*🌹NAANAH🌹* Repost https://chat.whatsapp.com/Hbf1rpqVyiZCko3JyHNMcG?mode=ems_copy_c Page 1.. AUN Academy, Yola. 1:25pm Ranar ta kasance ta musamman, rana ce da kowacce daliba yar SS3 ke jira tun farkon shekara wato graduation day. Harabar makarantar ta cika da hayaniya, kiɗa-kiɗe da iface -iface sai tashi yake ta ko’ina. Girls ɗin boarding school ɗin suna ta zagaye da juna, wasu suna ɗaukar pictures da wayoyinsu, wasu kuma suna rubuce-rubuce a jikin graduation gown: “Don’t forget me please,” “Call me when you get home.” A cikin dormitory kuwa, akwati da jakunkuna sun cika ko’ina. Wasu na ta nannade kayan da ba su riga sun shirya ba, wasu kuma suna jiran iyayensu su zo ɗaukarsu.Kowacce yarinya idan ka kalli fuskarta zaka ga farin ciki mara misaltuwa. A bakin wani hostel suke tsaye, Yan' mata guda uku, farare masu kama da juna, suna sanye da rigunan graduation suna magana da juna. Da gudu ta ƙaraso wajen tana jan trolley ɗin hannunta, ta tsaya gabansu tana haki. “Kin gama packing komai?” Ɗaya daga cikin yan matan ta tambayeta, gyaɗa mata kai ta yi tana goge gumin daya tsatsafo, Ɗaya daga cikinsu ta matso kusa da ita ganin how weak she looks ta dafata ta ce“Ko wani abun yana maki ciwo Nana?” Girgiza kanta ta yi cikin sassanyar murya ta ce“a'a I'm fine kawai na matsu naje gida ne” Hameeda ta jinjina kanta kana ta ce“oh really, to ai dai duk saurin ki sai kin jira ko?” Nana ta ɗan kwaɓe fuska ba tare da ta ce komai ba. Komawa ta yi ta jingina da bango suka ci gaba da kallon jama'a, iyaye sai zuwa suke ana ɗaukan yara. Wata budurwa ce ta ƙaraso wadda ba zata shige 16yrs ba ta rungume Nana tana kuka ta ce“you know what Nana? Zan yi missing ɗinki.. dan Allah karki manta dani kinji” Kukan itama ta saka tana sake ƙanƙameta. Sai da suka ci kukansu sannan ta janye jikinta tana goge hawaye ta ce“Daddyna yazo tafiya dani, Dan Allah Nana ki zo Kano watarana kinji” cikin shessheƙar kuka ta ce“Zan zo in sha Allah bestie” sake rungume juna suka yi sannan ta janye jikinta ta maida idanunta kan yan'uwan Nana dake tsaye ta ce“Hameeda, Maimoon, Amrah Allah ya ƙaddara saduwarmu” Murmushi suka yi a tare suka ce"Amin Khadijah, ki gaida gida” ta ɗaga musu hannu sannan ta kalli Nana ta ce"bestie na tafi" "Ki gaida Mommy". Daga haka ta juya ta tafi tana ɗan waiwayenta. Tana barin wajen Nana ta sake fashewa da kuka, tasan zata yi kewar Khadijah fiye da komai, ƙawarta tun Jss1 har SS3 duk wanda ya san Nana a Aun to tabbas ya san Khadijah, yanda bata ji itama haka take bata ji, ko sanda suna Juniors senior ɗinsu basu isa suyi dealing nasu ba, har suma suka zamo seniors kuma aka basu muƙami, Nana ita ce Amira ta Aun ita kuma Khadijah ita ce health prefect. She wish a ce garinsu ɗaya da Khadijah da tabbas tasan amintarsu zata ɗore, amma yanzu kasancewar suna mabanbantan gari ta tabbata ba lallai bane su ci gaba da ƙawance. "Ke Nana ki zo zamu tafi" Muryar Maimoon ta dawo da ita daga tunanin da take, kallonta kawai ta yi sai kuma taja trolley ɗinta ta yi hanyar parking space na makarantar. Tana tafe student na mata magana, wasu su kirata da Amira, wasu kuma su ce A-shuwa. Har sun yi gaba sai kuma Maimoon ta dawo taja hannunta tana faɗin “Kina son a tafi a bar ki ne ko Nana?” banza ta yi mata ta ci gaba da janta suna tafiya har suka ƙaraso gaban babbar motar ƙirar Lexus jeep, black colour sai kyalli take. Tsayawa duk suka yi an kasa samun wanda zai yi knocking ƙofar, Hameeda ta ɗan kalli Nana murya can ƙasa ta ce“je ki buɗe” da sauri Nana ta kalleta sai kuma ta ɗauke kai. A ƙalla sun ɗauki 3mins suna tsaye kafin Maimoon ta yi shahada ta ƙarasa ta yi knocking glass ɗin gaban motar, a hankali glass ɗin ya fara yin ƙasa, zaune yake cikin motar idanunsa sanye da shade glasses black, fari ne tas mai dogon hanci sannan ga beauty beard data cika fuskarsa. Sanye yake da wata dakkakiyar shadda milk colour sai kyalli take, Maimoon ta ɗan ja numfashi kafin ta ce"Ya..Yaya Sultan" Shiru ya yi bai bata amsa ba, dan babu alamar ma yaji abin da ta faɗa, ta sake cewa "Yaya mu shigo?" Sai a sannan ya juyo da gaba ɗaya fuskarsa ya kalleta, Asalin kyakkyawan bafulatani mai cikar kamala da sura. Ya zare glasses ɗin idanunsa still looking at her ya ce"ance muku ni driver ne da zan tsaya ina zaman jiranku right?" Da sauri suka shige motar sanin halin jarabarsa. Nana ta dinga kallonsu ganin sun cike backseat ɗin motar, ta tsaya kamar statue. Maimoon ce ta mata alama data shiga da ido, ta girgiza kanta kawai sai ta fashe da kuka, bin ta ya dinga yi da wani irin mugun kallo kafin ya yi kafa ya kunna motar. Da sauri Amrah ta ce"ke ba zaki shiga ba?" Cike da masifa ta ce" to ina zan shiga? Ba yan duk kun cike motar" kallonta suka dinga yi, Maimoon ta kalli front seat ɗin ganin babu kowa ya sanya ta ce"baga gaba nan ba, ki shiga mana" "Ni bana son zama a gaban namiji" Da sauri ya kalleta sai kuma ya sauka daga motar, zagayowa ya yi inda take ya ɗago fuskarta a zafafe ya ce"Kee ni abokin wasanki ne?" Fashewa ta yi da kuka ta riƙe gefen kanta ta ce" ni bana son gaba wallahi, ni a baya zan zauna" Bai sake magana ba kawai taga ya fizge hannunta ya buɗe motar ya turata sannan ya koma ɗaya side ɗin, shiga ya yi ya kulle motar gaba ɗaya sannan ya yi mata key suka bar harabar makaranta. Kuka ta dinga yi kamar wadda aka daka, Hameeda ta dinga kallonta tana tsaki. Sun yi nisa Amrah ta ce"wai ke dallah can ki yiwa mutane shiru, wa ki ka fi iya shagwaɓa?" A fusace ta juyo baya tana kallonta fuskarta caɓa-caɓa da hawaye ta ce"ba zan yi ba ɗin, ko na shiga harkar ki?" Harararta Amrah ta yi amma bata ce komai ba. Nana ta murguɗa baki sannan ta juya ta ci gaba da kukanta. M-Shuwa Estate, No. 1–50, Off Girei Road, Dougirei, Yola North LGA, Adamawa State, Nigeria. Tun daga bakin titin ƙaton symbol yake maƙale da sunan M-Shuwa Estate, Suka dinga kallon titin cike da murna da farin cikin dawowa gida, A bakin wani katon gate suka tsaya gate ɗin ya dinga zugewa da kansa sannan ya danna hancin motar cikin estate ɗin, M-Shuwa Estate shi ne sunan dake maƙale jikin wani dogon gini wanda yafi kowanne tsayi a cikin gidan, gidaje ne birjik a ciki kowanne ɗauke da fenti fari da zinariya, kusan duk gidajen kansu ɗaya, guda ɗaya ne wanda ya sha bambam dasu, yafi kowane gida girma da tsayi. Akwai ɗan ƙaramin clinic cikin estate ɗin, hakana akwai islamiyya a ciki da kuma masallaci wanda ke haɗa duk al'ummar dake cikin estate ɗin. Wannan estate ɗin mallakin wani babban attajiri ce wato Alhaji Muhammad Shuwa, Babban mai kuɗi a cikin Adamawa dama Nigeria baki ɗaya, yana da ƙanne guda uku, Alhaji Ahmad Shuwa, Alhaji Kabeer Shuwa, sai kuma ƙaramar wato Mariya Shuwa. Sun kasance ƙannensa wanda ya raina da hannunsa sakamakon rasuwar da iyayensu suka yi tun suna ƙananu, shi ne wanda ya kula dasu har zuwa girmansu ya kuma aurar dasu bayan shima ya yi aure, ya auri wata bafulatanar mata wato Hajiya Khadijah, Mace mai halin kirki da kuma sanin ya kamata. Alhaji Muhammad Shuwa ya gida wannan estate ɗin ne domin samun ci gaba da kuma zumunci a tsakanin ahalinsa, yana da ya'ya guda shida huɗu maza biyu mata, mazan sune Abdusammad, Aliyu, Hameed, sai kuma Safwan. Yayinda matan sune Fatima da kuma Hafsa. Duk wanda ya san tarihin estate ɗin an sansu akan halaye nagari, nagarta da kuma kamewa. Hakan yasa mutane da dama ke sha'awar haɗa zuri'a dasu, sai dai ba'a samun damar haka domin a family na Muhammad Shuwa i junansu suke aure, tun yarinya na ƙarama ake mata miji a cikin gidan, da zarar ta kammala makarantar secondary sai a aurar da ita, wannan tsari an fara shi ne tun samuwar estate ɗin, kuma har zuwa yanzu tsarin yana nan, duk da Alhaji Muhammad Shuwa ya mutu shekaru goma sha biyar da suka gabata, a lokacin Nana tana da shekara ɗaya a duniya. Ba za'a taɓa cewa baya raye ba idan har aka yi la'akari da irin yanda suke gudanar da rayuwarsu cike da tsari. A yanzu Alhaji Kabeer Shuwa shi ne matsayin M-Shuwa domin shi ne wanda yake bin sa, daga shi sai Alhaji Ahmad wato mahaifin Nana. Kuma Hajiya Khadijah ita ce wadda take zartar da hukunci har yanzu a cikin gidan sannan kuma kowa yana bin ta koda baya so... A bakin wani katon duplex ya yi parking, suka sauka daga motar da gudu kowanne ya nufi apartment ɗinsu, sai da suka gama sauka sannan ta murɗa handle ɗin ƙofar amma ga mamakinta sai ta ji shi a rufe, ta juyo ta ɗan kalleshi taga danna wayarsa yake hankali kwance, muryarta na rawa ta ce"ka buɗe min zan tafi gurin Amma" shiru ya yi mata, ta dinga kallonsa kafin ta sake cewa"Yaya Sultan ka buɗe min zan sauka" ɗago kansa ya yi ya ɗan kalleta, idanunta sun cika taf da hawaye ya ajiye wayar ya gyara zamansa yana kallonta ya ce" me ki ka ce ɗazun? Ba zaki zauna kusa da namiji ba" ɗauke kanta ta yi ta dinga kallon compound ɗin gidan wanda ya cika da shuke-shuke. Hannunsa ya sanya ya jawota ta juyo da sauri tana kallonsa, tuni hawaye ya fara zubowa kan fuskarta ta ce"dan Allah Yaya ka bar ni, ka rabu dani na tafi" hannunta ya kama duk biyun ya riƙe cikin nasa still looking at her ya ce"Nana ni ki ke sharewa ko? Baki sona ko? Ni Yayanki dan nace ina sonki shikenan ki ka daina zuwa inda nake ko, ki ke gudana ko?" Fashewa ta yi da kuka ta shiga girgiza kanta tana cewa"Ni Yaya ka barni na tafi, ka barni naje naga Amma" Hannunsa ya sanya ya goge mata hawayen sannan ya ɗan hura mata iska a fuska, lumshe idanunta ta yi saboda ƙamshin mouth listener ɗin daya daki hancinta. Ya ɗago fuskarta yana kallonta sosai ya ce"kin san yanda nake sonki kuwa Nana? Ina son ki amince na aureki kin ji, zan je na faɗa Hajiya Babba nasan ba zata ƙi ba Nana, na aureki muyi rayuwarmu cikin farin ciki, kinji cutie ɗita" Kallonsa ta dinga yi can kuma ta janye hannayenta daga nasa, ta juya tana kallon waje ta ce"ka buɗe min mota na fita" yanda ta yi maganar a sanyaye ya sanya ya ɗan kalleta, ya sauke numfashi sannan ya yi unlocking motar. Da sauri ta buɗe ta fice ko takan jakarta bata bi ba, ta nufi hanyar apartment ɗinsu da gudu. Sultan yabi bayanta da kallo yana jin wani irin so da ƙaunar yarinyar a cikin ransa. Yana shirin sauka daga motar idanunsa ya sauka akan wani yanki, ɗauka ya yi ya dinga juyashi kafin ya warware a hankali “Karki manta dani, ina sonki Nana! Ina son ki! Sannan ina muradin na aureki, dake zan ƙare rayuwata, ki jirani! Wait for me NAANAH!” 08106608363 Nanameera.*🌹NAANAH🌹* Page 2... Sultan yaja dogon numfashi ya sauke har sannan idanunsa na zube kan yankin, ya karanta rubutun yafi sau biyar kafin ya linke ya ajiye gefe, ya sauka daga motar kai tsaye kuma apartment ɗin su ya nufa. Knocking ƙofar ta dinga yi kamar zararriya tana kiran "Amma! Amma!" Kusan mintuna biyu kafin azo a buɗe ƙofar, wata farar mace ce fuskarta ɗauke da mabayyanin murmushi take kallonta, ihu ta saki sannan ta rungumeta tana wata irin dariya. Amma tayi murmushi ta ɗagota tana kallonta ta ce" Yaushe zaki girma Nana?" Langwaɓar da kai ta yi ta sake rungumeta tana cewa"nayi missing naki ne fa Ammata" girgiza kai kawai Amma ta yi ta janyenta daga jikinta ta yi ta ce"to shigo ciki" gyaɗa mata kai ta yi sannan ta nufi cikin parlon da sauri. Tamkar wadda ta warke daga ciwon makanta haka ta dinga bin ƙaton parlon nasu wanda aka ƙawata shi da abubuwan more rayuwa. Ta lumshe idanunta saboda ƙamshin turaren wutar daya game ɗakin mai matukar daɗi, daman in dai ana maganar tsafta da ƙamshi to Amma ƙarshe ce. "Idan kin gama kallon sai ki shiga ciki ki yi wanka ki zo ki ci abinci" Amma ta ƙare maganar hannunta riƙe da remote tana rage gudun ac. Kallonta Nana ta yi ta ce"Amma me ki ka dafa?" Ganin irin kallon da ta yi mata ya sanya bata sake cewa komai ba, ta nufi hanyar ɗakinta. A hankali ta tura ƙofar bedroom ɗin nata, ta dinga taka fluffy rug ɗin dake shimfide akan tiles, sanyin ac da kuma turaren wuta ya daki hancinta, ta sauke ajiyar zuciya. Ɗakin nata neat and organized, royal bed ɗinta madaidaici a tsakiyar ɗakin mai shimfiɗe da farin bedsheet,sai katon teddy bear a gefe. Daga can kusurwar ɗakin a saman study table an jera littattafai na makaranta,da yar ƙaramar fitilar karatu a gefensu. Ko ina tsaf yake tamkar tana rayuwa a ciki, duk da bata nan hakan baya hana Amma gyara mata shi kullum. Ta ƙarasa ta zauna gefen gadon ta jingina da jikin fuskar gadon ta ja idanunta ta rufe tana jin wata irin nutsuwa na saukar mata. Kasancewar ta gaji sosai ga kuma yanayi mai daɗi data samu ya sanya bacci ya ɗauketa a wajen. Iska ta dinga kaɗawa a hankali, yanayin sanyin da ake ciki ya sanya taji ta takura, ta haɗe jikinta waje ɗaya. Kallonta ya dinga yi kamar ya samu tv, ganin ɗalibai na sauri ya sanya ta ɗago narkakkun idanunta ta kalleshi, murmushi taga ya yi, ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba. Gyara tsaiwarsa ya yi still looking at her ya ce"Kin gaji?" Ta girgiza kanta, kallon right hand side ɗinsa ya yi ya hango Senior master dan haka ya maida idanunsa kanta ya ce"yanzu zaku tafi?" Nan ma ta girgiza masa kai, ɗan haɗe rai ya yi kamar tana ganinsa ya ce"hala kina fama da ciwon baki ne?" Da sauri ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta girgiza kanta murya a sanyaye ta ce"sai an zo ɗaukarmu" Sir Junaid ya sauke numfashi sannan ya ce"yanzu idan ki ka je gida a ina zan dinga ganinki? Zaki dinga fitowa mu haɗu? Ko ni zan dinga zuwa estate ɗinku?" Ji ta yi gabanta ya yi wani irin faɗuwa, ta kalleshi hawaye kwance cikin idanunta ta ce"i wish so, amma ba zai taɓa yiwuwa ba, ba za'a bar ni na fito ba idan har na koma gida. Bama fita, duk abin da muke so sai dai a kawo mana, idan kaga mun fita waje to sai dai da yayyenmu maza ko kuma uncles ɗinmu and..." "And what?" Junaid ya yi saurin tambayarta. "Ba za'a bari ka zo gidanmu ba, ba zan sake ganinka ba idan har na shiga cikin M-Shuwa estate!" Nana ta ƙare maganar cikin rauni. Ya dinga kallonta bai ce komai ba, ta ɗago kanta ta kalleshi sai kuma ta sake sunkuyar da kan, Junaid ya numfasa sannan ya ce"kenan me ki ke nufi Nana? Na rabu da ke? Na rabu da soyyayar da nake miki tsayin shekaru shida? Na bari ki auri ɗan danginku? Na haƙura dake! Kin yimin adalci kenan?" Ta girgiza kanta hawaye na zubowa kan farar fuskarta ta ce"Ya zamu yi haka ƙaddara ta zaɓa mana, ban isa na bijirewa gidanmu ba, ban isa na sauya abin da suka ginu akai ba! Ban isa..." "Ki min shiru Nana! Kimin shiru! Just keep quiet!" Junaid ya daka mata tsawa yana nunata da yatsa, shiru ta yi ta kafeshi da manyan idanunta. Ya dinga huci kamar zaki kafin ya ɗauke kansa yana kwafa ya ce"Ba zan bar ki ba, sai na tabbatar dana sameki a matsayin mata, wallahi tallahi Nana ba zan bari a rabani dake ba! Ina sonki! Ina sonki! Ina sonki Nana!" A firgice ta buɗe idanunta, ta dinga kallon ɗakin tana zare idanu, hannunta ta sanya ta dafe ƙirjinta jin yanda yake wani irin bugu. Amma dake tsaye kusa da press tana linke wasu kaya data shigo dasu ta ce"lafiya?" Ta girgiza kanta murya a sanyaye ta ce"babu komai" Amma ta ɗan juyo ta kalleta sai kuma ta ce"tashi kiyi wanka, ki zo parlon ina jiranki" gyaɗa mata kai ta yi sannan ta sauko daga kan gadon ta nufi toilet tana tafe kamar babu laka a jikinta. Amma ta bita da kallo sai kuma ta girgiza kanta ta mayar da press ɗin ta rufe sannan ta fice daga ɗakin. After 20mins ta fito daga toilet ɗin jikinta na ɗigar ruwa, ta ƙarasa gaban mirror ɗinta tana gyara ɗaurin towel ɗin jikinta. Ta ƙurawa kanta kallo a jikin mirror ɗin, Nana fara ce tas kuma asalin bafulatanar yarinya, tana da kyau mai sanyi da ɗaukar hankali, hancinta dogo har bakinta, idanunta manya manyan kamar zasu yi magana, bakinta ɗan ƙarami kuma jajur dashi, gashin girarta a cuccure kuma mai yawa, haka ma gashin idonta zara-zara. Babu yanda za'a yi ka yi mata kallo ɗaya ka ɗauke idanunka, wannan shi ne sirrin duk wata budurwa a cikin dangin Shuwa, Allah ya yi musu kyau daga mazan su har matan. Shiryawa ta yi cikin wata doguwar riga ta atampa ɗinkin A-shape, ta ɗaura ɗankwalin sannan ta shafa lip gloss a bakinta, she looks so quiet, ta kalli fuskarta a madubi a fili ta ce"nayi kyau sosai" ta ƙare maganar tana murmushi sai kuma ta fice daga ɗakin da sauri. A parlon ta samu Amma zaune tana karanta wani littafi, Ta ƙarasa ta zauna kusada ita, ta ɗora kanta a gefen kafaɗarta a shagwaɓe ta ce"Ammata nagaji sosai" ba tare da ta kalleta ba Amma ta ce"ɗagani ki ci abinci sai ki huta" ɗago kanta ta yi tana kallon Amma ta ce"Ba hutawa zan yi ba wajen Hajiya Babba zan je" kallonta kawai Amma ta yi babu yabo babu fallasa ta ce"i see" sannan ta miƙe ta nufi kitchen. Ko rabi bata ci ba a abincin plate ɗin ta miƙe duk yanda ta yi missing girkin Amman kuwa, ta miƙe tana riƙe da robar exotic tana sipping, ganin tana shirin yin waje ya sanya Amma ta ce"haka zaki fita babu ko mayafi?" tsayawa ta yi tana kallonta ta ce"Amma wajen Hajiya fa zan je, yanzu zan dawo" daga haka ta yi waje da sauri, Amma ta bita da idanu sai kuma ta girgiza kai ta ci gaba da abin da take. Tafiya ta dinga yi tana yan waƙoƙinta na turanci, kowane gida a rufe yake, kai tsaye kuma gidan Hajiya Babba ta nufa. Babban duplex ne dan yafi kowane gida girma a cikin estate ɗin, ta dinga kallon gidan fuskarta ɗauke da annuri dan rabonta da Hajiya Babba wata shida kenan, ta ƙarasa da sauri ta murɗa handle ɗin ƙofar, karo suka ci, ta yi baya tana dafe goshinta. Tsayawa ya yi a jikin ƙofar ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonta. Ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta ɗauke kai tana tura baki, hannunsa ya sanya kamar zai taɓa ta, ta sake ja da baya. Harararta ya yi kana ya ce"gashi zan cire miki" hannunta ta shafa a gefen fuskarta taji gashinta a waje, da sauri ta mayar dashi cikin ɗankwalin ba tare da ta kalleshi ba ta ce"zan shige" ɗan murmushi Sultan ya yi sannan ya ce"to shige malama" daga haka ya koma ciki. Ɗago kanta ta yi ta kalleshi sannan ta shiga cikin parlon. Wani irin ihu ta saki data hango Hajiya Babba zaune kan sofa, ta tafi da gudu ta faɗa jikinta tana dariya ta ce"Hajiya Babba, nayi missing ɗinki" murmushi Hajiya Khadijah ta yi ta ce"takwara so ki ke sai kin ƙarasani?" Ɗagata Nana ta yi ta zauna gefenta tana cewa"Ni na isa Hajiya Babbarmu mai Makkah da Madina" Hajiya Babba ta dinga kallonta tana murmushi ta ce"shikenan an gama makarantar" Nana ta gyaɗa kanta tana kwance ɗankwalin kanta ta ce"Eh mana, mun zama manya" Dariya irin ta manya Hajiya Babba ta yi sannan ta ce"ai yanzu yan'uwan naki suka shiga ciki" "Su Maimoon?" Nana ta tambaya tana miƙewa tsaye, jinjina mata kai Hajiya Babba ta yi ta ce"eh su mana, kitchen suka shiga" bata sake cewa komai ba ta nufi hanyar kitchen ɗin da sauri. Tsaye ta samesu suna magana ƙasa-ƙasa, ta dinga kallonsu sai kuma ta ce"ashe kuna nan" Amrah ce ta ce"da mun yi niyyar mu zo apartment ɗinku idan muka bar nan ashe zaki zo kema" ɗan taɓe baki Nana ta yi kafin ta ce"to hirar me kuke?" Maimoon ce ta ƙarasa ta jawota murya can ƙasa ta ce"hirar Yaya Sultan muke, Hameeda ce tace wai tana mugun son shi, shi ne muke addu'a Allah yasa Hajiya Babba ta ce ya aureta, tun da daman duk ta girmemu kuma ta fimu hankali" Nana ta dinga kallonsu amma bata ce komai ba, Hameeda da ke tsaye tun ɗazu bata ce komai ba ta ƙaraso gabanta, hannunta ta kama cikin sanyin murya ta ce"Nana ina son Yaya Sultan tun ba yau ba, duk da naga shi bai fuskanci hakan ba, amma wallahi duk sanda na ganshi ji nake zuciya kamar zata fito. Ina son shi, shi nake burin na aura" ita dai Nana kallonta kawai take tana ayyana wawta irin tata, Ganin bata ce komai ba ya sanya Hameeda ta sauke ajiyar zuciya ta ce"ba zaki taimakeni bane Nana?" Numfasawa Nana ta yi still looking at her ta ce"amma kin yi ganganci Hameeda, akan me zaki fara jin kina sonsa bayan kina da tabbacin ba lallai bane ki same shi? Kin san a gidan nan babu ruwansu da wanda ki ke so, wanda ya dace dake kawai za'a baki. Akan me ki ka fara son yaya Sultan?" Hameeda ta dinga kallonta sai kuma ta juya ta fara tafiya toward direction ɗin window muryarta na rawa ta fara faɗin"kaddara! Kaddara ce Nana, ita soyyaya babu ruwanta da wanda ya dace, ina son yaya Sultan tun bansan kaina ba, wallahi ina jin idan bashi na aura ba bazan taɓa iya biyayyar aure ba. Nana inason Yaya Sultan fiye da yanda ki ke son Sir Junaid!" With so much surprised Nana ke kallonta, Ba ita kaɗai ba har da sauran dake tsaye. Ji tayi ƙafafunta suna neman gagara ɗaukanta, ta dinga kallon bayan Hameeda zuciyarta na ɗagawa. Bata ce komai ba ta juya ta fice daga kitchen ɗin gaba ɗaya. A parlon ta samu Hajiya Babba tana ganinta ta ce"Allah dai yasa ba ɓarna ku kemin a kitchen ba" ko amsa Nana bata samu damar bata ba ta fice daga parlon da sauri kamar zata tashi sama, Hajiya ta dinga bin ta da kallo sai kuma ta taɓe baki sanin halinta ta ce"abun ne ya motsa kenan". Bayan fitar ta Maimoon ta ƙarasa gaban Hameeda ta dafata cike da damuwa ta ce"meyasa zaki ce mata haka? kin san batasan ana dawo da maganar sir Junaid ko?" Juyowa ta yi tana goge hawayen fuskarta ta ce"shine zata gane halin da nake ciki, kamar yanda Nana ke son Junaid kuma take da yaƙinin ba zata sameshi ba haka nima nakeson yayanki Maimoon, Dan Allah idan har kina da dama ki taimakeni na aureshi" ta ƙare maganar kuka na kwace mata. Rungumeta Maimoon ta yi cikin shessheƙar kuka itama ta ce"zan so ace ina da wannan damar wallahi da tuni na saka kin aureshi, amma ban isa nace ga abin da zai faru ba, Allah ne kawai yasan ƙaddarar kowane ɗayanmu, kuma ba zamu iya guje mata ba, kawai ki yi addu'a" Hameeda ta dinga gyaɗa mata kai ba dan ta gamsu da maganganun nata ba. ****Koda ta shiga parlon bata samu kowa ba dan haka kawai ta wuce ɗakinta da sauri ta rufe ƙofar, jingina ta yi da jikin ƙofar ta shiga sauke numfashi da sauri da sauri, kafin daga bisani ta fashe da wani irin kuka ta sulale ƙasa kan tiles ta shiga rera kukanta. She wish zata iya ci gaba da zuwa AUN, she wish a ce ita bata kasance ƴa a cikin dangin M-Shuwa ba, da tabbata Sir Junaid shi ne wanda zai zamo miji a gareta, mutumin daya nuna mata ƙauna tun bata san kanta ba, mutumin daya sota saboda Allah ba dan wani abu ko halitta nata ba. Mutumin da take jin bazata iya haƙura da soyyayarsa ba, sai dai ƙaddara ba zata bata ikon rayuwa dashi ba, bata isa ta ce ga wanda take so a cikin gidansu ba, ba za'a taɓa yarda ba! Ba zasu yarda ba!. Nana ta sauke dogon numfashi sannan ta miƙe daya inda take ta koma kan gadonta ta kwanta a hankali kamar me tsoron wani abu, haka ta dinga tunawa da masoyinta Junaid gami da kewarsa, ta dinga jin kamar ta tashi ta koma AUN suyi rayuwarsu cikin farin ciki. Tana nan kwance tana yan matan hawayenta har bacci ɓarawo ya saceta. Ƙarfe 7:20pm ya shigo cikin gidan, kai tsaye kuma apartment ɗin Hajiya Babba ya nufa, zaune take kan sallaya tana jan cazbahar hannunta, ya ƙarasa ya zauna bayan ya yi sallama ya yi shiru yana jiranta. Sai da ta kammala laziminta sannan ta juyo tana kallonsa ta ce"Aliyu sai yanzu?" jinjina mata kai ya ce fuskarsa ɗauke da fara'a ya ce"wallahi Hajiya, na ɗan tsaya ne da wani former friend ɗina" Hajiya Babba ta ce"to bari a kawo maka abinci" girgiza kansa ya yi ya ce"a'a yanzu na dawo sai nayi wanka na shirya nagaji sosai" Hajiya Babba ta gyaɗa kanta kana ta ce"to shikenan nima isha'i zan yi na kwanta yau yaran nan duk sun gaji dani" "Su Juwaira sun shigo miki ne?" "Ai yau ba yaran bane yan matan gidan ne suka dawo daga makaranta" Aliyu ya ce"to ai ni shaf na manta wallahi su Nana danger an dawo gida kenan" Hajiya ta yi murmushi ta ce"ai har ma ta fara halin nata, daga zuwa ɗazu ta yi baƙar zuciya. Ai jira nake gobe ta yi idan Allah ya ara mana rai na kira su Kabiru azo a yi maganar aurensu kowa ya huta!" Aliyu ya ɗan yi murmushi ya ce"Daga dawowarsu Hajiya da an bari sun ɗan huta ai" Wani kallon sheƙeke ta masa kafin ta ce"hutun me zasu yi Allah na tuba? Kowacce ta huta a gidan mijinta aurar dasu zan yi!" 08106608363 Nanameera✌️*🌹 NAANAH 🌹* Page 3... Shiru ya yi yana kallonta ba tare da ya ce komai ba, Hajiya ta ci gaba da fad'in "In sha Allah zuwa gobe zan yiwa su Kabiru magana, azo a san yanda za'a yi, dan bana son akai watan gobe ba'a san matsayar aurensu ba" Aliyu ya jinjina kansa ya ce"To Hajiya Allah ya kaimu" Ta amsa da Amin sannan ta ci gaba da laziminta. Tashi ya yi bai ce mata komai ba ya nufi sama, ta bishi da kallo sai kuma ta taɓe baki. Ƙarfe 8:20 na dare Amma ta dinga knocking ƙofar, ganin har sannan bata buɗe ba ya sanya taja tsaki da ɗan ƙarfi ta ce"Nana! Nana!" Sai da ta goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta saita nutsuwarta a sanyaye ta ce"na'am Amma" "Ki fito ina jiranki" To kawai ta ce sannan ta tashi jiki a sanyaye ta zare hijabin jikinta. Sai da ta ƙarasa gaban mirror ta kalli fuskarta ta tabbatar babu alamun kuka, duk da idanunta sun ɗan kumbura. Ta gyara ɗaurin kanta sannan ta nufi ƙofa ta fita. Turus ta yi tana kallonsa, zaune yake kan sofa idanunsa zube akan tv, daga bayansa zaka gane babban mutum ne mai ƙiba, da sauri ta ƙarasa gabansa, ta zauna kusa da shi ta ɗora kanta a gefen kafaɗarsa. Ɗago kansa ya yi ya kalleta yana murmushi, Kyakkyawan bafulatani ne mai matuƙar kama da ita, ya shafa kanta cike da nutsuwa ya ce "Khadijatou" madadin ta amsa masa kawai sai ta fashe da kuka tana sake rikeshi, Ya girgiza kansa fuskarsa a sake ya ce"rigimar na mene ne kuma?" kasa magana ta yi sai shessheƙar kuka take, Amma dake zaune kujerar dake facing tasu ta dinga kallonta sai kuma ta taɓe baki. Ganin bai ce komai ba ya sanya ta kalleta a ɗan tsawace ta ce"Idan baki da abin faɗa tashi ki bar nan!" Ƙin juyowa ta yi amma tafara rage kukan nata, Alhaji Ahmad ya yi murmushi ya ce"ki yi shiru ki faɗa min me aka yi miki?" Sauke ajiyar zuciya ta dinga yi kafin ta ɗago daga jikinsa tana kallonsa ta ce"Abba kawai nayi missing ɗinka ne fa" girgiza kansa ya yi dan daman ya san kwanan zancen, ya ce"to ba gashi kin dawo ba Nana? Uhm, yanzu kukan na mene ne?" Tura baki ta yi ta ce"Abba shikenan yanzu na bar Aun? Duk friends ɗina mun rabu" Abba ya ce"Ai daman haka yake Nana, komai akai kira zai zo ya shige" ta gyaɗa kanta ta ce"Eh haka Mommy ta ce mana, ta ce daman haka rayuwa take" Abba ya jinjina kansa ba tare da ya sake cewa komai ba. Shiru parlon ya ɗauka kafin ta sake gyara zama ta ce"Abba ina alƙawarina?" Tashi ya yi yana gyara zaman hular kansa ya ce"baki manta ba kenan?" "I'll not" Ta faɗa tana washe baki. Hannunsa ya miƙo mata ta ɗora nata a kai ta miƙe tsaye, waje suka nufa Amma ta bisu da kallo kafin ta ce"a haka zata fita?" Sake kallonta ya yi sai kuma ya ce"and what's wrong with her dress?" Amma ta girgiza kanta ba tare da ta sake cewa komai ba, ya juya suka fice daga parlon. Tafiya suka dinga yi suna hira kamar abokai, yana ɗaya daga abin da ya sanya take son dawowa gida saboda Abbanta. Yanda suke hira dashi koda Amma bata yi, dan ita Amma tana da ɗan zafi wani lokacin, saɓanin Abba da kome take so shi yake yi. Ganin sun nufi gidan kawu ya sanya ta ce"Abba wajen Uncle zamu je?" Eh ya ce mata yana gyara zaman glasses ɗinsa. **** Bakinsu ɗauke da sallama suka shiga, Ummi dake zaune kan kujera ta tashi tana murmushi ta ce"wa'alaikummusalam, Sannu da zuwa Alhaji" Abba ya jinjina kansa ya ce"Yawwa sannu Maryam, Yaya yana ciki ne?" Ummi ta ce"Eh yana nan, bismillah" Abba ya saki hannun Nana sannan ya nufi hanyar apartment ɗin Alhaji Kabir ɗin. Ummi ta kalli Nana ganin yanda ta tsaya ta ce"Mai sunan Hajiya Babba zo ki zauna mana" To kawai ta ce sannan ta nemi gefen kujera ta zauna, Ummi ta ce"Nayi tunanin ai ba zaki shigo ba, kin dawo babu ko ziyara" ɗan murmushi ta yi ta ce"to ai daman jira nake Abba ya dawo sai na biyoshi" Ummi ta harareta ta ce"da yake bakisan hanyar nan ɗin ba ko" tuntsirewa ta yi dan dariya ganin irin kallon da Ummin ke mata kafin ta ce"Ai Amma ce ta hanani fitowa, cewa ta yi na zauna na huta" ta taɓe baki ta ce"ita Rabi'an?" Ta gyaɗa mata kai, Sallamar da aka yi ya sanya ta ɗaga idanunta ta kalleshi. Ya ƙaraso parlon ya zauna akan kujera ya ɗan yi baya yana jingina da kujerar ya ce"subhanallah!" Ummi ta kalleshi ta ce"har ka dawo?" Ya gyaɗa mata kai ba tare da ya yi magana ba. Ummi ta mayar da idanunta kan Nana wadda ta haɗe rai kamar ba ita ba, ta ce"zo muje kitchen na baki abu ki kai wa su Papa" kamar jira take ta miƙe tsaye tana cewa"to Ummi" daga haka ta nufi kitchen ɗin ba tare da ta yarda ta kalli inda Sultan yake ba. Sai da yaga duk sun shige kitchen sannan ya ɗago kansa ya kalli hanyar, ya miƙe ya nufi upstairs da sauri. Drinks ta zuba mata akan wani ɗan madaidaicin tray ta miƙa mata tana cewa"kai sai ki dawo ki kai musu abinci" to kawai Nana ta ce ta karɓa sannan ta fita daga kitchen ɗin. Da idanu tabi inda ya zauna da kallo ganin bayanan ya sanya ta taɓe baki, tana gama hawa saman ta kalli hanyar ɗakinsa sai kuma ta shige da sauri. Zaune ta samesu suna tattaunawa, Ta ajiye tray ɗin a ƙasa sannan ta durƙusa cike da ladabi ta ce"Papa ina yini?" Alhaji Kabeer dake zaune kusada Abba ya yi murmushi ya ce"lafiya kalao Nana, an dawo lafiya?" "Alhamdulillah" Ta bashi amsa tana wasa da fingers ɗinta, jinjina kansa ya yi ba tare da ya sake magana ba, ganin haka ya sanya ta tashi ta fice daga ɗakin. Ta dinga kallon ƙofar ɗakin kamar ta shige sai kuma ta ƙarasa, a hankali ta murɗa handle ɗin tana ɗan runtse idonta. Ta ɗan sauke ajiyar zuciya jin ƙofar a buɗe, tura ƙofar ta yi ta shiga, tayi saurin jan numfashi saboda wani irin ƙamshi daya daki hancinta, ga wani irin sanyin ac mai shiga jiki. Ta maida ƙofar ta rufe a hankali a ranta ta ce"ko meyasa yake son sanyi oh!" Ta dinga kallon tsaftace ɗakin wanda yaji luxury furnitures, komai na ɗakin white colour ne, dan ita ce favorite colour nasa, ba zaka taɓa cewa ɗakin namiji bane saboda yanda yake neat dashi, komai a muhallinsa. Ganin baya cikin ɗakin ya sanya ta nufi inda press ɗin kayansa take tana tafiya kamar mara gaskiya, buɗewa ta yi without making any sound, kayan ciki a linke suke kuma a tsaftace, komai an jera shi a inda yake, ta taɓe baki sannan ta fara dube-dube. Above 2mins amma bata samu abin da take nema ba, dan haka kawai ta miƙe ta rufe press ɗin. Drawer dake dressing mirror ta kalla sai kuma ta ƙarasa wajen da sauri ta buɗeta, murmushi ta yi ganin abin da take neman. Ta sanya hannu ta ɗauko empty bottle ɗin ta buɗe, gaba ɗaya ƙamshi ya gauraye ɗakin, ta kai bottle ɗin hancinta ta shanshana sai kuma ta yi murmushi a fili ta ce"A siyan turare kuɗinsa ke ƙarewa" daga haka ta mayar da drawer ta rufe sannan ta janyo babbar kwalbar turaren dake gaban mirror ɗin, buɗewa ta yi ta tsiyaya dayawa a ciki sannan ta mayar ta rufe ta ajiye. Ta ɗauki wanda ta ɗiba ɗin ta rufe shima sannan ta juyo, Tsabar yanda ta tsorata ya sanya ta jefar da kwalbar ta faɗi ƙasa ji ka ke "tass!" Ta tawarwatse a wajen. Nana ta dinga kallonsa tana haɗiyar miyau dakyar, tsaye yake gabanta daga shi sai ɗan boxer jikinsa sai ɗigar ruwa yake da alama daga wanka ya fito. Ta ƙurawa faffaɗan ƙirjinsa wanda gashi ya rufe shi idanu lokaci ɗaya kuma ta saki ƙara tana rufe fuskarta da hannayenta. Saurin rufe mata baki ya yi yana mata wani irin kallo, ta dinga zare idanu hawaye na biyo gefen fuskarta, jawota ya yi daga inda take tsayen suka yi very close dashi har suna jin hucin numfashin juna. Ya janye hannunsa daga kan bakinta still looking at her eyes, Sauke numfashi ta dinga yi tana riƙe da ƙirjinta. Cikin kakkausar murya taji ya ce "Me ki ke yi a ɗakina?" Yanayin yanda ya yi maganar in a serious tone ya sanya ta yi shiru bakinta na rawa, a tsawace ya ce"I said who brought you here!?" A mugun rikice ta dinga kallonsa tana girgiza kanta, magana takeson tayi masa amma tsoro ya hanata, ya yi kwafa sannan ya ce"Saboda bakida kunya ko? Haka ki ke shiga ɗakin maza without knocking ko?" Ta sake girgiza kanta. Sake tamke fuska ya yi ya ce"Ba zaki daina gyaɗa min kai kamar kadangaruwa ba" Gyaɗa masa kan ta sake yi ba tare da ta san tayi hakan ba. Wata muguwar tsawa daya daka mata ya sanya ta fadi ƙasa tana fashewa da kuka, ta riƙe ƙafafunsa cikin kuka ta ce"A... Dan...dan Allah Yaya Sultan ka yi haƙuri, daman turare fa zan ɗiba" Hannu ɗaya ya sanya ya ɗagota yana kallonta ya ce"wa ki ka tambaya da zaki ɗebi turaren?" Ta girgiza kanta sai kuma ta ce"babu kowa" ya ce"oh sata zaki fara kenan?" Muryarta na rawa ta ce"A'a dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba" Kallonta ya dinga yi ba tare da ya ce komai ba, ta sunkuyar da kanta har sannan tana ɗan shessheƙar kuka. An ɗauki aƙalla mintuna biyar kafin ya janye idanunsa daga kanta, ya bar wajen yana faɗin"bar ɗakin nan" kallonsa ta yi sai kuma ta nufi ƙofa da gudu ya juyo yana kallonta har ta fice, ya girgiza kansa yana wani irin murmushi ya ce"my mumu girl". ****Kallonta Maimoon ta dinga yi ganin yanda take haki, ta ce"Lafiyarki dai?" Kasa magana Nana ta yi sai hanyar ɗakin Sultan data nuna mata, Maimoon ta tuntsire da dariya sai kuma ta ce"ke mene ne ya kai ki ɗakinsa?" Sai da ta saci kallon Ummi da hankalinta ke kan tv sannan ta kalleta murya can ƙasa ta ce"turare naje ɗauka shine ya kamani" Rufe bakinta ta yi da hannunta ta ce"me ya ce miki?" Nana ta ɗan haɗe rai tana kallon gefe ta ce"tsawa ya yimin har sai da na faɗi ƙasa" Maimoon ta dinga dariya kamar zararriya, ganin haka yasa ta sake haɗe rai ta ce"dan baki ga yanda ya yimin bane da sai kin tausaya min" ta ƙare maganar kamar ta yi kuka. "Nana ɗauka abincin ki kai musu mana" Maganar Ummi ta katse su, toh kawai ta ce sannan ta nufi kitchen. Maimoon ta bita da idanu, sai da ta ɗebo warmers ɗin da plates sannan ta kalli Maimoon ta ce"help me mana" daga haka ta miƙa mata plates ɗin, amsa ta yi sannan suka nufi saman a tare, Ummi ta bisu da idanu. Ko minti biyu basu yi a ɗakin Papa ba suka fito, Maimoon ta tsaya tana kallonta ta ce"wai wane turaren ki ka je ɗiba?" ɗaga kafada ta yi ta ce"ni ina ma na sani, kawai naji yana da ƙamshi, sai na ɗiba" "To ina yake?" A sanyaye ta ce"ya fadi ya fashe" taɓe baki Maimoon ta yi ta ce"asara". Nana ta ce"wai kuma a haka Hameeda take cewa tana sonsa? Wannan ai sai ya kasheta da masifa barin ita da bata iya ramawa ba" harararta Maimoon ta yi ta ce"ki bari aji wannan maganar a bakin ki wallahi babu ruwana yawwa" tura baki ta yi tana yin gaba da ƙarfi ta ce"to aji ɗin mana, sai me?" Daga haka ta sauka daga stairs ɗin, Maimoon ta girgiza kai sannan tabi bayanta. **** Mama ta dinga kallonta da mamaki kafin ta ce"mene ne haka Hameeda? Meke damunki?" sunkuyar da kanta ta yi a sanyaye ta ce"babu komai Mama" rai ɓace Mama ta ce"ni ki ke cewa babu komai ko? Ni zaki kalla ki cewa babu komai!" Sallamar da aka yi ya sanya ta yi shiru, ya dinga kallonsu kafin ya ƙarasa gabanta. Ya kalli Hameeda dake zaune kan kujera kanta a ƙasa sai kuma ya kalli Mama dake tsaye ya ce"lafiya dai Mama?" "Ina fa lafiya Safwan, wai ni Hameeda ke kalla ta cewa lafiyarta kalao bayan tun da rana nagane akwai abin da ke damunta, amma ta faɗa min taƙi" Safwan ya kalleta a sanyaye ya ce"Hameeda ke dawa?" Tashi tsaye ta yi muryarta na rawa ta ce"babu komai fa Yaya, kawai ina missing Aun ne shiyasa" daga haka tabi ta gefensu ta nufi ɗakinta. Da mamaki duk suka bita da kallo, ya sauke numfashi ya ce"Allah ya kyauta" Amin kawai Mama ta ce, ya miƙa mata ledojin hannunsa ya ce"Abbansu Hamid ya ce na kawo miki" okay kawai ta ce sannan ya juya ya fita. Koda ta shiga ɗaki kwanciya ta yi ta ci gaba da rera kukanta kamar wadda aka yiwa albishir da mutuwa, ita kanta bata san dalilin kukan nata ba, a haka har bacci ɓarawo ya saceta. 2weeks later. 7:30 na safe Amma ta turo ƙofar ɗakin ta shigo hannunta riƙe da mug, kwance ta sami Nana kamar yanda ta barta. Ta ƙarasa ta ajiye mug ɗin akan drawer sannan ta hau gadon, yaye duvet ɗin data lulluɓa ta yi, idanunta a rufe yake sai rawar sanyi take ga kuma gumi daya cika fuskarta. Amma ta riƙe hannunta ta ce"tashi ki ɗan sha tea ɗin kafin Abbanki ya fito ya kai ki asibiti" dakyar Amma ta taimaka mata ta tashi zaune ta jingina da jikin gadon tana hawaye, sauka tayi ta ɗauko mug ɗin ta dawo ta miƙa mata. Hannunta na rawa ta karɓa ta kai baki, ko kwata bata sha ba ta miƙawa Amma tana girgiza kai. "Kin shanye zai taimaka miki" Muryarta na fita da kyar ta ce"Amma ba zan iya ba" daga haka ta sake komawa ta kwanta ta ci gaba da birgima akan gadon. Kallonta kawai Amma ta dinga yi cike da tausayawa dan tasan azabar irin wannan ciwon, ta tashi ta fice daga ɗakin da sauri. Tana ƙoƙarin shiga ɗakin ya fito, sanye yake da wata shadda sky blue, daka gansa kasan kuɗi ya zauna. "Daman kiran ka zan yi" Amma ta yi maganar da damuwa a fuskarta. Abba ya ce"ya jikin nata?" Girgiza kanta ta yi ta ce"da sauƙi za'a ce, kaje ka kaita asibitin dan Allah" okay kawai ya ce sannan ya nufi ɗakin nata da kansa. A durƙushe ya sameta ya ƙarasa ya tsaya yana kallonta ya ce"Daughterna" ɗago kanta ta yi ta kalleshi kawai sai ta fashe da kuka, da kansa ya kamo hannunta ya sakko da ita, ya taɓa jikinta. Zafi sosai yaji ya janye hannunsa ya jingina da jikinsa yana cewa"Ya jikin naki?" kasa magana ta yi sai kuka da take faman yi, girgiza kansa ya yi daidai lokacin da Amma ta shigo ya kalleta ya ce"ɗauko mata riga" okay kawai ta ce sannan ta ƙarasa press ɗinta. Abaya ta ɗauko da veil ta miƙo masa, da kansa ya sanya mata sannan yaja hannunta suka fita daga cikin ɗakin. Suna fitowa daga gidan motarsa na yin parking a compound ɗin, Abba ya dinga kallon motar har ya fito daga ciki, sanye yake da ƙananun kaya daga ganinsa kasan shirin fita ya yi. Ya dinga kallonsu har ya ƙaraso wajen ya ɗan risina ya ce"Good morning Abba" fuska a sake Abba ya ce"Morning Sultan, ka tashi lpy?" "Alhamdulillah" Ganin irin yanda take kwance a jikinsa ya sanya ya ce"Abba lafiya dai?" Girgiza kai Abba ya yi ya ce"wallahi Sultan wai bata da lafiya, cramps ke damunta tun cikin dare, kuma kasan yanda take yi, so shine zan kai ta asibiti" Sultan ya ɗan girgiza kansa ya ce"Ayyah subhanallahi, to ko zan tafi da ita asibitin ne Abba? Kai sai ka huta kaga" Abba ya yi murmushi sannan ya ce"Da naji daɗi wallahi dan daman ina da appointment da Ig kawai dai zan kai ta ne" Sultan ya ce"kawai ka je Abba, bari mu tafi tare" okay ya ce sannan ya ɗagota daga jikinsa. Kuka ta saka muryarta bata fita ta ce"a'a Abba ni ba zan bi Yaya ba" cikin rarrashi ya ce"sorry daughter ki bishi kin ji, idan nagama da wuri zan zo" kuka ta dinga yi ba tare da ta yi magana ba. Shi dai Sultan ya tsaya yana kallonta. Abba da kansa ya kai ta motar ya kwantar da ita sannan ya rufe ƙofar yana faɗin"take care son" Sultan ya yi murmushi ya ce"in sha Allah Abba" daga haka ya shige motar ya juya ya bar compound ɗin. Sai da suka fita daga estate ɗin gaba ɗaya sannan ya yi parking, ya juyo yana kallonta fuskarsa a haɗe kamar bai taɓa dariya ba ya ce" 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Masu nema daga farko su yi following WhatsApp channel nawa https://whatsapp.com/channel/0029Vb250h2HVvTaF6S0UP3L Page 4... "Malama rufe min baki, sai shegen son jiki ki ka ajiye, ki tashi zaune tun kafin ranki ya ɓaci" Nana ta dinga kallonsa hawaye na biyo kan fuskarta, daman tasan haka zai yi mata idan sun rabu da Abba. Kwafa ya yi ganin bata tashin ba ya juya ya ci gaba da driving ɗinsa. A babban parking space ɗin specialist hospital yola ya yi parking motar, ya sauka ba tare da ya kalleta ba. Sai da ya fito sannan ya buɗe back seat ɗin ya dinga kallonta, kwance take kamar matacciya sai sauke numfashi take. Ya gyara tsaiwarsa sannan ya ce"sakko" shiru ta yi masa ba dan bata ji maganar tasa ba, sai dan ba zata iya bashi amsa ba. Ya ɗan haɗe rai ya ce"ina magana da gunki ne Nana?" sai a sannan ta ɗago kanta, tana kallonsa da idanunta wanda suka kumbura ta ce"wallahi Yaya ba zan iya tafiya ba" ta yi maganar da iya gaskiyarta, baki buɗe Sultan ke kallonta sai kuma ya ce"to yanzu ya ki ke son nayi miki?" madadin ta bashi amsa kawai sai ta sake fashewa da wani sabon kukan, tana dafe mararta. Ganin da gaske take ya sanya ya zura kansa cikin motar ya jawo hannunta. Ya fito da ita daga motar, ganin ta yi baya zata faɗi ya sanya ya jawota jikinsa ya riƙeta sosai. Ƙoƙarin rufe motar ya yi idanunsa ya sauka akan kujerar ganin yanda gaba ɗaya ta ɓaci da stain, ya girgiza kansa sai kuma ya mai da idanunsa kanta, ya rufe motar sannan ya janyeta daga jikinsa ya jingina da motar gudun kada ta ɓata masa jiki. Idanunta a rufe yake tana sauke numfashi dakyar ko ba'a faɗa maka ba kasan ba ƙaramar wahala take sha ba. Sosai ta bashi tausayi dan hakan ya kwantar da muryarsa cikin sanyi ya ce" ki daure ki taka kinji, kin ga jikinki ya ɓaci da sai na ɗaukeki" shiru tayi har sannan bata daina hawaye ba, ya sake cewa "Nana" Gyaɗa masa kai kawai ta yi sannan ta buɗe idanun nata, hannunta ya riƙe suka fara tafiya a hankali har suka shiga cikin reception na asibitin. Gaisheda shi nurses suka fara yi, ya dinga amsawa cike da fara'a. Wata nurse ya samu ya ce ta raka Nana ɗaki yana zuwa, ta riƙe hannunta sannan ya nufi hanyar office ɗinsa. **** Ƙarfe 8:20am Aliyu ya shigo parlon, zaune ya samesu suna breakfast, ya ƙarasa yaja kujera ya zauna idanunsa zube kan Hajiya Babba ya ce"ina kwana Hajiya?" Da murmushi a fuskarta ta ce"lafiya kalau Aliyu ka tashi lafiya?" "Alhamdulillah" ya ce a takaice. "Good morning Yaya" "Good morning Bro" Suka gaida shi a tare, ɗago kansa ya yi ya kallesu. Hameed ne da Safwan, ya ɗan yi murmushi sannan ya ce"morning ya kuke?" "Alhamdulillah" Cewar Hameed yana miƙewa. Kallonsa duk suka yi kafin Aliyu ya ce"ina kuma zaka je?" Hameed ya ce"wallahi Bro I have alot to do ne a office, shiyasa nake sauri na tafi" jinjina kai Aliyu y yi sannan ya ce"Alright a dawo lafiya" Amin ya ce sannan ya mai da idanunsa kan Hajiya ya ce"Sai na dawo Hajiya" "Allah ya bada abin da ake nema" Ya amsa da murmushi sannan ya dafa Safwan ya ce"Barrister sai na dawo" harararsa Safwan ya yi sannan ya ce"Judge a dawo lafiya" dariya suka yi duka sannan ya juya ya bar wajen. Aliyu ya bishi da kallo har ya fita sannan ya ce"sometimes idan Hameed na yin abubuwa sai naga kamar Buddy wallahi" Safwan ya ajiye spoon ɗin hannunsa yana cewa"wallahi nima haka Yaya, irin halayensu ɗaya, kawai dai Yaya ya ɗan fisa rashin son hayaniya" Aliyu ya ce"Eh shi ne kawai abin da ya raba su, shi Buddy baya wasa, shi kuma Hameed yana son wasa" Safwan ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce"Wai yaushe zai dawo Yaya? Wallahi we miss him alot" Ɗan murmushi Aliyu ya yi sannan ya ce"to sai dai ka tambayeshi dan ni ban sani ba" Safwan ya tashi yana cewa"Ni babu ruwana" dariya kawai Aliyu ya yi, Hajiya da ke cin abincinta tun ɗazu ta ce"zai maka faɗa ne dan ka tambayeshi?" Safwan ya ce"Hajiya kin fa san halin kayanki, yanzu sai ya ciremin supsidy" Murmushi irin na manya ta yi ta ce"kuna gulmarsa sai na kira shi na faɗa masa" haɗe hannaye Safwan ya yi kamar zai yi kuka ya ce"Allah ya huci zuciyarki Hajiya Babba mai makkah da Madina, sai na dawo" daga haka ya yi gaba yana faɗin"Yaya sai na dawo" Allah ya tsare Aliyu ya ce yana murmushi. Hajiya Babba ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Aliyu ta ce"yaushe ya ce maka zai dawo?" sai da ya yi sipping ruwan dake hannunsa sannan ya ajiye cup ɗin ya kalleta cike da nutsuwa ya ce"cewa ya yi wai abubuwa sun yi masa yawa yanzun, amma zai duba ya gani" Hajiya ta yi shiru ba tare da ta sake cewa komai ba, sai dai yanayinta gaba ɗaya ya sauya. Lura da hakan ya sanya Aliyu ya dafa hannunta cikin sanyin murya ya ce"don't worry Hajiya, ni zan saka ya dawo in sha Allah" jinjina masa kai kawai ta yi sannan ta tashi ta bar wajen, ya bita da idanu sai kuma ya girgiza kansa. ****Ƙarfe 2:15 na rana ya turo ƙofar ɗakin, kwance take kan gadon ta rufe idanunta. Ya ƙaraso ya tsaya a gabanta, kallonta ya dinga yi ganin how beauty she's da take baccin, ya ɗan yi murmushi yana jin wani sabon so da ƙaunarta a cikin zuciyarsa, idan har ba'a aura masa Nana ba bai san halin da zai shiga ba. Yanzu idan ba ita aka zaɓa masa ba fa? ya yi tambayar cikin zuciyarsa, kawar da tunanin ya yi yana jin ƙirjinsa na wani irin zafi. Ya sunkuya ya taɓa wuyanta, babu zafi sosai sai ɗan ɗimi da ba'a rasa ba. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juya zai bar ɗakin "Yaya Sultan" Yaji ta kira shi a hankali, juyowa ya yi yana kallonta ba tare da ya amsa ba, ganin yanda ya kafeta da idanu ya sanya ta ɗan sunkuyar da kanta a sanyaye ta ce"ka maidani gida" wani irin kallon rainin hankali ya dinga yi mata kafin ya harɗe hannayensa a ƙirji still looking at her ya ce"idan naƙi fa?" shiru ta yi bata bashi amsa ba, ya zabga mata wata uwar harara sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Sai a sannan ta ɗago kanta tana murguɗa masa baki a fili ta ce"tun da dai nasan hanya sai nayi tafiyata" daga haka ta sake komawa ta kwanta tana lumshe idanu, tun gurin asuba sai yanzu taji mararta ta yi sauƙi, shiyasa take mugun tsoron ganin ƙarshen wata ya yi dan idan ta tashi menstruation ɗaiɗaikun mutane ne da ba zasu sani ba a cikin estate ɗin su, dan ciwo take kamar me naƙuda. Koda a ce tana Aun to sai an dawo da ita gida ko kuma Abba ya sanya Sultan ɗin yaje ya dubata a can. Tana nan kwance after 10mins wata nurse ta shigo, kallonta ta yi fuskarta cike da fara'a ta ce"Nana ya jikin?" ɗan murmushi ta yi ta ce"da sauƙi sister Zahra" Nurse ɗin ta gyaɗa kai ta ce"ai gashinan nagani, dan ɗazu da alama bakisan inda kanki yake ba, kedai sannu. Kina cikin irin matan da ake jarraba da ciwon mara yayin al'ada, ciwo kamar na haihuwa" langwaɓar da kai Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce"wallahi sister Zahra ji nake kamar zan mutu, ni dama bana period wallahi! Daman ni juya ce!" Tuntsirewa da dariya Zahra ta yi, Nana ta dinga kallonta sai kuma ta haɗe rai dan ta tsani a dinga mata dariya. Sai da tayi mai isarta sannan ta ce"Ban da shirme irin naki Nana wane ya ce miki juya bata period?" tura baki ta yi ta ce"nima haka naji" "Ki ka ji a bakin wa?" Zahra ta tambayeta, ɗauke kai ta yi ba tare da ta bata amsa ba. Sanin tun da tayi hakan ba magana zata yi ba ya sanya ta ce"Daman doctor ya ce nazo na tafi dake" bata ce komai ba ta sakko daga kan gadon, mayafin rigar data gani a gefen gadon ta ɗauka ta yafa sannan ta yi waje ba tare da ta sake bi ta kan Zahra ba, murmushi kawai Zahra ta yi sannan tabi bayanta. Tsaye ta sameshi a reception suna magana da wani likitan, ya dinga kallonta fuskarsa babu alamar walwala ya ce"kin zo kin shige ko sai na makeki anan wajen" tura baki ta yi sannan ta nufi hanyar fita daga asibitin tana tafe tana waiwayensa, ganin bai tawo ba ya sanya tana fita daga ƙofar reception ɗin taja ta tsaya kusa da wata flower. Ta dinga kalle-kallen sauran flowers ɗin da aka ƙawata wajen dasu, cike da sha'awa. Tun daga nesa yake kallonta da mamaki fal akan fuskarsa, he just can't believe ace ita yake gani, kasa jurewa ya yi ya nufi inda take tsaye da sauri har yana tuntuɓe, daga gefenta ya tsaya ya harɗe hannayensa a ƙirji cikin shaky voice ya ce “Nana!” A ɗan firgice ta kalli side ɗin dan bata san da mutum a tsaye ba, sai dai wanda ta gani ya sanya ta ɗan ja baya. Murza idanunta ta yi ko mafarki take amma koda ta sake buɗesa shi ta gani tsaye gabanta cikin kyakkyawar shigarsa sai murmushin da yake ƙara masa kyau yake. Girgiza kanta ta dinga yi nan take hawaye ya cika idanunta, muryarta na rawa ta ce"si...sir...sir Junaid!" sake faɗaɗa fuskarsa ya yi duk da yanda yake jin ransa a cunkushe ya ce"Nana, kin gani ko?mena faɗa miki? Idan har ke rabona ce zan sake ganinki, and gashi na ganki that's means we destined to be together.” Kuka ta fara yi, kuka na farin ciki bana baƙin ciki ba, kukan da ke nuna irin so da ƙaunar da take masa, cikin shessheƙar kuka ta ce“sir daman zan sake ganinka? kana can kana rayuwarka ko?” Saita nutsuwarsa ya yi jin kukan na neman kwace masa shima, ya ce“ina can cikin begenki da kuma tunaninki Nana, bana iya baccin yanda ya kamata. Kullum tunanina yanda zan samu haɗuwa da ke, Nana ki bani dama nazo gidanku, ki bani dama na gabatar da kaina a wajen iyayenki, na tabbata zasu karɓeni” fashewa ta yi da kuka tana ci gaba da kallonsa, she wish zata iya bashi wannan damar, ta juya tana kallon ƙofar reception ɗin gudun kada Sultan ya fito. Ganin bata ganshi ba ya sanya ta juyo tana kallonsa ta ce“Sir baka gane halin da nake ciki ba ko? Baka gane abin da nake ta faɗa maka ba ko? They won't allow me! Ba zasu taɓa barina da kai ba ni na sani...” “Amma ai baki gwada ba Nana! At least give it a try, koda sau ɗaya ne ki gwada faɗa musu kina da wanda ki ke so, ki gwada sanar dasu abin da ke cikin ranki ki ga” Ta dinga kallonsa amma ta kasa cewa komai, numfasawa ya yi sannan ya sake cewa“me ya kawo ki asibiti?” a ɗan rarrabe ta ce“da...da Yayana muka zo” “Ba dai shi zaki aura ba?” Junaid ya yi tambayar a sanyaye, girgiza masa kai ta yi, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce“yanzu ina zan sake ganinki Nana? Akwai abubuwan da nakeson faɗa miki” shiru ta yi kamar me tunani, Junaid ya sake faɗin “ko zaki je gidan Aunty ɗinki? Sai mu haɗu acan” Da sauri ta kalleshi dan ta gane in da yake nufi, sun saba haɗuwa acan idan taje hutu daga Aun. “Kin yi shiru Nana” Muryarta na rawa ta ce“But sir...” Katseta ya yi ta hanyar faɗin “just for me Nana, saboda ni!” Ta runtse idanunta tana jin zuciyarta nayi mata wani irin suya, “Nana ko...” “shikenan I'll” Ta faɗa tana goge hawayen fuskarta wasu na sake zubowa, ɗan murmushi ya yi sannan ya ce“thank you, yaushe zaki je, gobe?” “zan kiraka ranar da zan je, cause ba za'a bar ni na fita ba gobe” Ta faɗa a sanyaye. Junaid ya dinga kallonta yana jin kamar ya tafi da ita amma sanin hakan ba mai yiwuwa bane ya sanya ya ce“okay, zan jira kiran ki” gyaɗa masa kai kawai ta yi, ya sauke numfashi ya ce“i love you Nana” Kuka na ƙoƙarin kwace mata ta ce“love you too sir” Juyawa ya yi ya bar wajen da sauri jin hawaye na ƙoƙarin zubo masa. Ta dinga bin bayansa da kallo har ya nufi parking space ɗin asibitin. “Nana!” Muryar Sultan ta daki kunnuwanta, sai da ta ɗan firgita, ta sake goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta juya tana kallonsa. Bin ta ya dinga yi da kallo sai kuma ya taɓe baki, bai ce komai ba ya kama hannunta suka nufi hanyar fita daga asibitin, mamaki ya sanya ta kasa yin shiru duk yanda take jin zuciyarta a dagule ta ce“Yaya ina zamu je? Where's ur ride?” Cak taga ya tsaya, ya saki hannunta ya juyo yana kallonta fuskarsa a tamke kamar bai taɓa dariya ba ya ce“which ride? Bayan motar da ki ka gama ɓata min da ƙazanta” Saurin kallonsa ta yi ya gyaɗa mata gira, ta sunkuyar da kanta tana jin wata irin kunya na rufeta, she wish ma bata tambayeshi ba, da wannan amsar daya bata. Lura da yanda jikinta ya yi sanyi ya sanya ya ci gaba da tafiya yana ɗan murmushi, ta dinga bin sa a baya kamar babu laka a jikinta. Napep ya tsaida musu ya shiga ciki, ganin yanda ta tsaya yasa a fusace ya ce“sai nazo na ɗauke ki ne?” bata ce komai ba ta shiga ta zauna ta takure jikinta a gefe ɗaya ta zuba uban tagumi, ya kalleta sai kuma ya dauke kansa. Sai da suka zo off Girei road sannan ya sauka daga napep ɗin ya tsallaka ya shiga wani eatery dake ɗaya side ɗin, har ya dawo bata san ya fita ba dan zuciyarta tana can gurin masoyinta Junaid, tun da suka rabu take tunaninsa, tana jin ina ma ta bishi sun tafi tare. “Keee!” Sultan ya yi maganar yana kallonta, da sauri ta karɓi ledar da yake bata murya a sanyaye ta ce“an gode” “me ki ke tunani?” Girgiza kanta ta yi ta ce“babu komai” taɓe baki ya yi bai sake bi ta kanta ba har me napep ɗin ya yi parking a bakin estate ɗin. Sauka suka yi ya miƙa masa kuɗin sannan ya nufi ciki, ta dinga bin sa a baya kamar raƙumi da alaka har suka kawo gidansu dan shi ne a farko sannan nasu Sultan, tsayawa ya yi yana kallonta ya ce“tafi gida to” bata ce komai ba ta juya ta nufi ƙofar ta dinga knocking, sai da yaga ta shiga sannan ya yi gaba shi ma. Amma ta dinga kallonta kafin ta ce“sannu ya jikin?” murya a sanyaye ta ce“da sauƙi” daga haka ta dire ledar akan table ta nufi hanyar ɗakinta. Koda ta shiga ciki zare Abayar dake jikinta ta yi, ta ajiye kan drawer ta kwanta kan gadonta tana sauke numfashi. Duk da yanda ta gaji amma kasa bacci ta yi, tunanin Junaid yaƙi barinta, ko dai ta gwada abin da ya ce mata? Ta dinga saƙa haka aranta har bacci ɓarawo ya saceta. Koda aka yi la'asar Amma ta shigo ta sameta a zaune kan ladduma, hakan yasa bata sake ce mata komai ba ta juya ta fita, haka ta ƙarasa yinin ranar sukuku kamar wadda aka zane, ko wajensu Maimoon da take zuwa kullum bata je ba. Haka ma gurin Hajiya Babba. Around 8:00 na dare Abba ya shigo ɗakin da kansa, kwance ya sameta ta yi shiru tana tunani, ya zauna gefen gadon ya taɓa fuskarta yana faɗin “ya jikin naki?” tashi tayi zaune sannan ta ce"Abba sannu da zuwa” yawwa ya ce, sannan ya miƙa mata ledar dake hannunsa. Karɓa ta yi t dinga kallon ledar kafin ta sanya hannunta ta buɗe, kwalin waya ta gani ta zaro tana murmushi, iphone 13pro max ce sabuwa, ta saki wani irin ihu tana rungumeshi. Dariya kawai Abba ya yi ya ce“now you are happy ba?” gyaɗa masa kai ta yi tana sake rungumeshin ta ce“thank you so much Abbana, Allah ya biya maka buƙatunka na Alkhairi, ya baka abin da ka ke nema, ya jiƙan iyayenka, ya faranta maka yanda ka ke faranta min” Murmushin jin daɗi ya yi, wannan shi ne dalilin daya sanya baya gajiya da yiwa tilon ƴar tasa abu, koda abin dole ne akansa idan har ya yi mata sai ta yi masa irin wannan addu'ar. Ya shafa kanta cike da so da ƙauna ya ce“Amin ya hayyu ya Ƙayyum Khadijah, kema Allah ya yi miki albarka” ɗago kanta ta yi tana cewa“Amin Abbana” daga haka ta mayar da kwalin ledar ta sauka daga kan gadon tana faɗin “bari naje na nunawa su Maimoon” murmushi kawai Abba ya yi sannan ya tashi ya fito daga ɗakin, da gudu ta yi waje saboda jikinta har rawa yake taje ta nuna musu wayarta. Ta kusa kai wa gidan haske ya ɗauke, ko ina na gidan ya yi wani irin duhu, wani irin tsoro taji ya kamata, da alama solar ce ta samu matsala dan su basu san wutar nepa ba. Tun da suka tashi bai fi sau uku ta taɓa ɗaukewa ba, shi ma kuma by mistake ne sai kuma yau. Rasa yanda zata yi tayi, dan duhu na ɗaya daga abin da take tsoro a rayuwarta. Ta dinga juyi a wajen ta kasa gaba ta kasa baya, ledar hannunta ce ta fadi ƙasa ta sunkuyar da sauri tana lalubenta, dakyar ta sameta tana ɗago kanta taji ta a gaban mutum, ihun ta buɗe baki zata yi taji an rufe mata bakin, ya fizgota ta fado jikinsa. Tsabar yanda ta tsorata ya sanya ta sume a wajen daidai nan hasken ya dawo ko ina ya yi tarr dashi. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Page 5... Sultan ya dinga kallon fuskarta yana murmushi, sakinta ya yi faɗi a wajen sannan ya buɗe gorar ruwan dake hannunsa ya tsiyaya mata shi tas, a firgice ta buɗe idanunta tana sauke ajiyar zuciya saboda sanyin ruwan data ji. Ganin ƙaton mutum ta yi tsaye akanta fuskarsa babu yabo babu fallasa, sanye yake da ƙananun kaya hannunsa riƙe da empty bottle ɗin sai kuma ledar takeaway. Ganin yanda take kallonsa baki buɗe ya sanya ya ce"kin tashi anan ko sai nabi ta kanki na wuce" tura baki ta yi sannan ta tashi tana kaɗe jikinta murya can ƙasa ta ce"saboda mugunta" "Me ki ka ce?" Sultan ya tambayeta yana kafeta da idanu, girgiza kanta ta yi tana ɗaukar ledar wayarta ta ce"ni ba magana nayi ba" daga haka ta juya ta ci gaba tafiya. Da kallo ya bita har ta tura ƙofar ta shiga, ya sauke numfashi sannan ya nufi part ɗin Hajiya Babba. Zaune ta samesu a parlon suna kallo, kusan kowa na gidan yana nan, Maimoon, Juwaira, sai kuma Suhaila. Tana ganinta ta tashi tana cewa"kece da daren nan?" gyaɗa mata kai Nana ta yi sannan ta ce"eh abu nazo nuna miki" "Na ganki a jiƙe? A wannan sanyin" Maimoon ta tambayeta ganin yanda take rawar sanyi, kamar zata yi kuka ta ce"to ba Yaya Sultan bane ya watsa min ruwan sanyi" da mamaki Maimoon ta ce"me ki ka masa? Kema ki ci gaba da shiga harkarsa" Tura baki ta yi tana zama kan sofa ta ce"to ni harkarsa na shiga, kawai fa wuta ce ta ɗauke shi ne naji tsoro ashe shi kuma yana wajen, shi ne ya watsa min ruwa" Taɓe baki ta yi ta ce"ikon Allah. Me zaki nuna min?" Ledar hannunta ta miƙa tana washe baki ta ce"Abba ya bani ɗazu" Maimoon ta buɗe ledar ganin kwalin waya ya sanya ta saki ihu tana dariya ta ce"woww irin wayar Hameeda" gyaɗa mata kai Nana ta yi ta ce"nima haka nace, yanzu ya bani nace bari nazo na nuna miki" . Maimoon ta dinga juya wayar fuskarta ɗauke da mabayyanin farin ciki ta ce"wallahi na taya ki murna ke kam, daman ni ce nake da waya" A ɗan dame Nana ta ce"wai har yanzu Yaya Sultan bai bari kin yi waya ba?" "Wallahi ya hanata, kuma muma ya hana mu" Juwaira ta bata amsa daga zaunen da take. Kamar su ɗaya da Maimoon sai dai ita ce ƙarama dan Maimoon ta bata wajen 2yrs. Juyawa Maimoon ta yi ta zabga mata harara kana ta ce" dake nake magana da zaki saka min baki?" Kama bakinta ta yi tana cewa"Allah ya baki haƙuri" daga haka ta ci gaba da kallon da take. Ɗan tsaki Nana ta yi ta ce"yaran nan sun fiye raini wallahi, sai kace mu haka muke yiwa na gaba damu" Da sauri Juwaira ta kalleta sai dai bata ce komai ba, Maimoon ta yi murmushi tana faɗin"bar ta dai, ni yanzu tashi muje wajensu Hameeda sai a buɗe wayar" Miƙewa Nana ta yi tana faɗin"muje dan nima na ƙagu na buɗe wayar" okay ta ce sannan ta ware mayafin data ɗaura ta yafashi suka fita suna tafe suna hira har suka kawo apartment ɗin su Hameeda. Tsayawa suka yi a bakin ƙofar gidan suna kalle-kallen juna, Nana ta ce"after you" harararta Maimoon ta yi ta ce"wallahi ba zan shiga ba, nasani ko Daddy baya nan, kin san dai halin faɗan Mama" Nana ta ce"to me zata magana, daga zuwa wajen Hameeda?" "Ki fara shiga ke dai" Haɗe rai ta yi ta ce"to tsoron me nake ji ni, wallahi shigata zan yi" daga haka ta murɗa handle ɗin ta shige, Maimoon ta dinga kallon ƙofar ganin har wajen 2mins bata fito ba ta sauke ajiyar sannan itama ta shiga. Zaune ta sameta kusa da Mama suna magana, ta ƙarasa ta tsuguna kusa da kujera a sanyaye ta ce"Mama ina yini?" Kakar jira take kuwa ta ce"lafiya Maimuna, wannan shigar fa?" Ta ƙare maganar tana kallonta, Maimoon ta kalli kayan jikinta, riga da wando ne kuma basu wani kama jikinta ba. Jin tayi shiru ya sanya Mama ta sake faɗin "I'm talking to you fa" muryarta na rawa ta ce"na...Nana ta zo tace na rakota nan shiyasa kuma...kuma ban hau sama ba" Mama ta dinga kallonta babu yabo babu fallasa ta ce"saboda haka ya sanya ki ka fito kamar ƴar arna right? Wato kun dawo daga boarding zaku zo ku dinga yi mana irin wannan halayen ko? To na sake gani" shiru duk suka yi dan daman idan da sabo sun saba da faɗan Mama. Shiru parlon ya ɗauka na wasu sakwanni, kafin Mama ta rufe littafin dake hannunta ta zare glasses ɗin ta kalli Nana ta ce"baku san hanyar ɗakin nata bane?" Da sauri suka tashi suka bar parlon. Ta bisu da idanu sai kuma ta girgiza kanta a fili ta ce"Allah ya kyauta". Suna shiga ɗakin Maimoon taja ta tsaya tana sauke numfashi, Hameeda na tsaye jikin dressing mirror tana shafa mai da alama daga wanka ta fito, ta kallesu ganin kamar an koro su ta ce"lafiya dai? Daga ina?" Tskai Nana ta yi ta nemi gefen gado ta zauna. Ta kalleta sai kuma ta kalli Maimoon wadda ke tsaye har sannan tana sauke numfashi sai kawai ta fashe da dariya. Kallonta suka dinga yi, ta ɗaure kanta tana cewa"Mama ce ta muku faɗa right?" "Ya aka yi ki ka sani?" Cewar Maimoon a sanyaye, taɓe baki Hameeda ta yi ta ƙaraso ta zauna kan drawer sannan ta ce"Mama fa nace miki, wane bai san halin faɗanta ba" "Ai wallahi shiyasa nake tsoron zuwa wajenki, ta dinga faɗa" cewar Nana fuska a haɗe, ɗan murmushi Hameeda ta yi ta ce"sorry love, na ganku da dare?" Maimoon ce ta ƙaraso ta miƙa mata ledar tana cewa"waya Abba ya kawowa Nana, shi ne muka zo nuna miki fa" waro idanu ta yi tana karɓa ta ce"woww masha Allah, gaskiya na taya ki murna, ke Nana" Nana ta ɗan juya Idanunta tana murmushi ta ce"ke dai bari, yau ji nake kamar ba zan iya bacci ba." Hameeda ta ɓare ledar kwalin tana faɗin "sanda zaki yi baki sani ba, ranar da Yaya Hameed ya kawo min wayata haka naji" Maimoon ta ce"ki ka dinga dariya ba, ranar mun kusa haukacewa" "Yauwa ai har pictures ɗinmu zaki turan dana Aun" Nana ta faɗa tana janyo wayar Hameeda dake ƙasan pillow. Hoton Sultan ne akan screen ɗinta, yana sanye da kayan likitoci a airport ya yi murmushi, iyaka haɗuwa da kyau hoton ya haɗu. Nana ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, Maimoon ce ta lura ta taɓa ta tana cewa "what are you looking ne?" saurin ɗauke kanta tayi tana ɗan murmushi ta ce"hoton masoyin naki ki ka saka a screen?" Ta ƙare maganar tana kallon Hameeda. Fizge wayarta ta yi tana harararta ta ce"ina ruwanki da wayata?" dariya Nana ta yi tana kallonta ta ce"haba dai daga naga hoto? Maimoon ki faɗawa Yaya Sultan wallahi Hameeda na ƙaunarsa" Maimoon ta yi murmushi tana leƙa wayar Hameedan kafin ta ce"ikon Allah wayyo love! Nana kin ga wata ƙauna" tuntsirewa suka yi da dariya, Hameeda ta yi shiru tana kallonsu fuskarta a haɗe kamar ta fashe da kuka, sai da suka yi mai isarsu sannan suka yi shiru, ita dai ta ci gaba da buɗe wayar Nana duk da yanda take jin wani iri a ranta. Da kanta ta haɗa mata komai dan har da sim card a ciki, ta sai ta mata icloud sannan ta tura mata duk pictures da videos nasu, sai wajen 9:20pm sannan suka bar gidan kowa ya nufi hanyar gidansu. Koda taje gida bata ga kowa a parlon ba, dan haka ta shige ɗakinta ta rufe ƙofar, ajiye wayar ta yi a gaban drawer sannan ta shige toilet. Tana fitowa daga wanka ta shirya a gurguje sannan ta nufi kan gado ta kwanta tana riƙe da wayarta, kalle-kallen hotunan ta dinga yi har wajen goma saura, sannan ta shiga WhatsApp ɗin da Hameeda ta buɗe mata. Hira ta ɗan yi da few friends nata ana ta yaushe rabo, sun daɗe suna magana da Khadijah kafin ta fara jin bacci dan ta saba da wuri take kwanciya. Dan haka suka yi sallama ta kashe datar ta ajiye wayar gefen side drawer sannan ta kwanta abin ta.. Washegari ya kasance juma'a ce dan haka bata tashi da wuri ba, around 9 na safe ta fito parlon hannunta riƙe da wayarta tana dannawa tana murmushi. Abba ne zaune a parlon sai Sultan da shigowarsa kenan bayan kiran da Abban ya yi masa, sam bata lura dasu ba, dan hankalinta gaba ɗaya na kan wayarta saboda hirar da suke da Khadijah. Amma ta fito daga kitchen hannunta riƙe da ɗan madaidaicin tray me ɗauke da kayan tea, kallonta ta dinga yi har ta ajiye tray ɗin sannan ta kalleta ta ce"Nana!" Da sauri ta ɗago kanta ta kalli Amman sai kuma ta ce"morning Amma" "Baki da kayan kasawa ne?" Amma ta yi tambayar, kallon kayan jikinta ta yi wata armless vest ce a jikinta sai wando wanda bai shige gwuiwarta ba, masu kala ɗaya, kanta ko ɗankwali babu dogayen kitson kalbar ya sakko kan kafaɗunta. "Tambayarki nake" Murya a ɗan shaƙe ta ce"a..ai daman yanzu zan sauya kaya" Harararta Amma ta yi sannan ta nufi hanyar kitchen abinta, tura baki ta yi tana shirin komawa ɗakin Abba ya kira sunanta, dawowa ta yi ta ƙarasa parlon tana kallonsa ta ce"morning Abbana" murmushi ya sakar mata yana jan hannunta ya ce"morning daughter kin tashi lpy?" Sai da ta zauna a kusada shi sannan ta ce"Alhamdulillah, jiya kwana nayi ina tunanin wayata Abba" ya girgiza kansa jin zata fara shirmen ya ce"baki ga yayanki ba?" Sai a sannan ta ɗago kanta ta kalleshi, zaune yake kan sofa sanye da sport wear, ta ɗan tura baki murya can ƙasa ta ce"morning Ya Sultan" babu yabo babu fallasa ya ce"morning ykk?" "Alhamdulillah" Ta faɗa tana mai da Idanunta kan Abba ta ce"Abba dan Allah zan je gidan Aunty Ramlah an jima" shiru Abba ya yi yana kallonta can kuma ya ce"har kin ji sauƙi ne?" saurin gyaɗa masa kai ta yi ta ce"Eh naji sauƙi Alhamdulillah" numfasawa ya yi kana ya ce"shikenan Allah ya kaimu" murmushi ta yi tana kallonsa ta ce"Amin thank you Abba" murmushin shima ya yi sannan ya ce"ki shirya idan Sultan zai fita sai ya yi dropping ɗinki" da sauri ta kalleshi lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke, murya a sanyaye ta ce"Abba ba kai zaka kai ni ba?" jan kumatunta ya yi ya ce"i have alot to do Nana, kuma kin ga next week zan je Abuja dole nayi covering abubuwan da ke gabana" langwaɓar da kai ta yi ta ce"ayyah to Abba kawai sai na hau napep, na hutar da Yaya" girgiza kansa ya yi ya ce"a'a Sultan zai tafi dake" Tura baki ta yi ta ce"amma Abba..." "Nana!" Ya kirata a ɗan tsawace, sunkuyar da kanta ta yi sanin halinsa ta ce"I'm sorry" fuska a haɗe kamar ba shi ba ya ce"tashi ki tafi" bata sake cewa komai ba gudun kada ya hanata ta tashi ta nufi ɗakinta a sanyaye..sai da ta bar wajen sannan ya kalli Sultan ya ce"dan Allah kar ka bari ta tafi ita kaɗai" murmushi ya yi ya ce"in sha Allah Abba" okay Abba ya ce sannan Sultan ya mike dai-dai nan Amma ta fito daga kitchen riƙe da wani tray, ganin yana shirin tafiya ya sanya ta ce"a'a kai what do you mean?" Shafa kansa ya yi yana ɗan murmushi y ce"tafiya zan yi Amma" harararsa ta yi ta ce" zauna ka yi breakfast my friend!" Ganin yanda ta haɗe rai babu alamar wasa ya sanya ya koma ya zauna ba dan yaso ba, ta yi serving ɗin su shi da Abba suka yi breakfast ɗin.. Tun da ta koma ɗaki take kwance tana yan matan hawaye, koda wasa bata son bin sa, to amma kuma tana son taje gidan Aunty Ramlah ko dan alƙawarin da ta yiwa Junaid, haka ta dinga tunane-tunanenta har wajen ƙarfe 11 na safe, sannan ta tashi ta nufi toilet, wanka ta yi ta shirya cikin wata atampa glitter mai coffee and pink, ɗinkin t-boubou da straight skirt, ta yi ɗaurin ture kaga tsiya wanda ya yi mata kyau sosai atampar ta haskata sosai. Kallon kanta ta yi a madubi sai kuma ta dauki eye pencil ta yi zagayen baki dashi, sannan ta saka a idonta ta shafa lip gloss nan take ta zama wata babbar mace mai aji da kyau, pink ɗin dan kunne da sarka ta saka sannan ta yafa coffee ɗin mayafi, ta dauki handbag coffee da takalmi golden ta saka. Sosai ta yi kyau abin ta kamar sabuwar amarya, ta ɗauki wayarta sannan ta fito parlon lokacin 12 na rana ta kawo kai, zaune ta sami Amma tana karatun Alkur'ani, tana ganinta ta rufe qur'anin kana ta ce"tun yanzu zaki tafi?" gyada mata kai ta yi ta ce"Eh haka Abba ya ce da wuri zai yi dropping ɗina, idan ya dawo sai ya biya ya ɗaukoni" Amma ta ce"to ki gaisheda Ramlam kuma kar ki kai dare" to kawai ta ce sannan ta nufi waje da sauri. A compound ɗin ta iske Maimoon tana watering flowers tana ganinta ta ajiye butar tana murmushi ta ce"Hajiya Nana duniyar ƙawa, ina kuma zaki je haka?" She just roll her eyes sai kuma ta ce"gidan Aunty Ramlah zan je" Maimoon ta dinga kallonta sai kuma ta ce a hankali "wajen sir Junaid zaki je?" gyaɗa mata kai ta yi cikin raɗa ta ce"Eh zai zo can sai mu haɗu" Maimoon ta girgiza kanta ta ce"Nana baki tsoron abin da zai je ya dawo?" Taɓe baki ta yi ta ce"ni babu abin da nake tsoro in dai zan haɗu da sir Junaid ai shikenan" ƙarar buɗe ƙofar da suka ji shi ya hanata magana, a tare suka juya suna kallon wajen, Sultan ne ya fito, yana sanye da wani yadi mai shara-shara ɗinkin riga da wando, ya ɗora hula akansa idanunsa maƙale cikin shade glasses. Daga ganshi kaga rich and classic guy, ya ƙaraso wajen cikin takunsa na isa. Nana ta kalli Maimoon sai kuma ta ce"sai na dawo" "Dashi zaku tafi?" Ta gyada mata kai. Fuska a haɗe kamar koda yaushe ya ce"sai nace ki zo mu tafi?" tura baki ta yi sannan ta yi gaba, ya bita da harara sai kuma ya yi gaba shima yana amsa addu'ar Maimoon.. Har suka fita daga cikin estate ɗin babu wanda ya ce uffan, ganin ya ɗauki hanya ya sanya ta ɗan ƙara sauri har ta cimmasa, murya a sanyaye ta ce"Yaya ina motar to? Nifa nagaji" Hannunta ya riƙe cikin nasa ba tare da ya kalleta ba ya ce"mota, wace motar? Ai a ƙafa zamu tafi!” 08106608363 Nanameera..*🌹 NAANAH 🌹* Page 6... Cak ta tsaya tana kallonsa da mamaki, shi kuwa ya haɗe ransa ya ce"mene haka?" kwantar da murya ta yi ta ce"Haba Ya Sultan sai ƙafata ta yi ciwo ai, dan Allah ka ɗauko motar ka ko ta tsaida mana napep" Sultan ya zare glasses ɗin idanunsa yana kallonta fuska a haɗe ya ce"ni nace ki lalata min mota da ƙazanta? To ba'a kawon daga car wash ba, saboda haka let's go malama!" Muryarta na rawa ta ce"amma Yaya..." "Shhhhhh!" Sultan ya faɗa bayan ya ɗora hannunsa bisa bakinsa, kasa cewa komai ta yi amma tuni idanunta suka sauya kala, ya riƙe hannunta suka ci gaba da tafiya. Har suka zo babban titi bai ce komai ba, ita dai binsa kawai take duk da yanda take jin ƙafafunta kamar zasu ɓalle. Ganin suna shirin tsallaka titi ya sanya ta rikeshi da ɗaya hannun nata, juyowa ya yi yana kallonta sai kuma ya ce"lafiya dai?" Cikin shassheƙar kuka ta ce"dan Allah Yaya Sultan ka samar mana napep, ko kuma ka maidani gida nagaji" harararta ya yi ya ce"ba zan yi ba" daga haka ya ja hannunta suka tsallaka titin. Ci gaba da tafiya suka yi, tana tafe tana gudu-gudu saboda yanda yake tafiya cike da zafin nama. Ana kiran sallar ƙarfe 1:00 na rana suka ƙaraso gaban wani babban masallacin juma'a, kallonta ya yi ya ce"zo ki zauna acan nayi sallah sai mu ci gaba da tafiya" saurin gyaɗa masa kai tayi dan daman neman wajen hutawa take. Sai da ya rakata har wajen data zauna sannan ya ce"kar ki kuskura ki bar nan, kuma kar ki kula kowa" gyaɗa masa kai ta sake yi, ya juya ya nufi cikin masallacin. Lumshe idanunta ta yi ta jingina da kujerar hawaye na zubowa kan kuncinta, iyaka azaba yau Sultan ya gana mata, bata saba tafiya irin haka a ƙasa ba, dan duk inda zasu je kai su ake yi. Tana nan zaune har aka idar da sallar mutane suka fara fitowa, ta dinga bin su da kallo a ƙoƙarinta na son ganin Sultan, sai dai har bayan mintuna ashirin babu shi babu dalilinsa. Nana ta sauke idanunta kawai ta fashe da kuka, to ko dai tafiya ya yi ya bar ta anan? Wani ɓangare na zuciyarta ya sanar da ita hakan. Kawar da tunanin ta yi dan tasan ba zai tafi ya bar ta ba, ta ci gaba da kallon harabar masallacin tana jiran tsammanin fitowarsa. Ƙarfe 1:43pm ya ƙaraso wajen hannunsa riƙe da wayarsa, sam bata lura dashi ba dan idanunta a rufe suke tana faman hawaye. Ɗan murmushi ya yi sai kuma ya ce “Nana!” Da sauri ta ɗago bayan ta buɗe idanunta, kallonsa ta dinga yi amma bata ce komai ba. Gaba ɗaya ta birkice kamar ba ita taci kwalliya ta fito daga gida ba, ɗankwalin kan nata ma tuni ya kwance. Fuska a sake ya ce"kin yi sallah?" Girgiza kanta kawai ta yi, ya ce"but why? Ko baki yin sallar?" ɗago idanunta ta yi suka haɗa ido ta sauke nata ba tare da ta ce komai ba. Sarai ya san da bata sallahr amma ya tambayeta, jin tayi shiru ya sanya ya ce"ina magana da statue ne Nana?" "Bana yi!" Ta ce a takaice, murmushi ya yi sai kuma ya ce"alright, tashi mu tafi" dakyar ta miƙe saboda yanda ƙafafunta suka kumbura, ya riƙe hannunta suka bar wajen. Suna fitowa daga gate ɗin taga ya nufi wajen motarsa, ta dinga kallon baƙar motar da ke kyalli, ashe daman da motar ya zo? To ko yanzu aka kawo masa? Ta yi tambayar a zuciyarta.. "Shiga mana" Maganar Sultan ta katseta. Bata ce komai ba ta buɗe murfin ta shiga front seat tana sauke numfashi, juyawa ya yi ya shiga driver seat sannan ya yiwa motar key ya yi reverse suka bar wajen. Har suka je Gimba road babu wanda ya ce wani abu, Nana sai faman matsa ƙafarta take tana runtse ido, ta gefen ido ya kalleta ba tare da ya ce komai ba. A No.34 state lowcost ya yi parking, daidai wani ƙaton gida, sai a sannan ya juyo ya kalleta ganin yanda take riƙe da ƙafar yasa ya ce"mene ne?" Jin yanda ya yi maganar cike da kulawa ya sanya ta saki jikinta a ɗan shagwaɓe ta ce"Yaya Sultan ƙafata zata cire zafi take min!" Ta ƙare maganar tana yarfe hannu, kallon ƙafafun ya yi sai kuma ya ce"to ko za ki shafa man zafi?" saurin gyaɗa masa kai ta yi, ya zaro kwalbar aboniki daga aljihunsa ya miƙo mata. Karɓa ta yi sai kuma ta ɗago ƙafafun nata tafara janye skirt ɗin, fararen ƙafafunta suka bayyana, Sultan dai sai kallonta yake ba tare da ya ce komai ba. Sai da ta buɗe cealing ɗin jikin kwalbar sannan ta cire murfin, ƙoƙarin shafawa ta fara yi amma sai taji gaba ɗaya ta matsu saboda yanda ta yi da ƙafafun nata, ɗago kanta ta yi ta kalleshi murya a sanyaye ta ce"Yaya ko zaka shafa min?" "Baki da hannu ne?" Langwaɓar da kanta ta yi kamar zata yi kuka ta ce"i can't ne" bai sake cewa komai ba ya amshi kwalbar yana kallonta, saurin ɗoro ƙafafun nata ta yi tana shirin sauke su kan cinyarsa, ganin irin kallon da yake mata ya sanya ta ce"can i?" tsaki y yi ya jawo ƙafafun ya ɗora kan cinyarsa sannan ya fara shafa mata man a hankali yana bin ko ina yana shafawa, lumshe idanunta ta yi ta buɗe tana kallonsa, ɗago kansa ya yi ya kalleta ta yi murmushi tana dauke kanta, murmushin shima ya yi ya janye ƙafafun yana girgiza kansa. Sauke skirt ɗinta ta yi ta ɗauki jakarta tana kallonsa ta ce"Yaya na jiraka?" gyaɗa mata kai ya yi ta buɗe motar ta sauka tana ɗaga masa hannu, sai da yaga ta shiga cikin gidan sannan ya sauke zazzafan numfashi, gaba ɗaya ji ya yi wata irin kasala ta rufe shi, ya ɗan jima a wajen kafin ya yiwa motar key ya bar kofar gidan.. **** Nana ta dinga kallon Inteesar tana murmushi ta ce"ina Aunty take?" yarinyar da bazata shige 10yrs ba ta ce"tana ɗakin Daddy" okay Nana ta ce sannan ta gyara zamanta kan sofa ta maida idanunta kan tv inda ake haska wani cartoon a MBC 3, after 5mins sannan Aunty Ramlah ta buɗe ƙofa ta fito, washe baki ta yi tana kallonta ta ce"Nana ce a gidan?" murmushi ta yi tana kallonta ta ce"eh auntie ina yini?" Sai da ta zauna kan kujera sannan ta ce"lafiya kalao, Ya Amma?" "Tana nan klao Aunty, ta ce na gaisheki." Aunty Ramlah ta mike ta ce"ina amsawa" daga haka ta nufi kitchen, drinks ta kawo mata ta ajiye kan table ta ce"drink it Ina zuwa" okay kawai Nana ta ce, ta juya ta koma kitchen. Kunun aya ta ɗauka ta sha tana lumshe ido, ta gaji sosai kuma ga yunwa da take ji, wayarta ta zaro a jakarta ta kunna taga 3missed calls da wata number, tashi ta yi tana kallon Inteesar ta ce"bari naje toilet" okay ta ce sannan ta nufi hanyar ɗakinta ta shiga. Sai da ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta shiga dialing numbern, ringing biyu aka ɗauka daga ɗaya ɓangaren ya ce "Nana you keep me waiting" Ƙasa ta yi da muryarta ta ce"sorry, ina gidan yaushe zaka zo?" Sir Junaid dake kwance kan gadonsa ya ce"zuwa 4 ya yi?" Gyaɗa kanta ta yi kamar tana gabansa sai kuma ta ce"Eh nima yanzu nazo, zuwa sannan naci abinci na huta" okay ya ce sannan ta kashe wayar. Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon screen ɗin wayar sannan ta juya ta fice daga ɗakin. Zaune ta sami Aunty Ramlah tana magana da Inteesar, ta ƙarasa ta zauna gefenta ta jingina daga jikinta, murmushi Aunty Ramlah ta yi ta ce"to mage sarkin son jiki, ni kar ki tausheni" a shagwaɓe ta ce"nagaji ne fa, Yaya ne ya sanya nayi tafiya a ƙafa" "Wane yayan?" "Yaya Sultan mana" cewar Nana. Aunty Ramlah ta gyaɗa kanta ta ce"shi ne ya kawo ki?" she just nodded her head tana sake narkewa a jikin aunty Ramlah, murmushi ta yi ta ce"to ko dai dashi za'a yi ne Nana?" saurin tashi zaune ta yi tana cewa"Allah ya kiyaye ni bana son sa" yanda ta yi maganar ya sanya Aunty Ramlah dariya sai kuma ta ce"to mene ne aibunsa? Sultan me hankali da nutsuwa, Ni zan iya cewa duk cikin samarin shuwa babu wanda ya kai shi" taɓe baki Nana ta yi ta ce"taɓ! Me zan yi dashi, mugu ne wallahi" harararta Aunty Ramlah ta yi ta ce"to ai duk wannan yanzu ne, kuma kin san ma'anar namiji ya dinga yi miki mugunta?" Shiru Nana ta yi sai kuma ta girgiza kanta, Aunty Ramlah ta gyara zama ta ci gaba da fad'in "idan har ki ka ga kuna zaune da namiji yana miki mugunta ko kuma yana takureki fiye da sauran yan uwanki that's means yana da feeling akan ki, yana sonki ne. Kuma na fahimci haka a gurin Sultan" tura baki Nana ta yi ta ce"nifa Aunty ba haka bane, babu abin da zai haɗani da Yaya Sultan yaje can inda ake sonsa" murmushi kawai ta yi ta ce"ai shikenan, naji watarana kin cemin kina sonsa" "Har abada ma wallahi" ta ƙare maganar tana tashi daga wajen. **** Zaune suke cikin parlon kowa ya bada full attention ɗinsa zuwa ga abin da take cewa, Hajiya Babba ta sauke numfashi sannan ta ci gaba da faɗin "Yanzu na riga da na yanke hukunci akan yanda za'a yi, idan kuma kuna ganin hakan bai yi ba sai a sauya" Alhaji Kabir ya yi murmushi sannan ya ce"ai babu wani sauyi Hajiya, hakan ma ya yi Allah yasa haka ne mafi alkhairi ya kuma kai mu lokacin" Amin ta ce sannan ta maida idanunta kan Abba ta ce"kai fa Alhaji?" girgiza kai Abba ya yi fuskarsa ɗauke da mabayyanin murmushi ya ce"Alhamdulillah Hajiya, hakan ya yi dai dai, Allah ya kai mu da rai da lafiya ya kuma basu zaman lafiya" duka kowa ya ce Amin. Mama ta ce"to yanzu zuwa yaushe za'a saka kenan?" Hajiya Babba ta gyara zamanta sannan ta ce"ai wannan yana wajensu, ni dai nagama nawa" Daddyn su Sultan wato Alhaji Kabir ya ce"i think zamu fara magana da yaran sai aji yaushe za'a tsaida, but before that yaushe Arɗo zai dawo? Akwai buƙatar ayi komai a gabansa" Abba ya jinjina kai sannan ya ce"haka ne, in sha Allah zan masa magana ya sanya rana ya dawo, zaman ya isa haka" Hajiya Babba ta ce"to wata kila ku yaji maganarku, amma na saka Aliyu ya masa magana ya ce masa wai yana da abubuwan yi ne dayawa acan" murmushi Abba ya yi ya ce"Allah sarki ai yana ƙoƙari sosai, amma duk da haka zai zo in sha Allah" Mama ta ce"Allah ya yarda ya kuma nuna mana" Amin suka ce sannan kowa ya tashi ya watse, Hajiya Babba ta sauke numfashi tana fatan wannan haɗin da ta yi ya zama mai albarka. ****Around 5:20 na yamma wayarta ya fara ƙara, tana zaune gefen closet ɗin Inteesar tana gyara mata kaya, ta daga idanunta tana kallon wayar da ke kan drawer, rigar da ke hannunta ta ajiye sannan ta tashi ta ɗauki wayar, ɗagawa ta yi kafin ta yi magana taji ya ce "I'm outside" Okay ta ce sannan ya kashe kiran, ta ɗan yi jim sai kuma ta sauke nunfashi ta koma ta ƙarasa kwashe kayan. Mayafinta ta ɗauka ta yafa bayan ta ɗan gyara fuskarta ta fito parlon, Inteesar ce kawai zaune tana game a tap ɗinta, Nana ta kalleta ta ce"Intee ina Mom?" Inteesar da idanunta ke kan tv ta ce"tana ɗaki bacci take" Ajiyar zuciya Nana ta sauke tana godiya ga Allah a ranta, a fili kuma ta ce"to bari naje na siyo recharge card kin ji" gyaɗa mata kai kawai tayi dan gaba ɗaya hankalinta na kan kallon da take, Nana ta fice daga parlon da sauri. Babu kowa a compound ɗin dan haka ta ƙarasa har wajen gate, ganin da gaske babu wanda ya shigo ya sanya ta fita daga waje ta tsaya, wayarta ta ɗago ta yi dialing numbernsa bugu ɗaya ya ɗauka murya a sanyaye ta ce"na zo ban ganka ba" sir Junaid da ke bayanta ya ce"gani a bayanki" da sauri ta juya tana kallon bayan nata. Tsaye yake jikin motarsa Camry yana sanye da wata shadda fara tas ɗinkin jamfa, ya ɗora hular zanna bukar akansa, sai kallonta yake hannayensa naɗe a ƙirji. Kallonsa ta dinga yi ko kiftawa babu ya yi mata kyau matuƙa, ta ƙarasa wajen har sannan bata dauke idanunta daga kansa ba, shima kuma kallonta yake dan ba ƙaramin kyau tayi masa ba. Sunkuyar da kanta ta yi a sanyaye ta ce"ina yini?" bai amsa ba sai gyara tsaiwarsa da ya yi yana kallonta ya ce"sorry na taso ki Nana" ɗan murmushi ta yi ta ce"babu komai sir" haɗe fuska ya yi ya ce"bana son wannan sunan" da sauri ta kalleshi sai kuma ta sake mai da kanta ƙasa ba tare da ta ce komai ba. Sun daɗe a haka kafin ya numfasa ya ce"kin san me yasa nace mu haɗu?" Girgiza masa kai ta yi ya gyaɗa kansa kana ya ce"good, ina son mu san abin yi ne Nana, ina son na san ta hanyar da zan iya mallakar ki, wallahi tallahi ina sonki Nana! Ina ƙaunar ki! Amma naga kamar ke baki gane hakan ba, yarinta ta hana ki fahimta" Runtse idanunta ta yi saboda jin furucinsa, tayaya ma zai ce bata fahimta ba? Ya san yanda ita ma take ji a cikin ranta ne? Ya san irin son da take masa? Me yasa yake nanata ita yarinta ta mata yawa? Why?. "Nana baki ji na?" Maganar Junaid ta dawo da ita daga tunanin da take, numfasawa ta yi sai kuma a hankali ta ce"na fahimta mana, nima ina sonka, kuma ka san da haka, da ba don son da nake maka ba babu yanda za'a yi nayi abin da na san iyayena ba zasu ji daɗi ba idan suka ji, da ba zan fito nazo dan na haɗu da kai ba. Dana haƙura da koda kiran ka ne, amma ka san me? Bana iyawa, idan nayi tunanin na rabu da kai nabi zaɓin dangina sai zuciya ta dinga faɗa min ba dai dai bane hakan, sai ta dinga kwaɗaita min irin alkkharanka, sai ta dinga tuna min baya. Wallahi sir ina sonka, tun ban san mene ne son ba, tun ban fahimci abin da yake nufi ba, amma ya zan yi? So ka ke na bijirewa gidanmu? ko kuwa na kai ka nace su aura min kai?" Junaid ya dinga kallonta yana nazarin kalamanta, yanda take magana wani lokacin har tsoro yake bashi, maganganunta suna shige shekarunta, ta iya tsara zance. Agogon dake maƙale a hannunta ta kalla sai kuma ta ce"ba'a san na fito ba a gida" Junaid ya sauke zazzafan numfashi kafin ya saita nutsuwarsa ya ce"ba haka nake nufi ba Nana, what I mean is koda sau ɗaya ne ki gwada faɗawa iyayenki abin da ke cikin ran ki, ki gwada sanar dasu akwai wanda ki ke so, tun da har yanzu ba'a yi maganar wanda zaki aura ba. I Maybe idan ki ka yi haka ke ki samu a bar ki da wanda ki ke so, daga sanda ki ka tambaya ni kuma zan fara zuwa gidanku, tun ana korata na tabbata wata rana ba za'a koreni ba Nana" ya ɗan yi shiru yana karantar yanayinta, ganin kamar ta fara ɗaukan abin da yake cewa ya sanya ya ci gaba da faɗin" ki samu ki yi maganar da mahaifiyarki cikin nutsuwa da fahimta, na san ba zata ƙi ba, domin da wuya ki ga iyaye mata suna son irin wannan auran haɗin. Ki yi mata magana yanda zata fahimceki ba da sauri ba sannan kuma ta sigar da zata ji daɗi, ba wai da hargagi ba, na tabbata idan har ki ka yi hakan zamu iya cin nasara!" Sauke numfashi ta yi tana kallonsa dan har cikin ranta taji ta gamsu da abin da ya ce dan haka ta ce"shikenan I'll give it a try in sha Allah, zan yi maganar da Amma idan na koma gida" Murmushin jin daɗi Junaid ya yi ya ce"yauwa Nana, shiyasa nake sonki" dariya ta yi tana rufe fuskarta, ya girgiza kansa sannan ya koma ya buɗe motarsa. Wata leda ya fito da ita sannan ya dawo ya miƙa mata yana fadin"your favorite" kallon ledar ta dinga ba tare da ta amsa ba, ya sake cewa"karbi mana" girgiza kanta ta yi ta ce"ba'a san na fito wajen ka ba, idan aka ganni da leda dole ne a tambayeni" Junaid ya ce"bafa wani abun ba ne, naman kaza ne na siyo miki" murmushi ta yi ta ce"tom nagode, amma ka bar shi" Babu yanda bai yi da ita ba amma taƙi yarda ta amsa ledar daga ƙarshe ya hakura ya bar ta dan Nana ta fi shi gardama. Sallama suka yi ta koma gida shi kuma ya bar wajen cike da begenta, koda ta shiga parlon zaune ta sami Aunty Ramlah tana danna wayarta, tana ganinta ta ce"daga ina ki ke ne?" a ɗan rabe ta ce"a'a...a'a daman recharge card naje siyowa zan yi waya nawa ya ƙare" Aunty Ramlah ta ɗago ta kalleta sai kuma ta ce"shi ne ba zaki faɗa min na miki transfer ba?" ɗan murmushi ta yi ta ce"ai kina bacci shiyasa" taɓe baki ta yi ta ce"to kin samo katin?" gyaɗa kanta ta yi tana shirin zama suka ji ana knocking. Koda ta buɗe gate man ɗin gidan ne tsaye yana ganinta ya ce"Yauwa hajiya wai Nana ta zo in ji Sultan zasu tafi" okay kawai ta ce sannan ta mai da ƙofar ta rufe, Aunty Ramlah da bata motsa ba ta ce"mene?" tura baki ta yi ta ce"wai Yaya ne ya zo yana jirana" "Da wuri zaku tafi kenan?" Gyaɗa kanta kawai ta yi sannan ta nufi cikin ɗaki ta ɗebo sauran abin da ta bari, ko minti goma bata ƙara a gidan ba suka yi sallama ta fito. Zaune ta sameshi cikin mota idanunsa zube kan titi kuma cikin glasses kamar ɗazu. Buɗe motar ta yi ta shiga ba tare da ta ce komai ba, shima ɗin bai yi magana ba ya yiwa motar key suka bar unguwar. Tafiyar mintuna talatin ta kawo su gida. Nana ta sauke ajiyar zuciya jin ya gama parking ta fara ƙoƙarin buɗe motar ta sauka, gam ta jita a rufe dan haka ta juyo tana kallonsa kamar zata yi kuka ta ce"Yaya dan Allah ka buɗe min na fita" banza ya yi mata ya ci gaba da danna wayarsa, gajiya ta yi da magiyar ta koma ta zauna tana takure jikinta waje ɗaya kamar daga sama taji ya ce "Wane ne wanda ya tsaida ke ɗazun?" Sai taji gabanta ya yi wata irin faɗuwa, nan take miyan cikin bakinta ya ƙafe ta dinga kallonsa amma ta gagara furta koda kalmar 'A' ce, a fusace ya juyo ya daka mata wata irin tsawa mai firgitarwa yana kallonta jijiyoyin kansa dun sun mimmiƙe idanunsa ya yi wani irin jaa, ko ba'a faɗa maka ba kasan ransa ya gama ɓaci. Kasa magana ta yi sai rawa jikinta yake, rabon da a yi mata irin wannan tsawar har ta manta, ganin bata ce komai ba ya sanya ya sake daka mata wata razananniyar tsawar ya ce"Ba da ke nake magana ba!" fashewa ta yi da kuka, bata yi aune ba kawai ta ji ya sauke mata mari akan fuskarta, iyaka rikicewa Nana ta rikice, ta kasa koda kukan saboda tsananin azabar marin sai jan numfashi take, tun da take a rayuwarta babu wanda ya taɓa marinta sai yau, dan haka ta fice hayyacinta. Sultan ya dinga kallonta yana wani irin huci kamar zaki, har wani ruwa ne ya kwanta a cikin idanunsa saboda masifa. Cikin tsananin ɓacin rai ya ce"Yau sai kin faɗa min wane ɗan iskan ne yake zuwa wajenki, tun da har kin yi girman da zaki dinga haɗuwa da maza. Wallahi tallahi ba zaki bar motar nan ba har sai kin faɗa min alaƙar ki dashi!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Page 7... Nana ta dinga kallonsa hawaye na sauka kan fuskarta, ganin yanda ya kafeta da idanu ya sanya ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da shessheƙar kuka. Ɗauke kansa ya yi daga kallonta ya zubawa compound ɗin gidan ido, ƙoƙarin saita kansa yake amma zuciyarsa a cunkushe take, he just can't believe a ce Nana na kula wani, wanin ma a wajen estate, how? Furzar da numfashi ya yi daga bakinsa sannan ya juyo yana sake kallonta. Kuka take sosai, fuskarta ta yi jajur, ɗauke kansa ya yi sannan ya ce"baki shirya tafiya gida ba kenan?" kasa magana ta yi sai hawaye dake fama zuba kan fuskarta kamar an buɗe famfo, kwafa ya yi ya ce"wato ga ɗan iska yana magana ko? shi yasa ki ka min banza nayi ta yi ko? wane ne wanda na gan ki dashi? wane ne wanda ya baki yanki har da kalaman soyyaya a jiki? wane shi? A ina yake? har kin yi girman da ki ke ganin zaki fara soyyaya?" Da sauri ta kalleshi amma bata ce komai ba, harararta ya yi ya ce"I'm talking to you, har kin girma?" Tura baki ta yi muryarta na rawa ta ce"n..nifa ba wani abun bane, ai kowa yana da wanda yake so, to nima shi nake so, kuma shi zan aura, naga..." Wata irin tsawa ya daka mata ba tare da ya san ya yi hakan ba, ya dinga mata wani irin kallo yana huci kafin ya ce"shi zaki aura? Da gaske? Daman ke zaki yanke wanda zaki aura? ke ki ke da wannan alhakin bamu sani ba?" Murguɗa masa baki ta yi ta ce"ai Abba zan faɗawa kuma na san zai yarda" Sultan kasa magana ya yi sai kallonta da yake baki buɗe ganin bai ce komai ba ya sanya ta ɗan ɗago kanta ta kalleshi, har sannan kallonta yake da alama dai abin faɗa ya rasa. Wayarsa xe ta fara ringing hakan ya dawo dashi daga tunanin da ya tafi, kallon screen ɗin ya yi ganin sunan Hameed ya sanya ya ɗauka, maganar 2mins suka yi ya kashe wayar bai sake bi ta kan Nana ba ya sauka daga motar, ganin haka ya sanya itama ta sakko ta nufi hanyar gidansu da sauri. **** Babu kowa a parlon sai tv dake aiki ita ɗaya, kai tsaye ɗakinta ta shige tana zuwa ta faɗa kan gado ta fashe da kuka. Maganganun Junaid ne suka dinga dawo mata, sai kuma maganganun Sultan wanda suka sake tuna mata irin ƙalubalen dake gabanta, tana nan kwance har aka fara kiran sallahr magriba. Ta tashi ta shige toilet ta yi wanka sannan ta ɗauro alwala, sauya kaya ta yi zuwa doguwar riga mara nauyi sannan ta gabatar da sallahr, ta daɗe tana rokon Allah akan ya taimaketa ya kuma yi mata zaɓi nagari kafin daga bisani ta tashi ta naɗe laddumar ta fito daga ɗakin jiki a sanyaye ta nufi ɗakin Amma. Zaune ta sameta kan ladduma tana jan carbi, ta ƙarasa ta zauna a kusa da ita ba tare da ta ce komai ba, sai da ta kai inda zata tsaya sannan ta juyo ta kalleta ta ce"kin dawo?" gyaɗa mata kai Nana ta yi, Amma ta dinga kallonta ganin yanda fuskarta ta yi jajur yasa ta sake cewa "meya sami fuskarki?" A sama Nana ta ji maganar dan bata yi tunanin Amma zata tambayeta ba, dan haka ta shiga kame-kamen abin cewa "U...un... Wani kwaro ne ya hau min kan fuska shine ya cijeni kuma da zafi sosai" Amma ta kalleta ba dan ta yarda da abin da ta ce ba, sai ta taɓe baki ta ce"Ya Ramlan?" "Tana nan klao, ta ce tana gaishe ki" "Ina amsawa" Amma ta ce tana jawo wayarta daga kan drawer, shiru wajen ya ɗauka ita tana danna wayarta ita kuma tana tunanin ta inda zata fara sanar mata halin da take ciki. Above 5mins kafin ta gyara zamanta muryarta a sanyaye ta ce"Amma!" ɗago idanu ta yi ta kalleta sai kuma ta ce"ina jin ki lafiya?" gabanta na tsananta faɗuwa ta ce"daman ina son nayi wata magana da ke ne" Ajiye wayar hannunta ta yi tana mai da hankalinta gareta ta ce"okay Ina ji" Nana ta dinga wasa da fingers ɗinta tana tunanin ta inda zata fara, kusan 3mins bata ce komai ba, hakan yasa Amma ta jawo wayarta tana cewa"shikenan idan baki da abin faɗa tashi ki bani waje" girgiza kanta ta yi, sai kuma ta sauke nunfashi ta ce"daman... Daman akwai wani malamin makarantarmu ne, sanda muna Aun, to shi ne.. shi ne..!" Amma ta dinga kallonta tana jiran taji me zata ce, ganin ta yi shiru ya sanya ta ce"shi ne me? Ina jin ki?" Fashewa ta yi da kuka tana cewa"shi nake son na aura Amma! Ni shi nakeso, bana son auran zumuncin da ake yi mana, ni shi zan aura dan Allah ki faɗawa Abba" Tashi tsaye Amma ta yi tana mata wani irin kallo cike da tashin hankali da kuma ɓacin rai ta ce"Nana kin san me ki ke faɗa? Har yaushe ki ka yi girman da har ki ka san ki ce ga wanda ki ke so? A nan gidan? Wane kalar hauka ne yake damunki? so ki ke ki ja min masifar da ba zan iya da ita ba ko me? wato a ce yata ta bijire ko? kina son a saka ubanki a bakin duniya ko? To bari kiji koda wasa kar na sake jin makamanciyar wannan maganar a bakin ki Nana, wallahi idan ba haka ba sai ranki ya yi mugun ɓaci! Sai na saɓa miki fiye da yanda ki ke zato. Kuma Allah nagode maka daya sanya ki ka faɗi wannan maganar naji, daman nan bada jimawa ba za'a ɗaura aurenku, ki bar gabana kafin ki dauko min maganar da ba zan iya da ita ba" Da sauri ta ɗago idanunta wanda ke zubar hawaye ta kalli Amma, furucinta na ƙarshe shi ne abin da ya dagula nutsuwarta, aure! Aure za'a musu? Innalil lahi wa ina ilayhi raji'un, ta dinga maimaitawa cikin ranta, kafin ta tashi tana kallon Amma bakinta na rawa ta ce" ki yi hakuri, banida niyyar ɓata miki rai Amma, wallahi daman sai da na faɗa masa ba zaku yarda ba, amma ya ce na gwada, Amma naji ba zan sake miki maganarsa ba, amma dan Allah kada ki saka a min aure yanzu, banaso Amma, bana so dan girman Allah, ki taimakeni Amma!" Wani irin wawan mari Amma ta sauke mata tana huci ta ce"kin ji an tambayeki abin da ki ke so? ko kuma wanda baki so? ko daman ni ce nake zaɓar lokaci da kuma wanda zaku aura? Idan baki bar ɗakin nan ba sai ranki ya yi masifar ɓaci Nana! Leave my side!" Wata irin azaba ce ta yi mata yawa, ga zafin mari ga kuma zafin kalaman Amma, madadin ta fita daga ɗakin sai kawai ta durƙushe a wajen ta riƙe ƙafafun Amma cikin matsanancin kuka take faɗin "Ki yi hakuri Amma, ki yi hakuri ki taimakeni Amma! Ki yi hakuri Ammaa..!" Kasa cewa komai ta yi, kawai ta janyeta daga jikinta ta fice ta bar ɗakin, Nana ta dinga bin ƙofar da kallo tana wani irin kuka kamar ranta zai fita, ita ba rabuwarta da Junaid ne abin da ya fi damunta ba, maganar auren da aka yi shine tashin hankalinta. Wa zata aura? Wa aka zaɓa mata? Da wa zata yi rayuwa??.. **** Sultan ya dinga kallon Papa yana jin wata irin zufa na keto masa duk da ac dake ɗakin, ganin bai ce komai ba ya sanya Papa ya sake faɗin "lafiya dai Sultan?" girgiza kansa ya yi dan bakinsa ya gagara magana, Papa ya ce"saboda haka ina fatan ka zama miji nagari a wajen matarka, ka bata kulawa iyaka iyawarka, ka sota, ka ƙaunaceta, kamar yanda kaga muna yi da iyayenku" zazzafan numfashi ya sauke kafin ya shiga jinjina kansa. Papa ya ce"kana iya tafiya" ko rufe bakinsa bai yi ba Sultan ya tashi ya fice daga ɗakin da sauri, A corridor ya haɗu da Juwaira wadda take tafe hannunta riƙe da tray, sannu da zuwa ta yi masa amma ko ta kanta bai bi ba ya shige ɗakinsa ya rufo ƙofar. Dakyar ya ƙarasa gefen gado ya zauna yana sauke numfashi, bai san sanda hawaye suka fara zuba kan kuncinsa ba, ashe ba zai samu Nana ba? Ashe ba zai zama mijinta ba? Wane irin dangi ne wannan? Wace irin al'ada ce wannan? Kenan baka da yancin zaɓar matar da zaka yi rayuwa da ita? haka zasu ci gaba da rayuwa? Ya ilahi. Maganganun da Sultan ke yi kenan cikin zuciyarsa, a fili kuwa bakinsa kamar an rufe shi da gam haka yake ji, ya gagara cewa komai, ya gagara furta wata kalma ballantana yaji sauƙi a ransa. Daga ƙarshe ma kwanciya ya yi kan gadon yana kuka kamar ƙaramin yaro. ****Mami ta dinga kallonta ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita ya sanya ta ce"Amrah zo nan" tasowa ta yi ta ƙaraso gabanta ta zauna kusada ita, rungumeta Mami ta yi tana faɗin"kukan na mene ne Amrah? Baki farin ciki?" kasa cewa komai ta yi, sai ma wani sabon kukan data fara, Mami ta dinga rarrashinta amma sam taƙi yin shiru, suna haka ya buɗe ƙofar ya shigo, Har ya zauna kallonsu yake da mamaki, ganin yanda take kuka ita kuma tana faman rarrashinta, Alhaji Abubakar kenan, mahaifin Amrah, kuma ɗan yaya a wajen Hajiya Khadijah, Mami kuma wadda ta kasance yarta ta biyu wato Fatima, yaransu kuma su ne Amrah da Sa'eed. Mami ta kalleshi ta ce"yauwa gara da Allah ya shigo da kai dan wallahi nagaji da rarrashinta" Daddy ya ce"me aka mata?" "Akan maganar auren nan ne, tun da aka yi maganar shikenan take faman kuka" Da mamaki Daddy ya ce"and kukan ne mene ne? wa ya ɓata mata?" Mami ta girgiza kanta ta ce"ban sani ba wallahi" tsaki ya yi yana mai da idanunsa kan Amrah ya ce"Ke Amrah!" ɗago kanta ta yi sanin halinsa yasa ta ce"na'am Daddy" "Lafiyarki? Ko an yi miki wani abun ne?" Girgiza kanta ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce"a'a kawai kaina ne yake ciwo" Jin jina kansa ya yi ya ce"okay bari na kira Sultan ya zo ya dubaki" da sauri ta ce"a'a Daddy idan na kwanta ma zai daina" "And what are you waiting da baki kwanta ɗin ba?" Daddy ya yi magana babu yabo babu fallasa, tashi ta yi jiki a sanyaye ta bar parlon, ya bita da kallo sai kuma ya yi tsaki ya ce"i don't know what wrong with this childrens wallahi" Mami ta sauke numfashi kana ta ce"Allah dai ya kyauta" . **** Hameed ya girgiza kansa still looking at her ya ce"amma Hajiya ni sai naga daman ba haka aka yi ba, ko mu ba za'a tambayemu ba at least a tambayi yaran, kowacce dole akwai wanda take ganin idan aka aura mata she's will be okay ko?" Hajiya Babba dake zaune kan sofa tana jan cazbaha ta ce"Yanzu da aka zaɓawa kowa mene ne ai bu Hameed? Kowacce ɗan uwanta aka bata, zata fara sonsa bayan aure, yanda zaku kyautata musu shi ne zai sanya su so ku" Hameed ya numfasa sannan ya ce"shikenan Hajiya, Allah yasa haka ne mafi Alkhairi" murmushi ta yi dan daman tasan shi bashida matsala ta ce"Amin, Allah ya baku zaman lafiya" a sanyaye ya ce"Amin" sannan ya tashi , dai-dai nan Aliyu ya shigo parlon bakinsa ɗauke da sallama. Amsawa suka yi sannan ya ƙaraso ya gaida Hajiya ta amsa sannan ya zauna, Hajiya ta ce"Aliyu lafiya dai?" murmushi ya yi ya ce"Alhamdulillah Hajiya, daman mun yi waya da Buddy ne ya ce gobe yana tafe in sha Allah" Ba Hajiya Babba ba har Hameed sai da ya yi murmushi sannan ya ce"da gaske Yaya?" gyaɗa masa kai Aliyu ya yi ya ce"haka ya ce min, kuma nasan tun da ya ce haka to zai zo ɗin" Hameed ya jinjina kansa ya ce"Tom Allah ya kawo shi lafiya" da Amin ya amsa sannan ya haye sama da sauri. Hajiya Babba data kasa ɓoye farin cikinta ta ce"shi da kansa ya ce maka zai dawo ɗin?" gyaɗa mata kai Aliyu ya yi ya ce"Eh Hajiya yana nan tafe in sha Allah" ajiyar zuciya ta sauke ta ce"to Allah ya kawo shi lafiya" Amin ya ce sannan ya miƙe yana kallonta ya ce"zan je wajen Abba ya ce na faɗa masa zai zo" toh ta ce sannan ya juya ya fita. A bakin ƙofar shiga apartment ɗin ya ganta hannunta riƙe da warmer, tana ganinsa ta sunkuyar da kanta murya na rawa ta ce"s..sannu da zuwa Yaya" ɗan murmushi ya yi ya ce"yauwa Maimuna ina zuwa?" ba tare da ta ɗago ba ta ce"Hajiya zan kai wa abinci" Aliyu ya jin jina kansa ya ce"okay kai mata ki zo ina jiranki" toh kawai ta ce sannan ta shige gidan da sauri. Ko minti biyu bata yi ba ta fito ta sameshi tsaye inda ta bar shi, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta sake sunkuyar da kanta ta ce"Yaya gani" Aliyu ya ɗan kalleta sai kuma ya yi murmushi ya ce"muje to" bata musa masa ba suka fara tafiya a jere, sai dai tunaninta yana wani wajen daban, Sun kusa kai wa Apartment ɗin sannan ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin "Maimuna" saurin ɗago kanta ta yi dan duk sanda ya kirata da wannan sunan sai taji zuciyarta ta buga, ya tsaya cak yana kallonta ya ce"Are you happy or not?" kasa cewa komai ta yi sai sunkuyar da kai take, hawaye ya fara sauka kan fuskarta. Ɗan rage tsawonsa ya yi ya leƙa fuskarta ganin yanda take kuka ya sanya ya ce"haushi ki ke ji kema?" girgiza kanta ta yi, ya ce"to tell me meyasa ki ke kuka? uhm" kasa cewa komai ta yi har sannan sai kuka take a hankali, Aliyu ya sauke numfashi kafin ya ce"okay tun da ba zaki faɗa min ba daina kukan, kin ga Abba zai tambayeki me ki ke wa kuka" gyaɗa masa kai ta yi sannan ta shiga share hawayenta da gefen mayafin dake jikinta. Ya ɗan yi murmushi kafin ya ce"to muje" daga haka suka ci gaba da tafiya. **** Ƙarfe 9:10pm aka buɗe ƙofar ɗakin, kwance take har sannan akan gado sai hawaye take, Abba ya dinga kallonta kafin ya ƙaraso cikin ɗakin ya zauna gefen gado ya ce"Nana lafiya?" da sauri ta ɗago kanta, ganin Abbanta ya sanya ta tashi zaune, ta ƙarasa wajensa kawai ta rungumeshi tana fashewa da kuka. Abba ya dinga shafa kanta ba tare da ya ce komai ba, kuka take bana wasa ba, har wani jan numfashi take kamar zata shiɗe. Abba ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce"mene ne? faɗa min" Cikin kuka ta ce"Abba wai aure za'a yi mana?" Da mamaki yake kallonta kafin ya ce"wane ya faɗa miki wannan maganar Nana?" Cikin shassheƙar kuka ta ce"Amma ce, Amma ta ce aure za'a yi mana" numfasawa ya yi sai kuma ya jinjina mata kai ya ce"haka ne, an kusa muku aure in sha Allah" sake fashewa ta yi da wani sabon kukan, Abba ya ce"mene ne kuma?" "Abba ni bana son aure karatu nake son nayi, bana son nayi aure yanzu dan Allah Abba" Ɗan murmushi irin na manya ya yi kafin ya ce"in dai karatune zaki yi a gidan mijinki, amma nan ba da jimawa ba zaki yi aure Nana" Tashi ta yi daga jikinsa, ta sauko daga kan gadon ta tsuguna a gabansa tana kuka ta ce"dan Allah Abba kada ka bari a yimin aure yanzu, ka bari nayi karatu Abba, bana son aure wallahi" Bai ce komai ba sai kawai ya tashi ya fice daga ɗakin, Nana tabi bayansa da kallo sai kuma ta sake fashewa da wani kukan tana dafe kanta. Daren ranar babu wanda ya yi bacci wadatacce a cikinsu, kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa, kowacce da irin nata matsalar. Nana kuwa kwana tayi tana kuka, sai da aka fara kiran sallar asuba sannan ta tashi ta yi sallah ta shiga rokon Allah akan ya hana su haɗa auren nan da ita domin ko kaɗan bata son ta yi aure da yarinta. Washegari ya kasance asabar, dan haka babu wanda ya fita daga mazan gidan har mata, tana ta kwance har ƙarfe goma kafin kiran Junaid ya tayar da ita, kasa ɗaukan wayar ta yi dan tasan bata da wani amfani. Ta dinga kallon wayar har kiran ya katse, ganin wani sabo ya shigo ya sanya ta kashe wayar gaba ɗaya, ta sake fashewa da kuka. Amma ce ta shigo dakin tana sanye da wata doguwar riga ta lace, ta dinga kallonta kafin ta ce"da kin tashi shi ne baki fito ba?" shiru ta yi bata ce komai ba, Amma ta sake cewa" ki tashi ki fito zan aikeki" ji tayi kamar ta zunduma ihu ta cewa Amma ba zata je ba, dan ko kaɗan bata son fita daga ɗakin, amma babu dama, dan haka ta tashi ta shige toilet ɗinta ta yi wanka a gurguje ta fito. Doguwar rigar yadi ta sanya sannan ta dauki hijabi har ƙasa ta saka ta fito, zaune ta sami Abba a parlon yana karatun news, ta gaishe shi a sanyaye ba kamar yanda ta saba ba, amsawa ya yi shima kuma bai sake bi ta kanta ba ya ci gaba da abin da yake, Amma ta fito daga kitchen tana kallonta ta ce"ki je wajen Mama ki ce wai gaki" shiru Nana ta yi bata amsa ba kuma bata tafi ba, Amma ta zabga mata harara kana ta ce"baki ji ne ina magana" waje ta yi ba tare da ta amsa ba, Abba ya bita da kallo har ta fice sannan ya kalli Amma ya ce"ki bita a hankali" bata ce masa komai ba ta koma kitchen ta ci gaba da aikin da take. Tafiya ta dinga yi a hankali tana tunane-tunanenta, har suka ƙaraso gabanta bata sani ba, sai da Maimoon ta riƙe hannunta sannan ta ɗago kanta da sauri tana kallonsu, kowanensu idanunsa a kumbure yake, basu ce mata komai ba suka ja hannunta suka ci gaba da tafiya. Har suka je garden ɗin babu wadda ta ce komai, ita dai Nana bin su take da kallo har suka shiga ciki, sai a sannan Maimoon ta saki hannunta ta ce"kin ji abin da ya faru ko?" gyada mata kai ta yi sannan ta ce"ke wa zaki aura?" shiru Maimoon ta yi bata amsa mata ba, ta juya ta kalli Hameeda ta ce"kefa Hameeda?" madadin ta amsa mata sai kawai ta fashe da kuka, ta faɗa jikinta, duk yanda Nana take jin jikinta babu kwari haka ta riƙe Hameeda itama kawai sai ta fashe da kuka. Amrah ce tayi ƙarfin halin cewa"ku daina wannan kukan kar wani ya zo ya ganmu" a fusace Nana ta ce"to a gani ɗin, wallahi ni ba zan auri wani ba idan ba Junaid ba! sai dai na mutu babu aure na rantse, amma ba zan auri wani ba idan ba shi ba!" Kallonta suka dinga yi babu wanda ya tanka, Amrah ta dafa Hameeda dake kuka kamar ranta zai fita ta ce"da a ce za'a bar ni, da a ce zan iya dana bar miki Yaya Sultan Hameeda, wallahi da sai na barki kin aureshi, ni auri koma wane, domin nima ba shine zaɓin zuciyata ba, bashi nake so ba!" Da sauri Hameeda ta kalleta cikin kuka ta ce"na sani Amrah, na san zaki iya bar min shi, ko kaɗan ban ga laifinki ba, kawai zuciyata ce ta kasa yarda, na kasa haƙura dashi, ji nake kamar mafarki nake, kamar zan aure shi, amma na san har abada hakan ba zai faru ba, Allah ba haka ya so ba, bai ƙaddara ya zama mijina ba, Yaya Hameed shi ne zaɓin Allah kuma zaɓin iyayena" da sauri Nana ta ce"Amrah Yaya Sultan za ki aura? Ke kuma Hameeda Yaya Hamid za ki aura? To ke kuma fa Maimoon?" "Ya Aliyu" Amrah ta bata amsa, shiru Nana ta yi lokaci ɗaya jikinta ya yi wani irin sanyi, ji tayi ta gaji da tsaiwar dan haka kawai ta zauna cikin ciyayin da ke wajen. Hawayen da bata san dalilin su bane suka dinga zuba kan fuskarta, kallonta duk suka dinga yi kafin Maimoon ta yi karfin halin cewa "Me ki ke yiwa kuka Nana?" "Yaya Sultan!" Maganar ta suɓuce mata ba tare da ta yi aune ba. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* https://chat.whatsapp.com/Hbf1rpqVyiZCko3JyHNMcG?mode=ems_copy_c Page 8... Hamida ta durƙusa gabanta tana kallonta da mamaki ta ce"me ki ka ce Nana?" girgiza kai ta yi a sanyaye ta ce"nothing" daga haka ta miƙe ta bar wajen ba tare da ta sake kallonsu ba. Kai tsaye apartment ɗin su Hamida ta nufa kamar yanda Amma ta ce mata, koda ta shiga bata samu Mama a parlon ba dan haka ta nufi daƙinta kanta tsaye, bakinta ɗauke da sallama ta tura ƙofar ɗakin, Mama na zaune ƙasan gado tana karatun Alqur'ani, ta ɗago kanta tana kallonta ta ce"wa'alaiki assalam Khadijah shigo" jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa ta zauna kusa da ita sannan ta ce"Mama ina kwana?" "Lafiya kalau Nana" Sunkuyar da kanta ta yi tana jan fingers ɗinta ta ce"daman Amma ta ce wai na zo" jinjina kai Mama ta yi, ta rufe Alkur'anin hannunta ta ajiye kan drawer sannan ta gyara zamanta cikin nutsuwa ta ce"eh ni na ce ki zo, daman zan yi wata magana da ke ne" sosai Nana ta ji jikinta ya yi sanyin barin yanda taga Mama na mata magana cikin kulawa. Mama ta numfasa sannan ta ce"Nana wane wanda ki ke so?" Da sauri ta ɗago kanta ta kalleta, kenan Amma ta faɗa mata abin da ya faru? ta tambayi kanta, Mama ta dinga kallonta ganin bata ce komai ba ya sa ta ce"ina jin ki faɗa min" cikin shessheƙar kuka Nana ta fara cewa"malamin mu ne a Aun, Amma kuma ta ce kar na sake kulashi" Mama ta jinjina kanta cike da gamsuwa sannan ta ce"meyasa ki ka fara son sa bayan kin san tsarin gidanku Nana? baki ganin za'a ga rashin kunyarki? duk cikin yan uwanki babu wanda ya yi miki sai a waje? Uhm. Ko kina son ki ɓata mana zumunci ne?" Da sauri ta shiga girgiza kanta tana jan numfashi ta ce"a'a wallahi Mama, bani da niyyar tarwatsa zumuncin da aka gida tun iyaye da kakanni, nima zan yi farin ciki idan har nabi wannan dokar, amma kuma..." Ta sunkuyar da kanta kuka na kwace mata, Hannunta Mama ta kama ta riƙe cikin nata ta ɗago fuskarta tana kallonta ta ce"amma kuma me? ba zaki iya sadaukar da soyyayarki ba saboda danginki? ba zaki zo farin cikin mahaifinki ba? Na faɗa miki wani abu?; sanda aka ce za'a min aure ban yi shekarunki ba, I'm just a 17yrs old, aka aura min babansu Hamida, ban san shi ba, ban taɓa ganinsa ba sai a ranar da aka kawoni gidansa. And kamar ku muma boarding school aka kai mu tun daga Junior har candy. Saboda haka bamu saba da wasu mutane ba daga gida sai makaranta, a lokacin da muka dawo gida bayan mun kammala makaranta marigayi da kansa yake ɗaukanmu ya kai mu unguwa, duk inda ake shaƙawata sai da ya kai mu, har Umrah muka je. A sannan kuma na gamu da wanda nake so, sunansa Sagir, na so shi kamar ba zan daina ba, har cikin estate ɗin nan yake zuwa, time ɗin duk ba'a yi wadannan gine-ginen ba. Ya zo ba tare da kowa ya sani ba, kin san me aka yi? Rana ɗaya na dawo daga islamiyya aka ce an ajiye min kaya a ɗaki naje na saka, ban yi tunanin komai ba naje na shirya cikin leshin mai kyau da tsada, sai da na fito sannan Baba ya sa aka kirani ɗakinsa ya faɗa min an ɗaura min aure da babansu Hamida, ban ce komai ba a sannan duk da yanda na dinga ji a zuciyata, haka na haƙura nace to, aka ɗaukeni aka kawo ni gidan nan. Sai da dare ya yi sannan ya shigo na gansa, a lokacin bana son sa har cikin raina, amma ba zan iya ce masa ba, kuma ban isa na faɗawa wani ba, dan haka na riƙe abun a raina har zuwa sanda kyautatawarsa tasa na fara jin ƙaunarsa. Naji zan iya rayuwa dashi, rayuwa mai ɗorewa, na manta da cewa shi zaɓin iyayena ne, muka ci gaba da rayuwarmu cikin farin ciki da son juna" Mama ta sauke nannauyan numfashi sannan ta ci gaba da faɗin"kin san me yasa na baki wannan labarin?" Nana ta girgiza kanta hawaye na sake zubowa kan kuncinta, Mama ta ce"saboda ki san ba komai ka ke so kake samu ba, a lokacin dana bijire na ce sai na auri Sagir da ban san me zai sameni ba. Ban san wace rayuwa zan yi dashi ba, amma biyayyar da nayi ya sanya Allah ya dubeni ya haɗani da wanda yake sona yake kuma tausayina. Ba dole sai kin auri wanda ki ke so ba, amma dole ne ki auri wanda yake ganin girmanki dana iyayenki, wanda ki ke da tabbacin ba zai cuceki ba a iya zamanki dashi. Kuma wannan shi ne irin mijin da muke fatan kowaccen ku ta samu, duk wadda ki ka ga an haɗata da wani, to an duba an ga wannan shi ne zai dace da rayuwarta ne, saboda haka ki zama mai biyayya Nana ba mai son zuciya ba. Ki sani wannan abun da ki ke shirin yi ba ƙaramin yaƙi bane, faɗa ne tsakanin zuciya da kuma al'ada, dan haka ba abu bane mai yiwuwa ki yi nasara a kai. Dan haka ina mai baki shawarar ki yi haƙuri da abin da aka tsara, ki ɗauka wannan shi ne Alkhairin rayuwarki" Nana ta dinga gyaɗa kanta tana kuka, jikinta ya yi sanyi sosai kuma maganganun Mama sun shigeta, ita ma ta san ba lallai bane ta yi nasara akan abin da take so. Mama ta sanya hannunta ta share mata hawayen dake zuba sannan ta ce"ki daina kukan kin ji" sake jinjina kanta ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce"To Mama, ni daman na haƙura dashi amma dan Allah ki ce kada su aurar dani yanzu, tsoro nake ji mama, tsoro nake ji..." Sosai ta bawa Mama tausayi dan akwai ƙalubale ba ƙarami ba a cikin auran yarinta, amma ta ɗan yi murmushi ta ce"mene ne abin tsoro Nana? Yayanki zaki aura fa, kuma kin san ba zai cuceki ba" girgiza kanta tayi ta ce"ni bana son aure yanzu Mama, ni karatu nakeson nayi, kuma ban san wa zan aura ba ma" "Ba'a faɗa miki ba?" Da sauri ta gyaɗa kanta, Mama ta ce"Safwan zaki aura Nana" sake fashewa ta yi da kukan da bata san dalilinsa ba, Mama ta ce"mene ne hakan?" kasa cewa komai ta yi, sai kuka take rusawa. Tashi Mama ta yi ta ce"ai shikenan" daga haka ta fice daga ɗakin, kwanciya ta yi a wajen ta ci gaba da rera kukanta kamar an kunna radiyo. **** Ƙarfe 2:12 na rana baƙaƙen motocin suka fara shigowa cikin estate ɗin, nan da nan hayaniyar convey ta cika ko ina, a bakin apartment ɗin Hajiya Babba suka yi parking,black ride ne guda bakwai a jere, suna gama parking aka fara buɗe murfin kowace mota, sojoji ne suka dinga fitowa, kowannesu sanye da uniform da kuma bindiga. Suka jere a gaban motar da ke tsakiya wadda har sannan babu wanda ya fito, ƙofar da ke left side aka buɗe Aliyu ya fito daga ciki, sannan ya zagaya da kansa zuwa ɗaya side ɗin dai dai nan wani soja ya buɗe murfin, ƙafarsa ta dama ya fara sakowa wajen motar mai sanye da takalmin Gucci black colour sai sheƙi yake, sannan ya dafa murfin motar ya fito. Wani babban mutum ne mai cikar kamala da sura, wanda a ƙiyasi ba zai shiga 37-38yrs ba, fari ne tas kuma asalin kyakkyawa, kai tsaye ba za'a iya cewa bature bane haka kuma ba za'a ce bafulatani bane, fatarsa har wani ja take saboda tsananin fari. Yana sanye da wasu Tom ford suit black colour wanda suka tsaya a jikinsa kamar dan shi aka yi su, hannunsa maƙale da agogon Richard mille sai kyalli yake, idanunsa maƙale suke da Dita sunglasses, gashin kansa akwance har gaban kansa ya yi luf irin na larabawa, murmushi ya yi wanda ya sanya farare kuma rabbabun haƙoransa suka bayyana, kowane haƙori shi kaɗai yake ba tare da ya jingina da ɗan uwansa ba, sai kuma ƙatuwar wushirya a tsakiya. Yana da ƙasumba mai yawa kuma wadda tasha gyara sai kyalli take, iya ka haɗuwa da kuma tsafta wannan mutumin ya cikata. Kana ganinsa kaga babban mutum wanda ke ji da kansa, Aliyu ne yayi murmushi ganin yanda yake bin gidajen da kallo ya ce"Buddy muje mana" bai ce masa komai ba sai gaba da ya yi ya fara takawa cikin izza da taƙama. Parlon Hajiya Babba a cike yake da mutanen gidan, su Papa, Abba, Daddynsu Hamida, Safwan, Hamid,Sultan, Mama, Amma, Ummi, Mami, da ma sauransu duk suna zazzaune suna jiran shigowarsa. Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga parlon, ya tsaya daga gefe yana bin kowa da kallo, kafin a hankali ya zare glasses ɗin idonsa. Manyan idanunsa suka bayyana ya dinga kallon kowa fuskarsa ɗauke da murmushi, da sauri kuma ya ƙarasa ciki yana zuwa ya shige wajen Abba yana rungumeshi.. Murmushi shi ma Abban ya yi yana shafa kansa ya ce"Yaron kirki" langwaɓar da kansa ya yi yana jin wata irin nutsuwa na saukar masa, ya daɗe jikin Abba kafin ya tashi ya ƙarasa wajen Papa, haka ya dinga bin su ɗaya bayan ɗaya yana gaishe dasu kafin ya ƙarasa wajen Hajiya Babba. Ya shige jikin mahaifiyar tasa yana lumshe idanunsa, kasa ɓoye farin cikinta ta yi ta dinga taɓa jikinsa tana murmushi. Above 5mins kafin ya tashi ya zauna gefenta yana kallon sauran ƙannen nasa, cike da girmamawa suka dinga gaishe dashi, yana amsawa cikin sakin fuska. Abincin kala-kala aka dinga jerawa kan carpet, dan ranar a wajen zasu ci lunch tare, Abba ne ya ce"Abdusammad ina iyalin naka?" dafa kansa ya yi cikin daddadar muryarsa ya ce"suna mota Abba" Girgiza kai Abba yayi ya ce"a kira su mu gaisa ko" okay ya ce sannan ya kalli Aliyu ya ce"Buddy pls" ya gane me yake nufi dan haka ya taɓe baki ya ce"ni ɗan aikenka ne?" langwaɓar da kai ya yi ya ce"yi haƙuri kaje mana, ka ga ni baƙo ne and baƙonka Annabin ka" taɓe baki Aliyu y yi sannan ya juya ya fita. Kowa ya dinga murmushi a wajen dan daman an san halin dramar su. Tashi ya yi Hajiya ta kalleshi ta ce"ina kuma zaka je?" "Wanka zan yi Hajiya" Harararsa ta yi ta ce"daga zuwanka Abdu?" komawa ya yi ya zauna yana faɗin"okay Hajja mai Makka da Madinah na zauna" murmushi ta yi ta ce"da ya fi maka dai" After 2mins Aliyu ya dawo hannunsa ɗauke da wata ƙaramar baturiyar yarinya wadda ba zata shige 5yrs ba, sai murmushi take, sai kuma wata mata wadda ba zata shige 27yrs ba a bayansa, tana sanye da Abaya black colour, wadda ta haska farar fatarta. Ƙarasowa ciki ta yi ta dinga gaida kowa cike da fara'a, suma suka amsa sannan ta nemi gefen kujera ta zauna, Abba ne ya karbi yarinyar yana mata wasa sai dariya take, ganin kamar bata jin Hausa ya sanya ya ce"Abdusammad bata jin hausa ne?" girgiza kansa ya yi ya ce"tana ji amma kaɗan, Zahra nayi mata" "Kai baka mata kenan?" Ɗago kansa yayi ya kalleshi sai kuma ya ce"ina ruwanka dani? Kaji da kanka da rashin aurenka ma" tuntsirewa suka yi da dariya Aliyu ya riƙe baki sai kuma ya ce"oh gori ka ke min kenan?" "Yeh!" Cewar Abdusammad yana kafeshi da idanu, taɓe baki ya yi ya ce"to kaci kan ka, nima dai soon zan yi auren nan" "Better" ya ce a takaice sai kuma ya mayar da kansa wajen Abba suna ci gaba da hira. Da sallama suka shigo parlon kowannensu sanye da hijabi, aka amsa sannan suka ƙaraso ciki, cike da nutsuwa suka gaishe shi ya amsa yana cewa"Maimoon ko?" ya ƙare maganar yana nuna Maimoon da hannunsa, gyaɗa masa kai ta yi a nutse ta ce"Eh Uncle" jin jina kansa ya yi ya ce"ashe nagane ki" sai kuma ya nuna Hamida ya ce"Amrah right?" Girgiza kanta tayi ta ce"a'a Hamida, ga Amrah nan" ta nuna Amrah da ke gefenta kai a sunkuye, dafe kansa ya yi ya ce"ya aka yi ban gane ki ba Hamida, yarinya mai ƙoƙari" murmushi kowa ya yi sannan ya kalli Amrah ya ce"ita kuma wannan daman bata magana kurma ce" dariya suka yi ban da Amrah wadda jikinta ke rawa,ya ce"yara duk sun girma, sai aure ba" Dariya aka yi suka tashi kowacce ta koma kusa da mahaifiyarta ta zauna, maids suka fara serving kowa, koda aka zuba masa nasa ƙasa ya sakko ya zauna ya tankwashe ƙafafunsa sannan ya yi bismillah ya fara ci, tasowa yarinyar ta yi daga jikin Abba ta dawo wajensa, akan cinya ya ɗorata sannan ya fara bata abincin kamar yanda ya saba. Turo ƙofar ta yi ta shigo, sai dai ganin yanda aka cika parlon ya sanya ta tsaya tana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya, "Nana". Da sauri ta kalli wajen sai kuma ta yi murmushi ta ƙarasa ta tsuguna gabanta ta ce"Aunty Zahra ina yini?" murmushi Zahra ta yi ta ce"ashe za ki gane ni, haka ki ka girma?" Murmushi Nana ta yi ta ce"eh mana, kin manta kin tura min pictures ɗinki" Zahra ta jinjina kai sai kuma ta ce"eh haka aka yi" tashi Nana ta yi ta ƙarasa gabansa ta tsuguna cikin sanyin murya ta ce"sannu da zuwa Uncle" ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya haɗe rai, sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta. "Ina hijabin ki?" Sai da gabanta ya faɗi jin yanda ya yi tambayar, bata ɗago kanta ba ta ce"yana gida" Abdusammad ya ce"tashi ki je ki dauko" jiki a sanyaye ta tashi ta bar parlon, Aliyu ya sauke numfashi ya ce"ga Sheikh ɗin gidan ya dawo, yara duk sai sun shiga nutsuwarsu" Bai kalli Aliyu ba ballantana ya saka ran bashi amsa, ya ci gaba da cin abincinsa hankali kwance. Koda ya gama ci tashi ya yi bayan ya janye yarinyar da ke jikinsa yana cewa"Nur je ki wajen Ummi" gyaɗa kanta ta yi sannan ta koma jikin mahaifiyarta ta zauna, shi kuma ya kalli Hajiya ya ce"ina key ɗina Mama?" Kafin ta yi magana Safwan ya ce"an gyara komai Yaya, kuma a buɗe yake" ɗan kallonsa ya yi sai kuma ya ce"okay i see" daga haka ya nufi kofa ya fita daga parlon. Ba'a fi 2mins ba ta dawo sanye da dogon hijabi, kalle-kalle ta dinga yi ganin bata ganshi ba ya sanya ta ce"ina uncle ɗin?" yanda ta yi maganar muryarta na rawa ya sanya mutanen wajen dariya, Zahra ta ce"yana apartment ɗinsa, ki je yanzu ya fita" toh kawai ta ce sannan ta juya ta fita da sauri. Ta fi 2mins a gaban kofar tana tunanin shiga ko ta haƙura, daga ƙarshe dai kawai ta tura kofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Babu kowa a parlon sai tv dake faman aiki, ko ina neat sai tashin ƙamshi yake, tsayawa ta yi a tsakiyar parlon kamar zata yi kuka ta shiga faɗin "Uncle! Uncle! Uncle" Shiru babu amsa, ta sunkuyar da kanta hawaye na biyo fuskarta, tura baki ta yi sai kuma ta juya ta fito daga parlon. Tsaye ta sami Amrah tana zazzare idanu, ta dinga kallonta sai kuma ta ce"mene ya kawo ki nan?" sunkuyar da kai Amrah ta yi tana ƙoƙarin ɓoye hawayenta ta ce"kin gan shi?" girgiza kai Nana ta yi still looking at her ta ce"na kira shi bai amsa ba, maybe wani abun ya ke, zan je sai na dawo an jima" Amrah ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta ce"daman Abba yake kiran ki" daga haka ta juya, Nana ta dinga kallonta tana mamakin yanda take abu kamar mara lafiya, sai dai kuma tunawa da ita da abin da ke gabansu ya sanya ta sauke numfashi sannan tabu bayanta.. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Page 9... Ƙarfe 4:15 na yamma ta fito daga ɗakin tana murza idanunta, Amma ta dinga kallonta sai kuma ta ce"sai yanzu ki ka tashi?" gyaɗa mata kai ta yi tana ƙoƙarin rufe bakinta saboda hammar da take yi, ƙarasowa parlon ta yi ta zauna gefen Amma murya a sanyaye ta ce"Amma wai Yaya Safwan zan aura?" Shiru Amma ta yi tana kallonta, Nana ta ɗora kanta gefen kafaɗarta sannan ta ci gaba da faɗin "Amma me ya sa sai shi? Ita Amrah Yaya Sultan zata aura, ita kuma Maimoon Yaya Aliyu, shi ne ni zan auri Yaya Safwan?" Har sannan Amma bata iya cewa komai ba, ba dan bata ji abin da ta ce ba, sai dan bata da abin fadar. Hawayen Nana suka dinga sauka kan kafaɗarta, wanda ya sanyata ɗagowa ta kalleta a nutse ta ce"to mene ne dan kin auri Safwan ɗin? Shi ma kamar sauran yake, yana da sauƙin kai ma fiye da na sauran" Tashi ta yi daga jikin Amma ta miƙe tana shirin barin wajen ta ce"ni bana sonsa" daga haka ta nufi ɗakinta. Da idanu kawai Amma ta bita sai kuma ta sauke numfashi, da tana da dama to da tabbas ba zata bari a aurar da Nana yanzu ba, amma sanin bata da wannan ikon ya sa ta kawar da tunanin daga cikin ranta, ta mai da Idanunta kan tv tana kalla duk da ba fahimtar abin da ake take ba. Tana nan zaune har bayan mintuna goma Nana ta sake fitowa daga dakin, wannan karon sanye take da Abaya baby pink ta yi rolling mayafin abayar akanta, Amma ta dinga kallonta ba tare da ta tambayeta inda zata ba, Nana ta ƙaraso gabanta murya a ɗan shaƙe ta ce"zan je wajen uncle" toh kawai ta iya ce mata, ta juya ta fice daga parlon. Zaune ta hangeshi kan farar kujera a cikin flowers ɗin da ke garden, ta ɗan yi jim kafin ta ƙarasa wajen tana tafiya a hankali. Sultan na zaune yana danna waya ta ƙaraso gabansa, kujerar da ke gefen tasa ta ja ta zauna sannan ta ce"Yaya" yanda ta yi maganar a sanyaye ya sanya ya ɗago kansa, kallonta ya dinga yi ganin yanda fuskarta ta faɗa kamar ba ita ba, above 2mins kafin ya sauke numfashi ya ce"Nana ina zuwa?" "Yaya Amrah zaka aura?" Tambayar ta zo masa a bazata, dan haka ya gyaɗa mata kai kana ya ce"but why do you ask me?" Sunkuyar da kanta ta yi tana ƙoƙarin ɓoye hawayenta ta girgiza kanta. Sultan ya gyara zamansa yanda zai dinga kallonta sosai sannan ya ce"Nana" "Na'am Yaya" ta amsa masa muryarta na rawa. "Ɗago ki kalleni" A sanyaye ta ɗago kanta ta kalleshi sai kuma ta sake sunkuyawa hawaye na zubowa kan kuncinta. Mamaki ne ya cika shi, ya dinga kallonta baki buɗe kafin ya yi ƙarfin halin cewa"kuka ki ke Nana? Mene ne ya sanya ki kuka?" Girgiza masa kai ta yi tana goge hawayen da hannunta ta ce"babu komai" daga haka miƙe tana shirin barin wajen "Kina sona ne Nana?" Sultan ya yi maganar bayan ya miƙe tsayen shima. Wani irin dukan uku-uku ƙirjinta ya dinga yi, ta kasa magana haka kuma ta kasa barin wajen, takowa Sultan ya yi ya dawo gabanta yana kallonta ya ce"faɗa min kina sona ne? kin taɓa jin kina son na zama mijinki cikin estate ɗin nan? Or you daman u're just pretending all this time!" Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi, ya gyaɗa mata kai fuskarsa babu yabo babu fallasa. Ganin bata ce komai ba ya sanya ya ɗan furzar da iska daga bakinsa kana ya ce"shikenan, ai yanzu ma komai ya ƙare, zan auri wadda ba ita ce zaɓina ba, zan auri wadda ban taɓa mata kallon daya shige na ƙanwa ba, zan auri wadda ba lallai bane nayi farin ciki iya tsawon rayuwata" Cikin shassheƙar kuka ta ce"a'a Yaya, ni ban taɓa jin sonka ba, amma naji babu daɗi da aka ce min Amrah zaka aura, ban sani ba ko hakan na nufin na soka, ko kuma kawai ina maka kallon yaya ne all the time, Yanzu ma da nake kuka ba wai ina yi bane saboda na rasa ka, a'a ina kuka ne saboda irin kaddara ɗaya ce take bibiyarmu, kamar yanda zaka auri wadda baka ra'ayinta haka nima zan auri wanda bana so, wanda ko a mafarki ban taɓa tunanin zai zama miji a gareni ba. Sai dai gara kai namiji ne, kana da damar auren wadda ka ke so koda bayan wannan auren, amma ni wannan auren tamkar ƙarshen labarina ne, irin karshe mara kyau da ba'a fatan samu!" Daga haka ta yi gaba da sauri kamar zata faɗi ta bar wajen, Sultan ya dinga bin ta da kallo har ta ɓacewa ganinsa, ya runtse idanunsa yana jin zuciyarsa na masa wani irin suya da raɗaɗi, taya zai bar ta? Ta ya zai fara rayuwar aure da Amrah bayan Nana tana raye? "Innalil lahi wa ina ilayhi raji'un" Ya furta yana mai neman taimakon Allah akan masifar da take tunkarosa. **** Yana zaune kan ɗaya daga cikin luxury sofa ɗin da suka zagaye parlon ta fito daga kitchen, kai tsaye wajensa ta ƙaraso tana tafiya kamar babu laka a jikinta ta zauna gefensa. A hankali ta ɗora kanta bisa ƙirjinsa tana lumshe idanu saboda ƙamshin turaren daya gama cika ta, sanye yake da wata farar riga armless wadda ta fito da kowace sura ta jikinsa, ƙaton tatu ɗin da ke damtsensa na hagu ya bayyana, hoton zaki aka zana a jiki, sai kuma maciji ya faso kansa, abun gwanin ban sha'awa, Ajiye wayar da ke hannunsa ya yi jin yanda take sake narkewa a jikinsa yasa ya ce"lafiya dai?" Ya ƙare maganar yana jan kumatunta, sake lumshe idanu ta yi a karo na biyu cikin wata sassanyar murya mai kashe zuciyar wanda ake yiwa ta ce"Yallaɓai nawa, Abu Noor ɗina, mijina abin alfaharina, Allah ya kula min da kai, ya kare ka sharrin maƙiya, ya raba ka da Hajiya lafiya" bai san sanda ya saki wani yalwattacen murmushi ba, ya ɗago fuskarta da hannunsa yana kallonta ya ce"Amin ya rabbi Zahra" daga haka ya ɗora bakinsa kan nata ya mata light kiss dai dai nan Nana ta turo ƙofar ta shigo, da sauri ta saki handle ɗin tana sauke idanunta ƙasa. Zahra ta tashi tana gyara zamanta a ɗan dabarbarce ta ce"un..Nana... Nana ke ce?" "Ku yi hakuri ban san kuna nan ba na shigo" Cewar Nana ta juya zata bar parlon, "Kee zo nan!" Sai da taji hantar cikinta ta kaɗa saboda yanda taji ya yi kiran nata, ta juyo a hankali ba tare da ta yarda ta kalleshi ba. Gyara zamansa ya yi kan kujerar ya kafeta da idanu, a hankali ta ƙaraso wajen ta tsuguna gabansa muryarta na rawa ta ce"ga...gani uncle" Matsowa ya yi ya riƙe kunnenta da ke cikin mayafi fuskarsa a haɗe ya ce"baki iya sallama ba?" Girgiza kanta ta yi tana ƙoƙarin fashewa da kuka ta ce"nayi sallama wallahi, baku ji ni bane" Tashi Zahra ta yi tana kallon su ta ce"bari na ɗauko wayata" daga haka ta nufi hanyar upstairs a nutse, da idanu ya bita sai kuma ya sauke idanunsa kan Nana dake faman shessheƙar kuka ya ce"oh baki daina halin naki ba kenan ko?" shiru ta yi bata bashi amsa ba, ya saki kunnenta ya koma ya gyara zamansa. Wayarsa ya ɗauka ya ci gaba da dannawa yayinda take tsugune har sannan kanta a ƙasa, after 5mins ya ajiye wayar ya ɗago ya ɗan kalleta, hannunsa ya miƙa mata ba tare da ya ce komai ba, ɗago kanta ta yi ta kalli hannun sai kuma ta ɗora nata akai ta miƙe tsaye, gefensa ya zaunar da ita kana ya ce"kin yimin shiru ko kuwa?" Kamar ƙaramar yarinya haka ta dinga sauke ajiyar zuciya tana rage kukan nata, sai da ya ga tayi shiru gaba ɗaya sannan ya girgiza kansa ya ce"u will never change ko Nana?" sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta, taɓe baki ya yi ya ce"kurma ki ka zama?" da sauri ta ɗago kanta sai kuma a sanyaye ta ce"Uncle sannu da zuwa" Kallonta kawai ya yi sai kuma ya ɗauke kansa, ta ɗan yi murmushi sannan ta sake cewa"uncle ina tsarabata?" "Daga zuwana ɗazu? To ban zo da ita ba" tura baki ta yi ta ce"ai nasan ka siyo mana ko Uncle, ka siya min da Abaya?" ɗauke kansa yayi yana murmushi ya ce"kin bada kudin ne?" girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce"to ai ni ka san banida kuɗi" yanda tayi maganar da iya gaskiyarta ya sanya shi dariyar da bai shirya ba, ya ce"to nima ban dashi ai" Langwaɓar da kanta ta yi tana murmushi ta ce"kaii kana da kuɗi dayawa ma kuwa" "Nace miki?" Ya tambayeta muryarsa a sake, girgiza kanta ta yi tana murmushi ta ce"ai kowa ya sani, ko a goggle aka yi searching AM Shuwa za'a ganka" "Ko?" Ya sake faɗa a takaice, gyada masa kai ta yi dai dai nan Zahra ta dawo parlon hannunta riƙe da wayarta. Kallonsu ta yi tana murmushi ta ce"amma dai yau Nana a nan zaki kwana ko?" Da sauri ta girgiza kanta, Zahra ta ce"haba dai, ba zaki zauna wajen Uncle ɗin naki ku yi hira ba? Ko yanzu kin girma?" Murmushi kawai Nana ta yi bata ce komai ba, tashi ya yi ba tare da ya sake bi ta kansu ba ya haye sama, Zahra ta zauna in da ya tashi tana kallon Nana ta ce"wai Nana naga kin girma" kwaɓe fuska ta yi kamar zata yi kuka ta ce"kaii Aunty Zahra, ni ɗin!" Jinjina kai Zahra ta yi cikin zolaya ta ce"eh mana, gashi za'a miki aure, ai wadda ta girma ita ake yiwa aure" shiru Nana ta yi bata ce komai ba, lokaci ɗaya yana yinta ya sauya, daga na farin ciki zuwa na damuwa. Zahra ta lura da hakan dan haka ta riƙe hannunta cike da damuwa ta ce"mene ne? Ko dai u're not happy about it?" kasa ɓoye damuwarta ta yi duk yanda ta yi ƙoƙarin yin hakan, ta faɗa jikin Zahra tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi. Hannunta duka biyun ta sanya ta rungumeta tana jin yanda take kukan kamar ranta zai fita, shafa bayanta ta dinga yi da hannu ɗaya tana cewa "yi hakuri Nana, faɗa min mene ne?" Cikin kuka ta ce"aunty bana son sa, ni bana son auren, bana so a yimin aure yanzu, tsoro nake ji Aunty.." Ta ƙare maganar tana sake ƙanƙameta, sosai Zahra ta ji tausayinta, ta yi shiru na wasu mintuna kafin ta yi karfin halin cewa"haba Nana mene ne abin da ki ke tsoro ɗin? Ɗan uwanki zaki aura fa, mu ma ba duk haka muka yi auren ba, sanda na auri Uncle naki ban fi 18yrs ba, yanzu kusan shekaru tara kenan, ai a haka zaki saba, da an yi auren zaki daina jin tsoron kin ji" girgiza kanta ta dinga yi tana kuka ta ce"a'a Aunty ni bana so, karatu nake so nayi, bana son auren nan, mutuwa zan yi idan aka yimin wallahi!" "Keee!" Suka ji muryar Abdusammad a kansu, da sauri ta saketa jikinta na rawa, Zahra ta dinga kallonsa ganin yanda ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba, idanunsa ƙur akan Nana wadda ta sunkuyar da kanta sai kuka take a hankali, bai ce komai ba ya durƙusa gabanta yana kallonta ya ce"why?" ɗago kanta ta yi kawai ta shige jikinsa shima tana sake sakin wani sabon kukan, kasa cewa komai ya yi yana jin yanda hawayenta duk ya jiƙa masa riga. Ganin taƙi daina kukan ya sanya ya zauna ta sake shigewa jikinta tana ci gaba da kukanta. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH🌹* Page 10... Sai da ta yi shiru dan kanta ta fara sauke ajiyar zuciya sannan ya ɗago kansa ya kalleta, ta rufe fuskarta a jikinsa dan haka ya sanya hannunsa na dama a hankali ya ɗago kanta, fuskarta a jiƙe da hawaye haɗi da majina sai sauke numfashi take, ya ɗan girgiza kansa kafin ya goge mata da gefen hannunsa yana cewa"ba zaki girma ba ko? komai kuka ki ke masa" tana jin sa amma bata buɗe ido ba ta ci gaba da shessheƙar kukanta a hankali. Tashi ya yi bayan ya janyeta daga jikinsa ya kalli Zahra dake zaune tun ɗazu tana kallonsu ya ce"zan je wajen Aliyu" to kawai ta ce a sanyaye. Ya mai da idanunsa kan Nana dake zaune a kujerar ya ce"taso mu tafi" bata yi masa musu ba ta tashi ta riƙe hannunta cikin nasa sannan suka bar parlon. Har suka ƙaraso apartment ɗin Aliyu babu wanda ya ce komai a cikinsu, ya samu Aliyu zaune cikin garden dashi da Maimoon, tana ganinsa ta miƙe muryarta na ɗan rawa ta ce"barka da yamma uncle" ba tare da ya kalleta ba ya ce"Barka" ta bi ta gefensu ta bar wajen da sauri. Zama ya yi kan farar kujera yana kallon Aliyu babu yabo babu fallasa ya ce"and what's this? mene zaka kira yarinya apartment ɗinka? kome zaka tattauna da ita ba kai ya kamata kaje gidansu ba?" Aliyu ya ɗan yi murmushi ya ce"to malam naji ba zan sake ba" harararsa Abdusammad ya yi ya ce"kana ɗaukan maganata wasa ba? kai a matsayinka da shekarunka kana ganin ya dace ka dinga keɓancewa da mace wadda ba muharramarka ba?" Dafe kansa ya yi ya ce"oh my god, naji ba zan sake ba, shikenan?" taɓe baki ya yi ya ce"idan ma ka sake mene nawa a ciki?" Daga haka ya kalli Nana da ke tsaye a wajen kamar statue ya ce"tafi gida" bata ce komai ba ta juya ta bar wajen da sauri. Aliyu ya ɗan kalleta sai kuma ya mai da idanunsa kan Abdusammad ya ce"wannan yarinyar ko kai ne ka haifeta sai haka" kwalin dabinon da ke wajen ya farka ya ɗauka guda ɗaya ya sanya bakinsa bayan ya yi bismillah sannan ya ce"to ai ni ɗin na haifeta, kuma ma da ace nayi auren wuri ai da na haifi kamarta, she's 16 fa yanzu" "Bata ma cika ba" Aliyu ya yi maganar yana dariya. Shiru ya yi kamar me tunani sai kuma can ya ce"ni ko na tambayeka mana" Aliyu ya gyara zamansa ya ce"ina ji" "Yaushe aka yi maganar auren yaran nan?" Kallonsa ya yi sai kuma ya ce"wani abun ya faru ne?" Haɗe rai ya yi ya ce"amsa zaka bani malam" Murmushi Aliyu ya yi sannan ya ce"ba'a fi 3days ba, nan da 1 month za'a ɗaura auren idan Allah ya kai mu" jin jina kai Abdusammad ya yi kafin ya sake cewa"da wa da wane za'a musu auren?" Murmushi kawai Aliyu ya yi sannan ya ce"dukansu mana, Maimuna, Hamida, Amrah sai kuma Nana" "Nana dai?" Gyaɗa masa kai ya yi, ya zare kwallon dabinon daga bakinsa kana ya ce"wannan yarinyar? Ba sun girmeta ba?" Aliyu ya ce"eh ita ce ƙarama a cikinsu, sa'ar Juwaira ce fa, kawai dai tana da garin jiki ne shiyasa ta shiga cikinsu, kuma ita ma ta kammala karatun secondary" taɓe baki ya yi ya ce"and saboda haka yasa za'a aurar da ita yanzun? Wane ya bada wannan shawarar?" Aliyu ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce"masu bada shawarar aurar da ya'yan gida mana, su Uncle ne da Hajiya" tashi ya yi yana gyara zaman rigar jikinsa kafin ya ce"I'll talk to them in sha Allah, ya kamata a ɗan bar irin wannan auren haka nan" Tashi shima Aliyun ya yi a ɗan dame ya ce"haba Buddy, me ya sa koda yaushe ka ke Ƙoƙarin creating problems ne? haka fa ka yi akan aurenka, ka je ka auri Zahra duk da ka san ba'a irin wannan auren, ba ka yi shawara da kowa ba, ka yanke hukunci sannan yanzu ma ka ce zaka yi magana akan auren yara?" Ɗauke kansa ya yi ba tare da ya ɗauki maganar Aliyun da muhimmanci ba ya ce"eh na auri Zahra saboda ita nakeso, and na yaba da hankalinta da kuma tarbiyyarta, saboda haka yasa na aureta duk da bata kasance ƴar cikin wannan dangin ba. Ba wai ina son tayar da hankalin dangi bane, a'a ina so ne naga sun yi abin da ba za'a tauyewa wani ko wata haƙƙi ba! yanda ban yarda da auren zumunci ba haka ba zan bari a tilastawa yara auren zumunci ba! Idan ma za'a yi to a zauna a yi zube ban kwarya kowacce ta faɗi wanda take so kafin sannan a aura mata shi, idan kuma ba haka ba sai dai a haƙura da auren wlh!" Ya ƙare maganar a ɗan zafafe, sai kuma ya bar wajen, Da idanu kawai Aliyu ya bi shi yana tunanin maganganunsa, Allah ya kiyaye dai kada ya tada tarzoma irin ta wancan lokacin, Aliyu ya yi maganar a ransa yana sauke numfashi sai kuma ya juya shima ya bar wajen. Kai tsaye apartment ɗinsa ya koma, sanda ya shiga zaune ya tarar da Noor jikin Zahra tana danna wayarta, tana ganinsa ta sakko daga jikinta da gudu ta zo ta riƙe ƙafafunsa cikin muryarta ta yarinta ta ce"welcome Abbiey" hannunsa ya sanya ya ɗauketa ya ɗagata sama ya yi juyi da ita, ta dinga sheƙa dariya wadda ta fito da asalin kyanta da kuma kamarta dashi, kafin daga bisani ya mai da ta kafaɗarsa yana murmushi ya ce"thank you my baby girl, yau kin yini wajen su Hajiya Babba ko?" gyaɗa masa kai ta yi tana kwanciya a kafaɗar tasa ta ce"ina can wajen Hajiya da su Aunty Juwaira, muna ta wasa" sauketa yayi yana faɗin"yarinyar ƴar gata, je ki wajen Ummi" da gudu ta tafi shi kuma ya nufi hanyar upstairs da sauri. Da idanu kawai Zahra ta bishi sai kuma ta sauke numfashi ta kalli Noor ta ce"baby zo nan ki kwanta" hawa jikinta ta yi ta kwanta kasancewar ta gaji sosai ya sanya nan da nan bacci ya ɗauketa. Zahra ta dinga shafa kanta har baccin nata ya yi nisa sannan ta ɗauketa ta haura sama da ita. A bedroom ɗinta ta kwantar da ita, ta rufa mata duvet saboda sanyin yamman daya buso, sannan ya fita daga ɗakin kai tsaye kuma nasa bedroom ɗin ta nufa. Zaune ta sameshi kan sofa yana danna system ɗinsa, ya zare rigar jikinsa duk da sanyin da ake, faffaɗan ƙirjinsa ya bayyana mai ɗauke da zanen tato a jiki, wajen ya yi luf da kwantaccen gashi wanda ya ƙara masa kyau. Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zauna a ƙasansa ganin bai kalleta ba ya sanya ta ce"wane ya taba min kai ne?" ta ƙare maganar tana ƙoƙarin taɓa fuskarta, janye hannunta ya yi yana faɗin "babu komai" Zahra da ɗan murmusa kafin ta ce"kamar ban sanka ba? Dan Allah me aka yi maka?" Ɗago dara-daran idanunsa ya yi ya zuba mata, ta yi saurin sunkuyar da mata saboda kwarjinin da ya yi mata, hannunta ya kamo yana faɗin "har yau baki daina jin kunyata ba?" Murmushi ta dinga yi ƙasa-ƙasa, ya tashi yana riƙe hannunta ya ce"zo ki ji" miƙewa ta yi tabi bayansa kamar yanda ya umarceta. **** Bayan sallar magriba tana zaune a parlon tana karatun wani novel mai taken “Wrong decision” wayarta dake gefenta ta fara ƙara, ta gefen ido ta kalli wayar ganin numbern ya sanya bata ɗauka ba, ta mai da Idanunta kan karatun duk da ba fahimta take ba. Amma na zaune opposite ɗin ta tana buɗe sabbin mayafan data siyo ɗazu taji wayar nata ringing, ɗan tsaki ta yi ba tare da ta kalleta ba ta ce "ki ɗaga kiran ko kuma ki kashe wayar kin daman" Toh kawai ta iya cewa sannan ta ɗago wayar ta saka ta a Flight mode ta mayar ta ajiye, after 5mins Amma ta tashi bayan ta gama haɗe veils ɗin ta diba ta nufi daƙinta, tana rufe ƙofar Nana ta tashi ta ɗauki wayarta da gudu ta fita daga cikin parlon. A jikin balcony ta tsaya ta leƙa compound ɗin bata ga kowa ba sannan ta kunna wayar ta danna numbern da aka yi kiran, buga ɗaya aka ɗauka daga ɗaya ɓangaren Junaid ya ce "Why aren't picking my calls?" Murya can ƙasa ta ce"an hanani ne a gida" Junaid ya ɗan yi shiru kafin ya numfasa ya ce"kin faɗa musu abin da nace miki?" Gyaɗa kai ta yi kamar yana gabanta sannan ta ce"eh" "Me suka ce?" Ya faɗa a takaice. "They refused!" Ta yi maganar babu gwarin gwuiwa. Furzar da iska ya yi daga bakinsa har taji a cikin wayar kafin ya ce"yanzu kenan ya za'a yi?" Girgiza kanta ta yi ta ce"nima ban sani ba, ina ga kawai mu haƙura sir" "Mu haƙura? Nana ko dai daman baki sona ne?" Girgiza kanta ta yi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce"A'a ina sonka mana, amma ba zan iya bijirewa gidanmu ba, koda na gwada ba zan yi nasara ba sai dai na ɓata kaina a wajen kowa, sannan Ammata ta ce kar na sake maganar idan har ta isa dani, kaga dole nayi shiru. Bana son abin da zai tada hankalin yan gidanmu, zan haƙura na auri wanda suka zaɓa min koda hakan na nufin rugujewar farin cikina!" Junaid ta dinga kallon screen ɗin wayar baki buɗe, he can't believe a ce ta haƙura da sauri haka, jin an ɗauki lokacin bai ce komai ba ya sanya ta kalli wayar ko kiran ya katse, gani ta yi yana kan layi dan haka ta sake maidawa kunnenta a sanyaye ta ce "Zan yi haka ba wai dan bana sonka ba, sai dan na kare mutuncin iyayena da kuma gidanmu gaba ɗaya" Runtse idanunsa ya yi yana jin kalamanta kamar tana ɗiga masa dalma ne a cikin zuciya, koda wasa bai yi tunanin rabuwa da ita nan kusa ba, kuma ba zai taɓa barin hakan ta kasance ba. Ya saita nutsuwarsa kafin ya ce "Shikenan Nana naji, amma ina son na ganki idan har babu damuwa" Muryarta a ƙarye ta ce"again kuma sir?" Gyaɗa kansa ya yi sannan ya ce"eh Nana, ina son magana da ke, koda hakan na nufin magana ta ƙarshe tsakaninmu, ki min wannan alfarmar Nana!" Lumshe idanunta ta yi hawaye na zirarowa kan kuncinta, ta sauke ajiyar zuciya tana jin ba zata iya rejecting ɗinsa ba ta ce "Shikenan sir, I'll, a gidan Aunty Ramlah?" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"eh ko anan ɗin ma, zan faɗa miki sanda nakeson mu haɗun sai ki zo" Ta numfasa sannan ta ce"okay sir" "Thank you Nana" Ta gyaɗa masa kai sannan ta kashe wayar, kifa kanta tayi jikin ƙarfe hawaye na zubowa kan fuskarta kamar an buɗe famfo, ji take kamar ta je ta fadawa Abbanta bata son Yaya Safwan sir Junaid take so. Amma ta san ko ta faɗa ba zai taɓa tasiri ba, sai dai ya haddasa gaba tsakaninta dashi, domin Abba na ɗaya daga cikin wanda suka riƙi wannan al'adar kamar addini. Ta jima a wajen kafin ta ɗago kanta jiki babu kwari ta koma gida, zaune ta sami Amma a parlon tana cin abinci, ta dinga kallonta sai kuma ta ce"ina ki ka je?" Sai da taji zuciyarta ta buga, ta ɗan haɗa kalmomin bakinta da kyar ta ce"da....daman naje waje ne zan yi waya, kuma nan babu network" "Dawa ki ke wayar?" Amma ta yi tambayar tana kai spoon ɗin shinkafar bakinta, rasa abin cewa ta yi dan bata yi tsammanin zata mata tambayar ba, jin bata ce komai ba ya sanya Amma ta ce"baki ji me nace ba ne?" "eh?" Nana ta yi maganar tana kallonta, harararta ta yi kafin ta ce"kina tunanin banza da wofi baki ji me nace ba right?" ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, tsaki Amma ta yi ta ce"je ki ɗebi abinci ki ci my friend, and kada ki daina tunani ki bari hawan jini ya kamaki" sauke ɓoyyayiyar ajiyar zuciya ta yi sannan ta nufi kitchen ɗin da sauri tana godewa Allah a ranta. **** Ummi ta dinga kallonsa ganin yanda yake maganar da zallar gaskiyarsa yasa ta ce"Sultan! Sultan! Sultan!" ɗago jajayen idanunsa ya yi ya kalleta murya a ciki ya ce"na'am Ummi" "Sau nawa na kira ka?" Kallonta ya yi sai kuma ya ɗauke kansa yana huci, kwafa ta yi sannan ta ce"kar ka jawo min magana, kar ka jawon abin da zai dameni, ni ban aikeka ba, mahaifinka shi ne babba a wajen zartar da wannan hukuncin, saboda haka dole ka yarda dashi. Kar ka je ka yi abin da zai zo ya ɓata zumunci" Tashi tsaye ya yi yana kallonta muryarsa a dake ya ce"nifa ba ɗauko miki magana zan yi ba Ummi, ni babu abin da zan yi, kawai zan fadi gaskiyata ne, ni ba za'a min auran dole ba wallahi! Kamar yanda Yaya Abdusammad ya dage akan ba zai ba kuma a ka bar shi haka nima ba zan yarda ba wallahi, saboda wannan ba adalci bane, shi an bar shi ya auro wadda yake so sannan dan an zo kan mu a ce za'a ci gaba da auren zumunci, wallahi ba zamu yarda..." Marin da Ummi ta sauke masa shi ne ya hana shi ƙarasa faɗar abin da ke bakinsa, ya dinga kallonta hannunsa dafe da kuncinsa, cikin tsananin ɓacin rai take kallonsa tana nuna shi da yatsa ta ce "Wallahi idan na sake jin makamanciyar wannan maganar a bakinka sai na saɓa maka fiye da tunaninka! Dole ne ka yi biyayya ga manyanka! Da kai da Abdusammad ba abu ɗaya bane! Kuma ba zaku taɓa zama ɗaya ba, dan haka kai baka isa ka ce zaka ɓata abin da aka gida shekara da shekaru ba! Idan kuma har ka ce zaka yi hakan to sai dai ka nemi wata uwar ba dai ni ba!" 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Page 11... Kallonta ya dinga yi ba tare da kiftawa ba, Ummi ta yi tsaki sannan ta juyar rai ɓace ta bar wajen, sauke idanunsa ƙasa ya yi yana ƙoƙarin mai da hawayensa, dakyar ya ja ƙafarsa ya bar wajen jiki a sanyaye. Abba ya dinga kallonsa yana jin jina kai har ya kai ƙarshen maganar sannan ya sauke numfashi ya ce"yanzu me ka ke nufi Abdusammad?" gyara zamansa ya yi kana ya ce"yauwa Abba, what i mean is kada a tilastawa yaran nan, a bari su zaɓi wanda suke ganin zasu iya rayuwa dashi. Saboda aure ba fa ƙaramar magana ba ce, rayuwa ce wadda ake tunanin a yi ta har abada, so idan har za'a ɗorasa a bisa son zuciya ina ganin za'a samu matsala ne babba ba ƙarama ba" Girgiza kai Abba ya yi yana ƙoƙarin tashi daga kan sofar ya ce"kana so ka ce a bar magana auren nan? Kada a musu aure ko me ka ke nufi?" da sauri ya ƙaraso gabansa ya ce"a'a Abba ba wai haka nake nufi ba, ina son dai a tambayi kowacce wanda take so a cikinsu, haka suma mazan a tambayesu" "Akan me? A saboda mu bamu isa mu zaɓa musu mazajen aure ba?" Abba ya yi maganar a ɗan fusace. Furzar da iska ya yi daga bakinsa sannan ya ce"a'a Abba, kun isa mana, amma kada a yi musu abin da zai ɓata farin cikinsu, ni nawa tunanin kenan" "To an gode da shawara, amma ba za'a fasa wannan auren ba!" Daga haka ya juya ya bar parlon kamar zai tashi sama, Girgiza kai Abdusammad ya yi yana tunanin ta inda zai ɓullowa al'amarin, yafi 3mins a tsaye kafin ya sauke numfashi ya fice daga parlon shima. **** Hajiya ta dinga kallonta sai kuma ta ce"ban gane ba?" tura baki Nana ta yi ta ce"haka Mama ta ce wai Yaya Safwan zan aura, haka ne Hajiya?" Jinjina mata kai ta yi ba tare da ta yi magana ba, Nana ta ɗan kwaɓe fuska ta ce"amma Hajiya me ya sa sai shi zan aura? naga...." "Bana son sake jin wannan maganar a bakinki kin ji Nana!" Hajiya ta yi maganar fuska babu wata walwala, numfashi Nana ta sauke sannan ta gyaɗa mata kai. Ta ce"ki je kitchen wajen Rabi ki ce ta baki robar" Toh kawai ta ce sannan ta tashi jiki a sanyaye ta nufi kitchen ɗin, After 2mins ta fito hannunta riƙe da wata farar roba mai ɗauke da dambun nama. Ta dinga kallonsa kafin ta ƙaraso a sanyaye ta ce"Hajiya sai da safe" "Allah ya tashe mu lafiya" Hajiya ta bata amsa idanunta na kan Abdusammad, Amin ta ce sannan ta ɗan kalleshi ganin ba ita yake kallo ba ya sa a sanyaye ta ce"uncle sai da safe" Jinjina kansa ya yi ba tare da ya ce komai ba, ita ma kuma bata tsaya jiran amsar tasa ba ta juya ta fice daga parlon. Hajiya Babba ta ɗan yi murmushi mai kama da na takaici kafin ta ce"Abdusammad! Abdusammad! Abdusammad!" "Na'am Hajiya" Ya amsa mata still looking at her. Fuskarta babu alamun fara'a ko annuri ta ce"kana son ka ɓata min rai ne daga zuwanka? ko kuma kana son tarwatsan iyali daga dawowarka?" Numfasawa ya yi kafin ya ce"Allah ya huci zuciyarki Hajiya, amma ba haka nake nufi ba, kawai dai..." Dakatar dashi ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu, ya dinga kallonta bai ce komai ba. Tashi ta yi tana kallonsa ta ce"kai ka yi abin da ka ke ganin shi ne dai dai, ka auri wadda ka ke ganin ita ce dai dai da kai, duk da baka shawarceni ba a matsayina na mahaifiyarka. Amma na yi haƙuri na kau da idona daga kan ka, ba dan ban ji zafin abin da ka yi min ba, ba dan ba'a dinga ƙananun maganganu a cikin gidan nan ba, ba dan zuciyata bata min zafi kullum ba, sai dan nayi hakuri kuma ina jin wata rana zan sauya wannan al'amarin. Saboda haka kada ka zo ka bata min rai da zan ji daman baka dawo ba dan Allah Abdusammad!" Sunkuyar da kansa ya yi yana jin ransa a dagule dan ko kaɗan baya son ɓacin ranta, ta sauke numfashi sannan ta juya ta shige ciki abinta. Da idanu ya dinga bin ta har ya daina hangota, ya mike jiki a saluɓe ya fice daga parlon shima. Koda ya shiga gida zaune ya tadda Zahra a parlon tana jiransa, sanye take da wata sleeping dress doguwar riga mara nauyi wadda ta tsaya mata iya gwuiwarta, ta yi parking ɗan gashinta da bashi da yawa a ƙasan ƙeyarta. Sai tashin ƙamshi take gwanin sha'awa, tana ganinsa ta tashi tana murmushi ta ce"sannu da zuwa" jinjina mata kai kawai ya yi sannan ya nufi hanyar upstairs, Zahra ta bishi da kallo ganin har ya haye sai kuma tabi bayansa. Yana shiga ɗakin ta shigo, ta saki handle ɗin ƙofar har sai da ya yi ƙara wadda ta sanya ya juyo ya ɗan kalleta sai kuma ya ɗauke idanunsa. "Lafiya da Abu Noor?" Bai juyo ba haka kuma bai bata amsa ba, ya zare rigar da ke jikinsa ya nufi toilet. Zama ta yi gefen gado tana tunanin wanda ya sake ɓata masa rai da daren nan, ta dinga jiransa har bayan 20mins sannan ya fito daga toilet ɗin sanye da bathrobe jikinsa sai ɗigar ruwa yake. Gaban dresser ya tsaya ya gyara kansa sannan ya ɗan shafa body lotion ɗin da yake sakawa ya feshe jikinsa da turare nan da nan ɗakin ya ɗauki wani ƙamshi na musamman. Press ya ƙarasa ya buɗe ya dauko pyjames maroon colour ya saka sannan ya juya yana shirin fita daga ɗakin, ganin haka ya sanya ta tashi tana kallonta muryarta na rawa ta ce "Ina kuma zaka je? Idan wani abun aka yi maka ka sanar dani dan Allah" Cak ya tsaya amma bai juyo ba, ta ƙarasa wajensa da sauri ta rungumeshi ta baya tana shessheƙar kuka, ji ya yi jikinsa ya yi sanyi, ya janyo hannunta ya dawo da ita gabansa yana kallonta ganin yanda take kuka yasa ya ɗan juya gajiyayyun idanunsa ya sauke a kanta, dakyar ya iya laɓɓansa da juna kafin ya a sanyaye ya furta "And what is this?" Shigewa jikinsa ta yi tana kukan a hankali, ya girgiza kansa sannan ya ɗago fuskarta yana murmushi ya ce"tafi ki kwanta" a shagwaɓe ta ce"a'a ka faɗa min abin da aka yi maka dan Allah" jan kumatunta ta yi yana kallon wani wajen ya ce"idan na faɗa miki akwai abin da zaki iya ne? Uhm.." Yanda ya yi maganar ya sanya ta yi murmushi ta shiga jan cute beard ɗinsa sannan ta ce"eh mana, I'll, zan yi faɗa da duk wanda ya taɓa min mijina, I won't take it likely with that person" Faɗaɗa fuskarsa ya yi yana sake janta jikinsa ya ce"ko?" Da sauri ta kalleshi fuska a ɗan kwaɓe ta ce"eh mana, just tell me wane ne" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Hajiya Babba ce!" Saurin rufe bakinta ta yi tana girgiza kai, ta sake shi tana murmushi ƙasa-ƙasa, kamo hannunta ya yi ya ce"ina kuma zaki, ki ka ce za ki yi faɗa da koma wane?" Zaro idanunta ta yi tana faɗin "Allah na tuba, ban san Hajiya Babba ba ce, Allah ka yafeni" Ta yi maganar tana daga hannunta sama alamar roƙo. Dariyar da bai yi niyya ba ya yi kafin ya ce"ashe? Daman ba za ki iya tsayawa mijin naki ba ko?" Jan kumatunsa ta yi tana murmushi ta ce"zan iya mana, amma ban da akan Hajiya, in dai akan Hajiya Babba ne to sai dai na kwanta maka" Janye jikinsa ya yi yana dariya ya nufi hanyar fita daga ɗakin yana faɗin "ina Noor?" "Ta yi bacci" Zahra ta bashi amsa tana bin bayansa. **** Around 11pm tana kwance tsakiyar gadonta ta yi nisa cikin karatun littafin HASKEN CIKIN DUHU wanda Nanameera ta rubuta kira ya shigo wayarta, ɗan tsaki ta yi dan ji take kamar an katse mata jin daɗi, ta kalli numbern sai kuma ta ɗaga ta yi shiru. Daga ɗaya ɓangaren Junaid na zaune tsakiyar parlon da ke apartment ɗinsa idanunsa bisa tv yana kallon game ya ce "Nana" Murya can ƙasa ta ce "Uhm" "Kin yi bacci ce?" Girgiza kanta ta yi kamar yana gabanta ta ce "A'a ban yi, kawai I'm doing something ne" Junaid ya rage sound ɗin tv jin ana ihu kafin ya ce "Me ki ke yi da daren nan?" Kamar ba zata ba shi amsa ba sai kuma ta ce "Karatun novel nake" Gyara zamansa ya yi yana faɗin "Ashe? Wani novel ne haka da har ya hana ki bacci da wuri ke da ki ke kwanciya da wuri Nana?" Ƙaramin yatsarta ta sanya a baki tana taune farcenta ta ce "Karatun ne yake min daɗi" Junaid ya jinjina kansa yana murmushi ya ce"lailai, kina jin daɗin ki, to ki bani labarin littafin" Murmushi ta yi tana tashi zaune a kan gadon ta ce "Toh kana ji" Shiru ta ji ya yi, ta ɗan kwaɓe fuska a shagwaɓe ta ce"ba ka ji ne?" Yana sake jingina da kujerar da yake kai ya ce"ina jin ki fa" Murmushi ta yi ta ce"to sunan jarumar Salma, shi kuma jarumin sunansa Zayyad, Yaya Yad me paracetamol, ita ƴar talakawa ce shi kuma ɗan masu kuɗi, yana da girman kai kuma baya ji, sai yake zuwa garinsu a lokacin tana sai da lemo a bakin kasuwa suka fara haɗuwa ya mata rashin mutunci ta masa rashin kunya..." Ta tsaya tana dariya a hankali. Dariyar shi ma ya yi ya ce"ina jin ki" "To sai wata rana ya taimaketa wasu sun biyota, shikenan ya kai ta gidansu, ta fara zama yar gayu za'a sakata a makaranta kawai sai aka masa asiri ya haukace, kuma aka ce ita ta haukatashi dan haka tare zasu tafi duk in da zai je, abun tausayi, ta dinga wahala dashi ta samo masa abinci, ta basa kudi, ya daketa ya shaketa a haka har ya samu lafiya. Aka musu aure, kawai! Kawai sai iyayensa suka zo tafiya dashi ya ce wai ya saketa..." Ta fashe da kuka tana jan numfashi, da sauri Junaid ya ce "A'a Nana sorry kin ji, bar bada labarin haka kin ji" Gyaɗa masa kai ta yi tana ci gaba da kukanta, ya kwantar da murya ya ce"nace ki yi shiru ko, ki kwanta sai da safe" Toh kawai ta ce sannan ta kashe kiran, ta juya ta kwanta tana ci gaba da kukanta har bacci ɓarawo ya saceta. **** Kusan sati biyu kenan, abubuwa sai kankama suke a cikin estate ɗin, ana ta shirye-shiryen biki wanda za'a yi nan da wata ɗaya da rabi. Duk yanda Abdusammad ya so ya sauya lamarin abun ya ci tura, dan Hajiya Babba ta hana shi magana a kai, dan haka dole ya saka ido kawai ba dan ya so ba. A ɓangaren Sultan kuwa kullum cikin damuwa yake, shi ma tun bayan da Ummi ta ce kar ya yi magana bai tada zancen ba, amma ko kaɗan bai ji wani abu ya ragu a zuciyarsa daga son da yake wa Nana, sai ma wani sabbin abubuwa dake son bijiro masa. Dan yanzu baya iya yini ɗaya bai sakata a idanunsa ba, ko dai su haɗu a Apartment ɗin Hajiya Babba, ko kuma ya je gidansu da sunan gaisar da Abba. Tana zaune gefen famfon tana wanke inner ɗinta Amrah ta ƙaraso wajen hannunta riƙe da ƙaramin bucket, zama ta yi gefenta ba tare da ta ce komai ba, ita ma kallonta kawai ta yi sai kuma ta ci gaba da abin da take, ba'a fi 2mins ba Maimoon ta ƙaraso wajen ita ma hannunta riƙe da nata bucket ɗin, ta zauna itama ta zuba uban tagumi, Nana ta ɗan kallesu ganin yanda suka yi sai kuma ta ce"ina Hamida?" "Mama bata barta ba ina ga" Cewar Maimoon hannunta tallafe da haɓarta, numfasawa ta yi sai kuma ta ce"to ko muje gidansu ne?" girgiza kai Amrah ta yi ta ce"idan muka je can ba zamu sake ba, that's why yasa nace mu zo nan ɗin ma" Maimoon ce ta ce"eh nima haka nake tunani, wai yanzu da gaske auren nan za'a yi?" murmushin takaici Nana ta yi kafin ta ce"gashi kuwa, ni yanzu kullum hankalina a tashe yake, ji nake kamar wani abu mara kyau zai faru dani ɗin nan wallahi" tsaki Maimoon ta yi ta ce"ki ci gaba da ɗaukan haka, sai ki ga ya faru" Kallon Amrah ta dinga yi ganin yanda ta ƙura masa idanu bata ko kiftawa, sam ba kula dasu ba dan haka ya yi shigewarsa. Nana ta janyo hannunta tana faɗin"keee wannan kallon...." Maganar ta maƙale ganin yanda hawaye ki biyo kan fuskarta kamar an buɗe famfo, suka dinga kallonta da mamaki kafin Maimoon ta yi ƙarfin halin cewa" lafiya dai Amrah?" Cikin shassheƙar kuka ta ce "Kowa yana faɗar abin da ke ransa dan yaji daɗi, dan haka nima gara na faɗa ko zan samu sauƙi, wallahi tallahi ban taɓa son Yaya Sultan ba, ban taɓa masa kallon wanda nake so na aura ba, kullum zuciyata da tunanina suna wajensa, kullum fatana ya dawo ƙasar nan a haɗani aure dashi, kullum dashi nake kwana da shi nake tashi, ina sonsa! Ina son sa tun ina ƙarama wallahi!" With so much confused suke kallonta, Nana ɗan girgiza kanta tana faɗin"ban gane ba? wane? Wa ki ke so?" Ta jera mata tambayoyin a lokaci ɗaya tana mai da kallonta dan jiran amsar da zata bata. Amrah ta sauke nannauyan numfashi hawaye na sake zubowa fuskarta ta ce "Uncle Abdusammad mana! Ina son shi, ina ƙaunarsa wallahi, ko mai ya yi birgeni yake, ko faɗa yake kyau yake, ina sonsa! Shi nake so na aura ni! Shi nake so Nana!" 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Page 12... Yan channel ɗina masu quality ❤️ This page na dedicated to guys, na bar muka kayanku, ku yi sama dashi abin ku, Nanameera heart u guys💃. Tuntsirewa da dariya Nana ta yi tana yin baya, ta yi zaman dirshan a wajen, Amrah ta kalleta sai kuma ta sunkuyar da kanta hawaye na zubowa kan kuncinta, Maimoon ce ta kalleta ganin how serious she's ta ɗan taɓa Nana a sanyaye ta ce"me ya sa ki ke dariya ne?" Ba ta ce komai ba sai ci gaba da dariyarta da tayi kama zararriya, suka dinga kallonta baki buɗe. Sai da ta yi mai isarta sannan ta tsagaita tana ƙoƙarin saita nutsuwarta. Sai dai bata san sanda ta sake tuntsirewa da wata dariyar ba da suka haɗa idanu da Amrah, duka Maimoon ta kai mata tana tsaki ta ce"wai ke baki da hankali ne?" girgiza kanta ta dinga yi bayan ta rufe bakinta da hannunta ɗaya gudun kada ta sake dariyar. "Wai me ki ke wa dariya to?" Maimoon ta sake tambayarta a dame, gyaran murya ta yi fuskarta a sake ta ce"wai uncle take so, uncle fa, wannan tsohon, ya fa girmi duk ya'yan Hajiya, taɓ subhanallahi..." Ta sake tuntsirewa da wata dariyar, a fusace Amrah ta mike tsaye tana kallonta rai ɓace ta ce"ke ki ke ganinsa a matsayin tsoho, amma ni bana masa wannan kallon, kuma kin san yafi kowane mutum a gidan nan daraja da martaba. Saboda ya fi kowa kyau, ya fi kowa kuɗi, ya fi kowa ilimi, sannan yafi kowa sanin abin da ya dace!. Ke bari ki ji ma ko Yaya Safwan ɗin da zaki aura a karkashinsa yake, daga jikinsa suke samun abin da suke yiwa kan su buƙata. Rabin arzikin wannan estate ɗin nasa ne, ke bama rabi ba, kusan duk arzikin nasa ne! Dan haka ki iya bakin ki wallahi tun kafin ran ki ya ɓaci!" Wani irin kallo Nana ta dinga mata sai kuma ta yi shewa cike da ƙwarewa a masifa ta ce"banza kawai! Au she daman ba shi ki ke so ba, arzikinsa ki kewa. To sai me dan ya fi kowa kuɗi? Ke kudinsa ya dama, dan da alama abin da babanku yake baki baya isarki, domin da yana wadatarki da ba zaki taɓa zuwa kina faɗar irin waɗannan maganganun ba, da kin godewa Allah da ni'imar da ya yi miki. Amma da yake son zuciya ki ke sa a gaba har kin gano cewa yafi kowa arziki, to ina ruwana da arzikinsa? Mene abin da ya shafeni dashi, ni abin da ubana yake min shi ne abin tunƙawona ba wai wani can ba, banza kawai me son zuciya!..." Cikin tsananin ɓacin rai Amrah ta jawota ta shiga faɗin"ke har kin isa ki zageni? Dan kin ga ina zama tare da ke? Ni sa'ar wasarki ce?" Cikin azama Maimoon ta ƙarasa gabansu tana faɗin"mene haka? Sai wani ya zo shigewa ya gan ku, ke Amrah cikata mana" Ta ƙare maganar tana ƙoƙarin janye hannun Amrah daga jikin Nana, tureta Nana ta yi tana faɗin"Eh na faɗa ɗin, ko ba banzar bace? Ai duk wanda ya ga abin da ki ka yi zai tabbatar da cewa ke banza ce, irin banzar ma da bata san abin da take ba! Saboda haka..." Cikin zafin nama Amrah ta sauke mata mari a kuncinta na dama, wanda ya sanya ta yi shiru ba tare da ta ƙarasa maganar data fara ba, ta ɗora hannunta kan fuskarta tana faɗin "ni ki ka mara?" Amrah ta ɗora hannunta a ƙugu tana faɗin "an mare kin ko zaki..." Ko gama maganar bata yi ba Nana ta sauke mata wani lafiyayyen mari itama. Da sauri Maimoon ta rufe bakinta da hannunta tana kallon Nana da ke faman huci kamar ƴar damisa, Amrah ta dafe kumatunta tana gyaɗa kai, kwafa ta yi kafin ta yi wani kukan kura ta janyo Nanar ta shaƙeta tana faɗin "Ni zaki mara? Ni sa'arki ce! Ko dan kin ga ina miki wasa?" Ita dai Maimoon tsayawa ta yi a wajen tana kallonsu tana girgiza kai, ganin da gaske faɗa suke ya sanya ta ƙarasa tana ƙoƙarin janye Nana da ke kai mata duka ta ko ina ta ce"ke Nana sai na faɗawa Abbanki ba zaki bari ba!" Hannayenta biyu ta sanya ta ingiza Maimoon tana faɗin "dallah can rabu dani!" Daga haka ta mai da hankalinta kan faɗan da suke. "Ke!! Kee!!" Safwan ya yi maganar yana ƙarasowa wajen, da mamaki ya dinga kallonsu kafin ya janye Nana da sauri a ɗan tsawace ya ce"mene haka? Ba zaku bari ba!" "Ni rabu dani, ba zan bari ba ɗin, wallahi ba zan bari ba!" Nana ta yi maganar tana ƙoƙarin sake jawo Amrah, daka mata tsawa Safwan ya yi, kawai sai ta fashe da kuka ta juya ta bar wajen tana ihu kamar wadda aka daka. Da idanu ya dinga bin ta har ta sha kwana kafin ya dawo da idanunsa kan Amrah rai ɓace ya ce"mene ne haka Amrah? Da hankalinki?" Cikin shassheƙar kuka ta ce"wallahi Yaya bata da kunya ne, marina fa tayi" "Mari kuma?" Safwan ya faɗa da matuƙar mamaki. Gyaɗa masa kai kawai ta yi tana ci gaba da shessheƙar kukanta, ajiyar zuciya ya sauke kafin y ce"to ki yi haƙuri kin ji, kar ki ɗaga maganar dan Allah" sake gyaɗa masa kai ta yi ya kalli Maimoon ya ce"ke kuma kina kallonsu ba zaki raba su ba?" Marairaice fuska ta yi ta ce"Yaya nima fa tureni suka yi" taɓe baki ya yi sai kuma ya juya ya bar wajen ba tare da ya sake cewa komai. Ƙarasowa gabanta ta yi ta riƙe hannunta tana faɗin "ki yi haƙuri kin ji, zo mu tafi" Fizge hannunta ta yi ta ce"rabu dani wallahi ba zan yarda ba na rantse da Allah!" Da mamaki Maimoon ta ce"to sake kamata za ki yi da kokawar? Kina dai gani tafi ƙarfinki, ji yanda ta yakushe miki fuska" Sai a sannan Amrah ta kai hannunta gefen fuskarta ta taɓa, jini ta gani a hannunta ta sake fashewa da kuka tana fadin"shegiya mayya, na rantse ba zan yarda ba sai naje na faɗawa Abba" Girgiza kai Maimoon ta yi ta ce"ke kar ki yi haka, kin dai san halin Abba ko? Ki yi haƙuri kawai" tsaki Amrah zaka ta yi ta juya ta bar wajen kamar zata tashi sama. Numfashi Maimoon ta sauke sannan ta nufi hanyar gidansu da sauri dan daman ba'a san ta fito ba. **** Amma ta kafeta da idanu ta ce"ba magana nake da ke ba?" shiru ta yi tana sake murza hannunta dake kan idanunta, a tsawace ta ce"ba zaki faɗa min da wanda ki ka yi faɗa ba Nana har ki ka yi squeezing da kayanki haka?" Cikin shessheƙar kuka ta ce"babu kowa fa" daga haka ta nufi daƙinta da sauri. Da idanu kawai Amma ta bita sai kuma ta girgiza kanta dan tasan ƙarya take ta ce babu kowa dole faɗa ta yi da wani. Komawa ta yi ta zauna tana jiran ta fito ta sake tambayarta. Ƙarfe 6:30 na yamma ta fito tana sanye da hijabi, ko gida bata shiga ba tun bayan abin da ya faru dan ta san Mami ba zata barta ta fito ba. Dan haka ta yi zamanta a Apartment ɗin Hajiya Babba har yammar ta yi. Ta kusa apartment ɗin su Nana ta gamu da Hamida tana tafe sanye da hijabi har ƙasa, ta dinga kallonta sai kuma ta ce"Amrah lafiya? Me ya sami fuskarki?" "Babu komai" Ta ce a takaice sai kuma ta yi gaba abin ta, Hamida ta sake juyawa tana kallonta kafin ta numfashi ta ce"Allah ya kyauta" daga haka ta juya ta ci gaba da tafiyarta. Cikin Sa'a ta tarar da motar Abba a compound ɗin gidan da alama dawowarsa kenan daga wajen aiki, Amrah ta ja ta tsaya a balcony jar ya fito ya nufo wajen, yana zuwa gabanta ta durƙusa har ƙasa murya a sanyaye ta ce"Abba sannu da zuwa" fuska a sake ya ce"Yauwa Mamana sannunki" daga haka ya juya zai ci gaba da tafiya, da sauri ta ce"Abba!" Cak ya tsaya ya juyo yana kallonta ya ce"lafiya dai?" sai a sannan ya lura da fuskarta ya sake cewa"subhanallahi, meya sami fuskarki haka?" madadin ta bashi amsa sai kawai ta fashe da kuka tana murza idanunta, ya girgiza kansa yana faɗin"faɗi mene ne bana son kukan nan" cikin shessheƙar kuka ta ce"Abba Nana ce ta mareni" da wani irin mabayyanin mamaki ya dinga kallonta kafin ya ce"wace Nanar?" "Nana dai, kawai dan nayi mata magana shi ne ta dinga zagina ta ce min banza mahaukaciya, wai bana son iyayena bana ganin girmansu, kuma Daddyna talaka ne bashi da komai, Abbanta yafi kuɗi, shi ne dan na mareta ta rama, kuma ta kama ni da kokawa ta dinga dukana har sai da ta yakushe min fuska" Amrah ta ƙare maganar tana wani irin kuka, Kallonta kawai Abba ya dinga yi fuskarsa ta sauya kala daga fara zuwa ja, jijiyoyin kansa sun firfito ko ba'a faɗa maka ba kasan ransa ya yi masifar ɓaci.. Bai ce mata komai ba ya juya ya nufi cikin gidan da sauri, Amrah tana ganin ya shiga ta sauke hijabinta tana murmushi a fili ta ce"yauwa! Yau na nasan sai kin gane kurenki yarinya!" Daga haka ta bar wajen ranta fes. "Nana! Nana! Nana!" Abba ya dinga kiran sunanta yana tsaye a tsakiyar parlon, Tashi Amma ta yi tana kallonsa ganin yanda fuskarsa take a ɓace ta ce"lafiya dai yallaɓai?" "Ina Nana take?" Ya tambayeta a fusace, da hannu ta nuna masa daƙinta ya yi gaba da sauri ya bar ta tsaye a wajen. Tana zaune a gefen gadonta hannunta riƙe da wayarta tana game ya turo ƙofar ya shigo, da sauri ta ɗaga idanunta tana kallonsa ganin yanda ya shigo a fusace yasa ta ce"sannu da zuwa Abba..." Ko rufe bakinta bata yi ba ya sauke mata wani zazzafan mari har sai da ta tafi ta faɗi ƙasa, ihu ta saki wanda ya yi dai dai da shigowar Amma, ya ƙarasa ya fincikota yana mata wani irin kallo ya ce"wato kin dawo da halin ki ko? Wane sa'anki a cikinsu da har zaki dinga faɗa dasu? Har ki iya zaginta, sannan bayan ita ki iya haɗawa da babanta! Yaushe ki ka dawo da wannan mummunar ɗabi'ar taki?!" Tafa hannaye Amma ta shiga yi tana salati kafin ta ce"ni daman na san tun da na gan ta ta shigo a birkice to magana ta dauko ashe kuwa haka ne, da wa ta yi faɗa kuma?" Abba bai tsaya bata amsa ba ya zare belt ya dinga dukan Nana kamar Allah ya ai ko shi, ban da ihu babu abin da take, ta dinga kiran sunan Amma ta taimaketa amma ta mata banza. Sai da ya yi mata lilis sannan ya wurgar da belt ɗin yana kallonta ya ce"daga yau ko kallon banza ki ka sake wa wani wanda ya girmeki a cikin gidan nan zaki ga yanda zan yi dake!" Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin rai ɓace. Amma ta tsaya a wajen tana kallonta ganin yanda take kuka, duk ta fice hayyacinta dan ba ƙaramin duka ya yi mata ba, ta sauke numfashi sai kuma ta juya ta bar ɗakin.. Tsaye ta same shi a ɗakinsa ya dafa study table, ta ƙarasa ta tsaya daga bayansa tana kallonsa a sanyaye ta ce"amma yallaɓai dukan nan bai yi yawa ba? She's too small fa, beside ma kasan ba lafiya ne da ita cikakke ba!" Kamar ba zai magana ba sai kuma ya juyo yana kallonta da idanunsa wanda suka yi jajur ya ce"kenan na barta ta dinga dauko mana magana? kin san wannan faɗace- faɗacen nata shi ne dalilin daya sanya na kai ta boarding school ba, to akan me zan bari ta dawo ta ɗora daga inda ta tsaya. Amrah fa mara! Sa'arta ce?" Numfasawa Amma ta yi kafin ta ce"haka ne, amma dai bai kamata ka mata irin wannan dukan ba gaskiya, nayi shiru ne kawai saboda a gabanta ne, da ba zan barka ba wallahi, ka dinga tunawa da ita kaɗai muke da, duk abin da ya sameta mu ne a ciki!" Ta ƙare maganar jiki a sanyaye, Abba kallonta kawai ya dinga yi sai kuma ya juya ya shige toilet ba tare da ya ce komai ba, itama bata damu da rashin maganar tasa ba ta juya ta fice daga ɗakin.. Bayan sallar isha'i Amma ta buɗe ɗakin ta shigo, tana kwance akan gadonta ta rufa da lallausan duvet, ta ƙaraso gabanta ta ajiye tray ɗin kan drawer sannan ta dafata a sanyaye ta ce"Nanata" shiru ta yi mata duk da taji abin da ta ce, Amma ta sake cewa"tashi kin ji, tashi" juyawa ta yi ta mai da kanta ɗaya side ɗin, Amma ta ɗan yi murmushi sannan ta yaye duvet ɗin ta leƙa fuskarta ta ce"taso mana yar autar Ammarta" sake dunƙule jikinta ta yi hawaye na sintiri kan kyakkyawar fuskarta. Amma ta janyo hannunta tana faɗin "taso mana" dakyar ta tashi zaune har sannan idanunta a rufe suke fuskarta ta yi jajur jikinta duk alamun jini ya kwanta, Amma ta dinga kallonta tana jin wani irin ɗaci a ranta, koda wasa bata san ganin abin da zai taɓa lafiyar tilon ƴar tata, shiyasa bata taɓa gwada dukanta komai zata yi sai dai ta mata faɗa. Ganin yanda take numfashi da kyar ya sanya ta ce"sannu, zo ki sha tea" girgiza kanta ta yi ba tare da ta ce komai ba, ta koma ta kwanta. Tashi Amma ta yi ta fito daga parlon, Abba na zaune da Abdusammad suna magana ta ƙaraso wajen, gaisawa suka yi dashi kafin ta maida idanunta kan Abba ta ce"Daman cewa nayi ko zaka je kaga jikin yarinyar, naji zazzaɓi sosai a jikinta" Da sauri Abba ya ce"subhanallahi" daga haka ya miƙe, tashi shima Abdusammad ɗin ya yi yana faɗin "lafiya dai Abba?" "Nana ce bata jin daɗi" ya yi maganar da damuwa akan fuskarsa. Girgiza kai Abdusammad ya yi ya ce"subhanallahi tana ina?" Daƙinta Abba ya nuna ya yi gaba sannan ya bi bayansa, Amma ta dinga kallonsu kafin ta bi bayansu itama. Ƙarasawa jikin gadon ya yi ya durƙusa ya taɓa jikinta kafin ya ce"Kee Nana!" da kyar ta buɗe idanunta dan da gaske zazzaɓi ne sosai ya rufeta, ya riƙe hannunta ta tashi zaune da kyar. Kallon jikinta ya dinga yi dan vest ce a jikinta, ya daga idanunsa ya kalli Abba da mamaki ya ce"wane ya daketa Abba?" Murya a sanyaye Abba ya ce"ni ne" Abdusammad ya dinga kallonsa kafin ya ce"but why? me yasa zaka daketa Abba? she's too young fa" girgiza kai Abba ya yi ya ce"raina ne ya ɓaci Abdusammad, na kasa danne fushina" "Kome ta maka bai kamata ka daketa ba Abba, duka baya gyara, yanzu kaga ya taɓa lafiyarta" Shiru shi dai Abba ya yi dan bashi da abin cewa tun da ya san ya yi laifin. Abdusammad ya kalleta a nutse ya ce"sannu, zaki iya tafiya?" kamar jira take ta shiga yarfe hannu tana girgiza kanta, ya durƙusa daidai tsayinta ya ce"oyaa hau muje" bata yi musu ba ta hau faffaɗan bayan nasa, ta zura hannayenta wuyansa ta rike shi sosai. Tashi ya yi yana riƙe da ita a bayansa ya ce"da safe na dawo da ita" okay Abba ya ce sannan ya fita daga ɗakin, Kamar jira Nana take ta sake narkewa a bayansa tana sauke numfashi a hankali. **** Junaid ya sauke wayar yana yin tsaki, saurayin dake zaune gefensa ya ce"what?" rai ɓace ya ce"bata ɗaga ba, wallahi ji nake kamar naje na ɗauketa daga wancan kurkukun gidan nasu, yarinya bata isa ta sake ba!" Taɓe baki Al-ameen ya yi ya ce"kai ma wallahi kana bada maza, sai ka ce ita kaɗai ce yarinya mace, ga yan mata nan sai wanda ka zaɓa, kai da ka yi zaman Lebanon ma har a faɗa maka ganin mata zafafa" Harararsa Junaid ya yi ya ce"ita fa ba irin waɗancan matan ba ce, wannan so nake na aureta, amma danginta sun ƙi yarda, su a dole sai dai ta auri ɗan uwanta" wani murmushin mugunta Al-ameen ya yi ya ce"then baka san yanda zaka sameta ba?" kamar ƙaramin yaro Junaid ya gyaɗa masa kai, ya ɗan cije baki sai kuma ya ce"bani kunnenka ka ji" babu musu ya saki steering motar ya miƙa masa kunnen, Al-ameen ya raɗa masa magana sai kuma ya ɗago yana kallonsa fuskarsa ɗauke da murmushi. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Page 13... Junaid ya dinga kallonsa da mamaki, Al-ameen ya ƙifta masa idanu yana faɗin"ya ka ji shawarar tawa?" Girgiza kansa ya yi yana jingina da kujerar motar ya ce"gaskiya i can't" haɗe rai ya yi sannan ya ce"but why?" Junaid ya ɗauke kansa yana kallon tsirarin motocin da ke titin kafin ya ce"saboda ina sonta! aurenta nake son yi" tsaki Al-ameen ya yi yana faɗin"ai sai ka yi ta fama kuwa" shi dai Junaid bai ko kalleshi ba ballantana ya bashi amsa, zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa suna can tunanin dalilin daya hana Nana ɗaga kiransa. **** Zahra na zaune gefenta ya dawo ɗakin hannunsa riƙe da injection, Nana na ganin haka ta sake matsawa jikinta a hankali. Tsayawa ya yi ya haɗa allurar kafin ya kalleta yana faɗin"tashi na miki" kasa cewa komai ta yi ta miƙe a hankali, skirt ɗin jikinta ya janye ƙasa sannan ya yi bismillah ya kafa allurar, runtse idanunta ta yi saboda azaba ta dinga yarfe hannu, ya janye empty sringy ɗin daga bayanta ya ajiye gefen dresser. Komawa ta yi ta zauna kusa da Zahra ta ɗora kanta akan cinyata, zazzaɓi ne sosai a jikinta dan haka Zahra ta ɗora hannunta akan bayanta tana taɓata a hankali. Juyawa ya yi ya fice daga ɗakin not too long kuma ya dawo hannunsa riƙe da wayarsa, kallonsu ya yi sannan ya ce"kin ci abinci?" gyaɗa masa kai ta yi a hankali duk da bata ci abincin ba, ya ɗan yi shiru can kuma ya ce"to ki gyara kwanciyarki sai da safe" ya ƙare maganar idanunsa ƙur akanta. Da taimakon Zahra ta gyara kwanciyar sannan ta rufa mata blanket, ta dinga sauke numfashi a hankali har bacci ya dauketa, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juya ya bar ɗakin, ita ma ta tashi ta kashe hasken ɗakin sannan ta fita. Koda ta shiga ɗakinsa bata same shi ba dan haka ta tabbatar da yana gurin Noor dan duk dare sai ya shiga ya ganta kafin ya kwanta. Gefen gado ta zauna tana danna wayarta a hankali, ba'a fi 5mins ba ya buɗe ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Amsawa ta yi sannan ta ci gaba da danna wayarta, shi ma bai bi ta kanta ba ya nufi toilet dan watsa ruwa. Gajiya ta yi da jiransa ta tashi ta fita daga ɗakin ta koma nata, bayan 30mins ta kashe wayar hannunta ta tashi ta koma ɗakin. Zaune ta same shi gefen gado yana sipping coffee a hankali, ta ƙarasa ta zauna gefensa ta yi shiru, sai da ya gama ya ajiye mug ɗin sannan ta ce"wai me ya sameta ne? Naga jikinta duk a fashe" girgiza kansa ya yi sannan ya ce"Wallahi wai Abba ne ya daketa saboda ta yi faɗa" ɗan zaro idanu ta yi sai kuma ta ce"faɗa kuma, ita dawa?" kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce"wai da Amrah suka yi ɗan rigima sai ta mareta, shi ne shi kuma ya zaneta" Zahra ta langwabar da kai ta ce"Ayyah daman Nana bata son zaman lafiya tun tana ƙarama, amma nayi mamaki ma ganin tun da mu ka zo ba'a ce ta yi faɗa da kowa ba" murmushin da bai yi niyya bane ya kuɓuce masa, ya janye kafafunsa kafin ya ce"to ai an samu lafiya ne, shi ne yanzu take neman dawowa da halin nata" Zahra ta murmusa ta ce"shima Abba da ya yi haƙuri kwana nawa ne zata yi aurenta ta bar wajensa" Abdussamad ya dinga kallonta ba tare da ya amsa maganar tata ba. Ganin bai ce komai ba ya sanya ta ce"yauwa daman inason na tambayeka" "Uhm ina ji" ya ce yana ƙoƙarin kwanciya, sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers dinta ta ce"dan Allah gobe ina son naje gurinsu Umma idan babu damuwa" jinjina kansa ya yi ya ce"daman jira nake naji zaki ce zaki ko sai na tuna miki, Allah ya kaimu lafiya" dariya ta yi ta ce"zan ce mana, kawai dai bari nayi mu ɗan kwana biyu tukun" sake jinjina kansa ya yi yana lumshe idanu dan ba ƙaramin bacci yake ji ba, ganin haka yasa ita ma ta haura kan gadon ta yi kwanciyarta. Washegari da sassafe ta tashi ta je ɗakin da Nana ta kwana, sai dai bata sameta a ciki ba, dan babu ma alamar an kwanta ko ina tsaf yake. Tana ƙoƙarin juyawa suka kusa karo ya ɗan yi baya yana kallonta, fitowa ta yi tana cewa"wai ka ga na duba ban ga Nana ba a ciki" "Bata ciki kuma?" Abdussamad ya tambaya da ɗan mamaki, gyaɗa masa kai ta yi ya ce"ko ta tafi ne?" "Kuma sai ta tafi bata faɗa mana ba?" Zahra ta yi maganar a ɗan dame, jan kumatunta ya yi ya ce"ai da ke da Nanar ban san wanda ya fi wani son rigima ba, to mene zai hanata tafiya tun da ta san hanya abin ta?" Tana ƙoƙarin maganar suka ji an turo ƙofar, kamar haɗin baki suka kalli wajen a tare, tsaye take ita da Noor suna kallonsu, Zahra ta sauke ajiyar zuciya ta ƙarasa wajen da sauri tana faɗin"Nana na ɗauka tafiya ki ka yi ai?" girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce"ina kwana Aunty?" Murmushi ta yi ta ce"lafiya kalau ya jikin?" "Da sauki" ta ce tana yin gaba, wajensa ta ƙarasa ta ɗan durƙusa cike da ladabi ta ce"ina kwana uncle?" "Ya jikin?" ya ce yana zama kan sofa, bin bayansa ta yi tana faɗin"da sauki ya daina min zazzaɓin, sai jikina ne kawai yake ciwo" jinjina kansa ya yi ya janyo hannunta ya zaunar da ita gefensa a nutse ya ce"Nana me ya haɗa ki faɗa da Amrah?" sunkuyar da kanta tayi ba ta ce komai ba, ya juya yana kallonta sosai ya ce"baki ji bane?" Cikin shesshekar kuka ta ce"babu komai uncle kawai zagina ta yi fa, kuma ta mareni shi ne na rama" "Me ya sa ki ka mareta bayan ta gaba take dake? Wannan ne abin da aka koya miki raina na gaba da ke?" Girgiza kanta ta yi tana murza idanunta, ya ce"kar ki sake faɗa da kowa kin ji yarinyar kirkina" yanda ya yi maganar cike da kulawa ya sanyata gyaɗa masa kai, Zahra dake tsaye bayansu ta yi murmushi. Ƙarasowa wajen ta yi tana riƙe da Noor, ya kama hannun yarinyar ya dorata akan cinyarsa yana murmushi ya ce"my angel" wasa ta fara yi da gemunsa tana dariya, Zahra ta nufi hanyar kitchen dan ɗora musu abun breakfast. Tashi Nana ta yi tana faɗin"na tafi uncle" haɗe fuska ya yi ya ce"dawo nan" ganin yanda ya yi maganar babu alamun wasa ya sa ta koma ta zauna tana kallonsa. "Korar ki ake anan ɗin da ki ke sauri haka?" Ya ƙare maganar yana harararta, sunkuyar da kanta ta yi tana murmushi, ya mai da idanunsa kan Noor ya ce"kin yi azkar?" gyaɗa masa kai ta yi cikin ƙaramar muryarta ta ce"mun yi da Aunty Nana" jin jina kansa ya yi ya ce"uhm, Aunty Nana ta iya ashe?" kamar jira take ta ce"eh Abbiey ta iya sosai, har ma fa karatun Qur'an muka yi, gashi muryarta da daɗi, kamar kai" daga shi har Nana dariya suka dinga yi, Ya ja kumatunta ya ce"to ko dai ita zata koma tutor ɗin ki?" gyaɗa masa kai ta yi tana wani juya idanu kamar babba ta ce"eh Abbiey, ta iya koya karatun" "Na kai Abbiey?" Nana ta yi maganar tana jawo hannunta, jin jina kanta ta yi tana murmushi, ya ɗan yi murmushi kafin ya ce"iyye au ta fini? Oya sauka ki koma jikinta to" sake narkewa ta yi a jikinsa ta dunƙule hannunta na dama ta daki ƙirjinsa ta ce"a'a fa Abbiey, babu wanda ya fika even Ummina sai dai ta biyo bayanka, u're the best Daddy in the world" rungumeta ya yi tsam a jikinsa yana murmushi ya ce"daɗina dake hankali princess" dariya ta dinga yi ƙasa-ƙasa dai dai nan Zahra ta fito daga kitchen ɗin tana kallonsu ta ce"kun bar ni ina ta faman aiki ku kuma kuna nan kuna hira ko?" Tashi Nana ta yi tana fadin"Ayyah Aunty mu je na tayaki" taɓe baki ta yi ta ce"da can baki ce zaki tayanin ba sai da na roƙa? To ki yi zamanki, nima dai an jima zan je gidan namu yan'uwan tun da abun haka ne" tuntsirewa da dariya Nana tayi tana nufar kitchen ɗin ta ce"aaa kar ki kai mu in da Allah bai kai mu ba" Zahra ta yi murmushi ta ce"ai gaskiya ce" daga haka ta sake kallonsa ta ce"yallaɓai kai ba zaka taya mu ba?" Ɗan zaro idanu ya yi sai kuma ya kwaɓe fuska kamar ƙaramin yaro ya ce"a'a dai Ummi ku je ni zan zauna da princess" ko ƙarasa maganar bai yi ba ta fara jan hannunsa tana faɗin "ai ko sai ka taya mu wallahi!" Babu yanda ya iya haka ya tashi bayan ya sauke Noor ya nufi kitchen ɗin, ta yi murmushi sannan ta sauyawa Noor tashar cartoon ta bar wajen. Nana ta dinga kallonsa ganin ya shigo kitchen ɗin, ya ɗan haɗe girarsa babu walwala ya ce"mene ne ki ke wani kallona?" Girgiza kanta tayi tana ƙoƙarin ƙunshe dariyar da ke cinta, y yi kwafa yana saka slice cucumber a bakinsa kafin ya ce"zan yi maganinki ne yarinya" ita dai bata ce masa komai ba har Zahra ta shigo, ta ɗan kallesu sai kuma ta nufi gaban cooker tana fadin"ku ka wani tsaya min a tsaye" gyara tsaiwarsa ya yi jikin fridge sannan ya ce"to ai bamu san me zamu yi ba Hajiya" sai da ta murɗe gas ɗin sannan ta ce"ga albasa nan ka yanka min, ke kuma Nana ki ferayen dankalin nan" toh Nana ta ce sannan ta ɗauki wuka ta fara abin da ta sakata. Zahra ta juyo tana kallonsa ganin har sannan bai ko motsa ba yasa ta ce"ai ko idan baka yi aiki a gidan nan ba yau ba zaka yi breakfast ba!" Kamar zai yi kuka ya ce"wai da gaske?" "Abbiey da gaske nake" ta ƙare maganar tana matsowa gabansa, hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta ya dinga kallonta kafin a hankali ya kai bakinsa kan nata, saurin janyeshi ta yi tana rarraba idanu, ya ɗan haɗe fuska ya ce"mene?" da idanu ta nuna masa Nana wadda take faman feraya, ya taɓe baki sai kuma ya ce"and so?" Daga haka ya sake kai bakinsa, kasa hana shi tayi tana ji ya yi kissing ɗinta a deep one. Ƙarar kissing ɗin ya sanya Nana juyowa, amma ta yi gaggawar ɗauke idanunta ta ci-gaba da abin da take, cikin rashin sa'a wuƙar ta shige mata hannu saboda yanda ta diririce tamkar ita aka wa kiss ɗin. Ta saki ƴar ƙara tana janye hannunta, da sauri Zahra ta janye jikinta daga wajen ta ƙarasa gabanta, sai dai jinin data gani ya ɗan ɗaga mata hankali, ta ce"subhanallahi Nana garin yaya?" Ƙarasowa wajen ya yi ya kama hannun wanda yake ta zubar jini sai kuma ya ce"garin gulma ya sanya ki ka yanke ko?" wata irin matsananciyar kunya ce ta rufeta, ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba. Jan hannun ya yi wajen sink ya kunna ruwan, sai dai yana wankewa wani jinin na sake zuba, dan haka ya kashe kawai ya kalli Zahra ya ce"ban tissue" cikin hanzari ta zari tissue ɗin ta miƙa masa, ya naɗeta dayawa sannan ya ɗora a wajen, ta ɗan runtse idanu saboda zafin da taji. Cikin yan sakanni tissue ta jiƙe jagab da jinin ya ɗan yi tsaki sai kuma yaja hannunta bai ce komai ba suka fita daga ɗakin. Zahra ta yi kamar ta bi su taji ya ce"Madam concentrate on what you are doing" cak ta tsaya ba dan taso ba, ta juya ta ci gaba da aikin zuciya babu daɗi. Ɗakinsa ya shiga da ita, ta ɗan lumshe idanu saboda wani sassayan ƙamshi daya cikata, ya ƙarasa gaban dresser nashi ya dauki wani perfume na kwalba ya buɗe, ƙoƙarin janye hannunta ta fara yi ganin yana shirin fesa mata kamar za ta yi kuka ta ce"Uncle zafi fa" banza ya yi mata ya feshe wajen da turaren, tsananin azabar da taji ya sanya ta faɗa jikinsa tana sakin wani marayan kuka, ɗauke kansa ya yi yana kallon gefe bai ce mata komai ba, ya mayar da turaren ya ajiye sannan ya janyeta daga jikinsa yana faɗin "next time ki tsaya gulma kin ji" daga haka ya juya ya nufi toilet, tura baki ta yi sai kuma ta koma gefen gadon daya sha gyara ta zauna, ta yi shiru tana tunanin yanda maganar, ita kaɗai ta dinga tura baki har kusan 5mins kafin ya fito fuskarsa a jiƙe da hannunsa, da mamaki ya dinga kallonta sai kuma ya ce "Kee!" Yanda ya yi maganar ya sanyata firgita ta sunkuyar da kanta ƙasa, fuska a haɗe ya ce"me ki ke min akan gado? Salon ki lalata min? Tashi my friend" ɗago idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce"ayyah uncle zama nayi na ɗan huta fa" a ɗan tsawace ya ce"baki ji me nace ba? Tashi ki fita!" Da sauri ta tashi ta fice daga ɗakin, ya bita da harara sai kuma ya yi tsaki. **** Bayan sun kammala breakfast ta tashi ta kwashe duk kayan ta kai kitchen sannan ta kalli Zahra ta ce"Aunty na tafi" "Ke Nana ba zaki bari sai an jima ba?" Girgiza kanta ta yi ta ce"zan je na ɗauki wayata ne, na san an yi min magana ta WhatsApp ban gani ba" Zahra ta ce"okay amma da kin bari an jima zan je gidanmu sai mu tafi tare ki rakani, kin ga kema kya ga gari ko?" Nana ta ɗan yi shiru tana tunani “ki bita, This is great opportunity da zaki haɗu da Junaid!” Wani ɓangare na zuciyarta ya sanar da ita hakan, Zahra ta sake cewa"Nana fa?" Ɗan murmushi ta yi ta ce"Tom Aunty zan je" Zahra ta ce"yauwa yar gari, to je ki yi wanka sai ki bawa Atu tama Noor " to kawai ta ce sannan ta nufi hanyar upstairs bayan ta kira Noor ɗin. Zahra ta mai da Idanunta kan Abdusammad da ke danna wayarsa hankali kwance ta ce"Yallaɓai kai zaka kai mu?" bai kalleta ba ya girgiza kansa ya ce"a'a driver ya kai ku dai, zan fita idan na dawo sai na biya na dauko ku, mun gaisa dasu Mommy ma" Zahra ta sauke numfashi kafin ta ce"okay tom bari na tashi naje na shirya kar mu yi late, idan zamu fita sai mu biya ta wajen Amma na faɗa mata ba?" "Tare zamu fita da Abba, zan sanar dashi" cewar Abdusammad yana tashi daga wajen, okay kawai ta ce sannan ita ma ta nufi upstairs. Ɗakin da Nana take ta fara shiga ta sameta zaune ta yi shiru, ta dinga kallonta kafin ta ce“Nana baki shirya ba?” ɗan murmushi ta yi ta ce“yanzu zan shirya” okay kawai Zahra ta ce sannan ta juya ta fita, koda ta sake dawowa bata sami Nana a wajen ba sai ƙarar ruwa da taji wanda ya tabbatar mata da tana bayi, ta ajiye mata welfolded Abayar a gefen gado sannan ta fita. Ƙarfe 11:45 na safe Nana ta fito parlon sai zuba ƙamshi take, ta shirya cikin ash colour ɗin Abayar me manya flowers a jiki, ta yi rolling mayafin abayar akanta ta yi wani irin kyau. Zahra ta dinga kallonta tana murmushi kafin ta ce“kaga shuwar asali irin wannan kyau haka?” tura baki ta yi ta ce“ayyah Aunty Zahra banso wallahi” dariya Zahra ta yi tana gyarawa Noor hular kanta ta ce“to naji” shiru ta yi can kuma ta ce“yauwa aunty Zahra ina wayarki?” kan kujera ta nuna mata tana faɗin “gata can” okay kawai Nana ta ce sannan ta ƙarasa ta ɗauka, face id ne akai dan haka ta miƙa mata ta ce“ki cire min zan yi hoto” murmushi kawai Zahra ta yi sannan ta cire mata, ta karɓa ta fice daga parlon tana murmushi. Garden ɗin gidan ta ƙarasa ta shiga dial ta saka numbern Junaid wadda ta gama haddacewa sannan ta danna kira, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga, Junaid da ke tuƙi ya ce “Hello wake magana?” Ajiyar zuciya Nana ta sauke jin muryarsa, ta ɗan yi shiru har sai da ya sake magana ya ce “hellooo” “sir ni ce” Junaid ya gangara gefen titi yayi parking sannan ya ce “Nana ina ta kiran ki baki ɗaga wayata why?” Numfasawa ta yi ta ce “bana gida ne, ina wajen uncle ɗina” Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya ce “okay, yanzu ya ake ciki?” Sai da ta sake leƙawa ta tabbatar da babu wanda ya tawo sannan ta ce “zamu fita da matarsa, zan kira ka idan mun je gidan sai ka zo” Jinjina mata kai ya yi ya ce “okay, shikenan zan kira ki” Girgiza kanta ta yi da sauri ta ce “no kar ka kirani, ni zan kira ka” Okay ya ce sannan suka yi sallama ya kashe wayar. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta goge call log ɗin ta shiga Snapchat, ko hoto biyu bata yi ba Noor ta ƙaraso wajen da gudu ta ce"Aunty Nana ki zo in ji Ummi” okay ta ce sannan ta riƙe hannunta suka bar wajen, Zahra da ke bayan motar ta kalleta ta ce“hoton ya isa haka ai Nana zo mu tafi” murmushi kawai ta yi sannan ta zagaya ɗaya side ɗin ta shiga motar tare da Noor, drivern ya ja motar suka bar compound ɗin. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Page 14... Abba ya ɗan yi murmushi kafin ya ce"like how kenan tayaya ka ke tunanin haka zai yiwu?” Abdusammad ya ɗan kalli compound ɗin gidan inda bishiyu ke kaɗawa da sauri da sauri saboda iskar da ake da sauri da sauri, ya sauke numfashi sannan ya ce“Abba so nake abar maganar auren nan dan Allah, yara ne ƙanana fa” ɗan murmushi irin na manya ya yi kafin ya ce“to mene ne dan an yi aurensu yanzun? sun kammala karatun secondary, to mene ne abin da za'a jira?” Abdusammad ya girgiza kansa ya ce“a'a Abba, at least ya kamata ace ko degree sun haɗa, kaga sannan sun ƙara hankali sai a musu auren” shiru Abba ya yi bai sake magana ba, shima Abdusammad ɗin bai damu da rashin maganar ba ya ci gaba da danna wayarsa. **** Barraks road, Gibson jalo. A babban compound ɗin gidan motar ta yi parking, Zahra ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito daga motar, ita ma Nana ta fito tana ƙarewa babban compound ɗin gidan kallo, bishiyu da flowers sun cika ko ina, Zahra ta zagayo tana riƙe da hannun Noor ta ce“muje Nana” okay kawai ta ce sannan suka nufi hanyar balcony ɗin gidan. Bakinsu ɗauke da sallama suka shiga, Ta ajiye wayar gefenta ta tashi tana murmushi ta ce“laaa aunty sannu da zuwa” Zahra ta yi murmushi tana kallon budurwar mai matukar kama da ita ta ce“Safeena kina zaune, yauwa” daga haka ta nufi kan kujera ta zauna. Safeena ta ɗan kalli Nana ta ce“welcome sis” murmushi Nana ta yi ta ce“thank ya ki ke?” “Alhamdulilah” Ta ce tana komawa ta zauna, ita ma Nana tafiya ta yi ta zauna kan ɗaya daga royal cushion ɗin dake zagaye da ƙaton parlon, Safeena ta kama hannun Noor tana faɗin “wow aunty ashe Noor ta girma” ta ƙare maganar tana ɗorata kan cinya. Murmushi Zahra ta yi ta ce“eh yar taku ta girma mana, Ina Aunty Khadijah da Umma?” “Umma tana sama fa, ita kuma Aunty bata nan sun fita da Siyama” Okay Zahra ta ce sannan ta miƙe ta nufi saman da sauri, Nana ta bita da kallo sai kuma ta ɗan jingina da kujerar tana sauke numfashi. Zahra ta tura kofar bedroom bakinta ɗauke da sallama, Umma dake zaune ƙasan gado tana jan carbi ta ce“wa'alaiki salam, Fatima” ta ƙare maganar tana gyara zamanta, fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa ta zauna gefenta ta ce"Ummata” “ya mai gidan naki?” Sai da ta kwanta kan cinyarta sannan ta ce“lafiya kalau, ya ce an jima zai bi yo ya gaisheku” Jinjina kai Ummar ta yi sannan ta ce“Ina Noor ɗin?” Murmushi Zahra ta yi ta ce“tana ƙasa wajen Safeena” Okay Umma ta ce. Shiru ne ya biyo baya kowa da abin da yake tunani can kuma Zahra ta ce“laa Umma wai ina Aunty Khadijah?” “ta fita kin san halinta dai ba son zama take ba, tuni ta fice” Murmushi Zahra ta yi ta ce“hajiya Aunty Khadijah kenan, Allah ya kawo mata miji ta yi aurenta dai” “to san auren take Zahra? Ai bai dameta ba, tafi son ta yi ta yawo daga nan sai nan” girgiza kai Zahra ta yi ta ce“a'a Umma tana so mana, ai kowa ce mace na son ta yi aure duk da ta taɓa yi amma zawarci ai bashi da daɗi” taɓe baki Umma ta yi ta miƙe sannan ta ce“ai duk kun fita hankali, ita ce babba amma babu abin da ta iya sai shirme” daga haka ta nufi ƙofa ta fice daga ɗakin, jim Zahra ta yi a wajen tana tunani kafin ta miƙe ta fito ita ma. Umma ta dinga kallon Nana fuskarta ɗauke da fara'a har ta ƙaraso wajen ta ce“wa nake gani kamar Nana?” zamowa ta yi daga kan kujerar ta gaisheta, Umma ta zauna kusa da Safeena tana faɗin “lafiya kalau Khadijah, haka ki ka girma?” sunkuyar da kai ta yi a hankali, Umma ta sake cewa“ina mamanki?” “tana gida” Ta yi maganar a sanyaye, jinjina kai Umma ta yi ta ce“Allah sarki na kwana biyu rabon da na ganta” ɗan murmushi Nana ta yi bata ce komai ba dai dai nan Zahra ta sakko daga saman, ta ƙaraso wajen Nana tana faɗin “umma kin ga yanda Nana ta girma ko?” Jin jina kai Umma ta yi ta ce“yanzu nake faɗa nima, kamar ba ita ba ce ki ke zuwa da ita ba lokacin tana ƴar ƙarama, bata fi girman Noor ba” Zama Zahra ta yi sannan ta ce“wallahi amma yanzu ta zama ƙatuwa ta kamoni a jiki” langwaɓar da kai Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce“kai Aunty” “ƙarya nayi? Yanzu fa kin yi girmana wallahi sai dai a ce idona ya fi naki buɗewa, kin ga Umma aurensu fa za'a yi nan da 6weeks” Riƙe haɓa Umma ta yi ta ce“Allah alhakamu, har lokaci ya zo? Daɗina dasu auren wuri na huta kafin yaro ya fanɗare, to wa zata aura a cikin samarin gidan? Ko sun daina auren Zumuncin?” Ummar ta jera mata tambayoyin a tare. Murmushi Zahra ta yi idanunta zube kan Nana ta ce“Safwan zata aura, ina zasu daina auren zumunci Umma?” Waro idanu Umma ta yi ta ce“Ikon Allah wane Safwan ɗin? Ban san shi ba” Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“a'a dai baki gane shi ba, Safwan fa ɗan autan su Daddyn Noor” jinjina kai Umma ta yi ta ce“eh na gane shi kuma, wani mai kama da Abdusammad ko?” “eh shi fa kin gane shi ma” cewar Zahra tana murmushi. Kallon Nana Umma ta yi ta ce“Allah ya sanya Alkhairi Khadijah ya baku zaman lafiya, amma ki yi ta haƙuri, aure sai da haƙuri” Jiki a sanyaye Nana ta ce“to Umma in sha Allah” “Ni kam suna burgeni wallahi Aunty, ko nima zaki sama min miji a cikin estate ɗin ne?” Safeena ta yi maganar cike da zolaya, riƙe baki Zahra ta yi tana faɗin “kee rufa min asiri, su basu auren haɗi” ta ƙare maganar cike da raha, Safeena ta ce“assha da dai kin duba, a yan samarin nan nasu a sama min ɗaya na aura, wallahi suna mugun burgeni bama ni kaɗai ba, ko a cikin jama'a zaki ji ana maganar dangin. Haka rannan wata course mate ɗina wai zata min ƙarya ai tana dating da ɗaya daga cikin ya'yan gidan na ce to wallahi ƙarya take dan Yayata babban ɗan gidan take aure” tuntsirewa da dariya Zahra ta yi ta ce“wato ke ga gwana ko?” murmushi Safeena ta yi ta ce“ai gaskiya ce, ke fa Allah ne ya baki shi wallahi, daman ance matar mutum ƙabarinsa amma idan ba dan haka ba ya za'a yi ki aure shi” ɗan haɗe rai Zahra ta yi ta ce“to kar ki faɗa min magana kuma” Zazzaro idanu Safeena ta yi tana murmushi ta ce“nii to Allah ya baki haƙuri Hajiya” ta ƙare maganar tana gyarawa Noor gashin kanta. **** Junaid ya girgiza kansa idanunsa zube kan wayar hannunsa ya ce“ni fa ba zan yi ba, kai wai kana ma da hankali ne? Ce maka nayi fa ina son na aureta, idan ba zaka iya bani shawarar arziki ba ka rabu dani dan Allah” ya ƙare maganar yana ɗago kansa, Taɓe baki Al-ameen ya yi sai kuma ya ce“Baba ka ji fa, ana bashi shawara yana gwale mutane, to kaje ka ci gaba da bin ta tana jan ka a ƙasa” ya yi maganar cikin ɓacin rai, Harararsa Junaid ya yi ya ce“eh naji mene ne dan ta jani a ƙasa? Ai daman ita mace an santa da haka, kuma kaf cikinku babu wanda yake dating yar babban gida irin yanda nake, sai dai idan baƙin ciki ku ke min” “kai ka isa mu maka baƙin ciki akan waccan kwailar yarinyar? Mu da muke da mata waɗanda suka san kansu” cewar Habib a ɗan zafafe. Kallonsu ya yi sai kuma ya taɓe baki ya ci gaba da danna wayarsa ba tare da ya sake bi ta kansu ba. **** “Sultan! Sultan! Sultan...” “na'am Ummi” Ya amsa mata yana kokarin tashi zaune, kallonsa ta dinga yi daga tsayen da take kafin ta ce“mene haka? Kwanciyar me ka ke a ɗaki har wannan lokacin?” Ummi ta yi tambayar tana kallon fuskarsa wadda ta rame sosai, girgiza kansa ya yi ya ce“babu komai Ummi, kawai ina ɗan ciwon kai ne shi ne ya hana ni tashi, amma yanzu zan tashi” “ciwon kai ne ya hana ka tashi daga kwance har la'asar ko? Sultan ko dai kana son ka zaja min masifar da ba zan iya da ita bane? Akan maganar aure ka bi ka ɗaga hankalinka, ita matar mutum ai ƙabarinsa mene ne abun wannan damuwar?” Lumshe shanyayyun idanunsa ya yi kafin ya ce“na haƙura fa Ummi, na bar wa Allah komai, idan Nana ce Alkhairina Allah ya sani kuma zai bar min ita a duk yanda take, amma idan ba ita ba ce ba na san ba zan sameta ba, so ki bar damun kan ki” ya ƙare maganar a sanyaye, girgiza kai Ummi ta yi sannan ta zauna gefen gadon ta dafa kafaɗar sa cike da kulawa irin ta uwa ta ce “na sani akwai ciwo ka rabu da wanda ka ke so, na sani kana son Nana, ita kuma tana sonka, amma ka sani baka isa ka bawa kan ka abin da Allah bai baka ba, idan ba ita Allah ya ƙaddara maka ba, ba zaka taɓa samunta ba, sai dai ka yi ta damun kan ka kana shiga wani hali, mata su aka sani da irin wannan ba maza ba, ka zama mai ɗaukan ƙaddara a duk yanda ta zo maka, ka daina wannan ƙuncin da damuwar. Ka fawallawa Allah komai dan Allah Sultan” Faɗawa jikinta ya yi yana sakin wani marayan kuka mai ban tausayi, kuka yake ko ya samu sauƙin abin da yake ji a zuciyarsa, ya sani ba lallai bane ya samu Nana tun da aka yi haka, amma zuciyarsa ta kasa haƙura ta daina tunaninta. Ummi ta shiga shafa kansa a hankali tana jin babu daɗi a ranta, tabbas da tana da dama da sai ta bawa Sultan matar da yake so, sai dai ko kaɗan bata da wannan damar, ba zata iya cewa koda ƙala ba akan maganar auren, dan haka dole ta ci gaba da rarrashinsa da kuma yi masa addu'a har ya manta da Nana. **** Around 5:20 na yamma ta sakko ƙasan hannunta riƙe da wayar Zahra, babu kowa a parlon dan haka ta yi waje da sauri kafin wani ya zo. Tafiya ta dinga yi tana waiwaye har ta fice daga gidan, ta tsaya a jikin gate ta fara dialing numbern tasa, sai dai kafin ta kai ga kira taji ana yin horn daga gefenta na dama, dan haka ta juya tana kallon wanda yake horn ɗin, kamar yanda ta zata haka ce ta faru, Junaid ne zaune gaban motar hannunsa maƙale kan steering motar yana kallonta, ta sauke numfashi sannan ta ƙarasa wajen. Buɗe motar ta yi ta shiga tana kallonsa, ya dinga kallonta shima yana murmushi, sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta ta ce “ina yini?” Yanda ta yi maganar ya sanya shi murmushin da bai yi niyya ba, ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta sake sunkuyar da kanta tana murmushin itama. “kin yi kyau abin ki” Ya yi maganar cikin nishadi, ɗago kanta ta yi ta kalleshi ta ce“kai ma haka sir, ka yi kyau kamar ango” “ango ranar bikinsa ko?” Gyaɗa masa kai ta yi ya ce“to yaushe ne bikin namu?” ɗan zaro idanu ta yi sai kuma ta ɗauke kanta bata ce komai ba, ya dinga kallonta can kuma ya ce“kin san me yasa na zo wajenki?” Girgiza kanta ta yi ya ce“daman ina son na sake tambayar ki ne akan maganar aurenku, shin da gaske nan da 6weeks ɗin ne?” She just nodded her head fuskarta babu walwala, ya sauke numfashi sannan ya ce”and har yanzu Abbanki bai karbeni ba?” Kamar zata yi kuka ta ce “ban fa faɗawa Abba komai ba, da Amma kawai muka yi maganar saboda nasan ta fi shi sauƙin kai, but unfortunately sai naga ita ma bata yarda ba, ta ce idan na yiwa Abba maganar sai ta ɓata min rai, and nima na san koda na yi masa ba zan taɓa samun abin da nake so ba, ba zasu barni ba, in dai ina cikin estate ɗin M-Shuwa ba zan taɓa kasancewa da kai ba, sai dai...” Ta ɗan yi shiru tana kallonsa idanunta cike taf da hawaye “Sai dai me?” Junaid ya yi maganar yana ci gaba da kallon kyakkyawar fuskarta. Furzar da numfashi ta yi sannan ta ce “Sai dai idan barin gidan zan yi, sai dai idan na bika mu gudu, sai muje wani wajen muyi aure” Da wani irin matsanancin mamaki Junaid ke kallonta, ya girgiza kansa kafin ya ce “mu gudu kuma Nana? Kin san me ki ke faɗa kuwa?” Jinjina masa kai ta yi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce “eh mu gudu, ka gudu dani dan Allah, muje mu yi aurenmu muyi rayuwarmu mu kaɗai” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Page 15... Junaid ya dinga kallonta baki buɗe, ta goge hawayenta tana fadin“saboda idan har ina cikin gidan to sai dai mu haƙura da juna, amma idan muka yi aure basu sani ba, koda na dawo zasu haƙura kuma...” “Nana!” Ya daka mata tsawa wadda ta sanya ta yi shiru, cikin ɓacin rai ya ce“baki san me ki ke faɗa ba! Baki da hankali ne shiyasa, har yau yarinta ke damunki, kin san irin yanda iyayenki ke son ki da har zaki yi yunƙurin rabuwa dasu? Kin san halin da zasu shiga? Do you have any idea about how much they care about you? Kin san irin soyyayar dake tsakanin iyaye da ɗan su kuwa? Kin bani mamaki. Ko zan rasa ki ba zan taɓa yarda da wannan gurguwar shawarar taki ba, ba zan taɓa aminta da ita ba! Ki sake magana!” Kallonsa ta dinga yi hawaye na zirarowa kan kuncinta sai kuma ta ce“Ai shikenan tun da ka ce haka, daman ba sona ka ke ba, a baki ka ke faɗar son amma babu shi cikin zuciyarka, har ka ke iƙirarin ka rasani, to kaje ɗin, nima na rabu da kai, ba zan sake kula ka ba! Ba zan sake kiran ka a waya ba! Ba zan kuma ba wallahi!” ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka dake ƙaryata kalaman bakinta, ta buɗe motar a fusace ta fita. Junaid ya dinga kallonta har ta buɗe gate ɗin gidan ta shige, ya sauke numfashi yana jin babu daɗi a cikin ransa ganin yanda ta yi fushi. Sanin saurin fushinta da kuma saurin saukarta ya sanya bai damu ba ya yiwa motar key ya juya ya yi reverse ya bar unguwar. Wata irin faduwar gaba ce ta risketa saboda ido biyu da suka yi da Zahra tana tsaye ta naɗe hannayenta a ƙirji, ta dinga kallonta ba tare da ta ce komai ba. Sunkuyar da kai Nana ta yi tana goge hawayenta da gefen mayafinta, Zahra ta fizgi hannunta ta fara janta. Bin ta Nana ta dinga yi tana jin zuciyarta na wani irin bugawa, tsoro da fargabar abin da Zahra zata ce mata suka shigeta. A gaban wasu fararen kujeru ta tsaya, ta dangwarar da ita akan ɗaya sannan ta zauna a wadda take facing ɗinta. Ganin irin kallon tuhumar da take mata ya sanya jikin Nana ya sake sanyi, ta ɗago kanta cikin shassheƙar kuka ta ce “wallahi Aunty...” Dakatar da ita ta yi ta hanyar ɗaga mata hannu, ta yi shiru a dole ba dan ta fadi abin da ta yi niyya ba. Shiru wajen ya ɗauka na wasu mintuna kafin Zahra ta buɗi baki cikin kakkausar murya ta ce “Nana wane wannan? A ina ki ka san shi? Mene ne alaƙar da ke tsakaninki dashi? And why you dey called him here!” Zahra ta jera mata tambayoyin tana kafeta da idanu, shiru Nana ta yi tana matsar kwalla, hakan kuma ya ɓatawa Zahra rai matuƙa dan haka a fusace ta ce “okay kar ki yi magana, wallahi idan baki faɗa min wane shi ba sai na faɗawa uncle ɗin ki, idan ya so ya sanar da Abba!” Da sauri ta ɗago kanta, ta dinga girgiza kan tana hawaye a kiɗime kuma ta ce“a'a aunty zan faɗa miki, dan Allah kar ki faɗawa Abbana!” Haɗe rai Zahra ta yi ta ce“oya faɗa min wane ne shi?” Sai da goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta buɗe bakinta a hankali ta fara faɗin “saurayina ne, malamin mu ne a Aun, tun ina jss muke tare, at first na ɗauka kyautatawa ce kawai tsakaninmu, dan tun da ya zo school ɗin ban sake rasa wani abu ba, shi ne yake koya min karatu idan ban iya ba, shi ne yake sakani na gyara kuma ya hanani ba dai-dai ba. Sai da muka zo senior sannan ya faɗa min abin da ke ransa, to nima daman ina son shi a sannan ɗin, duk da ban san mene ne son ba, amma naji yana burgeni, kuma naji ina son na aureshi. Dan haka muka fara soyyaya dashi sosai, kullum sai mun haɗu a Aun, saboda ni yaƙi barin makarantar duk da iyayensa sun yi kokarin saka shi yin haka, a kwana a tashi naji son shi na ƙaruwa a zuciyata, duk da a lokacin nasan mataki da kuma tsarin gidanmu, amma a duk lokacin da naji ina son na bar shi sai naji zuciyata tana yimin zafi, sai naji numfashina na ƙoƙarin barin ƙirjina. To a sannan na gane ba zan iya rabuwa da sir Junaid ba, ba zan iya barinsa ba, dan haka na ɗauki aniyar sai na aure shi koda hakan na nufin zan ɓata da kowa, ma ɗauki aniyar sauya al'adar danginmu, yanda za'a dinga bawa kowace yarinya yancin auren wanda take so. Za'a daina mana auren haɗi, domin yawanci ba wanda ka ke so ake baka ba, dan haka ni sir Junaid nake son aure, kuma sai na aureshi!” Ta ƙare maganar tana shessheƙar kuka, Zahra ta dinga kallonta tana nazarin kalamanta, she just can't believe a ce Nana ke faɗar irin wannan maganar, magana irin ta manya cike da nutsuwa. Ta numfasa kafin ta ce “kenan kina shirin tarwatsa dangin ku? Kin yarda ki zama almakashin da zai datse zumuncin da ke cikin dangin ku? Kin yarda ki zama wadda iyayenta zasu yi Allah wadai da haihuwarta? Kin yarda ko Nana?” Girgiza kanta ta yi still crying ta ce“a'a Aunty, bana son na tarwatsa zumunci kawai ina so...” “kawai me Nana? Shirin ki na auren bare dai dai yake da tarwatsa dangin da iyayenki suka sha wahala wajen samar dashi, kin san mene ne zumunci kuwa Nana? Kin san girman da yake dashi? Kin san falalar da take cikinsa? Kin san yanda ubangiji ke kallon duk wanda ya sadar dashi? Mene ne yake damunki Nana? Yarinta? Ko kuma wannan ba yarinta ba ce son zuciya ce, tun da har ki ka gane ki lalata zumuncin Allah to tabbas son zuciya ce a cikin lamarin ki.” Ban da kuka babu abin da Nana ke yi, ta ɗago runannun idanunta tana kallonta ta ce“to aunty ya zan yi? Na bari na auri wanda bana sonsa? Na bari a lalata min farin ciki? Na yi shiru ina gani” Jinjina kai Zahra ta yi ta ce“eh ki yi shiru, domin babu wanda ya taɓa bin iyaye kuma ya taɓe, Nana kin san wani abu?” girgiza kai ta yi, Zahra ta gyara zama sannan ta ci gaba da faɗin “idan har ki ka ƙi wannan auren tamkar kin raba tsakanin ki da Abba ne, saboda Abba ma ɗaya daga cikin ƙashin bayan wannan zumuncin, su ne suka assasa shi, suka sanya ake auratayya a tsakani saboda a samar da tsaftacen dangi da babu bare a cikinsa. To i dan har ƴar sa zata bijire me hakan ke nufi? Kina son tozarta mahaifinki ne, kina son lalata farin cikin wanda ya fifitaki fiye da komai, wanda yake ɓata lokacinsa da ƙarfinsa domin samar miki da abin da ki ke buƙata, wanda yake baki komai ba tare da ya miki gori ba, idan ki ka raunata zuciyarsa kina nan kin yi dai dai kenan? Kina ganin zai yi alfahari da ke? Ke kaɗai ce yarsa dan haka duk wata taƙama da uba ke yi akan yayansa ke dake kaɗai yake da wannan damar, idan har ki ka ƙi wannan auren tamkar kin wulaƙanta shi ne a idon duniya, kin nuna ce shi bai isa da ke ba, ballantana har wasu su ga girmansa su girmama hukucinsa. Idan har kina ganin wannan shi ne abin da ki ka zaɓa shikenan Nana, ba zan takura ki, ba kuma zan miki dole ba, amma idan da ni ce a matsayin ki...” “za ki haƙura da Junaid domin kare martabar mahaifin ki da kuma dangin ki” Zahra ta gyaɗa mata kai, ta runtse idanunta tana hawaye ta ce “to nima zan yi hakan aunty, zan bar wanda nake so domin kare martabar Abbana, ba zan taɓa yin abin da zai sanya shi a damuwa ba, nayi alƙawarin zan zame masa farin ciki, ba zan saka shi takaici ba, ba zan bari a daina ganin girmansa ba, na haƙura da Junaid aunty, na haƙura dashi na haƙura Aunty...” Zahra ta dinga kallonta cike da farin ciki, ta tashi ta ƙarasa gabanta ta tsuguna sannan ta kama hannayenta ta riƙe cikin nata ta ce“da gaske Nana? Kin haƙura dashi? Ba zaki sake kula shi ba? Ba zaki sake shiga harkarsa ba?” Jinjina mata kai Nana ta yi ta ce“eh aunty, na bar shi wallahi na haƙura, ba zan sake ɗaga maganar ba” Zahra rasa abin yi ta yi sai kawai ta tashi ta rungumeta tana murmushi ta ce“Allah ya yi miki albarka Nana, ya baki zaman lafiya a gidan mijinki, ya haɗa ki da mai ƙaunar ki wanda ba zai ɓata miki ba, wanda zaki so shi fiye da tunanin ki” Ƙanƙameta Nana ta yi sannan ta ce“amin aunty, Nagode, Amma dan Allah kada ki faɗawa uncle ko Abbana” Ɗagota ta yi daga jikinta tana murmushi ta ce“har abada ba zan taɓa faɗawa kowa ba Nana, ki ɗauka mun rufe wannan maganar a nan” Jinjina kai ta yi cike da farin ciki ta sake rungumeta tana fadin “nagode auntyna, Allah ya bar mana ke” Zahra ta yi dariya ta ce“amin tare da ke Nanarmu”. **** Wani irin banza kallo ya dinga masa kafin ya ce“amma dai an yi banza wallahi tallahi, yarinyar ta baka dama sannan ka yi wasa da ita? Ashe ba sonta ka ke ba daman, ba ƙaunarta ka ke ba, a baki ne son wallahi” taɓe baki Junaid ya yi ya ƙarasa kan sofa ya zauna hannunsa riƙe da coffee ya ce“kai dai baka san abin da ka ke ba, yarinyar da nake son na aureta mu samu zuri'a mai kyau da tsafta ita ce zan gudu da ita? Na aureta bada yardar iyayenta ba? Kidding!” Zama shima Al-ameen ɗin ya yi ya ce“to mene ne shirin ka? Taya zaka sameta bayan kasan babu wata hanya?” Ɗan murmushin baka san me ka ke ba ya yi masa kafin ya ce“ba dole ba ne na faɗa maka shirina, but when it goes well zaka ji” murmushi Al-ameen ya yi ya ce“daɗina da kai kwanya, dan Allah ka faɗa min mene ne plan ɗin” Sai da ya yi sipping coffee ɗinsa sannan ya ja gajiyayyun idanunsa ya rufe yana sauke numfashi a hankali, Al-ameen ya ce“ka faɗa min mana dan Allah” “ba fa zaka ji ba yauwa!” cewar Junaid yana kallonsa, taɓe baki Al-ameen ya yi ya ce“to ka ci kanka” **** Ana idar da sallar isha'i suka shigo cikin estate ɗin, Nana ta dinga kallon jama'ar da ke fitowa daga cikin masallacin har idanunta ya sauka akan Abbanta dake tsaye suna gaisawa da Abbansu Hamida, ta ɗan kalleshi sai kuma ta ce“Uncle a sauke ni anan” yana ƙoƙarin parking ya ce“akan me?” “Abba na hango zan bi shi” Ta ce a sanyaye. Gyaɗa kansa ya yi sai kuma ya ce“to sauka” ya yi maganar bayan ya ƙarasa parking ɗin. Buɗe handle ɗin motar ta yi ta sauka, babu wanda ya ce komai a cikinsu ta juya ta nufi inda ta hango Abban. Da idanu kawai ya bita sai kuma ya ci gaba da driving ɗinsa. Sai da taga ya baro cikin mutane ya nufi hanyar gida sannan tabi bayansa a hankali har ta iske masa dan ba sauri yake ba “Abba” Ta kira shi a sanyaye, cak ya tsaya kafin ya jiyo yana kallonta, mamaki ne ya kama shi ya ce“Nana daga ina ki ke?” tana kallonsa ta ce“tare muka dawo da uncle” jin jina kansa ya yi dan sai sannan ya tuna ya ce masa sun fita da Zahra. Ya ce“to tawo mu tafi” ya yi maganar yana miƙo mata hannunsa na dama, ɗora nata tayi akai sannan suka ci gaba da tafiya. Babu wanda ya ce komai a cikinsu, sai dai kowa da abin da yake tunani cikin ransa, shi yana tunanin yanda zai hanata faɗa da mutane, ya yinda take tunanin maganganu da Zahra ta faɗa mata ɗazu. Ta ɗaga idanunta tana kallonsa ba tare da ya sani ba, tabbas ta yi gaskiya, Abba bai cancanci wulakantawa daga gareta ba, bayan duk irin so da ƙaunar da yake nuna mata, bai cancanci ta bijire masa ba, domin bai taɓa zaluntar ta ba. To amma me ya sa take jin zuciyarta kamar ba zata iya haƙura da Junaid ba? Ta sauke ajiyar zuciya tana kawar da tunanin daga ranta, domin ta bar shi har abada. Koda suka shiga gidan basu sami kowa a parlon ba sai tv kawai dake kunne, bai saki hannunta ba ya nufi ɗakinsa, ita ma bata yi kokarin janye hannun ba ta bi shi ɗakin. Ɗakin was neat and organized, komai na ciki a tsaftace yake, ta kalli kan gadonsa wanda ya sha gyara farin bedsheet ɗin sai kyalli yake, sakin hannunta ya yi ya nufi wajen gadon, ta dinga kallon ɗakin tana tuna how long rabonta dashi, wajen study table ɗinsa ta ƙarasa ta dinga kallon tarin awards ɗinsa da kuma certificate as a MD of M-Shuwa group of companies, daga can be gefe ta hangi wasu sticky notes ta kai hannunta ta dinga tabawa kafin ta ce“laaa Abba kana da rubutuna har yanzu? Ni na rasa su” ajiye abin da ke hannunsa ya yi ya ƙaraso wajen ya tsaya a bayanta yana murmushi idanunsa ƙur akan note ɗin farko inda ta rubuta “Abba's first born” ɗayan kuma ta saka “world best Daddy” Lumshe idanunsa ya yi sannan ya buɗe su akanta ya ce“lokacin kina ƙarama sosai, kamar kin fi yanzu hankali” juyowa ta yi tana kallonsa fuska a shagwaɓe ta ce“nafi hankali kuma? Ba an ce mutum yana girma yake ƙara hankali ba?” yanda ta yi maganar da zallar gaskiyar ta ya sanya shi murmusawa ya ja kumatunta sannan ya ce”eh wasu ba, amma ke da kin fi hankali” kallonsa ta dinga yi sai kuma ta ce“to me ya sa Abba?” “saboda da kin fi son Abbanki, da baki ɓata min rai, u're always been my favorite” rungume shi ta yi tana sauke numfashi a hankali ta ce“yanzu ma ina sonka Abba, ni ina sonka, na fi son ka yanzu” shafa kanta kawai ya dinga yi ba tare da ya ce komai, bai san me ya sa kullum yake ƙara jin yarinyar cikin ransa ba, ko dan ita kaɗai gare shi? Ya tambayi kansa. Jan hannunta ya yi har gaban gadon sannan ya miƙo mata katon ledar dake wajen, ta amsa tana murmushi ta ce“Abba me ka siya min? Ko...” Wani irin ihu ta saki ta ƙanƙameshi tana dariya, dai dai lokacin Amma ta shigo tana kallon su a ɗan kiɗime ta ce“subhanallahi, lafiya dai?” ban da murmushi babu abin da Abba ke yi, ita kuwa sai faman ihu take tana tsalle, ya janyeta daga jikinsa still smiling ya ce“ya isa haka murnar” girgiza kanta ta yi sai kuma ta juya ta ɗauki system ɗin tana dariya ta ce“wow Abba, thank you so much, ashe baka manta ba?” Jin jina kansa ya yi sannan ya ce“ya za'a yi na manta?” Ta lumshe idanu tana murmushi ta ce “shiyasa nake sonka sosai” ta ƙare maganar tana kissing ɗinsa a kumatu, dariya kawai ya yi sannan ya bar wajen, ta ƙarasa inda Amma ke tsaye kamar an dasata ta ce“Amma kin kalla Abba ya siya min new system” Murmushi kawai Amma ta yi dan ta san ƙaunarta da system ta ce“yar gatan Abba, congrats” ta ƙare maganar tana jan kumatunta, Dariya kawai Nana ta yi sannan ta ratsa ta gefenta ta fice daga ɗakin da sauri. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Page 16... Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har tsawon sati uku, abubuwa suka dinga matsowa kusa, ban da shirye-shirye babu abin da ake ciki estate. Zuwa sannan duk sun haƙura akan zaɓin da aka musu, babu wanda ya sake tada zancen yana so ko baya so. Ranar Alhamis wajejen ƙarfe 12:00 na rana tana zaune cikin daƙinta wayarta ta fara ƙara, kallon screen ɗin wayar ta yi sai kuma ta ci gaba da danna system ɗinta. Kiran na katsewa wani ya sake shigowa, ta ɗan kalla sai kuma ta matse gefen wayar, ko kaɗan bata son ɗaga kiransa, bata son magana dashi, ta riga da ta haƙura dashi ta yarda da zaɓin da aka mata. Duk da ta san abu ne mawuyaci ta iya mantawa da Junaid cikin ranta, ƙarar da wayar ta yi ya sanya ta ɗan ɗago idanunta kamar zata yi kuka, ta kalli wayar kafin ta sanya hannunta na dama ta dauƙa ta kai kunne. Junaid ya sauke nannauyar ajiyar zuciya jin ta ɗaga wayar, muryarsa cike da damuwa ya ce “Nana” Shiru ta yi tana tura baki, ya sake faɗin “kina jina?” Nan ma ta sake masa shiru tana jin kamar ta katse wayar, “Nana ko dai...” “ina ji” Ta ce murya a ɗan kumbure. Jin jina kansa ya yi yana ɗan suɗe laɓɓansa ya ce“kin daina sona ko? Kin yar dani ko?” Ciro wayar ta yi daga kunnenta ta dinga kallon screen ɗin kafin ta sake mayarwa, Junaid ya ce“Nana wane ya sauya miki tunani? Wane ya baki shawarar rabuwa dani? Ashe daman zaki iya barin a rabamu? Ashe zaki iya mantawa da alƙawarinmu? Kin bani mamaki Nana” Sosai ta ji jikinta ya yi sanyi, nan da nan hawaye suka kawo idanunta, ta yi shiru ba tare da ta furta koda kalma ɗaya ba. Jan numfashi Junaid ya yi ya ce“shikenan Nana, tun da kin zaɓi rabuwa dani shikenan, zan haƙura dake, amma ina son ki sani ba zan taɓa iya daina sonki ba, ba zan iya mantawa da ke ba Nana, I'll not! Kuma ina son ki sani bani na bar ki ba, ke ce ki ka bar ni” Ya ƙare maganar hawaye na zubowa kan fuskarsa, shirun da taji ya yi ya sanya ta sauke wayar daga kunnenta, har sannan bai katse kiran ba, tana jin yanda yake sauke numfashi da sauri da sauri, kashe wayar ta yi gaba ɗaya ta yi wurgi da ita kan ƙarshen gadon sannan ta kwanta tana fashewa da wani raunataccen kuka. Tabbas tana son Junaid, kuma tana jin sa a ranta, amma ta riga da ta yi alƙawarin rabuwa dashi domin farin cikin iyayenta. Tana nan kwance har ƙarfe 1:00 tana faman kuka a hankali, agogon da ya buga ƙarfe ɗayan ne ya sanya ta tashi tana goge hawayenta, ta tashi daga wajen ta ƙarasa gaban mirror ɗinta. Kallon kanta ta dinga yi a jikin madubin, kamar ba ita ba, ta rame, idanunta sun yi jajur kuma sun kumbura. Haka ma fuskarta, ta sauke numfashi sannan ta nufi hanyar toilet tana haɗa hanya. After 10mins ta fito tana goge fuskarta da towel, ta ƙarasa gaban gadonta ta ɗauki prayer mat da hijab ɗin da ta yi salla da asuba ta zura sannan ta shimfiɗa laddumar ta fara gabatar da salla, koda ta ida zama ta yi a wajen ta dinga addu'o'inta har wajen 1:30 na rana, kafin daga bisani ta tashi ta naɗe laddumar ta ajiye inda take sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin sanye da hijabin. Kallonsu ta dinga yi kafin ta ƙarasa tana murmushi ta ce“laa aunty” ta ƙare maganar zama kusa da Ramlah. Murmushi ita ma Ramlah ta yi ta ce“Amarsu Nana” sunkuyar da kanta ta yi tana ɗan murmushi a hankali. Cikin zolaya Ramlah ta ce“wai sauran kwana nawa kenan?” kamar zata yi kuka ta ce“ni aunty ban so wallahi” dariya Ramlah ta yi ta ce“ƙaryar banza dai, muna nan zaki zo kina cewa Yaya Safwan kaza, wai ke ga me miji” tashi ta yi daga wajen da sauri tana satar kallon Amma da ke zaune gefe ɗaya, ta ɗan kalleta ta ce“Amma zan je wajen Aunty Zahra” Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“a dawo lafiya” to kawai Nana ta ce sannan ta yi waje da sauri, Ramlah ta bi bayanta da kallo tana murmushi ta ce“abun mamaki wai Nana ce zata yi aure” girgiza kai Amma ta yi ta ce“nima kullum da auren nan nake kwana nake tashi, Allah dai ya bada zaman lafiya” cikin fara'a Ramlah ta ce“to ya za'a yi? Amin ya rabbi” **** Murmushi kawai Maimoon ta yi ta ce“to ya za'a yi?” Nana da ke tsaye jikin mota ta ce“bari dai naje na dawo sai mu yi maganar” “okay zan faɗawa Amrah ma” Wani irin banzan kallo ta watsa mata sai kuma ta ce“to ba zan je ba” murmushi kawai Maimoon ta yi ta ce“ai ko baki isa ba yarinya, wallahi kamar kin je kin gama” gaba Nana ta yi ba tare da ta sake bi ta kanta ba, Maimoon ta dinga kallonta har ta shige apartment ɗin sai kuma ta juya tana murmushi a hankali. Tura ƙofar parlon ta yi bakinta ɗauke da sallama, Wata babbar mace ce zaune akan kujera ta ci ado da wani ubansu lace mai kyau da tsada, ta yi ɗaurin ture kaga tsiya kitson attachment ya zubo ta ƙasan daurin sai taunar cew gum ta yi tana ƙas ƙas, Nana ta dinga kallonta sai kuma ta sake cewa“Salamu alaikum” ɗago kanta ta yi daga danna wayar da take ta ɗan kalleta babu yabo babu fallasa ta ce“wa'alaiki salamu” daga haka ta sake sauke kanta tana ci gaba da abin da take. Shiru Nana ta yi tana son ta tambayeta ina Zahra take tana kuma jin tsoron yi mata magana. Ganin mintuna biyu sun shuɗe ya sanya ta ce“dan Allah Aunty Zahra fa?” “Tana ciki” matar ta ce a takaice tana taunar cew gum ɗinta, okay kawai Nana ta ce sannan ta nufi hanyar upstairs tana tafiya a nutse, matar ta ɗago ta bita da kallo sai kuma ta ɗan yi siririn tsaki. Kai tsaye ɗakin Zahra ta buɗe ta dinga kallon ko ina ganin bata ciki ya sanya ta mayar da ƙofar ta rufe, ta juyo tana ɗan kalle-kalle corridor ɗin. Ɗakin Noor ta buɗe nan ma taga babu kowa a ciki dan haka ta dawo downstairs tana tunanin inda Zahra ta yi, Tsaye ta same su a parlon, Zahra na kallon matar tana faɗin “okay bari na faɗawa Safeena sai ta miki” toh kawai matar ta ce, Nana ta dinga kallonta kafin ta ce“Aunty Zahra” sai a sannan Zahra ta lura da ita, ta yi murmushi tana faɗin “au Nana ke ce?” gyaɗa mata kai ta yi ta ce“na shigo ban sameki ba, shi ne naje na duba daki naga bakya nan” “Ayyah ina kitchen ne, girki muke, zo ki taya mu” Zahra ta yi maganar tana murmushi, girgiza kai Nana ta yi ta ce“a'a bari naje gida an jima zan dawo, daman magana nake son muyi” ɗan harararta ta yi ta ce“to ki tsaya na ƙarasa mana sai muyi maganar” satar kallon matar dake zaune Nana ta yi daga yanda ta haɗe rai dan haka ta ɗan yi murmushi ta ce“a'a zan dawo ɗin” okay Zahra ta ce dan bata son ta takura mata, ta juya ta fice daga parlon da sauri. Sai a sannan matar ta ɗago kanta ta kalli Zahra ta ce“wace wannan?” “Nana ce fa, yar ƙanin babansu doctor, zama ki ganeta wadda nake zuwa da ita gida fa da, kawai dai ta girma ne” taɓe baki ta yi sai kuma ta ce“shi ne har take shigar miki ɗaki kanta tsaye?” ɗan juya idanu Zahra ta yi sai kuma ta ce“kai Aunty Khadijah Nana fa, ai Nana yar ɗakina ce tun ina amarya” jinjina kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“eh i see” Zahra bata sake cewa komai ba ta koma kitchen ɗin, tsaye ta same su suna aiki suna hira, ta ƙarasa bayan Safeena tana duba carrots ɗin da take yankawa ta ce“wato bama aikin ku ke ba hirar ku kawai ku ke abin ku” Siyama da ke tsaye gaban tukunyar da aka ɗora ta ce“kai Aunty aikin fa muke, kawai hirar ce ta zo” taɓe baki ta yi ta ce“ku dai ku ka sani” daga haka ta juya ta fice. **** Bayan sun gama cin abincin suka kwashe kaf kayan da suka ɓata suka koma kitchen suna wankewa, Zahra ta dinga kallon Aunty Khadijah jin abin da take faɗa, murmushi kawai ta yi ta ce“anan family ɗin? Ai ko abin da kamar wuya” ɗan haɗe rai ta yi ta ce“wuya kamar yaya? Kina cikin dangi sannan ki ce ba zaki samar mata wanda zata aura ba” girgiza kai Zahra tayi ta ce“a'a nifa ba wai ba zan samar mata bane, idan Siyama ta auri ɗaya daga cikin ya'yan gidan nan zan fi kowa murna dan nasan ta samu miji wanda kowace mace ke fatan samu, amma fa kin sani su basu auren bare, i junansu suke aure” wani kallon sheƙeke Aunty Khadijah ta yi mata sai kuma ta ce“eh mana ai shiyasa naga ke an auro ki, tun da kema yar dangin ce” kallonta Zahra ta dinga yi baki buɗe, can kuma ta ce“nifa Aunty ba maganar tashin hankali ba ce wannan ko kuma cin mutunci, na auri Doctor ne saboda Allah ya ƙaddara ni matarsa ce, babu kuma wanda ya isa ya goge wannan abun” “Eh to yanda kema ki ka aure shi saboda Allah ya ƙaddara, haka ita ma zata auri ɗaya daga cikinsu, nifa tun da daman na shirya a gidan nan nakeson Siyama ta samu miji, dan haka aiki ya rage naki, ko dai ki taimaka mata wajen samun abin da muke so ko kuma ni nayi da kaina, ai kin san ba zai gagara ba, wato kina cikin daula da arziki shi ne baki son wasu su zo su ci to wallahi baki isa ba, Sai Siyama ta auri ɗan dangin nan!” Tashi Zahra ta yi ta bar wajen ba tare da ta sake cewa komai ba, Aunty Khadijah ta bita da harara tana fadin “sai dai ki yi, amma wallahi babu wanda ya isa ya hanata! Idan bata auri ɗan dangin nan ba sai dai idan bana raye” . **** Dafata Maimoon ta yi ganin yanda take hawaye yasa jikinta ya yi sanyi, ta ɗan numfashi kafin ta ce“ki yi haƙuri Nana, tun da har ki ka ce kin rabu dashi to kawai ki daina ɗaga wayarsa, ki yi blocking lambarsa ta inda ba zai sake samunki ba, ballantana kuma ya faɗa miki abin da zai karya miki zuciya” Girgiza kanta ta yi wasu hawayen na sake zubowa fuskarta ta ce“na kasa jurewa ne Maimoon, na kasa mantawa dashi, idan ya kirani ta zuciyata zafi take min, I feel like na koma na ci gaba da kula shi, amma da zarar na tuna da Abba sai naji na ƙara sarewa, shin ya zan yi ne ni? Me ya sa nake cikin ruɗani? Me ya kamata na kare? Soyyayata ko kuma iyayena?” “iyayenki!” Maimoon ta yi maganar muryarta a dake cike da kwarin gwuiwa, jin jina kai Nana ta yi ta sanya hannunta tana share hawayenta wasu na sake zubowa ta ce“alright, zan manta da sir Junaid, zan ci gaba da bawa zuciyata haƙuri har ta saba da rashin sa, amma wallahi wata tana zuciyata zata iya bugawa na mutu, zan iya mutuwa Maimoon” rungumeta Maimoon ta yi suka dinga rera kukan tare kamar waɗanda aka yiwa mutuwa. **** Ƙarfe 5:34 na yamma suka fito daga gidan, sai da ta rako su har wajen motarsu sannan ta ce“to Aunty ku gaida gida, a gaida min da Umma da Abba” okay Aunty Khadijah ce, ta juya zata shiga motar sai kuma ta ce“au na manta, da kin kaimu wajen uwar mijin naki ai mun gaisa” to kawai Zahra ta ce duk da ba haka taso ba, ta ce“muje” daga nan suka nufi hanyar apartment ɗin Hajiya Babba. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga sannan suka biyo bayanta, Hajiya Babba na zaune kan kujera hannunta riƙe da azkar tana dubawa, ta amsa sallamar tana ɗago kanta, har ƙasa Zahra ta durƙusa sannan ta ce“Hajiya ina yini?” fuskarta a sake ta ce“lafiya kalau Fatima” tashi ta yi tana kallon su ta ce“to ku gaisa” cikin girmamawa Aunty Khadijah ta gaisheta haka ma su Safeena da Siyama, Zahra ta ce“Yayata ce Hajiya shi ne na ce bari na kawota ku gaisa” jin jina kai Hajiya Babba ta yi ta ce“Oh Masha Allahu, y yaran?” ta yi maganar tana kallon Aunty Khadijah, “Suna nan kalau Alhamdulillah” ta ce da murmushi a fuskarta, masha Allah kawai Hajiya ta ce sannan kowa ya yi shiru, Siyama ta dinga kallon parlon kamar idanunta zasu fito, After 2mins Zahra ta ce“to Hajiya zamu tafi” Allah ya tsare ta musu sannan ta sanya aka ɗauko musu turamen atampa vilisco Holland wadda kimaninta ya kai 240k, suka dinga godiya kafin suka bar gidan. Apartment ɗin su Zahra suka koma ta sake musu sallama sannan suka shiga mota ita kuma ta juya ta koma ciki. Basu yi nisa a cikin estate ɗin ba, Siyama ta dinga kallonsa sai kuma ta taɓo Aunty Khadijah tana fadin “Mom! Mom! Kin ga wannan” ta ƙare maganar tana nuna shi da hannunta, ɗan tsayawa ta yi da tuƙin ta dinga kallonsa ita ma, fitowarsa kenan daga motar ya dauko briefcase ɗinsa sannan ya nufi hanyar apartment ɗin Hajiya Babba, sai da ya shige ta gaban motar su sannan ta kalleta ta ce“ya yi miki ne?” gyaɗa kanta ta dinga yi tana murmushi ta ce“sosai ma Mom, kalleshi fa, ga kyau ga kuɗi kuma saurayi” Ɗan murmushi Aunty Khadijah ta yi ta ce“shikenan” Safeena dake baya ta ɗan yi murmushi sannan ta ce“Hajiya Aunty Khadijah to ya za'a yi ta auri wannan?” ta madubi ta kalleta ta ce“ki jira ki gani” Safeena ta yi murmushi ta ce“to shikenan” daga haka ta ja motar suka ci gaba da tafiya. **** Bayan magrib Aunty Ramlah ta fito hannunta riƙe dana ... tana kallon Amma ta ce“to shikenan yanzu yaushe zata zo?” Amma ta miƙewa.. chocolate sannan ta ce“ko gobe ne, dan yanzu ma ban ganta bane da sai ku tafi tare” “to goben sai ta zo, ina gida ai, idan ya so sai muje na rakata” okay Amma ta ce daidai lokacin da suka ƙaraso balcony suna hango Daddyn... da ya yi parking motarsa yana kallonsu ta ce“to ku gaida gida” zasu ji ta ce sannan ta juya ita kuma Amma ta koma gida. Bata fi 3mins da zama ba Nana ta shigo hannunta riƙe da bowl, Amma ta kalleta sai kuma ta ce“sai yanzu?” zama ta yi gefenta ta ajiye bowl ɗin farfesun kayan cikin ta ce“eh ina gidan su Maimoon ma fa” “Zahran bata nan?” Girgiza kai Nana ta yi ta ɗauki hanta ta kai bakinta sannan ta ce“tana nan, baƙi naga ta yi, wata mata kamar yar tiktok” Amma ta ɗan kalleta sai kuma ta ce“ita Zahran?” Nana ta gyaɗa kanta tana ci gaba da cin namanta, shiru Amma ta yi bata sake cewa komai ba, ta ci gaba da danna wayarta. Da daddare tana kwance around 10:20pm wayarta ta fara ƙara, ta tashi zaune ta janyota ganin numbern Junaid ya sanya ta yi tsaki sannan ta mayar ta ajiye ta koma ta yi kwanciyarta, kiran ne ya sake shigowa ta yi banza har ya katse sannan ta lumshe idanunta, ba'a fi seconds biyu ba taji ƙarar message dan haka ta ɗauki wayar, buɗe message ɗin ta yi taga an rubuta “Ki ɗaga wayar akwai abin da za'a faɗa miki” Nana ta dinga kallon message ɗin fuskarta ɗauke da mamaki, abun mene ne zai faɗa mata? Kuma za'a faɗa mata? To wane kenan?. Bata gama wannan tunanin ba wani sabon kiran ya sake shigowa, ta ɗan sauke numfashi kafin ta ɗaga ta kai kunne, daga can ɓangaren aka ce “Salamu alaikum” Sai da gabanta ya faɗi jin ba muryar Junaid ba, murya a sanyaye ta ce “wa'alaika assalam, sir?” Ta yi maganar da sigar tambaya, girgiza kansa ya yi yana rike da hannun Junaid da ke kwance ya ce“bashi bane” Da mamaki sosai ta ce“bashi bane? To wane ne? Ina yake?” ta jera masa tambayoyin hankali a ɗan tashe, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce“ɗan uwansa ne, daman kira nayi na faɗa miki bashi da lafiya, yana kwance a asibiti, sai kiran sunanki yake shiyasa ma na ce bari na kira ki” Dafe ƙirji Nana ta yi ta sauko daga kan gadon ba tare da ta sani ba, muryarta a raunace ta ce“innalil lahi wa ina ilayhi raji'un, me ya same shi?” “har yanzu likita bai sanar damu ainihin abin da ya same shi ba, amma dai sun ce yana da bukatar kulawa” tuni hawaye suka fara zubowa kan fuskarta kamar an buɗe famfo, ta girgiza kanta cikin shessheƙar kuka ta ce“Allah sarki, Allah ya bashi lafiya, zan zo na duba shi da safe idan Allah ya kaimu” jinjina kai ya yi ya ce“to Allah ya kaimu” Amin ta ce sannan ya kashe wayar, ta silale ƙasan rug ta fashe da kuka, kenan bashi da lafiya saboda ya rasata? Me zai same shi?. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Masu tambaya daga farko su yi following channel akwai acan dan Allah🙏 Page 17... Daren ranar haka ta ƙarasa shi cike da damuwa, ta kasa bacci sai juye-juye ta dinga yi, har aka fara kiran sallar asuba ta tashi ta gabatar da sallah, addu'a ta zauna ta dinga yiwa Junaid tana nema masa sauƙi har gari ya fara haske sannan ta tashi ta koma ta kwanta. Ƙarfe 9:20 na safe ta farka, ta tashi zaune tana mitsitsika idanunta, wayarta ta ɗauka ta kalli screen ɗin taga missed calls har uku da numbern Junaid, ji ta yi gabanta ya yi wata irin faɗuwa, ta danna call back ƙirjinta na bugu da ƙarfi, ringing ɗaya ya ɗauka a sanyaye ya ce“Assalamu alaikum” “ya jikin nasa? Yana iya magana? Me likitan ya ce” Ta jera masa tambayoyin muryarta na rawa, numfasawa Al-ameen ya yi ya ce“da sauƙi Alhamdulillah, yanzu zan fita naje asibitin na gan shi” Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ta runtse idanunta hawaye ya dinga zirarowa ta gefen idanun, jin ta yi shiru ya sanya Al-ameen ya ce“Nana” “shikenan nima zan zo asibitin, ka faɗa min address ɗin” Jinjina kansa ya yi kafin ya ce“bari zan turo miki da text message ɗin, private asibiti ne nan gefen Jalo” toh kawai ta ce sannan suka yi sallama ta kashe wayar, ji ta yi jikinta ya ƙara yin sanyi, me zai faru idan wani abun ya samu Junaid ta dalilinta? Ya za'a yi ta yarda? Sai kawai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, ta dinga rerashi har bayan mintuna ashirin. Jiki babu kwari ta tashi ta shige toilet ta yi wanka ta fito, a gurguje ta shirya cikin wata umbrella pattern Abaya black colour, ko rolling mayafin ba ta yi kawai ta yafa shi loosely, har ta kai bakin ƙofa sai kuma ta dawo ta ɗauki wayarta da atm card ɗinta sannan ta juya ta fita. Koda ta fito parlon bata samu kowa ba, dan babu alamar ma sun fito daga ɗaki, dan haka kawai ta yi waje without second thought. Tafiya ta dinga yi da sauri da sauri har ta fice daga cikin estate ɗin, ta ƙarasa gefen titi, ta ɗauki a ƙalla 10mins a wajen kafin ta samu wani napep ya kawo mutane, ta tsaida shi ta shiga sannan suka bar wajen. **** Barraks road. Siyama ce zaune kan sofa idanunta zube kan wayarta ƙirar iphone 13pro max tana dannawa a hankali, Aunty Khadijah ta fito daga bedroom tana gyara zaman mayafin jikinta ta kalleta ta ce“zan fita idan Umma ta dawo sai ki faɗa mata” sai da ta ajiye wayar sannan ta ɗago ta kalleta, sanye take da wata embroidery Atampa ja mai adon baki, ɗinkin t-boubou wadda ta sha stones sai kyalli take, wuyanta da hannunta sanye da kayan ado na ƙarfe sai wal-wal take, Siyama ta ɗan yi murmushi kafin ta ce“Mom kin yi kyau sosai wallahi” murmushi kawai Aunty Khadijah ta yi ta ce“nima nasani, kina ji idan na fita zan biya ta gidan Hajiya Baturiya sai muga yanda za'a yi” cikin farin ciki Siyama ta ce“yauwa Mom dan wallahi tun jiya hankalina ya kasa kwanciya, idan na rufe idona fuskarsa nake gani, ji nake kamar na shirya na koma gidan yau wallahi” “A'a kar ki je, ba yanzu ba, ki bari na dawo sai mu ƙarasa maganar” to kawai ta ce sannan ta mata Allah ya tsare ta nufi hanyar fita daga parlon ta fice, ita kuma ta ci gaba da danna wayarta. **** Misalin ƙarfe 10:30 na safe ta ƙaraso Jabo road, dan haka ta sauka daga napep ɗin ta tsaya tana tunanin yanda za'a yi ta bashi kudi dan babu ko biyar cash a hannunta, ganin yana jiranta ya sanya ta ce“yauwa ko zan maka transfer ne na manta ina sauri ban dauko cash ɗin kuɗi ba” kallonta mai napep ɗin ya dinga yi sai kuma ya ce“to shikenan yimin” numfasawa ta yi kafin ta buɗe wayarta ta shiga Opay ɗinta ya dinga karanto mata lambobin har ta gama ta tura masa sannan ya bar wajen, kalle-kalle ta dinga yi ganin titin babu wasu mutane sosai sai ɗaiɗaikun motoci dake shigewa, ta yi dialing numbern Junaid har ta katse ba'a ɗaga ba, ɗan tsaki ta yi ta sake dialing ta kai kunne, sai da ta kusa katsewa sannan aka ɗaga da sauri ta ce “yauwa gani a bakin titin” “Nana!” Junaid ya kirata muryarsa a ɗan shaƙe, dafe ƙirji ta yi nan da nan hawaye ya kawo idanunta ta ce“sir ya jikin naka? Kana lafiya dai?” jin jina kansa ya yi yana jingina da jikin gadon ya ce“da sauƙi Alhamdulillah Nana” ajiyar zuciya ta sauke ta ce“to gani a bakin titin ya sunan asibitin?” cikin sassanyar muryarsa ya ce“Al-ameen ya fito zai tawo dake kin ji, da baki wahalar da kan ki ba” Girgiza kanta ta shiga yi kafin ta ce“ba zan iya zama ban zo na ganka ba, ba zan iya ba!” ta ƙare maganar cike da rauni, Na hannunsa na dama ya sanya ya goge hawayen daya zubo masa ya ce“shikenan Nana sai kin zo” to kawai ta ce sannan ta kashe wayar, ta dinga tunanin halin da yake ciki, koda bata ganshi ba ta san jikinsa babu daɗi, domin ba haka ya saba maganarsa ba. Tana nan tsaye har wajen 11:00 na safen kafin su ƙaraso titin, kasancewar ana rana ya sanya ta ɗan ja mayafin Abayar jikinta ta rufe gefen fuskarta. A gabanta motar ta yi parking ya sauke glass ɗin yana kallonta ya ce“shigo muje” duk da bata san shi ba amma ta gane shi ne wanda ya zo ɗaukanta, dalilin muryarsa da taji, dan haka ta karasa ta buɗe passenger seat ɗin motar ta shiga sannan ta rufe, kallonta ya dinga yi a hankali kuma ya ce“sannu ko” yauwa kawai ta ce dan hankalinta gaba ɗaya yana wajen Junaid, shima bai sake cewa komai ba ya yi reverse ya bar wajen. Tafiya kusan 10mins ta kwo su bakin asibitin The Medicare, ya yi horn aka buɗe gate ɗin sannan ya zura hancin motar ciki, a parking space ɗin asibitin ya yi parking sannan ya sauka ita ma ta buɗe gefenta ta fito ta tsaya tana ƙarewa babban asibitin kallo, “muje ko” Maganar ta dawo da ita daga tunanin data tafi, ta jinjina kanta sannan ya yi gaba tana biye dashi, cikin vip suka shiga ita dai sai kallon wajen take har ya buɗe wani daki ya shiga, bin bayansa ta yi ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Junaid ne zaune tsakiyar gado ya jingina kansa da ƙarfen gadon idanunsa a lumshe, kallonsa ta dinga yi ganin yanda ya rame cikin kwanaki kaɗan, ya yi baƙi kamar ba shi ba, Alameen ya ƙarasa gabansa ya taɓa shi a hankali ya ce“Junaid gata” buɗe idanunsa ya yi a hankali kai tsaye kuma akanta ya sauke su, ya dinga kallonta ganin yanda ta yi kyau abin ta kamar babu abin da ke damunta, murmushin ƙarfin hali ya yi mata kafin a sanyaye ya ce“Nana” Ƙarasowa wajen ta yi a hankali ta tsaya jikin gadon still looking at him ta ce“sir sannu, ya jikin naka?” ”Alhamdulilah Nana, naji sauƙi sosai” ya ce shima yana kallonta, shiru ta yi bata sake cewa komai ba, ta sunkuyar da kanta hawaye na zubowa kan fuskarta, girgiza kai Junaid ya yi ya ce“mene ne haka Nana? Stop crying mana” kamar jira take kawai ta fashe da kuka, ta sanya hannunta ta rufe fuskarta, kasa hanata ya yi, ya dinga kallonta dakyar kuma ya iya cewa“Nana kina son wani ciwon na daban ya sameni?” girgiza masa kai ta yi ba tare da ta kalleshi ba, ya ce“to zauna ki daina kukan” Zama ta yi gefen gadon kamar babu laka a jikinta, ta kifa kanta bisa cinyarta ta ci gaba da kukanta a hankali. Juyawa Al-ameen ya yi ya bar dakin, Junaid ya numfasa sannan ya ce“Nana ɗago kan ki na ce” rage kukan ta fara yi a hankali sannan ta ɗago kan nata bayan ta goge hawayen ta kalleshi cikin shessheƙar kuka ta ce “ka yi haƙuri sir, ka yi haƙuri, ban gaza ba wallahi, amma babu yanda zan yi ne, ba zan bijirewa iyayena ba, i can't ruined my father's image, ba zan iya ba!” ta ƙare maganar tana kecewa da wani sabon kukan, numfasawa ya yi sannan ya ce“Na sani Nana, na san ba laifinki bane, nima kuma ban riƙe ki ba, dan haka ki daina wannan kukan dan Allah kin ji” sake goge hawayen ta yi sannan ta ce“to me ya sa baka da lafiya? Mene ya sameka?” murmushi ya yi ya ce“bafa wani abun bane, zazzaɓi ne kawai nake, kin ji kar ki damu kan ki” kallonsa ta dinga yi kafin ta ce“ni nasan ba zazzaɓi bane, zazzaɓi ba zai saka ka dinga kiran sunana ba! Wani abun ne dai yake damunka ka ke son ka ɓoye min” girgiza kansa ya yi still smiling ya ce“kin san ai bana ɓoye miki abu, so ki yarda dani kin ji, na samu sauƙi Alhamdulillah” Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce“shikenan, Allah ya ƙara sauki” sosai ya ji daɗi ganin ta haƙura ya ce“Amin Nanata, yanzu bari na akawo miki abu mai sanyi ki sha ya sauƙaƙa zuciyar” ya ƙare maganar yana kashe mata idanu, murmushi ta yi ta ce“babu abin da zai sauƙaka zuciyata face na ganka cikin farin ciki” waro idanunsa ya yi ya ce“da gaske?” gyaɗa kanta ta yi a hankali ya ce“tom shikenan, nima ina son naga kina farin ciki Nana Khadijatou” kafin ta yi magana ya buɗe kofar ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, amsawa suka yi sannan ya ƙaraso hannunsa riƙe da drinks da ruwa ya ce“kun gama kukan masoya?” sunkuyar da kanta ta yi tana murmushi, Junaid ya ce“kai zan maka rashin mutunci” harararsa ya yi ya ce“malam kaji da kanka kaji” ya ƙare maganar yana dariya, robar coke ya miƙawa Nana ya ce“Amarya ga drink ki sha ko kya samu sauƙi” Amsa ta yi tana murmushi ta ce“okay thanks alot” jinjina kansa yayi sannan ya miƙawa Junaid ɗin ya ce“bawan Allah kai ma gashi” karɓa shima ya yi ya ce“to Allah ya maka albarka yaron arziki” buɗe baki ya yi yana kallonsa sai kuma ya yi kwafa ya ce“zaka gane ne wallahi” daga haka ya juya ya fice daga ɗakin. Da idanu Nana ta bishi sai kuma ta mai da Idanunta kan Junaid ta ce“abokin ka ne?” gyaɗa mata kai ya yi yana bude robar hannunsa ya ce“childhood friend ɗina kenan, tare muka yi karatu a Paris” gyaɗa kanta ta yi ta ce“Allah sarki, yana da kirki” “eh sosai kuma yana da barkwanci, let me help you” ya kare maganar yana miƙo mata hannu, robar ta miƙa masa ya buɗe mata sannan ya bata ta ɗan yi murmushi ta ce“thank you” taɓe baki ya yi ya ce“sannu to” she just smile sai kuma ta kai robar bakinta ta kurɓa, kallonta ya dinga yi sai kuma shima ya sha nasa sannan ya ce“ina Amma” “tana nan kalau, ban ma faɗa mata ba fa na fito” ta yi maganar da iya gaskiyarta, zaro idanu ya yi sai kuma ya ce“but why Nana?” kwaɓe fuska ta yi ta ce“zan fito sai naga bata parlon maybe ma bacci take, that's why yasa kawai nayi fitowa ta” “yanzu idan ki ka koma sai ki ce mata kin je ina?” ya yi maganar da sigar tuhuma, shiru ta yi can kuma ta ce“kawai zan ce ina Apartment ɗin Hajiya Babba, ba zata ce komai ba” girgiza kansa ya yi sai kuma ya ce“kar ki sake irin haka Nana, babu kyau” toh ta ce a sanyaye, sai kuma shiru ya biyo baya, ta dinga sipping lemon hannunta a hankali har ta kusa shanyewa. **** Da ɗan mamaki Abba ya ce“to ina taje?” Girgiza kai Amma ta yi ta ce“wallahi ban sani ba, amma maybe tana Apartment ɗin su Maimoon dan nan ne wajen zuwanta, ko kuma wajen Zahra” wayarsa ya zaro a aljihu ya ce“but it's getting late fa, kusan ƙarfe 2pm bata dawo ba” zama ta yi kan sofa tana faɗin “haka take, sai ta yini a can fa, ko jiya bata dawo ba sai dare” Abba bai sake cewa komai ba ya juya ya fita, ta bi shi da kallo sai kuma ta ɗauki wayarta, lambar Ramlah ta yi dialing ringing ɗaya ta ɗauka daga ɗaya ɓangaren Aunty Ramlah ta ce“Yaya ina yini?” Amma ta ce”lafiya kalau Ramlah ya ku ka je gida?” “Alhamdulilah" Ta yi maganar tana ajiye plates ɗin data ɗebo, jinjina kai Amma ta yi bata ce komai ba, Aunty Ramlah ta ce“au Yaya naji Nana shiru bata zo ba” ɗan siririn tsaki ta yi sannan ta ce“yo bana manta ba, ita kuma ta tafi yawon magana tun safe har yanzu ban ganta ba” murmushi Aunty Ramlah ta yi ta ce“oh Nana sabga, to ko gobe sai ki turo ta” to kawai Amma ta ce sannan suka ci gaba da wata hirar. **** Al-ameen ya dinga kallonta ganin yanda take bacci sai kuma ya kalli Junaid ya ce“yanzu mene ne abu na gaba?” murmushi kawai Junaid ya yi sannan ya ƙarasa kan gadon ya ɗan janye mayafin data rufe fuskarta dashi, kallon kyakkyawar fuskarta ya dinga yi yana murmushi kafin a fili ya ce“sai abin da na shirya” ya kare maganar yana dariya, dariyar shima Al-ameen ya yi ya ce“kaya ya zo hannu” ɗan haɗe rai Junaid ya yi kafin ya ce“kai wannan ba kaya ba ce, kadara ce malam!” tuntsirewa da dariya ya yi ya ce“to naji” janye mayafin kanta ya yi nan take lallausan gashinta ya bayyana akan gadon, ya ɗan suɗe down lip ɗinsa ya ce“ke tawa ce Nana, kuma babu wanda ya isa ya rabani da ke, ke ɗin mallakina ce, ni kaɗai, ni kaɗai NAANAH!”. Idan ba next chapter sai kun biya dan wannan harkar ba za'a yi ta kyauta ba🤭😂❤️ 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Follow my account, Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 18... Amma ce tsaye tsakiyar parlon tana kallon Ummi ta mamaki ta ce“what? Bata zo nan ba? Nana bata zo nan ba tun safe?” girgiza kai Ummi ta yi tana kallonta cike da damuwa ta ce“bata zo ba, ni rabonda na ganta tun jiya da daddare” dafe ƙirji Amma ta yi, lokaci ɗaya wata matsananciyar faduwar gaba ta risketa, to ina Nana ta tafi?. “ko dai taje wajen Zahra?” Girgiza kai ta yi kafin ta ce“a'a bata je ba, dan ɗazu ma Zahra ta shigo take tambayar ina Nana take, shiyasa ma na fito” Ummi taja numfashi kafin ta ce“to ina yarinyar nan ta shiga dan Allah? Ko wani wajen ta tafi da taga yamma ta yi ba sai ta dawo ba?” Kwafa kawai Amma ta yi sannan ta juya ta bar parlon da sauri, da idanu Ummi ta bita sai kuma ta ce“kai Allah ya shirya mana yaran nan” Koda ta koma gida zaune ta sami Abba kan sofa hannunsa riƙe da jarida yana dubawa a hankali, ganin yanda ta ɗan birkice yasa ya ce“lafiya da Rabi'a?” girgiza kanta ta yi jiki a sanyaye ta ce“babu komai” daga haka ta nufi daƙinta ba tare da ta sake kallonsa ba, shima bai damu ba ya ci gaba da abin da yake. Tana shiga ɗaki ta zauna gefen gado muryarta na rawa ta ce“Allah ka dawon da yarinyar nan lafiya koma ina ta tafi, Allah kada ka ɗora mana abin da ba zamu iya ba, Allah ka bata ikon dawowa gida cikin ƙoshin lafiya” “Ina Nanan ta tafi? Bata wajensu Yaya?” Abba ya yi maganar yana daga tsaye a gefen ƙofa, kallonsa ta yi da fuskarta wadda hawaye ya fara zubowa ta ce“bata can, sun ce bama taje ba kwata-kwata” Da matuƙar mamaki yake kallonta sai kuma ya ce“and shi ne baki faɗa min ba? Kina cikin hankalinki kuwa? What idan wani abun ya samar min ƴa?” buɗe baki ta yi zata yi magana ya ɗaga mata hannu da sauri, ta dinga kallonsa ganin yanda ya haɗe rai, lokaci ɗaya kuma ya juya ya bar dakin a fusace. **** A hankali ta shiga buɗe idanunta wanda take jin sun yi mata nauyi, ta dinga kallon cealing ɗin ɗakin ba tare da ta gane inda take ba, da sauri kuma ta miƙe zaune tana ƙarewa ɗakin kallo, bacci ta yi anan? how and why? Ta tambayi kanta, kwayayen data gani a kunne shi ne ya tabbatar mata da cewa dare ya riga da yayi, lokaci ɗaya ta tuna da abin da ta zo yi dan haka ta ɗora hannunta aka cikin tashin hankali ta ce “na shiga ukuna!” Ta sauka daga kan gadon da sauri tana ɗaukan mayafinta dai dai nan ya buɗe ƙofar ya shigo, kallonsa ta dinga yi ganin kamar bashi ba, yana sanye da wata polo t-shirt red colour sai trouser black, murmushi ya yi ya ce“kin tashi?” “ƙarfe nawa yanzu? Na shiga uku me zan ce a gida?” ta ƙare maganar hawaye na zirarowa kan kuncinta, numfasawa Junaid ya yi ya ce“yanzu kusan 7:20pm, naso na tashe ki sai kuma naga kamar bai dace ba, that's why yasa na bar ki” Wani irin kallo ta dinga yi masa sai kuma ta ce“daka tasheni ai, yanzu me zance a gida?” Girgiza kai Junaid ya yi ya ce“ki bar wannan maganar ki tawo na mai da ki, kar daren ya sake yi” Wayarta ta ɗauka sannan ta yi waje kamar zata tashi sama, wani kyakkyawan murmushi ya yi kafin ya bi bayanta. Tun da suka fara tafiya take kuka kamar ƙaramar yarinya, shi dai bai ce mata komai ba, kuma bai yi yunƙurin hanata kukan ba, ya dinga driving ɗinsa a hankali time to time yana ɗan murmushi. **** Abdusammad ya dinga kallon Abba can kuma ya ce“to daman tana fita ba'a sani ba?” Girgiza kai Abba ya yi ya ce“nima ban sani ba wallahi, koma mene ne ai laifin uwarta ne da har zata bari ta fita bata sani ba, yarinya kamar Nana a ce ta kai har yanzu a waje, to ina ma ta sani ballantana taje?” Abba ya ƙare maganar yana sauke wani zazzafan numfashi, ko ba'a faɗa ba kasan ransa ya gama ɓaci, ɗan dafa shi Abdusammad ya yi ya ce“calm down dan Allah kada wani abun ya sameka, bari naje wajen Hajiya Babba ko taje can” saurin riƙe hannunsa Abba ya yi ya ce“a'a kar ka sanar mata, ban son hankalinta ya tashi, shiyasa ban bari an sanar da ita ba” shiru Abdusammad ya yi can kuma ya ce“alright ka koma gida, zan dawo da ita in sha Allah” jinjina masa kai kawai Abba ya yi sannan ya saki hannunsa ya nufi balcony ɗin gidansa, sai da yaga ya shige ciki sannan ya sauke numfashi ya juya shima ya bar wajen.. **** Zaune ya same su a parlon suna faman hira, yana shigowa kowacce ta yi shiru murya can ƙasa suka ce“sannu da zuwa Uncle” bai amsa ba, sai kallo daya dinga bin su dashi wanda ya sanya suka sunkuyar da kawunansu, harɗe hannayensa ya yi a ƙirji yana tawowa toward them ya ce“ina Nana take?” Da sauri suka kalleshi sai kuma suka sake sunkuyar da kai, ya jinjina kansa sannan ya sake cewa“okay, ba zaku faɗi inda take ba ko? Then zan yi maganinku duka yanzun” ɗago kansu suka yi, kowacce ta dinga girgiza kanta dan ba ƙaramin tsoronsa suke ba, Maimoon da tafi kowa firgita ta ce“wallahi tallahi uncle ban sani ba, ni ban ma ganta ba yau, ban san ma bata gida ba” ta ƙare maganar tana girgiza hannunta, kallonta ya dinga yi rai a haɗe, lokaci ɗaya kuma ya mayar da idanunsa kan Hameeda, girgiza kanta tayi cikin sanyin muryarta ta ce“uncle ban ganta ba wallahi, rabon da naga Nana an fi kwana uku ma, bata fitowa yanzu” taɓe baki ya yi sannan ya kalli Amrah wadda taƙi ɗago kanta, ganin yanda take rawar jiki ya sanya ya daka mata tsawa wadda ta firgita su duka ya ce“ina Nana take?” “wallahi ban sani ba, ban sani ba Uncle, bama magana da ita dan haka bata zuwa inda nake, ban san inda take ba wallahi” ta ƙare maganar tana fashewa da kuka, Numfasawa ya yi dan ya tabbatar basu san inda take ban, ya juya ya fice daga parlon ba tare da ya sake ce musu komai ba, dafe ƙirji Maimoon ta yi a fili ta ce“wallahi Allah ya isana ba zan yafewa Nana ba data sanya aka ɗaga min hankali” girgiza kai Hameeda ta yi ta ce“mene haka? Ki ka sani ko wani uzurin ne ya fitar da ita?” “Na rantse da a ce na san inda ta tafi sai na faɗa masa, to dan dai kawai ban sani bane” Amrah ta yi maganar cikin ɓacin rai, harararta Hameeda ta yi ta ce“saboda ba zaki iya rufawa yar uwarki asiri ba?” “ai ita ba wadda za'a rufawa asiri ba ce, ke kina ganin da a ce kece ba zata faɗa ba?” Hameeda ta gyaɗa kanta ta ce“eh wallahi, ni nasan da ni ce Nana ba zata taɓa faɗa ba, ke koma ta san yawo na tafi ba zata faɗa ba, saboda bata da baƙin hali” daga haka ta tashi ta fice daga parlon. Da harara Amrah ta bita kafin ta ce“ai daman ni ce mai baƙin hali, naji ɗin to, wallahi sai na faɗa?” Ita dai Maimoon shiru ta yi tana tunane-tunane cikin ranta. **** Ƙarfe 7:45pm ya yi parking a bakin estate ɗin, ganin bata ma san sun zo ba ya sanya ya juyo ya ɗan kalleta murya a sanyaye ya ce”Nana mun zo fa” janye mayafin data rufe fuskarta ta yi, ta ɗan kalleshi da kumburarrun Idanunta sai kuma ta buɗe motar ta sauka ba tare da ta ce komai ba ta nufi gate ɗin estate ɗin jiki a sanyaye. Ajiyar zuciya Junaid ya sauke sannan ya juya ya bar wajen lokacin da yaga ta shiga, koda ta shiga ciki bata samu kowa ba, dan daman i wannan lokacin ba'a fiye samun jama'a ba kasancewar akwai sanyi a garin, kowa yana cikin gidansu, ta dinga tafiya kamar wadda aka cirewa laka har ta ƙaraso bakin balcony ɗinsu, banda faɗuwa babu abin da gabanta ke yi, tunanin ɗaya abinda zata ce dasu Amma idan ta shiga ciki, dan haka ta ɗan tsaya tana sauke numfashi da sauri da sauri. “Nana!” Sai da taji sautin zuciyarta ya ɗan buga saboda tsoron da taji, ta juyo a hankali idanunta ya sauka akan Maimoon da ke tsaye sanye da hijabi, kallonta ta dinga yi sai kuma ta ce“ina ki ka je Nana?” kasa bata amsa ta yi sai kawai ta faɗa jikinta ta rungumeta tana kuka a hankali, tsoro da fargaba ne suka ziyarci Maimoon, ta ɗago fuskarta tana tattaba jikinta ta ce“kina lafiya dai?” “Tsoro nake ji Moon, tsoro nake ji wallahi!” Ta yi maganar cikin kuka, kallonta Maimoon ta dinga yi sai kuma taja hannunta suka fara tafiya, ita dai Nana sai bin ta take da kallo ba tare da ta san inda suka nufa ba. A bakin apartment ɗin Hajiya Babba ta tsaya ta kalleta murya can ƙasa ta ce“Hajiya ce kawai bata san bakya nan ba, dan haka ki shiga ki salallaɓa ki shige ko ɗakinta ne ki kwanta, ki cire wannan rigar ta jikin ki sannan kada ki nuna ba'a nan ki ka yini ba, ki ce baki da lafiya ne, ni kuma zan je na karbo abinci a wajen Ummi idan na shigo zan zo na taso ki kin ji” gyaɗa kanta kawai ta dinga yi still crying ta ce“to idan kuma Hajiyar tana ɗakin fa?” sai da ta kalli compound ɗin ta tabbatar babu kowa sannan ta ce“tana parlon, yanzu zan shiga na sanya ta shiga kitchen sai ki shigo kin ji” to kawai ta ce sannan Maimoon ta nufi ƙofar parlon ta murɗa handle ɗin a hankali, Hajiya Babba na zaune kan sofa tana cin abinci a hankali, Maimoon ta ƙarasa tana murmushi ta ce“hajiya Babbarmu” kallonta kawai ta yi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“kin zo ki hana ni cin abinci ko?” kitchen Maimoon ta nufa tana faɗin“ni na isa na hanaki cin abinci, kawai nama zan ɗauka” zumbur Hajiya ta tashi tsaye tana kallonta ta ce“kar ki taɓa min abu a kitchen kin ji ko” ko saurarenta Maimoon bata yi ba ta shige kitchen ɗin tana dariya, ganin haka ya sanya itama Hajiyan ta bita da ɗan saurinta tana faɗin “yau naga tsiya da wasali!” Nana data kasa kunne tana saurarensu ta tura ƙofar a hankali ta shiga, ganin babu kowa a parlon ya sanya ta cire takalman ƙafarta ta kwasa da gudu ta yi sama. Hajiya Babba ta kwace robar dambun naman tana faɗin “fita ki bani waje” kwaɓe fuska Maimoon ta yi ta ce“kai Hajiya duk kin fi son Nanar nan haba!” daga haka ta fito daga kitchen ɗin tana leƙan parlon, ko tsayawa ba ta yi ba ta nufi hanyar fita daga parlon ta fice abin ta, ta dinga kallon balcony ɗin ganin babu Nana ya sanya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta nufi hanyar gidansu da sauri. Tana hawa saman ta shige ɗaya daga cikin bedrooms ɗin saman wanda ta tabbatar ba anan take kwana ba, ta ajiye wayar gefen madubi sannan ta nufi toilet da sauri, wanke fuskarta ta fara yi sannan ta ɗauro alwala ta fito, ta sake naɗa mayafin akan ta sannan ta fara gabatar da sallolin da ake bin ta. Bayan ta idar da sallar ta tashi ta fice daga ɗakin a hankali ta shiga ɗakin Hajiya Babba ta buɗe press ɗinta, kasancewar tana ajiye kayanta a ɗakin ya sanya ta ɗauko wasu riga da wando na bacci ta mayar ta rufe sannan ta fice da sauri. Ɗakin ta koma ta cire Abayar jikinta ta shiga toilet ta watsa ruwa sannan ta fito ta sanya kayan, ta naɗe Abayar da mayafin ta tura ƙasan gadon sannan ta hau kan gadon ta kwanta har da jan duvet ta rufa.. Bata ƙarasa gida ba ta haɗu da Juwaira hannunta riƙe da warmer, kallonta ta yi sai kuma ta ce“Hajiya zaki kai wa?” gyaɗa mata kai ta yi, ta yi saurin karɓa tana faɗin “bari na kai mata” murmushi Juwaira ta yi dan daman ba son zuwa take ba ta ce“yauwa Yaya, nagode miki daman kallo nake” daga haka ta juya ta nufi hanyar gida, taɓe baki Maimoon ta yi sannan ita ma ta juyo ta nufo gidan Hajiya Babba. Koda ta dawo zaune ta sameta tana cin abincin har sannan ta ajiye warmer sannan ta ce“ba zaki jira a dinga kawo miki abinci ba sai ki dinga ci ko?” murmushi ta yi ta ce“to ai duk ina ci idan aka kawo min ɗin, yanzu wannan gobe da safe shi zanci” “ɗumamen abinci zaki ci?” jinjina kai Hajiya ta yi ta ce“eh” Maimoon tana faɗin “tab ni ba zan iya ba” ganin ta nufi sama ya sanya ta ce“ina kuma zaki je?” zata bata amsa kenan sai ga Abba ya shigo shi da Abdusammad, Maimoon ta kallesu jiki a sanyaye ta ce“Abba an ganta?” girgiza mata kai ya yi yana ƙoƙarin zama kan sofa ya ce“a'a Maimunatu” kamar zata yi kuka ta ce“allah sarki, Allah yasa ba ɓata tayi ba” kallonsu Hajiya ta dinga yi sai kuma ta ce“wane ba'a gani ba?” furzar da numfashi ya yi daga bakinsa kafin ya ce“Nana ce!” da sauri ta miƙe tsaye tana kallonsa ta ce“Nana kuma? Yaushe? Kuma a ina?” Hajiya Babba ta jera masa tambayar da tashin hankali sosai akan fuskarta. Abdusammad ne ya ce“Ki zauna Hajiya sai a miki bayani” jiki a sanyaye ta koma ta zauna ta zuba musu idanu tana kallonsu. Tana hawa saman ta buɗe ɗakin ta shiga, kwance ta hangeta dan haka ta ƙarasa ta taɓa ta ta ce“ke Nana tashi” buɗe idanunta ta yi sai kuma ta tashi zaune tana kallonta ta ce“mene ne?” “yanzu zan sauka nace na gan ki, gasu Abba nan a ƙasa” jinjina kanta ta yi sai kuma ta ce“zazzaɓi nake ji Maimoon” hannunta ta kai wuyanta ta ji zafi sosai ta ce“sannu daman baki da lafiya?” lumshe idanu ta yi ta buɗe sannan ta ce“a'a yanzu kawai naji zazzaɓin” sannu kawai ta ce sannan ta mike ta ce“bari naje kar ace a na daɗe” daga haka ta fice daga ɗakin. Da gudu ta sakko ƙasa tana fadin “Abba! Abba! Abba!” tsaye ta same shi yana kallonta ya ce“lafiya dai Maimuna?” sama ta dinga nuna masa da hannunta kafin ta ce“Nana! Nana tana sama daman” da wani irin mamaki suka dinga kallonta, Abba ya yi gaba ya haura saman da sauri, ɗakin Hajiya ya buɗe yaga bata ciki, ya sake buɗe ɗayan, turus ya yi a wajen yana kallonta ganin yanda ta juya baya, a sanyaye kuma yace “Nana!” Da sauri ta juyo ta kalleshi, ya ƙarasa ciki yana kallonta ya ce“yaushe ki ka zo nan? Me yasa baki je gida ba?” muryarta a sanyaye ta ce“Abba banida lafiya, tun safe nake nan kuma na kasa tashi” ta ƙare maganar hawaye na zubowa kan fuskarta, Hannunsa ya kai wuyanta ya ji zafi sosai ya janye hannun dai dai sanda Hajiya Babba da Abdusammad suka shigo ya riƙe hannunta ya ce“sannu to, taso” miƙewa ta yi ta jingina da jikinsa tana lumshe idanu, Hajiya ce ta ƙaraso gabanta ta riƙeta tana faɗin “ke daman kina nan? Me ya sa baki sakko ba? Baki da lafiya?” “wai ashe bata da lafiya ne, ta zo ta kwanta kuma bata tashi ba, bari muje a dubata” Hajiya Babba ta ce“koda naji, sannu kin ji takwara” gyaɗa mata kai kawai Nana tayi, Abdusammad dake tsaye jikin ƙofa ya harɗe hannayensa a ƙirji ya ce“kawai bari na tafi da ita Abba sai na dubata zuwa an jima na dawo da ita” Girgiza kai Abba ya yi ya ce“a'a Abdusammad, ka gaji dayawa tun ɗazu ka ke wahala kawai na kira likita a waje ya dubata” murmushi ya yi ya ce“babu komai Abba” daga haka ya ƙaraso wajen, hannunta ya riƙe suka fito daga ɗakin, Maimoon ta sauke ɓoyyayiyar ajiyar zuciya tana dafe ƙirji. Sai da suka fito Abba ya nufi apartment ɗinsa dan sanar da Amma sannan ya saki hannunta ya ce“muje ko” babu musu ta fara tafiya a hankali har suka ƙarasa gidansa, A parlon suka sami Zahra da Noor tana ganinsu ta miƙe tsaye tana faɗin “Alhamdulilah, a ina aka ganta? Nana ina ki ka je?” kafin ta yi magana ya riga ta ya ce“wai tana kwance ɗakin Hajiya ne tun safe bata da lafiya” girgiza kai Zahra ta yi ta ce“ayyah sorry kin yi, sannu Nana” gyada mata kai kawai ta yi, bai sake cewa komai ba ya ja hannunta suka bar wajen. Ɗakinsa suka shiga, ya mayar da ƙofar ya rufe da key sannan ya jingina da jikin ƙofar yana kallon bayanta ya ce“keee!” a ɗan tsorace ta juyo saboda yanda taji ya kira sunan nata, ya dinga kallonta sai kuma ya ƙaraso wajen yana tafiya cike da izza, in a very calm voice ya ce“ina ki ka je?” da ɗan mamaki ta dinga kallonsa, ya yinda ƙirjinta ke wani irin bugu na tsananin tsoro da fargaba, cikin rawar murya ta ce “Bab..bba..babu inda naje, ina Apartment ɗin Hajiya tun safe kuma...” Cak maganar ta tsaya saboda zazzafan marin daya sauke mata a fuska, ta runtse idanunta tana jin kamar idanunta sun makance, nan da nan fuskarta ta yi wani irin jaa, cikin zafin nama ya fizgota ta faɗo jikinsa, ya sanya hannunsa na dama ya riƙe gashin kanta da kyau cikin tsananin ɓacin rai da kakkausar murya ya ce“ina ki ka je nace!?” Azaba da tashin hankali su ne suka hanata bashi amsa, ya hankaɗata ta tafi ta faɗi kan tiles, ta saƙi ƙara saboda azabar data mata yawa, belt ɗin da ke ajiye gefen drawer ya ɗauko ya shiga naɗeshi a hannunsa yana kallonta ya ce“sai kin faɗa min in da ki ka je tabbas!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Follow my account, Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 19... Ganin da gaske dukanta yake shirin yi ya sanya ta buɗe baki cikin shessheƙar kuka ta ce“dan Allah uncle ka yi hakuri, wallahi babu inda naje” ko rufe baki bata yi ba taji saukar belt a bayanta, ta dafa wajen tana wani ƙandarewa cikin tsananin azaba, ya durƙusa dai dai tsayinta ya riƙe kanta yana kallonta yana huci ya ce“ina ki ka je? And wane wanda ya sauke ki” kasa basu amsa ta yi sai jan numfashi take tana dafe ƙirji, ya saketa sannan ya yi kwafa, wurgi ya yi da belt ɗin sannan ya ce“bari naje na kira Abban sai ki fadi in da ki ka je a gabansa” daga haka ya juya zai bar ɗakin, cikin zafin nama ta tashi da gudu ta ƙarasa inda yake ta riƙe ƙafafunsa tana kuka ta ce“dan Allah uncle kada ka faɗa masa, wallahi dukana zai yi, dan Allah ka yi haƙuri” cak ya tsaya amma bai juyo ba, ta ɗora fuskarta jikin ƙafarsa ta dinga rera wani irin marayan kuka. Juyowa ya yi ya kama hannunta har gaban gado sannan ya zaunar da ita ya ɗan durƙusa dai dai fuskarta ya ce“shikenan ba zan faɗa masa ba, faɗa min ina ki ka je? Me ya sa ki ka yi ƙarya? Yaushe ki ka koyi ƙarya Nana?” yanda ya yi tambayar ya sanya jikinta ya sake sanyi, ta sunkuyar da kanta bakinta na rawa ta ce“dan Allah ka yi haƙuri, wallahi gidan su ƙawata naje, kuma na san idan na faɗawa Amma ba zata bar ni ba shiyasa...” Kasa ci gabawa ta yi ganin irin kallon da yake mata, ko bai faɗa ba ta san ya gane ƙarya take faɗa masa, dan haka ta cigaba da hawayenta. Numfasawa ya yi kafin ya tallafi fuskarta da hannunsa ya ce“ba zaki daina min ƙarya ba ko? Ni ki ke tunanin za ki yiwa ƙarya ban gane ba Nana? Kina cikin hankalinki kuwa?” Girgiza kanta ta dinga yi sai kuma ta sanya hannunta na hagu ta goge hawayen sannan ta ce“ka yi haƙuri” sakinta ya yi ya koma gefenta ya zauna sannan ya ce“tell me ina ki ka je?” Shiru ta yi tana tunanin abin da zata ce masa wanda zai yarda da ita, dan ko karen hauka ne ya cijeta ba zata taɓa faɗa masa gaskiya ba, dan haka ta shiga tunanin irin ƙaryar da zata masa. Gyaran muryar da ya yi ne ya dawo da ita daga tunanin da take, without looking at her ya ce“ina jin ki” wasa ta fara yi da fingers ɗinta cikin shessheƙar kuka ta ce“makarantar mu naje” kallonta kawai ya yi da neman ƙarin bayani, dan haka ta ci gaba da faɗin “Daman ƙawata ce ta ce min an fara bada admission a Aun University, to shi ne nace zan je na tambaya yanda ake yi, kuma nasan idan na faɗawa Amma ba zata barni ba, cewa zasu yi ba zamu ci gaba da karatu ba, shiyasa..” ta ƙasa ƙarasa maganar saboda kukan daya tawo mata, kallonta kawai yake ba tare da ya ce komai ba, ganin ya yi shiru ya sanya ta ɗago ta ɗan kalleshi sai kuma ta sake sauke idanun ƙirjinta na bugawa da sauri. “To me ya sa ki ka kai dare? Sannan wane wanda ya ajiye ki a bakin gate?” Kamar daga sama haka taji tambayar tasa, ta ɗan yi shiru kafin ta ce“da naje ne aka ce sai na jira saboda basa nan, shi ne na dinga jira har yamma sannan aka ce min ba zasu zo ba ranar, to bayan na fito kuma babu kudi a hannuna sai nafara tawowa a ƙafa sai bayan magrib sannan na haɗu da wannan mutumin yaga ina kuka shi ne ya ce mene ne na faɗa masa shi ne ya ce bari ya kawo ni gida” Ta ƙare maganar cikin sanyin murya tana mai fatan samun yardarsa. Jinjina kansa ya yi sannan ya ce“saboda haka yasa ki ka yanke shawarar ki yi ƙarya a gida? Bayan kin ɗagawa kowa hankali? Kin san me kuwa babu inda ban saka an duba ba amma ba'a same ki ba, amma kina tunanin zan yarda dan ance kina ɗakin Hajiya” ya ɗan yi murmushi sannan ya ci gaba da faɗin “kina tunanin har kin yi girman da zaki dinga yin ƙarya ko? Har kin san mene rayuwa ko?” girgiza hannunta tayi ta ce“a'a wallahi uncle, ka yi hakuri ba zan sake ba dan Allah” tashi ya yi yana furzar da numfashi kafin ya ce“duk ranar da ki ka sake fita ba'a sani ba sai ran ki ya ɓaci fiye da tunanin ki Nana, I'll show you the other side of me, so take care” daga haka ya nufi hanyar waje da sauri, da idanu ta bishi har ya rufe ƙofar sannan ta sauke ajiyar zuciya tana dafe ƙirji, muryarta na rawa ta ce “Allah astagfirullah, Allah ka yafe min” Sai kuma ta kai hannunta kan fuskarta, wani irin raɗaɗi taji wanda ya sanya ta runtse ido a fili ta ce“wayyo” sannan ta tashi da sauri ta ƙarasa jikin madubi, kallon gefen fuskar ta ta dinga yi ganin yanda ya yi jajur dashi ya ɗan kumbura, ta tura baki sai kuma ta ce“kuma sai ya dakeni” ta ƙare maganar a shagwaɓe, buɗe dakin aka yi ya shigo ta juya da sauri ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta, taɓe baki ya yi sai kuma ya ce“zo ki tafi” kamar zata yi kuka ta ce“uncle kaga fuskata” ta yi maganar tana nuna masa gefen daya maretan, haɗe rai ya yi ya ce“to sai aka yi Ya ya?” “zafi yake min” ta ce a shagwaɓe, kamar ba zai magana ba sai kuma ya yi alamar ta zo da hannunsa, ta ƙarasa a hankali ta sunkuyar da kanta, tallafo fuskarta ya yi da hannunsa ya dinga kallon wajen ganin yanda ya yi jajur, hannunsa ya kai ya matsa gurin, ai ko kamar jira take ta fashe da kuka tana yarfe a hannu, haɗe rai ya yi yana kallonta ya ce“Quiet” shiru ta yi tana hawaye, ya ja hannunta suka fita daga ɗakin. A parlon ya samu Zahra zaune tana jiransu, ta miƙe ganin sun ƙaraso ta ce“sannu Nana ya jikin?” a sanyaye ta ce“da sauƙi Aunty Zahra” daga haka ya nufi hanyar waje da sauri. Har Apartment ɗin su ya rakata sai da ta kai balcony sannan ya ce“kin ji abin da nace miki ko?” gyaɗa masa kai ta yi a hankali, ya juya ya bar wajen sannan ita ma ta juya, tan ƙoƙarin knocking ƙofar parlon taji an ce “Nana” A hankali ta juyo tana kallonsa sai kuma ta ce“Yaya Sultan” Ƙarasowa wajen ya yi yana tafe a hankali hannunsa zube cikin aljihun trouser ɗin da ke jikinsa, ya tsaya a jikin balcony ɗin yana kallonta ya ce“daga ina ki ke?” kamar mara son magana ta ce“daga wajen uncle nake, shi ne ya rakoni yanzu” Sultan ya bi inda ta kalla ɗin dan har sannan ana gano Abdusammad ɗin, sai kuma ya mai da idanunsa kanta ya ce“yanzu kin zama yar gidan uncle ko?” ɗan murmushi ta yi ta ce“a'a fa yau a gidan Hajiya Babba na yini da daddare naje wajensa” jin jina kai ya yi sai kuma ya ce“nagane, to je ki gida dare ya yi” Toh kawai ta ce sannan ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shige ciki. Sultan ya ɗan jima a wajen yana tunani kafin daga bisani ya juya ya ci gaba da tafiya, koda ta shiga parlon bata sami kowa ba dan haka ta nufi daƙinta kai tsaye, bata fi 2mins da shiga ba Amma ta buɗe ɗakin ta shigo tana kallonta a fusace ta ce“ wani sabon rashin hankalin ki ka fito dashi na fita baki sanar ba? Dan baki da lafiya shi ne yake nufin ki je ki yini a can? Ba zaki iya dawowa gida ba? Kin fi so ki ɗaga min hankali ki hanani sukunin rayuwa?” Shiru Nana ta yi tana sauraren faɗan Amman dan daman ta san sai ta yi mata, ganin yanda ta yi tsaye bata ce komai a ya sake fusatata dan haka ta ce“wato ga mahaukaciya na magana ko? Shi yasa kina ji ki ka min banza!” girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce“dan Allah Amma ki yi haƙuri, ba zan sake ba” “Ai daman kin iya bada haƙuri, tun da kina da baki, to ki ci gaba kar ki fasa ja min magana Nana! Ki ci gaba idan ma so ki ke jinina ya hau saboda ke ɗaya to ki yi, kar ki fasa!” ta juya ta fice daga ɗakin tana buga ƙofa, ita dai Nana da idanu kawai ta bita sai kuma ta ƙarasa gefen gadonta ta zauna tana sauke numfashi. Around 9pm ta fito daga ɗakin dalilin wata irin matsananciyar yunwa da taji, dan kwara kwata yau bata ci abinci ba, ta ƙarasa parlon tana kallon Amma da ke zaune tana kallon wani Film da ake haskawa a Arewa24, zama ta yi gefenta ta jingina kanta da jikinta kamar zata yi kuka ta ce“Amma yunwa nake ji, yau ban ci abinci ba” zafin da taji a jikinta shi ne ya sanya ta ɗago tana kallonta, sai kuma ta kai hannunta wuyanta tana faɗin “zazzaɓi ki ke?” gyada mata kai kawai ta yi, Amma ta ce“kin sha magani?” a sanyaye ta ce“eh uncle ya bani” tashi kawai Amma ta yi ta nufi kitchen da sauri, ita kuma ta kwanta akan kujerar tana lumshe idanunta. After 5mins ta dawo hannunta riƙe da plate mai ɗauke da farar shinkafa da miya wadda taji naman kasuwa, ta ajiye akan table ɗin sai kuma ta ƙarasa wajen freezer ta dauko mata ruwan roba da lemo ta ajiye suma sannan ta kalleta ganin yanda ta rufe idanunta ta ce“tashi ki ci abincin” a hankali ta buɗe idanun nata sai kuma ta tashi zaune ta jingina da fuskar kujerar tana sauke numfashi. Amma ta zauna gefenta sannan ta miƙa mata plate ɗin abincin ta ce“ci” kamar zata yi kuka ta ce“Amma ki bani a baki ba zan iya ci ba” kallonta kawai Amma ta yi sai kuma ta ɗauki spoon ta ɗiba abincin ta kai bakinta, buɗe bakin ta yi Amma ta yi mata bismillah sannan ta fara bata, ta dinga lumshe idanunta saboda daɗin da shinkafar ta yi mata. Sai da ta cinye tas sannan ta ɗauki ruwan tasha, Amma ta kalleta ta ce“ko na da ɗa miki?” girgiza kanta ta yi ta ce“na ƙoshi, bacci nake ji” ta yi maganar kamar za ta yi kuka, jinjina kai Amma ta yi ta ce“to tashi ki ke ki kwanta” gyaɗa kanta kawai ta yi sannan ta tashi ta bar wajen, koda ta shiga ɗakin kan gado kawai ta faɗa ta yi kwanciyarta dan a gajiye take sosai dan haka yasa nan da nan bacci ya ɗauketa. **** Washegari around 6:00 na yamma Zahra ta sakko ƙasan hannunta riƙe da wata babbar leda tana kallon Siyama ta ce”gashi ki kai mata, ki ce size ɗin idan bai mata ba sai ta bayar a rage” to kawai Siyama ta ce sannan ta karɓi ledar ta ce“na tafi” “ki gaida gida, ki cewa Umma wai Noor ta ce zata zo ta mata kwana biyu kafin mu shige” murmushi Siyama ta yi ta ce“to shikenan ko da mun tafi tare ai” Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“a'a dai ki fara sanar da ita” to ta ce sannan ta nufi hanyar fita daga parlon ita kuma Zahra ta zauna kan sofa tana jawo wayarta. Tafiya ta dinga yi cikin estate ɗin tana kalle-kalle, ko ina gwanin ban sha'awa, in dai maganar kyau da tsari ne to M-Shuwa Estate na kan gaba, ta lumshe idanunta a fili ta ce“nan bada jimawa ba nima zan shigo cikin wannan duniyar, ya ilahi can't wait” ta ƙare maganar tana wani irin murmushi. Tun daga nesa take kallonsa cike da farin ciki, murya can ƙasa ta ce“yauwa daman an ce zan gan ka” daga haka ta ci gaba da tafiyar ta tana kallon wani wajen daban, ganin sun kusa dab da dab ya sanya ta ɗan matsa gefe ta yanda zasu haɗu, sai da taga ɗan taƙin da ke tsakanin su bai fi ta mutum ɗaya ba sannan ta gurɗe hills ɗin ƙafafunta da gangan ai kuwa ta faɗi ƙasa tare da ledar kayan. Da sauri Safwan ya kalli wajen jin faduwar abu, ganin mace ce ya sanya ya ƙarasa da sauri yana kallonta cikin sanyin muryarsa ya ce“subhanallahi sannu” ɗagowa ta yi tana masa wani irin kallon ƙurilla kafin ta ce“yauwa thanks” daga haka ta shiga kwashe abayoyin da suka faɗo, tsugunawa ya yi ya tayata kwashewa ya zuba cikin ledar ba tare da ya kalleta ba ya ce“ki dinga tafiya a hankali” jinjina kanta ta yi fuskarta ɗauke da murmushi ta ce“tom in sha Allah nagode sosai” daga haka ta miƙe tana kaɗe jikinta, jinjina kansa ya yi sannan ya yi gaba abin sa. Ta dinga bin bayansa da kallo tana jin wani irin sanyi a ranta sai kuma ta yi murmushi a fili ta ce “wow wannan shi ne haɗuwar” ta yi dariya mara sauti sannan ta zaro wayarta daga jaka, numbern Mom ɗinta ta yi dialing dan ba zata iya jira sai ta koma gida ba, ringing ɗaya ta ɗauka daga ɓangarenta ta ce“Siyama ba zaki dawo ba ne jiran ki fa nake masu kayan sun zo” murmushi ta yi ta ce“Mom Albishirinki?” Aunty Khadijah ta ce“goro mene ne?” “Na haɗu dashi” Da sauri ta tashi daga zaunen da take ta ce“haba da sauri haka? Daman malam ya ce zaku haɗu, yanzu ya ku ka yi?” Siyama ta lumshe idanunta kafin ta ce“ya tafi ma, yanzu nima zan dawo, sai mu san me zamu yi nan gaba” Aunty Khadijah ta jin jina kanta ta ce“haka ne kuma ki yi sauri ki dawo ina jiran ki, bari na kira Baturiya na sanar mata, daman na san aikin wannan malamin ba dai kyau ba” toh kawai Siyama ta ce sannan ta kashe wayar ta numfasa sannan ta ci gaba da tafiya.. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH🌹* Follow my account, Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 20... Bayan kwana biyu wajejen ƙarfe 9:00 na safe Zahra ta fito daga ɗakinta hannunta riƙe da waya, sai da ta rufe ƙofar sannan ta kai wayar kunne cikin sanyin murya ta ce“dan girman Allah Aunty ki rufa min asiri, so ki ke aurena ya mutu ne?” daga ɗaya ɓangaren Aunty Khadijah da ke zaune kusa da wata ƙawarta ta ce“kamarya aurenki ya mutu? Saboda kin ce wa mijin ki ga yarinya a bawa ƙaninsa sai aurenki ya mutu?” Zahra ta girgiza kanta kamar zata yi kuka ta ce“baki gane ba, wai ya za'a yi na cewa Doctor ga mata ya bawa Safwan? Bayan nasan basa haka, kuma ma bama wannan ba Safwan fa an riga da an yi maganar aurensa, yanzu ma maganar da nake miki sauran sati uku bikin wallahi tallahi, to kin ga idan na bijiro da wannan maganar ai kamar ban yi daidai ba” taɓe baki Aunty Khadijah ta yi a ɗan fusace ta ce“kin ga shikenan bana buƙatar taimakonki zan yi da kaina, kuma idan ma baƙin ciki ki ke kada Siyama ta shigo ta ci irin arzikin da ki ke ci to wallahi sai dai ki mutu” Zahra ta buɗe bakinta tana jin jin karfin hali irin na Aunty Khadijahn, jin bata sake magana ba yasa ta ɗan kwantar da murya ta ce“ni fa Aunty ba haka nake nufi ba, kin ga...” Tsaki ta yi sai kuma ta kashe wayarta, Zahra ta mai da wayar hannunta ta dinga kallon screen ɗin da mamaki, can kuma ta numfasa sannan ta koma ciki. Can ɓangaren Aunty Khadijah ta kalli ƙawar tata mai suna Kaddu ta ce“kin ji baƙin halin ko? Kin dai ji abin da ta ce da kunnenki, ai wallahi ba zata taɓa yarda ta haɗa su ba! Wannan mai baƙin halin” Kaddu take zaune ta hakimce akan kujera ta ce“na ji kuwa, amma ki kwantar da hankalin ki, wallahi sai ya auri Siyama, haba sai ka ce ba yar mu ba ce” Aunty Khadijah ta dinga kallonta can kuma ta ce“to ai kin ga yaron ne kamar akwai tsari a jikinsa, ki ga fa duk irin aikin wannan malamin amma ya kasa tasiri akan sa” tsaki Kaddu ta yi tana watsa hannu ta ce“dallah bar maganar wannan malamin, wake ta irin waɗannan? Ai wannan daman ba aikin malami ba ne, ni na san inda zamu je wallahi ko a gobe ki ke son ya auri Siyama sai ya aureta, me kuma aka yi aka yi shi?” Gyara zama Aunty Khadijah ta yi tana murmushi ta ce“ke ƙawata taɓani da alkhairi, wai da gaske ki ke dan Allah? Ina ne?” wani shu'umin murmushi ta yi kafin ta ce“ke dai ki bari zamu je ki gani da idon ki” Aunty Khadijah ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta ce“har naji sanyi a raina wallahi, kai wannan abu” Kaddu ta yi murmushi sai kuma suka ci gaba da wata hirar. **** Ranar Saturday misalin ƙarfe 4:20 na yamma ta fito daga ɗakin tana gyara zaman jakar hannunta a kafaɗarta, Amma da ke ajiye drinks a freezer ta ɗan kalleta sai kuma ta ce“kin shirya?” gyaɗa mata kai ta yi bakinta ɗauke da murmushi ta ce“eh Amma, yanzu zan tafi” sai da ta rufe freezern sannan ta mai da Idanunta kanta sosai tana kallonta, wata doguwar rigar material up white ce a jikinta mai zanen flowers manya-manya, ɗinkin boubou wadda bata kama jikinta ba, sai ta yi rolling jersey veil baƙi, babu kwalliya a fuskarta amma ta yi tas da ita sai sheƙi take. Amma ta ce“driver ne zai kai ki?” jinjina kanta ta yi kafin ta ce“eh ai Maimoon ma ta ce zata je, wai perfume ɗinta ya ƙare” Toh kawai Amma ta ce sai kuma ta nufi hanyar daƙinta, da idanu Nana ta bita har ta shiga sannan ta ɗauke kanta, bayan minti biyu ta fito hannunta riƙe da Atm card ta tana miƙa mata, amsa Nana ta yi sai kuma ta ce“yauwa Ammata” “sauran ki tsaya siyan banza da hofi” murmushi ta yi ta ce“ba zan siya ba, kawai dai chocolate zan ɗauka” ta ƙare maganar tana langwaɓar da kai, taɓe baki Amma ta yi ta ce“shige kuma kar ku daɗe” to kawai ta ce sannan ta waje da sauri. Tana sauka daga balcony ta hango Maimoon tana tawowa, sanye take da Abaya Egyptian ruwan ƙasa, ta yi rolling mayafin akanta, ta ƙaraso gabanta tana murmushi wanda ke ƙara mata kyau, “ai na ɗauka sai na yi jiranki” Ta yi maganar tana kallon Nana, harararta Nana ta yi ta ce“a'a abin da ya fi jirana zaki yi, ni muje” murmushi kawai Maimoon ta yi sannan suka riƙe hannun juna gwanin sha'awa suka nufi parking lot ɗin gidan. Sun yi nisa Maimoon ta ɗan kalleta cike da zolaya ta ce“wai ina sir Junaid kuwa?” taɓe baki Nana tayi ta ce“ni na daina kula shi, kina ganin saboda shi rannan uncle ya dakeni” tuntsirewa da dariya Maimoon ta yi dai dai sanda motar ta yi kwana ta ce“au wai daman wajensa ki ka je?” kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“ba fa wajensa naje ba, bashi da lafiya ne sai abokinsa ya kirani ya faɗa min shi ne naje duba shi” Maimoon ta gyaɗa kanta kafin ta ce“kuma shi ne ki ka kai dare?” ɗan siririn tsaki ta yi ta ce“ke baccine ya kwashe ni, daren ranar ne ban yi bacci ba, kuma da wuri na tashi na fita shi ne da naje bacci ya ɗaukeni” Maimoon ta dinga dariya sai kuma ta ce“eh lallai Ashababba a asibitin ki ka hau bacci?” gyaɗa mata kai Nana ta yi, ta ci gaba da dariyarta, haɗe rai ta yi ta ce“ni ki daina min dariya ke kuma” kallonta ta yi sai kuma ta rufe bakinta da hannunta saboda wata dariyar da ta tawo mata. Nana ta harareta ta ce“banza kawai” ta ƙare maganar tana kallon titi. Har suka ƙarasa supermarket ɗin babu wanda ya sake cewa komai, bayan driver ya yi parking suka fito suka nufi cikin mall ɗin. Banda turaruka da maya-mayai babu wani abu mai amfani da suka siya, sai tarkacen kayan zaki chocolate da biscuits, sai ƙarfe 6:00 sannan suka fito daga cikin mall ɗin, kai tsaye kuma in da drivern su yake suka nufa, suna cikin tafiya kamar daga sama suka ji ya kira sunanta, Cak Nana ta tsaya amma bata juyo ba, ya ƙaraso gabanta hannayensa zube cikin aljihu, kallonsu ya dinga yi duka kafin ya yi murmushi yana kallon maimoon ya ce“hii Moon” ɗan durƙusawa ta yi ta ce”afternoon sir” ya jinjina kansa sannan ya mai da kallonsa ga Nana wadda ta yi shiru ya ce“Nana me nayi miki da zafi haka ki ka daina ɗaga kirana? Uhm, meyasa? Ko na yi wani laifi ne” ya ƙare maganar yana murmushi. Wata uwar harara ta watsa masa sannan ta ce“saboda banida buƙatar kiran naka, bana son kana kirana, dan Allah kar ka sake ƙoƙarin neman yin magana dani, ka barni na yiwa iyayena biyayya” ta ƙare maganar tana haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo, da wani irin mamaki Junaid ya dinga kallonta, duk zatonsa wasa take dan haka yayi murmushi ya ce“haba Nanata, duk cikin fushin nan? Rannan Abba ya bugeki ne? Ki yi hakuri kin ji” wani irin kallo ta dinga masa sai kuma ta yi tsaki ta kama hannun Maimoon dake tsaye kamar an dasata ta ce“muje dan Allah” daga haka suka yi gaba, da sauri shima ya sake biyo su ya sha gabansu yana kallonta ya ce “wait Nana me ki ke nufi ne? Ban gane inda ki ka dosa ba? Wane ya sauya miki ra'ayi?” sakin hannun Maimoon ta yi a fusace ta ce“baka gane me nake nufi ba? Hala baka ji abin da na ce ba, to bari na maimaita maka, ni Nana na rabu da kai rabuwa ta har abada, ba dan na daina sonka ba sai dan ba zan iya bijirewa iyayena saboda kai ba! Dan haka kaje na nemi wata nima zan zauna da wanda Allah ya zaɓa min, Allah ya baka wadda ta fini” Tamkar zararre haka Junaid ya dinga kallonta, nan da nan kammaninsa ya sauya, idanunsa suka circiko da hawaye ya shiga girgiza kansa yana faɗin“a'a Nana, wallahi ba ke ba ce, ba zaki taɓa yanke wannan hukuncin ba, ni na san ba haka bane, ƙarya ki ke Nana! Ƙarya ki ke ki ce zaki iya rabuwa dani! Wallahi ba zai taɓa yiwuwa ba!” shiru ya yi yana kallonta ganin yanda ta haɗe rai, ya mai da idanunsa kan Maimoon muryarsa na rawa ya ce“yauwa Maimuna ki faɗa mata ta daina cewa haka dan Allah, ki faɗa min wane ya sauyata? Me ya sa zata min haka?” kallonsa ta dinga yi cike da tausayawa, Nana ta ja tsaki sai kuma ta yi gaba fuuu ta bar wajen, da idanu ya bita sai kuma ya kalli Maimoon kafin ya yi magana ta ce“ka yi hakuri dan Allah, ka bar ta haka, tun da har ta haƙura mu ma haka muke fata, dan Allah kada ka sake nemanta koda a waya ne, ka manta da Naana!” ta ƙare maganar a sanyaye sai kuma ta ratsa ta gefensa ta yi gaba itama. Junaid ya juya yana kallonsu har suka shige mota suka bar wajen, ya durƙushe a wajen yana rike saitin zuciyarsa saboda wani irin bugawa da ta yi. Basu daɗe da hawa babban titi ba Maimoon ta ɗan kalleta ganin yanda take sharar hawaye tun ɗazu ta ce“amma Nana me ya sa ki ka yi haka? Da gaske kin haƙura dashi? Ko kuma haushi ya baki?” kallonta ta yi sai kuma ta ɗauke kanta cikin shassheƙar kuka ta ce“wallahi na haƙura dashi, na haƙura da sir Junaid, zan zauna da Yaya Safwan koda hakan na nufin mutuwata, ba zan bawa Abba da Amma kunya ba, ba zan bari su yi dana sanin haihuwata ba, ba zan bar su ba!” ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka, matsawa kusa da ita Maimoon ta yi ta dafata kamar jira take ta faɗa jikinta tana ci gaba da kuka, shafa bayanta ta dinga yi a hankali tana sauke numfashi. Driver na ƙarasa parking suka buɗe motar suka fito, Maimoon ce ta ɗebo kayan nasu duka tana kallon Nana da ke goge hawayenta ta ce“kar ki bari a gane kin yi kuka dan Allah” gyaɗa mata kai ta yi har sannan bata bar sauke ajiyar zuciya ba, suka jera suka fara tafiya babu wanda ya ce komai. Siyama ta dinga kallonsu har suka matso dab da ita, Nana ta ɗan kalleta sai kuma ta ɗauke idanu dan ta ganeta, murmushi ta sakar musu bayan ta tsaya wanda suma ya sanya dole suka tsaya ta ce“sannunku” Maimoon ce kawai ta amsa dan ita Nana ko kallonta bata yi ba, bata damu da rashin amsawar ta ta ba ta ce“yauwa daman na zo wajen Aunty Zahra ne to amma ban ganta ba, shi ne nake tambaya ko kun san inda take” girgiza kai Maimoon ta yi ta ce“ayyah wallahi bamu sani ba, mu ma kin ga dawowar mu kenan” jinjina kai Siyama ta yi, suna shirin tafiya ta sake cewa“au afuwan dan Allah D Safwan fa?” Ganin irin kallon da suke mata ba tare da sun bata amsa ba ya sanya ta ɗan yi murmushi tana basarwa ta ce“daman zan ɗan amshi saƙo ne a hannunsa” jinjina kai Maimoon ta yi kafin ta ce“eh Yaya Safwan yanzu ya dawo daga office na san, maybe yana apartment ɗin Hajiya Babba, tun da ba'a fara kiran sallah ba, yana ma can” ta ƙare maganar tana bata tabbacin inda yake, faɗaɗa murmushinta ta yi ta ce“okay na gode sosai bari naje can ɗin” to kawai Maimoon ta ce sannan ta bi bayan Nana wadda ta yi gaba abin ta, Siyama ta juya ta sake bin su da kallo sai kuma ta yi murmushi a fili ta ce“nan gaba kaɗan zaku fara girmamani” ta ɗan yi dariya sai kuma ta bar wajen, Maimoon ta dinga kallon Nana sanda ta tsaya a balcony nasu kafin ta ce“wai me ya sa baki bata amsa ba?” taɓe baki ta yi ta ce“ke ni bata min ba wallahi, rannan na gansu a Apartment ɗin Aunty Zahra, kawai na tsaneta” murmushi Maimoon ta yi tana miƙa mata tata ledar ta ce“ji min baƙin hali kawai sai ki tsaneta, to Allah ya kyauta miki” karɓa Nana ta yi ta ce“ki gaida gida” okay kawai ta ce sannan ta nufi nasu gidan, ita kuma ta juya ta murɗa handle ɗin ƙofarsu. **** Zaune suke cikin ɗaya daga cikin sorayen gidan guda biyar, wanda kuma shi ne ya kasance na huɗu a lissafi, gabansu wani mutum ne ya durƙusar da kansa yana dube-dube, wuyansa rataye da ƙaton carbi irin mai dubun nan, Mutumin ya yi gyaran murya ya ɗago mummunar fuskarsa irin ta gardawan tsangaya ya kallesu, Kaddu dake zaune kusa da Auntt Khadijah ta ce“Malam ya ake ciki?” atishawa ya yi kafin ya ce“wannan aikin naku zai yiwu, amma domin samun biyan buƙata dole ana da buƙatar juyar da tunaninta” Kaddu ta ce“wace Malam?” sai da ya sake wata atishawar sannan ya ce“ita yarinyar, dole ne a juyar da tunaninta ta dawo ɓangaren ku, dole ne ta sanya baki cikin maganar auren, domin ta haka ne za'a iya jawo hankalin sa har ya fara sonta” Aunty Khadijah dake saurarensa tun ɗazu ta ɗan zaro idanu kafin ta ce“wai kana nufin Zahra za'a juyarwa da tunani?” gyaɗa mata kai ya yi, ta ɗan girgiza kanta ta ce“a'a Malam idan kuma ba'a yi nasara ba fa?” tuntsirewa ya yi da dariya sai kuma ya ce“da baki yarda da aikin namu bane? To idan har ki ka ga an samu matsala sai dai inda ba yanda na ce ku yi ba ku ka yi, dole ne a sauya tunaninta, ta dawo bayanku ta shiga cikin maganar auren, daga nan sai ta jawo hankalin yaron ta hanyar abubuwan da zamu dinga yi, shi kuma a gefe ɗaya zamu yi aiki a kansa, daga nan komai zai zo da sauki zai auri yar ki ya dawo yi miki biyayya kamar ke ce uwar da ki ka haifesa!”. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 21... Aunty Khadijah ta dinga murmushi ba tare da ta ce komai, Kaddu ce ta kalleshi ta ce“tom malam yanzu nawa za'a bada?” girgiza kansa ya yi sai kuma ya ce“a'a ba zan karɓi komai daga hannunku ba, amma nima ina da abin da za'a yi min kamar yanda ki ka sani” Kaddu ta jinjina kanta dan daman ta san da hakan, lokaci ɗaya ta juya tana kallon Aunty Khadijah da ke kallonsu a hankali ta ce“muje ki ji” okay kawai Aunty Khadijah ta ce sannan suka miƙe a tare suka nufi ɗaya soron. Wani irin kallo ta dinga yi mata kafin a ɗan fusace ta ce“Haba Kaddu ya ma za'a yi na yarda da wannan ƙazamin mutumin? Ta ina? Gaskiya ba zan iya ba, idan yana son kuɗi kawai a bashi” tsaki Kaddu ta yi tana jan hannunta ta ce“ashe ba biyan buƙatar ki ke so ba, to mene a ciki dan dai sau ɗaya, daga wannan fa shikenan ba sake neman wani zai yi ba” shiru ta yi tana tunani, Kaddu ta ɗan yi murmushi ta ce“muje dan Allah” girgiza kai Aunty Khadijah tayi ta ce“kai Kaddu! Kai! Gaskiya bana jin zan iya wata mu'amala da wannan mutumin, to wait idan ma na yarda dashi aka zo aikin bai yi ba shikenan ya cuceni kenan?” harararta ta yi ta ce“kin ga ni ba zaki ɓata min rai a banza ba wallahi tallahi, ya ina ƙoƙari akan ki kuma bakya gani, kin san aikin nasa ne? Wane ya ce miki idan aka yi za'a iya rashin nasara? To ki zauna, idan bakya so kawai mu shige mu tafi daga nan” furzar da iska ta yi daga bakinta tana tunanin abin da ya kamata ta yi, ta yarda dashi ta bashi kanta domin biyan buƙatarta? Ko kuwa ta yi tafiyarta ta nemi wani?. **** Sati ɗaya a tsakani lokacin shirye-shiryen biki ya kankama, ranar wata Litinin ta kama ita ce ranar da aka kai wa kowace yarinya kayan aurenta, dan haka estate ɗin a cike take da yan uwa da abokan arziki. Zahra ce ta buɗe ɗakin tana kallonta ta ce“Nana har yanzu baki tashi ba?” tana kwance kan gadon ta juya mata ba, ta sanya hannunta ta share hawayenta sannan ta ce“na tashi Aunty” “to ki fito ki yi breakfast kin ji” toh kawai ta ce, Zahra ta juya ta fita, sai a sannan ta tashi zaune tana sake fashewa da wani sabon kukan, she just can't believe ace aurenta nan da one week, auren ma kuma bada Junaid ba, da Yaya Safwan wanda ko a mafarki bata taɓa tunanin irin haka zata kasance a tsakaninsu ba, ta goge hawayenta sannan ta janye duvet ɗin data rufa dashi ta sakko daga kan gadon, gaban dresser ɗin ɗakin ta tsaya ta dinga ƙarema kanta kallo a jikin ƙaton madubin, ta rame sosai, idanunta sun firfito har ɗan duhu ta yi wanda yake nuni da rashin kwanciyar hankalin da take ciki. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta bar wajen ta shige toilet, after 20mins ta fito ɗaure da towel, ta ƙarasa press ɗin Aunty Zahra ta buɗe, wata simple gown ta ɗauka mara nauyi ta saka, ta shafa mai a jikinta sannan ta ɗaure kanta da mayafin rigar ta nufi hanyar fita daga ɗakin. Hayaniyar data dinga ji a parlon shi ne ya hanata ƙarasowa, ta maƙale jikin benan tana kallon su ɗaya bayan ɗaya, Aunty Khadijah ce sai Siyama da Safeena sai kuma wata wadda bata taɓa ganinta ba amma bata fi girman su Safeenan ba. “Laa Nana ki ƙaraso mana” Safeena ta yi maganar sanda ta lura da ita, gaba ɗaya suka kalli wajen da taken, ta ɗan sunkuyar da kanta sannan ta ƙaraso a hankali ta ɗan durƙusa tana kallon Aunty Khadijah ta ce “ina yini?” Babu yabo babu fallasa ta ce“lafiya sannu” daga haka ta ɗauke kanta, ita ma Nanan bata damu ba ta mai da Idanunta kan Safeena ta ce“sannu sister ya ki ke?” washe baki Safeena ta yi ta ce“Alhamdulillah kefa Nana? Ya shirye-shirye?” “Suna nan muna fama” Nana ta yi maganar a sanyaye, sai kuma ta kalli Zahra ta ce“aunty bari naje” harararta Zahra ta yi ta ce“ki je ina Nana? Shiga kitchen ki ɗauka breakfast ɗin ki har kusan 1pm baki karya ba” langwaɓar da kai ta yi ta ce“a'a ai zan karya a wajen Amma” girgiza kai ta yi ta ce“ban yarda ba ɗauki ki koma sama ki ci idan ma zaman nan ne baki so” babu yanda ta iya dan bata san musu da Zahra yasa ta tashi ta nufi kitchen ɗin, ba'a jima ba ta fito hannunta riƙe da plate ɗayan kuma ta riƙe mug ta nufi sama da sauri, da idanu suka bita har ta ɓacewa ganinsu sannan Siyama ta taɓe baki ta ce“wai ita wannan yarinyar wace ce a gidan nan? Naga ta fiye girman kai, can you imagine rannan nazo ina musu magana ko kallona bata yi ba” ɗan murmushi Zahra ta yi ta ce“ayyah ai daman Nana bata da magana sosai, in dai bata sanka ba, ba zata taɓa sakin jiki da kai ba, yar ƙanin babansu doctor ce” Aunty Khadijah ce ta ce“har da ita a waɗanda za'a aurar ɗin ne naji Safeena na cewa ya shirye-shirye?” gyaɗa mata kai Zahra ta yi kafin ta ce“eh mana, ai ita ce zata auri Safwan!” Da wani irin mamaki suka dinga kallonta duka, barin ma Aunty Khadijah da hankalinta ya tashi matuƙa, ta buɗe baki a hankali ta ce“kenan dai ita ce zata fasa aurensa Siyama ta aureshi” Zahra ta kalleta amma bata ce komai, Ɗayar wadda tun zuwansu bata yi magana ba ce ta ce“to ba dolenta ba, ai wallahi sai Siyama ta yi aure s cikin gidan nan!” Safeena ce ta kalleta sai kuma ta ce“ke Amal me ke damunki ne? Wai mene haka?” harararta ta yi ta ce“bansani ba, wallahi ke duk abin ki sai ta aure shi, to mene amfanin arzikin idan ba'a ci ba, yanzu duk inda ta aureshi mun zama muna da mutum biyu namu a family ɗin nan, nan da wani ɗan lokaci sai ki ga mun mamaye dangin” Aunty Khadijah ce ta ce“yauwa Amal daɗina da ke hankali, su ai basu gane hakan ba, idan yanzu Siyama ta auri ɗan dangin nan ai kin ga mun ƙara yawa, sunanmu zai daukaka mu ma” murmushi Amal ta yi ta ce“wallahi fa Aunty, ai ki saka ran ki a inuwa da tuggu da makirci sai ya aureta wallahi sai dai idan bai shigo hannunmu ba” tsaki Safeena ta yi ta ce“to sai naga a lokacin da har zai shigo hannun naku bare kuma ya yarda ya auretan, yanzu haka nan da wani satin ma shi ya yi aurensa” wata dariyar mugunta Siyama ta yi sai kuma ta ce“to ai shi tuni yana hannu bari ki ji ba'a shiga dawa dan ƙarya, ko yanzu na kira shi a waya nace masa gani a gidansu ya zo wallahi sai ya zo” ba Safeena kaɗai ba har Zahra sai da ta yi mamaki, ta kalleta a sanyaye ta ce“Siyama me ya sa? Akan me ki ke son dole sai kin shiga tsakanin zumucin su? Mene haka dan Allah?” yanda ta yi maganar cikin sanyin murya ya sanya Aunty Khadijah yin tsaki kafin ta ce“ni ba wannan ba yanzu za ki taimaka ayi maganar nan ko ba zaki yi ba?” Zahra ta girgiza kanta ta ce“a'a gaskiya ni ba zan jawo abin da zai dameni ba, kudai ku ke ku yi ta yi” Shiru Aunty Khadijah ta yi tana tunanin yanda zata yi, ashe daman mutumin ƙarya yake mata? Ya ce idan ta tambayi Zahra ba zata bijire ba, sai ma ta fi kowa ɗaukan abun da gaske, but why?. “Danƙari!” Ta ce a ranta, amma sam bata yi tunanin duk sun ji maganar ba, Zahra ce ta sake cewa“ni dai dan Allah dan Annabi ku bar wannan maganar, ni wallahi dana san irin abun da zai faru kenan da ban zo ƙasar nan ba, wannan wace irin masifa ce?!” Taɓe baki Amal ta yi sai kuma ta ce“haba Yaya Zahra ke baki son ci gaban gidanku sai na wani gidan?” Miƙewa tsaye Zahra ta yi a fusace ta ce“ke kar ki ɓata min rai Amal! Ni idan wannan abun ne ya kawo ku to gaskiya nagode da ziyara ku tashi ku tafi!” A fusace ita ma Aunty Khadijah ta ce“iyee wato korarmu ki ke daga gidan ki ko Zahra? Korarmu ki ke” ɗauke kai Zahra ta yi ta harɗe hannayenta a ƙirji ta ce“ni in dai irin wannan maganar ce ta kawo ku to wallahi gara ku tafi, dan banga amfanin zuwan naku ba!” ta ƙare maganar tana wara hannayenta. Jin jina kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“eh lallai kin isa! To bari ki ji zamu tafi amma wallahi tallahi sai Siyama ta auri Safwan koda hakan na nufin ke zaki bar gidan!” Da wani irin expression Zahra ke kallonta sai kuma ta yi murmushi yaƙe ta ce“to Allah ya baki sa'a Aunty, Allah kuma ya tabbatar?” daga haka ta yi hanyar sama fuu ta bar su tsaye. Tashi itama Safeena ta yi tana kallonsu rai ɓace ta ce“gaskiya wannan ba adalci bane, akan me za'a lalata auren wadda take ciki saboda na wadda ba'a yi ba? Wannan gaskiya ba adalci bane! Kuma Allah ba zai bar ku ba wallahi” daga haka ta ɗauki gyalenta ta yi sama da sauri itama. Zaman daɓaro Aunty Khadijah ta yi akan kujera tana tunanin mafita, yanzu ya zata yi da Zahra? Ita ce makamin da zata riƙe domin ganin auren nan ya yiwu amma gashi sam taƙi bada haɗin kai, wayarta ta zaro ta shiga danna kira sannan ta kai wayar kunne, ringing ɗaya ta ɗauka kafin ta yi magana Aunty Khadijah ta yi saurin katseta ta hanyar faɗin “Kaddu ni wannan mutumin zai cuta? Ni zai yaudara? To wallahi ƙarya yake” Kaddu dake kwance kan gadon hotel ɗin ta tashi zaune tana faɗin “mene ne ya faru? Ki min bayani yanda zan gane” “Kaddu Zahra taƙi aminta da buƙata ta, tama ƙi saurarena ke ƙarshe ma dai korata take daga gidanta” Girgiza kai Kaddu ta yi ta ce“haba da sake wallahi, ita ta isa, na rantse miki ko kaffara ba zan yi ba akan dole ta yi biyayya, sai dai idan ba wajensa muka je ba, ki jira kawai ki ga da kanta zata dawo tana baki haƙuri wallahi yanda zata yi a maganar auren nan ke ba zaki iya yi ba, kawai ki zuba mata idanu” Numfasawa Aunty Khadijah ta yi kafin ta ce“amma hankalina ya ƙi kwanciya Kaddu, na kasa samun sukuni sauran sati ɗaya fa bikin” Tsaki tayi ta ce“ko ranar ɗaurin auren ne sai ya auri Siyama, kuma ki jira ki gani” Okay kawai ta ce sannan ta kashe kiran, ta dago kanta ta kalli su Siyama da ke tsaye cirko-cirko ta ce“ku tashi mu tafi” okay kawai suka ce sannan ta tashi itama suka fice daga parlon. Acan sama kuwa Zahra ce zaune gefen gado tana hawaye, Safeena dake kusa da ita ta dafata a sanyaye ta ce“dan Allah dan Annabi Aunty ki yi haƙuri, Allah yana tare da ke babu abin da suka isa su yi” cikin shessheƙar kuka Zahra ta ce“tsoro nake ji Safeena, babu abin da Aunty Khadijah ba zata iya ba domin biyan buƙatarta, tana iya kashe min aure indai Siyama zata auri Safwan, ni ba wannan ne ma abin da ya dameni ba, yanda take ƙoƙarin sakani ciki shi ne abin da yafi daga min hankali. Ya zan yi Safeena? Ta ina zan fara ƙoƙarin haɗa Safwan da Siyama? Bayan kuma Nana zai aura, Nana fa, ba zan taɓa iya ruguzawa Nana aurenta ba wallahi, ba zan iya ba, Nana bata cancanci haka daga gareni ba, ita ɗin tamkar ƙanwa take a wajena, idan har zan iya hanaki aure na tozarta ki to tabbas zan iya yiwa Nana haka, kinga ko ba zan taba iyawa ba!” Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka, Girgiza kai Safeena ta yi itama tana kukan ta ce“nasani Aunty, na san baki da zuciyar mugunta, dan haka kawai ki riƙe addu'a, nima zan tayaki sannan zan faɗawa Umma” da sauri Zahra ta kalleta sai kuma ta girgiza kanta ta ce“a'a kar ki faɗa mata, domin zata ci gaba da ganin baƙin Aunty Khadijah ne, ni kuma ba zan zo haka ba, kawai ki bari Allah ya san yanda zan yi dasu” jinjina kai Safeena ta yi sai kuma ta ce“to Aunty”.. **** Fitowarta kenan daga toilet taji ringing ɗin wayarta, ta ƙarasa kan drawer tana kallon mai kiran, sabuwar number ce dan haka ta goge ruwan hannunta sannan ta dauki wayar, Muryar wanda taji ya sanya ta runtse idanunta, lokaci ɗaya ta ji zuciyarta na wani bugawa da ƙarfi, cikin sanyin murya Junaid ya ce “tun ɗazu ina ta kiran ki da lambata shi ne ba zaki ɗaga ba ko Nana?” Shiru ta yi masa, bai damu da shirun nata ba ya ci gaba da faɗin “shikenan faɗa min kin sauya shawara ko kuwa har yanzu kina nan akan waccan maganar ta ki?” Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta dake ta ce “Eh ban sauya ba, ko da kana tunanin zan sauya ne? To ka sani har abada ba zan taɓa sauyawa ba! Ba zan dawo gareka ba! Na bar ka, bari irin na har abada” Lumshe idanunsa ya yi nan take hawaye suka zubo daga cikinsu, ya jinjina kansa yana ƙoƙarin saita kansa ya ce“okay, shikenan Nana, Allah yasa haka ne mafi Alkhairi, sai dai ina neman wata alfarma a wajen ki koda zata zama alfarma ta karshe da zaki iya min” Ban da hawaye babu abin da Nana take, ta jinjina kanta cikin shessheƙar kuka ta ce“ina ji” “Akwai wani hanky da ki ka taɓa bani kin tuna? To ina son na dawo miki dashi ne, ina waje ko za ki iya fitowa ki karɓa?” Shiru ta yi kamar me tunani can kuma ta ce “okay” Daga haka ta katse wayarta, hijabi ta ɗauka har ƙasa ta saka sannan ta fito daga dakin, koda ta zo parlon bata samu kowa ba dan haka kawai ta yi waje abin ta, da sauri ta dinga tafiya har ta ƙaraso wajen estate ɗin. Ta yiwa mai gadin wajen murmushi da yake mata magana sannan ta ce“bari na karbo sako” to ya ce sannan ta buɗe gate ɗin ta fita. Tsaye ta hangi wata Camry blue colour ta yi parking sai sheƙi take, kamar me tsoron ƙasa haka ta dinga takawa har taje gaban motar, Junaid ya buɗe driver side ɗin ya fito ya zagayo inda take yana kallonta, kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta, ya jingina da motar yana murmushin ƙarfin hali ya ce“Nana kin rame” kallonsa ta sake yi a ranta ta ce “har kura ce zata cewa kare maye?” Dan shima ya ƙaramar rama ya yi ba, a fili kuma ta ce“bani zan tafi” ɗan murmushi ya sake yi ya ce“ba zamu gaisa ba?” “idan babu abin da zaka bani zan koma ciki dan ina da abin yi” Ta yi maganar a ɗan fusace, numfasawa ya yi sannan ya buɗe side ɗin da yake tsaye ya dauko yar ƙaramar jakar, juyowa ya yi ya miƙa mata yana kallonta, amsa ta yi itama tana kallonsa ta dinga kallon yar kit ɗin wadda aka yi cealing ɗinta da fari yanki da kuma wasu flowers jajaye, ta dinga kallon kit ɗin dan har ta manta da ita ma, Above 2mins kafin ta ce“sai an jima” jinjina kansa kawai ya yi sai kuma ya ce “Allah ya haɗa kowa da Alkhairinsa, amma ni nasan ni ne alkharinki Nana” kallonsa ta yi sai kuma ta juya ta yi gaba ba tare da ta bashi amsa ba. Ya tsaya yana kallonta har ta shige ciki sannan ya sauke numfashi shima ya zagaya ya shige motarsa ya bar wajen. Koda ta koma apartment ɗin Zahra bata samu kowa ba kamar ɗazu dan haka ta haye sama da sauri ta koma ɗakin da take, tana shiga taji wayarta ta yi ƙara alamar message ya shigo, sai da ta zare hijabin jikinta ta ajiye gefen gado haɗe da kit ɗin data karbo sannan ta ƙarasa ta dauki wayar, Junaid ta gani a jikin numbern dan haka ta buɗe sakon gaba ɗaya _Nana kenan, kin ɗauka zan iya rabuwa da ke haka cikin sauƙi? Kin ɗauka ban san me nake ba, ban fara son ki dan na barwa wani ke ba, ina sonki ne dan na rayu da ke, ina son ki kalla saƙon dana baki da kyau kafin ki yankewa kan ki hukuncin, amma ki sani ba zan taɓa yarda ki bar ni ba, komai runtsi komai walaha ke tawa ce, tawa ni kaɗai NAANAH!_ 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 22. Nana ta dinga kallon saƙon da wani irin mamaki, me yake nufi to? Wace magana yake? Girgiza kanta ta yi da sauri kuma ta kalli inda ta ajiye kit ɗin data shigo da ita, cikin hanzari ta ƙarasa gaban gadon ta zauna sannan za jawo kit ɗin ta fara buɗeta a hankali, har ta gama buɗewa gabanta faduwa yake, ta zaro hanky ɗin da yake magana sai ƙamshin turare yake, kallonsa ta dinga yi tana jujjuya shi, a fili ta ce“to me yake nufi?” sai kuma ta ajiye shi a gefe tana ƙoƙarin tashi idanunta ya sauka akan envelope ɗin da take cikin. Ƙura mata idanu Nana ta yi kafin ta sanya hannunta na dama ta ɗaukota, haka kawai ta ji gabanta yana wani irin faɗuwa, ta runtse idanunta a hankali ta ce “Ya Allahu” Ta sauke numfashi kafin ta fara ƙoƙarin buɗe envelope ɗin bugun zuciyarta na sake tsananta, hannunta ta sanya ciki tana taɓa takardun dake ciki, da mamaki ta janyo su duka tana sake ware idanunta dan ganin mene ne a ciki, wata irin zabura Nana ta yi ta miƙe tsaye jikinta ya fara wani irin rawa kamar ana kaɗa ganga, baki buɗe take kallon hoton wanda ya kasance hotonta ne kwance kan gado daga ita sai ƙaramar vest wadda bata kai ga rufe cibiyarta ba, sai ɗan ƙaramin underwear, kanta a buɗe babu dankwali. Ta durƙushe a ƙasa tana wani irin numfashi dan tsabar tashin hankali kuka ya gagara zuwar mata, hannunta na rawa ta janye hoton inda na biyunsa ya bayyana kuma wanda ya fishi muni, hotonta ne da waccan shigar wannan karon ma a kwance sai dai a kusa da ita Junaid ne daga shi sai boxer, ta sanya hannunta ta rufe bakinta jin wani irin kuka yana neman tawo mata. Haka ta dinga buɗe hotunan ɗaya bayan ɗaya har ta kai ƙarshe, lokaci ɗaya ta yi jifa da hotunan tana sakin wata irin matsananciyar ƙara, dai dai lokacin Zahra ta shigo ɗakin da sauri tana kallon ta ta ce“Nana lafiya mene ne?” Bata iya bata amsa ba sai wani irin numfarfashi take, ganin haka yasa Zahra ta ƙarasa inda take durƙushe da sauri ta dafata tana faɗin “mene ne Nana? Meke damunki? Baki da lafiya ne?” madadin ta bata amsa sai kawai taga ta faɗo jikinta a sume, Zahra ta dinga jijjigata cikin tashin hankali tana faɗin “ke Nana! Mene ne? Me aka miki?” Ganin bata san ma tana yi ba ya sanya Zahra ta kwantar da ita a ƙasa ta tashi da sauri ta fice daga ɗakin, ba'a jima ba ta dawo hannunta riƙe da rogar ruwa mai sanyi, ta ƙarasa inda take sannan ta buɗe robar ta ɗan yayyafa mata ruwan, ajiyar zuciya Nana ta sauke ba tare da ta buɗe idanunta, Zahra ta ajiye ruwan a gefe sannan ta ɗagota tana cewa“mene ne Nana? Meya faru? Ke da wa?” Bata ce komai ba, dan babu alamar ma tana fahimtar abin da Zahran ke cewa, Banda numfarfashi babu abin da take. Zahra ta rasa yadda zata yi da ita, dan haka ta tashi da niyyar ɗaukan wayarta ta kira Abdusammad, Sai dai takardar da taji ta taka a ƙasa ya sanya ta kalli wajen da sauri, da mamaki take kallon farar takardar dan hoton a kife yake, ta ɗan sunkuya ta ɗauko sannan ta juya shi, saurin ja da baya ta yi ta riƙe gefen dresser ta dinga kallon hoton baki buɗe, lokaci ɗaya kuma ta mai da Idanunta kan Nana da ke kwance gefe, girgiza kanta ta dinga yi hawaye na zubowa kan fuskarta, ta yi wurgi da hoton sai kuma ta sake kallon ƙasa sai a sannan taga tarin hotunan dake warwartse a wajen, ta bi kowanne ta ɗauko sannan ta ajiye gefen drawer ta koma kusa da Nana ta zauna tana kuka ta ce“Nana garin Ya ya? Me ya sa? Me yasa zaki yiwa kan ki haka? Me yasa?” Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka, Kasa cewa komai Nana ta yi sai wani irin kuka daya kwace mata, ta ɗora kanta kan cinyar Zahra ta dinga rera kuka kamar ranta zai fita. Kasa hanata Zahra ta yi dan ta san akwai buƙatar ta yi kukan duk da ba shine mafitarta a yanzu ba, Kusan mintuna goma kafin ta fara rage sautin kukan nata, Zahra ta ɗago kumburarrun Idanunta ta kalleta cikin kuka ta ce“Akan me ki ka yi haka Nana? Yaushe haka ta faru? Meya sa?” Ɗago kanta ta yi daga jikin Zahra, ta kasa kallonta dan har sannan hawaye basu bar zuba kan fuskarta ba, Zahra ce ta yi ƙarfin halin sanya hannunta ta fara goge mata hawayen, kafin ta ce“ki daina kuka dan ba shi ne mafita ba a yanzu ki faɗa min ya aka yi haka?” Tana ƙoƙarin magana wayarta ta shiga ringing dan haka ta kalli wajen a tsorace sai kuma ta tashi da sauri ta ƙarasa inda ta yar da wayar ɗazu ta ɗauka, Sunan Junaid ne akan screen ɗin dan haka ta ɗaga wayar da sauri bakinta na rawa ta ce “Sir...sir dan Allah... Allah dan girman Allah kada ka yimin haka kaji kada ka yi haka dan Allah” Murmushi Junaid ya yi yana kallon titi ya ce “Me nayi miki Nana? Kin ga saƙona ne?” Fashewa ta yi da wani sabon kukan tana girgiza kanta ta ce “Dan Allah kada ka bari wani ya ga hotunan nan, dan Allah kada ka tozarta min rayuwa, ka yi haƙuri dan Allah..” Dariya sosai Junaid ya yi kafin lokaci ɗaya ya haɗe rai cikin kakkausar murya ya ce “Ai daman babu wanda zai gani Nana, ya za'a yi na bari wani ya ga lalatattun hotunan ki? Ai ba zan bari ba daman, idan har kin bi abin da zan faɗa miki babu wanda zai ji kuma ya gani, amma idan har ki ka kasa yimin biyayya to ki sani ina da irinsu-irinsu copy biyar, zan sake su a duniya kowa ya gani, kin ga ba iya ke kaɗai ba shi kansa dangin da ki ke taƙama dashi saina lalata shi wallahi tallahi kin ji har na rantse Nana!” Sakin wayar ta yi ta faɗi ƙasa, ita kuma ta silale a hankali ta yi zaman daɓaro akan tiles, Zahra ta dinga kallonta daga inda take zaune, ganin yanda take hawaye kamar an buɗe famfo ya sanya ta taso ta dawo kusa da ita ta riƙeta tana cewa“me ya ce miki Nana?” Kasa cewa komai ta yi sai kawai ta tashi ta shige toilet da sauri, Zahra ta bita da kallo sai kuma ta tashi itama ta kwashe pics din ta mayar dasu cikin envelope ɗin sannan ta fice daga ɗakin. **** Siyama ta dinga kallonsa tana murmushi kafin a hankali ta ce“ai na ɗauka ba zaka zo ba” Safwan da ke tsaye jikin motarsa ya girgiza kansa yana murmushin shima ya ce“haba dai naƙi zuwa, ai na ɗauka har yamma zaku kai a gidan namu” langwaɓar da kai ta yi ta ce“eh ai da yamman muka so kai wa amma sai aka ɓata mana rai” da ɗan mamaki ya ce“wane ya ɓata muku ran kuma?” taɓe baki ta yi ta ce“wata yarinya ce, ta ɗan zagemu to gudun mu ya hatsaniya da ita ya sanya kuma tawo kawai” Gyara tsaiwarsa ya yi sannan ya ce“yarinya kuma? Wace yarinya?” Shiru ta yi tana kallonsa can kuma ta ce“wai ko Nana naji suna ce mata, yauwa ita ce ma yarinyar da zaka aura ko?” Kallonta ya dinga yi bai ce komai ba, ta ɗan yi murmushi sai kuma ta ce“naga ka yi shiru” Girgiza kansa ya yi yana faɗaɗa fuskarsa ya ce“bakomai, ita Nanan ce ta zageku?” gyaɗa masa kai ta yi ya ce“okay I'll talk to her, ki yi haƙuri kin ji” jinjina kanta ta yi ta ce”bakomai Yaya ai na haƙura tun da dai ƙanwar ka ce” Safwan ya ɗan yi dariya ya ce“to ya garin?” kamar jira take ta fara masa hira babu kama ƙafar yaro, y dinga murmushi yana saurarenta wani ya tanka ta wani kuma ya yi shiru. **** Bayan sallahr magriba Zahra ta buɗe ɗakin ta shigo hannunta riƙe da tray, Nana na zaune ƙasan gado ta ɗora kanta gefen gadon sai hawaye take, karasowa ta yi ta ajiye tray ɗin gefe ɗaya sannan ta kalleta a sanyaye ta ce“Nana” shiru ta yi mata, dan haka ta sake kiran sunanta, nan ma bata amsa ba, Zahra ta dinga kallonta sai kuma ta kai hannunta ta taɓata ta ce“Nanaa!” A ɗan firgice ta ɗago kanta, sai kuma ta goge hawayenta ta ce“Na'am Aunty” “ki tashi ki ci abinci kin ji” Girgiza kanta ta yi hawaye na zubowa kan kuncinta ta ce“naƙoshi aunty” Zahra ta dinga kallonta cike da tausayawa sai kuma ta ce“a'a Nana baki ƙoshi ba, zo ki ci abinci” sake girgiza kanta ta yi ta ce“wallahi bana jin yunwa, ba zan iya cin abinci ba Aunty” shiru Zahra ta yi can kuma ta numfasa ta ce“Nana faɗa min garin ya ya haka ya kasance tsakaninki da shi? A ina ya ganki har ya miki waɗannan ƙazaman hotunan?” madadin ta bata amsa sai kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikinta tana faɗin “wallahi aunty tsautsayi ne, ban yi tunanin haka daga gare shi ba, abokinsa ne ya ce min bashi da lafiya shi ne naje duba shi, ya bani lemo nasha sai bacci ya ɗaukeni, ina ga a sannan ya yi min haka, na yarda dashi but he deceive me, they trick me aunty, sun lalata min rayuwa, ya zan yi aunty? Ya xan yi dashi yanzu?” Ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka, rungumeta Zahra ta yi itama tana kukan ta ce“kin yi kuskure Nana, ba'a bawa namiji yarda irin haka, kin yi kuskuren zuwa wajensa ba tare da shawara ba, amma yanzu aikin gama ya riga da ya gama, sai dai a yi addu'ar Allah ya kawo wa lamarin sauki” “ya zan yi aunty? Ban san me zai buƙata daga gareni ba, kuma yace idan ban yi masa ba sai ya yaɗa hotuna na kowa ya gani, sai ya tabbatar ya ɓata sunan gidanmu, taya zan bari haka ta kasance aunty? Ba zan iya ba, tsoro nake ji aunty Zahra, wallahi zuciyata bugawa take yi da karfi aunty...” Zahra ta dinga shafa bayanta tana jin yanda take kuka mai ban tausayi, tunda take da Nana bata taɓa bata tausayi irin na yau ba, yarinya ce ƙarama amma yanzu rayuwarta ta faɗa wani hali wanda Allah ne kawai zai iya fitar da ita, wace irin jarrabawa ce wannan?... Sai ƙarfe 9:00 na dare sannan ta bar apartment ɗin Zahra, koda ta koma gida Amma ta samu zaune a parlon bayan ta haɗe kayan lefen can gefe guda, ta ƙarasa jiki a sanyaye ta zauna kusa da ita, Amma ta dinga kallonta sai kuma ta ce“Nana sai yanzu?” gyaɗa mata kai kawai ta yi, Amma ta sake cewa“kin ci abinci?” gyaɗa mata nan ma ta yi, ta yi shiru can kuma ta ce“ko zaki ga kayan auren naki?” tashi ta yi tana girgiza kanta ta ce“a'a Amma bacci nake ji” Amma ta dinga kallonta sai kuma ta taɓa jikinta, zafi taji amma ba can ba dan haka ta ce“kuka ki ka yi ko Nana? Ba zaki yi haƙuri ki yarda da ƙaddarar ki ba kenan? Kin fi so ki ɗaga hankalinki sannan ki ɗaga namu? Ba zaki haƙura ba ko?” kasa jurewa ta yi dan haka ta fashe da kuka tana rungume Amma ta ce“na haƙura Amma, wallahi na haƙura, ba wai ina kuka bane saboda ban sami wanda nake so ba, ina kuka ne kawai saboda ban san wace irin rayuwa zan yi ba bayan auren, amma na haƙura wallahi, tuntuni na cirewa raina wannan, dan Allah ki yi min addu'a Amma, ki dinga yi min addu'a wallahi tsoro nake ji” Amma ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin tausayin tilon ƴar tata, ta shafa kanta a sanyaye ta ce“to Nana daman ina miki addu'a kullum sannan zan ci gaba da yi miki, kema ki dinga addu'a kin ji, kuma ki daina jin tsoro babu abin da zai faru sai Alkhairi” Jinjina kanta ta yi sannan ta tashi ta bar wajen ba tare da ta sake cewa komai, Amma ta bita da kallo har ta shige daƙinta. Washegari around 10:40 na safe ta fito daga ɗakinta bayan ta shirya cikin wata atampa tana kallon Amma ta ce“zan je wajen Aunty Zahra” to kawai Amma ta ce sannan ta fice daga gidan. Tafiya kawai take har ta kusa kaiwa apartment ɗin nasu ta hangoshi tsaye suna magana da Hamid, kallo ɗaya ta yi musu har ta ƙaraso inda suke ta ɗan rusuna a sanyaye ta ce“ina yini?” Hamid ne ya amsa, shi kuma ya dinga kallonta ganin zata shige ya ce“Nana zo” runtse idanunta ta yi sai kuma ta dawo ta tsaya kusa da su ta sunkuyar da kanta, Hamid y ce“to ni dai nayi gaba” okay kawai Safwan ya ce sannan ya mai da idanunsa kanta, above 5mins kafin ya ce“jiya wai kin yiwa su Siyama rashin kunya kin zage su?” da mamaki ta dinga kallonsa sai kuma ta ce“wace Siyama?” kallonta kawai ya yi sai kuma ya ce“je ki kawai” tura baki ta yi sannan ta juya ta bar wajen dan daman ba son magana take dashi ɗin ba. Tana ƙoƙarin shiga parlon su Zahra wayarta ta yi ƙara alamar message ya shigo, ta kalli message ɗin tana kokarin buɗewa sai ga kiran waya ya shigo, tsayawa ta yi sannan ta ɗaga kiran ta kai wayar kunne, kafin ta yi magana ya ce “Kin ga saƙona?” Girgiza kanta tayi kamar yana gabanta ta ce “A'a” Junaid ya gyaɗa kansa sannan ya ce“okay to ba komai bane sai ina son sanar da ke cewa kisan duk yanda zaki yi kada a ɗaura miki aure da wannan mutumin, dole ne ki ƙi aurensa sannan dole ne ki gabatar dani a wajen iyayenki, ki ce musu ni ki ke so ba wanda suke shirin aura miki ba, idan ki ka yi haka to zan ƙona hotunanki da suke wajena, amma idan har ki ka saɓa abin da nace miki to wallahi sai na fitar dasu kowa ya gani, sannan har gida zan saka a kawowa mahaifinki ya gani, dan haka yanzu shawara ta rage ga mai shiga rijiya, ko dai ki yi abin da nace ko kuma na lalata rayuwarki!” Jingina ta yi da jikin bango tana sauke numfashi da sauri da sauri, nan da nan hawaye suka ciko idanunta, ya kashe wayarsa ba tare da ya sake cewa komai ba. Kasa kukan ta yi sai ajiyar zuciya da take saukewa, above 5mins kafin ta ja ƙafafunta a hankali ta buɗe parlon ta shiga, Aunty Khadijah ce zaune sai Zahra a kusa da ita suna magana, ta kallesu muryarta na rawa ta ce“ina yini” babu wadda ta amsa a cikinsu dan haka ta haye sama abin ta, Zahra ta kalli Aunty Khadijah sai kuma ta ce“ina zuwa” okay kawai ta ce sannan ta tashi ta bi bayanta, tana shiga ɗakin Zahra ta buɗe ƙofa ta shigo, Nana ta ɗan kalleta sai kuma ta ce“aunty yanzu Junaid ya kirani” babu yabo babu fallasa ta ce“me ya ce miki?” jiki a sanyaye ta faɗa mata duk abin da ya ce mata, Zahra ta sauke numfashi sai kuma ta ce“zo ki zauna zamu yi magana” ta ƙare maganar tana zama gefen gadon, to kawai Nana ta ce sannan ta ƙarasa ita ma ta zauna gefenta. Zahra ta dinga kallonta can kuma ta ce“kin san me nake so dake Nana?” girgiza kai Nana ta yi ba tare da ta ce komai, Zahra ta ci gaba da faɗin “Ina son ki rabu da auren Safwan, ina son ki ce baki son shi da kanki, idan ta kama ki ɓata da kowa ma ki ɓata amma ina so ki bar maganar aurensa!” Da wani irin mamaki Nana ta dinga kallon Zahra sai kuma a sanyaye ta ce“Aunty idan na ce haka kowa zai tsaneni, nima bana son auren Yaya Safwan amma babu yanda na iya, ba zan iya cewa a'a ba” Zahra ta gyaɗa kanta sai kuma ta ce“ba zaki iya ba? To ai dole ki yi Nana, saboda Yar Yayata Siyama nakeson ta auri Safwan, ki cewa Abba bakya son sa ya zaɓa miki wani, amma ba dai Safwan ba!” a razane ta tashi tsaye tana kallonta, ta dinga kallonta tana hawaye kafin ta ce“a'a aunty ki daina min irin wannan wasan, zuciyata bugawa zata yi, ki bari dan Allah” tashi tsaye Zahra ta yi ita ma ta dafa kafaɗarta tana murmushi ta ce“ba zolayarki nake ba Nana, ina faɗa miki ne a matsayin shawara, bana son mu kai jallin da zamu ɓata dake akan wannan dan haka ki rabu da Safwan kin ji” ta ƙare maganar tana jan kumatunta. Janye hannunta Nana ta yi daga fuskarta sai kuma ta girgiza kanta ta ce “a'a aunty, A'a! Wallahi ba zan iya ba, ba zan taɓa yi ba, zan auri Yaya Safwan muddin ba shi ne ya ce ya fasa aurena ba, ba zan ɗauki wannan shawarar taki ba!” Zahra ta kalleta sai kuma ta ce“okay wait!" Daga haka ta fice daga ɗakin, Nana na tsaye tana tunanin abin da Zahra ta ce mata har ta dawo hannunta riƙe da envelope ɗin jiya, Nana ta dinga kallonta lokaci ɗaya gabanta ya shiga faɗuwa, zaro hotunan ta yi gaba ɗaya tana bubbuɗesu ta ce “Idan baki ɗauki shawara ba na san zaki ji barazana, dan haka ki bar maganar auren Safwan muddin baki son waɗannan hotunan naki su fita” da wani irin mamaki Nana ke kallonta sai kuma ta kawo hannunta zata karɓe hotunan, Zahra ta janye hannunta tana murmushi ta ce “so ki ke na baki hotunan ki? Zan baki Nana, da zarar kin yi abin da nace zan baki hotunanki, amma idan har baki yi yanda na ce ba to ki sani kai tsaye Abba zan kai wa wannan hoton, sannan kuma na bawa uncle ɗin ki wasu, na san ba zaki so hakan ba ko Nana?” Shiru Nana ta yi dan ta kasa cewa komai banda hawaye babu abin da take, Zahra ta tako har gabanta ta sanya hannunta ta goge mata hawayen tana faɗin “stop crying lil sis, ki zama yarinyar kirki kin ji, babu abin da zai sameki, ni ba zan cutar da ke ba kin ji, kawai do as i said!” Zahra ta ƙare maganar tana murmushi sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 23... Mutuwar tsaye Nana ta yi a wajen, ta kasa koda ɗaga ƙafarta ballantana ta yi ƙwaƙwaran motsi, above 5mins kafin ta sulale ƙasa a hankali ta zauna kan tiles lokaci ɗaya ta fashewa da wani irin raunataccen kuka na zallar baƙin ciki da damuwa, gani take kamar a mafarki abin da ke faruwa, kenan bayan Junaid yanzu har da Zahra cikin masu son treating ɗinta? Me ya sa Zahra zata mata haka? Me ya sa mutanen data fi yarda dasu sune suke son cutar da zuciyarta, sai kawai ta sake rushewa da wani sabon kukan tana kifa kanta akan cinyoyinta. Can ƙasa kuwa Zahra ce ta kalli Aunty Khadijah sai kuma ta yi murmushi ta ce“ai kar ki wani damu wallahi kamar an yi auren nan ne, Nana ba zata taɓa bijirewa abin da nace mata ba, ni na sani” Aunty Khadijah ta jinjina kanta kafin ta ce“na yarda dake Zahra amma duk da haka akwai buƙatar mu sake kama yaron hannu biyu, saboda kin ga shi ne wanda zai je ya gabatar da Siyama a wajen iyayen nasa” “Ai Aunty kawai ki bar komai a hannuna, ni zan kira Safwan nan muyi magana dashi, ba dai yana son Siyama ba?” Zahra ta ƙare maganar cikin sigar tambaya, gyaɗa maya kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“eh mana, har gida fa yake zuwa, ko jiya suna tare har wajen isha'i baki ga abun arzikin daya kawo mata ba” Zahra ta sauke numfashi sai kuma ta ce“to indai haka ne kar ki wani damu, Safwan ba zai taɓa bamu matsala ba, kin san me?” girgiza kai Aunty Khadijah ta yi, Zahra ta gyara zamanta sannan ta ce“Ba Safwan ne zai rabu da Nana ba, a'a ita da kanta ce zata ce bata sonsa, idan har ta ce haka to a sannan ne za'a saka ya fito da zaɓinsa, kin ga sai ya nuna Siyama” Murmushin jin daɗi Aunty Khadijah ta yi ta ce“gaskiya kuwa kin kawo shawara mai kyau Zahra, shiyasa nake son ki ƴar ƙanwata” murmushin kawai ita ma Zahra ta yi tana shirin magana suka ji ƙarar taku wanda ya sanya suka kalli wajen a tare, Nana ta ce take sakkowa daga benan a hankali tamkar wadda aka zarewa laka, fuskarta ta yi caɓa-caɓa da hawaye, bata kalli inda suke ba ta nufi hanyar fita daga parlon, Zahra ta taɓe baki sai kuma ta mai da Idanunta kan Aunty Khadijah ta ce“kin ga abin da na faɗa miki ko? Ba zata iya ja dani ba yanzu” gyaɗa kai kawai Aunty Khadijah ta yi, ƙasan zuciyarta tana jin wani irin farin ciki mara misaaltuwa, koda wasa bata yi tunanin Zahra zata amince nan kusa ba, ta yi zaton duk maganganun da malamin nan yake faɗa mata karya ne sai gashi yanzu ta tabbatar da hakan da kanta. Nana na sakkowa daga balcony ɗin gidan suka ci karo dashi, ta ɗan ja baya a hankali idanunta a lumshe dan bata san ma ya tawo ba, kallonta Abdusammad ya dinga yi ganin yanda fuskarta ta yi jajur ga alamar hawaye a tattare da ita, ta sunkuyar da kanta muryarta na rawa ta ce“uncle ina yini?” shiru ya yi bai amsa mata ba, ya gyara tsaiwarsa kafin ya ce“mene ne?” girgiza kanta ta yi kuka na ƙoƙarin kwace mata ta ce“babb...babu komai!” taɓe baki ya yi sai kuma ya ce“baki ji me nace ba?” kasa jurewa ta yi kawai ta faɗa ta jikinsa ta ƙanƙameshi tana sakin wani marayan kuka, Kallonta ya dinga yi da mamaki kafin a hankali ya sanya hannayensa duk biyun ya riƙeta sosai ta dinga rera kukanta kamar daman jira take a tambayeta, shiru ya yi mata ba tare da ya yi yunkurin hanata ba, Above 5mins kafin ta fara rage sautin kukan nata, ta dinga shessheƙar kuka tana sauke ajiyar zuciya, Sai a sannan ya ɗan kalleta dan gabaɗaya ta yi wata yar ƙarama a gabansa, a iya ƙirjinsa kanta ya tsaya, ya sanya tattausan hannunsa ya ɗago fuskarta wadda ta gama lalacewa da hawaye da majina, hannunsa na hagu ya zura cikin aljihun trouser jikinsa ya zaro wani hanky coffee sai ƙamshi yake, da kansa ya goge mata hawayen sannan ya ce“now tell me mene ne?” janye jikinta ta yi daga nasa tana shessheƙar kuka ta ce“babu komai” Abdusammad ya haɗe ransa kamar ba shi ba ya ce“yaushe na fara wasa dake Nana?” girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce“babu komai wallahi kawai tsoro nake ji” “tsoron me?” Ya ce yana kafeta da idanunsa masu kaifi. Bakinta na ɗan rawa ta ce“ba..bana son auren nan uncle, tsoro nake ji sosai” dariya ce ta kusa kufce masa, amma ya maze ya sanya hannunsa ɗaya ya ja kumatunta sannan ya ce“silly girl, saboda za'a miki auren ki ke kuka? Ba kin girma uhm?” ya kare maganar yana murmushi, tura baki ta yi ta ce“ni ban girma ba uncle, I'm still a baby” jinjina kansa ya yi ya ce“yeh! U're still a baby tun da har yanzu baki daina kukan banza ba, anyway zan faɗawa Safwan ya dinga siya maki chocolate kin ji, so don't worry aure ba abin tsoro bane, daɗi fa zaki ji” Waro idanunta ta yi dan har ta manta da ƙalubalen dake gabanta cike da yarinta ta ce“daɗi kuma uncle? Bayan ni zan dinga girki, sannan ba zan dinga fitowa kullum ba, ba zan dinga zuwa wajen Ammana kullum ba, sannan malamin mu ya ce sai an yi aure ake haihuwa, zan samu baby” Murmushi sosai Abdusammad ya yi dan sai yau ya sake tabbatar da yarinyar ta, ya ɗauke kansa yana kallon compound ɗin gidan mai cike da shuke-shuke sannan ya ce“and u want a baby ba?” gyaɗa masa kai ta yi tana murmushi ta ce“ina son Baby, tun da Amma bata haifa mani ba, ni zan haifa ai ko?” ta ƙare maganar tana kallonsa, gyaɗa mata kai ya yi yana ƙoƙarin barin wajen ya ce“toh tun da kina son Baby that's means kina son aure” girgiza kanta ta yi tana tura baki gaba ta ce“ni bana son aure, baby kawai nake so” daga haka ta yi gaba ta bar wajen, da idanu kawai ya bita sai kuma ya yi dariya a fili ya ce “ƙuruci dangin hauka” Daga haka ya ci gaba da tafiya shima. Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga parlon, Zahra ta yi saurin miƙewa daga zaune da take tana ƙirƙiro murmushi ta ce“welcome back doctor” jinjina kansa kawai yayi sannan ya nufi upstairs, Aunty Khadijah ta bi shi da kallo dan daman can ba shiri suke ba har ya haye sama. Sai a sannan Zahra ta kalleta ta ce“aunty why baki masa magana ba?” harararta ta yi ta ce“dani dashi wa ya kamata ya fara yiwa wani magana? Ni fa sirikarsa ce” Zama Zahra ta yi sannan ta ce“but he's older than you, beside ma kowa a gidan nan ganin girmansa yake, kuma kema ya kamata ace yanzu kin ga girmansa kodan Siyama, saboda wallahi idan har ya ce a yi auren nan babu wanda ya isa ya hana, haka idan har ya ce baya so wallahi babu wanda ya isa ya yi shi” Aunty Khadijah ta jinjina kanta sai kuma ta ce“haka ne?” gyaɗa mata kai Zahra ta yi, Ta tashi tsaye tana faɗin “to idan haka ne shi ya kamata mu mallake ba Safwan ba, dashi ya kamata mu yi amfani ba Nana ba” da sauri itama Zahra ta mike sai kuma ta girgiza kanta ta ce“a'a Aunty koda wasa kada ki ce zaki yi haka, wallahi ba zai mallaku ba, saboda ba'a zaune yake ba, sannan koma zai mallaku mijina ne fa, uban Yayana kin san irin yanda nakeson Doctor? Kin san irin yanda na damu dashi? Wallahi a'a ba zai yiwu ba” tsaki Aunty Khadijah ta yi kafin ta ce“to sannu me miji, ni dai abin da zai fisshemu shi zan yi” Zahra ta ce“eh you can do whatever you want, amma ban da taɓa min mijina!” Kallonta kawai Aunty Khadijah ta yi ganin yanda ta haɗe rai kamar ba ita ba, ta dafata tana murmushi ta ce“to Shikenan” ajiyar zuciya Zahra ta sauke sannan ta kalli upstairs tana faɗin“bari naje gurinsa na dawo” tana ƙoƙarin barin wajen Aunty Khadijah ta ce“a'a nima tafiya zan yi mayi waya kawai” juyowa Zahra ta yi kamar zata yi kuka ta ce“aunty ba zaki jira na sakko ba?” girgiza kai ta yi ta ce“a'a akwai wanda muka yi alƙawarin haɗuwa dashi, Gara naje kawai” numfasawa Zahra ta yi ta ce“okay to ki gaida su Umma” “Zasu ji” ta ce tana ɗaukan mayafinta, sai da ta fita daga parlon sannan Zahra ta nufi sama da sauri. A hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar tana leƙen ɗakin, zaune yake gefen gado idanunsa zube kan system yana dannawa, ya rage kayan jikinsa daga shi sai wando 3-quater da kuma armless, farar fatarsa ta bayyana sai sheƙi take. Zahra ta ja ta tsaya tana ƙare masa kallo, sometimes tana tambayar kanta anya akwai mutum irin mijinta? babban mutum wanda ya san kansa, mai tarin dukiya da ilimi, mai kyau da nasaba, daɗin daɗawa hali nagari. Sai kawai ta lumshe idanunta a fili ta ce “Alhamdulilah!” Ɗago kansa ya yi ya kalleta dan bai san ma ta shigo ba, ta sakar masa kyakkyawan murmushi tana ƙarasowa, ta zauna gefensa ta ɗora hannunta kan nasa a sanyaye ta ce“sannu da dawowa” kallonta kawai ya yi sai kuma ya ce“yauwa, ina Noor?” murmushi ta yi ta ce“kai ma kasan tun da muka zo ƙasar nan ba zama take ba, kullum tana apartment ɗin Hajiya Babba” jinjina kansa ya yi hankalinsa na kan system ɗin ya ce“ai ta yi ta gama nan da 3weeks mun koma gida” da sauri ta kalleshi sai kuma ta ce“tafiya zamu yi?” jin yanda ta yi tambaya da damuwa ya sanya ya ɗago kansa ya sake kallonta murya a sake ya ce“lafiya dai?” girgiza kanta ta yi tana kirkiro murmushi ta ce“kawai dai tambaya nayi” ɗauke kansa ya yi ya ce“to tafiya zamu yi, karatunta ya tsaya duk da ana yi mata anan, sannan nima abubuwa sun fara min yawa” a sanyaye ta ce“tom Allah ya kaimu, amma sai bayan biki ko?” gyaɗa mata kai ya yi ya ce“eh Abba ya ce na tsaya a yi, that's why yasa na ce miki 3weeks da next week zamu tafi” “ai next week ɗin ne bikin right?” “eh haka ne” Ya ce yana rufe system ɗin, Zahra ta dinga kallonsa har ya tashi ya ɗauke system ɗin ya mayar inda yake ajiyewa sannan ya nufi toilet. **** Al-ameen ya kalleshi sai kuma ya ce“da gaske kana ganin wannan zai yi aiki?” Junaid ya ajiye wayar hannunsa ya zauna kan sofa sannan ya ce“eh mana zata yi bari kuma ka ga” dariyar mugunta Al-ameen ya dinga yi sannan ya ce“Allah sarki har ta bani tausayi wlh, yarinyar so calm da ita” harararsa Junaid ya yi dai dai nan aka buɗe ɗakin aka shigo. Wata babbar mata ce mai ƙiba sosai ta dinga kallonsu sai kuma ta ce“kuna nan kuna sana'ar taku ko?” sosa kai suka shiga yi, Al-ameen ya ɗan durƙusa ya ce“Mama ina yini?" “lafiya kalau Al-ameen ya Mamanka?” Murmushi ya yi ya ce“tana nan kalau wallahi, ta ce ma na gaisheki” jinjina kanta ta yi ta ce“ina amsawa, ku dai yiwa kan ku faɗa ku fito da matayen aure ku yi aure, wannan zaman babu inda zai kai muku” sunkuyar da kansa ya yi ya ce“tom Mama in sha Allah, Allah ya ƙara girma” Amin kawai ta ce sannan ta mayar da idanunta kan Junaid ta ce“daman Farhana ce ta zo take nemanka” ɗan tura baki ya yi kamar ƙaramin yaro ya ce“Mama dan Allah ki ce bana nan” wani banzan kallo ta masa kafin ta ce“ka fito ina jiranka malam” daga haka ta juya ta rufe musu ƙofar. Kallonsa Al-ameen ya dinga yi sai kuma ya fashe da dariyar yana zamowa daga kan sofa, Junaid ya dinga kallon sa fuskarsa a haɗe sai kuma ya mike yana faɗin “banza mara hankali” ko ta kansa Alameen bai bi ba ya ci gaba da dariyarsa, Ya yi tsaki sannan ya fice daga ɗakin shima.. **** Ƙarfe 5:00 na yamma Amma ta buɗe ɗakin ta shigo, kwance ta sameta ta rufe jikinta da bargo sai numfashi take a hankali, ta ƙaraso ɗakin tana yaye duvet ɗin ta ce“ke Nana” a hankali ta buɗe idanunta wanda take jin sun yi mata wani irin nauyi. Muryarta a sanyaye ta ce“na'am Amma” “ki taso Hajiya Babba na kiran ku” kamar zata yi kuka ta ce“Amma ki ce banida lafiya wallahi ba zan iya zuwa ƙauye ba” harararta Amma ta yi ta ce“ka da Allah yasa ki iya zuwa sai ki je ki faɗa mata hakan” daga haka ta saki bargon sannan ta juya ta fice daga ɗakin. Dakyar ta tashi zaune ta jingina da fuskar gadon tana hawaye a hankali, wani irin nauyi ta yi ƙirjinta y yi mata, daga jiya zuwa yau ji take kamar zuciyarta zata tarwatse, ban da tunani babu abin da take, she wish ace mutuwa ta zo ta ɗauketa yafi wannan halin da take ciki, she wish ace duk abin da ke faruwa mafarkine ba gaskiya ba, da sai ta yi sallar godiya ga Allah idan ta farka, sai dai ganin lokaci na tafiya ya sanya ta tabbatar da ba mafarkin take ba. A hankali taja idanunta ta rufe wanda hakan ya bawa hawayen dake kurmin idon samun damar zubowa, ta taune down lip ɗinta tana shessheƙar kuka a hankali, kiran sunanta da taji Amma nayi ya sanya ta tashi jiki babu kwari ta nufi toilet, wanka ta yi sannan ta fito ta sanya wata doguwar rigar material sannan ta ɗauka wani gogaggen hijab ta saka wanda ya saukar mata har ƙasa, ko mai bata samu zarafin shafawa fatarta ba ta fice daga ɗakin, tsaye ta samu Maimoon da Hamida sai Amma dake zaune, ta kalleta rai ɓace ta ce “da kin bari na dawo dakin sai ranki ya ɓaci wallahi” Bata ce komai ba ita dai, Maimoon ta ce“mu je mu ake jira” har ta fara tafiya sai kuma ta ce“oh i forgot my phone” daga haka ta koma daƙinta da sauri, a gaban mirror ta ɗauki wayar bata tsayawa kunnawa ba ta nufi waje, a compound ɗin gidan Hajiya Babba suka tadda sauran wanda za'a yi tafiyar dasu, domin yana ɗaya daga al'adar gidan duk sanda zasu yi auren ya'ya sai an kai su can Yola ruga sun gaida kakkaninsu na can, Hajiya Babba ce tsaye sai Abdusammad a kusa da ita, sai Safwan, Sultan, Hamid da kuma Aliyu. Matan kuma akwai Zahra dake riƙe da Noor, Juwaira, Hamida, Maimoon, Amrah, sai kuma Nana. Papa da ke gefen Hajiya Babba na dama ya kallesu ya ce“a kula dan Allah, Abdusammad kai ne babba na san ba zaka bari su yi wani wajen ba amma dan Allah su kula sosai” jinjina kansa ya yi a sanyaye ya ce“okay Papa in sha Allah” daga haka ya nufi motarsa. Ɗaya bayan ɗaya suka dinga shigewa mota, ita kuwa Nana taja ta tsaya dan sam bata ji zata iya zuwa ba, ganin kowa ya shige an barta ya sanya Hajiya Babba ta ce“a'a takwara lafiya dai?” kamar zata yi kuka ta ce“Hajiya banida lafiya fa” ƙarasowa inda take ta yi ta dafa jikinta jin babu zafi ya sanya ta ce“to meke damunki?” a sanyaye ta ce“kaina ciwo yake” Papa ne ya ce“to shiga mota idan kun tafi a hanya a siya maki magani” hawaye ne ya fara zubowa kan fuskarta ta ce“Papa ba zan iya zuwa ba wallahi, kaina ciwo yake sosai” haɗe rai ya yi a ɗan tsawace ya ce“kin shige mota ko sai ran ki ya ɓaci Nana!” yanda ya yi maganar cikin fargagi ya sanya ta dafe saitin zuciyarta tana wani irin numfashi, Hajiya Babba na ƙoƙarin magana Abdusammad ya fito daga motar yana kallonsu ya ce“mene ne?” “wai ba zata je ba” Papa ya yi maganar rai ɓace, kallonta ya yi sai kuma ya ja hannunta ba tare da ya ce komai ba, ya ƙarasa motar Safwan ya buɗe front seat ɗin ya turata yana mata wani irin mugun kallo ya ce“kar na sake jin bakin ki kin ji” gyaɗa masa kai kawai ta dinga yi dan gaba ɗaya ba'a hayyacinnta take ba, Ya rufe motar sannan ya nufi tasa motar ya shige back seat dan shi da driver zasu tafi suka ja motar suka yi gaba, ɗaya bayan ɗaya motocin suka dinga fita har suka bar cikin estate ɗin sannan kowacce ta fara gudu akan titi. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 24... Tun da suka fara tafiyar babu wanda ya ce da wani ƙala, kowa da abin da yake tunani cikin ransa, sai da suka ci rabin tafiyar sannan ya ɗan kalleta ta gefen ido, idanunta a lumshe suke sai dai babu tabbacin bacci take ko kuwa idanunta biyu, dan haka ya ɗan yi gyaran murya. Sarai Nana ta ji shi amma bata ko motsa ba ballantana ya saka ran da zata kalleshi, Safwan ya ɗan fara rage gudun da yake murya a sanyaye ya ce“Nana!” Dakyar ta iya raba laɓɓanta da juna murya can ƙasa ta ce“na'am” sai da ya yi kwana sannan ya sake cewa“meke damun ki na gan ki so quiet kamar ba ke ba?” a hankali ta juyo da idanunta ta ɗan kalleshi sai kuma ta ɗauke ta maida su kan titi tana kallon yanda suke shige bishiyu da tsaunuka ta ce“babu komai” jin yanda ta yi maganar da wata irin muryar wadda bai santa da ita ba ya sanya ya juyo da kansa ya kalleta, ganin ba shi take kallo ba yasa ya mayar da hankalinsa kan tuƙin da yake kafin ya ce “ko baki son auren nan?” Kallonsa kawai ta yi amma bata ce komai ba, bai damu da rashin amsawar tata ba ya sake faɗin “ki sanar dani tun yanzu, cause naga yanda yan uwanki ke shirye-shirye ke bakya yi, gaba ɗaya kin zama wata so silent ba kamar yanda ki ke ba, ki faɗa min ba ki da sha'awar aurena or what?” A hankali ta dinga kallonsa tana jin kamar ta ce masa eh bata so. Sai dai koda wasa ba zata iya furta hakan gare shi ba, dan haka ta yi shiru tana jin yanda bugun zuciyarta ke tsananta. Safwan bai sake cewa komai ba ganin ba amsa masa take ba, dan haka ya mai da hankalinsa gaba ɗaya kan tuƙin da yake, After 15mins ya ɗan saci kallonta ta gefen ido ganin idanunta a lumshe kamar ɗazu ya sanya ya ce “tun da ba zaki yi magana ni bari na sanar dake abin da ke raina” Buɗe idanunta ta yi ta ɗan kalleshi ba tare da ta ce komai ba, amma gaba ɗaya hankalinta yana kansa tana son taji shi mene ne nasa ra'ayin akan auren. Numfasawa ya yi cikin nutsuwar data gama ratsa shi ya fara cewa “Nana tun da nake ban taɓa miki kallon wadda watarana zan iya aura ba, na yi tunanin za ki ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin ƙannena, sai dai babu wanda ya san abin da zai faru gaba, ban yi tunanin irin wannan lokacin zai zo ba, da har za'a haɗani aure dake, duk da yarintar ki.” ya ɗan numfasa sannan ya ci gaba da faɗin “sai dai a wannan yan kwanakin ina ganin komai kamar mafarki, tamkar ba gaskiya ba, har yanzu zuciyata ta kasa yarda cewa kece wadda zan aura, ta kasa aminta da hakan, gani nake kamar za'a fasa auren nan.” ya ƙare maganar yana kallonta to see her reactions. Nana da ke kallonsa tun ɗazu ta ɗan janye idanunta tana kallon fararen kyawawan faratanta muryarta a sanyaye kamar koda yaushe cikin kwanakin nan ta ce “nima haka Yaya, kullum gani nake kamar ba gaske ba, ji nake kamar za'a ce an fasa aurena da kai, but u no what?” Ta yi maganar tana kallonsa, girgiza kansa ya yi yana ɗan ƙara gudun da yake, ta sauke numfashi sannan ta ce“i wish a ce an fasa ɗin, cause am not ready to get married, ban shirya zama matar gida ba, I'm too young to carry that burden..” ta yi shiru jin kuka na neman kwace mata, Safwan ya dinga kallonta fuskarsa ɗauke da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, ya kasa tantance abin da yake ji game da ita a wannan lokacin, tausayi ne? Ko kuwa soyyaya ce?. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana ɗan faɗaɗa fuskarsa ya ce“kamar dai ni Nana, sai dai ni ba wai ina son a fasa aurena bane, a'a ina son nayi aure da wata ne bake ba?” Da sauri ta kalleshi fuskarta ɗauke da mamaki gami da farin ciki, ta ɗan girgiza kanta ta ce“da gaske Yaya? Baka sona? Baka son ka aureni? Are ur sure?” Girgiza kai Safwan ya yi yana kallon titi ya ce“that was not what i meant, ba wai bana sonki bane Nana, ina sonki, akan me zan ce bana son ki? Look at you, babu namijin da zai ce baya son yarinyar kamar ki, ga kyau ga hankali sannan ga nutsuwa, kina da qualities daya kamata ace an so ki saboda su, dan haka ba wai bana son ki bane, a'a kawai dai akwai wadda zuciyata ke ƙauna, wanda a yan kwanakin nan nake jin idan bada ita ba bazan iya rayuwa ba, ko bacci nake sai na farka na yi tunaninta, idan dare ya yi burina gari ya waye naje na ganta. And you know what?” Ta girgiza kanta tana sake gyara zamanta, numfasawa ya yi ya ce“duk wannan son da nake mata bai kai rabin wanda take min ba, tana sona fiye da yanda nake sonta, but unfortunately we two can't be together!” ya ƙare maganar jiki a sanyaye babu wani kwari. Girgiza kanta ta yi a hankali tana kwaɓe fuskarta kafin ta ce“ayyah Yaya sorry kaji, to mene ya hanaka ka faɗawa kowa ita ka ke so?” ɗan murmushin ya yi ya ce“idan na faɗa ma ba zai wani amfani ba, babu wanda zai ɗauka maganata serious balle har a dubata, kawai na yanke shawara araina ne” Nana ta dinga kallonsa sai kuma ta ce“mene shawarar?” “Idan na aureki daga baya saina aureta as a second wife” ya yi maganar da zallar gaskiyarsa dan shi sam ƙarya bata daga cikin layinsa. Kallonsa kawai Nana ta dinga yi lokaci ɗaya jikinta ya yi sanyi, ta koma ta jingina da bayan kujerar ta yi shiru tana tunani. Safwan ya ɗan kalleta sai kuma ya ci gaba da tuƙinsa jin bata ce komai ba. Njomboli, Yola South. Karfe 7:10 na magriba motocinsu suka fara parking a ƙofar babban gidan, ɗaya bayan ɗaya kowa ya fara fitowa suna sauke ajiyar zuciya wasu na hira ƙasa-ƙasa, Nana ta dinga kallon ƙaton gidan wanda ya kasance shine kaɗai kerarren gida kaf Njomboli da kallo, Babban gida ne wanda aka ƙawata shi tamkar a cikin gari yake, kasancewarsa shi ne asalin gidan su Late Alhaji Muhammad Shuwa, kuma nan ne inda sauran danginsu suke, Mutanen gidan suka firfito fuskarsu ɗauke da farin ciki mara misaaltuwa suna musu sannu da zuwa, kafin daga bisani suka musu jagora har cikin gidan. A ɗakin Baba Atta suka sauka, wadda ta kasance yar uwa ga late Muhammad Shuwa wadda suke uba ɗaya, tsohuwa ce sosai amma Allah ya mata kyan jiki dan ba zaka taɓa cewa ta yi shekarunta ba idan tana wasu al'amuran, gaba ɗaya a ɗakin suka zauna dan ba ƙarami bane, ta dinga kallon su fuskarta ɗauke da fara'a cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce “Sannunku da zuwa, sannu sannu!” Wasu a ciki ne suka amsa, wasu kuma suka yi shiru dan duk a gajiye suke, Abdusammad ne ya tashi ya koma kusa da ita dan daman tafi saninsa a cikinsu kasancewar babba kuma da yana zuwar musu sosai sanda yana ƙarami, Ya ja kumatunta yana murmushi cikin harshen fulde ya ce “Yar tsohuwa mai ran ƙarfe” Doke hannunsa ta yi tana Harararsa ita ma cikin harshen da ya yi mata magana ta ce“rabu dani kai, ai nayi fushi da kai” murmushin da yake ƙara masa kyau ya yi kafin ya ce“fushi kuma ki rufa min asiri Atta, idan ki ka yi fushi dani ina na kama? Har yarinyata fa na kawo miki” Washe bakinta wanda haƙora suka fara zubewa daga ciki ta yi ta ce“haba da gaske oh ni Atta ahe zan ga jikata?” dariya ya yi yana kiran Noor da ke hannun Zahra ya ce“gata nan kamar ku ɗaya da ita” ya ƙare maganar yana miƙa mata hannun Noor, riƙeta ta yi tana murmushi ta ce“masha Allahu wannan yarinyar ba da kai take kama ba kuwa?” Girgiza kansa ya yi ya ce“a'a ki kalleta da kyau ko sai na saka an miki tabarau?” duka ta kai masa tana cewa“kaji min ɗa? Idanuna sun fi naka kwari bari kaji” Sai da ta ɗora Noor kan cinyarta sannan ta ce“wai ina ma matar taka?” da hannu ya nuna mata Zahra dake zaune opposite ɗin su ta sunkuyar da kanta. Atta ta kalleta sai kuma ta kalli su Nana da ke zaune a ƙasa ta ce “Oh lalashewa ta sameka Arɗo” Da ɗan mamaki ya ce“lalacewa kuma Atta?” Gyaɗa masa kai ta yi sannan ta sake kallon Zahra tana taɓe baki ta ce“saboda baka jin magana, ka je ka haɗu da arnakun banza ya sanya ka auri wadda ba jininka ba, ko kunyar Ubangiji baka ji, to wallahi da sake sam ba zan yarda ba, sai ka auri jininka wallahi, dan Yaya ba zai taɓa alfari da kai ba idan ka mutu akan wannan turbar” Ta ƙare maganar tana lakuce masa hanci, murmushi kawai ya yi yana satar kallon Zahra wadda ta sunkuyar da kanta ya ce“haba Atta, mene ne haka? Daga zuwanmu sai ki fara faɗa?” wani kallon tara saura kwata ta masa sannan da ƙarfi ta ce “Kaltume! Salame!” Shigowa suka yi a tare suna faɗin “gamu Atta” kallonsu ta yi sai kuma ta kalli su Nana ta ce“a kai su ɗaki su huta sai a kawo musu abinci” “Ni dai fura nake so Atta” Abdusammad ya ce da sauri, murmushi ta yi ta ce“to jikin Ahmadu ai daman nasani shiyasa tun da Kabiru ya ce min kuna hanya na sa aka tatso nono” jinjina kansa ya yi ya ce“Allah Atta? To nima na zo miki da tsaraba” washe baki ta yi ta ce“me ka kawon?” maƙe kafaɗa ya yi kamar ƙaramin yaro ya ce“sai kin fara bani fura sannan zan baki nima” taɓe baki ta yi ta ce“to ai sai ka yi ta yi” ta mai da Idanunta kan su Salame da suke tsaye har sannan ta ce“wai baku ji bane ku ke kallona kamar wasu gumakan farko?” ta ƙare maganar a ɗan fusace, murmushi kawai Abdusammad ke yi dan daman ya san halin jarabarta. Jiki na rawa suka kalli su Maimoon cikin gurɓatacciyar hausar su suka ce“mu je kun ji” Ɗaya bayan ɗaya suka miƙe ban da Nana data ko motsi bata yi ba, Atta ta kalli Aliyu wanda tun shigowarsa bai ce komai ba ta ce“wannan ba Ali bane?” a sanyaye Aliyu ya ce“ni ne Atta” harararsa ta yi ta ce“aa to kaje da mugun halin ka, tashi ku je a buɗe muku sabon sashin can na yan jimeta” to kawai ya ce dan shi ba wani hira suke da ita saboda jarabarta ya kalli su Sultan ya ce“mu je ko” okay kawai suka ce sannan suka tashi suma suka fice, wajen ya rage daga Abdusammad sai Zahra da kuma Nana, wani kallo Atta ta yiwa Zahra sannan ta ce“ke ba zaki tashi bane?” jiki a sanyaye Zahra ta mike ta fice daga ɗakin dan ita bata taɓa haɗuwa da Atta ba tun da ta auri Abdusammad, duk yanda yake bata labarinta yau ta tabbatar da tafi gaban nan, ta mai da idanunta kansa dan sam bata lura da Nana ba ta ce“daman na ajiye maka gilishi so nake su hita na sa a ɗauko maka” murmushi kawai ya yi sannan ya ce“yauwa shiyasa nake sonki ai” “bari kaji amma wallahi sai ka sake aure dan ba zaka zauna da jinin da ba naka ba, idan mata sun ƙare a jimeta sai ka ɗauki ɗaya anan ka shige da ita” Kallonta kawai Abdusammad ya yi sai dai ban tanka ta ba, dan yana sake magana zata iya rantsewa, Kaltume ce ta dawo ɗakin tana kallonta cike da girmamawa ta ce“Atta ita wannan ba tafiya zata yi bane?” ta ƙare maganar tana nuna Nana dan tun ɗazu take jiran taga ta fito kuma ta ji shiru. Mitsi-mitsi Atta ta yi da idanu tana kallon Nana ta ce“wace wannan?” Abdusammad ne ya juya yana kallonta ganin yanda ta sunkuyar da kanta, babu yabo babu fallasa ya ce“Nana” a hankali ta ɗago kanta ta kalleshi da kumburarrun Idanunta wanda hawaye ya cika su,Baki buɗe Atta ke kallonsu sai kuma ta ce“wace Nana?” “Nana da ki ka sani ya gidan Abba” Atta ta dinga kallon Nana da bayyanin mamaki kafin ta ce“iko sai mai sama! Yanzu wannan yar jaririyar ce ta girma haka, yarinyar wajen Ahmadu dai?” gyaɗa mata kai Abdusammad ya yi ta sake jinjina kanta sannan ta kalleta ta ce“ke zo nan” dakyar ta iya miƙewa tsaye dan zazzaɓi ne a jikinta ta ƙarasa gaban Atta sannan ta tsuguna. Taɓa ta ta yi tana ɗago fuskarta sosai ta ce“gata kuma kamarta ɗaya da babanta” murmushi kawai Abdusammad ya yi ya ce“eh suna kama da Abba” sakinta ta yi tana cewa“amma girmanta ya bani mamaki, rabon dana ganta tun sanda naje Jimeta kafin mutuwar Yaya” Abdusammad ya ce“ai kin daɗe rabon ki da Jimeta gaskiya” sake kallon Nana ta yi ta ce “To ai kuwa ka samu mata, wannan zankaɗeɗiyar yarinyar ba'a bari ta auri wani ba, daga ganinta za'a yi mace! Dan haka na maka mata ta biyu!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 25... Kallonta ya dinga yi, sai kuma ya ɗan haɗe ransa yana kallon Nana ya ce“ke tashi ki tafi” kafin ta yi magana Atta ta yi saurin faɗin “a'a ba zata tafi ba wallahi, ban gama ganin jikata ba” ɗauke kansa ya yi bai sake magana ba, Atta ta tashi ta shige kitchen ɗinta. Bata jima ba ta fito hannunta da wani madaidaicin bowl mai tsafta, ta miƙa masa tana cewa“gashi nan na dama maka” amsa bowl ɗin ya yi yana murmushi idanunsa zube kan tsaftacciyar damammiyar furar wadda aka zubawa zuma akai, Nana ta ɗan leƙa bowl ɗin tana murmushi, ganin bai ce komai ba yasa Atta ta ce“idan ka gama sai kaje sashen Baba ka kwana” toh kawai ya ce yana ɗaukan ludayin da ke ciki furar ya fara juyawa a hankali. Atta ta ja hannun Noor ta ce“muje ciki yar nan” daga haka ta fice daga parlon gaba ɗaya, Bismillah ya yi sannan ya kai ludayin furar bakinsa, daɗi da garɗin nonon ya sanya shi lumshe idanu. Nana da ke kallonsa ta lashe baki kamar ita ce ke shan furar, ganin yana ta shan furarsa ba tare da ya kalleta ba ya sanya ta tashi ta zauna gefensa tana murmushi ta ce “uncle” Yanda ta yi maganar a ɗan shagwaɓe ya sanya ya ɗago kansa ya kalleta, washe masa baki ta yi ta ce“nima zan sha furar” sai da ya ajiye ludayin cikin furar sannan ya ce“mene?” yanda ya yi maganar babu alamun wasa a tattare dashi ya sanya ta ɗan kama kanta. Murya a shagwaɓe kuma ta ce“to ni ba zan sha ba?” dungure mata kai ya yi ya ce“ni abokin wasanki ne? Tashi anan” rau-rau ta yi da idanu kamar za ta yi kuka, ya taɓe baki sai kuma ya ci gaba da shan furarsa. Tana nan zaune har ya kusa shanyewa ta ɗan leƙa bowl ɗin taga sauran kaɗan sai kawai ta fashe da kuka tana murza idanunta, ɗago gajiyayyun idanunsa ya yi ya ɗan kalleta sai kuma ya ce“mene kuma?” “Sai ka shanye baka bani ba” Ta yi maganar cikin kuka, girgiza kansa ya yi sannan ya ɗebo furar ya kai mata ludayin baki, kallonsa kawai ta yi sai kuma ta kalli ludayin. A hankali ta buɗe bakinta ya zuba mata furar, lumshe idanunta ta yi tana tauna furar, ya kalleta yana murmushi sai kuma ya dungure mata kai ya ce“kwaɗayayyiya kawai” turo bakinta ta yi a hankali ta ce“ni ɗin uncle” sai da ya sake kai furar bakinsa sannan ya ce“eh ɗin ke” daga haka ya ɗebo ya kai mata baki, haka suka dinga shan furar tare har suka shanye, ya miƙa mata bowl ɗin yana gyatsa a fili ya ce “Alhamdulillah” Sannan ya miƙe yana kallonta ya ce“tashi ki tafi wajen su Maimoon” Toh kawai ta ce sannan ita ma ta miƙe ta fara kai bowl ɗin kitchen sannan suka fito a tare. Kalle-kalle ta dinga yi a babban tsakar gidan, ganin yanda mutane ke ta shige da fice yasa ta rasa in da zata yi, ganin yana shirin barin wajen yasa ta ɗan ƙara sauri har ta cimmasa sannan ta ce“uncle to ina zan je?” juyowa ya yi yana kallonta fuskarsa a haɗe ya ce“Nana ba zaki kyaleni na huta ba kenan?” sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta, ya ɗan kalli tsakar gidan sai kuma ya ja hannunta suka bar wajen. **** Washegari da sassafe suka yi wanka suka shirya dan zuwa gaisar da sauran dangi da yan uwa, Nana na ƙoƙarin rufe ƙaramar trolley ɗin Maimoon bayan ta ɗauki mayafin Zahra ta shigo ɗakin, Kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kanta, lokaci ɗaya ƙirjinta ya dinga wani irin bugu. Zahra ta zauna gefen gadon tana kallonta fuska a sake ta ce“Nana!” ɗago fuskarta ta yi ta ɗan kalleta a sanyaye ta ce “Na'am” Sai kuma ta mayar da kanta kan abin da take, Murmushi ta yi ta ce“ya muke ciki ne da ke akan maganar mu?” ɗago jajayen idanunta ta yi ta kalleta amma bata ce komai ba. Zahra ta girgiza kanta ta ce“naga kina shirin kuka? Mene ne abun kuka anan?” “Dan Allah dan annabi aunty ki yi hakuri, dan girman Allah...” ta ƙarasa maganar cikin shessheƙar kuka, haɗe rai Zahra ta yi ta mike tana kallonta ta ce“da kin yi min wani abu ne Nana? Ni na ce ba zan haƙura ba? Ai bani za ki bawa haƙuri ba, zuciyarki ita zaki bawa haƙuri akan Safwan, ki san yanda zaki yi ki ce baki sonsa” Cikin kuka Nana ta ce“wallahi ba zan iya ba Aunty, ke da kanki ki ka ce kada nayi abin da zai ɓata sunan Abbana, to idan har zan ce ba zan auri Yaya Safwan dai dai yake da ɓata sunansa ai” “To ki ɓata ɗin. Sai me dan kin ɓata sunansa Nana?. Look ni bai dameni ba ko ki ɓata sunansa ko kar ki ɓata, kawai abin da na sani shi ne ki fasa aurensa!” Zahra ta yi maganar cikin ɓacin rai. Ganin bata ce komai ya sanya ta yi kwafa ta sake cewa“kuma ki sani idan har baki yi abin da nace ba nan da kwana uku wallahi tallahi sai na tona miki asiri Nana! Sai na tabbatar da hotunan ki sun shiga in da bakya tsammani” Cikin kuka ta rarrafa gabanta ta rike ƙafafunta ta ce“dan Allah Aunty kada kimin haka, dan girman Allah ki rufa min asiri, wallahi idan Abbana ya gani zai iya mutuwa” hankaɗeta Zahra ta yi tana mata wani shegen kallo ta ce“to sai me. Idan ya mutu ni ce na mutu? Ai gara ma ya mutu domin yana ɗaya daga cikin waɗanda suke haddasa wannan fitinar ta auren zumunci, wallahi Nana kin ji har na rantse idan har baki yi abin da nace ba sai na bata miki” Ta janye jikinta ta fice daga ɗakin fuuu.. Ban da kuka babu abin da Nana take, ta dafe saitin zuciyarta dake mata wani irin zafi. Sannan ta tashi ta koma gefen gadon ta zauna tana ci gaba da rera kukanta. Ƙarfe 1:20 na rana Maimoon ta shigo ɗakin hannunta riƙe da ƙaramin kofi, sai da ta zauna gefen gadon sannan ta taɓa Nana tana cewa“ke Nana! Ke!” a hankali ta buɗe idanunta wanda suka kumbura saboda kukan da taci, ta tashi zaune tana kallon Maimoon fuskarta a haɗe ta ce“mene ne?” “kina ta faman bacci tun ɗazu har mun je gidajen wasu” Taɓe baki Nana ta yi sai kuma ta ce“to ni daman bana son naje ko ina ai” Maimoon ta tashi tana harararta ta ce“to kar ki so kuma ki je Atta na kiranki” sauka tayi daga kan gadon tana gyara zaman hular kanta ta nufi toilet, da idanu kawai Maimoon ta bita sai kuma ta tashi ta fice daga ɗakin. Ƙarfe 2:30 na rana suka haɗu dukkansu a parlon Atta, sai hira ake gwanin ban sha'awa, Atta ta kalli su Maimoon ganin babu Nana a ciki ya sanya ta ce“wai ina yarinyar nan naga tun da safe ban ganta ba” Maimoon na kokarin magana Nana ta yi sallama ta shigo dakin, Atta ta washe baki tana cewa “yauwa yarinyar kirki shigo kin ji” jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa inda take zaune ta zauna gefenta, Atta ta riƙe hannunta ta ce“baki da lafiya ne?” girgiza mata kai ta yi a sanyaye ta ce“a'a lafiyata kalau” jinjina kai Atta ta yi sannan ta ci gaba da musu hira tana basu tarihin rayuwarsu a da, Nana ta ɗan zame jikinta ta ɗora kanta bisa cinyar Atta tana lumshe ido. Suna nan zaune har aka fara kiraye-kirayen sallar la'asar sannan mazan suka tashi dan tafiya masallaci, Matan kuma ta ce su shiga cikin ɗakinta su yi sallar acan, Zahra ta miƙe ganin Abdusammad yana ƙoƙarin fita, Da idanu Atta ta dinga binta ganin tana shirin bin bayansa yasa ta ce “Ke ina zuwa ne?” Cak Zahra ta tsaya kafin ta juyo a hankali tana kallon Atta data tsareta da idanu.. “Naga kina wani kokarin bin sa lafiyarki dai?” Murya a sanyaye ta ce“a'a Hajiya daman zan masa magana ne” Cike da faɗa Atta ta ce“lalashewa ta same ki ƴar nan, sabidda baki da kunya irin ta fulani yasa zaki iya bin miji a gabana? To mu ba haka muke ba.Sam wannan ba ɗabi'ar mu ba ce, kuma ba zamu lamunci wannan abun ba!” Ita dai Zahra shiru ta yi tana kallon Atta, ganin bata sake cewa komai ba ya sa ta koma ta zauna dan ita tana fashin sallah. A hankali Atta ta tashi Nana da bacci ya fara ɗauketa ta ce“tashi muje ki yi sallah” to kawai ta ce a sanyaye sannan ta tashi tana murza idanunta ta nufi cikin ɗakin Atta. Sai da taga Nana ta bar wajen Sannan ta kalli Zahra da tayi shiru ta ce“kin ga wannan yarinyar. Ita ce wadda mijinki zai aura nan kusa, dan ba zai yiwu ya zauna da ke ɗaya bare ba! Dole ya auri jininsa” Da sauri Zahra ta kalleta fuskarta da wani irin mamaki, Atta ta jinjina kanta tana watsa mata wani kallo ta ce“eh!. Haka na ce, kuma dole ya bi umarnina. Dan babu wanda ya isa ya bijirewa abin da nake so kaf dangin Shuwa wallahi, Saboda haka ba zai yiwu ya ci gaba da zama da wadda bata danganci danginsa ba, dan ni ban ji daɗin haihuwar da ku ka yi dashi ba! So nayi ya haihu da jininsa wadda zamu yi alfahari da ita!” Zahra ta dinga kallon Atta ganin yanda take gasa mata magana hankali kwance, ta mike tana shirin barin ɗakin Abdusammad ya shigo, faɗawa ta yi jikinsa tana fashewa da kuka, Ya ɗora hannunsa ɗaya a bayanta yana kallonta da mamaki ya ce “Mene ne?” Kasa cewa komai ta yi sai sake ɗora kanta da ita a ƙirjinsa tana ƙara sautin kukan nata. Atta ta miƙe tana harararta ta ce“to da ki ke kukan dukana zai yi? Kuma aurene babu fashi muddin ina raye sai ya yi wani aure wallahi kuma sai ya auri Nana?” Da sauri Abdusammad ya kalleta rai ɓace ya ce“Atta!” Wani mugun kallo ta yi masa kafin ta ce“zaka dakeni ne? Na ce zaka dakeni ne? Wallahi sai ka auri Nana muddin ina numfashi a duniyar nan” Janye Zahra ya yi daga jikinsa yana kallonta cikin ɓacin rai ya ce “Atta wai maganar me ki ke yi haka ne? Wace Nana? Ko zan auri kowa a duniya me zan yi da Nana? Yarinyar dana raina da hannuna kuma ita ki ke son na aura?. And beside ma Nanar da ki ke magana har da ita a wanda za'a ma auren next week, Safwan zata aura, dan haka dan Allah ki daina wannan maganar kina zubar min da mutuncin gaban mutane. Sannan Zahra matata ce, na aureta saboda ina sonta ki daina zaginta dan Allah! Dan Allah Atta” Atta ta yi mitsi-mitsi da idanunta cike da masifa ta ce “To ina ruwana da matarka ce? Kai ta dama bamu ba, abin da muka sani shi ne sai ka ƙara aure. Sannan da ke maganar wai za'a yiwa Nana aure, ai ba auren aka yi ba, to wallahi bari kaji ko auren aka yi sai ya saketa ka aureta! Kai nake so ka aureta ba wani ba, kuma babu wanda ya isa ya hanani zartar da wannan hukunci!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 26... Zahra dake tsaye tana kallon Atta ta fashe da kuka ta juya ta gudu ta bar ɗakin tana rufe bakinta da hannunta, Bai kalleta ba haka kuma bai yi yunƙurin bin bayanta ba. Sai ma takowa daya fara yi ya zo gaban Atta, ganin yanda ta haɗe ranta sai huci take ya sanya ya ɗan sassauta nasa fushin babu yabo babu fallasa ya ce“Atta dan Allah abar wannan maganar, ki daina sako Nana cikin maganar nan, aure fa za'a mata” wani irin kallon sheƙeke Atta ta yi masa a zafafe ta ce“to ba zan barta ba. Idan ka ji na bar maganar nan to an yi abin da nake so ne” Abdusammad ya dinga kallonta dan ya rasa abin da zai ce mata kuma, Ya girgiza kansa sai kuma ya juya ya bar ɗakin. Da harara ta bishi sannan ta ce“to zan ji tsoronka ne? Wallahi sai an yi abin da nake so idan ba haka ba hankalin kowa ba zai kwanta ba!” Atta ta ƙare maganar tana nufar ɗakinta.. Yana tura ƙofar ɗakin ya fara jin shessheƙar kukanta, Ya ƙarasa shiga ciki yana kallonta tana haɗe yan kayan da ta zo dasu a ƙaramar trolley ɗin gabanta, Sakin ƙofar ya yi sai kuma ya ja ya tsaya a wajen ya naɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata idanu. Zahra ta kammala haɗe kayan nata tana kuka ta zura hijabi har ƙasa sannan ta juyo da shirin fita ta ganshi tsaye jikin ƙofa. Kallonsa ta ɗan yi sai kuma ta ɗauke kanta tana sake nufo ƙofar da shirin fita, murya a sanyaye kamar babu abin da ke damunsa ya ce “Fateemarh!” Yanda ya yi maganar cike da nutsuwa ya sanyata dakatawa, ta tsaya cak inda take har sannan tana shessheƙar kuka. Furzar da iska ya yi daga bakinsa sannan ya baro jikin ƙofar ya shiga takowa har gabanta, ƙamshin turarensa daya cika mata hanci da kuma kaifin idanunsa ya sanya ta sunkuyar da kanta lokaci ɗaya taji tsigar jikinta na tashi. Kallonta ya dinga yi kafin a hankali ya sanya tattausan hannunsa ya ɗago haɓarta yana kallon kyakkyawar fuskarta ya ce “Mene ne?” Kamar jira take ta faɗa jikinsa tana sakin wani irin kuka, ta ƙanƙameshi kamar zata ɓara ƙirjinsa gida biyu. Abdusammad ya ɗan yi murmushi sai kuma ya saka hannayensa duk biyun ya zagayeta a jikinsa, a hankali kuma cike da nutsuwa ya dinga shafa bayanta ba tare da ya ce komai ba. Bayan mintunan da basu shige biyar ba ta fara rage sautin kukan nata. Ya yi shiru yana lumshe idanunsa har ta yi tsit gaba ɗaya sai shessheƙar kukan da bata daina ba. Sai a sannan ya ɗago kansa daga bayanta yana kallonta ya ce“kukan na mene?” Girgiza kanta ta yi tana shirin fashewa da wani sabon kukan ya ɗora hannunsa a baki cikin wata irin murya ya ce “shiiiii!” Haɗiye kukan nata ta yi, Ya ja kumatunta sannan ya ce“ just tell me kukan me ki ke?” Zahra ta dinga kallonsa da runannun idanunta, kenan bai ma san kukan me take ba? Bai san abin da aka yi mata ba? Sai kawai ta sake jin wani sabon kukan na kwace mata. Abdusammad kallonta ya dinga yi sai kuma ya girgiza kansa wannan karan fuskarsa a haɗe ya ce“Idan baki min shiru ba zan ɓata miki rai kuma!” Sanin babu wasa acikin lamarinsa ya sanya ta yi shiru tana murza idanunta, ya taɓe baki yana ƙarewa trolley ɗin hannunta kallo ya ce“get ready nan da 1hr zamu tafi” Tamkar ta zuba ruwa a ƙasa tasha haka taji saboda daɗi da farin ciki, dan kwata-kwata bata ji daɗin garin ba, kuma ba kowane sanadi ba illa Atta, wadda tun zuwansu bata barta ta huta da jarabarta ba. Sai da ta goge hawayen fuskarta sannan ta ce“Doctor tafiya zamu yi?” gyaɗa mata kai kawai ya yi yana nufar toilet. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta zare hijabin jikinta ta koma ta zauna gefen gadon. **** Sultan ya dinga kallon Safwan rai ɓace ya ce“amma baka cikin hayyacin ka ko? Baka san me ka ke cewa ba ko?” Safwan dake tsaye yana rufe agogon hannunsa ya ɗan yi gajeran murmushi sai kuma ya ce“Ya Sultan na san me nake mana, kaga maganata ta yi maka kama da ta wanda bai san me yake ba?” a fusace Sultan ya mike tsaye yana masa wani irin kallo ya ce“amma idan haka ne baka da hankali wallahi! Wace irin rayuwa ce wannan Safwan?” “Me nayi kuma? Dan na sanar da ita gaskiya?. Wallahi Yaya ban taɓa jin son wata yarinya cikin raina sama da Siyama ba, Ni ita zuciyata ke so, amma nasan banida ikon aurenta a yanzu. Dan haka ba zan zafafa na ce dole sai ita ba, zan karbi Nana hannu bibbiyu. Amma dole ne na sanar da ita cewa ina da wadda nake so, kuma nake da burin aure. Saboda haka kar ta saki jikinta tayi tunanin da ita ɗaya zan zauna”. Jinjina kai Sultan ya yi yana kallonsa sai kuma ya ce“okay kayi duk yanda ka ke ganin shi ne dai dai, ba zan hanaka ba, amma ina son ka sani idan har ka cutar da yarinyar nan wallahi tallahi Allah ba zai bar ka ba, idan har ka yi amfani da aurenka wajen zaluntarta Allah sai ya saka mata!” Yana gama faɗar haka ya fice daga ɗakin fuu ba tare da ya jira ta bakin Safwan ba. Taɓe baki Safwan ya yi ya bi shi da idanu sai kuma ya ci gaba da abin da yake. **** Ƙarfe 5:10 na yamma suka fito ƙofar gidan, Atta dake riƙe da hannun Nana ta kalli Abdusammad daya haɗe ransa kamar ba shi ba ta ce“to da ka ke haɗe rai shi ne zai hanani abin da naga dama?” kallonta kawai ya yi amma bai ce mata komai ba, ta taɓe baki ta ce“aaa to kaje da baƙin halinka, Ni kada ka tafi dani a baki, baƙonka Annabinka” duk yanda ta bashi dariya dakewa ya yi babu yabo babu fallasa ya ce“Sai kun zo Atta” To kawai ta ce masa dan sam bai bata fuskar da zata sake wata maganar ba, ya shige motarsa dan daman tuni Zahra ta shiga. Da kyar su Maimoon suka rabu da Atta dan magiya suka dinga mata akan ta zo su tafi tare amma sam taƙi yarda ta ce sai ana i gobe ɗaurin aure zata zo. Babu yanda suka iya da ita haka suka haƙura suka shiga mota, ta sake sallama dasu Aliyu sannan ta kalli Nana fuskarta ɗauke da damuwa ta ce “Ai da bake za'a yi aure ba ai zaman ki zaki yi anan ma tafi tare” murmushi kawai Nana ta yi dan ita ma taji daɗin zama da ita, Muryarta a sanyaye ta ce“to Atta ki zo mu tafi tare mana” girgiza kai ta yi ta ce“a'a ku dai je ina nan tawowa” Langwaɓar da kai Nana ta yi ta ce“to sai kin zo” daga haka ta nufi motar Safwan tana daga mata hannu. Sai da motocinsu suka bar ƙofar gidan sannan Atta da sauran jama'ar suka koma ciki cike da begensu. Har bayan mintuna talatin da fara tafiyarsu babu wanda ya ce wa wani komai, Nana ta mai da kanta gefen titi tana kalle-kalle wanda take jin yana ɗan ɗebe mata kewa, she wish ace ba yau zasu koma gida ba, dan daga jiya zuwa yau ta ji wani abu yana ɗan ragar mata daga cikin damuwarta. Saɓanin kwanakin baya da kullum take yini babu walwala. Ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar data tafi, ta kalli wayar dake kan cinyarta sai kuma ta ɗauka, ganin wanda yake kiran ya ta matse gefen wayar ta mayar ta ajiye sannan ta ci gaba da kallon da take. Ko sakan biyu ba'a ayi ba aka sake kira, ta ɗan saci kallon Safwan dake tuƙinsa ba tare da yana lura da ita ba. Ta sake katse kiran tana tura baki a hankali, ko ajiye wayar bata yi ba ƙarar faɗowar saƙo ya shigo, ta buɗe wayar ganin a WhatsApp ne ya sanya ta shiga, numbern Junaid ta gani dan ta yi unblocking ɗinsa tun bayan daya nemi hakan, a hankali ta buɗe saƙon ganin kamar hotuna aka turo ya sanya ta danna downloading tana jin bugun zuciyarta na tsananta, kamar kiftawar idanu haka hotunan duka suka buɗe, ta yi saurin kifa wayarta bayan ta ga abin da ya turo. Dakyar ta iya mai da kanta gefen titi hawayen dake cikin kurmin idonta ya samu damar gangarowa kan fuskarta, ta ɗan ja numfashi ba tare da sauti ba tana kallon hotunan a cikin idanunta. Sabon sakon daya shigo ya sanya ta sake firgita, ta kasa ɗago wayar saboda fargabar abin da zata gani, sai dai sanin bata da wata mafita data shige ta buɗe saƙon ya sanya ta ɗago wayar, sakone ya rubutu kamar haka _Ina sake tuna miki ne, idan har ki ka ɗauki maganata wasa to tabbas ranar Lahadi za'a wayi gari da maganar waɗanda hotunan naki a kowace kafa ta sada zumunta, sannan bugu da ƙari Abba zai yi farin cikin da bai taɓa yi ranar ba, domin ranar ta kasance daya daga cikin ranaku mafiya tsada a cikin rayuwarsa. Wato ranar auren yar sa! na san ba zaki so ya rasa wannan farin cikin ba, ko nace baƙin ciki mara misaaltuwa ya maye gurbinsa. Dan haka ki san duk yanda zaki yi a fasa daura miki aure da wannan mutumin, shawara nake baki._ Nana ta dinga kallon screen ɗin wayar tana jin wani irin abu nayi mata yawo tun daga tsakar kanta har zuwa ƙafafunta, gaba ɗaya jikinta ya yi wani irin saki, dakyar ta iya danne hoton da maganar ta yi deleting ɗin su daga kan wayarta. Kafin ta kashe wayar gaba ɗaya tana lumshe idanunta, hawaye suka dinga zuba daga cikinsu kamar an buɗe famfo. Safwan dake lura da ita tun ɗazu ya ɗan taɓe baki dan duk tunaninsa maganar auren ce har yanzu bata haƙura ba. Ganin sun fara shigowa cikin gari ya sa ya yi gyaran murya ba tare da ya kalleta ba ya ce “Ina son maganar da muka yi dake jiya ta zama sirri tsakanina da ke, koda wasa banson na ji ta a wani wajen, ka da ki kuskura ki faɗawa wani koda kuwa a cikin labari ne” Ya ƙare maganar yana kallonta, Bata amsa mata ba, dan babu alamar ma tana sauraren abin da yake cewa, she's just busy crying. Dan haka a ɗan tsawace ya ce “Ke Nana!” Wannan karon ta ji shi sai dai nauyin da idanunsa suka mata shi ne ya hanata buɗe su, muryarta cikin wani irin sanyin da ya shige misali ta ce “na'am” “kin ji abin da na ce ko?” Gyaɗa masa kai ta yi duk da bata jin ba, kuma bata da burin jin koma mene ya ce mata ɗin. Ya jinjina kansa ya ce“good” sannan ya ci gaba da tuƙinsa ba tare da ya sake cewa komai ba. Har suka ƙaraso gida bata daina kuka ba, kuma ko sau ɗaya bai yi tunanin rarrashinta ba, a ranta ta dinga tunanin Yaya Sultan wanda ta tabbata da ace shi ne yaji tana kuka ba zai taɓa barinta ba, koda ace ya san dalilin kukan nata to sai ya tsaya ya sake jin ba'asi sannan kuma ya yi iya yin sa wajen ganin ya sanya ta yi shiru. Har ya yi parking a compound ɗin Hajiya Babba bata sani ba, sai da ya ga da gaske bata san zo ɗin a sannan ya kai hannunsa na dama ya taba ta. Ta buɗe idanunta da kyar tana kallonsa, sosai ta bashi mamaki da bai yi tunanin kukan da take har ya kai yawan wannan ba, Babu yabo babu fallasa ya ce “it will be better for you if you stop this nonsense, ki sauka ki tafi gida” Bata ce komai ba ta ɗauki wayarta da ke kan cinyarta sannan ta sauka daga motar, kowa apartment ɗin Hajiya Babba ya nufa amma ita juyawa ta yi ta nufi nasu sashin dan bata jin zata iya magana da kowa. Babu kowa a parlonsu sai tv dake aiki ita ɗaya, ta ɗan kalli hanyar kitchen jin ƙamshi na tashi yasa ta tabbatar da Amma na kitchen dan haka kai tsaye daƙinta ta nufa, koda ta shiga zame doguwar rigar jikinta ta yi ta faɗa kan gado ta rufe jikinta gaba ɗaya sannan ta sake fashewa da wani irin kuka tana jan numfashi da kyar.. **** Around 9:30pm Zahra ke zaune gefen gadon tana shafa bayanta a hankali, sai da ta tabbatar da baccinta ya yi nisa sannan ta tashi ta rage gudun ac ta rufeta ruf da duvet sannan ta sauya mata hasken zuwa blue ta fice daga ɗakin. Sai da ta koma daƙinta ta fashe jikinta da turare sannan ta nufi ɗakinsa tana gyara zaman doguwar sleeping dress ɗin dake jikinta. A hankali ta tura ƙofar ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, A zuciya ya amsa idanunsa maƙale da farin glasses wanda ya ƙara masa kyau, yana danna system da hannunsa na dama ɗayan hannun kuma ya riƙe mug ɗin coffee sai tiriri yake, yana sipping a hankali. Gefen gadon ta zauna tana kallonsa ba tare da ta ce komai ba, Jin har bayan mintuna biyar bata yi magana ba ya sanya ya ɗago kansa yana kallonta fuskarsa a sake ya ce“Da matsala dai?” girgiza kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta, ya ɗan yi jim kafin ya ce“to mene ne?” ɗan kallonsa ta yi ganin ya kafeta da manyan idanunsa yasa ta sake ƙasa da nata a sanyaye ta ce“daman ina son magana da kai ne” rufe system ɗin gabansa ya yi yana gyara zamansa ya ce“okay go ahead” Zahra ta ɗan yi shiru tana tunanin ta in da zata fara can kuma ta ɗan numfasa cikin sassanyar murya mai cike da ladabi ta ce “Dan Allah dan Annabi dan girman Allah Doctor kada ka auri Nana, ka da ka yarda da maganar Atta. Wallahi zan iya mutuwa idan ka aureta, ba zan jure ganin ku tare ba, Dan Allah kada ka bari maganganunta su yi tasiri akan ka. Ka rufa min asiri dan Allah...” ta ƙare maganar cike da damuwa mai tarin yawa. Abdusammad ya dinga kallonta ba tare da ya ce komai ba, fuskarsa kuma sam babu alamun damuwa ko kuma mamaki. Jin shirun nasa ya yi yawa ya sa ta ɗago jajayen idanunta ta kalleshi sai kuma ta sake faɗin “na sani ka aureni ne ba da soyyayar danginka ba, na sani daman dole wata rana zasu iya cewa ka ƙara aure, kuma wallahi ba zan taɓa ja da wannan ba, ba zan yi yunkurin hanaka ba. Amma dan Allah dan Annabi ka auri wata ba Nana ba! Ka samo mata wadda ban sani ba, dan girman Allah kada watarana ka ce zaka haɗani kishi da Nana, zan mutu ne Doctor.. wallahi mutuwa zan yi...” Ta kasa ƙarasa maganar saboda wani irin kuka daya kwace mata. Furzar da iska kawai ya yi daga bakinsa still looking at her, Lokaci ɗaya ya saki wani yalwattacen murmushi yana ɗan ɗauke kansa zuwa gefe guda kafin ya yi gyaran murya cikin nutsuwar data gama ratsa shi ya ce 08106608363, Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 27... “Fateemarh kenan. Kina tunanin zan iya auren Nana? Ko da ace ya zama dole na ƙara aure. Kina tunanin zan iya zama da yarinyar da nake ma kallon ƴata? Yarinyar da ya ci ace na haifi kamarta, how?” Ya dakata da maganar yana furzar da iska daga bakinsa. Gyara zamansa ya yi yana riƙo hannayenta duk biyun cikin nasa ya ci gaba da faɗin “Ba zan taɓa auren Nana ba, koda ace zan ƙara aure to ba zan aureta ba. Ballantana ma kawai kina son ɗaga hankalin ki ne akan abin da ki ke da tabbacin ba zai yiwu ba, ko kin manta nan da wani satin i yanzu Nana matar aure ce?” Ya ƙare maganar yana kafeta da idanu, Zahra ta sunkuyar da kanta tana sauke ajiyar zuciya murya a sanyaye ta ce“ban manta ba, kawai dai na tsorata ne da kalaman Atta. Kai da kan ka kace ba'a tsallake umarninta idan har ta ce ayi abu to dole sai an yi shi, to kuma kana gani da kanta abin da ta ce. Wallahi ba zan taɓa hanaka ƙara aure ba, saboda na san ka yi min, ka aureni duk da kasan hakan ba abu ne wanda aka yarda dashi ba cikin danginka. Sannan kana shige min faɗa idan har wani ya yi yunkurin takani ko kuma aibatani. Kuma ka bani damar haifa maka ƴa wadda na san ba dan ka yarda dani ba, ba zaka taɓa yin hakan ba. Kaga kuwa dan yanzu ka ƙara aure ba zan ja da kai ba!” Ta ƙarasa maganar hawaye na zubowa kan fuskarta. Murmushi kawai ya yi dan ya san ta dai faɗa ne amma ba har ranta ba. Ya ɗago fuskarta da hannunsa ɗaya yana ƙare mata kallo ya ce“Zahra kenan, ki daina damun kan ki kinji. Ni Abdusammad Muhammad Shuwa banida niyyar ƙarin aure, ban da niyyar yi miki kishiya. A tsarin rayuwata mace ɗaya kaɗai ta wadaceni, muddin na samu mai kyakkyawan hali kamar dai ke ɗin nan” ya ƙare maganar yana jan kumatunta cike da zolaya. Bata san sanda dariya ta kufce mata ba, ta kifa kanta akan cinyarsa tana yi a hankali. Shima murmushi kawai yake dan yaji daɗin ganinta cikin farin ciki. **** Bayan sallar magriba babu daɗewa ta fito parlon tana sanye da wasu English wears riga da wando wanda basu kamata ba, gashin kanta a gyare kamar koda yaushe ta tufke da riboom ya sauka har gadon bayanta. Ta ƙaraso parlon jiki a sanyaye tana kallon Amma da ke zaune a kusa da Abba tana nuna masa abu a waya, Amma na ganinta ta mike tana faɗin “gata nan ma” da idanu Abba ya kalli Nana sai kuma ya ce“yauwa daughter zo nan” babu musu ta ƙarasa ta zauna in da Amma ta tashi tana kallonsa. Abba ya dinga kallonta ganin yanda ta rame kamar ba ita ba ya ce“Nana lafiyar ki? Akwai abin da ke damunki?” Ƙirƙiro murmushi ta yi ta ce“Babu komai Abba, kawai nagaji ne” shiru ya yi yana nazarin maganarta can kuma ya ce“anyway tashi muje ki rakani” to kawai ta ce sannan ta mike ta koma daƙinta. Wayarta da ke gefen drawer ta dauka dan yanzu sam bata yarda ta yi nesa da ita, ta buɗe press ta ɗauki wata Dubai chiffon Abaya mara nauyi ta ɗora kan kayanta sannan ta fito parlon. Tsaye ta same shi hannunsa riƙe da car key da alama ita yake jira, tana fitowa ya kama hannunta suka fice daga parlon. A cikin wata Lexus jeep black colour suka fita daga gidan, Abba da kansa ke driving dan baya buƙatar wani a tafiyar tasu. Nana ta dinga kallon titi ba tare da ta tambayeshi inda zasu je ba, saɓanin da, da idan zai fita da ita ta dinga tambayarsa kenan har sai ya gaji. Abba ya ɗan yi mamaki rashin tambayar tata dan haka ya gyara zamansa yana murza steering motar a nutse ya ce “Nana” Ɗago idanunta ta yi ta kalleshi a sanyaye ta ce“na'am Abba” Yana ƙoƙarin shan kwanar round about ɗin ya ce“tell me me ki ke so? Like abubuwan da ki ke so irin na amare” Nana ta ɗan yi shiru can kuma ta ce“a'a Abba bana son komai” sai da ya juyo da fuskarsa ya kalleta dan ba ƙaramin mamaki hakan ya basa ba. Ya mai da idanunsa kan titi yana faɗin “Na riga da na gama shirya komai, akwai waleema da za'a yi bayan ɗaurin aure wanda duk abokaina zasu halarta, and I want to you to be there saboda akwai waɗanda muka haɗu dasu a makkah time ɗin da muka ce Hajj dake last two years sun ce suna son su ganki, basu san kin girma haka ba” ya ƙare maganar yana murmushi. Nana da ke saurarensa ta jinjina kanta ba tare da ta ce komai ba, Abba bai damu da rashin maganar ta ta ba ya ci gaba da faɗin “And ina son ki kula sosai Nana, aure ba ƙaramin abu bane, ki yi kokarin zama yarinyar kirki a gidan mijinki, idan ki ka yi haka zan yi alfahari dake. Kin san ke kaɗai ce yata, ke kaɗai Allah ya bani a matsayin kyauta, so duk wani abu da iyaye ke yiwa ya'ya ko kuma suke so daga gare su ni akan ki nake da wannan burin. U're my last hope Nana, Dan Allah kada ki bawa Abbanki kunya, na sani kina da sauƙin hali amma bakya ji Nana, bakya son zaman lafiya. Dan Allah dan Annabi ki bar wadannan ɗabi'un a matsayin yarinta, ki sani idan ki ka yi aure kin riga da kin girma. Ke ba yarinya ba ce kamar da. Zaki zama uwa ne, dan haka dole ki sauya kin ji ƴar albarka, kada ki bari nayi kuka da ke Nana. Idan har ban samu kwanciyar hankali daga gareki ba ki sani babu wani wajen da zan samu kuma, daga gani har mahaifiyarki ba zamu so koda dana rana ɗaya a kawo mana ƙararki ba. Hakan zai sosa ran mu and na san ba zaki so ran mu ya ɓaci ba ko?” Abba ya ƙare maganar yana kallonta dan tabbatar da abin da yake son sanin, Allah sarki Nana ban da kuka babu abin da take, dan ba ƙaramin tausayi Abba ya bata ba. Me ta aikata ne? Taya zata iya kaucewa abin da yake gabanta domin ta faranta ran iyayenta? Ya zata yi da Junaid da Aunty Zahra? Wadannan tunanin su ne suke hanata bacci duk dare. Waɗannan tunanin su ne abin da ke neman haifar mata da ciwon zuciya, Ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta tana sake rushewa da wani irin kuka. Abba da mamaki ya cika shi ya gangara gefen titi ya yi parking ya juyo gaba ɗaya yana kallonta fuskarsa cike da damuwa ya ce “Nana why? Mene ne? Maganar dana faɗa ce ta saka ki kuka?” Abba ya jera mata tambayoyin yana ƙoƙarin ɗagota. Madadin ta bashi amsa sai kawai ta rungumeshi tana sake fashewa da sabon kukan, Abba ya dinga shafa kanta yana cewa ta yi shiru amma sam bata saurarensa. Sai da ta yi mai isarta sannan ta fara sauke ajiyar zuciya tana shessheƙar kuka, Ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce“mene ne?” Cikin shassheƙar kuka ta ce“Abba tsoro nake ji, wallahi tsoro nake ji Abba” ta ƙare maganar wani kukan na tawo mata, Murmushi irin na manya Abba ya yi sannan ya ce“ki yi haƙuri kin ji, ki daina jin tsoro ina nan babu abin da zai sameki” Abba ya yi magana cikin sigar rarrashi. Da kyar ta daina kukan amma bata bar jikinsa ba shima bai takura mata ba ya yi wa motar key suka ci gaba da tafiya. Har suka je wajen babu wanda ya sake cewa komai, Abba ya yi parking yana kallonta ya ce“Nana taso” a sanyaye ta ɗago kanta wanda take jin yana wani irin sara mata saboda tsabar kukan da take. Ya sauka daga motar sannan ita ma ta sauko tana ƙarewa wajen kallo, Babban shagon furnitures wanda yana ɗaya daga cikin manyan shagunan furnitures a cikin garin Yola. Abba ya riƙe hannunta cikin nasa sannan suka nufi cikin store ɗin. Kai tsaye second floor suka nufa, Nana ta dinga bin ko ina da kallo dan bata taɓa zuwa irin wajen sai da kayan furnitures ba, duk da yanda take jin babu daɗi hakan bai hanata sakin jikinta tana kallon komai ba, a wani waje mai kama da reception suka zauna Abba ya ɗauko wayarsa ya danna wata lamba sannan ya kau kunne, ita dai Nana ta dinga kallonsa ba tare da ta ce komai ba, after 2mins ya sauke wayar ya sakar mata murmushi ganin yanda take kallonsa. Dakyar ta iya mayar masa da murmushin sai kuma ta sauke kanta ƙasa tana jin wani irin abu ya tsaye mata a ƙirji. Suna nan zaune har bayan mintuna biyar sannan mutumin ya sakko daga sama ya ƙaraso wajen yana kallon Abba cike da girmamawa ya gaishe shi, Abba ya amsa sannan ya tashi yana rike da hannun Nana suka bi bayan mutumin. Can hawa na uku suka hau, wanda komai na wajen yafi kyau da tsada, Nana ta dinga kallon kayan furnitures ɗin masu matuƙar kyau. Ko ba'a faɗa maka ba ka san kuɗi ke magana a wannan wajen, Abba ya yi murmushi yana sakin hannunta ya ce“yanzu ki zaɓa wanda ki ke so anan” Da sauri ta kalleshi. Ya gyaɗa mata kai, sai kawai ta shige jikinsa tana sakin marayan kuka, girgiza kai Abba ya yi ya ɗago kanta yana murmushi ya ce“ke ba zaki daina rigima ba ko?” hannunta ta sanya ta rufe fuskarta tana ɗan dariya ƙasa-ƙasa. Ya ɗan kalli wajen sai kuma ya ja hannunta ya ce“c'mon muje na tayaki zaɓa” jiki a sanyaye Nana ta bi bayansa, suka dinga kallon kayan tare yana nuna mata wanda suka yi kyau. Abba ya taɓota sanda idanunsa suka sauka kan wasu Fendi casa Italian furniture ta dinga kallonsu ba tare da ta ce komai ba, Abba ya ja kumatunta yana fadin“ko basu miki kyau ba mu sauya?” girgiza masa kai ta yi dan itama kayan sun burgeta. Ya kalli mutumin dake tsaye bayansu ya nuna masa kayan ya ce“wannan muke so” okay kawai ya ce sannan ya nuna musu inda zasu biya, Abba ya yi gaba tana biye dashi. Cashier ɗin ya kalli kayan da suka nuna sannan ya ɗan duba system kafin ya ce “10.5m” Okay kawai Abba ya ce sannan ya miƙa masa atm card ɗinsa, Nana ta dinga kallonsa baki buɗe dan gaba ɗaya ta rasa abin cewa. Sai da aka cire kuɗin sannan aka basu receipt sannan ya juyo ya kalleta ya ce“muje” muryarta a ƙarye ta ce “Abbaaa.” Yanda ta yi maganar a sanyaye kamar wani abin na damunta ya sa ya ce“mene ne?” kamar zata yi kuka ta ce“sun yi tsada fa” taɓe baki Abba ya yi sannan ya ce“Ko?” ya yi maganar yana yin gaba ba tare da ya jira amsarta ba. Da idanu kawai Nana ta bi shi sai kuma tabi bayansa ganin yana shirin tafiya ya barta. Har suka koma mota babu wanda ya ce wani abu, ita gaba ɗaya zuciyarta a dagule take, ta rasa wani irin abu ya kamata ta yi, farin ciki ko kuma baƙin ciki. Taya ya zata iya bijirewa umarnin Abba? Ta ya zata iya cewa ba zata auri Safwan ba? To amma idan ta yarda da auren Safwan mene ne makomarta a wajen Junaid da Zahra? Zasu fitar da hotunanta domin su shiga tsakaninta da iyayenta da kuma danginta ko kuwa zasu haƙura ne su daina mata barazanar?. “Ki zauna anan zan amso invitation cards ɗin ku” Maganar Abba ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi, a hankali ta gyaɗa masa kai tana ɗan kallon in da suka tsaya ɗin dan sam bata lura ma da sun daina tafiya ba. Sai da Abba ya fita daga motar sannan ta samu damar sakin wani irin kuka mai ban tausayi, a fili ta dinga faɗin “wayyo Allahna, na shiga ukuna. Allah ka gani, kaga abin da ke damuna,Allah ka yi min maganinsa, idan ba zan iya da wannan masifar ba Allah ka ɗauki raina na huta, Allah kada ka bari na tozarta iyayena a idanun jama'a. Allah ka dubeni, Allah ka shiga lamarin nan...” Ta kasa ƙarasawa saboda kukan daya kwace mata, haka ta dinga rerashi har sai da jijiyoyin kanta suka fara tashi, kanta ya yi mata wani irin nauyi, idanunta suka ƙara kumbura. Ganin Abba yana tawowa ya sanya ya tayi saurin goge idanun tana jan numfashi a hankali. Koda ya shigo bai kalleta ba ya yi wa mota key suka bar wajen. **** Safeena ta dinga kallonta amma bata ce komai ba, Zahra da ke Ƙoƙarin haɗa miya ta sake cewa“kina ji na kin yimin banza, ban son iskanci fa” Ajiye wuƙar hannunta ta yi tana jingina da jikin cabinet ta ce“ni ban san abin da zance mikin bane Aunty,saboda ban san yaushe ki ka sauya har ki ka fara goyon bayan su Aunty Khadijah ba. Bayan kina da tabbacin abin da suke shirin yi ba dai-dai bane. Ta ya za'a ce sauran sati ɗaya bikinta ku yi yunkurin hanata aurensa? Ba ma wannan ba yanzu ke da kanki ki ka ce kun je ƙauyensu an nuna miki ba'a son ki, sannan kuma har matar tayi iƙirarin sai ya ƙara aure, kuma fa ki ka ce Nana aka ce ya aura.” Safeena ta yi maganar tana kallonta. Jinjina kai Zahra ta yi jiki a sanyaye ta ce“eh haka ne, amma kuma ai doctor ya faɗa min ba zai aureta ba, kuma na san tun da ya ce haka ba zai taɓa aurenta ba. Sannan kuma ya ce min nan da next week ai ta zama matar aure...” Zahra ta yi shiru tana nazarin abin da tace. Jinjina kai Safeena ta yi kafin ta ce “you see, kin ji abin da ki ka ce da kan ki, idan har an yi auren nan next week shi ne ki ke da tabbacin ba zata auri Daddyn Noor ba. Amma idan har ki ka dage sai kin hana auren to ki sani kamar kina kirawowa kan ki kishiya ne da kanki, domin wallahi ba zasu fasa aura masa ita ba. Muddin ba'a yi aurenta da waninsa ba!” Shiru Zahra ta yi tana kallon Safeena fuskarta cike da damuwa, kenan idan har ta matsawa Nana akan kada ta auri Safwan zata dawo ta auri mijinta? “Impossible! Ba zan taɓa bari ba wallahi, Nana ba zata taɓa auren doctor ba” Zahra ta ce tana girgiza kanta, Safeena ta dafata cikin sanyin murya ta ce“mu ma ba zamu miki wannan fatan ba Aunty. Amma ki sani domin ki tabbatar da Nana ba ta auri Daddyn Noor ba dole sai kin bari ta auri Safwan, ki janye jikinki daga gurinsu Aunty Khadijah, wallahi! Wallahi Aunty zasu kai ki ne su baro!” Zahra ta dinga kallon Safeena ba tare da ta ce komai ba, gaba ɗaya tunaninta ya tsaya cak, ba zata iya barin Nana ta auri Safwan ba muddin Siyama na son aurensa. Haka kuma ba zata bari Nana ta auri Doctor ba dan ba zata jure zama da ita a matsayin kishiya ba, to idan haka ne mene ne abun yi? “A lalata rayuwarta, a raba ta da kowa nata, ta yanda zata gudu tabar gidan da kanta. Ta yanda zata zama abar kyama a wajen kowa, walau iyayenta ko kuma dangin gaba ɗaya!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Assalamu alaikum everyone fatan kowa yana lafiya. Kamar yanda ku ka sani I'm Nanameera, CEO NM couture, Muna siyar da kayan sakawa irinsu: Abaya, Gowns, Veils, Bags da dai sauransu, Delivery Nation wide. For more information contact me 08106608363 Nanameera. Page 28... Kamar daga sama haka suka ji maganar dan haka suka juya a tare suna kallonta. Aunty Khadijah ce tsaye jikin ƙofa ta harɗe hannayenta a ƙirji, Safeena ta sauke numfashi tana kallon Zahra wadda ita ma take kallonta. A hankali ta shiga takowa har gaban Zahra ta dafata cikin kakkausar murya ta ce “Idan har ki na gudun kada daga baya ta zo ta auri mijinki to kawai a rabata da gidan, kin ga hakan zai fi mana sauki gaba ɗaya. Siyama ta auri Safwan ba tare da tashin hankali ba.” Ta ƙare maganar tana ɗan murmushi, Zahra ta dinga kallonta da mamaki can kuma ta janye hannunta daga kafaɗarta tana faɗin “A'a aunty wannan ba shawara ba ce, kuma ni gaskiya ba zan iya saka hannu cikin lalacewar rayuwar Nana ba. Saboda babu abin da ta yi mana, kuma ni ba tsanarta nayi ba, kawai dai zan yi abin da zai sa Siyama ta auri Safwan amma ban da lalata rayuwarta gaskiya.” Aunty Khadijah ta yi murmushi tana gyara tsaiwarta ta ce“To kenan kin shirya zama da ita a matsayin kishiya?” Rai a haɗe Zahra ta ce“akan me zata zama kishiyata?” “Akan zata fasa auren Safwan mana, ko kina tunanin zasu fasa haɗata da mijinki ne?” Aunty Khadijah ta yi maganar tana kallonta. Shiru Zahra ta yi tana tunani can kuma ta girgiza kanta ta ce“Ni na san doctor ba zai taɓa auren Nana ba, kuma shi ba'a masa dole ma, dan haka kawai zan yi abin da zata rabu da Safwan. Amma fa ki sani Aunty idan har rabuwarta da Safwan na nufin zata auri mijina wallahi sai dai Siyama ta haƙura, ta auri wani a gidan, tun da akwai sauran samari wanda basu aurar ba.” Safeena dake gefe tun ɗazu ta yi murmushi sai kuma ta ce“Nima dai abin da nagani kenan Aunty, gara Siyama ta haƙura dashi idan yaso ta auri wani” Wani mugun kallo Aunty Khadijah ta watsa mata wanda ya sanya ta sunkuyar da kanta, Ta mai da idanunta kan Zahra fuska a haɗe ta ce “Yanzu ke me ki ke nufi?” Zahra ta kalleta sai kuma ta ɗauke kai tana kallon gefe ta ce“ni kawai ina nufin ba zan yi abin da zai zo ya dameni ba, ba kuma zan gyara auren wata na lalata nawa ba!” Murmushin yaƙe Aunty Khadijah ta yi babu yabo babu fallasa ta ce“Alright kin yi ƙokari, abin da baki ƙarasa ba ni zan ƙarasa shi da kaina” Daga haka ta juya ta fice daga ɗakin kamar zata tashi sama. Safeena ta ƙaraso gaban Zahra tana murmushi ta ce“Yauwa Aunty, kin yi dai dai. Ki bar su suje can su ƙarata” Shiru Zahra ta yi bata ce komai ba, dan gaba ɗaya zuciyarta ba tai mata daɗi ba yanda suka yi da Aunty Khadijah. Sam bata son tana ɓata mata rai, Safeena ta dinga kallonta jin bata ce komai ba yasa ta ce “Aunty lafiya?” Sauke numfashi ta yi sannan ta ce“babu komai Safeena, bari na zo na tafi gida kada dare ya yi min” to kawai Safeena ta ce sai kuma ta koma ta ci gaba da abin da take. Koda Zahra ta fito zaune ta samu Umma da Amal suna magana, kai tsaye sama ta shige ta dauƙo mayafinta da kuma jakarta sannan ta dawo ƙasan. Umma ta dinga kallonta kafin ta ce“tafiya za ki yi?” tana yafa mayafin akanta ta ce“eh Umma dare ya fara yi” Umma ta jinjina kanta ta ce“haka ne, ki gaida mutan gidan” “Zasu ji in sha Allah Umma” Ta ce tana ɗaukan wayarta da ke kan kujera. Amal ta kalleta babu yabo babu fallasa ta ce“ki gaida gida” “Zai ji” Zahra ta amsa tana yin waje cikin hanzari. **** Kaddu ta dinga kallon Aunty Khadijah sai kuma ta ce“to yanzu mene ne abun yi?” tsaki Aunty Khadijah ta yi rai ɓace ta ce“to nima ina na sani, kawai ya cuceni a banza gashi gaba ɗaya asirin nema yake ya saketa” girgiza kai Kaddu ta yi ta tashi daga zaunen da take ta shige bedroom ɗinta. After 5mins ta fito hannunta riƙe da mayafi tana ƙoƙarin yafawa ta ce“tashi mu je kiga” “Ina zamu je?” Aunty Khadijah ta tambaya tana kallonta. “wajensa mana, komawa zamu yi ya faɗa mana yanda ya kamata a yi” Okay kawai ta ce sannan ta dauki wayarta da jakarta suka fita. **** Tun da ta shigo gidan take kallon motocin da suka yawaita fiyeda da, ta dinga mamaki wadanda suka zo da yawa har haka. A compound ɗin apartment ɗin su ta yi parking sannan ta sakko ta nufi cikin gidanta kai tsaye. Bata samu kowa a ciki ba dan haka ta haye sama ta shige daƙinta ta zauna tana sauke gajiya. A can Apartment ɗin Hajiya Babba, Atta ce zaune ta hakimce kan sofa two seater tana sauraren maganar da Abba ke faɗa mata, Har ya kai ƙarshen maganar babu wanda ya ce komai ba, sai jinjina kai take kamar gaske. Sai da taji ya yi shiru sannan ta ce “To yanzu me ku ke nufi?” Abba ya ɗan yi murmushi ganin yanda ta haɗe rai ya ce“Ai kin ga Atta kamar a bar wannan maganar ko? Tun da an riga da an gama komai na aure bai kamata a sauya ba” Taɓe baki ta yi kafin ta ce“wato dai nufi ake ba zai aureta ba?” Abba ya girgiza kansa ya ce“ba haka ake nufi ba Atta. Da ace ba'a fara maganar aurensu da Safwan ba sai a bari ya aureta, amma tun da har an fara magana kuma yau sauran kwanaki 4 a ɗaura auren kin ga kamar zai zama fitina abun” Atta ta yi shiru ba ta ce komai ba dan tana matuƙar ganin girman Abba, ko Papa da yake gaba dashi bata fiye yarda da zancensa ba kamar na Abba. Jin bata ce komai ba ya sanya Abba ya sauke ajiyar zuciya dan ya san ta haƙura, Above 2mins kafin ta ce “To idan bai auri Nana ba ni zan saka a kawo masa mata daga gidana, Akwai yarinyar wajen Kaltume Haule sai ya aureta dan wallahi sai ya ƙara aure” ta ƙare maganar tana gyaɗa kai. Abdusammad da ke zaune kusa da Papa ya kalleta sai kuma ya ɗauke kansa, Abba ya yi shiru can kuma ya ce“Amma Atta...” Katse shi ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu. Cike da masifa ta ce “Wallahi ba za'a fasa maganar auren nan nasa ba, dole ne sai ya yi aure dan ba zai ci gaba da zama da wadda ba danginsa ba, tana haifa masa ya'ya muna haɗa zuri'a da wasu can bare” “Atta kina da gaskiya, Nima ina goyan bayan ya ƙara aure. Dan daman nayi shiru ne kawai dan na ya ba da hankalin yarinyar, amma tun da har akwai wadda za'a iya haɗa sun kawai a haɗa su, son samu ma a haɗe da auren duka a yi ranar Juma'an” Da sauri Abdusammad ya kalli Hajiya Babba wadda ta yi maganar a nutse, Lokaci ɗaya ya ji jkinsa ya yi wani irin sanyi. Dan ya san ko da wasa ba zai taɓa tsallake umarninta ba. Dan haka ya sauke kansa a hankali. Abba daya lura da yanayinsa ya ɗan yi jim can kuma ya kalli Papa da har yanzu bai ce komai ba ya ce “Yaya kana ji fa” Jinjina kai Papa ya yi ya ce“Ai duk abin da suka yanke dai dai nan Ahmad. Daman bai yi shawara da kowa ba sanda zai aurota, bai kallemu matsayin iyaye ba yaje ya yi son ransa. Dan haka yanzu dan an aura masa ƴar dangi ai bana jin zai ƙi amincewa.” Shiru Abba ya yi dan tun da yaji duk sun ce haka to babu makawa sai sun saka ya sake auren, Abdusammad ya tashi ba tare da ya ce komai ba ya fice daga parlon. Da harara Atta ta bi shi sai kuma ta ce“Ka daɗe baka yi zuciya ba. Wallahi tallahi sai ka yi auren nan, idan ma wani surkullen aka yi maka sai mun warware shi” Murmushi irin na manya Papa ya yi kafin ya ce“Atta kenan” “To ai naga kamar ba kansa ɗaya ba, ji ana maganarsa ya tashi ya mai da mu gantallalu” Abba bai sake cewa komai ba ya mike ya musu sallama ya bar parlon shima. Atta ta buɗe baki sai kuma ta yi kwafa ta ce“Ɗan uwan ɗayan, wato dan ya tashi shi ne shima ya tashi to ku je da baƙin halinku” Murmushi Hajiya Babba ta yi ta ce“Atta ki shiga ciki ki huta kin deɓo gajiyar hanya” Girgiza kanta ta yi ta ce“A'a kafin na shiga cikin a kira min Sulaimanu ya je ya ɗauko Haule a gida” Toh kawai Hajiya Babba ta ce dan ta san halinta da kafiya, tun da ta ce hakan ba zata tashi ba har sai ta gama abin da ta yi niyya. **** Aunty Khadijah da ke zaune gefen Kaddu ta girgiza kanta idanunta cikin na malamin ta ce“to yanzu mene ne abun yi? Gaba ɗaya Zahra ta fara bijirewa maganata, sam bata ɗaukan abin da nake faɗa mata. Ni kawai gara da kan ka ka yi min maganin waccan yarinyar, ko a yi mata kurciya ta bar gidan kawai. Ko kuma ta shiga duniya” Malamin ya yi shiru kamar me tunani, can kuma ya fashe da dariya ya ce“babu wata duniya da zata shiga. Sannan babu ruwanmu da yarinyar a cikin aikin da zamu yi yanzu” Aunty Khadijah ta kalli Kaddu sai kuma ta kalli malamin da mamaki ta ce“Ta yaya haka zai yiwu?” Ɗan murmushi ya yi sannan ya ce“wannan ba damuwar ki ba ce, ni na san yanda zan saka ta yiwun. Ke dai abin da nake buƙata daga gareki shi ne ki bada haɗin kai” “Ni wannan ba damuwata ba ce, muddin zan samu biyan buƙata to koma mene ne zan yi shi. Kawai ka tabbatar da cewa Siyama ta shiga cikin wannan gidan a matsayin suruka. Ko suna so ko basa so” Aunty Khadijah ta yi maganar a ɗan fusace. Jinjina kai Malamin ya yi ya ce“Ki ɗauka an gama wannan maganar!” **** Washegari ta kama ranar Laraba, wanda a ranar ne zasu yi henna's party a cikin estate ɗin. Ƙarfe 8:00 na safe Maimoon ta shigo apartment ɗin, Amma na ƙoƙarin shiga kitchen dan fitowar kenan ta ganta. Gaisheta ta yi ta amsa sannan ta ce“Nana tana ciki?” gyaɗa mata kai Amma ta yi kafin ta ce“eh tana ciki” okay kawai ta ce sannan ta nufi bedroom ɗin Nana. Tura ƙofar ta yi ta hangeta zaune ƙasan gado ta jingina da jikin gadon fuskarta a rufe, mayar da ƙofar ta yi ta rufe sannan ta ƙaraso ciki tana kallonta a sanyaye ta ce “Nana!” Shiru taji ta yi mata, dan haka ta durƙusa tana ƙoƙarin janye hijabin jikinta ta ce“Nana mene ne...” Cak maganar ta maƙale a maƙoshinta saboda jinin data ga yana zuba daga bakinta, ta ɗagota a ruɗe tana faɗin “ke Nana, mene ne ya same ki? Mene ne?” Kasa bata amsa Nana ta yi sai hannunta data riƙe gam tana sauke wani irin numfashi. Maimoon ta mike da niyyar barin wajen ta sake riƙeta tana girgiza mata kai. Dawowa ta yi ta tsuguna tana riƙe da hannunta ta ce“Bari naje na faɗawa Amma” girgiza kanta ta dinga yi hawaye na zubowa kan fuskarta. Maimoon ta rasa abinda zata yi sai kawai ita ma ta fara kukan, Haka suka dinga rera kukansu ba tare da wani ya jiyo su ba. Sai da suka yi mai isarsu sannan suka bawa kan su haƙuri, Maimoon ta ɗago fuskarta wadda ta yi caɓa caɓa da hawaye tana kallon Nana ta ce“tashi ki wanke jikinki” gyada mata kai kawai ta yi sannan ta mike a hankali ta nufi toilet. Ita kuma ta naɗe laddumar ta ajiye kan drawer tana ƙoƙarin juyawa wayarta da ke gefen drawer ta fara ringing, dan haka ta kai hannu ta dauki wayar tana ƙarewa sunan da ta gani akan screen ɗin da kallo. “Junaid?” Ta ce a fili da mamaki. Ganin wayar ta katse yasa ta mayar zata ajiye sai ga text message ya shigo, kamar bata duba ba sai kuma ta kai hannu ta buɗe wayar gaba ɗaya dan ta riga da ta san password ɗinta. Text message ne da bai shige layi biyu zuwa uku ba an rubuta _Kina ɗaukan maganganuna wasa ko? To idan Allah ya kai mu an jima lalatattun hotunanki zasu isa ga mahaifinki, dan yanzu ma haka na samu numbern wayarsa. Idan kina son ki tabbatar ki hau WhatsApp na tura miki._ Maimoon ta dinga karanta saƙon ba tare da ta fahimci inda ya dosa ba, lalatattun hotuna? Mahaifinta? Sai kawai ta shiga WhatsApp dan already wifi ɗin ta a kunne yake. Babu inda bata duba ba amma sam bata ga lambar Junaid ba, ballantana taga saƙon da yake magana akai, kaf unreads ɗin dake wayar Nana da basu shige ashirin ba babu wanda bata duba ba, ganin wadda ta yi magana da ita last Khadijah ce ƙawarta ta Aun yasa ta shiga tana duba chats ɗin su. Ganin bata samu komai ba ya sa ta fita tana sake duddubawa. Can ta hango lock chats ta yi ƙoƙarin buɗewa ta ga ya nuna mata sai ta saka Face id, Ta yi tsaki har sannan tana rike da wayar. Nana ta fito daga toilet ɗin tana goge fuskarta wadda take a jiƙe. Ganin Maimoon tsaye da wayarta a hannunta yasa taji gabanta ya yi wani irin faɗuwa, nan da nan tari ya turnuƙeta, da gudu ta karasa gabanta ganin tana shirin faɗuwa ta riƙeta tana mata sannu. Har gaban gado ta kawota sannan ta zaunar da ita ta fice daga ɗakin. Kai tsaye kitchen ta shiga ganin Amma bata ciki yasa ta ƙarasa wajen freezer ta buɗe ta dauki ruwan gora da cup ta fito da sauri. Ɗakin ta koma ta samu Nana in da ta bar ta sai sauke numfashi take dakyar, ta zauna gefenta sannan ta ɓalle murfin robar ta tsiyaya mata ruwan ta miƙa mata. Amsa ta yi ta shanye tas sannan ta bata cup ɗin tana sauke numfashi. “Ko na ƙara miki?” Girgiza kanta ta yi tana lumshe idanu. Maimoon ta ajiye robar a ƙasa tana kallonta, After 5mins ganin kamar ta dawo nutsuwarta yasa ta ce “Nana” A sanyaye Nana ta juyo ta kalleta sai kuma ta ce“na'am" Yanda ta yi maganar kamar ba ita ba yasa Maimoon ta dinga kallonta. Sai a sannan ta lura da ramar da ta yi, gaba ɗaya ta sauya kamar ba ita ba. Wuyanta duk ƙasusuwa sun fito duk da daman bata da wata ƙibar arziki, amma ramar tata tafi ƙarfin ta fargabar aure. Idanunta kuwa sun ƙara firfitowa waje kamar zasu faɗo. Maimoon ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce “Wane hotuna Junaid yake magana akai Nana? Yaushe ki ka ci gaba da kulashi? Wasu lalatattun hotunanki ne a hannunsa? Kuma ya akai ya same su.? Me ya sa yake cewa zai faɗawa Abba?” Maimoon ta jera mata tambayoyin tana kallonta. Da sauri Nana ta kalleta Lokaci ɗaya hawaye ya cika kurmin idanunta, ta kalli wayarta dake hannun Maimoon sai kuma ta kai hannu da sauri zata karɓa, Maimoon ta janye hannunta ta ce “Sai kin fara faɗa min mene ne abin da ya haɗa ki da Junaid?” Cikin kuka Nana ta ce“Dan Allah Maimoon ki bani wayata, dan Allah ki bani” Tashi tsaye Maimoon ta yi tana mata wani irin kallo ta ce“Wallahi ba zan baki ba har sai kin faɗa min abin da ya haɗaki dashi. Ki faɗa min wasu hotunanki ne a hannunsa, Idan ba haka ba na rantse sai naje na faɗawa Amma yanzun nan, idan yaso ita ta saka ki faɗa!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 29... Shiru Nana ta yi tana kallonta idanunta cike taɓ da hawaye. Ganin bata ce komai ba ya sanya Maimoon gyaɗa kanta ta ce“Alright tun da ba zaki yi magana ba bari na kira Amma sai ita ki faɗa mata” daga haka ta juya tana shirin ficewa daga ɗakin. Tashi Nana ta yi ta riƙota da sauri a lokacin hawayen dake cikin idanunta suka samu damar zubowa kan kuncinta, ta riƙe gefen hijabin Maimoon tana hawaye a hankali. Haɗe rai Maimoon ta yi tana ƙoƙarin janye hannunta daga jikinta ta ce“Ni sakeni. Wallahi idan har baki faɗa min ba ba zan fasa kiranta ba” Sauke numfashi Nana ta yi cikin kuka ta ce“shikenan zan faɗa miki ki dawo ki zauna dan Allah” yanda ta yi maganar a mugun sanyaye shi ne ya sake bawa Maimoon mamaki, dan sam ba haka Nana take ba. Ta ɗan kalleta sai kuma ta nufi ciki ta zauna gefen gadon tana kallonta ta ce“Ina jin ki” Nana ta sanya gefen hannunta ta share hawayen dake zubowa kan fuskarta sannan ta fara bata labarin duk abin da ya faru, tun daga sanda suka rabu dashi a supermarket da kuma sanda ya zo gida ya kawo mata wannan hotunan. Da kuma yanda suka yi da Zahra. Nana ta sauke ajiyar zuciya cikin shessheƙar kuka ta ce “Ban san ya zan yi ba Maimoon. Bana son Junaid ko kuma Aunty Zahra su fitar da hotuna na, idan Abba ya gani ban san wane hali zai shiga ba, sannan kuma bana son na ce ba zan auri Yaya Safwan ba. Maimoon ji nake dama na mutu, daman ban zo duniyar ba, zuciyata zafi take min wallahi” Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Maimoon da ke zaune tana kallonta fuskarta ta yi caɓa caɓa da hawaye ta taso jiki a sanyaye ta rike Nana cikin kuka ta ce“Nana shi ne baki faɗawa kowa ba? Shi ne ki ka bar abin a ranki?” girgiza kanta ta yi ta ce“wa zan faɗawa Maimoon? Kowa tunani yake saboda bana son auren nan yasa nake damuwa. Babu wanda ya zauna dani ya tambayeni abin da ya dameni, To taya zan iya fadawa wani?” Maimoon ta sanya hannunta dake rawa ta share mata hawayenta sannan ta ce“shikenan ki daina kuka, ki zauna mu ga ta inda zamu ɓullowa al'amarin” Jinjina mata kai kawai Nana ta yi, Ta kama hannunta suka ƙarasa gaban gadon suka zauna sannan ta ce“Yanzu ina ga abin da yafi shi ne a sanarwa da manya. Maganar Aunty Zahra ina ganin uncle ya kamata mu faɗawa, shi ya san yanda zai yi da ita” Zaro idanu Nana ta yi sai kuma ta shiga girgiza kanta murya a sanyaye ta ce“a'a bana son kowa ya sani, bana son su sani dan Allah” Maimoon ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce“to Nana idan bashi ba wane ki ke ganin zai fahimceki? Wane ki ke ganin faɗa masa zai kawo sauƙi a lamarin?” Ta yi maganar cike da damuwa. Cikin kuka Nana ta ce“nima ban sani ba, kuma bana tunanin faɗawa kowa. Amma ya zan yi? Junaid ya ce muddin nayi auren nan sai ya fitar da hotunan, sannan ita Aunty Zahra ta ce in dai na auri Yaya Safwan sai ta fitar dasu. Kenan duk basu son na aure shi ne. Dan haka mafita ɗaya kawai nake nema” Maimoon ta dinga kallonta can kuma ta ce“wace mafita kenan Nana? Idan baki auri Yaya Safwan ba to hakan na nufin zaki bijirewa maganar gidan nan, kuma hakan na nufin lalata al'amarin” Nana ta rasa abin cewa sai kawai ta fashe da kuka ta ɗora kanta a cinyar Maimoon. Ita kanta Maimoon kasa daina hawaye ta yi, dan ta san dole sai wani abu mara daɗi ya faru. Ƙaddara ta riga da ta faɗawa Nana, mai fitar da ita sai dai Allah. Bayan mintuna biyar ta ɗago kanta tana kallon Maimoon ta ce “Maimoon na tambayeki” “Ina ji” Ta ce tana gyara zamanta. Nana ta ɗan numfasa sai kuma ta ce“ashe daman ana barazana a soyyaya? Ashe daman mai sonka zai iya abin da zai cutar da kai? Da gaske sir Junaid yana sona kamar yanda nake son shi?” Ba ƙaramin tausayi ta bawa Maimoon ba, amma ta dake ta girgiza kanta a sanyaye ta ce“a'a Nana, babu yanda za'a yi wanda yake sonki ya yi ƙoƙarin yi miki barazana. Mai son ki tsakani da Allah ba zai taɓa tunanin samunki ta kowace irin hanya ba. Ba zai tunanin cutar da ke ba, Nana na faɗa miki wani abu.?” Gyaɗa mata kai Nana ta yi, ta numfasa ta ce“Wallahi sir Junaid ba sonki yake ba! Ke ce ki ke son shi fiye da yadda ya dace, amma shi akwai wani abu a ransa” Nana ta yi shiru tana kallonta, can cikin zuciyarta kuma tana tunanin irin dadewar da suka yi da Junaid. Yanda ya dinga kulawa da ita, ya bata duk taimakon da take buƙata, ya sota ya ƙaunaceta, to ya za'a yi ace ba sonta yake ba? To idan ba sonta yake ba me yake?. Maimoon ta dinga kallonta ganin ta yi shiru yasa ta ce“ki bar wannan tunanin mu tashi mu yi abin da yake gabanmu” Girgiza kanta ta yi ta ce“ni ƙirjina ciwo yake ba zan iya yawo ba” Maimoon ta mike tana cewa“a'a ki taso mu je, Atta tun ɗazu ta ce ina ki ke” Kamar zata yi kuka ta ce“to ni sai an jima zan fita” tana gama faɗin haka ta koma ta kwanta tana juya mata baya. Maimoon bata sake bi ta kanta ba ta tashi ta fice daga ɗakin dan ta san tunda tace hakan ba tashin zata yi ba.. Amma na tsaye jikin drawer tan haɗe wasu takardu na Abba da ya zube, yayinda shi kuma yake zaune gefen gado idanunsa maƙale da glasses yana duba system a hankali. Sai da ta haɗe takardun ta zuba a envelope sannan ta ajiye su gefe guda, ta ɗaga car key ɗinsa zata ɗauke taga wata takarda kamar receipt. Ɗauka ta yi a hankali ta ware ta, ta dinga kallon takardar sai kuma ta kalleshi daga inda take tsayen. Numfasawa ta yi a hankali ta ce “Yallabai” “Uhm” Ya ce ba tare da ya ɗago kansa ba. Amma na sake karanta rubutun takardar karo na uku ta ce“amma sai naga kamar wannan kuɗin is too much” sai a sannan ya ɗago kansa ya kalleta sai kuma ya kalli takardar hannunta. In a very calm voice ya ce“too much for what?” “Sun yi yawa kuɗin, 10.5m kawai na furniture?” Kafeta Abba ya yi da idanu sai kuma ya ce“hala akwai wata yar da zan aurar bayan Nana right?” Amma ta ɗan kalleshi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“a'a ba wai haka ba, amma koma ita kaɗai ce ai wannan kayan sun yi tsada” taɓe baki ya yi kafin ya ce“to ni basu min tsada ba. Kuma da a ce ta zaɓi wanda suka fi haka kuɗi ni mai siya mata ne. Sanin kan ki ne bayan Nana bani da wata yar ko ɗan da zan aurar har na masa hidima, ita kaɗai Allah ya min kyautarta. Dan haka idan ba zaki tayani ba, ki yi shiru da bakin ki” Amma ta yi shiru sanin halinsa yasa yasa ta mayar da receipt ɗin ta ajiye sannan ta ce“to Allah ya ƙara arziki da wadata” “Amin. Idan kuma kin shirya haihuwar wata yar ne sai ki faɗa min na rage” Murmushi ne ya kubuce mata, ta kalle shi ta ce“a'a to ni na hana kai na haihuwa ne?” ta ƙare maganar tana zama kusa da shi. Rufe system ɗin gabansa ya yi ya juyo yana kallonta ya ce“to laifin wane? Ni dai kin san jarumi ne ba?” Amma ta ɗauke kanta tana murmushi, Ya tashi yana zare glasses ɗin idanunsa ya ce“bari na zo zan nuna miki” tashi itama ta yi ta ce“Allah ya huci zuciyarka. Ni breakfast ma na ɗora” daga haka ta nufi hanyar fita daga ɗakin da sauri. Da idanu kawai ya bita sai kuma ya yi murmushi ya juya ya shige toilet. **** Karfe 4:00 na yamma aka fara henna's party ɗin, gaba dayansu suna apartment ɗin Hajiya Babba dan duk yafi ko ina girma. A compound ɗin gidan aka kira masu decorations suka tsara wajen, kai ka ɗauka wani event ɗin aka je. Gaba ɗaya dangi na kusa dana nesa sun zo gidan, dan haka wajen ya cika da jama'a. Amaren suna sanye da dogayen riguna na saki maroon colour, kasancewar su farare yasa ya yi musu kyau sosai. Fuskarsu fresh dan basu yi kwalliya ba, sai powder da lip gloss da suka shafa. Kowacce sai harkokinta take da ƙawayenta dan duk an gama masu ƙunshin, Nana kuwa na gefe ɗaya ta zauna kusa da Aunty Mariya da suka zo daga Abuja. Ta yi shiru tana kallon fararen hannunta wanda suka yi kyau da lallen da aka yi musu, sai dai zuciyarta a dagule take da tunane-tunane kala-kala. Sai kusan magriba sannan aka tashi, Kai tsaye apartment ɗinsu ta nufa tana zuwa ta shige ɗakinta tun kafin mutanen gidan su taru. A gefen gadonta ta zauna tana wani irin numfarfashi dan tun ɗazu take jin ƙirjinta na mata wani irin zafi, Ta kwanta a hankali tana lumshe idanunta, a hankali kuma ta fara jin azabar na ƙaruwa, numfashinta ya fara ɗaukewa dakyar take iya jawo shi. Tana nan kwance har bayan mintuna ashirin sannan wani wahalallen bacci ya ɗauketa, Cikin baccinta taji kamar a mafarki ana kiran sunanta, dan haka ta buɗe idanunta a hankali tana ware su a ɗakin. Babu kowa a ciki dan haka ta tashi zaune tana dafe saitin zuciyarta wanda ya ci gaba da bugawa da sauri, Ta lumshe idanunta sannan ta tashi ta shige toilet. Wanke fuskarta ta yi sannan ta ɗauro alwala ta fito, ta zura hijabinta ta gabatar da sallar magriba sannan ta zare hijabin, tana ƙoƙarin tashi daga wajen Amma ta turo ƙofar tana kallonta ta ce “Nana ki zo inji Abbanki” Toh kawai ta ce ta juya ta fita. Ta karasa zare hijabin jikinta sannan ta ɗauki mayafin abayar dake kan gadonta ta rufe kanta dan tuni ta cire ɗaurin sego ɗin ta fito. Bata gan shi a parlon ba, sai taron mutanen gidansu Amma da suka zo. Ta ƙarasa tsakar parlon ta ɗan gaishesu sama-sama sannan ta kalli Amma a sanyaye ta ce“Ina Abban yake?” “Yana balcony da Abdusammad” To kawai ta ce sannan ta nufi waje jiki a sanyaye. Tsaye ta same su da uncle suna magana, ta ƙaraso a hankali tana wasa da fingers ɗinta, sai da ta gaishe da uncle ya amsa yana kallonta sannan ta kalli Abba muryarta na fita a hankali ta ce“Abba gani” envelope ɗin da ke hannunsa na hagu ya miƙo mata yana faɗin “Yanzu na haɗu da malamin nan naku, shi ne ya ce na kawo miki” Nana ta sanya Hannunta duk biyun ta karɓa sannan ta ce“Abba wane malamin?” “I can't recall his name, but ina yawan ganinsa idan naje Aun” Nana ta yi shiru sai kuma ta juya a hankali ta koma ciki. Abba ya bita da idanu sai kuma ya kalli Abdusammad ganin shi ma itan yake kallo yasa ya ce“gaba ɗaya ta zama wata so silent da ita. Ban taɓa tunanin akwai lokacin da Nana zata nutsu irin haka ba” murmushi kawai ya yi sannan ya ce“ai fa. Kamar ba ƴar rigimar nan ba” Abba ya ɗan yi dariya sannan ya kawar da zancen ya koma kan maganar da suke ya ce“Ni ina ga kawai ka yi haƙuri. Tun da kaga Atta ta riga da ta dage, and sanin kanka ne ba zamu iya ja da ita ba. Idan har muka ce a'a zata ga kamar dan babu ran Yaya ne ya sanya” Abdusammad ya furzar da iska daga bakinsa sannan ya ce“amma Abba ni bani da niyyar ƙara aure, beside ma koma zan ƙara aure sai na rasa wadda zan aurar sai wannan yarinyar? She's too young wallahi gaba ɗaya fa da kaɗan ta girmi Nana. Ni bana son auren yarinya ƙarama wallahi” Abba ya ɗan murmusa kafin ya ce“To ya zaka yi? Tun da dai har kana da matarka wadda kake so to ka bari ayi auren nan kawai. Bayan Atta kana ganin Hajiya ma ta dage, kuma dai ka san ba zata bari a fasa ba, bayan haka ma yau an saka ma yara lalle ai kaga aure ya tabbata” Abdusammad ya yi shiru can kuma ya ce“ai shikenan. Amma ni gaskiya bana jin zan iya tafiya da ita can, sai dai ta zauna anan kawai a samar mata schl ta shiga” Abba ya jinjina kansa ya ce“a'a da dai ka tafi da ita. Cause school ɗin can yafi nan” Numfasawa ya yi kawai sannan ya ce“tom bari naje dare nayi” jinjina kai Abba ya yi sannan suka yi sallama ya tafi. **** Nana na shiga daƙinta ta ajiye envelope ɗin gefen gado sannan ta sake ficewa daga ɗakin. Apartment ɗin su Maimoon ta je, ta samu basu nan wai suna gidan Mama. Babu yanda ta iya haka ta dawo gida dan ita ba wani son zuwa Apartment ɗin su Hamida take ba saboda faɗan Mama. Kai tsaye daƙinta ta shige, ta kalli envelope ɗin data ajiye saman gado sai kuma ta nufi kan drawer in da ta ajiye wayarta, missed call ɗin Khadijah ta gani. Dan haka ta ɗauki wayar ta koma ta zauna kan gadon tana dialing numbern nata, ringing biyu ta ɗauka, Nana ta sauke numfashi bata ce komai ba. Khadijah da ke zaune kan sofa ta gyara zamanta tana faɗin “Ina ki ka shiga ina ta kiranki?” A sanyaye Nana ta ce“na ɗan fita ne” Khadijah ta jin jina kanta kafin ta ce “To ya shirye-shiryen?” “Yaushe za ki taso?” Nana ta mayar mata da tambayar ba tare da ta amsa tatan ba. Murmushi kawai ta yi ta ce“Da gobe nake saka rai. Ina jiran Daddy ya dawo ne” Ɗan haɗe rai Nana ta yi kamar tana gabanta ta ce “Har sai gobe?” Khadijah ta waro idanu tana murmushi ta ce“to yanzu da daren nan ki ke son na biyo Flight or what?” Nana ta yi shiru can kuma ta ce“amma da sassafe zaki tawo?” Khadijah ta girgiza kanta still smiling ta ce “a'a zuwa azahar dai, zan biyo flight ɗin 9 kin ga idan na zo zan fara zuwa gidan Ammi” To kawai Nana ta ce jin kira na shigowa wayarta ta ce“alright sai goben” okay Khadijah ta ce sannan ta katse kiran. Nana ta dinga kallon numbern Junaid da ke ruri akan screen ɗinta, sai kawai ta yi jifa da wayar kan gado ta yi kwanciyarta a gefe. Ganin bai tsaya da kiran nata ba ya sanya ta tashi ta kalli wayar sai kuma tayi tsaki. Ta sanya hannunta ta janyota ta dinga kallon screen ɗin sai kuma ta yi rejecting call ɗin ta kifa wayar kan cinyarta. Ta dafe kanta tana sauke numfashi, Above 5mins kafin ta ɗago fuskarta idanunta sun sake yin jajur kamar me shirin kuka. Ta ajiye wayar tana shirin tashi idanunta ya sauka akan envelope ɗin, Hannunta na dama ta kai ta ɗaukota ta dinga juyawa tana tuna maganar da Abba ya faɗa mata. “Malaminmu? A Aun?” Ta tambayi kanta. Sai kuma ta shiga ɓare envelope ɗin ta leƙa, tun da taga tarin takardu taji gabanta ya faɗi. Ta ƙarasa zaro su hannunta na rawa, A firgice ta miƙe tsaye hannunta riƙe da hotunan jikinta sai wani irin rawa yake kamar ana kaɗa ganga, Nana ta dinga girgiza kanta hawaye na biyo kuncinta. Ta ɗauki wayarta da sauri ta shiga dialing numbernsa tana hawaye, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka. Bata jira ya yi magana ba ta fara faɗin “Dan Allah dan Annabi kada ka sake turo min da hotunan nan, wallahi zuciyata na gab da tarwatsewa. Idan har da gaske ka ke sona, so kuma na tsakani da Allah to ka taimaka min ka rufa min asiri” ta ƙare maganar kuka na kwace mata. Junaid da ke tsaye a balcony ya saki kyakkyawan murmushi muryarsa wasai babu alamar damuwa ya ce “Da dana ke kiran ki shi ne ba zaki ɗaga ba ko?. Sai yanzu saƙona ya iso gare ki kenan, fatan dai ke kaɗai ki ka gani?” Nana ta haɗiye wani miyau mai ɗaci ba tare da ta ce komai ba. Junaid ya ci gaba da faɗin “Ki ɗauka wannan shi ne karo na ƙarshe da zan gargaɗeki akan maganar auren nan. Wallahi idan har aka kai gobe ban ji labarin fasa aurenki ba to ba saƙo zan bawa mahaifinki ya kawo miki ba. A'a shi da kansa zan bawa a matsayin kyautar auren ki” Runtse idanu Nana ta yi saboda yanda zuciyarta ta yi wata irin bugawa, ta zauna gefen gadon hawaye na zubowa kan fuskarta. Cikin sabon yanayin daya risketa ta buɗe bakinta a sanyaye ta ce “Shikenan zan fasa auren!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 30... Nana ta sauke numfashi tana jiran abin da zai ce. Ɓoyyayiyar ajiyar zuciya Junaid ya sauke sai kuma ya ce“Taya zan tabbatar da haka?” Runtse idanunta ta yi wanda ya bawa hawayen dake cikin idanun damar gangarowa kan fuskarta. Ta ɗan suɗe laɓɓanta na ƙasa kafin ta ce“zan faɗawa Abba bana son auren” jinjina kai Junaid ya yi sai kuma ya ce “Ok. Na baki daga yau zuwa gobe, idan har ban ji an fasa auren ba to ki sani zan kawo ƙarshen wannan wasan namu” Nana ta yi shiru tana shessheƙar kuka a hankali. Jin bata ce komai ba yasa ya ce “Zan katse wayar” “A'a dan Allah... Ina son na tambayeka” Junaid ya gyara zaman wayar da ke kunnensa yana saurarenta da kyau ya ce“ina ji” “Da gaske kana sona kuwa?” Nana ta yi maganar cikin wani irin sanyi daya zarce misali. Junaid ya ɗan murmusa ya ce “Tambaya ki ke Nana?. Duk abin da nake bakya gani kenan?” Ta girgiza kanta kamar yana gabanta ta ce“ance masoyin gaskiya baya son yaga masoyiyarsa cikin matsala. Amma me ya sa kai ka ke kokarin yin abin da zai zame mini matsala?” Junaid ya yi shiru kamar me tunani. Jin haka yasa Nana ta ɗan yi wani murmushi mai haɗe da hawaye ta ce “shikenan sai da safe” Daga haka ta katse wayar ta ajiye gefenta. Rasa abin yi ta yi sai kawai ta fashe da wani irin raunataccen kuka, Dai dai nan aka buɗe ƙofar ɗakin. Aunty Ramlah ta dinga kallonta sai kuma ta ƙaraso ciki tana faɗin “Nana kukan me ki ke?” Girgiza kai Nana ta yi cikin kuka ta ce“Aunty ki kira min Ammana. Dan Allah ki kirata mutuwa zan yi” Aunty Ramlah ta dinga kallonta sai kuma ta juya da sauri ta fice daga ɗakin. Nana ta yunƙura da kyar ta mike ta haɗe hotunan ta tusa ƙasan katifar gadonta dai dai nan Amma ta shigo ɗakin Aunty Ramlah na biye da ita. Amma ta dinga kallonta ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita, Ta zauna gefen gadon ta dafata cikin rauni ta ce “Nana mene ne kuma?” Kasa bata amsa ta yi sai kawai ta shige jikinta tana sake rushewa da wani sabon kukan, Amma ta ɗora hannunta akan bayanta ta dinga shafawa a hankali. Gaba ɗaya bata jin daɗin yanda Nanar ta koma, ta rasa dalilin daya sanya taƙi kwantar da hankalinta. Suna nan zaune har bayan mintuna biyar sannan ta fara rage sautin kukan nata, dan haka Amma ta ɗagota tana kallonta ta ce“kukan me ki ke Nana?” cikin shessheƙar kuka Nana ta ce “Amma dan Allah ina son magana da Abba. Dan Allah Amma, zuciyata zafi take min” Ganin yanda take numfashi da kyar ya sanya Amma ta ce“to tashi muje na raka ki yana ɗakinsa” dakyar Nana ta miƙe Aunty Ramlah na kallonsu ta ce“ku je bari na jira anan” okay kawai Amma ta ce sannan ta riƙe hannun Nana suka fita daga ɗakin a hankali. Aunty Ramlah ta girgiza kai tana kokarin zama gefen gadon ta ce “oh Allah ya yi mana maganin masifa” Zaune suka tadda Abba kan kujerar da ke ɗakin, yana waya da wasu abokansa da zasu zo daga Paris. Ganin hawaye a fuskar Nana ya sanya ya katse wayar ba tare da ya gama ba. Ya dinga kallonsu sai kuma ya ce “lafiya dai?” Ya yi tambayar yana miƙewa tsaye. Amma bata ce komai ba, sai sakin hannun Nana da ta yi. Ta ƙarasa gabansa a hankali tana kuka ƙasa-ƙasa, Ba ƙaramin rikicewa Abba ya yi ba, dan duk wani abu daya shafi Nana baya ɗaukansa da sauƙi. Ya riƙe hannayenta duk biyun muryarsa cike da damuwa ya ce “Nana mene ne?” Sunkuyar da kanta ta yi wasu zafafan hawaye suka shiga sakkowa kan fuskarta. Ta kasa cewa komai sai murɗa yatsun hannunta take, Abba ya yi shiru sai kuma ya kalli Amma ya ce“what's going on?” girgiza kai ta yi a sanyaye ta ce“wallahi nima ban sani ba. Ramlah ta zo ta ce min wai gata nan tana kuka, da naje shi ne ta ce na kawo ta wajenka” Abba ya mai da idanunsa kan Nana wadda har sannan bata ce komai ba. Ya zaunar da ita sannan ya zauna gefenta yana kallonta sosai ya ce“Nana tell me meya faru? Why are you crying?” Ɗago jajayen idanunta ta yi ta kalleshi, bakinta ya fara rawa kamar zata yi magana sai kuma ta sake sunkuyar da kanta tana sakin wani sabon kukan. Abba da ransa ya fara ɓaci ya ce “Kin faɗa min mene ne ko sai na bugeki?” A hankali ta sake ɗago kanta tana kallonsa, sai kuma ta ɗaga kanta ta kalli Amma dake tsaye kusa da su. Ganin duk ita suke kallo yasa ta saukar da idanunta ƙirjinta na wani irin bugawa da ƙarfi, ta buɗe bakinta da take jin kamar ba nata ba. In a very polite tongue ta ce “Abba daman akwai abin da nake son faɗa maka, but...but I can't, saboda ban san ya zaku ɗauki al'amarin ba” Abba ya yi shiru yana saurarenta. Jin babu wanda ya ce komai a cikinsu yasa ta ɗago kanta hawaye na biyo fuskarta ta ce “wallahi bana son Yaya Safwan. Bana son aurensa, dan Allah dan Annabi Abba a fasa auren nan. Wallahi ba zan iya zama dashi ba, dan girman Allah kawai...” Bata samu zarafin faɗin ƙarashen abin da ke bakinta ba, sakamakon zazzafan marin da Abba ya sauke mata akan both checks ɗinta. Ta sanya hannunta ta dafe kuncinta tana jin wata irin raɗaɗin azaba. Dakyar ta iya buɗe idanunta wanda take jin kamar sun fashe ta ɗago kanta. Tsaye taga Abba a gabanta yana wani irin huci kamar yunwataccen Zaki. Yanda yake kallonta zai tabbatar maka da tsananin ɓacin ransa da yake ciki, gumi sai tsatsafo masa yake duk da ac dake ɗakin. Amma ta ƙaraso wajen da sauri ta jawo hannun Nana itama ta sauke mata wani zazzafan mari a kuncinta na dama, Nana ta rasa yanda zata yi saboda azabar data mata yawa. Cikin tsananin ɓacin rai Amma ke faɗin “Wato duk irin abin da na faɗa miki baki ji ba kenan ko Nana? Duk nasihar da nayi miki ta tashi a banza kenan ko? Baki ji abubuwan da nace miki ba ko?” Ban da girgiza kai babu abin da Nana ke yi dan gaba ɗaya magana ta gagareta. Ta zube a ƙasa ta riƙe ƙafafun Abba da duka hannayenta biyu cikin wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fara magana “Na sani Abba ban kyauta ba, ban kuma yi dai dai ba idan har naƙi bin umarninka a matsayinka na mahaifina. Ka cancanci nayi maka kowace irin alfarma Abba, amma wallahi ba zan iya wannan ba, ba zan iya auren Yaya Safwan ba. Zuciyata ba zata jure zama dashi ba, na so na danne na kuma yi haƙuri akan haka, amma ina gudun abin da hakan zai haifar daga baya. Dan haka dan girman Allah, dan soyyayar ka da Annabinsa. Ka raba auren nan dan Allah, kada ka bari na aure shi Abbana, ka rufa min asiri!” Ta ƙare maganar tana sakin wani irin marayan kuka. Dakyar Abba ya janye ƙafafunsa daga gurin, ya shiga zagaye ɗakin ba tare da ya ce komai ba. Amma ta tsaya a wajen kamar statue, sai ta kalleshi sai kuma ta kalli Nana. Above 5mins kafin yaja ya tsaya a tsakiyar ɗakin hannayensa naɗe a ƙirjinsa yana kallonta. Idanunsa sun kaɗa sun yi jajur dasu, har wani ruwa-ruwa ne ya kwanta a cikinsu na zallar baƙin ciki. Ya furzar da zazzafan numfashi daga bakinsa sai kuma ya shiga girgiza kansa yana faɗin “Wai Ƴata! Wai ƴar dana haifa ce zata faɗi irin wannan maganar. Ƴar da nake saka ran zata yimin biyayya koda ace bata son abu, Yar dana ɗauki dukkan yarda na ɗora mata ita ce take shirin watsa min ƙasa a idanu!. Yar da nake tunanin ba zata taɓa bani kunya ba, ita ce ke shirin tona min asiri a cikin dubban jama'a.” Ya tsaya da maganar yana sauke numfashi, Sai kuma ya sake mai da idanunsa kanta a zafafe ya ce “Wallahi tallahi baki isa ba Nana! Ban haifi Yar da zata juyani ba. Duk abin da ki ke so zan iya miki shi, amma ba zan taɓa yarda ki zubar da mutuncin gidanmu ba! Baki isa ba Nana!” Kasa ɗago kanta ta yi sai hawaye take dan yanzu ko sautin kukan nata ma ba'a ji. Amma ta yi shiru tana kallonsa duk da bata ji daɗin abin da Nana ta yi ba, hakan bai hanata jin tausayinta ba a matsayinta na mahaifiyarta. Sai dai ganin yanda ran Abba ya ɓaci ya hanata cewa komai. Da kansa ya tako har gabanta ya sanya hannunsa ya ɗagota yana kallonta ya ce “Koda auren Safwan na nufin rasa rayuwarki wallahi Nana sai dai ki mutu. Na kuma yarda na rasa ki, akan ki zubar da martaba da kuma ƙimar da muka ɗauki shekaru masu yawa muna tattalinta. Dan haka ki shirya zama matar aure daga yau zuwa jibi.” yana gama faɗin hakan ya saketa ya juya ya fice daga ɗakin yana bugo ƙofar. Amma ta sulale a ƙasa tana jin ranta na mata wani irin suya, ita kuwa Nana kasa motsi ta yi sai numfarfashi take. Har bayan mintuna sha biyar suna zaune a wajen zuciyoyinsu babu daɗi, Nana ta yunƙura da kyar ta tashi ta fice daga ɗakin tana riƙe da kanta, Amma ta bita da idanu har ta fice. Lokaci ɗaya ta fashe da wani irin kuka, wanda rabonta da ta yi kuka tun rasuwar mahaifiyarta sai gashi yau tana sake kuka akan auren NAANAH.. **** Ƙarfe 9:30 na dare ta buɗe ɗakin ta shigo. Zaune ta hangeshi tsakiyar gado ya tankwashe ƙafafunsa yana sipping coffee a hankali, hannunsa ɗaya akan system yana operating ɗinta. Zahra ta dinga kallonsa can kuma ta sauke numfashi ta ƙaraso ciki, A gefen gadon ta zauna tana kallonsa har sannan ba tare da ta ce komai ba. Idanun da yaji suna yawo akan sa ya sanya shi ɗago kansa, suka yi ido biyu da Ita, a hankali ta sauke nata idanun. Ya dinga kallonta sai kuma ya rufe system ɗin ya sakko daga kan gadon, a gefen drawer ya ajiye system ɗin ya kuma ajiye mug ɗin hannunsa. Sannan y koma ya zauna yana kallonta yace “Zahra” Yanda ya yi maganar a sanyaye ya sanyata ɗago kanta, hawaye ya gani kan farar fuskarta. Ya yi shiru can kuma ya ce“zo mana” jiki a sanyaye ta tashi ta ƙarasa inda yake sannan ta zauna, ya jawo hannunta yana shafawa a hankali ya ce “Mene ne?” Muryarta na rawa ta ce“doctor da gaske aure zaka yi?” Ta ƙare maganar tana ɗago idanunta wanda hawaye ke zuba daga cikinsu. Abdusammad bai iya ɓoye-ɓoye ba dan haka ya gyaɗa mata kai ba tare da ya ce komai ba. Ta sunkuyar da kanta tana kuka a hankali, girgiza kansa y yi sai kuma ya ɗago fuskarta da hannunsa na hagu yana kallonta ya ce ”but you promised cewa ba zaki tada hankalin ki ba right?” Zahra ta gyaɗa kanta lokaci ɗaya ta shiga goge hawayen idanunta ta ce“i'll not. Allah ya bamu zaman lafiya” Amin kawai ya ce sai kuma ya yi shiru yana nazarinta. Tabbas bata ji daɗi ba, kawai dai bata son ta nuna tashin hankalinta har ya ɓata masa rai, dan haka shima bai sake maganar ba suka shiga wata hirar ta daban. Daren ranar babu wanda ya runtsa tsakanin Abba, Amma da kuma Nana. Kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa, Amma na tunanin yanda zata saka Abba ya yarda a fasa auren Nana, yayinda Abba ke tunanin yanda zai ɓoye al'amarin kada kowa ya samu labari. A ɓangaren Nana kuma ta kwana tana kukan rashin sanin abin yi, ya zata yi da Junaid da kuma Zahra? Junaid ya yi alkawarin idan har bai ji maganar fasa aurenta gobe ba zai turowa Abba hotunanta. Haka ma Zahra, dan haka abin duniya ya isheta ta kasa koda runtsawa sai juyi take akan gadonta, ana fara kiraye-kirayen sallar asuba ta mike daga kwancen, ta shiga toilet ta ɗauro alwala sannan ta fito ta fara gabatar da sallolin nafila har aka yi assalatu. Koda ta idar da sallah zama ta yi nan kan ladduma ta ci gaba da saƙa da warwara har gari ya fara haske. Ringing ɗin wayarta ne ya sanya ta tashi daga wajen, ta ƙarasa gaban mirror ta ɗauki wayarta, ganin kiran Junaid ya sanya gabanta ya yanke ya faɗi, hannunta na rawa ta ɗaga kiran ta kai kunne. Junaid na fitowa daga masallaci ya ce “Ya dai Nana?” Shiru ta yi tana tunanin ta hanyar da zata fara faɗa masa. Jin bata ce komai yasa ya sake cewa “are you there?” Ta gyaɗa kanta kamar yana gabanta. Sai kuma ta numfasa ta ce “eh.” “Ya ku ka yi dasu?” Girgiza kanta ta yi ta ce “basu yarda ba, Abbana ya ce dole sai na aure shi. Dan Allah dan Annabi sir ka yi haƙuri, ka barni na yi auren nan. Ni na haƙura da soyyayar, Allah ya baka wadda ta fini” Junaid ya yi wani murmushi sai kuma ya ce “shikenan Nana. Allah ya baku zaman lafiya, zuwa an jima kuma saƙona zai iso ga mahaifinki.” Daga haka ya katse kiran, girgiza kai Nana ta yi sai kuma ta sake dialing number amma sai aka ce mata a kashe. Ta koma gefen gado ta zauna lokaci ɗaya ta fashe da kuka, kifa kanta ta yi akan cinyarta ta fara rera kukanta, ta dinga jin zuciyarta na mata wani irin zafi da suka, tana nan zaune har bayan mintuna biyar wayarta ta fara ruri dan haka ta ɗago kanta da sauri ta ɗauki wayar da tunanin Junaid ne. Sai dai ganin lambar babu suna yasa ta kawar da wannan tunanin, ta yi kamar ba zata daga kiran ba sai kuma wata zuciyar ta ce mata “Idan kuma shi ya sauya lamba ya kira ki fa?” Ta sauke numfashi sai kuma ta ɗaga kiran bakinta na rawa ta ce “Salamu alaikum” Daga ɗaya ɓangaren aka ce “Ina magana da Nana ne?” Nana ta yi shiru tana tunanin inda ta san muryar, ganin ta kasa tunawa yasa ta ce “Eh ni ce.” Siyama ta gyara zamanta kan sofa sannan ta ce “kece wadda ki ke shirin auren Safwan ko? To ki sani tun wuri gara ki rabu dashi. Domin Safwan ba mijinki bane, ni zai aura. Ki fita a sabgarsa tun kafin ran ki ya ɓaci wallahi, dan zan iya komai akan sa, ke zan iya kasheki akansa” Nana ta yi shiru sai kuma ta ce “tam na gode.” Daga haka ta kashe wayarta ta yi jifa da ita, sai kawai ta sake fashewa da wani irin kuka. Nan da nan tari ya fara turnuƙeta, sai kuma ta fara aman jini har da guda-guda dai dai nan Amma ta buɗe ɗakin ta shigo hannunta riƙe da mug. Sai dai halin da taga Nana ya sanya ta saki mug ɗin a ƙasa ta ƙarasa gabanta cikin tashin hankali ta ɗagota tana faɗin “Nana! Nana! Ke Nana” Ko kaɗan Nana bata jin abin da take faɗa, dan babu alamar tana tare da ita. Dan haka ta tashi da gudu ta fice daga ɗakin, Abba na tsaye a balcony shi da Sultan ta ƙarasa cikin tashin hankali take faɗin “Yallabai Nana! Nana” Abba ya kalleta ganin yanda take kuka yasa ya ce“lafiya me ya samu Nanan?” Bata iya bashi amsa ba sai girgiza kanta kawai take, Sultan kuwa bai jira sun gama maganar ba ya nufi cikin gidan da sauri. Ganin haka yasa Amma da Abban suka bi bayansa. Sultan ya dinga kallonta ganin halin da take ciki yasa ya sunkuya ya ɗauketa kamar ƙaramar yarinyar suka fito daga ɗakin, Abba ya biyo bayansa. Aunty Ramlah kuma ta rike Amma ganin babu ko mayafi a jikinta, cikin kuka take ƙoƙarin janye hannunta tana faɗin “Ramlah ki cikani dan Allah, ki bar ni na bisu” “To Yaya amma ki fara saka mayafi” Aunty Ramlah ta ƙare maganar cike da damuwa. **** Around 3pm Sultan ya fito daga ward ɗin hannunsa riƙe da wata takarda, Abba da Amma da ke zaune suka mike a tare suna kallonsa. Ganin bai ce komai ba yasa Abba ya ce “Ya jikin nata?” Miƙewa Abba takardar hannunsa ya yi cike da damuwa ya ce “Ban san mene ya dameta haka ba da har ya haifar mata da wannan ciwon, but koma mene ne ya kamata a ɗau mataki akansa” Abba ya warware takardar ya shiga karantawa. Bayan ya gama ya ɗago kansa yana kallon Sultan cike da mamaki da kuma tashin hankali ya ce “Nana ce ke fama da ciwon zuciya?” Sultan ya gyaɗa masa kai jiki a sanyaye. Amma ta riƙe Abba cikin tashin hankali ta ce“ciwon zuciya kuma? Nanan tawa?” Abba ya riƙe hannunta ba tare da ya ce komai ba. Fashewa ta yi da kuka tana kallon Sultan ta ce“ina take? Ina son na ganta” da hannu ya nuna mata ɗakin da aka kwantar da Nanan. Ta yi gaba da sauri ba tare da ta sake cewa komai ba, Abba ya numfasa sai kuma ya naɗe takardar yana kallon Sultan ya ce“ya jikin nata?” “Da sauƙi sosai ta farfaɗo ma. Muje ka ganta” Okay kawai Abba ya ce sannan yabi bayan Sultan jiki a sanyaye. Zaune suka tarar da Amma gefen gadon ta riƙe hannun Nana sai kuka take, Abba ya tsaya jikin ƙarfen gadon yana kallon Nana wadda idanunta ke rufe tana sauke numfashi a hankali. Sultan ne ya yi ƙarfin halin cewa “Dan Allah Amma ki yi haƙuri” Tashi ta yi daga wajen ta juyo tana kallon Abba ta ce“Idan har kana son Nana. Idan har baka shirya rasata ba dan Allah dan Annabi ka bar maganar auren nan. Wallahi shi ne abin da ya haifar mata da wannan mugun ciwon, ka taimaka ka bar maganar auren nan. Kada ka yi abin da zamu rasa yar mu da kanmu” Abba bai ce komai ba, sai numfasawa da ya yi. Sultan ya kalli Amma da mamaki ya ce”Nana bata son auren nan?” Cikin kuka Amma ta ce“Bata so Sultan, tun ranar da aka fara maganar ta ce bata so. Amma na hanata faɗa, na gargaɗeta akan ta yi shiru. Ban yi tunanin abun zai kai haka ba, ban yi tunanin Nana zata damu kanta irin haka ba, tun daga sanda aka fara maganar auren nan ban sake ganin walwalarta ba. Yarinya ce ƙarama, aure ba dole bane akanta, dan Allah ka fahimtar dashi” Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka. Shiru Sultan ya yi, lokaci ɗaya ya ji jikinsa ya yi wani irin sanyi. Ya kalli Amma wadda ke faman kuka sai kuma ya mai da idanunsa kan Abba wanda tun ɗazu bai ce komai ba, Ya taka har gabansa cikin sanyin murya ya ce “Abba dan Allah...” Ɗaga masa hannu Abba ya yi, Sultan ya yi shiru yana kallonsa. Amma ta juyo tana kallon Abba da mamaki jin bai ce komai ba. Ya numfasa sannan ya taka har gaban gadon ya dafa goshin Nana jin babu zafi yasa ya sauke numfashi. Amma ta dawo gurin tana kallonsa ba tare da ta ce komai ba. Abba ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonsu duka ya ce“Babu yanda za'a yi na janye maganar auren nan, dole sai Nana ta auri Safwan. Wannan shi ne matsayata!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Happy independence day. Page 31. Kallonsa suka dinga yi da mamaki, Sultan ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba, amma gaba ɗaya ransa babu daɗi, bai so a ce haka Abba ya ce ba. Amma dake tsaye gefen Nana ta ƙaraso gabansa dan sam ta kasa jurewa cikin tsananin ɓacin rai ta ce “Me ka ce Yallaɓai? Ba za'a fasa auren nan ba? Kenan ka shirya ta mutu ta bar duniya?” Abba ya ɗan kalleta sai kuma ya mayar da idanunsa kan Nana da ke sauke numfashi ɗaya bayan ɗaya ya ce“Eh. Ba za'a fasa auren nan ba, sai Nana ta auri Safwan, idan ki ka ga an fasa auren nan sai dai idan Safwan ne da kansa ya zo ya ce min baya son Nana, ke to ko haka ne bai isa ba, dole sai ya aureta. Babu yanda za'a yi yara su zo daga baya sannan su nemi ruguza mana dangi, ba zai taɓa yiwuwa ba” “Kenan gara ka aurar da ita ta mutu ko? Haba dan Allah Nana ce fa, ur one and only daughter, bayan ita fa baka da wata. Ita kaɗai ce amma har ka yi tunanin gara ta mutu akan ƙima?” Amma ta ƙare maganar a mugun fusace. Abba ya gyaɗa kansa jin tana neman ɓata masa rai ya ce“haka na faɗa Rabi'ah, kuma babu wanda ya isa ya sauya wannan hukuncin dana yanke! Idan har ni Ahmad ni ne na yi cikin Nana kuma ki ke haifeta to wallahi ba zan janye maganar auren nan ba, idan ta so ta mutu.” Abba ya juya ya fice daga ɗakin rai ɓace. Amma ta bishi da kallo sai kuma ta mai da Idanunta kan tilon ƴar tata da ke kwance tana bacci, ta durƙushe a wajen tana fashewa da kuka. Sultan ya dinga kallonta cike da tausayinta, lokaci ɗaya kuma ya juya ya fice daga ɗakin. Tsaye ya samu Abba a kofar dakin ya harɗe hannayensa a ƙirji, gumi sai tsatsafo masa yake, ko ba'a faɗa ba kasan ransa a ɓace yake, haka kuma hankalinsa a tashe yake. Sultan yaja ya tsaya yana kallonsa cike da damuwa. Above 5mins kafin ya sauke numfashi ya gyara tsaiwarsa cikin tattausan harshe ya ce “Abba dan Allah ka yi haƙuri” Ɗan murmushin yaƙe Abba ya yi yana girgiza kansa ya ce“Babu komai Sultan. Zuwa yaushe za'a iya discharging nata?” Sultan ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce“ai jikin nata da sauki ma, ko zuwa magrib za'a iya sallamarta. Kawai dai abin dubawar shi ne halin da take ciki” Toh kawai Abba ya ce sai kuma ya juya ya koma ɗakin ba tare da ya sake cewa komai ba, Sultan ya sauke numfashi yana cin ransa babu daɗi. Dan ya san halin Abba, muddin ya kafe akan magana to babu wanda yake sauya shi. Ko da ya koma zaune ya samu Amma gefen gadon sai kuka take a hankali. Hannunta ɗaya akan goshin Nana tana shafawa, ɗayan kuma riƙe da nata hannun. Kallonsu kawai ya dinga yi ba tare da ya ce komai ba. Shi kansa baya jin daɗin halin da Nanar ke ciki, amma hakan ba zai taɓa sakawa ya bari a zubar da mutuncin gidansu ba, dama ace wata ce ba ƴarsa ba, da zai iya yin shiru idan har iyayenta sun aminta. amma hakan ba zai taɓa faruwa da yar sa ba “Never!” Maganar ta suɓuce masa ba tare da ya yi aune ba. Amma ta juyo tana kallonsa sai kuma ta ɗauke kanta ba tare da ta ce masa komai ba, shima bai damu da shirun nata ba dan daman bai saka ran zata masa magana ba. **** Siyama ta dinga kallon Aunty Khadijah sai kuma ta kalli Kaddu, lokaci ɗaya ta zumɓura baki tana hararar malamin ta ce “wallahi ba zai yiwu ba, tabɗijan, ni ba zan iya ba!” Ta ƙare maganar tana mai da kanta ga kallon waje. Aunty Khadijah ce ta matse hannunta murya can ƙasa ta ce“ke wace irin shashasha ce?” Juyowa ta yi tana kallonta kamar zata yi kuka ta ce“Mom kin ji fa abin da ya ce, ya ma za'a yi na yarda da wannan mutumin ya wani taɓani. Ni gaskiya a'a!” Ta sake ɗauke kanta. Shiru Aunty Khadijah ta yi sai kuma ta mai da Idanunta kan malamin wanda yake kallonsu tun ɗazu ba tare da ya ce komai ba, ta ɗan kirkiri murmushi kana ta ce“Malam babu wata hanyar ne? Ko ni na fansheta, ka ga budurwa ce wallahi bata taɓa sanin namiji ba” Haɗe rai ya yi muryarsa babu wasa ya ce“to idan kin fansheta kece zaki aureshi? Kada ku manta gobe ne ɗaurin aure nan, dan haka ni babu ruwana zaɓi ya rage naku” Aunty Khadijah ta yi shiru dan jikinta ya yi sanyi, ta kalli Kaddu wadda ita ma su ɗin take kallo sai kuma ta mayar da idanunta kan Siyama ganin yanda ta juyar da kai yasa ta ce“zo ki ji” daga haka ta miƙe tana riƙe hannunta. Soro na biyu ta jata tana mata wani irin kallo ta ce“kina son ki lalata mana aiki ne? Kin san wahalar da muka sha har muka kawo i yanzu?” Siyama ta tura baki tana leƙan ciki ta ce“to wai Mom baki ji me ya ce ba, wai na bashi jikina zai min wani aiki. Ni wallahi ba zan iya ba” Tsaki Aunty Khadijah ta yi ta ce“to mene ne a ciki? Duk ba ke ake nemawa farin ciki ba? Shi ne zaki watsa mana ƙasa a ido” Siyama ta yi rau-rau da idanu ta ce“kenan na yarda na bashi kaina? To shi kuma Safwan ɗin fa? Idan aka yi auren ya gane ni ba budurwa ba ce” Tsaki Aunty Khadijah ta yi ta ce“to taya za'a bar shi ya gane? Ko ma ya gane me zai iya bayan kin riga da kin mallakeshi. Ai babu yanda zai yi da ke, kuma wannan aikin da za'a yi shi ne zai saka ya bijirewa gidan ya ce shi ke yake son aura ba wacce yarinyar ba. Kin ga idan har baki yarda ba shikenan mun ɓata lokacinmu a banza, kuma burinmu ba zai taɓa cika ba” Siyama ta yi shiru tana kallonta ba tare da ta ce komai ba, tunaninta ya kasu gida biyu, ta yarda da abin da ake faɗa mata ko kuma ta ƙi yarda. Jin bata ce komai ba yasa Aunty Khadijah faɗin “Mu je ko” Kasa yi mata musu ta yi, ta samu kanta da bin bayan mahaifiyar tata wanda ke nuni da cewa ta amince da duk abin da ta ce. **** Around 6:00 na yamma motarsu ta yi parking a compound ɗin gidan, kasancewar ranar ake yinin yan mata yasa ko ina yake a cike. Jama'a an taru sai shige da fice ake. Amma ce ta fara fitowa daga motar sannan Nana ta fito, Amma ta riƙeta tana sake mata sannu, Abba ya kalli Sultan wanda ke tsaye ya ce “Kaje ka huta Sultan ka sha wahala” Girgiza kai ya yi ya ce“ba komai Abba. Bari naje na faɗawa Hajiya Babba” Abba ya ce“a'a kada ka sanar da ita yanzu, a bari ko zuwa gobe idan Allah ya kaimu. Ka ga yanzu jama'a sun taru” Sultan ya jinjina kansa kafin ya ce“,haka ne kuma, to bari naje ciki” okay kawai Abba ya ce sannan ya amshi ledojin drugs ɗin da ke hannunsa. Yabi bayan su Amma dan tun fitowarsu ta shige ciki ita da Nana. Ta ƙofar baya ta shiga gudun kada mutane su damesu, ta kai Nana bedroom ɗinta ta zauna sannan ta ce “Sannu bari na kawo miki abinci” Riƙe hannun Amma ta yi tana girgiza kanta ta ce“na ƙoshi Amma” Amma ta zauna gefenta ta jawota jikinta ta rungumeta muryarta na rawa ta ce “Nana dan Allah ki kwantar da hankalinki, kada ki yi abin da zai sa mu rasaki. Ba zamu jure ba, dan Allah dan Annabi ki yi hakuri ki bar maganar nan kin ji" Amma ta ƙare maganar tana ɗago kanta. Murmushi mai haɗe da hawaye Nana ta yi kafin ta ce“na bari Amma, wallahi na bari. Ba zan sake maganar ba, koda auren Yaya Safwan na nufin rasa rayuwata zan aureshi, ba zan bari Abba ya yi baƙin ciki dani ba” Amma ta sauke ajiyar zuciya tana jin shessheƙar kukanta. A hankali ta dinga shafa bayanta tana sake bata haƙuri. Ana haka Aunty Ramlah ta buɗe ɗakin ta shigo tana kallonsu ta ce“Yaya ya jikin Nanar?” Ganin yanda duk suke kuka ya sanya jikinta ya yi sanyi fiye da misali, ta zaune gefen gadon murya a sanyaye ta ce “Lafiya dai Yaya?” Amma ta ɗago kanta tana janye Nana daga jikinta ta ce“da sauƙi Alhamdulillah” daga haka ta tashi ta fice daga ɗakin. Da idanu Aunty Ramlah ta bita sai kuma ta kalli Nana wadda ta kwanta kamar gawa ta ce “Nana ya jikin?” “Da sauƙi” Ta ce a sanyaye tana rufe idanunta. Aunty Ramlah ta ɗan yi jim sai kuma ta tashi ta fice daga ɗakin. Bayan sallar magriba Zahra ta shigo parlon Amma tana neman Nana, Amma ta sanar da ita tana cikin daƙinta dan haka ta nufi ɗakin kai tsaye. Bata samu kowa a ciki ba sai Nanar dake kwance tsakiyar gado idanunta a lumshe sai dai ba bacci take ba, ta tsaya a gefen gadon tana ƙare mata kallo sai kuma ta ce “Nana” Kamar a mafarki haka Nana taji saukar maganarta, dan haka ta buɗe idanunta a hankali tana kallonta. Lokaci ɗaya kuma ta tashi zaune tana girgiza kanta cikin kuka ta ce “Dan Allah dan Annabi Aunty Zahra ki barni haka, ki rabu da rayuwata haka. Na fadawa Abba bana son auren amma yaƙi saurarata, dan Allah dan Annabi ki bar ni haka, ki rufa min asiri” Zahra ta yi wani irin kyakkyawan murmushi sai kuma ta kai hannunta ta dafata. Nana ta dinga kallonta ganin bata ce komai ba, after 2mins ta sauke numfashi ta ce“Nana ni ba wai ina son cutar da ke bane, Ni bana nufinki da sharri. Yanzu ma naji an ce baki da lafiya ne nace bari na zo na duba ki, dan haka ki kwantar da hankalinki” Nana ta yi shiru tana kallon Zahra da mamaki, Zahra ta sanya hannunta ɗayan ta goge mata hawaye da ke zubowa kan fuskarta ta ce“let bygone be bygone, ki bar damun kanki kada wani ciwon ya sameki” ban da gyaɗa kai babu abin da Nana ke yi dan duk zatonta Zahra ta zubar da makaman yaƙinta ne. Dan haka taji damuwarta ta ɗan ragu da kashi 40, suna nan zaune kowa ya yi shiru aka buɗe ƙofar ɗakin, Maimoon ce ta shigo tana sanye da doguwar rigar lace ɗin da aka musu, fuskarta ta sha makeup wadda ta ƙara mata kyau. Ta dinga kallon Zahra fuska a haɗe sai kuma ta ƙaraso wajen ta zauna gefen Nana na dama ta riƙe hannunta ta ce “Nana ya jikin naki?” A sanyaye ta ce“Da sauƙi” “ɗazu make up artist ta zo za'a mana make up aka zo kiranki aka ce wai kuna asibiti, Nana ki daina damun kan ki kinji” Gyaɗa mata kai kawai Nana ta yi, dan da gaske magana wahala take mata. Zahra ta dinga kallon Maimoon ganin bata kulata ba, Maimoon kuwa ɗauke kanta ta yi dan ba zaka taɓa cewa taga Zahra a wajen ba, cikin son cusa mata takaici ta ce “Yanzu uncle zasu shigo ma, dashi da Haule amaryarsa. Nana kin ganta kuwa? Kyakkyawa da ita” Nana ta ɗan kalleta sai kuma ta ce“ni na warke fa” Maimoon ta harareta tana sake riƙe hannunta ta ce“to dan kin warke ba za'a zo a dubaki ba? Harda angonki ma Yaya Safwan zasu zo” Nana ta yi shiru tana jin ƙirjinta na tsananta bugu, haka kawai idan taji an yi maganar Safwan sai taji ƙirjinta na bugu da sauri. Ta lumshe idanunta wanda ya bawa hawayen dake cikin kurmin damar gangarowa kan fuskarta. Zahra na ƙoƙarin tashi aka sake buɗe kofar ɗakin, dan haka ta tsaya tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya har suka gama shigowa. Sultan ne sai Safwan, Aliyu, Hamid, Abdusammad, Hamida, Amrah, da kuma Haule. Zahra ta koma ta zauna ba tare da ta ce komai ba, sannu suka dinga yiwa Nana kowa na jinjina al'amarin barin ganin yanda ta rame ta ƙarmashe kamar ka hureta ta faɗi. Maimoon da ke son baƙanta ran Zahra ta kalli Safwan ta ce “Yaya baka ga matarka ba? Abar tausayi” Murmushi kawai ya yi idanunsa zube kan Nana wadda yake ganin ta ƙara wani irin kyau duk da ramar da ta yi, Ganin haka yasa Maimoon ta ce“gobe i yanzu dai ai tana gidanka sai dai idan ɗan baƙin ciki ya mutu!” ta ƙare maganar tana hararar iska. Babu wanda ya fahimci abin da take nufi a wajen sai Abdusammad duk da shima bai gane da wata take ba. Hamida ta girgiza kanta tana sake kallon Nana ta ce“Allah sarki Nana kamar ba ke ba duk kin rame, ki daina saka komai a ranki kin ji” “To me zata saka a ranta daman? Bayan tana cikin rufin asirin dangi da yan uwa, ji fa kowa anan nata ne. Duk nan danginta ne, ai yan uwa sun fi komai daɗi” Maimoon ta sake maganar tana satar kallon Zahra, kamar yadda ta yi tunani haka ce ta faru kuwa dan iya ɓaci ran Zahra ya ɓaci amma gudun kada a gane ya sanya ta danne bata ce komai ba. Haka suka dinga hira ana zolayar juna wanda ya sanya Nana ta saki jikinta har da dariya wadda rabonta da dariya har ta manta. Aliyu ya dinga kwasar Abdusammad da maganar Haule wadda ta yi shiru ta sunkuyar da kai saboda kunya irinta Fulani, hakan kuma ya sake tunzura Zahra ba kaɗan ba. Daga ƙarshe ta tashi tana kallon Nana ta ce “Nana Allah ya ƙara sauƙi bari naje” toh kawai Nana ta ce ta juya ta fice daga ɗakin ba tare da ta cewa kowa komai ba, suma hakan bai damesu ba dan ba da ita suke hirar su ba. Suna nan har kusan ƙarfe 10:00 na dare sannan Abdusammad ya ce kowa ya tafi. Nan da nan kuwa kowa ya watse ya yi apartment ɗinsu aka bar wa gobe sauran. Zahra na zaune gefen gadon bayan sun gama waya da Aunty Khadijah idanunta ya yi luhu-luhu da alama ba ƙaramin kuka ta ci ba, ta dinga jujjuya envelope ɗin hotunan dake gabanta. Ganin lokaci na tafiya ya sanya ta mike ta zura hijabi sannan ta fice daga ɗakin. Around 11:00 na dare Amma ta buɗe dakin ta shigo, kwance ta samu Nana ta juya baya ta zauna gefen gadon sannan ta taɓa ta a hankali ta ce “Nana!” Buɗe idanunta ta yi dan daman ba bacci take ba, ta tashi zaune tana jingina da jikin gadon. Amma ta dinga kallonta sai kuma ta ce“ya jikin naki?” “Da sauƙi Amma” Ta ce a sanyaye. Jinjina kai Amma ta yi sai kuma kowa ya yi shiru, can kuma Amma ta ce“ko zaki dada abincin?” Girgiza kai ta yi kafin ta ce“a'a Amma na ƙoshi ma” Amma ta jinjina kanta sai kuma ta mike ta ce“to ki kwanta ki yi bacci sai da safe” To kawai Nana ta ce sannan ta zame jikinta ta kwanta. Amma ta rage mata gudun ac sannan ta kashe hasken ɗakin ta juya ta fita. Nana na ganin ta fita ta tashi zaune sannan ta jawo wayarta, ta buɗe password ta koma WhatsApp cikin sa'a ta samu Khadijah na online, dan haka ta tura mata message tana tambayar meya hanata zuwa. Khadijah da ba zata iya tsayawa bata amsa ba ta kirata ta WhatsApp bayan ta ɗaga ta ce “kin san me ya hanani zuwa Nana?” Shiru Nana ta yi dan ba ƙaramin haushinta taji ba, Khadijah ta yi murmushi dan tasan halinta ta ce “to Daddy ne bai dawo ba. Kin da daman nace miki sai ya dawo zan zo” Nan ma Nana ta yi shiru tana kwanciya a kan gadon, Khadijah ta yi tsaki ta ce “Ina miki magana kina jina banza” Sai a sannan ta sauke wani wahalallen numfashi cikin sanyin murya ta ce “Yaushe zaki zo?” Ta yi maganar a takaice. Khadijah ta taɓe baki ta ce “wai dan zaki yi aure shi ne ki ka wani fara magana da isa? To gobe” Nana ta ce“alright zan jira ki. Ki gaida Mami” “Zata ji, ta ce da bata da patient ai har Yola zata zo” Ɗan murmushi Nana ta yi dan ta san Mami farin sani ta ce“Allah sarki. Ki ce ina gaisheta” Okay kawai Khadijah ta ce sannan suka katse wayar. Nana ta ajiye wayar a gefe tana lumshe idanunta, gaba ɗaya ji take kamar ba ita ba. Tunanin abin da zai faru gobe idan har Junaid ya ji an ɗaura aurenta shi ne ya fado mata, dan haka ta gaza samun sukuni balle ta samu nutsuwar bacci. **** Safwan ya dinga kallon wayarsa kafin ya ƙarasa da mamaki ya ɗauketa yana tsane ruwan kansa dan fitowarsa kenan daga wanka, ya ɗaga wayar ya kai kunne kafin ta yi magana ya ce “Aunty Zahra lafiya?” Murya can ƙasa Zahra ta ce“lafiya kalau Safwan kana gida ne?” gyaɗa mata kai ya yi kamar yana gabanta sai kuma ya ce“Eh ina ciki” “To ko zaka ɗan fito dan Allah ina compound ɗin” toh kawai ya ce sannan ya kashe wayar har sannan bai daina mamaki ba. Ya ɗauko jallabiya a press ɗinsa ya zura sannan ya saka slippers ya fito daga ɗakin. Babu kowa a parlon dan har an kashe haske, ya buɗe ƙofar ya fito. Tsaye ya hangeta ita ɗaya ya ƙarasa a sanyaye yana kallonta ya ce “Aunty Zahra lafiya dai?” Zahra ta juyo tana kallonsa sai kuma ta yi murmushi ta ce“lafiya kalau Safwan kawai ina son magana da kai ne” Safwan ya ɗan yi jim sai kuma ya ce“to ina ji” Zahra ta ɗan kalli both hand side ɗinta sannan ta sauke numfashi ta zaro envelope ɗin daga cikin hijabi ta miƙa masa. Safwan ya dinga kallon envelope ɗin ba tare da ya karɓa ba, ganin irin kallon da yake mata na neman karin bayani yasa ta sauke hannunta sannan ta ce “na san kasan Siyama yar Yayata ce ko? Kuma ka san nasan kana sonta, kana da burin aurenta sai dai ka rasa ta inda zaka ce baka son Nana. Ko kuma ka ce ka fasa aurenta” Safwan ya yi shiru yana kallonta, ta ɗan murmusa sannan ta ci gaba da faɗin “zan so ace ka auri Siyama ko dan na samu yar uwa a gidan nan. Haka kuma zan so ace ka aureta kodan farin cikinka saboda haka na zo maka da abin da zai iya sakawa a fasa aurenka da Nana koda a filin ɗaurin auren ne!” Da wani irin mamaki Safwan ke kallonta, Zahra ta sake mika masa envelope ɗin, wannan karan samun kansa ya yi da amsar envelope ɗin, ya dinga kallonta ba tare da ya yi yunkurin buɗewa ba. Ta numfasa sannan ta ci gaba da fad'in “Idan har ka yi amfani da abin da ke cikin envelope ɗin nan to zaka samu Siyama cikin sauƙi, koda a gobe ka ke so za'a ɗaura maka aure da ita” Safwan ya girgiza kansa cikin rashin fahimta ya ce “Nifa ban gane abin da ki ke faɗa ba Zahra, ban fuskanci in da ki ka dosa ba” “Ba dai kana son Siyama ba? Kuma ita ka ke son aura ba Nana ba?” Safwan ya jinjina kansa ya ce“Haka ne. Ina son Siyama, so irin wanda ban taba yiwa wata ƴa mace shi ba. Ina jin idan ban sameta ba kamar ba zan iya ci gaba da rayuwa ba” Zahra ta yi murmushi dan ta tabbata ta samu abin da take so ta ce “To idan har kana son Siyama ka yi amfani da abin da na baka, ka ce ka fasa auren Nana. Kana iya kafa hujja dashi” “Hujja!?” Safwan ya ce da matuƙar mamaki, gaba ɗaya kansa ya ɗaure. Zahra ta gyada kanta ta ce“Eh hujja, gobe ka gabatar dashi a gaban kowa sannan ka ce ka fasa aurenta saboda abin da kagani. Daga nan ka ce Siyama zaka aura a maimakonta” Ji ya yi kawai ya gyaɗa mata kai ba tare da ya san ya yi hakan ba. Ta sake murmushi ta ce“ka koma sai da safe” Daga haka ta juya ta bar wajen, Yafi mintina goma tsaye a wajen baki a sake, kafin yaja jikinsa ya koma ciki dakyar. A kan gado ya ajiye envelope ɗin sannan ya zare rigar jikinsa ya shafa mai ya dauko pyjames ɗinsa ya saka, gaba ɗaya tunani ya hana shi sakat, maganganun Zahra sai kai komo suke masa cikin ransa, yana gamawa ya koma ya zauna yana ƙarewa envelope ɗin kallo. “Hujja?” Ya sake furtawa da mamaki, sai kuma ya ɗauki envelope ɗin ya ɓare dan ganin abin da ke ciki, a hankali ya zaro hotunan da suke ciki, lokaci ɗaya ya mike tsaye zumbur yana ƙare musu kallo, so yake ya ƙaryata abin da yake gani amma sam ya kasa, ya sake ƙara light ɗin ɗakin ko idanunsa ke masa gizo, amma ga mamakinsa sai ya ci gaba da ganin abin da ya gani ɗazun. Cikin wani irin tashin hankali da faduwar gaba ya dinga kallon hotunan ɗaya bayan ɗaya, hannunsa sai rawa yake yana girgiza kansa da sauri, gaba ɗaya kusan rasa nutsuwarsa ya yi. Ya yi zaman yan bori a ƙasa kawai sai yaji wasu zafafan hawaye na zubowa daga cikin Idanunsa, bakinsa na rawa ya shiga furta “Innalil lahi wa ina ilayhi raji'un!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 32. Ya dinga maimaitawa ko zai samu sauƙin abin da yake ji cikin ransa. Yana nan zaune har bayan mintuna talatin sannan ya miƙe jiki a sanyaye ya kwashe hotunan ya haɗe su waje ɗaya ya mayar inda suke sannan ya zura cikin drawer. Dakyar ya ja jikinsa ya koma gefen gado ya zauna ƙwaƙwalwarsa cike da tunani kala-kala. A ina aka sami wannan hotunan? Da gaske kuma Nanar daya sani ce? How? Su ne tambayoyin da suka fi tsaya masa arai. Ya ji kamar ya tashi ya koma ya tambayi Zahra sai dai bashi da halin yin hakan, dan lokacin 12 na dare ta kawo kai. Dan haka ya dinga saƙa da warwara shi kaɗai yana tunanin abin da zai wakana gobe. A ɓangaren Zahra kuwa tana koma gida kitchen ta shige, ta zaro wayarta dake cikin hijabi ta yi dialing numbern Aunty Khadijah. Kasancewar ta san da kiran yasa ringing ɗaya ta ɗauka daga ɗaya ɓangaren Aunty Khadijah ta ce “Zahra ya dai.” Sai da ta kalli ƙofar kitchen ɗin dan tabbatar da babu kowa a wajen sannan ƙasa-ƙasa ta ce “Nagama komai fa, na bashi hotunan” Aunty Khadijah ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi ta ce“yauwa Zahra aikinki ya yi kyau. Yanzu sauran ya rage namu, daman gobe da wuri zamu zo gidan” Jinjina kai Zahra ta yi sannan ta kashe wayar, ta jingina da jikin cabinet tana tunanin abin da ta aikata, dai dai tayi? Ko kuma ba dai dai ba. Sanin babu wanda zai faɗa masa gaskiya a sannan ya sanya taja jikinta ta fice daga kitchen ɗin. Koda ta shiga daƙinta kwanciyarta ta yi dan ko Abdusammad bata nema ba, shima kuma bai nemetan ba saboda ayyuka da suke neman shan kansa. A ɓangaren Nana kuwa kasa bacci ta yi, haka kawai taji zuciyarta na karyewa, taji kamar wani mummunan abu na shirik faruwa da ita. Dan haka ta tashi ta shige toilet ɗin Amma ta ɗauro alwala sannan ta fito ta sanya hijabi ta fara gabatar da sallolin nafila. Bayan ta idar ta zauna ta dinga addu'o'i kala da kala har kusan 3 na dare. A ɗakin Abba kuwa Amma ce zaune ƙasan gado hannunta riƙe da cazbaha tana ja dan sam ta kasa bacci, idan ta tuna gobe za'a ɗaura auren Nana ta yi nesa da ita sai taji duk jikinta ya sake sanyi, kamar yau ta haifeta aka dinga zuwa kallonta amma ace har ta yi girman da za'a aurar da ita, itama ta zama matar gida. Wannan tunanin shi ne abin da ya hanata bacci, ga kuma tausayin Nana sanin ba son auren take ba, babu yanda bata yi da Abba ba amma sam yaƙi fahimta, ya kuma kafe akan dole sai Nana ta auri Safwan. Dan haka ta rabu dashi bata sake cewa komai ba, shi ma bai sake yi mata magana ba sai sabgoginsa yake a ɗakin, ya dinga waya da mutanensa na ƙasar waje wadanda zasu halarci ɗaurin auren da za'a yi gobe, a zahiri idan ka ganshi zaka iya rantsewa akan babu abin da ke damunsa, amma cikin zuciyarsa fal take da ƙunci da kuma damuwa. Ji yake kamar kada gobe ta yi domin bai shiryawa jin kukan tilon ƴar tasa ba, duk da bai san dalilinta na ƙin auren ba, amma yaji shima baya son auren. Sai dai ba zai taɓa iya yarda ya ce haka ba saboda gudun lalacewar zumunci. Dan haka ya dinga ƙoƙarin riƙe kansa da kawar da komai daga ransa, wanda haka yasa Amma ta dinga tunanin ko dai bai damu da Nanar bane. Kiran Sallar asubahin farko mutane suka fara tashi, masu ɗora tuwon ɗaurin aure suka fara aikinsu haka ma masu yin sauran girke-girke. Wajejen ƙarfe 6 na safe kuwa sai mutum ya ɗauka 12 ce ta yi saboda yanda ake shige da fice a cikin estate ɗin, dangi da abokan arziki sai kai kawo suke. Burin kowa ya gama abin da yake gabansa domin ɗaurin auren karfe 10:30 na safe ne. Ƙarfe 7 saura Hamida ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Nana na zaune gefen gado ta zuba uban tagumi dan bata san ma ta shigo ɗin ba, Hamida ta girgiza kanta tana mamakin yanda Nana ta fi kowa damuwa akan auren, a hankali ta taɓata ta ce “Nana” A ɗan firgice Nana ta kalleta sai kuma ta sauke numfashi ta ce“na'am” “ki zo in ji Mama” To kawai Nana ta ce sannan ta fara ƙoƙarin miƙewa, ta zura hijabin da ta yi sallah sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin Hamida na biye da ita. Gaisar da mutanen dake parlon suka yi sannan suka fice, Hamida sai hira take mata ita kuwa ta kasa cewa komai sai uhm da uhm'uhm, a haka har suka ƙarasa apartment ɗin su Hamidan. Koda suka shiga ciki Nana turus ta yi ganin su Amrah, Maimoon da kuma Haule. Kowannensu zaune sun yi shiru suna jiran su ji abin da Mama zata ce, zama Nana ta yi gefen Maimoon sannan ta gaida Mama, Mama ta amsa fuska a sake sannan ta gyara zamanta tana kallonsu duka ta ce “Nasan kun san abin da ake nufi da aure, ba sai na yi wani dogon jawabi ba. Kawai dai zan ɗan tunasar daku ne na kuma ƙara muku haske akan wasu abubuwan wanda na san ba lallai bane kun san su” shiru duka suka yi suna saurarenta. Mama ta sauke numfashi sannan ta fara masu nasiha cikin salo na yanda zasu gane me take nufi, duk wani abu mai muhimmanci sai da ta tabbata ta sanar dasu, sannan ta sanya suka yi addu'a a tare kafin ta sallami kowa ya tafi don shiryawa lokacin wajejen ƙarfe 8:00 na safe. Koda suka fito Maimoon ce ta ja Nana gefe tana kallonta ta ce“ya ake ciki?” Nana ta sauke numfashi kafin a sanyaye ta ce“nima ban sani ba Maimoon. Abba ba zai taɓa bari a fasa auren nan ba, kawai yanzu ina tsoron abin da sir Junaid zai yi ne, domin jiya Aunty Zahra ta ce min komai ya shige ita” “komai ya shige ta ce?” Nana ta gyaɗa kanta. Shiru Maimoon ta yi tana mamaki can kuma ta ce“to ta baki hotunan?” girgiza kai Nana ta yi ta ce“a'a suna hannunta, so nake idan komai ya lafa sai naje na amsa na hada dana wajena na ƙona” Maimoon ta buɗe baki zata yi magana kenan ta hangi su Aunty Khadijah suna tawowa, Siyama ce ke biye da ita sai Safeena da Amal, kowaccen su ta ci uwar kwalliya kamar bikin gidansu ake. Ta gaban su Nana suka zo suka shige, Maimoon ta taɓe baki sannan ta ce “gayyar tsiya” Ɗan murmushi Nana ta yi ta ce“ke ina ruwanki dasu?” “to banda neman magana uban me ya kawosu gidan mu? Har su ci wata kwalliya” Nana ta girgiza kanta tana kawar da zancen ta ce“ke ni ƙirjina ciwo yake bari na tafi na kwanta kafin karfe 9 ta yi, Khadijah ta ce min da wuri zata tawo” “Zuwa zata yi?” Gyaɗa mata kai Nana ta yi, Maimoon ta ce“Khadijah bala'i ta zo mu sha dariya” Nana ta ɗan yi shiru tana ƙarewa compound ɗin gidan kallo can kuma ta ce“sai an jima” “ok. Duk yanda ake ciki ki faɗa min ko a waya ne” Toh kawai Nana ta ce sannan ta saketa ta nufi hanyar apartment ɗinsu, Itama Maimoon juyawa ta yi ta nufi nasu apartment ɗin. Safwan ya sauke wani zazzafan numfashi sannan ya juya ya bar wajen bayan ya gama kallonsu. Koda ya shiga gida sama ya shige ya zauna a gefen gadonsa yana tunanin mafita. Tabbas idan ya ce ya fasa auren Nana a yau to komai zai zo masa da sauki, kuma zai samu damar auren Siyama. to amma ta ina zai fara fitar da wadannan hotunan nata? Ya girgiza kansa a fili ya ce “No i can't! Ba zan iya ba wallahi” Ya ƙare maganar yana kawar da tunanin daga ransa. **** Around 9am Zahra ta shiga sakkowa daga saman hannunta riƙe da Noor wadda aka mata kwalliya da wata doguwar riga ta atampa Holland ɗinkin t-boubou wanda yasha aiki, ɗinkin ya mugun yi maga mata kyau kamar ba ƙaramar yarinya ba. Zahra kuwa sanye take da wani ubansu lace ash colour ɗinkin doguwar riga yaji stones sai kyalli yake, ta yi yar simple make-up a fuskarta wadda ta ƙara mata kyau. Safeena na murmushi ta ce“woww Aunty wallahi kin yi kyau kamar kece amaryar” Murmushi kawai Zahra ta yi sannan ta zauna kan sofa tana cewa“ban san sharri Safeena” “Ai ba sharri ta miki ba wallahi kin yi kyau” Amal ta yi maganar itama tana murmushi, kallonsu Zahra ta yi sai kuma ta gyaɗa kanta irin ta jin nan ta ce“tofa ai shikenan” daga haka ta kalli Aunty Khadijah ta ce“har na fara tunanin kiran ki” Aunty Khadijah na taunar cew gum wanda ya zame mata dabi'a ta ce “wallahi mun biya ta wajen Kaddu ne na amshi saƙo shiyasa ki ka ga mun daɗe. Hope dai komai na tafiya dai dai?” jinjina kai Zahra ta yi tana kallon Noor ta ce“eh in sha Allah komai zai tafi kamar yanda muka tsara” “Ummi zan tafi wajen Hajiya” Noor ta yi maganar tana wasa da ɗankwalin dake hannunta, Zahra taja hancinta ta ce“ba zaki jira mu tafi tare ba?” maƙale kafaɗa ta yi, ta ce“to je ki Allah ya tsare” tsalle Noor ta yi sannan ta fice daga parlon da gudu. Miƙewa Siyama ta yi tana danna wayar hannunta ta ce“ina zuwa” “Ina zaki je Siyama?” Aunty Khadijah ta tambayeta. Juyowa ta yi tana kallonta ta ce“Safwan ke kirana yana waje” Jawo hannunta Aunty Khadijah ta yi ta zaunar da ita sannan ta buɗe jakar hannunta tana ƙoƙarin zaro abu ta ce “ke wace irin banza ce ne? Ba sai ki faɗa min ba, ko kin manta?” Ta ƙare maganar tana fito da kwallin ta miƙo mata, amsa Siyama ta yi sannan ta buɗe tana ƙoƙarin sakawa ta ce“to bana manta ba, kin san...” maganar ta maƙale saboda waya irin azaba da taji ta ziyarci ƙwaƙwalwarta, ta saki kwallin sannan ta miƙe tsaye tana fashewa da ihu ta ce “wayoooo Allah na na shiga ukuna Mommy, idona na shiga uku” tashi Aunty Khadijah ta yi ta riƙeta tana faɗin “meya samu idanun” “barkono, wallahi barkono ne a ciki wayyo idona, na shiga uku na makance Mom” Ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani kukan, sai murza idanun take da duka hannayenta biyu. Gaba ɗaya rikicewa suka yi, suka dinga yi mata sannu ana zuba mata ruwa, Safeena ce kawai zaune tana dariya ƙasa-ƙasa dan ita daɗi taji da hakan ta kasance. Kusan mintuna 15 kafin ta iya buɗe idanun, amma sun kumbura sun ji jajur dasu. Ta miƙe kamar me cutar makanta tana dafa gefen kujera ta ce“wallahi Mom bana gani” Ta ƙare maganar tana sake gwale idanun nata, Zahra ce ta riƙe hannunta ta ce“wai duk bakya ganinmu?” sai dai ta gwalalo idanun sannan ta ce“ina ganinki kaɗan-kaɗan” dariya ce ta kusa kama Zahra amma ta dake ta ce“to za ki iya zuwa wajen Safwan ɗin?” kamar ƙaramar yarinya ta gyaɗa kanta ta ce“eh zan iya, Mom ara min glasses ɗin ki” tsaki Aunty Khadijah ta yi tana nuna ta da hannu ta ce “Ji banza, to uban me zai gani idan idanun na cikin glasses?” Siyama ta yi shiru sai kuma ta juya ta nufi hanyar waje jin wayar na ringing. A can wani garden na bayan estate ɗin ta samu Safwan tsaye yana jiranta, sanye yake da jallabiya baka a jikinsa, ya dinga kallonta har ta ƙaraso wajen. Murmushi Siyama ta sakar masa sannan ta ce “Ina kwana?” Kasa dauke idanunsa ya yi daga cikin nata sai murmushi da ya yi ya ce“lafiya kalau my love kin zo ashe?” Tana wasa da fingers ɗinta ta ce“Eh ba dole na zo aurenka ba” Haɗe rai Safwan ya yi ya ce“aurena kuma?” Siyama ta sake fari da idanunta sannan ta ce“eh aurenka mana, ba yau za'a ɗaura maka aure da Nana ba?” tsaki ya yi yana kallon gefe ya ce“sai aka ce miki ita zan aura?” Ganin kamar ransa ya fara ɓaci yasa Siyama ta langwaɓar da kanta ta ce“a'a ai haka naji ne” “To ba ita zan aura ba. Ki je ki jirani kinji” Siyama ta saki murmushin jin daɗi ta ce“tom shikenan sai ka zo” daga haka ta juya ta bar wajen tana tafe cike da kwarkwasa. Safwan ya haɗiye wani yawu sannan ya juya ya bar wajen. Ƙarfe 10:00 na safe Abba ya shigo ɗakin yana sanye da wata dakkakiyar madam gezner fara ƙal ɗinkin jamfa da babbar riga, ya sanya hular zanna akansa sai zuba ƙamshi yake. Ko ba'a faɗa maka ka san ba ƙaramin kuɗi aka kashe a gurin ba, Ya tura kofar dakin Amma bakinsa ɗauke da sallama. Zaune ya sameta tana sanye da wani lace mai azabar kyau da tsada itama, sai dai sam fuskarta babu annuri, musamman yanda taga Nana ta yi shiru tun ɗazu bata ce komai ba. Abba ya dinga kallon su sai kuma ya ce“Nana ki je apartment ɗin Hajiya Babba” Sai a sannan Nana ta ɗago kanta ta kalleshi da idanunta wanda suka sake kumbura da alama ba ƙaramin kuka tasha ba. Sanye take da wani ubansu lace blue colour mai adon pink a jiki, an yi musu ɗinkin straight gown wadda ta ɗan kama jikinta amma ba sosai ba, ɗankwalin lace ɗin na ajiye gefen gadon kanta wanda yasha gyara sai sheƙi yake. Murya a sanyaye ta ce “to Abba” Ya jinjina kansa sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Amma ta sauke numfashi ta kalleta ta ce“zo na ɗaura miki ɗankwalin” babu musu Nana ta tsaya ta daura mata duk da ba wani ɗaurin me kyau bane amma sai ya saka ta ƙara kyau, ta miƙa mata pink ɗin mayafinta wanda ya kasance big size ta ce“saka ki tafi” a gefe ɗaya Nana ta yafa sannan ta tashi tsaye tana gyara zaman rigar jikinta. Amma ta ce“bari naje wajensu Ramlah” to kawai Nana ta ce Amma ta fice daga ɗakin. Komawa ta yi ta zauna tana fashewa da wani sabon kukan, ta kalli wayarta sai kuma ta sake rufe fuskarta da hannayenta cikin kuka ta ce “nashiga ukuna, ya zan yi da raina. Allah ka yafe min” Ta faɗa tana ƙara sautin kukan nata. **** A can compound ɗin Hajiya Babba kuwa jama'a ne a cike na birnin Yola dama cikin ƙauyuka, sai shige da fice ake ana kai komo, kowa ka ganshi tsaf dashi babu alamar babu ko talauci a tare da duk wani ɗan dangin Shuwa. Angwayen duk sun yi shiga iri ɗaya, Shadda gezner milk colour an yi aikin sirfani da brown ɗin zare, sai baza manyan riguna ake, ko ina ka gifta sai ƙamshi ne ke tashi. Papa kuma da Abdusammad irin kaya ɗaya suka yi da Abba. Hajiya Babba ma ta ci kwalliya cikin wani tsaddajen lace ɗinkin boubou. Ta yafa mayafinta aka sai zuwa dibar gaisuwa ake, haka ma Atta irin kayan Hajiya Babba ne a jikinta amma ita sam ta kasa zama sai shiga take tana fita. Atta ta leƙa dakin dasu Maimoon ke zaune kowacce da lace irin na Nana a jikinta, ta dinga kallonsu ganin babu mutuniyarta a ciki yasa ta ce“Ke Maimuna ina Nana?” Maimoon ta miƙe tana gyara mayafinta ta ce“har yanzu bata zo ba bari naje na kirata” to kawai Atta ta ce sannan ta saki ƙofar ɗakin. Moon ta zura takalmanta wanda suka kasance pink colour sannan ta fice daga ɗakin. Sanda ta fito har an baza carpet a compound ɗin Hajiya Babba dan daman a nan ne ake daura auren, Ta shige da sauri tana jan mayafinta ya rufe kanta. Koda ta shiga ɗakin zaune ta samu Nana sai kuka take, ta rufe ƙofar da key sannan ta ƙarasa ciki tana kallonta ta ce“Nana wani abun kuma?” Ɗago kanta ta yi hawaye sai zubowa yake daga idanunta ta ce”na shiga uku Maimoon, na shiga ukuna, mutuwa zan yi” da mamaki Maimoon ke kallonta, lokaci ɗaya taji gabanta ya yi wata irin faɗuwa, ta zaune gefenta tana rike hannunta ta ce“ki faɗa min mene ne? Meya faru?” Kasa magana ta yi sai kuka da take kamar ranta zai fita, ta ɗora kanta akan cinyar Maimoon tana ci gaba da kukanta. Ƙarfe 10:20 Safwan ya ƙaraso wajen yana gyara zaman babbar rigarsa, idanunsa ya sauka kan mutane da ke zaune a compound ɗin kowanne jira yake a zo a ɗaura auren. Ya yi jim sai kuma ya ƙarasa inda su Aliyu ke tsaye ya tsaya, kallonsa Aliyu ya dinga yi ganin yanda idanunsa suka yi jajur ya ce “Safwan ko kai ma kukan auren ka yi?” Cike da zolaya ya yi maganar, dan haka Hamid ya yi dariya ya ce“ai kasan ɗan auta ne zai auri yar auta za'a ga shagwaɓa” suka yi dariya duka. Shi kuwa Safwan kasa dariyar ya yi, murya can ƙasa ya ce“Yaya nifa na fasa auren nan” Aliyu da yaji kamar daga sama ya ce“me ka ce Safwan?” ɗago kansa ya yi ya ɗan kalleshi sai kuma ya ce “cewa nayi na fasa auren nan, ni ba zan auri Nana ba!” ”What!” Hamid ya yi maganar yana zare idanu, sai kuma ya girgiza kansa yana dafa kafaɗarsa ya ce“kai dallah kar ka kawo mana wasa anan kaji” “Wasa? Kuma kawai sai nayi wasa? Wallahi na fasa auren nan, ba zan auri Nana ba!” Ya ƙare maganar yana zazzaro idanu. Aliyu da yaga abun nasa na neman zama na gaske ya riƙe shi ya ce“Safwan lafiya?” “kawai a tara kowa a Apartment ɗin Hajiya wallahi ba ita zan aura ba!” Daga haka ya fizge jikinsa ya yi hanyar balcony ɗin Hajiya. Kamar wasu marasa wayo haka suka dinga bin sa da kallo, cike da mamakin furucin nasa, Aliyu ya numfasa ya ce“bari dai na samu na yi magana da Papa” daga haka ya bar wajen shima. Sultan kuwa shiru ya yi dan daman tun ba yau ba ya lura da take-taken Safwan ɗin. **** Tsaye suke gaba ɗaya a parlon, Abba, Papa, Sultan, Aliyu, Hamid, Atta, Hajiya Babba, Mama. Idanunsa duka akan Safwan wanda ke tsaye tsakiyar ɗakin, kansa a sunkuye, Papa ne ya yi ƙarfin halin faɗin “Safwan me ka mayar da mutane? Abokan wasanka?” Shiru ya yi bai ce komai ba, dan tun ɗazu suke tambayarsa amma ya gagara cewa komai. A fusace ya buɗe ƙofar parlon ya shigo, kai tsaye wajen Safwan ɗin ya karasa yana zuwa ya ɗaukeshi da mari har guda biyu sannan ya cakumi kwalar rigarsa yana masa wani irin kallo cike da tsananin ɓacin rai ya ce “Ashe daman baka da mutunci? Ashe baka da hankali ban sani ba? Are you out of ur sense!” Ya ƙare maganar a tsawace yana jijjigashi, gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun tashi sai huci yake kamar mayunwacin damisa. Abba ne ya ƙaraso wajen ya riƙe hannunsa ba tare da ya ce masa komai ba, Abdusammad ya fizge hannunsa ya ce “Abba dan Allah rabu dani! Mu yaron nan zai zubarwa da mutunci! Da can bai ce ba zai aureta ba sai yau da aka tara dubban al'umma a waje? Shi ya isa?” ya ƙare maganar yana huci, sai kuma ya sake cakumar Safwan ya ci gaba da faɗin “To wallahi tallahi sai ka aureta! Kai baka isa ka ce ba zaka aureta ba” Ya hankaɗa shi har sai da ya kusan faɗuwa Papa ya tare shi. Gaba ɗaya parlon ya ɗauki tsit babu wanda ya yi magana. Safwan ya numfasa sai kuma ya ce “Ni fa Abba ba wani abun nace ba, kawai cewa nayi ba zan auri Nana ba! Kuma ita ma yarinyar a kirata a tambayeta ta ce ba zata aureni ba, kaga kuwa babu amfanin na auri wadda bana ra'ayi kuma bata ra'ayina, dan haka dan girman Allah kada ku tilasta min, wallahi ba zan iya auren Nana ba, akwai wadda take cikin raina tun ba yau...” Bai ƙarasa maganar ba Abdusammad ya rufe shi da duka ya shaƙe nasa wuya cikin masifa ya ce“to kar ta so kan, ko tana so ko bata so wallahi sai an yi auren nan!” Aliyu ne ya janyeshi daga jikinsa yana fadin “Ya isa haka Buddy, abi komai a hankali” banza Abdusammad ya yi masa ya fizge jikinsa yana kwafa. Abba ya sauke numfashi sannan ya kalli Safwan ya ce “Ka san da baka sonta ka bari muka tara jama'a Safwan? And wait, wane ya ce maka sai kana sonta sannan zaka aureta? Mu ba haka tsarinmu yake ba, kuma ku baku isa ku zo ku lalata mana tsari ba! Dole ne ka auri Nana!” Safwan ya dinga kallon Abba dan yana matukar ganin girmansa kuma baya jin zai iya sa'insa dashi. Dan haka ya sunkuyar da kansa murya a sanyaye ya ce“ka yi haƙuri Abba wallahi ba zan taɓa auren Nana ba!” Hajiya Babba ce ta ƙaraso wajen ta dinga kallonsa sai kuma ta dauke shi da wani marin cikin matsanancin ɓacin rai ta ce“Mu zaka wulaƙanta Safwan? So ka ke a yi mana dariya? To wallahi idan har ka sake wannan maganar sai dai ka nemi wata uwar amma bani Khadijah ba!” Da sauri ya ɗago kansa hannunsa dafe da kuncinsa, Hajiya Babba ta maka masa wata uwar harara tana barin wajen, Papa ne ya sauke numfashi sai kuma ya ce“su wane a ciki?” “Yaran ne” Mama ta bada amsa. Papa ya kalli ƙofar sai kuma ya ce“to su fito” ok kawai Mama ta ce sannan ta ƙarasa ta buɗe ɗakin, suna zaune kowacce ta yi shiru jiki a sanyaye dan duk abin da ake faɗa suna ji. Mama ta ce musu su fito sannan ta bar wajen, a sanyaye suka shiga fitowa ɗaya bayan ɗaya, suka ƙaraso parlon suka tsuguna cike da ladabi. Papa ya dinga kallonsu sai kuma ya ce “Ina Nana?” “tare muka fito ta ce bari taje ta manta wayarta.” Maimoon ta yi maganar kanta a ƙasa, Papa ya ɗan numfasa sai kuma ya kalli Abba ya ce“kira Rabi'ah ta tawo da Nana nan” ok kawai Abba ya ce sannan ya zaro wayarsa a aljihu ya yi dialing numbern Amma, ringing ɗaya ta ɗauka dan wayar na hannunta, Abba ya ce “Ki zo da Nana apartment ɗin Hajiya yanzu” “Dama bata tafi ba?” Amma ta tambaya da mamaki, Eh kawai Abba yace sannan ya katse kiran, Amma ta tashi ta nufi daƙinta. Sai dai me koda ta buɗe babu Nana babu alamarta, ta girgiza kai sannan ta buɗe ɗakin Nanar, ga mamakinta sai ta tarar nan ma bata nan. Amma ta dawo parlon tana kallon Aunty Safiya ta ce“Aunty Nana bata fita ba kuwa?” “Nana gaskiya bata fita ba, na dai ga ta shiga daƙinta ɗazu” Amma ta ɗan ja siririn tsaki sai kuma ta koma ɗakin, ganin bata ciki yasa ta nufi toilet tana cewa“Nana ke Nana” jin bata amsa ba yasa ta ce“yi sauri Abbanki na jiranki” daga haka ta koma gefen gado ta tsaya, tana nan tsaye har bayan mintuna biyar kiran Abba ya sake shigowa wayarta, ta daga ya ce “jiranki fa muke” Amma ta ce “ban ganta a ɗakin bane, I thought tana toilet kuma naji shiru” Rai ɓace Abba ya ce“to ba zaki duba ba?” Amma ta ce to sannan ta kashe wayar, toilet ɗin taje ta murɗa sai ta ga wayam babu alamar mutum. Ta juyo tana faɗin “To gidan ubanwa ta shiga so take ya yi ta...” Maganar ta tsaya cak saboda takardar data gani akan gado iska sai kaɗata take, ta ɗan ware idanunta tana mamakin abin da ya kawo takardar, sai kuma ta ƙarasa a hankali ta ɗauka tana ƙarasa wareta. Amma ta buɗe idanunta sosai tana karanta rubutun dake jikin takardar kamar haka; _Abba, Amma dan Allah ku yi haƙuri, ba zan iya ci gaba da ɓata muku rai ba, ba zan bari kuji mummunan labari akaina ba, nasan ba zaku jure ba. Ina fatan koda kun ga abin da za'a nuna muku ya kasance bana wajen, Ban tafi dan son raina ba, a'a na tafi ne dan babu yanda zan yi, ba zan iya jure ganin halin da zaku shiga ba. Dan Allah dan Annabi ku yafemin, wallahi ko me za'a nuna muku ba haka abun yake ba, idan Allah ya so watarana zan muku bayanin komai, idan kuma ban sake ganinku ba, ina roƙon ku daku manta dani. Ku manta da kun haifi ƴa kamata, ku manta dana rayu tare daku. Dan Allah ku manta da NAANAH!_ 08106608363 Nanameera. *🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08 Page 33... Amma ta dinga kallon takardar cikin tashin hankali, ilahirin jikinta rawa yake. Ta girgiza kanta sai kuma ta fice daga ɗakin da gudu. Kai tsaye apartment ɗin Hajiya Babba ta nufa tana tafe kamar zararriya, gaba ɗaya bata cikin hankalinta. Koda ta tura ƙofar tsaye ta samesu sun yi jigum-jigum da alama zuwan Nanan suke jira. Ta ƙarasa ciki kai tsaye kuma wajen Abba ta nufa tana faɗin “Kaga! Kalli kaga” Ta ƙare maganar tana miƙa masa takardar hannunta, Abba ya dinga kallonta da mamaki sai kuma ya karɓi takardar ya buɗe. Sai da ya sake kallon Amma da ke tsaye tana girgiza kanta sannan ya mai da idanunsa kan takardar ya fara karantawa. Wata irin zufa ce ta dinga keto masa tun daga tsakiyar kansa, Ya kasa cewa komai hannunsa sai rawa yake, ganin haka yasa Abdusammad ya ƙaraso gabansa ya zare takardar ba tare da y ce komai ba. A fili kuma ya karanceta tas, ban da salati da sallalami babu abin da ke tashi a parlon, Su Hamida kuwa sai kuka suke kamar ransu zai fita. Atta ma ta ɗora hannu aka cikin tashin hankali ta ce “*** wace irin masifa ce wannan? Ina yarinyar nan ta shiga? Mun lalashe” Ta ƙare maganar tana sakin kuka. Sultan kuwa girgiza kansa kawai yake yana tunanin abin da yasa Nana ta yanke wannan ɗanyen hukuncin. To mene ne abun da take magana akai? wane zai fadi wani abu akanta. Lokaci ɗaya ya mai da idanunsa ka Safwan wanda babu alamar fargaba ko tashin hankali a tare dashi. Ya girgiza kansa yana tabbatar da cewa tabbas akwai abin da ya haɗata da Safwan ɗin. Abba da ƙafafunsa suka fara gagarar ɗaukansa ya yi baya kamar zai faɗi, Abdusammad ya tare shi da sauri yana fadin “Abba stay still pls” Riƙe hannunsa Abba ya yi yana jinjina masa kai. Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi, idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, amma babu alamar tashin hankali a tare dashi a zahirance. Hajiya Babba da tun ɗazu bata ce komai ba ta numfasa sannan ta kalli Abba ta ce “Aje a gabatar da ɗaurin auren, babu abin da zai hana Safwan auren Nana!” Kusan a tare duk suka kalleta, Safwan ya girgiza kansa lokaci ɗaya hawaye ya kawo cikin idanunsa ya ƙarasa gabanta ya tsuguna murya a tausashe ya ce “Dan Allah dan Annabi Hajiya kada amin dole, wallahi ba zan iya auren Nana ba! Ba zan iya ba, dan girman Allah a bar wannan maganar!” Ya ƙare maganar yana haɗe hannayensa alamar roƙo. Ɗauke kai Hajiya Babba ta yi kamar bata ji abin da ya ce ba, dan haka yaja jikinsa da rarrafe ya ƙarasa inda Abba yake tsaye, ya dafa ƙafafunsa cikin kuka ya ce “Abba na san kana da fahimta, na san kai ubane. Kuma zaka fahimci abin da nake nufi, wallahi tallahi ba zan iya auren Nana ba, kuma bani da burin sanar da ku wani abu game da haka. Dan haka dan Allah dan Annabi abar maganar aurena da ita” “Kai ka isa, wallahi sai ka aureta! Kuma ita ma duk inda ta shiga sai ta fito! Dole ne a ɗaura wannan auren!” Abdusammad ya yi maganar yana fincikoshi. Safwan ya dinga kallonsa hawaye na zubowa daga kan fuskarsa, ganin yanda ran Abdusammad ɗin ya ɓaci yasa ya ce “A''a Yaya kada mu fara haka da kai, kada mu yi dan Allah. Ina jin maganarka, ina ganin girmanka. Ba zan so na ɓata maka rai ba, dan haka dan Allah ku fahimceni” Wani irin kallon ka zama mahaukaci Abdusammad ya dinga yi masa can kuma ya sake shi ya girgiza kansa ya ce“ko kaɗan ban yi tunanin irin wannan daga wajenka ba Safwan. Wallahi ban taɓa tunanin zaka zo da irin wannan maganar ba, ka bani kunya! Ka bani kunya Safwan!” Ya ƙare maganar a tsawace. Shiru parlon ya ɗauka kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa, Amma ta yi zaman dirshan gefen Hajiya Babba sai kuka take kamar ranta zai fita, tunaninta shi ne ina Nanarta ta shiga? Me ya sa ta tafi ta bar su?. Papa ne ya numfasa sannan ya tako daga inda yake ya zo gaban Safwan, ya sanya hannunsa na dama ya dafashi murya a ɗan cunkushe ya ce “Safwan meyasa ba zaka iya auren Nana ba? Na san dole kana da hujjarka ta yin haka. Idan har ka faɗa mana hujjar kuma muka duba muka da abin da ka faɗa kana da gaskiya ba za'a maka dole ba, domin tun da har ka furta ba zaka aureta ba koda an yi auren ba za'a samu zaman lafiya ba” Safwan ya dinga kallonsa fuskarsa caɓa da caɓa da hawaye kamar karamin yaro. Ya janye hannun Papa daga jikinsa sannan ya yi taku biyu gabansa ya ja ya tsaya, muryarsa a sanyaye ya ce “Papa ba zan auri Nana ba, akwai wadda nake son na aura, kuma yau nake son a ɗaura mana auren da ita.” Da wani irin mamaki suka dinga kallonsa. Sultan ya girgiza kansa a fili ya ce“daman na san wannan ne shirin ka, amma baka da hankali Safwan!” ya yi maganar rai ɓace. Papa ne ya ɗaga masa hannu sannan ya mai da idanunsa kan Safwan ya ce“ina jin ka, idan har ka faɗi hujjar da ta dace na yarda zaka auri wadda ka ke so” Da sauri ya juyo ya kalleshi. Papa ya gyaɗa masa kai alamar tabbatarwa. Shiru Safwan ya yi yana tunanin mafita, can kuma ya nufi hanyar upstairs, da gudu Maimoon ta tashi ta ƙarasa inda yake ta rike babbar rigarsa ta baya tana kuka. Lamarin da ya sanya hankalin kowa ya koma kansu, Safwan ya juyo yana kallonta da mamaki, ta sake ruƙunƙumshe tana kuka ta ce “A'a Yaya, dan girman Allah kada ka yi haka. Kada ka yi haka kaji” Sosai jikin Safwan ya yi sanyi, ya janyeta daga jikinsa hawaye na biyo kan fuskarsa. Kuka take sosai gaba ɗaya ta birkice kanta, Ya yi shiru yana tunani sai kuma ya fara ƙoƙarin sakkowa daga saman. Maimoon ta sauke ajiyar zuciya sannan ta biyo bayansa tana kuka a hankali. Ganin yanda kowa ke kallonsa yasa ya sunkuyar da kansa yana kallon Papa ya ce “I'm sorry Papa” Murmushin takaici Papa ya yi kafin ya ce“sorry? Sorry for what Safwan?” Kasa cewa komai ya yi, lokaci ɗaya ya shiga lalubar aljihunsa, cikin yan sakanni ya zaro envelope ɗin. Ban da kallonsa babu abin da ake a ɗakin, ita kuwa Maimoon mutuwar tsaye ta yi dan ko kukan ta gagara yi, ta tabbata asirin Nana ya gama tonuwa. Papa ya dinga kallon envelope ɗin da Safwan ya bashi ba tare da ya ce komai ba. Safwan ya goge hawayen fuskarsa sannan ya ce “wannan dalilin ya sanya ba zan iya auren Nana ba! Kuma na san idan ku ka gani zaku tabbatar da gaskiyata” Daga haka ya sake sunkuyar da kansa. A hankali Papa ya buɗe envelope ɗin ya zaro hotunan gaba ɗaya, Sai dai abin da idanunsa suka gane masa sune suka sanya shi cikin wani hali na kiɗima da tashin hankali. Ya yi baya kamar zai faɗi Hamid ya tare shi yana amsar hotunan, ɗaya bayan ɗaya ya dinga buɗe su zufa na keto masa. Papa kuwa zaman daɓaro ya yi kan sofa ya tallafi fuskarta da duka hannayensa biyu, ban da innalil lahi babu abin da yake maimaitawa cikin ransa. Sultan ne ya ƙarasa wajen Hamid ya fizge hotunan yana buɗe su, ya kasa ɓoye tashin hankalinsa a fili ya shiga furta “Innalil lahi wa ina ilayhi raji'una, Ya subhanallahi!” Ya ƙare maganar yana jifa da hotunan. Ban da kallonsu babu abin da sauran ke yi, Maimoon kuwa sai ajiyar zuciya take saukewa ta ruƙube a jikin bene. Abba ne ya sunkuya ya ɗebi hotunan dan gabansu suka faɗo, Ya dinga buɗe su ɗaya bayan ɗaya. Baya ya yi ya faɗi ƙasa, jikinsa sai rawa yake, Abdusammad ya sunkuya da sauri yana kallonsa ganin kamar bata cikin hayyacinsa ya amshi hotunan. Waro idanunsa ya dinga yi akan ko wane daya daga cikin su, Lokaci ɗaya ya miƙe tsaye ya ƙarasa wajen Safwan ya shaƙeshi yana faɗin “Tell me ina ka samu wannan? Wane ya baka? A ina ka samu Safwan?” Ya ƙare maganar yana jijjigashi kamar zai tsinke masa jiki. Girgiza kai Safwan ya yi bai ce komai ba, Abdusammad ya hankadashi sannan ya koma in da Abba yake ya riƙe shi yana faɗin “Abba kada wannan ya dameka kaji, nothing will happen” Wani murmushi mai ciwo Abba ya yi sannan ya dafa Abdusammad ya miƙe, sai da ya kalli kowa na parlon da idanunsa wanda suka kusa rufewa sannan ya yi murmushi mai haɗe da hawaye. Ba ƙaramin mamaki da kuma tausayi ya bawa kowa ba, domin rabon da ya zubar da hawaye tun mutuwar late Muhammad Shuwa, dan haka ba kowane ya taɓa ganin hawayen nasa. Amma ce ta taso da sauri ta ƙaraso gabansu kamar zararriya ta ce “mene ne? Me ya samu Nana?” Ganin babu wanda ya ce mata uffan yasa ta dinga kallon kasa cikin sa'a kuwa idanunta ya sauka kan hotuna guda biyu, kusan yar tsere suka yi da Sultan sai dai kafin ya ɗauka hoton ta riga da ta ɗauka. Ta dinga kallonsu tana girgiza kanta bakinta na wata irin rawa ta ce “a... A'a... Wannan ba Nana ba ce, ba Nanata bace..ba ita ba ce wallahi!” Sai kuma ta zubar da hotunan ta koma inda Abba yake tsaye ta riƙe kwalar rigarsa cikin tashin hankali ta ce “Ahmad ka faɗa min, ka faɗa min gaskiya, ai ba Nana ba ce ba ko? Ba ita ba ce ba ko! Ni nasan ba ita ba ce, wannan ba Nanata ba ce, ka sanar dani dan Allah” Ta ƙare maganar tana rushewa da wani raunataccen kuka. Abba rasa abin yi ya yi sai kawai ya rungumeta a jikinsa yana sauke numfashi a hankali, murya can ƙasa ya ce “Ki yi haƙuri Rabi'ah” Da sauri ta ɗago kanta tana kallonsa sai kuma ta ce“Nana ce?” Jin bai ce mata komai ba ya sanya ta sake sakin wani marayan kukan ta ce“ka faɗa min mana!” A hankali ya shiga gyada mata kai, Amma ta dinga kallonsa kai kuma ta yi baya ta faɗi ƙasa Sumammiya. Cikin hanzari Mama dasu Maimoon suka yi kanta. Abba kuwa kasa koda motsi ya yi sai numfashi yake saukewa. Da hannu ya yiwa Safwan alamar ya zo, ya ƙaraso kansa a ƙasa dan kunyar haɗa idanu yake da Abban. Shafa kansa Abba ya yi muryarsa a kusan ƙarye ya ce “Safwan ni na amince ka auri wadda ka ke so, ba kai ba bana fatan kowani daga cikinku ya auri Nana!” Da sauri duk suka kalleshi, Papa ya miƙe idanunsa sun yi jajur shima. Zai yi magana Abba ya ɗaga masa hannu ya ce”a'a Yaya kada ku hana shi dan Allah, Ni ina neman wannan alfarmar a bar shi ya auri wadda yake so” Rungume shi Safwan ya yi yana kuka, ya rasa farin ciki zai yi ko kuma baƙin ciki. Abba ya shafa kansa yana murmushin ƙarfin hali. Can ya ɗago kansa yana kallon Abba ya ce“Abba koda ba yar cikin gidan nan bace?” Gyaɗa masa kai kawai Abba ya yi dan ya fara daina ganewa, Safwan ya yi murmushi mai haɗe da hawaye ya ce“to daman ƙanwar matar Yaya nake so” Da mamaki Abdusammad ya dinga kallonsa, lokaci ɗaya kuma ya girgiza kansa ya ce“kai ka isa, ba zaka aureta ba wallahi, ba zaka auri wadda ba yar danginmu b!” Rufe masa baki Abba ya yi ya ce“a'a Abdusammad ka yi kaffara, zai yi aurensa. Wannan alƙawarina ne, ku je ku gabatar da komai, a ɗaura auren kowace cikin farin ciki zan je na huta” Kasa cewa komai suka yi, gaba ɗaya wajen tausayinsa suke, ko bai faɗa ba sun san ƙarfin hali kawai ya ke. Ya juya yana ƙoƙarin tafiya, sai dai sarawar da kansa ya yi masa ya sanya shi dakatawa, ya dafe kan yana kiran sunan Allah. Ji ya yi an riƙe shi ya ɗago jajayen idanunsa yaga Abdusammad ne, murya a sanyaye ya ce“bari na raka ka Abba” daga haka ya gyara riƙon da ya yi masa. Kasa cewa komai Abba ya yi har suka fice daga parlon. Har ɗakinsa ya kai shi ya zaunar dashi kan gado sannan ya zare masa hular kansa ya ajiye gefe, Abba ya sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan ya jingina da jikin gado, ya lumshe idanunsa lokaci ɗaya hawaye suka fara sintiri akan fuskarsa. Shiru Abdusammad ya yi yana kallonsa cike da tausayawa, can kuma ya tsuguna a gabansa ya riƙe hannunsa jiki a sanyaye ya ce “please Abba, kada ka damu kan ka, ni nayi maka alƙawarin zan dawo da Nana, zata dawo cikin aminci” Dakyar ya iya buɗe idanun nasa, dan da gaske jikinsa ya yi sanyi sosai, ya dafa kan Abdusammad yana murmushi mai haɗe da hawaye ya ce “me yasa ta yi haka Abdul? Why? Bata san halin da zan shiga ba, yau da safe na tashi da farin ciki, irin farin cikin da baya misaltuwa. Naji ni cikin annashuwa da nutsuwar zuciya saboda ina tunanin zan aurar da tilon ƴata wadda Allah ya bani matsayin amana.” Abba ya yi shiru saboda kukan dake neman tawo masa, ya numfasa sannan ya ci gaba da fad'in “sai dai sam ban yi tunanin Nana zata tafi ba, ban yi tunanin zata bari na tozarta idon duniya ba. I feel ashamed Abdul...na tursasa yara dayawa sun yi auren dangi, domin samar da al'umma mai kyau, sai dai ƴata dana haifa ta guji hakan. Na gayyaci mutane domin su tayani farin ciki sai dai yanzu ban san da wane idanu zan kallesu na ce musu an fasa auren Nana ba, na kuma faɗa musu cewa Nana ta gudu ta barni..” ya dakata saboda tarin daya turnuƙeshi. Abdusammad ya riƙe shi sosai yana hawaye shima ya ce“a'a Abba, dan Allah kada wani abun ya sameka” Murmushi kawai Abba ya yi yana kallon enlargement ɗin hoton Nana dake maƙale a jikin bangon ɗakinsa, lokacin bata fi 3yrs ba, tana tsaye hannunta riƙe da teddy bear ta kwaɓe fuska kamar mai shirin kuka. Wasu zafafan hawaye ne suka shiga sakkowa kan fuskarsa, Ya lumshe idanunsa sannan ya sake buɗe su ya ce “Ashe bani da rabon aurar da ɗiyata, haka Allah ya ƙaddara min, shiyasa ya bani Nana ita kaɗai” Da sauri Abdusammad ya girgiza kansa ya ce“a'a Abba ya zaka ce haka? Me zai hana ka aurar da Nana? Nace maka zan dawo da ita” Girgiza kai Abba ya yi cikin kuka ya ce “To ko ta dawo wane zai aureta Abdul? Nobody! Babu wanda zai auri Nana! Babu mai iya aurenta” Yanda ya yi maganar a mugun sanyaye shi ne ya ƙara bawa Abdusammad tausayi, gaba ɗaya Abba ya yi loosing hope. Agogon hannunsa ya kalla sai kuma ya ce“kaje domin kai ne a bigirena, just go” Dakyar Abdusammad ya miƙe yana sake kallon Abba. Ganin haka yasa Abba yin murmushi ya ce“kar ka damu I'll be fine. Just go” Jiki a sanyaye ya juya ya fice daga ɗakin, Abba ya numfasa sannan ya kwanta a gefen gadon yana lumshe idanunsa. A balcony ya tsaya ya goge hawayensa da hanky sannan ya nufi apartment ɗin Hajiya Babba kamar babu abin da ya faru. A zaune ya samu su Papa da angwayen dan haka ba'a tsaya sake ɓata lokaci ba aka gabatar da ɗaurin auren. **** Tsaye suke jikin ƙarfen bene, Aliyu sai kallonsa yake ganin yanda ya yi shiru kamar me tunani. Ya numfasa sannan ya ce “Buddy are you sure abin da ka yi shi ne daidai?” Buɗe gajiyayyun idanunsa ya yi akan Aliyu sai kuma ya ɗauke kai yana kallon gefe, Aliyu zai sake magana Papa da Baba Lawan na Njomboli suka ƙaraso wajen, dafashi Baba ya yi cikin jin daɗi da farin ciki ya ce “Allah ya yi maka albarka Abdusammad, ya sanya albarka cikin auren, tabbas abin da ka yi shi ne dai-dai. Kuma muna alfahari da kai” Jinjina kansa ya yi jiki a sanyaye ya ce“Amin Baba. But ina jin kamar ban yi dai dai ba idan ya kasance ni ne na auri Nana, wallahi ban taɓa yi mata kallon wadda zan aura ba, ban taɓa kallonta matsayin mace bama. Kawai ganinta nake kamar ƴata, yanda zan yiwa Noor abu haka nake ganin zan yiwa Nana, ya zata ji idan aka ce mata ni ne wanda aka ɗaura mata aure dashi?” Ya ƙare maganar da damuwa sosai akan fuskarsa Dafashi Papa ya yi kafin ya ce“mun sani Abdusammad kuma abin da ka yi shi ne dai-dai. Ahmad ba zai manta da wannan abun ba, ka share masa hawayensa sannan ka fitar dashi kunyar jama'a. Gefe guda kuma ka wanke kanka akan aurenka na farko wanda ka yi bada yardar danginka ba. So you don't need to be worry kaji” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* This page na dedicated to u jama'ar Nanameera's forum. Page 34... Shiru Abdusammad ya yi yana kallon Papa. Ya ɗan bubbuga kafaɗarsa sannan ya juya suka bar wajen. Harɗe hannayensa ya yi a ƙirji yana jin wani irin abu cikin ransa, mamaki da damuwa sun yi masa yawa, idan ya tuna cewa yanzu Nana matsayin matarsa take amsawa sai yaji gabansa ya faɗi. “Ya rabb!” Ya furta yana furzar da zazzafan numfashi daga bakinsa. Dafashi Aliyu ya yi ganin yanda ya damu yasa ya ce“Buddy ka daina damuwa kaji dan Allah. Always Allah's plan is the best” Kallonsa ya yi da gajiyayyun idanunsa ya ce“Buddy Nana fa. Nana fa” “to mene a ciki?” Ɗauke kansa ya yi yana kallon mutanen dake ta faman kai koma a compound ɗin sannan ya ce“ba zaka fahimta ba” taɓe baki Aliyu ya yi ya ce“da ka fahimtar dani ai” kallonsa kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba. Sultan ya ƙaraso wajen hannunsa riƙe da babbar rigarsa wadda ya daɗe da cirewa. A gefensu ya tsaya jiki a sanyaye ya ce “Yaya” Kallonsa Abdusammad ya yi ba tare da ya ce komai ba. Cike da damuwa Sultan ya ce“Yaya Nana fa? A ina za'a ganta?” numfasawa Abdusammad ya yi sai kuma ya dafa kafaɗarsa ya ce“za'a ganta kaji” daga haka ya kalli Aliyu ya ce“bari naje wajen Abba” “muje tare” Aliyu ya faɗa yana tattare babbar rigarsa. Ok ya ce sannan ya yi gaba Aliyu ya bi bayansa. Sultan ya jima tsaye kafin ya sauke numfashi ya nufi hanyar apartment ɗinsu. **** Fitowa ta yi daga kitchen hannunta riƙe da plate tana murmushi ta kalli su Aunty Khadijah dake ta faman dariya ta ce“yau dai murna har kunne” Aunty Khadijah ta gyara zamanta tana kallonta ta ce“ai yau ko bacci ban jin zamu iya. Wannan abu. Kai Allah na gode maka” Ta ƙare maganar tana ɗaga hannunta sama alamar godiya ga Allah. Murmushi Zahra ta yi bayan ta zauna ta ce“amma tafiya zaku yi ko? Tun da kun ga yanzu ku surukai ne” jinjina kai Siyama ta yi ta ce“eh fa Aunty. Gara mu tafi, to amma ke naga baki damu ba” Taɓe baki Zahra ta yi ta ce“akan me zan damu to? Yarinyar da aka aura masa bagidajiya ce, ke bayan haka ma anan zata zauna mu kuma US zamu koma. To kin ga ba zan kirata kishiyata ba ai” Gyaɗa kansu suka yi sai kuma Aunty Khadijah ta dafata ta ce“koma tare zamu zauna ai ba zamu bari ta yi nasara akan ki ba. Mu da muke da malamai” shiru Zahra ta yi can kuma ta janye hannunta daga jikinta ta ce“a'a Aunty ni babu ruwana da bin malamai ko bokaye. Kawai dai na san ba zata zama kishiyata ba” ta ƙare maganar tana haɗe rai. Murmushi kawai Aunty Khadijah ta yi dan ita yanzu bata da wata damuwa. Safeena da ke zaune tun ɗazu ba tare da ta ce komai ba saboda takaici ta miƙe tana ɗaukan jakarta ta ce“ni zan yi gaba” “ba zaki bari mu tafi tare ba?” Amal ta tambayeta da mamaki. Gyaɗa mata kai Safeena ta yi fuska babu walwala ta ce“a'a tafiya zan yi, ni ba zan zauna ba” daga haka ta juya ta nufi hanyar fita daga parlon. Taɓe baki Siyama ta yi ta ce“ni na rasa abun da ke damunta wallahi.” Aunty Khadijah ta bita da harara sannan ta ce“Allah ya raka taki gona” Suka tuntsire da dariya a tare. Ban da Zahra wadda lokaci ɗaya taji lamarin auren ya dameta. **** Tura ƙofar ɗakin ya yi bakinsa ɗauke da sallama, cikin tashin hankali ya ƙarasa gaban gadon ya dafashi yana faɗin “Subhanallahi. Abba! Abba!” Ya ɗago shi ya jingina shi da jikinsa, ban da tari babu abin da Abba ke yi, idanunsa a rufe jikinsa sai wani irin rawa yake. Aliyu ya ƙaraso ciki hankali tashe ya ce “mene ne? Me ya same sa?” Girgiza kai ya yi bayan ya miƙe riƙe dashi ya ce“i don't know bari muje asibiti” daga haka ya fice daga parlon da sauri. Aliyu ya dafe kansa a sanyaye ya ce“Ya Allah” sannan yabi bayansu da sauri. A hankali ta fara buɗe idanunta wanda suka yi mata nauyi, ta dinga kallon ɗakin da take kwance, Lokaci ɗaya kuma ta tashi zaune a ɗan firgice. Da sauri Mama ta riƙeta tana faɗin “kin tashi” Amma ta dinga kallonta, can kuma ta saki wani kuka tana fadin “Mama Nana, me ya sa Nana zata yi haka? Wane ne wanda ta yarda dashi haka! Mama zuciyata zafi take min. Innalil lahi wa ina ilayhi raji'una” Amma ta yi maganar tana sake rushewa da wani kukan. Sake riƙeta Mama ta yi cike da tausayinta ta ce“yi haƙuri Rabi'ah, ki yi haƙuri dan Allah” cikin kuka ta kalli Mama ta ce“to ina take? Yanzu shikenan ba zata yi aure ba? Babu wanda zai aureta. Wallahi ban bar Nana tana fita ban sani ba, ban santa da yawo ba, ban san yaushe haka ta faru ba. Iya kar ƙoƙarina ina yi akan tarbiyyarta. amma me yasa? me ya sa zata yi mana haka? Me yasa zata yi fatali da tarbiyyar da muka bata..” Mama ta yi shiru tana sauraren sautin kukanta. Ta san tabbas ba ƙaramin abu ne, ba abu ne wanda zuciya zata iya dauka ba, ace yarka daka haifa aka samu da irin wannan ƙazaman hotunan. Garin ya ya? wane ya yaudari Nana har ta yarda dashi haka?. Mama ta sauke numfashi sai kuma ta mai da idanunta kan Amma a sanyaye ta ce “ki bar zubar da hawayenki, domin shi ɗin masifa ne gareta. Addu'a zaki yi mata, kuma ki yi mata fatan Alkhairi” Amma ta jinjina kanta wasu hawayen na sake zubowa ta ce“ina son na ganta. Ina son naga Nana Mama, ina so na tambayeta meyasa ta yiwa rayuwarta haka? ina son ta faɗa min dalilinta na tafiya ta bar mu. Ina son na ganta Mama...” ta sake fashewa da wani raunataccen kukan tana ɗora kanta a cinyar Mama. Kasa cewa komai ta yi dan tasan dole ta yi kuka, ta dinga shafa bayanta a hankali. **** Ana kiran sallar la'asar Ummi ta shigo ɗakin, ta dinga kallonta ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita. Tun bayan da aka gama ɗaurin aure bata yi shiru ba, dan haka ta saki ƙofar ta ƙarasa ciki tana ci gaba da kallonta. Zama ta yi gefen gadon ta riƙo hannayenta a sanyaye ta ce “Maimoon” Ɗago kanta ta yi a hankali tana kallon Ummi, gaba ɗaya idanunta sun kumbura sun yi jajur dasu. Har wani janyewa sukayi saboda azabar kuka, Ummi ta girgiza kanta sai kuma ta shiga share mata hawayen tana faɗin “kukan ne har yanzu? me ki ke wa kuka kuma?” Samun kanta ta yi da faɗawa jikin Ummin ta sake fashewa da wani sabon kukan, Ummi ta dinga kallonta ba tare da ta ce komai ba. Above 5mins kafin ta fara rage sautin kukan dan kanta. Sai a sannan Ummi ta ɗagota tana murmushi ta ce “Shikenan ya isa haka, ki tashi ki yi wanka ki ci abinci, sai ki je apartment ɗin Hajiya Babba” Gyaɗa mata kai kawai Maimoon ta yi dan ita sam ba wannan ne ya dameta ba. Ummi ta tashi tana cewa“bari na kawo miki abincin” da sauri ta mike ita ma tana ƙoƙarin yafa mayafinta ta ce“a'a zan je gurin Hajiya Babba” Ummi ta yi shiru can kuma ta ce“abincin fa?” “na ƙoshi” Ta ce a sanyaye. Ummi bata sake cewa komai ba barta ta fita, dan ta san daman ba lallai bane ta iya cin abincin a sannan. Tafiya ta dinga yi tana kuka, ta rufe fuskarta da mayafin kanta ko gabanta bata gani. Ji ta yi an riƙeta tayi saurin ɗago kanta ba tare da ta buɗe idanun nata ba, Aliyu ya dinga kallonta ganin tana shirin faɗuwa. Hannunsa ya sanya ya janye mayafin ya dawo goshinta, sai a sannan ta kalli fuskarsa, ta yi saurin sunkuyar da kanta. Kallonta ya dinga yi can kuma ya ce “ki kula kar ki faɗi” Gyada masa kai kawai ta yi ya saketa ta yi gaba da sauri. Da idanu kawai ya bita sai kuma ya juya ya nufi inda ya yi parking motarsa dan komawa asibitin. Ta ƙofar wajen kitchen ta shiga gudun kada ta haɗu da mutane, sai dai ga mamakinta Safwan ta gani tsaye a wajen ya jingina da jikin flowers da alama tunani yake yi. Ta dinga kallonsa cike da tsana sai kuma ta juya zata bar wajen, kamar daga sama taji ya ce “Maimoon!” Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya ƙaraso gabanta ya tsaya ba tare da ya ce komai. Ganin mintuna biyu sun shuɗe bai yi magana ba ya sanya ta ratsa ta gefen shi zata shige, ya yi saurin riƙe hannunta kafin ya ce “Wait pls!” Tsayawa ta yi har sannan bata kalleshi ba, ya numfasa sannan ya ce“na san zaki ce ban yi dai dai ba. Wallahi babu yanda na iya ne Maimoon, ban so na faɗawa kowa ba, amma ina son Siyama, ina son na aureta. Ba zan iya bari na rasata ba, kin ga...” “Ya isa haka Ya Safwan! Ya isa!” Maimoon ta faɗa a mugun tsawace, wanda ya tilasta shi yin shiru ba tare da ya gama faɗar abin da ke bakinsa ba. Ta dinga wani irin huci hawaye na zubowa kan farar fuskarta, lokaci ɗaya kuma ta cakumeshi cikin ɓacin rai ta fara faɗin “Kai mugu ne! Kai azzalumi ne Yaya Safwan! Ka cuceta. Ka cuci rayuwarta! Wallahi ko wanda ya sanya aka yi hotunan na bai kai ka lefi ba. Akan me zaka yaudareta? Akan me zaka sa ta bar gida? Akan me zaka yi mata alƙawarin rufe sirrinta sannan kuma ka buɗashi a gaban kowa? Me ya sa zaka tozarta ta?. Me ya sa? Me yasa Yaya Safwan?” Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi. Kasa magana Safwan ya yi, sai hawaye da yake zubowa daga idanunsa. Har sannan Maimoon na rike da kwalar rigarsa. Suka dinga kuka a tare kamar ƙananun yara, shi kansa bai san dalilin daya sanya ya fito da hotunan ba, dan bai manta alƙawarin da ya yiwa Nana ba. Bai manta sanda ta tsaya a gabansa ba tana kuka ta ce “Yaya Safwan zan tafi, zan haƙura da komai. Zan bar gidan nan kuma ba zan sake dawowa ba, zan tafi kamar yanda kace, zan ɗorawa kaina laifin cewa ni ce bana son aurenka. Amma dan Allah, dan Annabi kada ka bari kowa ya ga hotunan, ka ƙonasu kamar yanda kace, kada ka bari Abbana ya gani, kada ka bari dan Allah...” Ta ƙare maganar tana durƙushewa a gabansa. Safwan ya runtse idanu yana jin wani irin zafi a zuciyarsa, da gaske bai kyauta mata ba, da gaske ya yaudareta. Yanzu kowa laifinta yake gani, ya cutar da rayuwarta. A ina zai ga Nana ya nemi gafararta? Me ya sa bai tambayi inda zata je ba?. Sakinsa Maimoon ta yi ta ɗauki mayafinta wanda ya faɗi ta juya zata bar wajen, da sauri ya sake biyota yana cewa “Kin san inda Nana ta tafi?” Kamar ba zata kulashi ba sai kuma ta juyo tana kallonsa ta ce“mene ne abun da ya shafeka da inda ta tafi? ko zaka bita can ne ka dawo da ita domin kowa ya tsaneta?” girgiza kansa ya yi a sanyaye ya ce“a'a zan bata haƙuri ne” Da wani mamaki Maimoon ta dinga kallonsa, can kuma ta girgiza kanta ta ce“haƙuri? haƙuri zaka bata saboda ka cuceta? to wallahi koda na san inda Nana take ba zan taɓa faɗa ba! Ba zan bari kowa ya sani ba!” Daga haka ta juya ta bar wajen a fusace kamar zata tashi sama. Safwan ya bita da kallo zuciyarsa cike da damuwa. **** Around 5:00 na yamma ta fito daga kitchen ɗin hannunta riƙe da wata ƙatuwar warmer, ta ajiye akan table sannan ta ɗauki mayafinta da ke kan sofa ta yafa, sai baza ƙamshi take. Ta ɗauki warmer ta fito daga apartment ɗin kai tsaye kuma apartment ɗin Hajiya Babba ta nufa. Zaune ta samu mutane ana ta hira, Hajiya Babba na zaune kan sofa two seater ita da Atta. Jiki a sanyaye ta ƙarasa ciki dan sam bata ji daɗin ganin Attan ba, ɗaya bayan ɗaya ta dinga gaisar da mutanen parlon, suka amsa cikin fara'a sannan ta tsuguna gaban Hajiya Babba ta gaisheta itama. Fuska a sake ta amsa mata, ta kalli Atta ta gaisheta. Ciki-ciki ta amsa tana ɗauke kai, Zahra bata damu ba dan daman ta san haka zata yi ta mai da kallonta ga Hajiya Babba ta ce“hajiya daman abinci na kawo miki” ta tura mata warmer. Murmushi Hajiya Babba ta yi ta ce“tom nagode Fatima” Zahra ta murmusa sannan ta mike tana shirin fita. Ɗaya daga cikin matan da ke zaune ta kalleta sai kuma ta kalli Hajiya Babba ta ce “au wannan ce matar tasa ta farko?” Kafin Hajiya Babba ta yi magana Atta ta yi saurin faɗin “ita ce. Yaje ya auro bare, to da Allah yasa yanzu ya wanke kansa ya auri yar danginsa. Abun nan ya min daɗi, daman can ni ina nake son ya aura wallahi, sai dai aka fi ƙarfina ashe dai rabonsa ce. Yarinya yar dangi ga kyau ga diri” Atta ta ƙare maganar rai a sake. Murmushi duka suka yi banda Hajiya Babba, Zahra ma na tsaye dan ta kasa tafiya, Ɗaya bafulatanar ta ce “oh naganeta, yarinyar ita ce wadda suka zo ruga tare ko? Ai daman aradu sun dace da juna. Ni na ɗauka ma a sannan ɗin matarsa ce” Atta ta girgiza kanta ta ce“a'a sannan bai aureta ba, ai ni gara da Allah yasa aka yi haka ma. Dan da ya auri Haule gara Nanar” Wani irin abu ne ya zo ya tokarewa Zahra a ƙirji, ta juyo tana kallon Atta a firgice. Kasa ɓoye tashin hankalinta ta yi bakinta na rawa ta ce “Hajiya... Atta me ki ka ce?” Tsuke fuska Atta ta yi ta ce“cewa nayi gara daya auri Nanar!” A mugun firgice ta dawo gaban Atta, ta zube tana kallonta bakinta na rawa ta ce “Babba...ban gane ba, wa ya aura? wa Doctor ya aura Atta?” “Naanah mana!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewaboooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Assalamu alaikum jama'a, ina son nayi amfani da wannan damar na sanar daku cewa duk wanda ya ga wannan littafin na NAANAH ba'a channel ɗina ba, sannan ba forwarding aka yi daga channel ba to ba nawa bane, saboda an fara ɗora wasu links wanda basu dace ba akan page ɗin book ɗin, so kada aga wani abu wanda bai dace ba a yi tunanin daga gareni ne. Ban sani ba, kuma banida hannu a ciki, a channel ɗina kawai nake posting littafin nan, sai dai nayi sharing ɗinsa daga can.Nagode 🙏. Page 35... Atta ta bata amsa kai tsaye. Wani irin zaman yan bori Zahra ta yi a wajen, ta dinga kallonta hankali tashe, nan take hawaye suka fara zubar shar daga cikin idanunta. Sam ta kasa gane abin da Atta ke nufi, ta kasa gazgata maganarta. Dan haka ta rarrafa gaban Hajiya Babba ta dafata cikin wani irin yanayi wanda yafi kama dana tashin hankali ta ce “Hajiya bangane me Atta ta ce ba. Wa Doctor ya aura?” Dafata Hajiya Babba ta yi babu yabo babu fallasa ta ce“Naanah ya aura, ɗiyar Ahmad.” Wani irin abu ne ya zo ya tokarewa Zahra a ƙirji, ta kasa koda haɗiyar yawu sai kallon Hajiya Babba take. Can kuma ta sake cewa“Hajiya daman ba Haule zai aura ba? Daman Naanah zai aura?” Girgiza kai Hajiya Babba ta yi kafin ta ce“Eh Haule zai aura. Amma saboda matsalar da aka samu ya sanya ya fasa auren Haule, aka maye gurbinta da Naana. Ita kuma Haule ta auri Safwan da kuma ƙanwarki!” Shiru Zahra ta yi tana tunani, gaba ɗaya sai taji kamar mafarki take wanda zata farka taga babu abin da ya faru. Ta dinga sauke numfashi da sauri da sauri hawaye na biyo kuncinta, ganin yanda jikinta ya yi sanyi ya sanya Hajiya Babba cewa“tashi ki je. Idan ya dawo sai ya miki bayani yanda zaki fahimta” kasa cewa komai ta yi, ta miƙe da kyar tana dafe kanta saboda sara matan da ya yi, a daddafe kuma ta fice daga parlon. Atta ta bita da harara sannan ta ce“ai daman ni na san ba son auren zata yi ba! Kuma babu yanda ta iya wallahi. Idan bata yi wasa ba ma sai ya saketa” kallonta kawai Hajiya Babba ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ta sauke numfashi a sanyaye ta ce “Allah ya kyauta” **** Zahra na komawa apartment ɗinta ta haye sama da sauri, daƙinta ta shiga ta rufe ƙofar sannan ta fara dialing numbern Aunty Khadijah hannunta na rawa. Ringing ɗaya ta ɗauka, kafin ta yi magana Zahra ta yi saurin cewa “nashiga uku aunty, na shiga ukuna!” Da mamaki Aunty Khadijah ta ce “Lafiya dai Zahra?” Cikin kuka Zahra ta ce“ya aureta! Wallahi ya aureta Aunty. Ya zan yi da raina? Taya zan jure ganin Nana matsayin matar mijina? Nana fa aunty!” Aunty Khadijah da bata gane inda zancen ya dosa ba ta ce “kin ga Zahra nutsu ki min bayani. Wace ya aura? Kuma wane ki ke magana akai?” Girgiza kai Zahra ta dinga yi cikin tashin hankali ta ce “Nanah mana! Doctor ya auri Nana, ashe da ita aka ɗaura masa aure ɗazu.” A firgice Aunty Khadijah ta tashi daga zaunen da take ta ce “what?!” Zahra ta gyaɗa mata kai kamar tana gabanta. Cikin shessheƙar kuka ta ce “Eh Aunty. Wallahi ita aka aura masa, yanzu Nana ce kishiyata, wayyo Allah na zuciyata aunty, wallahi ba zan iya ba. Mutuwa zan yi Aunty” Ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka. Shiru Aunty Khadijah ta yi tana ayyana irin abin da zasu yi, jin yanda Zahra ke kuka kamar ranta zai fita yasa ta yi ƙasa da murya ta ce “Ya isa haka Zahra. Zaki iya fitowa yanzu?” Girgiza kanta ta yi ta ce“a'a ba zan iya ba wallahi” Aunty Khadijah ta sauke numfashi sannan ta ce “tom shikenan. Ki bari gobe da safe zan zo sai mu san yanda zamu yi Kinji, ki daina kukan” Shiru Zahra ta yi tana shessheƙar kukanta. Aunty Khadijah ta sake ƙasa da murya cikin sigar rarrashi ta ce “ki yi haƙuri kin ji. Ki ɗauka kamar ba'a miki kishiya ba, in dai ina da rai ba zan bari yarinyar nan ta tare ba” Zahra ta gyaɗa kanta a sanyaye ta ce“tam Aunty.” Jin ta kwantar da hankalinta ya sa ta sake cewa“to ki daina kukan, ki share hawayenki” To kawai Zahra ta ce sannan suka yi sallama. Ta wurgar da wayar tsakiyar gado sannan ta durƙushe a wajen tana fashewa da wani sabon kukan, idan ta tuna yanzu ita da Nana suna ɗaya suke amsawa sai taji zuciyarta ta tsinke. **** Tsaye suke a ward ɗin asibitin kowa ya yi jigum-jigum, Sultan ne ya fito hannunsa riƙe da wata takarda ya ƙaraso wajen, da sauri Abdusammad ya ƙarasa wajensa ya amshi takardar without say anything. Warware ya yi ya karanceta tas sai kuma ya ɗago kansa cike da damuwa ya ce “Ya jikin nasa to?” Numfasawa Sultan ya yi kafin ya ce“da sauƙi za'a ce. But har yanzu bai farfaɗo ba” Miƙa masa takardar ya yi sai kuma ya nufi ɗakin da aka kwantar da Abban. Kwance ya sameshi idanunsa a rufe yana sauke numfashi a hankali da taimakon na'urar da aka saka masa. Abdusammad ya riƙe hannunsa na dama yana jin zuciyarsa sam babu daɗi. Abba na ɗaya daga cikin mutanen da ya fi ƙauna a duniya, idan ka cire Hajiya Babba babu wanda ya kewa kallon mahaifi sama da Abba, he's not just his father but a friend. Yanda suke zama su yi hira da Abba koda Hajiya Babba baya yi, dan haka ganinsa cikin wannan halin babu abin da yake face tada masa hankali. Idan kuma ya tuna Nana ce sanadiyyar wannan abun sai yaji zuciyarsa ta sake ɓaci, sai yaji dama ya bar nan yaje ya dawo da ita gida ya nuna mata kuskuren abin da tayi. Furzar da zazzafan numfashi ya yi daga bakinsa still looking at Abba's face. Ƙarar na'urar da yaji ce ta sanya shi gyara tsaiwarsa, ya dinga kallon Abba wanda yake ƙoƙarin buɗe idanunsa. Da sauri ya zauna a gefen shi har sannan yana riƙe da hannunsa ya ce “Abba!” A hankali Abba ya buɗe idanunsa wanda suka yi jajur dasu, ya kalli Abdusammad sai kuma ya sake rufesu. Jiki a sanyaye Abdusammad ya ce “Abba ka yi haƙuri dan Allah, kar ka damu kan ka kaji” Shiru Abba ya yi kamar ba zai magana ba can kuma ya ce. “Abdul” “Na'am Abba” Ya amsa kamar zai yi kuka. Numfasawa Abba ya yi ya sake buɗe idanunsa akansa, a hankali kuma ya kai hannunsa na hagu wanda aka maƙala masa canola ya shafa fuskarsa yana murmushi ya ce “karka damu kaji, I'm fine” “you are not Abba. Kalleka fa, baka da lafiya Abba, dan Allah ka daina damuwa kaji. I'm promise, I already promised cewa zan dawo da Nana. Zata dawo gida Abba!” Ya yi maganar hawaye na kawowa cikin idanunsa. Lumshe idanu Abba ya yi wanda ya bawa hawayen dake cikin idanunsa damar sakkowa kan fuskarsa, ya girgiza kansa a sanyaye ya ce “bana son ganin Nana Abdul. Bana son ta dawo, just leave her, bana son na sake ganinta har abada!” Da wani irin mamaki Abdusammad ke kallonsa, lokaci ɗaya ya shiga girgiza kansa kafin ya ce “a'a Abba. A'a, zaka sake ganinta, zata dawo gida. Komai zai shige kamar bai faru ba” Shiru Abba ya yi yana kallon gefe, dan ko kaɗan baya son magana akan Nana. Idan ya tuna ta zuciyarsa zafi take masa, dan haka ya fawallawa Allah komai zai kuma manta da ita, duk da ya san hakan ba ƙaramin abu bane. A tare suka shigo ɗakin bakinsu ɗauke da sallama, Abdusammad ya amsa a sanyaye dan babu lallai ma sun ji. Papa ne ya tsaya a gefensa a sanyaye ya ce “Ahmad!” Ɗago kansa ya yi ya kalleshi sai kuma ya sakar masa murmushi, Papa mai yi mamakin haka ba dan ya san halin Abba, da wuya ka gane halin da yake ciki. Da wuya ka gane asirin zuciyarsa, duk abin da ya kai shi ga barin a gane damuwarsa to ba ƙaramin abu bane, yana da zurfin ciki fiye da tunani, wannan dalilin ya sanya Nana ta yi gadonsa. Baka taɓa jin damuwarsu cikin sauƙi. Murmushin Papa ya mayar masa kafin ya ce “stop pretending Ahmad, ya jikin naka?” Lumshe idanunsa ya yi ya buɗe ya ce“Alhamdulillahi” Papa ya jinjina kansa sannan ya ce“Allah ya ƙara sauƙi, ya kuma kiyaye gaba” Amin duka suka ce. Sannan suka yi masa ya jiki suma, ya amsa a sanyaye. Kallon Sultan ya yi wanda ke tsaye kusa da Hamid ya ce “Sultan zamu iya tafiya gida ko?” Girgiza kai ya yi ya ce“a'a Abba. Har yanzu baka da lafiya fa, kawai kana daurewa ne, ba za'a iya sallamarka ba” Abdusammad ya jinjina kai ya ce“Eh. Sai ka samu sauƙi sosai Abba” Shiru Abba ya yi yana kallonsu sai kuma ya ce “Alright but you have to go, Kun bar matayenku a gida” Girgiza kai Hamid ya yi ya ce“idan muka tafi kai fa Abba?” Murmushi kawai ya yi sai kuma ya ce“ba komai. Ku je kawai” Girgiza kai Abdusammad ya yi ya ce “A'a ku kawai ku tafi. Zan zauna dashi” Da sauri Abba ya kalleshi sai kuma ya girgiza kansa ya ce“a'a ku je duka” Shiru Abdusammad ya yi dan ba tafiyar zai ba. Papa ya ce su tafin tun da jikinsa da sauki, suka yi masa sallama sannan suka tafi. A can estate kuwa, Amma ce zaune gefen gado Aunty Ramlah na gefenta sai kuka take ƙasa-ƙasa. Aunty Ramlah ta sauke numfashi sannan ta ce “Dan Allah Yaya ki yi haƙuri. Kaddara ce kuma ta riga da ta faru, babu wanda zai sauya hakan, ki yi haƙuri kin ji” Cikin kuka Amma ta ce “Ya zan yi na yi haƙuri Ramlah? Nana fa bata nan. Kuma kin ga hotunan da ake dangatawa da ita, har mahaifinta ya yarda. Ya za'a yi na samu natsuwa, ina so naga Nana, ina son na tambayeta ta faɗa min gaskiya” Dafata Aunty Ramlah ta yi tana jin wani irin tausayin ƴar uwar tata ta ce“ki yi haƙuri Yaya. Na sani abu ne mai wahalar yarda amma ki sani duk abin da ki ka ji ko kika gani to gaskiya, don nima kaina na san yaron” Da sauri Amma ta kalleta sai kuma ta riƙe hannayenta duk biyun cikin kuka ta ce “Da gaske? Kin san shi Ramlah?” Gyaɗa mata kai Aunty Rahmah ta yi. Amma ta matse hannayenta ta ce “to kai ni wajensa dan Allah, kai ni na tambayeshi meyasa zai yiwa Nana haka. Kai ni na tambayeshi ina ƴata take!” Kasa masa Aunty Ramlah ta yi sai kuka da take a hankali, ta rungumeta cikin shessheƙar kuka ta ce “Ki yi shiru Yaya, in sha Allah komai zai shige” Amma bata sake cewa komai ba sai kuka da take a hankali. **** No. 045 Sultan road, Kano State. A hankali ta tura ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama, Zaune ta same su gefen gado. Ta ƙarasa ciki tana kallonsu, Babbar mata ce da zata yi kaiwa 50 to above ɗin nan, fara mai ɗan jiki. Ta zauna ɗan nesa dasu har sannan idanunta na kan su,ganin yanda suka riƙe hannun juna sai kuka suke a tare. Ta ɗan numfasa sannan ta ce “Nana” A hankali ta ɗago idanunta ta kalleta, Mami ta yi mata alamar da ta zo da hannu, ta saki hannun Khadijah sannan ta tashi a hankali ta ƙarasa gabanta. Zama ta yi gefenta, Mami ta jata ta rungumeta tana shafa kanta, Ji tayi kamar a jikin Amma take dan haka ta sake fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Mami ta yi shiru ba tare da ta hanata ba. Khadijah sai kallonsu take tana kukan itama. Above 5mins kafin ta ɗago kanta jin har sannan bata daina kukan ba, ta goge mata hawayen duk da wasu basu bar zuba ba ta ce “Ya isa haka Nana. Kar wani abun ya sameki” Sake shigewa jikinta ta yi cikin kuka ta ce “Mami Ammata, Abbana.” Sosai ta bawa Mami tausayi dan tun da ta zo babu abin da take cewa daya shige wannan. Ta shafa kanta a sanyaye ta ce “Zaki koma kin ji, zasu ganki” Girgiza kanta ta dinga yi tana cewa “A'a Mami, ba zan iya ba. Ba zan iya komawa wajensu ba, na tozarta Abbana! Na wulaƙantashi gaban mutane, na san yana can hankalinsa a tashe. Gara na mutu Mami! So nake na mutu!” Ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan. Kasa cewa komai Mami ta yi, dan ta san ko ta faɗa mata ba zata fahimta ba yanzu. Ita kanta bata ji daɗin guduwar da ta yi ba, sai dai idan ta tuna abin da ta faɗa mata sai taji sam bata da nutsuwa. Sai taji gara da ta bar gidan akan rashin son aure da ace an fitar da irin hotunan wanda zasu iya tarwatsa zuciyar duk wata uwa ko uba. Ganin ta fara rage kukan yasa ta ɗagota ta ce “Ya isa haka tashi ki ci abinci sai ki kwanta” girgiza kanta ta yi ta ce“na ƙoshi Mami” Mami ta yi shiru tana kallonta,can kuma ta mike tana kallon Khadijah ta ce“zo ki karɓar muku abinci” a sanyaye ta ce to sannan Mami ta fita. Ta tashi ta dawo gefen Nana ta riƙe hannunta cikin kuka ta ce “Nana ki daina kuka kinji. In sha Allahu sai Allah ya saka miki” Tari ta fara yi tana dafe saitin zuciyarta, lokaci ɗaya ta nemi fita daga hayyacinta. Da gudu Khadijah ta tashi ta fita tana kwalawa Mami kira, Mami dake tsaye a corridor ita da Adeel ta kalleta da mamaki ta ce “Mimi lafiya?” Girgiza kanta ta yi tana nuna mata hanyar dakin ta ce“Nana! Nana Mami” Da sauri Mami ta yi hanyar ɗakin, Khadijah ta jawo Adeel da ke tsaye ta ce“Yaya zo muje kai ma” Bai mata musu ba ya bi bayanta suka nufi ɗakin. Tsaye suka tarar da Mami gabanta ta riƙeta ganin yanda take aman jini, suna shigowa ta kalleshi hankali tashe ta ce“Adeel zo ka ɗauketa mu kaita asibiti” Shi kansa sai da hankalinsa ya tashi, ya dinga kallonta ganin how weak she's yasa ya ƙaraso ya ɗauketa sannan ya yi waje da ita da sauri. **** Washegari da sassafe around 8:00 Aunty Khadijah ta shigo parlon, zaune ta samu Zahra ta zuba uban tagumi. Kayan jiya ne a jikinta. Ta ƙarasa ta zauna kujerar dake facing tata tana kallonta ganin yanda ta fice hayyacinta, gaba ɗaya ta zama kamar ba ita ba, fuskarta ta wani irin zugewa. Idanunta sun kumbura, har wata ramar tashin hankali ta yi daga jiya zuwa yau, musamman daya kasance babu kowa a gidan dan tun jiya take zaune jiran Abdusammad ya shigo amma babu shi babu alamarsa. Noor kuma tana apartment ɗin Hajiya Babba. Numfasawa Aunty Khadijah ta sai kuma ta girgiza kanta ta ce “Zahra! Zahra!” Shiru babu amsa, dan babu alamar ma taji shigowarta. Dan haka ta taso ta dawo inda take ta zauna sannan ta ɗan jijjigata ta ce “Zahraaa!” A firgice ta kalleta, sai kuma ta sauke numfashi ta ce “Aunty” Kallonta Aunty Khadijah ta yi ganin duk ta birkice kanta ta ce “mene ne haka? Ba cewa nayi ki bar damuwa ba?” Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da fingers ɗinta lokaci ɗaya kuma wani kuka ya tawo mata, ta dinga rerashi ba tare da ta ce komai ba. Kusan mintuna biyar kafin Aunty Khadijah ta ce “yanzu kukan za ki ci gaba ko kuma shiru zaki yi mu san abin yi?” Kallonta Zahra ta yi sai kuma ta fara share hawayenta da hannunta ta ce“na kasa haƙura ne aunty. Zuciyata ta kasa jurewa, ji nake kamar ba gaske ba, ji nake kamar zuciyata zata fito daga ƙirjina. Ya zan yi aunty?” Dafata Aunty Khadijah ta yi sai kuma ta ce “Dole akwai abin da zamu yi. Ba dai yarinyar bata gidan nan ba yanzu?" Gyaɗa mata kai Zahra ta yi, ta numfasa ta ce “To ba zamu bari ta dawo ba. Ta tafi kenan!” Da mamaki Zahra ke kallonta sai kuma ta ce “amma Aunty ban fahimceki ba.” Dan murmushi Aunty Khadijah ta yi ta ce “Cewa nayi ba zata dawo gidan nan ba. Koma ina ta tafi ba zamu bari ta dawo ba, ballantana har ta tare a matsayin kishiyarki” Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“ni dai babu ruwana Aunty, kada ki saka a yi mata wani abun. Babu ruwana wallahi!” Tsaki Aunty Khadijah ta yi ta miƙe tsaye tana kallonta ta ce “Ke daɗina da ke ba'a iya miki. Ina ƙoƙarin yin abin da zai taimakeki amma ke bakya gani, to sai me idan an yi mata asirin? Le dai ba burinki ta rabu da mijinki ba?” Tashi itama Zahran ta yi tana kallonta ta girgiza kanta ta ce “Ni ba ina nufin a cutar da ita bane. Kawai dai bana son ta zauna matsayin kishiyata, amma wallahi ba zan iya saka hannu cikin sake cutar da ita ba!” Harararta ta yi ta ce“to ai sai ki yi ta yi, kina nan kuwa zata rabaki da gidan da ki ke taƙama dashi!” Tura baki Zahra ta yi tana kallon wani wajen ta ce“ni dai babu ruwana!” Aunty Khadijah bata sake saurarenta ba ta ƙarasa ta ɗauki jakarta inda ta ajiye ta yi waje fuuu. Sai da taga ta fita sannan ta koma ta zauna kan sofa ta fashe da kuka, ita sam bata da niyyar sake cutar da Nana. Amma ba zata iya zama da ita matsayin kishiya ba. Tana nan zaune tana kuka aka buɗe parlon, ta ɗago kanta da sauri ganin wanda ya shigo. Sanye yake da kayansa na jiya sai dai babu babbar rigar, ta dinga kallonsa ganin yanda ya fice hayyacinsa. Kallo ɗaya ya yi mata ya nufi sama da sauri, ta bi shi da idanu sai kuma ta tashi tabi bayansa da sauri. Tsaye ta same shi a tsakiyar ɗakinsa, ya zare rigar jikinsa sai fara singlet a jikinsa. A hankali ta saki ƙofar tana kallonsa, Ta ƙarasa gabansa muryarta a sanyaye ta ce “Doctor” Kallonta ya yi sai kuma ya ce“na'am” Ƙoƙarin magana take amma ta kasa, sai rawa bakinta yake. Ya ɗan kalleta sai kuma ya ce “I want to take shower” Gyada masa kai ta yi hawaye na biyo kuncinta. Ya nufi toilet ba tare da ya sake kallonta ba, da idanu Zahra ta bi shi sai kuma ta zauna kan kujerar dake ɗakin, lokaci ɗaya ta haɗe kanta da gwuiwa ta fashe da kuka. Tana nan zaune har bayan mintuna ashirin ya fito daga toilet ɗin yana goge kansa da towel, Ya kalleta sau ɗaya sai kuma ya nufi wajen dresser tashi. Cikin yan mintuna ya shirya cikin wasu kananan kaya t-shirt fara da jeans blue colour. Ya gyara sumar kansa sai sheƙi take, turaren arabian oud ya fesa sannan ya dauki wayarsa yana shirin fita. Zahra na ganin haka ta mike da sauri bakinta na rawa ta ce “Dd... Doctor!” Cak ya tsaya lokaci ɗaya kuma ya juyo yana kallonta. Sunkuyar da kanta ta yi ganin yanda fuskarsa take babu alamar walwala. Ya gyara tsaiwarsa yana kallonta sosai ya ce “Ina ji” A sanyaye ta ce “Daman i just want to ask you ne” Gyaɗa mata kai ya yi ya ce “uhm..” Ta ɗan numfasa tana ƙoƙarin riƙe kukanta ta ce “wai da gaske ka auri Nana?” “Eh” Ya bata amsa kai tsaye, Durƙushewa Zahra ta yi a wajen, ta haɗe hannayenta duk biyun alamar roƙo ta ce “Dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri. Kada ka aureta doctor, ka rufa min asiri, wallahi ba zan iya zama da Nana matsayin kishiya ba. Ba zan iya ba doctor, na san baka sonta! Na san dole aka maka, ba yin kanka bane!” Ban da kallonta babu abin da Abdusammad ke yi, sam babu alamar damuwa akan fuskarsa. Ya yi mata alama data tashi, babu musu ta mike tana kuka har sannan. Furzar da numfashi ya yi kafin ya ce “Ki yi haƙuri!” Ya yi maganar yana juyawa, ganin ya fice daga ɗakin yasa Zahra sake fashewa da wani kukan, lokaci ɗaya kuma ta bi bayansa da gudu, a parlon ta same shi yana shirin fita. Cikin kuka ta ce “Kana nufin zaka zauna da ita? Zaka haɗa zuri'a da ita? Yarinyar da aka tabbatar da bata da tarbiyya! Yarinyar da kowa yaga hotunanta da namiji? Yarinyar da ke bin maza!” Ta yi shiru tana girgiza kanta, sai kuma ta tako har gabansa ganin bai ko motsa ba. Cikin kuka ta ce “Kada ka zauna da ita doctor, na san baka sonta. Na san wallahi baka son Nana dole aka maka, dan girman Allah ka saketa! Ka saketa mu yi komawar mu US, kada ka ce zaka haɗa zuri'a da lalatacciyar yarinya ka...” “Shut up!” Ya daka mata wata razananniyar tsawa wadda ta sanyata firgita. Gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun tashi, idanunsa sun kaɗa sun yi jajur sai huci yake, rai ɓace ya ce “Kar na sake ji kin haɗata da wadannan munanan kalaman! Zan bata miki fiye da tunanin ki Zahra. And you know what? Babu wanda ya yi min dole sai na auri Nana, Ni ne na aureta saboda raɗin kaina, kuma kin san me yasa na aureta?” Samun kanta ta yi da girgiza masa kai. Ya ƙara taku ɗaya gabanta wanda yasa suka yi kusa sosai har suka jin hucin numfashin juna ya ce “Cause i love her! Na aureta ne saboda ina sonta! Ina son Naanah! Kuma ba zan taɓa sakinta ba! She's my wife!” 08106608363, Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 36. Ya yi maganar yana watsa mata wani irin kallo. Girgiza kai Zahra ta yi ta riƙe shi a kiɗime ta ce“A'a wallahi na san baka sonta. Kawai dai ka faɗa ne, baka sonta wallahi!” ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka. Shiru Abdusammad ya yi yana kallonta, can kuma ya janye hannunta daga jikinsa ya juya ya fice daga ɗakin zuciyarsa a dagule babu daɗi. Zahra ta durƙushe a wajen tana kuka kamar ranta zai fita, she just can't believe a ce doctor ya ce yana son Nana, how? Ta girgiza kanta tana tashi zaune ta ce“A'a impossible”Ta tashi da sauri ta haye sama. Kai tsaye apartment ɗin Hajiya Babba ya nufa, ya murɗa handle ɗin bakinsa ɗauke da sallama, zaune ya same su suna tattauanawa. Ya ƙarasa ciki ya tsaya gefen kujera ba tare da ya ce komai ba. Papa ne ya ce “Ya jikin Ahmad ɗin?” Numfasawa ya yi kafin ya ce “Da sauki Alhamdulillah, bacci ya daukesa ma" Papa ya jinjina kansa sai kuma ya yi shiru. Atta ta ce ta girgiza kanta tana hawaye ta ce“oh ni Maryama, ko ina yarinyar nan ta shiga Allah masani” Sultan ne ya yi saurin faɗin “maybe ai tana wajen wanda aka hoton nasu tare” Cikin kuka ta ce“to ina zamu san wane shi?” “where are the pictures?” Abdusammad ya yi maganar yana kallon Sultan dan shi ne ya ɗauke su. A sanyaye ya ce“suna ɗakina” “Bring them” Okay kawai ya ce sannan ya tashi ya fice daga parlon. Sai a sannan Hajiya Babba ta ce“Abdussamad a samu a yi reporting wajen yan sanda” Okay kawai ya ce yana gyara tsaiwarsa. After some minutes Sultan ya dawo parlon hannunsa riƙe da envelope ɗin, ya miƙa masa ya karba yana faɗin “Good job” Murmushi kawai Sultan ya yi sannan ya koma ya zauna. Papa ya miƙe tsaye kana ya ce“bari naje na duba shi, we should talk later” okay kawai suka ce sannan ya fita daga parlon. Abdusammad ya zauna idanunsa na kan Hajiya Babba ya ce“Hajiya” “Na'am” ta amsa a sanyaye.. “Ina Safwan yake?” Ya yi tambayar fuskarsa a ɗan haɗe. Hajiya Babba ta kalli hanyar sama sai kuma ta ce“Da dai yana nan bai tafi ba, amma ban sani ba ko ya je gidansa wajen Haule. Tun da ita ɗayar yarinyar har yanzu basu kawota ba” Miƙewa ya yi ya ce“okay bari naje sai an jima” daga haka ya fice daga ɗakin yana tafe cike da taƙama. **** Papa ya yi shiru yana kallon Abba jiki a sanyaye. Can kuma ya girgiza kansa ya ce “A'a Ahmad ba'a haka, yarinya ce ƙarama, akwai rashin hankali a tattare da ita. Bai kamata a ce ka ɗauki wannan mummunan hukuncin ba, beside ma yarinyar ta yi aure yanzu!” Da sauri ya kalli Papa sai kuma ya ce “Ta yi aure? Yaushe ta yi aure ban sani ba Papa? and wa ta aura?” Murmusawa Papa ya yi sai kuma ya ce “Wa ka ke tunanin zai share maka hawaye irin haka?. Abdusammad ne ya aureta, dashi aka daura mata aure” Da wani irin mamaki Abba ke kallon Papa, sai kuma ya girgiza kansa ya ce “Yaya ban da wasa, ka faɗa min da gaske Abdusammad ya aureta?” Dafa shi Papa ya yi ya ce“Eh da gaske ne, kasan bama irin wannan wasan da kai ai” Tashi Abba ya yi ba tare da ya ce masa komai ba ya zura slippers ɗin dake ƙasan gadon sannan ya yi waje da sauri, duk da yanda yake jin jikinsa babu daɗi. Da idanu Papa ya bi shi sai kuma ya tashi ya biyo bayansa dan ganin inda zai je. A parlon suka ci karo dashi, Ya yi saurin riƙe kwalar rigarsa rai ɓace ya ce “me yasa? Me yasa Abdul? Why? I said why!” Ya ƙare maganar yana jijjigashi. Kallonsa kawai Abdusammad ke yi ba tare da ya san akan abin da yake magana ba, Amma da ke zaune ita da Aunty Ramlah suka miƙe tsaye. Ta ƙaraso wajen tana kallonsu, dai dai nan Papa ya fito daga ɗakin. Da sauri kuma ya ƙaraso gabansa yana ƙoƙarin janye hannunsa ya ce “Subhanallahi Ahmad mene haka?” Girgiza kai Abba ya yi yana sake matse kwalar rigarsa ya ce “Ka faɗa min meyasa zaka yi haka? Me ya saka zaka aureta! Akan mene ne!” Sai a sannan Abdusammad ya fuskanci inda ya dosa. Ya ɗan yi murmushi yana janye hannunsa ya ce“to mene ne Abba? Nana ce fa” A tsawace Abba ya ce “Nanan! Ita Nanan bana son ganinka da ita. Bana son kowace mu'amala ta haɗata da yan gidan nan, ta riga da ta bar cikin dangin nan, yanzu bata kasance daya daga cikin mu . Akan me zaka aureta Abdul? Ka san zafin da naji?” Shiru ya yi yana kallonsa ganin da gaske yake faɗar maganganun, Ya riƙe hannunsa a sanyaye ya ce“Abba ka yi haƙuri mana” “Ba zan yi ba!” Ya ce a zafafe. Kallonsa suka dinga yi da mamaki, Amma da tuni hawaye ya wanke mata fuska ta ƙaraso wajen ta rike gefen rigarsa cikin kuka ta ce “me ka ce? Ka cire Nana daga cikin dangin nan? Kenan ka zareta daga matsayinta na yar ka?” Juyowa Abba ya yi yana kallonta sai kuma ya janye jikinsa ya ce“Eh haka nace!” Daga haka ya koma ɗakinsa rai ɓace.. Silalewa ƙasa Amma ta yi ta fashe da wani raunataccen kuka, Aunty Ramlah ta riƙeta ba tare da ta ce komai ba. Numfasawa kawai Papa ya yi sai kuma ya fice daga parlon, Shi kuwa Abdusammad ciki ya shiga gurin Abba. **** Ƙarfe 11:30 na safe Mami ta shigo ɗakin, suna zaune tare sai dai babu wacce ke magana cikin su. Mami ta girgiza kanta sai kuma ta ƙaraso ciki ta zauna kan sofa tana kallonsu duka ta ce “Kukan ne har yanzu baku gama ba?” Kallonta kawai suka yi ba tare da sun ce komai ba, Ta ɗan yi murmushi sai kuma ta ce“Nana kin ci abincin?” Gyaɗa mata kai Nana ta yi a hankali dan har ga Allah ba son yin magana take ba. Mami ta sake cewa“to ku tashi ku shirya sai ku rakani” “Ina zamu je Mami?” Khadijah ta yi tambayar a sanyaye. Tashi Mami ta yi tana gyara zaman rigarta ta ce“idan mun je zaku gani” daga haka ta fice daga ɗakin. Khadijah ta bita da kallo sai kuma ta sauke numfashi tana kwanciya kan gadon ta ce“ni wallahi bana son fita” kallonta kawai Nana ta yi ba tare da ta ce komai ba. Can kuma ta tashi zaune ta ce “Yauwa Nana to yanzu sir Junaid ɗin ya fitar da hotunan?” A sanyaye Nana ta ce“ban sani ba Khadijah,ina ga ya fadawa su Abba. Na san Abba yana can yana jin haushina” ta ƙare maganar tana fashewa da kuka. Dafata Khadijah ta yi a sanyaye ta ce“ki daina kukan nan mana, kin ga dai jiya daga haka aka kai ki asibiti” Cikin shessheƙar kuka Nana ta ce“to me zan yi? Ni gaba ɗaya bana jin daɗin rayuwar, wallahi da zan iya da sai nasha guba na mutu” saurin rufe mata baki Khadijah ta yi tana zare idanu, Nana ta janye hannunta daga kan bakinta rai ɓace ta ce “Ni rabu dani” Sake rufe bakin ta yi sannan ta ce“wallahi idan abin da zaki ce kenan ba za ki yi magana ba” A fusace Nana ta hankaɗeta sannan ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet. Khadijah ta tashi zaune tana riƙe bayanta ta ce “Banza mai son faɗa kawai” **** Aunty Khadijah ce zaune kan sofa sai Sojan a gefenta, daga ɗaya kujerar kuma Safeena ce zaune sai Ummarsu. Kamar daga sama Zahra ta shigo parlon babu ko sallama, ta ƙarasa wajen Umma ta faɗa jikinta tana fashewa da kuka. Umma ta riƙeta da mamaki ta ce “Zahra'u lafiya? Mene ne?” “Ba zan iya ba Umma, ba zan jure ba wallahi. Ba zan iya zama da Nana matsayin kishiya ba, Umma na shiga uku..” Ta sake fashewa da kukan, Girgiza kai Umma ta yi cikin son kwantar mata da hankali ta ce “Ya isa haka, tashi ki ji” A sanyaye ta tashi ta zauna gefenta tana ci gaba da kukan, Umma ta dafata ta ce “Duk abin da haƙuri bai baka ba to rashinsa ba zai taɓa baka ba Zahra'u, Idan baki hakura ba to me zaki yi?” Cikin kuka Zahra ta ce “umma ta ya zan jure zama da Nana matsayin kishiya bayan da ina mata kallon yar karamar ƙanwata, taya zan fara sharing mijina da ita? Wallahi ba zan iya ba!”. Murmushi irin na manya Umma ta yi kafin ta ce“daman haka abun yake Zahra, sau dayawa abin da baka yi tunani ba shi ne yake kasancewa. Wani abun ƙaddara ce, wani kuma ganganci ne” Zahra ta tsaida kukan nata tana kallon Umma. Numfasawa Umma ta yi sannan ta ci gaba da faɗin “Na san duk abin da ku ka aikata. Sai dai ban yi tunanin haka daga gareki ba, kin biye mata kun yi abin da ku ke ganin shi ne son zuciyarku, idan kuwa haka ne to dole ki yarda da abin da ya biyo baya.” Umma ta ƙare maganar tana kallonta, Sunkuyar da kai Zahra ta yi dan sam bata yi tunanin Umma ta san abin da ya faru ba, Umma ta girgiza kanta hawaye na biyo kuncinta ta ce “Ban ji daɗi ba! Sam bai min daɗi ba ganin yanda ki ka lalata rayuwar yarinya, kin san me yarda ke nufi? Ya yarda da ke, ta aminta da ke, tana miki kallon ƴar uwa wadda zata iya fadawa kowace damuwarta. Amma kin yi amfani da wannan yardar kin cutar da ita, kin yi mata abin da zai jawo kowa ya tsaneta, bayan ke da kan ki kin san cewa bada gangan ta yi hakan ba. To me ki ke tunani Zahra? Allah ya barki, ki ci bulus?” Umma ta girgiza kanta sai kuma ta ce “Inaaa ba zai taɓa yiwuwa ba, shi daman a kullum sharri ɗan aike ne, duk abin da ka ƙulla zai dawo maka, Ubangiji na kishin bawansa, kuma yana ƙaunarsa. Dan haka ya yi mata sakayya,ya nufi mijinki da aurenta.” Fashewa da kuka Zahra ta yi tana danasanin abin da ta aikata, ita kanta ta san bata kyauta ba, sannan bata san dalilin daya sanyata yin hakan ba. Ta ɗago kanta tana kallon mahaifiyar tata wadda ke hawaye itama. Umma ta goge fuskarta da hannunta wanda ke riƙe da cazbaha sannan ta ce “Na yi ƙoƙarin baku tarbiyya tun bayan rasuwar mahaifinku, na yi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin kun zama ya'ya nagari, kun zama mutane nagari wanda kowa zai yi alfahari dasu. Sai dai a duk lokacin daya kasance babbar ƴata bata kasance mutuniyar kirki ba, dole sai sauran sun zama haka. Dole sai taja wasu daga cikin ƴan uwanta. Kamar yanda Khadijah ta jaku ku ke ƙoƙarin faɗawa halaka” Umma ta ƙare maganar wani kukan na kwace mata, Safeena ce ta riƙeta tana kukan ita ma ta ce “Dan Allah Umma ki yi haƙuri. Ki daina kuka kin ji” Riƙe hannunta kawai Umma ta yi dan bata jin zata iya daina kukan a halin da take ciki, Zahra ta girgiza kanta tana kuka ita ma ta ce “ki yi haƙuri Umma. Wallahi ba zamu sake ba, babu abin da zai sake faruwa in sha Allah” Tashi Aunty Khadijah ta yi ta bar wajen dan sam bata ga abin kuka anan ba, Siyama ta ƙaraso wajen ta zauna a ƙasa tana kallon Umma ta ce “Umma ki yi haƙuri dan Allah” Ganin duk sun ruɗe suna kuka ya sanyata tsagaita nata kukan. Ta dafasu tana murmushi mai haɗe da hawaye ta ce “shikenan ya shige, Allah ya yi muku albarka ya shirya ku" Da Amin suka amsa suna goge hawayensu.. **** Bayan sallar magriba ta dawo gidan, gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, musamman yanda taga Umma na kuka akan su. Sai taji danasanin abubuwan data aikata. Koda ta shiga gidan bata samu kowa ba kamar yanda ta yi tsammani, dan haka ta shige daƙinta ta yi wanka ta zauna gefen gado tana tunani. Tana nan zaune har aka yi sallar isha'i ta gabatar da sallah sannan ta sakko ƙasa ta shiga kitchen. Jollof rice ta yi wadda taji kayan haɗi, ta yi haɗin salad sannan ta fito ta koma sama ta zauna dan ko kaɗan bata jin yunwa. **** Ƙarfe 9:30 na dare ya shigo ɗakin, zaune ya hangeta gefen gado ta sunkuyar da kanta sai kuka take a hankali. Ya ƙaraso ciki yana kallonta, zama ya yi gefenta kafin ya ce “Maimoon” A sanyaye ta ɗago kanta ta kalleshi sai kuma ta mai da ƙasa tana shessheƙar kuka, Aliyu ya ɗan yi murmushi kafin ya kama hannunta na dama yana kallon red henna ɗin da aka zana mata wanda ya yi matuƙar kyau a hannunta, Ya kai hannun bakinsa ya sumbace shi yana lumshe idanu. Yana yin daya haifar mata da wani irin sanyin jiki, ta ɗago ta kalleshi a sanyaye. Ba tare da ya saki hannun ba ya janye mayafin da ta yi lulluɓi dashi, sannan ya ce “tashi mu yi sallah” Babu musu ta mike ta nufi toilet ta sake dauko alwala, bayan ta fito shi ma ya shiga ya yo alwalar sannan ya shimfiɗa musu ladduma. A tare ya ja su sallar nafilar bayan sun idar suka yi addu'a, daga bisani ya dafa kanta ya yi mata addu'o'i sannan ya tashi ya zare babbar rigar jikinsa yana kallonta ya ce “Mu je ki ci abinci” Girgiza masa kai ta yi a sanyaye ta ce“na ƙoshi” Ya ɗan yi murmushi sai kuma ya kamo hannunta ya taimaka mata ta miƙe tsaye kafin ya ce“to muje ki ci kazarki” ya ƙare maganar yana jan kumatunta. Sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba, ya ja hannunta suka fita daga ɗakin. Sosai Maimoon ta saki jikinta ta ci kazar bayan ta ƙoshi ta tashi ta bar wajen, Aliyu ya bita da idanu yana murmushi sannan ya biyo bayanta. Daren ranar haka suka raya shi cike da so da ƙauna, sam ba zaka ce ba auren soyayya suka yi ba, ya dinga riritata kamar kwai, ita kuwa sai sake narke masa take. A ɓangaren Sultan kuwa kasa taɓuka komai ya yi, ya dinga kallon Amrah da ke baccinta hankali kwance, gani yake kamar a mafarki. Zuciyarsa ta kasa aminta da cewa ya rasa Nana, idan ya kalli Amrah sai yaji damuwa ta sake masa yawa, ya so a ce Nana ce a wannan dakin, a kuma kwance akan wannan gadon, da shi kansa bai san halin da zai shiga ba. Ya ja idanunsa ya lumshe yana jin babu daɗi. Washegari da sassafe around 7:30am aka fara buga ƙofar gidan, Aliyu ya janye jikinsa dakyar ya fita daga ɗakin bayan ya sake rufe Maimoon, yana buɗe kofar ya shigo yana kalle-kalle. Aliyu ya dinga kallonsa da mamaki sai kuma ya ce“Buddy lafiya?” “Ina Maimuna?” Da mamaki Aliyu ya ce“tana ciki” “i want to see her” Ya ce yana nufar dakin. Bin bayansa Aliyu ya yi da sauri, tsaye ya same shi gaban gadon ya harɗe hannayensa a ƙirji. Aliyu ya ƙaraso ciki yana kallon Maimoon ya ce “Maimoon” Dakyar ta buɗe kumburarrun Idanunta, ta ɗan zame duvet ɗin daga kanta tana kallonsa, idanunta daya sauka kan Abdusammad ne ya sanya ta fara ƙoƙarin tashi, zama Aliyu ya yi gefenta ya ɗagota ya jinginata da jikinsa, Abdusammad ya taɓe baki yana kallonta ya ce “Ina Nana take?!” “Nana kuma? Ya za'a yi ta san inda Nana take Buddy?” Aliyu ya tambaye shi da mamaki. A tsawace Abdusammad ya ce “Nace ina Nana take!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08 Page 37. Sunkuyar da kanta ta yi hawaye na biyo kuncinta, Ya gyaɗa kansa sai kuma ya ƙara taku ɗaya zuwa gabansu yana ware idanunsa sosai akanta ya ce “don't ever let me ask you again! Ina Nana take?” Ganin yanda ta firgice yasa Aliyu dafata ya ɗago yana kallonsa ya ce “Haba Buddy she's not feeling well ka barta mana dan Allah” a fusace shima ya ce “to ni ina ruwana? Mene ne nawa da rashin lafiyarta?” Aliyu shiru ya yi yana kallonsa ganin yanda ya haɗe rai. Ya maida idanunsa kan Maimoon cikin sanyin murya ya ce“pls idan kin san inda take talk to him” sake fashewa ta yi da kuka tana maƙalewa jikin Aliyu ta ce “wallahi uncle ban sani ba, ban san inda take ba!” Wani irin kallon kin zama mahaukaciya Abdusammad ya dinga mata, can kuma ya gyaɗa kansa ya ce“okay!” Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin rai ɓace. Aliyu ya bishi da kallo sai kuma ya maida idanunsa kan Maimoon, Ya shafa kanta a hankali ya ce“sorry ki daina kukan, ya tafi ai” gyaɗa kanta kawai ta yi ya taimaka mata ta kwanta dan har sannan zazzaɓi ne rau a jikinta. Abdusammad na fita apartment ɗinsa ya nufa, ya samu Zahra zaune a parlon ta zuba uban tagumi kamar koda yaushe. Kallo ɗaya ya yi mata sai kuma ya haye sama dan ransa a ɓace yake, ta bishi da idanu kawai dan tasan kota kulashi ba amsawa zai yi ba. Tana nan zaune har after 15mins sai kuma ta tashi tabi bayansa, zaune ta sameshi gefen gado ya jingina da fuskar gadon idanunsa a rufe. Ta yi shiru tana kallonsa kafin taja jikinta ta ƙarasa inda yake a sanyaye, ta zauna gefen gadon ba tare da tace komai ba. Sun ɗauki lokaci mai tsayi a haka kafin ta ƙara matsawa kusa dashi, a hankali ta ɗora kanta akan faffaɗan ƙirjinsa. Ko motsi bai yi ba, ballantana ta saka ran zai kulata, dan ta tabbata ba bacci yake ba. A hankali ta zura hannayenta duk biyun a bayansa ta riƙe shi ƙam sai kuma ta fashe da kuka kamar ƙaramar yarinya. Duk yanda ya so yin shiru kasawa ya yi dan sam baya son jin kukan mace, ya ware idanunsa akanta kafin a hankali ya ɗagota yana kallonta da birkitattun idanunsa ya ce “mene ne?” Cikin kuka ta ce “Doctor bana jin daɗi ne kawai. Dan Allah mu koma US” Numfasawa ya yi kafin ya ce“in sha Allah zamu koma but not now” “amma meyasa?” Ta tambaya da damuwa sosai akan fuskarta. Sai da ya janyeta daga jikinsa ya miƙe tsaye yana gyara rigar jikinsa ya ce“cause i have alot to do” daga haka ya nufi toilet. Da idanu kawai Zahra ta bi shi sai kuma ta dauke kanta, ta zame jikinta ta kwanta akan gadon ta lumshe idanu.. Kusan 3 weeks kenan, abubuwa sun fara shigewa, sai dai wanda aka yiwa shi ne mai manta ba, duk matan sun tare gidan mazajensu har da Siyama wadda take ta faman gigi. Amma har sannan ta kasa daina zancen Nana, kullum bata da magana sai tata, koda yaushe cikin son ganinta take. Sai dai koda wasa bata isa tayi maganarta gaban Abba ba indai ba tana son ɓacin ransa bane, ko sunan Nana baya son yaji an ambata. Duk da ƙasan zuciyarsa bai manta da ita amma sam yaƙi bari mutane su gane hakan. A ɓangaren Maimoon kam kusan kullum cikin kuka take, dan har cikin zuciyarta bata san inda Nanan take ba, sam tunaninta bai bata ta tambayeta inda zata je a ranar. Gashi ta kasa samunta a waya, hasalima kullum ta kira wayar a kashe suke ce mata, wannan yasa har sannan ta kasa sakar jikinta duk yanda Aliyu ke nuna mata so da ƙauna. **** Wasu ƙattin maza ne tsaye su huɗu, sun yi masa ƙawanya kowannesu hannunsa riƙe da bindiga sai zazzare idanu suke yi. Kasancewar fuskarsa a rufe take da wani abu mai kamada buhu ya sanya bai san su wane ba, dan ko numfashi baya samun damar yi. After 5mins aka buɗe ƙofar, nan take duk suka juyo suna kallonsa, cike da girmamawa kuma suka durƙusa a tare suka gaishe shi. Ya gyaɗa musu kai sannan ya ƙarasa gabansa ya janye buhun. Wani irin jan numfashi Junaid ya yi, ya sauke shi a wahalce fuskarsa ta yi jajur dan ba ƙaramin duka yasha ba, gaba ɗaya sun sauya masa kammani. Bai ƙarasa dawowa daidai ba yaji ɗaya daga cikinsu ya cafki maƙogaronsa cikin ƙaraji ya ce “Hey ina yarinyar take?” Kasa magana ya yi dan bai bashi damar haka ba, ganin yana neman rasa rayuwarsa ya sanya ya ce “Stop!” Cak ya tsaya ya kuma zare hannunsa, ya umarce su da su yi baya, kamar jira suke kuwa suka koma bayan. Ya dafashi yana zare face mask ɗinsa da ɗayan hannun, nan take kyakkyawar fuskarsa ta bayyana, gyara tsaiwarsa ya yi kafin a sanyaye ya ce “Ina Nana take?” Ganin yanda ya yi magana a dake ya sanya Junaid haɗiyar yawu, Ya girgiza kansa yana kallonsa cikin tashin hankali ya ce “Nana kuma? Me ya samu Nana? Dan Allah kada ka cemin wani abun ya sameta” Wani irin duka ya kai masa da ƙasan bindiga nan take haƙoransa uku na gaba suka zube, Ya dafe bakin yana jin wata irin azaba na kawo masa ziyara. Bai bari ya wartsake ba ya shaƙe wuyansa wannan karon cikin ɓacin rai ya ce “Ina take? Ina ka kai ta?” Girgiza kai Junaid kawai yake, dan sam bai san abin da yake magana akai ba. Ya dinga wani irin numfashi dakyar kamar zai mutu, sakinsa ya yi yana ɗauke kai ya ce “kar ka bari na sake tambayarka tana ina?” Junaid da azaba ke neman hallaka shi ya fashe da kuka jini na zubowa daga bakinsa ya ce “Wallahi ban san me ku ke magana akai ba, Mene ne ya samu Nana? Dan Allah kada ku cemin wani abun ya sameta” Ɗauke kai Abdusammad ya yi yana murmushi ganin yanda yake neman raina masa hankali. Junaid ya bishi da idanu yana fatan ya sanar dashi abin da ke faruwa. Cikin wani irin zafin nama ya dawo gabansa ya ɗora hancin bindigar hannunsa a tsakiyar kansa yana kallonsa rai ɓace ya ce “ina Nana take?” Girgiza kai kawai Junaid yake, jikinsa sai rawa yake. Ya sake matse kunamar bindigar ya ce “ka faɗa min ko na harbeka, kuma idan na kasheka na kashe banza!” Bakinsa na rawa ya ce “Waam... wallahi, wallahi ban sani ba, ban san Nana ta bar gidan nan ba” Shiru ya yi yana kallonsa da ɗan mamaki, dan ya lura babu ƙarya a maganarsa ya ɗauke bindigar ya miƙewa ɗaya daga cikinsu sannan ya zaro hotunan da suke aljihunsa, buɗesu ya yi ya kara masa a fuska yanda zai gani ya ce “ba kai bane wannan?” Da mamaki Junaid ke kallonsa sai kuma ya kai hannu zai kwace hoton yana faɗin “ina ka samu wadannan hotunan?”wani banzan kallo Abdusammad ya watsa masa sannan ya mayar da hotunan envelope ɗin ya ce“ina Nana take?” Junaid ya sake girgiza kansa a karo na barkatai kafin ya ce“wallahi ban sani ba! Ban san ma bata gida ba, yaushe ta bar gida?” Kujera yaja ya zauna yana kallonsa sosai fuskarsa a haɗe babu alamar wasa ya ce“tell me ina ka haɗu da ita? And kada ka ɓoye min koda abu guda ɗaya ne” Junaid ya dinga kallonsa sai kuma ya sunkuyar da kansa, Da hannu ya yi musu alama dasu dawo suka dawo kansa suka tsaya kowanne yana riƙe da bindigarsa har sannan. A hankali ya daga idanunsa yana kallonsa sai kuma ya sake saukewa, kusan 2mins kafin ya buɗe baki ya fara bashi labarin duk abin da ya faru daga farko har zuwa ƙarshe. Ban da kallonsa babu abin da Abdusammad ke yi, Junaid da ke kuka kamar ransa zai fita ya sake cewa“wallahi ban yi da niyyar cutar da Nana ba, sam bana nufinta da mugun abu” Numfasawa Abdusammad ya yi yana saurarensa har sannan, gaba ɗaya kansa ya kulle, ya lura babu ƙarya a cikin zantukan Junaid. Ya tashi tsaye yana kallonsa ya ce “baka nufinta da sharri amma ka iya ɗaukanta hotuna har kake mata barazana? Sannan baka nufinta da sharri har ka iya cutar da ita duk da cewa ita da zuciya ɗaya taje wajenka? Haka ne baka nufinta da sharri?” Girgiza kai Junaid ya yi yana jin wanda irin ɗaci a ransa ya ce“wallahi bana nufin Nana da sharri, na san ban kyauta ba, kuma ban yi dai-dai ba. Amma nima zugar aboki ce ta yi tasiri akaina, sai bayan dana aikata abun sannan nafara danasani. Wallahi ban taɓa tunanin fitar da hotunan Nana ba, hasalima bayan wanda na tura mata bani da wasu, dan na goge ba zan juri kalla ba. Kawai na so yin amfani da hakan ne wajen sakata ta yi duk mai yiwuwa kar ta ga an rabamu.” Ya sauke numfashi hawaye na gangarowa kan fuskarsa ya ci gaba da faɗin “sai dai hakan bai yi wani amfani ba. Na rasata, gefe guda kuma na haifar mata da baƙin ciki wanda zata dade tana tunawa, a yanzu banida wani buri daya shige naga Nana domin na nemi yafiyarta duk da na san ban cancanci hakan ba. Ta ɗaukeni masoyi na gaskiya ni kuma na cutar da ita, Dan Allah ina zan ga Nanaa?...” Ya ƙare maganar yana sakin wani raunataccen kuka. Shiru Abdusammad ya yi can kuma ya furzar da iska daga bakinsa ya ce“kana son ka ce min baka san inda take ba?” “wallahi ban sani ba. Ban ma san bata gida ba, ni tun ranar data kirani na ƙarshe ana i gobe ɗaurin auren ban sake magana da ita. Wane ya saceta? Dan na san Nana ba zata taɓa guduwa da kanta ba” Junaid ya yi maganar yana kallonsa hankalina tashe. Zura hannayensa ya yi cikin aljihun trousern dake jikinsa kafin ya ce “ta bar gida tun ranar ɗaurin aurenta da safe, kuma babu wanda ya san inda ta tafi. She's afraid akan zaka fitar da hotunanta” Girgiza kai Junaid ya yi yana jin wani matsanancin tausayinta ya ce“Allah sarki Nana, yarinya ce ƙarama. Ba komai take iya ɗauka ba, but wait ya aka yi ka san da maganar hotunan nan? Na tabbata Nana ba zata faɗawa kowa ba” Abdusammad ya ce“me ka ke nufi ba kai ne wanda ka bawa Safwan hotunan ba?” da mamaki Junaid ya ce“ban san shi ba, kuma ban bawa kowa ba. Ban da Nana babu wanda ya san da maganar hotunan nan, taya aka yi suka je hannun wani?” Sai a sannan tunanin Abdusammad ya kawo wajen, a ina Safwan ya samu hotunan Nana? Wane ya bashi?. Ya girgiza kansa sai kuma ya kalli guards ɗin dake tsaye ya ce“ku ci gaba da tsare shi.” cike da girmamawa suka amsa sannan ya juya ya bar ɗakin, Junaid ya bishi da idanu.. **** A hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar bakinta dauke da sallama. Zaune ta hangeshi kan kujera yana operating system ɗin dake gabansa, ta sauke numfashi sai kuma ta ƙarasa ciki a hankali. A kan table ɗin dake gabansa ta ajiye mug ɗin sannan ta zauna gefensa. Ya ɗan kalleta sai kuma ya mayar da kansa ga system ɗin ba tare da ya ce komai ba. Itama Amma shiru ta yi ta sake zuba uban tagumi dan yanzu shi ne kaɗai abin da take yi, Abba ya kai hannunsa ya ɗauka tea ɗin ya fara sipping a hankali yana kallon abin da yake. Sai da kusan mintuna biyar suna shuɗe kafin ta sauke numfashi ta gyara zamanta tana kallonsa sosai ta ce“yallabai” Juyo da idanunsa kanta ya yi yana kallonta ya ce“lafiya dai?” gyaɗa masa kai ta yi sai kuma ta ce“lafiya. Daman ina son nayi maka magana ne akan Nana naga...” Dakatar da ita Abba ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu, lokaci ɗaya ya haɗe ransa kamar wanda ta yiwa zancen mutuwa. Ya kuma ce“idan wannan maganar ce kar ki yimin dan Allah” Amma ta dinga kallonsa jiki a sanyaye lokaci ɗaya hawaye ya cika kurmin idonta ta ce“to idan ban maka ba wa zan yiwa? Kana ganin fa kusan wata daya babu Nana babu labarinta. Ko gidajen rediyo da aka kai report da station ba'a samu wani magana ba. To kuma ka ce ba zan maka maganarta ba?” “To mene ne nawa da zaki yi min magana akanta? Kin ji na ce kina son na ganta? Kin ji nace ina son ta dawo?. To bari kiji ni babu a akan maganarta, sannan I'm warning you karki sake min maganarta! Kar ki sake Rabi'ah” Abba ya yi maganar rai ɓace, ya tashi ya rufe system ɗin gabansa ya fice daga ɗakin ya barta zaune. Amana binsa kawai ta yi da kallo sai kuma ta fashe da wani irin kuka, kenan ba zai nemo mata yarta ba? Babu wanda ya damu da ɓatan Nanar?. Ta sake rushewa da wani sabon kukan tana dunƙule jikinta waje ɗaya. **** A compound ɗinsu Aliyu motar ta yi parking, ya buɗe back seat ya fito yana karewa compound ɗin kallo kafin ya furzar da numfashi ya nufi cikin gidan. Maimoon na zaune a parlon hannunta riƙe da wayarta ya shigo, tana ganinsa ta miƙe tsaye a ɗan firgice ta ce “Welcome uncle” Ganin yanda ransa yake a haɗe babu alamar wasa ya sanya ta sunkuyar da kanta. Ya shigo tsakiyar parlon yana kallonta har sannan, zama ya yi kan sofa ya ce“zauna magana zamu yi” kallonsa ta yi da mamaki ganin yanda ya yi maganar ba'a sigar faɗa ba, dan haka ta koma ta zauna tana kallonsa har sannan. A nutse ya ce “Maimuna” Ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta a sanyaye ta ce “na'am uncle” “zan tambayeki kuma ki tabbata kin sanar dani gaskiya. Kar ki ɓoye min koda abu guda ɗaya da ki ka sani” Gyaɗa masa kai ta yi sai kuma ta ɗago fuskarta da hawaye ya fara zuba ta ce“tam uncle, zan faɗa maka duk abin da na sani wallahi” Jinjina kansa ya yi kafin ya ce“mene ne abin da yasa Nana ta bar gidan nan? Who forced her? Wane yake treating ɗinta da hotunan, nd wane ya san da maganar hotunan har ta fita ta je wajen Safwan?” Wata irin faduwar gaba ce ta ziyarceta. Ta haɗiye yawu da kyar sai kuma ta ce“uncle nima ban san wanda ke treating ɗinta ba, kawai dai na san Nana ta bar gidan nan a saboda tilastawar da Yaya Safwan ya yi mata. I was there da safen ya zo ya nuna mata hotunan ya ce idan har ta yarda aka ɗaura aurensu to sai ya fitar dasu kowa ya gani. Idan kuma ta bar gidan nan to ba zai faɗawa kowa ba, ya ce ta tafi idan aka gama maganar daurin auren sai ta dawo. Shi ne ta ce to saboda tsoron kada a fitar da hotunan da kuma barazanar da Junaid ke mata, yasa ta haƙura ta tafi duk da bata so, ta tafi ba tare da mun tambayeta inda zata je ba, wallahi uncle kullum da Nana nake kwana da ita nake tashi. Na kasa daina tunaninta, ko wane hali take?...” Ta fashe da kuka tana girgiza kanta. Shiru ya yi yana saurarenta can kuma ya sauke numfashi ya ce“it's alright. Kenan baki san wanda ya fitar da hotunan ba?” shiru Maimoon ta yi tana tunanin abin da faɗar gaskiyar tata zai haifar, what idan ya saki Zahra saboda haka? Ko kuma hakan yasa kowa ya tsaneta?. Ta girgiza kanta tana fatan kada gaskiyar ta bayyana, kallonta ya dinga yi sai kuma ya ce “ya dai? Kin san wanda yake treating ɗinta da hotunan?” Girgiza masa kai ta yi har sannan tana hawaye ta ce“ban sani ba uncle, kawai a wajen Junaid na san su” Abdusammad bai sake cewa komai ya miƙe ya fice daga parlon. Ta bishi da kallo sai kuma ta silale ƙasa ta fashe da wani sabon kukan tana jin tausayin Nana. Ko'ina take?. **** Yana fita kai tsaye apartment ɗin Safwan ya nufa, ya ɗan tsaya a bakin ƙofar dan bai taɓa zuwa ba tun da ya tare, can kuma ya murɗa handle ɗin ƙofar bakinsa ɗauke da sallama. Haule ce kawai a parlon ta zuba uban tagumi dan bata ma san ya shigo ba, ya kalleta sai kuma ya sake sallama. Sai a sannan ta ɗago ta kalleshi lokaci ɗaya ta mike tsaye jikinta na ɗan rawa ta ce “in...ina yini?” Amsawa ya yi kafin ya ce “Safwan fa?” Haule ta sake sunkuyar da kanta ta ce“yana sama” Kallon hanyar saman ya yi sai kuma ya sake kallonta ya ce“ok kira min shi” “ai bahida lafiya. Ko tashi ma baya yi” Ta yi maganar a sanyaye. Shiru Abdusammad ya yi can kuma ya nufi saman da sauri, ɗakin daya tabbatar shi ne nasa ya buɗe, Kwance ya hangeshi kan gadon ya lulluɓe jikinsa da ƙaton duvet. Siyama na zaune gefensa taci uban kwalliya sai kallonsa take, tana jin an buɗe kofar ta ɗago a fusace dan ta yi tunanin Haule ce. Sai dai ganin Abdusammad ya sanyata miƙewa a sanyaye ta ce “Barka da zuwa Yaya” Jinjina kansa kawai ya yi dan bai zo dan su gaisa ba, ganin idanunsa na kan Safwan ya sanya ta fice daga ɗakin ta basu waje. Ya karasa gabansa cikin takunsa na isa da taƙama. Ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonsa ya ce “Safwan” A sanyaya janye duvet ɗin daga kansa. Ya kalleshi sai kuma ya tashi zaune da kyar yana cije baki, Abdusammad ya dinga kallonsa ganin yanda ya rame ya lalace. Safwan ya ɗan yi murmushi wanda yafi kama da na ƙarfin hali sannan ya ce “Yaya sannu da zuwa” “Yauwa” Ya amsa a takaice. Shiru ɗakin da ɗauka na wasu mintuna kafin ya numfasa yana kallonsa ya ce “Nazo ne na tambayeka abu, kuma bana son ka ɓoye min komai daga ciki. Idan ka kuskura ka faɗa min abin da ba shi ba wallahi sai ranka ya ɓaci!” Jin yanda ya yi maganar in a serious tone ya sanya Safwan kallonsa, bashi yake kallo ba, dan haka ya sunkuyar da kansa a sanyaye ya ce “in sha Allah Yaya zan faɗa maka gaskiya” “A ina ka samu hotunan Nana? Wane ya baka?” Da wani irin mamaki Safwan ke kallonsaz lokaci ɗaya kuma ya yi kasa da kansa ya ce “but Yaya...” Ɗaga masa hannu Abdusammad ya yi sai kuma ya gyara tsaiwarsa yana kallonsa rai a haɗe ya ce“i'm just asking you, wane ya baka?” Shiru Safwan ya yi yana tunanin abin yi, an ya ya ce Zahra ce? me hakan zai haifar? To amma idan har fadar na nufin dawowar Nana dole ya sanar dashi gaskiya. Dan haka ya numfasa ya ɗago yana kallonsa a sanyaye ya ce “i'm sorry to say Yaya, Zahra ce ta bani!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 38. Da wani irin mabayyanin mamaki Abdusammad ke kallonsa, Ya girgiza kansa kafin ya ce“me kace Safwan?” Safwan kasa haɗa idanu ya yi dashi, muryarsa na rawa ya ce“Zahra ce ta bani Yaya” kusan mutuwar tsaye Abdusammad ya yi a wajen, tuni idanunsa suka kaɗa suka yi jajur, jijiyoyin kansa suka fito sosai. Ganin yanayin da yake ciki ya sanya Safwan tashi tsaye yana kallonsa ya ce “Kayi haƙuri Yaya. Wallahi ban yi niyyar faɗa ba, ban so kowa yaji maganar nan ba. Sai dai son da nakewa Siyama shi ne ya sakani aikata hakan” ya ƙare maganar yana share hawayen dake zubo masa. Furzar da iska ya yi daga bakinsa kafin ya dafashi a hankali ya ce“ita Zahra wane ya bata?” Girgiza kai Safwan ya yi kafin ya ce“ban sani ba wallahi, kawai zuwa ta yi ta kirani da daddare ta bani. Ban san wanda ya bata su ba” Jinjina kai kawai ya yi sannan ya dafa kafaɗarsa ya ce“okay thank you.” Daga haka ya janyeshi gefe ya fice daga ɗakin, da idanu Safwan ya bi shi sai kuma ya sulale a ƙasa ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro. Yana sauka parlon ya ga ta fito daga kitchen, ganin yana shirin fita ya sanya ta ce“Yaya na ɗora maka abinci ba dai tafiya zaka yi ba?” kallo ɗaya ya yi mata, wanda ya sanyata sunkuyar da kai. Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce “No need thanks” Daga haka ya fice daga parlon kamar zai tashi sama. Tafiya ya dinga yi baya ko kallon gabansa, Allah Allah yake ya isa Apartment ɗin su yaje ya samu Zahra. **** Sultan road, Kano state. A tsakiyar compound ɗin gidan motar ta yi parking, Drivern ya buɗe ya fito sannan ya zagayo ya buɗe masa. A hankali ya zuro ƙafafunsa waje, yana ƙarewa gidan nasa kallo. Khadijah ta fito da wani irin gudu tana zuwa ta shige jikinsa tana ƙanƙameshi ta ce “welcome back Dadyyyy!” Rungumeta ya yi yana murmushi ya ce“Thank you Mimina” Ta sake zagaye hannayenta a bayansa a shagwaɓe ta ce“Daddy shi ne baka dawo da wuri ba ko?” Ɗago fuskarta ya yi da hannunsa na dama yana kallonta ya ce“abubuwane suka riƙe ni, kin je Yolan?” girgiza masa kai ta yi kafin ta ce“ai baka dawo ba shiyasa ban je ba. Nanar ma kuma tana nan” Da ɗan mamaki ya ce“really?” Ta gyaɗa masa kai dai-dai sanda Mami ta ƙaraso wajen ta kalleshi tana murmushi ta ce“sannu da zuwa Daddy” murmushin shima ya mayar mata kafin ya ce“Yauwa ya gidan?” “Alhamdulillah ya hanya?" Ta sake tambayarsa. Amsa mata ya yi sai kuma ya mayar da kansa ga Khadijah ya ce“ina ji fasa bikin aka yi data zo?” kafin ta yi magana Mami ta ce“daga zuwanka zata isheka da magana anan, ku shiga ciki mana” tura baki Khadijah ta yi ta ce“to Mami yaushe rabon dana ganshi.” “Muje ciki sai ki bani labarin” Daddy ya yi maganar yana riƙe da hannunta, to kawai ta ce sannan suka nufi cikin gidan. Nana na zaune a parlon ta yi shiru idanunta zube akan tv duk da ba fahimtar abin da ake yi take ba suka shigo, ta tashi da sauri tana gyara mayafin rigar jikinta. Sai da ya zauna kan sofa sannan ta masa sannu da zuwa, ya amsa da murmushi a fuskarsa kafin ya ce “Nana yaushe rabon dana ganki?” Murmushi ta yi tana sunkuyar da kanta. Ya kalli Khadijah ya ce“zo ki ci gaba da bani labarin” kallon Nana ta yi dake tsaye sai kuma ta zauna gefensa ta ce“tam Daddy” Nana ta dinga kallonsu tana tuna sanda take zama da Abba haka tana masa hira a duk sanda ya yi tafiya ya dawo. Ganin kuka na son kwace mata ya sanya ta yi excusing kanta ta bar parlon da sauri. Mami ta bita da idanu cike da tausayinta sai kuma ta kalleshi ta ce“da dai ka fara cin abinci sai ta baka labarin tunda yana da tsayi” Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“ai bana jin yunwa, na sauka a Abuja” to kawai Mami ta ce dan ta san babu abin da zai hana bada labarin kuma. Khadijah ta gyara zamanta ta fara bashi labarin duk abin da ya faru in details, tun daga farko har ƙarshe. Sosai Daddy ya yi mamaki, sannan kuma yaji tausayinta. Ya sauke numfashi yana ganin yanda Khadijah ke hawaye, da kansa ya goge mata hawayen sannan ya ce “Ya isa haka. In sha Allah komai zai zo da sauƙi Mimi” Cikin kuka ta ce“Daddy tausayin Nana nake..gaba ɗaya kamar ba ita ba, ko hira bama yi, kullum sai dai ta yi ta kuka. Kuma ta ce tana son ganin Abbanta da Ammarta, amma tana tsoron ta koma gidan Yaya Safwan da Aunty Zahra su nunawa kowa hotunanta.” Girgiza kai Daddy ya yi ya ce“zata koma in sha Allah, babu abin da zai faru. Kira min ita” to kawai ta ce sannan ta ta miƙe tana shirin barin wajen shima ya tashi ya ce“ko barta. An jima sai muyi magana, let me take a bath” tom kawai ta ce sannan ta nufi saman da sauri. Ya sauke numfashi yana kallon Mami ya ce “But why baki kirani kin faɗa min ba Amina?” “Abun ne babu dadin ji. Shi yasa na kasa kiranka wallahi” girgiza kai Daddy ya yi ya ce“a'a wannan ba hujja bace, yanzu duk inda iyayenta suke suna can suna nemanta. Kuma hankalinsu ba zai taɓa kwanciya ba, sannan kuma Allah kaɗai ya san baƙin cikin da suka shiga na guduwarta. Sam bai kamata abar wannan maganar haka ba” shiru Mami ta yi dan ita ta rasa abin cewa, tabbas ta san iyayenta ba zasu ji daɗi ba, to amma da ace sun ga abin da zai ɗaga musu hankali na har ƙarshen rayuwa gara ace iya wannan suka gani. Daddy bai sake cewa komai ba ya nufi hanyar upstairs. Khadijah na shiga ɗakin ta samu Nana zaune gefen gado ta haɗe kai da gwuiwa sai kuka take a hankali. Jiki a sanyaye ta ƙarasa gabanta ta dafata sannan ta ce“Nana ki daina kuka” kasa ɗago kanta ta yi Khadijah ta zauna gefenta ta jawota jikinta tana kukan itama ta ce“koda da ƙaddararsa a rayuwa, ki ɗauka wannan ita ce ƙaddararki. Kuma komai ya yi farko zai yi ƙarshe, nan bada jimawa ba in sha Allah komai zai shige kamar ba'a yi ba. Dan Allah ki daina kukan nan” Cikin shassheƙar kuka Nana ta ce “Na sani Mimi. Amma ya zan yi? Zuciyata zafi take min kullum, na kasa yarda da cewa ni ce na zama haka. Na kasa yarda cewa ni ce na bar gidanmu saboda tsoron tonan asiri. Na kasa yarda cewa sir Junaid ya cutar dani, mutumin dana bawa yarda fiye da kowa. Mutumin da nake masa kallon wanda zai zama garkuwata, mutumin dana so nayi rayuwar aure dashi...” taja numfashi ta sauke sannan ta ci gaba da faɗin “Ya cutar dani Mimi. Ya ruguzamin farin cikina, koda ace babu wanda ya san da wannan maganar a gidanmu da wane ido zan dinga kallon Yaya Safwan? Kullum zai yi tunanin ni ba mutuniyar kirki bace. Wallahi da zuciya ɗaya naje duba shi, ban yi tunanin zai iya aikata haka gareni ba!” Khadijah ta sake ƙanƙameta tana kuka, ta kasa magana saboda tausayin Nana daya cikata, can dai da kyar ta ce“na sani Nana. Na san ba zaki taɓa aikata irin haka da gangan ba, kuma suma yan gidanku zasu san haka, sai dai kin yi kuskure tun farko, ba'a taɓa bawa namiji yarda, bai kamata ace kin je duba shi dan an ce miki bashi da lafiya ba, wannan ba daidai bane. Koda kuma ya kama dole sai kinje sai ki tafi da wani, amma kin fita ba tare da kowa ya sani ba, sannan kuma kin dawo kin musu ƙarya, iya wannan ya isa Allah ya jarrabeki Nana.” Lumshe idanu Nana ta yi, hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce“sai yanzu nagane hakan, sai yanzu nagane bai kamata na yarda da namiji ba matuƙar ba muharramina ba, ina jin kamar mutuwa zan yi wlh Mimi. Idan na tuna abin da ya yi min sai naji bana son ci gaba da rayuwa, ina ma na mutu na huta kawai...” ta sake fashewa da wani raunataccen kuka. Shiru Khadijah ta yi tana kukan ita ma, after some minutes ta ɗagota tana goge mata hawayen fuskarta ta ce “Kina ji ki daina kukan, kada ciwonki ya tashi. Bari naje na dawo” gyaɗa mata kai kawai Nana tayi, ta tashi ta fice daga ɗakin da sauri, ita kuma Nana ta kwanta kan gadon a hankali tana lumshe idanunta.. **** A fusace ya tura ƙofar parlon ya shiga, babu kowa a ciki sai tv dake aiki. Ya haura sama kai tsaye ya shige ɗakinta, tsaye ya sameta jikin mirror tana shafa mai, Ya saki handle ɗin kofar da ƙarfi wanda ya sanyata juyowa ta kalleshi. “Doctor” Ta ce a sanyaye, ganin yanda yake kallonta ya sanya ta sunkuyar da kanta. Haka kawai taji gabanta na faduwa, ya ƙaraso tsakiyar ɗakin yana ci gaba da kallonta cikin wata murya mai nuna zallar ɓacin ran da yake ciki ya fara cewa “ashe daman zaki iya haka Zahra? Ashe zaki iya cutar da Nana ban sani ba?” Da sauri ta ɗago kanta, lokaci ɗaya kuma ta shiga girgiza masa kai da hannayenta ta ce “wallahi a'a ba zan iya ba doctor, ba zan iya ba, Nana kamar...” Tsawa ya daka mata wadda ta tilasta ta yin shiru, Ya ɗan kalli gefensa na dama zuciyarsa cikeda tarin ƙunci da bakin ciki, sai kuma ya sake takowa har gabanta yana kallonta cikin ido ya ce“bana son na sake jin wata magana daga bakinki. Kin bani mamaki, koda wasa ban taɓa tunanin zaki iya aikata haka ba Zahra! Ban yi tunani ba, yanda yarinyar ta ɗaukeki tamkar ƴar uwarta wadda take iya fadawa sirrinta ashe ke ba haka ki ka ɗauketa ba. Har zaki iya fitar da hotunan da ki ka san zasu iya lalata mata rayuwa su ɓata mata suna a idon kowa, kin ji kunya!” Zahra kasa cewa komai ta yi sai kuka da take kamar ranta zai fita, ta durƙushe a ƙasa tana wani irin kuka mai kunji ta ce “na tuba doctor, wallahi na tuba ba zan sake ba. Ni kaina banso na fitar da hotunan nan ba, domin kamar amana ne Nana ta bani saboda ta yarda dani. Tana ganin ba zan taba faɗawa kowa ba, sai dai...” ta yi shiru saboda kukan daya ci ƙarfinta. “Sai dai me?” Ya daka mata wata irin tsawa wadda ta sanyata gigita. Girgiza kanta ta yi still crying ta ce “Idan ban yi haka ba Siyama ba zata samu Safwan ba, ba zai aureta ba! Shiyasa nayi haka saboda na dakatar da aurensu.” Girgiza kansa ya yi yana jin wani irin haushinta kamar ya shaƙeta ya ce“kenan saboda son zuciyarki ki ka aikata haka? Saboda ƴar uwarki ta aureshi?” Shiru ta yi tana kukanta. Ya shiga zagaye ɗakin hannunsa goye a bayansa, can kuma ya tsaya cak yana kallonta daga inda yake ya ce “Kin cutar da ita shi kuma Allah ya saka mata. Kin hanata auren mijin ƴar uwarki ta kuma auri mijinki. Babu buƙatar a yi miki wani hukunci, iya wannan kaɗai ya isheki ki gane irin abin da ki ka aikata. Ya isheki ki fuskanci Allah na kishin bawansa, tun da kin cutar da ita ne ba akan laifinta ba!” Sake durƙushewa Zahra ta yi tana ƙara sautin kukanta, tabbas Allah ya nuna mata ishara. Ya kuma sakawa Nana tun a duniya, ta miƙe da kyar tana ci gaba da kuka ta nufi inda yake. Da hannu ya dakatar da ita, idanunsa kamar garwashi saboda jan da suka yi ya ce “kar ki kuskura! Stay away from me!” Cikin kuka ta ce“dan Allah ka yi haƙuri, ka yafe min wallahi ba zan sake ba. Na sani na cutar da Nana kuma zan nemi yafiyarta, dan Allah doctor ka yi haƙuri kada ka ce zaka gujeni” Cije laɓɓansa ya yi yana jin da ace duka ɗabi'arsa ce to babu abin da zai hana shi dukan Zahra. Ya ja dogon numfashi ya sauke yana ƙoƙarin saita kansa ya ce “ni ki ka yiwa laifi?” Girgiza masa kai ta yi, ya gyaɗa kansa sannan ya ci gaba da fad'in “to akan me zaki nemi yafiyata?.” Shiru Zahra ta yi tana kallonsa hawaye sai zuba yake daga fuskarta kamar an buɗe famfo. Ya tako kusa da ita har tana jin sautin fitar numfashinsa ya ce “Yarinya ce ƙarama. Yarinyar da bata gama sanin ciwon kanta ba, amma ke da girmanki da kuma hankalinki ki ka cuceta, ki ka mata zamba cikin aminci. Ki sani kar ki ɗauka iya hukuncin kenan, idan har Nana bata yafe miki ba to wallahi tallahi kin ji har na rantse babu ni babu ke!” Manage this pls, I'm not feeling well🙏. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 39. Ya ƙare maganar yana jefa mata wani mugun kallo, sunkuyar da kai ta yi tana shessheƙar kuka. Ya ratsa ta gefenta ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama, da idanu Zahra ta bishi sai kuma ta sulale a ƙasa ta rufe bakinta da hannunta tana kuka a hankali. Yana fita apartment ɗin Hajiya Babba ya nufa. Koda ya shiga bai samu kowa a parlon ba, dan haka ya haye sama. A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar, ya hangeta zaune gefen gado tana jan cazbaha a hankali. Numfasawa ya yi sannan ya karasa ciki, Hajiya Babba ta dinga kallonsa har ya zauna a gefenta. Ganin bai ce komai ba ya sanya ta dafa kansa ta ce “Lafiya dai?” Madadin ya amsa mata sai kawai taga ya shige jikinta, ya dinga sauke ajiyar zuciya a hankali. Ajiyar zuciyar ita ma ta sauke kafin ta sanya hannunta cikin sumar kansa ta fara hargitsata a hankali. Numfashi ya dinga saukewa yana jin wata nutsuwa ta musamman na saukar masa, ya dinga jin duk ƙunci da damuwar zuciyarsa na narkewa. Sun ɗauki mintuna masu tsayi a haka kafin ta ɗago kansa tana faɗin “mene ne?” Girgiza mata kai ya yi dan ya san bashi da hurumin sanar da ita abin da ke damunsa yanzu, dan shi ne wanda ya jawo komai. Ya sauke numfashi kafin ya ce “bakomai Hajiya” Kallonsa ta dinga yi sanin ƙarya ba ɗabi'arsa bace yasa ta girgiza kanta ta ce“Abdusammad kenan. Na san halinka fiye da kowa, ko ka manta ni na haifeka? Fuskarka ta nuna akwai damuwa a tare da kai, faɗa min mene ne.” Ta ƙare maganar tana riƙe hannunsa na dama. Murmusawa ya yi cike da son kawar da zancen ya ce“Hajiya babu komai fa, kawai ina tunani ne akan Nana. Abba ya damu da ita fiye da ƙima, kawai yana sharewa ne, so ina son sanin inda take naje na dawo da ita gida.” Zazzafan numfashi ta furzar kafin ta ce “nima da tunanin yarinyar nan nake kwana nake tashi. Duk da ta ɓata mana sunan dangi hakan ba zai sa mu fasa nemanta ba, na tabbata yarinta da rashin jin magana sune suka yi tasiri a tare da ita har taje ta aikata abin da tayi.” Shiru Abdusammad ya yi dan shi ya san abin da ya faru kuma bashi da niyyar sanar da kowa yanzu har sai sanda yarinyar ta dawo. Dan haka ya jinjina kansa ya ce “nima i think so.” ya sauke ajiyar zuciya yana miƙewa tsaye ya ce“Allah ya kyauta” Da Amin ta amsa tana kallonsa ganin ya tashin ta ce“tafiya zaka yi?” Gyaɗa kansa ya yi ya ce“Eh. Zan je wajen Aliyu ne” “Tam ka gaishe shi” ta ce tana ci gaba da jan cazbahar hannunta. **** Da daddare suna zaune a parlon bayan sun gama cin abinci Daddy ya kalli Khadijah da ke kwance jikin Mami ya ce“Mimi je ki kira min Nana” to kawai ta ce sannan ta tashi tana gyara zaman hular sanyin kanta ta nufi upstairs. Miƙewa Adeel ya yi yana danna wayarsa, Daddy ya kalleshi ya ce “son idan Allah ya kaimu gobe ka fita da wuri zaka yankar mana ticket” Zare airpode ɗin kunnensa ya yi yana kallonsa ya ce“Daddy wata tafiyar kuma?” Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“a'a zan je Yola ne” “But ai da ka bari ka huta ko zuwa next week ne” Adeel ya yi maganar a dame. Daddy ya ce“No dole naje gobe, ba abun da za'a ci gaba da jira bane” Adeel bai ji daɗi ba ganin Daddy na son stressing kansa. amma sanin bai isa ya hana shi ba ya sanya ya ɗaga kafaɗa ya ce “anyway. Allah ya kaimu lafiya” Bai kuma tsaya jiran amsarsa ba ya bar parlon. Mami ta bishi da kallo sai kuma ta mai da Idanunta kan Daddyn ta ce“Nima dai har zance ka bari sai next week ɗin” babu yabo babu fallasa ya kalleta ya ce“sai a ci gaba da zama da yarinya bayan ba'a san matsayin da take ba? Iyayenta na faman nemanta” Girgiza kai Mami ta yi. Ya ce“to kin ga dole ne na mayar da ita ga iyayenta, da ina nan ma ba zan bari ta yi wannan satikan ba” Mami ta numfasa ta ce“Tom shikenan Allah ya kaimu goben lafiya” Dai-dai nan suka dawo parlon. Khadijah ce a gaba sai Nana dake biye da ita, ta zauna a ƙasa tana gyara zaman hijabin jikinta, Girgiza kai Daddy ya yi ya ce “No! No! Tashi a ƙasa” A sanyaye ta tashi ta zauna kan kujera idanunta a ƙasa. Khadijah ta koma kusa da shi ta zauna tana jingina da jikinsa wanda ya zame mata dabi'a. Numfasawa Daddy ya yi kafin ya mai da hankalinsa kan Nanar ya fara magana a nutse. “Nana na kira ki saboda na miki magana akan abin da Khadijah ta faɗa min ɗazu. Garin ya aka yi haka ta faru Khadijah? Mene ya saka ki ka yarda da namiji? Baki san illar dake cikin hakan ba?” Tuni hawaye suka fara zuba kan kyakkyawar fuskarta. Ta sanya hannunta ta goge cikin shessheƙar kukan ta ce “Tsautsayi Daddy. Wallahi ban yi tunanin zai min haka ba, kawai na san ina son shi, kuma ina son na aure shi. Amma ban yi tunanin zai iya cutar dani ba, haka ita ma Aunty Zahra ban yi tunanin zata yi amfani dasu wajen cutar dani ba. Na san ban aikata abin da ya dace ba, amma ni na ɗauka hakan da nayi shi ne daidai.” Ta yi shiru kuka na kwace mata. Girgiza kai Daddy ya yi still looking at her ya ce“ya isa haka. Daina kuka, duk abin da ya faru ya riga da ya faru, ƙaddara ce wadda ba'a guje mata. Duk da kin yi wawta da yarinta amma wannan ba zai zama matsala ba, in sha Allah gobe zan mayar dake gida!” Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi, sai kuma ta fara girgiza kai tana kuka ta ce“a'a Daddy, dan Allah ka yi haƙuri. Tsoro nake ji, wallahi tsoro nake ji, Yaya Safwan yace sai ya faɗawa kowa idan har na dawo” ta ƙare maganar tana fashewa da kuka. Tashi Mami ta yi ta koma kujerar da take zaune ta riƙeta, Nana ta faɗa jikinta tana sakin wani marayan kuka. Shiru Daddy ya yi yana kallonsu can kuma ya ce“it's enough. In sha Allah gobe zan mayar dake, kuma babu abin da zai faru, ni zan fahimtar dasu” Cikin kuka Khadijah ta ce“Daddy idan kuma kowa ya ga hotunan fa?” “To ai dole sai an gani ko nan kusa ko kuma nesa, idan haka ne kin ga ɓoyewar bashi da wani amfani” Shiru Khadijah ta yi tana sharar hawaye. Ya mai da kallonsa ga Nana ya ce“Zo nan” sakinta Mami ta yi ta miƙe a sanyaye ta koma inda yake, gefensa na hagu ta zauna ya dafata cikin son kwantar mata da hankali ya ce “Babu abin da zai faru kin ji. Ba zan bari kowa ya taɓa ki ba, ba zan bari su ji haushin ki ba. Amma ai na san kina son ganin Mamarki da Abbanki ko?” A sanyaye ta gyaɗa masa kai sai kuma ta ce“eh Daddy Ina son na gansu, amma ina tsoron Yaya Safwan da Aunty zahra.” Murmushi Daddy ya yi ya ce“to ki daina tsoron kowa. In sha Allah komai ya zo ƙarshe, zamu zauna dasu gobe a san yanda za'a yi kinji” gyada masa kai ta yi, Ya sanya hannunsa ya share mata hawayenta sannan ya ce“tashi ki je ki kwanta” Toh kawai ta ce sannan ta tashi a sanyaye ta haye. Khadijah ta miƙe tana shirin bin bayanta ya ce“ku kwanta da wuri saboda da wuri nake son mu tafi yanda zamu tadda kowa a gida” ta amsa masa da toh sannan tabi bayansa. Sai da suka bar wajen sannan ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Mami ya ce“ta bani tausayi, she's still young girl” gyaɗa masa kai ta yi sannan ta ce“sosai. Dan ko Mimi ta girmeta, she's just 17 fa” Daddy ya girgiza kansa ya ce“shiyasa, sam bata da wayo” Jinjina kai Mami ta yi ta ce“Eh nima na lura da haka.” Koda suka shiga ɗakin zama suka yi suka ci gaba da rera kukansu a tare. Sai da suka yi mai isarsu sannan suka yi shiru dan kansu, Khadijah ta ce“Daddy ya ce mu kwanta da wuri yanda zamu iya tashi da wuri” toh kawai Nana ta ce a sanyaye sannan ta kwanta a hankali tana lumshe ido. Khadijah ma kwanciyar ta yi a ɗaya side ɗin dan daman sun gama shirin kwanciyar ta ja duvet ta rufe jikinta. **** Da idanu ya dinga kallonsu sai kuma ya ɗauke kai, Aliyu ya kalli Maimoon dake tsaye a jikinsa ya ce“zaki iya shiga gidan?” gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh Yaya” Ya saketa sannan ya ce“Tom jeki ki huta kafin nazo” ta gaishe da Abdusammad ya amsa sama-sama sannan ta shige gidan. Sai da yaga ta bar wajen sannan ya gyara tsaiwarsa yana ƙarewa compound ɗin kallo iska mai daɗi sai kaɗawa take a hankali, Ya ɗan yi jim sai kuma ya kalli Aliyu wanda ke ta murmushi fuskarsa kamar gonar auduga, Ɗan mitsi-mitsi ya yi da idanu ya ce “Lafiyarka dai?” Madadin ya bashi amsa sai kawai ya ga ya ruƙunƙumeshi yana dariya, Abdusammad ya riƙe hannunsa ya ce“A'a wallahi nutsu, kar ka illatani” ɗago kansa yayi yana murmushi ya ce “Buddy guess what?” Ɗan juya idanunsa ya yi sai kuma ya ce“ni ban gane ba, kawai ka faɗa min” Aliyu ya fara jan fingers ɗinsa kamar mace ya ce“soon zan zama father” Ware idanu Abdusammad ya yi, lokaci ɗaya kuma ya saki wani kyakkyawan murmushi wanda ya daɗe bai yi irinsa ba. Ya kai masa duka yana fadin “amma kai akwai ɗan iska wallahi, har yaushe aka kawo maka yarinyar har ka mata ciki?” Harararsa Aliyu ya yi kafin ya ce“to mene ne a ciki? Ba dai matata bace?” Ɗauke kai Abdusammad ya yi ya ce“ɗan iska kawai. Daman ni tun da naga kana wani maƙalƙale mata baka ko fita waje na san ba zaka shuka abin arziki ba. Kawai ka saka yarinya ta rainaka” Tuntsirewa da dariya Aliyu ya yi sai kuma ya ce“nima kenan, kai naga yanda zaka yi” Haɗe rai Abdusammad ya yi kamar bashi ba ya ce“kamarya ni? Da aurena da mutunci na” Dariya Aliyu ya yi ya ce“kai mana. Allah ne kaɗai ya san abin da zaka yiwa ƴar rainon taka idan an kawota, wa yaga show” Wani mugun kallo ya watsa masa, ya ƙara masa da harara sannan ya yi tsaki ya ce”aikin banza. Kai daɗina da kai baka da hankali wani lokacin” Ban da dariya babu abin da Aliyu ke yi, Ya dafe cikinsa sannan ya ce“daga faɗar gaskiya? Allah ya nuna mana to” wani dogon tsaki yaja ya yi gaba dan ba zai ma iya zama a wajensa ba ya ce“Allah ya baka sauƙi” Aliyu ya amsa da Amin yana dariya har sannan. Ganin ya yi gaba abin sa yasa shima ya juya ya nufi cikin gidansa. Ya yi nisa yaja ya tsaya maganar Aliyun na masa yawo a ƙwaƙwalwa, yaja wani sabon tsakin yana ayyana ta inda zai iya wata mu'amala da Nana, yarinyar da yake ma kallon yarsa. Saurin kawar da tunanin ya yi a fili ya ce “Astgfirullah” Sannan ya yi gaba yana sake girgiza kansa. **** Washegari da sassafe around 7:00am suka gama shiri cikin wata atampa glitter da Mami ta ɗinka musu. Ko powder babu wadda ta shafa a cikinsu dan duk jikinsu a sanyaye yake, suka fito parlon suna jiran Daddy. After 5mins ya fito yana gyara zaman babbar rigar jikinsa Mami na biye dashi da kuma Adeel, Tsaye ya samesu suka gaisheshi ya amsa cike da fara'a sannan ya maida idanunsa kan Mami ya ce“to sai mun dawo ko” murmusawa ta yi ta ce“Allah ya dawo daku lafiya.” sannan ta ƙarasa inda suke tsaye ta dafa Nana ta ce“daughter sai yaushe?” rungumeta Nana ta yi ta fara kuka ƙasa-ƙasa. Mami ta ɗagota tana goge mata hawayen ta ce“haba dai kuka, shikenan kuje Allah ya tsare.” Cikin shassheƙar kuka ta ce“Mami yaushe zaki zo?” murmushi Mami ta yi kafin ta ce“nan kusa in sha Allah kinji.” Toh kawai Nana ta ce sannan Daddy ya ce“to idan kun gama muje kun san jirgi baya jira” sakinta Mami ta yi tana musu Allah ya tsare, Khadijah ta rungumeta ta ce“sai mun dawo Mami” Allah ya tsare ta ce sannan tabi bayansu Daddy da suka yi waje. Adeel ne yaja motar kai tsaye kuma filin tashin jirage na Malam Aminu Kano suka nufa, basu daɗe ba kuma jirginsu ya tashi zuwa Yola. 08106608363, Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 40. Tafiyar awa ɗaya ce ta kawo su Adamawa, jirginsu ya sauka a filin tashin jirage na Yola international airport. Bayan sun fito daga airport suka shiga mota dan already Daddy ya yiwa wani friend ɗinsa magana akan zuwansu, kai tsaye kuma M-Shuwa Estate suka nufa. Tun da suka fara tafiya babu wanda ya ce komai, Nana ta yi nisa cikin tunani, gabanta sai faɗuwa yake. Tsoronta ɗaya abin da zai faru idan ta koma gidan, Khadijah dake danna wayarta a hankali ta dinga kallonta time to time a haka har suka ƙarasa estate ɗin. Sai da suka tsaya a bakin gate ɗin wajen securities kafin suka basu damar shiga da motar ciki. A compound ɗin su Nana suka yi parking, saboda mutanen da suka hango tsaye, Nana ta ɗan waro idanunta tana son ganin su wane a tsaye, sai dai kai tsaye ba zata ce gasu ba saboda sun juya baya. Daddy ya sauke ajiyar zuciya sannan ya buɗe motar ya fito, Sai a sannan Khadijah ta kalleta ganin bata da shirin sauka ta ce“Nana mun zo fa” numfasawa ta yi sai kuma ta gyaɗa mata kai. Khadijah ta buɗe side ɗinta ta fito tana gyara zaman mayafin jikinta, A sanyaye Nana ta buɗe motar ta fito tana riƙe da wayarta. Ganin Daddy ya yi gaba ya sanya ta kalli Khadijah kamar zata yi magana sai kuma ta yi shiru, Daddy kuwa wajensu Abba ya ƙarasa da suke tsaye shi da Papa da Abdusammad. Sallama ya yi musu suka amsa sannan suka gaisa fuskarsa a sake ya ce “Yallabai wajenka nazo” ya yi maganar yana kallon Abba dan ya riga da ya san shi. Murmusawa shima Abba ya yi ya ce“Tom Alhaji muje ciki” jinjina kansa ya yi sannan ya juya ganin yanda suka cake ya ce “Ku tawo mana” Maganar ta sanya hankalinsu kai wa inda su Nana ke tsaye, cikin rashin sa'a idanunta ya sauka cikin na Abba. Wani irin abu taji ya zo mata wuya, ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa. Abba ya haɗiye wani miyau mai ɗaci sannan ya kalli Daddyn Khadijah murya a shaƙe ya ce “lafiya dai Alhaji?” Dafa shi Daddy ya yi ya ce“idan mun shiga ciki zaka ji” shiru kawai Abba ya yi yana kallonsa, Jiki a sanyaye suka ƙaraso wajen, barin Nana data sunkuyar da kanta bakinta na rawa ta kalli Papa ta gaishe shi. Da murmushi a fuskarsa ya amsa, dan har ga Allah yaji daɗin ganinta, Ta saci kallon Abdusammad wanda ya ɗauke kai kamar bai ganta ba, a hankali ta sunkuyar da idanunta sannan ta gaishe shi. Ba zaka taɓa cewa dashi take ba, dan ko motsi bai yi ba ballantana ta saka ran yaji abin da tace. Ta ɗan yi shiru tana jin hawaye na neman zubowa kan fuskarta, ta kalli Abba wanda ke kallonta sai kawai ta tafi zata shige jikinsa. Ɗaga mata hannu ya yi wanda ya sanyata dakatawa, cikin kakkausar murya ya ce “Kar ki kuskura!” Ya faɗi maganar yana nufar cikin gida kamr zai tashi sama. Daddy ya sauke numfashi sai kuma ya kalli Papa da Abdusammad ya ce“muje ciki kuma dan Allah” toh Papa ya ce masa, Abdusammad kuwa girgiza kansa ya yi ya ce“sorry ku je kawai” Daddy ya ɗan murmusa kafin ya ce“Da ka yi haƙuri mun shiga cikin” ya buɗe baki zai yi magana Papa ya riƙe hannunsa ya ce“muje” daga haka suka nufi cikin gidan. Daddy ya juyo yana kallonsu ganin Nana sai kuka take ya dafata cikin son kwantar mata da hankali ya ce“kar ki damu komai zai shige kin ji." Gyaɗa kanta kawai ta yi ba tare da ta daina kukan ba, Ya kalli Khadijah ya ce“ku samu guri ku zauna ko ku koma mota kafin mu gama” toh kawai ta ce masa sannan ta riƙe hannun Nana. Ya juya ya nufi gidan shima. Kalle-kalle ta fara yi can ta hango wata bukka ta zamani nesa dasu kaɗan, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ja hannun Nana suka ƙarasa wajen. Zama ta yi sannan ta saki hannunta, Nana ta ja kujera ta zauna ta ɗora kanta kan table ɗin wajen ta ci gaba da kukanta a hankali. **** A parlourn kuwa Abba ne zaune kan sofa sai Abdusammad a kusa da shi, ɗaya kujerar kuma Papa ne zaune. Daddy kuma na zaune kujerar dake facing ta Abba idanunsa maƙale a kansa ya ci gaba da fad'in “Kamar yanda na faɗa dole sai mun yi haƙuri. Saboda mu iyayene, babu alfanu cikin fushi da yara. Yanzu idan ka yi fushi da ita Alhaji hakan ba zai haifar mata da ɗa mai ido ba, ba zata shiryu ba, sai dai ma ta sake lalacewa. Domin fushin iyaye akan ya'ya masifa ce babba, kome suka aikata dole ne mu yi haƙuri. Kuma ba'a cewa an sallama ɗa, idan ka sallamata ka nunawa Allah ka zaga akan amanar daya baka, ka butulce masa. Na san kuma ba zaka so kayi hakan ba, Laifi ne ta riga da ta aikata shi, wanda idan aka biyo abun tun daga farko ma bata da wani laifi, ƙaddara ce, duk abin da ta yi yarinta ce. Laifin na yaron daya ɗauketa hotunan ne” Daddy ya yi shiru yana kallon Abba wanda ya yi ƙasa da kansa yana jin zuciyarsa na tafasa. Ganin halin da yake ciki ya sanya Daddy numfasawa kafin ya ci gaba da faɗin “Dan Allah Alhaji Ahmad kayi haƙuri. Ka yafe mata, ka ɗauki komai a matsayin ƙaddara, kada ka ce zaka riƙeta a ranka. Yarinya ce ƙarama, har yanzu bata kai munzalin hankali ba. Ballantana ace tana sane ta aikata abin da tayi. Maganar aure kuma ka aura mata kowane, tun da daman ita ba ƙi ta yi ba, tana gudun abin da zai je ya dawo ne, kuma har yanzu bata san kun ga hotunan ba. Da nasan ba zata taɓa biyoni ba, bana gari sanda ta zo, da wallahi a ranar zan dawo muku da ita.” Ya ƙare maganar a tausashe. Girgiza kai Papa ya yi cikin mutuntawa ya ce“haka ne Alhaji, wannan haka yake. Haƙuri shi ne ribar zaman duniya, kuma dole mu yi hakuri da wawtar ya'yanmu. Kamar yanda mu ma iyayenmu suka yi haƙuri da tamu, Babu wnada ya shige ƙaddara ta faɗa masa, komai girmansa komai ƙanƙantarsa. Ni wallahi tausayi ma yarinyar ke bani, Allah ya jarrabeta da ƙananun shekaru, sauran ƴan uwanta duk suna zaune hankali kwance.” Daddy ya ce“Allah sarki. Daman haka Allah ke ikonsa, wani bawan sai ya yi ta jarrabashi daga wannan sai wannan, wani kuma kamar bai zo duniya dan wahala ba. Amma ubangiji da kansa yake faɗa gwargwadon jarrabawarka, gwargwadon kusancinka gareshi. Kaga ashe jarrabawa na tafiya da imanin mutum ne” Jinjina kai Papa ya yi ya ce“Allah mai girma, Allah ya bamu ikon cinye jarrabobinmu” da Amin suka amsa a tare sai kuma parlon ya dauki shiru. Abdusammad hankalinsa na ka Abba wanda har sannan bai ce komai ba, ganin kamar jiransa ake ya sanya ya ce“Abba dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba laifinta bane, idan ma tana da laifi to bai shige na kula yaron data san ba ɗan danginta bane. Kuma nayi magana dashi yaron kansa, ya tabbatar min da cewa shi ne ya sanya aka ɗaukesu hotunan saboda ya dinga mata barazana ta yarda ta aureshi, amma bai ce mata ta gudu ba. Batun guduwarta nada alaƙa da Safwan ne da Zahra. They're behind it” Ya yi shiru yana jin ɗaci a kasan ransa. Da mamaki suka dinga kallonsa, Har Abba sai da ya kalleshi. Papa ya ce“ka yi mana bayani yanda zamu fahimta Abdusammad” numfasawa ya yi sannan ya basu labarin duk abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe. Papa ya dinga girgiza kansa cike da mamaki da al'ajabi, Shi kansa Daddy sai da abun ya taɓa shi. Ya kalli Abba wanda ya yi shiru har sannan ya ce “Ka gani Alhaji. Gaba ɗaya ma ba laifinta bane, yaudararta aka yi. Dan haka dan Allah ka yafe mata” Ɗago kansa ya yi ya kalleshi. Sai kuma a hankali ya zare glasses ɗin dake idanunsa, ya sanya hanky ya goge hawayen dake maƙale cikin kurmin idonsa. Ya yi gyara murya kafin ya ce “Ni daman ban riƙeta ba. Ban kuma taɓa tunanin aibatata ba, kawai tana bani tausayi ne, yanda rabuwarta ta lalace da ƙananun shekaru. Amma tun da an yi haka babu komai, Allah ya yafe mana gaba ɗaya, ya rabamu da mummunar ƙaddara.” Da Amin suka amsa masa sannan Abdusammad ya ce“Abba babu abin da ya sameta fa. Ba wai ya lalata bane ko wani abu, kawai dai ya ɗauketa hotunan ne, ka daina damun kan ka dan Allah.” Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalleshi a sanyaye ya ce“da gaske?” gyaɗa masa kai Abdusammad ya yi. Ya zame jikinsa daga kan sofar ya durƙusa ya yi sudujusshukur ya godewa Allah sannan ya tashi ya koma ya zauna. Daddy ya yi murmushi ya ce“mun gode sosai Alhaji, Allah ya ƙara girma” girgiza kai Abba ya yi ya ce“a'a kai ne ka cancanci mu yiwa godiya. Ka tunasar dani abin da na manta, sannan ka tawo tun daga wani gari dan kazo ka gyara ɓarna. Allah ya biya ka da gidan aljanna” Da Amin suka amsa sannan ya sake cewa“To yanzu ya maganar auren nata? Za'a bari ta huta ne ko kuwa akwai wanda zai aureta yanzu?” murmushi Abba ya yi ya girgiza kansa ya ce“ai an ɗaura mata auren tun ranar” washe baki Daddy ya yi ya ce“masha Allahu. Wane mijin?” da hannu Abba ya nuna masa Abdusammad wanda ya yi shiru ya ce“shi ne ya aureta tun a ranar” murmushin jin daɗi Daddy ya yi yana kallonsa ya ce“naji daɗi sosai wallahi, Allah ya sanya albarka ya bada zaman lafiya.” Suka amsa da Amin sannan ya miƙe yana gyara rigar jikinsa ya ce”to Alhaji ni zan shige a ƙara haƙuri” miƙewa duk suka yi Abba ya ce“da sauri haka? Ba zaka yini ba?” girgiza kai Daddy ya yi ya ce“da wuri nake so na koma ne. Jiya na dawo ƙasar” Papa ya ce“Allah sarki. To Allah ya bada lada, mun gode sosai” ya amsa da Amin sannan suka fito daga parlon a tare. Ganin bai gansu ba ya sanya ya kira wayar Khadijah, bayan ta ɗaga ya ce ta fito dan haka ta taso tana riƙe da hannu Nana suka dawo wajen. Daddy ya dafa Nana ganin yanda idanunta suka kumbura ya ce“Mamana ya isa haka kukan. Komai ya shige kinji.” da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi sai kuma ta kalli Abbanta, ganin ita yake kallo yana murmushi ya sanya ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa tana ƙanƙameshi. Abba ya rungumeta tsaf a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Ita kuwa sai faman kuka take, Murmushi duka suka yi ban da Abdusammad wanda har sannan fuskarsa babu yabo babu fallasa. Daddy na murmushi ya ce“to ba zaki zo muyi sallama ba?” sakin Abba ta yi ta dawo wajensa kanta a ƙasa. Ya ce“Allah ya yi albarka ya kiyaye gaba kin ji.” a sanyaye ta amsa da Amin. Ya sake musu sallama sannan ya kalli Khadijah ya ce“muje ko” da sauri Nana ta kalleshi sai kuma ta ce“Daddy ba zata zauna anan ba?” Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“a'a Nana. Idan an kwana biyu sai ta zo” bata ji daɗi ba, kuma ba dan taso ba suka yi sallama da Khadijahn ta rakasu har mota sannan ta dawo gurin Abbanta. Sam taƙi yarda da bar jikinsa, Papa ne ya kalleta yana murmushi ya ce“to ni bari na shige office, kije Apartment ɗin Hajiya Babba kin ji” to kawai ta ce ya juya ya bar wajen sannan suka nufi gida ita da Abba.. Amma na zaune gefen gadonta ta rufe fuskarta da hannunta tana tunani wanda ya zamar mata dabi'a taji an bude ƙofar ɗakin. Da sauri ta ɗago kanta, sai dai wadda ta gani ya sanya ta miƙe tsaye zumbur bakinta na rawa ta shiga nunata da yatsa tana cewa “Naaana. Nana?! Ke ce?" Da gudu ta tafi ta rungumeta. A tare suka fashe da kuka, Amma ta dinga taɓa ta kamar zata zare ta ce “Nana. Nana ke ce? Ina ki ka tafi ki ka bar mu? Me yasa Nana?” Kasa bata amsa ta yi sai sake ƙanƙameta da take. Abba ya shigo ɗakin yana kallonsu, bai ƙoƙarin hana su ba ya ɗauki abin da ya zo ɗauka sannan ya fice daga ɗakin ya nufi apartment ɗin Hajiya Babba dan sanar da ita.. **** Is been a days da dawowar Nana gida, lokacin kowa na estate ɗin ya san ta dawo, Safwan har sannan bai iya zuwa ya sameta ba duk da ya ji sauƙi, Zahra kuwa idan hankalinta ya yi dubu to ya tashi, dan tsoronta ɗaya ranar da za'a ce Nana ta shigo gidan a matsayin matar Abdusammad. Bangaren Nana kuwa babu abin da ke damunta, sai dai koda yaushe tana ɗakinta dan tun bayan sanar da ita da aka yi cewa Safwan ya fitar da hotunanta bata sake samun sakewa ba. Kunyar kowa take ji, Idan har ka ganta a waje to sai dai apartment ɗin Hajiya Babba idan Atta ta kirata dan har sannan taƙi komawa Njomboli. Yau ma kamar kullum tana zaune a daƙinta tana game aka buɗe ƙofar ɗakin, bata ɗago kanta ba amma ta katse game ɗin tana jiran abin da Ammar zata ce. Jin an yi shiru ya sanya ta ɗago kanta a hankali, idanunta ya sauka akan Zahra dake tsaye bakin ƙofar ɗakin. Sauke idanu ta yi ƙasa, Zahra ta numfasa sannan ta shigo ɗakin ta mayar da kofar da rufe. Ƙarasowa ciki ta yi ta zauna gefen gadon tana kallon Nana. Ita kuwa ɗauke kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta a hankali, Sun ɗauki mintuna a haka kafin Zahra ta yi ƙarfin halin cewa “Nana” Kamar ba zata amsa ba. Sai kuma ta tuna da abin da Amma ta ce mata, dan haka ta amsa ciki-ciki, hakan bai damu Zahra ba dan bama ta yi tunanin zata amsa ba ɗin. Ta numfasa sannan ta ce“na san ba lallai bane abin da zan nema amma ya zama dole na faɗa miki koda ba zaki yarda ba. Dan Allah Nana...” “Babu komai Aunty, Ni ban riƙe ki ba. Allah yaga zuciyata” Nana ta katseta da sauri. Kallonta kawai Zahra ta yi ta kasa cewa komai, Nana ta sauka daga kan gadon ta ɗauki Jersey veil ɗin dake kan gado ta ɗora kan riga da wando jikinta, kasancewar jeans ne a jikinta blue sai yar ƙaramar riga me bottles itama blue, ta gama yafa mayafin sannan ta ɗauki wayarta ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake kallonta ba. Da idanu kawai Zahra ta bita sai kuma ta sunkuyar da kanta, daman ta san ba lallai bane ta saurareta, sai dai ta yi hakan ne a bisa umarnin da Umma ta bata. Zaune ta samu Amma a parlon tana cin abincin rana, ta dinga kallonta sai kuma ta ce“har kun gama?” gyaɗa mata kai ta yi tana shirin fita waje ta ce“eh.” “Nana!” Cak ta tsaya jin yanda Ammar ta kira sunanta, ganin irin kallon da take mata ya sanya ta sunkuyar da kanta ƙasa. “A haka zaki fita?” Amma ta yi tambayar tana kafeta da idanu. Kallon jikinta ta yi ba ƙarya jeans ɗin ya matseta sosai, dan duk surar jikinta ta bayyana. Amma ta ajiye spoon ɗin hannunta still looking at her ta ce“bana son shashanci fa” Sum-sum ta koma daƙinta, bata ko kalli Zahra dake zaune tana kuka ƙasa-ƙasa ba ta ƙarasa press ɗinta ta ɗauki wata After dress baƙa ta ɗora akai sannan ta fito parlon. Kallo Ɗaya Amma ta yi mata ta ɗauke kai, ta fice daga parlon da sauri kai tsaye kuma apartment ɗin Maimoon ta nufa. Koda ta shiga bata sameta a parlon ba, ƙamshin girkin da taji ya sanya ta nufi kitchen ɗin, tsaye ta sameta tana juya stew, ta jingina da jikin cabinet tana murmushi ta ce “Amaryar Yaya Aliyu” Kallonta kawai Maimoon ta yi sai kuma ta ɗauke kai ta rufe tukunyar sannan ta dawo gabanta ta ce“uwar gida” daga haka ta fice daga kitchen ɗin. Bin bayanta Nana ta yi suka dawo parlon, ta zauna kan kujera ta ɗauki remote ta ƙaro gudun ac dan zafi take ji, Nana ta zauna gefenta ta ɗora kanta a cinyarta ta ce“ke yanzu dan Allah duk sanyin da ake bakya ji?” gyaɗa mata kai Maimoon ta yi. Nana ta taɓe baki ta tashi zaune kamar wadda aka tsikara ta ce tashi zaune tana kallonta ta ce“kin san me?” girgiza mata kai Maimoon ta yi, Nana ta hankaɗeta ta ce“ke ji banza. Ina miki magana kina wani shareni wai ke matar aure” murmushi kawai Maimoon ta yi ta ce“to ke me ce ce?” tuntsirewa da dariya Nana ta yi ta ce“matar gida mana. Wai abun mamaki duk kun yi aure” ta sake tuntsirewa da dariya. Kallonta kawai Maimoon ke yi ba tare da ta kanta ta ba. Nana ta ce“wai Zahra ce ta zo apartment ɗin mu yanzu wai na yafe mata” gyara zama Maimoon ta yi ta ce“sai ki ka ce mata me?” ɗan juya Idanunta ta yi kafin ta ce“na ce mata ai na yafe mata” wani mugun kallo Maimoon ta watsa mata ta ce“amma ke banza ce wlh” murmushi kawai Nana ta yi ta ce“to me zance mata? Ai idan ta yimin da kyau ta sani, idan kuma ta cutar da shima ta sani.” Tashi tsaye Maimoon ta yi tana kallonta cike da masifa ta ce“Ada kenan da baki da damar ramawa, yanzu kuwa kina da damar da zaki rama ki nuna mata ke ba yarinyar da zata rainawa hankali ba ce.” Kallonta kawai Nana ta dinga yi, Maimoon ta ci gaba da faɗin“koda wasa kada ki bari ta huta, ki nuna mata cewa ke ki ke da gida kuma ke ce yar uwarsa” Ita dai Nana kallonta kawai take dan ba fahimtar abin da take cewa ta yi ba. Ta taɓe baki ta ce“to wai akan wa zan rama?” “Akan uncle Abdusammad mana!” Shiru Nana ta yi sai kuma ta ce“to a matsayina nawa?” Harararta Maimoon ta yi ta ce“a matsayinki na matarsa mana! Kuma kishiyarta.” Nanameera 08106608363.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 41. Wani kallon sheƙeke Nana ta yi mata sai kuma ta ce“ke me ki ka ce?” sai a sannan Maimoon ta tuna abin da ta faɗa. Lokaci ɗaya ta sanya tafin hannunta na dama ta rufe bakinta a fili ta ce “Ya ilahi” Leƙa fuskarta Nana ta yi. Ta ɗago tana kallonta, da hannu ta yi mata alama da mene ne, ta girgiza kanta tana murmushi ta ce“ke babu komai. Zauna ki ji” taɓe baki Nana ta yi sai kuma ta koma ta zauna tana kallonta, Maimoon ta furzar da iska daga bakinta sannan ta zauna ita ma tana kallonta ta ce“kin je wajen Hamida kuwa?” girgiza mata kai ta yi ta ce“to kawai sai na dinga yi muku yawo a gida mazajenku na nan” tsaki Maimoon ta yi tana kai mata duka ta ce“kin ji banza. Dallah can ki je bata da lafiya” Ƙasa-ƙasa Nana ta yi da murya, ta ɗan matso kusa da ita sosai ta kara hannunta a gefen kunnen Maimoon ta ce“ko dai itama irin abin da ya same ki ne ya sameta?” ta ɗago tana kallon fuskar Maimoon ɗin to see her reaction. Haɗe rai Maimoon ta yi ta turata tana cewa“ke daɗina dake hauka wallahi. Bata da lafiya ne kawai” kamar jira Nana take ta fara sheƙa dariya kamar zararriya, Maimoon ta dinga kallonta cike da takaici, ji ta yi kamar ta shaƙeta saboda haushi, dan gaba ɗaya cikin ya mayar da ita masifaffiyar ƙarfi da yaji. Sai da Nana ta yi mai isarta sannan ta tashi ta gyara zamanta tana kallon yanda Maimoon ɗin ta haɗe rai. Ta tsuke bakinta kamar gaske ta ce“Tam na daina muku dariya. Allah ya sauke ku lafiya, in sha Allah mace zaki haifa a saka mata sunana” Banza ta yi mata, ta yi murmushi sai kuma ta dafata ta ce“to bana baki haƙuri ba?” madadin ta bata amsa sai kawai taga ta fashe da kuka. Nan da nan hankalin Nana ya tashi, ta dinga taɓa ta cike da damuwa ta ce “mene ne? Ko baki da lafiya? Ina ne ke miki ciwo? Ko na kira miki Ummi?” Shiru Maimoon ta yi mata, sai kukanta take.. Nana ta sake matsawa kusa da ita ta riƙe hannunta cikin nata a sanyaye ta ce“to bana ce ba zan ƙara ba? Wallahi ba zan sake miki dariya ba.” Janye hannunta ta yi daga nata, ta shiga goge hawayenta cikin shessheƙar kuka ta ce“to nima ance miki son cikin nake? Gaba ɗaya tsoro nake ji. Wallahi bana so na haihu yanzu, shikenan kowa ya yi ta kallona” ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan. Girgiza kai Nana ta yi tana kallonta cike da tausayawa ta ce“Allah sarki to ki yi haƙuri. Idan Yaya Aliyu ya shigo sai ki faɗa masa ke bakya son cikin nan a zubar” ko saurareta Maimoon bata yi ba ta ci gaba da kukanta a hankali. **** Da daddare bayan sallar isha'i tana zaune kan cinyar Amma tana danna wayarta a hankali. Ita kuma Amma tana kallon dramar da ake a tv, kamar wadda aka tsikara haka ta tashi zaune ta juya tana kallonta sosai ta ce “Amma” Kallonta Amma ta yi kafin ta ce“na'am mene ne?” Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“Allah Maimoon tausayi take bani, ɗazu fa da naje sai kuka take.” Da ɗan mamaki Amma ta kalleta ta ce“ita Maimoon ɗin? To meya ke damunta?” Langwaɓar da kai ta yi ta ce“akan wannan cikin ne fa. Gaba ɗaya ta zama abar tausayi, ni kuwa nace ta cewa Yaya Aliyu yasa a zubar da cikin ko dan Allah?” ta ƙare maganar tana kallon Amma dan ta ji me zata ce. Wata uwar harara ta maka mata kafin ta ce“saboda ke ce gwana uwar iya ko? Ina ruwanki?” tura baki ta yi ta sunkuyar da kanta daman ƙaikaiyin bakinta yasa ta fadawa Ammar. Amma taja tsaki tana janyeta daga jikinta ta ce“ni tashi ki bani waje. Na sake jin irin wannan maganar a bakinki” tashi tayi ta ɗauki wayarta ta bar parlon jiki a saluɓe. Tana shiga daƙinta ta mayar da ƙofa ta rufe ta sake zumɓura baki a fili ta ce “To daga na faɗa mata gaskiya?. Taɓ” Ta ƙare maganar tana zame hular kanta, kyakkyawan gashinta wanda ya sha gyara ya sakko har gadon bayanta dan ba'a kitse yake ba. Ta ƙarasa wajen gado ta zauna tana sauke ajiyar zuciya. **** Bakinsa ɗauke da sallama ya murɗa handle ɗin ƙofar parlon, Turus yayi ganinsu zaune dan bai yi tunanin kiran na meeting bane. Ganin yaja ya tsaya yasa Atta ta ce “To kai kuma tun da ba soja bane ai ka ƙaraso ciki ko?” Kallonta kawai ya yi sai kuma ya saki ƙofar ya ƙaraso ciki. Kujerar da Abba ke kai ya ƙarasa ya zauna sannan ya gaida Hajiya Babba da kuma Mama dan su ne yau bai gani ba. Bayan sun amsa Papa y yi gyaran murya kafin ya ce “Ba wani abu ya saka muka taru anan ba sai don maganar zumuncinmu...” Bayan sun gama tattaunawa Abdusammad ya tashi zai wuce dan Allah Allah yake ya bar parlon, Sai dai cikin rashin sa'a Hajiya Babba ta kira sunansa. A dole ya koma ya zauna yana kallonta fuskarsa babu annuri, Kallonta duk suka yi dan basu san me zata ce ba, ta gyara zamanta tana kallon Papa ta ce “Kabeeru ai ina ga ba'a gama ba” Da ɗan mamaki ya ce“To muna ji Hajiya” Ta numfasa sannan ta ce“ba wani abun bane daman maganar aurensa ne. Ina ga ya kamata ace Nana ta tare a ɗakin mijinta tunda dai komai ya riga da ya saisaita” Atta ta cafke maganar kamar daman jira take ta ce “Ashe bani kaɗai nake wannan tunanin ba.. wallahi kullum dashi nake kwana dashi nake tashi, to yarinya sai zama take da aure aka. Ita ba'a danganata da ɗakin aurenta ba. Gashi sa'annin auren duk kusan Allah ya bada rabo, to dan Allah itama ba ƙara ta tafi nata ɗakin ba, ko mun sake samun jikoki?.” Murmushi suka yi, Ban da Abdusammad wanda ya sake haɗe rai kamar yaga mala'ikan mutuwa. Hajiya Babba ta ce“In sha Allah Atta nan bada jimawa ba zata tare” Yatsine fuska ta yi ta ce“ban gane nan bada jimawa ba?. Ai ina, dole ta tare gobe, bana son wani neman magana, an riga da an gama komai na al'adar auren budurwa da ita, dan haka gobe a sadata da dakin mijinta. Dan so nake na koma Njomboli kuma ban tafiya sai naga yanda zaman nasu zai kasance aradu!” Shiru Hajiya Babba ta yi dan bata son musu da ita. Abba ya buɗe baki zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta ce“kul kul Ahmadi, ina ganin girmanka dan haka kar ka ce zaka saka baki anan. Ko ka manta batun yarka ake?” shiru Abba ya yi bai yi maganar ba, ta kalli Mama wadda ke faman murmushi tun ɗazu ta ce“Ke Fatime ki shiryata gobe ki kaita ɗakin mijinta. Nima zan biyo bayanku” Da fara'a sosai Mama ta amsa. Abdusammad ya ɗan kalleta ganin yadda ta zaƙalkale tana magana, ji yayi kamar ya maƙureta saboda haushi, sai dai sanin babu yanda ya iya da ita ya sanya shi yin kwafa yana sake maida hannunsa ga fuskarsa. Duk abin nan da yake Papa na lura dashi, ya girgiza kansa a hankali. Kasa ci gaba da zama ya yi, ya miƙe yana gyara zaman rigar jikinsa ya ce “excuse me pls” Daga haka ya yi waje da sauri, da harara ta bi shi sai kuma ta ce“kaga shashashan ɗa? Ina magana ya yi wani fitarsa. To idan ma yarinyar ce baya son a kai masa wallahi sai dai ya ƙarata, dan gobe sai ta tare a gidansa.” Murmushi kawai suka yi sanin halin faɗanta yasa babu wanda ya tanka, ta gama barbaɗin jarabarta ta tashi ta bar wajen, Sai a sannan Abba ya sauke numfashi ya ce “Allah ya kyauta.” Da Amin suka amsa sannan ya yi musu sallama ya tashi ya bar parlon dan dare ya fara. Da idanu Papa ya bi shi sannan shima ya fice daga parlon. **** Kai tsaye gidansa ya nufa, yana jin wani irin ɗaci a ransa. Zaune ya sameta a parlon Noor na kan cinyarta tana bacci, ya haye sama ba tare da ya amsa sannu da zuwan da take masa ba. Ɗakinsa ya shige ya zame duk kayan jikinsa ya nufi toilet, ruwan sanyi ya sakarwa kansa, ya dafa bango yana sauke ajiyar zuciya jin yanda ruwan ke ratsa fatarsa. Abu ne ke neman haɗe masa goma da ashirin, idan ya tuna Nana matsayin matarsa take sai yaji duk hankalinsa ya tashi, he just can't believe a ce wannan yar yarinyar sunan matarsa take amsawa. Babu abin da ya sake ƙona masa rai sai maganganu da Atta ta yi ɗazu, kenan har wani tunanin samun wani abu take daga gare shi? Da wannan yar yarinyar, yaja wani dogon tsaki wanda bai san sanda ya kubuce masa ba. Ya ɗauki mintuna masu tsawo a haka kafin ya rage gudun showern ya yi wanka sannan ya ɗauro alwala ya fito yana sanye da bathrobe. Zaune ya sameta kan gadonsa ta yi jigum da alama jiransa take, Ya ɗauke kansa daga gareta ya nufi mirror ɗinsa, mai ya shafa sannan ya gyara kansa. Yana gamawa ya buɗe press ya dauko wasu riga da wando na bacci masu taushi ya saka, sannan ya feshe jikinsa da turare. Duk wannan abun ya dake akan idanun Zahra yake yin su, dan koda na sakan ɗaya ta kasa ɗauke idanunta daga kallonsa, wata sabuwar soyyayarsa take ji na yawo a cikin zuciyarta, ji take inama ta tashi ta rungumeshi ta yi bacci a jikinsa kamar da. Sai dai ta san yanzu hakan ba mai yiwuwa bane, dan sharadin daya kafa mata ba zata iya dashi ba, Nana ba zata taɓa yafe mata ba. Wannan tunanin ya sanya zuciyarta tsinkewa, ta sunkuyar da kanta hawaye na biyo fuskarta. Sam bata san sanda ya zo gabanta ba, bata san sanda ya zauna a gefenta ba. Sai kawai tattausan hannunsa da taji akan nata, ta yi saurin kallon hannun nata sai kuma ta kalli gefenta na dama. Gani ta yi yana mata murmushi, ai kuwa kamar jira take ta faɗa jikinsa tana fashewa da wani raunataccen kuka. Hannunsa ɗaya ya ɗora a bayanta yana shafawa a hankali, ta dinga kuka kamar ba zata daina ba. Sai da ta fara jin abin da ke damunta ya fara raguwa sannan ta ɗago kanta daga jikinsa har sannan tana shessheƙar kuka. Hannunsa ya sanya ya goge mata hawayen fuskarsa a sake kamar ba shi ba ya ce“Ya isa haka to” jinjina masa kai ta yi tana murmushi mai haɗe da kuka ta ce“Doctor tam.” Ya ɗan yi shiru yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya ta rame kamar ba ita ba, har wasu kasusuwa ne suka mata ƙawanya a wuya. Duk wanda ya ganta sanda suka zo ƙasar nan ya kalleta yanzu ba lallai bane ya ganeta. Ya riƙe fuskarsa da duk hannayensa biyu yana murmushi ya ce “naga kin ƙara kyau?” Murmushi ta yi a sanyaye ta ce“doctor ka yafe mini yanzu?” shiru ya yi kamar ba zai bata amsa sai kuma ya ce“shikenan ya shige. But kada ki sake irin haka kin ji, na san ba halinki bane, ƙoƙarin ɓata ki ake but karki biye musu Zahra. Na yarda dake fiye da yanda ki ke tunani, bana son ace daga gareki aka samu matsala..dan hakan zai haifar da maganganu acikin gidan nan, ni kuma duk wanda ya zageki ko ya aibata ki ba zan ji daɗi ba. Dan haka dan Allah Zahra kar ki sake.” Ya ƙare maganar in a very polite tone. Kasa cewa komai ta yi kawai ta sake rungumeshi tana jin wani sabon so da ƙaunar mijin nata na shigarta. Ya yi shiru yana sauke numfashi, ba komai ya sanya ya yi hakan ba sai dan zuwan da Nana za ta yi. Idan har ya nuna mata baya shiri da Zahra ba zasu taɓa zaman lafiya ba kuma hankalinsa ba zai taɓa kwanciya ba, dan ya san halin Nana kamar yunwar cikinsa. Janye jikinta ta yi daga nasa tana lumshe idanu, ya sake jawota jikinsa yana ƙoƙarin kunce zaren sleeping dress ɗin dake jikinta. Ɗago kanta ta yi ta kalleshi ya manna mata kiss a goshi, ta sake maƙalewa a jikinsa tana rufe idanunta, tana jin sa har ya sauke rigar ƙasa, Jin hannunsa akan fatar jikinta ya sanyata sauke wata ajiyar zuciya tana ɗan ƙanƙameshi. Cikin yan sakkani kuma wasan nasu ya fara neman sauyawa.. **** Amma ta dinga kallonsa ganin kamar bai san abin da take cewa ba, Ta ajiye cup ɗin akan table sannan ta zauna gefensa a hankali ta dafashi, Ya juyo a ɗan firgice yana kallonta, a sanyaye ta ce “tunanin me kake ne? Ina ta maka magana baka saurarena” Girgiza kansa ya yi yana furzar da iska daga bakinsa ya ce“Abun ne, hankalina ne sam yaƙi kwanciya.” da mamaki ta ce“dame fa?” “Akan auren Nana da Abdusammad. Gobe zata tare inji Atta, kuma kin san babu wanda ya isa yaja da maganarta, tsoro nake kada wata fitinar ta ɓullo tsakaninsu dalilin zuwan Nana.” Shiru Amma ta yi, lokaci ɗaya taji jikinta ya yi wani irin sanyi. Can dai ta numfasa ta ce“gobe kuma? Me yasa ba'a faɗa mana da wuri ba amma?” Girgiza kai Abba ya yi ya ce“ai babu wani abu da za'a yi shiyasa, kawai Fatima ce zata rakata.” “But at least ya kamata a sanar dani ko da abin da zan shirya mata.” Abba ya kalleta wanda ya sanyata yin shiru, Ya ɗauke kansa yana kallon tv ya ce“kira min ita.” Toh kawai ta ce sannan ta mike jiki a saluɓe ta nufi ɗakin Nanar. Kwance ta sameta har ta yi shirin bacci. Ta taso ta sannan ta dawo parlon ta zauna, after 2mins Nana ta fito tana jan ƙafa a hankali, hannunta ɗaya akan idanunta tana murzasu saboda baccin data fara yi. A gefen Abba ta zauna ta jingina da jikinsa, Ya gyara mata zama dan so yake ta fahimceshi ya ce “Tashi zaune ki ji Nana.” Toh kawai ta ce sannan ta gyara zamanta, dan tun bayan abin da ya faru bata sake masa musu ba. Ya dinga kallonta dan har ga Allah tausayinta yake, Ita ma kallon nasa take. Ganin damuwa akan fuskarsa ya sanyata wartsakewa gaba ɗaya, Ta yi shiru tana jiran abin da zai ce. Sauke nannauyan numfashi ya yi kafin ya fara magana cikin nutsuwa. “Nana ina son ki buɗe kunnawanki ki ji abin da zan faɗa miki. Ba'a fasa aurenki ba saboda bakya nan, an ɗaura miki aure a ranar kamar yanda aka ɗaurawa yan uwanki!” Sai da taji gabanta ya fadi, Ta zaro idanu tana kallonsa, Lokaci ɗaya hawaye ya fara zuba daga idanunta, bakinta na rawa ta ce“Abb...Abba nima an yi min aure? Wa aka aura min?” Kallonta ya yi ganin yanda take kuka a hankali yasa ya ce“banason wannan kukan kin ji. Duk abin da na faɗa miki kuma ki yarda” gyaɗa masa kai kawai ta yi, dan ita daman bata ji zata musa masa ba ko me yace kuwa. Ta shirya karɓar duk abin da Allah ya bata. Ganin ta kwantar da hankalinta yasa ya ce “An ɗaura aurenki da uncle ɗinki Abdusammad!” A tsaye suka ganta ta dinga kallonsa bakinta na rawa ta shiga girgiza kanta, can kuma ta yi luuu ta faɗi ƙasa a sume.. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 42. Murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta yi bakinta ɗauke da sallama, Zaune ta hangeta tsakiyar gado ta kifa kanta akan cinyoyinta sai kuka take a hankali. Amma ta sauke numfashi sai kuma ta saki ƙofar ta ƙarasa ciki hannunta riƙe da mug ɗin, A kan drawer ta ajiye mug ɗin sannan ta zauna tana kallonta a sanyaye, kasa ce mata komai ta yi, ta yi shiru tana sauraren sautin kukanta dake tashi a sanyaye. Sun ɗauki mintuna a haka kafin daga bisani Amma ta sauke ajiyar zuciya ta dafata cikin tattausar murya ta ce “Nana!” A hankali ta ɗago kanta. Amma ta ƙura mata idanu ganin yanda hawaye da majina suka cika mata fuska, Amma ta girgiza kanta tana kai hannunta fuskarta ta ce“ya isa haka kin ji. Ki daina kuka” “Amma uncle fa? Uncle fa Amma. Ya ma za'a yi ace uncle ne mijina? Ya za'a yi na aureshi?” Nana ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan, Ta kifa kanta kan cinyar Amma tana jan numfashi. Shafa bayanta Amma ta dinga yi a hankali cike da tausayinta ta ce“to mene ne Nana? Ba uncle ɗin ki bane. Kuma ai kin san ba zai taɓa cutar dake ba ko?” Sake ɗago kanta ta yi tana kuka ta ce“Amma ya za'a yi na zauna dashi a matsayin miji? Uncle ne fa. Ya za'a yi na aureshi? Ni wallahi ba zan iya baaa!” Ta sake faɗawa jikinta tana kuka har da birgima. Shiru Amma ta yi bata sake cewa komai ba dan ta san ba saurarenta zata yi ba, Ta ɗauke kanta tana kallon ƙofa, ita kanta ba son auren nan take ba. Saboda Abdusammad ya yi wa Nana girma. Ta sauke zazzafan numfashi tana maida idanunta kanta jin har sannan bata daina kukan ba yasa ta ce “Ni ɗagani idan ba zaki yi shiru ba. Mene ne dan kin aureshi? Ina ruwanki da kasancewarsa uncle ɗinki? Ke ba matsayin miji zaki ɗaukeshi ba.” Tashi zaune ta yi cikin gunjin kuka ta ce“to me yasa za'a ce na aureshi? Ita Maimoon ta auri Yaya Aliyu, ita Amrah ta auri Yaya Sultan, ita kuma Hamida ta auri Yaya Hamid. To sai ni kuma a aura min uncle? Bayan kuma tsoho ne!” Ta faɗa tsakiyar gado tana kuka kamar ranta zai fita. Murmushi Amma ta yi dan cikin kukan nata har da na banza, ta tashi dan ba zata iya da halin Nanar ba ta ce “Abdusammad ɗin ne tsoho?” “wallahi tsoho ne Amma. Kalli fa babu mai aure sai shi, kuma har ƴa ce dashi. To ni ya za'a yi na zauna dashi a haka?” Amma ta ɗan waro idanunta tana kallonta ta ce“au dan yana da aure shi ne ya tsufa? To shi Aliyun ba kusan sa'ansa bane. Daga shi naga sai shi” Ɗago kanta ta yi tana murza idanunta cikin kuka ta ce“to ai dai ya girme shi, duk fa ya girmi kowa.” Amma ta ɗan ja tsaki ta ce“to tun da ba zaki haƙura ba bari zan je na faɗawa Abban naki shi sai ya san yanda zai yi dake.” Daga haka ta nufi ƙofa ta fice daga ɗakin. Nana ta sakko ƙasan gadon ta zube a wajen ta sake fashe da wani sabon kukan mai cin rai, a fili kuma ta dinga cewa “na shiga ukuna, wayyo Allahna. Wallahi bana sonsa.” Ta dinga maimata maganar can kuma ta baje a wajen tana birgima. Amma na fita ɗakin Abba ta shiga, zaune ta same shi gefen gado ya gama shirin kwanciya. Ta ƙaraso ciki ta tsaya jikin mirror ta yi shiru, kallonta ya yi sai kuma ya ɗauke kansa yana gyara zama pillow ɗin gabansa ya ce “Madam lafiya dai?” Sauke numfashi ta yi tana kallonsa ta ce“Ni ko baka ganin auren nan akwai matsala?. Nana yarinya ce ƙarama, shekarunta 17 fa kawai. Abdusammad kuma ya girme mata, girma bana wasa ba. Sai nake ganin kamar zamansu ba zai yi dai-dai ba.” Abba ya dinga kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa, Can kuma ya yi mata alama da ta zo da hannunsa. A sanyaye ta ƙaraso wajen ta zauna gefensa, Abba ya kama hannunta na dama yana murzawa a hankali ya ce “Rabi'a kenan. Ya kamata a ce kin kwantar da hankalinki, na san kin san wane Abdusammad, kin san abin da zai iya da kuma wanda ba zai iya ba. Bana da damuwa akansa na san zai kula da Nana, kulawa irin wadda ba kowane namiji ne zai yiwa mace ba. Ba zai taɓa bari ta yi kuka ba, saboda ba tun yau ba na san yana sonta, kawai ba zai iya faɗa bane saboda yana ganin kamar hakan bai kamata ba. Yanzu kuma da ya samu dama kina ganin zai bari ta yi kuka a gidansa? Kina ganin zai gaza wajen kulawa da ita?.” Numfasawa Amma ta yi ta girgiza kanta kana ta ce“nima na san ba zai bari ta yi kuka ba, amma fa ka sani ba shi kaɗai bane. Yana da mata har da ƴa, sannan matarsa babba ce wadda ta mallaki hankalin kanta, kuma tana da wayo. Sannan ita ce ta yi yunƙurin cutar da Nana, yanzu kana ganin idan ta shiga gidan a matsayin kishiyarta zata barta ta zauna lafiya? Nana yarinya ce. Duk da rashin jinta da kuma neman faɗanta bata da wayo, cikin ruwan sanyi za'a iya cutarta ba tare da ta gane ba. Tana da saurin yarda da mutum. Shi ne abin da nake tsoro wallahi” Abba ya yi shiru yana nazarin maganarta, tabbas tana da gaskiya, Nana bata da wayo ko kaɗan. Ya sauke numfashi sannan ya ce“Duk wannan ba zai zama damuwa ba in sha Allah. Babu abin da zai faru, mu yi musu fatan zaman lafiya” jiki a sanyaye Amma ta ce“tam shikenan, Allah ya basu zaman lafiya ya sanya albarka cikin auren.” murmushin jin daɗi ya yi kafin ya ce“Amin ya rabbi.” Ta mike tsaye tana fadin“sai kuka take yi na yi nayi da ita taƙi shiru.” Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“Allah sarki, tausayi take bani, zata shiga cikin wata rayuwa wadda bata san da ita ba. Ki barta ta yi kukan, ba koda yaushe ake hana mutum kuka ba, tana buƙatar ta yi, so just leave her.” Jinjina masa kai Amma ta yi ta ce“daman na rabu da ita in sha Allah. Gobe da safe zan kira Ramlah ta zo” okay ya ce mata sannan ya zare glasses ɗin idanunsa ya kwanta dan dare ya yi sosai, Amma ta ɗan kalleshi sai kuma ta nufi ƙofa ta fita dan bata gama abin da take ba. Daren ranar kasa bacci Nana ta yi, ta dinga kuka har sai da muryarta ta dashe, ganin dare ya yi sosai ya sanya ta tashi ta shige toilet ta ɗauro alwala sannan ta fito ta zura hijabi ta fara gabatar da sallolin nafila, bayan ta gama ta zauna a wajen ta dinga addu'o'i neman yafiyar ubangiji sannan kuma da samun zaman lafiya. Daga bisani kuma ta ci gaba da kukanta har asubahi, Gari ya fara haske wajejen 6 na safe aka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin, bata iya ɗaga kanta ba, hasalima bata san an shigo ɗin ba saboda tunanin da ta yi zurfi a cikinsa. Abba ya ƙaraso gaban gado ya zauna yana kallonta ganin yanda ta kifa kanta kan cinyoyinta. Ya dade yana kallonta kafin ya yi gyaran murya ya taɓata, a firgice ta buɗe idanunta, ganin shi ne ya sanya ta sunkuyar da kanta jiki a sanyaye ta ce “Abba ina kwana” Duk da muryarta da bata fita hakan bai hana shi jin abin da ta ce ba. Sai dai bai amsa ta ba, Madadin hakan ma sai ya sakar mata murmushi, ya yi mata alamar ta zo ta hannunsa. A danya ta mike ta dawo kusa da shi ta zauna Abba ya ware mata hannayensa duk biyun, kamar jira take kuwa ta shige jikinsa tana sakin wani marayan kuka, Kuka take mai tsuma zuciya, kuka ne wanda ke nuna irin rauninta gaban mahaifin nata. Shi kansa Abba sai da jikinsa ya yi sanyi, Ya dinga dukan bayanta a hankali ba tare da ya yi yunkurin hanata kukan ba, Madadin hakan ma sai ya dinga cewa “Cry! Cry Nana, cry as much as you can. Cry Nana.” Kamar kuwa turatan yake haka ta dinga ƙara sautin kukan nata tana ƙanƙameshi. Shima ya sanye duk hannunsa biyun ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya, Allah ya sani yana mugun sonta, yana son gudaliyar ƴar tasa fiye da tunanin mai tunani. Koda wasa baya son abin da zai ɓata ranta, ballantana har yaji kukanta, shiyasa a tsawon rayuwarsu tare zai iya ƙirga sanda ranta ya ɓaci a dalilinsa. Sun ɗauki lokaci mai tsawo a haka har sai da ta fara rage sautin kukan nata don kanta. Ya ɗagota daga jikin nasa ya fara goge mata hawayen nata da hannunsa, ita kuwa sai ƙara narkewa take dan ta samu abin da ta ke so. Kuma sosai taji zuciyarta ta mata sanyi sakamakon kukan da ta yi, Sai da yaga ta yi shiru gaba ɗaya sai shessheƙar kuka kawai take sannan ya ce “Yanzu kin haƙura?” Gyaɗa masa kai ta yi a hankali, Ya yi murmushi sannan ya ce“Yauwa Allah ya yi miki albarka, Ya baki zaman lafiya a gidan mijinki. Ya...” “Abba da gaske uncle zan aura? Da gaske ni matarsa ce?” Ta katse shi da sauri jin ya yi maganar gidan mijin. Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi ya ce “Eh Nana, da gaske ne, Abdusammad shi ne mijinki. Kuma ina fatan ki yi masa biyayya, ki rufe sirrin mijinki, ki zauna dashi lafiya. Ki kula da dukiyarsa, ki zama mata tagari a cikin gidansa. Koda wasa kada ki bari mijinki ya yi kuka dake, kada ki bari ya kawo ƙararki. Ki zama yarinyar kirki kin ji Khadijatou.” Samun kanta ta yi da sake fashewa da wani sabon kukan, ta sake rungumeshi tana kukan ta ce“Abba uncle fa? Uncle ɗina ne, daman ana auran uncle? Ustaz ɗin mu ya ce mana ba'a aure da uncle. Me yasa ni zai aureni?” Murmushi irin na manya uncle ya yi sannan ya ɗago kanta ya gyara mata zama yanda zata fahimce shi sosai ya ce“Haka ne, ba'a aure da uncle. Amma ba irin naki uncle ɗin ba” Da ɗan mamaki ta kalleshi, ya jinjina mata kai ya ce“Abdusammad ɗan Yayana ne, hakan na nufin shi ɗin cousin ɗinki ne. Kuna ce masa uncle ne dalilin kallon mahaifin da ku ke masa, ba wai dan shi ɗin ƙanina bane. Abdusammad ɗana ne kamar yanda ki ke ƴata, dan haka aure a tsakaninku halattaccan abu ne, aure ne na raya sunnar ma'aiki, dan haka idan kina kallon babu aure tsakaninku ina son ki daina daga yau kin ji.” Sunkuyar da kai ta yi tana gyaɗa masa kai, Daman ta san da wannan bayanin tun tuni. Amma ita sam bata masa kallon wanda zata iya aura, a koda yaushe kallon mahaifi take masa. Ɗaukansa take kamar Abbanta, ashe watarana zai iya zuwa ya aureta?. Miƙewa Abba ya yi yana ɗaukan cazbaharsa ya ce“Idan Allah ya kaimu an jima za'a sadaki da ɗakin mijinki, don haka ina mai miki nasiha da kiji tsoron Allah, ki kasance haske mai haska zuciyar mijinki. Ki zame masa ƙawa kuma abokiyar arziki, dan Allah Nana kada ki bamu kunya.” Yanda ya yi maganar a tausashe ya sanyata kallonsa, Hawaye na biyo kuncinta ta ce“Tam Abba in sha Allah ba zan baku kunya ba, ba zan bari ku sake kuka dani ba.” Ta ƙare maganar kuka na kwace mata, Murmushi kawai Abba ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin, Nana ta bi bayansa da kallo sai kuma ta sake fashewa da kuka, ta faɗa kan gadonta ta shiga rera shi kamar waƙa. **** Zahra ta dinga kallonsa ganin yanda yake cin abincin hankali kwance, idanun da yaji na yawo a kansa ya sanya ya ɗago kansa, cikin rashin sa'a idanunsu suka sarƙafe da juna. Ta yi saurin janye nata tana ɗaukan mug ɗin tea ɗinta, Ɗan murmushi ya yi sai kuma ya ajiye spoon ɗin hannunsa still looking at her ya ce “why are you staring at me?” Yi ta yi kamar bata san me yake nufi ba, ta kalleshi ta ce“magana ka yi doctor?” Ɗauke kansa ya yi yana murmushi ganin tana shirin raina masa hankali, Zahra ta saci kallonsa ta gefen ido ganin yanda yake murmushi ya sanyata yin murmushin itama. Bai sake bi ta kanta ba har ya kammala breakfast ɗinsa, Ya tashi yana goge bakinsa da tissue ya ce “To zan fita sai na dawo.” Tashi itama ta yi tana murmushi ta ce“Tom a dawo lafiya Allah ya tsare hanya.” Da Amin ya amsa sannan ya juya zai bar wajen, kamar wanda ya tuna wani abun kuma sai ya tsaya cak. Ta ɗan kalleshi sai kuma ta ce“doctor lafiya dai?” juyowa ya yi yana kallonta ya ce“wallahi na kusa mantawa ne. Idan Allah ya kaimu an jima za'a kawo Nana, so get ready please.” Ji tayi kamar an zare mata lakar jikinta, taji ƙafafunta na neman gagarar ɗaukan gangar jikinta. Numfashinta ya tsaya na wasu sakwanni, Ganin haka yasa Abdusammad cewa “Lafiya dai?” Girgiza masa kai ta yi a sanyaye. Ya dinga kallonta ganin yanda ta sunkuyar da kanta, Taku ɗaya ya yi ya koma gabanta, Ya sanya hannunsa ya ɗago kanta. Hawaye ya gani na zuba daga cikin idanunta, Ya ɗan ware idanunsa da mamaki ya ce“Zahra mene haka?” Saurin goge hawayen ta yi da hannunta tana shessheƙar kuka ta ce“babu komai. Ban sani ba ne” Ta ƙare maganar tana kirkiro murmushi. Wani irin kallo ya dinga yi mata sai kuma ya ce“Saboda nace miki Nana zata zo ki ke kuka?” Saurin girgiza masa kai ta yi tana ƙoƙarin ɓoye hawayenta ta ce“A'a doctor, babu komai fa.” Taɓe baki ya yi dan ya san ƙarya take ya ce“na miki kama da wanda zaki ma karya Zahra?.” Kallonsa kawai ta yi sai kuma ta sake sunkuyar da kanta kuka na sake tawo mata, ya kalli agogon Rolex ɗin dake maƙale a hannun hagunsa sai kuma ya mai da idanunsa kanta ya ce“But you promised me cewa komai ya shige? Gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh doctor babu komai Allah ya kawo su.” “Amin” Ya amsa a takaice. Sai kuma ya sake cewa“make sure kin shirya kinji. Ki yi kyau abin ki” Ya ƙare maganar yana jan kumatunta. Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce“In sha Allah I'll” ya yi murmushi sannan ya juya ya bar wajen. Sai da taga ya fice daga parlon sannan ta sulale a ƙasa a hankali, kamar jira take ta fashe da wani raunataccen kuka.. Yana ƙoƙarin shiga mota yaga kiran Papa, Ya tsaya hannunsa ɗaya riƙe da handle ɗin motar ɗayan kuma riƙe da wayarsa ya ɗaga kiran, gaishe shi ya yi amsa sannan ya ce “Abdusammad ka zo ina nemanka” Shiru ya yi sai kuma ya ce “Papa lafiya dai?” “Lafiya fa. Idan ka zo kaji” Papa ya bashi amsa kai tsaye, To kawai ya ce sannan ya kashe wayar, Abdusammad ya sauke wayarsa yana mamakin kiran, can kuma ya sauke numfashi ya shige motar. **** Abdusammad ya girgiza kansa da rashin fahimta ya ce“Papa ban gane abin da ka ke nufi ba.” Gyara zama Papa ya yi kan sofar yana kallonsa ya ce“abin da nake nufi shi ne idan ka san ba zaka iya zama da yarinyar nan ba gara tun yanzu ka saketa!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanamera08 Wattpad@Nanameera08. Page 43. Da wani irin mamaki yake kallon Papa can kuma ya ce“But why?” cike da nutsuwa Papa ya ce“saboda baka sonta. Bayan haka ban ga alamun zaka kula da ita ba.” “Wani abun nayi mata Papa.?” Girgiza kai Papa ya yi kafin ya ce“ko kaɗan zuwa yanzu babu abin da ka yi mata. Amma alamunka sun nuna nan gaba zaka iya yi mata, Jiya duk ina kallonka kuma naga yanda ka yi, baka shirya zama da yarinyar nan ba. Ko kaɗan baka ji daɗin cewar da aka yi ta tare ba!”. Papa ya ƙare maganar yana jingina da kujerar da yake kai. Numfasawa Abdusammad ya yi dan sai a sannan ya gane inda ya dosa, har ga Allah shi kansa ya sanya bai shirya da karɓar tata ba, amma ya zai yi?. Jin bai ce komai ba ya sanya Papa gyaran murya kafin ya ci gaba da cewa “Ina son ka dinga tuna abu guda ɗaya, ba yarinyar nan ta ce ka aureta ba. Ba mahaifinta bane, ba tilastaka aka yi ba, kaine ka yi hakan saboda raɗin kan ka. Idan har ka ce zaka cutar da ita a zaman da zaku yi tare to ka sani Allah ba zai bar ka ba, Dan haka da azo ana ɓacin rai daga baya gara kawai ka saketa tun yanzu.” Papa ya yi shiru yana kallon sa. Ajiyar zuciya Abdusammad ya sauke kafin ya fara magana “Ni fa ba wai ina jin haushin yarinyar nan bane Papa, na san bata da laifi. Kuma koma tana da shi ai abin da ya wuce ya riga da ya wuce, dan haka babu amfani tado shi. Kawai na kasa yarda ne a ce wai Nana matata ce, na kasa yarda zata shigo gidana ta yi rayuwa dani irin rayuwar miji da mata, bayan yanda na ɗauketa yar ƙaramar ƴata a wancan lokacin.” Murmushi irin na manya Papa ya yi kafin ya ce“Na gane abin da ka ke nufi, amma ba hujja ba ce. Babu yanda za'a yi ka ce dan kana yi mata kallon ƴa ba zata zama matarka ba watarana, baya da haka ma kasan akwai aure a tsakanin ku. Dan haka ina ganin ka bar wannan tunanin zai fi, sannan kuma kada ka kuskura ka ce zaka yi treating ɗinta a kar yarinya ko ƙarama da ka ke ganinta. Dole ne ka sauke duk wani haƙƙinta da yake kan ka, dole ka bata kulawa irin wadda miji ke bawa matarsa, dole ka saurari matsalarta sannan ka yi mata maganinta.” Numfasawa ya yi jiki a sanyaye ya ce“Tom Papa in sha Allah.” “Allah ya yarda ya sanya albarka cikin auren, ya baku zaman lafiya.” Da Amin ya amsa sannan ya tashi ya masa sallama ya fito. **** Ƙarfe 9:00 na safe Aunty Ramlah ta sauka a gidan, ta ajiye jakarta tana kallon Amma da ke haɗa wasu turaren wuta ta ce“To amma dan Allah sai a ce yau zata tare? Ina ma laifin a ce gobe fisabilillahi.” ɗan murmushi Amma ta yi ba tare da ta ɗago kanta ba ta ce“to basu ce haka ba Ramlah. Ni yanzu ki tashi ki je idan da abin da zaku yi ku yi, saboda na san tunda aka haɗa sabgar nan da Atta to wallahi ba zata jira ba, tana iya zuwa ta ce dole sai ta tafi da ita.” Tashi Aunty Ramlah ta yi tana murmushi ta ce“Atta ko jaraba” daga haka ta yi dakin Nana da sauri. Bakinta ɗauke da sallama ta tura ƙofar ɗakin, Sai dai turus ta yi a bakin ƙofar saboda Nanar data hango tana kuka a ƙasa ta yi baje-baje sai birgima take. Aunty Ramlah ta saki ƙofar da sauri ta ƙarasa ciki tana faɗin “Subhanallahi. Nana mene ne haka?” Ko kallonta bata yi ba sai ma sake ƙara sautin kukan nata da ta yi, Aunty Ramlah ta ɗagota tana kallonta hankali tashe ta ce“baki ji ina miki magana ne? Sai ran ki ya ɓaci tukun” Ganin yanda ta yi maganar babu wasa a kan fuskarta ya sanya Nana tsagaitawa da kukan. Ta fara sauke numfashi tana shessheƙa a hankali, Zama Aunty Ramlah ta yi a ƙasan tana kallon ta ta ce“Yanzu faɗa min kukan me ki ke?” “Anty wai uncle zan aura. Uncle fa, Ya za'a yi a ce shi ne mijina...” Ta ƙare maganar tana sake rushewa da kuka. Girgiza kai Aunty Ramlah ta yi ta ce“a'a ban gane ba Nana, mene ne da uncle ɗin?” ɗauke Hannunta ta yi daga fuskarta cikin son yi mata bayani ko Allah zai sa ita ta fahimceta ta ce “Anty uncle Abdusammad fa. Kina ganinsa ai kin san Babba ne ko? Kuma fa har mata ce dashi, ni kuma ai yarinya ce, duk su sauran sun yi aurensu da Yara sai ni a aura min tsoho? To dan Allah ba babba bane shi. Ni kuma kalleni fa, Sai a dinga cewa ni ce matarsa?..” Ta sake fashewa da kuka tana faɗawa jikin Aunty Ramlah. Murmushi Ramlah ta yi sannan ta ce“ke kuma kin fi son ki auri yaro ko? Kin fi son wanda zai nuna miki soyyaya? Wanda ba zai dinga miki faɗa ba ko?.” Jin ta faɗi abin da take so yasa ta ɗago kanta cikin shessheƙar kukan ta ce “Eh mana Anty. Yanzu dan Allah kamar Yaya Sultan, ai kin ga bai min girma ba sosai, to amma ji fa uncle, ƙato ne shi fa. Kawai sai a dinga yimin dariya, Kuma har ƴa ce dashi, wallahi tsoho ne, ni saurayi nake so na aura” Ta sake komawa kan cinyar Ramlah tana kukanta. Girgiza kai Aunty Ramlah ta yi dariya na son kwace mata ta ce “To ai duk wannan abun dana lissafo shi uncle ɗin naki zai dinga miki. Ba zai bari ki dinga kuka ba, zai kula dake sosai kin ji” Ɗago kanta ta yi ta ce“To bayan ma har mata ce dashi, kuma ni wallahi bana son kishiya.” Haɗe rai Aunty Ramlah ta yi ta ce“to ke ina ruwanki da matarsa? Babu abin da ya shafeki da rayuwarta.” Tura baki ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce“ni Allah bana son zama da kishiya, wallahi sai dai ya saketa!” Kallon kin zama mahaukaciya Ramlah ta yi mata kafin ta ce“to don't ever, kar ki sake koda wasa ki fadi wannan maganar a gaban wani kin ji abin da nace.?” Gyaɗa mata kai ta yi, Aunty Ramlah ta sauke numfashi ta ce“ki daina wannan shirmen ki saurari abin da zan faɗa miki kin ji.” Shiru ta yi kamar gaske, Aunty Ramlah ta kama hannunta na dama cike da kulawa ta ce “Nana ki daina wannan kukan haka. Kin san dai tun da an riga da an ɗaura auren na babu wanda ya isa ya sa a kwance shi, saboda haka ki kwantar da hankalinki. Babu wata matsala dan ance Abdusammad ne mijin ki, me ake buƙata ne a aure ba zaman lafiya ba? Da soyyayar juna. Na tabbata Abdusammad ba zai ce baya son ki ba, saboda ke ɗin mace ce irin wadda kowane banki ke fatan samu, kina da kyau kina da tarbiyya. Sannan bugu da ƙari kina da ɗabi'u irin wanda maza ke so, Idan har kin kwantar da hankalin ki, to babu yanda za'a yi ya zama na wata. Dole ke zaki kwace shi, musamman daya kasance ke ɗin ƴar uwarsa ce, saɓanin waccan da kawai a wani wajen ya ganta ya aureta. Dole kina da alfarma a wajensa, Sannan idan har bai ji zai iya zama dake ba ba zai taɓa yarda ya aureki ba, kina dai gani babu irin macen da ba'a nuna masa ba a cikin gidan nan a lokacin da zai aure amma sam ya ce babu wadda ta yi masa, babu yanda ba'a yi dashi ba. Amma ke babu wanda ya yi masa dole, shi da kansa ya ce a ɗaura muku aure, ya biya sadaki mai yawa kina ganin ba zaki iya kwace shi daga hannunta ba.?” Aunty Ramlah ta yi shiru tana kallonta, ganin yanda ta ƙura mata idanu wanda ke nuna tana fahimtar abin da take cewa yasa ta ci gaba da faɗin“Idan har zaki bi abin da zan faɗa miki to tabbas uncle ɗin zai zama naki. Zaki mulki gidan fiye da yanda ki ke tunani, duk da kasancewarsa tsayayyen namiji zaki iya cin galaba a kansa, dan haka ki buɗe kunnunwanki ki ji abin da zan ce miki.” Ganin bata ce komai ba ya sa Anty Ramlah ta haɗe ranta ta ce“ba magana nake miki ba.?” A sanyaye ta ce“Ina ji” Anty Ramlah ta gyara zamanta sannan ta ce“Yauwa kina ji...” Around 11am Amma ta shigo ɗakin, zaune ta sameta, Nana na kan cinyarta ta yi shiru. Amma ta ce“Ramlah babu abin da zaku yi lokaci fa na tafiya?” Girgiza kai Anty Ramlah ta yi ta ce“a'a zamu yi, Nana tashi muje.” Tura baki ta yi sannan ta tashi zaune tana haɗe-haɗen rai. Anty Ramlah ta sauka daga kan gadon tana kallonta ta ce“taso nace.” kamar zata yi kuka ta ce“to bari nayi wanka.” Girgiza kai Anty Ramlah ta yi tana jan hannunta ta ce“a'a idan mun je can kya yi” da ɗan mamaki ta ce“Anty to ina zamu je?” Harararta Anty Ramlah ta yi ta ce“kin tashi ko isata zaki yi da magana?” Zumɓura baki ta yi sannan ta tashi a hankali, Hijabin dake ajiye kan drawer ɗinta ta ɗauka ko gama zurawa bata yi ba Anty Ramlah taja hannunta suka yi waje. A parlon suka tsaya Amma ta ce“dan Allah Ramlah kar ku dade a zo a isheni.” Murmushi Ta yi ta ce“To idan ba'a gama ba ai ba zamu dawo ba Yaya.” Shiru Amma ta yi, can kuma ta sauke numfashi ta ce“to Allah ya tsare hanya.” da Amin ta amsa sannan suka yi waje, suna ƙoƙarin shiga mota, suka ƙaraso compound ɗin, Da idanu Nana ta dinga bin su ganin sun zo inda take yasa ta ɗaga mata hannu. Ita ma Amrahn daga mata hannu tayi tana murmushin, ganin ya kalli inda take yasa ta ɗan sunkuya a sanyaye ta ce “Ina kwana Yaya.” Fuska a sake ya amsa mata sannan ya gaisar da aunty Ramlah ta amsa ta ce“Sultan ya gida ya iyalin?” murmushi ya yi ya ce“Alhamdulilah Anty ya kids?” “Suna nan kalau” ta ce a sake. Jinjina kansa ya yi ya ce“Tam a gaishe min dasu pls” zasu ji ta ce sannan suka yi gaba ita kuma ta buɗe motar ta shiga, a sanyaye Nana ta shiga motar lokaci ɗaya taji ranta ya sake ɓaci. Aunty Ramlah bata ko kalleta ba ta yiwa motar key suka bar Estate. **** Wajejen ƙarfe 3:00 na rana Maimoon ta shigo parlon bakinta ɗauke da sallama. Bata samu kowa a ciki ba, kamar ta juya ta fita sai kuma taja ta tsaya tana jiran taga ta inda zata fito, bayan mintinan da basu shige biyar ba Zahra ta fito daga kitchen Saboda kiran wayarta da taji, sai dai ganin Maimoon ya sanyata tsayawa ta ce“Laaa Maimoon ke ce a gidan yau?” babu yabo babu fallasa ta ce“Eh ina yini?” “Lafiya kalau ya gida?” Zahra ta amsa mata da fara'arta. Taɓe baki Maimoon ta yi dan ba abin da ya kawota ba kenan ta ce“Daman Atta ke kiranki.” shiru Zahra ta yi da mamaki ta ce“Atta kuma? Meya faru” girgiza kai Maimoon ta yi cike da rainin hankali ta ce“A'a ni ban sani ba gaskiya sai dai idan kin je kya ji. amma kuma kamar akan maganar tariyar amaryar da za'a yi an jima ne.” Maimoon ta ƙare maganar tana sakin wani kyakkyawan murmushi na zallar rainin hankali, Kallonta kawai Zahra ke yi can kuma ta danne zuciyarta ta ce“Tom gani nan in sha Allah.” “Yauwa da yafi dai.” Ta ce tana juyawa, sai da taga ta fice daga ɗakin sannan ta zauna kan sofa hawayen da take ta maƙalewa suka gangaro kan fuskarta. Wani irin zafi take ji a zuciyarta, kenan tun kafin ta shigo sun fara nuna mata irin abin da zasu yi, kenan zata zama shara a cikin gidan, Ta ɗora kanta bisa cinyarta tana fashewa da kuka. Ta dade a wajen tana kukan ganin ba zai kai mata ba ya sanya ta ɗago kanta ta ɗauki wayarta da ke kan table ta danna numbern Aunty Khadijah. Sai da kusa katsewa sannan ta ɗaga. Zahra ta kasa cewa komai sai kuka da take a hankali, Aunty Khadijah da ke zaune gaban motar wani Alhaji ta ce “Lafiya dai Zahra?” Cikin kuka ta ce“Aunty basa sona. Mutuwa zan yi wallahi, ƙirjina zafi yake min” cike da rashin fahimta ta ce“ban gane ba Zahra, me ya faru? Su wane basa sonki” “Yan gidan nan mana, basa son zama dani. Wai an jima zata tare, ya zan yi Anty?” Girgiza kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“ba dai bakya jin shawara ba Zahra? Yanzu kin ga Siyama na samun matsala dasu tun da taje? To ya ma za'a yi ta samu matsala bayan mun yi maganin matsalar, amma ke sam kin ƙi yarda, kin biyewa Umma da bata san me duniya ke ciki ba. Dan haka kuka yanzu ki ka fara shi wallahi, nan gaba ma sai sun koro ki daga cikin gidan baki ɗaya.” Zahra ta girgiza kanta tana kuka ta ce“A'a wallahi, in sha Allah ba zan bar gidan nan ba. Ba zan rabu da mijina ba, ki faɗa min me zan yi Anty? Wallahi zan yi koma mene ne muddin zan zauna lafiya a cikin gidan nan, dan Allah ki faɗa min me zan yi.?” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 44. Jinjina kai Aunty Khadijah ta yi sannan ta ce“alright we should talk later.” daga haka ta katse wayar saboda mutumin da yake gabanta. Zahra ta sauke numfashi ta sanya hannunta ta goge idanunta sannan ta tashi ta haye sama, Mayafi kawai ta dauko sannan ta dawo ƙasan, ta fito daga parlon jiki a sanyaye ta nufi apartment ɗin Hajiya Babba. **** Anty Ramlah ce tsaye gabanta. Ta kai mata duka tana cewa“ke Nana tashi mu tafi!” a ɗan firgice ta buɗe idanunta sai kuma ta tura baki, Ta sanya hannunta wanda yaji red henna gaba da baya. Ya yi wani irin kyau kamar a fatar hannun aka halicce shi. Ta murza idanunta a shagwaɓe ta ce“To Anty yanzu zamu tafi?” Gyaɗa mata kai ta yi ta ce“to ba an gama komai ba?” Sai a sannan ta kai hannunta kanta, jin yanda ya yi wani irin santsi ya sanya ta miƙe tsaye tana kallon console mirror ɗin da ke wajen. Juyowa ta yi tana washe baki ta ce“Anty ji kaina ya yi kyau.” murmushi Anty Ramlah ta yi kafin ta ce“Eh mana gashinan kinyi kyau abin ki, da an ganki an ga amarya.” sunkuyar da kanta ta yi tana sosa kai, Anty Ramlah ta sake murmushi sannan ta ce“oyaa zo mu tafi Amma ta fara kira.” To kawai ta ce sannan ta ɗauki hijabinta ta zura, Anty Ramlah ta ƙarasa cashier ɗin wajen ta biya kudaden sannan suka fita daga shagon. Bayan sun shiga mota sun fara tafiya Anty Ramlah ta ce“Nana zamu je na amso saƙo nan Jalo” Kallonta Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce“Kuma dai Anty? Ni fa na gaji” harararta ta yi tana shan kwana ta ce“to ai sai ki yi ta gajiyar.” Tura baki Nana ta yi kafin ta koma ta jingina da kujerar motar idanunta ƙur akan titi tana kallon motocin da ke shigewa, Time to time take tuna maganganun Anty Ramlah, wani ta yi dariya wani kuma ta tura baki, murya can ƙasa ta ce “Wai uncle ɗin tab!” “Magana ki ka yi?” Anty Ramlah ta tambayeta ba tare da ta kalleta ba, girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce“A'a.” Bata sake ce mata komai ba har suka ƙarasa Gibson Jalo ɗin, Ta buɗe motar ta sauka tana kallonta ta ce“ki jirani ina zuwa” gyaɗa mata kai ta yi, Ta juya ta nufi gidan da yake kallon su. Tun Nana na jure zaman motar har sai da ta gaji, ga yunwa da take ji, ga kuma gajiya. Kanta har wani ciwo yake mata, sai bayan kusan mintuna talatin sannan Anty Ramlah ta ƙaraso wajen hannunta riƙe da wata jaka mai ɗan fadi, Ta buɗe back seat ta ajiye sannan ta dawo driver seat ɗin ta tada motar suka bar wajen. Har suka ƙarasa gida babu wanda ya ce komai a cikin su, Tana gama parking Nana ta fito ta nufi balcony ɗinsu da sauri, Sai dai kafin ta kai ga ƙarasawa taji an kira sunanta. Cak ta tsaya tana zumɓura baki a fili ta ce“Na shiga uku!" Ta juya tana kallon Maimoon dake ƙarasowa wajen, Kamar zata yi kuka ta ce“mene ne dan wallahi nagaji” hararara ta zabga mata sannan ta ce“To Atta ke kiranki” haɗe rai ta sake yi sannan ta ce“to ni wallahi ba zan je ba!” daga haka ta juya ta nufi cikin gidan su da sauri. Da idanu kawai Maimoon ta bita dai-dai nan Anty Ramlah ta ƙaraso wajen, Ta gaisar da ita cike da girmamawa, Amsawa ta yi kana ta ce “Maimoon ya jikin?” Sunkuyar da kai ta yi sannan ta ce“Alhamdulilah Anty” “Sannu Allah ya raba lafiya.” Anty Ramlah ta yi maganar tana kallonta, Da amin ta amsa sannan ta ce“Anty kawo na riƙe miki kayan” waro idanu ta yi lokaci ɗaya kuma ta girgiza kanta ta ce“haba dai rufa min asiri, na wahalar da ke. Shiga ciki kawai” Ɗan murmushi ta yi dan daman ba wani daɗin jikinta take ji ba kawai dan Atta ta takura mata ne ya sanya ta fito. Ganin tana ƙoƙarin yin gaba yasa ta ce“Aaa Anty dan Allah idan kin shiga ki saka Nana ta zo, Atta ke kiranta kuma ta ce wai ba zata je ba.” Girgiza kai Anty Ramlah ta yi ta ce“Allah ya shiryi Nana, tam zan turota” okay kawai ta ce sannan ta juya ta bar wajen, ita kuma ta nufi cikin gidan. Kwance ta sameta a parlon kan cinyar Amma, ta ajiye jakar hannunta ta zauna ta ce“wash!” “Sannu sai yanzu?” Amma ta tambaya tana kallonta. Jinjina mata kai ta yi kafin ta ce“wallahi Yaya, kin san sai da suka mata gyaran jiki sannan aka mata Henna da saloon. Kuma na biya gidan matar can na amso magungunan da turaren” Amma ta ce“Shiyasa ku ka daɗe, Yanzu ku fara cin abinci sai ki ƙarasa.” zare mayafin jikinta ta yi sannan ta ce“a'a ni a ƙoshe nake wlh, Nana tashi muje” kamar zata yi kuka ta ce“Ina kuma? Ni Allah fa nagaji sosai, kaina ciwo yake.” Harararta Amma ta yi ta ce“ɗagani ni. So ki ke kakarki ta zo ta fara azazzalata ko me? Tashi mana.” dakyar ta miƙe zaune har da yan hawayenta ta ɗauki hijabinta ta shige ciki, Da idanu kawai Amma ta bita sai kuma ta ɗauke kanta ta ce“Allah ya shiryeki.” Miƙewa Anty Ramlah ta yi ta ɗauki jakar da ta shigo da ita sannan ta bi bayanta. **** Ana idar da sallar isha'i Atta na shigowa parlon, Ta dinga ƙarewa ko wace kusurwa kallo kafin ta taɓe baki ta shiga kiran sunan Amma. Amma da ke kitchen ta fito hannunta riƙe da spoon da bata san ta ɗauko ba saboda kiran Attan. Ganin ita ce tsaye a tsakiyar parlon ya sanyata sakin murmushi kafin ta ce“Atta ke ce da daren nan?” “Yo ba dole ki ganni da daddare ba, kin ƙule ƴa a ɗaki kamar zaki mayar da ita ciki. Cewa nayi da la'asar za'a kaita amma gashi har ana sallar magriba babu ita babu labarinta, to zuwa nayi na tafi da ita.” Murmushi kawai Amma ta yi dan ba zata iya da halin Atta ba ta ce“ai tana ɗaki Nanan” Bata sake kallon inda take ba ta nufi hanyar ɗakin Nanar tana gyara mayafinta da ke sakkowa kafaɗarta. Suna zaune a ɗakin, Ban da ƙamshi babu abin da ke tashi. Wani irin sassayan ƙamshin humra ne wanda ya hadu dana turaren kwalba haɗi dana kabbasa. Ita kanta Anty Ramlah da ba ita aka sakawa turaren ba ƙamshi take, Nana na zuane gefenta ta rufe fuskarta da wani golden ɗin mayafi mara kauri, sai shessheƙar kuka take a hankali. Atta ta shigo ɗakin babu ko sallama, Turus ta yi ganinsu zaune, ta ƙarasa ciki tana kallon su ta ce “A'a wallahi kul Ramlah ki ke ko wa? Akan me zaki riƙe min ƴa anan? Yarinya za'a sadata da ɗakin mijinta kin zo kin wani sakata a maƙata ko me ki ke ce mata ohho?” Murmusawa Anty Ramlah ta yi tana tashi daga wajen ta ce“Allah ya huci zuciyarki Atta. Gata anan ai mun gama” ”Ku ka gama me? Hala dai ba wani mugun abun ki ka kitsa mata ba.?” Atta ta yi maganar tana ɗage lulluɓin dake kan Nanar, Kifa fuskarta ta yi a tsakanin cinyoyinta tana ƙara volume ɗin kukanta. Ɗago kanta Atta ke son yi amma fur taki yarda, ta saketa tana yin baya ta ce“a'a wallahi ki je dan kan ki. Tashi ni muje a kai ki ɗakin mijinki” Tamkar ta sake tura Nana haka ta sake rushewa da wani sabon kukan, Anty Ramlah ta koma ta riƙe hannunta dake cikin mayafin ta ce“Ba na ce miki ki daina wannan kukan ba? Taso maza.” Sake kwace hannunta ta yi tana ci gaba da kukanta. Anty Ramlah ta yi tsaki ganin tana son bata musu rai ta ce “Ran ki zai ɓaci kuma Nana tashi na ce miki!” Ta ƙare maganar a tsawace, Harararta Atta ta yi cikin tsawa ita ma ta ce“A'a dakata! Ya yarinya ita kaɗai ubanta ya mallaka zaki dinga mata tsawa? Ƴar da za'a lallaɓata ko kin manta gidan miji za'a kaita?” Ko saurarenta Anty Ramlah ba ta yi ba ta ja hannun Nana ta sakko da ita daga kan gadon. Lace ne a jikinta mai kyau da tsada golden mai ratsin coffee, ɗinkin doguwar riga wadda ta kama mata jiki. Anty Ramlah ta gyara riƙon da ta yi mata bayan ta sauke mata mayafin ta ja hannunta suka bar ɗakin, Da idanu Atta ta bi su can kuma ta biyo bayansu kamar zata faɗi saboda sauri. A parlon suka sami Mama wadda shigowarta kenan don tafiya da Nana, Anty Ramlah ta miƙa mata hannunta. Riƙewa Mama ta yi kamar jira Nana take ta sake fashewa da kuka, Amma da ke tsaye ta ƙarasa gabanta. Ɗaga mayafin ta yi tana murmushi mai haɗe da hawaye ta ce “Haba Nanata ki daina kin ji. Yanzu kin zama babba fa” Sake fashewa ta yi da kuka ta faɗa jikin Amma ta ƙanƙameta, ita kanta Ammar kasa bata haƙuri ta yi dan ita ma kukan take, koda wasa bata yi tunanin nan kusa zata kai Nana ɗakin miji ba. Sai gashi yau zata rabu da ita, duk da ba nisa zata yi ba sai taji kamar zasu rabu ne. Anty Ramlah ce ta ƙarasa wajen ta janye Nana daga jikinta cikin son kwantar mata da hankali ta ce“Yi haƙuri mana Yaya. Idan kina kuka to ita ta ina zata yi shiru?” Gyaɗa mata kai Amma ta yi tana goge hawayenta. Mama ta sake riƙe hannun Nana tana kallon su ta ce“to Ramlah ko zaki biyo mu ne?” Girgiza kai Anty Ramlah ta yi dan ta san sai sun fara kaita apartment ɗin Hajiya Babba ta ce“a'a kawai ku je, Allah ya bada zaman lafiya.” da Amin suka amsa duka sannan suka yi waje, Atta ta bi bayansu da sauri. Kai tsaye apartment ɗin Hajiya Babba suka nufa da ita, koda suka shiga gaba ɗaya sauran suna zazzaune, Papa, Abba, Hajiya Babba, Aliyu. Mama ta shiga da ita ta zaunar da ita can kusa da Hajiya Babba sannan ita ma ta nemi kujera ta zauna, Papa ya buɗe wajen da addu'a sannan aka yi salati, kafin ya fara magana ya ce“Ina Abdusammad ɗin kuma?” “Yana hanya Papa." Aliyu ya bashi amsa da sauri, ko rufe baki basu yi ba ya buɗe ƙofar parlon ya shigo. Nan da nan ƙamshi turarensa ya gauraye parlon, sanye yake cikin wata dakkakiyar shadda Madam gezner ash colour, Ya ɗaura hular zanna akansa. Ɗinkin babbar rigar ya amshe jikinsa sosai ya zauna akan a jikin aka ɗinka, ƙafafunsa sanye da Gucci shoes ash colour, Idan aka ce ka yi rating nasa to tabbas za'a iya bashi ɗari a ciki goma. He looks quite and elegant, Duk da fuskarsa a haɗe take babu annuri hakan bai hana kyansa bayyana ba, farar fatarsa sai sheƙi take, kana ganinsa kada ango sabon aure. Ya saki ƙofar ganin yanda suke kallonsa ya sanya ya sake tsuke fuskarsa, Kujerar da Aliyu ke kai ya ƙarasa ya zauna sannan ya gaishe su ɗaya bayan ɗaya, suka amsa a sake sannan Papa ya fara bayanin da zai yi. Nasiha sosai ya yi musu daga shi har ita, kana ya yi fatan Alkhairi, Hajiya Babba ma ta yi tata maganar sannan Atta. Abba kuwa cewa ya yi bashi da abin faɗa, dan haka Mama ta rufe taron da addu'a suka shafa. Bayan an kammala komai Mama ta miƙe tana shirin wucewa gidanta, Atta ta yi saurin cewa“to idan ki ka tafi kuma wa zai kai yarinyar ɗaki?”. Kafin Mama ta yi magana ya miƙe yana kallonsu fuskarsa a sake saɓanin ɗazu ya ce“no need Atta. Zan tafi da ita” ya yi maganar babu alamar damuwa ko kunya akan fuskarsa, Jinjina kai Papa ya yi ya ce“hakan ma ya yi, ku je kawai Allah ya bada zaman lafiya.” Da Amin ya amsa sannan ya nufi inda Nana ke zaune, kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce“taso mu tafi” ya ƙare maganar yana miƙa mata hannunsa na dama, Ta cikin mayafinta ta ga hannun nasa, amma ta ƙi ɗora nata ta mike tsaye tana kuka ƙasa-ƙasa ta yi gaba. Bin bayanta ya yi bayan ya sake musu sallama, Abba ya lumshe idanunsa yana jin wata nutsuwa na saukar masa, at least dai ya aurar da ƴarsa. Cikin zuciya ya furta “Alhamdulilah, ur home is blessed Nana.” A fili kuwa kasa cewa komai ya yi, sai jingina kansa da ya yi da jikin kujera. Atta kuwa haɗe rai ta yi ta tashi ta haye sama dan sam ba haka ta so ba, ta so ne ta je gidan saboda ta ga Zahra. Da idanu Papa ya bita dan ya riga da ya gama gano shirinta ya girgiza kansa yana murmushi, tashi Aliyu ya yi ya musu sallama sannan ya nufi sana sashin. Su kuma suka ci gaba da maganarsu. Tafiya suka dinga yi yana gaba tana bin sa a baya, gaba ɗaya ta kasa yin sauri, ga matsewar da lace ɗin jikinta ya yi mata, ga kuma gajiya, ga yunwa dan sam bata samu damar cin abincin ba. Ganin yanda ya yi gabs abin sa ya sanyata tsayawa, ta dinga kallon sa ganin ko sau ɗaya bai waiwayo ba, Tana tsaye a wajen har ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shige ciki. Silalewa ta yi a wajen ta fashe da kuka, ita wace irin Amarya ce? Babu wanda ya rakota gidanta, sannan kuma shi kansa mijin ba zai iya jiranta ba ballantana ya jera da ita. Ta kifa kanta akan cinyoyinta tana kuka kamar ranta zai fita. Abdusammad na shiga ya mai da ƙofar yana shirin rufewa, sai a sannan ya lura da cewa bata bayansa, ya ɗan ware Idanunsa sai kuma ya saki ƙofar da sauri. Dube-dube ya dinga yi a balcony ni ɗin amma sam bai hangeta ba, dan haka ya fara tafiya yana kalle-kalle. Ya yi nisa ya hangeta tana tafiya a hankali, ya ɗan ja tsaki sannan ya ƙara saurinsa. Gabanta ya sha yana kallonta fuska a haɗe ya ce “Ke mene ne haka? Ina zaki je?” Banza ta yi masa, ta matsa ɗaya gefen ta ci gaba da tafiyarta tana kuka fuskarta rufe da mayafinta, Rai ɓace ya sake yin gaba ya jawota ta dawo gabansa yana kallonta fuska babu alamar walwala ya ce “Yaushe na fara wasa da ke Nana?. Shige mu tafi!” Cikin kuka ta ce“Wallahi ba zan bika ba, ni gida zan koma. Ai baka sona” Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka, Kallonta ya dinga yi yana mamakin abin da ta ce, can kuma ya saki murmushi ya kamo hannunta ya ce“sai ina son ki zaki bi ni kenan?” ƙoƙarin kwace hannunta take sai dai rikon da ya yi mata bana wasa bane, dan haka ta ci gaba da kukanta tana cewa“Ni wallahi ba zan zauna da ku ba.. Ni wajen Ammata zan koma” ta juya tana shirin tafiya, Dafe kansa ya yi ganin tana son wahalar dashi a banza. Ya juyo da fuskarta ba tare da ya zare mayafin data rufe fuskar ba ya ce“Kina son na makeki anan ne?” Madadin ta bashi amsa sai kawai ya ga ta zauna a wajen, ta sake rushewa da wani sabon kukan tana ƙoƙarin birgima a ƙasan. Wani dogon tsaki ya ja ganin tana shirin raina masa hankali yasa ya sunkuya kamar zai mata magana kawai taji ya ɗauketa tamkar Baby ya fara tafiya da ita, zille-zille ta fara yi tana son kwace kanta, sai dai sam bai bata wannan damar ba ya sake matseta da jikinsa yana ci gaba da tafiya. Ta dinga kuka tana cilla ƙafafunta har suka ƙarasa gidan, ya murɗa handle ɗin ƙofar da hannunsa ɗaya sannan ya shige ciki da ita. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 45. A parlon ya direta yana watsa mata wani mugun kallo ya ce“Idan wasa nake miki ki sake fita.” tura baki ta yi, Ta ɗan janye mayafin nata ba sosai ba, ɗaya bayan ɗaya ta dinga ƙarewa komai na parlon kallo. Ko ina tsaf dashi sai tashin ƙamshi yake, Ya nufi hanyar upstairs ba tare da ya sake bi ta kanta ba. Gajiya ta yi da tsaiwar, cikinta ban da ƙugin yunwa babu abin da yake. Ta kalli hanyar upstairs ɗin sai kuma ta nufi wajen da sauri, A corridor ɗin saman ta tsaya, ta dinga ƙarewa ɗakunan kallo dan babu inda bata sani ba. Extra room ɗin ta buɗe ta shiga, kamar yanda ta yi tunani kuwa anan ne aka zuba mata kayan furnitures ɗinta da Abba ya siya mata. Ta ƙarasa ciki tana sauke numfashi, Cire mayafin ta yi ta ajiye a gefen gadon, Ta zame ɗankwalin lace ɗin ta ajiye shima sannan ta hau gadon ta zauna tana sauke numfashi. Koda ya shiga ɗakin zaune ya sameta gefen gado ta yi shiru tana tunani, tun bayan kiran da Umma ta yi mata taji jikinta ya yi sanyi kalau. Ya karasa ciki yana kallonta ya ce“Zahra" Ɗago kanta ta yi ta kalleshi da kumburarrun Idanunta wanda suka sauya kala, wata embroidery Atampa ce a jikinta mai pattern, ɗinkin t boubou mai kyau. Sai dai sam babu walwala akan fuskarta, Ya tsaya a gaban gadon yana kallonta ya ce“Tashi muje ƙasa.” “Sun kawota ne?” Ta tambaya a sanyaye, Jinjina mata kai ya yi dan bai ji zai iya magana ba. Zahra ta miƙe a sanyaye ta yafa mayafin dake hannunta sannan ta yi gaba. Ya sauke ajiyar zuciya sannan yabi bayanta. Da mamaki ya dinga kallon parlon ganin wayam babu Nana babu dalilinta, Ya dafe kansa yana tunanin Allah ya sa ba wani wajen ta sake fita ba, gaba ɗaya so take ta wahalar da rayuwarsa. Ɗan tsaki yaja sai kuma ya nufi ƙofa fita daga parlon, Zahra ta bi shi da idanu tana mamakin inda zai je. Babu in da bai duba ba a compound ɗin amma bai samu Nana ba, kuma shi ba zai iya zuwa Apartment ɗin ba yanzu ya ce ina take. Ya tsaya yana tunanin yanda zai yi, Can kuma ya juya ya koma gidan, yana shiga parlon ya tsaya turus ganinta da ya yi tsaye tana rarraba idanu. Ya ƙarasa gabanta da sauri kamar zai daketa ya ce “Ina ki ka je?” Hawayen da yake maƙale cikin kurmin idonta ne ya shiga zirarowa kan fuskarta. Ta kwaɓe fuska kamar ƙaramar yarinya ta ce“Uncle cikina” “Ina miki wata maganar kina min wata? Na ce ina ki ka je.?” Tura baki gaba ta yi ta ce“Ni fa babu inda naje, ɗakina na tafi.” ya maka mata wata uwar harara sannan ya nufi kujera ya zauna, kamar jira take tabi bayansa ta zauna kusa da shi ta ɗora kanta gefen kafaɗarsa, ƙoƙarin janyeta ya dinga yi amma sam taƙi yarda, ta zura hannayenta duk biyun ta cikin hannunsa ta riƙe shi gam. Zahra ɗauke idanunta ta yi kamar bata gansu ba, Ya sauke numfashi kafin ya yi gyaran murya cikin nutsuwar data gama ratsa shi ya fara musu nasiha, Duk wani abu wanda ya kamata ya sanar musu akan haƙƙin zaman tare sai da ya sanar musu, daga bisani ya yi wa Nana faɗa dan ya san tsaf zata iya nemar fitina. Sannan ita ma Zahra ya yi mata nata faɗan daban, Bayan ya kammala ya sanya suka yi addu'a sannan ya miƙe yana janye Nana daga jikinsa ya ce “Sai da safe.” Ya yi maganar yana kallon su duka, Tashi Nana ta yi ta ce“uncle.” kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce“mene ne?” “Ni ina kazata?” Ɗan mitsi-mitsi ya yi da idanunsa kafin ya ce“kaza? Kazar me?” Kamar zata yi kuka ta ce“to ba amarya ba ce ba ni? Kuma ai ana siyawa Amarya kaza. Kuma ni naga baka siya min ba” tsuke fuska ya yi ya gyara tsaiwarsa yana kallonta sosai ya ce“yaushe na fara wasa da ke Nana?” sunkuyar da kanta ta yi saboda kaifin da idanunsa suka mata, Ya ja dogon tsaki sannan ya nufi upstairs da sauri. Shiru Nana ta yi tana kallon ƙasa, ta maƙale hawayenta gudun kada Zahran ta gani ta nufi saman ita ma, Zahra kuwa tashi ta yi jiki a saluɓe tabi bayansu, kowa ɗakinsa ya shige daban. Nana na zuwa ta faɗa kan gado ta fara birgima tana kuka, To ina aka taɓa kai Amarya ba'a siya mata kaza ba? Daman haka ake auren?. Ta sake rushewa da wani sabon kukan, Ji tayi kamar ta tashi ta yi tafiyarta, sai dai sanin dare ya yi ya sanya ta fasa ta ɗauki aniyar gobe da sassafe zata yi wucewarta. Da wannan tunanin ta tashi ta zame kayan jikinta sannan ta nufi toilet ɗin da yake dakin, wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala kamar yadda ta saba duk dare, tana fitowa ta nufi press ɗinta inda aka jera mata kayanta sabbi ta buɗe. Wata sleeping dress ta ɗauko mara nauyi ta saka sannan ta nufi kan gadon, ta kwanta ta ja lallausan duvet ɗin ta rufe gaba ɗaya jikinta. Gajiya da kuma yunwar da take ji su ne suka taimaka wajen hanata bacci, ta dinga juyi akan gadon tana riƙe da cikinta, can kuma ta miƙe kamar wadda aka zabura ta tashi ta nufi toilet. Ƙaƙarin amai ta dinga yi amma kasancewar babu komai a cikinta ya hana aman zuwa, ta gaji ta kuskure bakinta ta dawo ɗakin. A wahale ta koma ta kwanta, ta ci gaba da mata gungun ɗinta a wajen har bacci ɓarawo ya ɗauketa. Da asubah ya shigo ɗakin bayan ya dawo daga Masallaci, kwance ya hangeta ta dunƙule jikinta waje ɗaya. Ya girgiza kansa sannan ya ƙarasa ciki, ɗan dukanta ya yi da hannunsa yana faɗin “Nana! Ke Nana!” Dakyar ta buɗe idanunta, ta kasa tashi saboda ciwon da cikinta ke mata. Daga kwance ta dinga kallon sa tana murza idanunta, Ya kafeta da idanu ya ce“tashi ki yi sallah” ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya sake cewa komai ba. Da idanu kawai Nana ta bi shi sai kuma ta rufe idanun, hawaye suka fara zirarowa ta gefen idanun. Ta daɗe a haka har sai da gari ya fara haske sannan ta yunƙura ta tashi, ta zura slippers ɗin dake ƙasan gadon sannan ta nufi toilet tana tafe kamar iska zai hureta. Wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala ta fito tana gyara ɗaurin towel ɗin jikinta, a hankali ta ware idanunta lokaci ɗaya kuma ta saki wani ihu ta sanya hannayenta duk biyun ta rufe fuskarta. Da mamaki ya dinga kallonta can kuma ya miƙe ya karasa wajen ganin yanda take abu kamar wata zararriya, duk tunaninsa wani abun ta gani dan haka ya jawota jikinsa gaba ɗaya ya rungumeta. Ai kamar ya sake turata haka ta ci gaba da ihunta tana ƙoƙarin janye jikinta, kallonta ya yi jin towel ɗin dake jikinta na neman kwancewa, Ya sanya hannunsa na hagu ya riƙe shi gam kafin ya ce “Ke lafiyarki? Mene ne?” Janye jikinta ta yi tana ci gaba da kukanta, Ya kai hannu ya taɓa wuyanta yana cewa“ko baki da lafiya ne?” “Ni ka fita uncle!” Ta yi maganar cikin kuka. Da mamaki yake kallon ta sai kuma ya ce“me yasa?” “to babu kyau ganin tsirarar mutum, kuma sai ka shigo ban saka kaya ba?” Cewar Nana ta sake ƙanƙame idanunta ita a dole ba zai ganta ba. Wani dogon tsaki ya ja, ya dinga kallon ta rai ɓace, to me take tunani? A ɗan fusace ya ce “mene ne a tsirarar naki da har zan kalla?.” Turo baki ta yi tana ɗan buɗe idanunta, ganin yanda ya haɗe ransa ya sanyata sakin idanun. Ta bar wajen da sauri, Press ta buɗe ta ɗauki Abaya sannan ta koma toilet ɗin. Takaici da baƙin ciki ne ya sanya shi fita daga dakin, a ransa yana jinjina haukanta. Koda ta fito daga bayin samu ta yi baya nan, ta sauke ajiyar zuciya tana rike da veil ɗin Abayar. Can kuma wata zuciyar ta ce mata “To wane bai san jikin ki ba? Bayan hotunan ki da kowa ya gama gani? Da gaske yake mene ne abun ɓoyewa a jikin ki?.” Nana ta ja dogon numfashi lokaci ɗaya hawaye na kawowa cikin idanunta. Tabbas bai cancanci ta ɓoye jikinta ba, dan kowa ya gama gani. Ta koma gefen gado ta zauna ta haɗe kanta ta gwuiwa ta fashe da kuka. Ta jima sosai a wajen har sai da ta yi mai isarta sannan ta tashi, ta koma toilet ta wanke fuskarta sannan ta fito, veil ɗin rigar ta yafa akanta, ta sake shi loosely sannan ta fito daga ɗakin. Bata samu kowa a main parlon ba dan haka ta yi ficewarta ba tare da damuwa ba. Kai tsaye apartment ɗinsu ta nufa, tana zuwa ta tsaya a bakin ƙofar ta dinga knocking, sai dai har bayan mintuna goma babu alamar za'a zo a buɗe. Dan haka ta juya ta bar wajen tana yan matan hawayenta. Rasa inda zata je ta yi, gashi yunwa na neman illatata, dan haka kawai ta nufi apartment ɗin Hajiya Babba dan ta san nan ne kawai a buɗe. Bakinta ɗauke da sallama ta murɗa handle ɗin ƙofar, Hajiya Babba da ke zaune kan sofa ta amsa tana kallonta da mamaki. Jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa ciki ta durƙusa har ƙasa ta gaisheta. “Nana lafiya dai? Ina Abdusammad ɗin?” Hajiya Babba ta yi tambayar tana kallon ta bayan ta zauna gefenta. Madadin ta bata amsa sai kawai ta fashe da kuka tana faɗawa jikinta, Hankalin Hajiya Babba ya tashi ta ɗagota tana faɗin “mene ne? Me ya yi miki?” Kasa magana ta yi saboda kukan da ya ci ƙarfinta. Dai-dai nan Atta ta fito daga kitchen hannunta riƙe da madaidaicin plate mai ɗauke da soyayyen dankalin turawa, Ta ƙaraso wajen da sauri tana faɗin “wa nake gani kamar ƴar gidan Ahmadi?” Gyada mata kai Hajiya Babba ta yi kafin ta ce“Eh ita ce Atta.” “Subhannallahi, Ba dai yaron nan har ya aikaceta ba babu tausayi, mu sam lokacin mu ba haka ake ba wallahi tallahi, sai yarinya ta girma sannan. Amma saboda jaraba ta ya'yan yanzu da an kai musu yara sai su haike musu, wannan ai magunta ce fisabilillahi.” Atta ƙare maganar cikin kunfar baki. Shiru Hajiya Babba ta yi dan ita ma abin da ta ya zo ranta kenan. Ta sake ɗago Nana da ke kuka kamar ranta zai fita ta ce“Ya isa haka Nana. Faɗa min me ya yi miki?” “To me za ki tambayeta kuma fisabilillahi, bayan ga abu nan ƙiri-ƙiri?” Atta ta jawo hannun Nana tana makon ta ta ce“Saboda Allah Hadiza faɗa min me ya yi miki? Ni wallahi yanzu sai na shirya naje na ci masa mutunci. Ina ganinsa kamar mai hankali ashe ba haka bane?” Dakyar Nana ta kwace jikinta saboda yanda Attar ta cacumeta, Ta yi baya tana fadin “Ni ki cikani jikin ki duk ƙashi!” Ta yi maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan. Mitsi-mitsi Atta ta yi da idanu kafin ta ce“Ji min ruɓaɓɓiyar yarinya! To a shekaruna idan ba'a samu ƙashi a jikina ba me za'a samu?” Babu wanda ya tanka ta a cikin su, dan haka ta yi shiru tana kallon su. Hajiya Babba ta kalli Nana murya a sanyaye ta ce“faɗa min me ki kewa kuka?” Nana ta fara murza idanunta tana ƙoƙarin tsagaitawa da kukan ta ce“Hajiya ko ba uncle bane. Tun jiya ban ci abinci ba! Kuma yunwa ta kusa kasheni” Da mamaki Hajiya Babba ta ce“babu abinci kuma? Baki ci abinci ba?” gyaɗa mata kai Nana ta yi tana kuka. Hajiya Babba ta girgiza kanta kafin ta kira wata maid, bayan ta zo ta ce ta kawo mata abinci. Ba'a fi 5mins ba ta dawo hannunta riƙe da tray, Ta ajiye gabansu sannan ta juya ta bar parlon. Nana ta zame ta sauka kasa ta ja tray ɗin, tea flask ɗin ta buɗe ta tsiyaya tea ɗin sannan ta saka sugar kaɗan ta fara sha. Dakyar take haɗiyewa yana ƙoƙarin dawo mata saboda yunwar data riga da ta gama cinyeta, ta ajiye mug ɗin sannan ta fara cin soyayyen Irish potato ɗin tana haɗawa da kwan. Tass ta cinye sannan ta miƙe tana gyatsa, Hajiya Babba da ke jan counter ɗin hannunta ta ce “kin ƙoshi?” Gyaɗa mata kai Nana ta yi, ta karasa kan doguwar sofa ta kwanta nan da nan bacci ya ɗauketa. Hajiya Babba ta dinga kallonta ganin yanda take ta kwaɓe fuska a cikin baccin. Kafin daga bisani ta ɗauke kanta tana murmushi. **** Ringing ɗin wayar data ji ne ya sanyata fitowa daga parlon, ta kalli Haule dake kallon tv sai kuma ta kalli inda ta ajiye wayar tata. A ɗan fusace ta ce“ke baki ga ana kirana ba? Ba zaki iya zuwa ki faɗa min ba?” jiki a sanyaye Haule ta kalleta sai kuma ta ce“Allah shi baki haƙuri” ta yi maganar tana ɗauke kai, Kwafa Siyama ta yi sannan ta ƙarasa ta ɗauki wayarta ta koma kitchen ɗin. Ganin sunan Mommynta ya sanya ta ɗaga, Aunty Khadijah da ke zaune gefen gado ta ce “Siyama ya gidan?” Ɗan taɓe fuska ta yi kafin ta ce“Gashi nan dai. Amma kin san me Mom?” girgiza kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“a'a sai kin faɗa” “Ni fa wallahi ban ga kuɗin da ki ke magana ba. Safwan bashi da kuɗi kamar mijin Anty Zahra. Bana ganin zamu samu abin da muke so, and kuma kwanan nan gaba ɗaya bashi da lafiya, ko kusa dashi naje sai ya ce na tafi, ballantana na yi aiki da maganin da malamin ya bamu.” Shiru Anty Khadijah ta yi tana tunani, Siyama ta ci gaba da cewa “wallahi Mom ban jin zan iya zaman nan. Cause gaba ɗaya ba yanda nake son namiji na gansa ba, kuma ni bana son zaman gida shi kuma ba zai bari na fita ba. Kin ga kuwa ai akwai matsala” “Ke wace irin shashasha ce? Kina so ki ce min bashi da kuɗi ko me?” Anty Khadijah ta yi maganar rai ɓace. Girgiza kai Siyama ta yi ta ce“ba wai bashi da kuɗi ba, yana da shi, amma ba kamar mijin Anty Zahra ba. Ni wallahi dana sani ma shi na ce ba wannan ba” Numfasawa Anty Khadijah ta yi ta ce“wannan duk daga baya ne, ko kina nufin zaki auri mijin Zahra ne ku zauna tare?” Girgiza kai Siyama ta yi ta ce“haba dai mu zauna tare, Ni ba zan iya zama da kishiya ba wallahi. Ita ma wannan dan ban ɗauketa kishiya bane, kin san bai taɓa kwana daƙinta ba.” “kin ga wannan maganar bata waya ba ce, ki bari zan zo gidan na sameki.” Anty Khadijah ta faɗa saboda Umma da taga ta shigo ɗakin, to kawai Siyama ta ce sannan ta katse wayar, ta ajiye ta kan cabinet sannan ta ci gaba da abin da take. Tana gamawa ta fito ta tsaya tana kallon Haule dake zaune har sannan a parlon ta ce“Tashi na aikeki” Toh kawai ta ce sannan ta miƙe ta zura hijabin da ke Hannunta. Siyama ta nuna mata warmern data ajiye a kitchen ɗin tana cewa“ki ɗauka ki kai wa Hajiya Babba, saura ki zauna magana.” Babu musu Haule ta shiga kitchen ɗin, ita kuma ta nufi sama don shiryawa saboda magriba ta tawo. **** Around 9pm suna zaune a parlon, Noor na zaune a gefenta ta yi shiru tana kallonta ganin yanda take kuka kamar ƙaramar yarinya. Karasowa jikinta ta yi ta riƙeta cikin ƙaramar muryarta ta ce “Anty stop crying! Stop plsss!” Ta ƙare maganar tana sakin kuka ita ma, kallon ta kawai Nana ta yi sai kuma ta jawota jikinta tana ci gaba da kukanta. Suka dinga rera kukan a tare babu mai rarrashin su, wajejen 9:20 na daren aka buɗe handle ɗin ƙofar, Noor ta sauka daga jikinta da gudu ta ƙarasa inda yake ta rungumeshi. Durƙusawa ya yi dai dai tsayinta ya dinga kallon ta ganin yanda take kuka yasa ya ɗauketa yana faɗin “wane ya taɓa wa Abbie ƴar sa?” cikin shessheƙar kuka ta ce“Abbie kuka muke yi” yanda ta yi maganar cike da yarinta ya sanya shi murmushi. Ya zauna a kujerar da ke facing ta Nanar ya ɗorata kan cinyarsa ya ce “Kuka kuma? Me yasa?” Hannunta ta kai kan gemunsa tana murzawa a hankali ta ce“koba Anty Nana ba ce take kuka, to shi ne nake tayata.” Jinjina kansa ya yi sannan ya ce“Ai ko kin kyauta. Tashi ki je ki kwanta it's already late” to kawai ta ce sannan ta yi masa kiss a goshi ta sauka daga jikinsa ta ce“good night Abbie” “Allah ya tashe mu lafiya.” ya ce yana jan kumatunta. Murmushi ta sakar masa sannan ta ƙarasa inda Nana ke zaune ta ce“good night Anty.” gyada mata kai kawai ta yi, Noor ta nufi sama tana tafe da gudu. Sai da yaga ta bar wajen sannan ya zame jikinsa ya jingina da jikin kujerar yana kallonta ya ce“zo nan” jiki a sanyaye ta tashi ta ƙarasa wajen tana goge hawayenta wasu na sake zubowa. Ta zauna gefensa ta sunkuyar da kanta. Shiru parlon ya ɗauka na wasu mintuna kafin ya gyara zamansa yana kallonta sosai ya ce“mene ne kuma?” kamar jira take ta fashe da kuka, Ya dafe kansa a fili ya ce“oh ni Na shige su da Nana” ɗora kanta ta yi akan cinyarsa ta dinga rera kukan ta, ya yi shiru yana saurarenta kafin daga bisani ya ɗago kanta yana kallonta ya ce“rigimar mene ne? Me ki ke so?” Cikin shassheƙar kuka ta ce“uncle ko ba kai bane” ta yi maganar a shagwaɓe yana sake narkewa a jikinsa. Hannunsa ya sanya yana share hawayen fuskarta ya ce“too me nayi miki?” “Ba zaka siya min kaza ba?” Shiru ya yi yana kallonta, can kuma ya ce“kazar mene ne Nana?” Cikin son fahimtar dashi ta ce“kazar amarya mana. Maimoon ta ce min Yaya Aliyu ya siya mata kaza, kuma haka ma Hamida da Amrah suka ce min. To nima ba sai ka siya min ba dan Allah?” ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan. Murmushi ne ya kusa kwace masa, ya yi gyaran murya kafin ya ce“to ai ban shirya cin amarcin ba ballantana na siya kazar amarci” “To uncle ka shirya karɓar amarcin mana. Sai ka siya min kazar kaji!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 46. Ta yi maganar tana marairaice fuska. Ɗauke kansa ya yi yana kallon gefe, bai san sanda wani kayataccen murmushi ya kwace masa ba. Nana ta sake matsawa jikinsa tana leƙa fuskar sa. Juyowa ya yi yana kallon ta, Lokaci ɗaya kuma ya tsuke fuska kamar ba shi ba. Langwaɓar da kanta ta yi taja hannunsa na dama ta ce“kaji uncle...” janye hannunsa ya yi daga nata yana cewa“to idan na shirya siyan kazar zan miki magana. Ni yanzu bani da kuɗin siyan wata kazar amarci” zaro dara-daran idanunta ta yi can kuma ta tsuke baki ta ce“uncle kai ne baka da kuɗin?” jinjina mata kai ya yi yana ƙoƙarin tashi daga kan sofar, Nana ta mike tana riƙe da hannunsa ta ce“wallahi kana da kuɗi, kuma ma bayan duk ka fi su kuɗi” girgiza kansa ya yi yana ƙoƙarin ɓoye dariyarsa ya ce“ni ɗin?” ta gyaɗa masa kai tana marairaice fuska. Taɓe baki ya yi ya saki hannunta ya ce“to ni bani da wani kuɗi, gara ki kama kan ki.” daga haka ya yi gaba ya barta tsaye a wajen. Ɗan buga ƙafafunta ta yi a ƙasa kafin ta ce“to ni wallahi so nake na ci kazar!” Ta ƙare maganar tana hawaye. Ko saurarenta bai yi ba ya haye sama abin sa. Ta koma ta zauna kan sofar tana matsar kwalla, Bayan wasu mintina Zahra ta sakko daga sama tana kallon ta. Can kuma ta shige kitchen abin ta, bata jima ba ta zo ta sake shigewa sama, Nana ta miƙe tana ɗaukan hular saƙin dake kanta ta nufi saman ita ma. Ɗakinta ta tashi ta ƙarasa gefen gado ta ajiye hular sannan ta zauna ta jawo wayarta da ke gefen pillow. WhatsApp ta shiga dan daman wifi ɗin ta a kunne yake, Ta yiwa Khadijah sallama. Ganin bata online ya sanya Nana jan ɗan siririn tsaki ta yi wurgi da wayar sannan ta miƙe. Toilet ta nufa bayan ta zame yar rigar dake jikinta, ta yi wanka sannan ta fito tana tsane jikinta da towel. Press ɗin ta ta buɗe ta ɗauki wata yar yalolon riga mara nauyi ta saka sannan ta nufi gaban mirror ɗinta ta shafa mai, Bayan ta kammala ta nufi kan gadonta ta faɗa tana sakin numfashi. A hankali ta dinga ɗaga ƙafafunta Salam kwanciyar ruf da cikin da ta yi, Tana nan kwance a haka har bayan kusan mintina goma wayarta ta fara ringing, Hannunta ta saka ta janyo wayar tana daga kwancen, Ganin numbern Mimi ya sanyata juyawa ta kwanta dai-dai sannan ta daga kiran. Khadijah da ke kwance kan nata gadon ta ce “Hi Nana!” Haɗe rai Nana ta yi kamar tana gabanta kafin ta ce “Sai yau zaki nemeni?” Murmushi Khadijah ta yi ta ce“Afwan baby girl,Yar autar Ammarta.” Taɓe baki Nana ta yi ba tare da ta ce komai ba. Suka ɗan yi shiru can kuma Khadijah ta ce“gobe zan koma Kano fa” “Daman kina Yola?” Nana ta tambaya tana ɗan zaro idanu. Gyada mata kai ta yi kafin ta ce“eh fa. Ai da muka tafi gidan friend ɗin Daddy naje so ina can all this while.” Tashi zaune Nana ta yi ta ce“amma shi ne ko sau ɗaya baki faɗa min ba? Khadijah ki zo gidanmu dan Allah. Ki zo bestie i have alot to talk wlh, Dan Allah ki zo” Shiru Khadijah ta yi tana jin ta, Can kuma ta ce“To bayan na ce miki goben zan koma Kano?” “Kenan ba zaki iya zuwa saboda ni ba?” Nana ta tambayeta muryarta a sanyaye. Khadr ta yi murmushi sai kuma ta ce“alright zan ga abin da ya kamata nayi. Idan zan zo I'll call you da safe” Taɓe baki Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce“amma kin san an yi min aure ba?” Tashi zaune Khadijah ta yi da mugun mamaki ta ce“da wa? Yaushe kuma Nana?” ta jera mata tambayoyin tana zaro idanu. Numfasawa Nana ta yi lokaci ɗaya hawaye ya fara zuba kan fuskarta, Can numfashinta da Khadijah ta yi yasa ta ce“Nana, Are you there?” Gyaɗa mata kai ta yi kamar tana gabanta sai kuma ta sake jan numfashi cikin shessheƙar kuka ta ce“Idan kin zo gobe zan faɗa miki.” Gudun kada ta sakata kuka yasa Khadijah ta ce“tom shikenan, goben zaki ganni da wuri in sha Allah.” “Tom sai kin zo.” cewar Nana, Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar, Jifa ta yi da wayar can ƙarshen gado, ta koma ta kwanta tana kuka ƙasa-ƙasa ji tayi gaba ɗaya maganar auren ta dawo mata sabuwa. Ta daɗe tana rera yan matan hawayenta har bacci ɓarawo ya yi gaba da ita. Washegari da sassafe Anty Khadijah ta zo gidan, Lokacin Safwna na shirin fita, Ya gaisheta cike da girmamawa ta amsa sannan ya bar gidan. Siyama ta sauke numfashi tana kallonta ta ce“Mom welcome” Fuska babu annuri Anty Khadijah ta ce“ba wannan ya kawoni ba Siyama, muje ciki mu yi magana.” okay kawai ta ce sannan ta yi hanyar upstairs ɗin tana biye da ita. Kalle-kallen corridor ɗin ta dinga yi can kuma ta kalli Siyama da tayi gaba ta ce“Ina ita kishiyar ta ki?” Cak ta tsaya sai kuma ta juyo ta ce“haba Mom ya za'a yi ki ganta anan parlour da safe? Ai indai mai gidan bai fita ba, ba zaki taɓa ganinta a waje ba.” jinjina kai ta yi ta ce“Hakan ma yana da kyau” Siyama ta ɗan yi murmushi sai kuma ta juya ta buɗe ɗakin. Bayan sun zauna Aunty Khadijah ta ce“yauwa me ki ke cewa jiya a waya?” girgiza kai Siyama ta yi cike da damuwa ta ce“Mom wallahi ba Safwan ne wanda ya kamata mu rike a matsayin target ba. Mijin Anty Zahra shi ne wanda ya dace da buƙatar mu. Kin san kuwa tarin dukiyarsa? Kin san da Safwan yana bani ɗan labarin wasu daga cikin abin da ya mallaka sai da naji kaina ya yi min nauyi?. Idan fa kina neman babban mai kuɗi wanda ya amsa sunansa mai kuɗi, mai faɗa a ji to wallahi Abdusammad ne! Sam bamu yi dabara ba.” Aunty Khadijah ta yi shiru na wasu sakwanni kafin ta sauke numfashi ta ce“To daman shi Safwan ɗin bashi da komai?” Siyama ta ce“ba wai bashi da komai ba. Yana da shi mana, Yana da arziki sosai shima, amma ba kamar wancan ba, duk fa a ƙarƙashin sa suke, kusan duk arzikin gidan nan ɗin nasa ne” Jinjina kai Anty Khadijah ta yi cike da mamaki ta ce“ikon Allah, ban ɗauka ya kai haka ba.” “Ai wallahi Mom ya kai har ma ya wuce. Shiyasa fa kowa yake ganin girmansa a gidan nan, Ba zaki taɓa jin ya yi magana an musa masa ba. Kowa girmama shi yake har manya” Anty Khadijah ta ce“To yanzu ke ya ake ciki dake? Babu wani labari? Ya kamata a ce kin samu ko ciki ne Siyama” Ɗauke kanta ta yi cike da takaici ta ce“Hmmm to Mom mene ne bana yi? Wallahi duk abin da muka shirya a gida babu wanda bana aiwatarwa, amma kin ganni ko sauyi ban ji a jikina ba. Kuma kin san me? Duk sauran da aka kai mu tare sun samu ciki, ina ga wannan Amran ce kawai bata samu ciki ba. Ni kaina abun sai ɗaure mun kai yake” Anty Khadijah da duk jikinta ya yi sanyi ta ce“Tab idan haka ne zama bai kamani ba. Dole na tashi tsaye, Gashi daman maganar babanki na nema ta dawo sabuwa, naji yan uwan babanki na ƙishin-ƙishin ɗin kai ni koto” Zaro idanu Siyama ta yi sai kuma ta ce“to kuma yanzu me ki ka musu Mom?” taɓe baki Anty Khadijah ta yi ta ce“kema kya faɗa, babu abin da na musu. Shi kansa kuɗin da suke magana babu sun ƙare, Yanzu ban da gidan nan na wajenki bani da komai, ni dama yana rayen ya ci gaba da nemo mana. Amma dai nan kusa zan yi aure” “Aure kuma Mom? Da girmanki?” Siyama ta yi maganar a sanyaye. Wani banzan kallo Anty Khadijah ta watsa mata sannan ta ce“Ji min banzar ƴa? Har yaushe nayi girman da zan kasa aure? Akwai wani Alhaji dana samu yana da tarin dukiya nan bada jimawa ba zan aureshi, kin ga idan har mun samu yanda muke so ai babu buƙatar mu ci gaba da wannan abun, sai kawai ki kashe auren naki ki fito.” Siyama ta girgiza kanta ta ce“a'a Mom ni ba zan kashe auren nan ba wallahi. Saboda ina sonsa har ga Allah.” Ta ƙare maganar tana harɗe hannayenta a ƙirji, Taɓe baki Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“to ai sai ki yi ta yi. Ni bari ki ga na tashi na tafi kar a zo a ganni a nan” “Ba zaki je wajen Anty Zahra ba?” Girgiza kai ta yi ta ce“ke bar ni da wannan shashashar, ko naje ɓata min rai zata yi a banza. Kin san ita yanzu duk Umma ta kuma canzata, ganin bukatata ta biya ya sa ban sake bi ta kanta ba.” Siyama ta miƙe tana kallon ta ta ce“Allah sarki, wallahi tausayi take bani Mom. Kin san wannan Nanar ba mutunci gareta ba” Shiru ta yi tana tunani can kuma ta ce“to Allah ya rufa asiri, Ni babu ruwana. Daga nan ma gidan Kaddu na nufa” “To muje na raka ki Mom” har ta yi gaba sai kuma taja ta tsaya, Siyama ta kalleta ta ce“mene ne Mom?” “Babu wasu yan kudi a wajenki ne ki ban?” Girgiza kai Siyama ta yi ta ce“wallahi bani da cash, amma zan miki transfer ɗazu Safwan ya bani nima.” Jinjina kai Anty Khadijah ta yi ta ce“yauwa ai hakan yana da kyau. Ni har cash ɗin ma ki dinga amshewa, sanda muke tare da mahaifinki bai isa ya shigo da kuɗi ba sai na ɗauke ko ya bani ko bai bani ba. A haka na tara duk abin da ki ka ga na mallaka.” Shiru Siyama ta yi jiki a sanyaye ta ce“Tom Mom.” Anty Khadijah ta yi gaba Ita kuma ta ci gaba da bin ta a baya. Har compound ɗin su ta rakota, sai da ta shige motarta sannan ita ma ta juya ta koma ciki. Ƙarfe 10:20 na safe ta sakko daga saman, Sanye take da wasu riga da skirt, rigar irin mai kama jikin nan, sai skirt ɗin na jeans mai ɗan kauri. Wata hula ce mai ado akanta, blue colour wadda ta yi matching da skirt ɗin. Ta yi simple make-up a fuskarta dan haka ta ƙara mata kyau. Bakin nan sai shining yake na lip gloss, kasancewar bakin nata pink colour mai ɗan zagaye kamar na liner ya sanya ta yi wani irin mugun kyau. Tun da ta sakko Zahra ke bin ta da kallo, Ita kuwa ko lura bata yi da ita ba ta nufi kitchen tana waƙar Alan walker ta Unity. Zahra dake kan kujera tana danna wayarta ta sauke numfashi, kalle-kalle Nana ta dinga yi a kitchen ɗin, ita ba wani iya girki ta yi ba dan ba yi take ba. Dan haka ta rasa abin da zata dafa ta ci, gashi yunwa take ji, haka ta ƙaraci kalle-kallenta a kitchen ɗin ta juya ta fito, Bata samu Zahra a wajen ba, dan haka ta nufi sama da sauri, master bedroom ɗin sa ta murɗa ta ji a rufe. Taja ta tsaya tana knocking a hankali, tafi minti biyar tsaye a wajen amma babu alamar za'a buɗe, kuma tasan yana ci dan yau saturday ne ba fita yake ba. Gajiya ta yi da tsaiwarsa ta juya ta bar wajen, tana ƙoƙarin shiga daƙinta ta ji kamar amon muryarsa, dan haka ta nufi ƙofar da sauri, ɗan kasa kunnenta ta yi ta ji da gaske muryarsa ne, dan haka ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shige kai tsaye. Zaune ta sameshi kan gadon, Zahra na tsaye jikin mirror tana masa magana tana murmushi. Buɗe ƙofar ɗakin da ta yi ya sanya su kallon ƙofar a tare, Tsaye take kusa da ƙofa, ta kafesu da idanunta fuskarta a ɗaure. Gyara zamansa ya yi yana kallonta ya ce “Nana mene ne haka?” Tura baki ta yi tana kare masa kallo, wata riga ce armless a jikinsa coffee colour mai zanen tiger a jiki. Gaba ɗaya surarsa ta bayyana, Tatoo ɗin dake gefen hannunsa na hagu ya fito raɗau, gargarsa kuma ta kwanta luf a farar fatar tasa. Ganin bata ce komai ya sanya ya sake cewa “Mene na ce miki?” Ɗauke idanun ta ta yi ta kalli Zahra da ke kallonta ita ma, sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin ta buga musu ƙofar. Baki a buɗe ya dinga kallon wajen, Zahra kuwa ta ɗauke kanta tana sauke numfashi, Ya sauka daga kan gadon ya zura ƙafafunsa cikin Gucci slippers ɗin da ke gefen gadon masu taushi, Ya zura hannayensa cikin aljihun 3-quater dake jikinsa sannan ya yi waje. Zahra ta bi shi da idanu sai kuma ta koma gefen gadon nata ta zauna. A fusace ya tura ƙofar ɗakin, Ya sameta zaune gefen gado ta rufe fuskarta da hannunta sai kuka take a hankali, Karasowa ciki ya yi yana watsa mata wani mugun kallo ya ce “And what is this? Baki da hankali ne ko me? Are you out of ur sense da zaki shigo mana ɗaki babu ko sallama ballantana ki yi alerting ɗin mu?.” Ya ƙare maganar a zafafe, Shiru Nana ta yi masa dan ba zaka taɓa ɗauka da ita yake ba, Ya yi kwafa sannan ya sake cewa “Na fuskanci sai na fara gyara miki zamanki a cikin gidan nan. Kina da buƙatar lesson” Buɗe fuskarta ta yi wadda ta yi caɓa-caɓa da hawaye da majina ta ce“To ni ka sakeni mana, kawai ka sakeni, wallahi ba zan ci gaba da zama a haka ba. Tun ɗazu nake ta knocking a ɗakin ka ashe baka nan, kuma sai kaje wajenta” ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka, Da mamaki ya dinga kallon ta, can kuma ya sunkuya daidai tsayinta ya sanya hannunsa ya ɗago kanta ya ce “Ban ji ba sake faɗa.” Ɗauke fuskarta ta yi ta mike tsaye bayan ta goge hawayenta ta ƙarasa press ɗinta, wata yar ƙaramar trolley ta janyo ta buɗe sannan ta fara kaso kayanta ta fara zubawa ciki tana yi tana tsayawa share hawaye. Abdusammad kuwa tsayawa ya yi a wajen kamar gunki yana kallonta, Sai da ta cikata da kaya sannan ta mayar da rufe dakyar ta ɗagata ta fito da hannunta ta fara ja tana ƙoƙarin fita daga ɗakin. A gabanta ta gansa yana watsa mata wani mugun kallo wanda ya sanyata sunkuyar da kanta tana ci gaba da hawayenta. Ya fizge trolley ɗin daga hannunta rai ɓace ya ce“Ina zaki je kenan?” a fusace ita ma ta ce“gidan mu mana, wallahi sai na tafi gida..Ni ba zan zauna kana zuwa wajenta ba, Allah tafiyata zan yi, ai daman ban ce ina sonka ba!” Shiru ya yi yana son fahimtar abin da take nufi, Ya ja dogon numfashi ya sauke yana ƙoƙarin saita kansa ya ce“Saboda naje wajen Zahra shi ne zaki tafi? Idan ban je wajenta ba gurin wa zan je?.” Ya ƙare maganar yana harɗe hannayensa a ƙirji, Cikin kuka ta ce“to nima ba matarka bace? Ai haka Abba ya ce min, kuma shi ne ka ke zuwa wajenta a haka?” Ta ƙare maganar tana nuna masa jikinsa, Kallon jikinsa ya yi da ɗan mamaki sai kuma ya kalleta ya ce“to me shigar jikina ta yi Nana?” “To ni dan Allah zan iya zama a haka ne? Kuma ita ma sai ta saka riga yar ƙarama!" Ta rushe da wani sabon kukan tana jan numfashi. Murmushi ne ya tawo masa, Ya ɗan ci mur yana takawa gabanta, gaba ɗaya ya gama gano inda ta dosa, Dan haka ya ɗago fuskarta yana kare mata kallo ganin yanda ta shagwaɓe ya ce “Kenan ba zan je wajenta da kayan jikina ba? Ita ma kuma haka? To ai matata ce. Ko ke ɗin nan zaki iya zama a haka idan ina nan, ko baki sani ba?” Ɗago idanunta ta yi da sauri ta kalleshi, lokaci ɗaya kuma ta shiga girgiza kanta kafin ta ce“a'a ni a'a wallahi, ba zan iya ba. Ni bana so” “Ko?” Ya ce yana kafeta da idanu. Tura baki ta yi gaba tana dauke kanta daga gare shi ta ce“ni Allah bana son iskanci.” Jinjina kansa ya yi sai kuma ya ɗan yi baya ya ce“Dan kin zauna a gurina da karamar riga shi ne iskancin?” Sunkuyar da kanta ta yi sannan ta gyaɗa masa kai. Ya jinjina kansa sannan ya juya kamar zai fita, Key ya sakawa ƙofar ya rufe ruf sannan ya juyo yana kallonta ya ce “To yanzu nake son ki yi iskancin!” Daga haka ya nufota yana ƙoƙarin cire agogon dake maƙale a hannunsa. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 47. Ja da baya Nana ta fara yi tana zazzaro idanu. Sai da ta kai ƙarshen bango ta maƙale tana kallon sa kamar zata yi kuka, Abdusammad ya yi wurgi da agogon kan gado ya matso dab da ita har suna jin hucin numfashin juna. Ta sunkuyar da kanta ƙasa bakinta na rawa ta ce“Nin...Ni dai uncle bana so wallahi, Dan Allah ka matsa.” Shiru ya yi mata har sannan sai kallonta yake. Ya sanya hannunsa na dama ya ɗago fuskarta, Ya sauke wani zazzafan numfashi yana ƙarema kyakkyawar fuskarta kallo, Ita kuwa sai sake turo baki take tana ƙunƙuni. Ɗayan hannunsa ya kai ya shafi lips ɗinta, Ta yi saurin rufe idanunta lokaci ɗaya jikinta ya fara wani irin rawa kamar mazari. A hankali ya dinga shafar lips ɗin nata masu taushi, kafin daga bisani ya goge gaba ɗaya lip gloss ɗin data saka. Bata yi aune ba taki taji ya kai mata rankwashi aka, Ta dafe kanta da hannunta kamar zata yi kuka ta ce “wayyo zafi fa uncle.” Taɓe baki ya yi yana watsa mata wani kallo ya ce“kar na sake ganin kin shafa wannan abun kin ji abin da nace.?” Gyaɗa masa kai ta yi tana marairaice fuska. Ya ɗauke hannunsa daga kan fuskarta sannan ya ce“da ki ka je ɗakin nawa me zaki ce min?” Ya yi maganar yana ƙarasawa kan Italian bed ɗin nata, Ya zauna. Da sauri tabi bayansa ta zauna gefensa ta ɗora duka hannayenta biyu akan cinyarsa sannan ta ce“To ba yunwa nake ji ba uncle. Kamar zan mutu fa” Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba can kuma ya ce“To me ya hanaki cin abincin?” “Uncle ai ban iya girki ba.” Ta yi maganar a shagwaɓe, Jinjina kansa ya yi babu yabo babu fallasa ya ce“ai daman baki yi kama da wadda ta iya girkin ba.” Tura baki ta yi kafin ta ce“To bayan boarding school nayi, dan Allah a ina zan iya girkin?” sai da ya gama maƙale agogonsa ya mike sannan ya ce“haka ne.” ganin yana shirin fita yasa ta ce“uncle cewa nayi fa yunwa nake ji.” “To Nana cinyeni” Ya yi maganar yana kallon ta, Murmushi ta yi ta ce“to ai bana cin mutun, ni muje ka siya min abincin dan Allah.” harararta ya yi ya ce“ki je apartment ɗin Hajiya Babba a baki.” “To Atta ce zata yimin faɗa fa.” Ta yi maganar kamar zata yi kuka, Bai sake bi ta kanta ba ya fice daga ɗakin. Nana ta yi shiru tana kallon sa, kafin daga bisani ta koma ta kwanta akan gadon tana hawaye, dan har ga Allah yunwa take ji bata wasa ba. Ba'a fi 10mins ba aka sake buɗe ɗakin, Bata ɗago kanta ba sai kukanta da take a hankali, ya tsaya daga bakin ƙofar ya ce “taso mu tafi” Jikinta har rawa yake ta tashi daga kwancen ta sauka daga kan gadon ta nufosa. Wani mugun kallo da taga ya watsa mata ya sanyata tsayawa, Ya kalleta frm head to toe sannan ya ce “Kin koma kin rufe jikin ki ko sai na makeki anan?” Jiki a sanyaye ta koma ciki, ta buɗe press ɗinta ta zaro wani hijabi har ƙasa baby pink ta saka. Ya yi kamar riga dan mai babban hannu ne, Yana kallon ta har ta gama sakawa sannan ta ɗauki wayarta dake gaban mirror. Ya ɗauke idanun sa daga kanta ya juya ya fice daga ɗakin, ta tura baki gaba sannan tabi bayansa. Babu kowa a parlourn ya yi waje abin sa tana biye dashi. Cikin wata Lexus jeep ya shiga, Nan da nan guards ɗin dake wajen suka taso, ya girgiza musu kai alamar shi kadai yake son fitar. Har ya gama warming motar tana tsaye tana bin sa da kallo, Ya ɗan kalli side ɗin da take fuska a haɗe ya ce“sai na bi ta kan ki ne?” sai a sannan ta sauke idanunta ta buɗe motar ta shiga passenger seat ɗin, Ya taɓe baki sannan ya juya ya bar wajen. Sun yi nisa ta kalleshi kamar wadda aka tsikara ta ce“uncle ina zamu je?” “siyar dake zan yi.” Ya ce ba tare da ya kalleta ba, Tuntsirewa ta yi da dariya, Ya ɗan kalleta sai kuma ya ɗauke kansa yana murmushin shima. Har suka ƙarasa gaban gidan babu wanda ya sake cewa wani abu, Ya yi horn aka buɗe gate ɗin sannan ya tura hancin motar cikin babban compound ɗin gidan. Yana gama parking ya sauke ba tare da ya kalleta ba, Itama ta buɗe side dinta ta sakko tana ƙarewa gidan kallo, Babbar gida ne wanda aka yishi cikin tsari na turawa, Daga gani ka san guest house ne, Zagayowa ya yi side ɗinta ya riƙe hannunta suka yi gaba. Nana ta dinga bin sa tana mamakin dalilin zuwan su gidan. A babban parlourn gidan suka tsaya, parlourn an ƙawata shi da kujeru na zamani masu kyau da kuma tsada, Ko ina tsaf dashi sai ƙamshi mai daɗi dake tashi wanda ya gauraye da sanyin ac ya bada wani yanayi mai daɗi. Nana ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta nemi kujera ta zauna ta jingina kanta da kujerar tana lumshe idanu, Kallon ta kawai ya yi sai kuma ya buɗe wata ƙofa ya shige, Ta ɗauki a ƙalla 15mins a wajen kafin aka buɗe wata ƙofa, tabi wadda ta shigo da kallo, wata maid ce hannunta riƙe da ƙaton tray, ta ajiye a gaban Nana sannan ta koma ciki. Nana ta dinga kallon tray ɗin wanda aka cika shi da kayan shayi, tana nan zaune maid ɗin ta ƙara dawowa hannunta riƙe da warmers guda biyu. Ta sake ajiyewa gaban Nana tana murmushi ta ce “Can i serve you ma?”. Girgiza mata kai Nana ta yi, Ta sunkuya sannan ta juya ya bar parlour. Sai a sannan Nana ta zamo ƙasa a hankali tana sauke numfashi, Ta ɗauki tea flask ɗin sannan ta janyo wani mug ta tsiyaya shayin, bayan ta zuba wanda take ganin zai isheta ta mayar ta rufe sannan ta saka madara da kuma bounvita da yake wajen, ta saka sugar kaɗan dan bata son zaƙi. Juyawa ta yi sannan ta ajiye, Ta buɗe warmer taga soyayyen dankalin turawa a ciki sai kuma wainar kwai masu kauri, murmushi ta yi sannan ta ɗauki plate ta zuba dankalin sannan ta saka wainar guda biyu, ta tankwashe ƙafafunta sannan ta fara shan tea ɗin. Da fari sai da ta kusan amai sakamakon dadewar da ta yi bata ci abincin ba, Ta ajiye mug ɗin tana sauke numfashi a hankali. Can kuma ta fara cin dankalin tana haɗawa da kwan, idan ta ci sai ta sha tea ɗin a haka har ta cinye na gabanta tas. Ta yi gyatsa dan ta ƙoshi, amma ta gyara zamanta sannan ta buɗe ɗayar warmers, farfesun catfish ne sai tiriri yake, Ta washe baki tana dariya sannan ta saka yatsanta ta dangwali romon, lumshe idanu ta yi a fili ta ce “woww!” Ta ajiye murfin a gefe sannan ta janyo wani sabon plate ɗin da spoon, yanda zai isheta ta saka sannan ta zuba uban romo akai. Ta tura warmer gefe sannan ta fara ci a hankali, Sam bata lura da sanda ya shigo parlourn ba, har ya zo kusa da ita ya zauna a kujera. Ya yi Shiru yana kallon yanda take ta cin kifin tana tsince ƙaya tana tarawa a gefe. Sai da ta cinye shi shima tas sannan ta ɗago kanta tana shirin ɗaukan ruwa suka haɗa ido dashi, Ta yi saurin ɗauke nata tana tura baki. Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“har kin ƙoshi?” sai da ta ɓalle murfin robar ta sha ruwan kusan rabi sannan ta ajiye tana kallon sa ta ce“na ƙoshi sosai uncle.” jinjina kansa ya yi ba tare da ya yi magana ba, Ta tashi ta kwashe kayan ta nufi hanyar da taga maid ɗin tayi, dan ita a rayuwarta bata son taga an bar waje da datti. Bayan ta kai kayan na farko ta dawo parlourn da niyyar ɗaukan sauran, sai dai abin da ta gani ya sanyata tsayawa cak, ta sake ware idanunta tana son tabbatar da abin da take gani. Da gudu kuma ta nufi inda Abdusammad yake ta faɗa jikinsa ta ƙanƙameshi tana wani irin kuka, Abdusammad ya riƙeta gam yana shafa kanta a hankali. Junaid dake zaune kan kujera ya dinga kallon ta idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, Sun ɗauki mintina a haka kafin ya ɗago fuskarta yana share mata hawayen ya ce “mene ne to?” Sake rungume shi tayi tana kuka ta ce“uncle dan Allah, dan Allah uncle, bana so. Wallahi ba zan ƙara ba, kace ya tafi, ka ce ya yi tafiyarsa dan Allah uncle...” ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka. Shiru Abdusammad ya yi yana jin yanda hawayenta ke zuba a jikinsa. Ya ɗago kansa ya kalli Junaid babu yabo babu fallasa ya ce “I think kaje kawai. Komai ya shige” Jiki a sanyaye Junaid ya ce“dan Allah Yallaɓai ka barni na nemi yafiyarta, ka barni na nemi afuwarta, ko na samu sauƙin abin da nake ji a zuciyata. Dan Allah...” Abdusammad ya ɗan yi shiru can kuma ya sake ɗago kanta da kyar ya ce“Nana nace ki tsaya ko, ki bar kukan” Girgiza kanta ta yi ta ce“bana son na ganshi uncle. Ya cuceni, shi ne fa ya cuceni, kace masa ya tafi uncle. Wallahi ba zan sauraresa ba, ba zan amsa maganarsa ba!” Junaid ya yi shiru, can kuma ya sakko daga kan kujerar da yake, ya durƙusa akan ƙafafunsa, ya haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo. Bai damu da juya masa bayan da ta yi ba, Cikin wata irin murya mai fito da asalin raunin mutum ya fara cewa “Na sani Nana, ban cancanci ki yafe min ba. Ban cancanci ki kalleni ba, ban kuma dace daki tausaya min ba. Na aikata kuskure wanda na san ba zan taɓa iya gyarasa ba, amma ki sani Nana wallahi duk abin da nayi soyyarki ce ta janyo min, duk abin da ki ka ga na yi ƙaunar da nake miki ce sanadi. Nana ina son ki, ina son ki, ina son ki fiye da yanda ki ke tunani, wallahi ban yi tunanin cutar dake ba, na yi haka ne saboda tunanin zaki hana ayi aurenku da ɗan uwanki ni kuma na samu na aureki. Ban taɓa tunanin turawa wani hotunan ba, kuma ban da wadanda na bada aka sake kawo miki wallahi tallahi bani da su Nana! Gurguwar shawarar abokina ce tayi tasiri akaina, na ɗauka hakan zai yi aiki ashe ba haka bane, madadin na sameki sai ki ka min nisan da har abada ba zan iya kamo ki ba.” Junaid ya yi shiru yana jan numfashi saboda kukan daya tawo masa, Ya dinga shessheƙar kuka a hankali. Nana dake jikin Abdusammad ta sake riƙe shi ƙam tana kuka itama, Junaid ya ci gaba da faɗin “Zan tafi Nana, ba zan nemi afuwarki ba, na san koda nayi hakan haƙƙin cutarwa da nayi miki ba zai barni ba. Amma ina son ki sani, ina sonki Nana. Kuma har abada ba zan daina sonki ba!.” Janyeta Abdusammad ya yi daga jikinsa, ya miƙe tsaye ya ƙarasa inda Junaid yake, Hannunsa ya sanya ya ɗago shi, Junaid dake kuka ya girgiza kansa ya ce“nagode sosai daka bani damar magana da ita. Dan Allah yallaɓai ka fahimtar da Nana ban da niyyar cutar da ita, idan har zan ga wani ya cutar da ita to wallahi sai inda ƙarfina ya ƙare. Ƙaddara ita ta kaini ga aikata hakan, ƙaddarar data ka aureta.” Murmushi Abdusammad ya yi kafin ya ce“ba komai ta yafe maka. Allah ya kiyaye gaba.” Junaid ya jinjina kansa sai kuma ya ce“Ina yi muku fatan Alkhairi a cikin aurenku, Allah ya baku zaman lafiya, da zuri'a ta gari.” Jiki a sanyaye Abdusammad ya amsa, sannan Junaid ya yi gaba yana biye dashi. Duk wani taku da suke yi tafiya yake da bugun zuciyarta, Ƙirjinta har ɗagawa yake, Ban da kuka babu abin da take. Ji tayi kamar suna tafiya da duk wani kwarin gwuiwarta, nutsuwarta, farin cikinta. Ita kanta ta san tana son Junaid, so mai tsanani, son da bata yi tunanin zata iya yiwa wani ɗa namiji shi ba. Amma me yasa ta ji zuciyarta ta kasa yafe masa? Me yasa ta ji bata son ganinsa, Bata son jin muryarsa. Tana nan zaune tana kuka har Abdusammad ya dawo, Ya dinga kallonta kafin ya ƙaraso wajen, Bai ce komai ba ya kamo hannunta ya niƙar da ita tsaye. Har sannan bata yi shiru ba, Ya goge hawayen duk da sabbin dake sake zubowa. Waje ya nufa yana riƙe da hannunta cikin nasa, Ya buɗe passenger seat ya sakata sannan ya rufe ya koma driver seat ya shiga. Kifa kanta ta yi akan cinyarta ta ci gaba da kukanta, Bai yi yunƙurin hanata ba ya yi shiru yana sauraren sautin kukan nata, kafin daga bisani ya yiwa motar key su bar gidan. Sun kusa zuwa gida ya ɗan saci kallon ta, ganin har sannan bata daina kukan ba yasa ya yi gyaran murya kafin ya ce“Ko na siya miki ice-cream?” girgiza masa kai ta yi a hankali. Ya gangara gefen titi ya yi parking, Bai kalleta ba ya sauka daga motar, ta bi shi da idanu tana goge hawayenta. Jingina ta yi da kujerar motar ta lumshe idanunta, gaba ɗaya ji tayi jikinta ya yi wani sanyi, ga ƙirjinta dake mata wani irin zafi she wish bata bishi ba, da bata haɗu da Junaid ba. Taja numfashi ta sauke hawaye na zubowa kan kuncinta, Bai wani jima ba ya dawo ya buɗe motar ya shigo, ajiye mata ledar ya yi akan cinyarta sannan ya yiwa motar key suka bar wajen. Har suka ƙarasa gida bata yi magana ba, shima kuma bai yi mata ba. A tsakiyar compound ɗin gidan ya yi parking sannan ya juyo yana kallonta ya ce“Ki ke gida I'll be back.” Bata ce komai ba ta sauke ledar daga cinyarta sannan ta buɗe motar ta sauka, Ya bita da kallo har ta shige gidan sannan ya yi reverse ya bar compound ɗin. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga parlourn, Zahra na zaune kan sofa tana gyarawa Noor kanta. Ta amsa ba tare da ta ɗago kanta ba, itama Nanar bata bi ta kanta ba ta haye sama da sauri. Daƙinta ta buɗe ta shiga, ta ajiye ledar ice-cream ɗin a ƙasan carpet sannan ta haye kan gado, ta ƙanƙame pillow tana fashewa da wani sabon kukan. **** Anty Khadijah ta dinga kallon Kaddu da rashin fahimta. Can kuma ta ce“kin ga ni wlh ban gane abin da ki ke nufi ba. Kamar ya Zahra?” wani murmushi Kaddu ta yi tana gyara zamanta ta ce“bari na fahimtar dake. Idan har kina son ki samu kuɗaɗen daga hannunsa to ai dole sai dai ki yi amfani da Zahra, saboda ita kaɗai ce wadda zata iya wannan aikin.” Shiru Anty Khadijah ta yi tana tunanin maganar Kaddun, Kaddu ta miƙe tana ɗaukan wayarta ta ce“Kin ga idan baki yarda dani ba, muje wajen Malam ya faɗa miki.” Tashi Anty Khadijah ta yi ta ce“bari na fara sallah sai muje.” **** Murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ya yi ya shigo, Ya ƙaraso ciki ya tsaya gaban gadon yana ƙare mata kallo. Agogon hannunsa ya kalla yaga kusan 1 na rana, ya kalli ledar ice-cream ɗin dake ajiye a ƙasan wanda ke nuna bata sha ba. Durƙusa ya yi ya taɓa ta ya ce“Nana!” Ɗago kanta ta yi a hankali, ta goge hawayenta sannan ta gyara zamanta, zama ya yi gefen gadon idanunsa akan ta ya ce “Har yanzu baki daina kukan ba?” Sunkuyar da kanta ta yi bata bashi amsa ba, Ya ɗan matso kusa da ita sannan ya ce“zo nan.” kamar jira take ta shige jikinsa tana sakin wani sabon kukan, Ya shafa kanta a hankali ya ce“Ya isa haka. Ki yi shiru kin ji, ai ya tafi” “Uncle ƙirjina ciwo yake min, zafi nake ji.” Ba ƙaramin tausayi ta bashi ba, Ya sake rungumeta ya ce“sannu kin ji, ki daina kukan zai daina.” Cikin kuka ta ce “uncle shikenan kowa ya ga hotuna na? Shi kenan kowa yana ganin ina bin maza? Ba zan iya ba, mutuwa zan yi uncle...” ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani kukan, Girgiza kansa ya yi cikin son kwantar mata da hankali ya ce“wane ya ce miki haka? Kowa ya san ba ki da laifi, baki ga babu wanda yake jin haushin ki ba?” Ɗago fuskarta ta yi tana kallon sa ta ce“to uncle shikenan ai kowa ya ganni amma. Kuma da baka aureni ba ai babu wanda zai aureni a haka..” Shiru ya yi yana kallon fuskarta wadda ta gama kwaɓewa saboda kuka da kuma shagwaɓar da suka haɗe mata. Abdusammad ya ɗan yi murmushi kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce “To bana aurekin ba?” Gyaɗa masa kai ta yi hawaye na sakkowa kan fuskarta. Ya jinjina kansa sannan ya ce“oyaa stop crying” ganin tana shirin sake fashewa da wani sabon kukan ya sanya ya shiga jijjigata kamar ƙaramar yarinya kafin ya ɗora kanta akan hannunsa ya ɗan durƙusa kansa kusa da fuskarta ya ce“Haa.” Kallon idanunsa ta yi sai kuma ta buɗe bakin nata a hankali, Bata yi aune ba kawai sai jin warm lips ɗinsa ta yi cikin nata. Nana ta ja wani irin dogon numfashi tana jin wani abu na mata yawo a jiki, Kokawar kwace bakinta ta fara yi, sai dai sam bai bata wannan damar ba, ya sake zura bakin nasa cikin nata yana sauke mata wasu hot kisses yana kuma tsotsar harsheta, Tuni ta nemi ficewa daga hayyacinta, Ta rufe idanunta ruf jikinta na wani irin rawa. Abdusammad daya fara kasa gane inda yake ya fara ƙoƙarin kai hannunsa kan ƙirjinta, Sai dai sulɓin hijabin da yaji ya sanya shi dakatawa. Ya zare bakin nasa daga nata a hankali yana sauke wani zazzafan numfashi, Hannunsa ya sanya ya yaye hijabin jikinta. Nan take ƴar ƙaramar t-shirt ɗin dake jikinta ta bayyana, Gaba ɗaya ana ganin shatin breast ɗinta sakamakon kamanta da rigar ta yi. Ya ja idanunsa ya lumshe sannan yake buɗe su a kan ƙirjin nata. Sam ya manta da wadda take hannunsa, Ita kuwa Nana ban da kuka babu abin da take, Hannunsa na rawa ya fara ƙoƙarin ya ye rigar jikinta, tuni numfashinta ya fara ƙoƙarin barin jikinta, Ganin rigar na neman ɓata masa lokaci ya sanya ya jata da wani irin ƙarfi nan take ta yage, Idanunsa ya sauka kan ƙirjinta wanda yake fari ƙaƙal dashi, sai numfashi take saukewa. Kamar wanda ake tura shi haka ya kai hannunsa kan ƙirjin, Nana ta saki wani irin ihu lokaci ɗaya fitsari ya fara zubowa daga jikinta, hannunsa ya kai bayanta yana ƙoƙarin ɓalle bra dake jikinta, Ta sanya hannayenta duk biyun ta rike rigarsa gam tana wani irin kuka mai haɗe da numfashinta. Cikin wani irin yanayi ta buɗe bakinta wanda ke rawa ta ce “uncleee..!” Yanda ta faɗi sunan nasa in a romantic style ya sanya shi mai da idanunsa kan bakinta, A hankali kuma ya sake ɗora bakin nasa kan nata ya fara tsotsa kamar ya samu alawa, yayinda hannunsa ɗaya ke bayanta yana ɓalle bra ɗinta. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 48. Wani irin jan numfashi ta dinga yi, idanunta a rufe sai hawaye ne ke zubowa ta gefensu, Ta kasa koda motsi gaba ɗaya jikinta ya yi sanyin. Shi kuwa kamar ana ƙarar wutar abin da yake yi, Ya gyara zamanta akan cinyarsa tasa bayan ya zare bakinsa, Yana ƙoƙarin kwantar da ita kan gadon aka fara knocking ƙofar. Dakyar ya iya buɗe idanunsa, Ya janye jikinsa ya miƙe tsaye, Sai a sannan Nana ta samu damar tashi zaune ta koma can ƙarshen gadon ta cure jikinta waje ɗaya. Murɗa handle ɗin ƙofar ya yi ya tsaya a jiki yana kallon ta da lumsassun idanunsa. Zahra dake tsaye ta ɗan sunkuyar da kanta kafin ta ce “Daman Aliyu ke nemanka.” Gyaɗa mata kai ya yi kawai sannan ya mai da ƙofar ya rufe. Wata irin zabura Nana ta yi tana sake ja da baya, Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai, Ya juya ya fice daga ɗakin. Ɗakinsa ya shige kai tsaye kuma toilet ya nufa, Wanka ya yi sannan ya fito ya shirya cikin wata jallabiya maroon colour mai taushi, Ya gyara gashin kansa sai sheƙi yake. Turaren oud ya fesa mai daɗin ƙamshi. Gaba ɗaya a sanyaye yake komai, Ya dafa dressing mirror yana karewa kansa kallo, lokaci ɗaya scene ɗin ɗazun ya dawo masa. Wani dogon tsaki yaja, Sam bai san garin ya ya haka ta faru ba. Hannunsa ya kai kan lips ɗinsa ya shafa sannan ya ce “Astagfirullah!” Ya faɗa yana barin wajen, Wayarsa ya ɗauka gefen gado ganin missed calls ɗin Aliyun ya sanya shi yin waje. Kallon ƙofar dakin nata ya yi sai kuma ya nufi upstairs da sauri, Zaune ya samu Zahra tana cin abinci ta kalleshi amma bata ce komai ba. Kamar zai wuce sai kuma ya tsaya idanunsa a lumshe har sannan ya ce “Ina Noor?.” “Juwaira tazo ta tafi da ita.” Zahra ta bashi amsa jiki a sanyaye. Bai sake cewa komai ya juya ya fice daga parlourn. Tsaye ya samu Aliyun a balcony ya harɗe hannayensa a ƙirji idanunsa maƙale da sun glasses. A hankali ya ƙarasa cikin takunsa na isa da taƙama, Aliyu ya zare glasses ɗinsa yana kallon sa, Shi kuwa ɗauke kansa ya yi yana kallon wani wajen daban. Aliyu ya yi murmushi ya ƙaraso gabansa ya ce “Buddy na ganka haka?” Haɗe rai ya yi sosai ya ce“mene? Me ka gani?” Tuntsirewa da dariya Aliyu ya yi ganin yanda ya wani cure gira, Ya ce“Gani nayi ka yi fresh da kai kamar ango, ko dai?.” Wani banzan kallo daya watsa masa ya sanya shi tsuke bakinsa. Abdusammad ya zabga masa harara sannan ya ce“idan kaga dama ka zauna anan.” Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin yin gaba, Murmushi Aliyu ya yi ya biyo bayansa yana cewa“To mene abun fusata anan?” shi dai ko kallon sa bai yi ba ballantana ya saka ran zai amsa masa, deep down nasa kuwa baya son Aliyun ya gane abin da ya faru tsakaninsa da Nana ne. Back seat suka shiga, driving ya shiga gaba suka bar gidan tare da excort ɗinsa. **** Tafi awa kwance a wajen, Ita kanta bata san abin da ke damunta ba. Ji take yi kamar ba ita ba, Idan ta tuna abin da uncle ɗin ya yi mata sai taji kuka ya sake tawo mata, Tana nan kwance har wajen ƙarfe 3:00 na rana, Wayarta ta fara ringing. Dakyar ta tashi zaune sai a sannan ta tuna da rigarta da take a rabe, Ta ɗan kalli ƙirjin nata sai kuma ta sake fashewa da kuka, Taya ma za'a ce uncle ya yi mata haka? Akan me zai ga jikinta, ringing ɗin da wayar ta sake ne ya sanyata tsagaita kukan, Ta jawo wayartata ta kai kunne. Khadijah dake cikin mota ta ce “Na kusa fa.” Gyaɗa mata kai ta yi kamar tana gabanta, Khadijah ta sake cewa“Nana ko bakya jina?” Jan numfashi ta yi kafin ta ce“Ina ji. Sai kin zo” “Kuka kuma? Me aka yi miki?” “Babu komai fa sai kin zo.” Nana ta bata amsa a hankali, ok kawai Khadijah ta ce sannan ta kashe wayar ba dan ta yarda da abin da ta ce ɗin ba. Nana ta miƙe tsaye a sanyaye ta nufi toilet hannunta dafe da ƙirjinta. Wanka ta yi ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga ta material mai sulɓi, Ta ɗaure kanta da ɗankwalin yadin sannan ta saka hijabi ta gabatar da sallar azahar. Bayan ta idar ta jingina da jikin gadonta ta yi shiru tana tunane-tunane, hawaye ya ci gaba da zuba daga idanunta. Bayan mintuna sha biyar wayarta ta sake ringing ta ɗaga bata ce komai ba, Khadijah ta ce “Na sauka fa, ina Apartment ɗin ku.” “To bari na zo mu tafi tare” Nana ta yi maganar a sanyaye. Kafin Khadijahn ta yi magana Amma dake jin su ta ce“kin tambayeshi ne da zaki fito?” Wata irin faɗuwar gaba ce ta risketa, ta yi saurin girgiza kanta dan ba son maganarsa take ba ta ce“A'a. Khadijah ki ƙaraso” Toh kawai Khadijahn ta ce sannan ta kashe wayar. Amma ta mike tana cewa“bari na baki saƙo ki tafar mata dashi.” to Khadijah ta ce tana gyara zamanta. Bayan wasu mintina aka fara knocking ƙofar daƙinta, Nana ta kalli ƙofar da sauri hankalinta a ɗan tashe ta ce“wa...wane?” “Ke ni ce.” Khadijah ta bata amsa. Sauke numfashi ta yi sannan ta miƙe ta zare hijabin dake jikinta ta ƙarasa ta cire key ɗin data sakawa ƙofar, Tsaye ta ganta hannunta riƙe da wata warmer tana mata murmushi. Rungumeta Nana ta yi tana sauke ajiyar zuciya, Khadijah ta ce“Ke sai kin karyani?” Ko saurarenta Nana bata yi ba, Ta karɓi warmern hannunta sannan suka shiga ciki, Tana ganinta mayar da key ɗin ƙofar ta rufe. Khadijah ta ƙarasa ta zauna gefen gadonta tana cewa “wash, wasa-wasa da nisa fa daga apartment ɗin ku.” Ita dai Nana bata ce komai ba ta ajiye warmern a ƙasa sannan ta zauna gefenta. Shiru Khadijah ta yi tana kallon ta, Nana ta ɗan yi murmushi ta ce “Na ɗauka ba zaki zo ba. Ya su Ameema?” “mene ya same ki Nana?” Khadijah ta tambayeta tana kafeta da idanu. Girgiza kai Nana ta yi a sanyaye ta ce“bakomai fa” wata uwar harara ta maka mata kafin ta ce“nabi ba komai da gudu. Just tell me my friend!” Shiru Nana ta yi tana kallon ta, ba zata taɓa iya faɗa mata ba abin da uncle ɗin ya yi mata ba. Dan ta san hakan ba daidai bane, Jin yanda ta yi shiru ya sanya Khadijah cewa“Idan kina ganin na takura ki bar shi kawai.” “Mimi baki ji ba wai na auri uncle? Bai baki mamaki ba? Dan Allah kuma sai na zauna da uncle?” Nana ta jera mata tambayoyin tana kallon ta. Murmushi Khadijah ta yi ta ce“To mene? Ni daɗi naji wallahi, saboda na san zai kula dake fiye da kowa a gidan nan.” Taɓe baki Nana ta yi kafin ta ce“to ta ina zai kula dani ɗin? Bayan kuma yana da mata.” Kallon ta Khadijah ta yi, kamar ba zata yi magana ba can kuma ta ce“ke wait! Ba matar dana gani a ƙasan ba ce Zahra?” gyaɗa mata kai Nana tayi. Khadijah ta ce“kenan ita ce kishiyarki yanzu?” nan ma sake gyaɗa mata kan tayi. Khadijah ta gyara zamanta sannan ta ce“Yanzu tsaya wani abun ya taɓa haɗaki dashi? Ai na san kin gane me nake nufi” girgiza mata kai Nana ta yi dan ta fuskanci abin da take nufin. Khadijah ta ce“But why? Bazai taɓa yiwuwa ba!.” Da mamaki Nana ke kallon ta, can kuma ta ce“Mimi me ki ke nufi ne? Ni ban gane ba” Kamo hannunta Khadijah ta yi ta sake matsowa kusa da ita yanda zata fahimce abin da zata faɗa ta fara cewa“kina ji...” **** Anty Khadijah ce zaune gaban Malam sai Kaddu a gefenta, Ganin sai dube-dube yake bai ce komai ba ya sanya ta ce“Malam lafiya dai?” ɗago kansa ya yi bakinsa ɗauke da asiwaki yana taunawa ya ce“an gama. Bukatar ki zata biya, zaki aure shi, sannan kuma waccan yarinyar zata fito daga cikin gidan ke kuma ki maye gurbinta.” wani kyakkyawan murmushi Anty Khadijah ta yi, Ta juya ta kalli Kaddu, itama murmushin take kafin ta ce “To malam abun sadaƙa fa?” Girgiza kansa ya yi ya ce“Kamar dai yanda aka saba. Sai dai wannan karan zan baki wani abu da zaki yi amfani dashi” Ko kaɗan bata damu ba ta ce“Tom Malam, an gode Allah ya ƙara girma.” Murmushi kawai ya yi yana kallonta ta ƙasan ido yana suɗe baki. Anty Khadijah ta kalli Kaddu ta ce“To zaki jira mu ko tafiya zaki yi?” girgiza kai Kaddu ta yi ta ce“no I'll wait.” To kawai ta ce sannan ta miƙe ta nufi ɗayan soron, Shima ya tashi yana tattare babbar rigarsa yabi bayanta. **** Khadijah ta dinga kallon ta ganin yanda take abu kamar wadda bata da kala, Ta ɗan ja tsaki ta ƙarasa gabanta ta karɓi plate ɗin ta ce “kin tsaya sai wani tafiya ki ke kamar kwai ya fashe miki.” Tura baki Nana ta yi, Ta ƙarasa gaban tukunyar ta buɗe, Saurin matsawa ta yi daga wajen tana dariya ta ce“Mimi kin ga.” Khadijah dake jera plate ɗin akan tray ta ce“mene?” “Ya dahu wallahi” Ajiye plate ɗin ta yi ta ƙaraso gaban tunkuyar, Leƙawa ta yi taga yanda fried rice ɗin ta yi kyau ko a ido, Ta yi murmushi tana kallon Nana ta ce“ai kuwa, ashe kin iya girkin iskanci ne.” dariya kawai Nana ta yi, ta mayar da murfin ta rufe taja ta tsaya, Khadijah ta koma ta ɗauko tray ɗin tana kallon ta ta ce“A nan parlourn zan ajiye ko a ɗaki?” “ko a parlourn zai fi ina ga.” Okay kawai Khadijah ta ce sannan ta fice daga kitchen ɗin. Nana tabi ta da kallo, lokaci ɗaya maganganun Khadijah suka fara dawo mata. Murmushi ta yi can kuma kamar wadda ta tuna wani abu ta tura baki. Tana nan tsaye har Khadijahn ta dawo. Ta dinga kallon ta sai kuma ta wuce ta ɗauko wata sabuwar warmer ta ƙaraso wajen tunkuyar ta ce“kina nan tsaye har sai ya dawo ma.” “To ai ba yanzu yake dawowa ba.” Nana ta yi maganar a ɗan ƙufule, Sai da ta gama zuba shinkafar a cikin warmern ta mayar da rufe sannan ta ce“to zauna sai ya dawo, dalla ki je ki yi wanka.” Tura baki ta yi ta ce“nifa wallahi tsoro nake ji.” Sak Khadijah ta yi tana kallonta, can kuma ta ce“tsoro? Tsoro fa ki ka ce Nana. Kenan duk abin da nayi ya tashi a banza kenan?” “To dan Allah ya zan yi? Uncle ne fa.” “Da yake uncle ɗin ki amma yanzu mijinki ne.” Saurin kallonta Nana ta yi, Ta gyaɗa mata kai fuska babu walwala. Bata sake cewa komai ba ta yi waje, Khadijah ta bita da idanu sai kuma ta girgiza kanta tabi bayanta. Nana ta fita daƙinta ta shige, ta daɗe tsaye a tsakiyar ɗakin kafin daga bisani ta sauke numfashi ta nufi toilet. Wanka ta yi ta fito tana tsane ruwan jikinta da towel, Gaban dresser ɗinta ta ƙarasa ta fara shafe-shafen mayuka. Bayan ta gama ta saka turaren da Amma ta bada aka kawo mata, nan da nan ɗakin ya gauraye da sassayan ƙamshi. Yar simple make-up ta yiwa fuskarta ta shafa lip gloss, Bayan ta gama ta ƙarasa gaban press ɗinta ta buɗe. Shiru ta yi tana kallon jerin kayan da suke cikin press ɗin a jere, Tana nan tsaye aka buɗe ƙofar. Khadijah dake tsaye tun ɗazu tana kallonta ta ce“wai har yanzu baki ga kayan da zaki saka bane?” juyowa ta yi tana kallonta kamar zata yi kuka ta ce“To dan Allah me zan saka?” taɓe baki Khadijah ta yi ta ƙaraso ciki tana kallon ta, tsayawa ta yi kusa da ita tana ƙarewa press ɗin kallon. Ta jima a tsayen can kuma ta jawo wata doguwar riga, Miƙawa Nana ta yi tana murmushi ta ce“ki saka wannan zai miki kyau” amsa Nana ta yi tana shafa rigar, ta juya ta koma toilet. Murmushi kawai Khadijah ta yi sai kuma ta koma kan kujerar dake jigin gadon. Bata jima ba ta fito tana sanye da Egyptian Abayar nude colour, wata mai flower a ƙirji da kuma hannun rigar. Tashi tsaye Khadijah ta yi tana murmushi ta ce “wowww! Kin ga yanda ki ka yi kyau?” Murmushi Nana ta yi ta ƙarasa jikin madubi, Ita kanta ta san rigar ta yi mata kyau. Ta kai hannunta ta shafa rigar tana murmushi ta ce“nayi kyau?” Gyaɗa mata kai Khadijah ta yi, ta karɓi veil ɗin rigar dake hannun Nana ta ce“Zo na ɗaura miki.” To kawai Nana ta ce, Khadijah ta ɗaura mata ɗankwalin mai tuta a gefe. Wani irin kyau ta yi kamar ba ita ba, Khadijah ta ja kumatunta ta ce“Sai dake kyakkyawar matar uncle” wani irin fari Nana ta yi da ido suka tuntsire da dariya a tare. **** A dai-dai round about ɗin ta tsaya, Ta juya tana kallon Kaddu dake gefenta ta ce“Ba gida zaki yi bane?” girgiza mata kai Kaddu ta yi tana shafa wayarta ta ce“A'a akwai wanda zai zo ya ɗaukeni kawai saukeni anan.” okay Anty Khadijah ta ce, Kaddu ta buɗe motar tana shirin sauka, kamar wadda ta tuna wani abu sai kuma ta koma ta zauna ta ce“Mantawa nayi zan tafi. Yanzu ya za'a yi wai?” “Yanda muka shirya mana. Dole Zahra ta fito daga gidan, idan Allah ya kaimu gobe zan yi je gidan na kai mata maganin.” Jinjina kai Kaddu ta yi kafin ta ce“Eh ki yi da sauri. Saboda kada su bar ƙasar” wani shu'umin murmushi Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“ai idan ki ka ga an bar ƙasar nan to da ni ne bada Zahra ba!”. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 49. Murmushi Kaddu ta yi ta ce“Nagode ƙawata. Ki ce nan bada jimawa ba zamu fara ƙirga dollars?” Anty Khadijah ta sake murmushi tana cije laɓɓanta ta ce“Ai idan ki ka ce dollars kaɗan ma kenan, Ke idan da abin da yafi kuɗi wallahi sai kin same shi. Ai ko ke zaman ƙasar nan sai ya gagareki, Ballantana kuma ni, Daga Us nayi uk, daga uku na yi Paris, daga Paris nayi Qatar. Woww!” Tuntsirewa da dariya suka yi a tare. Kaddu ta ce“tom Allah ya tabbatar ya nuna mana” da Amin ta amsa, Kaddu ta sauka daga motar tana murmushi, Anty Khadijah taja motar ta bar wajen. Bata fi 2mins a tsaye ba wata babbar mota ta yi parking a wajen, Kaddu ta gyara tsaiwarta tana murmushi kafin ta nufi inda motar take.. **** Ana shirin kiran sallar magriba suka fito, Khadijah ce a gaba sai Nana dake biye da ita, Sai haɗe rai take. A bakin ƙofar parlon suka tsaye, Khadijah ta dafatan ganin yanda ta haɗe rai ya sanyata murmushi kafin ta ce “To wai mene abun haɗe ran? Da ban zo bafa” Kamar zata yi kuka ta ce“To dan Allah ba sai ki kwana ba. Daga zuwanki” Waro idanu Khadijah ta yi, Ta girgiza kanta ta ce“flight ɗin safe zan bi zuwa Kano. Kin ga ai ba zan kwana ba, Ke dai ki bari nan bada jimawa ba zan zo idan kuma kun tafi US shikenan” “Ni ba zan bisu ba” Cewar Nana a shaƙe. Taɓe baki Khadijah ta yi ta ce“To sai ki yi ta zama a gida ai. Ni kin ga tafiyata, ki koma ciki” “Ba zaki zo na rakaki wajen Maimoon ba?” Tsayawa Khadijah tayi akan stairs ɗin balcony ɗin, Ta juyo tana kallonta kafin ta ce“To ai baki tambaya ba.” Tuni Nana ta ware mayafin dake kanta ta yafa ta yi gaba tana cewa“Ke ni ba'a hanani fita ba." Murmushi kawai Khadijah ta yi sai kuma tabi bayanta. Maimoon na riƙe da turaren wuta aka buɗe kofar parlourn, Duk zatonta Yaya Aliyu ne ya dawo. Ganin su Nana ya sanya ta ajiye kaskon ta nufosu tana murmushi ta ce“Laaa amarya ce da ƙawarta?. Sannunku da zuwa” Murmushi suka yi Nana ta janyeta daga jikinta tana cewa “Ni bari kar ki shafa min ciki” Harararsa Maimoon ta yi tana riƙe da hannun Khadijah ta ce“Ai ba sai na shafa miki ba, nan bada jimawa ba zaki ganki dashi” “Bakin ki ya sari ɗanyen kashi!” Cewar Nana bayan ta zauna kan ɗaya daga cikin luxury sofa ɗin dake zagaye da parlon. Maimoon bata sake bi ta kanta ba ta shige kitchen, Drinks ta kawo musu sannan ta sake komawa. Nana ta kalli Khadijah wadda ta yi shiru ta ce“Ke kar ki sha” “A saboda me zaki hanata sha?” Ta tsinkayi muryar Maimoon ɗin a kanta, Komawa ta yi ta jingina da jikin kujera ta ce“To sai ta cika cikinta da abinci” “To ina ruwanki?” Maimoon ɗin ta sake tambayarta a fusace. Harararta Nana ta yi sanin halin jarabarta ta ce“Da ruwana ɗin, Kuma wallahi sai na faɗawa Yaya Aliyu.” Wani dogon tsaki Maimoon ta ja sannan ta ƙarasa gaban Khadijah da kanta ta zuba mata ruwan a glass cup ta miƙa mata, Khadijah ta karɓa tana murmushi sannan ta sha. Hira suka dinga yi da Khadijahn kasancewar ta santa sosai a Aun, Ita kuwa Nana ko kallon inda suke bata yi ba, hankalinta na kan wani movie da ake haskawa a mbc max. Suna nan zaune har after 15mins Khadijah ta miƙe tana kallon agogon dake maƙale a parlourn ta ce“Bari naje kar dare ya yi min” Miƙawa Maimoon ta yi ta ce“Ayya daga zuwanki?” murmushi Khadijah ta yi ta ce“Wallahi da shigewa ma fa zan yi, Nana ce ta ce mu zo.” sai a sannan ta mai da Idanunta kan Nana wadda ke kallon tv,Ta yi murmushi kamar ba ita ta gama yi mata masifa ba ta ce“Hajiya Nana irin wannan kwalliya haka? Ki ce amarcin ake zubawa.” ba zaka taɓa cewa da Nana take ba dan ko inda take bata kalla ba, Maimoon ta kalli Khadijah wadda ita ma take kallon Nanar sai kuma ta ce“kin san halin mutuniyar. Ina zuwa Mimi” Okay kawai Khadijah ta ce, Maimoon ta bar parlour da sauri, Sai a sannan Khadijah ta ƙarasa Kujerar da take ta zauna tana murmushi ta ce“Haba mana Nanar uncle fushi fa ba naki bane” “Ce miki nayi fushi nayi?” Ta yi tambayar tana kallonta, Girgiza kai Khadijah ta yi, Nana ta sake ɗauke kanta ba tare da ta sake cewa komai ba. Itama Khadijahn shiru ta yi dan ta fuskanci abun ne ya motsa, ba'a wani jima ba Maimoon ta dawo parlourn hannunta riƙe da wata leda mai ɗan fadi,Ta miƙawa Khadijah dake tsaye ta ce “Sorry dan Allah ba yawa kin ji.” Murmushi Khadijah ta yi kafin ta amsa ta ce“Allah sarki Maimoon uwar kyauta. Thank you, Allah ya raba lafiya” Da Amin ta amsa, Nana ta miƙe ta yi waje without say anything. Da idanu duk suka bita, Sai kuma Maimoon ta dafata ta ce“kada ki biye mata kin san halinta” murmushi Khadijah ta yi ta ce“nii I'll not.” Suka sake sallama sannan ta bar parlour, Koda ta fita tsaye ta hangeta gaban motar da aka kawota ta cake a wajen kamar wadda aka dasata, Khadijah ta girgiza kanta sai kuma ta ƙarasa wajen, Buɗe motar ta yi ta shiga bayan Nanar ta matsa, Ta kalleta ta ce“Sai an jima.” “Ki gaida su Mami” Ta yi maganar a shaƙe. “Zasu ji” cewar Khadijah tana rufe motar, drivern ya ja motar suka bar wajen, Da idanu Nana tabi motar tasu har suka ɓacewa ganinta, ta sauke numfashi sannan ta nufi hanyar komawa apartment ɗinta. Tunda ta tawo ta hangeshi tsaye gaban motarsa, da alama dawowarsa kenan. Dan haka ta ƙara saurin da take dan ba son magana take dashi ba, Cikin rashin sa'a idanunsa ya kalli inda take, Kasancewar da wadataccen haske a wajen kuma gari bai gama duhu ba ya sanya ya ganeta, Gaba ta yi ba tare da ta kalli ko inda yake ba. Safwan ya biyo bayanta da sauri yana kiran sunanta, Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba. Ya karasa gaban nata yana haki saboda saurin da ya yi kasancewar ba lafiya gare shi ba. Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta masu ɗauke da zanen henna har sannan, Safwan ya ja dogon numfashi ya sauke kafin ya ce “Nana na san na aikata kuskure, na karya alƙawarin da nayi miki. Amma dan Allah ina neman afuwarki, ki yafe min, wallahi zuciyata ta kasa samun sukuni. Na kasa samun abin da nake so, koda yaushe tunanin ki nake, ina tunanin abin da nayi miki. Dan Allah dan Annabi Nana ki yafe min.” Ya ƙare maganar cikin wani irin sanyin murya. Sosai taji jikinta ya yi sanyi, Duk da riko ta kasance ɗabi'arta amma taji zata iya yafewa Yaya Safwan ɗin, dan haka ta sauke numfashi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce “Ni na riga da na yafe maka Ya Safwan. Na san duk abin da ya faru ƙaddara ce, kuma ban isa na guje mata ba, dan haka ka daina damuwa akan wannan abun, Ya riga da ya shige har abada.” Ajiyar zuciya Safwan ya sauke yana jin wani abu na faɗa masa wanda da ya tokare masa a ƙirji, Ya jinjina kansa kafin ya ce“Allah sarki, nagode sosai Nana, Allah ya baku zaman lafiya da Yaya, Ya kaɗe fitina a cikin auren ku. Ya baku zuri'a ta gari.” “Amin na gode Yaya.” Ta amsa cikin wani irin yanayi, Ita kanta ta gaza gane abin da hakan ke nufi. Zuciyarta sai bugawa take, sun ɗauki a ƙalla mintina biyu babu wanda ya ce da wani ƙala, can dai Safwan ɗin ya ce“Tom sai da safe Nana, Allah ya bamu alkhairi.” Kamar jira take ta ce“Amin ya rabbi.” Daga haka ya matsa mata ta yi gaba. “Nana!” Safwan ya sake kiran sunanta, Juyowa ta yi ta kalleshi. Ya tako har gabanta ya ce “Mantawa nayi zan faɗa miki ki dinga addu'a Nana. Ki riƙe addu'a kin ji” gyaɗa masa kai ta yi kafin ta ce“Tom in sha Allah Yaya” Murmushi kawai ya yi, Ta dinga kallonsa ganin yanda kamarsa da Uncle Abdusammad ta fito. Ya ce“tom jeki” gyaɗa kanta kawai ta yi sannan ta juya ta ci gaba da tafiya, Shima ya koma inda ya bar key ɗin motarsa ya dauka sannan ya nufi cikin gidansa. **** Gajiya ta yi da jiransa ta yi kwanciyarta akan sofa, nan da nan kuma wani bacci ya ɗauketa. Sai kusan ƙarfe 10:30 na dare ya shigo gidan, Kai tsaye kuma ɗakinsa ya nufa, Ya watsa ruwa ya fito ya koma ƙasa. Kasancewar Zahra ke girki ya sanya ya zauna a ƙasan, Ta kawo masa abinci, fuskarsa a sake suka ci tare. Bayan sun gama wani guard ya shigo hannunsa riƙe da ledoji guda biyu, A gabansa ya ajiye sannan ya juya ya fice. Abdusammad ya tura mata ɗaya daga cikin ledojin, Karɓa ta yi ta buɗe gasasshiyar kaza ce a ciki guda biyu, Sai ice-cream na roba manya guda biyu. Ta yi murmushi ta ce“to an gode Allah ya ƙara arziki.” da Amin ya amsa sannan ta tashi ta kwashe kaf kayan da suka yi amfani dasu ta kai Kitchen, Koda ta sake dawowa a tsaye ga ganshi ya kalleta ya ce“sai da safe ko.” Murmushi ta yi duk da yanda take jin babu dad'i ƙasan ranta haka ta daure ta ce“tom Allah ya tashe mu lafiya.” Amin kawai ya ce sannan ya nufi upstairs hannunsa riƙe da ɗaya ledar. Sai da ya yi jim a bakin ƙofar kafin ya murɗa handle ɗin a hankali, Kwance ya hangeta kan sofa ta rufe fuskarta da hannayenta. Sam bai yi tunanin bacci take ba, Dan haka ya ƙarasa ciki ya ajiye ledar hannunsa akan table sannan ya taɓa ta ya ce “Nana! Nana!” Kasancewar bata da nauyin bacci ya sanyata buɗe idanunta, Ta tashi zaune tana murza idanun, lokaci ɗaya kuma ta zabura ta sauka daga kan kujerar. Bai ce mata komai ba ya gyara zamansa kan kujerar, Ta koma can nesa dashi ta zauna sannan ta ce“Sannu da zuwa” “Yauwa!” Ya ce ba tare da ya kalleta ba. Shiru wajen ya ɗauka, Ta dinga kallon sa ganin yanda ya yake danna wayarsa hankali kwance. Can dai ta miƙe tuna abin da Khadijah ta ce mata, Ta nufi dining area ɗin dake cikin parlon, ta gefen ido ya kalleta sai kuma ya ci gaba da abin da yake. Ɗaya bayan ɗaya ta kwaso kayan tsaf ta jera akan dining, Bai san sanda ya ajiye wayar hannunsa ba ya dinga kallon ta da mugun mamaki. A gabansa ta tsuguna ta ɗan kalleshi sai kuma ta dauke kanta ta dauko plate ta ce “Me zan zuba maka?” Abdusammad da mamaki ya kusa daskarar dashi ya girgiza kansa a sanyaye ya ce“Girki ki ka yi Nana? Wane ya saka ki girki?” Ya jera mata tambayoyin har sannan idanunsa akan ta yana mamakin abun. Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta kamar ba ita ba ta ce“Ni ce na dafa maka, ai kai mijina ne kuma ni zan dinga yi maka girki yanzu.” ta yi maganar a shagwaɓe. Murmushi ya yi yana girgiza kansa ya ce “To naji nagode Nana, amma ni yanzu na ƙoshi naci abinci.” Da sauri ta kalleshi, lokaci ɗaya annurin dake man fuskarta ya ɓace, Ta yi sak tana kallon sa. Kamar ba zata yi magana sai kuma ta ce“Shi ne kaci abincin? To a ina kaci abincin?” “To ay ban san kin yi girki ba Nana. Zahra ce ta dafa naci a ƙasa” Da wani irin mamaki take kallon sa, nan da nan hawaye ya cika fuskarta, Ta tashi daga wajen ta koma can ƙarshen parlourn ta silale a ƙasa ta fashe da wani raunataccen kuka. Abdusammad ya dinga kallonta lokaci ɗaya kuma ya tuna abin da ya ce, Ya kai hannunsa ya rufe bakinsa ya ce “Na jangwalo masifa.” Ya miƙe yana shirin zuwa wajen da take, Tana ganin haka ta mike tsaye tana wani irin kuka kamar zararriya ta ce “Ni kada ka zo kusa dani! Kada ka zo inda nake! Tun da ita kake so, Ai daman ita ce matarka. Ni kuma baka sona, Saboda ni ba irin wadda ka ke so ba ce, Shi ne kaje ka ci abincinta bayan kuma kwana na ne, Shi ne kaje ka ci abincinta tun da ita ka ke so...” Ta kasa ci gaba da maganar saboda kukan da yaci ƙarfinta, Girgiza kansa ya yi yana tsaye a inda yake ya ce“Ba haka bane Nana, ban san kin dafa abinci ba ai, dana sani ba zan ci a wajenta ba. Ke kuma ki ka ce min baki iya girki ba ko..” “Ai daman saboda haka kaje ka ci a wajenta, saboda ni ƙazanta zan yi maka. Daman ai ita ka ke so, Kuma ita ka ke fara zuwa ka gani, ni kuma babu ruwanka dani. Wallahi ba zan yarda ba!” Ta ƙare maganar cikin gunjin kuka, Sake yo gaba ya yi a ƙoƙarinsa na son zuwa inda take, Ta daka uban tsalle ta bar wajen da gudu. Bedroom ɗinta ta shige ta garƙame ƙofar da maƙulli, Ya dafe kansa sai kuma ya nufi wajen gudun tashin hankali yasa ya taya a bakin ƙofar muryarsa a sanyaye ya ce “Look Nana, ba nace miki ban sani ba, Ki buɗe ƙofar ki ji. Ki daina kukan” Tana tsaye jikin ƙofar sai kukanta take, Jin bata ce komai ba ya sanya shi sake cewa “To shikenan ki buɗe ƙofar zan baki abin daɗi, har kaza na siyo miki kin ji ki buɗe ƙofar” A hankali ta tsagaita da kukan, Ta matsa daga jikin ƙofar har sannan tana shessheƙar kuka, Jin ta fara yin shiru ya sanya ya ce “Yauwa buɗe kin ji Nanata, Yar ƙaramar matar uncle ɗinta. Buɗe kin ji” “Ka miƙo min kazar kawai” Ya tsinkayi muryarta. Shiru ya yi sai kuma ya ce“to ai kin ga babu window anan, ki buɗe ƙofar sai na miƙo miki na tafi.” Shiru ta yi tana jin kamar ta buɗe ƙofar, Ta goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta ce“to ina kazar?” “Bari na ɗauko” Ya ce a hankali. Daga haka ya koma inda ya ajiye ledar kazar ya ɗauko ya dawo bakin ƙofar sannan ya ce “Gata a hannuna, Buɗe sai ki karɓa.” A hankali ta zare key ɗin dake jikin ƙofar, ta ɗan buɗe kaɗan ta zuro hannunta na dama ta ce“Bani ga hannuna.” yanda ta yi maganar ya kusa sanya shi tuntsirewa da dariya amma ya dake ya miƙa mata kazar, Tana ƙoƙarin ƙarba ne taji ya jawo hannun nata gaba ɗaya. Ta zunduma ihu jin ya buɗe ƙofar ɗakin duka, Ya shigo ciki har sannan yana rike da hannun nata da kuma ledar kazar, Ƙoƙarin janye nata hannun ta dinga yi, sai dai irin riƙon da ya yiwa Hannun bana wasa bane. Dan haka ta kasa, Da ɗaya hannun nasa ya ɗagata cak bai sauketa ko ina ba sai kan gadon, Ya saki hannunta yana ƙoƙarin zama, Juyawa ta yi tana shirin barin wajen taji ya jawota ta faɗo jikinsa. A hankali ya sanya duk hannayensa biyu ya rungumeta a faffaɗan ƙirjinsa, Nana ta fara ƙoƙarin janye jikinta tana kuka a hankali, Murmushi ya yi ya ja hancinta ya ce “iyye! Ƴar yarinyar ƙarama zata min wayo. Kin san shekarun dana baki kuwa?” Ko saurarensa bata yi ba ta ci gaba da kukanta, Ya kalli ɗan ƙaramin bakin nata wanda ya sha lip gloss sai sheƙi yake. Haka kawai yaji tsigar jikinsa na tashi, Koda wasa bai son yaga mace ta saka lip gloss musamman idan yana da alaƙa da ita, Yanzu zai yi jikinsa na neman sauyawa. Ya fara ƙoƙarin kai hannunsa domin ya goge mata, danƙon da yaji yasa ya tabbatar da ba kaɗan ta shafa ba, kuma ba lallai ya fitan a hakan ba, Dan haka ya ɗago fuskarta da hannunsa ɗaya. A hankali kuma ya durƙusar da kansa daidai fuskarta, Lokaci ɗaya kuma ya ɗora bakin nasa akan nata ya fara tsotsa a hankali. Wata irin zabura Nana ta yi, Ta ƙamkameshi tana jin wani irin fitsari na tawo mata, sai da ya suɗe kaf man leɓan bakin nata sannan ya sanya ɗayan hannunsa ya buɗe bakin nata, Cikin hanzari kuma ya zura bakin cikin nata. Kusan sumewa Nana ta yi jin yanda yake sauke mata wasu azababbun kisses, nan da nan jikinta ya saki ta gagara koda motsa ɗan yatsanta ne. Jin hannunsa akan ƙirjinta ya sanya sakin wani marayan kuka, Cikin ikon Allah ta sanya hannayenta duk biyun ta ture shi, Kasancewar jikinsa a sake yake ya sanya ya yi baya, Ta tashi da gudu ta shige toilet ta rufe ƙofar gam. Tashi ya yi ya biyo bayanta ya tsaya a bakin ƙofar muryarsa a ɗan shaƙe ya ce “Kee! Nana! Nana!” Ban da kuka babu abin da take, Ta sulale a ƙasan bayin tana kukanta, Buɗe gajiyayyun idanunsa ya yi akan ƙofar kamar ba zai magana sai kuma ya ce “Ki ka ce na shirya cin amarci na siyo miki kaza. To gashi na kawo miki ai” Girgiza kanta ta dinga yi cikin kuka ta ce“a'a uncle ni bana son kazar, wallahi bana so! Bana son kazar amarcin, ka ɗauki kazar ka tafi da ita.” Sauke zazzafan numfashi ya yi jikinsa har wani rawa yake ya ce “Ai baki isa ba! Tun da ki ka yarda na kawo kaza dole ki fito naci amarcin!” 08106608363 Nanameera. *🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 50. Sake rushewa ta yi da wani sabon kukan ba tare da ta ce komai ba, Ya yi shiru yana sauraren sautin kukan nata kafin ya sake cewa“Idan ki ka bari na buɗe ƙofar nan da kai na sai na baki mamaki!” Sake cure jikinta ta yi waje ɗaya ta sanya hannunta ta rufe bakinta tana ci gaba da kukanta a hankali. Above 5mins kafin ya sauke numfashi ya juya ya bar ɗakin, Tana jin ƙarar rufe ƙofa amma sam taƙi tashi ta fito, Dan tunaninta ba tafiyar ya yi ba. Tana nan zaune har kusan ƙarfe 11:00 na dare, Bacci ya fara ɗaukanta a zaunen, Gajiya ta yi dan kanta ta tashi ta buɗe ƙofar toilet ɗin a hankali tana leƙa ɗakin. Ganin da gaske babu kowa a ciki ya sanya ta fito, Kai tsyae kuma wajen ƙofa ta nufa ta murɗa key kuma ta bar shi a jiki, Sannan ta koma ta cire kayanta ta ɗauki na bacci ta saka ta hau kan gadon, Ko ta kan ledar kazar dake wajen bata yi ba. Ta duƙunƙune jikinta da duvet sannan ta rufe idanunta, Sai dai kuma sam baccin yaƙi zuwar mata gani take idan ta rufe idanunta Abdusammad zai dawo ɗakin ne. Dan haka ta fara kuka a hankali, A haka har bacci ɓarawo ya saceta. Washegari around 9am ya tsaya jikin ƙofar, Kamar ya tafi sai kuma ya fara knocking a hankali. Nana dake zaune ƙasan gado ta jingina kanta da jikin gadon ta ɗago kanta a firgice, Kallon ƙofar ta dinga yi jiki a sanyaye. Ya ci gaba da knocking dan duk tunaninsa bacci take yi, Ganin bata da niyyar buɗewa ya sanya ya ce “Nana! Nana! Nana!” Kasa amsawa ta yi, Nan da nan jikinta ya fara rawa. Dan ita har ga Allah yanzu tsoronsa take, Ta miƙe ta koma can ƙarshen gado ta zauna tana ci gaba da kallon ƙofar. Gajiya ya yi da bugun ya ce“Idan ki ka bari na ɗauko maƙulli na bude ƙofar sai ranki ya ɓaci!.” Tura baki gaba ta yi ta sunkuyar da kanta, Ya bar jikin ƙofar, Shirun da taji an yi ya sanya ta miƙe a hankali ta ƙarasa gaban ƙofar. Ta kasa kunnenta a jikin ƙofar amma bata ji alamar yana nan ba, Dan haka ta zare key ɗin ta buɗe ƙofar ta leƙa a hankali. Cikin rashin sa'a taji ya turo ƙofar da ƙarfi, Ta yi baya ta faɗi cikin ɗakin. Tsayawa ya yi a bakin ƙofar yana ƙare mata kallo, Ta miƙe da gudu ta nufi hanyar toilet, Sai dai kafin ta kai ga ƙarasawa ya sanya ƙafa ya taɗeta, ta yi baya zata faɗi ya riƙota ta faɗa jikinsa. Wata irin zabura Nana ta yi tana ƙoƙarin kwace jikinta, Ya haɗe fuska babu alamar wasa ya ce “Kin nutsu ko saina mareki?” Girgiza kanta ta fara yi tana hawaye ta ce“Dan Allah uncle ka yi hakuri, Dan girman Allah wallahi ba zan sake ba. Ba zan ƙara ba, Ka sakeni!” Ta ƙare maganar tana kuka. Bai ce mata komai ba ya jata har gaban gadon, ya zauna sannan ya zaunar da ita gefensa har sannan babu alamar walwala akan fuskarsa ya ce “Ni abokin wasanki ne da zan dinga kiran ki kina ji ki min banza? am I play with you?” Girgiza kanta ta yi a hankali tana sunkuyar da kanta, Ya yi kwafa sannan ya ce“Duk ranar da ki ka sake min irin haka sai na ɓata miki, Kinji abin da na ce.?” Gyaɗa masa kai ta yi nan ma, Ya yi shiru yana kallon yanda take ta rawar jiki, Ɗauke kansa ya yi yana karewa ɗakin kallo. Lokaci ɗaya idanun sa ya sauka akan ledar kazar dake kan drawer, Miƙewa ya yi ya ƙarasa wajen ya ɗauko ledar ya dawo. Nana na ganin haka ta fara ja da baya, Buɗe ledar ya yi yaga babu abin da ta taɓa a ciki, Ya mayar ya ajiye a ƙasa sannan ya ce “Kin ci kazar?” Saurin girgiza masa kai ta yi ta ce“A'a wallahi, Ban ci maka ba uncle. Ban ci ba wallahi!” Ta ƙare maganar tana kuka, Sake haɗe rai ya yi kafin ya ce“Me yasa? Ba cewa nayi ki ci ba?” “Na ƙoshi, Ni bana ci.” Ta yi maganar a sanyaye. Taɓe baki ya yi kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce“To ni yunwa nake ji, Tashi ki mana warming ɗinta sai ki kawon” Jikinta har rawa yake ta mike, ta ɗauki ledar sannan ta fice daga ɗakin. Ya bita da kallo sai kuma ya girgiza kansa yana murmushi. **** Zahra ta dinga kallon Anty Khadijah da mamaki can kuma ta ce“Lafiya Anty da safen nan?” haɗe rai Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“Dallah magana na zo mu yi dake.” Zahra ta kalli hanyar sama sai kuma ta kalli Anty Khadijah ta ce“Doctor yana nan, muje waje.” Taɓe baki Anty Khadijah ta yi sai kuma ta juya ta fice daga parlourn tana taunar cew gum, Zahra ta sauke numfashi sannan tabi bayanta dan daman hijabi ne a jikinta. A ƙasan wata bishiya suka zauna kan fararen kujeru, Zahra ta yi shiru tana jiran taji abin da Anty Khadijahn zata ce. Ita kuwa Aunty Khadijah Shiru ta yi tana kallon Zahra kamar yanda malamin ya ce mata, After some minutes Zahra ta ce “Anty mene ne? Naji kin yi shiru.” Numfasawa Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“Daman akan maganar auren nan naki ne, na ce wai kin haƙura zaki zauna da kishiya kenan?” Shiru Zahra ta yi kamar mai tunani, Anty Khadijah ta yi murmushi sannan ta ce“Ki yi tunani Zahra. zamanku da ita ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba, Saboda kin san ita yar uwarsa ce, a gabanki zai dinga nuna mata tafi ki, kuma ma ban da abin ki ya za'a yi mutum ya zauna da yarinyar da ya raina. Har da ke fa aka yi rainonta, Ace kuma yanzu ta zo ta aure mijinki, Tana kwana ɗaki ɗaya dashi, Haba wannan abu har ina!” Aunty Khadijah ta ƙare maganar tana kallon Zahra to see her reaction. Zahra da duk abin duniya ya dameta ta girgiza kanta jiki a sanyaye ta ce “To ya zan yi Anty? Dole nayi hakuri kamar yanda Umma ta ce min. Da badan na shiga na fita na saka Siyama ta auri Safwan ba da Nana bata auri mijina ba, kin ga ashe Allah ne ya mata sakayya, Dole na yi haƙuri.” Taɓe baki Anty Khadijah ta yi ta ce“To kenan zaki ci gaba da zama a haka kamar wata mara yanci kenan?” Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“A'a. Na san doctor ba zai taɓa fifita Nana akaina ba, saboda ya san me yake, Yana da ilimi kuma yana aiki da iliminsa. Har zuwa yanzu ban ga ya yi min wani abu da ke nuna rashin kyautatawa ba.!” Anty Khadijah ta yi shiru can kuma ta gyaɗa kanta ta ce“Haka ne, To Allah ya ƙara haɗa kan ku.” “Amin Aunty.” Zahra ta yi maganar a sanyaye, Anty Khadijah ta ce“Amma duk da haka bai kamata ki zauna haka babu wani abun tsare jiki ba. Kin san ita kishiya muguwar aba ce, Shiyasa na karbo miki wani magani ki samu ki jiƙa da ruwan ɗimi ko shayi ki sha, Babu abin da zai sameki in sha Allah.” Ta ƙare maganar tana laluba jakarta, Zahra ta yi shiru tana kallon ta har ta dauƙo wani ƙullin magani karami. Zahra ta karɓa sannan ta ce“To Anty Nagode sosai Allah ya ƙara girma.” Da Amin ta amsa sannan ta ce“Yaushe zaku koma ne?” Zahra ta yi murmushi ta ce “Gobe idan Allah ya kai mu.” Zaro idanu Anty Khadijah ta yi ta ce“Da wuri haka? Amma shi ne baki zo gida ba?” Zahra ta ce“Nima jiya da daddare yake faɗa min, An jima ai zan zo in sha Allah.” Anty Khadijah ta jinjina kanta tana ƙoƙarin miƙewa ta ce“To Allah ya kai mu.” Tashi ita ma Zahran ta yi ta amsa da Amin sannan ta ce“Ba zaki je wajen Siyama ba?” girgiza kai Anty Khadijah ta yi ta ce“a'a yau ai ba wajenta na zo ba, Sauri nake akwai inda zan je.” Zahra ta yi murmushi ta ce“To Anty ki gaida gida.” “Zai ji. Dan Allah Zahra kada ki yi wasa da maganin nan!” Gyaɗa mata kai ta yi tana murmushi ta ce“in sha Allah Anty.” Daga haka suka sake sallama ta nufi motarta ita kuma ta koma ciki. **** Bakinta ɗauke da sallama ta shigo dakin, Ya amsa a hankali sannan ya kalleta. “Na gama uncle.” Ta ce tana wasa da fingers ɗinta, Jinjina kansa ya yi sannan ya tashi tsaye ya ce“okay muje” bata ce komai ba ta juya ta koma parlourn, Yabi bayanta shima. Durƙushe ya sameta gaban kayan tea ɗin data ajiye, Ta hada masa tea ɗin kamar yanda ta san yana sha sannan ta miƙa masa inda ya zauna. Ta jawo masa bowl ɗin data zuba kazar da kuma plate ɗin data zuba Irish potato ɗin data soya, Kallon ta kawai yake har ta gama ajiye komai ta tashi ta koma kan kujera ta zauna, Ya kalleta kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce “Ke ina naki abincin?” “Na ƙoshi.” Ta ce a takaice, Haɗe rai ya yi ya ce“zo nan.” y nuna mata gefen sa, Kasa masa musu ta yi ta taso ta dawo wajen ta zauna ta sunkuyar da kanta, Ya dauko wani mug ɗin ya tsiyaya mata rabin shayin nasa sannan ya tura mata gabanta. Ita dai ba ce komai ba, Ya yi bismillah sannan ya kai tea ɗin bakinsa, Kallon sa ta dinga yi kamar ta samu tv, Ya kalleta ya ce“Wasa nake miki?” Sai a sannan ta ɗauki mug ɗin ta kai bakinta dan ba ƙaramar yunwa take ji ba, kasancewar jiya bata ci abinci ba ta zauna jiransa. Ganin shayin kawai take sha ya sanya ya ce“Ba zaki ci abincin ba?” Ya kare maganar yana tauna naman dake bakinsa, Girgiza masa kai ta yi kafin ta ce“Ni bana ci, na ƙoshi.” Ya dinga kallon ta can kuma ya ce“Da ki ka ci me?” “Ni bana ci, Ba zan ci ba." Yanda ta yi maganar tana yatsine fuska ya sanya shi murmushi, Ya ce“Saboda me?” Kamar zata yi kuka ta ce “To ba ka ce idan naci kazar sai ka ci amarcin ba, ni kuma bana so. Dan haka ai ban ci kazar taka ba ko?” Ta ƙare maganar tana kallon sa hawaye ya cika kurmin idonta. Sosai ta bashi dariya amma ya dake ya ce“To ai ko kin ci ko baki ci ba ni sai naci amarcin yarinya, Dan haka it's better for you ki ci abincin ki.” Shiru Nana ta yi tana kallon sa, nan da nan hawaye ya fara zubowa akan fuskarta. Abdusammad kuwa ɗauke kansa ya yi yana kai naman bakinsa ya fara taunawa a hankali, Yana jin yanda take shessheƙar kuka a hankali, Ya juyo yana kallonta sai kuma ya janye kanta ba tare da ya yi magana ba ya buɗe bakinta da hannunsa, A hankali kuma ya kai nasa bakin ya juye mata kaf naman dake bakinsa. Wani irin jan numfashi Nana ta yi, Ya saketa ya ɗauke kansa, Ta dinga kallon sa tana kuka kuma taƙi tauna naman, Kamar ba zai magana sai kuma ya ce “Cinye nace” Cikin kuka ta ce“wallahi ni ba zan ci ba. Ni bana so, Ni ka bar ni kawai!” Ganin yanda duk ta daga hankalinta ya sanya shi yin murmushi kafin ya ce“Shikenan na fasa cinye abin ki.” Ya tura mata bowl ɗin gabanta, Kallon sa ta yi taga ya gyaɗa mata kai. Ta ɗauke idanunta hawaye na sake zubowa ta fara tauna naman, Tashi ya yi ya koma kan kujera ya zauna dan ya ƙoshi, ita kuwa gyara zamanta ta yi a ƙasan ta fara cin kazar tana lumshe ido, kasancewar naman kaza na daga cikin abin da take so. Sai da ta kusa cinyewa sannan ta fara gyatsa, Dan haka ta haƙura ba dan ta daina mata daɗi ba, Ta ɗauki ruwa ta sha sannan ta tashi ta koma kujerar daya zauna ta zauna ita ma, Kallon ta ya yi sai kuma ya dauke kansa ya mayar kan tv inda yake kallon aljazeera, Ta fara lumshe ido saboda ƙoshin da tayi ga kuma sanyin ac dake dukanta. “Bacci zaki yi?” Ta ji ya tambayeta, Gyaɗa masa kai ta yi ya ce“Zo ki kwanta” ya nuna mata cinyarsa, Kamar jira take ta matsa kusa da shi ta ɗora kanta akan cinyarsa ta sanya hannayenta duk biyun ta zagaye ƙugunsa. Ta rufe idanunta tana shirin baccin ta ji ya ce “Ki yi baccin idan kin tashi sai ki je wajensu Amma, cause gobe zamu shige.” Cikin magagin bacci ta ce“Uncle ka bar ni anan.” Kallon ta ya yi sai kuma ya girgiza kansa ya ce “Naƙi ɗin. Tare zamu tafi in sha Allah, Da a ce baki da visa ne shi ne zan bar ki amma tun da kina da tare zamu tafi.” Tura baki ta yi tana ƙoƙarin rufe idanunta ta ce “Ni ba ran bika ba.” Murmushi kawai ya yi sai kuma ya ja dogon hancinta ya ce“To bari muga.” bata sake cewa komai ba ta fara baccinta, Shima ɗin bai sake mata magana saboda saukar numfashinta da ya fara ji. **** Safwan na zaune gefen gadonsa, hannunsa rike da wata farar takarda yana dubawa, Can kuma ya linke takardar ya ja idanunsa ya lumshe, hawaye suka fara zirarowa ta gefen idanun sa. Yana nan zaune aka buɗe ƙofar dakin, bai daga kansa ba dan duk zatonsa Siyama ce, Haule ta ƙaraso ciki hannunta riƙe da ruwan gora ta tsaya gaban gadon tana kallon sa, Ta jima a tsaye ganin bai buɗe idanunsa ba ya sanya ta ce “Hamma!” Muryarta da yaji ya sanya shi buɗe idanun sa, Ya kalleta ba tare da ya ce komai ba. Haule ta sunkuyar da kanta ta ce“Ga ruwan in ji Anty Siyama.” Jinjina kansa ya yi sai kuma ya miƙa mata hannu, Ta miƙa masa ruwan ya karba sannan ya ce“Nagode!.” bata ce komai ba taja ta tsaya, Safwan ya buɗe ledar dake gabansa ya fara zaro drugs ɗin, ɗaya bayan ɗaya ya dinga ɓalla yana sha har ya kammala. Ita dai Haule sai kallon sa take cike da tausayi, Bayan ya kammala ya ajiye empty bottle ɗin akan drawer. Sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya ta juya zata fita taji ya ce “Haulat!” Cak ta tsaya, kafin ta juyo tana kallonsa, Da hannu ya yi mata alama da ta zo. Ta dawo gefensa ta zauna ta sunkuyar da kanta. Safwan ya dinga kallon ta ba tare da ya ce komai ba, Ita ma ɗin bata yi yunkurin yin wata magana ba, Can dai ya numfasa ya ce “Haule ina son ki yafe min kin ji, Ki yafe min abin da na yi miki da kuma wanda zan miki, Dan Allah kin ji...” Ya yi shiru hawaye na biyo kuncinsa, Haule da hankalinta ya tashi ya girgiza kanta tana kuka ta ce “Babu abin da ka yi min Hamma, idan ma kuma ka yi min to na yafe maka. Wallahi ban taɓa riƙe ka ba, Na yafe maka Hamma!.” Cikin shassheƙar kuka ya ce“Kin yafe min Haule? Har zuciyarki kin yafe min?” gyaɗa kanta ta yi tana hawaye itama. Safwan ya ja numfashi ya sauke sannan ya janyo takardar dake gefensa ya miƙa mata, Sai da taji gabanta ya faɗi, Amma ta karba ba tare da ta ce komai ba. Safwan ya jingina da jikin gadon sannan ya ce “Ki je ki kai wa Hajiya Babba, Ko kuma Yaya Abdusammad duk wanda ki ka samu kin ji.” Gaba ɗaya sai taji jikinta ya yi sanyi, wani irin sanyi wanda bata san dalilinsa ba, Ta miƙe hannunta riƙe da takardar ta ce“To Hamma Safwan.” yanda ta fadi sunan nasa ya sanya shi rufe idanun sa, ƙirjinsa na tsananta bugu, Ta juya ta fice daga ɗakin ya bita da kallo lokaci ɗaya kuma ya fashe da wani irin kuka kamar ƙaramin yaro. Tana fita Siyama ta shigo ta tsaya gaban gadon tana kallon sa, Ta daɗe a tsayen har sai da taji ya fara daina kukan ya koma jan numfashi sannan ta ce “Ka sake tan?” Gyaɗa mata kai ya yi ba tare da ya buɗe idanunsa. Siyama ta yi murmushi sannan ta ce “Better!”. 08106608363 Nanameera. *🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 51. Shiru Safwan ya yi bai ce mata komai ba, Siyama ta sake cewa“Yanzu ka ga sai muyi zaman mu tare, babu wadda zata sake shigowa gidan nan da sunan mata. Ni kaɗai na isheka” Jinjina kai kawai ya yi kafin ya zame ya yi kwanciyarsa akan gadon, ta daɗe tsaye a wajen kafin daga bisani ta juya ta fice daga ɗakin. Haule na fita ta nufi apartment ɗin Hajiya Babba tana tafe tana tunani, Haka kawai taji zuciyarta bata yarda da takardar ba. Dan haka ta ja ta tsaya a wajen tana ƙoƙarin warwarewa, Abdusammad ta hango tsaye shi da Aliyu suna magana. Sai kawai ta fasa buɗewa ta nufi wajen da sauri, Kallon ta suka dinga yi har ta ƙaraso wajen ta gaishesu suka amsa sannan ta ce “Arɗo daman Yaya Safwan ya ce na baka.” Kallon takardar da take miƙo masa ya yi, Sai kuma ya kalli fuskarta. Can dai ya karɓi takardar ya warwareta. _Ba sai na faɗi dalilina ba, amma ina son ku yafe min. Ni Safwan Muhammad Shuwa na saki Matata Haule saki ɗaya, saki biyu. Ina fatan zata yafe min abin da nayi mata, Safwan Mhd shuwa._ Da wani irin mamaki Abdusammad ya ɗago ya kalli Haule, ganin yanda tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskarsa ya sanyata cewa “Arɗo lafiya? Ko wani abun ya samu Hamma?” Bai iya bata amsa ba, Aliyu ya karɓi takardar ya karanta, Ban da innalil lahi babu abin da yake ja. Ya kalli Abdusammad wanda ya yi shiru yana tunani ya ce “Me yasa zai yi haka? Mene yake damun Safwan? Ni gaba ɗaya na kasa gane kansa.” Bai bashi amsa ba, dan idan har ransa na ɓace baya iya magana. Dan haka Aliyu ya yi shiru yana kallon sa, Above 5mins kafin ya sauke wani zazzafan numfashi ya kalleshi ya ce“Kai ta apartment ɗin Abba. Ina zuwa” bai tsaya jiran amsar Aliyun ba ya yi gaba abin sa. Da idanu duk suka bi shi , Haule ta ce“Hamma me ya faru?” yanda ta yi maganar a sanyaye ya bawa Aliyu tausayi, Shikenan ya mayar da yarinya ƙaramar bazawara?. Ya sauke numfashi sai kuma ya ce“Ba komai muje." Jiki a sanyaye tabi bayansa suka nufi apartment ɗin su Nanar. **** Zahra ce tsaye gaban gadonta tana ƙoƙarin yafa mayafi akan atampar dake jikinta wayarta ta fara ƙara, Ɗauka ta yi ganin lambar Anty Khadijah ta ɗaga ta kai kunne kafin ta yi magana Anty Khadijah ta ce “Zahra kin yi amfani da maganin kuwa?” Dafe kai Zahra ta yi dan har ta manta ta ce“wayyo Anty wallahi har na manta. Bari na ɗauka na sha yanzu zan tawo gida ma” Anty Khadijah ta ce“Okay ki yi maza ki sha sai ki tawo.” Ohk Zahra ta ce sannan ta kashe wayar, A jaka ta sakata sannan ta ɗauki maganin dake kan dresser ɗinta ta nufi parlour, Ruwan zafi ta ɗan zuba a cup sannan ta kwance maganin ta zuba, ta saka cokali ƙarami ta juya sannan ta kafa kai ra shanye tas. Bayan ta gama ta ɗauki ruwa ta sha sannan ta fita ta koma saman. **** Nana na zaune kan cinyar Amma tana danna wayarta aka yi knocking ƙofar, Amma dake haɗa turaren wuta ta ce“Nana je ki ga wane” To kawai ta ce sannan ta sauka daga jikinta ta ɗauki hularta data faɗi ta saka sannan ta nufi ƙofar. Koda ta buɗe tsayawa ta yi tana kallon su, Aliyu ya ce“Nana zata zauna anan zuwa an jima.” Kallon Haule ta yi sai kuma ta ce“Tam Yaya.” Aliyu ya juya ya bar wajen, ta matsa daga jikin ƙofar sannan ta ce“Zo ki shige.” Babu musu Haule ta shigo parlourn a sanyaye. Amma ta dinga kallon ta kafin ta yi magana Nana ta ce “Yaya Aliyu ne ya ce ta zauna a nan zuwa dare.” Amma ta ce“Tom shigo ki zauna mana.” “Ina yini?” Haule ta yi maganar bayan ta durƙusa, Da murmushi Amma ta amsa sannan ta ce“Ya gidan?” “Alhamdulillah.” Cewar Haule, Amma ta ce ta zauna kan kujera sannan ta zauna ta sunkuyar da kanta. Itama Nana komawa ta yi ta zauna kusa da Amma ta ci gaba da game ɗin da take yi, Bayan Amma ta gama abin da take ta miƙe ta nufi kitchen. Ta dawo hannunta riƙe da plate mai ɗauke da drinks, table ta ja gaban Haule sannan ta ajiye mata ta ce “Maza ki sha bari na kawo miki abinci.” “Na gode Amma.” Ta ce a sanyaye. Murmushi kawai Amma ta yi sannan ta koma kitchen ɗin, Nana ta tashi tabi bayanta. Tsaye ta sameta tana ƙoƙarin zubawa Haule abinci, Ta jingina da jikin cabinet sannan ta ce “Amma nima zan sake cin abincin.” Yanda ta yi maganar a shagwaɓe ya sanya Amma ta kalleta, Ta haɗe rai ta ce“Wanda ki ka bar min fa? Ko ba cewa ki ka yi kin ƙoshi ba.?” Tura baki Nana ta yi kafin ta ce“To ai yanzu ya sake bani sha'awa.” “To ba zaki ci ba!” Amma ta yi maganar tana harararta. Zumɓura baki ta yi ta ƙarasa wajen freezer ta buɗe ta ɗauki coke sannan ta fice daga kitchen ɗin, Amma ta bita da kallo sai kuma ta girgiza kanta tana tsaki. **** Bayan sallar isha'i suna zaune a babban parlourn Hajiya Babba. Papa ya numfasa kafin ya ce“To mene dalilin daya sanya ya yi haka? Akan me zai saketa? Me ta yi masa.?” Shiru parlourn ya ɗauka, Can dai Sultan ya ce“Nifa daman Papa ba tun yau ba na fuskanci sauyi daga gare shi. Safwan ya sauya kamar bashi ba, rabon da na gan shi har na manta.” “Sauyi? Wane sauyi ne da har zai iya sakin yarinya ba tare da ta masa wani laifi ba? Kuma saki mafi wulaƙanci har saki uku. Wannan shi ne sauyin?” Abba ne ya yi maganar a zafafe. Papa ya ce“Ya isa haka Ahmad, dole a bi komai a sannu. Yanzu dai idan ya dawo daga asibitin sai aji dalilinsa na yin haka.” “Babu buƙatar jin dalilinsa, Tun da har ya riga da ya yanke hukunci to magana dashi bata da amfani. Ku bar shi, ku manta dashi kawai dan Allah...” Hajiya Babba ta yi maganar cikin wata irin murya mai nuna asalin damuwar da take ciki. Abdusammad ya girgiza kansa zai yi magana ta ɗaga masa hannu. Miƙewa tsaye ta yi tana kallon sa ta ce “Kar ka damu ƙaddarata ce a haka. Mahaifin ku ya tafi ya bar ni daku, Ya huta bai san abin da ke faruwa ba. Duk abin da Safwan ya yi kai ne ka bashi dama, A matsayinka na babba ka iya watsa mana ƙasa a ido, Ka auri wadda ka san ba yar danginka bace. Baka damu da wane hali zan shiga ba, Baka damu da kallon da za'a dinga yi min ba, Sannan kuma ka koyawa ƙaninka rashin yin biyayya a gare mu” Dakatawa ta yi saboda hawayen dake zubowa daga cikin idanunta, Ta sanya hannunta ta goge kafin ta ci gaba da faɗin “Ba komai. Na haƙura, kuma mun haƙura gaba ɗaya, daman duk abin da muke yi, muna yi ne saboda ku, saboda gobenku data ƴaƴa yanku, Amma tun da hakan bai zama abin da zai saka ku ga ƙimar mu ba. Babu komai, A yi lafiya!.” Hajiya Babba na gama faɗin hakan ta nufi sama da sauri. Shiru parlourn ya ɗauka, kowa da abin da yake tunani. Abba ya kalli Abdusammad wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa ba tare da ya ce komai ba, Dafashi Abba ya yi, ya ɗago runannun idanunsa ya kalli Abba. Girgiza masa kai Abba ya yi dan haka ya mai da kansa ƙasa, Allah ne kaɗai yasan yanayin da yake ciki a sannan. Shi kaɗai ya san abin da yake ji a cikin zuciyarsa, Bai taɓa tunanin Hajiya Babba zata zubar da hawaye akan su ba, Sai gashi duk haƙuri irin nata ta buɗi baki ta faɗi irin wannan maganganun. Atta ce ta miƙe tsaye tana kallon su duka ta ce“Ai shikenan, Gobe idan Allah ya kai mu zamu koma gida nida ita.” “Amma Atta da kin bar ta anan, Ai kin ga...” Daga masa hannu ta yi, Fuskarta babu walwala ta ce“kada ka ƙarasa Ahmadi, Gobe da Haule zan tafi naje na bawa iyayenta haƙuri.” Shiru ya yi bai sake cewa komai ba, Ta bar parlourn itama. Tashi ya yi ya ƙarasa inda Abdusammad yake tsaye ya ce“taso muje.” Miƙewa ya yi suka bar parlour. Suna zuwa compound ɗin gidan Abba ya saki hannunsa sannan ya ce“Na san zaka ji babu daɗi. Kamar yanda mu ma muka ji babu daɗi, amma ka sani abin da ta faɗa gaskiya Abdusammad. Da baka auro wata ba Safwan ba zai taɓa wannan tunanin ba, A rayuwa shi Babba har kullum madubi ne, kuma abin koyon na ƙasa dashi. Kai ne babba kuma kai ka fara fito da wannan abun. Yanzu ka ga irin matsalar da muke gudu ko?” Girgiza kansa ya yi hawaye na biyo kan fuskarsa ya ce“Na gani Abba. Yanzu ya zan yi? Hankalina a tashe yake, Ya za'a yi a ce Hajiya na zubar min da hawaye, ban san hakan me yake nufi ba. Abba idan har bata so wallahi zan iya rabuwa da Zahra, Domin samun farin cikinta.” Wani murmushi irin na manya Abba ya yi, Ya dafashi sannan ya ce“Akan me zaka saketa? Kana ganin sakinta zai zama abin da zai sauƙaka wannan matsalar? Idan ka saketa ita laifin me ta yi maka? Kana ganin baka cuceta ba?.” Shiru Abdusammad ya yi, Abba ya ce“Kawai ka ci gaba da addu'a kana neman yafiyar ubangiji, Amma maganar saki sam bata taso ba, kuma ba zan taɓa bari ka yi hakan ba.” Ƙarasowar Papa ya dakatar da maganar tasu, Ya tsaya yana kallon Abba ya ce“Ahmad yarinyar nan ta zauna a wajenka, Saboda ba zai taɓa yiwuwa Atta ta tafi da ita ba. Gara ta zauna a nan muga abin da hali zai yi.” Jinjina kai Abba ya yi kafin ya ce“Nima abin da nayi tunani kenan. Idan Allah ya kaimu gobe zan yi magana da Safwan” “Ku bari zan masa magana yanzu.” Abdusammad ya yi maganar jiki a sanyaye. Girgiza kai Papa ya yi ya ce“a'a wani ɓacin ran zaka janyo, ka je gida kawai." Dan murmushin ƙarfin hali ya yi ya ce“Babu abin da zai faru Papa, idan Allah ya kai mu gobe ma zan bar ƙasar.” “Da wuri haka?” Papa ya yi maganar da mamaki dan bai san da batun tafiyar ba, Gyaɗa masa kai Abdusammad ya yi sannan ya ce“Eh. Abubuwane suka fara yin yawa acan ɗin, so i have to go.” Jinjina kai Papa ya yi kafin ya ce“Haka ne. To Allah ya yi jagora, amma bada sassafe ba dai?” “Da wuri maybe ma around 7:00am mun tafi.” Papa ya ɗan yi shiru can kuma ya ce“To Allah ya kaimu goben da lafiya.” da Amin ya amsa sannan ya juya zai bar wajen, kamar kuma wanda ya tuna wani abu sai ya dawo, Abba ya ce“lafiya dai?” “Nana bata koma gida bane, naga kuma dare ya fara yi bari sai na bika mu tawo tare.” Jinjina kai Abba ya yi kafin ya ce“Eh dan kusan ka san halinta yanzu sai ta ce tsoro take ji.” Koda suka je a ƙofar apartment ɗin ya tsaya, Abba da ya shiga ya kira masa ita. Yana tsaye a ƙasan balcony ta fito hannunta riƙe da mayafinta tana ƙoƙarin yafawa akan doguwar rigar jikinta. Bayan ta ƙaraso waje ta kalleshi ta ce“uncle ni sai an jima zan dawo fa.” bai ce komai ba ya ja hannunta suka fara tafiya, Ko nisa basu yi ba ta tirje a wajen ya juyo yana kallonta da shanyayyun idanunsa. Ganin yanda take yarfe hannu yasa ya ce “What?” “ƙafan uncle, zafi take min. Wallahi ba zan iya tafiyar ba” Da buɗe idanunsa ya yi kamar ba zai magana sai kuma ya ce“To sai ki yi ya ya?” “Ka goyani.” Ta ce a shagwaɓe. Harararta ya yi ya ce“Abokin wasanki ne ni?. C'mon my friend!” Madadin ta tawo sai kawai ya ga ta nemi waje ta zauna, ta harɗe ƙafafunta ta fara kuka a ƙarfi. Baki buɗe yake kallonta, ganin tana son tara masa jama'a ya sanya ya ɗan durƙusa dai dai tsayinta ya ce“Tashi muje mana, zan siya miki abin daɗi.” Maƙale kafaɗa ta yi kafin ta ce“a'a ni sai ka goyani...” Ya jima yana kallonta ganin yanda ta yi da fuska kamar jaririya, agogon hannunsa ya kalla ganin dare ya fara yi ya sanya ya ɗan yi tsaki. Sannan ya juya mata baya ba tare da ya ce komai ba, Jin ta yi shiru ya sanya ya ce “Kin hau ko sai nayi tafiyata?.” Da sauri ta mike ta tattare rigarta ta hau bayan nasa, Ya mike tsaye yana rike da ita. Hannayenta ta sanya ta zagaye wuyansa, Ta ɗora kanta akan faffaɗan bayansa tana dariya. Yana jin ta amma bai ce mata komai ba, Sun yi nisa sosai ta ɗan leƙo fuskarsa ta ce “Uncle.” “Uhm” ya ce yana ci gaba da tafiyarsa. “To da kana goya Anty Zahra?” Shiru ya yi yana tunanin dalilin tambayar, Can kuma ya girgiza kansa ya ce“A'a.” dariya ta sake yi ta koma ta yi lamo a bayansa sannan ta ce“yauwa Uncle ɗina, ai ni kaɗai ka ke so ko?” shiru ya yi mata gudun ya bata amsa ya zama fitina. Bata damu da rashin amsawar da ya yi ba ta ce “Ita kuwa Maimoon Yaya Aliyu baya goyata. Kuma ma ita cikine da ita” ta ƙare maganar tana tuntsirewa da dariya, Duk yanda yake jin ransa a dagule bai san sanda ya yi murmushi ba. Ya girgiza kansa bai ce komai ba. Suna zuwa bakin ƙofar ya ce“sauka!” ta sake ƙanƙameshi a shagwaɓe ta ce“ni sai ka kai ni sama.” girgiza kansa ya yi ya ce“sauka na ce!” Ta sake maƙale kafaɗa tana kwanciya a bayansa. Wata azabbabiyar tsawar daya daka mata ce ta sanya ta sauka daga bayan ba shiri. Ta nufi cikin gidan da gudu tana kuka, Tsaki ya yi sannan ya shiga parlon. Zahra na zaune akan sofa ita da Noor, Ta yi masa sannu da zuwa ya amsa sannan ya ƙarasa ya ɗauki Noor ya ɗorata a cinya, Kama gemunsa ta yi wanda ya zame mata dabi'a ta ce “Abbie gobe zamu tafi?” Jan kumatunta ya yi ya ce“Yeh!” Ta yi dariya har sai beauty point ɗinta suka loma sannan ta ce“yauwa Abbiena ɗan albarka. Daman ina son naje naga su Abeeha” Murmushi shima ya yi ya ce“tom zaki gansu nan kusa. Muje ki kwanta kin ga da wuri zamu tafi ko?” gyaɗa masa kai ta yi ya miƙe da ita a hannunsa suka nufi sama, Zahra ta bi su da kallo. Nana na shiga daƙinta ta faɗa kan gado ta fashe da kuka har sannan jikinta bai daina rawa ba, Ba'a taɓa yi mata tsawar data gigitata irin wannan ba. Ta dunƙule waje ɗaya tana ci gaba da kukanta a haka har bacci ya ɗauketa. Around 10:20 na dare aka fara knocking ƙofar, Da mamaki ya dinga kallon ƙofar sai kuma ya janye laptop ɗin dake gabansa ya miƙe ya nufi ƙofar ya buɗe. Tsaye ya gan shi a wajen, Bai ce komai ba ya matsa daga wajen ƙofar. Safwan ya sauke numfashi sannan ya shigo ciki, komawa Abdusammad ya yi ya zauna kan kujera yana jiran ya ji abin da zai ce. Jiki a sanyaye Safwan ya zauna kujerar dake kusa da ta sa, Ya sunkuyar da kansa. Sun ɗauki mintuna a haka kafin Abdusammad ya ce “Idan baka da abin faɗa zan tashi.” Sauke numfashi Safwan ya yi kafin ya ce “Na san na aikata ba dai-dai ba Yaya. Amma ina da hujjata ta yin haka, kuma Hujjar ta kai na aikata haka. Domin abin da nayi shi ne dai-dai, Na san babu wanda zai fahimceni a cikin su, amma ina da tabbacin kai zaka fahimta shiyasa na zo wajenka Yaya.” Safwan ya yi shiru yana kallon Abdusammad, Da ɗan mamaki Abdusammad ya ce “Hujja! Safwan mene hujjarka? Akan me zaka sake ta? Me ta yi maka? Ka san halin daka saka mutanen gida?. Ka san me Hajiya ta ce akan haka? Akan me zaka yi abu babu neman shawara?” Tuni hawaye suka fara wanke masa fuska, Ya tashi ya dawo kujerar da Abdusammad yake ya tsuguna a wajen, ya ɗora hannayensa akan cinyarsa cikin kuka ya ce “Yaya bani da wata mafitar ne. Ba zai yiwu na ci gaba da zama da Haule ba, Yaya ina da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV! Ta ya zan iya zama da ita a haka?” Abdusammad bai san sanda ya ture shi daga jikinsa ya miƙe tsaye ba. Fuskarsa ɗauke da mabayyanin tashin hankali ya ce “What! Me ka ce Safwan? Hiv kamar ya ya? Yaushe kuma a ina ka samu cutar!?.” Abdusammad ya jera masa tambayoyin yana tsare shi da idanu. Jan numfashi Safwan ya yi kafin ya ce “A sanda na auri Siyama. Ita ce wadda take ɗauke da cutar ta shafa min ba tare da ita ma ta san tana da ita ba. Ita kuma Haule bata da ita, saboda na kira likita ya gwada ya tabbatar min da bata da cutar, shiyasa na saketa saboda kada na cuceta!” Ya ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka. Durƙusawa Abdusammad ya yi ya ɗago shi yana kallon sa ya ce“Ita Siyaman take da Hiv? How? A ina ta samu?” Girgiza kai Safwan ya yi kafin ya ce “Nima bana ce ba Yaya. Amma kawai abin da na sani ban samu Siyama a matsayin budurwa ba, Wannan ke nuni da cewa a wani wajen ta shafa itama. Saboda haka idan har ina son na zauna lafiya dole na rabu da Haule, bana son na cutar da ita, bana son na shafa mata. Wallahi shiyasa na saketa ba dan wani abu ba Yaya!” Girgiza kai Abdusammad ya yi cike da mamaki da kuma tashin hankali ya ce“to ta ya ita Haule bata shafi cutar ba? Ko kana son ka ce bata da iddarka?” Girgiza kai Safwan ya yi still crying ya ce “A'a tana da ita. Saboda Haule ce ta fara tarewa kafin Siyama, Bayan Siyama ta zo sai naji bana son mu'amala da Haule, bana son ta zo inda nake. Wannan dalilin ya sanya na ƙaurace mata, Sai daga baya kuma na gano ina da wannan cutar shi ne ya sake sakawa na bar ta din. Na san zaka fahimceni Yaya, wallahi tallahi bani da niyyar cutar da rayuwar Haule, kuma bani da niyyar bijirewa gidanmu, na ɗauki wannan ɗin a matsayin Ƙaddara! Wadda ba zan iya guje mata ba.” Rungumeshi Abdusammad ya yi yana shafa kansa, Safwan ya sake fashewa da wani matsananci kuka. Shi kansa Abdusammad ɗin kukan yake, saboda Safwan na ɗaya daga cikin abin da yafi soyuwa a gare shi. Yana son sa tun yana ƙarami, ƙaunar da yake masa ya sanya ya mayar dashi ɗan ɗakinsa, musamman daya kasance suna kama da juna. Koda wasa bai son yaji an ce wani abun ya sameshi yanzu zaka ga hankalinsa ya tashi, A yanzu kuwa sai yaji kamar shi ne ƙaddarar ta faɗawa. Sun daɗe a haka kafin daga bisani Abdusammad ya ɗago shi ya shiga goge masa hawayen fuskarsa ya ce “Shikenan na gane, kuma na fahimceka Safwan. Kada ka damu komai zai zo da sauki, zan saka a ɗoraka akan magani sai ka dinga zuwa US check up. Saboda haka ka kwantar da hankalinka, and zan faɗa musu yanda zasu fahimta. Duk da gobe da wuri zan tafi, bayan sallahr asubah zamu yi magana dasu, Kada ka damu kaji. Abin da ka yi shi ne dai-dai, Allah ya baka da lafiya” Sake rungume shi Safwan ya yi kafin ya ce“Amin Yaya. Nagode sosai, dan Allah ka ce duk su yafe min, ji nake kamar mutuwa zan yi Yaya” Girgiza kai Abdusammad ya yi yana shafa bayansa ya ce“In ji wane? Ka taɓa jin cuta ta kashe mutum? Sai dai kwanansa ya ƙare. Saboda haka bana son na sake jin makamanciyar wannan maganar a bakin ka kaji!” Gyaɗa masa kai ya yi, Ya yi shiru suna sauke numfashi. Daren ranar kasa baccin kirki Abdusammad ya yi, gaba ɗaya ji ya yi duniyar tayi masa babu daɗi. Dan haka ya dauro alwala ya fara sallar nafila har aka fara kiran sallar asuba. Bayan sun fito daga masallaci ya sanya suka tsaya, Ya kuma yi musu bayani yanda zasu fahimta. Sosai jikin su ya yi sanyi Abba ya ce “Abin da ya yi shi ne dai-dai. Allah ya gajarta walaha, In sha Allah zamu yi magana da Hajiya Babba gobe.” Jinjina kai Abdusammad ya yi sai kuma ya ce“Yauwa Abba, ni ka ga da wuri zan tafi. Amma in sha Allah nan bada jimawa ba zan zo” A haka suka rabu kowa ya yi hanyar gidansa jiki a sanyaye. Yana komawa ya nufi ɗakin Nana, Koda ya shiga zaune ya hangeta jikin gado sanye da hijabi. Ya ƙarasa ciki ya zauna gefen gadon yana kallon ta, Bayan ta abin da take ta tashi ta naɗe laddumar sannan ta nufi can ƙarshen gadon ta zauna jiki a sanyaye ta ce “Ina kwana?.” Shiru ya yi bai amsa ba, Ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers ɗinta. Ya dade yana kallonta kafin ya ce“zo nan.” Komawa kusa da shi ta yi ta zauna kanta a ƙasa. Ya ɗan yi murmushi ganin yanda ta nutsu kamar ba ita ya ce “mene ne? Haushina ki ke ji?” Girgiza masa kai ta yi, Ya jawota jikinsa ya ce “Shikenan ba zan ƙara ba. Kin ji Nanata” Kamar jira take ta ɓare masa baki ta fara kukan data saba. Ya yi shiru yana saurarenta, Can kuma ya ce“To ya isa haka ki tashi ki shirya” banza ta yi masa ta ci gaba da kukanta. Ya ɗago fuskarta ya riƙe cikin tafin hannunsa ya ce“Idan baki min shiru ba zan saka ki mai dalili.” Tura baki ta yi ta janye fuskarta, Ya tashi tsaye yana riƙe da cazbaha a hannunsa ya ce“Ki shirya kin ji. Ina zuwa” A sanyaye ta ce to sannan ya juya ya bar ɗakin. **** Misalin ƙarfe 6:30 ne na safe, gaba ɗaya jama'ar estate ɗin suka taru a compound ɗin gidan. Kamar yanda ranar da ya zo suka taru haka ma yau ɗin suka sake taruwa, Sai da ya yi Sallama da kowa sannan ya nufi wajen Hajiya Babba, Jiki a sanyaye ya yi mata sallama, Ta amsa babu yabo babu fallasa. Noor dake hannunsa ya ɗaga mata hannu, Murmushi Hajiya Babba ta yi ita ma ta daga mata hannun. Jiki a sanyaye ya bar wajen, A bayan mota ya sakata sannan ya sake ma su Abba sallama. Nana kuwa dakyar ta bar jikin Amma tana kuka, ko ranar da aka tafi da ita gidan bata yi kuka kamar yau ba, Dakyar Amma ta rarrasheta ta shiga motar. Tsayawa ya yi yana karewa estate ɗin da kallo, kamar yau ya zo gashi har zai koma. Ya sauke numfashi sannan ya nufi cikin motar bayan an bude masa, Shiga ya yi yana sake daga musu hannu. Atta kuwa komawa gefe ta yi ta zauna ta dinga rusa kuka, a haka har motocin suka fara fita daga gidan ɗaya bayan ɗaya kamarkamar yau ya zo gashi har zai koma. Ya sauke numfashi sannan ya nufi cikin motar bayan an bude masa, Shiga ya yi yana sake daga musu hannu. Atta kuwa komawa gefe ta yi ta zauna ta dinga rusa kuka, a haka har motocin suka fara fita daga gidan ɗaya bayan ɗaya kamar dai yanda suka shigo, Ajiyar zuciya suka sauke sannan kowa ya nufi hanyar gidansa. 08106608363 Nanameera. *🌹 NAANAH 🌹* Follow my account Wattpad@Nanameera08 Arewabooks@Nanameera08. Page 52. Around 4:00am jirgin nasu ya sauka a JFK airport na New York. Bayan sun fito daga ciki suka tarar da jerin motocin dake jiransu wanda aƙalla sun kai guda 10. Ita dai Nana sai sake jan mayafinta take saboda ɗan yayyafin da ake, Abdusammad ya shiga cikin wata Bentley black colour, Nana tabi bayansa itama. Ganin haka ya sanya Zahra yin gaba, ta buɗe wata motar ta shiga hannunta riƙe da Noor wadda ta yi bacci, Nan da nan kuma motocin suka bar wajeni. Park avenue road, Upper East side, New York. A dai-dai bakin wani madaidaicin gate motocin suka ɗan tsaya, kafin daga bisani gate ɗin ya fara zugewa da kansa, Wani irin ƙaton gida ne iya ganinka, wanda ta wajen ba lallai ka yi tunanin ya kai girman haka ba. A tsakiyar compound ɗin gidan na biyu motocin suka yi parking dan iya nan ne mota ke tsayawa, Sai a sannan Abdusammad ya sauke numfashi sannan ya zare seat belt ya buɗe motar ya fito. Jiki a sanyaye ita ma Nana ta fito tana ƙarewa compound ɗin kallo, Gurin an ƙawatashi da furanni masu kyau da ƙamshi irin su white rose da lavender. Ta ja lumsassun Idanunta ta rufe tana shaƙar iskar wajen mai daɗi, Duk yanda take jin babu daɗi data bar gida sai da ta manta. Ta gyara tsaiwarta ganin Zahra ta fito har sannan tana rike da Noor, Gaba ya yi suka fara bin sa a baya, Duk inda ya shige sai ma'aikatan wajen sun gaishesa a haka har ya shiga third gate ɗin wanda yake da launin golden, Wani irin haɗaɗɗen compound ne mai kyau da tsari. Ya lumshe idanunsa sakamakon iskar data doke shi mai ɗauke da ƙamshin mint da fresh flowers. A hankali yake taka pathway ɗin wanda ya ɗan lanƙwashe har zuwa ga kofar entrance ɗin gidan, Nana kuwa tun da ta shigo idanunta ke kan fountain ɗin dake ɓangaren damanta, Sai zubar da ruwa yake duk da yayyafin da ake, ga wasu leds masu kyau da haske dake ƙawatashi. A gefensa kuma flowers ɗin orchids da ross sun ƙara taimakawa wajen ƙawata wajen ɗin, Ta janye idanunta tana kallon ɗaya side ɗin, ƙananun bishiyun marble da cherry blossom ne, daga gefensu suka wasu red leds ne waɗanda ke kawowa suna ɗaukewa. Ɗaga kanta ta yi ta hangi dogon ginin gidan, lokaci ɗaya kuma ta sauke kan nata ta ci gaba da tafiya. Sai da ya saka password a jikin ƙofar entrance ɗin wadda ta kasance ta glass sannan ta zuge a hankali, Ya tura kansa ciki bakinsa ɗauke da sallama da ba lallai sun ji ba. Ɗaya bayan ɗaya suka shiga, Nana ta tsaya tana ƙarewa ƙaton parlourn kallo, Wasu Italian sofas ne a ciki yayinda marble tiles ya yi kamar carpet a wajen, A tsakiyar parlon kuma crystal chandelier ce mai bada launin golden. Daga can left side kuma pione ground ne, wanda aka ƙawata shi da kayan sauti masu tsada. Nana ta juya ta kalli gefenta da dama daga jikin bango, fireplace ne wanda ke ci a hankali, kuma shi ne ya taimaka wajen raguwar sanyi a parlon. Ɗaga kanta ta yi tana kallon staircase ɗin da suke can nesa da ita, Bene huɗu ne a wajen, Biyu a haɗe, biyu kuma a rarrabe. Ya jima tsaye a wajen kamar ba zai magana ba sai kuma ya juyo yana kallon su duka “Nana here it's ur apartment. Ki je ki huta” Ya ƙare maganar yana nuna mata benan dake right hand side ɗin biyun, Zahra kuwa gaba ta yi abin ta dan already ta san nata ɓangaren. Shima bai tsaya jiran amsar Nanar ba ya nufi nasa ɓangaren da sauri dan a mugun gajiye yake, Tamkar gunki haka Nana ta tsaya a wajen. Can kuma ta tura baki ta nufi hanyar benan daya nuna mata tana tafe kamar wadda kwai ya fashewa a jiki. A hankali ta dinga taka fluffy rug ɗin dake cikin ƙaton parlourn, komai na ciki coffee and white ne, kaya masu kyau da kuma tsada, Tun daga kan kujeru har zuwa kayan wutar dake ciki, gaba ɗaya sai taga ashe parlourn ƙasa ba ma kyau ne dashi ba. Ta ja dogon numfashi ta sauke hannayenta riƙe da ƙugunta, daman tuni veil ɗin abayar ya zame ya dawo kafaɗarta sai hula ce kawai akan. Ta ja jikinta a sanyaye ta nufi ƙofar data gani wadda take da tabbacin nan ne bedroom ɗin. Kamar yanda ta yi tunani haka ce ta faru, haɗaɗɗen bedroom ɗin mai ɗauke da furnitures kalan na parlourn, a shimfida farin bedsheet akan gadon yayinda aka ɗora duvet coffee colour. Ta jima tana ƙarewa ɗakin kallo kafin ta ajiye wayarta gefen gadon ta nufi banɗaki, Shima sai da ta tsaya ta gama dube-dubenta, ta karance duk shower set ɗin da aka ajiye sannan ta ɗauki wanda take ganin zai fi mata ta fara wankan dashi, tana gamawa ta ɗauro alwala sannan ta fito ɗaure da towel. Ta ƙarasa gaban dogon press ɗin da tagani ta buɗa. Yawancin kayan ciki English wears ne, sai dogayen riguna tsirari, ta ɗan tura baki sannan ta janyo wata riga doguwa wadda bata shige gwuiwarta ba ta zura sannan ta naɗe gashin kanta ta ɗaure da riboom. Rasa hijabin sallah ta yi, dan haka ta sake buɗe press ɗin ta ɗauko abaya da veil ɗinta ta saka sannan ta gabatar da sallolin da ake binta... Bayan ta idar ta zare doguwar rigar ta faɗa kan gadon, Taja duvet ɗin ta rufe har kanta tana jin wata nutsuwa na saukar mata, kasancewar ta gaji sosai ya sanya nan da nan bacci ya ɗauketa. **** A hankali ta fara buɗe idanunta tana ƙarewa saman ɗakin kallo, leds ɗin a kunne suke har sannan duk da hasken daya gaureye ɗakin. Ta tashi zaune tana murza idanunta, Ba wai baccin ne ya isheta ba kawai tashin taji ta yi. Kallon gefenta ta yi inda Hasken ke shigowa da glass window ɗin dake wajen, Ta ɗauke kanta tana tura baki kafin daga bisani ta yaye bargon dake jikinta ta sauka daga kan gadon, kai tsaye kuma banɗaki ta nufa. Wanke fuskarta ta yi a jikin sink kafin ta ɗago kanta tana kallon madubi, Fuskarta ta ɗan kumbura dalilin baccin da tayi, ta kai hannu ta rufe bakinta saboda hammar data tawo mata. Sabbin brushes ɗin data gani ta ɓare ta ɗauki ɗaya sannan a ɗauka toothpaste ta zuba ta hau wanke bakinta. Bayan ta gama ta ɗauki mouth listener ta fesa sannan ta zare rigar jikinta ta fara wanka, Tana gamawa ta fito ɗaure da towel. Ta karasa jikin madubi ta fara dube-duben mayukan da suke wajen, can dai ta ɗauki wani olive lotion ta shafe jikinta dashi. Babu abin da ta saka bayan man ta buɗe press ɗinta, wata riga ta zaro a jakarta ta ɓare ta warwareta tana kalla. Doguwar riga ce mai manyan flowers a jiki, saman rigar an saka roba mai talewa, Ta daɗe tana juya rigar kafin ta sanyata a jikinta. Ba ƙaramin kyau rigar ta yi mata ba, Ganin babu dankwali a ciki ya sanya ta sauke gashin kanta ya sakko kafaɗarta. Sai ta yi kamar wata baturiya, Ta rufe press ɗin sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin. A balcony ɗin saman ta tsaya, ganin hanyoyin sun rabu. Kamar ta je ta duba sai kuma ta nufi ƙasa kai tsaye, Parlourn net kamar jiya sai tashin ƙamshi yake, Ta kalli hanyar benan Zahra ta taɓe baki lokaci ɗaya kuma ta nufi benan da taga Abdusammad ɗin ya hau jiya. Ba karamar benansu bane wanda ana hawa za'a tarar da parlour, wannan wata ƙofa ce ta glass gefenta da wasu maddane na sirri. Ta daɗe tsaye a wajen kafin ta ƙarasa ta fara knocking bell ɗin jikin ƙofar, Ganin ba'a zo an buɗe ba ya sanya ta koma knocking ɗin da hannu. After 5mins taji an fara buɗe ƙofar, Ta tura baki tana ɗauke hannunta daidai nan ƙofar ta buɗe. Fuskarsa ya zuro yana kallonta, Ta kalle shi ganin bai ce komai ba, daga gani ka san bacci yake dan idanun sa sun ɗan janye, kuma babu riga a jikinsa sai faffaɗan ƙirjinsa dake bayyane. “mene?” Ya tambaya a shaƙe. Kallon sa ta sake yi sai kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers ɗinta, Ya yi shiru kamar mai tunani sai kuma ya matsa daga jikin ƙofar still looking at her ya ce“shige.” kamar jira take ta shige cikin, Ya Girgiza kansa sannan ya mayar da ƙofar ya rufe. Wata irin ajiyar zuciya Nana ta dinga saukewa a jere a jere, Idan kana neman inda aka kashe masa kuɗi to parlourn ɗakin ya kai. Ko makaho ya shafa ya san an ɓarnatar da dukiya a wajen, Wasu set ɗin kujeru ne white colour masu taushi ko a ido, Bango ɗakin mai zane-zanen abstract art na Paris,Ta sake lumshe idanunta saboda ƙamshin cherry blossom air freshener ɗin dake dukanta. Bai ce mata komai ba taga ya zo ya nufi bedroom ɗin, itama ta bishi da sauri. Colours ɗin da aka yi amfani dasu a parlourn sune a cikin ɗakin, Komai fari ne, rabin bangon ɗakin an yi zane irin na manyan artist, ga wasu manya manyan frames ɗinsa dake maƙale a kowace kusurwa ta ɗakin, Hotunan tamkar sa yi magana saboda girmansu. Gaban gadon ya ƙarasa ya zauna yana kallon ta, Ganin hankalinta baya wajen yasa ya ce “Ke zo nan.” Ƙarasawa gabansa ta yi da sauri ta zauna a gefen ta sunkuyar da kanta. Shiru ya yi kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce“mene ne?” Girgiza kanta ta yi a hankali, Ya sake cewa“saboda ki takurani ki ka zo kina min knocking da safiyar nan?” ɗago kanta ta yi ta kalleshi sai kuma ta sake sunkuyar da kan nata kafin ta ce“uncle ai rana ya yi fa.” “Karfe nawa?” Ya tambaya yana ƙoƙarin kwanciya, Kallon agogon bango dake maƙale a sama ta yi ta ce“ƙarfe 11:20 na safe.” Hannunta ta ji ya jawo ya kwantar da ita gefensa sannan ya ce“Oyah ki koma bacci sai an jima zan tashi.” kwaɓe fuska ta yi dan ita har ga Allah bata ji zata yi wani bacci ba, Ganin ta juya tana kalle-kalle ya sanya ya jawota jikinsa ya ɗora kansa akan fuskarta yana jin yanda take sauke numfashi ya ce“cewa nayi ki yi bacci.” “Unclee!.” Ta kira sunansa a shagwaɓe, Ɗaga mata gira ya yi alamar mene ne?. Ta tura baki ta ce“to ai bana jin bacci” “Yanzu zan saka ki ji shi to.” Girgiza kanta ta yi da sauri, Taja duvet ɗin ta rufe har fuskarta tana sauke numfashi, Ya yi murmushi sannan ya kashe hasken ɗakin nan take ya koma kamar ba rana ba, Jan duvet ɗin ya yi ya rufe jikinsa, Ya dinga kallonta ganin yanda take ta raba idanu.. “Ba zaki yi baccin bane?” “Zan yi.” Ta ce kamar zata yi kuka, Ji ta yi ya jawota jikinsa sosai ya ɗora hannunsa a bayanta wajen kanta ya fara shafawa a hankali kafin ya ce “Sleep.” Gyaɗa masa kai kawai ta yi, ya ci gaba da shafa kan nata ba tare da ya ce komai ba. Kasancewar daman baccin ba isarta ya yi ba, Ta fara lumshe ido, yana kallonta duk abin da take a haka har baccin ya yi awon gaba da ita. Sai a sannan ya zare hannunsa, Ya gyara mata kwanciyar sannan shima ya rufe idanun sa ya koma baccin. **** Nigeria. Atta ce tsaye a compound ɗin gidan tana gyara mayafin rigar jikinta, Abba ya yi shiru yana jin abin da take cewa. Papa ne ya ce“Atta ai gara ta zauna anan ta yi idda, kin ga idan Allah ya yi ma sai ta samu wani mijin ta yi aurenta.” wata uwar harara ta maka masa kafin ta ce“To bama so, iyayenta zan maidawa ƴarsu. Bayan yaro ya riga da ya saketa? To zaman me zata yi muku kuma ban da son zuciya.” Shiru Papa ya yi dan ya fuskanci ba fahimtarsa zata yi ba. Abba ya taka har gabanta sannan ya ce “Atta dan girman Allah ki je kawai zan kawo yarinyar nan da kaina daga baya.” Shiru ta yi tana kallon sa, can kuma ta tsuke baki ta ce“Ai gara na tafi da ita Ahmadi, kawai ka bari na tafi da ita.” Girgiza kai Abba ya yi yana kallon Haule dake tsaye ta sunkuyar da kanta ya ce“Ki barta anan ɗin, zan kawota da kaina daga baya.” Taɓe baki ta yi ba dan ranta ya so ba ta ce“Ai shikenan tun da kafi ƙarfina. A faɗawa Khadijah na tafi” Murmushi Abba ya yi ya ce“Tom in sha Allah, Allah ya tsare hanya ya kai ki lafiya.” Da amin ta amsa sannan ta ƙarasa gaban Haule ta dafata ta ce“Kar ki damu kin ji. Zan aura miki wani wanda ya fi shi kin ji” Haule bata san sanda ta fashe da kuka ba, Ta rungumeta Atta tana kuka kamar ranta zai fita. Allah ya sani tana son Safwan, a ɗan zaman da suka yi tare ta koyi ƙaunarsa. Burinta kullum ta gan shi, koda ba zai kulata ba, ashe zaman nasu ba zai yi tsayi ba. Itama Attan kukan take, Da kyar Abba ya rarrashesu ta bar jikinta, ta shige mota bayan an saka mata kayanta. Drivern yaja motar suka bar compound ɗin, Ban da kuka babu abin da Haule ke yi, Abba ya kalleta cike da tausayinta ya ce “Ya isa haka, Je ki ciki.” Bata ce komai ba ta nufi apartment ɗinsa, dan daman tun shekaranjiyan anan take.. Sai da ta tafi sannan Abba ya kalli Papa wanda ya yi shiru tun ɗazu. Papa ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce“Allah ya kyauta.” Abba ya amsa da Amin sannan kowa ya nufi hanyar gidansa jiki a sanyaye. **** Anty Khadijah ta dinga kallon sa da mamaki ganin har sannan bai ce komai ba. Ta gyara zamanta dan ita kaɗai ta zo wajen ta ce“Ina jin ka malam, ka ce na zo cikin gaggawa me hakan ke nufi? Ko akwai matsala ne?” Girgiza kansa ya yi ya ce“Babu wata matsala Khadijah, daman ina son sanar dake wani abu ne.” Anty Khadijah da kanta ya fara ɗaurewa ta ce“To ina ji Allah dai yasa lafiya” Jinjina kansa ya yi yana murmushi ya ce“ai lafiya ma idan ki ka ce to ɗaya kenan.” Ita dai ta dinga kallon sa, Ya ɗan yi gyaran murya kafin ya fara cewa “Wato Khadijah tun ranar dana fara ganinki naji ina ƙaunarki, naji sonki ya ɗarsu a zuciyata. Irin son nan mai tsanani, Ina son kasancewa dake Khadijah, bana gajiya da kallon ki, wannan dalilin ya sanya nake yawan gayyatar ki nan, saboda ƙaunar da nake miki. Ina son ki bani dama na zama abokin rayuwarki, na aureki mu zauna ƙarkashin inuwa ɗaya.!” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Wattpad@Nanameera098 Arewabooks@Nanameera08. Page 53. Wata irin zabura Anty Khadijah ta yi ta miƙe tsaye, Ta dinga watsa masa wani kallo bakinta na rawa. Miƙewa ya yi yana kallon ta, kafin ya yi magana ta ce “Kai ɗin banza! Kai ka isa na aureka? Ashe ma mahaukaciya ce ta raine ni, wallahi kaci ƙarya! Dube ka, wani ƙazami dakai. To ko auren saurayi da budurwa ban auri lalataccen namiji ba ballantana yanzu.” Ta ƙare maganar cikin bala'i, Shi dai bai ce komai ba sai kallonta da yake. Ta jujjuya a gabansa kafin ta ci gaba da faɗin “Kalleni! Ni Khadijah nafi ƙarfin ka ce zaka aureni wallahi! Ban da ma ƙaddara ta kawoni wajenka kai baka isa ko ganina ka yi ba. To idan ka aureni sai ka ajiye ni a ina? A wannan kejin gidan naka? Dame zaka ciyar dani? Ko kana son kace min da wannan banzar lalatacciyar sana'ar taka? To ka kama kanka tun wuri. Na rantse makamanciyar wannan maganar na sake ji a bakinka sai na saka an ɓatar min da kai. Baka san hau ɗina bane...” Taja wani dogon tsaki ta sunkuya ta dauki jakarta ta zura takalmanta ta bar soron a fusace. Malam Garba ya bita da idanu sai kuma ya girgiza kansa ya koma ya zauna yana sauke nunfashi.... Kasa haƙuri ta yi taje gida, Ta gangara gefen titi tayi parking ta zaro wayarta daga jaka ta hau kiran Kaddu. Sai dai har kiran ya katse bata ɗaga ba, Anty Khadijah taja wani dogon tsaki sannan ta yi wurgi da wayarta ta ci gaba da driving ɗin, Lokaci zuwa lokaci take yin kwafa ko kuma ta girgiza kanta, har wani cije baki take na zallar masifar dake cinta. **** Amma ta dinga kallon ta ganin yanda take kukan har sannan, Ta ajiye mug ɗin a gefen drawer sannan ta hawo kan gadon. A hankali ta dafa kafaɗarta cikin son kwantar mata da hankali ta ce “Ya isa haka Haule, Ki yi haƙuri ki yarda da ƙaddara. Haka Allah ya yi aurenku ba zai daɗe ba, ki daina damun kanki kin ji.” Gyaɗa mata kai Haule ta yi bayan ta goge hawayenta, Amma ta yi shiru tana kallon yarinyar cike da tausayawa, Dole taji babu daɗi dan mutuwar aure ba ƙaramin abu bane. Ko faɗa kuke idan ku ka rabu sai kun ji a jikin ku, ballantana kuma ana zaune lafiya babu wani tashin hankali a ce miki an sake ki. “Tashi ki je ki wanke fuskarki ki zo ga tea na kawo miki.” Amma ta yi maganar a sanyaye. Toh kawai Haule ta ce duk da bata jin zata iya shan tea ɗin amma ta sauka daga kan gadon ta nufi hanyar banɗakin jiki a sanyaye, Wanke fuskarta ta yi ta fito ta ɗan ja ta tsaya a jikin ƙofar ta riƙe kanta. Amma dake lura da ita ta ce “Lafiya?” Girgiza mata kai ta yi, sannan ta fara tafiya hannunta dafe da kanta. Idanunta ne suka fara lumshewa, ta riƙe kanta da hannu bibbiyu saboda wata irin sarawa, Ganin haka ya sanya Amma tasowa sai dai kafin ta iso gabanta tuni Haule ta faɗi ƙasa a sume. Cikin tashin hankali Amma ta durƙusa a gabanta, Ta ɗagota tana kiran sunanta, lura da bata cikin hayyacinta ya sanya Amma tashi ta fice daga ɗakin da sauri. **** Upper East side, New York. A hankali ya fara buɗe idanunsa, Ya kalli Nana wadda ta riƙe shi sosai fuskarta a kwaɓe kamar mai shirin yin kuka, Hannunsa ya sanya ya janyeta daga jikinsa sannan ya tashi zaune yana kallon agogon dake maƙale a ɗakin, Ƙarfe 1:20 na rana. Dan haka ya zame duvet ɗin daga jikinsa ya sauka daga kan gadon, bedroom slippers ɗin dake ƙasan gadon ya zura a ƙafafunsa sannan ya nufi toilet. Bayan kusan mintuna talatin ya fito yana tsane kansa da towel, Yayinda jikinsa ke ɗigar ruwa, Gaban mirror ɗin sa ya ƙarasa, Ya saka dryer ya busar da kansa sannan ya shafa mai, Bayan ya gama ya gyara kansa ya feshe jikinsa da turaren Arabian oud mai daɗin ƙamshi. Ya ƙarasa gaban katon press ɗin dake gefen mirror ya buɗe, kayane a jere a ciki, kowane abu an ajiye shi a mazauninsa. Wasu t-shirt da 3-quater ya dauƙo, Ya warware su daga jakarsu sannan ya saka. Rigar fara ce tas sai ƙaton hoton mage a jiki kamar ya yi magana, Wando kuma blue colour ne mai aljihu dayawa. Wata p-cap ya dauko white ya ɗora akansa, gashin kansa ya sauka a gefe da gefe na kafaɗunsa. Ya ɗan kalli kansa a jikin madubi yana suɗe lips ɗinsa yana kuma taunesu a lokaci ɗaya. Ta jikin madubin ya hangota sai wargaza gashin kanta take, Ya sauke numfashi kafin ya juya yana kallon ta. Ita ma kallon nasa take da lumsassun Idanunta, Ya ƙarasa wajen cikin takunsa na isa da tagama. Wayarsa ya ɗauka akan drawer ya ɗan danna ganin har sannan tana zaune yasa ya ce “Idan na fita ba zan dawo ba sai dare.” Miƙewa tsaye ta yi tana kallon sa, sai a sannan ta tuna da ƙofar key gareta. Ta nufi toilet da sauri gudun kada ya tafi ya barta. Sabon brush ta ɗauka ta wanke bakinta sannan ta wanke fuskarta ta goge da towel sannan ta fito. Bata gan shi a ɗakin ba, Taji gabanta ya yi wani irin faɗuwa. Kamar mara gaskiya haka ta fara leƙa kowace kusurwa ta ɗakin tana cewa “Uncle... Uncle... Uncle!” Wani zaburraren ihu ta saka jin an riƙeta, Ya yi baya yana murmushi ya ce“Matsoraciya kawai.” marairaice fuska ta yi kamar zata yi kuka ta ce“Uncle ka bani tsoro wallahi.” Bai ce mata komai ba sai murmushi da yake a hankali, Dimple ɗinsa na lotsawa kamar ka yi ajiya a wajen. shagala ta yi da kallon sa, ganin yanda asalin kyawunsa ya bayyana. Ya ja hancinta ya ce “Bar kallona yarinya.” Ji ta yi kamar ta nutse saboda kunya, Ta yi gaba ba tare da ta ce komai ba ta fice daga bedroom ɗin. Girgiza kansa ya yi sannan yabi bayanta shima, Tana tsaye ya saka password ɗin ya buɗe ƙofar sannan suka fito. Kai tsaye kuma downstairs suka nufa, Xahra dake zaune akan sofa ita da Noor ta dinga kallon su da ɗan mamaki dan bata san sanda Nanar ta je apartment ɗinsa ba. Ita kuwa Nana hannunta ta zura a tsakanin nasa, ta riƙe shi gam kamar wadda taga abun tsoro. Zahra ta ɗauke kanta tana ci gaba da nunawa Noor videon da suke gani. Yarinyar na ganinsa ta taso da gudu ta rungumeshi ya sunkuya ya ɗauketa ya ɗorata a kafaɗarsa yana murmushi ya ce “Yarinya kin dawo gida ko?” “Abbie gobe zan ci gaba da zuwa school?” Ta yi maganar tana ƙoƙarin jan gashin kansa. Gyaɗa mata kai ya yi kafin ya ce “Yeh! Idan naci abinci sai ki zo muje a siya miki kayan tafiya school ko?” Sake ƙanƙameshi ta yi tana dariya ta ce “Yeeee Abbie i love u so much!” Ya ja kumatunta yana dariya ya ce“love you too my baby girl.” Ya ƙarasa kan sofa ya zauna yana kallon Zahra ya ce “Madam ki shirya idan na gama cin abinci zamu fita.” “Okay doctor.” Ta ce a sanyaye sannan ta tashi ta bar wajen, Nana ta bita da kallo sai kuma ta taɓe baki na zauna can nesa dasu tana kallon su ganin yake ta yiwa Noor ɗin wasa ita kuma tana dariya. After some minutes aka fara shigo da abinci, Cikin ƙankanin lokaci aka cika tsakiyar parlourn da nau'in abinci kala-kala, Dan shi ya ce masu ba zai ci a dining ba. Nana ta dinga kallon su har suka gama suka bar wajen, Ita dai bata motsa daga inda take ba ballantana taje inda abincin yake. Ya sauke Noor daga jikinsa sannan ya zamo ƙasa ya zauna dan ba ƙaramar yunwa yake ji ba. Kallon abincin ya yi sai kuma ya kalli Nana dake zaune kan kujera ya ce “Zo ki ban abinci.” Da ɗan mamaki ta dinga kallon sa, kamar wadda ta tuna wani abu kuma sai ta taso ta ƙaraso wajen, Da kansa ya dinga nuna mata yanda zata yi har ta gama haɗa masa ta miƙa masa. Ganin tana shirin tashi yasa ya ce “Ke ba zaki ci abincin ba?” Girgiza kanta ta yi kafin ta ce“Ni na ƙoshi.” “Ko?” Ya yi maganar yana watsa mata wani kallo wanda ya sanyata shiga taitayinta. Kasa motsi ta yi, Ya ɗauki mug ɗin coffee ɗin ya kai bakinsa bayan ya yi bismillah. After ya cire daga bakinsa ya miƙo mata, Ta dinga kallon sa sai kuma ta saka hannu zata karba, Ya doke hannun yana sake matsowa dashi wajen bakinta. Jiki a sanyaye Nana ta buɗe bakinta ya bata coffee ɗin, Ta ɗan lumshe idanu saboda zaƙin da taji. Haka ya dinga shan coffee ɗin yana bata yana haɗawa da hamburger, Sai da yaji ya ƙoshi sannan ya zare hannunsa yana kallon ta ya ce “Kin ƙoshi?” Saurin gyaɗa masa kai ta yi dan daman tun ɗazu take jiran taji ya ce mata hakan. Ya zabga mata harara ya ce“to sai kin cinye wannan raguwar” Ya nuna mata ragowar wadda ke plate ɗin wadda tafi rabin guda. Marairaice fuska ta yi tana tura ragowar ta bakinta ta ce “wallahi uncle na ƙoshi, zan yi amai.” “To ki yi ɗin.” Ya faɗa in i don't care manner ɗin nan. Ganin ya ƙara dauƙowa yana nufo bakinta ya sanyata fashewa da kuka, Ta rufe bakinta tana girgiza masa kai. Kallon ta ya dinga yi can kuma ya mayar ya ajiye rai a haɗe ya ce “Tashi ki bani waje.” Kamar jira take ta tashi da gudu ta bar parlourn ta nufi benanta. Ya bita da kallo sai kuma ya girgiza kansa, A parlour ta fadi tana sauke numfashi, Ta dafe cikinta wanda take jin ya yi mata wani irin nauyi. Ita bata saba cin abinci dayawa haka ba, Duk haɗamarta abinci kaɗan ke isarta, Ta jingina da gefen kujera tana sauke numfashi. Wajejen ƙarfe 3:00 na rana ya turo ƙofar ɗakin, Kwance ya hangeta cikin bargo ta lulluɓa har kanta, Ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonta ya ce “Nana!” “Na'am...” Ta amsa muryarta na rawa. Sam bai fahimta ba dan ya yi zaton bacci ne akanta, Dan haka ya ce “Taso muje unguwa.” Girgiza kanta tayi tana daga kwancen da take ta ce“Ni bana so.” Shiru ya yi yana kallonta, Ya ɗaga kafaɗarsa sannan ya juya ya fice daga ɗakin, Ta sake juyi ta koma can ƙarshen gadon tana runtse idanunta. Tsaye ya samu Zahra a parlourn tana gyarawa Noor bottle ɗin rigar sanyin dake jikinta, Ya ƙarasa ya ɗauketa yana faɗin “Ya kamata mu yi sauri, cause naga garin da hadari sosai.” Zahra tabi bayansa tana zura hannayenta cikin aljihun rigar sanyin dake jikinta. **** Yola, Nigeria. Amma ta dinga kallon takardar da mamaki kafin ta ce“Allah mai iko, kaji rabo?” Abba ya ɗan yi murmushi dan har cikin zuciyarsa yaji daɗin kafin ya ce“Allah mai yanda yaso. To Alhamdulillahi Allah ya raba lafiya.” “Idan ka fita ka sanar da Safwan ɗin.” Abba ya yi maganar yana kallon Sultan dake tsaye gefe ɗaya ya harɗe hannayensa a ƙirji, Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce“Ni da ba shiga harkarsa nake ba Abba.” “A saboda me? To ko baka shiga harkarsa wannan saƙo ne na baka ka faɗa masa Haule tana dauke da cikinsa. Saboda haƙƙinsa ne a sanar dashi, koda ya saketa kuwa.” Jiki a sanyaye Sultan ya ce “Tom Abba, in sha Allah zan faɗa masa. Allah ya raba da lafiya” Abba ya amsa da amin sannan ya kalli Amma dake tsaye hannunta rike da takardar har sannan ya ce “Ki je ki sanar da Fatima, Idan na fita zan faɗawa Yaya. Sai a san yanda za'a yi a faɗawa Hajiya Babba” Amma da lokaci ɗaya taji jikinta ya yi sanyi saboda Hajiya Babba da aka ambata ta ce“tom in sha Allah zan je.” “Yanzu ki fara zuwa ki dubata, Bari muje.” Okay kawai ta ce sannan ta nufi hanyar bedroom ɗin Nanar, Sultan ya sauke numfashi sannan ya juya ya Fice daga parlon Abba na biye dashi. **** Kaddu ta yi tagumi tana kallon Anty Khadijah dake ta zazzaga masifa tunda ta shigo. Ta yi shiru tana saurarenta har sai da taga ta tsagaitan dan kanta sannan ta ce “Ke matsalata dake rashin sanin abin da zaki yi. To sai me dan yace yana sonki? Yana son ki aurar ki ya yi? Ko zai miki dole ne? Ni ban ga abin tashin hankali anan ba wallahi tallahi. Ba dai sai kin sake zuwa wajen nasa sannan har zai faɗi wannan maganar ba? Ai ba shi kaɗai ne malami ba, Gasu nan malamai da bokaye kamar jamfa a Jos, mene ne naki na tada jijiyoyin wuya dan Allah?” Girgiza kai Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“Ba zaki gane ba Kaddu. Ya raina min hankali ne fa, Idan ba rainin hankali ba ina shi ina ni Khadijah? Ina yake da abin da zai aureni? Wannan abun shi ne yake ƙonamin rai wallahi.” Kaddu ta ja tsaki sannan ta ce“Kin ji ko? To mene na ɓata ranki anan. Kawai ki bar shi mana. Ki kwantar da hankalinki zamu samo wani nan ba da jimawa ba, Yo ko maza sun ƙare me zaki yi da wannan gajan? Ai ke daga nan sai new York in sha Allahu.” Murmushi Anty Khadijah ta yi ta nemi waje ta zauna kafin ta ce“Har naji sanyi a raina ƙawata.” Kaddu ta kashe mata ido daya sannan ta ce“Yauwa ni bana son naga kina saka kan ki cikin damuwa.” Anty Khadijah ta dauki ruwan da aka ajiye mata tun ɗazu ta balle murfin ta hau sha. **** New York. Basu suka dawo gidan ba sai wajen ƙarfe 7:00 na dare. Abdusammad ya sauke Noor dake hannunsa sannan ya ce“maza ki je ki shirya, Zan je nayi sallah.” To kawai ta ce tana riƙe da ledar dake hannunta, Ya ɗan kalli Zahra wadda ranta ke haɗe har sannan sai kuma ya juya ya fice daga parlon. “Bari naje na kai wa Anty Nana nata.” Noor ta yi maganar tana ɗaukan ɗaya daga cikin ledojin da guard ɗin ya ajiye a parlourn, wata irin tsawa Zahra ta daka mata ta ce “Kin bar nan ko sai ci ubanki!” Bata saba da irin haka ba dan haka ta fashe da kuka ta yar da ledar hannunta, Zahra ta yi tsaki ta wuce sama ta bar ta a wajen. Har ya dawo daga sallah bata daina kukan ba, Ya ƙarasowa wajen yana kallon ta da mamaki ya ce “Noorie me aka miki?” Cikin kuka ta ce“Ummi ta min tsawa Abbie, Kaina zafi yake min.” Ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan, Sosai ransa ya ɓaci dan ko da wasa baya son yaga an ɓatawa yaro rai. Ya durƙusa daidai tsayinta yana goge mata hawayen kafin ya ce “Shikenan ya isa daina kukan kinji, Ke da zaki ci gaba da zuwa school gobe?” Tuni ta manta da batun tsawar ta washe baki tana dariya ta ce“Abbie ina son naga Afeefa.” Murmushi ya yi ya ja kumatunta ya ce“Okay zaki ganta ai, Maza je ki ɗaki.” Sakin hannunsa ta yi ta nufi saman da gudu, Ya bita da kallo kafin ya miƙe tsaye. Kallon apartment ɗin Zahran ya yi, Kamar ya shige sai kuma ya nufi sama. Zaune ya sameta gefen gado tana danna wayarta ya ƙarasa ciki ya tsaya a jikin madubi hannayensa harɗe a ƙirjinsa ya ce “Akan me zaki dinga yiwa yarinya ƙarama tsawa? Me ta yi miki?.” Ɗago kanta ta yi da kalleshi sai kuma ta sake sunkuyar da kai tana ci gaba da danna wayarta. Ba ƙaramin mamaki ta bashi ba, dan Zahra bata saba haka ba, Ya yi shiru yana kallon ta kafin ya sake cewa “Zahra dake nake magana fa...” Miƙewa tsaye ta yi a fusace tana kallon sa ta ce“To bani da ikon yi mata tsawa ne? Ko ka manta nima ƴata ce? Laifin ta min shiyasa nayi mata!” ta ƙare maganar a mugun fusace. Shiru ya yi yana kallon ta, ganin haka ya sanya ta ɗauki wayarta ta fice daga ɗakin kamar zata tashi sama. Ya daɗe tsaye a wajen yana mamakin abin da ta yi, Can kuma ya sauke numfashi ya juya ya bar ɗakin shima. Wajejen ƙarfe 8:00 na dare ya fito sanye da ƙananun kaya, Kai tsaye kuma apartment ɗin Nana ya nufa. Kwance ya hangeta tsakiyar gado sai juyi take gaba ɗaya ta yamutse bedsheet ɗin, Ya ƙarasa ciki yana kallonta ya ce “Nana mene haka?” Jin bata bashi amsa ba ya sanya shi hawa kan gadon, hannunsa ɗaya ya sanya ya jawota. Kamar jira take ta saki wani marayan kuka tana riƙe shi, Da mamaki yake kallon ta, Ya janyota jikinsa gaba ɗaya yana kallon fuskarta ya ce “Nana mene ne? Meke damunki?” Ya yi tambayar yana taɓa jikinta, Zafi yaji sosai dan haka ya sake cewa“Baki da lafiya? Mene yake miki ciwo.?” Cikin shassheƙar kuka ta ce“Uncle ka kaini wajen Abbana, ni gida zani.” “To zan kai ki, Yanzu faɗa min meke damunki?” Rufe idanunta ta yi hawaye na zubowa ta cikinsu ta ce“cikina ne yake min ciwo.” Girgiza kansa ya yi ya ce“Sannu to, kwanta ina zuwa.” Ya kwantar da ita sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin, Tashi ta yi da kyar ta sakko daga kan gadon, Ta yi durƙusa a wajen ta ɗora kanta a gefen gadon kamar me kneel down. Har ya dawo tana haka, Ya ajiye drip ɗin hannunsa da allurar ya tsaya yana kallon ta, can kuma ya ce “Ke cikinki ke ciwo ko mararki?” Kamar daga sama taji tambayar tasa, Ta ɗago idanunta da kyar tana kallon sa. Ƙarasowa wajen ya yi ya zauna gefen gadon ya ɗagota ya zaunar da ita a jikinsa ya ce “Mararki ne ke ciwo ko cikin ki?” “Marata...” Ta ce cikin shessheƙar kuka. Dungure mata kai ya yi kafin ya ce“shi ne zaki ce min cikin ki? Me ki ke ɓoyewa?” Ita dai bata iya magana ba saboda ciwon da yaci ƙarfinta. Ya kwantar da ita akan gadon sannan ya tashi ya fice, After 5mins ya dawo hannunsa riƙe da mug da wata injection, Ya ajiye allurar kan waɗancan sannan ya zauna kusa da ita, Ɗagota ya yi da hannu ɗaya ya jinginata da jikinsa ya ce “Oya drink it.” “Ni ba zan iya sha ba.” Ta yi maganar tana yarfe hannu, Haɗe rai ya yi ya ce“zan makeki, drink it my friend!” kuka ta fara yi a hankali, Ya kai mata mug ɗin bakinta, Dakyar ta buɗe bakin ta fara sha a hankali. Ko rabin shayin bata sha ba ta ɗauke kanta, Ya sake miƙo mata fuskarsa a haɗe ya ce “Yaushe na fara wasa da ke?” Toshe bakinta ta yi tana girgiza masa kai, Ya janye hannun daga kan bakinta kamar jira take ta fara wanke shin da amai. Shiru ya yi yana kallon ta ganin yanda take kwarara aman har da na abincin da taci ɗazu, gaba ɗaya ta ɓata masa jikinsa, ta ɗora kanta akan ƙirjinsa tana sauke numfashi idanunta a lumshe. Hannunsa ya sanya ya dafa kanta a sanyaye ya ce “Sannu.” Bata ce komai ba, Ya tashi da ita a jikinsa ya nufi toilet, Zaunar da ita ya yi sannan ya fara ƙoƙarin zare mata kayan jikinta. Ta yi saurin riƙe hannunsa tana kuka a hankali, Haɗe rai ya yi ya doke hannunta sannan ya ƙarasa zare mata rigar dake jikinta. Wata irin ajiyar zuciya suka sauke a tare, Ya yi saurin ɗauke kansa daga kan ƙirjinta wanda lokaci ɗaya yaji yana neman tada masa da hankali, sam bai yi tunanin yarinyar ta kai haka ba. Ya kawar da tunanin daga ransa ya miƙar da ita tsaye, Da kansa ya yi mata wankan sannan ya saka mata bathrobe, Ta sake kwantowa jikinsa tana maƙalƙalesa. Ɗaukanta ya yi ya fice daga banɗakin, Ya zaunar da ita kan doguwar Kujerar dake gefen gadon sannan ya yaye bedsheet ɗin ya naɗeshi ya kai toilet ya saka cikin washing machine. Bayan ya fito ya dauƙo sabon bedsheet ya shimfiɗa akan gadon sannan ya ɗaukota ya kwantar da ita akai, Ta dunƙule jikinta waje ɗaya saboda sanyin da take ji, Press ɗinta ya buɗe ya dauko mata wata yar ƙaramar riga mara nauyi, Ya haɗo mata da pant da kuma pad. Ajiyewa ya yi a gefen gadon ya fara ƙoƙarin jawota, saurin riƙe hannunsa ta yi kamar zata yi kuka ta ce “Zan yi da kaina uncle.” Ko saurarenta bai yi ba ya jawota gaba ɗaya, Ya kunce bathrobe ɗin ta yi saurin shigewa jikinsa tana sakin kuka a hankali, Girgiza kansa ya yi sannan ya ɗauko rigar ya zura mata. Bayan ya kammala ya juya ya fice daga ɗakin, After 15mins ya dawo cikin wasu sabbin kayan fuskarsa ta sake fresh da alama wanka ya sake, Ya ƙarasa wajen injection ɗin daya ajiye ya fara haɗawa, Nana ta dinga kallon sa da ɗan mamaki, bayan ya gama haɗawa ya hawo kan gadon hannunsa riƙe da syringe ɗin, Ta yi saurin tashi zaune duk da jikinta babu ƙwari, Ganin tana neman guduwa ya sanya ya riƙota, Ya jawota jikinsa fuskarsa a haɗe babu alamar wasa. Kuka ta saka masa ta fara yarfe hannu, Ya jingina da fuskar gadon yana kallon ta, Cikin kuka ta ce “Uncle dan Allah kada ka yi min allura ban so, zafi take min.” Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce “Baki son allurar?” Saurin gyaɗa masa kai ta yi tana hawaye, Ya ɗan taɓe baki sai kuma ya ce“To kina son na baki sweet?” gyaɗa masa kai ta sake yi, gaba ɗaya fuskarta a shagwaɓe take tamkar jaririya sai narke masa take. Ya zaro wata chocolate a aljihun wandonsa yana kallonta. Ta haɗiye yawu tana kallon ledar chocolate ɗin, ɓarewa ya yi ya kutsuro yana kallonta ya ce “Haa.” A hankali ta buɗe bakin nata, Ya saka mata chocolate ɗin ta fara taunawa a hankali tana lumshe ido. Murmushi ya yi sannan ya ɗauke kansa, Ta kwanta akan ƙirjinsa tana ci gaba da tauna chocolate ɗin, sam bata san ya dauƙo allurar ba, Ya ɗan janye rigarta dan daman ta tattare, ya ɗora tsinin allurar a jikinta sannan ya yi bismillah ya yi mata. Wani irin ƙara ta saki tana ɗagowa daga jikinsa, Ya yi saurin saka bakinsa cikin nata yana shafa bayanta, Kuka ta dinga yi tana ƙoƙarin cizonsa a bakin, Shi dai ya yi shiru yana tsotsar lips ɗinta a hankali. Ta ci gaba da kukanta tana dukansa a ƙirji, Ya ɗan yi murmushi yana riƙe hannunta. Cikin yan mintuna kuma jikinta ya fara saki, Ta mai da kanta ƙirjinsa har sannan bai zare bakinsa daga nata ba, Itama ta fara tsotsar nasa lips ɗin a hankali a haka har bacci ya yi awon gaba da ita. Sai da yaga baccin nata ya fara nisa sannan ya janyeta daga jikinsa ya kwantar da ita, Ta saki ajiyar zuciya tana turo baki gaba wanda yake ta sheƙi, Murmushi kawai ya saki ya ɗan ja kumatunta a fili ya ce “Rigimammiya!” 08106608363 Nanameera. *🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 54. Ya gyara mata duvet ɗin ya rufeta gaba ɗaya sannan ya sauka daga kan gadon, Remote ya ɗauka ya ƙaro gudun ac sannan ya kashe leds ɗin dakin ya juya ya fice. A parlour ya samu Zahra tana bawa Noor abinci, Ya zauna ɗan nesa dasu. Ta sauka daga jikin Zahra hannunta riƙe da ƙaramin plate mai ɗauke da chips ta nufosa, Murmushi ya yi yana ajiye wayar hannunsa ya ce “Noorie.” “Abbie ka bani abinci.” To kawai ya ce sannan ya ɗauketa ya ɗorata kan cinyarsa. Ya fara bata abincin tana masa hira, wani ya amsata wani kuma ya yi shiru. Zahra kuwa ta dinga kallon su ba tare da tace komai ba, daga ƙarshe ta tashi ta bar parlourn. Da idanu ya bita sai kuma ya ci gaba da abin da yake, bayan ya gama bata abincin ya sauketa yana cewa “Oyah muje ki kwanta. Dare ya fara yi” “Abbie ka ɗaukeni to!” Ta yi maganar tana miƙo masa hannu, Murmushi kawai ya yi sannan ya ɗauketa ya fara juyi da ita, ta dinga dariya tana ƙanƙamesa. Kafin daga bisani ya nufi apartment ɗin Zahran da ita. **** Nigeria. Safwan ne zaune kan kujera idanun sa zube akan Haule wadda ta sunkuyar da kanta ƙasa, Tun da ya shigo yake kallon ta. Ya kasa gane wane yanayi yake ciki, farin ciki ne ko kuwa baƙin ciki? Ya ɗan numfasa kafin ya ce “Allah ya sauke ki lafiya, Ya bamu mai albarka.” A zuciya ta amsa da amin dan bakinta ya yi mata nauyi, Ya ɗan yi jim sai kuma ya tashi yana ajiye ledojin dake hannun sa ya ce “Sai da safe.” Sai a sannan ta ɗago kanta ta kalle shi da runannun idanunta, Tayi saurin sauke su ƙasa kafin ta ce “Allah ya tashe mu lafiya.” Da amin ya amsa sannan ya juya ya bar parlourn, Haule tabi bayansa da kallo kuka na tawo mata. Yana fita Amma na fitowa daga dakin, Ta ƙaraso wajen jin shessheƙar kukan Haulen, Zama ta yi gefenta ta dafata ta ce “mene ne abun kuka kuma Haule?” “Amma shikenan na rabu da Yaya Safwan? Shikenan ba zamu tafi gida tare ba? Ni ban ce sai ya zo inda nake ba. Kawai ya maidani gidansa, zuciyata zafi take min Amma!...” Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka. Shiru Amma ta yi tana saurarenta cike da tausayawa, Can dai ta ɗan bubbuga bayanta ta ce “Kaddara ce ta haɗaku, kuma ita ce ta raba ku. Ba zai yiwu ki ci gaba da zama da Safwan ba Haule, Saboda dalilin yana da ƙarfi. Ki sakawa ran ki haƙuri, har Allah ya saukeki lafiya ki samu wani mijin ki yi aurenki.” Haule ta sake fashewa da wani sabon kukan tana faɗawa jikin Amma, Ta dinga rera kukanta kamar ranta zai fita. Ita kanta bata san sanda ta fara son Safwan ba, bata san kuma dalili ba. amma ji take kamar ta tashi tabi bayansa, kamar taje ta roƙe shi akan ya maidata daƙinta. Sun ɗauki lokaci a haka kafin Amma ta ɗago fuskarta ta fara goge mata hawayen ta ce “Kuka yanzu ba naki bane Haule, ki kwantar da hankalin ki. Ko dan lafiyar abin da ke cikinki.” A hankali ta gyaɗa kanta, Amma ta ce“Tashi ki shiga ciki, idan aka yi Isha'i sai ki je apartment ɗin Hajiya Babba dan ta ce tana nemanki.” “ko naje yanzu?” Haule ta yi tambayar a sanyaye, “Baki gaji ba?” Amma ta ce tana kallon ta, gyada mata kai ta yi ta ce“Eh Amma zan iya zuwa.” Numfasawa ta yi kafin ta ce“to tashi ki je Allah ya tsare” Haule ta amsa da amin sannan ta miƙe tana gyara zaman hijabin jikinta ta fice daga parlon, Amma ta bita da kallo sai kuma ta girgiza kanta. Nana ce ta faɗo mata arai, dan haka ta jawo wayarta dake kan table ta fara dialing numbernta, sai dai har ta katse ba'a ɗauka ba dan haka ta mayar da wayar ta ajiye ta tashi ta koma ciki.. Tsaye ta hangesu bakin apartment ɗin Hajiya Babban, ta ƙarasa a sanyaye tana sunkuyar da kanta. Kasa shigewa ta yi dan haka ta ɗan durƙusa ta ce “Hamma ina yini?” Sultan ya kalleta dan bai ma ganeta ba, can kuma ya ce“au Haule lafiya kalau, ke ce a daren nan?” gyaɗa masa kai ta yi kafin ta kalli Amrah ta ce“Sannu ya jikin?” “Da sauƙi Alhamdulillah.” cewar Amrah tana murmush, Safwan ne ya kalleta kamar ba zai magana sai kuma ya ce “Ina zaki je da daren nan?” Sai da taji zuciyarta ta buga, Ta ɗan runtse idonta murya can ƙasa ta ce“Hajiya Babba ke kirani.” “Okay, amma idan kin daɗe ki kwanta anan kawai. Ki daina yawo” toh kawai ta ce sannan ta bar wajen a sanyaye. Sultan ya girgiza kansa yana kallon Safwan fuska babu annuri ya ce “amma ka cutar da yarinyar nan wallahi. Ni ban so ma wannan cikin ba, yarinya ƴar ƙarama zata zama bazawara har da ɗa...” Shi dai Safwan bai ce komai ba, dan shima zuciyarsa ba wani daɗi ta yi masa ba. Can dai ya ce “Goben zan shigo asibitin.” Sultan ya ɗan harararesa sannan ya ce“kada ma ka shigo, ka zauna ka kashe kanka. Kusan 1 week ina maka magana amma kana shareni” girgiza kai Safwan ya yi cikin sanyin murya ya ce“ba zaka gane bane. Zan zo dai” “Allah yasa.” cewar Sultan, Ya ɗan yi murmushi sannan ya kalli Amrah dake ta yatsine fuska ya ce“Sai da safe, Allah ya raba lafiya.” da Amin ta amsa sannan ya sake yiwa Sultan ɗin sai da safe ya bar wajen, Sultan ya ɗan kalleta ganin ta durƙusa ya ce “mene ne?” “Yaya nagaji, cikina zafi yake min.” Riƙo hannunta ya yi ya ce“Sorry muje gida.” ta ɗan gyaɗa kanta sannan suka fara tafiya a hankali. **** Gibson Jalo. Anty Khadijah ta ɗan kalli Umma sai kuma ta yi dariya ta ce“Ai Umma na kusa auren da gaske in sha Allah. Nan bada jimawa ba zaki ga an fara zancen auren” Umma ta ɗan taɓe baki ta ce“Yo Khadijah kalar wannan zancen yau na fara jin sa a wajenki?.” Anty Khadijah ta yi murmushi ta ce“Allah wannan karon da gaske nake Umma” Umma ta ce“To Allah ya tabbatar da alkhairi.” “Amin kuma kin ga...” maganar ta tsaya saboda wayarta dake ringing, Ta ɗan kalli screen ɗin wayar ganin sabuwar lamba ya sanyata ɗagawa, Ta ce “Hello.” “Assalamu alaiki.” Tashi Aunty Khadijah ta yi ta haye sama da sauri, Ɗakinta ta shiga ta saka key ta rufe sannan ta ce “Akan me ka ke kirana? Bana faɗa maka ni ba sa'ar aurenka ba ce?” Girgiza kansa ya yi yana murmushi can kuma ya ce“Khadijah kenan, daman kiran ki nayi na nemi yafiyarki. Wallahi bada wani abu nayi wannan maganar ba, amma ina son ki yi haƙuri ki yafe min.” Anty Khadijah taja wani dogon tsaki kafin ta ce “An faɗa maka ni irin waɗanda zaka yiwa wayo ce? To bari kaji wallahi koda wasa ka sake kirana sai nayi maka rashin mutunci, Wani ƙazami da kai!” Bata jira amsar da zai bata ba ta sauke wayar daga kunne ta katse kiran tana jan wani dogon tsaki. Tsabar takaici ya sanya ta yi wurgi da wayar ta faɗa tsakiyar gado, Ta nemi gefe ɗaya ta zauna tana tunani. Ta fuskanci idan bata yi maganin mutumin nan ba sai ya sakata a masifa, Ta yi kwafa ta tashi ta fice daga ɗakin gaba ɗaya.. **** Safwan ya dinga kallon Siyama ganin yanda ta ɗan haɗe rai, Ya girgiza kansa ya ce “Ba wai dawowa zata yi ba fa. Kawai dai na faɗa miki ne” Taɓe baki ta yi ta nemi gefe ɗaya ta zauna tana kallon sa ta ce“Ai saboda ita ka ɗauka da muhimmanci gashi har ta samu ciki a ɗan zaman da ku ka yi tare, amma ni da baka ɗaukeni a bakin komai ba ai gashi ka bar ni sai dai naci na kasayar!” Safwan ya dinga kallonta da mamaki, can kuma ya ce“Siyama ban gane me ki ke nufi ba? Daman ni ne wanda nake da alhakin samun cikin ki ko rashin sa? Mene nawa a ciki?.” Tashi tsaye ta yi tana harararsa ta ce“A'a ba kai bane, ya za'a yi ya zama kai daman! Amma ka sani wallahi idan dan ka zalunceni ka ke min haka Allah ba zai bar ka ba. Ai nima matarka ce, kuma nima ina son naga na haihun, amma shi ne ka fifita ƴar uwarka akaina...” Ta bar parlourn da sauri tana kuka, Safwan ya bita da kallo sai kuma ya sunkuyar da kansa yana sauke numfashi. After some minutes kuma ya tashi yabi bayanta. Zaune ya sameta gefen gado sai kuka take a hankali, Ya ƙarasa ciki ya tsaya a zauna akan drawer yana kallon ta ya ce “Ina son ki gane wannan ba laifina bane Siyama, ban kyamace ki ba, ban guje ki ba. Na ɗauki hakan matsayin ƙaddararmu gaba ɗaya dani dake, amma ki sani ba ni ne wanda ke bada haihuwa ba, tsarin Allah ne. Kuma shi yaga damar ya hukunta Haule ta samu ciki, Shi ne ya yi mata kyautarsa, dan haka ki daina damun kan ki, idan Allah ya so sai ki ga ya sake bamu wasu. Kuma ai a ganina abin da zan haifa kamar naki ne, duk abin da Haule ta haifa karɓarsa zan yi, mu raine shi tare. Kin ga zamu samu ɗa mai lafiya...” “Ai daman dole ka ce haka, dole ka ce kana son ka samu ɗa mai lafiya. Saboda ni ba zan iya haifar maka ɗan ba, ko kuma baka son irin wanda zan haifa kai da danginka. Shi ne zaka ce min tsarin Allah ne!” Safwan ya yi shiru yana kallon ta, sam bata fahimci abin da yake nufi ba, dan haka ya taso daga inda yake ya dawo gefenta ya zauna. Hannunta ya riƙe cikin nasa murya a sanyaye ya ce “Ba haka bane Siyama. Wallahi ko yau Allah ya baki ciki zan yi farin ciki, kamar yanda nayi farin ciki dana Haule. Kuma ai likita ya faɗa mana zamu iya haifar ya'ya wanda basu da cutar, dan haka ki daina damun kan ki dan girman Allah” Siyama ta sanya ɗayan hannunta ta goge hawayenta, cikin shessheƙar kuka ta ce“Ai shikenan. Allah ya sauketa lafiya.” Murmushin jin daɗi ya yi dan daman ya san zata fahimce shi ya ce“Amin, Ya bamu wasu Ya'yan.” da amin ta amsa sannan ta ce“muje ka ci abinci.” To kawai ya ce duk da ba yunwa yake ji ba, Ta tashi tana riƙe da hannunsa ta ce“muje to” Ya gyaɗa mata kai bayan ya miƙe tsaye suke fice daga ɗakin. **** New York, America. Zahra na zaune tana danna wayarta ya shigo, Sanye yake da pyjames white colour ya ɗaure kansa da ribbon, Ya ƙaraso ciki ya zauna gefen gadon yana kallon ta. “Sannu da zuwa.” Ta ce a sanyaye bayan ta ajiye wayar a gefenta. Babu yabo babu fallasa ya ce“Yauwa.” shiru wajen ya ɗauka can kuma ta ce“Ko na kawo maka abinci?” girgiza kansa ya yi yana kallonta ya ce“A'a thank you.” “But you didn't eat anything fa. Ko dai Nana ta baka abinci?” Sake girgiza kansa ya yi ya ce“a'a ban ci komai ba, Nana ma bata jin daɗi.” Zahra ta kalleshi a karo na farko ta ce“me ya sameta?” zare ribbon ɗin kansa ya yi ya ce“nothing serious fa, wai cramps ke damunta” Zahra ta girgiza kanta a sanyaye ta ce“Allah ya sawwaƙe.” Amin kawai ya ce, can kuma ya ce“yau mene ya same ki?” girgiza kanta tayi tana murmushi ta ce“babu komai fa, kawai mood swings ne” Abdusammad ya ɗan taɓe baki sai kuma ya jawota jikinsa ya ce “shi ne zaki dinga wani shareni?” Murmushi ta yi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa ta ce“to ai kai ma sharenin ka yi.” ta ƙare maganar tana shagwaɓe fuska, Ɗago kanta ya yi ya ce“da gaske?” Ta gyaɗa masa kai tana sake narkewa a jikinsa, Murmushi ya yi ya ce“to yanzu zan daina share kin” murmushi ta yi ta ɗago kanta tana kallon sa ta ce“gobe Noor zata tafi school, dan haka da wuri zan tashi.” Gyaɗa kansa ya yi ya ce“haka ne to dan haka sai ki kwanta da wuri, naga ta damu ta koma da sai ta bari sai ta huta.” Zahra ta ce“wannan ƴar taka mai wutar ciki, ya za'a yi ta jira?” ta ƙare maganar tana murmushi. Dariya ya yi ya ce“Eh ai ke ta gado” Zahra ta ɗan kalleshi da mamaki ta ce“a haba dai ni doctor” Murmushi ya yi ya ja hancinta ya ce“Eh mana.” Zahra ta maƙale kafaɗa ta ce“a'a sai dai idan kai ta gado wallahi.” “Ko?” Ya ce yana ƙoƙarin kwanciya, Ta ɗan yi murmushi sai kuma ta kwanta a gefensa... Around 2:00 na dare ta buɗe idanunta, Ta tashi zaune ta dakyar saboda ciwon da marar ke mata, ta ɗora hannunta akan mararta tana kuka a hankali. Ta daɗe zaune a wajen kafin ta sauka daga kan gadon dakyar, Ta kunna bedside lamp nan da nan haske ya gauraye ɗakin, kalle-kalle ta dinga yi ganin bata ganshi ba ya sanya ta zura slippers ɗinta ta nufi waje a hankali. Kai tsaye apartment ɗinsa ta nufa, Ta tsaya bakin ƙofar tana murza idanunta wanda har sannan bai gama wartsakewa ba. A hankali ta fara knocking ƙofar tana kiran sunansa, Sai dai har bayan mintuna biyar babu alamar za'a zo a buɗe, Nana ta fashe da sabon kuka tana ɗan buga ƙafafunta, ita kaɗai ta san azabar da take ji. Ta juya ta sauka daga benan, Tsayawa ta yi a wajen tana kallon benan Zahra, lokaci ɗaya kuma ta hau tana tafe tana dafe mararta. Knocking ta dinga yi kamar zata jijjige ƙofar. Abdusammad ya janye Zahra daga jikinsa ya tashi zaune yana kallon ƙofar da mamaki. Itama Zahra buɗe idanunta ta yi dan ba wani nauyin bacci gareta ba, “Kin ji?” Ta gyaɗa masa kai tana hamma, bayan ta rufe bakinta ta ce“waye to?” “Ko Noor ce?” Y tambaya yana sauka daga kan gadon, Zahra ta gyara zamanta tana jiransa. Ya ƙarasa ya buɗe ƙofar. Da mamaki yake kallonta, ganin yanda ta yi tsaye a wajen tana murza idanunta tana kuka, Ya ɗan ware idanunsa kafin ya ce “Mene ne Nana?” Cikin kuka ta ce“uncle ni bana son kwana ni kaɗai, kuma cikin ciwo yake min...” ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan, Zahra ta taso tana kallon sa ta ce “mene ne?” Ya ɗan girgiza kansa bayan ya bar jikin ƙofar, Nana ta gani tsaye tana kuka. Ta kalleshi ta ce“Lafiya dai?” “Uncle ni tsoro nake ji. Ka zo mu tafi tare” 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 55. Daga shi har Zahra suka kalleta, Ta janye hannunta daga idanun tana kallon su sai kuma ta ɗauke kai tana tura baki. Abdusammad ya ce“zo nan.” jiki a sanyaye ta ƙarasa gabansa, Ya sanya hannunsa na dama ya taɓa wuyanta. Zazzaɓi ne sosai a jikinta, Ya ɗan girgiza kansa kafin ya ce“to ki zo ku kwanta da Zahra anan.” A hankali ta kalle shi sai kuma ta sunkuyar da kanta tana maƙale kafaɗa, Zahra ta ɗan yi murmushi ta ce“Kawai doctor kaje.” wani banzan kallo ya watsa mata kafin ya kalli Nana ya ce“koma ki kwanta to. Babu abin da zai same ki” Cikin kuka ta ce“Allah ni ba zan iya kwanciya ni kaɗai ba, Tsoro nakeji. Kuma ai bani da lafiya...” Ta sake fashewa da kuka, Haɗe ransa ya yi in a serious tone ya ce “koma nace!” Ganin babu wasa akan fuskarsa ya sanyata ficewa daga ɗakin, Ya mai da ƙofar ya rufe ya koma kan gadon. Zahra ta dinga kallon sa kafin ta ce“amma ka ce bata da lafiya fa, da kaje wajenta.” Bai bata amsa ba ya yi kwanciyarsa, dan ya riga da ya san halin Nana, rashin son zaman lafiya ne kawai irin nata. Zahra bata sake cewa komai ba itama ta koma ta kwanta. Nana ta dinga kallon ƙofar hawaye na sakkowa kan idanunta, Ta juya ta fice daga parlourn ta koma ɓangarenta. Kwanciya ta yi akan gadon ta dinga kuka tana juyi, can kuma ta tashi ta gudu ta nufi banɗaki. Amai ta yi ta wanke bakinta ta dawo ɗakin ta kwanta, ko kaɗan ta kasa bacci sai juyi take tana kuka, tun da ta fara period bata taɓa yin irin wannan ba. Saboda ba'a taɓa barinta babu magani, idan bata yi bacci ba babu wanda zai kwanta a gidan, ko tsakar dare ne sai Abba ya fita ya kai ta asibiti. Ta sake rushewa da kuka tana jin haushin biyoshin da ta yi, tana nan kwance har aka fara kiraye-kirayen sallar asuba a masallacin gidan, ta dinga ƙoƙarin tashi zaune amma ta kasa, daga ƙarshe kuma bacci ya ɗauketa. Murɗa handle ɗin ƙofar ya yi bakinsa ɗauke da sallama, Ya shigo ciki ya mai da ƙofar ya rufe yana kallon ta, gaba ɗaya ta rufe jikinta da bargo ko kanta ba'a gani. Ya ɗan girgiza kai sannan ya ƙarasa ciki ɗakin, zama ya yi gefen gadon ya sanya hannunsa mai maƙale da counter ya ɗan taɓa ta ya ce “Ke Nana.” Shiru bata amsa ba, Ya janye bargon yana kallon ta, ba bacci take ba, amma idanunta a rufe suke sai hawaye dake zubowa ta gefensu. Hannunsa ya kai ya taɓa wuyanta yaji har sannan da zafi sosai, Ya tashi ya fice daga ɗakin ba tare da ya ce komai ba. Bayan kusan mintuna goma ya dawo hannunsa riƙe da wani ƙaramin tray, Ya jawo table ya ajiye sannan ya koma ya zauna yana kallon ta ya ce “Taso.” Ba zaka taɓa cewa da ita yake ba, dan ko buɗe idanunta bata yi ba. Sai shessheƙar kuka da take a hankali, Murmushi ya yi sai kuma ya sanya hannunsa ɗaya ya ɗagota. Kamar jira take ta fashe da kuka tana ƙoƙarin janye hannunsa, sai dai rashin gwarin jikinta ya sanya ta gagara yin hakan. Ya zaunar da ita akan cinyarsa yana kallon ta ya ce “ina miki magana kina share ni?” Ɗauke kanta ta yi tana ƙoƙarin sauka daga jikinsa, Ya riƙe gam ya ɗago fuskarta ya ce“me aka miki?” bata san sanda ta sake fashewa da kuka ba, Ta fara dukansa tana cewa “Ni ka rabu dani, ni bana so kana taɓa ni. Wallahi sai na faɗawa Ammata, ni gidanmu zan tafi...” Ban da murmushi babu abin da yake, Ya riƙe fuskarta cikin tafukan hannunsa ya ce “Yaushe zaki tafi gidan?” Kallon sa ta yi, ganin yanda yake murmushi ya sanyata ɗauke kanta tana sake rushewa da wani kukan, Janyo fuskarta ya sake yi ya rungumeta ya ce “Shikenan ya isa haka. Ki yi shiru kin ji” “ka mayar dani gida” Ta ce tana kuka, Shafa kanta kawai ya yi ya ce“tom zan mai da ke. Zo ki ci abinci” “A'a ni ba zan ci ba ɗin.” Ɗago fuskarta ya yi ya ce“tashi nace, je ki wanke bakinki ki zo ki ci abinci” sake maƙale kafaɗa ta yi tana shirin yin magana taji ya daka mata tsawa, Da sauri ta sauka daga jikinsa ta nufi toilet ɗin tana kuka. Sai da ta tsaya a banɗakin ta gama kukanta sannan ta wanko bakin ta fito,Ta zauna a gefe ta sunkuyar da kanta. Mug ɗin tea ɗin ya miƙo mata ya ce “ki shanye tas kar ki rage min ko kaɗan.” Kallon tea ɗin ta dinga yi fuska a yatsine, can dai ta kai shayin bakinta ta yi saurin ɗaukewa tana yarfe hannu ta ce “zafi fa uncle.” Kallon ta ya yi, sai kuma ya miƙa mata hannu, ta bashi shayin tana kallon sa. Doke hannunta ya yi ya jawota jikinsa ya karbi mug ɗin, bakinsa ya sa ya ɗan hura mata shayin sai kuma ya miƙa mata bakinta ya ce “Haaa.” Buɗe bakin ta yi ya fara bata, ko rabi bata sha ba ta ɗauke kanta ta ce“ni Allah na ƙoshi.” “shanye ko na mareki” Kamar zata yi kuka ta ce“na ƙoshi wallahi.” Ya ajiye mug ɗin akan tray ɗin sannan ya janyo plate ɗin soyayyen dankalin, Da kansa ya dinga bata shi ma har ta kusa cinyewa sannan ta ce“na ƙoshi.” bai ce komai ba ya ajiye plate ɗin yana kallonta ya ce“zo ki kwanta to.” Kamar jira take ta rarrafa kan gadon ta yi kwanciyarta tana lumshe idanu. Ya ɗan kalleta sai kuma ya tashi ya fita hannunsa riƙe da tray ɗin, after 2mins ya dawo hannunsa riƙe da syringe, Ya zauna gefenta bayan ya ɓoye syringe ɗin a bayansa ya ce“dawo nan ki kwanta.” ya yi maganar yana nuna mata cinyarsa, Son jiki irin nata ya sanya ta taso ta ɗora kanta akan ƙirjinsa ta zagaye hannunta a bayansa ta rufe idanunta. Shiru ya yi yana kallon ta, sai da yaga ta fara bacci sannan ya zaro syringe ɗin, Ya sauke wandon jikinta ya saita allurar ya tsira mata. Wata irin ƙandarewa ta yi tana sakin kuka, Ta gasa masa cizo a ƙirji tana kuka. Murmushi kawai ya yi ya ɗauke syringe ɗin yana shafa kanta ya ce “Sorry yi baccin ki.” Bata ce komai ba, sai kukanta da take ƙasa-ƙasa dalilin baccin daya fara ɗaukanta, Shima ya yi shiru idanunsa a lumshe har bacci ya ɗauketa. Saukar numfashinta daya fara ji ya sanya ya ɗan kalleta, bacci take hannunta ɗaya a baki ta kwaɓe fuska, Ya girgiza kansa ya janyeta ya kwantar kan gadon sannan ya tashi ya rufeta da duvet. Ganin tana motsi ya sanya ya koma ya zauna, ta yi juyi sannan ta ci gaba da baccinta. Sauke numfashi ya yi sannan ya rage gudun ac ya juya ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ɗakinsa ya nufa yana zuwa ya yi kwanciyarsa dan shima baccin yake ji. **** It's been a months da zuwansu New York, gaba ɗaya aiki yayi masa yawa. Kusan kullum baya shigowa gidan sai dare sosai, shiyasa basa wani ganinsa idan ba asuba ce ta yi ba. Ɓangaren Zahra abun nata kullum gaba yake, yau a zauna lafiya gobe ta tada balli. Shi dai baya biye mata, dan bama shi da lokacin tsayawa faɗa da ita. Nana ce kawai ki biye mata idan ta dawo daga makaranta baya nan su yi ta tashin hankali, Yau ma kamar kullum tana zaune a main parlourn tana chatting, Abdusammad ya sauko daga ƙasa yana kallon ta ya ce“baki shirya ba?” miƙewa ta yi tana kallon sa ta ce“kai nake jira fa.” Ya kalli Noor dake zaune kusa da ita ta yi shiru ya ce“zo” ta shi ta yi ta koma wajensa ta tsaya ya ɗauketa ya ce“me ki ke so?” “Abbie chocolate zan ɗauko nida Afeefa da Sumshi” Ya ɗan ware idanunsa yana murmushi ya ce“iyye iya su kaɗai zaki ɗaukowa?” ta gyaɗa masa kai tana kwanciya a jikinsa. Bai sake ce mata komai ba ya kalli Nana wadda ke sakkowa daga sama hannunta rike da jakarta. Ƙarasowa ta yi ta tsaya tana rike da wayarta ta ce “uncle na gama.” Okay ya ce sannan ya kalli Zahra ya ce“Madam muje.” Fuskarta a haɗe ta ce“ita kuma ina zata je?” ta yi maganar tana nuna Nana, Ɗauke kai Nana ta yi dan bata da lokacinta. Ya ɗan kalleta da mamaki ya ce“ina zamu je dai zaki ce” “To ai naga dai yau ba kwananta bane ballantana ta bika unguwa. Dan Allah wallahi ba zata je ba!” Zahra ta yi maganar tana zabgawa Nana harara. Kafin ya yi magana Nana ta ce“to ai sai ki hanani zuwan, wallahi sai naje” Kallon su ya dinga yi ganin zasu fara halin nasu ya ce“kun ga ni babu wadda zata ɗaga min hankali. Naji ba kwananta bane, kenan idan ba kwananta bane ba zata bi ni wani waje ba?” gyaɗa masa kai Zahra ta yi ta ce “Eh wallahi ba zata raka ka ba. Idan tana so aje da ita shopping ko wani waje sai ta bari sai ranar da ka ke daƙinta ku je, amma yau ranata ce nida ƴata Allah ba zata bimu ba.” Taɓe baki Nana ta yi tana kallon sa taji me zai ce. Ya ɗan yi shiru can kuma ya ce“shikenan tunda abun haka ne, duk ku zauna an fasa zuwa. Da Noor kawai zan je” “Ohho sai dai a fasa ɗin amma muddin dani wlh ba zata ba!” Zahra ta yi maganar tana zama akan sofa, Nana ta kalleshi cike da masifa itama ta ce“to ai idan ka je da Noor kamar ka je da ita ne. Sai ka tafi kai kaɗai” Girgiza kansa ya yi ya ce“wannan ne kuma baku isa ba.!” Daga haka ya nufi waje hannunsa riƙe Noor, Zahra ta mike tana kallon ta ta ce“kin ga ko? Ai ke baki isa ki na hana abu kuma ayi ba. Kuma wallahi kamr yanda na faɗa miki sai kin san kin auri mijina, sai kin yi dana sanin aurensa, wallahi duk wani abu dana san zai ƙuntata miki sai na saka shi ya yi sa, sai kin gwammace ace baki yi aure ba!” Dakewa Nana ta yi duk da kukan dake neman kwace mata, ta zabga mata harara ta ce “To idan kin fasa. Na auri mijin naki, na aure shin, kuma babu abin da ki ka isa ki yi min. Wallahi baki isa ba! Idan ma akwai wadda zata yi dana sani to ke ce bani ba, ke bare wadda ya auro ki daga waje. Wadda ta aure shi saboda kwadayin abun hannunsa, ke ce zaki fita ki bar ni a gidan nan. amma ni dai ƙarya ne na bar gidan nan saboda ke!” Zahra ta dinga kallon ta ganin yanda take gasa mata magana, can ta yi kwafa tana matsowa kusa da ita ta ce “Ai ko zan nuna miki ke baki isa ba, ni da ya auro ni a wajen na fiki ƙima da mutunci a wajensa. Ke da aka yi masa auren cushe? Ko an faɗa miki bamu san yanda aka yi bane? Ko kin manta? Ballagazar yarinya wadda ta gama zubar da mutuncinta a waje. Shashasha mai bin maza kawai! Wadda iyayenta basu bata tarbiyyar data kamata ba! Lalatacciyar yarinya wadda lalatattun iyaye suka haifeta!” Tuni Nana ta fara hawaye, ta cakumi wuyan rigarta tana kallon ta ta ce“Ke kin isa ki zagar min iyaye! Wallahi ƙarya ki ke! Sai dai idan kece latattun iyaye suka haifeki! Ubanki da uwarki ki ke zagi ba dai nawa ba, Banza...” Wasu zafafan maruka taji an sauke mata a both checks ɗinta, Ta haɗiye ragowar maganar ta dafe kuncinta tana jan numfashi. Tsananin azaba ya hanata koda kuka, ya fizgota daga jikin Zahran yana mata wani irin kallo fuskarsa a haɗe ya ce “abin da ki ke yi kenan? Abokiyar wasanki ce ita? Sa'arki ce da ki ke yi mata haka? Zagi? Zagi Nana!?” Zahra ta fara sharar hawaye tana kallon sa ta ce“gara da Allah yasa ka dawo ka gani yau a gabanka. Idan na faɗa maka ai nasan ba yarda zaka yi ba, kullum haka take min, kullum idan har baka nan ta dawo daga makaranta haka take zama tana zagina, ya za'a yi na jure? Nana fa? Ya za'a yi a ce Nana ke zagina! Ni fa...” . Zahra ta fashe da kuka, Fuskarsa a haɗe take, idanunsa sun sauya kala, ko ba'a faɗa ba ka san ransa ya yi matuƙar ɓaci. Ya hankaɗeta yana kallon Zahran ya ce “Muje!” Jiki a sanyaye ta ɗauki wayarta tabi bayansa, Nana ta kasa ko da kallonsu saboda idanunta da suka ƙi buɗuwa. Sai da suka fita sannan ta zube a wajen ta saki wani marayan kuka, ban da raɗaɗi da azaba babu abin da fuskarta ke yi, ta daɗe a wajen tana dafe da kuncinta kafin ta tashi ta haye sama da gudu. Tana shiga daƙinta ta faɗa kan gado ta ci gaba da kuka kamar ƙaramar yarinya, Koda wasa bata yi tunanin zai mareta ba, bayan kuma ba laifinta bane..ita ta fara zaginta, Ta dunƙule jikinta waje ɗaya tana sake fashewa da wani sabon kukan, da gaske baya sonta, da gaske Zahra yake so. Nana ta ci gaba da kukanta tana dana sanin yarda da auren, dama bata dawo ba sanda ta garin gidansu Khadijah, dama ba gidan taje ba duniya ta shiga. Da babu wanda ya ganta, ta ci gaba da kukanta kamar ranta za fita. Tafi awa kwance a wajen kafin ta tashi ta zura slippers ɗinta ta shige toilet. A gaban madubi ta tsaya tana kallon fuskarta, gaba ɗaya shatin hannunsa ne akan fuskarta, Sai jini a gefen bakinta. Cikin kuka ta kunna sink ɗin ta tara hannunta ta ɗebi ruwan ta wanke bakinta sannan ta wanke fuskarta. Bayan ta gama ta fito ta koma ta kwanta tana kuka a hankali. **** Anty Khadijah ce zaune kan sofa tana kallon Kaddu, Can ta ce“to ya za'a yi yanzu?" Kaddu ta ce“wallahi kin ga naje na karbo miki wannan maganin ma, wai ki saka ki a tea ki sha. Kina nan zaki gan shi ya zo har gidan nan” Anty Khadijah ta yi shiru kallonta kafin ta ce“to Zahra fa? Na yi magana da ita ta ce min wai tana shan maganin, to amma har yanzu ban ji ya saketa ba!” Kaddu ta yi murmushi ta ce“me ki ke ci na baka na zuba? Ai tunda aka ce miki zai saketa wallahi sai ya saketan. Kin manta yanda aka yi lokacin auren Siyama? Ai indai malam Garba ya faɗi abu to kamar ya faru ne.” Anty Khadijah ta ce“To shikenan, bani nasha yanzu ma.” Kaddu ta buɗe jakarta ta zaro ƙullin maganin ta miƙa mata. Tashi Anty Khadijah ta yi ta shige kitchen, Kaddu ta bita da kallo har ta fito hannunta riƙe da mug, a gabanta ta kwance maganin ta juye shi tas a ciki sannan ta saka spoon ta juya ta kafa kai ta shanye. Kaddu na murmushi ta ce“inda biyan buƙata?” “Rai ba'a bakin komai yake ba!” Anty Khadijah ta bata amsa, suka tuntsire da dariya a tare suna tafa hannu. **** Siyama ta shigo ɗakin tana kallon sa, ajiye ledar hannunta ta yi ta ce“ko na kira maka Sultan ne?” Safwan dake kwance yana rawar sanyi ya girgiza mata kai, Ta zauna gefen gadon ta ce“to tashi ka sha maganin.” murya can ƙasa ya ce“Bani wayata” Siyama ta juya ta ɗauko wayar dake kan drawer ta miƙa masa. Dakyar ya tashi zaune ya jingina da jikin gadon, Ya yi dialing numbernsa, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. Abdusammad da ke zaune kan kujera ya ce “Safwan ya jikin?” Madadin ya bashi amsa sai kawai ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro. Abdusammad ya tashi tsaye hankali a tashe ya ce “mene ne? Me ya faru?” “Yayaaa...” Ya kira sunansa cikin kuka. “Na'am Safwan.” Ya amsa a sanyaye, Safwan ya ja numfashi ya sauke ba tare da ya yi magana ba. Abdusammad ya sake cewa“ina jin ka, me ya faru?” “Yaya mutuwa zan yi. Wallahi mutuwa zan yi, dan Allah ka zo kaji" Girgiza kai Abdusammad ya yi sanin halin rakinsa ya ce“Ban son raki fa. Wane ya ce maka cuta mutuwa ce? Ka nutsu, zan saka a shirya maka Flight, zuwa next week sai ka tawo” Safwan ya ja numfashi sannan ya ce “Allah Yaya mutuwa zan yi, ka zo kafin na mutu.” Tsaki Abdusammad yayi ya ce “ranka zai ɓaci Safwan, kai ƙaramin yaro ne?” Murmushin ƙarfin hali Safwan ya yi ya ce “to shikenan Yaya.” “kana shan maganin dai yanda ya kamata right?” Safwan ya gyaɗa masa kai kamar yana gabansa sannan ya ce “Eh ina sha.” Abdusammad ya jinjina kansa ya ce “ka ci gaba da sha to, idan na koma gida zamu yi waya." To kawai Safwan ya ce sannan ya kashe wayar, Siyama ta dinga kallon sa sai kuma ta yi murmushi ta ce “Ji yanda ka ke kwaɓe fuska” Harararta ya yi ya ce“dan baki san ciwon da nake ji ba” yanda ya yi maganar ya sanyata dariya, Ta ce“ka ganka kuwa?” Ya dauke kansa yana sakin ajiyar zuciya. 08106608363 Nanameera. *🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 56. **** Basu dawo gidan ba sai wajen 8:00 na dare, Ya miƙa mata Noor dake bacci ya ce“Kai ta ɗaki ina zuwa.” Karɓarta Zahra ta yi tana murmushi ta ce“ina zaka je?” “fita zan yi.” Ya yi maganar yana juyawa. Zahra ta kalli security ɗin da ya shigo da kayayyakin da suka siyo, Ya ajiye a parlourn sannan ya fita. Sama ta nufa tana rike da Noor, Ta kwantar da ita akan gadonta sannan ta zare mayafin jikinta ta nufi toilet, Bayan ta fito ta zauna gefen gado dan already sun yi sallah a masallaci. Numbern Anty Khadijah ta yi dialing bayan ta ɗaga ta ce “Anty Ya gida?” Anty Khadijah dake kwance kan gadonta ta yunƙura ta tashi zaune tana cewa “Zahra muna nan kalau” Zahra ta jinjina kanta tana murmushi ta ce “Anty daman kiran ki nayi na faɗa miki wallahi maganin da ki ka bani yana aiki. Yau dana sake sha da safe kin ga ɗazu a gabana ya mareta har sau biyu, kuma yanzu ma da muka dawo ko nemanta bai yi ba.” Anty Khadijah ta yi murmushi ta ce“to bana faɗa miki ba daman? Yanzu zaki ga ko kwana daƙinta ba zai dinga yi ba, ballantana ki ji ance tana da ciki.” Zahra ta ɗan yi dariya ta ce “to ai Anty babu abin da ya taɓa shiga tsakaninsu fa, shi har yanzu baya yi mata kallon matarsa.” Anty Khadijah ta yi shiru kamar mai nazari can kuma ta ce “amma kina ganin haka babu matsala Zahra?” Zahra ta ɗan girgiza kai ta ce“eh babu matsala mana Anty, kin ga ai bani da damuwar ko ta samu ciki ko wani abu. A haka har ta gaji ta saka ya saketa” Anty Khadijah ta sauke numfashi ta ce“haka ne kuma. To Allah ya sake rufa asiri” Zahra ta yi murmushin jin daɗi ta ce“amin Antyna. Ki gaida su Umma” “Ba zaki kirata ba?” Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“kin san halin faɗanta. Yanzu idan nayi kiranta ba zata bari mu yi hira ba zata fara min wa'azi kawai na kirata gobe.” “Oh ku dare ne ko? To Allah ya kai mu” da Amin ta amsa sannan ta kashe wayar, Zahra ta ajiye wayar gefenta ta yi shiru tana tunani, ita kaɗai kuma ta fara murmushi saboda tunawa da abin da Abdusammad ɗin ya yiwa Nana. **** Nana na zaune gefen gado Around 9pm taji an fara knocking ƙofar, Ta ɗaga kumburarrun Idanunta ta kalli ƙofar sai kuma ta sauke kanta. Tana jin sa har ya gaji ya bar jikin ƙofar, Ta koma ta kwanta ta fashe da wani sabon kukan, yini ta yi tana kuka. Takaici ya hanata yin shiru, Ta jima a haka kafin ta tashi ta shiga banɗaki, ta wanko fuskarta ta dawo ta zauna gefen gadon ta zuba uban tagumi. Abdusammad kuwa yana barin jikin ƙofar ɗakin Zahra ya nufa, Ya sameta zaune ta sauya kaya zuwa na bacci da alama wanka ta yi, tana ganinsa ta fara murmushi. Babu yabo babu fallasa ya ce “Zahra mene ya haɗa ki da Nana ɗazu?” Da ɗan mamaki take kallon sa, Ya ɗaga mata gira ya ce“Eh. Mene ya yi causing faɗan naku?” Zahra ta ɗan juya Idanunta kafin ta ce“amma kusan a gabanka aka yi komai doctor, babu abin da nayi mata. Kawai daga muna magana akan fitar shi ne fa ta fara zagina, kuma ai ba yau suka fara min irin haka ba. Duk ƙannenka sun raina ni" “Kina nufin baki ce mata wani abu mara daɗi ba?” Ya yi tambayar yana kallonta. Zahra ta girgiza kanta ta ce“babu abin da na ce mata, yama za'a yi na tsaya ina faɗa da Nana?” Numfasawa ya yi ya girgiza kansa ya ce“To bana son kina biye mata, ke da kan ki kin san yarinya ce. Kuma kin san halinta ba tun yau ba, Nana ba son zaman lafiya take ba, dan haka duk abin da zata yi kada ki sake biye mata.” Rau-rau ta yi da idanu kamar zata yi kuka ta ce“kenan goyan bayanta ka ke?” Wani irin kallo ya watsa mata wanda ya sanyata sunkuyar da kanta. Ya tako har gabanta yana kallonta fuska a ɗaure ya ce “Babu wadda nake goyan baya a cikin ku. Ku duka matana ne, kuma duk wadda ta yi ba dai-dai ba zan mata magana. So behave ur self” Zahra ta yi shiru har sannan bata ɗago kanta ba, Ya juya ya fice daga daƙin. Taɓe baki ta yi sannan ta yi kwanciyarta. Koda ya fita ɗakinsa ya shiga, Ya duba keys ɗin ɗakunan ya zari guda ɗaya. Yana zuwa ya saka key ɗin ya murɗa, cikin sa'a kuwa yaji ya buɗe dan ba'a jiki ta bar keyn ɗin ba, Sam Nana bata ji alamun buɗe ƙofar ba saboda kukan da take. Sai mutum ta gani a gaban gadon, Ta yi saurin tashi zaune, ta koma can ƙarshen gadon ta dunƙule jikinta waje ɗaya. Kallon ta ya dinga yi sai kuma ya zauna gefen gadon, murya a sanyaye ya ce “Ke zo nan..” Sake matse jikinta ta yi tana kuka a hankali, Ya sake kiran sunanta ta yi masa banza. Ganin yana nufota ya sanya ta sauka ta ɗaya side ɗin gadon. Ya dinga kallonta lokaci ɗaya ya haɗe ransa ya ce “Baki ji me nace bane? Zo nan!” Ya daka mata tsawa. Sosai ta firgita amma hakan bai sa taje inda yake ba, Ta fara tafiya hankali da niyyar fita daga dakin, Cikin yan sakanni ya tashi ya fizgota ta faɗa jikinsa. Kokawar kwace kanta ta dinga yi, sai dai sam ta kasa, saboda ba ƙarfinsu ɗaya ba. Ya matseta a ƙirjinsa yana watsa mata wani irin kallo ya ce “Kin nutsu ko sai na sake marin ki?” Ci gaba ta yi da kokawarta tana kuka kamar ranta zai fita, Komawa ya yi ya zauna har sannan bai saketa ba. Ya sanya hannunsa ya rufe mata baki sannan ya ce “Ki nutsu ki faɗa min me ya faru. Me ta yi miki? Akan me ki ka zageta...” Ya saki bakinta yana janyeta daga jikinsa, Tashi tsaye ta yi tana kallon sa cike da masifa ta ce “Bazan nutsun ba, kuma ba zan faɗa maka ba ɗin! ai sanda ka mareni baka tambayi me ya faru ba. Ko ce maka aka yi banida hankali? To wallahi ba zan yarda ba, kuma sai na tafi gidanmu. Wallahi sai na faɗawa Abbana!...”. Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan, da mamaki ya dinga kallonta dan tun da yake da ita bata taɓa faɗa masa magana irin haka ba. Ya miƙe tsaye yana kallonta ya ce “Ni? Ni ki ke cewa ba zaki nutsu ba? Ni ki ke yiwa ihu aka?” Ɗora hannayenta ta yi akan ƙugunta tana kallon sa idanunta babu alamar shakka ko tsoro ta ce “Eh kai ɗin!” Wani irin gudu ta saka ganin ya yo inda take, ta shige banɗaki ta murɗa key ɗin ta bar shi a jiki. Tsayawa ya yi a wajen yana kallon ƙofar toilet ɗin, Ya daɗe tsaye a wajen sai kuma ya juya ya fice daga ɗakin. Sai da ta tabbatar da ya tafi sannan ta buɗe ƙofar, Ta fito da gudu ta rufe ƙofar ɗakin ta saka key ta bar shi a jiki, sannan ta koma ta zauna gefen gadon ta kifa kanta akan cinyoyinta ta fashe da wani sabon kukan. Washegari da safe ta shirya cikin wasu riga da wando na jeans da t-shirt, ta ɗaura after dress akai ta ɗauki jakarta ta fito. A parlour ta same su suna breakfast, Ko kallon inda suke bata yi ba ta nufi ƙofar fita daga parlon, Zahra ta bita da kallo sai kuma ta taɓe baki. Tashi ya yi yana shirin barin wajen, Ta ajiye pork ɗin hannunta ta ce“A'a ina zaka je?” bai bata amsa ba ya juya yabi bayan Nanar, Zahra ta bisu da kallo sai kuma ta ɗauke kanta. Can ya hangota tana tafiya toward direction ɗin fita daga first gate ɗin, Yabi bayanta da sauri har ya kamota, Janyo hannunta ya yi yana kallonta fuska babu walwala ya ce “Ina zaki je?” Kallon sa ta yi, sai kuma ta janye hannunta daga nasa ta ce“makaranta.” daga haka ta juya ta ci gaba da tafiya. Abdusammad ya dinga kallonta cike da mamaki, can dai ya sake bin bayanta ta fizgota wannan karon babu alamar wasa ya ce “Daman haka ki ke tafiya makarantar? Kin fi abinci?" Tuni hawaye ya fara wanke fuskarta, Ta fizge hannunta ta ce“Ni bana so abincin naku. Ba zan ci ba, kuma bana son a kai ni makarantar, bana buƙatar taimakonka, ka rabu dani!” Ta ƙare maganar a fusace. Kasa cewa komai ya yi, ganin tana sake shirin barin wajen ya fizgota ta faɗa jikinsa, kuka ta saka tana dukansa. Ya matseta a jikinsa yana kallon ta ya ce “Ni ki ke yiwa rashin kunya ko? Zan yi maganin ki.” Daga haka ya fara tafiya da ita har suka fita daga gate ɗin, Kafin ya ƙarasa wajen parking space ɗin guards dake zazzaune suka taso suka nufo wajen, Ya miƙa ma drivern hannu ba tare da ya ce komai ba. Ya gane mai yake nufi dan haka ya miƙa masa key ɗin, Ya ƙarasa gaban wata Rolls-Royce fara ƙal ya danna key ɗin nan take ta yi ƙara. Passenger seat ya buɗe ya zurata sannan ya mayar ya rufe, Ya zagaya ɗaya side ya buɗe ya shiga. Sai da ya yi warming motar sannan ya yi reverse ya fice daga gidan. Har suka kusa zuwa Columbia babu wanda ya ce komai a cikinsu, Barin ma Nana data juya kanta gefe ɗaya tana kallon titi. Dan tun bayar wayar da suka yi da Anty Ramlah ta faɗa mata yanda zata yi bata sake ɗaga hankalinta ba. A gefen titi ya yi parking sannan ya sauka daga motar, ita dai inda yake bata kalla ba ballantana ta yi masa magana. After 10mins ya dawo hannunsa rike da leda, Ya ɗora mata kan cinyarta sannan ya yi wa motar key suka ci gaba da tafiya. Har suka ƙarasa makarantar Columbia ɗin, A parking space yayi parking, Ta buɗe motar tana ƙoƙarin fita taji ya ce “Make sure kin ci abinci, and when zaku tashi?” Bata kalleshi ba tana ƙoƙarin ɗaukan jakarta ta ce“2:00pm.” ta ce tana sauka daga motar, Da idanu kawai ya bita sai kuma ya girgiza kansa yana murmushi. Ita baya yarda ba fushi take yi, Sai da yaga ta nufi department ɗinsu sannan ya juya ya bar school ɗin. Nana na shiga class ta samu ƙawarta Surry wadda ita ma yar Nigeria ce take zaune da mijinta a new York ɗin, Ɗaga mata hannu ta yi Nana ta ɗan yi murmushi sannan ta ƙarasa inda take. Zama ta yi gefenta, Surry ta janye glasses ɗin dake idanunta, Fara ce tas kuma kyakkyawa ta sakar mata murmushi ta ce “Yau baki makara ba Nana? Ko Uncle ne ya kawo ki?” Ta yi tambayar cike da zolaya, dan kusan kullum tana bata labarin uncle yafi sau 20. Nana ta gyaɗa mata kai fuskarta babu walwala ta ce“Eh, na tashi da wuri ne yau.” Surry ta yi shiru tana nazartar yanayinta, can kuma ta ce“what's wrong Nana?” Bata ji abin da ta ce ba, saboda tunanin data fara. Surry ta taɓata ta ce “Nana...” Kallon ta ta yi tana murmushi, Surry ta sake cewa“meke damunki?” Girgiza mata kai Nana ta yi tana ƙoƙarin kawar da zancen ta ce“ba komai fa. Kawai bana jin daɗi ne, Dr Makh bai shigo ba?” Surry ta taɓe baki ta ce “Ina tambayar ki wani abun kina faɗan wani abun, Ƙarya ne ki ce babu abin da ke damunki Nana. Ba haka ki ka saba zuwa makaranta ba, and what's wrong with ur face? Wane ya mareki” sai a sannan Nana ta kai hannunta kan kuncinta, bata yi tunanin tabon bai baje ba dan bata kalli madubi ba ta fito. Surry ta kamo hannunta ta ce“Tell me meke damunki?” Sake girgiza kai Nana ta yi dan ko kaɗan bata son ta fitar da sirrinta, Ta buɗe jakarta ta ɗauko water bottle dinta ta buɗe ta sha ruwan sannan ta ce “Babu komai fa, kawai mun ɗan samu saɓani ne da kishiyata.” “Shi ne ta mareki?” Surry ta yi tambayar tana kallon ta, girgiza kai Nana ta yi, lokaci ɗaya hawaye ya fara zubowa kan fuskarta, cike da ƙunci da baƙin ciki ta ce “Uncle ne ya mareni...” Ta ƙare maganar kuka na kwace mata. Surry ta kalli ɗaiɗaikun student ɗin dake shigowa da basu shige mutun uku ba, sai ta matso kusa da ita sosai ta rike hannunta dake kan fuskarta ta ce “Saboda ita ya mareki? Me ki ka mata?” Girgiza kai Nana ta yi tana kuka ta ce “Ita ta fara zagina, ita ce ta fara tsokanata. amma kuma ita bai daketa ba, ni kaɗai ya daka, wallahi bana son auren nan, bana son zaman nan, gidanmu zan tafi. Ni ba zan koma ba!” Surry ta ɗan girgiza kanta tana kallon ta cike da tausayawa, zata bawa Nana kusan 3yrs dan ta fita wayo sosai duk da girmansu ɗaya. Ta sanya hannunta ta fara goge mata hawayen kafin ta ce “Idan ki ka bar gidan sai ki je ina?” Nana ta buɗe jakarta ta zaro passport ɗinta har da visanta ta ce“Gida zan tafi. Ba zan zauna ba, ni bana son auren, bana son uncle.” Surry ta yi shiru can kuma ta ce“Idan ki ka tafi kin bar mata gidan kenan? Kin yarda ta ci nasara ta koreki? Unbelievable, Ba haka ya kamata ki yi ba. Dole ki zauna a gidan dole ki nuna mata kece amarya kuma mijinta na sonki, Wallahi Nana uncle ɗin nan yana son ki, kuma kema kina sonsa. Kawai kuna wahalar da kan ku ne, Ki bari a tashi zan faɗa miki duk yanda zaki yi, da kansa zai dawo ya baki haƙuri.” Nana ta sake goge hawayenta sannan ta ce“Baya sona wallahi, uncle baya sona. Alfarma ya yimin nida iyayena ya aureni, ba dan yana sona ba. Kin taɓa ganin amaryar da mijinta bai damu da ita ba? Ko sanda aka kaini gidansa babu ruwansa dani, baya kwana a ɗakina, a haka har kwanana ya ƙare. Kuma koda muka zo nan bai taɓa kwana a ɗakina ba, sai dai duk ranar da nake da girki naje ɗakinsa na kwanta, ita kuma duk ranar kwananta har daƙinta zai bita. Gaba ɗaya baya sona, idan nayi waya da sisters ɗina suna bani labarin yanda suke zaune da sauran yayyenmu, kowacce mijinta na sonta kuma yana kulawa da ita, duk da ba auren soyayya bane. amma ni a nan....” Ta yi shiru saboda kukan da yaci ƙarfinta, Surayyah da taji tausayinta ya rufeta ta jawota jikinta, Nana ta ci gaba da kuka kamar ranta zai fita. **** Nigeria. Aunty Khadijah ce zaune bayan ta idar da sallar magriba, wayarta dake kan gado ta fara ringing, zare hijabin ta yi sannan ta hau kan gadon ta janyo wayar. Sabuwar lamba ta gani, dan haka ta ɗaga ta ce “Assalamu alaikum.” Daha ɗaya ɓangaren ya gyara tsaiwarsa ya ce “wa'aiki assalam da Khadijah, kina lafiya.” sosai ta ɗau muryarsa, amma madadin ta fusata sai ta samu kanta da yin murmushi ta ce “Ina nan kalau Alhamdulillah.” Ya jinjina kai sannan ya ce “Daman ina ƙofar gidanku ne, nazo mu ɗan zanta.” Aunty Khadijah ta ce“tom gani nan” daga haka ta kashe wayar, tashi ta yi tana murmushin da bata san dalilin sa ba, Ta ƙarasa press ɗinta ta fiddo wata dakkakiyar shadda maroon colour sai sheƙi take. Ta zare kayan jikinta ta saka shaddar ta feshe jikinta da turaruka kala-kala, kwalliya sosai ta yiwa fuskarta sannan ta ɗauki wayarta bayan ta yafa mayafi ta fito daga ɗakin. Umma na zaune tana lazumin bayan magriba taga Aunty Khadijah ta fito. Ta dinga kallon ta da mamaki ta ce “Khadijah ina kuma zaki je?” Murmushi Anty Khadijah ta yi ta ce“daman baƙo nayi Umma, shi ne zan je.” Umma ta jinjina kanta ta ce“to a dawo lafiya.” amin ta ce sannan ta juya ta fice tana murmushi, Amal dake zaune kan kujera tana danna waya ta kalleta sai kuma ta taɓe baki. Tsaye ta same shi jikin gate ɗin gidan, ta ƙarasa tana kallon sa saboda wadataccen hasken da yake wajen. Shima kallonta yake yana murmushi, Ta ɗan durƙusa ta ce “Ina yini?” Malam Garba ya yi murmushi yana gyara rawanin kansa ya ce“lafiya lau Hajiya Khadijatul kubra. Ya su Mama?” Anty Khadijah ta sake murmushi ta ce“suna nan kalau, ta ce ma na gaishe ka.” Malam Garba ya jinjina kansa ya ce“Allah sarki, ina amsawa sosai da sosai.” shiru wajen ya ɗauka, can kuma ya ce“daman fa zuwa nayi mu ɗan gaisa yauwa, naga kwana biyu kin janye ƙafa” Anty Khadijah ta girgiza kanta ta ce“Ayyah abubuwane suka min yawa. Na gode amma” Jinjina kansa ya yi ya ce“Ba komai. Aaa ba komai, bari na koma” “Da wuri haka?” Ta yi maganar tana murmushi, gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh gara naje. Sai kuma wani lokacin” Anty Khadijah ta ce“To na gode.” Tana tsaye har ya bar wajen sannan ta koma cikin gidan. **** Suna tsaye da Surry har mijinta yazo ɗaukanta. Ta kalli Nana wadda ke mata hira ta ce“Ga Albee ya zo, zan tafi. Kin dai ji duk abin da na faɗa miki ko?” gyaɗa mata kai Nana ta yi ta ce“tom sai monday.” Surry ta yi murmushi sannan ta bar wajen, Basu daɗe da tafiya ba motarsa ta yi parking. Sarai ta gan shi amma ta ɗauke kanta, Gajiya ya yi da jiranta ya fito daga motar, sanye yake da wasu English wears na Gucci masu kyau da taushi, wanda suka dace da weathern damunar da ake ciki, Gashin kansa ya zubo gefen kafaɗunsa dan bai daure shi ba. Har gabanta ya ƙaraso yana kallonta ya ce “Sai na zo nace ki tawo?” Kallon sa ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta tace“ban ganka bane.” Shiru ya yi yana kallonta dan ya san ƙarya take ta ganshi, Ya ce“to muje.” Ya yi maganar yana karɓar jakar hannunta, ita dai bata ce komai ba ta yi gaba, ta shiga motar tana jiransa. Bayan ya shiga ya ajiye jakar a jikinsa yana kallon ta fuskarsa a sake ya ce “Kin daina fushin?” Kallon sa ta yi, kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“Fushi kuma?” Ɗauke kansa ya yi ganin tana shirin raina masa hankali, Ita ma ta mai da kanta ga jikin glass ɗin ƙofar tana kallon garin wanda ya ɗan yi duhu kamar hadari na kwance. Har suka je gida babu wanda ya yi magana, yana gama parking bata jira shi ba ta sauka daga motar ta nufi cikin gidan. Da idanu kawai ya bita sai kuma ya zare key ɗin ya fito hannunsa riƙe da school bag ɗin tata ya nufi cikin gidan shima. Ko a parlour bai sameta ba, dan haka ya nufi apartment ɗinsa kai tsaye. Da daddare wajen ƙarfe 10:00 na dare ya fito ganin har sannan bata zo ba, kuma ranar kwananta ne. Kai tsaye apartment ɗinta ya nufa, a buɗe ya samu ƙofar ya shiga yana kallonta. Zaune take tsakiyar gadonta tana danna system ɗin dake gabanta, Ya zauna gefen gadon ya ce “Nana baki ga dare ya yi bane?” “Nagani.” Ta ce ba tare da ta ɗago kanta ba. Abdusammad ya ɗan yi shiru ganin ko kallon sa bata yi ba, bai taɓa ganin ta yi masa haka ba. Hasali ma bai taɓa ganinta in a serious mood irin haka ba, Ya numfasa kafin ya ce “Ina jiran ki naji shiru, tashi mu tafi.” sai a sannan ta ɗago ta kalle shi. Fuskarta a haɗe babu alamar wasa ko kuma yarintar daya saba gani, Bakinta sai sheƙi yake dalilin lip gloss ɗin data saka, wanda duk cikin shawarwarin da Surryn ta bata ne. Lokaci ɗaya yaji jikinsa ya yi sanyi, Ta ɗauke kanta ganin irin kallon da yake matan. Rufe system ɗin ta yi ta sauko daga kan gadon, Riga ce mara nauyi a jikinta, wadda ta tsaya iya gwuiwarta, fararen ƙafafunta sun fito sosai. Ajiye laptop ɗin ta yi a kan drawer ta juyo tana shirin barin wajen, Tsaye ta gan shi a gabanta. Sai da ƙirjinta ya buga, amma ta dake ta haɗe fuska babu alamar wasa ta ce “uncle ka matsa.” Janyota jikinsa ya yi ya fara ƙoƙarin kai bakinsa ga nata, ta sanya hannayenta duk biyun ta ture shi tana cewa“Ni bana son irin haka uncle. Ka daina min wallahi” Ganin yanda ta yi maganar ya sanya shi yin murmushi, kamar wanda ya tuna wani abu sai ya saketa ya ce“shikenan zo mu tafi” Barin wajen ta yi sannan ta ce“to muje.” daga haka ta yi gaba yana biye da ita a baya. Sai da suka je tsakiyar parlour sannan ta ja ta tsaya. Ya juyo yana kallon ta yace “Mene ne?” Ɗan kwaɓe fuska ta yi ta ce“Na manta wayata.” Ya ce“to zaki je ki dauko ne?” gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh ina zuwa.” daga haka ta juya ta koma ɗakin, Yana nan tsaye har bayan mintuna biyar amma bata dawo ba. Ya juya yana kallon ƙofar sai kuma ya ƙarasa wajen, Sai dai me? Yana murɗawa ya jita a rufe, Ya ɗan bubbuga ƙofar ya ce “Nana! Nana!” Shiru babu amsa, tana zaune gefen gadon tana jinsa. Ya dinga kiran sunanta ta yi banza, har ya gaji ya bar wajen. Ta koma ta yi kwanciyarta ta ja duvet ta rufe jikinta, hannunta ta sanya ta kashe side lamp ɗin dake gefen gadon, nan take duhu ya mayaye ɗakin, Ta lumshe idanunta nan da na bacci ya ɗauketa. 08106608363 Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 57. Tun daga wannan ranar kuma bata sake bari wani abu ya haɗa su ba, da safe idan ta tashi bata tsayawa jiransa take tafiyarta makaranta. Haka idan ta dawo ko zama a parlourn bata yi ballantana ya ganta. Gaba ɗaya ta zama kamar ba ita ba, koda ya shigo daƙinta bata yarda ta kula shi daga Eh sai A'a, duk abin da Surry take faɗa mata shi take yi, sosai kuma hakan ya dameshi. Dan yanzu ta tashi daga Nanar daya sani yarinya mai rigimar banza, ta zama wata daban wadda magana ma bata dameta ba. Idan kaji tana dariya to a waya ne ita da Amma ko kuma su Maimoon, Ɓangaren Zahra kuwa abun sai a hankali, yau a zauna lafiya gobe abu yaci tura. Kwata-kwata bata wani ganinsa da mutunci, ganin haka ya sanya shima ya tarkatasu ya watsar da lamarinsu gefe, idan ya shiga apartment ɗin kowacce da safe baya sake nemansu sai idan wadda take da kwana taje ɗakinsa, a haka har kusan wata guda ya shuɗe. Ranar wata Juma'a around 9pm ya shigo ɗakin yana sanye da kayan bacci, Zahra na zaune gefen gado tana kitsema Noor dake bacci kanta. Ya ƙaraso ciki ya tsaya a bakin gadon yana kallon su, sau ɗaya ta kalle shi ta ɗauke kai, Ya numfasa sannan ya nemi gefen gadon ya zauna. Har ta gama mata kitson bai ce komai ba, Ta ɗauketa ta fita da ita daga ɗakin, After some minutes ta dawo ta zauna gefen gadon tana shirin kwanciya taji ya ce “Zahra ina son magana dake.” Fasa kwanciyar ta yi ta koma ta zauna tana kallon sa babu yabo babu fallasa ta ce“To ina ji.” “Akwai abin da nake miki ba daidai bane da har ki ka sauya haka? Ko akwai abin da na rage ki dashi da ki ka koma kaurace min? Did i done something wrong to you?” Abdusammad ya jera mata tambayoyin yana kallon ta a nutse. Wani murmushin takaici Zahra ta yi ta ce“Au tambaya ka ke doctor? Baka sani ba kenan? To bari kaji ba wani abun bane kawai na gaji da zama da kai ne! Wallahi na gaji. Bana son zaman nan” Da mamaki yake kallonta, Can kuma ya girgiza kansa ya ce“Zahra ƙarya ki ke wallahi, ƙarya ne ki ce kin gaji da zama dani. Cause i know you love me, kamar yanda nake sonki, ke kan ki shaida ce na aureki ne saboda ina son ki. Na bijirewa dangina saboda ke, dan Allah Zahra kada ki ce zaki bar ni. Kada ki ce zaki gujeni” Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin rungumeta, Ture shi ta yi tana watsa masa wani kallo ta ce “Kada ka sake kuskuren taɓa ni, bana so nace maka.” Miƙewa tsaye ya yi wannan karon a fusace ya ce“idan na taɓa ki me zaki yi? Ko kin isa ki hanani na taɓa ki ne?” Tashi tsayen itama ta yi tana kallon sa ta ce“Ai ko ba zaka taɓa ni ba, kuma idan ka manta bari na tuna maka. Yau ba kwanana bane, sai kaje wajen ita yarinyar daka aura ka kwanta da ita amma wlh ba dai ni Zahra ba!” Ta ƙare maganar tana zabga masa wata uwar harara. Gyaɗa kai Abdusammad ya dinga yi cike da mamakinta ya ce “Oh haka ki ka ce?” Ta gyaɗa masa kai tana faɗin“Eh haka na faɗa!" “To bari ki ji, ke baki isa ki hanani nayi abin da nayi niyya ba. Idan naso yin abu ban ga wadda zata hanani ba, kuma da ki ke maganar Nana, ita yarinya ce ƙarama. Bata san komai ba, dan haka ni ba azzalumi bane da zan cutar da ƴar mutane. Amma ke dole ne nayi yanda nake so dake!” Ƙoƙarin magana take taji ya hankaɗata, Duk yanda Zahra ta so kwatar kanta kasawa ta yi dan ba ƙaramin ƙarfi ya saka mata ba, a dole ta rabu dashi. Bayan ya gama abin da ya yi niyya ya tashi ya fice daga ɗakin ya bar ta a wajen, Ta dinga kuka saboda muguntar da ya yi mata, Baƙin cikin kalmar daya faɗa ta sanyata sake rushewa da kuka. Tana cije laɓɓanta da ƙarfi. Koda ya koma ɗakinsa bai tarar da Nana ba kuma daman ya san ba zata taɓa zuwa ba, koda kuma yaje kiranta ba zata biyo shi ba,dan haka ya faɗa banɗaki ya yi wanka ya fito ya sauya kaya ya yi kwanciyarsa. Washegari da safe ya kama Saturday, ranar Nana bata da lecture dan haka ko ƙasa bata sakko ba, tana daƙinta a kwance saboda sanyin da ake. Zahra na zaune kan sofa tana tunanin yanda zata yi, ba zata taɓa bari abin da ya ya mata ya tashi a banza ba. Dan haka ta miƙe ta huce sama, Daƙinta ta shiga ta zauna gefen gadon tana sake maimaita maganar daya faɗa mata, Can dai ta miƙe ta ɗauki veil ɗinta ta yafa sannan ta fito, bata ko tambayeshi ba ta fice daga gidan, After 30mins ta dawo da wata ƙaramar leda. Shiryawa ta yi cikin wata doguwar riga ta abaya nude colour, Ta yi simple make-up a fuskarta sannan ta nufi ɗakin Noor, tana zaune da maid ɗin dake kula da ita suna hira ta shigo. Ta taso da gudu ta rungumeta ta ce “Ummi" Murmushi Zahra ta yi ta ɗauketa ta ce“Muje ki raka ni unguwa.” “Ummi da Abbie zamu je?" Girgiza mata kai Zahra ta yi ta ce“Abbie na gida za'a bar shi ya huta, dani dake zamu je.” Tura baki Noor ta yi ta ce“ni na fison har da Abbie” Zahra ta ja kumatunta ta ce“Eh ai gobe dashi zamu je, yau amma mu kaɗai zamu, har da gidansu Afeefa.” washe baki ta yi tana dariya ta ce “Da gaske Ummi?” Zahra ta gyaɗa mata kai bayan ta ajiyeta kan kujera. Ta ɗauki ledar data shigo da ita a gefen gadon sannan ta juya ta fita. Kitchen ɗin saman ta shiga ta haɗa coffee kamar yanda ta san zai masa, ta haɗa da hamburger guda biyu a plate. Buɗe ledar ta yi ta dauko wani tablet ta ɓalli guda huɗu ta zuba a coffee ɗin, ta ɗan jira har ya narke sannan ta ɗora a tray ta fita.. Side ɗinsa ta nufa ta murɗa ƙofar parlourn ta shiga, Zaune ta hangeshi kan sofa yana operating system ɗin dake gabansa. Ta yi sallama sannan ta ƙarasa ciki, Ya ɗago fuskarsa ya ɗan kalleta. Murmushi ta sakar masa bayan ta ajiye tray ɗin kan table ɗin gabansa ta ce “Ina kwana?” A sanyaye ya amsa, Zahra ta ɗan sunkuyar da kanta ba tare da ta sake cewa komai ba. Shiru parlourn ya ɗauka, Ya ƙarasa abin da yake a system ɗin sannan ya rufe yana kallon ta ya ce “Lafiya dai?” Saurin girgiza kanta ta yi ta ce“babu komai, kawai daman ina son zan ɗan fita ne” wani kallon sheƙeke ya yi mata kafin ya ce “Daman idan zaki fita tambayata ki ke? Bana ce ki dinga tafiyarki ba?” Murmushi ta yi ta ce“Tom shikenan sai na dawo.” “Allah ya tsare” Ya ce yana jan mug ɗin dake saman tray ɗin. Miƙewa ta yi tace amin sannan ta juya ta fita tana ɗan leƙensa , Murmushi ya yi bayan ya yi sipping coffee ɗin ya ce “Ko na zo na raka ki?” Girgiza masa kai ta yi, sannan ta rufe ƙofar dakin. Ya ɗan yi murmushi shima kafin ya ci gaba da shan coffee ɗin. Zahra na fita ta koma daƙinta ta zurawa Noor rigar sanyi sannan ta ɗauki jakarta da wayarta suka bar gidan a gaggauce. Yana gama shan coffee ɗin ya tashi ya shige ɗakinsa, Toilet ya faɗa ya wanke bakinsa sannan ya fito ya yi kwanciyarsa. **** Aunty Khadijah ce zaune kusa da Umma hawaye na zubowa kan fuskarta, Umma ta yi shiru tana kallon ta, can kuma ta kalli Kaddu ta ce“To yanzu mene abun yi?” girgiza kai Kaddu ta yi ta ce“wallahi Umma nima bana ce ba, Khadijah ta yi nisa a cikin sonsa, tun ina ɗaukan abun wasa har ya fara bani tsoro.” Umma ta numfasa tana kallon Anty Khadijah da har sannan bata daina kuka ba ta ce“Khadijah ke kin yarda zaki aure shi?” saurin gyaɗa mata kai ta yi kafin ta ce“Eh umma, wallahi na yarda. Ina son Garba, zan aure shi, daman ba so ki ke nayi aure ba to wallahi zan aure shi!” Jin jina kai Umma ta yi ta ce“To zan yiwa kawunku magana, ki ce masa ya turo magabatansa sai a yi maganar aure.” Aunty Khadijah ta sauke ajiyar zuciya ta shiga goge hawayenta ta ce“Nagode sosai Umma, bari naje na faɗa masa yanzu.” Ta miƙe ba tare da ta jira abin da zasu ce ba ta nufi sama, Da idanu duk suka bita, Kaddu ta girgiza kai ta ce “Umma ni wallahi bana son auren nan.” Numfasawa Umma ta yi jiki a sanyaye ta ce“To ya za'a yi Kaddu? Tun da har taga tana sonsa ai babu yanda za'a yi da ita. Khadijah ba yarinya ba ce, ba sabon aure bane balle ace iyaye keda ikon zaɓa mata wanda ya dace da ita. Tana da ikon zabar wanda take so ta zauna dashi” Kaddu ta jinjina kanta jiki a sanyaye ta ce“haka ne, to Allah yasa haka ne yafi alkhairi.” Umma ta numfasa sannan ta ce“Amin Kaddu. Kema ya kamata ki fito da miji ki yi auren ki” sunkuyar da kai ta yi tana murmushi ta ce“ai nima in sha Allah nan bada jimawa ba zan sake auren” Umma ta ce“To Allah yasa, dan zaman haka bashi da wani fa'ida” Kaddu dai bata ce komai ba kanta a ƙasa. **** Amma ce zaune kan sofa tana kallon Haule dake faman cin gyaɗa, Ta girgiza kanta ta ce“Yanzu gyadar ce zata miki abinci Haule?” kallon ta Haule ta yi, sai kuma ta ce“Amma bana jin yunwa fa. Ɗazu naci abinci wajen Hajiya Babba” Amma ta ce“To shikenan, kin je duba Safwan ɗin?” gyaɗa mata kai ta yi tana ajiye ɓawon gyaɗar kan table ta ce“Eh mun je dasu Maimoon, da sauƙi jikin nasa, dan ma ya gane mu” Amma ta tashi tana ƙoƙarin shiga kitchen dan duba girkin da take ta ce“To Alhamdulillah, Allah ya ƙara sauƙi, mu ma an jima zamu koma.” “Zan biku Amma” Ta ce tana marairaice fuska, Harararta Amma ta yi ta ce“ɗazu kin je shi ne zaki sake bin mu? To ba zaki ba.” ta nufi kitchen ba tare da ta jira amsarta ba, Shiru Haule ta yi tana jin babu daɗi a ranta. Har ga Allah tana son sake zuwa ta gan shi, taga wane hali yake, amma ta san tunda Amma ta ce haka ba zata bari taje ba. Tashi ta yi bayan ta kwashe ɓawon gyaɗar a faranti ta nufi waje, a dustbin ɗin dake balcony ta zuba sannan ta dawo parlourn ta ajiye plate ɗin ta nufi ɗakin Nana, tana zuwa ta yi kwanciyarta akan gado tana lumshe ido, nan da nan kuma bacci ya ɗauketa. **** New York, Lower East side. Zahra ce zaune kan sofa tana kallon wata baƙar mata wadda ba zata shige shekarunta ba, Murmushi ta yi ta ce“Ke Zahra, to me yasa zaki yi haka?” harararta ta yi ta ce“Lailah ba zaki gane ba, kin san me ya ce min kuwa jiya? Ita yarinya ce ƙarama, ba zai iya yi mata komai ba saboda yana tausayinta sai dai idan ta ƙara girma, kenan ni ce banza wadda ban san ciwon kaina ba? Ni zai dinga yin yanda ya so dani ita kuma ya adanata.” Murmushi Lailah ta yi ta ce“Gaskiya dai bai kyauta ba, amma kema da baki yi haka ba. Tun da yarinyar ce da gaske, Doctor yana da shekaru ba lallai ta iya ɗauke buƙatarsa ba, ko haka kawai ballantana kin bashi pills gaskiya zai iya cutar da ita.” taɓe baki Zahra ta yi tana kallon Noor da Afeefa dake can ɗaya parlourn suna wasa ta ce“ai so nake ya cutar da itan, yanda iyayenta zasu yi dana sanin bashi aurenta, wallahi ba zan iya zuba ido ina gani yarinya ƙarama ta mulkeni ba, Dole ne na ɗauki mataki akanta, yanda nan gaba idan an ce ya auro wata shi ma ba zai yi gigin yin haka ba.” Lailah ta ce“mazan namu ne sai a hankali, Ban da neman magana mai zai yi da wannan ƙaramar yarinyar? Ni fa ina gano sanda ki ke zuwa da ita Columbia time ɗin baku daɗe da aure ba ki ka ce ƙanwar mijin ki ce, amma ace har ta yi girman da zai aureta? Maza! Maza!” Cike da ɓacin rai Zahra ta ce“kin gane abin da ke ɓata min rai kenan. Ni da wata aka aura masa ba zan damu ba, amma ya za'a yi ya auri Nana ina raye? Ai idan ma na bari suka zauna lafiya wallahi Allah ba zai bar ni ba.” tuntsirewa da dariya Lailah ta yi kafin ta ce“Ke ƙawata kin iya masifa kema” Zahra ta yi kwafa ta ce“ai in dai mutum ya taboni anan zai gane nima ba haƙuri gareni ba. Ni za'a ci amana?”.... **** Nana na kwance a parlourn ta sai juyi take saboda yunwar data dameta. Ta ɗan ja tsaki sannan ta tashi zaune tana jan hular dake ajiye a saitin kanta ta saka akanta wanda yake a gyare. Tashi tsaye ta yi tana gyara wandon jikinta, wasu up and down English wears ne brown colour a jikinta, ta nufi kitchen ɗin dake parlourn tana tafe kamar iska zai hureta. Tsayawa ta yi a tsakiyar ƙaton kitchen ɗin tana kalle-kalle, Can dai ta nufi store ɗin dake ciki dan duba abin da zata dafa. Kwalin indomie ta buɗe ta ɗauki guda ɗaya sannan ta dawo kitchen ɗin, Ta kunna gas ta ɗaura ruwa cikin ƙaramin tukunya. Dubawa inda take ajiye kwai ta yi taga babu, ta ja dogon tsaki tana dire ƙafarta a ƙasa cike da shagwaɓa ta ce “Yanzu sai naje ƙasa..” Ta mai da murfin tukunyar ta rufe sannan ta rage gas ɗin ta fice daga kitchen ɗin. **** Abdusammad na zaune gefen gadonsa, tun bayan daya tashi daga bacci yaji mararsa ta ɗaure, Rabonsa da jin irin wannan yanayin tun kafin ya yi aurensa na farko. Gajiya ya yi da zama ganin ciwo na neman illata rayuwarsa ya sanya shi miƙewa, kajeran wando ne kawai a jikinsa, dan tuni ya cire rigar saboda zafin da ya yi masa yawa. Faffaɗan ƙirjinsa ya bayyana wanda gargasa ta kwanta akan farar fatarsa ta yi lub gwanin sha'awa, Ya zura slippers ɗin dake wajen sannan ya nufi waje da sauri. Kai tsaye kitchen ɗin dake main parlon ya nufa dan ya san nan ne zai samu abin da yake so, Koda ya shiga bai sameta a ciki ba, ya ƙarasa ya ɗauki mug sannan ya duba inda ake ajiye kayan vegetables ya dauki lemon tsami guda biyu sannan ya zuba tea a cikin mug ɗin, Ya yanka lemon tsamin guda biyu ya zuba a ciki sannan ya fice daga kitchen ɗin, A parlourn ya zauna ya shanye tas sannan ya ajiye mug ɗin yana sauke numfashi. Amma madadin ya samu sauƙin abin da yake ji, sai yaji kamar sake tunzura wutar abin da yake ji din ya yi. Abdusammad ya runtse idanunsa, tun yana iya dauriya har ya fara kasawa. Ya zamo daga kan kujerar ya durƙushe a wajen. Nana ta shigo kitchen ɗin ta kofar baya hannunta riƙe da fresh mangoes da alama a waje ta ciro, Ta ɗauki kwan da ta ajiye a cikin bowl sannan ta fito daga kitchen ɗin. Da idanu ta dinga kallon sa, ganin yanda ya durƙushe a wajen yana nishi da kyar, Kamar ta ƙarasa taji me ya same shi, sai kuma ta nufi sama abin ta da sauri. Kitchen ɗinta ta tashi ta samu ruwan har ya tafasa, ta wanke kwan guda biyu ta zura a ciki sannan ta fara yanka albasa, after some minutes ta ɓare indomien ta zuba akai ta saka seasoning da spices, ta ja kujera ta zauna ta yi shiru tana jiranta ta dahu. Tunaninsa ta dinga yi bata taɓa ganin sa a haka ba, to ko bashi da lafiya? Taji zuciyarta ta tambayeta. Ta girgiza kanta tana kawar da zancen, bayan ta sauke indomienta ta zuba acikin wani plate mai kyau, ta ɓare kwan ta ɗora akai ta saka pork sannan ta fito parlon. Ajiyewa ta yi akan table ta koma kitchen ɗin ta dauko drinks ta dawo, Ta zauna ta fara juya cokalin cikin taliyar, sai dai ko loma ɗaya ta kasa kai wa bakinta, Gaba ɗaya taji hankalinta bai kwanta ba. Ta tabbata idan da ita ce bata da lafiya ba zai taɓa barinta ya shige ba, ta ajiye pork ɗin ta tashi bayan ta yanke shawarar zuwa taji me ya same shi. A parlourn ta same shi har sannan, Ta ƙarasa da sauri ta durƙusa a gabansa ta dafa shi cikin sanyin murya ta ce “Uncle! Uncle!” Rabon da ta kira sunansa har ta manta, Ya ɗan saki ajiyar zuciya dalilin riƙe shin da ta yi, Bai iya ɗago kansa ba, Jikinsa sai wani irin kyarma yake. Tashi hankalin Nana ya yi, Ta fara girgiza kanta ta riƙe hannunsa ta ce “uncle ka tashi, dan Allah ka tashi. Ba zan sake ba kaji uncle, ai ina kula ka yanzu ka tashi” Ta dinga kuka tana ƙoƙarin ɗago shi, Hannunta ta ji ya riƙe cikin nasa wanda ke rawa, Ya ɗan girgiza kansa murya can ƙasa mai nuni da zallar azabar da yake sha ya ce “Nana tafi daga nan!” Girgiza kanta ta yi tana kuka ta ce “Uncle ba zan sake ba, ba zan ƙara ba. Ka tashi kaji... Ka tashi muje asibiti...” Kasa cewa komai ya yi, saboda tsananin azabar da yake ciki, ko sanda yake saurayi bai taɓa shiga irin wannan yanayin ba sai sau ɗaya. Wanda har sai da ya kwanta a asibiti, Ya matse hannunta dake cikin nasa cikin ya ce “Nana ki bar nan na ce!” Madadin ta fuskanci abin da yake nufi, sai kawai ta shige jikinsa tana sakin wani marayan kuka, Ta riƙe shi ƙam tana girgiza kanta ta ce “Uncle ka yafe min, ba zan sake ba. Wallahi ba zan ƙara bata maka rai ba, dan Allah kada ka mutu ka barni. Kada ka bar ni Uncle, tsoro nake ji...” Ta fashe da kuka tana sake ɓoye kanta a ƙirjinsa, Wani irin nunfashi Abdusammad ke saukewa, Ƙoƙarin janyeta yake daga jikinsa amma taƙi bari, shi kuma bashi da wani kwari da zai gwada mata ƙarfi. Ya ɗora kansa a bayanta wasu irin hawaye na zubowa daga cikin idanunsa, Ɗumin ruwan da taji a bayanta ya sanyata ɗago kanta, Ganin hawaye a cikin idanun uncle ɗinta ya ƙara tada mata da hankali, ta dinga girgiza kanta tana kuka ta ce “Wallahi ba zan kuma ba uncle! Ba zan sake ba. Ka faɗa min me ka ke so? Ko na dafa maka abinci uncle? Zaka sha ruwa?” Shiru Abdusammad ya yi mata yana jan numfashi, Nana ta rasa yanda zata yi ta ganar dashi cewa ta daina abin da take masa. Ta daina share shi, ta daina yi masa rashin kunya. Ta saki sabon kuka tana kallon jajayen lips ɗinsa wanda suke a jiƙe da hawaye. A hankali ta sake matsawa kusa da shi, Ta kai bakinta kan nasa ta sauke masa wani light kiss, wani irin jan numfashi Abdusammad ya yi, Tana ƙoƙarin ɗauke bakinta taji ya riƙe gam, Nana ta ɗan kalleshi tana hawaye, Lokaci ɗaya taji ya fizgota ya sake maƙaleta a jikinsa, Ya riƙe fuskarta cikin tafukan hannunsa, Cikin wani irin yanayi dake fizgarsa ya zura bakinsa cikin nata ya fara sauke mata wasu azababbun kisses ta ko ina. Shiɗewa Nana ta kusa yi, ganin yana ƙoƙarin tsinke mata baki ya sanyata yunƙurawa zata bar wajen, Sai dai ga mamakinta sai taga ya sake mata ƙarfinsa ya kwantar da ita a kan lallausan rug dake malale a wajen, sannan ya bita ya danne yana ci gaba da kissing ɗinta as if his life depends on it. 08106608363 Nanameera. *🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 58. Ƙoƙarin janyewa numfashinta ya fara yi dalilin abin da yake mata, Ya yunƙura dakyar ya ɗagata yana sauke numfashi. Ɗaukanta ya yi kamar yar baby ya nufi apartment ɗinsa da ita, Ban da kuka babu abin da Nana ke yi. Akan royal bed ɗin dake ɗakin ya kwantar da ita, Sannan ya hau gadon yana ƙoƙarin ci gaba da abin da ya fara, Ta yi saurin ja da baya tana kuka kamar ranta zai fita. Hannunsa ya sanyata ya jawota jikinsa ta saki ƙara tana ƙoƙarin kwace hannun nata, Ko saurarenta Abdusammad bai yi ba ya sake haɗe bakinsu waje ɗaya yana wani irin tsotsa kamar zai tsinke bakin, Tun tana ƙoƙarin ture shi har sai da jikinta ya fara saki. Ta kasa koda motsi sai hawaye dake zubowa daga idanunta, gaba ɗaya kamar ba uncle ɗinta ba. Sam baya lura da abin da yake, yama mance wacece a gabansa, Hannunsa da taji yana ƙoƙarin farka rigar jikinta ya sanyata zabura tana sake sakin wani kukan. So take ta roƙeshi akan ya bar abin da yake, amma sam bata da kuzarin yin haka, Ya farke rigar ƙasa, har sannan bakinsa na cikin nata, Hannayenta biyu ta saka ta riƙe shi gam gudun kada ya ganar mata jiki. Ya ɗago fuskarta yana ci gaba da kissing dinta. Ɗaya hannunsa ya sanya ya ɓalle bra dake jikinta, ta saki wani irin numfashi tana sake ƙanƙameshi. A hankali ya zare bakinsa daga nasa yana sauke numfashi, Ya gyara mata kwanciyar ta koma ƙasa shi kuma a sama, Hannunsa ya kai kan tsayayyun breast ɗinta farare sol dasu, Hannunsa na rawa ya ɗora akansu. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke saboda laushin da yaji, ya kai bakinsa kai ya fara tsotsa a hankali. Nana ta saki wani irin marayan kuka tana ƙoƙarin janye jikinta, Ya sake janyota jikinsa yana ci gaba da abin da yake. Tun tana fahimtar abubuwan da yake yi har ta fara daina gane komai, Gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta ta yi hijira daga kanta. Ta gagara koda motsa hannunta, Yanda yake so haka ya dinga sarrafata. Daga ƙarshe ya fara karanto addu'ar saduwa da iyali, A sannan Nana ta gane da ba komai yake ba, A sannan ta gane ana shan wata wahala wadda babu kamarta, a sannan ta gane duk abin da ake faɗa mata labari ne kawai ake ba. Iyaka azaba babu irin wadda bata sha ba a wajen Abdusammad, Musamman daya kasance yin komai yake ba tare da lura ba. Tun idanunta na rufewa yana buɗewa har sai da suka rufe gaba ɗaya ta sume a wajen... **** Around 5:00 na yamma ya murɗa handle ɗin ɗakin ya shigo hannunsa riƙe da ƙaramin tray, Kwance ya sameta inda ya barta gaba ɗaya jikinta a rufe yake da duvet. Ya ajiye tray ɗin kan table sannan ya ƙarasa ya hau gadon ya zauna, Hannunsa ya sanya ya jawota jikinsa. Zazzaɓi ne bana wasa ba a jikinta, Ban da numfarfashi babu abin da take. Ya rungumeta a ƙirjinsa ba tare da ya ce komai ba, Ya rasa wane irin hali yake ciki, farin ciki ne ko kuma damuwa ce? Shi kansa bai ji dadin abin da ya yiwa yarinyar ba, domin bashi da wannan tsarin akanta. Ba yanzu ya shirya maidata cikakkiyar matar aurensa ba, Sai dai tunawa da abin da ya samu yake sanya zuciyarsa wani irin farin ciki mara misaaltuwa. Tabbas ya samu abin da kowane namiji ke fatan samu a wajen ɗiya mace, Koda wasa bai yi tunanin ƴar rainon tasa ta kai haka ba. Dan da ya sani da tun ranar da aka kawota gidansa ba zai barta ta kwana haka ba, Tun bayan ɗazu murmushi ya kasa kaura daga kan fuskarsa, sai nishaɗi yake. Ko sanda yaci amarcinsa na farko bai kai masa wannan lokacin tsada ba, domin ba iri ɗaya bane. Shi kansa ya yarda Nanansa da ban take, ƴar ƙaramar yarinyar da yake rainawa ta iya ɗauke buƙatarsa. Duk da wahalar data bashi, dan ko magana bata yi ba tun da abun da faru. Sake shigar da ita jikinsa ya yi ya ɗora kansa a wuyanta yana shaƙar daddaɗan ƙamshinta, Ya sauke ajiyar zuciya yana shafa gashin kanta. Sun daɗe a haka kafin ya ɗagota yana kallon idanunta dake rufe ya ce “Nana zo ki ci abinci kin ji.” Wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyarceta dalilin muryarsa da taji, Ta ci gaba da kuka a hankali dan ko muryarta ba'a ji, Girgiza kansa ya yi cikin taushin murya ya ce “Ya isa kin ji. Uncle ba zai ƙara ba, ki yafe ma uncle ɗin ki” Ai kamar ya tura ta haka ta sake fashewa da wani sabon kukan, Ta fara kiciniyar kwace jikinta. Lokaci ɗaya kuma ta faɗa jikinsa dan ko motsi idan ta yi azaba yake zamar mata, Tausayi ta bashi dan shi kansa ya san bai mata da sauƙi ba. Ya dinga shafa kanta yana jin saukar hawayenta akan ƙirjinsa. Bayan kusan 10mins ya yi ƙasa da murya ya ce “I'm sorry my baby girl, Zo ki ci abincin ki.” Banza ta yi masa, Ya ɗagota ya fara share mata hawayen. Gaba ɗaya fuskanta ta ƙankance, idanunta sun janye, Ya kai bakinsa ya yi kissing goshinta ya ce “C'mon yar gidan uncle ɗinta, Ba na ce ki yi hakuri ba?” Ita dai bata ce komai ba. Ya jawo tray ɗin daya shigo dashi ya ɗauki mug ɗin da ya zuba tea ya kai mata baki ya ce “Buɗe bakin.” Sake tsuke bakinta ta yi, Ya ɗan yi murmushi ya ce“Ko sai na buɗe bakin?” kuka ta saka ta juyar da kanta. Ya girgiza kansa ganin tana neman wahalar dashi ya ce “Nana zan bata miki rai fa, tun ɗazu ki ci abinci ya gagara? So ki ke wani ciwon ya same ki?” Cikin kuka ta ce “Ni ka kaini wajen Ammata! Ni ba zan zauna ba, mutuwa zan yi anan...” ta ƙare maganar tana yarfe hannu. A sanyaye yaji maganar tata, dan muryarta a dashe take saboda kukan da ta ci. Ya gyaɗa mata kai ya ce “To zan kai ki, amma sai kin fara sha tea ɗin nan.” Girgiza masa kai ta yi ta koma ta kwanta a kusa da shi tana ci gaba da koke-kokenta. Duk yanda ya yi da ita ƙin yarda ta yi ta ci komai, Ya gaji ya rabu da ita, Gyara zamansa ya yi akan gadon ya yi shiru yana kallon ta. Ita kuwa ta gaji da kukan baccin wahala ya sake ɗauketa, Sai da aka fara kiran sallar magriba sannan ya bar ɗakin. Ya koma nasa ɗakin ya yi alwala sannan ya nufi masallacin dake gidan. Bayan an idar da sallah gari ya fara duhu ya ɗauki mota ya fita... Tana ji aka idar da sallahr amma babu damar yi, ko motsa ƙafarta ta kasa saboda azaba. Abun kuma ya haɗe mata biyu da ɗangwalolo irin nata, tana nan zaune tana kuka ƙasa-ƙasa har aka yi sallar isha'i. Yunwa ta fara damunta, ga zazzaɓin daya dawo mata sabo. Gaba ɗaya jikinta ciwo yake kamar wadda aka yiwa duka, Ta kwanta a gefen gadon tana kuka tana kiran Ammarta da Abbanta. Murɗa handle ɗin ƙofar aka yi, Ta sake cure jikinta waje ɗaya dan duk tunaninta shi ne. Tsakiyar ɗakin ta tsaya tana ƙare mata kallo, lokaci ɗaya kuma ta sheƙe da dariyar mugunta. Dakyar Nana ta yunƙura ta tashi zaune, Zahra da ke kallon ta tana dariya ta ce “Ya aka yi yar gold?” Ita dai Nana kallon ta kawai take dan bata fahimci abin da take nufi ba. Zahra ta ƙaraso gaban gadon fuskarta ɗauke da mabayyanin farin ciki ta ce “ashe haka abu ya faru? Hala dai bai ji miki ciwo ba?” Haɗe rai Nana ta yi duk da yanda take jin jikinta bai hanata harararta ba. Zahra ta girgiza kanta ta ce “Yaro kenan, yaro man kaza. Yanzu kin gane abin da nake faɗa miki ko? Kin gane shi ba sa'an aurenki bane ko? Kin gane cutar kanki ki ka yi da ki ka yarda zaki zauna dashi ko?. Abdusammad yafi ƙarfin ki, madadin ki samu farin ciki wahala zaki sha. Daga ƙarshe kuma ki bar mana gida, dan muddin ina raye wallahi sai kin bar gidan nan Nana.!” Wani irin abu ne yazo ya tokarewa Nana a ƙirji, Ta dinga kallon Zahra ba tare da ta bata amsa ba. Ita kuwa Zahra dafata ta yi babu alamar damuwa a tare da ita ta ce “Ai yanzu kin shigo filin, kuma zaki ji yanda ake ji. Da kan ki zaki gudu ki bar shi, domin ke baki isa in yi sharing mijina dake ba! Kin yi kaɗan” Shar-shar haka hawaye suka dinga zuba akan fuskar Nana. Ta sanya hannunta ta goge kafin ta ce “To ai naji ɗin, kuma uncle ya ce min yana sona. Ɗazu ya ce min da ya san zan girma da wuri da ba zai aure ki ba, domin ba dadinmu ɗaya ba. Kuma ya ce min yana sona sosai! Kuma wallahi ba zan bar gidan nan ba” Ta ƙare maganar tana harararta sai kuma ta sake fashewa da kuka, Zahra ji ta yi dama bata shigo ɗakin ba. Wato har ya fara faɗar maganganu akanta, Ta buɗe bakinta zata yi magana kenan ya shigo ɗakin. Da mamaki yake kallon su duka, lokaci ɗaya kuma ya shigo ciki yana kallon Nana dake kuka. Gabanta ya ƙarasa ya dire ledojin daya shigo dasu ya durƙusa daidai tsayinta yana kallon ta ya ce “Nana mene ne? Kukan me ki ke?” Cike da shagwaɓa ta ce“uncle ko ba ita ba ce, Uncle wai baka sona? Wai kuma zaka rabu dani!” Wani irin mugun kallo ya watsawa Zahra, ta yi saurin sunkuyar da kanta..sai kuma ya mai da idanunsa kan Nana ya ce“Babu abin da zai saka na rabu dake sai dai mutuwa Nana, and uncle na sonki. Bana faɗa miki ba?” Gyaɗa masa kai ta yi, Ya ja kumatunta yana murmushi ya ce“Stop crying.” Ya fara goge mata hawayen ba tare da ya kalli inda Zahra take ba, Ita kuwa suman zaune ta yi tana kallon su, lokaci ɗaya hawaye ya cika kurmin idonta. Nana ta ɗan kalleta sai kuma ta ɗora hannayenta ta sarƙafe wuyansa ta ce “Uncle fitsari zan yi.” Tashi tsaye ya yi yana ƙoƙarin rike hannunta ya ce“to muje.” fashewa ta yi da kuka ta faɗa jikinsa ta ce“kafata zafi take min uncle, ba zan iya tafiya ba. Ka ɗaukeni...” ta ƙare maganar tana sake narke masa, Tamkar Hajiya Babba ce ta yi masa maganar haka ya shiga gyaɗa kansa kafin ya ce “Okay tawo” Daga haka ya ɗauketa kamar yar baby ya nufi toilet ɗin da ita. Zahra ta dinga kallon ƙofar toilet ɗin zuciyarta na wani irin tafarfasa, Ta tashi ta fice daga ɗakin tana ganin duhu-duhu, Tana shiga daƙinta ta faɗa kan gado ta fashe da wani irin kuka na zallar takaici, har ita Abdusammad zai wulaƙanta a gaban Nana? Ita zai yi wa irin wannan abun. Ta sake rushewa da wani sabon kukan tana dafe ƙirjinta. Da kyar ta yi sallar tana koke-kokenta wai ita zafi ƙafarta zata ɓalle, shi dai sai rarrashinta yake kamar zai maidata ciki. Gaba ɗaya tausayinta ya cika shi, Ya jawota jikinsa ya rungume yana sakin ajiyar zuciya ya ce “Ki daina kukan, ko kina son uncle ya daina son ki?” Banza ta yi masa kuma bata daina kukan ba. Ya girgiza kansa dan daman Nana maje birni ne, balle da aiken sarki. Jira take a taɓata ta fara damun rayuwar mutane. Duk yanda ya yi da ita akan taci abinci ƙi ta yi a sannan ma, Daga ƙarshe ya haɗe ransa yana kallon ta babu alamar wasa ya ce “Wallahi idan har baki ci abinci na baki magani ba, sai na sake miki abin da nayi.!” Kallon sa ta yi ganin how serious he is ya sanya ta shiga girgiza hannayenta tana kuka ta ce “A'a uncle, wallahi mutuwa zan yi. Ka yi hakuri” Ɗauke kansa ya yi saboda dariyar da ta so bashi, Ya fuske ya janyo plate ɗin daya zuba mata gasasshiyar kazar sai tiriri take saboda da zafinta, Ya ɗauki tsoka ɗaya ya kai mata baki ya ce “Open ur mouth.” Kallon sa ta tsaya yi, Ya ajiye plate ɗin a gefe ya fara ƙoƙarin zuge zip ɗin dake gaban rigarsa. Wani irin ihu ta saki ta yi saurin rungumeshi tana kuka ta ce“zan ci wallahi, dan Allah ka bari!” Ɗagota ya yi daga jikinsa ya tura mata plate ɗin ya ce“cinye yanzun nan.” ta kalli plate ɗin sai kawai ta sake fashewa da kuka, Da ɗan mamaki yake kallonta. Kafin ya yi kwafa ya janye plate ɗin ya fizgota ta faɗo jikinsa, Kafin ta yi wani yunkuri taji ƙarar farkewar rigarta, Ya keta rigar tun daga sama har ƙasa. Kasancewar babu komai a ciki ya sanya shi haɗiyar yawu yana ƙarewa surar jikinta kallo, Ta runtse idanunta tana ƙoƙarin rungume shi ya mai da ita ya kwantar akan gadon. Ban da kuka babu abinda take yi, ta sanya hannayenta duk biyun ta rufe ƙirjinta tana ci gaba da kukanta. Tsaki ya yi lokaci ɗaya ya fizge hannunta, Ya kai bakinsa kan nipples ɗinta. Tun yana abu da wasa sai taga ya fara komawa na gaske, Ta ware iya muryar da ubangiji ya yi mata tana yi masa kuka, Tana yi tana cizonsa amma duk a banza. Wannan karon ma sai da ya samu abin da yake so sannan ya mirgina gefe yana sauke numfashi. Ko motsi Nana bata yi, numfashin ma da kyar yake fita, idanunta a rufe sai hawaye dake zubowa a gefensu. Sai da ya daɗe kwance a wajen kafin ya tashi ya nufi toilet, Bayan ya gyara jikinsa ya dawo ya tsaya a gaban gadon yana kallon ta. Jiki a sanyaye ya sunkuya ya ɗauketa ya koma toilet ɗin, Cikin ruwan da ya haɗa mata ya zurata,Ta zabura tana ƙoƙarin fitowa daga ciki. Riƙeta ya yi sosai yana shafa kanta, Ta langwaɓar da kanta tana ci gaba da hawayenta. Da kansa ya gyara mata jikinta sannan ya sako mata bathrobe ya fito da ita, Sai da ya sauya bedsheet sannan ya kwantar da ita. Sanin ba zata karbi abincin ba ya sanya bai wahalar da kansa ba, Ya haɗa injection ya yi mata sannan ya rufeta da duvet. Ba'a jima ba ya ji saukar numfashinta, ya yaye duvet ɗin yana kallon kyakkyawar fuskarta wadda ta kumbura, Ya saki wani yalwattacen murmushi yana jin so da ƙaunar yarinyar a cikin ransa, Kissing kumatunta ya yi a fili ya ce “Allah ya yi miki albarka.” Ya saki duvet ɗin yana murmushi sannan ya tashi daga wajen, Ƙaro gudun ac ɗakin ya yi sannan ya rage mata hasken ya juya ya fice daga ɗakin. A parlournsa ya zauna aka kawo masa abinci, Ya ci sosai saboda ji ya yi cikinsa ya rarake, bayan ya gama ci ya tashi ya koma ɗakin. Sai da ya kalleta sannan ya nufi toilet ya wanko bakinsa sannan ya fito, Har sannan baccinta take, duk da kana jin yanayin sautin numfashin zaka san ba baccin me daɗi take ba. Ya fice daga ɗakin kai tsaye kuma apartment ɗin Zahra ya nufa. Zaune ya sameta tsakiyar gado ta kifa kanta akan cinyarta tana kuka a hankali, Ya tsaya a tsakiyar ɗakin yana ƙare mata kallo. Ɗago kanta ta yi ta kalleshi da idanunta wanda suka yi luhu-luhu saboda kuka, Ya ɗan yi jim kafin ya fara cewa “And this should be the last time da zaki sake shiga harkar yarinyar nan idan har kin san ba zaman lafiya zaku yi ba. Duk abin da ki ke nayi miki shiru ne kawai na ɗauke kaina ba dan ban san gaskiya ba, ina sane koda yaushe nake bata rashin gaskiya just to see zaki gyara. Amma na fuskanci ba zaki sauya ba, saboda kin canja halaye, da ba haka ki ke ba. Idan har ki ka sake shiga inda take ki ka nemeta da faɗa wallahi sai na saɓa miki Zahra! I'll show you the other side of me. Bana son tashin hankali, idan zaku iya ku zauna lafiya. Idan kuma kun ba zaku zauna lafiya ba ni zan saita ku, dan na san maganinku!” Ya ƙare maganar yana yi mata wani kallo, Lokaci ɗaya kuma ya juya ya fice daga ɗakin. Kwafa Zahra ta yi hawaye na zubawa kan fuskarta. Ta yi kwanciyarta tana jin wani irin baƙin ciki da takaici kamar zata mutu, ji ta yi ina ma bata aure shi ba. Ina ma bata san shi ba, da babu abin da zai haɗata da wannan ɓacin ran. Ta kifa kanta jikin pillow tana kuka kamar ranta zai fita. Daren ranar bai yi wani baccin kirki ba, dan Nana bata bar shi ya huta ba. Daga wannan sai ta ce wancan, daga wannan kukan sai ta komawa wani, daga ƙarshe ma tashi zaune ta yi ta ce sai ya kira mata Abbanta ta faɗa masa. Abdusammad ya dinga kallon ta can kuma ya ce “To zan kira shi amma fara zuwa ki kwanta!” Maƙale kafaɗa ta yi tana kuka ta ce“Ni ba zan bacci ba sai ka kira min Abbana! Ni ka kira min shi.” Dafe kansa ya yi ya ce“idan baki zo kin kwanta kin daina min rigima ba wallahi zan bata miki” Ko saurarensa bata yi ba ta ci gaba da kukanta. Ya tashi ya fice daga ɗakin, After some minutes ya dawo hannunsa riƙe da wani ɗan ƙaramin remote. Ya koma ya kwanta ya juya mata baya, sannan ya danna remote ɗin. Lokaci ɗaya wasu irin ƙwaruka masu kama da kyankyaso suka fara tashi a cikin ɗakin, kasancewar da haske sosai ya sanya idanunta ya sauka akan su. Ganin suna ƙaruwa ya sanya ta tsaya da kukan, Ta kalle shi taga ya juya baya, Tashinsa ta fara yi muryarta na rawa ta ce “uncle! Uncle ka ga.” Janyeta ya yi daga bayansa sannan ya ce“Dan Allah Nana ki bar ni na huta.” “Uncle kalli, kalle su kaga!” Kallon ƙwarukan ya yi ya sake matsa remote ɗin hannunsa nan take suka cika ɗakin sai tashi suke, Ya ɗan ware idanunsa kafin ya kalleta ya ce “Nana kamar kyankyaso?” Kafin ta yi magana wani ya tawo ta inda take, Ta saki wata razananniyar ƙara ta faɗa jikinsa tana kuka. Murmushi ya yi sannan ya fara ƙoƙarin ɗagota amma sam taƙi yarda, Ya kwanta ta shige jikinsa ta rufe su da duvet tana kuka, hannayensa ya sanya a bayanta ya sake jawota jikinsa fuskarsa babu alamar wasa ya ce “Kwanta kar su kama ki” Gyaɗa masa kai ta yi tana sake ƙanƙameshi. Ya dinga shafa bayanta yana murmushi shi kaɗai, Shiru ta yi tana sauke numfashi, after 5mins ta ɗago kanta tana kallon gemunsa ta ce “uncle sun tafi?” Girgiza mata kai ya yi ya ce“kina so su hau miki jiki?” saurin girgiza kanta ta yi tana hawaye, Ya dafa kanta ya ce“To ki yi baccin ki, ba zan bari su zo nan ba.” Toh kawai ta ce sannan ta koma ta yi lamo a jikinsa, Da gaske duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, cikin ƴan mintuna ya yi maganin rigimar tata. Dan daman ya san babu abin da take tsoro sama da kyankyaso, after some minutes yaji saukar numfashinta, Ya kalli fuskarta dake kan ƙirjinsa sai kuma ya yi murmushi ya rufe idanunsa nan da nan bacci ya ɗauke shi shima. 08106608363 Nanameera. *🌹 NAANAH 🌹* Arewabooks@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 59. Washegari yini ta yi a kwance ko parlour bata fito ba, iyakar maganar da ya yi da ita akan ta zo suje ƙasa ƙin yarda ta yi. Har ya gaji ya fita ya bar ta, Ta na nan zaune around 5:00 na yamma wayarta ta fara ringing. Hannunta ta saka ta janyo wayar ta kai kunne bayan ta ɗaga. Daga can ɓangaren Amma ta ce “Nana” Ji ta yi kamar ta yi tsuntsuwa taje Nigeria ta rungume Ammarta. Sanin babu hali ya sanya ta sauke numfashi murya a sanyaye ta ce “Na'am Ammata.” Amma ta yi shiru jin muryarta a sanyaye ta ce“lafiya dai Nana? Ko wani abun na damun ki?” Girgiza kai Nana ta yi dan ba iya faɗa mata zata yi ba ta ce“ba komai kawai a kwance nake.” Amma ta ce“To shikenan, Daman kiran ki nayi naga kwana biyu baki kirani ba” Murmushi Nana ta yi ta ce“Makaranta ce take hanani sakewa, shiyasa.” Amma ta jinjina kanta ta ce“haka ne Allah ya taimaka, ki dinga dagewa.” A sanyaye ta ce“Amma yaushe zaki zo?” ware idanu Amma ta yi kafin ta ce“Ni ce zan zo ɗin Nana?” turo baki Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce“dan Allah Amma ki zo. Kin ga babu wanda yake zuwa inda nake tun da na zo, kuma...” “Kuma me?” Amma ta ce tana gyara zaman wayar a kunnenta. Girgiza kai Nana ta yi ta ce“Kuma ai ban san kowa ba, uncle kawai na sani fa. Ko hira bana yi da kowa” “Ina ita Zahran?” Tura baki Nana ta yi ta ce“Uncle ya hanani kulata, Ya ce idan na sake kulata zai zaneni.” Da ɗan mamaki Amma ta ce“duka kuma? Akan me? Me ki ke mata?” ta jera mata tambayoyin tana jiran amsar da zata bata. Cikin shassheƙar kuka Nana ta ce“to ba ita ce take fara zagina ba, dan Allah Amma ai kin ga sai na rama ko?” Girgiza kai Amma ta yi dan daman ta san za'a rina ta ce “Nana! Nana! Nana ban son kina neman magana. Na san halin ki da rashin kunya, baki son a zauna lafiya, so ki ke a dinga kawo ƙarar ki? Kina son Abbanki ya dinga fushi a kan ki ne?” Girgiza kanta ta yi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce “wallahi Amma babu abin da nake mata. Ita ce take zagina, kuma ta ce sai uncle ya sakeni. To shi ne na rama” Ta ƙare maganar tana goge hawayenta. Amma ta ce “Ko me zata ce ki daina tankata, kada ki bata amsa. Ki yi shiru da bakin ki” “To ai daman na daina kulatan fa Amma.” Jinjina kai Amma ta yi ta ce“Yauwa haka yafi, Ki nutsu kuma, kada ki dinga son jikin ki. Idan baki da lafiya ki dinga faɗawa Abban Noor ɗin” Gyaɗa mata kai ta yi kafin ta ce“Tom Amma." “Ya isa daina kukan ɓaure.” Murmushi ta yi tana sake goge hawayenta ta ce“na daina Amma.” Jinjina kai Amma ta yi ta ce ta ce“Allah ya miki albarka.” da Amin Nana ta amsa sannan suka ci gaba da hirarsu. **** Zahra na zaune kan kujera a parlornta wayarta dake hannunta ta fara ringing, Ta ɗaga tana murmushi ta ce“Hello Anty” Anty Khadijah dake jan numfashi kamar wadda ke kuka ta ce“Zahra kina ji?” Gyara zamanta ta yi jin muryar tata ta ce“Anty lafiya dai? Me ya same ki?” “Zahra bana son auren Malam Garban nan, wallahi bana so. Gashi ɗazu sun zo sun kawo kuɗin aure nan da 2 weeks za'a ɗaura auren...” Tashi tsaye Zahra ta yi tana girgiza kanta ta ce “Haba dai Anty. Wallahi ba zaki auri wannan mutumin ba! Ya ma za'a yi ki aure shi? Idan ma wani asirin ya yi miki sai dai ya faɗa kansa wallahi Anty. amma ke dai kin fi ƙarfin aurensa” Cikin kuka Anty Khadijah ta ce“nima na san da haka Zahra. Wallahi ni ba sa'ar aurensa ba ce, akan mene ma zan aure shi?” Zahra ta yi shiru tana jin zuciyarta a dagule, Anty Khadijah ta ja numfashi ta ce“kina ji? Amma kina shan maganin nan?” Girgiza kai Xahra ta yi a sanyaye ta ce“Wallahi a'a Anty, kwana biyu kin ga ban sha ba. Ni mantawa ma nake dashi” Anty Khadijah ta yi shiru can kuma ta ce“To ki ɗauko ki shanye yanzu, saboda bana son ya kai wani satin zai lalace." To kawai Zahra ta ce sannan suka ci gaba da tattauna maganar auren... Sai bayan sallar magriba sannan ya shigo gidan, Kai tsaye ɗakin Nana ya nufa dan ranar kwanan Zahra ne. Ya sameta zaune ƙasan gado tana danna wayarta bayan ta idar da sallah, Ƙarasawa ciki ya yi ya ajiye ledar dake hannunsa ya zauna gefen gadon yana kallon ta fuskarsa a sake ya ce “Hey baby.” Ɗago kanta ta yi ta kalle shi, Ya sakar mata murmushi yana miƙa mata hannu. Tura baki ta yi ta tashi ta koma can ƙarshen gado ta zauna, Murmushi ya yi sannan ya juya inda take yana kallon ta, Fuskarta a haɗe babu alamar wasa. Ya hau tsakiyar gadon ya zauna kusa da ita yana jan kumatunta ya ce “Wa ya taɓa min ƴar rigimata?” Janye hannunsa ta yi tana tura baki, Ya sake kai hannunsa zai taɓa ta. Tsam ta tashi daga wajen ta koma wani ta zauna tana kallon sa, Ya girgiza kansa ya sake bin ta, Ƙoƙarin sauka take daga kan gadon ya jawota jikinsa. Tura shi ta fara yi kamar zata yi kuka ta ce “Ni Allah uncle bana so. Ni ka bari” Sake matseta ya yi a jikinsa yana kallon ta ya ce“Ni zaki dinga sharewa?” Ɗauke kanta ta yi tana kallon wani wajen, Ya yi kwafa kafin ya janyo fuskarta ya ce “Idan ki ka sake ɗaukewa sai na baki mamaki.” Ganin babu alamar wasa akan fuskarsa ya sanya ta fasa ɗaukewa, ta sunkuyar da kanta nan take hawaye suka fara zubowa kan fuskarta. Waro idanunsa ya yi yana kallonta kafin ya ce “me kuma nayi miki?” Cikin kuka ta ce“Ni bana so, bana so kana taɓani wallahi. Ka daina!” Kallon ta kawai yake. Can kuma ya yi murmushi ya ce“Yanzu warning ki ke min or what Nana?” tura baki ta yi tana ƙoƙarin kwace kanta. Ya sake matseta yana kallonta ya ce“ai sai kin amsa min yarinya.” marairaice fuska ta yi ta ce “uncleee!” “Auntyyyy..!” Ya ce yana kwaikwayon muryarta. Tuntsirewa Nana ta yi da dariya tana kallon sa, Shima dariyar yake. Ta duke shi a ƙirji ta ce“ni ka daina kwaikwayon magana ta Allah!” Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“To na bari Aunty.” “Ni bana sooo!” Ta ce a shagwaɓe. Murmushi kawai ya yi yana ɗora kansa a wuyanta ya ce“Zo ki ci abinci.” Turo baki ta yi kafin ta ce“ni bana ci” Bai ce komai ba ya janyeta daga jikinsa ya sauka daga kan gadon, Ledar daya shigo da ita ya ɗauko ya miƙo mata. Ta karɓa tana kallon sa, sai kuma ta buɗe, washe baki ta yi ta ɗago kanta tana kallon sa ta ce “Laaa kaza?” Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh bashin kazar ki ce.” Turo baki ta yi ta tura masa ledar ta ce“bana ci” “A kan me?” Ta koma ta kwanta ta ce“kawai bana ci.” Murmushi ya yi ya sanya hannunsa ya jawota, Ya ɗago kanta ya ce“Ko dai ki ci ko kuma...” “Zan ci wallahi!” Ta katse shi da sauri. Ta ɗauki ledar kazar ta buɗe ta fara ci tana taunawa a hankali, Ɗago kanta ta yi taga yana kallonta. Ta dauko tsoka ɗaya ta miƙa masa tana tauna ta bakinta ta ce “Cii” Yanda ta yi maganar ne ya bashi dariya, Ya ja kumatunta ya ce“Am full” bata sake cewa komai ba ta kai naman bakinta tana rausaya kai. Tashi ya yi yana kallonta ya ce“sai da safe.” To kawai ta ce a sanyaye, Ya juya ya fice daga ɗakin. Sai a sannan ta ture ledar gabanta ta kifa kanta akan cinyoyinta ta fashe da kuka tana birgima a wajen. Haka ta gaji da kukan ta haƙura ta tashi ta shige bayi ta wanko bakinta sannan ta yi wanka ta fito, Wasu riga da wando masu sulɓi ta ɗauka ta saka sannan ta yi kwanciyarta. Ta dade tana juye-juye kafin bacci ya ɗauketa, Abdusammad koda ya fita ɗakin Zahra ya shiga ya ce mata yana apartment ɗinsa. Amma har wajen ƙarfe 12 na daren bata zo ba dan haka ya yi kwanciyarsa. Washegari ma bai zauna a gidan ba saboda aiki da ya ya masa yawa, Zahra kuwa ko inda yake bata je ba. Ko Noor bata kai school ba tayi kwanciyarta a ɗaki doing nothing. Nana na zaune akan sofa wajejen ƙarfe 7:00 na dare, wayarta ta fara ringing, numbern Abba ta gani, Ta ɗaga ta kai kunne tana murmushi. “Happy birthday daughter!” Cewar Abba muryarsa cike da farin ciki. Tuntsirewa da dariya Nana ta yi dan ita har ta manta ma, Can kuma ta tsuke fuska ta ce “Abba yau birthday ɗina babu celebration” Murmushi ya yi ya ce“Uncle ɗin ki bai miki ba?” taɓe baki ta yi ta ce“uncle ɗin bai ma sani ba.” “Haba?” Abba ya yi maganar yana murmushi, Sake tura baki ta yi ta ce“Abba ina birthday gift ɗina?” Abba ya ce“To yanzu Nana ta ina zan baki birthday gift? But tell me what do you want, Sai na siya miki duk randa ki ka zo na baki.” Ɗan juya Idanunta ta yi kamar mai tunani ta ce“Yauwa Abba ina son ka siya min teddies da kuma sabon system!" Girgiza kai Abba ya yi yana murmushi ya ce“Nana kenan, you will never change. To naji” Dariya sosai ta yi ta ce“Yauwa Abbana thank you, Allah ya ƙara maka arziki, Ya baka lafiya ingantacciya!” Lumshe idanunsa ya yi yana jin zuciyarsa wasai babu damuwa ya ce “Amin ya rabbil alameen Nana Khadijah, Allah ya miki albarka ya zaunar min da ke lafiya, Ya kaɗe sharri daga cikin aurenku. Ya baki ya'ya na gari” Sunkuyar da kanta ta yi tana murmushi ta ce“Abba idan na haihu sai na bar muku ɗan ko?” Dariya ta bashi, Ya ce“Zaki bar min ɗan?” Ta gyaɗa kanta ta ce“Eh Abbana! Sai na bar muku kai da Amma.” Murmushi sosai ya yi ya ce“To Allah ya baki ya'yan Nana” Ta yi murmushi ta ce“Amin Abbana” Sun daɗe suna hira kafin ya kashe wayar. Ta sauke numfashi jin ana kiran sallah ta tashi ta shige bedroom ɗinta, Alwala ta yi ta gabatar da sallah sannan ta yi kwanciyarta dan ba yunwa take ji ba. Tana jin convey ɗinsa, Amma bai shigo gidan ba har sai da aka idar da sallahr Isha'i. Tana kwance tana kallon wata Chinese drama ya shigo dakin, Ta amsa sallamar ciki-ciki. Zama ya yi gefen gadon yana kallon ta ganin ko ɗago kanta bata yi ba, Ya ɗan yi murmushi ya ja yatsun ƙafarta ya ce “Heyyy” Ɗago kanta ta yi ta kalle shi sai kuma ta tura baki, Ya girgiza kansa ya ce”wato ke kullum baki so a zauna lafiya ko? Haka ake yiwa miji aka ce miki?” Ɗauke kanta ta yi tana zumɓura baki gaba. Ya taso ya dawo kusa da ita ya janye system ɗin ya rufe yana kallon ta ya ce“faɗa min yau kuma mene ne? Wa ya taɓan ƴan matana?” Janye hannunta ta yi ta ce“Ni bana so..” Haɗe rai ya yi babu alamar wasa ya ce“baki son me?” ta kalle shi amma bata ce komai ba. Tashi ya yi yana faɗin “tun da baki da abin cewa sai da safe.” Ganin da gaske tafiya zai yi ya sakata tashi tsayen itama, Ta kira sunansa cikin shessheƙar kuka, Juyowa ya yi yana kallonta da mamaki ganin hawaye akan fuskarta. Ya dawo ya riƙe hannunta ya ce “Mene ne?" Fashewa ta yi da kuka ta shige jikinsa tana cewa“Ba kai ne ba, baka san yau birthday ɗina ba? Kuma Abba ya ce kai ne zaka min birthday cake...” Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan, Wani lafiyayyen murmushi ne ya kwace masa, Ya dafa bayanta yana ƙoƙarin saita kansa kafin ya ɗago fuskarsa a haɗe ya ce “Ni bani da abin yi zan tsaya wasa? Sakeni ni” Ya janyeta daga jikinsa, Bai tsaya jiran abin da zata ce ba ya juya ya yi ficewarsa. Nana ta bi shi da kallo sai kuma ta koma gefen gado ta zauna tana fashewa da wani irin kuka.. Koda yaje dakin Zahra zaune ya sameta tana waya, Ya tsaya har ta gama kafin ya ce“Madam kwana biyu abun ne ya motsa?” Girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce“Ba komai fa doctor” Ya yi shiru yana kallon ta can kuma ya sauke numfashi ya ce“Alright bari naje ina zuwa.” To kawai ta ce ya juya ya fice, Ta bi shi da kallo sai kuma ta taɓe baki. Nana na kwance gefen gado Around 9pm taji ana knocking ƙofar, Ta goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta sauka daga gadon. Koda ta buɗe ƙofar Maid ta gani tsaye, Ta sunkuya ta gaisheta kafin ta ce“Madam ana kiran ki” Nana ta ɗan kalleta da kumburarrun Idanunta ta ce“ina?” “Downstairs” Ta bata amsa kai tsaye. Okay kawai ta ce sannan ta mai da ƙofar ta rufe, Ta koma ta ɗauki hularta akan gadon ta zura slippers a ƙafafunta sannan ta fito daga ɗakin. Da mamaki ta dinga kallon ƙasan, ganin duhu ya mamaye ko ina, Ta ɗan yi jim a bakin stairs ɗin benan, kafin a hankali ta fara takawa. Sai da ta sauka kasan sanan ta tsaya cak saboda bata ganin gabanta, Ta ɗan waro idanunta saboda inuwar mutum data gani. Muryarta na rawa ta ce “wa... waye?” Shiru ba'a yi magana ba, Ta sake cewa waye amma ba'a bata amsa ba. Shiru Nana ta yi tana kallon wajen ta cikin duhun, Lokaci ɗaya ta ga haske ya mamaye parlourn, Sai a sannan ta fara ƙarewa parlon kallo. An ƙawata shi da baloons gwanin ban sha'awa, Kafin ta yi magana taji spray na zubowa kanta, ta ɗaga idanunta tana kallon saman amma bata ga kowa ba. Murmushi ta fara yi tana kallon yanda baloons ɗin ke fashewa, Ta sauke idanun ta tana kallon jikin bangon parlourn. Wani ƙaton enlargement ɗin hoton ta ne na ranar da aka haifeta a kafe, Sai kuma wasu hotunan na sanda tana ƴar ƙarama Abdusammad ya ɗauketa, wasu tana kuka, wasu kuma tana masa dariya, Daga saman su kuma an saka "Happy birthday Naanah!"ƙasa kuma an ajiye number 1&8 wanda ya yi making 18yrs. Nana ta dinga kallon su tana jin wani irin farin ciki a cikin ranta, Lokaci ɗaya ta kalli inda yake tsaye yana kallon ta sai murmushi yake, Sanye yake da suit black colour wanda suka amshi jikinsa kai ba ka ce ya taɓa raɓar ƙasar Hausa ba. Fuskarsa a sake sai murmushi yake, Da gudu ta ƙarasa inda yake tana zuwa ta faɗa jikinsa ta rungumeshi tana sakin wani irin kuka. Ya dinga dariya yana shafa kanta jin yanda take kuka tana sake ƙanƙameshi, Ɗago fuskarta ya yi yana murmushi ya ce “Happy birthday ƴar rigimar uncle!” Ta kalle shi sai kuma ta sake mai da kanta ƙirjinsa tana ci gaba da kuka. Sake ɗago kan nata ya yi ya ce“Mene kuma abin kuka? Or are you not happy? Uncle ya shirya miki birthday party” Girgiza kanta ta yi tana kuka mai haɗe da dariya, ta ce“No uncle. Kawai...kawai...” ta kasa ci gaba saboda kukan daya sake kwace mata, Mai data ƙirjinsa ya yi ya rungume ya ce“Shikenan ya isa haka.” Ta dinga gyaɗa masa kai ba tare da ta daina kukan ba, Noor ce ta sakko daga sama ta ƙaraso wajen ta rungumeta ta ce “Happy birthday Anty Nana!” Sai a sannan Nana ta sake shi ta durƙusa ta ɗauketa tana murmushi ta ce“thank you Noorie.” Murmushi duka suka yi, Ya kalle su ya ce“to a yanka cake ɗin ko? Dare nayi” Sauka daga jikinta Noor ta yi ta ce“Abbie bari na kira Ummi” Girgiza mata kai ya yi ya ce“na kirata yanzu zaki ganta.” Ko rufe baki bai yi ba Zahra ta ƙaraso wajen tana sanye cikin wata Abaya green dark ta ɗaura veil ɗin akanta. Noor ta tafi wajenta da sauri ta rungumeta ta ce“Ummi daman kiran ki zan yi, Ki zo mu yanka cake.” Murmushi Zahra ta yi ta ja kumatunta ta ce“to gani nan.” Noor ta bar wajen ta koma wajen Nana ta tsaya, Inda aka ajiye manyan cakes ɗin suka ƙarasa, Cake ne yafi kala biyar manya wasu da hotunanta a jiki wasu kuma da stickers. Abdusammad ne ya miƙa mata wuƙar yana murmushi ya ce“oyaaa” ta amsa tana kallon sa, A hankali waƙar Birthday ta fara tashi sauran maids ɗin gidan suna ta tafi, a haka Nana ta yanka cake ɗin. Koda ta ciro Abdusammad ɗin ta miƙowa, Ya ɗan ware idanunsa sai kuma ya buɗe bakin. A hankali ta saka masa, Suka sake tafi Noor sai dariya take tana tafi abin ta, Zahra kuwa kasa tafin ta yi dan ji take kamar ƙafafunta na neman kasa ɗaukanta, Danne zuciyarta kawai take yi. Shima ya yanko cake ɗin ya bata ta amsa tana murmushi sannan ta bawa Noor, Da kansa ya ƙarasa inda Zahra ke tsaye hannunsa riƙe da cake ɗin ya ce “Haaa.” Babu musu ta buɗe bakin ya saka mata, Ta fara taunawa tana murmushin da bai kai zuci ba. Bayan sun gama yanke-yanke cake ɗin aka fara bata gift, Noor ce ta fara bata wasu manyan chocolate a cikin kwali tana murmushi, Nana ta amsa sannan ta rungumeta ta ce“Thank you Noor, Allah ya miki albarka.” Dariya ta dinga yi, Zahra ma ta ƙaraso wajen ta miƙo mata wata ƙatuwar jaka mai rubutun Happy birthday a jiki, amsa Nana ta yi tana murmushi ta ce“Thank you Anty zahra.” Karo na farko data kira sunanta da girmamawa tun bayan abin da ya faru, Zahra ta ɗan yi murmushi without saying anything. Juyawa ta yi tana kallon Abdusammad dake tsaye ganin bashi da niyyar bata waya gift yasa ta taɓo shi, Yana murmushi ya ce “mene ne?” “Gift ɗina” Ta ce a shagwaɓe. “au nima sai na bayar?” ya yi tambayar yana nuna kansa, Tura baki ta yi tana shirin barin wajen taji ya riƙo hannunta, Ya ƙarasa da ita har gaban wata sofa wannan aka rufe da farin veil. Da kansa ya janye veil ɗin yana murmushi ya ce “Happy birthday once again Nana.” Kallon sa ta yi sai kuma ta kalli tarin kayan dake kan kujerar, Ta durƙusa a wajen da sauri ta shiga ɗaga su. Teddies ne irin wanda take so manya, Sai kayan zaƙi da yawa, Ta dinga bubbuɗawa tana murmushi. Wata ƙatuwar teddy red colour ta ɗauka ta miƙe tsaye tana kallon sa fuskarta ɗauke da mabayyanin farin ciki ta ce “Thank you Unclena... Ina sonka!” Ta ƙare maganar tana faɗawa jikinsa, Murmushi ya yi kawai ya ce“da gaske kina sona Nana?” Gyaɗa masa kai ta yi, Ya ɗagota ya ce“tsohon?” wata irin matsananciyar kunya ce ta rufeta. Ta sunkuyar da kanta ba tare da ta ce komai ba, ganin yanda jikinta ya yi sanyi ya sanya shi jan kumatunta ya ce “Kee relax, I'm just kidding.!” Hannunta ta sanya ta share hawayenta, Ya taɓe baki sannan ya kama hannunta yana cewa“Allah ya miki sauki.” Bata ce komai ba suka koma inda su Zahra ke tsaye, Ya kalle su ya ce“muje.” To kawai suka ce sannan ya yi gaba yana rike da hannun Nana suka bi bayansa, A babban compound ɗin gidan suka tsaya, Nana ta dinga kallon motar dake gabansu wadda aka rufe da baƙin yadi. Da idanu ya yi musu alama da su buɗe, Wasu maids guda biyu suka ƙaraso wajen suka janye yadin daya rufe motar. Wata Lamborghini Aventador ce White colour, an yi mata ado da red bow wanda suka sake haskata. Nana ta dinga kallon motar babu ko kiftawa, bata san sanda ya zagaya hannunsa a jikinta ba, Kawai kallon Hannunsa ta dinga yi wanda ke riƙe da car key. Ya miƙo mata yana murmushi can gefen kunnenta ya ce “And this na virgin gift. Allah ya miki albarka Nanata. Kin sani farin ciki mara misaltuwa, naji daɗi. Na samu nutsuwa, Thank you, na gode da ki ka kare mutuncinki har zuwa ɗakin mijin ki. Allah ya miki albarka kin ji!” Wani irin abu taji ya tsaya mata a ƙirji, ta kasa koda motsi sai hawaye shar dake zubowa kan kyakkyawar fuskarta. Above 2mins kafin ta saki wani irin raunataccen kuka ta juya ta shige jikinsa tana kuka kamar ranta zai fita, Shiru Abdusammad ya yi ya ɗora hannunsa a bayanta yana ɗan bubbugawa a hankali, ganin bata da niyyar yin shiru yasa ya kai bakinsa kunnenta ya ce “Ko baki so ne?” Saurin girgiza masa kai ta yi, Ta ɗago tana kuka ta kalle shi ta ce “Thank You... Thank you Uncle, Na gode sosai, na gode uncle. Ina sonka Uncle, ina son ka sosai, na fi kowa sonka wallahi. Ina son ka uncle ɗina...” Caraf taji ya kame bakin maganar, ya fara kissing ɗinta a hankali in a different romantic ways. Karo na farko data fara mai da masa da martanin abin da yake mata, Hakan ya sanya shi sake chopping face ɗin su yana ci gaba da abin da yake... Ƙarar fashewar abin da suka ji shi ne ya dawo dasu daga duniyar da suka tafi, Ya janye bakinsa daga nata a hankali yana sakin numfashinta. A tare suka kalli inda suke jin ƙarar, Abdusammad ya ware idanunsa yana kallon ta da mugun mamaki... 08106608363 Nanameera. *🌹 NAANAH 🌹* Arewapen@Nanameera08 Wattpad@Nanameera08. Page 60. Zahra ce tsaye gaban motar ta tawarwatsa glass ɗinta, Hannunta duk jini sai kuka take. Sakin Nana ya yi da sauri ya ƙarasa wajen ya finciko hannunta ganin tana ƙoƙarin sake buga flower base ɗin, Fizge hannunta ta yi cikin kuka kamar wata zararriya ta ce “Ni ka rabu dani! Ka kyaleni, na rantse da Allah ba zan yarda ba!.” Abdusammad ya dinga kallonta da mamaki, Nana ta ƙaraso wajen tana kallon yanda Zahra ta ci mutuncin sabuwar motar tata, Wani ihu ta saki ta yi kanta ta shaƙe mata wuya. Zahra ta fara ƙoƙarin dukanta, Kasancewar ba ƙarfin su ɗaya ba ya sanya ta murɗe mata hannu ta kifa mata mari. Bata ɗauke hannunta ba taji an sauke mata wasu tagwayen maruka akan fuskar, Ya fizge Nana yana kallon ta rai ɓace. Ɗago kanta ta yi tana kallon sa hannunta dafe akan kuncinta. Ta dinga gyaɗa kai kafin ta ce “Doctor saboda wannan yarinyar ka mareni? Saboda wannan ƴar iskar ka mareni? Akan ta?” Wani banzan kallo ya dinga watsa mata, Ya juya ya kalli Nana dake tsaye kusa da shi tana kuka a hankali, Bai ce komai ba ya ja hannunta suka nufi cikin gidan. Zahra ta bisu da kallo ganin ya mayar ta mahaukaciya ya yi tafiyarsa, Sai kawai ta fashe da wani sabon kukan ta sake ɗaukan flower base ɗin ta ci gaba da dukan glass ɗin motar yana fashewa. Dan kanta ta gaji ta sulale a ƙasa tana ci gaba da kuka kamar ranta zai fita. Sai da ya kai ta har Apartment ɗinta sannan ya kulle ya dawo ƙasan. Noor dake tsaye tana kuka ya ɗauka, ta yi saurin rungumeshi tana faɗin “Abbie Ummina” Shafa kanta ya yi ya ce“Don't worry kin ji.” Sun daɗe a haka kafin ya miƙawa wata maid ita ya nufi wajen, Zaune ya tarar da Zahra gefen motar tana kuka har sannan. Ya ɗan yi jim sai kuma ya ƙarasa yana kallon ta ya ce “Tashi daga nan” “Ba zan tashin ba! Ina ruwan ka dani ma? Mene ruwanka da zamana?” Zahra ta yi maganar a fusace. Kallon ta kawai ya yi sai kuma ya dauke kansa yana kallon fountain ɗin dake zubar da ruwa as usual ya ce “Kada ki ɓata min rai. Ki tashi ki koma ciki nace!” Miƙewa ta yi tana kallon sa rai ɓace ta ce“au tunanin ka zan yi abin da ka ke so ne? Bayan ka mayar dani banza shara a gidanka? Bayan kana nuna rashin adalci a fili? To wallahi ba zan yi ba! Kuma ka sani wannan abun da ka yi tamkar ka buɗe wani sabon shafi ne na bala'i da tashin hankali a cikin gidan nan, ba zan taɓa bari a zauna lafiya ba! Ita kuma yarinyar za tayi dana sanin shigowa cikin gidan nan!” Zahra na gama faɗin hakan ta nufi cikin gidan kamar zata tashi sama, hannunta sai ɗigar jini yake amma ko damuwa bata yi ba, da idanu kawai Abdusammad ya bita sai kuma ya sauke numfashi. Ya dinga kallon yanda ta wulaƙanta tsaddajiyar motar, gaba ɗaya ta farfashe glasses ɗin ta. Girgiza kansa ya yi yana sake jin jina al'amarin mata, Kafin daga bisani ya yiwa wasu securities umarni dasu gyara wajen a ɗauke motar. Shi kuma ya koma cikin gidan. Nana na zaune gefen gadonta sai kuka take, idan ta tuna yanda Zahra ta farfashe mata glass ɗin sabuwar motarta sai taji ranta na ɓaci. Kasa jurewa ta yi ta janyo wayarta dake can ƙarshen gadon ta yi dialing numbern Hajiya Babba. Sai da ta kusa katsewa sannan Hajiya ta ɗauka, Daga ɓangarenta ta ce “Nana yau kuma kin tuna dani?” Fashewa da wani sabon kukan Nana ta yi, Hankalin Hajiya Babba ya tashi ta ce “Mene ne? Kukan me ki ke takwara?” Cikin shessheƙar kuka ta ce “Hajiya Anty Zahra ce!” Da mamaki Hajiya Babba ta ce “Me ta yi miki ita Zahra?” Nana na goge hawayenta ta ce “Dukana ta yi Hajiya, saboda kawai nayi magana shi ne ta mareni. Kuma ta fasa min motar da uncle ya siya min...” Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan. Hajiya Babba da ranta ya gama ɓaci sakamakon maganar dukan da taji ta ce “Shi Abdusammad ɗin yana gani ta mareki?” gyaɗa mata kai Nana ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce “Eh mana. Kuma Hajiya ta fasa min motar da ya bani...” Shiru Hajiya Babba ta yi can ta ce“shikenan yi shiru bari zan kira shi ya kai mata wayar naji dalilin da zata dake ki.” Nana ta gyaɗa kanta ta ce“To Hajiya na gode.” “Ki daina kuka” Hajiya Babba ta yi maganar a tausashe, To Nana ta ce sannan ta kashe wayar, Ta kwanta gefen gadon ta yi shiru tana tunani. Zahra na zaune tsakiyar gadonta tana waya da Anty Khadijah ya shigo ɗakin, Tana ganinsa ta sauke wayar daga kunnenta ba tare da ta kashe ba, Ya ƙaraso gaban gadon ya zauna yana kallon ta fuska a ɗaure ya mika mata wayar dake hannunsa. Kallon wayar ta yi sai kuma ta kalle shi, Ganin irin kallon da yake mata ya sanya ta amsa ta saka wayar a kunne. Hajiya Babba dake zaune kan sofa ta ce “Zahra'u” Cike da girmamawa ta ce “Barka da rana Hajiya, Ina yini?” “Alhamdulillah. Daman naji wani batu ne wanda bai min daɗi ba, na ce bari na miki magana. Akan me kina da hankalin ki zaki dinga biye wa yarinya ƙarama? Akan me zaki daketa? Kin san yanda muka ɗauketa? Kin san matsayinta a wajen mijin ki shi kansa? Akan me haka?” Hajiya Babba ta yi maganar a faɗace, Shi dai Abdusammad shiru ya yi dan duk abin da take faɗa yana ji saboda a handsfree wayar take. Zahra da hawaye ya sake cika idanunta ta girgiza kanta ta ce “Wallahi Hajiya ba laifina bane. Yarinyar ce bata da kunya, Har ni Nana zata dinga yiwa kallon kishiya tana faɗawa magana? Kasa jurewa nake wallahi!” “Shi ne ki ke dukanta? Idan mahaifinta yaji zai ji daɗi ne? Kin san son da yake wa ƴarsa? Bana son sake jin irin haka ta faru. Kada ki sake cewa zaki kai hannu ki daketa, idan ta yi miki laifi ai ga mijinku nan ki sanar masa, amma kada ki sake cewa zaki ɗauki hukunci da kan ki.” Zahra ta haɗiye wani miyau mai ɗaci kafin ta gyaɗa kanta ta ce“In sha Allah Hajiya ba zan sake ba.” Hajiya Babba ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce“Yauwa to, Allah ya yi albarka.” Da Amin ta amsa sannan ta miƙa masa wayar, Ya karɓa ya tashi ya fice bayan ya saka wayar a kunnensa. Zahra ta runtse idanunta wasu zafafan hawaye suka shiga sakkowa kan fuskarta, Anty Khadijah da ke kan layi har sannan ta taɓe baki ta ce “Zahra! Zahra! Zahra! Kina zaune a inda ba'a ganin darajarki? Kina zaune a inda ba'a ganin ki da ƙima? Ya ma za'a yi uwar mijin ki ta dinga faɗa miki irin wadannan maganganun? Taɓ!” Zahra da taji kamar ta fama inda ke mata kaikayi ta fashe da kuka tana cewa“Anty kin gani ko? Basa sona! Ba sa ƙaunata, basu damu dani ba. Kamar ba sirikar gidan ba, Daman Hajiya Babba ba son auren mu take ba kawai ta yi shiru ne. Yanzu kuma ya auri wadda take so dole ta nuna mana banbanci, wallahi ji nake kamar na gudu na bar gidan nan, kamar na yi tafiyata na bar su!...” Ta sake fashewa da wani kukan. Girgiza kai Aunty Khadijah ta yi kafin ta ce“ba za'a yi haka ba, dole a san abin yi. Babu yanda za'a yi na bar ki cikin wannan masifar Zahra! Yanzu ni babu kudi a hannuna. Duk na bawa Garba, idan kina da wasu kuɗaɗe ki samu ki turo ko ki karɓa a hannun mijin ki, na san abin da zan yi miki. Wallahi babu wadda ta isa ta fitar dake daga cikin gidan nan, Kuma ko kallon banza babu wadda ta isa ta yi miki har da uwar tasa.” Shiru Zahra ta yi kamar me tunani sai kuma ta ce“Ina da kuɗi zan turo miki Anty.” Anty Khadijah ta gyada kanta ta ce“Toh shikenan. Ki daina kuka amma” Share hawayenta ta yi ta ce“In sha Allah Anty.” “Ki saki ran ki, kada ki nuna ran ki ya ɓaci, Ku tashi ki je ɗakinsa. Kada ki ce zaki yi fushi yanzu, ki kwantar da kan ki” Toh kawai Zahra ta ce sannan suka yi sallama ta kashe wayar. Ta tashi kamar yanda Anty Khadijah ta ce mata ta shige toilet, wanka ta yi ta fito ta ɗauki kayan baccinta ta saka sannan ta fito daga nata apartment ɗin ta nufi nasa. Koda ta shiga zaune ta same shi tsakiyar gado ya yi shiru da alama wani abun yake tunani, ta ƙarasa ciki ta zauna gefen gadon tana kallon sa ta ce “Doctor!” Tamkar a mafarki haka yaji muryar tata, Ya ɗago ya kalleta. Sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba, Ya ɗan yi jim kafin ya ce “Zahra lafiya? Ko nan ɗin ma zuwa ki ka yi ki tadan hankali?” Saurin girgiza kanta ta yi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce“A'a wallahi, dama zuwa nayi na baka haƙuri. Dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri, ba zan sake ba, wallahi kasa jurewa nake doctor, kai kan ka ka san ina sonka. A duk sanda naga Nana ta raɓeka ji nake kamar zuciyata zata fito, sai naji ba zan iya barinta ba. Dan Allah dan Annabi doctor ka fahimceni, koda zaka nuna mata soyyaya kada ka yi a gabana. Wallahi ba zan jure ba, Ita tana da kowa, tana da danginta wanda suke sonta. Tana da dangin miji wanda suke goya mata baya, sannan kuma tana da kai. Ni kuma bani da su, kai kaɗai nake da! Da kai na dogara. Idan ka gujeni bani da kowa....” Zahra ta ƙare maganar tana kallon sa hawaye na zubowa kan fuskarta. Ban da kallonta babu abin da Abdusammad ke yi, Ya sani Nana ta fita gata. Nana na da gatan iyaye, tana da na yayye sannan kuma ga gatan miji. Saɓanin ita da shi kaɗai ne gatanta sai kuma Allah, Tashi ya yi ya dawo kusa da ita ya zauna gefenta ya kama hannunta murya a sanyaye ya ce “Na sani Zahra, kuma kema kin san bani da niyyar wulaƙanta ki, ban aure ki saboda na cutar dake ba. Na aure ki ne saboda ina son ki, saboda na shirya zama dake, kuma zan kare mutuncin ki da martabarki. But why ki ke son ɓata kan ki? Akan me ki ka sauya? Ba haka ki ke ba da Zahra. Wannan ba ɗabi'un ki bane, Kin zama mara haƙuri, kin zama mara kunya, kin koyi rashin mutunci kala-kala. Faɗa min wane yake son gurɓata tunanin ki?” Ya yi maganar cikin tausasa harshe, Zahra dake kuka ƙasa-ƙasa ta ɗago kanta ta kalle shi sai kuma ta girgiza kanta ta ce “Dan Allah ka yi haƙuri, ba zan ƙara ba.” Murmushi yayi ya shafa kanta ya ce“Ba komai ni ban riƙe ki ba. Kuma idan sabon mota ki ke so ba sai kin fasa nata ba, sai ki faɗa min na sauya miki. Naga kina da cars har biyu kuma ba hawa ki ke ba, that's why yasa ban sa an kawo dake ba. But za'a kawo miki kema” Girgiza kanta ta yi ta ce“a'a wallahi, ka bar shi.” Bai ce komai ba ya jawota jikinsa ya rungumeta, Zahra ta saki ajiyar zuciya tana jin duk wata damuwar na narkewa. Washegari da safe ya shiga apartment ɗin Nana, tana kwance akan gado tana kallo, Ya ƙarasa ciki ya zauna kan drawer yana kallon ta ya ce “Madam ko gaisheni ba zaki yi ba?” Ko kallon sa bata yi ba ballantana ya saka ran zata kula shi. Ya ɗan yi murmushi yana shafa kansa kafin ya ce “Yau kuma me nayi?” . Tashi ta yi ta rufe system ɗin dan ba son jin muryarsa take ba, ta sauka daga kan gadon tana shirin barin wajen taji ya jawota. Ƙoƙarin kwance kanta ta dinga yi amma ta kasa, Ya matseta sosai a jikinsa ya ce “Ke me yasa baki son hutawa da rigima?” Rufe idanunta ta yi ba ta ce komai ba, Ya sanya hannunsa ya janye nata yana Murmushi ya ce“Ko kallo ban ishe ki ba kenan?” “Ni ka rabu dani...” Ta ce kamr zata yi kuka, harararta ya yi yana jan kumatunta ya ce“naƙi ɗin, ba zan rabu dake ɗin ba.” Nana ta buɗe idanunta tana kallon sa, murmushi kawai yake, Kasa ɗauke idanunta ta yi ganin yanda murmushin ke ƙara masa kyau. Ganin tana kallon sa ko kiftawa babu ya sanya shi ɗago fuskarta ya yi chopping face ɗinsu suna jin saukar numfashin juna ya ce “Me yasa ki ka faɗawa Hajiya Babba jiya? Bana ce miki ban da surutu ba.” Saurin janye fuskarta ta yi ta sauka daga jikinsa ta koma gefen gadon tana kallonta. Tasowa ya yi ya dawo kusa da ita ya jawota yana fadin “Ina magana kina share ni ko? Kin raina ni” Turo baki ta yi tana kallon sa ta ce“Ni wallahi ba zan yarda ba. Sai ta biyani motata, kuma sai na rama marin da ta yi min” waro idanunsa yayi yana kallon ta jin abin da take cewa. Lokaci ɗaya kuma ya yi kwanciyarsa kan gadon yana murmushi, Kallon sa ta dinga yi sai kuma ta kwanta ta ɗora kanta a ƙirjinsa ta ce ”Kaji uncle. Ka rama min” Murmushi kawai ya yi ya janye hular dake kanta yana shafa sumar kanta ya ce “To naji zan rama miki.” Ɗago kanta ta yi ta kalle shi, ganin yana dariya ya sanya ta tashi zaune tana kallon sa ta ce “wallahi ba rama min zaka yi ba. Ni bari naje na rama da kaina” Ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon, Ji ta yi ya jawota ya kwantar da ita gefensa ya ɗago yana kallon ta ya ce “Bana son rigimar banza. Ki bar ni na huta” Turo ɗan ƙaramin bakinta ta yi ta ce“To ba kace kana sona ba? Ai sai ka rama min duka. Kuma kana gani fa ta dakeni” Murmushi kawai ya yi, ta sake buɗe bakinta zata yi magana taji ya kame bakin, Zaro idanunta ta yi tana kallon sa. Ya lumshe idanunsa yana kissing ɗinta a nutse, Shiru Nana ta yi tana karɓar saƙon nasa. Ganin yana yawo da hannunsa a jikinsa ya sanyata zabura zata tashi, Ya sake maidata ya kwantar ya sakar mata nauyinsa.... Tun daga wannan ranar bata sake samun sukuni ba a wajen uncle ɗin nata, Baya taɓa barinta ta huta, kullum yana maƙale da ita. Idan ba ranar kwananta bane da rana sai ya kirata apartment ɗinsa, Sai dai idan baya gidan. Tun tana kin zuwa tana masa kuka har Itama ta saki jikinta ta saba dashi, A ɓangaren Zahra kuwa bata wani shiga sabgar su. Idan ba Noor ce ta dawo daga school ba bata sakkowa ƙasa, Ta zama so silent abin ta. A haka har kusan sati huɗu suka shuɗe, Ranar wata Alhamis da daddare Nana na zaune ɗakinta suna video call da Maimoon take faɗa mata Haule ma ciki ne da ita, Nana ta dinga dariyar keta. Maimoon kuwa murmushi ta yi ta ce “Banza mara hankali, To kema kwana nawa ne? Gara mu duk kusan tare zamu haihu mun huta. Ke kuwa ki yi ta fama” Taɓe baki Nana ta yi ta ce“an faɗa miki nima irin ku ce? Ke yaushe zaki haihu na ƙagu mu zo Yola” Maimoon ta yi dariya tana sha cikinta wanda ya ɗan fito babu laifi ta ce“Ke banza wata biyar fa, ban kusa ba.” Tsaki Nana ta yi ta ce“sai ki yi ta fama ai, Bari ki ga na tashi uncle ya kusa dawowa.” Riƙe haɓa Maimoon ta yi ta ce“tooo kaji matar uncle. Je ki to, abinci zaki girka masa?” girgiza kai Nana ta yi ta ce“ke A'a kwalliya zan yi” “Yau ke ce da kwana?” Maimoon ta tambaya tana murmushi. Gyaɗa mata kai Nana ta yi ta ce“Eh mana. Kuma kin ga mu dare ne” Jinjina kai Maimoon ta yi ta ce“to tashi ki je sai an jima ki gaida shi.” To kawai Nana ta ce sannan ta katse kiran, Ta rufe system ɗin ta tashi ta shige toilet. Wanka ta sake yi ta fito ta ɗauki wata rigar bacci mara nauyi fara ta saka, Ta shafa mai a jikinta sannan ta saka turare, bayan ta gama ta ɗauki lip gloss ta shafa a bakinta ta tsaya jikin madubi tana kallon kanta. Murmushi ta yi sannan ta koma ta zauna tana game. Sai wajen karfe 10 na dare sannan ta tashi dan ta daɗe da jin shigowar su, Ta nufa dakin kai tsaye tana tafe tana yan waƙoƙinta. Murɗa handle ɗin ƙofar ta yi bakinta ɗauke da sallama, Amsawa ya yi yana jikin mirror yana gyara kansa dan fitowarsa kenan daga wanka, Ta ƙarasa ciki tana zuwa ta rungumeshi ta baya tana murmushi. Hannunsa ya sanya ya jawota gabansa yana ƙare mata kallo, Ta yi kyau sosai, tayi ƙiba ta zama wata ƙatuwa kamar ba ƴar rigimar Nana ba. Hannunsa ya sanya ya fara ƙoƙarin goge lip gloss ɗin dake bakinta ya ce “Baki son uncle ya samu salama ko?” Turo baki ta yi tana janye nasa hannun a shagwaɓe ta ce“uncle ni kada ka gogen abuna.” Bai ce komai ba ya riƙo fuskarta ya zura bakinsa cikin nata ya fara kissing ɗinta. Ji ta yi ƙafafunta sun fara rawa, ta riƙe shi sosai tana sakin numfashi, Sun daɗe a haka kafin ya ɗauketa gaba ɗaya ya karasa gaban royal bed ɗinsa ya kwantar da ita. Tun tana biye masa sai da fara kuka dakyar ta samu ya rabu da ita ya koma gefe yana sauke numfashi. Ita ma juyawa ta yi tana shessheƙar kukanta, ta yi dana sanin biyo shi da ta yi, Dan da tasan abin da zai yi kenan da ba zata zo ba, After some minutes ya tashi ya nufi toilet abin sa. Wanka ya sake yi ya tsaftace jikinsa sannan ya dawo, Kallon ta ya dinga yi ganin har sannan bata daina kukan ba, Ya janyota jikinsa muryarsa a sanyaye ya ce “C'mon mene ne kuma?” Kamar jira take ta fara kukan da ƙarfi, Ya yi murmushi bai ce komai ya tashi da ita a jikinsa ya nufi bayi. Bayan ta fito ta gyara jikinta sai dai babu rigarta ko daya a ɗakin, Ya buɗe press ɗinsa ya zaro mata wata rigarsa armless yana kallonta ya ce “Zo ki saka wannan.” Kallon rigar ta yi sai kuma ta tura baki. Ya ƙaraso wajen ya bata, karba ta yi ta koma toilet ɗin, Bayan mintuna ta fito tana jan rigar dan ko cinyarta bata gama rufewa. Kallon ta ya dinga yi sai kuma ya yi murmushi ya ce“kuma ta yi miki kyau, ko na bar miki?” Ita dai bata ce komai ba ta karasa kan gadon ta yi kwanciyarta. Sai da ya gama duk abin da yake sannan shima ya kwanta, tana jin ya kwanta ta matso ta shige jikinsa, murmushi kawai ya yi yana shafa kanta ba'a ɗauki wasu mintuna ba bacci ya ɗauketa. Ringing ɗin wayar da yaji ne ya sanya shi juyawa, Ya janyo wayar dake kan bedside drawer. Numbern Safwan ya gani, Ya ɗaga yana murmushi. Kafin ya yi magana Safwan ya ce “Yayaaa...” Girgiza kai Abdusammad ya yi jin yanda ya yi maganar kamar wani ƙaramin yaro ya ce“Kai! Kai! Ba zaka daina wannan banzar ɗabi'ar ba ko?” Safwan dake kwance kan gado ya lumshe idanunsa ya buɗe kafin ya ce“To me nayi?” “Dan iskanci da girmanka ka dinga wata shagwaɓa? Kai ba mace ba ba komai ba? Ko baka ga matarka nada ciki bane? Kuma haihuwa zata yi” Murmushi Safwan ya yi ya ce“Allah ko Yaya? Ai nima na ƙagu Haule ta haihu, Allah ya sa ta haifi namiji na saka masa sunanka.” Murmushi shima Abdusammad ɗin ya yi kafin ya ce “To Allah yasa. Amma ya kamata ka mayar da yarinyar nan daƙinta before ta haihu” Shiru Safwan ya yi lokaci ɗaya jikinsa ya yi sanyi, Jin bai ce komai ba yasa Abdusammad ya ce “Heyy are you there?” Gyaɗa kansa ya yi sannan ya ce“Yaya ina son na maida ita, amma na san ba zasu bari ba. Babu wanda zai yarda, kuma nima bana son na cutar da rayuwarta. Wallahi Yaya ina son Haule, ina son zama da ita. To amma babu yanda na iya da ƙaddara!” Girgiza kai Abdusammad ya yi a sanyaye ya ce “Babu abin da zai faru. Ai kana shan magani, kuma idan har yarinyar ta amince zata iya dawowarta. Zai fi daɗi a ce a gidanka ta haihu, shi kansa abin da za'a haifa sai yafi samun nutsuwa” Jinjina kai Safwan ya yi ya ce“Ban sani ba ko Haule zata yarda. Amma ni babu wadda nake tsoro sama da Hajiya Babba, ba zata amince ba.” Numfasawa Abdusammad ya yi ya ce“Kada ka damu gobe idan Allah ya kai mu xan yi magana da Abba, za'a ga abin da za'a yi. Just keep pray kaji” Gyaɗa masa kai Safwan ya yi ya ce“to Yaya na gode. Ina Nana?” Kallon ta Abdusammad ya yi ya shafa kanta ya ce“bacci take.” “A gaisheta, Da Noor.” To kawai ya ce sannan ya ci gaba da jan shi da hira, Gajiya Abdusammad ya yi ya ce“kai mu dare ne. Sai da safe” Safwan ya yi dariya ya ce“To Allah ya tashe mu lafiya Yaya” Da Amin ya amsa sannan ya kashe wayar. Ya ja duvet ya rufe su sannan ya kashe bedside lamp ɗin duhu ya mamaye dakin, Addu'ar bacci ya yi mata sannan shima ya yi ya rufe idanunsa nan da nan bacci ya ɗauke shi. Washegari da safe wajejen 10:00 Nana na kwance kan cinyar Abdusammad tana yi masa hira aka fara buga ƙofar ɗakin. Janyeta ya yi daga jikinsa ya tashi ya sauka daga kan gadon, Tsaye ya ga Zahra tana kallon sa. Ganin duk a ruɗe take yasa ya ce “Lafiya dai?” “A.aaliyu ke kiran ka” Wayarsa dake hannunta ya kalla sai kuma ya karɓa ya kai kunne, Abdusammad ya yi shiru jin Aliyu bai ce komai ba yasa ya ce “Buddy kana jina?” Jan numfashi ya yi yana ƙoƙarin ɓoye kukansa ya ce “Eh ina ji.” Wata irin faɗuwar gaba yaji ta ziyarce shi, domin duk abin da ya saka Aliyu kuka to ba ƙaramin abu bane. Hankali a tashe Abdusammad ya ce “Lafiya? Kukan me ka ke?” Aliyu Ya girgiza kansa kukan na ƙoƙarin cin ƙarfinsa, Ya kasa koda magana. Tsaki Abdusammad ya yi a ɗan tsawace ya ce “Malam idan ba zaka faɗa min abin da ya faru ba na kashe wayata” Maimoon dake gefensa tana kuka ce ta karbi wayar muryarsa na rawa ta ce “Uncl... uncle Yaya Safwan!” Wata irin bugawa yaji zuciyarsa ta yi, Da ƙarfi ya ce “Me ya same shi! Ina Safwan ɗin yake? Jikin nasa ne?” Maimoon ta girgiza kanta cikin kuka ta ce “We lost him,Ya mutu Uncle!” 08106608363 Nanameera. Page 61. Wani irin abu yaji ya tokare masa a ƙirji, Ya sauke wayar ƙasa har sannan Maimoon bata daina kuka ba. Kallon sa suka dinga yi ganin yan da ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba, Nana ta taso ta ƙaraso wajen tana kallon sa. “Uncle mene ne?” Ta tambaye shi tana jan hannunsa, Ɗago idanun sa wanda suka rine ya yi ya kalleta lokaci ɗaya hawaye ya kawo kurmin idanun sa, Ya girgiza mata kai murya a sanyaye ya ce“Ya rasu!” Da sauri Nana ta saki hannunsa, Zahra dake kusa da shi ta ɗago kanta tana kallon sa cike da tashin hankali ta ce“Innalil lahi wa ina ilayhi raji'una! Ya mutu kuma?” Gyaɗa mata kai kawai Ya yi, Nana ta yi dinga kallon sa can kuma ta fara ƙoƙarin barin wajen sai ganinta suka yi a ƙasa Sumammiya. **** Yola/Nigeria. Safiyar ranar Alhamis suka sauka a garin, wajejen ƙarfe 8:00 na safe suka ƙaraso cikin estate ɗin. Nana ta dinga kallon compound ɗin wanda yake cike da al'umma, Abdusammad bai sake kallon su ba ya yi gaba abin sa. Zahra kuwa kallon Nana ta dinga yi ganin ita ma ta yi gaba abin ta, Rashin sanin wajen wanda zata ya sanya ta ja hannun Noor suka nufi apartment ɗin su, Nana na shiga ta tarar da Haule zaune kan kujera tana sanye da hijabi sai kuka take kamar ranta zai fita. Maimoon da su Hamida na zaune gefen ta suna kukan suma, A sanyaye Nana ta ƙarasa dan ita har ta yi kukan ta gaji, Ta zauna a ƙasa ba tare da ta cewa kowa komai ba. Suma da idanu kawai suka dinga kallon ta can dai Maimoon ta ce“Nana kun zo?” “Da gaske ya mutu? Da gaske Yaya Safwan ya rasu? Dan Allah Maimoon ki faɗa min!” Nana ta yi tambayar hawaye na zubowa akan fuskarta, Maimoon ta rufe fuskarta da Hijabin jikinta tana kuka tana girgiza mata kai, Nana ta kalle ta sai kuma ta fashe da wani raunataccen kuka. Haka suka dinga kuka a wajen babu mai rarrashi dan suma su Amma kukan suke mutuwar Safwan ta girgiza kowa. Abdusammad kuwa tun da ya zauna kusa da Abba bai ce komai ba, Bai kuma kalli kowa ba, Haka kuma ba kuka yake ba. Sai dai idanun sa sun kaɗa sun yi jajur kamar garwashi. Jijiyoyin kansa duk sun tashi, Ba lallai bane ka ga tashin hankalin da yake ciki. Domin babu alamar hakan akan fuskarsa, Cazbahar dake hannun sa kawai yaje ja a hankali yana motsa bakinsa. Cikin ransa kuwa shi kaɗai ya san abin da yake ji, Duk yanda yake da Safwan ko gawarsa bai samu damar gani ba, Ballantana ya yi masa kallon ƙarshe, rabon ba zasu haɗu ya sanya ya ƙi zuwa duk da yanda ya dinga takura masan. **** Babu wanda mutuwar Safwan bata daka ba a gidan, Kowa jikinsa ya yi sanyi. Musamman Haule wadda ta kasa dawowa daidai duk da sati biyun da aka ɗauka, Kullum yini take cikin ɗakin Amma tana kuka, wani lokacin Nana ta dinga taya ta, wani lokacin kuma ta rarrasheta. Ta kasa mantawa dashi a ranta, Sam bata yi tunanin rabuwa dashi ba, bata yi tunanin Safwan zai mutu yanzu ba. Ɓangaren Siyama kuwa ita gaba ɗaya ta fice daga hayyacinta, Babu wanda yake zuwa wajenta, Ko gaisuwa ba'a wani zuwar mata, Sai ɗaiɗaikun mutane idan sun zo suke cewa a kai su wajen matarsa. Ta zama wata abar tausayi da ita, Ta rame ta yi baƙi, Ita kanta bata yi tunanin mutuwa Safwan zai yi ba, Duk da ta san bashi da lafiya sosai daurewa kawai yake amma bata yi tunanin abun zai zamar masa haka ba. Idan ta tuna ita ce wadda ta shafa masa cutar sai taji ta ƙara tsanar kanta, Ko kaɗan ta kasa sukuni, ko abinci bata ci, babu mai rarrashinta. Anty Khadijah ce kawai ke zuwa gidan ta zauna da ita, wani lokacin kuma Amal da Safeena su zo. Zahra kuwa idan ta shigo da safe ta ganta bata sake komawa, Gaba ɗaya ma ba shiga harkar jama'ar gidan take ba. A haka har Sati uku suka shige, Ranar wani Alhamis misalin ƙarfe 4:00 na yamma Anty Khadijah ta buɗe ƙofar parlourn ta shigo, Zahra na zaune kan sofa ta yi yin game a wayarta. Ta kalleta sai kuma ta ajiye wayar a gefe tana cewa “Au Anty, Ke ce a gidan?” Anty Khadijah ta ƙaraso ciki ta zauna kusa da ita ta ce“Eh wallahi Zahra ni ce. Daman cewa nayi bari na biyo na duba ki, naje wajen Siyama ne.” Zahra ta ce“Okay Bari na kawo miki ruwa” Ta miƙe ta shige kitchen, Anty Khadijah ta bita da idanu, After some minutes ta dawo hannunta riƙe da plate mai ɗauke da kayan drinks. Ta ajiye mata a kan table sannan ta koma ta zauna, Murmushi Anty Khadijah ta yi ta ɗauki ruwa tana ƙoƙarin buɗewa ta ce “Wai ke ya zaman naku?” Taɓe baki Zahra ta yi ta ce“Wallahi gashi nan Anty, Babu wani daɗi. Ni dama jira nake komai ya lafa na miki magana, Ya ake ciki da kuɗin da ki ka sa na bayar?” Murmushi Anty Khadijah ta yi ta buɗe jakarta ta zaro wani ƙullin magani a baƙar leda ta miƙo mata tana cewa “Kin ga wannan shi ne maganin, wallahi idan ki ka yi aiki dashi yanda zan faɗa miki to nan bada jimawa ba sai ya saketa!” Ɗan zaro idanu Zahra ta yi ta dafe ƙirji ta ce“Saki kuma Anty? Na faɗa miki ba asiri ba kama shi zai yi ba. Wallahi shi ma ba'a zaune yake ba” Tsaki Anty Khadijah ta yi ta ce“Kaji banza, To wane ya ce miki shi za'a yi wa?” Zahra ta yi shiru kamar mai tunani, Can kuma ta ce“To wa za'a yi wa?” Wani murmushi Anty Khadijah ta yi tana juya ledar hannunta ta ce “Mahaifiyarsa za'a bawa!” Miƙewa tsaye Zahra ta yi tana kallon ta ta ce“Wai wa ki ke nufi? Hajiya Babba? So ki ke ya sakeni ni?” Wata uwar harara Anty Khadijah ta maka mata kafin ta ce“Ke daɗina dake bakya cin ribar zance, to wane ya ce miki zai sake ki? Ai ke da fita a gidan nan sai dai a mafarki, muddin ki ka yi amfanin da wannan, to wallahi ko a mafarkin ma ba zaki bar gidan nan ba.” Zahra ta dinga kallon ta jiki a sanyaye, Anty Khadijah ta miƙa mata ledar tana cewa“Ba fa wani abun zaki yi ba, kawai a abinci zaki zuba mata, Da zarar ta cinye shikenan! Sai yanda ki ka yi dasu duka” Zahra ta ɗan kalleta sai kuma ta amsa ledar tana kallon ta. Anty Khadijah ta gyara zamanta ta ce“Idan har kin yi yanda na ce to babu wanda ya isa ya raba ki da mijin ki, Ita kanta sai yanda ki ka yi da ita! Kawai a abinci zaki zuba. Ki duba girkin da tafi so ki yi mata, Idan ba haka ba ki ci gaba da zama ran ki na ɓaci a banza” Zahra ta sauke numfashi ta ce“Toh Anty. In sha Allah zan yi, ai abinci ne kawai, zan kai mata” Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya Anty Khadijah ta sauke kafin ta ce“To shikenan, Allah ya bada nasara. Ni bari ki ga na je” Ta ƙare maganar tana tashi tsaye. Itama Zahran miƙewa ta yi har sannan maganin na hannunta ta ce“Da wuri haka, da kin bari na gama abincin dare” Girgiza kai Anty Khadijah ta yi ta ce“A'a ba zan bari ba wallahi. Sauri nake, Wai ina yarinyar ne?” Taɓe baki Zahra ta yi ta ce“ai kin san tun da muka zo gidan nan tana apartment ɗin su, bata taɓa kwana anan ba, daga mu sai shi.” Jin jina kai Anty Khadijah ta yi cike da fahimta ta ce“To kin ga idan kin yi komai yanda ya dace sai dai ta yi ta zama a can!” Murmushi Zahra ta yi a sanyaye ta ce“Kai Anty, da wuri haka?” “Kina ɗauka wasa ne Zahra?” Girgiza kai ta yi har sannan tana murmushi, Anty Khadijah ta ce“To ki gwada ki ga, wallahi zaki yi mamaki” “In sha Allah Anty zan yi, gobe goben nan ma” Zahra ta yi maganar tana kallon ta. Jinjina kai Anty Khadijah ta yi ta ce“To Allah ya kai mu, Sai mun yi waya” Sallama suka sake yi sannan ta fice daga parlon, Zahra ta koma ta zauna tana sauke numfashi. **** Nana na zaune kusa da Haule wadda ta yi shiru ta yi nisa a cikin tunani aka buɗe ƙofar ɗakin, Atta ce ta shigo hannunta riƙe da wata warmer. Nana ta dinga kallon ta ba tare da ta ce komai ba, A gaban gadon ta zauna tana kallon Haule ta ce “Zo nan maza ga abinci na kawo miki, Yarinya ki dinga zama a haka? Sai wani abu ya samu ɗan cikin ki? To da me zamu ji? Da rashin uban sa ko kuwa da ke?” Ita dai Haule bata ce komai ba, Sai kallon ta take. Atta ta kalli Nana wadda ta yi shiru ita ma ta ce“Ke kawon faranti nan” Tura baki Nana ta yi tana miƙe ƙafarta ta ce“Ni fa Atta na gaji” Duka Atta ta kai mata tana cewa“Kin gajin uban ki? Dalla tashi ni!” Kamar zata yi kuka ta sauka daga kan gadon ta fice daga ɗakin. Zaune ta hange shi kan kujera, Abba na kusa da shi yana masa magana, Nana ta tsaya a wajen tana kallon sa, gaba ɗaya kamar bashi ba, Ya ɗan yi duhu ya kuma rame. Ta jima a wajen ganin bai ganta ba ya sanya ta nufi kitchen ɗin da sauri, Koda ta dawo parlourn bata same shi ba sai Abba kawai. Ta kalleshi ta ce“Abba!” Kallon ta Abba ya yi ya ce“Na'am Nana” “Ina uncle ya tafi?” Ta tambaya tana kallon sa itama. Dan murmushi Abba ya yi yana miƙe tsaye ya ce“Naji ya ce apartment ɗin Hajiya Babba zai je” To kawai ta ce sannan ta nufi ɗakinta da sauri. Miƙawa Atta plate ɗin ta yi, Atta ta warce tana cewa“Ke ban da banza ina ta jiran ki yarinya mai ciki kin bar ta da yunwa?” Tura baki Nana ta yi ta ce“To wai ba gashi na kawo miki ba?” Harararta Atta ta yi ta ce“Ki je dan kan ki, Ke kin zauna sa'annin auren ki duk sun kusa haihuwa ana ta abun arziki ke kin zauna!” Tura baki Nana tayi ta juya tana cewa“Ni ina ruwana! Ni yar iska ce to?” Riƙe haɓa Atta ta yi tana ƙoƙarin buɗe warmern gabanta ta ce“Kaji banza! Dan uba ki ƙarya ki ke yi ki ce baki san namiji ba, dama a ce bashi bane da sai na yarda!” Ita dai Nana kallon ta kawai take sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin. Babu kowa a parlorn dan haka ta fice da sauri, Tafiya ta dinga yi tana ɗan kalle-kalle. A bakin kofar gidan Hajiya Babba ta tsaya tana tunani, Can kuma ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Shi kaɗai ta hango kan kujera yana danna wayarsa, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ƙarasa ciki, Tsayawa tayi a gabansa a sanyaye ta ce “Uncle!” Jan hannunta ya yi ya zaunar da ita kan cinyarsa bayan ya ajiye wayar hannunsa ya ce“Na'am Nana, Kin ɓuya” Kwantar da kanta ta yi akan ƙirjinsa a shagwaɓe ta ce“To ai kaina baka nemana” ɗan waro idanunsa ya yi ya ce“Ni ɗin?” Gyaɗa masa kai ta yi, Ya ɗan murmushi ya ce“To na tuba. Ban samu sukuni bane, amma da zarar na samu ai zan neme ki” Shiru ta yi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa, Sun jima a haka kafin ta ɗago kanta tana kallon sa ta ce“Uncle!” “Babyn uncle!” Ya ce yana ɗaga mata gira. Murmushi ta yi ta ce“ka ci abinci?” Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi shima, Ta ɗan haɗe rai ta ce“Ni wallahi baka ci ba!” Ɗan zaro idanu ya yi ya ce“Ni na ce miki?” Tana ƙoƙarin yin magana aka buɗe ƙofar parlourn, Sultan ne ya shigo sai kuma ya sunkuyar da kansa a sanyaye ya ce“Afwan pls” Ya juya ya fice daga parlon, Shiru Nana ta yi lokaci ɗaya jikinta ya yi sanyi, Abdusammad da ke lura da ita ya ce “Mene ne?” Girgiza masa kai ta yi ta ce“Ba komai.” “Kin tabbata?” Ya ce yana kafeta da idanu, Gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh uncle” Murmushi ya yi ya ce“Alright” Ya yi maganar yana jan kumatunta. Murmushi ta yi sai kuma ta sauka daga jikinsa ta ce“Na tafi kada Amma ta neme ni” Gyaɗa mata kai ya yi dan bai ji zai iya riƙe tan ba ya ce“Okay bye” ta ɗaga masa hannu sannan ta fice daga parlourn. Da daddare bayan ya shiga gidan ya tarar da Zahra har ta yi shirin kwanciya. Bai ce komai ba ya juya zai bar dakin, Ta miƙe zaune ta ce“Doctor!” Cak ya tsaya, Ta ɗan yi murmushi ta ce“Daman zan tambaye ka ne” “Mene?” Ya ce yana juyowa, “Wane abinci Hajiya Babba ta fi so?” Da ɗan mamaki ya ce“me zaki yi da sanin hakan?” Girgiza kanta ta yi ta ce“A'a fa kawai dai na tambaya ne, ka faɗa min idan ba damuwa” Numfasawa ya yi ya ce“Tuwon shinkafa miyar egusi” Murmushi Zahra ta yi ta ce“na gode.” murmushin shima ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin, Zahra ta sauke numfashi sai kuma ta kwanta. **** Anty Khadijah na ƙoƙarin rufe jikinta da duvet wayarta dake gefen gadon ta fara ƙara, ta sanya hannunta ta dauka ganin lambar Kaddu ya sanya ta ɗaga wayar tana murmushi ta ce “Ƙawata ya aka yi? Fatan komai na tafiya dai-dai?” Murmushi Anty Khadijah ta yi ta ce “Ke dai bari, na bata kuma ta amsa, nan bada jimawa ba zan yi Wuff...” “Dashi!” Kaddu ta ƙarasa tana dariya, tuntsirewa da dariya Anty Khadijah ta yi ta ce “Nan bada jimawa ba zan zama matar Abdusammad, Zahra kuma zata fito, ita da waccan yarinyar!” 08106608363 Nanameera.Page 62. Murmusawa Kaddu ta yi cike da nishadin jin abin da ta ce, Anty Khadijah ta ce“Ke ni sai da safe dare ya yi” Sallama suka yi sannan ta kashe wayar, Ta kwanta tana tunanin irin rayuwar da zata yi a gidan Abdusammad Idan ta aure shi. **** Washegari da safe Nana na zaune gefen gado tana danna wayarta aka buɗe ƙofar ɗakin, Haule ce ta shigo hannunta riƙe da ƙaramin bowl, Nana ta kalleta amma bata ce komai ba. A gefenta ta ajiye ta juya zata fita, tashi Nana ta yi tana haɗe rai ta ce“Mene wannan?” A sanyaye Haule ta kalleta kafin ta ce“Atta ce ta kawo min, wai faten dankali ne.” Yatsine fuska Nana ta yi ta sauka daga kan gadon tana cewa“Taɓ, Ai sai ki yi ta zama tana kawo miki kayan ƙazanta kina ci.” Bata ce komai ba, Itama Nanan bata tsaya sauraren abin da zata ce ba ta fice daga ɗakin, Haule ta kalli bowl ɗin dankalin sai tiriri yake, Sai kuma ta sauke numfashi ta juya ta fice daga ɗakin. Zaune ta sameta a parlon ta kunna tv tana kalla tana cin chocolate, Haule ta nufi kitchen kai tsaye, Murfi ta ɗauko ta koma ɗaki. Ita dai Nana bata kalli inda take ba, After some minutes ta tashi tana ajiye ledar chocolate ɗin ta kunce veil ɗin data ɗaura a kanta ta yafa sannan ta fice daga parlourn. Apartment ɗin Maimoon ta nufa, Koda ta shiga zaune ta sameta akan kujera ta dafe cikinta wanda ya fito sosai. Nana ta ƙarasa ciki ta zauna tana cewa “Sannu matar nan!” Harararta Maimoon ta yi tana murmushi ta ce “Yauwa sannun ki ƴar nan” Nana ta tuntsire da dariya kafin ta ce“Me ki ka dafa?” “Ni bani nayi girki ba, Ya Aliyu ne ya yi idan zaki ci” Waro idanu ta yi tana murmushi ta ce“Shi Yaya Aliyun ne ya yi miki kirki ki ka ci? Lallai!” Taɓe baki Maimoon ta yi ta ce“To mene ne? Ai shi ne yake girki yanzu, Saboda ni ba zan iya ba, wahala nake sha.” Jinjina kai Nana ta yi tana riƙe da haɓarta ta ce “Eh lallai! Kin isa” “Idan ba zaki ci ba ki tashi ki girka naki daban” Tashi ta yi ta zare mayafin kanta ta nufi kitchen tana cewa“To tun da yunwa nake ji ai dole nayi girki.” Ita dai Maimoon kallon ta kawai ta yi sai kuma ta ɗauke idanunta, Nana na shiga kitchen ɗin ta fara buɗe-buɗen kaya tana duba abin da zata dafa, Can dai ta yanke shawarar yin shinkafa da wake dan tana ɗaya daga cikin abincin da take so. Sai da ta tsince waken wanda ya kasance manya sannan ta wanke ta zuba a tukunya ta ɗora, Ta koma parlour tana kallo time to time tana zuwa tana dubawa, Bayan ya dahu ta zuba shinkafar wadda bata da yawa sannan ta saka gishiri da maggi ta rufe, Ta tsaya ta fara yanke-yanken kayan lambunta har ta gama, ta wanke sannan ta ajiye gefe. Bayan ta sauke abincin ta zuba a plate ta zuba salad ɗin data yanka da cabbage da cucumber ta ɓare kwai guda biyu ta ɗora akai, Robar yajin da tagani a wajen ta ɗauka ta fito parlour, Turus ta yi ganin Aliyu zaune shi da Abdusammad, Maimoon na zaune tana kallon su, Jiki a sanyaye ta ƙarasa parlourn ta ajiye wayar plate ɗin akan table ta koma ta zauna kusa da Maimoon. “Nana daman kina nan?” Gyaɗa masa kai ta yi sannan ta ce“Eh Yaya ina nan, ina kular maka da matarka” wata harara Maimoon ta watsa mata kafin ta kalleshi a shagwaɓe ta ce“Wallahi Yaya ƙarya take, tsokanata kawai take.” Taɓe baki Nana ta yi ta mai da Idanunta kan Abdusammad wanda bai ce komai ba tun ɗazu ta ce “Unclee...!” Ɗaga mata gira ya yi ya ce“Na'am” “Ba zaka kulani ba?” Ta tambaya tana marairaice fuska. Ɗan murmushi ya yi sannan ya yi mata alama da ta zo da hannu, Ta tashi jiki a sanyaye ta ƙarasa inda yake ta zauna gefensa. Dafa kanta ya yi murya a nutse ya ce “Ƴar rigimar uncle” Jingina kanta ta yi akan kafaɗarsa ta ce “Uncle...” Murmushi ya yi ya ce“Nana kar sunan ya ƙare” Turo baki ta yi ta ce“To ba zan kira ka ba?” Girgiza mata kai ya yi yana kallon plate ɗin data ajiye ya ce“Ni na nace miki?” Murmushi ta yi ta tashi daga wajen tana kallon Maimoon dake kallon ta, Ta ɗauki plate ɗin ta koma inda yake ta zauna tana miƙa masa ta ce “Uncle ga abinci da kaina na girka maka, anan gidan wai Yaya Aliyu ne yake girki..” ta ƙare maganar tana dariya, Kallon ta ya yi sai kuma ya kalli Aliyu wanda ke murmushi, Fuskarsa a tsuke ya ce “Kai ne ka koma girkin abincin?” Gyaɗa masa kai ya yi kafin ya ce “Eh mana, tun da bata da lafiya ai dole na taimaketa.” Jinjina kai Abdusammad ya yi yana shafa gemunsa, Aliyu ya kalli Maimoon ya ce “Tashi muje ciki ki kwanta” Jiki a sanyaye ta miƙe ya yi gaba yana riƙe da hannunta, Gaba ɗaya kunyar Abdusammad ɗin ta rufeta. Shi kuwa ɗauke kansa ya yi yana taɓe baki. Bayan sun bar wajen ya mai da idanunsa kan Nana wadda ke danna wayarta, kamar ba zai magana ba sai kuma ya sanya hannu ya karbi wayar yana kalla, Game take as usual, Ya ɗan yi murmushi ya ce “Ke ba zaki taɓa girma ba ko?” Turo baki ta yi ta kawo hannu zata amshi wayar, Ya ɗauke yana tsuke fuska ya ce“Ina wasa da ke?” “Uncle ka bani wayataaa.!” Ta yi maganar kamar zata yi kuka, Bai ce komai ba ya zura a aljihunsa yana ɗauke kansa, Ta dinga kallon sa sai kuma ta fara hawaye tana cewa “Ka bani dan Allah.” Ba zaka taɓa cewa dashi take ba dan ko kallon ta bai yi ba, Ganin tana shirin ɓare baki ya sanya shi kallon ta fuskarsa a tamke babu alamar wasa ya ce “Kina min kuka ina buge ki anan, Ɗauka abincin ki.” Ya yi maganar yana nuna mata plate ɗin data ajiye a ƙasa. Kasa cewa komai ta yi, ganin yanda ya yi da fuska, Ya dauko plate ɗin abincin ya ɗiba a spoon yana kallonta ya ce “Haaa..” Kallon sa ta tsaya yi, Ya ajiye spoon ɗin ya rankwasheta a goshi, Dafe goshinta ta yi tana marairaice fuska kamar zata yi kuka. Ya sake diban abincin ya kai mata baki, Babu yanda ta iya haka ta buɗe bakin, Ya dinga feeding ɗinta har ta kusa cinyewa. Bayan ta gama ya ɗora mata plate ɗin akan cinyarta sannan ya ce “Oyah tashi anan. Sai da safe” “Sai da safe kuma? Yanzu fa rana ce” “To ko zaki bi ni ne?” Ya yi maganar yana miƙewa tsaye, Gyaɗa masa kai ta yi duk da bata san inda za shin ba. Bai ce komai ya juya ya fice daga ɗakin, Ta ajiye plate ɗin a wajen ta biyo bayansa tana gyara zaman mayafin kanta. A compound ɗin ta same shi yana shirin buɗe motar sa, Ta ƙaraso wajen da sauri tana cewa “To ba zaka tsaya ni ba?” “Za dai ki bi ni ki ka ce?” Ya yi tambayar yana ƙoƙarin shiga motar, Gyaɗa masa kai ta yi. Ya jinjina kansa ya ce“Zagayo to” Da sauri ta koma ɗaya side ɗin ta buɗe ta shiga tana murmushi. Shi dai bai ce mata komai ba ya yi motar key suka bar compound ɗin. Tun Nana na kallon titi tana murmushi har sai da ta fara kallon sa da mamaki, ganin tafiya kawai suke yasa ta ce “Uncle.” Sam bai ji ta ba, Saboda yanda ta yi maganar a can ƙasa shi kuma yana bin karatun Alkur'anin da ya kunna. Ta sanya hannunta ta taɓa shi ta ce“Unclee...!” Sai a sannan ya ɗan kalleta, Ya rage volume ɗin karatun ya ce “Mene ne?” “Ina zamu je?” Ta ce kamar zata yi kuka, Ɗan murmushi ya yi ya ce“Sai da ke zan yi.” Dariya ta yi ta ce “Sai dani kuma? Ni ɗin?” Gyaɗa mata kai kawai ya yi sannan ya ƙara volume ɗin karatunsa, Ita ma bata sake cewa komai ba ta mai da kanta jikin mirror tana kalle-kalle. A bakin wani ƙaton mansion ya ɗan yi parking, Nana ta dinga kallon gidan dan bata taɓa ganinsa ba. Horn ya danna aka zo aka buɗe gate ɗin, Ya tura hancin motar ciki. A tsakiyar compound ɗin gidan ya yi parking sannan ya kashe motar ya sakko, Nana ta buɗe side dinta ta fito tana karewa babban compound ɗin kallo. Iyakar haɗuwa wajen ya haɗu, Ya ja hannunta suka nufi main entrance ɗin gidan, Wani katon parlour ne wanda aka ƙawatashi da kujeru na alfarma, Sai tv babba sai curtains masu kyau da tsada, Bai zauna a parlourn ba ya ja hannunta suka nufi sama. Ita dai Nana sai bin sa take da kallo duk inda ya yi, Wani ɗaki ya buɗe ya shiga yana rike da hannunta, Babban bedroom ne mai ɗauke da furnitures da kuma kujera, ya saki hannun ta yana ƙoƙarin kwance agogon hannun sa.. “Bari na kwance ma” Yaji saukar muryarta tana ƙoƙarin taɓa hannunsa. Bai ce komai ba ya dinga kallon ta har ta kwance agogon ya juya ya bar wajen ita kuma ta nufi gefen gado ta zauna tana riƙe da agogon. Tana nan zaune har kusan 20mins kafin ya fito daga toilet yana sanye da bathrobe, Nana ta dinga kallon sa dan bata yi tunanin wanka ya yi ba. Press ya buɗe ya ɗauki wasu kaya masu sauƙin nauyi ya saka sannan ya dawo gefen gadon yana kallon ta ya ce “Ba zaki yi wanka ba?” Girgiza masa kai ta yi kafin ta ce“Nayi ai.” Bai ce komai ba ya hau tsakiyar gadon ya kwanta, Ta daɗe zaune a wajen kafin taji ya ce “Baki jin bacci?” Kallon sa ta yi sai kuma ta girgiza masa kai duk da baccin data fara ji. Ya ɗan yi murmushi sannan ya jawo hannunta, A gefen sa ya kwantar da ita ya zame mayafin kanta gashinta mai kyau wanda ya sha gyara ya bayyana, A hankali ya kai hannunsa ya fara shafa gashin, Nana ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe idanun ta. After some minutes ta fara ƙoƙarin tashi zaune jin abin da yake yi ta ce “Uncle mu tafi gida!” Hannu ɗaya ya sanya ya dawo da ita ya kwantar yana murmushi ya ce “Ba rakoni ki ka yi ba?” Girgiza kanta ta yi jin yana ƙoƙarin jan rigar jikinta ta ce“a'a ni gida zan je! Wallahi gida zan je uncle...” Bai tsaya saurarenta ba ya haɗe bakinsu ya fara sauke mata wasu irin kisses masu tsayawa a rai, Nana ta dinga ƙoƙarin kwace kanta amma hakan ya gagara dan ƙarfi ya sakar mata. Tun tana dauriya da shi har sai da ta fara kuka, amma sam bai san tana yi ba ya ci gaba da abin da ya yi niyya.. Sai da dan kansa ya haƙura ya koma gefe yana sauke numfashi. **** Basu suka dawo gidan ba sai wajen karfe 6:00 na yamma, Yana gama parking ta buɗe motar ta fita babu ko sallama, Murmushi kawai ya yi yana girgiza kansa sannan ya yi gaba, Bayan ya fito daga motar yana ƙoƙarin shiga gidan Noor ta tawo da gudu ta rungumeshi tana dariya. Sunkuyawa ya yi ya ɗauketa yana murmushi ya ce “Noor ina ki ka je?” “Naje wajen Anty Juwaira ne Abbie.” Jinjina kansa kawai ya yi sannan ya buɗe kofar suka shiga, Babu kowa a parlourn sai tashin ƙamshi da yake. Ya kalleta ya ce“Muje ciki ko?” gyada masa kai ta yi suka nufi upstairs tare, Zahra dake kitchen tana girki sam bata ji shigowar su ba. Ta ƙarasa kwasar kayan abincin ta fita dasu ta ajiye a parlourn, Da sauri kuma ta koma kitchen ɗin, ledar maganin data zuba ta ɗauka ta yar a shara sannan ta gyare ko ina ta fito. Zaune ta same shi a parlour yana danna wayarsa, ta dinga kallon sa da mamaki can kuma ta ce “Doctor dama ka dawo?” Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh na dawo, Ai naga kamar kina aiki ne” Murmushi ta yi ta ce“Ai na gama ma, Daman abincin Hajiya Babba ne.” “Kin yi abincin ne?” Gyaɗa masa kai ta yi tana murmushi, Ya ɗan jinjina kansa fuskarsa a sake ya ce“Su Hajiya masu surukai. To maza ki kai mata” “Zan fara wanka ne” Toh kawai ya ce, Ya nufi sama da sauri. Ko minti biyar bata yi da hawa ba Noor ta sakko tana riƙe da teddy ƙato a hannunta, Ta ƙaraso wajensa tana dariya ta ce“Abbie!” Murmushi ya yi ya ja kumatunta ya ce “Nooriya!” “Abbie yunwa nake ji!” Ta yi maganar tana yatsine fuska, Girgiza kansa ya yi ya ce“Da gaske? Ko zaki ci tuwo to?" gyaɗa masa kai ta yi, Ya kalleta sai kuma ya kalli inda Zahra ta ajiye warmern ya ce “To bari na baki.” Daga haka ya tashi ya ƙarasa gaban warmern, A kitchen ya saka ta ɗauko plate ya buɗe warmern farko, Tuwon shinkafa ne wanda ya yi kyau an zuba shi a ledoji, Ya ɗauki ɗaya ƙarami ya raba biyu ya saka mata rabi dan ya san ba cin abinci take ba, Sannan ya buɗe ɗayan ya ga miyar egusi ce lafiyayya, Da ɗan yawa ya zuba mata miyar ya miƙa mata, Karɓa ta yi sannan ta yi masa kiss a kumatu ta ce ”Thank you Abbie.” Murmushi kawai ya yi sannan ya tashi ya koma kan kujera ya zauna, Itama ta koma can kujerar da ke kusa da tv ta zauna ta fara cin tuwon tana lumshe ido. 08106608363 Nanameera. *Page 63*. Amma ta dinga kallon ta babu yabo babu fallasa ta ce“Shi ne ki ka yi wannan daɗewar?” Sunkuyar da kanta ta yi a sanyaye ta ce“Eh fa Amma. Kuma ai har da uncle ma yana can” Taɓe baki ta yi ta tashi tana kallon ta ta ce“Tashi ki dafa min shinkafa”Toh kawai ta ce sannan ta miƙe ta nufi kitchen duk da yanda take jin jikinta babu gwari. Ruwan shinkafar kawai ta ɗora ta fito ta dawo parlour ta zauna tana jiran ya tafasa, Haule dake zaune kan kujera ta kalleta ta ce“Nana ɗazu Atta ta ce na kira ki” Kallon ta Nana ta yi tana riƙe da wayarta ta ce“To ni ba zan je ba wallahi, haka kawai ta dinga zagina.” Ita dai Haule bata sake cewa komai ba ta ci gaba da kallon ta, After some minutes ta tashi ta koma kitchen ɗin dan duba abin da take. **** Zahra ta sakko tana kallon Noor dake cin tuwon a hankali dan daman ita ba gwanar cin abinci ba ce, Da mugun mamaki ta ƙaraso wajen, Ta ɗago kanta hankali a ɗan tashe ta ce “Ke! Wane ya baki wannan abincin?” Noor ta kalleta ganin yanda take zare ido ya sanyata sunkuyar da kanta, Ta daka mata tsawa ta ce “Ba magana nake miki ba?” Sai a sannan Abdusammad ya kallesu dalilin tsawar da yaji, Ya buɗe baki cike da mamakin ganin yanda ta cakume yarinyar ya ce “Zahra lafiya dai?” Kallon sa ta yi sai kuma ta mai da Idanunta kan Noor ta ce“Ba zaki faɗa min ba? A ina ki ka samu tuwo?” “Abincin da zaki kai wa Hajiya Babba ne na ɗibar mata tana jin yunwa, mene?” Wani irin abu ne ya zo ya tsaya mata a ƙirji, Ta saki rigar Noor tana jin zufa na yanko mata, Abdusammad da ke lura da ita ya ce“Ko akwai wata matsala ne?” Girgiza masa kai Zahra ta yi tana ƙoƙarin magana Noor ta saki wani irin ihu tana wurgi da plate ɗin hannun ta. Da sauri ya taso ganin yanda take ƙandare jiki tana dafe da cikinta, Zahra ta yi saurin durƙusawa gabanta ta riƙeta tana jijjigata, Yana zuwa ya sanya hannunsa ya ɗauketa ya zauna akan kujerar ya riƙe fuskarta ya ce “Ke Noor! Noor mene ne?” Ɗan ƙaramin hannunta ta saka ta riƙe nasa muryarta na rawa ta ce “Ab...Abbi... Abbiena..” Wani irin faɗuwar gaba yaji ya ziyarce shi, Ya riƙeta sosai a jikinsa ya ce“Mene ne?” Kasa magana ta yi sai kuka da take a hankali, Ya kalli Zahra wadda ke kuka ita ma ya ce“Kawon ruwa” Toh kawai ta ce sannan ta nufi kitchen da gudu, Abdusammad ya tallafi fuskarta a hannunsa yana kallon ta ya ce “Nooriena, Me ya faru?” Ta kasa magana sai hannunsa data ɗora kan cikinta ta runtse ido, Kallon cikin ya yi sai kuma ya taba wuyanta yaji wani irin zafi, Gaba ɗaya sai ya rikice, dan bai san abin da ya sameta ba. Ya girgiza kansa ya ce “Cikin ki ne yake miki ciwo?” Gyaɗa masa kai ta yi tana ƙoƙarin magana sai ga dafara ta fara fitowa daga Bakinta. Abdusammad ya miƙe tsaye da ita a hannunsa cikin wani irin yanayi mai kama da tashin hankali ya ce “Noorie stay still, Bari na kai ki asibiti.” “Abbiena...!” Yaji ta kira sunansa idanunta na neman rufewa, Hannunsa ya sanya ya bubbuga fuskarta ya ce“Na'am Noor!” Bata ce komai ba ta buɗe Idanunta wanda hawaye ke zubowa ta gefensu ta kalle shi, Sai kuma ta sake rufewa. Ji ya yi ta kwanto a jikinsa, Jikinta ya saki gaba ɗaya, Da wani irin tashin hankali ya ɗagota ya tallafeta a hannunsa yana girgizata ya ce “ke! Ke Noor! Noor!” Shiru babu amsa, Ya sauketa a wajen ya shiga taɓa jikinta, Babu alamar tana numfashi. Zahra ta dawo parlourn hannunta riƙe da cup da ruwa, Ta yi saurin sakin su a ƙasa ganin yanda yake kiran sunan Noor ɗin bata amsawa. Durƙushewa ta yi a gabansu ta fara ƙoƙarin tashin ta tana kuka, Abdusammad ya yi jim sai kuma ya ɗauketa ya fice daga parlourn da sauri. Da gudu Zahra ta biyo bayansu, Ta tarar har ya shiga back seat tabi bayansu da sauri. **** Amma ta toshe hancinta saboda ƙaurin da taji, Ta ƙarasa gaban gas ɗin dakyar ta buɗe tukunyar. Gaba ɗaya shinkafar ta yi baƙi ta babbake, Sai ƙauri ke tashi, ta kashe gas ɗin sannan ta juya ta fice daga kitchen ɗin rai ɓace tana kiran sunan Nana.. A parlour ta sameta tana baccinta hankali kwance, Amma ta kai mata duka tana kiran sunanta a fusace. Buɗe idanu Nana ta yi ta dinga kallon Amma sai kuma ta tashi zaune tana mitsitsika idanu, Amma da ranta yake a ɓace ta ce “wani sabon iskancin ne ya sanya ki ka bar min abinci ya babbake? Meke damunki Nana?” Saurin rufe bakinta ta yi da hannunta sai kuma ta tashi tsaye tana ɗaukan hular ta ta ce“Wallahi bacci ne ya ɗaukeni Amma..” ta nufi kitchen ɗin da sauri, Tana shiga ta samu Amma ta kashe gas ɗin, Ta buɗe tunkuyar sai kuma ta yi saurin rufe bakinta tari na tawo mata. Rufewa ta yi ta juya ta fice daga ɗakin, A tsaye ta samu Amma inda ta bar ta, Ta dinga kallon ta ganin irin yanda ta haɗe rai, Jiki a sanyaye ta ce “Ki yi haƙuri Amma, wallahi....” Dakatar da ita Amma ta yi ta hanyar ɗaga mata hannu, Rai ɓace ta fara cewa “Wato ke ba zaki taɓa hankali ba? Ba zaki nutsu ba? Mene ne amfanin auren da ki ka yi? Haka ki ke a gidan mijin ma kina bari ana zagina. Ace common white rice ba zaki iya dafawa a nutse ba? Uban ki ki ke yi?” Girgiza kai Nana ta yi jiki a sanyaye ta ce “Dan Allah Amma ki yi haƙuri, baccin ne ya ɗaukeni ban sani ba.” “Ai dole bacci ya ɗauke ki! Dole mana! Tun da baki san abin da ki ke ba. To na rantse duk ranar da ki ka sake yimin irin wannan abun sai ran ki ya yi mummunan ɓaci, Kuma ki sani daga yau har ranar da zaki bar garin nan ke ce zaki dinga girka abinci, Ke zaki dinga aiki, duk wani abu da ki ka san ana yi a gida kece zaki dinga yin sa. Idan kin so ki ci gaba da ba dai-dai ba!” Amma ta ƙare maganar tana harararta, Sai kuma taja tsaki ta bar wajen, Ita dai Nana bata iya ko motsi ba, Dan ta san halin faɗan Ammar. Sai da taga ta shige daƙinta sannan ta ƙarasa kan kujera ta zauna, Ko minti biyu kuma bata yi ba ta kwanta wani baccin ya sake ɗauketa.. **** Tun da aka shiga da ita yake kai komo a wajen, Zahra kuwa sai kuka take ta ɗora hannunta aka. Kusan 30mins kafin Sultan ya buɗe ƙofar ɗakin ya fito, Da Sauri Abdusammad ya ƙarasa gabansa muryarsa a dake ya ce “Ya jikin nata? What happened to her?” Kallon sa Sultan ya dinga yi, ya kasa cewa komai. Abdusammad ya ɗan kanƙance idanunsa kafin ya ce “Sultan mene haka? Do i look like ur mate?” Girgiza masa kai ya yi, Abdusammad ya kalle shi sai kuma ya sanya hannu ya hankaɗeshi daga wajen ya buɗe ƙofar ɗakin ya shige. Zahra na ganin haka tabi bayansa da sauri, Sultan ya sauke wani zazzafan numfashi hawaye na biyo idanun sa. Kwance Abdusammad ya sameta, Sai dai ya kasa gane dalilin daya sanya suka rufeta har fuska, Ya ƙarasa gaban gadon ya zauna ya buɗeta. Fuskarta fresh kamar wadda ke murmushi, asalin kamarta dashi ya sake bayyana, Ya kai hannunsa ya taɓa ta a sanyaye ya ce “sorry ƴar gidan Abbie, zaki samu sauƙi.” Zahra dake tsaye ɗan nesa dashi ta kalleta jin abin da ya ce. Ta sauke ajiyar zuciya tana dafe ƙirjinta, Sultan ne ya shigo ya tsaya a ɗaya side ɗin gadon yana kallon su, Ganin yanda yake ta nanata zata samu sauƙi. Sun daɗe a haka kafin Abdusammad ya mai da bargon ya rufeta amma ban da fuskarta, Ya tashi tsaye yana kallon Sultan ya ce “Me ya sameta?” Kallon sa kawai Sultan ya yi idanunsa cike taf da hawaye. Abdusammad ya girgiza kansa rai ɓace ya ce “Sultan yaushe ne na fara wasa da kai?” Jiki a sanyaye ya girgiza kansa yana ƙoƙarin ɓoye damuwarsa ya ce “Yi haƙuri Yaya. But we lost her!” Tamkar mafarki, ko kuma almara haka Abdusammad yaji kalaman Sultan na ƙarshe. Ya ɗan ware idanun sa yana son fahimtar abin da ya ce, Sultan ya sake Girgiza kansa wannan karon hawaye na zubowa kan fuskarsa ya ce “Yaya a ina Noor ta samu guba? Wane ya bawa Noor abinci? A ina ta samu guba!" Wani irin ihu Zahra ta saki sai gata a ƙasa Sumammiya, Abdusammad da ya kasa koda motsi daga inda yake ya sunkuyar da kansa sai sauke ajiyar zuciya yake akai akai. Da sauri Sultan ya nufi inda Zahra take yana kallon ta, Sai kuma ya fice daga ɗakin da sauri, Not too long suka dawo tare da wasu nurses mata guda uku, Akan wheelchair suka ɗorata suka fita daga ɗakin. Har sannan Abdusammad bai motsa daga inda yake ba, Gumi ne kawai ke tsatsafo masa duk da acn dake wajen, Zuciyarsa ta kasa yarda da abin da Sultan yake, Tunanin sa ya tsaya cak, ƙwaƙwalwarsa ta toshe. Yana nan tsaye har after 15mins Sultan ya dawo, Ya dinga kallon sa cike da tausayawa, Ya san ba lallai a fahimci halin da yake ciki ba, domin kuka ko magana baya ɗaya daga cikin abin da yake yi yayin da baƙin ciki ya yi masa yawa. Sultan ya sauke numfashi ya ƙarasa inda Noor take ya rufe mata fuskarta, Yana ƙoƙarin ɗagowa yaji Abdusammad ya riƙe hannunsa gam, Cikin wata irin kakkausar murya ya ce “Don't ever try that!” Sultan bai ce komai ba ya janye jikinsa ya bar ɗakin, Abdusammad ya zauna gefen gadon ya ɗaukota ya ɗora a jikinsa, Ya sanya hannunsa ya tallafi fuskarta muryarsa a sanyaye ya fara cewa “Noorie! Noorien Abbie, Kina jina ko? Kina ji ko? Ai ƙarya suke yi na sani, babu abin da ya same ki, kina nan tare da Abbie, Ba zaki bar ni ba na sani. I know!” Bata bashi amsa ba, Domin bata jin abin da yake cewa, ruhin ta ya yi ƙaura daga gangar jikinta, Jin bata ce komai ba ya sanya shi girgiza kansa yana ɗan murmushi ya ce “Fushi ki ke yi da Abbie? Ki yi haƙuri kin ji. Next time zan kawo ki asibiti da wuri, But...!” Sai ya sami kansa da yin shiru, Ya zubawa kyakkyawar fuskarta ido yana kallon ta, ba zaka taɓa cewa bata raye ba, Kamar bacci take..irin baccin data saba yi da yamma ta tashi bayan magriba, Wani lokacin kuma idan ta yi baccin shikenan sai gobe. Yana nan zaune sama da mintina ashirin bai sani ba, Shi kansa bai san a wane hali yake ba. Idanunsa dai har sannan na kan fuskarta, Buɗe kofar ɗakin aka yi, Ya daga idanunsa yana kallon su. Abba ne ya shigo sai Aliyu a bayansa, Ya yi saurin cewa “Yauwa Abba zo kaji wai Noor ce taci guba? A ina Noor ta samu guba?” Girgiza kai Abba ya yi ya janye Noor daga hannunsa ya miƙawa Aliyu, Abdusammad zai yi magana Abba ya kama hannunsa a sanyaye ya ce “Muje gida tukun” “But Abba ai bata ji sauki ba, Ya za'a yi mu tafi gida da ita a haka? At least ta samu lafiya” Abba ya gama gane ba fahimta yake ba, Dan haka ya shafa kansa ya ce “To shikenan sai a dawo da ita. Muje yanzu kaji" Bai ce komai ba yabi bayan Abba dan tuni Aliyu ya fice da ita. A compound ɗin Hajiya Babba suka yi parking, Abba ya fito yana kallon Abdusammad wanda ko motsi bai yi ba, Zagayowa ya yi ya kama hannunsa ya fito daga motar ya ce “Abdussamad muje” Gyaɗa masa kai kawai ya yi sannan suka nufi cikin gidan Hajiya Babba, Shimfiɗe ya samu Noor akan carpet an rufeta da farin kyalle har kanta, Ya yi saurin sakin hannun Abba ya ƙarasa ya yaye kyallen cikin ɓacin rai ya ce “Bana son irin haka! Kada wanda ya sake rufe min ƴa, akan me?!” Shiru duk suka yi, Hajiya Babba da ke zaune ta dinga kallon sa, Tausayi ya bata ta san irin son da yake yi wa Noor ɗin, Ta san irin shaƙuwar da ke tsakaninsa da ita. Dan haka ta san dole zai shiga hali na ɗimuwa. Abba ne ya yi ƙarfin halin zuwa gabansa ya dafa shi, Abdusammad ya ɗago idanunsa ya kalleshi sai kuma ya tashi tsaye ya ce “Abba ka ce su daina rufe min ita, akan me? Me ta yi musu? Yarinyar nan karama ce sai ta kasa numfashi?” Girgiza kai Abba ya yi yana jin wani irin zafi a ransa, Ya dafa shi hawaye na ƙoƙarin fitowa daga cikin idanunsa ya ce “Abdul ka yi haƙuri kaji! Allah shi ne ke bada haihuwa, Shi ne ke bamu ɗa, kuma shi ne ke karɓa a duk sanda ya so, Duk mai rai mamaci ne, dole sai kowa ya mutu. Dan haka ka ɗauki haƙuri, Allah ya yi mai ƙaramin kwana ce, Allah ya yi ba zaka girma da ita ba, Ka yi haƙuri!” Janye hannun Abba ya yi daga jikinsa ya ce“Bangane ba Abba, meya sameta to?” “Ta mutu!” Abba ya faɗa kai tsaye, Wani irin abu ne ya zo ya tokare masa a ƙirji, Ya ja wani irin dogon numfashi sai kuma ya dafe kansa saboda sara masan da ya yi. Abba ya riƙe shi ya ce “Ka nutsu dan Allah.” Jinjina kansa ya yi ya juya yana ƙoƙarin komawa inda take, Sai dai kafin ya ƙarasa yaji kamar an daki ƙirjinsa sai gashi a ƙasa a sume. 08106608363 Nanameera.*Page 64.* A hankali ya shiga buɗe idanunsa wanda suka yi masa nauyi, Motsin da taji ya sanyata riƙe shi muryarta a sanyaye ta ce “Uncle.” Kallon ta ya yi amma bai ce komai ba, Nana ta shiga goge hawayenta tana kallon sa. Buɗe kofar ɗakin aka yi, Abba ya shigo yana kallon su ya ce “Nana ya tashi ne?” A sanyaye ta gyaɗa kanta tana janye hannunta daga nasa, Abba ya ƙaraso wajen ya zauna gefen gadon yana kallon sa ya ce “Abdul ya jikin?” Lumshe idanu Abdusammad ya yi kafin ya ce “Abba da gaske Noor ta mutu?” Wani irin abu ne ya tsayawa Abba arai, Ya jinjina masa kai a sanyaye. Bai ce komai ba ya sake rufe idanunsa, Abba ya kalli Nana wadda ke kuka a hankali ya ce “Tashi ki je ina zuwa.” Toh kawai ta ce sannan ta mike ta fice daga ɗakin, Abba ya gyara zamansa yana kallon sa sosai a nutse ya ce “Ka yi haƙuri Abdusammad, na sani babu daɗi, kowa ma yaji babu daɗi. Amma dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri, kayi mata addu'a, Allah yasa mai ceto ce.” A hankali ya tashi zaune, Abba ya dinga kallon sa jin bai ce komai ba. Can ya sauke numfashi ya ce “Ba komai Abba, Na sani Allah ya jiƙanta.” Sosai Abba yaji sanyi a ransa, dan ya san tun da ya ce haka to ya bar zancen. A sanyaye ya sauka daga kan gadon ya nufi toilet, Abba ya tashi ya fice daga ɗakin shima. Ban da kuka babu abin da Zahra ke yi tun bayan da aka sanar da ita mutuwar Noor ɗin, Ta zama tamkar wata zararriya, Ta rasa inda zata kama. Tunanin ta ɗaya, maganin da ke cikin abincin ne ya kashe Noor ɗin? To akan me? Dama maganin mutuwa ne?. Tana nan zaune aka buɗe ƙofar ɗakin, A hankali ta ɗaga idanunta tana kallon sa. Tsaye yake ya harɗe hannayensa a ƙirji, Idanunsa sun ɗan janye sun yi jajur dasu. Sai da gabanta ya faɗi saboda irin kallon da taga yana yi mata, Ya sauke nunfashi ba tare da ya ce komai ba. Itama kasa magana ta yi sai hawaye dake zubowa kan fuskarta, Sun daɗe a haka sai kawai taga ya juya ya fice daga ɗakin without saying anything. Zahra ta dinga kallon wajen daya bari cike da mamakin abin da ya hana shi maganar, Yana fita ɗakinsa ya nufa, Ya zauna gefen gado ya yi shiru yana tunani, Can kuma ya tashi ya shige toilet. **** Washegari da safe wajejen ƙarfe 8:00 aka kai Noor, Tun da suka dawo bai ce da kowa komai ba ya nufi cikin gidansa. Yinin ranar babu wanda ya gan shi, A ɓangaren Zahra kuwa suna zaune a parlourn ta ita da Anty Khadijah, Amal, Safeena da kuma Siyama. Ta yi kuka har ta gaji, Ta suma yafi sau biyar, Daga ƙarshe ta haƙuri ta yi shiru sai kukan zuci. Haka ma Nana ta yi kuka har ta gaji, Duk yanda Amma ta yi da ita ƙin cin abinci ta yi, Sai kuka sai tunani. Bayan kwana uku kowa ya watse, Sai wanda abun ya shafa. Ranar Litinin around 9:00am Aliyu da Sultan suka shigo parlour, Yana zaune gefen Abba ya yi shiru idanunsa a lumshe. Hajiya Babba na zaune akan kujera tana kallon su, Bayan sun zauna suka gaisar da kowa sannan wajen ya yi shiru. Papa ne ya fara cewa “Sultan muna jin ka" Sauke zazzafan numfashi Sultan ya yi kafin ya ce “Papa na rasa abin cewa, Wane ya sanya guba a cikin abinci?” Shiru duk suka yi, Can dai Abba ya ce “Sultan kun duba sosai kuwa? Guba kuma? Me ta ci? Wane ya bata abincin?” “Ni ne na bata!” Kamar daga sama suka ji muryar tasa, Kallon sa duk suka yi, amma ga mamakin su sai suka ga basu yake kallo ba, Hasalima idanun sa a lumshe suke. Abba ne ya ce “To a ina aka samu guba Abdusammad?” Sai a sannan ya buɗe idanun sa, Sosai suka yi jaa, Hawaye ya kwanta a cikinsu. Ya sauke numfashi sannan ya ce“Nima ban sani ba Abba. Pls excuse me!” Ya yi maganar yana miƙewa tsaye, Bai tsaya jiran abin da zasu ce ba ya fice daga parlourn da sauri. Shiru duk suka yi suna mamakin abin da ya faɗa ɗin, Papa ya sauke numfashi yana girgiza kansa ya ce “Allah ya kyauta.” “To a ina aka samu guba a cikin abincin? Ni ban gane ba” Aliyu ya yi maganar a dame, Ajiyar zuciya Papa ya sauke sannan ya ce “Kawai abar maganar tun da baya so a yi.” “But Papa...” Ɗaga masa hannu Papa ya yi, Ya miƙe tsaye yana gyara zaman rigarsa ya ce“Ya isa haka nace!” Ya yiwa Hajiya Babba sallama sannan ya fice daga parlourn, Ita ma tashi ta yi ta nufi sama ba tare da ta ce komai ba. Abba ya kalli Aliyu wanda ya yi shiru ya ce “Ka bar maganar ka ji, Zan yi masa magana” Gyaɗa masa kai ya yi a hankali, Abba ya tashi ya fice daga parlourn shima. Taɓe baki Sultan ya yi ya ce“Ai shikenan, amma wallahi Yaya guba ce a ciki, Kuma a abin da ta ci ne.” Da mamaki Aliyu ya ce“To akan mene yasa baya son a yi maganar?” Girgiza kai Sultan ya yi ya ce“Nima ban sani ba Yaya, But definitely there is something fishy.” Shiru Aliyu ya yi can kuma ya gyaɗa kansa ya ce“Dole na nemo mene ne. I'm coming” Ya ƙare maganar yana tashi tsaye, Sultan bai ce komai ba har ya fice daga parlon, Shima ya tashi yabi bayansa. **** Nana na zaune kan gado ta yi shiru tana tunani, Amma ta buɗe ɗakin ta shigo tana kallon ta. “Naana.” Amma ta kira sunanta, A hankali ta buɗe idanunta, a sanyaye ta ce“Na'am Amma!.” “Ki tashi ki yi breakfast.” “Na ƙoshi” Ta ce a hankali, Da mamaki Amma ke kallon ta, Can kuma ta ce“Da ki ka ci me?” Bata ce komai ba sai yamutse fuska take, Amma ta harareta ta ce “Malama tashi na ce!” Madadin ta tashin sai kawai ta fara kuka, Amma ta yi tsaye tana kallon ta. Can kuma ta ƙarasa gaban gadon ta zauna ta jawota, Faɗawa jikinta tayi tana sakin wani marayan kuka, Amma ta dinga shafa kanta without saying anything, Cikin kuka Nana ta ce “Amma shikenan Noor ta mutu ta bar mu? Shikenan Amma, ba zan sake ganinta ba? Amma ya zan yi?” Girgiza kai Amma ta yi, Ita ma jikinta a sanyaye ta ce“ki yi hakuri Nana, Allahn daya bamu ita shi ne ya ɗauketa, Babu yanda zamu yi sai dai mu yi haƙuri kin ji. Ki daina kuka” Bata ce komai ba ta ci gaba da kukanta tana jikin Amma, After some minutes Amma ta ɗagota ta ce “Tashi muje ki ci abinci.” Bata yi musu ba ta tashi daga jikinta, Amma ta sauka daga kan gadon tana riƙe da hannunta suka fice daga ɗakin. **** Ya jima zaune gefen gadon yana jujjuya pen ɗin hannunsa, Can dai ya sauke numfashi ya tashi ya ɗauki car key ɗinsa ya fice daga ɗakin. Zahra na zaune akan sofa a ƙasa ta zuba uban tagumi, Ya ƙaraso parlourn yana kallon ta ya ce “Zahra ko zaki rakani?” A sanyaye ta kalle shi, dan rabon da ya yi mata magana tun ranar da Noor zata mutu, Ta yi saurin gyaɗa masa kai tana tashi tsaye. Bai ce komai ba ya ja ya tsaya, ta gane abin da yake nufi dan haka ta nufi sama da sauri, After some minutes ta dawo sanye da hijabi har ƙasa, Ya nufi waje tana biye dashi. Wata black Lexus ɗinsa dake compound ɗin gidan ya shiga, Zahra ta buɗe passenger seat ɗin ta shiga a hankali. Sai da ya yi warming motar sannan ya bar gidan, Tun da suka fara tafiya babu wanda ya ce komai, Can dai ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin “Can i ask you?” Gyaɗa kanta ta yi kafin ta ce “Eh doctor.” Jinjina kansa ya yi sannan ya ce“Zahra faɗa min, ina miki wani abu wanda baki so?” Da ɗan mamaki ta kalleshi can kuma ta ce“But doctor...” Kallon ta ya yi wanda ya sanyata yin shiru, Ya ɗan yi murmushi kafin ya ce“Kawai tambaya nayi fa” A sanyaye ta girgiza kanta ta ce“A'a doctor, kana zaune dani saboda Allah, baka cutar dani, kai mutum ne wanda kowa yake so. Kana da kyan hali, kana da kawaici, Sannan kuma kana da ilimi. A duk zaman da muke tare baka taɓa cutar dani ba, Ina jin daɗin zama da kai, Hasalima wasu lokutan ni ce nake ɓata maka.” Zahra ta ƙare maganar tana murmushi, Sai da ya sha kwana sannan ya jinjina kansa ya ce “Really?” Ta sake gyaɗa kanta tana murmushi. Murmushin ne shi ma ya kwace masa, Ya gyaɗa kansa fuskarsa a sake ya ce“Kenan ban cutar dake? Kin tabbata?” langwaɓar da kai ta yi ta ce“Eh mana doctor.” Shiru Abdusammad ya yi kamar me tunani, Can kuma ya sake kallon ta ya ce“kin tabbatar da hakan Zahra?” Shiru Zahra ta yi jin abin da ya sake cewa. Ta tura baki tana kallon titi ta ce “Ni ka bar wannan tambayar doctor” Bai sake cewa komai ba ya ci gaba da tuƙinsa hankali kwance, Ta ɗan kalle shi ta gefen ido sai kuma ta ɗauke kanta. Sam bata san inda suke nufa ba, Dan hankalinta gaba ɗaya baya wajen, Tana can tunanin Noorie sai ji ta yi ya kira sunanta. Ɗago kanta ta yi ta kalle shi, Fuskarsa a ɗan cure babu yabo babu fallasa, Ya ɗan numfasa cikin nutsuwar da ta gama ratsa shi ya fara cewa “Kin faɗa da kan ki ban cutar da ke ba Zahra, Bana yi miki abin da baki so sai dai idan da rashin sani. Ina zaune da ke tsakani da Allah, ina zaune dake saboda ina son ki, saboda na yaba da hankalin ki, naji zaki iya zama uwar Yayana” Zahra ta yi shiru tana tunani sa, ta girgiza kanta a sanyaye ta ce “Doctor na sani, wallahi na sani.” “But why? Akan me zaki kashe mahaifiyata? Akan mene ne Zahra? Me nayi miki.” Girgiza kanta ta fara yi cikin tashin hankalin daya ziyarceta ta ce “Wallahi! Wallahi! Wallahi ban yi niyyar kasheta ba! Wallahi doctor ban yi niyya ba, Bana nufin kowa naka da sharri, na rantse maka da Allah...!” “Idan haka ne me yasa zaki saka mata guba? Akan mene? Kin jawo na rasa ƴata, na rasa Noor Zahra! Kin kasheta da hannun ki. Kin kashe ƴar da muka haifa, Yarinyar da nake so fiye da komai, Yarinyar da nayi burin ganin girmanta,Me yasa Zahra?” Tuni hawaye ya fara zubowa kan fuskarta, Sai girgiza kai take tana kuka, Tama kasa magana saboda tashin hankali. Jin bata ce komai ya sanya shi jan numfashi yana ƙoƙarin saita nutsuwarsa ya ce “Ba zan tambaye ki ba, Ba zan nemi naji dalili ba. Na haƙura, na yafe miki Zahra, Na yafe miki har gaban abada wallahi.” Ita dai bata ce komai ba sai kukanta take ci gaba da yi, Ya zaro wata farar welfolded paper daga aljihunsa ya ɗora mata akan cinya, Zahra ta kalli takardar sai kuma ta kalle shi, Ji ta yi tana neman rasa nutsuwar, Ta girgiza kanta cikin wani irin kuka ta ce “Na shiga ukuna, Dan girman Allah, dan Allah, Dan Annabi kar ka rabu dani. Na shiga uku Doctor, Wallahi ban yi niyyar cutar da Hajiya Babba ba, Ban san maganin yana kisa ba, Anty Khadijah ce ta bani wai zai saka ta dinga sona. Wallahi ban san na kisa bane...” Ta ƙare maganar tana sakin wani raunataccen kuka, Girgiza kansa ya yi muryarsa a ɗan dausashe ya ce “Ba komai Zahra, Duk abin da ki ka yi ba zan rike ki ba. Naji daɗi daya kasance Noor ta fara cin abincin kafin Hajiya Babba, Duk da naji ciwo, naji zafi, naji raɗaɗin rashinta. Amma da ace Hajiya Babba ta rasu gwara Nooriya, Domin ita ni kaɗai zan yi rashin ta, ni kaɗai na san zafinta, Ita kuma Hajiya Babba gaba ɗaya dangin mu ne zai yi rashi. Ko da gangan ki ka yi, ko kuma bada saninki ba, Na haƙura na yafe miki Zahra. Amma ba zan iya ci gaba da zama dake ba, Domin zan ta kallon ki da abun, sannan ba zan iya kyautata miki ba, Sannan bana son dangina su riƙe ki idan suka ji wannan labarin, Tun asali na aureki bada yardar su ba, dan haka duk abin da ya faru zasu dinga ɗora laifin akaina. Ki yi haƙuri amma ni Abdusammad Muhammad Shuwa na sakeki saki ɗaya, na sake ki saki biyu, na sake ki saki uku! A zaman da muka yi da ke, idan na cutar dake Allah ya saka miki, idan kuma ni ki ka cutar to na yafe miki har abada, Ina miki fatan Alkhairi a ragowar rayuwar ki Zahra!.” 08106608363 Nanameera.*Page 65* Zahra ta dinga kallon sa hawaye sai biyo fuskarta yake, Ta girgiza kanta cikin tashin hankali ta ce “Na shiga ukuna doctor, Dan Allah dan Annabi kada ka bar ni, Kar ka rabu dani. Wallahi ina sonka, Ina son ka sosai fiye da tunanin ka, Idan ka rabu dani ya zan yi?” Kallon ta kawai Abdusammad ya yi, Shi kansa zuciyarsa a dagule take. Ya numfasa sannan ya ce“Ko da na so zama da ke to ba zai yiwu ba Zahra, dole ne sai mun rabu. Ba zan iya ci gaba da zama dake ba domin zan ta tunawa da abubuwa da dama, ke kan ki kin san ba zan iya ba. Kin kashe Noor da hannun ki, Ta ina ki ke tunanin zan ci gaba da zama da ke? Bayan haka da a ce ba Noor ce ta ci ba da Hajiya Babba ki ka kashe, Zahra ba zan iya ba!” Ya ƙare maganar yana girgiza kansa, Bata sake cewa komai ba, ta kifa kanta akan cinyarta tana kuka kamar ranta zai fita. Above 5mins kafin ya sauke numfashi ya juya yana kallon titin Gibson's jalon wanda yake shiru babu hayaniya, Muryarsa a nutse ya ce “Allah ya sani ban sake ki dan na tozarta ki ba, Babu yanda zan yi ni. Ki yi haƙuri” Ɗago kanta ta yi tana kallon sa, Lokaci ɗaya ta shiga goge hawayenta. Cikin shessheƙar kuka ta ce“Na sani doctor, Ba komai Allah yasa haka ne mafi alkairi. Amma nima ka sani, ban zauna da kai da niyyar cutarwa ba, na soka domin Allah doctor, na yarda ƙaddara ce zata rabamu, Na gode doctor!...” Ta yi shiru tana jan numfashi, Bai iya cewa komai ba, Dan a duk sanda damuwa ta yi masa yawa baya iya magana. Tsawon mintuna biyu kafin ta buɗe motar ta zura kafarta daya a waje, Juyowa ta yi tana kallon sa ganin har sannan idanun sa na kan titi. Ta sauke numfashi sai kuma ta fice daga motar ta rufe masa, Jiki a sanyaye ta juya ta fara tafiya hannun ta riƙe da wayarta da kuma divorced paper ɗinta. Sai da ta buɗe gate ɗin gidan ta shiga sannan ya juyo ya kalleta, Ta mayar da gate ɗin ta rufe. Zazzafan numfashi Abdusammad ya sauke sannan ya dauƙe idanun sa. Ya jima zaune cikin mota yana saƙa da warwara kafin daga bisani ya yiwa motar key ya yi reverse ya bar unguwar. **** Amma ta dinga kallon ta ganin taƙi cin abincin tun ɗazu, Ta girgiza kanta a ɗan fusace ta ce“Wallahi Nana ba zan iya ba, Ba zaki tayar min da hankali ba. Akan me? Wannan damuwar ki ke zai saka wanda ya tafi ya dawo ne? Ba ki da tawakkali?” Kallon ta kawai Nana ta yi da idanun ta wanda suke a kumbure, Amma ta tashi ta dawo gefenta ta janyo tray ɗin dake kan table ta ce “Ki ci abinci ko kuma yanzu na kira Babanki.” Ta ɗan kalli tray ɗin sai kuma ta sake langwabar da kanta kamar zata yi kuka ta ce“Amma ni bana jin yunwa fa” Shiru Amma ta yi ta zuba mata idanu, Ganin haka ya sanya Nana tura baki kamar an mata dole ta ce “To zan ci fa.” Ita dai Amma bata sake cewa komai ba, Nana ta ta shige kitchen, After some minutes ta dawo hannun ta riƙe da mug. Ta dawo ta zauna sannan ta dauki tea flask ɗin ta tsiyaya shayin kadan, Sugar kawai ta saka sannan ta fara sha a hankali. Amma ta ajiye mata tray ɗin gefenta ta tashi ta shige ɗaki, Da idanu kawai Nana ta bita sai kuma ta sanya hannu ta fara cin wainar kwan, Ko loma uku bata yi ba ta cire hannunta. Shayin ma a wajen ta bar shi ta tashi ta nufi ɗakinta. Toilet ta shige ta fara amai, Sai da ta amayar da duk abin da ta ci sannan ta wanken bakinta ta fito tana sauke numfashi. Kwanciya ta yi gefen gado ta lumshe idanun ta, cikin yan mintuna bacci ya ɗauketa. **** Kiraye-Kirayen sallar magribar da aka fara shi ne ya sanya shi tashi zaune, Tun bayan daya dawo daga gidan su Zahra bai sake fita ba, anan ɗaki ya yi sallolin sa. Ya ɗan yi jim sai kuma ya tashi ya zura slippers ɗin dake gaban gadon ya nufi bandaƙi, Wanka ya yi sannan ya ɗauro alwala. Yana fitowa ya buɗe press ɗinsa ya dauƙi wata embroidery jallabiya nude colour ya saka, sannan ya shafa mai da turare bai tsaya gyara kansa ba ya dauƙi ƙaramin counter dake gefen mirror ya fice daga ɗakin. Kai tsaye masallacin dake estate ɗin ya nufa,Bayan an idar da sallah suka fito tare dasu Papa. Abba dake lura da yanayin sa tun sanda ya shigo ya kalle shi ya ce “Abdul mene ne?” Girgiza kai ya yi a sanyaye ya ce “Ba komai Abba.” Ya bashi amsa yana ƙoƙarin saita nutsuwarsa. Ɗan murmurshi irin na manya Abba ya yi kafin ya ce “Alright, Ina son magana da kai” Jinjina kansa ya yi ya ce“Nima dama Ina son zan yi magana amma a gidan Hajiya Babba.” “Lafiya dai?” Papa ya tanbaya yana kallon sa, Girgiza kansa ya yi ya ce “A'a nothing serious, kawai dai ina son maganar ne.” Jinjina kai Papa ya yi ya ce“Okay to a bari sai an idar sallahr isha'i” To kawai ya ce sannan ya yi mus sallama ya nufi apartment din sa, Da idanu Abba ya bi shi dan ya lura akwai abin da ke damun sa. Suka yi sallama da Papa sannan ya nufi apartment din sa, Yana shiga ya tarar da Haule a parlour ita da Amma suna hira, Suka yi masa sannu da zuwa ya amsa. Ganin yana kallon su ya sanya Amma ta ce “Lafiya dai yallaɓai?” Girgiza kansa ya yi ya ce “Ba komai, Ina Nana ta ke?” “Tana ɗakinta” Ta bashi amsa tana kallon sa, “Kira min ita.” Ya yi maganar yana zama kan sofa, To kawai Amma ta ce sannan ta tashi ta nufi ɗakin Nanar, Haule na ƙoƙarin tashi ya girgiza kansa ya ce “Yi zaman ki mana, yanzu zan tashi.” Sunkuyar da kanta ta yi sannan ta ce to, Ba'a fi 2mins ba Amma ta dawo parlourn ta zauna tana cewa “Gata nan” Ko rufe baki bata yi ba Nana ta fito tana gyara zaman mayafin abayar dake kanta, Kujerar da yake ta ƙarasa ta zauna tana kallon sa ta ce “Abba gani” “Ki je wajen Abdusammad.” Kallon sa ta dinga yi, can kuma ta ce to sannan ta tashi tana shirin komawa ɗaki ya ce “Ina zaki je?” “Wayata zan dauƙo” ta ce tana nuna masa ɗakin,Okay kawai ya ce, Ta juya ta nufi ɗakin.. after some minutes ta dawo hannunta riƙe da wayar ta sauya riga, Ta yi musu sallama sannan ta fice daga parlourn. Sai a sannan ya tashi ya nufi ɗakin sa, Amma ta bi bayansa.. Jiki a sanyaye ta murɗa handle ɗin kofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama, Babu kowa a parlourn, komai a nutse. Ta nufi sama kai tsaye, ɗakinsa ta buɗe ta shiga. Zaune ta same shi kan sofa ya jingina da jikin kujerar idanunsa a lumshe kamar me tunani, Ya rame sosai, Kamar ba shi ba. Ya ɗan yi duhu, Ta sauke idanunta sannan ta ƙarasa ciki, Zama ta yi gefen sa a sanyaye ta ce “Uncle.” A hankali ya buɗe idanun sa, Ya ɗan kalleta da mamaki ya ce“Nana yaushe ki ka zo?” Tana kallon sa ta ce“Yanzu, Na zo ban ga kowa ba. Kuma naga kamar tunani ka ke, Me ka ke tunani?” Ta yi maganar tana leƙa fuskarsa, Girgiza mata kai ya yi ya ce“Ba komai Nana.” Yanda ya kira sunan nata a sanyaye ya sake tabbatar mata da akwai abin da ke damun sa, Ta haɗe rai ta ce “To ba zaka fada min ba? Na daina kula ka!” ta ƙare maganar tana tura baki, Bai ce komai ba ya mai da kansa jikin kujerar yana sauke numfashi, Kallon sa ta dinga yi, can kuma ta miƙe a fusace ta ce “To na tafi tun da ba zaka fada min ba. Kuma nima ba zan sake faɗa maka abuna ba!” Murmurshi kawai ya yi ya sanya hannunsa ya jawota ta faɗo jikinsa, Ƙoƙarin tashi ta fara ya sake matseta ya ce “Sorry mana” “Ni ka cikani, na daina kula ka!” Ta yi maganar tana tura baki, Gyara zaman sa ya yi ya ɗago fuskarta yana kallon ta sosai ya ce“Shikenan zan faɗa” Tsayawa ta yi da kokawar tana kallon sa ta ce“To faɗa min.” Ɗan murmurshi ya yi sannan ya ce “To rufe idanun ki” Ɗan juya idanunta ta yi ta ce “Ni kawai ka faɗa min wallahi.” Girgiza kansa ya yi ya ce“Ai sai kin rufe” Ta tura baki gaba sannan ta sanya hannunta ta rufe fuskarta gaba daya, Numfasawa ya yi, Bata yi aune ba taji ya rungumeta tsam a jikinsa, Ya ɗora kansa a gefen wuyanta, Ajiyar zuciya Nana ta sauke. Ta sanya hannayenta duk biyun ta riƙe shi ita ma, Bata yi aune ba sai jin zubar hawaye ta yi a bayanta, Ta ɗago dan ganin abin da ke faruwa amma ya sake riketa gam, Yanda ba zata iya ganinsa ba. Lokaci ɗaya kuma yana ci gaba da kukansa. “Uncle.” Ta ce a sanyaye, Bai bata amsa ba sai sake rufe fuskarsa da ya yi a jikinta. Shiru Nana ta yi tana sauraren sautin kukansa, Gaba ɗaya jikinta ya yi wani irin sanyi,Tun da take bata taɓa jin kukansa ba. Bata taɓa gani ba, Duk yanda abu ya dameshi ba lallai ya zubar da hawaye ba. Koda zai zubar Hajiya Babba da Abba ne kawai suke iya ganin hawayensa, amma yau gashi yana kuka a gabanta. Sun ɗauki mintina a haka har sai da ya yi shiru dan kansa, Abdusammad ya janye fuskarsa daga jikinta yana ƙoƙarin goge ragowar hawayen da ke kan fuskarsa. “Uncle..” Ta kira sunansa a sanyaye, Ɗan tsuke fuskarsa ya yi hannunsa riƙe da ƙaramin hanky yana goge hawayensa. Shiru ta yi tana kallon sa har sai da ya gama, Sannan ya buɗe bakinta tana shirin yin magana taji ya ce “Nana!” Yanda ya kira sunanta in a serious tone ya sanyata nutsuwa, Ta kalleshi ta ce“Na'am uncle.” “Kar naji maganar kuka a bakin wani, Understood?” Shiru ta yi bata ce komai ba, Ya sanya hannunsa yaja hancinta sannan ya ce “Ina wasa da ke?” Girgiza masa kai ta yi, Ya janyeta daga jikinsa ya tashi ya shige toilet. Tana nan zaune har ya fito, Ta dinga kallon sa ganin yana shirin fita yasa ta ce “Uncle ina zaka je kuma?” Sai da ya ɗauki wayarsa saman kujerar sannan ya ce “Sallah zan yi, Kema ki yi” Tashi ta yi tana ƙoƙarin gyara mayafinta ta ce“To bari na tafi” Wani irin kallo ya watsa mata wanda ya sanyata sunkuyar da kanta, Fuskarsa a tsuke ya ce “Idan ki ka bar nan sai na ɓata miki” Turo baki ta yi ta koma ta zauna, Ya juya ya fice daga ɗakin. **** Umma ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, Zahra na zaune gefen gado ta kifa kanta akan cinyoyinta sai kuka take a hankali. Umma ta ƙaraso ta zauna gefen gadon tana kallon ta, Tun bayan da ta dawo ɗazu da safe bata yi shiru ba, Dakyar ta yiwa Ummar bayanin abin da ya faru da kuma dalilin sakin nata. Duk irin yanda Umma ta dinga bata haƙuri kin ji ta yi, Ta dinga kuka kamar ranta zai fita, Dan kanta kuma ta gaji ta yi shiru da yamma, Bayan sallahr magriba kuma ta ci gaba da kukan. Umma ta sauke numfashi tana kallon ta ta ce “Zahra'u” “Na'am Umma” Ta amsa cikin kuka, Shiru Umma ta yi zuciyarta a dagule, Ba ƙaramin tausayi ta bata ba, Gefe guda kuma ga takaicin biyewa Khadijah da tayi. Can dai ta ce “Kenan ba ki san ƙaddara ba? Baki yi imani da ita ba? Ba zaki haƙurcewa zuciyar ki ba?” Dakyar Zahra ta ɗago kanta tana kallon ta cikin kuka ta shiga girgiza kanta ta ce “Wallahi Umma ina son Doctor, Ina son Abban Noor. Bana son rabuwa dashi, Zuciyata zafi take min Umma. Ji nake kamar zan mutu, Na kasa yarda ya sakeni, Na kasa Umma!” Ta ƙare maganar tana sakin wani raunataccen kuka, Shiru Umma ta yi tana kallon ta, Can dai ta dafata cikin sanyin murya ta ce “Na sani, Na sani Zahra'u, Amma ina so ki sani duk abin da ubangiji ya hukunta babu makawa sai ya faru. Allah ne ya hukunta zaki aure shi, Wannan shi ne dalilin daya sanya ku ka haɗu tun farko, Har ku ka haifi ƴa tare. Sannan sakin ki da ya yi shi ma Abu ne wanda ubangiji ya hukunta ba mutum ba, Shi aure rai ne dashi, Duk ranar daya ƙare to dole sai an rabu. Dan haka ki ɗauki sakin nan matsayin ƙaddara, Kada ki ce zaki damu kan ki dan Allah Zahra'u. Kada ki sakani cikin wata damuwar bayan wadda nake ciki, Ki taimaka” Sosai Ummar ta bata tausayi, Dan ta san duk abin da faru ita ce sila, Sun kasa barinta ta samu nutsuwa, kullum cikin ɗawainiya take dasu tun bayan rasuwar mahaifin su. Ta gyaɗa mata kai duk da yanda take jin abu ne mai wahala ta manta dashi ɗin ta ce “To Umma....” Ta ƙare maganar cikin kuka, Numfasawa Umma ta yi ta ce “Allah ya shige mana gaba, Ki daure ki ci abinci.” “To Umma” Shi ne kawai abin da ta iya furtawa, Umma ta tashi ta fice daga ɗakin a sanyaye. Zahra na ganin ta fita ta sake rushewa da wani sabon kukan, Ta sani ba zata mance da Abdusammad nan kusa ba, Ba zata manta rayuwar su tare ba. Abu ne mai wahalar gaske ta iya cire shi daga ranta, Ta sake kan numfashi tana ci gaba da kukanta. Buɗe ƙofar ɗakin aka yi, Ta ɗaga kanta tana kallon ta, Anty Khadijah ce ta shigo tana kallon ta, Zahra ta yi saurin tashi tsaye tana girgiza mata kai cikin kuka ta fara magana 08106608363 Nanameera.*Page 66.* “Kar ki matso kusa dani, Kin cuceni Anty! Kin cuceni, Wallahi ba zan taɓa yafe miki ba.” Zahra ta ƙare maganar tana sakin wani raunataccen kuka, Kallon ta Anty Khadijah ta dinga yi, Ta taɓe baki tana girgiza ƙugu ta ce “Na cuce ki fa ki ka ce Zahra? Na cuce ki a ina? Ni na saka ki? Dole nayi miki?” Zahra bata iya cewa komai ba sai kuka kawai take, Anty Khadijah ta ɗan yi murmushi ta ce“Ai ni ba cuce ki ba, Duk abin da nayi saboda ke na yi sa, Saboda ina son na taimake ki ne, Dan haka mutuwar aurenki ba laifina bane. Sakacin ki ne ya janyo miki” Ta ƙare maganar tana zabga mata wata uwar harara, Can kuma ta juya ta fice daga ɗakin rai ɓace. Silalewa a ƙasa Zahra ta yi tana ci gaba da kukanta, ta yi dana sanin yarda da maganganun Anty Khadijah, Ta yi dana sanin biye mata, Da duk hakan bata faru da ita ba. Da Noor bata mutu ba, Da Abdusammad bai saketa ba, da ace ta ɗauki duk maganganun da Umma take faɗa mata da yanzu tana zaune gidan mijinta cikin kwanciyar hankali, Ta sake fashewa da wani sabon kukan tana ɗora kanta gefen gado. **** Bayan sallar isha'i ne suna zaune a parlon wanda suka haɗa da Abba, Papa, Sultan, Hamid, Aliyu, Daddy, Mama, Hajiya Babba, Atta da kuma Abdusammad. Papa ya kalli Abdusammad jin bai ce komai ba ya ce “Abdusammad muna jin ka.” Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon su ɗaya bayan ɗaya, Can kuma ya ɗan numfasa kafin ya fara magana cikin nutsuwa. “Na rasa ta ina zan fara, Na rasa me zan yi? Na rasa da wane ido zan kalle ku duka” Da ɗan mamaki Papa ya ce “Me ya faru Abdusammad? Wani abun aka yi?” Shiru ya ɗan yi kamar me tunani, Can kuma ya girgiza kansa muryarsa a sanyaye ya ce “Komai ma ya faru Papa, Nayi laifi, Laifin da ban gane girmansa ba sai daga baya. Laifin da ya zama sanadiyyar saka dangina cikin matsala, Na yi kuskure, Na rasa ta ina zan fara gyara shi” Ya ɗan yi shiru yana sauke numfashi, Su dai babu wanda ya ce komai a cikin su sai kallon sa suke, “Na san ba lallai ku gane abin da nake nufi ba, Ina magana ne akan auren da nayi. Duk abin da faru ya faru ne ta dalilin auren da nayi, Tabbas duk abin da babba ya hango yaro ko ya hau saman dutse ba zai hango shi ba. Ban kyauta ba, Na ƙarya doka da tunanin cewa auren dangi tamkar take haƙƙi ne. Ban nemi shawarar kowa ba, Ban yi tunanin abin da hakan zai jawo ba, Ban yi aiki irin na masu hankalina ba. Kawai na yi abu dai-dai da son zuciyata, Na auri wadda nake ganin ita nake so, Ita ce zan iya rayuwa da ita. Ita ce zata haifa min ya'ya mu yi rayuwa irin wadda na shirya, amma abin da na kasa ganewa shi ne aibun dake cikin bijirewa iyaye.” Tsayawa ya yi da magana, Ya ɗan gyara zamansa yana mai da idanun sa kan Hajiya Babba sosai ya ci gaba da cewa “Hajiya ban kyauta ba, Na bijire miki, na yi ba dai-dai ba. Ban ɗauki shawarar ki, Ban ma baki wannan damar ba, Na sani duk abin da faru ya faru ne dalilin bijire miki da nayi, Dan Allah dan Annabi ki yafe min...” Ya ƙare maganar yana sunkuyar da kansa, Idanun sa suka circiko kamar me shirin yin kuka, Dafa shi Abba ya yi a sanyaye ya ce “Abdul me ya faru ne? Mene ne haɗin auren ka da abubuwan da suka faru?” Kallon Abba ya yi da jajayen idanun sa, Sai kuma ya girgiza kansa muryarsa a sarƙafe ya ce “Abba komai ma ya faru ne sanadiyyar aurena. Zahra ita ce wadda ta fitar da hotunan Nana, Daman kowa ya san da wannan, Ita ce wadda ta fara tarwatsa rayuwar yarinyar har ta kai ga ta samu ciwon zuciya. Sannan da ban auri Zahra ba da ƴar uwarta ba taga Safwan ba, Kuma da Safwan bai auri Siyama ba da bai rasu ba Abba. Domin Siyama ita ce wadda ta shafa masa cutar Hiv ɗin da ta yi ajalin sa!” A firgice duk suka dinga kallon sa, Hajiya Babba da tun da ya fara magana bata ce komai ba ta gyara zamanta muryarta a dake ta ce “Siyama kuma?” Kallon ta Abdusammad ya yi kafin ya gyaɗa mata kai ya ci gaba da cewa “Eh Hajiya, Ita ce, Safwan ya faɗa min komai. Ya kuma nuna min komai, Siyama ita ce take ɗauke da cutar, sannan ita ta shafa masa, wannan dalilin ya sanya ya saki Haule gudun ta kamu da cutar ita ma. Hajiya na yi kuskure, Duk abin da Safwan ya yi ba shi da laifi, domin da bai ga nayi ba shima ba zai yi ba, Da bai ga na auri Zahra ba ba zai taɓa cewa zai auri Siyama ba. Da bama zai ganta ba, Sun asirce shi ne ita da mahaifiyarta domin kawai ya bijire muku, Duk abin da Safwan ya yi ba shi da laifi.” Babu wanda ya iya cewa komai a cikin su, Atta kuwa tuni ta fara kuka tana girgiza kanta. Ajiyar zuciya Abba ya sauke jikinsa duk a sanyaye ya ce “Ka daina faɗin haka Abdul, Duk abin da ya faru ba laifin ka bane. Ƙaddara ce! Ita kuma ƙaddara ba'a iya guje mata, Haka Allah ya tsara babu yanda zamu iya” Girgiza kai Abdusammad ya yi ya ce “A'a Abba wannan ganganci, Sakaci na ne, Wannan shi ne dalilin daya sanya Allah ya jarrabeni. Abba na muku ba dai-dai ba, Na rusa muku dangi da abin da ku ka daɗe kuna ginawa, amma duk da haka baku ce min komai ba. Baku yi fushi dani ba, Kun ci gaba da zama dani kamar ma babu abin da ya faru, Me ya sa Abba?” “Saboda mun san wata rana dole zaka gane gaskiya kamar dai yau ɗin nan!” Papa ya bashi amsa kai tsaye idanunsa zube akan sa. Juyawa Abdusammad ya yi ya kalle shi sai kuma ya jinjina kansa ya ce “Haka ne, Cikin ikon Allah gashi na gane gaskiya, Dan haka zan yi duk mai yiwuwa wajen ganin na gyara abin da na ɓata. Zan karɓi abin da yake nawa, zan ɗauki girman da Allah ya bani. Ba zan sake aikata irin abin da na aikata ba har abada” Murmushin jin daɗi Abba ya yi, Zuciyarsa wa sai dan daman ya san dole wata rana sai Abdusammad ya gane abin da ya yi, kuma ya karɓi laifinsa. Duk da bai yi tunanin abun nan kusa ba, Ita kanta Hajiya Babba zuciyarta ta fara sanyaya, Takaicin ta ya fara raguwa. Duk da daman ita bata taɓa rike shi a ranta ba. Ganin babu wanda ya ce wani abu ya sanya ya ci gaba da cewa “Na rabu da Zahra, Ba dan na tozarta ta ba, sai dan ba zan iya ci gaba da zama da ita a haka ba. Zan zauna da Nana, zan kula da rayuwarta, Ba zan taɓa bari wani abun ya sameta ba in sha Allah.” Da mugun mamaki duk suke kallon sa, “Akan me ka saketa?” Ya tsinkayi muryar Hajiya Babba tana tambayarsa, Sosai yaji san yi a ransa jin yanda ta yi masa maganar. Ya numfasa kafin ya ce “Saboda ba zan iya ci gaba da zama da ita ba Hajiya, Zahra ta kashe min Noor, ita ce wadda ta saka guba a cikin abincin da sunan ke zata kawowa. Sai kuma Nooriya ta fara cin abincin wanda ya yi sanadiyar rasa rayuwarta, Dan haka ba zan zauna da ita ba. Ba zan iya ci gaba da kallonta da igiyar aurena ba, dole na rabu da ita!” Salati da sallalami aka fara a parlourn, Kowa na fadar abin da ke ransa. Shi dai bai iya cewa komai ba ya sunkuyar da kansa, Cikin kuka Atta ta ce “Amma wannan yarinya ba zamu yafe mata ba, Saboda mugunta shi ne har zata iya zuba guba a abinci? Na shiga ukuna! Wace irin rayuwa ce muke ciki ne? Me yasa mutane basu ɗaukan ran mutum a bakin komai?” Babu wanda ya ce wani abu, Ta ci gaba da kukanta tana maganganunta. Can dai Hajiya Babba ta ce “Ya isa haka, Ku bar aibata ta, Ni na yafe mata. Idan tana sane ta yi Allah ya shiryeta, Idan kuma cikin rashin sani ta aikata to ubangiji ya yafe mana baki ɗaya, Allah yasa mufi ƙarfin zuciyoyin mu.” Da Amin Abdusammad ya amsa. Papa ya ce “Amin. Dan Allah abar wannan maganar a nan, duk abin da ya wuce a bar shi a ya wuce ɗin. Tun da har ya saketa to kar a sake tada maganar, ita kuma wacce da zarar ta gama takabarta za'a sallameta ta tafi gida, Dama ba wani abu ya sanya muke kin auren bare ba, muna ƙi ne saboda irin haka. Baka san wa zaka je ka auro ba, Idan ma ka yaba da halayenta to baka san su wane danginta ba, Dole shi kuma kowane tsuntsu kukan gidan su yake. Duk halin kirkinta za'a iya jan ra'ayin ta, Dan haka ya sanya muke zaba muku mata a cikin dangi inda ka san su wane iyayenta da kuma ahalinta, Ba wai muna yi bane saboda mu cutar da ku, Mu a ganin mu gata ne muke muku a matsayin ku na ya'yan mu, Dan haka dan Allah dan Annabi ku zama masu biyayya, Su iyaye ba'a ja dasu. Koda abin da suka ce bai maka ba to ka yi musu biyayya tabbas zaka ga ribar hakan, Bijire musu babu abin da zai jawo sai dana sani, Dan haka ku kiyaye.” Jinjina kai kawai suka yi kafin suka amsa da in sha Allah, Abba ya gyaɗa kansa cike da gamsuwa ya ce “Wannan haka yake. Allah ya ci gaba da haɗa kan mu, Ya bamu ikon yiwa iyayen mu biyayya, Ya jiƙan magabatan mu, da kuma yaran mu, Allah ya jiƙan Yaya, Allah ya jiƙan Safwan, Allah ya jiƙan Fatima. Ya gafarta musu, Ya sanya Annabi ya san da zuwansu. Mu kuma Allah ya sanya mu cika da imani, Da mu da sauran al'ummar musulmai, Allah ya sanya mu mutu muna masu ambaton sunan Allah!” Da Amin duk suka amsa, Suka ɗan yi shiru kafin kowa ya fara tashi yana tafiya ɗaya bayan ɗaya, Sai da ya rage kowa ya fita sannan ya tashi ya koma kusa da Hajiya Babba ya zauna a ƙasan kujerar da take, Cikin sanyin murya ya ce “Mamaa...” Yanda ya faɗi sunan nata ya sanyata kallon sa, Bai ce komai ya ɗora kansa akan cinyarta lokaci ɗaya ya saki wani kuka mara sauti, Shiru Hajiya Babba ta yi tana sauraren sa, Koda wasa bata son abin da zai ɓata ransa, Tun yana ƙarami Allah ya dora mata ƙaunar sa, Kaf cikin ƴaƴanta ta fi son sa, Daga shi sai Safwan. Bata son abin da zai saka su a damuwa, yanzun nan itama hankalinta zai tashi, Ta ɗan sauke numfashi muryarta a nutse ta ce “Mene haka?” Ci gaba ya yi da kukansa, Ya girgiza kanta ta ce “Arɗo!” Da sauri ya ɗago kansa, Rabon da yaji ta kira shi da sunan har ya manta. Hannunta ta buɗe yayi saurin tashi daga ƙasan ya koma kan kujerar ya zauna yana shigewa jikinta, Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya Hajiya Babba ta sauke, Ta sanya hannunta na dama tana shafa sumar kansa a hankali. Tun yana kuka har sai da ya yi shiru dan kansa ya komai sauke ajiyar zuciya, Gaba ɗaya sai yaji damuwarsa ta kau, Yaji ya daina jin abin da ya tokare masa a ƙirji, Yaji nutsuwar daya rasa tana dawowa a hankali. Sun ɗauki lokaci mai tsayi a haka har sai da taji ya yi shiru sannan ta ɗago kansa tana kallon sa ta ce “Kai yaushe zaka girma?” Sake mai da kansa ya yi jikinta yana murmushi, ta girgiza kanta kafin ta ce “Allah ya shirye ka” A zuciya ya amsa da Amin, A fili kuma ya ɗan yi murmushi. Bai bar apartment ɗin Hajiya Babba sai wajen karfe 10 na dare, Shima ita ta kore shi ta ce masa bacci zata yi, Bayan ya gama yi mata hira. Kai tsaye kuma apartment ɗinsa ya nufa, Koda ya shiga bai samu kowa a ƙasan ba dan haka ya haye sama kai tsaye, Ɗakinsa ya murɗa ya shiga, Ya ajiye wayarsa akan gado sannan ya nufi toilet. Wanka ya yi ya shirya cikin kayan baccin sa na campanyn Gucci sai zuba ƙamshi yake, Ya ɗauki wayarsa ya fice daga ɗakin. Daƙinta ya murɗa ya shiga, Zaune ya hangeta can tsakiyar gado sai danna wayarta take a hankali, Ya ɗan saki murmushi sannan ya ƙarasa ciki. A gefen gadon ya zauna yana kallon ta, Ta ƙi yarda ta kalli inda yake fuskarta a ɗaure, Girgiza kansa ya yi sannan ya hau kan gadon ya zauna gefenta ya zare wayar daga hannun ta yana cewa “wa ne ya taɓa min Nanata?” Wani irin kallo ta yi masa sai kuma ta ɗauke kanta tana tura baki, Ya jawota jikinsa yana murmushi ya ce “Am sorry kin ji, me nayi?” “Ni ka sakeni wallahi.” Ta yi maganar kamar zata fashe da kuka, Bai saurarenta ba ya sake matseta a jikinsa yana shafa dogon gashin kanta a hankali. Ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi muryarta a sanyaye ta ce “Ni ka barni na ce, bana so!” Bai tsaya saurarenta ba ya haɗe bakinsu waje ɗaya yana sauke mata wasu zafafan kisses masu tsayawa a rai, Sam bata san sanda ta sakar masa jikinta ba, Ta fara ƙoƙarin taya shi. Cikin yan mintunan da basu shige ashirin ba ta fara ƙoƙarin kwace jikinta jin abin da yake shirin yi, Sai dai sam bai bata wannan damar ba, Cikin kuka ta ce “Uncle ka sakeni, Ni bana so wallahi. Zan je gida kada Amma ta dinga nemana” Ko amsa bata samu ya bata ba, Dan babu tabbacin ma yaji abin da ta ce ɗin, Haka ta ƙaraci koke-kokenta ta rabu dashi. Around 2:00am ta buɗe idanun ta, Lokaci ɗaya kuma ta tashi zaune tana ƙarewa dakin kallo, gaba ɗaya jikinta ciwo yake ga wani irin zazzaɓi mai ratsa ƙashi da take ji. Ta ɗan kalle shi ganin baccinsa yake hankali kwance, Yaye duvet ɗin jikinta ta yi ta sauka daga kan gadon, Ta zura slippers ɗin dake gaban gadon sannan ta nufi bayi a sanyaye. Bata jima ba ta dawo ta kwanta, Ta dinga juyi dan sam ta kasa baccin, Daga ƙarshe ta saka kuka tana rufe idanun ta. Shessheƙar kukanta ce ta tashe shi daga baccin, Ya tashi zaune ya kunna haske sosai yana kallon ta. Kuka take sosai idanunta a rufe, Ya jawota jikinsa da mamaki ya ce “Nana mene ne?” Bata bashi amsa ba sai ci gaba da kukanta da ta yi, Ya kai hannunsa wuyanta ya ji wani irin zafi. Sake kallon karamar fuskarta ya yi ya ce “Wani abun ne ke miki ciwo?” Girgiza masa kai ta yi a hankali ta ce “Ni gida zan je, ka kai ni wajen Abbana” Girgiza kansa ya yi dan ya san so take kawai ta daga masa hankali, Ya kwantar da muryarsa ya ce “To zan kai ki, yanzu kwanta anan” Ya ƙare maganar yana nuna mata gefen gadon, Maƙale kafaɗa ta yi tana sake sakin wani sabon kukan, Ya yi shiru yana kallon ta. Sun fi 20mins a haka kafin ya janyeta daga jikinsa ya tashi ya fice daga ɗakin, Bai jima ba ya dawo hannunsa riƙe da injection, Ya ajiye kan drawer sannan ya hau kan gadon yana kallon ta ganin yanda ta rufe fuskarta da hannayenta tana kuka, Ya girgiza kansa kafin ya ce “Nana” Kallon sa ta yi sai kuma ta ci gaba da kukanta, Ya jawota jikinsa ya ɗorata kan cinyarsa a sanyaye ya ce “Abba ki ke so ki gani?” Gyaɗa masa kai ta yi, Ya ce “To me zai yi miki?” Cikin shassheƙar kuka ta ce“Magani zai bani, Bayana ciwo yake min, kuma...” “Kuma me?” Ya ce yana janyo syringe ɗin, Kwaɓe fuska ta yi ta ce “Kuma yunwa nake ji, Cikina ciwo yake min sosai.” Jinjina kansa ya yi ya ce “To haa bakin ki na ga” Ya yi maganar yana kallon ta, Tura baki ta yi ta ce “Ni bana so Allah..” Murmushi kawai ya yi ya ce “Babu abin da zan miki fa”. Shiru ta yi tana kallon sa, Can kuma ta buɗe bakin nata. A hankali ya ɗora nasa bakin ta yi saurin rufe idanunta, Da dabara ya janye rigar jikinta ya sai ta syringe ɗin sannan ya ya yi mata allurar, Kuka ta saki ta janye bakinta, Ya yi saurin rungumeta yana murmushi. “Uncle zafi.” Ta faɗa cikin kuka, Shafa bayanta ya yi ya ce “Sorry Yar albarka.” Ci gaba ta yi da kukanta can kuma bacci ya ɗauketa, Girgiza kansa ya yi sannan ya fara ƙoƙarin kwantar da ita, Ta riƙe gefen rigarsa idanunta a rufe ta ce “Uncle ka bar ni” Sam bai gane abin da take nufi ba dan haka ya ƙara ƙoƙarin kwantar da ita, Ta saki kuka tana ƙanƙame shi. “Na bar ki a jikina?" Ya tambayeta a hankali, Gyaɗa masa kai ta yi har sannan idanunta a rufe, Ya girgiza kansa dan yasan halin rigimar ta, Ya mai da ta jikinsa ya kwantar da ita. Ya jingina da jikin gadon ya lumshe idanunsa, Sai da aka fara kiraye-kirayen sallar asuba sannan ya kwantar da ita, Ya rufeta da duvet ya tashi ya shige toilet. It's been a while da rabuwar su da Zahra, Gaba ɗaya ya tattara lamarinta ya mayar gefe, Duk da tana yawan fado masa a rai amma sam baya bari tunanin ta ya yi tasiri cikin zuciyarsa, A yanzu babu wadda yake son ganin fara'arta sama da Nana, Indai yana gida to tana maƙale dashi, Baya taɓa barinta ta huta sai dai idan ya fita, Sannan ita ma take zuwa wajen Amma. Gaba ɗaya gidan ya dawo kamar yanda yake da, kowa sai harkokin sa yake, Siyama da Haule ne kawai har sannan basu saki ran su ba. A bangaren Zahra ma ta fawallawa Allah komai, tun bayan ciwon da ta yi wanda har sai da ta kwanta da Asibiti, Umma ta dinga yi mata addu'o'i a ruwa tana bata tana sha, A hankali ta fara rage damuwar da take. Har zama take hira tare da ƴan uwanta, Ban da Anty Khadijah wadda ko kallon in da take bata yi, ita ma ba shiga harkar ta take ba. Dan gaba ɗaya hankalinta na kan auren da zata yi da Malam Garba, Sai ta fara daina son sa, Sai rana ɗaya ta birkice ko bacci taƙi yi har sai an kira shi. Duk yanda Umma ke ƙiƙiyar auren nan haka ta haƙura ta rabu dasu aka gama magana. **** Ranar wata Juma'a misalin ƙarfe 10:00 na safe ya shigo ɗakin, Sanye yake da dakkakiyar shadda Madam gezner Nude colour, Ɗinkin Jampa da Babbar riga sai zuba ƙamshi yake. Gaba daya ya zama kamar bashi ba, Ya ƙara girma da haiba kana ganinsa kaga babban mutum. Girgiza kansa ya yi ganin har sannan tana kwance tana bacci, Ya ƙarasa ciki ya taɓa ta a hankali ya ce “Nana” Kasancewar bata da nauyin bacci ya sanyata buɗe idanunta, Ta tashi zaune tana murza idanun ta. Ta zama wata babba da ita kamar ba Nana ba, Ta yi ƙiba ta ƙara haske har wani jaa fatar ta take. “Ba zaki tashi haka nan ba?” Abdusammad ya tambayeta yana murmushi, Langwaɓar da kai ta yi ta ce “Uncle ina zaka je to?” Murmushi ya yi dan daman ya san sai ta tambayeshi, Ya ja dogon hancinta kafin ya ce “Zan je Abuja ne, amma an jima zan dawo kin ji” Shiru ta yi kamar me tunani, Ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta ya ce “I promise fa yau zan dawo” Gyada kanta ta yi a sanyaye ta ce “To nima zan je wajen Amma.” Murmushi ya yi ya ce“Naji amma bana son yawo, Ki zauna waje ɗaya.” To kawai ta ce, Ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet, Yana zaune har ta fito daga wankan. Ta buɗe press ɗinta ta zaro wata Shayla Abaya sea green ta saka, Kasancewar yadin yana da santsi ya sanya duk motsin da ta yi sai jikinta ya amsa. Ta ƙarasa gaban madubi ta fara shafa mai, Ji ta yi an rungumeta ta baya, Ta sauke numfashi tana kallon sa ta madubi ta ce “Uncle...” Bai ce komai ba ya fara ƙoƙarin juyo da ita, Saurin girgiza masa kai ta yi ta ce “Uncle ba fita zaka yi ba?” Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh ai sai an jima Flight ɗin zai tashi, Zo ki ji” Shiru ta yi tana kallon sa, Ya ɗan haɗe fuska ya ce “Baki ji ba?” Sauke idanun ta kasa ta yi, kamar zata yi kuka ta ce “Dan Allah uncle ka yi haƙuri, wallahi bani da lafiya..” Ta ƙare maganar tana rau-rau da idanu, Shiru ya yi yana kallonta, Can kuma ya gyaɗa kansa ya ce“Okay sai na dawo.” “A dawo lafiya, Allah ya tsare.” Ta ce a sanyaye. Da Amin ya amsa sannan ya fice daga ɗakin, Nana ta sauke ajiyar zuciya tana dafe ƙirjinta, a yan kwanakin nan har tsoro lamarin sa yake bata, Ta ƙarasa shiryawa a gurguje ta bar gidan ita ma. Tana zuwa ta samu Amma zaune a parlon ita da Haule, Ta zauna bayan ta gaida su, “Amma me ku ka dafa?” Harararta Amma ta yi sannan ta ce“Me zaki yi da abin da muka dafa?” Langwaɓar da kai Nana ta yi ta ce“Yunwa nake ji Amma!” “Ke baki yi girki ba?” “Nayi bana ci” Ta amsa tana ƙoƙarin kwanciya. Ɗauke kai Amma ta yi ta ce “Ki je kitchen akwai abinci” Ƙarasa kwanciya ta yi sannan ta ce“to bari na tashi” Ita dai Amma bata sake bi ta kanta ba suka ci gaba da maganar su da Haule. Bayan an sakko daga sallar juma'a suka je apartment ɗin Hajiya Babba, Gaba ɗayan su suka haɗu, Amrah, Haule, Hamida, Maimoon, Sai kuma Nanar. Su duka da ciki Nana ce kawai babu, Duk wanda ta kalla a cikin su sai ta fara dariya. Maimoon da Amrah ne kawai ke biye mata, Su ko sauran sai kallo da ido. Wajejen ƙarfe 3:00 na rana Atta ta fito parlourn ta zauna suna hira duka. Koda aka kawo abinci Maimoon ce ta zubawa kowa, Nana ta dinga kallon abincin sai kuma ta ajiye, Tun safen babu abin da taci. Atta ta dinga kallon ta sai kuma ta ce “Ke ba zaki ci abincin ba?” “Na ƙoshi?” Ta amsa tana ɗauke kai. Taɓe baki Atta ta yi ta ce“To kar ki ci ɗin, Shi mijin naki idan ya dawo sai na faɗa masa, Ni babu ruwana ba zai zo ya ce na bar ki da yunwa ba!” Tura baki Nana ta yi, Hajiya Babba da ta zo parlourn sannan ta kalle su ta ce “Mene ne?” “Wai ba zata ci abinci ba, Salon mijinta ya zo yana yi mana rashin ɗa'a” Da ɗan mamaki Hajiya Babba ta dinga kallon ta, Can kuma ta ce “Nana ɗauki abinci ki ci” Kasa cewa komai ta yi. Ta ɗauki plate ɗin jallof rice ɗin wadda ta sha kayan haɗi ta fara ci a hankali. Ko loma huɗu bata yi ba ta ajiye spoon ɗin tana yamutse fuska. Hajiya Babba da ke lura da ita tun ɗazu ta ce “Mene ne?” Girgiza kanta ta yi ta buɗe bakin ta da niyyar yin magana sai ta fara ga amai, Durƙushewa ta yi a wajen tana kwarara aman kamar zata amayar da kayan cikinta. Hajiya Babba ta taso ta riƙeta, Atta ki tsayawa ta yi a wajen tana kallon ta, Duk suka yi shiru. Sai da ta gama aman sannan Hajiya Babba ta sanya ta tashi ta rakata ciki, Mai aiki ta gyara wajen, Koda ta shiga ɗakin banɗaki ta wuce ta zare kayan jikinta ta yi wanka. Bayan ta fito ta zauna gefen gadon tana jiran Hajiya Babba ta dawo, Koda Hajiya Babba ta dawo samunta ta yi ta yi bacci a wajen, Ta girgiza kanta sannan ta ƙarasa ta rufeta da duvet ta ƙaro gudun ac sannan ta ajiye rigar ta juya ta fice daga ɗakin. 08106608363 Nanameera.*Page 67.* Koda Hajiya Babba ta dawo ƙasan zaune ta same su sun yi shiru suna sauraren Atta da ke faman magana, Tana ganinta ta ce“Khadijah me ya sami yarinyar ne?” Sai da Hajiya Babba ta zauna sannan ta ce“Ba komai Atta, Maybe ta ci abin da bata so ne, tana sama.” Shiru Atta ta yi kamar me nazari, Can kuma ta ce“To ni dai kada mijinta ya dawo ya ganta a kwance, Yanzu sai ya ce na bar ta da yunwa. Gwara ta zo ta faɗi abin da take so a dafa mata taci ko dan Allah?” Girgiza kai Hajiya Babba ta yi kafin ta ce“A'a Atta, kawai rabu da ita.” Taɓe baki Atta ta yi sannan ta mai da idanun ta kan su Maimoon ta ce “Ina faɗa muku...” **** Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i, Kai tsaye kuma apartment ɗinsa ya shiga, Ya yi wanka sannan ya fito ya nufi apartment ɗin Hajiya Babba. Koda ya shiga zaune ya same su a parlour suna hira, Ya ƙarasa ciki bayan ya yi sallama ƙasa-ƙasa ya zauna kan sofa, Murmushi Aliyu ya yi ya ce “Buddy sai yanzu?” Furzar da iska ya yi daga bakinsa kafin ya ce “Na gaji wallahi, Da kwana zan yi to ina son gobe naje gurin can da wuri, Cause nan da 2 days nake son komawa.” “A haba dai 2days? Bai yi wuri ba?” Wani kallon sheƙeke Abdusammad ya yi masa sai kuma ya ɗauke kansa ya ce“Da yake baka san abubuwan da ke gabana ba. Ina Hajiya?” Kafin ya yi magana ta fito daga kitchen hannun ta riƙe da ƙaramin bowl, Ta ƙaraso parlourn ta zauna kan sofa sannan ta ce“Kiran me ka ke min?” Langwaɓar da kansa ya yi yana murmushi ya ce“Kawai na zo na gaishe ki ne, kuma sai naga ban gan ki ba.” Jinjina kanta kawai ta yi sai kuma ta kalli Maimoon da ke gyangyaɗi ta ce “Aliyu ka raka yarinyar nan gida ko ta shiga ciki ta kwanta.” Sai a sannan Aliyun ya kalleta, Baccinta take a zaune hankali kwance, Ya girgiza kansa sannan ya ce “To Hajiya.” Daga haka ya tashi ya ƙarasa kan kujerar da take, Tashin ta ya yi sannan ya riƙe hannun ta, Ya yi musu sallama sannan ya fice daga parlon, Ɗaya bayan ɗaya suka dinga ficewa. Ya rage sai Abdusammad kawai zaune, Hajiya Babba ta kalle shi ta ce “Yaushe zaka tafi?” “Nan da Sunday nake so” Shiru ta yi tana tunani kafin ta ce“Har da Nana zaka tafi?” Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh in sha Allah, Kin ga tana zuwa school ai.” “To Allah ya kaimu lafiya” Ta ce tana ɗaukan spoon ɗin da ke cikin naman, da Amin ya amsa sannan ya tashi ya ce“Sai da safe.” “Ita yarinyar fa?” Da ɗan mamaki ya ce“Tana nan ne?” Kallon hanyar sama ta yi ta ce“Tana can tana kwance” Toh kawai ya ce sannan ya nufi saman, Ɗakin Hajiya ya buɗe ya shiga, ya sameta kwance kan gadon ta rufe idanun ta amma ba bacci take ba. Kamar ba zai magana sai kuma ya ce “Taso mu tafi” Yanda ya yi maganar a shaƙe ya sanyata tashi zaune tana murza idanun ta. Ya juya ya fice daga ɗakin, Jiki a sanyaye Nana ta sauka daga kan gadon, Ta ɗauki mayafin rigar da Hajiya Babba ta bata ta ɗan yafa kanta sannan ta fara tafiya a hankali. A tsaye ta same shi a parlourn yana yi wa Hajiya Babba magana, Ta ƙaraso ta tsaya a gefe tana kallon su, Sai da suka gama sannan ya nufi waje, ta yiwa Hajiya Babba sallama sannan tabi bayansa. Koda ta fita samu ta yi har ya yi nisa abin sa, Ita dai ta ci gaba da tafiyarta a hankali har suka ƙarasa gidan. Ɗakinsa ya shige ita ma ta nufi nata ɗakin, Tana shiga ta faɗa toilet ta yi wanka sannan ta shirya cikin wata sleeping dress doguwar riga wadda ta tsaya mata iya gwuiwarta, Ta ɗaure gashinta da ribbon sannan ta fito daga ɗakin. Koda ta shiga ɗakin sa zaune ta same shi gefen gado yana danna system ɗinsa gefensa kuma wani ɗan madaidaicin tray ne mai ɗauki da kayan fruits, Ta ƙarasa ciki ta zauna gefen gadon ta yi shiru tana kallon sa. Har bayan mintuna goma babu wanda ya ce da wani ƙala a cikin su, Daga ƙarshe dai ta numfasa ta ce “Uncle..” “Uhm.” Ya amsa ba tare da ya ɗago kansa ba, Sanyi jikin Nana ya yi, Dan indai taga ya yi mata haka ta san wani laifin ta yi, To amma ita bata san me ta yi masan ba. Dan haka ta yi ƙasa da muryarta ta ce “Uncle ba zaka ci abinci ba?” Girgiza kansa ya yi yana ci gaba da abin da yake, Ta dinga kallon sa amma bata sake cewa komai ba. After 5mins ya rufe system ɗin ya tashi hannunsa rike da plate ɗin ya fice daga dakin, Tana nan zaune har ya dawo ya nufi toilet, wanka ya sake yi sannan ya fito, Wani boxer kawai ya saka a jikinsa ya nufi kan gadon ya yi kwanciyarsa can tsakiyar gadon ba tare da ya kalli inda take ba. Tuni hawaye suka fara zubowa kan fuskarta, Ta jima zaune a wajen kafin ta tashi ta hau kan gadon ta ɗora kanta akan bayansa cikin shessheƙar kuka ta ce “Uncle me nayi maka to?” Bai yi magana ba, Duk da idanun sa a buɗe suke, Jin bai ce komai ba ya sanyata sake cewa “Dan Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba wallahi! Ba zan kuma ba uncle.” Har sannan bai ce komai ba, Ta leƙo fuskarsa taga idanunsa a rufe. Ta jima tana kallon kyakkyawar fuskarsa kafin ta tashi daga jkinsa, ta share hawayenta sannan sauka daga kan gadon ta fice daga ɗakin. Sai da yaji ƙarar rufe ƙofa sannan ya buɗe idanun sa, Ya tashi zaune yana kallon ƙofar. Can kuma ya koma ya yi kwanciyarsa. Nana na shiga daƙinta ta faɗa kan gado ta fashe da wani sabon kukan, Ita bata san laifin da ta yi masa ba, Gashi a rayuwarta ta tsani a shareta. Shi kuma sararsa kenan duk sanda ta yi masa wani laifi to ba zai kulata ba ranar, Gajiya ta yi da kukan bacci ya ɗauketa a wajen, Around 11pm ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, Kallon ta ya dinga yi ganin yanda ta kwanta akan hannunta sai numfashi take sauketa a jere a jere alamun baccin baya yi mata daɗi. Ƙarasawa kan gadon ya yi ya gyara mata kwanciyar, Ta sauke ajiyar zuciya tana motsa bakinta, Ɗan murmushi ya yi sannan ya shafa dogon gashinta. Ya rufeta da duvet, Ya jima zaune yana kallon ta kafin ya kwanta shima, Ya jawota jikinsa ya rungumeta, Kamar jira take ta sake shigewa jikinsa tana sakin ajiyar zuciya. Ya kashe hasken ɗakin sannan ya lulluɓe su a tare nan da nan bacci ya ɗauke shi. Kiran sallar farko ya tashi ya bar ɗakin, Ya koma nasa ya ɗauro alwala sannan ya wuce masallaci, Koda ya dawo bai shiga daƙinta ba ya shige nasa ya yi kwanciyarsa. Sai ƙarfe 11:00 na safe sannan ta tashi daga bacci, Ta shiga banɗaki ta yi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wata atampa glitter ɗinkin A-shape, Ta ɗaura ɗankwalin akanta sannan ta fito parlour. Neman waje ta yi ta zauna duk da yunwar da take ji, Bata fi 5mins da zama ba ya shigo parlourn, Ganin yana shirin wucewa ya sanyata tashi tsaye, Ta ƙarasa ta tare gabansa tana kallon sa a sanyaye ta ce “Dan Allah uncle...” Kallon ta ya dinga yi fuska a ɗaure,Kafin ya ce“Matsa min hanya.” Madadin ta yi abin da ya ce sai kawai ya ga ta faɗa jikinsa tana kuka, Shiru ya yi yana saurarenta, Ta dinga rera kukanta kafin daga bisani ta ɗago kanta tana kallon sa ta ce “Dan Allah uncle ka yi hakuri, Wallahi ba zan sake ba kaji.” Janye jikinsa ya fara ƙoƙarin yi, Ta sake ƙanƙameshi tana sakin wani sabon kukan, Ya ɗauke kansa saboda dariyar da ke neman kwace masa, Sai da ya yi clearing throat ɗinsa sannan ya kalleta fuska ɗaure ya ce “Me ki ka min?” Girgiza kanta ta yi cikin kuka ta ce “Wallahi ban sani ba, Ban san me nayi maka ba” “Ko?” Ya tambayeta yana kafeta da idanu, Gyaɗa masa kai kawai ta yi. Ya janyeta daga jikinsa ya ce “Idan ki ka tuna abin da ki ka yi min sai ki zo ki bani haƙuri” Daga haka ya ratsa ta gefenta ya haye sama abin sa, Tsayawa ta yi a wajen tana nazarin maganar da ya faɗa, To me ta yi masa? Ta buga ƙafafunta a ƙasa kafin ta bi bayansa a hankali. Zaune ta same shi gefen gado yana danna wayarsa, Ta ƙarasa ciki ta zauna gefensa ta ce “To ai ban san me nayi ba Uncle.” Kallon ta ya yi kamar ba zai magana sai kuma ya ce“To tun da baki sani ba tashi ki ban waje” Langwaɓar da kanta ta yi, Ta kwanta akan cinyarsa sannan ta ce“To ai na ce ka yi haƙuri kuma” “Ba zan haƙura ba!” Ya yi maganar yana ajiye wayar hannunsa, Shiru Nana ta yi tana kallon sa. Can kuma ta ce“To idan baka haƙura ba ya zan yi?” Yanda ta yi maganar kamar zata fashe da kuka ya kusa bashi dariya, Ya tsuke fuska ya ce“Ina ruwana da yanda zaki yi?” Tura baki ta yi, Ta sauka daga jikinsa ta kwanta a kan gadon ta rufe idanunta. Bai ce komai ba ya tashi ya fice daga ɗakin, After some minutes ya dawo hannunsa riƙe da wata leda, Ya ajiye a ƙasan gadon yana kallon ta ya ce “Tashi ki dafa min abinci” Jiki a sanyaye ta tashi ta fice daga ɗakin, Ya girgiza kansa sannan ya nemi waje ya zauna. Sai da ta ɗan yi jim a wajen tana ƙarewa kitchen ɗin kallo kafin ta ɗauko wuƙa. Doya ta ɗauka ta feraye sannan ta wanke ta zuba a tukunya ta ɗora akan wuta, Ta nemi kujera ta zauna tana jiranta, Bayan ta dahu ta kwashe sannan ta fasa kwai ta saka albasa da kayan ƙamshi, Ta saka maggi sannan ta ɗora mai akan kasko ta fara soyawa. Bayan ta gama ta dauko wani flask mai kyau ta zuba a ciki, Sannan ta ɗora farfesun kayan ciki a wata tukunyar, Ta gama shima ta zuba a flask sannan ta ɗiba ta ɗora akan tray ta nufi saman, A parlour ta ajiye ta koma ta dauko tea flask da cups ta dawo ta ajiye. Sannan ta shiga ɗakin, Zaune ta same shi ya sauya kaya zuwa wasu English wears riga armless da cargon 3-quater gashin kansa ya zubo gefen kafaɗarsa gwanin ban sha'awa. “Uncle na gama” Ta ce tana kallon sa, Ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya ajiye wayar hannunsa ya ce “Okay I'm coming" To kawai ta ce sannan ta juya ta fice daga ɗakin, Zama ta yi kan kujera ta kunna tv ta fara kallon wata drama da ake haskawa a Netflix, After some minutes ya fito hannunsa riƙe da ledar ɗazu, Ya nemi waje a ƙasa ya zauna ya tankwashe ƙafafunsa. Kafin ya yi magana ta taso ta tsuguna a gabansa, Plate ta ɗauka ta zuba masa abincin sannan ta haɗa masa tea ɗin ta miƙa masa. Ta koma ta zauna tana ci gaba da kallon ta, “Kefa?” Taji ya tambaya, Kallon sa ta yi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“Na ƙoshi” Wani banzan kallo ya watsa mata kafin ya ce “Kin taso anan ko sai na ɓata miki rai?” Tura baki ta yi sannan ta tashi, Ta koma ƙasa kusa dashi ta zauna. Wani empty cup ɗin ya dauka ya zuba mata tea ɗin, Ya miƙa mata sannan ya saka plate ɗin a tsakiyar su ya ce “Ohya eat!” Kamar zata yi kuka haka ta ɗauki shayin ta kai baki, Ta yi kurɓa ɗaya ta ajiye, Haɗe rai taga ya sake yi ya ce “Ba zaki ci ba?” Girgiza kanta ta yi sannan ta saka hannu ta ɗauki guda ɗaya ta kai baki, Dakyar ta tauna tana yamutse fuska. Ya gyara zamansa yana kallon ta har sannan, Ganin ta jingina da jikin kujerar ya sanya ya ce “Nana yaushe na fara wasa dake?” Kamar zata yi kuka ta ce“wallahi uncle na ƙoshi” “Idan na sake miki magana sai kin gwammace baki sanni ba Nana!” Ganin how serious he's ya sanya ta sake ɗaukan ɗaya ta kai baki,Dakyar ta dinga taunawa, Tana dira cikinta ta tashi da gudu ta bar wajen, Da idanu ya bita sai kuma ya miƙe bayan ya ajiye cup ɗin hannunsa, Bayanta ya bi, Ya sameta durƙushe cikin banɗaki sai kwarara amai take. Da mamaki ya ce “Subhanallahi” Ya ɗagota yana kallonta ya ce “Mene ne?” Bata iya cewa komai ba sai numfashi take saukewa, Ya girgiza kansa sannan ya janyeta daga wajen. Sai da ta wanke bakinta sannan ya sanya ta fito, Ya gyara wajen ya biyo bayanta. Zaune ya sameta kan sofa sai numfarfashi take, Ya ƙarasa ya zauna gefenta sannan ya jawota jikinsa, Sosai yaji zafi a jikinta, Ya ɗago kanta ya ce “Baki da lafiya ne?” Girgiza kanta ta yi kawai, Ya rungumeta ya ce “Sannu to” Kwace jikinta ta yi ta tashi da gudu ta koma toilet ɗin, wani aman ta sake yi, Ya dinga kallon ta ganin yanda take aman kamar zata amayar da kayan cikinta, Sai da ta gama ta wanke bakinta sannan ya kalleta ya ce “Zo nan” Jiki a sanyaye ta ƙarasa gabansa, Ya ɗauketa kamar ƴar baby suka fita daga toilet ɗin, Ɗakinsa ya kai ta ya kwantar da ita sannan ya zauna kusa da ita ya kai hannunsa goshinta ya ce “Sannu, Bari na shirya mu je asibiti” Ita dai bata ce komai ba sai lumshe idanunta da ta yi, Ya tashi ya fice daga ɗakin. Koda ya dawo samu ya yi ta yi bacci, Dan haka ya zauna kusa da ita ya jawota jikinsa, Shi kaɗai ya dinga murmushi yana shafa kanta, Can kuma ya tashi ya ɗauki car key ɗinsa ya fice daga gidan. Yinin ranar a kwance ta yi sa, Sai wajen ƙarfe 6:30 na yamma sannan ta tashi ta yi wanka, Ta shirya cikin wata doguwar riga brown colour, Ta saka ɗan ƙaramin hijabi sannan ta sakko ƙasa, Yunwa sosai take ji, kuma bata jin zata iya cin abin da ta dafa, dan haka kawai ta tafi apartment ɗin Hajiya Babba. Koda ta shiga zaune ta samu Atta da Mama suna magana, Sai Hajiya Babba da ke zaune tana karanta azkar, Sallama Nana ta yi sannan ta gaishe su, Suka amsa a tare, Kallon ta Hajiya Babba ta yi ganin ta tsaya ta ce “Nana lafiya dai?” Gyaɗa kanta ta yi a hankali ta ce“Ba komai Hajiya.” “Nana zo nan” Mama ta yi maganar idanunta na kanta, Ƙarasawa ta yi ta zauna gefenta, Mama ta taɓa wuyanta sannan ta ce “Baki da lafiya ne? Me ke damun ki?” Ta jera mata tambayoyin, Sunkuyar da kai Nana ta yi ta ce“Zazzabi nake Mama” “Shi Abdusammad ɗin bai kai ki asibiti ba?” Cewar Hajiya Babba tana kallon su, Gyaɗa mata kai Nana ta yi tana hawaye. Hajiya Babba ta ɗauki wayarta da ke gefenta ta yi dialing numbern sa, Ringing ɗaya ya ɗauka murya babu walwala ta ce “Abdusammad kana ina?” Daga can ɓangaren Abdusammad da ke zaune parlon Aliyu ya ce “Ina gidan Aliyu Mama” “Ka zo ina neman ka yanzu” Toh kawai ya ce sannan ta kashe wayar, Ta mayar da idanun ta kan Nana wadda ta sunkuyar da kanta tana hawaye ta ce “Kin ci abinci?” Girgiza kanta ta yi, Hajiya Babba ta ce “To me zaki ci?” “Ni bana cin komai” Ta bata amsa cikin shessheƙar kuka. Haɗe rai Hajiya Babba ta yi, Kafin ta yi magana Atta ta ce “Mene ne haka ne ke faruwa? Me ya sameta? Ke zo nan” Jiki a sanyaye Nana ta tashi ta ƙarasa gaban Atta, ta zauna akan kujerar, Ƙare mata kallo Atta ta yi sannan ta shiga jinjina kanta ta ce “Eh lallai! Arɗo ya yi ƙokari, Ji yarinya ta ɗashe ta yi fari, Duk jiki ya circiko, Ba dai ciki ya mata ba? Wannan ƴar taliliyar ƴar” Babu wanda ya ce komai a cikin su, Dan haka Atta ta sake riƙe Nana ta ce“Ke kina jin tashin zuciya?” Ita dai Nana bata amsa ba, Ba kuma ta daina hawayenta ba. After some minutes aka buɗe ƙofar parlourn, Shigowa ya yi shi da Aliyu, Ya gaishesu idanunsa na kan Nana ganin sai shessheƙar kuka ta ke. Hajiya Babba ce ta kalle shi fuska a ɗaure ta ce “Abdusammad mene haka?” Da rashin fahimta ya ce “Wani abun ya faru Hajiya?” Kallon Nana ta yi sai kuma ta kalle shi ta ce “Idanun ka basu gane maka abin da ke damunta ba? Ko baka sani ba?” Sunkuyar da kansa ya yi, Duk da ba wai kunyar Hajiya Babban yake ba amma sai da yaji jikinsa ya yi sanyi. Ganin ya yi shiru ya sanya ta sake cewa “Wannan ya zama karo na ƙarshe da zan ganta haka, Idan ba zaka iya kula da ita ba to ka bar ta anan ka yi tafiyar ka.” “Ki yi haƙuri.” Ya ce a sanyaye, Bata sake cewa komai ba ta ci gaba da karatun azkar ɗinta. Ƙarasawa ya yi gaban Nana ya miƙa mata hannu, Ta ɗora nata hannun akan nasa sannan ta miƙe tsaye, “Da gaske dai ciki gareta kenan? Amma wannan akwai mugunta a lamarin, Yarinyar kwaya nawa take? Dan jaraba ba zaku bar yara su girma su yi hankali ba sai ku haɗa su da wahala.” Wata uwar harara ya zabga mata sannan ya juya ya fice daga ɗakin, Atta ta bi shi da kallo baki buɗe sai kuma ta ce “Uban ka Muhammad shi ka ke harara bani ba wallahi!” Shi dai Aliyu sai dariya yake, Ya juya ya fice daga parlon shima. Tsaye ya same shi a balcony ɗin gidan sai masifa yake mata, Ya ƙaraso yana kallon sa ya ce “Haba Buddy yarinya ce fa” “Yarinya? Ita yarinya bata da hankali ko? Bata san dai-dai da rashin sa ba ko?” Ita dai Nana sai kuka take a hankali, Ya saki hannunta cikin daka tsawa ya ce “Kin tafi daga nan ko sai na make ki!” Da sauri ta juya ta fara tafiya, Duk da jikinta babu kwari. Aliyu ya bita da kallo sai kuma ya girgiza kansa dan ya san rashin haƙurin ɗan uwan nasa ya ce “Gaskiya kada ka ce zaka dinga mata haka, She's too young, Kuma ka san halin wawtar ta, Ba lallai ma ta gane abin da ta yi ba dai-dai bane.” Kallon sa kawai Abdusammad ya yi amma bai ce komai ba, Dan ba ƙaramin ɓata masa rai ta yi ba, Sam bai so kowa ya san da maganar cikin ba, Shiyasa ma bai kai ta asibitin ba tun da ya gane ya bari idan sun koma US ya kai ta. Amma gashi ta zo ta sanya kowa ya gane “Wai Buddy ma ya aka yi haka? Garin ya har wannan ƴar ta samu ciki ne? Yarinya da kake yiwa kallon ƴar ka?” Aliyu ya ƙare maganar yana murmushi, Wani irin banzan kallo Abdusammad ya dinga yi masa, Sai kuma ya juya ya bar wajen kamar zai tashi sama, Aliyu ya dinga dariya kamar zararre kafin ya nufi hanyar nasa gidan shima. 08106608363 Nanameera.*Page 68.* Zaune ya sameta a parlour ta rufe fuskarta da hannunta sai kuka take ƙasa-ƙasa. Ya dan yi siririn tsaki sannan ya ƙarasa gabanta, Kallon ta ya dinga yi kafin ya sauke numfashi ya ce “Nana!” Ɗago kanta ta yi ta kalle shi, Sai kuma ta sake mai da idanun ta ƙasa. Abdussamad ya ce “Ke ba zaki yi hankali ba ko? Ba zaki nutsu ba ko!” Tashi tsaye ta yi tana kallon sa hawaye cike akan fuskarta ta ce“Ni ka mai dani gida, Ni wajen Amma zan kwana.” Takaici ne ya ishe shi, Ganin bama abin da yake mata magana akai bane a gabanta, Cikin tsawa ya ce “Yaushe na fara wasa dake Nana? Uban me ya fitar da ke ɗazu? Wa ki ka tambaya?” Ganin yanda ya kafeta da manyan idanun sa ya sanyata sunkuyar da nata, Tana jan yan yatsun hannunta ta ce “Yunwa nake ji, Shiyasa naje waje Hajiya Babban. Kuma...!” “A saboda baki san inda nake ba ko? Ko kuma ba zaki iya kirana a waya ba ko?” Ita dai bata ce komai ba sai shesshekar kuka da take. Ya yi kwafa ya ce “wallahi duk ranar da ki ka sake fita wani wajen ban sani ba sai kin gane baki da wayo! Sai na ɓata miki! Shashasha kawai!” Ya ƙare maganar cikin ɓacin rai, Bai kuma cewa komai ba kuma ya juya ya fice daga parlourn. Da idanu Nana ta bi shi sai kuma ta fashe da wani sabon kukan ta nufi sama da gudu, Ɗakinta ta shiga ta faɗa kan gado ta dinga rera kukanta tana birgima. Ta gaji da kukan daga ƙarshe bacci ya dauketa. Bata farka ba sai kusan ƙarfe 10:00 na dare, Ta tashi tana mutsutsuka idanu, Ta jima a zaune kafin ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet. Wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala, Ta fito ta shirya cikin wasu riga da wando masu taushi, Ta gyare gashin kanta sannan ta saka hula akanta. A jikin madubi ta tsaya tana karewa kanta kallo, Ta ita kanta ta san ta sauya, Ta zama babba, Jikinta duk ya buɗe, Ga wani uban haske data ƙara kamar wadda ke mai. Ta sake wani sihirtaccen kyau, Tura baki ta yi sannan ta juya ta bar wajen, Ta gabatar da sallah sannan ta koma gefen gado ta zauna tana jawo wayarta, Lambar Khadijah ta yi dialing amma har ta gama ringing bata ɗauka ba, Ta ja tsaki sannan ta tura wayar gefe ta kwanta, Yunwa take ji ba kaɗan ba, Cikinta har wani zafi yake mata. Amma ba zata iya dafa abinci ba yanzu, Dan haka ta haƙura ta ɗora hannunta na dama akan cikin tana sauke numfashi. Around 10:50 na dare Ya buɗe ƙofar ɗakin, Shigowa ciki ya yi yana kallon ta ganin idanun ta a rufe. Ya ajiye ledojin hannunsa a ƙasa sannan ya zauna gefen gadon, Hannunsa ya ɗora kan wuyanta yaji zafi amma ba can ba. Ya janye hannun sannan ya ce “Ke Nana!” Shiru ta yi masa, Duk da ba bacci take ba. Ya sake kiran sunanta ta yi banza, Kallon ta ya dinga yi dan ya riga da ya san ba baccin take ba. Ya tashi tsaye yana kallon ta ya ce “Idan ki ka bari na dawo ɗakin nan kina zaune ni da ke ne!” Yana gama faɗin haka ya juya ya fice daga ɗakin, Sai da taji ya rufe kofa sannan ta buɗe idanunta, Ta dinga kallon ƙofar kafin ta tashi zaune tana tura baki. After some minutes ya dawo hannunsa riƙe da empty plates. Ya zauna gefen gadon ba tare da ya kalleta ba, Ledar daya ajiye ya buɗe ya dauko take away din, Jallof rice ce wadda taji wadatattun kayan hadi sai tiriri take. Ya juye a plate din sannan ya buɗe dayan, Turkey ne a ciki an yi ferfesun sa, Ya saka spoon ya ɗauka yanka biyu ya ɗora akai. Sannan ya miƙa mata yana kallon ta, Kallon plate din ta yi sai kuma ta kalle shi, Fuskarsa babu alamar wasa dan haka ta amshi plate din a sanyaye. Ɗaya ledar ya buɗe ya zaro wani take away ɗin, Tuwon shinkafa ne wanda ya tuƙu sosai kamar pounded yam, Ya saka guda biyu sannan ya buɗe daya robar miyan. Miyar agusi ce wadda taji naman kaza, Ya zuba a gefe sannan ya mayar ya ajiye. Sai da ya wanke hannunsa sannan ya yi bismillah ya fara cin tuwon, After some minutes ya ɗago yana kallon ta, Ko taba abincin hannuntan ba ta yi ba. Sai kallon sa da take kawai, Ya tsuke fuska ya ce “Kina so na make ki ne Nana?” Sunkuyar da kanta ta yi sai hawaye shar suka fara zubowa, Ya dinga kallon ta baki buɗe kafin ya ajiye plate ɗin hannunsa ya kalleta da kyau ya ce “Mene ne kuma?” Cikin shesshekar kuka ta ce “Ni ba zan ci wannan ba, Ni bana so Wallahi!” Ta ƙare maganar tana hawaye. Girgiza kansa ya yi sannan ya ce “To me zaki ci?” Da hannu ta nuna masa abincin gabansa, Ya ɗan yi shiru dan bai yi tunanin zai burgeta ba ya ce “Wannan ɗin ki ke so?” Sauran gyaɗa masa kai ta yi tana hawaye. Ya numfasa sannan ya dauko plate din ya miƙo mata yana faɗin “Take it” Karba ta yi tana kallon sa, Ya janye wanda ya fara bata ya ce “Kuma idan baki ci ba sai na zane ki a gidan nan.” Ita dai bata ce komai ba ta shiga goge hawayenta, Ya dauraye hannunsa yana shirin ɗaukan spoon ta ce “Uncle ka bani a baki” Kallon ta kawai ya yi sai kuma ya girgiza kansa, Ya karbi plate din ya ce “Matso” Babu musu ta matso kusa dashi sosai, Ya yi bismillah sannan ya gutsiri tuwon ya kai bakinta, A hankali ta buɗe bakin ya saka mata. Ta fara taunawa a hankali tana kallon sa, Loma uku taci ta fara jin tashin zuciya, Ya kawo mata tuwon ta yi saurin tare hannunsa, Da mamaki ya ce “Mene kuma?” “Na ƙoshi uncle” Ta bashi amsa tana yamutse fuska, Haɗe rai ya yi kamar bai taba dariya ba ya ce “Kin buɗe bakin ki ko sai na miki bugun da zaki kasa motsi a nan?” Kamar zata yi kuka ta ce“wallahi uncle ba zan iya ci ba, Amai zan yi” “Ci ki yi aman” Ya faɗa yana sake miƙo mata tuwon, Ganin irin yanda ya haɗe ransa ya sanyata buɗe bakin nata, Ya saka mata tuwon yana harararta. Saurin toshe bakinta ta yi, Ta tashi da niyyar barin wajen ta ji ya rike ta, Girgiza masa kai ta dinga yi bakinta a rufe. Yaƙi barinta ta tashi, kuka ta saka tana ƙoƙarin kwace jikinta, Ya matseta a jikinsa ba tare da ya ce komai ba. Bata san sanda ta zare hannun nata daga kan bakin ba sai ganin amai tayi na zuba. Ta dinga kwarara amai tana riƙe da cikinta. Ban da kallon ta babu abin da Abdussamad ke yi, Gaba ɗaya ta wanke shi da amai, Ya kasa cewa komai, Ganin yanda ta galabaita sosai ya sanya shi jawota jikinsa, Kamar jira take ta ɗora kanta akan kirjinsa tana sakin wani irin wahalallen numfashi. Sai da yaga ta ɗan nutsu sannan ya tashi da ita a jikinsa suka nufi toilet, Wanka ta sake yi shi kuma ya gyara in da ta ɓata ya sauya bedsheet. Bayan ya gama ya fice daga ɗakin ya koma nasa, wankan shi ma ya yi sannan ya shirya cikin kayan bacci, Koda ya dawo ɗakin kwance ya sameta kan sofa tana daure da towel da alama tun da ta fito daga wankan take kwance a wajen, Ƙarasawa ya yi ya taba jikinta, Zafi yaji sosai. Ya girgiza kansa sannan ya ƙarasa press ɗin ta ya buɗe, Wata riga mai saukin nauyi ya dauko mata, Ya dawo ya taimaka mata ta saka sannan suka fice daga ɗakin. Ɗakin sa ya mai da ita, Ta kwanta akan royal bed ɗin sa ta lumshe idanu, Gaba ɗaya jikinta ciwo yake mata. Ga wani irin ciwo da mararta ke yi, Injection ya haɗo ya dawo ya zauna gefenta, Saurin tashi zaune ta yi duk da yanda take jin jikinta muryarta na rawa ta ce “Uncle wa zaka yi wa allurar?” Yana ƙoƙarin ɗaukan sringy ɗin ya ce “Kaina zan wa” Yana gama faɗin hakan ya jawota jikinsa, Kuka ta fara yi ta rike shi tana cewa “Dan Allah uncle kada ka min allura, Wallahi bana so zafi fa” Shafa dogon gashin kanta ya yi yana murmushi ya ce “To shikenan zo ki kwanta” “Ka fasa yi min?” Ta tambaya tana hawaye. Bai ce komai ba ya yi kwanciyar sa, Ta ɗan yi jim tana kallon sa kafin ta kwanta a kusa dashi ita ma, Kasancewar a gajiye take yasa nan da nan bacci ya dauketa, Saukar numfashin ta da yaji ya sanya shi ɗaga kansa ya kalleta. Sai kuma ya tashi zaune ya dauko allurar, A hankali ya janye rigar jikinta ya sai ta allurar ya yi bismillah sannan ya yi mata, wata irin zabura ta yi ta tashi zaune, Ta dinga kallon sa sai kuma ta fashe da kuka. Murmushi ya yi ya jawota jikinsa ya rungumeta yana bubbuga bayanta ya ce “Ya isa haka! Ya isa” Cikin kuka ta ce “Sai da nace bana so ka yi min, Wayyo Abbana zafi zai kasheni!” Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan, Murmushi kawai ya dinga yi dan ya san halin rakinta. Ya kwanta har sannan tana jikinsa, A kunnenta ya raɗa mata wata magana, Ta daga idanunta ta kalle shi sai kuma ta sake ɓoye fuskarta a jikinsa, Shafa bayanta yayi a sanyaye ya ce “Agreed?” Makale masa kafaɗa ta yi tana ci gaba da kukanta, Ya girgiza kansa yana murmushi bai ce komai ba. **** Washegari ta kasance ranar Lahadi, Bayan sallar azahar aka daura auren Anty Khadijah da Malam Garba. Gidan a cike yake da jama'a, Yawancin yan uwa da abokan arziki sun hallarci bikin, Musamman daya kasance an dade ba'a yi taro a gidan ba, Sai shige da fice ake, Ana shewa. Kowa na murna da Anty Khadijah ta samu miji, Ana ganin zata daina abubuwan da take ta zauna a ɗakin mijinta. Har mai dj aka ɗauko da Yamma ya zo compound ɗin gidan aka tashe, Amarya sai rawa take tana murna abin ta. Su Amal na tayata, Dan Siyama bata zo ba kasancewar tana takaba, Duk wannan bidirin da ake babu Zahra a ciki, tana sama a ɗakinta ta kulle, Yini ta yi zuciya babu daɗi, Gaba ɗaya mijinta ne ke faɗo mata, Sai kuma Noor, Shikenan babu wanda zata sake gani cikin su, Musamman Noor din, Kuma Anty Khadijah sai murnarta take zata tafi nata ɗakin mijin bayan ita ta rabata da nata. Wannan abun ya sanya Zahra yini tana kuka, Daga karshe ta kwanta, Sai dai sam baccin ya gagara zuwa, Data rufe idanun ta Abdussamad take gani. Haka ta dinga zama a ɗakin har bayan sallar magriba, Koda aka zo aka kirata su yi sallama da amarya ƙin fitowa ta yi, ta ce Allah ya bata zaman lafiya. Umma bata tilasta ta ba ta ce a rabu da ita, Anty Khadijah da abun ya ɓata mata rai ta nufi saman ba tare da an lura ba. Murɗa handle din ƙofar ta yi ta shiga, Ta samu Zahra na zaune kan dadduma tana jan carbi. Harararta ta dinga yi kafin daga bisani ta ce “Wato Zahra baƙin ciki ki ke min da auren da nayi ko? Shi ne yasa ba zaki iya fitowa mu yi sallama ba ko? To ni gashi na zo. Allah ya bamu alkhairi, zan tafi ɗakin mijina. Kin san dama ita rayuwa juyi-juyi ce, Yau gareka gobe ga waninka, Da kece mai aure ni kuma bazawara, Sai gashi yau na zama mai aure ke kuma kin zama bazawara. To Ubangiji ya kawo miji a kusa, Na tafi!” Anty Khadijah na gama faɗin haka ta juya ta fice daga ɗakin ba tare da ta jira jin amsar da Zahran zata bata ba. Ita ko Zahra kada koda motsi ta yi, Sai hawaye dake zubowa daga cikin idanun ta kamar an bude famfo. Tabbas ta yi wawta, Kuma ta yi nadama, Ta yi nadamar yarda da maganganun Anty Khadijah, Gashi yanzu ta cuceta. Ta bar ta a ruwa, Ta ɗora fuskarta a gefen gado tana fashewa da wani kuka mai sauti. Daren ranar Malam Garba ya zo ya tafi da Anty Khadijah, Dan cewa ya yi baya son rakiyar amaryar nan, Suma basu takura kansu ba, aka bar shi ya tafi tare da ita. Gidan dai da suka saba zuwa da Kaddu nan ne gidan da zata zauna, Anty Khadijah ta dinga kallon soran gidan ganin ya tsaya anan yana buɗe wani daki dake wajen, Kamar ta yi masa magana sai kuma ta kasa, Ya buɗe ɗakin suka shiga. Da mamaki ta dinga kallon ɗakin, Ganin duk kayanta anan aka zuba su, Ɗakin yana da ɗan girma dan haka aka saka furniture da kuma kujeru guda biyu, Sai gas ɗin ta a gefe, Sauran kayan kuma aka bar su a corridor ɗin ɗakin. Dakyar ta nemi waje ta zauna dan gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, Ba haka suka yi dashi ba, Cewa ya yi akwai dakuna guda biyu a cikin gidan na tsohuwar matarsa ta uku da ya saka sai ta zauna a can. Dan haka koda aka zo jere har dashi aka jera kayan, Su kuma da suka koma babu wanda ya ce mata ga yanda gidan yake. “Kin yi shiru Khadijah” Maganar ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi, Kallon sa ta yi ta ce “Afwan ban ji bane.” Murmushi Malam Garba ya yi ya ce “A'a ba komai ai, cewa nayi ki tashi ki yi sallah” To kawai ta ce sannan ta miƙe, Kalle-Kallen ɗakin ta dinga yi sai kuma ta ce “Babu banɗaki ne?” Girgiza mata kai ya yi yana nuna mata wata yar siririyar ƙofa wadda ta sha tsatsa ya ce “Ga shi can akwai mana. Ai banɗakin ki da ban babu ruwan ki da sabgar matan gidan” Jinjina kanta tayi sannan ta ajiye mayafinta a gefen kujera ta nufi banɗakin, Ɗan karami ne sosai, Amma a wanke yake sai kamshin hypo ne ke tashi, Dakyar ta iya yin alwalar a ciki ta fito tana yarfe hannu. Sallah suka yi tare sannan ya janyo ledar kazar daya shigo da ita, Ita dai tun da ta ci sau daya bata sake ci ba saboda gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake. Ta rasa wane irin hali take ciki, Farin auren Garba, Ko kuma dana sani. Ta rasa dalilin daya sanya ta yarda da auren ma, “Khadijah lafiya dai?” Ta tsinkayi muryarsa yana tambayrta. Bata ce komai ba ta tashi ta ƙarasa gaban wardrobe ɗin ta ta buɗe, Wata sabuwar rigar bacci ta dauka, Ya ce zai je cikin gidan ya dawo ta ce to sannan ya fita. Kafin ya dawo har ta gama shirin kwanciya ta zauna gefen gado ta zuba uban tagumi, Washe baki ya dinga yi yana dariya ya ce “Kin ga yanda ki ka yi kyau kuwa?” Da kyar ta ƙirƙiro murmushi ta yi masa ta ce “Na gode sosai.” Ya girgiza kansa ya ce “Ai babu godiya tsakanin mu Khadijah.” Ita dai bata sake cewa komai ba, Taga ya nufi banɗaki. Jiki a sanyaye ta kwanta gefen gadon ta rufe idanun ta, Sam zuciyarta ta kasa nutsuwa, Gani take kamar a mafarki. Bayan ya gama shirin kwanciyar sa ya hauro kan gadon, Ta dinga kallon sa ganin yanda yake murmushi, Ita bata taɓa ganin muninsa ba ma irin ranar, tamkar wani naman daji haka take ganin fuskarsa. Babu yanda ta iya dashi haka ta yarda suka kwanta tare, Sai dai abin da Anty Khadijah ta fuskanta shi ne ya ƙara tayar mata da hankali, Bata taɓa sanin akwai irin wannan tashin hankalin ba. Ta inda Allah ya haramta ta nan ya dinga nemanta, Tun tana dauriya har sai da ta sume ba tare da ta san ta yi hakan ba. Shi kuwa ko a jikinsa dan ba yau ya fara hakan ba, Hasalima wannan shi ne tsarin gidan sa!. **** Washegari da wuri Nana ta tashi don ranar zasu tafi, Ƙarfe 7:00 na safe ya shigo ɗakin yana sanye da riga da wando masu nauyi saboda sanyin da ake, Kallon ta ya dinga yi ganin yanda ta yi shiru ta zuba uban tagumi, Gabanta yar ƙaramar trolley ɗinta ce wadda ta gama haɗa komai nata. Ƙarasawa ya yi ya zauna kan drawer yana kallon ta ya ce “Nana mene ne? Ko jikin ne?” Kallon sa ta yi idanunta cike tab da hawaye, Muryarta a sanyaye ta ce “Uncle ni ka bar ni anan dan Allah.” Shiru ya yi yana kallon ta, Can kuma ya miƙe ya ce“Ba zan bari ba, Ki fito waje ina jiran ki” Daga haka ya dauki trolley din ya fice daga ɗakin. Da idanu ta bi shi, Hawayen da ke cikin idanun ta ya fara zubowa kan farar fuskarta, Ita ko kaɗan bata so ta bi shi, Saboda ta san zaman kadaice zata yi, Babu kowa ba kamar da ba da akwai Noor wadda suke hira tare, koma tana makaranta akwai Zahra duk da ba magana suke ba. Tana nan zaune har bayan mintuna sha biyar wayarta ta fara ringing, Ta kalli screen ɗin wayar ganin sunan uncle din ya sanya bata daga ba, Kawai ta tashi ta zura hijabin da ke gefenta sannan ta ɗauki wayar ta fice daga ɗakin. A compound din Hajiya Babba ta same su, Kamar yanda suka saba tsayawa anan a duk sanda zai yi tafiya, Jiki a sanyaye ta ƙarasa wajen tana zuwa ta shige jikin Hajiya Babba, Rungumeta ta yi ta shafa kanta ta ce “Allah ya tsare hanya kin ji” Dakyar ta ce Amin saboda kukan da ke neman tawo mata. Ta janye jikinta ta ƙarasa wajen Abba, Rungume shi ta yi tana sakin kuka, Duk da sun gama sallama tun asuba, Ya ɗan yi murmushi duk da yanda shi ma yake jin babu daɗi tafiyar da zata yi ya ce “Ba zaki daina rigima ba ko Nana?, Allah ya tsare hanya.” “Abba dama na zauna anan...” Ta yi maganar cikin kuka, Murmushi kawai Abba ya yi ya ɗago fuskarta ya fara goge mata hawayen sannan ya ce “Ai darajar ko mace ƴa mace gidan mijinta Nana, Dan haka ni zan fi alfahari da ke idan kina daƙin mijin ki. Ki zauna lafiya kin ji” Gyaɗa masa kai kawai ta yi, Ya ja kumatunta yana murmushi, Wajen Papa ta ƙarasa ta sake masa sallama, Sannan ta faɗa jikin Amma tana kuka kamar ranta zai fita. Ajiyar zuciya kawai Amma ta dinga saukewa, Dan ko kaɗan ba son tafiyar take ba, Dan babu yanda zata yi ne. Amma da anan za'a bar ta har ta haihu, Tausayinta kawai take ji, Nanar da bata iya kula da kanta yanda ya kamata ita ce zata kula da wani, Ta girgiza kanta jin yanda take ci gaba da kuka ta ce “Ke ya isa mana, so ki ke a yi miki dariya?” Girgiza kanta ta yi ba tare da ta ɗago kan ba, Amma ta ce“Ki zama yarinyar kirki Nana dan Allah, Ban da saka magana, Ban da rashin ji, Ki kula da kan ki da kuma lafiyar ki, Ban da neman magana.” A sanyaye ta amsa da to sannan ta saketa, Ta ƙarasa wajen su Maimoon suka sake sallama sannan ta koma wajen Atta. Girgiza kanta ta yi ta ce “A'a ba sai kin zo min ba, Kar ki shafa min ciki, Je ki kawai Allah ya sauke ki lafiya” Ba Nana ce taji kunyar ba, Abdussamad ne da ke tsaye, Yaji kamar ya daskare a wajen saboda kunya, Musamman saboda su Abba da Papa da ke tsaye. Atta ta kalle shi ta ce “Kai kuma kaji tsoron Allah, Ka dinga barin yar mutane tana hutawa. Yauwa, Dan bana son mugunta” Wata uwar harara ya zabga mata sai kuma ya dauke kansa yana kwafa, Atta ta taɓe baki kafin ta ce “Ohho! Kai ka ga zaka iya, Ni dai sai na faɗi gaskiya ko za'a kashe ni.” Bai tanka ta ba, Aliyu sai murmushi yake, Nana ta sake musu sallama sannan ta buɗe motar ta shiga, Sai da ya sake yi musu sallama shi ma sannan ya shige motar, Driven yaja motar suka bar compound ɗin. **** Wajejen ƙarfe 10:00 na safe ya shigo ɗakin, Har sannan tana kwance, Ya tsaya gaban gadon yana kallon ta ya ce “Khadijah ba zaki tashi haka ba? Mutan gidan na ta jiran ki ki fito” Dakyar Anty Khadijah ta kalle shi, Tsabar baƙin ciki kasa cewa komai ta yi, Ta tashi zaune ta nufi banɗaki kawai. Kallon ta ya dinga yi har ta shige, Bata jima ba ta fito ta dawo ta zauna gefen gadon “Ki samu ki fito ku gaisa da kowa” Toh kawai ta ce sannan ta juya masa baya, Shi ma bai sake cewa komai ya fice daga ɗakin. Sai kusan ƙarfe 12:00 na rana sannan ta fito daga ɗakin, Ta shirya cikin wata atampa glitter sai sheƙi take, Ta nufi cikin gidan dan ta jiyo hayaniyar jama'a, Abin da ta gani ne ya sanyata makalewa jikin bango, Gaba ɗaya matan gidan suna tsaye cirko-cirko suna kallo, Haka ma ya'yan gidan da basu tafi Makaranta ba, Malam Garba ne riƙe da ƙatuwar dorina sai dukan wata mata yake, Ita kuma sai tsala ihu take tana birgima a cikin ƙasar wajen. Ta dinga kallon sauran matan biyu da ke tsaye kamar gumaka, Babu wanda ya yi tunanin zuwa ya hana shi abin da yake. Sai da ya gaji dan kansa sannan ya hankaɗata da ƙafa, Ya juyo yana kallon sauran yana haki ya ce “Cikin ku wata ta sake irin abin da ta yi, Wallahi sai kin raina kan ki a gidan nan! Ni ba zaka kawon wannan iskancin na ɗauka ba!” Ya ƙare maganar yana haki... Babu wadda ta iya motsi a cikin su, Sai muzurai suke, Ya kalli Anty Khadijah da ta yi sak a fusace ya ce “Ke ma dallah shige mu je an fasa gaisawar!” Kallon sa ta dinga yi, Can kuma ta juya ta bar tsakar gidan. Zaune ta same shi a ɗakin ta sai haki yake saukewa, Ta ƙarasa gefen gado ta zauna ta zuba uban tagumi. “Na shiga uku ni Khadijah, wace irin rayuwa na jawowa kaina?” Wani ɓangare na zuciyarta ya yi mata tambayar. Rufe idanun ta ta yi tana sauke wani irin numfashi, Babu wanda ya fado mata a rai sai tsohon mijinta mahaifin Siyama. Mutun mai kirki da sanin ya kamata, Mutum mai addini da son ƴan uwansa. Amma sai da ta raba shi da kowa, Ta mallake shi daga ita sai ƴar ta. Runtse idanunta ta yi tana tuno wasu shuɗaɗɗun abubuwa da suka shige, Tana sake jin ina ma ace mafarki take ba gaskiya bane. **** It's been a while da komawar su New York, Kusan kullum tana kwance bata da lafiya, Koda ace lafiyar kalau ma to ba lallai bane ya gane dan ba zata fito ko parlour ta zauna ba. Ko kaɗan kuma basa wani shiri dashi saboda gaddamar ta, Kullum sai sun yi faɗa akan cin abinci, Ita ta ce ba zata ci ba saboda amai shi kuma ya rantse sai taci, Daga ƙarshe idan ta ci ta amayar sai bacci ya dauketa. Ranar wata Monday ta gama shirinta ta safe tsaf dan ranar ta tashi da sauki, Abdussamad ya shigo ɗakin da niyyar duba jikinta, Ya sameta tsaye tana shafa lip balm a bakinta. Ta ɗan rame kaɗan idanunta sun firfito saboda rashin cin abincin da take, Ya dinga kallon ta da mamaki kafin ya ƙaraso gaban mirror ɗin ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallon ta ya ce “Madam ina zuwa?” Kallon sa ta yi, Sai kuma ta tura baki ta ce “Makaranta zan je, Ni na gaji da zaman gidan nan...” Ta ƙare maganar kamar zata yi kuka, Sosai ta bashi dariya, Ya jinjina kansa ya ce “Wato kin gaji da zaman gida ko? To zaki bini asibiti?” Maƙale kafaɗa ta yi ta ce“Ni school zan tafi” Matsowa kusa da ita ya yi, Ya riƙe hannayen ta duk biyun cikin nasa ya ce “Ban son yawo fa Nana, ki yi zaman ki a gida mana” Rau-Rau ta yi da idanu tana shirin kuka ta ce “Dan Allah uncle ni zan je a haka. Ai na samu sauki fa” Shiru ya yi yana kallon ta, Ta shige jikinsa a shagwabe ta ce “Kaji uncle ɗinaa!” Numfasawa ya yi sai kuma ya ɗago fuskarta ya ce “But sai kin min alƙawari” “Alƙawarin me?” Ta ce da sauri. “Idan kin dawo ba zaki wahalar dani ba zaki ci abinci!” Kwabe fuska ta yi ta ce “To ba cikin ne yake hanani cin abinci ba! Nima ina so naci fa, Kuma nagaji ma..” Ta ƙare maganar tana turo baki gaba, Murmushi kawai ya yi sai kuma ya yi mata light kiss a baki ya ce “Alright muje nayi dropping ɗin ki” Cike da murna ta ce to sannan ta ɗauki jakarta suka fice daga ɗakin. A compound din makarantar ya yi parking, Ta ɗauki jakarta da ledar chocolate din daya siya mata a hanya ta ce “Uncle zaka zo ka ɗauke ni?” Gyaɗa mata kai ya yi ya ce “Karfe nawa zaku gama lecture din?” “3pm” Ta ce tana kallon sa, Shiru ya yi sai kuma ya ce“Okay idan zan zo I'll call you” “Ai zaka zo ma..” Ta ce a shagwaɓe, Murmushi kawai ya yi ya ce“To naji, A yi karatu dayawa” Toh kawai ta ce sannan ta buɗe motar ta sauka, Ta daga masa hannu sannan ta nufi department ɗin su. Karfe 1:30 na rana suka je cafeteria, Ita da wasu kawayenta Mu'ash da Amani, Kasancewar ranar Surry bata zo ba. Suka yi order abinci aka kawo musu, Nana ko loma uku bata yi ta fara amai, Har abin da taci da safe sai da ta amayar dashi, Su suka taimaka mata ta gyara jikinta sannan suka bar wajen. A kasan wani garden suka zaune, Amani ta dinga kallon ta ganin yanda ta jingina da jikin kujera ta yi shiru, Gaba ɗaya ta zama kamar ba ita ba. Taɓe baki ta yi ta ce “Gaskiya Nana kina bani mamaki, Ke a haka zaki ci gaba da zama?” Kallon ta kawai Nana ta yi da rashin fahimta, Ta gyara zamanta sannan ta ce “To ya zan yi Amani? Kullum ma a haka nake, Ni na gaji ma wallahi, Ji nake kamar na mutu.” Wani kallo Amani ta yi mata sai kuma ta ce “Au to zauna, Ƴar ƙaramar ki dake ki wani fara haihuwa, Da kin haifi ɗa ko ɗaya ne shikenan zaki ga kin fara canzawa, Komai ya nemi ya ƙare miki. Ya ma za'a yi na bari na haihu? Ai ko Deen ya sani wlh ba zan haihu ba har sai na gama karatu, Na koma na zauna sannan na haifi ko ɗaya ne” Mu'ash da ke danna wayarta ta ce “Bare kuma ni! Kin ga yanzu dai shekarar mu biyu da aure ko? To sau biyu ina ɓari, Dana samu ciki nake zubarwa, Akan me? Tab!”. Ita dai Nana kallon su kawai take can kuma ta ce “To ni ai ban san yanda zan yi ba. Sai dai na bari idan na haihu nayi planning” “Shi kuma wannan cikin fa?” Amani ta tambayeta, Ɗan haɗe rai Nana ta yi ta ce “Sai na haihu ai” Jinjina kai Mu'ash ta yi ta ce “Oh har sai kin jira kin haifi wannan cikin dai bai rufe wata biyu ba?” Kamar zata yi kuka ta ce“To Mu'ash ya zan yi wai?” “Ki zubar!” 08106608363 Nanameera.*Page 69.* Girgiza kai Nana ta yi muryata a sanyaye ta ce“Ni dai gaskiya ba zan iya ba. Uncle faɗa zai yi min..” Wani dogon tsaki Amani taja kafin ta ce“amma ke dai baki da tunani wallahi! Ki ji min hauka, to bari zaki yi ya gane?” Kallon ta Nana ta dinga yi da rashin fahimta. Mu'ash ta ce“Nima abin da na gani kenan, Ya za'a yi ma ki bari ya gane. Ai kawai yi zaki yi a zuwan ɓarewa ya yi da kansa” Marairaice fuska Nana ta yi ta ce“Ni gaskiya tsoro nake ji, Idan kuma ya gane fa?” Takaici ne ya ishi Amani, A ɗan fusace ta ce“Ai sai ki bari ya gane ɗin!” Tura baki Nana ta yi bata ce komai ba. Mu'ash ta gyara zamanta ta ce“Kina ji Nana, Kawai za'a baki tablet ne ki sha, Da zarar kin sha 15mins sun yi yawa cikin zai ɓare.” Ita dai Nana bata ce komai ba sai kallon ta take, Mu'ash ta ci gaba da cewa “Kin ga idan ya zube sai ki ce kema baki san garin ya ya ba, Sannan kada ki yarda ki sha yana gidan, Ki bari sai ya fita. Yanda zaki iya cewa faɗuwa ki ka yi, Kin ga shikenan kin huta, Bayan kwana biyu sai ki yi planning har ki gama karatun ki” Kasa cewa komai Nana ta yi tana kallon su, Jikinta ya yi sanyi gaba ɗaya, Taji tana son zubar da cikin, amma tana tsoron abin da zai iya biyo baya. Can dai ta ce “To zan fara shawara da uncle” Baki buɗe suka dinga kallonta, Amani ta miƙe cike da takaici ta ce“Idan ban bar wajen nan ba sai baƙin ciki ya kasheni, Sai ki je ki yi shawarar dashi!” Tana gama faɗin haka ta yi gaba fuuu kamar zata tashi sama. Da idanu suka bita, Sai kuma Mu'ash ta kalle ta ta ce “Kina ji Nana, babu maganar shawara dashi, ai ba zai bar ki ba. Musamman da ki ka ce ƴar sa ta mutu, ba zai taɓa yarda ki zubar da cikin ba. Kawai ki zubar” “To idan ya kamani fa?” Ta yi maganar kamar zata yi kuka. Girgiza kai Mu'ash ta yi ta ce“Ba zai kama ki ba. Babu abin da zai faru” Shiru Nana ta yi tana tunanin hukunci da zata yanke, Can dai ta numfasa ta ce“Ni dai wallahi bana so!” Daga haka ta tashi ta bar wajen da sauri, Da idanu Mu'ash ta bi ta sai kuma ta girgiza kanta a fili ta ce “Allah wadaran naka ya lalace, Nana! Nana!” **** Bayan sallar isha'i tana kwance akan cinyarsa yana operating system ɗin gabansa, Kamar wadda aka tsikara haka ta mike zaune tana kallon sa ta ce “Uncle” “Uhm..” Ya ce ba tare da ya ɗago kansa ba, Ɗan sosa kanta ta yi kafin ta kwaɓe fuska ta ce “Dama tambayar ka zan yi” Ɗago manyan idanunsa ya yi ya zuba mata, Ta yi saurin ɗauke nata. Babu yabo babu fallasa ya ce “Nana ki bar ni na gama abin da nake dan Allah.” “To magana zan yi fa” Ta bashi amsa kamar me shirin fashewa da kuka, Rufe system ɗin ya yi dan ya san tun da ta fara haka ba zata bar shi ya ƙarasa ɗin ba. Ya jawota jikinsa ya ce “Ina ji mene ne?” Hannunsa ta saka ta fara murɗa lallausan gemunsa kafin ta ce “Uncle wai ba zan iya karatu ba idan ina da ciki?” Da sauri ya kalleta ya ce “wane ya faɗa miki?” Tura baki ta yi ta ce“Ni kawai ka faɗa min!” Ɗauke kansa ya yi yana kallon saitin window, ya ce “Me zai hana ki karatun ki Nana? Muddin kina da lafiya ai zaki iya zuwa makaranta, Sai dai idan kin kuka haihuwa ki ɗauki hutu” Shiru ta yi tana nazari, Ya mai da idanunsa kanta ya ja kumatunta ya ce “Wane ya ce miki ba'a karatu da ciki?” Girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce “Babu kowa” “Ƙarya zaki min?" Ya ce yana tsuke fuska. Sunkuyar da kanta ta yi, Ya girgiza kansa ya ɗago fuskarta ya ce “Kwana biyu uncle ya yi missing Nanar sa” Sarai ta gane abin da yake nufi, Dan haka ta fara ƙoƙarin sauka daga jikinsa amma ya riƙeta gam. “Mene ne?” Ya ce yana ƙoƙarin zare ribbon ɗin data tufke kanta dashi, Kamar zata yi kuka ta ce “Uncle bacci zan yi” “To kwanta” Ya faɗa yana tura hannunsa cikin sumar kanta, Lumshe idanun ta ta yi, Saboda dadin susar da taji. Ya ɗauke system ɗin daga kan gadon sannan ya gyara mata kwanciyarta, Ya sanya hannunsa ya kashe hasken ɗakin nan da nan duhu ya mamaye ko ina. **** Yola, Nigeria. Yau wata ɗaya kenan da tariyar Anty Khadijah, Tana zaune gefen gadonta ta zuba uban tagumi aka yi sallama aka shigo, Ɗaga kanta ta yi tana kallon yaron da ke tsaye a kanta. Yana ɓare gyaɗar dake hannunsa ya ce “Wai in ji Baba ya ce baki gama abincin ba yunwa yake ji?” Tsabar baƙin ciki rasa abin ce masa tayi, Ta miƙe ta bar wajen tana kwafa. Tsayawa yaron ya yi yana kallon ta ganin ta koma kan kujera ta zauna, Ya juya ya fice daga ɗakin, After some minutes aka buɗe dakin aka shigo cikin ɗaga murya yana cewa “Khadijah! Khadijah! Khadijah!” Kallon sa kawai Anty Khadijah ta yi sai kuma ta ci gaba da danna wayarta, Rai ɓace Malam Garba ya ce “Ke tsabar rashin mutunci kina ji ina miki magana kin yi min banza! Bayan na aiko yaro baki bashi amsa ba? Me ki ke taƙama dashi ne?” Miƙewa tsaye ta yi a fusace ta ce “Ban sani ba ɗin! Ba kuma zan yi bane, Wallahi ba zan ci gaba da dafa uban abinci ba a cikin gidan nan, Ban haifa ba babu wanda zan yi wa girki! Dan haka idan ma zaka nemi mai girka maka abinci ka nema ni ba yar iska ba ce...” Saukar marukan da taji shi ne abin da ya sanya ta yi shiru da maganar tata, Ta sanya hannayenta duk biyun ta rike kuncinta tana kallon sa. Can kuma ta ce “Na rantse da Allah baka isa ba! Wallahi ba zan yarda ba! Kai ka isa ka dinga dukana” Ko rufe baki bata yi ba ya hau ta da duka ta ko ina, Tun tana ƙoƙarin kwacewa har sai da ta ƙasa koda motsi a ƙasan ya sanya ƙafarsa ya take hannunta cikin masifa da kumfar baki ya ce “Ke har kin isa a gidana? Ban auri wadda zata ɗaga min murya ba! Duk ranar da ki ka kara yi min irin haka wallahi sai na karya ki” Ya yi ball da ita kamar ya samu ƙwallo, Ta bugu da jikin gado, Ya juya har ya kai ƙofa sai kuma ya dawo yana kallon ta ya ce “Kuma idan baki tashi kin fito ba wallahi na dawo sai kin raina kan ki!” Ya zabga mata harara sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Tsananin azaba ta sanya Anty Khadijah kasa motsi a wajen, Ga ciwon da jikinta ke mata, Ga kuma na duka. Yau kusan kwana uku kenan kullum sai ya yi mata mugun duka da zarar ɗan abu ya haɗa su, Ta dinga kuka a wajen tana numfarfashi, Tafi awa ɗaya kwance kafin ta iya tashi zaune. Gefen bakinta sai jini yake sakamakon marukan da ya yi mata, Dakyar ta lallaɓa jikinta ta tashi ta shige banɗaki, Wanke fuskarta ta yi dan babu wadataccen ruwan da zai ishe ta ta yi wanka. Ta dawo ta kwanta akan kujera tana gursheƙen kuka. Bayan mintuna goma ta tashi tunawa da abin da ya ce, Dan ta san idan ya dawo wani sabon dukan zai mata. Ta dinga takawa dakyar ta fito daga ɗakin, Kasancewar yammacine ya sanya soron ya ɗan yi duhu, Ta nufi soron da yake zaune dan ta tambaye shi abin da za'a girka ɗin. Maganar data jiyo ya sanyata tsayawa cak a bakin ƙofar, Muryar Kaddu taji tana bala'i tana masa magana, Malam Garba ya yi murmushi ya ce “Ke ki rufe min baki idan har ba so ki ke na ɓatar da ke ba!” Kaddu da ke tsaye tana jijjiga ƙugu ta kalle shi ta ce “Idan ka fasa! Dan girman Allah kada ka fasa ɓatar dani, Ka manta duk abin da nayi maka. Haka muka yi da kai? Wallahi baka isa ba, Yanda ka ce zan auri mutumin nan idan na bawa Khadijah wannan maganin ka aureta to wallahi sai ka saka na aure shi! Dole ne wannan, Mahaukaciya ma zaka mayar dani kenan!” Da wani irin mamaki Anty Khadijah ke sake buɗe idanun ta, Ji ta yi kunnuwanta na neman jiye mata wani tashin hankali, Ko dai ba Kaddun data sani ba ce? . Malam Garba ya girgiza kansa yana wata irin muguwar dariya, Lokaci ɗaya kuma ya tamke fuska ya ce “Dani zaki ja? Me ki ke tunani? Na saka kin min aiki akan Khadijah saboda na biya ki da wanda take shirin aure?.” Ya tuntsire da dariya sannan ya ci gaba da faɗin “Har abada ba zaki aure shi ba, Ke bama zaki yi aure ba. Haka zaki yi ta gararamba a gari, Shi kansa barikin sai an daina nemanki. Kuma babu abin da ki ka isa ki yi min, Ni Garba ni ne me abin yi, Idan na so a yau sai nayi abin da zai sa ba zaki kwana da rai ba!” Wata irin shewa irin ta yan bariki Kaddu ta yi ta tafa hannu sannan ta ce “Ai ko zan nuna maka wace Kaddu! Zan shayar da kai mamaki! Wallahi ina da bokayan da sai sun kashe min kai! Kuma ka jira abin da zai biyo baya. Zaka gani!” Tana gama faɗin haka ta zura takalmanta ta yi waje ko mayafin bata yafa ba, Ban da dariya babu abin da Malam Garba ke yi, Ya dinga girgiza kansa yana daga zaune. Juyawar da zai yi suka haɗa idanu da Anty Khadijah, Ya tashi tsaye yana kallon ta a ɗan daburce ya ce “Kkk... Khadijah!” Girgiza kanta ta dinga yi hawaye na zubowa akan fuskarta, Ya tako har gabanta yana kallonta ya ce “Kina ji” Anty Khadijah bata ce komai ba ta juya ta nufi hanyar daƙinta, Tana kai wa bakin ƙofa ta faɗi a ƙasa Sumammiya. Malam Garba ya yi kanta da gudu yana kiran sunanta. **** Zahra na zaune kan kujera a parlour tana danna wayarta aka buɗe ƙofar dakin, Shigowa suka yi bakin su ɗauke da sallama. Ta amsa da fara'a tana fadin “Laaa Yaya sannun ku da zuwa” Babban ciki ne ya amsa da “Yauwa Zahra'u” Suka zauna kan kujera ta miƙe tana fadin “Bari na kira Umman” To kawai ya ce sannan ta nufi sama da sauri. Buɗe ɗakin Umma ta yi ta shiga, Ta sameta zaune kan dadduma tana jan carbi, ƙarasawa ta yi ta zauna gefen gadon tana kallon ta ta ce “Umma kin yi baƙi” Sai da ta ƙarasa lazumin da take ta shafa sannan ta juyo ta kalleta ta ce“Su wane?” “Yaya Bashir ne, Da Kamal ƙaninsa” Da ɗan mamaki Umma ta ce “Ikon Allah yaushe Bashir ya dawo?” “Kamar rannan naji a group ɗin gida an ce ya dawo" Sai da ta miƙe ta naɗe daddumar sannan ta ce “Allah sarki bari naje mu gaisa” To kawai Zahra ta ce, sannan ta kwanta gefen gadon, Ita kuma Umma ta fice daga ɗakin. Wayarta ta ɗauka ta shiga gallery tana kallon hotunan Noor, Can kuma ta kai kan wani hoton Abdusammad wanda yake zaune cikin office ɗin sa, Sanye da suit, Bai ma san ta dauki hoton ba sanda ta taɓa zuwa asibiti wajen sa. Iyaka kyau hoton ya yi kyau musamman yanda ya yi murmushi yana ƙoƙarin mata magana, Ji ta yi wani iri a jikinta, Ta yi saurin ajiye wayar a gefe, Cikin yan mintuna sai ga hawaye na zubowa gefen idanunta. Tabbas ta yi kewarsa, tana kan yi kuma, Kullum sai ta tuna shi, Idan ba shi ba to Noor. A duk sanda ta tuna shi sai taji ina ma ta tashi ta bi shi, ina ma bata dawo ƙasar nan ba, Ina ma ƙaddara bata rabata dashi ba, Har yanzu bata daina sonsa ba. Kamar yanda ta san shi ma bai daina sonta ba, Kawai dai yana ƙoƙarin mantawa da ita ne. Haka ta dinga tunanin sa a wajen tana sake-sake a zuciyarta, Can kuma ta ɗauki wayar kamar wadda aka yi wa dole haka ta hau dialing numbern sa. Ganin har ta katse bai ɗauka ba ya sanyata ajiye wayar, wasu zafafan hawaye suka ci gaba da zubowa kan fuskarta. Daga karshe ma tashi ta yi ta fice daga ɗakin ta koma nata. **** New York. Nana na zaune kan sofa tana kallon tv kasancewar ranar Saturday ne babu lecture taji wayarsa na ringing, amma har ta katse bata tashi a inda take ba. Tunawa ta yi da chocolate ɗin ta ta jiya da suka siyo ta miƙe ta nufi cikin ɗakin ta, Ledar gaba ɗaya ta dauko ta dawo parlour, Samu wayar ta yi tana ci gaba da ringing. Ta ajiye ledar kan kujera sannan ta nufi inda wayar take, Kafin ta ɗauka ta katse, Ta ɗan yi tsaki sai kuma ta koma ta zauna da wayar a hannunta, kasancewar ta san password ɗin ya sanya ta cire dan ganin wanda yake kira. Koda ta shiga call log ɗin sunan Buddy ta gani a sama, Ta taɓe baki tana ƙoƙarin ajiye wayar idanunta ya sauka akan sunan dake ƙasan na Aliyun. “Zahra!” Ta faɗa a fili tana sake ware idanun ta kan screen ɗin, Mamaki ne ya kusan kasheta, Duk da ta san da ba haka ya yi saving numbernta ba. Amma ta san bashi da wata mai irin sunan, Dan haka ta danna kira dan ganin wacece. Har ta gama ringing ba'a ɗauka ba, Tayi kamar ta ajiye wayar sai kuma ta sake danna kiran, Sai da ta kusan katsewa sannan aka ɗaga, Daga ɗaya bangare Zahra ta ce “Hello, Salamu alaikum.” Wani irin abu ne ya zo ya tokarewa Nana a ƙijri, Ta kasa koda haɗiyar yawu, Jin ba'a yi magana ba ya sanya Zahra ta yi ƙasa da murya ta ce “Docco... Doctor!” “Algunguma! Muguwa azzaluma, mai kashe mutane! Uban me yasa ki ke kiran sa? Me zai miki? Ko shi ma kashe shin zaki yi? To wallahi Uncle yafi karfin ki! Banza kawai, Dangin masu kisa!” Da mugun mamaki Zahra ke sauraren kalaman Nanar, Dan bata yi tunanin ita ce ta ɗaga wayar ba, Ta kasa cewa komai tana jin wani irin zafi a zuciyarta. Cike da masifa Nana ta ci gaba da faɗin “Na rantse duk ranar da ki ka sake kiran mijina sai na yi miki abin da ba zaki manta dani ba! Banza kawai masu kashe mutane! Dangin da babu Allah a ransu!” “Nana!” Ya kira sunanta a tsawace. Kallon sa ta yi ganin yanda ya yi tsaye a wajen yana kallonta da mamaki, Kafin ya ƙaraso ya karɓe wayar yana faɗin “Ke dawa? Wa ki ke zagi haka?” Ƙoƙarin fizge wayar ta fara yi tana cewa “ni ka bani, Ka bani na zageta! Kwartuwa mai kiran mazajen mutane!” Wata irin tsawa ya daka mata wadda ta sanyata shiga cikin hankalinta, Ta tsaya tana kallon sa. Sai a sannan ya kalli screen ɗin ya ga sunan wadda ke kiran, Bai ce komai ba ya juya ya bar wajen da wayar a hannunsa. Nana ta dinga bin sa da kallo kamar wata zararriya, Tama kasa gane abin da ya yi. Shi ko cikin ɗakin ya koma sannan ya kai wayar kunne muryarsa a nutse ya ce “Zahra lafiya dai ki ka kirani?” Zahra da taji wani irin abu ya tsaya mata a ƙirji ta kasa magana, Sai shessheƙar kuka da take. Ya gyara tsaiwarsa ya ce “Subhanallahi lafiya dai? Ko wani abun ya faru?” Girgiza masa kai ta yi tana ƙoƙarin ɓoye kukanta ta ce “Doctor ba komai, kawai kiran ka nayi na gaishe ka” Ta ƙare maganar hawaye na yar rige-rigen sauka kan fuskarta. Jinjina kansa ya yi dan yana da fahimta ya ce “Allah sarki to ya ku ke? Ya Umma?” “Tana nan kalau" Ta bashi amsa a sanyaye, Ya gyaɗa kansa kafin ya ce “To ki gaishe min da ita. Na gode, Sai an jima” Ji ta yi kamar kar ya katse wayar, Amma ta dake ta ce “Tom in sha Allah, Na gode.” Daga haka ta kashe wayar. Ajiyar zuciya Abdusammad ya sauke sannan ya girgiza kansa, Ya zura wayar cikin aljihun trousern da ke jikinsa sannan ya fito daga ɗakin. Durƙushe ya samu Nana a wajen sai kuka take, Ya yi kamar ya wuce sai kuma ya nufi inda take. Tsayawa ya yi a gabanta yana kallonta fuska babu walwala ya ce “And this should be the last time da za'a kirani a waya ki ɗauka, Koma wane kar ki sake ɗaga min waya. Sannan kada ki sake zagin wani tun da bake ya kira ba, Bana son tashin hankali. Ki nutsu ki kama kan ki! Idan ba haka ba sai na ɓata miki fiye da tunanin ki wallahi!” Ya ƙare maganar a ɗan zafafe, Ita dai ko ɗago kanta bata yi ba, Ya ja tsaki sannan ya juya ya fice daga parlon. Sai a sannan ta ɗago idanun ta wanda suka yi jajur, Ta kalli hanyar ƙofar sai kuma ta fashe da wani raunataccen kuka. 08106608363 Nanameera.*Page 70.* Yinin ranar Nana a ɗaki ta yi shi ko parlourn ƙasa bata sakko ba, Shi ma bai sake shiga harkarta ba har dare. Around 9pm ya shigo ɗakin cikin shigarsa ta ƙananun kaya hannunsa na dama riƙe da wayarsa yana dannawa, Tana kwance kan gado ta yi nisa cikin tunanin da take. Ya tsaya gefen gadon ya zura wayar a aljihu yana kallon ta ya ce “Ki tashi ki ci abinci” Ko daga kanta bata yi ba ballantana ya saka ran zata kula shi, Ya ɗan yi jim kafin ya sake cewa “Nana baki ji bane? Tashi nace!” A fusace ta tashi zaune tana kallon sa tana huci ta ce “To ba zan ci ba ɗin, Ina ruwanka dani ko dole sai na...” Saukar marin da taji ya sanyata haɗiye ragowar maganar tata, Ta sanya hannunta na hagu ta dafe kuncin daya mara tana kallon sa, Kuka take son yi amma ta kasa. Fuskarsa a haɗe babu alamar wasa ya ce “Duk ranar da bakin ki ya sake kuskuren ɗaga min murya sai kin gwammace baki sanni ba!” Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama. Sai da ta ga ya rufe kofar sannan ta kece da wani kukan baƙin ciki, Ta koma ta kwanta tana kuka kamar ranta zai fita. Abincin da bata ci ba kenan har bacci ɓarawo ya saceta, Cikin dare ta farka saboda ciwon da cikinta ke mata, Ta tashi zaune tana dafe da cikin nata. Ta jima zaune a wajen tana kuka kafin ta tashi ta shige toilet, Fitsari kawai ta yi ta dawo ta kwanta, After 5mins ta tashi da gudu ta koma toilet ɗin, Amai ta yi ta tsaya a wajen tana sauke numfashi. Sai da ta ɗan ji sauƙin cikin sannan ta fito daga toilet ɗin ta kwanta akan gadon, Ta jima kafin wani baccin ɗauketa. Da asuba ya shigo ɗakin yana sanye da jallabiya mai taushi hannunsa riƙe da counter da alama masallaci zai je, Kallon ta ya dinga yi ganin yanda ta cure jikinta waje guda, Daga jin yanayin yanda take numfashi ka san ba daɗi kwanciyar take ji ba. Ya ƙarasa ciki ya gyara mata kwanciyar sannan ya ja duvet ya rufeta, Ya ɗan yi jim yana kallon kyakkyawar fuskarta wadda ta kwaɓe ta kamar zata fashe da kuka, Girgiza kansa ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Sai ƙarfe 8:00 na safe ta farka, Tana tashi ta shige toilet ta yi wanka, Ta fito ta shirya cikin wasu riga da wando marasa nauyi, Ta koma gefen gado ta zauna ta yi shiru tana tunanin abin da ya faru jiya. Kenan har yanzu yana sonta? Har yanzu bai rabu da ita ba? Har yake iya yi mata tsawa akanta. Shar haka taji hawaye na zubowa kan farar fuskarta, Babu abin da ya fado mata a rai sai Junaid, Allah sarki, Duk da ya aikata mata ba daidai ba amma ta san da shi ne ba zai taɓa yi mata haka ba. Domin shi ne wanda ya nuna yana sonta, Wannan kuwa kowa ya san auren alfarma ne a tsakanin su, Da wannan tunanin ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta tana fashewa da wani sabon kukan. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta tashi ta shige bayi, wanke Fuskarta ta yi ta fito ta zura hijabi kan kayan jikinta sannan ta ɗauki wayarta da jakar makarantar ta ta fice daga ɗakin. Bata same shi ba ko a ƙasa duk da kasancewar ranar Sunday ne, Kawai ta samu driver ta ce ya kaita schl ɗin. Koda ya sauketa shiga ta yi, Babu wasu mutane sosai domin ba kowa ke da lecture Sunday ba, Suma wani lecturer ne ya kira su. Dan haka kai tsaye department ɗinsu ta nufa, Tana zuwa ta samu har an fara lecturen. Haka dai ta nemi waje ɗaya ta zauna tana saurara duk da ba fahimta take ba, Bayan sun gama tana shirin fitowa taga Amani. Kallon ta kawai ta yi sai kuma ta ɗan yi murmushi ta ce “Ina Mu'ash?” “Bata zo ba” Amani ta bata amsa kai tsaye, Jinjina kai Nana ta yi sai kuma ta ɗauki jakarta tana ƙoƙarin ratayawa ta ce “Zan tafi sai jibi.” “Nana me ya faru ne? Naga duk kin yi wani iri, Me ya samu fuskar ki?” Sai a sannan Nana ta kai hannunta kan fuskarta saitin daya mareta. “Wa ya dake ki?” Amani ta sake mata tambayar, Girgiza kanta ta yi hawaye na taruwa cikin idanun ta ta ce “Babu kowa.” Ɗan murmushi Amani ta yi sai kawai taja hannunta suka fice daga class ɗin. Can wajen wata coconut tree ta kai ta suka tsaya, Ta ɗan yi murmushi ta ce “Nana idan baki faɗa mana abin da ya dame ki ba wa zaki faɗawa? Kin san dai baki da kowa a ƙasar nan idan ba mu ba ko? To akan me zaki ɓoye mana abin da ya dame ki” Ai kamar jira Nana take ta fashe da kuka, Ta fara murza idanunta da hannunta na hagu, Amani ta ɗan yi shiru tana kallon ta can kuma ta riƙe hannunta ta ce “Ki yi haƙuri ki daina kuka, Ki faɗa min abin da aka yi miki” “Uncle ya tsaneni, Baya sona. Uncle bani yake so ba matarsa yake so, Nima bana son shi, Tafiya gidanmu zan yi, Ba zan koma gidan sa ba. Ƙasar mu zan tafi, Sai dai ya sakeni, Ba zan zauna dashi ba wallahi!” Amani da bata gama fahimtar abin da ya faru ba ta ce “Wai me ya yi miki? Me ya sake haɗa ki dashi? Shi ne ya mareki?” Gyaɗa mata kai Nana ta yi cikin kuka ta ce “Saboda na zagi tsohuwar matarsa shi ne ya ke min bala'i, Kuma ya mareni, ai baya sona. Ita yake so har yanzu, Nima ai gara na bar gidan kawai” Girgiza kai Amani ta yi ta ce “Akan me zaki bar gidan Nana? Gidan mijin ki ai, Kin san me ya sa yake miki haka?” Shiru Nana ta yi lokaci ɗaya ta shiga girgiza kanta. Amani ta gyara tsaiwarta sannan ta ce “Saboda wannan cikin ne! Shi ne abin da ya saka yake nuna baya sonki. Mazan yanzu haka suke, Zasu nuna suna sonki, Su dinga taraiyarki, Su saka ki farin ciki da nishaɗi, Amma daga sanda ya fahimci akwai ciki a jikin ki sai ya watsar. Sai ya daina ɗaukan al'amuran ki da girma, Ya mayar da ke kamar wata mara amfani, Sai ki yini bai shiga harkar ki ba. Wanda da a sanda ki ke lafiya ne yake morarki baya miki haka” Shiru Nana ta yi tana nazarin kalaman Amani. Amani ta sake cewa “Ke yanzu da haka yake miki? Sanda ya aure ki haka yake miki? Ko farkon zuwan ki ƙasar nan haka ya dinga miki?” Girgiza kai Nana ta yi, Amani ta ɗora da faɗin “To me ya sa yanzu ya sauya miki? Me yasa ya daina kulawa da ke? Me yasa yake iya dukan ki? Amsar guda ɗaya ce, Saboda yanda yana ganin ciki a jikin ki. Yana ganin kin gama masa amfani idan bana haihuwa ba, Wannan shi ne ya sanya sanda ya aure ki ya dinga yiwa Zahra haka ita ma. Ki nutsu ki fahimci komai Nana” Kusan mutuwar tsaye Nana ta yi a wajen saboda mamaki, Tunanin bai taɓa kawo wa nan ba, Sai yanzu da Amani ke faɗa ta fara tabbatar da hakan. Da gaske sanda bata da ciki ba haka yake mata, Daga samun cikinta zuwa yanzu basa kwana biyu basu yi faɗa ba, Kusan kullum sai ya mata tsawa. Kenan wannan shi ne dalili? Amani ce ta katse mata tunanin da take ta hanyar faɗin “Kin gane abin da nake nufi?” Nana ta gyada mata kai hawaye na zubowa kan fuskarta. Jinjina kai Amani ta yi kafin ta ce “Yanzu shawara ta rage naki, Idan har kina son zama cikin gidanki hankali kwance cike da soyyayar mijin ki to sai dai ki rabu da wannan cikin da ke jikin ki!” Shiru Nana ta yi, Ta rasa wace makama zata kama, Ta yarda ta zubar da cikin ko kuwa ta bar shi? Idan ta bar shi haka zata ci gaba da zama gidan Uncle cikin baƙin ciki daga nan har ta haihu? Ta girgiza kanta a fili ta ce “To ya zan yi na zubar?” Murmushi Amani ta yi ta ce“Yauwa kin zaɓi abin da zai fissheki. Kina ji yanzu ki zo muje na sauke ki sai mu biya da pharmacy ɗin da muke siyan magani na karɓa miki tablet ɗin.” Jiki a sanyaye Nana ta ce “To kuma zai zube ɗin?” Wani kallon sheƙeke Amani ta yi mata sai kuma ta ce“a'a ƙarya zan miki!” Daga haka ta yi gaba abin ta, Sauke numfashi Nana ta yi sannan tabi bayanta. Kamar yanda Amani ta faɗa haka ce ta faru, Ta barta a motar ta tsallaka ɗaya side ɗin inda babban Medcare pharmacy ɗin yake. Ta shiga bata jima ba ta dawo hannun ta riƙe da leda, Akan cinyar Nana ta ajiye ledar sannan ta yiwa motar key suka ci gaba da tafiya. Nana ta dinga kallon ledar ba tare da ta yi gigin taɓawa ba, A bakin mansion ɗin nasu ta yi parking sannan ta juyo tana kallon ta ta ce “To gashi nan, Guda ɗaya kawai zaki sha, Kada ki sha sama da haka. Sannan ki bari sai baya nan, Kamar kin san ya kusa dawowa ko kuma zai fita sai ki sha, Ki yi komai a nutse, kar ki bari ya gani” Ban da gyada kai babu abin da Nana ke yi, Ta sauke numfashi kafin a sanyaye ta ce “To babu matsala dai ko? Idan na sha kuma wani abun ya sameni fa?” Ɗan tsaki Amani ta yi ta ce “Ke wai yaushe zaki fara fahimtar abubuwa ne? Cewa nayi fa ki sha idan ya kusa dawowa, Ko kuma ya kusa fita, Yanda ba zai yi nisa ba. Sai ki ce ko faɗuwa ki ka yi ko wani abun, Kada ki bar ya gani! Kada ki kuskura ki bari ya gani” To kawai ta ce sannan ta ɗauki ledar ta mata sallama ta buɗe motar ta fita. Amani ta bita da idanu sai kuma ta girgiza kanta, Ita har cikin zuciyarta tausayi take bata. Sai da taga ta shiga gidan sannan taja motar ta ta yi gaba, Nana kuwa a compound ɗin farko ta tsaya ta zare maganin daga ledar ta yar a dustbin sannan ta saka maganin cikin ɗan ƙaramin aljihun jakarta sannan ta ci gaba da tafiya. A sanyaye ta buɗe ƙofar parlourn ta shiga, Zaune ta hange shi yana magana a system da alama vidcall yake yi, Ta ƙarasa ciki ba tare da ta ce komai ba. Tsayawa ta yi a bayansa dan ganin da wanda yake wayar, Sai dai fuskar wadda ta gani ya sanyata sunkuyar da kanta. Murmushi Zahra ta yi ta daga mata hannu ta ce “Hi Nana!” Sai a sannan Abdusammad ya juya yana kallon ta dan sam bai lura da shigowar tata ba, Bata ce komai ba ta juya ta nufi hanyar sama a sanyaye. Sai da ta bar wajen sannan Zahra ta ce “Dan Allah doctor ka tayani bata hakuri, Ta daina jin haushina” “Just leave her” Ya ce a takaice, Shiru Zahra ta yi duk sai taji bata ji daɗi ba, Ita yanzu bata da niyyar ganin wani abu mara kyau ya samu Nana dan haka ta numfasa ta ce “Sai an jima.” “Mu jima da yawa” Ya ce yana ƙoƙarin rufe system ɗin. Tashi ya yi ya nufi saman shima, Kai tsaye daƙinta ya buɗe ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, Tana zaune gefen gado ta kifa kanta akan cinyoyinta sai kuka take. Ya ɗan yi shiru sai kuma ya ƙarasa ciki, A gefen gadon ya zauna yana kallon ta still bai ce komai ba, Can dai ya numfasa ya ce “Nana!” Bata amsa ba haka kuma bata ɗago kanta ba, Ko kaɗan bata son jin muryarsa, Baƙin ciki isarta yake, Ji take kamar ta mutu ta huta da zama dashi. Ya jawo hannunta a sanyaye ya ce “Me akayi miki kuma?” Ya yi maganar yana ƙoƙarin matso da ita jikinsa, Janye jikinta ta yi ta sauka daga kan gadon ta shige toilet ba tare da ta yarda sun haɗa ido dashi ba, Ya yi shiru yana kallon ƙofar bayin, Can kuma ya tashi ya fice kawai. **** Yola, Nigeria. Zahra ta dinga kallon Umma jiki a sanyaye, Can dai ta ce “Umma Ya Bashir kuma?” Gyaɗa mata kai Umma ta yi kafin ta ce “Eh Zahra'u, Bashir, Yana son ki ya ce. Kuma zai aure ki, Dan haka kawai ki bashi dama, Da zarar iddar ki ta ƙare sai a ɗaura muku aure.” Shiru ta yi tana sauraren Ummar, Ita gaba ɗaya sai taji jikinta ya mata sanyi, Bashir ɗin da bata yi tunani ba shi ne zai zama mijinta na biyu, Shi ɗin ɗan yayar Umma ne, A Kaduna suke, Yana aiki a Saudiyya. Tun tana ƴar ƙarama ya taɓa cewa yana sonta, amma bayan tafiyarsa sai ta gamu da Abdusammad ta kuma ce shi take so, Har zuwa wannan lokacin bai yi aure ba, Gashi ƙaddara na neman sake hada su a matsayin mata da miji. “Zahra'u” Umma ta kira sunanta a nutse, Ɗaga kanta ta yi ta kalleta a sanyaye ta ce “Na'am Umma...” “Kin yarda? Bana son nayi miki abin da ba zai miki daɗi ba, Idan kin ce bakya son sa shikenan domin a yanzu kina da damar zaɓar mijin da ki ke so. Amma ki sani ba zan ji daɗi ba idan ki zama kamar yanda Khadijah ta zama, Kin ga dai yanzu halin data saka kanta” Zahra da hawaye ya fara sakkowa kan fuskarta ta ce “Ba zan sake ƙin biyayya ba Umma. Na yarda zan aure shi, Na yarda wallahi” Ajiyar zuciya Umma ta sauke dan daman ta san halin Zahra ba zata bata matsala ba, Ta dafata fuskarta ɗauke da mabayyanin farin ciki ta ce “Allah ya yi miki albarka, In sha Allah Alkhairi zaki gani a rayuwar ki Zahra'u, In sha Allah ba zaki sake samun matsala ba. Ki dinga yawan addu'a kin ji, Allah ya tabbatar mana da Alkhairinsa.” Jiki a sanyaye Zahra ta ce “Amin Umma, Na gode sosai." Murmushi kawai ta yi, Ta miƙe tana ƙoƙarin barin ɗakin ta tuna, dan haka ta tsaya ta ce “Na manta, Ki samu ki je ki duba Khadijah, Ina son ki manta da komai dan Allah.” Ba zata iya yiwa Umma musu ba, Duk da daman ita bata riƙe ta ba, Ta kalleta ta ce “To Umma zan je in sha Allahu.” “Allah ya yarda” Cewar Umma, Sannan ta juya ta fice daga ɗakin. Ajiyar zuciya Zahra ta sauke tana jin wani iri a ranta, Kaddara ta rabata da mijinta, Ta kuma rabata da ƴarta, sannan take shirin haɗata da wani sabon mutumin a matsayin abokin rayuwa. Tabbas Allah abun tsoro ne, Komai nasa akwai hikima da dalilin faruwa. Bayan sallar la'asar ta shirya suka je gidan Anty Khadijah ita da Safeena da Amal. Sanda suka je tana zaune a ɗaki ta zuba uban tagumi, Gaba ɗaya ta sauya kamar ba ita ba. Ta yi wata irin rama ta tashin hankali, Babu abin da ka ke gani a jikinta sai ƙashi da idanu, Ga wata irin yamushewa da fatarta ta yi. Sai kace wadda take fama da cutar ƙanjamau, Tun ranar data faɗi a soro bata sake takawa ba, Gaba ɗaya kafafun sun nannaɗe sannan Malam Garba ya hana akai ta asibiti ballantana a san abin da ke damunta. Sai ƙarewa take a banza, Babu ci babu sha, Sai kuka kawai, Babu abin da ke ɓata mata rai sama da abin da Kaddu ta yi mata, Ashe ƙawar da take ɗauka fiye da kowa nata ita ce take cutar da ita, Tabbas duk wanda ya bar Allah sai Allah ya bar shi, Kuma duk harkar da babu Allah kana zaune zata wargatse aji kunya. Zahra da ke zaune gefen gado ta kalleta ta ce “Sannu Anty, Allah ya baki lafiya” Anty Khadijah bata iya cewa komai ba sai hawaye dake zubowa kan yamusasshen fuskarta, Safeena da ke hawaye ita ma ta ce “Kin gani ko Anty? Abin da nake ta faɗa miki kenan amma ki ka ƙi ji, Yanzu kalli halin da ki ke ciki. Kin zama abar tausayi, Kin raba mata da mijinta, Kin yi silar mutuwar ƴarta, Ina zaki je da wannan haƙƙin?” Girgiza kai Zahra ta yi muryarta a sanyaye ta ce “Ki bar cewa haka Safeena, Ni wallahi na yafe mata, Na yafe har abada. Duk da naji zafinta a da amma yanzu ya huce, Na gane kuma ƙaddara ce ta sanya hakan ta faru, Dan haka ni na yafe kome ta yi min, Ina mata fatan Allah ya yafe mata.” Wani irin raunataccen kuka ne ya kwacewa Anty Khadijah, Ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta tana rera shi, Tabbas ta yi dana sani, Ta ji kunya, Ta yi nadama. Nadamar da baza ta amfanar da ita komai ba, Domin komai ya ƙare mata. Tashi Zahra ta yi ta koma gefenta ta ɗagota ta fara share hawayenta ta ce “Ki yi haƙuri Anty, Dan Allah ki daina kuka kada wata cutar ta same ki bayan wadda ki ke ciki” Gyaɗa mata kai Anty Khadijah ta yi sai a sannan ta ce “Na gode Zahra.” Zahra ta yi shiru hawaye na zubowa kan fuskarta, Ɗan uwa rabin jiki, Sai taji ina ma ita ce ciwon ya sameta ba Anty Khadijahn ba. Suna nan zaune har kusan magriba sannan suka tafi gida, Ko awa biyu basu yi da zuwa gida ba aka kira wayar Umma, Bayan ta ɗaga matar gidan ta sanar da ita halin da Anty Khadijahn ke ciki, Umma da ta gama ruɗewa ta faɗawa su Zahra haka suka sake ɗungumar jiki suka koma gidan, Koda suka je basu sameta ba, Dan an yi asibiti da ita. Dan haka suka wuce can, A asibitin suke samun labarin irin dukan da Malam Garba ya yi mata bayan tafiyar su Zahra, Ya kuma ce ya saketa, Akan ta tambaye shi gwala-gwalanta da ke hannun sa. Umma ta jingina da jikin bango hawaye na zubowa kan fuskarta. Su kansu su Zahra kuka suke, Duk da basu san halin da take ciki ba, Suka bugawa Siyama waya suka sanar da ita. Kasancewar gobe zata gama takaba yasa ta ce goben tana hanya zata zo, Suna nan zaune har kusan ƙarfe 10 na dare kafin likita ya fito, Da sauri suka ƙarasa inda yake, Zahra ce ta yi ƙarfin halin cewa “Doctor ya jikin nata?" “Ki sameni a office!" Shi ne kawai abin da ya ce sannan ya yi gaba, Zahra ta sauke numfashi ta bi bayansa. Koda ta shiga office ɗin a tsaye ta same shi, Ya yi alama data zauna ta zauna sannan shi ma ya zauna, Zare glasses ɗin idanunsa ya yi yana kallon ta ya ce “Ke ƴar uwarta ce?” Gyaɗa masa kai Zahra ta yi ta ce “Eh Yayata ce uwar mu ɗaya uban mu ɗaya” Shiru likitan ya yi can kuma ya ce“Me yasa baku kawota asibiti ba tun wuri? Sannan wa take aure? Ina yake?” Sosai gaban Zahra ya fadi, Ta ce“Tana gidan mijinta ne kuma malami ne baya bari ta fita” Da mamaki ya ce “Malamin ya yi mata wannan illar? I'm sorry to say ya gaba lalata mata jiki, Na ɗaya ba zata sake haihuwa ba, Na biyu tana da cutar Hiv. Na uku ƙafafunta ba lallai bane su sake takawa, Sakamakon faɗuwar da ta yi!” Zahra bata san sanda ta fashe da wani matsanancin kuka ba, HIV? Kenan ita ta shafawa Siyama? Siyama kuma ta shafawa Safwan? Innalil lahi wa ina ilayhi raji'una. Shi ne abin da kawai take iya maimaitawa cikin ranta, A fili kuwa ban da kuka babu abin da take. Tashi likitan ya yi ya fice daga ɗakin baki ɗaya. **** Washegari da safe Nana na tashi ta yi wanka, Ta fito parlour, Kitchen ta shiga ta haɗa breakfast sannan ta fito ta zauna anan kan sofa, Bayan ta gama ci ta tashi ta koma ɗakin da niyyar ɗaukan maganin da Amani ta bata, Dan ta san yanzu duk inda yake to ya gama shirin fita. Sai dai me? Duk irin duban da ta yi wa jakar bata ga maganin ba, Babu shi babu dalilinsa. Sai da ta zazzage gaba ɗaya takarcen da ke ciki duk da ta san a pocket ɗin jakar ta ajiye, amma aka ce idan raƙumin ka ya ɓata to har kafar allura ga duba. Tana cikin dube-dube aka buɗe ƙofar ɗakin, A ɗan zabure ta juya tana kallon sa, Sanye yake da suit black colour da alama fita zai yi. Hannayensa zube cikin aljihun trousern dake jikinsa, Kallon kallo suka dinga yi, Can dai ta ɗauke nata idanun tana ƙoƙarin kwashe kayan data zubar “What are you looking for Nana?” Ta tsinkayi muryarsa a sama, Girgiza kanta ta yi a ɗan rarrabe ta ce “Babb...Nothing” “Are you sure?” Ya sake tambayarta. Juyawa ta yi ta kalle shi, Ta ga ya sakar mata murmushi. Ya zaro tablet ɗin daga hannunsa ya daga shi yana faɗin “Ko dai wannan ki ke nema? Are you looking for ur abortion pill ko?” Bata san sanda ta tashi tsaye ba a mugun firgice, Ta fara girgiza kanta da hannayenta ganin yana murmushi har sannan. Ja da baya ta fara yi hankali tashe ta ce “Wallahi wallahi uncle ban sha ba, Na rantse ban sha ba, Sai da nace bana so. Wallahi ba zan ƙara ba!” Bai ce komai ba ya mai da maganin aljihun sa ya juya ya fice daga ɗakin. Nana ta yi zaman daɓaro a gefen gadon tana jin wani irin tashin hankali. Yaushe ya gani? Me yasa bai yi mata duka ba? Sai kawai ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, Sai da ta gaji dan kanta ta yi shiru wajen azahar. Ta tashi ta shige toilet ta wanke fuskarta sannan ta ɗauro alwala, Bayan ta fito ta gabatar da sallah sannan ta zauna a wajen, Har dare bata samu sukuni ba. Shirun da ya yi mata ta matuƙar ɗaga mata hankali, Haka ta koma balcony ta tsaya tana jiran dawowar sa, Bai dawo gidan ba har wajen ƙarfe 12:00 ta gaji da jiransa ta kwanta a wajen. Ba ita ta farka ba sai washegari wajen ƙarfe 9:00 na safe. Ta tashi ta shige toilet ta yi wanka sannan ta ɗauro alwala, Sallah ta yi sannan ta fice daga ɗakin ta nufi nasa, amma koda ta murɗa sai taji a rufe take. Ta kasa knocking haka kuma ta kasa barin wajen, Tana nan tsaye har bayan mintuna biyar taga wata maid ta hauro saman, Ta kalleta ta ce “Excuse me pls.” Tsayawa matar ta yi cike da girmamawa ta gaisheta, Nana ta amsa a sanyaye sannan ta ce “Ina doctor yake?” “He already gone” Ta amsa cike da girmamawa. Shiru Nana ta yi can kuma ta ce“Alright thank you” Ta ɗan sirina sannan ta ci gaba da tafiyarta, Jiki a saluɓe Nana ta koma daƙinta ta zauna. Yinin ranar ma haka ta yi shi a dame, Ko abinci kasa ci ta yi duk da yunwar da take cikinta, Sai wajen isha'i ta tashi ta sake wanka sannan ta yi sallah ta koma ta zauna. Ranar ma bai shigo gidan ba har bacci ya ɗauketa, Da asuba kuwa ta farka, Ta tashi tsam ta fice daga ɗakin gudun kada ya fita bata gan shi ba, Koda ta shiga ɗakin nasa samu ta yi ya tafi masallaci dan haka ta nufi banɗaki ta yo alwala ita ma, A ɗakin ta yi sallah dan akwai kayanta a ciki. Tana nan zaune har gari ya fara haske amma bai shigo ba, Dan haka kawai ta tashi ta fito waje ta tsaya. Ganin bashi da alamar shigowa ya sanya ta koma daƙinta zuciyarta kamar zata fito. Sai da suka jera kwana biyar suna wasan ɓuya dashi, Duk irin yanda take son ganin sa bata samun dama, Sai dai ta zauna ta yi ta kuka. Amani ta kirata yafi sau goma amma bata ɗauka ba, Daga ƙarshe ma blocking numbernta ta y, Ranar juma'a tana zaune ta zuba uban tagumi wayarta ta fara ringing, Kamr ba zata dauka ba sai kuma ta janyo wayar tana kallon mai kiran. Surry ce dan haka ta ɗaga ta kai kunne, Cikin faɗa ta fara cewa “Nana baki da hankali ko? Baki san abin da ki ke ba ko? Akan me zaki biye wa su Amani? Bayan kina da tabbacin basu da ilimin addini. Kin san laifin wanda ya zubar da ciki kuwa? Ya za'a yi ki zubar da ciki ma? Kina hauka ne Nana? Kenan duk wanda ya baki shawara sai ki ɗauka, ba zaki tsaya ki tantance mai kyau da mara kyau ba. Nana kina son ubangiji ya dube ki kuwa?” Allah sarki Nana, Tun da ta fara magana ta ke kuka, Ta san su Amanin ne suka faɗa mata abin da tayi. Surry taja dogon tsaki ta ce “Ki bar wannan kukan da ba zai amfane ki ba, Yanzu ki faɗa min kin yi amfani da maganin? Kin zubar da cikin?” Girgiza kai ta yi cikin kuka ta ce “A''a” Surry ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce “To kada ki kuskura ki zubar, Ke kada ma ki sake sauraren abin da zasu ce miki” “Tom. Ai ma Uncle ya ɗauke, kuma ya daina kulani, ko ganin sa bana yi a gidan nan”. Cikin faɗa Surry ta ce “To akan me ba zai daina kula ki ba Nana? Akan me? Ke ko tausayin sa bakya yi. Kina gani ƴar sa ce ta mutu ba'a jima ba, Yanzu akwai abin da yake buƙata sama da Ya'ya ne? Shi ne zaki zubar da ciki. Dole koma wane ya daina kula ki, wallahi ya yi miki da kauna ma, Da bai miki shegen duka ba, Ki nutsu ki kama kan ki wallahi, Idan ba haka ba ki gurguɗe auren ki.” Cikin kuka Nana ta ce “In sha Allah ba zan sake ba, Kuma ai inason na bashi haƙuri ne, amma bana ganinsa, kullum sai nayi bacci yake dawowa. Kuma da safe kafin na tashi yake fita, Yaƙi bari na ganshi” Rage murya Surry ta yi yanda zata fahimceta ta ce “Kina ji ki nutsu, Yau kada ki yi bacci, Ki san yanda zaki hana kan ki bacci har ya dawo.” “To ai idan ya dawo ya ganni ba zai kulani ba, Ɗakinsa zai shiga ya rufe” Shiru Surry ta yi tana tunani, Can kuma ta ce “To yanzu ke je ɗakin nasa ki zauna, Kada ki yi bacci har ya dawo, Idan ya shigo sai ki san yanda zaki bashi haƙuri.” Jiki a sanyaye Nana ta amsa sannan ta kashe wayar. Da daddare tana ganin 9:00 ta yi ta tashi ta yi wanka, Ta shirya cikin kayan baccinta riga doguwa wadda ta tsaya iya gwuiwarta, Fararen ƙafafunta sun bayyana. Ta gyare gashinta sai Sheƙi yake, Hijabi ta ɗauka ta saka sannan ta fice daga ɗakin, Nasa ɗakin ta shiga ta zauna kan kujera ta yi shiru. Tun tana saka ran dawowarsa har sai da ta yi giving up, Ban da gyangyaɗi babu abin da take yi. Tashi ta yi ta buɗe balcony ta shiga, Ta dinga kallon ƙasan gidan gwanin ban sha'awa. Tana nan tsaye har after 25mins ta hango shigowarsa a mota, Nana ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin daɗi, Duk da bata san ta inda zata fara bashi haƙurin ba. Sake rufe balcony ɗin ta yi ta yi shiru tana jiransa, Tana ji ya shigo ya ajiye wayarsa da car key a gefen gado sannan ya nufi toilet. Ya jima kafin ya fito sanye da bathrobe, Ya buɗe press ɗin sa ya dauki boxer ya saka sannan ya tsaya yana shafa mai. Sai da ta yi addu'a kafin ta buɗe balcony ɗin ta fito, Sam bai ji sanda take zuwa ba sai kawai ji ya yi an rungume shi ta baya, Ta riƙe shi da iya ƙarfinta sai kuka take. Yi ya yi kamar bai san tana gun ba, Ya ci gaba da shafa man sa. Cikin kuka ta ce “Dan Allah uncle ka yi haƙuri, Ba zan sake ba. Wallahi ba zan sake ba, Na daina, Na tuba uncle, Ba zan kuma yi maka ba. Ba zan sake ba wallahi, Na yi kuskure kuma ba zan ƙara ba, Ka yafe min dan Allah. Kada Mala'iku su dinga fushi dani...” Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka, Ba zaka taɓa cewa da Abdusammad take ba, Dan ko kezau bai yi ba, ballantana ta saka ran zai ce wani abu. Sai da ya gama abin da yake gaban mirror ɗin sannan ya janyeta daga jikinsa ya karasa gaban gadon, Hawa ya yi ya zauna ya janyo laptop ɗin sa ya kunna ya fara operating ɗinta, Nana ta yi kamar statue a wajen tana kallon sa tana kuka. Can kuma ta ƙaraso ta tsuguna gaban gadon cikin kuka take faɗin “Dan Allah uncle ka yafe min, Ba zan sake cewa zan zubar ba. Wallahi ban zubar ɗin ba, Ba zan ƙara ba. Ƙawayena ne suka ce wai baka sona saboda cikin, Idan na zubar zaka dawo yanda ka ke yi min da. Shiyasa na yarda, wallahi ba da wani abun ba, Dan Allah ka yi haƙuri, Kada ka faɗawa Abbana da Ammata. Dan Allah uncle...” Tashi ta ga ya yi ya fice daga ɗakin, Tabi bayansa da kallo sai kuma ta kifa kanta jikin gadon tana ci gaba da kuka, After some minutes ya dawo hannunsa riƙe da mug, Ya koma ya zauna ya ci gaba da abin da yake yana sipping coffee ɗin a hankali. Bata fasa bashi haƙuri da magiya ba, Haka shima ko da wasa bai kalli inda take ba. A haka har ya kammala abin da yake a system ɗin ya rufeta ya ajiye gefe, Tashi ya yi ya fice daga ɗakin bai jima ba ya dawo ya shiga toilet, wanke bakinsa ya yi ya dawo ya haura saman gadon yana shirin kwanciya. Wata irin zabura Nana ta yi ta riƙe ƙafafunsa tana wani irin kuka kamar wadda aljanu suka shafa, Tama masa maganar sai kukan kawai take tana buga kanta akan ƙafafunsa. Ganin tana neman zare masa ya sanya shi janye ƙafafunsa, Ya ƙura mata idanu yana kallon ta can kuma ya tashi zaune muryarsa a dake ya ce “Ɗagani” Ai kamar ya turata haka ta ci gaba da da kukan tana ƙanƙameshi. Ya girgiza kansa sai kuma ya ce “Me zan yi miki? Ki bar ni na huta mana, Ki yi abin da ki ke so. Ki dau duk hukuncin da ki ka ga ya dace miki, amma ki daina damuna. Ki bar ni dan Allah!” Ya ƙare maganar a nutse, Ai kamar jira take ta shige girgiza kanta cikin kuka ta fara cewa “Wallahi A'a uncle ba zan kuma ba, Na nutsu, Ba zan ƙara yi maka rashin kunya ba. Ba zan sake yin rashin jin magana ba, Zan zauna lafiya dan Allah ka yi haƙuri” Taɓe baki ya yi still looking at her ya ce “Kin ji na yi miki magana akan ki daina abin da ki ke? Kin ji nace Nana bari? Ai bana so ki bari. So nake ki ci gaba, Ki ci gaba da duk abin da ki ke, Ba dai burin ki hankalina kada ya kwanta ba? Ba dai burin ki ki dinga sakani damuwa ba? To ki je ki ci gaba. Zan auro wadda zata dinga jin maganata, Ta kuma dinga girmamani. Ki je ki yi abin da ki ke ganin ya dace da rayuwarki!” Haba ai ji ta yi kamar ta faɗi ta mutu saboda baƙin ciki, Ta saki wata irin ƙara tana ƙoƙarin yin baya, Cikin zafin nama ya tarota gudun kada ta faɗa kansa, Ya jawota jikinsa jin ta daina numfashi. Kumatunta ya dinga taɓawa yana cewa “Ke Nana! Nana! Open ur eyes. Nana! Mamanaa. Mamanaa! Open ur eyes kin ji, Da wasa nake miki, I'm just kidding, Ba zan auro wata ba, Stay still kin ji.” Ko kaɗan Nana bata jin abin da yake cewa dan tuni ta sume a wajen, Ya kwantar da ita ya tashi cikin tashin hankali ya fice daga ɗakin, Da sauri ya dawo hannunsa riƙe da gorar ruwa mai sanyi, Ya buɗe ya yayyafa mata. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana wani irin numfarfashi, Ya ajiye ruwan a ƙasa ya hau kan gadon ya ɗauketa ya riƙeta a jikinsa. Ganin tana ƙoƙarin tashi ya sanya ya sake riƙeta ya ce “Stay still kin ji, Da wasa nake miki. Babu abin da zai sa na sake aure” Fashewa ta yi da wani raunataccen kuka,Ta ɓoye fuskarta a jikinsa cikin kuka take fadin “Dan Allah uncle kada ka sake auren wata, mutuwa zan yi wallahi. Ka bari uncle ka ji,ba zan sake ba, ba zan kuma yi ba!” Gyaɗa mata kai ya dinga yi dan tausayi ta bashi, Ya shafa kanta ya ce “shikenan na haƙura Nana. Dama tuni na haƙura, baki ga ban miki faɗa ba? Na haƙura kinji. But ki saka a ran ki uncle ba zai taɓa kin ki ba, Ina son ki Nana! Ina son ki tun kina tsummanki, Ina son ki tun ranar da Amma ta haifeki, Da a lokacin na samu dama tuni zan aure ki Nana, Kawai nayi shiru ne saboda kada a ga son zuciyata. Na rayu da soyyarki Nana, a rashin ki na auri Zahra, kullum da tunanin ki nake kwana nake tashi, Aliyu ne kaɗai ya san abin da ke zuciyata, Shiyasa sanda na samu labarin aure ku na je Nigeria da tunanin yanda zan yi na mallake ki. Da yake Allah ya hukunta ina da rabon auren ki sai ya kawo wancan hatsaniyar, amma har na fitar da rai Nana. To ya za'a yi na ce bana son ki kuma? Ya za'a yi na ce haka Nana? Nafi kowa son ki, ko Abba sai da ya gane haka. Ina son ki sosai Nana, Sannan cikin da ke jikin ki babu abin da ya kara min illa ƙaunar ki, Ban taɓa son abu kamar yanda nake son ki ba Nana. Komai naki burgeni yake, Shirmenki, Wasan ki, Shagwaɓar ki, Tsiwar ki da kuma kukan ki. Ina son komai naki Nana, Ina son ki , Uncle na son ki! Uncle na son ki sosai Nana.” Ji ta yi kamar zuciyarta zata fito, ta rasa wane irin hali take ciki, Farin ciki ko kuwa baƙin ciki, Ta kasa magana sai kuka da take kamar ranta zai fita. Ɗago fuskarta ya yi yana goge mata hawayen ya ce “Ki yarda da uncle Nana, Duk abin da nake miki ba wai ina yi bane dan na cutar da ke. A'a ina yi ne saboda naga kin zama mutum, Idan da ta ni ne babu ruwana, Zan zauna da ke da halin ki wallahi. Amma jama'a nake ji Nana, Ina son ki zama mutum ki shiryu ki daina wasu abubuwan, Na yarda ki dinga yiwa uncle. Amma da zarar kin fita ki zama babbar mace, Matar minister of health Doctor Abdusammad M Shuwa, ki zama yarinyar kirki Nana.” Gyaɗa masa kai kawai ta dinga yi tana shessheƙa kuka, Ya ɗan yi murmushi ya ja kumatunta ya ce “My cry cry baby, Mamana sarkin kuka” Hannunta ta saka ta rufe fuskarta, Ya ɗauke kansa yana dariya. Sun ɗauki mintuna a haka kafin ta ce “Uncle”.. “Na'am Anty...” Ya faɗa a sigar da ta yi maganar, Tura baki ta yi ta ce “To nima ai ina son ka fa. Kuma ma shiyasa na ce bana son Yaya Sultan fa, Har muka yi faɗa da Amrah da ta ce tana sonka. Ai nima ina son ka, Shiyasa nake zuwa Apartment ɗin ku na zauna saboda na ganka. Kuma shi ne kai baka sona, kafi son Anty Zahr...” Caraf ya kame bakin maganar da nasa, Ya fara kissing ɗinta cikin salo mai rikita wanda ake yi wa, Tuni suka fara hargitsa nutsuwar kansu. Muryarsa na rawa ya ce “Nana i love you, I love you so much. I can't do without you, Please Nana kada ki bar ni, Ki so uncle ɗin ki. Ki yi min wannan alfarmar, Kada ki bar ni Mamana!” Cikin kuka ita ma ta ce “Toh uncle, Nima ina son ka ai, Kuma ina sonka sosai. Ina son komai naka uncle, Nafi sonka wallahi, Nafi Hajiya Babba son ka, Nafi Yaya Aliyu da Abba son ka. Ni kaɗai nake son ka Uncle ɗina!.” Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka mara sauti, Bai ce komai ba ya mai da bakinsa cikin nata yana kissing ɗinta as if his life depends on it. A daren ranar sun yi kamar su cinye junansu saboda ƙauna, Duk wani sirri da ke ɓoye sai da suka faɗawa junansu, Daga ƙarshe ta shige jikinsa tana sakin wata irin ajiyar zuciya mai nuna kwanciyar hankalin da take ciki. **** Ranar wata talata suna zaune cikin ɗakin Siyama na kallon Anty Khadijah da ke faman kuka, Umma da ke zaune kan farar kujera ta roba sai jan carbin hannunta take ta girgiza kanta ta ce “Khadijah ba zaki daina kukan nan ba? Ba zaki fawallawa Allah komai ba?” Anty Khadijah ta girgiza kanta tana hawaye ta ce “Umma na kasa, Zuciyata zafi take min, Umma ya zan yi da hakkin mutane? Ya zan yi Umma? Da wane ido zan dubi ubangijina? Na rasa wane irin tunani ma zan yi. Na cutar da ƴar uwata ta jini, Na rabata da gidan mijinta da kuma ƴarta saboda son zuciya irin tawa, Na cutar da ƴar dana haifa da kaina na kai ta inda aka lalata rayuwarta, wace irin uwa ce ni Umma? Wace irin zuciya gareni!” Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan. Gaba ɗaya kuka suke, Zahra, Siyama, Safeena da kuma Amal. Umma ma daurewa kawai take saboda ƙarfin zuciya irin nata, Ta girgiza kanta zuciyarta cike da tausayin ƴar tata ta ce “Ki gode Allah da ubangiji ya baki ikon ganin kuskuren da ki ke aikatawa, Ya kuma hukunta ki tun a duniya. Tabbas kina da rabon rabauta ne, Ba dan haka ba babu yanda za'a yi ki gane laifukan da ki ke aikatawar, Sai lokaci ya ƙure miki, A sanda babu damar da zaki gyara kuskuren. Amma a yanzu kina da wannan damar, Kuma kin nemi yafiyarta ta yafe miki, Allah ba zai kama ki da haƙƙinta ba, Ki ci gaba da istigfari na sauran laifukan da ki ka yi, Ba'a yanke tsammani da rahamar ubangiji, Allah mai yafiya ne. Kuma idan ya yafe baya kallon bawansa da abun, Mutum shi ne wanda yake cewa ya yafe kuma ya ci gaba da kallon ka da abun, Shi ko ubangiji idan ya yafe ya yafu. Ki ci gaba da tsarkake zuciyar ki, Ki kuma yi tuba na zahiri, Kada ki bari sheɗan ya sake cin galaba akan ki” Sosai jikin kowa ya yi sanyi, Anty Khadijah ta amsa da to tana ci gaba da kukanta. Washegarin ranar aka sallameta daga asibitin, Duk da bata takawa sai dai a wheelchair, Koda suka dawo gida Siyama ce ke zama a daƙinta. Itama gaba ɗaya ta sukurkurce kamar ba ita ba, Ta yi baƙi ta rame, Ko ba'a faɗa ba an san ciwo ne yake ɗawainiya da ita. Duk da bata wasa da karbo magani, Cikin satin basu sami zama ba, Domin a cikin sa ne aka ɗaura auren Zahra da Bashir, Da kuma Safeena da Kamal. Kasancewar auren zumunci ne duk ya sanya ba'a yi wani taro ba, Zahra da kanta ta kira Abdusammad ta faɗa masa zata yi aure, Sosai ya yi mata murna. Ya kira Umma ya yi mata murna ita ma, Sannan ya tura 5m account ɗin Zahran ya ce ta bawa Umma, Godiya sosai suka yi masa, Aka sha shagalin biki kowace aka sadata da ɗakin mijinta, Gidan ya rage daga Anty Khadijah, Siyama sai Umma, Dan Amal ta koma makaranta. Kusan kullum haka zaka gansu a zaune sun zuba uban tagumi, Basu da aiki sai tunane-tunanen rayuwa, Umma ce ke kwantar musu da hankali wani lokacin, Tana faɗa musu komai me wucewa ne. Ranar da aka zo aka faɗawa Anty Khadijah Kaddu ta haukace kwana ta yi tana kuka, Sai a sannan ta sake gane girman laifin da suka yiwa Allah, Kaddu ta bata tausayi ba kaɗan ba, Duk da itama abar a tausayawan ce amma gara ita da hankalinta. Nakasa kawai ta samu, kuma tana ƙoƙarin mai da kanta mutuniyar kirki, Ana idar da sallahr asuba Umma ta shigo ɗakin tana kallon ta, Zaune take kan dadduma sai kuka take bayan ta idar da sallahr. Umma ta ƙarasa ta zauna gefen ta tana kallon ta ta ce “Ki daina wannan kukan Khadijah, Ki mai da duk al'amuranki ga Allah, Ubangiji na son ki da rahama, Ki manta da abin da ya wuce.” Cikin kuka ta ce “Umma wani iri nake ji, Da Allah yaso da yanzu ina tare da Kaddu mun haukace ko? Na shiga ukuna, Umma dama na mutu, Dan Allah ki yafe min duk abin da nayi miki. Ki yafe min Umma” Ta ƙare maganar tana ɗora kanta kan cinyar Umman, Girgiza kai Umma ta yi ta ɗora hannunta akan ta ta ce “Na yafe miki Khadijah, Dama ban taɓa riƙe ki ba, Na san idan har ubangiji na karbar addu'ar da nake to tabbas wata tana zaki shiryu, Kuma gashi yanzu naga wannan lokacin. Allah ya yi miki albarka, Da ke da sauran ƙannen ki, Allah ya ci gaba da kare mu daga sharrin shaidan, Allah yasa mufi ƙarfin zuciyoyin mu, Da mu da sauran al'ummar musulmai baki ɗaya.” Anty Khadijah ta sauke numfashi sannan ta ce “Amin ya arrahamar-rahimin” **** Nana ce zaune gefen gado tana zuba kaya a cikin trolley ɗin da ke gabanta, A sanyaye take komai tana nishi, Sakamakon cikin da ke jikinta wanda ya fito sosai. Abdusammad ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo yana kallon ta, Zama ya yi gefenta ya ɗauki sauran kayan ya ce “Let me help you” To kawai ta ce sannan ta ɗan matsar masa da trolley ɗin, Sai da ya kammala zuba kayan sannan ya rufeta. Ya juyo yana kallon ta, Kallon sa ita ma take, Tana sanye da doguwar riga ta abaya baby pink. Murmushi ta ga yana yi, Ta ɗan haɗe rai ta ce “Uncle me ka ke wa dariya?” Gyaran murya ya yi yana son fuskewa ya ce “Nothing” Ta sake zumɓura baki gaba tana kafe shi da idanu. Kallon ta ya sake yi sai kawai ya ɗauke kansa, Bai san sanda dariyar ta suɓuce masa ba, Ya dinga yi mata dariya yana kallon ta. Ita ko ta cika ta yi fam dan ƙaramin abu ne yake ɓata mata zuciya yanzun, Gaba ɗaya cikin ya mai da ta wata masifaffiya. A fusace ta ce “Ni ai ba mahaukaciya ba ce da zaka dinga kallona kana min dariya.” Ta ƙare maganar kamar zata yi kuka, Girgiza kansa ya yi cikin dariya da raha ya ce “Kin san me? Gani na yi hancin ya yi kamar na Hippopotamus, Idanun ki sun sha kwalli kamar me bada maganin gargajiya...” Ya ƙare maganar yana tuntsire da wata sabuwar dariyar. Kuka ta saka ta fara dukansa ko ta ina tana cizonsa, Ya ci gaba da dariyarsa can kuma ya riƙe hannayenta still smiling ya ce “Na tuba madam, Kin yi min kyau ne fa.” Fashewa ta yi da kuka ta shige jikinsa tana cewa “Ai naga ba haka ka ganni ba, Kuma wallahi bana son cikin ma.” Dariya kawai ya yi ya rungumeta a jikinsa, Can ya shafa cikin nata yana jin yanda yaron cikin ke motsi ya ce “Hiii unborn, Ka samu ka fito duniya mamarka ta bar ni da rigima” Tura baki ta yi bata ce komai ba, Ya tashi da ita a hannunsa yana faɗin “Madam haka ki ka zama? Kin ji nauyin ki kamar bag ɗin shinkafa” Shiru ta yi masa dan ta san so yake ta yi maganar, a kwanakin nan ya mai da ita kamar wata kakarsa, Kullum cikin tsokanarta yake. Wani lokacin ta biye masa wani lokacin kuma ta yi masa kunnen uwar shegu, A haka suke fito daga gidan ya sakata a mota sannan shima ya shiga kai tsaye kuma airport suka nufa dan Nigeria zasu je suna. **** Cike estate ɗin yake da mutane, Na birni dana ƙauye, Ashe sunan matan gidan ake. Masu decorations na musamman aka ɗauko suka zo suka yi decorating wajen, Aka saka kujeru huɗu da bannern jarirai huɗu. Sai da masu jegon suka fito sannan aka fara gane su wane, Maimoon ce da Haule, Hamida da kuma Amrah, Sun ci kwalliya cikin wani uban su lace mai azabar kyau da tsada. Kowacce an yi mata make -up a fuska suna rike da jariran su, Suma mazan haka suka shirya cikin wata dakkakiyar shadda gezner brown colour, Sun yi ɗinki iri ɗaya har Abdusammad. Sai shige da fice kowa ke yi, Suna aka yi gagarumi dan haɗe shi aka yi, aka ce a bari duk su haihu sai ayi, Kasancewar Nana na da tazara dasu sosai yasa ba'a saka da ita ba, Maimoon Mace ta haifa, Hamida da Amrah ma haka, Haule kuma ta haifi namiji. Yar gidan Maimoon sunan Ummi aka saka mata, Suna ce mata Ummi, Ita kuma yarinyar Hamida sunan Hajiya Babba aka saka mata wato takwarar Nana, Suna ce mata Ikram, Ita kuma yarinyar Amrah sunan Mommynta aka saka ana ce mata Khairiyya, Shi kuma yaron Haule aka mayar masa da sunan mahaifinsa marigayi Safwan, Ake kuma kiransa da sunan. Taro aka yi bana wasa ba, aka ci aka sha aka watsa Naira, Da daddare kowa ya tafi sai ya'yan gidan kawai, Nana kuwa kuka ta dinga yi saboda gajiyar da ta yi, Ita sam bata saba kujiba-kujiba ba a gida, Daga kwanciya sai cin abinci take. Yau kuma ta zo ta sha uban wahala dan ko zama bata yi ba, Sai da Abdusammad ya siyo mata magani ta sha sannan ya samu ta yi bacci kan ƙafarsa. Sati ɗaya kawai suka yi ya cewa Hajiya Babba zasu wuce, Ta ce sai dai ya bar Nana a nan ya tafi ta haihu a gida. Da fari ƙin yarda ya yi, Saboda ya san Nanar ce ta kitsawa Hajiya Babba haka, Dan tun a New York take ce masa ya barta a gida, Sai da Papa ya shiga maganar sannan ya bar ta ya shige shi kadai, Ko sallama ko bai yi da ita ba. Ita ma bata damu ba saboda ganin ta da ta yi cikin yan uwanta tana shiga tana fita yanda take so. **** Tunda cikin Nana ya shiga watan haihuwa babu wanda ya ƙara samun sukuni, Ko ciwon kai taji ta dinga kuka kenan tana raki, Dama tuni Amma ta koreta daga apartment ɗin ta, A cewar ta ba zata iya da iya shegenta ba, Ta yi zamanta a Apartment ɗin Hajiya Babba dan ita ce kawai ke yi mata yanda take so. Anan ma kullum sai sun yi faɗa da Atta, Duk dare Abba zai shigo ya ganta, Da safe ita kuma taje, Duk yanda take son magana da Abdusammad basa yi, dan iyaka kiran da zata yi masa ba zai ɗaga ba. Tana ji wasu lokutan suna waya da Hajiya Babba, Sai dai ta yi kasaƙe tana saurara ko zai ce a bata wayar, amma har su gama wayar ba zata ji ya ambaceta ba, Tun Hajiyar bata fahimta har sai da ta gane, Ranar wata asabar ya kira wayar suna zaune a parlour tare tana cin abinci. Bayan sun gama hira Hajiya Babba ta ce masa “Arɗo kana sanin halin da Nana kuwa ke ciki? Yaushe zaka zo ne?” Tun da yaji Hajiya Babba ta yi maganar to ya san Nanar na kusa, Dan haka ya yi gyaran murya ya ce “Ba sai naji ba Hajiya, Kawai ki gaisheta, nan ba da jimawa ba zan zo. Akwai yarinyar da muka daidaita da ita ina son na zo mu yi zancen dake, bana son a ɗau lokaci mai tsayi.” Bata san sanda ta fara dawo da abincin data zuba a bakinta ba, Hawaye suka fara ambaliya akan fuskarta. Girgiza kai Hajiya Babba ta yi dan ta san ya yi ne dan ya kunno ta, Musamman data saka wayar a handsfree. Jiki a sanyaye Nana ta tashi sum sum ta bar parlourn, Tana zuwa ta shige ɗakin Hajiya Babba ta saki wani raunataccen kuka ta fadi a wajen, Ihu ta dinga yi tana birgima, Hajiya ta kashe wayarta ta tashi ta bi bayanta, A kwance ta sameta tana kuka kamar ranta zai fita, Ta ƙarasa ta ɗagota ta ce “Ke mene haka? Da wasa fa yake miki” Bata yi magana sai kukanta da take yi, Hajiya Babba ta ce ta tashi su koma ƙasa, Ta miƙe tana ƙoƙarin tafiya ta dafe mararta saboda wani irin murɗawa da taji ta yi. Ƴar ƙara ta saki wanda ya sanya Hajiya Babba ta kalleta ta ce “Mene ne?” “Marata zata cire Hajiya, Shikenan zan mutu...” Ta fara kuka kamar wadda ake duka, Ganin abun nata na gaske ne ya sanya Hajiya ta koma ƙasa ta ɗauki wayarta ta kira Sultan da Abba, Koda ta koma kwance ta sameta sai ihu take tana juye-juye wanda ya tabbatar da naƙuda ce ta zo mata. Abba ne ya ɗauketa ya kai har mota aka wuce da ita asibiti, Iyaka tashin hankali sun gan shi akan Nana, Dan ban da ihu babu abin da take. Duk wani makusancinta sai da ta kira sunansa, Abdusammad kuwa ta kira shi yafi sau ɗari. A haka har Allah ya hukunta ta haifi yaranta Mata guda biyu, Farare sol dasu kamar iyayensu. Gaba ɗayan su da Abdusammad suke kama, Idanun su ne kawai irin na Nana. Zo ka ga murna cikin Family ɗin Muhammad Shuwa, Kafin ka ce kwabo an cika asibitin da jama'a, Aliyu da kansa ya kira Abdusammad ya sanar da shi haihuwar bayan ya gama raina masa hankali. Ai ko awa bai ƙara ba ya fara shirye-shiryen dawowa Nigeria. **** Kwana ɗaya da haihuwar ya zo, lokacin har an sallamesu sun dawo gida, Tana apartment ɗin Hajiya Babba har sannan. Duk yanda Amma ta so tafiya da ita kasawa ta yi dan kar aga zaƙewarta, Musamman da taga yanda Atta ke zuba rashin ta ido akan duk wanda ya yi maganar uwar ya'yan ko kuma ya'yan. Around 2:00 pm ya shigo parlourn bakinsa ɗauke da sallama, Atta na ganinsa ta saki guɗa tana murmushi ta ce “Ga uban Ya'yan Allah ya kawo shi, Kai wannan ɗa ka ban mamaki. Ka ga yara Masha Allahu” Shi dai Abdusammad Ban da murmushi babu abin da yake, Dan tun da aka sanar dashi haihuwar bakinsa ya zaga rufuwa, Nana ta ɗaga kai ta kalleshi, Ya daɗa wani irin girma, Kwarjini da kuma haiba. Ya ƙara zama babban mutum kana ganinsa ka san kwanciyar hankali da jin daɗi sun zauna. Ya ƙarasa kan kujera ya zauna idanunsa zube kan yaran da ke hannun Mama, Ɗaya bayan ɗaya ya gaishe su, Suka amsa sannan suka yi masa Barka. Mama da kanta ta tashi ta miƙa masa yaran duk biyun, ya amsa ya riƙe a hannunsa yana murmushi, Bai san kalar farin cikin da yake ciki ba shi kansa. Ji yake kamar ya tashi ya taka rawa da ya'yansa, Allah mai kyauta da ya ɗauke masa ɗaya sai ya bashi biyu a tare, Sun daɗe a hannunsa kafin su Aliyu suka shigo, Nan fa aka zauna ana faman hira da shafta. Duk wannan abun da ake babu bakin Nana a ciki, Hawaye taf cikin idanunta, Bata yi tunanin zai kasa yi mata magana ba, Daga ƙarshe ta tashi ta haye sama jiki a sanyaye. Hajiya Babba na lura dasu, amma bata ce komai ba. Sai da aka fara kiran sallar la'asar sannan suka tashi suka fita, Bai sake dawowa gidan ba sai bayan sallar isha'i, Hajiya Babba kawai ya iske a parlourn Kowa ya tafi gida, Ya zauna suna magana can dai ta ce “Abdusammad mene haka? Me ke damun ka? Me yarinyar nan ta yi maka? Koma me ya haɗaku bai ci ka haƙura ba yanzu? Tun ka zo baka kalleta ba, Ballantana ka ce mata ya ta sauka ko ya jikinta, wace irin rayuwa ce wannan?” Shiru ya yi yana sauraren Hajiya Babba, Ta dinga yi masa faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Dakyar ya samu ta yi shiru bayan ta ce ya je ya ganta, Shi dai bai ce komai ya tashi ya nufi saman. Tana zaune gefen gado ta zuba uban tagumi, Yaran na kwance tsakiyar gadon suna bacci, Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo. Ta ɗaga kai ta kalle shi dan bata yi tunanin zai zo ɗin ba, Ƙarasawa ciki ya yi ya zauna gefen gadon yana kallon yaran, Can dai ya kalleta ya ce “Ya jikin naki?” Madadin ta bashi amsa sai kawai ta fashe da kukan dake cin ta tun ɗazu, Ya yi shiru yana saurarenta, Can dai ya tashi ya koma daf da ita ya kamo hannunta ya ce “Ke tambayar ki nayi ya jikin ba ba cewa nayi ki isheni da kuka ba, Ke baki san kin girma ba yanzu? Baki gan ki da ya'ya ba!” Kukanta ta ci gaba da yi, Ya rungumeta yana murmushi ya ce “Thank you kin ji. Allah ya yi miki albarka Mamana, Kin sakani farin ciki, naji kamar na yi kuka Nana. Thank you kin ji, Allah ya albarkaci rayuwar ki data ya'yanmu, Ya sa nan gaba ki haifa min yan uku” Ya ƙare maganar yana jan hancinta, Tura baki ta yi ta maƙale a jikinsa cikin kuka ta ce “Uncle zafi kamar zan mutu. Bana so na sake haihuwa” Shafa kanta ya yi ya ce“Sorry kin ji, ai next tare zamu raba zafin, yanzu ma dan kin gujeni ne.” Bata ce komai ba sai shigewa jikinsa data sake yi, Tana jin wata irin nutsuwa ta musamman na saukar mata, Wadda take da nasaba da kewar mijin nata da ta yi. Sati ya zagayo aka yi gagarumin suna mai ban mamaki, Ko sunan su Maimoon da aka haɗe bai kai shi haɗuwa ba. Iyaka kuɗi Abdusammad ya ɓarnatar da dukiya, Komai na wajen bana masu ƙananan ƙarfi bane, Tun daga kan mai jegon da shigarta da kuma ya'yan, Kafin azo ga uban Ya'yan. Ɗaiɗaiku ne basu zo ba a dangi, haka ma abokansa da ke America duk sun zo, Har da su Zahra sai da suka zo sunan, Khadijah ma sun zo ita da Mami. Yara suka ci sunan Amma da Atta, Ake ce musu Habibti da Noor. Hotuna kuwa wanda aka manta ne kawai ba'a ɗauka ba, Duk irin rashin son mutane na Abdusammad haka ya saki jikinsa aka dinga ɗaukan hotuna, Ana ɗaukan su wani hoto shi da Nana Aliyu ya yi dariya ya ce “Wai wannan ai kai ne Abul banin ɗin (Baban ya'ya mata)” Murmushi kawai Abdusammad ya yi ya ce “Faɗi ka ƙara.” Kyaututtuka kuwa ba'a maganar su, Nana ta samu abubuwa masu tarin yawa na kayan barka, Abdusammad kuwa takardun Company ya danƙa mata a matsayin kyautarsa, aka saka ihu a wajen ana tafi. Sai dare sannan kowa ya watse ya tafi gida, Suma suka koma ciki dan huce gajiya. **** Five years later(5). Saukar su kenan daga jirgin, Tana rike trolley ɗinta ɗayan hannun kuma ta riƙe wata yarinya, Shima tafiya yake rike da hannun ɗaya yarinyar suka nufi inda driver ya zo ɗaukan su, Suna ƙoƙarin shiga mota taji an kira sunanta, Ba ita kaɗai ba har Abdusammad sai da ya juya dan ganin wanda ke kiran sunan matar tasa, Junaid ne a tsaye yana murmushi. Nana ta dinga kallon sa sai kuma ta ɗan saki fuskarta, Ƙarasowa gabansu ya yi suka gaisa da Abdusammad cikin fara'a, Ya durƙusa daidai tsayin Habibti dake rike da hannun Abdusammad, kyakkyawar baturiyar yarinya sai kallon rashin sani take masa, Ya miƙa mata hannu ya ce “Hi” Cikin siririyar muryarta irin ta yara ta ce “Hello.” Ya yi murmushi sannan ya miƙawa Noor ma, Kamar su ɗaya da juna, Idan har ba wani sanin su ka yi ba to zai maka wahala ka tantance su. Sai da Junaid ya gama yi masu wasa sannan ya mike tsaye yana kallon Abdusammad ya ce “Yara sun girma Sir, Allah ya raya.” Murmushi Abdusammad ya yi ya ce“Amin ya rabbi thank you.” Sai a sannan ya kalli Nana ya ce “Nana Allah ya raya” Da Amin kawai ta amsa dan ta san Abdusammad ba son yaga tana hira da maza yake ba. Shi ma Junaid bai damu ba ya yi musu sallama ya juya ya bar wajen, Sai a sannan ta sauke idanunta ƙasa tana jin babu daɗi a ƙasan ranta wanda bata san dalilin sa ba. Mota suka shige kai tsaye kuma estate ɗin su suka nufa, Tun daga bakin estate ɗin zaka gane arziki ya ci uban na da, Domin gaba ɗaya an sauya mata fasali zuwa na wannan zamanin. Wani kallon sai ka shiga ciki, Apartment ɗin Hajiya Babba suka nufa dan anan ne ake taron kasancewar lokacin ƙaramar sallah ne ana taron family, Suna shigowa aka fara murna. Nana ta ƙarasa ta rungume Abbanta da gudu, Girgiza kai Abba ya yi ya ce “Na ga ranar da zaki girma Nana” Murmushi ta yi sannan ta koma ta rungume Ammarta, Amma ta ce “Ni wallahi ba zaki ƙarashe ni ba, Ji yanda ki ka zama wata ƙatuwa kin fini” tura baki ta yi tana kallon jikinta. Da gaske ta zama babbar mace, Hamshaƙiya mai faɗa aji a gidan mijinta, Kai daka ganta kaga wadda ke hutawa. Ɗaya bayan ɗaya ta gai da mutanen parlour kafin ta ƙarasa ta faɗa jikin Hajiya Babba, Murmushi kawai Hajiya Babba ta yi ta ce “Takwarata.” A shagwaɓe ta ce “Hajiyar mu mai Makkah da Madina” Murmushi duka aka yi, Nana ta juya ta kalli Atta wadda ke tabar baki, Tashi ta yi tana zuwa ta rungumeta tana murmushi ta ce “Attar mu, Har yanzu ba zaki mutu ba wai?” Turata Atta ta yi tana mele baki ta ce “Ki gani akan ki, In sha Allah ba zan mutu yanzu ba.” Ban da dariya babu abin da jama'ar parlourn ke yi, Nana ta koma cikin sauran yan uwanta su Hajiya Maimunatu wanda aka girma, Sun wani nutsu kamar manyan gaske su basu yarda ba sun ajiye iyali dan Maimoon da Amrah Ƴaƴansu biyu, Hamida kuma nada ciki. Sai Haule wadda aka aurawa Saddiq ita ma ta ɗan ƙaramin goyo. Hajiya Babba ta dinga kallon su ɗaya bayan ɗaya can kawai ta fara murmushi mai haɗe da hawaye, Tashi Abdusammad ya yi ya koma kusa da ita ya zauna ya ce “Hajiya lafiya?” “Farin ciki nake Arɗo, Allah ya cika min burina, Wasiyyar mahaifin ku bata tafi a banza ba, Allah na gode maka, Allah ya yi muku albarka, Ya baku ikon ci gaba da tafiya akan wannan turbar ta zumunci, Ya ƙara muku arziki da wadatar zuci, Allah ya jiƙan magabantan mu, Ya sa sun huta. Mu kuma ya bamu ikon ci gaba da imani.” Da Amin kowa ya amsa, Sannan aka ci gaba da hira. Da gudu Ikram ta shigo ta ƙaraso wajen Nana tana kuka ta ce “Ammi kin ga Noor ko? Sai dukana take” Girgiza kai Nana ta yi ta kwala wa Noor kira, Shigowa ta yi ta tsaya tana kallon su, Yanayin yanda ta yi kamar Nana na ƙarama, Nana ta haɗe rai ta ce “Ban hana ki rashin ji ba? Ban ce ki daina dukan mutane ba?” Tura baki yarinyar ta yi sai kawai ta saka kuka ta fadi a wajen tana birgima, Papa da ke kallon su tun ɗazu ya ce “Allah mai iko, Dama duk abin da ka yi sai an yi maka. Yau ga Nana ta haifo mai irin halinta, To idan yar Nana taji magana a ina ta samu?” “A wajen Babanta mana!” Abdusammad ya amsa yana murmushi, Tuntsirewa da dariya aka yi duka Nana ta tura baki ta ce “Ai shikenan!.” *Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah. Anan zan ɗiga aya cikin wannan littafi mai taken NAANAH, Ina rokon Allah abin da na rubuta na daidai Allah yasa a ɗauka ayi amfani dashi, wanda kuma nayi kuskure Allah ya gyara mana baki ɗaya. I'm really really appreciate it, Na gode da ƙauna da kuma soyyayar da ku ka nunawa wannan littafi, Allah ya bar mu tare. Ku kasance dani Ameenatou I Ibrahim(Nanameera) Cikin Wani sabon littafin dan ganin abin da zan kawo muku. Tabbas ba zan baku kunya ba🥺🥰, Nanameera heart you guys❤️.* © Nanameera. Rate me