya k'yaleta kawai intaji sauk'i ta dawo , haka Alhaji Nasir yatafi yana shirya ta yadda zai d'auketa daga gidan... *Bayan kwana biyu* Hanan sosai jikinta yayi sauk'i , har hira suke ita dasu Zunnur daya tare a Asibitin , Haidar ma yana zuwa sosai saboda yaga Nasma dan yana ganinta yaji tashiga ransa , itama sosai take sakin jiki suyi hira da shi , ga Afrah data zama tamkar 'Yar uwarta saboda shak'uwa , Koda jikin Hanan yayi sauk'i sosai aka sallamesu suka koma gida.... Kawu Idi ne ya dira a gidan su Zunnur , Yayi sa'a kuwa yasamu Alhaji Bashir wato Baban su Zunnur d'in , nuna masa yayi baisan Hanan tazoba saboda yaji da wacce yazo , aikuwa Kawu ya karkace yanafad'in wai Hanan sunyiwa Alhaji Nasir sata ita da 'Yarsa sungudu , shine yazo nemanta ko Allah yasa sunzo nan , aikuwa tuni ran Alhaji Bashir yakuma b'aci tuni yafara fad'a " Hanan sunzo nan tunda acan ana neman kasheta bata da gata , Nan yashiga yiwa Kawu sababi tare da sheda masa komai da Alhaji Nasir yakeyiwa Hanan d'in , tuni jikin Kawu Idi yayi sanyi yafara hawaye sosai , Alhaji Bashir yaci gaba da cewa " karka ga wannan abun dakayi ko Allah zai barka dole sai Allah yasaka mata , kana matsayin Mahaifin a gunta saboda san abin duniya ka d'auketa kabawa me shan jini ita , sosai Nadama ta shiga Kawu yadunga kuka yana neman afuwa tare da cewa araka shi gidan Ammi yaga Hanan d'in ya rok'eta gafara , tare suka shirya shida Alhaji Bashir suka nufi gidan Ammi..... Alhaji Nasir yanzu hankalinsa a mugun tashe yake saboda Dodon tsafinsu yana buk'atar jini , gashi Hajiya Hajjo ta kwashe yaran gidan duka sungudu har Alawiya ba wanda aka bari , neman duniya yayi musu amman bai gansuba , dan tun randa Hajiya Hajjo tagansa da wuk'a tafara yadda da rad'e rad'in mutane , shiyasa ta sulale ita da yaran gidan suka gudu tare da Alawaiya ..... Lokacin da Kawu yaje gidan Ammi suna ganinsa Hanan ta b'uya a bayan Hajiya Asma'u , gaisawa sukayi da Hajiya Asma'u itakuwa Ammi ko kallonsa batayi ba , sosai Kawu yanuna nadamar sa akan Abinda yayiwa Hanan d'in , Anan yakejin Nasma 'Yar gidan Alhaji Nasir itama ta had'u da Mahaifiyar ta , sosai yayi dad'i tare da neman afuwar Hanan d'in , tayafe masa inda suka tsaida ranar tafiya Jos dan zuwa karb'owa Hanan takardar sakinta... Alhaji Nasir cikin dare ya fito da niyyar zuwa gidan su Safara'u , dan Dodonsa yabashi kwana biyu akan indai bai zubar masa da jini ba to duk zai nemi dukiyar sa yarasa ta , yana zuwa gidan su Safara'u yasamu gidan nasu a bud'e ba'a rufe ba , lokacin zafi akeyi duk suna tsakar gida a kwance , yana zuwa yafara lalub'en Safara'u ita kuwa lokacin tana cikin d'aki tana surutan ta wanda tasaba , aikuwa kamar an mintsineta tafito tsakar gida aikuwa sukayi ido biyu da Alhaji Nasir take ta kurma ihu tana fad'in " gashinan yazo yankani wayyo , dukansu suka mik'e aikuwa sukaga Alhaji Nasir tuni suka bishi da gudu aikuwa yayi maza ya fad'a motar sa yagudu........ [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Zee* *MD* ✍🏻 24. Su Hanan sunyi k'alau dasu tamkar basu ba , tuni sun sake a cikin gidan tamkar daman sundad'e da zuwa , Ammi kullum cikin siya musu kayan k'yale k'yale take , itama Hajiya Asma'u haka ga 'Yayanta suna girma ma su Hanan , yanzu abinda yake damun Hanan shine yawan ciwon ciki dayasako ta a gaba , gashi tak'i tafad'awa kowa tana ciwon ciki , Nasma ma dasu kwana tare itama batasani ba , Yauma kamar kullum suna cikin d'aki a kwance wajen k'arfe goma da rabi na dare , ciwon cikin ne yafara mintsinin Hanan tafara cije leb'e tamkar me Nak'uda , Nasma ta dubeta tace " ke kuma meye yake damunki haka ? tund'azu naga sai cije leb'e kike tamkar wacce take labour room , Hanan data fara fita hayyacinta tace wa Nasma " kiramin Ammi Dan Allah wayyo cikina wallahi inajin mutuwa zanyi , da sauri Nasma tatashi zaune tana dubanta ganin da gaske Hanan tana wani irin Abu yasa Nasma fita da gudu tana kiran Ammi .... Lokacin Ammi tana zaune kan sallaya tana karatun Alkur'ani me girma , jitayi ana kiranta kuma daga jin kiran ba na lafiya bane , da sauri ta rufe Alkur'anin tana shirin mik'ewa , dai dai lokacin Nasma ta shigo tana fad'in " Ammi kizo Hanan bata da lafiya da sauri suka juya zuwa d'akin Hanan d'in , lokacin Hajiya Asma'u itama tafito daga d'akin Alhaji Murtala , dukansu suka shiga d'akin da Hanan d'in take , suna zuwa suka sameta wata kumfa na fitowa daga bakinta tamkar wacce tasha guba , da gudu sudukansu sukayi kanta suna kiran sunanta , Nasma tuni tafara kuka tana fad'in " dan Allah Hanan karki mutu kibarni , duk duniya dake nasaba bazan iya bud'e ido inga bakya tare dani ba , tuni Hajiya Asma'u tafita kiran Alhaji Murtala dan suje asibiti , Ammi kuwa tana rungume da Hanan sai addu'a take tofah mata hawaye na zubowa ta cikin idanunta , Hajiya Asma'u ce tadawo ta sunkuya ta d'auki Hanan da dukka k'arfinta tace " kuzo muje Asibiti ga Alhaji can ya fito da motar...... Acan b'angaren Alhaji Nasir kuwa " Safara'u tafara zuba mulki a cikin gida , dan Hajiya Hajjo duk bala'inta bata saka Safara'u aiki , dan kusan kullum sai sunyi fad'a da ita , yauma tamkar kullum Safara'u ce ta fito sai taunar cingum take tamkar wata karuwa , Hajiya Hajjo tana gayara kayan miya lokacin Safara'u ta dubeta tace " wai daman haryanzu baki d'oramana Abinci ba kinbar mutane da yunwa ? Hajiya Hajjo tadubeta shek'e k'e tace " ban d'oraba kozaki yimin hukunci ne daboda hakan ? Safara'u tayi wani shu'umin murmushi sannan tace " bazan yi miki hukunci ba , sai dai zakiga Abinda zai faru dan wallahi sai kin raina kanki , ta juya ta nufi d'akin ta tana turo mazaune ...... Alhaji Nasir shida Abokinsa Alhaji Hamza suna gurin dodon su suna magana dashi , Anan ne dodon nasu yake ce musu yanason shan jinin Mata d'aya da yara guda uku , Bayan sungama magana dashi Alhaji Nasir ya dubi Alhaji Hamza yace " yanzu kai wanne zaka bayar daga ciki ? tunda jinin mutum hud'u yakeso dole kai biyu nima biyu haka zamu bashi , Alhaji Hamza yayi ajiyar zuciya sannan yace " a gaskiya yanzu mata ta taragemin kuma yanzu haka cikine da ita , inaso ta haihu saboda kasan yanzu banida d'a ko d'aya duk nabada su , kai kuma kaga gidan ka akwai mata har guda uku kuma ga yara kana dasu dayawa , Alhaji Nasir yayi shuru yana nazari suwa yakamata yabawa dodo ? tabbas da Hanan na nan wallahi saiya bada ita ita da Nasma , ammam yanzu dole ya zauna yayi shawara yaga wad'an da yadace yabayar , da yayi niyyar bada Safara'u amman yaji tana da dad'in harka ta baya sosai , duk matan da yake aura ba wacce take bashi had'in kai wajen kusan tar ta ta baya kamar ita , yankewa yayi zai bada Alawaiyya da kuma wasu daga cikin yaran nasa , duk dayaga mutane sunfara saka ayar tamabaya akansa ganin yadda akeyin mutuwa agidansa kuma duk iri d'aya........ Tunda aka shigar da Hanan asibiti likitoci suka rufu akanta , Nasma inbanda kuka babu abinda takeyi , Ammi ta janyota cikin jikinta tana rarrshin ta , dan tasan dole tayi kuka dan ko ita data haifi Hanan yanzu bazata nuna mata shak'uwa dasukayi ba ..... Likitane yafito daga cikin d'akin Da Hanan take , cewa Alhaji Murtala yayi yabiyoshi Office yanason magana dashi , tuni Jikinsu Ammi yafara rawa cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ba mutuwa tayi ba , Alhaji Murtala tuni ya mik'e yabi bayansa suka shige cikin office d'in , samun guri Dr. Yayi ya zauna sannan ya nunawa Alhaji Murtala guri yazauna shima , glass d'in idonsa yacire sanna yadubi Alhaji Murtala yace " A gaskiya Alhaji wannan yarinyar taka akwai Babbar matsala atare da ita , wato binciken da mukayi akanta mun gano wata tsutsa da aka saka mata a cikin cikinta wacce ake sakawa masu yin Mad'igo , ina nufin maza masu neman maza 'Yan uwansu ta baya , salati Alhaji Murtala yayi sannan yadubi likitan yace " yanzu meye mafita Dr. ? wallahi Mijinta ne yayi mata wannan Abun haka , Dr. Ya dubi Alhaji Murtala yace " kana nufin kace tana da aure kuma mijinta ta baya yake kusan tar ta ? Alhaji Murtala yace " tana da aure amman a yanzu bata dashi kuma saboda hakan aka rabasu da Mijin , numfashi likitan yaja sannan yace " tabbas wannan mijin nata ya cuceta sosai , dan yanzu haka tana gab da fara zubar da wani irin ruwa me wari ta gabanta mutuk'ar ba'ayi gaggawar yi mata aiki ba , Alhaji Murtala yace " Dr. Inaso ayi mata aikin ko nawa zamu biya plss tunkafin tafara zubar dashi d'in , Dr. Yadubi Alhaji yace " bamayin irin wannan aikin a wannan asibitin , sai dai akwai wani Abokina sunayin aikin a Asibitinsu zan had'a ku dashi sai kuyi magana , godiya Alhaji Murtala ya shiga yiwa likita , nan Dr yabawa Alhaji number Dr Tahir sannan shima yakirashi a waya sukayi magana a gaban Alhajin , likita yace " sai kuyi gaggawar kaita dan ciwon yadad'e yana cin jikinta baku sani ba sai yanzu ya nuna , nan Alhaji yayi masa godiya sannan yafito daga office d'in , su Ammi dukansu suka mik'e suna tamabayar sa lafiya kuwa ? bai ce musu komai ba ya nufi d'akin da Hanan take a kwance lokacin bacci take sabida alluran da suka yi mata ... Duk yadda sukayi da Dr. Sai da yagaya musu , salati suka saka tare da yin Allah wadai da halin Alhaji Nasir , Nan suka d'auketa aka nufi wancan asibitin daza'ayi mata aikin da ita..... Kawu Idi yana sane da auren da Safara'u sukayi ita da Alhaji Nasir , yau takanas ya shirya dan zuwa gidan yaga Hanan dan yaji shuru Alhajin bai ce tadawo ba , yana zuwa gidan dayake me gadi ya sheda sa tuni yabarsa ya shiga ciki , koda shigar sa yasamu wani yaro daga cikin yaran Alhajin yace yaje yakira masa Hanan acikin gidan , dayake yaron bashi da wayo dan haka baisan Hanan d'in ba tuni yashige cikin gidan yana kiran sunan Hanan , dai dai lokacin Safara'u ta ci uwar kwalliya wai zataje yawo ita ala dole ga matan masu kud'i , tarar yaron tayi tana fad'in " waye ya aiko ka kairan shegiyar yarinyar data shiga duniya ? yaron yace " wani ne a waje yana jiranta , Safara'u ana rik'e da mayafi a hannu da jaka akayi hanayar fita , Hajiya Hajjo tana hango fitar ta tabiyo bayanta sadaf sadaf tana lek'en ta , koda Safara'u ta k'araso wajen da Kawu yake wani tsaki taja tare da murgud'a baki , cikin kallom rashin mutunci ta dubesa tace " wai dama kaine kake kiran Hanan d'in ? to mu anan gidan bawata me wannan sunan , dan haka ka iya jan jiki ka ficemin daga cikin gidan mijina , inkuma ba haka ba wallahi yanzu zanhad'a maka mutane ince kazo guna kwarton ci , Kawu ya dubeta sama da k'asa wani takaici yakamasa yace " ni bana magana da wacce bata san mutuncin kanta ba bare na aure , tunkafin ranki yayi mugun b'aci inaso kibar wajen nan yanzu yanzu , wata shewa Safara'u tayi tare da tafa hannuwa tace " nafi k'arfinka ta ko'inah wallahi Idi , kadubeni sama da k'asa ni ba matar Matsiyaci bace wanda bashi da ko anini , tuni zuciya ta d'ebi Kawu Idi ya d'auke Safara'u da wani mahaukacin mari , dai dai nan Alhaji ya kunno hancin motar sa cikin gidan , akan idonsa Safara'u ta cakumi wuyan Kawu Idi tana tura kanta cikin jikinsa tamakar wata k'aramar yarinya masu kokawa , aikuwa Alhaji Nasir tuni yaji wani kishi ya turnik'eshi wato dama munafika tana son tsohon mijinta take raina masa hankali , tuni ya bud'e motar a fusace yana nufo wajen dasuke , yana zuwa ya wanke Safara'u da wani mahaukacin mari yana nunata da d'an yatsa " wato ni zaki ciwa Amana kenan ? duk irin kud'in danake turamiki sai kin dunga nemo tsohon mijinki kina munafinta ta , Kawu Idi yace " wanda da Allah ya kawoka Alhaji , dan tun d'azu take jana wai saina shiga ciki munkwanta da ita , Safara'u jikinta yana rawa tafara fad'in " wallahi k'arya yakemin bancd masa haka ba , Muryar Hajiya Hajjo sukaji tana fad'in " bawani k'aryar dayake miki inajinki ina kuma kallonki , tuni ran Alhaji Nasir yakuma b'aci yafasa bawa dodonsu Alawiya wallahi Safara'u zaibada ya auro wasu matan, tuni ya shige ciki da sauri tare da tunkarar d'akin sirrinsa , Safara'u ganin haka ta rud'e satake sakinta zaiyi tuni tabi bayansa batare da yasani ba.......... [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Zee* *MD*✍🏻 26. Tun daga lokacin 'Yan gidan su Safara'u suka fahimci Alhaji Nasir matsafine , tunda ga ranar suka fara taka tsantsan suma dan sun tsorata sosai , Safara'u kuwa hauka take tuburan tana zabure zabure , tuni suka fara fafutukar nema mata magani....... Alhaji Basir tuni suka gama magana akan zuwa Jos ansowa Hanan takardarta ,dan baza tai ta zama da igiyar aure akanta ba , Kawu yace " kayi zamanka kawai basai kajeba tunda nine nahad'a to kuwa nizan rabashi , Hakan kuwa akayi Kawu ya shirya yayi musu sallama ya koma... Hanan tuni jikinta yayi sauk'i sosai , yanzu ma Alhaji Bashir yayi magana da Zunnur akan asamar mata makaranta tafara zuwa , Zunnur tuni ya sanar da Umman sa yanason Hanan , sosai taji dad'in Abin amman tace yabari komai ya lafa sai ayi magana , Abban su Zunnur dagewa yayi akan Hanan ta dawo gidansa amman Alhaji Murtala yak'i , dole haka yabar ta taci gaba da zama a gidan , Nasma kuwa tuni dangin Hajiya Asma'u suka d'auketa Kano zataga 'Yan uwa , Haidar sosai yaji dad'in zuwan Nasma kano , dan tuni suka koma sch sunfara shirye shiryen kammala Degree d'insu , Kawu Idi so biyu yana zuwa gidan Alhaji Nasir amman a kulle , ko megadi baiganiba cikin ransa yace " kowa ya gudu kenan , Anan yasamu labari ba kowa a gidan shima megidan kwana biyu ba'a ganin gilmawar sa , dawowa gida yayi anan ya had'u da k'anin Safara 'u yabashi labarin Abinda yake faruwa da Safara'u , ko kad'an Kawu Idi bai tausaya mata ba saima Allah yak'ara dayace , ya kad'a kansa yayi gida dan shiyanzu tsoron duniyar ma yakejin , yanzu yagama magana da wata bazawara zasuyi aure sati me zuwa ..... Hanan tafara zuwa sch ga wayar ta me kyau da Hajiya Asma'u tasiya musu ita da Nasma , Suna waya da Zunnur sosai kusan kullum suna manne a waya , tuni Alhaji Bashir sunje kotu an ansawa Hanan takardar sakinta wajen Alk'ali , dan kwata kwata annemi Alhaji Nasir anrasa ..... Nasma tadawo Lagos wajen Hajiya Asma'u da zama , karatun ta taci gaba dayi gefe guda kuma suna tare da Haidar suna zabga soyayyar su....... *Kuyi hakuri wlh yau fita nayi*🙏🏻🙏🏻 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Zee* *MD* ✍🏻 28. *THE* *END* *THE* *END* *THE* *END* Ranar suna yarinya taci sunan Ammi wato Hadiza suke kiranta itama da Ammi , sosai Ammi taji dad'in karar da akayi mata , Su Hanan ma sosai suka tayata farin ciki , Ana cikin shagalin suna saiga Safara'u tazo , Da Hanan tafarayin karo a tsakar gida ita da su Nasma , sunkuyar da kai tayi k'asa kamar munafuka tana tafiya a hankali , Hanan kuwa tayi murmushi sannan tace " Aunty Safara'u sannu da zuwa ashe kinanan ? Safara'u ta yashe baki tana fad'in "la Hanan kune agari haka sannunku da zuwa , Ina Ammin ki ? Hanan tace tana cikin wannan d'akin , da sauri Safara'u tashige cikin d'akin ta addu'ar Allah yasa Ammi tasa baki Kawu Idi ya maidata...... Afrah tadubi Hanan tace " Sister wannan ai kamar matar Kawu ta da ? Hanan tayi murmushi sannan tace "ea itace kinga yadda takoma ko ? ta dubi Nasma tace itama fa saida ta auri Daddynki kinganta nan duk ta lalace tamkar me Hiv , Nasma tace " ai tunda naji kince aunty Safara'u naganeta , Allah ya kyauta daman ai wanda ya hau motar kwad'ayi zai sauka a tashar wulak'anci ....... Safara'u koda tashiga cikin d'akin da Ammi take kasa ganeta Ammi tayi , da k'yar tagane ta suka gaisa Ammi tashiga mamkin yadda Safara'un takoma , duk da Kawu yabasu labarin Abinda tayi kaf amman saida ta tausaya mata , nan Safara'u tafashe da kuka tana rok'on Ammi gafara duk abinda tayi mata , Ammi tausayin tane yakamata tace " Allah yayafe mana baki d'aya , Sa'ade ce tashigo cikin d'akin Safara'u ta kalleta , ko ba'afad'a mata ba tasan wannan itace matar da Kawu Idi ya aura , dan yaranta insunje suna gayamata yadda take yi musu komai tamkar uwar data haifesu , Safara'u tagaida Sa'ade tare dayi mata barka , Sa'ade bata gane taba amman ta amsa cike da fara'a , Ammi tacewa Sa'ade " Babar su Baffa ce fa naga baki ganeta ba , Sa'ade tace " au itace Safara'u wallahi bansanta ba shiyasa , sake gaisawa sukayi Safara'u tayi mata godiyar hidima da yara , Sa'ade tace " bakomai yiwa kaine ai ..... Kawu Idi yashigo gidan ai anshi Abincin su shida Abokansa , Safara'u yagani take ya canza fuska tamkar bashine me dariya ba , tuni ta zube kan gwuiwoyin ta tana kuka tana neman gafarar sa , kowa dayake gidan saida yatausaya mata ganin yadda takoma , Sai da Ammi tasa baki sannan yace ya yafe mata , batun komowa gidan sa kuma yace tayi hak'uri bazai iyaba Allah yabata wani mijin ........ Washe gari su Ammi suka shirya komawa gida , dan Zunnur yadamesu da sutafi yagaji kuma ogansa kwana biyu yabashi , haka sukayi wa su Kawu sallama suka d'au hanyar lagos...... Bikin su Hanan sai tahowa yakeyi , dan tuni Hajiya Asma'u tasasu gaba su ukun suka nufi garin kano za'ayi musu gyaran sati biyu , tunda da suka sauka A gidan su Hajiya Asma'u kwanan su d'aya suka nufi gidan *MD* me gyaran Amare da da k'amshi , tuni tafara yi musu dilka da gyara na musamman saiga su sunfara canzawa , Hanan tamkar balarabiya haka takoma saboda tsabar kyau , Zunnur kullum suna mak'ale a waya tamakar su cinye kansu , takuramata yayi da tayi masa pic d'inta ta turo masa yayi missing d'inta sosai , Hanan tace " My Dear kayi hak'uri bazaka k'ara ganina ba sai acikin gidanka , Shagwab'e mata Zunnur yayi tamkar k'aramin yaro yana kukan wasa , itama kwai kwayonsa tashigayi tana masa dariya , sunyi nisa a hakan Nasma tashigo ta d'aga mata duka tace " to Laila da Majnun ki fito Mama tana kira , kinwani shige cikin d'aki kamar zaku cinye juna , Hanan ta gallawa Nasma hararar wasa tace " wai meyasa kika rainamu mufa yayyenki ne dan haka ki bimu a hankali , Afrah ce tashigo tana fad'in "Sister Mama na kiranki fa zakisha tsuminki muma duk munsha namu , Hanan ta dafe kai tana yiwa Afrah nuni datayi shuru waya take , Zunnur dayake jinsu duk abinda suke cewa a hankali yace " Dear kije a tsumamin ke kinsan zansha aiki ranar , da sauri Hanan ta katse wayar tana dariya...... Sati biyun da sukayi sosai suka sha gyara , inkagansu saika zata wankan inji akayi musu saboda kyau , ga wani sihirtaccen K'amshi dake tasowa a jikinsu gaba d'aya tamkar an musu b'arin turare , tuni Haidar ya iso kano dan yace yagaji da rashin Habibty d'insa , sosai Yabawa su Hajiya Asma'u dariya ganin yadda ya susuce daga ganin Nasma , haka suka tattaro suka baro kano a jirgi saboda Haidar yace baza akalle masa mata ba...... Suna dawowa gida suka shiga rabon katin bikinsu , Zunnur k'ememe yahana Hanan yawon rabon kati sai Nasma da Afrah sune suke rabawa , Ranar Kamu a gidan Alhaji Bashir akayi wato gidan su Zunnur , sosai Amare sukayi kyau cikin shigar lifaya sai k'amshi suke , an yi musu kamu sannan *Aunty Hadiza D Auta* tayi musu lacca me ratsa zuciya akan zaman gidan aure , sannan taja hankulansu da yin biyayya da mazajensu tarufe taro da addu'a , Washe gari Hajiya Asma'u ta shirya musu Dinner lafiyayya a wani Babban holl , komai ita tad'auki nauyinsa nan ma amare sosai sukayi shigar Alfarma da angwaye , Anci ansha anzubar da kud'i sosai Mawak'iya Nabeela sosai ta wak"e Amare sannan aka tashi .... Sai kuma Angwaye suma suka shirya Reception suda abokansu da Amaren da k'awayensu , Ankashe kud'i sosai tamkar ba neman su akeyiba..... Washe gari aka d'aura aurensu su a k'ofar gidan Alhaji Murtala , Kawu Idi shine waliyin Hanan da Nasma aka bashi sadakinsu dukansu , Nan aka d'aura aure aka sha yinin biki..... Magriba nayi tuni Zunnur ya turo da motocin da za'a d'aukar masa Amaryar sa , sai tsokanar Hanan akeyi akan Angon ta yafiye zumud'i itakuwa jikinta yayi sanyi takasa yimusu magana , Nan aka kaita d'akin Ammi dan tayi mata fad'a za'a wuce da ita , Ammi kasa magana tayi kawai tace Allah yabasu zaman lafiya.... Hanan kuka tashigayi tamkar k'aramar Yarinya har aka fito da ita , lokacin motocin d'aukar Nasma suma suka zo , haka aka Sakasu cikin motocin tafiya gidansu aka kaisu , Unguwar su d'aya da Hanan da Nasma , Afrah ce Unguwar ta daban tayi musu nisa amman ba sosai ba , gidan Hanan aka fara zuwa ka kaita sannan suka wuce gidan Nasma , sosai gidajen su ya had'u matuk'a ga kayan Furniture da aka jera musu sosai falukan su suka had'u , dan komai iri d'aya akayi musu babu bambanci , sai muyi musu fatan zaman lafiya da junan su.... Tuni Abokan Zunnur sun rakoshi suntafi dan cewa yayi bayason dogon zance , dariya sukeyi sosai suna tsokanar sa har suka fice , gidan Haidar ma suna zuwa sukaga tuni ya kulle gidan sai waya sukayi masa suna tsokanar sa.... Zunnur yana shigowa yasamu Hanan tana kuka , da k'yar ya lallab'ata tayi shuru yace tatashi ta d'auro Arwala , sunyi sallar godiya ga Allah sannan yadafa kanta yayi mata addu'ar neman tsari da dukkan wani abin k'i , bayan ya kammala ya mik'e ya d'auko musu ledojin daya shigo musu dashi , kajine a ciki da lemuka tare da sauran tarkacen kayan k'walam da ma k'ulashe , janyota yayi jikinsa yana lallab'ata har saida taci ta k'oshi , shima ci yayi sannn ya d'auki sauran yaje yasa a frizer.... Wanka ya shiga bayan ya fito itama tashiga tayi , tana fitowa taganshi zaune a gefen gado dagashi sai gajeran wando , kauda kanta tayi sannan taje gaba mirror tashafa mai sannan ta shafa had'in kulacca da humra , mik'o mata wata riga yayi yace tasaka ta a kunyace ta ansa tasaka sannan ya janyota suka kwanta , can Zunnur yafara rikitata da wani irin salo wanda bata tab'a ji ba , sai da yabari ta fita hayyacinta sannan yafara k'ok'arin shigarta , wata k'ara tasaki saboda zafin dataji ya ratsata dan tunda take ko Alhaji Nasir baitab'a shiga wajen ba shiyasa bata saniba , shikuwa Zunnur tuni ya fita hayyacinsa saboda ya d'auki hanyar jindad'i sai sambatu yake haryasamu yashige ciki , tuni jikinta yafara gayamata sosai yake sarrafata tamkar wani inji tuntana kuka hartayi shuru saboda azaba , saida yagaji dan kansa sannan ya k'yaleta , d'aukar ta yayi cak yanufi toilet da ita yayi mata wanka yagasata sosai sannan yabata magani shima yayi wankan sannan suka kwanta , haka suma su Nasma da Afrah ta kasance dasu anasu gidajen , sati d'aya sukayi suna shan Amarcinsu batare da kowacce tayi girkiba sai dai akawo musu Abinci daga gidan Ammi , Zunnur kullum yana manne da Hanan yahanata sakat , wani zubin sai ta had'a masa da kuka sannan yake k'yaleta...... *Bayan shakara biyu* Hanan ta haifi yarinyar ta wacce taci sunan Hajiya Asma'u suke cemata Hibba , Nasma kuma sunan Umman su Zunnur wato Aminatu suke cemata Meenal , sai Afrah dake goyon d'anta me suna Areef , dukansu sunzama manyan mata ga Business dasukeyi na kayan gyaran jiki da turaruka , ga shi suna order kaya daga dubai sosai sukayi suna , Zunnur yazama wani Hamshak'in me kud'i tuni yagina musu katafaren gida suka tare , lokacin Nasma tasamu labarin yan uwanta taje ta kwasosu tasiya musu gida tare da maidasu makaranta me tsada , Hanan itama ta taka rawar gani sosai wajen taimakawa k'annen Nasma , nan suka samu Labarin mutuwar Hajiya Hajjo , Safara'u kuwa tuni tasamu wani direba ta aura kuma suna zaune lafiya abinsu , sosai suke zumunci da Sa'ade kuma tana taimaka mata , dan Kawu idi sosai shima yake samun kud'i yanzu....... Hanan na saune a falor Hibba sai rigima takeyi mata , ta dubeta tace " mekikeso ne kika sakani agaba da rigima ? Hibba cikin gwarancin su nayara tace " akaita gidan su Meenal da Areef , Alhaji Zunnur ne yashigo cikin falor d'auke da murmushi a bakinsa , Hanan tana ganinsa tace " Abban Hibba tasamu kenan tunda naga kana murmushi , kashe mata ido yayi sannan yace " ganinai gidan namu yayi mana girma dayawa mu uku kad'ai , dan haka zan k'aro miki k'anwa wacce zata tayaki rainona nida Hibba , Hanan tayi murmushi tace " ai kishiya 'Yar uwace Allah yabamu tagari , Zunnur ya rungumeta yace " ashe bakya kishina ko Dear ? kissing d'inta yashiga yi har saida ta turesa tana nuna masa Hibba , murmushi yayi ya durk'usa ya d'auki Hibba yana cewa " Babyna shine baki min oyoyo ba ko , turo baki tayi sannan cikin gwarancin ta tace " Daddy inaso ka kaini gidan su Meenal da Areef tunda Mumy tak'i , murmushi yayi yana lakace mata hanci yace " zankai ki gobe in Allah yakaimu kinji Babyna , bayan yakaita d'akinta tare da d'auko mata kayan wasa da chocolate yafita , yana zuwa ya d'auki Hanan itama yana fad'in " muje insamowa Hibba k'anwa ko k'ani dan nagaji da kallonki haka , tana zille zille har suka shige cikin d'akinsu suka rufo k'ofah ....... Anan nima na ajiye alk'alamina ✍🏻dan bana bisu naganowa idona ba😜 *ALHAMDULILLAH* *Anan nakawo k'arshen Book d'in Ni Bora ce* *Abinda nayi ba daidai ba Allah kayafemun , Abinda nayi daidai kuma Allah yasa ya Amfanemu baki d'aya* *Nagode sosai Masoyana yadda kuka dunga bibiyata har Allah yasa nakawo k'arshen wannan littafin nawa , Allah yabar k'auna 🙏🏻🙏🏻ina mutuk'ar godiya kuma nima inasonku kamar yadda kuke sona* 🥰 _ILuv U All My Fan's_ *Godiya ta Musamman gareku* *'Yan K'ungiyar Hamdala Writer's Association*💪🏻🤝🏻 *Allah yak'ara d'aukakata*🙏🏻🙏🏻 *'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ 😍🌹🌹 [1/29, 16:19] +234 704 610 7812: *NI* *BORA* _Ce_ 👩🏿‍🦳👩🏿‍🦳 *Zee* *MD* ✍🏻 27. Kawu tuni yayi aurensa da wata Bazawara me suna Sa'ade , tana da kirki sosai ba kamar Safara'u ba , tahad'a 'Ya'yan Safara'u tana rik'onsu Amana tamkar itace ta haifesu..... Hajiya Hajjo gidan Marayu takai 'Yayan Alhaji Nasir , dan batada k'arfin rik'esu wad'an da tasan gidan iyayensu kuma tuni takaisu , Dan itama yanzu ciwon baya take fama dashi sosai , gashi ita ba yaraba bare tasamu masu jinyar ta , sai 'Yayan 'Yan uwa sune suke kula da ita.... Lokacin da Hanan tagama Iddar ta , tuni Su Zunnur sun kammala karatunsu harya samu aiki a wani Company a anan Lagos d'in , Tuni yabayyanawa Hanan sirrin zuciyarsa , dafarko bata amince masa ba ta nuna masa itafa ta tabayin aure taya yana saurayi zai aureta , sosai yayi fushi da ita yadaina kulata , nan tasamu Nasma sukayi magana Nasma tace " gaskiya Hanan kinyi kuskuren cemasa hakan , ni aganina Zunnur shine masoyin dayafi kowa dacewa kiyi rayuwa dashi , ai yasan kintab'a auren kuma karki manta irin fad'i tashin dayayi harkika samu kanki , inaso ki tura masa da message na amincewar ki tare da ban hak'uri , hakan kuwa akayi tuni Hanan ta karb'i Soyayyar Yayan ta Zunnur da hannu biyu suka fara shan luv kamar basuba ... *Bayan shekara d'aya* Abubuwa sunfaru da dama ciki harda Haihuwar Ammi , ta haifi d'anta santalele me kama da Mahaifinsa , murna a gurin su Hanan ba'a magana , Anyi shagalin suna sosai yaro yaci sunan Mahaifin Hanan wato Mahmood suke cemasa Aman. lokacin Aka saka ranar Auren Hanan da Zunnur itakuma Nasma da Haidar sai kuma Afrah da Usman Abokin Haidar ... Matar Kawu Idi koda yaushe suna waya dasu Hanan , lokacin da Ammi ta haifi Aman Har suna tazo suna zuminci sosai ,.... Bugo musu waya Kawu Idi yayi yace itama ta haihu , nan su Hanan suka fara tsalle zasuje Jos suna , da farko Ammi cewa tayi Hanan bazataje ba ita da Nasma , nan sukaita magiya dan Allah tabarsu suje insha Allah babu abinda zaifaru , Ana gobe zasu tafi Zunnur yazo shima, da farko shima tuburewa yayi akan Hanan d'in bazataje Jos ba , sai da Nasma tasaka baki suka lallab'ashi yace to ya yadda amman shine zai kaisu , haka kuwa akayi washe gari suka d'au Hanya da Ammi da Hanan da Afrah sai Zunnur ...... Sun isa lafiya Abinsu sunsamu tarba me kyau dan Sa'ade akwai mutunci , Bayan sun huta Nasma tacewa Afrah da Hanan suzo su rakata gidan wata k'awarta , Ammi nacan tana hira da 'Yan uwan Sa'ade suka fice zururu Abinsu , Zunnur shima tuni yashiga gari dan akwai wani Abokinsa da sukayi karatu tare shine zai kai masa ziyara...... Bayan su Hanan sunje gidan k'awar Nasma sunfito , Nasma tace " inaso dan Allah muje gidan Babana dan ina kewar 'Yan uwana sosai , Hanan tace " Amman kinsan kasada zamuyi zuwan mu gidan ku ko , Nasma tace " basai munshiga ciki ba kawai sonake ko megadi ne insa yaturo mana su ingansu plss , ganin Yadda Nasma ta marairai ce yasa Su Hanan suka Amince mata , haka suka nufi gidan su Nasma gidan Alhaji Nasir ..... Koda zuwansu suka samu k'ofar gidan cike da mutane , da sauri suka k'arasa suna tambayar wani yaro meyake faruwa ? Nan yace musu gidan ne yake wani irin wari , gashi 'Yan unguwa har sunfara amsi da gudawa saboda warin gidan , shine aka kirawo jami'an lafiya dan suduba sugani ko meye a ciki , Adai dai lokacin aka fito da Gawar Alhaji Nasir harya fara zama tsutsa , da sauri mutane suka fara gudu suna toshe hancinsu , Hanan ma da Afrah tuni suka ja da baya suna toshe hancinsu , Nasma kuwa tsayawa tayi tana kallon gawar Mahaifin nata ana k'ok'arin sakashi a cikin Ambulance , Hawaye idanunta yashiga yi ba k'ak'k'autawa tamkar anbud'e famfo , yanzu wannan gawar mahaifintace ya mutu a wulak'ance tabbas wanda yayi nagari kansa , can saigashi anfito da kawunan mutane dayawa sunafara zama k'warangwal acikin gidan , take mutane suka fara tsinewa Alhaji Nasir suna fad'in " inama bai mutu ba wallahi dasai sun k'oneshi da taya , Kuka sosai Nasma tashiga yi tamakar ranta zai fita , Hanan da Afrah tuni suka kamata suka bar wajen da ita..... Basu suka dawo gida ba sai magriba , suna shigowa sukaga Ammi da Zunnur a tsaye Ammi na goya Aman zasuje neman su , yanayin da suka gansu dakuma Nasma yasa suka san ba lafiya ba , Samun waje sukayi suka zauna sannan suka shiga gayawa su Ammi duk Abinda ya faru , Nan Ammi tashiga lallashin Nasma tare da cewa tayi masa addu'a tasanadin hakan saiya samu sassauci , Kawu Idi shima yana shigowa da zancen yayi karo , cikin ransa yayi godiya tare da addu'ar arrage mugun iri , amman saboda Nasma saida ya tausaya..... Safara'u da k'yar tasamu sauk'i , tunda taji sauk'i takeson zuwa wajen Kawu Idi ta nemi gafararsa, sai dai takasa zuwa saboda tanajin Nauyin irin abuwan datayi masa , haka dai ta yanke shawara yau zataje tabashi hak'uri tare da neman gafara ko Allah zaisa ya maidata.... *Insha Allah gobe zan kammala Littafin Ni bora ce* *Inaso kowa gobe yafito dan tayani murna tare da celebration*💃🏻💃🏻🤝🏻🤝🏻