(Daga Fushina) 2 Littafin Sumayyah Abdulkadir takorikabara@gmail.com SADAUKARWA NE GA DUK MAKARANTA LITTAFAI NA A DUK INDA KUKE. NA HUCHE 2! Habibu Mustapha Nahuche ya sauka a filin jirgin saman Abuja daga Frankfurt ta kasar Jamus da misalin karfe shidda na safiyar Jumaah, yana rungume da dan sa Abdallah a kafadun sa na dama, wanda ke ta barci sadidan cikin gajiya tun suna cikin jirgi. Kai in ka ga irin rikon tsantsenin da yayi ma dan na sa, gami da tsantsar kulawar da ya ke baiwa kankanin yaron, tsammani za ka yi cikin sa zai maida shi don tsananin So da kauna irin ta mahaifi. Mahaifin ma irin Habibu Nahuche wanda samun Uban da ke son dan sa kamar sa sai an tona. Har ila yau, tsatstsauran rikon da ya yi wa yaron, yana da nasaba da kasantuwar sa cikin fargaba da tsoron ko Raheenah za ta biyo bayan su afujajan kafin su kai ga sauka a kasar su ta haihuwa, Najeriya. Duk da ya san hakan ba mai yiyuwa bane ba tare da shiri ba. Amma hanakalin sa bai kwanta ba har sai da ya gan shi a filin jirgin saman birnin tarayyah. Saboda yana da tabbacin abu daya: A yadda Raheenah ke son Dan ta, da yadda ta damu da kasancewa tare da shi ko barci bai taba raba su ba, da kuma yadda ya san ta wajen kafiya da naci akan abun data ke so, da bakin cikin shammatar da ya yi mata, ya tabbata za ta iya takowa ko da da rarrafe ne ko da akan gajimare ne tun daga Frankfurt, ta biyo bayan su ta cikin hazo don ta kwace dan ta Abdallah, shi ya sa bai je dauko Abdallah daga gidan Ambasada bama sai da ya kayyade ya kuma kintaci lokacin tashin jirgin su. A yayin da jirgin ya karci kasa ya bar babban birnin Frankfurt din Jamus, sai ya ji tamkar ya nannade komai na Raheenah Omar daga zuciyar sa, tamkar yadda ake nade tabarma, ya baro shi a can. Ya cire ta kenan HAR ABADA daga rayuwar sa, ya hakura da ita, ko da ita ce autar mata a duniya, kamar yadda babu shi babu kara yin aure a duniya. Raheenah Omar, ta kassara shi, ta raunata shi, ta ji masa ciwo mai muni a zuciya, bashi da sauran wata soyayya da zai iya baiwa wata diya mace, ta kashe duk wani burin sa a kan yaya mata (ko dama can bai da buri akan su, ita kadai Allah ya sallada zuciyar sa kan ta, ya jarrabce shi akan ta da mafi girman jarrabawa). Juya masa baya da ta yi da sulhun da ya nufa na alkhairi a gare su ya dauke duk wani farin ciki da walwalar sa, ta zagwanyar da farin cikin achievements din da ya dawo da su daga kasar Germany. Wato kwalayen sa guda biyu, masu daraja ta farko. A kan ta ya san so, a kan ta ya fara so, haka a kan ta ya kare so, kamar yadda daga kan ta ya rufe SO. Ta tafi da dukkan (charming and amiable) Habibu Nahuche bata bar shi da ko guda ba cikin dabiun sa da halayen sa na baya. Amma a matsayin sa na musulmi kuma haihuwar musulunci, ya san komai muqaddari ne daga Allah watakila Allah ya rubuta iya rayuwar auren da zai yi da Rahinah kenan ta kwanaki bakwai, watakila a rubutun kaddarar su; babu sauran zama a tsakanin su. Hakan ba zai sa ya kasa rayuwa a kasar haihuwar shi ba. Hakan ba zai hana shi godiyar Allah da ya bashi tsatso daga gare ta ba. Zai yi gammo ya dauki rayuwa a duk yadda ta zo masa, ba tare da Rahinah Omar a cikin ta ba. Abin da zai sa a gaba yanzu shi ne: hanyoyin da zai bi ya maida kobo ya koma dari don tserewa bakin ciki da takaicin duniya, don samawa Abdallah kyakkyawan future, da kuma hanyar da zai bi wajen rainon gudan ran sa (ABDALLAH), zai yi duk yadda zai yi wajen ganin ya bashi rayuwar da ta dace da kowanne Da mai gatan UBA har ma da UWA (tunda Hajiya da Badiya na raye) da kuma ilmi mai inganci. Ko a lahira ba ya fatan Allah ya sake hada shi ko a hanya da uwar Abdallah.. Infact, abinda ya lura a tare da Raheenah Omar; babu zuciyar imani ko kankani a cikin tsakiyar kirjin ta, babu compassion, babu love, babu affection, ita da sassakakken dutse basu da maraba. Taurin kai ko irin na mutanen farko, she has no love in her talk more of offering it to someone. To Idan so cuta ne. Hausawa suka ce hakuri ma magani ne!. Zai hadiyi hakurin nan komin dacin sa, komin baurin sa, komin girman sa, zai kuma hada da addu'a da rokon Allah dare da rana kan ya fidda Rahinah da komai nata daga zuciyar sa da rayuwar sa bakidaya. Daga Abuja shatar karamar mota ya dauka kai tsaye har garin su Zamfara, tun a wancan lokacin jihar Zamfara babu filin jirgi. Ya tsaya ya yi canjin kudin sa a Abuja daga Euros zuwa Naira, ya saya wa Abdallah abincin da zai rika ci a cikin mota har su isa Zamfara. A lokacin Abdallah ya tashi daga barci sai faman kalle kalle yake na ganin sa a bakon wuri da bakin fuskoki, amma ko tari bai yi da sunan kuka ba, tunda dama ya saba da Baban sa sosai. ****** UNGUWAR KOFAR JANGE ZAMFARA STATE (GIDAN MARIGAYI ALH. MUSTAPHA BILYAMIN NAHUCHE) Y au unguwar kofar Jange cike take makil da matasa, ana ta hada-hadar siyasa, unguwar ta cakude da hargowar samari da 'yan jagaliyar siyasa masu yawo da fastocin 'yan takara suna musu kamfen. Don haka da kyar direban da ya dauko su ya samu hanya suka kutsa suka isa har kofar gidan da ake kira 'GIDAN NAHUCE'. Duk inda suka gifta cikin unguwar tasu sai Habibu ya bi wurin da kallo (with nostalgia) da tsananin begen gida, yana mai tuno wani abu na dabdalar kuruciya da ya yi a wurin, shekaru bakwai kenan da barin sa gida idan har lissafin da yake yi daidai ne. Yau ga shi ya dawo gida lafiya, amma ba shi kadai ba kamar yadda ya tafi, ya dawo ne tare da wani replica din sa (photocopy of Habib Nahuce). Wanda kaddara ta tanadar masa, ta kuma ba shi ba tare da ya tsara ba. Yana godiya da wannan kaddara tasa da hannu bibbiyu, domin kyautar Da sukutum! Rahma ce daga Ubangijin Talikai. Wadda ba kowa Allah yak e baiwa ba. Hajiyar Nahuce (kamar yadda kowa a dangi dama jamaar unguwar ke kiran ta) tana alwala da buta a gindin famfo lokacin da Habib ya yi sallama. Muryar sa ta dira a cikin kunnuwan ta kamar cikin mafarki. Sai ta dakata daga wanke kafafun ta da ta ke yi, ta yi tsam! Da ran ta, tana son gasgata abin da ta ji. Kafin ta dago manyan idanun ta wadanda da gani ka san babu tambaya ita ce ta haifi Habibu Mustapha Nahuce. Alamun girma da ya soma kamata bai boye zahirin kamannin su ba na Rumawan Nahuche. Bude baki ta yi cikin mamaki, da tuajjibi, don ko shekaranjiya sun yi waya dashi Habibun, amma bai ce mata yana tafe ba. "Wa nake gani kamar Habibuna? Habibullahi?" Duk yadda Da ya kai ga canjawa, cikin halin jin dadi ne ko akasinsa, to fa Uwa ba ta kasa gane abinta. Don haka komawar Habibu kyakkyawan Bajamushe kuma gogaggen bakin bature bai hana Uwarsa Hajiya Kaltume gane shi ba, daga kallo na farko da ta yi masa. Har gabanta ya karaso ya sunkuya, cikin gajiya, sannan ba tare da ya ce komai ba ya mika mata Abdallah da ke hannunsa makale a kafadun sa. Amma sai Abdallah ya ki zuwa, ya makale sosai a jikin Baban nasa. Jikin Hajiyar Nahuche ya hau rawa da makyarkyata. "Ni Kaltume Nahuce! Habibullahi ina ka samo yaro mai kama da kai haka???" Ba jikin ta kadai ba, hatta muryar ta Hajiya karkarwa take yi. Magana ya shiga yi wa Abdullah da harshen German"Abdallah Sie istmeine Mutter, geh zuihr (she's my mother go to her)". Yaron ya make kafada cikin rashin yarda, tare da sake makalewa cike da tsoro da kyuya a jikin Abban sa. Yara suka soma shigo da jakunkunan Habibu manya-manyan trollies. Haj. Kaltume gabadaya mamaki da tsoro ya hana ta kokarin karbar yaron da yake ta faman son ta karba. Sai ta fara hawaye daga tsaye. Sakamakon abinda zuciyar ta ta hasaso ta kissimo mata. "Sai ka fara gaya min ina ka samo shi tukunna zan karbe shi, Habibu Allah ya sa ba shegensa ka yi ba a can kasar masu jan kunne". Idanunta na zub da hawaye suna nuna tsananin kidima da fargabar da ta ke ciki. Da sauri Habib ya hau girgiza mata kai. Shima nasa idnun suka kawo kwallah. "Wannan ba rainon da ki ka yi min ba ne Hajiyata, ban taba yin zina ba, ban taba kusantar ta ba, tun ban san ma'anar ta ba kike nusar da ni illar ta, kuma har in mutu ba zan yi ba insha Allahu. Ina baki hakuri Hajiyarmu, domin hakika na miki laifi, (na yi aure a Jamus ba da saninki ba)". Dogon Salati Hajiyar Nahuce ta saki, "Aure kamar ya ya?" Habibu bai bata amsa ba, sai ya kara mika mata Abdallah, wannan karon ba musu ta sa hannayen ta biyu ta karba, tunda dai ta samu tabbacin ba shegen sa akai ba. Sannan kalmar aure ta gitta. Komai zai biyo baya a ganinta zai kasance da sauki. Daki suka shiga, Habib ya shigo da jakunkunan sa, kafin ta yi komai flask ta jawo wanda dama ba ta rabo da kunun tsamiya a cikin sa, ta zuba a kofi ta saka dan suger ta motsa ta soma kokarin baiwa Abdallah. Kasancewar Yafendo tana ba shi ya san kunu sosai, ya karba yana sha, ta dora shi a cinyoyinta tana rirriga shi, sannan ta maida hankalinta kacokam a kan Habibun, wani irin mabayyanin bacin rai kwance-kwance baro-baro a kan dattijuwar fuskarta. "Yanzu Habibullahi wuyan ka har ya yi kaurin da za ka yi aure kan gaban kanka babu sanin kowa naka? In Shafa'atu ce ba ka so ai ba sai ka yi haka zan san ba ka son ta ba, wane irin aure ni 'ya su sai ka ce wasan yara? Ina uwar dan da za ka dauko wannan dan tatsitsin yaron tun daga wata uwa duniya kai kadai?" Habibu Nahuche, bai taba barin weakness din sa ya bayyana a gaban kowa ba, amma wannan UWA ce MAHAIFIYA ce, kafadar da kowanne dan Adam ke iya sauke damuwar sa babu haufin komai. Don haka sanda ya fara hawaye bai san sun zubo ba, dacin tuno kiyayyar Rahinah gare shi, sai da ya ji saukarsu a kan kundukukinsa, da damshinsu a kan fuskarsa. "Na yi duk iya kokari na a kan ta so ni, ta zauna da ni mu raini dan nan da Allah ya bamu tare abu ya faskara. Ban san meye aibu na har haka ba da Rahinah ta ki ni. A karshe mun rabu, rabuwa ta har abada, ni kuma na dauke Dan ba da saninta ba, amma marikanta sun san na dauke shi". Ya kwashe gaskiyar komai, har sanadin auren ba-zatan ya gaya mata, sai dai wani sirrin ai bai faduwa, balle sirrin aure. Ya tsaya ya kafe a kan Raheenah ba ta sonsa kawai, sabida ya aure ta baa hannun iyayen ta ba, yace aurensu kaddara ne kawai da rabo rantsatstse daga Allah. Haj. Kaltume ta rasa abin da za ta ce, amma sai ta ji ya fi mata a kan a ce Habibu zina ya yi ya kawo mata yaron nan. Ta rungume Abdallah sosai a kirjinta, wanda zuwa lokacin ya samu barci yana sauke ajiyar zuciya. A daren ranar ta kira Badiyya wadda ke aure a garin Kaduna, ta ce duk abin da ta ke ta bari gobe ta zo Zamfara maganar ta fi karfin waya. Sannan ta sa almajiri ya share wa Habibu dakinsa, ya wanke masa toilet dinsa, sannan ya shigar masa da dukkan kayansa. Girki na musamman ta yi musu, tuwon shinkafa da miyar taushe da naman saniya zuku-zuku a ciki, ta yarfa man shanu sannan ta hadawa Habibu kunun zaki kasancewar yana son shi sosai mutumin sa ne, amma na gasara ziryan ba na farau-farau ba. Da dare ya yi Abdallah ya rikice kan bai kwana tare da Hajiya, sai Momin sa, don haka tare suka tafi dakin sa dake zaure yana ta rarrashin sa, sai da ya yi barci ya dauko shi ya maido wa Hajiyar shi. Hajiya Kaltume tana sallahr dare kamar yadda yake a aladar ta, jefe-jefi tana juyawa tana kallon kyakkyawan yaron dake barci cikin nutsuwa a gefen ta mai tsananin kama da Habibu, tamkar Habibun a lokacin da yana kamar sa, kaunar yaron na dada shiga ran ta, a cikin kowacce sujjadah data yi tana yi masa addua Allah ya raya shi rayuwa mai tsayi da albarka. Cikin wannan daren mai dimbin tarihi a rayuwar Habib da Raheenah. Dukkan su babu wanda ya runtsa. Ya fidda layinsa na kasar Jamus ya karairaya shi, ya taune shi ya zubar, ya saka MTN NG da ya saya a filin jirgin saman Abuja. Yana fatan yadda ya karairaya shi haka ya zubar, zuciyar sa ta karairaya Raheenah Omar ta zubar, da duk abinda ya shafe ta. Amma ko da ya so yin barci, sai barci ya ce dauke ni inda ka ajiye ni. Shin ko yaya rayuwa za ta ci gaba musu shi da Abdallah? Shi maraicin matar da yake so daya da daya a duniya? Abdallah maraicin uwar da ya budi ido da ita? Wata Tambaya ce mai wuyar amsawa farat daya, da ya kasa amsawa kan sa, ya ce bai son ta ma ya san wannan yaudarar kai ne. Raheenah Omar, ta shigo rayuwar sa da wani irin karfi, ta yi tasiri mai yawa a cikin ta cikin auren da bai gaza kwanaki bakwai ba. Tasirin da kafin ya yi nasarar cire ta kwata-kwata, shi ma ya san zai sha wuya, kuma abu ne da ba zai tabbata a lokaci guda ba. But gradually, by trying to follow the path of reality; yana fatan canzuwar kaddararsu, yana fatan Raheena ta bar zuciyarsa ta sha iska haka, ta bar kwakwalwarsa ta sarara, ta bar gangar jikinsa da ruhin sa su huta. Ta bar sababbin abubuwa da suka fi ta muhimmanci su shigo. Ba shi ya iya runtsawa ba sai da ya dawo masallacin Kofar Jange sallar asubahi, sannan ne barcin gajiyar da ya tara ta zaman jirgi da shirye shiryen dawowa da ya jima yana yi ta karkashin kasa suka taru suka danne shi bakidaya. ****** Kukan Abdallah ne ya tashe shi wajejen takwas na safe, ya karade gidan da kuka yana kiran ABBANSA da MOMIN SA... cikin harshen Jamusanci. Zuciyarsa ta yi wani irin karyewa, anya cikin hukuncin da ya yanke babu zalunci a ciki ga yaron da ma uwar kan ta? Yanzu haka yaron zai tashi bai san mahaifiyarsa ba alhalin tana raye a kololuwar duniya? Da tsananin mutuwar jiki ya fito tsakar gidan hannayensa zube cikin aljihu. Ya zubawa yaron ido daga bakin kofar shigowa cikin gidan. Idanun sa sun kada Abdallah na ganin sa ya taho da mugun gudu ya rungume shi, sannan ya soma gaya masa cikin harshen da yafi iyawa ya maida shi gun Mummyn sa, tashi Mummy din ba wannan ba, yana nufin Hajiyar sa. Hajiya Kaltume ta fito daga daki tana ta mita. "Dan nema rigimamme, sakaltacce, ni bana son shagwaba ko kadan, da alama gidan ku can sun gama sangarta ka, in ba haka ba ta ya ya gotai-gotai da kai za ka saki kashi daga tsaye? A ba ka foo ka ki hawa?" Murmushi Habib ya yi, shima ya san da gaske gidan Ambassada sun sakalta Abdallah, ya karaso inda ta ke yana dauke da Abdallahn. "Ke da maigidan naki za mu gan ku a rana, Maman shi pampers ta ke saka mishi ba ta dora shi a wani foo". Hajiyar Nahuce ta ce, "Au? Tunda irin 'ya'yan Badiya ne, to ba zan iya ba, ta zo ta dauki abin ta (Badiyar), su ma haka ta sangarta su da kin hawa foo, yaro dan shekara biyar sai ya saki kashi cikin auduga, mu ba haka iyayen mu suka raine mu ba, to ni ba zan iya wankin kashi a cikin pampers ba da girman yaro da komai". Karshe Habibu ya je ya siyo pampers gari guda ya kawo mata, yana rokon ta kan ta lallaba Abdallah, a hankali zai koyi hawa foo din. Shi zai dinga yi masa tsarkin ya fidda pampers din. Hajiya sai ta ji su duka sun bata tausayi. Sai wajen la'asar Aunty Badiyya ta iso daga Kaduna, Aunty Badiya ba ta kama da Habeebu sam, bazaka ce ma cikin su daya ba, don ita mahaifin su sak ta dauko, fara ce ita Barumiyar Nahuce, sabanin Habeeb da yake wankan tarwada. Aunty Badiya 'yar boko ce sosai, domin kuwa (PHD holder) ce. A wannan lokacin ita ce mataimakiyar Provost ta (Kad-Poly), yayin da mijin ta babban ma'aikaci ne a Abuja, sabida aikinta ta ke zaune a Kaduna sai karshen mako yake zuwar musu. Yaran Aunty Badiya hudu ne duk maza ta karshen ce kawai mace, Zarah, wadda ba ta fi sa'ar Abdallah ba. Zuwan Badiya gida da ganin kanin ta da ta yi da Da, da labarin da ta tsinkaya daga bakin mahaifiyar su ya bata mata rai ba kadan ba. Ta yi fadan kamar ta yi ya ya! A karshe ta ce, "Allah ya kara da ba ta son naka, Allah ya kara karawa, yanzu ai sai ka hakura ka zo ka auri mai son ka (tana nufin yar uwar sa Shafa'atu)". Ita babban bacin ran ta yadda ya boye musu maganar auren nasa a Jamus, kamar wani wanda bashi da kowa, amma Hajiya Kaltume da ta ga fadan Badiya ya yi yawa, duk hakurin da Habibu ke ta bata ta ki sauraron sa, sai ta ce "Maman Zarah, hakuri za ki yi mana, laifi kam ya riga ya yi sai dai tunda ya bada hakuri kuma ya ce ya yi ne don ya ceci kansa daga aikata zina a can, ai ina ga wannan ya isa hujjah, ni tuni na dauki kaddara. Yaro Allah ya raya mana shi, Ya sa Mahaddacin Alqur'ani ne". Badiya ta ce "Hakuri na daya ne Habibu ya auri Shafa'atu, ban ce ta rike masa yaro ba, ni zan hada da na waje na in rike, amma auren sa da Shafa'atu ya zama tilas". Habib da yake neman a yafe masa, ba abinda ba zai yi ba a lokacin. Ya ce da Yayar sa Badiyya "ki bari na gama NYSC sannan a yi maganar auren, ni yanzu da ba ni da abin yi, da me zan yi auren?" Badiyya ta ce, "A can Jamus da me ka yi auren? Cewa nake karatu kake a inda baka da kowa ma? Balle anan da mu zamu rike maka matar. Ka yi auren ka dandani dadin sa da rashin dadin sa ne zaa kyale ka ka ci gaba da zama a haka? In dai Shafa'atu ce ba bakuwar zafi ba ce, za ta iya zama a gidan nan tare da Hajiyar mu, sai a gyara muku sassan Baba". Mikewa ya yi daga gurin yana kakkabe rigar sa, har da kunkuni kamar kuturu yana fadin. "Ke za ki dinga ciyar min da matar? An ce miki a Jamus ko kai dalibi ne kana rasa aikin yi da zai rike iyali? Nan kuwa fa? Ai ki ji da kan ki kawai Yaya Badiya, ki kyale ni in nemi kobo. In gwaninta za ki min, kawai ki kular min da Abdallah". Yaron da ya riga ya shige zuciyar Dr. Badiyatu Nahuce farat daya, har fiye da son da takewa Habibu, ta kara rike shi sosai a jikin ta tana hararar Habibu, a lokaci guda tana mamakin irin karfin jinin sa. Yaro kamar Habibu yayi kakhi ya tofar, bai da maraba da shi a lokacin da yana kamar shi. Addu'a ta ke cikin ran ta Allah ya ba ta lafiya da tsawon ran kula da Abdallah, kamar, ko ma fiye da yana gaban mahaifiyar shi. A washegari ta juya da Abdallah gidan ta a Kaduna. ****** Ba jimawa da dawowar sa ya yi registration na tafiya hidimar kasa. Aka tura shi Kwara State, ya tafi ya bar Abdallah hannun Yayar sa Aunty Badiya. Haka yaro Abdallah ya rayu karkashin kulawar Kakar sa Hajiyar Nahuce da Yar mahaifin sa Dr. Badiyatu Mustapha Nahuce, suna zuwa Kaduna ta sanya shi a Kindergarten na (Kad-Poly) tare da diyar ta Zahrah, kullum sai ta sauke su sannan ta wuce aiki. Sha biyun rana ta sa masinjanta ya dauko su, a can ofis din ta za su yi ta wasan su a gaban ta har ta gama abin da za ta yi su koma gida. In aka yi hutu kuma ta kawo shi Zamfara ya yi hutu a hannun Hajiya Kaltume, sabida wayon yaron da kokarin sa a karatu da hikimar sa da saurin shiga rai a wajen malamai (double promotion) aka yi ta yi masa ya koma Nursery 3 daga Nursery 1. Sanan duk karshen zango shi yake zuwa na daya a aji, kuma sai ya dawo da prizes gida. Dr. Badiya (is highly proud of her son Abdallah) tana fada a koda yaushe. Yana tuna mata da kuruciyar Abban sa shima haka yake da yana kamar sa. Duk inda yayi karatu sai yayi tambari. Zuwa wannan lokacin Abdallah ya manta da Raheenah, ya dauki Badiya a matsayin mahaifiyar sa. Hajiya Kaltume da yake kira "Granny kuma ya san Kakar sa ce wadda ta haifi mahaifin sa. Yana kara girma yana fahimtar alaqar sa da kowa. Tsakanin shi da 'ya'yan Aunty Badiya ba za ka taba iya bambance wanne ne nata wanne ne na kanin ta Habib ba. Yayyen nasu Musaddiq, Mubaraq da Mu'allim suna kula da shi sosai shi da Zarah, don kuwa Uncle Habib (yadda suke kiran Habibu) ba su ajiye shi nan kusa ba, suna matukar son shi, sabida yadda yake nuna musu kauna shima duk lokacin da ya zo ganin Abdallah daga Kwara. Kaunar jini ce ta cakude da kauna ta musamman wadda suke yi wa Uncle Habibu, ta shafi dan sa Abdallah. Ko kuda in suna da iko ba zai sauka akan Abdallah ba. A haka ya kammala NYSC, sai Aunty Badiya ta karbi takardun sa ta baiwa Baban Musaddiq ya tafi da su Abuja don nema masa aikin yi. Kasancewar Baban Musaddiq babban ma'aikaci ne a Federal Ministry of Commerce and Industry wadanda Federal Govt. ke damawa da su a lokacin. Ga shi ya san manyan ma'aikata a can Abuja domin ya dade yana aiki, sai bai sha wahalar samar wa Habibu aiki ba tunda abu ne na wa ka sani, gashi da (qualifications) na Cologne University, ya samu aiki mai gwabi a babban Hotel din NICON NOGA, a lokacin shi ne hotel din da babu na biyun sa a Nigeria. Kuma fannin da Habibun ya karanta kenan wato (Hotel Administration). Habib ya dade a Nicon - Noga, matsayi iri-iri a ya rike a cikin ta, daga karamin matsayi zuwa sama, promotion kan promotion akai-akai. Wani irin mutum ne shi mai nasibi akan duk abinda ya sa gaba. Ba don haka ba manyan mukaman da yake samu akai-akai a NICON cikin 'yan shekaru kalilan da bai isa ya same su a yan shekarun ba. Don akwai wadanda suka fi shi jimawa amma basu kawo matakin shi ba, abin kuma har da kwarewa da baiwa ta daban (exceptional talent) da Allah ya bashi. A lokacin ne aka bude babban hotel din Najeriya watau TRANSCORP HILTON inda Habib da wasu daga cikin manyan ma'aikatan (Nicon - Noga) suka samu karin matsayin komawa (Transcorp - Hilton), inda Habeeb ya rike mukamin mataimakin manager, ba kananan kudi ke shigo masa ba domin kuwa a Nigeria gabadaya babu hotel din da ya kama kafar (Transcorp - Hilton) a birnin tarayyah. Yawanci turawa, larabawa da sauran jajayen kunnuwa ke sauka a can idan suka zo Nigeria kan harkokin su, sai ko kusoshin kasar mu, da manyan 'yan kasuwanni, da ke yin conferences acan. ****** NAHUCHE HOTELS, ZAMFARA I dea din mallakar hotel nasa na kansa ta dade da ginuwa a ransa. A hankali yake saving, har ya tada tubalin ginin karamin gidan saukar baki 'guest inn' a kasar shi ta haihuwa wato ZAMFARA. Da nan ya fara kamar da wasa, sai gashi Allah ya sa masa albarka da ilhama a ciki, ya fadada guest inn din ya maida shi babban hotel mai zaman kan sa a jihar ta Zamfara cikin Gusau. Sabida yadda ba ya tsauwalawa ne da kuma kyawun hotel din gami da nagartar ma'aikatan sa ya sa ya yi attracting customers da masu kudin Zamfara nan da nan, inda ya fara da yi masa branch a birnin Tarayya, daga nan sai Lagos, inda can ne ya zamo (headquater) na (NAHUCHE GROUP OF HOTELS). A cikin shekaru goma da dawowar sa daga kasar Jamus ya mallaki hotels manya-manya a duka manyan jihohin Najeriya. Ba ya wata sana'a sai wannan wadda ya karanta yake kuma da experience a kai, wato (Hotel Administration), ya san duk wata hanya ta bunkasa hotels (gidan saukar baki) a zamanance daga (Cologne) inda ya yi digirgiri da masta. Daga nan ne kuma 'yammata suka ce salamu alaykum, ta hanyar budewa Habibu wutar so da kokon bara, kamar za su cinye shi danyen sa, ga kuruciya ga rufin asiri ta ko'ina ya samu, amma babu iyali. Ga kyau na Zamfarawan usli tushen garin Nahuche. Ko marmarin aure ba ya yi, ba abinda baa cewa a kan sa a dalilin rashin aure, lokacin da sunan sa ya fara karade kafafan yada labarai a matsayin (Young Nigerian Hotels Owner) wasu ma sun ce neman maza ya hana shi aure. Irin wadanan miyagun maganganu da aka soma yi a kan Habibu Nahuche suna dawowa kunnen Yayar sa Badiya, kasancewar ta mai taammali da mutane daban-daban, ta sha titsiye shi ta ce, sai ya gaya mata ko ba shi da lafiyar da zai iya aure ne? A irin wadannan lokutan, Habib Nahuche, dariya yake yi sosai, ya cewa Badiya, "Ba ni da lafiyar ki ka gan ni da Da na mai tsananin kama da ni?" Sai Badiya ta ce cikin kankantar da murya, "To Habibu ko dai da gaske kana deviating ne saboda bakin cikin Maman Abdallah ta ki ka?" A wannan karon ma murmushi ya yi wanda Badiya ta kasa fassarawa, yayi kasa da kai, sannan nan da nan murmushin ya bace daga kan kyakkyawar fuskar shi, sabida wannan ba shine karo na farko da yaji hakan ba (ana masa mummunan zargi), ya ce cikin Bazamfariyar Hausar shi mai dadin sauraro; "Wannan kuma ai tsakkanin bawa... da Ubbangijinsa ne". ***** Zuwa yanzu kam Shafa'atu 'ya'yan ta biyar kenan, tana auren ta a Talata-Mafara. Da farko ta gwada jiran sa kamar yadda Badiya ta kwadaitar da ita har ya gama NYSC ya samu aiki, amma tunda ya sa kafa a (Nicon - Noga) ba ta kara jin komai a kan sa ba. Bata kara jin duriyar Habibu ba. Zumunci ma ya yi rauni tsakanin iyayen su a dalilin hakan don iyayenta sun dauki laifin komai sun aza a kan Hajiyarsa, a ganinsu da ta takura masa da tuni ya auri Shafa'atu. Ita kuwa Hajiya Kaltume kullum Allah ta ke kai wa kukanta a kan auren dan ta Habibu, shi kuma ta bar wa zabi. Baa shaidar dan yau, amma ita kam ta shaidi nata. Sabida yawan ibada da tsaida sallah yana hani dga aikata alfasha wanda kuma kowa ya san dabiun Habibu kenan, ga yawan azumin tadawwui. Ta dade da sanin akwai abinda ya kulle a zuciyar sa tun daga kan Maman Abdallah. Wadda ita tasa ya ki jinin mata. Duk ya hada su yayi musu kudin goro. Har ila yau, Hajiya Kaltume ta gama fahimtar ba ya son Shafa'atu, in ta takura masa ya aure ta zaa bata goma ne daya ba ta gyaru ba. A lalata zumunci kuma auren bazai dore ba. Sannan ta fahimci baya yin wani abu na banza duk da ba tare take da shi ba a yawancin lokuta amma ta fi kowa karantar sa, bata taba jin yana waya da 'yammata ba. Don ba wayar da ba ya iya amsawa a gaban ta. Ta fahimci in ta takura masa ya auri Shafa'atuba zai kula da ita ba don kwata-kwata yanzu hankalinsa bai kan mata. A duniya abu uku ya sanya a gaba; (bautar Allah da neman kudi, sai rainon dansa Abdallah, Dan da Raheenah Omar ta haifa masa). Ita kan ta Dr. Badiya ba karamin gata ta ke samu a wurin Habibu ba, duk da kasancewarta mai albashi mai tsoka nata na kanta itama, to balle kuma mahaifiyarsa da Dansa. Wadanda duk abin da ya samo nasu ne, a cewar sa su yake nemawa. Duk fadi-tashin sa a rayuwa sabida su ne. Sau uku a jere Haj. Kaltume da Badiya na tafiya aikin Hajji duk shekara. Tuni ya buge gidan su an zuba gini na zamani na gani na fada, kai ka ce gidan wani minista ne ba gidan tsohuwa Kaltume matar marigayi Bilyamin Nahuce ba, duk fadin unguwar Kofar Jange babu gida mai fasali da zubin zamani da ya kai kwatankwacin GIDAN NAHUCE. Ga maaikata rututu Habibu ya zuba mata. Kullum zaka sameta zaune a tankareren falon ta akan kilishi mai taushi tana lazumi tana ibadah, don a cewar ta su kadai suka rage mata yanzu, sai ko ganin auren Habibullahi. Hajiyar Nahuche ta zama wanke goma ka tsoma biyar. Jawur da ita, tsafta da naira sun kama jikin ta. Ga hasken rikon addini. Gidan ta kullum cike da yan cin arziki daga jamaar unguwa dana garin su Nahuche. Daga baya Hajiya Kaltume ta soma karbar tayin hotunan 'yammata da ake kawo mata daga Nahuche da Bungudu, sannan yayan masu da shi anan Zamfara da iyayensu ke son hada auren 'ya'yansu da Lucky Habibu Nahuce duk haka ake kawowa Hajiyar Nahuche. Eh, wasu kan kira shi 'Lucky' sabida kafin ka samu mutum mai sa'a a kan duk abin da ya sa gaba kamar Habibu Mustapha za a dade. Komai ya sanyawa hannu na harkokin sa sai ya zama kamar magic sai ka ga ya bunkasa ya shahara ya yi albarka cikin dan lokaci. Wannan kuma albarkar bakin UWA ne da addu'o'inta da ba sa yankewa a gare shi. Kullum Haj. Kaltume a kan dugaduganta take kwana sallah, kuma duk yawancin addu'o'in ta akan Habibu ne. Nasarar rayuwa, kariya daga sharrin Shaidan, albarka a dukiyar sa, da mata tagari (wadda zata kaunace shi saboda Allah ba don dukiyar sa ba) su ne abubuwan da kullum take roka masa. Hotunan 'yammata iri-iri 'ya'yan manya a garin Zamfara da garin Bungudu da Nahuce an sha kawo wa Hajiya Kaltume, amma a duk lokacin da ta dumfari Habibu da su ko dubawa ba ya yi zai ce, "Ki yi hakuri Hajiyata, ni na riga na gama aure a duniya". In ta takura masa kan sai ya duba kuma sai ya fara mata yan kanan kwallah, da dole zata mayar dasu inda ta dauko cikin mutuwar jiki. In ya so tsokanar ta kuma sai yace. Hajiya kada ki damu akwai (hurul eeni a aljannah, inshaAllahu). Bata taba daukar maganar sa a bakin komai ba, face lokaci ne bai yi ba, in lokacin yayi shi da kan sa zai kawo mata matar da yake so, bacin ran uwar Abdallah (Rahinah) ta yi amanna da cewa shi ke walagigi da shi har zuwa lokacin. Ya ke ganin don ita ta ki shi, ba zai samu mai kaunar sa ba. Ko kuwa an ce ita ce autar mata da za'a debewa sauran mata tsammani a kan ta??? A bisa wannan dalilin Hajiyar Nahuche ta ji ta fara tsanar wannan Rahinah duk da bata taba ganin ta ba ko a hoto. ****** MUTANEN JAMUS (BAYAN BARIN HABIBU FRANKFURT). Tun daga lokacin da Habibu ya dauke mata Abdallah, rayuwa bata kara komawa yadda ta ke a baya ba ga Raheenah Omar. Sauran kadan ta zama depressed wato ciwon damuwa ya kama ta. Ita kadai sai ka same ta a dakinta tana magana cikin safah da marwah, karatu ta daina fahimtarsa kwata-kwata, zuwa makarantar tana yi ne kawai bisa tursasawar Nene da Ambasada Shehu, amma ta kasa concentrating a kan komai. Komai ya fice mata a ka. Hatta kasar Jamus bakidayan ta. A jarrabawar karshen zangon da suka yi Ambasada Bichi bai ji dadin sakamakon Raheenah ba ko miskla zarrah; ta fadi courses har biyar. Don haka ya kira ta falonsa don su yi magana ta Uba da Da. "Rahinatuh. Ina son sanin hakikanin abinda ke damun ki? Akalla in ban miki maganin sa ba a matsayina na Uba zan baki shawara wadda nake ganin ta dace. Wannan wane irin mummunan sakamako ne nake gani haka?" Raheenah ta share zufar da ta jika goshinta, cikin rauni da karaya ta ke wa Baban ta Ambasada magana. Ba tare da ta san maanar abinda take furtawa ba. "Ni kai na Daddy (ban san hakikanin abin da ke damuna ba), rayuwar ce kawai na gaji da ita. Na fi so in mutu in huta. Ji nake kamar ni kadai na yi saura a duniya, kamar rayuwata ta zo karshe......... Kamar babu wani sauran farin ciki da zan cimma a karshen ta, kamar duniya ta ta kare. Ji nake kamar wani tsuntsu ko kuma shaho ya zo daga sama ya tattare dukkan farin ciki na da burika na ya tashi sama firrr! Da su". Wani irin murmushi Ambasada Shehu ya yi, irin nasu na manya da suka karanci halayyr dan adam, kafin ya ce, "Kuma wannan TSUNTSU ko SHAHO ba kowa ba ne, HABIBU ne!!!. He ran away with all your hopes and happiness... (ba tare da sanin ki ba ya tafi da dukkan fata da farin cikin ki). Habibun da ki ke gujemawa da gangan, amma ruhin ki da zuciyar ki na tare da shi da Dan da ki ka haifa masa.. It's either two options; ko dai ki yi hankuri ki ba wa zuciyar ki abin da ta ke so don samun farin ciki da kwanciyar hankali, ko kuma ki ci gaba da horar da kan ki da kan ki a bisa kuskuren ki. Allah Ubangiji mai afuwa ne, Annabi (S.A.W) mai afuwa ne. Allah Ubangiji kuma yana son masu afuwa. Amma Rahinatu ke kin ce ba za ki yi afuwa ga Habibu ba a kan kankanin laifin da ya yi miki. Wanda ku kadai kuka san abin ku. Don haka sai ki koya wa zuciyarki juriyar rashin su, in har kina nan a kan bakanki, ki fuskanci rayuwar da ke fuskantar ki. Kina da babban aiki a gaban ki wanda ba ya son damuwa da rudani (karatun ta). A matsayi na na Baban ki, shawarar da zan ba ki ita ce ki koma addu'a, idan rabuwar ki da Uban dan ki ita ce mafi alkhairi, Allah ya ba ki zuciyar dangana. Idan dawowar su cikin rayuwar ki shi ne alkhairi Allah ya sanyaya miki zuciya su dawo cikin rayuwar ki ba da jimawa ba". Raheenah ko kadan ba ta son yarda da abin da Ambasada ke fadi, wai- wai wai Habeebu ne tsuntsun da ya tashi da farin cikin ta. Za ta fi yarda in ya ce rashin dan ta Abdallah! Don haka ba ta ce komai ba, amma tana can tana kokawa da zuciyar ta a kan shin abin da Daddy Amb. ke fadi shi ne hakikanin damuwar ta ko kuwa? Wato rashin Habibu Nahuce??? Idan kuwa shi ne zuciya ba ta yi mata adalci ba, domin Habeeb bai bar wani (green momeries) ba cikin rayuwar ta da ya cancanci ta bishi da kewa, sai (black memories and black episodes...) wadanda da su ne kullum take kallon sa, suka kuma sa ta kasa bashi gurbin masoyi, wane irin rashin adalci na zuciya ne zai sa rashin sa ya dagula lissafin ta har haka, ya hana ta ci gaba da harkokin rayuwar ta? Daga wannan ranar Raheenah ta yi aniyar fighting da zuciyar ta, mai neman kai ta ta baro, har sai ta manta da Habibu da Dan sa, dan da bata taba zaton ma za ta so ba har sai bayan da ta haife shi. Wannan wani kudiri ne da ta ke fatan Allah ya ba ta nasara da iko a kan sa, wato gusar da duk wani burbushi da Habibu ya bari cikin rayuwar ta. Daga wannan ranar, Rahinah Omar ta maida hankali a karatunta, don in ba karatun ba wa za ta kama? Ranar da babu su Ambasada? Habibu ko sunan garinsu ba ta sani ba, balle inda ya fito, bare ta sa ran watarana za ta je ta kwato danta. Abin da ta sani a kansa kawai shi ne dan kasarta Nigeria ne. Bayan wannan bata san komai akan sa ba. Sannan Nigeria kasa ce ba gari ba. Da sabon zango ya zagayo. Ta sake maimaita takardun da ta fadi, kuma cikin ikon Allah ta haye wannan karon. Da taimakon nasihohin Yafendo, Ambasada da lallashin Nene Balki. ******* Ana gab da hutun summer Ambasada ya karbi passport din ta ya hada da nasu don yi musu shirin zuwa Nigeria hutu, kamar yadda suke yi duk karshen shekara. Ta shiga dakin Yafendo a wani dare, sai ta tadda ita tana daure kaya. Tsibi-tsibi tana daurewa tana ajiyewa kamar in ta tafi ba za ta dawo ba. Raheenah ta ce, "Yafendo? Wannan kaya ina za ki kai su haka? Ai sai ki karar mana da kilo" Yafendo ta ce, "Duk tsaraba ce da na ke tarawa tsayin shekara guda ta mutanen Bichi. Sannan ke ma na yi sayayya ta musamman don ki kai wa 'yan uwanki in Allah ya sada mu da su". Wani dadi ya ratsa Raheenah, sai ta ji tamkar Dadanta ce a tare da ita. Allah ya sa wadanda Yafendo ke hasashe su kasance su ne dangin nata. Da duk wasu matsaloli da damuwoyi sun karasa zama tarihi a gare ta. Habibu ya je ya dafa dansa ya cinye. A washegari ita ma ta hada nata kayan, amma ba ta dauki sun fi kala bakwai ba. Don Daddy ya ce ita sati daya za ta yi ta dawo ita da Safeenah don ba ya so gidan ya zauna babu kowa. Safeenah kuma ba ta son zaman Bichi ko kadan, a cewarta zafi ke damunta. Daddy Ambasada dan garin Bichi ne ta Jihar Kano, kowa ya san 'yan Bichi 'yan boko ne na ga-ni-kashe-ni. Gidan iyayensa har gobe yana garin Bichi, suna da family mai tsohon tarihi. Sun sauka a Kano da daddare, daga filin jirgi wadanda suka zo tarensu kannen Ambasada ne su uku suka dauke su suka wuce dasu Bichi. Kwanan su uku suna zaga dangi Yafendo da Nene na rabon tsaraba, suna kuma shan tambaya a kan bakuwar fuska Raheenah, cewa ta ke Daddy ke rikonta a Jamus, karatu ta zo. Sai da suka kwana hudu Yafendo ta kira Muqaddas kanin Daddy kuma cousin a gare shi, ta ce ya shirya mota gobe zai kai su Girei ita da Nene da Raheenah, Daddy Abuja zai wuce akwai taron da zai halarta na Ambasadodin Najeriya kafin nan da dawowar su daga Girei din. Ambasada ya yi musu fatan alkhairi na Allah ya sa a dace ya kawo kudin fetir da na kashewa ya babbasu. ****** GIREI, ADAMAWA T afiyar su daga Bichi zuwa Adamawa ta basu wahala ba kadan ba. Musamman dake tafiyar mota ce zuwa Adamawa daga Kano. Sun jigata sun jijjiga wuni guda sur don ma motar lafiyayya ce. Sai magriba suka shiga garin Girei, inda Yafendo ta ce Muqaddas ya tambayi gidan sarkin Fulanin Girei can za su je. Raheenah sai rarraba ido kawai ta ke yi, tana jin wani irin nutsuwa da wani irin kwanciyar hankali na shigar ta, tun ma kafin a ce ga dangin Daadan ta. Kasar Girei da mutanen cikin ta kawai ta ke ta bi da kallo, irin feeling din da dan Adam ke ji lokaci na farko da ya taka fatherland din sa. An kai su har gidan Sarkin Fulanin Girei mai ci a lokacin. Farin dattijo, siriri dan shafal da shi. Yana zaune a karkashin bishiyar darbejiya da ta yi wa kofar gidan sa rumfa. Suka sauko daga mota suka taka zuwa inda yake zaune, sai binsu yake da ido har suka karaso. Tun daga nesa Raheenah ta kura wa siririn dattijon ido gaban ta na tsananta faduwa domin sosai yake kama da Dadarta. "Jabbama-Jabbama (maraba-lale)". In ji Sarkin Fulani, su kuma suka tube takalman su suka karasa inda yake zaune a kan makekiyar tabarmar kaba, suka gaida shi ya amsa da madaukakiyar fara'a, sai kallon Raheenah yake yi da mamaki, domin da ganinta ka ga Sarkin fulani mai rasuwa, wato Umaru Modibbo. Fuskar ta sak ta jikoki sa dake cikin gida. Yafendo ta kara gaishe shi, sannan ta gabatar da su daya bayan daya, "Wannan sunanta Rahinatu, wannan Nene Balki, nikma Yafendo Mairama, mun taho tun daga Bichi ta jihar Kano don mu yi tambaya a kan tsohuwa (Rahin) da dan ta Modibbo Umaru Sarkin Fulani na nan Girei mai rasuwa shekaru kusan talatin da suka wuce. Tunda na san shi ne a matsayin dan Rahin kuma sarkin fulanin Girei, shi ya sa kai tsaye na ce a nuna mana gidan sarkin Fulani mai ci a yanzu, wai an ce matambayi ba ya bata, hakane ko ba haka ne ba? Dadin dadawa muna da hoton ita marigayiya Rahin tare da mu". Har ta kai karshen bayanin ta dattijon bai katse ta ba, sai ya kalle ta sannan ya kalli Raheenah, sannan ya kalli Nene, sai da ta dasa aya sannan ya ce, "Allah mai iko, ikonSa da girma yake. Bana raba daya biyun wannan yarinyar jinin Adda Rahin ce. Don shi jinin mu karfi gare shi ba ya buya a ko'ina, balle a idanun mu. Kwarai kun zo gidan su Adda Rahin, wadda ta kasance Yaya a gare ni. Kafin mu tattauna ku shiga cikin gida wajen iyali na a ba ku ruwa, ku yi sallah ku sha fura sannan mu zauna". Suka mike suna godiya, farin ciki fal zuciyar Raheenah, ta kasa tashi daga gaban dattijon sai da ya ce je ki bada farali tukunna kin ji? Suna tafe zuwa cikin gida amma ba ta bar waiwayen dattijon ba don tsoro ta ke kada su shiga su fito su neme shi su rasa. Har sai da ta ga ya dauko butar sa ya biyo bayan su sannan hankalin ta ya kwanta. Ta sa kai cikin gidan. Matan aure hudu ne a gidan, Fulani duka farare sol da su kamar mijin su. Uwargidan na da tsagin kalangu a fuskar ta wadda Rahina ta ji an kira Dudu, sai Baba Amina da Goggo Tani da amaryar Sarki, Surbajo. Cikin fulatanci ya yi wa matan nasa bayanin bakin, wadanda kowacce da aikin da suka samu tana yi a tsakar gida, ga yara da matasa suna ta shige da fice. Nan suka hau rige-rigen ba su ruwan alwala suna masu sannu da zuwa cikin karamci da girmama bako irin wanda Fulanin Girei suka gada. A dakin uwargida Dudu aka shimfida musu karauni suka yi sallah, sannan kowacce cikin matan gidan ta shigo musu da kwanuka cike da kabakin abin da ta dafa wa iyalin ta, kasancewar 'yar tukunya ake yi a gidan wato kowacce tukunyar ta daban, Sarki kuma ya aiko musu da damammiyar fura ta ji kindirmo kwarya guda, da gasasshen nama mai laushi. Nan suka baje suna ci suna hirar karamcin mutanen gidan a tsakaninsu. Rahinah kam farin ciki da doki sun hana ta iya cin komai, sun cika mata zuciya da ruhi taf! Sai furar ta sha bai fi ludayi uku ba da Nene ta matsa. Sai da suka huta Sarkin Fulani ya shigo har tsakar gida aka shigo masa da kujerar shan iskar sa a waje tsakar gidan, ya zauna sannan ya ce Surbajo ta zo da bakin sa. Sai da suka sake sabuwar gaisuwa sannan ya ce, "Ko me ye dalilin su na zuwa neman gidan su Rahin?" Yafendo ta nuna masa Raheenah da dan alin ta ta ce, "Domin mu sada wannan yarinya da dangin ta na uwa da uba, jikar Rahin ce, ba ta san kowa nata ba bayan Rahin, Allah bai sa Rahin ta taba gaya mata asalinta ba. Ni ma zance ne ya yi zance...to ka ji". Ta ba shi labarin yadda aka yi ta yi zargin diya ce ga Umaru Modibbo, ta kwashe duk yadda suka yi da Raheenah shekarar baya ta fada masa, sannan ta dauko hoton Dada da Raheenah ta ba ta tun lokacin ta boye ta mika masa. "Tsarki ya tabbata ga sarki Allah, wannan Yayata ce Rahin, uwarmu daya ubanmu daya. Ita ce ta haifi Umaru da Usmanu da Dije mai rasuwa. Abinda ya faru shine, Umaru ya kasance bayan haihuwar wannan yarinya Raheenah uwar ta ta koma, sai ya auro wata mace daga zuwa ci rani Shagamu, ya taho da ita nan Girei, ya kawo ta gidan nan inda a da nan ne gidan da yake zaune tare da mahaifiyar sa (Rahin). Wannan mata da ya aura babu tarbiyyah ko kankani a tare da ita, ta yi ta azabtar da Rahin da 'yar marainiyar Allah ba tare da sanin Umaru ba. Ko abinci ba su da kwanonshi a gidan nan. Ni lokacin bana nan don sana'ar mu ce kai shanu kudu ni da Ummaru, kuma in mun tafi muna jimawa ba mu waiwayi gida ba sai mun sayar da shanun da muka kai tas! A kan hanyar Umaru ta dawowa ya yi hatsari sai gawarsa aka kawo wa mahaifiyarsa, a lokacin ba a jima da ba shi sarkin Fulanin Girei ba. Har gobe cikin mu babu wanda ya san abin da ya shiga tsakanin matar Umaru da Adda Rahin, bayan rasuwar Umaru ta hada komai nata da na yarinyar nan ta yi asubanci ta bar Girei. Matar Umaru kuma mai suna Kulu ta hada bakidaya shanun Umaru ta sayar ta kulle kudin ta bar garin nan kafin dawowa ta, don haka Rahin da jikanyar ta ba su karbi gadon Umaru ko kwandala ba. Kulu ta san makarkashiyar da ta yi mata ta korata inda har yau ba wanda ya kara ganinta cikinmu, don kawai ta wawashe gado ita kadai. Bayan na dawo matata Dudu ta gaya min abin da suke zargi, cewa Kulu ta yi wa Adda Rahin barazanar kashe jikanyarta Rahinatu muddin ba ta bar Girei ba. Don dai ta cinye gado ita kadai. Ta sayar da komai na Umaru ta gudu cikin dare ba tare da sanin kowa ba. Damuwar mu a lokacin ba ta ina Kulu ta tafi da dukiya ba ne ko dukiyar da ta handame sai ta ina Adda da Rahinatu suka fada? Mun yi neman duniya ba mu same su ba. Abin kamar hadin baki, shi ma Usman bai kara zuwa ba tunda ya tafi Karatu Zaria. In takaice muku zance, Usman bai waiwayi gida ba sai bayan shekaru biyar da barin Rahin Girei, a lokacin babu wayar tarho, san da ya dawo ya gama karatu har ya samu aiki a Kaduna. Da ya dawo ya tadda tashin hankalin da muke ciki na mutuwar dan uwansa, da rashin sanin inda mahaifiyar su Rahin da Rahinatu suka fada. Gari-gari haka muka dinga yawo neman su Rahin, ni da Usmanu, a lokacin babu kafafen yada labarai ban da radio duk wani gari da yake makwabtaka da mu mun je mun bincika ba mu same su ba. Fadin halin da Usman ya samu kansa a ciki a wancan lokacin ba zai yiwu ba, don gara mutuwar iyaye a kan batansu da ransu. A karshe dole Usman ya koma Kaduna ya ci gaba da aikinsa, amma akai-akai yana zuwa muna kara bincikawa Allah bai sa an dace ba. A shekaru biyu da suka gabata ne wani dan garin nan ya zo mana da labarin ya ga Rahin a cikin Adamawa a kasuwa, ko kafin ya yi mata magana ta bace masa. Don haka na gaya wa Usman, wanda a halin yau ya zama babban ma'aikaci a gwamnatin tarayyah, ni kuma an jima da maida sarautar Modibbo Umaru a kaina. Wato dai ni ne sarkin Fulanin Girei tsayin shekarun nan bayan rasuwar Modibbo Ummaru. Usman ya zo muka durfafi cikin Adamawa cike da bakin cikin ashe duk wahalhalun nan da muke sha wajen neman su Rahin ashe ba nisa ta yi ba, don dai bawa ba ya hada sani da UbangijinSa ne. Kasancewar zuwa lokacin an samu ci gaban zamani mun kai hotunan Rahin kafafen yada labarai na Adamawa, mun saka cigiya musamman a talbijin. Kuma ba a fi sati biyu ana cigiyar ba wani likita daga asibitin jihar Adamawa ya bayyana kansa a matsayin wanda tsohuwa Rahin ta mutu a hannunsa a dalilin cutar ciwon zuciya na farad daya. Ya bada dukkan shaidun da suka tabbatar mana cewa Rahin ce. Daga nan ne muka yi ta bibiya har muka samo muhallin ta, makwabtanta sun tabbatar mana cewa ta rasun, kuma tana da jika budurwa wadda aka biya wa karatu a kasar waje ta tafi shekara guda kenan da tafiyar tata a lokacin binciken namu. Amma su basu san kowacce kasa ce ba. Yau Allah cikin ikonsa ga Rahinatu ta dawo gidan su da kafafunta. Zan so ganin murmushin da zai bayyana a fatar bakin Usmanu, don haka tunda kun zo da mota, gobe in Allah ya kai mu za mu yi asubanci zuwa Kaduna, in sada Rahinatu ga Babanta Usmanu". Raheenah ba ta san sanda ta karasa gaban dattijon ta rike kafafunsa tana kukan farin ciki ba. Yafendo da Nene sai kabbara suke yi suna gode wa Allah tare da yi wa Daada Rahin addu'ar neman rahma da gafarar Ubangiji. Kafin su kwanta sai da Nene ta kira Ambasada ta gaya masa duk halin da ake ciki, cikin farin ciki ya ce shi ma zai same su a Kadunan don gobe zai baro Abuja, da sun shiga Kaduna ta shaida masa don za su tsaya a can su jira isowarsu. A daren duk 'ya'yan Sarkin Fulani da ke gidan aure sai da iyayensu mata suka aika musu suka zo suka ga Raheenah duk da cewa dare ya yi. Nene ta yi alkawarin dawo musu da Raheenah in sun sake zuwa karshen shekara, idan kuma ta gama karatunta bakidaya za ta dawo Girei bakidaya ko wajen kanin Baban nata. Godiya da fatan alkhairi gami da shi albarka su Yafendo sun sha shi daga Sarkin Fulani da iyalin sa, washegari bayan sun yi wanka sun karya kumallo daga tukwanensu Dudu suka kama hanyar Kaduna tare da Sarkin Fulani a gaban mota da babban dan sa Ilyasu. Tun a hanya ya sanar da Alhaji Usman cewa ga su nan tafe tare da diyar Modibbo Ummaru ta hannun Adda Rahin, wadda aka ce ta tafi karatu ketare. A lokacin Alhaji Usman yana Abuja, amma haka ya ajiye duk ayyukan da ke gaban sa ya taho Kaduna a safiyar don su yi taho mu gama, ya kuma sanar da matar sa cewa ta shirya musu kyakkyawar tarba ta musamman. Suna shiga Kaduna Nene ta kira Ambasada ta gaya masa, ya ce ai su tuni suna cikin kaduna suna jiran su, Ilyasu ne ya bai wa Nene lambar Alhaji Usman ta tura wa Ambasada don haka Alhajin da kan sa ya kwatanta wa direban Ambasada gidan sa wanda ke unguwar Sarki. Alhaji Usman Girei na tsaye a kofar tankareren gidan sa yana jiran isowarsu. A gefensa babban dansa ne Musaddiq dan kimanin shekaru goma sha biyar. Suna fitowa daga mota Alhaji Usman na karasowa, burin sa kawai ya dora idanun sa a kan diyar dan uwansa. Raheenah na fitowa daga mota ta gane shi ne Alhaji Usman kani ga mahaifin da ba ta taba sani ba. Ya buda mata hannuwa ta tafi da sauri ta shige, Nene sai da ta ji hawayen tausayi da farin ciki ya cika idanunta. Daidai lokacin da motar su Ambasada ta iso, suka jira har direban sa yayi parking ya bude masa mota ya fito, sannan Alhaji Usman yayi musu jagora zuwa babban falon sa, tarba ta girma da karamci sun ganta gun iyalin Alh. Usman, bayan an gaggaisa Sarkin Fulani ya sake maimaita labarin da ya basu a Girei, Ambasada kuma ya dora nasa na yadda aka yi Raheenah ta zo hannunsa a kasar Jamus. A lokacin maidakin Alhaji Usman ta fita, tana kitchen tana hada-hadar hada abincin alfarmar da ta tanadarwa bakin nasu. Don haka bata ji labarin da Ambasada ya bayar ba. Amma ta san yar Yayan sa ce mai rasuwa data tafi karatu ketare aka kawo masa. Wadda ta dade tana jin labarin batan su a bakin sa tare da mahaiyar sa. Hatta auren Raheenah da Habibu sai da Daddy ya labarta masa komai da yadda auren ya kare. Abinda ya hana Rahinah yarda da sulhun da komen ne shi har gobe bai sani ba. Alhaji Usman ya ce ya zama dole su yi tracing Habibu, wannan ai zalunci ne, dauke yaron da ke shan nono daga uwar da ta haife shi ko kotu za a je sai ya kwatowa Raheenah dan ta. In ya koma wajen ubansa to ya balaga ne, yana bayan hukuncin da Rahinah ta yi wa aurenta da Habibu ta karbi 'yancinta, inda gaske yana son ta ya kasa hakurin ya nemi iyayenta ya nemi aurenta cikin mutunci a hannun su mana? Sai wata watsatsiyar mata Laura? Shi kwata-kwata bai ga laifin Raheenah ba. Maza-maza a ba shi lambar Habibu yanzu zai je ya karbo wa Raheenah dan ta. Amma me? Lambar Habibu da Daddy ke da ita ta kasar Jamus ce, sai a lokacin ya tuna tunda Habibu ya zo Nigeria bai kira shi a waya da lambar sa ta Najeriya kamar yadda suka yi alkawari ba. Haka ya yi ta gwada ta Jamus din duk da ya san ba shiga za ta yi ba. A karshe ya gaya wa Alhaji Usman tunda ya taho bai kira shi ba, amma yana da yakinin zai kira shi komai daren dadewa, domin yaro ne mai hankali da biyayya, sannan da zuciya daya yake son Rahinah. Ya kwantar da hankalinsa ya sa a ransa cewa, Dan Raheenah yana a kyakkyawan hannu. Domin yaron Uba ne har da rabi. Daidai lokacin da Hajiya Badiya ta shigo masu aiki biyu a bayan ta dauke da kabakin abinci, suka shirya komai tare da ita a kan tebirin cin abinci, ta zo tana tsokanar Raheenah wai anya ko tana jin 'ZO' da harshen Hausa? Ta gan ta sullubebiya kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba. Yafendo ce ta tare mata da cewa "ko jakar Kano nan ta ganta ta barta wajen jin hausa". Hajiya Badiya ta gabatar mata da kannenta, Musaddiq da Mubaraq da Mu'allim da Zarah. Raheenah ta rungume Zarah sosai kaunar yaran na shigar ta, tana ta yi musu tambayoyi a kan karatun su, sun tattauna muhimman abubuwa a kan Raheena tsakanin Daddy da Alhaji Usman kafin su yi sallama tare da amsar lambobin juna. Shi da su Nene washegari da asubah suka juya zuwa Bichi a motar da Daddy ya zo, direban su Nene kuma ya juya da mutanen Girei zai maida su. An bar Raheenah sai za su wuce Jamus jibi ita da Safeenah direba zai tsaya ya dauke ta a nan Kaduna su karasa Abuja su hau jirgin Jamus. ****** Zaman Raheenah na kwana biyu a gidan Kawun ta tare da matar kanin mahaifinta Aunty Badiya da 'ya'yanta hudu gwanin ban sha'awa, ba ta bambanta Raheenah da Musaddiq ko magana za ta yi sai ta ce, sai Raheenah ta fara kaza sannan Musaddiq zai yi tunda ta girme shi. Jininta ya fi haduwa da na Musaddiq sabida ilminsa, ga Raheenah da son yara masu kwazo. Zarah ma suna shiri don sai ta ke kwatanta girmanta da na Abdallahnta a halin yanzu, ita in ba idonta ne ma ke mata gizo ba sai ta ce, Mu'allim yana mata yanayi da danta Abdallah. Sai dai yadda ta binne uban Abdallah a ranta a yanzu, haka ta ke so shi ma Abdallahn ta daina ko tuno shi duk da ta san hakan ba mai yiwuwa ba ne. Lokaci-lokaci sai ta tsaya ta bar abin da ta ke yi tana tunanin Abdallah, ko me yake yi yanzu? Ko ya manta ta? Ko ya daina kiran sunanta? Wannan da wancan.... Amma ko ya ya tunanin Habibu ya kutso cikin kan ta da zuciyar ta sai tayi kokarin yakice shi da dukkan karfin ta. Ba shakkah ta ji dadin zama da Aunty Badiya da yaranta da Kawun ta, tsayin kwana biyun, ji ta ke kamar kada ta koma Jamus, but she want to be that Otorhinolaryngologist she promised to be. Wannan ne kadai ya sa ta yarda ta koma Jamus tare da Safeenah a washegarin ranar da suka biyo don tafiya da ita, inda suka tashi ta filin jirgin saman Abuja. Kudi mai yawa Alhaji Usman ya ba ta, ya ce ta rage wa Ambasada nauyi, kuma ya yi alkawarin aika mata kwatankwacin su duk karshen wata. (Ranar da Rahinah ta tashi Abuja da safe, da yammacin ranar aka dawo da Abdallah daga Zamfara inda ya je ya yiwa Hajiyar Nahuce hutu). ***** KOMAWAR RAHEENAH JAMUS B ayan sun koma Frankfurt ita da Safeenah, kowacce tana dakinta babu mai shiga shirgin kowa. Ko da ma can jininsu ba wai ya hadu ba ne, don haka kowa sabgar karatunta ta ke yi ita kadai a dakin ta. Ta kan dai ji wani lokacin Safeenah na waya da saurayin ta Muktar a barandar dakunan nasu. Raheenah Omar ta fuskanci karatunta da wani irin zeal saboda a halin yanzu ba ta da damuwa, tana cikin farin ciki na haduwa da danginta. Sai ta dauki hankalin ta da nutsuwarta kacokam ta mika wa MBBS dinta. Har zuwa lokacin da su Daddy suka dawo, suka ci gaba da gudanar da rayuwar su cikin gidan yadda suka saba. Amma me? Ita diya mace a yayin da ta samu contentment na rayuwa, nutsuwa da kwanciyar hankali, abin da ya saura mata shi ne, DA NAMIJI a gefenta. A matsayin mijin aure ko manemin aure. Wannan ne kadai gibin Raheenah a rayuwa. Somehow, wani bangare na zuciyarta kewar Habeebu yake yi, tana karyatawa da gangan. Tana bai wa tunanin rashin muhimmanci, tana ganin she can overcome it by force, amma a hankali sai tunanin Habib Nahuce da wata sabuwar kakkarfar soyayyarsa suka zo suka soma cin karfintaba tare da ta ankara ba. Wannan wani sirri ne tsakanin ta da zuciyar ta, wanda daga ita sai Ubangijin ta suka san da shi. Bata kuma fatan wani cikin gidan ya san da shi. Raheenah Omar ta gama MBBS a wannan shekarar, da sakamako mai madaukakiyar daraja, ta kammala ne (as the overall best student). A wannan lokacin Alhaji Usman Girei sai da ya taka kafafunsa har Jamus da taimakon cuku-cukun visa da Ambasada ya yi masa ya taya Raheenah murnar karbar kwalinta. A wannan ranar Raheenah sai da ta yi kuka don farin ciki amma duk da haka; ta rasa dalilin da ya sa farin cikin nata ya zama incomplete, tamkar tana missing someone important, musamman da ya kasance kusan duk abokan karatunta mazajen su ne suka taya su karbar nasu kwalin, wasu kuma fiances dinsu. Ita ce kadai mai Uncle da Daddy a gefe, babu mijin da ya taya ta karbowa ya karba a nashi hannun bayan ta karbo ya bi ta da murmushin kauna. A hakan ma ta fi kowa godiyar Ubangiji domin ba ta taba tunanin haduwa da wani nata ba har zuwa sanda za ta bar Jamus kwata-kwata. Amma yau ga ta tare da kanin uban ta har Jamus din. Kafin ta fara specialization dinta sai da ta zo Girei ta yi sati biyu da su Goggo Dudu, sannan ta wuce Kaduna can ma ta yi sati biyu. Ba tare da ta sani ba, a ranar da ta je Kaduna, a jiyan ranar Habibu Nahuce ya zo ya dauki Abdallah daga wajen Aunty Badiya zuwa Zamfara don ya yi hutun kirsimetin sa tare da Hajiyar Nahuce. Satin ta biyu ta koma Jamus ta fara specialization din ta a otorhinolaryngology. Daga lokacin da ta fara specialization din kasancewar wahalar sa bata kai ta MBBS ba ta kan samu lokacin kan ta da lokacin tunani, a lokacin abubuwa suka fara rikice mata. Soyayyar (her ex Habibu) ta kada ita wanwar. Ta soma tunani da neman hanyar samun labarin sa. Ba don ta kula shi ba, sai don kawai shes curious ga son ta san me yake ciki shi da gudan ran ta, don haka ta soma sha'awar bibiyar Habibu Nahuce a kafafen sadar da zumunta, amma ko daya ba ya kai. As the busy person that he is, bashi da lokacin wadannan abubuwan (social media platforms). A karshe ta yanke shawarar duba shi a yanar gizo (google) ta san bazata kasa samun wani abu da shafe shi ba komai kankantar sa. A wani marece ne ana tafka ruwan sama mai karfi a garin Frankfurt, ta rufe tagogi da kofar dakin ta, ta saki fararen curtains din dakin, sannan ta kunna (room-heater), ta dauko kwamfutar bisa cinya (loptop) ta shiga google kawai ta rubuta sunan sa HABIBU MUSTAPHA NAHUCE. Ita kuma googlesai ta kai ta LinkedIn. Kasancewar sa (professional platform). A can bata samu wani cikakken bayanin sa ba sai na profession din sa (as a Hotel Administrator), sai kuma a wani website na hotels din sa. A canne ta ga cikakken sunansa da cikakken bayaninsa a halin yanzu. "Habibu Mustapha Nahuce (Lucky), Young Nigerian Hotels Owner, the Proprietor of NAHUCE GROUP OF HOTELS, Excutive Director TRANSCORP HILTON, NIGERIA....... (With so much interest) hadi da mamaki da dokantuwa, wani irin inquisitivity and curiousity, Raheenah ta ci gaba da surfing tana bin bayanan wadanda duk sun kunshi gwagwarmayar rayuwar Habibu ne, ta neman ilmi, ta fadi-tashi a Jamus, da ayyukan Hotels a gida Nigeria, saicurrent hotunansa wadanda suka kusan gusar da numfashinta. Yana nan a handsome HABEEBUNsa, dan gayun nan wankakke, mai iya daukar wanka, mai iya sanya karin hula, kuma dan kwalisar shi yadda ta san shi a baya cikin birnin Cologne, sai wata 'yar kiba ta hutu da zaman naira a muhallin ta ya sabbaba kawai da ya kara, hadi da wani irin kwarjini da kamala wanda rikon addini ke haifarwa mutumin da ya rike addinin sa da gaskiya, ya kuma san ciwon kan sa (at approaching 40). Numfashin Raheenah yayi balaguro na tsayin lokaci daga kirjin ta. Ba ta iya ci gaba da karantawa ba, haka bata iya cigaba da kuma kallon hotunan tallbuildings din NAHUCHE HOTELS dake kasa ba ta kifa fuskar kwamfutar ba tare da ta kashe ta ba. Numfashin ta na racing...cikin sassarfa, zuciyar ta na wani irin bugu cikin ragaita... So Habibu yana can kasar shi Nigeria yana progressingto such extent harya manta da ita. Ya manta an yi halitar ta. Mai wannan tarin achievements din ina zai tuna da wata halittar Allah mai suna RAHEENAH! Ya gama cimma komai na rayuwa, da duk wani buri da dan adam ke da shi, watakila ma har aure ya yi ya dau Dan ta Abdallah ya baiwa wata, in ba haka ba yaya zai yi da yaron??? Wannan tunani ya dugunzuma zuciyar Rahinah. Kishi da bakin ciki matsananci suka lullube ta. Kawai sai ta ji hawaye na saukar mata duk da ba na regret bane, na tunanin ya dau dan da ta sha wahalar dakon cikin sa wata tara da nakudar sa ya baiwa wata ne. Watan da ta ke da tabbacin ba zata rike mata Da sabida Allah ba sai don wannan dukiyar HOTELS da aka tara. Ba ta san lokacin da ta sake kunna kwamfutar ba ta koma kan browser din ta ta rubuta 'HABIBU NAHUCE'S WIFE', amma kuma no result matched her search, ta yi sau ba adadi ba ta ga wata mace associated with him as a spouse ba, sai Daractoci da manajoji na hotels din shi, wadanda duk kabilu ne. Wata nannauyar ajiyar zuciya ce ta kufcewa Raheenah, amma sai wata zuciyar ta ce, "Kada ki yi saurin sauke numfashi Rahinah, watakila yana daga cikin mazan da ba sa exposing matan su a internet, ko da gani ma wadannan bayanan duka ba shi ya dora su ba, website ne na hotel din sa ya dora, ya kuma kunshi dukkan bayanan da suka shafe shi. Da sauri ta soma binciken babban location na shedkwatar Nahuche Hotels, da kuma ainahin jihar da garin NAHUCHE yake, ba jimawa adireshin ya bayyana; 'ZAMFARA STATE, NIGERIA'. Ta koma da baya ta jingina da allon gadon ta tana wani irin lumshe idon ta. So Habibu dan Zamfara ne kenan all these while ba ta taba sani ba. Yau har karamar hukumar da garin Nahuce ke ciki sai da Rahinah ta binciko (aiki ya samu manyan mata) Ranar dai baki dayan ta ta zama ta DAN NAHUCHE jikan NAHUCHE ce a wajen Raheenah..... Gabadaya ta birkice a searching din komai da ya dangace shi, sai da ta binciko komai concerning Young Nigerian Hotels Owner Habibu Mustapha Nahuche. Ba kuma da nufin za ta taba neman sa ba; she is only infatuated and truely in LOVE... ba tare da ita kanta ta san soyayyar gaskiya ke dawainiya da ita a daidai wannan lokacin ba. Dankwalin kan ta yayi nasa wuri gashin kanta na fulanin usli duk ta hargitsa shi kamar yadda ta hargitsa zuciyar ta da tunanin ta. Duhu na neman shigowa, har zuwa lokacin Raheenah na bisa kwamfuta ba tare da ta tuna da abincin rana ba. Wanda ta ce ma Nene in ta gama abinda take yi zata zo ta dauka. Jin shiru har karfe shidda na yamma Rahinah bata fito ba sai Nene ta shigo mata da shi tana tambayar ko lafiya ba ta fito cin abinci ba gashi har an gama na dare? Idanun Nene Balki suka kai kan allon kwamfuta (screen) inda ta hango fuskar Habibun su ta cika screen din, da alama zooming hoton ta yi. Tana kara kallon kyakkyawar fuskar sa da kyau. Da sauri ta kife fuskar kwamfutar ba tare da ta kashe ta ba. Nene ta yi kamar ba ta gani ba, amma ta kusa sakin salati don mamaki, ta ajiye mata abincin da ta biyo ta da shi, ta ce. "Ki daure ki ci abinci ki koshi, sai ki fi jin dadin tada tsumin tsohuwar soyayyah". Raheenah ta yi maza ta rufe ido ruf! Tare da dora hannayen ta biyu a kai kamar ta ce, "wayyo Allah kasar ta tsage ta shige". Nene ta gani, ta gan ta da hoton Habibu cikin kwamfutar ta! Yau ina za ta sa kanta da wannan dingimemen abun kunya??? Nene ba ta tsaya sauraron borin kunyarta ba ta juya ta fice daga dakin. Ba ta kuma tsaya ko'ina ba sai falon Ambasada, ta labarta masa abin da ta gani a kwamfutar Raheenah yau. Mamaki kamar ya kashe ta. Ambasada Shehu Bichi murmushi ya yi, ya ce, "Shin ke Nene da can kin dauka wai ba ta sonshi ne? Ai ki bar bacin rai a lokacin da yake cin zuciyar diya mace. Sannan shi bacin rai (is mortal but love is inevitable). Amma kuma duk da hakan zuciyarta mai rauni ce a kan ta Da namiji. Bari ta gama karatun ki sha kallo, da kan ta za ta nemo shi duk inda yake. A lokacin ne yake gaya mata shi ya san inda Habibu yake, (Habibu is now a successful business tycoon) a garin Zamfara, amma har gobe bai yi aure ba, me ye dalili? Wanda ke nufin uwar dan sa yake jira TA HUCE DAGA FUSHIN TA. Ya kara da cewa, abin da ki ka ga tana yi yanzun, alamu ne na ta fara HUCEWA, sai mu ba su lokaci su duka, mu kuma bi su da kyakkyawar addu'a. Amma a yadda na fahimta Habibu na da zuciya, soyayyah ba ta rufe masa ido ya kasa sarrafa kan sa. Idan kin ga ya yarda ya maida Raheenah to fa sai dai idan ita da kanta ta neme shi, ta ba shi tabbacin amincewar ta a kan komawar ta dakin ta. Ya riga yayi zuciya da Raheenah. Yayin da ita kuma Rahinatu in kin lura akwai ta da ki-fadi (mawuyaci ne hakan ta kasance daga bangarenta)". Nene ta dinga jinjina kai. Ta rasa abinda zata ce. ***** COLOGNE, ALUMNI A yau ne jamiar Cologne ta kasar Jamus, jamia mai dadadden tarihi, ke bikin kammala karatun su Raheenah daga jami'ar wato (convocation ceremony). Duk inda ka duba dalibai ne daga kasashe daban-daban na duniya, tun daga Amurka, Birtaniya, Asia, Africa and Latin-America. Suna saye da bakar rigar kammalawa (convocation gown) da hular ilmi, farare sun cakude da bakake ba ka iya tantance nationality din kowannen su. Dr. Raheenah Omar, ta fita da matsayin overall best student a department din ta (Otorhinolaryngology) ta karbi wannan kambu daga shugaban jami'ar Cologne. Ta karbi membership daga (AFHNS) wato (African Head and Neck Society) da kuma (ORLSON) wato (Otorhinolaryngocological Society of Nigeria). Kamar yadda ta yi wa kasar ta alkawari, wannan ne lokacin dawowar ta gida bakidaya domin ta taimaka wa kasar ta ta amfana daga ilmin da ta tsaya mata ta yi. Yau gidan Ambasada Shehu Bichi komawa ya yi kamar gidan mutuwa don koke-koke, sakamakon cewa gobe ne Raheenah za ta bi Uncle din ta zuwa gida Nigeria. Wanda ya kara zuwa Jamus a karo na biyu don tafiya da ita. Ahlan kuka har da majina, Yafendo kuwa habar zani ta sa tana ta fyace hanci kamar an aiko musu da manzon mutuwa, Nene ce kadai mai lallashin kowa tana tuna musu suma kwanan nan za su koma Nigeria, sabida tenure din Ambasada Shehu ta kusan karewa. Rabuwar Raheenah Omar da iyalin Ambasada wata irin rabuwa ce veryemotional. Wadda mai raguwar zuciya ba zai iya tsayawa a wajen ba. Abu daya ya kwantar musu da hankali, shi ne, su ma ahalin gidan na gab da dawowa Abuja bakidaya. Suna sauka a Kaduna, Alhaji Usman ya sa direban sa ya wuce da ita Girei, kafin ta huta ta zo ta wuce NYSC, lokacin har an fara daukan batch A, don haka Uncle (yadda ta ke kiran sa) ya shigar da sunan Raheenah cikin masu tafiya hidimar kasa na wannan shekarar. Ba ta fi sati biyu da dawowa Kaduna ba ta wuce NYSC a Ibadan inda suka yi posting dinta zuwa asibitin koyarwa na Ibadan. Duk inda Raheenah ta shiga farin jinin ta da kyawun ta ke sayo mata soyayyar jama'a. Ga ta nan kamar ka taba jini ya yi tsartuwa (jazir sumul da ita) bafullatanar usli, wadda ta samu gogewa cikin zuzzurfan ilmin zamani. Ta wanke ta yi sumul ba za ka taba tunanin bafulatana ba ce, ta fi kama da larabawan Oman, Qatar haka, ko kuwa na Maghrib. A Ibadan Teaching Hospital ne wani babban likita dan uwanta ya like mata wai shi Dr. Aryan dan jihar Minna ne, aiki ne ya kai shi Ibadan kuma karkashin team dinsa ta ke aiki. Rahinah ta yi duk iya kokarin ta don ta nunawa Aryan ba auren sa za ta iya ba, amma ya ki ganewa, mutum ne mai nacin gaske kuma girman mukamin aiki da ke tsakanin su ya sa ba ta isa ta wulakanta shi ba don ba ya shiga hurumin aikin ta sam-sam ya san lokacin da yake damunta da nacin kira da zarya a inda duk ya san zai ganta kasancewar sa ya manyanta don ya jima yana aiki a nan, matarsa ta mutu da jimawa ba shi da Da ko daya. Don haka da Allah ya kawo lokacin kammala NYSC din ta, ji ta yi tamkar an raba ta da kaya, ta dawo gidan su a Kaduna a ranar matsayin cikakkiyar Otorhinolaryngologist mai lasisin aiki tare da Hukumar Lafiya ta kasa, ba da jimawa ba aka tura ta National Hospital Abuja matsayin ENT Surgeon. Dr. Rahinah Omar ta fara gudanar da ayyukanta na likitancin kunne, wuya da makogaro cikin dumbin nasara. Ita ce likitar kunne ta farko a Africa da ta gudanar da dashen dodon-kunne (cochlear Implant) a Nigeria gabadaya. Kuma kafafen yada labarai suka yada nasararta a wannan surgery na kunne mai hadarin gaske, wanda ya zamo na farkon yi a kasar Najeriya. Kuma wanda ta sanyawa din ya ji magana sosai. Don haka manyan asibitoci masu zaman kansu na birnin tarayyah da wajen ta suka ankara da ita, ta yi attracting asibitocin kunne masu yawa suna masu gayyatar ta aikin part-time job tare da su. Amma duk ciki sai ta zabi babban asibitin NIZAMIYE ta hada da aikinta na gwamnati a National Hospital Abuja. An bai wa Raheenah gidan likitoci a cikin National Hospital. Uncle ya ce bai son ta je ta zauna ita kadai ba muharrami don haka Aunty Badiya ta samo mata mai aiki a nan kaduna suka tare tare, wai ita Sahura. bazawara ce da ba ta fi shekaru arba'in ba. Daga lokacin da Raheenah ta gane dangin ta zuwa yanzu ta zo Kaduna ya kai sau shida, amma cikin wani hukunci na Ubangiji ba ta taba haduwa da Abdallah ba, duk lokacin da ta zo yana Zamfara ko wajen mahaifin sa a Lagos inda harkokin sa suka fi karfi yanzu. Sai dai cikin hirarrakin su da Aunty Badiya da su Musaddiq ta fuskanci akwai dan kaninta da ta ke riko tare da Zarah, Baban sa bai cika barin sa ya zauna a Kaduna ba cikin hutu wanda ita lokacin take zuwa sai lokacin makaranta. Haka a bakin su Musaddiq tana yawan jin sunan Junior sunan da duk jamaar gidan suke kiran Abdallah, kasancewar shi ne karami a cikin su. Tun komawar su Abuja ita da Baba Sahura Raheenah ta zama ba ta da lokacin kan ta, sabida documentation na kama aiki. Tana jin dadin zama da Sahura don kullum kafin ta dawo ta gyare musu dan madaidaicin gidan su tsaf! Ta kunna turaren wuta, ta kuma dafa musu abinci. In Raheenah ba ta ra'ayi daga waje ta ke taho da abin da za ta ci. Uncle ya mallaka mata karamar mota KiaPicanto don ta samu saukin zirga-zirgar ayyukan ta. Wannan ya taimaka ainun wajen kwashewa Raheenah hankali a wannan dan tsakanin. Ba ta da lokacin da za ta zauna ta yi tunani. Ko bibiyar lamuran dan mutanen Nahuce. Aiki ta ke tukuru da kwarewa da patriotism domin saka wa gwamnatin Najeriya da ta tsaya mata, ta tallafi ilmin ta da (scholarship). Ranar da ta fara daukan albashin ta na farko ko naira ba ta ci a ciki ba ta kasafta wa iyayen ta, bayan ta ware wa Ambasada kaso mafi tsoka, sannan Yafendo da Nene. Tana mai dakacen ina ma Daada tana raye? Wannan ihsani da girma da Raheenah ta bai wa iyayen dakinta ya kara mata martaba a idanun su, ba don ba su da shi ba, sai don ganewa da suka yi ita din mutum ce mara manta alkhairi. Bayyanar iyayen ta bai sa su ta daina kallon su da matsayin iyaye ba. Asibitin Nizamiye wani babban asibiti ne mai zaman kansa a birnin tarayyah. Suna matukar ji da Dr. Rahinah Omar wadda ke aiki part-time da su a matsayin ENT Surgeon (otorlaryngologist). Nizamiye Hospital na nan a (Life-Camp). They have the latest technology for the treatment of most common ENT cases irin su Rhinitis, Sinusitis, Myringoplesty, Tympanoplasty, Mastoidectomy, Septoplasty da sauransu. The World Class Private Hospital wanda Turkawa suka kafa a birnin Tarayyah. Don haka Raheenah ba karamar sa'a ta taka ba a rayuwarta da ta samu kujera a Nizamiye. Kudi sosai ya soma shiga account din yar mutanen Girei. ***** Wata ranar Litinin, Dr. Raheenah ta dawo aiki a gajiye likis, tana yin parking a apartment din ta Baba Sahura na fitowa za ta zub da shara. Da sauri ta aje kwandon sharar ta iso ta karbi jakar uwargijiyar ta tare da (lab coat) da ke hannun ta tare da yi mata barka da zuwa, Rahinah ta bata mukullin booth din motar ta ce ta fidda cefanen da ta yo musu ta sanya a freezer. Wayar Raheenah ta yi kara a lokacin da ta ke fidda leshin jikin ta za ta shiga wanka. Dakatawa ta yi ta dauki wayar inda ta ga Aunty Badiya ke kiran ta. "Maman Musaddiq ya ku ke?" Ta ce, "Muna lafiya cikin alkhairi Raheenah, Uncle ne ya ce in tambaye ki yaushe za ki samu shigowa Kd? Akwai muhimmiyar magana da ya ke so ku yi". Raheenah ta ce, "Aunty a wannan watan duka ba zan samu lokacin shigowa ba, due to my tight schedules, amma insha Allahu weekend din karshen wata zan shigo". Aunty Badiya ta ce, "Ni kuma zan je gida Zamfara lokacin, zan dauko dan kani na Junior daga wajen Hajiyar mu, Baban sa zai dawo daga Belarus ina so kamin ya wuce Lagos ya gan shi, amma kwana daya zan yi. So, insha Allah za mu hadu kafin ki koma, a kula da aiki, a kula da mutunci. Allah ya kara wa rayuwar ku da nema albarka". Sati biyu bayan nan Ambasada Shehu da iyalinsa da mahaifiyarsa Yafendo suka sauka a kasar Nigeria. Sun jima a Bichi cikin 'yan uwa da danginsu kafin su yi relocating a gidan da Ambasada ya saya a Abuja tun kafin barowar shi Jamus. Gidan yana nan a unguwar Maitama. Raheenah na dakin tiyata, fitowar ta kenan ta samu kira daga bakuwar lamba. Sai da ta zauna bisa kujerar ofishin ta ta warware nadin mayafin da ke kanta, sannan ta bi bayan kiran. Muryar wa za ta ji? NENE! Sannan lambar ta kasar Nigeria ce. Wata zabura da Raheenah ta yi daga kujerar ta tana kiran sunan "Nene!" Sai da ta bai wa Nene Balki dariya, ta ce, "Finally, ga mu a Abuja, kuka ya kare ko?" Hawayen farin ciki suka zubowa Raheenah, da ma kewarsu da kadaici sun addabe ta musamman da ta fara samun saukin ayyukan da ke gaban ta. Sannan ba ta da kowa a Abuja bayan Uncle Usman, shi kuma ba haduwa suke ba sai idan ta samu lokaci ta je ofis din sa ko shi ya zo nata. Don haka dawowar iyalin Ambasada Shehu Abuja ba karamin kwanciyar hankali ya kara wa Dr. Raheehah ba. A ranar a gidan Nene suka kwana dakin Yafendo ita da Sahura ana ta hirar yaushe gamo. Daga wannan lokacin ne kuma rayuwar Raheenatu ta dauki sabon direction. Rayuwa ce ta 'yanci ta ke ciki wadda kowanne mai ilmin boko ita yake yi wa buri, ga aiki, ga gida ga albashi ga motar kan ta, ga kuma rayuwar Abuja. Don haka abu daya ya rage mata shi ne mahadin rayuwar diya mace, wato mijin aure. Mazan da har gobe ta kasa daga ido ta yi musu kallon maza, sai muna-maza, domin kowa ya zo gare ta da kalmar so ji ta ke tamkar ya daba mata mashi a kahon zuci, bai kai ba, bai isa ba. Wanda ta ke binnewa da gangan a karkashin ran ta, shi kadai ne namiji a idanunta a zahiri da badini, dan Hajiyar Nahuce (Habibu). Ta zama infatuated a kan Habibu kwarai, ta ci gaba da follow up a kan duk wani takunsa na rayuwa, da halin da yake ciki. Duk wasu nasarorin sa na rayuwa a kan kunnen ta, Amma ta yanke shawarar never to look for him ever! A wurin ta kaddara ta riga ta gama playing game din ta, tsakanin ta da Habibu Nahuche. Amma ta rasa dalilin da ya sa har gobe ta kasa daina bibiyar halin da yake ciki. Shin da gaske ne kaddarar ta gama playing game din ta a tsakanin su??? Ta tambayi kan ta a ranar da ta ji (live programme) din sa da British Broadcasting Corporation wato gidan rediyon BBC Hausa. Ta kashe rediyon ta koma jikin taga ta tsaya standstill tana kallon harabar gidan ta wanda shuke-shuken korran ciyayi suka yi wa kawanya. Abdallah ko yanzu in ya gan ta zai iya shaida ta? Ko ya taba gaya masa yana da uwa a duniya? Ko kuwa bacin ran ta ya sa bai taba gaya masa ba? Habibu kadai ya san duka amsoshin wadannan tambayoyin. ****** Yau juma'a ba ta da aiki sosai a ofis don haka ta yanke shawarar tattara komai nata ta wuce Maitama wajen su Nene ta kare ranar yau tare da su. Ta kira Sahura a waya ta ce, kada ta dafa abinci da ita ta wuce wajen su Yafendo sai dare za ta dawo. Rahina na tuki cikin nutsuwa kamar yadda ta saba, lokacin da direban sa Yohan dan kabilar Igala ya shararo motar su a guje kirar 'Discussion Contineous' saura kadan ya goga mata. Da sauri ta dauke kan motar ta tana mai Allah wadai da halin wasu direbobin, shi ko Yohan Ubangidan sa ke azalzalarsa a kan ya yi sauri, saura mintuna goma sha biyar meeting din zai halarta a Transcorp Hilton. Amma me? Motar da ta kauce musu is a glimpse of her Fulani face. That magical beauty of her's, wanda cikin kowanne hali ba zai kasa shaidawa ba. Cikin hali na mafarki ko ido biyu ba zai taba mancewa da kamannin Raheenah Omar ba. Waiwaye wani abu ne da ba ya yi sam, amma yau ya yi waiwaye har ba adadi kamar wuyan sa ya karye amma motar ta bace masa. Abu daya ya gane, motar fara ce sol! Kirar kia picanto, kuma yana da tabbaci a kan-kan sa (self-assurance) na ko da ba ta bace masa ba, ba zai bi bayan ta ba. To ya bi ta yace mata me? Ko ya yi mata me? Ta bar shi da tabo a zuciya, it's a deep wound that can never be healed, watakila har sai ranar da Raheenah Omar ta nemi KOME zuwa auren su da kan ta da bakin ta. Wanda kuma yake da tabbacin abu ne mai matukar wuya a kafiya da taurin kai irin nata da ya dade da fahimta. Wannan na nufin ta dawo Nigeria... Wannan na nufin she's progressing without him, shi da dan sa ta ba su baya, ta manta da su kwata-kwata. A duk lokacin da ya tuna Raheenah, fada yake da zuciyar sa ta ci gaba da yin tauri, kada ta karaya, kada weakness din ta ya bayyana. Amma yau fa? Raheenah ya gani ba hotonta ba, her humble self bayan wucewar shekaru goma, which is hard for him to control himself domin kuwa ko meeting din da yake gaggawar zuwa har aka yi aka gama bai tsinci komai a ciki ba. Ta iso gidan Nene wajejen karfe sha daya na rana. Da Ahlan ta soma cin karo suna wasan kwallon kwando da abokan sa a harabar gidan. Ya baro abokan nasa ya zo ya bude mata kofa yana fadin, "Yayata tafi ta kowa, Yayata likitar da babu kamar ta'. Dariya ta yi suka rankaya zuwa ciki. Nene na kicin tana girki lokacin da suka shigo. Ta kama mata suka karasa komai, suna aikin Nene ta ke gaya mata Yafendo ba ta jin dadi tun jiya. "An je asibiti?" Ta tambaya cikin damuwa. Ba yadda Daddy bai yi ba dazu su tafi asibiti ta ki, wai in mutuwa ce a bar ta ta mutu a cikin dakin ta. Ba ta son zakule-zakule, Raheenah sai ta bar komai ta nufi dakin Yafendo. A kwance ta same ta tana lazimi ta tsaya daga bakin kofa ta ce, "Yafendo me ya same ki?" Yafendo ta sauke idanun ta da suka kada sabida zafin zazzabi, ta ce, "Ya ki 'yar albarka, da ma yanzu zan ce wa Ahlan ya danno min ke a waya, ki zo ki ba ni magani, bana son zuwa asibiti a yi ta jagwalgwala ni". Ai kuwa sosai Rahinah ta bincike ta, ta kuma ba ta treatment din da ya kamata, domin ta fahimci zazzabin typhoid ke son kamata, har allura ta yi mata wadda ta aika Ahlan ya sayo. Zuwa la'asar Yafendo ta ji dadin jikin ta sosai, sai suka koma hira, Yafendo ta ce, "A yi magana cibi ya zama kari, amma bari Baban naki ya shigo". Raheenah ba ta gane me Yafendo ke nufi ba sai da Daddy ya dawo, ya kuma shigo don ya duba jikin Yafendon, nan ya ga Raheenah ya fadada fara'ar fuskar sa, yana fadin, "Lale-maraba, da manyan otorlaryngologists". Yafendo ta ce, "Ai gara da ka zo, da ma yanzu zan ce ta latso min kai. Shigo ka zauna, magana za mu yi ta gaskiya ni da ku". Ambasada ya samu wuri gefen Yafendo ya zauna, ita kuma sai ta fara magana cikin tsananin damuwa. "Yanzu saboda Allah haka za ku zuba wa Rahinatu ido ta kare rayuwar ta babu aure? Talatin ta ke nema fa rabin sittin ba ashirin ba. Ni ban ce lallai sai ta koma wa Baban Abdullahi ba, tunda wannan shi ta ga zai fishshe ta, amma ta fidda miji ta yi aure ko wane ne tunda ta ki komen mai kaunar ta da gaskiya. Amma wallahi ku yi a hankali daga ku har ita, kada bokon ku ya kai ku wutar jahannama". Shi kam Ambasada murmushi kawai yake yi domin a yau din nan ya gano wani muhimmin al'amari, wato Yayar Habibu Nahuche Uncle din Rahinah Alhaji Usman Girei ke aure. Ya gane hakan ne daga hirar da suka yi da Uncle Usman yau a ofishin sa, inda yake gaya masa ai NAHUCHE HOTELS na kanin maidakin sa ne Badiya, lokacin da aka nuno sabon ginin NAHUCHE HOTEL da ya yi launching a jihar Rivers (PortHercourt) a talbijin din da ke cikin ofishin a gaban su lokacin da suke hirar. Shi kuma Ambasada bai gaya wa Uncle komai a kan sanin da ya yi masa yana dalibi ba, ko girman alakar da ke akwai a tsakanin su yanzu. Shi Uncle Usman din da Habibun (wato surakuta). Ya bar wa Allah ikon Sa ya ci gaba da yin hukuncin Sa a kan Rahinah da Habibu Nahuche, don ya gane ba karshen kaddarar su kenan ba, tunda har wannan babbar alaka ta sake bayyana kan ta a tsakanin su. Da wannan Ambasada Shehu ya samu ya rarrashi tsohuwar sa Yafendo cewa, shi da Uncle Usman za su zauna da Raheenah don jin hakikanin halin da ta ke ciki, kuma za su yi duk mai yiwuwa su ga cewa ba ta kara shekara daya a nan gaba babu aure ba. "Ah toh ya rage naku kuma, ni dai aikina tunatarwa da tsoratarwa a inda na ga an yi ba daidai ba. Ya rage naku ku yi ta biye wa boko kuna bautar sa ba Allah ba. Ni rayuwata ta yi kyau, na kare ta cikin bautar aure har ya koma ga mahaliccin sa, shi ya sa nake mata kwadayi ita ma ta mutu karkashin igiyoyin aure, don ni rayuwata ta kare, rakawa muke yi, dole kuma mu yi muku tunatarwa a lokacin da ku ka nemi kauce hanya". Jiki a sanyaye Dr. Rahinah ta koma gidanta sabida irin maganganun da Yafendo ke yi sun karya mata zuciya, sai fada ta ke ita rayuwarta ta kare. Alal hakika ganinta ta ke kamar Daadarta. Kamar yadda ta yi alkawari, a ranar asabar din karshen wata ta shirya suka kama hanyar Kaduna ita da Sahura don amsa kiran Uncle Usman. Wajejen azahar suka shiga Kaduna, ba ta samu Anty ba sun wuce Zamfara ita da Zarah da Musaddiq sai Mu'allim da Mubaraq da mai aikin Aunty sai kuma Uncle da kansa kawai a gidan. Dakin na gidan wanda anan ta saba sauka in ta zo a can ta sauka, amma yau jin duk jikin ta ta ke wani irin dizzy kamar zazzabi na son shigar ta. Uncle bai kira ta ba sai da ya dawo sallar isha'i. Ta nutsu a gaban shi tana sauraron abin da zai ce mata, wanda muhimmancin sa ya wuce su tattauna shi a ofis sai ya kira ta har Kaduna. "Rahinatu yau na kira ki ne a matsayin mahaifin da ya damu da 'yar sa, ina so in san hakikanin shin me ya hana ki aure? Ko kusa kada ki ce min miji ne Allah bai kawo ba, don kuwa ko ta bangarena mutane hudu ne ke son ki ba su dama. Haka Chief-Medical Director na Nizamiye Dr. Irshad mutumin nan shi ma ya yi tattaki gare ni har ofishi na a kan maganar ki. Ga wannan Aryan na Minna shi ma har gobe ba wai ya hakura ba ne, lokaci-lokaci yana kira na a kan batun ki. Ya gaya min kin sanya layin shi ma a divert call sabida ba ki da lokacin sauraron shi. Shi ne nake so in san matsalarki ta hakika, wadda ta sa ki ke gudun masu kaunar ki, ko kuma ki gaya min gaskiya, har gobe Uban dan ki ki ke kwadayin komawa ko me?" Da sauri Raheenah ta cira kai ta dubi Baffan ta, me ya sa zai yi mata wannan hukuncin? To amma in ta kalubalanci Uncle za ta kalubalanci zahirin abin da ke karkashin zuciyar ta ne? Maza ba sa burge ta ko kadan, sai dan mutanen Nahuche... The one that took away her pride na diya mace. Ya san sirrinta ta san nasa, reality din shi ne ba za ta iya kara hada jiki da wani Da namiji bayan shi ba. Ba za ta iya kara hada rayuwar ta da kowa ba shi ba. Amma kuma ba za ta taba neman sa ba balle ya yi tunanin kome ta ke nema, ko tana so ya dawo mata da dan ta, har ya yi amfani da damar hakan ya gina wata sabuwar mu'amala a tsakanin su. Yaro Abdallah Allah ya raya shi, ta tabbata duk inda yake yana cikin koshin lafiya, yana samun ilmi mai nagarta kamar na Bajamushen mahaifin sa, watarana da kafafun sa zai neme ta in har ita ta haife shi. Uncle sai a lokacin ya ankara da cewa, Rahinah kuka ta ke yi tana share hawaye da gefen gyalen ta, kukan da in za a kashe ta ba za ta ce na hakikanin mene ne ba. Ta fi alakanta shi da cewa, kuka ne na tausayin kai, tausayin yadda Habibu ya yi shattering (daidaita) zuciyar ta da rayuwar ta bakidaya, ya hana ta jin dadin achievements din ta na rayuwa ko kadan. Tun rabuwar ta da Habibu Nahuche abu daya za ta ce ya sanya ta farin ciki (zuwan ta Girei) bayan wannan babu abin da ya kara faranta mata zuciya sai kunci maras dalili, har kuwa da kwalinta na Overall Best Otorlaryngologist. A hankali ta ke kuka, sautin na ratsa zuciya da kwanyar Uncle Usman. Bai san sanda ya ce, "Ki yi hakuri Rahinatu, I don't meant to hurt your feelings.But I must perform my role as a father in tabbatar da cewa a wannan stage din kin shiga gidan aure. Na ji ba Baban Abdullahi ki ke jira ba, amma akwai abin da ke damun ki a karkashin zuciyar ki wanda nake so in sani yanzu?" Rahinah ta shiga girgiza kai tana fadin, "Babu komai Uncle, I'm just finding life boring...". "...Without him ko?" Uncle ya karasa mata yana murmushi. Za ta iya cewa ta firgita da wannan furucin na Uncle din ta. Me ya sa duk wani makusancin ta yake alakanta damuwar ta da Habibu Nahuche? Me suke gani suke fadar haka? Ita kawai har gobe ba ta ga wanda ya yi mata ba ne, amma ba shi ta ke jira ba. "Alright Rahinatu, je ki kwanta. Amma na ba ki kwana daya, wato zuwa gobe da daddare, tunda jibi da safe za ku koma, ki zo ki gaya min mijin da ki ka zaba cikin maneman ki, ko in bai wa duk wanda Allah ya tsaga da rabon sa auren ki. Idan ba ki gaya min mijin da ki ka zaba a gobe ba ya tabbata Baban Abdullahi ki ke jira. Wanda na tabbata duk inda yake zuwa yanzu shi ya manta da ke tunda har aka kai DECADE bai neme ki ba. Bayan ya san inda ki ke, wanda ke nufin bai da sauran bukatar ki a rayuwar shi ke kadai ki ke dakon wahala". Raheenah kuka ta ke yi ta ce, a hankali. "Uncle I'm not waiting for him..." "To in ba shi ki ke jira ba wane ne? Na gaya miki kwana daya na baki ki zo min da abin da ki ka yanke ko in bai wa (Chief Medical Director of Nizamiye) damar fitowa". A hectic night for Raheenah, ta kasa barci a tsayin daren bakidayan sa, zaben miji a kwana daya ai ba mai yiwuwa ba ne, da ace ta san abin da kiran Uncle na yau ya kunsa kenan da ba ta zo Kaduna ba, da ta yi ta bada uzuri da aiki har sai ya gaji ya manta. Ya aura mata Dr. Irshad ta kai shi ina? Wannan mayen matan idon sa kullum a kan matasan likitoci mata masu tashen kwarewa a ayyukan su, bin mata kamar bunsuru. Ita farin mutum ma ba ya burge ta sam, this gentle handsome black man ya dusashe hasken fatar kowanne namiji a idanun ta. "Yaa Salamu Sallim!" Raheenah ta furta a fili, ko dai Habibu na da alaka da cin kurwa ne (Maita)? Ta yadda ya cinye kurwar ta bakidaya bai barta da ko guda daya na extra-space a zuciyar ta da za ta iya sanya wani a muhallinsa ba. Idan har mayen ne da gaske, hakika ta yarda ya gama lashe kurwar ta. A washegari da safe Aunty Badiya ta kira ta, ta ba ta hakurin rashin samunta a gida ta ce, amma tana bisa hanyar dawowa daga Zamfara ta je kai Junior ne. "Ni wannan Junior wane ne ne? Babu ranar Allah da za ta fito ta fadi ban ji an ambaci sunan sa a gidan nan ba". Rahinah ta tambayi Aunty Badiya cikin raha. Murmushi ta yi, ta ce, "Kada ki damu, yau za ki ga Junior Abdallah, dan kanina ne, gwauro mai gudun aure irin ki, da za ku taimaki juna ku auri juna da kun taimaki kan ku, mu ma kun taimaka mana". Nan da nan Rahinah ta yi fuska, kamar Anty na ganin ta, amma sunan yaron da Aunty Badiya ta ambata ya tsaya mata a rai, yana son tono da tsohuwar soyayyar nata Abdallah din, da ta bi ta sa block ta bibbinne a zuciyar ta. Kafin Aunty Badiya ta iso Raheenah ta yanke shawarar barin Kaduna don dai ta guje wa haduwar su yau da daddare da Uncle. Bata da amsar da zata bashi. Ta soma shirya karyar da ya kamata ta yi masa, amma da yake karyar ba dabi'ar ta ba ce, duk wadda ta kama sai ta kubce, ga shi ba ta shirya fuskantar sa a yau ba don ba ta da amsa ga umarnin sa. Na farko ba za ta iya auren Dr. Irshad ba don halayen sa kwata-kwata ba su yi mata ba. Ba ta son namiji mai son mata, sannan ga shi foreigner ba kasa daya ba, ba kabila daya ba. Ko dan kasa ne ita kam farin mutum ba da ita ba, sannan ita ba Habibu ta ke jira ba, to me ta tanada da za ta gaya wa Uncle? Ta iso kofar dakin mai aikin Anty ta tadda Sahura suna hira ita da Labo mai aikin Aunty Badiya. "Sahura taso tafiya za mu yi". Sahura ta ce, "Tafiya ran ki ya dade? Yanzu Labo ta ce Aunty na hanya fa sun kusa shigowa Kaduna. Na dauka kin ce sai gobe za mu koma har ina shirin shiga Malali (gidansu) in dawo?" "To na fasa kwanan, tafiya za mu yi, in kuma in barki kya taho a motar kasuwa ne to?" Da sauri Sahura ta mike tana janyo hijabinta tana fadin, "A'ah uwargijiya ta, ba zan barki ki kama hanya ke kadai ba". Uncle ya fita bai nan tun safe, ta ji hakan a bakin Mu'allim, don haka ta jefa jakarta a bayan mota ta shiga ta tayar, Sahura ma ta shiga ta yi reverse ta durfafi get, maigadi ya bude musu za su fice sai ga Mubaraq na shigowa. Ta dan dakata ta sauke glass ya ce, "Aunty unguwa za ku je ne? Mummy sun kusa isowa har da Uncle din mu da Junior, ya dawo daga Belarus kuma anan gidan zai fara sauka ya ga Junior". Murmushi ta yi, ta ce, "Mubaraq ana kirana da gaggawa a asibiti, so I must go now, na yi wa Daddy text, ka gaya wa Aunty zan kira ta in na isa Abuja. A gaida min Junior da Uncle din mu, wani lokaci za mu hadu ai insha Allah". Da haka suka yi sallama da Mubaraq ta ja motar da gudu suka hau kwalta. Da ta tabbatar ta yi nisa da Unguwar Sarki, ta hau titin fita garin Kaduna fintinkau, har wata ajiyar zuciyar samun kubuta ta saki. Daidai lokacin da direban Habibu Mustapha Nahuche, ya karya kan motar su kirar Camero, onedoor, mai dauke da tambarin (NahucheHotels4) mai lambar jihar Lagos wadda a ciki ya dauko Habibu daga filin jirgin saman Kaduna ya shiga gidan Aunty Badiya, da yake suna waya shi da aunty da kamar mintuna biyar da isowar su yana cikin motar yana waya bai kai ga fitowa ba itama ta iso tare da nata direban, wanda ya daukota daga Gusau, Junior a gefen ta, Zarah a gidan gaban motar. Yana kokarin parking Mu'allim na isko su da gudun gaske sabida jin dadin ganin Uncle Habibu, kusan watanni ukku kenan basu gan shi ba, shi ya bude bangaren (owners side) don Habibun ya fito, tun kafin direban sa ya gama parking, ya kuma karasa ya bude wa mahaifiyar sa tata motar. Yana yi musu oyoyo dukkan su. Aunty Badiya ta fito tana mika, cikin tsabar gajiya tana, "Wash Allah!". Sabida gajiyar zaman mota tun daga Zamfara har Kaduna. Mu'allim ya ce, "Welcome Uncle, welcome Junior". Tare da rungumo kyakkyawan dan uwan nasa Abdallah wanke hannu ka taba dan Habibu Nahuche. Wanda ke sanye cikin tsadaddun shirt da wando masu duhun kala samfurin (Dolce&Gabbana). Junior ya na fitowa ya ce, "Yaya Mu'allim ina kwallona da na ba ka ajiya?" Hararar sa Daddyn sa ya yi, ya ce, "Kwallo? Kwallo daga zuwan mu za ka fara ko Abdallah?" "Afuwan Daddy, ka sani in ban yi kwallo ba bana jin dadi, ni so nake ma in na gama jarabawa ka kai ni Manchester inzamadan Manchester United". Dariya Aunty ta yi, ta ce, "Karewar buga kwallo kenan, wallahi Baban Junior in ba mu yi da gaske ba Junior dan kwallo zai zama". "Allah ya sauwaqe!". In ji Habibu cikin takaici, a ran sa kuwa cewa ya yi, "Ranar da Alhuda-hudar uwar shi ta gan shi ya kare da zama dan kwallo da me zan mata tutiya da shi na cewa da na yi, zan fi ta iya kula da shi? Suna takawa zuwa cikin gidan Mu'allim ke cewa, "Aunty Rahinah ta tafi, ta ce in ta isa Abuja za ta yi miki waya, an kira ta on emergency a wajen aiki". Kwakwalwar Habibu ta tsaya cak! Da aiki, kamar yadda ya dakata da tafiyar da yake yi. Sakamakon ambaton sunan Raheenah da Mu'allim ya yi, but he didn't take it further, and he did not show any reaction. Rahinah nawa ce a duniya kuma ba tun yau ba yake jin zancen ita wannan Aunty Raheenar a bakin su. Ya fahimci wata 'yar uwar su ce makusanciya ta bangaren mahaifin su. Aunty ta ce cikin takaici, "Amma Rahina ba ta kyauta min ba, sai fa da na ce ta tsaya yau za su hadu da Junior". Takaicin ta daya ta so yau Raheenah da Habibu su hadu, ko Allah zai sa a dace su yi wa juna, don dai ta dade tana shaawar gwada wannan saar tata a ran ta, don a ganin ta Rahinah ba daya take da sauran mata da Habibu yake gudu ba, tafi karfin namiji yayi mata kallo daya. Habibu ya yi gaba zuwa cikin gida ya bar su yana ta amsa wayoyin da ke shigo masa, bai saurari zancen da suke yi ba. Bai tafi ba sai da Uncle Usman ya dawo, sun dade suna tattaunawa a falon Uncle a kan harkokin su. Suna cikin maganar sako ya shigowa Uncle daga Rahinah. Uncle I'm so sorry, an kira ni on emergency ba zan iya jiran dawowar ka ba, yanzu har mun shiga Abuja, Uncle ba ni da amsa ga umarnin ka, I have no one, I have only myself". Rahinatun ka. Murmushi ya yi, ya san da ma za ta gudun, amma kawai sai wani bakon tunani ya shigo kan sa, a lokacin da ya daga ido ya dubi Habibu da ke cin abinci a dining din falon sa. -Wace ce uwar dan sa? Me ya sa ko zancen ta bai taba yi ba? -Habibu ya rayu ne a Jamus, haka diyar sa Raheenah, Habibu na da Da Abdallah, Raheenah na da Da ita ma mai suna Abdallah, amma ko zancen dan ba ta yi. Habibu ba ya zancen tsohuwar matar sa, Raheenah ba ta zancen tsohon mijin ta. Ambasada ya ce mijin dan Zamfara ne...! Matar sa Badiya da kanin ta Habibu sun fito daga Zamfara ne... A fili Uncle Usman ya ce, "Ya Jamilal Munzar! (Wato, Ya Mafi Kyawun Masu Gani) Ka taya ni duba al'amarin nan". "Habibu!". Ya kira sunansa da karfi, wanda hakan ya sa Habibu dakatawa da cin abincin sa, ya dago lumsassun idanun sa yana kallon Uncle cikin mamakin karfin tone din da ya kira sunan sa da shi, Uncle ya mike jikin sa har rawa yake, ya isa ga dining din. Ya ja kujera wadda ke fuskantar Habibu ya zauna. "Ka gaya min sunan Babar Abdallah, da garin da ta fito". Da wani irin mamaki yake duban mijin Yayar sa, wanda yake tamkar ubangida a gare shi. Duk wasu achievements din sa a rayuwa Usman Girei shi ne sila, don haka yana da matsayin da ya zarta na siriki kawai, yana kallon sa ne a matsayin Yayan sa da suka fito ciki daya kamar matar sa Badiya. Yana da wannan kimar. Ban da haka shi tun barin sa Jamus harshensa bai kara ambaton sunan Rahinah Omar ba... In ya ji mutum dan Adamawa ne ma ba ya tsayawa a inda yake, kada tsautsayi ya sa ya kasance ya san Raheenah Omar ya yi masa zancen ta. Muryar sa na rawa ya ce, "Uncle Usman me za ka yi da sunan ta da garin ta? Ina fatan ba neman ta za ka je yi ba? I don't need her in my life anymore...!" Girgiza masa kai Uncle yayi. "Ba neman ta zan je ba, ba kuma bikon ta zan maka ba, hakkin haihuwa zan ba ta in kai mata dan ta ta gan shi ta san yana raye, kada hakkin su ya kama ka. Shekaru goma decade guda ka raba Uwa da Dan ta.... Yaa Subhanallah! Sai a yanzu Uncle Usman ya kara tabbatarwa yar sa Rahinarsa ce uwar Abdallah da ya tuna farkon bayyanar Rahinah gare su an gaya masa Habibu ya sato shi ne daga hannun ta yana dan shekara daya. Kuma tabbas Junior ya zo hannun su ne bai fi shekara dayan ba, ina kwakwalwar su da lissafin su ya tafi tuntuni suka kasa gane hakan daga shi har Badiya? "Ka gaya min sunanta na ce Habibu, da garin da ta fito". Ya fada wannan karon cikin karyewar murya da karewar kuzari a jikin sa. Cikin in'ina da magana daga kasan can makoshi ya ce. "Rah...Rahinah Omar... Adamawa...!!!" Uncle Usman ya tsura masa idanu, ya kasa cewa komai. Hawaye suka cicciko a idanun sa, hawayen da bai san na tausayin Habibu ne ko na tausayin Rahinah ba? Shekaru goma suna dakon soyayyar juna da kuma Da a tsakanin su? Habibu bai gane halin da Baban Musaddiq ke ciki ba, kuma bai san dalilin ganin cikowar hawaye a idanun sa ba, sai gani ya yi ya tashi daga wajen, ya dauki wayar sa da hanzari ya yi waje. Mikewa ya yi don ya kasa ci gaba da cin abincin ya nufi sassan 'yar uwar sa. Tana falo ita da su Junior sun kunna kwallo (ball) suna kallo shi da Mu'allim sai iface-iface suke. Tambayar da Baban Musaddiq ya yi masa ta sa duk ya birkice, idanun sa sun kada, afterten years yau ya ambaci sunan ta. Kuma ba a fatar baki kawai ya fada ba, ya fada ne tun daga karkashin zuciyar sa, wanda hakan ke bankado rufaffen gyambon yana kaikayi da son neman agaji. A yadda Aunty Badiya ta gan shi ya shigo falon sai ta ce da karfi. "Junior, kashe kwallon nan ku tafi dakin ku, zan yi magana da Daddy". Mu'allim ne ya kashe suka fita, Junior na cewa da Abban sa, "Don Allah kada ka je hotel ka kwana, ka zo mu yi sharing daki na". Amma ga mamakin Junior Daddyn nasa bai iya ya ce masa komai ba, which is very unusual Junior ya yi magana ya ki kula shi. "Zai zo Junior, ka karkade masa shimfida". Inji Aunty. Da murnar sa ya fita yana cewa, "Thank you Mummy. You know I love you ko? Ke da Daddy?" Murmushi Aunty Badiya ta yi, ta ce, "I know Abdallah, and Mummy da Daddy loves you more". Da haka ya fice yana tsalle. Habibu ya zauna gefen Yayar sa, tamkar wanda ya dauki azumin rashin magana. Aunty Badiya ta ce, "Tsakani da Allah Habibu me ye reality na rashin auren ka? Habibu ko dai ka zama ba namiji ba ne bayan haihuwar Junior da ka yi?" Duk halin da yake ciki sai da Dr. Badiya ta ba shi dariya. Ta gefen ido ya kalle ta ya yi murmushi, ya ce, "Auren ne kawai bana ra'ayi, tunda kuma ina azumin litinin da alhamis ina iya rike kaina. Stop all these silly thoughts. Yau ki ce wannan, gobe ki ce wannan. Badiya ta yarfar da kai gefe, ta ce, "Tsakani na da Maman Abdallah Allah ya isa! Ita ta ki zama da kai, sannan ta hana ka auren kowa. Wa ma ya sani ko asirin su irin na fulani ta yi maka?" Mikewa ya yi yana dan murmushi kafin ya ce da Yayar sa Badiya. "Ai ita ba ta so na ma ko kadan, balle ta yi min asiri. Masu yin asirin ina ce sai suna son zama da mutum suke yin sa? Ba ta taba so na ba, kuma har abada ba za ta so ni ba". Yana fadin hakan ya doshi kofa ba tare da ya juyo ba, kada Aunty Badiya ta ga kwayar idanun sa, ta hango weakness din da ya bakunce su. "Gobe ba zan biyo ta nan ba, daga Hotel zan wuce Lagos". Badiya ta yi masa Allah ya kiyaye hanya, ya wuce ba tare da ya kara waiwayowa ba, ya bar ta da hannu bisa haba. A harabar gidan ya ga Baban Musaddiq zaune bisa fararen kujeru yana waya, ga yadda ya bada nutsuwar sa kacokam ga wayar za ka fahimci waya ce mai muhimmanci yake yi. Habibu na dosowa ya kashe ta, ba tare da ya gama ko ya yi sallama ba. "Baban Musaddiq zan wuce masauki, gobe zan wuce Lagos, ba zan shiga Abuja ba sai upper week". Baban Musaddiq sai kallon sa yake kamar yau ya soma ganin sa yana kissima abubuwa masu yawa a cikin ran sa. Ashe surukin sa ne... Ashe shi da Badiya har jini sun hada... Ashe shi ya sa yake matukar son ABDALLAH... Abubuwa da yawa yake kissimawa wadanda sai a yanzu suka samu damar dawowa suna warware kan su, yana kara mamakin ta yadda har ya kai tsayin wannan lokacin bai gane din ba. Hannu kawai ya iya mika wa Habibun, ba tare da ya ce komai ba suka yi musabaha ya wuce zuwa motar sa. Ya shiga ya tayar da kan sa don ya sallami Solomon tun dazu, Baban Musaddiq bai bar wajen ba sai da Habibu ya fita daga get gabadaya. Wayar da Uncle Usman ya fito waje yana yi, ba da kowa yake yi ba da Ambasada Shehu ne. Har kuka ya yi a cikin wayar, a lokacin da yake gaya masa ashe Habibu shi ne mijin Raheenah ba su taba ganewa ba? Murmushi Ambasada ya yi, murmushi mai sauti kafin ya ce. "Finally kai ma ka gano da kan ka kenan, kamar yadda na dade da ganewa. Da ma na ce ba zan gaya maka ba ne sai ranar da ka gano don kan ka...". Nan aka dauko tsohon tarihi, Ambasada ya warware wa Uncle Usman rikicin auren su a Jamus kaf! Ya kare zancen sa da cewa. "Har gobe daga ni har Nene Bilki da kawar ta Yafendo, babu wanda ya san hakikanin laifin da Habibu ya yi mata. Bata taba fada ba. Which means tana sirran ta sirrin sa. Amma kuma tana fushi da shi, ban yarda rashin so ne ba, kada ka takura sai ka ji, don tsakanin mace da miji sai Allah. Yanzu neman hanyar sulhunta su za mu yi, in ba haka ba ina mai tabbatar maka Habibu da Rahinah za su yi furfura a kan su ba tare da sun yi aure ba". Uncle Usman da Ambasada suka ci gaba da kulla mai yiwuwa a tsakaninsu su biyu ba da sanin Aunty Badiya ba, haka ba da sanin Habib da Rahinah ba, sun aje kwanaki uku masu zuwa za su hadu su je Girei su samu Sarkin Fulani a san ta yadda za a shawo kan al'amarin. Bayan nan, sun yanke tabbas za su hada Habibu da Rahinah a gidan Uncle Usman ba tare da sanin kowannen su ba, don su ga irin reaction din kowannen su. Don a cewar Ambasada Rahinah ta HUCE daga fushin ta tuntuni, ki-fadin ta ne ba zai bari ta nemi Habibu ba. Shi kuma Uncle ya musanta da cewa har yanzu ba ta huce ba, don ko jiya da ya matsa mata da zancen aure, kuka ta yi masa. Ta kuma gudu. Ba za su gane hakikanin abin da ke zukatan su ba har sai sun hada su sun ga juna unexpectedly. Abin da dattijan biyu ba su sani ba shi ne, daga Habibu har Rahinah babu wanda bai san garin da dan uwan sa ke rayuwa ba... Babu wanda bai san duk wani taku na dan uwan sa ba. Babu wanda bai san ci gaba da nasarorin dan uwan sa ba. Abin da ba su sani ba shi ne, alakar da ke tsakanin su, wadda Badiya da Uncle Usman suka hada, wato kasancewar Habibu kanin matar Uncle din ta, da kasancewar Rahinah diya ta halali ga ubandakin sa, kuma sirikinsa Baban Musaddiq Alh. Usman Girei. ****** Sarkin Fulani ya gama jin duk abin da ke akwai, ya yi kabbara takbir da tahlili cikin jinjina kudurar Ubangiji. A karshe ga bayanin da ya yi musu, a matsayin sa na babba, wanda dukkan su ya fi su shekaru da tsinkaye. "Bana bayan shawarar ku, ta a maida musu aure ba da sani da amincewar su ba. Kada ku manta Rahinatu na a matsayin bazawara ne a halin yanzu, addini ya ba ta damar zaben mijin aure. Alhamdulillahi tunda saki daya ne a tsakanin su, abin da za ku yi yanzu shi ne, ku yi kokari su hadu da juna, ta ga dan ta ta san shi ne. Ya gan ta, ta ganshi su san alakar zumuncin da ke tsakanin su. Daga nan ku bar komai a hannun su, ni na gaya muku za su sulhunta kan su. A wannan lokacin addu'a ce tsakanin ku da su ba tirsasawa ba". Daga Uncle har Ambasada sun yi na'am da shawarar Sarkin Fulanin Girei. ****** Ta fito daga bedroom dinta a shirye tsaf, likita mai aji, rike da 'yan mukullayen motar ta ta tadda Sahura a falo tana kallo, ta ce, "Sahura, yau in na fita sai Allah, don haka kada ki yi girki da ni, ki yi daidai cikin ki, za mu yi dashen dodon kunne har biyu (cochlear implant transplantation) a Nizamiye, don haka sai kin gan ni kawai". Sahura ta ce, "Allah ya yi jagora, Allah ya bada sa'a uwar daki na, Allah ya bada ladan ceton kunnuwan al'umma". Dariya ta yi ta wuce ta fita tana karanto addu'ar fita daga gida. "Ina so ki ba ni hankalin ki". Baban Musaddiq ya ce da Aunty Badiya. Ta gyara zaman ta tare da tattara masa kafatanin hankalin ta. Baban Musaddiq tun jiya ta ke ganin shi upset, ga waya akai-akai shi da wadanda ba ta san ko su waye ba, abu kadan ya dau waya ya fice ya gama magana sannan ya dawo, abin da ba halin sa ba, babu wayar da ba ya iya amsawa a gaban ta a baya. Yanzun dai Nene Balki ce ta ba wa Ambasada shawarar ya kamata Badiya ta san komai, kuma a gidan ta ya kamata Habib ya ga Rahinah ba a Abuja ba, tunda a can Junior yake. Ba ta ga amfanin kin sanar da Badiya da wuri ba. Shi kuma Ambasada ya gaya mata cewa, Badiya tana kullace da tsohuwar matar Habibu a kan ita ta hana dan uwan ta aure, da yadda ba ta taba neman ta ga dan da ta haifa ba inji Uncle Usman, Nene ta ce, "Akwai fahimta da kyakkyawar mu'amala tsakanin Rahinah da matar kawun nata, insha Allah komai zai zo da sauki". Don haka shawarar Nene Balki Uncle Usman ya bi yanzu. Ya ce, "Maman Junior I have something special for you, mene ne zai zama tukwici na?" Murmushi Dr. Badiya ta yi, ta ce, "Duk abin da ka ke so shi zan ba ka Daddy". Ya ce, "Shin wace ce babar Abdallah ne, kuma a ina ta ke?" Nan da nan Aunty Badiya ta canza fuska kamar ba ita ke ta fara'a yanzun ba, ta ce, "Daddy da zan ganta Allah kadai zai raba ni da matar nan, na tabbata surkullen su na fulani ta yi wa Habibu ya kasa yin aure. Ban san ta ba, ko sunanta ban taba tambayar sa ba, sabida ba ni da wata alaka da ita. Yaron da ta haifa ta yasar, babu ko waiwaye ga shi nan Allah ya raya shi. Ita kuma Allah ya yi mana shari'a da ita a lahira". Uncle sai ya kama dariya, ya ce, "Wato fulani surkulle gare mu? Kuma 'yan Nahuche ai fulanin ne in miki kirarin garin ku Zamfara GALMA UWAR RUFI, ko ba ku son mutum ba ku hwadi. Ke kam ba ki yi galmar ba kin hwadi ba ki son matar Habibu, ga shi kuma ta zame miki dole, sai ki dau na Annabawa ki soma tunanin hanyar sulhunta su, tunda kuwa ba kowa ba ce 'yar ki ce Dr. Raheenah". Kusan za a ce Aunty Badiya shidewar wucin gadin razana ta yi, sabida ta san Baban Musaddiq ba ya yin joke shi kai tsaye yake fadar komai. Ta kura masa ido ta kasa daukewa, shi kuwa sai lumshe mata ido yake yana gyada mata kai cikin ba ta tabbacin maganar sa. Da kyar Aunty Badiya ta iya cewa, "Wace Dr. Rahinar?" Shi kuma bai bata lokaci ba ya ce, "Ya ta Raheenah". Ya kwashe labarin komai ya gaya mata, sak! yadda Ambasada ya labarta masa. "Idan Ubangiji ya lullube al'amari, babu dan Adam din da ya isa ya bankado shi, sai a lokacin da Ya nufa. Don haka ki sauke duk wasu makaman yakin ki a kan Maman Abdallah mu taru mu taimaki yaran nan su koma auren su, don zan iya yi miki rantsuwa kan cewa soyayyar juna ta hana su aure. "Yanzu me ye abin yi? Da me zan iya taimakawa?" cewar Badiya cikin mutuwar jiki. Uncle Usman ya gyara zama. Tiryan-tiryan suka soma tsarawa. ****** "Kin kyauta Rahina, ni da ma na san kafin in dawo za ki gudu, to duk abin da ki ke yi ki bari ki zo karshen satin nan, I'msure ba kya aiki asabar da lahadi, Sarkin Fulani ma ya ce ki biya ku gaisa idan kin zo". Raheenah ta marairaice murya abin tausayi, ta ce, "Uncle, bana son zancen aure, don Allah Uncle ka kyale ni, idan ka takura zan iya kamuwa da depression, I have a lot to do I can't put myself in any relationship... Zan iya rike kaina Uncle, don Allah kada ka sake yi min zancen aure". Murmushi Uncle ya yi, ya ce, "Na yi alkawari ba zan sake ba, za ki zo din? Weve planned a get together dinner na kammala karatun Musaddiq". A hankali ta ce, "Insha Allahu zan zo Uncle, tunda ka yi alkawari". Murmushi ya yi yana kallon matar sa Badiya. "Finally, ta amince za ta zo din". "To Allah ya sa shi ma ya yarda ya zo don ka san shi kamar tsuntsu yake, yanzu haka sai ka ji ya bar Lagos din ma". Ta fada tana dialling number din Habibu Nahuche. Har ta yi karar ta ta gama bai dauka ba. Tana kokarin sake kira sakon sa ya shigo. "In a meeting, call later". Murmushi ta yi, ta tura masa nata sakon. Call me da zarar ka fito". Yana fitowa din kuwa ya kira ta. "Ya ya ku ke Aunty, ya Abdallah?" "Sarki mai Abdallah, ni boarding zan kai shi in huta kallon kwallo. Za ka iya zuwa karshen satin nan? Baban Musaddiq ke gayyatar ka get together dinner iya mu i'mu na gama degree din Musaddiq and zaa yi hotuna da bidiyo don tarihi, don haka presence dinka is very vital". Habibu ya yi dan murmushi, zumunci da 'yar uwar sa ba ya hada shi da komai, don ba shi da wanda ya fita a duniya bayan mahaifiyar su. Ya ce, duk muhimancin uzrurrukan sa yana bari sabida hidimar Aunty Badiya da iyalin ta. "Zan yi squeezing time don ina da muhimman abubuwa a gabana a weekend din nan". "A bar komai a zo mana, in babu kai abin ba zai yi armashi ba". "I know Maman Abdallah". Da haka suka yi sallama. Kusan a tare Habibu Nahuche da Raheenah Omar suka shigo garin Kaduna, shi a jirgi daga Lagos, ita a motar ta daga Abuja. Sahura na gefen ta tana zuba mata hira, amma ga mamakin ta ta kasa ce mata komai. Yau jin kan ta ta ke kamar an dinke mata baki, an cire dukkan kuzarin ta. Ba ta san hakikanin abin da ke damunta ba. Raheenah ta riga Habibu isowa gidan Uncle, kuma kai tsaye sai ta wuce dakin ta na gidan ta kwanta, don duk yaran gidan Aunty ta kwashe su ta kai su gidan aminiyar ta a Malali, ta ce sai takwas na dare za ta turo a dauko su. Musaddiq ne kawai a gidan, don haka bayan sun gaisa da Aunty ta ce ba ta jin dadi, kwanciya za ta yi kamin Uncle ya shigo gida. Da ma kuma tana hutun sallah. Ba a fi awa guda da kwanciyar Rahinah ba Habibu ya iso, karkashin rakiyar ma'aikatan Nahuce Hotel na garin Kaduna, wadanda suka dauko shi daga filin jirgi. Motoci uku jibga-jibga kamar su fashe don koshi da sheki, kowacce dauke da logo na NAHUCE GROUP OF HOTELS. Sanye yake cikin black-greyGerman-Suit wadda ta fiddo zahirin ilhama da cikar zatin sa, kwarjininsa ya fiddo zahirin matashin miloniya mai tashe, HABIBU MUSTAPHA NAHUCHE wanda kallo daya za ka yi masa ka tabbatar Allah ya gama yi masa kowacce irin ni'imar rayuwa. Kallo daya ba zai gamsar da idon ka a kan HABIBU NAHUCHE ba, ba tare da marmarin ka yi masa kallo na biyu ba. Idaniya ba sa taba gajiyawa da kallon sa sabida wani sassanyan sirrantaccen kyau da haiba da Allah ya yi masa. "The successful business tycoon of Zamfara". Kamar yadda kafafen yada labarai ke kiran sa. Habibu Mustapha Bilyamin Nahuche, ya fito daga motar hotel dinsa yana taku majestically, zuwa cikin gidan Aunty Badiya. Musaddiq ne ya fara taren sa a bakin kofar shiga falon, da runguma mai karfi yana fadin. "Welcome Uncle Habib!" Muryar Musaddiq ce ta fiddo Aunty daga kicin, murmushi fal bakinta ta ce, "Ban zaci za ka sauka haka da wuri ba. Musaddiq ka je ka taho da su Abdallah". Musaddiq ya ce, "Aunty da kin kyale Abdallah sai Uncle ya ci abinci ya huta, yana zuwa zai ishe shi da zance da dumi ba comma ba full-stop". Aunty ta ce, "Sai kuma Uncle din ya ce maka bai son ya cika shi da dumin? C'mmon je ka dauko su maza gidan Anty Hassu". Habibu na jin su amma rabi-da-rabi don hankalin sa ya tafi ga wayar da yake ta amsawa akai-akai. Kafin dawowar Musaddiq Uncle ya dawo, ita kuma Aunty da mai aikin ta ba su zauna ba sun dukufa shirya abinci bisa makekiyar darduma da aka shimfida a falon Uncle. Fita goma ko shiga goma za ta yi sai ta kalli Habibu ta yi murmushi, ba abin da ta ke tsananin so irin ganin reaction din da zai nuna idan ya ga Raheenah yau a gidan ta. Ko za a kashe ta ta san Raheenah ce ta farko, kuma ta karshe a zuciyar Habibun, ko da kuwa su duka a yau sun nuna musu ba su taba sanin juna ba. Uncle Usman ya bi Aunty kicin ya ce, "Tana ina ne?" Aunty ta yi dariya ta ce, "Tunda ta zo, tana daki a kwance ba ta fito ba, kamar wadda aka yi wa duka". Uncle ya girgiza kai ya ce, "Bari in je in yi serving din sa abinci ya ci, idan ya gan ta ba zai iya cin abinci ba, ga shi ban san yadda kowannen su zai karbi dan uwan sa ba". Ya juya ya fito, ita kuma Aunty ta hau kiran Musaddiq a waya don ta ji ko sun taho? Uncle da kan sa ya zuba ma Habibu duk abin da Aunty ta dafa a kan plate guda yana ta jan shi da zance yana loda abincin a kan faranti har sai da Habib ya ce, "Abincin nan ya yi min yawa fa!". Uncle Usman ya ce, "So nake ka tada komada daga wannan ramar taka, kai kenan kullum kamar a bushe ka fadi?" Murmushi ya yi, ya ce, "Yaya dan Adam zai yi kiba alhalin rayuwar sa ba ta taba hutawa ba? Kullum cikin kujuba-kujubar nema yake, sannan babu iyali a gefe wadanda taimakon su zai sa ya yi kibar?" Baban Musaddiq ya ce cikin halin ko'in kula, "I can relate, I see". Sannan ya tura masa plate din abincin gaban sa. Bayan ya aza cokali da fork akai. Gab da zai gama cin abincin Abdallah da Zarah suka shigo, Abdallah ya yi kan sa da mugun gudu yana, "Daddy na, oyoyo!"Ya rike shi sosai cikin jikin sa tamkar zai maida shi cikin sa yana sunsunar sa, ya ce, "Junior, me ka ke ci haka? Ni girman ka tsoro yake ba ni". Dariya Abdallah ya yi daidai lokacin da Aunty ta shigo, ta ce, "Junior, je ka dakin Zarah za ka ga bakuwa tana barci, ka taso ta, ka ce ta zo in ji Daddy ya dawo". Da gudu Abdallah ya fita don shi yaro ne mai bin umarni, yana fadin, "Daddy kada fa ka je ko ina, yanzu zan dawo". Aunty ta zauna gefen Habibu tana yanka mishi apple, Daddy kuma na diban sa da zance. Barci ta ke sosai, lokacin da Abdallah ya shiga dakin. Yatsun kafarta ya hau ja yana fadi da karfi, "Bakuwa ki taso ki zo in ji Maman mu, Daddy ya dawo". Kamar a mafarki 'yar siririyar muryar yaron ta ke ratsa kunnuwan Rahinah Omar. Jin muryar ta yi tamkar busar sarewa cikin kunnuwan ta, ga shi sai kara maimaitawa yake yi. A hankali ta ke bude fararen idanun ta, wadanda barci ya sa suka canza launi tana kallon kyakkyawan yaron. Har idanun ta suka gama washewa sosai a kan sa. The cute face looks so familiar... and the feelings for him is not a strange feeling. Abin nufi ji ta yi ba yau ya ginu a zuciyar ta ba. Wani daddadden feeling ne wanda babu irin sa (maternal love) irin wanda kowacce uwa ke da shi a kan dan ta, walau ta san shi ko ba ta san shi ba. Amma a halin da ake ciki, Rahinah Omar ta ji kaunar yaron ne kawai a ranta ba tare da ta san daga ina kaunar ta keto ta fito daga karkashin zuciyarta ba. Murmushi ta yi masa, sannan ta yunkura ta tashi daga kwanciyar ta sa hannu ta yafito shi. Matsowa ya yi gaban ta ya tsaya, a kintacenta zai yi shekaru goma, amma ba ta taba ganinshi cikin gidan ba, don haka tunaninta ya ba ta shi ne Junior da suke yawan ambata. Hannu ta sa a kan lallausar sumar kansa ta ce, "Kai ne Junior?" Gyada mata kai ya yi, sannan ya juya zai fice. Raheenah sai ta samu kanta da cewa cikin rawar murya, "Junior ya ya sunanka na gaskiya?" Sai da ya kai bakin kofa zai fice ya juyo ya ce, "Sunana Abdallah Habibu Nahuche!!" "ABDALLAH NAHUCHE!!! Rahinah ta maimaita a fili. A ina ta taba sanin wannan sunan? Tamkar wadda aka fizga a zuciya ko kuwa aka tsikara sai ta samu kan ta da mikewa wuf! Ta bi bayan sa ko kallabin ta ba ta tsaya daurawa ba. Dakin Aunty Badiya ta fara zuwa, babu kowa! Da sauri ta fito zuwa inda ta jiyo tashin muryoyin jama'ar gidan, wato falon Daddy. Nan ta tadda su complete family yadda sukan zauna koyaushe. Amma a kusa da Aunty a tall, giant, handsomeman, ya bata baya, wanda duk hayaniyar da ke tashi a falon babu tashin muryar sa. It's either kamar bai falon, ko kuma akwai abin da yake yi da ya hana shi magana. Waya ce a hannunsa yana daddannawa, sallamar Rahinah Omar ta sanya shi wani irin dagowa in a slow motion. Ita kuma ba tare da ta lura da shi ba ta nufi inda Junior yake can gefen Musaddiq yana ta zuba masa zance. Tamkar wadda ake controlling da remote haka ta nufi gurin yaron absentmindedly ta tsugun na a gaban sa, tafin kafarsa ta kama tana son tantance abin da ke cin ta a zucci. Tawwadar Allahn data ke son gani tana nan a kan babban yatsar kafar sa, sai girma da fadi da ta kara. "ABDALLAH!" Habibu ya fada da karfi tamkar ya ga wani abun da zai cutar masa da Da. Irin tsugunnon da ta yi a gaban yaron, irin sa ta yi a gaban Ambasada Shehu Bichi tana rokon sa ya karbar mata 'yancin ta daga hannun sa. Bafullatanar mai yawan sumar kai, da hasken fatar da ko a cikin farare ita fara ce lamba daya tsugunne gaban dan sa, wadda cikin kowanne hali ba zai kasa gane ta ba, image din kyakkyawar fuskar ta ba zai taba gushewa daga zuciya da kwakwalwar sa ba. Balle ma cikin shekaru goman da suka gabata, canjin da Rahinah Omar ta samu na halitta ba wani mai yawa ba ne. Canji ne kawai irin wanda nauyin shekaru ke haifarwa diya mace ba tare da ya canza appearance na kuruciyar ta ba. She is still that ravishing, glowing and sparkling lady fiye da yadda ya baro ta a Germany. Sai ma wata 'yar kiba-kiba da ta kara mai nuna sukuni, wadata da kwanciyar hankalin da ta ke ciki. Kiran da Babansa ya yi masa haka da karfi ya firgita shi, don haka da sauri ya kwace kafar sa daga hannun Rahinah ya nufi baban sa yana buya a bayan sa. "Daddy boye ni, ni ma ban santa ba". Ya yi daidai da lokacin da Rahinah ta juyo ta sauke ragaitattun idanunta a kan Habibu Nahuce, wanda ke kallonta babu ko kiftawa. Her Ex- Habibu ne! wanda ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta kasa gane shi ba, balle dan da ke tsakaninsu. Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Habibu Nahuche da Rahinah Omar, kallon da ke rewinding duka incidents din shekarun can baya a Jamus, abubuwa da yawa da suka gabata na gilmawa a idanun su. A take Rahinah ta soma ja da baya cikin tsoro da kidima. Tsoron da ya haifar mata da karkarwar jiki da ta zuciya, amma ga Habibun, ba zan iya cewa ba. Domin kuwa bayan idanun sa sun farfado daga shock din ganin ta a inda bai taba tsammani ba, wato a gidan Yayar sa, ya kara yi mata kallo na biyu, kallon da ya tattaro duk wani kundi da ya lullube a karkashin zuciyar sa. Ya bude shafukan sa filla-filla, shafukan tun shigowar Raheenah cikin rayuwar sa, and the roles she played in shattering it (da rawar da ta taka wajen yagalgala ta). Eh, ya kira shigowar ta cikin rayuwar sa ba komai ba sai kacaccala ta (shattering dinta intopieces) tunda har yau ga shi nan a gantale bisa titi yana ragaita babu iyali, in an kuma bi salsala wannan bafullatanar ita ce sila. Domin kuwa soyayyar ta ce har gobe ke azabtar da shi ko na second daya bai taba hutawa ba. The marital physical relationship din da ya wanzu tsakanin su, will forever remain green a zuciya, gangar jiki da kwakwalwar sa, wanda ya dusar da hasken duka sauran mata daga idanun sa yake musu kallon ba bambancin da nasa jinsin, sai ita kadai ce mace a idanunsa. Ba zai gaji da cewa ba Rahinah Omar ta tafi da dukkan farin cikin sa, sannan dawowar ta a yau ya san yana nufin abubuwa da dama in bai yi wa tufkar hanci ba. Tunda ita tamkar mala'ikar daukar rai ta ke, ba ta zuwa ta tafi, ba tare da ta kashe zuciyar mutum ba. Ta zame masa tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba ALHERI ba. Yana cikin tattala 'yar ragowar rayuwar sa da ta riga ta kashe ya samu control din ta a yanzu, shi ne kuma ta dawo cikin rayuwar sa ta inda bai zata ba. A wannan karon, a wannan lokacin, a wannan 'yan dakikan, Habibu Nahuche, ya kudiri aniyar yaki da dawowar Rahinah Omar cikin rayuwar sa. Ba zai bari ta sake yin galaba a kan sa ba. Ko da wacce ta zo zai tarbe ta kyakkyawar tarba irin ta yakin ceton rai. Ko da ma can ya san tana existing a garin Abuja matsayin cikakkiyar otorlaryngologist din National Hospital da NIZAMIYE. Yadda aka yi ta zo gidan Yayar sa ne bai sani ba, watakila wani ya gaya mata ga inda dan ta yake shi ne ta zo, za kuwa ta sha mamaki in ya ce mamaki, yana nufin mamaki mai gigita kwanyar diya mace. Domin daga yau Abdallah zai bar gidan Badiya. Hannu ya sa ya janyo Abdallah da ke faman buya a bayan sa, ya yi masa kyakkyawar mafaka a kirjin sa, ya rungume shi sosai idanun shi a lumshe. "Don't be afraid Abdallah, I'm here with you babu mai taba ka sai ruwan sama". Daga nan ya mike tsaye rike da hannun yaron, kyakkyawan kallo na biyu wannan Rahinah Omar ba ta samu daga gare shi ba, "Maza Abdallah debo kayan ka tafiya za mu yi". Daga Aunty Badiya har Daddy bin sa suka yi da kallo kallo na mamaki. Domin ba haka suka yi zato ba. Yayin da Dr. Raheenah ta sunkuyar da kai, hawaye fal idanun ta. (Between happiness and excitedness) ba ta san wanne ta ke dulmiyewa a cikin sa ba. Abdallahnta... her only son Abdallah... after a decade, yau shi ne tsaye a gaban ta gidan Uncle din ta. To ta ina ya zo? Wannan na nufin... shi ne Junior din, dan kanin Aunty Badiya... wannan na nufin Habibu Nahuche... shi ne kanin Aunty Badiya. Ta wani irin lumshe idanun ta a hankali, tsigar jikinta na tashi, ko kafin ta farfado daga shidewar wucin gadin da ta tafi babu Habibu babu dan sa Abdallah a falon. Ta ina za ta bari Abdallah ya sake kubuce mata A KARO NA BIYU? Ai ko yakin duniya na biyu (World War II) za su yi ita da Habibu wannan karon sai ya ba ta dan ta. Da gudu-gudu ta bi bayan su tana kiran sunan "ABDALLAH". Yayin da jamaar falon duka suka bi su da kallo. Ba ta cimmasu ba sai a harabar gidan yana kokarin saka katuwar jakar kayan Abdallah a bayan jibgegiyar motar da ke ajiye a ma'adanar motoci. Sai ta rasa kwarin gwiwar karasawa gare su, sabida kallon dibar karen mahaukaciyar da Habibu ya yi mata, ta tsaya daga bakin kofar shiga falon Daddy Usman tana kallon su kawai suna shiga mota, kaunar Dan ta na kara bunkasa a zuciyar ta kwatankwacin ta ranar da ya zo duniya, hanyoyin da zata bi ta karbi Abdallah ta take tunani, koda hakan shine struggle na karshe da zata gudanar a rayuwar ta. Daga nan har supremecourt! Wato kotun daga ke sai Allah ya isa!!! Ganin sa da ta yi yau matsayin kanin Aunty Badiya matar Baban ta, ta san Allah ke nufin farawar sababbin alamura da dama a gare su, wadanda a iya kintacen ta da tsinkayen ta bata hango farkon su balle karshen su ba. Na baya duk shimfida ne, wato wanda ya faru a Jamus, yanzu ne zasu fara ta babu dadi ita da dan mutanen Nahuche. Domin ko sama da kasa zata hade sai ya bata dan ta. Abu daya ta sani shine (maintaining self-esteem) din ta yanzu ta fara, ko da soyayyar ita ce ajalin ta, amma tana da right din ta na rikon Abdallah wanda addini da shariah suka bata har sai ya balaga ya zaba tsakanin ita da shi. Idan a da bata da gata shi yasa yake walagigi da ita da dan ta yadda yake so to a yanzu tana da gata kamar koma fiye da kowa. Sannan ta tsaya da kafafun ta ta wuce wargin kowanne da namiji. Don haka ita da Habibu a je zuwa..wai mahaukaci ya hau kura SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI KE CEWA, MU KARASA LABARIN "NAHUCHE. (DAGA FUSHI NA) A LITTAFI NA 3 NAN BA DA JIMAWA BA INSHA ALLAHU. 20/2/2022