*WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 1 Cikin tsananin bacin rai, da nuna ya isa da ita ya ɗaya hannu zai mareta, amma sai ya ga ta riƙe hannun tana kallonsa. "Ubana bai haifar maka jaka ba Faruk! Tun da na rasa Ya Ahmad Marwana ta fita daga cikin rayuwata. Na riga na zauce da tunanin ɗaukar fansa. In har ka yi kuskuren kai hannunka jikina, wallahi ka ji na rantse sai na aikata abin da ba za ka taɓa tunani ba. Bari na gaya maka Faruk, tuni ka mayar da ni mahaukaciyar ƙarfi da ya ji." Ta numfasa tana kallon shi sannan ta ɗora da cewa." Cusgunawar da kake mini ya sanya na haukace na kuma kurumce. Ban dawo gidanka da ninyar zama ba, saboda ka fita a raina. Zan iya komai don na rabu da kai. Bani da yadda zan yi ne Baba ya dawo da ni. In har kace zaka ci gaba da wulakanta ni. Zan aikata abin da zai sanya ka yi danasani a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada. Zan aikata abin da zai sanya maza masu dukan mata su yi nadama, domin abin da zan yi maka zai sanya ya zama darasi a gare su." Dariya ya kece da shi, jin abin da ta ce sai ya ƙwace hannunsa yana kallonta. "Na yarda kin haukace. Ko da yake tuntuni nake miki kallon mahaukaciya Nasreen tun ranar da kika fara bijire wa umurnina." "To shikenan lokaci ya yi da zan tabbatar maka da cikakkiyar haukata. Lokaci ya yi da za k yi dana sanin aurena, duk dana sanin da kake cewa ka yi, wannan karon zai fi muni, domin xan aikata abin da duniya za ta la'ance ni. Ta katse shi tana faɗin haka. "Kashe ni za ki yi? In kashe ni za ka yi then go ahead. Ke har kin isa ki gaya mini abin da zan tsorata da ke? Ke ɗin banza mara tarbiyya." Ya faɗa yana kallonta. "Rashin tarbiyar xan nuna maka. So nake ka gane ba ka auri mai tarbiyya ba." Ta ce mishi babu kunya ko tsoro. Zuciyarta tafasa take yi sam ta tsane shi ko inuwarsa ba ta son gani. Ƙoƙarin zare bell ɗin sa ya fara."Ok, bari na fara dukanki tun yanzu sai na ga abin da za ki yi." "Karka tsaya jira Allah ya ba ka sa'a." Ta faɗa fuskarta a dake. Duk da cewar ta a zuciyarta cike take da tsoro, amma dole ta zama mace kamar yadda Marwana take gaya mata, dole ta mike ta ƙwaci yancinta. In har ita ta yi saken da ya fara rainata, ta yi wa kanta alƙawarin ƙwato wannan 'yancin nata. Faruk kuwa ya shiga ciki tsananin tashin hankali. Mamakin kalaman da ta ke gaya masa ya yi. Duk da cewar ya yi mamaki, amma sai ya daure ba tare da bari ta gane hakan ba. Kunya sosai ya ji yadda ya gaya wa Rashida ba ta isa ta ɗaya idanu ta kalle shi ba, amma sai ga shi yau ita take gaya masa za ta iya ɗaukar fansa ta aikata komai. Bell ɗin ya ɗaga zai zuga mata, sai ta kai hannu za ta kama. Neman abin da za ta ƙwaci kanta da shi ta fara a falon. Rashida ta riƙe hannunsa ganin yadda ya ɗaga da ƙarfi zai zuga mata. Mamakinsa take yi, saboda sam Nasreen ba ta yi kama da mai irin halin da ya bayyana mata ba. Bacin kishin sun haɗa miji za ta iya cewa, irin mutanen nanne da ka ga kamalarsu da suffarsu za ka kyautata zaton yan aljanna ne. Ganin yadda ya rufe idanunsa kamar zai duki gardi, sai abin ya bata mamaki."Kenan watarana ni ma zai duke ni? Ta yi wa kanta tambayar haka, domin tana ji a yadda yake nuna maƙo da iya haɗawa mace magana, sam ba ta tunanin za ta jure halinsa. Ba ta da haƙuri Allah ya gani ba ta cikin matan da za su jure ƙankamo daga mazajensu. Jira take yi Malam ya kammala haɗin da zai yi mata, in har bai yi aiki ba. Alokacin za ta nuna masa ainihin kalarta. A lokacin za a yi yunwa halin kowa ya fito. Tana lura da shi da ya shigo kayan abinci ɗakinsa ya kai. Tun da suka yi auren bai taba yarda ta ga pin numbarsa ko inda yake ije ATM ɗinsa ba. A yadda ta fahimta da son kuɗinsa, ko shi bai yarda da kansa ba. In ya in ya ije ƙuɗi ya ringa dubawa kenan."Kenan ni ma watarana haka zai duke ni?" Ta yi wa kanta tambayar tana girgiza kanta tamkar kaɗangaren kutu. Domin hakan ba zai taba yiwu wa ba. Hannunsa ta ƙara kamawa tana kallon Nasreen da ko gezau."Please honey ka ƙyaleta, kasan in aka ƙara wa mace kishiya mahaukaciyar take zama." Ta ce tare da kama jikinsa. "In mahaukaciya ta zama ta san cewa nima mahaukacin kaina ne, saboda ko ubanta bana shakkarsa ballantana ita." "Ka aitaka duk abin da ka ga dama Faruk mahaifina shi ne abin rainawarka, amma kuma ya gama maka komai saboda ya haifa ya baka." "An gaya miki alfahari nake da aurenki? Sau nawa ina gaya miki na yi dana sanin aurenki? Kawai ba zan sake ki bane, saboda na san so kike yi na sake ki ki je can ki auri wannan ɗan iskan ne, ni kuma kin ji na rantse da na sake ki ki aure shi, gara na ga ranar mutuwata. Zan zauna dake ba zan sake ki ba, amma kuma rayuwarki sai kin gwammace mutuwa." "Allah ya ba ka sa a in har rayuwata a hannunka take. In da ace bawa ya isa da rayuwar mutum da tuni ka kashe ni a duniya, amma da yake Ubangiji yake tsarawa bayinsa, har yanzu ina nan ban mutu." "Nasreen, ina gargaɗinki wallahi kika ce rashin kunya da fitsara za ki yi mini, sam ba za ki ji daɗina ba zan munana rayuwarki. Kar ki biye wa sheɗaniyar ƙawarki, saboda dawowar cikin gidana ya isa ya nuna miki babu abin da za ta iya." Banzan kallo ta watsa mishi, ta shige cikin ɗakinta tare da buga ƙofar da ƙarfi. Mamaki ya hana shi cewa komai, har na wani lokaci. Mamakin yadda ta canza yake yi, ashe dama ba ta da kunya ta iya rashin kunya haka. Rashida ta watsa kishi banzan kallo ta koma kan kujerar ta zauna. Za ta iya yarda ya wulaƙanta, amma ba ta son dukan mace. Akwai dukan da mahaifinta ya yi wa mahaifiyarta, da ya zama sanadin da ta daina jin magana da ɗayan kunninta. Ta tsani dukan mace. Ta sha alwashin duk ranar da ya yi gigin taɓata lafiyarta, sai ta yi masa abin da zai gane kalar wacce ya aura. "Lallai yarinya na san iskancin nan saboda na sake ki ne, kuma wallahi ba zan saki ba. " Ya ce tare da komawa ya zauna gefenta yana huci. Nasreen kuwa da ta shiga cikin ɗaki matuƙar mamaki ya kamata. Ashe zan iya ta ce. Tana dage zuciyarta da take ta bugawa kamar za ta fito waje. Daurewa kawai ta yi, amma a lokacin da ya ɗaga bulalar ji ta yi kamar ta gudu. Zama ta yi gefen gadon tana kallon yadda ɗakin ya yi ƙura. Bayan ta cire hijabinta ta shiga bayi. Ganin yadda ya koma sai ta fara kwalemar ɗakin. Tana aikin tana jin dariyarsu a falo. Dariya suke yi har da shewa. Da gayya yake dariya don ya ƙular da ita. Ai kuwa ta shaƙa, tunawa da ko farkon aurensu bai sakin mata fuska ba. Hakan ya sa ta ji ta ƙara tsanarsa sosai a ranta, ganin bai ba ta daraja da mutunci ba. Tana aikin tana jin suna ta dariyar har suka gaji suka shige cikin ɗaki. Hira suke yi da Raihan da take ta yi mata surutu, har ta kammala gyaran ɗakin ta wanke bayi. Turaren wuta ta sanya sannan suka yi wanka. "Umma yunwa na ke ji." Raihan ta faɗa tana shafa cikinta. "Ok, my angel. Muje ki in na samu abin da zan baku. Na ga Musaddik yaron kirki yana ta hamma. Ko dayake ni ma yunwar nake ji." Ta ce tare da ɗaukar Musaddik da yake kan gado ya miƙo mata hannu. Ɗaukan shi ta yi tare da cilla shi sama tana masa wasa."Yarana kune farinckina Allah ya raya mini ku." Ta ce tana masa kiss "Amin Ummana, ina girma na yi makaranta zan siya miki gida da mota, na kai ki makka, amma ban da Abba tun da ba ya sonki." Raihan ta ce fuskarta ɗauke da damuwar abin da yake cikin ranta. "Allah ya yarda Raihan ya albarkance ku." Amsawa ta yi ta kama hannunta suka shiga kicin. Lafiyayyen abinci ta ga sun girma. Shika fa da miya sai tsokan nama da basu wuce yanka tara ba. Dubawa ta yi ko ta ga zai ije abinci a store ko ita ma ɓoyewa zai yi. Wayam babu komai sai Lipton da gishiri a buhu. Ba ta san lokacin da ta saki dariyar takaici ba. "Wato Faruk a jininsa maƙo yake?" Ta yi wa kanta tambayar tare da iban abincin a filet ɗin suka fito falo. Suna zaune ta kunna musu katoon suna kallo. Sun fara cin abinci sai ga shi sun fito. "Ke! Ubansa ya ba ki ikon shiga kicin ki ibi abinci?" Ta ji muryar Rashida tsaye kanta, da wata 'yan iskan rigar baccin da tun da ta yi mata kallo ɗaya ta ɗauke kanta, saboda komai na jikinta ana gani. Idanunta ta mayar ga Faruk da yake tsaye kusa da ita."Ba an dafa bane don aci?" Ta ce mata cikin rashin tsoro. "Da aka dafa sai aka ce ki zo ki ke da 'yan iskan ya'yan..." "Kul karki sake! Don't ever try it, bana yi wa yarana mummunar zagi, kuma ban zan yarda wata yar isa..." "Ke Nasreen ki kiyaye ni wallahi." Ya daka mata tsawa yana faɗin haka. Sai kuma ya kalli Rashida da take jijjiga."Allah ya ƙara ɗazu xan duketa, ba hana ni kika yi ba?" "Tun da ba ta da mutunci babu ruwan da ita in kaso ka kasheta." "Na gaya miki Nasreen ba ta ji yarinya ce mara kunya da ɗa'a." Harararsa ta yi jin abin da ya ce, ta ci gaba da cin abinta don ba ta da lokacinsa. Hannu Rashida ta sanya ta ƙwace abincin tana faɗin,"Wallahi ba ki isa na yi girki ki ci ba, saboda ba ki da wannan darajar mijina na dafawa." "Ki barta daga yau ita za ta rinka mana girki." Ya ce saboda sam girkinta ba ya mishi daɗi. Kafin ya aure ta yana tunanin akwai macen da ta fita iya girki, amma da suka yi auren girkinta ba ya yi masa test irin nata. "An gaya maka abinci na dawo na rinƙa dafa muku?" "No, ba zan yi miki dole ba, saboda kin san halina na ba ki girki sau ɗaya, in har ba za ki rinƙa yi ba, ba sake saninsa ta yi ba." "In ka ga dama ƙarka bani abincin ka ga inshi zai sanya na mutu." Ta ce masa tare da miƙewa za ta bar falon. Galala ya yi yana kallonta. Tun da ta dawo take ba shi matuƙar mamaki. A zuciyarsa ya lailayo ashar ya dannawa Marwana, domin ita ta shigo rayuwarsu har take kwaɗaita mata kuɗi. Tana ganin cewa in ya rabu da ita, za su taimake ta. Ko da wuƙa za sanya kishi a maƙoshinta rantse ba zai sake ta. Kallon Rashida ya yi da fuskarta yake a tamke. "Ki barta ta yi mana girki yamma bari na je na fito da abin da za a dafa." Ya faɗa yana ƙoƙarin juyawa. Wani banzan kallo ta watsa ma a lokacin da ya juya baya. Haushin yake ba ta sosai. Don bala'i da masifa gida daga ita sai shi, amma a ce kayan abinci a ɗaki da zai ije. Komawa ta yi ta zauna tana cika tana batsewa. Da ya fito da taliya da makaroni ganin yadda ta canza fuska, sai ya wuce ɗakin Nasreen. Babu sallama ya tura ƙofar ya shiga. Kallonsa ta yi a sakarce ta mayar kan Musaddik da take shinfiɗar da shi. "Ga shi ki kirga mana, kuma wallahi in har ba ki yi ba, ba za ki ci abinci ba." Bata daga kanta ba ballantana ya yi tunanin za ta amsa. Ganin haka ya ja tsuka yana duba agogonsa."Lallai Nasreen ashe kwananan za ki koma ba haƙora." Ya ce tare da shiga cikin motarsa. Har ya fita sai kuma ya dawo tunawa da ita take buɗe masa get. Da fari hon ya rinƙa sakin mata, domin in har yana son ta buɗe masa jin yake mata. Tana jin sa ta yi banza da shi, har ya gaji ya fito. "Sai na ga uban da zai buɗe maka." Ta ce tare da zama kan stool ta ɗora ƙafarta ɗaya kan ɗaya. Tura ƙofar ya yi cikin fusata."Saboda iskanci ina hon ba za ki zo ki buɗe mini get ba?" Dariyar takaici ta saki tana kallonsa."Na ga yanzu mu biyu ne, kuma yau na dawo, ita take da girki ka je ta buɗe maka ranar girkina sai na buɗe maka." "Yaushe kika samun ƙarin gwiyar mayar mini da magana? Ada akwai Ahmad wani lokacin ina shakkarsa, amma yanzu wallahi babu shi. Zan yi miki raunin da sai kin kwanta asibiti." "Allah ya ba ka sa'a. Babu Yaya Ahmad, amma ni zan ƙwaci yancin kaina." Har ya buɗe baki zai tursasata sai kuka ya fasa ya juya zuwa ɗakin Rashida. A ransa ya ji ya kamata ita ma ta rinƙa buɗe masa, kamar yadda take yi masa. Tana riƙe da waya tana kiran Malam. Wayar ta shiga kenan ya amsa da sallama, sai ya tura ɗakin ya shigo. Da sauri ta kashe wayar ba tare ta yi amsa sallamar da malam ya yi mata ba. "Haba Faruk what's this nonsense? Na gaya maka ka rinƙa sallama in za ka shigo." "Ke!" Ya faɗa yana zare mata idanu jin abin da ta ce cikin tsawa."Ni da gidana sai an bani izinin shiga? Ban yi sallama ba da uban da ya..." "No Faruk! Karka sake ka zagi ubana saboda ba zan ɗauki cin kashin da kake yi wa matarka ba, domin in ita shashasha ce ta zubar da kanta na san darajar kaina." Ta furta da muryar da bai taɓa tunanin tana da shi ba. Kallonta ya yi cikin tsananin mamaki."Rashida! Ni kike gaya wa magana?" "To sai na zauna ka zagar mini iyaye? Na lura kwanakin nan tun da muka yi watanni ka fara canza mini." Ta faɗa cikin kissa. "Saboda na ina ɓoye abinci a ɗakina ko?" "Eh, ai ka san hakan babu kyau, in har matarka tana sata sai aka ce maka ni ma sata zan yi?" Ta ba shi amsa a gatsale. Nasreen ba ta taɓa satar mini abinci ba, saboda bana son albazaranci ya sa nake ɓoyewa, domin kuɗina ba kuɗin lukudu bane, da zan sayi abinci ki wulaƙanta. Na gaya miki gidana bana son baƙi, amma daga aurenmu mata nawa suka zo gidannan? Ga su tiƙa-tiƙa da su, so kike su cinye abincin da na siya." Mamakin abin da ya ce sai ta kalle shi a birkice."Faruk yan'uwana kake zagi?" "Ƙarya na yi ba tiƙa-tiƙa bane?" "Lailai Faruk ban taɓa tunanin haka kake ba...." "Ke bani da wannan lokacin zan fita ke ki buɗe mini get. Tun da kika tare nake tunanin za ki fara, amma da yake ba ki san abin da ke miki ciwo bai, sai kika bar ki ina wahala." Ya furta yana nuna mata hanyar fita. "You are seriously jorking ko? Ni ce zan buɗe maka get? You must be jork." Ta ce masa cikin zallar mamaki tana kallon sa. "Wasa nake yi miki in kin ɗauke ni abokin wasanni, ko kuma mahaukaci." Ya ba ta amsa fuska a ɗauke. "Dole na yi maka tambayar, saboda na kasa gane zaman aure zan yi ko mai gadi ka ɗauko." Ta ce masa tana watsa masa kallon raini. "Matata Nasreen ita take buɗe mini mota har ta wanke, in na dawo ta kwaso kayan, saboda ban ce ki fara ba sai yanzu?" "Kace 'yar aiki take a gurinka. For God sake ina matarsa zan buɗe maka get na wanke maka mota? Da ma kana mini duk abin da na ke so ne, sai na yi maka don na faranta maka, Wallahi ba zan yi ba. Sam ba ka da sakin hannu dubi irin cimar da ake yi a gidanka." Kallonta ya bita da shi, yadda take ɗaya masa murya, kamar ba ita da ya sani tana masa magana cikin taushi ba. "Dole ki yi in ba haka ba za mu samu saɓa ni dake." Ya ce tare da juyawa zai koma gurin Nasreen ta buɗe masa. "Faruk!" Ta kira sunan shi cikin ƙaraji, wanda ya sanya shi juyowa babu shiri. "Look, let's face the reality. Ina son na yi magana da kai. Tsawon lokacin da muka yi aure, amma ban ji ka yi maganar za ka bani kuɗi na fara business ba." Wata bazawara dariya ya saki tare da dawowa gabanta ya tsaya."Rashida ni zan ba ki jari ki yi sana'a? Kin san wa kike aure kuwa? To sana'ar ma ba zan amince ba, ballantana na ɗauki kuɗina na baki." "Aikuwa ba za ta saɓu ɓa, saboda ka san matan yare, dole da sana'a muke rayuwa. Sam na tsari rashin kuɗi kuma kai komai na ka a maƙe..." "Ok ruwan kuɗi zan rinƙa miki tun da magana nake suna zuba? Ki cire wannan a ranki." "Ka san Allah dole sai na fita na nemi kuɗi, ko ka bani jari na yi sana'a ko kuma ka samar mini aiki." "Duka ba zan yarda ba, aure kike yi don haka ba zan aminta." "Wasa kake yi Faruk." Ta ce masa tana harararsa. Mamaki ya kama shi tsayawa ya yi yana kallon ta. Ganin yadda ya tsaya sai ta matsa kusa da shi, ta marairaice fuska ta kamo sa."Faruk, don Allah mu tsaya mu fahimci juna. Gaskiya rayuwar da kake yi ba ta yi mini ba, ka bukatar hanyar da zan samu kuɗi. Ko namar miya ka siya sai ka faɗa mini kwanakin da zai yi..." "A haka na ke rayuwata in kin ga za ki iya shikenan." Ya ce mata tare da juyawa zai fita. "Ba zan iya ba gaskiya, you need to adjust." Ta ce masa tare da juya masa baya. "To sai na ga uban da zai sanya na gyara." Ya bata amsa tare da juyawa zai fita. Saboda takaici daƙuwa ta yi masa ta baya. A ranta tana jin in har ya cigaba da haka, za a haifi ɗa mata ido. Mamaki take yi yadda Nasreen ta iya zaman aure da shi har suka haifi yara biyu. A yadda take ji ba za ta iya komawa a gidansa ba. Mutum sai shegen maƙo da iya bakar magana. Yana fita ta janyo wayarta Malam ta kira. Bugu ɗaya ya ɗauka."Wallahi mutun nan yana da taurin kai da maƙon tsiya. Sai ka yi mini babban aiki a kansa." Ta faɗa cikin takaici. "Ƙarki damu kanki ki samu lokaci ki zo akwai aikin da zan yi miki mai ƙarfi a kansa." "Yauwa Malam yana da makon tsiyar wallahi baya don fitar da kuɗi sai kace tare aka haife su." "Ki dai zo kawai." *_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 2 Yauwa Malam yana da maƙon tsiya, wallahi ba ya son fitar da kuɗi sai kace tare aka haife su." "Ki dai zo kawai." "To," Ta amsa tare da katse wayar tana takaicinsa. Kai tsaye ɗakin Nasreen ya shiga, yana mamakin halinta mai ladabi kunama. Ya tura ɗakin ya shiga, amma sai ya ji ta kulle."Ke Nasreen buɗe mini ƙofar nan, kuma ki zo ki buɗe mini get." "Wallahi ba zan buɗe ba, domin raba kwanakin aiki za a yi. In har na ga matar da kake kira ta mai biyayya da komai tana yi zan yi, saboda yanzu tun da ka samu matar ƙwarai zan koyi komai daga gare ta." Ta furta masa da ƙarfi yadda zai ji. Haushi ya sanya shi kaɗa kansa ya fice daga gidan. Tunanin dukan da zai yi mata in ya dawo yake yi. Tana kwance har aka kira sallah. Ta yi sallah ta ɗauki Alqur'ani tana ƙarantawa. Addu'a sosai ta yi wa Ahmad tana roƙon Allah ya bayyana shi, sannan ta yi wa Batula. Tana addu'ar hawaye yana sauka daga ƙuncinta. Tana zaune har biyar da rabi ta yi. Kamar ba za ta yi girkin ba, sai kuma ta tashi ta shiga kicin don ta girka, tun da in bata yi ba ta san ba za ta ci ba. Tana girki tana sauraren karatun Alkur'ani. Bayan ta gama ta fito da ta shiga cikin ɗakinta. Rashida ta gani zaune a falo da wasu 'yan iskan ƙananan kaya tana kallo. Kallon banza ta yi mata kafin ta mayar da idanunta ta rama. Abincinta ta sanya a kula ta shige cikin ɗakinta. Kamar yadda ba ta sanya a ranta ba zai shigo ɗakinta haka ta ya faru. Bai shigo gidan ba sai da aka yi Isha, saboda ya san ba zata buɗe ba, da kanshi ya buɗe get ya shigo. Babu kowa a falon sai Rashida da take zaune cikin wasu arnan kaya. Ta yanke shawarar ta yi mishi kissa da lalama ta ga ko za ta samun kansa. In har ya fujire to za ta fito masa da ainihin kalarta. Ganin ya shigo, ya sa ta miƙe da sauri kamar wata ƙaramar yarinya ta faɗa jikinsa. Ture ta ya yi ya zauna yana harararta."An gaya miki ni sakarkarun maxan nan ne, da za ki gaya mini magana , sai ki dawo ki rarrashe ni?" Ya tambaye ta fuskar a ɗaure. Ganin ya gwasile ta da kuma tambayar da ya yi mata, sai ta koma ta zauna jikinta a saɓule."Gaskiya na gaya maka Faruk da ga ƙinta sai ɓata." "To ki riƙe gaskiyar ta ki bana so, saboda wallahi in har kika ce za ki yi mini shishshigi, a lamarina zan gurza miki rashin mutunci." "Allah ya ba ka sa'a. Ni ma ba kanwar kasa bace." Ta gyara zama tana faɗin haka a ranta, amma a fili kallonsa kawai ta yi ta tura baki. Ganin ba ta ce komai ba ya saki tsuka."Tashi ki ɗauko mini abinci ko sai na roƙa za a bani?" "Na ga ba ni na girka ba? Sai ka kira wacce ta girka ta ɗauki maka, na fahimci girkin nawa ne ba ka so, shi ya sa daga dawowarta ka ce ta karɓa." Ta ba shi amsa ba tare da ta motsa ba. "Ashe kin san kwaɓa kike mini kin san ba ki iya girki ba. Wannan dahuwar cikin shigen ne bana so, sannan ki cika yaji kamar na wasu mayu." "Sai ka ci gaba da ba ta tun da ta iya." Ganin ba za ta tashi ba, sai ya saki tsaki ya miƙe. Har ya nufi ɗakinta sai kuma ya fasa. Kicin ya shige ya ɗauko kular abincin. Yana fitowa ta saki tsaki ta shige cikin ɗakinta. Kallonta cikin mamaki yake yi ganin yadda ta canza lokaci guda. Sai da ya kammala abin da yake yi, sannan ya ɗauki wayarsa ya shige cikin ɗakinsa. "Yana ƙoƙarin kulle ƙofa sai ga shi ta shigo da kayan bacci a jikinta." "Ki koma inda kika fito ba hushi kika yi ba?" Ya ce mata cikin tsawa tare da nuna mata hanya. "Ai dama na san ka kitsa abu a zuciyarka. Wato so kake ka kwana da matarka ko?" "Wa Allah ya kyauta ga yar duma-duma mai zan yi da jiki duk ƙashi, amma ki sani ba zan ɗauki iskanci ba, saboda ba a yi macen da za ta juya ni ba." "Sai ni Faruk ka jira lokacin da zan juya ka tamkar waina a cikin tanda." Ta ce a ranta amma a fili kallonsa ta yi sai kuma ta shiga cikin jikinsa. "Haba my love ka san ba zan iya fushi da kai ba." Ta ƙarashe maganar cikin kissa tana son haɗa bakinsu. Ganin tana son nasara a kansa sai ya tureta ya zauna a bakin gado. Biyo shi ta yi ta faɗa jikin shi."Wallahi in har kika ce za ki rinƙa tambayata kuɗi, kina shiga lamarina za mu sa ƙafar wando ɗaya dake, saboda ina ba ki abinci dama aure ba ci da sha bane." Jin abin da ya ce sai ya ba ta mamaki, amma da yake sulhu take nema. Ƙara rungumeshi kawai ta yi tana mishi salo. Ba tare da ya ja aji ba, ya ba da kai bori ya hau. A lokacin da Nasreen ta ji uhunsu hankalinta ya tashi sosai. Saboda takaicin rayuwar dabbobin da suka ɗauki kuka ta fashe da shi. Tunani ta fara ya za ta yi ranar da Raihan ta girma ta fahimci abin da suke yi. Da sake wallahi ba za ta saɓu ba, an yi sadaka da bazawara." Ta furta tana share hawaye. Bata kwanta bacci ba, har sai da suka dawo hayyacinsa Sannan ta samu ta rintsa. Faruk kuwa har da biyu ya yi don ta ji su. Babu irin yadda bai yi ba, don su rinƙa haka, amma ta kawo masa ƙauli da ba'adi, yanzu kuwa tun da ya samu sai ya more abinsa. Kasancewar sun sha love, ba su tashi ba har aka kira sallah aka sallame. Nasreen tun kiran sallar farko ta tashi ta yi sallah. Bayan ta gama addu'ointa ta ninke daddumar. Raihan ta tayar a lokacin shidda har da rabi. Ta yi sallah, sannan ta yi mata wanka ta shiga kicin don ta shirya abin kari. Tana shiga taga dankalin hausa ya siyo sai ƙwai guda biyu. Tsaki ta saki, ta fara fere ɗankalin. Bayan ta soya ta ibi na ta sannan ta sanyawa Raihan a kula da ruwa. Ɗakinta ta fara gyarawa, sannan farko tun da ba datti ya yi ba, cikin ne da yake yana buƙatar goge-goge ta barshi sai ta dawo kai ta makaranta. Bayan ta karya sai ta fice zuwa kaita. Biskit da bobo ta tsaya ta siya mata sannan ta kai ta makaranta. Da ta dawo ba ta shiga cikin gidan ba. Gidan Maman Muwaddat ta shiga. Da sallama ta shiga cikin gidan. Maman Muwaddat da take falonta, tana kaye-kayen kwanonin da suka yi breakfast. Cikin sauri ta ƙaraso ƙofar falon jin muryarta. "Nasreen," Ta kira sunanta tare da kama hannunta suka shiga ciki. "Nasreen, ashe Baba dai sai da ya tilasta miki kika dawo?" "Ya zan yi? Baba sam ba ya yi wa rayuwata adalci." "Gaskiya ba ya kyautawa." "Ai na san cewa tun da ya Ahmad ya ɓace dole ya mayar da ni." "Nima yana ɓacewa na sanya dawowarki a raina, amma sam kar ɓacewarsa ya zama karayar gwiwarki, saboda Nasreen ke ya kamata ki tashi ki ƙwaci 'yancin kanki. Ko da ace yana nan ya yi mishi hulɗin kuka rabu, in kika je wani gidan ba fata nake miki ka, kin san yanzu maza sai shiryar Allah. Akwai nagari amma da wasu sam ba su da kirki. In yana miki wulaƙanci shi ma hakuri za ki nuna Ahmad shi zai ƙwayar miki 'yanci? Bacewarsa kamar Allah ya ɗauke shi, don ki tashi ki zama jaruma ki fuskanci rayuwa. Jarrabawar rayuwa ba ta ƙare wa, domin Allah subhanahu wata'ala ya ce a cikin littafinsa mai tsarki,"Shin kun yi imani kuma kuna tunanin ba za mu jarrabce ku ba?" Da zarrar kin gama da wannan ƙaddara sai wata ta shigo. Matuƙar ba mutuwa kika yi ba, Ubangiji ba zai daina jarrabtarki ba, don haka ki tashi ki zama jaruma ki fuskanci ko wane irin ƙalubale. Nasreen haƙurin ki yana da yawa. Ban ce kar ki yi hakuri ba, amma ya kamata ki rage, saboda a yanzu rayuwa mutum mai hakuri ake takawa. Kina ganin halin da dangin mijina suka sanya ni. Da ina musu sanyi har cikin gidan nan ƙanwarsa take zuwa ta yi mini rashin kunya, amma tun da na rage hakuri na yi maganin ta, ga ba shi na zauna lafiya ba? Kamar haka za ki yi Nasreen a yanzu kar ki bari Faruk ya yi miki abin da ya saba. Kin ga ya yi aure wallahi in kika yi sakwa-sakwa har da amaryarsa za su haɗu su ci kashi a kanki." Murmushi mai ciwo ta yi tana kallonta."Kin san wace ce Nasreen a yanzu? Kin san yadda zuciyata ta bushe? Tun da aka nemi Yayana wanda nake ganin shi ne tamkar ubana aka rasa. Wanda na ɗauka a matsayin haske a gare ni, amma y tafi ya bar ni. Zuciyata ta bushe bana jin tsoron kowa. Ji nake yi a yanzu ko a dokar daji zan iya rayuwa. Faruk ba ya gabana ba ce za yi masa rashin mutunci ba, saboda rayuwar aure ba rayuwar dabbobi bane da za mu rinƙa dabbaci, amma wallahi ba zan ƙara yarda ya wulakanta rayuwata ba. Ya fita a raina. Ba ni da yadda zan yi ne, bisa tursasawar Baba ya sanya na dawo gidan nan." Kallonta ta yi cikin tsananin mamakin kalamanta. Hannunta ta kama ta riƙe tana fatan har cikin zuciyarsa maganganun suke fitowa."Da kyau Nasreen ina fatan hakan. Ki miƙe ki ƙwaci 'yancinki. Allah ya yi miki daraja ga ki mace kuma mutum, sannan ki kama sama'a kar ki ji tsoron hana ki da yake yi. Yanzu rayuwa ta canza komai ya koma social media in dai kina da waya androin za ki yi sana'arki ba tare da an sani ba. Kin ga tun da mahaifinmu ya rasu, aka raba mana gadon sai na sayi gida. Ragowar kuɗin dama akwai ƙanina Musa da yake ɗinka hijabi ko wane iri. Kuɗi na ba shi ya ɗinka mini da yawa. Daga ɗorawa a status na shiga groups da yawa, kin san ya kare?" "Da kyau Masha Allah! Ubangiji ya kawo kasuwa." Ta ce mata tana kallon ta. "Ke ma ki fara sana'a tun kina gida na yanke shawarar san zo mu yi maganar. Zan rinƙa baki kan sari kina ɗora na ki. Idan Allah ya sanya kina da rabon sai ki ga Allah ya ɗaukaka ki. A waya za ki yi Faruk ba zai san kina business, sannan kina zuwa makaranta za ki yi ciniki." Kallonta ta yi cikin farin ciki ta ce,"Gaskiya na gode sosai. Zan gwada Allah ya sa na samu, duk da na sayar da wayar na sayi ƙarama ba ta rike caji sosai, kuma makarantar ai na kusa gamawa." "In har kika fara sana'a kwana nawa za ki canza. Kin san wani lokacin rayuwa tana cakuɗe wa mace ne, in ba ta da sana'a. In har kina da abin yi ɗin namiji yana wulakanta ki wallahi ba ki da lokacinsa. Abinci ne zai baki, kuma ya san ko bai baki ba, kina da abin da za ki siya. Ko da za ku samu matsala da sauki ba kamar ace kina zaune komai sai ya ba ki ba." "Haka ne zan gwada in sha Allahu. Ni ma akwai sauran dubu hamsin da ban kashe ba, a cikin kuɗin lapton ɗina. Dama na ije na makaranta saboda biyan kudin makaranta, amma da zarar har mun kashe hamsin." "Ki sai waya da shi Nasreen sai ki fara business. Akwai groups kala-kala na sana'a cikin ƙankanin lokaci in sha Allahu za ki samu kuɗin. Sannan ki rinƙa hawa social media kina karanta labari ɗan Whatsapp ɗin nan ki shiga groups groups za ki samu farin ciki, kuka ki san halin da duniya take ciki. Ga kuma marubuta suna ƙoƙarin su gurin sanya mutum nishadi har ma da darasi." "In sha Allahu zan kira shi na ba shi kuɗin ya nemo mini. Facebook ɗin don tun da ya Ahmad ya ɓace ban ƙara shiga ba, Whatsapp ɗin kuwa ina ya yi expired." "Zai yi tun da an daɗe." Ta ce mata tana kallonta. "Miƙewa ta yi tana kallon agogo."Bari na tafi suna bacci na taho, kar ya tashi ya ga bana nan ya kira Baba." "Ok, ki je kin san Baba da faɗa. Zan kira Musa in ya gama ɗinkin sai ya ƙara da wanda zan baki." "To na gode Allah ya saka da alkhairi." Ta ce mata. Har bakin ƙofa ta rako ta sannan ta tafi. Da ta koma har lokacin ba su tashi ba. Kicin ta wuce ta gyara sannan ta fito. Tana ƙoƙarin rufe kicin ɗin Rashida ta fito tana wani takun yanga ita a dole ta kwana da miji. Wucewa ta yi tana mata kallon ƙaskanci bisa abin da suka yi jiya. Za ta shige cikin ɗakinta Faruk ya fito da alamu ya shirya zai fita. Kanta ta ɗauke ganin yana kallon tsabar idanunta ya ga ko za ta ji haushi, amma sai ya ga saɓanin haka. Har za ta wuce sai kuma ta ga in ba ta gaishe shi ba, zai yi tunanin ta ji haushin ƙin kwana ɗakinta da ya yi. "Ina kwana." Ta ce masa ba tare da ta jira amsar ba ta shige cikin ɗakinta. Ƙuta ya yi yana kallon hanyar ɗakinta."Wato kin dawo da raini. Ni kike gaishewa kamar kina gaida sa'an ki?" Ya ce cikin ɓacin rai. Yana tsaye yana yana gyara zaman takalmin da Rashida ta fito ranta a ɓaci."Baby, dankali na ga an siya da wani barbaɗaɗɗen kwai, aka sanya a kula?" "Da kular kike so ya cika. Guda biyu na siyo in aka sanya kayan miya yawa yake yi sosai. Ita Nasreen ta san yadda take yi ai." Ya ce mata yana gyara takalmin da ba tare da ya ɗago ya kalleta ba da take jin kamar ta kifa masa mari. *_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 3 "Da kular kike so ya cika. Guda biyu na siyo in aka sanya kayan miya yawa yake yi sosai. Ita Nasreen ta san yadda take yi ai." Ya ce mata yana gyara takalminsa, ba tare da ya ɗago ya kalleta ba da take jin kamar ta kifa masa mari. "Kwai biyu duk mutanen gidanan? Shi ya sa na ga ko kama kayan miyan baya yi. Haba don Allah ace rai kusan biyar su karya da ƙwai biyu? Ni fa wallahi na gaji da maƙon ka, kana da shi Allah ya buɗa maka, amma ba za ka wadata iyalinka ba. Haka fa ranar nan ka siyo ƙullu na sayarwa Faruk da matsayin ka kana babba a gwamnati? Wannan zaluncin ya yi yawa." Miƙewa ya yi a fusace yana kallonta."Ok, so kike na zauna na siyo crek ɗaya sai ku soye a lokacin, tun da kina auren ɗangwate ko Aliko ko? Don ina aikin gwamnati sai na dinga watsa muku kuɗina. Ba ki da hankali ya kamata ki dawo hayyacinki, saboda ni Faruk ba mahaukaci bane, na san yadda na tara kuɗina. To ki sani a gidana cimar da na ga dama ita zan bayar, kuma babu wanda ya isa ya sanya na canza mini ra'ayi. Yauma mai da ya ji zan bayar ku dafa, sannan wallahi ki daina zuba mai da yawa, don in ya ƙare sai dai ku siya da kuɗin ku, sisina ba zan bayar ba." Ya ƙarashe maganar yana nuna ta da yatsa sai kuma ya ce,"Na manta ba ke za ki yi girkin ba, ita wacce za ta girka ta san dokar gidan." "Kan uban nan!" Rashida ta lailayo ashar ta ƙunduma. "Ke zagina za ki yi?" Ya yi mata tambayar tare da ɗaga hannunsa. "No Faruk! Ba zan iya daukar cimar gidan ka ba, wallahi in har kana son zama da ni dole ka canza. Kana ba matanka abinci kamar kana ciyar da 'yan gidan yari?" "Guri kika samu, saboda ba ki zo lokacin da na ke bawa Nasreen abinci sau ɗaya ta girka ba, don kin ga ina bari ki yi girki duk lokacin da kike so. To ki yi gigin da zan hana girki a gidan nan, sai na dawo daga gurin yawona." "Ka isa wallahi ba ka isa ba, saboda ba dabbobi ka ije ba, da za ka rinƙa ciyar da su lokacin da ka ga dama." "Tun da haka kika ce sai mu zuba in na fara idonki zai raina fata." Gabansa ta sha ganin zai fita."Ba zan taɓa yin irin wannan rayuwar ba, dole ka canza ko mu hau sama da kai. Idan matarka ba ta san darajar kanta ba, ta bari kana mata abin da ka ga dama wallahi ba zan ɗauka ba, zaman aure ba zaman bauta bane." "Ok haka kika ce?" "Eh Faruk fiye da hakan zan faɗa." Ta furta tana kama ƙugu. "To shege ka fasa."Ya tureta ya fice daga falon. Nasreen dake cikin ɗauki ta tana zaune tana jin sa'insar da suke yi. Dariya ta saki tana faɗin,"Daɗina da gobe saurin zuwa." Rashida kuwa cikin takaici ta tura ƙofar ɗakin Nasreen ta shigo. Ganinta ya sanya ta miƙe tana kallonta. Ganinta ya sanya ta ɗan razana, amma sai ta daure ta ce,"Lafiya kika shigo mini ɗaki babu sallama, kamar ba ki san hukuncin yin sallama ba?" "Eh saboda ba ita ta kawo ni ba. Na shigo na gaya miki tarbiyar da kika ɗora mijinki sam ba ki yi masa tarbiyar kirki ba, kin koya masa maƙo kin zauna kin zubar da kanki, yana da kuɗi yana baki cimar talakawa." Jin bin da ta ce sai ta ba ta dariya sosai."Ok, kena kina da believe cewar uwargida take ɗora mijinta kenan? Ba zan yi miki musu ba, amma ba irin mijin da kika aura ba. Faruk yana cikin WASU MAZAN da mace ba ta isa ta sanya shi ba kuma ta juya shi. Faruk yana cikin WASU MAZAN da ba su ɗauki mace a bakin komai ba, abin da suka gama shi suke yi. Idan ya je ya gama gaya miki ƙarya da gaskiya cewar bana masa biyayya ni ba macen ƙwarai bace, kin shigo da ninyar ƙwace zuciyarsa ta hanyar yi masa jin da bana yi, sai na ce alhamdulillah ga fili ga mai doki sai sukuwa." "Ai wallahi ba zan ɗauka ba, saboda na san daraja ba zan yarda ya rinƙa ciyar da mu, kamar yana cutar da bursunoni ba." "Allah ya ba ki sa'a sai ki gyara shi yadda kike so, tun da ni uwargida ban ɗora shi a kan turbar ƙwarai ba." Ta buɗe baki za ta yi magana, amma sai takaici ya sa ta kasa cewa komai. Cikin fushi ta fice tare da buga kofa. Nasreen ta sanyawa ƙofarta makulli tana faɗin,"Shashashar banza! Suna zuwa suna gaya muku ƙarya da gaskiya kuna yarda. Yanzu sai na ga abin da za ki iya." Ta koma ta kwanta. Wayarta ta ɗauka ta kira ƙaninta Bala, ta yi masa bayanin tan sun canza wayarta. Babu ɓata lokaci ya zo get ɗin gidan ya kira ta ta fita. Wayar ta ba shi sannan ta cika masa dubu arba'in. Tana kwance a dakinta kasancewar hutu ake yi na makaranta girki kawai ta yi sannan ta ɗauki Raihan. Tana cikin ɗaki suka wunin binsu. Bayan magariba Bala ya kawo mata waya mai kyau. Ta yi murnar wayar da ya canza mata, don ta yi mata kyau Infinix hot eleven play. "Allah ya sanya ka sanya mini caji?" Ta ce tana kallon sa. "Haba Anty Nasreen, sai da na cika ta sannan na gwadata har layinki na sanya miki. Za ki ji dadin wayar tana riƙe caji." "To ka shigo gidan na ba ka ko na mota." "Allah ya kyauta Faruk ya yi mini tozarta." "Ba ya nan." "Kawai tafiya zan yi ba sai kin bani kudi ba, ke da kike buƙatar taimako Allah dai ya bayyana ya Ahmad." "Amin," Ta ce sai hawaye suka zubo mata. "Ya zamu yi? Sai haƙuri dana haka rayuwar take sai a yi ta ɗauke na gari. Da ace ana shawara wallahi Baba zan ce a ɗauke, saboda ba shi da amfani." "Kar ka yi masa fatan hakan, duk lalacewarsa mahaifinmu ne, mu yi masa fatan ya shiryu ba." "An gaya miki yana nadama ne? Har yau babu nadamar da ya fara." "Allah ya shirya shi." "Amin," Ya ce tare da yi mata sallama ya wuce. Ɗaki ta koma ta fara danna wayar. Data ta siya ta shiga play store ta ɗauki facebook lite da gb Whatsapp. Bayan ta yi installing ɗin su, sannan ta buɗe. Da ta gama duba facebook ta shiga groups da take so, sai ta sauka a ta koma Whatsapp da tsaƙwanni suke ta shigowa daga group na su na makaranta. Maman Muwaddat ta yi wa sallama ta gaya mata ta canza wayar. Ganin ba ta a online sai ta fara duba tsaƙonnin da suke shigowa. Bayan ta gama duba tsaƙon dai ta bi shawarar da zuciyarta take ba ta. Numbar Marwana ta ɗauki ta kwafe tare da saving a wayarta. Ta yi hakanne don ta rinƙa ganin status ɗinta, ta santa mayyar sanya status ne. Yawanci hotonta Damir sai na matarsa da kuma Little Marka da ƴaƴanta. Bayan ta sanya babu yadda za a yi mutun ya san ta kalli status ɗin mutum, sannan ta kashe wayar ta kwanta tana tunanin rayuwa. Tana son ta san halin da suke ciki. Tana son ta san ko yanzu suna farinciki. Addu'a take musu kullum Allah ya dawo musu da farincikinsu. Da ta yi isha'i ta yi gama abin da za ta yi ta kwanta. Wayar ta janyo ta kunna data. Ta daɗe a facebook wani zubin ta ga labarin dariya, wani zubin takaici har ta gaji ta sauka ta koma Whatsapp. Tana duba status sai ta ga Marwana ta ɗora status. Da sauri ta fara dubawa jikinta har yana kyarma. Hoton farko ita da Little Marwana, sai kuma ta sanya hoton Marigayiya Batula da stickers na kuka da addu'a da ta rubuta da turanci. Ganin hoton ya sanya hawaye zuba daga ƙuncinta. "Allah ya jiƙanki Batula ya sanya kina kyakkyawar matsayi." Ta ce tare da ƙara duba status na gaba. Wani irin faɗuwar gaba ya same ta har sai da ta miƙe. Ganin hoton Damir Gabakiɗaya ya canza kamar ba shi ba. Duk da cewar ba sau biyu ta ganshi, amma fuskarsa da ya zauna a idanunta kamar an zama shi yana nan. Har yau tana tuna fuskar da take saukar da annuri, amma yanzu sai ta ga saɓanin haka. Ya ɗan yi duhu ga wata ƙasuma da ya tara. Yana sanye da jallabiya fara tar farin har yana kashe idanu. Inda aka ɗauki hoton zai tabbatar maka da ƙasa mai tsarki suka je. Wataƙila ummra suka je don Alllah ya kawo masa ɗauki. Ta ayyana hakan a ranta tana kallon hoton zuciyarta na bugawa. Hoton Gaba ta kalla duka family ɗinne suka ɗauka. Sai ta rintse idanunta tana jin ƙaunar waɗannan ahalin, duk da cewar sun tsaneta tana son su, kuma za ta ji gaba da musu addu'a. Kallon Marwana take yi cikin tsanannin ƙauna, tana share hawaye da ke gangarowa a fuskarta. Ta san cewa ba ta yi wa waɗannan ahalin adalci ba, kamar yadda rayuwa ba ta amarya adalci take raba ta da mutanen da suke ƙaunarta. A ranar kasa bacci ta yi tana ta juye-juye tamkar wata maciya. Ganin bacci ya ƙauracewa idanunta, sai ta tashi ta yi alwala. Addu'a sosai ta yi goshinta na ƙasa. Tasha kuka tana kaiwa sarki ɗaya wanda ba shi da abokin tarayya a gurin bauta, da ya bayyana musu Ahmad in yana raye, sannan ta yi sallar istikhara kan sana'ar da za ta fara. Kwanciya ta yi kan daddumar bacci mai ƙarfi ya kwashe ta. Saboda ruwan da aka yi cikin dare, sai bacci ya yi mata daɗi. Ba ta tashi ba sai kusan bakwai don ta makara. Da sauri ta yi alwala ta yi sallah sannan ta tashi Nasreen. Kicin ta nufa don ta ga abin da za a girka, sai ta ga ya ije musu taliya leda ɗaya da kayan miya. Ba ta ji wani abu ba, domin idan da sabo ta saba, za ta iya cewa yanzu ta samu ci gaba, tun da albarkacin auren da ya yi ba ya bari sai ya dawo ta yi girki. Komawa ɗaki ta yi, ta ɗauki kudi don ta siya wa Raihan indomie ta dafa mata, domin kafin ta gama lokaci ya ƙure. Duk da saurin da ta yi, hakan bai hana yin lattin ba. Tana tsaye a falo tana gyara ma Raihan zaman hijabinta ya fito. Da alamu fita zai yi. "Ina kwana?" Ta ce masa ba tare da ta kalli inda yake ba. Shi ma bai kalle ta ba, ballantana ya kalli 'yarsa ya sa ya kai ya fice. Sai ta miƙe tana kallonsa tare da mamakinsa. Inda ace uban ƙwarai ne yadda Raihan ta yi lattin. Jikinsa na rawa zai kaita. Ba za ta ce masa bai san darajar karatun ba, tun da da karatun yake cin abinci, yaran ne kawai ba ya so. Bayan ta kai Raihan ta dawo kasancewar ya fita, sai kawai ta faɗa gyaran gidan sai da ta gama ta ɗora girkin. Tana zuba taliyar Rashida ta fito. Ganin abin da take yi sai ta ƙarasa gurinta cikin ɓacin rai. Yunwa take ji sosai, saboda dankalin da aka yi ba ta ci sosai ba. Amaimakon ya yi mata daɗi ƙarnin ƙwan ya dame ta, sannan da dadddare shinkafa da mai da ya ji shi ma ba ta ci da yawa ba. Ita a rayuwarta tana don cimma mai daɗi, a lokacin tana gida duk inda za ta samu kuɗi ta ci abinci da kyau sai ta yi. Maza kuwa kullum cikin roƙon ayi mata take away take yi. Da zarar sun kira ta sun gaya mata za su zo. Buƙatar da za ta bijiro a kawo mata abinci. Ta saka a ranta a gidansa za ta ci abin da ta ga dama, amma sai ta ga saɓanin haka. Yanzu haka ma ganin taliya ake dafawa ya ƙara ƙular da ita za ta sauke fushinta kan Nasreen. Ko jiya sun kai kusan ƙarfe ɗaya tana masa magiyar ya canza cimar gidansa, amma ya shafawa idanunsa toka, ya yi kunnen uwar shegu da ita, domin da ga ƙarshe filo ya sanya ya toshe kunninsa. Da ya ga ba zai yi ba, sai ya ɗauko wayarsa ya sanya iyafis ya barta tana ta ɓaɓatu. "Sai yanzu kika da damar girki?" Ta furta a gajarce tana kallonta. Jin abin da ta ce ya sanya ta yi murmushi ta kalle ta."Akwai uban da na ke yi wa aiki?" "Babu, amma shi wanda ya aure ki ya ga kin fi dacewar ki tsaya a matsayin kukunsa." "Alhamdulillah tun da kin ce babu kin samu amsar tambayarki." "Ke ni fa ba sa'arki bace, domin ko kalona kika yi kin san babu abin da za ki mora a jikina."Ta ƙarashe maganar tana juya makamakan mazaunanta. Eh tabbas in har ta ce za ta yi faɗa da ita, san babu abin da za ta tsira, amma duk da hakan sai ba ta karaya ba." Ni ba ni da lokacin ki saboda ban dawo don na rinƙa faɗa ba." Tsaki ta ji jin abin da ta ce,"Wallahi zan yi maganin ki da ke har mijinki." "Allah kawai ke da wannan ikon." Ta ba ta amsa tare da ɗaukar ruwa tana wanke albasa. Tsaki ta yi ta juya ta fita. A falo ta zauna ta kunna kallo. Ƙara ta ƙure sosai kuma waka ake yi. Nasreen ba ta kula ta ba. Ta gama abincin sannan ta ibi nata ta fito zata shiga ɗakinta. Rashida da take tsaye tana rawa tana juya mazaunanta ganinta ya sanya ta ƙara ƙaimi. Kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kanta, domin abin dariya ya bata. In tana mata gwaɗashe da jikinta ba da shi, sam hakan ba zai dame ta ba, domin Allah ya halicce ta. Tana son kiɓa amma bata fatan ta yi irin nata da ya wuce misali. Bayan ta karya sai ta hau Whatsap. Ganin Maman Muwaddat, ta tura mata hotunan hijaban da za ta ɗaura a status, ya sanya ɗora sannan ta shiga facebook ta yi posting. Sauka ta yi sannan ta ɗauki littafan makarantarta tana dubawa. Tana ta karatun har zuwa karfe ɗaya. Bayan ta yi sallah ta miƙe don ta shirya ta ɗauko Raihan. Tana tafiya wayar Mama ta shigo da sauri ta ɗauka. "hello mama," "Na'am kina lafiya?" "Lafiya lau, ɗazu ka kira ba ki ɗaya ba?" "Eh ina sallah da kuma na gama sai wayar ta mutu babu caji, ya zaman na ku?" Ta karashe maganar da tambaya. "Lafiya lau Mama." "To ki ci gaba da haƙuri Allah ya yi miki albarka." "Amin," Ta amsa sannan ta kashe wayar. Rungume wayar ta yi tana jin ƙaunarta. Fatanta Ubangiji ya ba ta abin da za ta ɗauke ɗawainiyarsu, ta zame gurbin Ya Ahmad ko ta yi fiye da shi. Kamar yadda ba ta yi tunanin zai dawo ɗakinta ba, haka ya faru domin har ta yi sati ɗaya a gidan bai leƙo inda take ba. Hakan bai dame ta domin tafi bukatar ya yi rayuwarsa ta yi nata. Ta ci gaba da harkanta cikin kwanciyar hankali. Faruk kuwa da biyu ya yi, ya yi haka ne don ta gane yanzu ba ta a gabansa, amma sai ya ga ko a kwalara rigarta. Ganin duk abin da yake yi sam ba ta damuwa, sai ya tsiri zama da Rashida a falo su yi ta rungume-rungume yana shafa jikinta. Hakan ba ƙaramin tayar da hankalinta ya yi ba saboda tarbiyar yaranta. Da fari ba ta nuna musu komai ba, sai ta rinƙa kulle su a ɗaki. In suka damu za su fito su yi kallo, sai ta kunna musu a wayarta. Duk a kan wannan ta yi alƙawarin ba za ta tanka masa ba, ballanatana ya yi tunanin ko tana kishinsa ne. Duk abin da yake mata sai tana kawar da idanunta, wanda hakan ba ƙaramin ɓata masa rai ya ke yi ba. Ya so ace ta tanka ya nuna mata iyakarta, musamman yanzu da take masa wani gani-gani. *_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 4 Da daddare bayan ta kwanta duka lokacin bai fi ƙarfe tara da rabi ba. So take su Raihan su yi bacci ta karɓi wayarta, ta ci gaba da karanta wani littafi mai suna "Sakacina ko halin maza" wanda Jamila Lawal Zango jamsy ta rubuta. Sam ba ta da ra'ayin karatun novel, domin asali tana kallon masu karantawa a mutanen da ba su da aiki, musamman da ta ji ana maganar Marubuta ba su da aiki sai rubutun batsa, da sanya mata su yi rashin kunya ga mazajensu, amma sai Maman Muwaddat ta yi recommending ɗin ta a kan ta ƙaranta litaffin saboda tsayuwarsa da ilmin dake ciki, kuma yana ɗauke da kewa, musamman ita da take cikin kaɗaici, wannan dalilin ya sa ta yarda ta tura mata labarin duk da cewar hankalinta bai kwanta ta fara karatun Hausa novel ba, amma kuma ba ta son ta ƙaryar mata da gwiwa. Don haka ta tura mata ta fara karanta. Da fari ta ji kamar ta daina, saboda ba ta jin wani daɗin karatun, tun da ba ta saba ba, amma da ta jure, sai ta fara jin daɗinsa, ta ji tana son ta kai ƙarshen labarin ganin yadda jarumar ta ke shan wahala, tare da mamakin ɗaya jarumar Zainab da ta yi watsi da damarta Allah ya ba ta mijin da yake mugun sonta, amma sakacinta da sakarcinta ya sanya wata ta ƙwace mata shi.Tunanin jarumar labarin take Juwairiya yadda ta sha gwagwarmayar rayuwa. Tabbas Allah ya jarrabce ta da ta yi rayuwa a gidan mijinta a matsayin 'yar aikin matarsa, alhalin babu wanda take so kamarsa, duk da cewar babu wanda ya ja mata sai mugun ƙanin babanta Bana Sani. Saboda cakwakiyar da ke littafin ta ƙasa su yi bacci ta ga yadda za ayi da ta yi auren kwangila don ta haifi yaro ya bawa matarsa. Tsananin mamakin mugun son zuciyar M.D da son matarsa da ya rufe masa ido ya kamata. Sai duk ta ƙosa ta ga ƙarshen labarin. Saboda zumuɗin ta ƙarshe karanta labarin ta fisge wayar tana faɗin,"Raihan ku yi barci gobe zan sanya muku karatu zan yi." Raihna ta saka kuka tare da miƙa mata hannu tana faɗin,"Umma, don Allah ki ba ni cartoon ɗin ya kusa ƙare wa." "Ba zan ba ki ba, na ƙasa na ga shin in Zainab ta gane matarsa ce ya za a.." Maganar ta maƙale sakamakon jin ihun faruk da Rashida wanda ya tabbatar mata da saduwa suke yi. Hankalinta ya tashi matuƙa har sai da ta kasa ganin abin da yake rubuce a wayar. Tana cikin wannan tashin hankalin ta ji Raihan ta ce,"Umma Abba da Anty Rashida na kuk.." Toshe mata baki ta yi tana hawaye."Ba kuka suke yi ba, al'janu ne suke kwaikwayon irin kukan su, maza ki kwanta kar su cinye ki" Tsananin tsoro ya kamata da sauri ta kwanta ta rufe fuskarta da bargo. Nasreen kuwa tsabar takaici ya kamata. Saboda ganin rashin hankali sai ta ji kamar ta je ta yi musu rashin mutunci. Karatun qur'ani ta sanya a wayar ta kai ta kusa da kunninta, ta yadda ba za ta ji ihun ba, a zuciyarsa ta sa ya sai ta yi masa magana, domin ba za ta yarda ya ɓata tarbuyar yaranta ba." Sai da ta daina jin ihun sannan ta kashe wayar. Karatun da ba ta yi ba kenan, saboda takaici ta kwanta bacci. Washegari da safe bayan ta kammala musu abin kari. Tana zaune a falo ya fito cikin shirin fita. Ganinta zaune ya ɗauke kansa bayan ya wurgar mata harara. Tana lura da ya fito ta miƙe. "Ina son magana da kai." Ta ce masa tare da shan gabanta. Kallonta ya yi a wulaƙance, kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya ja ya tsaya."Ina fatan ba ƙorafi za ki yi mini kan bana kwana a ɗakin ki ba? Saboda kin san ba zan zo ba, don na samu wacce take da duk bin da na ke so." Jin abin da ya ce ya sa ya ta saki murmushin takaici."Saboda me zan tambaye ka? An gaya maka na dawo don ina son na ci gaba da rayuwar aure da kai ne?" "Na sani shi ya sa na ije ki a matsayin yar aiki." Ya ba ta amsa yana mata kallon mugunta. "Lokaci ne komai zai wuce kuma ya zama tarihi." Ta ce masa kafin ya yi wata magana sai ta katse shi ta hanyar cewa,"Abin da kake yi kana tunanin wayewa ce? Kana da yara za ka zauna kana aikata haka? Dole yin hakan zai bayyana cewa ka samu macen da take iya biya maka buƙatunka?" "Kina kishin haka tun da kin kasa yi?" "Ko ɗaya ina dai maka nasiha ne saboda ba shi da alfanu, duba ga kana da yara kuma sam ba tsarin addi..." "Ke!" Ya daka mata tsawa cikin ɓacin rai." kin isa ki kafa mini doka a cikin gidana? Ko da uban wani aka gida?" Ya ce mata yana zare idanunta. "Ko ɗaya ina dai gaya maka ka bari ko don yaranka." "To ba zan bari ba, kuma haka na yi ra'ayi zan cigaba. Idan ke kin kasa sanya ni a cikin wannan dadin na damu sai ki yi baƙinciki?" "To shikenan, tun da haka ka ce inka so ka cika duniya da ihu." Ta ce masa tare da galla masa harara ta shige ɗakinta. "Lallai yarinyar nan ta raina ni." Ya ce yana jinjina kansa. Wata zuciya ta ba shi shawarar ya je ya yi mata tijara, amma kuka sai ya fasa, a tunaninsa kishi ya sanya ta yi masa magana. Ficewa daga gidan ya yi. Tun daga nan suka tsiro haka abun babu kyan tsari. Ganin haka da an yi magariba su Raihan sun ci abinci za ta sanya su baccin dole. Hakan da ta yi ta samu ta shawo kan damuwarta. Da suka ga ba ta ƙara musu magana ba, sai ya tsiri zama a farko yana ma Rashida waƙa. Nasreen duk ta zo wucewa sai su kwashe da dariya Faruk ya fara waƙa yana cewa," Kalarki kalar ajebota jiki duk madara ko ina yana rawa." Rashida kuwa sai ta yi ta jin daɗi tana juya masa jikin. Ranar da ya fara dariya ya ba ta, saboda gani take kamar jahilci ya sanya shi yin wakan. A haka dai suka ci gaba da zama sam ba ya shiga cikin sabgarta. Kamar wasa ta fara zuwa da hijaban makaranta, sai ga shi mutane da yawa sun siya. Ba a ɗauki tsawon lokaci ba ya suka ƙare. Ita kanta mamaki ta rinƙa yi, domin wasu har cewa aka yi ta kawo. Cikin farin ciki ta cire ribarta ta kawo mata kuɗin. Maman Muwaddat ta kalle ta ta ce,"Dama sana'a sa'a ce. Da gwaji in kina da abinci, sai ki ga Ubangiji ya dafa miki. Nima da haka na fara kamar wasa ya bani shawarar, amma yanzu har a unguwar nan ana saye. Kina nan tallar da kike yi a social media suma za su siya. Da sannu yaro ke iya tafiya. Wallahi in har kina sana'a za ki samu sauƙin rayuwa." "Sosai Maman Muwaddat kin san kuɗin nan da nake gani, duk da ba nawa bane, wallahi ba ki ji yadda na ke ji ba." "Za ki ji kuma bari na gaya miki sirri na sana'a, kin ga wannan dubu ashirin da biyar da kika samu? Kamata ya yi ace kin fara sai da ko da 'yan kunnaye ne da su, sai ki yi amfani da biyar ɗin, sai ki ga kin samu karin kanki." Jim ta yi sai kuma ta kalle ta ta ce,"Kuma kin kawo shawara wallahi, amma kin san na fita na je kasuwa wata matsalar za..." "Ai dama ba zuwa za ki yi ba, yanzu fa rayuwarmu a sauƙaƙe take. Ƙanina zan turawa kuɗin sai suyi ya tura miki a mota. Kuma ana samun riba sosai za ki yi dariya." "Allah ina ga haka za a yi, saboda ba ki ji farin cikin da na ji ba, gaskiya riƙe kudi rahma ne." Dariya suka kwashe suka tafa."Ba ki ji ance kuɗi sune abokan rayuwa, duk iskancin da Faruk yake miki, da ace ya san kina da su, kin ji na rantse ko zai yi kaɗan tun da shi tajararre ne." "Hmmmmh! Allah dai ya shirya sa, amma Faruk ya yi nisa." Ta ce tana gyara zamanta. "Har yanzu ba ya kwana a ɗakinki?" "Ya kwana? An gaya miki yana ƙaunata ne? Baba ke tilasta masa zama da ni, amma Faruk ba shi da maƙiya kamata." Ta ce cikin takaici. "Ki ci gaba da haƙuri kar ki sanya damuwa don baya kwana." "Wallahi ban damu ba, saboda sam ba shi a gabana. Kawai iskancin da yake yi ne yake damuna." "Duk zai wuce in kika jure komai zai zama tarihi. Zaƙaƙa fari yake mata, in dai Faruk ne. Kina ganin za ta ci gaba da jure maƙonsa?" "Ina fa ko jiya sai da suka yi a kan ya fito mata madara sachet ɗaya na naira ɗari." "Kina nan za ki ji sun yi uwar watsi zama da Faruk, sai ke da ake miki dole." Ta ce tana kallonta. "Ko ni haƙurina ya zo ƙarshe ai." "Kin ga yanzu bari na yi masa transfer na kuɗin nan, don a ɗinka mana hijaban a kawo da wuri." "Gaskiya ki tura masa sa dubu ashirin ɗin sai na riƙe biyar na turawa Mama su yi amfani da shi." "To bari na yi masa yanzu." Ta ce tare da ɗaukar wayar ta. Ba ta bar gidan ba sai, da ta huta saboda dama daga makaranta take. Da su Raihan suka dawo, sannan suka koma gida. Kicin ta nufa ta ɗora girki ta zauna a kicin ɗin ita da yara. Suna wasa tana karanta wani littafin mai suna ranar wanka duk na Jamila Lawal Zango, don har ta gama Sakacina. So take ta rinƙa karatun saboda akwai tarin ilmi a ciki, sannan ga ɗebe kewa. Tun da ta fara karatun tunaninta yadda ƙarshen book ɗin zai kasance sam ba ta da lokacin shiga ƙunci da damuwa. A fara karatun ta ko yi darussa da dama. Duk wani abin da jarumar take yi na gari take ƙoƙarin koya. Kamar su kula da ibada tsafta, gyara jiki da kuma yanayin zamantakewa da al'umma. Hatta gyaran jiki sai ta ji tana don ta fara duk da cewar wani lokacin rashin kuɗi yake hanata. Abin mamaki Nasreen da kullum tana cikin damuwa, tare da tunanin rayuwarta babu wani amfani, sai ga shi ta sayi lalli da kurkur ta shafa a fuskarta. A lokacin da ta je gidan Maman Muwaddat ta ce mata."Don Allah ina son ƙunshin da aka yi miki wanda ya fita, ya yi mini kyau in son na yi." Kallonta ta yi galala cikin tsananin mamaki."Nasreen ke ce za ki yi ƙunshi? Zan iya cewa na manta rabon da ki yi ƙunshi, duk irin nacin da na ke miki da minti, saboda kina da haske ƙunshi ba ƙaramin ɗaukar ki zai yi ba." "Ada ina tunanin tun da miji ba ya sona wa zan yi wa, amma kin san yanzu da na fara karatun novel sai kawai na ji ina son na yi don na gyara kaina, kuma na gani na yi sha'awa. Ni fa na cire takaicin ɗa namiji rayuwata zan yi mai daɗi, saboda in ba haka na yi ba wataƙila sai dai na yi bugga." "Haka ya kamata dama, saboda in har kika sanya abin a ranki, to ke za ki yi wa kanki asara." "Wallahi kuwa ga takaicin miji ga na mahaifina." "Allah ya kawo miki mafita." Ta ba ta amsa tana ƙoƙarin ɗaukar wayarta. "Bari na kira mai ƙunshi har gida take zuwa ta yi mini, da ma ina son ya yi mini kitso, sai ta fara miki lallin kin san Allah saboda farinciki ni zan biya." Dariya ta yi ta ce,"Kai Maman Muwaddat, zan biya akwai 2k a hannuna, kuma ni ma zan yi kitson." "To bari na kirata dai ta yi mana tun da akwai sauran time, kuma tana da sauri, amma kafin ta zo ki tsife na wanke miki sai na budar Miki." "To aikuwa na gode da yake kitson ba shi da waya." Ta ƙarashe maganar tare da cire hijabinta, ta saɓule gashin kanta. Tana da gashi sosai ga shi baƙi Ana busar da kan mai ƙunshin ta zo. Zuwa uku da rabi ta kammala har ta fara wa Maman Muwaddat. Ƙunshi ya yi kyau sosai. Nasreen ana mata tana karatunta. Da aka gama sai ta kalli ƙunshi cikin farin ciki ganin yadda ya yi kyau. Bayan an gama ta koma gida wanka ta yi, sannan ta saka doguwar riga ta fito kicin. Abinci ta ɗora suka dawo falo suna kallo, saboda Rashida ba ta nan. Ba su jima a falon ba ta dawo hannu ta cike da kaya. Babu sallama ta shigo kamar ba musulma ba, kai tsaye ɗaki ta wuce ta yi wanka, sannan ta fito ta zauna a falo. Wani banzan kallo ta wurgar mata tare da ɗaukar remote ta canza tashar daga catoon da su Raihan suke kallo zuwa Nigeria Film. Ganin haka Musaddik ya saka kuka yana kallonta. Da sauri ta ɗauke shi ta kama hannun Raihan. "Ku zo mu je na kunna muku a wayata." Babu musu suka bita. Wawan tsaki ta tsaki tare da gyara zama tana cewa,"Na ɗauka za ki karba ki mayar musu, sai na gaya miki wanda ya haife su ba ya ƙaunarsu." Bata tanka mata ba ta wuce ciki abinta. Sai da ta kunna musu sannan ta koma kicin ta ci gaba da girkinta. Rashida kuwa da ta shigo cikin dakin a lokacin da ta dawo. Ganinta a falon babu ɗankwali da kuma ƙunshi inda ta yi, sai da ya sanya gabanta ya fadi. Ta yi kyau sosai da gaske. Lallin da take shafawa ƙwana biyu ya ƙara hasken fuskarta. In ban da rashin ƙiba sai ta ce tana cikin matan da za a iya sanya su a cikin kyawawan jerin farko. Wani irin mugun kishinta ya kamata. Bisa wannan dalilin ya sanya ta fito falon don ta kore ta, duk da ta san cewar ba ta a gabansa, amma kyawun da ta yi ya firgita ta. Tana zaune har ta kammala abincin ta ibo nasu ta shige ciki. Da sauri ta tashi ta shiga ɗaki ta ɗauki maganin da Malam ya ba ta. Zubawa a cikin abincin Faruk ta yi tana faɗin,"Yau zan yi wannan shegen maƙon naka, ace mutum sam ba ya ƙwantaluwa." Bayan ta gama zubawa ta juya sannan ya koma ta zauna a falon. Tana zaune aka yi magariba, amma ta ci gaba da kallonta, ba tare da ta damu ta yi sallar ba. Har aka yi isha'i ba ta tashi ba. Sai da ta ji motar Faruk sannan ta miƙe ta buɗe masa ƙofa. Tana shigowa ta faɗa jikinsa tana masa shagwaɓa. Shi kuma ya wani susuce. Bayan ya yi wanka ya ci abincin sosai. Cikin jin dadi take kallonsa ganin yadda y ci sosai. A ranar ta yi masa duk abin da yake so, wanda hakan ya ƙara sanya ya shi zuzucewa, yana tunanin duk soyayya ce, ba tare da sanin abin da ke zuciyarsa ba. Cikin sama magani ya fara cin Faruk. Wani irin mugun ƙauna yake mata kamar zai lashe ta. Ganin haka sai ta kalle sa ta ce,"Baby gaskiya bana son cimar da muke yi, ya kamata ka raba mana abinci, tun da ita ta saba." Zuciyarta na bugawa domin a tunanin ta ta ɗauka zai taso mata ne, amma ga mamakinta sai ta ga ya kalle ta ya rungume ta, tare da kai bakinsa cikin nata. "Ba ki da matsala anjima sai mu fita mu siyo duk abin da kike so, ita kuma sai na rinƙa ba ta nata." Jin abin da ya ce sai ya sanya ta cikin farin ciki sosai. Ganin tarkonta ya kama kurciya zai zamo mata janitalau. Da yamma kamar yadda ya gaya mata suka fita. A kayan abincin har da su indomie ƙwai madara milo duk wani abin kayan ci. Bushashshen kifi da su ƙwai. Siyayya taga-raga ya yi mata ita kanta sai da ta yi mamaki, saboda cewa ya yi ta zaɓi duk abin da take so. Da suka dawo Nasreen ta cika da mamaki. Satan kallon siyayyar take yi tana mamaki. A zuciyarta tabbata ba a cikin hayyacinsa ya yi ba, sai dai in ta bi ta bayan ƙasa, domin Faruk ko mai za ta yi masa maƙonsa a jininsa yake. Hatta 'yan'uwansa fama suke da shi. Shi kansa a irin rayuwar da yake yi status ɗin da ya wuce haka. A store aka sanya kayan sannan ta kulle abinta. Farouk ya tsaya a falon yana kallonta."Daga yau na raba muku girki, zan rinƙa ba ki na ki da kaina, ita kuma za ta rinka mana ni da ita da abincin da yake store." Ya ce mata cikin ɗaurarriyar fuska yana kallonta. "Ok ba matsala." Iya abin da ta ce masa kenan ta mayar da kanta ba tare da ta kalle shi ba. Jin abin da ta ce sai ya kalle ta. Ya lura da ita kwanakin nan ta saki har ɗan murmurewa ta yi. Mamaki yake ganin ko da yaushe tana cikin ɗakinta. In dai ba girki za ta yi ba, kuka hakan ba ta nuna alamun ya dameta. "Ko tana waya da su Marwana?" Ya yi ma kansa tambayar yana girgiza kansa, domin ya san yadda suka yi rabuwar rashin mutunci da wuya, wai auren mace da ciki. "To mai take yi?" Ya yi ma kansa tambayar yana son gano canjin da yake hange daga gare ta. In da ace ada ne sai ta yi masa ƙarafi, amma yanzu ya lura ko kallon sa ba ta son yi, ballanatana dogon magana. Nasreen ganin ya tsaya mata a kai kamar soja yana kallonta, sai ta miƙa tana cije baki, saboda ta yaye Musaddik nonota zafi yake mata. Ɗauki ta shige hankalinta kwance. Kallo ya raka ta da shi yana mamakin canjin da ta samu. Ko fuskarta ya bayyana farinciki, saboda ada kullum kamar ta yi kuka, amma yanzu har wani annuri yake gani a fuskar. Zuciyarsa ya fara zargin wayarta don haka ya ɗau alƙawarin sai ya duba. Washegari aka gyara gyara garin aka sanya drinks. Wannan lamarin sai ya ba ta mamaki. Rayuwarsa ta zamo ta 'yan gayu, sai daɗi suke ci, saboda kullum in zai dawo, sai ya yi mata take away. Ko ya siyo mata nama ba ta san ran ci, domin ba ta sanya wa a ka za a bata, kuma kamar yadda ta yi tunani haka suke cinyewa. Wani irin love ake zubawa a cikin gidan. Ita kam dariya suke ba ta, duk da cewar wani abun da biyu ake mata. Kamar yadda yake ba su abinci haka yake bayarwa, domin mai da yaji yafi yawa. Ba a kwana biyu bai ce mai da yaji za su ci ba. Sam bai dame ta ba, saboda yanzu ba shi a gabanta. Burunta ta kammala karatunta, ta samu aiki ta rabu da shi. Da aka kawo hijaban da ɗan kunnayen ta cigaba da siyarwa a makaranta. Sosai take yin ciniki har ɗan kunnayen, domin Maman Muwaddat ta sa ya yarinya sun kai mata maƙota. Saboda ba a shiga gidanta, sai dai in ana so ta yi mata waya ta kawo. Ganin haka sai ta raba biyu ta ije a gidanta. *_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 5 Da aka kawo hijaban, da ɗan kunnayen ta cigaba da siyarwa a makaranta. Sosai take yin ciniki har ɗan kunnayen, domin Maman Muwaddat ta sa ya yarinya sun kai mata maƙota. Saboda ba a shiga gidanta, sai dai in ana so ta yi mata waya ta kawo. Ganin haka sai ta raba biyu, ta ije a gidanta. Nasreen ta cika da mamaki, da aka fara mata maganar ana son hijaban ta online. Da fari ta ɗauka ba siyan kaya ta midiya, amma ga mamakin ya sai wata ta kirata za ta canza hijabai taba son guda goma. Kamar wasa ta gaya mata kuɗin tare da tura account number, sai ga shi ta yi mata transfer. Mamaki ya cika ta da sauri ta kira ƙaninta ya kai mata kayan. Tun daga lokacin ciniki ya ɓalle. Har ɗan wani kiɓa ta yi ta canza. Da aka sayar da hijaban sai ta haɗa kuɗi ta cire ribarta. Siyayya ta yi musu ma ɗan abin da ba a rasa ba, musamman abin da Raihan za ta je makaranta da shi. A cikin kuɗin har hijabai biyu jalbab ta siyasa kanta da Raihan. Sosai take jin ɗadin sana'ar tana godewa Maman Muwaddat, tun da ga shi har za ta saya wa kanta abin da take so, kuma ta taimakawa Mama. Washegari da safe, tana zaune a falo saboda ba ta da lecture. Wayarta riƙe a hannunta tana karanta littafi. Daidai lokacin da Faruk ya fito zai fita aiki, sai ta karanta gurin dariya, wani irin dariya ta kece da shi har da riƙe ciki ta duƙa. Mamaki ya kamasa, tsayawa ya yi yana kalonta, wacce ba ta san yana gurin ba. Nasreen garin dariya har da hawaye. Farouk kuwa sai ya tsaya ya kasa karasawa gurinta. Zai iya cewa tun da yake da ita, bai taɓa ganin ta yi dariya haka ba. Da sauri ya ƙasa ya fisge wayar. "Da uban wa kike chatting?" Ya ce mata tare da kallon wayar yana son ya gani. Da sauri ta ɗago kanta kallonsa jin abin da ya ce. Da fari har ta tsorata ta, don ba ta san yana tsaye ba. "Ka ba ni wayata." Ta ce masa tare da miƙa hannu. Duba wayar ya yi yana kallon facebook da kuma Whatsapp ɗin da ta buɗe,"Uban wa ya ba ki damar buɗe su?" Ya ce mata yana zare mata idanu, domin a tunaninsa su take kallo ya sa ya sanya ta yi dariya, don bai ga numbar da zai zarge ta ba. "Saboda ina buƙatarsu." Ta ce masa cikin gatsali. "To na hana ki hawa midiya daga yau, din bana kaunar na ga kina farinciki." "Wallahi ka yi kaɗan, don ba zai daina abin da yake kawo mini farinciki ba." Ta ce masa tana kallon sa. "Sai na ga da wani wayar za ki yi." Ya ce tare da saka wayar a aljihu. Takaici ya sa ta kalle shi kawai. Tana ƙoƙarin kamasa ta riƙe ya ɗaga wayar. "Zan fasa wayar nan kina ƙara magana, wallahi sai na fasa ta." Ya ce fuskarsa na gasganta abin da yake fada. Ta san zai iya sai kawai ta kalle shi gudu ta yi ɗakinta, amma a ranta ta sanya wallahi dai ya ba ta, in ba haka ba sai ta ɗauki wani abu na sa ta lalata. Faruk da ya isa ofis bincike ya yi sosai a cikin wayar, yana fatan ganin wani abu da zai sanya ya tozarta, amma har ya ƙara shi bincikensa, bai ga koma ba sai tarin groups na siye da siyarwa. Ransa ne ya ɓaci, ganin sana'a take yi. Mamakin inda ta samu kudin da ta fara jari ya yi, duk da ya san za ta iya samu. Komai ya goge na cikin wayar, sannan ya ije ta a ofis. Da ya tashi aiki gidan su Nasreen ya wuce, ya gaya wa Baba ƙarya da gaskiyar sannan umurce sa da ya sanyaya dole ta daina rike wayar, saboda ganin yadda take ciniki ya tsorata shi, domin in ta ci gaba za ta iya rike kanta watarana.Baba ya yi masa alkawarin zuwa gidan gidan don ya ja mata kunnin. "No zan kawo ta gidan da dadddare." Ya ce masa cikin ɓacin rai. "Yauwa hakan zai fi yadda zan yi mata kaca-kaca. Ina ga yarinyar nan bokon da Amadu ya sanya ta shi yake ƙara mayar da ita mara jin magana." Ba tare da ya ce masa komai ba ya tafi. Cikin tsananin takaici. Haka ta wuni sukuku. Da magariba tana zaune bayan ta idar da salla. Bata tashi daga gurin ba, ya shigo "Ki zo mu je gida Babanki yana son ganinki." Ya faɗa fuskarsa a ɗaure. Bata tanka masa ba ta miƙe jin abinda ya ce. Ganin haka ya sa ya shi fara tafiya ta bi bayansa. Mamakin ta yake yi yadda ta dawo masa kamar kurma. Tun da ta shiga cikin motar ta yi shiru, a zuciyarsa ta shirya duk abin da Baba zai ce, amma ta rantse ba za ta daina amfani da wayar ba. Da suka isa cikin ɗakin Baba suka shiga. Tana kallonsa yadda yake yi wa dakin kallon ƙaskanci. Ko kujerar tsugunon da aka kawo masa da kyar ya iya zama. Ɗakin ciki ɗaya ne sai tabarmar don shi kansa ba shi da katifa. "Ke Nasreen ba za ki daina ma mijin ki rashin kunya ba ko, saboda ya gaya mini ba ki da lokacinsa, kullum kina kan waya kina danne-danne. Don ya ce ki daina kike masa zafin fitar arziki.Don ubanki yaushe kika ga mahaifinyarki ta zage ni?" Kalonsa ta yi da ya ɗauke fuska, ba tare da kunyar ƙaryata da ya yi mata ba. Cikin damuwa ta kalle shi ta ce,"Ban zage shi ba, amma na gaya masa wallahi Baba wanda ya isa ya raba ni da wayar, saboda in ya karɓe wancan xan ƙara siya." "Au Nasreen yaushe kika fanɗare har ni kike wa fitsarar?" Ya ce cikin mamaki yana kallonta jin tana magana, domin ada in ya kawo ƙararta sai kuka. "Gara ta yi maka sai ka san haƙuri na ke yi da ita, saboda tun da ta dawo ta canza." Ya ce da murya mai ƙarfi yana kallonta. "Ka yi hakuri Baba, ni ba rashin kunya nake maka ba, gaskiya ne ke faɗa. Sana'a na ke yi da wayar, ina samun kuɗi ina yi wa kaina buƙata, saboda Faruk cimar wahala yake bani. In ya ga dama sai ya kwana uku yana bani mai da ya ji.." "Au ba ki gode ba wai suna ne ma basu samu ba." "Gaya mata kasan ba ta da godiyar Allah. Ni dai na shiga uku na auri mace mara tarbiyya." "To ka sake ni mana ko ɗaure maka ni aka yi a ƙafa?" Ta ce masa tana kallonsa cikin ɓacin rai jin abin da ya ce Dariyar mugunta ya yi,"Ba zan sake ki ba haka, za ki ci gaba da zama a gidana, kula na hana ki amfani da wayar." "Wallahi ba zan daina amfani da waya ba, sai dai ka yi abin da za ka yi." Ta ce masa agadare. "To shikenan mu zuba mu gani." Ya ce yana mamakin ta domin ta canza sosai. "In har kana son ta ci gaba da zama sai ka sanya ta daina amfani da wayar." Ya ƙarashe maganar tare da ficewa daga ɗakin "Ke ta shi ki nushi kar ya tafi, sannan in dai ni na haife ki kar ki ƙara sayen wayar ko kuma ki sayi mai botira." "Ka yi haƙuri amma ba zan daina sanata ba, ina fatan na ɗauki ɗawainiyar da Ya Ahmad yake yi." "Au Nasreen.." Ya ce yana neman abin duka da sauri ta fice a zuciyarta tana jin ko sama da ƙasa za ta haɗe babu wanda ya isa ya hanata. A mota yana ta suratansa ta yi banza da shi. Ganin ba ta kula shi ba ya yi shiru. Da suka koma ta kwanta duk sai ta ji ta takura, saboda ta saba da wayar tana ɗebe mata kewa. Washegari da safe ta kira musa ta bashi daira dubu sha biyar."Wayar dubu sha biyar sam ba za ki ji dadin ta ba, zan cika miki sha biyar da kuɗin neco da na ke tarawa zan sake yi, tun da da sauran lokaci sai ki mayar mini, duk da ita ma ba wani daɗinta za ki ji ba, kin san yanzu wayoyin suna tsada." "Haka nan na yi maneji tun da ya ƙwace na gode kafin lokacin zan cika maka." Kwana biyu ya kawo mata wayar. Kallonta ta yi don ba ta kwanta mata ba, amma da babu gara ba daɗi. A gurin Maman Muwaddat ta karɓi kuɗi ta yi welcome back na layinta, ta ci gaba da harkanta ba tare da ya sani ba. Farouk kuwa tun yana tunanin za ta ƙara masa maganar wayar, sai ya ga kallon kirki baya samu daga gare ta, ta ci gaba da sabgarta. Hakan ya baƙanta masa rai, domin ya so ace ta nace ya samu abin duka. Ganin haka sai ya yanke shawarar ya rinƙa zuwa ɗakinta watarana ya kwana ya ga abin da take yi, take ba ta farinciki. Da ya sanar wa Rashida zai kwana ba ƙaramin tsuya suka yi ba. Har sai da ya yi mata alkawari kallon banza ba zai hada su ba. Mamakinsa yake yi yadda take sa ya shi abu ba tare da yana so ba, musamman siyayyar da yake mata, amma sai ya ji dole sai ya yi. A tujaninsa a buɗe take barin ɗakin don haka ya tura don ya mamaye ta, amma sai ya ji ta a kulle. Cikin ɓacin rai ya buga kofar da ƙarfi. Jin bugun ya tabbatar mata da shi ne. Da sauri ta kashe wayar Gabakiɗaya, ta buɗe ƙofar tana tunanin jarabar da ya kawo shi Ɗakin ya bi da idanun, kamar baƙo ganin yana ƙoƙarin shiga ya sa ya ta ba shi hanya. Zama kan gadon ya yi, wanda hakan ya ba ta mamaki. "Lafiya?" Ta ce masa tare da yin tsaye. "Ki tambaye ni tun da uban wani ya gina gidan" Ya ce tare da ɓalla mata harara. Jin abin da ya ce sai ta zauna kan stool taka kallon sa. Ganin ba ta tanka masa ba ya ce,"Kwana na zo yi, ko akwai uban da ya isa ya hana ni kwana da matata?" A maimakon ta amsa nushi ai ta saki dariya jin tambayar da ya yi mata. Gefen gadon ta kwana ba tare da ta ce masa komai ba. Ganin sun yi shiru bacci na son ɗaukar ta ya sanya shi tashi ya zauna."Ke tashi ina son magana da ke." Babu musu ta tashi ba tare da ta ce masa komai."Mai kike yi wanda yake sanya ki farinciki?" "Mai ya sa ka tambaye ni kuma so kake na tabbata cikin damuwa?" "Ya ina tambayarki kina mini?" Ya ce cikin fushi. "To ai tambayar tana ba ta da amsa." Jin abin da ta ce ya sanya shi matsawa kusa da ita."Wallahi zan yi matuƙar saɓa miki duk ranar da na ganki da wata wayar." Ya daɗe a dakin komai ya gani, sai ya fasa kwana ya saki tsaki ya fice daga ɗakin. Yana fita ta shi ta rufe ƙofarta. Rashida ta samu kan Faruk sosai take yin abin da take so a cikin gidan, domin har an kai mizanin da ta san pin ɗinsa. Shi kansa mamakin wani irin so da take mata, kamar zai kashe kansa. Gabakiɗaya ya juyawa 'yan'uwansa baya. Ko ita kanta Nasreen ta ga canji saboda watarana baya ba ta abincin da za ta ci. Ganin haka ta ƙara ƙaimi kan sana'arta, domin tana matuƙar rufa mata asiri. Wata tsirfa da ta tsiro sai ta shiga kicin ta yi girki ta ɓata ta bar shi haka. Tun Nasreen tana haƙuri har ta kai maƙura. Ta ɗauki aniyar duk ta yi girki za ta gyara iya inda kayanta yake, ta bar mata na. Haka kuwa aka yi ranar da ta yi girki da gayya ta ɓata gurin. Da ta shigo ta ga yadda gurin ya yi datti. Ita inda kayan kicin ɗin ta, kawai yake ta gyara. Bayan ta gama dafa musu shinkafa da mai da ya ji ta koma dakinta. Suna zaune suna ci ta boko kofa tana huci. Ba tare da ta kalle taba ta ci gaba da cin abincinta tana bawa Musaddik a baki."Uban wa kika bari ya gyara miki gurin?" "Uban da ya yi girki ya bata gurin." Ta ce mata hankalinta kwance ba tare da ta kalle ta. "Ke ni kike zagi?" Ta tambaye ta sai kawai ta ɗaure ta da mari. Marin ya shige ta sosai ita ma bata ta sauke hannu ba, ta mayar mata da nata sai da ta ga wuta."Lallai yarinyar nan yau kin tsokano tsiliyar dodo." Ta ce tana gyara hannun rigarta. Nasreen duk da ta ji tsoron don yadda ta fusata ta tabbatar yau sai buzunta, amma sai ba ta nuna mata ba."Jiki ya fi jiki ne?"Ta ce mata tana kallon ta. Har Rashida ta ɗaya hannu za ta cakume ta, sai ta ji ƙarar hon ɗin Faruk. Da sauri ta fita tana kuka. Jin kukanta hankalinsa ya tashi sosai."Lafiya mai ya faru?" Ya ce mata lokacin da ya karaso gurinta yana kama hannunta. "Wato Faruk ya na gaji da iskancin da yarinyar nan take mini. Ina haƙuri amma wallahi ba zan yarda ta ƙara marina ba?" "Mari?" ya tambayeta ba tare da bata lokaci ba ya shiga ciki, yana zuwa ya ɗauke tada mari. Tsananin mamaki ya kamata."Saboda zalunci ba za ka tambayi abin da ya faru ba sai ka mare ni?" "Tsoron ki na ke yi da zan tambaye ki?" Jin abin da ya ce sai ta lalle sa tana hawaye,"Allah ya sai ya saka mini, duk abin da ya faru yana gani shi zai yi mata alƙalanci." "Ka ji makirar yarinya? Mai na yi miki kawai fa na yi girki, bana jin dadi na ce ta gyara gurin shi ne kawai ta hau zagina." "Lallai Nasreen ba ki da kunya, kuma wallahi zan yi maganinki. Ma za ki je ki gyara gurin." Wani banzan kallo ta watsa musu."Wallahi babu wanda ya isa ya sanya na gyara abin da ba ni na bata ba. Girkin da in an yi sai dai na ji ƙamshi ni da yarana, amma sai dai ku cinye ku barmu da abinci kamar a gidan bursuna." "Shi yafi dacewa da ke, saboda na ga a gidanku ba kuma samun kamarsa." "Shi kenan ka ci gaba da yin rashin dalci Allah yana ganinka." "Wuce ki gyara gurin." Ya daka mata tsada yana faɗin haka. "Wallahi babu wanda ya isa ya sa ya ni." Ta ce ba tare da ta ji tsoronsa ba "Ok, dama tun da kika dawo ban taɓa lafiyarki, jikin ki ne yake miki ƙyaikyayi." Ya ce yana ƙoƙarin kwance bell. "Ƙyaleta hubbina karka duke ta." Ta kama hannunsa tana faɗin haka. "Da kin bar ni na taɓa lafiyarta." "No ka ƙyaleta haushin rashin kulawar da ba ka yi mata ne ya sanya." "Mai zan yi da ita bayan ina dake?" "Ni ma na tsane ka na tsane ka Faruk, kullum ina rokon Allah ya raba ni da kai." Ta ce tare da shigewa bayi ta rufe ƙofa. Tana jinsa yana suratansa ta yi banza da shi har sai da suka fita, sannan ta fito. Tana jinsa da zai fita yana faɗin,"Ki tabbatar da kin gyara kicin ɗin nan." "Sai na ga uban da ya isa ya sanya ni mugu azzalimi kawai." Ta ce tare da sanya wa ɗakinta makulli. Saboda sa'insar da suka yi sai da ya kwana biyu bai bata komai ba, ba tare da ta damu ba ta dauki kuɗinta ta yi girki. Ganin yadda sana'ar yake rufa mata asiri, sai ta godewa Allah da Maman Muwaddat da ta ba ta wannan shawarar. Jarrabawar su ta ƙarshe duke ƙoƙarin zanawa. Gabakiɗaya hankalinta yana kan karatu. Burunta sakamakon ta ya ci gaba da kyau har ta kammala. Cikin sa'a ta kammala karatunta. A ranar tasha kuka sosai har sai da muryarta ta rushe da ta tuno Ahmad, yadda ya sadaukar da rayuwarsa don ta samu ilmi. Kullum ba shi da burin ta kammala ta samu aiki. Ashe ba zai ga kammalawar ba. Marwana ita fa ta faɗo mata a rai, ta yi burin ta gama shekarar ta je masters a waje, sai ga shi a sanadin taimakon ta ita ta gama, amma ita ba ta a ƙasar. Ta yi kuka sosai. Ganin kuka ba shi da magani ta dawo gida cike da farin ciki. Rigimar da suka fara da Faruk ya kafe ba za ta yi service. Da ya sanar da Baba jinsa kawai ta yi, amma a ra ta ta sanya duk abinda zai faru sai dai ya faru. Baƙincikin kuɗin da za ta samu yake yi. Tana ganin kamar wasa bayan ta kammala karatun tana zaune ƙawarta ta kira ta kan ta je ta karbi takaddunta. Da ta shirya har za ta fita ba tare da sanin sa ba, sai kuma ta fasa sanin abin da zai haifar. Wayarta ta ɗauka ta lalubo lambarsa. Da sauri ya ɗauka ganin numbarta. "Nasreen, gidan uban wa kika samu waya, ashe da na karɓe wancan wata kika siya?" Ya yi mata tambayar cikin ɓacin rai. Gabakiɗaya ta manta ya karɓi layinta ganin ya kamata sai ta ce."Ba wayata bace aro na yi." "Kar ki gaya mini maganar banza layin fa? Ai na karɓe shi yana gurina da wayar sai kika je kika yi welcome Don Allah ayi mini haƙuri daga yau zan rinƙa posting page ɗaya, sai bayan sallah na ci gaba da biyu.🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏 *_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 6 "Nasreen, gidan uban wa kika samu waya, ashe da na karɓe wancan wata kika siya?" Ya yi mata tambayar cikin ɓacin rai. Gabakiɗaya ta manta ya karɓi layinta, ganin ya kamata sai ta ce."Ba wayata bace aro na yi." "Kar ki gaya mini maganar banza layin fa? Ai na karɓe shi yana gurina, da wayar sai kika je kika yi welcome back, saboda kin mai da ni mahaukaci ko?" "Ni fa ba wannan ya sa na kira ka, saboda ba ni da katin da zan ji ƙorafin ka. Fita zan yi ina son na je makaranta, na haɗa takadduna saboda na samu ayi tura ni service da wuri." "Amma kin san na rantse ba za ki yi ba ko? Saboda wannan iskanci da ake yi a gurin kina matar aure ba zan bar ki ba." Ƙaramin tsaki taja jin abin da ya ce."Kishin banza bayan ka jingine ni." "Na gaya maka wallahi sai na yi service ka yi haƙuri kawai." "Ashe kuwa za ki ɗauko wa kanki tashin hankali." "A shirye na ke wane dare ne jemage bai gani ba." Ta ce masa. Jin abin da ta faɗa sai ya ce,"To babu inda za ki kuma in kika fita sai na yi mugun saɓa miki..." Kafin ya gama maganar ta daƙile wayar ganin yana ɓata mata lokaci. Jakarta ta ɗauka ta kai Musaddik da Raihan gidan Maman Muwaddat, sannan ta tafi hankalinta kwance. Sai da ta gama komai ta dawo, saboda rashin tsoro gidan Maman Muwaddat ta yi zamanta har sai da ta yi ninyar tafiya. Farouk kuwa tun da ya san ya hana ta kuma za ta iya tafiya, don ya ga yanzu tashen rashin kunya yake damunta. Bai jima ba ya kashe kayan wutar ofis ɗin da ya dawo gida. Ganin ƙofarta a kulle ya kalli Rashidat ya ce,"Ina wannan 'yar iskar yarinyar ta tafi?" A banza ce ta kalle shi don yanzu ba ta tsoron shi."Ka ba ni ajiyarta ne?" Ta ce tare da ɗauke fuska. Zagayowar ya yi ya zauna a a gurinta."Wato saboda ta raina ni sai da ta fita?" "Ai kana son rainin me tun yaushe na ke cewa ka sake ta, sai ka ce sai ka wulaƙanta rayuwarta." "Ban shirya sakinta yanzu ba domin sakin na ta kamar farinciki za ta yi, ni kuma sam bana son ganin farincikinta." Tsuka ta ja mai ƙarfi tana cin cingam ba tare da ta kula shi ba."Ai sai ka ci gaba da zama da ita, kana ciyar da ita ba ta maka amfani, kuma wallahi na gaji dole a raba kwana, matuƙar ba zaka bani wannan kuɗin na fara jari ba." "Ya yi yawa gaskiya saboda da wannan kuɗin zai yi wani abu ko na sayi fili." "To shikenan Faruk, in ka tashi mutuwa don Allah a haɗaka da kuɗaɗen da kake tarawa ba ka sakar mini. Haba ina matsayin matarka, amma ko mota ka kasa siyen mini alhalin kana da shi." "Ban yi ninya ba kin san ba kwanciya na ke yi ba ina amansu." "Jin abin da ya ce sai ta yi shiru ta fara tunanin komawa gurin Malam. Tsaki ya yi ya wuce cikin ɗakinsa. Saboda bala'i yana zaune a falo da ya yi wanka. Ganin ta shigo ya tashi zuɓbur. "Daga ina kike?" "Ai na kira ka na gaya maka, da na dawo sai na zauna a gidan Maman Muwaddat." "Da izinin uban wa?" "Nawa don na ga Rashida ita ma ba ta gaya maka sai ta fita." "An gaya miki ke da ita matsayinku ɗaya? Ita na yarda da ita, amma ke ina tantama a kanki." "To shikenan duk abin da ka zarga a zuciyarki shi na yi." Ta ce masa ciki gatsali. Matsota ya yi amma sai da take tana kallonsa."Nasreen kin san Allah in har ina aurenki ba za ki yi service ɗin nan ba." "Saboda kana tsoron kar na yi na tara kuɗi na kaika kutu, ko baƙi cikin da kake mini ya kai haka." "Yin ne ba ni da ra'ayi, kin san in na sake ki, na huta da kaina ne da ciyar dake babu amfani." "To tun da ka san haka ka sauwaƙe mini, na gaji da zama da kai, don ban ga amfanin rayuwar aurenmu ba, tun da ka jingine ni." "Eh, ba zan iya kwanciya dake bane, saboda na samu wacce take da komai, ke kuwa ƙashi ne zai soke ni." Watsa masa banzan kallo ta yi za ta wuce."Ni kike harara?" "Abin da ya fi harara zan yi maka. Fatana na tara kuɗi na biya ka, wallahi na gaji da zama da kai, da na ci gaba da rayuwa a gidanka gara na yi a burtsuna." Ta ce masa cikin ɗaya murya. Da sauri ya nufota cikin ɓacin rai ganin yadda take masa magana. Da sauri ta shige cikin ɗakinta ta kulle ƙofa."Mugu azzalimi na gama yarda ka duke ni." Ta ce tare da cire hijabinta ta shiga bayi don ta yi alwala jin an fara kiran sallah. Tun tana tunanin lamarin da wasa yake yi, har ta cire ganin ya kafe dole ba za ta yi ba. Magana har gurin Baba suka je."Kallonta ya yi ya ce,"Tun da ya ce ba ya so, sai ki yi haƙuri ki bi maganar mijinki." "Wallahi Baba, inhar ka ga ban yi ba, sai dai in bana raye. Farouk baƙinciki yake mini, kuma sai dai ya mutu." "Baƙincikin me zan yi miki, bayan kin san abin da za ki samu ina da ninkin su?" Ya ce a harzuƙe kamar zai mareta. "In kasan kana da su, ban ga dalilin da zai sanya ka damu kanka sai ka hana ni ba." "Service ɗin ne na ce ba za ki yi ba, kuma ki bar mafarkin za ki yi aiki, wallahi ba ki isa ba." Dariyar rainin wayo ta saki tana kallon sa."Wasa kake yi Faruk in har ka ga ban yi aiki ba, sai dai in na mutu, amma wallahi ko koyarwa ce sai na samu." "Haka kika ce to mu zuba shege ka fasa." Ya ce mata sannan ya juya yana kallon Baba da ya yi shiru yana mamakinsa. Shi a kam harkan kuɗi ba zai goyi bayansa ba, saboda ya san ana samun kuɗi a service musamman yanzu da aka ce an ƙara musu, ya san in har ta yi zata tuna da shin watakila tafi shegiyar dubu goma ko biyar da yake basa, bayan ya gama tijarasa. "Kana jin abin da fitsarrarriyar harka take cewa ko? Wallahi na yi dana sanin auren mace mara tarbiya irin ta, sam ba ka iya ba da tarbiyya ba." Ya ce tare da ficewa. "Sai ka ɗauki mataki ba wai ka tsaya kana kumfar baki ba."Ta ce masa daidai lokacin da ya fice. "Yaushe kika ko yi fitsara da rashin kunya Nasren? Ke da ada na sanki ko hannu aka sanya miki ba za ki cika ba?" "Tun ranar da Ya Ahmad ya ɓace na san ba ni da gata sai Allah da kuma kaina. Tun ranar da na san cewa Baba, ba ka damu da halin rayuwar da na ke ciki ba. Tun ranar da na gane ko da Ya Ahmad yana nan ya raba aure da shi, inhar na ƙara wani auren na bari yana cusguna mini, sai dai ya sake ni, ko na ƙara masa hulɗi. Na zauna na yi wa kaina shawara na gane cewar kuka da haƙuri ba shi ne zai ƙwatar mini 'yanci ba. Kuma wallahi duk ranar da ya ƙara ce mini bani da tarbiyya, sai na goranta masa uwarsa da ta bar ƙasar ta tafi takaru neman kuɗi, don ta ciyar da su, shi ya sa shi ma ya tashi cikin rashin tarbiyya kamar ni." Zare idanunsa ya yi yana girmama abin da ta ce. Shi kansa tsoro ta ba shi ganin yadda take magana ba tare da jin shakka ba. "Kar ki gaya masa haka, kin san lamarin ba zai yi dadi ba." "Na gaji ne ya yi ta gaya mini, bani da tarbiyya sai ka ce shi yana da ita." Ta ce tare da ficewa daga ɗakin ba tare da damu da kiran da yake mata ba. Tun daga ranar sai ya daina ba ta abinci ba ta damu ba, ta ci gaba da ciyar da kanta. Ta riga ta kammala komai jira kawai a fara posting ɗin su. Yayi maganar wayarta da ta siya a boye A ranar da aka kira su don a yi musu tantancewa ba tare da shakkar koma ba ta shirya. Kasancewar da wuri za ta fita, don haka ta shirya Raihan ta yi wa Musaddik wanka. A falo ta zauna bayan ta gama soya musu dankalin Hausa ta sanya mata a jaka, ita ma ta ibi na ta. Tana zaune ya fito da shirin fita Rashida na bayansa ɗauke da jakarsa. Ganin sa ya sanya ta miƙe. Tana lura da mugun kallon da yake aikata mata. "Sai ka dawo honey." Ta ce masa tare da miƙa masa jakarsa. Jawota ya yi ya rungume ta ganin haka ta kauda fuskarta."Ki kula mini da kan ki." Far ta yi masa tare da ɗaga kanta. "Farouk, zan je makaranta maganar service ɗin mu, a cikin watannan za a fara raba mu." "Ai mun riga mun gama magana, na gaya miki ba da yawuna sai dai dai in za ki je ba da izinina ba." "Ok to shikenan ba matsala na amince." Ta furta hankalinta a kwance tare da kama hannun yaranta za ta fita. "Nasreen, tafiya za ki yi, a shirye kike duk abin da zan miki?" Ya yi mata tambayar yana kallon ta "Eh," Ta ce za ta fice. 'in har kika fita gidan a ba...." Sai ya fasa furucinsa ganin babu nadama a fuskarta. Tuni ya san ta gaji da zama da shi saki take so. "Ka ƙarasa mana tuntuni nake jiran wannan ranar, saboda babu amfanin aurenmu." "Ba zan saki ba, amma wallahi in har kika bar cikin dakin nan sai na lahira ya fi ki jin dadi." "Ko kashe ni za ka yi sai na je." Ta ce masa tare da fara tafiya da sauri. Ganin haka ya iske jakarsa ya fisgota tare da kaura mata mari. Jakarta ya fisge ya fito duk takaddun ciki ya yaga su. Ganin haka ta sa ya ƙara ta yi kansa, ganin ya yaga mata takuddun da za ta kai."Mugu azzalimi wanda mugunta ce kawai aikinsa." Ta cakume shi tana faɗin haka. Cikin fusata ya ƙara kai mata mari sannan ya haɗata da gini."Wawuya mara tarbiya kawai!" '"Kai ne mara tarbiyya! Kai ma har wani tarbiyya kake da shi? Mahaifiyarka da ta tafi takaru ta barka shi ya sa ba ka samu cikakkiyar tare..." Wani irin mari da ya yi kukan kura ya kaura mata, ya sanya ta kasa ƙarasa maganar. Lokaci guda ta daina ganin haske, har sai da walƙiya ta gifta mata. Kanta ya yi mata nauyi. Kafin ta gama dawowa cikin hayyacinta ta ji ya rufe ta da duka ta ko ina."Mara mutunci 'yar iska har kin isa ki zagi Mahaifiyata?" "Iyayenka sun fi nawa ne? Wane irin zagi ne ba ka yi wa nawa ba?" Ta yi masa tambayar cikin kuka. "Wallahi ai ko ban kashe ki ba sai na kusa banza kaka kawai." Dukanta yake yana haurinta tana ihu amma bai kula ba. Rashida ganin zai yi kisa, domin a lokacin ta suma sai ta riƙe hannunsa ta ce,"Faruk, za ka yi kisa domin dukan da kake mata ba na wasa bane, kar ka aikata abin da za ka yi nadama." Ta ce masa tare da kama hannunsa. Huci yake kamar mesa ya ƙara yin kanta. Da sauri ta kama hannunsa tare da ɗaukar ruwa a frij ta yayyafa mata. Ganin ta saki ajiyar zuciya ta farfaɗo, sai ya ce,"Ki bar ni na kashe shegiya tun da har za ta iya zagin iyayena, kuma ki je ba zan ƙara zama dake ba, na sake ki saki ɗaya." A lokacin da ya furta sakin Rashida ta ɗauka duka zai yi mata, ganin yadda ya harzuƙa yana huci kamar mesa, amma jin ya yi ɗaya sai ta lalle shi kawai. Nasreen kuwa ji ta yi kamar an yaye mata ƙaya. Furta sakin ya sanya ta cikin farinciki, domin ba ta taɓa tunanin zai aikata ba. Ƙoƙarin miƙewa ta yi amma sai ta ji ta kasa sakamakon ƙafafuwan ta da ya sanya ƙafarsa ya taka. Hannunsa ya sanya ya ƙara har ƙofar gida, sannan ya kwaso su Raihan da suke kuka. "Ki bar minii gida kuma wallahi tsinke ba zan bari ki ɗauka ba, tun da matsiyacin uban ki bai kawo ki da komai ba, sannan yaran nan ba zan riƙe su ba, saboda ba ina so kika haife su ba." Yana gama faɗin haka ya maimda ƙofa ya rufe. Kuka ta sakin mawuyacin halin. Raihan ta duƙa tare da kama hannunta."Umma, ba ki da hijabi ya koro ki, kuma mutane suna wucewa. Ki tashi muje gidan Maman Muwaddat ki sanya hijabi." Ta ce tana share mata hawaye. "Ba zan iya tashi ba, je ki kira mini ita." Ta furta cikin kuka. Da gudu yarinyar ta ruga tana share hawaye. Tana ƙoƙarin shiga cikin gidan suka ci karo da ita, wacce tun da ta ji ƙarar dukan ta tsaya a harabar gidan tana safa da marwa. Ganin ta sheƙo da gudu sai ta kamata."Raihan, ina ummar ta ƙi daina kuka." "Ta ce in kira ki tana waje Abba ya kore ta." Yarinyar ta furta tana share hawaye. Kafin ta gama maganar ta ruga zuwa ƙofar gidan su. Da sauri ta ƙarasa tana faɗin,"Innalillahi wa inna ilahir raju'un?" Anya Faruk ma da hankali?" Kalli yanda ya koro ki babu mayafi, wannan dukan ɓarawo ya kama?" "Ki taimaka mini akwai lulluɓi a jikinsa ya fisge Faruk Allah kawai zai saka mini." Ta ce cikin muryar kuka tana jin kamar ta nitse ganin yadda mutane suke wucewa suna kallonta, don ma unguwar ta su ba ta da yawan jama'a. Kamata ta yi suka shiga cikin gidan ta. Tishu ta ɗauka tana goge mata gefen bakinta da ya fasa."Allah ya saka miki Nasreen, amma kin bar gidansa ko?" "Ya sake ni saki ɗaya." "Alhamdulillah! Allah mun gode maka, ba a son saki saboda in aka yi Al'arshin Ubangiji sai ta girgiza, amma duk wanda ya ji ya sake ki, dole ya yi miki murna, yau ki zuba ruwa a ƙasa ki sha, duk da saki ɗaya ne, zai iya mayar dake kuma kin san halin mahaifinki." "Wallahi ko Baba zai yi ba zan dawo ba, na gwammace na shiga duniya akan na dawo gidansa." "Yauwa ki jajirce sai ka yi jan ido kake samun yanci." Ta ce mata tare da miƙar da ita."Mu je ki yi wanka da ruwan zafi sai ki canza kaya." Ta ƙarashe maganar tana miƙar da ita. Ba zan yi wanka ba, don Allah ki sa ya mashin ya kai Ni gida, so na ke Baba ya ga abin da ya yi mini, don ya zama hujjar da zan kafe a kanta." "Kuma haka ne, amma da kin bar masa yaran, saboda kin san mahaifinki ba zai yarda ki zauna da su ba." "Ya ce baya son su na tafi da su, kuma ina barsu ban san halin da za su kasance ba, baya ƙaunarsu duk abin da Rashida za ta yi musu ba zai kula ba." "Kai Allah ka nuna wa Faruk iyakansa saboda shi da imani. Har yaran da ka haifa da cikinka ba babu tausayi a tsakani?" "Ni dai na gode da ya furta mini saki, wallahi ko kashe ni zai yi, ba zan koma ba." Ganin ba za ta iya zama kan mashin ba sai ta kira napep. Tun a cikin napep take kuka sosai. Alokacin da ta shiga gidan, Baba yana cikin ɗakinsa kwance yana ta zabga hamma. Tana shiga cikin gidan ta faɗa kan Mama da take durkushe tana wanke-wanke."Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Nasreen lafiya wa ya yi miki haka?"Ta ce tana share mata jinin da yake fitowa daga bakinta. "Mama, Faruk ne ya yi mini duka kuma ya sake ni, saboda na ce masa zan je makaranta." "Kai amma Faruk ba shi da imani dubi yadda ya yi miki, kamar ya kama ɓarawo?" Ta ce hawaye na zuba a ƙuncinta. Jin abin da suke cewa, kuma an ambaci sakin sai ya fito da sauri yana faɗin,"Saki wace 'ya banzar ta ja aka sake ta?" Ya yi tambayar yana zare ido. Ganinta ya sanya shi kallonta cikin cikin ɓacin rai."Yanzu Nasreen sai da kika yi abin da ya sake ki ko?" "Haba Baban Maryam tambayar da za ka yi mata kenan, dubi yadda ya fasa mata jiki? Ko ɓarawo aka duka haka ai yakamata ka ga rashin imanin wanda ya yi dukan, ballantana matarsa uwar 'ya'yansa." Goggo ta faɗi haka tana kallon da cikin mamaki. "Saki nawa ya yi miki?" Ya yi mata tambayar ba tare da ya amsa abin da ta ce ba. "Saki ɗaya kenan? Alhamdulillah dole za ki koma.." "Wallahi Baba, ko kashe ni za ka yi ba zan koma gidan Faruk ba, na gwammace na yi bara a titi da na koma gidansa. Ba ya soma kashe ni yake don yi." Ta ƙarashe maganar cikin kuka "Kisha kurumin ki Nasreen, a wannan lokacin wallahi sai dai na rabu da mahaifinku, amma sai na tsaya na ga kin rabu da wannan matsiyacin. In har ya tilasta miki, Ni ma zan bar mishi gidansa." "Ki sa da ni Maman Ahmad, wallahi in har ya kafe sai mu bar mata gidansa." "Au haka ku ka ce?To sai dai ta mayar da yaran, tun da kun ɗaure mata gindi, amma wallahi ba za ta zauna da yarannan a gidan nan ba." Don Allah ayi mini haƙuri daga yau zan rinƙa posting page ɗaya, sai bayan sallah na ci gaba da biyu.🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏 *_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 7 "Ki sa da ni Maman Ahmad, wallahi in har ya kafe sai mu bar mata gidansa." "Au haka ku ka ce?To sai dai ta mayar da yaran, tun da kun ɗaure mata gindi, amma wallahi ba za ta zauna da yarannan a gidan nan ba." Jin abin da ya ce sai hankalinta ya tashi matuƙa gaya. Da sauri ta rarrafa ta ƙarasa gurinsa ta dafa ƙafafunsa."Baba, don Allah ka yi hakuri ka bar ni na riƙe yarana, wallahi Faruk ba ya ƙaunar yarannan, kuma matarsa ba ta kirki ba za ta riƙe su ba." "Oho sai ya kai su ƙauye ban damu ba ko gidan marayu zai kai su. Tun da ya sake ki na rantse ba zan bari 'ya'yansa su zauna mini a gida ba." Ya ce tare da kama hannun Raihan da take ɓoyewa a gurinta jin za a tafi da ita. Musaddik da ya ɗauka ya sanya kuka yana kiran Umma, ganin zai fita da shi. "Umma, zan zauna dake don Allah kar ki kai ni gurin Abba." Ta ce tana miƙa mata hannunta. Kuka take yi sosai tana kallon yaran da suke kuka. Hannu ta kai ganin zai fita dasu."Ka taimaka mini rayuwarsu za ta shiga garari. Don Allah ka bar mini su, zan tsaya na jure ruwa da rana na ciyar da su, sannan na inganta rayuwarsu." "Ba zan bar su ba, in muka barsu ba zai yi dana sanin sakin ki ba. Tun da ɗan iska ne sai ya riƙe 'ya'yansa." Ya ce tare da fita. Ganin duk haƙurin da suke ba shi, amma kamar tunzura shi su yi, sai suka kama hannunta."Nasreen ki bar kuka ki yi haƙuri Allah zai duba rayuwar su. Yara nawa uwa take fita ta barsu, kuma su rayu? Da baƙiciki a gidansa ya kashe ki gara ki haƙora ki zauna a gidanku, wallahi watarana za su ne ki duk inda kike" "Mama, wahala za su sha Faruk ba ya ƙaunarsu." "Allah yana tare da su ki yi haƙuri." Ta ce tare da kamata suka shiga ciki tana kuka sosai. Tausayi yaranta take yi ta san cewar ba ƙaramin wahala za su fuskanta a gidan ba, watakila abin da za su ci ya gagare su, duk da cewar anan ɗin ma babu tabbacin samu, amma za ta nemo musu duk inda yake. Kuka take yi sosai har Mama ta gama dafa mata ruwan wankan ta kuka mata bayi. Tana wanka tana kuka. Abin da take gudu kenan, wannan dalilin ya sanya ta jure duk wani tozarci, amma ga shi daga ƙarshe dai dole hakan ta faru. Bayan ta gama wankan ta shafa mai. Ta kwanta sakamakon zazzaɓi mai zafi da ya rufe ta. Tunanin haɗuwarta da Faruk da zaman auren da suka yi take yi. Lokaci guda ta fashe da kuka tana jin babu wani namijin da za ta kuma yarda da shi. Ya kamata mu ji asalin su sannan auren soyayya ko ƙiyayya suka yi da rayuwar aurensu ta ƙare a haka. WAIWAYE, ADON TAFIYA. Bukar Nadamu. Shi ne sunan mahaifin Nasreen. Mutum ne mafaɗaci da ita faɗin magana da za ta ɓatawa mutum rai tun yana ƙuruciyarsa. Ya tashi cikin rayuwar talauci domin tun yana ƙarami, Allah ya yi wa mahaifinsa rasuwa. Mahaifiyarsa ta ije shi a gurin ƙanin mahafinsa ta ƙara aure. A maimakon ya taimaki maraicinsa sai kawai ya ɗauki rayuwar nanaye.. Babu ruwan shi da zuwa islamiya ballantana boko da ba ta yi suna a ƙauye su ba. Ƙanin mahaifinsa Bala ya so ko karatun Muhammadu ya yi don ya taimaki maraicinsa, amma sai ya shafawa idanunsa riƙa ya yi kunnen uwar shegu da duk wata barazana da yake masa. A haka ya ta so rayuwa babu tsari, sai dai neman kuɗin da ya sanya a gaba babu dare babu rana. Haka ya girma har ya isa aure. A wannan lokacin Allah ya buɗa masa, har ya gina gida kuma yana samu babu laifi. Take ya fara neman aure inda ya samu Mariya ta kafe sai shi. Cikin ƙankanin lokaci aka tsayar da bikin har lokaci ya yi. Bayan sun yi aure ta yi haihuwa biyu. Ya ƙara rakito wani auren. Sai dai matar ba su yi shekara biyu ba, suka rabu ta bar masa yaro ɗaya da suka haifa. Ya fara zuwa birni sai likafa ta ci gaba, har ya sayi gida mai ɗauke da ciki huɗu sai turakarsa. Take ya ɗauki burin auren mata kala-kala ya sa ya wa ranshi. Kasancewarsa mai hange-hange. Bayan sun tare ya ƙara auri wata matar ta yi haihuwa ɗaya suka rabu da cikin na biyu. A ƙalla sai da ya auri mata biyar, suna rabuwa kuma ko wacce sai ta haifa masa. Wasu su rabu da cikin na biyu. A unguwarsu ya ƙalla idanu ya ga Fatima. Tun da ya ganta ya kashe ya tsare tare da kashe mata mahaukacin kuɗi, amma san ba ta taɓa ɗaya idanunta ta kalle shi ba. Fatima mahaifiyarta ta rasu tun tana ƙaramar. Tana zaune da mahaifinta da matarsa Mama Hajja. Tun da ta ga mahaukacin kuɗin da yake kashewa ta mace dole a ba shi ita. Ta yi kuka ta yi kuka domin sam ba shi a cikin mazan da take so. Abin da yafi ɗaga mata hankali auri sakin da yake yi. Tun da Mama Hajja ta na ce kan dole ta amince, don ta san babu makawa sai an yi. Cikin ƙankanin lokaci ka sanya ranar bikin. Tun bayan da aka yi auren ta fara nadama, saboda mugayen halayensa da tuntuni tana da labarin wasu. Sam bai damu da ibada ba, kuma babu ruwanda da kula da tarbiyyar 'ya'yansa. Wani irin rayuwa ake yi a gidan mara tsari da kan gado. Bayan ya aureta ta yi burin ta bar gidan, amma haƙarta ba ta cimma ruwa ba. Sai ta haƙura ta daina zubar cikin da take samu. Cikin ikon Allah ta ƙara samun wani cikin. Wata tara ta haifi yaro namiji aka sanya masa suna Ahmad. Bayan ta haife shi, ya ƙara auren wata jarabbabiyar mata bazawara. Sai dai, ba su dade ba ya sake ta, saboda ita kanshi ta hayyace shi. Kasancewar a lokacin da ɗan kuɗinsa ya ƙara neman aure. Bazawara mai haihuwa uku. Tunda ta zo gidan ta shiga jera masa 'ya'ya kwanuka har sai da ta yi shidda. A lokacin ko da ya yi ninyar sakinta babu wanda zai kula masa da 'ya'yan da ta tara masa. A lokacin Ahmad ya girma har an yi masa kanni guda uku. Rayuwa ta fara tafiya girma ya zo masa. Ga shi ya tara 'ya'ya da yawa. Shi kansa a wannan lokacin arzikin nasa ba kamar da ba. Kasancewar yadda komai ya canza. Ga shi Allah ya jarrabce sa sana'ar ɗan kunnin da yake yi ba kamar da ba, saboda nauyi sun yi masa yawa. Don watarana jarin da zai saro sai ya gagara. Tun da ga wannan lokacin ya sakin musu komai, duk da cewar ko da can ba ɗawainiyarsu ya ɗauke ba, domin sau ɗaya ake girkin tuwo da daddaren, sai kuma safiya a dama koko. Da rana kuwa, kowa ta sa ta fishshe shi. Abin sai ya lalace don wani lokacin tuwon ma gagara yake yi. Abin takaici a haka ya je ya tattara 'yan kuɗaɗen da yake juyawa ya ƙari aure. Tun daga wannan lokacin lamarin ya ƙara rikicewar sosai, domin wasu wannan suke yi wasu kuma tsurfau. Fatima ta ƙara haihuwar yara biyu suka zama biyar, Yayarsu Mariya sai Ahmad da Musa, da Nasreen sai kuma Zainab. Ta yi iya matuƙar ƙoƙarin ta ta ba su tarbiyya, kuma ta ci sa a yaran sun taso daban. Gidan kullum cikin fada da zage-zage suke yi, amma ban da 'ya'yanta. Karatu kuwa bai damu da ya sanya kowa ba. Makaranta ce ta firamari duk wanda ya ga dama ya je. Islamiya kuwa da dole sai an bayar da kuɗi, in har ya daure ya yi maka rijistar ba zai ƙara kula ka ba da maganar kuɗin makaranta. Daga baya ma, ɗan kayan makaranta da islamiyar da yake sanyawa duk sai daina. Banu ruwanda sai dai ya haifa ya barwa uwa, domin ai kai yanayin da abinci sai ayi wata bai ba da ba. Rayuwa ta miƙa yara sun girma kuma sun taso. Gidan ya cika da yara sosai marasa tarbiyya, sai waɗanda Allah ya tsallakar. Ya aurar da mata sosai duk wanda ya zo babu bincike zai aura musu, domin burinsa duk ya aurar da su ya daina ganinsu. Ahmad yaro mai hankali da tunani. Tun da ya girma ya fahimci irin mahaifin da suka samu. Ya yi ma kansa karatun ta natsu. Daga ƙarshe haƙura da makarantar ya yi. Aikin garaji ya fara zuwa, in ya dawo ya yi sallar magariba sai ya tsaya, karatun da ake koya wa a masallaci kafin kiran isha'i. Yana matuƙar ƙoƙarin ganin ya biya wa ƙanninsa bukatu. Tuni ya ije makaranta don su yi, musamman Nasreen da ya ga tana da hazaka da don makarantar. Nasreen yarinya kyakkyawar gaske mai hakuri. Wankan tarwaɗa ce ga hanci da gashi. Sannan ga ta doguwar sosai. Tana da hakuri saboda kusan yaran gidan babu wanda ya isa ya nuna musu ɗan yatsa. Ko ya taɓa su ya kwana lafiya, amma ita duk a unguwar koya ya sa ta da haƙurin gaske. Ba ta da surutu ga saurin kuka. Duk lokacin da ka shiga gidansu za ka ganta tana zaune da littafi tana koyon Turanci, domin Allah ya yi ta da don ta ga tana turanci. Wannan dalilin ya sanya ta dage matuƙa gaske! Ganin haka ya sanya Ahmad duk ya fita sai ya fito mata littafin koyon Turanci da Novels. Haƙarta kuwa ta cimma ruwa, domin ta iya turanci sosai, a lokacin tana aji shidda tana shirye-shiryen zana neco. Ahmad ya biya mata duka za ta zana. Yana da burin ta yi karatu. Duk da dawainiyar ci da su da yake yi, amma hakan nan ya yi ƙutu-kutu ya biya mata duka, don zai iya gwammacewa su kwana da yunwa, amma ta yi karatu. So yake ya cika burinsa na karatu a kanta, ganin yadda take da hazaƙa da saurin ɗaukar abu. Cikin ikon Allah ta cinye jarrabawar har da jamb, da ya biya mata ta samu admission za ta karanta microbiology. A jami'ar Ahmadu Bello University Zariya. Ahmad ya yi murna sosai, don haka ya dake ko da zai yi dako sai ya tara kuɗin da za ta yi karatun. Ta fara karatunta cikin sa'a da nasara. Matsalarta ɗaya rashin kuɗi, duk da cewar yana ƙoƙarin, amma wani lokacin ta kan fita makarantar na ta karya ba, kuma sai dai ta taka ta je a ƙasa, duk da akwai tazara a tsakaninsu. Ta kama kanta sam ba ta kula 'ya'yan masu hannu da shuni, domin ƙawarta ɗaya ce. Fadila wacce ita ma 'yar gidan Malam Shehu ne kamar ita. Ta dage ba ta ji ba ta gani kullum cimin karatu take. A lokacin da result din su na first semester ya fito. Kowa a abin sai da ya cika da mamaki, domin babu wanda zai yi tunanin ita ce wacce ta fi ƙoƙarin a cikin abin, kasancewar wasu ba su santa ba. Wasu suka cika da mamaki, musamman kallon da suke mata na yar talaka, don ko kayan da take sawa ba su da wani kyau sosai. Suna cikin shirye-shiryen zana jarabawar su na second semester. Kwasam ta dawo makaranta, suka haɗu da Faruk da ya shigo cikin rayuwata babu zato babu tsammani. A ranar an yi ruwan sama. Sun daɗe a makaranta, suna jiran ruwan da ake tsugawa, tamkar da bakin ƙwarya ya tsaya su tafi, amma kamar ana ƙarawa. Hankalinsu ya tashi ita da Fadila, don ita Nasreen ko kuɗin mota da za ta koma gida babu. Sun yi jugum-jugum har aka fara kifaye-kitlrayen sallah, sannan suka samu ruwan ya tsaya. Fitowa suka yi zuwa bakin titi. A lokacin duhu ya yi. Ga shi duk keke napep ɗin da suka tsayar a cike. Suna cikin wannan halin na tarabbbi, suka ga mota ash colour ta ja ta tsaya a gaban su. Tsaki Fadila ta yi tare da jan hannunta a tana faɗin,"Ji wannan wawan mutumin, muna tsaye muna neman napep kuma ya tsaya mana a hanya." Ba tare da ta ce komai ba, ta yi shiru saboda yunwar dake ƙwaƙwularta don ko da safe ruwan koko ta sha. "Bayin Allah." Ta ji wata murya ta furta a cikin taushi. Da sauri suka tsaya inda suka ga Faruk, a tsaye da gilashi a idanunsa yana kallonsu. Fara tafiya suka yi wanda ya sanya ta ƙara sauri ya isa in da suke. "Haba 'yan mata taimako zan yi fa. Ku kalli garin yadda hadari ya ƙara lulluɓe shi, kuma in kwana za ku yi da ƙarfi ku samu mota, don haka ku zo na rage muku hanya. Ni ma na tashi aiki zan koma gida." Ya ce yana kallon Nasreen da hasken mota yake gaskata. "Karka damu za mu samu napep. Thanks for your help." Nasreen ta ce tare da kama hannun Fadila. "Haba Nasreen, kina gani mun kusa awa ɗaya muna jiran napep babu. Don Allah ki zo kawai mu shiga." Shiru ta yi tana kallonta don ko ita za ta so ta shiga. "Ku shiga wallahi bani da nufin na cutar da ku. Ma'aika ci ne a makarantar." Ya faɗa tare da nuna musu identity card ɗin sa. Za ta yi musu Fadila ta ja hannunta, tare da buɗe mata motar. Baya ta shige ta bar Fadila wacce dole ta shiga ciki. Suna shiga aka cigaba da ruwan mai ƙarfi. "Kun ga na taimak ko? Da yanzu ruwan sama ya yi muku dukan tsiya, kuma na san wacan mara ƙibar za ta fara ciwo. Kin san dogaye ba sa son ruwa." Ya faɗa cikin tsigar tsokana. Fadila ta yi dariya, amma ita ƙara ɗaure fuska ta yi tana kallon hanya. "Ko zan iya sanin sunanku?" "Ni sunana Fadila ita kuma Nasreen." "Wow, nice name." Ya ce yana girgiza kansa. "Ni kuma sunana Faruk, ina zama a Zangon Shanu Hayin Jarumi. "Allah Sarki. Mu kuma duk a samaru muke." "Ni ma mahaifiyata a samaru take zama, amma yanzu tana Saudiyya. Samaru shi ne ainihin family house ɗinmu. Kwananan na gama ginin gida ina neman matar aure." "Allah ya ba ka ta gari." Fadila ta ce masa cikin sakin fuska. "Ai kamar na samu in har za ki bani ƙawarki, ko da yake kamar haushina take ji, kin ga tun da ta shiga cikin motar ba ta magana." Dariya Fadila ta yi."Ikon Allah! Daga ganin Sarkin Fawa sai miya ta yi zaƙi?" Shi ma dariya ya yi ba tare da ya ce komai ba. Nasreen kuwa ƙara tsuke fuska ta yi don sam bai yi mata ba. "Da gaske na ke yi za ki bani ita?" "Allah zai ba ka in kuma ta amince." "In Sha Allahu! Ai ba za ta watsa mini ƙasa a ido ba ko Nasreen?" Ya ja sunan yana tambayarta. Ba ta tanka musu ba ta ci gaba da tunaninta. "Amma kamar ba zan samu matsuguni ba? Duba ga yadda take haɗe rai?" "Kar ka yi mata mummunar fahimta. Haka take ba ta cika magana ba, kuma bayan nan ka ga daga makaranta muke har da distress." "Haka ne." Ya ce ba tare da ya ƙara cewa komai ba. "Ka sauke mu a nan mun gode." Ta ce mishi tare da nuna gurin. "Nan ne unguwarku?" "Eh, amma unguwar da nake zaune. Ita na ta akwai nisa ba sosai ba." Cewar Fadila. "Ok, bari na sauke ki sai na kaita." "No, na gode bana buƙata." Ta faɗa da sauri tana ƙoƙarin buɗe motar. "Kwantar da hankalinki bana cin mutane." Ya ce tare da fitowa. "To 'yanmata tun da ruwa ake ba zamu iya magana ba. Don Allah ko zan samu numba?" "Ba ta da waya sai dai na ba ka numbata." "Kamar ki ba ki da waya?" Ya yi mata tambayar yana kallonta Haushi ya sanya ba ta ba shi amsa ba, ta fara tafiya. "Bari na ba ka yawa kusan tare muke in ka kira sai na haɗa ku."Ta ce tare da ciro wayarta tecno mai botira ta gaya masa ya kwashe. "In ta amince zan siya mata wayar." Ya faɗa tare da kwashe numbar da ta ƙara to masa. "Kyawawan 'yan mata mu tashi lafiya." Ya ƙarashe maganar yana murmushin sannan ya buɗe motarsa. "Kin bani haushi haba ni ban san ba ki da aji ba, sai magana kike da shi kamar ba mace ba." "Ya taimaka mana sai na wulaƙanta shi? Da bai ɗauke mu ba, wataƙila da yanzu muna can kan hanya ruwa ya cika mu, kuma kin ga kuɗin da na so na yi mana kudin napep gobe ko gurasa ma ci." "Haka ne." Ta ce tana gyara jakarta. "Amma gayen da motarsa har da ƙamshinsa sun yi." "Ni kuma sam bai yi mini ba, saboda yana da arha da yawa ga surutun tsiya." Ta buɗe baki za ta yi magana ta katse tare da rugawa da gudu. "Kin ga ruwa ya fara dawowa sai gobe." Murmushin ta yi tana kallon yadda take gudu har ta ɓule. Nasreen har ta manta da zancen wani Faruk, tare da mayar da hankalinta kan karatun. Bayan kwana biyu da kaisu gida da ya yi. Suna tafiya za su makaranta Fadila ta kalleta."Kin san ko wannan mutumin ya kira?" "Wake nan?" Ta yi mata tambayar domin har cikin zuciyarta ta manta da shi. "Ba na son wulakanci. Wannan mutumin da ya ɗauke mu, ko nifinki har kin manta alkhairi da?" "Oh, wallahi na manta da shi. Gaye za ki ce mini. Ba ki ga shigarsa ta matsu bane?" "Kai ke dai kin cika sa'ido wallahi. Ya kira ni yana son magana dake." "Kin ga Fadila. Ya kamata ace kin gaya masa ni ban shirya aure ba, saboda ba zan watsa wa Ya Ahmad ƙasa a ido ba, na kasa ci gaba da karatuna." "Karatu yana hana boko ne? Ni kawai ina miki sha'awar shi ne, saboda yana da abin yi, kuma yadda yake ɗan boko zai tallahi karatun ki, sannan Ya Ahmad zai samu sauƙi." "Kawai bai yi mini ba don Allah ki sanar masa." Ta ce tare da yanke fuska tana kallonta. Ganin yadda ta sha kunu ya sanya ta bar zancen, amma a ranta tana mata fatan ta aure shi, domin ta so ace ita ya ce yana so. Faruk kuwa ya kasa sukuni saboda lokaci guda soyayyarta ya hana shi sukuni. Duk da lokacin ba wani fuskarta ya gani sosai ba, amma muryarta da natsuwarta sun tabbatar masa da kyakkyawan gaske ce. Da ma burinsa ya samu mace mai kyau kuma fara doguwa. Duk yadda ya so Fadila ta haɗa su abin ya ci tura. Bisa umurni da ta ba ta. Cikin kwantar da murya ya, ya yi nasarar roƙon Fadila har ta amince za ta kai su gidansu. Da bisa ni da ya ga gidan ransa ne ya ɓaci. Ya rinƙa kallon gidan a wulaƙance, wanda har Fadila ta so ta fahimci hakan. "Bari na shiga na kira ta." "Wai tsaya." Ya dakatar da ita yana faɗin haka tare da ma gidan wani irin kallo. "Wai kina nufin Nasreen a wannan gidan take rayuwa?" Tambayar ya yi matuƙar ba ta mamaki."Eh, ko na fasa kiranta ne?" Ta tambaye shi tare da canza fuska ganin lamarinsa da rainin wayo. "No, ba haka nake nufi ba, amma don Allah ɗan bari sai gobe." Ya ce yana sosai kansa da makullin mota. "Ok, ba damuwa." Ta ce za ta shige cikin gidan. Har ya fara taki sai ya ja ya tsaya saboda sonta da ya ji ba zai haƙura da shi ba. "Fadila," Ya kira sunanta da sauri ganin za ta shige. Fasa shigar ta yi ta ja ta tsaya, tare da juyowa tana kallonsa, sai kuma ta dawo gabansa ta tsaya tare da tamke fuska. "Kira mini ita Please." Ya ce tare da haɗa hannunsa. "Ok," Ta amsa sannan ta shige cikin gidan. ' "Yanzu yarinyar wannan gidan zan nema da aure? Kai impossible!" Ya bawa kansa amsa. "Mai za su kawo mini kuma abin kunya ne ace kamata Ummar Faruk zan auri 'yar gidan nan, amma dai bari ta fito." Ya furta a ransa idanunsa ƙyar a bakin ƙofa, burinsa kawai ta fito. Fadila ta shiga gidan da sallama. Babu wanda ya amsa mata, domin kowa harkar gabansa yake yi. Ganin haka ya sa ta nufi ɗakin su Nasreen. Tana zaune a falon da babu komai sai siminti. Shi ma duk ya gyabure. Ganinta ya sanya da ta kai ƙarshen ayar ta tsaya tana murmushi. "Sahiba." "Na'am, da baƙo ki ka yi a waje." "Baƙo?" Ta yi mata tambayar cikin mamaki. "Eh, Ummar Faruk ne. Wallahi ya hana ni sukuni dole sai na kawo shi gidanku, wai yana son ya yi maganar ƙarshe da ke." "Kuma sai ki jawo shi har ƙofar gidanmu? Kin taɓa ganin na yi zance? Ko so kike ran Ya Ahmad ya ɓaci?" "Don Allah ki yi haƙuri ki zo ku yi magana kawai ni ma ya daina mini naci." Ta ce tare da miƙewa tana jan hannunta. Ƙwace hannun ta yi." Ki je ki ce masa ba zan zo ba." "Haba ke kuwa. " Ganin da gaske ba za ta je ba ya sanya ta shiga ciki inda Mama take ninke kayanta. "Don Allah Mama, ki ce Nasreen ta fita ta gaya mata ɓakonta ba yanzu za ta yi aure ba." Ta faɗin haka bayan ta gaishe ta. Murmushin ta yi."In ban da abinki zama za ki yi ta yi a gida? Ma za tashi ki je, kuma kika yi masa wulakanci ni da ke ne." Zuɓɓura baki ta yi tare da miƙewa tana hararar Fadila. Hijabinta ta janyo suka fita."Zan gaya masa ya fita harkana, in kuma ya ƙi zan shuka masa rashin mutunci." "Eh, gara ki yi masa ni ma ya shafa mini lafiya." Fadila ta furta haka. Nasreen ja ta yi ta tsaya gefensa can nesa da shi. "Assalamu alaikum." Ta yi masa sallamar cikin ɗaure fuska. Juyowa ya yi da sauri yana kallonta. Dama ya ƙosa da kuma ɓacin rai ganin sun shanya shi kamar kayan wanki. Shi mutum ne wanda sam ya tsani jira. Idanu ya zuba mata yana kallonta kamar zai cinyeta. "Eh, tabbas kyakkyawar gaske ce. Sam ba ta dace a ce daga gidan nan ta fito ba." Ya furta hakan yana mata kallon tun daga sama har ƙasa. Ranta ne ya ɓaci ganin kallon up and down da yake mata."Ina wuni?" Ta furta tare da cuno baki. "Lafiya lau Nasreen." Ya amsa yana murmushin saboda komai na ta ya yi masa. "Amma zan iya aurar 'yar talaka? Dubi irin gidansu." Ya ce yana kallon gidan a wulaƙance. "Please, Nasreen gani da ƙokon bata domin tun da na ganki na ga matar aure?" "Gaskiya karatu zan yi kuma bayan haka sam ba ni da ninyar aure yanzu." Da sauri ya yi mata wani banzan kallo da mamakin ƙarfin halinta. Ganin mutum mai aji da 'ya'yan banki kamarsa ya zo tana 'yar gidan talaka liƙis tana gaya kishi zabinta. "Da dai kin duba lamarin saboda duka taimakon juna za mu yi, kuma gane da karatun ki zan ɗauki nauyin karatun." Ya ce cikin ƙosawa saboda shi mutum ne wanda bai iya roƙo ba. "Na gaya maka zaɓina kuma ina fatan za ka je gaba ka nema. Allah ya ba ka wacce ta fini." Ta faɗi haka za ta juya. Baba da ya dawo daga kasuwa. Yana tafe yana surutu tare da surfawa wasu yara da suke ball suka kusa buge shi zagi. "Ka ga mini 'ya'yan Allah bani, yan banza marasa tarbiyya." Ya ce yana huci. Turus! Ya tsaya daga nesa yana hango tsaleliyar motar dake dake a gaban gidansa. Shafa idanunsa ya yi tare da sungulin kansa don ya gane ko mafari ne. "Ikon Allah! Ko dai aljanu suka ije motar nan na ke ganin su a zahiri? Ni dai na san unguwannan ta matsiyata ne, sam babu wa da yake da arzikin mota. Daga keke sai mashin." Ya ce tare da fara tafiya cikin sauri. Don Allah ayi mini haƙuri daga yau zan rinƙa posting page ɗaya, sai bayan sallah na ci gaba da biyu.🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏 *_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 8 Shafa idanunsa ya yi, tare da tsungulin kansa don ya gane ko mafari ne."Ikon Allah! Ko dai aljanu suka ije motar nan na ke ganin su a zahiri? Ni dai na san unguwannan ta matsiyata ne, sam babu wa da yake da arzikin mota. Daga keke sai mashin." Ya ce tare da fara tafiya cikin sauri. Shafa motar ya fara yi yana kallon ta yadda take sheƙi. "Kai wasu dai wallahi duniya na maraba da zuwansu. Dubi mota sai kace yau aka ƙero ta?" Ya ce tare da ƙara shafata yana bin gefe-gefe. Tsananin mamaki ya kama shi ganin Nasreen tsaye da kyakkyawar saurayi. "Nasreen!" Ya ƙwala mata kira yana faɗin haka. Jikinta ne ya kama rawa ganinsa. Ba tsoron ya ganta tana zance take yi ba, ta san cewa dole sai ya kwafsa. "Ga Babana ya dawo bari na tafi. Ina maka fatan alkhairi." Ta ce tare da kama hanyar gida da sauri. "Dawo don ubanki na ce. Ki dawo munafukai banza." Ya ce da sauri ganin za ta shige. Ƙwalla suka cika mata idanu ganin toxarcin da yake mata. "'Yar banza. Ni za ki wa alaye? Dama abin da kike zuwa kina yi ke nan a jami'a, kike fakewa da karatu kika hana yaron nan ya tara kuɗinsa." "A'a Baba, wallahi yau ne kawai na taɓa tsayawa zance." "Gaya wa banza wanda bai da wayo." Ya ce tare da ƙarasowa ya jingina da motar yana wa Faruk kallon sama da ƙasa. Faruk shi ma kallonsu yake a wulaƙance. Ya sausauta kallon jin ta ce masa Baba. "Mahaifinki ne?" Ya yi tambayar cikin rashin yarda. "A'a kai ka haife ta. Ko don ka ganni baƙi?" Ya yi masa baƙa tare da tambayarsa. "Allah ya ba ka haƙuri." Ya ce zai buɗe motarsa. Shawarar fasa auren ya yi ganin kalar mahaifinta. "Dawo ɗan saurayi dawo mana." Ya ce tare da jawo masa riga. "Don na dawo kuma sai ka tafi? Ba ni da matsala ai. Ka ganni sam ba ni da damuwa. Mai yake tafe da kai?" "Gani ta na yi ina so zan aure ta, amma kuma na fasa saboda ta ce mini karatu..." "Kara me? Kuma a gidan uban wa?" Ya katse shi yana faɗin haka. "Karatu za ta yi don haka Allah ya ba ta sa'a." Ya furta zai shiga. Da sauri ya riƙe hannunsa tare da rufe motar. "Kana sonta ko?" Ya yi masa tambayar da ya kasa amsa masa. "Wallahi na ba ka ita, ko yau za a ɗaura aure zan ba ka ita. Da ma tuntuni nake ta ma 'yar banzar yarinyar nan, maganar ta fito da miji, amma ta shafa ma idanunta toka, tare da yin kunnen uwar shegu da magana. Yanzu kuwa tun da Allah ya kashe ya ba ta mai ƙubbar susa. Ba zan bari ta yi sake ba. Kasan su mata ba hankali ne da su ba." "A'a, tun da ba ta sona ba zan yi mata dole ba, ta yi karatunta Allah ya ba ta sa'a." Ya ce yana mamakin zagin da yake yi kamar ya fito daga zuriyar maguzawa. "Ai tun da kazo ɗan saurari babu tafiya. Karatun banza? Mutane nawa suka yi karatun babu aiki. Shi Ahmad shi na ke kallo shashasha da yake ɓata kuɗinsa gurin karatunta." "Da ma ba kai kake biya mata ba?" "An gaya maka jikin banza ne da ni? Da zan je na yi ƙwadigo banci ba na kaiwa Nasara? Yayanta da ya yanke kazar wahala yake biya. Yanzu kuwa tun da tarkota ya kama kurciya, na rantse ba ta da miji sai kai." Nasreen kallon sa take yi tana hawaye, ganin toxarcin da yake ja mata. Da ma ta san tun da ya zo gurin sai ya yi abin da zai ja mata kunya. Tun ɗazu take alla-alla Faruk ya tafi." "Baba, ka.." "Rufe mini ba ki kafin na ci ubanki." Ya ce yana harararta. "Ka kawo kuɗin sadakin yanzu ma sai a ɗaura." "Sai ka ce wata bazawara?" Faruk ya yi masa tambayar cikin tsananin mamaki. "A to mene ne, ko kanta farau? 'Yan mata nawa aka ɗaura ma aure da ga zuwa jin magana." "To ni ma ina da magabatana saboda ba daga sama na faɗo ba, dole na je na sanar da iyayena." Ya ce yana masa kallon mamaki. A ransa kuwa ya sanya cewar shi da gidan har abada, saboda ko mutuwa zai yi saboda sonta ba zai dawo ba. "Bari na kama kaina ban ga gidan aure ba." Ya ce yana ƙoƙarin shiga mota. "Tafiya za ka yi ɗan saurayi?" Cewar Baba yana riƙe rigarsa. "Lafiya mai ke faruwa a nan?" Ahmad da ya dawo daga gurin kanikanci, ya faɗa yana kallon Nasreen ganin tana kuka. "Yauwa Amadu, zo ka ga wannan mara ƙashin arzikin, wai ba ta son wannan saurayin da ya zo neman aure ta." Tamke fuska ya yi yana kallon Nasreen."Shi ga cikin gida." "Baba kai ma ina son magana da kai." Ya ce ba tare da ya kalli Faruk da ya riƙe sitiyarin mota yana masa kallon ƙasƙanci ba. Faruk kuwa raka shi da idanun ya yi cikin kallon ƙyama. Ganin yadda kayansa suka yi duƙu-duku. "Tafiya za ka yi?" Cewar Baba yana kallon sa da ya shiga motar ya tada. "Anya wannan yaron zai yi kyauta kuwa? Kai daga ganinsa marowaci ne.Ko 'yar fara ai ya miƙa mini." "Da ma zance kike yi da maza ba karatu ba?" Cewar Ahmad cikin fushi yana kallonta ba tare da ya damu da kukan da take yi ba. "Wallahi Yaya Ahmad ba na kula kowa." Ta ba shi amsa cikin muryar kuka tana share hawaye. "To mai ya kawo shi ƙofar gidanmu?" Gaya mishi yadda suka haɗu ta yi."Ki tsaya ki kula da karatun ki, kar ƙi kara yarda wani namiji ya biyo ki. Kina ganin abin kunyar da Baba ya yi miki." "To," ta ce tana share hawaye. Jikin Fadila ya yi sanyi sosai ta ji babu daɗi ganin lamarin da ya faru. "Don Allah ki yi haƙuri duk ni na ja miki." "Babu komai Fadila, domin na san shi ma ya kori kansa ba zai dawo ba" Ta ce tare da jan majina tana share hawaye. Faruk kuwa, tsananin mamakin halin mahaifinta yake yi. Shi tun da yake a rayuwa bai taba ganin mahaifi irin sa ba. A ransa ya sanya shi da gidan har abada. Amma me tun da ya koma gida ya rasa sukuninsa. Da ya rufe idanu ita yake hangowa. Ganin abin na son fin ƙarfinsa ya sa shi tsaida tunaninsa cak. Saboda takaici har marin ka sa ya yi, amma ya kasa mantawa da hoton fuskarta. Kwana ɗaya biyu tun yana tunanin zai daina, sai ƙaramar magana ta zama babba. Ya rasa yarda zai yi. Numbar Fadila ya nema a cikin call da suka yi, saboda tun a hanya a ranar da ya bar ƙofar gidan ya goge. Da ƙyar ya gane numbar da ta ƙare da sifili da biyu. Kira har sau uku ya yi mata ba ta ɗauki ba, duk da cewar ta yi mamakin kiran shi. A tunaninta abin da Baba ya yi masa ba zai ƙara marmarin ko ganin numbarta ba. Ganin ya ƙi daina kiran ya sa ta amsa tare da sallama a daƙile. "Don Allah Fadila ki taimaka mini na ji muryar Nasreen?" Ya ce mata cikin damuwa. Mamakin abin da ya faɗa ta yi take ta fahimci don Allah yake sonta. "Nasreen ba ta sonka ba za ta saurare ka ba. Don Allah ka yi haƙuri kamar yada ta gaya maka. Bana son a sanadin ka mu samu matsala da ƙawata." Ta ƙarashe maganar tare da kashewa ba tare da ta ji mai zai ce ba. Da fari ya yi nufin haƙura amma sai ya kasa. Cikin rashin kuzari ya ɗauki motarsa sai ƙofar gidansu. A lokacin da aka ce mata ana sallama da ita ta yi mamaki ƙwarai. Tun da ta fahimci shi ne ta ƙi fitowa. Babu yada Mama ba ta yi da ita ba, amma ta ƙi wanda daga ƙarshe sai ta sanya mata kuka. Ganin haka ta haƙura ta kyale ta. Faruk da damuwa suka yi masa yawa ganin yadda ta shanya shi. A ransa ya ji sam ba za ta fito ba. Don haka ya juya zai shiga motarsa. Yana mamakin yadda ya tsaya gidan talakawa tana wulaƙantashi. "Ɗan saurayi." Ya ji muryar Baba yana kiransa. Waigawa ya yi tare da fasa shiga cikin motar. "Na ɗauka ba za ka dawo ba?" "Ni ma ban so na dawo ba." Ya ba shi amsa yana masa wani irin kallo. "Takura maka aka yi ko jawo ka?" "Zan iya cewa haka domin bani da zaɓi face na bi umurnin zuciyata." "Soyayya ruwan zuma soyayya ruwan maɗaci.." Ya fara waka yana dariya. "To yanzu da me ka zo?" "Na kira ta ba ta fito ba." "Nasreen ɗin?" Ya tambaye shi jin abin da ya ce. "Eh, ita ɗin fa. Ta aiko mini cewar na yi haƙuri kar na ƙara zuwa ƙofar gidan nan." "Inda uban kuturu ya yi kaɗan kenan! Ita da za ta yi godiya Allah ya kashe ya bata. Ai daga ganin ka ba ka yi gadon tsiya ba. A maimakon ta yi wa kanta murna, na wannan tagomashi da Allah ya yi mata sai ta tsaya iya shege?" Ya yi masa tambayar wanda bai ce komai ba, sai karkaɗa makullin motarsa yake yi. "Jira ni ina zuwa." Ya ce tare da wucewa duk cikin gidan kamar guguwa. "Nasreen, ina kike? Mara mutunci kawai!" Ya furta cikin tsananin fushi. Da sauri ta miƙe jin hargaginsa tana zare ido." Ato, ba kya jin magana yanzu sai ki tashi ai." Cewar Mama tana gyara allayahu. "Fito da mayafinki na ce mata hankali kawai! Saboda kamar wancan zankaɗeɗen yaron za ki wulaƙanta?" Shiru ta yi sai hawaye daidai lokacin da Ahmad ya shigo gidan. "Ahmad, da ma kai kake hure mata kunne ko? To walllahi bari na yi mata gargadi da kakkausar murya. In har kuka fake da karatu ba ta auri yaron nan ba, to karatun sai dai ta yi a wani gidan uban. In banda rashin godiyar Allah. Duk cikin yaran gidan nan wa ya gama sakandire. Kece kawai kika fita zakka, amma saboda ɗiban albarka za ki ce sai kin ƙare jami'a. To ko fara ta da kika yi babu yadda zan yi ne." Ya ce ciki kumar baki. Ganin ta sanya kuka ya fara neman icce yana faɗin,"Bari na sheme ki sai ki yi kukan mai dalili, saboda yanzu na daɗi kike yi." Da sauri ta ruga don ta san zai iya."Ka ga mini ja'irar banza!" Fita ta yi tana hawaye ta je gabansa ta tsaya tana ba tare da ta ce komai ba. "Ga ta nan in ta yi maka rashin kunya, ka gaya mini ka ga yadda zan yi da ita." Ya furta tare da shiga gidan. Jin abin da ya ce ya sanya ta bude baki da ƙyar ta ce,"Ina wuni." Sai hawaye shar. "Don Allah, ki daina kuka. San ban shigo rayuwar ki da nufin cutarwa ba. Sonki na ke da aure, kuma na yi miki alƙawarin in har za ki aure ni hatta kayan ɗauki zan yi miki." Ba ta ce komai ba sai kuka. Duk maganar da ya yi mata, ta ƙi cewa komai. Ganin haka ya ce,"Je ki gida." Kafin ya gama faɗin haka ta juya da sauri ta shige tana kuka. Raka ta da idanu ya yi, har ta shige. Sani irin ƙaunarta ke fisgarsa. "Ina fatan ba ta yi maka rashin kunya ba?" Da sauri ya juyo yana kallonsa da yake faɗin haka."Ba ta yi ba. Don Allah ga waya ka ba ta ina son jin muryarta." "Madallah sannu da ƙoƙari, amma mai zai hana na riƙe wayar in ka kira sai na bata?" "Na fi son duk na kira na ji a hannunta." Ya faɗa cikin zallar mamaki. "To za a siya mini kenan ko ƙaramar din ni ma bani da ita. Tun da ta faɗa masai ban siya ba." Kallon mamaki ya yi masa, sai ya fara ƙoƙarin shiga mota, ba tare da ya ce komai ba. "Kai ba ka san ana ba da kuɗi ba in aka je zance?" Tambayar ta yi matuƙar ba shi mamaki. Faruk akwai maƙo da son kuɗi. Lura da ya yi matuƙar bai saki kuɗi ba, ba zai ba shi yarinyar ba. Ya sanya shi zaro naira dubu biyar ya miƙa masa. "Ga shi ka bata."Sannan ya ciro dubu biyu. "Wannan ka yi cefane." Kallon kudin a raine ya yi domin shi ba haka ya so ba. A tunaninsa ruwan yan dubu-dubi zai yi masa. "Wannan za a je da shi kuwa? Da babu gara ba daɗi." Ya ce a ransa sannan ta kalli kuɗin. "An rufa asiri da shi. Ko shinkafa da mai da yaji a yi." Ya faɗi haka yana tuna in zai ƙara masa. Nuna ya yi kamar bai ji ba sannan ya shige motarsa. "Ɗan banza, daga ganinsa rowa zai yi." Ya ce tare da tura duka kuɗin aljihunsa. Yana shiga cikin gidan ya faɗa ɗakin Mama."Ki jawa 'yarki kunne ta aminta da auran nan, domin matuƙar ta ƙi, wallahi ba za ku sha da daɗi a hannuna ba." Ya wuce yana bambami. "Kina jin abin da ya ce?" "Wallahi ni bana sonsa." Ta furta tare da fashewa da kuka. Ahmad shiru ya yi cikin tausayinta, domin tun da ya ce sai anyi, matuƙar ba da wasa ya zo ba babu abin da zai hana. Abin da ya kamata ya yi shi ne ya rarrashe ta don ta amince. "Kina ji ko kamar auren na sa zai fi? Tun da yana da kamala." "Kai ma biyewa Baba za ka yi? Karka manta ko binciken halinsa ba a yi ba." "Haka ne, ai dama sai na bincika na gane shi wane ne, saboda kin san ba zan yarda ayi miki zaɓen tumin dare ba." "Ko dai ka gaji da biya mini kuɗin makaranta ne?" Tambayar ta ba shi mamaki har ransa ya ɓaci."Matuƙar ina raye zan gaji da ɗawainiyarki ne?" Ya yi mata tambaya a maimakon amsa. "To bana son shi, saboda ya ci ka gadara kamar ba zai yi haƙuri ba. Kuma Yaya, ina 'yar talaka wacce mahaifin ta ya zubar mata da mutunci. Kana ganin inya aure ni zai ganni da mutunci? Masu kuɗin nan sam ba sa girmama mace." "In har yana sonki zai yi mana. Zan fara binciken halinsa." Shiru kawai ta yi don ko hirar ba ta so. Faruk kullum sai ya zo zance. Ganin yadda Baba ke son abin duniya, ya sanya shi ƙoƙarin rage mako sa yana kawo abu gidan. A ranar da ya fito masa buhun shinkafa. Sujjada ce kawai bai yi masa ba, amma har da kuka ya yi a gabansa. "Da ma rabon da mu ci shinkafa, tun ranar da ka yi mana kyautar nan. Sai ga shi yau za mu ci 'yar gwamnati." Kallonsa yake cikin mamakin baƙin talaucin da suke fama da shi. Yana mamakin girman kanta da kauda ido ga abin wani. Duba ga yadda mahaifinta yake kamar zai yi ƙwace. Baba maganar aure yake yi ba tare da ya yi bincike ba. Ahmad ne ya je ya fara binciken, inda aka sanar da shi ba shi da matsala, domin yana da abin hannunsa da tanƙamemen gida ya gina. Mahaifiyarsa tana Saudiya tun lokacin da yake yaro ta tafi, bayan ta yaye shi. Da auren mahaifin su, saboda matsanancin talaucin da suke fama da shi. Wata 'yar'uwarta ta yi mata hanyar zuwa takaru. Tun da ta tafi ba ta dawo ba, amma tana tura musu da kuɗi. Da haka suka samu suka fita daga talaucin da suke ciki, har suka samu su ka yi karatu. Su biyar bakwai mahaifiyarsa ta haifa. Uku mata biyu maza. Matan duk sun yi aure sai Faruk da shine babba a namiji. Da kuma ƙanninsa da yake jami'a yana karanta agriculture. Yayinda mata masu hannu da shuni suka aura. Tun suna sanya ran mahaifiyarsa za ta dawo, amma har mahaifinsu ya mutu ba ta dawo ba. Sai da aka yi rasuwar ta zo ta yi wata biyu. Wata biyu na cika ta tattara inata-inata ta koma. Matsalar da ɗaya zafin rai da rashin haƙuri, saboda wannan sam ba shi da tanƙamemen aboki, domin da sun fara za su ɓata, sannan ba shi da kyauta sosai. Ahmad ya sanar da Baba binkicen da ya yi. Dariya ya yi tare da kallonsa ya ce,"Ni ban damu na yi bincike ba, tun da ba za ta rasa ci da sha a gidansa ai shikenan. Mata nawa suke zama da maza su babu ci ba sha?" "Bincike a aure yana da kyau baba. Na tabbata da ace kai za ka je sai an gaya maka abin da ba a gaya mini ba. Rashin bincike da ba'a yi, ya sanya yawan mace-mqcen aure a tsakanin Hausa Fulani." "To ubana gaya mini gaskiya, kuma tun da ka yi karabbanin yi ai shikenan." Har ofis ya samu Faruk. Bayan an yi masa izinin shigowa. Ya buɗe ƙofar ya shiga da sallama. Ganinsa Faruk ya amsa sallamar fuskarsa babu yabo babu fallasa, don sam jininsa bai haɗu da na Ahmad ba, musamman yadda yake cin magani da girman kai shi ba ɗan kowa ba. "Na zo kan maganar auren ka da ƙanwata Nasreen." "Ok," Ya ce masa tare da cigaba da aikinsa. "Game da karatun ta ne." Ya daure ya ce masa yana kallon yadda yake cin magani. Shi kansa da yana da halin a za ayi auren nan ba, musamman da ba ta so. Ya san cewa ko sun amince ko ba su amince ba, tun da ya sa ya ran dole ayi, to babu makawa. Don haka ya yanke shawarar ya aminta kawai. "Nasreen, na son makaranta.." Cewa na yi ba zan biya ba? Ai ban yi maka kama da jahili wanda bai yi boko ba. Don haka ba zan so matata ta kasance jahila ba." Cije lebbensa ya yi don ya san magana ya gwaɓa masa amma sai ya daure. "Haka nan na nufin za ta ci gaba kenan?" "Ba ni da matsala matuƙar za ta kiyaye sharuɗan da zan kafa mata, kasancewar ina da kishi." "Nasreen, tana da tarbiya na san ba za mu samu matsala ba." "Ai shikenan, ni kuma zan biya mata har ta gama." "Alƙawari ka yi." "Eh, ina da abin yi." Ya ce tare da miƙewa. Ba tare da ya ce masa uffan ba ya fice daga ofis ɗin. Harara ya raka shi da shi har ya fice. Wawan tsaki ya ja sannan ya kwashi fayal ya fice daga ofis ɗin bayan ya kulle ƙofa. Nasreen ta yi kuka ta nuna ba ta son auren, amma ita kanta ta san ihu take bayan hari, domin babu abin da zai fasu game da auren, tun da ya amince. Tun tana yin bore har ta aminta ganin babu yadda za ta yi. Baba ya so ya ba shi sadakin a hannunsa, saboda ya ci burin ya kashe kuɗin, don ba zai yi mata komai ba, tun da ya ce ba ya buƙata. Kamar ya san bin da ke ransa ya sanya aka je har gurin aikin Ahmad aka kai masa dubu ɗari biyu. Karbar kuɗin ya yi tare da haɗawa da na gurinsa, aka siya mata kayan kicin masu tsaɗar gaske. Zagi kuwa babu wanda ba su sha ba, da ya ji sun kaiwa Ahmad kuɗin. A ranar Ahmad da Faruk Allah kaɗai ya san zagin da ya yi musu.Shi dai Ahmad bai damu ba, tun da ya yi abin da ya kamata. Saboda baƙi cikin abin da ya yi masa, ya rantse ko masara ƙwaya ɗaya ba zai kawo ba, kuma haka akayi duk abin da aka ci ƙoƙarin Ahmad da Faruk ne. Faruk ya cire maƙo ya zabga akwati na ban mamaki. Ita kanta da ba ta son auren sai da ta kalli akwatin. Ba tare da sanin cewar da ƙyar ya ba da ƙudi masu ɗan soka. Yayinda da mahaifiyarsa suka yi akwati na gani na faɗa. Fadila ita ce amara ƙirjin biki. Anci an sha kuma an cashe. Da ma Faruk na jiran ranar ya haɗa shagalin da zai fi na abokan sa. Da wannan ƙudirin ya haɗa dinner lunche. Amarya ta yi kyau iya kyau sosai, domin Su Anty sun yi matukar ƙoƙarin su gurin gyara ta da su dilka. Faruk ya kashe kuɗi sosai, gurin siyen tibin bango kayan furniture da kuma su gas. Ba ta shiga tashin hankalin ba, sai da aka tasa ta ana mata nasiha za a tafi da ita. Ta yi kuka sosai ta so ace ta yi auren soyayya, amma ga yadda ƙaddara ta kasance, saboda ko kaɗan babu soyayyar Faruk a ranta. Sai dai, dole ta yi ƙoƙarin sakawa ganin ya zamo mijinta, wanda aljannarta take tafin ƙafarsa. Ya zama dole ta koya ma kanta sonsa. Nasreen bayan an kaita, kowa ya watse sai Fadila da take ta ba ta baki. Ita kanta ta yi mamakin gidan Faruk, domin ya haɗu iya haɗuwa. Kallon gidan take cikin sha'awa tana tunanin ina ma ace ita ce a gidan, musamman falon ta da ya sanya kujeru masu kyau da ƙaton tibin bangon dake barazanar cinye bangon falon. Nasreen rungume ta yi cikin kuka tana faɗin,"Yanzu tafiya za ki yi ki bar ni da mutumin da babu sonsa a zuciya?" "Haba Nasreen, kar ki zamo mai taurin kai mana. A tunanina nasiha da su Anty suka yi miki ya wadatar. Ke da za ki ɗaga hannu ki godewa Allah. Ki tuna gidan da kike rayuwa, amma yau dubi gidanki." "Ina jin babu daɗi ne, saboda sam babu shaƙuwa a tsakaninmu ban san yadda zaman namu zai kaya ba." "Alkhairi. Ki yi wa auren ki fatan alkhairi kin ji?" "To," Ta ce tare da share hawaye har ta saketa sai kuma ta rungume ta ta fashe da kuka. "Ki ta ya ni addu'ar na so shi kar na faɗa halaka saboda ƙiyayyar da na ke masa." "In sha Allahu, za ki so shi ku zauna lafiya." Bayan sun tafi gidan ya yi shiru. Sai ta fara jin tsoro, saboda girman gidan. Ji ta yi kamar ana magana a cikin ɗaki. Da sauri ta dawo falo ta zauna. Wayarta ta ɗauki wanda ya siya mata tun tana gida, amma ko da aka ba ta kasheta ta yi, ta sanya ta can kasan akwatinta. Sai yau da ta ga babu makawa aurensu ta ba wa Ahmad ya yi mata caji. "Ya Ahmad.." Ta ce cikin muryar kuka. Tsoro ya ji da ya ji muryar ta a haka. "Lafiya Nasreen?" "Tsoron gidan na ke ji, babu kowa." "Kai Nasreen rigima. Dole ki koyi zama ke kaɗai, saboda yanzu kin girka kin zama matar gida. Zai shigo ki ci gaba da fadin La'ilaha illa anya subuhaka inni kuntu mizzalimin." "To Yaya," Ta ce tare da kashe wayar cikin jin kunya. Miƙewa ta yi tare da shiga cikin bayin, ta yi wanka sannan ta shirya cikin less mai kyau. Tsayawa ta yi tana ƙare wa ko ina kallo a cikin gidan. Mamaki sosai take yi don ba ta yi tunanin Faruk yana da kuɗi haka ba. Tana zaune ta ji alamun an buɗe gidan da makullin. Gabanta ne ya faɗi sosai. Faruk kuwa bakinsa har kunne saboda tsananin murnar da ya ke ciki. Duk da cewar ba ta wani saki jiki da shi ba har aka yi aure, amma ba shi zai hana shi more aurensa ba. Ya sanya a ransa yau zai fanshe duk kuɗin da ya kashe ma ƙwaɗayyan tsohon ta. Ya yi kyau abin da matuƙar gaske! Yana cikin shiga ta alfarma. Shadda bugaggiya gizna ya ɗin ka. Sai ɗaukar idanu take tana sheƙi. Farar ƙal mai kyau. Yana tafe a gaba suna binsa abokansa.Mus'ab ya kalle shi cikin tsuma ya ce,"Ka ga ango jiki har rawa yake ya isa ga amarya?" Dariya suka kwashe da shi suna kallonsa. "Laifina za ku gani? Ba kwaka ganin yadda Allah ya kashe ya bani zuƙeƙiyar mata. Ai yau duniya tamu ce daga ni sai ita a ciki." "Haka ne kuwa domin duk wayon amarya, sai an sha manta." Suna wannan barkwancin suka hada baki suka yi sallama. Da fari ɗaki ta shige, amma sai ta ga rashin dacewar hakan. Da sauri ta dawo falo ta ƙudundine da gyalenta. Sallamar ta amsa murya ƙasa-ƙasa, yayin da ganbanta yake dukan tara-tara. Faruk kai tsaye kujerar da take, ya nufa ya zauna dap da ita sun jin numfashin juna. Ƙoƙarin matsawa nesa da shi ta yi ta kasa ce musu komai. "Amarya ba kyau laifi." Mus'ab ya ce yana kallonta cikin lulluɓi. "Ko da ta kashe ɗan masu gida." Faruk ya amsa sannan suka kwashe da dariya. Ki gaisuwa ba su samu ba, domin jinta yi ta matuƙar takura. Tana ji suna ta barkwancin su da tsokanarta, wanda Faruk yake kare ta har suka gaji suka yi addu'a, tare da yi musu fatan alkhairi sannan suka tafi. Raka su ya yi har bakin get, bayan sun fita ya rufe get ɗin ya dawo ciki. Zama ya yi gaba da ita. "Nasreen," Ya kira sunanta cikin wata irin murya. Ɗagowa ta yi ta kalle shi daidai, lokacin da ya ɗaya gyalenta tare da ƙura mata idanu. "Kina ta kaucewa ba kyau sona, ga shi Ubangiji ya ƙaddara aurenmu." Hawaye ta fara wanda ya ɗan ja ƙaramin tsuka. "Ni fa Malama ban ce ki yi mini kuka ba. In kika kike son yi za ki.." Don Allah ayi mini haƙuri daga yau zan rinƙa posting page ɗaya, sai bayan sallah na ci gaba da biyu.🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏 *_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 9 Ɗagowa ta yi ta kalle shi daidai lokacin da ya ɗaga gyalenta tare da ƙura mata idanu. "Kina ta kaucewa ba kyau sona, ga shi Ubangiji ya ƙaddara aurenmu." Hawaye ta fara wanda ya ɗan ja ƙaramin tsuka. "Ni fa Malama ban ce ki yi mini kuka ba. In kuka kike son yi za ki yi mai dalili ai. Ni sam bana son kukan yaro, ballantana ke ƙatuwa dake." Ya ce cikin ɗaya murya tare da miƙewa ya rage babban rigarsa. Ledar da ya shigo da ita ya janyo.Kaji guda biyu ya fito da su da lemu. "Ga shi ki ci mu je mu kwanta." Gabanta ne ya fadi! Ta kasa ko da motsawa jin abin da ya ce. Ganin ba ta ɗauka ba, ya sa ya hannu ya buɗe kazar ya ɗauki nasa, sannan ya miƙa mata na ta. Ki mai ya tuna oho sai ya tashi ya je kicin, ya ɗauko filet ya yanka mata. A baki ya miƙa mata. Ganin haka ta kauda kanta cikin jin kunya. Ijewa ya yi ya fara gayar ta sa. "Tun da kunya kike ji bari na ci tawa." Ya ce yana kai kai cinya a bakinsa. Tana zaune ya ci ya ƙoshi ya yi gyasa sannan ya kira da juice. A maimakon ya tattasheta ta ci saboda rabonta da abinci, za ta iya cewa tun safe shi ma Ahmad ne ya sanya ta ci shinkafar ɗaurin aure da ya sanya aka dafawa abokansa. "Tashi mu je mu kwanta." Ya ce mata yana mata wani irin kallo. "Ni bana jin bacci." Ta furta masa cikin muryar kuka. Dariya ya yi sai kuma ya zauna a gefenta."Haba Nasreen kamar ba wayayyiya 'yar jami'a ba? Matan jami'a da idanunsu yake a buɗe wayewa ta yi musu yawa. Su ne fa ranar da aka kai amarya take seducing ɗin angon ta, ba tare da kunya da jan aji ba. Ke ni don ina son mace mai ilmi da wayewa ne, amma babu abin da zai sanya na auri yar jami'a domin yawancinsu ragowar lecturer ne." Da sauri ta ɗago idanunta tana kallonsa."Faruk, ka yi musu mummunar fahimta, domin wasu ke ɓata wasu..." "Don Allah ki yi mini shiru. Yanzu ni da kaina zan tabbatar da hakan. Da na yi maganar makaranta kin iya tanka mini. Cases nawa muke ji a cikin makarantar namiji ya yi lalata da su?" Share ta ji zubowar hawaye, ganin ya aure ta ba tare da yadda a tsakaninsu ba. "Na lura dake fa kan karatu ne kawai zamu samu saɓani, saboda yadda kika ɗauki boko, bana tunanin turawan da suka kawo sun ɗauka da mahimmanci haka. Kuma wallahi matuƙar za ki tauye haƙƙina kan boko za mu samu matsala da ke." Ya ce cikin fushi. Ba ta yi mamaki ba yadda yake mata magana cikin ɗaga murya. Ko kafin su yi aure in ya zo zance yana ɗaga murya. Tuni ta gama fahimtata sam ba shi da haƙuri. "Ki tashi mu je mu kwanta na ce!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka. Da sauri ta miƙe ganin yadda ya canza fuska. Ganin ya yi hanyar ɗaki ta bishi idanunta na zubar hawaye. Bayi ya shiga da nufin ya yi wanka. Ganin haka ta zauna a bakin gadon tana ƙare wa ɗakinsa kallo, don ya tsaru matuƙar gaske. Gefen gadon ta samu ta kwanta. Bacci har ya suma ɗibanta, saboda kanta da yake ciwo ta ji yana dukan filon da take kwance. "Wannan wane irin wulakanci ne za ki zo ki kwanta da less a jikin ki? Ke ni fa ina son mace mai wayewa da iya rayuwar aure, don haka ki buɗe idanunki bani kula, saboda in har kika ƙi haka to za mu sanya ƙafar wando ɗaya ni da ke." Jin kalamansa ya sanya ta miƙe ta za ta fita. Komawa gadon ya yi, tare da jan tsuka yana harararta domin shiru-shirunta haushi yake ba shi. Ya fi don macen da idanunta suka buɗe wacce za su ci duniyarmu da tsinke. Wannan dalilin ya sanya har yau yake ganin zuciyarsa ba ta yi masa adalci ba, na son bagidajiyar mace. Nasreen kuwa tana zubar hawaye, tana duba kayan baccin da za ta sanya. Ta san cewa a yau babu wata ƙauna da tattashin da za ta samu. Allah ne kawai zai ƙwace ta a hannunsa. Da ƙyar ta iya saka wata doguwar riga, sannan ta sanya hijabinta ta dawo ɗakin. Tsaki ya yi." Shi kuma hijabin da kika saka kamar wata mai zaman makoki ko matar liman fa?" Banza ta yi da shi ta zauna tana faɗin,"Na fa ɗaya." A ranta don ko mai zai yi mata ba za ta iya cire hijabin ba. Gani da gaske ba za ta cire ba, ya sa ya shi miƙewa ya zo inda take. Janyo ta ya yi ya rungume tare da sakin ajiyar zuciya. Jikinta ya fara rawa sai kuka amma bai kulata ba ganin za ta kawo masa matsala. Faruk ba tare da tausaya wa ko tuna sabon shiga bace ya amshi sadakinsa. Ta yi kuka sosai har sai da muryarta ya rushe amma babu tausayi a zuciyarsa. Yana kwance idanunsa a rufe yana jin yadda take ajiyar zuciya. Shiru ya yi a ransa yana mamakin yadda aka yi ta kula da mutuncin kanta, duk da halin talaucin da suke ciki. "Ki yi shiru kin dame ni da kuka, bacci zan yi." Ya furta tare da juyawa sai bacci. Tsananin mamaki ya kamata, domin tasha jin ango yana taimakawa matarsa a ranar amarcinsu. Tana zaune cikin damuwa ta ji yana jan rago. A hankali ta ɗan miƙe, amma sai ta koma ta zauna da sauri tana jin raɗaɗin azaba. Rintse idanunta ta yi cikin muryar kuka tana kiran sunan Allah. "Faruk, ka taimaka mini na ba zan iya tashi ba." Ta furta cikin muyar kuka. "Ki yi shiru ki kwanta mu yi bacci." Ya ce yana jawo ta jikinsa. Da sauri ta ƙwace jikinta cikin hawaye. "Ba zai tsabtace kansa ba?" Ta yi ma kanta tambayar haka duk da ta san cewa ba wai ya haramta bane, amma kwana da tsarkin yafi. Cikin dabara ta bi bango zuwa kicin. Ruwan zafi ta ɗora ta zo ta bawa kanta duk wata kulawa. Sannan ta samu sama-sama. Falo ta dawo ta ɗauki kazar da ya rufe mata ta ci, jin yadda cikinta yake juyawa. Ba ta wani ci sosai ba ta ije kazar saboda hatta bakinta ba ya mata daɗi. A maimakon ta koma ɗakinta, kwanciyarta ta yi kan kujera tana mamakin halin angonta. Cikin dare zazzaɓi mai zafin gaske ya kamata. Ta miƙe don ta rufa jin yadda kyarmar sanyi ya kamata. Ga mamaki ta sai ta ji ta a jikin mutum. Da sauri ta fara kiciniyar matsawa daga jikinsa. Buɗe idanunsa ya yi, yana hamma a lokacin kuma aka fara kiraye-kirayen sallah. "Gari ya waye haka? Gaskiya ban yi bacci sosai ba." Ya ce mata yana kallonta. "Ba ki da lafiya da safe zan siya miki paracetamol." Iya abin da ya furta kenan ya ci gaba da baccinsa. Ranta ya ɓaci sosai cikin mamaki take kallonsa. Miƙewa ta yi tana mamakin yadda aka yi ya ɗauko ta, ba tare da ta ji ba. Tuna da paracetamol a jakarta da Ya Ahmad ya kawo mata juya da rana. Ya sanya ta miƙe ta ɗauki jakarta sha maganin. Ɗan komawa ta yi ta kwanta don ta bawa jikinta hutun mintina. Bacci mai ƙarfi ya ɗauke ta. Ba ta farka ba sai ta ji ana sallar asuba. Da sauri ta tashi tana salati. Gefen Faruk ta kalla da yake shara baccinsa kamar ba musulmi ba, domin duk musulmin ƙwarai wanda ya yi riƙo da addininsa ya kuma tsaida sallah. Bai kamata ace lokacin sallah sai an tashe shi ba. "An ya na yi dacen miji kuwa? Wanda zai ɗora ni a tafarkin tsira ina kauce? " Ta yi wa kanta tamabayar cikin damuwa "Faruk, sallah ake yi." Ta tana kallonsa. "Ke ki kyale ni zan yi ta ina tashi saboda na gaji jikinsa ko ina ciwo yake mini. Ga gajiyar biki ga wanda kika sa ya ni." Ya ce yana kallonsa sai kuma ya miƙe mata hannu. "Zo mu kwanta in muka tashi mu yi tare." Ta kasa ce masa komai, wanda ganin haka ya juya ya ci gaba da baccinsa. Hawaye take zubarwa, hawaye da ta san in har haka rayuwarsa za ta ɗora ta rinƙa yi har ƙarshen rayuwarta. Alwala ta yi ta yi sallah sannan ta yi azkar. Miƙewa ta yi ta shiga bayi ta ƙara gasa jikinta. Tana zaune tana jan carbi har gari ya waye. Ganin bakwai ya yi ya sanya ta ƙara tashinsa. Hannunsa ya sanya ya ja jata ta faɗa jikinsa. "Bari na sanya ki taya ni wankan." Duk yadda ta so ta ƙwace jikinta ya ƙi har sai da ya gama abin da zai yi. Mamaki da takaici suka cika ta. "Zo mu je mu yi wankan." Ya ce mata babu alamun ya damu da wucewar lokaci. Miƙewa ta yi wanda bai ja da tsawo ba ya shige bayi, musamman ganin kallon da take masa. "Na shiga uku! Wani irin miji na samu wanda baya kula da addininsa?" Ta furta cikin zubar hawaye. Da ya fito daga wankan sai da ya gama ɓata lokacinsa gurin shirya wa. Sannan ya reshe jikinsa da turare, ya shinfiɗa dadduma ya yi sallar da ba ta ɗauke shi tsawon minti biyar ba. "Baby ba gaisuwa?" Ya yi mata tamabayar ba tare da damuwa da kallon tuhuma da take masa ba. "Ina kwana? Amma ka san lokacin da ka yi sallah bai kamata ba?" Kallon banza ya yi mata tare da amsa gaisuwar a gajarce. "Takwas ɗin?" Tambayar da ya yi mata ya ƙara ninka tashin hankalinta. Cikin rawar murya ta ce,"Eh, saboda a loka..." "Nasreen dakata..!" Ya katse ta yana fadin haka. "Sallah sallah ce in har mutum da safe zai yi. Da ma kin ga na barta har zuwa azabtar sai ki yi mini karabbanin wa'azi. Kuma ai na fi wasu, domin wasu suna nan ba sa yi sallar, suna kuma amsa sunan su na musulmai." Hankalinta ya ƙara tashi jin abin da tace, wanda ta gane tsantsan jahilci damunsa. "Faruk, don wani na aikata zunubi bai kamata ace kana duba wannan ba, domin wannan dalilin ya sanya Ubangiji yake kar mutum ya duba halin wanda ya yi masa nasiha, abin da ya fado..." "Mu bar maganar nan, tun kafin ki ɓata mini rai, don ni ban shirya jin wa'azi ba 'yar gidan malamai." Ta san abin da ya faɗa gatse yake mata. Jin haka ya sanya ta miƙe zata fita daga falon ba ta ce masa komai ba. "Yunwa na ke ji. Ina fatan kin zo da gara?" Katsa da kanta ta yi jin abin da ya ce, wanda kamar ba za ta amsa ba, sai kuma ta ce,"Eh, amma iya shinkafa ce kawai da taliya." Wawan tsaki ya ja, tare da miƙewa saboda tsananin talauci garar ma ba za a kawo ma? Bayan duk wahalar da na yi?" "Za a kawo sai yau Ya Ahmad zai je da Anty su siyo." "Kar ma su suyi su bar shi, ai ba zan mutu da yunwa ba." "Da ma na san za a rina, wai an saci sanin mahaukaciya. Na san cewa rayuwar aure a da kai ba zan kurɓi ruwan daɗi ba, wadannan abubuwan na yi ta kaucewa, amma Baba ya nace auren mu, bayan ya gama zubar mini da mutunci." Ta furta cikin zuciyarta. Takalminsa ya saka tare da ficewa daga gidan yana ƙunkunai. Ta ɗauka abin kirki zai siyo, amma ga mamaki ta sai ta ga ya siyo biredi saba da ɗaya da madara na sachet, sai Lipton da siga gwangwani ɗaya. Da kwai guda biyu, sai magi biyar da gwangwani mangyada da kuma kayan miya. "Ki tashi ki haɗa mana breakfast." Jikinta na ɓari ta miƙe ganin yadda ya ci magani. Kallon kayan take cike da maimakinsa. A yadda yake da wadata mai kamata ace ya fito wadannan kayan ba. Sai ta yi masa uxuri, domin ba ta son ƙara sanya kanta cikin damuwa. Haɗa komai ta yi ta kawo masa da yake zaune a falo yana kallo. Jawo ta ya yi ta zauna kusa da shi. "Mu karya." Ya ce mata wanda babu musu ta zauna a gefensa. Cikin jin kunya take juya ruwan tea din, tana kallonsa da yake ta aika ma cikinsa, don har ya kusa cinye ƙwan. Sai da ya ci abinci da sosai, sannan ya ture ya ci gaba da kallo, ba tare da ya kula ta ba da take ta juya cokali Yunwa take ji sosai amma bakinta babu daɗi. Haka nan ta daure ta sha ruwan tea sannan ta cinye ɗan ragowar ƙwann ya rage mata. Miƙewa ta yi ta kai kayan kicin tare da ƙara gyara gurin. Bacci take ji sosai domin da kyar take buɗe idanunta.Kama hanyar ɗaki ta yi tana hamma. "Nasreen," Ya kira sunanta. Dawowa ta yi ta zauna a can nesa da shi. "Ina da wasu dokoki da zan kafa miki a gidan nan, wanda matuƙar kika kiyaye su, to ba za mu rinƙa samun matsala ba, amma kin ga in kika yi kunnen uwar shegu da su. Tsakanina da ke babu sausauci. Jin kalamansa ya sanya ta yi shiru, ta kasa cewa komai, sai wasa take da yatsun hannayenta. "Na farko ni mutum ne mai tsananin tsafta. Sam ba na son ƙazanta in kika zama mai tsafta, ba za ki samu matsala da ni ta wannan ba. Sannan na biyu kuma ba na son mutane, saboda yadda na kashe maƙudan kuɗi, ba zan bari ko wane banza ya shigo mini gida ya ɓata ba, saboda haka, sai ki kiyaye waɗanda za su shigo mini gida. Kayan abinci kuma gwada miki zan rinƙa yi, don ku amaren zamanin nan, sam ba ku san yadda kayan masarufi suka yi tashin Gwauron zabi ba. A takaice ba na son albazaranci. Sannan kin sanni bana son ƙawayenki su rinƙa zuwa gidan nan, ko Fadila ban lamunta ta rinƙa mini safa da marwa a cikin gidana ba." Da sauri ta kalle shi jin abin da ya ce tana mamakinsa. "Na ga kin ɗago da sauri, Fadila tare aka haife ku?" Ba ta amsa ba sai ta ɗauke idanunta kawai. Ganin ba ta ce komai ba ya ɗaura da cewa. "So na ke na huta in har ba gara aka kawo mini ba, kar ki sake ki buɗe wa kowa gida." Jin abin da ya ce ya sanya ta daina mamakinsa don ya zarce tunaninta. "Ki na jina kin yi shiru?" "Zan kiyaye." Ta furta tare da fara tafiya. Ɗaki ta shiga ta kwanta cikin damuwa. Baccin da take ji ta nema ta rasa..Kwanciya rub da ciki ta yi tana hawaye. Tana kwance ta ji ya tura ƙofar ya shigo. Gabanta ne ya faɗi da sauri ta juyo tana kallon sa. "Bacci ya kamata mu yi kin san ya kamata mu huta lokacin amarcinsu." Ya furta tare da kwanciya a gadon ya ja bargo ya rufe su. Nasreen sai ta ji ta takura damuwa ta yi mata yawa. Ga tsanarsa ga takura ta da ya yi. Ji ta yi sam amarcin na su ba ya mata daɗi. Ta ɗauka wasa yake mata kan maganar babu wanda zai shigo. Sai ta ga ashe da gaske yake. Haka aka rinƙa dukan ƙofar, amma ya hana ta ta je ta buɗe. Wayarta da ke kan mirror ta yi ƙara alamun ana kira. Da sauri ta kai hannu za ta ɗauka. Hannunsa ya sanya ya hana ta."Ƙila wadanda suke buga ƙofar ne suka kira. Kar ki ɗauki wayar, saboda babu wanda ya isa ya hana ni cin amarci. Jarabbabu kawai mutum da aure su da nacin zuwa ganin amarya." "Zan duba ne watakila Anty Maryam ce, saboda ta ce in suka dawo kasuwa za su zo." Ta ce masa cikin rawar murya tana son yin kuka. Ƙaramin tsaki ya ja yana kallonta." Ok, ki duba su ɗin ma ban yi maraba da zuwan su ba, don na san ba abin arziki za su kawo ba." Ba ta ce masa komai ba ta duba wayar cikin damuwa."Su ne." Ta ce masa tana kallon sa. Tsaki ya yi tare da sauka a kan gadon ya wuce ɗakinsa. Ganin haka ya sanya ta sauko ta je ta buɗe musu. Anty Maryam da Binta babbar ƴaƴansu su. Ganin su ya sanya ta faɗa jikinsu tare da saka kuka. "To kuma mene abin kuka daga zuwanmu." "Ba na jin daɗin zaman gidan ina son na koma gida." Dariya suka yi jin abin da ta ce."Allah Sarki! Kowa da haka ya fara dole ki jure." Cewar Binta tana kallon su. "Ga shi in ji Mama, da ƙyar ta samu ta yi miki wannan siyayyyar, wannan kuma cincin da dibilan ne aka yi miki sai ki iba ki ce ya kai ma danginsa.." "To," Ba ta ji daɗin kawo wa ba, don ta san wanda aka yi don shi ba yabawa zai yi ba. Yana jin maganar su amma ya ƙi tasowa su gaisa. "Kamar na ga motar mijin ki na nan?" "Eh,"Ta furta cikin jin kunya. "Amma shi ne ya ƙi zuwa mu gaisa?" "Bacci ya ke yi." Ta tsinci kanta da yi musu wannan ƙaryar. "Ko idanunsa biyu da wuya ya zo, saboda ya raina ƙurarmu. Nasreen, sai kin haƙuri da mijin da Allah ya ba ki, sannan ku dage da addu'a." Kuka ta fashe musu da shi. Da ma mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Rarrashinta suka shiga yi sannan suka yi mata sallama suka tafi. Yana jin sun fita ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya fito. Kallonsa ta yi cikin jin kunya lokacin da ya ƙara so daga da ita ya zauna. "Abin da suka kawo kenan?" Ta kasa ce masa komai wanda hakan ya sanya ya ja tsuka ya miƙe. "Yunwa na ke ji ki je ki yi mana abinci. Allah ya sa kin iya saboda na ji ƙwan da kika dafa ya yi gishiri da yawa." Ba tare da ya kalleta ba yake faɗin haka, bayan ya ɗauki remote yana canza tasha. Kicin ɗin ta shiga tana tunanin abin da za ta yi. Babu abin da za ta iya girkawa wanda ya wuce shinkafa da taliya, domin su kaɗai ne a cikin gidan. Shinkafa da taliya ta haɗa ta yi jalop sannan ta shirya abincin a ciki kula ta kai masa. Ta yi tunanin zai yi ƙoƙarin, amma sai bai ce komai ba. Ya dai ci abincin fuskarsa babu yabo, babu fallasa. Bayan ya gama cin abincin ya yi wanka ya fita daga gidan. Sai a lokacin ta samu ta sake a cikin gidan. Ɗaki ta koma ta zauna tare da ɗaukar wayarta, tana duba waɗanda suka kirata. Ganin numbar Fadila ya sanya ba ta ji ba daɗi ba. Tana ƙoƙarin kira sai ga kiranta ya shigo. "Amarya ba kyau laifi." Murmushin yaƙe ta yi mata kamar tana ganinta. "Mun zo da sauran ƙawayenmu, amma mun yi bugun duniyar an, ba ku zo kin buɗe ba." Ƙasa ce mata komai ta yi, domin ba ta san mai za ta ce mata ta yarda ba. "Hala ba ku yi bacci ba jiya cin amarci ya hana?" Ta yi mata tambayar cikin zolaya. Jin ta yi shiru ya sanya ta ce,"Gobe zan zo ni kaɗai tun da sun tafi. Ki aje mini dibilan da cincin." "To, sai kin zo." Ta yi mata sallama tare da kashe wayar. Farouk bai dawo gidan ba sai, bayan kiran sallar isha. A lokacin ta yi wanka, tana kwance kan doguwar kujera da wayarta tana karatu. Jin ƙarar motarsu ya sanya zuciyarta bugawa, saboda tsoransa take yi sosai. Ji take yi kamar karya dawo gidan, don takurar da yake mata. Jin yana magana da mutane maza a waje. Ta gane ba shi kaɗai bane. Da sauri ta tashi ta shiga cikin ɗauki, ta sanya hijabinta. Ya shigo da kaya niki-niƙi a hannunsa ga kuma sauran abokan nan su ma ɗauke da kayan. Mamakin soyayyar da ya yi ta yi, ɗin ba ta yi tunanin zai siya komai ba. A maimakon ta ga ya zuba a store, sai ta ga ya shirya cikin ɗakinta da su. "Sannun ku da zuwa." Ta ce tana tsaye. "Amarya ba kyau laifi." Suka haɗa baki gurin faɗin haka. Murmushin ta yi sannan ta gaishe su cincin da dibaln ta kawo musu. Farouk ya ibo musu drinks ya kawo musu. Ɗaki ta wuce takwanta tana jin suna hira har ƙarfe goma da rabi, sannan suka yi musu sallama suka tafi. _WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 10 Ɗaki ta wuce takwanta, tana jin suna hira har ƙarfe goma da rabi, sannan suka yi musu sallama suka tafi. Tafiyarsu ya sanya ta ji babu daɗi. Ta so ace su yi zamansu har gari ya waye. Tana kwance ya shigo cikin ɗakin bayan ya gama kulle ƙofar gidan. Kallon ta ya yi, tare da zama gefen ganin ya ja tsuka. "Yanzu abin da kika yi wayewa ce, a matsayin ki na mace 'yar boko?" "Tana son ta tambaye sa abin da ta yi, amma kuma ta kasa, tun da ba ta san laifin da ta yi masa ba." "Ni fa bana son gidadanci da rashin wayewa. Kina ganin abokaina sun zo, a madadin ki shiga ɗauki ki ɗauko mayafi mai kyau. Ki fito musha hira, amma sai kika saka wani zubbulelen hijabi, kamar wata matar liman." Ba ta amsa masa ba, kamar yadda ya yi tunanin ba za ta amsa masa ba. "Kuma ba zan ɗauki wannan shiru-shurin ba, domin buɗe baki za ki yi, in na yi magana ki amsa mini." "To," Ta ce mishi tare da gyara zama. "Yauwa kin ga kayan abinci na siyo, amma ban amince ki ɗauki komai ba, sai da izinin a, domin kulle ɗakin zan rinƙa yi innzan fita." "To," Ta ƙara ce masa don ya daina ba ta mamaki. Miƙewa ya yi tare da kashe fitila sai ya kuma kunna yana ƙare mata kallo. "Nufin ki da wannan kayan za ki kwanta?" "A,a." Ta ce a gajarce. "Ta shi ki canza kaya bacci za mu yi." Ya ce tare da kwanciya kan gadon ya rungume filo yana mata kallon ƙurilla. Kunyarsa take ji sosai duk da abin da ya faru a tsakaninsu, ba ta jin ta fara sakewa da shi, amma ba ta da wata mafita da ya wuce ta canza kayan. Riga da wando ta ɗauka masu kyan gaske ta sanya. Sun yi mata matuƙar kyau, amma ta kasa haɗa ido da shi, ballantana ta taho kan gadon. Ganin haka ya miƙe ya janyo ta, ta faɗa jikinsa."Wow! Kin ga yadda kika yi kyau? Kina da matukar kyau Nasreen. Da ace za ki tattala halittar ki, za mu ci duniyarmu da tsinke, don zan more wannan jikin na ki." Ba ta ba shi amsa ba sai kallon gefe take yi cikin jin kunya. Ganin ta yi shiru, ya sanya ya ƙara mannata a jikinsa tare da ɗauke numfashi. Bakinsu ya haɗe sannan ta jawo ta suka faɗa gadon. Washegari da asuba jin kiran sallah, ya sanya ta miƙe zuwa bayi. Tun cikin daren ta buƙaci ta yi wankar tsarki, amma sai ya ƙi ya haɗata da jikinsa ko motsin kirki kasawa ta yi. A haka suka kwana har asuba. Da ƙyar ta janye jikinta ta shige bayin. Bayan ta yi wanka, ta yi Raka'atul fijr ta zauna tana karatun Alkur'ani, cikin muryarta mai sanyi. Karatun da take yi ya sanya shi miƙewa tare da jan tsuka ba don ya so ba. Ɗaki da ya wuce ya yi wanka. Sallah a gida ya yi, sannan ya kwanta. Bai tashi ba har zuwa tara da rabi. A lokacin Nasreen tana farko tana ta gyaran gidan, domin kamar yadda ya gaya mata ba ya son ƙazanta, so take ta kiyaye don su zauna lafiya, kuma ko ita ba mace bace mara tsafta. Ganinta a falo tana gyara ya sanya sakin fuskarsa, tare da ƙara sawa inda take ya rungume ta. Kiss ya sakar mata a fuska. "Ina kwana?" Ta ce mishi cikin murya mai sanyi, domin ta riga ta saki tun da har ya mayar da ita cikakkiyar 'ya mace. Ba ta da zaɓin da ya wuce ta aminta da aurensa su zauna lafiya. "Lafiya lau, amma ni fa so na ke ki nuna wayewarki. Ki rinƙa nuna mini ƙauna da kulawa. Gaisuwar ina kwana ta 'yan kauye ne " Ware hannunsa ya yi, yana kallon ta wanda babu musu ta shiga jikinsa cikin jin kunya. Sun daɗe a haka sannan ya sake ta bayan ya ba ta hot kiss. "Bari na baki abin da za ki yi mana breakfast." Ya ce tare da juyawa cikin ɗakinsa. Bayansa ta bi da kallo, tana son gane makusarsa da zuciyarta ba ta ƙaunarsa, amma ta kasa ganowa. Sai ta danganta ƙinsa da take yi da rashin kyawun halinsa. Tana wannan tunanin ya ɗauki indomie gida uku da ƙwai uku."Ki soya mini ƙwai biyu, sai ki soya wa kanki ɗaya." Karɓa ta yi har da rissinawa ta ce,"To," Cikin girmamawa sannan ta nufi kicin ɗin ba tare da ta ji wani abu ba. Kamar yadda ya ce haka ta dafa masa. Da ta zo zuba masa abincin, sai ta kusa biye masa. Bayan ta kai mishi ta sanya ragowar indomie ta ci. Da ta ji ba ta ƙoshi ba, sai ta ɗumama ragowar abincin da ta girka jiya. Bayan sun karya komawa suka yi suka kwanta bisa umurninsa. Duk yadda yake takura mata hakan nan take haƙura don zaman lafiya. Sai kusan ƙarfe ɗaya da aka kira sallah ya yi wanka ya fita gidan a mota. Sosai ta ji daɗin fitarsa. Bayan ta ci kuskus ɗin da ta dafa ta koma ta kwanta kan gado. Ba ta ji ma ba ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. Tana don ta buɗe tana tsoron karya dawo. Da sauri ta miƙe ta je ta buɗe, saboda shawarar da zuciyarta ta bata. Wata doguwar mata ta gani tsaye da yaranta biyu a ƙofar gidan. Murmushin ta sakar mata, tare da matsawa suka shiga ciki. Bayan ta zauna a falo, ta kalli Nasreen da take wasa da ƙaramar 'yarta da ta ɗauka. "Sunana Aisha, amma ana kirana da Maman Muwadda. Ni maƙociyarki ne, a unguwar nan na ke. Ga gidanmu nan mai mulki ɗin get, wanda katangar da yake kusa da na ku." "Allah Sarki! Sannu da zuwa, ni kuma sunana Nasreen." Murmushi suka sakar wa junansu. Nasreen ta kawo mata cincin da diblan da yawa. Suna ta hira, amma gabanta na faɗi. Inda ta godewa Allah ba ta wani jima ba ta miƙe. "Bari na tafi na gode sai na ƙara shigowa." "Ni ma na gode sai anjima kuma zan shigo." "Shikenan, Allah ya ba ki iko." "Amin," Ta amsa tare da rakata har bakin ƙofa. Tana ƙoƙarin kulle ƙofar sai ga Fadila.Da sauri ta rungume ta har da hawayen murna. "Dallah ni cika ni. Kina can naniƙe da miji na yi ta buga ƙofa da kiranki, amma kika shanya ni." "Ki yi haƙuri ban ji ba." Ta furta cikin muryar kuka. "To kukan me za ki yi don kin ganni? Kin ga yadda kika ƙara kyau? Gaskiya Faruk na kulawa dake." "Hmmmmh!" Ta ce tare da kama hannunta suka shiga cikin gidan. Abinci ta kawo mata da ruwa da diblan. Suna ta hira ji take kamar kar ta tafi. "Ina angon na ki? Na tsokane shi." Gabanta ne ya faɗi ta ce,"Baya nan, tun da ya fita sallah bai dawo ba." Dirin motarsa da ta ji ya sanya ta ji gabanta ya faɗi. "Kamar buɗe get za a yi?" "Eh, shi ne ya dawo." Ta ce mata cikin fargaba. Ganin fuskarta ya canza ba ta yi tunanin komai ba. Ya shigo da siriyar sallama a bakinsa. "Sannu da zuwa." Ta ce masa tare da ƙara sawa gurinsa da sauri za ta karɓi kayan hannunsa. "Ango kasha ƙamshi." Ta ce tare da miƙewa tana dariya. "Kina lafiya?" Tambayar da ya yi mata kenan, ya shige ɗakinsa bayan ya kira Nasreen. Cikin jin kunya Nasreen ta kalle ta. "Farouk ni zai yi wa haka?" Narai-narai ta yi kamar za ta yi kuka."Ki yi haƙuri abin da na guda kenan, amma Allah ya riga ya zaɓa mini shi a matsayin miji, tun ranar da aka kawo ni ya gaya mini baya son mutane. Ke ƙawata ce ba zan ɓoye mini komai ba." "Ikon Allah! Ba komai ki je kiran da yake miki bari na tafi." Ta ce tana mamakinsa. "Don Allah ki yi haƙuri."Ta furta tare da kama hannunta. "Wallahi babu komai ba zai raba mu ba, matuƙar ba cewa ya yi karna ƙara shigo masa gida..." "Nasreen, ba na son wulakanci na kira ki za ki shanya ni. Ko ƙawarki tafi mijinki daraja?" Ta ji yana ƙoƙarin buɗe ƙofa tare da faɗin haka. Da sauri ta ƙarasa ƙofar ɗakin, tana ɗaga wa Fadila hannu da ta cika da mamaki, domin ta ɗauka ko zai yi wa kowa haka ban da ita. Jakarta ta ɗauka gwiwa a dage ta fice gidan. "Mai na gaya miki?" Ya furta tare da kama kunnenta da ƙarfi. Cikin tsananin mamaki ta kalle shi yayin da hawaye suka wanke masa fuska. "Eh, kalle ni da kyau, saboda wallahi in har ba za ki bi umurnina ba, sam ba za ki ji daɗi a hannuna ba. Zamanki lafiya a gidan nan duk abin da na ce bana so ki kiyaye." "Ka yi haƙuri ba zan iya wulakanta ya ba."Ta ce tana matsawa jin kamar zai cire mata kunnen. "Kin san ƙanwar uwarki ce." Ya faɗa cikin ɓacin rai tare da ture ta ta bugu da bango. Kuka ta fashe da shi cikin mamakin abin da ya yi mata. "Wallahi ba ki ga komai ba, domin ba ni da kirki in har zan sanya kara ki tsallaka, saboda iskanci na kashe maƙudan kuɗi na aure ki, amma kawai mutane ne bana so sai ki kasa bin umurnina, ina matsayin mijinki." Kuka sosai take amma bai kula ba ya shige bayi yana faɗin,"Ki je ki kawo mini abinci." Da ta fita daga cikin ɗakin ta shiga kicin. Jingina da ƙofar ta yi bayan ta kulle, tare da fashewa da kuka. "Allah na gode bisa jarrabtar da ka yi mini na miji irin Faruk. Allah ka bani ikon cinye wa." Gyaran muryar da ya yi a falo, ya sanya ta goge hawaye tare da fitowa bayan ta haɗa masa abinci. "Tun da kika ba ta abinci yau sai dai ki kwana da yunwa." Ya ce mata cikin ɓacin rai. Ta ɗauka wasa yake, amma bai ba ta abin da za ta girka ba. Ba wani yunwa take ji ba, amma ranta ya ɓaci sosai. Bayan ta yi sallah ta kwanta tana ta jan carbi a hannunta. Shigowa ɗakin ya yi, tare da tsayawa a bakin ƙofa. "Ke fa ba yarinya na ce, da sai na rinƙa binki, kuma ina koya mini yadda ake zama da miji. Ko ba ki san matan aure gayu suke ɗauka da kayan bacci masu ɗaukar hankali ba, suna zuwa turakar miji?" Shiru ta yi ba ta ce masa komai ba. Ganin haka ya ɗora da ce wa,"Ki shigo ɗakina ina jiran ki, kuma in har kika taho da hijabi wallahi dai kin raina kanki, don ban ga uban da kike ɓoyewa ba, wanda ban gani ba." Ta rasa kuka za ta yi ko mamaki. Ganin lokaci guda ya canza kamar ba shi ba. Miƙewa ta yi da sauri cikin minti goma ta shirya kamar yadda ya buƙata. Da kyar ta cire ragowar kunyarsa ta shiga ɗakin kamar yadda ya umurce ta. Banza ya yi da ita har ta gaji ta zauna a gefen gadon. Sai da ya gama abin da zai yi a laptop ɗin, sannan ya kashe ya miƙe mata hannu. Jikinta na rawa na tsoransa ta isa gareshi." Matuƙar kika ce saɓa mini za ki yi sai kin raina kanki, don haka ki kiyaye kin ji?" Ya ƙarashe maganar cikin ɓacin rai. "To, ka yi haƙuri." Ta furta cikin muryar kuka. Ba tare da ya ce komai ba ya ƙara tsuka kwanta. Ganin abin da ya yi mata ya sanya take matuƙar taka tsantsan. Inda ta godewa Allah 'yan gidansu Ya Ahmad ya hana kowa zuwa gidan, domin ya san halinsa. Mutane ne dai 'yan unguwada abokan da abokan arziki suke zuwa, amma ba ta da halin da za ta buɗe. Ganin an yi sati biyu da bikin, bai yi mata maganar zuwa makaranta ba ya sa ya ta shirya. Ya Ahmad ya fara kira ta bayan ta ɗaya ya ce,"Nasreen, maganar makaranta ko har yanzu amarcin kike ci?" Tambayar da ya yi mata, ya sanya ta ji kunya har sai da ta rufe idanunta."A'a shi ne dai bai yi mini maganar ba." "To ki shirya ki yi masa magana, ai dama an yi da wajewa." "To Yaya Ahmad." Ta ce tare da kashe wayar. Ranar Monday da safe da suke da lecture ƙarfe bakwai da rabi. Yana kwance ta shigo cikin ɗakin bayan ta gama shirya wa. Ƙarar buɗe ɗakin ya sanya ya buɗe idanunsa. "Ina kwana?" Ba tare da ya amsa mata ba ya ce,"Nasreen, ɗauko mini wayata na ga lokaci, yau takwas zan fita ina da meeting." "To," Ta ce masa tare da miƙa masa wayar. "Bakwai da kwata ta yi." Ta furta masa. "Da sauran lokaci bari na koma bacci." Ya ce mata. "Na shirya zan wuce makaranta." Jin abin da tace ya sanya shi ta shi zaune yana kallonta, don sai a lokacin ya gane shirin fita ta yi. "Makaranta da wuri kuma daga aure sai komawa makaranta?" Mamakin abin da ya ce, ya kamata wanda ya sanya ta yi shiru ta kasa magana. "Ba yanzu ba, domin daga aure ba zan bari kina gantali a titi ba." "Na ga kai ma ka koma aiki kuma test za mu fara..." "Karki gaya mini maganar banza!" Ya katse ta yana fadin haka wanda ya sa ta yi shiru. "Ok, na koma aiki, goyyaya za ki yi da ni? Ke ni fa ba zan lamunta da zuwa makarantar nan ba, saboda na aminta ne kawai don a lokacin ba ni da zaɓi." Jin abin da ya faɗa hankalinta ya yi mummunan tashi. "Farouk, don Allah ina son karatuna kar ka hana ni." Ta furta cikin muryar kuka. "Dole ki so mana tun da za ki rinƙa fita gantali." Ya ce tare da miƙewa ya shiga bayi. Kuka ta saka ta fita falo ta kira Ahmad. "Ya ce shi bai lamunta da karatuna ba." "Zancen banza! Ai wallahi ya yi kaɗan " Cewar Ahmad cikin zafi tare da kashe wayar. Kiransa Ya shiga yi wanda ya ƙi ɗauka kuma yana ganin kiran. Sai da ya gama shirya wa, ya fito daki ya same ta tana zubar hawaye."Kin haɗa ni da Ahmad. Kin san shi ya haife ni, dole na ji tsoron sa na barki. Ina aurenki ba uban da zai rinƙa kafa mini doka." Ya ciro naira ɗari biyar ya wuta mata. "Ga shi ki nemi abin kari, don kin ɓata mini rai ba zan baki abinci ki dafa ba." Share hawaye suka ƙara zubo mata. Ɗari biyar ɗin tabi da kallo tare da tunanin abin da za ta siya da shi. Kuka sosai take yi ganin ya fice daga gidan. Ahmad kuwa cikin ɓacin rai yake zaginsa ganin ya ƙi ɗaukar wayar. "Wallahi uban kuturu ya yi kaɗan dole ta ci gaba da karatunta." Cewarsa yana safa da marwa a tsakar gidan. Baba da ya fito daga ɗaki, da asuwaki yana goge bakinsa ya tsaya yana kallonsa ganin yadda ya ke huci "Kai kuma da uban wa kake ɓata rai da zage-zage da sassafe nan?" "Ni da wancan tijararren mijin Nasreen." "Mai ya faru?" Ya tambayesa jin abin da ya ce. "Wai ba za ta ci gaba da karatu ba, bayan duk abin da na kashe?" "To shi ne me, ba mijinta bane? Ga ga ka fitar harkar rayuwar gidansa kar ka sanya ya yi fushi, don ba zan lamunci zawarawa biyu a gidan nan ba. Kana ganin tujarar da mijin Abida ya yi, har da saki ɗaya ya yi mata ko? Roƙon sa na ke ya zo ya kwashi matarsa, don babu shegiyar da za ta zauna a gidana, ballantana ta zo da yaro." "Ka san Allah Baba? Dole ya bar Nasreen ta gama karatunta don bai isa ba." "To sai ka je ka tilasta masa tun da uban shi ne kai." Ya ce masa daidai lokacin da zai fice daga gidan. Daga nan kai tsaye ofis ɗin da ya wuce. Kamar ya san zai zo, da aka gaya masa ana nemansa sai da ya shanya shi, sannan ya ba da umurnin ya shigo. Ahmad da zuciya ta tiƙo shi, amma babu yadda zai yi, ya daure ya tura ƙofar. "Wa alaikissalam," Ya amsa sallamar ba tare da ya kalle shi ba. "Na zo kan maganar karatun Nasreen." "Ba ta gaya maka abin da na ce ba?" "Kai ma kasan wasa kake Faruk! Wallahi ka ji na rantse maka, dole ta ci gaba da karatunta, domin zan iya komai don na ga ta kammala digiri." "Nasreen, mallakina ce, kuma ina da iko na hana ta abin da ban yi na'am da shi ba." "Kai ɗan boko ne amma na fika iya amfani da bokon. Duk maganar da muka yi da amincewar da ka yi za ta yi karatu, duk na yi recording ɗinsa. A addini in har mutum ya amince da abu kuma ya musa, mace na da damar da zata zaɓi rayuwa da shi ko rabuwa. Nasreen za ta zaɓi karatunta ko da ace tana sonka, in har na tilasta mata, ballantana kasan babu soyayya a tsakanin ku." Jin abin da ya ce ya ɗan firgita amma sai bai nuna masa ba. "Rayuwarta ka cuta saboda ko yau muka rabu na fanshe kuɗina, tun da na mayar da ita ƙaramar bazawara. Don haka, ka je duk abin da za ka yi." Ya ce masa yana huci. "Ok, to shikenan tun da haka kace?"Ya buga ƙofar ya yi da ƙarfin gaske. Rintse idanunsa ya yi, saboda ƙarar ya firgita shi, kamar yadda barazanar da ya firgita shi. Yana son Nasreen sam ba zai iya rabuwa da ita ba. Da sauri ya miƙe ya shiga motarsa. Kamar yadda ya zargi gidansa zai wuce. Aikuwa yana shiga cikin gidan ya ga mashin ɗinsa a cikin gidan. Gabansa ne ya faɗi ya shiga cikin falon da sauri. Nasreen na zaune Ahmad yana ba ta baki tana ta kuka. "Ya Ahmad, ina son karatuna, amma kuma bana son na zama bazawara." "Karki damu Allah yana tare da ke, in kuma kin haƙura da karatun ba zan yi miki dole ba." Miƙewa ta yi za ta bishi Faruk ya shigo. "Wallahi in har ka fitar mini da mata sai na yi ƙararka." Ya faɗa tare da riƙe hannunta. "Ka kai ni kotun ƙoliya, amma matuƙar ba za ka amince da karatunta ba, sai ta bar gidan nan." Ganin da gaske yake hankalinsa ya tashi. "Na aminta ta ci gaba, amma ƙwandalana ba za ta yi ciwo ba." Jin abin da ya ce ya sanya ta zare idanunta. "Ni ma na amince." Cewar Ahmad cikin ɓacin rai. "Nasreen ɗauki Hijabinki, ki wuce makaranta." "Girgiza kanta yi cikin damuwa tana kuka. "A'a Ya Ahmad, mu bar zancen karatun nan, kana da ɗawainiya a kanka." "Karki damu je ki shirya, na yi miki alƙawarin in har Ina raye sai kin kammala karatun ki." Farouk tsuka ya ja ya fice daga gidan cikin ɓacin rai, domin ya so kar ta yi karatun. Kallonsa take yi cikin mamakin muguntarsa. Tabbas ya cika maƙetaci wanda ba ya son cigabar matarsa. "Ya Ahmad, ban yi dacen miji ba." Ta furta tare da ƙara fashewa da kuma ta rungume shi. "Ki yi haƙuri. Matuƙar ina raye ba zan bari ki yi kuka ba." Kuɗi ya miƙa mata dubu ɗaya." Ga shi ma za ki ɗauki Hijabinki na kaiki makaranta, in kin gama sai ki dawo. Zan tura miki kuɗi a account ɗinkin, wanda zai ishe ki da transport da abinci na satin nan." "Na gode Yayana haƙiƙa bani da kamar ka." Ta ce masa cikin kuka. Wanke fuskarta ta yi ta shafa gida sannan ya kaita har cikin makarantar. "Ki kula da kanki sannan ki yi karatu. Ke yanzu matar aure, ban da kula wasu samari da kuma 'yan mata marasa tarbiyya." "In sha Allahu, zan kiyaye." Ta ce masa tana ɗaga masa hannu har ya tafi. Ajiyar zuciya ta yi ganin Ubangiji bai ba ta miji da uba na gari ba, amma sai ya ba ta Yaya wanda ya cike dukkan gurbin. Fadila ta taso ta rungume ta cikin murna. "Mara mutuncin ya barki?" "Hmmmmh! Ke dai akwai labari." Ta ce mata. Bayan sun gama lecture kai tsaye gida ta dawo. Tana zaune a falon ta ci ye sauran gurasar da ta siya. Kwanciya ta yi ta huta, sannan ta miƙe ta ƙara gyara gidan. Farar taliya ta dafa ta ci da mai da yaji da daddare ta kwanta. Bai dawo gidan ba sai goma da rabi. "Sannu da zuwa." Ta ce masa tana kallon sa. Tsaki ya yi ganin ta a falo ya shige ɗauki sa da leda niƙi-niƙi. Sai da ya ci ya yi tam, sannan ya kwashe ragowar ya sanya a frij. Ta shi ta yi ta shiga ɗaki ta kwanta. Dama ta gaji bacci kawai take son yi. Ɗaki ta ya shiga ya yi tsaye a kanta."Yanzu ke saboda ba ki da mutunci ko? Kin zaɓi karatunki fiye da samun kwanciyar hankali a zaman aurenki?" "Ka yi haƙuri ba ni da zaɓi ne. Ina son karatun, kuma ba zan iya watsa ma Ya Ahmad ƙasa a ido ba. Bayan wahalar da ya yi da ni." "Aikuwa kin sayi rashin kwanciyar hankali a cikin rayuwar aurenmu, tun da har ni da nake ci da ke zan hana ki abu, amma ki bi maganar wani banza can. Wallahi Nasreen, in har na canza miki sam ba za ki ji dadi ba. Da kika ganni nan ba ni da kirki. Macijin sari ka noƙe ne ni." Shiru ta yi ba ta amsa masa ba domin karatu ta dai babu fashi, wanda ta gane shi ne kawai gatanta a halin yanzu. Ganin ta ƙi magana ya sanya shi hawa gadon."Ina sonki wallahi ina ƙaunarki. Ki zauna a gidana, ni kuma zan kula dake. Karatun wahalar da kanku kawai za ki yi. Mutane nawa suke da phd babu aiki?" Ya yi mata tambaye tare da rungimeta yana haɗa fuskarsa, cikin tsigar rarrashi. Ba ta ce masa komai ba." WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 11 Ganin ta ƙi magana ya sanya shi hawa gadon."Ina sonki wallahi ina ƙaunarki. Ki zauna a gidana, ni kuma zan kula dake. Karatun wahalar da kanki kawai za ki yi. Mutane nawa suke da phd babu aiki?" Ya yi mata tambaye tare da rungumeta yana haɗa fuskarsa, cikin tsigar rarrashi. Ba ta ce masa komai ba, har ya gama lallameta ya rungume ta yana sauke numfashi. Washegari da safe saboda ba ta da lecture sai ƙarfe sha ɗaya zuwa magariba. Ganin bata fita ba, ya sanya ya yi tunanin ko ta haƙura ne. Abinci ya ba ta ta yi musu mai rai da lafiya sannan ya fita. Tana shara alert ya shigo wayarta. Dubu bakwai. Murmushi mai ɗauke da hawayen murna suka zubo mata, domin ta san da ace ana samun yaya irin Ahmad da mata da yawa ba su shiga cikin damuwa ba. Bayan ta gama aikin ta yi wanka, ta shirya cikin shiga mai kyau ta wuce school. Farouk kuwa don ya gane ko ta haƙura da karatun. Tun ƙarfe huɗu ya dawo gidan. Ga in ba ta a gidan ransa ya ɓaci. Zama ya yi tare da kunna kallo yana cika yana batsewa. Yana zaune har magariba ba ta shigo ba. Ana sallame magariba ta yi sallama a falon cikin tsoro ganin yana nan. "Da ga ina kike?" "Makaranta." Ta ba shi amsa kai tsaye. "A wannan lokacin?" "Ƙarfe shidda muka tashi kuma rashin abin hawa ya sanya sai da na yi tafiya mai nisa na samu napep." "Ke!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka. "Wallahi ba zan lamunta da wannan tsinannen karatun na ki ba, da za ki gane da shi kina gantali." "Wallahi babu inda na je." Ta ba shi amsa. Kanta ya yi kamar zai shake ta domin ya rasa bakin magana. Ganin haka hankalinta ya tashi matuƙar gaske! "Kin san Allah tun da kin zaɓi karatun nan, kin siya ma kanku tashin hankali a cikin gidan nan." Ya ce tare da jan tsuka ya fice daga gidan. Raka shi da kallon mamaki ta yi domin yanzu ta rage tsoronsa. In dai a kan karatu ne ta shirya ta ɗauki duk abin da zai yi mata. Ɗaki ta wuce ta je ta tube kayanta ta zauna kan gado tana tunanin mugun halinsa. Saboda wata ƙawar su ta kawo musu abinci. Sam ba ta yi tunanin cin abinci ba, ta yi kwanciyarta musamman da ba ta sallah. Farouk ya ɗauki tsananin fushi kan karatunta, domin har sai da suka shafe sati ɗaya babu magana a tsakaninsu. Cikin kuka ta sa ta da Ahmad amma ya ƙarfafa mata gwiwa tare da tura mata kuɗin da za ta rinka siyan abinci. Ganin ta ƙi haƙura da karatun, babu yadda zai yi, kan dole ya haƙura suka ci gaba da zama. Da daddare tana kwance ya shigo cikin kayan bacci. Kallonsa ta yi tare da tashi ta zauna. "Sannu da shigowa." "Yauwa." Ya amsa a gajarce tare da miƙa mata ƙwayar magani a hannunta. Karɓar maganin ta yi tana mamaki domin ba ta gaya masa ba ta da lafiya ba. "Kisha maganin?" "Saboda me, lafiya ƙalau?" "Eh, na sani umurni na yi miki a matsayina na mijinki, in kuma ban isa dake ba to." Sororo ta yi da maganin da ba ta san na mene ne ba tana juya shi. Ta san cewa ba zai bata maganin mutuwa ba, amma rashin sanin fa'idar shan maganin ya sanya ta ƙi sha. "Maganin tsarin iyali ne, saboda na ga ya kamata kisha. Ba mu gama fahimtar juna ba, sannan ga karatunki." "Ni bana buƙata don ba zan lalata mahaifa ta a banza ba." Ta ce tana tura masa baki. "Ni kuma ban shirya haihuwa ba, don ko ɗa daya bana buƙata a halin ya zu da na ke cin ganiyar ƙuruciyata ba. Sam ba zan aminta ki tara mini 'ya'ya ba. Su zame mini wahala a rayuwa." "Gaskiya ni ba zan sha ba, saboda ƙuruciyata ba zan cuci kaina ba." "Ba za ki sha ba?" "Eh," Ta ba shi amsa kai tsaye tare da kwanciyarta. "Nasreen, ki karɓi maganin nan kisha tun kafin zuciyata ta sa ya na aikata miki abin da bana fata." Jin yadda ya yi maganar tsoro ya kamata, amma sai ta daure ta ce,"Ka yi haƙuri kawai! In har ba ka buƙatar haihuwar sai abi wata hanyar, amma ba zan cuci kaina ba. Kuma ban gaya maka don ina karatu ba zan iya rainon yara ba." "Bana son haihuwar ce gabakiɗaya, domin ban ƙi ba na ƙare rayuwata ba tare da na haihu ba. Ko kina son na tara 'ya'ya kamata yadda mahaifinku ya yi na kasa ciyar dasu? Sam haka ba zai yiwu ba, domin ina da planning a rayuwata." Hawaye ya wanke mata fuska."Haihuwar ta yi maka rana tun da ka gani a cikin 'ya'yansa ka aura." Mari ya kawo mata sai ta kauce tare da ƙwala ƙara za ta gudu. Ganin yadda ta firgita ya sa shi sausautawa ya kamota. "Please, kisha maganin nan. Bana son yanayin structure ɗin jikinki ya canza. Kina da kyau Nasreen, komai na ki ya yi mini, amma wallahi da zarar kin samu ciki kina haihuwa za ki ragwaɓe." "Haihuwar shi ne ribar aure. Annabi ya ce mu yi aure ne don mu hayayyafa ranar gobe kiyama ya yi alfahari da mu. Kuma yaran da ba ka so sune gatanka. Matuƙar ka ba su tarbiyya watarana sune za su tallahi rayuwarka." "Bana bukata a yadda na tsara wa kaina ba zan jira yarana ba, har su girma su tallafi rayuwata." "Ubangiji na juya lamura ba ka son me gobe zata haifar ba." "Ba za ki sha ba kenan?" Ya yi mata tambayar cikin ɓaci rai. "Ka yi hakuri ba zan cuci kaina ba" Ta ce masa. "Tashi kisha maganin nan!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka. Nasarar ɗauka mata marin ya yi ninya ya yi, wanda ta canyara ƙara ta dafe da ƙuncinta. Duk yadda ya so ta sha ta ƙi. Takaicin haka ya sanya ya yi mata duka, sannan ya fice daga cikin ɗakin. Kuka take yi sosai domin a yau ta gane ya aureta ne ba don yana sonta ba, dai don kyawu da surar jikinta. Tsoro da tunanin makomar rayuwar ta ya kamata, domin a haka yana wulaƙanta ta, in kuma kyawu da surar ta ya gushe ya zaman aurensu zai kasance. Kuka take yi sosai domin ta san cewa rayuwar aurenta na cikin halin gaba kura, baya siyaki. Sai dai, ko kasheta zai yi ba za ta ci kanta ba. Ta yi kuka tana mamakin irin WASU MAZAN masu mugun son zuciya, su hana matansu haihuwa Don kawai su more jikinsu. Sai daga baya in sun ɓata musu mahaifa su yi aurensu. Cikin ikon Allah ana wannan rikicin sai Nasreen ta fara ciwo. Da fari tashin zuciya da zaɓan abinci take yi. Daga bisani dai amai da kuma zuba miyau. Ga shi ta yi wani irin kyau sosai kamar ka sa ce ta ka gudu. Jikinta ko ina ya ciko ga shi ta yi kyau har ɗaukar ido take yi. Farouk ganin hakan hankalinsa ya tashi domin ko ba a gaya masa ba, ya san ciki ne da ita, ganin yadda halittunta suka canza. Tun lokacin da ya ji canji a jikinta ya zargi ciki ne da ita, wanda bisa wannan dalilin ya sa ya shi siyo maganin hana ɗaukar ciki. Dana-sani da takaicin yadda zuciyarsa ba ta fara ba shi shawara, tun farkon auren su ya ba ta maganin ba, domin ya san da a wannan lokacin ne da take matuƙar tsoronsa za ta sha. Yanzu kuwa ta ga gadon baccinsa sam ba ta shakkarsa sosai. Cikin dare ta kasa bacci sai amai take yi ta kasa cin komai. Ganin halin da take ciki ya tabbatar wa kansa ciki ne da ita. "Nasreen, ciki ne da ke?" Ya yi mata tambayar yana tsaye a kanta cikin bayi da take ta kwara amai. Ɗago idanunta ta yi a galabaice tana kallonsa. Rashin imanin sa take mamaki, ganin tun safe bata da lafiya, amma ya kasa yi mata sannu. Ya tsare ta yana tambayarta. "Farouk, ka tausaya mini ka kai ni asibiti, wallahi ba ni da lafiya sosai." "Na kaiki asibiti kin bani ijiyar kuɗin ne? Ai ba kya tausaya wa kanki, tun da na kawo miki mafita, amma kika kunnen uwar shegu da maganata tare da shafawa idanunki toka. Da ace kin sha maganin ai da duk hakan ba ta faru ba, muna nan muna cin amrcinmu." Ta kasa ce masa komai sai kaƙarin amai take yi. "Zubar da cikin nan za a yi, don ba za ki rinƙa mini ƙazanta a cikin gidana ba." Ya ce tare da komawa ya kwanta yana jin kamar ya shaƙeta. "Ni kuma wallahi ba zan zubar ba, saboda ban sani ba, ko shi kadai ne rabona a duniya." "To sai me? Mata nawa suke rayuwa ba tare da sun haihu ba?" Ba ta tanka masa ba, ta koma ta zauna tana jin yadda cikinta ke juyawa. Da sassafe ya fice gidan ba tare da ya kula da halin da take ciki ba. Kwanciya ta yi domin ba za ta iya zuwa makaranta ba. Fadila ta kira ta sanya mata attendance. Tana kwance har zuwa sha biyu, sannan ta samu zazzabin ya sauka. Miƙewa ta yi don ta nemi abincin da za ta ci. Shinkafa ta dafa da mai da yaji ta ci. Tana zaune tana kallo a falo ta ji alamun shigowar motarsu ya dawo. Ya shigo babu sallama ya samu gefenta ya zauna."Sannu da dawowa." Wata uwar harara ya jefa mata wanda ya ba ta dariya. "Tashi ki kawo mini ruwa " Ya faɗa fuskarsa a ɗaure. Miƙewa ta yi ta ibo masa ruwan."Saboda iskanci a tsaye za ki bani don ki tabbatar mini da ba a gidan tarbiya na auri ki ba?" Ƙasa magana ta yi saboda miyau da ya taru a bakinta. Burinta ya karɓa ta je ta zubar. Miƙewa cikin zafi wanda ya santa ta razana za ta matsa. Cikin rashin sama ruwan ya zube masa a jiki. Mari masu kyau guda biyu ya wanka mata, wanda ya sanya ta haɗiye miyau babu shiri. "Saboda kin raina ni za ki zuba mini ruwa a jiki? Wawiya mara tunani." Ya ce tare da ficewa daga gidan. Nasreen da wani irin hajjiiya ya kamata. Daina gani ta yi na wuccin gadi. Ji ta yi ta faɗi ƙasa saboda rashin ƙarfin jikinta. Sai kawai ta fashe da kuka. Miyau da ta haɗiye bisa dole ya hautsina kayan cikinta. Wani irin amai ya turniƙota wanda ya sa ta ruga cikin bayi, amma ba ta ƙara ba ta shiga kwaro shi. Tana kuka tana amai ji take yi gara mutuwa da auren. Fadila da take ta sallama ta ji ba'a amsa mata ba, ya sa ta shigo har cikin falon. Ganin babu motarsu a cikin gidan. Jin kakarin amai ya sanya ta shiga cikin ɗakin a razane. "Subuhanallahi! Nasreen jikin ne?" Ganinta ya sanya ta miƙe tare da share bakinta ta faɗa jikinta tana kuka. "Gaskiya Faruk ba shi da imani. Kina cikin wannan halin ya iya tsallake wa ya bar gidan nan?" Ta ce tana kallonta. "Nasreen, lafiya mai ya samu fuskarki haka?" Farouk ne." Ta faɗa cikin tsananin kuka. "Kina nufin faruk ya mare ki?" "Eh, saboda na zuba masa ruwa a jiki bisa kuskure." "Ruwa wuta ne? Anya akwai ɗigon imani a zuciyarsa?" Kuka take yi ba tare da ta ce komai ba. "Gaskiya ba ki dace miji ba. Ga shi ciki ne dake zaman aurenki zai ɗore kuwa?" "Ya ce na zubar da cikin ba ya son haihuwa, ni kuma ba zan iya kisa ba, kuma ina son na ga ɗan cikina." Ta ce mata cikin rawar murya. Tsananin tausayinta ya kamata musamman yadda ta yi maganar."Sam ba shi da ɗigon imani a cikin zuciyarsa. Ki yi haƙuri ki yi addu'a Ubangiya ya kawo miki ɗauki." Kamata ta yi ta kwantar da ita. Ganin yadda take rawar sanyi ya sanya ta lulluɓa mata bargo. Fara gyara gidan ta yi ganin duk ya yi ƙura. Bayan ta gama gyara gidan ta dawo kusa da ita. "Za ki iya cin wani abu na girka miki?" "Wainar fulawa na ke so na ci tun jiya, amma na san ko na yi masa magana, ba zai siya mini fulawar ba, kuma kuɗin da Ya Ahmad ya bani sun kusa ƙare wa." "To bari na fita na je bakin titi na sayi fulawar." Ta ce mata tare da miƙewa ta ɗauki mayafinta. Tana tafe tana tunani tare da fargabar aure. Sosai halin Faruk ya tsorata ta, ganin yadda yake cutar da ita. Gwangwani uku ta siya, sannan ta yi cefane da yajin da za ta daka mata. Bayan ta dawo ta kwaɓa fulawar ta fara soyawa. A lokacin da ta kawo mata tana kwance. Taimaka mata ta yi ta mike sannan ta ije mata filet ɗin. "Na gode Ubangiji ya biya ki." Ta furta hawaye na bin fuskarta. Sai da ta cinye wainar tas! Sannan ta koma ta kwanta. Fadila na wanke kayan da ta ɓata ta ji shigowar motarsa. A ranta ta ɗauki aniyar yi masa magana. Yana shigowa falon ta fito, daidai lokacin da ya fara kiran sunan Nasreen. "Ba ta da lafiya ba za ta iya fitowa ba." Ta furta masa daidai lokacin da ta fito daga kicin ɗin. Kallon banza ya watsa mata, ba tare da ya tanka mata na zai wuce. "Faruk, ina son magana da kai." Ta furta masa haka. Kamar ba zai juyo na sai kuma ya tsaya yana kallonta a wulaƙance."Nasreen, ba ta gaya miki ki daina zuwa gidan nan ba? Domin ina zargin harda sanya hannunki, gurin hure mata kunne ta daina yi mini biyayya." "Ka ji tsoron Allah, ka daina cutar da rayuwarta. Nasreen, mata ce a gurinka ba baiwa ba, amma..." "Ke dakata!" Ya katse ta da sauri yana faɗin haka. "Har gidana za ki biyo ni kina gaya mini maganar banza? Matata ce ita, kuma ba ki isa ki gaya mini yadda zan zauna da ita ba. Don haka, kar ki ƙara kuskuren sanya bakinki a lamarin aurenmu." Kalamansa su ka yi matuƙar ba ta mamaki."Faruk, ni...." "Get out of my house!" Ya furta da ƙarfi cikin ɓacin rai. "Gidan banza na ka, in sha Allahu ba zan ƙara shigowa." "Ki shigo ki ga yadda zan karya ƙasusuwan jikinki." Ya furta mata yana kallonta. Harararsa ta yi, tare da sakin tsaki ta shiga cikin ɗakin don ta ɗauko jakarta. Nasreen kuka take yi cikin tashin hankali. Tun da ya shigo ta zauna kan gadon, duk da azababben ciwon kan dake damunta. Tsoron ta kar ya wulaƙanta Fadila, sai kuma ga shi bai shanye raɗa ba. "Nasreen, ki yi haƙuri bisa jarrbawar da Allah ya yi miki, domin mijinki bai san darajar mace ba. Allah yana tare dake." Hannunta ta riƙe, amma sai ta fisge ta fice gidan cikin kuka, tana tausayin halin da ƙawarta take ciki. "Zama kika yi kina gaya mata ina cutar dake ko?" Ya yi mata tambayar yana matsowa kusa da ita. "A'a, wallahi ban gaya mata ba." Ta furta cikin muryar kuka tana matsawa. "To, uban mai yasa ta tsareni tana gaya mini maganar banza?" "Ka yi haƙuri ni ma ban sani ba, kuma zan yi mata magana." "Kar ki yi mata Allah ya sa ta ƙara mini rainin wayo. Wallahi saina karya ƙafarta, sai na ga yadda za ta ƙara shigowa cikin gidana ta yi mini rashin kunya. Ki ma godewa Allah kin samu miji, ita fa ga shi nan babu mashinshini sai yawo a gidajen ƙawaye take yi." Shiru ta yi ta kasa ce masa komai, domin ba ta da abin da za ta ce. "Tashi ki dafa mini abinci." Ya furta tare da zama kan gadon. Da sauri ta ɗago kanta tana kallonsa jin abin da ya ce, don ko makaho ya kalle ta ya san ba ta da lafiya, ballantana shi da idanunsa biyu suke ras! "Ba ni da lafiya, ba zan iya ba." Kallon da ya yi mata ya sa ta mike babu shiri, sai kuma jiri ya ibeta za ta faɗi. "Ka tausaya mini ba zan iya tsayuwar ba." "Kin san Allah ko suma kike sai kin yi mini abinci. Ai ban aike ki ba, in da kina jin maganata, da ba ki ɗaurawa kanki wahala ba." Sau uku tana ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa, sai a na huɗu ta yi nasarar miƙewa. "Kuma kika sake kika yi mini ƙazantar da kika tsira, wallahi sai kin raina kanki." Ya ce tare da fitowa ɗakin ya shige ɗauki sa. Kicin ta nufa ta wanke kayan miyan, domin shinkafa da miya yake son ciki. Tana girkin tana kwanciya a ƙasa tayas ɗin, har ta samu ta gama, sannan ta sanya masa a kula ta kai masa. Tana gamawa ta fito daki ta kwanta sai nishi take yi. Ba tare da ya damu da halin da take ciki ba, ya cika cikinsa sannan ya fice daga cikin gidan. Nasreen tana kwance kan kujerar tana kuka. Ganin za ta mutu ta ɗauki wayarta ta kira Ahmad. "Hello Ya Ahmad, ba ni da lafiya zan mutu." Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka tana nishi da ƙyar. "Nasreen, da na ba ki da lafiya ne?" Ya yi mata tambayar cikin damuwa. "Kwana biyu ina zazzaɓi kuma jikina babu ƙarfi." "Ina Faruk ɗin, ya san ba ki da lafiya?" Ya yi mata tamabayar jin abin da ta ce. "Eh, ya sani amma ya ce ba zai kai ni asibiti ba." "Ok, gani nan zuwa gidan." Ya furta cikin ɓacin rai yana huci. "Lafiya mai kuma ya same ta?" Mama ta dake gefensa tana cin dambu ta yi masa tambayar. "Nasreen ba da lafiya kuma yaƙi kaita asibiti." "Kai wannan yaro sam ba ya kyautata rayuwarsa. Ace tun da aka yi aure, matsalar yau daban ta gobe daban." Ta yi maganar cikin takaici. "Bari na je na ga halin da take ciki." "Don Allah Ahmad, karka kula shi ku raba abin faɗa." "To Mama, zan je na kai ta kyamis, in kuma ya wuce kyamis sai mu je asibiti, amma in har ya yi mini hauka, ba zan lamunta ba, domin mutumin nan sam ba shi da hankali." "Ka yi haƙuri ya ci darajar 'yar'uwarka." Ba tare da ya ce mata komai ba ya fice daga cikin gidan. Mashin ɗin da ya hau ya buga sai gidan. Tana kwance ta ji ana ƙwanƙwasa get ɗin gidan. Da ƙyar ta samu ta je ta buɗe masa. Ganin tana layi ya kamata yana faɗin,"Ba ki da lafiya, amma ba za ki fada ba, sai ciwo ya ci ƙarfinki Nasreen?" "Kwana biyu ne na fara ciwon Ya Ahmad." "Ma za shiga ki ɗauko mayafinki, mu je asibiti, domin ciwon nan ya wuce kyamis." Suna zuwa asibitin likita ya tabbatar masa da ƙarin ruwa za a yi mata, saboda yadda jikinta ya yi weak. Duk da babu wasu isassun kuɗi a hannunsa, ya ba da umurnin a sanya mata ruwan. Fita ya yi bayan ya ɗauki wayarta. Numbar Faruk ya ɗauka a cikin wayarta, sannan ya kira shi. "Hello," Ya furta ba tare da ya ce komai ba. "Ahmad ne Yayan Nasreen." Ahmad ya ce bayan ya yi masa sallama. "Ok, lafiya?" Ya yi maganar cikin sham ƙamshi. Ƙoƙarin danne ɓaci ransa ya yi."Nasreen ce babu lafiya muna asibiti." "Allah ya ba da lafiya, ai na gaya mata ƙwandalata ba za ta yi ciwo ba, tun da shegen taurin kanta ya kai ta ta yi ciki. A yadda ransa ya ɓaci matuka, in har da yana kusa da shi, babu abin da zai hana bai kai masa duka ba. "Faruk, da kake ganina ni ma ƙwallon shege ne, saboda wallahi in iskancinka haye ka yi, to ni gadonsa na yi. Albarkacin Nasreen kake ci, in bacin haka ko kallon banza ba ka isa ka yi mini ba." "Ai ba abin mamaki bane, in ka gaya mini kai cikakken ɗan bariki ne, tun da ba ku samu tarbiya ba. To ni ma daidai na ke da kai, in saboda ita kake daga mini. Ga tan nan sai ka je ka yi kwaɗonta ka ci, domin in har ba ta amince an zuba cikin nan ba, sam ba za ta dawo gidana." Yana faɗin haka ya yanke wayar. Sororo ya yi da wayar a hannunsa cikin takaici. Ji yake kamar ya janyo ta wayar ya yi masa dukan tsiya. Komawa cikin ɗakin ya yi, ganin tana bacci sai rufe ƙofar ɗakin ya fita. Da ƙyar ya samu bashin dubu biyar ya biya kuɗin asibitin. Bayan an ƙara mata ruwan aka ba ta sallama da daddare. "Nasreen, na kira mijinki amma ya yi mini rashin mutunci, kuma ya ce in har ba ki zuba cikin jikin ki ba, sam ba za ki zauna masa a cikin gida ba." Barka da sallah fans ɗina ina yi muku Barka da sallah tare da fatan Allah ya karbi ibadunmu. Sai na zo muku yawon sallah. Tamu Jamila lawal Zango Jamsy❤️❤️❤️❤️❤️🙏🙏🙏💃💃 Nasreen, Damir, Marwana, har ma da Faruk capacity yana muku barka da sallah. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 12 Hawaye suka wanke mata fuska jin abin da ya ce. Cikin jin kunyar sanin tana ɗauke da juna biyu ta ce,"Ni ma bana buƙatar ci gaba da zama da shi, kuma duk abin da zai faru ba zan zuba cikin jikin ba, amma kuma ina tsoron Baba, wataƙila ba zai lamunta na zauna ba." "Ki koma gidanki Nasreen in har ba takadda ya ba ki ba, kar ki sake ki dawo. Ga wannan ki sayi abin da za ki ci." "To Yaya, na gode Allah ya saka da alkhairi." Ta ce masa tare miƙa hannunta ta karɓa kuɗin. Har ƙofar gida ya ije ta sannan ya tafi. A lokacin da ta shiga gidan baya nan. Kwanciya ta yi bayan ta sha magani. Bai dawo gidan ba, sai goman dare. Hankalinsa kwance ya shigo cikin gidan har da 'yar waƙarsa, domin a tunaninsa babu kowa a cikin gidan. Kai tsaye ɗakinsa ya wuce, amma sai ya dawo ganin haske a cikin ɗakinta. "Nasreen," Ya kira sunanta cikin ɓacin rai. "Sannu da dawowa." Ta ce masa tana ƙoƙarin tashi. "Ba na ce kar ki dawo gidan nan ba, in har ba ki zubar da cikin jikinki ba?" "Gaskiya ba zan zubar ba, kuma ni ba zan tafi gidanmu da sunan yaji ba." "Ok, uban me kike so?" Shiru ta yi ba ta ce masa komai ba. "Kin san dai ba zan sake ki ba, don ban gama more kuɗi a ba, kika yi ciki. In har saki kike nema sai dai a biya ni duk abin da na kashe." Ya ƙarsahe maganar cikin murmushin ƙeta. Jin abin da yasa hankalinta ya tashi matuƙar gaske! "FARUK, ka ji tsoron Allah akan abin da kake akata mini. Ka san ba ka son haihuwa da ni, mai ya sa ka aure ni?" "Sai aka ce miki duk wanda kika ga ya yi aure don ya haihu ne?Ina sam ba zan tarawa kaina ɗawainiyar yara ba, tun ina ƙaramin a ban girma ba, ba zan cuci kaina na mai da kaina tsoho ba."Ganin ta yi shiru tana kallonsa ya sanya shi kama hannunta. "Ki fahimci abin da na ke son ki gane Nasreen. Guda nawa muke? Muna da time da za mu ci amrcinmu. Mu more rayuwarmu sai mun girma mun ci ƙuruciyarmu, sai mu haifi yara biyu ko ɗaya." "Ka fito fili ka gaya mini sai ka lalata mini mahaifa da magungunan hana haihuwa, kai kuma sai ka je ka auro wacce za ta haifa maka yara. Sam ba zan yarda da daɗin bakinka, na lalata mahaifa ta ba." "Shegen taurin kanki da rashin mini biyayya suke ƙara tunzura zuciyata na ke miki wulakanci. Kin san Allah? In har ba za ki cire cikin nan cikin lalama ba, sai dai na ba ki zaɓi biyu. Ko ki cire cikin nan ko kuma ki koma gidanku." Shiru ta yi tana kallonsa cikin tsananin mamaki. "Ba zan cire cikinta ba, kuma ba zan koma..." "Wallahi ba ki isa ba! In har kin zaɓi barin cikin jikinki. To ba za ki kwantar mini agida ba." Ya ce mata tare da miƙewa yana zare idanu. Miƙewa ta yi ta ɗauki mayafinta, don ta san yadda ya nuna ba zai ƙyaleta ta kwana ba. Ba tare da ta ce masa komai ba ta kama hanya. Tana fita ya rufe ƙofarsa da ƙarfi bayan ya zabga tsaki. Tsananin mamakin rashin tausayinta ya kamata. Dare ya yi sosai domin a lokacin goma har ta wuce. Sauran kuɗin dake hannunta ta tari mashin har ƙofar gida. Babu kowa a tsakar gidan ta yi sallama ta shiga cikin ɗaki. Mama da ta ɗauki muryarta, da sauri ta tashi tana kallonta. "Nasreen, lafiya da daddaren? Ahmad bai jima da dawowa ba, ya sanar mini da ya mayar dake gida." "Eh Mama, zabi ya ba ni ko na xubda cikin cikin ko kuma na bar masa gidansa." "Anya Faruk na da hankali kuwa?" Mama ta yi mata tambayar cikin damuwa. Za ma ta yi a gefen gadon tana share hawaye."Ya ce sai kin xubda ciki, sai ka ce shi ba da aure aka haife shi ba? Kuma duk wanda ba ya ƙaunar aure, ba ya ɗabbaka sunnar da ya zama tushen sa ke nan." "Lamarin Faruk sai shi Mama. Sam ba ya ƙaunata. Na fi buƙatar a raba auren, don ban san nan gaba yadda rayuwar aurenmu zai kasance ba." "Kul Nasreen! Zawarcinma babu daɗi. Wataƙila don ba ki taɓa yi bane, shi ya sa kike faɗin haka, amma ko zawarcin kika dawo kina yi, shi babu wani samun kwanciyar hankali, musamman da kin san yanayin rayuwar da muke ciki. Ga shi in auren na ki ya mutu, tunanin wane irin miji da za ki aura ya ishi rayuwarki. Sannan shi ɗan cikin kin san gararin rayuwar da zai yi? Mahaifinsa bai riƙe shi ba sai wani. Ko a nan gidan za ki watsar da shi shi ma ya tashi a irin halin da kika tashi? Don haka kar ki ƙara to wa kanki fatan zawarci, sam ba shi da alfanu ga 'ya mace." "To Mama ina ji ina gani saboda takaici da tsoron zawarci sai na bari baƙincikin Faruk ya kashe ni? Ba ki san halin da na ke ci ki ba, in har yana cikin gidan nan, ban isa na zauna kan kujera na tashi lafiya ba, sai ya yi mini gori." "Ki yi hakuri laifin mahaifinki ne. Shi ya ja mini duk abin da yake miki." "Lafiya Mama ta dawo?" Ahmad ya miƙa mata ledar sabar biredi da ya shigo mata yana tambayarta. "Ga ta nan wai ya ba ta zaɓi, ko ta xubda ciki ko kuma ta dawo gida." "Kai! Anya wannan ɗan iskan yana da kirki kuwa? Cikin dare zai turo ta gida, in 'yar'uwarsa ce aka yi wa haka zai ji dadi?" "Allah dai ya kyauta na gaba kawai, amma mijin Nasreen yana buƙatar gyara a rayuwarsa." "Ki bar ni da shi sai na koya masa hankali." "Mai za ka yi masa? Kar dai ka je ka cutar da shi, tun da dai an riga an haɗa zuriya." "Shi ke nan sai na ƙyale sa ina kallo yana cutar da ita?" "Allah ya shirye shi. Addu'ar da za mu yi masa kenan." Mama ta karashe maganar cikin damuwa. "Ki kwanta ki huta kar ki sa ya abin a ranki. In sha Allahu, ba za ki wulaƙanta ba." Ahmad ya ce yana kallonta. Gyara kwanciya ta yi kan gadon Mama sai bacci. Babu wanda ya san da zuwanta sai da safe. Bayan ta yi sallah komawa bacci ta yi, don har lokacin jikinta babu ƙarfi. Da gari ya waye Mama ta dama musu koko da ragowar biredin da ta rage suka sha. "Ki tashi ki je ki yi wanka Ahmad ya kai ki allura. Ya ce na gaya miki ki shirya ya fita ya shigo miki biredi, ki haɗa da wannan." "Da ma ya barshi saboda ba wani cin biredi na ke yi ba." Ta ce tana ƙoƙarin saukowa daga gadon. "Ko za ki fara yin wanka ne?" Mama ta yi mata tambaya tana kallon ta. "Eh bari na yi wankan na fi jin ƙarfi." Ta ce tare da miƙewa. Bayan ta sauke mata ruwan ta sanar mata da take ta yi wanka. Tana ƙoƙarin shiga cikin bayin, Baba ya fito daga cikin ɗaki yana miƙa da alama lokacin ya tashi. "Ke Nasreen, lafiya na ganki a gidan nan? "Farouk ya ce na dawo gida." "Da ya ce ki dawo sai kuma kika dawo saboda ba ki da hankali?" "So kake ta zauna ya kashe ta ko?" Mama da take gindin murhun ta yi masa tambayar a maimakon amsa. Harara ya zabga mata yana kallon ta."Ok, ke kika ɗauke mata gindi kenan?" "Cikin dare ya koro ta, kuma ba ta da lafiya sai na ce ta koma? Saboda rashin imanina?" "Dole za ta koma don ba za ta zauna a cikin gidan nan ba." "Nasreen, babu in da za ta Baba. Ka ji tsoron Allah ka tausaya rayuwar ta. Jiya tun safe muna asibiti da ita ba ta da lafiya, amma mutumin nan ya ƙi kaita kuma bai zo ba. Bayan ta dawo ya ba ta zaɓin ta zubar da ciki ko ta bar masa gidansa. Sam ba shi da imani. A matsayinka na uba, bai kamata ace ka barta ta ci gaba da zama da wannan mijin ba." "Ok, na sanya ta kashe auren na zo na rinƙa kasata a tire ko? Mata nawa ne suke haƙuri a gidan aurensu? Ai yanzu duk macen da kaga tana gidan mijinta haƙuri ne ya zaunar da ita." "Baba, ko me za ka ce Nasreen ba za ta koma ba, in har ba Faruk ne ya buƙaci haka ba." "Sai ka zaunar da ita kana kallonta. Abincin da za ka bata ta ci ya isheka wahala." Ya furta tare da ɗaukar buta babu kunya ya yi ƙofar gida. Inda Nasreen da take zubar hawaye ya ƙarasa."Ki shiga ki yi wanka babu in da za ki je, kuka in sha Allahu ba zan rasa abin da zan ba ki kici ba." "To," Ta amsa cikin muryar kuka ta shige bayin. "Baba matukar bai canza halinsa ba, Allah sai ya hukunta shi. Kina jinsa Mama, saboda abin da za ta ci yake don ta koma ta ci gaba da zaman wahala a gidansa? Abinci shi ne kawai damuwar bawa, da har zai ce ya koma don yana ba ta abinci?" "Ku yi masa fatan shiriya amma yana buƙatar ya gane gaskiya." "Allah ya shirye shi." Ya faɗa jin abin da ta ce. Da ta fito ta canza kaya sai ta shafa mai. Zama ta yi ta tafka tagumi hawaye yana bin ƙuncinta. Da ƙyar Ahmad ya rarrasheta sannan ta samu ta karya. Kwanciya ta yi kan gadon Mama cikin damuwa. Farouk kuwa bayan fitarta hankalinsa kwance ya yi kwanciyarsa. Washegari da safe ko tunanin ta bai yi ba, ya shirya kansa ya wuce gurin aiki. Kwana ɗaya biyu har sati suna tunanin zai zo, amma shiru ya kar malam ya ci shurwa. Ganin haka Baba ya wanke ƙafarsa ya je har gidansa. Yana ta bugu da kwaɗa sallama. Tun da ya fito ya ji muryarsa, ya koma ya yi zai iyarsa yana kallo. Sai da ya tabbatar da ya gani sannan ya je ya buɗe gidan. A lokacin har ya gaji ya jiya zai tafi." Da sassafe ba za a bari mutum ya huta ba, in har maula ya kawo mutum Gara ya juya, tun da babu uban da ya ba ni ajiya." Ya buɗe ƙofar yana faɗin haka. "Au Ashe kai ne?" Ya yi masa tambayar cikin ɗauke fuska tare da haɗe hannunsa ya riƙe a cikinsa yana kallonsa. "Na yi tunanin babu kowa a cikin gidan, saboda na kusan awa ina ƙwankwasawa?" "Ina nan bacci na ke yi." Ya ba shi amsa fuskarsa babu fara'a. "Ina kwana?" Ya yi masa gaisuwar a gajarce. "Ai na ɗauka ba za ka gaishe ni ba, domin Faruku na san za ka aika." Banza ya yi da shi yana kallonsa, don ba shi da abin da zai ce masa. "Nasreen, da ka turi gida har sati ba ka zo ba, mene ne nufinsa?" "Ba ta gaya maka abin da ta yi mini ba?" Ya yi amsa tambayarsa a maimakon ya ba shi amsa. "Ta ce mini ba ka son haihuwa?" "Eh, saboda ban shirya tara 'ya'ya ba na kasa ciyar da su." Ya ba shi amsa yana kallonsa. Ya san cewa magana ya gaya masa, amma sai ya basar bai tare da ya ce masa komai ba, don ya san zai fadi abin da ya fi haka." "Ba a haihuwa aka haife ka, ko daga sama ka faɗo?" "Ba haihuwar ba ce ba ni da ra'ayi. Na gaya maka bana son na tsufa da wuri ne. Na yi mata maganar mu yi tsarin iyali, amma sai ta bijire mini. Ni kuma ba zan zauna ina ciyar da matar da ba ta mini biyayya." "To yanxu mene ne nufinka?" Baba ya yi masa tambayar ganin yadda yake cika yana batsewa. "Ba ta gaya maka ba? Na gaya mata sai dai ta zaɓa. Ko ta bi umurnina, ko kuma a biya bi abin da na kashe don ba zan yi asara ba." Zare idanunsa ya yi jin abin da ya ce. Dariyar ya saki yana kallonsa."Ka san Allah, ko kana tsafi Faruku, ka ce na biya ka kuɗin da ka kashe, wallahi biyar ba za ka samu ba. Don haka tun wuri ka sasanta da matarka ku zauna lafiya." "Kai dai za ka yi wa 'yarka faɗa ta zauna a ɗakinta in ba haka ba, duk abin da na kashe sai an biya ni, don babu abin da na mora a aurenmu. Haka kawai ka haifi yara ka kasa basu tarbiyrt da za su yi wa miji biyayya? Wallahi da na san haka take babu abin da zai sanya na ɓata kuɗinta na aureta." Duk rashin mutuncin Baba sai ya tsaya kawai yana kallonsa yadda yake gasa masa magana. Ƙasa ce masa komai ya yi, saboda ya san ya fi shi iskanci. "Shikenan zan je na lallaɓata ta amince sai a xubda cikin, innya so kuka ƙara fahimtar juna sai ku haihu." "Da dai yafi maka alkhairi kai da ita." "Bari na wuce, in sha Allahu yau za ta dawo." "Kar ta dawo in ta so. Ka ta za ta cuta ba ni ba." Ya ƙarashe maganar yana watsa hannunsa. "Umhm! Farouk, haka za ka barni na tafi? Kasan da nisa tsakaninmu kuma wallahi a ƙasa na taho?" Babu kunya ya watsa mishi harara yana faɗin,"Ban kira ka ba kuma ni ba ni da kuɗi a jikina. Kai kuma ba waya ce da kai ba." "A dai duba ba a rasa ba." Dudar dubu ya zaro ya miƙa masa cikin ɗauee fuska. Da sauri ya karɓa yana washe baki. Faruk kuwa tsaki ya yi tare da raka shi da kallon ƙaskanci. Baba na komawa gida ya shiga, ɗakin Mama da take zaune da carbi a hannunta tana ja. Babu sallama ya ɗaga labulen yana faɗin,"Kin san Allah? Dole Nasreen ta koma gidanta, don ba zan yarda ta haifar mini ɗan wani a gidana ba." "Haba Baban Ahmad! Yaron nan tun da ta zo ya ƙi zuwa, shi ne kuma kake son ta koma?" "Eh, dole ta koma sannan ta bi umurnin mijinta, na gaya musu ai duk wacce na aurar ba za ta dawo ta yi mini zawarci ba." "Nasreen ba za ta koma cikin gidanta ba, in har bai amince ta haifi cikinta ba." Ahmad ya furta haka. "Amaduu! Wallahi ka kiyaye ni. Ka bar ganinka shirgege tsaf zan sanya maka tafi." Ya ce yana nuna sa da yatsa. "Baba ka ji tsoron Allah. Ka da Nasreen ta mutu saboda baƙincikin da take fuskanta a gidan aurenta. In ban da don zuciya. Mijin da ba ya buƙatar haihuwa har kake so ta koma gidansa?" "Ka fito kai tsaye ka zage ni. Dama na san ba ka ɗauke ni da daraja ba. A yanzu ma ba ku ƙi na gungure na faɗi na mutu ba." Shiru kawai ya yi cikin ɓacin rai, ba tare da ya ce masa komai ba har na wani lokaci, sannan ya kalle sa ya ce,"Ba za ta koma gida...." "Wai Nasreen 'yarka ce ko yata?" Ya yi masa tambayar cikin tsawa. "Kai ka haife ta, amma ni ɗan'uwa ta ne. Dole na ƙwatar mata 'yancinta." "To shikenan, mu zuba ni da kai shege ka fasa." Ya waiwaya inda take tana ta kuka. "Ta shi ma za ki koma ɗakin mijinki." Ya ce mata cikin tsawa. Miƙewa ta yi tare da ƙara sautin kuka ta tana haɗa kayanta. "Babu inda za ki wallahi har sai A ya zo bikonki, kuma ya gane kuskurensa." Cewar Ahmad ya kama hannunta. "Bari na fita na dawo, kar ta koma gidanta za ka ga abin da zan yi muku." Ya ce cikin fushi tare da fita fuu kamar kububuwa. Kuka take yi sosai cikin damuwa. Ta san cewa in har ta koma gidan ba tare da ya zo ba, wulaƙancin da zai yi mata sai yafi wanda ta baro. "Ki yi shiru ki share hawaye ki babu inda za ki." Cewar Ahmad. Mama kuka take yi tana tausayinta sai dai babu abin da za ta iya yi. Farouk kuwa ya yi tunanin za ta dawo. Don haka ya ƙi fita a ranar kwata-kwata, ya ƙudiri in har ta dawo maganganun da zai gasa mata. Maganin da ya bata ta ƙi sha ya ɗauko, tare da ije su a fili. Ya ƙosa ta dawo ya ba ta tasha. Tun da ta samu ciki hankalinsa yake tashe, don kar ta haihu ta ragwaɓe. Shiru yana zuba ido har cikin dare ba ta dawo ba. Tun yana sa rai, har ya cire ganin kwana biyu ba ta dawo ba. A ranar da ta cika kwana uku, yana zuba idon za ta dawo har ya cire rai. Da safe yana zaune a falon. Ya ji sallamar Yayarsa Asiya. Cikin fara'a ya karɓe ta yana gaishe ta. Bayan sun gama gaisuwar sai ta kalle shi. "Farouk, na ga gidan duk ya yi datti? Ko kana nufin karatun da take yi ba ta da lokacin da za ta kula da gidanta?" "A'a tsawon sati biyu ba ta gida ta yi yaji?" "Ya ji a wannan zamanin da maza suke tsada?" "Shi ne ni ma na gani, saboda ko abincin da za ta ci a gidansu aiki ne a gareta." "Amma kuma ta zauna ko? Wannan ya nuna maka ko babu abincin za ta iya zama. Kuma in ban dai Faruk, kafin ka aureta ba a gidansu take rayuwa ba. Ya kamata ka cire wannan tunanin talaka da mai kuɗi duk Allah ya yi su, kai da ka ga Allah ya azurta ka ba wayonka bane." Shiru ya yi ba tare da ya ce mata komai ba, sai tsuke fuskarta da ya yi. "Na san ba ka da kirki wani lokacin Faruk. Ga baƙar zuciya gaya mini mai ya haɗa ku, saboda yarinyar nan tana da haƙuri." "Hmmmmh! Ba ki san ta bane saboda kin ganta shiru-shiru, wallahi ni kaɗai na san baƙincikin da na ke sha." "Mai ta yi maka?" "Ciki ta yi ni kuma na gaya mata ta zubar ban shirya haihuwa ba!" "Kana da hankali kuwa? Cikin da ta samu shi ne ba ka so? Bayan wasu na nema." "Gaskiya, ban shirya haihuwa ba. Na gaya mata muci amarcinmu kafin ta haihu, amma ta ƙi." "Gaskiya Faruk, ba ka da kirki ko kaɗan, saboda wannan shi ya sa ka tura ta gidansu?" "Ba ta jin magana babu yadda ban yi da ita ba, amma ta yi kunnen uwar shegu da ni." "Mama zan kira na gaya mata abin da ka aikata. Ba a haihuwa aka haife ka. Kuma in ban da kai shashasha ne ai ka bari ta haihu ko sau ɗaya ne, amma da ƙuruciyarta sai ka lalatata mahaifa." Tura bakinsa ya yi kamar ƙaramin yaro yana dana-sanin gaya mata. "Hello, Mama ƙarar Faruku na kawo." Ta furta hakan bayan sun gaisa. Ba tare da ɓata lokaci ba ta sanar mata da duk abin da ke faruwa. Cikin tsananin fushi ta ce a ba shi wayar. Tatas ta yi masa tare da yi masa umurnin ya je ya dawo da ita. Tsananin ɓacin rai ya kamashi, saboda da yasan za a yi masa dole, sam ba zai gaya mata ba. Saboda fuskar da ya canza ba ta jima ba ta yi masa sallama. Bayan ta ƙara masa faɗa. A ranar da ta ce ya je ya dawo da ita. Ƙin zuwa ya yi, duk da kiransa da ta rinƙa yi, kan ya haɗa su. Ganin ta yi fushi da safe ya shirya kafin ya tafi aiki. Hon ya rinƙa yi babu ƙauƙautawa. Baba ne ya fito tsakar gida. "Ki shirya ma za ki bi tijararren mijinki." Jikinta a sanyaye ta ɗauki mayafinta ta fito. Tana shiga cikin motar ya saki wawan tsaki yana kallonta."Kin ji na rantse miki da ga wannan cikin ba za ki ƙara haihuwa ba, sai lokacin da na shirya." Ba ta ce masa komai ba ta ja bakinta ta tsuke. Ya gama bambaminsa ya gaji ya yi shiru. Da suka koma gida yana sauke ta ya juya. Ciki ta shiga ta gyara gidan, don tun da ta tafi ko tsinke bai taɓa kawar wa ba. Bayan ta gama gyaran gidan, sannan ta dafa musu taliya. Da dadddare ya dawo tana kwance a kan doguwar kujera. Ganin ya shigo ya sa ta miƙe tana gyara ɗaurin ɗankwalinta, tana kallonsa don ba ta ji shigowarsa ba, saboda baccin da ya kwashe ta. "Sannu da dawowa." "Yauwa,"Ya amsa da fuskar shanu. Abinci ta kawo masa ya ci ba tare da ya ce komai ba. Ganin yadda yake cika sai ta tashi ta bar masa falon. Sai da ya gama duk abin da yake yi, sannan ya buɗe ɗakinta ya shigo. "Kin yi bacci ne?"Ya ce tare da zama a gefen gadon yana bubbuga gadon. Buɗe idanunta ta yi sannan ta kalle shi.Hawa gadon ya yi babu kunya ya janyota ya rungume yana sauke numfashi. Sai da ya gama abin da zai yi, sannan ya koma gefe ya fara bacci. A haka suka ji gaba da rayuwar yau fari gobe tsumma. Duk abin da yake mata haƙuri take yi, domin haƙurin shi ya fi. Ganin Ahmad yana matuƙar kula da ita sai hankalinta ya kwanta. Ta ci gaba da rainon cikinta tana karatunta. Cikin har ya shiga wata bakwai, amma ko ɗan kamfai bai taɓa siye ba. Ganin haka ta same shi yana zaune."Ina son magana da kai." Ta ce masa tare da zama kusa da shi. Kallonta ya yi hankalinsa na kan wayrsa da yake chatting. "Ina jin ki." Ya furta tare da mayar da hankalinsa kan wayarsa. "Yaushe za ka fara siyayyan kayan haihuwa? Cikina wata bakwai ƙarshen watannan zai shiga takwas." Daina typing ɗin ya yi yana kallon ta."Kamar ya ya siyayya? Me kike so na siya? Ba kayan da jariri zai sanya ɗan kala ɗaya ko biyu sai famfas da zan siya ba, kafin ki samu na suna?" Jin tambayar rainin wayon da ya yi mata ya sanya ta kalle shi cikin mamaki."Faruk, ko wace mace in ta samu ciki za ta haihu, mijinta yana ba ta kuɗi ko ya ɗauke ta su je kasuwa, don ayi wa jaririn siyayya." "To sai ki gaya mini tun da ban sani ba. Nufin ki so kike na ba ki kuɗi ki je kasuwa tun da ban san me na ke yi ba ko?" "Za ka iya zuwa ka siyo, damuwata kar na ta shi haihuwa babu kayan da za a sa." "Kar ki gaya mini maganar banza. Tun da gani matsiyaci ko? Zan baki naira dubu goma ki je ki yi siyayyar.." "Dubu goma da ka ce Faruk?" Ta tambaye shi cikin zallar mamaki. "In kin raina ki siya da kanki tun haƙosu na ke yi." Mamakinsa ya kamata don a tunaninta dubu gomar bai wuce su sayi pampas ba. Washegari ya cire dubu goma ya ba ta. Galala ta yi tana kallonsa. Ganin ba za ta karɓa ba ya sanya shi ije kuɗin ya fice. Ahmad ta kira tana kuka ta gaya masa. Bayan ya ba ta haƙuri ya bata dubu goma sha biyar ta haɗa ta yi siyayyar. Duk da ranar da za ta awo sai sun yi faɗa, watarana ma Ahmad yake ba ta ta je. A haka ta rainin cikin har ya isa haihuwa. Cikin dare na naƙuda ta kamata. Da fari banza da ita ya yi yaci gaba da baccinsa, sai da ya ga lamarin ya girmama ta fita hayyacinta, sannan ya kwashe ta suka tafi asibiti. Cikin ikon Allah bayan ta sha baƙar wuya, ta haifi yarta mace aka sanya mata . Ranar suna ƙin taro ya yi sai dai kawai ka radawa 'yar suna da Raihan. Tun kafin ta yi arba'in ya so ta fara planning amma sai ta ƙi tashin yin hakan ya ƙara sukurkuta rayuwar aure su. Raihan na da wata goma ta ƙara samun ciki, inda ya buga tsalle kan sai ta zubar da ciki. An kai ruwa rana kafin ya haƙura don har sai da mahaifiyarsa ta sanya baki. Tun da ta haifi Musaddik rayuwar aurensu ta ƙara tabarbarewa. Faruk irin maza nan ne wanda suke son kulawar mace, ga kuma shegen maƙo baya barinsa ya ba da abun da za a gyara masa jikin. Idanunsa a buɗe suke sosai, domin yana san mace wacce take 'yar bariki, sai aka ci rashin Sa'a ya auri Nasreen mai kunya da hankali. Ga shi dai zaman su ya ƙare kuma ya auri mace da yake so, sai mu yi musu fatan zaman lafiya. AN DAWO LABARI Barka da sallah fans ɗina ina yi muku Barka da sallah tare da fatan Allah ya karbi ibadunmu. Sai na zo muku yawon sallah. Tamu Jamila lawal Zango Jamsy❤️❤️❤️❤️❤️🙏🙏🙏💃💃 Nasreen, Damir, Marwana, har ma da Faruk capacity yana muku barka da sallah. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 13 Kuka take yi sosai, har Mama ta gama dafa mata ruwan wankan ta kai mata bayi. Tana wanka tana kuka. Abin da take gudu kenan, wannan dalilin ya sanya ta jure duk wani tozarci, amma ga shi daga ƙarshe dai dole hakan ta faru. Bayan ta gama wankan ta shafa mai. Ta kwanta sakamakon zazzaɓi mai zafi da ya rufe ta. Baba kuwa yana tafiya yana zagi da surutu kamar mahaukaci. Takaicin sakin yake yi sosai, saboda kafin ta zo da yunwa ta ishe shi har ya fara tunanin kiransa. Duk da ya san sai ya wulaƙanta shi kafin ya ba shi, amma da yanzu ƙila ya samu abin da zai ci. Da ya isa gidan da ƙarfi yake buga get ɗin gidan. Farouk na zaune tun da ya yi sakin ya zauna ya kasa fita. Sai ɗura mata ashar yake yi. Kulle ɗakinta ya yi, don kar ta aiko wani daga gidansu, sannan ya gargaɗi Rashida a kan kar ta sake ta bari a shigo. Ita dai shiru ta yi masa dukan da ya yi masa ta ga rashin imaninsa. Tana zaune a gidansa yana ta danna ashariya kamar wani bamaguje, duk da cewar ta ji daɗin sakin, domin yanzu za ta sakata ta wala a gidan, amma zagi da tijarar da yake ya matukar ba ta mamaki. Yana cikin ɗura wa duk ahalinta ashar ya ji bugun get kamar za a karye. Da sauri ya nufi get ɗin yana huci kamar mesa."Wane ɗan iska..." Maganar ta tsaya sakamakon ganinsa, da ya yi fuskarsa babu rahma. "Ɗan iskan da ya ba ka auren yarsa, ka ci moriyar ganga ka yada kyaurenta ne." Ya ce a harzuƙe yana kallon sa "Babu sauran abin da ya haɗani da kai, 'yarka ce kuma na sake ta, wallahi in har ka zo ka ɓata mini rai zan gurza maka rashin mutunci." Ya furta ba tare da shayi ba. "Yanzu kam babu kare bin damo, tun da ka saketa shi ya sa na dawo maka da yaranka, ka san ban ɗoro su a kayan gara." "Ina baƙin talauci ya barka ka yi garan ma." Ya ce masa yana kallon sa. "Haka ne dangin ƙaruna shi ya sa na dawo maka dasu, saboda wallahi ka san ba zan yarda su zauna ba. Nasreen na ji xan haƙura ta zauna tun da ni na haife ta, amma ban da waɗannan yaran." "Ni kuma ba zan amshe su ba, saboda tun da muka yi aure na nuna mata bana son haihuwa, amma sai da ta na ce ta haihu." "To ka kai bolansu ka zubar, amma ba zan riƙe 'ya'yan mara mutunci kamar ka ba." Ya ce tare da tura masa yaran, ya fara tafiya yana ja masa tsinuwa tun daga kakanninsa. Faruk sai ya yi sororo yana kallon sa har ya ɓule. Tsawa ya daka wa Raihan tare da mangareta jin kukan da take yi."Rufe mini baki 'yar banzan yarinya kawai." Ya ce tare da daka mata tsawa, wanda ya sa ta yi shiru ba tare da ta ƙara ko tari ba, saboda mugun tsoronsa da take yi. Jan Musaddik ya fara da yake kuka sosai, tun da Baba ya ɗauko shi, saboda kuka har muryarsa ta dushe. Ko rarrashinsa bai yi ba, ya ja su yana zagi zuwa cikin gidan. Yana shiga cikin ɗakin Rashida ta miƙe tana kallonsa."Faruk, waɗannan yaran fa?" Ta yi masa tambayar cikin gatsali. "Sato su na yi." Ya ce mata tare da zama yana harararta. "No, ban gane bane wai an yi yamma da kare. Ka san dai ba zan riƙe 'ya'yan uban kowa ba? Saboda ka hana ni haihuwa babu 'yar iskar da zata haihu na yi mata wahala." "Ubana kike zagi kenan?" Ya taso a harzuƙe ya tsaya a gabanta. Ganin yadda ya fusata sai ta sausauta."Ni ban zage ba, amma wallahi ba zan riƙe su ba, kuma ba za su zauna a gidan nan ba, don haka ka mayar da su." "Idan gidanki ne sai ki mayar da su." Ya ce mata ba tare da ya kalle ta ba, sai kuma ya miƙe ya shige ɗakinsa yana faɗin,"A gidan nan za su zauna, kuma dole ki kula da su in har kika son zama a gidan nan." "Ka daina cewa dole don wallahi ba ka isa ba. Wannan ai zalunci ne ka hana ni haihuwa, sannan ka rabu da matarsa sai ka kawo mini wasu tarkacen yaranka." Jin bai amsa ba ta gane ya shiga ciki. Wata uwar tsawa ta daka musu tana kallonsu."Rufe mini baki don uwarka wanda ya gadon masifa." Ta ce wa Musaddik tare da sanya hannu ta buge masa baki da yake kuka. A maimakon ya yi shiru, sai ya ƙara sakin kuka ya faɗa jikin Raihan yana kiran Umma. Harara ta zabga musu tare da shigewa ciki. Raihann ta rungume shi tana kuka sosai. Miƙewa ta yi ta koma hannunsa da nufin su fita gidan, amma ganin sun kulle ƙofa, sai ta koma ta ci gaba da kuka. Suna zaune a gurin har kusan awa ɗaya. Farouk da ya shiga cikin ɗaki da wanka ya yi ya kwanta. Bai san mai ya sa tun da ya yi sakin yake cikin damuwa ba. A tunaninsa rashin mutuncin da ta yi masa ya ɓata masa rai. Zagin da tasha Allah kawai ya sani. Sai dai ya gama baccin ya tashi ya fito falo. Turus ya yi ganin Raihan rungume da Musaddik ya yi kuka har ya gaji yana bacci. Ita ma gyangyaɗi take yi a haka. "Raihann," Ya kira sunanta cikin damuwa. Karon farko ya ji wani iri game da yaran. Da sauri ta buɗe idanunta tana sosa kanta."Tashi ku shiga cikin ɗakinku." Ya ce tare da kamata ya ɗauki Musaddik da ya yi nisa cikin bacci. Babu musu ta mike zuwa cikin ɗakin. Kwantar da shi ya yi, sannan ta kwanta ya ja musu ƙofa, ya fita zuwa ɗakin Rashida. Tana zaune a tsakiyar gado da waya a hannunta. Jin shigowarsa sai ta ije wayar tana kallon ƙofa."Saboda iskanci yaran a falo kika barsu, in har na ki ne za ki yi musu haka?" Cikin gadara ta ce,"Ba ka bar ni na haifa ba ballantana na san xafinsu." Jin abin da ta ce ta sa ya ɓaci.'Yarannan babu inda za su je, don haka ki kwantar da hankalinki ki kama su ki riƙe...." "Wallahi ba zan riƙe su saboda ba, zan sha wahala da yaran da ba nawa ba, sai sun girma su kama mahaifiyarsu." "Aikuwa zaki fuskanci matsala da na...." "Faruk, ni fa bance ka saki mahaifiyarsu ka ɗaura mini wahala ba, tun da ka ga na aminta da planning ka san bani da ra'ayin kula da yara. Don haka ba zan wahala da ɗan kowa ba." "Ke! Gidan ki ko nawa? In har kina son zama da ni, ki kula da su, sannna ki yi musu abinci ki ba su." Ya daka mata tsawa tare da magana cikin tsanannin ɓacin rai. "Ba zan iya ba ka dawo da uwarsu don bai ce ka sake ta ba, in har ba za ta tafi da yaranta ba. Ni kuma ba zan yi wahala da su ba." "To shikenan ni da ke mu zuba shege ka fasa." Ya ce tare da juyawa ya fice daga gidan. Nasreen tun da Baba ya fita take ta kuka kamar ra ta zai fita."Mama don Allah ki yi sani abu ya bar ni na kula da yarana, wallahi zan tsaya tsayin daka na basu abincin da za su ci. Yaran wahala za su yi, sam ba zai kula da su ba." "Ki yi haƙuri kawai tun da ya ce ba za su zauna ba, ki barwa Allah komai ki yi musu addu'a. Yara nawa iyayensu suke mutuwa a barsu a hannun matan babaninsu, kuma su rayu cikin wahala su zama wani abu? In kika yi haƙuri komai zai wuce." Ta ce mata tare da dafa kafaɗunta. "Wash! Na shiga uku! Abin da na guda sau da ya faru. Yau Faruk ya sake ni. Kuma yarana suna hannunsa." Ta ce tare da sakin razanannen kuka. Da ƙyar suka rarrasheta ta yi shiru, ta zauna ta zabga tagumi tana addu'a a ranta. Jin muryar baban ya sanya ta miƙe da sauri. A tunaninta ko ya dawo da su, amma sai ta ga babu su yana ta masifa shi kaɗai. "Ɗan iska matsiyaci an gaya mishi shi kaɗai ya iya tijara." Ya shigo yana faɗin haka. "Baba, do...." "Ke Nasreen rufa mini baki, kafin na gaura miki mari, duk abin da ya faru ke kika ja. Da nace ki haƙura tun da ya nuna baya so, amma sai kika kafe ga abin da kika jawa kanki nan. Kin san kina son zama da su, kika kasa zaɓan su ki haƙura da yin bautar ƙasar?" Kuka ta ke yi ta kasa cewa komai jin abin da ya ce. "Ban ga laifinta ba, mene amfanin zama da mutum mugun wanda ba ya son cigaban iyalinsa? Saboda ya san kuɗi za ta samu shi kuma ba ya son cigaban ta." Cewar Goggo. Ganin ta yi shiru ba ta ce komai ba. Ba tare da ya kalle ta jin abin da ta ce ba ya ce,"Bari ki ji tun da ya yi sakin babu yadda zan yi. Kina gama idda aure za ki yi." "Allah ya kaimu ta samu mai hankali mene amfanin zawarcin?" Mama ta ce masa. Ita kuwa da gudu ta shige ɗaki a ranta tana jin ita da aure sai a lahira. Da dadddare kasa bacci ta yi tana ta juye-juye. Kuka sosai take yi tana tunanin halin da za su kasance, musamman Musaddik yaron da kullum yana jikinta. Ta yi kuka har ta ji babu daɗi. Ganin kukan ba mafita bane, sai ta tashi ta ɗauro alwala ta yi sallah. Raihann da baccin dole ya kwashe ta. Rungume Musaddik ta yi suka kwanta. Da ya tashi ita ta cire masa wando ta sanya shi ya yi fitsari. Hannunta yake ja yana kuka."Anty Rai'an, ummaa." Haka yake kuka yana jan hannunta. Kama shi ta yi ta rungume sam ba ta son su fita waje. Ganin kukan ba ƙare wa zai yi ba sai ta ruɗe ita ma ta saka kuka, suka cika gidan da kuka. Rashida wacce take kicin tana girki. Tun da suka tashi suka fara kuka take surfa musu ashar. Ganin kuka na su ba zai ƙare ba, sai ta fito cikin tsanannin ɓacin rai. Wata uwar tsawa ta daka musu da ya sanya suka yi shiru."Ka ga mini 'yan iskan yara! Ko ni na sanya aka saki uwarku? Za ku yi mini shiru kafin na kashe ku da duka!" Ta daka musu tsawa tana kai wa Raihan duka. "Har da ke da girmanki kin kuka dai ka ce an miki wani abu. Bacin ina tsoron abin da tijararren ubanku zai yi mini, wallahi buɗe muku ƙofa zan yi ku tafi gurin uwar na ku. Don bai haifa ba ballantana na yaya." Ta ce tare da juyawa ta fita. Shiru suka yi babu wanda ya ƙara tari sai hawaye da suke yi. Wata uwar tsuka ta saki ta ci gaba da girki. Da ta gama sa ya musu ta yi kaɗan ta kai musu, ba tare da ta damu ko sun ci ba. Saboda yunwar da suke ji da sauri suka ɗauka, sai dai suna kai baki suka ije. Yaji sosai ta sanya domin da biyu ta ƙara yajin. Musaddik yana kuka yana tsoronta. Haka suka wuni har dare sun kasa cin abincin, kuma sun kasa fitowa saboda tsananin tsoronta da suke ji. Farouk da ya bita bai dawo ba sai cikin dare. Da ya dawo ya buɗe gidan ya shiga. Har ya dumfari ɗakinsa sai ya tuna da su. Da sauri ya shiga cikin ɗakin ganin babu haske. A tujaninsa ba su a ciki, amma dai ya ji ƙunkunan Musaddik da sauri ya hana shi bacci. "Raihan," Ya kira sunanta cikin tashin hankali tare da kunna fitilar wayarsa. "Na'am," Ta amsa cikin muryar kuka. Hankalinsa ya tashi sosai. Da sauri ya ƙarasa yana kallon abincin dake gabansu."Ba ku ci abincin ba, kuma mai ya sa kuka zauna sauro yana cizon ku?" "Abincin da yaji ba zamu iya ci ba, kuma Anty ce ta ce mu shiga ciki." Ransa ne ya ɓaci jin abin da ta ce. Hannunsu ya kama su ka fita waje. Bai taɓa tunanin yana son yarana ba, sai a yanzu da ya ji ransa ya ɓaci game da abin da ta yi musu. Cikin fusata ya tura ƙofar yana huci kamar mesa."Saboda uban me za ki barsu a cikin duhu?" Ya yi mata tambayar yana kallon ta. "So kake na kai musu wayata su kunna da ita? Tun da tsabar maƙo ya hana ka ko ɗan solar ka sanya mana. Kana ganin ko wane gida an sanya, amma kai ko maganar ban taba jin ka yi b.." "Ba zan sanya ba in da uban da zai sa.." "Farouk na gaya maka ka daina zagina.." "Ramawa za ki yi?" "Wallahi tsaf zan iya saboda uba bai fi uba ba" Ta ce masa tana aika masa da mugun kallo. Mamaki da takaici suka hana shi magana sai kuma ya yi ƙuta ya ce,"Na gaya miki ba ki isa ki canza tsarin da nake rayuwata ba, kuma wallahi a kan yaronnan za mu yi mummunar saɓawa." "Ka mayar da su gurin uwarsu ba zan iya ba." Ta ce tare da jan tsaki ta juya masa baya. Shi ma tsaki ya yi ya kama hannunta suka fita. A falo ya zaunar da su sannan ya shiga cikin ɗakinsa. Indomie ya ya dafa musu ya bawa Raihan. Ita ta bawa Musaddik har ya ɗan ci ya kwanta. Ɗaki ya shiga ya yi wanka, sannan ya zauna a gefen gado, yana tunanin yadda zai yi da ita ta karɓi yaran. Sai da ya gama abin da zai yi sannan ya fita daga cikin ɗakin. Ɗaki ya kai su bayan ya sanya musu maganin, sauro ya fito ya ja musu ƙofar. Tana tsaye a cikin ɗakinta ya shigo. Ganinsa ta ja tsuka ta mayar da kanta ta kwanta. Ba tare da ya ce mata komai ba ya kwanta. Kusan minti biyu babu wanda ya yi wa juna magana. Hannunsa ya sanya ya rungumeta. Da sauri ta ture hannunsa."Ka cika ni matuƙar ba za ka mayar da yarannan ba, ni kuma babu ruwan da kai." Kallonta ya yi sai kuma ya ce,"So kike na watsar da su a titi? Tun da ubanta ya dawo mini da su ya zan yi? In dai ba gidan marayu kike so na kai su ba." "Ni fa ban damu ba, saboda in har za ka hana ni haihuwa, ba zan zauna na yi wahala da su ba." Jan bargo ya yi ba tare da ya ƙara kulata ba ya yi kwanciyarsa. Gajiya ta yi da mita ta kwanta. Cikin dare Musaddik ya kasa bacci sai kuka yake yi. Ganin haka Raihan ta saka kuka suka cika gidan. Duk rarrashin da ya yi musu sun ƙi yin shiru, har sai da ya yi musu tsawa. Musaddik kuwa har dukansa ya yi, sannan ya yi shiru bacci ya kwashe shi. Ɗaki ya koma ya kwanta, zuciyarsa na ba shi shawarar ya kai mata yaran ko ba za su karɓa ba. Washegari duk yadda yake son ya yi bacci, kan dole ya tashi zuwa ɗakin Nasreen. Bayan Raihan ta sanya shi a fo. Ta kama hannunsa suka fito. Shi ya dafa musu ruwan wanka ya yi musu, sannan ya shirya Raihan makaranta. Ya shiga ɗaki da nufin ya ɗan rintsa. Bacci mai nauyi ya ɗauke shi bai farka ba, sai takwas har da rabi. Kallonta ya yi cikin takaici."Saboda ba yaranki zan kai ba, shi ne za ki ƙi tashina?" "Dama ka aure ni ne don na rinƙa tsaronka, ina tashin ka don ka kai 'ya'yanka makaranta?" Ganin yadda ta yi masa tambayar sai bai ce komai ba. A gauguace ya shirya ya same su a falo."Abba na yi latti ina ta jiran ka, har ƙofar ɗakinka na zo Anty ta kore ni." "Wuce muje." Ya ce na tare da ya amsa mata ba tare da ɗaukar Musaddik. Ranar kuwa sun sha latti don sai ƙarfe tara ya kaita makarantar. Da ya dawo da Musaddik, wanda fuskarsa a kyaɓe jira yake yi a taɓa shi ya saka kuka. Rasa yadda zai yi da shi ya yi, don ya san Rashida ba za ta kula da shi ba. A ranar dai fasa zuwa aiki ya yi. Lokacin ɗauko Raihan ya yi, ya ɗauko ta. Shi da kansa ya haɗa musu a binci. Wuni ranar ya yi aikin kula da su. Kafin dare ya gani sosai don har ya ƙosa. Da daddare ya samu suka yi bacci. Wanka ya yi sannan ya kwanta. Nasreen ta shiga damuwa sosai na rashin yaranta, amma sai dai duk yadda take roƙon Baba ya kafe ba za su zauna ba. Ganin ya ƙi amincewa kuma kuma ba shi ne magani ba sai ta haƙura, amma a cikin zuciyarta Allah kaɗai ya san halin da take ciki. Ko ruwa ta ɗauko za ta sha, sai sun faɗo mata a cikin ranta. Wunin ranar har ta zurma sai ɗan wuya. Da rana tana zaune sai ga Maman Muwaddat. Ganin ta ta rungumeta ta fashe da kuka. "Abin da nake gudu ya faru. Baba ya mayar masa da su Raihan." Ta ce tana share hawaye. "Ki yi haƙuri ki bar shi da yaran, wallahi ba zai iya kula da su ba. Kina ganin matarsa za ta riƙe masa su?" Barka da sallah fans ɗina ina yi muku Barka da sallah tare da fatan Allah ya karbi ibadunmu. Sai na zo muku yawon sallah. Tamu Jamila lawal Zango Jamsy❤️❤️❤️❤️❤️🙏🙏🙏💃💃 Nasreen, Damir, Marwana, har ma da Faruk capacity yana muku barka da sallah. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 14 Abin da nake gudu ya faru. Baba ya mayar masa da su Raihan." Ta ce tana share hawaye. "Ki yi haƙuri ki bar shi da yaran, wallahi ba zai iya kula da su ba. Kina ganin matarsa za ta riƙe masa su?" "Halin da za su shiga nake tunani, ina son yarana ina jin babu daɗi." "Za su dawo gare ki in har kika ɗan yi haƙuri na ɗan lokaci." "Bana jin zan iya." "Daurewa za ki yi, ko wace uwa ba da sonnta rabu da yaranta, duk wacce kika ga ta yi nesa da su, babu yadda za ta yi ne." "Haka ne Allah ya ba ni ikon jurewa, amma Baba bai yi mini adalci ba da ya raba ni da su." Haƙuri da rarrashi ta yi ta mata har ta ji sanyi a zuciyarta. Ta jima sannan ta yi mata sallama. "Don Allah ki rinƙa duba mini su." Ta ce tana share hawaye. "Zan yi iyakan ƙoƙarina, amma kin san ganinsu da wuya, saboda Yasir ya ce mini ba ta je makaranta ba sai da rana ta yi." "Kin ji ko? Dama na gaya miki ba zai iya kula da su ba." "Komai zai wuce ki yi haƙuri wahala ba ya kisa. In mutuwa kika yi dole za ki tafi ki barsu." "Haka ne." Ta ce tana jin kewar yaran. Da daddare ta kasa bacci, har sai da ta ɗauki maganin damuwarta, sannan ta samu ta yi bacci mai cike da kewarsu. A tunanin Faruk zai iya rarrashinta ta riƙe mishi su, amma sai ya ga ta funjire ta shafawa idanunta toka. Babu rarrashin da bai yi mata ba, amma ta ƙi daga baya ta ƙi, daga baya sai ta ce masa za ta iya rike su a bisa sharaɗi ɗaya. Kallonta ya yi yana mamakin kafiyarta."Ina jin ki." Ya ce cikin rashin dubara, domin ko sati ba a yi ba, ya gaji matuƙar gaske. Babu abin da yake damunsa fiye da kukan Musaddik. Sannan shi bai iya rainon yara ba. Ko lokacin da yana yaro tsakaninsa da yara sai kallo. "Ka ba ni dama na haihu da kai. In har ka yi mini haka zan iya tausasa zuciyata na ga ko zan riƙe su." Tsaki ya yi jin abin da ta ce,"Ba zan amince ba, saboda ban aure ki don ki tara mini yara ba. Jikinki ya burge ni na sanya kuɗina na aura." Mamakin abin da ya ce ya kamata, sai ta kalle shi cikin mamaki ta ce,"Ai wallahi tun da haka ka ce, sai dai ka nemi inda za ka kai su." Banza ya yi da ita ya juya mata baya. Shawara ya yanke ya kai su gurin Yaya Asiya. Da safe ya haɗa musu kaya ya kaisu. Tana zaune a falo ya shigo da jakarsu yana rungume da Musaddik. "Lafiya Faruk, na gan ka da yara haka?" Ta ce masa tana kallon sa. Ba tare da ya amsa mata ba ya ƙara sa kan kujerar ya zauna."Na kawo su nan ne." Ya ce yana kallonta. "Hutu za su yi mini ina uwarsu?" "Mun rabu na sake ka..." "Ka yi me? Anya kana da hankali kuwa?" Ta yi mishi tambayar cikin tsananin razana. "Sakin ta na yi, saboda a rayuwata ba a yi macen da za ta ce za ta duke ni na ƙyale ta." "Alhamdulillah! An zo gurin dama na san cewa watarana dole hakan zai faru. Dole watarana za ta kai hannu jikinka ta rama dukan da kake mata." "Aikuwa ma koya mata hankali saboda ban sake ta ba, sai da na yi mata jina-jina." Ya ce kamar ya aikata abin kirki. Kallon sa ta yi cikin tsananin takaici."Tur da halin ka Faruk! Tur da halin WASU MAZAN da ba su san darajar mace ba. Wallahi tun da ka yi gigin rabuwa da ita, ka yi asarar mace na kirki. Ina yi maka jaje a rayuwarka. Ina tausayin ranar da za ka zo kana kuka a kan rabuwa da ita da ka yi." "Haba Yaya Asiya wannan fata kike mini ko so kike haka ya faru da ni?" "A'a abin da zai faru na ke gaya maka. Ka san wace ce ita? Kasan kyautar da Allah ya yi maka da ya ba ka ita. Nasreen uba ne kawai ba ta dace da shi ba, har Allah ya sa ta shigo rayuwarta, amma wallahi ba sa'ar aurenka bane. Ba ka da kyawawan halayen da ya kamata ka zamo mijinta." "Ni dai ba wanann ya kawo ni ba ina matar da ta fita. Kece kawai kike ganin qualities ɗin nan a gurinta, amma ni a gurin mace ce mara tarbiya wacce ba ta samu uba wanda ya bata tarbiyar ƙwarai ba." "Lokaci ne zai nuna mana haka, amma ina maka jaje na rashin matar kirki kamar ta." Ƙaramin tsaki ya ja ba tare da ya ce komai ba. "Yara na kawo miki don Allah su zauna a gidanki. Ɗan Iskan mahaifinta ya hana ta riƙe wa." "Ya yi mini daidai ai gara da ya yi maka haka, sai ka san akwai inda zai iya ƙuntata maka." "Ni dai ki taimaka mini ki riƙe su." "Ni? Allah ya kyau, wallahi ba zan riƙe su ba. Ina matar da kake ganin ta kirki ce?" "Ta ƙi karɓarsu." "Sai ka yi rainon su tun da ka saki uwarsu, abin da ya sanya ba zan kira Mama ba. Ya kamata ta rabu da kai ta je ta samu mijin da zai daraja ta." Tsuka ya yi bai ce mata komai ba.Miƙewa ya yi a tutaninsa wasa take yi za ta riƙe su. Ganin ya tashi ta kama hannun yaran ta ce,"Wallahi ka tafi da su ba zan riƙe su ba. Nawa ma ya na ƙare da su?Kana sane da malamar makaranta ce ni." Ta ce masa tare da saka masa kamar kayansu a mota. Ganin da gaske ta ke yi dai kawai ya fi motarshi ya fice. Ƙuta ta yi tana kallon get ɗin da ya fita."Za ka yi dana sani mara amfani." Ta ce tare da juyawa ta shigo ciki gidan. Farouk damuwa ta yi masa yawa, ya rasa yadda zai yi da yaran. Da ya koma gida zaunar da su a falo ya yyi ya fice daga gidan. Haka suka ta walangiya har yamma ta yi. Raihann ta kama hannunsa suka shiga cikin kicin. Kujerar ta ije sannan ta hau sama zata ɗauko abinci."Anty ci." Musaddik ya ce mata yana nuna kula. "Yanzu zan ɗauko maka." Ta ce tana ƙoƙarin janyo ƙular. "Ke!" Ta ji muryar Rashida wanda ya sanya ta saki ƙular abinci ya zube a ƙasa. "Kan uban nan! Kika zubar da abincin bayan kin san maƙoƙon ubanki ba ƙara mana zai yi ba? Ai ko yau din uwarki sai kin kwana da yunwa." Ta ce tare da kai mata mari wacce ta firgice. Kuka ta sanya tana bata haƙuri. "Yi mini shiru din ubanki in kika ƙara buɗe baki sai na fasa miki shi." Ta ce tare da kai wa bakin duka. Jin abin da ta ce, ya sa ta yi shiru ko tari ba ta ƙara ba."Ku fita yan banza kawai." Ta ce tare da daka musu tsawa. Da sauri ta fice saboda tsoro Musaddik a gurin ta barshi. Ganin ta fita tana kuka ya ruga shi ma. Duka ta maka masa a ɗuwawu."Yan banza gayyar jaraba." Ta ce tana huci. Kuka sosai suke yi, ganin sun dame ta sai ta kai su waje ta rufe ƙofarta ta kunna kallo. Haka suka wuni a rana har sai da ta gaji don kanta ta dawo da su. Abinci wanda ya zube ta kwashe ta ba su, saboda yunwa haka nan suka ci. Ganin dare ya yi ta tura su ɗaki ta sanya su baccin dole. Farouk kuwa sai ya fita sabgarsu bai damu da ya duba ko sun ci abinci ba. Gabakiɗaya sun dame sun fita hayyacinsu. Makaranta kuwa tun yana kai ta a makare har ya kasa ya daina. Hankalin Nasreen ya tashi sosai da ta je makaranta gaba da za a tashi. Har cikin aikin ta je, amma sai malamar ta gaya mata rabin da ta zo makaranta. Hawaye ta share cikin tashin hankali."Na gode." Ta ce cikin muryar kuka tana ƙoƙarin haɗiye kukan da yake son goce mata. Ji ta yi kamar ta je gidan, amma ta san hakan ba zai yiwu ba. Gidan Maman Muwaddat ta je. Ganin ta hankalin ya ya tashi."Yanzu sai da kika biyo yarannan? Ya kamata ki ɗauke idanunki na wani lokaci." "Ya kike so na yi? Ina son yarana. Makarantar Nasreen na je, amma malamar su ta gaya mini ta daina zuwa. Na san cewa tun da na bar gidan nan, rayuwarsu tana cikin wani hali. Haƙiƙa Baba sam ba ya yiwa rayuwata adalci da ya raba ni da su." Ta ƙarashe maganar cikin kuka. Sannan ta ɗora da cewa,"Ina ga zan je na ɗauki su, sai na bar masa gidansa. Na je can na yi rayuwata da yarana. Zan tashi na nemi abin da za mu rinka ci." Hannunta ta kama ta rungumeta ganin yadda take kuka."Ki yi haƙuri Allah yana tare da ke. Ki kauda idanunki a kan yaran nan. Farouk ba zai iya riƙe su ba, yana dawo da su sai ki muna wa Baba in har zai kore su sai dai ki bar masa gidansa." "To," Ta ce kamar ƙaramar yarinya tare da share hawayenta. Ta jima tana bata baki sannan ta haƙura ba za ta je gidan ba. Ganin yadda hankalinta ya tashi sai ta rako ta har ta bar layin.Tana hanya tana kuka har ta isa gida. Saboda sauro da yake cizon su cikin dare zazzaɓi ya kama Raihann. Tashi ta yi ta zauna tana faɗin,"Umma, ruwa zan sha sanyi." Ta ce cikin muryar kuka tare da kyarmar sanyi. Jin ba ta amsa mata ba sai ta tuna inda suke. Zazzabin ya ci ƙarfinta ta kasa magana sai kyarmar sanyi. A haka ta kwana har gari ya waye. Da safe kuwa jikin ta ya gashe kamar wuta. Tana kwance a kan gadon Faruk ya shigo cikin ɗakin ganin ba ta fito ba. Musaddik yake zaune a kan gadon yana kallonta. Alamun fuskarsa ya ci kuka ya ƙoshi. "Raihan, lafiya?" Ya ce mata tare da janye bargon da ta lulluɓa. Da sauri ya toshe hancinsa jin ɗakin yana wari, Musaddik ya yi fitsari ga shi bayin ba a wankewa. "Ba ni da lafiya." Ta furta masa cikin muryar kuka hawaye yana zirarowa ta gefen idanunta. Jikinsa ne ya yi sanyi sosai har ya ji babu daɗi."Anya na kyauta ma yaran nan kuwa?" Ya yi tambayar cikin damuwa. Ƙaunarsu da tausayin su ya cika masa zuciyata. Ɗauko ta ya yi tare da kwantar da ita a falo. Sai a lokacin ya lura da yadda suka rame sosai. Babu wanka ga kayansu sun yi dadti. Ɗakinta ya wuce ya samu Rashida wacce take ƙudundune cikin bargo. Duka ya ɗaɗa mata. Cikin sauri ta miƙe za ta ƙunduma ashar. Ganinsa ya sanya ta fasa tana mazurai."Saboda me za ka duke ki ina bacci?" "Abin da yafi wannan ya kamata na yi miki. Anya kia da tausayi kuwa? Dubi yadda yaran nan suka lalace ina ga ko abinci ba kuma basu?" "So kake na kashe kaina saboda su? Ni fa ban ce maka rabu da uwarsu ba. Ba zan iya wahala da su ba, sai dai ka kai su gurinta, kuma wallahi duk ranar da ka ƙara sanya hannu ka buge ni sai na rama, saboda ni ba banza bace da zan bari ka rinƙa dukana." "Ashe ko watarana zan karya ki, don duk ranar da kika kuskura kika duke ni dai na yi miki abin da ya fi wanda na yi wa Nasreen." "Za dai mu karya juna a tunaninka zan zauna kamar ita ka duke ni? To ko ubana ba zan yarda yanzu ya duke ni ba, ballanatana kai da ka ganni da haƙorana." "Lailai watarana zan zubar miki da haƙorar." "Ni kuma duk ranar da ka yi mini haka na rantse maka sai na ƙona gidan nan, saboda ba ka sanni bane shi ya sa kake mini rashin mutuncin da ka ga dama. To ni zan iya ƙunan wake duk a mutu a huta." Ya buɗe baki zai yi magana sai ya fasa ya saki tsaki ya fita daga ɗakin, ganin ta koma ta kwanta tare da jan bargo ta rufe fuskarta."Jarabbabe matsayaci kawai, wallahi na yi dana sanin aurenka, kuɗin da na saki baki zan ci ban samu ba, sai jarabar tsiya da rashin mutunci, da sannu zan yi maganinka" Ta furta hakan cikin takaici tare da jan tsuka. Ɗaukar ta ya yi suka je asibiti, a maimakon ya tsaya a binciki lafiyarta, sai kawai ya ce a ba shi magani. Bayan sun dawo shi da kanshi ya yi musu wanka ya ba ta magani. Kwana biyu ta yi ta ɗan samu sauƙin ganin ta warke ya ci gaba da sabgarshi. A rana na uku yana gurin aiki zazzaɓin ya dawo. Falo ta zo ta kwanta. Tana makyarkyata. Rashida wacce ta fito daga kicin hannunta ɗauke da filet na shinkafa. Ganin abincin tana ci Musaddik ya ƙura mata ido. Tsawa ta daka mishi tare da yi masa daƙuwa."Ma za ke ɗauke shi ku shiga ciki kar ku sanya na kware mayu kawai." Ta ce tana zare musu idanu. Raihan ta miƙe da sauri saboda tsananin tsoronta da take yi, amma sai ta kasa jiri ya ibeta ta faɗi. Idanunta ya ƙaƙƙafe ganin haka hankalin ta ya tashi sosai. Da sauri ta inda abincin tana faɗin,"Ke kar ki jaza mini bala'i ki mutu a yaɗa ni a duniya na kashe 'yar kishiya." Ta ce tare da watsa mata ruwa, amma ko motsi ba ta yi ba. Ganin haka ya sanya ta ɗauke ta tasa ihu za ta fita maƙota. Maman Muwaddat tana zaune tana tunanin rayuwar Nasreen. Bayan sun gana waya ta ƙara kwantar mata da hankali. Roƙon da ta yi mata kanta je ta duba mata yaran, take jin kamar ba za ta iya cikawa ba. Ta san halin Faruk tijararre ne, ba ta son ya yi mata rashin mutunci, duk da cewar tana tunanin ba za'a same shi a gidan ba. Jikinta a sanyaye ta ɗauki hijabinta ta shiga cikin gidan, daidai lokacin da ta fito da Raihan a sume. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Mai ya faru?" Ta yi mata tambayar tare da karɓarta. "Ba ta da lafiya ne ta sume." Ta ce a firgice. Bata jira abin da zata ce ba ta shiga cikin gida. Motar mijinta ta ɗauka suka kaita asibiti. Da ƙyar suka yi nasarar dawo da numfashinta. Bayan likitan ya gama bincike ya kira ta. "Saboda me za ku bari maleriya ya kama yarinyarki haka? Bayan akwai net ko kuma maganin sauro ga kuma yunwa?" Shiru ta yi cikin tausayi ba tare da ta ce komai ba. Ganin haka mijinta ya ce." In sha Allahu za mu kiyaye." "Ya zama dole saboda yana shirin taɓa ƙwaƙwalwarta. Don Allah ka kula in mahaifiyarta ba ta nan kai uba ne a gareta." Ya ce yana kallon Maman Muwaddat a tunanin sa ba mahaifiyarta ba ce. "Shikenan mun gode." "Zan kira Nasreen ta zo asibitin nan, yanzu zan koma na ɗauko mata Musaddik na sanya Amina ta ɗauki shi. Ta karɓi yaranta in mahaifinta zai kore ta, sai dai ya kore ta amma kar ta bar haramta su mutu." Ta ce tare da danna mata kira. Nasreen tana zaune a tsakar gida kan turmi ta zabga tagimi. Hira mutanen gidan suke yi, amma gabakiɗaya hankalinta ba shi kan hirar. Sai kallon wayarta take yi tana jiran kiran Maman Muwaddat ta gaya mata yadda yaran suke. Ganin kiran har sai da ta miƙe."Hello ya yarana suke?" Ta yi mata tambayar cikin rawar murya. "Ki zo asibin Almadina muna can da Raihann ba...." "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta furta tare da yanke wayar ta saka kuka. "Lafiya Nasreen?" Mama ta yi mata tambayar cikin ruɗani. "Raihann ba ta da lafiya tana asibiti. Na shiga uku dama na san Faruk ba zai iya rike mini yarana ba. Wallahi zan kawo su gidan nan, in Baba zai kore su sai dai ya haɗa da ni." Ta ce tana kuka. "Ki natsu mu je asibiti..." Ko kafin Mama ta gama magana har ta kai baƙin ƙofa. Ganin yadda ta ruɗe ya sanya ta rinƙa ba ta baki, amma ba ta jin bin da take cewa. Burinta kawai ta yi toxali da yaranta. A ƙofar shiga asibitin ta haɗu da Maman Muwaddat da suka je ɗauko. Musaddik. Da sauri ta ƙara da ta karɓe shi wanda tun da ya ganta ya fara miƙa mata hannu sai ya saka kuka. "Na shiga uku Musaddik ne ya dawo haka?" Ta yi mata tambayar cikin kuka. "Yaranki suna buƙatar ki, duk abin da Baba zai yi miki karki rabu da su. Ban taɓa ganin mugun uba ba irin sa." Kuka take yi sosai tana tausayinsu. Da suka shiga cikin ɗakin da aka kwantar da ita. Rungumeta ta yi tana kuka sosai har sai da suka rarrasheta "Wallahi ko kashe kin zai yi ba zan yarda ya ƙara raba ni da yarana ba, Faruk mugu ne Allah ka saka mini yarana." "Umma, don Allah kar ki tafi ki barmu Abba ba ya sonmu." Raihan ta ce cikin sanyin murya na masu ciwo, sai kuma ta fara tari alamun yunwa ta kamata. Kamata ta yi ta rungume tana hawaye. A ranar wuni suka yi a asibitin sannan aka ba su sallama. Da ga asibitin gida suka wuce. A ranta ta shirya duk abin da Baba zai yi mata sai dai ya yi, amma ba za ta bari su koma gidannan ba." Da ya shigo ya gansu, Raiha tana kwance a tsakar gida, an shinfiɗa mata tarbarma tana sha iska Barka da sallah fans ɗina ina yi muku Barka da sallah tare da fatan Allah ya karbi ibadunmu. Sai na zo muku yawon sallah. Tamu Jamila lawal Zango Jamsy❤️❤️❤️❤️❤️🙏🙏🙏💃💃 Nasreen, Damir, Marwana, har ma da Faruk capacity yana muku barka da sallah. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 15 Da ya shigo ya gansu Raihan tana kwance a tsakar gida, an shinfiɗa mata tarbarma tana sha iska. "Waɗannan kuma fa?" Ya tambaya tana nuna su. "Haba kai kuwa, kamata ya yi ka tambayi mai ke damunta, amma ba wai daga ganinsu ka tambayi abin da suka zo yi ba." Mama ta ce cikin sanyin murya. Nasreen kuwa hawaye ta goge jin ya ɗaga kafaɗa ya ce,"Ba wannan ya dame ni ba, kawai so na ke na san abin da 'ya'yan Faruk su ke mini a gida." "Ka zauna na yi maka bayani." Ta ce cikin takaici. Zama ya yi yana faɗin,"Duk abin da za ki faɗa, ba zan yarda su zauna mini a gida ba." Bayan ta gama gaya masa abin da ya faru, sai ya kalle yaran da fuskar ko in kula ya ce,"Ya kashe su mana ai yaransa ne. Shi ya kasa tausayinsu sai ni? Dole su koma gidan ubansu, yadda ya kasa riƙe mini 'yata don ubansa ba zan riƙe na sa ba." "Baba, ba zan iya barin yaraba ba, in har ka tilasta mini dole su koma ni kuma zan bar gidan dasu. Zan je na samu inda zan zauna na kula dasu." "Allah ya ba ki sa'a in kin so ki tafi bangon duniya, amma ba za su zauna ba." Ya ce tare da wucewa fuu kamar kububuwa. Rungume su ta yi a ranta tana jin babu abin da zai raba ta da su. Duk bala'in da ya rinƙa yi sun shanye, saboda babu wanda yake tanka masa har ya gaji ya gama. Gabakiɗaya suka ɗaure mata gindi har da yaran gidan, sun rantse in har ya kori 'ya'yan Nasreen, sai su ma sun bar masa gidan, kuma daga ranar sisi ba za su ƙara taimaka masa ba. Goggo da Mama kuwa kowa ce ta haɗa kayanta jira suke ya kwashi yaran ya mayar, kamar yadda ya ce, su kuma su bar masa gidansa. Ganin haka sai hankalinsa ya tashi sosai, saboda ko kallonsa ba sa yi, jira kawai su ke yi ya mayar da su, ya ga aiki da cikawa. Ranar duk wacce ta yi girki babu wacce ta ba shi, haka ya wuni yana hamma tun da haka yake yi, sai dai in sun samu su sam mishi, ranar da yake da shi ba ya ma wuni a gidan. Wannan abu da suka yi masa ya sanya jikinsa ya yi sanyi, har ya kasa mayar da su. Sai dai ya rinƙa tsiya yana zage-zage sun raina shi, babu wanda yake kula shi. Ya yi bala'i ya yi masifa da tijara, ko kofi ya gani a tsakar gida, in ya yi ball da shi ya fara tsiya, sai dai su yi mishi shiru kawai. Ganin faɗan shi a banza har ya gaji ya haƙura, amma kullum sai ya gaya mata tana gama idda a za ta yi aure, ta mayar masa da yaransa. Ita dai shiru kawai take yi masa tana addu'ar Allah ya kai ta lokacin. Auren fari dai ya yi mata dole, amma a wannan karon ba ta tunanin zuciyarta za ta iya aminta da wani ɗa na miji. In ya matsa mata da zancen aure za ta je ta kama haya ta raini yaranta. Farouk da ya dawo gida bai ga yaran ba kallonta ya yi da take ta zare idanu alamun rashin gaskiya."Ina su Raihan na duba ɗakinsu ban gan su ba?" Jin tambayar da ya yi mata sai da hantar cikinta ya kaɗa."Mahaifiyarsu ta turo an..." Ganin yadda ya zare idanunsa yana kallon ta cikin ɓacin rai, sai ta fasa ƙaryar da za ta yi masa ta ce,"Ta tashi ba ta da lafiya ta sume shi ne na ruɗe na fita ina neman taimako, sai na ci karo da Maman Muwaddat ƙawar Nasreen ta karɓe ta..." "Uban me ya sa ba ki kira ni ba, kika bata ita?" Ya furta yana huci. "To ka ije ni na yi maka gadinsu ne, ina laifina don na yi taimako?" Ta mayar masa da tambaya a maimakon amsa. Mugun kallo ya watsa mata ya fice daga gidan. Cikin isa ya rinƙa doka sallama a gidan. Kasancewar mijinta ba ya nan, sai ta sanya hijabi ta leƙa wajen domin da ma tana addu'ar ranar da za su haɗu."Ina yarana?" Ya ce mata babu sallama bare gaisuwa. "Ka bani ajiyarsu ne?" Ta furta tana harararsa. "Babu ruwan ki da rayuwar gidana, saboda har da ke ku ka zuga Nasreen take mini rashin kunya. Ki bani bani yarana na wuce, don ba ni da lokacinki." "Ko kuma ni ne ba ni da lokacinka domin ba ka cika namijin da zan yi sa'insa da shi ba. Wanda ya kasa riƙe matarsa ya zama mugu azzalumi hatta yaranka ba ka daga..." "Da mijin ki zan yi ba da ke ba, saboda ke ban ɗauke ki da wata darajar da zan yi sa'insa da ke ba." "Ba ka da abin cewa dai Faruk! In sha Allahu zalincin da ka yi wa Nasreen dai Allah ya saka mata. Sai ka zo da hawayenka kana dana sani." Ba tare da ya kula da abin da ta ce ba ya bar ƙofar gidan. Gida ya koma ya tasa Rashida da masifa. Da fari ta yi banza da shi, amma ganin yadda yake gaya mata yake neman zaginta sai ta miƙe ta ce,"Tsaya Faruk! Na gaji da rashin mutuncin ka, ɗin ka saki matarka ba zan yarda ka ci kashin da kake ci a kanta ba. Haka kawai saboda wasu banzan yaranka da ka kasa kula da su, sai ka nemi zagina." Ta furta cikin murya mai ƙarfi. "Ok, haka kika ce?" "Eh, don wallahi ba a yi namijin da zan zauna yana mini ihu kamar wata 'yarda ba." "Ihu yanzu na fara miki watarana fukanki zan yi za ta yi jini, matuƙar kika ce ba za ki bi umurnina ba." "Heeee!" Ta yi shewa tana tafa hannayenta sannan ta ce,"Ashe watarana za mu daku, saboda wallahi ba a yi wani gardi da zan bari ya taɓa lafiyata ba." Mamakin sunan da ta kira shi da shi ya yi, amma sai ya kasa ce mata komai, ganin yadda ta tsaya babu alamun tsoro a fuskarta. Ƙuta ya yi sai ya wuce cikin ɗakinta ya kwanta yana jin zuciyarsa babu daɗi, yana mamakin yadda take gaya masa magana, ya kasa ɗaukar mataki. Ya yi tunanin Baba zai dawo masa da yaran, amma dai ya ga har sun yi kwana biyu, ba su dawo ba. Hankalinsa ya kwanta ya ƙi zuwa don kar ya sanya dole ya dawo da su. Shi kansa zai fi samun natsuwa in suna can. Nasreen ta samu kwanciyar hankali sosai, domin tun ranar da yaran suka dawo gurinta take ji kamar an zare mata ƙaya. Hankalinta a kwance, yake gudanar da shirin fara bautar ƙasar da za ta yin domin kira kawai take jira har an yi posting ɗin ta za ta je Maiduguri ta dawo, sai ta ci gaba da koyarwa a makarantar sakandiri babu nisa sosai a tsakaninsu. A ranar da aka kira su ta shirya ya tafi duka sati ɗaya ta yi sannan ta dawo. Ji take yi rayuwarta kamar ba ita ba, ganin ta samu farinciki da kwanciyar hankali. Bayan ta dawo ta fara koyarwa a makaranta. Sosai take jin rayuwarta ta canza. Inka ɗauke kwamacalar rayuwar zaman gidansu, babu abin da yake damunta. Dama kuma wannan ta saba. Jarrabar Baba ne ya zu ba ya ba ta tsoro. Haka sai yi ta surfa ma yaransa zagi yana tsine musu albarka. Shi da ya kamata ace ya tallafi rayuwarsu, amma kullum ba shi da aiki sai roƙon su kuɗin da zai ci abinci. A ranar da aka yi musu biya cikin tsana farinciki ta wuce kasuwa. Siyayar abincinta yi musu sannan ta Kafin a fara biyanta sha wuya sosai, domin kuɗin motar ma sai ta roƙa gurin ƙanninta. Kasancewar akwai tazara sai an hau napep. Ta ci gaba da kai Raihann makaranta a ranta ta sanya ko da Faruk ba zai biya ba, za ta ci gaba da biyan mata. Rayuwar haka take gwara musu yau fari gobe tsumma. A haka har aka fara biyansu. A ranar ta je ta shigo duk abin duk abin da suke buƙata, domin duka naira dubu goma ta shigo da shi cikin gida. Baba ta ba wa naira dubu goma sai Mama ta cire dubu biyar ta bata na cefane. Sannan ta cire kuɗin mota da wanda za ta rinƙa siya wa Raihan biskit. Hankalinta kwance tana ta zuwa aikinta sati da lahadi islamiya. Kasancewar yadda yanayin rayuwar na su yake, sai kuɗin da take samu ba ya biya mata buƙatunka. A haka dai suke tafiya da rayuwar yau fari gobe tsumma, amma rayuwar da take yi yafi mata na gidan Faruk. A ranar da Maman Muwaddat ta zo ta kawo mata hijabai, ta yi farinciki sosai ta karɓa, kuma babu laifi yana shiga. Damuwarta ɗaya yadda Baba kullum yake isarta da bani-bani. In ta ce masa babu ya rinƙa tozarta yana ƙunduma wa yara ashar, tare da barazanar mayar da su. Wannan dalilin y sa ta gwammace ba ta a gidan da zama. In kuma tana nan za ka dame ta a cikin ɗaki da qur'ani a hannunta tana karantawa. Damir da su Hajiya zaune a filin jirgi yana jiran fasinja su gama haɗuwa, don jirgin ya tashi zuwa Nigeria. Yana sanye da suit baƙaƙe sun yi matuƙar yi masa kyau. Ya murje ya yi kyau kamar bashi ba. Kullum yana yi mata addu'a, ganin ƙunci da shiga damuwa ba zai dawo masa da ita ba. Abu ɗaya zai yi ya tabbatar da yana ƙaunarta, ya ƙara sa rayuwarsa batare da ya yi aure ba. Tabbas duk barazanar da Hajiya take masa, ya sanya duk abin da za ta yi ba zai auri ko wace 'ya mace ba. Hannunsa riƙe da wayarsa yana tura message, chattin yake yi da Muhsin. Marwana take gefensa da ƙatuwar teddy na Little Marwana da ta ba ta ijiya, tana cinyar Hajiya bacci ya kwashe ta. Sosai take jin daɗin za su dawo gida. Damuwarta ɗaya ita dawo ba za ta iya zuwa ta ga Nasreen ba, saboda baƙi da Hajiya ta yi mata. Sosai take kewarta har yau tana jin sonta, babu abin da ya ragu. Ta san cewa a wannan lokacin ta rabu da mugu FARUK, wataƙila ta canza ta yi kyau kamar ba ita ba. Tana son ta je gidansu ta ganta, sannan ta yi wa Ya Ahmad godiya na zama mata bango da ya yi, sai dai mugayen kalaman da Hajiyar ta yi mata ya sanya ta kasa kiranta ko da a waya ne. Damir ya miƙe tare da ɗaukar Little Marwana da ta farka tana goge idanunta. Kiss ya sakarwa yarinyar yana murmushi. My little angel ta tashi, daidai da lokacin da jirginsu yake shirin tashi ku zo mu shiga." Ya ce masu yana kallonta. A yanzu bashi da abin so kamarta. Duk son da yake wa mahaifiyarta ya ɗaura shi kanta. Yana dinga fiye da kansa. Tun da ya saki ya fara rage damuwa. Shi yake mata wanka da komai na ta. Ji suke yi da yarinyar sosai, suna tausayin za ta tashi cikin maraici. Bayan sun shiga direban jirgin ya fara tuƙawa. Addu'a suke yi Allah ya sauke su lafiya. Bayan wasu awanni jirginsu ya iso Nigeria. Kasancewar da daddare suka dawo, kowa ɗakinsa ya wuce ya yi wankan sannan suka kwanta. Da safe ko da suka yi sallah baccin gajiya suka yi. Marwana ta fara tashi sai Hajiya. Dama tuni sun sanar da mai aikinsu za su dawo. Ta zo ta gyara gidan kuma ta yi musu abinci, sannan ta fara aikinta tun kafin su dawo, domin a gidan ta kwana. Kicin suka nufa don su samarwa little Marwana abinci da take musu ƙorafin yunwa. Marwana na ƙoƙarin ba ta abinci a baki Damir ya shigo falon. Ganinsa ya sanya ta rungume shi. "Angel kin tashi?" "Yes daddy ina kwana?" "Lafiya lau." Ya ce tare da jan kumatunta. "Ina kwana Ya Damir?" Marwana ta ce tana kallon sa ganin yadda ya yi kyau. "Lafiya lau sis." Ya ce ba tare da ya kalle ta ba, bayan ya ja filet ɗin abincin da za ta bawa Marwana ya fara bata. Hajiya ce ta fito tana tafiya da kyar saboda ƙafafunta, tun a jirgi take korafi. Gabakiɗaya suka kalleta daidai lokacin da Muhsin shi ma ya shigo. "Ina ga fa sai kin je clinic ko?" Ya yi mata tambayar yana kallon ta. "Man zafi na shafa tsufa ce kawai kafar zai saki." Ta ce nushi tare da zama gefensa. "Allah ya ƙara sauƙi ni da Muhsin za mu je campany in na gama zan biya na suyi miki wani maganin." "Ok, sai kun dawo Allah ya tsare Please ku mayar da hankalinku." "In sha Allahu." Ya ce sai kuma ya kalli Marwana. "Ke ma sai ki shirya ki koma makaranta kin san duka bai fi 2weeks ku zama exam fa, don kin yi deffering semester da ba za su bar ki ba." "Haka ne Ya Damir da kuma taimakon amininka." "Ki mayar da hankali ban da wasa." Muhsin ya ce mata. "In sha Allahu Yaya You know me." Kansa ya ɗaga mata jin abin da ta ce. "Wallahi Marwana kika koma makaranta kika kula wannan yarinyar sai ka matuƙar bata miki rai, innhar ni na haife ki ban aminta ki yi hurɗa da ita ba." Ta ce cikin kakkausar murya. "Mommy ba zan ga Nasreen ba, saboda ta kammala karatunta, sannan ban taɓa zuwa gidan iyayenta ba, yanzu dai na san ta rabu da mijinta Faruk." "Ko ma dai mene ne na hana ki hurɗa da ita." Ta ce mata tare da miƙa ta isa dining. Damir gabansa ya faɗi sosai jin an yi maganarta. Tun da ya bar Nigeria ya fara ƙoƙarin manta komai ya yi ƙoƙarin mantawa da ita, ya ɗauki mutuwar Batula a matsayin lokacin ta ne ya yi, domin ta hakan ne kawai zai iya mantawa da ita. Da sauri ya fice ba tare da ya ji abin da Hajiya ta ce ba. Da suka je campany ma'aikatan sun yi matuƙar farincikin ganin ya yawo sai Damir ɗin da, abin da kawai ya rage yawan ɗaure fuska. Duk da cewar Muhsin ya yi ƙoƙari, amma ya samu aiki sosai har sai da ya gaji. Ba tare da ya kammala aikin ba suka dawo gida. Wanka ya yi sannan ya wuce masallaci. Bayan sun yi sallah ya shigo cikin gidan. Bayan sati ɗaya da dawowarsu hankalin Hajiya ya kwanta sosai, ganin yadda ya kwantar da hankalinsa. Marwana sai da ta gama hutun gajiya sannan ta shirya don ta je makaranta. Tafiya take cikin farin ciki tana tunanin rayuwar da ta yi da ƙawayenta musamman su Nasreen, yau ga shi ƙaddara ta sanya duk sun gama, amma ita sai wanann shekarar za ta gama. Ba ta manta ranar da wasu ƙawayenta suka yi posting hotonsu da kayan copper har sai da ta yi kuka, amma babu komai za ta ɗauki hakan a matsayin ƙaddarar rayuwar ta in har Nasreen tana cikin farinciki. Bayan ta isa makarantar ta kashe motarta tare da fitowa ta kulle ta. Sai da ta gama lecture sannan ta fito daga cikin makarantar. Tana ƙoƙarin shiga cikin mota ta ji an ƙwala mata kira. Da sauri ta waiga tare da zare gilas ɗin idanunta."Asmy, ke ce ko idona gizo yake mini?" "Ni ce mana ko na canza kama ne? Ke ya kamata na yi mamakin ganinki saboda na san kina waje." "Wallahi sati ɗaya da dawowarmu ya service?" Ta ce mata tare da kama hannunta ya riƙe. Barka da sallah fans ɗina ina yi muku Barka da sallah tare da fatan Allah ya karbi ibadunmu. Sai na zo muku yawon sallah. Tamu Jamila lawal Zango Jamsy❤️❤️❤️❤️❤️🙏🙏🙏💃💃 Nasreen, Damir, Marwana, har ma da Faruk capacity yana muku barka da sallah. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 16 "Wallahi sati ɗaya da dawowarmu ya service?" Ta ce mata tare da kama hannunta ya riƙe. "Hmmmmh! Ki bar tuna mini abin haushi kar kisa na ɗorawa lecturer Tukur zagi, kin san ɗan Iskan malamin nan, sai a semester na ƙarshe ya bani spill ov..." Kafin ta ƙarashe ta saki salati tana faɗin,"Yanzu duk ƙoƙarin ki Asmy? Amma bai kyauta miki ba." "Wallahi na yi kuka da zaginsa yafi sau nawa." "Ki yi haƙuri rabon zamu ƙara ganin juna ne." "Haka ne wallahi dana ganki dai na ji makarantar ta yi mini daɗi." "Dariya ta yi tare da rungume ta."Wallahi I couldn't forgot those day memorable kenan." "Sosai wallahi don ma kin haɗu da Nasreen sai kika share mu." Gabanta ya faɗi jin abin da ta ce,"Allah Sarki, Nasreen ai kamar 'yar'uwa na ɗauke ta sai ga shi ƙaddara ta raba zumuncinmu." "Sosai lamarin bai yi daɗi ba. Ina Ya Damir amma yanzu ya manta komai?" "Sosai ya dawo kamar da dama zafin mutuwa ce." "Wallahi ai yana ƙaunar matarsa sosai kowa ya sani." "Haka ne Allah ya saka masa ya jiƙanta." "Amin," Ta ce tare da kallonta ta furta,"Kamar kin gama lecture ko zan fita dake ne?" "Da kin kyauta wallahi saboda na gaji." Jin abin da ta ce sai ta fara tafiya zuwa motar ta suna hira. Sun shiga cikin motar ta fara tuƙawa. Waiwawoya ta yi ta kalle ta."Na san cewa Nasreen tana cikin farinciki, Ƴaƴanta Ahmad ya raba aurenta da ɗan iskan mijinta Faruk. Wataƙila lokacin ku kammala makaranta ta canza ta yi ƙiba?" "Allah Sarki ba ki da labarin abin da ya faru?" Cikin razana ta yi ƙoƙarin taka burki tana kallonta.Mai ya faru?" "Ai ba ta rabu da Faruk ba har muka gama makaranta." Tsananin mamaki ya kamata jin abin da ta ce."Saboda me bayan na mu bar ƙasar ya ce zai yi masa hulɗi." "Hmmm! Bayan tafiyarku aka ne ni Ahmad aka rasa har muka kammala karatu bai dawo ba, wannan dalilin mahaifin ta ya tilasta mata ko....." "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta fira sai kawai ta fashe da kuka. "Ban gane an nemi Ya Ahmad an rasa ba? Kina nufin live bayan tafiyarmu ba a ga Ya Ahmad ba?" Yadda ta fita hayyacinta, tana kuka tana tambayarta ya sanya ta yi dana-sanin gaya mata. "Don Allah Marwana ki faka motar nan, sai na yi miki bayani karki kashe mu." Ta furta cikin tana tana hawaye. Da ƙyar ta yi nasarar gangara ta yi parking."Don Allah ki gaya mini da gaske Ya Ahmad ya ɓata?" "Wallahi an neme shi an rasa kuma har muka gama karatu ba a gan shi ba, saboda har jaje muka je mata, domin ta yi kamar za ta zauce. Rashin ganinsa mahaifinta ya tilasta mata ta koma. Har muka kammala karatu Nasreen tana da aure, kuma kin ga ni ban je service ba, wataƙila da na gan..." "Wayyo Allah! Haƙiƙa Nasreen kina ganin jarrabawa. Anya ba Faruk ya ɗauke shi ba? Domin ba abinda imani zai iya." "Hakan zai iya yiwuwa saboda mutum mugun icce ne. Ni dai sauke ni anan zan ƙarasa, saboda ban shirya mutuwa ba." Ta ce tare da buɗe motar ta fita. Tana fita ta kece da kuka sosai. Kuka take yi tana tunanin halin da take ciki na rashin Ahmad. Zuciyarta ta karaya da tausayinta, har ta ji ba za ta iya biyayya ga Mommy ba da ta yi mata tsakani da ita. Ba tare da dogon tunani ba, ta fi motarta cikin tashi hankali zuwa gidan Faruk. "A wannaan karan Mommy ki yi haƙuri zan saba wa umurninki. Sai na cike gurbin Ya Ahmad. Zan tsaya mata na maka Faruk a kotu." Tafe take tana sumbatu kamar sabuwar kamu har ta isa get ɗin gidan. A lokacin da ya isa sai ta yi parking a ƙofar gidan ta fito. Ta ɗan ɗauki lokaci tana tunanin ƙwakwansa gidan. Tsoro take ko Faruk zai fito ya yi mata tijara. Kusan 'yan sakanni ta ɓata tana tunani, kafin ta yi namijin ƙoƙarin ta fara buga get ɗin gidan. A lokacin da ta ƙwankwasa Rashida ce a falo tana zaune tana kallo. Miƙewa ta yi ta je ƙofar gidan ta buɗe. Ganin mace 'yar gayu sai ta ba ta hanya ta shiga cikin gidan. Kallo Marwana ta yi mata tana ƙoƙarin danne dariyar da take sin kubce mata. Tuni ta raina abin Faruk ganin matar da ya aura. A tunaninta za ta girme shi ko su zo tsara. "Mu shiga ciki." Ta ce mata duk da bata taɓa ganin ta. Babu musu ta bi bayanta har zuwa cikin ɗakin tana raba idanu. "Baiwar Allah daga ina?" Ta ce mata ganin ta mayar da hankalinta cikin gidan, burunta ta yi idanu biyu da Nasreen ko yaranta. "An sorry, Nasreen na zo nema Ummu Raihann." Jin abin da ta ce sai ta ɓata fuska ta ce,"Yaushe rabon duniya da ayyaraye, hala kin yi tafiya ne?" "Eh, mun fita waje ne." Tana ƙoƙarin bata amsa sai kawai Faruk ya fito daga cikin ɗakinsa. Ganinta ya sanya zare idanu yana kallonta. Yadda ya kalle ta a wulaƙance ya ce,"Uban me ya kawo ki gidan nan?"Ya tayar da hankalinta. Miƙewa ta yi tana kallon sa,"Ba faɗa ya kawo ki ba, gurin Nasreen na zo." "Gidan ubanki ne za ki shigo kai tsaye?" "Ba zan ɗauki rashin mutunci ba duk da gidanka na zo." Ta ce tare da miƙewa ta rataya jakarta "Fita daga gidan nan mara mutunci kin san yadda na tsane ki?" "Farouk, ka santa ne?" Rashida ta yi mata tambayar ganin yadda ya harzuƙa. "Ita ce ƙawar Nasreen wacce ta lalata mata rayuwa, ta mayar da ita mai ƙwaɗayi har ta raina ni. Ita ce wacce ta sanya ɗan iskan ƴaƴanta ya ba ta jini aka sanya wa matata da aurena." Jin abin da ya ce sai ta ɓata fuska ta koma ta zauna."To kuma mene na damuwa bayan ka rabu da ita?" Ta ce masa cikin gatsali. Marwana jin abin da ta ce ba ta san lokacin da ta saki murmushin farinckin ba."Alhamdulillah! Allah na gode maka da wannan azzalumin ya rabu da Nasreen." Ta ce cikin farin ciki. Jin bin da ta faɗa sai ya harzuƙa ya yi kanta."Fitan mini a gida, tun kafin zuciyata ta sanya na kassaraki. Ki fita wallahi xan iya ɗaukar ranki." "Zan fita saboda yanzu babu abin da zai ƙara haɗa ni da kai. Allah zan godewa da ya gabata da mugun miji kamarka, kuma sai ka yi dana-sanin ƙuntata mata da kayi." Cikin tsananin ɓacin rai ya nufota yana kumfar baki. Ganin zai iya dukanta ya sanya ta fita da sauri." Da ki tsaya ki ga yadda zan illata ki." Har ƙofar gida ya biyota yana zaginta da jawo mata alkaba'i iri-iri. Marwana ba ta tanka masa ba ta fara ƙoƙarin shiga cikin motarta. Matuƙar farinciki take ji saboda ya sake ta. Sai da ta bar ƙofar gidan sannan ya koma yana zaginta. Har ta wuce gidan Maman Muwaddat sai kuma ta dawo ta tsaya, ganinta ta fito tana ƙoƙarin kulle gidan za ta fita. Da sauri ta kashe motar ta fito so take ta tambaye ta, domin ta san cewa ba zata rasa sanin gidansu Nasreen ko labarin, inda take ba tun da maƙota suke. "Ni fa kamar na sanki?" Maman Muwaddat ta ce tana ƙoƙarin son tuna inda ta santa. "Ayya da wu..." "Marwana." Ta furta tare da nuna ta da yatsa cikin tsananin farinciki. Kallonta ta yi ta kasa cewa komai tana mamakin inda ta santa. "Don Allah kece?" Ta yi mata tambayar kamar za ta shiɗe. "Ni ce." Jin abin da ta ce sai kawai ta rungumeta."Wallahi ita ce dole na gane ki, saboda Nasreen duk ta shigo cikin gidana sai ta nuna mini hotonki har kuka take yi." "Allah Sarki," Ta furta tare da share hawayen da suka zubo mata sai kuka ta ce,"Sati ɗaya da dawowa daga waje, sai na je makaranta na haɗu da maye ɗina, na tambayeta Nasreen take gaya mini ba su rabu ba, saboda Ya Ahmad ya ɓace." Ta ƙarashe maganar cikin hawaye. "Allah Sarki! Labari mai tsawo ba su rabu ba, a wannan lokacin amma yanzu ya saketa. Mu je na kaiki gidan su Nasreen." Ta ce tare da kama hannunta cikin tsananin farin ciki. Babu musu suka shiga cikin mota ta ja motar. A hanya duk ta ƙosa ta yi toxali da Nasreen. Tsananin mamaki ya kamata a lokacin da suka shiga wata unguwa ta talakawa sosai. Ta kasa daurewa har sai da ta biyo ta kalle ta. "Eh, nan za ki shigo da motar na ki lungu ne, ki yi a hankali karki faɗa cikin kwalbati, musamman da an yi ruwa." Ta ce mata tana nuna mata inda za ta bi. "To,"Ta ce a zuciyarta tana mamakin nanne gidan su. "Anan ta yi rayuwa Faruk ya aure ta?" Ta yi ma kanta tambayar tana mamaki tare da gane dalilin da ya sanya ya rainata kuma ya raina mahaifinta. Da ƙyar ta samu ta yi parking don har sai da ta zurma cikin kwata."Oh kin ga dai duk gudun da muke yi kar ki faɗa, sai da kika faɗa." "Wallahi kuwa bari na yi parking kawai in za mu tafi sai mu nemi yara su fitar mana." Ta ce tare da fita daga motar burunta kawai ta yi toxali da Nasreen. "Ok, to mu shiga ciki." Ta ce mata tare da nuna mata wani gida da babu ƙafa sai buhu aka sanya aka kare gidan. "To,"Ta ce tare da satan kallon gidan tana mamaki sosai. Da sallama suka shiga cikin gidan. Babu kowa a tsakar gidan sai hayaniya da yake tashi a cikin ɗakunan. Sai da Maman Muwaddat ta ƙara sallama sau biyu a ƙofar ɗakin Mama, sannan Mama dake zaune kan ƙaramar kujerar ta amsa. "Shigo kamar muryar Mama Muwaddat?" "Ni ce Mama baƙin yamma ku ka yi." "To shigo sannu da zuwa." Ta ce mata daidai lokacin da ta buɗe ɗakin tare da sallama. Amsa sallamar ta yi idanunta na kan Marwana tana son gane fuskar."Nasreen, ki fito Maman Muwaddat ce." Amsawa ta yi ta ce,"Gani nan Mama, ina canzawa Musaddik kaya ya jiƙa su." "To," Ta amsa tare da kawo musu ruwa. Ganin Maman Muwaddat ta ɗauki ruwan tasha, ya sanya ta ɗauka ta ɗan kurɓa sannan ta ije. Tana kallon gidan yayin da matuƙar tausayin Nasreen yake ƙara shiga cikin zuviyarta."Ashe haka suke cikin ƙangin talauci? Shi ya sa Faruk yake wulaƙanta ta, saboda ya san cewa rayuwar gidansa, tafi na gidan su. Da yake mahaukaci ne bai san Allah yake azurtata ba?" Ta yi ma kanta tambayar daidai lokacin da ta fito tana faɗin,"Yar halak kin ƙi ambato. Dama yanzu na gama maganarmu ya kamata na tura miki kuɗin hijaban, jira na ke a yi mana albashi, saboda na taɓa kuɗin na kai Musaddik asibiti." "Ai ba shi ya kawo ni ba don na zo miki da da abin da yafi..." "Mene?" Ta ce tana shaƙar ƙamshin da take jin kamar ta san mai shi. "Kalli wacce take gefena." Ta ce ta tana nuna Marwana da fuskarta ya kike da hawaye. A hankali ta ɗaya idanunta tana tunanin wacce take gefenta, domin sam ba ta lura da kowa ba. Idanuwansu ya tsarƙe da na juna. Kasa cewa komai ta yi har na tsawon lokaci cikin tsananin mamaki. A hankali ta yi nasarar buɗe bakinta cikin rawar murya ta ce,"Marwan..." Ta furta sai kawai ta kasa ƙasarwa ta tsaya tana kallonta kamar kungi. Mamaki da al'ajabi ya kamata domin ba ta taɓa tunanin ganinta ba, ta ɗauka ita da ganin ta har abada. Marwana miƙewa ta yi tare da ware hannunta sai kawai ta faɗa suka fashe da kuka."Ashe dama Idanuwsa za su ƙara toxali da ke Marwama? Ashe zan ƙara ganinki a cikin duniyar da kewarki da ya Ahmad suka cika zuciyata?" Na yi kewar rashinki na zubar da hawaye har sai da na ga cewar hakuri she ya zamar mini dole. Hotonki da na Ya Ahmad su suka zama abincin idanuna a duk lokacin da na tuna ki." Sai ta ƙarshe maganar tare da ƙara rungumeta tana kuka. Kuka suke yi sosai kamar ransu zai fita. Har sai da Maman Muwaddat ta ga ba za su daina ba, sai ta kama su ta zaunar da su."Ba kuka za ku yi ba, godiya za ku yi ga Allah da ya ƙara haɗa fuskokin ku." Kara rungume juna suka yi suna hawaye."Ya Allah yadda ka nuna mini Marwana ka bayyana mini ya Ahmad." Ta ce tare da share hawaye ta ta riƙe hannunta kamar za ta ɓace mata. "Ashe zan ƙara ganinki?" Ta ce tana dariyar farinciki. "Na ji abin da ya faru dake Nasreen ki ci gaba da addu'a. Allah zai kawo miki mafita, kuma zai bayyana mana Ya Ahmad. Na ji duk abin da ya faru Asmy ta gaya mini. Da na je gidan Faruk ya yi mini rashin mutunci." Murmushi mai ciwo ta yi."Zai yi miki fiye da haka, saboda ya tsani duk wanda ya sanni. Ballantana ke da ga lamarin da ya faru." "Ni fa ina zargin shi da sace..." "Farouk ba zai sace Ya Ahmad ba, saboda na san halin abinnda zai iya. Farouk ba ya ƙaunata ba zai taɓa sace Ya Ahmad ba, don na koma rayuwarsa. Akwai dai abin da ya faru Ubangiji kawai ya barwa kansa sani." "Allah ya bayyana mana shi." "Amin," Ta furta tana kallon ta. Sun kasa ɗauke idanunsu a kan junansu sai murmushi suke yi, idanunsu na cikin junansu, suna sakar wa junansu murmushi tamkar wasu sabbabin masoya. "Ina Mommy da Little Marwana?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin farin ciki. Marwana fuska ta haɗe kadan jin ba ta ambaci Damir ba, domin a tunanin ta shi za ta fara tambaya. "Ba zan gaya Miki ba domin ba su ya kamata ki tambaya ba." "Ki yi haƙuri Ya Damir ko?" Ta yi mata tambayar yayin da zuviyarta ta yi wani irin bugu. "Yes," Ta ce tare da ɗaya mata gira. "Yana lafiya? Fatana ya manta mugun dafin da bar masa na..." "Kar ki tuna lamarin domin Ya Samir ya manta komai ya ci gaba da rayuwarsa, abu ɗaya ya koya bayan rasuwar ta." "Mene?" Ta yi tambayar cikin sanyi murya. "Masifa he is very strict." Ta ƙarshe maganar tana murmushi. "Allah Sarki Allah ya sanyaya masa zuciyarsa." Ta ƙarashe maganar tare da zubosar hawaye na tausayinsa. Dariya ta yi tare da ɗauke hawayen da yatsa."No, kar ki yi kuka ai tun da kika rabu da Faruk a rayuwar ki, kin daina kuka. Yanzu za ki yi farinckin ki kwantar da hankalinki ki samu aiki za ki ga namijin da zai zo ya aure ki. Faruk sai ya raina kansa." "Ba zan yi aure ba na haƙora zan raini yarana." "Za ki yi aure Allah zai kawo miki miji na gari." Marwan ta ce tare da kama hannunta. Hira suke yi cikin tsananin farinciki wani su yi dariya wani kuka. Marwan ta dade sosai a gidan. Nasreen ta rasa inda za ta sanyata. Ita gani take yi kamar wasa wai yau Marwan ta zo gareta. Sun jima sosai har sai da dare ya yi sannan ta yi mata sallama, tare da alƙawarin za ta dawo. Maman Muwaddat ta mayar gida sannan ta koma gida. A zuciyarta tana tunanin yadda zata shawo kan ajalinta su aminta ta koma rayuwarta, don yanzu ne take buƙatar taimakonta. Yanzu ya kamata ta tallafa wa rayusarta saboda rashin Ahmad, ta zama wata ana ta yadda Faruk zai gane kuransa, amma to ta yaya? Bayan danginta sun tsane ta."Gabanta ne ya yi mummunar faɗi tuna mummunar lafazin da Mommy ta yi mata. Da dadddare da ta zo bacci ta kasa saboda Nasreen da take gani da yanayin rayuwar da take ciki. Ta shi ta yi ta zauna a tsakiyar gado. Barka da sallah fans ɗina ina yi muku Barka da sallah tare da fatan Allah ya karbi ibadunmu. Sai na zo muku yawon sallah. Tamu Jamila lawal Zango Jamsy❤️❤️❤️❤️❤️🙏🙏🙏💃💃 Nasreen, Damir, Marwana, har ma da Faruk capacity yana muku barka da sallah. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 17 Da dadddare da ta zo bacci, ta kasa saboda Nasreen da take gani da yanayin rayuwar da take ciki. Ta shi ta yi ta zauna a tsakiyar gadon, hawaye tana bin ƙuncinta. Har cikin zuciyarsa take son taimaka mata. Allah ya ga zuciyarta na son taimakon da take son ta yi, don haka za ta bijirewa umurnin Mommy, don Allah zai fahimci ninyarta. Wani irin sonta a da ƙaunarta, ya ƙara shiga cikin zuciyarta fiye da yadda take ƙaunarta. Washegari da ta tashi ta yi wanka ta shirya. Sallama ta yi wa Mommy za ta tafi makaranta. Mommy na zaune a cikin ɗakita da waya tana dannawa. Ganin ta shigo da sallama ya sanya ta ije wayar. "Yauwa Marwana, dama ina son magana dake." "To Hajiyata." Ta ce tare da zama a gefen ta tana matsa mata ƙafafunta "Yayanki ya gaya miki ya kamata ku je gwajin jini da Ashaman?" "Eh, ya gaya mini kuma shi ma ya gaya masa. Weekend ɗin nan ya ce zai zo." "Ok, Allah ya kaimu." "Amin," Ta amsa cikin jin kunya. "So na ke na kira Hajiya A'isha, yarinyarta Shufa'a na ke son na yi mata magana Yayanki ya aura." Wani irin faɗuwar gaba ta ji har sai da fuskarta ya nuna."Hajiya, kin yi masa magana ne? Kin san halin Ya Damir.." "Sai na yi masa zan haɗa auren, in na biye masa kina ganin zai yi aure? Ba zan gaya masa ba, sai magana ta kankama sai na ce ya je ya ganta." "Da kin yi masa.." "Ke tafi ki ba ni guri ni na haife shi ko shi?" Ta daka mata tsawa tana faɗin hakan. "Allah ya ba ki haƙuri." Ta ce tare da ficewa cikin ɗakin hankalinta a tashe. Kai tsaye mota ta nufa bayan ta buɗe ta shiga. Zama ta yi tana jin yadda kanta ke juyawa. "Mai ya sa ba ke jin kamar akwai wata alaƙa da za ta ƙullu da Damir da Nasreen?" Ta yi wa kanta tambayar cikin ruɗani, jin abin da Hajiya ta ce. "To, in haka zai faru ta yaya?" A wannan karon tashin hankalinta ya fi na ko yaushe tuna abin da ya faru. Cikin sanyin jiki take tuƙa motarta. Kai tsaye kasuwa ta wuce ta siya kayan abinci da yawa. Gidan su Nasreen ta je a lokacin tana zaune a tsakar gida Raihann a kan cinyarta tana mata tsifa. Ganinta ya sanya ta sauke ta tare da nufarsa cikin tsananin farinciki."Jiya na kasa bacci ina ta tunanin ki Nasreen." Dariya ta yi jin abin da ta ce."Ni ma jiya bacci ɓarawo ne kawai ya sace ni, saboda na cire tsammanin dawowarki cikin rayuwata." "Allah ya haɗamu shi ya san dalilinsa." Ta ƙarashe maganar hankalinta na gurin Raihan da ta riƙe hannunta. "Haka ne." Nasreen ta ce sannan suka shiga ciki. Cikin girmama ta gaishe da Mama. Bayan sun ɗan jima suna hira ta miƙe,"Zan je school, in sha Allah zan dawo ba da jimawa ba, sannan akwai kaya a motata ko za ki sanya yara su kwaso." Jikinta ya yi sanyi jin abin da ta ce,"Marwana, ba na..." "Please, don Allah kar ki ce komai ko tuna abin da ya faru." "Yarinya dole ne saboda rabuwar rashin mutuncin da aka yi, kuma mahaifinyarki ta yi miki mummunar lafazi, bai kamata ace kin ƙara shigo rayuwarmu ba." Murmushi ta yi tare da ƙarasawa gurinta."Kar ki damu Mama, Ubangiji ya ga zuciyata na don taimakawa, kuma shi zai kawo mini mafita." "Allah ya yi miki albarka." Ta furta tana mamakin kirkinta. "Amin,"Ta amsa sannan suka fita waje. Ganin kayan da ta kawo mata ya matukar razanata. Kallonta take yi cikin tsananin mamaki."Kina da kirki ban taɓa ganin mutum mai kirki da son talaka ba, irin ki. Haƙiƙa zuciyarki daban take da sauran masu hannu da shuni." "Akwai banbanci a tsakaninmu ne? Ubangiji bai bambanta mu ba, sai ta gurin ibada." "Na gode Allah ya saka da alkhairi." Ta ce tare da rungumeta tana murna. A lokacin da aka fara shiga da kayan, Baba ya fito ya tsaya yana kallon ikon Allah. Babu kunya ya fara murna yana jin kamar zai sume. Zama ya yi yana kallon kayan sai kuma ya fice zuwa waje. Marwana tana ƙoƙarin tayar da mota ya ƙaraso. Addu'a ya shiga yi mata mai kama da roƙo. Kallonsa take yi tana jin sam ta tsane shi, amma saboda Nasreen ta cire dubu goma ta ba shi. Kamar zai goyata haka ya rinƙa godiya ya shiga ciki. "Kina ganin abin da yake miki ko? Fiye da hakan ya rinƙa yi wa Faruk a lokacin da ya zo neman aurena. Baba shi ne silar da mutuncina ya zube, kuma ya wulaƙanta rayuwata." "Haƙiƙa bai kamata ya zama uba ba, amma ki ɗauki hakan a matsayin ƙaddararki." "Babu komai na ɗauka, domin ni musulma ce, kuma na yi imani da ƙaddara." Ta ce tare da share hawayenta. "Saura wata biyu ki gama service ko?" "Eh,"Ta amsa tana kallonta. "Allah ya ba da sa'a." Ta ce mata tana mata murmushi a zuciyarta ita kawai ta san abin da take tsaƙawa. "Amin,"Ta amsa tana mayar mata da murmushin. Sai da ta bar ƙofar gidan, sannan ta juya ta shiga ciki gidan. Tana jin ta kamar 'yar'uwarta na jini. Tana shiga cikin gidan, ta samu Baba ya zauna kan kayan yana ta zuba."Yauwa Nasreen, na tsare miki kayan ne, kin san gidan nan kamar 'ya'yan ɓera suke yanzu sai ki zo kiga an iba." "Yaranka kake kira 'ya'yan ɓera? Anya kana neman musu shiriya kuwa?" Goggo ta furta tana kallon sa. Ba tare da ya ce mata komai ba ya zabga mata harara. Jikinsa har rawa yake yi yana kallon kayan "Nasreen, ko zo ki bani nawa kasan ɗaki za ki shiga?" Ya ce mata ganin yadda ta sha kunu za ta wuce. "Mama, za ta raba kayan." Ta ce tare da shiga cikin ɗaki, ba ta ji mai ya faɗa ba. Mamakin yadda ya yi mata maganar cikin taushi ta yi. "Shege ɗan iska Faruk, dole hankalinsa ya tashi ganinta da waɗannan yan gayun, ashe dama mutanen da take tarayya da su ba ya so, sun fi shi arziki?" Babu wanda ya tanka masa. Ganin haka ya sanya hannu ya ibi kayan da yake so ya shiga ciki. Mama ce ta kwashi sauran kayan, ta kai ɗakinta a ranta tana takaicin halinsa. Duka mutanen gidan zaune a dinning suna karyarwa. Damir hankalinsa a kan Little Marwana da take shan tea. Kallonta yake kamar ya lashe, musamman yadda ya ga ta ƙara girma. "Damir, maganar Ashman da aka yi na gwajin jini kamar gobe zai zo ko?" "Eh, Mommy ya sanar mini." "To ina so da zarar an kawo gwajin sai a gaya wa iyayensa su turo." "In sha Allahu." Ya ce tare da tura wainar ƙwai a cikin bakinsa. Ta ɗan saci kallonsa tana tsoron abin da za ta gaya masa, sai kuma ta daure ta ce,"Ka san yarinyar Hajiya A'isha?" Gabansa ne ya faɗin ganin yadda ta maida hankalinta kan zancen tana kallonsa."Eh, ƙanwar Moh?" "Ita fa yarinyar ai tana da hankali da kyau?" Jin abin da ta ce sai ya kalle ta, ya dakata da cin abincin ba tare da ya ce komai ba, sai kuma ya daure ya ce,"Mommy, tun da Batula, ta mutu har yau ban ga mace mai hankali da natsuwa kamarta ba." "Ina maka maganar rayyaye kana mini na matacce. Da zarar na yi maka magana, sai ka kawo mini ita. Tsawon wane lokaci, za ka ɗauka kana tunaninta?" Ransa ya ɓaci sosai jin abin da ta faɗa."Yanzu Mommy, har kin manta da ita kina danganta ta da matacciya?" "Tana da rai ne? Ta riga ta mutu Damir dole za ka manta da ita ka auri wata." Ta ƙarashe maganar cikin tsananin fusata. "Ba zan iya ba Mommy, saboda na riga na yi mata alkawari, kuma babu macen da zan iya so..." "Zancen banza!" Ta daka matsa tsawa da ya sanya shi miƙewa a razane yana kallonta. "Matuƙar ina raye wallahi sai ka yi aure, na yi maka umurnin ka je ka ga yarinyar saboda tare na ke son na haɗa bikinka da na Marwa.." "What?" Shi da Marwana suka zare ido tare da haɗa baki gurin faɗin haka. "No, Mommy, gaskiya ba zai aure ta ba, saboda sam ba kalar sa ba ce." Marwana ta furta zufa na keto mata, domin zuciyarta akwai wacce take son ya aura. "Don ƙaniyarki uwar wa kike so ya aura? Kin kashe masa mata so kike ya ƙare da rayuwar sa a haka?" Mommy ta furta cikin zafi tare da jefa mata filet. Da sauri ta fice fakon ganin za ta illata ta. "Ba zan iya auren wata 'ya mace ba, don haka ki janye maganar matukar ba so kike na aikata abin da zai kawo miki matsala da iyayenta ba." Ya karashe maganar tare da kwashe tarkacensa zai fice. Ganin haka ta miƙe tana faɗin,"Dole za ka auri yarinyar nan, a matsayina na mahaifiyarka na yi maka umurni da ka je ku sasanta kanku." "No, Mommy, impossible!"Ya ce tare da ƙarashe ficewa. Mommy ranta ya ɓaci ji ta yi kamar ta rufe shi da duka. Faɗa sosai take yi Muhsin yana ba ta hakuri. Ganin yadda shi kansa ta rufe shi da faɗa, kamar shi ya aikata laifin, sai Marwana ta shige cikin ɗakinta. Safa da Marwa take yi tana tunanin mafita. "Ina wallahi Ya Damir, ba zai aure ta ba, saboda akwai macen da ta fi dacewa da shi." Ta furta tana zagaye ɗakin. Damir kuwa cikin tsananin tashin hankali ya isa cikin motarsa ya fige ta. Yana zuwa ofis ya shige ya kulle kansa."Ba zan iya auren wata bayan ita ba, mai ya sa Mommy take son sanya ni cikin damuwa?" Ya ce cikin damuwa yana kai wa bango naushi. "No, Batula kar ki damu alƙawarin da na yi miki zan cika shi." Ya ce tare da ɗaukar fayal yana dubawa. Ganin ba ya fahimtar komai, sai ya ije kawai ya jingina da kujerar da yake zaune yana tunani. Muhsin ya yi sallama ya shigo. Jin muryarsa ya amsa ba tare da ya buɗe idanunsa ba. "Please Yaya ina son magana da kai." "Then go ahead." Ya ce masa yana duba takaddun da ya shigo da shi. "Kan maganar da Mommy ta gaya maka, You need to do something. Dole ka yi aure saboda ni kaina ina jiran ka yi sai n.." "Na hana ka ne? Kana gani matata na rasa, amma shi ne take gaya mini ta zaɓa mini mata." "Saboda kana buƙatar aure sannan little Marwana tana buƙatar." "No, we are ok, I can take all the responsibility of her." "No Yaya kana buƙatar wasu yara..." "Please, Muhsin go don't provoke me." Ya ce tare da ɗaga masa hannu. "You need to sleep on it." Ya ce sannan ya fice daga cikin ofis ɗin. Tsaki ya yi tare da miƙewa yana zagaye cikin ofis ɗin. Wayarsa ta yi ƙara alamun shigowar tsako, da sauri ya duba. Ganin Mommy ce take jaddada masa kar ya sake ya dawo ba tare da ya je ba, sai jikinsa ya yi sanyi. Wata dubara ta faɗo masa tun da ba zai iya ƙin bin umurninta ba. Sai da ya kammala aiki sannan ya tafi gidan. Tun a hanya ya canza fuskarsa ya haɗe rai. Da ya yi hon maigadi ya buɗe masa ya shiga. Shufa'a cikin kwarkwasa ta ƙaraso girinsa tana jin kamar za ta sume, wai yau ita Damir zai aura. "Barka da zuwa." Ta ce masa tare da ƙarasawa gurin da ya faka motarsa ya ƙi fitowa. Banzan kallo ya yi mata ba tare da ya amsa ba. Jikinta ya yi matuƙar sanyi, ganin yadda yake kallonta kamar ya ga kashi."Ummana ta je ta shigo ciki ka ci abinc.." "Na yi miki kama da mai ciwon yunwa ne?" Tambayar da ya yi mata cikin faɗa ya sanya ta zare ido. Jikinta ya fara rawa ganin yadda yanayinsa yake. "Ka yi haƙuri." Ta ce tare da matsawa tana kallonsa. "To ba cin abinci ya kawo ni ba, na zo na yi miki kashedi da kar ki kuskura ki aminta da aure a da ake son yi miki, saboda bayan Batula babu macen da zan iya so. Kuma ina son ga gaya miki karki yadda a ba ki mahaukaci, saboda na haukace na zama kurma, in har kika ce sai kin aure ni sai na kashe ki, duk ranar da kika ce zaki taɓa jikina. Komai nawa nata ne ita kaɗai babu wata mace da za ta mallake su bayan ita." Ya karashe maganar yana matsota tana matsawa. "Da fatan kin ji sharaɗin da na yi miki?" Ya tambayeta yana zare idanu. "Eh, na ji kuma zan gaya musu bana sonka." Ta faɗa cikin rawar murya da sauri. "Good girl." Ya ce yana shafa sajensa, bayan ya sakin murmushin mugunta ganin yadda ta ruɗe. Da sauri ta ruga da jiki ta fashe da kuka. Dariya ya yi ya shige motarsa ya tafi. Tun a hanya Mommy take ta kiran wayarsa cikin tsanannin ɓacin rai. Sanin abin da ya aikata sai ya ƙi ɗaukar wayar. Texts ta yi masa amma bai ɗauka ba. Ganin haka ta zauna kan kujera tana cika tana batsewa. Tana zaune ya yi hon maigadi ya zabura zai buɗe masa. Da sauri ta tashi za ta je waje ta same shi, sai kuma ta ga rashin dacewar haka. Zama ta yi tana cika tana batsewa, har ya buɗe ƙofar da sallama ya shigo."Yanzu abin da ka yi ka kyauta?" Ta yi masa tambayar tamkar za ta buge shi. "Na gaya miki ba zan iya auren ko wace 'ya mace ba. Ki yi haƙuri kawai Mommy..." "Wallahi ba ka isa ba, dole ka yi aure sai na ƙara nema maka wata matar, kuma in har ka ƙara kuskuren abin da ka aikata sai ka gwammci kiɗa da karatu." Ta ce masa daidai lokacin da ya shige ciki ba tare da ya ce mata komai ba. A ranar da Ashman da zo suka je gwajin jini. Zuciyoyinsu cike da ɗari-ɗar na sakamakon gwajin. Cikin rashin sa a likita ya tabbatar musu da ba za su iya aure ba, sakamakon dukanninsu A.S. Nan take Ashman ya yanke jiki ya faɗi. Marwana kuka take yi sosai tana tausayin halin da za su shiga, domin suna matuƙar son junansu. Da ƙyar iyayen Ashman suka yi nasarar shawo kanshi ya haƙura, amma da ya kafe sai ya aure ta. Marwan ta ci kuka sosai har ta godewa Allah. Nasreen ta kira tana kuka ta gaya mata. Hankalinta ya tashi sosai, musamman yadda ta san suna son junansu. Cikin damuwa da irin kukan da take yi ta sauke ajiyar zuciya tana hawaye."Ki yi shiru ki bar kuka ni ma za ki sani na yi kuka." Ta ce tana share hawayen da yake gangaro mata. "Dole na yi kuka ina son shi kawai a aura mini shi. Ina son shi ban damu ba da dole sai mun haihu ba." "Yara sune rayuwar aure ko da yanzu ba ki damu ba, nan gaba dole ki damu. ki yi haƙuri ki roki Allah ya kawo wanda za ki so shi kamar shi." "Babu shi Nasreen, ina matuƙar son shi, saboda he deserve to be my husband." "Allah ya san dalilin da ya raba ku, kuma zai ba ki wanda ya fi shi " Ta ce mata cikin kuka. Rarrashinta ta rinƙa yi ganin ta ƙi yin shiru sai ta buƙaci su haɗu. Saboda halin da take ciki direba ya tuƙa ta. Tana ganinta ta ƙara fashewa da kuka sosai. Ta jima kafin ta yi shiru sannan ta share hawaye ta. Sun daɗe tana ba ta baki kafin ta haƙura suka rabu. Mommy kuwa, ba tare da ta dandara ba ta ƙara nema masa 'yar ƙawarta, sai dai abin da ya aikata har yafi wancan, domin har sai da ya mareta a gidansu, ganin za ta yi masa kwarkwasa da fitsara. Rashin mutunci sosai mahaifiyarta ta kira ta yi ma Mommy. Ranta ya ɓaci amma babu yadda za ta yi haka nan ta daure. Yana dawowa ta sauke masa . Ba tare da ya kula ba har ta gaji ta haƙura domin babu halin duka. A ƙalla sai ta da nema masa 'yan mata biyar yana wulaƙanta su, da yi musu barazanar da zai sanya su ce ba za su aure shi ba. Ta yi fadan ta yi rarrashin, amma duk a banza tura agwagwa a ruwa, saboda har yanzu yana nan kan bakanshi na cika alkawarin da ya ɗaukar wa Batula. Daga ƙarshe fushi ta yi da shi mai zai fi, amma shi ma ba ta samu nasara ba, saboda kullum sai dai ya zo ya isheta da magiya, kuka yana nan kan bakanshi. Tafiya ce ta kama shi zuwa waje shi da Muhsin, sai ya ji daɗi sosai don zai huta da ƙorafin da take masa. Ganin da gaske yake yi, sai kawai ta nema masa mata aka fara shirye-shiryen aure. Ba tare da sanin sa har aka ɗaura aure. A ranar da ya dawo ta sanar masa.Hankalinsa ya tashi sosai. Tsananin mamaki ya kamata a lokacin da ta sanar masa da ta yi masa aure. Sosai yake hawaye ya ce,"Mommy, ko gafarce ni domin ba zan iya rayuwar aure da matar da kika aura mini ba, ki yi hakuri zuciyata b za ta iya zama da wata 'ya mace ba." "Dole ka zauna da ita maza ka je ga matarka." Tamkar kububuwa ya fice daga cikin gidan. Tuƙi yake da kyar ya isa gidan yana tunanin abin da zai yi mata. Ikram tana jin alamun shigowar motarsa ta mike tana son ganin angon na ta. Murmushi ta saki ganinsa cikin shiga mai kyau. Dama ta san shi sosai tuntini take fatan ya zama mijinta, amma ta san da wuya tun da ko kallon kirki ba ta taɓa samu ba. Ina yana tare da Batula ko iya kallon mace ba ya yi. Turare ta ƙara fesawa ta fito fili tana jiran ya shigo. Tana tsaye ya murɗa ƙofar ya shigo." To mijin marigayiya ko za a iya amarcin oho? In ana son na ci gaba da posting safe da yamma sai na ga ruwan comments. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 18 Turare ta ƙara fesawa ta fito fili tana jiran ya shigo. Tana tsaye ya murɗa ƙofar ya shigo."Sannu da zuwa babyna ya hanya?" Ta furta tare da isa gare shi za ta faɗa jikin shi. Mari mai kyau ya saukar mata tare da daka mata tsawa."Maza tattara komai na ki ki bar gidannan nan, sake ki saki uku, saboda ba da ra'ayina aka aura mini ke ba, kuma ba zan zauna da ke ba" Kuka ta fashe da shi jin wulaƙancin da ya yi mata."Sakina ka yi fa da aurenmu kwana uku?" "Ko yanzu aka ɗaura sai na sake ki!" Ya ce yana zare mata idanunsa, sai kuma ya ɗora da cewa,"Ma za kafin na fito ki tattara ki bar mini gidana, in ba haka ba na fito na ganki, sai na lahira yafi ki jin daɗi." Ya ce tare da haye wa sama. Cikin kuka ta ɗaga waya ta kira Mommy ta sa ta mata."Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Ya sake ki saki nawa?" Ta furta cikin tsanannin tashin hankali, domin ba ta taɓa tunanin zai iya sakin ba. "Saki uku fa ya yi mini lokaci ɗaya, wallahi na yi dana sanin yarda da na yi aka haɗa auren, ga shi zai ja mini zama bazawara." Ta karsshe maganar tana kuka mai sauti. "Ki yi shiru gani nan zuwa dole ya mayar da sakin ba uku ba. Mara mutunci kawai." "Ni kawai gidanmu zan koma, tun da ba ya sona sai ya kashe kansa ya je ya samu matacciyar matarsa, amma ba zan yarda ya wulakanta ni kan wacce ba ta raye ba." Ta ce cikin kuka tare da kashe wayar. Sororo ta riƙe wayar tana kallo jin yadda ta yi mata maganar. Ƙuta ta yi tare da miƙewa ta nufi gidan. Kamar ya san za ta zo. Ikram na fita ya kulle gidan zuwa gidan abokinsa kafin ta huce. Da ta shigo maigadi kawai ta samu, ya gaya mata da baya nan. Ta san cewa guduwa ya yi. Ciƙin damuwa ta rinƙa kiran wayarsa, ita ma a kashe. Kan dole ta haƙura ta koma gida. Rashin mutuncin da iyayen Ikram suka kira ta suka yi mata, ya ƙara tunzura ta. Ya yi ninyar gurza masa rashin mutunci in ya dawo, amma har sai da ta gaji ta yi bikonsa. Haƙura ta yi ta zuba masa idanu tana yi masa addu'a. Marwana hankalinta ya tashi lokacin da ta rinƙa tursasa shi auren, amma da ta ga ya ƙi zama da matar sai hankalinta ya kwanta. Yanzu ne za ta fito da abin da take ninyar yi, kuma tana fatan Allah ya bata nasara. Washegari da safe bayan ta tashi ta gama abin da za ta yi. Kicin ta shiga ta haɗa breakfast. Suna zaune a dining suna karyarwa ana hira. Ganin suna cikin nishaɗi sai ta yi ƙundumbala tana son ta fara aiwatar da ƙudurinta. "Ya Damir, kwana biyu ba kwa updating ɗina kame da activities na kampany?" "Kin san na yi busy, amma ai Muhsin yana ƙoƙari?" "Ni ma wallahi ban gaya mata ba, saboda na ga tana faɗin mu yi komai." "Yanzu I need to know everything." Ta ce tare da saka loma fuskarta a ɗaure. Gabakiɗaya suka bita da kallon mamaki jin abin da ta ce,"Lafiya kina zargin wani abu ne? Ko kuɗi kika nema aka hana ki?" Muhsin ya ce cikin ɗaga murya. "No, kawai ina son na rinƙa sanin komai, ko laifi ne?" "A,a kai Muhsin ka rinƙa ba ta update, dama ita ce ta ce ba ta buƙatar haka, tun da yanzu ta girma tana so babu laifi." Cewar Damir yana kallonsa. "Ok," Ya ce tare da gallah mata harara, don ya san wata rigamar za ta ɓallo ƙila abu take son a siya mata. "Yauwa game da appointment an ɗauka ne recently?" Ta ƙara tambayar da ya sa suka ƙara mamaki. "Eh, guda goma yanzu muna son mu ƙara ɗaukar uku." Damir ya ce mata yana kallon Hajiya da ta tsaya da cin abincin tana kallonsu. "Na gane to ina son a ba ni ɗaya." Ta daure ta furta zuciyarta na lugude, cike da tsoron ruwan da take son ɓallowa. "Mai za ki yi da shi?" Muhsin da Hajiya suka haɗa baki gurin fadi. "Zan bawa wata ce, saboda duk suna kawo waɗanda suka ga dama, amma babu wanda na taɓa kawo wa." Damir da ya gama fahimtar inda take son zuwa. Tuntuni da ya ji ta yi maganar ya san akwai abin da take so, amma bai yi tunanin aiki za ta nema wa wata ba. Tunanin wacce za ta ba wa yake yi. "Wace ce za ki bawa aikin?" Hajiya da Muhsin suka tambaye ta. Satan kallonsu ta yi, ganin yadda suka mayar da hankalinsu kanta. Jikinta ne ya fara rawa, har ta ji tamkar kar ta furta wacce take son ba ta aikin, amma kuma tuna matsoraci ba ya zama gwani, sai kawai ta yi namijin ƙoƙari ta kawar da tsoron cikin dakuwar zuciya ta ce,"Nasreen ce." Gabakiɗaya suka mike suna kallonta."What?" Suka haɗa baki gurin faɗin haka. Ganin yadda suka tayar da hankalinsu kamar wacce ta gaya musu ta yi kisa, sai ta daure cikin rashin tsoro ta ce,"Nasreen, ƙawata wacce kuka sani, ita na ke son na wa aikin, saboda tana buk..." Kafin ta ƙarashe Mommy ta ɗauke mata mari."Ashe dama kina tare da wannan yar iskan yarinyar da ta wargaza mini farincikin yarona, kuma ta hana shi aure? Duk da irin mugayen kalaman da na yi miki?" Ta ƙarashe tambaye cikin tsananin ɓacin rai. Dafe ƙuncinta ta yi tana hawaye ba tare da ta amsa mata ba, saboda marin ya shige ta, sai kuma ta ce"Am sorry to say mommy duk abin da za ki yi mini ba zan iya rabuwa da ita ba, saboda she needs help Yayanta ya ɓata mijinta ya sake ta ya barta da yara guda biyu, babu cinsa bare kulawar makarantarsu ko magani. Kowa ya san yadda a mace bazawara take fama da wahala a duk lokacin da namiji ya saketa ya barta da yara. Nasreen tana cikin rayuwa na wahala, iyayenta basu da shi, kuma Allah ya haɗata da azzalumin namiji da ya barta da wahalar yaransa. Babu ƴaƴanta Ahmad a duniya. Ni kuma Allah ya sanya mini sonta ba zan iya ganinta cikin mawuyacin hali ba. Ki gafarce ni saboda tun ranar da na dawo na ga halin da take ciki, na ci gaba da ba ta taimakon da na saba. Ina so ta ina jinta kamar 'yar'uwa ta wacce kika Hai..." "Rufe mini ba ki shashashar banza! Kin ji na rantse sai kin rabu da yarinyar nan.". "Ba zan iya ba Mommy ba zan iya ganinta a cikin wani yanayi ba, na ɗauke kaina. Zan zame mata bango na maye gurbin ƴaƴanta Ahmad." "Idan na ce ki zaɓi daya daga cikin ni da ita fa?" Ta ji muryar Damir cikin ɓacin rai yana magana. Kallonsa ta yi jin bin da ya ce, ta san cewa ba ƙaramin wahala za ta sha ba."Kai ɗan uwansa ne ko da ace na zaɓi Nasreen kana nan a matsayinka, saboda jinin da yake yawo a jikinmu irin ɗaya ne." "Kenan kin zaɓe ta kin bar ni?" Ya yi mata tambayar yana rintse idanunta, tare da ƙara tsanarta ganin ta raba shi da Batula kuma za ta raba shi da 'yar'uwarsa. "Sorry, zan iya rabuwa da kowa in har zan taimaka mata, saboda a gurin Ubangiji ina da lada sosai." "To sannu philanthropy, tun da kin zaɓe ta sai ki je kici gaba da rayuwa da ita, amma ki sani mun bar mata ke da iyayenta." Mommy ta ce cikin ɓacin rai. "A ba ni gadona, ina da gado a ciki." ta furta tana share hawaye. Mamaki ya kama su ganin yadda fuskarta babu nadama."Yanzu kin zaɓi ki barmu saboda wata bare can? To ba za a bayar ba, sai ki je can ku ci gaba da rayuwar tala..." "Ka isa ka faɗi haka? Ka manta ina da gado ko don ka ga na bar muku komai bana magana. Ko kuma da believe cewar mace ba ta da matsayin da za ta iya juya duniyarta, mai rauni ce shi ya sa kuke abin da ku ka ga dama a kampanin har ba. Ni ma ina da ikon da zan ɗauki wacce na ke so aiki." Mari Damir ya wanka mata cikin fusata."Ki kiyaye harshen ki ba zan ɗauki raini daga gareki ba, duk son da na ke miki." Muhsin kuwa hauri zai kai mata yana faɗin,"Da ka tsaya na yi maganinta fitsarrarriyar kawai." "Ai wallahi in har ana son zaman lafiya a gidan ko a ɗauki Nasreen aiki ko kuma a bani share nawa." Ta ce tana kuka tare da zama a ƙasa kamar ƙaramar yarinya tana birgima. Ganin haka Little Marwana ta faɗa jikinta ta saka kuka tana taya ta birgimar. Mamaki lamarin ya basu sai kawai suka tsaya suna kallonsu. Tsaki Hajiya ta saki."Sai dai ki mutu amma ba za mu bawa maƙiyarmu aiki ba." Ta shige dakinta. Damir ganin yadda suke kuka sai hankalinsa ya tashi. Ya kalli Hajiya da ta haye sama Muhsin ya zuba mata rankwashi yana dariya ya fita. "Little Marwana zo mu tafi Anty Marwan rigima take yi, ba ta son Daddy tafi son wacce ta sanya ni cikin damuwa." Ya ce mata tare da miƙa hannu yana maganar cikin karayar zuci. "No, dad do what Anty Marwana wants." "I won't let's go." Ya ce mata cikin tsawa, amma sai ta maƙe ta ƙara rungumeta da take kuka. Ganin haka ya saki tsaki ya fice daga gidan bakiɗaya. Suna fita ta share hawaye ta tana dariya. Mamaki ya kama Little Marwana."Anty, dama ba kuka kike yi ba?" Dariya ta yi jin abin da ta ce,"Kuka ne kuma dadinki na ke yi wa ya fita. Mene ne amfanin kukan?" Kallonta ta yi tana share hawaye na don ita bilhaƙƙi take kukan."Kar ki damu kin ji? Kukan ina yi ne saboda dadinki ya amince na ƙulla alaƙar da zai sanya miki Mommy, mai kirki wacce za ta so ki fiye da ni." Ta ce tana jan kumatunta. "Ko ba kyau so?" Ta yi mata tambayar gani yadda ta yi shiru."Ina so Anty Marwana ina son wacce za ta sanya dadi ya daina hawaye da daddare yana rungume hoton Mommy." Tausayinsu ya kamata jin abin da ta ce."In sha Allahu Ya kusa dainawa." Ta ce tare da kamata ta rungume. Da sauri ta ƙara sakin kuka jin kamar Hajiya na saukowa."Da ma na san a gidan nan ba a sona, ana nuna mini bambanci, saboda ni mace ce ina da rauni." Ta faɗa da ƙarfi yada za ta ji. Hajiya ba ta kula ta ba, ta shige kicin taja jan tsuka ta wuce kicin. Dirama sosai take yi a gidan har fushi da abinci ta yi, amma a bayan idanunsu za ta ci ta ƙoshi. Tun daga ranar ta daina cin abinci da su babu ruwanta da kowa. Su ma hakan bai dame su ba saboda abin da take so ba mai yiwuwa bane. Ganin sun ƙi kula ta sai ta daina zuwa makaranta. Kullum tana cikin ɗakinta tana kuka. Hakan ba ƙaramin tayar da hankalin Hajiya ya yi ba. Ganin yadda ta rame ta fige sai ta same ta a cikin ɗakinta. Tana kwance ta yi rub da ciki da waya suna chatting da Nasreen ta ji alamun murɗa ƙofa. Da sauri ta kashe wayar ta tura cikin ƙarƙashin filo. Shigowa ta yi ta tsaya a bakin ƙofar tare da jingina."Yanzu rayuwar da kika zaba wa kanki kina ganin kin yi adalci kenan? Kina huci don an ƙi ɗaukar ta aiki bayan ta yi sanadin da karatun ki ya zama shiririta ga shi yanzu ma a dalilinta kina son wasa da karatunki?" Juyowa ta yi cikin hawaye jin abin da ta ce."Mommy, Nasreen ba ta da aifi a duk abin da ya faru, domin komai muƙaddari ne. Taimako na ke son yi in har ana son farincikinta dole a bata aiki tun da ta cancanci hakan, kuma ina da haƙƙin da zan ce a ba duk wanda na ke so." "To ba za a bayar ba yar banza mara kunya, sai ki yi abin da za ki yi. Kin san waɗanda kike wa gorin kina haƙƙi duk sun fi ƙarfin abin da kike ikirarin kina da shi." "Mommy, taimako zan yi kuma ba kyau tunanin Nasreen ce kawai za ta dawo da Yaya cikin hayyacinsa? Ita ce ta yi sanadin da ya kasa aure. Wataƙila za ta iya yin nasarar saka soyayyarta a cikin zuciyarsa, saboda ƙiyayya na iya zama soyayy.." "Amma ba ki da hankali sai na rasa wacce zan yarda ya aura sai ita? Idan ma wannan ne tunaninki tun wuri ki cire banza mai tunanin yara kawai." "Saboda ita talaka ce ko kuma bazawara?" "Ko kaɗan kin san bana damuwa da kuɗi saboda Allah suke yi, kuma Annabi da bazawara ya fara aure, kin ga ba ni da hujjar da zan hana shi aurenta. Ba na son haɗa zuriya da ita sannan abin da kike tunani hakan ba zai taɓa yiwuwa ba, ko mata sun ƙare Damir ba zai so ta ba, tun da ya kasa don wata 'ya mace bayan Batula." "Ni kuma jkina yana ba ni zai so ta, na san cewa za ta fuskanci wulaƙancin a girinsa, amma tana da haƙuri kuma in har ya cutar da ita dole ya yi nadama." "Ki bar wannan maganar hakan ba zai yiwu ba." Ta ce mata tare da fara tafiya tana ganin wautarta na wanann maganar. "In har ba kina gudun haɗa zuriya da ita saboda tana talaka bane, to Mommy ki amince, domin ita ne kawai za ta iya kawo farinciki a rayuwarsa." Mommy shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba, tunanin abin da ta ce take yi, yayin da wani ɓangare na zuciyarta yana hango mata gaskiya."Anya Damir zai aminta ya so ta?" Ta yi ma kanta tambayar tana girgiza kanta tare da ƙarashe ficewa. Da ta fita kai tsaye ɗakinta ta shige ta rufe ƙofar. Tunani take yi sosai gane da ta ce. Har ga Allah sam ba ta son Nasreen, amma kuma tana tausayinta. Tun ranar da Marwana ta gaya mata aurenta ya mutu kuma kuma ɗan uwanta ya ɓace ta fara tausayinta. A ranar da Marwana ta zo tana kuka ta gaya musu dukan da mijinta ya yi mata ta fara tausayinta, amma dai kuma lamarin ya caɓe tun lokacin da Batula ta rasu. Kwana ta yi tana tunanin maganganun da ta gaya mata. Cikin dare ta tashi ta yi sallah, saboda yadda ta kasa bacci maganar na yi mata kuwwa a kai. Addu'a ta yi bayan ta gama istikhara sannan ta shafa ta koma ta kwanta. A ƙalla sai da ta yi sati tana neman zaɓin Allah. A yadda ta ƙasa ta ga Damir ya ƙara aure za ta iya aminta da ko wace ce in har za ta kawo farin ciki a rayuwarsa. Ta auna ta ga ya cancanta Nasreen tun da aurenta ta mutu ta ga halin da ta sanya ɗan ta. Washegari da safe Marwana tana ɗakinta ta fito daga wanka ta shigo. Kauda fuskarta ta yi ta ce,"Ina kwana?" Ba tare da ta amsa ba ta zauna tana kallonta."Marwana fushi kike da ni ko?" Ba tare da ta tanka ba ta tura bakinta sai kuma ta ce,"Ina son ki fahimci abin da na ke shirin yi ne." "Na fahimta kuma na gane mai kike son yi, kuma na amince." Da sauri ta juyo tana kallonta cikin tsananin mamaki. Kama hannunta ta yi tana faɗin,"Marwana in har kina ganin Nasreen za ta iya sace zuciyarsa, ya dawo kamar da na aminta kuma zan yi masa dole ya bata aiki." "Ina kyautata zaton hakan Mommy. Nasreen za ta iya sace zuciyarsa saboda tana da kyau da haƙuri ba ko wane ɗa namiji zai ɗauke idanunsa ba. Haƙurin da ta yi a gidan Faruk shi zai sanya Allah ya ba ta nasarar jefa soyayyarta a zuciyarsa, sannan shi kuma ya ba shi mata na gari kamarta." "Shikenan, na aminta in har kina tunanin zata dawo masa da farincikinsa." "In sha Allahu ina kyautata zaton haka." Miƙewa ta yi tana faɗin,"Zan yi masa magana ya ba ta aiki." Rungumeta tana hawaye cikin tsananin murna ganin ta shawo kanta. "In sha Alah Nasreen za ta dawo da Ya Damir kamar yadda yake da." Tana zaune a falo ya shigo cikin falon. Ɗauke kansa ya yi, ba tare da ya kula ta ba. Shi a dole har yanzu fushi yake da ita."Ya Damir, sannu da shigowa." Ta ce masa tana masa dariyar mugunta ƙasa-ƙasa. Ba tare da ya amsa ba ya ƙara ɗauke kansa. "Da ki ci gaba da fushin ki gani in zan aminta da buƙatarki, saboda ba ni da hankali sai na ɗauki wacce ta yi sanadin da na rasa matata? Tana farinciki ina ciyar da ita." Ganin bai amsa ba sai ta fashe da dariya tana kallonsa har ya shige ɗaki Hajiya, wanda hakan ya tabbatar mata da kiransa ta yi. Cikin girmamawa ya zauna yana kallonta."Mommy gani." "Yauwa zauna magana na ke son mu yi." Gabansa ya faɗi domin a tunanin da ya ɗauka wani auren ta jajibo masa, don haka ya sha kunu."Maganar da Marwana ta zo mini da shi, na auna na ga tana da gaskiya. Ita ma tana da haƙƙin da zata iya kawo kowa a cikin kampanin, don haka na amince ka ba wa Nasreen.." "Yanzu Hajiya za ki iya ɗaure mata gindin ta kawo wannan yarinyar kampaninmu ta yi aiki?" "Haƙƙinta na ke ƙoƙarin a bata. Tun da ta kafe dole sai mu bata, ai tana da gado a ciki." "To shikenan, yadda kike so haka za a yi. In dan ma duka share ɗin ta zan bata sai na fitar mata da nata ta kula da gurin." Ya faɗa a xafafe cikin ɓacin rai ganin ta biye mata. "Ba wannan nake nufi ba tun da ta kafe sai a bata." "Ok, ta bawa Muhsin takaddunta." Ya ce tare da ficewa daga ɗakin. In ana son na ci gaba da posting safe da yamma sai na ga ruwan comments. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 19 "Ok, ta bawa Muhsin takaddunta." Ya ce tare da ficewa daga ɗakin. Ganin ya fito kamar fusataccen zaki sai ta miƙe za ta gudu. Da sauri ya fincikota ya dawo da ita."Sakayyar da za ki nuna mini na fifita ki da na yi? Na gode tun da kika nuna bare ta fini, baren wacce ta jefa rayuwata cikin damuwa." Ya furta tare sakinta zai fice. "Ya Dami..." Wani irin kallo da ya yi mata ya sanya ta yi shiru. Yana fita da daka tsalle murna domin fusatar da ya yi, kawai zai tabbatar da ya amince bisa dole. Ɗakin Mommy ta shiga tana faɗin,"Ya amince?" "Na yi masa dole sai ya ce ta bawa Muhsin takaddunta." Na gode sosai in sha Allahu sai shigowarta ya zama alkhari. Ta ce tare da ficewa cikin ɗakin tana tsallen murna. Ɗaki ta shiga ta shirya a gauguace ta fice. A hanya sosai take jin daɗin nasarar da ta samu gane da Mommy. Hakan ya ƙara ƙarfafa mata gwiya sosai. Tana yin parking ta fito sannan ta shiga cikin gidan Raihann na ganinta ta taso da gudu ta rungume ta."Anty Marwana oyoyo." Ta ce tare da ƙara rungumeta "Oyoyo, ina Ummun ki?" "Tana islamiya." "Ok, mu shiga ciki Mama na nan?" "Eh yanzu ta shiga bayi za ta yi wanka." Kai tsaye ɗakin ta shiga bayan ta tayi sallama. Ba ta jima da shigowa ba Mama ta fito."Yar halal ta ƙi ambato, kafin ta tafi islamiya ta gama mini hirarki, wai ta yi kewarki." Dariya sosai ta yi jin abin da ta ce,"Ni ma Mama kewarta ya sanya na zo." "Allah Sarki ita ma ta na ta maganarki." Ta ce tare da zama gefenta suka gaisa. Bata jima ba ta shigo sanye da hijabin islamiyarta. Dariya ta yi tare da ƙarasowa kusa da ita."Wai kina nufin niƙabi kike sawa?" "Eh, kin san maza unguwarmu kan ba ka riƙe mutuncin ka ba, sai su yi ta maka kallon mutuniyar banza." "Haka ne in kika sanya ba lailai a gane ki ba." "Wallahi har na je na dawo." Ta ce mata tare da zama kusa da ita. "Da alkahiri na zo." Ta furta tana kallon ta cikin farin ciki. "Ai kullum ganinki alkhari ne saboda ko fuskarki na kalla ina jin farinciki." "Aiki na samar miki ina son ki bani takaddunki?" Ta ce tana kallonta. Tsananin mamaki ya bayyana a fuskar ta."Aiki?" Ta ce tana kallonta. "Aiki fa kika ce? Aikin share-share a gidan mutane?" Takaicin abin da ta ce ya sanya ta kai mata duka."Ubangiji ya tsare ni da ganin ranar da za ki yi wannan aikin ina raye. Aiki a campany na sanar miki aiki mai kyau wanda zai inganta rayuwarki." "Mama, zo ki ji abin mamaki wai Marwan ta samar mini babban aiki." Ta furta cikin tsananin mamaki tana kallon ta yayin da hawaye ya cika idanunta. "Aiki fa kika ce?" "Eh, Mama ni ma yanxu take gaya mini." "Masha Allah, Alhamdulillah!" Ta furta cikin tsananin farin ciki. Ganin yadda suka ruɗe sai ta lalle ta ta ce,"Aikin yana buƙatar ki mayar da na hankali dole ki ije islamiya, in har kika natsu rayuwarki za ta canza ciƙin ƙanƙanin lokaci za ki manta ƙunci rayuwar da kika shiga." "Allah na gode maka. A ina kenan?" Ta yi mata tamabayar cikin farinciki. Zuciyarta ta buga domin ta san cewa in har ta gaya mata, da wuya ta amince."A wani campany ne na samar miki, wani cousin ɗina ya sanar mini suna buƙatar ma'aikata shi ne na sanya ya samar mini." "Ni kam Marwana ba ni da abin da zan saka miki, sai dai na karashe rayuwata ina miki addu'a." Ta ce cikin tsananin murna tana hawaye. "Addu'ar ma ta wadatar ina godiya, sannan ki riƙe aikin kar ki yi wasa da shi." "Na gode sosai." Ta ce tare da kama hannunsu ta haɗa tana kallonta. "Tsakaninki da Nasreen sai Allah. Ubangiji ya biya ki, domin na rasa kalmar da zan miki godiya da ita." "Babu kalmar da zamu iya faɗin mu saka mata, sai dai addu'a." Nasreen ta furta. "Allah ya baki miji na gari." "Amin," Ta amsa cikin jin kunya. "Akwai buƙatar ki yi updating kanki saboda guri ne da ya haɗa manyan mutane masu kuɗi da kuma masu class. Ya kamata gobe ki shirya mu shiga kasuwa, sannan ki ɗan samu abin da zai sanya ki ciko ki ƙara kyau. Bana son wani ya yi miki kallon up and down a gurin." Bakinta ta kama cikin mamakin abin da ta ce."Aiki zan je ki nema mini ko mijin za ki ce sai na yi wani updating kaina? Ni da na ke tunanin na rinƙa saka niƙabi." Banzan kallo ta watsa mata."Amma tsokanata kike yi ko? Gyale za ki rinƙa sanyawa da abayoyi, kin san inda za ki fara aiki?" "A,a ban sani ba sai na je." "Zamu je amma kafin nan sai kin gama shiryawa." "Allah ya kaimu." Ta ce tana ganin abin kamar a mafarki. Har ta yi mata sallama ta tafi suna zaune suna ta maganar aikin. "Ni fa gani na ke kamar bada gaske ba! Wai ni ta sanar wa aiki kuma da albashi mai tsoka?" "Kina mamaki ne da lamarin Ubangiji? Ko shigowarta cikin rayuwarki ya ishi ya sanya ki gane Allah yana taimakon bayinsa a duk lokacin da ya so." "Haka ne Mama, Allah ya sa na fara aikin na ɗauke duk wani ɗawainiya ta ƙi." "Amin, a hakan ma kina ƙoƙarin ki sana'ar da kike yi." Kwana suka yi suna maganar aikin har sai da suka gani suka kwanta. Marwana da ta koma gida, zama ta yi ta gama list ɗin abubuwan da za ta siya mata, dangin su abaya takalmi hijabai da kuma kayan kwalliya. Suna zaune a falo ta fito da jakarta. Ganinta suka ɗauke kai ba tare da sun ƙara kallonta ba. Murmushi ta yi ta ƙarasa gurinsu. Fuskarta a ɗauke ta mika wa Muhsin credentials ɗin Nasreen. "Na gani sai ki gaya mata ta zo interview, kin san dai ba haka za mu bata aiki ba bamu gwadata ba?" "Kan me sai kun yi mata interview Nasreen tana da ƙoƙari. She is very talented." "Kampanin na mahaukata bane ai. Idan kuma son a bata aiki dole ayi mata interview, matuƙar ta kasa ba za mu ɗauke ta ba, saboda competent muke ɗauka." Kallonsu ta yi na rashin yadda, a tunaninta so suke su yi mata ta yadda za su kayar da ita. "Ni fa ban yarda ba." "To sai na ga uban da zai bata aikin." Cewar Muhsin yana harararta tare da ture takaddunta. Ɓata fuska ta yi daidai lokacin da Mommy ta fito."Mommy wai dole sai sun yi mata interview?" Kallonsu ta yi da suka mayar da hankalinsu kan wayoyinsu."Damir.." "Don Allah Mommy, yarinyar nan ba ta da hankali. Kin taɓa ganin inda aka ɗauki mutum aiki ba tare da an gwada shi ba? Kamar haka na ke son a yi mata, saboda mu ba mahaukata bane kamarta." "Na matsala in har za a yi tsakani da Allah, za ta ci ai tana da kwanya first class ce." "Allah ya sa kar ta ba ki kunya wa ya sani sata take yi?" Cewar Muhsin tare da miƙewa. "Allah ya kyauta sam ba ta sata." "Ba abin mamaki bane sanin halin mata da malpractise." Ya ƙarashe maganar yana ƙoƙarin hawa sama. Harara ta banka masa ta mayar da hankalinta kan Damir do ko kallon inda take bai yi ba, sai na ya miƙe zuwa waje. Raka shi da idanun ta yi, har ya fice sannan ta mayar da hankalinta kan takaddun Nasreen. Da ta shiga ɗaki zama ta yi ta kira ta."Zan zo gidanku don Allah ki shirya dole sai an yi miki interview." "Babu matsala Allah ya kaimu." Ta ce mata. Hira kaɗan suka yi sannan ta kashe. Sai da ta je kasuwan ta yi mata siyayya, da yawa sannan ta tafi gidansu." A lokacin da ta iso Nasreen ta gama shiryawa. Ganinta da kaya niƙi-niƙi sai ta tsaya tana kallonta. "Babu time ki shiga ki canza kaya muje." Kallo ta bita da shi ta kasa karɓar kayan." Ba kyauta na kawo miki ba da zarar kin fara salary za ki biya ni." "In sha Allah salary farko na ki ne." "Je ki shirya Nasreen." Ta ce mata tare da tura mata kayan. Ciki ta shiga ta samu wata abaya mai kyau sosai. Kalarta marun mai an yi mata ado da duwatsu da aka yi mata. Da ta fito kallonta ta yi domin ta yi kyau. Ramar da yake jikinta ya ke rage kyawunta. "Kin yi kyau mu je." Ta ce tare da yi wa Mama sallama. A hanya suna tafe suna hira. Hirar ta su kan aikin ne. Marwana take ta gaya mata ta kula da aikin da zuwa kan lokaci."Dole ki kula kin san aikin campany ba kamar na gwammati ba, saboda suka sanya idanu sosai, don suka ana yi musu aikin kuɗin da suke biyanka." "Zan kiyayye in sha Allahu, ina son na yi aikin don na ɗauki hidimar Mama." "Za ki yi abin da ya fi haka saboda suna biya da tsoka, amma fa shugaban kampanin yana da tsaurin ra'ayi." "Zan kiyaye tsakanina da shi gaisuwa, sai kuma in ya bani umurni na yi." "Da kyau na san ba zan samu matsala da ke ba." Ta ce daidai lokacin da suka kawo kampanin. Cikin tsananin razana ta kalle ta tana faɗin,"Kina nufin a wannan tanƙamemen companin kika samar mini aiki?" "Eh, shi ya sa na ke ta gaya miki da ki kula." Jinjina kanta ta yi tana kallon gurin, cikin mamakin girmansa da kyawunsa. "Please Nasreen, kin ga yanzu Mommy ta yi mini text na dawo gida ba ta jin daɗi ba zan samu shiga ba, don Allah ki shiga ciki akwai da na gaya mata za ki zo. Ga numbarta ki kira ta in kin gama sai ki koma gida." "Ok, ba matsala Allah ya ƙara sauƙi." Ta ce tana ƙoƙarin ciro wayarta ta kwafe numbar. "Buɗe data na tura miki ta Whatsapp." Ta ce mata bayan ta mayar da wayarta cikin jaka. "Bari na shiga to." Tare da fara tafiya. Marwana kallo ta bita da shi sai kuma ta ce,"Fatan nasara don Allah ki natsu kar ki ji tsoro, ki amsa duk tambayar da aka yi miki na san za ki iya." "In sha Allahu, I won't disappointed you." " I know da zarar kin gama give me a call." "In sha Allahu." Ta ce sannan ta tayar da motarta. Sai da ta nace sannan ta shiga ciki. Marwana kuwa ta yi hakan ne don kar ta ga yadda ake girmamawa, ta gane cewar kamafaninsu ne. Kiran wacce ta ba ta numbarta ta yi ganin ta kasa gane ko ina. Kasancewar kampanin saman ginin gilad ne aka ƙawata da shi. Ba ta jima da kiranta ba sai ga ta ta fito. Tana sanye da abaya baƙa. Tana da kyanta tana da kiɓa daidai, sannan za ta iya girma ta ko su zo tsara. "Nasreen ko?" Ta tambaye ta hakan tana mutmushi "Eh, ni ce." Ta amsa bayan ta gaishe ta. "Ok, mu shiga ciki." Ta ce tare da juyawa. Babu musu ta bi bayanta, tana ta kallon gurin da mamakin a nan za ta yi aiki. Da suka tsaya ofishin Muhsin kallonta ta yi sai kuma ta kallo masinjarsa."Ki shiga da ita Please." "Ok," Ta ce tare da mata nuni da alamun ta biyo ta. Da sallama ta shiga cikin ofishin tana kallon cikinsa. Wani irin ƙamshi mai daɗi ya bugu hancinta. Muhsin yana zaune yana duba fayal. Jin sallamar ya ɗaga idanunsa yana kallonta. Tun da suka iso Marwan ta yi masa text tare da mishi kashidin karya kk pmayar da ita. Murmushi kawai ta yi yana mamakin yadda akai suka yi sake ta raina su. Kallonta ya ƙara yi tare da yi mata izinin ya zauna. A hankali ta zauna tana kallonsa. Natsuwarta da hankalinta, da yadda take kama kanta suka sanya shi kasa mata wulaƙanci. Yana shirin fara mata interview biyu sai aka buɗe ƙofa. Damir ne ya shigo hannunsa da ƙaramin tawul da ya gana wanke hannunsa yana gogewa. "Please, Muhsin na manta ban gaya maka ba, baƙin nan they are on their way kuma zan fita na kai Marwana gidan su Batul..." Da sauri ta ɗago idanunta zuciyarta na wani irin bugawa. Saboda tsananin razanar da ta yi sai da ta ji kamar ƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba. Karab idanunsu ya haɗu da na juna. " Ya Damir." Ta furta cikin ranta tana mamakin ganinsa. Shi ma kallonta ɗago ya yi, ya gane ta tun ranar da ya ganta ya kasa manta kamanninta, saboda tabon da ta yi masa a zuciya. Wani irin tafasa zuciyarta ta yi har baya iya hangen abin da ke gabansa. Ganinta ya dawo masa da mikin rashin Batula da ya yi. Ganin ta ya sanya shi tuna rana ɗaya wace ta tarwatsa rayuwarsa. Rana ɗaya da ya haɗu da ita ta zame masa baƙar rana. Ta sanya masa mikin da ya ke tashin masa kuma ya kasa mantawa. Rana ɗaya da ya yi nufin mata alkhairi, ana sai ta zame masa tauraruwa mai wusutsiya, ta hanyar sanadin mutuwar matarsa wacce yafi so fiye da komai Nasreen kuwa wani irin juya ya fara ibanta. Da kyar ta iya dafa bango jikinta na ɓari ta fara neman hanyar fita. Ganin tana shirin fita Muhsin ya buɗe baki zai kira ta."Ƙyaleta ta tafi ita kanta ta san bata cancanci ta yi aiki anan ba, saboda in har ba mahaukaciyar kamar Marwana, za ta fahimci ya kamata ta ci gaba da ɓoye kanta, daga idanuwana har ƙarshen rayuwarta." Kuka ta fashe dashi ganin yadfa tsantsar tsanarta yake idanunsa."Eh, tabbas ba ka yi ƙarya ba Ya Damir. Haka ya kamata na yi ta gujewa haɗuwarmu, in har na san mai na ke yi. Kaicona da na bari muka ƙara haɗuwa bayan ka nemi alfarmar na yi nesa da kai." Ta karashe maganar cikin kuka tare da ficewa da gudu. Ajiyar zuciya ya fara saki akai-akai yana jin zuciyarsa na zafi, yayin da komai ya dawo masa sabo. Ga mamakinsa sai hawaye suka zuba masa. "Please Ya Damir, be a man." Ya ce masa ganin yadda ya rikice. "Why? Marwana za ta zaɓi ta kawo ta cikin kampanin nan, why za ta zaɓi ta yi hurting ɗina bayan duk soyayyar da na sadaukar mata." "Ka yi hakuri Please take easy." Ya ce masa cikin rarrashi. Shiru kawai ya yi yana ganin Marwana ba ta yi masa adalci ba Nasreen sai da ta tabbatar da ta fita daga cikin campany sai ta tsaya ta fashe da kuka."Mai ya sa Marwana za ki yi mini haka?" Wayarta ta ciro cikin ɓacin rai tana ƙoƙarin kiranta, amma sai ta ta j tana mata hon a bayanta. Marwana da tun da ta shiga ta dawo ta tsaya a cikin motar. Jira take yi ta fito ta gaya mata su ɗauke ta aiki ganin ta fito cikin kuka ya sanya ta ruɗe. "Saboda me za ki buƙaci na je kampanin mu na yi aiki? Bayan kin san Ya Damir ya tsane ni? Ya riƙi na yi nesa da shi, amma yau na tayar masa da mikin da yake ƙoƙarin warkewa?" "Ki fahimce ni do.." Ta ce tare da ƙarasowa gurinta ta kama hanunnta. Fisgewa ta yi tana faɗin,"In har ba kina son ɗan'uwanki ya ɗauki fansar abin da na yi masa ba, to ki janye maganar yin aikina a campanininku." Ta karashe maganar tana share hawaye. Hankalin ta ya tashi sosai ganin duk rarrashin da take mata, tana son ta fahimce ta, amma ta ƙi saurarenta. Daga bisani sai kawai ta fara tafiya cikin sauri. Ganin haka ya sanya ta sha gabanta."Don Allah koma ayi miki interview, wallahi na kawo ki aiki a nan don ki tallafawa rayuwarku." "Bana so ki bar taimakon bana buƙata, saboda idanuwana ba za su iya ganin Ya Damir ba. Shi ne mutumin da na ke jin kunyarsa matuƙar gaske. Idanuwana ba za su iya haɗa ido da na shi ba, da suke nuna mini tsantsar zalintarsa da na yi. A duk lokacin da na kalle shi sai naga tsantsar nadamar haɗuwa da ni a idanunsa." Kanta ya kulle sosai ta rasa abin da za ta ce." Ok, na fahimci ki shiga in kaiki gida Please." Ta ce cikin marairaicewa. Ganin yadda ta yi ya sanya ta shiga babu musu. A cikin motar shiru suka yi kowa da abin da yake tsaƙawa a cikin ransa. Nasreen rintsa idanunta ta yi tana jin kamar a lokacin lamarin ya faru. Ganinsa ya tayar mata da mijin da Faruk ya yi mata. Da suka isa ƙofar gidan fita ta yi daga cikin motar."Na gode da taimakon ki, amma ba zan iya aiki a campany ba." Ta ce tare da rufe motar ta shiga gida. Kallonta ta yi ba ta ce komai ba har ta shige. Ajiyar zuciya ta yi sannan ta tayar da motar zuciyarta cike da damuwa. Nasreen kuwa gida ta shige tana mamakin dalilin da zai sanya ta buƙaci ta je kampaninsu aiki. Ganinsa yai sai ta ji wani iri. A wancan haɗuwarsu ta farko da take da auren Faruk a kanta, ta yi masa kallon irin abin da kake fatan samu sai ka rasa, amma a yau da ta gansa. Duk da tsantsar tsanar da take hangowa a cikin zuciyarsa sai ta ji wani irin yanayi daban da ranar haɗuwarsu. Yanayin da ta kasa ta ta ce wani irin yanayi ne. Cikin ɗakinta shiga daidai lokacin da hawaye suka ƙara wanke mata fuska. Sallamar da ta yi, cikin muryar kuka ya tsoratar da hankalin Mama da take zaune tana gyara wake. Ba tare da ta amsa sallamar ba ta miƙe tana faɗin,"Lafiya Nasreen?" Kuka ta fashe da shi ta faɗa jikinta."Ban san dalilin da ya sanya Marwana ta zaɓi na je kampanin su na yi aiki ba, ba zan yi mata mummunar fahimta ba, amma da sai na yi tunanin tana son yayanta ya ɗauki fansar abin da na yi masa ne." "Kul! Karki sake ki zargi haka Marwana yarinyar kirki ce, wacce a kodayaushe take son faranta miki. Akwai dalilin ta na aikata hakan, ki yi mata uzuri ki fahimce ta." Miƙewa ta yi tare da janye Musaddik a kan jikinta."Ko ma mene ba zan iya aikin ba, zan gaya mata gaskiya, saboda bana fatan abin da zai ƙara haɗa ni da shi." "Allah dai ya zaba abu da yafi alkhairi." Ta cikin damuwa. Marwan da ta koma gida kai tsaye ɗakin Mommy ta shige. Ganin ta ranta a ɓaci ya sanya ta kalle ta."Lafiya Marwana?" Tambayar da ta yi mata ya sanya ta fashe da kuka."Dama na san cewa ba ni da matsayin da zan iya kawo ma'aikaciya a kampanin. Na kai Nasreen amma da Ya Damir da Ya Muhsin sun haɗu sun yi mata rashin mutunci, kuma wallahi in har ina da gado a campanin dole sa sun ɗauke ta." Kamata ta yi tana rarrashi."Dama abin da yake zuciyarsu kenan? Shi ya sanya suka ce sai sun yi mata interview? Ki bar ni da su dole su ɗauke ta." Jin abin da ta ce ya sanya ta saki murmushi tare da share hawayenta. Saboda rigima sai da ta daidaici lokacin da za su dawo ta zauna a falo. A lokacin da ta ji alamun buɗe get sun shigo da mota. Ƙara tamke fuska tayi tana kallon bakin ƙofa. Muhsin ne ya fara shigowa da suit ɗinsa a hannunsa yana ƙoƙarin cire neck tie ɗinsa, Damir kuma yana bayansa waya yake yi. Yana shigowa ta banka masa harara tare da shan gabansa."Saboda me za ku ƙi ɗaukar ta aiki?" Ta ce fuskarta babu tsoro. "Ke! Matsa kafin yanzu na wanka miki mari ina wasa dake ne?" Muhsin ta ce cikin fusata. "Ba zan matsa ba har sai na ji dalilin.." Da sauri ta matsa tare da kiran Mommy da ƙarfi ganin ya ɗaga hannunsa. "Mara kunya da ki tsaya ki ga yadda zan ɓata miki fuska da mari." Har yanzu dai ana nan ana posting a paid group mai kuke tunani? Nasreen za ta amince ta yi aikin sannan ya za ta kasance tsakaninsu da Damir? In ana son na ci gaba da posting safe da yamma sai na ga ruwan comments. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 20 A lokacin da ta ji alamun buɗe get sun shigo da mota. Ƙara tamke fuska tayi tana kallon bakin ƙofa. Muhsin ne ya fara shigowa da suit ɗinsa, a hannunsa yana ƙoƙarin cire neck tie ɗinsa, Damir kuma yana bayansa waya yake yi. Yana shigowa ta banka masa harara tare da shan gabansa."Saboda me za ku ƙi ɗaukar ta aiki?" Ta ce fuskarta babu tsoro. "Ke! Matsa kafin yanzu na wanka miki mari ina wasa dake ne?" Muhsin ya ce cikin fusata. "Ba zan matsa ba har sai na ji dalilin.." Da sauri ta matsa tare da kiran Mommy da ƙarfi ganin ya ɗaga hannunsa. "Mara kunya da ki tsaya, ki ga yadda zan ɓata miki fuska da mari." Mommy ce ta ƙara so cikin falon tana faɗin,"Dole za su ɗauke ta, ko da ace ba su yi mata interview ba." "Dama babu abin da muka yi mata, rashin dacewar ta a gurin ya sanya ta kori kanta." Muhsin ya ce tare da zama a falon. "In har ina da iko daku ku ɗauke ta." Mommy ta furta tare da shigewa ciki. Damir da ya ji tana maganar daidai lokacin da ya gama wayar, ya sanya a cikin aljihunsa zai shigo. Kallo ya bi ta da shi, saboda ba ya son ya yi magana, tun da ya ganta mood ɗinsa ya canza damuwa ta yi masa yawa. Raka shi da idanu suka yi har ya haye sama."Ki je ki kai masa abincinsa." Mommy ta ce wa Marwana tare da shiga ɗakinta. Ganin haka shi ma ya yi hanyar na sa ɗakin. Bayan ta gama haɗa abincin, ta shiga cikin ɗakin na sa. Yana kwance ya yi rigingine yana tunani. Sunan shi ta kira, amma bai ji ba ganin haka ta ƙarasa ta sauke abincin."Yaya.." Ta furta tare da janye hannunta ganin yadda ya ɗan firgita alamun bai san ta shigo ba. "Ya..." "Fita ba kin sanya dole a bata aiki ba? Fita ki ba ni guri." Ya daka mata tsada yana faɗin haka.. Kafin ya rufe bakinta fice da sauri cikin ɗakin. Tsaki ya yi tare da miƙewa ya shiga toilet. Wanka ya yi, sannan ya saka gajeren wando da riga ya zauna a gefen gadonsa. Wayarsa ya ɗauka tare da kunna hoton Batula yana kallo. Washegari da safe Marwana ta shirya don ta je ta kai ta gurin aiki. Da ta shiga gidan da sallama. Turus ta yi tana kallonta da take kan turmi tana gyarawa Musaddik wandonsa. Tamkar babu abin da ya haɗa su ta miƙe."Musaddik, Anty Marwana." Ta ce masa tana nuna masa ita. Da sauri ya ruga ta ɗauke shi tana murna. Sai dariya yake mata, saboda ya saba da ita. "Lafiya na ganki babu shiri aiki, kuma ba ki ga misscalls ɗina ba?" "Wayar tana kan kujerar na barta, na gaya miki ba zan yi aikin nan ba." "Dole ki yi kina buƙatar aikin nan, in don Ya Damir ne ba za ki rinƙa haɗuwa da shi ba, wannan ranar ma kuskure ne, saboda bai san za ki so ba, amma in har ya san kina kampanin zai yi ƙoƙarin ba ku haɗu ba." Kallonta cikin mamaki ta yi,"Saboda ne zan takura masa haka? In har kina don na yi aiki, to don Allah ki nema mini amma ba a kampanin ku ba." "Za ki yi dole za ki yi don cigaban ki." Ta furta tare da ƙara da wa gurin Mama da ta shigo. "Don Allah ki sanya ba ku ta yi aiki nan, wallahi a zuciyata ba ni da nufin ta yi aikin don a tozartata. Tun ranar da na ji matsalarta nake burin mu kammala karatu, na sanya Yayana ya ba ta aiki, don ta tallafi kanta, sai kuma ƙaddara ta sanya ki komai ya rikice." Mama shiru ta yi tana kallonta, yadda fuskarta ya tabbatar da abin da take faɗi."Kina ganin babu cutarwa ga ɗan uwanki?" "In har akwai ba zan yarda ta yi ba, saboda duk yadda na ke son ta da burin ganin farincikinta, ba zan so na ƙuntata wa ɗan'uwana da yake kamar uba a gare ni." "To shikenan, in sha Allahu za ta yi..." Jin abin da Mama ta ce sai ta yi saurin kallonta tana faɗin,"Mama..." "Ki yi aikin kar ki tsorata ki yi fatan alkhairi." Ta katseta tana faɗin haka. Shiru ta yi ta kasa cewa komai. Tunanin yadda za su rinƙa haɗuwa take yi, saboda tsoronsa zuciyarta bugawa take yi kamar za ta fito waje. Ganin ta yi shiru ta zauna tana tunani sai ta zauna a gefen ta."In sha Allahu za ki ga yadda rayuwar ki za ta canza, sannan ki kama mutuncinki kar don kina tunanin sun fi ki arziki mutanen gurin ki ce za ki ɗauki wulaƙanci." Shiru ta yi har yanzu zuciyarta ba ta gama amincewa da aikin ba. "Bari na wuce gobe in sha Allahu zan zo na ɗauke ki na kai ki har ciki.". "Shikenan Allah ya kaimu." Ta furta cikin sanyin murya tare da miƙewa. Jin abin da ta ce sai ta cika da farinciki. Da dadddare ta gana shirinta tsaf wanka ne kawai ba ta yi ba, amma har kayan da za ta sanya ta cire. Cikin dare kasa bacci ta yi tana ta juye-juye tunanin yadda za ta yi aiki a kamfanin take yi. Tana kwance har aka kira sallar asuba. Ta miƙe ta ɗora ruwan zafi a gawayi. Wanka ta fara yi wa su Raihann ta kwantar da su. Sai da ta gama shirya kanta, sannan ta tashe su ta gyara su. Raihann da za ta wuce makaranta, ta saka mata biskit a jakarta bayan ta ba ta ruwan koko ta sha. Tana gyara fuskarta wayarta ta yi ƙara ganin Marwana ce sai ta ɗaga."Please, ina ƙofar gida, mun yi latti ba zan shigo gaida Mama ba." "Ok, tana gaishe ki gani nan." Ta ce tare da kashe wayar, ta kama hannun Raihann da za su sauke ta a makarantar su. "Musaddik, na tafi bye." Ta ce masa tare da shafa kumatunsa da yake hannun Mama. Tuni ya saba da zama a gurin ta in za ta fita. Hannu ya ɗaga mata yana mata yana dariya har ta fice. Da ta fita ƙofar gidan ta same ta a cikin motar tana jiranta. Ba tare da ɓata lokaci ba suka tafi. Raihann suka sauke sannan suka wuce. A hanya tun da ta ga sun dumfari get ɗin gidan, gabanta yake dukan tara-tara har sai da Marwana ta fahimci haka. "Don Allah ki zama jaruma babu wanda zai wulaƙanta ki, sannan kar ki sake ki bayar da fuskar da wata ko wani zai kawo miki raini. Kowa haƙƙinsa ya zo nema. Yadda kika miƙe a gidan Faruk kika ƙwaci 'yancin kanki, haka za ki yi rayuwa anan, domin wasu mutanen in kina tsoronsu, sai su nemi su taka rayuwarka yadda suke so." "In sha Allahu zan yi iya bakin ƙoƙarina." Ta ce mata tare da fita daga cikin motar. Kama hannunta ta yi suka shiga cikin kampanin ganin yadda ta ɗan tsorata. Nasreen mamaki ta rinƙa yi yadda ake girmama Marwana tana wani shan ƙamshi. Har ofishin Muhsin ta kaita. Yana zaune da waya a hannunsa. Ganin ta ya ɗauke fuska."Ya Muhsin ga Nasreen ta dawo." "Ok, ta zauna na yi mata wasu tambayoyi." Zama ta yi babu musu tare da furta,"Ina wuni?" Amsawa ya yi fuskarsa babu yabo babu fallasa. Tambayoyi ya yi mata cikin harshen turanci, tana ba shi amsa, sannan ya sanya ta yi dogon magana da turanci. Yadda ta yi maganar cikin rashin tsoro ta yi introducing kanta, sai abin ya burge shi sosai. Murmushi ya yi yana kallon ta."Akwai ma'aikacinmu da ba ya jin daɗi, ina ga za ta yi replacing ɗin sa kafin ya dawo. Marwana je ki haɗata da Khausar za ta nuna mata aiyyunkan da za a iya ba ta ɗaya a ciki. In ta ɗan kwana biyu, sai na san abin da za ta iya." "Ok, Yaya." Ta ce tare da miƙewa ta kama hannunta suka fita. "Zan kai ki gurinta, sannan zan haɗaki da 'yar ƙanwar Momi, kuma wacce da Ya Muhsin yake so. She is very nice za ki ɗan saki a cikin kampanin." "Na gode Marwana, Allah kawai zai biya ki." Ta furta cikin farincikin. Ofishin Hajar ta fara shiga wacce take zaune a kan kujera, mai irin juyawar hankalinta na kan kamputar dake gabanta. Idanunta sanye da farin gilas ta ci kwalliya tamkar za ta je gasar kyau. Ganin su ya sa ta saki murmushi ta miƙe tare da zare gilashin fuskarta. "Sis! Kece da ziyarar bazata?" Ta yi mata tambayar tare da rungumeta. "Ya kike kwana biyu kin ɓuya?" "Wallahi ya Damir ne, You know how strict he is, tun da ya rasa matarsa ya tsaurara doka, mutum dole sai ya cika aikinsa. In na koma gida na gaji kuma..." "Ke dai ki faɗi gaskiya kunyar Mommy kawai kike yi, wai ke a dole ga surika." Dariya ta yi jin abin da ta ce."Bana son sharri Marwana Mommy, uwa na ɗauke ta ina nan zan kawo miki ziyarar bazata." Ta ƙarashe maganar tare da isa gaban, ƙaramin frij dake ofishin ta ɗauki musu drinks. "Wannan fa ƙawarki ce?" Ta yi mata tambayar tana zama a gefen ta idanunta na kan Nasreen. "Eh, ƙawace sabuwar ma'aikaciya ce a gurin nan, shi ne na kawota gurinki. Ki kula da ita kamar yadda za ki kula da ni, tana da matuƙar girma da matsayi a gurina. She is like sister to me." "In sha Allahu kar ki ji komai. Kin san da ba ni da matsala, Allah ya sa za ta iya jure surutuna?" Ta yi tambayar tana kallon ta. Dariya suka yi gabakiɗaya ɗaya. "Bari na kai ta gurin Khausar ita za ta nuna mata aiki." Ta ce tare da miƙewa. "Ok, mu je na raka ku am less busy." Ta ce tana nuna hanya. A hanya suna tafe suna hira har suka shiga ciki. Ganin yadda Khausar ta karɓe ta sai ta ji sanyi sosai. Zama ta yi kan kujerar ma'aikatan tana kallon Marwana da ta ce,"Zan wuce ina da lecture. Allah ya ba da sa'a." Kasa magana ta yi dai hawaye da suƙe ƙoƙarin zubo mata. Da sauri Marwana ta girgiza mata kanta sannan ta fara tafiya. Ganin haka Dukansu suka rako ta. Bayan ta tafi Khausar sai hanya da jira take yi. Ganin haka ya sanya ta ɗan saki jikinta. Tana kallon aikin da take yi a cikin kamputar tana mata bayani. Wuni ta yi tana mata bayanin duk abin da take yi, yayin da ta tattara hankalinta ta mayar kanta. So take ta iya aikin don Marwana ta yi alfahari da hakan. Da rana aka kawo musu lafiyayyen abinci a take away. Soyayyar doya da ƙwai sai drinks mai sanyi da ruwan gora faro. Kasancewar rashin sabo ta kasa cin abincin sai dai Khausar ta sanya mata a jakarta. A cikin ofishin ta wuni har lokacin ta shi ya yi. Hajar ce ta leƙo ofis ɗin tana faɗin,"Ko kwana za ku yi Khausar? Na san ki in kika kama computer ba kya mata da wasa." Dariya ta yi tana faɗin,"Mun gama ai aikin da oga Damir ya ba ni nake son na ƙarasa, kar a samu matsala kin san halin shi?" "Haka ne aikin oga kwata-kwata ne dole a mayar da hankali." Ta furta sai kuma ta mayar da hankalinta kan Nasreen da take tsayar saɓe da jakarta. "Zan wuce na ce bari na yi miki magana, saboda Marwana yanzu ta kira ki na rage miki hanya, da alama tana matuƙar ji dake?" Murmushi ta yi jin abin da ta faɗa tana kallonta. "Ok, mu je." Ta furta cikin sanyi. "Ni ma a motarki zan koma gida. Jiya na kai yawa gurin gyara, an sanya ƙanina ya ɗauko mini Allah ya sa ya gyara." "Amin mu je." Su uku suka rankaya zuwa cikin motar. Da ta koma gida cikin tsananin murna ta sanar da Mama duk abin da ya wakana."Mama, na kasa yarda cewar nice na ke aiki a campany nan, kin ga kyan sa kuwa? Mutane ne masu aji da class suke aiki a gurin, wallahi ji na ke yau rayuwata kamar mafarki." "Ba mafarki bane lamarin Ubangiji ne da yake azurta bawa a lokaci guda. Tsakanin mu da yarinyar nan babu abin da za mu ce sai godiya." "Sosai Mama na so ace Yaya Ahmad yana nan, ya ga inda na ke yin aiki sai ya yi alfahari da ni." "To yayanki tun ina tunanin zai dawo har ba fara cire rai, saboda an ɗauki tsawon lokaci." "To ni ma kaina ina shiga damuwar hakan, amma duk lokacin da na yi kuka na yi addu'a, sai na ji na samu natsuwa da kwanciyar hankali." "Allah ya bayyana mana shi." "Amin, " Ta amsa tare da miƙewa don ta yi sallar magariba. A cikin sati ɗaya da fara aikin ta fara sakin jiki da gurin, musamman yadda ta ga ma'aikatar gurin suke rayuwa cikin sanin darajar ɗan adam. Abin da ya ƙara kwantar mata da hankali, yadda tun da ta zo bata ƙara da haɗuwa da shi ba. Sai dai ta ji an ce oga Damir ya shigo yana kiran wance ko ya yi wa wane kasa. Yadda ba ta ganinsa sai abin ya yi mata daɗi. Ga abinci mai rai da lafiya har karin safe duk anan suke yi. A cikin sati biyu ta fara kyau da ƙiba, saboda abincin dare kawai take nema. Shi ma ba kullum ba in har ta ci ta ƙoshi a gurin aiki, sai kuma gobe da safe za ta kara cin abinci. Tun da Baba ya ji ta samu aiki ya fara rara gefe burinsa ta yi albashi ta ba shi nasa kason. Kamar wasa ta yi wata ɗaya da fara aikinta. Duk da cewar ba a ba ta ofis ba, amma sai da aka yi mata albashi. Tsanananin farinciki ya kamata ganin maƙudan kuɗin a account ɗinta. A ranar kowa ya ganta ya san tana cikin farin ciki. Daga ma'aikatar kasuwa ta wuce. Sai da ta yi musu siyayyar komai duk abin da suke buƙata, sannan ta dawo gida. Naira dubu goma ta bawa Baba sai mutanen gida ta raba musu. Ta kuma umurci a rinƙa girki duka gida, da kayan abincin da ta siyo, saɓanin da kowa sai dai ya nema abincinsa. Kuɗi ta basa Mama ta ja jari hatta Zainab sai da ta bata kuɗi. Ta shiga kasuwa ta tsintowa su Raihann kayan sawa. Zobe mai kyau ta siyawa Marwana, domin ta rasa abin da za ta siya mata. Kasancewar ta son tana son zobe sai ta siya mata tare da turare. A ranar da ta cika wata da kwana goma a ka bata ofis dinta, mai ɗauke da kujara zamanta sai kuma na zama guda uku. Computer biyu ne a cikin da desktop sai kuma lapton mai tsadar gaske mai ɗauke da logo na kampanin. Sosai take murna ganin katon ofis ɗin mallakinta ne. Tabbas karatun boko yana da daɗi, domin yau ya kaita matsayin da bata taɓa tunanin kaiwa ba, duk da cewar ba a cire rai da rahamar Ubangiji, amma bata taɓa tunanin za ta yi mingling da mutane irin waɗanda take yi da su ba. Ta fara aikinta cikin nasara da kwanciyar hankali. Gabakiɗaya ba ta da damuwa Inta fito aiki tun safe sai huɗu take komawa gida. Duk wani hidimar iyayenta ita take ɗauke wa. Duk bani bani da Baba yake mata, ba ta taɓa gazawa ba, duk da cewar abin na sa yana wuce gona da iri. Albashinta na biyu ta koma ta kudin da Marwana ta kashe ta yi mata siyayya za ta bata. Babu musu ta tura mata account ta tura mata. Shiryawa ta yi ta je kasuwa ta siyo masa kayan masu kyau. "Kina da buƙatar kaya sosai Nasreen in kana shiga cikin manya dole ka yi kaya. Yada kike da kyau in kina sanya kaya mai kyau ba ƙaramin haskaka za ki yi ba, dubi yadda kika yi kiɓa kika canza kamar ba ke ba. Farouk mugu ne kashe ki ya so ya yi a gidansa. Dubi fatar jikinki har canzawa ta yi. Da ace yanzu zai ganki sai ya yi mamaki." Bana fatar ƙara haɗuwa da shi Marwana. Bana son ko jin sunan da domin ya cutar da ni." "Tabbas amma komai ya zama tarihi ai, domin bayan wuya sai daɗi. A wanna lokacin za ki tsaya ki yi hankali ki natsu, saboda maza da yawa za su zo miki ganin kina aiki ba za ki zamar musu liability ba, sai kin natsu kin tsaya kin fahimci mutum kafin ki aminta da shi." Kallon mamaki ta yi mata jin abin da ta ce."Kin tunanin akwai wani ɗa namiji da zan kara aminta da shi? Aini da aure kuma babu shi a tsarina, burina na inganta rayuwata." "Ko da ace ni na kawo miki mijin?" Dariya ta yi mai sauti jin tambayar da ta yi mata."You Are so funny Marwana mu bar maganar aure, kin san dai kin da matsayi a cikin rayuwata?" Ita ma dariya ta yi, sai ta bar maganar duk da cewar ba ta amsa mata tambayar ta ba. Nasreen rayuwa ta canza ta yi ƙiba sosai kamar ba ita ba. Ita da ada babu tsoka a cikinta sai kashi, amma yanzu ta jiki ta yi hibs kamar ba ita ba. Duk wannna ramar babu. Hatta su Raihann sun murje saboda yanzu ba su da matsalar abinci. Albashinta yana isa ya siya musu abincin da za su. A ɗan wata biyu da ta yi ta san mutane sosai a cikin kampanin. Ta saki jiki ta yadda suke haba-haba da ita. Ganin haka ta sari hijabai da yawa da dan kunnaye tana musu tallah. Sosai kuwa suke siye. Kuɗi ko ta ko ina suke shigo mata ga shi ana yawan basu alwus a kampanin. Shawara ta yanke ta siyawa Mama firiza ƙaton gaske, sannan ta ja musu wuta, saboda dama Ya Ahmad yake biya tun da ya ɓace aka yanke. Aiko ta yi shawara mai kyau. Kasancewar unguwar marasa ƙarfi ne ba ƙaramin ciniki suke yi ba, don ruwan sanyi kawai da ake siye ba ƙaramin samu suke yi ba. Gashi tana zoɓo, dinja kunun aya da su fanta da duk sana'ar da ake yi da frij. Zainab kuma tana cincin da sayar da gawayi. Lokaci guda suka samu sauƙin daga cikin tsananin talaucin da suke ciki. Baba ne kullum yake aikin bani-bani in aka hana shi ya yi ta zage-zage yana mata gorin ba ita kaɗai ta haife ta ba. Ko kunya ba ya ji tun da ya ga ta samu abin yi bai ƙara mata maganar aure ba. Duk a gidan yanzu babu wacce yake so kamarta. Hatta yaran da yake hantararsu, a yanzu ba shi da masoya irin su. Yusuf ya ba ta shawarar su yi noma ya ce,"In har za ki yi xan kula da komai, saboda yanzu in har kana noma lokaci guda za ka yi kuɗi. Wadannan masu kuɗin da noma suke haɗawa ." "In ban da abin ka ina mace ina ni ina noma?" Jin tambayar da ta yi masa sai ya yi dariya."Mata nawa suke noma? In har kina kuɗin ki za ki yi noma, abin da kawai kike buƙata wanda zai kula miki." "To shikenan, ka je ka yi magana zan biya komai ka samu gonakin." "To," Ya ce tare da fita. Masha Allah Nasreen ta zama celebrity.💃💃💃💃💃💃 Ta fara zama ajebota jiki duk madara kalar ganta💃💃💃 Yau wannan Page din na gas ɗin Nasreen ne sai su fito su yi ruwan comments na murna. In ana son na ci gaba da posting safe da yamma sai na ga ruwan comments. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 21 Jin tambayar da ta yi masa sai ya yi dariya."Mata nawa suke noma? In har kina kuɗin ki za ki yi noma, abin da kawai kike buƙata wanda zai kula miki." "To shikenan, ka je ka yi magana zan biya komai ka samu gonakin." "To," Ya ce tare da fita. Damir tun lokacin da ya san cewa tana cikin kampanin yake wasan ɓuya da ita. Sam baya ƙaunar ya ganta. So yake har ta bar kampanin ba tare da ya ganta ba. Akwai ranar da suka fito daidai ya fito daga masallacin kampanin yana lura da ita, ya koma har sai da suka wuce. Ko meeting zai yi in har duka ma'aikatan ne sai dai Muhsin ya jagora. Damir ne ya shigo da motar da cikin kampanin shi da abokinsa Annur. A harabar kampanin suka tsaya suna hira yana nuna masa gurin da yake son ya gini, kasancewarsa injiniya ne shi. Bayani yake masa hankalinsa na kan gurin yana sauraren bayaninsa. Kamar ance ya ɗaga idanunsa sai ya yi arba da Nasreen da ta shigo hankalinta na kan wayarta, da suke chatting da Marwana. Labarin lecture da suka yi da kuma iskancin da lecturer ya so ya yi mata rashin mutunci Dariya take mata jin abin da ta yi masa. Sosai take murmushi idanunta kan wayarta. Damir da yake wa Annur bayanin yadda yake son ya yi ginin, sai ya fahimci magana yake yi, amma hankalinsa na wani gurin. Bin inda yake kallo ya yi, daidai lokacin da ya buɗe baki ya ce,"Wow! Ji wata kyakkyawar halitta a kampanin ka Damir, ma'aikaciyarka ce tun da na ga rigar kampanin ku a jikinta. Is she married?" Kallon da yake mata da tambayar da ya yi masa ya ƙular da shi. Kallon banza ya watsa masa, sannan ya ƙara kallonta a wulaƙance ganin Nasreen ce. "Annur are you insane!" Ya ce masa tare da fisge zanen ginin da ya yi."Bana son aikin na fasa ba ka contract ɗin, I will look for another person." Ya ce cikin tsananin fushi yana aika masa da mugun kallo. "Why Damir? The girl is so pretty, wallahi aurenta xan yi in ba ta da aure. ." "Annur, get out of my company!" Ya daka masa tsawa yana faɗin haka. Nasreen ya bi da kallo yana admiring ɗin ta har ta ɓace."Ina sonnta kuma in har za ta so ni, I will marry her Kai ne gaba a auren tun da worker ɗin ka ne." Ganin abin da ya ce ya ƙara tunzura shi sai ya yi dariya ya shige cikin motar sa."Gobe zan gyara inda bai yi maka ba, sannan ka fara kai ƙoƙon barata kafin ka raka ni zance."Ya ƙarashe maganar cikin tsokana. Yana fita ya bi inda ta wuce da kallo cikin tsananin fushi. Dariyar da ya gani a fuskar ta da yadda ta yi kyau ta ciko, ya sa shi jin haushi. Ganin tana cikin farinciki kenan? Bayan shi ta sanya shi cikin damuwar da ya kasa mantawa. Ransa ne ya yi ɓaki zuciyarsa na tafasa, sai ya ɗauki aniyar jefa ta cikin ƙunci kamar yadda yake yi. Zai takura rayuwarta kuma ya hana ta jin daɗi, ballanatana ta yi kyan da WASU MAZAN za su kalle ta su aureta. In har bai aure ba, shi kuma ba zai barta wani ya aure ta ba. Ruwan sanyi ya buɗe frij ya ɗauko tare da ɓalle gorar ya kafa kai. Sai da ya shanye ya yarda robar a trash. Zagaye ofis ɗin ya yi, yana tunanin abin da zai rinƙa mata ya ƙuntata rayuwarta, ta ije aikin ba tare da Marwana ta zarge shi ba. Tun da Annur ya furta yana sonta ya san da gaske yake yi. Abun mamaki sai ya ji ya fara tsanarshi da raina ajinsa ganin ya rasa wacce yake so dai ita. Saboda takaici kulle ofis ɗin ya yi, ya ce kar wanda ta shigo yana buƙatar hutu. Yana kwance yana ta ƙulla wulakancin da zai rinƙa mata, har bacci ya kwashe shi. Nasreen zaune a ofis ɗinta hankalinta na kan wayarta. Idanunta sanye da gilas mai kyau. Hannayenta ƙunshi ne da Marwana ta kaisu aka yi musu, saboda bikin wata ƙawarsu da za su yi cikin satin. Wayarta ce ta yi ƙara da sauri ta ɗauka ganin Mama ce. Jikinta har yana rawa ta ɗauka, saboda ta bar Raihan ba ta da lafiya."Hello Mama," "Nasreen ki dawo gida jikin Raihan ya rikice domin ya yi zafi sosai, yanzu na ƙara mata magani, ga shi babu kowa a gidan Zainab na makaranta da na kai ta asibiti." "Subuhanallahi! Mama gani nan zuwa." Tana ƙoƙarin miƙewa bayan ta kashe wayar. Ɗaya daga cikin ma'aikacin mai suna Ingawa ya shigo da sallama. Ɗan ƙaramin tsuka ta ɗan ja, saboda yana son takura wa rayuwarta. Tun da ta fara aiki yake shige mata da yawan zuwa ofis ɗin ta, amma sam ba ta son hakan, duk da cewar he is decent person kuma looking attractive, amma ita sam ba ta son wani namiji ya rinƙa shige mata, domin Faruk ya sanya ta tsani maza. "Nasreen lafiya na ga damuwa ɗauke a fuskarki?" Ya tambaya da sauri ganin yadda innocent face ɗinta ya canza. A hankali ta ɗago idanuta ta dora su a kansa jin tambayar da ya yi mata, sai kuma ta sauke su taka kallon wayarta"Ba wata damuwa bace, yarinyata ce ba ta da lafiya shi ne aka kira ni?" Gabansa ne ya faɗi domin ya ɗauka budurwa ce, saboda jikinta babu inda ya nuna cewar ta taɓa aure."Are you married?" Ya yi mata tambayar cike da fargabar amsar da za ta ba shi, domin zuciyarsa ta gani kuma ta ƙyasa. Kallonsa ta yi ganin yadda ya kashe ta da idanunsa. Wani iri ta ji game da hakan, amma sai ta yi saurin kawar da wannan tunanin ta ce masa,"Yes am married." "Oh, sorry Allah ya ba ta lafiya." Ya ce tare da matsawa ya ba ta guri ta wuce . "Amin,"Ta furta tana ƙoƙarin ɗaukar key ta kulle ofis. "Na ga kin tayar da hankali ki ina mahaifinta ba sai ki kira shi ba?" Ya ce mata domin bai yarda da cewar tana da aure ba, domin kamar ya ji Khausar ta gaya masa ba matar aure bace. "Baya nan ya yi tafiya." Ta furta cikin sanyin murya ganin yana son mata ƙure. "In babu damuwa bari na kai ki tun da emergency ne." "No, ka bar shi na gode." Ta ce masa tare da fita tana jiran ya fito Kasheta da idanunsa ya yi, har sai da ta tsargu, sai ta kauda idanunta zuciyarta na tabbatar da zarginta. Bayan ya fita ta kulle ofis ɗin ta je gurin Khausar."Please, ina son na je gida zan kai yarinyata asibiti." Khausar ta kalleta fuskarta ɗauke da damuwar ciwon."Allah ya ba ta lafiya, amma ba zan iya ba ki permission ba, sai dai ki je gurin oga Muhsin ko Damir, saboda jiya ya sanar za a yi meeting akwai sabon system da zai kawo a ma'aikatar. Gabanta ne ya yi wani irin bugawa tana kallonta."Na haƙura zan jira in an tashi na kaita." Ta furta cikin damuwa za ta fita. "Nasreen, saboda me? Zai fahimce ki rashin lafiya ne." "No, kar ki damu bar shi kawai." Ta ce tare da juyawa za ta fita. Mamakin canzawar fuskarta da yanayin da ta nuna ya kamata. "Ok, wallahi shi ya hana wannan meeting ɗin da za mu yi, na tabbata wani tsaurin zai tsaurara." Ba tare da ta ce komai ba ta koma ofis ɗinta cikin damuwa. Ingawa da ya ga dawowarta ya shigo."Lafiya kin fasa zuwa ne?" Ɗan firgita ta yi domin ba ta san ya shigo ba."Am sorry." Ya ce mata ganin yadda ta razana. Da fari watsa masa kallon da ya rikita tunaninsa ta yi, ba tare da ta tanka masa ba, amma kuma sai ta buɗe bakinta cikin sanyin murya ta ce,"Na fasa zuwa sai an tashi zan kaita." "Why yarinyar ki ba lafiya kuma mijinki baya nan, za ki ce sai an tashi? Aikin yafi miki yarinyar ne?" Kasa amsa mishi tambayar ta yi domin tana cikin damuwa, sai kuma ta ce,"Na je na gaya wa Khausar ta sanar da ni oga Damir ya hana fita, dole da an nemi izininsa." Ta ƙarashe maganar tare da kiran sunan kamar an mata dole. "Ki je ki yi masa magana ai ba zai hana ki ba, wani lokacin ne kawai yake very strict." Girgiza kanta ta yi alamun a'a. "Ok, tun da ba za ki iya ba, zan je na tambayar miki sai na kai ki gida ki ɗauko ta." Zare idanunta ta yi tare da miƙewa ganin ya murɗa ƙafa zai je."Please, Ingawa don Allah kar ka je." Ta yi maganar kamar tana son kuka. Kallon yake yadda ta bata fuskasai ta ƙara masa kyau sosai"Yarinyar ki ta fi aikinki mahaimmaci. Kin gani in har mahaifinta, ya ji kin kasa zuwa kaita asibiti ba za ku samu matsala ba?" "Na fahhmce ka zan je da kaina." Ta furta cikin sauri da in'ina. "Ok, mu je sai na ga kin shiga ofis ɗin." Wani birkitaccen kallo ta yi masa, ganin yana son takurawa rayuwarta. Hannunsa ya watsa yana faɗin,"Am just trying to help." Fita ta yi daga ofishin zuciyarta na bugawa, ganin yadda ya takurawa rayuwarta. Tana fita ya bi bayanta, saboda tsoron da ta nuna sai ya bi bayanta da murmushi yana kallonta. A hankali take tafiyar, cikin tashin hankali da ta kai ofis ɗin har ta murda sai ta fasa, saboda rashin ƙwarin gwiya ofis ɗin Muhsin ta je, duk da shi ma tsoronsa take jii, amma ba kamar Damir da take hango tsanarta ƙarara. Namijin ƙoƙari ta yi ganin in har ba ta daure ba, zuciyarta da take cike da tsoro ba ta za ƙarfafafa ta ba. Da siririyar sallama ta shiga zuciyarta na bugu, yayin da bakinta ke ɗauke fatan Allah ya sa ba ya ciki, sai dai fatanta ba ta karɓu ba, domin shi ya fara juyowa yana kallonta, da hankalinsa yake kan tarin takaddun da suke cikawa. Ji ta yi tsoronta ya nunku idanunta suka firfito, musamman kallon da ya watsa mata. Muhsin jin ya yi shiru ba tare da ya amsa sallamar ba, sai ya kalli wacce take sallama. Shi ma fuskarsa babu yabo babu fallasa ya amsa. Kasa ƙarasawa ta yi kuma ta kasa fita."Akwai sa'onki a ciki da za ki tsaya mana a kai?" Damir ya furta zuciyarsa na harbawa. Ya rasa duk lokacin da ya ganta sai ya ji ya rikice numfashinsa yana sauka da sauri. Danganta hakan da tsanarta da ya yi, da kuma abin da ta yi masa na raba shi da wacce yake so. "Um..eh..ina.." Ta fara in'ina ta kasa maganar "Get out stupid!" Ya daka mata tsara yana faɗin haka. Da sauri ta fice cikin hawaye. Ganin ta fita ya saki tsaki ya miƙe."I think I need to rest, mu bar aikin wani lokacin." "To," Ya ce tare da fara tattara takaddun. Nasreen cikin hawaye ta fita tare da jingina da ƙofar tana hawaye. Ga mamakinta sai ta ga Ingawa yana tsaye kusa da ƙofar yana kallonta. Ganin yadda ta fito dai ya fara tahowa gurinta. Haushi da takaici ya cika mata zuciya ganin yana son ya takurata. Da sauri ta fara taku za ta bar gurin, amma sai ya tari gabata ya ce,"Nasreen, ba dai hana ki ya yi ba? Saboda na san yadda yake son 'yarsa, ba zai hana ki kula da ta ki ba?" Tambayar da ya yi mata ya sa ta kalle shi kamar za ta kifa masa mari. Fara tafiya ta yi ganin yana son takura mata. "Ok, tun da kin ƙi ba ni amsa bari na tambaye shi da kai..." Ya ce tare da buga kofar ofis ɗin. Da sauri ta tare shi ta hanyar tokare ƙofar tana kallonsa."Don Allah kar ka je, na san cewa ba zai bar ni ba." Ta yi masa maganar cikin muryar shagwaɓa kamar za ta yi kuka. Yadda ta yi maganar ya tafi da tunaninsa."Saboda me, akwai wani abu tsakaninku ne?" Jin tambayar ya sa ta girgiza kansa da sauri."A'a babu saboda ban san shi ba sai anan, wataƙila akwai abin da yake damunsa ne ya sanya..." Sai ta yi shiru ta kasa ƙarashewa don ba ta san me za ta ce masa ba, tun da ba ta samu damar tambayar sa ba. Kallon rashin yarda ya bita da shi, ganin haka dai ta juya za ta tafi."Nasreen," Ya kira sunanta da muryar da ya sanya ta juyo da sauri babu shiri. "I found out that you are divorcee it either ki bari na yi masa magana, ko kuma ki ba ni address na gidanku na kaita." Jin zaɓi da ya ba ta, ya burkita tunanin ta har ta kasa zaɓar ko ɗaya, amma daga ƙarshe sai ta zabi ta ba shi address." Murmushi ya saki yana kallonta ganin yadda ta birkice. Ƙara kallonta ya yi daga sama har ƙasa yana kashe mata ido, sannan ya wuce zuwa inda motarsa take Saboda haushin kutsen da yake son ya yi mata, raka shi da idanun ta yi cikin tsanannin takaici tana jin kamar ta rufe shi da duka. Ganin ya nace sai ta jingina da bango tare da sakin nannauyar ajiyar zuciya. Cikin sanyin jiki ta koma ofis tana ƙoƙarin kiran Mama ta sanar da Mama zuwansa. Ingawa kuwa a hanya tafiya yake yana murmushi. Tun ranar da ya fara ganinta ya ji ta yi masa, musamman natsuwarta da sanyin ta. Sannan tana da kyawu da yadda take komai nata cikin tsari. So yake ya aureta in har za ta ba shi dama. Matarsa ɗaya ce da yaransa gida uku. Da ya isa ƙofar gidan ya cika da mamaki saboda kalarta bai yi kama da gidan ba. Wani irin ƙaunarta da tausayinta ya ƙara kama shi, har ya ɗauki alƙawarin kula da rayuwarta. Cikin natsuwa Mama ta fito duk tafi asibitin. Shi ya kula da komai har aka gama mata allura. Ya so sanya mata drip, amma sai kuma likitan ya sanar masa da su bata maganin kawai. A hanya siyayya sosai ya yi wa Raihan da Mama, har sai da ta kasa masa godiya saboda mamaki. Kallon Raihan yake yi ganinta kyakkyawar gaske kamar uwarta. Yana son ya tambaya yaranta nawa, amma yana shakkun tambayar. Haka nan ya Masha Allah Nasreen ta zama celebrity.💃💃💃💃💃💃 Ta fara zama ajebota jiki duk madara kalar ganta💃💃💃 Yau wannan Page din na gas ɗin Nasreen ne sai su fito su yi ruwan comments na murna. In ana son na ci gaba da posting safe da yamma sai na ga ruwan comments. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 22 Dage kansa ya yi da yake bugawa yayin da yake jin zuciyarsa babu daɗi, domin a duk lokacin da ya kalle ta ya ga tana farinciki, sai ya ji ransa ya ɓace bayan ta gusar masa da na shi farincikin. A hankali ya shiga da motar, tare da watsa mata mugun kallo, da take son ta gaishe shi amma ta kasa. Idanu ta raka motar da shi, yayin da zuciyarta ke bugawa da sauri, saboda tana tsoron ke su haɗu a farfajiyar kampanin, sai ta kasa shiga har sai da ta tabbatar da ya shige ciki. Tana ƙoƙarin shiga motar Ingawa ta sanyo kai. Da sauri ta ɗauke kanta, tana jin kunyar abin da ta yi masa ta shige ciki. Ganinta ya ƙara gudun motar da ya shiga ya yi parking. Yana ƙoƙarin buɗe motar ta ƙara da sauri za ta wuce."Nasreen," Ya kira sunanta yana takowa inda yake. Jin ya ambaci sunanta, ya sanya ta tsaya tare da rintse idanunta xuciyarta san babu daɗi. Da ya ƙaraso ganin ba ta juyo ba, sai ya tsaya bayanta yana kallonta. Da sauri ta juyo domin a tunaninta bayanta yake kallo. "Ina kwana?" Ta ce masa tana son gane inda ya kalla. Dariya ce ta kubce masa ganin yadda ta yi."Lafiya lau gimbiyar mata." Ya ce mata yana kashe mata murya. Jin abin da ya ce sai ta kalle shi kawai, domin sam kalaman ba su burge ta ba. A yanzu tana jin babu wata kalma da ɗa namiji zai gaya mata ya sosai zuciyarta. Don haka ko da ya gaya mata cikin salon shi n jan hankalinta, ba ta ji komai a xuciyarta ba, sai ma wani haushi da kallon yaudara da ta yi masa. "Jiya kin kyauta?" Ya yi mata tambayar tare da ƙara matsawa kusa da ita. "Ka yi haƙuri don Allah." "Babu komai na fahimta, dama samun matsayi a cikin zuciyarki ba abu bane mai tsauƙi. Kina da kyau da hankali sannan da ilmi dole sai na zama almajirai na miƙa ƙoƙon barata." Yadda ya yi maganar sai ya ba ta tausayi."Ka yi haƙuri duk abin da zan ka yi, ba za ka taɓa mallakar xuciyarta ba, saboda na riga na jingine aure, sannan bana tunanin akwai wani namijin da zan iya mallaka masa xuciyarta. Xuciyarta cike take da tabon ɗa namiji. Kana da kyau da kuɗi za ka iya auren wacce ta fini." Hankalinsa ya tashi sosai jin abin da ta ce. Kallonta ya yi, yana gasganta duk abin da ta faɗa a cikin zuciyarsa. "Wannan dalilin ya sa za ki tsani maza? Nasreen kamar yadda mata ba halinsa ɗaya ba, haka maza don Allah kar ki wa maza jam'i ki cutar da waɗanda za su so ki. Ance yabon kai jahili, amma zan iya sanya kaina a cikin mazan da suke koyi da yadda Annabi ya gudanar da rayuwarsa da matansa. Matata akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninmu sannan ita ce murfin sirrina. Ko auren nan da zan yi, wallahi ba ta rage ni da komai ba, ina da burin auren mace fiye da daya, kuma ba ni da matsala domin mun samu kyakkyawar fahimta a nan." A karo na farko da ya fara samun matsayi a zuciyarta, jin yadda yake yabon matarsa. Ta tuna lokacin da Faruk zo ƙara aure, har faɗawa Rashida cewa bata iya kwanciya ba, sirrin da ya kamata daga ita sai shi su sani. Ya burgeta sosai domin tana matuƙar son taga namiji yana kula da matarsa, wannan dalilin Damir ya samu matsayi sosai a cikin zuciyarta duk da tsanarta da ya yi. "Ka yi hakuri duk da cewar ka burge ni, saboda yadda kake faɗin kirkin matarka, saɓanin WASU MAZAN, amma ba zan iya auren ka." Ƙara kallon ta ya yi jin yadda take gaya masa ba ta sonsa, duk da cewar ya san ba shi da makusa, amma yadda ta bayyana masa abinda ke xuciyarta, sai ta ƙara burgesa." To shikenan na gode da kika bayyana mini abin da ke zuciyarki, amma za ki iya ɗaukana a matsayin aboki?" "Dariya ta saki jin abin da ya ce,"Babu abota a tsakanin mace da namiji, amma na ba ka matsayin ɗan'uwana." "Ina godiya domin matsayin da aka ba ni yafi wanda a nema ƙanwata." Ita ma dariya ta yi jin abin da ya ce. A tare suka jera suka fara tafiya. Damir tsaye a cikin ofis ɗin da yana kallon windo. Tunanin yadda zai takurar mata yake yi, saboda ya tsani ganinta a cikin campany. Ji yake yake ganin Marwana ba ta yi masa adalci ba, domin duk lokacin da ya tuna sai mutuwar Batula ta dawo masa sabuwa. Ga shi tun da ta fara aiki ba ya iya minti biyar, ba tare da ya tuna maƙiyiyarsa tana cikin campany ba. Yana buɗe windon idanunsa suka hango masa ita, da Ingawa suna tafe suna murmushi suna dariya. Wani irin ɓacin rai ya ziyarci zuciyarsa. Da sauri ya saki labulen yana jin yadda zuciyarsa take tafasa tamkar za ta fito waje. "Mai yarinyar nan take nufi?" Ya yi ma kansa tambayar dai kuma ya ba wa kansa amsa da cewa,"Tana nufin ta kashe matata, ta bar ni cikin sha'awa da kewa, sai kuma ta biyo ni cikin rayuwata tana nuna mini tana farinciki? Ina hakan ba zai taɓa faruwa ba, saboda yada ta raba ni da matata ta bar ni cikin kewa da sha'awa haka ita ma za ta ƙare babu aure matukar tana cikin rayuwata." Ya ce tare da sakin labulen cikin fushin zai fita, sai kuma ya fasa, zuciyarsa ta ba shi haƙurin kar ya je ya yi musu rashin mutunci. Dawowa ya yi ya zauna yana tunanin abin da zai yi musu. Ya san Ingawa mutumin kirki ne domin yana cikin ɗaya daga cikin ma'aikatan da ya yarda da su. Tun da ya ga masa tare da ita aurenta zai yi,wanda hakan ba zai taɓa yiwuwa ba in har yana duniya. Wayarsa ya ɗauka ya kira numbar Muhsin. Muhsin da yake hanyar shigowa ofishinsa don ya kawo masa takaddun da ya manta da su. Ganin kiran sai ya ɗauka da nufin ya gaya masa ya ɗauko masa, domin a tunaninsa saboda takaddun ya kira shi. "Ina kan hanyar hawa ofishinka, kuma Marwana ta ba ni takaddun da ka ije a dining." Tsaki ya yi tare da kashe wayar yana jiransa. Da ya shigo sai ya ƙarasawa tebur dinsa ya ije. "Ga shi Yaya na san dama mantawa ka yi dasu." Amaimakon ya ba shi amsa, sai ya buɗe baki cikin ɓacin rai ya ce,"Ina so ka haɗa mini meeting yanzu nan, kowa ya halasta zan akwai wasu daga cikin ma'aikatan da suka ɗauki aikin for granted suna wasa da shi, zan ja musu kunni saboda wallahi duk uban da ya yi wasa da aiki, zan sallamae shi kuma ba zan samu da uban da ya kawo su ba, ko mutuwa za ta yi ba zan damu ba." Ya ce cikin fushi. Kallonsa ya yi yana mamakin abin da ya ce,"Yaya meeting at this time? Sauran ma'aikata ba su gama zuwa ba, saboda har yanzu akwai fifteen minutes lokacin ya cika." "I don't bloody care, haɗa mini meeting na gaggawa, kuma duk wanda bai zo ba sai na cire kuɗin da, daga yau in har na zo kowa ya zo daga baya latti ya yi." Da sauri ya kalle shi jin tsautsaurar hukuncin da ya yanke." Ya Damir lafiya, why all this passive aggressive things?" Ya tambaye shi ganin yadda ya bircike. "Go and tell them the meeting will hold in the tree minutes, duk wanda ya wuce lokacin ba tare da ya shigo ba ni da shi ne, sannan har da wannan yarinyar da Marawana ta kawo." Ya ce tare da wucewa ɗakin taron.. Da sauri ya fita daga ofishin cikin damuwa jin ƙayyadadden lokacin da ya ba su. Mamakin abin da ya tunzura zuciyarsa lokaci guda yake. Ya san lafiya suka rabu a gida har yana gaya masa ya tsaya ya gama abin da yake yi."To mai ya faru ya yi sa kansa tambayar cikin rashin amsa." A lokacin da ya da sanar da taron mamaki ya kama su, amma saboda lokacin da ya bayar dai suka fara tashi da sauri suna tunanin dalilin taron." Nasreen tana zaune tana waya tsaƙon ya riƙe ta. Da sauri ta miƙe tana zare idanunta."Innalillahi! Na shiga uku meeting yanzu har da ni?" Ta yi wa Khausar tamabayar tana zare idanu. "Ok, tambaya kike yi? Ki ga na tafi ga Hajar can ta kusa shiga." Jin haka ya sa ta ja kujerar da take zaune ta bi bayanta. A hankali take taku har ta isa cikin dakin taron. Ba tare da ta ɗaga idanunta ta kalli kowa ba ta nemi guri ta zauna. Zuciyarta bugu take yi haka kawai ta tsargu game da taron da ya haɗa. "Innalillahi! Kun ga yadda yake fushi yana nishi kamar mesa? Allah ya da ba haɗiye mu zai yi ba." Hajar ta furta cikin raɗa tana kallonsa. Jin abin da ta ce sai ta ɗaga idanunta tana kallonsa. Da sauri ta mayar da idanunta kasa tana fatan kar ta ƙara kallonsa. Ɗakin taron ya yi shiru ba ka jin komai sai ƙarar A.C da bugun zuciyoyinsu suna tunanin abin da zai ce. Cikin fusata ya buɗe baki ya fara magana ba tare da ya kalle su ba."Saboda na sakin muku da yawa, har kina da lokacin da za ku zo kuna tsayawa hira? To daga yau na kafa dokar zuwa gurin aiki kafin na zo, kuma ba zan gaya muku lokacin da zan zo ba, duk wanda ya sake na riga shi zuwa ya kori kansa, don ba kuɗin banza na ke samu hada har na ke biyanku kuna zuwa lokacin da kuka ga dama har ku tsaya hira ba, sannan waɗanda ba su ba, in suka zo ku gaya musu na ba su hutun wata ɗaya, kuma babu albashi." Maganar da ya yi ya bawa kowa mamaki. Dakin taro sai ya fara surutu ƙasa-ƙasa, kowa na mamakin dokar da ya saki. Kallonsu da ya yi yasa suka yi shiru. Ta shi ya yi ya fice ba tare da ya samu da yadda suke kallonsa ba. Muhsin ya mike da sauri ya bi bayansa yana mamakin dokar da ya sanya, da kuma tunanin abin da ya sanya shi dokar. Nasreen tun da ya fara magana, ta kasa daga idanunta ta kalle shi har ya gana ya fice. Mamaki take yi saboda ko ita kanta dokar ta yi mata tsauri. Idan ta tashi tana samu ta yi sallah da asuba, sannan ta yi karatun Alkur'ani, bayan ta yi azkar ta shirya Raihann har ta haɗa musu abin kari. In har ya sanya wannan dokar ta yaya za ta yi ga shi tana tunanin sanya Musaddik a makaranta? Kuma ta yaya zai kafa dokar tun da ba shi da takaimainan lokacin zuwansa?" Irin tambayoyin da take yi haka sauran ma'aikatan suke yi. Ganin surutun ba mafita bane, sai suka tashi kowa ya nufi gurin aikinsa. Da ya shiga cikin ofis yana zaune P.A dinsa ta shigo."Sir, ga shi na gama singing ɗin, zan kai wa Hajar da Khausar su ƙarasa aiki." Ta furta cikin sanyi da girmama. "Ok, shi kenan files ɗin?" "No akwai wasu zan ƙaro." Good ya ce yana murmushin mugunta."Ki haɗa su duka ki kawai wannan sabuwar ma'aikaciyar wacce take kusa da ofis ɗin S. Ɓako. Ki gaya mata kafin awa uku ta gama aik.." Zare idanunta ta yi tana kallon sa."Awa uku sir? Ko ni sai da na yi kwana uku ina yi, sannan aikin ba nata bane na..." "Will you shut up!" Ya daka mata tsawa tare da miƙewa. "An sorry sir." Ta ce tare da fara ƙwasan files din za ta fita. Tsaki ya yi, ya koma ya zauna ba tare da ya ce mata komai ba ya ɗauki wayarsa. Cikin mamakinta isa ofishin na ta tana tunanin uban aikin da ya ba ta. Da sallama ta shiga. Amsawa ta yi tana kallonta "Ga shi in ji oga Damir, ya ce na kawo miki za ki kawo nan da awa uku." Zare idanunta ta yi bayan xuciyarta ta buga jin abin da tace, sai kuma mamaki ya kamata ganin uban akin."Sister Salima wannan aikin a cikin awa uku? " Ta tambaye ta fuskar ta da mamaki. "Am sorry that was what he said." "Ok," Kawai ta ce tare da fara duba takaddun cikin mamaki. "Have a nice day." Ta ce mata sannann ta fice daga ciki. Jaɓar ta zauna tana share zufa. A ranta ta san kawai so yake ya wulaƙanta ta, amma in har ba ijin bace ita ba zata iya gama aikin ba. Idanunta suka kawo ruwa sai ta yarda da zargin da xuciyarta take yi kan meeting da ya haɗa. Fara aikin ta yi cikin ɗaurewar gwiwa saboda ta san duk takura kanta ba za ta iya gamawa ba. Tana cikin aikin ta yi nisa hankalinta yana kai. Ingawa ya yi sallama tare da murɗa ƙofar ya shigo. Ganin yadda hankalinta ya ɗauki ya ƙaraso."Ƙanwata haka kika yi busy?" Ya ce mata tare da ɗaukar files ɗin yana dubawa. "Eh wallahi tun safe?" "Waya kawo miki wannan aiki saboda na su Hajar ce?" Kallon sa ta yi ta ce,"Oga Damir ne ya ba P.A ta kawo mini." "Shi da kan shi? Na yi mamaki saboda ba aiki ki bane." "Wallahi kuwa kuma awa ɗaya da rabi na kai masa, saboda ya ce awa uku ya bani." Dariya ya saki yana kallonta."Wasa yake miki wataƙila, domin ko shi kansa a wuni ba zai iya gamawa ba ballantana ke." "He is serious ba ya wasa da ni." Ta furta cikin gajiya. Ganin yadda fuskarta ya yi na don ta gama aikin sai ya yarda."I don't know why he is so strict kwana biyu. Ki na jin nonsense dokar da ya kafa?" Ajiyar zuciya ta yi kawai ba tare da ta ce komai ba."Nasreen, komai za ki yi ba fa za ki iya ba, just do you best ki je gobe ki ƙarasa." "Ya zan yi? Ta ce da gaske yake so." "You are not a robot, amma bari na taimaka miki." Ya faɗa tare da zaunawa kusa da ita ya ɗauki files ɗin "Ka bar shi kai ma kana da aiki." "Kar ki damu sister." Ya ce. "Na gode." Ta furta tana kallon sa ganin yadda yake kallonta. Ƙasa da kanta ta yi suka fara aiki. Yana mata hira sai dai ta amsa da um a'a, ko ta yi murmushi. Gabakiɗaya hankalinta a kan aiki. Hirar ya ci gaba da yi mata, bature da ya kula da jan ajin da take ma ba, domin so yake ya sanya shaƙuwa da soyayya yadd za ta aminta da shi. Damir yana zaune a ofis ɗinsa, tun lokacin har yanzu zuciyarsa tafasa take yi. Ba ya son a taya ta aikin so yake ta kasa ya yi mata tijara. Da sauri ya miƙe zai je ya gani, amma sai ya fasa yan jin girman kan ya je ofis ɗin ta. Da sauri ya kunna C.T Camera don ya gani. Zuciyarsa be ta buga ɓacin ransa ya nunku ganin su zaune suna aiki. Kaima tv ɗin duka zai yi, amma sai ya fasa ya fice daga ofis ɗin kamar kububuwa. Duk wanda ya hadu da shi ya gaishe shi. Kallon banza ba ya samu. Wasu daga cikin ma'aikatan suka tsaya gulmar, ganin inda za shi cikin fushi kamar fusataccen zakin da ya yi kwanaki a dawa babu abinci. Da karfi ya buga ƙofar har sai da ta miƙe saboda razana. "Are You stupid! Na ba ki aiki kin kira wani ya yi miki, ko ke kike biyansa da za ki hana shi na ki aikin ya yi na ki?" Ya yi mata tambayar tare da zare mata idanu. Jikinta ya kama rawa sai ta ɗago idanunta tana kallonsa hawaye fall a idanunta. Ta buɗe baki za ta yi magana ya daka mata tsawa, sai ta yi shiru hawaye yana zuba a ƙuncinta. "Ba ita ta kira ni ba, kuma ba ni..." "Please get out, kuma daga ya bana son a rinƙa taya co-workers aiki. Kasan ina ganin mutuncinka da wani ne sai na embarrassing ɗinsa." "Ok sir." Ya ce tare da juyawa ya fice bayan ya kalle ta. "Ma za ki gama a lokacin da na baki." Ya juya ya fice yana huci. Kuka ta saki tana jin ba za ta iya jure wulaƙanci ba. Duk yadda ta so ta gama aikin kafin a tashi kuma daidai lokacin da ya ba ta hakan yaci tura. Ganin lokacin ya yi tattara zuciyarta na bugu ta kai wa P.A ɗinsa. "Don Allah ki ba shi haƙuri wallahi ban ga..." "An sorry that I can help ya ce ke za ki kai masa." Da sauri ta ɗago idanuta kamar za ta yi hauka." Ba zan iya ba.." "Zuwa ya zamar miki dole gaifis ɗin." Ta nuna mata tare da wucewa bayan ta daga kafaɗunta. Jikinta ya na rawa ta rasa yadda za ta yi. Har ta juya dai kuma ta tsaya ta zare ido, cikin rashin dubara ganin saura minti uku lokacin ya cika. A hankali ta tura ƙofar bakinta ɗauke da sallama. Yana zaune da Little Marwana da take kwance a jikinsa bacci yana son kamata. Ganinta ya sha kunu ya canza daga dariyar da yake mata, yana shafa bayanta don har waƙa yake yi mata don ta yi bacci. "Um..eh. ga.." Ta kasa magana xuciyarta na bugawa, amma ganin ya mike a xafafe sai ta daure ta ce,"Ka yi hakuri saura kaɗan..." "Kin san Allah sai kin gama za ki tashi. Ke da masu gadi za ku rage." Zare idaunta ta yi dai hawaye da gudu ta fice da sauran aiki. Tsayawa ta yi a bakin ofis ɗin ta goge hawayen gudun kar wani ya gani. Komawa ta yi ta ci gaba da aikin tana hawaye. Da aka tashi kowa ya fara tafiya. Saboda kar su Hajar su nemeta, sai ta kulle ofis ɗin. Wayarta da suka kira bata daga ba, sun yi tunanin ta tafi don haka kowa ya tafi. Tana zaune har shidda maraice ya fara tana aiki. Hawaye take yi tana aiki. Wayarta ta ɗauko ta kunna don ta sanya karatun Alkur'ani, saboda tsoron da ya fara kamata, ga shi gurin ya yi shiru. Tana buɗewa messages na Ingawa suka fara shigowa. Kafin ta buɗe dai kiransa ya shigo. Da sauri ta ta katse. Tana ƙoƙarin kashe wayar tsaƙo ya shigo. "Nasreen, ki ɗauki wayata, saboda na san kina ciki baki fito ba, kuma wallahi kin ji na rantse ba zan tafi gida ba ina nan ina jiranki har sai kin gama aiki." Zare idaunta ta yi kan dole ta kira shi."Hello," Ta ce cikin muryar kuka. "Ban taɓa tunanin oga Damir mugu bane sai yau. Nasreen, akwai abin da yake tsananin ku? Don Allah mai kika yi mishi?" Hawaye suka ƙara zubo mata"Babu komai don Allah ka tafi gida na kusa gamawa." Ta ce tare da kashe kiran. Tsaki ya yi ya tura mata da cewar yana jira ta gama. Ba ta gana aikin ba har sai da aka kira sallar magariba. Da sauri ta fito bakinta ɗauke da addu'a, domin tsoro take ji sosai. Oga kale ko sir Samir wai ya haka ne😄😄😄😄 WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 23 Ba ta gama aikin ba har sai da aka kira sallahr magariba. Da sauri ta fito bakinta ɗauke da addu'a, domin tsoro take ji sosai. Tana addu'ar Allah ya sa ya tafi, amma sai ta gan shi ya fito daga masallacin kampanin hannunsa ɗauke da carbi. Ganin ta nufi waje da sauri ya fita ya shiga motar. Gabanta ya faka."Ki shigo na kaiki gida saboda na san cewa Mama hankalinta ya tashi." Ba musu ta shiga domin ta gaji matuƙar gaske! Idanunta har wani zafi-zafi suke mata. "Mai ke tsakaninki da shi? Tabbas kin san shi kuma akwai alaƙar da ya taba haɗaku?" Ya yi mata tambayar tare da waiwayo wa ya kalle ta. "Tabbas mutumin kirki ne tun da har kai sai daka zargi na yi masa wani abu. Ba zan gaya maka ba, wataƙila ka tsane ni." "Ba zan taɓa tsanarki ba saboda Allah ya sanya mini sonki." "Ka yi hakuri bana fatan tuna abin da ya faru." Ta ce masa cikin hawaye. Ganin haka ya ja bakinsa ya yi shiru, yayin da zuciyarsa take ta tunani. Da suka kofar gida sai ya kalle ta daidai lokacin da ta buɗe ƙofar."Na gode da kulawarka. Hakan ya tabbatar mini da na samu Yaya mai kaunata." Murmushi ya yi yace,"Kin cancanci haka ki shiga gida ki yi wanka sannan sallah ki huta Please kin gaji." "Na gode sai da safe." "A gaida Yarana da Mama." Ɗaga masa kanta ya yi sannan ta fice daga motar. Tana ƙoƙarin shiga sai ga Baba ya fito."Nasreen lafiya kika daɗe haka?" "Aiki ya tsare mu." Ta ce masa tare da shiga ciki. Juyawa ya yi ya koma dama yana ta jiranta ta dawo ta ba shi kuɗi. "Hankalina ya tashi sosai na kira wayarki a kashe, mai ya faru kika daɗe?" Mama ta yi mata tambayar ba tare da ta amsa salamar ba. "Aiki ne Mama yau kowa sai lokacin da na tashi aka tashi." Ta yi mata ƙaryar haka. "To hankalinsa ya kwanta shiga ki yi sallah ki huta." "To,"Ta amsa tare da ɗaukar Musaddik tana shafa kan Raihann. "Ki aje yaron nan ki je ki huta. Ke Raihan zo na sa ya muku tuwo ku ci, kamo hannu Musaddik ku bari ta huta." Mama ta ce tana janyo robar tuwon da ta gama. Sakin hannunta ta yi suka shiga ciki. Tana shiga cikin ɗaki ta fashe da kuka takaicin abin da ya yi mata. Tana cikin kuka wayar Marwana ya shigo. Kamar ba za ta dauka ba, sai kuma ta share hawaye ta ta daga wayar da sallama. "Nasreen kina lafiya?" Ta yi mata tambayar jin muryarta. "Lafiya lau gajiya ce." "Na ga Ya Damir y shigo cikin ɓacin rai. Ya Muhsin ya gaya mini abin da ya faru, so dai suka bar ki a kampanin. Mai ya faru?" "Jin tambaya ya sa ta fashe da kuka."Wallahi ban san abin da na yi masa ba. Ina ganin aje aikin nan zan yi..." "No, kar ku yi tunanin haka Nasreen. Aiki shi ne gatanki, kuma a tunanina zaman da kika yi da Faruk kin daina wa namiji kuka. Ya Damir mutum ne mai sanyi, in har za ki daure wallahi ba zai ja da fadanku ba zai sauko." "Hmmmm! Haka kika ce saboda dan'uwanki ne." "Zan shigo za mu yi maganar gobe. Ko ce Mama ta yi mini dambu gobe." "In sha Allahu sai kin zo." Ta ce tare da kashe wayar. Bayan ta yi sallah ta huta, tana zaune tana takaicin abin da ya faru. Kiran Ingawa ya shigo wayarta. Da sauri ta katse tunaninta ta ɗauka. Hira sosai sukayi har sai da katin ya ƙare. Sosai ta sake da shi ganin mutuncinsa, kuma kalaman da yake gaya mata yana sanya tana jin daɗi, har take gane ashe ita na tana daga cikin mata masu daraja da da namiji zai rinka gaya mata kalamai masu dadi. Duk da cewar suna ya da ƙanwa ne, amma maganganunsu duk na soyayya ne. Burinsa ta amince da shi akwai ya yi wuf da ita. Da suka gama wayar kwanciya ta yi xuciyarta cike da tunaninsa. Faruk Faruk zamansu da Rashida ya yi daɗi tun da yaran suka koma gurin Nasreen ba. Bai yi tunanin zuwa ba kamar yadda ba ta kira shi a game da yaran. Hankalinsa ya kwanta dai ya ci gaba da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali, domin ya shanye mangaron ya yarda ƙwallon ya huta da ƙuda. Hankalinsa kwance, yake shan soyayya da Rashida yana jin ya huta da maular Baba. Rashida kuwa hankalinta ya kwanta, ta kara ƙiba ta zama ƙatuwa da kyar ake juyi. Kullum cikin yi masa asiri take yi tana ba shi yana sha. Da wannan ta samu ta shanye jikin saura kan ta mallake sa. Abinci kuwa saboda yadda ta samu kansa komai yan siyen mata, rayuwa ta canza komai ta ga dama shi take yi. Miji da gida ya zama nata. Soyayya suke ci sosai kamar za su lashe kansu, saboda duk abin da ya ce ta yi masa babu shakka ko kunya. A gadon ma, yadda yake so haka take masa harma da abin da bai bukata ba. Hankalinsa ya kwanta ya samu macen da yake so. A yanzu komai na sa ta san sirrinsa, duk wani abun da ya mallaka sai ya gaya masa. Hatta ATM dinsa da ake ɓoyewa yanzu duk ta sani domin ya canza daga maƙoƙo ya zama mai sakin hannu. Kayan ɗaki komai ya canza mata. Hatta kayan kallo su da ya canza mata. An sanya su solar ya siya mata waya mai kyau. Da ta sanya masa naci, har mota ya daure ya siya sai ya gyara mata nasa. Da fari ana zaman lafiya sosai tana cin duniya da tsinke, amma ganin ta samu kansa sai kawai ta bawa 'yan'uwanta ƙafa su rinƙa zuwa maza da mata. Nan fa ya buga tsalle ya ce bai yarda ba, saboda rashin son mutane a jininsa yake. Ga kuma rowar abin da zai ba su ciki. Rigima sosai suka yi da ƙyar ta samu ta shawo kansa ya amince. Daga baya sai ta ɗauƙo ƙanwarta Maimuna ta sanya ta a makaranta za ta ƙaranci English language. Ya nuna ɓacin ransa sosai, musamman da ba ta yi shawara da shi ba har korar ta yi yi, amma ta dawo ita tursasawar Rashida kan dole ya barta ta zauna. Babu yadda zai yi haka ya ƙyaleta ta zauna. Aci wannan a dafa wannan. Ɗakin Nasreen aka ba ta da komai da komai. Hatta kaya ta ya ce ta ɗauka, wanda bata so ta yi kyauta da shi. Rayuwa ake yi mai daɗi sosai domin ya saki ya canza. Ta mai da shi irin janitalau komai dai abin da ta ce masa. Danginsa sun yi matuƙar mamakin haka, sanin wane ne Faruk, amma ko da suka shigo dan su tsawatar rashin mutunci ta sanya ya yi musu, sannan ya ja musu iyaka da shi. Sai suka zuba idanu suna tausayin ranar da zai yi nadama. Haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya musu cikin farin ciki. Ƙwasam Rashida ta samu ciki ta fara ciwo amai da laulayi. Nan take Faruk ya daka tsalle ya ce sai da a zubar, yayin da ta kafe kan baza ta zubar ba. Rigima sosai suke yi da shi, saboda cikin, suka rasa zaman lafiyar da suke yi. Tuni ya canza mata babu tausayi sai ma kyamarta da yake yi. Ga shi irin laulayin ta mai zafi ɗin nan, saboda tun da ta samu cikin ta daina wanka in har ta yi wanka ranar ba za ta kwana lafiya ba. Wani irin miyau take tarawa sosai a bakinta, saboda miyau ƙatuwar roba ta samu take tarawa. Idan ta zuba miyau Faruk dai ya ji kamar zai yi amai, domin sai gabakiɗaya kayan hajinnsa sun motsa. Ya san Nasreen tana laulayi har da amai, amma ba ya wuce sau biyu ko ɗaya. Ita kuwa tun da ta fara laulayin kullum da safe kafin ta ci komai sai ta yi amai, don ya zame mata ƙa'ida. Sabida aman datake yi ko cokali ta ɗauka baya iya taɓawa. Duk iƙirarin son da yake ma jikinta baya iya zuwa kasa da ita, domin ji yake tana wani irin wari kama da na albasa. Farouk duk ya takura kansa ko gidan zai shigo gabansa sai ya faɗi. Babu irin rarrashin da bai yi mata ba, kan a zubar da cikin, amma ta rantse sai ya fito duniya. Tun daga lokacin ya ɗauke mata wuta, kullum cikin fada da jaraba yake yi. Ƙanwarta kuwa ya rantse sai ta mayar da ita. Tun tana tunanin wasa ne har ta ɗauka da gaske. Magani kuwa kullum dai an ba shi, amma a banza domin rashin mutunci yake mata gane da cikin. Mamakinsa sosai ta yi, saboda ya kamata ya tausaya mata halin da take ciki. Ganin daga samun cikin, yadda ta koma sai ya yanke shawarar zubar da ciki. Ba tare da ta sani ba ya siyo maganin zubda ciki ya bata. Cikin dare ta tashi da wani irin azzabben ciwon ciki. Ihun da ta kurma ta ɗaka masa duka ya sanya shi zabura da sauri. "Farouk zan mutu cikina marata." Hankalinsa ya kwanta ganin cikin zai zuba. Da sauri ya kwashe ta sai sibiti. Ganin jini tun a hanya take ihu tana ƙunduma masa ashar, saboda ta san shi ya zubar da ciki. A ranar kuwa tasha kuka don azaba, saboda sai da aka yi mata wankin ciki. Ga shi cikin ya fara girma har ya kai wata huɗu. Da suka dawo babu irin kalar zagin da ba ta yi masa ba, amma ya ji kuma ya shanye tun da burinsa ya cika. Tun da ta warke ta hana shi kanta, saboda ta fahimci jikinta kawai yake buƙata. Tana kwance da daddare ya shigo bayan ya yi wanka ya kwanta a bayanta. Wani irin zagi da yarensu ta ƙunduma ta tashi zaune jin ya rungumota. "Wallahi ka daina taɓa jikina, saboda babu amfanin zama da mijin da ba zai bar matarsa ta haihu ba." "Tun da na zo da maganar aure na gaya miki ba na son yara. In har za ki samu ciki suka ɗari sai na zubar, saboda ina son Nasreen kafiyar da ta yi mini ya sa na yi mata wulanƙanci, in har kika kafe rayuwar da zamu yi sai ta fi nata wulanci." "A shirye na ke duk abin da za kayi, saboda wallahi bazan zauna da kai sai da ka more jikina ba, ina gani na mutu ba tare da samu magaji ba, kuma dukiyar da kake tarawa, wa kake son inka mutu ya gada?" Tambayar ya fusata shi cikin zafi ya kalle ta."Ok, dama kin aure ni don ki haihu ina mutu ku gaji dukiyar? To wallahi ba za ki haihu ba." "Sake ni Faruk ba zan iya zama da kai ba." Ta ce masa cikin zafi. Wata yar iskan dariya ya saki."Ai aurenmu babu daki dole kuma ki bi umurnina." "Wallahi in har ba ka sake ni ba, sai na yi maka abin da b za ka taɓa mantawa da ni ba, sai na zame maka ƙadangaren bakin tulu!" "Ni ma ƙwallon shege ne mu zuba mu gani." Ya ce tare da ficewa daga ɗakin Tun daga ranar zamansu ya canza. Kowa ƙoƙarin ya cusgunawa junansu suke. Soyayya da zaman lafiya duk sai aka daina. Da ya shigo sai faɗa da zagi. Ganin haka Faruk ya daina bata abinci sai ya ga dama. Kamar yadda ya yi rayuwa da Nasreen ya so ya yi mata, amma sai ta nuna ba za ta saɓu ba. Da zarar ya fita za ta shiga ɗaki makullin da ta ɗauke ɗaya na sa ta ibi abin da take so ta dafa. In ya dawo ya yi ta bala'i da zage-zage. Gidan sun mai da shi na faɗa, kullum maƙota suna jin su su yi ta tsiya. Ga shi Rashida akwai murya in ta danna masa ashar sai anji. Gabakiɗaya rayuwarsu babu tsari.A haka suka ci gaba da rayuwar. Ganin ya canza makullin ɗaƙinsa sai ta saci ATM ɗin da ta cire naira dubu ɗari. A lokacin da ya ga an yi debeting ɗinsa, tamkar mahaukaci ya dawo gida, da ya tabbatar da ita ta cire kuɗin. Yana zuwa tana kicin tana soya nama da ta siyo. Tana ƙoƙarin fitowa ya riga ta shiga. Idanu ya bi kayan da ta suyi da kallo. "Da izinin uban wa kika cire kuɗin da kika yi siyayya?" "Da izinin uban da ya aje ni, saboda wallahi ba zan zauna ka mayar da ki akuya, ba sai lokacin da ka ga damar ba n..." Marin da ya kawo mata ya hana ta ƙarashe maganar. Ba tare da jinkiri ba ta wanka masa ita ma."Ke don ubanki ni za ki za ki mara?" "Na rama nan gaba duka zan yi maka abin da ba za ka manta ba, domin wallahi in har na sanya karfi ba ka fi..." "To shikenan bari mu gwada ƙarfin." Ya ce tare da kai mata hauri ya fara dukanta. Ba tare da jinkiri ba ta fara mayar masa. Da yake karfin namiji da mace ba daya ba. Ganin yana shirin illantata sai kawai ta wawuri abin tibi da aka yi kwalliya ta maka masa iya ƙarfinta. Wani irin gigitaccen ƙara ya saki dai ga shi a ƙasa kwance jini yana zuba."Yau na yi maganin dukan mata da yake yi. Na kassara idanun sai na ga idanun, da za ka ƙara gani har ka duki wata mace." Ta furta tana haki domin ita ma ta ji jiki. Taɓa shi ta yi ganin baya numfashi. Da sauri ta ƙara girgiza shi. "Kai kar ya zo ya mutu!" Ta ce cikin tsananin tashin hankali. Da sauri ta ibo ruwa ta watsa masa, amma ko motsi bai ba. Ganin haka xuciyarta ta ayyana mata lokaci ya yi da ita za ta tsotsee ƙwallon mangwaro ta huta da ƙuda. Yana cikin jinin ta sanya hannu ta ɗauki ɗan makullinsa ta shiga ɗakinsa. Duk wata ƙaddara ta shi su da ta ɗauke takaddun. Hatta ATM dinsa duka ta kwashe tun da ta san pin. Babu tausayi ta barshi cikin jini ta gudu. Bayan ta rubutawa ƙaninsa Usman text ya zo ya taimaka masa. A lokacin da ta tura bata hannunsa. Har sai da aka kira sallar magariba sannan ya ga tsakon. Cikin tsananin tashin hankali ya nufi gidan nasa. Tun da ya get ɗin gidan a buɗe gabansa ya faɗi. Da sauri ya shiga cikin gidan tana kiran sunansa. Jin shiru babu wanda ya amsa hankalinsa ya tashi. Yana ƙoƙarin shiga cikin dakinsa, da ya ga komai an bincike sai ya ji yayi tuntuɓe da abu. Duk juriyarda sai da ya tsorata. Da sauri ya kalli gurin. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Ya Farouk!"Ya duƙa yana girgiza shi cikin tsananin tashin hankali. Ganin baya numfashi, ga jini sosai a gurin har ya daskare, ya sanya shi kurma ihu yana neman taimako. Jin ihun maƙota suka fito zuwa cikin gidan."Mai ya faru da shi anya bai mutu ba, ina matarsa?" Tambayar da mutane suka rinƙa yi kenan. Ganin tambayar ba ita ce mafita ba, da sauri aka kwashe shi zuwa asibiti. Ko da aka kai shi sun ɗauka ya mutu, amma sai suka gane yana numfashi. Da kyar suka samu ya farfaɗo sannan aka bukaci jini, saboda ya zubar da jini da yawa. Ɗinkin gurin da ya ji ciwonka yi masa. A lokacin ya farfaɗo, amma ba shi cikin hayyacinsa sai surutu yake yi. Allah ne ya taimake shi saura kaɗan idanunsa su taɓu, domin sun yi wani irin na kamar jan gauta saboda dukansa maka masa abin da ta yi a gurin. Sai da ya kwana ya wuni sannan ya san inda yake. Yana dawowa hayyacinsa ya fara kiran sunanta yana zaginta."Ni za ki kashe? Wallahi in har na warke sai na yi ajalinki." Ya ce cikin ƙara yana son ya tashi. "Ahalin yanzu ka kula da lafiyarka ba ka ganin ɗinkin da aka yi maka?" "Ina Rashida?" Ya tambaye shi cikin zafi. Yaya Asiya da take gefensa tana share hawaye ta ce,"Ta gudu bayan ta kwashe komai na dukiyarsa, motarka kawai ta bar maka." Zare idanunsa ya yi kamar zarrare. "Ina wayana kuɗin da yake account ɗina wayyo miliyoyina." Ƙarar da ya saki ya sanya na zabura cikin tsananin razana. To fa Faruk Capacity yau dai ranar babu sa'a . Rashida ina soyayyar za ki yi masa haka. Kin san dai yadda Faruk yake da kudi. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 24 Zare idanunsa ya yi kamar zarrare. "Ina wayana kuɗin da yake account ɗina wayyo miliyoyina." Ya ce tare da zunduma ihu. Murmushin takaici ta yi masa tare da miƙa masa wayar. "Tun da aka kawota asibiti ake ta cire maka kuɗi, a lokacin da Usman ya ɗauko ka, muka yi ƙoƙarin kulle account ɗin, amma ta zare komai naira dubu goma ta bar...." "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Na shiga uku wayyo kuɗina. Na rantse ba zan yarda ba, saboda ko lahira ta je sai na bita." Ya faɗa yana surutu kamar mahaukaci. "Sai ka shirya ka je inda ka jajibo ta, in ka yi sa'a tana nan to." Cewar Anty Asiya. Ihu sosai yake yi yana surutai daga ƙarshe miƙewa ya yi."Zan je inda take ba zan iya haƙuri na warke ba." "Mu je na raka ka." "Usman ya goya shi a motarsa har gidansu, amma babu kowa sai sauran masu haya gidan." Wani bayerabe ya kalli Faruk da yake shirin hauka ya ce,"Reshiidaaa ba ta nan tun da ta yi aure bata ƙara...." "Na shiga uku na lalace. Usman zan mutu wallahi account ɗina miliyoyin ne a ciki. Har da kuɗin da na karɓa na Alhaji Adamu kan maganar gidan da ya ɗora ni a kai. Usman hauka zan yi in har ta sace kuɗaɗen nan! Gara na mutu kan ta sace kuɗaɗen da na ki ci na ki kula da iyalina na tara su." Ya furta cikin razana yana zambarwa. "Ya za ka yi da jarrabawa? Yakamata mu je inda aka ɗaura muku aure." "Ta gaya mini babanta ba ta son shi, mahaifiyarta ta mutu. Wani ta samu ya ɗaura mana aure." "Wannan dalilin ya sa ya ake son mutum ya auri mai asali, shikenan ka kai kaka baro." "Wallahi kuwa, saboda gara na mutu da ace na rasa wannan kuɗin, domin ba zan iya daukar ƙaddararsu ba." "To kashe kanka za ka yi?" Ya yi masa tambayar cikin jin haushin abin da ya ce. "Ina ga hakan ne mafita mutuwa kawai yafi a gareni." Ya ce tare da zabura ya yi titi yana ihu. Ganin da gaske yake yi ya kwala ihu taimaka mishi suka sanya shi a mota. Da ƙyar suka koma gida Anty Asiya na ganinsu hankalinta ya tashi. " Da gaske ta gudu da kuɗin ko?" "Ba ta domin babu labarinta." "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!Faruk ka jawa kanka asara. Kana zaman ka da matarka mai kirki, ka je ka auro yare ga shi nan ka jawa kanka." "Anty Asiya ki taimake ni mutuwa zan yi babu kuɗin Faruk babu Faruk." Haka yake ta faɗi yana sumbatu marasa kan gado. Hauka tuburan ya fara domin yana ganin ya yi rayuwa a haukan yafi masa da zama babu kuɗi. Sosai ya zama mahaukaci domin babu maganar da yake yi dai ihu yana faɗin,"Babu kuɗi babu Faruk." Ganin ya zauce suka tattara suka kai shi asibitin mahaukata, saboda ko acan sai da aka sanya masa ankwa. Ihu yake yi yana kiran sunanta tare da kunduma mata ashar. Nasreen kamar yadda Marwana ta ce za ta zo ta shirya ta zo. Nasreen na zaune a falo ta yi sallama ta shigo. Cikin farinciki ta kamo hannunta suka zauna. Suna ta hira har wani lokaci sannan aka kira sallar azahar suka ta shi duk yi. Bayan sun idar Mama ta gama dambu ta kawo musu. Sosai take cin dambu tana santi har ta gama. Nasreen da take zabar musu material, da za su siya su ɗinka ta kalli Marwana da hankalinta yakan wayarta ta ce,"Kin ga wannan yadin yana da kyau?" Karɓar wayar ta yi tana kallo."Yana da kyau in har ya yi miki ai ya mini, amma mu canza colour ɗin." "Ok, bari ki ga wannan." Ta ce tare da karɓa ta nuna mata. Wayar ya ƙara karɓa tana kallo."Yauwa ya yi sosai kuwa." Ta ce tana ci gaba da kallon yadin. Wayar da ke hannunta na Nasreen ta fara ƙara alamun ana kira. Miƙa mata wayar ta yi tana faɗin,"Ana kiran ki." Da sauri ta karɓa, ganin Ingawa ne sai ta ije ba da ta ɗauka ba. Bayan kiran ya katse ya ƙara shigowa. Marwana da ta bita idanu ta yi, ganin yadda ta tsargu dai ta ce,"Ki ɗauka mana ba kiran ki ake yi ba?" "Eh zan kira ɗaga baya." Ta furta hakan cikin tsarguwa. "Ok, na manta a yi mantuwa tsaƙon Raihann da Little Marwana ta ba ta bari na ɗauko." "To,"Ta ce mata daidai lokacin da aka ƙara kiran Da ta fita sai ta tsaya a hanya ta kuma dawo. So take ta gane soyayya take yi. Ganin ta fita kai hannu ta amsa kiran."Yayana."Ta furta cikin sanyin murya. Jin alamun shigowar yasa ya ta ce,"Zan kira ka." Ta kashe da sauri ganin ta shigo. "Nasreen har akwai abin da za ki ɓoye mini, ko kina waya da Faruk..." "Ban yi tunanin za ki zarge ni da aikata hakan ba." "Abin ne da mamaki, ganin kin kasa ɗaukar wayar a gabana, wannan dalilin ya sanya na fita, don na tabbbatar da haka, saboda bana tunanin za ki iya ɓoye mini abu." Ganin yadda ta harzuƙa, sai ta kamata suka zauna."Yi haƙuri kunyar amsawa na ke yi a gaban ki, saboda nasan za ki yi mamakin, har na manta wahalar dana sha a gidan Faruk na faɗa soyayya." "Soyayya kike yi?" Ta zare idanunta tana tambayarta. "Shi ne dai yake sona Ingawa ne a gurin aki, amma na gaya masa ya yi haƙuri don ba zan ƙara aure ba, sai ya roƙe ni kan na amince mu zama ya da ƙanwa, saboda mutuncinsa ya sa na amince." Hankalinta ne ya tashi sosai, har sai da Nasreen ta yi mamaki. "Za ki yi aure amma ba shi ba, saboda akwai wanda na ke son ki aura, kuma ba ke ganin akwai alkhairi a auren." Kallo ta yi cikin rashin fahimta." "So na ke ki auri Ya Damir..." "Amma ba ki da hankali ko? Kin san yada ya tsane ni kuwa. Kin san abin da ya yi mini yau? Ki cire wannan mentality a ranki, saboda babu ta yadda za a yi hakan ya faru." "Babu abin da ba zai iya faru ba, in har Allah ya ƙaddara. Addu'a na ke yi kuma Allah ya ga nufinka. Ya Damir yana cikin damuwa muna buƙatar ya dawo da rayuwarsa ya samu mata. "Please Marwana stop hallucinating, it will never happen. Ya Damir ya tsane ni, babu wacce ya tsana kamar ni. Gaskiya ba ni da courage da har zan iya tunkararsa na sanya soyayyata a zuciyarsa, kin san yadda na ke matuƙar tsoronsa? Na rantse miki a gurin aiki ko sunan shi aka faɗa sai gabana ya faɗi. "Gwada za ki yi in sha Allahu za mu dace." "Hummmm!" Kawai ta ce mata, saboda maganar ta gundureta. Jakarta ta ɗauka ganin yadda ta yi shiru."Ni zan wuce, amma ki yi tunanin abin da na gaya miki." Ba tare da ta ce mata komai ba ta miƙe don ta raka ta. Har suka isa motar ta kasa magana, sai da taga za ta tayar da motar." Ki gaida Mommy." "Za ta ji ina son ki je ki gaishe ta, saboda sai ƙorafin sai dai na je gidanku, amma ba kyau zuwa namu." Gabanta ya faɗi don har yanzu tana jin nauyin Momi."Zan zo watarana." "To shikenan, sai mun yi waya." "Allah ya tsare hanya." Ta ce tare da juyawa ta shiga gida, bayan ta tayar da motar ta fara tafiya. Da ta koma gida ita abin dariya ma ya bata. Gani take shirme irin na auta ya sanya Marwana ta yi wannan tunanin. Ta kwana tana tunanin ya za ayi har Damir ya sota? Saboda tuna dokar da aka sanya a gurin aiki, tun asuba ta yi wanka ta shirya Raihann. Ƙarfe shidda ba ta yi ba ta fice daga gidan. A lokacin da ta je wasu daga cikin ma'aitan da yawa sun iso. Saboda rashin mutunci bai zo ba har sai da goma ta yi. Ya shigo cikin taƙun taƙama ya wuce ofis ɗinsa. Burinsa ace ba ta yi aikin ba ya mata tijara, saboda jiya da tunani abin da ta yi masa ya kwana. Da ya buɗe idanunsa sai ya ga Ingawa a cikin ofis ɗinta. Da ya shiga kai tsaye gurin files da ya iske masa ya duba. Ganin ta yi aikin da kyau sai ransa ya ɓace, amma duk da haka ya ɗauki alwashin sai ya tozartata. P.A ɗin da ya tura ta je ta kira ta, amma sai kuma ya fito don ya je da kansa. Nasreen tun da ta ganta gabanta ya yi mummunar fadi. Jin yana kiranta hankalinta ya tashi, har hawaye suka taru a idanunta. Cikin sanyin jiki ta miƙe xuciyarta na bugu. Da sauri ta ja ta tsaya ganin sa yana sakkowa zuwa ofishinta. Neman inda za ta ɓoye ta fara, saboda yadda ya taho tamkar fusataccen zaki. Ta san wulakanci ya shirya mata, amma ba ta ga inda za ta ɓoye ba, domin ya riga ya ganta. Tsayawa ta yi tana kallon sa har ya ƙaraso. Files ɗin ya watsa mata a fuska."Saboda ba ki da hankali, da ki yi mini abin da ba sanya ki ba? An gaya miki kuɗin banza na ke samu da zan ɗauki wacce ba ta iya aiki ba? Ko ki gyara ko kuma na sallame ki." Yadda yake maganar ya ɗauki hankalin wasu daga cikin ma'aitan. Har ma waɗanda suke ciki sai dai suka leƙo. Takaddun suka zube daidai da gangarowar hawayenta. Ta rintse idanunta tana jin tashin hankali da kunya. Ɗago idanunta ta yi tana kallon sa, ganin yadda ya cika ya batse. "Ma za ki gyara in ba haka ba sai na kore ki." Ya ce tare da wucewa yana takun taƙama. Duƙawa ta yi, ta fara kwashe takaddun hawaye yana bin kuncinta. Ji take yi za ta ake aikin saboda baza ta ɗauki wulanƙanci ba. Takaici da haushin tunanin da Marwana take yi ya kamata. Hajar da ta fito za ta kai masa aikin da ta gama, ganin abin da ya faru sai ta tsaya tana kallon sa. Da sauri ta ta ƙarasa ganin ya wuce."Am sorry Nasreen, gaskiya Yaya bai kyauta ba." Kuka ta fashe da shi tare da cewa,"Zan ije aikin ba zan iya jurewa ba." "Ki yi haƙuri mu je ofis ɗina na duba kuskuren da kika yi." Ta faɗi tare da kama hannunta suka nufi ofishin. Zama Hajar ta yi tana dubawa."Wannan aikin ai bama na ki bane, sannan ban ga abin da kika yi ba?" Ta yi tambayar tana ɗaga files ɗin. "So yake kawai ya wulaƙanta ni, har yanzu ya kasa manta abin da na yi masa." "Wannan ba hujja bace, ya kamata ya dauki ƙaddara a matsayin sa na musulmi." "Zan gaya wa Marwana zan aje aikin kawai." "Wannan ba shi ne mafita ba. Ki kaiwa Muhsin files ɗin kawai zan yi mishi magana." "To," Ta amsa tare da fita ofis ɗin. Muhsin yana zaune hankalinsa kan desktop da yake aiki a ciki. Jin buɗe ƙofar ya ɗago idanunsa yana kallonta wanda zai shigo, bayan ya ba da izinnin shigowa. Ganin Nasreen ce dai ya biya da kallo cikin tausaya, domin abin da Damir ya yi sam bai mishi daɗi ba. Miƙa masa takaddun ta yi ya karɓa sannan ta fita. Tana komawa ofis ta fashe da kuka. Tana jin Ingawa yana bugawa, amma ta ƙi buɗe masa. Kiranta ya yi tana ganin kiran har ya gaji ya daina kiran. Da ta tashi aikin tana zaune ta tura wa Marwana tsaƙon ta ke aikin. Marwana na kicin ta ga tsakon. Cikin damuwa ta fito motarta zuwa gidan. "Mai ya faru za ki aje aikin?" Ta yi mata tambayar ba tare da bari sun amsa sallamar. Mama ta kalle ta cikin mamaki ta ce,"Ake aiki kuma? Mai ya faru saboda ba ni da labari." "Nima yanzu ta yi mini text wataƙila aure za ta yi, saboda soyayya take yi Mama. Kila mijin da za ta aura baya so." "Auren babu laifi, amma aikin yana da amfani " Mama ta ce tana kallonta. Dariyar takaici ta yi sai hawaye."Ya Damir ba ya son ganina kora da hali yake mini, saboda in kika ga yadda ya tozarta ni sai kin tausaya mini, kuma wallahi na yi aikin da ya sanya ni daidai." Ranta ya bace sosai musamman da ta ke hawaye."Don Allah kar hakan ya sanya ki aje aikin, zan yi wa Momi magana daga ya bazai ƙara faruwa ba." Ta furta tare da share mata hawaye. "Ki bari na bar aikin kawai, saboda yanada gaskiya. Bai kamata ace yana ganina, bayan na wargaza masa farincikinshi, kuma bana son na ƙara baƙi jini a girinsa, domin in har kika gaya mata ta yi masa faɗa zai ƙara tsanata." "Zan yi mata magana ta yi masa faɗa, kuma in sha Allahu ba zai ƙara ba." Ta jima tana bata baki sannan ta yi mata sallama ta tafi. A lokacin da ta koma Hajiya tana sallah a ɗakinta. Saboda ba ta sallah Zama ta yi tana tunanin yadda za ta ɓullo ma lamarin. Jin motarsa ta miƙe don ta shiga ciki ta sanar da Hajiya, amma sai ta ga Hajiyar ta fito daga dakinta. Damir yana shigowa ya harari Marwana"Hajiya zan sallami yarinyar da Marwana ta kawo, saboda ba zan iya biyan kuɗi ba ta aiki ba." Ya ce cikin zafi yana kallonta. Muhsin haushinsa yake ji, tun abin da ya faru don haka ya fara hawa sama ba tare da ya tsaya ba. "Momi kin ga wulaƙancin da Ya Damir ya yi mata? Ki gaya masa ya fita cikin rayuwarta ni na ɗauke ta aiki ba shi ba." "Ke Marwana ki iya bakin ki yayanki ne. Ka kuma Damir babu ruwan ka da ita." Ta furta tana kallon su. "To shikenan tunda kina nuna kina da share a kamfanin, zan rinƙa biyanta da kuɗinki ko da ace ba ta zuwa aikin." Ya ce fuu ya yi sama. Momi za ta yi cikin takaici domin lamarinsa na damunta. Tun daga ranar babu ruwanda da ita. Ta ci gaba da aikinta cikin kwanciyar hankali. Tsakaninta da Ingawa kuwa sai abin da ya karu, saboda tun ana ya da ƙanwa har aka fara soyayya. Ita kanta mamaki tayi yadda ta aminta da shi, domin a tunaninta ita da ta ƙara aminta da wani ɗa namiji ba, amma sai ga shi fara jin soyayyar Ingawa a xuciyarta. Ko dayake baza ta ga laifinsa ba, domin a dalinsa ta gane tana da ƙima da daraja. Kalaman da yake gayamata suke matuƙar tasiri a xuciyarta. Ya iya kwantar da kai ya samu zuciyar mace, sannan hannunsa a sake yake. Kullum hidima yake da rayuwarta da yaranta. Kayan wasan da ya siya musu har yawa ya yi musu. Sosai ta sake da shi in har ba aiki take yi ba, wuni suna online. A gurin aiki suke ɓoyewa, saboda babu wanda ya san suna soyayya. Saboda yadda ta Marwana ta nuna ɓacin ranta, dun daga ranar ba ta ƙara bari ta zargi wani abu ba, ta ci gaba da soyayya da Ingawa hankalinta kwance batare data ƙara tunanin maganar da ta yi mata ba, domin ta san babu hanyar da zata iya jawo hankalin Damir gareta. Mutumin da inya ganta kamar ya ga kashi. Kullum tsanarta kara nunkuwa yake a zuciyarsa. Ranar safiyar Laraba ya kasance birthday ɗinta. Ita har ta manta da ranar sai da safe ta ga tsaƙon Ingawa na wishing. Murmushi ta saki ta kara ta tsakon fiye da sau ɗaya, sannan ta ije ta yi wanka. Saboda birthday ɗinta ta yi kwalliya mai kyau. Kuma ta yi wa su Zainab alƙawarin in ta dawo Marwana ta ce za su fita PG. Sosai suka yi murna suna jiran dawowarta. Kallon kanta ta yi cikin mamaki ganin yadda ta canza. Idan aka gaya za ta yi kyau da ƙiba haka sai ta ƙaryata. Murmushi ta yi ganin yadda fuskarta ta kyau, domin ita kanta burge kanta ta ke yi. Turare mai sanyin ƙamshi ta fesa, sannnan ta ɗauki jakarta ta fice bayan ya yi wa Mama sallama. Saboda kyan da ta yi har yangan tafiya take yi, domin abayar ta yi mata kyau. Da ta isa kampanin ta buɗe get ɗin, daidai lokacin da motar Ingawa ta sawo kai. Murmushi ta sakin masa tare ɗaga masa hannu. Kallonta ya yi ganin yadda ta yi kyau. Ganin za ta shige da sauri ya kashe motar ya fito. "Nasreen," Ya ƙwala mata kira ya tahowa inda take da sauri ya ƙaraso. Matsawa ta yi can dan lungun da babu mutane sosai. Murmushi ta sakar masa. "kin ga yadda kika yi kyau kuwa? Anya yau zan iya aiki." Kunya sosai ya ba ta, ganin yadda yake kallonta kamar zai cinye. Karka manta birthdayna ne." "Ina zan manta da wannan ranar! Shi ya sa na siyo kyauta don na bada." Ya ce tare da ya hannunsa cikin aljihunsa ya zobe mai kyau. "Happy birthday Nasreen kawo hannunki na zura miki." Yadda ya yi maganar da kashe ta da idanunsa, da ya yi suka sanya ta jin kunya sosai. Da sauri ta zare idanunta, tare da kai hannu za ta karɓa a maimakon ya zura mata. Ɓata fuska ya yi."Don Allah ki tsaya na sanya miki please." Ya yi maganar cikin shagaɓa. Sai ta kasa cewa komai tana kallon shi. Mamaki take yi ji take kamar ba ita ba. Daga bayan su Damir ne a gefensu yana ƙoƙarin kiran waya. Saboda tankin ruwa da ya ɗan kare shi ba su gan shi ba. Duk maganganun da suke yi a kunninsa. Wani irin bugawa zuciyarsa ta yi lokacin da ya juya zai shiga ciki, ganin ba samu wanda yake kira ba. Nasreen ya gani ta miƙa hannunta Ingawa yana murmushi zai sanya mata zobe. Ji ya yi jiri ya ibeshi lokaci guda zuciyarsa ta buga. Kansa ya sara ta kamar zai fashe. Idanunsa suka yi ƙanana saboda tashin hankali. Tun ranar da Momi ta ce ya fita cikin rayuwarta. Ya ji haushi ko sunanta ba ya son ji, amma kuma abu ɗaya da bai gane ma zuciyarsa ba. Kullum sai ya tuna yana jin haushinta, musamman dai ya shiga yanayin dayake bukatarka matarsa wacce za ta kula da shi. A wannan yanayin Allah kaɗai ya san haushin ta da yake ji, domin shi ma namiji ne dayake buƙatar mace. Alƙawarin da ya yi wa Batula kawai yake mantar da shi wannan yanayin, sannan duk a cikin mata, har yau bai ga wacce zai iya mallaka mata jikinsa. Ransa ne ya ɓace, idanunsa suka yi ja har ya ji jiri yana ibansa WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 25 Ransa ne ya ɓace, idanunsa suka yi ja har ya ji jiri yana ibansa. Mamakin hakan da ya ji ya yi, sai ya fara tafiya da sauri zai bar gurin, amma tamkar an riƙe shi a gurin ya tsaya. Yana gurin har ya kusa zura mata zoben. Ga mamakinsa sai ya ji ya fara taku cikin ɓacin rai zuwa gurin. Gabakiɗaya hankalinsu na kan yatsunta da ya sha adon lalli zai zura mata. "Na ɗauke ku aiki ina biyanku, kuna amfani da lokacina kuna shirmenku?" Da sauri suka ɗago idanunsa suna kallon shi. Jikin Nasreen ya fara rawa har ta ji ƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba. Hawaye ya fara sauka a kuncinta. Sun kasa ce masa komai har Ingawa, domin bai taɓa tunanin zai zo gurin ba. Ganin sun yi shiru sun kasa cewa komai, sai ya ci gaba da magana." Ina ganin ka mutumin kirki ashe mara kamun kai ne kai?" Ingawa ya daure yana kallon sa ganin yadda ransa ya bace, kamar ya ga su suna aikata masha'a sai ya ce,"Wallahi ban canza daga yadda ka sanni ba, son ta nake yi kuma aurenta zan yi. Na samu labarin ƙawar ƙanwarka ce in har zaka shige mini gaba, a shirye na ke na aur.." Wani irin kallo ya watsa masa kallon daba shi ba, hatta Nasreen sai da ta yi mamakin kallon. Ta rintse idanunta cikin tashin hankali, ganin yana matsawa kusa da shi. "ka je gidan iyayenta ɗan ƙaruna ka aureta, amma ni na wuce ƙarfin na yi maka gaba ka aureta, kuma daga yau na ƙara ganin ku a tare, wallahi saina sallame ku." Ya furta cikin ɓacin rai yana huci. Har ya fara taku sai kuma ya dawo ya kalli Nasreen da ji take kamar ta yi ihu, ganin yadda ransa ya ɓaci. Buɗe baki ya yi zai yi magana, sai kuma ya murza mata yatsunsa guda biyu, ya wuce da sauri yabar su da shaƙan daddaɗan turarensa . Har ya ɓace daga gurin sun kasa magana. Zoben dake hannunsa ya kalla, sai kuma ya ɗago ya watsa mata kallo. Kallon data kasa gane wane iri ne. Ganin haka ta fara tafiya za ta bar gurin."Nasreen," Ya kirata tare da fara taku zai bita. Da sauri ta bar gurin zuwa ofishinta hawaye sosai take yi. Ta rasa wane irin zuciya gare shi har yau ya kasa yafe mata. Yake tijarata a gaban kowa. Ingawa tsaya ya yi har ta shige. Hankalinsa ya tashi sosai ganin abin daya faru. Idanun Damir yake hangowa lokacin da yake magana. Gabansa ne ya fadi da ya yi tunanin wani abu. Ya daɗe a gurin yana tunani cikin rashin mafita, sannan ya ja jiki ya haye sama zuwa ofishinsa. Ko da ya shiga kasa aiki ya yi, yayin da zuciyarsa ke ta auna masa, fushin da ya bayyana a fuskar Damir yana tunanin wani abu. "Tabbas akwai alaƙar da ta haɗa su." Ya ce tare da cige biro a bakinsa. "Amma why ta ki gaya mini duk da yarda muka shaƙu da juna?" Ya yi wa kansa tambayar cikin damuwa. Damir kuwa da ya shiga ofis cikin fushi ya buga ƙofa. Kansa ya buga da gini tare da kaiwa bango naushi. "Mai yasa na ke damuwa da ita baya abin da ta yi mini?" Ya yi wa kansa tambayar yana dage kasa da take barazanar rabuwa gida biyu. Rintse idanunsa ya yi, yana hangen a yanayin da ya gansu. Tamkar zai yi hauka, domin zuciyarsa wani irin tafasa take yi. Yana cikin wannan yanayin Bilal abokinsa kuma yana aiki a gurin ya shigo. Ganin halin da yake ciki ya karasa yan kallon sa. "Lafiya Damir?" "Na tsaneta bana son ganinta?" "Wa kenan?" ya yi masa tambayar cikin damuwa. "Wancan yarinyar da ta kashe mini mata, sannan ta zo har kampany na ta soyayya bayan ta sanya mini tabon dana kasa aure." Mamakin abin da ya ce ya yi."Damir yaushe za ka manta da abin da ya faru? Bata hana ka aure ba, saboda Mommy ta yi maka aure amma ka saki matar." "Saboda ta sanya tabon da ba zan iya gogewa na auri wata mace ba." "Ba ta da lafi in har tana da shi hakuri shi ya fi, domin Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana, kuma ni dan har ya bana ganin laifinta." "Ai dama ba za ka gani ba, abu daya na sani tun da ta yi gigin kashe auren ta ta kuma shigo kampanin nan ba ta yi aure ba." Da mamaki ya kalle shi."To mai kake nufi, ko zuwa za kayi ta rinƙa ɓata ta a gurin waɗanda suke sonta? In ma wannan ne gara kar ka wahalar da kanka, saboda in ka hana wani WASU MAZAN zasu zo. Yarinyar tana da kyau da hankali ko ni zan iya nem..." Wani irin juyowa ya yi yana kallon sa."Get out of my office na raina ajinka." Yadda ya daka masa tsawar ya sa shi dariya."Har wani aji namiji yake da shi a gurin mace? Damir yadda ka razana ko...." Kafin ya ƙarashe maganar ya bishi wanda ya sanya shi rugawa da gudu yana fice yana dariya. "Ni na san mai zai yi." Wayarsa ya zaro ya tura wa Muhsin tsakon ya haɗa meeting na gaggawa. Kowa mamakin meeting ɗin yake yi. A lokacin da Ingawa da Nasreen suka ji sanarwar meeting ɗin, hankalinsu ya tashi sosai, domin sun ɗauka tozarta su zai yi, musamman Nasreen da ta ji kamar kar ta je. Haka dai ta daure ta shiga meeting ɗin. Yana zaune a kan kujerar sai huci yake yi. Duk wanda ya shigo ya kalle shi, ba ya fatan ya yi na biyu, saboda yadda ya haɗe fuska kamar an aiko masa da tsaƙon mutuwa. Nasreen kanta a kasa ta shigo ba ta kallon kowa. Tana shigowa ya saki tsaki cikin jin haushinta. Da sauri Muhsin ya kalle shi sai kuma kalli ƙofa. Ganin Nasreen jikinsa ya yi sanyi, domin ya fara zargin a kanta zai yi meeting. Kallonta ya yi ganin yadda ta natsu bata kallon kowa, sai tausayinta ya kama shi, saboda ya fara jin haushin tsanar da yake nuna mata. Ba tare da bata lokaci ba, ya shiga gasa musu magana yana faɗin kalaman da suka gaza fahimtaarsa. Nasreen da Ingawa kawai suka san inda zancen yake. Nasreen shiru ta yi, har wasu hawaye suke taruwa gefen idanunta. Tun da ya fara magana ba ta daga kanta ba, sai muryarsa da yake faɗin kalamai cikin zafin rai take dukan kunninta. Ingawa kallonsa yake yi wani abu yake zargi, amma ba ya son ya tabbata domin shi ne zai kwana ciki. Yana ta tsit har ya gaji ya sanar da su dalilin taron Kalmar da ta ƙarshe ya sanya cece-kucece a ɗakin taron. Suka ɗago da sauri suna kallonsa cikin mamakin abin da ya furta. Ganin yadda suka razana sai ya miƙe idanunsa a dake ya ce,"Maganar da na fada muku, duk wanda ya saɓa ya sallami kansa. Na hana soyayya a kampanin nan, saboda ban ɗauke ku don ku zo kuna mini ba." Bilal ya miƙe cikin tsokana zai fara magana."Yallaɓai kana nufin har mu da matanmu suke gurin kar mu yi soyaya?" Wani banzan kallo ya watsa masa."Eh, in har hakan na nufin waɗanda ba su da aure za su yi. Aiki na ɗauke ku baku zo kuna soyayya ba." Ya faɗi cikin zafi yana huci. Kallon sa ya yi yana ƙoƙarin ɓoye dariyarsa. Tuni ya harbo jirginsa. Ganin sun kaure da hayaniya sai ya fice daga ɗakin. Haka suka rinƙa magana kan dokar sannan suka fita. Nasreen ta yi shiru ta san cewa duk abin da yake faɗi da ita yake yi. Namijin ƙoƙari ta yi don kar hawaye su zubo mata, saboda bata son kowa ya gane da ita yake yi. Da suka fito ita da Khausar da Nasreen sai Hajar. Kallon su Hajar ta yi ta ce,"Amma fa Yaya wallahi ya sanya doka mai tsanani, saboda bana tunanin zan iya haɗuwa da ya Muhsin na ƙyale shi. Shi ma ya san wannan dokar ba za ta je ko ina ba. Haka kawai don shi baya soyayya, sai ya hana kowa? Tun da matarsa ta mutu ya kasa ɗaukar ƙaddara?" "Gaskiya lamarin ya yi tsauri ina ta kokarin gina soyayyata, sai dana samu an karɓa ya ce kar a yi soyayya? To wai mai ya faru ya sanya wannan dokar?" Ta yi tambayar cikin damuwa. "Wallahi ban sani ba, wataƙila ya ga ba a kula da aiki ne." Hajar ta ce. "Ai kuwa muna ƙoƙari wallahi." Jin suna ta magana tare da ta tanka musu ba. Sai Hajar ta ce,"Nasreen," A hankali ta ɗago idanunta da suka yi ja ta kalle su. "lafiya kin yi kuka ne?"suka haɗa baki gurin tambayarta. Girgiza musu ka ta yi ba tare da tace komai ba, sai wasu guntun hawayen da take ƙoƙarin mayar da su, suka ganganro kan fuskarta. Hajar ta kalle ta cikin mamakin hawaye."Ya Damir ya gan ki da wani ne?" Jin tambayar da ta yi mata da sauri ta girgiza kanta alamun a'a. "To lafiya mai ya sanya ki kuka?" Khausar ta tambaya tare da share mata hawayen. "Babu komai." Ta ce ta wuce da sauri. Idanu suka raka ta da shi har ta ɓule. Tana shiga ofis ingawa ya kirata. Wayar ta ɗauka ta kanga kunninta. "Ina son mu yi magana please in an tashi zan zo gidanmu." "Allah ya kaimu." Tace tare da kashe wayar ta yanke shawarar ta gaya masa kar ya yi tunanin wani abu da daban. Damir a ranar cikin ƙunci ya wuni, da ya rufe idanunsa sai ya hango ta zai saka mata zobe. Saboda takaici lokacin ta shi bai ba ya kwashi tarkacensa ya fice. A falo ya samu su Mommy suna zaune. Little Marwana tana bacci kan kujera, yayin da Hajiya ke zaune Marwana tana gyara mata farce. Ya shigo da sallama fuskarsa babu annuri. Sallamar da ya yi suka amsa."Ya Damir barka da shigowa." Marwana ta furta tare da mayar da hankalinta aikin da take yi. Bai amsa ba sai ya fara magana cikin fushi "Dama kin sanya na ɗauke ta aiki ne, don tana tara mini maza tana zawarci a kampanina?" Da sauri suka ɗago jin tambayar da ya yi musu."Lafiya mai kuma ya faru?" Momi ta yi masa tambayar tana kallon sa. "Momi kamata ya yi, ki raba Marwana da wannan yarinyar, saboda ba tada tarbiyya." "Ita Nasreen ɗin mai kuma ta yi?" Momi furta tambayar tana kallonsa. "Da idanuna na ga ta miƙa wa gardi yana sanya mata zobe a hannunta." Zare idanunsu su ka yi, saboda sun ɗauka sai ce ya ganta tana aikata masha'a, ganin yadda yake tada jijiyan wuya. Marwana sai ta yi murmushi tana kallon sa. Hajiya kuma ta jinjina kanta, suka haɗa idanu suka yi murmushi. Ganin sun mayar shi kamar mahakaci dai sai ya kaɗa kansa ya ce,"Na rantse sai na kori yarinyar nan, ko kuma na bar kampanin sai ki je ki kula da shi." "Ni fa ban ga abin faɗa ba, saboda Ya Damir sau nawa kake riƙe hannun Anty Batula ka sanya mata zobe a ranar birthday ɗin ta, yau ne ranar birthday ɗinta, wanda zai aure tane ya bata gift." Ba ta gama magana ba ta ji saukar mari."Saboda iskanci a gabana za ta rinƙa soyayyar." Dafe kuncinta ta yi ta sanya kuka."To Ya Damir mai na yi za ka mare ni?" "Saboda ke kika kawo ta duk lokacin da ta baƙanta mini a kanki zan huce." Ya ce tare da wuce wa ciki yana huci ganin kallon da suke masa. Ya fita suka kalli juna."Alhamdulillah!" Momi ta ce tare da zama tana murmushi. "Wallahi Momi kishi yake nunawa kishi ne zalla a idanunsa." "Maganarki takusa zama gaskiya." Sosai suke murna Momi kamar za ta yi tsalle. Marwana sai tsalle take tana jin dadi, ba tare da ta damu da marin da ta sha ba. Da gudu ta haye sama tana faɗin."Ina zuwa." Wayarta ta ɗauka jikinta na rawa ta kira Nasreen. Nasreen na zaune tana gyara fuskarta. Ganin kiran sai haushi yakamata, saboda duk it ta ja mata. Ɗaukar wayar ta yi tare da sallama."Hello Marwana, dama ina shi...." "Nasreen akwai abin da za ki iya ɓoye mini?" Tambayar da ta yi mata ya sanya gabanta faɗin."Lafiya mai na aikata?"Ta yi mata tambayar cikin sanyi. "Ya Damir mana kin sa na sha mari a banza saboda kishin ya ganki da wani." "Kishi ya Damir ne yake kishina?" Ta yi mata tambayar cikin zallar mamaki. "Eh, ya ce ya ganki da Ingawa yana sanya miki zobe." "Au haka ya faɗa wayyo Allah na haɗu da terere." Ta furta a ranta sai kuma ta godewa Allah da tsanar da yake mata bai sanya shi yin mata sharri ba. "Sai kuma ya ce miki kishina yake? Marwana kina wani irin tunani, saboda da kin san abin da ya yi mana za ki gane abin da yake nufi. Saboda ya taramu cewa yayi kar wanda ya kara soyayya har ma'auratan gurin." Dariya ta kwashe da shi cikin jin daɗi."Ikon Allah haka ya ce?" "Hmmmmh! Ni fa wannan aikin watarana sai dai na aiko mini da resignation letter, saboda bazan jure wulaƙanci ba." "Wallahi Ya Damir kishi ya sanya shi faɗin haka, kuma watarana za ki gane hakan." "Ki ci gaba da yarda da zuciyarki tana ɗora ki kan keken ɓera, kin san babu yadda za a yi haka ya faru." "Sai mun haɗu za mu yi magana." Ta ce tare da kashe waya ganin ta ƙi fahimtarta. Da yamma Ingawa ya zo saboda ya kasa barin dare ya yi. Baba na zaune ta zo ta wuce zuwa motarsa. Kallonta ya yi yana faɗin,"Oh ashe dai jinin masu kuɗi a jininki yake dubi yadda kika samu daƙwale yana ba ni kuɗi ko ban tambaya ba." Motar ta shiga ta zauna tare da gaishe shi.Kura mata idanu ya yi na wani lokaci, sannan ya yi ajiyar zuciya. Shiru suka yi zuwa wani lokaci sannan ya katse shirun ta hanyar cewa,"Ki gaya mini abin da yake tsakaninku, saboda a fara zargin kishinki...." Kallon da ta yi masa ya katse abin da yake faɗi yana kallonta. "Ni ka ga kishina a idanunsa, kasan mai ya haɗamu kuwa? Ya Damir ba shi da maƙiya kamata." Labarin abin daya faru a tsakaninsu ta yi. Ta share hawaye tana faɗin,"Wannan dalilin ya sa ya gane ki baya ƙaunar ganina, tun lokacin da abin ya faru ya riƙo ni, na yi nesa da shi, amma da suka dawo Marwana ta sanya rigimar sai ya bani aiki." Shiru ya yi cikin tsanannin tausayi yana kallonta. "Haka kika sha wuya Nasreen? Tabbas ban ga laifin ki na kin amincewa da wani namiji ba. Farouk azzalumi ne ya cuce ki. Haka WASU MAZAN suke ɗaukar mace ba a bakin komai ba, bayan sun manta Allah shi ya sanya mu yi aure, kuma ranar gobe kiyama sai ya yi alƙalanci a tsakanin. Duk wanda ya cuci wani sai Allah ya saka masa. WASU MAZAN suna aure ne don kawai sha'awa ba sa ɗaukarsa a matsayin bauta." WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 26 Shiru ya yi cikin tsanannin tausayi yana kallonta. "Haka kika sha wuya Nasreen? Tabbas ban ga laifin ki na kin amincewa da wani namiji ba. Farouk azzalumi ne ya cuce ki. Haka WASU MAZAN suke ɗaukar mace ba a bakin komai ba, bayan sun manta Allah shi ya sanya mu yi aure, kuma ranar gobe kiyama sai ya yi alƙalanci a tsakani. Duk wanda ya cuci wani sai Allah ya saka masa. WASU MAZAN suna aure ne don kawai sha'awa ba sa ɗaukarsa a matsayin bauta. Wannan dalilin ya sanya auren Hausa Fulani yake mutuwa. Suka ɓata mata da shaye-shayen magungunan mata, da kuma supplements don su jawo hankalin mazaje garesu, waɗanda suke jawo musu cutar kansa da wasu cututtukan. Allah sai ya saka miki domin Faruk ya zalince ki." "Babu komai na bar shi da Allah." Ta ce tana kallonsa. Shiru ya yi yana tunanin Damir ya cancanta ya aureta, kamar yadda ya hango kishinta. Haƙiƙa in dai haka ya faru shi ne ya dace ya aureta, to kuma shi da ya kamu da sonta ya zai yi? Domin sam bazai iya haƙuri da ita ba, zai ci gaba da ƙoƙarinsa idan Damir girman kansa da izza ya hana shi fahimtar yana so ta sai ya aure ta." Ire-iren tunanin da yake yi, har suka hana hirar tasu ba ta yi armashi ba, saboda jikinsa ya yi sanyi sosai. Nasreen data ta fahimci haka dai ta yi shiru tana kallonsa. Sallama ya yi matata tafi gida zuciyarsa cunkushe da tunani. Da daddare kasa bacci Damir ya yi, duk yadda ya so ya kwanta abin ya ci tura. Da ya kwanta sai ya rinƙa tuna abin da ya faru. Ganinta yake a matsayin mai son kanta. Wannan dalilin ya sa yake jin haushinta sosai. Da ƙyar ya samu bacci ya kwashe shi. Da safe sai ya tashi ba ya jin damuwar sosai, sai dai mugun haushinta da yake ji. A ranar an ta shi da ruwa sosai domin tun safe ake ruwa, kasancewar watan ogus ne. Da ruwan ya lafa ta samu ta je gurin aiki. Tana isa aka tsuge da ruwa. Haka aka wuni ana ruwa har lokacin tashi ya yi, Amma ruwa wa ake zubawa tamkar da bakin ƙwarya. A tunaninta sai ruwan ya tsaya za a tafi, ashe duk masu abin hawa sun tafi. Dama a ranar Ingawa bai zo ba, saboda zazzaɓin da ya tashi da shi. Ganin ruwan ya lafa, sai ta sauko ƙasa taga duk sun watse. Fita ta yi daga get ɗin ta fara tafiya tare da kunna lemarta. Tana cikin tafiya Damir ya zo zai wuce ta. Ba tare da ta lura da shi ba ta ci gaba da tafiya. Tun daya fara tafiya ya hango ta tana tafe da sauri. Gajeren tsaki ya ja yayin da zuciyarsa ke kimtsa masa ya rage mata hanya. A maimakon ya bi abin da take kimtsa masa, sai ya rage gudun motar. Yana bin bayanta a hankali har sai da suka zo gurin da ruwa ya taru. Da sauri ya ƙarasa gurin, ya watsa mata ruwa sannan ya wuce yana murmushin mugunta. Nasreen da ba ta san da haka ba, ji ta yi ruwa ya wanke mata fuska har kayanta. Saboda rashin sanin faruwar hakan sai kawai ta firgita, ashe kwalbati ne kusa da ita ta faɗa. Ƙara ta saki tana kiran sunan Allah! saboda hannunta da ya amsa ƙas! Sannan ta ji ciwo a hannun da gwiyar ƙafarta. Da ta yi ƙoƙarin ta tashi dai ta kasa kawai sai ta saka kuka. A zuciyarta ta sanya ko mai Marwana za ta yi mata, ba zata ƙara zuwa aikin ba. Wani irin haushi da takaici ya kamata, har ta ji daga yau babu sauran ragowa a tsakaninsu. Ganin ta kasa tashi ya sanya ta tsaya kawai tana hawaye. Wani mai mashin ya zo wucewa ya ganta a cikin kwalbatin. Shi ya taimaka mata sannan ta miƙe ta hau mashin ɗin. Asibiti ya kaita jin tana ta kuka da hannunta. Ko da suka je aka sanar mata da ta yi tsaguwar kashi. Rintse idanunta ta yi tana jin tsananin zafin yana shiga ƙwaƙwalwarta. Kallon hannun ta yi yadda ya fara kumbura. "Za mu yi miki ɗauri bayan mun gama goge ciwon da kika ji." Kanta ta ɗaga tare da rintse idanunta saboda yadda hannun yake mata zafi. "Ni zan wuce ki kira gidanku sai ki gaya musu."Ɗan achabar ya furta yana kallonta. "Na gode Allah ya saka da aikhairi, amma don Allah ka bani wayarka na kira gidanmu, saboda wayata ta lalace." "Ok," Mai mashin ɗin ya ce tare da miƙa mata wayarsa mai botira. Mama tana zaune cikin damuwa tana kallon wayarta. "Wai har yanzu wayar Anty Nasreen ba ta shiga?"Zainab ta yi mata tambayar ganin yadda ta damu. "Tun ɗazu na ke gwada layin, amma baturiya take magana. Ko za ki kira Musa ki Yusuf su dubo ta." "To ki kira Anty Marwana ƙila suna tare, ko ta san inda take." "Kuma haka ne bari na kira ta." Ta ce tare da danna numbarta. Bayan sun gaisa sai ta ce,"Marwana Nasreen ko kuma tare, saboda tun da ta ke aiki ba ta dawo ba, kuma ina ta kiranta baya shiga." "Ba ta zo ba kuma mun yi waya da ita gab da za ta tashi. Ko dai ruwa ya sanya ta fake a wani gurin?" "To Allah dai ya sa haka, amma da za ta kira."Mama ta ce gaban ta yana faɗi. "Bari na zo zan kira su Khausar." "Da kin kira su ba sai kin zo ba, saboda har yanxu garin cida ake yi ga kuma hadari." "Bari na kira su to." "Allah dai ya sanya lafiya." Ta ce mata tare da kashe wayar. Marwana Khausar ta kira, amma sai ta ce mata."Wallahi ban zo da motata ba, kuma na ɗauka da Ingawa za su tafi." Kashewa ta yi ta kira Hajar, ita ba ma tare suka dawo ba. Wayar Nasreen ta ci gaba da kira amma a kashe Tana ƙoƙarin ƙara kiran wayar kiran Mama ya shigo. Cikin sauri ta ɗauka saboda ta fara shiga damuwa."Mama duk sun ce ba tare suka tafi ba, amma in sha Allahu tana lafiya, bari na sanya a tura mini numbar Ingawa." Jikinta ya yi sanyi, damuwa ya ƙara kamata jin abin da ta ce. Kashe wayar ta yi, sannan Marwana ta kira Ingawa. Bayan ya amsa da sallama ta yi masa bayani. Jin abin da ta ce sai hankalinsa ya tashi."Ban jin daɗi yau ban je aiki ba. Mun dai yi waya da ita da safe, saboda mura ban ƙara kiranta ba." "A'a subuhanallahi!" Ta furta bayan ta yi masa sallama ta kashe wayar. Ɗakinta fito da makullin mota Mommy ta kalle ta.'Ina za ki je da daddaren nan?" "Mommy Maman Nasreen ta kira ni wai ba ta dawo gurin aiki ba." "Lafiya to?" "Wallahi ban sani ba shi ne zan je na gani." Ta ƙarashe maganar tana kallon Damir da hankalinsa yake tibi ko kallon inda take bai yi ba. "Ma za ki je to Allah ya sa lafiya." "Amin," Ta amsa tare da ficewa hankalinta a tashe. Mama bayan ta kashe wata cikin damuwa tana zagaye ɗakin. Har ta kai kofa don ta gaya wa Baba, sai kira ya shigo wayarta da sabuwar numba. Tsayawa ta yi jikinta na kyarma ta ɗauki wayar. Tana fatan Nasreen ce. "Assalamu alaikum." Ta yi sallama bayan ta amsa kiran. "Wassalamu alaiki Mama Nasreen ce." "Lafiya kina ina hankalinmu ya tashi." "Mama ina asibiti na samu tsaguwar ƙashi faɗuwa na yi." "Subuhanallahi! Wane asibiti na zo da Yusuf ko Musa?" Gaya mata ta yi bayan ta sanar mata zo mata da kaya. Hankalinta ya kwanta jin inda take. Hijabinta da ta yi sallah ta ɗauka, sannan ta shiga cikin ɗaki don ta ɗauko mata kayan. Tunawa ta yi da Marwana, da sauri ta ɗauki wayar ta sanar mata da inda take, sannan ta koma ciki don ta haɗa mata kayan. Cikin sanyi yake tuƙa motar, tamkar ba ya son ya karasa inda yake son zuwa. Zaune yake a cikin motar yana tuƙi cikin ƙwarewa. Idanunsa sanye da farin tabarau da ya ƙawata fuskarsa. Yana cikin shiga ta alfarma. Layin gidansu ya shigo, zuciyarsa na bugawa yana tunanin halin da zai cidda su. Iya lokacin daya ɗauka ba tare da ya gansu ba ya sanya zuciyarsa bugu. Can nesa da kofar gidan, ya faka motarsa yana tunanin fitowa daga ciki. Kusan yan sakanni ya kwashe yana zaune a ciki ba tare da ya motsa ba, sannan ya yi namijin ƙoƙari ya fito tare da zare gilashin idanunsa, yana kallon unguwar cikin yanayi na kewa. Siraren hawaye suka sauka a kan fuskarsa, tuna irin rayuwar da ya yi a baya. A hankali ya fara taku zuwa cikin gidan, zuciyarsa tana bugawa na tunanin halin da zai riski mutanen, da ya sadaukar da rayuwarsa saboda su. A hankali ya yi siririyar sallama, ya buɗe ɗakin Mama yana kallon ɗakin cikin mamaki ganin wasu canje-canje. Zainab da ta ji muryar da sauri ta ɗago kanta don ta tabbatar. Idanu ta zare taba nuna shi da yatsa, amma ta kasa magana kamar wacce ciwon kurumta ya kamata lokaci guda. Sai da ta ɗauki 'yan daƙiƙa sannan ta takura iya ƙarfinta ta ƙwala ƙara. Mama na ƙoƙarin buɗe akwatin Nasreen, ta ji razanannen karan tare da kiran sunanta. Ƙarar ya gigita ta ta fito a gigice tana faɗin,"Zainab lafiya?" Ganin Zainab tsaye, numfashinta yana son ya shiɗe tana nuna mata mutum, sai kawai ta bi gurin da kallo tana mamakin wane ne. Mutumin da ta cire rai da ganinsa. Wanda take masa addu'ar samun rahma a makwancinsa. Mutumin da ta rayu saboda shi, take jin rayuwarta da nasarar ta sun jingina gareta. Mutumin da ta haife shi, amma dai ya zame mata gurbin uba da uwa. Mutumin da adalilin da ta samu hasken rayuwa. Ta haife shi da kanta, amma sai ya zame mata fitila mai haskaka rayuwarta. Ya zamo bango abin jingina da tubali mai kyawu. Mutumin da ta cire rai da ganinsa yau ga shi a tsaye gareta. Cikin shiga ta alfarma, ya zama mutum nagartacce. Ya zama wayyaye mai arziki. Jikinta ya kama rawa, domin ta ɗauka gizo da yake mata ko famarkin da ta sha yi ne zai dawo mata kamar haka take yi. Baki ta buɗe za ta yi magana, amma sai ta kasa. Hannu ta ɗaga tana nuna sa da yatsa."Ahmad kai ne ko idanuna ke mini gizon ka?" Ta furta tambayar cikin tsananin mamaki. "Ni ne Mama, nine ɗanki da yake jin ranshi fansa ne a gareki da Nasreen. Yau na dawo gareku zan zame muku bango abin jingina. Daga yau babu wanda zai ƙara nuna muku don yatsa. Zan tsaya na kula da rayuwarmu, na ba ku irin jin daɗin da na ke fatan samar muku." Mama sai kawai ta zube luuu kasa ta sume. Da sauri ya yi mata yana kiran sunanta. Kafin kace me gida ya rikice kowa ihu yake ana murna. Masu sume-sume suna ta yi Ahmad ya dawo. Babban abin da ya fi murna, wata irin ƙatuwar mota mai kama da jirgi ya zo da ita. Sannan ya zama ɗan gayu ya yi ƙiba ya ƙara girma. Kowa kallonsa yake yi, yana mamakin canzawarsa. Sai shafa jikinsa suke yi suna ihun murna. A ƙalla Mama sai da ta yi suma uku, domin abu ne tun tana sakarai har ta fara sarewa. A na ƙarshen ya rungume ta yana kuka."Mama don Allah kar ki ƙara suma walllahi nine na dawo gareki, na san na yi kuskure na nisanta kaina da na yi damu, amma a wannan lokacin hakan shi ne kawai mafita a gareni." "Ahmad ka bar ni na ci gaba da suma don na ci gaba da ganinka, bana son na dawo daidai ace mini mafarkin da na ke yi ne " Ta kamashi tana kuka tana girgiza shi. "Ba zan taba barin ki ba Mama na dawo gare ki ina Nasreen? Yanzu ne zan tsaya na yi fito na fito da Faruk. Nasreen za ta bar gidan Faruk ayau zan sanyata a cikin farinciki. Zan tsaya a rayuwarta na yi fito- na fito da Baba har sai ta samu miji na gari. "Labari mai tsawo Nasreen ta bar gidan Faruk sun rabu ai." Wani irin farinciki ya kama shi jin abin da ta ce. "Da gaske kike Gwaggo?" "Eh Nasreen ta bar gidansa mugun azzalumi. Rayuwarta ta canza duk adalilin wannan yarinyar 'yar albarka Marwana. Yanzu haka tana aiki a kamfanin su. Ka duba rayuwarmu ya canza duk a dalilinta." Hawaye ta ga yana yi tare da kabbara. Mama ta kama shi ta ce,"Mu je ɗaki na ɗauko kaya zan kai mata tana asibiti ta faɗi ta goce." Zare idanunsa ya yi, sai ya kamata hannunta suka ɗauko kayan. "Mu yi sauri Mama na kai ki a motata." Ya ce tare da ƙarasawa gurin motar. Shafa idanunta ta yi sai ko mafarki take yi."Ahmad, satan mutane ko garkuwa da mutane ka yi ka siya wannan motar mai kama da jirgi?" Ta yi masa tambayar cikin tsanannin tashin hankali. "Allah Ubangiji ya tsare ni da haka. Mu je na halin da take ciki zan yi miki bayani saboda labarin mai tsawo ne." Da kyar ya samu ta shiga cikin motar tana zare ido. Har suka isa cikin asibitin hawaye take sharewa. Suna isa ya fito da sauri ya kama hannun ta suka shiga. Burinsa ya yi toxali da yar ƙanwansa da ya yi mata laifi. Suna shiga ɗakin Mama ta hango ta, tana zaune tana dage da hannun a lokacin aka gama gyarawa. Da sauri Mama ta ƙarasa gunta."Kin ga tsautsayi sannu ya hannun?" "Da sauki."Ta furta tana cige baki." "Na zo miki da wani albishiri Nasreen." Ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushin da rabon ta ganshi a fuskarta tun ranar da Ahmad ya ɓata Xuciyarta ta buga haka kawai ta ji faɗuwar gaba."Mama mai ya faru?" "Kalli can." Ta nuna mata Ahmad dake tsaye, yana rungume da hannunsa, yana kallonta cikin tsanannin mamaki ganin yadda ta canza ta yi kyau ta zama 'yar gayu. "Ya Ahm..." Ta kwala ƙara har sai da asibitin ya ɗauka tana nuna shi da yatsa Abin da bata taɓa tunanin ganinsa a wannan rana ba. Xuciyarta cike yake da damuwar abin da Damir ya yi mata, amma kuma ya Allah ya share mata hawaye ta. Ya dawo mata da mutumin da ta ke gani a matsayin uba, uwa shi ne rayuwaarta gabakiɗaya. Mutumin da ya tsaya mata ya yi yaki da duk wanda ya zalince ta. Ya ga shi a gabanta yana kallonta ya canza ya samu kyakkyawar rayuwa "Mama ki mare ni na gane ko mafarkin da na saba ne. Don Allah ku yi ta dukana har sai na farka in mafarki na ke yi." Ta furta tana hawaye "Ba mafarki kike yi ba Ahmad ne dan'uwanki a gabanki." Sai kawai ta faɗi ƙasa ta sume ganin haka suka yi kanta. Da ta farfaɗo kuka take yi tana faɗin, "Wayyo Allahna na gode maka da ka dawo mana da farincikin rayuwata." Ganin tana son miƙewa sai ya rungumeta. Kuka take yi sosai tana ƙara rungume shi."Ya Ahmad ina ka tafi ka bar ni da kewarka? Kasan halin da na kasance a lokacin da na rasa ka? Kasan damuwar da na shiga. Yaya Ahmad duniya ta yi mini ƙunci rayuwata ta munanta. Na shiga kunci da tashin hankali na rashinka. Don Allah kar ka ƙara guduwa ka barni." "Is ok ƙanwata na dawo gareki kuma ba zan ƙara gudun ki ba." Kuka suke yi sosai Mama ta haɗu ta rungume tana hawaye. Sun daɗe a haka cikin farinciki, sannan suka zauna suna kallon juna. Ahmad na shirin magana wayar Mama ta fara ringing."'Yar albarka Marwanaa take kira, dama na san hankalinta ba zai kwanta ba." Ta ƙarashe maganar tare da amsawa ta kanga a kunninta. "Hello Mama ina kofar asibitin don Allah a fito a shiga dani." To bari na fito." Ta ce mata tare da kashe wayar. "Marwana tana waje bari na shigo da ita." "Mama zauna bari na shigo da ita." Ahmad ya ce tare da fara tafiya. Jin haka ta koma ta zauna tana kallon sa cikin farinciki. Nasreen ita ma kallo da take yi gani take kamar dawowarsa a mafarki ne. Ahmad kuwa sai watsa idanunsa yake yi, burinsa kawai ya kalli Marwana da ta kula da 'yan'uwansa a lokacin da ba ya nan. Sosai yake ganin girmansa da ƙimarta. Sau biyu ya taɓa ganinta, don haka ba zai iya shedata ba, a ranar da ya ganta ranar ba shi cikin hayyacinsa sakamakon lamarin da ya faru. Wannan dalilin ya sanya shi karɓar wayar Mama. Numbarta ya kira wanda ringing ɗaya ta ɗauka."Hello Mama, ina waje har yanzu cikin motata." Zuciyarsa ya ji ta yi wani tsau jin zazzaƙar muryarta. Rintse idanunsa ya yi yana jin matuƙar girmanta. Da ƙyar ya yi nasarar buɗe bakinsa ya ce,"Ok," Tare da kashe wayar. Muryarsa ta doki kunnenta har sai da ta cire wayar tana kallo. Wayyo Ya Ahmad ya dawo💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 Na ga murnar kowa a comment Wayyo Yaya Ahmad ya dawo yau dadi kashe Ni 💃💃💃💃💃 WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 27 Muryarsa ta doki kunnenta, har sai da ta cire wayar tana kallo a tunaninta ko ba layin ta kira ba. Ƙaramin tsuka ta ja saboda a yi tunaninta Ingawa ne. Ahmad cikin tafiya a hankali ya ƙaraso gurin motar. A lokacin da ya isa ta fito, sai ya tsinci kansa da shiga cikin wani irin yanayi. Zuciyarsa na bugawa ya ɗago ya kalle ta. Idanu suka zuba wa juna na ɗan wani lokaci."Nasreen ta ƙara samun wani saurayin ne?" Ta yi wa kanta tambayar hakan cikin zallar kishin yayanta. "Mama, ta ce ki biyo ni." Ya furta cikin natsuwa tare da juyawa. A da ya yi nufin ya fara mata godiya, amma tun da ya kalli idanunta sai ya ji ya kasa, saboda yadda zuciyarsa ke harbawa da sauri. Marwana kuwa da sauri ta kauda idanunta, saboda ƙwarjinin da ya yi mata. Sai kuma ta saci kallonsa don sun so su yi kama da Nasreen. Kauda tunanin hakan ta yi nan take. Da suka shiga cikin ɗakin da sauri ta ƙarasa gurinta cikin damuwa."Nasreen garin yaya kika faɗi? Sannu ya jikin mai ke miki ciwo?" Ta yi mata tambayar cikin damuwa tana tattaɓa jikinta. "Idan akwai abin da ke damuna ɗazu yanzu babu." "Masha Allah sannu ya jikin?" Ta ƙara ce mata. "Marwana dole na warke saboda ranar yau ba zan taɓa mantawa da ita ba." "Mai ya faru?" Ta yi mata tambayar ganin yadda yake cikin tsananin farin ciki. Hannunta ta daga tana faɗin,"Ya Ahmad ya dawo gare ni...." Zare idanunta ta yi tana kallon inda take nuna mata."Don Allah in wasa kike ki daina Ya Ahmad ɗinki, ina yake?" Kara nuna mata shi ta yi cikin mamaki ta ɗago tana kallon sa. Mamakin wayewa da shigar ɗaya yi ta yi. Sosai ya yi kyau kuma ya yi mata kyau. "Wai da gaske wannan ne Ahmad ɗin ki?" Ta yi mata tambayar kamar zata zauce. Ƙarasa gabansa ta yi kamar za ta rungume shi, sai kuma ta ji kunya ta kama hannunsa."Alhamdulillah Allah mun gode maka." Ta ce tare da sakin hannunsa ta rungumeta duk suka fashe da kuka. Ahmad sai ya tsaya cikin tsanannin mamaki yana kallonta, ganin yadda take hawayen murnar dawowarsa. Shi kuwa ba shi da abin da zai saka mata face ya ƙarasa sauran numfashinsa yana mata addu'a, ganin yadda ta ɗauki ahalinsa a matsayin nata.Yana wannan tunanin ta ji muryarta tana faɗin,"Ya Ahmad ina ka shiga ka sanya xuciyoyinmu cikin damuwa? Kasan halin da suka shiga kuwa?" Murmushi ya yi yana mata wani irin kallo."Ayi haƙuri a gafarce ni, sannan a shirye na ke da duk hukuncin da za ku yi mini, duk da cewar na aikata hakan cikin rashin mafita, amma kuma nayi farinciki da na dawo na ga sun samu wacce ta zama tamkar ni. Haƙiƙa ya zama dole na yi miki godiya." Murmushi ta yi tana cewa,"Duk mai imani ya ji halin rayuwar da take yi da Faruk dole ya tausaya mata. Nasreen tamkar 'yar'uwata na ke jinta, bana buƙatar ka yi mini godiya, amma don Allah kar ka ƙara tafiya ka barsu." "In sha Allahu ina tare da su har ƙarshen rayuwarmu." Sun jima a asibitin har zuwa dare aka sallame su. Marwana ta wuce gida da nufin za ta dawo. Damir tun lokacin da ya ji ba a ganta ba sai ya ji damuwa har ya kasa ci gaba da kallon. Ɗakinsa ya wuce a karo na farko ya damu da abin da ya yi mata. Zama ya yi yana tunanin inda ta je. Fitowa ya yi ya zauna a falo yana kallon Marwana da ta rikice tana ta kiran waya. Hankalinta ya kwanta da Mama ta ta kira ta tana asibiti. "Mommy bari na je na ga halin da take ciki." "Da kin bari zuwa gobe tun da kin ji inda take." "Ba zan iya bacci ba, ai ba zan daɗe ba." Ta ce tare da fita da sauri. Wani banzan kallo ya watsawa hanyar da ta wuce. Haushinta yake ji yadda take nuna sonta kamar ƙanwar uwarta. Ajiyar zuciya ya saki ya koma ɗaƙinsa. Ga mamaki sai ya ga ya samu kwanciyar hankali da aka san inda take. Ya daɗe ya kasa bacci yana tunanin ruwan da ya watsa mata ya sanya ta faɗi har ta ji ciwo. Nan take ya ji abin da ya yi bai kyauta ba. Daga ranar ya sanya ba zai ƙara shiga sabgarta ba, soyayya ce dai ba za ta yi masa a campany ba, saboda in har ya ganta sai gabansa ya yi ta fadi yana jin xuciyarsa na harbawa. In kuwa da wani ya ganta ji yake kamar ya je ya rufe su da duka. Rashin adalci da Marwanata yi masa wanda yake tunzura shi har ya yi mata wulakanci, da ya bukaci ta yi aiki a campany, domin shi kaɗai ya san mikin da take tayar masa, duk a lokcin da ya ganta ko ya tuna tana cikin kampanin, wanda ya ɗauki hakan duk a rashin matarsa da ta sanya ya yi. A lokacin da Marwana ta dawo cikin farinciki don ta gaya musu, amma sun kwanta. Mommy dama wuni tayi bayanta yana danunta. Ganin babu kowa a falon sai ta shiga ciki ta tube kayanta. Kwanciya ta yi cikin farinciki sosai. Ta yi murna da Ahmad ya dawo kuma da alamun ya samu abin duniya, duba ga yadda ya canza ya zama ɗan gayu. Ita kanta ya tafi da hankalinta. Gaskiya talauci musiba ne, duk da a lokacin da ta ganshi ba za ta gane suffarsa ba, amma ba za ta taɓa haɗawa da yanzu da ya goge ya samu masu gidan rana ba. Motar da suka shiga shi ya ƙara ɗaure mata kai, har ta fara tunanin wane irin aiki ya samu har ya kuɗance lokaci guda. Ta yi musu murna sosai da sosai domin ta san daga yau sun gama bankwana da baƙinciki. Rayuwar su za ta yi kyau kuma su samu ingantacciyar rayuwa. Nasreen gani take kamar har yanzu mafarki take yi, musamman da suka ƙarasa motar da ya ce mallakinsa ce. Hawaye sosai take yi ta ce,"Ya Ahmad in addu'ar Allah ya sa burin son mu fita daga rayuwaar talauci bai sanya ka kauce hanya ba? Saboda garamu dauwama cikin ƙunci, kan ka bi hanyar daba ta dace ba don ka fitar damu." Shafa kanta ya yi yana murmushi."Kar ki damu ƙanwata. Labarin mai tsawo ne zan gaya miki zuwa gobe, amma kafin nan ki muje gida ki huta." Ya ce tare da kamata ya suka shiga ciki yayin da take ta kallo da shafa motar ta yi tare da jan numfashi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin da yake fitowa a cikin motar. Mamaki take yi sai yau shi ne da mota. Ba ta ƙara shiga cikin mamaki ba sai da ta ga wata irin waya mai tsananin kyau a hannunsa. Tsungulin kanta ta yi domin ha yanzu gani take ganin lamarin tamkar hikaya. Suna shiga gidan Baba ya sheƙo da gudu ya faɗa jikinsa. "Ashe da gaske ne abin da mutane suke faɗi, ba kanzen kurege bane. Amaduuna ya dawo ya yi kudi." Ya furta yana rungumi shi har da hawaye. Sai kuma ya ƙara zabura ya rungume shi yana faɗin,"Wayyo Amaduuna ya zama mai kuɗi ka ga yaron albarka ya fita bariki a sa'a? Kai ni dai Bukar na iya haihuwa." Kalaman da ya faɗa suka sanya su cikin duniyar mamaki. Ahmad ya ja jikinsa daga gare shi, cikin yanayin da ba za ka fahimci abin da yake zuciyarsa ba. Kama hannun Mama da Nasreen ya yi za su shiga ciki. Da sauri ya biyo su yana ta kallon sa yana yi wa Allah godiya. Da suka zauna Nasreen kamar za ta shige jikinsa ta zauna kusa da shi, tare kama hannunsa. Mama ta kalle shi cikin mamakin yadda ya dawo."Ahmad ka ba ni labarin guduwa da ka yi ka barmu a halin gaba kura baya siyaki, sannan arzikin da ka yi a ina ka same su? Saboda bana fatan ka..." "Daɗina dake wallahi kina da matsala. Yaro ya dawo da abin alkhairi, amaimakon ki yi ta murna rayuwarmu za ta ci gaba, amma sai ki tsaya kina tambayarsa inda ya samu?" Jin abin da Baba ya ce sai ya ɗaure musu kai."Ya zama dole na tambaye shi domin rayuwarsa damu da shi, ba abin duniya ba. Bana fatan daboda halin da muke ciki, ya faɗa cikin mummunar rayuwa. Gara ya bar ni na mutu a halin dana ke ciki." "Kina wannan zancen, an gaya miki yawancin masu kuɗin yanzu ta hanyar Allah suke samu? Murna kawai za mu ɗanmu ya yi arziki." Mamakin abin da ya ce ya ƙara kamasu Ahmad ya katse shi ya ce,"Baba duk talaucin da na ke ciki ba zan kauce hanya ba, arziki na da gumina na yi, zan gaya muku yadda na yi arziki zuwa gobe in sha Allahu." "Ni wallahi ba sai ka gaya mini ba ai kai ɗan kirki ne kawai mu ci arziki." Ya ce tare da sakin labulen ya fita cikin murna. Girgiza kai ya yi yana faɗin,"Baba yana nan da halinsa Allah ya shirye shi." "Hummh dama zai canza ne? Ai sanin hali yafi sanin kama." Nasreen ta ce Mama kuwa takaici ya hanata magana. A daren ranar san ba su rintsa ba haka suka kwana hira, domin gani suke kamar zai ɓace. Dariya ya rinƙa yi musu cikin farinciki yana ƙara jin ƙaunarsu. Da suka ga bacci ya ƙi zuwa miƙewa suka yi suka yi ta sallah suna godiya ga Allah. Da asuba ya fita sallah sannan Zainab ta tashi ta ɗora musu abin kari. Mama bayan ta yi sallah ta miƙe ta gyara ɗakin. Da safe suna karyarwa sai ga Baba tsulum ya shigo."Saboda Allah kuma karyarwa da irin wannan ƙaton biredi, amma ba za ku kira ni ba? Na fa lura so kike ki rinƙa nuna mini iko da yarannan, kin san dai nine mahaifinsu, don haka wallahi ba zan yarda ba, ai ina lura haka kike baza iko da arzikin Nasreen, ni kuwa sai abin da kika dama suka bani." Kallonsa suka yi dukkanin su babu wanda ya tanka musu. Ganin haka ya ɗauki sabar biredi ƙato, wanda Ahmad ya siyo musu ya zauna tare da jan ruwan tea na gaban Nasreen. "In ba za ba ni ba ina da hannu ai." Zainab ce ta shigo da filet na ƙwai da ta soya. Kafin ta ije ya kai hannu ya iba."Yauwa yar albarka ije na ci arziki." Ya furta tare da turawa a cikin bakinsa Shiru suka yi masa yana ta sumbatu har ya gama ya tashi, sai kuma ya koma ya zauna. Anan zan rinƙa zama saboda na lura cutata kike son yi. So kike komai sai dai su yi miki, bayan inda ba ni ai ba za ki haife su ba. Mama dai ba ta ce uffan ba ta miƙe Ahmad ya buɗe baki zai yi magana ta dakatar da shi. Ganin haka ya miƙe,"Bari na je gidan ogana akwai kayan da za a kawo mana gidansa." "Adawo lafiya Amadudu yaron kirki." Baba ya ce tare da miƙewa ya fita. "Mama sai na dawo Nasreen bari na je." "To a dawo lafiya." Suka amsa suna kallonsa. Sai da tafiya Nasreen ta kalle shi."Mama wallahi Baba ba shi da ta ido. Kina ganin abin da yake yi? Ko da yake na daina mamakin tun lokacin da na fara samun nawa ya canza na zama shalelensa." "Allah ya shirye shi duk wanda ya bashi shine nasa." "Hmmmmh! Lamarinsa sai shi." Ta ce tare ƙwalawa Zainab kira don ta kwashe kayan da suka karya. A lokacin da Marwana ta tashi safe ɗakin Momi ta shiga cikin farinciki ta rungume. "Momi kin san mai ya faru?" "A'a amma na san daga ganin yadda kike farinciki alkahiri ne." Murmushinta ya ƙaru ta ce,"Eh Momi Ya Ahmad ɗan'uwan Nasreen ne ya da..." "Da gaske kike yi?" Ta furta cikin tsananin murna tana zare idanunta. "Eh, momi wallahi ya dawo." "Masha Allahu Alhamdulillah! Dole na je na yi musu murna. Ya jikin Nasreen ɗin?" "Da sauƙi jiya ai ba ta damu da ciwo ba ganin Ya Ahmad." "Dole ke kuwa, a wannan zamanin da zumunci ya yi ƙaranci a cikin al'umma." "Wallahi Momi ai Ya Ahmad ya yi." "Allah ya saka mishi in sha Allahu da yamma zan je na yi musu murna." Jin abin da ta ce sai farincikinta ya ƙaru."Da nayi farincikin haka, yanzu zan shirya na ƙara duba jikinta in zan wuce makaranta." "Ya kamata ke dai da Nasreen Allah ne ya haɗa ku." Ta furta tana kallon ta gani yadda take murna. "Allah ne kuwa saboda jin ta nake kamar 'yar'uwa ta jini. Momi wataƙila don ba ni da 'yar'uwa na mace ne." Dariya ta yi tana kallonta ita kuma ta shige ciki don ta shirya. A hanya tan tuƙa mota tana ayyana farincikin da take ciki. Har ta isa kofar gidan. Shiga ciki ta yi a lokacin da ta yi sallama. Nasreen tana kwance kan kujerar tana chatting da Ingawa. Sanar mishi da dawowar Ahmad ta yi. Sosai ya taya ta farinciki. Jin sallamar Marwana ta ije wayar tare da amsawa. Zama ta yi gefenta baya ta shigo."Ya kike jin jikin na ki?" Ta tambaya tana daga hannunta da ya kumbura." Na ji sauƙi sosai saboda farincikin da na ke ciki, sam bana jin zafin ciwon." "Dole ki yi farinciki ko ni da kyar bacci ɓarawo ya sace ni." "Mu jiya ba mu yi bacci ba." "Da ma ba za ku iya bacci ba." Bayan ta gama duba ciwon suka shiga hira. Nasreen ta kalle ta ta ce."Marwana na gode da kulawar da kika ba ni sosai, amma na aje aiki har na rubuta resignation letter ki kaiwa Ya Damir." Miƙewa ta yi a zabure tana kallonta cikin tsanannin mamaki."Sakayyar da za ki yi mini kenan Nasreen? Na tsaya na kula da rayuwarki, ina fatan ki saka mini ta hanyar dawowa da dan'uwana cikin hayyacinsa, amma saboda kin ga Yayanki ya dawo da abin duniya ya yi kuɗi shi ne za ki guje ni? Ko da ace za ki yi butulci bai kamata ki yi mini ba, musamman da kece silar faruwar komai." "Na sani kuma na yarda ni ce na sanya shi cikin damuwa, amma duk abin da za ki ce na riga na gama yanke shawara, saboda Ya Damir ba zai taɓa sausauci a gare ni ba. Ko da ace Ya Ahmad bai dawo ba, wallahi na yi ninyar aje aiki. Shi ne ya ya watsa mini ruwa a hanya har na faɗi na ji ciwo." Zare idanunta ta yi cikin tsananin mamaki tana jinjina rashin imaninsa."Kina nufin shi ya watsa miki ruwa?" Ta yi tambayar cikin zallar mamaki. "Shi ne ya watsa mini ruwa a yadda ya so ina tunanin buge ni zai yi, saboda in har da ban matsa ba sai ya ture ni." Ranta ne ya ɓace har ta yi dana sanin gaya mata. "Ya Damir mutuwar Anty Batula ya sanya shi rashin imani har zai iya kisa. Shikenan na yarda ki aje aikin bazan yi miki dole ba. Ya Ahmad ya dawo gareki zai kula dake. Shi kuma ki bar shi ya ƙare rayuwarsa a haka, har ya je ya samu wacce ya yi wa alƙawarin sai su ci gaba da rayuwa a can." Yadda take maganar cikin zafi ya tabbatar mata data harzuƙa. Kama hannunta ta yi tana faɗin,"Ni ban gaya miki don ki je ki gaya masa babu daɗi ba. Bana son ki yi abin da zai sanya ya ja babu daɗi. Duk abin da ya yi mini na cancanta, amma zan aje aiki don na yi nesa da shi, kamar yadda ya buƙata." "I understand, babu matsala ki bani resignation letter ɗin zan kai masa. Kuma kar ki tunanin hakan zai kawo matsala a tsakaninmu, kina nan a matsayinki na yar'uwata." "Na gode da kika fahimce ki." Ta ce tare da umurtar Zainab ta kawo mata takaddar. "Zan wuce makaranta ki kula da kanki." "Sai kin dawo in sha Allahu." Ta furta sannan ta yi mata murmushi tare da ɗaga kanta ta tafi. Mama ta fito daga ɗaki tana kallonta."Mai ya sa kika ake aikin yarinyar nan ba za ta ji daɗi ba, saboda tana iya ƙokarinta a kan ki." "Mama aje aikin shi ne mafita a garemu Gabakiɗaya. Sam ba ya jin daɗin ganina har ta kai ga yana ƙoƙarin taɓa lafiyata. Gara na haƙura dama tuni na yanke shawarar haka, ga kuma ya Ahmad ya dawo cikin rayuwarmu." "To Allah ya sanya haka shi ne mafi alkhairi." "Amin." Ta amsa. A fusace ta fice daga gidan, saboda abin da ya yi wa Nasreen ya bata mata rai. Saboda ranta da ya ɓace ba ta lura da Ahmad da ya faka motarsa ya fito don yazo su gaisa ba. Da gudu ta ja motar ya yi zuru yana kallonta. Har sai da motar ta ɓace, sannan ya kashe na sa ya fito yana tunanin mai ya ɓata ranta a gidan. Mutane suka yi masa caaa ana murna. Da ƙyar ya samu ya shige cikin gidan bayan ya sallame. "Sannu da dawowa Yaya." Ta ce tare da tashi ta zauna. "Yauwa, Marwana ta fita cikin fushi da wa ya ɓata mata rai." "Nasreen ce saboda ta ce ta ije aikin da ta samar mata a kampanin su." Mama ta ba shi amsa. "Saboda me?" "Kasan abin da ya faru Yaya tsakaninta da yayanta." Kansa ya ɗaga, sai ta ba shi labarin ɓacewarsa da kuma komawa gidan Faruk da yadda suka rabu har ta samar mata aiki. Hawaye ya share cikin mamaki ya ce."Faruk ya cutar dake ɓacin albarkacin su Raihann sai na maka shi kotu, amma ya ci albarkacin haihuwa. Marwana kuwa kamar ke na ɗauke ta. Tabbas ta zama ƴar'uwarmu, duba ga irin yadda tasha artabu da su har suka amince ta dawo cikin rayuwarki. Anya ana samun ƙawance haka?" "Gaskiya ko ana samu sai kaɗan yarinyar nan 'yar albarka ce. Shi ya sa duk na yi sallah nake mata addu'ar miji na gari, domin ta haka ne kawai za mu iya biyanta." WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 28 "Gaskiya ko ana samu sai kaɗan yarinyar nan 'yar albarka ce. Shi ya sa duk na yi sallah nake mata addu'ar miji na gari, domin ta haka ne kawai za mu iya biyanta." "In sha Allahu za ta samu tana da kyawawan halaye. Kuma aje aikin da kin yi shi ya fi. Yana da kyau ki yi nesa da shi kamar yadda ya buƙata. A yanzu na dawo cikin rayuwarku ba zan ƙara bari ku yi kuka ba. Tun kafin na dawo ni da ogana muka sanya aka yi mana ginin ƙaton gida an saka komai. Yanzu za ku tashi kayan jikin ku kawai za ku ɗauka mu koma gidan. Zan sanya Baba ya sake ki. Ni zan kula da rayuwarki, saboda Mama sam ba ki dace da rayuwarsa ba. Albarkacin haihuwata da ya yi da kuma sauran ƙannina waɗanda muke uba ɗaya zan gyara musu gidan nan, sannan na rinƙa basu abinci, amma ƙwandalata baba ba zai ci ba. Ko abincin da zai rinƙa ci saboda kannina ne. Baba ya cutar da rayuwarmu. Ya yi aure don biyan buƙatar sa ba, wai don ya haihu ya tarbiyar tar damu ranar gobe kiyama Annabi ya yi alhafari da shi ba. Irin wahalar da na sha, kafin na samu na gina rayuwata ya ƙara jefa mini tsanar shi." Tsananin mamakin siyan gidan da ya faɗa musu ya sanya suka kasa magana, sai kallon sa suke yi cikin rashin hayyaci yana ta zuba. Ganin ashe ba saurarensa suke yi, ba sun shiga duniyar mamaki ya sanya shi kama hannayen su. "Da gaske na siya mana gida mai kyau, da komai da komai ku tashi ku shirya mu koma." "Ya Ahmad don Allah ka duke ni, ko zan farka da mafarkin da nake yi tun jiya." "Ni ma ya haɗa da ni Nasreen." Mama ta ce cikin ruɗani. "Da gaske ne na siya mana gida daga yau rayuwarmu ta canza." "Ahmad wane sana'a ka yi ka tara kuɗi ka yi gini a wannan shekaru?" Mama ta ce tana kallon sa. "Mu je sai a can gidan xan gaya muku." "Ihun murna suka ɗauka wanda ya janyo hankalin mutanen gidan." Gwaggo da ta ji abin da suke wa ihun ta ce,"Masha Allahu Allah ya ƙara buɗi." "Amin, kuma zan sanya a gyara gidan nan kuma zan rinƙa ɗaukar ɗawainiyarku na kula da karatun ƙannina." Murna da koke-koke suke ta yi har na wani lokaci, kafin suka shirya suka gidan cikin farinciki suka tafi inda ya gina gidan Cikin tsananin mamaki suka kalli juna. Mama da ta fito daga cikin mota ta tsaya tana kallon da ta ce,"Wai kana nufin Ahmad wannan gidan ka gina mana?" Ta karashe maganar tana shafa get ɗin gidan. "Eh Mama, sannan har da nawa na gida duk a cikin unguwar nan. Ku shiga ciki nan ne za ki yi murna." Ya ƙarashe maganar tare da buɗe get ɗin gidan. Cikin tsananin mamaki suka shiga gidan. Zuwa yanzu sun daina mamaki sai al'ajabi. Ji suke kamar a mafarki wai yau sune a ciki gidan nan mallakinsu wanda Ahmad ya siya musu. Kai lamarin Ubangiji sai kallo. Sosai suke murna kamar za su shiɗe. Ba su ƙara shiga cikin mamaki ba, sai da suka cikin falon. Sai suka tsaya suna kallon yadda fakon ya sha kujeru, manya da katon plasma ga kuma dinning. Mama kuka ta saka da shi ta kama shi ta shaƙe."Ba zan kara farinciki ba, har sai ka gaya mini sana'ar da ka yi ka gina gidan nan. Wallahi Ahmad in har wani hanya mummunan ka ji ya sanya ka gudu ka je ka aikata don ka fitar damu cikin ƙangin talauci, ban yafe maka ba." Ta ƙarashe maganar tana jan mjina. Nasreen ita ma kuka ta saka."Don Allah ka gaya mana yadda aka yi ka samu kuɗin nan." Hankalinsa ya tashi ganin yadda suka rikice." To shikenan ku zauna zan gaya muku." Kamasu ya yi ya riƙe ganin yadda suka tayar da hankalinsu."Wallahi Mama, ban taɓa kauce hanya don na samu abin duniya ba." "To ka ba ni labarin yadda aka yi ka tara kuɗi." "Shikenan, ku zauna zan ba ku labari, amma sai ogana yana nan, domin ku tabbatar da abin da zan faɗa muku. Ya ce mini yana kan hanya ku jira shi." Jin ya faɗi haka sauri suka zauna suna kallon sa. Ba su jima ba sai ga shi ya shigo cikin gidan. Bayan sun gaisa ya zauna Ahmad ya gyara zama sannan ya gyara murya ya fara da ce wa," A lokacin da muka shiga mota za mu tafi, duk na ƙasa mu kai mu kammala aikin, saboda tunanin Baba zai iya tursasa Nasreen ta koma gida Faruk, tun da babu idanuna. Sai dai abin takaici da muka isa mun kira gayen da ya yi mana hanya, amma wayarsa a kashe. Hankalinmu ya tashi amma sai muka yi masa uzuri, duk da ya san da muka kan hanya. Shiga cikin tasha inda ake sayar da abinci muka yi, sannnan muka samu abin da za mu ci, tare da rama sallolin da yake kanmu. Muna gurin har zuwa magariba muka ƙara gwada numbarsa. Cikin sama ta shiga ya yi mana alkawarin zuwa ya tafi da mu. Ba tare da ya ɗauki dogon lokaci ya iso muka tafi. Bayan ya kaimu inda za mu huta zuwa gobe ya nuna mana aikin. Da ƙyar na yi bacci duk na ƙasa mu fara aiki. Abin takaici ko da ya zo muka tafi, ya nuna mana aikin, sai muka shiga cikin tsanannin tashin hankali, domin a yadda muka ƙiyasta kuɗin ko kuɗin motar da za mu koma ba zai biya mana ba. Hankalinmu ya tashi matuƙa gaya muka shiga masa fadan cewar ya san aikin ba shi da yawa zai kira mu? Kawai sai ya hau mu da zagi yana yare. Daga ƙarshe cewa ya yi ya fasa bamu aikin tun da mu Hausawa ba mu da mutunci. Ya yi tsaki ya tafiyarsa. Nan fa idanunmu suka raina fata, saboda duka kuɗin dake hannunmu bai wuce na cin abinci ba. Na shiga tsananin tashin hankali da damuwa tuna dalilin da yasa a zo aiki, sannan ga bashin da na ci na kuɗin da bar muku abinci. Haka muka wuni cikin rashin dubara. Ogana ya bamu shawarar mu yi dako ko kuɗin mota mu tara sai mu koma gida. Akwai sauran kuɗin da ya bawa matarsa zai jiranta ta tura masa, duk mu haɗa. Na rasa tunanin da zan yi, domin hanyar na kawai nake tunanin zan samu kuɗin da zan yi wa Faruk hulɗi. Na shiga damuwa da tunanin inda zan samu kuɗi, domin ina jin kunyar na dawo babu kuɗin, na san tijarar Baba da gorin da Faruk zai yi mana sun ishe ni. A raina sai na ji ina har ban samu wannan kuɗin ba, sam ba zan iya ƙara haɗa idanu dake da Mama ba, domin na gaza amatsayina na yayanki." Muna cikin wannan halin dare ya yi haka muka kwana a waje. Washegari da safe muka zage dako, babu laifi kuma mun samu kuɗi. Tun a ranar da muka je na ji babu aikin na kashe wayata, saboda bana son ku kira ni ku fahimci halin da na ke ciki. A ranar da muka fara dakon a gurin aka sace mini wayata. Mun ɗauki tsawon sati muna duk aikin da muka samu sai muka haɗu da wani Tanimu, amma shi ɗan Kano ne ya zo neman kuɗi a can. Take muka fara hirar duniya har muka zama abokai. A nan ne yake sanar mana da cewar zai je inda ake haƙo ma'adai neman kuɗi. Da faru ban kula da labarin gurin dayake bani ba, amma da na ji yace mutum zai iya arziki acan in har ya dace ya haƙo zinare, rayuwar mutum za ta iya canzawa, amma fa gurin akwai tashin hankali, saboda mutum zai iya samu wani ya kashe shi ya kwace, sannan kuma ƙasa na yankewa ta kashe mutum, saboda rami ne zuƙuƙuƙu. Haka ya rinƙa gaya mini tashin hankalin da yake ciki, da kuma hasashen zama mai kuɗi lokaci ɗaya. Sai na yi shiru, na shiga cikin damuwa ina tunanin halin da na ke ciki na gaba kura baya siyaki. Ba tare da dogon tunani ba xuciyarta ta aminta da na bi shi can. Saboda ku xan iya sayar da rayuwata, kula na gwammace na mutu, da na dawo babu kuɗin da zan yi wa Faruku hulɗi. A lokacin na kallii ogana nuna masa sha'awar zuwa sai ya zare idanu yana kallonta."Ka da talauci ya sa ka je ka sayar da rayuwarka. Ka san wahalar da ake sha acan kuwa? Wallahi tsaf wahala za ta kashe ka. Mutane nawa suka je ba su yi arzikin ba, sai dai aka dawo da gawarsu." "Zan je duk abin da Allah y yi daidai ne. In har na yi arziki zan yi farin ciki, in kuma na mutu hakan zai fi mini kwanciyar hankali da bakina gida ba tare da abin da na zo nema ba." Na faɗa masa xuciyata tana karfafa ni. "To shikenan ni zan koma saboda ina da mata da yara ba xan kashe kaina ba." Ya ce tare da fara tafiya. Da dadddare, ko da muka zo kwanciya hak ya rinƙa gaya mini tashin hankalin da zan fuskanta, sannan ya yi ta roƙona na koma gida don kar iyayena su tuhume shi, amma na yi kunnen uwar shegu da shi. Na hau shiri ina jiran lokacin da ya ce mana zamu tafi ya yi. Ganin na yi nisa bana jin kira, sai ya fara haɗa kayansa zai koma, amma a ranar ko tunanin mai ya yi, sai ya sanar da ni shi ma yana son zuwa, saboda yana tsoron in ya koma yan bashi su dame sa. Cikin daren da za mu je muka yi sallah na neman sa'a. Washegari muka kama hanya. Tafiya sosai muka yi har sai da muka gaji sannan aka isa. Sai da muka yi hutun gajiya sannan muka fara aiki. Haka muke haƙin ƙasa babu ji gani, amma bamu taɓa hako komai ba. Gashi kullum ramin kara zurfi yake yi. Gabakiɗaya mun rame mun fita hayyacinmu. Har mun cire rai da samu domin na sare sosai a wannan lokaci. Na fara tunanin mu koma gida saboda ina jin kamar zan mutu, don tsabar wahalar da muke sha. Shi ma kansa ogana ya sare sosai don har na fishi juriya. Ƙwasam watarana muna cikin haƙi mu uku sai kawai muka haƙo zinari. Wani irin zabura Tanimu ya yi tare da fasa ihu." Yeeee! Wallahi mun samu." Jin abin da ya faɗa sai kawai aka yi kanmu ana zare idanu. Tsoro ne ya kama shi ganin ihun da ya yi duk an kewaye mu. Kamar wasa suna gani dai kawai suka kama mu dabbe za su ƙwace. Ganin wahalar da muke sannan muka samu, sai na zama mahaukaci kawai na shiga ka musu duka. Tunani na ke in har suka kwace shi ne kaɗai damar da zan iya fitar damu cikin halin ƙuncin. Da muke ciki. Faɗa sosai ya kaure a tsakaninmu, babu tsoron Allah burin su kawai su karɓa. Wani ganin za mu gudu, sai ya samu abin da muke haƙi ya ƙwala wa Tanimu aka. Nan take ya saki ƙara ya faɗi ƙasa jini yana zuba a kansa. Ganin haka na yi kukan kura na na yi kansu ina kai musu duka. Ganin na haukace sai suka gudu, domin ni kaina mamakin abin da na aikata na yi. Da kyar muka samu suka gudu. Kan Tanimu muka yi muna kiran sunansa."Don Allah ka tashi kar ka mutu kai ka ce mu zo, kuma ga shi mun samu don Allah ka tashi." Murmushi ƙarfin hali ya yi,"Lokacina ya yi saboda ba zan iya tashi ba, mutuwa zan yi. Don Allah ku kaiwa ahalina kasona." Ganin yana bamu wasiya sai muka saka kuka muka rungume shi, cikin tashi hankali."Don Allah kar ka mutu ka tashi ka mori wahalar da ka yi. Kai ne fa ka kawo mu gurin nan, don Allah kar ka mutu." Hannunsa ya daga mana sai kuma ya saki sharaf babu numfashi. Rungumesa muka yi muna kuka sosai. Mutuwarsa ta gusar da farincikinmu, domin mutum ne mai kirki yana da hankali mun saba da shi sosai." Mutuwarsa ta sanya muka rage farinciki da muke yi, domin sai damuwa yi kusa sati ba tare da mun saki ranmu ba. Mun kaiwa iyayensa gawarsa sannan muka yi musu bayani. A lokacin da muka je siyarwa aka gaya mana kuɗin da muka samu. Sai da muka yi suman wurin gadi, saboda kuɗi ne wanda zai canza rayuwarmu da ahalinmu bakiɗaya. A Kano muka yii sannan muka tura kuɗin da za a yi mana gini. Ba sai da aka kammala komai sannan muka fara shiri, domin so nake aranar dana dawo washegari mu tashi. Saboda yadda muka rame muka fita hayyacinki sa muka yanke shawarar mu tsaya a Kano sai mun dawo kamamminmu. Cikin ƙanƙanin lokaci ka canza nayi kyau, saboda abincin da muke ci. Muka siya kaya, mota da wayoyi." Dago kansa ya yi yana kallonsu, ganin yadda idanunsa suka kike da hawaye. Ogan Ahmad ya nuna musu hotunan da ya ɗauka yana faɗin,"Tabbas wannan shi ne sanadin da muka samu kuɗi. Ga hotunan mu lokacin da muke aikin za ku tabbatar da haka. Har ma da zinari samu duk mun ɗauka don ya zamar mana sheda." Mama da Nasreen rungume shi suka yi."Haƙiƙa Ya Ahmad bamu da ain da za mu ce maka, domin ka cike gurbin yaya da uba. Haka kasha wahala ka daure da rayuwarka don kawo mu fita daga talauci?" Murmushi ya yi."Rayuwarku tafi mini komai a duk lokacin da na tuna irin rayuwar da muke yi, da kuma halin da Nasreen take ciki a gidan aurenta, sai na ji tamkar zan kashe kaina, ganin ba ni da halin da zan fitar da ku." "Allah ya yi maka albarka ya ba ka mata ta gari da yaran da za su ji ƙanka Ahmad. Hakika duk uwar da ta haifi yaro irinka ta yi sa'ar haihuwa. Ubangi ya kare mini kai kula ya yi maka albarka." "Amin Mama." Ya ce cikin tsanannin farikciki. Nasreen kallonsa ta yi sai kawai ta faɗa jikinsa ta fashe da kuka."Ki yi shiru kuka ya kare. Yanzu farinciki zamu kasance Nasreen. Zan kula da rayuwarki babu namijin da zai ƙara wulaƙanta ki in har ina raye." Murmushi ta yi tare da ɗaga masa kanta tana murmushi. A ranar sun kasance cikin tsananin farin ciki sosai. Wuni suka yi a gidan sannan su Gwaggo duk kom zuciyarta na fatan ina ma ace ita ta haife shi. Nasreen sai kallon gidan suke yi. Sun takure a falo suna ta raba ido. Gani suke kamar in suka shiga ciki za a ce su fita, har yanzu sun kasa yarda wai gidansu ne. Su kansu Zainab da Raihann har Musaddik jikinta ya kwanta ya ɗauka baƙunta suka zo. Ba ta yarda gidansu bar sai da aka yi ta shigowa da abinci aka sanya a store. Ahmad ne ya kalle ta ya ce,"Ku je ku ɗora mana abinci su ma su Gwaggo na sanya an kai musu." Rungume shi tayi ta kar fashewa da kuka."Har yanzu ka kasa yarda gidanmu ne." "Je ki yi mana girki sarkin kuka." Ya ce tare rabata da jikinsa. Share hawaye ta yi tana murmushi sannan ta shige kicin ɗin. Abinci kala-kala ga su nan sai abin da ta so ta girka. Sai kawai hawaye suke dubo mata tuna a gidan Faruk bai taɓa aje abinci a store ba. Bayan ta yi musu girki ya ci ya fita. Baba yana dawowa ya shiga cikin ɗakin Mama, amma sai ya tsaya turus cikin mamaki. Ciki ya buɗe labulen ya shiga. Gabansa ya faɗi ganin kamar sun ɗauke kayan sawarsu."Guduwa duk suka yi?" Ya yi wa kansa tambayar cikin ruɗani. Da sauri ya fito zuwa ɗakin Gwaggo. Tana zaune tana cin shinkafa da miya har da nama. Ba tare daya kula da abincin da take ci ba ya ce,"Ina Maman Ahmad?" "Duk sun tashi Ahmad ya siya mata sabon gida suna...." "Ya siya mata ko ya siya mana? Saboda rashin mutunci ba za a gaya mini ba?" Ya faɗa cikin ɓacin rai. "Sai ka sanya yara su kaoka, domin babu bin da za ka ji a bakina." "Ke Nabila ta shi ki kaini gidan." Ya furta tare da ɗauko jakar buhunsa. Marwana cikin hawaye ta ƙarasa gidan. Cikin sa'a ta same su duka a falo suna zaune. Kai tsaye inda Damir yake zaune da jaridar daily trust a hannunsa yana karantawa ta nufa, duk da cewar karatun yake, amma gabakiɗaya ɗaya hankalinsa babu a jikinsa. Marwana yake son ya tambayi inda ta je, sai dai ya kasa saboda bai san fassarar da Momi za ta yi mishi ba. "Ya Damir ban tana sakin muguntar ka ta kai har za ka iya kisa ba sai yau?" Tambayar data yi mishi da kukan da take yi ya daga hankalinsa da Momi. "Kisa kuma Marwana, kan ki ɗaya?" Muhsin ya ce yana kallonta. "Eh, kisa ya yi ninyar yi. In har ka tsane ta haka ba ka buƙatar ganinta da ka gay mini, bawai ka je ka yi niyyar kashe ta ba. Ya Damir anya akwai Tauhidi a cikin zuciyarka. Ka yarda Allah shi yake kashewa kuma ka yi imani da babu wanda ya isa ya kashe wani? In har Kanada wannnan imanin ba za ka tsani Nasreen saboda mutuwar Anty Batula ba, har ka watsa mata ruwa ta faɗi ta ji ciwo." Jin abin da ta ce duk zare idanunsu. Momi ce ta kalle sa cikin tsananin mamaki."Wai haka ya faru?" Ba tare da ya amsa tambayar da ta yi masa ba, ya miƙe zai shige cikin ɗaƙinsa, saboda kansa da yake juyawa tamkar ana murza sitiyarin mota. Ganin haka ta sha gabansa babu tsoro a fuskarta."Da gaske ne Momi ya Damir ya watsa mata ruwa bayan ya ganta a ruwa ba tare da taimaka mata ba, sanadin haka ta faɗa kwalbati har ta goce hannu kuma ta ji ciwo a ƙafafunta " "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Damir saboda me za ka zama mugu azzalimi shin mutuwa kanka aka fara, ko kana so kace mini ka fi son mace da wanda ya kawo ka duniya. Mahaifinka a hannunka ya mutu, amma ka manta komai kuma ka ci gaba da rayuwa. Karka manta ana iya canza mata, amma mahaifinka da? Ka ba ni mamaki Damir ka sanya mini kokwanto a raina. Wallahi in har ka ƙara gigin shiga cikin rayuwar yarinyar nan sai na yi mugun saɓa maka." "Momi ki kwantar da hankalinki, saboda ba zai ƙara ganin ta ba, kamar yadda ya roƙa ta yi nesa da shi hakan zai faru. Ƴaƴanta Ahmad ya dawo da dukiya na san cewa zai kula da rayuwarta, don haka ga resignation letter ta ba ni na kawo maka." Ta ɗora masa kan jikinsa tana faɗin,"Ubangiji shi yake arzurtawa yau Nasreen ta fita daga cikin jerin da za ta buƙaci' taimako. A lokacin da Ya Ahmad ba shi da shi ya kula.da rayuwarta, ballantana da yanzu Allah ya yi masa arziki." Sakin takaddar ya yi ta faɗi, ƙasa ya tureta ya shige cikin ɗakin cikin tashin hankali. Yana shiga ya karasa gurin frij ya ɗauki ruwa mai sanyi ya sha. Kansa ya hada da gini yana bugawa. So yake ya mutu sam ba ya jin daɗin rayuwar sa. Ya rasa yadda aka yi ya kasa yafe mata abin da ya faru, domin in har zai ganta sai ya rinƙa jin bugun zuciya da damuwa, wannan dalilin ya sanya shi ƙuntata mata. Lokaci guda rikice hawaye yana sauka ƙuncinsa jin har ya yi mata rauni. Shi da ko kiyashi ba ya cutar da shi, amma saboda mutuwar Batula mace da yake tausayi a rayuwarsa ya ita cutar. Damuwa ce a ransa sosai yana buƙatar wanda zai ba shi shawara. Ya rasa yadda zai yi domin duk ya ganta sai ya ji ya shiga cikin damuwa. Da tsintar kansa a yanayin da ya kasa ganewa domin zuciyarsa da tunkinsa rikicewa suke yi. Wani irin tausayi da kunyarta suka kamashi har ya ji yankin kunyar haɗa idanu da ita. Kansa ne ya kulle damuwa ta yi masa yawa. Sai kawai ya miƙe zuwa bayi ya sakarwa kansa shower ba tare da ya tube kayan jikinsa ba. Saukar ruwan da hawayen da yake zubarwa, suka taru suka ƙara sanya masa damuwa a maimakon ya ji sanyi. Tsawon lokaci ya ɗauka a haka domin gani yake kamar hakan ne mafita, amma jin damuwarsa tana ƙaruwa da sauri ya yi alwala ya fito ya ɗauko maganin damuwar komai ya fara karantawa. A hankali zuciyarsa ta fara sakkowa har ya ji ɗan natsuwa. Sosai yake jin babu daɗi abin da ya aikata mata. Rintse idanunsa ya yi yana tuno lokacin da ya ganta cikin ruwan tare da watsa mata ruwan da ya yi. Haƙiƙa ya zama azzalumi kuma matsoraci ya rasa wanda zai yi faɗa da ita sai mace macen ma, wacce tasha wahala a rayuwaarta take buƙatar tallafawa. Jin ɗan'uwanta ya dawo ya yi matuƙar farinciki da haka. Tuna ta bar aikin gabansa ya yi wani irin faɗuwar da sai da ya dage gurin. Marwana zama tayi tana cika tana batsewa saboda abin da ya yi. Zuciyarta ta sare kan haɗa su soyayya. Ayi mini hakuri na koma gurin aiki ne malamar makaranta ce ni. In ana son na ci gaba da safe da yamma a rikitani da comments sai na cigaba da safe da yamma. Kusan ina mugun yinku.❤️❤️❤️❤️❤️ WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 29 Marwana zama tayi tana cika tana batsewa saboda abin da ya yi. Zuciyarta ta sare kan haɗa su soyayya. Hawaye sosai take yi domin ya ba ta haushi. Hajiya ce ta zauna a gefenta ta kama hannunta. "Ki yi haƙuri zan je na bata haƙuri da kaina ba za ta ije aikin ba, kuma in sha Allahu sai ya saukko da kansa ya aureta." "Momi ki ƙyale shi kawai yaje ya yi ta fama da soyayyar marigayiyar matarsa, amma lamarin Ya Damir ya fara ba ni haushi. In ya ga dama ya ƙare rayuwarsa babu aure. Ba zan takura mata ba, saboda she had enough tana buƙatar tayi farincikin. Ina ga zan turawa Ya Annur numbarta dama yana ta yi mini magiya, sai ya ganta a campany yana so." Murmushi Momi ta yi ta c,"Ki tura masa wannan ma zai taimaka. Ki tura masa numbar kuma ki yi ƙoƙarin ki ga takula shi. Damir yana sonta zafin kishi da girman kai yake sanya shi wannan haukar, amma ki bari ya ga abokinsa a gurin, da kansa zai bayyana abin da ke dawainiya da shi." Kallonta da sauri ya yi tana mamakin fasaharta."Aikuwa Momi yanzu zan tura masa da nambar." Ta karashe maganar tare da miƙewa ta shige cikin ɗaki da sauri. "Ki shirya an jima sai ki kaini gidan." "To Mommy," Ta ce tare da ƙarashe shigewa ta rufe ɗakin. Tana shiga ta kwanta kan gado tana ganin shawarar Mommy za ta yi aiki. Numbar ta tura masa sannan ta kira wayar Nasreen. Nasreen da take ƙoƙarin kiranta wayar ya shigo. "Hello, yanxu na ke shirin kiranki na sanar miki da abin mamaki." "Ai tun da Ya Ahmad ya dawo, kullum cikin abin mamaki za ki yi ta gani." Ta furta cikin dariyar jin yadda take matuƙar farinciki. "Wallahi kuwa Marwana wai ashe da ya tafi ba su samu aikin ba, kawai sai ya tafi gurin haƙin ma'adanai Allah ya taimaka mishi ya samu. Kin san tun kafin ya dawo ya sanya aka gina mana gida?" Da sauri ta miƙe ta ce"Don girman Allah!" Jin yadda ta nuna farinciki sai ta ƙyalƙyace da dariya ta ce"Wallahi Marwana gida mai kyan gaske na yan gayu. Na ƙarƙare miki zan ce yanzu muna cikin gidan, kuma ya ce gobe zai je da ni kasuwa." "Iyye Masha Allah mahaƙurci mawadaci. Kin zama yar gata Yaya Ahmad." "Sosai yau ina cikin farinciki sai na ke ganin kamar a mafarki." "Haka za ki gani wanka kawai xan yi, za mu zo da Hajiya sai ki yi mini text adireshin gidan." "Ok sai kun zo bari na yi miki." Ta ce tare da kashe wayar. Bayan ta fito daga wanka suka shirya zuwa gidan. Mamaki sosai Marwana ta yi ganin get ɗin gidan, sai kuma ta daina mamaki data tuna motar da ya zo da ita. "Wai da gaske wannan gidan ya gina musu?" Momi ta yi tambayar cikin mamaki ganin get ɗin gidan. "Masha Allah haihuwa ta yi rana." Ta furta daidai lokacin da Zainab ta ji hon ta buɗe musu gidan. Marwana tana ƙoƙarin paking Nasreen ta fito cikin sauri. Idanunta a ƙasa ganin Hajiya. Abin da ya faru ya dawo mata har sai da ta yi ƙwalla. Ita kanta Hajiyar wataƙila ta tuna abin da ya faru ne, domin ganinta jikinta ya yi sosai. "Ina wuni momi?" Ta ce tare da durƙusawa sai hawaye. Hannunta ta kama ta miƙar da ita."Nasreen ya kike da yaranki ina Mamanki." "Tana ciki yanzu ta shiga wanka, mu shiga ciki." Ta furta tana kallon Marwana da ta kulle motar ta rungumeta. "Gida ya yi kyau Allah ya sanya alkahiri." "Amin," Ta amsa sannan suka rankaya suka shiga ciki. Mamaki sosai suka rinƙa yi ganin yadda gidan ya haɗu. Mama ta fito daga cikin ɗakinta daidai lokacin da Ahmad ya yi sallama ya shigo. Da sauri Marwana ta daga idanunta tana kallonsa. Tun daren jiya ta ƙosa ta ganshi da rana. Zuciyarta ce ta buga wanda ya sa ta saukar dakanta daidai lokacin da ya sanya idanunsa cikin nata. A tare suka kauda idanunsu. Ahmad ya karaso cikin jin kunya ya durƙusa. "Ina wuni Hajiya?" Ya ce mata idanunsa a ƙasa domin kunyarta yake ji. "Wannan shi ne Ahmad ɗan albarka ko?" Momi ta kalli Marwana tana faɗin haka. Satan kallon shi ta yi da idanunsa yake kasa. A hankali ta ce,"Eh, shi ne." "Masha Allah Allah ya yi maka albarka haƙiƙa ka zama ɗan halak." Cikin jin kunya ya amsa sannan ya tashi ya shige ciki. So yake ya yi wa Marwana magana, amma sosai yake jin kunyarta sam ya kasa saki da ita. Nasreen da Zainab suka kawo musu drinks da ruwa, sannan ta zauna tan shafa kan Raihann da take gefenta. Sai suka yi shiru ganin shirun ya yi yawa Momi ta katse shurin ta hanyar cewa,"Ga shi Allah ya sake haɗamu a karo na biyu, ko a wancan shi ya haɗamu tsautsayi ya gifta, amma a wannan karon ina fatan ya zama ɗorewar xumuncin da zai sanya mu zama 'yan'uwa. Mu manta komai mu yi kokarin gida kyakkyawar alakar da zai mayar da jininmu daya?" "In sha Allahu ai an zama ɗaya Marwana kamar Nasreen na ɗauke ta, abin da ta yi mana Ubangiji ne kawai zai bata lada, saboda ta bamu taimako sosai a rayuwar mu, sai dai mu yi mata fatan samun miji na gari." Mama ta faɗa tana kallonta. "Masha Allah Ubangiji ya yi mata albarka." "Amin,"Suka haɗa baki gurin faɗin haka. Saboda rashin sabo, Hajiya da Mama ba su yi hira sosai ba, sai Nasreen da Marwana suke ta hira. Sai da za su tafi Mommy ta kalli Mama ta ce,"Ayi haƙuri abin da Damir ya yi, don na yi masa faɗa sosai kuma hakan ba zai ƙara faruwa ba, don Allah kar ya zama silar da zai raba zumunci ko ta aje aiki, domin duk yadda kuka samu buɗi aikin zai taimaka." "Sosai kuwa ai aikin ma ya taimaka kuma yana kan yi. In sha Allahu da zarar ta warke za ta dawo aiki." "Allah ya ba da lafiya yaran ne sai a hankali. Har yau ya kasa mantawa ya rungumi ƙaddara." "Komai zai wuce aci gaba da masa addu'a." "Muna nan muna yi." Mommy ta ce sannan suka shiga cikin motar suka tafi. Suna fita Baba ya tsaya a ƙofar get ɗin gidan cikin tsananin mamaki."Ke don ubanki kar kar ki sanya na shiga gidan mutane su yi mini duka?" Ya ce mata cikin mamaki yana kallon gidan. "Allah baba nan ne su Anty Nasreen suka dawo, muma Ya Ahmad ya ce zai mayar da gidanmu na zamani." Mamaki sosai ya kama shi musamman da ya ga ta tura gidan ta shiga."Baba ka shigo su Anty Sha'awa ma suna ciki." Ta ce masa bayan ta leƙa cikin harabar gidan. "Ikon Allah!" Ya furta daidai lokacin da ya tura kofar ya hango Musaddik da yake wasa a cikin gidan. Da sauri ya shige da mulkin buhunsa. Anty Sha'awa ta fara ganinsa yana zare idanu, sannan ta nuna wa Nasreen da take riƙe da wayarta. "Saboda ba ni daraja da ƙima ina mijinki za ki bar ni a cikin talauci ki dawo gidan da ɗana ya gina miki?" Ya yi wa mata tambayar cikin takaici yana kallon gidan. Ahmad ne ya fito daga cikin gidan jin muryarsa."Baba sakin Mama za ka yi domin sam bata dace da kai ba." Jin abin da ya ce sai ya kalle shi cikin fushi."Kai Amadu ka kiyaye ni kar nayi masa baki, saboda ko yi arziki sai ka sanya na rabu da matata, kar ka manta duk arzikin da ka yi nine ubanka." "Na sani amma dole yau ka sake ta. Kullum ranar duniya sai na yi dana sanin fitowa daga tsatsonka, domin ka haife mu ka kasa bamu kyakkyawa kulawa da za mu tashi cikin tarbiyya. Haihuwarmu kawai ka sani, amma ba ka san cinmu da shan mu ba. Na yi kuka sosai da ka kasance mahaifina, kullum fatanta Ubangiji ya bani abin da zan siya mana gida mu bar rayuwar ka ta dabbo..." "Kul! Ahmad karka ƙarashe." Mama ta ce masa ganin yadda ya fusata. "Ki bari kawai Mama na gaya masa Allah kaɗai ya san kuma da na yi saboda dana sanin kasancewarsa mahaifina. Ya cutar da mu ya sanya wasu daga cikin 'yan'uwanmu cikin wulaƙantacciyar rayuwa. Ya yi sanadin da wasu yan uwansu suka zama faɗɗararru." Ya ƙarashe maganar yana hawaye. "Ka yi haƙuri don zai sake ni, saboda ni kaina rayuwa nake yi cike da dana sanin kasancewarsa mijina." Baba sai ya shiga cikin tashin hankali ganin ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Ga arziki amma za su yi masa bore."Wallahi ko kashe ni za ku yi ba zan sake taba, kuma aurena da mahaifinyarki mutu ka raba.... In har kana tunanin zan iya aminta gara ka daina, duk arzikin da ka samu da ni za a ci." Hannun Ahmad ta kama ta kalli Baba ta ce,"In har ni ce zan ci gaba da auren da kai na haƙura da kai, don haka ka faɗi sadakinka yanzu zan biya ka." Hankalinsa ya tashi ganin da gaske yake yi."Na gaya muku ko wuƙa za ku sanya mini a maƙoshi ba zan sake ki ba." "Ni kuma ba za ka zauna mini a gida ba " Ahmad ya ce tare da jan hannun Mama suka shiga. Kafin su shiga har ya riga su shiga ya zauna a falo yana raba idanu. Babu wanda ya kula shi, haka ya gama surutunsa ya shige cikin ɗakin Mama. Bayan Ahmad ya gama hutun gajiya, ya shigo falon Nasreen na zaune a falo da wayarta. Gefenta ya zauna tare da kama hannun Musaddik yana mishi wasa." Barka da shigowa yayana." Ta furta tana kallon sa. "Yauwa ya hanunn na ki? Na ga raunin ƙafarki ya yi sauƙi." "Eh sosai har na daina ɗingishi." "Allah ya ƙara sauƙi tun da kin samu sauki ki shirya zamu je boutique ku siyo kaya, sai ki zubarwa Mama muje da yaran." Murmushi ta yi jin abin da ya ce."Allah ya ƙara buɗi Yaya." "Amin." Ya furta tare da miƙewa. "Bari na shiga ciki na gaida Mama." "To Yaya." Ta ce tare da mayar da hankali ta kan wayarta. Har ya fara taku sai kuma ya tsaya ya ce,"Ki gaya wa Marwana ta shirya sai mu je tare ita, ma ta zaɓa abin da take so sannan ta taya ki zaɓar kaya, saboda so na ke ki suyi kaya masu tsadar gaske." "To Yaya Ubangiji ya ƙara buɗi." Numbar ta ta kira ta sanar mata tare da miƙewa don ta fara shirya yaran. Marwana ba ta ɗauki lokaci ba ta zo. A motar Ahmad suka shirya tafiyar don haka ta shigo da na ta motar cikin gidan. Tun da ta shigo kaya yake kasa. Gabakiɗaya daya ta kasa sakin jikinta, har sai da Nasreen ta fahimta. Wani irin kunyar Mama take ji sosai. Ahmad kawai suke jira daya shiga wanka. Bayan ya fito ya shirya cikin yan kaya kuma ya yi kyau sosai. A gogonsa yake ɗaurawa Nasreen ta yi sallama ta shigo. "Mun shirya Yaya Marwana ma tun ɗazu ta zo." Jin ta ambaci sunanta sai ya ji gabansa ya faɗi."Ok ina zuwa." "Wow! Ka ga yadda ka yi kyau?" Ta ce masa tare da kama ƙofar za ta fita. "Ko ƙanwata? Kema kin yi kyau sosai na yi mamakin yadda kika canza." "Aikin Marwana ce ita take kula da ni sosai." "Marwana yar aljanna ce babu wacce ta kai ta a gurina, saboda ta kula da ahalina." Daga masa kanta ta yi sannan suka fito tare. Ganin sun fito sai Marwana ta miƙe cikin jin kunya ta ce,"Ina wuni Ya Ahmad." Kallonta ya yi na dan daƙiƙa."Kina lafiya ya Mommy." Kasa amsa tambayar ta yi ganin yadda ya yi kyau kuma ya yi mata ƙwarjini. A gidan baya suka shiga sai suka sanya yaran a gaba. Tun da suka shiga motar Ahmad da Marwana sun kasa magana, sai Nasreen take ta zuba sai dai su amsa da um ko a'a. Ganin haka ta ja bakin ta ta yi shiru tana kallon titi. Marwana kuwa kasa sakewa ta yi, saboda duk ta kalli madubi sai sun haɗa ido da Ahmad. Wani iri take ji game da shi har ta kasa jurewa. Da suka isa cikin boutique ɗin. ATM ɗinsa ya miƙa musu."Marwana ku sayi duk abin da kuke so, sannan ki zaɓawa Nasreen kayan da kika san za ta zama babbar mace mai aji." Murmushi ta yi cikin jin kunya ta karɓa."Ya Ahmad kana son Nasreen sosai." "Ya zama dole na kula da ita. Ku je ku zaɓa bari na duba abin da na ke so." Godiya suka yi masa sannan duk wuce don su fara siyayyar. Kamar yadda ya ce kaya sosai na manyan mata ta siyawa Nasreen. Ganin tun da suka shiga kayan take zaɓa mata sai takama hannunta."Please ki zuwa kanki kayan sun isa, kar ki manta da zan fara aiki kin siya mini wasu." "Akwai buƙatar ki yi updating kanki Nasreen,musamman yanzu da kika yi babban catch up. Abokin Yaya Damir ya ganki yana so. Na share batun ya Damir yanzu campain ɗin Ya Annur na ke miki. Yana da kyau sannan akwai ya'yan banki, kuma yana da ilmi sosai injiniya ne shi, shi yake yi wa kampaninmu zane." Mamakin abin da take faɗi ta yi, sai kawai ta yi dariya ta ci gaba da duba kayan."In har kika kula shi ba za ki yi nadama ba, saboda gayen ya haɗu ta ko ina." Ba tare da ta ce mata komai ba ta cigaba da duba kayan."Kin ga wannan zai yi miki kyau, bari na fara zabar miki tun da kin kasa." Nasreen ta ce tana nuna mata doguwar riga. Siyayya sosai suka yi har sai da suka gaji. Ko da suka gama suka kai masa ATM ɗinsa kallonsu ya yi."Saura bags and shoes ki zabar mata dayawa, waɗannan sun yi kaɗan." Jin abin da ya ce yana miƙawa Marwana katin sai ta kama hannunsa."Wallahi sun yi ina zan kai kaya?" "Je ki zaɓar mata so nake duk inda ta wuce sai an kalle ta." Ta kasa magana kawai kallonsu take yi da hawaye. Sai da yamma sosai suka dawo, sannan Marwana ta yi musu sallama ta tafi. Kallon kayan Mama ta yi sai alkbarka take sanya mishi. Nasreen ba ta ƙara yarda ta zama yar gatan Yaya Ahmad ba, sai da ya shigo da makullin mota. Miƙa mata ya yi ta karɓa tana zare idanu. "Mota na siya miki Nasreen tun da kina aiki kina buƙatar mota ga kuma dauko yara." Zare idanu ta yi, tana kallon sa cikin tsanannin murna da mamaki. Sunan Mama ta kira da karfi sai ta rungume shi tana hawaye."Ikon Allah ashe ni ma zan tuƙa mota? Mota Yaya Ahmad ya siya mini." Mama cikin murna ta ce,"Masha Allah rayuwa ta canza Allah ya yi albarka." "Amin can gidan ma na sanya za a zo a rushe a gyara musu." "Da kyau Ubangiji ya ƙara buɗi." Jin hayaniya Baba ya fito daga ɗakin Mama, tun da ya zo gidan da ƙyar ranar kwanarsa yake tafiya, duk da cewar kallon arziki baya samu a gurin ta. "Amadu yanzu kana da kuɗi amma ba ni da maraba da almajirin gidan nan. Kowa ka canza masa kaya, amma ni ina yawo cikin tsumma?" "Haka ya kamata ka yi rayuwa saboda sam bana tausayinka, ko gidan nan da kake zama ina jiran na gama abin da ake yi sai ka saki Mama bisa dole." "Wallahi ba zan saki matata ba in har mafarki kake ka farka." "Banza ya yi da shi ya miƙe cikin jin hushinsa ya fice. Sam a zuciyarsa baya jin tausayinsa. Kallon Mama ya yi yana Ayi haƙuri da wannan 🙏🙏🙏🙏 WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 30 "Banza ya yi da shi ya miƙe cikin jin hushinsa ya fice. Sam a zuciyarsa baya jin tausayinsa. Kallon Mama ya yi yana faɗin,"Kina ganin har mota ya siya wa Nasreen, amma ni ubansa ko wayar kirki bai siya mini ba?" "Mai zan ce masa? Alokacin da na ke gaya maka, irin wanna rana kar yazo ai ba kasaurare ni ba. Haka ka haife su kara zube suna yawo kaman awakai a gari, ba tare da kula kula da rayuwarsu ba, sai yanzu ya samu ya inganta kansa nayi masa dole? Sam ba zan takura masa ba domin haka ya kamata ga azzalumai iyaye irinku, waɗanda suke yin aure don biyan buƙatarsu ba wai don su haihu, ranar gobe ƙiyama Ubangiji ya yi alfahari da su ba." "Amma ko mai nayi masa ai ba a sake wa tuwo suna? Saboda har yanzu ina nan da matsayina na mahaifinsa?" "Ana sakewa in har ya kwana ya zama ɗumame." Mama ta ce masa tare da shigewa cikin ɗakinta. Nasreen tana shiga cikin ɗaki ta kira wayar Marwana."Na yi mota Marwana Ya Ahmad ya siya mini mota." Ta ƙarashe maganar cikin ihu. Ita ma ihun murna ta sanya sannan ta ce,"Na yi miki murna sosai sai na zo gani." "Ya ce zan fara zuwa gurin koyon mota." "Ki gaya masa zan koya miki." "Yauwa na gode sosai." "Su Nasreen an zaman yan mata wayyo Allah ina ma Faruk zai ganki?" Tsaki ta yi ta ce,"Bana fatan Allah ya ƙara haɗa ni da shi." Sallama ta yi mata kashe wayar. Cikin nasara ta fara koyon moton don har ta fara iyawa. Mai mai tsada da suka siyo ta fara shafawa. Lokaci guda ta canza ta zama mace mai class. In har ka san Nasreen a da to ina tabbata maka yanxu ba za ka gane ta ba. Ita kanta sai ta yi ta kallon madubi wai ita ce kuwa. Dan kwanakin da suka yi a cikin daula, ta jikinta ya canza ta goge sosai ta zama tamkar tarwaɗa. Ko ina ya ciko sai juyi ta ke yi abinta tubarkallah. Ranar da Marwana ta biyo mata za su je wankin kai. Mamaki ya kamata tsaya tana kallonta. "Nasreen kin ga kuwa yadda ki koma?" Dariya ta yi tare da kama hannunta."Mu je don Allah. In kowa yana mamakin canzawata har da ke?" "Hmmmmh! Ba ki ga yadda kika koma bane wallahi ni kaina da nake mace kamar na haɗiye ki. Ina ga gobe zan kawo Ya Annur gidanku na huta da mitar da yake mini." Ba ta ce mata komai ba, sai ta yi dariya kawai. Ƙara kallonta ta yi tana fatan ina ma ace Damir zai ganta. Da suka shiga mota. A motar Nasreen suka fita. Ita ce take tuƙa su. "Yaushe za ki koma aiki?" Jin tambayar da ta yi mata ta bata fuska."Ni fa aikin nann." "Karki manta Mommy da kanta ta zo ta bada haƙuri, sai dai kuma in za ki bijire mata." "Ni na isa ƙarshen wata in sha Allahu. Ingawa ma yana ta mini ƙorafi." Tsaki ta yi ba tare da ta ce komai ba jin abinda ta ce. Damir ya shiga cikin wani yanayi tun ranar da abin ya faru. Ji yake rayuwarsa wani iri. Hatta Little Marwana ya shafe ta, domin ya daina kula da ita kamar yadda yake yi a da. Ya daina surutu komi sai kallo, in yan gida to yana ɗaƙinsa a kulle yana kwance. Ba bacci yake yi ba, amma ya gwammce ya zauna shi kaɗai. In kuwa gurin aiki ya je shi ma baya samun sauƙin domin duk ma'akacin da zai shigo yana kalla da ta window. Burinsa zancen aje aikin ya zama wasa, amma har akayi sati biyu da faruwar haka ba ta zo ba. Hankalinsa ya yi matuƙar tashi, saboda wani yana yi da ya tsinci kansa. Sai ya rinƙa shiga damuwa ina y tuna ba ta kampanin, saboda damuwar da ya sanya wa kansa har faɗawa ya yi,ga shi Momi ta yi halin ko ina kula da rayuwarsa. Ko abinci ta ce masa ga shi ya ce ba zai ci ba, to ba za ta ƙara masa maganar ba, saɓanin da za ta tas shi a gaba kamar wani karamin yaro har sai ya ci. Lamarin Marwana kuwa shi yafi ƙona masa rai, saboda kullum a gidan nan ba ta da zance sai Ahmad ya yi wa Nasreen kaza. Nasreen kaza kuma abin takaici Momi da Muhsin su yi ta biye mata ana hirar.. Gabakiɗaya ya zame musu bare a cikin gidan. Hatta Little Marwana fita sabgarshi take yi, ganin yadda yake ci magani ta maƙale wa su Hajiya. Damuwa ta yi masa yawa. Ga yawan tunanin abin da ya yi mata, wanda suke sanya yan jin takaicin cutar da ita da ya yi, hakan kuma ke nasarar saka tausayinta da yake rikiɗewa yan zama masa abin da baya fatan shi ne. Wani lamarin da ya kara damunsa a yanzu feelings ɗinsa yana canzawa, saɓanin da yake jin ya yi isolating kansa da kowa, domin in har yana cikin mutane hatta atmosphere na gurin ba ya yi masa daidai, amma yanzu sai ya ji he is feeling lonely a lot. Lonely da yake sa zuciyarsa cikin tsananin buƙatar some one that will keeps his accompany, if possible ya ji mutum a jikinsa har ya yi hugging ɗinsa, wannan sabon al'amari da yake ji dai ya rikita tunaninsa, don haka ya jawo yarsa Little Marwana kullum yana tare da ita, don ta ɗauke masa wannan kewar, amma kuma sai dai babu abin da ya ragu, domin wannan kewar daban ce ba irin wanda za ta ɗauke masa ba. Ganin yana ƙoƙarin cutar da kansa sai yake kokarin fitowa falo, amma babu amfani, domin da alama mutanen gidan sun gaji da halinsa, domin babu wanda ke kula shi sai dai su yi ta hirarsu. Shi ne da ya ke binsu dai idanu yana fakewa da kallo yake yi, amma duka bin da suke cewa babu wanda ba ya ji,musamman in suka ɗauko hirar gidansu Nasreen sai ya mayar da hankali fiye da da. A hankali ya tashi ya fara hawa sama tamkar marayan da ya rasa uwarsa. Kallo suka bi shi da shi har ya haye. Momi ce ta yi tsaki ta ce,"Wallahi Yayanki haushi yake bani sosai, saboda na tabbata da ace shi ya mutu, Batula ba za ta yi wannan jimammin haka ba." "Mai zai sanya ta yi Mommy? Musamman zai bar mata arziki, amma shi har yanzu ya kasa mantawa da ita ya fuskanci rayuwarsa na gaba." Shiru kawai ta yi saboda takaici ba ta tare da ta ce komai ba. Da ya shiga cikin ɗaƙinsa kan gado ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, tare da janyo filo ya matse a ƙirjinsa. Idanunsa suka canza daga farare tare zuwa wasu kalar. Ya daɗe a wannan halin ya jin tamkar ya mayar da filon cikin jikinsa kafin bacci mai karfin gaske ya kwashe shi. Bacci da ya yi, ya ɗan samu raɗaɗin ƙuncin da zuciyarsa take ciki. Yana zaune ofis ransa na ƙuna Muhsin ya yi sallama ya shigo."Na rasa yadda aka yi ma'aikatan nan suka raina ni, sam ba sa son zuwa aiki kowa sai ya rinƙa fashi duk lokacin da ya ga dama. To ka gaya musu duk wanda ya kara fashi sai na cire kuɗinsa." Kallonsa ya yi cikin mamaki."Amma kuma Ya Damir suna ƙoƙari fa, kuma yau kowa ya zo aiki Nasreen ce kawai ba ta zuwa, kuma Marwana ta kawo maka resignation letter, sai mu nemi wanda zai yi replacing ɗinta." Wani wawan tsaki ya ja don ba haka ya so ya ji ba. So yake ya gaya masa zai kara tuntubar Marwana ta dawo aiki, tun da ya ji Mommy ta je gidan, wataƙila ta ba ta haƙuri kuma ta haƙura. Tattara tarkacensa ya yi ya fice daga ofis ɗin. Muhsin raka shi da idanun ya yi tare da murmushi ya girgiza kansa. Ya dawo daga gurin aiki ya shigo falo. Suna zaune suna kallo ya yi sallama. Zama gefen Momi daidai lokacin da Marwana ta fito da ɗan kunni tana faɗin,"Mommy taimaka mini ki sanya mini dan kunnin nan, Ya Annur ya kira ni yana hanya za mu je gidansu Nasreen." Wani irin kallo ya watsa musu yayin da ya ji maganar ta duki zuciyarsa."Ke ma kin cika nawa tun safe ya sanar miki sai ki shirya." "Mommy little Marwana ta wahalar da ni gurin parking gashinta." Jin abin da ta ce sai ta yi dariya. "Na lura yau tsiya ta ke ji." "Sosai har sai da na ce mata zan kaita gurin Raihan." Murmushi Mommy ta yi bayan ta sanya mata dan kunnin ta ce,"Ga hon ɗinsa nan kamar yana kofar gida sai ki yi sauri." "To kafin ya shigo bari na ɗauko mayafina. Momi da sawa Little Marwana takalminta." Ta ƙarashe maganar tana hawa upstairs da sauri. Damir sai ya tsinci kansa da tashin hankali.Miƙewa ya yi yana jin kamar ya ja hannunta ya ce ba za ta je ba, amma sai kuma ya fara tafiya ba tare da ya kalle su ba." Yana ƙoƙarin hawa sama Annur ya shigo. Cikin girmama ya gaishe da Mommy tare da ƙarasawa gurina ya miƙa masa hannu. Haushinsa sosai yake ji tamkar ya rufe shi da duka. A maimakon ya ba shi hannu sai ya zura cikin aljihun wandonsa. Ganin haka ya zauna yana kallonsa. Miƙewa Mommy ta yi."Bari na sanya Hajjo ta kawo maka ruwa, kafin Marwana ta fito." Ta nufi hanyar kicin. "Yane Damir?Zan je zance tun da ka ƙi yi mini hanya, ka je ɗaurin aure ai?" Wani banzan kallo ya watsa masa tare da jan ƙaramin tsaki ya haye sama da sassarfa. Marwana ce ta sauko tana murmushi."Sarkin nawa har yanzu ba ki shirya ba?" "Kai Yaya Annur na shirya muje." Jin abin da ta faɗa ua miƙe yana yi wa Hajiya sallama. Nasreen tana kicin tana haɗa salat, cikin sauri saboda Marwana ta kira ta ta sanar mata suna hanya. Tana ƙoƙarin kaiwa dinning ta shiga wanka Ya Ahmad ya shigo. '"Babu inda zan je, saboda ina son na ga ƙanwata tana zance." Dariya ta yi tare da rufe idanunta cikin jin kunya. Yana ta tsokanar ta su Marwana suka iso. Fita falo ya yi domin ya ƙosa ta zo, tun da aka ce za ta zo ya ƙosa, ya rasa dalilin da ya sa yake jin nauyinta da son ganinta. Tana shigowa ganinsa a falo ta ji nauyi. Cikin jin kunya duk gaisa sannan ya saki ajiyar zuciya ya fita. Nasreen ce ta fito cikin shiga ta alfarma. Cikin jin kunya ta saci kallon Annur saboda ba ta san shi ba. Ganinsa kyakyawa sai ta ji ya kwanta mata. Annur kuwa duk ya susuce domin sai ya ga kamar ta canza a ranar da ya ganta. Ganin yadda ta yi kyau sai ya ji kamar a ɗaura auren. Sun fahimci juna sosai tare da musayar numba. Nasreen ta ji ya kwanta mata sosai. Kasancewar haɗuwar farko ce ba su jima ba ya tafi. Shiryen-shiryen komawa aiki take yi, da saboda Mama da ta takura mata. Duk wani shiri ta yi jira take Monday ya yi. Farouk kuwa hauka tuburan ya yi saboda in ya tuna kuɗinsa, sai ya ji gara ya dawwama a cikin haukar. Sai dai nacewar da danginsa suka yi da magani Allah ya ba shi lafiya, domin a sanadin ciwon mahaifiyarsa sai da ta zo Nigeria. Tun da ya warke ba shi da aiki sai kuka ya ƙi cin abinci duk irin rarrashin da suke masa. Yana warkewa aka zo da motar 'yan sanda kan maganar kuɗin gidan da aka shi. Da ƙyar aka samu aka biya kuɗin don sai da aka sayar da gidansa da ya fara gini, sannan mahaifiyarsa ta cika sauran. Ya rage ba shi da wata ƙaddara da ga gidan da yake ciki sai kuma motarshi da aikin yi. Duk lokacin da ya tuna, ya rasa maƙudan kuɗin da ya ɗauki tsawon shekaru yana tarawa ba tare da ya ci ba, sai ya ji kamar haukar za ta dawo sabo. Ganin dai an neme ta wa ƙaura da wambai, amma ba a samu ta ba, sai dangana, amma ba don ya haƙura ba. Gabakiɗaya ya rame, ya fita hayyacinsa ko aiki sai da mahaifiyarsa ta yi masa da gaske ya fara zuwa. Yana zaune a cikin ɗakinsa ya tasa ruwan Lipton yana kallo, wai yau shi ne zai sha ruwan bunu, saboda ba su yi albashi ba. Tun bayan da lamarin ya faru, da ƙyar yake iya kai abinci bakinsa, don shi ma an yi masa dole, da kuma yunwar da ta kusa kaishi lahira. Kallon gidan ya yi cikin ƙuna yana tuna rayuwar da ya yi da Rashida. Rintse idanunsa ya yi cikin takaici ashe makashinsa ya rinƙa kiwatawa yana bata abinci. A ransa ji yake da ace zai ganta babu abin da zai hana bai kashe ta ba. Ya yi kuka har hawayen sun daina fitowa, musamman inya duba duk bankinsa ba shi da komai dai kuɗin albashi da yake jira, wannan lamari yana sanya duniyarsa ƙuntata. Yana kwance kan dogon kujerar idanunsa rufe yana hawaye. Zuciyarsa ta tuno masa da Nasreen. Saboda tsananin razana har sai da ya miƙe, saboda yadda zuciyarsa ta buga da karfi. Tun bayan da suka rabu bai ƙara tunainta ko da na sakan ba, ballanatana ya tuna yaransa da suke gurinta. Zaman da suka yi, abin da rinƙa dawo masa kamar yanzu yake faruwa. Rintse idanunsa ya yi cikin tsanannin tashin hankali yana tuna rayuwar da suka yi. Ga mamakinsa sai ya ji hawaye lokaci guda wani irin nadama ya fara shigarsa, tare da sonta mai tsananin. Sosai yake nadamar rayuwar da suke yi, musamman abubuwan da ya yi mata na ƙuntatawa."Ko yanzu tana ina?" Ya yi wa kasa tamabayar cikin tsananin tsoro. Ya san dai tana gidansu domin a yadda ta ke cewa ta tsani aure ba za ta yi aure da wuri ba. Ya dan har yanzu tana nan a cikin ƙangin talauci, saboda service ba zai canza rayuwar talaucin da suke ciki ba. Tashi ya yi yana zagaye falon yayin da zuciyarsa take ba shi shawarar ya je ya samu Baba kawai ya lallaɓo shi da kuɗi ya dawo da ita, domin a yanzu ya fahimci Nasreen ita ne kawai da za ta iya jure halinsa. Kamar an tsiƙare shi, ya miƙe domin a zuciyarsa ya yi na'am da shawarar da ta ba shi. Ya san Nasreen tana da haƙuri, duk da cewar ta fara canzawa kafin su rabu, amma in ya bawa Baba kuɗi ya kuma roƙe ta, saboda talauci da su Raihann Baba na yi mata dole za ta dawo, don haka bai yi kasa a gwiwa ba, ya shiga ciki tare da fesa wanka, duk da ya rame, amma yana nan a Faruk dinsa ɗan kwalisa da isa. Sai da ya gama wanka ya shiga motarsa zuwa biko, amma sai ya tayar da motar ta ƙi tashi. Tunawa ya yi da mai ya ƙare ya sanya shi sakin tsuka cikin takaici. Ga shi ba shi da ko sisi, domin ko abincin da zai ci kafin ƙarshen wata sai ya ranta. Kan dole ya kashe motar ya fito ya bar zuwa bikon sai an yi albashi. A ranar da ta kasance Monday za ta je aiki. Tun safe ta tashi ta sanya musu ruwan wanka. Wanka ta yi bayan ta gama azkar ɗin ta. A yanzu suna da mai aikin da take share-share a gidan. Zama ta yi ta bata lokacinta gurin gyara jikinta, amma ba ta yi heavy make up ba sai ta yi light. Bayan ta ta ma ta ɗauki abayarta sabuwa ta sanya sannan ta yi rolling gyalen abayar. Sabuwar wayarta ta ɗauka da key ɗin motarta ta fice. A falo ta samu Baba da ya zauna a gaban tibi yana kallo kamar zai shige ciki. Gaishe shi ta yi sannan ta wuce ɗakin Mama. Tana zaune da carbi a hannunta. "Ina kwana Mama?" "Lafiya lau kin shirya?" "Eh, zan wuce." "Shikenan sai kin dawo Allah ya yi miki albarka. Don Allah ki haƙuri da halin Damir, ki rinƙa kauda idanunki kin ga mahaifiyar sa da kanta ta zo ta bada haƙuri." "Mama, babu ruwan da shi amma wallahi ba zan ɗauki rashin mutunci da ba, saboda na lura in har ba cire tsoronsa na ke yi na nuna masa ba ya tsorata ni ba zai barni na zauna lafiya ba." "Don Allah kar ki yi masa rashin kunya duk abin da yake yi, ganin sanadin taimakon ki hakan ya faru." "Amma ban yi masa dole ya taimake ni ba, sai yanzu nake takaicin jininsa da yake yawo a jikina, saboda sam ba shi da tausayi da tafiya." Mamakin abin da ta ce ta yi kafin ta yi magana ta fice tana cewa,"Mama, na tafi kafin na yi latti jarabbaben ya samu abin mini rashin mutunci." Kasa amsawa ta yi ganin kodayaushe gogewa take tana rage tsoro. Ɗakin Ahmad ta shiga yana kwance da waya a hannunsa."Yayana na shirya zan wuce." Ta shi ya yi ya zauna yana kallonta. "Kin ga yadda kika yi kyau? Sai kin dawo kar ki sake wani ta raina mini ke." Dariya ta yi ta ce,Babu shi yanzu a duniyar nan tun da ina da kai." "Drive safe sis." Amsawa ta yi sannan ta fice. Da bismillah ta shiga motar ta tayar a hankali take tuƙi har ta isa get ɗin shiga kampanin. Wani abin mamaki duk tsoro da bugun zuciya babu. Hankalinta a kwance maigadi ya buɗe mata. Tana ƙoƙarin shiga motar Damir ta sanyo kai sai kuma Hajar da take bayansa. Kallon motar ta yi, ba tare da ta ji komai ba ta shiga ciki. Ita ta fara yin parking sai shi ya wuce inda yake ije motarsa, Hajar ta yi parking kusa da ita. A hankali ta buɗe motar ta ɗauki wayarta da jakarta. Hajar ce ta rugo da sauri ta rungumeta. "Nasreen jin ya kika yi ko kin je canza halittar ki ne?" Ta yi mata tamabayar cikin tsananin mamakin yadda ta koma. Damir da yake ƙoƙarin rufe motarsa, yana jin ance Nasreen da sauri ya kalli gurin zuciyarsa na bugu. Cire idanunsa ya yi cikin mamaki yana tunanin ita ce ko gizo idanunsa suke masa, amma kuma sunanta da aka kira ya gaskata masa da ita ce. Mamaki sosai ya kama shi ganin yadda ta yi kyau ta canza kamar ba ita ba. Da sauri ya rufe kofar da ƙarfi har sai da suka waiwaiya suna kallonsa "Kin ga ganinki ya mantar da ni Ya Damir ya shigo. Mu je mu gashe sa." Ta ƙarashe maganar tare da kama hannun ta da nufin su ƙarasa inda yake. Zare hannunta ta yi, tare da nuna mata alamar ba za je ba. Hajar ta buɗe baki za ta yi magana, sai ta ga ya fara tafiya zai wuce, kuma dole ta inda suke zai biyo. "Ina kwana Ya Damir." Suka haɗa baki a tare gurin faɗin haka. Da sauri ya juyo, jin muryarta rangaɗaɗau babu alamun tsoro ko rawar muryar da take yi ada, saboda muryarta har ta fi na Hajar. Kasa amsawa ya yi, sai kawai ya yi motsi da bakinsa tare da ƙara saurin tafiyarsa. Hajar ta bishi da kallo ganin mood ɗinsa, ita kuwa ƙaramin tsaki taja tare da sakin yar dariya yadda zai ji tana yi wa Hajar magana. A ranta ta sanya bazata ƙara tsoron kowa ba, tun da ya Ahmad yana nan ko ya koreta ba ta da matsala. Allah kaɗai ya san yadda ya ji a lokacin da ta saki dariyar. Mamakin maganar da ta yi masa ba tare da shakka ko rawar murya ba, da kuma yadda ta yi kyau ta canza kamar ba ita ba suka kama shi. A maimakon ya ƙarasa kujerar ya zauna, sai dai ya dawo kujerar da hannunsa saboda ba shi da ƙarfin da zai iya ƙarasawa inda kujerar take. Wani irin yanayi ya shiga idanunsa suke masa gizonta. Da sauri ya rintse idanun yana fatan kar su ƙara masa gizagonta. Saman kansa ya shafa, yana jin ephoric feelings yana taso masa tun daga yatsun ƙafafunsa har zuwa kwanyarsa, amma saboda taurin kai da girman kansa sai ya ƙaryata haka. Hannunsa ya haɗa ya dunkule tare da fara zarya a ofis ɗinsa. Idanunsa ya rintse da suke ƙara muradin ganinta. Ƙoƙarin hana hakan yake yi, amma zuciyarsa na yi masa ingiza mai kantu da ya buɗe windonsa ya ganta. Ba tare da shiri ba ya aiwatar da muradin zuciyarsa. Da sauri ya saki saboda wani irin bugawa da zuciyarsa ta yi. Ta canza ta yi kyau. Da ya ga sabuwar mota, san sai yi tunanin ita ba, saboda yadda mai motar yake tunawa cikin natsuwa. "Mai ya sa take shiga cikin farincikin baya ta sanya ni cikin damuwa, haka na nufin ba ta laifi kan abin da ya faru?" Ya yi wa kasa tambayarta yana shafa sajensa da ya kwanta a kyakkyawar fuskarsa ya kuma ƙawata fuskar. Komawa ya yi ya zauna yana tuna shigarta. Ga mamakinsa dawowarta aikin sai ya tsinci kansa cikin tsanannin farinciki, domin ji ya yi zuciyarsa kamar ana sauke masa dutsen dala. Ba tare da sani ba wani laulausar murmushi ya kubce masa, har bai san lokacin da ya jawo laptop dinsa, ya fara aiki ba. Jefe-jefi zuciyarsa na tuno masa ita, tana bugu da sauri. Nasreen kuwa bayan ta shiga ofis ɗinta ta zauna. Wayarta ta fara ƙara, ganin Annur ne ta saki laulausar murmushi ta ɗauki wayar. Ba su jima ba, ta kashe saboda sallama da ya yi mata sanin tana gurin aiki. Marwana ta kira ta sanar mata da ta zo, sannan ta kashe wayar ta fara aiki. Hankalinta na kan aiki Ingawa ya shigo. Murmushi ta yi tana kallonsa."Nasreen tauraruwar mata kin ga kyawun da kika ƙara? Gaskiya zan iya cewa kamar hurul ain." Dariya maganar ta bata sai kawai ta kalle shi." Finally ƙanwata matata to be ta dawo aiki." Ya ce mata yana kashe mata idanu. Murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba. Sun ɗan taɓa hira ya tashi ya koma ofis dinsa. Wayo shafin nan ya tayar mini da tsohon tsimi har na ji ina son rera waka. Habibi kai duniya ne💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃❤️❤️❤️❤️ su Damir an faɗa lambun soyayya. Ayi haƙuri da wannan 🙏🙏🙏🙏 WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whats *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 31 Murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba. Sun ɗan taɓa hira ya tashi ya koma ofis dinsa. Oga Damir a ranar haka ya tsinci kansa da matsanancin farinciki. Aiki sosai ya yi har yana mamakin kansa, domin rabon da ya yi irin aikin har ya manta. Ganin aikin da ya yi Muhsin ya riƙe baki."Please Ya Damir ka huta tun safe kake aiki." Files ɗin hannunsa ya karɓa."Karka damu I will do it." Sai kuma ya kalle shi ya ce,"Bari ka gama wannan sai mu je lunch, saura minti goma lokacin break ya yi." Zare idanunsa ya yi ya ce,"Ya Damir yaushe rabonka da ka je gurin lunch take away ake maka?" "Yau ina son na je naci abinci da ɗan'uwana laifi ne?" "A'a." Ya ce yana mayar masa da murmushin da yake masa. Mamakin ya ƙara kama shi ganin yana ta yi masa surutu. Ya ma rasa bakin amsawa sai dai ya ɗaga masa kai. "Time up let's go." Ya ce masa tare da miƙewa yana kashe laptop ɗinsa. Shima miƙewa ya yi cikin mamakin abin da ya sanya shi farikciki. Shi ya fara gaba ya bishi a baya cikin mamaki. Damir kuwa tsintar kansa ya yi, da zuciyarsa na kitsa masa ya je inda ma'akaita duke lunch, wataƙila ya ga Nasreen da zuciyarsa ke ƙara son gani. Shi lamarin mamaki ya bashi, ganin duk yadda yake son hana xuciyarsa abin da take so ya ci tura, saboda a yadda yake ji ganinta shi ne maslahar, da za ta bar zuciyarsa bugawa da sauri tamkar za ta fito waje. Suna tafiya yana raba ido tamkar wanda matarsa ta ɓace, amma cikin rashin sa'a bai ganta ba. "Yaya, what for lunch?" "Water." Ya ce masa domin da gaske baya jin cin komai. Kallonsa ya yi cikin mamaki ya ce,"Amma ka ce mu je mu yi lunch?" "Yanzu na rasa appetite ɗina please I need only water." Ya ce cikin ɗan damuwa ganin ba ta a gurin. "Ok,". Ya ce tare da fara tafiya zuwa gurin. Kamar ance ya ɗaga kansa, ya hagota tana tafiya da Ingawa sai Khausar. Wani irin mugun ɓacin rai ya ziyarce shi, har sai da ya yi dana sanin zuwa gurin. Da sauri ya miƙe tare da sakin tsaki zai bar gurin. Ganin haka Muhsin ya ƙaraso da sauri da lemu da ruwa da ya karɓo masa, sai kuma abincin da zai ci. "Ya Damir." Ya kira sunansa ganin ya tashi zai fice. Ba tare da ya kula ba, ya fice daga gurin zuciyarsa na tafasa. Muhsin ya bi gurin da kallo yana son ganin bin da ya ɓata ransa, ganin Nasreen da Ingawa sai ya kauda kansa ya bi bayansa da sauri. Yana shiga ya yi jifa da flower vest da aka yi kwalliya da shi a ofis ɗin."Mai yasa in na ganta da wani nake damuwa har na ji tamkar zan kashe wanda yake tare da ita?" Ya yi maganar cikin tsananin damuwa yana rintse idanunsa. Ba tare da ya bawa kansa amsa ba, sai Muhsin ya shigo."Ya Damir na.." "Please Muhsin I need my space can you go?" Jin tambayar da ya yi masa ya ce,"Ok,"Ya juya ya fita baya ya ije masa ruwan da lemon roba, yana mamakin ƙarfin halinsa. Kulle ofis ɗin ya yi, sannan ya zauna ya jingina kansa a danna kujeran yana jin wani ƙunci yana mamaye zuciyarsa. Nan take ya nemi farincikin da ya rasa. Sosai yake jin tsanar Ingawa a cikin ransa, har yana jin in har ya ci gaba da ganinsu zai iya rasa aikinsa, domin ba zai mayar masa da campani gurin soyayya ba. Haka ya wuni sukuku, kamar mara lafiya har lokacin tashi yayi. Da yazo zai tafi tare ya gansu sun fito. A wannan karon daurewa kawai ya yi ba tare da ya kalli inda suke ba. Nasreen kuwa ɗauke kanta ta yi ba tare data ji komai ba, ta yi wa Ingawa sama ta shige motarta. A daren damuwa ta yi masa yawa har ya kasa bacci. Ji yake zuciyarsa ba za ta iya cigaba da ganinsu ba, ya zama dole ya ɗauki matakin da zai kusanta su. Da tunanin matakin da zai ɗauka ya je aiki. Yana cikin wannan tunanin a ofis Annnur ya yi sallama ya shigo. Ransa ne ya ɓaci don ya san ba gurinsa ya zo ba. Kauda kansa ya yi ya ci gaba da aikinsa, bayan ya amsa sallamar tamkar an yi masa dole. Ƙarasowa ya yi, cikin sakin fuska ya ba shi hannu don su gaisa. Kamar am masa dole ya miƙa masa yana wani shan ƙamshi. Shi abin ma dariya ya ba shi. Ganin sun yi shiru sai ya katse shirun da cewar."Na zo gurin gimbiyarce, saboda ina son in ganta, gabakiɗaya na kasa sukuni jiya ne fa kawai ba mu...." Kasa ƙarashe maganar ya yi, ganin wani mugun kallo da ya watsa masa. "An gaya maka kuɗin banza nake samu da za to aiki ka biyo ta?" "To ya zan yi? Ka san dai yadda so yake ma zuciya, soyayyarta ya mini kamun kazar kuku.." "Annur ba na son ji. Please as you can see am busy." Ya katse shi yana faɗin haka. Dariya ya yi tare da miƙewa ya ce,"To ya zan yi yarinyar ce zazzafa ga shi ta iya kalamai tana kashe mini murya..." "Get out Annur before I show you my madness!" Ya daka matsa tsawa yana faɗin haka. Dariya ya saki ganin yadda ya kunna shi."Shikenan tun da ba za ka kai ni ba, bari na je Hajar ta nuna mini ofis ɗinta. Na ganta ko zan samu matsawa." "Ka san Allah? Daga nan sai fita ka tafi gurin aiki, amma wallahi babu wanda ya isa yazo ya yi soyayya da ma'aikaciya, ka bari in ta koma gida ka je ka haɗiyeta " Ya furta cikin tsanannin zafi yana huci. "Wai ni kan Damir ko son yarinyar nan kake yi?" Ya yi masa tambayar da ya razana shi. Zare idanunsa ya yi da sauri ya ce,"Allah ya kyauta mai zan yi da ita, karka manta ita ta raba ni da matata ta bar ni a gwauro?" "Wannan dalilin ya sanya na yi maka wannan tambayar, ka ga sai ka aureta ta maye gur..." "Allah ya tsare ni." Ya tsinci kanshi da faɗin abin da bashi ne a zuciyarsa ba. "Mene ne na tayar da jijinyar wuya? Tambaya ce, saboda naga yadda kake tada jijiyar wuya ne na ɗauka ko kishinta kake." "Aini na wuce da ajinta." Ya ƙara furta wa. "Haka ne mai aji, na manta ni dai bari naje na bawa fulawa ruwa." Biyo shi ya yi ya hana shi zuwa gurinta, har sai da ya raka shi gurin motarsa ya shiga yana ta yi masa dariya. Sakin ajiyar zuciya ya yi, ganin ya ci nasarar ƙorarsa ya koma ciki. A cikin kwanakin da Nasreen ta dawo aiki ya shiga cikin tsananin damuwa, yadda ita da Ingawa suke kunna shi, saboda a tare suke fitowa su shiga mota, kuma wani lokacin kamar haɗa bakin zuwa suke yi. Ga shi shi ma kamar an masa dole ya daidaici lokacin da take zuwa yake zuwa. In kuma ya riga ta zuwa, ba tare da ya ganta ba sai ya shiga cikin tashin hankali. Ya rinƙa safa da marwa har sai ya ganta. Ga kuma Annur da ya dame shi da maganarta. Wannan lamari ya jagula tunaninsa, har ya ɗan faɗa. Ya tabbata da za a gwada jininsa sai ya hau. Ana wannan diramar yarinyar kaninn mahaifinsa Hindatu ta tashi aure. Damir shi ne jigon bikin domin komai shi ya yi mata. Mommy ta ce amarya ta yi zaman biki a gidan, musamman da yake ƙawar Marwana ce suna shiri sosai, kuma mahaifiyarta da mahaifinta sun rasu. Tun da aka shiga satin bikin gidan ya fara kacamewa. Su Marwana babu zama kullum sai sun fita. Anko ta yi musu kusan kala biyar, duk wani events sai da suka yi ankon shi. Ana saura kwana uku bikin, ta shirya ta zo gidan Mama ta roƙe ta ta bar Nasreen, ta koma gidan su har a gama biki. Tana zaune a falo da Mama suna hira Nasreen ta dawo daga aiki. Tare suka shigo da Ahmad da ya dawo daga unguwarsu, duba gyaran da ake yi wa tsohon gidansu. Ganinta da sauri Nasreen ta ƙarasa tana murmushi, ta kama hannunta tare da zama kusa da ita. Shi ma cikin murmushi ya zauna gefen Mama, yana kallon Marwana, da shigowarsa ya sanya ta ije ɗanwaken da take ci. Ahmad kallonta ya yi, cikin wani kalan yanayi ya riga ya gama yarda tsananin ƙaunar da take yi wa ahalinsa ya sanya mishi matsanancin sonta kamar zai haɗiye ta. Wani irin sonta ya kamu da shi, mai kashe jiki da saukar da tsaƙo a ƙwaƙwalwa. "Sannu da shigowa Ya Ahmad." Ta ce masa cikin murya mai taushi. "Ƙanwata kina lafiya?" Tambayar da ya yi mata ya sanya ta ɗago idanunta, cikin jin kunya ta saci kallon sa, ganin ita yake kallo sai ta ƙara takura. "Ɗanwake ake ci babu ta yi?" Jin abin da ya ce sai ta miƙa masa filet ɗin ta ce,"Mama, ta iya girki sosai musamman dambu da ɗanwake, har da abin da kika yi nayi ta santi Mama, mene ma sunan shi?" Murmushi ta yi tana kallonta cikin tsanannin ƙaunarta kamar Nasreen take jinta, a ranta so take ta yi wa Ahmad umurnin aurenta ko da ace baya sonta, ballantana ta san babu wanda zai ƙi ta. "Ɗangauda." "Yauwa Mama shi ina son shi sosai. Da na koma har Mommy na gaya mata ina ta santi." "Allah ya sa sun yi miki waigi ba ki faɗi ba." Dariya ta yi tare da rufe idanunta jin abin da Ahmad ya ce. "Aiko zan yi miki da wara na sanya ki kaiwa Hajiya." Mama ta ce tana kallonta. "Mama don Allah na zo roƙonki, kan Nasreen ta ce gidanmu akwai bikin yarinyar ƙanin mahaifinmu da za ayi, da zarar an gama bikin za ta dawo." "Kai haba ai mun zama ɗaya, Ubangiji ya ba da zaman lafiya ya nuna mana naku, ni ma in sha Allahu zan leko." Shiru ta yi ta kasa cewa komai. Hira suke yi, amma sai duk ta takura ganin yadda Ahmad ke kashe ta idanu. Mama ce ta miƙe ta ba su guri, suka ci gaba da hira su uku. Nasreen ta miƙe,"Bari na rage kayan jkina yunwa na ke ji." "Ma za ƙanwata grabs something to eat." Tana miƙewa Ahmad ya bi Marwana da kallo. Ji ta yi kaman yana kallonta ta ɗaga idanunta. Da sauri ta sauke nata."Marwana ni ba za a gayyace ni ba?" Ya furta cikin sanyin murya yana shafa kansa. "Kai Yaya, in na gayyaci Nasreen ai dukanku nagayyata. Ba ka ji Mama ta ce za ta zo ba sai ku zo tare." "Na ƙi wayon nawa gayyatar na musamman na ke so." "To shikenan you are invited." "Good sis ki ba ni contact naki sai na kira ki, saboda ke zan zo ma bikin bana son Nasreen ta sani." Da sauri ta ɗago idanunta tana kallon sa jin abin da ya ce."Yes laifi ne ina zo gurin ki ba ta sani ba?" Ya ƙarashe maganar yana shafa suman kansa idanunsa a kanta. "A'a." Ta ce a hankali saboda wani irin kunyarsa da take ji. "To a bani numba." Babu musu ta karanta masa ya sanya a wayarsa."Thanks, bari na kira ki sai ki yi saving nawa ko." Ɗaga masa kanta ta yi daidai lokacin da kiran ya shigo. "Sai na zo bikin." Ya ce tare da miƙewa da sauri jin Nasreen za ta shigo falon. Kallo ta bishi da shi tana jin yadda gabata yake faɗi. "Sorry na barki ke kaɗai." Nasreen ta furta lokacin da ta shigo falon. Hira suka ci gaba da shi, daga nan ta kwashi kayanta suka tafi. A lokacin da suka isa gidan sai gabanta ya rinƙa faɗuwa, tuna ranar da ta shige shi da kuma dalilin shigar. Cikin sanyin jiki ta shiga cikin ɗakin da yake da mutane ana hayaniya. Sallama suka yi Marwana ta ja hannunta suka ƙarasa gurin Mommy. Duƙawa tayi cikin girmama ta ce,"Ina wuni Momi?" Fuskarta a sake ta amsa, sannan suka shiga cikin ɗakin Marwana. Sun jima a ɗakin suna duba ɗinkunan da ta yi musu. Cikin farinciki take duba kayan tana mata godiya. Nasreen kwanciya ta yi saboda ta gaji ga kuma kunyar Mommy da take ji. Ko da aka yi sallah a cikin ɗaki ta yi sannan ta kwanta ta ja wayarta tana ta chatting abin ta. Aka yi ishata yi sallah sannan ta kwanta. Marwana da ta zo bacci kasa bacci ta yi, da ta rufe idanunta sai fuskar Ahmad ke mata gizo. Numbarsa ta lalubo da ta yi saving da Ya Ahmad tana gani. Da sauri ta kalli wayar ganin kiransa na shigowa. Kasa ɗauka ta yi domin a tunaninta ko flashing ta yi masa, ba tare da ta sani ba, amma da ya gama kiran ta duba, sai ta ga don ra'ayin kansa ya kira ta. Kallon Nasreen ta yi, da take bacci saboda tsoron ko ba ta yi bacci ba, sai ta miƙe zuwa falo ta zauna. Ɗaukar wayar ta yi, tare da kangawa a kunninta ta yi sallama cikin sanyin murya. Daga can ɓangarensa ajiyar zuciya ya saki."Da fatan ban tashe ki daga bacci ba?" "A'a Nasreen ce ta yi bacci dai ƙila ka kira ne tana bacci." "Kiran na ki ne ba ita ba, saboda mun yi waya kafin ta yi bacci na tambaye ta ke ta ce kina ɗakin Mommy." "Ok, ina wuni?" Ta furta tana juyawa kan kujerar. "Kina lafiya ya hidimar biki?" "Alhamdulillah Yaya Ahmad." Shiru ya yi yana tunanin abin da zai ce mata."Kin ɗauke mini kanwa shi ya sa na kira ki don mu yi hira." Ya furta haka ba tare da shiri ba, domin ya rasa mai zai ce mata. "Kai Yaya kwana uku za ta yi fa?" "Haka ne don kene kawai. In na zo bikin me za ki bani?" "Duk abin da kake so Ya Ahmad ai ka wuce ƙarfin komai a gurina?" "Har da zuciyarki?" Ya yi mata tambayar da sai da ta zauna. Jin ta yi shiru sai ya sake ajiyar zuciya ya ce,"Marwana ina sonk za ki bani zuciyarki? Tun ranar da kika yi wa Nasreen kyautar lapton ki samu matsayi sosai a zuciyata, a lokacin ban yi wani tunani ba, saboda na san cewa babban goro sai magogin ƙarfe, amma ga shi yau Allah ya canza komai. Ina da dukiyar da zan iya aurenki, sannan ina yin digiri a online." Tsintar kanta ta yi da kashe wayar, domin ta kasa ba shi amsa. murmushi ta saki sai kuma ta rungume wayar tare da ba ta kiss."Ya Ahmad yana sona? Allah na gode maka ashe ni rabonsa ne shi yasa ka raba ni da Ya Ashaman?" Ta yi tambayar cikin farinciki tare da miƙewa ta shige daki. Kasa bacci ta yi, don haka ta hau online. Ahmad da yake kan online ɗin yanar dariyar abin da ta yi. Fatan shi ta Gandi yi maganar tun da ta kasa bashi amsa. Ganin ta hau ya yi mata magana. Sai ta ɗan saki suka ci gaba da hira ba tare da ta amsa mishi ba. Murna sosai yake yi, domin ganin yadda ta saki da shi suna hira ya san ta aminta da shi. In har ya same ta zai yi murna, saboda ya san ba shi da matsala tsakaninta da danginsa. Numbarta ya duba sannan ya tura mata da alert na kuɗi, musu yawa ta opay ɗinta."Ayi mini kitso da ƙunshi sai na zo biki." Cikin farikciki ta karanta tsakon tana murmushi. Da kyar ta samu bacci ya kwashe ta da tunanin sun yi aure. Washegari da safe da suka tashi bayan sun yi sallah da azkar. Da gari ya sha sai suka miƙe don su haɗa breakfast. Ita da Nasreen suka shiga kicin. Suna aikin Nasreen tana kallonta da kusan hankalinta yana kan wayarta. Da ta fara fere ɗankalin turawa sai ta saki ta duba wayarta."Wai hala kuɗi za a tura miki?" Ta yi mata tambayar tana kallonta. "A'a mai kika gani?" "Ban yadda ba saboda tun ɗazu kike ya kallon waya, ko kin fara soyayya ne?" "Wataƙila hakanne I'm in love with extraordinary guy." Ta furta tana murmushi. "Ai to, kuma sai ba za ki gaya mini ba?" "Akan me? Na ga lokacin da kika fara soyayya da Ingawa babu labari sai dai na gane, don haka yanzu sai ki gano da kanki." "Shikenan idan ta yi wari za mu ji, amma shi kuwa wane mai sa'an ne ya dace zuciyarki? Bayan kin rasa Ashman na ga mutane da dama suna ta kawo ƙoƙon bara, amma ba a basu dama ba?" "Saboda wannan daban yake a cikin maza, kuma na san na yi dace zai kula da ni." Baki ta kama cikin tsanannin mamaki."Yaushe kika haɗu da shi har kika yi masa wannan shedar?" "Ban sani ba daga ganin farko na sheda daban yake cikin maza." "Hmmmmh!" Kawai ta ce tana mamakinta a ranta ta yi mata farinciki duk da ta so ta haɗata da Ahmad, amma ganin ta samu wanda yake sanya farinciki sai ta daure abin ta ce,"Lallai kin zurma da yawa." "Sosai kuwa. Bari na je na tambayi abin da Mommy za ta yi break da shi." "To," Ta masa sannan ta fita daga kicin ɗin. Hankalinta ya ɗauki gurin suyan tana ta juyawa. Damir ne da kayan ɓacci ya sauko kasan yana hamma, saboda tunani bacci bai ishe shi juya ba. So yake yashi'a coffee na shi na ƙa'ida sannan ya ya yi exercise. Tura kicin ɗin ya yi yana faɗin."Marwana Please coffee ki haɗa...." Maganar ta katse masa, sakamakon ganin Nasreen a kicin ɗin tana suya. Sosai ya razana domin ya ɗauka fatalwarta ce da kuma gizon da take yi masa ne. Sai ya yi matsaya jingina da bango yana salati, ganin lamarin ya fara yin nisa, ganin yana ganin 'yar'uwarsa da siffarta. Nasreen tsoro ta ji, ta matsa da sauri tana kallonsa ganin yadda ya razana."Ina kwana Ya Damir?" Ta ce masa tare da kauda kanta. Watsa mata wani irin kallo ya yi, wanda ya sanya a karo na farko ta ji wani abu ya harba har cikin zuciyarta. Ba tare da ya amsa gaisuwar ba, ya fita daga kicin ɗin yana jin yadda zuciyarsa ke bugu bisa rashin ƙa'ida. Yana ƙoƙarin barin gurin Marwana da dawo. Ganinsa ya sanya ta ƙaraso sauri." Sorry coffee ko? Yanzu na tuna da shi na je tam..." Binsa da kallo ta yi, lokacin da ya fara tafiya ba tare da ta ƙarashe ba. Kicin ɗin ta shiga tana kallon Nasreen."Ya Damir ya shigo nan ne?" "A'a." Ta yi mata ƙaryar haka tana sai ta natsuwarta. Bin ta da kallon rashin yadda ta yi, sai ta haɗa masa coffee ta haye sama. Yana jin tana buga masa ƙofa da kiran sunansa, amma ya yi banza da ita cikin jin haushinta. A ransa ya gane so kawai take ta kashe shi da ransa game da Nasreen, domin da ta san halin da yake shiga inya ganta da ta tausaya masa. Bayan sun kammala breakfast, suka shirya 'yan matan suka je gyaran jiki sannan in suka dawo za a yi musu lalli. Nasreen da Marwana kamar su ne amaren domin sun yi kyau sosai. Da aka zo lallin Marwana ta kalli mai ƙunshin ta ce,"Please ki yi mini yafi na amaryar zan biya ki ko nawa ne, saboda habibina ya biya kuɗi sosai." Nasreen kama bakinta ta yi cikin tsantsar mamaki."Wai yaushe kika fara soyayar da har kika haukace haka?" Dariya ta yi ganin yadda suka yo kanta suna tsokanarta. "Ki dai zauna kina jin kunya bakya iya more soyaya. Ni wallahi ina educated ba zan zauna ina jin kunya ba." "Lallai Marwana kin fi ƙarfina." Ta ce tana mamakinta. A gurin lallin haka ta yi ta soyayya da ya kira, kuma ta hana su magana. Ganin ta ishe su Nasreen ta miƙe za ta karɓe wayar, ganin haka ta kashe tare da miƙa mata tana dariya."Saboda irin ku 'yan sa ido na canza password ɗin wayata, yadda kika ja mini aji kafin na san kina tare da Ingawa sai na rama." "Allah ya kaimu dole mu gansa in har ba auren sirri za ku yi ba." Ta ce tare da komawa ta zauna Sosai suka fito sun yi kyau kamar saman alale. Tun da ya fuskanci tana cikin gidan ya daina sakkowa in sun falo, saboda in ya ganta sai ya ji kamar zai haɗiyeta. Ya gane sonta yake yi, amma kuma ba shi da courage da zai iya tunkararta. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whats *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 32 Ranar ɗaurin auren sun sha kyau sosai. Bayan an ɗaura aure Ahmad ya gaya mata yana waje, domin shi ya kawo Mama, sannan ya wuce masallacin da za a ɗaura auren Marwana tasha kyau sosai kamar ka sace ta ka gudu. Ahmad ne ya kira ta, don haka ta gudu ba tare da Nasreen ta sani ba. Tarba ta musamman ta yi masa suka sha soyayyarsu. Duk hidima da ake yi tana can gurinsa suna shan soyayya. Sosai ta saki jiki ta da shi, domin zuciyarta ta gama aminta da shi. Tana zaune a gefensa, Nasreen da ta gama nemanta ta gaji ta kira wayarta. Kallon wayar suka yi tare da sakin murmushi."Ɗauka amma kar kice mata kina gurina, so na ke mi yi mata bazata." "Ok,"Ta ce masa idanunta na kansa. "Hello kina ina ana ta neman ki Ya Damir ya aiko ki je ki kai masa abinci da abokansa." "Ina can ina bawa fulawa ruwa." "Marwana wai yaushe kika zama haka ne?" Kallon Ahmad ta yi da yake ji kamar ya lashe ta."Tun ranar dana samu muradina" "To ya yi, in kin ga dama ki zo ki kai ma fusataccen ɗan'uwanki abinci." "Na ga kema yayanki ki ne don Allah ki..." "Ba ki da hankali wannan damisar ya'yan na ki sai ke, saboda na hango shi yana ta huci." Kashe wayar ta yi ta suna dariya. Miƙewa ta yi ganin shi ma ya miƙe."Ki je ki ba shi kulawa bari na je mu yi waya, sannan ki kula mini da kanki, bana son ki bari maza su yi miki magana." "Shikenan Ya Ahmad ba ka da matsala." Har ta juya za ta tafi ya kira sunanta.Waigowa ta yi ganin yadda yake kallonta da idanunsa da suke saukar mata da kasala. "Yaushe ne za a yi namu auren, ki zama 'yar Mama kuma Antyn Nasreen?" "Duk ranar da ka shirya, ina farin ciki na kasance cikin ahalinka." Ta ƙarashe maganar tare da rugawa da gudu. Dariya ya yi sannan ya tafi cikin tsanannin farinciki. Marwana abinci ta haɗa masa a kicin, sannan ta ɗauka ta nufi ɓangarensa. Yana zaune cikin abokansa suna ta hira. Yana kusa da Annur da ya ci wanka kamar za shi gasar kyau, saboda ya ga sahibarta, amma Damir ya hana shi sosai ya ɗauke fuska ya dake da suna hira. Da ya miƙe sai ya kamo shi ya zaunar da shi ya rantse babu inda za shi. Dariya sosai yake yi masa ganin kishinta. Wayarsa ya zaro ya fara chatting da ita. Damir kuwa tun da ciro wayar hankalinsa na kan wayar. Ji yake kamar zai kwace don ya san da ita yake chatting, musamman da yi kalli wayar sai ya yi murmushi. "Sannu Laila da majnun wato ke kina soyaya ki barmu da aiki?" "Kar ki ga laifina shi ɗin mai zafi ne." Tsaki ta yi ta fara tafiya tana faɗin,"Sai ki je ki bawa ƙawayenki abinci don na gaji." An shirya dinner, bayan an kai amarya su Marwana kowacce sai da ta kwashi mutane a cikin motarsu. Damir sam ba shi da ra'ayin zuwa, tun da ya ji Annur ya ce za shi, sai shi ma ya shirya. Kallon mamaki ya bi shi dashi lokacin da yake fesa turare. Gurin dinner ya cika maƙil, kowa sai murna yake yi. Duk inda Annur ya sanya kafa sai ya bi shi, duk ya hana shi sakewa. Annur da aka fara dinner ya so ya keɓe da Nasreen, amma sai Damir ya hana shi ko jirgawa suna tare. Dariya ya yi ya kalle shi,"In aka ɗaura aurenmu sai ka zo gidanmu, ka hana mu cin amarci, wannan masifa har ina ka ƙi aure ka kuma ce zaka hana ta." Tsaki ya yi, yana kallon wayarsa ba tare da ya ce masa komai. Tun da suka zo gurin yake kallonta kamar makahon da ya warke daga makanta. Nasreen ta yi kyau sosai sai ƙamshi take yi. Idanunsa na ƙasa da take ta hidimar ta ba tare data kula da shi ba. Sosai ta sake tana ta hidimar bikin. Da aka zo rawa zuciyarsa bugawa take kamar za ta fito, a tunaninsa ya ɗauka za ta yi rawa, Annur ya yi mata manni, amma karo na farko da ta fara burge shi duk rawar da suke yi, domin har Marwana ta taka, amma iya kallon su kawai take yi. Ko da Marwana ta ja hannunta don su shiga filin sai ta noƙe tana dariya, wannan abu da ta yi, ya sanya zuciyarsa nishaɗi har sai da ya murmusa, domin Annur bai samu damar yi mata manni ba. Bayan an gama dinner washegari aka yi kamu, sai a washegarin bikin Annur ya samu suka sha hira. Duk yadda ya hana shi keɓewa da ita, zuciyarsa tafarfarfasa take yi. Haka dai aka yi biki aka ka amarya gidansu. Duk da cewar tsoron fitowa yake yi da take gidan, amma da ya ji Marwana tana faɗin yau za ta tafi, sai ya ji hankalinsa ya tashi, ji ya yi tamkar ta zauna a cikin gidan. A kwanakin ya rasa gane kansa, domin shi kansa bai tabbatar da lamarin da yake ji a cikin zuciyarsa ba. Wannan zafin na ta da yake ji, ya rage sai yawan tunani ta, musamman kwalliyar dinner da ta yi ya kasa manta shigar. Sannan a duk lokacin daya tuna ta, amaimakon ya ji haushinta kamar yadda yake ji a da, sai ya ji zuciyarsa ta yi sanyi tare da sakin laulausar murmushi a fuskarsa. Damuwarsa ɗaya, da suka koma aiki sai ya kasa sukuni ya yi ta zarya a harabar gurin. Burinsa ko zai ga gilmawarta, amma haka zai gama kaiwa da komowa tsakanin sama da ƙasa ba tare da ya ganta ba. In kuma ya yi sa'ar ganinta da Ingawa da yake jin kamar ya sallama me shi. Washegari da safe, ya zo aiki tun daren jiya ya ƙasa gari ya waye, don babu bin da yake so sai ya ganta. Cikin sama ya ganta tsaye ita da Hajar da S. Bako suna tsaye a kusa da hanyar da zai shige ofis ɗinsa yana nuna musu aiki. Nasreen sam ba ta lura da shi ba, domin hankalinta yana gurin S. Baƙo tana sauraren bayanin da yake musu. Hajar da S.Baƙo kawai suka fahimci safa da marwar da yake yi, tamkar mi ɗawafi, domin ko da ya shiga ya ije jakarsa, sai ya tsinci kansa da kasa zama ya fito. So yake ya ganta musamman shigar da ta yi ya burge shi. Tana sanye cikin hijabi jalbab kalar maroon color, sosai ya karɓe ta. Ƙananan kaya ta sanya, don haka ta saka hijabin har ƙasa. "Wai ko oga Damir ya yarda wani abu ne na taya shi nema? Tun ɗazu yake sintiri ya wuce yafi sau biyar." Jin tamabayar da Hajar ta yi, tana kallon S. Bako sai ta ɗago ta kalle shi. Da sauri ta ɗauke kanta ta mayar gurin S. Bako xuciyarta ya buga da sauri. Yana sanye cikin suit kayan sun karɓe shi. Idanuwana sanye cikin gilashi da wayarsa riƙe a hannunsa. "Ya Damir ka yarda wani abu ne?" Hajar ta tambaye shi daidai lokacin da ya zo zai wuce su. Ɗago kansa ya yi, ya kalle ta sai kuma ya watsa wa Nasreen kallo, wacce gabakiɗaya hankalinsa ba shi a kansa."No." Kawai ya ce tare da sakin ajiyar zuciya ya shige ofis ɗinsa. Ganin kallon da ya watsa mata, sai suka kalle ta wacce ba ta san abin da yake faruwa ba. Murmushi suka saki sannan S. Baƙo ya cigaba da musu bayani. Damir zama ya yi cikin ofis ɗin, yana saukar da numfashi da sauri. Idanunsa sun canza sun yi ja. Shi kaɗai ya san yanayin da yake ji in ya ganta. Yana saukar da numfashi a hankali ya kwantar da kansa. Haka ya ci gabas ɗawainiya da sonta, amma tsabar girman kansa da izza ya kasa gane ya fahimci haka. Kullum sai da ya yi ta fama da damuwa, wanda har ta kai shi bp dinsa ya hau sosai. Tsakanin Marwana da Ahmad kuwa lamarin ya ci gaba, domin soyayyar su sai ci gaba take yi. Wani irin ƙauna suke yi wa junansu, amma ba tare da sun yarda kowa ya sani ba. Nasreen ce ta fara zargin Ahmad ganin yadda kodayaushe yana tare da wayarsa yana chatting, sannan ya yi ta murmushi. Ganin hakan hankalinta ya tashi sosai domin a xuciyarta akwai wacce take son ya aura, aurenta kawai shi ne za su saka mata abin da ta yi musu, don haka ta yanke shawarar za ta same shi ta sanar da shi, kamar yadda ta lura ita ma Mama tana son haɗa auren, amma kuma da ta tuna soyayyar da Marwana take yi, sai jikinta yayi sanyi sosai. Annur ya ci gaba da zuwa gurinta, tun tana ɓoyewa har Ingawa ya sani. Ganin hakan sai ha kalinsa ya tashi sosai. Sai ya fara mata ƙorafin tun da sun fahimci juna kawai a sanya rana. Ta gefen Annur kuwa yana ta nuna matakalar soyayyarshi, sannan yana ƙara sanya jinin Damir yana hawa, domin duk abin da ya faru tsakaninsu sai ya gaya masa, wanda yake tayar da hankalinsa matuƙar gaske. Ta bangaren Baba duk nacin Ahmad ya bar gidan, amma ina domin ta tamkar ya zama kurma haka ya koma, kuma ya rantse ko kashe shi zai yi ba zai saki Mama ba, duk da ba ta kula shi kwana kawai yake yi a ɗakinta, amma ita kanta ta rantse sai ya sake ta. Ahmad tun da ya dawo ko sisi bai taɓa haɗa su ba, saboda ya tsane shi sam babu tausayin ɗa da mahaifi a tsakaninsu. Nasreen ce kawai yake takurawa, ta yi masa hidima ita ma ba tare da Ahmad ya sani ba. Faruk sai da aka yi musu albashi, sannan ya sanya mai a mota, ya kuma wanke motar ya shirya zuwa gidansu Nasreen. A lokacin da ya isa kofar gidan, sai ya cika da mamaki ganin an gyara gidan. Tunanin da ya faɗo masa Baba ya ɗauko rigimar da aka sayar da gidan. Hankalinsa ya kwanta sosai, domin hakan zai ba shi damar mayar da ita cikin ruwan sanyi, domin yasan cewa yanzu tana nan cikin mugun halin da za ta gwammace zaman gidansa da zawarci. Yana tsaye a gurin, cikin tunanin yadda za a yi a kira masa ita, sai ya ga wani yaro ɗan maƙocinsu. "Yauwa kai zo nan."Ya ce tare da fara tafiya gurin yaron. "Nasreen za ka kira mini." Kallon sa yaron ya yi yana son gane ko baƙo ne.Yadda yake kallonsa cikin mamaki, sai ya ƙara tabbatar da abin da zuciyarsa ta gaya masa. "Nasreen sun tashi ai yanzu bata a gidan ita da mamansu." "Ya sayar da gidan." Ya ce a ransa yana ayyana rayuwar wahalar da suke ciki. "Don Allah za ka kaini gidan?" "Eh mu je, amma akwai nisa sosai." "Karka damu zan dawo da kai." Yaron cikin murna, ya shige gaban motar Faruk yana ta zare idanu. Sun yi nisa sosai, yaron ya nuna masa unguwar masu kuɗi ya ce,"Nan za ka shiga a nan unguwarsu take." Da sauri ya zaro ido tare da rage gudun motar."Nasreen fa na ke gaya maka yar gidan Bukar ƙanwar Ahmad!" Ya ce masa yana kallonsa cikin mamaki gain inda ya kaisu. "Eh ba wacce ƴaƴanta ya ɓata ba kuma tana da yara biyu?" "Ita wata yar fara-far siririya." "Na santa nan ne unguwarsu." Tsoro ya bayyana a fuskarsa, da sauri ya kalle sa ya ce,"Ta yi aure ne?" "A'a mu je ai mun kusa zuwa gidansu." Yaron ya faɗa cikin ƙosawar tambayar da yake masa. Ganin haka sai ya yi shiru, ya ƙara gudun motar zuciyarsa na bugawa da sauri tunani sosai yake zuwan masa. Take ya fara tunanin ko su Marwana sun dawo rayuwarta ne? Wannan tambaya da zuciyarsa ta yi masa sai, da ya ji kamar sama za ta faɗo kansa, domin ko alokacin da yake Faruk ɗinsa da yana masifar shakkarta, ballanatana yanzu da duniya ta yi masa atishawar tsaki. Bai gama shiga cikin mamaki ba, sai da suka kai kofar gidan. Yaron ya dakatar da shi tare da nuna masa get ɗin gidan, yana jira ya ba shi tukuci. Wani irin tashin hankali ya ziyarce sa. Lokaci guda kansa ya fara juyawa tamkar ana murza sitiyarin mota. Da sauri ya kalle shi cikin tsanannin mamaki."Nan ne gidan?" Ya yi masa tambayar cikin rashin hayyaci. Cikin fariciki yaron ya washe baki, ya fara magana ba tare da ya lura da halin da ya shiga ba."Eh nan ne sabon gidan da Yay..." Kafin ya gama maganar, sai ya ji ana ƙoƙarin buɗe get gidan. Da sauri Faruk ya ƙuraawa get ɗin gidan ido yana kallo. Burinsa Nasreen ta fito don ya tabbata da maganar yaron, amma sai ya ga Baba ya buɗe get ɗin gidan ya fito, da sabuwar rediyo da yana saurara. Ya yi ƙiba ya canza hatta shigar shi ta canza. Matsawa ya yi, cikin tsananin razana yana zare ido. Tsoro firgici da tashi hankali suka ziyarce shi. Baba da yake cikin fariciki har da yar waƙarsa yana tafiya. Ba tare da ya lura da Faruk yake cikin tsanannin tashin hankali ba. Yaron da ya ga Faruk ya shiga cikin ruɗani sai ya kalle shi ya ce."Ga Baban Nasreen nan ma ya fito." Da sauri Baba ya kalle shi, tare da zabura cikin tsananin mamaki. Shi ma zaburar ya yi, yana jin lamarin kamar a mafarki. Goge idanunsa Baba ya yi, tare da aro rigar rashin mutunci ya sanya. Lokaci guda fuskarsa ta canza ya ci magani. Faruk ganin yadda ya yi, sai tsoro ya kama shi jikin shi ya kama rawa. Kallon Baba ya yi, da ya ɗora hannunsa a kirji yana dariyar muguntar ganin yadda ya koma. "Wayyo Duniya mai kirari da yawa; in ji kwaɗo ya ce wai juyi-juyi da ya ji shi a cikin ruwan zafi. Duniya rawar 'yan mata, mai karambani a gaba sai ta watso shi baya; Duniya mai halin ɗan mangwaro, sai an sakankance ana tsotsar ta sai ta sulluɓe ta gudu." Baba ya ƙarashe karin maganar cikin muryar waƙa yana wata irin shegiyar dariyar da ko kyau ba ta yi masa ba. Kallon Faruk ya yi, da ya zare ido yana kallo da kamar zai yi hauka. Tamke fuska ya yi yana ƙarasowa gurinsa. "Kai tijararre uban mai ya kawo ka gidan nan?" Ya yi masa tambayar yana zagaye shi yana kallonsa kamar ranar ya taɓa ganin. Farouk da yake cikin tsananin tashin hankali. Zare idanunsa ya yi ya kasa magana sai kallonsa yake. "Dangin ƙaruna magana na ke yi." Ya daka masa tsawa yana faɗin haka. Jikinsa na rawa ya kalle shi ya buɗe baki zai yi magana, sai ya kasa yana raba idanunsa. "Tambayarka nake yi uban mai ya kawo ka gidan nan?" "Eh... am na zo ganin yarana ne." Ya furta cikin rawar murya, yana mamakin yadda aka yi suka canza gida. "Au dama akwai yaranka a gidan nan? Har kana da bakin da zaka iya furta yaranka? Yaran da ka wulaƙanta su da mahaifiyarsu, sai yanxu da duniya ta yi maka tutsin mage sai ka lallaɓo ka kwaso ƙafafunka kamar na biri ka zo?" Kasa magana ya yi, yana ta masa tijara, amma ya kasa cewa komai. Tunanin yadda aka yi rayuwarsu ta canza yake yi. Ganin zai tara masa mutane, saboda magana yake yi da karfi ya sanya shi sausauta murya ya ce,"Bab..." "Kul Karka sake ka kira ni da ubanka uban Nasreen dai." Ya daka matsa tsawa yana faɗin haka. Kasa magana ya yi, yana shafa kansa cikin tashin hankali, daidai lokacin da Ahmad ya fito zai shiga cikin mota zai fita. Maigadi ya wangame get yana jiran ya fito. Faruk jin an buɗe get ɗin gidan, da sauri ya kalli cikin gidan burinsa kawai ya ga Nasreen. Ahmad fasa shiga cikin mota ya yi jin muryar Baba. Fitowa ya yi daga gidan, yana son ganin wanda yake tsaye a kofar gidan. Cikin tsananin mamaki Faruk ya kalle shi ya ce,"Ahmad!" Ahmad kallon sa ya yi, shi ma cikin tsananin mamakin ganinsa, sai kuma ya ci magani yana watsa masa mugun kallo. Kallon juna suka ƙara yi, kowa zuciyarsa da abin da yake tsaƙawa. Mamaki sosai Faruk yake yi, ganin yadda Ahmad ya canza ya dawo dan gayu jikinsa ya yi kyau ga hutu ga ƙiba da ya yi. "Yauwa Ahmadu ɗan albarka, zo ka ga wannan ɗan iskan mijin Nasreen ada ya zo wai ganin yayansa." Ahmad cikin taƙun kasaita ya ƙaraso. Jikin Baba har rawa yake yi lokacin da yake tahowa inda suke. Fuskarsa tsoronsa bayyane yana yi kamar zai ɗuka masa. "Wane yara kake da shi a gidan nan?" Ahmad ya yi masa tambayar yana kallon sama da da kasa yana mamakin yadda ya rame. Daurewa ya yi ya cire tsoro da firgicin da yake ciki, don kar Ahmad ya gane ya ce,"Please kar mu yi kamar bamu san juna ba, Raihann da Musaddik na zo ganinsu yarana da muka haifa da matata Nas...." "Kul! Ka tofar da miyau bakinka, domin Nasreen ta wuce matsayin da zaka kira ta da matarka, da ma cewa ka yi ada zan iya saurarenka." "Eh amma ina da..." WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Wh *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 33 "Kul! Ka tofar da miyau bakinka, domin Nasreen ta wuce matsayin da zaka kira ta da matarka, da ma cewa ka yi ada zan iya saurarenka." "Eh amma ina da yara da ita ko, kuma ka san ina da haƙkina na matsayin uba? To su na zo gani a fito mini da su." Ya ƙarashe maganar, yana ɗan daga murya ganin kallon ƙaskancin da yake musu. Ahmad kallon sa ya yi, duk da rayuwa ta canza masa, amma girman kansa da isa yana nan."Ba ka da yara a gidan nan, saboda wulaƙanta mahaifiyarsu da su da ka yi. Ba za ka gansu ba don baka cancanci zama ubansu ba." "Wallahi karya kake yi, don in dai ni na yi silar zuwansu duniya, sai na gansu in ina buƙatarsu dole hukuma ta ƙwatar mini su." "To shikenan na ga uban da zai karɓar maka su, mara mutunci tijararre kawai, saboda baka da kunya har ka iya takowa ka ce ka zo ganin yaranka?" Baba ya furta cikin tsawa yana zare masa ido. Ahmad taku ya yi zuwa gabansa ya zare masa ido."A yanzu kasan ni ba sa'an yin ka bane Faruk.Idan a da ka yi mini abin da ka ga dama, yanzu kuwa zan rama, saboda daga kallona ka san Ubangiji ya yi mini arzikin da kake mini gorin shi. Ina da kuɗi in har ka ce zaka yi mini wulaƙanci, wallahi sai na sanya a ɗaure ka har igiya ta yi rara, ko da ace zan rasa abin da na mallaka ne." Jikin Faruk ya yi sanyi tsananin tashin hankali ya kama shi. Ganin yadda suke masa musamman Baba. Kasa magana ya yi sai kawai ya fara tafiya ya shiga cikin motarsa. Da ka tsaya, ka ga yadda zan wulaƙanta ka mara mutunci kawai, kana tunanin kai kaɗai Allah ya ke so." Ahmad sai da ya ga bar kofar gidan, sannan ya kalli Baba da yake ta kumfar baki ya ja ƙaramin tsuka ya shige motarsa. Faruk sai da ya bar kofar gidan sannan ya tsaya jiran yaron da ya rako shi. Kiransa ya yi sannan ciro naira ɗari ya ba shi."Mu je na mayar da kai." Ya furta cikin tashin hankali yana tuna Ahmad yadda ya koma. Sai da yaron ya shigo sun fara tafiya ya kalle shi ya ce,"Ka san wa ya siya musu gidan nan?" "Ahmad ne da ya dawo ance yana da rijiyar haƙo zinare, to sai dai kawai ya ibo ya siyar." Tsaki ya ja jin abin da ya ce."Ina Nasreen ƙanwarsa?" "Anty Nasreen ai tun kafin ya dawo ta samu aiki. Ance kamar ƙawarta na makarantarsu ta samar mata aikin, kampanin yayanta. Ba ka ga yadda ta yi kyau ba, domin tun kafin yayanta ya dawo ta canza." Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi. Shi da yar tunanin zai zo ya gansu a cikin wulaƙantacciyar rayuwa, amma sai ya kurɓi ruwan mamaki. Hankalinsa ya tashi ya rasa wane tunani zai yi. Wani irin ƙaunarta da sonta ya ƙara bijiro masa tun kafin ta ganta. Yaransa da ya wulaƙanta su yake son gani. "Fita ba hanyar ku zan yi ba." Ya furta wa yaron cikin ɓacin rai saboda labarin da ya gaya masa. Yaron ya fice tare da rugawa da gudu ba tare da ya fahimci halin da yake ciki ba. A maimakon ya koma gida, sai ya wuce binciken inda Nasreen take aiki, saboda a ransa ya ji ba zai iya haƙura da ita ba, ya san tana da haƙuri za ta kula shi ko don su Raihann, musamman da in ya yi mata barazana da kwace su. Bayan ya gama binciken, ransa ya ɓaci da ya ji a campanin su Damir take aiki. Wani irin ɓacin rai ya kama shi. Take kishi ya rufe masa idanu har ba ya iya ganin abin da ke gabansa. Daga gurin binciken kasa koma gida ya yi gida. Kampanin ya je ya samu wani guri ya laɓe don ya ganta. Ya daɗe a gurin yana jiran su tashi. Da lokacin tashi ya yi. Duk motar da ta wuce sai ya kalle ta. A lokacin da ta fito da motar. Har ta fara tafiya sai ta tuna ta yi mantuwa. Da sauri ta yi parking ta fito daga cikin motar. Tafiya take cikin yauƙi, tana karkaɗa makullin mota har ta shige ciki. Farouk da ya yi toxali da ita ji ya yi kamar zai yi hauka. Da fari sam bai gane ta ba, domin gani ya yi kama ita kamar ba ita ba. Mace ya gani mai jiki kalar wacce yake so. Abaya data sanya ya ƙara rikitar da shi. Ga takalminta da jakarta ma kyau. Tamkar balarabiya haka ya gata koma, bambancin su kawai ita ba ta da haske sosai. Ji ya yi ƙasa ba zata iya ɗaukarsa ba, har sai da ya jingina yana jin wani irin tashin hankali mara muslatuwa. Ya goge idanunsa ya fi sau nawa don ya tabbatar da ita ce. Yana gurin cikin tsanannin tashin hankali, har ta dawo ta shiga cikin motarta. Ji ya yi kamar ya bita, domin har ya fara taku sai kuma ya ja ya tsaya. "Nasreen ce haka?" Ya yi ma kansa tamabayar yana mamakin abin da ya canza ta. "Ko dai supplements da nayi ta kawo mata don ta sha, ta ƙi sha ne yanzu ya sha ta yi kyau don ta burge Damir ya so ta?" Ya yi wa kansa tambayar cikin rashin hayyaci. Idanunsa suka rufe saboda tsananin kishinta. Ji ya yi kamar ya buɗe idanunsa ya ga bashi a cikin duniyar. Da ƙyar ya samu ya shiga cikin motar ya bar gurin. A ranar sai dai bacci ɓarawo ya ɗauke shi domin kasa bacci ya yi. Daya rufe idanunsa, ita yake hangowa cikin shiga ta alfarma. A ransa ya gama yanke shawarar ba zai taba yarda Damir ya aureta ba matuƙar yana raye. Ya sanya wa kanshi zai je ya fafata don ya dawo da matarsa. Sai ya yi na'am da hakan musamman da zuciyarsa take karfafa mishi, dole ta dawo in ya yi mata barazana da raba ta da su Raihan. Sosai yake son ganinsu ya ga yadda suka koma. Washegari da safe, da ya tashi gidan abokinsa ya wuce ya nemi ya ba shi aron kuɗi. Babu musu ya ba shi sannan ya wuce kasuwa. Kaya sosai ya siyawa kansa da turare na fara zuwa biko, saboda yadda ya ga Nasreen ta koma dole yana buƙatar ya yi updating kansa. Da ya dawo daga siyayyar, ya zauna yana dubawa sai abin ya ba shi mamaki, cewar yau shi ne yake siyayyan kayan don ya burge Nasreen. Ya tuna da yadda take son ya yi kwalliya ya zauna a gida. Wasu hawayen nadama duk gangaro masa da ya yi wautan sakinta, ina ma ace ba sakinta yayi ba, kawai ya tura ta gidansu. Tashi ya yi ya shigar da kayan, sannan ya zauna ya shiga kogin tunanin, yadda zai fara shawo kanta. Nasreen ta dawo aiki yana bakin get tana yin hon. Maigadi ya taso ya buɗe mata shiga da motar bayan ta gushe shi. Data fito daga motar ta yi sallama cikin falon. Raihann da Musaddik suka rugo suna mata oyoyo. Mama da Ahmad suna zaune, tun da yazo suke mamakin zuwansa da abin da ya ce. "Babu haddar yamma na ganku a gida?" "Umma, malamin haddar babansa ya rasu shi ne ba a yi ba." Raihann ta ce tare da karɓar jakarta. "Allah Sarki! Ubangiji ya jikansa." Tare suka haɗa bakin gurin amsawa da Amin. Sai da ta zauna ta natsu, har ta ci abinci mama ta kalle ta. "Kin san yau Faruk ya zo gidan na..." Da sauri ta miƙe jin sunan wanda aka kira."Ya zo yin me?" Ta zare idanu tana kallonsa. "Ya zo ganin yayansa." "Gaskiya Faruk ba shi da kunya." Ta ce sai hawaye ya zubo mata, take gani tsoron karya raba ta da yaran. Hannunta Ahmad ya kama ya zaunar ganin yadda ta razana. "Ni kaina abin ya bani mamaki, sai bayan ya tafi na sanya ayi mini bincike, ashe matar da ya aura ta gudu bayan ta fasa mishi kai ta kwashe dukiyarsa." Zaro idanunta ta yi, cikin tsananin mamaki da firgici. "Ikon Allah Rashida ta yi masa haka?" Ta yi tambayar cikin mamaki tana tuna irin zama da suke yi. "Farouk ya ga bala'i, ance har da kuɗin wani da ya tura masa zai shi masa gida, hauka tuburan ya yi fa, har sai da aka kai shi gidan mahaukata, da ya dawo mai kuɗin ya kulle shi." "Sakayyar Ubangiji ne ai ya zalinci Nasreen sosai, musamman dukan da ya yi mata ranar da zai saketa, kamar ya kuma ɓarawo." Mama ta ce tana kallonsu. "Aikuwa Allah ya sakamata tun kafin aje ko ina."Ahmad yace yana duba wayarsa. Ita dai shiru ta yi, tana jinjina lamarin sai ta kalle su ta nisa ta ce,"Ina ga zan canza wa su Raihann makaranta kar yaje ya ɗauke su don ya ƙuntata mini, saboda ba zan iya barin masa yarana ba." "Babu abin da zai yi musu, ki kwantar da hankalinki ina tare da ke." Miƙewa ta yi jikinta babu ƙwari ta shige cikin ɗakinta. Bayan ta yi wanka, tana zaune tana tuna rayuwar da suka yi a baya. Hawaye ya wanke mata fuska tuna wulaƙancin da ya yi mata. Hawayen ta share, sannan ta kwanta tana juya wayarta cikin damuwa. Zuwan Faruk ya ɓata mood ɗin ta, ko aikin da ta kwaso don ta yi kasawa ta yi. Washegari da yamma, Faruk ya ɗauki wanka sosai ya ƙure a daka, saboda ya san ba zai ji daɗi ba in yaje gidansu don haka ya bita gurin aiki. A lokacin da ya iso basu tashi aiki ba, har ya faka motarsa zai kira, sai wata zuciya ta ba shi shawarar ya sanya a kira ta don Damir ya gan shi. Maigadi ya tura kiranta. Tana cikin ofis hankalinta na kan aikin da take sauri ta gama kafin a tashi, maigadin ya tura kofa ya shigo. "Barka da hutawa Hajiya." Ya ce mata lokacin da ya yi sallama ya shigo. "Yauwa barka Baba." Ta amsa tana kallon sa. "Kina da baƙo a waje yace nayi kiran ki." "Ni?" Ta dago tana kallonsa tare da yi masa tambayar hakan. "Eh yana waje don a waje ya faka motarsa." Mamaki sosai ya kamata, a ranta tana tunanin waye, domin ba ta yi da wani zai zo ba. Har ta buɗe baki za ta ce masa ba ta nan, amma sai ta miƙe ta kashe laptop ɗin. "Ok Baba muje." Ta ce mishi tana tunanin baƙon ko kaɗan ba ta yi tunanin Faruk bane. Tana wannan tunanin ta sauko ƙasa. A lokcin Damir yana tsaye a windo yana kallon waje. So yake ya tafi gida, amma yana son ganinta kafin ya tafi. Ganin ta a ƙasa da sauri ya kwashi tarkacensa zuwa ƙasa. Cikin mamaki Nasreen ta tsaya tana kallon Faruk da ya juya baya. Mamaki sosai ta yi, sai kuma ta fara juyawa zata koma ganin bai ganta ba. Faruk da yaji taku, ya juyo gabansa na faɗuwa yana addu'ar Allah ya sanya ita ce. Wani irin razana ya yi, ganinta domin a ranar bai ganta da kyau ba, ganin yadda ta canza ya wuce tunaninsa. Idanu suka haɗa yayin da yake kallonta cikin shaukin so, ita kuma tana yi masa na tsana. Sosai ta ji tsanarsa a cikin zuciyarta har ba ta son ganinsa. Ranta ya ɓaci take fuskarta ta canza. Fara tafiya ta yi, ganin haka ya biyota yana kiran sunanta, amma ba ta kula shi ba, wanda ganin hakan ya ja mayafinta, karab sai a idanun Damir da aka buɗe masa get zai fita. Jiri ne ya ibe shi har sai da ya jingina da motar. Sau daya ya taɓa ganinsa, amma kuma kammanninsa sun zauna masa a idanunsa, saboda baya manta ranar da ta zama baƙar ranar da ya rasa Batula, amma ya zo ya yi masa rashin mutunci. Wani irin tashin hankali ya kama shi, sai ya yi luuu zai faɗi. Muhsin da ya ƙaraso don su tafi tare ya ga halin da yake ciki. "Subuhanallahi! Yaya take easy." Ya ce masa, tare da kama shi yana kallon inda yake kallo, dai dai lokacin da Nasreen ta watsa wa Faruk mari mai zafin gaske! "Ƙarka sake kiran sunana har ka yi tunanin riƙe mayafina, saboda ba ni da alaƙa da kai." Ta furta cikin zafi tana kallon sa, sai kuma ta fara tafiya. Cikin tsananin mamaki ya dage ƙuncinsa yana kallonta, sai kuma ya shanye mamakinsa, ganin za ta koma ciki ya ce,"Please Nasreen ki tsaya ki saurare ni wallah..." "Na gaya maka karka ƙara kiran sunana, saboda bani da alaƙa da kai, in har ka kuma ka ƙara gigin haka ko ka biyo ni gurin aiki, wallahi sai na gurza maka rashin mutuncin da ba ka taɓa tunani ba, domin na tsane ka nayi dana sanin ranar dana fara haɗuwa da kai. Ko mai sunanka bana fatan na sake ganinka." "Ina da alaƙa dake karki manta ina da yara dake." "Yaran da ka wulaƙanta sai yanzu ka san da su? Wallahi ka fita cikin rayuwata domin bana ƙaunar ganinka." Tana gama faɗin haka ta wuce ciki tana huci. Damir da Muhsin suka raka ta da idanu, wacce ba ta kula da suna gurin ba. Tana shiga cikin ofishin ta zauna tana huci tare da mamakin yadda akayi yasan gurin har ya biyo ta. Ranta ya ƙara ɓaci sosai tana ƙara jin tsanarshi. Frij ta buɗe ta ɗauki ruwa ta sha, sannan ta ji ta fara dawowa daidai. Farouk ya daɗe a gurin, cikin yanayi na nadama yana kallon inda ta bi. Hankalinsa ya tashe yayin da madarar sonta da ƙaunarta ya kara shigarsa. Shi da yake son mace kalar madara kuma ya kasance komai ya ji. Yau ga Nasreen ta dawo irin matar da yake so, amma kuma ba ta a hannunsa. Ji ya yi ko mai zai faru ba zai bar ma wani ita ba. Da ƙyar ya ja jiki, ya shiga motarsa cikin tsananin tashin hankali hawaye yana bin fuskarsa. Damir rasa tunaninsa ya yi, gabakiɗaya ji ya yi kamar zai yi hauka. Mota Muhsin ya buɗe masa ya shiga."Please ka ja motar mu bar gurin nan." Ya furta yana furzar da numfashi mai huci. Waiwawoya ya yi, ya kalle shi ganin yadda ya rikice. Muhsin tuni ya gama fahimtar son da yake yi wa Nasreen, amma ya kasa fahimtar hakan, ko kuma ya gane girman kansa da izza bazu bar shi ya furta ba. A cikin wannan halin suka isa gida. Da ƙyar ya samu ya fito daga cikin motar. Kai tsaye falo ya shiga sannan ya haye sama. Da sauri Momi ta miƙe tana kallon Muhsin da ya shigo. "Lafiya?" Ta ce masa cikin damuwa. Ya kasa bata amsa sai ya bi shi ganin yadda yake tafiyar kamar zai faɗi. Da suka shiga cikin ɗakin ya taimaka masa ya kwanta. "Please kunna mini A.C da fanka." Ya haɗa maganar da ƙyar yana jin kamar numfashinsa zai ɗauke. Babu musu ya kunna masa, sannan ya dawo kusa da shi ya ce,"Ya Damir y...." "Please Muhsin go." Ya daka masa tsaya yana faɗin haka. Da sauri ya fice cikin tausayawa ɗan'uwansa. Yana fita hawayen da suke ƙoƙarin zubo masa suka zubo."Yaushe na kamu da sonta, haka har na ke jin zan yi hauka ganin tsohon mijinta?" Ya yi wa kansa tambayar cikin damuwa. "Dole na bar ƙasar nan ba zan zauna ba, domin matuƙar ina ganinta da shi xuciyata za ta iya bugawa. Ba zan iya jure ganin ta da wasu ba ballanatana tsohon mijinta da na son za ta iya haƙuri ta koma duk da abin da ya faru." Ya ƙarashe maganar tare da ɗaukar wayarsa ya nemi flight, domin ya gama yanke shawarar haka shi ne kawai mafita. A falo da Muhsin ya sauko, gabakiɗaya suka yi kansa suna tambayarsa."Mai ya faru da shi?" "Tsohon mijin Nasreen ya gani ya zo gurinta." Cikin mamaki Marwana ta zare idanunta ta ce,"Kana nufin faruk?" "Eh shi shi." "Lallai Faruk ba shi da kunya, duk abin daya yi har yana da idanun da zai kalle ta?" "Namiji ne ai musamman da yana taƙama da yana da yara a gurinta, wataƙila ya gane kuskuren shi ya dawo gareta." "Haba Mommy, a tunanina Faruk ko mai zai fuskanta ba zai iya nuna mata fuskarsa ba. Mutumin nan azzalumi ne." "To shine don ya gansu da ya rikice haka? Ya san yana sonta yake tayin hauka. Sai ya zauna in hakan da yake yi zai sanya ta fahimci yana sonta Allah ya bashi sa'a." Mommy ta ce cikin takaici. "Ya yi ta sanya wa kishinta yana cutuwa, haka sai wani ya aure ta." Marwana tace cikin takaici. Momi saboda jin haushinsa miƙewa ta yi ta wuce cikin ɗakinta.Marwana jikinta na rawa ta ɗauki wayarta. Numbarta ta kira wacce ringing biyu ta ɗaga."Da gaske Faruk ya zo gurinki?" Mamaki sosai ya kamata na jin tambayar da ta yi mata."Ya akai kika sani?" "Ya Damir ya shigo a birkice shi ne ya Muhsin ya ce Faruk ne ya zo gurinki." Ƙara shiga cikin mamaki ta yi."Wallahi ban gan su ba, amma ya zo Marwana ko kunya bai ji ba. Ai dama da kika gaya yazo gidanku na gaya miki zai dawo. Nasreen cutar da ya yi mini dole Allah ya hukunta shi, abin da za ki yi kawai ki yi aure." "Ni ma shawarar dana yanke kenan, saboda naji tsoron da ya bini gurin aiki, har marin shi na yi amma wallahi bai ɗauki mataki ba." "Lallai duniya ta yi masa kamun kazar kuku. Gara da kika wanka masa mari. Don ya gane Nasreen ɗin yanzu ta bambanta da wacce ya sani." "Ki bari kawai yau ya ɓata mini rai." Maganar suka ɗan yi sannan suka kashe wayar. Aje wayarta ta yi, tana mamakin yadda a ka yi ya gani da kuma rikicewar da ya yi. "Wai hakan sona yake yi.?" Ta yi wa kanta tambayar cikin shakku, sai kuma ta ce,"Kai da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa.." Farouk ya haukace, idanunsa sun rufe burinsa kawai ya samu hanyar da zai dawo da Nasreen. Cikin dare gaza bacci take yi, domin da ya rufe idanunsa ita yake hangowa. Gabakiɗaya ya susuce ganin yadda ta koma. Hango Nasreen ta dawo gidan a matsayin matarsa kawai yake yi. Damir ba tare da sanin kowa ya yi burking viser. Yana ta shiryen-shiryen tafiya, domin yana ganin hakan shi ne mafitar da zai kawo sauƙi a rayuwarsa. Ranar sati, Nasreen tana zaune ta ji sallamar mace a kofar falon su. Cikin mamaki ta tashi ta buɗe kofar."Fadila? Dama kina duniyar?" Fadila ita ma tsayawa ta yi da tsohon cikinta, tana kallonta cikin mamaki."Nasreen kece kika dawo haka?" Harararta ta yi tana faɗin,"Ko da yake bai kamata na yi miki magana ba, haba Fadila tun da kika auri soja kika manta ni." "Wallahi ba haka bane kina raina, kawai rashin mutuncin da Faruk ya yi mini ya sanya na yi nesa dake, kuma kin san matan sojoji kullum cikin yawo muke." "Duk wannan ba hujja bace na kare kanki. Tun lokacin da kika karɓi tranfer kika daina kirana ko a waya." "Mu bar wannan tashin-tashin yanzu nadawo gareki. Waje Baban Sayyid ya fita, shi ne na dawo gida zan yi masters Mamana take gaya mini ai kun rabu da Faruk." "Wallahi kuwa ke dai bayan ba ki na shiga jarrabawa." Kwashe duk abin da ya faru ta yi ta gaya mata. "Kai Faruk dan iskan duniya ne, mugu shi ne yanzu har yana da idanun da zai ƙara kallonki." "Hmmmmh! Ni ma na yi mamaki sosai ba ki ga yadda ya dawo ba." "Aini wallahi matarsa ta yi mini da zan gaya sai nayi mata kyauta, saboda abin da ya yi ya cancanci fiye da haka. Kiriƙiri ya raba tsakaninmu bayan ni ya sanya na yi masa hanya, wallahi in na tuna hakan da halin da kike ciki sai kaji kamar zan haɗiye kaina na mutu, saboda har da hakan ya sanya na fita daga rayuwarki." "Allah ya kawo mini ƙarshe ai na huta da azabarsa." "Amma ya kamata ki auri Damir ɗin nan, saboda yana sonki kuma ki sakawa Marwana." "Ina mamakin yadda ake cewa yana sona. Ya Damir ya tsane ni sosai in ya gani kinga yadda yake mazurai yana bata fuska?" "Zafin kishi ne da kuma irin tasa kalar soyayyar kenan." Shiru kawai ta yi ba ta ce komai ba. Hira sosai suka yi suna tuna rayuwar baya da irin wahalar da suka sha. Sun jima suna hira, sannan ta yi mata sallama ta tafi bayan ta yi mata alkawarin zuwa gidansu. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 34 Shiru kawai ta yi ba ta ce komai ba. Hira sosai suka yi suna tuna rayuwar baya da irin wahalar da suka sha. Sun jima suna hira, sannan ta yi mata sallama ta tafi, bayan ta yi mata alƙawarin zuwa gidansu. Washegarin ranar Monday Damir yana zaune a falo Muhsin ya shigo. Turus ya yi ganinsa yana kallon news ba tare da ya shirya zuwa gurin aiki ba. "Ya Damir ba za ka je aiki bane?" Ɗaga masa kansa ya yi hankalinsa naka tibin."Maganar kayan nan fa za ka sanya hannu..." "Please ka kula da komai daga yau, saboda ina son zan yi tafiya zuwa Dubai." Mamakin abin daya faɗa ya kama shi."Amma kuma baka gaya mini ba? Kuma na ga tafiyar ni zan yisai kuma nan da wata biyu." "Ba wancan tafiyar bane, ina son na yi nesa da gida ina buƙatar na saita kaina. Zan je in sha Allahu da daddare jirgin mu zai tashi, kuma ban san lokacin da zan dawo ba, domin zan iya wata goma shekara ko fiye..." "Haba Yaya saboda me za ka je waje ka yi wannan daɗewar, wa zai kula da campanin?" Ya masa tambayar yana zare ido cikin mamaki. "Kai za ka kula da kampanin, ya kamata ka saba da kulawa da shi kai kaɗan, saboda watarana zai iya kasancewa babu ni, kasancewar ba a san gawar fari ba." "God forbid Ya Damir in sha Allah ni zan riga ka mutuwa." Murmushi ya yi, tare da dafa shi yana jin tafiyar ita ce mafita, saboda in har zai zauna watarana sai dai su ga ya yi bunga. "Ka daure ka kula Marwana ma za ta iya tayaka kulawar. Ta girma yanzu tun da har tana ba da zaɓin waɗanda za a ɗauka." "Waye zai yi tafiya kuma saboda me?" Hajiya da ta shigo, tana sauraren abin da suke cewa ta yi musu wanan tambayar. "Ya Damir ne kuma wai bai san lokacin dawowarsa ba, domin ya ce he might stay long." "Saboda me zai tafi wata ƙasa ya bar campany?" "I don't know Mommy you can ask him." Ya ce yana watsa hanunnsa cikin damuwa. "Ina son na je na huta ne, sam bana jin daɗin Najeriya kuma na riga na gama komai yau in sha Allahu zan tafi." Ya ce bata amsa ba tare da ya ji mai da za ce ba ya haye sama. Kallon juna suka yi Muhsin ya bi shi sama. Tura ƙofar ya yi tare da shiga ya hange sa a gurin kayansa, ya haɗa kai da wadrop ɗinsa hawaye yana bin fuskarsa. "Saboda Nasreen za ka bar ƙasar?" Da sauri ya ɗago, cikin razana yana ƙoƙarin goge hawayen da ke fuskarsa ba ya son ya gani. "Saboda me zan bar ƙasata, kan wata mace wacce ta ruguza farincikina?" Ba tare da ya amsa mishi ba, ya ƙaraso kusa da shi, sannan ya kai hannu ya dafa kafaɗunsa."You love the girl. Da gaske kana mata mahaukacin so, ba ka sani ba ya kamata ka sani. Ya Damir kana sonta sosai and you have to go to her. Swallow you pride and seek love. Na gane kana sonta sosai, kuma kishi ya sa za ka gudu ka bar ƙasar ka. A maimakon ka tsaya, ka shiga cikin manema a fafata da kai har ka yi nasara." "I didn't tell you that I love her k...." Stop pretending Ya Damir! Wallahi babu kaffara sonta yake ɗawainiya da kai da kuma kishin ta. Tun ranar da ta fara aiki a campaninnu na gane kana sonta, soyayya sosai wannan dalilin ya sa kake shiga tashin hankali in har ka ganta da wani. Kana son abu amma kana nisanta kanka da shi? Sai yaushe za ka cire girman kai da izza ka gaya mata that you adore her, or are you going to hide it until when she got married. Is that what your intention?" Kasa magana ya yi, domin ya san cewa duk bin da ya faɗa gaskiya ne. Juyowa ya yi, da idanunsa da suka rine suka yi jajir ya kalle shi, ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya kasa. "You love her, amma kana ganin kamar furta mata zai zubar da ƙimarka? Ya Damir saboda me za ka yadda zuciyarka ta cutar da kai saboda tunanin ka mara tushe. Eh komai ya faru ta sanadinta, amma kuma ka tuna mutum bai isa ya kashe wani ba. Nasreen tana da hankali da natsuwa sannan da ilmi. Ba ta da hayaniya irin kalar macen da kake so, ka kuma samu sai girman kai ya hana ka furta mata?" "Da gaske ina shiga ciki tashin hankali da firgici duk lokacin da na ganta da wani. Tun ranar da na ganta kwance a gadon asibiti na ji wani lamari dangane da ita, amma sai na danganta jin da tausayi. Bayan lamarin ya faru dai na ke jin ƙunci in na tuna tana gidan wani da jinina a jikinta. A tunanina abin da ya faru ya sanya nake jin haushinta, ashe kishinta na ke yi. Sai dai bani da courage da za iya tunkararta." Kallon mamaki ya yi masa."Ya Damir kamar ba ɗan boko ba? Ina wannan hot kalamai da kake gayawa Anty Batula? Shi za ka yi amfani da su ka sace zuciyarta, kuma na tabbata za ta kauda kowa ta zaɓe ka, saboda halaccin da Marwana ta yi mata, don haka kar don tsohon mijinta ya dawo ka yi zuciya ka bar ƙasar. Kaura da kasar ba na ka bane, saboda ko da ka je dole zuciyarka za ta hana ka zukuni ka dawo." Shiru ya yi cikin tunanin, yadda zai iya kallon ta ya gaya mata ƙauna. To amma kuma in ya rasata zai yi da ƙaunarta da yake yi. Wata zuciya ta ba shi shawarar gwadawa. "Go for her adore her and pampered her." Kalaman da gaya masa, sai ya ji wani ƙwarin gwiya har zai iya fara tunkararsa. Ganin ya yi shiru sai ya karɓi jakar kayan da yake haɗawa."Please ka samu soyayyarka da kanka kar ka bari su Mommy su sani ballanatana ka ci arzikin Marwana. Nasreen za ta iya mallaka maka zuciyarta saboda Marwana, amma bana son haka ya faru. Ka tsaya ka zama namiji samu ƙaunarta sannan ka aure ta." Kama shi ya yi ya rungume yana faɗin."Na gode da ka gane bin da yake damuna, kuma ka bani shawara in sha Allahu zan yi matuƙar ƙoƙarina don na mallake ta." "I wishe you all the best." Ya ce tare da ɗaga masa hannu alamun fatan nasara. Murmushi ya yi tare da shafa bayansa. Ya daɗe sosai a cikin ɗakin yana ƙarfafa shi, har sai da zuciyarsa ta samu kwarin gwiya sannan ya fita. Da ya fita kwanciya ya yi a kan gado, tare lumshe idanu yana tunanin yadda zai fara tunkararta da soyayya. Duba ga yadda yake ɗaure mata idanu yana mazurai. Shafa kansa yayi cikin jin kunya tun kafin ya fara. Yana zaune ya yi oder na kaya masu kyau, da yawa da takalma hatta agogo dai da ya siya da kuma turare, domin so yake ya je da mutuncinsa, kallo ɗaya ta faɗa tarkon ƙaunarsa ba tare da ya sha wahala ba. Mamaki sosai suka yi, a lokacin da Muhsin ya sanar musu da ya fasa tafiya. Sai dai, duk tambayar da suka yi masa bai gaya musu dalilin fasa tafiyar ba. Duk da haka sun ji daɗi duk da cewar Mommy ba ta shiga sabgarshi saboda kafiyarshi. Da safe bayan ya yi wanka, ya daɗe yana ƙyalƙyale jikinsa kamar mace. Dama Damir akwai iya ɗaukan wanka, tun lokacin da Batula ta rasu ya daina gayu sai dai ya sanya kaya ya fesa turare. A falo ya fito don su karya yana ta zuba ƙamshi. Marwana da ta fito daga kicin da fulas a hannunta tana ƙoƙarin isa dinning sai ta tsaya cikin mamaki tana kallonsa. Mommy ma da take zaune kallonsa take yi."Damir za ka ɗaurin aure ne daga gurin ofis?" Tambayar da ta yi masa, ya sanya shi kallon jikinsa yana murmushi sai kuma ya kalle su ganin yadda suke kallonsa. Kunya sosai ta kama shi har sai da ya murmusa ya shafa kansa."No mommy I feel like to, shi ya sa na yi." "Daddy you look so good and handsome."Little Marwana ta ce masa tana dariya. Mommy ta ji daɗin dariyar da yake yi, har yana tsokanar Marwana da take ta cusa ƙwai a bakinta cewar ta cika ci. Sosai suka yi murnar ganin yadda ya saki. Ya karya ana hira ana raha sannan ya yi musu sallama ya fice. Rigar Muhsin Marwana ta ja tana kallon sa."Kai ɗan'uwa zo mu yi gulma. Mai ya sa ya Damir yake farinciki kuma ya yi kwalliya haka? Sannan don Allah ka gaya mini dalilin da ya sanya shi fasa fita waje." "Munafuka ba zan gaya miki ba, sai ki je ki tambaya shi." Ya ce mata tare da yi mata dundu. "Wayyo Momi to shine har da dukana." Ta ce cikin muryar kuka tana shafa bayanta. "Sabon kamu ya yi ƙanwar abokin sa..." "Kan uba! Ai wallahi bai isa ya yi aure ba in ba Nasreen ba."Marwana ta furta lokacin guda fuskarta ta canza. "To tun da ke kika haife shi sai ki sanya shi." Ya ce mata tare da zabga mata harara ya fara tafiya. "Muhsin ba za ka gaya mini ba?" "Mommy sauri na ke yi Ya Damir kin ji yana jira na." Ya ce tare da ficewa. Marwana ta cika ta batse."Ai wallahi ki gaya masa ba zai auri kowa ba sai ita." Kasa magana ta yi domin ita kanta ta fi son ya aure ta. A mota suna tafiya suna hira sosai har da dariya. Sosai Muhsin ya ji daɗin yadda ya canza. Duk da cewar zuciyarsa tana bugu na tunanin yadda zai nuna mata soyayya, amma yarda da ya yi yana sonta, kuma zai gwada sa'arshi sai ya ji ya samu natsuwa. Da suka isa cikin kampanin, idanunsa na kan inda take aje motarta. Sakin ajiyar zuciya yayi ganin har ta zo. Kalar motarta da numbobinta tuni ya riƙe su aka. Ofis ɗinsa ya shiga ya zauna yana jin matsanancin frinciki. Bai jima da shigowa ba p.a ɗinsa ta shigo da files ta kawo mishi. Gama jin bayanin ta ya yi sannan ya kulle ta yace,"Ki kawai Nasreen aikin sannan ki nuna mata, in ta gama kice ta kawo mini da kanta." Da sauri ta kalle shi jin ya ambaci sunanta, saɓanin da sai dai ya ce yarinya. Ƙara kallon da ta yi, ganin yadda ya yi kyau da fara'ar da yake fuskarsa. Dama tun a ƙasa ta ji ana gulman wankan da yayi kamar mai zuwa zance. Ganin ya haɗe rai, yadda take kallon shi sai ta ɗauka da sauri ta fita. Nasreen tana zaune a ofis tana cike takaddun ta shiga. Murmushi duk yi wa juna sannan suka gaisa."Oga Damir ya ce na kawo miki, sannan na nuna miki aikin da za ki yi, kuma in kin gama ki kai masa." Cikin dakewa ba tare da ta firgita ba ta ce,"Ok, ina da aiki sai na gama." Mamaki sosai ta yi jin abin da ta ce."Na je na gaya masa ne don ban san lokaci da yake so ba." "You can tell him, tun jiya akan wannan aikin kin ga dole na gama kafin na sa?" Ta yi mata tambayar tana murmushin da ya ƙara bata mamaki. "Ok, I will inform him." Ta ce tare da juyawa ta fita Hankalinta kwance ta ci gaba da aikin, har tana mamakin kanta jin babu ɗigon tsoronshi a ranta. A lokacin da ya shigo wayarsa, a ganinsa yana kallon lokaci yan tunanin lokaci da za ta ɗauka kafin ta gama, domin ya ƙosa ya ganta don idanunsa har wani ƙaikayin son ganinta suke yi. "Ya dai?" Ya yi mata tambayar ganin ta shigo. "Ta ce she has a lot of work, sai ta gama za ta yi naka." Mamaki sosai ya kama shi, sai kuma ya ya ji sam bai ji haushin abin da ta ce ba. Mamakin maganar ya yi har yaushe ta daina jin tsoronsa, amma da ya tuna tun da ta dawo yadda take masa wani gani-gani, sai ya daina mamakin." "Ok, you can go." Ya ce mata fuskarsa ɗauke da murmushin da ba ya son ta gani. Cikin mamaki ta fita tana tunanin canjin da ya yi. Hankalinta kwance ta ke aikin ta har ta gama. Ko da ta gama zama ta yi, tana huwatawa har lokacin tashi ya yi. Wayyo Damir an ije girman kai da izza za a fara nuna wa Nasreen soyayya. Na matsu na ga wannan soyayya. Ko zai iya ko kuma girma kai zai hana shi? WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 35 Hankalinta kwance ta ke aikin ta har ta gama. Ko da ta gama zama ta yi tana hutawa har lokacin tashi ya yi. Ta kwashi tarkacenta za ta fice. Tana ƙoƙarin sauka ƙasa suka haɗe da P.A ɗinsa. Turus tayi sai kuma ta shafa kai."Na manta na sanar miki ban gama ba, saboda aikin da na ke yi ya riƙe ni. Ki gaya masa gobe xan yi." Ta ƙarashe maganar, tana sauka ba tare da ta tsaya ta ji abin da za ta ce mata ba. Kallonta ta yi, yadda ta daina tsoronsa su kuma ta juya zuwa ofis ɗinsa."Sir, ta ce aiki ya riƙe ta gobe za ta yi." Da sauri ya juyo yana kallonta jin abin da ta ce. "Ok go." Abin da ya iya cewa kenan sai ya zauna yana mamakinta. Damuwa ce ta kama shi, domin tun safe yake son ganinta. Ko da ya ce gurin lunch kamar a ofis ta yi nata. Da sauri ya kwashi tarkacensa ya fice don ya ganta, amma yana zuwa motarta na ficewa. Ji ya yi jikinsa ya yi sanyi sosai. Wani irin sonta ya ƙara mamaye shi. Cikin kasala ya shiga cikin motarsa ya tafi. Nasreen tun ranar da Faruk ya zo, ta shiga damuwa saboda tana tsoron kar ya ɗauke yaranta. A dalilin wannan tunanin ta shawarci Ahmad ta canza musu makaranta, amma sai ya hanata ya ƙarfafa ta da cewar ba zai aikata ba tun da ba shi da wacce za ta riƙe masa. Abin da ya ce mata ya ɗan kwantar da hankalinta tamkar ta yi baƙo ya mutu. Washegari da safe, ta yi wanka sannan ta sha kwalliya cikin shiga ta alfarma ta wuce ofis. Tana shiga jakarta ta ake kan tebur ta kama aikinsa. Zuwa ƙarfe sha biyu ta gama yunwa take ji sosai, saboda bata karya ba ta taho, domin da safe ta ji ba ta son cin komai, saboda da dadddare cikinta ya so ya ɓace. Sai data gama aikin sannan ta ɗauka ta nufi ofishinsa. Ba ta ji tsoro ko faɗuwar gaba ba, har sai da ta kama murfin ƙofar za ta murɗa, sai kawai ta ji gabanta ya faɗi yana kuma harbawa da sauri. Da sauri ta saki ƙofar tana ƙaranto addu'a, sannan ta samu ƙarin gwiyar shiga. Yana zaune da waya a gabansa. Aiki yake yi amma duk bayan minti sai ya kalli wayar, tare da tunanin wani lokaci za ta yi aikin ta kawo. Ganin har sha biyu ta yi dai ya fara tunanin, ko ta yi masa rainin da zai ba ta aiki ta ƙi yi. Zuciyarsa ta sare a lokacin da ya kuma ƙara tunanin ko ba ta son ganinsa ne. Yana ƙoƙarin ɗaukar waya ya kira p.a ɗinsa ya ji an murɗa ƙofar. Idanun ya zura a ransa yana addu'ar ita ce. Cikin sama addu'arsa, ta karɓu ganin ta shigo da siririyar sallama a bakinta. Ɗago idanunsa ya yi, yana kallon ta yayin da ya ji matsanancin faɗuwar gaba. Yayin da yake kallonta, amma tun da ta kalle shi sau ɗaya ba takara ba domin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri kuma bisa rashin ƙa'ida. Ƙarasawa ta yi, har gaban teburinsa cikin yanayi na ta ƙura ganin yadda ya zuba mata idanunsa kamar zai haɗiyeta. "Ina kwana?" Ta yi masa tambayar tare da ije aikin a gabansa. Files ɗin ya kalla, sannan ya ɗora shanyayyun idanunsa a kanta yana ƙoƙarin saita natsuwarsa ya amsa gaisuwar. "Lafiya lau." Iya abin da ya yi nasarar furta wa kenan, saboda yadda harshen da suke harɗewa, tamkar wanda yaron da yake koyon magana kuma ya nace sai ya yi. Da sauri a ɗago ta kalle shi, jin karo na farko ya amsa maganarta cikin sanyi. Saurin mayar da idanunta tayi, yadda ya kashe ta da mayun idanunsa.Ganin ya yi shiru sai ta juya za ta tafi da ƙyar ya saita ɗan natsuwarsa ya ce,"Nasreeeeen." Ya ja sunan tare da yi masa gunna yana kallonta. Tsayawa ta yi cak! Zuciyarta na bugu domin yadda ya kira sunan ta ji shi har cikin zuciyarta. Kasa juyowa ta yi har na 'yan daƙiƙa, sannan ta yi nasarar sakin murfin ƙofar da ta kama za ta fito ta juyo tare satan kallonsa. Zuciyarsu ta buga a tare karan farko da ya ji yana son ya ji ta a jikinsa, domin wani irin shaukin ta da madarar ƙaunarta ya ƙara kama shi, saboda kallon da ta watsa masa, wanda ya sanya ya ji ta tamkar ya je gareta. Nasreen satan kallon idanunsa ta yi. Ganin kallon tuhuma yake mata a tunainta, aikin da bata yi masa ba ne zai yi ƙorafi kamar yadda ya saba."Am sorry Ya Damir aikin Ingawa ne ya ba ni, kwana biyu ban yi ba, kuma ya gaya mini a ranar yake so zai tura..." Ransa ne ya ɓaci, jin abin da tace har da wani gulmar ce masa Yaya, saboda hakan yayan da ta ce masa bai zama unique a gurinsu ba, ganin ko wane karabiti yana samun matsayin yaya. "Aikinsa yafi nawa ne?" Ya tsinci kansa yana tambayarta cikin daga murya Da sauri ta cire ido ta kalle shi ganin ya yi fushi lokaci guda. "A'a ka yi haƙuri." Ta furta da muryar da ya sauko da fushinsa. "Daga yau duk wanda ya baki aiki, in har na kawo nawa a ranar kar ki sake yi, ki mayar mishi da aikin." "Ok sir." Ta furta a hankali tana kallonsa. Guntun tsaki ya ja, saboda sir da ta kira shi dashi ya ƙara ƙular da shi. So yake ya ji ta kira shi da sunan soyayya, sai kuma ya shafa kansa yana murmushi ganin ya cika zaƙewa. Nasreen kuwa kallonsa ta yi, tana tunanin anya bai zare ba, saboda ganin lokaci guda ya yi fushi sai kuma ya yi murmushi. Ɗan tsorata ya yi ganin yadda take kallonsa kamar xararrre. Shi kam ya manta da ita zuciyarsa ta faɗa kogin tunani. "You can go I know what I will do." Ya ce mata ba tare da ya kalle ta ba. Jin haka ta murɗa ƙofar ta fice tana mamakinsa. Tana fita sai ya saki murmushi tare da buga hannunsa."Anya zan iya tunkararta da soyayya, ganin yadda na susuce na rikice kamar ba Damir wanda mata da yawa suke crushing ɗina ba?" Tambayar ya ƙarashe yana shafa kansa. "Mai ya sa take mini kwarjini?" Ya kara furtawa yana kallon ƙofar da ta wuce. Nasreen kuwa, tana fita ta je ta ji abinci hankalinta kwance batare da tunanin komai ba, sannann ta koma ofis ɗinta ta ci gaba da aiki. Da ya koma gida, sai ya kasa sukuni kalmar ina wuni da ta furta masa yake ta masa kuwwa. Wanka ya yi sannan ya fito falo. Marwana tana zaune tana waya da Ahmad, wacce take jin kamar yanzu a ɗaura. Ganin yana saukkowa ta yi masa sallama, tare da ije wayar, bayan ta sanar mishi da za ta kira shi. "Sannu da saukkowa Ya Damir."Harararta ya yi, ganin tana soshe-soshe alamun bata da gaskiya. Ba tare da ya amsa ba ya zauna kusa da ita. So yake ya samu numbar Nasreen a wayarta, amma ba ya son tambayarta. Yana zaune yana ta kallonta yana son ta ɗauki wayar ta fara dannawa, sai ya aike ta ya kwashe numbarta, amma sai ya ga ta riƙe wayar ta mayar da hankalinta kan tibi. Sun daɗe a haka tana jiran ya tashi ta ci gaba da wayarta. Ganin ya zauna har da ɗora ƙafarsa kan stool sai ta gane ba yanzu zai tashi ba. Wayarta ta ɗauka, ta buɗe data sannan ta fara yi wa Ahmad magana ganin yana kai. "Go give me water." Ya furta da sauri yana kallonta. "Ok," Ta ce tare da miƙewa za ta nufi kofin ta ɗauko kofi. "Zo ki ije wayar nan, saboda in kika tafi ban san lokacin da za ki dawo ba. Na lura kwana biyu gabakiɗaya hankalinki na kan waya." Da sauri ta ije ba tare da ta ce masa komai ba. Tana fita ya ɗauki wayar. Saboda kar ta kama shi da wayarta, so ya duba numbar ya ga an sanya mu sister tare da heart na stikers. Da sauri ya tura a Whatsapp ɗinsa, ya yi maza goge tare da gogewa ya ije wayar. Marwana har ta shigo sai ta ganshi da wayar yana dannawa, ganin bai ganta ba ya sanya ta koma baya sannan ta yi masa sallama yadda zai ji ta shigo. Mamaki sosai ta yi, tare da tunanin dalilin da ya sanya shi ɗaukar wayar. "Ga ruwan." Ta ce mushi tare da ije wa kan stool tana masa kallon tuhuma. "Ok," Ya ce tare da tsare gida ganin kallon da take masa. Mantawa da an kawo masa ruwan ya yi, yana ta tunanin yadda zai fara mata magana."Na kira ta ne ko na yi chatting ɗinta?" Ya furta cikin ransa. "To ina kirata na ce mata me?" Ya kara yi wa kasa tambayar. Miƙewa ya yi cikin damuwar rashin abin da zai ce mata. Mamaki sosai ta yi, ganin ya ƙi shan ruwan har ya fara hawa stairs ta ce,"Your water." "Oh!" Ya ce tare da dawowa ya ɗauki bottle ɗin. Idanu ta raka shi da shi har ya shige."Something is definitely fishy." Ta ce tana mamakin canzawar da ya yi. Wayarta ta ɗauka ta shige ɗakinta don kar ya zo ya ƙara takura mata. Damir bayan ya shiga cikin ɗakinsa ya kulle tare da sanya ɗan makulli. Safa da marwa yake yi, yana tunanin mai zai ce mata in ya kirata. Ije wayar ya yi cikin damuwa, rashin abin da zai ce yana kallon numbarta da ya haddace a yanzu. "Your numbers is special as you are special too." Ya ce ganin numbobin ba su da wuyan haddacewa. Kwanciya ya yi, tare da ɗora wayar a ƙirjinsa yana ji tamkar ita ya rungume. Ya daɗe a haka yana tunanin mafita, sannan ya ake waya ya fasa kira dai dare. Kafin ya samu courage, na kiranta zuciyarsa ta gama azabtar da shi da tunaninta. Da ya rintse idanunsa ita yake kallo more especially wannan kissable lips ɗinta. Sosai ya yi mamakin kasa ganin tunaninsa na son haukatar da shi. Kafin dare yayi, duk ya ƙosa saboda ji yake kamar ya jawo kiran sallar magariba. Ya rinƙa kallon agogo yana jan tsuka, tare da jin haushin ladanin ganin ya ƙi kiran sallar da wuri. Ana kiran magariba ya fice masallaci. Zama ya yi yana ta lazimin nasara har aka kira Isha yi sannan ya yi. Ko da aka yi masa maganar abinci kasa ci ya yi, saboda ji yake ba ya son cin komai. Burinsa kawai ya ji zazzaƙar muryarta ta doki kunninsa. Sai dai abin takaici, duk wannan ɗokin yana hawa gadon ya rungume filo, sosai a ƙirjinsa yana jin kamar ita ya rungume. Layinta ya kira zuciyarsa na bugu, amma sai yar baturiya ta fara masa turanci tana gaya masa tana another call. Saboda takaici da kishi da suka rufe masa ido,har ya ɗaga wayar zai buga da ƙasa, sai ya fasa tuna maƙudan kuɗin da ya siya, da kuma abubuwa masu mahimmanci da suke ciki. Tsaki ya yi, tare da jifa da filon amaimakon wayar. Ransa ya ɓace hankalinsa ya tashi. "Da wa take waya? Tsohon mijinta ko wannan mayun Annur da Ingawa?" Ya tambayi kansa cikin takaici. Kashe wayar tasa ya yi, sannan ya koma gadon ya kwanta, kamar wani marayan zaki. A ranar sai dai bacci ɓarawo ya ɗauke shi, domin ya kasa ba ci ga shi ya kasa ƙara kiran layin, yana tsoron kar ya kara jin tana wayar har zuwa lokacin, saboda a yadda yake ƙunsa zuciyarsa za ta iya bugawa. Da ƙyar ya samu ya rintsa shi ma, don daa ya yi ta sallah yana karatun Alqur'ani, sannan ya samu bacci mai nauyi ya ɗauke shi, da tunanin sun yi auren suna cikin rayuwar su na soyayya har ta haifa masa yara. Da ya farka rintse idanunsa ya yi don ya koma, domin ya ci gaba da mafarkin hugging ɗin ta da ya yi, amma iya ƙoƙarin da ya kasa, sai ma jikinsa da ya fara ciwo. Yana nan yana tunani aka kira sallah, sannan ya miƙe zuwa bayi don ya yi wanka ya fita Masallaci A maimakon ya ji haushi, ta fita a ransa sai ya ƙara jin mugun ƙaunarta, tare da jin ƙarfi da jarumtar fitowa a fafata da shi don ya ɗauke abarsa. Tunanin inda zai samu hotonta ya fara yi, saboda idanunsa da suke masa ƙaikayin son ganinta. So take da ya yi aiki ya kalle ta don ta ji ƙarfi a jikinsa. Tunawa da Marwana ya san tana ta hotunanta sosai. Da sauri ya sanya jallabiya ya fito saɓanin da yake zaune da gajeren wando iya gwiwa. Tana ɗakin momi da waya a hannunta ya shigo."Wai ke uban me kike yi kullum da waya a hannu?" Ya daka mata tsawar da ya firgitata, domin ba ta san ya shigo ba. "Babu komai." Ta ce masa tare da aje wayar. "Ba ni in duba saboda ban yarda dake ba." "Saboda me Damir? Na ga tana da kula kuma sam ba ta kula samarin shaho?" "Mommy kar ki yabe ta ki bari kawai na duba, kin san ba a yabon ɗan kuturu..." Ya ce mata tare da amshe wayar yana harararta. "Ai na yi tunanin kamar ta ƙara samo mini suruki ne, saboda yadda na ga tana murmushi. In dai kin samu wanda kike so ne sai ku je ku yi gwaji jini kar yi na Ashaman. "Ai tun da Allah ya kawo mini wannan da shi za a yi in sha Allah." Ta furta a ranta amma a fili sunkuyar da ka ta ta yi cikin kunya, wanda ya ƙara tabbatar wa Mommy da zarginta har ta yi murmushi. Amaimakon ya duba, sai ya sanya wayar a silent ya kunna data. Gallary na ta ya shiga, inda ya ci karo sosai da hotunnanta. Da sauri ya tura da yawa, sannan ya goge ya miƙa mata. Ba tare da ya ce komai ba ya fice. Kallo suka bi shi da shi har ya fice. "Anya Ya Damir ba satan mini kuɗi yake yi ba?" Ta yi tambayar daidai lokacin da Muhsin ya shigo. "Ke! Ya Damir kike zargi da sata, uban me zai yi da kuɗin ki?" "Abin ne da mamaki wai yaro ya tsinci haƙori. Jiya na kama shi yana duba mini waya bayan ya aike ni. Yau kuma ya karɓa amma bai ce komai ba." "Amma kin san babu abin da zai ci da wasu yan ƙalilan kuɗinki? Ko kin ga an cire miki kuɗi ne?" "Zargi na ke yi bari na duba alert." Ta ce tana ƙoƙarin checking balance." "Wai da gaske zarginsa kike yi? Uban me kike da shi har zai ɗauka? Ki yi minimizing wayar sai ki duba abin da ya yi." "Yauwa haka ne kuwa kaina ya kulle." Ta ce tare da yin abin da ya ce. Ganin gallary ya shiga sannan ya kuma shiga Whatsapp. Shiga cikin Whatsapp ɗin ta yi tana dariyar farinciki don ta gano shi, musamman da ta ga an buɗe data, saboda messages sun shigo a lokacin. "Ok, wato hutunanta ya tura sai ya goge?" Ta yi ma kanta tambayar tare da kwashe wa da dariya. "Lafiya mai ya yi?"Muhsin ya tambaye ta ganin yadda farincikinta ya ninku. "Ban sani ba ranar da na tambaye ka ba haka ka ce mini ba? To ba zan gaya maka ba sa..." "Ke ina wasa dake ne?" Ya ce mata tare da nufota a fusace. Ganin haka ta ruga da gudu suka shiga zagaye ɗakin daga baya kuma suka yi falo, ba tare da sun kula da kiran da Mommy take musu ba. Saura kaɗan su buge shi da ya fito zai tafi aiki."Ba ku da hankali ne Muhsin mene ne haka?" Ya yi musu tambayar yana daka musu tsawa. Natsuwa suka yi, amma tana kallonsu tana mishi dariya. "Yauwa ya Damir cewa ta yi wa..." Da sauri ta toshe masa baki tana faɗin,"Wallahi ƙarya ne ban ce komai ba, wai sharri zai yi mini kar ka bani kuɗin da na tambaye ka." Tsaki ya yi tare da fita ba tare da ya kar kallonsu. "Kin san Allah in baki faɗa mini ba, sai nace kin ce masa ɓarawo." Zare idanunta ta yi, tana kallon da da yake mata dariya zai fita."Wallahi in har ka furta ni kuma sai na gaya wa Hajar, yarinyar da kake waya da ita kana fakewa da mate ɗinka ne." "Da na karya ki a gidan nan." Ya ce mata da sauri. "Allah ya ba ka sa a ka gaya masa to." Ta ce tare da yi masa gwalo ta wuce ɗakinta. A cikin ɗakin murna take yi sosai da tabbatar da ya kamu da ƙaunarta. Zama gefen gado cikin farin ciki, sai hankalinta ya kwanta yanzu kuwa za ta tunzura shi yadda zai furta yana sonta, ba tare da ya wahalar da su ba. A ofis wuni ya yi yana ta kallon hotunan da ya tura. Wani ya yi murmushi wani kuma ya saita bakinsa daidai bakinta ya yi kissing. Haka ya kasance cikin farinciki har zuwa aka tashi. Kasancewar aiki suke yi sosai sai bai samu damar ganinta ba, duk da yana yi yana sauka ƙasa don kawai ya ganta. Da dadddare suna dinner, mommy ce take masa hira, amma gabakiɗaya hankalinsa ba ya gunsu. Ji yake a zuciyarsa ba zai iya kwanciya ba tare da ya kira ta. "Mommy, Ya Annur gaskiya ya iya soyayya har na ji Nasreen tana faɗin za ta bashi dama ya turo, ganin Faruk zai takura ma...." Wani irin tari da ya tsarƙe shi, ya sanya ta kasa ƙarashe maganar. Gabakiɗaya suka yi kanshi suna faɗin,"Sorry." Ruwa Marwana ta miƙa masa sai ya karɓi na Muhsin ya kurɓa."Sannu ka ci abinci a hankali." Momi ta ce masa dariya na son kubce mata ganin yadda ya koma. Tun da ta faɗi haka ya ji abincin ya fita a ransa. Ko da Mommy ta tura masa abincin bai ci ba. "Aiko da Annuri ya dace mata ni fa yarinyar nan burge ni take yi, saboda sanyin halinsa da kuma natsuwarta." Marwana ta karɓe da cewar,"Ga hakuri Mommy in har ya aure ta zai yi farin ciki, saboda haƙurinta a lokacin da take auren Faruk sai kin ga haƙurin da ta yi." "Wallahi the girl is innocent." Cewar Muhsin. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 36 "Wallahi the girl is innocent." Cewar Muhsin. "Ai ga shi nan Allah ya saka mata da miji na gari, domin yaron yana da haƙuri ko Damir?" Da sauri ya ɗago kansa cikin damuwa jin abin da ta ce,"Ni ma ban sani ba, abokina ne ba kwana nake da shi ba, ballanatana na san halin da duka." "Amma tsawon shekara nawa kuna tare? Bana manta aurensa na farko har dakai aka je jin magana?" "Hmmmmh! Ya canza yanzu sam ba ta dace da shi ba." Ya tsinci kansa yana faɗin haka, domin shi kansa bai san lokacin da ya furta hakan ba. "Saboda me zaka ce haka, kuma da wa ta dace?" Da sauri ya miƙe yana hararar Marwana jin tambayar da ta yi masa."Mommy gaggawa aikin sheɗan ne. Yai dai kamata ta zauna ta natsu ta samu miji na gari, kuma duka yaushe auren na ta ya mutu?" "Babu zancen gaggawa Damir, tun da ta samu miji ta yi aurenta kawai." Fara hawa sama yayi, ba tare da ya ce komai ba. A tare suka kalli juna suka yi murmushi. Yana shiga cikin ɗaki ya kulle kofar tare da nemo numbarta ya kira. Cikin sa'a ta shiga ta fara ringing. Da sauri ya kashe wayar, don ƙarar da kiran yake yi tamkar zuciyarsa ke bugawa. Cikin takaici ya kaiwa kansa duka, ganin ya kasa samun ƙarfin gwiyar kiranta. "Mai ya sa nake jin tsoronta?" Da sauri ya ƙara kiran cikin dakuwar zuciya. Nasreen tana zaune a kan gado da waya tana murmushi. Ta gama waya da Annur kenan. Ganin baƙon number sai ta yi tunanin Faruk ne. Ƙin ɗaukar wayar ta yi har sai da ta yi ringing sau biyu. Cikin sarewa ya ije wayar ya zauna jikinsa a sanyaye. Har ya yi fushi ba zai ƙara kira ba, sai kuma ya kasa sakamakon zuciyarsa da ke addabar sa daya kira ta, domin hankalinsa ya tashi sosai jin an fara zancen a tura. A kiran na uku har ta kai ƙofa, sai kuma ta dawo cikin tsanannin fushi ta ɗauka. A zuciyarta ita kaɗai ta san irin zagin da za ta yi masa. Da ta ɗauki wayar, sai wata zuciya ta ba ta shawarar ta bari yayi magana, don haka ta yi shiru tana sauke numfashi. Da sauri Damir ya kanga wayar a ƙuncinsa cikin rashin abin da zai ce. A tunaninsa za ta yi masa sallama, sai ya samu abin da zai furta. Cire wayar ta yi a kunninta don ta yi tunanin an kashe, amma sai ta ga ba a kashe ba. "Assalamu alaikum." Ta furta cikin sanyanyar murya. Zuciyarsa ta buga ya kasa amsawa. Ganin haka sai cire wayar a kunninta." Wa alaikis sallam. Nasreen." Ya samu damar iya furtawa yana rintse idanunsa. Cikin tsananin razana, ta kalli numbar tana tunanin ko muryarsa ke mata gizo. Mamaki sosai ta yi har ta kasa cewa komai." Nasreen ce?"Ya yi mata tambayar da ya sanya ta kasa amsawa har na wani lokaci, kafin ta saita zuciyarta dake bugu. "Eh ni ce ina wuni Ya Damir?" Ta ce masa cikin sanyin muryarta. Gaisuwar da ta yi masa, sai ya samu ƙarfin gwiya, duk da cewar ba shi da abin da zai ce. Dubara ta faɗo masa ganin sun yi shiru sai zuciyarsu da ke bugawa. "Na kira na yi miki godiya saboda kin yi aiki da kyau." Ya furta yana jin takaicinsa. "Ok ba komai." Ta furta bayan ta ja numfashi. Tsintar kansa ya yi da kashe wayar ya jefe da ita kan gado. Kasa bacci ya yi, yana ta tunanin yadda zai hana auren da Annur ya bayyana mata sirrin zuciyarsa. A daren bai iya rintsawa ba har sai da ya samu mafita. Murmushi ya yi, tare da cusa hannunsa a a cikin sumar kansa. Washegari da safe cikin farinciki ya isa ofis. Sanarwa ya yi akwai canje-canje da zai yi a gurin aiki. Ya canza wa ma'aikata da dama ofishin daga ƙarshe jin canjin da ya yi wa Nasreen ya shayar da su mamaki. Hajar ta kalle ta cikin mamaki, wacce tun da ta ji inda ya mayar da ita ta kasa cewa komai. "Ikon Allah gaskiya na fara zargin wani abu. Kamar Ya Damir akwai wani abu a zuciyarsa, domin in ka ga kare yana shinshinar takalmi ɗauka zai yi." "Wallahi Hajar tun da ya ce ta zama sakatariyarsa na shiga mamaki. Ke Nasreen ki gaya mana ko soyayya kuke yi a ɓoye?" Jin tambayar da suka yi mata sai ta ɗago a birkice tana kallonsu. "Abin ne da mamaki lokaci guda ya ba ki sakatariyarsa?" Ta kasa ce musu komai, saboda kamar yadda kansu ya kulle haka ita ma. Fara tafiya kawai ta yi suka rakata da ido. Tana tafe tana tunanin dalilin sa na yin haka har ta isa ofis ɗinta. Zama ta yi tana tunani sai ga Ingawa ya shigo a birkice."Nasreen na shiga cikin tashin hankali sosai jin oga Damir ya mayar dake sakatariyarsa. Na fara jin tsoro kamar rasa ki zan yi! Please in har kika sona ki ba ni damar na tura gidanku, saboda duk abin da ya faru tsakaninku ba zan iya zuba idanu ya aure ki ba, ina son ki kan soyayyarki zan zamo mai son kaina." Kasa ce masa komai ta yi, tana kallon sa ganin yadda ya tayar da hankalinsa."Please Nasreen in har kin sona ki ba ni dama na tura iyayena a cikin satin nan." Yana ƙarashe maganar ya fice daga ofis ɗin yana jin tamkar zai yi kuka. Damuwa ce ya yi mata yawa sosai har ta kasa cewa komai. Ta kasa gane nufinsa na mayar da ita sakatariyarsa, in har ya yi hakan ne don ya ƙuntata mata, sai dai su ƙuntata wa juna. Tana zaune tana karanta wasikar jaki, kiran Marwana ya shigo. Ɗagawa ta yi tare da yin shiru bayan ta yi mata sallah. "Nasreen lafiyarki kuwa?" "Ya Damir ne ya mayar da ni sakatariyar...." Kafin ta ƙarashe ta ji ta zabga uban ihu tana kabbara. "Addu'a ta ta karɓu Nasreen Ya Damir sonki yake ɗawainiya da shi. Neman hanyar da zai kusanta kan shi dake yake yi." "Hummh! Tunanin ki kenan, in har ya yi hakan ne don ya ƙuntata mini daidai na ke da shi." "Bana tunanin haka, kin ga ya kira ki just to say thanks. Kuma ya zu ya dawo dake sakatariyarsa. Wallahi sonki yake yi tsabar girman kai ya hana shi furtawa, saboda har kama shi na yi yana tura hotonanki." "Haka kika ce ya batun fitarmu?" Ta yi mata tambayar tana son kauda zancen. "Dalilin da ya sanya na kira ki kenan. Ya Ahmad yake tambayata da ƙarfe nawa za mu je?" "Shi ya Ahmad ɗin?" Ta yi mata tambayar cikin zallar mamaki tana zargin su. Tuna katoɓarar da ta yi, sai ta daure ta ce,"Eh mene ne kike mamaki ko ba yayana bane, da zai kira ni ki yi mamaki?" "Hmmm ki ci gaba da munafunci ku Allah zai tona asirinku." "Tsakanina da shi girmamawa ne saboda kamar Ya Damir na ɗauke shi ba maganar soyayya." "In ta yi wari maji." Ta ce tare da kashewa sai kuma ta yarda saboda da suka soyayya ba zai ɓoye mata ba. Kan dole ta tattara ta koma ofishin ba don ta so ba. Tun data dawo sai hankalinsa ya kwanta. A rana sai ya kai mata aiki sau nawa. So yake su shaƙu su rinƙa magana, amma har yanzu ya kasa samun hanyar da zai kusanta kanshi da ita, yayin da ita kuma ta kasa shaƙuwa da shi. In ya ji tana magana tana dariya sai ya ji kamar ya je ya yi ta kallonta. Farouk kuwa, hankalinsa ya tashi sosai kamar zai yi hauka. Ya rasa hanyar da zai yi ya rinƙa ganinta, domin tun ranar da ya je kampanin ta sanya securities kar su kar bari ya zo ko ƙofar gurin. Yana zaune cikin tsananin damuwa hawaye yana bin fuskarsa. Da sauri ya miƙe tsaye tare da yin murmushi mai kama da kuka, ganin ya samu sabuwar shawara. Kai tsaye ya tuƙa mota sai makarantar su Raihann. Ofishin Principal ya je tare da yi masa bayani. Bai yi wani dogon bincike ba, domin shi ya sanya ta a makarantar. Shiga cikin aijinsu ya yi ya ɗauko musu shi. Raihann na ganinsa sai hankalinta ya tashi sosai. Hannu ya sanya ya riƙe ta ganin kamar tana son kunyata shi. Musaddik kuwa har zai fara kuka. Da sauri ya fita da su cikin makarantar kamar wanda ya yi sata. Sai da suka yi nisa, sannan ya faka motar tare da rungume su ya fashe da kuka. Ba tare da sun damu da murnar da yake yi ba, sai suka sanya kuka Musaddik yana faɗin,"Anty Rai'an Ummm zan je." Ƙara kamasu ya yi rungume su."Ku bar kuka ni ma mahaifinku ne. Kaicona da son kuɗi ya sanya na kasa jawo ku jikina. Ya furta ganin yadda suka tayar da hankalinsu. Kuka suke yi sosai ganin ya kai su gidansu. Hannun Raihan ya ja tare da ɗaukar Musaddik suka shiga ciki. A falo ya zaunar da su kan kujera. Zama ya yi yana kallonsu, cikin dana-sani ganin yadda suka takure suna kuka. Kicin ya shiga ya ɗauko musu abinci ya kawo gabansu, amma babu wanda ya yi shiru sai kuka da suka ƙara fashewa da shi. Ta sa su ya yi, yana kallon suna kuka shi ma yana jin kamar zai yi kukan. A kwanakin Ahmad yake ɗauki su saboda yana zama gida, amma a ranar sun fita da ogansa kan wani business ɗin za su fara, har lokaci ya yi bai dawo ba. Ganin haka ya kira numbar mai mashin da wani lokacin yake ɗauku su. Bayan ya je ya neme su, amma ba sa nan don haka ya kira wayar Ahmad. Mamaki ne ya kama shi domin sun yi waya da Nasreen har yake gaya mata, ba zai samu zuwa ba, amma ya tura mai mashin. "Ok to na gode." Ya ce tare da kashe wayar ya fara neman layinta. "Hello Ya Ahmad." Ta ce masa bayan ta amsa sallama. "Yaran nan suka wajenki ne?" Tambayar da ya yi mata ya sanya ta miƙe a razane. "A'a ba su dawo ba ne?" "No, kin san ba ni a gida mai mashin ya ce a ɗauke su." "To ko Mama ta tura Zainab." "May be bari na kira ta." "To," Ta ce masa xuciyarta na bugu. Kasa jiran shi ta y,i ya kira ta sai ta kira shi a lokacin yana waya. Sai da ya gama sannan ya kira ta. "Nasreen yaran nan fa ba su a gida, kuma na kira Principal yake gaya mini Faruk ya ɗauki y....." "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Saboda me zai ɗaukar mini yara? Don ya ƙuntata mini ko? Ni dama sai da na ji a jikina kamar haka za iya faruwa." Ta furta cikin muryar kuka. "Please ki na su dole ya dawo da su ai." "Wallahi kuwa domin ko kotu sai na kai shi. Sam ba zan iya ba shi yarana ba, ina son su tashi cikin tarbiyya." Ta ce sai kuma kuka. "Ki natsu yanzu yanzu zan dawo gida." Ya ce mata tare da kashe wayar, bayan ya rarrasheta ganin yadda ta tayar da hankalinta. Nasreen uwar son yara. Yana kashe wayar ta miƙe saboda ɓacin rai ji take kamar ta rufe Faruk da duka. Ta fito za ta je gurin Damir da shi ma ya fito zai fita. Saura kaɗan su ci karo saboda ba ta ganin gabanta. Da sauri ya kai hannu zai riƙeta ganin ta yi taga-taga za ta faɗi, saboda takalminta mai tudu daya goce. "Please take easy Nasreen." Ya furta cikin tsananin tashin hankali. Ganin zai riƙe ta sai ta ja baya har ta gwammce ta faɗi, sai kuma Allah ya ba ta sa'a ta tsaya. "Are you ok?" Ya tambaye ta cikin damuwa. "Yes." Ta ce masa tana ƙoƙarin saita natsuwarta. Kunya sosai yadda ya rikice ya ji, sai ya fara shafa kansa zai wuce, ba tare da ya iya ɗaga idanunsa ya kalle ta ba. "Ya Damir." Ta kira sunanshi cikin rashin dubara. Cak ya tsaya ba tare da ya juya ba. Ganin ya tsaya sai ta ce,"Ina son zan je gida. Please akwai abin da ya taso." Da sauri ya juyo yana kallonta, ganin yadda take ba a cikin natsuwarta ba. "Lafiya?" Ya tsinci kanshi da tambayarta. Har ta buɗe baki za ta ce babu komai, sai kuma damuwar da take ciki, ta gwammace gaya masa, domin ya ƙyaleta ta tafi. "Faruk ne ya je makaranta ya ɗauke su Raihan." Ta ƙarashe maganar tare da zubowar hawaye a fuskarta. Tsoronta kar ya gudu da yaran. Jin ta ambaci Faruk ya sanya kishi ya lulluɓe shi, amma abin daya yi da kuma yadda hankalinta ya tashi sai ya kauda batun kishi. "Ok, sai kin dawo." Ya ce mata ba tare da ya juyo ba. Kafin ya gama maganar har ta juya cikin sassarfa. Ganin yadda ta tashi hankalinta sai ya kasa komawa ciki ya fito zuwa ƙasa. Tana ƙoƙarin tayar da motarta cikin damuwa ya ƙaraso. Ba ta lura da shi ba har sai da ya kira sunanta, ya tsaya saitin da take. "kashe motar." Ya ce mata ba tare daya haɗa idanu da ita ba. Har za ta yi musu, sai ta fasa tana jin kamar ta yi mishi kuka. Ga mamaki sai ta ga ya ce,"Lemme drive you a halin da kike ciki ba za ki iya tuƙi ba." "I can dri..." Maganar ta katse mata, sakamakon idanunsa da ya watsa mata. Kasa magana ta yi, sai ta fito kawai, saboda yadda idanunsa suka kashe mata jiki. Motarsa ya nufa, bata da mafita ta bishi domin buƙatar ta kawai ta ƙwato yaranta a hannunsa. Gaba ya shiga ta zauna a mai zaman baza. Cikin gwanancewa ya fara tuƙin suka bar harabar kampanin. Fitarsu ya janyo cece-kuce a cikin ma'aikatan, wanda ɗaga hankalin Ingawa har ya kasa jurewa. Kiran waya ya shiga yi, amma ba ta ɗaga ba, daga bisani sai ta kashe wayar. Hakan ya saya shi cikin damuwa ƙwarai, yana ta safa da marwa a ofishinsa, tare da tunanin dalilin da yasa ya suka fita a tare. A mota tuƙi yake yi da sauri, ganin yadda ta tayar da hankalinta, domin har hawaye ya ga tana sharewa. Ganin haka sai ya tsaya da motar ya jingina yana kallonta."Please ki bar kuka yaran naki ne dole za su dawo gareki." Yadda yayi maganar da taushin murya, ya sanya ta share hawayen tana kallon gefe sai kuma ta fashe da kuka. Kukanta ya sanya zuciyarsa bugu sosai, da wani tsananin tausayinta ya fitar masa. Yana matuƙar tausayin macen mai saurin kuka, domin kukan shi ne hanyar da zai nuna tana cikin damuwa, sosai yake ɗaukar hawayen da matuƙar daraja, kuma zuciyarsa tana sarewa duk lokacin da ya ga mace na kuka don wani damuwa. Tsoro ne ya kamata yadda ya koma lokaci guda. "Na daina." Ta ce masa kamar wata ƙaramar yarinya, tare da sanya gefen gyalenta ta share hawayen. "Good!" Ya ce sannan suka fara tafiya. Tana mushi kwatance ya kaita har kofar gida."Go and take your kids they are your belongings and you need to take care of them." "Thank you for you concerned." Ya ce masa tare da fara tafiya zuwa cikin gida. Yana gurin har ta buɗe ƙofar ta shiga sannan ya yi murmushi yana kallonta.Murmushi ya yi ganin yadda ta rikice yasan cewa in har ya aure ta ta haifa masa yara, za su samu kulawa sosai, ganin tana matuƙar son yara. Jan motar ya yi cikin farinciki ya koma kampanin. Da ya koma sai ya tsinci kansa da kasa yin aiki yana son ya ji ko ta karɓo su, amma sai ya daure zuwa anjima sannan ya kira. Nasreen tana shiga cikin gidan tagan su a falo suna tsaye cirko-cirko."Saboda me zai ɗauke mini yara? Wallahi bai isa ba, saboda ko zan ƙarar da komai nawa sai na ƙwatonsu." Ta ce daidai lokacin da Ahmad ya kamata ya zaunar da ita. "Ki yi haƙuri na je makarantar sun ba ni numbarsa. Na kira shi tun da ya ji muryarta ya kashe kuma abin damuwa suna ta kuka." "Kin ji ko Mama, na san cewa ba zasu ƙaunace sa ba, mutumin da ya wulaƙanta su?" Ta ce tare da sakin kuka sai kuma ta ce,"Damuwa ta Musaddik ya ba shi da lafiya, har nayi tunanin ko ba zai je makarantar ba, amma sai na bashi magani ya tafi." "Za su dawo in sha Allahu yanzu ki karɓu numbarsa ki kira shi." "To,"Ta ce tare da share hawaye. Tana kiransa ya ɗaga cikin fushi ta miƙe ta ce,"Faruk ka dawo mini da yarana saboda baka da alaƙa da su." Ta ƙarashe maganar cikin fushi jin kukan Musaddik. "Yaranmu dai don Allah ki dawo mu riƙe su, wallahi na yi nadama ina son ki Nasreen." "Yaudarar kanka kake yi, saboda na san taɓa ƙaunarka ba." "To shikenan, tun da wannan ɗan iska yana hure miki kunne sa ki je ki haifi wasu da shi, amma matuƙar ba za ki dawo gare ni ba na ƙwace yarana." Yana gama faɗin haka ya kashe wayar. "Farouk ka dawo da su ko yanzu na kai ƙararka hukuma." Kallon wayar tayi ganin ya kashe sai kawai ta fashe da kuka. Rarrashinta suke yi, amma kamar suna tunzura ta. Su kansu hankalinsu a tashe yake domin sun shaƙu da yaran sosai. "Ina ga ba za a kira babanku ba?" Mama ta yi musu tambayar tana kallonsu, ganin har yanzu ƙarfe biyar bai kira ba, ballantana su yi tunanin za su dawo. "Baba ƙara rikita lamarin kawai zai yi. Mu bari ya dawo da su ta lalama, dai mu canza musu makaranta kawai." "Ni zan je gidansa, domin ba zan iya kwana babu su ba." Ta furta tare da miƙewa. Ahmad ya koma da ita ta zauna."Don Allah ki yi haƙuri dole ya dawo da su, saboda babu shaƙuwa a tsakaninsu ina tabbata miki yanzu haka sun addabe shi da kuka." Ya ce mata cikin tsigar rarrashi. Zaunawa ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ganin har magariba Isha ta yi sai kawai ta sanya musu kuka. Su kansu duk sun damu sosai. Tana zaune kiran Marwana ya shigo. Sosai ta ba ta baki sannan ta kwantar mata da hankalin cewar za su dawo.. Ta shi ta yi zuwa ɗaki, ta yi sallah sannan ta zauna a daddumar tana addu'a. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 37 Ta shi ta yi zuwa ɗaki, ta yi sallah sannan ta zauna a daddumar tana addu'a. Damir da ya koma gida hankalinsa ya kasa kwanciya. Wayarsa ya ɗauko ya kira ta, duk da Marwana ta gaya mishi har magariba bai dawo da su ba. Tana zaune kan daddumar kiransa ya shigo. Kamar baza ta ɗauka ba, sai kuma ta tuna mutuncin da yayi mata, domin halin da take ciki ya shanye mamakinta. Wai yau ita Damir ya damu da halin da take ciki har ya kawo ta gida? Ɗaukar wayar ta yi, tare da yin sallama da muryar da ta bayyana alamun anci kuka. Ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce,"Nasreen still crying?" Ya yi mata tambayar cikin damuwa. "Na daina." Ta ce masa tana share hawaye. "No you are still crying muryarki ta bayyana haka. Please ki kwantar da hankalinki. In har bai dawo dasu da safe ba, gobe mu shigar da ƙara." Da sauri ta ce,"To," Jin ya karfafa ta a je kotu saɓanin su Mama. Kwantar mata da hankali ya rinƙa yi cikin sanyin murya har ta yi mamakin dama haka yake. Ba don ya so ba, ya kashe wayar ya kwanta cikin tunanin halin da take ciki. Farouk ya yi kwanar wahala, saboda yadda ya ga rana haka ya ga dare. Yaran sun ƙi bacci sai kuka ga jikin Musaddik cikin dare ya rikice su da ya kai shi asibiti. Ko da ya dawo kin shan maganin ya yi sai da ƙyar. Kuka suke yi sosai ga shi sun ƙi cin abinci. Washegari da sassafe, gari bai gama washewa ba ya kwashi yaran gidan Asiya. Ta idar da sallah kenan ya yi kiranta don a buɗe basa gidan. Saboda tunanin abin da ya kawo shi cikin sauri ta buɗe masa da kanta. Ganinsa da yaran, sai mamaki ya kamata ta yi turus tana kallonsa. "Yanzu Faruk duk kashedin da na yi maka sai da ka ɗauko su? Kasan yadda Nasreen take da masifar son yara tsanarka za ta yi?" "To ya kike son na yi Anty Asiya? Nasreen ta ƙi saurara, kuma wallahi ba zan iya rayuwa babu ita ba." Ya ƙarashe maganar hawaye yana zuba a ƙuncinsa. "Ka yi sake Faruk ka cuci kanka, amma dole ka mayar da yaran nan. Ka kwantar da kanka, sannan ka zama tamkar maraya ƙila ta dawo gidanka." Shiru ya yi yana tunani, ganin haka ta yi masa dubara har ya aminta zai mayar da su. Miƙewa ya yi tamkar marayan zaki ya fita. Kallon tausayi ta bi shi dashi, domin ta san ihu yake bayan hari. Nasreen ta riga ta yi masa nisa." Daga gidan ƙofar gidan su Nasreen ya je, saboda tsoron kar su yi masa rashin mutunci, musamman Baba yafi tsoronsa, sai ya tura yaran ciki, bayan ya tura mata kalamai na ban haƙuri da ƙauna. Rungume su ta yi, tana farinciki sosai. Dukanninsu sun yi murnar dawo da su da ya yi. "A canza musu makaranta kawai, saboda duk ranar da ya ji za ki yi aure zai aikata abin da ya fi haka." Mama ta ce tana shafa kan Musaddik. "Hakan za a yi Mama, zan duba makaranta sai a canza musu." Ahmad ya faɗa. Saboda murna kasa zuwa aiki ta yi, haƙata wuni da su cikin farin ciki. Ta girka musu wancan ta siyo musu wannan. Marwana ma ba a barta a baya ba, domin da ta tashi zuwa sai da ta yi musu siyayya. A lokacin da Damir ya kira ta sai ta ɗauka cikin farinciki."Ya Damir sun dawo na gode da kulawarka." Ta ce masa saboda yadda ya nuna damuwarsa ta ji daɗi sosai, domin duk wanda zai damu da su Raihan za ta ba shi matsayi. Da ya ji yadda take farincikin sai hankalinsa ya kwanta. Oder kayan ciye-ciye ya yi musu, sannan ya kira Marwana ya sanar mata. Murmushi ta yi, ganin ta gama kauce-kauce ya fara nuna mata soyayya. Lokcin da aka kawo aka aka kira ta sai ta fita ta amso. Sosai ta yi murna kuma ya ƙara samun matsuguni zuciyarta. Da safe da ta shirya za ta je aiki. Wanka ta yi musu suka tafi tare, tun da ba su makaranta ba. Yaran sun yi kyau sosai kamar ka sace su ka gudu. Mota suka shiga sannan suka tafi suna ta murnar za ta je da su. Cikin sa'a a ranar sai Damir ya zo little Marwana. Tana tsaye sai ya sauko zuwa ƙasa zai ɗauko Teddy da Marwana ta manta da shi a mota, kuma take ta yi mishi ƙorafin za ta sakko ta ɗauko, don haka ya kama hannunta suka saukko Ganinta ya cika da mamaki, don bai yi tunanin za ta zo ba. Murmushi ya saki ganin sun haɗa idanu ta yi ƙasa da kanta. Yana son yi mata magana, amma ganin idanun mutanen da suke gurin yana kansu, sai ya buɗe motar ya ɗauko mata Teddy wacce ta saki hannunsa ta ruga gurin su Raihan. Tsayawa ya yi, yana kallon su domin sun burge shi. Ganin haka sai ta kama hannun Marwana suka ƙaraso gurinsu. "Ina kwana." Kasa amsawa ya yi sai kuma ya yi motsi da bakinsa. "Na gode jiya Ya Damir." Murmushi kawai ya yi wuce ba tare da ya ce komai ba. Karo na farko ta bi bayan shi da kallo. Little Marwana tun da ta gansu Raihan ta ƙi zuwa gurin Damir. Tana zaune gurinsu suna ta wasa sosai. Ganin haka sai ya ci gaba da aikinsa. Suna gurin ta dukanninsu sai lokacin da za a yi lunch, sannan little Marwana ta kama hannunsu Musaddik zuwa gurinsa. Yana ganin su, ya yi murmushi tare da sakin aikin da yake yi. "Daddy they are my friends." "You love them kina son ki yi rayuwa da su?" Ya yi mata tambayar yana nuna su. "I want musamman yaron nan Musaddik na rinƙa goya shi." Dariya ya yi tare da jan kumatunta jin abin da ta ce. "Wato kin girma ko?" "Daddy let's go and buy chocolate." Ta ce mishi tana jan hannunsa. "Ok, go."Ya ce tare da kama hannunsa suka fita. Nasreen tana hangen da ta window har suka fice. Sosai take mamakinsa ashe yana da sauƙin kai haka. Ko da yake Marwana tasha gaya mata, mutum ne mai kula da iyalinsa kuma koma ba shi da damuwa. Abin da ya faru ya canza shi zuwa haka. Murmushi ta yi ta koma ta zauna ta ci gaba da aikinta. Tana aikin Ingawa ya shigo."Nasreen ina kids ɗin mu na ɗauka za ki kawo su mu fita?" Kallon sa ta yi jin abin da ya ce. Gabanta ya faɗi, amma sai ta daure ta ce,"Yaya na ga ka yi busy, wannan dalilin ya sa ya ban kawo su ba kar su dame ka." "Ok, where are they now? Saboda am less busy." "Sun fita da oga Damir har da yarinyarsa." Ta daure ta faɗa masa. Jin abin da tace lokaci guda fuskarsa ta canza. Kallonta ya yi cikin zargi."Nasreen akwai abin da kike ɓoye mini ne?" Ya yi mata tambayar cikin ɓacin rai. Kallonsa ta yi ganin yadda ya canza kishi ya rufe masa ido."Babu yarintarsa ce ta..." "Please Nasreen kar ki rufe ni ta baibai, domin kwananan, na ga Damir yana kusanta kansa dake, domin dawo dake sakatariyarsa wannan ma duk shirin sane da. Duk da cewar abubuwan da suka faru a baya ya cancanta ya aurenki, amma ya yi saken da na shigo cikin rayuwarki, don haka sai dai mu fafafa, ba zan iya barin mishi ke ba, saboda ina sonki." Jin abin da yace kanta ya buga kallonsa ta yi cikin damuwa sosai, ganin yadda ya canza yana huci. Tana matuƙar ganin mutuncinsa don sam ba ta son su yi rabuwar babu daɗi. "Don Allah ka fahimce tsakanin.." "In har kina son na fahimce ki, ki amince na tura iyayena gidanku mu zama abu ɗaya. Na yi miki alƙawarin zan ba ki kulawa, kuma zan kula da yaranki tamkar ni na haife su. Idanu ta zura masa ta kasa ce masa komai, domin ko ta yi masa bayani ba zai gane ba. Damir da suka fita, kai tsaye makarantar su little Marwana yaje da su, ya ba da sunansa kan gobe za su zo a yi musu rijista. Take ya biya maƙudan kuɗi domin makarantar mai tsada ce sosai, don tafi ta su. Uniform da textboks aka ba shi. Gobe in suka zo sai ayi musu rigister, tun da har interview an yi musu. Daga makarantar sai suka wuce shagon siyen chakulet ya yi musu siyayyya sosai, sannan ya kaisu gurin wasa yara. Sosai suka yi wasa yana musu bidiyo. Ganin lokaci zai ƙure sai ya sanya su a mota ya kaisu gida. Mommy tana zaune ta ji little Marwana tana faɗin,"Mommy, Anty Mawarna come and see my friends." Ta faɗa tana jan hannun Raihann. Shigowa ya yi yana dariya ganin abin da take yi. Mommy jin kiran da sauri ta tashi suka haɗu a falo. Marwana ma da take kwance a ɗakinta tasowa ta yi. Ganin su Raihann, da sauri ta ƙarasa gurinsu tana mamaki."Raihann ku ne?" Ta ce mata tana kallonsu. "Yaran Nasreen ne ko?" Mommy ta yi tambayar cikin farinciki. "Eh su ne Little Marwana ta sanya na fita da su, saboda kuka ta saka wai abokananta ne." Ya yi maganar cikin basarwa ganin yadda suke farinciki. Wani kallo suka watsa masa suna murmushi. Kallon ya ba shi kunya har ya fara ƙoƙarin hayewa sama. "Marwana ba su abinci don Allah, zan mayar da su lokacin tashi ya kusa." Ya ce mata tare da haye wa sama. Wanka yayi sannan ya canza kaya, saboda Musaddik ya ɓata masa riga da chocolate. Yana saukkowa ya ji little Marwana tana faɗin,"Anty Marwana guess what?" "You know am not good in guessing, just tell me baby." Ta ce tana shafa kanta don ta yi mata wayo. "No until you guess, Anty try." "Daddy buy you a new teddy?" Ta yi mata cinkar da tambaya. "No daddy enrolled my friends in my school." Tsannanin mamaki ya kamata sosai ita da Mommy. "Kai Marwana yaushe kika fara ƙarya?" Mommy ta yi mata tambayar cikin mamaki. "Wallahi da gaske ne ga shi nan yana saukkowa You can ask him." Ta ce tana nuna shi da yatsa. Damir sai ya ji kamar ya koma sama saboda kunya. Karo na farko da ya ji suruntunta ya yi yawa. "Wai haka Damir?" Mommy ta tambaya. Kansa ya shafa, cikin tsannanin kunya yana hararar little Marwana. Daurewa ya yi, domin yana jin lokaci ya yi da zai daina ɓoye-ɓoye ya samu muradinsa. "Ganin yadda ta tashi hankalinta, sai na yi tunani na canza musu makaranta, sannan kuma na gaya musu iya waɗanda za su rinƙa ɗaukar su." "Ai ko ka yi abin kirki Allah ya yi albarka." "Amin." Shi da Marwana suke amsa. Sannan ya fita. "Mommy Ya Damir da gaske yake yi?" Ta ce cikin zallar murna. "Ya gama kumbce-kubcen sa, da ya tsaya kallon ruwa kwaɗo ya yi masa ƙafa." Abincin ta basu sannan suka fito da su tafi. Sosai ya ji kunyar yadda suke ta kallon shi. Miƙewa ya yi ganin har lokacin tashi ya yi. "Bari na mayar mata da yaran." Ya ce tare da fara tafiya suka bi shi. Sosai suka yi farinciki, musamman Marwana ashe dama ƙaunarta da take yi za su zamo dangi ɗaya, tun da gashi ita da Ya Ahmad kamar za su cinye juna. Damir kuma ya saukko ya fara nuna mata ƙauna Nasreen tun tana tunanin za su dawo awa ɗaya, har ta cire rai ta fara tunanin yashe za su dawo? Ganin har an yi la'asar lokacin tashi ya yi. Kowa ya fara fita ban da ita, tun tana jiransu ofis har ta fito ta tsaya harabar kampanin. Ingawa saboda kishi bai ce mata komai ba ya tafi. Murmushi ta yi kawai tana kallon motarsa. Kallon agogo ta yi tana mamakin abin da ya sa suka daɗe. Har ta ɗaga wayar za ta kira shi, sai kuma ya ga rashin dacewar haka, kar ya ga ta cika son yara. Marwana ta so ta kira, amma tuna shaƙiyancin da za ta yi mata, sai ta fasa ta ɗan zauna. Wata zuciya ta ba ta shawarar ta koma gida tun da ya san gidansu. Wataƙila ya ga lokacin tashi ya yi ya mayar da su can. Cikin motarta ta shiga hankalinta duk yana gurinsu. Sosai take murmushi saboda ta san cewa tana matuƙar son yara. Ta tayar da motar, har an buɗe mata get sai ta ga motarsa zai shigo. Fasa fita ta yi don ya samu ya shigo da motar. Cikin natsuwa ya shigo da motar, ta fito daga cikin motarta tana tsaye. Da gudu su Raihann suka fito tare da rungumeta."Oyoyo Mommy mun dawo. Daddyn Marwana ya yi yawo damu har ya kaimu mun ga Anty Marwana, kuma kin san me?" Ta ce mata tana kallonta. Ba tare data amsa ba, sai ta fara ƙoƙarin zuwa gurinsa da yake shirin rufe ƙofar."Sannu da dawowa yau ka sha rigimarsu?" A hankali ya ce,"Yauwa," Tare da satan kallonta. "Yaran suna da natsuwa ba su yi wata rigima ba." Ya ce sai ya buɗe bayan mota ya ɗauko musu siyayarsu. Kasa amsa yi tana kallonsa."Ya Damir sanya ka suka yi ka kashe kuɗi? Ke Raihan ba na hana ki cewa a siya muku abu ba?" Ta kuma mai da tambayar gurinta tare da zare mata idanu. "Umma wallahi bamu ce ya siya mana komai ba, ko bindiga da teddy shi ya zaɓar mana. Umma kuma ya sanya mu, makarantar su Marwana kayan makarantar na ciki." Mamaki sosai ta yi, tana kallonsa da ya haɗe hannunsa yana murmushi."Wai haka Ya Damir?" Ta yi masa tambayar cikin rashin dubara. "Eh akwai buƙatar a canza musu makaranta. Na kaisu makarantar da Marwana take yi, sannan na gaya musu iya waɗanda za su rinƙa zuwa ɗaukarsu. Gobe za ki je da komai na su na yi musu rijista, sannan za su ba ki id card in har ba a zo da shi ba, to babu wanda ya isa ya ɗauke su." Hawaye suka wanke mata fuska na farinciki."Na gode Ya Damir dama Ahmad yace zai canza musu, sai kuma ka riga shi. Allah ya saka da alkahiri." "Stop crying please."Ya ce mata tare da ƙara ɗauko mata uniform ɗinsu da textbooks. Cikin sanyin jiki ta kai hannu za ta karɓa. Miƙa mata ya yi yana kallon ta. Garin ta karɓi ledar hannunsu ya haɗu. Da sauri ya janye nasa jin shokin ya kama shi. Itama karɓar lefar ta yi, da sauri saboda yadda wani irin maganaɗisu ya taso mata. "Na gode Allah ya ƙara buɗi." Ba tare da ya amsa ba ya fara tafiya zuwa motarsa. Sosai yaran suka burge shi hannu ya ɗaga musu tare da juyowa da sauri jin suna faɗin,"Daddyn Marwana thanks you bye."Sai ya ji kamar ya aureta yau su zama yaransa. Murmushi sosai yake musu, har suka shiga cikin mota suka tafi. Kallonsa ta yi tare da murmushi, domin a tsakanin jiya da yau ya wanke duk wani haushinsa da take ji. Motarsa ya shiga yana shafa kansa."Daddy ina son ka kai ni gida su na kwana." Zare idanunsa ya yi jin abin da ta ce."Gobe za ku haɗu a makaranta kun zama friends ai." "Yauwa sai na biyu gidansu." "No Marwana in za take zata tai da ke." Shiru ta yi ta ba don ta so ba. A mota tana tuƙa motar tana murmushi sosai ya burge ta, saboda kula da yaran da ya yi. Da ta isa gida, Ya Ahmad yana falo suka faɗa jikinsa suna murna."Ya Ahmad Daddyn Marwana ya sanya mu a new makaranta ba za a ƙara sace mu ba." Mamaki da dariyar abin da suka ce ya kama su. Kallonta ya yi lokacin da take ƙoƙarin zama a gefensa. "Sis wai da gaske?" Ya yi tambayar cikin tsananin mamaki. "Wallahi Ya Ahmad lamarin ya ba ni mamaki sosai, saboda ba ka ga yadda ya canza ba." "Dama ribar haƙuri kenan, domin duk tsanar da mutum yake maka da cutarwa, in ka yi haƙuri sai komai ya zama tarihi. In kika duba yau Damir ya saki ya cire tsanarki a cikin ransa, shi kuma Faruk Allah ya saka miki." "Haka ne Mama wallahi na ga ribar haƙuri." "Shi ya sa ake son mutum, ya zamo mai haƙuri da kawaici wani lokacin." Ahmad ya ce yana kallonta. "Allah ya ƙara mana haƙuri." "Amin,"Suka amsa gabakiɗaya. Cikin dare Nasreen ta kasa bacci, murmushin da ya yi mata ta kasa mantawa. Idanunta fuskarshi take zana mata. Sosai take mamakin kanta yadda ta kasa manta haɗuwarsu ta yau. Rungume filo ta yi cikin tsanannin farinciki, ganin mutum da take ji ba ta kyauta masa a rayuwarsa ba ya daina damuwa har ya fara kula ta. Wayarta ta janyo ta kunna data don ta samu bacci ya ɗauke ta. Har ta hau TikTok sai kuma ta koma Whatsapp ganin tsaƙon Marwana ya shigo. Abin da ta rubuta ya sanya ta sakin dariya sosai, domin ita kanta ta fara zargin yana sonta, saboda yadda yake zuba mata shanyayyun idanunsa waɗanda suke sanya ta kasala. Ga mamaki sai ta je calls ta duba numbarsa ta yi saving, sannan ta sauka online ɗin. Ba ta jima da sauka ba ta ƙara hawa, saboda har lokacin bacci ya ƙi ɗaukar ta. Tana ƙara duba status sai ta ga ya ɗaura biyido da hutunan su Little Marwana da Raihann, Musaddik ya rubuta my family da stikers na ƙauna. Sosai hakan ya burge ta, don ji ta yi kamar za ta shiɗe, saboda tsabar farinciki har ta kai hannu za ta yi masa reply, sai kuma ta sauka gabakiɗaya online don kar ya ga saƙewarta. Rintse idanunta ta yi, cikin damuwa ganin ta kasa daina tunaninsa, lokaci guda yana son doke Annnur a cikin zuciyarsa, da ma Ingawa a matsayin Ya ta ɗauke shi. Kamar yadda ta kasa bacci, haka shi ma yana cikin kogin tunaninta. Bayan ya ɗaura status ɗin, duk minti sai ya duba ko ta duba so yake ta gani. Yana son ya yi amfani da yaran ya sace zuciyarta, amma sai jikinsa ya yi sanyi ganin ba ta duba ba. Damuwa ya ƙara kama shi ya fara tunanin ƙila ba ta yi saving numbarsa ba. WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 38 Sosai hakan ya burge ta don ji ta yi kamar za ta shiɗe, saboda tsabar farinciki har ta kai hannu za ta yi masa reply, sai kuma ta sauka gabakiɗaya online, don kar ya ga zaƙewarta. Rintse idanunta ta yi, cikin damuwa ganin ta kasa daina tunaninsa, lokaci guda yana son doke Annnur a cikin zuciyarsa, da ma Ingawa a matsayin Ya ta ɗauke shi. Kamar yadda ta kasa bacci, haka shi ma yana cikin kogin tunaninta. Bayan ya ɗaura status ɗin, duk minti sai ya duba ko ta duba so yake ta gani. Yana son ya yi amfani da yaran ya sace zuciyarta, amma sai jikinsa ya yi sanyi ganin ba ta duba ba. Damuwa ya ƙara kama shi, ya fara tunanin ƙila ba ta yi saving numbarsa. Washegari da safe, ta shirya su Raihann suka tafi makaranta. Ƙarfe uku suke tashi daga makarantar, a ranar Damir ya ɗauko su, da yaje ɗaukar Little Marwana. Take away ya yi musu, sannan ya kawo su kafin a tashi. Dukansu a gurinta suka wuni, har sai da lokacin tashi ya yi, sannan ta koma gurinsa suka tafi. Tun da suka shiga makarantar, kusan tsawon sati shi yake ɗauko su yana kawo suna gurinta. Abinci mai daɗi yake siyan musu. A haka shaƙuwa sosai ta ƙullu tsakanin yaran. Ita kanta Nasreen ta saba da Marwana ji take kamar su rayu guri ɗaya. Little Marwana inta koma gida ba ta da magana sai na su. Shi kansa mamaki yake yadda ta shaƙu da su. A ranar Friday da yake suna tashi da wuri. Da ya ɗauko su ya kai su gurinta har lokacin tashi. Kai mishi little Marwana ta yi, amma sai ta noƙe kafaɗa ta ce,"Daddy zan bi Anty Nasreen." Zare idanunsa ya yi ya ce,"Oya let's go home." Hijabinta ta kama tare da riƙe wa sosai."No daddy." Rasa abin da zai ce mata ya yi yana kallon ta. Ganin yadda ta yi, sai Nasreen ta yi dariya ta kalle shi a kunyace. "Abban Marwana, ka bari ta bimu don Allah sai Marwana ta dawo da ita." Yadda ta yi maganar, da sunan da ta kira shi da shi suka sanya shi shiga cikin wani yanayi. Da sauri ya ɗago yana kallonta, wanda ya sanya ta sunkuyar da kanta cikin jin kunya. Shafa suman kansa yi, tare da ƙara watsa mata wani kallo. "Ba za ta takura miki ba?" "Haba babu takura tana da natsuwa." "Ok bye kar ki yadda su sanya miki ciwon kai." Murmushi ta yi tare da kallon sa kawai. "Idan ta takura miki call me na ɗauke ta, don haka in kina son zama be a good girl." "Ok dad." Ta ce masa jin abin da ya ce. Mota ta shiga sannan ta kunna. Tana ƙoƙarin fara tafiya, ta hange shi ta madubi yana ƙoƙarin ƙarasowa inda motarta take. Fasa tafiya ta yi, sai ta rinƙa kallonsa ta madubin, ta ci gaba da kallon sa tana ayyana surarsa. "Please drive safe kina tare da yarana." "I will." Ta ce masa tare da watsa masa kallon da ya birkita kwanyarsa, sannan ta fara tafiya. Yana tsaye har ta fice, sannan ya ja jiki tamkar mara lafiya, domin kallon ya sanya shi kasala. Mota ya shiga tare da kallonsa ta madubi. Kunyar kansa sosai yake ji. Abban Raihan da ta kira shi da shi sosai abin ya burge shi. Sosai yake son sunan, ya yi fatan ta ci gaba da kiran sa da haka. Surarta da fuskartarta, yake tunawa cikin yanayi na kewa. Tamkar mai koyon mota ya ja motar yana cikin nishaɗi, ba tare da jin kunyar ko an gansu tare ba. Da ta koma gida, Mama ta yi mamakin ganin Little Marwana da ta sake ta haye kujerar tana kallon cartoon. Sosai ta ba su mamaki, don ko da aka sako musu abinci ta ci sosai. Zama ta yi a cikin falon tana ta kallon yaran cikin so da ƙauna, ba tare da ta damu da surutun da suka cika falon da shi ba. Daga makaranta Marwana ta wuto gidansu Nasreen ba tare data gaya mata ba, domin zuwan ba na ta bane. Ahmad ta gaya wa ta yi sabon lallli wata 'yar ajinsu ta yi mata ya yi kyau. Ɗauka ta yi ta tura masa, amma sai ya roƙe ta ta zo ya gani. Don a waya bai yi masa ba. Babu musu ta biyo ta gidan. Da sallama ta shigo cikin ɗakin yaran suka sheƙo zuwa gurinta. Turus ta yi ganin Little Marwana. Ganin yadda ta cika da mamaki, sai Nasreen ta ƙaraso tana faɗin,"Kin yi mamakin ganinta ko? Rigima ta sanya wa Ya Damir ya barta muka taho, dama na ce za ki koma da ita. Kin zo kan gaɓa, in kin tashi tafiya sai ki tafi da ita." "No Umma, anan zan kwana." Ta ce za ta yi kuka. Sosai ta ji daɗin sunan da ta sanya mata, har sai da ta shafa kanta. "Kwatar da hankalinki Babanki ya zo ya ɗauke ki ai." Ta ƙarashe maganar tana kallon Nasreen cikin tsigar tsokana. "Ban gane ba wai an yi yamma da kare? Lamarin ke daYa Damir. Are You guys dating?" "Dating kuma? Kawai ya ɗauki ƙaddara ne ya haƙura, kin san kamar yayana na ɗauke shi." "Hmmmmh! Haka ne ni ma babyna ai yayana nake kiransa." "To ni ba iri na ki bane." "Ni kauce na zauna munafukai kawai." Ta ce tare da zama a gefen kujerar da take. "Ko kuma kece munafukar Marwana, da sannu zan gano wanda kike waya da shi." "Ashe za ki bushe kuwa." Ta ce mata tana dariya. Sallamar Ahmad ya katse hirar ta su. Haɗa idanu suka yi sannan suka sakarwa juna murmushi. Ahmad har da kashe mata ido. Nasreen da ta gama gane abin da yake tsakinisu, kallonsu tayi yadda suka wani bone. "Munafukai za ku sani." Ta ce saboda ta fakaice idanun Ahmad ta ɗauki wayarsa, inda ta sha ruwan mamaki ganin chatts ɗinsu na soyayya. "Marwana ina zuwa, bari na kawo miki abin da kike so yau Mama shi ta yi." Ta ce tare da miƙewa da sauri ta fita kafin ta amsa. A ranta tana faɗin,"Munafukai zan kama ku yau." Tana fita Ahmad ya dawo kusa da ita yana sakar mata murmushi."Yauwa baby a nuna mini ƙunshin." Cikin jin kunya ta miƙa masa hannun a gabansa yana kallo."Wow ya yi kyau, amma ita za ta yi miki ranar bikinmu ko?" Kunya sosai ya kamata jin abin da ya ce. Ganin ta rufe idanunta sai ya matsa kusa da kunninta cikin raɗa ya ce,"Please Marwana ki ba ni dama na tura iyayena sonki zai haukatanni." Da sauri ya matsa, yana zare idanu cikin jin kunya ganin Nasreen ta shigo ta kama su a haka. "Allah ya tona asirinku wallahi! Dama za ku iya soyayya ba tare da kun gaya mini ba?" Ta yi musu tambayar cikin zallar mamaki. Kasa cewa komai suka yi sosai suka ji kunya. Ahmad sosa kansa yake yi cikin jin kunya. "Na rantse na ɓata daku saboda ban ɗauka za ku yi mini haka ba. Ni da Mama muna ta tunanin yadda za mu haɗaku soyayya, amma ashe kuna nan kuna soyewa." Kamota ya yi cikin murmushi ya ce,"Sorry 'yar ƙanwar surprised muka so mu yi miki, don ki yi farin ciki sosai." Fisge jikinta ta yi tana harararsa ta ce,"Ban yarda ba, har dake Marwana duk yadda muke da ke?" "Haba Nasreen kin san ba zan yi miki haka ba. Dama yau xan gaya miki." "Na rantse babu abin da za ku gaya mini na yarda, kula yanzu zan gaya wa Mama cewar kuna ta soyayya a gidanta har da riƙe wa Marwana hann.." "Ke ban san sharri yau she kika ga haka?" Ya yi mata tambayar da mamaki. "Ba gani kuma sai na gaya mata." Ta ce tana neman hanyar fita yayin da dariya take subce mata, ganin yadda suka razana. "Ba ni za ku munafunta ba? Sai na yi maganinku." "Zo ki ji 'yar ƙanwata kar ki gaya mata zan canza miki mota." Ya ce cikin sigar rarrashi, yana kallon Marwana da ta ɓata fuska cikin jin kunya za ta yi hawaye. "Bana so ina da kuɗina" Ta ce mishi zata fice. Ganin da gaske yake yi sai suka riga da gudu za su kamata, ita kumata fara gudu zata fita. Tare ƙofar Ahmad ya yi sai kuma ya bita ganin ta yi falo, suka cigaba da zagaye falon har suka kamata. Takura ta yi ta ce,"Mama Ya Ahmad da Marwana ashe so...." Da sauri suka rufe mata baki suna roƙonta. Dariya tayi cikin farin ciki ta rungume su."Ina fatan soyayarku ta ɗora har ku yi aure, Ya Ahmad ka riƙe ta da kyau, domin hakan ne kawai za ka saka mata. Na yi tsananin murnar fara soyayyarmu, dama ni da Mama muna ta tunanin yadda za mu haɗaku, yau sai ta yi matuƙar farinciki." "In Sha Allahu za ki same ni mai adalci ga ƙawarki." Ya ce yana mata kallon ƙauna "Allah ya ba ka iko ta cancanta." "Yanzu an going to be your Anty start calling me anty." Marwana ta faɗa tana dariya. "I will call you Anty Marwana, am so excited you will be my Anty, and a spouse to my brother." Dariya suka kwashe da shi cikin tsananin farinciki. "Saura soyayyar ku da Ya Samir muna fatan ku haɗa kanku kuma." Kunya ta ji ta riga da gudu, zuwa ɗakin Mama ta bar su suna mata dariya. Cikin tsannanin mamaki, ta ƙarasa tare da zama gefenta da take shafa mai."Mama wai kin san Ya Ahmad da Marwana soyayya suke yi?" Mamaki, firgice, da al'ajabi har ma da farinciki ya kamata."Wai kina nufin da gaske?" "Wallahi Mama ashe tun da ya dawo suka fara soyayya." "Alhamdulillah Masha Allah. Ubangiji na gode da ka nuna mini wannan ranar." Ta furta cikin tsannanin farikciki. Marwana saboda kunya, ba ta yi wa Mama sallama ba ta fice gidan da gudu, don ko Little Marwana da za ta tafi da ita ba ta tsaya ba. "Kin ga Anty Marwana ta tafi ba ta ɗauke ki ba." "Umma, ni ba zan bi ta ba ki gaya wa Daddy na dawo nan." Dariya ta yi jin shirmen ta cikin kaunarta. Da daddare bayan sun yi dinner ta yi musu wanka, sannan suka zauna suna kallo, tana kwance tare su. Damir da ya kasa bacci ya kira wayarta. Ganin kiran tsadadden murmushin ya bayyana a fuskar ta. Ɗaga wayar ta yi, tare da kanga ta a kunninta, sannan ta yi sallama cikin sanyi. Jin muryarta ya sakar masa da natsuwa, har sai da ya saki ajiyar zuciya. Rintse idanunta ta yi tana jin wani iri domin saukar nishinsa kawai kawai yana kai mata tsaƙo. "Little Marwana na ɗauka za ta dawo da Marwana?" Ya yi mata tamabayar jin sun yi shiru bayan sallama. "Na yi da ita amma ta ƙi zuwa." "Ko na zo na ɗauke ta ne?" Ya ce mata yana addu'ar amincewar domin so yake ya ganta. "Ok ba matsala." Ta ce masa. Da sauri ya kashe wayar sannan ya ɗauki makullin motarsa ya fice. A hankali ya ke tuƙin cikin farinciki har ya isa ƙofar gidan. Kiranta ya yi sannan ya gaya mata ya iso. Kama hannun Little Marwana ta yi, sauran yaran suka biyo ta. Yana zaune a cikin motar ta karaso da sallama. Ƙamshin turarenta ya bugi hancinsa. Lumshe idanunsa ya yi yana shaƙa. "Sannu da zuwa." "Yauwa." Ya amsa yana kallon yaran. "Daddy ni fa babu inda zanje, ina son na zauna a gidan nan, ko kuma su koma gidanmu." Dariya suka yi yana kallon ta. Hannunta ya kama ganin ba sa hira."Mu je gida." Ga mamakinsa sai ta saka mishi kuka. Kan dole ya saki hannunta yana kallonta. Nasreen sai ta ji babu daɗi, sam ba ta son ya ga kamar za ta rabu su, musamman yadda yake sonta sosai. "Ki je gida gobe sai ki dawo." "Ok, zan je amma Daddy ya fita damu har da ke Umma." Maganar da ta yi ya sanya su zaro idanu."Ke! Wai yaushe kika iya zance ne?" "Please daddy." Ta ce mishi a maimakon ta amsa. "Ki tafi gobe ni zan fita dake, na siya miki teddy." Ta ce tana shafa kanta. "In babu damuwa let's go akwai wani guri babu nisa sai mu je." Ya ce yana kallon agogonsa. Kallonsa ta yi kuma ta kasa musa mishi. Buɗe bayan motar ta sanya yaran ya tabbatar masa da za ta je. Sun shiga motar yaran kawai suke murna da hayaniya, amma sun yi shiru babu mai magana. Damir ne kawai ya ke waiwaya wa yana kallonta wani lokacin, yayin da hankalinta yake kan titi. Sam ba ya son yadda suka kasa sakewa da juna. So yake su saba suna hira da wasa da dariya tsakaninsu, domin shi mutum ne wanda yake hira sosai, musamman ga abin da yake so. Da suka isa parking ya yi sannan suka fito. Shi ya zagaya da yaran tana bin shi a baya, har suka gama soyayyar, sannan ya dawo da su gida . "Umma, sai da safe." Little Marwana ta ce tana sha ice cream ɗin ta. Kalmar da ta ce mata, ya sanya shi waigawa yana kallonta don ya ga reaction ɗin ta. "Sai da safe babyna." Ta ce mata tana ɗaya mata hannu fuskarta ɗauke da murmushi. Harɗe hannunsa ya yi yana kallonta, sosai ji yake kamar ya rungume ta. Wani irin ƙaunarta yake ƙara kama shi duk lokacin da suka haɗa ido. "Nasreen." Ya ji ya furta sunanta ba tare da ya shirya hakan ba. A hankali ta kalle shi tare da motsi da bakinta ta amsa. "Wane hanya kike tunanin za mu bi don ki zama kusanta yaran tun da sun saba da juna?" Yadda ya yi maganar da muryar da ya yi amfani da ita ya sa ta kauda fuskarta ta rasa amsar da za ta na shi. Ganin haka ya gyara tsayuwarsa har zuwa lokacin ita yake kallo. "Ina nufin duk hanyar da kike ganin ya kamata kuma zai kusanta su. Bani da matsala zan amince domin farinciki yaran. Ɗago kanta da sauri ta yi, tana kallon da wato so yake ya yi mata wayo ita ta furta tana son shi kenan. Har yanzu akwai sauran girman kai shi ne zai biyo mata ta wannan hanyar. Tuni ta gane wayonsa, don haka ta lalle shi ba tare da ta ce komai ba. "Zan ba ki lokaci ki yi tunani, any time kika dama gaya mini, ni kuma na amince da duk shawarar da kika kawo." kunya ta kamata ganin idanunsa kawai sun gaya mata tsaƙon zuciyarsa, amma ya gaza furta mata. Hannun yaranta kama."Sai da safe." "Ok bye, good night." Ya ce mata yana kallon ta. Juyawa ta yi ta fara tafiya, sannan ta shige cikin gida. Murmushi ya saki, tare da shafa suman kasa yana mamakin kansa. So yake ya yi mata wayo ta fara furta abin da yake zuciyarta, ganin yadda ta kamu da sonsa. Cikin nishaɗi suke tafiya har da Marwana dake ta ba shi labarinsu. Nasreen da ta shiga cikin gidan, sai da ta tsaya tare da dafe zuciyarta."Da gaske Marwana take Ya Damir sona yake yi." Ta furta cikin tsananin farin ciki, tana tunanin wani irin soyayya za ta samu in suka yi aure. "Aiko an zamo baiwa a gareka matuƙar zan samu farinciki, zan saka maka da da jinin da ka ba ni ya zama sanadin matarka." Ta furta a fili sannan ta shiga cikin gida. Tun daga ranar, ta fara jin kunyarsa take kasa haɗa ido da shi. Ko muryarshi ta ji sai ta rasa sukuninta. A ranar talata suna zaune za yi meeting. Hankalin Nasreen a tashe yake, saboda ita ya sanya za ta yi bayanin sabon tsarin da aka kawo. Cikin natsuwata fito ta amshi mic ɗin. Bayani ta fara muryarta na rawa ganin yadda ya kasheta da ido. Da ƙyar take bayanin domin so take ta fita hayyacinta. Ganin haka sai ya miƙe ya fice yana murmushi sosai. A yadda ta canza kwanakin take rikicewar, ya san cewar duk cikin waɗanda suke sonta shi ne gwarzon. Yana fita ta saki ajiyar zuciya, tare da satan kallon hanyar da ya bi, sannan ta fara bayani cikin natsuwa da burgewa. Lamarin da ya faru da kuma ganinsu tare, da yadda yake farinciki ya tabbatar musu da gulman da suke yi na tunanin soyayya suke yi. Wasu sun yi mata murna sosai, domin samun miji kamarsa ba ƙaramin abin farin ciki bane. Kowa ya san yadda ya gudanar darauwarsa da matarsa. Soyayya ya ke yi da ita ba tare ba tare daya ji shakkar kowa ba. Hatta kallon da yake mata daban ne. Ko kampani ya zo da ita shi yake buɗe mata mota kuma ya rufe. Damir yana girmama mace sosai ya ɗauki mace a matsayi mai girma. Idan yana son abu sam ba ya iya ɓoyewa, domin ko kallon da zai yi mata ya bambanta da sauran na mutane, wannan dalilin ya sanya aka gano soyayarsu da wuri tun kafin ta yi nisa, saboda idan ya yi mata kallon sai ta rikice ta ji kamar za ta bar gurin. Ita da Faruk kallon da yake yi wa mutane a waje ya fi na ta mutunci, amma sai yanzu kuma ta samu wanda zai kalle ta da daraja kuma yana aika tsaƙo a zuciyarta WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 39 Duk da bai furta mata soyayya ba, amma ta haukace ta xuxuce a kansa. Ita kanta san tana son shi sosai, domin ya goge fadar kowa. Hatta Annur ba ta yin sa, saboda shi kansa ya gane hakan. Ingawa kuwa fushi sosai ya ɗauka da ita, duk yadda ta so ta fahimtar da shi ta kasa, domin ta fahimci da gaske yake sonta. Fushi sosai yake yi da ita. Yanzu haka sun tashi daga meeting ɗin ta fito ita da Hajar da Khausar. "Anty Nasreen ashe soyayya kuke yi da Ya Damir?" Tambayar ya sanya ta gwalalo ido ta ce,"Ni?" "Don Allah stop pretending, ki yi kamar ba ki sani ba, ko mahaukaci ya kalle ku ya san soyayya kuke yi." Za ta ba wa Khausar amsa, sai ta kasa ganin Ingawa ya nufo su fuskarsa babu rahma. "Ina taya ki murna sosai domin kin yi dace Nasreen, ba ni cikin masu miki baƙinciki Allah ya baku zaman lafiya." Khausar ta furta tana kallonta. Kasa amsa ta yi, ta sauke numfashi daidai lokacin da ya ƙaraso."Ina son magana dake." Ya furta tare da matsawa gefe yana jiranta. Kallonsa ta yi su kuma ta kalli su, Hajar da suka yi mata alama ta je. Bayan ta fara tafiya sai Khausar ta ce,"Ihu yake bayan hari. Irin su Ya Damir a guri sai ya ce dole sai ya soyayya? In dai ba so yake ya rasa aikinsa ba, ya kamata ya yi backup." "Wallahi kuwa domin ina ganin irin mijin indiya mai zan yi da na Nigeria." Dariya suka kwashe da shi sannan suka fara tafiya. "Nasreen mai ya sa za ki ɓoye mini gaskiya? Shin abin da idanuna suka gani a ɗakin taro gaskiya ne?" Ya yi mata tambayar cikin tsananin tashin hankali. "Ya Ingawa, har yanzu ba soyayya muke yi kuma wallahi bai furta mini ba." "Zan iya rantsuwa da Kur'ani, kuna son junanku ko da ace ba ku furtawa juna ba." Shiru ta yi, ta kasa ce mishi komai ba."Nasreen ina sonki wallahi ina masifar sonki. Kar ki kalle ni a matsayin mai son kansa da na kasa haƙura, na bar masa domin ya cancanta ya aure ki. Don Allah ki aure ni wallahi za ba ki farinciki sosai." Yana wannan maganar Damir ya zo zai wuce. Ganin haka sai ya ƙara murya yana faɗin kalamai na soyayya. Ransa ya ɓace jin abin da yake cewa. "Ke Nasreen mu je ina son ganinki." Ya furta cikin ɓacin rai tare da tsayawa ba tare da ya tafi ba, yana yi masa mugun kallo sosai. Kishi ɗauke a idanunsu. Ganin haka ya sanya ta kalle su, sai ta fara tafiya da sauri ofishinsa. Sai da ta wuce ya yi masa kallon gargaɗi ya wuce yana huci. Tsayawa ta yi a ofishin na sa cikin damuwa. Sosai take tausayin sa domin ta gane da gaske yake sonta. A birkice ya shigo idanunsa sun canza sosai. Tsanannin kishinta ya rufe masa ido. Sosai yake jin haushinta, domin abin da yake mata ya kamata ta daina kula kowa. Ko da ace ba gaya mata yana sonta ba, ya kamata ta gane mahaukaci ne a kan sonta. Ganin yadda ya shigo yana numfarfashi, ya sanya ta ɗan razana tana matsawa, ganin yana matsota. "Mai ya sa za ki zaɓi ki rinƙa hurting ɗina? Why ko kina nufin ba ki san halin da nake ciki ba?" Ya yi mata tambayar, lokacin da ya tsaya kusa da ita ta tamkar zai rungumeta. Tsoro ya kamata sosai jikinta ya kama rawa, musamman ganin yadda ya ke huci. Da kusantarsu ta yi yawa, domin suna jin bugun numfashin juna. Kasa magana ta yi, saboda yadda ƙamshin turarensa ya cika hancinta. "Ya Damir." "Kina son kice mini baki gane abin da yake zuciyata bane?" Ya katseta da wannan tambayar. Ganin ba ta ce komai ba sai ya fara faɗin." Na yi tunanin saboda abin da ya faru tsakaninmu nake jin haushi ina ganki da wani, amma na gane tsananin kaunar da na ke miki. Ya sanya na ke jin kishin haka. In har kika ce za ki rinƙa kula su, ya za ki yi da ni da soyayyarki ta mayar da ni mahaukaci?" Zare idanunta ta yi, ganin yadda ya cire girman kai yana ta sakin batun soyayya. "Wallahi ina sonki na yi tunanin zan iya cikawa Batula alƙawarin, amma sai na gane zan iya hakanne kawai idan kina gidan mijinki. Tun ranar da aka sanya miki jinina in na tuna jinina yana yawo a jininki, sannan kina auren wani ji na ke kamar zan yi hauka. Ina son ki Nasreen kallon farko asibiti na ji abu da game dake, amma sai na basar domin matar wani kike. Ki ba ni dama na auren ki. Na nuna miki bambanci a tsakanina da WASU MAZAN domin na bambanta da su. Zan shayar dake kalar soyayyata. Zan mayar dake tauraruwa kuma zinariya a cikin mata. Ina buƙatar mace a rayuwata. Macen ma ke Nasreen zan canza duniyarki." Yadda lokaci guda ya canza, ya dawo mata mutumin da bata sani ba,sai ta tsorata ta duƙa kasa don ta samu gudu ta tsakon hannunsa, amma sai ya duka shima ya ƙara kusancinsu. "I dore You Nasreen! Will you marry me?" Tambayar da ya yi mata, sai da ta ji kamar duniya za ta faɗo mata. Yau ita ce Damir yake roƙonta ta aure shi. Tsaddaden mutum ɗan gayu kamar sa. Yau shi ne a duƙe a gabanta cikin yanayi na shauki yana gaya mata ta aure shi. Rayuwa ta canza mata haƙika ta ba ta zaɓi mai kyawu. Tana cikin wannan tunanin sai ta ji ya kama hannunta. Da sauri ta kalle shi cikin tsananin razana. Ba tare da ya kula da furgicinta ba ya ce,"Wannan zoben a ranar da zan auri batula na siya mata, da shi na tambaye ta in tana sona. In har kina sona ki amince na sanya miki a yatsunki." Ya ƙarashe maganar yana ƙoƙarin sanya mata. Ta kasa cewa komai sai ta kalle shi cikin mamaki. Yana shirin zura mata aka turo ƙofa. Da sauri ta ture shi tare da janye hannunta. Muhsin da ya shigo da sallama, sai ya yi dana sani ganin lamarin da yake faruwa. Cikin tsananin jin kunya ya koma yana faɗin,"Subuhanallahi! Am so sorry." Ya juya zai fita. Kafin ya fice Nasreen da take jin kamar za ta nitse saboda kunya ta yi waje. "Ya Damir don Allah ka..." "Is ok, karka damu." Ya ce cikin jin kunya yana shafa kansa tare da jan tsaki. Ganin yadda ya yi sai ya koma cikin takaici, domin shi kansa ya ji haushin ɓata musu show da ya yi. Sai kuma ya fara dariya ganin yadda ya yi mata rumfa."Hummmm su yaya baban soyayya tun kafin auren har an fara wannan." Nasreen kuwa, da ƙyar ta samu ta kai kanta zuwa ofis ɗin ta. Tana shiga ta sanya makulli tare da jingina da ƙofar tana ganin abin da ya faru kamar a mafarki. Ƙamshin jikinsa da take ji a kayanta ya tabbatar mata da ba mafarki take yi ba. Mamaki sosai take yi, domin furta mata yana sonta ya zaman mata bazata. Zama ta yi kan kujerar, tare da rintse idanunta tana son tuna lamarin da ya faru. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta saki, sai ta lumshe idanunta ta buɗe. "Ashe haka ya ke. Dama akwai maza da suka ɗauki mace zinariya? Idan har na ce bana sonsa na yi wa kaina ƙarya, to amma ya zan iya kallon tsabar idanunsa na gaya masa ina sonsa? Yana da sexy eyes da kuma ƙwarjinin sosai. Ya Damir ya haɗu ta ko wace sigar da zai dace a soshi." A zuciyarta take ta wannan tunanin. Da sauri ta koma ƙara duba wa ko ta sanya ɗan makulli, jin kamar ina tahowa ofishinta domin a halin da take ciki ba kowa zai iya gane wa. Ta daɗe a gurin kafin ta saita natsuwarta, har ta samu ta saita natsuwarta. Zama ta yi ta fara aiki zuciyarta cike da shaukin ƙaunarsa. A ranar saboda kunya ka sa fita zuwa cin abinci ta yi, domin ta san zai iya zuwa gurin. Ko da su Hajar da Ingawa suke kiranta, sai ta yi musu ƙaryar azumi take yi. Tana zaune har aka fita break suka dawo. Damir haka shi ma ya wuni sukuku. Yaso ya ji ra'ayinta game da soyayyarshi, domin in har tana son shi ba za a ɗauki lokaci ba, za a yi aurensu. Ya huta da su Ingawa da suke son haukatar da shi. Yana ta dakon ya ga ta fito, amma har aka gama break ba ta fito. Wayarsa ya janyo yana murmushi ya danna layin ta. A ƙalla sai da ta yi ringing sau biyu, sannan ta yi namijin ɗauka tare da sallama. "Na je ɗauko Raihan Zainab ta kaisu gida." "Eh ni ma sun kira ni sun gaya mini." Ta furta mishi maganar cikin sanyi. "Ok," Ya ce don bai yarda ba, ya san cewa ta sanya su ɗauke ta don kar su haɗu. "Ya maganarmu saboda da gaske na yi. A shirye na ke da na aure ki in har za ki amince." Kasa ce masa komai ta yi zuciyarta na bugu tamkar ana buga ganga. A lokacin da aka tashi dai da aka gama tafiya sannan ta fito. Damir kuwa da ya fita sai ya tsaya a waje, domin ya san cewa ba za ta fito ba in har bai tafi ba. Yana ganin ta fito, ta tafi sai ya bi bayanta a hankali sai da suka yi nisa ya fara mata hon. Jikinta ne ya kama rawa ganin motarsa yana binta. Ta rasa yadda za ta yi kan dole ta gangara ta yi parking, ganin haka ya yi parking na shi motar. Kashewa ya yi sannan ya fito yana taku har ya ƙaraso gareta. Da sauri ta ɗauke kanta da suka haɗa idanu. "Nasreen," Ya kira sunanta yana ƙoƙarin haɗa ido da ita."Ki bani amsar tambayar da na yi miki." Ta kasa ce musu komai kuma ta kasa amsa mishi.Ganin haka ya ɗube ta ya ce,"Shurin yana nufin kin amince?" Tambayar da idanunsa da ya kafe ta da su ya sanya ta ƙara jin kunyarsa sosai. Gane da ya yi tana cikin mata sosai masu kunya, sai kawai ya buɗe motar ya fita yana murmushi. Ganin ya tsaya a cikin motar ba tare da ya tafi ba, sai ta gane jira yake ya ga tafiyarta. Murmushi ta yi sannan ta ta fara jan motar. Sai da ya ga ta yi nisa sannan ya tayar da na shi. A ranar babu wanda ya rintsa a tsakaninsu domin saboda abin da ya faru kasa bacci suka yi. Nasreen ta yi tunani har ta ji kanta ya fara ciwo, don haka ta tashi ta ɗauro alwala, ta yi sallah tare da yin istikhara neman zaɓin Allah. Kamar yadda ta yi haka Damir ya raya daren da sallolin, yana fatan ta fara nuna mishi ƙauna. Ba su samu sun rintsa ba, sai da asuba bayan sun yi salla. Da ta tashi da safe, sai ta ji hankalinta ya ƙara kwanciya da shi sosai. Har zumuɗin zuwa aiki ta ji tana yi don ta ganshi. Kamar yadda take cike da ɗokin ganinsa haka shi ma. Kuma cikin sa'a ta zo zata hau sama zai sauka ƙasa, don ya rigata zuwa. "Ina kwana?" Ta ce masa cikin murya mai tashi. "Da fatan kin tashi lafiya gimbiyar mata." Abin da ya ce sai ta haye sama da sauri tana murmushi. Shi ma murmushi ya yi yana waigenta. A cikin kwanakin suka saki makamansu suka kama soyayya. Duk da cewar babu wani shaƙuwa a tsakaninsu, domin ko kiranta ya yi daga gaisuwa za su yi shiru, amma hankalinsa ya kwanta sosai. Kullum cikin tunainta da son ganinta. A lokacin da ta sanar da Marwana ta yi murna sosai. Rungumeta ta yi cikin farinciki."Mun zama ahali ɗaya." Ta ce tana kallonta. Mommy ma hankalinta ya kwanta haka Mama duk sun yi farinciki. "Kai lamarin Ubangiji sai shi. Sai ya haɗa ka da mutumin da baka taɓa tsammani ba." "Haka ne Ahmad shi ya sanya ba a son wulaƙanta mutum. Yai ga shi a dalilin Marwana muna shirin zama dangi ɗaya." "Haka ne Mama na yadda domin a lokcin da na haɗu da ita, ban taɓa tunanin zamu ƙulla alaƙar da zai mayar da mu dangi ba." Cewar Nasreen cikin mamaki. Gabakiɗaya Damir ya susuce mata tamkar ba shi ba. Sam ba ya jin kunyar nuna mata soyayya a gaban kowa, domin kallon ta kawai da yake yi, mutum zai gane akwai soyayya a tsakaninsu. Kusan yawanci shi yake ɗauko su Little Marwana da Raihann makaranta, saboda ya fi samun lokaci, domin Zainab tana makaranta Ahmad gurin kasuwancinsa. Mama ce don haka yake hirar da ita, domin ya fi son ɗauki su kan masu keke ko acaɓa da ba sa gudu sosai. Farouk ya shiga cikin damuwa, ganin babu wanda ya sanya masa hannu kan Nasreen ta dawo gidansa. Da fari gurin Anty Asiya ya je, amma sai ta katse shi ta ce,"Ba zan iya haɗa idanu da iyayen yarinyar nan ba, saboda abin da ka yi ba ka kyauta ba. Har na je na ce musu su yi haƙuri Nasreen ta dawo ɗakinta. Ka samu wata matar ka aura kawai, amma da wuya ta dawo gareka." "Ba zan iya auren ko wace 'ya mace ba, saboda tsoron matan na ke yi. Nasreen kawai na ke so ita ce kawai na ke jin za ta iya jure halina, kuma walllahi na tuna na zan zame mata miji na gari. Ina son na rayu da yarana. Ji na ke yi kamar na kashe kaina, in na tuna Damir yana soyayya da ita." "Ya za ka yi ka riga ka yi sake Faruk, da ma duk wanda bai ji bari ba, ya ji hoho." "Ki bar tuna baya, don ji na ke yi kamar zan yi hauka in ba ta dawo gidana ba." "Ka je ka gwada wataƙila ka dace." Ta ce mishi cikin takaici. Shiru ya yi cikin nadama mata amfani. Ya daɗe zaune yana tunanin yadda zai shawo kanta ta mince, amma sai ya ga babu fuska domin da gaske yake yi. Jiki asanyaye ya miƙe ya fice cikin damuwa. Rakashi da idanunta ta yi har ya fice. Takaici sosai yake ba ta, sai ta ji kamar za ta rufe shi da duka, in ta tuna lokacin da take ta gaya masa ya zuwan wannan ranar, amma ya yi kunnen uwar shegu tare da shafama idanunsa toka. Yanzu wa gari ya waya? Dama duk wanda ya ƙi ji, ba ya ƙi gani ba. Daga gidanta gurin abokansa ya je yana roƙonsu, amma babu wanda ya saurare sa, domin su kansu bai ba su mahimmanci ba, duk yadda suka so ya daina cutar da ita, amma ya ƙi kula su. Haka ya koma jiki a saɓule cikin tsanannin tashin hankali. Da ya koma zama ya yi a falo hawaye sosai yana bin ƙuncinta. A da abin da Rashida ta yi masa kawai yake sa ya sa zubar hawaye, amma a yanzu hawayen rashin matarsa da yaransa yake yi. Miƙewa ya yi yana jin ba zai iya haƙura da ita ba. In har an ƙi taimaka masa zo je da kansa ya zamar mata mahaukaci har sai ta dawo gurbinsa. Ba tare da ya ji gargaɗin da ta yi masa ba ya tafi campany. Can nesa da get ɗin ya yi parking yana jiran ta fito sai ya bita, domin ya san cewa ta hana securities su bar shi shiga. Yana tsaye a gurin, ma'aikatan suka fara fitowa da motocin su suna tafiya. A ranar Nasreen ta zo aiki sai morarta ta lalace. Kiran mai gyara ta yi ya ɗauka. Damir ya sanar mata in an tashi zai kaisu gida. Sun fito tana gidan gaba Damir yana jan motar sai yaran a baya. Tuƙi yake wani lokacin yana waigowa yana watsa mata kallon da yake rikitar da ita. Ba wani hira suke yi ba, domin har yanzu babu shaƙuwa a tsakaninsu, ya rasa yadda zai yi ta sake da shi. Sun fara tafiya kamar ance Faruk ya ɗaya kansa, kawai sai ya hango motar Damir yana tuƙi tana ciki da yaranta. Wani irin kishi ya turniƙe shi har ya kitsa masa matakin da ya kamata ya ɗauka. Da sauri ya shiga cikin motar ya binsu a baya. Sai da suka yi nisa, sannan ya bugi motar ta baya! Sam idanunsa sun rufe ba tare da ya damu da yaransa da suke ciki ba. Salati suka ɗauka jin abin da ya faru. Da sauri Damir ya taka burki hankalinsa na gurin yaran da duka fara ihu. Nasreen ta tsorata sosai domin ta ɗauka hatsari za su yi. Ganin motar ta tsaya dai ta fito da sauri ta zaga ta buɗe su suka fito. Damir ganin babu abin da ya faru sai ya zaga baya don ya ga mahaukacin da yake son kashe su."Amma kai dabba ne k...." Maganar ta maƙale mishi ganin Faruk ya fito yana huci. "Har akwai dabban da ya fika? Mai bin matar wani tun kafin aurenta ya mutu. Har akwai wanda ya kamata a kira dabba kamar ka." Jin muryar Faruk, cikin tsananin fushi sai hankalinta ya tashi. Da sauri ta saki yaran ta ƙarasa gurin motarsa."Kana da hankali kuwa? Ninyar kashe mu ka yi?" Ta yi masa tambayar ciki tsanannin mamakinsa. "Nasreen zan iya abin da yafi haka matuƙar ba za ki dawo gare ni ba." "Ban taɓa sanin mahaukaci ne kai ba sai yau. Farouk har da yaranka a ciki kishi hauka ne?" "Don Allah, ki rabu da wannan mara mutuncin ki dawo gare ni. " Ya furta a maimakon amsar tambayar da ta yi masa. "Wallahi ko maza sun ƙare ba zan zauna da kai ba, domin na gwammace na ƙarashe rayuwata a matsayin bazawara da na koma gidanka." "Au haka kika ce? Saboda wannan ɗan iskan za ki guji uban yayanki?" To bari na nuna miki zallar haukar da kike ce wa na yi." Kawai sai ya ɗauki dutse ya nufi kansu. "Da na rasa ki gara na kashe ki kuma na kashe shi. Na zaɓi na kashe kaina ko kuma a kai ni prison." Kansu ya yi gadan-gadan fuskarsa babu rahma Ganin haka ta ƙwala ƙara ta razana sosai. Ganin abin da yake yi Damir ya shiga tashin hankali. Da sauri ya tureta ya ƙwala masa dutsen iya shi kaɗai, amma cikin sa'a sai bai same shi sosai ba saboda tureta da ya yi suka faɗi. A kansa ya same sa ta gefe nan take jini ya fara zuba. Rintse idanunsa ya yi cikin tsananin tashin hankali, sosai yake jin zafin ciwon. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Don Allah ku kawo mana ɗauki zai yi kisa." Nasreen ta furta cikin ƙaraji ganin babu imani ya ƙara nufe su. Ganin haka yaran suka sanya kuka. "Gara na kashe ku na rama cin ma'anar da kika yi mini. Soyayya kuka ƙulla da aurena kanki." Ya furta yana kumfar baki kamar taɓaɓɓe. Da sauri mutane suka farka da bin da ke faruwa, jin ihunta suka zo suka riƙe Faruk. "Farouk ya haukace kashe mu zai yi." Damir ya ce tare da dafe inda jini yake zuba. "Na shiga uku Ya Damir don Allah ka yi haƙuri." Ta ce ganin jinin yana zuba sosai. Da sauri ta cire ɗankwalinta na rigar atamfa da sanya. Danne masa gurin ta yi ganin yawan jinin da yake zuba. Ganin ya ƙi tsayawa sai ta ɗaure masa gurin cikin tashin hankali. "Kai Mahaukacin ina ne? Za ka ga mata da miji da yaransu ka kai musu farmaki?" Wani ya furta zai kai mishi duka. "Wallahi ba ma'aurata bane, matata ce yake son raba ni da ita, yaran nan gida biyu ni da ita muka haifa. Da aurena a kanta ya ƙalla soyayya da ita." Kallonsu mutane suke yi, cikin mamaki suna son gane gaskiyar zancen. "Kai matarka ka ce?" Suka tambayi Damir da yake cikin damuwa ganin tozarcin da yake musu. "Ba matata ba ce, a.." "Yauwa kun ji, wallahi da aurenta ya rinƙa bibiyarta ya raba ni da ita." Ya faɗa cikin ɗaga murya. "Tur da irin masu kuɗi irin ku, saboda ka ga matarsa tana da kyau shi ne ka yi amfani da kuɗinka ka ɗauke masa ita? Haka al'umma suka lalace babu tsoron Allah. Matarsa har da yara dai ka raba su?" Ya yi masa tambayar cikin kallon ƙaskamci. Jin ihun da yake yi yana kira musu mugun alkaba'i har da hawaye, sai wasu daga cikin mutanen suka yarda, yayin da wasu kuma suke kallon kima da kamalarsa suke tunanin ba zai iya aikatawa ba. Damir duƙar da idanunta ƙasa ya yi, da jini yake ɗiga sama goshinsa. Ji ya yi ya muzanta sosai. Anya Faruk! Ko dai ciwon haukar ya dawo me🙄🙄🙄🙄 WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 40 Damir duƙar da idanunta ƙasa ya yin da jini yake ɗiga sama goshinsa. Ji ya yi ya muzanta sosai. A zuciyarsa yana ganin anya yana da maƙiyi kamar Faruk? Cece-kucen da mutane suke yi, suna la'antarsu ya sanya shi kasa cewa komai. Yana jin kukan Nasreen yana damunsa. "Kawai a miƙa case ɗin nan zuwa gurin 'yan sanda, idan matarsa ce sai su ƙwatar masa ita." Cewar wani dattijo a gurin. "Eh kuma haka ne bari na kira su." Wani ya ƙara cewa, sannan suka ci gaba da maganar lamarin suna tur da halin Damir. Jin abin da suka ce har a ciro waya za a kira su, sai hankali Faruk ya tashi."Don Allah kar ku kai lamarin gurin 'yan sanda, yana da kuɗi sosai zai basu cin hanci. Kawai ku bani matata da yarana na gudu na bar garin da su " "Mu je na yi alƙawarin tsaya maka acan, ɗan'uwana babban ɗan sanda ne." Cewar wani ya riƙe hannunsa. Ganin 'yan sandar sun zo, sai hankalin Fatuk ya tashi. Ya rinƙa magana da ƙarfi yana kumfar baki kar aje gurin 'yan sanda. Ganin sun iso sai Nasreen ta shiga mota ta ɗauko wayarta, numbar Ahmad ta kira. Yana ɗagawa ta fashe masa da kuka. Ahmad da yake zaune a falo yana cin abinci. Jin ta fashe masa da kuka sai ya miƙe cikin tsananin razana. "Lafiya Nasreen hatsari kuka yi ina yaran?" Ya yi mata tambayar hankalinsa a tashe. Kuka ta ci gaba ta kasa ce masa komai. "Please ki natsu ki gaya mini." Ya furta cikin damuwa daidai, lokacin da Mama ta zo ta tsaya cikin tashin hankali. "Farouk ne ya buga mana mota, kuma ya fasawa Ya Damir kai, ya tara mana mutane yana faɗin matarsa ce ni. Zi.." "Farouk ɗin?" Ya yi mata tambayar cikin tashin hankali. Hawaye ta share, tana kallon Damir da yake ƙoƙarin shiga cikin mota. "Eh shi yanzu an tura mu police station." "Innnali wa inna ilahir raju'un! Farouk ɗin yana da hankali kuwa?" Ya furta cikin tsananin mamaki. "Eh shi don Allah ka zo Ya Ahmad. Farouk ya tozartamu ya kira mu da mazinata." "Ya Salam. Ga ni nan zuwa ki tambayi wane police station ne." Ya ce mata tare da kashe wayar cikin tashin hankali. "Wallahi Mama saina wulaƙanta faruk." Ya furta cikin tsananin ɓacin rai. "Mai ya faru?" Gaya mata ya yi cikin ɓacin rai."Faruk ya haukace. Ka saki mace kuma ka koma kana bibiyarta da sharri?" "Ki bari kawai bari na je sai na sanya ɗaure shi." Ya ƙarashe maganar tare da ɗaukar makullin motarsa. "Ahmad kaje da takaddar sakin karya ƙaryata." "Kuma fa haka ne Mama kin kawo shawara ɗauko mini."Ya ƙarashe maganar bayan ya zauna. Shiga ciki ta yi sannan ɗauko masa ya karɓa ya fita bayan ya yi sallama. Bayan ta gama waya da Ahmad, sai ta kira numbar Marwana. Tana kicin tana haɗawa ƙanin Babansu Alhaji Sani da ya zo ganin da Mommy yana jiran Damir ya dawo. A lokacin da kiran ya shigo tana wanke hannunta. Murmushi ta yi ta ɗauki wayar. "Hello..." "Marwana na shiga uku!" Ta furta tare da fashewa da kuka. "Lafiya mai ya faru?" Ta yi tambayar cikin tsananin tashin hankali. "Don Allah ki cewa Ya Muhsin ya zo asibiti, Faruk ne ya fasawa Ya Damir kai ya kuma yi mana ƙazafi. Yanzu za akai shi asibiti, mu kuma za mu je police statio.." "Innalillahi wa inna ilahir raju'u! Farouk yana da hankali kuwa?" Ta furta cikin mamaki. "Ki gaya wa Muhsin ya zo Ya Damir ya ji ciwo sosai. Kuma ya kafe matarsa ce ni alfasha muke aikatawa." "Shikenan daina kuka bari na gaya wa Ya Muhsin." Ta ce tare da kashe wayar. Falo ta shigo jikinta yana rawa ta sanar da su. Mamaki sosai ya kama su. Mommy ta miƙe cikin tsannanin tashin hankali. "Yanzu Damir yana ina?" "Asibiti Nasreen tana police station." "Ikon Allah ka saki mata, kuma ka yi ta bibiyarta?" Mommy ta ce. Muhsin ya miƙe ya ce,"Bari na je." "Ai ni ma dole na je." Cewar Alhaji Sani. Bayan sun fita sai Mommy ta ce,"Marwana mu je asibitin ba zan iya zama ba." Ɗaukar makullin mota ta yi suka bi su. Ahmad ya fara isa police station ɗin. Tana tsaye tana kuka, ganinsa da gudu ta rugo ta faɗa jikin shi. "Ki yi shiru ki daina kuka, wannan shi ne na ƙarshe da zai ƙara shiga rayuwarki." "Ya tozarta mu ya ce mana zina muke yi, tsakanina da Faruk sai dai na barshi da Allah." Ta furta tana share hawaye Hannunta ya kama, suka shiga cikin police station ɗin. Farouk yana ganinsa jikinsa ya kama rawa, musamman ganin yadda fuskarsa ta yi. Kumfar baki yake yi yana borin ƙarya. Anty Asiya da mijinta sai Isma'il suka zo ta gurinsa. A asibiti kuwa, ana dressing ciwon Muhsin da Alhaji Sani. Da sauri suka ƙarasa ganin bandeji a kansa ga kuma jini. "Ya Damir sannu." Ya ce masa cikin damuwa. "Please ka ce su sallame ni, Nasreen tana police station ina so zan je, tana cikin damuwa sosai." "Y kamata a bashi bed rest ya zubar da jini. Ya kamata ya yi two days a asibiti." Cewar likita yana danna saman kansa da ya kumbura. "No ko za a yi admiting ɗina a bari a kashe ces ɗin. Farouk ya tozarta mu ya wulaƙanta mu. Na tsane shi sosai bana son ganinsa." Ya furta cikin tsananin damuwa. "Komai ya zo ƙarshe zan yi muku tsakani. Ya zama da sauƙi tun da an je gurin 'yan sanda." "Please mu je in an gama sai na dawo." "Ya Damir ka bari muje ni da Baba Sani kuma Ahmad yana can." "No mu je ba zan iya zama ba alhalin tana can." Ya furta tare da miƙewa yana rintse idanunsa, jiri yake gani don ya zubar da jini sosai. "Ok mu je in an gama sai na ɗauko motarka." "Ok,"Ya ce sannan suka shiga cikin mota. Da suka isa suna zaune, suna jiran a gama ces ɗin wani sannan a shiga na su. Ganinsa da sauri, tashi ta isa gurinsa hankalinta dama yana gurinsa tana tunanin halin da yake ciki. Ba tare da jin kunya ba, ta ƙara da gurina idanunta yana kanshi. "Ya jikin?" Ta furta muryarta da sanyi. "Am ok Nasreen. Please stop crying." Ya ce mata yana kallonta da idanunsa da suka canza kalla. Kallonsa sosai take yi, cikin tsananin ƙauna saboda ta ɗauka tozarcin da ya yi musu zai sanya ya janye aurenta, amma sai ta ga wani irin sonta ne ya ƙaru ganin kallon da yake mata. Ji ta yi ita ma ta ƙara jin sonsa har ba ta jin kunyar nunawa a gaban kowa. Zama ya yi sai ta zauna a gefensa, ba tare da ta ji kunya ba. Kansa take kallo tana hawaye tuna awanni biyu kafin nan lafiya lau yake suna hira cikin farinciki, amma ga shi a sanadinta Faruk ya illanta shi. Farouk kuwa sai zare ido yake yi. Ko da su Anty Asiya suka zo. Faɗa sosai suka haushi da shi kamar za su duke shi. Ganin haka ya fara hawaye."Don Allah ku taimake ni kuce matata ce, wallahi ina sonta ba zan iya bar masa ba." "Ka san kana sonta ka wulaƙanta ta? Farouk gaskiya zan faɗi ba zan yi karya ba. " Ta furta masa cikin jin haushinsa. "Ka ƙyale rayuwarta ka rasa ta har abada ba za ta dawo gurin ka ba, domin in har tana da ninya abin da ka yi mata ka ruguza ninyarta." Cewar Ismail ya dafa shi. "Ya zan yi wallahi ina sonta." Ya furta cikin tsanannin tashin hankali. Bayan an gama wannan ces ɗin suka shiga. Farouk ya fara magana sannan Damir sai Nasreen. Kansu ya kulle suka rasa gane zancen. Ga shi ta ce ya sake ta har ta yi idda amma kuma ya rantse bai saki ba. "Akwai shida ga shedar sakinta." Ahmad ya ce tare da miƙa musu takadda. Mamaki ya ƙara kamasu sai suka lalle shi. "Kai ka yi sakin?" "Ban yi ba ita ce ta saki kanta don ta je ta aure shi, kuma ina son ta don Allah ka dawo mini da matata." Kansa ya ƙara kullewa."Ina ga zamu miƙa ces ɗin nan zuwa kutu." "Ba sai an shiga mutu ba yallaɓai. Farouk ƙanina ne kuma da gaske ya yi sakin. Zamansu ya cutar da ita na sha gaya masa dole zai yi nadama, amma bai ji ba yanzu nadamar ne ya yi a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada, domin ni da mahaifiyarmu da sauran ƙannina duk mun san da sakin...." "Anty Asiya don Allah kar ki gaya musu gaskiya. Ni fa ban san na yi sakin ba, kuma idan na yi ai na mayar da ita kafin ta gama idda. Ku taimaka ku riƙe ta ta dawo hannunna." Ya furta kamar zarrare. "Babu abin abin da za mu iya maka, tun da 'yan'uwanka sun bayar da sheda babu abin da za mu iya, don haka ka daina bibiyarta." "Wallahi ba zan daina ba domin matukar ina raye sai na mayar da matata. Nasreen tawa ce babu uban da ya isa ya aureta. Kutu zan kai a ƙwatar mini matata." Ya ƙarashe maganar yana kumfar baki kamar zarrare, sai kuma ya juya ya ce,"Nasreen ki taimaka na ci albarkacin yarana mu koma da aure mu, wallahi na yi nadama zan riƙe ki da kyau." Kallon sa ta yi cikin hawaye ta ce,"Ka riga ka yi sake na yi kuka na riƙe ka, alokacin don na zauna a gidan auren kar na yi zawarci. Na sha yi maka kuka don mu zauna lafiya, don kawai mu zauna mu rungumi yaranmu. Ba zan aure ka ba, Ya Damir na ke so shi zan aura, domin ina da yaƙinin zai ba ni kulawar da na kasa samu a gurinka." "Karya kike Nasreen so kike ki aure shi saboda abin duniya, wannan dalilin ya sa kika rinƙa cin amanata, don haka ba zan taɓa barin ki aure shi ba." "Haka kace?" Ta yi masa tambayar cikin tsananin mamaki. "Eh ba zan taɓa barin ya aure ki ba." Kallon Damir ya yi da ya tsaya yana kallon da cikin mamaki."Ya Damir kana sona?" Ta yi masa tambayar cikin murya da ƙarfi. "Ina sonki Nasreen a shirye na ke na kashe ko nawa don na aureki, saboda haukar da yake yi ya tabbatar mini da macen ƙwarai ce ke, za ki cike gurbin matata da na rasa. Ni kuma na yi alkawarin zan mayar dake zinariya a cikin mata." "Alhamdulillah!" Ta ce tare da murmushi hawayen da yake bin fuskarta. Ta kalli Ahmad ta ci gaba da cewa,"Ya Ahmad ka zama waliyin aurena, kuma a nan nake so ka ɗaura mana aure ka zama waliyina. Ina son ya ƙaryata kansa da ya sha gaya mini na babu namijin da zai iya aurena, saboda ba ni da tarbiyya." Ahmad kallon ta ya yi, sai ya kalli Damir da ya cika da mamakin abin da ta furta. Sosai magantarta ya bawa kowa mamaki. "Damir ka shirya aurenta?" Wani murmushin ya kubce masa ya ce,"Eh na shirya kuma a shirye na ke na ba da sadaki mai tsada koda ya kai darajar raina ne. Ga Baba Sani ya karɓa mini aurenta." "Shikenan a bada sadaki naira dubu talatin, domin mu yi koyi da abin da Annabi ya faɗa don aurenku ya yi daraja." "Alhamdulillah na gode Ya Ahmad zan bayar da sadakin, amma darajarta ya wuce haka. Na bayar da mota kuma ko tsinke bana buƙata na kayan ɗaki da kayanta, da kuma kujerar maka." "Alhamdulillah!" Ɗakin ya ɗauki kabbara ban da Faruk da yan uwansa. "Wayyo Allah! Na shiga uku! Don Allah kar ku ɗaura auren wallahi ina son matata. Zan kashe kaina da su in har aka ɗaura auren. Nasreen haka za ki yi mini? Saboda ba ni da kuɗi sai ki guje ni? Marwana na tsane ki domin kece ki kik canza matata kika nuna mata kuɗi." Ya ƙarashe maganar yana ihu tamkar zautacce, sai kuma ya kama hannun Asiya da Isma'il. "Kuna gani matata za ta auri wani? Wallahi auren ake ɗaurawa ga shi can za a ɗaura. Shi kenan na mutu a bani yarana don ba zan yarda ba." Ya furta sai kuma ya saki dariya yana kallonsu. Anty Asiya kama shi ta yi, tana hawaye sosai take yin kuka domin ta sha gaya masa ranar nan, amma ya ƙi ji ya yi kunnen uwar shegu. Yau ga shi Nasreen ta wuce da ajinsa, ta samu ingarmar namiji wanda ta san zata ji daɗi a gidansa, shi kuma babu mata babu kuɗin da ya kasa wadata iyalinsa, sannan ya koma haukarsa, domin yadda yake ihu yana zambarwa, ya tabbatar mata da ya koma gidan jiya. Wani tsaddaden murmushi ya saki ganin an ɗaura auren. Ya saci kallon ta cikin farinciki, daidai lokacin da Alhaji Sani ya kalle shi."Alhamdulillah an ɗaura sai fatan zaman lafiya." Sai kawai ya yi dariyar farinciki, sai ya mata da ciwon daya ji ganin Nasreen ta zama matarsa, duk cewar har lokacin bai gama yarda ba. "Ikon Allah ni da nake neman hanyar da zan kusanta kaina da ita, sai ga shi Allah ya sauƙaƙa mini ta zama matata a lokaci guda." Ya furta cikin zallar mamaki yana kallon ta da take share hawaye Marwana kuwa rungumeta ta yi cikin farinciki."An ɗaura kin zama matar Ya Damir Anty Nasreen." Kuka ta fashe da shi ta ƙara rungumeta domin ita kanta auren ya zamar mata bazata. Shi kuwa ya kasa cewa komai, sai kallonta yake yi yana ta mamaki sosai. "Allah ya sanya alkhairi." Mommy ta ce cikin farin ciki. "Amin," suka haɗa baki gurin faɗin haka. Kallon Faruk suka yi, da aka riƙe shi yana zambarwa sai ya kashe su, kuma a ba shi yaranshi. Hawaye ya wanke mata fuska domin abin tausayi ne, duk da tsanar shi da ta yi, sai da ta ji tausayinsa musamman da yake uban 'ya'yanta. Suna tsaye aka wuce da shi yin ihu yana faɗin,"Nasreen haka ka zaki yi mini? Kin auri wani kin manta da ni uban 'ya'yanki. Wayyo na mutu na lalace Allah ka ɗauki raina huta." "Anyi Asiya ta tsaya tana kallon ta ta tsare hawaye."Nasreen ina miki fatan zaman lafiya a gidan aurenki. Kin cancanci samun miji kamarsa, haƙiƙa haƙurin da kika yi Allah ya saka miki. Allah ya baku zaman lafiya. Farouk kamar ya koma hauka irin lokacin da Rashida ta sace masa ƙaddararsa. Farouk duk abin da ya faru da shi ya cancanta. Faruk ya cutar dake ya wulanƙanta rayuwarki, amma kuma Allah ya saka miki duba ga irin mijin da ya baki, kuma abin da ya faru da shi ya kamata saboda ya zama iska ga WASU MAZAN da suke wulaƙanta matansu suke ɗaukar su ba'a bakin komai ba. Rayuwarsa ta ishi ya zama ina izna ga WASU MAZAM masu dukan mata da musu horon yunwa. Mace mutum ce tana da daraja domin ita ce tushen kowa. Uwa ce kuma mata ce tabbas ta cancanci a mutunta. Don Allah ki yafe wa Faruk domin ya samu ya rage haƙƙin ki ɗaya ɗauka. Ki yafe mishi wataƙila Ubangiji ya ba shi lafiya, ya samu ya canza rayuwar sa." Ta ƙarashe maganar cikin kuka. Hawaye ta share ta ce,"Allah ya ba shi lafiya ba komai na yafe masa." "Amin mun gode. Sannan zan rinƙa zuwa in duba su Raihann." Ɗaga mata kanta tayi sannan ta wuce. Duk maganar da suke yi idanun Damir yana kanta. Har yanzu ya kasa yarda ta zama mallakar sa zai iya komai da ita na aure. Tsawon lokacin da ya ɗauka babu mata ya kasa yarda cewar yanzu ya tashi a matsayin gwauro mai rungumar filo. Daga yanzu cikin jikinta su rinƙa kwana ba zai lulluɓa da bargo ba. Shi kam sai ya ce gwamma da hakan ya faru, domin Faruk ya yi mishi hanyar da ya mallake ta cikin sauƙi. Nasreen ɗauke idanunta ya yi ta ƙarasa gurin Ahmad da yake ta kallota. Sai a yau ya ƙara kallon Damir sosai yake murna ganin irin mijin da ta samu. Ta ko ina ya kai ya kai matsayin da duk wacce ta same shi su ta yi ta godiya ga Ubangijinta. Ga kyau ga kuɗi ga jiki na maza sannan ga ilmi both Islamically and academically. Kai gaskiya mahaƙurci mawadaci. Da ya duba halin da ta shiga. Farouk ya ɗaga hannu a gaban Baba da shi ya kai wa Nasreen duka babu kunya. Ta yi kuka ta yi kuka har wani lokcin ya yi saɓon tunanin kamar Allah ya manta da rayuwarta. Ya tuna ranar da ta kira shi da tsohon cikin Musaddik ya hana ta abinci sannan ya duke ta, bayan ya sanya wankinsa da guga. Nasreen ta ga jarrabawar aure, amma kuma Allah ya saka mata. "Yanzu sai mu koma asibiti, sai Muhsin ya zauna da shi ko?" Mommy ta ce tana kallonsa. Zare idanunsa ya yi, jin ta faɗi Muhsin zai zauna da shi. Ya kalli Nasreen da take jin kamar ta ce za ta bi shi zuwa, asibitin amma tana jin kunya. Gurin Ahmad ta tsaya tana kallon ƙasa. "Ok, bari mu wuce gida in sha Allahu za mu zo anjima da su Mama." Cewar Ahmad yana kallon su, sa kuma ya kalli Marwana da take ta farinciki tana tunani itama yaushe za a yi nasu, domin ta so ace tare za a yi bikin, amma kuma sai ga yadda auren na su ya kasance. Damir kuwa kallo ya bi su da shi, so yake ya ga inda matarsa za ta wuce. A tunaninsa tun da an ɗaura ta zama nasa shikenan gida za su wuce, musamman da ya ce ba ya son komai, amma sai ya ga ta bi bayan Ahmad za su shiga mota, duk da cewar tana son ta yi jinyarsa. Gyaran murya ya yi, duk suka kalle shi."Mommy ina matata za ta tafi?" Ya yi tambayar ba tare da ya ji kunya ba. Kallonsa suka yi sai ta yi murmushi."Gida mana Damir. Ai ba kaza bace kawai da za a kamata a kaita gidanka, dole za a yi bikin, kuma an ɗaura iyayenta ba su sani ba, don haka dole gida za ta koma kai ma kana buƙatar lokaci a gidanka za ka zauna, kuma tun da Batula ta mutu ka kauracewa gidan dole a gyara." "Mommy sai ta zauna a ɗakina, in ma gidan ne a yau zan iya oder na komai gobe a gyara." Dariya suka yi ganin rashin kunyarsa. *AN ƊAURA AN ƊAURA TA ZAMA MATAR DAMIR💃💃💃💃💃💃💃💃 SU DAMIR BABU KUNYA WAI MATATA😁😁😁😁😁 WATO AN DAINA ZAMAN GWARANCI DUK WACCE BA TA FITO AN SHA RUWAN COMMENTS DA MURNAR BIKI BA KO ZAZZAƁI YA SAUKA BA ZAN JE ƊAUKO RAHOTON ANGO DA AMARYA BA* Fans ina ba ku haƙuri domin yau da wuya a samu pages biyu, sakamakon zazzaɓi da na ke fama da shi. Wasu maxan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 41 Kallonsa suka yi sai ta yi murmushi."Gida mana Damir. Ai ba kaza bace kawai da za a kamata a kaita gidanka, dole za a yi bikin, kuma an ɗaura iyayenta ba su sani ba, don haka dole gida za ta koma, kai ma kana buƙatar lokaci a gidanka za ka zauna, kuma tun da Batula ta mutu ka kauracewa gidan dole a gyara." "Mommy sai ta zauna a ɗakina, in ma gidan ne, a yau zan iya oder na komai gobe a gyara." Dariya suka yi ganin rashin kunyarsa. "No ka yi haƙuri so nake a yi biki sosai, sannan Marwana kamar ta samu wanda take so. In ya so sai a sanya bikin da nata a sanya wata ɗaya kawai, sai ki gaya masa ya turo." Ɓata fuska ya yi yana kallon ta, domin yana jin ba zai iya wanna kunyar ya barta a gida har wata ɗaya ba tana matsayi matarsa. "Mommy don Allah ina bukatar matata, na haƙura da duk wani shagalin da za a yi. Mu ai ba yara bane." "Ka yi haƙuri kawai Damir dole ayi biki." Mommy ta ce masa tana mamakin zaƙewarsa. Tura baki ya yi, kamar ƙaramin yaro ba tare da ya ce komai ba. "Mommy wanda na samu Ya Ahmad ne Yayan Nasreen, kuma ya ce dama na gaya muku a yi maganar bikinmu. Dama ina jiran na ga Ya Damir da Nasreen sun haɗa kansu sai na gaya muku." "Alhamdulillah Masha Allah! "Suka furta lokaci guda. "Ka ga wani haɗin Allah! An zama jini ɗaya?" Mommy ta yi maganar cikin zallar mamaki. Da sauri Ahmad ya ƙara tafiyarsa ya isa mota cikin jin kunya. "Ahmad dawo da Nasreen ta yi jinyar mijinta. Kai kuma ka dawo na yi magada kai." Alhaji Sani ya ce. Ji ya yi kamar zai gudu saboda kunya. Tsayawa ya yi yana sosai kansa. "Nasreen je ki zan yi wa Mama bayani." Ya ce tare da shigewa cikin motar da yaran cikin jin kunya. Dariya suka yi sosai Alhaji Sani ya ce,"Aiko kin samu miji mai kunya don har ya fiki." Fuskarta Marwana ta rufe tana murmushi. "Lamari ya yi kyau ga shi shi ma nagartaccen namiji. Kawai ya kawo kun sa rana, sai a sanya bikin wata ɗaya da kuma tarewar." "Allah ya kaimu ya sa an ƙulla aikhairi." Ta furta cikin farin ciki. Nasreen sao sunne kanta take yi, ganin yadda yake ta kallonta. Da sun haɗa idanu sai ya yi murmushi. Ji yake kamar ya haɗata da jikinsa, so yake ya rungumeta ya yi kissing ɗin ta, don tabbatar da cewar da gaske matarsa ce ta zama gonar sa. Mota suka shiga sanan suka wuce asibitin, saboda hutun da yake buƙata. Nasreen aka bari sai Marwana da ta je ta kawo musu abinci. Kan dole ya kwanta ya rintse idanunsa, don dole kawai, domin hatta Nasreen waje aka koreta sai ya yi bacci na awa biyu, amma fa tun da ya shiga cikin ɗakin ya kasa bacci. Tana zaune tana karatun Alkur'ani, don ta samu natsuwa. Har yanzu ta kasa yarda cewar matar Damir ce ita. Ganin kiransa sai ta zare ido."Ya Damir bacci ka ce ka yi." "Please matata, ki shigo na yi abin da zai tabbatar da kin zama mallakina, har yanzu gani na ke kamar mafarki na ke yi." Dariya ta yi tare da rintse idanunta."Da gaske na zama mallakinka ina jiran ka yi bacci in ka tashi sai na zo na yi wa kyakyawar fuskarka kiss ka tabbatar da haka." Da sauri ya miƙe, ya tashi zaune yana mamakin da ma ta iya kalaman. Komawa ya yi ya kwanta, yana sakin tsaddaden murmushi kamar tana gabansa. A hankali ya furta,"Please peck or deep?" Kunya sosai ta ji, jin tambayar da ya yi mata, domin da agabansa ya yi tambayar ji za ta yi kamar za ta nitse. Ɗaurewa ta yi ta ce,"Your choice. Cikin sanyin murya ta furta. Jin abin da ta ce sai ya shafa kansa cikin murmushi ya ce,"Oh my God!" Da wata irin murya ma kashe jiki "Ashe ta iya kalamai? Kodayake she is educated, duk wannan kunyar zai tafi in har muka tare." Ya ce yana ayyana soyayyar da za su yi. "Promise?" Ya tambayarta bayan ya ɗauki lokaci yana tunani. "Yes promise if you sleep." "Ok baby right now sleep bye." Ya furta tare da kashe wayar. Ita ma murmushi ta yi, ta rungume wayar cikin tsananin frinciki. Ga mamakinsa sai kawai ya rintse idanunsa, ya fara bacci sosai mai ƙarfi ya ɗauke shi. Dariya ta yi ta cigaba da karatun. Ahmad ciki farinciki ya ƙarasa gida. Mama da take cikin damuwa ta kira shi ya fi sau nawa. Na ƙarshe ya lura da kiran ya amsa yana faɗin,"Mama gani zan shigo da mota." "To alhamdulillah." Ta ce tana kallon Baba da yake ta bata baki. Yana shigowa suka yi kansa."Ya aka ƙare?" Suka haɗa baki gurin faɗin haka. Kwashe abin da ya faru ya yi ya gaya musu. Sun cika da mamaki sosai."Yanxu da gaske an ɗaura auren?" Baba ya tambaya cikin mamaki. "An ɗaura tana asibiti jinyarsa, saboda Faruk ya ji masa ciwo sosai kuma ya zubar da jini." "Amma kana ganin ka ba ni haƙƙina na mahaifinta Ahmad? Tun da ka yi kuɗi ka mayar da ni bolar zuba shara? Duk abin da za kayi ba za ka shawarce ni ba, idan ba ni da matsayin da za a nemi shawarar sai a gaya mini ko ta waya ne, tun da yanzu ka zama uban gidan haihuwar maka yaran kawai na yi." Mamakin abin da ya ce ya kama su sosai. Ahmad saboda takaici ya rasa abin da zai gaya masa, sai ya zauna yana tunanin abin da zai faɗa ya baƙanta masa. Mama cikin zafi ta taso mishi tana faɗin,"Akan wane dalili zai nemi shawararka? Bayan haihuwar yaran ka yi ka bar mishi wahala? Ko don an ƙyale ka, an zuba maka idanu ka haifa ka bar mishi su, yana musu ɗawainiya shi ne za ka samu bakin magana?" "Haƙƙina ne Nasreen ni na haife ta." "Ba a kan haƙƙinka kake magana ba, abin da za ka samu kake jin takaicin ba a kira ba, saboda yaran kamar jari kake yi da su. In kana wannan maganar cewa haƙƙin ka, ya kamata ka yi magana haƙƙinka da ya kwashi yaran ya sanya su a makaranta, amma babu abin da ka ce sai wannan ka san da haƙƙinka?" "Eh mana Ahmad duk mai ya yi wa 'yan'uwansa, ya zamar mishi dole a matsayinsa na babba, sannan in da ya shawarce ni zan yarda ya sanya sadaki naira dubu talatin kamar ya siyar da kaza? Ai darajarta ya wuce haka. Kamata ya yi, a sanya musu miliyan ko rani tun da suna da kuɗi." "Darajar auren muke nema Allah ya albarkanci aurensu, kai da ka sanya wa zuciyarka son abin duniya sai ka je ka yi ta yi. Har yanzu za ka yi nadama ba Baban Ahmad? Ina ƙara jaddada maka rabuwarmu, domin zama da kai ba yi da amfani." "Auren zobe mu ka yi, in har kika mun rabu na mutu ne, amma wallahi sai dai ki yi abin da za ki yi ba zan sake ki ba." Dole ka sake ni bari a gama bikin Nasreen." Shiru ya yi, ya zauna ganin yadda take gasa masa magana. Har sai da ya yi dana sanin maganar da ya yi. Tun da suke sa'insar Ahmad bai tanka musu ba, sai da suka yi shiru sannan ya kalle shi cikin takaici ya ce,"Mama ki sha kurumunki ana gama bikin Nasreen zan kai shi kotu. Sam ba zai shiryu ba, don haka dole ku rabu da shi, tun kafin ya kuma je ya ƙara zubar mata da mutunci yana roƙon su kuɗi, tun da ga shi nan ya raina sadakin da aka abayar." "Allah ya ba shi sa'a, wallahi in har ya aikata haka sai ya yi dana sani, domin sai na yi mishi abin da bai taɓa tunani ba. Tozarci da rashin ƙima da ya ja mata a gurin Faruk ya isa. Wannan karon in har ya aikata ba daidai ba, na rantse a ranar sai ya ba ni takaddar saki." Ganin yadda ta harzuƙa, sai ya kalle ta cikin sanyi ya ce,"Ba zan aikata hakan ba saboda Nasreen tana bani duk abin da na roƙa. Don Allah ki daina gaya mini za mu ramu." "Dole na gaya maka, saboda ba ka cancanci rayuwa da ni ba." Ta furta masa tana watsa masa mugun kallo. Shiru ya yi, don ta bar maganar kuma cikin sa'a sai ta yi shiru. Nisa wa ya yi ya kalle ta ya ce, "Amma Faruk ɗan tasha ne mara hankali kawai. Ai shi da Nasreen yarda ya bar nonon uwarshi ya barta. Allah ya bata wanda ya fishi. Ni kaina na yi dana sanin aura masa ita da na yi. Kalƙo mai kafar biri." Banza suka yi da shi sai Mama ta nisa ta ce,"To shikenan Allah mun gode maka tun da abun ya zo da sauƙi. Shi kuma ya ga ƙarshen sa. Sai abin da ya faru ya zama izna ga WASU MAZAN da suke wulaƙanta mace, suna ganin zaman gindansu cikin ukuba shi ne kawai mafita." "Amin Mama, da kuma WASU MAZAN da suke haihuwar yara ba tare da sun kula da rayuwarsu ba, su barshi kara zube su zama annoba a cikin al'umma, bayan sun san ranar gobe kiyama, Allah sai ya tambaye su amanar da ya ba su." Mama ce kawai ta ce,"Amin," Baba kuwa sai ya muskuta, ba tare da ya ce komai ba, domin ya san magana ya gwaɓa masa. Ganin Ahmad ya shige ciki, sai ta miƙe ta shige ɗakinta, aka bar shi yana ta kallo. Kusan awa biyu ya ɗauka yana bacci, har sai data leƙa sau biyu. Ganin har lokacin bacci yake yi, mai ƙarfi sai ta koma ta zauna bayan ta yi magariba. A lokacin da ta idar, Marwana ta shigo cikin asibitin, da Muhsin riƙe da kulolin abinci. Kallon juna suka yi sai ta yi dariya ta ce,"Amarya." Dariya suka ƙara yi sosai sannan ta zauna."I can't believe wai kin zama matar Ya Damir in simple way. Da ace Faruk ya san abin da zai faru kenan, in ya aikata wallahi ba zai yi ba." "Sosai shi ya sa ake cewa mutum ya yi tunani kafin ya aikata abu. Ga shi ya yi sanadin aurenmu babu shiri." "Haka ne wallahi, to ya batun amarci ina ba a asibiti za ku yi ba? Saboda yadda na ga yana wani kallonki, kar dai ki bada kai tun ba ki tare ba." "Marwana, bana son rashin mutunci ni fa matar yayanki ne." Dariya ta kwashe da shi sosai tana kallonta."To ni ma na kusa zama matar yayanki? Ko ba ji ance za a sanya mana rana sai a yi bikinmu da tarewarki ba." "Na ji Allah ya sanya alkhari." "Amin, amma ki bani amsar tambayar. Ina angon na ki yake." "Yana can yana bacci, bawon Allah kanshi yake bani tsoro kamar ya ƙara tasawa." "Karki damu zai warke, Faruk mugu ne sam ba shi da imani." "Wallahi ai ya ga ƙarshen sa hauka." Muhsin ne ya shiga sai ya fito.'Ya Damir ya tashi za ku iya shiga." Ya ce musu sannan ya koma ciki. Ganbanta ne ya buga sosai, da ta tuna alƙawarin da ta yi masa. Sosai take jin kunyarsa, saboda ta iya zance a waya, amma a zahiri sai ta kasa. Kanta a ƙasa ta yi sallama ta shigo. Ɓata fuska ya yi, domin ya ji haushi da Muhsin ya fara shigowa. Ya so ace ta cika masa alƙawarinsa. Idanunsa na kanta, don haka ta ƙarasa cikin sanyin jiki ta zauna gefen Marwana."Sannu da jiki Ya Damir." Marwana ta ce tana kallonsa. "Yauwa sis ina little Marwana?" "Tana gida ganin ciwon da ka ji, ta yi ta kuka da tare za mu zo, amma sai ta fara zazzaɓi. Mommy ta bata magani bacci take yi na taho." Murmushi ya yi, jin abin da ta ce tana kallon Nasreen, da ta yi shiru motsin kirki ta kasa. "Anty Nasreen ga abinci, ki zuba wa Yaya. Hajiya ta ce ki lura sai ya ci sosai, saboda ba ya son cin abinci in ba shi da lafiya." Harara ta zabga mata, don ta san da biyu ta kira ta da Anty kuma take maganar. Kallonta ya yi, yana murmushi alamun ta ji abin da aka gaya mata. Ɗauke kanta ta yi ba tare da ta amsa ba. "Marwana zo mu je mu ba shi guri ya ci abinci." Da sauri ya kalli Muhsin yana shi masa da albarka a zuciya, domin kamar ya san hakan yake so su yi. Jin fita za su yi, sai ta takura tana kallonsu har suka fita. Tana jin Marwana ta ce,"Ki zuba masa abincin bari mu gaida marasa lafiya." Ba tare da ta amsa ba ta, je inda aka aje kulolin ta ɗauki filet. Sannan ta zuba masa. Tun da suka fita ya bi ta da ido, amma ta ɗauke na ta, saboda kallon tuhuma da yake mata. Bayan ta zuba sai ta tsinci kanta da kasa juyawa. Ɗaurewa ta yi ta juyo cikin sanyinta. Kamar yadda ta zarga, yana kallonta idanunsa suna kanta. Kan gadon ta ƙarasa ta miƙa masa abincin ba tare da ta lalle shi ba. Ganin ta tsaya bai karɓi abincin ba sai ta kauda idanunta. Ita yake kallo ganin ta kalle shi dai ya tura mata kumatunsa."My promised, I need deep kiss baby." Ya ce yana tura mata leɓensa. Saura ƙafan abincin ya zube, ganin haka da sauri ya sanya hannu ya tare abincin yana kallonta."Mene ne haka sai ka ce na aikata zunubi za ki razana haka?" "Kusan haka ya Damir. Don Allah ka bari na gama fita shaukin mamakin mun yi aure." "Yes, we are spouse from now on, kuma duk abin da ma'aurata suke yi ya kamata ki yi mini. Ko ba kyau tausayina ne duk a kanki a fasa mini kai?" Ya ƙarashe maganar, cikin zallar shagwaɓa wanda ya sanya ta juyo a birkice. "Dama namiji na shagwaɓa ne?" Ta yi wa kanta tambayar kanta na ƙara ƙullewa. Tun da aka ɗaura auren ya ƙara canzawa. Tun ranar da ya fara nuna mata ƙauna yake canzawa, ashe haka yake da rigima da haka. Lamarin sai ya yi mata bambaraƙwai, wai namiji da suna Hajara. Ganin ta shiga cikin duniyar tunani, sai ya langaɓe kansa yana kallon ta. Shi kansa mamaki sosai yake yi yadda ya saki da ita. Ada yana shakkarta, amma tun da aka ɗaura auren sai ya ji duk wani kunya da shakkarta ya fice, wataƙila don shi ne bos, shi ne zai fara bayar da ƙofar da za su zamo ɗaya. "Nasreen," Ya kira sunan a can ƙasar maƙoshi. Juyowa ta yi cikin kunya ta kalle shi."Please fulfill the promise kin san babu kyau saɓa alƙawari ko?" Kallonsa ta yi wani iri, tana mamakin rashin ta idonsa. Ta yaya zai kalli idanunta, ya ce ta yi masa kis a ranar da aka ɗaura aurensu. Wataƙila kuma don ya ganta bazawara ce dama ance basu da kunya. Ta yi tunanin hakan. Ko ya fahimci abin da take tunani ne sai ya ga zaƙewarsa. "Ok tun da baza ki yi mini ba feed me." Ya ce mata tare da gyara zama ya buɗe baki. "Ba Bukar ba Habu." Ta ce a zuciyarta domin hakan ba za ta iya ba. Ganin ta ƙi sai ya yi fushi, ya juya mata baya ya kwanta. Ba ta san lokacin da dariya ya kubce mata ba."Please Ya Damir stand up and eat, you are no like little Marwana." "Am more than her. Nasreen a gurinki tamkar ita ko jariri na ke. Har Batula ta mutu in ina gari tare muke ciyar da junanmu, and kuma da ga yau tun na Allah ya ƙara bani ke zan ci gaba." "Nan fa a asibiti what if wani ya zo ya gammu? And besides that, su Marwana suna waje zan ji kunya sosai su shigo su ganmu. Don Allah eat don't starve yourself." "Dole ki cire kunya sosai. Ki tambayi ƙawarki Marwana ganin idanu ba ya sanya na kasa nuna ma matata soyayya." "Akwai rashin sabo don Allah eat zan yi watarana." Juyowa ya yi, ya tashi zaune tare da karɓar abincin."I don't believe your promise, but lemme eat am starving to dead." "Good," Ta ce tare da ije mishi a gabanshi. Yana cin abincin idanunsa na kanta, so yake kawai ya gansu tare, ya matsu ya ga ranar ya tashi daga gwauro da runguma filo. Yana ci yana kallon ta cikin ƙauna har ya kammala. Tana ƙoƙarin kwashe kular Marwana ta shigo da Muhsin. "Ya Damir su Maman Nasreen da Ya Ahmad ne suka zo." "Ok, su shigo." Bayan ya gyara zamansa. Mama da Ahmad suka shigo tare da sallama. Damir cikin jin kunya ya ɗaga idanunsa yana kallon ta. Sun yi kama da Nasreen sosai, domin ita ta biyo. Duk da ya taɓa ganinta, amma bazai shedata ba, domin a wancan lokacin ba shi a cikin hayyacinsa. Sosai yake jin kunyarta da girmamata. Tuna mugayen kalaman da ya rinƙa faɗi a gabanta. Itama cikin kunya irin ta surukai suka gaisa. Ahmad ya ba shi hannu suka yi sallama. Cikin dakewa kamar sun saba suke hira. Sun ɗan jima kaɗan, sannan suka miƙe za su tafi. Nasreen ce ta miƙe ta ce,"Ni ma bin ku zan yi Mama, gobe da safe zan dawo." Jin abin da ta ce, ya watsa mata idanunsa yana son yin magana, amma kunyar Mama ya hana shi cewa komai. "Na yi tunanin anan sa ki kwana har na zo miki da kaya?" "A'a Muhsin zai kwana da shi. Da safe zan dawo." Ta faɗa ba tare data kalle shi. Kallon Muhsin ya yi sai yayi matsa ya ce,"Nan za ki kwana, asibitin mai kyau ne akwai gurin kwanciya kamar zai fi buƙatar ki." "Eto, tun da Mama ta kawo miki kaya ki kwana mana." Cewar Ahmad yana kallonta. Kamar za ta yi kuka, ta koma ta zauna ba don ta so ba. Dariya ce ta so ta kubce masa, amma sai ya daure ya kauda kansa. Bayan sun tafi, tana zaune shiru ba tare data kalle shi ba, sai ta ji ya yi gyaran murya ya ce,"Yanzu za ki iya tafiya ki bar mijinki a wannan halin?" Kallon sa kawai ta yi, don ta san rigima yake ji."Kamar kwanan Ya Muhsin zai fi amfani." "Na gaya miki haka? Na fi so ki zauna a gefenta in ta kallonki." Ba ta ce masa komai ba, don haka ya ɗauki wayarsa, yana dannawa wani lokacin yana kallonta. A haka suka zauna har na tsawon lokaci. Ganin tana hamma, sai ya nuna mata gadon da yake kwance tare da miƙa masa hannu ya ce,"Come and spleep baby." Kallon sa yi a birkice, sai kuma ta miƙe ta ɗauki kayan baccinta yi hanyar bayi tana faɗin,"Zan kwanta a wancan gadon." Bai ce mata komai ba, don shi ma tsokanarta ya yi. Brush ta yi sannan ta canza kaya ta fito ta kwanta. Ganin ta kwanta shi ma ya kwanta tare da sauke nauyyayyar ajiyar zuciya, yana mamakin yau yana kwance ɗaki ɗaya da ita. Ba su jima ba bacci mai nauyi ya ɗauke su. Nasreen bata tashi ba, har sai da ya farka jin kiran sallah. Miƙewa ya yi, yana girgiza kansa da ya ji ya rage nauyin da ya yi masa. A hankali ya isa gareta, yana murmushi ganin yadda ta dunƙule a cikin hijabi. Jin ya taɓa ta sauri ta miƙe."Ki tashi ki yi sallah." Ya ce tare da shinfiɗa sallaya. Miƙa ta yi mai haɗe da salati, sannan ta nufi bayi. Bayan ta yi alwala ta fito. Lokacin da ta fito yana Sallah don haka. Ta jira ya gama. Ɗaukar sallayar ta yi, zuwa gadon da ta kwana ta shinfiɗa. Da ta idar da sallar, yana zaune da waya a hannunsa da alama karatu yake yi. Ba ta san dai mai yake karantawa ba, bakinsa kawai yake motsi. "Ina kwana? Ya jiki?" Ta ce mishi tana tsaye nesa dashi. Hannu ya miƙa mata alamun ta zo ta rungume shi, amma maimakon haka sai ta ƙara matsawa nesa da shi. Ganin haka ya yi dariya ya amsa. Ta yi ninyar ta koma bacci har ta fara, sai ta ji muryarsa yana kiranta bayan ya gama karatun. Hira ya shiga yi mata tun tana gyangyaɗi har ta saki. Duk da ba wani amsa take masa ba, amma tana jin daɗin hirar sosai. Ganin yadda yake ta zuba yana bata labari. Suna zaune har ƙarfe tara ta yi, tun tana share shi har ta saki tana dariya sosai, domin labarin dariya yake bata. Kallonsa take yi cikin tsananin ƙauna, ganin yadda yake so simple. Sosai take mamakin sa, domin duk wannan ɗauke fuska cin magani babu. Idanunsa cike suke da ƙaunarta. Yana ganin ta yi shiru zai ɗauki wani hirar. Kallon da yake jifanta da shi, suke ƙara birkita tunaninta. Wasu maxan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 42 Suna zaune har ƙarfe tara ta yi, tun tana share shi har ta saki tana dariya sosai, domin labarin dariya yake bata. Kallonsa take yi cikin tsananin ƙauna, ganin yadda yake so simple. Sosai take mamakin sa domin duk wannan ɗauke fuska cin magani babu. Idanunsa cike suke da ƙaunarta. Yana ganin ta yi shiru zai ɗauki wani hirar. Yawancin hirar little Marwana da Marwana rigamar da suke yi a gida ne. Sosai ta fahimci yana sonsu su biyun. Don haka ta sanya a ranta, za ta nuna musu ƙauna musamman little Marwana. "Ki bani labarin abin da yaranki suke yi na dariya, musamman Musaddik na ga yafi wayo da rigima." Da ya san farincikin da ta shiga, da game da tambayar da ya yi sanya ta to da ya ƙara wasu. Sosai ta washe bakinta ta fara bashi labarin ball da suke yi da Ya Ahmad. Dariya yake yi yana kallon ta. Hakan ya burgeta ganin ya ɗauki shirmensu, a matsayin abin da zai zauna yana saurare. "Kids are very funny. Shi ya sa nake son yara sosai. Ina fatan za ki haɗa mini?" Kunya sosai ta ji, jin abin da ya ce ganin hakan yasa ya yi murmushi. Sallama ya katse maganar da zai yi mata. Mommy ce da Marwana sai Muhsin. Da sauri ta tashi ta tarbe su cikin jin kunya."Sannu da zuwa Mommy, ina kwana?" Ta ce bayan ta zauna. "Lafiya kau ya mai jiki?" Kasa amsawa ta yi ta zauna gefen Marwana. Little Marwana ganin daddynta, sai ta ruga da sauri ta haye jikinsa."Daddy sorry, wannan mugun ya ji maka ciwo?" Ta yi masa tambayar tana kallon kansa. "Na ji sauƙi ki daina kuka kin ci abinci?" "Eh Anty Marwana ta bani." "Ok, je ki gaida Ummanki." Da sauri ta sauka, zuwa gurin Nasreen jin abin da ya ce. Cikin murmushi ta amsa gaisuwar. "Nasreen ki sanya muku breakfast." Ta shi ta yi jin abin da Mommy ta ce ta zuba masa. Ita kuma ta sanya kaɗan ta koma ta zauna tana juya abincin. Hira suke yi cikin sanyin murya. Shiru ta yi tana saurarensu tana murmushi, don sai ta zamo ɓakuwa a cikinsu. Suna zaune sai ga mutane sun fara shigowa, daga gurin aikinsu. Jaje sukayi musu, sannan suka yi musu murnar ɗaurin aure. Hajar tun da ta shigo ga su Mommy da Muhsin, sai ta koma gefe ta zauna cikin kunya. Gurin Nasren ta zauna ta kama hannunta. "Mamaki sosai muka yi da aka ce an ɗaura aurenku. Na yi muku murna sosai Allah ya baku zama lafiya. Ingawa tamkar zai yi hauka, hawaye ya rinƙa yi lokacin da ya ji labarin, kin san tun da ya ɗauki jakarsa bai dawo ba." "Allah Sarki Ubangiji ya bashi wacce ta fini." Ta furta hankali. Mutane sosai suke ɗururuwar zuwa gaishe shi musamman ma'aikatansa. Mommy ce ta kalle shi bayan sun fita."Ai baka samun hutun Damir, anya ba gida za mu koma ko a hana shigowa?" Girgiza kansa ya yi don ba ya son a sallame shi, ta koma gida yafi son yi ta zama, har lokacin tarewarsu ya yi."A hana kowa shigowar dai, amma ina buƙatar hutu." Ya furta yana dafe kansa. Murmushi suka yi domin sun ɗago shi.Muhsin ne ya shigo da magunguna a hannunsa. "Ya Damir, likita ya ce sallamarka za a yi, ka koma gida sai ka dawo a kwance ciwon." Jin abin da ya ce sa ya ji haushi. Shiru kawai ya yi, ba tare da ya ce musu komai ba. Nasreen kuwa daɗi ta ji sosai, domin ta matsu ta koma gida anan takura take yi. "Likitan ma ya shigo sai mu fara haɗa kaya." Muhsin ya ce wanda ya sanya Marwana ta miƙe. Suna shirin tafiya Ahmad da Baba suka shigo. Sosai ta ji daɗi za ta wuce gida. Haka kuwa aka yi bayan an gaida, sun gaisa mai jiki ta yi musu sallama. A tare suka shige mota sannan suka tafi. Damir sa ya ji babu daɗi a ransa har sai da suka fahimta. Gani yake kamar wata ɗaya shekara ne. Da ta koma gida wanka ta yi, ta kwanta bata tashi ba, sai da kiran wayarsa ya tashe ta. Ba tare da ta gane wanda ya kira ba, ta kanga a kunninta cikin magagi ta yi sallama. "Nasreen har bacci kika iya yi? Ni kuwa inata tunaninki." Ya yi mata tabbayar cikin mamaki. Jin muryarsa, sai ta tashi ta zauna tana goge idanunta."Ya Damir, wata ɗaya ne fa za mu yi bamu a tare. Don Allah ka daure akwai shirye-shiryen da dole sai mun yi." "Wata kamar shekara ne a gurina" "Ka yi haƙuri zai zo." "Ya zan yi tun da Mommy ta ce haka? Amma za ki dawo aiki ko? Kuma za ki zo gaishe ni?" Dariya ta yi ganin rigimarsa kamar ƙaramin yaro."Zan iya zuwa ƙila, amma aiki sai bayan tarewarmu." "No dole ki dawo aiki, saboda ta nan ne kawai zan rinƙa ganinki, in kuma ba so kike na tare a gidanku ba, don haka ki yi tunani." Dariya kawai ta yi, ta sauka kan gadon ganin ya kashe wayarsa. Sallah ta yi ganin lokaci ya wuce, sannan ta fito falo. Zama ta yi gefen Ahmad da suke shawarar ranar da za a je maganar sa rana. Zainab ta ƙwalawa kira ta kawo mata abinci. Tare suka ci gaba da maganar. Sam Damir bai barta ta huta ba kullum kira, yana gaya mata ƙosa ya yi missing ɗin ta. In ya dameta har mamaki take yi yada ya yi a lokacin da ya zauna babu aure. Gabakiɗaya ya zama mara kunya. Maganganu yake sakin mata har sai ta ji kunya ta kashe wayar. Wani lokacin irin rayuwar auren da yake so da kuma abin da yake son ta rinƙa masa yake gaya mata. Duk yadda ya so ta zo duba shi, ammma ta ƙi don kunyar Mommy take yi. Tun yana fushi har ya gaji ya saki. A ranar da ciwon ya yi sati aka warware masa bandeji. Washegari ya shirya komawa ofis kuma ya matsa mata sai ta zo. Ta dai amsa masa ne don kawai ya barta ta kwana, saboda bacci take ji sosai, kuma ta san in har ba ta amsa ba ba zai kyale ta, ta kwanta ba. Washegari da ta tashi sai ta yi kwanciyarta, musamman da bata sallah. Har ten ba ta fito ba tana bacci abinta. Wayarsa ya tashe ta ganin kiran ta yi murmushi ta ɗaga."Kin ce za ki zo ofis, amma tun takwas na zo ba ki zo ba?" Ya yi mata maganar ba tare da ya bari ta ce komai ba. "Amma ka bari na amsa sallama." Ta ce mishi a maimakon ta amsa. Shafa kansa ya yi kamar tana ganinsa."Am sorry ganinki kawai na ke son yi don Allah ki zo." "Ya Damir, ni da aiki sai bayan tarewarmu." "Ok, na yarda amma sai kin zo kin gaya mini ko?" "Ga shi ina gaya maka kuma ai na gaya maka tun tuni." "Ina kira ki a matsayin miji za ki ɗauke ni, amma maganar ofis a can za ki zo mu yi ta. Ina jiran ki." Ya ce tare da kashe wayar. Dariya ta yi, ta shige bayi ta yi wanka tare da kintsa kanta ta koma gado, saboda hutu sosai take so ta yi. Shiru-shiru ba ta zo ba, don haka ya ƙara kiranta."Nasreen mai ya sa ba za ki bi maganar mijinki ba?" "Ya Dami..." "Bana son wata magana in har ba za ki zo ba shikenan." Ya ce tare da daƙile wayar cikin fushi. Miƙewa ya yi, yana zagaye ofis ɗin. Sosai yake jin ba zai iya jira har lokacin ba. Yana so ya shi kam ko babu biki a ba shi matarsa, amma ya san Mommy ba za ta yarda ba. Wani feelings yake taso masa sosai har ya kasa jurewa. Sai ya rinƙa mamakin kansa yadda ya iya haƙuri ba tare da mace ba, amma kuma kuma gashi lokaci kaɗan ya kasa jira. Kodayake a lokacin ba shi da matata, amma yanzu yana ganinta ana masa ƙwalele. Haka dai ya daure, domin tun yana sa ran zuwa har ya cire rai. Sai ya ji babu daɗi saboda takaici gida ya koma. Da fari fushi ya yi da ita, amma sai ya ga fushin a banza ne. Don haka ya sha gayunsa ya tafi gidansu da dadddare. Tana zaune a falo, suna ta shawarar bikin sai ga kiransa. Murmushi ta yi ganin ya sauko. Ba ta yi tunanin yana Kofar gida ba. Da sallama ta ɗauki wayar. "Ina ƙofar gidanku." Ya ce tare da kashe wayar bayan ya amsa sallama. "Innalillahi! Wai dama haka mutumin nan yake da rigima?" Ta yi wa kanta tambayar cikin mamaki. Dogon hijabi har ƙasa ta sanya sannan ta gayawa Mama."Amma da gida kuka shigo sai ku tsaya a waje?" Ahmad ya ce . "Gaskiya ki je ki ce masa ya shigo." Mama ta ƙarashe maganar tana kallonta. "Ok tom." Ta ce sannan ta fita. Tana hanya ta ga text ɗinsa ta taho masa da yaransa. Murmushi ta yi sai ta koma gidan ta taho da su. Da sallama ta ƙarasa, tana shaƙar turarensa da ya kashe mata jiki. Amsawa ya yi, yana basar da ita, hankalinsa na kan yaran kamar su ya zo gani. "Ina wuni?" "Lafiya mai kika yi wa Musaddik ya ƙi magana." "Rigima kawai yake ji shi da Raihan ne." Ta ce masa tare da zama bayan motarsa hakan ya ƙular da shi. "Ok, kira Zainab ta shiga da su ga tsarabarsu." "Tom Allah ya ƙara buɗi." Ta ce tare da kiranta. Ba ta ɗauki lokaci ba, ta fito da sallama ta kwashi yaran bayan ta gaishe shi. Sun yi shiru yana kallonta."Abin da kika yi kin kyauta?" "Ya Damir mai na yi? Ina da hidima sosai a kaina kuma har tafiya zan yi." "Ba matsala za mu je tare sai mu kama hotel." Dariya tayi kawai jin abin da ya ce."Mu bar ofis sai bayan bikinmu." "Maganar ya wuce ga shi ban ji haushi ba na zo." "Ina maka barka da zuwa my Hearthrop." Kalmar da ta gaya masa, ya ɗan sanyaya ransa har ya murmusa. "Please ki dawo gaba." Ya ce mata yana nuna mata kujerar mai zaman banza. Babu musu ta dawo gaban ta zauna tana kallon shi. "Mai kike shiryawa? Ina son ki gama tsarinki na sani." "Babu don ko wani taro ba xan yi ba bayan ɗaurin aure." "Dole za a yi karki manta ba mu kaɗai bane." "Haka ne sai dai don su." "Na yi magana da masu furniture da kuma kalar fenti. Za su tura mini komai da na ke so na zaɓa, saboda so na ke a canza komi na gidan. Zan tura miki sai ki duba wanda ya yi miki." "Ka zaɓa duk abin da ya yi maka ina son shi." "No gidanki ne kece Ya kamata ki zaɓi komai. Maganar lefe Mommy ta ce akwai wacce take zuwa Dubai za ta haɗo." Kanta ne ya faɗi jin abin da ya ce sai ta murmusa ta ce,"Shikenan, zan zaɓa Allah ya ƙara buɗi." "Amin kuma duk abin da kike so, na hidimar biki ki gaya mini. Nawa zan bayar gyaran jiki?" Hannu ta sanya ta rufe fuskarta cikin jin kunya."Ko nawa ne" "Don Allah stop behaving kamar ba ki san rayuwar aure ba, mun san yadda zaman aure yake. Ki cire kunya mu tsara rayuwarmu." "To," Ta ce ba tare da ta faɗa masa kuɗin ba. "Zan tura miki kuɗi sai ki fara in sun yi kaɗan ki sanar mini." "To," Ta ƙara cewa. "Ba ki gaya mini kina da ciwon magana ba?" "Ni? Ina magana sosai." "Na ga yanzu kin fara ai, kuma gara ki sake sani, saboda ni da iyalina bazan zauna mu yi zaman kurame ba. Sosai na ke sakewa da su." "To," Ta ƙara ce masa. Ganin haka ya matso daga kujerarsa zuwa inda take. "Bari na fara ƙoƙarin cire wannan kunyar, tun kafin daren amarcinmu ki hanamu shan amarci." A tunani ta ya matso ne, don haka fit ta fice daga cikin motar. Bayan takaici dariya ma ta ba shi."Ni zan tafi kafin ki sanya mini hawan jini, da wannan kunyar taki. Duk wayon amarya sai an sha manta." "Sai da safe." Ta ce tare da wucewa da sauri. Dariya sosai ya yi, sannan ya tayar da motar cikin takaici. Shi da ya zo ya rage zafi, amma ko hannunta bai samu damar riƙewa ba."Wannan kunyar ya yi yawa dole ki daina" ya ce yana girgiza kansa Da ta shiga cikin gida sosai take yi wa kanta dariya. Tana kwance tana tunaninsa, sai ga alert na kuɗi har sai da ta razana. Da ta kira shi kin ɗagawa ya yi kamar ya san abin da za ta yi. Juyawa ya yi tare da ɗora wayar a ƙirjinta. Tana mamakin mijin da Allah ya yi mata tagomashi da shi. Washegari da safe, tana zaune tana lissafin inda za ta fara hidimar bikin. Marwana ta kira ta."Hello Marwana?" Ta ce bayan ta ganka wayar a kunninta. "Nasreen ina maganar da na yi miki? Ki shirya muje." Ta ce mata cikin sigar rarrashi. "Ni fa babu inda za ni, zan dai gyara kaina, amma ba zan yi ɗinki ba na cutar da kaina. Kan namiji na je na kashe kaina." "Wallahi ba kashe kai bane. In har na san za ki cutu ba zan gaya miki ba. Ki kauda batun Ya Damir ɗan'uwane, kin san na zaɓe ki na ƙyamar shi ko? So nake ki kankaro ma kanki mutunci sosai. Hatta magunguna na siya miki supplements na gyaran jiki wanda basa cutarwa. Ni ma ina sha kin ga ba cutar da kaina ba." "Ni fa tsoro na ke ji, saboda an ce yana kawo kansa. Bana son na cutar da lafiyata." "Tabbas yana kawowa, amma akwai masu kyau waɗanda za su ƙara miki lafiya da kyau. Ya kamata ki kankaro ma kanki mutunci a gurinsa. Yadda yake rawar jiki ya ƙisa ki gyara kanki. Ko ɗazu sai da ya gama wa Momi magiyar a rage bikin." Murmushi ta yi ta ce,"Yaushe za mu je?" "Yauwa jibi ki shirya." Ajiyar zuciya ta yi, ta kashe wayar bayan ta ce,"Allah ya kaimu." Duk da tana tsoro amma, ita kanta tana son ta samu daraja da ƙima a gurinsa. Da ta shawarci Mama, ta amince ta bata goyon baya, domin yanzu ya zama ruwan dare. Ko haihuwa mata suka yi suna zuwa a yi musu ɗinki. Ballantana ita da za ta yi sabon aure. Ita kanta sai ta ji za ta jure zafin, don ta samu daraja a gurinsu. Shawara suka yanke, sai Damir ya yi tafiya sannan za ta yi, tun da sun ji ɗan zumuɗin yana maganar zai tafi jibi. Don haka dai suka bari sai ya tafi, saboda ba sa son ya sani, in babu kuma yana nan dole ya gane. A yadda ake kururuta abin, da ba ta ji zafin kamar haka ba, wataƙila kuma don asibitin da suka je ƙwararre ne. Baya sun dawo duk ta bi sharaɗin da likitar ta gaya mata. Ta ɓangaren Ahmad shi ma, waje ya ba da aka haɗo mata lefe, sosai yake shiri domin hatta sabon gidansa. Sai da akayi wasu gyare-gyare. So yake ya mayar da ita zinariya domin ta cancanta. Ya rage biki saura sati ɗaya Damir ya dawo. Washegari aka kawo lefe naban mamaki. Nasreen kama bakinta ta yi cikin mamaki. "Kai wannan kayan sun yi yawa kamar albazaranci ne." Mama ta furta tana kallon kayan, domin ta kasa ɗaga kayan, saboda tsabar yawansu. "Gaskiya Ya Damir kamar bai san zafin kuɗinsa ba." Ta furta tare da ɗaukar makullin motar tana murmushi. Haka mutane, suka rinƙa shigowa ganin lefen Nasreen, domin babu budurwar da aka taɓa ma irinsa. Ɗaki ta shiga ta zauna, tana ƙoƙarin kiran layinsa sai kiransa ya shigo. Cikin murya mai taushi ta yi sallamar. "Wannan muryar ta ki kar ta sanya yanzu na yi booking Hotel." Cikin jin kunya ta rufe idanunta." Please Nasreen ba ki ƙosa ki tare ba?" Ya yi mata tambayar da muryar da ya tabbata mana da matsuwarsa. "A'a da na so na ke na roƙe ka aka ƙara kwanaki..." "Please stop jorking, in har ba so kike kiga rashin kunyata ba, don wallahi da dai Mama ta kauda idanunta ɗakin ki xan za dawo." "Ya..." "Don't say anything, ba kya tausayina? Tsawon lokacin da na ɗauka babu mata ai ya kamata ki tausaya mini. Ina fatan ranar amarcinmu za ki cire wannan kunyar, saboda so na ke ranar ta zama memorable, duk lokacin da muka tuna sai mu kasace cikin farinciki?" Wayar ta cire tana kallon mumbarsa cikin mamaki. She was like dama haka yake? Saboda gabakiɗaya ya canza hatta muryar da yake mata magana da shi, mai sanya kasala da shiga wani yanayi ne. Shi ya sa tun da aka ɗaura auren ba ta son haɗuwa da shi. Those sexy eyes of him, suna sanya ta shiga cikin wani yanayin da bata son ya fahimta. Tana wannan tunanin, ta ji ya kira sunanta da muryar da ya kashe mata jiki. Sai da ta ja numfashi, sannan ta amsa can ƙasan maƙoshinta. "Mai kika shirya wa ranar amarcinmu? I mean wane irin tarba za ki yi mini ina shigo, Are you going to hugg me or give me a hot kiss?" Da sauri ta kashe wayar, ita kam yanzu ya daina ba ta mamaki sai dai al'ajabi. Kwanciya ta yi kan gado, domin ya saukar mata da kasalar da ko numfashi da ƙarfi take fisgo shi. Damir kuwa, ganin ga kashe wayar sai ya yi dariya sosai."Yarinya za ki sake ne, don wataƙila ba ki san mijin da kika aura bane." Tura mata da hotunan furnitures da aka kawo ya yi, sannan ya ɗauki fentin da aka canza. Tare da tura mata text ta duba duk abin da bai yi ba sai ta faɗa a gyara. Murmushi ta yi, tana duba gidan cikin tsananin mamaki. Wai yau ita ce za ta zauna a irin wannan gida? Mai kama da al-jannnar duniya. Bayan ta gama duba kayan, sannan ya fita zuwa falo, don ta je ta kira mai dilka ta ci gaba da mata. Amarya Marwana ita ma, ɓangaren su ana ta shiri domin har an yi danki an shirya komai. Gida ya tsaru sai jiran amare kawai. Ana saura kwana huɗu, aka kira mai lalli ta zo ta yi wa amare. Sun sha kyau iya kyau domin mai lallin ta iya sosai. Events kuwa tun ana saura kwana uku aka fara, duk da Nasreen ba ta so, ita da agonta, amma sun yi dole. Amare ana ya gyara da shirin biki Allah ya ba da zaman lafiya. Wasu mazan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 43 Damir sai zumuɗi yake yi sosai yake farinciki. Jin sa yake kamar bai taɓa aure ba, musamman yadda ya ga amaryarsa ta dawo. Ta yi kyau ta cika tamkar wata a cikin taurari. Annur ya same shi a ranar walima, yana dariya domin tafiya ya yi. Damir ganinsa ya ɗaure fuska. "Haka za ka yi mini Damir? Daga tafiya sai ka lallaɓe ka aure mini wacce nake so?" "Da ma ba gurin ka bane shishshigi ka yi." Ya ce masa yana harararsa. Dariya ya yi yana faɗin,"To kuma mene ma jin haushi bayan ka cinye wasan?" "Dama Nasreen tawa ce haɗin Allah ne ni da ita." Ya furta masa yana kallon sa. "Haka ne domin saura kaɗan a kashe ni saboda kishi, duk da cewar har ga Allah a lokacin da na ganta sonta nake yi, amma bayan Marwana ta gaya mini komai, sai na ga kai kafin cancanta ka aure ta, don haka a rinƙa kunnaka har ka furta mata soyayya. Yanzu ina girman kai da aji?" "Babu duk na manta ina da su, domin a gabanta kamar ƙaramin yaro na ke dawowa, sai na yi abin na yi ta mamakin kaina." Dariya suka kwashe da shi sai ya kalle shi ya ce,"Ya kamata kayi mini kyauta gaskiya, domin ƙila sai wani ya ɗauke ta za ka farga." "Kar ka damu, ɗanmu na farko sunanka zan sanya masa." Jin abin da ya ce sai suka ƙara kwashe da dariya. "Wato har an fara maganar yaro tun kafin a tare? Na san cewa Allah kaɗai zai ƙwace ta, a gurin wannan gwauron, saboda Damir duk a cikinmu yana son matarsa, kuma yana girmama aure da mata." Cewar Ibrahim yana dariya. "Mata ai abin kula ne domin su ne tushen kowa. Shi ya sa na ke mamakin WASU MAZAN da suke wulaƙanta su." Cewar Annur. Dariya suka yi, suka ci gaba da tsokanarsa har suka tafi gurin walimar. Ranar Juma'a aka ɗaura auren Marwana da Ahmad. Dubban mutane manya da masu kuɗi sun sheda, sannan aka ƙara gabatar da auren su Damir da aka ɗaura babu shiri. Su Maman Muwaddat da Fadila, an sha biki duk da tana jego, duk sai da ta halacci events ɗin. Sosai ta yi farin ciki ganin yadda Damir yake nan-nan da ita, domin ko a gurin events ɗin tamkar zai mayar da ita cikinsa. Kunyar da ya ba ta kuwa yafi a ƙirga. Idanunsa na kanta duk inda ta juya. Sun kasace cikin tsanannin farinciki sosai waɗannan ahalin, musamman ma'auratan. Damir da Ahmad ba ki har kunne suna karɓar baƙi cikin farinciki. Nasreen tana zaune a cikin ɗakinta cikin lulluɓi. Kuka take yi sosai dangin Mama da ita suna mata nasiha. Sosai take yin kuka duk da ta sa halin Damir, amma sai zuciyarta take mata tunanin in har ya canza fa? Ji ta yi tsoro ya kamata har ta ji auren ya fita a ranta. Tunanin wane irin zama za su yi ya fi ɗaga mata hankali. Wani shashi na zuciyarta ya kore wannan tunanin, tare da ba ta shawarar ta yi tunanin zaman lafiya da zuriya mai ɗorawa. Sai kuma ta tuna ta rabu da yaranta kenan, dole su zauna a gidan Mama. Tausayinsu ya kamata. Ta rungume su tana kuka sosai, ganin su ma suna kukan za su bita. Zainab ta ɗauke su ta fita ɗakin da su. Rarrashinta suka yi suna bata baki har ta yi shiru. Sosai suka yi mata nasiha, sannan aka sakata a mota sai gidan su Damir, wanda daga nan za a kaita gidanta. Mommy rungume ta ta yi cikin tsanannin farinciki. Sosai take masa murnar samun mata kamarta, musamman da tun da suka fara soyayya ta canza shi ya dawo kamar da. Ya koma cikin farinciki da annashuwa. Da ƙyar aka ɓamɓare amarya Marwana aka sanya ta a cikin mota, wacce take ihu tana kiran Mommy ganin da gaske za ta bar gidan. A motar ita da Nasreen ce da a kayi shawarar ta rakata, don sai da ta shiga cikin motar sannan ta natsu ta yi shiru. A cikin motar hannunsu rungume da juna sai hawaye suke yi. Da aka shiga Nasreen ta ji daɗin yadda danginta suke yabon gidan. Dirama bai tashi ba sai da Nasreen ta mike za su tafi. Sai kawai ta saka kuka ta rungume ta ka cewar babu inda za su tafi. "Nasreen don Allah kar ki tafi." Ta ce tare da ƙara riƙe ta saboda tsoron Ahmad ta fara ji. "Kar ki manta wanda zan barki da shi kamar ni ne. Ya Ahmad ne ɗan'uwana ne kuma yana da tausayi." Share hawayenta ta yi jin ta karfafa ta, sai ta kalle ta ta raɗa mata a kunni."Don Allah ki bawa Ya Damir kula sosai, kar kunyarki ta sanya ki cutar mini da shi. Kin san ya daɗe babu aure, kuma ina fatan ba ki ba da kai bori ya hau ba, saboda yau ne za ki samar wa kanki mutunci a ɗakinsa, kuma zai yi ɗokin ranar, amma in har kin amince da shi kafin tarewar babu wani ɗoki a tsakaninku." "Ba ki da kunya yayarki ce ni." "Or na manta, amma kuma ni ma haka yayarki ce." Dariya suka yi sai suka rungume juna. "Allah ya bamu zaman lafiya da mazajenmu. Mun zama 'yan'uwa jini ɗaya. Ina fatan zumuncin mu ya ɗore har abada." "In sha Allahu Anty Nasreen." "Ina fatan haka Anty Marwana." Sai kawai suka ƙara kwashewa da dariya a tare. Ganin ta sake ta yi mata sallama, sai suka tafi a barta ita da ƙawayenta da za su sayi baki. Nasreen daga gidan Marwana aka wuce da ita gidan Damir. Gida ne mai kyau sosai, domin yadda ta ga cikin gidan a hoto har yafi kyau a zahiri. Sosai gidan ya burgeta don ko ina ya yi mata. Ko a tarihin rayuwata ba ta taɓa tunanin zata zauna a irin sa ba, ko lokacin da Faruk ya aure ta gidan shi, gani ta yi ya wuce da zamanta, amma sai ga shi yau Allah ya ba ta gidan da ya fi shi kyau. Tabbas ta yarda da cewar raba bawa da arzikinsa mutuwarsa. Bayan kowa ya tafi ta ƙara duba cikin gidan. Sama ne kawai bata hau ba, domin kamar a kulle yake. Tana zaune zuciyarta na bugawa tana ƙaranto addu'a. Sosai take jin tsoron gidan da mai gidan. Lamarin da ya faru tun farkon haɗuwarsu ya dawo mata. Hawaye sosai take yi tana addu'a. Ɓangaren su ango kuwa, bayan dare ya yi sun tabbatar da amare sun isa ɗakinsu, sai aka kama shirin zuwa gida. Damir bai buƙaci kowa ba acewarsa shi ba yaro bane. Shi kaɗai zai sayi bakin amaryarsa da yake jin kamar ya yi tsuntsuwa. A ransa shi kaɗai ya san zumuɗin da yake ji. Dariya sosai suke mishi ganin har yafi Ahmad sabon shiga ɗoki. Shi da Ahmad tamkar abokai, suka zama domin sun ije sarakutan a gefe. Siyyayya Damir ya yi, sannan ya tafi zuwa gidansa. Wani iri ya ji tuna rayuwar da suka yi da Batula, har sai da hawaye suka wanke masa fuska, amma sai ya gode wa Allah tun da Ubangiji yaba shi mace ta gari, kuma wacce a yanzu yake jin in har babu ita rayuwar sa sai a hankali. Nasreen na zaune da carbi a hannunta tana ja, don har yanzu zuciyarta bugawa take yi da ƙarfi. Bugun zuciyarta ya ƙaru, daidai da ji an buɗe get ya shigo da motarsa. A hankali ta yaye labulen windon tana kallonsa, daidai lokacin da ya fito suna gaisawa da maigadi. Ƙoƙarin saita natsuwarta ta yi, jin alamun tafiya yana ƙoƙarin buɗe ƙofa. Bugun zuciyarta ya ƙaru, ganin ya buɗe kofar shigowa falo da sallama. Cikin murya ƙasa-kasa ta amsa masa kanta na duƙe, saboda bata tunanin ya ji amsawar da ta yi. Ya ɗan yi Jimm yana kallonta, zuciyarta cunkushe da ƙaunarta. Tsawon lokaci wata ɗaya da Mommy ta sanya yau ga shi ga matarsa a gida ɗaya. Daga shi sai ita, sai kuma iskan Ubangiji da yake kaɗawa, yana saukar musu da farinciki a wannan ranar. A hankali ya ƙaraso ya zauna a gefenta. Ajiyar numfashi ta sauke jin ya kira sunanta. Sai ta rasa abin da za ta je masa. Ganin ta yi shiru, sai ya ja gyalenta tare da duƙawa yana kallon fuskarta, murmushi ɗauke a fuskarsa. "Sannu da shigowa." Ta ce masa kamar wacce aka yi wa dole "Nasreen," Ya kira sunanta cikin shaƙaƙƙiyar murya, domin turarenta ya fara rikita shi. Cikin jin kunya ta amsa da."Na'am," Ba tare da ta ɗaga idanunta ta kalle shi ba. "Please look in to my eyes." Ya ce mata yana kallon fuskarta. Jarumta ta yi, ta ɗaga idanunta don ta kalle shi, amma da sauri ta mayar da idanunta ƙasa, saboda abin da ta gani a idanunsa sun rikitata. "Nasreen ina son ki. Wane irin tarba zan samu yau?" Mamaki sosai ya kama shi lokaci da ya ga hawaye a fuskarta. Lokaci guda ya firgita ya fara tambayarta. Tunawa ta yi ranar amarcinsa irin yada ya tafi. "Oh please stop crying ko kina so na yi?" Yadda ya yi maganar da ɓata fuska da ya yi, ya sanya ta saki dariya ba tare da shiri ba "Kin ga yadda kika yi kyau? Gaskiya kuka da ɗaure fuska ba ya miki kyau." Murmushi ta yi bata ce komai ba. Ganin sun yi shiru na wani lokaci sai ya yi ajiyar zuciya ya ce,"Wane fata kike yi wa aurenmu?" Ganin ya yi maganar cikin rashin wasa sai ta daure ta ce,"Ina fatan mu kasance cikin farinciki, sannan mu gudanar da rayuwar aurenmu, cikin tsarin Musulunci da koyarwa ta Annabi Muhammad (A.W.S)" A tare suka ƙarashe. Jin ta yi shiru ya ce,"In sha Allahu za mu yi rayuwarmu cikin tsarin Islama, sannan mu samu zuriya ɗayyiba. Fatana duk shekara ki yi wa Little Marwana ƙanni." Zare idanunta ta yi ba tare da ta ce komai ba. Dariya ya yi sannan ya miƙe. Mu je mu yi alwala, sannan mu yi sallah. Mu roki Allah ya bamu zaman lafiya mai ɗorawa." Ya ƙarashe maganar tare da kama hannunta. Wani iri ta ji haɗuwar hannunsu. Kasa cewa komai ta yi, tana jin kamar ta janye hannu. Duk da yanayin da ta shiga nasa ya fi nata, amma sai ya jure suka nufi bedroom ɗinsa a sama. Kallo ɗakin ta yi ganin yadda ɗakin ya tsaru. Damir rage baban rigarsa ya yi, sannan ya kalle ta ya yi murmushi ya wuce bayi. Tana tsaye ya fito daga bayi bayan ya yi alwala. ""Ki shiga ki yi." Ya ce mata sannan ya wuce wandrop na sa ya ɗauki dadduma ya shinfiɗa musu. Da ta shiga bayin, sai da ta ƙare masa kallo saboda ɗaukar hankalinta da ya yi. Bayan ta yi alwalar ta fito. Mamaki sosai ta yi ganin ya ije mata hijabi. Tunani ta fara ko ɗauko mata ya yi. Ba tare da ce masa komai ba, ta tsaya a bayansa ya fara ja musu sallah Nasreen hawaye ta ji yana zuba a ƙuncinta, jin yadda yake sallar cikin natsuwa yana jan aya. Ba ta ƙara farinciki ba, sai da ya ja sallar raka'a biyu, sannan ya dafa goshinta ya yi addu'ar da Annabi ya koyar da mu in mu yi sabon aure. Ya kuma shiga jero addu'a. Sai ta ji hawaye yana zuba mata, tuna ranar aurensu da Faruk kamar dole aka yi masa ya yi sallar. Yana gama sallamewa ya jawo kazarsa. Ya daɗe yana mata addu'a, sannan ya sauke hannunsa yana kallonta. Sunkuyar da ka ta ta yi ƙasa ta yi, tana godiya ga Ubangiji da ya ba ta mijin da take so, mai addini da aiki da shi. Damir kallonta yake yi sai ya rasa ta inda zai fara. Kunyarta ya yi yawa, kamar ba ta taɓa aure ba. Ya tabbata da wata matar ce ya aura a matsayin bazawara, abin da za ta yi mishi sai ya yi mamaki. Gyaran murya ya yi, sai ta kalle shi a kunya ce tana hamma. "Bacci? Bai kamata ki ji bacci a ranar yau ba." Abin da ya ce da kallon da ya yi mata ta kasa cewa komai. Janyo ledar da ya shigo da ita. Kayan ciye-ciye da kaji ne a ciki sai kuma naman balango, da kuma fannin drinks kala-kala. Da kansa ya miƙe zuwa kicin, ya ɗauko musu filet da spoon sai ƙaramar wuƙa. Yankan namar kazan ya yi, yana murmushi ya kai mata baki. Da sauri ta kauda fuskarta cikin jin kunya."Nasreen na fara gajiya da wannan kunyar ta ki, a haka za mu raya wanann daren?" Kasa amsa masa tambayar ta yi."Na ƙoshi Mommy sai da ta tabbatar mun ci abinci da Marwana, sannan ta barmu muka tafi gidan Marwana." "Amma tun yaushe kika ci? Kuma ko kin ci abinci dole na ciyar da ke a First night ɗinmu. Please ki ci ko babu yawa." Ya furta cikin sigar rarrashi Ba ta karɓa ba sai ta kalle shi za ta yi magana. Ganin yadda ya ɓata ransa sai ta buɗe baki a kunya ce."Good girl." Ya ce tare saka mata naman kazar. So take yi ta ɗan saki jikinta, amma sosai take jin kunyarsa, kuma shi yake ƙara sanya mata kunyar da irin kallon da yake mata. Har yau ta kasa sabawa da kallon da yake mata, domin ita kaɗai yake yi wa. In har zai yi magana da ita, sai ya canza kalar idanunsa. Ganin ba za ta ci ba sai ya yi mata dole tasha drink. Kayan ya kwashe ya kai kicin ya sanya a frij. Tana zaune ko motsin kirki ta kasa. Ganin ya nufi wandrop nasa, zai sanya kayan bacci cikinta ya ɗuri ruwa. "Ya Damir, zan je na canza kayan bacci." Juyowa ya yi ya watsa mata kallo, saboda ya fahimci guduwa za ta yi. Ganin yana ƙoƙarin cire rigarsa ta kauda idanunta, sai ya rage hasken ɗakin. "Please Baby stop calling me Ya Damir. Daga yau ina son ki canza mini suna ga sunaye masu daɗi na ƙauna." Ya ce baya ya cire rigar, ya rage da ga shi sai singeleti da dogon wandon shaddar. Yana ƙoƙarin cire agogonsa ya nufo inda inda take. Ganin haka sai ta yi kamar za ta ruga. Kamar ya sani ya sanya hannunsa ya riƙo ta yana dariya. Ita ma dariya abin ya ba ta, saboda yadda ta zabura kamar ta ga wani zaki. Kunyarsa sosai ta ji da ya haɗata da jikinsa. Jikinta ya fara rawa har sai da ya gane."Nasreen kin cika kunya don Allah ki saki da ni. I don't bite. Wannan abin ƙaramar yarinya ya kamata ta yi haka, amma ke kamata ya yi ki nuna mini soyayya kuma ki yi pampering ɗina." "Don Allah, ka bar ni na canza kaya bacci sun yi mini nauyi." Ta ce cikin rawar murya ganin yana ƙoƙarin haɗa fuskarsu. "Ok," Ya ce tare da kama hannunta ya ƙarasa dayan wadrop ya buɗe."Kin ga waɗannan kayan Nasreen, ni na siyo da na je Dubai, saboda ina son matata na ganta da ƙananan kaya. Lokacin Batula ta saba in har ba fita za ta yi ba, ƙananan kaya ne a jikinta kodayaushe. Haka kuma nake so ki zama, ga kuma kayan bacci nan suma duk na ƙaro miki." Wani irin azzabben kunya ya lulluɓeta, ganin ya ɗauko doguwar riga ya bata. Kallonsa ta yi, yayin da ya ɗaga mata gira alamun ta saka. Rigar ba ta da maraba da babu. Tana da kyau sosai, amma irin transparent ɗin nan ne." Girgiza masa kanta ta yi, sa kawai ta fara hawaye ƙila ya fahimci tsananin kunyarsa da take ji, tun da ta gama fahimtar ba yi da shi. Ashe dama haka yake. Ganin hawayen, sai ya ɗauko mata riga da wando purple masu kyau. Karɓa ta yi ba tare da ta ce mishi komai ba ta wuce bayi. Zama ya yi kan gadon bai ce mata komai ba, saboda yasan dama ba za ta iya canzawa a gabansa ba. Har ya zauna sai kuma ya miƙe ya canza kayan shi zuwa na bacci. Nasreen da ta sanya kayan, sai ta tsinci kanta da kasa fitowa. Ita kam ta ƙosa gari ya waye. Ko daren amarcinta da Faruk ba ta ji kunya haka ba. Wayarsa ya janyo yana duba pictures na bikin, amma har ya gaji da dubawa ba ta fito ba. Ije wayar ya yi, ya nufi bayin domin ya fara tunanin kwana za ta yi. Yana ƙoƙarin ƙwankwasawa ta fito kamar mara gaskiya."Da a bayin za ki kwana?" Ya yi mata tambayar cikin mamaki. Ba ta amsa mishi ba, sai ta ƙarasa tsakiyar ɗakin ta tsaya. Damir ya lura in har ya biye mata sai dai su ji kiran sallar asuba. Don haka ya jawota ya haɗata da jikinsa. Ajiyar zuciya suka saki a tare, lokaci guda kuma suka sauke numfashi. "Wannan ɗan kunnen, ya yi miki girma Please baby ki kiyaye, saboda ba son kina wahalar mini da kanki." Murmushi ta yi cikin farinciki, ba ta ce masa komai ba, har ya cire ɗan kunnen ya ije kan mirror. Fuskarsa ya kai a dogon wuyanta, yana saukar mata da numfashin da yake sanya mata kasala. "Nasreen kin ga ikon Allah ko? Ubangiji dama tun farko ya riga ya san zamu yi aure, shi ya sa ya haɗa ki da Marwana. Nasreen yau kin zama matata, bayan tsawon lokacin da na ɗauka ina dakon sonki. Ina sonki kuma na yi miki alƙawarin kulawa da rayuwaki har da yaranki. A shirye na ke na zama ubansu, in har kin amince za su dawo gidan nan." Da sauri ta kalle shi cikin mamaki."Yes na zama mahaifinsu tun da kin zama matata. Zan haɗa su da Little Marwana na riƙe." "Na gode Ya Damir, ba ni da abin da zan ce maka da 'yar uwarka." Ta furta tare da sakin kuka. Sai a lokacin ya tuna da Marwana, ya san tana can tana yi wa Ahmad shagaɓa, domin yau Allah kawai zai shawo masa kanta. "Is ok, kin cancanci haka domin kin sha wahala. Zan kula da rayuwarki yadda babu wata mace da za ta fiki." Ya ƙarashe maganar tare da rungumeta yana sauke numfashi. Duk da tana jin kunyarsa, amma albishirin da ya yi mata, sai ta ji ta kasa janye kanta daga gare shi. Ganin haka ya ƙara matseta sosai. A hankali ya haɗa fuskarsu yana ƙoƙarin ɗauke mata hawayen da harshensa. Ganin haka ta kauda fuskarta cikin wani yanayi. Janyota ya yi suka faɗa gadon ya yi mata rumfa. Damir Gabakiɗaya ɗaya ya birkice, mata domin ƙamshin turarenta ya fara aiki. Tun tana ƙoƙarin turesa har ta gaza don ya canza mata, saboda bai san tana yi ba. Tabbas a ranar ta shigar da shi wata duniya. A ranar ta san ta yi aure, kamar yadda ranar ta zamar mata ranar mai mahimmanci haka Damir. Gabakiɗaya ya rikice ya susuce sai aika mata da tsaƙon soyayya yake yi mai rikita zuciya. Kamar ba oga Damir mai ɗauke fuska da jiji da kai ba. Yau ya zamar mata daban, ya koma kalar da bata taɓa sanin sa ba, domin ya bata alakar kula da rayuwarsa. A wannan lokacin tamkar bawa yake da sarki. Ansha soyayya kuma an bawa soyayya haƙƙinta. Iya lokacin da soyayyar ta ɗauka tana wahalar da rayuwarsu. Damir sai da ya fashe musu ita, domin ya kaisu duniyar da suka shagaltu. Nasreen, ta gode wa Marwana sosai na shawarar ɗinkin da ta bata, domin ɗinkin da magungunan da ta sha, sun kai shi wata duniyar da ban. Shi kansa kunyar kasa ya yi, ganin babu ji da kai duk girman ya faɗi a gurinta. Nasreen kam an sha wahala sosai domin mijin nata gwarzo ne. Har kuka sai da ya sha, amma bai kula ta ba domin ya yi nisa a cikin duniyar da dole sai an isa. Saboda tsananin farinciki, rungumeta ya yi tamkar zai mayar da ita ciki."Ina alfahari da ke matata Nasreen, haƙiƙa yau ko kwana sallah na yi ba zan iya biyan Ubangiji na kyautar da ya yi mini ba. Ina godiya ga Allah da ya mallaka mini ke. Allah ya barmu tare mu yi tsawon rai, kuma ya albarkaci zuriyarmu." Ya ce yana shafa kanta. Hawaye sosai ya wanke mata fuska, bayan kukan da ta ci saboda ɗinkin ya sanya ta dawo tamkar sabuwar amarya. Ji ta yi kamar ta kauda saura kunyarsa da take ji. Ta rungume shi. Haƙiƙa yau ta fahimci ita ma macce ce, wacce duk namijin da ya same ta zai yi alfahari. Ba ta a cikin matan da Faruk ya sha gaya mata sun rako mata ne. Tana da nata baiwar domin ta ga zahiri, duba ga yadda tsadadden namiji kamar Damir ya rikice. Ita ma mace ce wacce za ta yi alfahari da kanta. Wayyo amarci mai daɗi amarya da ango sannunku da amrci. Wasu mazan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 44 Ta ga zahiri domin Damir rasa inda zai sanya ta ya yi. A wannan lokacin ya sanya ta miƙe suka yi wanka. Raka'a biyu na godiya ya sanya suka yi. Sai kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikinsa."Allah ya cika mini burina na samu miji mai addini. Allah na gode maka. Ina fatan za ka tarbiyantar da yaranmu su samu ilmi kamar kai?" Abin da ta faɗa, ya ƙara sanya masa darajarta a idanunsa."In sha Allahu Nasreen. Zan bawa yaranmu ilmi fiye da nawa." "Na gode mijina." Ta furta tana share hawaye. "Zo mu je ki kwanta kina buƙatar bacci." Ya ce mata ba ta yi aure ba sai ta ji ya ɗauke ta zuwa kan gadon. Kunya da farinciki suka lulluɓe ta. Jikinsa ya jawota yana shafa bayanta, domin har addu'ar bacci shi ya yi mata. Rintse idanunta ta yi alamun ta fara bacci take yi, amma ta kasa baccin saboda murna. Fahimtar haka da ya yi, ya kai libs ɗinsa saman nata. Bacci dai da ba a yi ba kenan, sai da aka ƙara raya daren, sannan ya ja bargo ya lulluɓe su saboda wani irin bacci da ya kama su. To amarya Nasreen sai na ce asuba ta gari ango har da kai. Gareku zawarawa, Allah ya sa ku yi koyi da kunyar da Nasreen ta yi. Bari mu leƙa gidan amarya Marwana da angon ta Ya Ahmad. Bayan Damir ya tafi, wasu daga cikin abokansa suka bi shi don siyen baki. Marwana tana zaune a falo ita da ƙawayenta, suna jiran ango da abokanansa. Jin alamun buɗe get sai zuciyarta ta buga. Duba wayarta ta yi, ganin ya yi chatting ɗinta ta Whatsapp sun shigo. Gyara zaman ta yi, tana jin yadda zuciyarta ke zillo kamar za ta fito waje. Da sallama suka shigo suna ta tsokanar Ahmad. Ahmad kai tsaye, inda take zaune ya ƙarasa ya zauna."Amaryata da fatan bamu barka jira ba?" Ya yi mata tambayar yana kamo hannunta. Ƙasa ya yi da kanta batare da tanka ba. Ƙawayen ta suka ta so wata daga ciki ta ce,"Mu ya kamata ango ya tambaya ba amaryarsa ba, domin iyayenmu suna can suna jiranmu." "Yanzu za mu sallame ku." Bilal ya ce. Sannan ya juya gurin amarya ya ɗora da cewa," "Ai ashe amaryar taka tana da kunya ba kamar ka ba?" Kwashewa da dariya suka yi. "Tana da kunya mana, ko ni zumar sonta ya sanya na rinƙa gaya muku haka." "A'a to, bari mu yi mu siya baki kar a kore mu." "Ku dai yi sauri kar ku ɓata mana lokaci." Ya ce yana dariya. Bayan sun gama barkwancin suka yi addu'a, sannan suka shafa suka siyi bakin. A motar su suka tafi da 'yan matan. Ahmad ya raka su har get ya dawo ya kulle ƙofar gidan. Ya shigo tana zaune a falo. Hannunta ya kama yana murmushi. "Marwana yau kin ga mun zama ma'aurata?" Ya ce mata cikin zallar mamaki. "Ni ma ina mamaki Ya Ahmad, ban taɓa tunanin haɗuwarmu da Nasreen zai haɗa mana zumunci." "Haka Allah ke lamarinsa autar Mommy." Rufe idanunta ta yi jin abin da ya ce. Kamar yadda addini ya sharada suka yi sallah, sannan ya yi mata addu'a. Marwana, ta ci naman kaɗan saboda ta saba da Ahamd sosai. Duk da yau ne amarcinsu ba ta ji kunyar sa sosai ba, sai dai tsoro da take jin kamar zai fasa zuciyarta, musamman yadda ta ga yana mata. Suna zaune suna hira, yana bata labarin yadda ɗaurin aurensu ya kasance. Ganin tana hamma ya kalle ta ya ce,"Ki je ki kwanta." Kamar jira take yi ya ce mata, sai ta miƙe ta shiga cikin ɗakinta. Bayan ta canza kayan baccin, sai ta yi kwanciyarta a ɗakinta. Tashi ya yi ya kulle falin, sannan ya shiga ɗakinsa, ya yi wanka ya ɗauki wayarsa zuwa ɗakinta. Bugawa ya yi, ta taso ta buɗe tana hamma don har bacci ya fara kamata. Matsawa ta yi ya shiga yana faɗin,"Na ɗauka ɗakina za ki kwanta babyna?" Kunya ta ji ta ce,"Am sorry Ya Ahmad baccin ne ya kwashe ni kan kujara." Ta yi masa ƙaryar haka. "Ok, babu komai gajiyar biki." Ya ce tare da zama gefen gadon. Sakin ƙofar ta yi, ba tare da ta kulle ba ta koma kan kujera ta zauna. Ganin haka ya kulle kofar ya koma kan gado. "Ki zo ki kwanta." "No, zan kwanta a nan ba, saboda a gida a kan kujera na ke kwana na fi bacci." "Shi ne ba ki gaya mini ba da sai na koya, don kin san babu yadda za a yi na barki ki kwanta ke kaɗai, dole na kula da amanar da Ya Damir, Nasreen, da Mommy har da Mama suka ba ni." "Ai muna ɗaki ɗaya ka yi baccinka." Ta ce tare da kwanciya kan kujera. "Ba za a yi haka ba, saboda in sauro ya cinye ki mai zance wa waɗanda suka ba ni amanarki?" Dariya ta yi jin wayon da yake son mata, kamar ƙaramar yarinya."Kujerar ya yi mana kaɗan." "Ok, to ki kwanta a gadon bari na kwanta a nan." Ta buɗe baki za ta yi musu, sai ya watsa mata kallo. Babu musu ta koma ta kwanta tare da jan bargo."Good night Ya Ahmad." "Good night." Ya ce mata yana dariya jin yau ko sunan soyayya ba a kira shi da shi ba. Tana kwancen a tunaninta wayo zai yi mata, amma tun tana tunanin zai jawo gadon, har ta cire bacci mai ƙarfi ya kwashe ta. Ahmad yana kwance, yana lura da ita sai da baccin ya kwashe ta, sannan ya hau gadon ya haɗata da jikinsa. Cikin bacci ta ji sa a jikinsa da sauri ta miƙe. "Let's sleep baby." Ya ce mata da wata kalar murya. Tsoro ta ji muryarsa sai ta kwanta. Duk dai kauce kauncenta sai da ya shawo kan abinda ya amshe sadakinsa. Yasha kuka don babu wanda ba a kira ba. Hatta Damir da Nasreen da suka tafi duniyar sama sun sha kira. Cikin farinciki ya rungume abinsa yana rarrashi. Bayan sun yi wanka sai bacci. Kamar yadda Damir yake jin daɗin baccin haka Nasreen, domin za ta iya cewa tun da take bata taba yin bacci mai daɗi irin sa ba. Kiran sallar asuba ya farkar da Damir. Ya buɗe idanunsa a hankali yana tuna daren jiya. Murmushi ya saki cikin tsananin farinciki tare da ƙara rungumeta. A hankali ya zare jikinsa tamkar wanda ya shinfiɗar da jariri, saboda har filo ya tura mata a kusa da ita. Duƙawa ya yi ya sumbaci gefen fuskarta, sannan ya nufi bayi ya yi wanka da alwala. Raka'atul fijr ya yi, sannan ya ɗauki Alqur'ani yana kara yawa cikin ƙira'a mai daɗi. Nasreen da take kwance, tana kasa kunne don ta saurari karatun, duk da ya rage muryarsa saboda kar ya tashe ta, amma ba tare da ya san ta riga shi tashi ba. Wasu hawayen farinciki suka gangaro mata. Yau ita ce Allah ya ba ta mijin da zai tashi tun asuba ya yi sallar nafila, sannan ya yi karatu yana jiran ayi sallah. Hawaye sosai yake zubar mata cikin tsantsar farinciki. Tana jin yadda yake rera ƙira'a yana fitar da tajweedi. Yana ta karatun idanunta lumshe tana saurarensa. A zuciyarta ji ta yi kamar ta ɗauro alwala su yi karatun tare. Sai dai tsanannin kunyarsa da take ji ba zai ta iya ba. Murmushi ta yi tuna abin da ya faru jiya. A daren jiya ta daina mamakinsa, domin ya wuce duk inda take tunani. Tabbas Damir ya san kan sace zuciyar mace. A irin zumar da ya shayar da ita na ƙauna, sai ta daina ganin kishin Batula domin tana jin a yadda ta kamu da sonsa, da yadda yake kula da mace za ta iya aikata hakan. Damir duniya ne tabbbas ɗan soyayya ne. Ya san yadda zai sarrafa mace, ta kasa ganin kowa sai shi ta kowa ne ɓangare. Tunawa ta yi zai iya ƙara aure lokaci guda ta ji zuciyarta na shirin bugawa.🙄🙄🙄🙄 Tana wannan tunanin ba ta san har an kira sallar asuba ba. Tashi ya yi, ya rufe qur'anin ya tafi masallaci. Yana fita ta miƙe da sauri ta shige bayi. A gurguje ta yi wanka ta ɗauro alwala. Saboda tana jin kunyar ya shigo ba ta ja doguwar raka'a ta sallame. A ka gado ta yi azkar na sallah. Bayan ya yi sallah sai ya shigo cikin gida don ya tashe ta, kar lokaci ya ƙure. Tana jin alamun buɗe ƙofa ta ja bargo har saman kanta. Sai dai kafin ta ja ya ganta. Murmushi ya yi tare da ƙarasa wa kan gadon ya hau. Mamakin yawan kunyarta yake ji. Shi da ya san ance mace bazawara sam ba su da kunya, amma ya yi mamaki ko kuma dai tasa ce a haka. Kan gadon ya hau tare da kai hannu zai ja bargon. Kamar ta gane nufinsa sai ta juya ta cukurkuɗe shi a jikinta. Murmushi ya yi."Matata Nasreen," Ya furta tare da ƙara kai hannu, ya fara ƙoƙarin cire bargon. "Lokacin sallah zai wuce ko tashi, dalilin da ya sanya na barki ki huta, saboda na san na wahalar da ke, amma da asuba ya dace ki yi." "Please Ya Damir nayi sallah." Ta furta da muryar kuka, ganin zai cire mata bargon kuma akwai wadataccen haske a ɗakin. Dariya ya yi,"Ban yarda ba domin kaya bacci ne a jikin ki." Ya ce bayan ya ja bargon. Da sauri ta riƙe tana faɗin,"Na canza wannan fa pink ne." Cikin muryar shagwaɓa ta ce mishi. Burge shi ta yi domin yana son shagwaɓar."Ok na yarda amma mene ne na jin kunyata? Ai na yi tunanin na cire duka kunyar?" "Don Allah ka bar ni bacci zan yi." Ta ce masa tare da satan kallon sa domin kunyarsa take ji. "Ni ma bacci zan yi mu kwanta matata. Yau hutu za mu yi." Ya ce mata tare da kwanciya ya jawota jikinsa. Duk kunyarsa da take ji, kan dole ta kyale shi suka kwanta, domin ta san ba zai barta ta kwanta ita kaɗai ba. Ba su tashi bacci ba har sai karfe goma shi ma kiran Muhsin ya tashe su. Goge idanunsa ya yi sannan ya ɗauki wayar yana faɗin,"Muhsin," "Na'am Ya Damir. Ina bakin get Breakfast na kawo in ji Momi." "Ok ina zuwa." Ya ce tare da sauka kan gadon. Yana fita Nasreen ta miƙe ta ɗauki wayarta ta nufi ɗakinta. Wanka ta shiga bayan ta gasa jikinta, saboda har yanzu duk joint ɗinta ciwo suke mata. Bayan ta fito daga wanka, ta zauna ta cancaɗa kwalliya, sannan ta sanya atamfa riga da siket mai kyau. Wayarta ta ɗauka ta kira Marwana. Marwana da an ci kuka har an bawa uku lada. Ko da Muhsin ya kawo abinci sai dai Ahmad ya karɓo, amma bai ganta ba. Tun dare yake aikin rarrashi, amma kamar kara tunzurata yake yi. Kalmar mugu kam ya sha babu adadi. Shi kansa ya tausaya mata, domin bai san ya zaƙe da yawa haka ba. Da kyar ya samu ta yi sallah sannan ta sha magani. Tsoro ya ji ko sai an yi mata ɗinki. Yanzu haka ma kiran likita ya tafi Nasreen ta kira. Tana ɗauka ta rushe mata da kuka."Nasreen kin ce Ya Ahmad zai kula da ni, ashe mugu ne?" Dariya ta ba ta sosai, duk da tambayar da gaske ta yi mata. Sai ta ba ta tausayi, domin ko ita da ta taɓa aure ta san wuyar da tasha. "Marwana ki yi haƙuri, wannan shi ne auren ke ma kin san haka?" "Na sani amma ai zalinci ya yi mini. Na rantse gun Mommy zan koma." Dariya ta yi jin abin da ta ce,"Ina Ya Ahmad ɗin?" "Ya fita kamar likita ya k.." Kafin ta gama maganar, kawai sai ta gan shi a tsaye ya fisge wayar yana huci. Kunya sosai ya kama shi, ganin da wacce take wayar. "Yanzu kin kyauta Baby. Nasreen ƙanwata ce, amma kika zauna kina gaya mata komai?" "Nasreen ƙawata ce, dole na gaya mata abin da ke damuna." Ta yi maganar cikin zallar shagwaɓa tare da karɓe wayarta. Kunya sosai ya ji dama ya san tun da suka aure su, shikenan sirrinsu yana hannun ƙanni. Ta gaya mata rayuwarsu ita kuma ta gaya mata na su da damir. "Mommy ta kawo abinci ta shi kiyi breakfast, sannan ki sha magani." "Ni ba zan sha ba gida zani." Jawota ya yi yana murmushi, saboda ya gane muguwar 'yar shagwaɓa ne. "Haba autar Momi zuciyar Ahmad." Abin da ya ce ba ta san lokacin da ta yi murmushi ba. "Yauwa haskena let's go and eat." Ya ce mata tare da kama hannunta. Da ƙyar ya samu ta ci abinci, sannan tasha maganin ta kwanta. Shi ma bacci ya koma, saboda jiya bai samu ya rintsa ba. Damir ɗa ya dawo ya ga ba ta a ɗakin. Bayi ya shiga ya yi wanka, sannan ya cancaɗa kwalliya tamkar wanda za shi gasar kyau. Ya yi kyau sosai a cikin ƙananan kaya. Tana cikin ɗaki, tana sanya ɗan kunne ya shigo da sallama. Da sauri ta koma gurin windo ta ɓoye a labule. Ganin haka babu shiri ya saki dariya tare da ƙarasawa kusa da ita. "Yau na zama surukin ki ko Nasreen?" Ya ce yana haɗa jikinsu. Fuskarta ta rufe tana furta,"Ina kwana Ya Dam..." "Shitttt!" Ya ce bayan ya kai hannunsa kan bakinsa. "Ba na son Yayan, saboda yau ya kamata a canza mini suna." "Abban Marwana." Ta ce cikin jin kunya. "Nope wannan is local I need special and extraordinary." "Ok, Rajlul salihi." "Umm partially, saboda so na ke duk za ki kira ni, ki canza mini suna." Zare idanunta ta yi jin abin da ya ce."Yes Nasreen ni da matata tamkar Hassan da Hussaini muke. Don Allah ki saki da ni mu ci amarcinmu, sannan na kwaso kyawawan yaranmu mu yi rayuwarmu cikin farinciki." Murmushi ta yi tare da sunne kanta."Please baby close you eyes, I wanna surprised you." Ya ce mata tare da ɓoye abin da yake hannunsa. "Ok, Husband." Ta ce masa sannan ta rufe idanunta. "Don Allah ki fi ce mini Husband, domin ni na gaya wa Batula ta rinƙa kirana haka, amma da yake ke 'yar baiwa ce kin kira." "Ok, baby." Murmushi ya yi jin ta bi umurninsa."Then did you close?" "Yes I did." Ta ce tare da ƙara rufe idanun sosai. "Ok, You can open." Ya ce bayan ya ɗora mata ɗan kunne da tsarkar gwal a hannunta. Ware idanunta ta yi cikin mamaki ta ce,"Wow! Masha Allah." "My gift for yesterday saboda jiya kin kai ni wata duniya." "Kai Ya Dam... Husband." Ta yi maza ta ce haka ganin kallon da ya watsa mata. "Na gode Allah ya ƙara buɗi, ya tsare mini kai ya kuma ba ni ikon maka biyayya." "Amin," Ya ce cikin farinckin addu'ar da ta yi masa. "Kawo na sanya miki." Ya ce tare da miƙa mata hannunsa ta saka masa. Haɗawa da hannun ya yi, ya sumbaci yatsun da suka sha adon lalli yana murmushi. Ita ma murmushi ta yi masa. "You You look pretty!"Ya ce tare da rungumeta. "Zo mu je mu karya." Ya kama hannunta suka nufi dinning. Duk kunyarsa da take ji sai da ya nace ya bata abinci, domin ta fuskanci ta karɓa shi ne kawai zaman lafiyarta. Bayan sun ci, duk da ba abincin kirki ta ci ba saboda kunya. Bacci ya jata suka koma, domin maigadi ya sanar kar wanda ya shigo. Bacci sosai suka yi, sai ƙarfe ɗaya suka farka. Da ya yi alwala, ya fita daga nan zai wuce gidan Hajiya. Yana fita ta gyara gidan sannan ta zauna tana kallo. Ba ta jima da zama ba, Momi ta kawo lunch. Su Anty Sha'awa suka kira ta suna waje. Suna shigowa ta rungume su cikin farinciki. "A Lallai ka ga amare su Nasreen har an fara kyau, ko dai kin samu ciki ne?" Dariya ta yi jin tambaye banzar da tayi mata."Anty Sha'awa yanzu ne na yi aure. Dama akwai maza 'yan aljanna irin mijina?" "Lallai Nasreen sabon shiga." Suka ce tare da kwashewa da dariya. "Ba za ku gane farincikin da na ke ciki ba. Haƙiƙa in har ya ɗore a haka sai na ce na fi ko wace mace sa'a. Mijina daban yake a cikin maza. Haƙiƙa dole matarsa ta yi kishinsa." "Ai Nasreen ko a ido aka kalle shi an san kin yi dace. Daga gidan Marwana muke ko kaɗan ba ta da matsala. Ba ki ga yadda ta karɓe mu ba, duk da ba ta da lafiya don shi ya yi hidimar gidan." "A Ya Ahmad dole ai ya yi aiki ya taɓo autar Momi." "Aikuwa abin ka da 'ya'yan hutu. Magana kawai ya yi mata, ta fara kuka tana gaya masa kanta bai daina ciwo ba." Dariya ta yi ta ce,"Zai sha shagwaɓa Marwana akwai raki." Shiga kicin ta yi tare da su su ci wannan su ɗauki wannan. Kaza ɗaya ta ɗauko musu suka yi warming ɗin ta. "Ke dai Nasreen, in miki ta Baba ya ce jinin arziki ne dake. Dubi wannan rayuwa, kana irin wannan rayuwa ai mantawa da kowa za ka yi. Farouk ina ma zai zo ya ganki? " "In ya warke daga haukan ba. Ai yanzu shi kansa ba shi da kuɗin da zai ci ko tsire ne, tun da ba lafiya ce da shi ba ya koma aiki." Dariya suka kwashe dashi banda ita."Kai Faruk ya yi tsiya wallahi." Suna zaune a a falo ya yi sallama ya shigo. Da sauri ta mike ta karɓi ledar hannunsa cikin jin kunya. Cikin mutunci suka gaisa, sannan ya haye sama bayan sun ɗan taɓa hira, saboda yadda ya ga ta kasa sakin jiki ta tana ta wani sunne kai sai ya hau sama. Bayan hawarsa sai Anty Sha'awa ta kalle ta. "Nasreen kin shiga uku! Ni fa mamaki kike bani saboda kin cika kunya. Na samu irin wannan mijin wallahi agaban kowa zan nuna masa ƙauna, amma sai wani sunne kanki ki ke yi kin kore shi." "Kai Anty Sha'awa hutawa zai yi." "Ba wani nan mu bari mu tafi ki je gurin mijinki. Haba sai ka ce ba yar boko ba? Ki zauna kina jin kunya, wallahi wata ta yi wuf da shi yadda yake da kyau nan." Nan take fuskanta ta canza, ita kanta ta yi mamakin haka.Kama ba ki suka yi suna dariya."Ai kuwa dole ki dage, don wallahi irin waɗannan mazan dole sai kin fetse don ki ɗauke hankalinsa." Suna ƙoƙarin fita ya sauko. Gyaran murya ya yi suka kalle shi."Anty Sha'awa tafiya za ku yi?" Ya ce yana kallon su. Ji ta yi kanta ya faɗi, har sai da ta kasa ɓoyewa, ganin mutum kamarsa ya kira ta da Anty. "Eh wallahi ai mun daɗe." "Ok bari na saya direba ya kaiku. Ga wannan mun gode da hidamar da kuka yi da biki, sai mun zo ban gajiya." Baki suka washe cikin farinciki. Kalmar zai kawo ta abin ya ba su mamaki, domin har ta gama zama gidan Faruk ba sa tunanin ya san gidansu. "Sai kun zo Allah ya kawo ku." "Amin ku gaida hanya." Tare suka raka su harabar gidan har suka tafi. Nasreen sai ta ji wani sonsa ya ƙara mamaye ta. Ganin yadda ya daraja 'yan'uwanta. Suna tafiya ya kamo ta ya haɗa da jikinsa."Wato ke har a gaban mutane ba za ki iya ɓoye kunyata ba ko?" "Akwai Baba maigadi fa." Ta ce za ta janye jikinta." Wasu mazan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 45 "Yana ɗaƙinsa, kuma ni da gidana sai na kasa rungume matata, saboda masu aiki? Ya san dokar gidan in har zan fito yana ɗakinsa." Shiru ta yi kawai, ganin haka suka shiga ciki tana jikinsa. Amarci ake ci sosai. Irin sosai ɗin nan, saboda duk yadda take jin kunyarsa kan dole take ɗan ɗaurewa. A wunin ranar dole ta saki da shi. Shi ya je ya ɗauko su Little Marwana da su Musaddik, suka wuni har dare, sannan ya mayar dasu. Su da tsohuwar mai aikin su sai Nasreen ta yi sati za su dawo. A cikin satin ya koya mata sonsa na hauka. Gabakiɗaya jikinsa ne gurin zama ko kwanciya in har yana nan. Duk kunyar sa da take ji, a cikin satin ya cire sai wanda ba a rasa ba. Sosai ya yi ƙoƙarin cirewa, domin ta saba dashi kafin mai aiki da su Little Marwana su dawo. Ranar da ta yi sati Damir ya kaita gidan Marwana. Saboda farinciki kuka suka saka. Ba tare da sun ƙara bi ta kansu ba, suka shige ciki har da kulle ƙofa. Damir da ba ya iya zaman mintina bai ganta ba ya ce,"Sun shige ciki Allah ya sa ba gulmarmu suke yi ba?" Dariya Ahmad ya yi domin ya san an gama komai."Allah ya kyau kawai." Ya ce sai suka kwashe da dariya. "Dama ai kowa ya sai rariya, ya san za ta zubda ruwa." Cewar Damir. "Sosai kuwa Marwana da Nasreen haɗin Allah ne." Hira suke yi yawancin hirar kan business, da yada ƙasar mu ta zama. Ko abinci sai dai Ahmad ya ɗauko musu, amma tun da suka shiga suke ƙus-ƙus. "Nasreen anya ba ki harbu? Dubi yadda kika koma, ke da nasan ba ki da haske sosai, amma kin dawo fara tass." "Yayan na ki ne babu dama, in har na harbun ba zan musa ba." "Sosai ni sheda ce Ya Damir akwai kula da mace. Shi ya sa tun lokacin da na haɗu dake naga Faruk yana wulaƙanta ki, sai na yi miki sha'awarsa, saboda mai irin halinsa zaki aura ki gane WASU MAZAN sun bambamta da wasu." "Tabbas Marwana na sheda. Na gode da kika haɗani da jarumin na miji kuma gwarzo. Ina alhafari samun sa a matsayin miji." "Ni ma godiya zan yi miki Babyna akwai kula." Dariya suka yi a tare. Damir ya ɗaga waya ya kira ta, saboda in har ya ƙyale su, ƙila ba su da ninyar fitowa. Suna fitowa ya harareta."Da ba za ku fito bane?" "Za mu fito Ya Damir muna hira ne." "Nasreen ce ta tsareta da surutu saboda hira ne da ita, amma babyna babu ruwanta ko?"Ya ƙarashe maganar yana kallonta" "Kai Ya Ahmad wato har ka manta da ni ka daina siding ɗina?" "Saboda yanzu kina da wanda zai tsaya miki. Kin samu bango abin jingina." "Ƙyale shi babyna. Matarsa ce mai surutu ni sheda ce. Wataƙila har labarin yarinyarta sai da ta baki." Dariya suka ƙara sannan suka yi sallama suka tafi. Daga gidan sai ya wuce da ita gidansu. Murna sosai ta yi don bai gaya mata ba. Rungume su Musaddik ta yi kamar zata cinye su. Cikin jin kunya suka gaisa da Mama."Mijin ki ya kira Zainab ta haɗa kayansu Raihan zai riƙe su?" "Ai ya kira ku?" "Na ɗauka kun zo ɗaukar su ne?" Ta yi mata tambayar a maimakon amsa. "A'a bai gaya mini ba, amma na san ya ce za su dawo." "Aiko ɗaukar su kuka zo yi, saboda har an haɗa musu kaya." Murna sosai ta yi cikin farinciki. Mama ta yi mata nasiha sannan ta ƙarashe da cewa,"Yanzu kika yi aure mijin ki ɗan albarka ne, ki yi masa biyayya." "In sha Allahu Mama." Sai da za su tafi, sannan ta ga an fito musu da kaya. Kallon sa ta yi, ya ɗauke kansa. Sosai kullum yake ƙara mata sonsa. Ko yanzu sai da ya yi wa mutanen gidan kyautar kuɗi. Su Raihann daɗi sosai suke yi ganin za su koma gurinta. Gidan Mommy suka wuce, wacce ta yi kamar za ta goya ta. Kunyarta take ji sosai. Little Marwana murna take yi, za ta koma gidan daddy da sabuwar Umma, sannan ga 'yan'uwa da aka kawo mata. Sun daɗe a gidan Mommy har dare ya yi, sannan suka yi mata sallama suka tafi. Saboda sun yi dinner wanka ta yi wa yaran Damir ya shirya su suka kwanta. Tana zaune a falonsa ya shigo ya zauna a gefenta."Zo muje mu kwanta baby ina son na je campany, saboda na dan yi aiki za mu je honeymoon." Dariyar jin daɗi ta yi, sannan ta miƙa masa hannu ya miƙar da ita. "Ina sonka mijina." Ta ce masa cikin shaukin so bayan ta rungume shi. "Da gaske kina so na?" Ya yi mata tambayar kamar bai yarda ba. "Eh Husband babu abin da nake so kamarka." "Ni fa ban yarda ba." Ya ce tare da ture ta cikin wasa. "Allah da gaske kai ne duniyata." Ta ce masa tana ƙoƙarin haɗa bakinsu. "Da gaske?" Ya tambaye ta cikin shaukin so ganin abin da take shirin yi. Ba ta ba shi amsa da baki ba, sai dai ta ɗaga masa kai, sakamakon haɗa bakinsu da yi. "To ki nuna mini yau Please ki cire kunyata kin ji?" "Tom haskena." Ta ce har cikin zuciyarta domin ta shirya kyautata masa. "To shikenan bari na tabbatar." Ya ce tare da ɗaukar ta kamar wata baby zuwa ɗaki. Tabbas ta shayar da shi mamaki, domin ta nuna masa ita mata iya soyyayya. Sun shayar da junansu farinciki. Washegari da safe, shi ya tashi ya shirya yaran sannan ya haɗa musu breakfast suka ci. A lokacin da ta fito mamaki ya kamata sosai. "Morning baby?" Ya ce mata yana ɗure da Apron. "Husband..." "Kar ki yi ƙorafi domin na saba taimakawa matata. Wani lokacin ni nake yin komai, duk da cewar muna da mai aiki. Ina da sha'awar taimakawa matata. Na yi wa yaran breakfast yanzu na mu na ke haɗawa." Hawayen farinciki ya wanke mata fuska."Don't cry just smile you deserve it." "I love you mijina." Ta ce tare da rungume shi ta baya. Duk yadda ta so su yi aikin tare ya ki, sai dai ya ja mata stool ta zauna tana zuba masa surutu. Yana ta murmushi yana kallonta har ya gama. Da kansa ya ciyar da ita, sannan suka saukko falon ƙasa inda su Little Marwana suke wasa. Shiga cikin su ya yi yana taya su, musamman Musaddik da bai gama saki da gidan ba. Tana zaune tana kallo. Sallama ya yi mata zai fita. Ita da yaran suka fito suka rako shi. A gurin motar sun daɗe ana hira sannan ya yi musu sallama ya tafi. Komawa ciki suka yi suna kallo. Wayarta ta ɗauko za ta karanta wani littafi, da Maman Muwaddat ta tura mata mai suna "ƘIYYAYYAR JINI". Sabon littafin Jamila Lawal Zango. Tun kafin ta yi nisa a labarin ta fara cin dariya da ganin wautar Jimmalo. Tun da take ba ta taɓa ganin ƙazamiya kuma ballagaza irin ta ba, sannan kuma ba ta taɓa ganin namiji mai izza irin Captain Aliyu ba. Duk yadda Ya Damir yake da shan ƙamshi da class ya shanye shi. Ga rashin haƙuri da zuciya kamar kuturu. Ƙosawa ta yi ta yi nisa cikin labarin don ta ga inda za a yi zaman doya da manja a rayuwar aurensu, saboda ta san babu yadda za a yi a haɗa zuma da maɗaci. Captain Aliyu da yake da ciwon tsafta da kuma amaryarsa Jimmalo. Lubaynah za ta zuba idanu kenan ya cuci rayuwarta? Gaskiya Captain Aliyu fuska biyu ne da shi, wanda ya sanya rushe yardar dake tsakaninsa da iyayen sa, kuma ya zama silar canzawar ƙaddarar rayuwarsa. Sosai ta zaƙu, ta ga yadda za a kwashe a ƙarshen labarin. Baba rayuwa ta canza duk da Ahmad baya taimaka masa, amma ya canza ya yi ƙiba ya yi kyau, saboda cimar da yake yi. Nasreen yake tursasawa ta yi mishi kaya, don ko da bikinta sai da ta yi mishi kala uku, har da takalmi da hula. Ɗaya daga cikin yaransa mai suna Aminu, amma ba haka ake kiransa ba, saboda ya canza suna tun da ya shiga harkar shaye-shayen da dabanci, domin farauta yana yi. Ya koma suna Goje. Sosai yake hurɗa da 'yan daba, sam ba shi da mutunci, domin shi ya yi ƙaura da gidan. In ya nausa ya bar gari ba a kara jin duriyarsa sai ya dawo. Ko da Ahmad ya dawo. Ya yi da shi ya canza rayuwarsa, amma ya ƙi kan dole ya haƙura ya na masa addu'a, domin ya yi nisa ba ya jin kira. Watarana faɗa ya shiga tsakanin su, a dalilin ƙanwar abokinsu da shi Goje yake so, amma mahaifin su ya yi musu zagin fitar arziki har ya kira shi da ɗan daba, sannan ya sanya manemin aurenta ya fito aka sanya rana. Takaicin abin da ya yi ma abokinsa, suka je suka yi masa duka shi da mabiya bayansa, sannan suka gudu domin sun san dole su ɗau fansa. Hankalin iyalansa ya tashi, ganin har sun ji masa ciwo sun karya shi. Cikin ɓacin rai suka neme su, amma sun gudu. Kai tsaye suka je suka samu Baba, yana zaune yana shan rediyo suka fara dukansa. "Kawai tun da ya gudu ga ubansa nan, ai dama ni ma mai dadtin hula ya taɓa. Wallahi mu karya shi sai na bi iyayen sauran na yi musu dukan mutuwa." Ɗansa Baushe ya ƙarashe maganar tare saukar masa da naushi a baki. Jini ya fara zuba yana ihu yana ba su haƙuri, amma ba su kula ba, har sai da suka yi masa karaya biyu. Hannu da kafa sannan suka farfasa masa jiki. Waɗanda suka ga abin da ya faru, suka je suka sanar da iyalansa. Ko da akwa washe shi zuwa asibiti ya riga ya suma. Sai da ya daɗe, sannan ta farfaɗo da ihu yana tsine musu albarka. "Maman Ahmad, kina ganin yadda su ka yi mini wallahi sun kashe ni, saboda hatta gabana sai da suka illanta. Wayyo na mutu na lalace." "Fansa suka ɗauka Baba Aminu ya ja maka. Kana da labarin dukan da suka yi wa ubansu." "To ni na duke shi da za su kashe ni? Su je can su kama shi mana?" "In baka duke shi ba, ai kai ka haife shi ka kasa bashi tarbiyyar da zai girmama uban wani. Abin da na ke yi maka kuka kenan, yau ga shi ka haifi ɗan kuka. Da ace ka inganta rayuwarsa duk haka ba zai faru ba." Mama ta ce tana kallon sa cikin rashin tausaya. "Wayyo abin da za ki ce kenan? ba kyau tausaya mini kalli yadda suka ƙassara ni." "Allah ya ba ka lafiya, amma duk abin da ya faru da laifinka." Ihu yake yi yana kuka, saboda ko ina na jikinsa ciwo suke mishi. A lokacin da za a yi gyara karayar har fitsari a wando ya yi. Ya yi ihu har muryarsa ta dusashe. Duk halin da yake ciki har aka wuni Ahmad bai zo ba. Hankalinsa kwance yana naniƙe da matarsa. Ko da ta ji labarin sai ta ji tausayinsa, amma tana buɗe baki ya dakatar da ita cikin tsawa. "Kin san yadda na tsane shi? Haihuwarmu kawai ya yi, ya barmu muna garari. Ba tare da ya bamu abinci da ilimi ba. Duk abin da ya faru da shi babyna ya cancanta, don haka kar ya dame ki."Ya ce tare da jawota ya ya haɗa da jikinsa ganin yadda ta tsorata. "Na san komai kuma ya cancanta, amma ka yi haƙuri ya ci albarkacin haihuwarka da ya yi." "Wane albarkaci zai ci? In da ace ban jajirce ba. Ni da Nasreen mun inganta rayuwarmu da na 'yan'uwanmu a haka za ta wulaƙanta. Baba ya cancanta ki barshi ya ɗanɗani halin da ya sanya mu." Shiru kawai ta yi, amma ba ta ji daɗi ba, duk da ta san cewa ya cancanta. Wayarta ta daga ta kira Nasreen. Bayan sun gaisa sai ta ce,"Kin ji labarin ne Baba ba shi da lafiya?" "Eh muna kan hanyar zuwa ni da Ya Damir." "Ok, Ya Ahmad na yi-na yi ya ƙi zuwa bari na ƙara rarrashinsa." "Ki ƙyale shi a yanzu da wuya ya je domin ya yi zuciya, in muka je asibitin zan biyo." "To Allah ya ba shi lafiya." "Amin," ta ce tare da kashe wayar. Da suka je halin da suka ganshi, sai da suka tausaya masa. Yana ganinta ya fashe da kuka. "Nasreen kinga abin da ɗan banza yaron nan ya yi mini. Wallahi in zan gan shi sai na kusan kashe shi." "Ka yi masa addu'a Allah ya shirya shi." Damir ya ƙaraso yana gaishe shi. Asibiti aka canza masa, sannan aka sake ɗorin don bai yi ba. Kuka da ihu har ya gaji ya daina Faruk Farouk tun da suka tafi da shi, yana ihu yana zambarwa sai gidansa, amma sai suka ga lamarin ya wuce ƙarfin a bar shi a gida. Asibitin mahaukata aka mayar da shi, nan take suka ba shi gado. Cikin kuka Anty Asiya suka bar asibitin. Ya daɗe yana jinya kafin ya warke, har lokacin inya tuna sai ya ji kamar zai kashe kansa. Ga shi kullum sonta ƙara nunkuwa yake yi a cikin zuciyarsa, duk da ya san cewar matar wani ce. A ƙalla sai da ya shafe tsawon watanni yana jinya, sannan ya samu lafiya bayan an kashe kuɗi, domin hatta motarsa sai da aka siyar. Ya yi kukan nadama, har ya gaji don dole da ya fahimci Nasreen ta yi masa nisa. Ya zama silent, ko magana cikin 'yan uwansa ba ya son yi. Kullum ya tuna Nasreen da yaransa suna rayuwa a gidan wani, sai ya ji kamar zai kashe kansa. Da ƙyar suka samu ya koma aiki, domin cewa ya yi ya daina komai. Rashida kuwa kullum ya yi sallah sai ya roƙi Allah ya tsine mata. Rayuwa yake cikin rashin daɗi, domin hatta iskan da yake shaƙa ba ta yi masa daɗi. Haka dai ya ci gaba da rayuwar ba tare da yana jin daɗin ta ba. Rashida Rashida an samu duniya, domin a lokacin da ta gudu da kuɗin ba ta tsaya ko ina ba su Legos. Kai tsaye gidan wata 'yar uwarsu ta wuce. Duk yadda Maman Iyabo, ta so ta gaya mata abin da ta yi ta samu kuɗi ta ƙi gaya mata. Ganin tana ba ta domin tun da ta zo ita take ciyar da gidan, sai ta kwantar da hankalinta suka ci gaba da cin arziki. Cikin ƙanƙanin lokaci ta sayi gida da mota, sannan ta shiga kasuwa ta sayi kaya masu kyau. Ta zama baban mace, sai facaka take yi da kuɗi abinta. A yawonta na shaƙatawa, ta haɗu da Abdurrashiiduu matashin mai tashe. Gayen ya haɗu ga ita turanci kamar ya haɗiyi Dictionary, don ko broken ba ya yi, amma gayu ne babu kuɗi, domin anci boko babu aikin yi. Sai dai irin aikinsu na Yahoo, duk da cewar bai yi wani ƙarfi ba, don bai daɗe da shiga ba. Tun da ta ƙyalla idanu ta ganshi sai ta susuce, domin soyayyarsa ya kamata. Da ya fahimci haka ya mayar da ita ATM ɗinsa. Duk hidimar da take mishi burinta ya aure ta, amma shi tunainsa yar da zai yi, ya yi gaba da kuɗin da ta gaya masa ta kwashe wa Faruk, saboda soyayyarsa ya sanya ba ta ɓoye masa komai ba. Tun daga ranar, ya shiga tatsarta ta canza mishi waya da laptop. Motarta kuwa duk inda za shi da ita yake zuwa, domin yawanci shi yake tuƙata. Ita take ciyar da shi komai har kwana a gidanta yake yi. Lumbu-lumbu ya yi mata, sai da ya tabbatar da ya san sirrinsa, kuma ta aminta da shi. Sannan ranar safiyar talata ya yi mata ƙaryar ba shi da lafiya. Magani ta tabbatar ya sha, sannan ta bar mishi gidan. Bayan fitarta komai ya kwashe mata, sai wayarta da motar da ta fita da shi. Pin ɗinta dama ya sani. Yana cikin haɗa kayansa ta dawo ta yi mantuwa. "Abdu- Rashiduu!" Ta furta cikin tsananin razana, ganin yadda ya yi watsa-watsa da gidan. Cikin yare take mishi magana, tare da kai masa duka ganin abin da yake shirin yi. Ganin haka ya ɗauki ƙaton abu ya maka mata, nan take ta zube a gurin babu numfashi. Wayarta da key ɗin mota ya ɗauka ya fice daga gidan. Gaba da gabanta, aljani ya taka wuta. Cuta ta ɗau cuta kenan Allah ya shiryamu ya sa mu daina hangen abin wani. Sai da ta yi kwana ta wuni, sannan aka gane halin da take ciki. Ko da aka kai ta asibiti ta nakasa, domin wuyanta ya karye. Amare ba tare da sanin su ba, angwaye suka yi musu viser zuwa honeymoon. Sai ana saura kwana biyu ya kawo mata tikiti jirgin Australia. Rungume shi ta yi cikin tsananin farinciki. Zainab da mai aiki aka bari su kula da yaran. A ranar safiyar Laraba jirginsu ya tashi zuwa Australia. Mamaki da alja'abi ta rinƙa yi wai yau ita ce zata je honeymoon da miji. Yana maƙale da hannunta, duk da idanun Marwana da Ahmad bai sa ya ji kunya ba. Ko motsi ta yi sai ya kalle ta. Yadda yake nuna mata ƙauna har mamaki take yi. A hotel ɗaya suka sauka mai suna; Four seasons hotel Sydney. Tun da suka sauka, wanka kawai Nasreen ta yi ta kwanta saboda gajiyar tafiya. Damir shi ma wanka ya yi, sannan ya ja bargon ya shiga ciki. Bacci sosai suka yi, sai da suka kwashe awa da rabi. Shi ya fara farkawa, sannan motsinta ya farkar da da shi. Cikin magagin bacci, ya miƙa mata hannu da nufin ta zo su ci gaba da bacci."Baby please yunwa na ke ji." Ta ce tare da kama hannun ta miƙar da shi ya zauna. "Ok, bari na yi waya a kawo abinci." Wanka suka sake yi sannan suka haɗu a gurin cin abinci. Marwana ta fito da Ya Ahmad. A tare suka ci abincin suna hira har suka gama. Bayan sun gama ciki suka shiga, domin har wannan lokacin akwai gajiya a tare da su. Sai da suka yi bacci gajiya, sannan suka fara ganin gari, sun je gurin shaƙatawa irin su;Stunning beaches da kuma Iconin cities har da Melbourne. Sun je guraren sosai musamman gidan tarihi irin su;Harper's Mansion Da Experiment Farm Cottage tarihi. Hotuna kuwa har sun gaji da ɗauka. Wani irin soyayya yake nuna mata tamkar ya cinye ta. Tun da suka je sai dai su fita yawo su yi siyayya, sanann su zaga gari su dawo. Kodayaushe suna maƙale da juna, in ba bacci ba suna tare ana soyayya, domin ya sabar mata a jikinsa take zama. Kafin su dawo dai da ya cire duk wani kunya na shi da take ji, saboda sosai ya nuna mata soyayya har ya daina ba ta mamaki, ta gane yana daga cikin maza da suka bawa soyayya mahimmanci. Siyyayyar da yake yi kuwa tun tana taya shi zaɓe har ta hana shi. Sosai ya siya mata kaya musamman ƙanana. Su Marwana ma kullum suna maƙale da juna ana soyewa Wasu mazan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 46 Wata ɗaya suka yi, sannan suka tattaro suka dawo. Nasreen daga ciwon gajiya sai kuma ya zama laulayi. Saboda cikin dare suna kwance Damir ya ji jikinta ya yi zafi sosai. Miƙewa ya yi sannan ya taɓa kanta. Mamaki sosai ya cika shi ganin ta takure guri ɗaya. "Nasreen ba ki da lafiya, amma ba ki gaya mini ba?" Ya ce mata bayan ta farka. "Zazzaɓi ne kuma na sha magani, amma kuma ya dawo." "Gobe da safe za mu je ganin likita, kuma ya zama na ƙarshe, da za ki ji zazzaɓi ba ki gaya mini ba. Kafin safiya jikinta ya rikice domin ta yi amai yafi sau uku. Damir rikicewar ya yi, ganin yadda take zazzaɓi tana kakkarwa kamar za ta jijjige gadon. Hankalinsa ya tashi sosai, domin bai taɓa sanin akwai masu zazzaɓi irin haka ba. Amai kuwa duk a jikinsa ta yi, domin duk yadda ta so ta raba jikinta da shi, don ta yi aman ya ƙi. Bayan ta gama ya canza kayan jikinsa ya yi wanka. Ita ma wanka ya yi mata, sannan ya sanya mata kaya. Kiran sallar farko ya nufi asibiti da ita. Gwajin farko aka gane tana ɗauke da cikin sati biyu. Ta yi mamakin murnar da yake yi, saboda kamar bai taɓa haihuwa ba, kawai sai ta ji ya manna mata kiss. Zare idanunta ta yi, tare da kallon inda likitan yake cikin jin kunya, amma sai ta ga ya yi kamar ba ya ganinsu. "Babyna kina da ciki za ki haifa mini baby?" Ya furta cikin tsantsar farinciki tare da rungumeta."Please doctor a ɗaura mata drip ta sha wahala sosai." "Ina ga ba sai an sanya mata ruwa ba, maganin da na ba ta sun isa." "No don Allah ka sanya mata ruwa." Ganin ya kafe sai ya sanya mata ruwan. Yana kusa da ita sai aikin sannu yake mata. Bacci ne ya kwashe ta, saboda har da maganin bacci ya buƙaci a sanya mata a ruwa. Kamar wanda ba a taɓa masa haihuwa ba, sai ya ɗauki waya ya shiga kiran dangi yana gaya musu. Kafin kace me duk sun zo asibitin, har da Marwana da Ahmad. Nasreen farkawar ta yi, kawai ta ga suna zaune suna jiran ta tashi. Ganin ta buɗe idanunta duk suka yi kanta suna mata ya jiki. Saura ƙiris! Ta saki kuka ganin yamaɗiɗi da ya yi da ita. Kallon sa cikin kunya ta yi da ya kama hannunta yana faɗin,"My wife kin tashi ya jikin?" Saboda takaici ba ta amsa masa ba. Sai ta kalli Marwana da ta riƙe ɗaya hannunta. Cikin tsananin kunya ta kalli Mommy da take mata sannu. Kunya sosai ta ke ji, amma duk suka zauna a asibitin har sai da ruwa ya ƙare aka sallame ta. Magunguna ya ba ta, sannan suka shiga mota don su tafi. Daga asibitin gida suka rakata. Duk yadda Mommy take kula da ita, ta sanya an dafa mata fate saboda shi take so, amma Damir baya gani. Yana gefen inda take zaune. Ko kallon sa ta yi sai ya ce mata sannu. A ranar ta ga gata sosai, domin rasa gane ta yi tsakanin Mommy da Marwana har da uban gayyar wanda yafi murnar cikin. Tun tana jin kunya har ta rage ganin yadda ko a jikinsu. Mommy na zaune yake addu'ar Allah ya sanya ta haifi namiji, ya sanya sunan mahaifinsa. Sai kuma ya fara addu'ar Allah ya sa 'yan biyu za ta haifa. Mommy da mahaifinsu. Ita kam ta ga inda aka riƙe boko domin babu kunya, Mommy ta zauna suna maganar cikin. Saboda kunya da suke bata ƙaryar bacci ta yi. Sai da daddare Mommy ta kom gida, Ahmad ma ya kawo su Mama, sannan ya ɗauki Marwana. Nasreen kam ta ga inda ake maraba da ciki. Tamkar za su cinyeta haka suke yi. Kullum yana cikin siyo mata fruit da kayan ƙwalama. Duk da cewar gidan akwai, amma sai ya nunka domin duk ya fita sai ya siyo. Sai ta tuna lokacin cikin Raihan da ta rinƙa na cin Faruk ya siyo mata fulawa, don ta yi wainarta, amma ai sai Fadila ta fito mata. Nan kuwa Damir, bayan ya siyo da kanshi zai gyara ya kawo mata yana riƙon ta ci. Laulayin wata ɗaya ta yi, ta warke tamkar ba ciki take da shi ba. Saboda ƙarfi sosai ta yi. Ta yi wani irin kyau da haske kamar ba ita ba. Cikin sosai ya sanya ta canza ta ƙara haske. Shiryen-shiryen komawa aki ta fara, amma da ya daka tsalle ita da aiki sai ta haihu. Hankalinta ya tashi sosai domin tana so yin aiki, kuma a gida babu bin da take yi, saboda bayan Baba ya ƙaro mata wata, ga kuma Zainab da ya ɗauko ta dawo gidansu gabakiɗaya. Cikin shagaɓa ta ƙarasa kan gadon, da ya zauna a gefensa yake ƙoƙarin sanya safa. Karɓa ta yi ta saka masa sannan ta ɗauki takalmin. A maimakon ta sanya masa, sai ta kalle shi kamar za ta yi kuka. "Don Allah, ka bar ni na je aikina zaman gidan ya ishe ni. Ingawa ba shi a campany ballantana ka ce don shi ne za ka hana ni zuwa." "Dama mahaukaci ne ni da zan barshi ya ci gaba da aiki a can? Yana kalle mini kyakkyawar matata yana haɗiye miyau." Zare idanunta ta yi ta ce,"Dama kai ka kore shi? Sam ba ka yi masa adalci ba, domin ka haɗa masa zafi biya." Jawota ya yi ya sumbace ta ganin yadda ta damu."Na tura shi gurin abokina a can aka ba shi aiki, sai ya tura mini na shi ma'aikacin. Ke ma kin san bai yadda za a yi na ƙyale shi, bayan ya yi takara da ni. Kin san yadda na ke ji a lokacin da na ke ganinku? In na koma gida bana iya bacci." Dariya ta yi tuna lokacin, amma ya yi ta shan ƙamshi yana bonewa. "Ki yi haƙuri, kar ki wahalar mini da yaro ki bari sai kin haihu." Ya ce yana shafa cikin nata da yake tamkar ba a sanya masa abinci. "Cikin da ko wata biyu bai yi ba. Don Allah ka bar ni na koma aikina." "Ok, bisa sharaɗin ba za ki wahalar mini da shi ba?" Cikin farinciki ta rungume shi ta ce,"Eh na yarda." "Ok, je ki shirya." Ya ce mata tare da kallonta. "Husband nurina." Ta ce bayan ta manna masa kiss. Murmushi ya yi, ya zauna yana jiranta. Shiga mai kyau ta yi kalar kayansa. Hakan da ta yi sai ya ji daɗi sosai. Hannunta ya kama suka fita suna hira har gaban mota. Sai da ya buɗe mota gurin mai zaman banza, ta shiga sannan ya gyara mata gyalenta ya za gaya ya shiga cikin mota. Tafiya suke yi tamkar ba za su je ba, saboda yadda yake yin tuƙin a lalace kasar wasu masoyan da suka haɗu a ranar. Bayan sun ɓata lokaci duka isa kampanin. Da kanshi ya zagaya, ya buɗe mata motar ta fito, sannan ya kama hannunta suka fara tafiya kamar za su shige jikin juna. Nasreen ɗaurewa ta yi, domin ta gane mijinta haka kalar tsarinsa yake. Ba ya jin shakkar nuna mata soyayya ko a gaban mahaifiyarsa. Don haka ta yi namijin ƙoƙari ta rage kunyar tana biye mishi. Sosai ake kawo gaisuwa yana amsawa. Kowa kallon su yake cikin tsananin sha'awa. Da masu kishi, da baƙinciki har ma da masu murna kallon su suke yi. Ofis ɗinsa suka shiga. Har za ta juya ya riƙe mata ƙugu."Matata ki kula da sharaɗinmu, domin in har kika wahalar mini da baby. Ko kika kasa ba ni kula da daddare na soke aikin,saboda na fi buƙatar ki kula da yarona da ni." "Ba ka da matsala mijina."Ta furta tare da yi mishi kiss. Har ofishinta ya raka ta sannan ya zaunar da ita. Bakinta ya sumbata."Ki kula da kanki ina sonki." Murmushi ta saki tare da ɗaga masa kanta ta kuma kashe mata ido. Gashin kansa ya shafa alamun tsakon ya isa. Da ya shiga ofis, sai ya kasa aiki yana tunaninta yana murmushi. Miƙewa ya yi, ya tafi zuwa siyo mata kaya maƙulashe. A lokacin da ya kawo dai ta kalle shi ta karɓa."Da ba ka wahalar da kanka ba, domin akwai abin da zan ci har mu tafi." "Ki cinye wannan ki ɗora da wannan." Dariya ta saki jin abin da yace,"Na lura so kake in zan fita sai an rinƙa cire ƙofa." "So na ke ki samu kulawa ke da yarona." Yana zaune har sai da ya tabbatar ta ci ya koma. Daga ƙarshe zuwa ya yi, ya tafi da ita ofis ɗinsa ya kwashi Laptop ɗinta, da sauran files ɗin da take cike wa. Aikin da ba a yi ba kenan, domin surutu suka fara ana hira ana soyewa, sannan suka tafi gidan Marwana, da ta kira ta gaya musu ba ta da lafiya don ita ma ta samu ciki. Sun jima a gidan suna kula da ita. Ahmad shi ma murna kamar zai cinyeta. Sun kula da ita har dare, sannan suka yi musu sallama suka dawo. Da daddare tana kwance ya shigo da kayan bacci a jikinsa. Kan gadon ya hau tare da ɗora ƙafafuwanta kan jikinsa yana matsa mata. "Babyna kin ga yadda kullum kike ƙara kyau, wai mene sirrin?" Dariya ta yi ta watsa masa kallo sai ta ce,"Kai ne sirrin da yaronka." "Ai to bari na zo na ƙara sirrin na kuma kula da shi." Ya ce tare da janyota jikinsa. Da ƙyar ta samu ta rarrashe shi ya barta ta je zuwa aikin, domin washegari cewa ya yi ba za ta je ba. In suka je aikin rabi soyayya rabi aiki. Sai da ya ga aiki na son cin karfin Muhsin, sannan yake ƙoƙari, amma da sai dai ya je ofishinta ko ya ɗauko ta zuwa na shi. Ranar Monday sun je gurin aiki, misalin sha biyu tana zaune hankalinta na kan aiki ya shigo."Yau kin manta da mijinki." Ya ce tare da kissing ɗin ta ya zauna. "An sorry babyna aiki ne ya riƙe ni, kuma kaima na ga kun fita da Muhsin." "Haka ne akwai matsala fa." Kallonsa ta yi, sai kuma ta basar domin ta gane matsala."Mai ya faru baby?" "Yunwana ke ji." "Ok, mu je na raka ka, ka ci abinci bana son kana zama da yunwa." "Nasreen ba wannan ba, Please kin san mai na ke nufi." Ya ce mata tare da kamo ta ya haɗata da jikinsa. "A gurin aiki muke." "Matata ce ke mu je ofis ɗin akwai komai." "Don Allah k je ka yi aiki na lura rigima kake ji." "Let's go home." Ya ce tare da kashe kayan wutan ofishin. Kallonsa ta yi kawai ganin babu halin roƙon shi, domin tun da ya ce hakan ba ta da zaɓi.Soyayya suke sha sosai suna rainon cikinta. Baba karayar da ya samu, ko da aka kwance ya samu naƙasa a ƙafarsa, domin ya zama gurgu da sanda yake tafiya yana jan ƙafar. Ganin lokaci guda halin da ya shiga sai ya fara nadama. Kuka sosai ya yi yana roƙon su yafiya, musamman Ahmad da duk abin da ya faru da shi, sam bai tausaya masa ba. Da ƙyar Damir da Marwana suka shawo kansa, amma har lokacin da ya yafe masa babu wannan soyayya tsakanin ɗa da mahaifi. Duk abin da zai yi, da Mama yake shawara sai dai ya ji a bakinsa. Farouk ganin ya canza rayuwarsa, ta zama wani iri sai 'yan'uwan da mahaifiyarsa, suka fara ƙoƙarin nema mishi mata. Da farko funjire musu ya yi, sai da suka tabbatar masa da ya rasa Nasreen har abada, sannan ya amince, amma duk yarinyar da aka haɗasa da ita sai ya ce ba ta yi masa ba. Ko ya ce ba ta da haƙurin Nasreen. Ganin suna ta haɗa shi da 'yan mata ya ƙi, kawai aka haɗa shi aure da Maimuna. Yarinyar ƙanwar Mamansa. Da fari ya ƙi kula yarinyar, amma haƙuri da ta yi dai ya ɗauki dangana ya rungumi matarsa, suna zaman lafiya. Har yanzu ya kasa mantawa da ita. Ya san cewa yayi rashi na har abada, domin ba zai taɓa samun kamarta ba. Ko Maimuna da ya aura iya sakandiri ta yi, sannan ba ta da zurfin addini, amma tana da natsuwa. Natsuwarta ya ja hankalinsa har ya kula ta, saboda natsuwarta Nasreen da sanyinta yake son mace mai natsuwa. Farouk ya canza domin Maimunatu na jin daɗin zama da shi. Sosai yake ƙoƙarin sauke haƙkinsa, domin har abinci yake ijewa a store kuma babu duka babu zagi, har zama yake yi suna hira kuma da ta samu ciki, duk abin da take so fito mata yake yi. A kodayaushe ƙoƙarin faranta mata yake yi, saboda Allah ya dubi zuciyarsa ya tuna ya yafe masa cutar da Nasreen daya yi. Yana son zuwa gurin yaransa kuma ya nemi yafiyarta, amma yana tsoron hukuncin da Damir zai ɗauka tun da an yi musu tsakani.. Yana dai zaman aure da ita, amma har yau babu macen da zai so kamar Nasreen. Ƙoƙarin neman cajin aiki ya yi, don ya bar garin na wasu shekaru ya manta da ita, kuma cikin ikon Allah ya samu suka tattara suka bar garin. Nasreen cikinta ya girma sosai, don har ya shiga watan haihuwa. Ita kuma Marwana yana wata takwas. Nasreen cikin ta sanya ta yi ƙiba, sannan ya yi girma sosai. Tun yana wata bakwai ganin girman shi, suka yi scanning aka tabbatar musu da 'ya'ya biyu za ta haifa. "Murna gurin Damir kamar zai yi hauka. Tun daga ranar ya sanya ta daina komai, kuma ta daina zuwa aiki. Sosai yake kula da ita. Ranar safiyar Alhamis ta tashi da naƙuda. Cikin tashin hankali suka nufi asibiti. Tun suna sanya ran za ta haihu da kanta har suka cire, ganin wahalar da take sha. Damir sai hankalinsa ya tashi. Ciki ya shiga ya kama hannunta. "Wash! Ya Damirr zan mutu ka yafe mini ka yi mini addu'a." Jin abin da ta ce da ganin halin da take ci, sai hankalinsa ya tashi ya ce, "Ke ma tafiya za ki yi ki barni? Don Allah kar ki tafi ki barni kamar yadda Batula tayi." "Please ka sanya hannu ayi mata aiki." Likitan ta ce tare da miƙa masa takkadda. Hannu ya sanya jikinsa a mace. Mommy ta dafa shi suka fita. Marwana hankalinta ya tashi. Kuka take yi sosai, ganin wahalar da Nasreen take sha. Ahmad shi kansa da Mama jikinsu ya yi sanyi. Addu'a sosai suke yi mata. Har an shiga da ita ɗakin tiyata Allah ya sauke ta lafiya, ta haifi mace da namiji. Sosai likitocin suka yi murna. Gyara yaran aka yi, sannan aka fito da su. Damir ba tare daya kalli yaran ba ya shiga cikin ɗakin."Sannu jarumtar matata." Ya ce mata tare da share mata zufan goshinta. "Ya Damir." Ta kira sunan shi tana mika masa hannu cikin wahala, saboda ko haihuwan Raihann da yake na farko ba ta sha wahala haka ba. Rungume ta ya yi, tare da manna mata kiss."Allah ya albarkanci yaran da kika haifa." "Amin." Ta amsa hawaye yana ganganrowa. Kwana biyu suka yi aka ba su sallama. Tun da ta haihu ya hana kowa ganinta, saboda ana buƙatar ta samu hutu kumburin ya sauka. Jariran kawai ake gani. Ko da aka sallame su gida babu wanda yake ganinta, domin suna ma ɗagawa ya yi, sai ta samu lafiya. Nasreen ta ga gata, don siyayyar da ya yi mata da yaran kamar ba shi cikin hayyacinsa. Kowa a dangi dai kawo mata alkhari yake yi, yaran sun yi mata goshi sosai. Ita kanta Mommy kaka akwati guda ta yi. Su Mama da sauran dangi ba a barsu a baya ba, don Ahmad da Marwana kam sun yi bajinta suma. Tun da akayi haihuwar Marwana ta tare a gidan. Duk da cikinta ya tsufa, amma sosai take bawa yaran kulawa. Yara sun ga soyayya ta ko'ina. An yi musu huɗuba da sunan Moomy da mahaifinsu ana kiransu namiji Ubaidullahi mace Ubaidah. An ci an sha ranar suna. Maijego ta yi shiga na kece reni. Su Maman Muwaddat da Fadila an sha suna. Bayan mai aiki sai da ya ɗaukar mata wata. Haihuwar Nasreen da wata ɗaya, ita ma ta haifo 'yarta mace bayan tasha baƙar wuya. Yarinyar kyakyawa sosai. Sunan Mama ta ci, ana kiranta da Sabrin. An ci ansha sosai Ahmad shi mata yi bajinta. Kaya kuwa har rasa inda za a sanya saka yi, domin kayan da Damir da Nasreen suka siya sun isa. Sosai suke kulawa da yaran, da suke girma suna kiɓa ga su kyawawa.Suna da wata uku amma kamar sun yi wata biyar. Cikin kula take rainon yaran ita da mahaifinsu. A lokacin da suka yi shekara kuwa babu inda basa zuwa. Shekarar su biyu ta yaye su, da yarinyar Marwana da kusan a gidanta take rayuwa, saboda yaran da take gani. Ta so ta yi hutu, amma ogan na ta babu wasa. Wata ɗaya da yaye ta samu wani cikin. Sosai ya nuna farincikinsa, don haka ta ci gaba da rainon cikin. Wasu mazan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_ *08144072423* Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What *WASU MAZAN* BOOK 2 NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 47 BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR. Rayuwa ta shuɗe da canjin da aka samu a cikinta. Damir da Ahmad Allah ya buɗa musu sosai sun ƙara kuɗi, domin Ahmad ya canza wa Mama gidan da take ciki. An yi auren Muhsin da Hajar har sun haifi yara biyu. Sannan Zainab ma an yi mata aure da saurayinta, da suka haɗu a lokacin da take service, har sun haihu ɗaya. Nasreen ta ƙara haihuwa biyu bayan Zahira da ta haifa. Ta haifi namiji an sanya masa Umaimah sai muka Nauwal sai ya zama yaranta bakwai kenan. Marwana ma ta ƙara uku maza biyu da mace. Raihann da Little Marwana an girma an zama 'yan mata, domin a lokacin suna shekara goma sha takwas. Sun kammala karatun su na sakandiri suna shekarar farko a jami'a. Musaddik shi ne ya rubuta jamb yana jiran result ya fito. Su Ubaidah da Ubaidullahi ana sakandiri. Alhaji Damir ya girma ya zama babban mutum. Ya ƙara kuɗi da wayewa. Hajiya Nasreen, tana zaune a katafaren falonta da ya sha kaya masu kyau da tsada. Tana sanye cikin tsaddaden leshi kalar golden doguwar riga. Kasancewar ranar juma'a ne, ya sa ya ta yi wannan shigar, amma har yau da ta girma in tana gida ƙananan kaya take sawa, babu ruwanta da yara, don su ma irin shigarsu kenan. Remote ne a hannunta tana canza tasha. Nauwal ne ya rugo da gudu Umaimah na bin sa a fusace. Da sauri ya ɓoye a bayanta daidai lokacin da Alhaji Damir yake sakkowa daga matakalen bene. "Umma, kin gan shi ko? Ki gaya masa Ni ba tsarar wasan sa bace, da zan sanya game Laptop ɗina, na shiga kicin ya canza." "Umma, alƙawari ta yi mini kuma taƙi cikawa." Ya ce yana nishin gudun da ya yi. "Nauwal zan zane ka fa, saboda ba tsararka bace. Oya tell her sorry." Ta ce tare da kama hannunta. "Anty Umaimah sorry." Ya ƙarashe cikin muryar kuka, daidai lokacin da Damir ya sauko. "Daina kuka boyna, zan siya maka na ka yau in sha Allahu zan yi maka oder." A madadin ya yi kukan sai ya washe baki "Abba thank you." Shafa kansa ya yi cikin murmushi. Yaron ya ruga yana murna sai Umaimah ta ji sanyi, domin siyan masa ita kanta za ta samu natsuwa. Damir jawota ya yi ganin yaran sun tafi."Matata." "Barka da fitowa mijina." Ta ce tana shafa sumansa. "Ban yarda da cin hancin nan ba, bayan kin ƙi kwanciya ki huta." "Yaran nan ba za su bar ni ba, kana ganin Husnah kuka ta rinƙa yi za ta sha tea." "Ai yarinyar nan da shagwaɓa halin uwarta Marwana ta gado." Dariya ta yi ta ce,"Marwana ko ita ka ta ƙorafi take yi da rigimarta, saboda ba ta barinta ta huta." Zama ya yi sai ta zauna kusa da shi."Baby wankan nan ya cige ni ina za ka?" "Wata ce tana ce wai don Allah, na taimaka na aure ta, shi ne na ke tunanin samo miki 'yar...." Fara diddira ƙafarta ta yi, kamar za ta yi kuka."Ashe kuwa kana son yau na yi kwana prison, domin sai na nemo ta ko a birnin Sin take, na aikata mata ba daidai ba." "Taimakon ki zan yi fa, yanzu kika gama cewa hidimar yara sun yi miki yawa." "Ba su yi mini ba, zan iya in dai wata za ta shigo mu yi sharing ɗinka na haƙura, ko da ace aiki zai kashe ni." "Zo nan kin ji matata, ke kaɗai kin ishe ni a rayuwata. Ina son ki ba zan iya haɗa ki da wata ba." "Ni ma ina son ka mijina." Ta ce tana ƙoƙarin haɗa bakinsu. Sallamar Little Marwana da Raihann ya sanya suka shigo. Yaran sun ga abin da za su yi, amma sai suka yi murmushi, domin sun saba da wannan. Sun yi kyau sosai. Yaran farare ga hutu da ya bayyana a jikinsu. Suna cikin shiga ta alfarma. Baƙar abaya ce a jikinsu da ta ɗauki fatarsu, sai suka yi rolling gyalen abayar. Kuma cikin ikon Allah dai suka tashi a tare. Raihann ce ta ɗan fi Little Marwana ƙiba, saboda ita ba ta son cin binci dai chocolate kamar ƙaramar yarinya. "Umma, Abba na gaji gaskiya, a canza mini mota tana wahalar da ni."Little Marwana ta ce tare da zama ta dafe kanta, ita a dole ta gaji sai ka ce a ƙasa ta dawo. "Magaji mafiyi. Umman yara kin san lokacin Marwana in tana son a canza mata mota, sai ta yi ta cewa motar ta yi kaza. Har sai ta san yadda ta yi ta aka canza mata, kin ga 'yarta ta gado ta." Dariya ta yi jin abin da ya ce,"Abba ba haka bane Allah ka tambayi sis. Har cewa na yi ta tuƙa ta ce ba za ta iya ba. Da yasan wahala za ta bani cewa ta yi da motarta ta tafi." "A canza mata tun da tana so." Cewar Nasreen tana kallonta. "Ok, kin goyi bayanta kenan? Ban yarda ba sai na tambayi Raihann. Sai ya mayar da idanunsa kanta ya ce,"Da gaske take yi?" Dariya ta yi ta kalle shi."Eh Abba." "Ba wani nan bakinku ɗaya." Ya ce yana dariya. "Ni ma Abba a siya mini mota." Musaddik ya shigo falon yana faɗin haka. "Ba za a siya ba sai ka girma." Cewar Nasreen tana harararsa. "Umma na girma jami'a zan shiga don Allah ka siya mini mota." "Kwantar da hankalinka in har ka ci jamb zan siya maka." "Oh yes! Zan ci I did read." Ya ce cikin murna. "Shikenan in sha Allahu zan yi wa Daddy Ahmad magana, in zai shigo da mota, sai ku faɗi wacce kuke so har da Raihann." "Thanks dad." Suka rungume shi sun faɗin haka. Murmushi yake yi cikin tsananin ƙaunarsu. Nasreen kallon shi take yi kamar ta lashe shi. Har yau ba ta taɓa ganin ya yi abin da zai bambanta su da yaransa ba. Haƙika babu abin da za ta iya saka wa Marwana, da ta shigo mata da shi cikin rayuwarta. Ya shayar da ita zuma, a lokacin da ta kwankwaɗi maɗaci take ganin ba za ta taɓa shan zuma ba. Damir ya zama hasken da ya haskaka rayuwarta. Ya kawo sauyi da dama a cikin rayuwarta. Ranar safiyar juma'a suka tashi da tashin hankali. Domin Baba ya fita mota ta kaɓe shi. A lokacin da aka kira Nasreen aka gaya mata yana cikin mayuwayacin hali. Kuka ta fashe da shi, sannan a kira Damir. Yana ganin kiran hankalinsa ya tashi domin yana cikin asibitin. Ganin halin da yake ciki sai da ya yi hawaye, domin sai dai addu'a. Jini yake fita daga bakinsa kansa ya kumbura. Kwantar mata da hankali ya yi, sannan ya sanya direba ya kawo ta asibitin.Ahmad shima kuka yake yi, ganin halin da yake ciki. Duk ƙoƙarin da likitoci suke yi kar ya yi magana, amma sai kuka yake yi yana neman gafara. Nasreen tun da ta ga Damir ta ga kuma yanayin fuskokin su. Sai ta shiga cikin tashin hankali." Ya Ahmad ya jikin Baba?" Ta yi masa tambayar tare da kama hannunsa. Hannunta ya ja suka shiga ciki, daidai lokacin da Zainab da Mama suka ƙaraso. Suna ganin halin da yake ciki sai kuka. "Baba addu'a yake so Nasreen." Damir ya ce mata yana share hawaye. Lokaci guda asibitin ya cika domin duk wanda ya zo, zai kira wani don ya zo in suna da rabon ganawa. Kuka sosai suke yi ganin halin da yake ciki. Kai rayuwa babu tabbas domin rai ba a bakin komai yake ba. Baba ya daina numfashi sai da taimakon oxygen. Hanunnsa yake miƙo musu da su zo. Suna kuka suka ƙarasa gurinsa." Kun ga yadda Allah ya mayar da ni ko? Ku yafe mini irin rayuwar da na gina kuna cikinta. Na yi dana sani na tuba, don Allah ku yafe mini kar na koma gurin Ubangijina da haƙƙin ku na haife ku ban kula da rayuwarmu ba. Don Allah ku yafe mini." Ya ƙarashe maganar numfashinsa na ɗauke wa. "Babu komai Baba, mun yafe maka Allah ya baka lafiya." Nasreen ta ce sai Ahmad ya riƙe hannunsa, ganin zai ƙara magana. "Don Allah ka yi shiru ka bari ka warke" "Ahmad mutuwa zan yi, kana ganin yadda na koma. Gara na roƙi gafararku. Maman Ahmad ku yafe mini." "Ina ga mu yi mishi viser a fita da shi." Cewar Damir cikin tausayi yana kallonsa. "Haka za a yi." Ahmad ya ce yana share hawaye. Suna cuku-cukun viser a daren Baba ya cika. Nasreen kuka sosai take yi kamar ranta zai fita, saboda kasa komawa gida ta yi ganin halin da yake ciki. Damir ya riƙe ta ganin yadda take kuka sosai. Haƙuri ya rinƙa ba ta tare da jawo mata aya. Shi kansa Ahmad sai da ya koka. Daya tuna irin rayuwar da suka yi da shi. Yau gashi a kwance ya yi kwanan keso. Kafin gari ya waye asibitin ya cika ana ta koke-koke. Hatta jikokin nasa sun ji mutuwarsa, domin ya canza ya ja su a jiki ga shi da tsokana. Sun saba da shi ya iya baƙar magana da barkwancin. Gida aka wuce da gawar, nan suka ci gaba da kuka suna roƙon masa gafara, har aka yi masa sutura aka kai shi makwancinsa, sannan suka zauna zaman makoki. Duk abin da ake ci Damir da Ahmad suke ɗawainiya, domin abincin mai kyau da ruwan faro ake sadaka dashi. Aka ci gaba da karɓar sadaka. Farouk, sai da ya ɗauki tsawon shekaru goma sha biyun, sannan ya samu ya haƙura da ita. Matarsa Maimuna ta haihu har sau biyar domin gwarne take yi, kuma ya kula da yaran, domin yanzu yana son yara. Ko su Raihann yana jin labarinsu ta gurin Anty Asiya da bata yin wata ba tare da ta zo ganinsu ba. Sannan ta hannunta yake musu ihsani, duk da Nasreen ta nuna ba sa buƙatar komai. Yana sonsu domin suna da numbarsa, amma cikin su babu mai kira, domin sam ba da ɗaukar sa a matsayin mahaifinsu. Damir suke kallo a matsayin ubansu. Jin rasuwar baba, sai ya sanya Maimamuna da yaransa suka shirya su je gaisuwa. Sosai ya ji mutuwar Baba abin da ya faru tsakaninsu ya yi ta dawo masa, har kuka sai da ya yi. Godiya ya yi da ya shiryu kafin ya mutu. A ranar sadakar uku suka je gaisuwa. A gurin maza ya zauna matarsa ta wuce ciki. Zama ta yi babu wanda ya santa. So take ta ga Nasreen da mijinta ya sha suɓutar kiran sunanta. Ya gaya mata har yau babu macen da ta kaita a duniya. Ta san cewa da zai yi mata ko rabin soyayyar da yake mata a yanzu ta yi sa'a. Tun tana jin haushin kiran sunan har ta haƙura domin ta san ba zai daina kira ba. A dalilin hirar da yake mata na Nasreen take saurarensa, tana taya shi jimammin rashinta, har ta samu matsuguni a zuciyarsa. Damir a lokacin da ya yi sallama sai da ya ji wani iri. Tsawon shekaru bai sanya ya manta da shi ba. Kalonsa ya yi, ganin ya zube ya rame tamkar ba shi ba. Gaisuwa ya yi cikin tausaya, sannan ya koma gefe ya zauna, yana satan kallon Damir da yake gefensa. Farouk sai ya ji hankalinsa ya tashi, ya kalli kansa ya muzanta. Ganin yadda Damir ya dawo. Ya tabbata ko Damir ya mutu, Nasreen ba za ta iya auren sa ba, domin babu macen da za ta rabu da shi ta aure shi. Da sauri ya yi ƙoƙarin mayar da hawayen da suka taru gefen idanunsa. Ganin yadda ya yi sanyi, Damirr ya miƙa masa hannu suka gaisa. Gaisuwa Faruk ya yi masa ya amsa. Ahmad ne ya fito da kulolin abinci, Marwana na bayanshi suna magana. Wani irin bugawa zuciyarsa ta yi ganin Marwana. "Ashe auren ta ya yi sun zama dangin juna?" Sai ya ji wani irin hawaye. Ya kalli Marwana da yaransu biyu suka riƙe mata hannu, da alama abu suke tambayarta yadda suke magana. Ahmad duk da rasuwar da aka yi masa, amma yana kallonta cikin tsananin soyayya. Damir ya miƙe ya kalli Faruk da ya zauna ya yi shiru."Mu je ka yi musu gaisuwa." Ya ce tare da miƙewa. Babu musu ya miƙe ya bishi ciki. Mamaki yake yi ganin kyawun gidan sun yi kuɗi. Ya ƙara tsorata da lamarin Ubangiji. Tabbas ya yarda bai kamata ace mutum ya yi ma wani gorin arziki ba. Yau ga su Nasreen, da ya raina yake ganin auren shi ne kawai mafita, Allah ya azurta su har sun fishi. Kiran Nasreen da take zaune gefen Mama ta yi. Tun da matar Faruk ta shigo take bin ta da kallo. Yaran ta kalla cikin mamaki, ganin suna mata kama da Faruk, amma saboda halin da take ciki dai ba ta gasganta ba, kuma ta san babu yadda za a yi ya zo. Tana ƙudundune cikin hijabi kiran Damir ya shigo. Da ta ɗauka sai ya ce,"Hello baby ki fito za a yi miki ta'aziya." "Ok," Ta ce ta fita domin a tunaninta 'yan'uwansa ko abokansa. Tana zuwa ya kama hannunta. "Har yanzu ba za ki daina kuka ba? Nasreen wanda ya mutu ya riga ya mutu." Jikinsa ta faɗa tana kuka ta ce,"Na kasa yarda Baba ya tafi ya bar mu. Ina tuna rayuwar da muka yi da shi. Duk da bai sauke haƙƙinsa ba, ina jin zafin rashin sa saboda soyayyar da Allah yake sakawa tsakanin iyaye." "Is ok, ki yi mishi addu'a. Ga wanda ya zo ta'aziya ku gaisa."Ya ce mata yana nuna mata Faruk. Kallonsa ta yi cikin tsanani mamaki. Yanzu ta gasganta matarsa ce. "Ya Damir don me za ka kira ni don ya zo? Ko kana son ka tuna mini abin da suka yi mini da Baba?" "Ko kaɗan Nasreen gaisuwa ya zo miki. Fuskarsa kawai kika kalla, za ki tabbatar da wanan ba Faruk ɗin da kika sani ba ne." Farouk da ya rikice ganin yadda ta zama babban mace, irin masu ji da kyau da hutu. Ya buɗe baki cikin rawar murya ya ce,"Na san za ki faɗi haka don Allah ki yafe mini. Nasreen na cutar dake da Baba, amma gani na duƙa ina neman mana yafiya ni da shi. Ki yafe mana mun cutar da ke. Haƙiƙa rayuwa ta koya mini darasi. Kaicona da na kasance daga cikin WASU MAZAN da ba su ɗauki mace a bakin komai ba. Kaicona da na kasance azzalumi ga rayuwar mace na ɗauke ta a matsayin baiwa. Wacce na ke biyan buƙata ba tare da na fahimci darajar da Allah ya ba ta ba. Haƙiƙa na cuci kaina na kasance daga cikin WASU MAZAN masu cutar da mata. Rayuwa ta koya mini darasi. Rashin ki ya sanya na gane sakacin da na yi wa rayuwata. Na rabuwa da mace kamarki. Kaicona ina ma ace duniya za ta ƙara bani zaɓi mu dawo da rayuwar aurenmu baya. Da na zama bawa a gare ki. Na yi kuka na yi dana sanin rikon sakainar kashi da nayi miki da yarana, saboda haka babu shaƙuwa da ƙauna a tsakaninmu. Ina son su, amma ba sa son ganina a matsayin mahaifinsu." Ya ƙarashe maganar yana hawaye sai kuma ya duka ya ɗaga hannunsa. "Don Allah ki yafe mini kar na mutu da haƙƙinki. Ki yafe mini cutarwar da na yi miki domin duniya ta koyar da ni." Sai ya fashe da kuka tuna haurinta a ciki da ya yi ta durƙushe tana kuka, amma bai kula ba. Kasa cewa komai ta yi, sai ta fashe da kuka zata tafi. Damir ya riƙo hannunta. "Please ki yafe mishi ya yi nadama." "Ya Damir ya cutar da ni." Ta ce tare da ƙara sakin kuka. "Ki yafe mishi Allah ma muna masa haƙuri ya yafe mana." "Don Allah ki yafe mini, wataƙila na samu farinciki a rayuwata, domin tun da na rabu dake na kasa samun sukuni." Ya furta mata cikin muryar kuka. "Na yafe maka Allah ya yafe mana." "Amin na gode." Ya ce tare da miƙewa. "Damir kai ma ka yafe mini, na wulaƙanta ka da na yi. Sannan ka yafe mini na barin maka ɗawainiyar yaran da na haifa. Duk da ba ni da abin biyanka, amma a shirye na ke don na biya ka saboda ku fahimci ina sonsu." "Ban yi don ka biya ni ba, saboda na yi don Allah da farincikin rayuwata matata Nasreen." Rintse idanunsa ya yi, jin sunan da ya kira ta da shi. Damir waya ya fito, ya kira yaran duka da kuma Ahmad har da Marwana. Suna fitowa suka ganshi sai suka yi tsaki za su koma. Ita da Damir suka yi ta ba su baki, sanan suka haƙura. Yaran kuwa da suka zo gaishe sa suka yi. Farouk sai ya rungume Musaddik da Raihan yana kuka."Don Allah ku yafe mini don Allah." Sororo suka yi suna kallonsa, duk da sun san Damir ba shi ne mahaifinsu ba. "Oya go to you Daddy Raihan and Musaddik forgive him." Cewar Damir yana kallon su. "Mun yafe mishi." Suka haɗa baki gurin faɗin haka. "Allah ya yafe mana duka." Cewar Damir. "Matata tana ciki da ƙannin Raihan, tare muka zo gaisuwa." Ya furta yana share hawaye. Marwana ta shiga ta yi kiranta. Da ta ƙaraso cikin natsuwa ta yi musu gaisuwa. "Maimunatu ga Nasreen Maman su Musaddik ga su nan." Ya ce ya a kallonta. Kallon kallo suka yi wa juna. Maimunatu sai da ta tsorata, ganin irin matar da ya aura ya saki. Tabbas ya yi saken da yake cewa. Irin waɗannan matan ya wulaƙanta. Tabbas dole ya kasa mantawa da ita. "Ki yafe wa Baban Namir, yana kuka sosai yana gaya mini cutarwar da ya yi miki. A dalilin ki ya fita daga cikin WASU MAZAN da suke cutar da mace ya zama na gari. Yana kyautata mini, duk saboda rashin ki da ya yi. Haƙiƙa Ni ma na ga saken da ya yi. Mace irin ki ba abun wulaƙanta wa bace, amma rabon ki auri wani ne." "Na yafe mishi ba komai." Nasreen ta ce tana share hawaye. Ciki suka shiga suka yi wa Mama gaisuwa, sannan ya tafi yana cizon yatsa. An yi bakwai na Baba, sannan kowa ya watse ana masa addu'a. Tun da aka yi rasuwar suka dawo gida sai Nasreen ta kasa komawa yadda take. Hankalin Damir tashi, domin hatta yaran suna ƙorafi. Sai dai ta shige ɗaki ta yi ta kuka tana tuna rayuwarsu. Ganin tana son cutar da kanta, sai ya shiga cikin ɗakin ya ce,"Yaushe kika fara daina bin umurnina? Nasreen kukan ki zai dawo da shi ne? Baba ya mutu kamar yadda ke ma za ki mutu. Ki yi mishi addu'a a halin yanzu bin da yake buƙata kenan." Ganin yadda ya fusata sai ta faɗa jikinsa."Ina jin tausayin Baba, ina jin babu daɗi yadda ya yi rayuwa da iyalansa." "Baba ya tuba kuma Allah zai yafe masa." "Allah ya gafarta masa." Ta ce tana share hawaye. "Amin, "Ya amsa tare da haɗa bakinsu. Bayan sun yi bacci sun tashi. "Za mu fita duka da yara ki shirya." "To,"Ta ce sannan ta yi hanyar bayi. Wanka suka yi duka suka ɗau gayu. Ita ce kawai ta shafa mai kawai, ta sanya kwalli. Duk da yar gayu ce amma ina babu wannan. A mota shi yake tuƙa su suna hira don su ɗauke mata hankali, amma murmushi kawai take yi in suka sako a zancen. Ganin sun je gurin shaƙatawa sai ta yi mamaki."Yes mu shiga so na ke yi anan ki manta komai. Kuma ki yi mini alƙawarin za ki rinƙa tuna baba ne ta hanyar masa addu'a." "In sha Allahu." Ta ce cikin sanyi. "Umma, happy birthday!" Suka haɗa baki gurin faɗin haka har da Damir suna tafi. Mamaki sosai ta yi gain haske da walƙiya yana tashi. Kallon Ahmad da Marwana ta yi da yaransu. Ashe suna bayanta ba ta sani ba. Babu shiri ta saki dariya, saboda ta manta cewar yau ne birthday ɗin ta. "Muna miki murnar ƙarin shekara. " Ahmad da marwana suka ce, sannan suka miƙa mata gift ɗin su. Karɓa ta yi, cikin farinciki tana murmushi. Damir ya mika mata makullin mota ya ce,"Happy birthday my wife." Karɓa ta yi tare da rungume shi. Yaran suka rinƙa miƙa mata na su gift ɗin. Duk damuwar da take ciki dai ta ji babu. Dariya sosai take yi, ganin yada suke son sanyata a farinciki. Kallon ƙananan yaran ta rinƙa yi, da suke ta wasa da ball suna guje-guje. Da aka zo yanka cek Nasreen ta yanka, ana kallonta suna tafi kowa ya buɗe bakinsa. Rasa wanda za ta sakawa ta yi, duba mahimmanci da suka yi a rayuwarta. Da ta yanko sai ta bi Ya Ahmad Marwana sai kuma ta sakawa Damir.Ihu suka ɗauka suna tafi shi kuma ya rungume ta.Yaran ma suka haɗata da shi suka rungume. Marwana da Ahmad suka rungumu su. Ƙarshe! Alhamdulillah Na sadaukar da littafi WASU MAZAN, ga duk wata mace da take sha wahala a gidan aurenta. Idan mai shiryuwa ne Allah ya sa ya shiryu kamar Faruk. In kuma ba mai shiryuwa bane Ubangiji ya ba ta miji kamar Damir. Godiya Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangiji, da ya ba ni baiwa da fikra da na rubuta labarin WASU MAZAN domin haƙiƙa ya ciri tuta. Ba zan iya cewa komai ba a kan littafin WASU MAZAN, saboda gaskiya Alhamdulillah. Ina godiya ga masoyana masu kirana da kuma waɗanda suka rinƙa biyu ni pc suna faɗin basirar da na saki a littafin. Masu comments, Allah ya saka da alkahiri kuma ina rokon za a yi mini zafafan comments, a sabon littafina, kamar yadda kuma yi a WASU MAZAN domin comments ɗinki yana sanya ni nishaɗi. Sai mun haɗu a sabon littafina mai suna ƘIYYAYAR JINI. Kun dai san alkalamin mutuniyar taku ba ya shirme.