Home / NAGA RAYUWA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 1 NAGA RAYUWA book 3 part 1 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 13:53 Adakata! Adakata! mukaji wasu yansanda suna fada daga bakin kofa,inda hankalin kowa yakai kanasu mata suka shigo dasu su 8 fuskarsu sanye da mask jikinsu kayane bakake daya daga cikin sojojin yaje gaban teburin Alkali abbana yace yamaigirma mai shariah hakika anyi kuskure wajen tsare wannan baiwar Allah ba ita akenemaba bawannan bace wacce ake zargi yanunani wani farin ciki ne yaxiyarceni hade da madaukakin mamaki daga can naji yan uwana suna furta Alhamdulillah. . ni ma sai alokacin nafurta Alhamdulillah cikin muryar data dashe alamar kuka dansandan yaci gaba dabayani hakika kamanni ne sak kwabo da kwabo da ita wacce ake neman maitsanin kama wanda Allah yabayyana tsantsar ikonsa akansu ayau muka yi dacen cafkesu acameroun zasu hau jirgi sutafi south africa yallabai ita wannan itace ainihin wacce ake nema yafada yana nuna wata daga cikin matan dasuka shigo dasu cikin daka tsawa ya umar yace ke bude fuskarki! yakwada mata kulki Araina nace karamata shegiya kinsaka ni abala'i iri-iri dazafin nama tasaka hannu tayaye rigar fuskar da take fuskarta kafcecen bakin gilas ne a fuskartata amma hakan bai hana ni ganin fuskarta ba . yadda kasan tawa fuskar aka dasa ajikin tata tasaka zara zaran hannunta tacire gilass din tayi wulli dashi tana ciccizon bakinta kaidaganinta ka ga wacce bata shakka,duk abinda zaibiyo baya bani kadaiba duk mutanen wurin cikin matsanancin al'ajabi suke kallonmu ni kaina nazare ido kawai nake ina nunata itama kuma nuna ni take fuskarta dauke da tsananin mamaki to wai yatake ne? mai shari'a alkali abbana ya razana balle ummana data kasa zama bakinta sosai yake bude ta ma kasa rufewa don tsananin mamaki na raya araina "Tabbas hukumullah la'ajaban". . Bayan tsawon mintoci da dakin shari'ar yabakunci hayaniyar mutane alkali Abbana yamayar da glass dinsa yakuma dakatar da surutun ta hanyar buga gudumar kotun da karfi nan take kowa ya,nutsu aka kuma kasa kunne don cigaba dasauraron shari'ar kowa yanason sanin dalilin wannan matsanan ciyar kama tamkar irin yaran nan yan biyu masu kama daya kamar kwabo da kwabo . da bature yake kira IDENTICAL TWINS.Abbana ne yadubesu dukkansu sannan yamayar da kallonsa akan carbon copy{mai kama dani} "baiwar Allah konace bayin Allah dagaske ne kune kuka yiwa minister sata bayan yaudarar sa dakukayi kuka kaishi hotel kuka bashi maganin barci bayan yayi barcin kukayi amfani dawannan damar kuka dauki hoton tsaraicinsa ma'ana kuka daukeshi tsirara kuka kuma watsawa internet don ku bata masa suna bayan kun masa awon gaba da kudadensa dalolin amurka? kodayake kafin nan zanso nasan sunayenku sunan uba ko wakili jiha ko unguwa?" Abba yafada yana duban su gaba dayansu suka shiga kallon junansu daya bayan daya sannan suka nuna mai kama dani da alama,itace zata wakilcesu ba tare da tsoron komaiba tawani watsa hannayenta tayi far-far da idonta "sunana SHANY,haka nataso agidan dana rayu naji ana kirana Aisha ne cikakken sunana sunan uba ko wakili kuwa bansan ko daya daga cikiba ko kuma nace bani dashi sam..." . Gaba daya naga yan gidanmu sunsake zaro ido sun zubamata Abbana cikin matukar mamaki yace . "Kamarya ya? mutuwa yayi ko kuwa sallamaki yayi kika koma rayuwar bariki?" Tabe baki tayi tare da kada harshe tace "lala lala,ni yar tsuntuwa ce kamar yadda wadannan dukkansu yantsuntuwane muna karkashin kulawar wata mata" Abbana yasake xuba mata ido yace yar tsintuwa kamar yaya? inakallon yarinyar sai data dan yamutsa baki da alama ta fara kosawa datambayar sai dai inaji kwarjini yayi mata don haka tayi kasa da idonta tace kamar yadda kasani duk wani dan tsuntuwa aibashi da sunan daya wuce shege. Dafarko sunana Shany kamar yadda na sanar tun abaya muna karkashin wata mata mai suna ATINE YAR HARKA mutalatin da,biyar ne cif karkashin kulawarta tunmuna yara tare da wadannan muka taso wanda dama su sa'annina ne agidan dukkanmu babu maicikakken asali hakan yasa sai yadda tayi da rayuwar mu tun muna yara muka tsinci kanmu acikin bautawa wannan mata tamkar bayi haka muke agidan kalilan daga cikinmu take warewa tasaka amakaranta wanda kyansu yakai kyau ciki kuwa harda ni don tasha fada wai ni BABBAN JARINTACE. . Nayi makaranta tun daga nursery har primary da secondary yanzu hakama ina jami'a tana bani ci da sha da suturu masu kyau amma fa duk acikin kudin damuke tara mata! shine kuma hakan baya samuwa sai yarinya takai shekara sha uku alokacin dazata ce wai tasan zata dawo mata da abinda takashe bata sakamu yin karuwanci saidai tana koyamana dabarun damfara ta yadda zamu yaudari mutum mukwace dukiyarsa mugudu yaudarar maza muke yi sosai ta hanyar nuna tsiraici ma'ana shigar banza wanda da zarar mutum yayi katarin haduwa damu sai ya fada tarkonmu saimu yasheshi mugudu club-club muke zuwa da inda mukasan attajirai da manyan gwamnati suna zuwa har dai kawo wannan lokacin da tsautsayi yakaimu muka yaudari wannan ministan Abinda yasa muka yada tsiraicinsa kuwa a internet yar'uwarmu yayiwa fyade..." daga haka taja dankaramin bakinta ta tsuke alamar bazata,sake cewa komai ba kotu kuwa tuni takacane da hayaniya mai shari'ah abbana yayi rubuce rubuce sannan yadago yana kallonta yanzu ina ita uwar dakin taku take . dan rausayar dakanta tayi kafin tace tana abuja tun ranar da abin yafaru tace muje muyi takanmu don minista yakai abin ga hukuma ita kuma bazata iya shari'ah da gwamnati ba da dai wanine da ta tsaya mana har iya inda karfinta yakare abba yasake gyada kai yace yanzu ina kudin?"yana wajenta dama ita ake bawa"Abba yasake yin rubuce-rubuce sannan yadago yakalli jamian tsaron dasuke wajen "sakamakon kotu takama yaran da ake zargi da aikata,wannan laifi kotu tawanke aisha daga zargin da ake mata bisa rashin sani da akasin da akasamu na matsananciyar kama da Ayshan take da ita wacce ake zargin takuma yi umar nin tsare Shany da yan uwanta tare dakawo uwar dakinsu tahanyar bin kwatancen dasukayi kotu ta dakatar da wannan shari'ar har zuwa 1/5/ 2016,alokacin da muke sa ran ganin wannan uwar dakin nasu ta bayyana kanta akotu" daga haka yabuga gudumar kotu daukacin jama'a kuwa suka amsa da koooootu" . Tundaga nesa nake hango fararen hakoran ustaz tare da yan uwana da ummana da suke fara'a saide nayi matukar mamaki danaga . Idanun mamina jawur alamar tasha kuka Na ayyana meyaparu kuma?itada yakamata tayi murna kuma take kuka Nazata zangan ta tana ta fara'a sakamakon yau mun wanku daga zargin da akemana tas. . Yau inason ganin mutane dayawa naga dawanne idon zasu kalleni bayan tarin abubuwan dasuka faru abaya babu wanda nakeson gani fiye da,ya usman masoyin gaske yadda yan jaridu suka baibayeni da tarin tambayoyinsu hakan yasa na saka kuka don sanin bazan iya basu amsar komai ba fatana kurum na hadu da mamina naji kukan me takeyi ganin bazan basu amsaba hakan yasa suka juya akalar tambayarsu gurin yan uwana kowa hamdala yake koda Ahmad yaji labari. . Ni kam duk basa gabana don dama nafada duk ranar da gaskiya ta bayyana akwai kallo da yawa Ganin Abbana yanufo wajenmu yana ta doka murmushi hakan yasa na sulale na gudu akunnen .ya usman na rada masa kaini gida.Sweet bros wallahi na gaji da azama yaja hannuna muka fice daga taron jama'ar bayan yashigar dani mota yana murmushi yace Aysha kinga lamarin ubangiji ko? dama nasanar dake kicigaba . da addu'a dasannu gaskiya zata bayyana yafada yana jan motar kafin mu isa gida saida yabiyadani ta shopwrite ya saya min kayan amfani bayan yafitone yakalleni Aysha inazan kaikine gidanki kocan gida kike nufi? wani kallo nawatsa masa "gidana kuma ya usman?ainagama auren ahmad ai da din ma don ba yadda zanyine yasa nakoma gidansa amma yanxu bamai tilastamini wallahi ya usman dan murmishi yayi yace kibi komai asannu aysha ta Gum nayi dabakina.Don ko kadan babu maisakani komawa gidan ahmad yaushe? . ai wallahi dolene yasakeni awannan karon kam ya usman yana fakin naga dandazon motocin yan uwana data Abbana data ahmad da alama tuni sundawo fuskata a daure tamau nashiga gidanmu atsaye cirko-cirko da alama suna jiran dawowata babu wanda nakalla nayi hanyar kazamin dakina dakin shirgi inda lokutan baya ummata,tace nan ne makwancina tamkar ba uwata data haifeni ba. . Inazama Abba yashigo yana dubana cike da tausayawa,yace . Ayshatu mezakiyi a wannan dakin dan Allah tashi maza.AGA RAYUWA book 3 part 2 NAGA RAYUWA book 3 part 2 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 13:55 Bani da damar yimasa musu amatsayinsa na mahaifina amma wannan lokacin kam sai na dana naraya azuciyata cikin taushin kalami nace Abba ina zani ina ce nan din shine makwancina dakuka za bamin? Abba yadurkusa gabana ya dago kaina "Ayshatu komai yafaru abaya Inaso kidaukeshi amatsayin kaddara ma kinki Aysha mu mahafankine kituna kafin fara abin wanne ga tane bamu nunamiki agidannanba? . ko wani uba ko uwa kaiga duk wani maisonki ma dole yaji,yataba amma ba tsanabace Ayshatu mun yine don samun nutsuwarki Ayshatu tunda abin nan yafaru ban taba fashin kaiwa Allah kukanaba akan yashirya minke...." Wani kukanne ya kwace min nace "Amma Abba kasani ankuntatamin an wulakanta ni duk akan laipin daba nawaba Abba baku taba tausaya minba akullum kallon tsana nake gani muraran,a idonku babu wanda yaji tausayina sai Ya usman da mamina da ita ma aka dora mata laifin da batajiba bata ganiba yanzu Abba dawane idon za ka kalli mamina? Abba yaruntse idonsa Nasani tabbas al'amarin yagirmama azuciyarsa ahankali ya bude idonsa . "Ba ni da idon dazan kalli fateema Ayshatu tabbas nayi nadamar abubuwan dasuka faru da ina da iko dana goge duk abinda suka faru abaya Ayshatu na zalinceku kiyi hakuri don Allah kiyafemin duk hakan yafarune akan rashin sani Don Allah kiyafemin..." Take naji zuciyata takaraya mahaifina ne yazanyi dashi? tilas na hakura,kasa nayi dakaina badon banyafe ba sai don tsananin tausayin Abbana waiyau shine yake kwantar da murya akaina bayan nidin.Ikonsace yana da dama ya aikata hakan koma fiye dahakan komafiye da hakan koda baya zargina da aikata kowane laifi Balle akan abinda ake kyutata zaton nice na aikatashi muryata na rawa nace Abba kadaina rokon yafiyata nidin wacece? . Abar ikonka cefa? kana da dama ka aikata fiye da hakan akaina..." Abba yadaga kai yace Na sani kedin yar albarkace ubangiji yayi miki albarka ya mike tashi muje dakin ummanki kiyi wanka kicire wadannan tsinannun kayan murmushi nayi namike Har a lokacin suna nan afarfajiyar gidanmu Ahmad sai zabga min murmishi yakeyi niko kodigon fara'a babu atare . dani na tattare fuskata nahade dakin umma nafada natarar da ita a toilet fitowa tayi tana murmushi tace kinshigo Ayshatu shigo kiyi wanka nahada miki ruwan wankan cikin tausasawar murya takemin magana nima tausayi tabani hakan ya sa nace to ummana Nafada ina murmushi Tunda nashiga toilet din nake faman dirzar fatar jikina tamkar Allah ya aiko ni,nacuda yakai sau ashirin gashin kaina kuwa haka nadunga dirzarshi har umma tagaji tafara bugamin kofar sannan nabude nafito umma tace wai! lallai kin dirzu dubi yadda fatarki harja take murmushi nayi nace Badoleba umma sai sati fa ake wanka wallahi nikaina har bashi- bashin kaina nakeji Umma cikin tausayawa tace. . Mungode Allah de dakomai yazama sai labari zama nayi agaban dressing mirror din umma nadau wani Nuetrogena body oil ina shafawa kasan cewar lokacin sanyine banyi wani make-up ba umma takawo wata riga sabuwa light Orange colour mai kyau tabani nasa ni kaina nasan nayi kyau gawata iska tana kada ni tanashiga kofofin jikina da kuwa dauda ta cikasu dankwalin rigar . nadaura akaina sannan na fito falonmu har alokacin mutane ne dan kam agidanmu dukkansu yan Zuwa murna Allah yakiyaye gaba ne dai dai lokacin ya usman yashigo,yanayinsa yanuna yanuna yana cikin matukar farin ciki yazauna yana dubana da dan murmushin gefen kumatu yace Aysha kije inji mijinki wani kallo na zuba masa nace "Ya usman miji kuma?Aini banida miji ahalin yanzu umma tadan dubeni tace banganeba Aysha ya,usman yamike yanafadin "Rabu da ita umarni nabaki kije yana sitroom yana jiranki idanma zaku rabu bai kamata kurabu tahakaba"ban mikeba sai da umma tace Aysha usman nefa yabaki umarni idan da amana kuwa usmanu baicancanci hakan daga wajenki ba dasauri namike jin furucin umma nayi saurin ficewa tamkar bazanyi sallama sai dai nadaure nayi sallamar ya amsa idanunsa. . Acikinnawa fuska ta daure nace masa lafiya malam gani ance kana kira na yadago yana murmushi hade dacewa to zauna mana my beautiful wife ba zama nazo yiba malam inada abubuwan yi acikin gida kuma kada kasake kirana matarka matarka tana gida . "Aikin daki ke haryafi kiran mijinki muhimmanci Aysha? kuma da kikace kada nakiraki matata yaushe nacireki amatsayin matata?nawaro idona ina harararsa ko baka cireni ba kwanan nan zakaji sammaci don wallahi saika sakeni mikewa yayi ya iso gabana yasunkuya yana duban fuskata madam dina babu murmushin nan mai sanya ni nishadi?wai me yafaru ne? yaufa ranar murnace tsaki nayi nace kadameni madam dinka nacan gidanka wannan dai Ayshatu ce aysha mazinaciya,karuwa,maibin yan fashi dafatan kagane yanzu lumshe idonsa yayi yace please ayshata forget the past nayi danasani banyi masa magana ba saima juyawa danayi nashige gida don kam alokacin ba na maraba da ahmad sulaiman . Daddare kamar kowanne lokaci muna zaune ayadda ake zaman cin abinci Abbane yadubi umma "ina tsammanin wani al'amari game da yarinyar nan maikama da aysha ina hasashen ko daga tsatsonmu tafito don tsananin kamar ta yi yawa kinsan kuma masu kamanceceniya da ita adangi suna dayawa kasancewar ance dama da kakarmu suke kama toshi,ne nake hasashen ko ita . ma jininmuce don haka nake dada tsaurara bincike akanshari'ar umma ajiyar zuciya tayi sosai kafin tace ashe bani kadai wannan abu yadama ba tsananin kamar yayi yawa kamar yan biyun da ake kira IDENTICAL TWINS sai dai kuma ai babu wanda yataba rasa yarsa adanginmu Abba yaja gwauron numfashi gaskiya babu wanda yataba rasa yarsa akaf zuri'armu ta potiskum wallahi sosai nakejin yarinyar nan acikin zuciyata tamkar yata kuma natausaya mata da ita da yan uwanta matukar.Tausayawa . koda anbincika ba zuri'ata bace nizan dauketa da sauran yan uwanta da ba asamu danginsuba umma tace gaskiya hakan yakamata kayi tunani mai kyau ubangiji yataya ka riko nikuwa nasan zancensu baishigeniba haushi yaringa bani dalili? sune silar fadawata duk wani bala'i don haka sam banji wani ko digon tausa yinsu ba . KASHEGARI Tun danatashi naji zuciyata takwadaita da son ganin mamina baiwar Allah don haka bayan dana karya naroki umma tabarni naje umma tace . "ayshatu yar gidan mami nina isa nahanaki zuwa gun maminki? kije amma dai karki . dade tunda mutane suna zuwa miki murna har namike tace aysha ki tambayi ahmad kinsan hakkinsane yasan da fitarki gabadaya nabata fuska nace umma wanne irin na tambayeshi kuma? nifa umma wallahi bazan koma gidansaba don haryanzu abinda yayi min banmanta ba kobama hakaba nibana son zama da kishiya inje inawani raba miji da ita baki umma tasaki tana kallona tace tabdi bashakka aysha kanki daya kuwa? . bazaki.Raba miji dawata ba to kinci gidanku idanzaki sauke wannan tunanin banzan tun wurima gwanda kisauke don ba inda zaikaiki sai tashar wahala menene laifin ahmad dazakice bazaki koma gidansa ba? naja kwafa nace umma bakiji irin maganganun daya dunga dankaramin ba duk akan laifi daba nawa ba sannan yayi min kishiya,batare dasani naba mahaifiyarsa babu tsanar dabata nunamin ba sannan yanzu ace nakoma auren sa? . Allah yakiyaye umma tace duk naji aimuma iyayenki duk munmuki laifi meyasa mu kika yafe mana? murmushi nayi nace kudaban shi daban bari nayi sauri natafi ina isa gidansu mami kamar kowanne lokaci hajiyarsu . da kallon banza tatareni ko gaisuwata ma da kyar ta amsa tana wani cin magani bankulata ba illa ma cewa danayi mamina ta na nan? . hajiya tawurgeni da wani kallon banza tace aysha fatima ba uwarki bace sau nawa zangaya miki banason ganin sillan kafafunki agidannan? Nidin ma kallo nawurgamata don tsohuwar tafara kureni,naturobaki nace dadinta ba wajenki nazo ba kuma wallahi babu wanda ya isa yace mmina ba uwata bace,Allah ne ya hada bazamu rabuba ehe! na mike,ina mata,dariya nahaye saman da mamina take ina hawa na juyo ina dubanta tarike haba tana fadin ba shakka nayi nata gwalo nashige dakin mamina.WA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 3 NAGA RAYUWA book 3 part 3 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 13:58 Wannan karon tsaf na sameta azaune tana karanta wata mujalla bataji shigowata ba kasancewar kofar abude take sai da taji nayi tsalle ajikinta afirgice tamike tace Ho ho ho! aysha sam bakya girma kwabe fuska nayi kamar zanyi kuka nace mamina mekuma nayi? tajawoni, jikinta tana cewa babu abinda kikayi sweet daughter me yafito dake madadin kizauna kihuta daga fitowarki jiya shine kika debo kapa kika taho yau?. Hawayene yazubo min daga idona mamina tace subhanallah meya faru ayshatu? Nace mami na wallahi gidan babu dadi tun da babu ke Don Allah mami yaushe zaki dawo gidanmu? . Dif naga mamina tayi da fuskarta tamkar dai ba ita ba ce take annashuwa yanzu tace "aysha ni da gidanku har abada babu sunan dana sakawa gidanku illa BAKIN GIDA anyi min abinda ba ataba yimin ba arayuwa kedin ma dandole nake kulaki saboda kaunarki ajinina take daga Rabbil Izzati idan ban da haka abinda akamin akanki yaci ace tuni nayi watsi da al'amarinki tobazan iyaba konayi kamar nafita harkarki sai naji nakasa jinki nake tamkar kedin jini . nace wane irin cin mutunci ne abbanki da zuri'arku basuyimin ba? hattasu muhammad usmanu ne kawai bai zargeni ba,kuma hargidan nan yazo yana bani hakuri don haka babu abinda zance masa,sai kuwa ummanku macece jaruma da ta dau duniya ba komaiba don tabbas hakika yar uwa ta daukeni har nan gidan tazo tana bani hakuri" shiru nayi sosai nagaza,cewa mami komai don kam nida kaina na sani anci zarafin,mami akan laifin da ba nata ba Nadade sosai,don sai karfe uku natafi na sake baiwa mami hakuri . murmushi kawai tayi ta ce aysha ni da gidanku har abada" Banga,laifin ta ba don kam anyi mata laifin dayaka mata tadau kowane irin hukunci kamar.Yadda nima nasha alwashin bazankoma gidan Ustaz ba don nima yashaka min maganganu masu kama da kamshin mutuwa ina isa gida natarar da galleliyar motar Ustaz akofar gidanmu tsaki naja azuciyata nace sarkin naci Baya cikin motar Aharabar gidan nagansu azaune shi da ya farouk gaba daya basu isheni kallo ba donsu kansu yayyen nawa bawani kallon arziki nake,musu ba Adage nake kallonsu . Dalili?lokacin da abin yafaru babu wani wanda yabawa iyayena hakuri acikinsu sai ya usman don haka gaisuwa ma dakyar nake gaishesu akan tilas Har nawuce ya farouk yataso dasauri ya biyo bayana Ahankali yakemin magana Aysha kina kallon mijinki kika shareshi tundazu fa wajenki yazo yana jiranki wani kallo na watsa masa hakan yasa baici gaba da magana ba Nace yaje yanemi matarsa amma bani ba don ni nawuce tunaninsa daga, haka da azama najuya zanshiga gida ji nayi an riko hannuna ko ba afadaba nasan Ahmad ne don kuwa ga mayataccen kamshin turarensa nan ya cika hancina da azama nafuzge hannuna fuskata ahade nawurga masa wani wulakantaccen kallo nace for the last time malam kada kasake yunkurin hakan..." mekike nufi? kina matsayin matata kiyimin warnin akan jikinki? kada ki manta fa mallakina ne yafada yana sake,wurgamin kallo tsaki nayi nace kaidin wai wane irin sarkin nacine.? Sau nawa zangaya maka kabar kiran aysha amtsayin matarka How I wish anaganin zuciya nabude maka kaga matsananciyar tsanar da nayi maka" . Baki asake yadubeni da alama yana mamakin kalamaina ne murmushi yasaka. . Yace aysha kenan Ni kuma da ina da hali danabude miki tawa sirrin zuciyar kin ga soyayyarki zalla da tacika ta muryarsa atausashe yasake cewa Allah ne yajarrabeni dasonki da ina da iko da na rabu dake tunda hakan shi ne burinki Ahankali yaja dabaya yafice ko kadan bai bani tausayiba don ni din ma baitausa yamin ba alokacin da nake neman ya a gajeni alokacin yabude min faifan rashin kirki da wulakanci Naja tsaki na shige gida ina guna guni . AN KOMA KOTU . ranar da za akoma kotu da wuri muka tafi da sam bazanje ba sai dai nashirya naje saboda inaso ayi komai akan idona mune asahun farko akotun kotun ta dinke da jama'a kowa nason jin karashen shari'ar ne yakawo shi ina hango Ahmad yana ta sakar min murmushi ni kuwa dauke kaina nayi tamkar banganshi ba wanda rabon da naganshi tun ranar daya ritsani aharabar gidanmu saboda koyazo bana fita ko umma tace nafita rokon ta nake ince tabari na huta Abba ma kuwa bai tilas taminba tsawon mintuna . Ashirin muka dauka akotun kafin alkali Abbana yashigo yana, zuwa kotu ta samu bakuncin shiru da kanshi yayi umarni afito masa da,su shany wadanda aka tsare awani daki daya bayan daya suka dunga fitowa Shany ce atsakiya gaba dayansu cikin.Wasu dogayen hijabai dasuka saukar musu har kasa ammafa fuskarsu ta nuna bazaman dadi akayi akotunba Abbana yakalle su daya bayan daya . sannan yace da jami'an tsaro sufito da da mama Atine wacce akayi nasarar kamo ta kwanaki biyu da suka wuce kanta akasa tafito amma daga ganin ta ka ga cikakkiyar yar duniya mutane kuwa suka zuba mata ido ciki kuwa hardani da nake mamakin karfin hali irin nata . nakuma yi tur da ita harcikin zuciyata Allah dai yashirya musulmi Abbana yace kece Atine? ba ta re dabata lokaci ko tsoro ba ta amsa da nice Atine kinsan wadannan yaran dasuke gabanki? Nan ma cikin comfidence ta amsa Nasan su." Abbana yace mene ne hadinki dasu? dan tabe baki tayi sannan tace akarkashin kulawata suke karkashin kulawarki kamar ya? kina nufin ya'yanki ko ya'yan yan uwanki . kike riko? Anan kam tsit tayi takuma sunkuyar dakanta azuciyata nace munafuka Abbana yadan girgiza kai yace malama atine muna sauraronki koko zargin,da ake miki gaskiyane kamar yadda yaran suka ce babu wata alaka atsakanin ku dukansu yan tsintuwane? ta daga kai alamar eh yace kina nufin dukkansu tsintarsu kikayi? to a ina? kuma da yaushe? awanne gari kikatsinci har mutum 35 musamman waccen yarinyar danake hasashen jini nace saboda matsananciyar kamar dasuke yi da diyata,Aysha dasauri takai dubanta,kaina ta sake mayar da dubanta akan yar rikonta Shany atake naga tasaka,hannu tana yarfe.Gumi alamar rashin gaskiya kuru-kuru yabayyana afuskarta . Abbana yadanyi rubutu sannan yadago yasake ce mata malama atine kinyi shiru inason sanin labarin wannan yarinyar shany da yadda kika sameta gaskiyarki ce hanya mafi sauki dazata kubutar dake karya kuwa itace zata tsunduma ki akogin nadama matukar na,gano gaskiyar lamari Ahankali ta dago kanta sanin cewa babu mai kubutar da ita hakan yasata shiga rattabo bayani "kamar yadda . ka fada dagaskene wadannan yara tsintarsu nayi wasu kuma aasibiti nasamesu shekaru da dama dasuka wuce nima karkashin wata mata nake da sana'arta kenan . FATAUCIN YARA MATA . kai har da mazan ma idan tasamu faraga "asibitoci takebi don samun yara marasa galihu kodai shegu kokuma wadanda iyayensu sukayi accident suka mutu akarasa danginsu kokuma idan anhaifi yan biyu tayi cinikin daya da nurses ko likitoci subata daya batare da mai haihuwar ta saniba Nikaina a irin hakan tasameni ma'ana ni shegiyace duk abinda takashe mana muna yara to idan mungirma fanshewa take akanmu kodai ta mayarmu karuwai kodai tayi futaucin wasu zuwa wata kasar ta yadda za adunga bata,kudi duk karshen wata wadanda tamayar karuwai kuwa da zarar sungirma andaina yayinsu ba ta samun komai atare dasu to sai ta sallamesu sukama gabansu don takan fada ba a aikin banxa akano . A irin haka nima nafito Ne acikin wadanda aka sallama nima nakama gidan kaina saina tsunduma kaina cikin harkar da takeyi na shahara sosai harnaso nafita nima asibiti nake . zagayawa aduk cikin kasashen Nigeria wannan yarinya da kake magana ina,matukar alfahari da ita aduk cikin yarana saboda tana da kwazo da basira wayo da hikima shiyasa bana manta tarihinta . A ASIBITI NA SAYO SHANY.... . Gaba daya naga abba yadago yana sake kallon ta muryarsa na rawa yace mata wa...wanne...wane asibitin? shiru tayi da alama,tatafi tunani sai can tazaro wayarta,ta kunne tashiga bincike kotun kuwa zuwa lokacin tuni tadau kace nace har saida Alkali yatsawatar sannan Atine ta dago kanta tace Na sa mota a . NASHE SPECIALIST HOSPITAL . aranar lahadi 17 gawatan july shekarar1995..." gaba daya naga Abbana yazaro ido umma kuwa arazane tamike tana nuna Atine da yatsa muryarta na rawa,kincu.Cemu... . tabbas wannan yatace jininace! ranar dana haifi ayshata kenan kuma a asibitin nashe..." novels / NAGA RAYUWA book 3 part 4 NAGA RAYUWA book 3 part 4 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:04 Gaba daya hankalin jama'a yakoma kan umma Abba ne yadaka tar da umma tahanyar yimata umarni tazauna umma tazauna tanajan "Innalillahi" Ni kaina bugun zuciyata alokacin yakaru Abba yace Atine ina jinki Awajen wa kika siyeta? likita? ko nurse? shiru tayi har saida yadaka mata tsawa,sannan tace awajen likita ne bisa jagorancin wata mata "wata mata wa? yasunanta? Abba yafada cikin matsanan cin mamaki Girgiza kai tayi tace gaskiya na manta saidai na bincika shiru . Abba yayi yashiga rubuce-rubuce sai can ya dago yace ina tunanin.Tilas sai annemo matar nan sannan kotu za ta san hukuncin dazata yanke matar ce da likitan zasu tabbatar mana da shany diyar wace ce don haka asakamakon haka kotu ta dage zama zuwa nan da wata guda za atsare Atine har zuwa lokacin kuma kotu ta ba da belin yarancan tunda ga babbar me lefi ankama sai dai zasu biya minista makudan kudaden da suka daukar masa idan yana bukatar hakan koda muka isa gida jikina asanyaye nake jan kafata ina lura da umma ita ma nata jikin asan yaye yake matuka . har raina ajagule yake gaba daya fatana daya kada Allah yasa zargin danake yatabbata bakomai kuwa nake tunani ba sai kada Allah yasa MAMINA tana da hannu dumu-dumu acikin wannan shari'a ba idan hakan ta faru ya makomar mamina zata kasance? wasu hawaye naji sun sulmiyo min. . haka na kwana da zancen azuciyata da safe ma ko karyawa, banyiba nasamu umma dazancen murmushi tayi tace ni ma ina tsoron faruwar hakan sai,dai kunyi daya da abbanki shima zargi da hasashen dasuka shiga zuciyarsa kenan sai dai zankwabeki kamar yadda na kwabe shi kada ku daga zan cen nan wani yaji don ba lallaine tunanin yaxama gaskiya ba amma ya,rantse idan dasaka hannun ta bazai mata,sassauci ba" Ahankali naja numfashi hade da furta kai jama'a duniya abar tsoro ce . wallahi sam hankalina yagaza kwanciya saboda tsoron kada akama mamina da wannan gundumemen laifin hakan yasa nayi saurin shiga wanka ina fitowa, ko mai bansha fa ba nazira doguwar riga ta da hijab Adaki nataradda umma karya naimata akancewa zanje gida nadebo wasu kayana bataki ba sai dai tacewai natambayi mijina kamar nafasa zuwa sai dai kawai,natura masa, text nasanar dashi zanfita, banga amsa ba amma haka nashir gama umma karya nace yace sai nadawo . Daga nan nasaka kai ko direba bannemaba don ba na so asirina yatonu,hakan yasa natare adaidaitasahu . . sai Nasarawa gidandsu mamina da sauri nafada gate,din gidan bayan na sallami mai adaidaita sahun A falo na sami hajiya da mami wannan karon hajiya da walwala fal afuskarta ta amsamin har mamaki abin yabani mamina kuwa tashi tayi ta rungumo ni tana fadar oyoyo ayshata . nidai murmushin yake nake saki bayan munshiga daki mamina tadubeni tana murmushi ayshata ya aka kare da zaman kotu? wannan karon tun da naga kintsira nace to mekuma zankoma nayi? dan murmushi najefeta.Dashi "Aikuwa da kinsha kallo don wannan yarinyar dai ana kyautata zaton nida ita twins ne...." da sauri mami tazaro ido tace Inji uban wa kuma? Nagyara zama cike da mamakin irin razanar da mamina tayi nace Inji matar data rainesu ta shaida haka Don kuwa rana daya da lokaci da asibitin da aka haife mu duk dayane matar ta tabbatar siyenta tayi a asibitin bisa jagorancin wata mata" Sake firgita tayi tace What? kina nufin ta fadi sunan matar? . girgiza kai nayi nace kodaya sai azama na gaba Abba yace lallai anemo wannan matar da likitan don sune za su . ba da tabbacin komai mamina zagaye ta shiga yi a dakin idan ba idona ba ne yagaya min sai naga kamar gumi take sai can tace Allah ya kyauta amma hakan da mamaki matukar gaske Ban dade sosai ba nabar gidansu mami yanzu kamzuciyata ta aminta,da zargina don haka na ratse wani lungu na sha kuka na Innalillahi kawai naketa ja harna isa gida sai danaje kofar gidan sannan na tuna karyar dana shirgawa ummana nacewa, kaya zandebo don haka dasauri najuya nanufi gidansu Asma'u Allah yataima keni tana nan Nadebo kayanta sannan na nafo hanyar gida Adai-dai sabon gidansa nahango shi da wannan kodaddiyar matar tasa da alama fita zasuyi haka, kawai sai naji wani iri araina bansaniba ko kishi ne oho. . Na sa kai zan wuce ba tare da na kulasuba amma, namakaro donjin Uztas nayi yana fadin yan mata ina kikaje? Najuyo namasa wani irin kallo mai fassara kala- kala gani nayi yasake wani fari yayi kyau fiye da lokutan baya Ban saniba ko don yanzu hankalinsa ya kwantane take naji wani kululu ya cake min zuciya bansaniba ko kishine . kishin da ake fada wucewa nayi ba ta re danace masa ko "A" ba Babu abinda,yafi bani haushi saiganin danayi Uztas kobi takaina bai sake yiba yakoma gurin matarshi hakan yasa naji wasu zafafan hawaye sun zubo min tabbas . KISHI MASIFA NE . ni kaina kuma na san ina da matsanan cin kishi don haka na sake damkewa araina na rabu da auren Uztas har abada koda soyayyarsa zata zama ajalina Azaune nasa mu ummana afalo ita da shany mamakine yayi matukar ka ma ni danaga shany da yan'uwanta kamar umma ta sani tashiga rattabo min bayani Ga shany nan da yan uwanta Abbankine ya kawosu suzauna kafin agama shari'a asan yadda za ayi dasu murmushi kawai nasakar musu nashige dakina saboda sam bana jin dadi aduk sanda natuno mamina nakuma tuno Uztas da shegiyar matarsa sai naji tamkar na sa kuka sai yamma sannan na fito daga, daki bayan da sakon Abbana ya sameni akan yanason ganina Da sallama nashiga falon abbana ya amsa cikin walwala da sakin fuska na durkusa agefe "Kinga yan uwa ankawo miki ko? Don Allah kidage wajen koyar dasu . addini don nalura babu batun sanin addini a al'amarinsu sonake koda angama shari'ar na roki alfarma gwamnati tabar min rikonsu koda yakasance shany ba 'ya ta bace balle ina ji ajikina Aysha su zama tamkar yan'uwanki kada kiyi la'akari da laifin dasuka aikata a baya duk ba laifinsu bane idan da ma mai laifin bai wuce uwar rikon suba,Nadaga kaina nace "Insha Allah abba zan kokarta yauwa aysha nagode na sanke diyar albarkace wai yakukayi da mijin ki batun komawarki? shiru nayi nakuma sunkuyar da kai na ce Abba bazan.Koma ba Abba yayi saurin zaro ido yace meyasa ayshata? Nadan sake sunkuyar dakaina kafin nace Abba lokacin da abin yafaru ba irin kyara da hanta rar da baiminba duk ba ma wannan ba Abba gaskiya indai zaku kyaleni nafi kaunar na zurfafa ilimina shiru Abba yayi sai can yace shikenan.Aysha bazanso takura miki akaro na biyu ba kije Allah yazaba abinda yafi alkhairi.Tun daga ranar naja su shany ajikina nake koya musu al'amuran addini don nalura babu abinda suka sani idan dai ba boko ba don kam sosai na . lura sudin kwarine aharkar boko don shany idan tana turanci yadda kasan baturiyar ingila tsabar kwarewa har mamakin tanake yi idan naji tacanja harshen ta Zuwa turanci wanda yake da dadin sauraro mun shaku sosai kuma Abbana yawadata su da suturu iri-Iri nima kuma na basu nawa idan muka zauna waje daya da shany bazaka taba bambance muba sai dai ita tana da rawar kai kuma ni ina da tawadar Allah agefen kuma tuna ita kuwa akasan habarta take dashi Idan suna ba ni labarin irin damfarar da Atine ta sa su ina tausaya musu matuka da gaske Atine ta cucesu sai dai abu daya ne yan group dinsu ba su yarda dashiba shine keta musu haddi har yanzu suna nan a matsayinsu na yan mata cikakku ta wannan bangaren kam na sa ra musu don bakaramar dabara sukayi ba don budurcin mace shine abin tinkahonta kuma babban jarinta Bayan ta gama bani labarin nace Amma an taba kawo min wani hotonki da anyi tsammanin nice (na ba ta labarin) nace kusan dai nace a tsirara kike ahoton.Murmushi suka saka gaba dayansu sannan shany tace ina . yaudarar maza da jikina saboda nasan ina da diri mai kyau sai ka sakankance barci ya dauke ka sai mu yashe ka tas mutafi haka nan sukayi tabani labarinsu na Al'ajabi nayi na dariya kuwa na saki murmushi . *** *** **** . KOTU . Ranar da aka koma kotu wannan karon cikar haryafi na kullum don mutane abin ba a magana ba dauki lokaci sosai ba Alkali Abbana yazo aka fara wata shari'ar kafin azo kantasu shany dasuke tsaye a layi reras cikin shigar mutunci da ta dawo musu da martabarsu da mutuncinsu na ya'yamata bayan dogayen jawabai da Abbana ya bayar dangane da shari'ar da aka guda nar sannan yadubi Atine yace Dafatan atine kin gamsu da abinda kika fada? Atine ta daga kai kamar kadan garuwa wannan karon jikinta yayi sanyi sosai da alama ta hango ba ta da mafita kokadan Abbana yadanyi rubuce rubuce sannan yadago yadubi dandazon jama'ar da suke kotun yace, "A sakamakon bincike da aka gudanar kotu tabinciko likitan da yayi cinikin yarinyar da ake kira SHANY sannan har ila yau kotu ta binciko matar datayi.novels / NAGA RAYUWA book 3 part 5 NAGA RAYUWA book 3 part 5 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:05 jagorancin cinikin..." Sosai hantar cikina ta kada don babu makawa nasan mamina ce don ban ganta awajen ba babu mamaki tana can saye acikin wani wajen Abbana yakalli dansanda [police] yace Ashigo da likita kafin azo da matar ko minti biyu ba ayiba police din yashigo da likitan wani shirgegen kato baki-kirin da alama ba bahaushe bane yazo kuwa yahau kan step din fuskarsa tacika da furfura alamar yafara tsufa ya tsaya shirim dashi Azuciyata nace cikakken mugu Abbana yadago yana kallonsa nasan yana mamakin tsananin muguntarsa ne naraba ya da,uwa tana cikin jinin haihuwa Abbana yayi gyaran murya kafin yace kaine Dr.Emmanuel? . yadaga kai alamar eh Amsa nakeso naji da baki ko baka jin.Hausa? inaji sosai ma muryarsa tangararan tamkar bahaushen asali "menene dalilinka na Siyarwa da waccan matar jaririya tuntana cikin jinin haihuwa? sannan kuma muna son mu san yarinyar yar waye? . zare ido yafarayi da alama baisan dalilin da aka kaso.Shiba kenan ya kuma dubi Atine sukayi kallon-kallo Abbana kuwa ya daka masa tsawa hade da fadin . kai muke sauraro! ina da record din komai agurina don haka idan kana shirin yin karya ne kashirya ta dakyau don kuwa ina da labarin komai ina dai so ne kawai ka gaskata dakanka Emanuel yayarfe gumi sannan yadago a sanyaye "yace tabbas da na san wannan ranar za ta zo daban aikata,abinda na aikata ba kaicona ni Ema ina cikin tarin dana sani dana biyewa son zuciya yau gashi yacillani cikin kogin nadama . " "sunana Dr.Emmanuel ina aiki ne a nashe specialist hospital tun tasowata na kasance mutumne ni mai matukar son kudi hakan yasa sam banida wani tunani sai na hanyar da kudi zasu shigomin "Ba na manta wata rana data kasance ranar lahadi ina zaune agidana dayake Ring Road,nayi baki ba wasu baki bane sai wannan matar yanuna Atine da ita da wata mata da ake cewa . HAJIYA FATEEMAH" . Shikenan tatabbata . MAMINA CE! . gaba na yasake faduwa jin gashi sunanta ma ya bayyana Amma kuma ai fateema da yawa da sauri nadaga nakalleshi jin yaci gaba da labarin "Nayi matukar murna da zuwansu don kuwa fateema akwai alheri ni likitan gidansu babansu ne ALHAJI MUHAMMAD" Dasauri nadafe kirjina donkuwa shikenan tafaru takare wallahi maminace Allah sarki MAMINA why.? . meyasa kika aikata hakan duk tarin alherinki agareni? . Likita yaci gaba "Naba su lemo da ruwa sannan na zauna ina fuskantar su don son sanin mene ne yake tafe dasu bayan sun dan sha drinks din sannan ita fateema ta dubeni tace Dr.ema shin kasan dalilin Ziyarar damuka kawo maka yau? na girgiza kai Akwai wata mata datake zuwa asbitinku awo Abinda nakeso dakai da zarar tahaihu kazare dan ko yar ka saka matacce idan ansamu idan kuma ba a samu ba kasan dai dabarar dakayi kasace abinda tahaifa ba ta re da,kowa ya sani ba zaka yi wannan aiki akan naira miliyan biyu Da sauri na zaro ido jin yawan makudan kudi bakina a sake na sake maimaita sunan batare da ba ta lokaci ba na amince da bukatarsu Nakuma tambayi sunan matar batare da bata lokaciba suka sanar da . MATAR IMAM KHALIL . A take nagane ta don ni nake mata awo da kaina nadaukar musu alkawarin ANYI ANGAMA" Sam ji nayi na daina gani saboda wannan.rikitaccen al'amari daya dumfaroni don kuwa yanzu yawuce zargi tabbas,mamina ce da,hannu dumu-dumu awannan KUNGURMIN LAIFIN umma nahango tamike tsaye tana zare ido kai duk . yayyena ma mike war sukayi yayin da naga Abbana yana ta sakin murmushi nayi mamaki matuka lallai ko ya ya kuke da kishiya ka guji sharrinta Na ayyana araina hawayen tausayin iyayena ya sulmiyo min daga ida nuna Abbana cikin matukar hade rai yadaka wa Emmanuel tsawa ina jinka! . Emmanuel kuwa yaci gaba da ba da labarin mai kamar almara "Ba ta dau lokaci tana zuwa awo ba rana daya aka kawota tana nakuda wanda kafin lokacin idanuwana suna kan masu labor.Na sha alwashin ko kashe wani jaririn sai naje nasaka mata na dauki nata kuma naje dakin jarirai wanda iyayensu suke guduwa suna barinsu ko dai na saci na wani ko ma ya nidai burina kawai kudi da murna ta na karbeta kasan cewarta matar manya yasa na kaita special room nakuma hana kowa shiga Ta sha matukar wahala harta fita hayyacinta kusan awa biyu daga bisani tahaifi yayanta yan biyu MATA ZALLA Tausayi ta bani ganin irin wahalar da tasha hakan yasa nabar mata 'ya daya ina murna ganin.Allah ya taimakeni na gudu da daya ba tare da sanin ta ba don lokacin hankalinta . Baya jikinta Bayan wani lokaci sukazo suka amshe ta, sai dai nasanar dasu gaskiya cewa yan biyu tahaifa sai dai ina kokarin dauke dayar wani likita yashigo haka yasa tilas da daya natsira wannan shine iya gaskiyar abinda nasani" Gaba daya kotun aka dauki kabbara bayan sauraren wannan abin Al'ajabi Bayan rubuce- rubuce da Abbana yayi ya umarci wani police yashigo da fateema zuciyata taci gaba da bugu tamkar zata faso kirjina ta fito nakumayi saurin sunkuyar da kaina don sam ba naso nayi ido biyu da MAMINA acikin wannan yanayin cikin wani zumbulelen hijabi MAMINA take da kuma nikab afuskarta takuma rufe kirif dashi Alama ce ta cewa ba ta muradin aga fuskarta Abbana yadan dube ta ya girgiza kai ahankali bakinsa yayi furucin . FATEEMA MUHAMMAD wanda muryarsa bata bayyanaba sannan yaja ajiyar zuciya yace Fateema zanso kiyiwa kotu cikakken bayani da dalilin daya sa kikayi silar da aka sace diyar mutane tun tana cikin jinin haihuwa? "Bakomai yaja ba sai . RAMUWAR GAYYA . Tafada da dakakkiyar muryarta . Abbana yajinjina kai Ramuwar gayya kamar ya ya? inaso kiyi wa kotu karin gamsasshen bayani hannu tasa tayaye nikab din da yake fuskarta Atake na zabura na mike wa na gani? Hamdala nayi ga sarki Allah alokacin danayi arba da ita . BA MAMINA BACE . madadin inga fuskar mamina kamar yadda nake zato a'a wata mata na gani fara da alama fulanin dajice Don naga tsagun fulanin atare da ita sai dai daga ganin ta ka ga cikakkiyar 'yar duniya ina kallon yadda umma itama tahau zare ido tana nuna ta da alama ta shaidata don naji ta ambaci sunanta da fateema fulani Abbana yayi rubutun da zaiyi sannan yadago yadubeta fateema munaso muji dalilinki nacewa ramuwar gayya kikayi kuma waye ya miki laifi da har kike ikirarin kinyi ramuwar gayya ta hanyar illata rayuwar yarinyar da bata san komaiba? . Azafafe tadubeshi "I dan kai kamanta abubuwan dasuka faru abaya Imamu ni bazan manta ba komai yana cikin kwanyata Ba irin rayuwar da ban fa da ba duka adalilinka da furucin 'yan kauyenku Imamu wane irin wulakanci ne banganiba acikin gidanku . duk adalilin nace inason ka zan aureka..." Tafada tana.Huci fuskarta ahade tasake cewa ko yanzu kasuwa tatashi wallahi dan koli yaci riba Abbana yace "Duk munji fada min dalilinki nasace yarinyar da kika sa akayi kowa yaji" Taja ajiyar zuciya sannan ta dubeshi "ya zama dole nafada kodon duniya tashaida sunanka MAYAUDARI danginka kuma AZZALUMAI . "sunana Fateema muhammad nida iyayena mazauna.Potiskum ne amma cikin kabilar IBRA munta so matsayin unguwa daya ni da su Imamu duk da ba wata alaka da take tsakaninmu saboda kasancewar mahaifina akabilar Ibra mahaifiyata kuma yar jihar yobe ce itama sai da aka kai ruwa rana kafin iyayenta su amince ta,auri babana duk a dalilin kasancewar sa ba bahaushe ba mahaifina mutum ne mai nagartattun halaye kowa yashaida hakan Bacin rai ne yasa yabaro can kabilarsu yadawo potiskum da zama ya ce mamana acan garinsu bashida kowa tuni iyayensa suka mutu kuma bashi da yan uwa sai yan'uba Akwana atashi cutar ajali ta riski mahaifina bai wani dade yana ciwo ba yamutu yabarmu da . tarin tashin hankali saboda duk kauyen ba asonmu Ana haka kwatsam mahaifiyar mu ita ma tafara cutar ajali Zuwa lokaci kalilan tace ga garinku nan wannan mutuwa ta daga hankalinmu nida yayana muftahu da, kanwata samira shi kenan daga mutuwar mahaifiyar mu sai rayuwa ta sake juya mana baya ba wanda yake ta,tamu agarin nan wani lokacin abincin dazamu ci ma gagarar mu yakeyi ganin zaman hakan ba zai yiwu ba ya sa ranar nayanke shawarar shiga gida-gida neman aikatau Alokacin shekaruna sha biyar Duk gidan da naje ban samu ba har na sare zankoma gida sai natuna da gidan maikudin garin wato gidansu Imamu Atake awajen Zuciyata tayarje min naje gidansu imamun Nakuwa isa bakin gate din gidan har mai gadin ya fa ra yimin hargagin bazan shigaba sai ga mahaifin Imamu nan dattijon arziki shi ya leko yake tambayar maigadin yadda akayi maigadi yace Rabu da ita Alhaji irin makarya tan mutanen ne masu basaja wai aiki tazo nema kona wanke-wanke Alhaji yadubeni yace baiwar Allah daga ina kike? Nayi kasa dakaina nashiga rattabo.A RAYUWA book 3 part 6 NAGA RAYUWA book 3 part 6 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:07 masa daga inda nake Alhaji yagirgiza kai yace kice yar gidan muhammadu mai hula ko? Na daga kai Alhajin yace Allah yajikan muhammadu mai hula shigo ciki muje wajen hajiyar Tun daga bakin tsakar gidan nafara jin hargagin fadanta da alama da ya'yanta take nan take naji zuciyata ta harba nayi fatan Allah yasa tayi maraba dani Alhajin da sallama yashiga hakan baisa tarage zazzaga kwandon masifarta ba tabi ni da kallo kafin tace lafiya Alhaji wannan bakuwar wace? sannan yakai duban sa kan Imamu yace Babana me kayi ne take zazzage maka fada? jinayi hajiyar tace min ke daga ina ban waye fuskarki ba Nayi kasa dakaina ina wasa da zoben hannuna Alhaji yace Aiki take nema na ga kuma kina da bukatar yar aikin tun da waccan tatafi shiyasa nace tashigo tsaki tayi takuma zabga min harara tace yo don ina bukatar yan aiki nace maka yan mata nake nema? . Alhaji dasauri yace hajiya kidai duba marainiya ce diyar muhammadu mai hula haba ko danaji kace min diyar tubabben mutumin nan ce shiya sa naga fuskar tayi yanayi data kabilu. . To na amince amma da sharadi idan na samu dattijuwa zata dire min aikina don ni ba na son kwashe-kwashe cikin kwashe- kwashen ace har kabilu kawai kajanyo min jangwan-gwan Nidai farin ciki yamamaye ni danaji ta yarda ta amince Bawani aiki bane shara ce filin tsakar gidan sai wanke-Wanke kasancewar matar gidan mace mai kazar- kazar ba komai take zama jagwab ayi mataba Da kadan-kadan shakuwa ta fara shiga tsakanina da imamu wasa-wasa sai nafara jin matukar son imamu azuciyata wanda har idan ban ganshi ba banajin dadi Har wata rana takai natambaye shi da kaina Imamu inajin soyayyarka araina kaifa? . murmushi ya saki hade da dage gira daya daga cikin abinda yake sake burgeni dashi yace fateemah ina matukar sonki sai dai kafin haduwata dake ina soyayya da wata yar'uwata Amma hakan bazai hana ni aurenki ba kidaici gaba da addu'a jikina ne yayi sanyi don nasan mawuyacin abune hakan yatabbata tunda dai ya sanar da ni yar'uwarsa ce shikenan na kaddara azuciyata ba zan auri imamu ba Tafi- Tafi soyayyar Imamu tana sake . bunkasa azuciyata duk da ina kokarin naga na yakice hakan amma abu ya faskara kwatsam wata rana ina cikin aikin yamma sai naji hajiya tana batun sa ranar Imamu tana aika yara gida-gida akansu je sufada Nashiga wani lungu agidan don kuwa ji nayi hawaye,na surnano min kwatsam sai ga imamu ya zagayo yakama hannuna muka shiga dakinsa. Rarrashin duniya da ban ba ki babu wanda bai,yimin ba amma na gagara yin shiru har sai da yayimin alkawarin aure na bayan bikinsa sannan hankalina ya kwanta Haka inaji ina gani akashiga gudanar da bikin Imamu duk da zuciyata na tukukin haka na hakura ina kuma taya imamu murna Bayan bikin Imamu da amaryarsa sai naji labarin wai a kano zasu tare, hankalina ya tashi, amma Imamu yasake jaddada min alkawarin aure kafin tafiyarsu hakan yakwantar min da hankali sai dai ko da suka tafi Imamu bai sake waiwayata ba ko ya zo kuma sai ya yi tahade min yana wani cin magani harnagaji. Wani zuwa da yayi nake tambayarsa ko ya janye kudurinsa na aurena bawani ja'inja ya shaida.Min eh ya fasa . Raina yabaci amma sai nasake tambayarsa menene dalili? amsar da ya ba ni ta gigitani domin cewa yayi fatima gaskiya ina matukar son matata kuma tana jajircewa wajen yi min biyayya ba na jin zan iya yimata kishiya domin yin hakan tamkar kawo wata barazanane ga rayuwar aurenmu zan miki addu'a Allah ya zaba,miki abinda yafi alheri...." Wani kallo nabishi dashi hawayen bakin ciki na zubowa akwarmin idona ahankali na lumshe ido nace Imamu ka cuce ni sai dai ina maka albishir da komu dade ko mu jima sai na dau fansa" Wannan dalilin shiyajanyo min koma wa rayuwar banza Na kuma kaddara, a Zuciyata sai na yima ramuwar gayya wanda ake cewa ta fi ta gayya zafi . kwatsam sai muka wayi gari anshiga har anyi wa kanwata datake bina fyade, lokacin yayanmu yatafi Lagos. Nayi kukan bakin ciki kamar raina zai fita nakuma ja bakina na tsuke ban gaya wa kowa ba saboda ba na son zancen ya bazu a garin ina gudun kada sunan mu yaba ci Al'amarin Allah bayan watanni sai ciki yabayyana na sa ta agaba tagayamin ko ta gane fuskarsa take . Tasanar dani kanin Imamu ne don yasha yaudararta da kudade tana kin bashi hadin kai shine ranar dayaga ba kowa agidan yashigo yakulle ta yayi mata fyade wani ashar nazunduma sannan namike nazira hijabina ina fadin wallahi ba a isa ba sai naje hargidansu Imamu tunda dan kanwar babarsa ne da take riko ita zanje na sanarwa idan taki ji hukuma tabi mana hakkinmu Akofar gida nahadu da baban Imamu banbi takansa ba ina huci ina komai nashige gidan don kuwa tabbas zuciyata a sama take na bankada labulen dakin ko sallama banyi ba Hajiyar ta dago tana kallona ke lafiya? . wane irin iskancine zaki shigomin ko sallama babu? Na shaka da yawa kafin nace Ba alheri ya kawo ni ba nazo nasanar dake ta'asar da danki ya tafka" Ahanzarce ta kalleni tace Hmmm ba shakka yanzu na gano bakin zaren ai wato saboda kin makale yasoki yaki shine Zaki yimasa sharri? Ina lura fa da take- takenki duk binbinin da kika dunga yimasa ido nazuba miki na ga iya gudun ruwanki.Don kuwani banga me Imamu zaiyi da diyar da ba asan asalin ubanta ba..." . Da sauri na daga mata hannu"saurara! Ba zancen Imamu yakawo niba zancen Hamidan ya kawo ni yaje yadibga ma kanwata ciki tahanyar fyade kuma wallahi ba zan yarda ba sai nakai shi ga hukuma" "Kikaishi ga hukumo ba hukuma ba saboda tsabar sharri yaro dan shekara sha bakwai zai iya yin ciki? Kwaje can inda kuka samu cikinku kuji dashi amma ba za alikawa dan marayan Allah ba yo dama har ku din wasu nagari ne ai barewa ba ta gudu danta yayi rarrafe wayasan asalin ubanku muhammadu mai hula mutumin da muka ganshi zikau agarin nan da girmansa har yakarar da nagartarsa... . " Lafiya nake jin hayaniya.?Baban Imamu yafada yana shigowa gidan Hajiya taja tsaki Duk bakai ka janyo mana wannan shirgin ba ga ta nan ta zo da sharri wai hamidan yayiwa kanwarta ciki kai kaji wata tatsuniya yaro dan shekara sha bakwai..." Alhaji murmushi yayi yace kada ki ja da ikon Allah yaran yanzu ba irin shaidancin da ba su sani ba ke dagaske kike ko wasa? Alhaji yatambayeni rantsuwa nayi akan cewa dagaske nake yagirgiza kai "To kinji hajiya . Sai asan abinyi Nidai data kai batun nan gahukuma gwara ayi hakuri adaura musu aure da zarar ta haihu Hajiya ta zabura "Au me? aure da wa? Allah ya kiyaye jinina yahadu da jinin shege kuma karya take kaf zuri'armu ba karuwa ba dan'iska Don haka ni ban amince da cewa hamidan yayi wa kanwarta ciki ba sudai da suka gado iskancin sa sunsan inda tayo ciki amma mu kam kaf zuri'armu 'yan mutuncine Duk yadda Alhaji yabulla sai matar nan ta bulla sam ta ki yarda hamidan ne yayi wannan ta'asar Haka inaji ina gani naja sangalalin kafata cikin mutuwar jiki nakoma gida ina kuka Abu yabazu akauye nan da nan aka shiga yimana gori ba shiri na hade kayanmu muka yi kaura kano inda na kama mana hayar daki awani gidan karuwai ta silar wannan abubuwa dasuka,faru ni da kanwata muka tsunduma kanmu acikin karuwanci kafin wani mutum Alhaji muhammadu ya mayar damu gidansa,mutum ne mai kudin gaske sai dai ba ya,haihuwa . matarsa mutuniyar arziki yar garin Bendel tayi mana rikon mutunci Daga,lokacin nafara binciken yadda zanga Imamu . don daukar fansa kwatsam ranar an Kai uwar dakinmu asibiti na hango shi shi da matarsa bai ganeni ba kasan cewar hijab nasaka da nikab nikuwa nan nashiga bincike amma har na gano gurin family doctor yake kai matarsa awo alokacin tsawon shekara goma bansan ya shi a idona ba.Kawai zuciyata ta rayamin DAUKAR FANSA wannan shine dalili" Gaba daya kotun tadauki hayaniya Abbana yadanyi murmushi don ya fuskanci daukacin jama,a shi suke jin haushi . "kina ganin yanzu ramuwar da kikayi akaina batayi.Yawa ba? 'yafa kika saka aka sace min sukutum sannan kika ba da ita ga magajiyar karuwai ta koya mata tarbiyya irin tata duk adalilin naki na aureki" Ya ja ajiyar zuciya hakika kincuceni iya cuta fateema Ni bazance miki komai ba sai dai Allah ya shiryeki Akarshe daga yau shari'ar ta bar hannuna takoma gun abokin aikina kasan cewa abin yashigo da ni aciki kuma shine zai kawo karshen wannan shari'ar" Daga haka Abbana yabuga guduma jama'a suka furta kotu. Nan da nan aka fa ra watse,wa muma jikinmu asalube muka mike,da niyyar. RAYUWA book 3 part 7 NAGA RAYUWA book 3 part 7 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:09 Tafiya gida ummana kuwa tana hada ido da shany take tasaki kuka Nasan radadin abinda takeji Nikuwa,damuwata daya ce mamina yanzu Abbana da wane idon zai kalli mamina kai.Jama'ar gidanmu ma gaba daya me za suce da ita? . Duk da tarin zargin da akayi marattabbas ancuceta ankuma zalunce ta shi kansa na lura Abba na jikinsa amatukar sanyaye yake don ko da yadawo gida sashen sa ya,shige yakulle kofa Nikuwa idan na kalli yar'uwata Shany sai naji tausayinta ya sake kwarara azuciyata Don itama kuka take sosai tare da sauran yan'Uwanta su shida. . Ummana tana can kuryar daki nayi sallama nashiga da kyar ta dago idonta da yayi jajur takalleni na,zauna a gefenta na ce Umma wai me yasa kuka damu kanku? Ba za ku yi hakuri ku gode wa Allah ba da ya kaddara muku saduwa, da diyarku tun kuna raye? Umma ta dago tana duba na Aysha Allah shi ne abin godiya ba komai yake damu na ba sai yadda wannan matar ta gurbata min tarbiyyar yarinya yanzu ta ina kike tunanin zan fara gyaran tarbiyyarta? Abu na gaba da yake damuna shine maminki . yanzu da wane ido Abbanki da yayyenki zasu dubeta? wannan shine matsalata Ajiyar zuciya naja nace Umma duk wannan mai sauki ne tarbiyyar shany dai ki kaddara Allah shine mai shiryarwa ki ci gaba da rokonsa ya da fa miki awajen tarbiyyarta da ta sauran yan'uwanta Mamina kuwa insha Allahu matsalarta mai sauki ce Umma girgiza kai tayi tace Bamai sauki bane fateema na da riko kuma tadau zafi sosai a maganar nan ba ita kadaiba ma gaba daya danginta kuma tabbas yakamata su aikata hakan ko fiye da hakan don kam tabbas an bata musu . shiru nayi don kam ni ma shaidace da yadda yan gidan mamina suka dau Zafi kuma tabbas yacancanta ayi hakan don an bata musu Umma ta ja ajiyar zuciya kafin tace Tashi kije kija yan'uwanki ajiki Aysha don Allah musamman yar'uwarki duk da Abbanki yace zaisa ayi tayi musu addu'a amma tarbiyyarsu kam sai antashi tsaye. Jikina asanyaye namike nafice daga dakin don na lura Umma babu abinda yake ta yar mata,da hankali sai yadda za ta daidaita nutsuwar Shany ta dawo abar kwatance. . Tabbas wannan matar tacuci iyayena kuma wannan shi ake cewa ramuwar gayya wacce tafi ta gayya zafi Nayi Alkawarin zantaimaka mata da gyaran tarbiyyarsu Afalo natararsu gaba daya suna zaune sunyi jugum-jugum sosai tausayinsu ya,tsirga min na zauna kusa da Shany tare da janyota jikina."Please! ya kamata ku cire damuwa daga ranku haka tunda dai duniya ta shaida ba ku da laifin komai tarbiyya akayi muku ahaka kuma ita ta cuci kanta duk da itama tashi tayi ta tsinci rayuwarta a haka amma bai kyautu ace ta dora da nata mugayen halayen ba" Shany ta ja ajiyar zuciya kafin kwalla ta,zuba sharr daga idanunta tace Sister ina jin matukar bakin ciki idan na tuna,rayuwata ta baya haka kawai banji ba bangani ba don wata manufa aka rabani da nagartattun. Halaye na aka,kaini wata banzar rayuwa banjiba banganiba wallahi Allah ya isa bazan taba yafewa wadannan mutane ba Ta sake fashewa,dakuka Ni kaina kukan ne yaci karfina can daya daga cikin kawayenta tace Kukan dadi kikeyi shany,saboda ke yanzu yar gata ce kinsamu iyayenki. . Mu a ina kike tunanin zamu ga namu iyayen? shegu ne mu bamu sani ba itama tafashe dakuka gaba daya gurin,sai muka saka kuka, Daidai lokacin Umma tafito tana sallallami yanzu mezan gani haka kuda zaku godewa Allah da rayuwarku ba ta kare ahakaba amma shine kuke kuka?, Dasauri ta fice nalura itama Umma kukan takeyi da kyar na mike bayan naji ana kwala kiran sallar la'asar nace musu muje muyi sallah jikinsu asalube suka mike tare da haramar alwala Abinda ya ba ni mamaki bai wuce ganin yadda suke sallah ba gaba daya dungurawa kawai sukeyi tausayinsu ya sake kamani Don kam na tabbatar ba karamin gyara suke nema a addininsu ba . nadauki damarar koyar dasu sallah kafin komai da daddare gaba daya muna zaune awajen da ake cin abinci bayan angama Abba yadube mu yace masha Allah" kafin ya karasa naji mayataccen kamshin Ahmad yacika harabar gidanmu take nahade raina sosai don ba na son abinda zai hada ni da Ahmad cikin takunsa na isa yakaraso wajen yan matan Abba kuwa, tuni suka zuba masa ido tsiyar namiji maikyau kenan. . Duk inda yashiga sai kallo Na kaddara hakan araina har rige-rigen yimasa sannu da zuwa sukeyi Shany da sauri tamike ta shimfida masa darduma "Nagode" yace mata cikin tausasshiyar murya sannan ya zauna ya sake rankwafawa ya gaida su Abba yasa ke jaddada musu murnarsa na bayyanar yarsu shany Ni kuwa tuni nazare jikina nashige dakin umma wai kuma sai naji ina kishin kallon da yan'Matan Abba sukewa Ustaz Na zauna turus akan kujera hade da dafe kunci inatunanin Ustaz da irin tsananin kyan da yayi . Yau shigar wata jallabiya yayi dark-blue sai shaking take. Ta kwanta lub ajikin lallausar fatarsa wanda yala-yalan gashin yakwanta ajikinta Asalin balarabe dole duk macen da ta ganshi ta kyasa Atake na dokanta naji Ustaz ya kirawo ni koda masifar da na saba na zazzaga masa. Sai dai shiru makatau take naji wani abu ya tsaya azuciyata na tabbatar yanzu Ustaz ya gama yayina Don haka kone mana ba ya yi Shany ce tashigo dakin tana murmushi tace "Sis,wannan ma dan' uwan mune?" Da sauri na dago nawur ga mata wani kallo ina son . Gane me take nufi da tace hakan Ban hango komai akwayar idontaba don haka hankalina yadan kwanta Ahankali nace mata "MIJINA NE" amma a da fa Takuwa bude ido tace Wow! Amma meyasa kikace a da kina nufin yanzu kun rabu? Cikin sanyin murya na fara sanar da ita labarin Ustazuna kafin nagama kuwa tuni hawaye ya fara zarya, akan kumatunta Da safe kuwa kasancewar lahadi ce yawanci surukan gidanmu anan suke wuni sai dare suke tafiya harda mazajensu da 'ya'yansu muna zaune na saka .khadija da A.Nafisa matar ya usman atsakiya sai hira muke cikin nishadi don ni sauran matan yayyena ba sa gaba na don dana shiga halin da za a tausaya min ba wacce ta kula dani tamkar khadija Abba ne yashigo yana kiranmu nida 'yan matansa Afalonsa muka zauna anan kuma muka tarar da wasu matasa daga ganin su ka ga malamai don yanayinsu ya nuna haka Abba ya nuna 'yan matansa yace "Alhamdulillahi, gasu nan su takwas ne nakeso kafahimtar dasu addini don basu san komaiba game dashi malami daya yagyara zama yace "Alhmdllh" sunana m.Kawu kuma . Zan dunga koya musu Alkur'ani zamu soma daga fatiha insha,Allahu" Dayan ma yagyara zama yace sunana M.Aminu zan koyar daku fik'hu da hadith insha,Allah" haka dayanma yagaba tar da kansa "sunana M.Amadu da yar dar Allah zandauke ku darasin Sirah da tauhidi." Abbana yasake gyara zama yace Alhmdllh nagode Allah dama na sanar da su labarinku duka sun kuma matukar tausaya muku da wannan dalili na san insha,Allahu zasu jajirce wajen koyar daku. . Ga aysha nan ma za ta sake tunasar daku abubuwan da ba ku, gane ba kaina yana kasa na dago inda muka hada ido da malm.Aminu yace A'a Aysha tana gidane? . murmushi nayi da yake na sansu malaman mune na tahfiz nasan M.Aminu da tsokana Abbana yace Aysha ta ki zaman aure yafada yana dariya Da,sauri na mike nashige gida da gudu Don ba na son fadan malamaina nasan su kamar yunwar cikina musamman malam amadu Tun daga ranar Abba yace adunga kiran shany da humaira tunda itama sunanta Aysha bazai yiwuba mutashi a suna daya sun kuma da ge sosai wajen karatu kuma duk inda zasu hadda hijab . suke zuwa Sosai nake jin kunyar haduwa da Mamina don haka haryanzu na kasa Zuwa gidansu duk da ba ni nayi mata lefin ba amma na ja janta tabargazar da Abbana yayi mata Na jin jina mata laifin da ba nata ba abinda,yafi komai ciwo arayuwa azarge ka da abinda ba,ka aikata ba . Ranar Lahadi sati biyu da faruwar lamarin gaba daya muke zaune aharabar gidanmu har da yayyena da matansu kawai mukaji sallamar MAMINA kafin kace me tuni yaya.farouk da yaya.Ali sukayi wani tsalle suka gudu can bayan gida mamina ta shigo cikin zumbulelen hijabi da nikab Da murna ta natashi ina tsalle na rungumota ita din ma rungumo ni tayi tana sakin murmushi Ummana ma da sauri ta mike ta tarota cikin murmushi mai kama da yake take fadin mamin Aysha kece da rana haka? Ba tayi magana illa bi na da tayi da kallo tace . aysha,wajenki nazo don tayaki murnar kubuta daga kangin da kika shiga In kuma tayaki murnar ganin yar'uwarki akarshe nayi miki sallama zan tafi England karo karatu" Tuni hawaye suka sulmiyo min daga idona nace novels / NAGA RAYUWA book 3 part 8 NAGA RAYUWA book 3 part 8 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:11 . "Mamina kina nufin ba za ki dawo gidannan ba kin.Rabu damu har abada? Hannu ta saka tasha remin hawayena kafin nata digon hawayen ya dirgo akan kuncinta tace "Na rabu da kowa daya dangance ki Aysha amma ke da usman bazan iya rabuwa da ku ba Ina tare da ku a waya ko lokacin da zanzo hutu ki kular min da kanki Ayshata" . Daga haka ta zame hannunta takuma juya da azama da sassarfa Zata,wuce Umma turus ta tsaya idonta na kwalla nikuwa da sauri nabi mamina shima yaya usman ya fello da gudu muka tsare mamin da magiya Daidai lokacin Abba ya shawo kwana zaishigo sukayi ido biyu da mamina Cikin sassarfa yajuya da azama yabar gurin shi kansa nasan kunyar gamayyarsu da mamina yake Mamina ta kalleni tayi murmushi ahankali ta furta . "SAI WATA RANA AYSHATU" . Daga haka ta zame tafice Tuni na durkushe awajen na saka kuka don sam gwiwata ta ka sa daukana yaya usman yakama hannuna muka shiga gida shi kansa na lura jikinsa yayi sanyi sosai Abba naji yana kwalamin kira cikin sanyin jiki na mike na isa falonsa Tarar dashi nayi idonsa . Yayi jajur da alama shima kukan yayi yace Ayshatu mamin naki ta tafi? cikin sanyin murya nace "Ta tafi Abba ta sanar dani cewa wai karatu zata tafi England Amma Abba me yasa bakaje biko ba? Abba yaja ajiyar zuciya,yace "Dalilai da dama Ayshatu ina matukar son fateema amma ina jin kunyar.Tunka rar ta da sunan biko Bayan tarin abubuwan da suka shude da wane ido zandu bi mahaifinta? . mutanen masu nagartar halaye ina jin kunya Aysha..."shiru ni ma din nayi don kam akaf hasashena ban hango mafitaba cikin dakiyar zuciya nace Abba kadai jarraba tura manya nasan babanta mai fahimta ne insha Allahu zai fuskance ka" Allah yasa ayshatu tashi kije" jikina asanyaye na mike na fice Amma ko dana shiga kasa katabus nayi na roki yaya usman yakaini gidan mamina sai dai,abin takaici anan take hajiyarta take sanar dani sunwuce Abuja tacan ne jirginsu zai tashi Hakan yasaka,na saka kuka don na tabbatar yanzu kam mamina tayi min nisa musamman idan ta auri wani mijin bai zama lallai ya bari mu'amalar mu tayi nisa ba. . ******* ******** ******* . Wani lokaci ina kwance lamo akan gadon Ummana matsanan cin tunanin Ustas ne yadabaibaye min zuciyata kwana da kwanaki ban samu labarin sa ba Hakan ya dan daga hankalina hade da tunanin Ustaz yagaji da wulakan cin da nake yarfa masa shiyasa ya ajiye ba tu na agefe amma kuma ai har alokacin bai furta min kalmar saki ba bai kuma aiko da takarda ba meya ke nufi da jingine ni da ya yi? . Ni kadai nake wannan tuna nin Na rasa wazan tunkara da wannan.Tambayar tawa gashi ni kuma jan'ajina bazai bari na kirashi ba Fitowata daga wanka kenan ina zaune da karamin towel ahannuna ina tsane ruwan jikina Humaira tashigo da sauri tamkar an cillo ta Na bi ta da kallo saboda,ta inda muka bambanta kenan ita akwai dan banzan rawar kai "Aysha Sis,kije Abba yana kira" Ina zuwa shine zaki shigo kamar an cilloki har yanzu kin gagara koyar sallama idan zaki shiga waje. . Murmushi tayi ta fice da dan tsallenta, Nabi ta da kallo ina mamakin yadda kullum ta Allah Humaira acikin walwala da farin ciki take ba ruwanta da . Miskilanci irin nawa Allah kenan mai halitta gashi yayo mu iri daya amma sai ya bambanta mu tabangaren halayya Na zira riga sannan nafita falon Afalon natarar da duk samarin Abba ko nace magidanta mamaki ya ka mani tare da tunanin taron me ake ne gefe daya yan matan umma ne sun za gayeta gaba daya cikin shigar mutunci suke don yanzu sunyi matukar nutsuwa tamkar ba wadannan tantiran na wancan lokacin ba Na isa nazauna agefe ina fuskantar Abba da son sanin dalilin kira na . . Abba yabude da addu'a kamar kowanne lokaci idan za.Ayi,taro sannan yasake dubana yace "Aysha wannan taron naki ne, so nake inji me kika yanke game da aurenki ko kuwa har yanzu kina nan akan bakanki akaro na uku bazan takura miki ba kamar yadda na gaya miki wancan lokacin ra'ayinki zan bi" Ustaz ya isheni yazo da kansa ya aiko,don haka yau nasanar dasu zan fada musu abinda kika yanke" Tamkar nace masa zankoma amma ina sai nayi tuna nin yadda Ustaz ya yasar dani don haka, dole ni ma inja ajina. "Ina jinki"Abba ya fada Na dago fuskata nace . "Abba ba zan koma gidansa ba karatu nakeso nayi..." Daidai lokacin Ustaz yayi sallama da wannan mayataccen turaren nasa Da sauri gaba na yahau bugu ganin azabar kyan da ya yi Cikin jallabiya dark cofee 'yar Asalin sai dai miskilanci na ya kawar da wannan kudurin Ina so ayau na ga karshen miskilancin Ustaz na san idan yaji ba nason sa hankalinsa ba karamin tashi zai yi ba Cikin fara'a Abbana yace "yauwa dan halak yanzu ake zancenka gwanda da Allah ya kawoka Aysha sake maimaita abinda,kikace" kaina akasa nace ."Abba ba na son sa karatu nakeso nakoma akasar waje . " Murmushi Abba yayi yace to kaji kai Ahmad sai ka ba ta takardarta ayanzu kuma ayau zansanar dakai na maye maka gurbin Aysha da yar'uwarta Humair..." Tuni hantar cikina ta kada tamkar na janye batuna nazaro idona ganin Ustaz ya zaro jotter da biro a aljihu ya shiga rubutu tsaf nade na fahimtar me ake. . Cewa gashi miskilancina yahana namaganu karshe runtse idanuna nayi daidai lokacin Ustaz yamika wa abba takardar yana fadin . "Abba nagode Allah yabar girma" . "Ya juya yana kallon daukacin mutanen falon yace ku yani murna,da wannan karamcin na Abba" Abba yace Bakomai Ahmadu kaidin mutum ne mai nagartar halaye sam ba zan so na,rasaka cikin ZURI'ATA ba Tamkar wani maganadisu haka idanuna suka game da idon Ustaz kawai sai naga ya dagan hannu ya saki murmushi alamar . SAI WATA RANA . Daga haka yayi wa Abba sallama ya fice jikina asalube namike har juri nake ji nashige gida zuciyata cunkushe da tunani nakuma tabbatar da cewa wata makarkashiya Ustaz yakullamin ya dai ga yanzu humaira tafi kwanta,masa azuciya kenan da sake-sake sam ba na ganin laifina nikuwa,ko son sa,zai kasheni bazan taba nunawa na damuba sai dai hakan yazama AJALINA . Ji kake kut nahadiye wani abu da ya tsayamin amakogwaro sai asannan hawaye ya zuba akan kuncina zuciyata cunkushe da tarin bakin ciki nadama da da na sani kuwa fal raina Nafara jin haushin humaira tamkar itace tace ta na sonsa Ban da ni jinin tace wallahi da sai nayi mata abinda za ayi na damar hada ta da mijina sai kuma nafara jin haushin kowa . Agidan da tunanin sun fi son humaira akaina Ni kam nasan narasa MAI SO NA MAMINA . Don haka wunin ranar ban yi magana da kowa ba koda nayi sallar asuba sake komawa barci nayi duk da ada ba na komawa barci da yanmatan umma muke haduwa mu gyara gida yau kam ko kallonsu banyiba balle susa ka ran zanyimusu karin karatu kamar yadda na saba duk Asabar din duniya Da humaira da maryam da khadija muke kwana daki daya wani lokacin kuma humaira ta tafi dakin Umma sukuma sauran biyar din suna dakinsu da yake a bangaren mami muke tare jin hargowar shirinsune yasa nabude idona cike da jin haushin su nace malamai kunda.Meni fa kunhana ni bacci . Humaira tadiro,gadon ta haye bargon da nake kwance nace ke meye haka? Langabe kai tayi tace "Am sorry Sis, kinmanta da batun komawa kotun kiyi sauri kishirya kibisu bros ni Ustaz zanbi wani kallo nazu ba mata ina shirin kunduma mata ashar sai kuma natuna ita din wacece da kuma matsayinta a wajena Tsaki naja nace kuje kawai ba na jin dadi bazan samu zuwa ba daga haka YUWA book 3 part 9 NAGA RAYUWA book 3 part 9 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:12 . ba na son wani Silly queastion ina kallo suka fice sai ga Umma ta shigo maganar duniya nayi shiru kamar mai barci don ba na son ta gane yanayin da nake ciki Inaji tace . "Humaira muje takoma bacci ma" suka juya suka fice Nabi bayansu da kallo ina sake jaddada jin haushin humaira acikin zuciyata sai azahar suka dawo inajiyo hayaniyar su umma nayi bulun-bukui adaki inajin umma ta sake dawowa dakinta dubeni wannan karon na bude idona har nayi mata sannu da zuwa, cikin wata cunkushasshiyar murya Umma da mamaki ta dubeni Aysha kalau kike har yanzu kike kwance?,kaina ne yake ciwo kunda wo umma? Ta gyada kai mundawo Nace ya shari'ar ta kaya angama kuwa? Umma tace shari'a angama tsaf an yanke wa fateema hukuncin zaman gidan wakafi na shekara biyar ko tarar miliyan biyar .Shikuwa doctor daurin shekara biyar babu tara Atine kuwa daurin rai da rai tare da tilasta mata wajen fadar inda,sauran 'yan'uwanta suke. Najijjiga kai hade da fadin hakan shine daidai da su ai umma " Umma tace kowa haka yake fada amma Aysha anya babu . Abinda yake damunki kuwa? Na ce babu komai Umma amma don Allah kiyiwa Abba batun komawata makaranta inda hali gaskiya,nafison nabar kasar nan? Umma ta girgiza kai da alama tana tunanin yadda za ta fuskanci Abba da wannan maganar ne batace komai ba tamike tatafi Nikuwa na rintse idona don kam zanfi son barin kasar nan ko ba komai bazan san lokacin da aka daura auren ba balle Zuciyata tayi kunci Don yanzuma jinake tamkar ciwon zuciya zai kama ni. . Shiru har kwana biyu banji amsa daga bakin Abba ba na tabbatar bai amince ba kenan hakan ya sanyayar min da gwiwa Ina kallon, Humaira kullum nanike da waya akunnenta na san ba komai take ba sai hirar soyayya da Ahmad hakan yasake bakanta min rai harnaji tamkar nacanja daki sai dai hakan ba zata yiwu ba don nasan kiri-kiri za ace BAKIN CIKI nake, . sai dai kullum fa ina cikin uwar daki har umma tagaji da tambaya ta taja,bakinta ta tsuke ina lura da ita kullum tana kitchen tana koyawa yan matan girke- girke ta tattara al'amarina ta saka agefe Hakan yatabbatar min danayi . Rashin UWA MAI SO NA MAMINA Yau da daddare bayan mun gama cin abinci har namike tsam zantafi Abba yasa baki yaki rani Bina yayi da kallo yace kishirya da wuri gobe akwai tafiya potiskum duk na lura yanzu kintsiro da wani hali na zama ke kadai ba tare da munsan laifin da aka yi miki ba" Mikewa kawai nayi nace to Allah yakaimu sam banso wannan tafiyar ba amma babu yadda zanyi Da asuba babu wanda yakoma barci har humaira da ta kusan raba dare tana waya,da ustaz Na lura ustaz,har yafi sonta akaina saboda bini-bini yayi mata waya ita kuma tamkar mayya kullum tana makale da waya babu jan aji babu komai sai wani rawar kai shiri suke haushinsu kawai nakeji sosai araina suna ta caba kwalliya nikuwa wanka kawai nayi nazira wata bakar doguwar riga ta,mai na shafa kawai kai kace nidin matar mamaci ce wacce take takaba karfe 9:00 muka hau motar yaya usman na fada da sauri yaja mu dani da matarsa yana yimin tsiyar ramar da yaga nayi bayan hankali ya kwanta murmushi kawai nayi masa ba tare da na tofa ba shi ma din bai sake . cewa komai ba duk da na so yace din kodon na gaya,masa abinda yake,sani rama sai dai gani da zurfin ciki Ba kasafai nake iya fadar matsalata ba ba tare da an tambaye ni ba Haka har muka isa potiskum Ni dai ina zaune cikin mota jigum sai yaya usman ko matarsa sun sakoo ni azance sannan nake shiga sai gaf da la'asar muka shiga garin potiskum din munriga kowa isa Hajiya da sauri ta tareni cikin farin ciki take cewa kaga baiwar Allah tun dazu nake zuba idon ganinku Ayshatu fargabata daya dawane idon zan dubeki? Murmushi kawai nayi na durkusa nagaishe ta Don ni dama ba sosai na kware da wani wasan jika da kaka ba Ta kama ni Zoki zauna nasake jaddada ban hakurina a wajenki Duk da dai,kince kinyimin afuwa Akunyace na zauna nace hajiya kibar maganar tariga ta wuce Daidai lokacin Abba da Umma suka shigo Abba dafada yashigo yana fadin ina usmanun wai kai yaushe zakayi hankaline? . ina ce har waya nayi maka akan cewa karage gudu yaya usman yace Abba ai banyi wani gudu ba Nan suka zauna suna gaisheta hajiya kuwa bakinta . A bude,take kallonmu,ni da humaira fadi take Ba shakka ga zahiri nan babu bambanci ko digo tsakanin ku Umma ta tuntsire da dariya tace uhm-Uhum,da bambanci sosai Ayshatu bata da kwaramniya humaira akwai dan banzan rawar kai humaira ta zunbura baki tace kai umma nidin? ya muhammad yace sosai ma kuwa kike da rawar kai Abba yace humaira kam ba da ma humaira kuwa gaba daya ta fara dire-diren kafa tana kukan shagwaba ya faruk ne yakamo hannun ta yace Quite my friend kada kiyi kuka rabu dasu Me za ayi da mutum mai kunbiya-kumbiya? Da abu aransa ya fada yana kunshe dariya aciki Nakuwa zabga masa,harara don na san dani yake. . *** *** *** . Kwana biyu mukayi a potiskum,bayan munzagaye dangi muka dawo gida Nidai fara'ar dole, nakeyi a kan babu yadda zanyi tunda muka dawo Umma tafara zancen shirye-shiryen sa ranarsu Don ance wai suhudu za a aurar su yaya muhammad kowa daidaya guda uku kuma malaman mu ne suka nemi aurensu don nuna tausayawar su garesu Ranar laraba 'yan sa ranar sukazo 'yangidan su Ahmad ne harda kanwarsa khadija ta saka ni adaki tana tuhuma ta akan son jin dalilin dayasa naki dan uwanta har aka musanya masa da kanwata murmushi kawai nayi na ce KADDARA CE! . zo kaga lefen humaira akwatina goma sha biyu harda nasaka rana kayane sosai dankar aciki tamkar ba asan ciwon kudi ba wata uku aka saka cif Humaira sai rawar kai take bini-bini ta daga waya kaji tana kashe murya hade da,cewa my Only wannan iyayi da take,shiyake dugunzuma min zuciya Nayi tunani ita ko kunyata ba ta ji Nashige daki kuka kawai nakeyi har zazzabi ya rufeni ruf ba ta re da sanin komaiba sai ga shi nice har da kiran wayar Ustaz amma sam yaki dagawa . sai rejecting call dina yake Balle na bashi hakuri ya janye kudurinsa na auren kanwata Yau da safe ko fita banyiba daga daki maryam tashigo take sanar dani wai ana kira na Afalon abba da kyar na mike nazira hijabina na isa falon Abban shi da yan uwansa,da suke yan maza har su baba yahya suke zaune sun tasa kayan lefen humaira agabansu Allah ya sa su ruguza maganar Auren... . na ayyana hakan araina su kansu na san sunsan hakan baidace ba sai dai sabanin haka ji na yi Baba yahya ya rufeni da fada da nasiha yace "Yanzu Ayshatu saboda wannan kaddara ta afku shike nan sai kice kinrataye sunnar manzo {S.A.W} kice wai ke abarki kitafi karatu waje? . to tur da wannan shawara taki Adanginmu kaf ba mu bar maza sun tafi waje karatu ba balle mubar mace kuma gata daya da za muyi miki shine kifitar da miji kiyi aure shine mutuncinki mutuncinmu mu ma yanzu tunda Ahmad ba kyason sa wa kika tsayar? . kasa ce musu komai nayi ruwan hawaye ya fa ra ambaliya akuncina nace babu wanda na tsayar To mun baki sati kifitar da miji tunda dai..ovels / NAGA RAYUWA book 3 part 10 NAGA RAYUWA book 3 part 10 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:14 Mijinki na baya ya sanar da mu bai dora miki idda ba Tashi ki tafi Allah ya kawo nagari Da kyar na ja jiki na isa daki "Na shiga uku" . Nafada ahankali Najawowa kaina masifa meya,kaini furta ba na son Ustaz? Nasan halinsu baba yahya sarai da zafin rai tunda ya furta sai na fitar da miji abu ne mawuyaci ya janye kaina yayi dum sakamakon rasa mafita da nayi alokacin kam na san tabbas na yi rashin uwa da da mami akusa, da duk hakan ba ta sameniba ga shi ko kira lambar da takira ni bana samunta Hakan yatabbatar min da bayan mungama waya canja layi tayi Nasake rintse idona wasu zafafan hawaye, suka zubomin Da daddare kamar wasa na dau Ipad dina da niyyar duba facebook ko whatsapp, wanda rabon da na bude su harna manta sakon Mamina ne yashigo ta Whatsapp da sabon account din data bude kawai.Cewa tayi Aysha yakike? cikin tsananin farin ciki na tura mata hoton dan aljani mai alamar kuka akasa na rubuta;"Rayuwa ta yimin zafi MAMINA, . saboda rashinki akusa dani wallahi mami yanzu na tabbatar ni marainiyace na rabu da, . Ustaz an maye masa gurbina da humaira kanwata kuma Allah mami inason sa haryanzu Gashi Baba yahya ya rantse sai na fitar da miji mami na rasa yadda zanyi kibani shawara" . Tsawon lokaci ina sauraron amsar mami shiru har na fitar da ran samun amsar ta saikuma ga sako ya shigo . "Aysha kenan haryanzu kinason Ustaz meyasa kika cuci kanki wajen rabuwa dashi?" . cikin kuwa na sake rubuta mata "mami wallahi kaddara da kuma son ja masa aji." Dariya taturo min sannan taturo min "kisami Abbanki ki sanar dashi ba ki da wani Zabi yazaba miki miji da kansa idan yaji kince hakan nasan zai fuskanci har yanzu kina son mijinki idan yaso sai adawo da auren kanki."Murmushi natura mata alamar jinjina cewa tayi kawai "Sai da safe ina karatune" . Daga haka ta bar online. Kwanciya nayi akan gado ina dariya Na tabbata shawarar nan ta mami tayi don haka nake Allah- Allah safiya tayi Da azama na mike nashiga toilet nayi alwala ina rokon Allah yasa abinda nake nema yatabbata da sassafe nayi wanka na shiga don tanadar, wa Abba hadadden . Break fast koyaji dadin amsa bukatata Da sauri ina ta addu'a azuciyata ina kallonsu humaira suna jifana da kallon mamaki ganin yadda nake sakin fara'a a zuciyata kuwa fadi nake . "yarinya kwaleleniki mijina yafi karfin ki ko ta kaka sai na kwato shi" . Ina yi ina wakar MAI SONA MAMINA Umma dai murmushi kawai take yi dakaina nakaiwa Abba breakfast bayan na gaishe shi cikin mamaki yake cewa Ayshatu yau cutar tawarke ne naga kina walwala? . Murmushi nayi na sadda kai na kasa Abba yasake cewa ko ansamo min surukine? Nasake sunkuyar dakai nace "Dama Abba akan zancen ne..." Da sauri yace sunce zasu turo ? Na girgiza kai ina wasa da hannu na nace da...da...dama Abba cewa zanyi na... baka dama kazaba min...mijin" . murmushi yayi yace yar albarka kenan ni da kaina kai amma naji dadi Insha Allah kuwa zan miki zabe na gari dazakiyi alfahari da shi Akwai wani kanin abokina dama ya dameni da maganar aure, . mutumin kirki ga nutsuwa da kamala yana da iyali zakuyi daidai da shi...sam ba na fahimtar sauran zancen don dai naji da gani . nayi sai can naji yace shikenan Ayshatu zaki iya tafiya Ubangiji yayi miki albarka Adaddafe na mike nashige cikin gida Awani lungu nashiga na zauna turus ina tunanin wace tabargaza nasake ragargazowa,kaina.?Innalillahi wa inna ilaihirraji'un nake ja, wannan shine ba wan ba kanin Na dade ina kuka amma da na shiga gida ko kallona Umma batayi ba hakan ya sake tunzira zuciyata Na tabbatar yanzu ba ta ta tawa tunda ta samu humaira yanzu wa zankaiwa kukana? . Ya usman ba ya nan yayi tafiya haka na kwanta lamo ina tunanin wai ni zan auri babban mutum mai iyali Duk wani shirye- Shirye na bikin yan matan ya kankama don yanzu har saura kwana uku Idan kaganni na rame nayi fayau don yadda naji wai tare za ahada da tariyata Hakan ne yake dagamin hankali Da safiyar Ranar da za akama amaren Abba yakira ni dakinsa kaina akasa yake Anan naji ya sanar dani wai yau zaiyi bako da azahar . ."Ayshatu kiyi masa tarba ta mutunci don babban mutum ne ba naso kiyi abinda zai zubar da mutuncin gidan nan daga kai kawai nayi hade dajin wani . Nauyi yadanne kirjina yana cewa tashi kije ki tanadar masa abin saukar baki wannan karon kasa amsawa nayi na mike da niyyar tafiya amma ina sai daddafa bango nayi sai dai banyi aune ba najini kasa ji kake yif. . Ban farka ba sai agadon asibiti na ganni ana yimin karin ruwa Nabude idona jama'a ne birjik afilin dakin Gaba daya aka shiga yimin sannu. Ummana taka ma hannuna cikin nata ta sake cewa sannu Aysha,ina yake yi miki ciwo yanzu? girgiza kai nayi alamar bakomai Abba,da yake gefe yace Allah karo afuwa Daidai lolacin likita yashigo sanye da kayansa na likitoci yaja hannun da ake min karin ruwan ya zare robar da take sadar da ruwan zuwa cikin jijiya sannan yamaida dubansa gare ni yace meke damunki yanzu? . Muryata adashe nace masa "Bakomai" domin ba shida maganin da muwata yasake aunani da abin awonsu na likitoci sannan yadubi Abba yace ta samu sauki sosai kamar yadda na ga ya maka ciwon nata yana tattare da damuwa sakamakon bincikenmu yanuna ba ta samu hawan jini ba amma dai ta rage damuwa saboda nan gaba . Ta iya samun hawan jinin Abba ya daga kai yace Insha Allahu za a kula daga haka ina kallo likitan ya saka kai yafice Daidai lokacin mayataccen kamshin turaren Ustaz ya mamaye asibitin hakan ya tabbatar min dashine ya iso Hakan yasa nayi saurin lumshe idona don ba na kaunar na ganshi ma Da sallama yashigo dakin sannan naji muryar humaira hakan yatabbatar min da cewa tare suke Da sauri na,sake runtse idon don ita kanta ba na son nagan ta Bayan gaishe da su Abba da ya yi ina jin takunsa yakaraso bakin gadon danake anan naji yace Bata farka ba haryanzu" Abba yace Ta farka sai dai idan sake komawa tayi Humaira ta karaso ta dafa kafada ta jinayi kamar namake hannun ta amma na kyale ta sai dai zuciyata na matukar tafarfasa har ban san sanda hawaye ya silmiyo ta gefen kunci na ba Inajin Humaira tace lah Abba mafarkin kuka ta ke yi? Abba yace,wane irin mafarkin kuka kuma ke dai humaira da shiririta kike matsa in gani Abba yasa hannu ya shafi hawayen yace da gaskiyarki sai daiba mafarkin kuka take ba kuka take dagaske . Wato Aysha ba zaki cire damuwa daga ranki ba ko? Ni banga abinda akayi miki ba da ya tsunduma ki cikin wannan damuwar Na san kina jina Humaira tace Abba kayi mata ahankali babu mamaki abubuwan da suka, faru da ne suke damunta azuciya Abba ya girgiza kai to ai shikenan Allah yayi mana magani Amma ya kamata kicire damuwar nan tunda komai yariga yawuce Gaba daya haushin maganganun su nakeji Don haka da sauri na mike namayar da gashina da ya kwanta agefen fuskata Ustaz yana gefe ya zubomin ido wata harara na watsa masa Madadin naga yahade rai sai na ga ya saki murmushi yace aysha yajiki? Banko amsa ba nashige toilet ban san me zanyi aciki ba amma zaman toilet din yafi min zama ina shakar kanshin Ustaz yana hadda samin tunani iri-iri Ina shiga na saki kuka ahankali mai tsuma.Zuciya Ba na so suji muryata don haka natoshe bakin tsawon lokaci ina toilet har umma tagaji ta shiga bugamin toilet din tana fadin ke ayshatu lafiya? kifito ga mijin naki yazo" wani bugun zuciya naji da karfi na kasa yunkurinnovels / NAGA RAYUWA book 3 part 11 NAGA RAYUWA book 3 part 11 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:17 Saboda ina tsoron ganin fuskar mijin nawa mummuna ne? kyakkyawa ne? Allah ne masani Banbude ba sai da naji Umma tana cewa Ba kys jine? nace ki bude ga mijin ki da abokansa nan Da kyar na bude nace Umma miko min hijabina janyoshi tayi tamiko min tas na goge idona don inason bawa Ustaz mamaki zan nuna masa ina son mijina nima turus... . YAN UWA SORRY WANNAN PAPER DIN COMPLETE YAYI DAMAGE TO DAN HAKA MUN SALLAKESHI DON BAZAI KARANTUBA . Sai naji yace Gaskiya Alhaji Amarya tayi Allah yasanya Alheri Inaji katon banzan yana dashe baki yana "Amin-amin Nagode yalabbai" sannan ya mike "Bara mu tafi na, ga kamar tana so tahuta kasan marar lapiya ba kasafai yake son hayaniya ba . Amma yayannan naki yanada kirki Ban ko kalle shi ba suka mike ya iso gurina ya ajiye bandir.Din kudi na 500 yana fadin "To my madam Allah yakaro lafiya" cikin wata dasasshiyar murya ga kana nan ido wasu jajaye mitsi-mitsi dasu sai fakadeden hanci baje, a fuskar tamkar faranti Ya juya yasake dashe gaftara- gaftaran hakoransa A zuciyata nace wai Allah yayi halitta a nan!" . "Amarya sai gani nabiyu" Tamkar nace amaryar ubanka sai dai na dauke kaina Jin buga kofar ne yatabba tar min da fitarsu Hakan yasa na fashe da kuka Har ma na rasa wane irin zafi Zuciyata take yi Da daddare likita ya rubuta min sallama kasancewar an fara gudanar da hidimar bikin gidan adinke yake da jama'a wanda suka zo daga garinmu Potiskum Ana ta yi min sannu ni dai na samu na shiga dakinmu Nan din ma . 'yan mata ne aciki amma cikin tunzura nace "Da Allah ku fita waje kuba ni waje na kwanta" Ba su musa ba suka yimin sannu suka fice falo na kwanta Daidai lokacin Humaira ta shigo da gudu ta fada jikina tace "Aysha sis,oyoyo, ashe an sallamo ki? amma naji dadi bara na kira My Ahmad na gaya masa" wata harara na watsa mata nace "ke ba na son munafunci na ce miki ina nemansa ne? . "Haba Aysha sis, shifa yace idan an sallamo ki na kira shi ya sake miki ya jiki" Girgiza kai kawai nayi nace "Humaira fice a dakin nan tun kan cimiki mutunci Keda Ahmad din"Ta zaro ido tace My Ahmad din? Tsaki naja nace "Ko uban Ahmad ne banzaye munafukai" ganin yadda na matse ina masifa ne hakan yasa Humaira ta fice sum-Sum jikinta asanyaye Naja tsaki nace "munafukai kawai ko kunya ba ta ji ba wani My Ahmad ko gidan ubanwa yazama na ta?" jinayi anturo kofa har najuyo zan banka ashar sai naga umma ce,hakan ya sa nawa bakina linzami Umma tazauna agefen gado ta ce "tashi Aysha magana za miyi " Dakyar na mike ta zubo min ido kafin tace . "me ya farune?" Nace Name fa Umma? "Yanzu 'yar uwarki taje,da kuka tana sanar dani wai tafasa auren Ahmad saboda ta lura kina son mijinki shin dagaske ne abinda ta fada?" Tamkar nace "ba haka bane amma sai wata zuciyar ta sanar da ni wannan ce dama ta takarshe hakan yasa cikin matukar kunya da jin nauyi nace Eeh Umma" Umma tazaro ido tace . "Kina son sa fa kika ce?" Na daga kai, sai naga Umma jikinta yayi sanyi, tace "Aysha Kirufa mana asiri don Allah kada kisa mu abakin duniya Ace duk sanda muka tashi sha'ani sai wani abu ya faru tunda an gama magana har ankarbi sadakin humaira to ki bar mata Ustaz tunda tun farko ke kika ce bakyason shi aka kuma biye miki yanzu kice kuma kin dawo kina sonsa . wallahi kada na sake jin zancen nan 'yar uwarki ce don kin rasa ta samu bai kamata yazama abinda muwaba . Ki share hawayenki shima wannan mijin naki maikudi ne kuma yanada kirki matarsa mutuwa tayi wajen haihuwar dansu na takwas" Da, sauri na zaro ido tace "takwas Umma? . wayyo na shiga uku Abba ya rasa wanda zai ba wa aurena sai wannan basamuden?" Umma tayi saurin cewa "Rufemin baki kada ki tara min jama'a to sai me don 'ya'yansa takwas ba tare dake za su zaunaba suna wajen kakarsu, kuma ya ce ma kuna auren Abu dhabi za ku wuce acan inda yake gudanar da harkokinsa ba ki ga gidanki ba da akaje gida tamfatsetse tamkar ba a duniya ba . " Runtse idona na yi ina jin Umma ta gama surutun ta fita. Tunani kawai na keyi ta yadda zan iya zaman aure da wannan mutumin Ni maison miji kyakkyawa na nunawa sa'a amma kudurar ubangiji ta sauka akaina Kana ta ka ne Allah na tasa kuma ayanzu na tabbatar ba duk abinda kakeso kake samu ba sai wanda Allah yaso Ina kallo Umma ta fice daga dakin zuciyata ina sake tuna zancen Umma da take ta koda arzikin mutumin wai har da cewa gida tamfatsetse tamkar ba a duniya ba to ni ina ruwana . Da arzikinsa? Na ja tsaki yafi a kirga. Haka aka shiga gudanar da shagalin biki ni.Kuwa ba na shiga kowace sabga koda yaushe ina daki akwance ina ganin yadda wasu suke kallo na a dafe da alama suna hasashen yadda nake yi wa 'yar'uwata bakin ciki ne ni dai bin kowa nake da kallo fuskata kuwa ta yi fayau ni kaina na san na rame matuka da gaske. Ranar da ya kama za akai amare a ranar naji labarin wai, ni ma zanbi mijina Abu- Dhabi, Hankalina ba karamin tashi yake yi ba idan na tuno yadda mijin nawa yake Tunda magriba na fara jin hayaniyar motoci Humaira ce ta shigo da gudu ta, fada jikina ta rungume ni tana wani kuka maitsuma zuciya Hakan ya sa ni ma na saka kuka ba tare da na shirya hakan ba. . A marairaice kanwar umma ta shigo, ta ja hannun Humaira tana fadin "Kuyi hakuri haka rayuwar mace ta ke takaitacciya ce agaban iyayenta" Ina kallo takama humaira suka fice.Nasan shi kenan na rasa Ustaz, har'abada zuciyata ta karye na sake fashewa da kuka Gidan yayi tsit duk an fashe,kai amare daga ni sai Umma ji nayi anturo . Kofa an shigo In bude ido naga Abba ne da Umma Abba yazauna abakin gadon cikin muryar rarrashi yake sanar dani natashi naje mijina yazo tafiya dani "Ayshatu ina sake baki hakuri akaro na biyu akan duk abubuwan da suka,faru a baya. . Sannan ina miki nasiha da kibi mijinki sau da kafa saboda ko ba komai aljannarki atafin kafarsa take. Na sani Ayshata mai biyayyace don Allah ko da bakya sonsa kidaure kibishi. Alhaji Danjuma mutumin kirki ne" Da sauri na sake fashewa da kuka jin sunan da Abba ya fa da wai Danjuma. Kai daga ji ka san an rayu akauye. . Umma tace "To mene ne na kukan tunda ta faru ta kare. Ubangiji ya ba ku zaman lafiya Tashi maza ki kintsa yana jiranki a mota airport za ku tafi." Cikin rarrashi Umma ta tilasta ni nashirya cikin wata rantsattsiyar laffaya, fara. Ta sha ado da zare marun. kayan kam sun amshi jiki na caras na fito tamkar 'yar tsana Na raya araina ina ma gidan Ustaz za a kaini ba gidan wannan mutumin ba." Da kyar nayi sallama da su ina kuka cikin karaji yaya usman ya rike hannuna ya rakavels / NAGA RAYUWA book 3 part 12 NAGA RAYUWA book 3 part 12 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:19 Ni har bakin motar yana sake jaddada min na yi hakuri duka rayuwa nawa ce. Idan dan Adam yayi duba da abubuwan zamanin baya da suka shude zai gane rayuwar duniya ba,komai ba ce jin Yaya usman kawai nake har ya bude bayan motar ya saka ni yana rufe motar na sake fashewa da kuka. Daidai lokacin Danjummai ya juyo daga kujerar gaban motar ta masu zaman banza sai ji nayi ya ce "Shatu sai hakuri a,rabuwa da iyaye akwai ciwo amma ga 'yanmata hakan yafi ciwo ba ga ke da ba wannan ba ne aurenki nafarko".Tsit nayi saboda jin haushin kalamansa Ji don Allah ko hakan shine salon da ya dace ararrashi amarya? Sam babu riba ga auren babban mutum. Harmuka isa airport ban sake tofa komai ba naja bakina na tsuke ina sake taraddadin yadda zan zauna da wannan mutumin Ina,jinsu suna ta shewa suna hirar kasuwancin su Isarmu airport tayi dai-dai da lokacin da ake ta kiran passenger ciki kuwa har da mu ana sanar sauran mintoci kadan jirgi yatashi raina a bace nake bin sahun mutuminda da za abani dama nakashe wani shi zanfara kashewa . Muna hawa jirgin hancina yafara shakar kamshin Ustaz Nan take na fara waiwaye awautata wai ko zanganshi amma sam ban ganshi ba take na amince yawan tunanin sa da nake yine yasa nafara jiyo kamshin sa Bat na nemi mijin nawa Na rasa hakan ya sa na fara waiwaye- waiwaye saboda ni sam ba taba shiga jirgi nayi ba balle nasan ka idojinsa Tsawon mintuna ina laluben mutumin amma ban gan shi ba hakan ya tunzira zuciyata na sami waje kawai na zauna ina fargabar yadda jirgi zai daga ni sama na zama tamkar tsuntsu a sama wani mutum ne yazo ya tsaya akaina tare da sanar dani wai wajen sane,nazauna har yana nuna min numbersa ajikin boarding pass. Take kwalla ta fara zubar min ganin yadda mijin nawa kiri-Kiri zai saka adauke ni 'Yar kauye Murmushi kawai na saki da furta kalmar"am sorry". shima yasaki murmushi ya ce "Ba komai 'Yan mata kiduba lambar sit dinki ajikin boarding pass dinki Na daga kai na nawuce ina laluben lambar kujerata Da sauri na isa wajen sai dai na tsaya turus domin daf dawani mutum aka ajiyeni wata . Lafiyayyiyar suit kuma daga jikinsa kamshin turaren Ustaz yana fitowa ya rufe fuskarsa,da wata magazine Mamaki ya kama ni nan na shiga waiwaye ina tunanin INA MIJINA? haka na zauna saboda ba na so adaukeni 'yar kauye Amma kamshin da mutumin yake ya ta kura min saboda kamshin.Turaren Ustaz Ahmad Tunda Nazauna bai tan kamin ba Ni ma kuma ban kula shi ba Na dai kaddara kawai barci yake ko kuma irin miskilayen mutanen ne shi din jigum na zauna ina ta addu'a a raina don kam a tsorace nae Dalili? ban taba shiga jirgi ba wani sauti naji yana sanar da mu muyi tightehing belt dinmu Gaba daya na rikice don ban ma san inda belt din yake ba Mutumin bai wani bude fuskarsa ba ya dana belt dinsa alamar shidin kwararre ne Na rasa yadda zan yi tamkar na tambaye shi amma, nafasa na hakura kawai na cigaba da addu'a a raina Jinayi kunnuwana sun yi dum dai-dai lokacin da jirgin ya fincika zai daga ban san lokacin da na kankame jikina ba ina salati jinayi wannan mutumin kawai yayi caraf ya riko hannu na Ahanzarce na juya zan masa . Masifa duk da tsoron da nakeji Cab ko kunsan WA NA GANI? . Da sauri na ware idona don natabbatar shidin ne? tabbas shine ustazuna . ya matse cikin wasu marun din suit sun amshe shi sosai abinka da farin mutum cikin matukar mamaki na zame hannu na nace Ustaz me yakawo.Ka nan? Ina humaira? Bai min magana ba sai zallar murmushi kafin yace "Humaira tana gidan mijinta" Na sake waro ido nace Wanene mijinta ban da kai da na sani? . " Ustaz ya lumshe ido kafin yace Ni ba mijin Humaira ba ne ni mijin Ayshata ne" Wani farin ciki ne ya,mamaye Zuciyata da sauri na ciji kaina inaso na tabbatar ba mafarkin da na saba ba ne Ustaz na,lura da ni ya jawo hannun ya matse yace "Ba mafarki kike ba Aysha nine,Ustaz dinki" Yakai min sumba a hannu sannan yace "Is a long story bari muje gida kisha labari" . Tuni maganar jin tsoron jirgi ya sha ruwa saboda, ga ni ga masoyina Ustaz dan gaske,Ban sake magana ba illa sakin murmushi Shi ma murmushin yake ya jawo ni gefen kafadar sa ya kwantar akan kafadarsa Akunne ya rada min "Aysha kiyi barci . Na san kin dade baki yi barcin farin ciki ba" Na saki murmushi don kam azahirin gaskiya ya fada Wani annuri ne yake shiga zuciyata na lumshe idona kamar mai barci sai dai sam ba barcin nake ba zallar soyayyar Ustaz ce take ratsa duk wani ilahirin jikina, . Ina kuma sake jaddada godiyata ga jalla ta'ala buwayi gagara misali Da son na san yadda reshe ya juye da mujiya al'amarin Allah kenan kana taka Allah na tasa .Ta jalla itace gaskiya Azaton Ustaz barci nake don haka bai tashe ni ba don ko da aka kawo abinci ma karba kawai ya yi ya ajiye min nikuma na yi lamo sam ba na son narabu da jikin Ustaz Ina shakar kamshin sa mai sake tsuma,soyayyar sa azuciyata sai asubar can garin sannan muka isa Gaba daya Ahmad ya kankame hannuna tamkar wani zai kwace ni awajensa Wani rantsattsen hotel ya kama mana tamkar aljannar duniya zuciya ta fari kal nake mayar da kafata duk inda Ustaz, ya ajiye tasa Shikuwa sai jifa na yake da wani salon murmushi Zama,yayi abakin gadon hade da fadin "Wash,Allah " ya lumshe,ido ni ma bin sa nayi . Da ido lna masa kallon zallar so Ustaz ya miko min hannu "Zo Ayshat" Ba musu na isa,ga ustaz cikin ta kun,jan hankali amma sam na ka sa,karasawa gareshi illa narungume hannaye ina jifanshi da murmushi shidin ma kashe ido yayi yace "mekenan aysha? Ina fatan ba kunyata kike jiba? . " Na dan makale kafada alamar ba za niba Da sauri ya mike ya,iso gareni "Why aysha? Don Allah kada muyi haka da ke kada ki disashe farin cikin danake shirin samu atattare dake awannan daren Ayshata please enough is enough komai ya wuce don Allah"yafada yana langa be kai Ni kuwa sake shagwabe fuska nayi nace Ustaz me ya sa kuka wahalar dani kuka ki bayyana,gaskiya? murmushi ya sake yi yace "Har na hango aysha a asibiti da angonta tana muzurai" ya tuntsure da dariya abinda ban taba ganin ustaz ya yi ba Don haka nabishi da kallon mamaki kuma sosai dariyar ta yi masa kyau ya sake bina da kallo "kina tuna bama- baman hara rar da kika dunga aika min a asibiti? . . Na kwace fuskata zan fashe da kuka Da sauri ya kamo hannu na "Come on Aysha,yau ba . Ranar kuka ba ce so nake kawai.na nu namiki zallarso Aysha I am in need" ya fada yana lumshe,ido Tare da janyo hannu na Nace "Ustaz don Allah kabani labari" Da sauri cikin dushewar murya yace "Ba zan iya komaiba yanzu sai na samu,nutsuwa" Shiru nayi da ba kina don na lura abin nasa ba sauki. . *** *** *** . WAYEWAR GARI A ABU DHABI . Duk da sanyin asuba da yake ratsowa ta window hakan bai sa na tashiba Ustaz, tuni ya tashi ina ta jin motsinsa har.Bacci ya sake dauke ni Diso-dison ruwa da yake digomin akan fuskata, shiya sa na bude idona. Ustaz ne tsaye akaina ya dan sunkuyo yana min wani sihirtaccen kallo da murmushi akan lebensa yace "Beauty a,tashi ayi wanka ayi sallah mana"Na,dan turo baki nace "wallahi na gaji Ustaz" Ya dafe hannu na yamikar dani yana fadin "am very sorry beauty, laifi nane na wahalar da ke dayawa But am very sorry Laifin so ne" ya fada yana kashe ido daya sai da ya rakani har kofar bandaki sannan ya ja min kofa yana fadin "ayi wanka sosai beauty banda jika- jika" Nayi murmushi . Na shige cikin toilet din koda na fito tuni Ustaz ya shimfida min daddumar sallah nan na tada sallah na dade ina gode Allah acikin sujjada bisa ni'imar da yayimin ta dawo da Ustaz cikin rayuwata akaro na biyu Duk da godiyar da na yiwa ubangiji anafilar ma'aurata da mukayi adaren jiya Ina zaune ina karatun littafi mai tsarki Ustaz,ya turo kofa yashigo cikin wata jallabiya light green colour yazauna agefena hade da sanya kansa akafada ta yace "kada ki roki ubangiji ya kara min sonki please Abar ni haka wallahi a hakan ma wahala nake sha Tuni sonki ya cunkushe,min zuciyata . Bana iya aikata komai sai zallan tunanin ki Idan za ki roki Ubangiji ki ro keshi ya rage min sonki" Wani kallo na dallare shi dashi yayi murmushi kafin ya lumshe ido ya kankameni cikin slow voice yace "Ya Allah ka ragemin..." Da sauri na toshe bakinsa nace "Ba amin ba" murmushi yayi yace zo ki sha,tea Allah yabarmu tare forever" Na saki murmushi ni kadai na san annurin da ya baibaye min zuciyata Zuba min tea yake a cup amma gaba daya hankainsa . Akaina yake Na sa hannu zan karbi tea din bayan yagama hadawa gaba daya ya hada hannuna ya matse "Allah yaki yaye ai inde ina raye kuma ina kusa dake kin daina ci da sha da kanki." Yajanyo ni gefensa yashiga san yamin cup din a baki maza kisha gimbiyata 'yar albarka mai tarin alheri da ni'ima Na lumshe idona ina hasashen dalilin da ya sa Ustaz yake min wannan sumbata tun daren jiya Bayan mun gama breakfast na koma gado da niyyar komawa,barci don barci nakeji har alokacin Ustaz yakawar da kayan ya biyo ni kan gadon Barci za ki koma? Na daga kai cikin muryar shagwaba na ce masa "wallahi Ustaz barci nakeji" Yajawoni jikin sa yana cewa maza kiyi bacinki dama labari zanbaki na abubuwan da suka faru bayan kince ba kya sona da sauri na mike nace please Ustaz gaya min Ya lumshe ido yana murmushi . *** *** *** . Tun Sanda kotu ta wanke ki tas daga zargin da ake miki naga kina watsomin kallon tsana tuni gwiwata tayi sanyi don nasan da kyar idan za ki sake amincewa da soyayyata akaro Na biyu.AGA RAYUWA book 3 part 13 NAGA RAYUWA book 3 part 13 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:24 Bansare da al'amarin ba saida na biki gida Nan ma naga babu wata mafita don kuwa karara kike min kallon tsana Haka natafi gidanmu gwiwata asanyaye mamata na zaune afalo ta dubeni itama cike da tausayawa don tsukun wannan lokacin sam ba ni da sukuni wallahi Aysha ko abinci ba na iya ci sai mama ta tursasa ni. . Lauyoyi kuwa na nemi sama da mutum ashirin sai su ce wai sunji labarin shari'ar lamarin yashigo da minister, kuma babu wanda bai san shiba wajen tsaurin rai. Abune mai sauki ya iya sa mutum yarasa aikinsa kuma ya bata record dinka gaba daya Hakan ya daga hankalina duk wani kasuwancina na dakatar dashi izuwa wannan lokaci na yarda da cewa Asiri aka yimiki ko kuma aljanu ne suka shiga jikinki mama taja ajiyar numfashi tace "Ya ya akayi shari'ar?" Na lumshe ido nace "mama shari'a yau ta kare don kuwa an wanke aysha daga zargin da ake mata,bata da laifi ko daya" Wallahi Aysha sai alokacin nasan mama tana son ki .Wancan abinda ya giftane ya sa kika fita aranta Hamdala tayi sosai ranar ta taba fadar sunana tace . Ahmad to ya akayi? Nan nabata labari na dora da cewa mama ina tsoron kada Aysha ta juya min baya mama ta dan yi jim kafin tace Ni kaina Ahmad ba kai ba ina fargabar kallon da Aysha za ta yi min na sani sosai mu ke da laifi awajenta amma insha Allahu baza ta juya maka ba ya ba Shi yasa kika ga mama har yau ta kasa zuwa inda kike saboda matsananciyar kunyarki da takeji Ban daddara ba nasake komawa wajenki sai dai ko fitowa baki yiba balle kizo ki saurare ni Usman ne yadunga ba ni hakuri hade da,sanar da ni da zarar komai yalafa zaki saurareni yanzun kam zuciyar ki azafi take wajen son kiga kinyi ramuwar gayya Hankalina kin yarda da shawarar Usman yayi na koma ta bangaren Abba shima exactly kamar yadda Usman yafada shima haka,ya fadamin hankalina ya sake tashi gani na ke kamar na sake rasa ki forever{har'abada} don tilas daddyna ya shiga maganar ganin yarda na ke ta sake daga,hankalina tsoron kada ciwona ya,sake, tashi akaro na biyu. Da kansa ya je ya sami Abba suka kuma kashe magana akan nabarki ki huta . Na daina matsa miki Abba ya sake jaddada min ya san kina sona kawai bacin raine ya jawo hakan da kuma miskilanci irin naki. Shi yasa kika ga kwata-kwata na daina neman ki akan dole na tilasta wa zuciyata duk da sautari kasa jurewa nake.... . TOFA KUDAI KARAYIN HAKURI NAN MA YAYI DAMAGE AMMA DAGA NAN HAR KARSHE BABU DAMAGE . Murmushi nasaki bayan na gama,jin labarin Ahmad ya matsa hannuna yace"hope kin gamsu My Angel"Runtse idona nayi na ce yanzu kana nufin Humaira itace matar mahmud? Ahmad ya daga kai yana wurgo min kallon kasan ido Nace amma Allah ya sani kunshamma ceni kun kuma bawa zuciyata matsananciyar wahala Don ko barci gagara ta yake yi Na fada fuskata adan hade Ahmad ya mintsini kuma tuna kafin yayi dariya har,wushiryar sa ta fito yace Ba komai yajawo minba sai miskilanci yanzu don Allah da ace da gaske wannan mutumin aka ba ki ya za kiyi? Babu yadda zanyi sai dai nasan ba abin Mamaki ba ne auren sa ya zama ajalina Don kam ina kinsa ina yimasa zazzafar kiyayya wacce ba zata kwatantu ba wai don Allah a ina kasamoshi? Ahmad ya saki murmushi yace Direban kamfanina ne na san Aysha na sani ta tsani mutum mummuna Don haka na hada ki dashi ko don na sha dariya Na mike daga cinyarsa da nayi matashi da ita Fushi kikayi? Haba Aishata How I Wish ana rewinding na komo miki yadda kika hade rai a jirgi duk fa ina kallon ki yadda kika . Yi tamkar ki zunduma ihu Ina sane, dama na saka suit don nayi miki BASAJA nasan bazaki taba kawowa ni ne ba Gaba daya na miki hanya da niyyar ficewa daga dakin don na lura Ustaz bazai fasa tsokanata ba ji nayi ya finciko ni Na, wuntsilo gaba daya nadawo gareshi Ina zaki? yace min cikin wata murya Ji na yi wayarsa ta hau ringing, ina kai dubana akan screen din naga an saka MY WIFE. Take wani kishi ya dabaibayeni duk annurin fuskata ya bace bat cikin hanzari na mike nafice daga dakin da sauri amma abin mamaki Ustaz baiyi yunkurin biyo niba Inaji yana kashe murya,yana amsa waya murya kasa- kasa sam bana jin me yake cewa Turus nazauna akan kujera wasu zafafan hawaye suka zubo min zuciyata tashiga bugawa saboda tsananin kishi . Tsawon mintuna kafin ya fito daga dakin yana kiran "My angel ina kike Ne?" Haushin sa naji ya turnike ni azuciyata turus yayi ganin ina kuka cikin sanyin jiki ya matso kusa dani ya zauna yana kokarin ja na Cikin zafin nama na kwace ina masa kallon munafiki Yanzu haka duk abinda yakemin . Yi tamkar ki zunduma ihu Ina sane, dama na saka suit don nayi miki BASAJA nasan bazaki taba kawowa ni ne ba Gaba daya na miki hanya da niyyar ficewa daga dakin don na lura Ustaz bazai fasa tsokanata ba ji nayi ya finciko ni Na, wuntsilo gaba daya nadawo gareshi Ina zaki? yace min cikin wata murya Ji na yi wayarsa ta hau ringing, ina kai dubana akan screen din naga an saka MY WIFE. Take wani kishi ya dabaibayeni duk annurin fuskata ya bace bat cikin hanzari na mike nafice daga dakin da sauri amma abin mamaki Ustaz baiyi yunkurin biyo niba Inaji yana kashe murya,yana amsa waya murya kasa- kasa sam bana jin me yake cewa Turus nazauna akan kujera wasu zafafan hawaye suka zubo min zuciyata tashiga bugawa saboda tsananin kishi . Tsawon mintuna kafin ya fito daga dakin yana kiran "My angel ina kike Ne?" Haushin sa naji ya turnike ni azuciyata turus yayi ganin ina kuka cikin sanyin jiki ya matso kusa dani ya zauna yana kokarin ja na Cikin zafin nama na kwace ina masa kallon munafiki Yanzu haka duk abinda yakemin . Haka yake mata koma fiye da haka? yanzu waya san irin dadin kalaman da ya gaya,mata? gashi yanzu nima yazo yan wani rangada min ANGEL Ahmad ya waro ido yana min kallon mamaki Ayshat lafiya? Na watsa masa harara karshe na,mike na fice lambun gidan inda wani makeken Swimming pool yake na zauna na zira kafafuna ina wasa dasu Gaba daya natafi duniyar tunani Allah ya sani tun farkona natsani kishiya musamman ga mijin da,nakeso Ji na yi,an dafa kafaduna na san Ahmad ne don haka najuyo cike da tsawa zan sauke masa kwandon rashin mutunci sai na kasa saboda salon kallon da Ahmad yake min tuni jikina ya mutu sai tarin kwalla kasan idona Ahmad ya kama hannuna "please Ayshat Ki zama good house wife mana MACE TA GARI mai kokarin faranta ran mijinta a kowane situation kada ki biye rudin zuciya shaidanne kawai mai kokarin son kai mutum ga halaka Na sani kishi ne yakai ki ga haka please ki fatattake shi ina son ki Aysha kuma babu macen da zata ka mo matsayinki a zuciyata To me zai saka ki kishi? Babu ruwan Allah da kishi . aduk yayin da mace ta bata ran mijinta mala'iku tsine mata suke Na lumshe idona tuni hawaye suka wanke,min fuskata cikin shisshikar kuka nace Ina son mijina Ustaz ba na so na aikata sabon Ubangiji Ya Allah ka gani kai ka dora min kishin nan Ubangiji ka yaye min..." Tuni kuka yakwace min Ahmad ya jani yamikar dani tsaye cikin sigar tausayawa ya hada ni da jikinsa yana lallashi na Yi addu'a Aysha duk tsanani yana tare da sauki Tabbas da ina da hali da na sauwakewa Hameedah to bai kyautu gareni ba, babu abinda tayimin na tayimin na saketa hakan ya sabawa koyarwa ta addinin Islama ki yi hakuro ki jajirce zuciyarki gurin ganin kin zama MACE TAGARI mai kokarin faranta ran mijinta akowane yanayi Har daki yakaini ya kwantar dani yaja bargo yalullu beni cikin ajiyar zuciya na saki murmushi nace masa Nagode. Yatsun kafata ya fara ja abinka da ka sa tuni barci yadauke ni Sai can yamma na bude ido Ahmad na gani zaune,yazuban ido Haba Aysha barcin ai ya isa kitashi mufita mu zaga"nGA RAYUWA book 3 part 14 NAGA RAYUWA book 3 part 14 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:26 . Namike ina kallon sa yayi kyau sosai cikin English wears mene ne kike kallo na ne? Murmushi nayi nace Wai yaushe kafara saka kana nan kaya? Dama ina sawa amma ba sosai ba sai time to time haka ki tashi ki watsa ruwa mu fita shan ice cream ki ga Dubai sisai Cikin slow na mike na shiga bandaki na dade ina wanka loko- loko na jikina sai da nagama kuma na rasa ta yadda zanfito don daga ni sai wani karamin towel na manta ban shigo da hijab Ba Don haka na make a toilet din na kasa fitowa sai na hau kwankwasawa hakan yasa Ustaz ya iso bakin toilet din cikin murya kasa-kasa yace Ya akayi matata? Ban bude kofar ba na ce masa Don Allah miko min zani Cikin matukar mamaki ya banko kofar yabude ta bakinsa asake yake kallo na Wai ke me kike nufi? Ni kikejin kunya? Na kuwa takure waje daya Murmushi yasaki ya tabe baki kafin yace 'yan'matan Ustaz kenan To kiyi ta zama idan kin gama jin kunyar kya fito Daga haka ya fice tsawon mintuna ina tsaye wallahi na kasa fita jinayi alamun anrufe kofar hakan ya sa nayi wuf nafice duk . Gudun kada Ustaz ya dawo ya tarar dani har da murza key na rufe kofar na isa bakin madubi na zauna akan kujera nashiga shafe jikina da body oil Gaba daya ina shafa na cinyata dagowar nan da zanyi na hango Ustaz ta madubi yana murmushi cikin wani lumshasshen kallo Fuskata a turbune na mike ina turo baki na hau tura shi ina fadin please Ustaz meye haka? Fita- fita nace Kakkarfan Namiji yana tsaye kikam dashi ko motsi baiyi ba yana ta sakin murmushi yace Aysha me karfi to tura ni inga ko za ki iya Cikin matukar galabaita na durkuse akasa na rike jikina Ustaz ne ya dago kaina Sarkin kunya na fita maza ki shirya am waiting Sai da na ga yafita sannan na saki ajiyar zuciya ina murmushi kai Ustaz ba dama Tsaf na fito cikin wata rigar Larabawa pitch colour mai adon baki na yane kai na da mayafi baki ni kaina da na dubi kaina amudubi sai da nagodewa ubangiji da ya halitta min kyakkyawar halitta jin takun tafiyata ne yasa Ustaz ya dago kansa Gani nayi kawai yana ta sakarmin Flasher da yagaji da daukar hoton yaza gayo ta . Gefena ya ja ni jikinsa yana daukar mu atare Zo ki ga tsagwaron kyau Ustaz ya latsa dimple dina I like you baby bazan iya fita ba Saboda me? Na tambaye shi da sauri Ya lumshe ido yace Saboda ke My Ange Anya zan iya rayuwa babu ke? Da sauri nace masa hameedah ba? Dariya ya gintse yace ba kyau zancen mutum ba ya nn sarauniyar yan rigima Na sani ba ya so ya tunzira zuciyatane ya kama hannuna muje mu sha ice cream" A shago sai da ice-cream Ustaz sai wani nan-nan dani yake tamkar wani zai kwace masa ni musamman da ya lura wani balarabe ya kafa min ido cikin masifa yaja hannuna mufita Aysha Har munje gida bai min magana ba sai mita yake "Iskancin banza sai kace bai san haramcin haka ba I llar mace mai kyau kenan daga yau kin daina fita saida nikab.Na gani idan wani dan iska zai daga nikab din yakalleki" Sati daya muka yi a Abu dhabi sannan muka tafi saudiyya a madina muka fara yada zango a Raudha zo kaga ruwan hawaye ganin ga ni kabarin sayyidina Rasulullah na zube dirshan bisa gwiwoyina ina,mika gaisuwata . Da kirarina agareshi gwarzon mazaje wanda akayi duniyar da abinda yake cikinta duk dominsa {S.A.W} Sati daya mukayi amadina muka nufi makka inda muka gabatar.Da umarar mu sosai Ahmad yake kaffa-kaffa da ni sam ba ya son ya aikata min abinda zai bata min rai ko waya da Hameeda ba ya yi agabana tunda ya fuskanci ina hassala Ahmad ya jibgo siyayya son ransa kuma duk inda ya ga kayan baby idan yayi sha'awa sai ya siya Idan nace masa me ya sa? Sai yace wai yasan nan da wata tara ya samu baby. Murmushi kawai nake don ni ma inason tabbas nasamu baby Don haka nake addu'a Allah ya amsa min bukatuna na sami babies Don ni nafi sha'awar Identical twins kamar ni da 'yar uwata humaira Abinda yabani mamaki bai wuce ganin yadda har yau babu wanda yanemeni awaya daga, gida ba sai dai Ahmad yace sunyi waya suna gaisheni kuma ba ni da waya balle na kirasu Mamina ma nasha nemanta ba na ganin ta online akullum naje ka'aba kuwa sai na roki ubangiji akan Allah yahuci zuciyar mamina ta amince ta dawo gidanmu kada Allah ya ba wa wani . Damar aurenta. Har hawaye nake ina sake jaddada bukatata ga jalla Rabbana Yau ma Ustaz shi kadai ya fita don kwana biyun da suka gabata wani matsanan cin zazzabi nake da amai Ina galabaita sosai shi kansa UstaZ gaba daya hankalinsa ba akwance yakeba Ba inda nake zuwa sai harami ina kwance na lumshe idona tamkar mai barci sai dai sabanin hakan tsagwaron tunani ne ya cunkushe min kwakwalwa ba tunanin komaib face yadda rayuwa take juyin waina na sama ya koma kasa Tabbas na amince da cewa duniya ba matabbata ba ce Ba komai acikinta fiye,da rudani rayuwar yanzu ta zama abin tsoro yau gareka gobe ga waninka Babu abinda bawa ya kamata yayi face ya tsaya ya jajirce wajen bautar Ubangijinsa. Idan bawa yayi hakan fakat ya gama sai ya mika lamarinsa ga Allah ya yi addu'a Allah ya sa ibadar da yayi karbabbiyace a wajen jallah Rabbana Saboda mutum bai san ranar mutuwar sa ba tafiya kawai kake adoron kasa baka san yaushe ne zaka mutuba kai da zaka koma kahadu da Ubangijinka to me ya kaika shagala da duniyar nan har kamanta . da makasudin da ya sa aka halicce ka? wanda ya halicce ka fa ba don ka shagala yahalicce kaba ba don ka sha ba da biki ko shan giya zuwa club neman mata ko kallon batsa ba duk manyan zunubai ne da Allah yake fushi da wanda ya aikata hakan Yi da mutum,zunde da kifce,da yafice,duka manyan laifu kane da ayanzu mutane suka dauke su ba komai ba musamman hassada da take cinye kyawawan Ayyuka kamar yadda wuta ke cinye kirare Lumshe idona na sake yi kawai sai ga hawaye na tsananin.Tsoron haduwata da Rabussamawati hakan kuma ya zama dole gare ni gareka ga kowanne dan'adam ma" Ji nayi anshafi hawayen da yake saman fuskata ko ba afadaba na san Ustaz ne,ina bude idona naganshi a durku she agabana gwiwoyin sa zube akasa ya kuma kura min ido cikin mummunan tashin hankali yakama hannuna ya damke cikin nasa kawai gani nayi shima Ustaz yana hawaye na ware idona sosai don son sanin me ya saka shi hawaye "Aysha ciwon ne yake wahalar dake tashi muje asibiti wallahi da ina da iko da na mayar da ciwon nan jikina" mikewa zaune vels / NAGA RAYUWA book 3 part 15 NAGA RAYUWA book 3 part 15 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:27 . Na saki murmushi hade da girgiza kai yallabai ba ciwo ne ya sakani kukaba natuno yadda rayuwar duniya yake kawai.Shiya daga min hankali Ustaz ya saki ajiyar zuciya kafin yayi kasa da kansa yace "Dole ya daga miki hankali Aysha ni kaina,na kanyi wannan tunanin ga duk mai tunani ma dole ya dinga wannan tunanin.Al'amarin duniyar nan dole ya baka tsoro. Abubuwan da suke faruwa acikinta dole kasan karshenta yazo saidai mutum ya na addu'ar haduwar sa da Allah salin-alin wallahi a duk sanda na tuna akwai hisabi akwai wuce siradi wanda masifarsa ta wuce kwatance amma akwai sauki ga wanda ya,dace ya yi aiki nagari, natuna akwai tsayuwa agaban wanda ya,halicce mu. Aysha ta shin hankali nakeshiga fiye da,zatonki. Nakan yi kuka tamkar raina zai fita.Amma wasu sam ba sa wannan tunanin sun shagala da duniya da abubuwan more rayuwa na duniya bayan ba don haka aka halicce mu ba. Tunda Allah {SWT} yana fada cikin littafinsa mai tsarki "WA MA KALAKATUL JINNI WAL'INSI ILLA LIYA'ABUDUN" [ba mu halicci mutum da aljanba sai don..] . Toh yanzu bawa idan dai har ya san bautar Ubangiji aka halicce shi mai zai saka ya shagala da Al'amarin duniya? sai dai fatan shiriya rayuwa yanzu tabbas ta zama abin tsoro kedai ki jajirce wajen sallolin ki biyar. Idan kin sami iko dare da rana azimin nafila musamman Litinin da Alhamis,ki jajirce wajen tilawar Alkur'ani, Zikirin safiya da maraice yawan salatin Annabi da Istig'fari hade da hailala. Idan kika aikata haka ina tabbatar miki zakije Lahira fresh MACE MUMINA matukar kin yi hakan da kyakkyawar niyya Allah yasa mudace." Cikin sanyin murya na amsawa Ustaz da "Amin" Gaba daya jikinmu yayi sanyi A ranar ko siyayyar da Ustaz yayo ban duba ba Muna,kwance Lamo sai da la'asar ta yi sannan muka fita harami wanda ba ma dawowa sai bayan isha sannan ne za mu zaga mudanyi siye-siye saikuma mudawo gida To yau bayan ishar asibiti muka nufa don jin yadda jikina yayi zafi Ustaz yakafe sai munje asibiti Dubawar farko da likitan ya yimin, ya bukaci naje agwada jinina akuma yimin test din fitsari Duk da larabci suke . Magana da Ustaz ni kam kadan-kadan nake tsinta don ban kware ba a,wajen Larabci Ustaz dai yana koya min kadan- kadan na sn dai nan gaba kadan zan iya kwarewa Larabawan da suke cikin lab din asibitin da mutunci da fara'a suka fara hidima da ni kai daga gani ka san addinin Islama ya shigesu sosai ta yadda suke koyi da sunnar mai'aiki wajen karrama dan Adam ba irin sauran wasu asibitocin mu na nan Nageriya ba da wasu ma'aikatan jinyan suke wulakanta dan Adam saboda 'yar dama da Allah ya ba su amma fa wasu na ce wanda yasan ba halinsa bane to baika mata ya damu ba. Bayan sun gama cikin mintuna kalilan suka miko min takardar sakamako suna murmushi hade da ce min "Congratulations" Shiru nayi hade da cewa "Thank you", Na juya na fice na san dai abin nema ne ya samu ciki ne dani Likitan ma murmushi yayi sannan ya,dago ya dubi Ahmad ya mika masa hannu sai da ya jijjiga hannun Ustaz din sannan ya ce "Weldone my friend congratulation" Sannan ya mika masa takardar. Ahmad yana budewa ya saki murmushi hade da daga hannunsa . Sama yace "ALHAMDULILLAHI BI NI'IMATIHI, TATUMMUSSALIHATI" ya juyo ya dubeni yace "Ayshata ki godewa Ubangiji don ya yi mana babbar kyautar da ba kowa ne yake samu ba Allah kuma ya raba ku lafiya" Murmushi na saki cikin matukar jin kunyar Ustaz. Doctor ya miko masa takardar Ustaz ya janyo hannuna ya ra bani da jikinsa cikin tausayawa yake, sake rada min "Sorry my dear how I wish zan iya mayar da shi jikina ki huta da wannan wahalar Amma ki saka azuciyarki Ibada kike Insha Allahu za ki samu rabo mai girma awajen ubangiji. "Ka ji mazan kwarai masu tausayawa matansu lokacin da suke cikin lalura kuma suke jin tamkar su mayar da cutar jikinsu. BA MUNA MAZA BA masu nuna halin ko in kula alokacin da matansa suke cikin lalura Su tsangwame su Wasu ma har kyamatar su suke nuna rashin tausawar su garesu Mu dai mun gode Allah dabai nufe mu da auren irin wadannan mutanen ba" Shukran Lillah. BAYAN SATI Jirgin mu ya ta so daga birnin Makka inda zamu yada zango akasar mu ta gado wato Nigeria. . Cikin walwala nake ta son haduwa da 'yan uwana sai dai awani barin ina alhinin barin kasa,mai tsarki Abin mamaki airport din damkam take da 'yan uwana da na Ustaz wai duk murnar an zo tarar mune farin ciki ya mamaye ni hango mami da nayi tana sakarmin da murmushi da sauri na saki Humaira da khadija kanwar Ustaz Na isa ga Mamina na rungume ta cikin matukar farin ciki ita dinma ta rungume ni ji nayi Ustaz yana cewa Mamin mu ta yi ahankali ba,ita kadai bace Mami ta sakar masa dakuwa Ni kuwa kunya ce ta dabaibaye ni ganin yadda,Ustaz ya fallasa ni ba ta re dayaji kunyar iyayen mu da suke wajen ba Ciki kuwa har da babana da nasa Sai alokacin ma na hango ashe harda mamansa Suna tsaye ne da ita da Ummana Da sauri na isa garesu ina niyyar durkusawa mama tayi saurin ka ma ni tace "Barshi Aysha ba sai kindur kusa,ba".Taraba ni da jikin tana sakarmin murmushi Ta ce Ya jikin naki? Ustaz yace kinsha jiki" Na sunkuyar da kai cikin matsanan ciyar kunya Yaya usman ne ya karaso wajen yana murmushi.Yace Aysha ina mijin naki? . Alhaji maitumbin Nair? Na wurge shi da hararar wasa duk gurin aka saki dariya Humaira Sis tace "Wai har na hango Aysha sis lokacin da take muzurai zan aure mata miji" Na kaimata duka da sauri ta buya a bayan maman Ahmad tana fadin "Taimake ni mamanmu" Duk gurin dariya ake haka muka rankaya aka shiga motoci da niyyar raka ni gida Tunda aka bude wawakeken gate din nake kallon gidan nawa da na yi wa lakabi da Aljannar duniya Titine fetal, kafin ka shiga cikin harabar gidan Shuke- Shuken da suka kewaye gidan sun matukar kawata shi. Kana shiga harabar gidan daga gefen da aka yi wani hadadden parkin space sai daya gefen da akayi wani hadadden garden da yaji grass carpet da kujeru masu lilo kala-kala sai fitulu daga can ciki kuwa wani babban Swimming,pool ne sai tsuntsaye kala- kala masu kyawun launi da suke ta yawo ciki kuwa harda aku da dawisu Gurin ya kawatu sosai Zaka hango wani step.Da wawakekiyar kofa sai karfe da ya zagaye wajen nan ne harabar gidan. Kina shiga kofa falone mai girman gaske sai kofofi guda 4 . Duk wacce kika bude falo ne guda biyu daya cikin daya sai bed room guda daya da kitchen, A babban falonma akwai wata kofa idan kika bude babban kitchen ne da ya hada kaya na al'farma akwai kofa a kitchen din da bukkoki guda uku masu kyawun fasali da kuma Swimming,pool haka tsarin gidan Ustaz tabbas gidan ya yi kyau matuka da gaske. Ina gefe jikin mamina ina kallon Humaira da su Jamila da A.Khadija da suke hada-hadar zuzzuba abinci suke kayatacci yar Walima suka hada mana ta murnar dawowa,lapiya Ni ba ta abincin nake ba so nake kawai na kebe da Mamina don haka na ja hannunta nace "Mami dan zo kiji" Wani kayataccen daki muka shiga Mami fadi take"Alhamdullahi, yanzu duk wani burina ya cika Aysha ta yi aure a inda ba za ta wulakanta ba" Ni dai murmushi kawai nake saki na zauna agefen hadadden gadon Mami kuwa stool ta ja ta zauna "mene ne wai kika rabo ni daga cikin mutane kika kawoni nan?" Na shagwabe fuskata nace "Mami tambarki zanyi, Inajinki sarkin shagwaba Ashe haryanzu wannan halin naki yana nan"UWA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 16 NAGA RAYUWA book 3 part 16 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:29 . Na yi murmushi nace "Mami don Allah anmayar da aurenki ne?, Taza ro ido tace Da wa? Na kara bata fuskata kamar karamar yarinya nace Da Abba mana A'a tace min Hawaye ya fara zubo min shikenan murnata ta koma ciki Ashe,hasashena bai zama gaskiya ba sai da ta bari na yi kukana mai isata sannan ta tuntsire da da dariya tace BURIN AYSHA MAFARKIN AYSHA YA CIKA NA KOMA GIDAN ABBANTA" Yeeeeh? yeeee'" Na saki ihu harda tsalle akan gado na ce "Alhamdulilla,mamina how comes?" Ta gyara zamanta kafin tace "Kawai dai na gaji da zarya da aiken da Abban-Aysha yake min hakan ya sa babana yace lallai sai na komo gidansu Aysha dama wani course naje na wata hudu ina dawowa babana ya mayar da aurenmu ba tare da sanina ko neman yardata ba. Sai bayan komai ya daidaita Ya kira ni ya sanar dani tilas na koma gidansu Aysha ba shawara yake ba ni ba umarni ne amatsayinsa na babana. "Haka na hakura ba koma bayan tarin hakuri da NADAMAR ABBAN AYSHA" Nayi murmushi na share hawayen dake Zubo min bayan nagama sauraren bayanin MAMIN AYSHA . Cikin zuri'ar GIDAN SU AYSHA. Mami.Tashare min hawaye hade da cewa Na sani duka,zuri'ar gidanku suna so na illa shaidan da ya so ya ruguza dukkan farin cikinmu Tun lokacin da abin yafaru na tabbatar da cewa dole,Abbanki ya shiga rudani har ya zartar da BAGAGON HUKUNCI akaina Banga laifinsa ba sam don ko waye zai iya zargin da hannuna dumu-dumu a ciki musamman yadda al'amarin yazo da sarkakiya, acikinsa. Tilas kowa ya jefa ayar tambaya akaina, duk da hakan ya jefani cikin tashin hankali ganin yadda mutane suke, kallo na ahagunce. Hakan ya sosa zuciyata abu daya da ya burgeni ganin yadda Ummanki sam ba ta amince da hakan ba. Hakan ya tabbatar min da nagartar Umma" Na ja ajiyar zuciya bayan sauraren jawabin Mami Daidai lokacin Humira ta shigo, da tsallenta turus tayi sai kuma ta juya ta na dariya Mami ta kwala mata kira Ba ta dawo ba illa amsa mata da ta yi tana cigaba da magana "Babu maishiga tsakanin uwa da 'ya dama Abba ne yace na kira masa amaryar sa suci abinci" Baki Mami tabude sai kuma ta saki murmushi . Tace "Mhn..Aysha wannan kanwar taki, da rawar kai ta ke amma Ummace take sake sangartata yarinya an mata aure amma koda yaushe sai taxo gida don tabara" Nace mami ai baki ga komaiba da bakya nan ba ki gani ba ko da yaushe Umma nanika ta take ajikinta wai ta sami gatan daba ta, samu ba Mami tace Umma ba ta da zance sai na Humaira yanzu tunda ta fuskanci ta na da ciki sai al'amarin ya bunkasa koda yaushe bakinta ba ya gajiya da fadin Allah sarki humaira Allah yaraba lapiya Yauwa da gaske kema Aysha juna biyun gareki?" Wata kunya ce talullubeni na sunne kai na ajikin mami ina dariya Mami ta dago da kaina ta ce "ke tsaya wani kike jin kunya.?" Idona na rufe na daga mata kai, Mami tace, Ba shakka amma fa aiki ja Ya sameki 'ya najin kunyar uwarta shige muje mu ci abinci." Ustaz ya na ganin mu ya taso ya tare mu yana kallon mami yace "Amaryar Abba tun dazu Abba yake aikawa a kira ki" Ya fada yana kunshe dariya Mami ta girgiza kai tace "Lallai Ustaz har da kai kenan kun mayar da ni kakar ku" Gabadaya aka dau dariya . Mamy ta zauna akujerar da take kusa da Abba aka fara cin abinci. Sai karfe 8:00 na dare kowa ya baje sai ni kadai don Ustaz ya tafi shopping.Sai alokacin na fara jin tsoron gidan musamman da na ji motsin kofa aibansan sanda na kudundune jikina ba Hankalina bai kwanta ba har sai da naji sallamar Ustaz jikinsa asanyaye ya zube ledojin da suke hannunsa ya zauna agefen kujera ya kuma zuba uban tagumi da duka hannayensa idonsa a lumshe. Da azama na mike na isa gareshi na durkusa gabansa Dafa gwiwoyinsa na yi nace Lafiya Ustaz.? Baibude idon ba illa ya matse hannayena cikin nasa Tsawon lokaci kafin ya bude idon. Araza ne,nadu be shi ganin yadda idonsa ya,yi jajir nace "Na shiga uku Ustaz waye ya mutu?" Ya hau girgiza kai "Ni namutu Aysha wallahi na kashe kaina Bansan dalilin da,ya sa mama ta tilasta min auren Hameedah ba Aysha ba zan iya adalci tsakanin ku ba wallahi yau daya da zanbarki ba kiji yadda zuciyata take bugu ba ba na son nafada halakar Ubangiji don kuwa ya umarce mu da muyi adalci atsakanin matanmu. . Ya sanar damu idan har ba za muyi adalci ba kada ma muyi biyun Aysha bazan iya adalci tsakaninku da hameeda ba ya ya zanyi? ya sake runtse ido Ni kaina hankalina yayi masifar tashi don wallahi na manta da wata Hameeda Yanzu kenan Ustaz raba mana kwana zai sunga yi? Zaidunga zuwa da kin wata ba niba Zan bude ido wata rana naga babu Ustaz agidan nan yana can wajen wata yana nunamata soyayya kamar yadda yake nuna min? na rintse idona kai ni ma wallahi bazan iya ba ban san lokacin da na fara kuka wiwi ba Ustaz ma kukan yake yi ahankali yana kuma bubbuga bayana alamar rarrashi. Daidai lokacin wayarsa tayi kara alamar ana kira Amma Ustaz yayi banza da wayar sai ni nasa hannu na dauka "MY WIFE 2" Naga an saka da sauri na ajiye masa wayar akan cinyarsa na kuma mike nashige daki da gudu Na fada kan gado tsawon lokaci sannan Ustaz ya biyo ni ya tsaya abakin gadon ban san me yake tunani ba har zuwa lokacin da ya hawo gadon ya dago fuskata na rintse Ido "Ta shi Aysha magana zamuyi" Na bude idona . "Kiyi hakuri kowa da irin tasa kaddarar mu.Tamu kaddarar kenan Zan tafi ga wata dattijuwa nan da zata tayaki zama a falo na miki kiyi ta jan Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Zan leko nagan ki gobe tunda sai jibi zandawo nan Da kudi a drawer dakina ko zaki bukaci wani abun" Rintse ido na sake yi na fashe da kuka hade da damke hannunsa kada katafi Ustaz wallahi in ka tafi zuciyata zata,iya fashewa. "Babu abinda zuciyar ki za tayi Aysha don ba akanki aka fara kishiy ba kiyi Nazari da hakan..." Ina kallo Ustaz yajanye hannunsa ya tafi Wani kukan ya sake kwacemin shi kenan ya tafi wajenta A yau ba Ustazun Aysha bane Ustazun hameeda ne kuka yaci karfina sosai tabbas kishi bala'i ne sai a yau na sake jaddada hakan Ni ce har karfe ukun dare ina kwance a haka sam na kasa rintsawa Juyi kawai nake akan gadon ina hango fuskar Ustaz yana ta zanga wa hameeda soyayya kamar yadda yakemin na sake rintse idona still hakan nake,sake gani Kawai ji nayi ina furta kalmar"Na shiga uku yanzu haka zanyi rayuwar aure da Ahmad duk . Sanda zai tafi gurin wata? Na ji kamar zan mutu Anya hakan zata yiwu? Na dau wayata ina duba lokaci karfe 3:00na dare na ga ni Ban ji shakkar komai ba na danna lambar mamina da niyyar kiranta Tsawon lokaci tana ringin kafin Mamina ta dauka ji nayi tace Aysha lapiya Atsahon daren nan? Cikin shisshikar kuka nace "Mamina na kasa barci zuciyata ciwo take ga kaina yayi nauyi Cikin kidima itama Mamin tace "Subhanallah! Shi Ustaz din yana ina?ya barki baku tafi asibiti ba?" Na sake sakin kuka da karfi nace Mami ya tafi wajenta Cikin kidima itama Mamin tace ita wa? Na ce Mami Matarsa mana hameeda"Mami tasaki nannauyan ajiyar zuciya tace "Wallahi kinbani tsoro Idan na fahimci matsalarki Aysha kishi ne ya kamata kuwa ki ajiye shi agefe duk da ansan yana da ciwo amma yana zuwar wa mutum a inda mutum yadau keshi idan kadau keshi da zafi zaizo maka da Zafi, idan kuwa kadau keshi da sauki sai ya zo maka asaukake Don haka inaso ki dauke shi da sauki please and please Aysha ki yi koyi dani da Ummanki, kada ki ba mu kunya" A novels / NAGA RAYUWA book 3 part 17 NAGA RAYUWA book 3 part 17 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:31 . Na rintse ido nace"wallahi Mamina bazan iyaba, kowacce mace da yadda Allah yayita ni Allah yayini acikin mata masu tsananin kishi Ba zan Iyaba mamina"Cikin tsawa mami tace "Zaki iya aysha kowacce mace koya take har ta saba. Haka ke wacce irin yarinyace mata nawa aka yiwa kishiya suka zauna lafiya..." Fashewa dakuka nayi ganin yadda Mami ta harziko Cikin tattausan lafazi mami tace "aysha saurare ni kiyi shiru haka maza ki tashi kije ki yi alwala kiyi sallah zaki samu sauki azuciyarki kinji?maza tashi aysha." To Nace sannan nabi shawarar mami na mike nashiga toilet cikakkiyar alwala na daura ina fitowa na fuskanci alkibla ina sallah ina hawaye acikin sujjada na dade ina kaiwa Allah kukana akan ya yaye min wannan matsanan cin kishi koda na gama agurin na kwanta ina mayar da ajiyar zuciya Tabbas wallahi kishi ciwo ne babu maganinsa sai addu'a bansan lokacin da barci ya daukeni ba Karar waya ne ya farkar dani daga nannaiyan barcin da ya dauke ni ina kai dubana kan screeb din wayar naga sunan REALITY ya bayyana. . Na san Ustaz ne nayi tsaki naduba agogo karfe 5:45 yaje yasha,soyayyarsa da barcinsa sai yanzu ya tuna dani. idan har ya damu dani meyasa bai kirani ba tun jiya? Gaba daya kashe wayar nayi namike nashiga toilet Ko da na idar da sallar barci ne ya sake yin awon gaba, dani akan sallayar. Shafar fuskata da naji anyi shi ya sa nabude idona. Ustaz ne zaune agabana ya zuba min ido cikin tausayawa Ban mike daga wajen ba illa ma dauke, kaina da nayi daga kansa na sake lumshe idona Ji nayi yasaki ajiyar zuciya yace "Aysha kiyi hakuri please ban san yadda zanyi ba Ni kaina sai ajiya na sake yarda ba Zan iya adalci atsakaninku ba Ina tare da hameeda ne kawai amma ruhina kacokam yana kan aysha ko da na kwanta juyi kawai nake ina tunaninki Gashi ba damar kiranki don ina tare da ita Zai zama kamar cin fuskane" Sake tunzira zuciyata yayi jin yace wai yana tare da ita Wato yana sanar da ni tare su ka kwana a daki daya. Yakamo hannuna tashi Aysha ba dai anan kika kwanaba akasa." Na dauke kaina cikin tsiwa nace "ina ruwanka . dani, tunda kai kayi kwanan farin ciki ka kwana a luntsumemen gado tare da farin cikin ranka Ajiyar Zuciya ya saki sannan ya saki murmushi yace kwantar da hankalinki MY ANGEL! Daga yau Ahmad ya zama naki ke kadai banbar gidan ba sai da NA SAKI HAMEEDA Wai don gulma kuma sai nazaro ido nace Saki? Ustaz why? Yalakuce min hanci "Kaji gulma Natabbatar har zuciyarki cikin farin ciki kike" Na girgiza kai "Ko daya Ustaz, ko ba komai Hameeda mace ce yar uwata ba zanso abinda yafaru da ita yafaru daniba me ya sa, ka sake ta Ustaz? Da ka barni ahankali zan saba", Ahmad ya dangirgiza kai "Ni ba zan saba ba Aysha, sam ba zan saba da rashin adalci ba koda Allah yace mu auri mace sama da daya saida ya umarce mu da muyi adalci. Idan nakasa adalcin me kike zaton zai faru dani? tashi fa,zanyi ranar lahira da shanyayyen barin jiki Me ya fi hakan takaici? shiyasa na amince rabuwar mu shine mafi alheri Tun daga mota da na fita, raina abace yake har naje gidan babu fara'a afuskata Hameeda na da kirki tatareni da abinci amma . wallahi ko fuskarta ba na gani Kece kawai acikin idona Har muka kwanta na kasa yi mata kulawa irin ta aure duk da na lura da bukatarta kenan "Shiyasa da safe na yanke shawarar rabuwa da ita bayan na mallaka mata makudan dukiya da gidaje sannan muka rabu kuma ta min kyakkyawar fahimta haka iyayenta ni ma su Abbana ba su yi fushi da ni ba don haka Ayshata takwantar da hankalinta Ahmad na tane ita kadai" Da safe na ga Mamina da ummana mamaki ya kamani ganin, dukansu fuskarsu ahade take gabana ya,shiga faduwa har ina hada harshe wajen fadin "Lafiya Mam?" Ai kuwa ta aiko min da wata harara hakan yasa na gumtse bakina Cikin fada Umma tace "kin kyauta Ayshatu saboda bakin kishinki shine kika sa sai da Ustaz ya saki matarsa" Da sauri na zaro ido nace "Ni kuma? wallahi Umma ba ruwana" Mami ciki zafin rai tace karya kike Aysha ya mukayi dake jiya? Babu ruwanta mami nida kaina na saki Hameeda saboda ba na daga cikin wadanda za su iya rike mata biyu. Bazan iya adalci atsakanin wata macen da aysha ba dakai na nayanke . Shawarar sakinta" Haka ya zauna ya dunga fahimtar da su har suka fahimta Mami tace "Dama Abba ne yace mu zo muyi mata fada, zata da hadin bakinta amma yanzu mun fahimta, hakan shine adalci, a wajen duk maza da zasu fahimci rashin adalci babbar masifa da sun rabu da auren mata matukar suka san ba za su iya adalci ba"Daga haka suka mike Ustaz yace "Umma har zaku tafi Tace "Dama abinda ya kawo mu kenan don hankalin Abba ya tashi da ka sanar dashi ka rabu Da matarka ya zata laifin Ayshatu ne" Ina kallo suka shige motarsu suna daga min hannu sai a lokacin wasu zafafan hawaye suka zubo min tunanin duka al'amuran duniya yanzu ni zasu zarga Ustaz na ji ta bayana ya hada ni da jikinsa ya ziro hannu yana share min hawaye "Mene ne na kuka My Angel? please stop it, I hate to see you crying." Cikin wata salon murya yasanar dani haka sannan yaja ni cikin gida yana sake jaddada,min zazzafar kaunar da ya sabar dani Ranar da nayi sati biyu da tarewa agidan gwarzon mijina Ustaz Ahmad Sulaiman da wuri na tashi, . Na fara shiri don zaikaini ziyara.Zuciyata cike da farin ciki don na dade ban fita ba, saboda Ustaz ba ya son yawo don haka ya rokeni ma nabar zancen karatu don shi sam ba ya sha'awar koda yaushe mace tana zarya ahanya ya mallakamin wasu manyan kamfaninsa guda biyu da gidan mai guda daya duk ya sa aka mayar da sunana akai. Tsaf na fito cikin wata hadaddiyar doguwar riga zubin misra, kalarta yelo ma adon ja. Na yi rolling da jan mayafi na yi kyau sosai, abinka da mai shigar karamin ciki fatata ta yi subul-subul tamkar bayan kifi don santsi Gidansu muka fara zuwa, nan na ga soyayyar surika ashe kawai surukai masu kirki. Mahaifiyar sa ta rungume ni sosai ajikinta da kanwarsa Khadija ita ma nan da sati biyu za ta amarce. Kayan motsa baki kala-kala mama ta sa aka ajiye min. Nakuwa ci sosai don kayan kwalama ne Sai la'asar sannan muka bar gidan Daga nan kuwa gidan Humaira muka wuce, don babu nisa sosai a tsakaninsu.Humaira sarkin rawar kai sai tsalle take da murnar ganina mahmud yana gaisheni ta cafe da cewa . "Darling ba kace ya bebinta ba" Da sauri na zabga mata harara "Wallahi Humaira sam ba ki da kunya" Ta tsuke baki "To kunyar wa zanji a nan mahmud ko Ya Ahmad?" Nayi tsaki hade da mikewa na kalli Ahmad ya hade rai tsaf wai shi yazo gidan kaninsa. Dariya ta so kubce min don sam hade girar bai karbe shi ba Sai da muka shiga mota na tuntsire da dariya nace "Yaya babba manya, irin wannan tsare gida haka?"Murmushi yayi yace "Usainan nan taki ce akwai rawar kan tsiya" Duka gidan yayyena sai da Ahmad ya kaini abinda ya ba ni mamaki bai wuce yadda suke zaman lafiya da kishiyoyin su ba tamkar 'YAN'UWAN JUNA. Na ayyana azuciyata Da ni ce bazan iya ba. Daga nan sai gidanmu karkaso kaga yadda na yi tsalle na rukunkume Mami Umma ta dakamin Tsawa tace "ke cikata ku har abada daga ke har uwar taki ba za kuyi hankali ba, bayan ga yadda kuke ita ma ba lafiyace da ita ba." Na waro ido ina kallon umma cikin mamaki na ce "Mamin? Dubifa yadda tayi kiba Umma, amma kice ba ta da lafiya?" Umma ta gallan harara To uwar maganaUWA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 18 NAGA RAYUWA book 3 part 18 Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:32 . Kibar tata ce miki aka yi ta lafiyace? Duk da ban so gaya mikiba..." Cikin magiya Mami tafa rokon Umma wai kada a gayamin na kuwa zaro ido nace "Na shiga uku me kuke boye min wane irin ciwo ne da,Mamina?" Ni sarkin hawaye tuni na sake su kamar famfo Umma ta saki salati tace "Yanzu Ayshatu kuka kike ke kam zanga lokacin da girma zaizo miki" Cikin shesshekar kuka nace "Don Allah Umma me ya same ta?" "Cikine da ita sai ki taya ta da addu'a."Aikuwa ban san lokacin da na saki dariya ba kuka yakoma dariya cikin tsananin farin ciki na sake rungume MAMINA in cewa "Alhadulillahi Allah na gode maka,da ka amsa min tawa addu'ar Allah ya raba su lafiya."Umma ma cikin fara'a take cewa "To me ye na kukan aikin gama tun da kika godewa Allah" Nace wallahi Umma kukan tsananin farin ciki ne ni na sani Umma yau wallahi ba zan iya barci ba." Umma Tace "Na sani aysha Na sake cewa "Da fa na yanke shawarar da zarar na haihu zan dankawa mami abinda na haifa ta raine shi kamar yadda ta yi min Allah na gode maka Umma tace Shine abin . Godiya Sai da na bugawa Ustaz waya atake agurin. Cikin dariya nake shaida masa shi din ma hamdala ya yi. Da Abba yadawo ma da fara'a nayi masa Murna shima dariya kawai yake yana fadin "aysha kenan" Sai dare UstaZ ya zo muka koma gida zuciyata fal da farin ciki. BAYAN WATANNI SHIDA Abubuwa da dama sun faru sun wuce. Ciki kuwa harda matsananciyar kulawa, kauna da tausayi da Ustaz yake yimin ganin ina dauke da cikin dansa ko kwakkwaran motsi Ustaz ba ya so yaga na yi. A yanzu haka ma shirye-shiryen tafiyar mu Egypt ake ni da mahaifiyarsa don yace ba zan haihu anan kasar ba Har da Mami na yake shirya mana tafiyar don ita awatan haihuwa ma take. Kwance kawai nake kaina yana wani azabar ciwo, cikina yayi turtsitsi a gabana. Kafafuwana sun yi luba- luba, haka hanci na yayi muni sosai kai gaskiya ciki ba karamin muzanta halittar mutum yakeyi ba Ammafa wasu fes za ka gansu babu abinda ya canja sai abinda ba za a rasa ba. Jin motsi nayi da kyar na juya sai naga Ustaz tsaye abayana yana doka murmushi da alamun . tsananin farin ciki a fuskarsa "Ayshatu My Angel, albishirinki?" Cikin kaguwa da son sanin mene ne nace "GORO fari katoto."madadin ya fada sai ya miko min hannu,"kama ni kitashi ki ba ni goron" Na waro ido sosai Ya kuwa tuntsire da dariya "Ayshatu kin yi kyau sosai da cikin nan." Harara na watsa masa don na san tsokana ta yake yi sannan ya cigaba da wakar da yake min "'yar beauty mai katon hanci 'yar beauty mai katon lebe." Gaba daya na shagwabe fuska nace "Kaga ka ga Ustaz ba na so" Shi ma kwaikwaya ta ya yi "Kin ga - kinga aysha ina so" Na wurge shi da pillow ya cafe yana murmushi hade da min wani fitinannen kallo "I LOVE YOU MY WIFE. Kin shagaltar dani ban gaya miki albishir din ba MAMINKI TA HAIHU" Da sauri na mike "Amma ka tsaya kana ja min rai me ta haifa tashi ka kaini" Cikin mamaki Ustaz yake kallona yace aysha ashe da kwarinki kike langabewa, dubi yadda kika tashi ahanzarce daga sanar da ke haihuwar Mami" Na kwabe fuska nace Don Allah katashi ka kaini" Babu musu ya mike ya zira min hijab dina . Muka fice daga gidan sai da muka shiga mota ya ce "Ba ki ji me ta haifa ba" Na ce metahaifa? 'yan biyu duka mata "SHUKURAN LILLAH" Nafada afili. Ustaz ya saki murmushi yace su aysha anyi kanne Da hawayena na shiga gidanmu ina tunanin ashe za mu ga wannan lokacin aduniya Tabbas Bahaushe bai yi karya ba da yace Mahakurci mawadaci kuma BAYAN WUYA SAI DADI. Na zauna a gefen gadon ina kallon mamina da fuskata cike taf da farin ciki sannan ahankali itama hawayen ya zubo mata. Umma ma hawayen take Tace "kukan farin ciki kam ya zama dole. Allah kenan da ba ayi masa dole shiya ke ba da haihuwa alokacin da yaga dama" Na dauki 'Yan biyun ina kallo kamar mu daya da su sak. Wallahi tamkar yadda nake ina yarinya Da sauri na dauki hotona babba da yake rataye a dakin mami na kara a fuskarsu. Cikin dariya mami tace "Ba saikin kara ba, kamar ku daya" Abba yace "Kwabo da Kwabo kuwa" Aka kwashe da dariya. Kafin a ce Mene ne wannan? tuni gidan mu yadinke da hayaniyar jama'a 'ya'ya da surukai da jikoki. . Kafewa na yi anan zan kwana, amma Abba ya ce tilas na tafi gidana na dawo washe gari. Amota Ustaz yake sanar da ni wai bizarmu tafito jibi za atafi Ni kuwa na zabga masa harara cikin wasa nace "Ai kai ma ka san ko birnin Lantsandan ne ba zan tafi ba ayi suna ba." "Kada muyi haka da,ke aysha kin ga watan haihuwarki ya kama, tun da dai ta haihun lafiya ba shikenan ba" Allah Ustaz kada ma ka fara don babu inda zani sai anyi suna Shiru yayi na lura ransa ne yabaci duk da haka bazan sauka daga kan ra'ayina ba.Har mukaje gida bai kula ni ba illa yadebo min abinci ya ba ni a baki harda tausar da ya saba min magana ce dai ta fatar baki ta gagara. ***** ***** ***** Tsakar dare naji bayana yayi wani irin amsawa ba shiri.Na mike jin marata ta amsa. Na daka wa Ustaz duka,shima a razane ya farka, yana duba na yace "aysha lafiya?Me ya faru?"Da kyar nace masa "Mutafi asibiti yallabai, marata kamar za ta balle" Da azama ya daukeni cak inata gumurzu Iya mai yi mana aiki da ita muka tafi asibitin. . Tsawon awa guda a asibiti ina abu daya kafim Allah ya yanke min na haifo santalelen yarona jajir da shi, gashi har gaban goshi da kibarsa dumimi tamkar diyan indiyawa. K da idona ya haskomin yaron anfita da shi wani farin ciki ne ya mamaye ni na tuna wai wannan da na ne mallakina kai Allah na gode maka "Alhamdulillah" na sake furtawa ahankali. Ahmad na ga yaturo kofar yashigo bayan da likitar tafita Cikin tsananin farin ciki ya dube ni yana da fa goshina"sannu ayshata da wahala ko? Ubangiji yasaka miki da mafificin alheri. Ayau na sake alfahari nakasan cewar ki matata da kika santalo min kyakkyawan da" Daidai lokacin Umma da Mami suka shigo mamaki ya kama ni ganin mami ita da ta haihu jiya amma tafito yau.Lallai na amince soyayyar gaskiya ce tsakaninmu kowa sannu yakemun, Maman Ahmad ta zo kafin asallatu asibitin yacika dan kam da 'yan'uwa da abokan arZiki Ahmad,kuwa sam bakinsa yaki rufuwa. Humaira ta dubeni cikin murmushi ta ce, "Aysha sis yaron nan da Ya ahmad yake kama ko kadan bai dauko ki ba Lumshe idoovels / NAGA RAYUWA book 3 part 19 the end NAGA RAYUWA book 3 part 19 the end Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:35 . Kawai nayi ta sake cewa "Ya aysha haihuwar da wahala? Wata dariyace ta kufcemin ganin ta da turtsetsen cikinta nace "Ba bayani yarinya sai ranar da kikazo yin taki sannan zaki gane shayi ruwa ne." Murmushi tayi tace tana shafa cikinta "How I wish na bude ido naga babyn.Kawai akwance a gefena batare da na sha wahala ba yana inya inya." Gaba dayan dakin aka saka dariya ganin yadda Humaira ta tsorata sosai Mamina ce ta shigo bayan ta dawo daga wajen likitan mace jaruma tamkar ba ita ce ta haihu ba Ta miko min hannu hade da cewa "Mike mu tafi na amso sallama" Dakyar na mike don jikina kam bai karasa warwarewa ba, duk inda nabi idon Ahmad a kaina "sannu aysha" shine kawai Kalaman da yake jerowa "Hope dai ba inda yake miki ciwo" Na lumshe idona hade da kada kaina koda mukaje gida Hajiyar potiskum ce ta tilastawa Mami tafiya gida fada take tana sakewa "Maza yar albarka ki tafi gida kema fa danya ce sharaf." Murmushi Mami kawai takeyi ganin yadda hajiyar potiskum take nuna mata kulawa hakan ya tabbatar Mata da dinma . bacin rai.Yasanya ta wanke kafa taje har gidansu taci zarafinta. To haka dai 'yan'uwa suka dunga nunamin kulawarsu. An yanke shawarar hada sunana da taron sunan Mami za ayi.Inda za ayi ababban hall dina wato AYSHA IMAM KHALIL {A..K RESTAURANT}. Ranar sunan da safe Ahmad ya sanar da sunan mahaifinsa aka saka wato,Sulaiman, hakan ya sa Humaira ta yi masa lakabi da AKBAR. An taru sosai ashagalin taron sunan. Manyan mutane sun halarci babban shagalin inda 'Ya'yan Mami suka ci suna NILFA da NAUFA. Sunan Mamina da ummana aka saka Mun samu kyaututtuka sosai daga manyan mutane Ustazu na kuwa yana makale da ni tamkar wani zai kwace masa ni. Tsummun idanunsa suna kaina. Daren ranar sunan Ya Ahmad ya sameni adaki azaune agefen gado na jingina da gadon ina lumshe ido tsabar gajiya ce take nukurkusata Akbar nake bawa mama. Fuskarsa adaure yake dubana Yana fareti atsakar dakin hakan ya dan razana ni. Zuwa can ya zira hannu a aljihu ya miko min ambulan fara tas. Gabana ne yafadi , narintse ido na ba ta re da nakarba ba . A zuciyata nace "shikenan an kuma" karbi mana yana fada cikin dakakkiyar murya da tsawa Hannuna na rawa na karba na bude Addu'a nake kafin na karanta. Abinda na gani ne yasaka ni mikewa ba shiri "Ni kuma da gaske Ya Ahmad? Ka ba ni kamfanin sarrafa shinkafa?" Dariya ya saki yace "Da tsorata kika yi My Angel?" Na zube gwiwa ta akasa ina sake godiya. Ya dago ni "Is enough Aysha, duk abinda nayi miki kin cancan ci fiye da hakan. Da ni da dukiyata duka mallakarki ne. Na yi miki wannan kyautar ne saboda jajircewa da kike wajen yimin biyayya akan duk abinda na umarce ki. Kin cancanci sunan MACE TA GARI, MACE MUMINA mai share hawayen mijinta a kowane,yanayi wanda hakan yayi karanci awannan zamanin da mata suke daukan kansu sune a sama bayan Ubangiji yace "Arrijalu kawwamuna alannisa'u" Ya Zama dole mace tayarda itace akasan mijinta shine shugabanta, wanda matan yanzu sundauki hakan rashin wayewa da gidadanci BURIN MACE A ce ita take juya mijinta awannan zamanin babu asarar da ta wuce hakan. Ba wayewa ba ce hakan . illa dabbanci da tabewa hade da rashin zurfaffan ilimin addini. A bayyane take macen da ta ke aikata hakan tana jayayya da hukuncin Ubangiji ne da kuma koyi da yahudu da Nasara. Da suke cewa "What man can do woman can do better". Karya ce wannan da tsagwaron jahilci.shi ya sa nake godewa Allah da ya tsame min matata daga sahun wadannan mutanen. Bayan wannan, yanzu fada min abinda kikeso." Na lumshe ido nace "Babu abinda nake so ka gama yimin komai yallabi sai abu daya kayimin Alkawarin ba za ka taba yimin kishiya ba." Cikin murmushi yace "Na yi miki alkawari Aysha ke kadai kin isheni rayuwa." Hawayen dadi ya sulmiyo min don Burina yagama cika nace . "ALHAMDULILLAH"