Typing ✍️ *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 1 to 5 ______________A fusace ya tashi ya nufi bakin ƙofa jin yanda ake ta buga ƙofar ba ƙaƙƙautawa. Baiwar ALLAH da ƙarfi ta tura ƙofa dai-dai lokacin da aka buɗe sai kawai tayi ciki bata ankara ba, ta faɗa kan Razhdeen gaba ɗaya suka je ƙasin carpet tana saman kan sa, da sauri ta ɗago tana kallonsa a yayin da shima idonsa yake kanta haka suke kallon juna ba bu mai ƙarfin motsa wa, sai da suka ɗau seconni kafin ta firgita a ruɗe ta tashi daga kansa cike da jin takaici... Wani abun mamaki kuma su Pinky sun biyo bayan Baiwar Allah ganin ta fita, suma suka sa security ya kawo su da mota amma daga wajen gate suka tsaya suka shigo gidan da ƙafa, suna tsaye a bakin ƙofar falon Razhdeen, faɗuwar da Baiwar ALLAH tayi akan Razhdeen akan idonsu dasauri pinky ta ciro wayar ta tare da musu video harda photo sannan ta ja hannun Rukky suka gudu ba tare da ganin me zai faru ba domin sun samu wani makamin sharri daga nan suka tafi a waje suka tarar da security da ya kawo su suka shiga mota cike da murna... Pinky Rukky sun ci alwashin raba Auren Roshan da Baiwar Allah kuma sun san Razhdeen ba Auren ta zai yi, su burin su ta fita musu daga cikin Ahali kuma suna so tayi baƙin jini a wurin Abbah... Razhdeen yana shirin tashi Baiwar Allah ta jefa masa ledar rigar gift akan ƙirjinsa ta cigaba da cewa "Razhdeen ka ke ko waye? to bari kaji na sanar maka Ni nafi ƙarfin ka wallahi, ni zaka yiwa sharri saboda ka raba ni da mijina? me nayi maka haka? meyasa kake son shiga mun rayuwa ne? kayi mun sharrin zina wanda tinda nake ban taɓa aikata wa ba saboda ka rabani da mijina, kana ta wani cewa hotel shin da wa zaka haɗu a hotel ɗin? to bari kaji daman wata ƙila can halin ka ne yawon zuwa hotel kana kaiwa ƴan mata can, to ni ba haka nake ba, ni ba mazinaciya bace kamar kai, Razhdeen ka fita daga shirgi na, ka nisanta kan ka daga gare ni, bana neman komai daga wurin ka saboda ka fita hanya ta, I hate you wallahi..." tana kammala wa ta juya zata tafi yayi saurin riƙo hannun ta tare da juyo da ita ya manno ta kan ƙirjinsa, dai-dai lokacin da Ƴar Amana ta shigo falon tana goye da jakar ta tayi shirin makaranta tsab, abun da ta tarar ne yasa ta ja da baya tana zazzaro ido waje ta tsaya a jikin labule tana rurrungume shi jikinta har rawa yake idonta akan su. Razhdeen ne ya riƙo sumar kan Baiwar Allah suna fuskantar juna kamar zasu haɗe baki har numfashin su yana haɗuwa ya yi saurin kai ƙaramin bakinsa sai tin kunnen ta yana magana a hankali cikin sassanyar murya yake faɗin "Duk ban fahimci mai kike nufi ba amma naji kin ƙirani da mazinaci, ki iya bakin ki domin wata rana zaki faɗi abun da zai sa na yanke miki harshe gaba ɗaya...." Cikin ɓacin rai da mugunta ya damƙi gashin kanta da ƙarfi har sai da ta ɗan yi ƙara sannan ya kuma cewa "inda kin san yanda na tsane ki a raina da baki yi gigin zuwa yanda nake ba, ki kiyayi ranar da zan raba miki ƙafa gida biyu, i hate you too....." Riƙe hannun sa tayi ta finciki kanta daga riƙon da yayi mata har sai da gyalenta ya za me, tana kuka ta tsuguna zata ɗauki gyalen sai ga sarƙar wuyanta shima ya faɗo bata lura da shi ba haka ta ɗago a fusa ce ta bugi ƙirjinsa tare da ture shi baya ta juya da gudu tana kuka da haka ta fice, shima ya daɗe yana tsaye yana kallon hanyar da ta bi sannan idonsa ya sauƙa akan sarƙar da yake a yashe, hannu ya kai ya ɗauko idonsa akan sarƙar yana jujjuya shi, yana tunanin aina ya taɓa ganin irin wannan sarƙar... Ƴar Amana ce ta tako har yanda yake tsaye tana kuka, ganinta yasa ya dunƙule sarƙar a tafin hannunsa, Ƴar Amana bata ga fuskar Baiwar Allah ba dake ata bayanta take, itama Baiwar ALLAH da ta tashi baya waiwaya ba kai tsaye gaba tayi ta fice. Ƴar Amana tsaya wa tayi a gaban Razhdeen fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ganin ta acikin wannan halin ne yasa shi faɗin "Sarah what's wrong?..." Ƴar Amana ɗaukar pillow kujera tayi ta fara kwaɗa masa tana kuka sai da ta gama dukan sa da pillow sannan ta wurgar ta juya da gudu ta koma room ɗin ta, tana shiga ta jefar da jakar goyon ta sannan ta ciccire uniform ɗinta, jin motsin mutum yana nufo room ɗinta ne yasa ta je ta rufe ƙofar ɗaki tareda saka sakata, tana jin yanda Razhdeen yake ta buga ƙofar yana ƙiran sunanta amma tayi kunnen uwar shegu, sai gajeren wandon ta da ta sanya wanda ya tsaya mata iya cinya sai best mai hannun breziyya ta haura saman gadonta ta mimmiƙe yau kam ba zuwa school tayi fushi da Uncle Deen ganinsa da wata, abinda yafi ƙona mata rai shine rungumarta da yayi kamar zasu haɗe kuma duk maganganun da Razhdeen ya faɗa wa Baiwar Allah a kunne babu wanda ya ji mai yake faɗa mata sai ita, Razhdeen ganin bazata buɗe ba yasa shi koma wa part ɗinsa... ★★★★★★ Baiwar ALLAH bayan komawar ta gida tana shiga falo ta tarar da Roshan zaune daga shi sai Three quarter da singlety yana facing ɗin plasman, jin sallama yasa shi kallon bakin ƙofa yana binta da kallo, jiki a sanyaye ta je har gabansa ta durƙusa ta gaishe shi zuciyar ta bugun uku-uku domin bata son yasan taje gidan Razhdeen, Amsa wa yayi cikin murmushi tare da riƙo hannunta ya ɗagota ta faɗa jikinsa, Ya ce "Ammata ina kike je ne da sassafen nan ko kammala breakfast bakiyi ba..." tunani ta fara yi shin me zata ce masa gashi bata iya ƙarya ba, ganin bata da abun cewa ne yasa ta ɗagowa suna kallon juna tasau murmushi tare da faɗin "Kayi haƙuri my D..." shima murmushi ya sake mata tare da sumbatar ta a kan lips ya ce "it's okay..." tana kwance akan sa ya ce "tashi muje muyi breakfast..." Tashi tayi ba musu suka nufi dinning ganin kuloli a jere kan dinning ta tsaya tana kallonsa gira a haɗe ta ce "kar fa kace kai ka haɗa breakfast?..." Murmushi ya yi sannan ya ce "to wa kike tunanin zai yi?..." tunawa tayi da lokacin da suka fara shiga kitchen tare da gishirin da ya zabga musu a abinci a fili ta ce "yau ma abinci bazai ci yu ba..." Zaro ido ya yi ya ce "ban gane ba, kina nufin ki ce duk shiga kitchen ɗin da nake yi har zuwa yanzu ban iya komai ba?..." Baiwar Allah tayi gaba tare da faɗin "shikenam muje nayi testing..." Murmushi yayi ya bi bayan ta, suka jeru a dinning shi da kansa ya zuba musu abincin, cukali ɗaya Baiwar Allah tayi ta ce "wow my D na baka award..." Yana caccakar indomie ya ce "Ni yanzu kyautar abu ɗaya zaki mun nasan kin mun kyautar da bazan taɓa manta wa ba har ƙarshen rayuwata..." Baiwar Allah ta dakatar da yin breakfast ta ce "wani irin kyauta ne haka?..." Wani irin kallo yake mata na so da ƙauna murya ciki-ciki ya ce "yaushe zaki kammala period ɗinki?..." Baiwar Allah ta ce "Ohhhh shine kyautar daman?..." Ya ce "Please Ammata am asking you, wallahi a duk sanda na kasance dake ji nake bani da kwanciyar hankali, gaba ɗaya hankali na tashi yake, Ammata i need you..." Kwashewa tayi da dariya ganin yanda ya zamo kalar tausayi, ta ce "haba D ka kwantar da hankalin ka remain 5 days..." A ruɗe ya ce "whattt?..." har sai da ta tsorata ta ce "meya faru Yaya Roshan?..." Ya ce "naji kin ambaci 5 days, shin har kwana nawa kike yi ne?..." Dukan ƙirjinsa tayi tana faɗin "har ka tsoratar da ni, 7 days nake nake yi, yau nayi 2 days remain 5...." Jinjina kai ya yi sannan ya ce "jiya Abbah ya sanar mun cewa gobe na tafi ƙasar Jidder ganin Yarinyar..." Baiwar ALLAH ta ce "daman baka santa ba ne?..." Girgiza kai ya yi sannan ya ce "Ramlat ce wai zamu ƙara fahimtar juna ne..." Lokaci guda Baiwar Allah taji wani bugun zuciya na tsananin kishi, hawaye ne yake shirin kuɓuto mata tayi saurin kawar da kanta gefe tana share wa..." Roshan riƙo hannun ta yayi tare da faɗin "meya faru ne?..." Juyowa tayi a wayance har da murmushin yaƙe ta ce "babu komai amm ya kamata ka fara shiri tin yanzu ko saboda nasan fitan sassafe zakayi..." Tashi tana cewa "muje na taya ka shirya kayan..." Riƙo hannunta yayi tare da zaunar da ita akan kujerar dinning ya ce "zauna mana tukun..." Ta zauna tana fuskantar sa cikin zuciyar ta kuwa kamar ana hura wuta... Idonsa akan ta ya ce "bazan tafi ba sai na jira kin mun kyautar da bazan taɓa manta wa ba..." Baiwar Allah kamar zatayi kuka ta ce "zaka iya jira har kwana biyar baka tafi ba?..." Ya ce "ke fa rayuwata ce, me zai hana na jira..." Dasauri ta girgiza kai tare da faɗin "bazai yu ba saboda zuwa lokacin Auren ka yazo, kuma bazai yu ace har zuwa lokacin Aure baka je ka gano Amarya ba, hakan kuskure ne..." Cije lips ɗinsa yayi na ƙasi har cikin zuciyarsa ba son Auren yake ba shima just saboda ba yanda ya iya ne... Ya ambaci sunan ta a hankali "Ammata..." Ɗagowa tayi tana kallonsa bata san lokacin da hawaye yake shirin gangaro mata ba, jawo ta yayi jikinsa ya riƙo gefe da gefen fuskarta suna fuskantar juna lokaci guda hawaye suka gangaro mata a duk ɓangare biyun, haka yasa harshensa yana lasar hawayen fuskar ta, tas sai da ya gama sannan yakai ɗan ƙaramin bakinsa kan nata ya fara sunbatar ta cikin salo da ƙware wa, cikin lokaci ƙanƙani ya cire mata damuwar da yake shirin wanzuwar mata, Cire harshensa yayi daga cikin bakinta yana mata wani irin kallo ya ce "Ammata ki gaya mun gaskiya shin kina son Auren nan ko kuma bakya so? idan bakya so a yau zan sanar cewa na fasa, ai daman ni nace ina so yanzu kuma zan iya janye wa..." Girgiza kai Baiwar Allah tayi sannan ta ce "kayi haƙuri Yaya Roshan ka Aure ta koda bana so ɗin, ko dan saboda Abbah da Uncle, kuma itama idan taji an fasa bazata ji daɗi ba, dan Allah Yaya Roshan tinda har Abbah yace kaje gobe to ka tafi Insha Allahu zaka samu abinda kake so..." Kiss ya manna mata akan kunci tare da miƙe wa tsaye yana faɗin "tashi muje ki shirya mu tafi shopping..." Ɗan turo ƙaramin bakin ta tayi cikin shagwaɓa take faɗin "duk kayan da nake da su sai naje shopping, Ni gaskiya a'a..." Bata ankara ba taji yayi mata ɗaukar luɗa ya nufi part ɗinsa da ita cikin wasa da ƙaunar juna, bai sauƙe ta a ko ina ba sai akan katafaren gadonsa yana kwantar da ita ya rufu kanta, bugan ƙirjinsa take tana faɗin "D ka sauƙa kar fa ka wuce gona..." Ƙibta mata ido ɗaya yayi tare da ɗage girar sa ya ce "to daman gonan na waye?..." Cikin shagwaɓa ta ce "naka ne amma ba'a halin yanzu ba..." Murya ciki-ciki ya ce "ai ba cewa nayi zan shiga gonar ba kawai dai nazo kewaye ne, ko laifi ne?..." Dariya tayi tare da rufe fuskarta domin ba ƙaramin bata kunya yayi ba... cire hannayenta yayi ya danne su duk biyun yakai fuskar sa sai tin nata yana hura mata iskar bakinsa, a hankali ta lumshe idanunta sakamakon yanayin da ta shiga bazata iya misalta shi ba, cikin yanayin shauƙi yake romance ɗinta, kissing na musamman yake bata, a cikin tana jin kunya har ta fara biye masa, a wannan lokacin Roshan ya gama fita hayyacin sa bai san lokacin da ya cire mata rigar jikinta ba, a cikin mayen feeling ya jawo drower jikin gado ya ɗauko wani bottle na zuma, ita kuwa tana kwance kamar ba rai a jikinta, idanuwanta a ƙanƙame domin ta shiga halin da tunda take bata taɓa shiga ba, haka Roshan yake zuba mata zuma a jikinta tin daga wuyanta har zuwa cibiyar ta haka yayi mata wanka da wannan zumar har da fuskar ta gaba ɗaya, A wahalce Roshan ya kafa bakinsa a saitin wuyanta ya fara lasa da harshensa cikin salo da ƙwarewa haka yake bin duk ilahirin jikinta yana lashewa.. Baiwar ALLAH gaba ɗaya ta fita hayyacinta sai yunƙurawa take tana jure-jure tare da surutai, jin ya kafa bakinsa akan breast ɗinta ne yasa ta ɗan yi ƙara wanda bata san lokacin da ta yi shi ba 🙈🙈🙈 A wannan ranar haka suka wuni suna bawa junan su hakki, duk da akwai abinda yayi musu cikass basu samu damar raya sunnah ba. Sai da kowa ya gamsu tukun suka haƙura haka, Roshan ne ya fara tashi ya shige bathroom, ya yo wanka sannan ya fito ɗaure da towel, Haurawa saman gado yayi ya ɗago da Baiwar ALLAH wacce jikinta ya mutu babu wani sauran ƙarfi a tattare da ita, ƙara narke wa tayi ta kifar da kanta akan cinyarsa tana daɗa ƙanƙame shi, jikinta haka yake empty ba ko breziyya suna wulle a gefe guda sai sket ɗin da yake jikinta ba'a zo nan wurin ba tukun, Roshan a hankali yake mata magana a kunne cikin lallami akan ta tashi taje tayi wanka, yana shafa gadon bayanta, ɗagowar da zai yi idonsa ya sauƙa akan drawing ɗin cartoon ɗin bindigar dake gadon bayan ta, cikin rashin fahimta yake bin zanen bayanta da kallo a yayin da ita kuma take kife akan cinyarsa, hannu yakai yana shashshafa zanen tare da mamakin daga ina ta samo wannan zanen, lokaci guda kuma sai ya fara tuna a yanda yaga irin wannan zanen, searching ya fara yi idonsa akan zanen, lokaci guda ya zabura tare da zaro ido waje a cikin ransa yake faɗin "irin wannan cartoon ɗin bindigar a jikin Rakesh da Mohandas na gansu, alamar tambarin family C.D.S Mohandra Marka (Chief Of Defence Staff) Australian Country. Roshan tunani ya zurfafa yana faɗin "to amma Ammata meya haɗa ta da tambarin nan?..." duk a cikin ransa yake wannan maganar... Shawara ɗaya ya yanke na cewa zai tambaye ta a ina ta samo wannan tambarin da aka zana mata ko dai tana da alaƙa da familyn domin iya sune suke da wannan. Shafa sumar kanta yayi sannan ya ce "Ammata..." Amsa masa tayi kamar wacce tayi maye da bugu... Ya ce "wannan tambarin bindigar da yake bayan ki shin meye dalilin da yasa aka yi miki zanen sa kuma hakan ma na bindiga, ki rasa zanen mai za'a miki sai na bindiga?..." Baiwar ALLAH jin irin tambayar da yayi mata ne yasa ta yunƙura ta tashi tana rurrufe jikinta da bedsheet, ta zauna tana fuskantar sa domin an taɓo mata tabon dake cikin zuciyar ta, nan danan sai ga hawaye har ya wanke mata fuska, Roshan ganin haka yasa ya fara goge mata hawayen fuskar ta yana faɗin "Ammata kiyi haƙuri dole wannan lokacin nayi miki tambayar nan, ta hanyar nan ne zan iya taimaka miki duk da nasan daga inda kika fito, nasan kin tashi a gidan marayu har kika kai wannan lokacin, amma dan Allah kiyi haƙuri ki sanar mun wannan tambarin na miye ne?...." Baiwar ALLAH goge hawayen fuskar ta tayi sannan ta ce "Yaya Roshan wallahi tallahi Nima kaina ban san komai dan gane da rayuwata ba kuma har yanzu ba'a gano komai ba, Abbah ya yi iya ƙoƙarinsa akan ganin na samu iyayena amma har yanzu babu labari, hakan yasa na saddaƙar cewa basa raye, wannan tambarin bindiga tin ina yarinya na tashi na ganni da shi, ban san dalilin wannan zanen ba, haka na nufin iyayena masu sayar da bindiga ne ko kuma sojoji ne ko kuma ƴan boko haram ne inason sanin hakan..." tana kaiwa nan ta fashe da kuka, daƙer ya samu ya rarrasheta ta cigaba da faɗin "wannan sarƙar ma tin ina yarinya nake tare da shi..." ta ƙarasa maganar tana kaiwa hannunta sai tin wuyan ta, ganin wuyan empty babu sarƙa yasa ta fara shashshafa wuyan a ruɗe tana zaro ido waje, A zabure ta tashi tana faɗin "na shiga uku sarƙa ta..." Haka ta tashi ba tare da ɗaukar bedsheet ɗin ba, haka ta zauna babu riga a jikin ta, tana kuka cikin ɗaga murya tare da faɗin "sarƙa ta, ka cire mun sarƙa ne? tin ina ƴar ƙaramar yarinya nake tattalin sarƙar nan yanzu kuma tashin farko na rasa shi bazaiyu ba wallahi..." haka ta rikice lokaci guda... Roshan ne shima ya miƙe yana rirriƙe ta tare da faɗin "look Ammata ki kwantar da hankalin ki zaki samu sarƙar indai yana cikin gidan nan, yanzu dai je kiyi wankan zan duba miki sarƙar kinji ko?..." Jinjina kai tayi tare da faɗin "dan Allah ka taimaka ka samo mun sarƙar nan kaji ko Yaya Roshan..." Murmushi yayi tare da shafan gefen fuskar ta ya ce "je kiyi wanka zan duba yanzu, amma ki daina kukan nan..." Ta ce "toh na daina..." ta shiga bathroom da sauri domin so take taga sarƙa a hannunta... Roshan zama yayi a bakin gado yana sauƙe nannauyar numfashi wanda ya tokare masa maƙoshi, zuciyar sa ce ta fara bugu da ƙarfin gaske domin hasashensa ya bashi cewa da Amreesh yake tare, ba tare da kowa ya sani ba, a hankali ya furta "Amreesh, Reesh Deen? Anya ba mafarki nake ba? kai Kai kai inaaa mafarki nake, Reesh Deen kuma, kenan ina tare da matar da akayi alƙawarin ta a Razhdeen?..." Gaba ɗaya yayi zuru-zuru kamar zai fashe da kuka haka ya miƙe tsaye yana ta zarya a cikin ɗakin lokaci guda damuwa ta bayyana akan fuskar sa, domin tsabar shaƙuwar da Razhdeen da Amreesh suka yi ne yasa ake ƙiranta da Reesh+Deen shi kuma Reesh Man hakan yasa aka sanya musu zoben alƙawari, shi Razhdeen har yanzu akwai wannan zoben a hannunsa ita ce babu wannan zoben a yatsar ta sai dai zoben bai ɓata ba yana jikin sarƙar yanda ta haɗe ta ɗaure da jikin sarƙar, yana cikin wannan zaryar sai gata ta fito tana ɗaure da towel a ƙirjinta, abun da ta fara furtawa shine "Yaya Roshan ka samu sarƙar ne? akwai wani zobe a jikin sarƙar idan suka ɓata na shiga uku domin sune rayuwa ta..." Roshan ƙare ta yake da kallo yana hasasho fuskar Amreesh da take yarinya, kallonta yake sosai ba ƙibtawa, Baiwar ALLAH ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta cewa "Yaya Roshan kallon meye kake mun ne haka, Ni damuwa ta sarƙa da zobe..." Roshan ya ce "shikenam kisa kayan ki tukun..." Ta ce "shikenam..." Shima buɗe wardrobe yayi ya ciro ƙananun kayansa ya saka, zuciyarsa tana saƙe-saƙen abubuwa da yawa, lokaci guda kuma ya tuno ahalin su da kuma ahalin Abbah basa shiri sai kuma zuciyarsa ta ƙara bugawa, da yayi niyar zuwa ya sanar wa Abbah amma yanzu ya fasa domin Abbah zai iya cewa ya haƙura da ita, shi kuma yanzu ta zamo masa ginshiƙin rayuwa bazai iya rabuwa da ita ba... A washe gari tafiya ƙasar Jidder ta fasaya domin a daren jiya Baiwar ALLAH kwana tayi bata rintsa ba sai kuka, saboda sarƙar ta da zobe, shima Roshan bai yi bacci ba haka yake ta faman rarrashin ta kuma already yasan ita ce Amreesh domin ya duba photunan ƴan uwan natan zanen dake jikinsu iri ɗaya da nata, photunan swimming pool ne kowa babu riga a jikinsa ga zane raɗau-raɗau sak.. Akwai photon Amreesh lokacin da take ƙarama a wurin Roshan shi da Razhdeen sai kuma Amreesh a tsakiya haka ya ɗauko ya ƙare wa photon kallo akwai wani abu da ya lura a jikin photon Amreesh, wani baƙin tawada ne wanda aka haife ta da shi a saitin wuyan ta wurin kunne, Roshan ya duba na Baiwar ALLAH yaga akwai wannan tawadar domin babu halin goguwa, anan ya ƙara tabbatar wa da cewa Amreesh ce... ★★★★★ Razhdeen yana zaune a bakin gadonsa sai juya sarƙar Baiwar ALLAH yake tayi domin kallo ɗaya yayi wa sarƙar ya gane domin a birthday ɗin Amreesh aka ƙero mata, A lokacin yayi tunanin lokacin da aka kawo Amreesh gidan su tin suna Nigeria ana washe gari birthday ɗinta a Razhdeen ta fara nuna sarƙar tana faɗin "Habeey Mommy ta kawo mun sarƙar birthday, bazan nuna wa kowa ba sai kai, saboda kai ɗin jarumi nane kuma na musamman..." Razhdeen jingina bayansa yayi a jikin gadon sa ido a lumshe sai murmushi yake ta zuba wa, domin yana tuno da surutun Amreesh, a lokacin tana da baki sosai, duk abinda taji an faɗa shikenam ta ɗauke shi a ƙwaƙwalwarta, hatta kalar soyayyar da Mommyn ta da Daddynta suke yi tas take kwashe wa tazo tana faɗan su a Razhdeen bata manta wa ko ɗaya, Razhdeen yana kwance sai kuma ya ƙara tuno lokacin da yake wasa da ita a cikin swimming pool take faɗin "Habeey kai fa rayuwata ce, haka Mommy na take gaya wa Daddy shiyasa nima nake faɗa maka kai ɗin rayuwa ta ce, bazan rayu in babu kai ba, zuciyata taka ce..." Idan ya tambaye ta aina take jin irin wannan kalaman sai ta ce a gurin su Mommy da Daddy. Akwai lokacin da ta taɓa cewa "Habeey ina dai nima idan na girma tare zamu na wanka a baho ɗaya ko da kuma swimming pool, haka Mommy da Daddy tare suke wanka fa, kuma kuma haka a swimming pool ma..." Razhdeen haka hawaye yake gangaro masa tare da sakin murmushi idan ya tuno irin yarintar Amreesh, kallon sarƙar ya ƙara yi yana dudduba wa ne kwatsam ya tarar da zobe a jikin sarƙar, a ruɗe ya tashi zaune idonsa akan zoben, wani irin haɗiyar yawu yayi zuciyarsa na bugawa da ƙarfi-ƙarfi... Tashi yayi ya jawo wata jakarsa wanda komai da komai yake ciki na sha'anin Amreesh, su photuna da abubuwan wasa da kuma ɗan ƙaramin laptop ɗinta wasu shirguna dai gasu nan, wani ƙaton photon Amreesh ya ɗauko mai jikin glass yasa a gaba yana ta kallo, sannan yana tunanin Amreesh tana nan kuma duk yanda akayi Baiwar ALLAH tasan a yanda Amreesh ɗinsa take a yanda yake ta tunani... A cikin ransa ya ce "dole yarinyar nan zata nemo mun a yanda Amreesh take, dole tasan a yanda take tinda ga abubuwan ta na yarinta a hannunta, sannan yana tunanin shin aina Baiwar ALLAH ta samo wannan sarƙar Amreesh da kuma zoben alƙawarin su.... Yana cikin wannan tunanin kwatsam sai ga Ƴar Amana ta turo ƙofa ta shigo, har ta shugo Razhdeen bai sani ba idonsa akan ƙaton glass picture ɗin Amreesh... Cikin ɓacin rai Ƴar Amana ta tsaya tana kallonsa ita bama photon ne a gaban ta ba, ga ɓacin ran tin jiya da safe da ya buga ƙofar ta yaji tasa sakata bai ƙara wai wayan ta ba har kwanan yau, kuma sai da Madam Blessing taje ta rarrashe ta tukun, yanzun ma ganin bazata iya juran rashin ganinsa ba yasa ta zo har room ɗinsa, Ganin hankalinsa duk yana kan photon hannunsa yasa ta zuciyo ga kishi ta ɗauki glass picture ta kwaɗa a jikin bangon ɗakin, glass kam ya dagargaje... A firgice ya miƙe tsaye tare da faɗin "whattttt?..." a ruɗe ya ɗago hannu ya yi mata wani irin kyakkyawan mari har sai da ta dungura zuwa bakin ƙofa, ran sa ba ƙaramin ɓaci yayi ba domin tinda yake da Ƴar Amana bai taɓa jin haushin ta kamar na yau ba, domin ta ɓangare masa wani sashi na zuciyar sa... A gigice ta ɗago tsabar ta shiɗe bata san ina ta nufa ba miƙewar da tayi ta fice tana riƙe da fuskar ta domin wani irin hajijiya ne yake ɗaukar ta, asan sauƙa daga beni ne tayi tuntuɓe ta kifu akan benin nan ta fara gangarowa tin daga saman beni har ƙasa, goshin ta yayi wani irin buguwa a ƙasin tiles nan danan goshin ya fashe... Kasa tashi tayi sai wani irin shiɗewar da take tayi numfashi yana sama da ƙasa daƙer... Madam Blessing da ta fito daga kitchen ganin halin da Ƴar Amana take cikin ne yasa tayo kanta da gudun gaske ta kawo mata agajin gaggawa, Ɗaukar ta tayi ta nufi part ɗin da room ɗinta yake, kafin su isa har ta sume akan kafaɗar Madam Blessing... Madam Blessing tana kwantar da ita ta fito da gudu ta haura saman ɗakin Razhdeen ta shiga ta tarar da shi a zaune a bakin gado yasa photo a gaba wanda ya dagargaje a ƙasi idonsa akai.. Madam Blessing ce ta buɗi baki zata yi magana Razhdeen yayi saurin katse ta da cewa "leave my room..." Madam Blessing ta ce "Sarah fa tana can acikin wani hali..." Wani irin kallo Razhdeen ya watsa mata tare da darara mata tsawa "i Said leave my room, I don't care about her..." A tsorace Madam Blessing tabar ɗakin domin al'amarin babba ne..... Typing ✍️ *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 6 to 10 ______________★★★__________ Bayan kwana biyu Roshan ne ya shirya tsab da sassafe bayan Baiwar ALLAH ta dawo hayyacinta daƙer Roshan ya rarrasheta ta haƙura da maganar sarƙa da zoben, tare suka fito falo suna riƙe da hannun juna, ya tsaya a gabanta suna facing juna, wani irin kallon so da ƙauna yake mata da kuma tausayawa kansa domin yasan duk lokacin da aka san Baiwar Allah ɗiyar CDS maƙiyin mahaifinsa ne dole Abbah zai nemi ya raba Auren indai ya ruguje alƙawarin da aka ɗaukar wa Razhdeen, in kuma an amince da ita to za'a samu matsala sosai da Razhdeen... Kamar zai yi kuka ya ce "Ammata..." ta amsa masa cikin kulawa su na riƙe da hannun juna, ya ce "akwai albishir ɗin da nake son sanar miki..." murmushi tayi sannan ta ce "wani irin albishir ne haka D?..." Ya ce "Albishir ɗin da zai sanya ki farin ciki har abada amma kuma sai dai za'a iya raba mu..." Lokaci guda ƙirjinta ya buga gira a haɗe ta ce "wannan ba albishir bane, indai har zai shafi tarayyar mu to ba albishir bane don haka bana son jin wannan batun..." Rungumo ta yayi yana shafar sumar kanta da murmushi akan fuskar sa ya ce "Ammata wannan albishir ne domin abun da ya shafi rayuwar ki ne kuma zaki kasance cikin farin ciki har ni kaina ma na fara taya ki farin ciki..." Baiwar Allah ta ce "to amma kace fa zamu rabu ni kuma bana son abunda zai shafin tarayyar mu na Aure..." Jan kuncin ta yayi tare da sumbatar ta akan goshi ya ce. "wasa nake miki..." Ta ce "to ka sanar mun albishir ɗin mana..." Ya ce "tukwuicin mai zaki bani?..." Gyara tsayuwar ta tayi sannan ta ce "mai kake son samu?..." Ƙibta mata ido ɗaya yayi sannan ya ce "kin san tukwuici na abu ɗaya ne, inaso kafin na dawo kina kammala period ki mun shiri na musamman wanda ina dawowa babu wani jira zan karɓi tukwuici na..." Bugan ƙirjinsa tayi tare da faɗin "ai daman nasan wannan ne a ranka, shikenam zan yi yanda kace amma yanzun fara gaya mun albishir ɗin..." Ya ce "a'ah saina dawo zan sanar miki ina sanar wa zaki bani tukwuici na cikin farin ciki, domin nasan idan na sanar miki yanzu bazaki iya bacci ba saboda tsananin farin cikin da zaki shiga..." Sauƙe nannauyar numfashi tayi sannan ta lanƙayo hannunta cikin nashi tana faɗin "to muje kar jirgin ku ya tashi, ga Abbah yana can yana jiranka a falo..." Da haka suka fita ta raka shi har wurin parking motoci... ★★★★★ Razhdeen har wannan lokacin bai je wurin da Ƴar Amana take ba, yana nan a room ɗinsa har zuwa yanzu zuciyar sa a tafashe take, yana kwance wani tunani ya faɗo masa, nan ya yanke shawarar zuwa ya samu Baiwar ALLAH akan maganar Amreesh, domin yasan duk yanda akayi tasan a yanda Amreesh ɗonsa take, daƙer ya tashi ya shige bathroom ya yi wanka sannan ya fito ya shirya cikin janpa purple colour sannan ya gyara sumar kansa har gadon bayan sa sai sheƙi yake, ya feffeshe jikinsa da turaruka kala-kala sannan ya ɗauki wayarsa da key ɗin mota ya fice daga room ɗin sa, a hankali yake taka matakalar beni har ya sauƙa falo, Har zai nufi hanyar fita daga falo ya ji Madam Blessing tayi masa magana ta bayansa tana faɗin "good evening Ogah..." Juyo wa yayi ya jinjina mata kai ba tare da ya yi magana ba, idonsa ne ya sauƙa akan Ƴar Amana dake zaune akan dinning table tasa plate ɗin abinci a gaba ko one spoon ta kasa yi, idonta na kallon gefe ko kallon yanda yake bata yi ba, ga goshinta a zagaye da bandeji yanda Madam Blessing tayi treatment ɗinta... Razhdeen tsaya kallon ta yayi yaga yanda taji ciwo a akan goshi sai kuma yaji tausayin ta, juya wa yayi ya nufi dinning table yanda take a zaune, tana jin motsin sa yanda ya zauna a kujerar gefenta sannan ya kalli Madam Blessing ya ce "kisa mun abinci..." Madam Blessing ta ce "which types?..." Ya kalli abincin Ƴar Amana ya ce "irin nata..." Ita kuwa ko kallon yanda yake bata yi ba, haka zuciyar ta yake ta harbawa da tsananin takaicin sa. Abincin ya fara ci idonsa akan ta sai da yayi Three spoon sannan ya dakata tare da ɗora hannunsa akan nata hannun dake ajiye kan dining, a firgice ta ɗage hannunta ta miƙe tana shirin barin wurin yayi saurin riƙo ta tare da janyo ta kan cinyar sa, Bubbugar sa ta fara yi akan ƙirji tana ture shi ga yanda hawaye yake gangaro mata, a halin yanzu ba ƙaramin jin haushin sa take ji ba, riƙe hannayen ta yayi duk biyun da hannun sa ɗaya tare da mannata sosai a jikinsa yanda bazata iya ƙwace wa ba, matso da fuskar sa yayi sai tin nata yana goga mata dogon hancinsa akan nata hancin, haka numfashin su yake haɗuwa, cikin takaicin ta ƙanƙame idonta tana jin yanda yake goga mata amma ta kasa aikata komai sakamakon riƙon da ya yi mata.. Bayan ya gama da wannan ya zo yana hura mata iskar bakin sa akan fuska sannan ya ce "Sarah.." ya ƙira sunan ta cikin sigar rarrashi, ya cigaba da cewa "Am so sorry please, kina fushi da ni ko? aina kika ji wannan ciwon?..." Buɗe idonta tayi tana masa wani irin kallon haushi, haka take masa kallon up and down haka ta tattaro ƙarfinta ta ture shi baya tana daga kan cinyar sa haka kujerar tayi baya da su suka tafi zuuu suka doku a ƙasi ita tana kansa shine a ƙasi, tashi tayi ta rufa da gudu ta haura ɗakin ta tana kuka... Madam Blessing da take gyaran falon tana kallon su ita kaɗai sai dariya take tayi, da haka ya tashi tare da kar kaɗe jikinsa dan ma akan carpet ne, ya girgiza kansa sannan ya yi waje zai je yanda ya shirya tafiya... ★★★★★★ A can ƙasar Jidder Ramlat sai shirye-shirye take tayi Roshan yana hanyar zuwa domin taji Mai martaba yana cewa Roshan yana jirgi, farin ciki kamar bazata mutu ba, har sabon kaya tasa aka ɗinka mata na taryar Roshan ga yanda taje aka tsara mata kwalliya na musamman, tin yanzu aka fara shirye-shiryen biki an sanar wa ƴan uwa da abokai yau sauran kwana biyar biki... Bayan awa ɗaya da mintuna sai ga Roshan a gidan mai martaba, a part ɗin mai martaba ya fara sauƙa suka gaggaisa cikin aminci, sannan Roshan ya je part ɗinsu da suke sauƙa shi da Razhdeen idan suka zo, daga baya kuyange suka kai masa kayan abinci kala-kala da kayan fruits na musamman, ga ɗakin da ya sauƙa a gyare an gyara ko ina tsab-tsab, ɗakin sai ƙamshin turaren wuta yake na masarauta, sai da ya tsaya ya kalli room ɗin ganin yanda ya tsaru ba ƙaramin burge shi yayi ba, da murmushi akan fuskar sa ya fa ɗa saman gado yana huta gajiyar hanya, ta falon ɗakin kuma an gama shirya kayan abinci akan dinning dake room ɗin falo and bedroom ne sai bathroom ta ciki, yana kwance yaji ana knocking a hankali ya furta "who?..." Wata ce daga cikin ƴan matan masarautar ta ce "an kammala haɗa kayan abincin..." Yana daga kwance ya ce "Ok thanks..." Bayan ya gama hutawa ya tashi ya shige bathroom ya watsa ruwa a jikin sa sannan ya fito ya chanza kaya tare da feshe jikinsa da turaruka kala-kala ya shirya tsab sannan ya nufi falo, kai tsaye dinning ya nufa ya je ya ci abinda zai iya ci sannan ya ɗan taɓa kayan fruits daga baya ya taso yana goge bakinsa da tishu, Sai da ya ƙara shiga bathroom ya shige toilet yayi brush tare da ɗauro wa alwala ya fito yabar ɗakin gaba ɗaya, bai tsaya a ko ina ba sai a masallaci.... Ramlat kuwa tana can part ɗin ta tana zaune a gaban madubi tana sanye da sari mai bala'in tsada irin wanda ƴan India suke saka wa a lokacin biki, ta rufe kanta da mayafin sarin wanda duk bakin sarin yake zagaye da duwatsu masu sheƙi da ɗaukar ido kai ka ce a yau ne ranar bikin ta, ga tayi wani irin gyaran gashi na musamman a gaban gashin an manna mata wani irin dutsi mai kama da ɗan kunne mai sheƙi, Ramlat ba ƙaramin kyau tayi ba, duk da Black beauty ce amma kyan ta ba zai misaltu ba, haka lips ɗinta yake ta wal-walin maiƙon glowlips. wata mata ce take ta bayanta tana shirin ɗaura mata sarƙa mai kalan sarin ɗin jikinta bayan ta sanya mata sarƙa, matar kana ganin ta kasan ɗaya ce daga cikin kuyangen masarautar, haka ta ɗauki turare ta feffeshe ta da shi sai wani irin ƙamshi take bada wa, ga wasu ƴan matan masarautar su uku suna tsaye ko wacce sai yabonta take, dake sune masu rakata wurin Roshan... Suna cikin wannan halin sai ga Aunth A'isha ta shugo Amaryar mai martaba tana ganin Ramlat ta zaro ido tare da faɗin "wayyo gimbiyar mata kinga irin kyan da kika yi kuwa? haba Ramlat ashe haka kike da irin wannan kyau amma shine bakya son yin kwalliya?..." Ramlat ta cikin madubi take kallon ta da murmushi akan fuskarta ta ce "da gaske Aunty A'isha nayi kyau sosai?..." Aunty A'isha ta ce "ai wallahi ko maƙiyin ki bai isa yace baki yi kyau ba, kinyi shiga irin na ƴar India sai kika sa je da su..." Ramlat ta ce "Aunty A'isha nifa baƙar mace ce su kuma ƴan indian farare ne tas, kuma inda kece kika yi irin wannan shigar tasun baza'a banbance ku ba saboda kema fara ce tass..." Aunty A'isha tana dariya ta ce "baki ji ance baƙar fata gimbiyar mata ba, baƙa sarauniya ce, sannan baƙa gimbiya cee, ke kyakkyawa ce asalin kyau, domin ke ɗin Black beauty ce..." Suna cikin wannan hirar sai ga Mamie ta shugo tana ta kallon ƙasƙanci wa kowa daga ƙarshe taja dogon tsuka, ta ƙarasa gaban mirrow yanda Ramlat take, Maamie tsaya kallon Ramlat tayi daga baya ta ce "wannan ɗin Ramlat ce ko kuma Amarya mai martaba yayo ban sani ba?..." Murmushi Ramlah tayi sannan ta ce "Ni ce mana Aunty Maamie, yau ɗin ke ce a ɗaki na?..." Maamie ta ce "Oh laifi nayi dana zo ɗakin ƙanwata wacce muke uwa ɗaya uba ɗaya? nake ga yau sauran kwana biyar ki tafi gidan mijinki shine nazo miki nasiha, ko dai nayi laifi?..." Girgiza kai Ramlat tayi sannan ta ce "a'ah bakiyi laifi ba, ai daman kece kika ƙi ni duk da muna uwa ɗaya uba ɗaya, maganar nasiha kuma sai dai mu nemi yafiyar juna kawai domin duk wani nasihar da ya kamata naji duk naji su daga bakin Aunty A'isha...." Wani irin kallo Maamie ta watsa wa INDO sannan ta juyo tana kallon Ramlat ta ce "Oh ni ban kai nayi miki nasiha ba kenan?..." Ramlat tana kallon Maamie ta cikin madubi ta ce "Nasihar ki bazai wuce akan kada na zauna lafiya da abokiyar zamana ba, da kuma wulaƙanta miji duk nasan wannan nasihar takin tinda shi kike yi anan gidan mijinki, Ni kuma bazan iya bin wannan nasihar ba kinga kuwa ba amfanin gaya mun su..." Maamie ta ce "shikenam tinda bakya buƙatar jin nasihar tawan, amma wannan kwalliyar da kika yi sai kace shugaban ƙasar America ne ya zo..." Ramlat tayi murmushi tare da juyo wa ta kalli Maamie sannan ta ce "Hmmm! Maamie kenam ai Roshan yafi ƙarfin wannan matsayin a cikin zuciya ta, idan akwai matsayin da ya wuce na shugaban ƙasar America to Roshan ya wuce wannan ma...." Maamie ta ce "Hmmm!! Dakyau, to Allah ya baku sa'a, Allah ya kaimu ranar bikin kuma..." Murmushi Ramlat tayi sannan ta ce "Amiin inda gaske kike..." Maamie bata juyo ba balle ta kalle ta haka ta bangaje Aunty A'isha ta wuce... Aunty A'isha girgiza kai kawai tayi ba tare da ta furta komai ba... Maamie tana fita sai ga wata ta shugo tana faɗin "Aunty Ramlat zamu iya kai ki yanzu saboda mijin nakin ya dawo, kuma mun kammala masa gyaran muhallin sa..." Aunty A'isha ta ce "to kije ki sanar masa cewa za'a kawo Ramlat idan a shirye yake..." Yarinyar ta amsa cikin girmamawa ta fice.... _______________ Roshan bayan ya koma room ɗinsa ya sake tarar da an kwashe kayan abincin dinning an gyara wurin tsab, zama yayi akan kujerar falo yana kallon Film ɗin da ake showing a plasman, Jin sallama ata bakin ƙofa yasa ya waiwaya yana kallon wacce ta shigo, durƙusa wa tayi har ƙasi ta ce "yallaɓai wai ka shirya a kawo Amaryar?..." Kallon ta yake cikin rashin fahimta ya ce "okay..." abunda ya iya furtawa kenam, ta tashi cikin farin ciki ta fice zata je sanar wa... Wayar sa ce ta fara ringing yana dubawa yaga suna "Suger wife" ya bayyana akan screen ɗin wayar, Murmushi yayi sannan ya ɗauka tare da furta "Ammata nah amun afuwa na iso ban ƙira ki ba..." Daga ɓangarenta ta ce "D fatan ka isa cikin ƙoshin lafiya..." Ya amsa mata da cewa "ina cikin ƙoshin lafiya, Allah yasa ke ma haka..." Ta ce "lafiya ƙalau ya Amaryar mu?..." Kafin ya bata amsa yaji anyi sallama an shigo da Ramlat ga ƴan mata biyu suna gefe da gefen ta ƴan rakiyar ta, Ramlat tana rufe da fuska da mayafin sari ɗin ta kamar wata amarya, Roshan ganin su yasa ya sake baki yana kallon su, a cikin ransa yake faɗin "duk wannan hidimar na miye? ko dai yau ne ranar Auren?..." Yana riƙe da waya ga bai kashe ba itama Baiwar ALLAH bata katse ba jin shuru yasa itama tayi shurun tana sauraron mai zai faru domin taji anyi sallama.. Ramlat zama tayi a kujerar da Roshan yake dake 3 seater ne, su kuma waɗanda suka rakota sallama suka musu sannan suka fice, Bayan sun fita ne Ramlat ta zamo daga kan kujerar fuska a rufe ta durƙusa cikin sassanyar murya ta ce "Amincin Allah ya tabbata a gare ka ya Amintaccen zuciya ta, fatan ka iso cikin ƙoshin lafiya ya ma'abocin son ibada da haƙuri da juriya, ina maka fatan alkhairi da cin nasarar rayuwa...." Baiwar ALLAH jin kalaman nan daga cikin waya yasa zuciyar ta bugawa da ƙarfin gaske nan danan hawaye ya fara gangaro mata ga wani irin kishi da ya ziyarto ta... Roshan jin irin waɗannan kalaman da rabon da yaji su tin lokacin da yake soyayya da marigayiya budurwarsa Mariam, ƙwaƙwalwarsa ne ya fara juyawa jin sautin irin muryar Mariam kuma irin kalaman da take masa sak irin wanda Ramlat tayi masa.... Ramlat tana tsugune kai a ƙasi ta kasa ɗagowa, Sauƙe nannauyar numfashi yayi sannan ya ce "Nagode sosai, tashi ki zauna ..." A hankali ta tashi ta zauna, Yana kallonta ya ce "Meyasa kike ɓoɓɓoye fuskar, shin meye amfanin kwalliyar? ko dai ba'a ni akayi wa ba?..." Murmushi tayi ta cikin mayafin sannan tasa hannunta waɗanda suka sha jan lalle da zanen baƙin lalle ta buɗe fuskar... Yana kallonta bai san lokacin da ya furta "Ma sha ALLAH..." Bata ƙarasa buɗe fuskar ba ta dakata haka yasa hannu ya yaye mayafin fuskar gaba ɗaya, cike da mamaki ya ce "amma ke ban sanki ba, aka ce Ramlat zan Aura..." Murmushi tayi sannan ta ce "Ni ce Ramlat ɗin ai..." Ya ce "ban yadda ba, ke kinfi Ramlat kyau sosai.." Ɗagowa tayi tana kallonsa sannan ta miƙa masa hannu ga yanda tafin hannunta ya sha jan lalle... Kallon hannun yayi fuska ɗauke da murmushi shima ya ɗora tafin hannunsa akan nata, riƙe hannunsa tayi a cikin nata sannan ta ɗora hannun akanta idonta akan sa shima ɗin ita yake kallo ta ce "wallahi Yaya Roshan Ni ce Ramlat Amaryar ka kuma Uwar ƴaƴanka zuwa nan gaba Insha Allahu..." Jinjina kai ya yi sannan ya ce "na yadda..." tukun ta sauƙar masa da hannun.... Baiwar Allah kuwa tana zaune akan kujerar falo ta kasa katse ƙira sai kukan da take tayi ita kaɗai domin alamun shima Roshan son yarinyar yake... Tana cikin wannan yanayin sai ji tayi an buɗe ƙofar falo an shugo, ganin wanda ya shugo ne yasa tayi saurin miƙe wa da sauri tana zazzaro ido, ganin Razhdeen yasa tayi saurin katse wayar, cikin ƙiƙƙina take ƙoƙarin cewa "me me me ya kawo ka gi gi gidan nan?..." Matsowa yayi gaban ta sannan ya goya hannayensa akan ƙirji ya zuba mata ido, duk da har yanzu akwai hawaye shaɓe-shaɓa akan fuskar amma bai damu da sanin dalilin kukan ta ba... Da sauri ta goge hawayen fuskar sai da ta dai daita nutsuwar ta kafin ta buɗi baki ta ce "Mijina baya nan..." Yayi saurin katse ta da cewa "wurin ki nazo..." Wani irin bugun zuciya taji lokaci guda ta tuno da saƙon da ya aiko mata daga nan ta ƙara ɗaure fuska cikin fushi ta ce "me ke tafe dakai?..." Ya ce "nazo ne game da sanin yanda rayuwa ta take..." Cikin zafin rai ya ce "Rayuwarka? to ina ruwana da rayuwar takan, da rayuwar ka da rashin sa duk bai dame ni ba..." ta juya zata bar wurin yayi saurin riƙo ta ya zaunar da ita akan kujera sannan ya ɗora ƙafar sa a gefen ta ya sa ta a gaba tare da ƙura mata ido fuska ba annuri, Ya ce "ina Amreesh?..." Hararar sa tayi sannan ta ce "wata ƙila tana ƙarƙashin gado na..." Cikin ɓacin rai ya damƙo dantsen ta tare da ɗagota yana faɗin "to muje ki nuna mun ita..." ya fara jan ta suka nufi bedroom, ƙoƙarin ƙwace wa take tana faɗin "meye haka Razhdeen? Ni ka sake ni shin ka manta cewa ni ɗin matar Aure ce? ka sake ni nace...." ta fizge hannunta tana huci ta cigaba da cewa "kana nufin bedroom ɗina zaka shiga? ɗakin kwanciyar Aure na zaka shiga?..." Cikin zafin nama ya riƙe hannunta tare da yin wurgi da ita yana faɗin "and so what..." Kanta ne ya bugu da jikin kujerar ta riƙe kanta tana shirin yin kuka.. Ya ƙarasa yanda take ya ce "ki fa ɗa mun aina Amreesh take? bana son shirme da rainin wayo, a wani wuri take sannan a gurin waye?..." Baiwar ALLAH cikin ɗaga murya ta ce "wai wata Amreesh kake fa ɗa ne haka?..." Ciro sarƙa yayi a cikin aljihunsa ya ɗaga mata shi idonsa akanta ya ce "ina neman mai wannan sarƙar shin tana ina?...." Baiwar ALLAH zaro ido waje tayi cikin nuna farin ciki takai hannu zata karɓa yayi saurin kawar da sarƙar tare da faɗin "ina tambayar ki tana ina?..." A ruɗe Baiwar ALLAH ta ce "sarƙa ta ce fa, wallahi sarƙa tace ina nema ban gani ba tin shekaran jiya, ka taimaka ka bani dan ALLAH...." Razhdeen jinjina kansa yayi jin irin rainin wayon da take shirin masa, ya zaro mata ido sannan ya ce "bana son shirme, nasan wannan sarƙar ba taki ba ce, shin aina kika samu?..." Baiwar ALLAH fashe wa tayi da kuka ta ce "wallahi sarƙa tacee ...." Bata ƙarasa maganar ba taji wani irin zazzafar mari akan fuskar ta har sai da taso shiɗe wa, Ya miƙe kamar zai yi kuka yake faɗin "Meyasa kike son yin wasa da rayuwa ta? kin gama raina mun wayo da kuma hankali, na gaya miki mai wannan sarƙar ita ɗin rayuwa tace kuma farin ciki na, ki gaya mun aina zan same ta, zan iya sadaukar da rayuwa ta domin na ceceta daga halin da take ciki, nasan Amreesh tana nan a raye, amma tinda bazaki iya sanar mun gaskiya ba shikenam zan fita na nemo ta da kaina...." Ya juya a fusace har ya buɗe ƙofa yaji ta ce "Uncle Deen Ni ce mai wannan sarƙar, idan ka rabani da sarƙar nan tamkar ka rabani da rayuwa tace, wannan sarƙar ina ɗaukar sa a mazannin uwata da kuma ubana, Meyasa zaka mun haka, tinda na tashi ina ƙarama nake ganin wannan sarƙar babu wanda yayi yunƙurin rabani da shi sai kai? me nayi maka haka? na rasa iyaye na tin ina ƴar shekara biyu zuwa uku amma inasa ran zan same su ta sanadiyar wannan sarƙar...." Nan ta fashe da wani irin matsanancin kuka mai cin rai... Razhdeen tin da ta fara magana ya tsaya yana sauraronta, zuciyarsa ce ta fara bugawa da ƙarfin gaske jin tana maganar ta rasa iyayenta sannan ta ambaci ta ɓata tin tana shekara biyu zuwa uku kuma lokacin da Amreesh ta ɓata tana ya wannan shekarun, Numfashinsa ne yake ƙoƙarin ɗage wa, dasauri yake girgiza kai tare da faɗin "I can't believe you...." Juyawa yayi ya nufi yanda ta miƙe tsaye tana kuka, ganin ya nufo yanda take gadan-gadan ne yasa ta haɗiye kukan ta fara ja da baya gudun kar ya sake dukan ta, Ji tayi ya riƙo ta tare da jawo ta jikinsa yasa hannunsa ta bayan rigar ta ya zuge zip ɗin rigar, Baiwar ALLAH ganin haka yasa ta zazzaro ido waje tana tutture shi cikin tsoro da fargaba, amma ta kasa domin yayi mata wani irin riƙo ne wanda bazata iya ƙwace wa ba.... Shi kuwa Razhdeen abinda yake son gani shine wannan tambarin zanen bindigar bayanta, buɗe rigar yayi sai breziyyar da yake ciki bai damu da ganin wannan ba domin shi abu ɗaya yake son gani, Abunda ya fara gani shine tambarin zanen, a firgice ya zaro ido waje yana kallon zanen, Ga yanda ya rungumeta sosai a jikinsa... Ɗaker ta tattaro ƙarfinta ta ture shi baya tana sauƙe numfashi, tare da masa wani irin kallo na rashin fahimtar abinda yake nufi da ita, Ƙara fashewa tayi da kuka tana faɗin "nifah matar ɗan uwanka ne, shine kake son cin amanar sa?...." Razhdeen tsabar hankalinsa ba'a jikinsa yake ba haka ya buɗe baki kamar wanda zai yi magana amma ya kasa sai ido da ya zazzaro yana kallonta, A ruɗe yake son faɗin "R R Res Reesh?..." Kar kata kansa yayi yana leƙa wani dabon baƙin tawadar da yake tsakanin wuyanta da kunne domin wannan da shi aka haife ta, yana leƙawa ne domin ya ƙara tabbatar wa da Amreesh ɗin ce, Ganin wannan ɗin ma hujja ce yasa ya dafe goshin sa sakamakon hajijiyan da yake shirin ɗaukar sa, har idanuwansa sun kaɗa sunyi ja lokaci ƙanƙani, Haka yake furta sunan "Reesh! Reesh!! Reesh!!!...." Baiwar ALLAH girgiza kai tayi ganin Razhdeen yana shirin zauce wa yasa ta rufa da gudun gaske ta nufi room ɗinta, tana shiga tasa sakata tana sauƙe numfashi daƙer, ga rigar ta a zuge sai kakkare ƙirjinta take da hannu bibbiyu.... Razhdeen jin hajijiya yana son kayar dashi yasa yayi saurin durƙusawa a ƙasin carpet yana riƙe da kansa, sai ambatar sunan Reesh yake..... Typing ✍️ *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 11 to 15 ________________★★★★★★ Razhdeen cikin yanayin damuwa da tsananin bugun zuciya haka ya tashi jiki ba ƙwari yake jan ƙafa da ƙer ya fice, tariyo abubuwan da ya gani yake tayi abu kamar a cikin mafarki, kai tsaye part ɗin Abbah ya nufa anan ya tarar da Abbah shima ya shirya zai bar ƙasar domin akwai Meeting ɗin da suke son gudanarwa a cikin satin nan, sai ana washe gari ɗaurin Auren Roshan zai dawo, Ganin Razhdeen idanu yayi jawur yasa shi faɗin "lafiya kuwa Razhdeen meya faru da kai?..." Razhdeen babu bakin magana haka ya nemi wuri ya zauna yana dafe da goshi cikin ƙarfin hali yake girgiza kai ya ce "kaina ciwo..." Abbah zuwa gefen sa yayi ya zauna tare da dafe kafaɗarsa ya ce "look Razhdeen ban saba ganinka a cikin wannan yanayin ba, dole na damu idan na ganka a cikin matsala, saboda haka ka gaya mun meke faruwa?..." Razhdeen ɗago kansa yayi yana kallon Abbah lokaci guda ya fara zubar da hawaye yana faɗin "Dad my Reesh..." Abbah haɗe gira yayi sannan ya ce "au yau kuma da abinda ka tashi kenam? meyasa bakinka bazai furta sunan wata mace ba sai Reesh? Amreesh ta mutu, inda tana raye to da yanzu ta bayyana sakamakon irin neman da akayi mata har gidan rediyo da television, kaga malam idan zakayi Auren ka kayi amma babu wani labarin Amreesher..." Girgiza kai Razhdeen yayi idonsa akan Abbah yana fargaban sanar masa cewa Baiwar ALLAH ita ce Amreesh domin a halin yanzu tana Auren ɗan uwansa twins, zuciyar sa harbawa kawai take ya ce "Reesh tana raye bata mutu ba..." Abbah ya ce "to ko tana rayen babu abinda zai haɗaka da ita, domin wannan alƙawarin na rushe ta, babu abinda zai haɗani da familyn nan, saboda haka ka cire sunan wannan yarinyar a bakin ka...." Abbah ya miƙe yana masifa ya cigaba da cewa "Reesh ɗin banza, Reesh ɗin wofi kazo kana damun mutane da wata Reesh koma Rariya ce babu damuwa ta..." Razhdeen kallon Abbah kawai yake domin yana tunanin idan yasan yarinyar da yake matuƙar so itace ɗiyar maƙiyinsa ba'a san ya za'a kaya ba. Hajiya Kilishi ce ta fito falo taci wanka tsab-tsab hannunta riƙe da jakar Abbah dake yau a ɗakinta yake, tazo har gabansa ta durƙusa har ƙasi ta miƙa masa tana masa fatan alkhairi, Abbah amsa mata yayi cikin jin daɗin yanda Hajiya Kilishi ta chanza kamar ba ita ba, Mar'atussalihan sa sun zama biyu.... Itama Ammy fito wa tayi zasu yi sallama, haka duk yaran gidan suka fiffito Uwar masu gida da Pinky da Rukky da ƴar tinny duk suka nufi hanyar waje zasu yi rakiyar Abbah, Razhdeen kawai aka bari a zaune a falo ga yanda yake dunƙule da sarƙar Baiwar ALLAH, yana tunanin maganganun Abbah... Bayan Abbah ya tafi ne shima ya tashi ya fice kai tsaye gidan da yake ya nufa... ★★★★★ Bayan kwana uku sauran kwana biyu ɗaurin Auren Roshan da Ramlat, har zuwa wannan ranar Roshan yana ƙasar Jidder sun gama fahimtar juna da Ramlat kuma ya gamsu da hankalin ta da kuma tarbiyyar ta, daman can Maamie ce take sakata yin wasu abubuwan da bai dace ba, kuma Maamie ce ta shafa mata baƙin jini a wurin ƴan uwan mijinta suke ganin cewa yanda halin Maamie take haka itama Ramlat, amma yanzu ta kuɓuce daga hannun Maamie, Aunty A'isha ta gyara mata ɗabi'un da Mamie ta raɓa mata, cikin ƴan kwanakin nan Ramlat ta gama saye zuciyar Roshan da kalamanta haɗi da kulawa da kuma biyayya, duk da shi Roshan hankalinsa yana wurin Baiwar ALLAH, gaba ɗaya ya kasa tunaninsa gida biyu, amma mafi rinjayen sa shine tunanin Baiwar ALLAH, sannan abunda yake ƙara ɗaga mishi hankali shine yanda Baiwar ALLAH ta bayyana a mazannin Amreesh, kuma yana tunanin Abbah bazai taɓa barin Baiwar ALLAH ta cigaba da zama a cikin ahalinsa ba indai ya gano ta, tinda a gabanta ya wulaƙanta babban yayanta wato Mohandas, Hankalinsa yana mungun tashi idan ya tuno da wannan al'amarin, most especially twins ɗinsa Razhdeen, shin ya zai kasance idan yasan cewa Baiwar ALLAH itace Amreesh ɗinsa, dalilin da yasa har yanzu bai koma Nigeria ba saboda gudun sanar wa Baiwar ALLAH Albishir ɗin da yayi mata alƙawarin gaya mata.... A yau ne Roshan ya yi shirinsa na komawa Nigeria, yana muradin ganin Baiwar ALLAH sannan baya son tafiya saboda Ramlat, babu yanda ya iya domin sauran kwana biyu akai masa ita, ita kuma Baiwar ALLAH zai je yaji da ita... ★★★★★ Baiwar ALLAH gaba ɗaya duniya yayi mata zafi, wani irin kishi take fama da shi, jin yanzu sauran kwana biyu Auren Roshan hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ba, yanzu ko part ɗin su Abbah bata zuwa kullum a cikin kuka take, a cikin ranta take faɗin "yanzu dole sai an mun kishiya? gaba ɗaya ƴan uwan Roshan basa sona sai iya Ummy da Ammy sai kuma yanzu Hajiya Kilishi da ta fara kulani bayan su shikenam, yaushe zan gana da iyayena ne kam? sarƙa ta a wurin Razhdeen ya zanyi ya bani sarƙa ta?...." nan ta ƙara fashewa da kuka... tana cikin wannan halin sai ga Ummy uwar masu gida ta shigo bedroom da sallama a bakinta, Baiwar Allah ɗagowa tayi tana kallonta tare da amsa mata cikin sassanyar murya.. Ummy ta ce "kiyi haƙuri Aunty Daughter na shugo miki kai tsaye..." Baiwar Allah ta ce "ba komai ki ƙaraso mana..." Ummy ganin hawaye kwance saman fuskar Baiwar Allah yasa ta ƙaraso ciki da sauri tana faɗin "subhanallahi kuka kuma Aunty Daughter me ya same ki?..." Goge hawayen ta tayi tana sauƙe numfashi ta ce "babu komai..." Ummy ta ce "haba Aunty Daughter ke dai kishi ne kawai yasa ki kuka, domin babu wacce za'ayi mata kishiya bata shiga damuwa ba indai tana son mijinta..." Baiwar Allah ta ce "Hmmmm!..." abunda ta iya cewa kenam. Ummy ce ta riƙo hannunta tare da faɗin "kiyi haƙuri ƙaddara ce tazo da haka, ni wallahi banso Auren Yaya Roshan da Ramlat ba domin yarinyar bata mun ba sam, jinin mu bai jitu da ita ba, tanada rashin kunya, nayi mamaki da akace Yaya Roshan ita zai Aura saboda bai taɓa sonta ba sai dai ta gama haukar ta akansa, amma meye dalilin yin Auren sa lokaci guda? daga dawowar sa a ƙasar Ethiopia ya bijiro da maganar Aure duk son da yake miki...." Baiwar Allah murmushi tayi sannan ta ce "ban taɓa jin haushin Yaya Roshan ba don zai ƙara Aure saboda nasan duk laifi nane, inda ace ya samu kulawa daga gareni wallahi nasan bazai taɓa yin tunanin Aure ba..." Ummy ta ce "to me kika masa haka har zai yi Aure?..." Nan Baiwar ALLAH ta kwashe komai ta sanar mata irin rayuwar da suka yi tin shekarar Auren su har zuwa wannan lokacin... Jinjina kai Ummy tayi sannan ta ce "innalillahi yanzu kina nufi kice tin lokacin da kukayi Aure baku taɓa sanin junan ku a mazannin ma'aurata ba? gaskiya Aunty Daughter laifin ki ne haba wannan wani irin rayuwa ne, shin kinsan a halin da kike ciki tsakanin ki da Ubangijin ki kuwa? wallahi ki nemi yafiyar Ubangiji domin kin cutar da mijinki da kuma kanki, shiyasa kika yi shiru ba maganar haihuwa ashe ba'a bada hanya bane...." Baiwar Allah fashewa tayi da kuka tana faɗin "ai daman na sani duk laifi na za'a gani, amma ba komai ni kaina nasan ina cikin fushin Ubangiji na...." Ummy dafa kafaɗarta tayi tare da faɗin "kiyi haƙuri tunda yanzu kin gane kuskuren ki komai ya wuce sai dai ki cigaba da istigfari da yin biyayya wa mijinki, Naga kwana biyu baki leƙa mana ba shine nazo naji ko lafiya, gashi anata baƙi a gidan, itama Aunty Yolash tazo, nasan zasu iya cewa zasu zo ganinki amma banaso su zo su tarar dake acikin wannan halin domin kowa cewa zai yi kishi kike, gashi ba wani sonki suke ba...." Baiwar Allah ce ta riƙo hannun Ummy tana faɗin "dan ALLAH ki mun wata alfarma kada ki bar kowa yazo mun, kice musu bana gidan, dan ALLAH bana buƙatar ganin kowa ina cikin wani halin da bazan iya control kaina ba dole sai an fuskanci ina cikin matsala..." Ummy ta ce "to ita Aunty Yolash da take cewa zata zo ta gyara ki fah?..." Baiwar Allah ta ce "ni bana son gyaran, a gyare nake itama kar ki barta tazo...." Ummy ta ce. "shikenam zan yi iya ƙoƙari na naga cewa babu wanda yazo miki..." Daga nan tayi ficewar ta. Baiwar Allah kuma cigaba da kukan ta take abu biyu ne suka tsaya mata a rai, Auren da Roshan zai yi da kuma sarƙar ta da yake wurin Razhdeen.... Ganin bazata iya haƙura da sarƙar ba yasa ta lalumo wayar ta tayi dialing call number Ummy wacce ta fice yanzu, Wayar Ummy kuma ta barshi a hannun su Pinky suna tura wani Film ɗin da ta ɗauko a YouTube, ita kuma Ummy bata ƙara isa part ɗinsu ba, Pinky ganin an rubuta Aunty Daughter akan number yasa ta kalli Rukky tana faɗin "ke duba mun wannan ba number Baiwar ALLAH ba ce?..." Rukky ta ce "ai itace Aunty Daughter da Ummy take ƙira, amma meyasa take ƙiran ta kuma?..." Pinky ta ce "damuwar ta ma kaɗai ya ishe ta, amma kinsan miye bari mu ɗaga mu ji me zata ce..." Pinky ta ɗaga ƙiran tare da sakawa a speaker sai ji suka yi ta ce "dan Allah Ummy ki turo mun number Uncle Deen yanzu Please..." Pinky da Rukky zaro ido sukayi waje tare da kallon juna, Pinky tayi saurin cewa "ok" ta katse wayar, Cikin nuna farin ciki Pinky ta ce "dama ta biyu wayyo farin ciki..." haka suka tafa hannaye tare da yin shewa... Pinky da sauri ta shiga cikin contact ɗin wayar Ummy ta tura wa Baiwar ALLAH number Razhdeen... Rukky ta ce "miye shiri na gaba yanzun?..." Pinky cije lips ɗinta tayi na ƙasi cikin murmushin mugunta ta ce "kin manta mun karɓi turaren feeling a wurin Lyona?..." Lyona wata ƙawarsu ce wacce sukayi makaranta ɗaya a ƙasar London, Christal ce kuma cikakkiyar ƴar lesbian, basa hurɗa da ita amma sakamakon suka buƙatar wani abu daga wurinta ne yasa suka nemeta ta basu wani turare wanda mutum yana shaƙa cikin ƙanƙanin lokaci zai fita hayyacinsa sannan ya dasa masa wani irin mungun sha'awa wanda bazai iya control kansa ba, wannan turaren iyakar sa awa ɗaya ne, da zarar awa ɗayan nan yayi to amfaninsa ya ƙare a wannan lokacin kuma anyi abinda akayi a rashin sani da fitar hayyaci.... RUKKY ta ce "to me zamu yi da shi?..." Pinky ta ce "da zarar Uncle Deen ya shiga part ɗinta mu kuma sai mu feffeshe ɗakin da turaren, kinga daga shi har ita babu wanda zai san ina hankalinsa yake, mu kuma sai mu gudu kar a kama mu..." Rukky ta ce "a'a wannan kasada ne, kinsan ita ɗin matar Aure ce..." Pinky ta ce "ina ruwana da ita matar Aure ce, wallahi yanda na tsani yarinyar nan kamar na kashe ta haka nake ji, Ni so nake tabar gidan nan..." Rukky ta ce "to video zamu yi musu ne?..." Pinky ta ce "yau Yaya Roshan yana hanyar dawowa, nasan Uncle yana zuwa ba jumawa Yaya Roshan zai dawo so nake Yaya Roshan yaje ya tarar da su a ɗaki..." Rukky ta ce "Amma bakya ganin zamu haɗa faɗa tsakanin Yaya Roshan da Uncle Deen?..." Pinky ta ce "nifa idan buƙatata ta biya babu ruwana da su, ai zasu shirya daga baya sukam tunda twins ne..." Jinjina kai Rukky tayi sannan ta ce "video da mukayi shin kin tura wa Yaya Roshan ne?..." Pinky ta ce "na tura masa da new number ta Whatsapp sannan na karya layin daman bamu mukayi rijistar sim ɗin ba...." Rukky ta ce "good hakan ma yayi, kice akwai chakwakiya a cikin gidan nan, gashi gobe Abbah zai dawo..." Haka suka sha hirarsu su kaɗai a ɗakin kamar wasu munafukai.... ★★★★★ Razhdeen yana zaune shima a ɗakinsa abun duniya duk yabi ya ishe shi, duk kwana biyun nan babu abinda yasa a cikinsa sai tunani da yawan kallon photon Amreesh, sannan yana tunanin taya zai fara sanar wa cewa Baiwar ALLAH itace Amreesh ɗinsa, ga kuma ɗan uwansa ya riga shi mallakar ta.... Yana cikin wannan tunanin yaji wayar sa tana ringing duba wa yayi ganin baƙuwar number ne yasa shi sharar wa domin shi baya ɗaukan baƙuwar number, ganin an dame shi da ƙira ne yasa shi duba location yanda ake ƙiransa, haka wayar tabi location har zuwa gidansu, da mamaki a kan fuskar sa ganin ƙiran daga gidan su ne, yana bin diddigi har har yakai part ɗin Roshan, zuciyarsa ce ta buga ganin daga inda ake ƙiran sa, kuma yaga Roshan baya nan, yana cikin wannan tunanin ne yaji message ta sauƙa masa, da sauri ya duba yaga an rubuta "dan Allah Uncla Deen ka kawo mun sarƙa ta, ka taimaka mun, ina cikin damuwa, ka zo zan sanar maka wacece Amreesh ɗinka domin mun zauna tare..." Razhdeen kallon screen ɗin wayar yake da shanyayyun idanuwansa domin ya rigada yasan ita ɗin ce Amreesh ɗinsa, Murmushi yayi cikin jin daɗi ya tashi ya shirya tsab zai je yanda take, tinda har ta nemi ya je... Yana sauƙa falo ya tarar da Ƴar Amana tana shirin haura ɗakin sa, ganinsa yasa ta dakata idonta akan sa yanzu an cire bandejin babu wannan ciwon, tsayawa yayi a gabanta tare da riƙo fuskarta da hannu biyu ya manna mata goshinsa akan nata yana goge mata dogon hancinsa sannan ya ɗago yana cewa "My Sarah am coming back okay, wait for me...." Daga nan ya wuce ya nufi hanyar fita. Ƴar Amana tsaya kallon sa tayi lokaci guda sai ga hawaye ya wanke mata fuska, ba ƙaramin shiga damuwa tayi kwana biyun nan ba sakamakon rashin samun lokacin Razhdeen, yanzu baya bata kulawar da yake bata a baya, sam yanzu bai damu da ita ba especially yanzu da Amreesh ta bayyana, indai ba sauƙo wa falo yayi ya ganta ba baya zuwa room ɗinta, hatta makaranta yanzu baya kaita, ita kuwa taƙi zuwa makaranta wai sai dai Razhdeen ya kaita, in kuma ba shine zai kaita ba to ta haƙura da makarantar, tana tsaye lokaci guda wani kuka ya yanko mata ta nufi room ɗinta da gudu ga Madam Blessing bata nan balle ta rarrashe ta... ★★★★★★ Baiwar ALLAH kuwa tana tsaye a falo sai zirga-zirga take tana jiran zuwan Razhdeen domin ya turo mata da reply da cewa Ok. Tana cikin wannan halin sai taji buɗan ƙofar falo da sauri ta waiwayo ganin Razhdeen ne yasa ta nufo yanda yake da sauri tana kuka, rufe ƙofar tayi sannan ta durƙusa a gabansa tana kuka ta ce "Uncle Deen Dan ALLAH ka taimaka mun wallahi ina cikin damuwa, a duk sanda na shiga matsala sarƙar nake gani hankali na ya kwanta domin ina gani tamkar ita tare da iyaye nane, hankalina ya kasa kwanciya dalilin da yasa na nemi kazo, dan Allah duk laifin da nayi maka ka ɗau hukuncin ka amma nidai ka ban sarƙa ta, wallahi zan iya dafa Alkur'ani mai girma akan cewa wannan sarƙa ta ce, kar ka rabani da iyayena dan Allah...." Tsaya kallonta yayi sai yanzu fuskar Amreesh yake bayyana akan fuskar ta, sai yanzu ya fara ganin kamannin Amreesh a kan fuskar Baiwar Allah, yana cikin kallon ta yaji ta riƙo masa hannu tana faɗin "Zo! zo!! zo dan Allah..." Haka taja hannunsa suka nufi bedroom ɗinta.. Pinky da Rukky ganin Razhdeen yazo daman musamman fitowa sukayi suka je part ɗin Roshan jiran zuwan Razhdeen cikin ikon Allah yazo, a bakin ƙofar falo suka tsaya duk suna jin maganganun da Baiwar Allah take faɗi dake ata bakin ƙofar suma suka tsaya, su Pinky jin sun yi gaba ne yasa suka kalli juna, Rukky ta ce "wannan ai ba amfanin saka musu turaren nan tunda a haɗe suke, kina ga har ɗakinta ta kai shi...." Pinky ta ce "duk da hakan sai mun saka saboda a lokacin da za'a kamasu basa cikin hankalinsu, idan kuma muka barsu suna jin motsin mutum zata ɓoye shi..." Rukky ta ce "wannan gaskiya ne to mu shiga mana tinda basa falon, nasan nan da awa ɗaya Yaya Roshan zai iso kafin ya iso kuwa turaren zai washe sannan kafin su dawo hayyacinsu zasu ɗau mintuna...." ★★★★★ Bayan sun shiga bedroom Baiwar Allah ce ta nufi drower ta ɗauko Alkur'ani izu sittin sannan tazo gaban Razhdeen ta durƙusa da gwiwowinta ta dafe Kur'anin tare da faɗin "na rantse da girman Allah da darajar wannan Alkur'ani mai girma wannan sarƙar tawa ce, tin ina ƙarama nake riƙe da ita, idan abunda na faɗa ba gaskiya bane wannan Alkur'ani mai girma ta ci Ni...." Razhdeen hannu yasa ya ɗago ta tare da karɓan Kur'anin yaje ya ajiye akan drower, sannan ya dawo yana kallonta fuska ɗauke da murmushi, domin bai taɓa tsintar kansa cikin farin ciki irin na yau ba, babban burin sa shine ya haɗu da Amreesh kuma gashi Allah ya cika masa buri yau ga shi ga Amreesh ɗinsa, cikin sassanyar murya ya ambaci sunan ta da cewa "Reesh..." Girgiza kai take tana faɗin "bani bace Reesh wata ƙila Ƴar Amana kake magana akai, haƙiƙan nin gaskiya mun zauna wuri ɗaya da ita a gidan marayu tin dana jaririya, ita ɗin kurmiya ce...." Razhdeen jin ta ambaci cewa yarinyar da ta zauna da ita kurmiya ce yasa yayi saurin buɗe eyes ɗinsa yana ƙareta da kallo..." Ta cigaba da cewa "a gidan marayu aka sace ta har yau ban sake jin labarinta ba, inasonta sosai domin na ɗauke ta tamkar ƴar uwata, shin ina zan same ta? shin kana nufi kace asalin sunanta Amreesh? kuma ƴar uwarku ce? amma nayi farin ciki sosai da naga ƴan uwan masoyiyata, ina zan ganta nayi mata albishir...." ta ƙarasa maganar tana sharar hawaye. Razhdeen lips ɗinsa na kakkarwa ya ce "kina nufin ki ce kurmiya ce?..." Baiwar ALLAH tana kuka ta ce "ey kurmiya ce, tana da tambari akan cinyarta na dama, zanen tambarin masarauta take da shi akan cinya, dan Allah ku nemo ta, kurmiya ce, ban san a wani hali take ciki ba..." Razhdeen idanuwansa ne suka shanye kamar wanda yayi maye tsabar tsananin ciwon kai da yake fama da shi ga baya iya cin komai tsabar tunani ga rashin yin bacci, matsaloli sun saka shi a gaba, tunanin Sarah ya fara yi yana maganar zuci da cewa "kodai Sarah itace Ƴar Amana?...." Yana cikin wannan tunanin yaji Baiwar ALLAH ta ɗan sau ƙara tare da dafe goshinta, wani irin sarawa kan natan yayi ga hajijiyan da yake shirin ɗaukar ta lokaci guda tayi baya zata faɗi, Razhdeen yayi saurin riƙo ta, Ƙanƙame shi tayi tana faɗin "wani irin turare-turare nake ji babu daɗi, kaina ciwo wallahi...." Su kuwa Pinky da Rukky suna bakin ƙofar ta waje suna sanye da facemark gudun kar su shaƙi ƙamshin, haka suka riƙa feffeshe ɗakin ta ƙasin ƙofar ɗakin yanda turaren zai rinƙa shigo musu, suna kammalawa suka ruga da gudu tinin suka bar falon, kai tsaye part ɗin su suka nufa domin sun gama aikin su.... Wannan turaren Baiwar ALLAH ce ta fara shaƙa har ta fara fita hayyacinta ganin yanda take ta surutai marasa ma'ana kamar wata taɓaɓɓiya yasa ya riƙe sosai yana mamakin yanda akayi ta shiga wannan halin lokaci guda, Shima turaren ne ya bugi hancinsa kansa ne yayi wani irin sarawa da ƙarfin gaske ga wani hajijiyan da yazo masa da ƙarfin gaske tin ya kayar da shi duk suka faɗa kan gadon dake bayan Baiwar ALLAH, Shine a saman ta a yayin da take kwance duk babu mai hankali a cikin su kowa ya zauce sai wani irin feeling da yazo musu lokaci guda, a tsakanin su babu wanda bai jiƙe ƙasin sa ba domin wannan maganin asalin mai ƙarfi ne, duk rashin sha'awar ki indai kika shaƙa shikenam bazaki san lokacin da zaki rungumi na kusa da ke ba... ★★★★★★ Roshan ne ya sauƙa a airport already akwai security da yazo ɗaukar sa, shiga cikin motar yayi tare da kunna wayar sa yana son sanar wa Baiwar ALLAH cewa ya iso tayi masa shiri na musamman da girkinta mai daɗin gaske, da yaso yayi mata bazata sai dai kawai ta gànshi amma yanzu ya yanke shawar sanar mata domin kar ya koma ya tarar bata shirya komai ba, Yana buɗe wayar sa yaji saƙo ya shigo masa waya ta whatsApp, cike da mamaki yake bin number da kallo ganin unknown number ne kuma alamu video aka turo, shiga ciki yayi abun da ya gani ne yayi mungun tayar masa da hankali tin kafin ya shiga cikin video, kamar Baiwar Allah ya gani kwance saman kan Razhdeen a ƙasin carpet... Ciro glass ɗinsa yayi ya sanya yana tunanin ko matsalar daga idonsa ne, play ya danna, haka ƙirjinsa yake bugawa da ƙarfin gaske ganin yanda video yake, video farko da akayi musu lokacin da Baiwar Allah taje gidan Razhdeen akan yi masa warning, Haka yake furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..." saida ya gama gani tukun ya sauƙe nannauyar numfashi daƙer lokaci guda har idanuwansa sunyi jawur kamar zai yi kuka, dake ma video short ne domin iya faɗuwa masa da tayi a kansa akayi, Roshan a cikin ransa ya ce "kenam basu rabu ba? daman Ammata tana zuwa gidan Razhdeen ba tare da sani na ba? amma meyasa cin amana haka why?...." Roshan bai yi ƙasa a gwiwa ba haka yayi dialing call number Baiwar Allah, tana ringing har ta katse ba'a ɗauka ba, sai da ya ƙirata kusan sau goma amma ba'a picking, ransa a matuƙar ɓace yayi wurgi da wayar kan kujerar mota..... ★★★★★ Al'amarin Razhdeen da Baiwar ALLAH ya wuce misali domin a halin yanzu gaba ɗayan su ba kaya a jikin su sai ma rufe kansu da suka yi da mayafi, kowa yana bawa junan su saƙonni, domin ba ƙaramin shiga yanayin uƙuba suka yi ba, sai fitar da numfashi suke amma a halin yanzu gaba ɗayan su babu wanda yasan mai yake aikata wa, duk basu san me suke yi ba domin hankali ya rigada yayi gaba domin har yanzu wannan turaren lokacin sa bai ƙare ba, da zarar ƙamshin ya washe a lokacin suma zasu dawo hayyacinsu.. Lokaci guda Baiwar ALLAH tasau wani irin ƙara haɗe da kuka tana ambatar sunan "Yaya Roshan! Yaya Roshan!! Yaya Roshan!!!..." sunan ne kawai yazo bakinta take furtawa amma ita kanta bata san mai take faɗi ba balle tasan a halin da take ciki... Shima Razhdeen ganin kansa yake a cikin gajimare ya kasa daina abinda yake aiwatar wa, ko ambatar sunan Yaya Roshan da take yi shi sam baya jinta, bai san a wani duniya yake ba, da za'a barshi a tunaninsa cewa zaiyi bashi da rai ya zama matacce domin a cikin gajimare yake ganin kansa... ★★★★★★ Ƴar Amana kuwa tana cikin halin kuka sai ga Madam Blessing ta shigo har ɗakinta ta zauna a kusa da ita a bakin gado, yanda tayi tagumi sai zubda hawaye take ga yanda zuciyar ta yake ta bugawa haka kawai bata san dalili ba. Madam Blessing ce ta dafa kafaɗarta tare da ambatar sunanta "Sarah..." A firgice Ƴar Amana ta ɗago tana kallon Madam Blessing ido a shashshanye domin tin safiya bata ci komai ba.. Madam Blessing ta ce "kina yarinyar ki ƙarama amma kina jefa kanki cikin matsalar da zai sanya miki hawan jini ko ciwon zuciya, nasan dai matsalar ki abu ɗaya ne bazai wuce akan Ogah Razhdeen ba, shima a kwanan nan ya shiga wani irin halin da na kasa gane masa, a halin yanzu bai iya control kansa ba balle yazo ya baki lokacin ki, kin daina zuwa school saboda baya kai ki, kin daina cin abinci sosai saboda baya nutsuwa ya ci shima, baya zuwa yanda kike yanzu kema kuma kin kasa zuwa yanda yake, amma duk laifin sa ne da ya gagara gane halin da kike ciki alhalin yasan ba iya magana zaki yi ba, shin inda bana zuwa nan gidan sai dai ya fito ya samu gawarki kenam?....." Ƴar Amana tsaya kallonta tayi wuya a karye kamar marainiyar da ta rasa gata, Madam Blessing ta cigaba da cewa "Sarah nasan soyayya ta shige ki tin ba yau ba, na fiskance ki kina tsananin ƙaunar Razhdeen, amma kin kasan sanar masa don babu yanda zakiyi tinda yanzu baya tsayawa ya baki lokacin sa balle kiyi masa alamu da hannu, Bazan iya juran ganin ki a cikin wannan halin ba kina ƙaramar yarinya dole zan same shi yasan abinda ya dace, sannan zan sanar masa cewa kina sonsa in zai tsaya ya kula da ke toh gwara haka...." Ƴar Amana jin Madam Blessing ta ce zata sanar masa tana sonsa yasa tayi saurin riƙe hannunta tare da girgiza mata kai alamun "A'ahh ta bar shi kawai...." Madam Blessing ta ce "to shi ya kasa ganewa, idan kuma wani ciwo ya kamaki fa? to ni saina gaya masa..." tana kaiwa nan ta fice a ɗakin, Ƴar Amana kuma ta cigaba da zubda hawayen ta..... ★★★★★★★ Roshan ya iso gida cikin ƙoshin lafiya haka motar su ta rinƙa tsallake gate gate a jere har suka yi parking a wurin ma'ajiyin motoci, Ummy uwar masu gida ya tarar ta fito jin sauƙar mota daman tana jiran isowar sa ta fara masa oyoyo, yanzun ma nufan yanda yake ta je tayi masa oyoyo tare da karɓan jakar sa suka nufi babban falon gidan kafin ya wuce part ɗinsa. A falo ya tarar da kowa da kowa anata shan hira ga baƙi ƴan uwa har sun zozzo, a ciki har da Aunty Yolash, duk tashi sukayi suna tsokanan sa da cewa "Ango yasha ƙamshi, Ango ya iso mijin Amarya..." Roshan zama yayi akan kujerar falon domin yanada son mutane, haka ya fara gaggaisa wa da su, anata tambayarsa Amarya... Duk family su ba ƙaunar Baiwar ALLAH suke ba hasali ma ganin laifin Abbah suke yi da ya Aurawa ɗansa yarinyar da ba'a san asalinta ba, yanzu kuwa jin zai ƙara Aure ne yasa kowa ya shiga yin farin ciki, Da yawan mutanen falon baƙin sunata masa complain akan Baiwar ALLAH ta cika baƙin hali, bata son ƴan uwansa, dalili shine tinda suka zo bata zo ta gaishe su ba sannan ta hana aje yanda take, Sam Roshan bai ji daɗin hakan ba, yafi son kowa ya yabi matarsa amma sai ya ga akasin haka, itama Aunty Yolash da take ji da Baiwar Allah yau ta kawo complain ɗinta a Roshan ta ce "yarinyar nan wai zan yi mata gwaninta musamman na aika Ummy akan zanje nayi mata gyaran jiki irin na Amare, nayi mata gyaran Uwar gida amma ta aiko cewa ita bata so ai raina na ɓaci wallahi, shiyasa banje part ɗinka ba tinda nazo..." Wasu daga cikin mutanen ne suka ce "mu kam munje amma taƙi buɗe mana ƙofa haka muka juyo, ita dai baƙin kishi zai hallaka ta saboda kowa yasan kishi ne, za'a kawo mata mai asali da tushe wacce zata haifa mana yara ƴan dagwai-dagwai tinda ita juya ce bata haihuwa, Aure shekara biyu...." Roshan ganin bazai iya juran maganganun nan ba yasa shi miƙe wa yana faɗin "Bari naje part ɗina, zan same ta da maganar Insha Allahu...." Hajiya Kilishi ce ta sauƙo tana faɗin "Ina kuma zaka je Roshan ga abinci yanda aka haɗa maka na taryan Ango..." Sakin murmushi yayi sannan ya ce "mutane sunyi yawa anan kawai a aika mun can part ɗina domin nasan Ammata bata yi ba saboda ban sanar mata ina kan hanya ba...." Hajiya Kilishi ta ce "to shikenam Insha Allahu za'a biyo ka da shi..." Ya amsa tare da fita zai nufi yanda yake da matar sa ga kuma Ummy ƴar rakiya tana ɗauke da jakarsa haka suka fita tareda, suka shiga mota zasu je domin da ɗan rata a tsakanin su, Roshan ne ya kalli Ummy sannan ya ce "Razhdeen ya zo ne?..." Ummy ta girgiza masa kai alamun "a'ah..." Roshan ya ce "why? naga motar sa fa a other side sannan na shiga ciki ban gan shi ba..." Ummy ta ce "zai iya ajiye tasa ya ɗauki wani motar ai...." Jinjina kai Roshan yayi tare da faɗin "na gamsu yanzu dai muje..." Roshan yana shiga part ɗinsa yaji zuciyar sa tayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske, riƙe saitin zuciyarsa yayi tare da sunkuyar da kai, Ummy ta ce "Yaya Roshan meya faru ne?...." Ya girgiza kai ya ce "ba komai, let us go..." Suka buɗe tare da fice wa.... Sai da suka zo bakin ƙofa sannan suka buɗe gani yayi falo yayi fes-fes sai ɗaukan ido yake sai dai babu kowa a falon... Ummy zama tayi akan kujera shi kuma ya ɗauki jakarsa ya nufi room ɗinsa... A wannan lokacin turaren ya wa she babu sauran ƙamshin da ya rage, Baiwar Allah da Razhdeen suna nan a yanda suke babu ƙwari a jikinsu, sai yanzu hayyacinsu ya fara dawowa, Razhdeen ne ya ɗan motsa yana shirin tash, jikinsa gaba ɗaya ba ƙarfi haka ya ƙara komawa kanta duk bai san akan mutum yake ba, hasali ma ya ɗauka a gidan sa yake hakan ma kan gadonsa... Roshan ne ya dawo falo yana faɗin bari naje ɗakin Ammata nasan yanzu haka tana ta shan bacci.... kai tsaye ya nufo room ɗin Baiwar ALLAH cikin rashin sa'a yana tura ƙofar ta buɗu, Fuska ɗauke da murmushi da sallama a bakinsa ya shiga, yana kaiwa idonsa kan gadonta zuciyarsa ta wani irin bugawa da ƙarfin gaske, a tsorace ya ja da baya yana jero Addu'o'i.... Wannan Addu'o'in bai sauƙa a ko ina ba sai a kan dodon kunnen Razhdeen da Baiwar ALLAH wacce yanzu take mutsil-mutsil tana shirin buɗe idonta, Razhdeen a hankali ya buɗe idonsa jin anata addu'a, idonsa ne ya sauƙa akan fuskar Baiwar Allah a ruɗe da firgici yayi saurin tashi daga kanta yana zazzaro ido waje haka zuciyarsa take harbawa da ƙarfin gaske, cike da mamaki yake bin ta da kallo yana tunanin taya hakan ta faru duk da har yanzu bai san ya aikata wani abu ba bayan wannan, Dasauri ya waiwaya ya kalli bakin ƙofa yanda yaji sallama yaga Roshan a tsaye idonsa akan su bai san lokacin da hawaye yake zarya akan fuskarsa ba, Itama Baiwar ALLAH buɗe idonta tayi wanda ta fara gani shine Razhdeen dake gefenta ko kaya babu a jikinsa itama a ruɗe cikin tashin hankali ta miƙe zaune tana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allahumma ajurni fi musibati ƙalu innalillahi wa inna'ilaihi raju'un...." Cikin tashin hankali ta ce "na shiga uku mai mai mai mai zan gani haka,?..." Buɗe baki tayi zata ƙara magama idonta ya sauƙa akan Roshan dake tsaye a bakin ƙofa, da sauri tasa hannu biyu ta toshe bakinta tana shirin yin ihu, Roshan cikin tashin hankali haka ya juya ya koma falo bai ce musu komai ba, ga hawaye ya ƙi tsayuwa har sai da ya je falo ya nemi kujera ya zauna tare da yin tagumi... Ummy ganin a halin da Roshan yake ciki ne yasa ta tashi taje kujerar da yake ta zauna tana rirriƙe shi kamar zata yi kuka tana tambayarsa "meya faru ne Yaya Roshan? Dan ALLAH ka sanar mun mana bana son ganin ka a cikin wannan halin...." Roshan shiru yayi bai ce komai ba, ji yake zuciyarsa kamar ta faso ƙirjinsa ta fito tsabar bugawar da yake... Ummy ta ce "to tinda ka kasa sanar mun ni zanje na gano menene..." Zata tashi yayi saurin riƙo hannunta tare da zaunar da ita still bai daina hawayen ba kuma ya kasa cewa komai... Baiwar ALLAH tsabar ja da baya da take ne yasa ta faɗo daga kan gado, abinda ya ƙara jefata cikin tashin hankali shine ganin kanta da tayi tsirara babu kaya yasa tayi saurin rufe jikinta da mayafin gadon ta tashi tana ja da baya ta ɗauko farin towel babba ta ɗaura daga kan ƙirjinta, haka jikinta yake ta kakkarwa zuciyarta na bugun uku-uku, A ruɗe take faɗin "Uncle Deen mene? me yake faruwa dani? meya same ni ne? shin mutuwa nayi za'a mun wankan gawa ne ko kuma meye? dan Allah ka sanar mun abinda yake faruwa dani...." nan ta fashe da matsanancin kuka. Shima Razhdeen ɗin kuka yake daƙer ya iya buɗe baki ya ce "ban sani ba nima, ban san meya faru dani ba, taya zan ganni akan gadon matar twins hakan ma tsirara? taya hakan zata faru?...." Girgiza kai Baiwar Allah ta fara yi tana shirin shiɗewa tayi hanyar fita da gudu taji ƙafarta ta riƙe, wani irin zafi take ji a farjinta da zogi, daƙer take iya taka ƙafar, zaro manya-manyan idanuwanta tayi waɗanda suka yi jawur lokaci guda, hannu tasa ta dafe wurin da take jin zafin ta waiwaya yanda gadonta yake, ihu tasau tare da rufe bakinta idonta akan tsakiyar gado yanda yake jiƙe da jini da ruwa gaba ɗaya, ta kuma kallon Razhdeen daga nan ta fahimci komai, fashewa tayi da kuka tana faɗin "Uncle Deen ka cuce ni wallahi, ka gama da rayuwata, ka zubar mun da mutunci na da kimata, kaci amanar ɗan uwanka, nifa matar Aure ce ...." Razhdeen bai san mai zai ce a wannan al'amarin ba domin ya rasa gane ta yanda hakan ta faru, murya na kakkarwa ya ce "Reesh...." A rikice Baiwar Allah take faɗin "a'a! a'a!! Bani bace Reesh dan ALLAH kada ka sanar mun cewa Zina na aikata, dan Allah kar kace nayi Zina, wallahi ban taɓa aikata zina ba, no no noooo....." Tana cikin wannan haukar ta ruga da gudu ta fice tana ɗingishi ta nufi falo tana ɗaure da towel a ƙirjinta ga yanda sumar kanta ya tartarwatse... Roshan kuwa yana zaune yana riƙe da hannun Ummy ya hanata tashi taje ta dubo me yake faruwa a ɗakin Baiwar ALLAH, suna cikin wannan halin sai ga Baiwar Allah ta shigo falon tana kuka, ganin Roshan yasa kai a gaba ko kallon yanda take baiyi ba sai kallo wuri guda yake kamar mai tunanin wani abu, tsananin tashin hankalin da yake ciki yanzu ya wuce misali... Baiwar ALLAH da sauri ta zo ta durƙusa ata gaban Roshan tana facing ɗinsa, kuka yaƙi tsayuwa lips ɗinta ne kawai yake kakkarwa ta kasa cewa komai... Ummy ganin a halin da take ciki ne yasa itama zuciyarta bugawa, tana kallonta tin daga kan sumar kanta da yake a tawarwatse har zuwa ɗaurin ƙirjin da tayi da towel hakan ma da ɗingishi ta fito sai abun yayi matuƙar ɗaure mata kai, Can sai ga Razhdeen ya fito shima daga ɗakin yana sanye da kayansa domin sai da ya tsaya ya saka su tukun ya fito fuska yayi jawur tsabar tashin hankali da yake ciki.... Roshan ɗago kansa yayi tare da sauƙe nannauyar numfashi ya maida idonsa kan Baiwar ALLAH da take gabansa a durƙushe sannan ya maida kallonsa kan Razhdeen dake tsaye, sannan ya jinjina kai tare da sakin murmushin baƙin ciki da takaici ya ce "hakan na nufin tin ba yau ba kuke cin amana ta, kuna aikata alfasha a tsakanin ku...." Ya kalli Baiwar Allah sannan ya ce "da Auren ki kika aikata zina shin kin san hukuncin haka?..." "tin kafin na gani da idona naga shaidar hakan a cikin wayata...? Baiwar ALLAH ƙara fashewa tayi da kuka tana faɗin "wallahi ban taɓa aikata zina ba, kada ka danganta ni da mazinata wallahi bansan zina baa...." Kafin ta rufe baki Roshan ya zuciyo a fusace ya zabga mata mari har sai da ta kife da kanta, A ruɗe Razhdeen ya miƙa hannu tare da faɗin "Reesh..." dunƙule hannunsa yayi cike da takaicin wannan ranar haka hawaye yake ta zuba masa... Roshan jin Razhdeen ya ambaci Reesh yasa ya juya da sauri yana kallonsa, daga baya ya jinjina kai tare da faɗin "bazan yi mamaki ba dan ka gano ko ita wacece, shine dalilin da yasa kaci amanata? meyasa bazaka ce in rabu da ita na baka matarka ba? duk da alƙawari ne ba ɗaura Aure ba, don haka babu abinda zai hana a ɗauki mataki akan ku...." Razhdeen cike da mamaki shima ya ce "daman kasan da cewa Reesh ce?..." Roshan ya ce "Yes nasan cewa Amreesh ce, na gano hakan ne ta yanda kaima ka gado...." Roshan ya ƙarasa maganar tare da wurga masa wani irin kallon tsana lokaci guda... Baiwar ALLAH ce ta ɗago idonta akan Roshan ga yanda take zubda hawayen jini akan fuskar ta, gaba ɗaya kukan ta ya koma na jini, ruwan hawaye duk ya sauya zuwa ruwan jini tsabar tashin hankali da damuwa da ruɗanin ƙwaƙwalwa, Ta ce "Yaya Roshan ko kashe ni za'ayi bazan taɓa yadda cewa ni baiwar Allah na aikata zina ba...." Tsawa Roshan ya darara mata tare da faɗin "enough please, shin kin mayarni mahaukaci ne? ko duk jikina kunne ne bazan taɓa yadda da kalaman ki ba sai dai ki cigaba da wannan kukan jinin nakin, wallahi kin fita mun a raina, bana sonki yanzu, bana ƙaunar ki haka bana ƙaunar mai ƙaunar ki, na tsane ki sannan na kawo ƙarshen alaƙar mu daga yau...." Yana kammalawa ya tashi ya nufi hanyar fita ya fice gaba ɗaya, itama Ummy kuka take duk ta fahimci halin da suke ciki haka itama ta tashi tabar falon ta fice.... Baiwar ALLAH hannu ta ɗora akanta ta fara rausa ihu ga hawayen jini yaƙi tsayuwa duk ruwan jinin ya ɓata mata fuska kuka kawai take tayi... Razhdeen ganin yanda take kukan jini ne yasa ya nufo wurin ta da sauri yana ƙiran sunanta da "Reesh! Reesh!! please stop dis cry I don't wanted...." Cikin zafin nama kamar mai aljanu haka taci kwalar rigar Razhdeen da hannu biyu tana ihu tana jijjiga shi da ƙarfin gaske, maganar ma ta kasa yinsa sai jijjiga da take tayi ta kasa daina ihun da take tayi ga kukan jinin da take ta zubar wa.... Tana cikin wannan halin numfashinta ya ɗage sai kawai tayi baya zata faɗi tayi saurin rungumota saman ƙirjinsa yana kuka sosai kamar ransa zai fita, ita kuwa ta rigada ta suma a wurin.... Typing ✍️ *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 16 to 20 Razhdeen ɗaukan Baiwar ALLAH yayi ya nufi room ɗinta da ita, yana zuwa ya kwantar da ita akan doguwar kujerar ɗakin sannan ya tsaya yana kallon kan gadon yanda ya ɓaci da jini, zuciyarsa sai yanke wa take tana masa suka domin wannan ranar itace ranar mummunan ƙaddarar sa wanda bazai taɓa manta wannan ranar ba har ƙarshen rayuwar sa, sai yanzu ya gama yadda da cewa akwai abinda suka aikata shi da Baiwar ALLAH, amma ya kasa gane ta yanda akayi har hakan ta faru, wasu zafafan hawaye ne suka fara zarya akan fuskar sa, hannu ya kai ya ciro bedsheet ɗin sannan ya ajiye a gefe, yaje ya ɗauko wani sabo ya shimfiɗa mata, zuwa yayi ya ƙara ɗago ta ya kwantar da ita akan gadon tare da ɗora kanta akan pillow, ya rufe ta da blanket domin iya towel ne a jikinta, Bazai iya tafiya ya barta a cikin wannan halin ba tare da ya tallafa mata ba, yana gamawa ya ɗauki bedsheet ɗin da suka ɓata yana riƙe da shi ya fice a ɗakin tare da rufe mata ƙofar ɗakin, zuwa yayi ya ɗauko ashana da petur ya fice kai tsaye bayan gidan ya nufa yanda ba kowa ne yake zuwa wurin ba, ya barbaɗa bedsheet ɗin da petur sannan yasa ashana, sai da ya ƙona bedsheet ɗin nan gaba ɗaya sannan ya tafi jiki ba ƙwari... Shi kuwa Roshan yana fito wa ya shiga motar sa yabar gidan, shi kansa bai san ina ya nufa ba, sai da ya shiga daji sosai da motar sa sannan yayi parking, yana kuka ya fito acikin dajin nan ya durƙusa da gwiwowinsa nan ya fara rausa ihu yana bugan ƙasi da ƙarfin gaske ga yanda hadari ya gangamo gari yayi baƙi ƙirin lokaci guda aka fara zabga ruwan sama, yana durƙushe ko motsa wa bai yi ba, haka yake ihu ruwan sama na jibgarsa, ji yake kamar ya hallaka kansa a dajin, yana cikin wannan halin jini ya fara burtsowa daga bakinsa, haka zuciyar sa take ƙuna kamar wanda ake caka masa mashi, kifar da kansa yayi a ƙasin wurin jini yana fita daga bakin sa, ruwan sama kuwa kamar ana zubo shi da bakin ƙwarya tsabar yawansa..... Shima Razhdeen cikin fitar hayyaci haka yake jan motarsa gaba ɗaya tunaninsa yana wani wuri, hawaye kuwa haka yake ta gangarowa ba ƙaƙƙautawa, yana cikin dogon tunani ba tareda ya duba hanya ba yaji wata ƙatuwar trailer tayi sama da motar sa, haka motar ta faɗo ƙasi tare da ƙara ɗaguwa sama anan murfin motar ya buɗu daga sama tayi wulli da shi, motar itama ta wulli cikin jeji, ɗan ratan ba nisa a tsakanin motar da Razhdeen, kafin mutane su taru nan take motar tayi boom ta kama da wuta, shima kansa Razhdeen sai da ya ƙara tashi sama ya ƙara dokuwa a ƙasi tsabar ƙarfin tashin wutar, tintinin har ya daina motsi, kowa ya saddaƙar da cewa Razhdeen ya mutu domin ba ƙaramin hatsari yayi ba, haka motar take ci da wuta ta gagara kasuwa sai da Allah ya koro ruwan sama tukun, acikin ruwan nan motar ambulance tazo ɗaukan Razhdeen babu yanda yake, ko gane shi ba'a iya yi sakamakon jinin da ya wanke masa duk ilahirin jikinsa da fuska gaba ɗaya, kai tsaye hospital aka nufa da shi.... A lokacin da hatsarin ya abku har an sanar wa Abbah dake can ƙasar waje, suna kan gudanar da Meeting ɗin ƙarshe kenam aka tura masa saƙon hatsarin Razhdeen, kuma bugu da ƙari abinda ya ƙara ɗagawa Abbah hankali shine da aka ce ya mutu... Abbah a ruɗe ya shirya komawa Nigeria ba tare da ya kammala aikin da yake ba... Ummy itama a wannan ranar ba ƙaramin shiga damuwa tayi ba ganin halin da Uncle Deen da Baiwar ALLAH suka fa ɗa, kowa sai tambayarta yake meke faruwa amma ta kasa sanar wa kowa, hatta mahaifiyar ta ma ƙin gaya mata tayi, A lokacin da mutanen gidan suka ji labarin hatsarin Razhdeen kowa gagara zama yayi haka duk suka nufi hospital, koda suka je ba'a barsu sun gànshi ba saboda a halin da yake ciki baza'a so wani ɗan uwansa ya gànshi ba, hatta likitocin tsammanta masa mutuwa suke... Duk suna asibiti babu wanda aka bari a gida, Rukky fashewa tayi da kuka tana bugan Pinky tare da faɗin "kinga duk mu muka jawo, sai da nace kada muyi wannan aikin amma kika dage gashi nan yanzu ɗan uwan mu zai mutu ata sanadiyar mu...." Pinky ta ce "dallah wa ya gaya miki saboda mu yayi hatsarin? Allah ne ya aiko kuma babu wanda ya isa ya tsallake ƙaddarar sa..." Rukky ƙasa-ƙasa take da murya ta ce "kinsan fa Yaya Roshan ya kamasu, nasan saboda damuwar nan ne yasa Uncle Deen hatsari kuma in ba sa'a ba bazai tashi ba..." Pinky ta ce "shikenam idan ya mutu Baiwar Allah babu wanda zata samu a cikin su, tinda nasan Roshan bazai ƙara kusantar yanda take ba, shi kuma Uncle Deen yabar duniya..." Rukky ta sauƙe numfashi tare da faɗin "ke fa bakida imani wallahi, Ni banga ribar hakan ba, wallahi zan daina biye miki muna aikata ɓarna, yanzu sai alhakin su ya kama mu...." Pinky tsuka taja sannan ta wuce tabar Rukky a wurin... Su Mommy da Ammy dasu Aunty Yolash basu bar asibiti ba har dare misalin ƙarfe 9 amma basu samu ganin Razhdeen ba, a wannan lokacin ne Abbah ya zo hospital da motar sojojin sa ƴan rakiya, a ruɗe Abbah ya shigo yana faɗin "aina aka kwantar da Razhdeen?..." Aunty Yolash ta ce "yana emergency room har yanzu basu bar kowa ya gànshi ba..." Abbah a firgice ya nufi hanyar ɗakin da aka kwantar da Razhdeen cikin sa'a sai ga Doctor ya fito daga room ɗin, Abbah ne ya tsayar da shi tare da tambayar sa Razhdeen. Doctor girgiza kai yayi sannan ya ce "a gaskiya har zuwa yanzu bamu iya ceto shi ba..." A ruɗe Abbah ya katse shi da cewa "ban gane baku ceto shi ba, shin me kuke nufi, dan Allah kada ku sanar mun yarona ya mutu..." Abbah ya ƙarasa maganar yana kuka.. Doctor rarrashinsa yake yana faɗin "har yanzu da sauran bugun zuciyar sa amma gaskiya bazai wuce wasu sa'o'i ba indai ba'a tare shi da wuri ba, kuma kamar ƙwaƙwalwarsa ta ɗan taɓu, koda ya farfaɗo ma dole sai ya ɗau dogon zango kafin ya iya dawo hayyacin sa...." Abbah a firgice ya ce "to me kuke jira da bazaku fara masa abinda ya dace ba?..." Doctor ganin yanda Abbah ya ruɗe ne yasa shi cewa "ka kwantar da hankalin ka Chief Insha Allahu zai tashi, akwai abinda bamuda shi a wannan hospital kuma dole sai da shi zamu iya ceto rayuwar sa, abun babu a Nigeria gaba ɗaya amma mun aika can ƙasar misrah zuwa nan da wasu mintuna jirgin zai iso..." Abbah yana zubda ƙwallah tinda har aka fara masa wannan lissafe-lissafen yasan ba ƙaramin ciwo bane, Ya ce "Doctor please idan kunsan bazaku iya dawo mun da yarona cikin hayyacinsa ba tin wuri ku sanar mun na fita dashi ƙasar waje..." Doctor ya ce "musamman muka aika can ƙasar waje akan muna buƙatar ƙwararru likitocin da zasu taya mu duba shi, suna nan tafe..." Abbah ya ce "yanzun yana ina?..." Doctor ya ce "amma sai dai ba'a barin kowa ya gànshi..." A fusace Abbah ya ce "idan kun hana kowa ganinsa ni baku isa ku hanani ganin ɗan cikina ba..." Doctor ya ce "hakane mu shiga kawai..." A tare suka shiga room ɗin da aka kwantar da Razhdeen, Abbah yana ido huɗu da shi zuciyar sa tayi wani kyakkyawan bugawa da ƙarfin gaske ganin halin da Razhdeen yake ciki... A ruɗe Abbah ya ƙarasa wurinsa yana ambaton sunan sa, Razhdeen an ɗaɗɗaure gaba ɗaya kansa da bande ji, har da fuskar sa, gaba ɗaya dai duk jikinsa an zagaye da bandeji domin ko ina na jikinsa yaji ciwo, an sanya masa oxygen sai bugun zuciyar da yake ɗan harbawa da kaɗan-kaɗan domin duk bugun zuciyar sa ana gani ta cikin computer dake manne a jikin bango, da zarar bugun zuciyar ta tsaya shikenam computer zai daina aiki shima, Kuma dole sai anyi masa aiki a ƙwaƙwalwarsa wannan gashin kan nashin ana buƙatar Aske shi gaba ɗaya... Abbah ne ya kifa kansa a bakin gadon sai sharar kuka yake, yana cikin wannan halin sai ga su Aunty Yolash sun shigo da sauran ƴan gidan, Duk wanda yaga Razhdeen sai ya zubar masa da hawaye, hatta suma Pinky da Rukky fashewa sukayi da kuka, basu yi tinanin hatsarin har ta kai haka ba, Ummy uwar masu gida zuwa tayi ta rungumi Abbah tare da fashewa da kuka tana faɗin "Abbah dan Allah kar Uncle Deen ya mutu, shikenam ya mutu ko? meyasa zai tafi ya bar mu muna sonsa sosai..." Daƙer Abbah yake rarrashin Ummy domin muryar ta tafi fitowa, daƙer Abbah ya kora su gida, duk shiga mota sukayi akayi driving ɗinsu zuwa gida, iya Abbah ne kawai ya rage a hospital... Can misalin ƙarfe 10 na dare likitoci ne ƴan ƙasar waje sunfi biyar duk akan Razhdeen ga na cikin hospital ɗin, Abbah yana daga waje zaman jiran su, kwatsam Roshan ya faɗo masa a rai, kuma Doctor ya sanar masa cewa tinda aka kawo Razhdeen bai ga Roshan yazo ba, sai abun ya bawa Abbah mamaki, zaro wayarsa yayi yana ƙiran wayan Roshan amma ba'a picking, ya ƙiƙƙira security gidan yana tambayar su Roshan amma kowa sanar masa yake da ba'a san yanda yake ba... Abbah ganin tambayar bazai kai shi ba yasa yayi tracking number sa a wurin da wayar ta nuna masa Roshan yana wajen abun ba ƙaramin ɗaure masa kai yayi ba, domin alamun a jeji yake... Abbah ƙiran wasu sojojinsa yayi ya sanar musu cewa suyi tracking number Roshan suje su same shi a yanda yake a cikin daren nan... Sojojin amsa masa suka yi a lokacin suka nufi hanya suna bin yanda wayan sa yake ta hanyar tracking... ★★★★★★ Baiwar ALLAH kuwa farfaɗowar ta ke da wuya haka ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazzaɓi tsabar kukan da tasha ga damuwa, haka jikinta yake kakkarwa gaba ɗaya ta zamo wata kala kamar ba Baiwar ALLAH ba, duk ta rarrame lokaci guda, daƙer ta tashi tana ɗingishi ta shige toilet tayi wanka sannan ta ɗauro alwala ta fito tana jan ƙafa jiki duk ba ƙwari, saka kayanta tayi doguwar riga marar kauri sannan ta zura hijab tare da shimfiɗa sallaya ta tsaida sallah, duk sallar da ya wuce ta sai da tayi su a ranar yau, sannan ta haɗa da lafula sujjadar ƙarshe da tayi ta juma bata ɗago ba tana jero Addu'o'i tare da neman gafarar Ubangiji, haka take kuka tana addu'a, har zuwa yanzu hawayen ta maimakon kaga ruwa sai jini, ta juma sosai kafin ta ɗago fuskar nan yayi jagab da hawayen jini, tashi tayi tana mai ƙara fashewa da kuka domin idan ta tuno da abinda ya faru yau sai taji kamar ta kashe kanta domin zaman duniyan ya ishe ta haka, zamar da hijab ɗinta tayi tare da durƙusa da gwiwowinta tana ambatar sunan Razhdeen tare da faɗin "meyasa zaka yi mun haka Razhdeen, ka cutar da rayuwa ta Razhdeen bazan yafe maka ba duniya da lahira, na tsane ka bana ƙaunar ganin fuskar ka wallahi, kaji daɗi ka rabani da mijina, ina son Roshan har cikin zuciyata amma lokaci guda an rabani da shi, da wani ido zan kalli Roshan? da wani ido zan kalli Abbah, da wani ido zan kalli sauran mutanen gidan wayyo Allah nah, na shiga uku Ya Allah ka ɗauki rayuwa ta cikin gaggawa, innalillahi wa inna'ilaihi raju'un zina! zina!! zina!!!, yau ni ce wai na aikata zina? da igiyar Aure nah 😭...." Haka take ta wannan surutan tana kuka gaba ɗaya ta jiƙe gaban rigar ta da kukan jini, haka ta tashi ta nufi wurin mirror haka ta tsaya tana kallon kanta, ganin yanda jini yake tsiyayo wa daga cikin ƙwayar idanuwanta yasa ta daki jikin madubin da hannunta, haka take dukan madubin da hannayenta biyu tana ihu kamar ranta zai fita, Gaba ɗaya duk ta dagargaje madubin da hannunta ga hannun yanda yake jini tsabar yayyankewar da tayi... Aunty Yolash ce ta shigo falon tana sallama jin shiru sai ihun da take taji a cikin ɗakin Baiwar Allah yasa ta nufi ɗakin da sauri, tana buɗe wa taga yanda Baiwar ALLAH take ta ruso da kayayyakin ta ƙasi, haka ta jawo wardrobe ya doku a ƙasi duk ta fiffirgice ɗakin ta faffasa abun fashe wa still tana ihu bata dakata ba..... Aunty Yolash ganin aika aikan da Baiwar Allah take ne yasa ta nufi ciki da gudu ta rirriƙe ta tana faɗin "lafiyar ki ƙalau kuwa Daughter? kin haukace ne? ki duba kiga yanda kika ji wa kanki ciwo a hannu...." Baiwar ALLAH girgiza kai take tana kuka na fitar hayyaci, Aunty Yolash ganin yanda take kukan jini yasa ta sakin baki tare da zaro ido waje tana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Daughter me zan gani haka, kukan jini fa kike wayyo Allah...." Haka Aunty Yolash ta rungume ta sosai a jikinta tana rarrashinta... ★★★★★★ Roshan kuwa an same shi a wurin da yake a kwance ko motsi baya yi, ruwan sama ya gama jibgar sa ga zuciyar sa yanda yake kawo masa hari, sojojin nan haka suka ɗauke shi ba yanda yake kai tsaye hospital suka kai shi domin a halin da yake ba buƙatar kai shi gida domin bakinsa haka take fitar da jini... Hospital ɗin da su Razhdeen suke nan aka kaishi shima, a wannan daren Abbah yana ganin sojojin sa ɗauke da Roshan yasa zuciyar sa bugawa da ƙarfi, a firgice ya miƙe tsaye yana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un me yake faruwa dani ne kam? Roshan again?...." Haka likitoci suka kwantar da shi akan gado suka shiga dashi emergency room shima, domin ciwon zuciyar Roshan ba ƙaramin hatsari ne da shi ba, Sai dai kowa da ɓangaren sa, wannan yana part ɗin heart emergency shi kuma Razhdeen yana ɗakin operation domin ana duba masa ƙwaƙwalwarsa ne... Abbah gaba ɗaya ya rasa ya zai yi, ibtila'i dai gashi yana cikinsa, haka ya cigaba da zama a asibiti yana zaman jinyar twins ɗinsa... Itama Baiwar Allah a wannan ranar Aunty Yolash ce ta taya ta kwana... __________★★★★★ Bayan kwana biyu. A yau ne ranar ɗaurin Auren Roshan da Ramlat, jikin Roshan Alhamdulillah domin a yau aka sallame shi daga hospital bayan kwana biyu da yayi, Abbah ne ya sanar masa cewa "Razhdeen yana kwance har yanzu bai farfaɗo ba sakamakon hatsarin motar da yayi... Abbah ya sanar wa Roshan ne saboda yasan Roshan bai san Razhdeen ya samu hatsarin ba saboda a ranar da yayi hatsarin shima Roshan baya cikin hayyacinsa, kuma sai jiya da daddare ya farfaɗo yau kuma da safe aka sallame shi, Roshan ne ya kalli Abbah da rinannun eyes ɗinsa wanda har yanzu bai dawo normal ba tsabar kukan da yasha, jin Abbah ya sanar masa Razhdeen yayi hatsari ne yasa shi cewa "Dad I need to go home..." Abbah ya ce "Roshan na ce Razhdeen yana kwan....." Kafin Abbah ya ƙarasa maganar Roshan yayi saurin katse shi da cewa "i don't care Dad, he is not my brother, na yanke alaƙata da shi, ba ni ba shi ganin fuskar sa ma bana buƙatar gani, domin bana shiri da maciyi amana..." Cike da mamaki Abbah yake kallon Roshan ya ce "Anya Roshan baka fara shaye-shaye ba kuwa? shin kasan me kake faɗi kuwa? shi twins ɗinka ne kake...." Nan ma Roshan ya ƙara katse shi da cewa "Yes naso ace mahaifiya ta daban ta haifeni, ban taɓa jin na tsani mutum ba sai akan Razhdeen da Ammata, na tsane su, sun ci amana ta...." Abbah ya ce "ka gaya mun me yake faruwa ne?..." Girgiza kai Roshan yayi sannan ya ce "ba komai, banaso a ɗaga mun Aure na, a yau nake so..." Abbah ya ce "Roshan idan baka sanar mun abinda ke faruwa ba taya zan sani har na shiga cikin lamarin..." Roshan ya ce "ai banaso kowa ya sani saboda kar a ƙara haɗani da maciya amana, nafi son yanda na yanke alaƙata da su ta wuce har abada, bana son sasanci..." Yana kaiwa ƙarshe ya miƙe tare da nufan hanyar waje, Abbah bayansa yabi suka fita tare domin yanda yake lallamin Roshan tamkar ƙwai domin yanada rauni sosai, abu kaɗan ne zai kwantar shi akan gadon asibiti shiyasa Abbah yake son bin komai a hankali... Abbah da Roshan ne suka shiga mota wani soja yake driving ɗinsu zuwa gida domin a yau ne ranar Auren sa... Razhdeen kuwa har yau kwana biyu kenam ko motsi babu, balle asa ran zai farfaɗo kwana kusa, ga yanda aka Aske masa sumar kansa sakamakon aikin da aka masa, sai ya fito kamar ba shi ba, domin sumar gaba ɗaya aka Aske.. Ammy Amaryar Abbah ita aka bari take jinyar Razhdeen domin tamkar uwa take a wurinsu, ko ba Auratayya a tsakaninta da mahaifinsu Ammy ƙanwar mahaifiyar su ce uwa ɗaya uba ɗaya... Su Abbah suna komawa gida ya shirya tsab zai je ƙasar jidder acan za'a ɗaura Auren sai a tafo da Amarya, da su mai martaba da matan sa gaba ɗaya... Roshan kam ƙin zuwa yayi saboda baya son hayaniya, Kai tsaye part ɗinsa ya nufa saboda akwai mutane acan part ɗin Abbah kowa sai tambayar sa yake da jiki shi kuwa ba son yin magana yake ba, Yana shiga falo yaga falon wayam ba kowa, zuwa yayi zai wuce idonsa ya sauƙa akan Baiwar ALLAH dake zaune a ƙasin bayan kujera ta kifa kanta da gwiwa, tsayawa yayi tare da kawar da kansa gefe domin idan yana ganinta zuciyar sa hargutsuwa yake, murya ciki-ciki ya ce "meya zaunar dake a part ɗina?..." Ɗagowa tayi tana kallonsa daƙer ta tashi sakamakon rashin ƙwarin jikinta da kuma rashin cin komai, hatta ruwa ta kasa sha duk leɓɓerin bakinta ya bushe yayi fari tass kamar wacce tayi shekara tana jinya, zuwa tayi ta tsaya a gabansa tana ƙiran sunansa cikin sassanyar murya ta ce "D......" Roshan yayi saurin katse ta da cewa "D ya mutu, wannan Roshan ne..." Haɗiyar yawu tayi duk baki ya bushe babu yawu ko ɗis ta cigaba da cewa "dan Allah kayi haƙuri, wallahi ban san ya akayi hakan ta faru ba, inasonka Yaya Roshan, Dan ALLAH kar ka rabu da Ni..." Roshan ji yake kamar ya shaƙe mata wuya domin wani irin takaici yake ji idan yana sauraron Muryar ta, ɗaga hannu yayi yana nuna ta da yatsa tare da faɗin "ke kinada bakin da zaki bani haƙuri? meye haƙuri? yanda na tsani shaiɗan haka na tsane ki domin ke babbar shaiɗaniyar cikin gidan nan ne, bana hulɗa da maciyar amana da kuma mazinaciya, ke babbar kafura ce marar imani wacce a ranar alƙiyama zaki dawwama ne a cikin wutar jahannama, la'ananniya mazinaciya wacce Allah ya kwashe miki kaya daga gaban ma'aiki....." Wani irin mari Baiwar ALLAH ta zabga masa, ƙara ɗagowa tayi zata mare shi yayi saurin riƙe hannunta yana huci, idonsa akan ta... Kuka ta fara yi tana faɗin "Ni ba mazinaciya ba ce sannan ni ba shaiɗaniya ba ce, haka kuma ni ba kafura ba ce sannan ina tare da Manzon Allah, ina kuma neman tsari daga faɗawa wutar jahannama....." Kukan jinin da ta saba yi shi take yi yanzu domin ya rigada ya zamo shine hawayen ta.... ganin hawayen ta na jini ne yasa yayi saurin kawar da fuskar sa daga kallon da yake mata domin bazai iya juran ganin wannan kukan ba, haka yasau mata hannu sannan ya wuce ta gefenta ya nufi part ɗinsa, yana shiga ya saka sakata .... Baiwar ALLAH durƙusawa tayi tana ƙara sabinta kukan ta.... ★★★★★★ Ƙasar Jidder an ɗaura Aure cikin ƙoshin lafiya, Roshan da Ramlat R+R😍... Gaba ɗaya zasu tafo Nigeria Maamie da kuma Aunty A'isha sai Amarya Ramlat, da shi kan shi Mai martaba, shi zai zo ne saboda duba jikin Razhdeen, har da sauran gaba ɗaya, Abbah ma yana tafe da su tare da wasu ƴan uwa... Bayan sun isa Nigeria a ɗaki na musamman aka ajiye Ramlat kafin a kaita can part ɗin Roshan, dole sai ta fara zama a yankin Abbah, Ana kawo Amarya duk baƙin fuskoki suka tattafi domin an sanar cewa babu wata hidimar da za'ayi sakamakon anada marar lafiya, kowa babu sukuni a cikin zuciyar sa... Misalin ƙarfe 8 na dare kowa na gidan ya hallaru a falo, bayan tafiyar baƙi, waɗanda suke gidan yanzu sune Hajiya Kilishi da yaranta huɗu a falon Pinky da Rukky da Ummy sai Ƴar tinny, sai kuma Aunty Yolash da kuma su Maamie da Aunty A'isha matan mai martaba da shi kansa mai martaba sai Abbah da kuma Amarya Ramlat duk sun hallaru, Abbah ne yayi gyaran murya sannan ya ce " ma sha ALLAH, anyi Aure lafiya ga Amarya sai dai babu Ango da uwar gida Kuma ina son ganin su suma, Bayan haka akwai wani babban al'amarin da yake faruwa a cikin gidan nan wanda babu wanda yasan meke faruwa hatta Ni kaina, Roshan da Razhdeen a halin yanzu wani irin ƙiyayya ne yake wakana a tsakanin su, amma a yau nake son jin abinda yake faruwa, shi Razhdeen yana can kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah, dan haka yanzu nake son ganin Roshan da kuma Daughter domin abun ya shafe ta...." Ummy tana zaune tana jin Abbah domin tasan dalilin samun matsalar Roshan da kuma Razhdeen da Baiwar ALLAH.... Pinky da Rukky suma kallon juna suka yi domin sun san matsalar... Abbah ne ya kalli uwar masu gida sannan ya ce "kije part ɗin Roshan ki ce ina nemansa shi da matar sa..." Ummy amsa masa tayi tare da miƙewa tsaye ta fice... Ummy mota ta shiga security ya jata suka nufi part ɗin Roshan, tana isa ta fara knocking ƙofar falo, ganin shiru ba'ayi magana ba yasa ta tura ta shiga, kai tsaye room ɗin Roshan ta nufa, tana isa ta tarar da Baiwar Allah zaune a baƙin ƙofar ɗakin Roshan... Ummy kallo ɗaya tayi mata ta kawar da kanta gefe tayi kamar bata ganta ba domin a halin yanzu Baiwar Allah ta fita mata a rai, Ummy tinda ta tsani mahaifiyar ta akan yawon bin hotel da Auren ta to babu wanda bazata tsana ba, ganin itama Baiwar Allah tabi layin nan yasa itama yanzu ta tsane ta... Ummy buga ƙofar ɗakin Roshan take tana ambatar sunansa "Yaya Roshan Ni ce Ummy..." Daga ciki ya ce "meya faru ne?..." Ta ce "Abbah ne yake ƙiran ka ..." Ya ce "ok I'm coming..." Ummy kallon Baiwar Allah tayi wacce take ƙasi a zaune sai kuka take tayi kamar zata ce mata taje itama ana ƙiranta taji ranta a ƙone yake bazata iya ɓata bakinta wurin mata magana ba, haka ta wuce bata kulata ba, barin falon tayi taje ta shige mota aka komar da ita part ɗinsu... Roshan ne ya shirya tsab cikin baƙar jallabiya ya fito zai je ƙiran Abbah yana buɗe ƙofa kwatsam ya tarar da Baiwar Allah zaune a bakin ƙofar ɗakin sa, jin fitowar sa ne yasa tayi saurin tashi tana fuskantar sa, Haɗe rai yayi fuska ba annuri ya rufe ƙofar ɗakinsa sannan ya riƙe hannunta yana janta suka fice daga falo, suna isa wurin mota ya buɗe back seat ya wurgata ciki, sannan shima ya shiga ya ja motarsa ya nufi part ɗin su Abbah.. Suna isa ya fita tare da buɗe back seat ya sake riƙo hannunta yana fizgarta da haka suka nufi babban falon Abbah, Suna shiga ya tarar da kowa da kowa a falon ko sallama bai tsaya yi ba cikin fushi yayi wurgi da Baiwar ALLAH kan tsakiyar carpet ɗin falon. Baiwar ALLAH a yanda ta kife ko ɗagowa bata yi ba haka ta fara rera kuka kai a kife a ƙasin carpet... Abbah da mai martaba ganin haka yasa suka miƙe tsaye suna faɗin "miye haka Roshan?..." Mai martaba ya ce "matar takan zaka na wulaƙantawa haka, ai duk laifin da tayi maka bai kamata kazo mana da ita ta haka ba, wannan rashin ɗa'a ne da tarbiyya...." Abbah yana kallon Roshan cikin takaici shi ba abun ya rufe shi da duka ba ya ce "kana hauka ne Roshan?..." Roshan kallon Abbah da mai martaba yayi sannan ya ce "kuyi haƙuri dan ALLAH ku zauna..." Mai martaba zama yayi haka shima Abbah, ita kuwa Baiwar ALLAH ta kasa ɗagowa... Aunty Yolash cike da mamaki take bin al'amarin da kallo domin itama bata san me yake faruwa ba, amma tasan a yanda taga Baiwar Allah har da kukan jini tasan akwai babban matsala kawai ta ɓoye mata ne, Ummy itama kawar da kanta gefe tayi cike da takaicin Baiwar Allah, Pinky kuwa ƙunsar dariya take domin abinda take son gani kenam, Rukky kuwa sai yanzu abun yake damunta domin ba ƙaramin tausayi Baiwar Allah ta bata ba ga Uncle Deen a gadon asibiti shima ta silar haka ya samu hatsari... Roshan ne ya kalli Abbah sannan ya ce "Dad da farko ni nace ina son wannan yarinyar, yanzu kuwa nace bana sonta, sannan kamar yanda aka ɗaura igiyar Aure na da ita yanzu ina so a since wannan igiyar domin daga yau na kawo ƙarshen alaƙata da ita...." Cike da mamaki Aunty Yolash da Hajiya Kilishi suke kallon lamarin abun ba ƙaramin kulle musu kai yayi ba, Aunty A'isha da Maamie kuwa sun kasa fahimtar komai sai dai ido, gwara ita Maamie ta shiga yanayin farin ciki jin Roshan yana faɗin zai saki Baiwar ALLAH, yanzu Ramlat ita kaɗai zata zauna ba kishiya.... Itama Ramlat abun ya ɗaure mata kai matuƙa ... Mai martaba ya ce "Roshan zauna..." Roshan ya zauna rai a ɓace, sannan mai martaba ya kuma cewa "shin meye dalilin ka na aikata haka?..." Roshan ya ce "kawai bazan iya rayuwa da ita ba ..." Abbah tsawa ya daka masa tare da faɗin "your very stupid Roshan, meye amfanin mu idan bazaka iya sanar mana damuwar ka ba? shin su waye suka ɗaura maka Aure? mune sannan idan matsala ka samu da matar ka a mu zaka kawo ƙara, mu kuma sai mu dubi abinda ya dace ayi...." Roshan idonsa ne ya cicciko da ƙwallah idonsa akan Baiwar ALLAH wacce take kife a tsakiyar falo har yanzu ta kasa ɗagowa, girgiza kai yayi sannan ya ce "kawai na gaji da zama da ita ne shiyasa nake buƙatar rabuwa da ita...." Mai martaba ya ce "Roshan shin sasanci kazo ayi ne ko kuma rabuwar Aure? bai kamata ace kayi saurin yin saki ba, gwara idan laifi tayi a ja mata kunne sosai in yaso kuje ku cigaba da zaman Auren ku..." Dasauri Roshan ya ce "Rabuwar Aure nake so ayi...." Abbah ya ce "idan baka sanar mana dalili ba wallahi bazaka sake ta ba ..." Roshan ya Ciro takardar saki a cikin aljihun jallabiyarsa ya miƙa wa Abbah yana faɗin "Abbah kayi haƙuri ga takardar sakin ta nan...." Abbah idonsa akan Roshan ya ce "taurin kai zaka mun ko Roshan?..." Roshan tashi yayi ya miƙe tare da nufan yanda Abbah yake ya miƙa masa takardar yana cewa "Gashi Abbah na sake ta saki uku..." Tsabar ɓacin rai Abbah ya ɗauke shi da mari har sai da ya faɗi ƙasin carpet ya ɗago yana kame da fuska... Ramlat hawaye ta fara zubarwa ganin yanda aka mari Roshan tamkar ita aka mara domin taji zafin haka sosai a ranta... Ummy ganin tana kallo bazata bari a cutar mata da ɗan uwa ba akan gaskiyar sa yasa ta miƙe tsaye tare da ambatar sunan Abbah... Abbah juyowa yayi yana kallonta ya ce "ke kuma fa, ko rama masa zakiyi?..." Tana kuka ta ce "Abbah inason yin magana da kai..." Abbah ya ce "su waye baƙin ki anan? duk iyayenki ne don haka ki faɗi abinda zaki ce ...." Roshan ɗagowa yayi yana girgiza mata kai alamar kar ta gaya, amma Ummy sam ta nuna bata gànshi ba ma, Ta ce "Abbah meyasa ita ɗin bazaku tambaye ta akan laifin da tayi ba?..." Abbah ya ce "bana son iskanci ki fa ɗi meye zaki ce?..." Ummy ta ce "dalilin da yasa Yaya Roshan zai rabu da Matar sa shine ya kamata a ɗaki ita da Uncle Deen suna aikata alfasha...." Abbah wani irin dimmmm yaji, kansa ne ya fara juyawa, kamar a mafarki yake jin wannan batun... Mai martaba shima cikin firgici ya ce "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..." Aunty Yolash zaro ido waje tayi tana jinjina batun.. Haka itama Hajiya Kilishi abun yayi matuƙar ɗaure mata kai.. Pinky da Rukky kallon juna suka yi, Aunty A'isha ba abinda take furta wa a cikin ranta illah "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..." Ramlat itama zuciyar ta ne yake bugu domin tayi matuƙar mamakin jin wannan batun, bata yi tunanin Baiwar ALLAH zata iya aikata zina ba kuma da Auren ta... Roshan dafe goshinsa yayi yana kallon ƙasi domin har cikin ransa bai so Ummy ta faɗi wannan kalmar a cikin mutane ba... Abbah kamar ba jini a jikinsa ya maida idonsa kan Baiwar Allah har zuwa yanzu bata ɗago ba.. A hankali ya furta sunan Baiwar Allah da cewa "Daughter..." Baiwar Allah kasa ɗagowa tayi saboda tana fargaban haɗa ido da mutanen falon, Abbah ya sake ƙiran sunan ta yana faɗin "ki ɗago maza ki kalle ni, shin abinda aka fa ɗa gaskiya ne ?..." shiru Baiwar Allah bata ɗago ba balle ta bada amsa, Abbah ne ya ƙara cewa "ɗago mana Daughter nah..." Baiwar ALLAH a hankali take motsi tana shirin ɗagowa jiki duk ya mutu, ga wani irin yunwan da ya kama jikinta sosai, da ƙer ta ɗago tana kukan jini, durƙusawa tayi a gaban Abbah tana fuskantar sa fuska a jiƙe da jini..." Abbah gaban sa ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin yanda Baiwar Allah take kukan jini, duk kallonta suke shima Mai martaba ya ce "kukan jini kuma?..." Aunty Yolash bata san lokacin da kuka ya yanko mata ba domin tana matuƙar jin tausayin Baiwar Allah especially kukan jini da taga tana yi... Abbah ya sauƙa daga kan kujera ya zauna a ƙasin carpet ya riƙo hannunta tare da furta "Daughter! Daughter!! Daughter kukan jini kuma? kina tare da cuta amma ban sani ba? tayaya hakan zata faru?..." Baiwar Allah tana kuka ta ce "Abbah na aikata laifi babba, nasan hukuncin aikata zina a matar Aure jifa ne da duwatsu, dan Allah Abbah inason mutuwa, inason barin duniyan nan..." Abbah shima hawaye ne suka fara gangaro masa tare da girgiza kai yana faɗin "Daughter nasan da hankalin ki bazaki taɓa aikata hakan ba, ni ban yadda da wannan ba dole sai nayi bincike akai, saboda haka ki share hawayen nan sannan zamu je hospital a duba lafiyar ki domin ke amana ce a gare ni, bayan zuwan ki gidan nan naje har gidan marayu na rubuta takarda tareda yin signing cewa na ɗauke ki a mazannin ɗiyata, na gaza samun iyayen ki saboda ke ƴar Amana ta ce, kuma na karanci duk wani ɗabi'un ki da halayenki nasan abunda zakiyi da kuma abinda baza kiyi ba, dole sai nayi bincike akai kafin na yadda....." Abbah ya kalli Roshan ya ce "Aure da zargi haramun ne don haka bani takardar ta..." Ummy ta ce "Abbah ba zargi bane da idonsa ya kama su..." Abbah ya darara mata tsawa da cewa "kiyi mun shuru nace..." Abbah yana karɓan takardar ya buɗe yana faɗin "ba saki uku ba shikenam..." Abbah ya karanta sakin da yayi mata saki biyu ne... Ya kalli Roshan ya ce "kace saki uku?..." Roshan ya ce "saki biyu nayi mata daga baya zan ƙaro ɗayan..." Abbah har zai rufe takardar ya ga wani rubutu a ƙasin sakin, An rubuta : "Ni Roshan matar da nake tare da ita wato Baiwar Allah ɗiyar Chief Of Defence Staff ce (C.D.S) Chief Suraj Mohandra Marka, wato shugaban sojojin ƙasar Austaraliya na yanzu, yarinyar da akayi wa alƙawarinta a Razhdeen tin kafin ta ɓata mai suna Amreesh........ Abbah cike da mamaki ya furta "whattttt!!!!" Abbah ɗagowa yayi yana bin kowa da kallo ya kasa faɗin komai... Aunty Yolash ce ta taso ta karɓi takardar a bayyanai take karantawa yanda kowa zai ji, yanda saƙon yake a rubuce haka ta karanta.... Baiwar ALLAH zaro manya-manyan idanuwanta tayi waje tare da juyowa da sauri tana kallon Aunty Yolash......... Typing ✍️ *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 21 to 25 Abbah da sauri ya juya yana kallon Baiwar ALLAH wacce idonta ke kan Aunty Yolash, cike da mamaki da kuma rashin fahimta take binta da kallo tana son sanin abinda take nufi, Abbah a hankali ya furta "ɗiyar Chief Suraj Mahendra marka?..." Duk kowa a cikin falon shuru yayi kowa yana jinjina batun, da kuma jiran matakin da Abbah zai ɗau, Pinky kam a cikin ranta cewa take "shikenam in ba'a kore ta don fasiƙancin da suka aikata ba, ai za'a kore ta ko dan ƙiyayyar dake tsakanin Abbah da mahaifinta..." Aunty Yolash haka zuciyarta yake bugu tsoronta kar Abbah ya kore ta, Mai martaba shima babu abin cewa kowa jiran Abbah yake akan batun, Abbah kallon mutanen falon yake ɗaya bayan ɗaya yana jinjina kansa, abinda ya fito daga bakinsa shine "Ikon ALLAH kenam! kana naka Allah na nashi, tsawon shekaru ina gava da mahaifinta, na kuma tsani haɗa zuriya da shi, a karo na farko ɗiyata Allah ya ɗora mata son ɗan su, har takai yanzu suna can zaman Aure, a karo na biyu kuma Allah ya ɗora mun son ɗiyar su wanda har na ɗauke ta a mazannin ɗiyata ta ciki na, har takai na Aura wa ɗa na ita a rashin sani, gashi dai kuma bana ƙaunar ahalin, amma sakamakon yanda nake jin Daughter a raina bazan iya tozarta ta ba saboda ita abar tausayi ce, tin tana ƙaramar ta take cikin ƙuncin rashin iyaye, duk gatan da ƴaƴa suke samu daga wurin iyayensu ita sam bata samu wannan gatan ba, ƙiyayyata sai dai na nuna a iya mahaifinta a halin yanzu amma ita na cire ta a layi...." Abbah ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "Daughter an samu iyayen ki, Roshan shine ya bayyana ki a yanzu don haka ki kwantar da hankalin ki...." Baiwar ALLAH kamar a mafarki take jin wannan batun, gaba ɗaya kanta ya kulle, nan ta fara kuka, ta rasa gane shin kukan farin ciki take ne ko kuma na baƙi ciki tunda duk tana cikin yanayin su, ga baƙin cikin halin da ta tsinci kanta sai kuma halin farin ciki da ta tsinci kanta a yanzu, leɓɓenta ne yake motsi tare da kakkarwa tana son yin magana amma ta kasa, kallon Roshan tayi tana kuka, shima ita yake gani sai kuma ta bashi tausayi, Daƙer ta iya buɗan baki ta ce "Iyaye na? suna nan da ransu daman? daman basu mutu ba?...." Lokaci guda ta ƙara fashewa da matsanancin kuka... Abbah rarrashinta yake tare da faɗin "kiyi haƙuri Daughter Insha Allahu zan sanar wa iyayen ki cewa kina hannuna, tinda a baya muna da kyakkyawan alaƙa..." Baiwar ALLAH girgiza kai ta soma yi tana kuka ta ce "dan ALLAH Abbah inaso ku mun wata alfarma dan Allah, ban taɓa neman alfarma a wurinka ba sai yau..." Abbah ya ce "ina jinki Daughter ko meye kike so zaki samu Insha Allahu..." Baiwar ALLAH ta ce "kayi alƙawarin haka Abbah?..." Abbah ya ce "nayi miki alƙawari..." Baiwar ALLAH ƙara fashewa da kuka tayi tana faɗin "bana so a sanar wa iyaye na cewa an same ni, inason ganin su amma banaso su san cewa ni ɗiyarsu ce..." Abbah ya ce "miye dalilin yin haka Daughter?..." Ta ce "a halin yanzu idan suka ganni maimakon suyi farin ciki sai dai su ji ƙunci sakamakon halin da na shiga, idan suka ji na aikata zina shin da wani ido zan kalle su, bana so ranar farko dana ga iyayena su fara jin takaici na, Dan ALLAH Abbah kada ku sanar musu..." Abbah ya ce "Nima kaina ina so ko zaku gana da juna ya zamana su ganki cikin ƙoshin lafiya, amma a halin yanzu banaso iyayenki su ganki a haka kina kukan jini, sannan kina cikin damuwa sosai, yanzu inaso ki kwantar da hankalinki ki daina shiga damuwa, idan hankalinki ya kwanta kika samu nutsuwa zan gayyato iyayenki da su zo ku gana da juna, ni kuwa nayi miki alƙawarin babu wanda zai sanar musu cewa kin aikata wani abun ɓatanci in ma da gaske ne domin sai nayi bincike tukun...." Mai martaba murmushin farin ciki yayi sakamakon yanzu Abbah ya fara sauƙo wa... Ummy ce ta tashi tare da barin falon ta haura saman room ɗinta, ba jumawa ta sauƙo hannunta riƙe da M.P da memory a ciki, tana zuwa ta miƙa wa Abbah... Abbah ya kalle ta sannan ya ce "wannan fa?..." Ummy ta ce "Uncle Deen ne ya bani ya ce idan ka dawo na baka, amma ni kaina ban san meye ba..." Abbah karɓa yayi tare da kunna wa daman iya recording ne a ciki na maganganun mahaifin su Baiwar ALLAH, kowa nutsuwa yayi ana sauraron recording ɗin.... Sai da suka saurara gaba ɗaya, Abbah ba ƙaramin regretting yayi ba, duk jiki sa yabi yayi sanyi kamar ba rai a jikinsa, ga idanuwansa yanda suka yi jawur, domin a labarin gaba ɗaya duk babu laifin Chief Suraj Mahendra, Abbah abinda yake furtawa shine "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, ya ALLAH, rashin sani yafi dare duhu...." Mai martaba ya ce "daman ai zaman gava bashi da daɗi musamman a wurin ka da kake ɗan musulmi jikan musulmai bai kamata ba, gashi dai shi Christal ne amma bai ɗauki rayuwa da zafi ba domin wata rana in mu ne wata rana bamu bane, mu rinƙa tuna kwanciyar kabari, shi rayuwan nan ba komai bane illa ruɗanin dake cikinta, a gaskiya shawarar da zan baka yanzu shine kaje ka samu Chief Suraj ka nemi gafarsa, domin yayi maka halacci a duniyan nan wanda da wuya ka samu masu irin halinsa na kirki, gashi dai duk ƙiyayyar da kake nuna masa bai hana Allah Ubangiji ya ɗora maka ƙaddarar zama da jinsin su ba, ɗiyarka ta bi ɗansu wannan ma jarabawa ce, sannan jininka ya haɗu dana ɗiyarsu har alaƙar Auratayya ta shiga tsakani nan ma jarabawa ne Allah ya ɗora maka, yanda ta faru tsakanin Fir'auna da Annabi Musa kenam, ya ɗora ƙiyayyarsa akan yara maza yasa duk macen da ta haifi namiji a kashe jaririn amma da aka haifi Annabi musa sai Allah ya ɗora masa son Annabi Musa a ransa yana jaririn, to kuwa kaga babu wanda yafi ƙarfin Allah ya jarrabe shi da jarabawar rayuwa...." Abbah ya jinjina kai sannan ya ce "Insha Allahu gobe zan je har ƙasar U.S na je na same shi na bashi haƙuri a bisa hukuncin da na ɗau a rashin sani, Ni ina ƙin nashi amma shi yana jan nawa a jikinsa Allah sarki...." Aunty Yolash ce ta yi magana itama tana faɗin "Yaya to akan maganar auratayyar tasun kuma fa? shi Roshan yace bazai iya zama da ita ba, kenam haka za'a barta cikin damuwa?..." Abbah ya ce "taya zan barta cikin damuwa?..." Ya kalli Roshan sannan ya ce "Kai kace ka rabu da ita ko?...." Roshan kawar da kansa gefe yayi yana hasasho yanda ya tarar da su kwance akan gado zigidir babu kaya a jikinsu, da sauri ya fara girgiza kai tare da faɗin "Ehh...." Abbah ya ce "to shikenam..." Ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "to kinji Daughter amma shin kina son Razhdeen?...." Dasauri Baiwar ALLAH ta ɗago tana kallon Abbah tare da girgiza kai tana hawaye ta ce "ko da maza sun ƙare a doron ƙasa bazan taɓa Auren Razhdeen ba, domin shi ya jefani a cikin wannan matsalar, bana son sa wallahi...." nan ta ƙara fashewa da kuka, Abbah ya ce "it's okay, insha Allahu baza ayi miki dole akan abinda bakyaso ba shiyasa na tambaye ki, amma tinda bakya so shikenam, amma yanzu meye a ranki?..." Baiwar ALLAH tana sharar hawaye ta ce "shawara ɗaya na yanke shine zan rabu da kowa a cikin su, kawai inason barin gidan nan..." Abbah ya ce "ina zaki je Daughter bayan kin ce bakya son haɗuwa da iyayenki yanzu?..." Baiwar ALLAH shiru tayi ta cigaba da kukan ta na jini... Abbah cewa yayi "shikenam zan duba lamarin kar ki damu, yanzu dai akai Amarya ɗakin mijinta sannan kowa ya je ya nemi wurin makwancinsa dare yayi...." Sannan Abbah ya kalli Baiwar Allah ya ce "uwar masu gida kizo ki kai Daughter ɗakinta anan part ɗin...." Ummy bata yi ƙasa a gwiwa ba ta tashi ta nufi Baiwar Allah sannan ta ce "tashi muje..." Baiwar ALLAH tashi tayi suka shiga room ɗin da take kafin tayi Aure, Ummy tana shigar da ita ta juyo ba tare da ta furta komai ba, domin a halin yanzu bata son yi mata magana.... Baiwar ALLAH saman gado ta haura ta fara sharara kuka ba ƙaƙƙautawa gaba ɗaya yanzu bata ma ɗaukin ganin iyayenta saboda matsalar da ta shiga.... Su Hajiya Kilishi da Aunty Yolash da Maamie da Aunty A'isha da su Pinky duk raka Amarya su kayi part ɗin Roshan... Shima Roshan ɗin nufan part ɗinsa yayi shima, Abbah da mai martaba su kuma fita sukayi suka nufi hospital ganin Razhdeen.... A wannan daren Baiwar ALLAH kwana tayi bata rintsa ba, daman yau waran kwana uku zuwa huɗu kenan bata samun yin bacci ba... Misalin ƙarfe 12 na dare Amarya tana zaune akan gado dake room ɗin Roshan, shi kuwa yana falo a zaune kan kujera, damuwa ce ƙarara akan fuskarsa rabuwa da yayi da Ammata tamkar ya rasa wani ɓangare ne na jikinsa domin ba ƙaramin sonta yake ba, amma zuciyarsa tana bashi cewa dole zai rabu da ita saboda budurcinta ɗan uwansa ya riga shi karɓansa a mazannin ta na matarsa, bazai iya zama da ita domin zaman ƙunci zasu shiga daga ita har shi ɗin, gwara kawai ya sallamar da ita ba dan zuciyarsa na so ba... Haka shi kaɗai yake ta tunanin Baiwar Allah da kuma baƙin cikin da yake fama da shi a cikin zuciyarsa, shi kan sa Razhdeen ba ƙaramin tsanar sa Roshan yayi ba, baya ƙaunar ya sake buɗe ido ya gànshi... yana cikin wannan tunanin ya tuno ashe dai an kawo masa mata, ya barta ita kaɗai acan.. Tashi yayi yana jan ƙafa ya nufi room ɗinsa, da sallama a bakinsa ya shiga, amsa masa tayi cikin so da ƙauna, ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba jin shugowar sa domin har ta saddaƙar cewa bazai shigo ba... Zama yayi a bakin gado yana kallon gefe guda sai yake tariyo Baiwar ALLAH lokacin da take Amarya itama kamar haka aka kawo ta fuska a rufe, lokaci guda ya ƙanƙame idonsa zuciyarsa na tafarfasa.... A hankali ya kalli yanda Ramlat take sannan ya ce "ki tashi kije kiyo alwala..." jiki a sanyaye ta tashi ta nufi bathroom ta ɗauro alwala sannan ta fito, tana fitowa ya ce mata "jira Ni..." Shima ya shiga ba jumawa ya fito tareda alwalarsa yazo ya samu ta shimfiɗa musu sallaya, tsaida sallah suka yi sukayi raka'a biyu sannan ya tottofa mata Addu'o'i tare da tambayar akan abinda ta sani game da addinin ta cikin sa'a duk ta bashi amsa, yayi farin ciki sosai ganin cewa ba jahila ya Auro ba, haka ya tashi yaje ya ɗauko ledar gashashshen naman kaza da lemuka kala-kala sannan ya zo ya baje musu shi, cikin jin kunya Ramlat take ɗan tura a bakin ta dan ma yana lallaminta akan ta ci... Bayan sun kammala duk brush suka yo sannan yaje ya ɗauko mata kayan bacci a cikin akwatunan Auran ta har sai da ya tallafa mata wurin cire kayan amarcin ta sannan ya sanya mata sleeping dressing duk da a cikin damuwa yake amma hakan bai hana shi bata kulawa ba, shima kayan bacci ya zura sannan ya jata suka nufi gado, (Ganin an kashe hasken ɗakin ne yasa nabar musu ɗakin, amma naji alamun motsi-motsi a cikin mayafin fa 😂). ★★★★★★★ Washe gari Abbah da mai martaba su biyu suka tafi ƙasar U.S, Chief ya yi matuƙa mamakin ganin Abbah, cikin farin ciki ya ƙarfe su hannu bibbiyu, anan Abbah ya sanar masa yanda akayi yaji duk maganganunsa sannan ya sanar masa cewa yazo neman yafiyar sa ne akan abinda yayi masa... Chief ya nuna masa ba komai, komai ya wuce sannan ya ce "yayi mamaki da Razhdeen ya yi recording amma yayi farin ciki tunda ko ba komai yayi sanadin shiryawar su... Su Abbah sun gama fahimtar juna komai ya zo ƙarshe na ƙiyayyar su kuma daman Abbah ne ya ɗau abun da zafi, Har suka dawo basu sanar musu cewa ɗiyarsu Amreesh tana hannunsu ba, shi Abbah baya son iyayen ta su tarar da ita a cikin wannan hali na cutar da take fama da shi na kukan jini, so yake sai ta warke ta dawo cikin hayyacinta tukun.... Bayan sati guda da dawowar su Abbah daga ƙasar U.S suma su Chief Suraj da matar sa Madam Parveen da Rakesh ne suka zo Nigeria duba jikin Razhdeen, Madam Parveen har da kukan ta domin jikin Razhdeen ba sauƙi tinda har zuwa yanzu bai farfaɗo ba, Abbah ya nuna wa Baiwar ALLAH iyayenta amma su ba'a sanar musu ba har yanzu, Baiwar ALLAH kawai jure wa tayi amma taso taje yanda suke, kuma taga Madam Parveen ta gane ta, tayi mamaki sosai da taga itace mahaifiyar ta, da haka har suka koma ƙasar U.S... Baiwar ALLAH tasha kuka sosai ganin sun tafi, amma ta wani ɓangare tayi farin cikin ganin iyayen ta.... ★★★ Bayan wata uku da Auren Roshan, har ila yau bai je ya dubo Razhdeen akan gadon asibiti ba itama Baiwar ALLAH anyi da ita akan taje ta gano Razhdeen fur taƙi domin bata ƙaunar ganin fuskar sa, Ita kuwa likita ya duba ta ya sanar cewa Depression ne, tsananin damuwa ne yasa har take kukan jini ga rashin bacci da cin abinci da kuma samun sukuni.... Fito wa falo tayi ta tarar babu kowa, dake ba fito wa cikin mutane take ba, Hajiya Kilishi tana ɓangaren ta, ita kuwa Ammy da Aunty Yolash su suke jinyar Razhdeen a asibiti, Maamie da Aunty A'isha suma part ɗinsu daban a cikin gidan Abbah, acan Maamie take tsula tsiyar ta, dake Aunty A'isha ta rigada ta saba da halin ta haka suke zaune kafin lokaci komawar su ƙasar Jidder. Har tsawon watannin nan basu koma ba, domin Mai martaba bazai iya koma wa yana ganin Razhdeen ko farfaɗo wa bai yi ba sakamakon dogon suma da ya yi.... Baiwar ALLAH Ummy kawai ta tarar ta fito a kitchen, har zata haura room ɗinta da plate ɗin abinci a hannunta Baiwar ALLAH tayi saurin tsayar da ita tana faɗin "Amm Ummy dan Allah..." Ummy juyo wa tayi tana kallon ta ba tare da ta ce komai ba, jin Baiwar Allah tayi shiru ne yasa ta cewa "inada abun yi fa domin yunwa nake ji..." Baiwar ALLAH wacce gaba ɗaya ƙashin wuya yayi mata sarƙa duk idanuwanta sun faffaɗa, fuskar nan tayi fiyau ga wani irin fari da tayi kamar ba jini a jikin ta, ta ce "daman akwatin kayana nake so ki ɗan ɗauko mun a can part ɗin Yaya Roshan..." Ummy ta ce "ƙafar ki jinin haila take da bazaki je da kan ki ba? ...." Baiwar ALLAH ta ce "shikenam je ki kawai..." Ita kuwa Ummy wucewar ta tayi, a yayin da ita Baiwar Allah ta nufi hanyar waje, tana fita ganin part ɗin Roshan da ɗan nisa kaɗan yasa ta cewa a security ya kaita da mota, shiga tayi ya kaita har bakin gate ɗin Roshan sannan ta sauƙa ta fara knocking a hankali... Shi kuwa Roshan da Ramlat suna filin gidan a jikin mota, Roshan ya fito zai fita ita kuma ta rako shi, tana rungume da shi a jikin mota a tsaye suna shan love ɗin su kwatsam suka fara jin knocking, Basu yi tunanin Baiwar ALLAH bace domin shi Roshan rabon da yayi ido huɗu da ita tin ranar Auren sa da daddare, haka itama Ramlat, Ramlat tana rungume da shi hannunta riƙe da fuskar sa kamar wacce zata yi masa kiss, ta kalli bakin gate ta ce "waye turo gate ɗin a buɗe yake...." still suna rungume da juna, Baiwar ALLAH ce ta turo da sallama a bakinta, ganinsu yasa ta dakata tana kallon su, zuciyar ta kuwa haka yake bugun uku-uku, Roshan ido ya haɗa da Baiwar ALLAH ji yayi gabansa ya yanke shima haka yake jin bugun zuciyar nan idonsa akan ta, Ramlat fuska ɗauke da murmushi ta ce "shigo mana, yau kece a part ɗin nan...?" wani irin yawu Baiwar ALLAH ta haɗiya tana jan ƙafa daƙer ta shugo, ba tare da ta isa yanda suke ba ta tsaya, Roshan kawar da kansa yayi gefe, sai lokacin Ramlat ta rabe jikinta da na shi tana faɗin "nima na rako mijina zai fita ne, yanzu nake shirin zuwa can part ɗinku, mu ƙarasa ciki koh...." Roshan yayi saurin katse Ramlat da cewa "ki tambaye ta me tazo yi tukun..." Ramlat kallon Roshan tayi ta ce "ta zo ziyara mana..." Baiwar ALLAH ta ce "nazo ɗaukan kayana..." Ramlat ta ce "oh daman kina da kaya ne? okay ki je ki ɗauko a room ɗin da kika zauna, kinsan ni tinda nazo ban shiga ba..." Baiwar ALLAH gaba tayi zata shige falo Roshan ya ce "bana son ƙara ganin ƙafar ta a cikin room ɗina, ke kije ki ɗauko mata..." Ramlat ta ce "toh shikenam Rabin Rainah an gama..." murmushi ya sau mata ita kuwa ta shige... Baiwar ALLAH kuwa idonta akan Roshan, shima idonsa yakai kanta tare da jefa mata wani irin kallo na harara, ganin bazata iya fita ba tare da tayi masa magana ba yasa ta nufi yanda yake a tsaye yana jiran fitowar Ramlat kafin ya fita, Ganin ta tsaya masa a gaba yasa shima ya ƙura mata ido, tasau murmushi sannan ta ce "Yaya Roshan na taya ka murnar ƙara Aure, amma ina so ka sani cewa nasan har yanzu akwai soyayya ta a cikin zuciyar ka, haka nima, soyayya takan koma wa ƙiyayya amma ita ƙauna har abada tana nan a matsayinta, to ƙaunar juna muke, duk abinda zaka yi nasan sai dai kayi don ka ɓata mun amma ba har cikin zuciyar ka ba......" Kafin ta ƙarasa maganar ya katse ta da cewa "ki daina wannan shirmen domin yanzu babu ke a cikin zuciyata, wacce ta fiki muhimmanci ta mamaye wurin, don haka bazaki samu shiga ba..." Baiwar ALLAH buɗan baki tayi zata yi magana ya katse ta tare da darara mata tsawa yana faɗin "na tsane ki, dan Allah ki fita daga cikin rayuwa ta, kije ki kama wanda ya fini muhimmanci a wurinki, wanda zai baki kulawar da bazan iya baki ba, wanda kika mallaka masa kan ki da Auren ki saboda tsananin ƙaunarsa da kike...." Bai ankara ba yaji ta ci kwalar rigar sa tare da jawo shi jikinta ta riƙo kanta da hannu ɗaya tare da haɗe musu baki wuri ɗaya, Dai dai lokacin da Ramlat ta fito ganin su yasa tasau akwatin hannunta ƙasi tare da zaro ido waje, Roshan yana jin sauƙar akwati ƙasin floor a ruɗe zai ɗago Baiwar ALLAH ta ƙara ƙanƙame shi bakinta a cikin nasa, itama tasan Ramlat ce ta fito hakan yasa ta ƙara shige wa jikinsa, sai da ta gama sumbatar sa kusan minti guda tukun ta sake shi, tana ja da baya idonta akan sa shima haka yake binta da kallo ko ƙibtawa baya yi, Baiwar ALLAH cikin barikanci ta ƙibta masa ido ɗaya sannan ta juya baya jin alamun ta iso dab da Ramlat, idonta akan Ramlat da murmushi akan furkarta ta ce "au har kin ɗauko akwatin? sannu fah..." ta durƙusa ta ɗauki akwatin a ƙasi ta ɗago tana zaro harshe tare da ɗage harshen saman lips ɗinta ta juya ta nufi bakin gate, tana fita ta shiga mota security da ya kawo ta ne ya juya da ita part ɗin Abbah... Ramlat idonta ta sauƙar kan Roshan idonta duk ya cicciko da hawaye ta juya da gudu cikin falo tana rera kuka, Gaba ɗaya jikin Roshan ne yayi sanyi ganin Ramlat ta juya tana kuka yasa shima ya bita ciki yana ƙiran sunanta..... Baiwar ALLAH tana isa part ɗin Abbah ta tarar da wasu manya-manyan motoci na alhurma a jere alamun anyi manya-manyan baƙi ne, dake kuma gidan basa rabuwa da baƙi masu zuwa duba jikin Razhdeen, har daga ƙasar waje ake zuwa, yanzun ma tasan masu zuwa duba Razhdeen ne... Haka ta shige falo jikinta na ɗar ɗar domin a rayuwar ta tana tsoron baƙi, daman can ba son zaman cikin mutane take yi ba, tana shiga ta tarar da wani babban mutum asalin mai kuɗi yana zaune a 3 seater, sai kuma a gefensa wata hamshaƙiyar mata ce fara tas alamar matarsa ce, a ɗayan kujerar kuma wani zankaɗeɗen saurayi ne zaune sai sakin murmushi yake, kallo ɗaya Baiwar ALLAH tayi mishi idonta ya sauƙa akan sarƙar wuyansa, ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin irin sarƙarta ne banbancin colour ne kawai, a ciki ranta tayi farin cikin ganin su saboda su ne wanda Abbah ya nuna mata cewa iyayenta ne, Ƙara kallon Madam Parveen tayi bata san lokacin da ta saki murmushi ba... Abbah ne ya ce "Daughter ƙaraso mana ya na ganki da akwati?..." Baiwar ALLAH shugowa tayi tana binsu da kallo hannunta ɗauke da akwati, murya na kakkarwa ta ce " zan kai kayana ciki..." Abbah ya ce "to je ki dawo yanzu..." Baiwar ALLAH gudu-gudu sauri-sauri ta shige room ɗinta domin tana muradin ganin iyayenta... Abbah ne ya ciro wayar sa ya ƙira wayar Roshan, bugu ɗaya aka ɗauka Abbah ya sanar masa cewa yazo yanzu anyi baƙi, Roshan ya amsa masa sannan suka katse wayar... Kowa ya hallaru a falon har da mai martaba da matansa da kuma Abbah shima da matansa domin Ammy ta dawo itama sai Aunty Yolash da yaran gidan, shima Roshan ba jumawa ya shigo da matar Ramlat wacce tasha kuka, itama Baiwar ALLAH fito wa tayi tana sanye da dogon hijab har ƙasi, Razhdeen ne kawai baya nan yana can kwance a gadon asibiti sai sojojin da suke gadin sa... Abbah ya kalli mutanen falon sannan ya fara magana kamar haka "a yau ne ranar farin ciki na da Allah ya kawo mun babban aminina wanda muka ɗau tsawon shekaru muna zaman gava sai a wannan lokacin Allah ya bayyano mana haske cikin lamuran mu, Allah na gode maka, a cikin ƴaƴana akwai waɗanda basu san Chief Suraj Mahendra Marka ba to wannan shine, mahaifin Mohandas da ya Auri ɗiyata Amina...." Abbah ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "Daughter kiyi haƙuri yau zan bayyana wa iyayenki ke ...." Baiwar ALLAH hawaye ne ya fara cicciko wa daga cikin ƙwayar idanuwanta, domin ta tabbata abinda mutanen gidan marayu suke faɗa gaskiya ne, na cewa iyayen ta Christal ne tunda take ɗaure da sarƙa irin nasu.... Madam Parveen haka jikinta ya ɗau rawa tana bubbugan cinyan mijinta tare da faɗin "Please me suke nufi ne?..." Chief ya riƙe hannun madam Parveen yana faɗin "wait ki kwantar da hankalin ki, nima kaina ban gane mai suke nufi ba..." Abbah buɗan baki yayi zai yi magana sai suka ji bugun ƙofa, Abbah ya ce "come in..." Duk bakin ƙofa suke kallo suna son ganin waye domin a cikin gidan nan babu wanda ya rage duk an taru a falo sai Razhdeen da baya nan, sannan duk wanda zai shigo gidan sai Soja ya ƙira waya ya sanar, A wannan lokacin kuma ba'a yi hakan ba... Ganin Minal ta shigo yasa duk mutanen falon suka mimmiƙe tsaye, gani suka yi shima Mohandas ya shigo yana ɗauke da yaro a hannunsa mai kimanin shekara ɗaya da rabi... Madam Parveen jiki na rawa ta buɗe baki tana faɗin "M m m Mohandas my son...." ta nufi wurin su da gudu ta rungume shi tana dariya haɗe da kukan farin cikin ganinsu. Hajiya Kilishi itama cike da farin ciki ta nufo su da sauri ta rungumi Minal sosai a jikin ta tana faɗin "Minal, Minal kin dawo gare ni Allah na gode maka...." Abbah kasa magana yayi ya koma ya zauna, shima Chief ɗin zama yayi idonsa akan su, Mai martaba ne ya ce "ku shigo mana..." Pinky da Rukky da Ummy da Ƴar tinny haka suka je duk suka rungumi Minal suna farin cikin ganinta, tare duk suka ƙaraso cikin falo, aka basu wurin zama, Minal bata zauna ba haka taje gaban Abbah ta durƙusa a gabansa tana kuka ta ce "Abbah dan ALLAH kayi haƙuri ka gafarce ni, nasan banyi maka adalci ba amma naga hakan shine mafita a gare ni, ina matuƙar ƙaunar Marshall Mohandas, mun yanke shawarar guduwa domin munga baku da niyar kawo ƙarshen ƙiyayyar ku, yanzu kuma mun san komai ya dawo dai-dai hakan yasa muka dawo gare ku..." Abbah ya ce "aina ku ka san da wannan maganar?..." Minal tana kuka ta nuna Roshan da yatsa ta ce "shine ya sanar mana cewa mu dawo gida..." Abbah idonsa yakai kan Roshan, Roshan kuwa ganin sun haɗa ido da Abbah yasa yayi saurin kawar da kansa gefe yana sosa ƙeyar sa.... Abbah ya ce "daman kasan a yanda suke shine baka sanar mun ba? ...." Roshan ya ce "kayi haƙuri Abbah hakan shine zaman lafiyan kowa..." Jinjina kai Abbah yayi tare da kallon yanda Minal take sannan ya ce "shikenam komai ya wuce, ki tashi kije ki zauna..." Minal share hawayen ta tayi ta tashi taje ta zauna, shima Mohandas neman yafiyar iyayensa yayi sannan ya sanar musu cewa "ya musulunta ba tare da sanin su..." Shima iyayensa sun lamunce masa, Rakesh tashi yayi ya rungumi Yayansa yana farin cikin bayyanowar sa... A wannan ranar kowa ya kasance cikin farin cikin cikar ahali, Ummy ganin yaro kyakkyawa yasa ta karɓe shi take rungume da shi, ta tashi ta miƙa shi a Abbah, Abbah ne ya karɓi yaron yana masa wasa dake yaron yayi wayo sosai domin har an yaye shi, Abbah ya ce "meye sunansa?..." Mohandas ya ce "Muhammad Afif...." Abbah ya yi murnan jin sunan... Chief ma miƙa masa yaron akayi kowa sai da yaron ya shiga hannun kowa na falo... Baiwar ALLAH kam duk wannan hidimar da akaita yi idonta akan Madam Parveen da kuma Chief da Rakesh, haka ta shiga tunanin lokacin da suka fara haɗuwa a hospital da madam Aliya, a lokacin madam parveen tana kukan ɓatan ɗiyar ta...." Lokaci guda Baiwar ALLAH ta fashe da kuka tare da miƙewa tsaye ta nufi wurin Madam Parveen ta rungume ta sosai tana kuka... Madam Parveen ganin ana cikin farin ciki kuma taga Yarinya ta rungume ta tana kuka yasa jikinta yayi sanyi, sai kuma ta tuno da maganar Abbah da ya fara yi wanda bata gama fahimta ba, Itama Madam Parveen rungumar ta tayi tana rarrashinta ba tare da sanin ko ita wacece ba, amma tabbas ta tuna yarinyar, tayi tunanin saboda mutuwar Madam Aliya ne yasa ta ke kuka... Kowa hankalinsa ne ya karkato kansu, da murmushi akan fuskar Abbah ya ce "kinga Daughter ki nutsu ki saurari abinda zan gaya miki..." Madam Parveen itama kukan take idonta akan Chief, shima idonsa akan Baiwar ALLAH domin jikinsa yana bashi wani abu. sai da kowa ya nutsu kafin Abbah ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "tinda ke kin fahimci komai sauran su zan musu bayanin komai..." Anan Abbah ya sanar musu cewa "wannan yarinya ita ce ƴarku wacce ku ka rasa tin tsawon shekaru wato Amreesh..." Chief girgiza kai yayi tare da faɗin "tayaya hakan zata faru?..." Madam Parveen sake baki tayi tare da zaro ido waje tana kallon Baiwar ALLAH..." Itama Baiwar ALLAH ita take kallo tana kuka, yanzu ba kukan jini take ba abun yayi sauƙi sakamakon ɗorata akan magani da Doctor yayi ... Abbah ya ce "idan kuna tunanin Ƴar ku Amreesh tana da wata shaida a jikin ta to ku bincika, idan ba ita bace shikenam...." Madam Parveen fuska a wanke da hawaye take kallon Chief, Chief jinjina kai yayi sannan ya ce "ina ji a jikina cewa ita ce Daughter na Amreesh...." Rakesh ne ya taso gadan-gadan yayo kan Baiwar ALLAH dake rungume da Madam Parveen yazo ya riƙo hannunta tare da ɗagota tsaye yana shirin cire mata hijab, Baiwar ALLAH ihu ta fara kurmawa tana ƙanƙame da hijab, Madam Parveen ce ta jawo Baiwar ALLAH jikinta tare da rungumar ta sosai tana faɗin "ka ƙyale ta bana son jin kukan ta..." Rakesh ya ce "idan bamu ga shaidar dake jikinta ba taya zamu san Amreesh ɗin mu ce?..." Mohandas a ruɗe ya ce "Amreesh kuma?..." Abbah ya ce "No ai komai a hankali ake binsa, da rarrashi zaku duba mata..." Aunty Yolash ce ta taso da murmushi akan fuskar ta tayo kan Baiwar ALLAH wacce take rungume da Madam Parveen, zama tayi a kusa da ita tana faɗin "Daughter kiyi haƙuri idan basu ga shaidar haka a jikin ki ba babu yanda zasu yadda cewa ke ƴar su ce, ki yi haƙuri kinji ko..." Baiwar ALLAH tana kuka ta ce "ni bani da wata shaida, ku kyale Ni...." Furr Baiwar ALLAH taƙi yadda ta cire hijab ɗinta, Chief ya ce "ku barta domin naji hakan a jikina cewa Daughter ɗina ne Amreesh...." ya ƙarisa maganar yana murmushi, Itama Madam Parveen jinjina kai tayi tana faɗin "Nima na yadda..." ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka... Mohandas da Rakesh babu wanda ya ce komai domin har yanzu basu tabbatar ba... Roshan ganin yanda Mazan basu yadda ba yasa ya tashi ya nufi wurin Baiwar ALLAH yasa hannu ya ɗagota, ganin Roshan yasa ta ƙafe idonta akan sa, shima ɗin ita yake kallo fuska ba annuri bata san lokacin da ya zamar mata da hijab ɗin ba, sannan yasa hannu ta bayanta ya zuge mata zip ɗin riga, still idonsa a cikin nata haka suke kallon juna, yana tsaye a ta gabanta ya buɗe musu bayanta kafin ta ankara, Chief a ruɗe ya miƙe tsaye yana zaro ido waje ganin zanen bayanta, itama Madam Parveen miƙe wa tayi jikinta har wani kakkarwa yake idonta akan zanen bayanta itama, Mohandas da Rakesh su ma a ruɗe suka tashi, domin ko wannen su yana ɗauke da wannan zaunen a bayansa kuma sak iri ɗaya babu banbanci, Madam Parveen hannu takai sai tin wuyan Baiwar ALLAH tana shafa tawadar baƙin wurin wanda da shi aka haife ta, Kowa a cikin su sai da ya duba wannan tawadar bayan zanen... Roshan ganin irin kallon da take masa ne yasa shi sakin murmushin da bai san yayi mata shi ba, sai kawai ya tuna sunbatar sa da tayi da taje part ɗinsa... Mohandas da Rakesh kallon juna suka yi tare da sakin murmushin farin ciki baki a haɗe suka ce Amreeeeshh...." Baiwar ALLAH jin an ambaci sunan Amreesh da ƙarfi yasa ta firgita ta dawo hayyacinta, haka take bin kowa na cikin falon da kallo, Madam Parveen kam yankan jiki tayi ta faɗi sumammiya, kafin takai ƙasi Chief yayi saurin riƙo ta, Baiwar ALLAH ganin haka yasa kanta yayi mungun sarawa, a firgice takai hannu ta dafe kanta itama tayi ƙasi luu zata faɗi Roshan ya yi saurin riƙo ta tare da mannata a jikinsa yasa hannu yayi mata ɗaukan luɗa, Ramlat kam ƙirjinta kamar zai faso tsabar bugu da tsananin kishi, kai tsaye room ɗinta ya nufa da ita, yana zuwa ya tura ƙofa ya shige yana zuwa ya kwantar da ita akan gadonta... A wannan ranar kowa ya kasance cikin farin ciki, Madam Parveen bata tashi farfaɗowa ba sai dare misalin ƙarfe 8 ta farka tana ambatar sunan Amreesh, "Amreesh! Amreesh!! tana ina Amreesh ɗina, ta fito falo tana Dube-dube domin daga cikin bedroom take yanda aka kwantar da ita akan gado, mutane ta samu a falo kowa a cikin farin ciki especially Chief Suraj bashi da wata damuwa yanzu da ya wuce Razhdeen ya farfaɗo domin yana matuƙar ji da shi... Madam Parveen ce ta fito tana dafe da kanta tana ambatar sunan Amreesh, Ganinsu yasa ta fashe da kuka tana faɗin "dan Allah kada wanda ya sanar mun cewa mafarki nayi Amreesh bata dawo gare ni ba, dan Allah ku ce mun tana nan, Daughter na tana ina? ku gaya mun..." Mohandas da Rakesh ne suka taso duk suka nufi wurin Mommy su suna rarrashin ta, Mohandas ne ya rungume ta tare da faɗin "ba mafarki kika yi ba, a wannan lokacin mafarkin ki ya zamto gaskiya...." Madam Parveen kwalar rigar sa ta riƙe tana jijjiga shi tareda ku kaini na ganta mana, meyasa kuke mun haka..." Rakesh ya ce "Ok muje to yanda take..." Haka suka nufi room ɗin da Baiwar ALLAH take a kwance wanda har zuwa yanzu bata farfaɗo ba, shima Chief bin bayan su yayi yana son ƙara ganin Daughter ɗinsa... A kwance suka tarar da ita, da gudu Madam Parveen tayo kan Baiwar ALLAH tana faɗin "wallahi ita ce, ita ce Daughter na Amreesh..." Haka ta rungumi Baiwar ALLAH sosai a jikinta tana kuka, ta ɗago Baiwar ALLAH tare da ɗorata akan cinya tana shafa sumar kanta, ita kuwa Baiwar ALLAH kamar mai yin bacci.... Chief shima zama yayi a bakin gadon yana riƙe da hannun Baiwar ALLAH, su kuwa Mohandas da Rakesh kamar wanda akayi musu bushara da gidan Aljanna, baki ya gagara rufuwa tsabar farin ciki..... ★★★★★ Ƴar Amana kuwa tana nan ba lafiya daga lokacin da ta kwanta jinya ta suma yafi sau a ƙirga duk saboda rashin ganin Razhdeen tsawon watanni uku, tayi kukan har ta gaji, gaba ɗaya ta rarrame ta fita hayyacin ta, Madam Blessing ce take ta ɗawainiya da ita, taji labarin hatsarin Razhdeen taje asibiti amma sojoji sun hanata shiga, kuma ta kasa sanar wa Ƴar Amana halin da Razhdeen yake ciki, sannan ta ɗauki Ƴar Amana sunce gidan su Razhdeen nan ma Sojojin gidan sun hana shiga, gaba ɗaya Madam Blessing ta rasa yanda zata yi, tsoronta kar Ƴar Amana ta mutu domin yanda take rashin lafiyan nan anyi magani taƙi warke wa, ko abinci ta kasa ci.. Madam Blessing tsabar tsananin damuwar da take ciki har ta yanke shawaran guduwa ta bar ta a gidan ita kaɗai amma zuciyar ta taƙi barinta tayi hakan, sai kuma take jin tausayin yarinyar, ga idan ta ƙira wayan Roshan baya picking, tana zaune tasa Ƴar Amana a gaba sai kallonta take, ita kuwa tana kwance akan gado yanzu farfaɗowar ta daga suma ta wuce da yin bacci, Madam Blessing ɗaukar wayanta tayi akan ta sake ƙiran Roshan ko zai taimaka ya ɗauka, domin tasha tura masa message akan Sarah ba lafiya amma ko sau ɗaya bai ƙira ba sannan baiyi reply ba, Shi kuwa Roshan duk yana gani, ya yanke cewar bazai ƙara shiga hidimar Razhdeen ba shiyasa bai saurare su ba, Madam Blessing bugu ɗaya zuwa biyu tayi masa ya ɗauka anyi dace, karawa tayi a kunne tare da faɗin "Hello Roshan..." Ramlat ce ta ɗauka tana faɗin "wace ce?..." Madam Blessing ta ce "Roshan nake nema ki taimaka mun dan Allah ki bashi wayan...." Ramlat ta ce "yana bacci tukun..." Har zata katse ƙiran taji Madam Blessing ta fashe da kuka, Ramlat dakata wa tayi tana faɗin "lafiya kuwa?..." Madam Blessing ta ce "Sarah zata mutu ya taimaka yazo ya duba lafiyar jikinta dan Allah...." Ramlat ta ce "to ki kaita hospital mana..." Roshan ne ya fito daga wanka yana ɗaure da towel ya ce "waye?..." Madam Blessing jin muryar Roshan ne yasa taji sanyi a ranta, Roshan karɓan wayan yayi tare da faɗin "hello..." Madam Blessing tana kuka ta ce "Roshan ka taimaka ganan Sarah zata mutu, babu magani dan Allah...." Roshan tunawa yayi da cewa Razhdeen yana kwance ba lafiya ya ce "ok ki jirani yanzu gani nan zuwa..." Shap-shap Roshan ya shirya tsab sannan ya fice da hanzarinsa, Ramlat tana masa maganar ya tsaya ya ci abinci amma sam ya ƙi, nan da nan sai tashin motarsa taji...... Madam Blessing farin ciki ne ya gama mamaye ta... Bayan wasu mintuna sai ga Roshan ya iso da motarsa, Madam Blessing jin tsayuwar mota yasa ta tashi da gudu ta nufi hanyar waje, a tare suka shugo suka ƙarasa cikin room ɗin Ƴar Amana, Roshan yana ganinta hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba, ganin yanda Sarah ta rarrame tayi fatt alamar babu jini a jikin ta, sakamakon haka yasa ko iya tashi da kanta bata yi, kwata-kwata babu jini a jikin ta shiyasa tana farfaɗowa sai ta ƙara sumewa kullum a cikin haka take, ga babu kuɗin kaita hospital duk sun cinye kuɗin da Razhdeen ya bari, babu komai a gidan ya ƙare, security gidan suma ganin babu Razhdeen yasa duk suka watse hatta mai gadi babu, sai iya su biyu kawai..... Madam Blessing duk ta kwashe irin matsalar da suke ciki ta gayawa Roshan, ta sanar yanzu babu komai, babu kowa a gidan, ta sanar masa cewa itama ta gaji tana son tafiya... Roshan ya ce "kinyi ƙoƙari Madam Blessing zaki iya tafiya, amma ki tura mun account ɗinki zan zuba miki wasu kuɗaɗen da zakiyi amfani da su...." Madam Blessing tayi godiya matuƙa sannan ta bashi account tayi tafiyar ta... Shi kuma Roshan ɗaukan Ƴar Amana yayi a saman kafaɗarsa shima yayi hanyar fita da ita, a cikin mota ya kwantar da ita back seat shima ya shiga motar suka fita waje, bayan ya fita ne ya sake fitowa ya rufe gidan gaba ɗaya, kai tsaye can gidan su ya nufa da ƴar Amana, acan za'ayi mata magani sannan zata fi samun kulawa sosai, duk da ba'a san alaƙar dake tsakanin ta da Razhdeen ba...... Typing ✍️ *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 26 to 30 Tana zaune a bakin gadon ɗakin da take sai sharar kuka take, Aunty Yolash dake gefen ta tana riƙe da hannunta tare da faɗin "haba Aunty A'isha kiyi haƙuri mana, duk abinda ya wuce ya rigada ya wuce idan Allah yasa kema da rabon ƴarki Reemah zata bayyana lokaci guda zaki ganta, idan ma ba ta raye labarin ta zai fito domin duk abinda akayi shi cikin sirri to wata rana sirrin nan zai bayyana, tinda har sace ta akayi to wallahi nasan wata rana sai asiri ya tonu ki kwantar da hankalin ki...." Aunty A'isha tana kuka ta ce "nasan yanzu haka ta mutu, ko nono na bata sha ba, inaji a jikina nima ƴata Reemah zata bayyana..." Aunty Yolash ta ce "kiyi ta addu'a Allah ya bayyano da ita..." suna cikin wannan halin sai ga mai martaba ya shigo da sallama a bakinsa, ganin yanda INDO take kuka ya ce "me yake faruwa ne?..." Aunty Yolash ta ce "ta ga iyayen Baiwar ALLAH sun bayyana ne shiyasa itama ƴarta ta faɗo mata a rai..." Mai martaba girgiza kai kawai yayi ba tare da ya furta komai ba, Ita kuwa Aunty Yolash fita tayi daga ɗakin ta basu wuri... Aunty Yolash a falo ta tarar da Maamie tana zaune, ganin ta fito daga room ɗin Aunty A'isha ne yasa Maamie yin murmushi tare da faɗin "an gama munafurci kenam, Ni dai duk wanda yayi gulma ta ban yafe masa ba ehen..." Aunty Yolash tsayawa tayi tana hararar ta sannan ta ce "wanda yakai ake gulmansa amma ke meye a jikinki da har za'ayi gulmar ki, kina nan talaka futuk da ke..." A firgice Maamie ta miƙe tsaye tana faɗin "ai kuwa uban kowa yaci tsinin uwar wanda ya ce mun ni talaka ce, domin nafi ƙarfin wannan layi, ki dube ni dakyau nafi ƙarfin uwar mutum..." Aunty Yolash tana mata kallon up and down ta ce "eh na ganki dakyau kalar zaren bai yo kalar yadin ba, in da ba'a san asalin ƙarago ba sai yace shi ɗan kamfani ne, kuma kar kin manta ke fa haɗaki akayi da mai martaba, ba wai shi ya ganki yace yana so ba, ya Aure ki saboda rashin kwanciyar hankalin da kike ciki na mungun talauci, ba bu abunda zaku ci yau bare gobe, saboda mai martaba ya azurta ki shine zaki nuna butulci a mutane? aikin banza kawai, bugu da ƙari amanar ƙawar ki kika ci kika aure mata miji, banza marar aji..." Maamie rasa abun cewa tayi sai kawai ido da tabi Aunty Yolash da shi.. Ita kuwa tinin ta fice, part ɗinsu gaba ɗaya ta bari ta nufi part ɗin Abbah anan take daman... ★★★★★ A babban falo Aunty Yolash ta tarar da Roshan zaune akan kujera sai Abbah dake ɗayan kujera ga kuma Ƴar Amana kwance a doguwar kujera bata farka ba, Ƙarasa shugowa tayi tare da faɗin "to pah wannan yarinyar daga ina?..." ta ƙarasa maganar tare da zama a 1 seater idonta akan Ƴar Amana... Abbah ya ce "Nima yanzu naga ya shigo da ita..." Abbah ya maida idonsa kan Roshan sannan ya ce "wannan yarinyar aina ka samo ta?..." Roshan ya ce "Yarinyar Razhdeen ce, tsawon shekaru biyu yana tare da ita a gidan sa..." A ruɗe Abbah ya ce "whattt?..." Roshan ya cigaba da cewa "Yarinyar bata da kowa haka take yawo a titi Sannan akwai waɗanda suke farautar rayuwar ta, hakan yasa Razhdeen ɗauko ta zuwa gidansa, kafin Allah yasa a gano ina ne asalin ta...." Abbah ya ce "shi Razhdeen ɗin meyasa bazai kawo ta nan gidan ba? ga nan ƴan uwanta mata amma sai ya fake da ita? wannan wani irin shirme ne?..." Roshan ya ce "ita ɗin kurmiya ce bata iya maida magana, zaman ta a cikin mutane zai iya takura mata, domin a yanda take bata juran zama a cikin mutane, i means tana da rauni sosai, still ba wai ita su biyu suke zaune a gidan ba, ya ɗauko mata wacce zata na kula da ita wato Madam Blessing, ita take kula da duk wani al'amuran ta, sannan ya sanya ta a school tin safe har zuwa yamma ƙarfe shida..." Jinjina kai Abbah ya yi sannan ya ce "to yanzun ya ake so ayi mata?..." Aunty Yolash ta ce "zata zauna da mu anan, Insha Allahu za'a binciko mata yanda iyayen ta suke, amma kamar asalin ta ba ƴar nan Nigeria ba ce domin daga sumar kanta zaka gane cewa ba ƴar nan ba ce..." Roshan ya ce "abinda nake so ayi kenam, zamu tsawaita bincika yanda take, amma a ganin ki ƴar wata ƙasa ce?..." Aunty Yolash idonta akan Ƴar Amana ta ce "akwai ƙasashe mabanbanta kuma ko wace ƙasa da kalar siffan mutanen ƙasar amma wannan ina tunanin kamar ƴar ƙasar birnin Niger ce..." Roshan ya ce "shin kin tabbatar da haka?..." Abbah ya ce "taya ya ta zamo ƴar ƙasar?..." Aunty Yolash ta ce "naga yanayin ta tana zubin kama da Aunty A'isha matar mai martaba, itama idan ku ka lura ai haka sumar kanta yake da suffar ta..." Roshan idonsa akan Ƴar Amana ya ce "to mai zai hana mu ƙira ita Aunty A'isha ko zata iya banbance mana tinda ita ƴar ƙasar ce..." Abbah ya ce "yanzu dai ku bari sai gobe, dare yayi ka ɗauke ta ka kaita ɗakin da uwar masu gida take, zata fi kula da ita..." Aunty Yolash zuwa yanda Ƴar Amana take tayi tana tattaɓa jikinta ta ce "amma fa kamar zazzaɓi ne a jikinta..." Roshan ne shima yazo wurin yana faɗin "eh bata da lafiya ne..." ya ƙarasa maganar yana duba tafin hannunta sannan ya buɗe mata ido yana duba ciki, girgiza kai ya yi tare da faɗin "ba jini a jikin ta, tana shan wahala sosai..." Abbah ya ce "to a kaita hospital mana..." Roshan ya ce "zan yi mata magani a gidan nan tinda inada kayan aiki basai anje asibiti ba, zan bata jini na..." Aunty Yolash kallon sa tayi sannan ta ce "jinin ka kuma?..." Ya amsa mata da "Eh..." Sannan yasa hannu ya ɗauke ta kai tsaye room ɗin Ummy ya kaita, Ummy kuwa har tayi bacci dake yanzu misalin ƙarfe 9 ne na dare... A wannan daren Roshan yasa Aunty Yolash taja masa jini leda guda sannan ya ɗaura mata, sai da ya gama mata abinda ya kamata yayi tukun suka bar ɗakin shi da Aunty Yolash daman iya su uku ne suka san da zuwan Ƴar Amana a wannan lokacin, Kowa yana room ɗinsa, Abbah shima part ɗin Hajiya Kilishi ya nufa dake yau kwanan ɗakin ta ne, itama Aunty Yolash room ɗinta ta shige tare da yi musu sallama, Shi kuwa Roshan har zai fita yakai idonsa kan ɗakin da Baiwar ALLAH take, nufan ɗakin yayi yana zuwa ya tura tare da shige wa, A kwance ya tarar da ita har ta farfaɗo ta shige da yin bacci sai kuma Madam Parveen mahaifiyar ta kenam dake gefenta itama a kwance tasa hannu ta rungumi Baiwar ALLAH kamar wacce za'a sace ta... Roshan idonsa akan Baiwar ALLAH daga baya ya fita tare da rufe musu ƙofa shima ya nufi part ɗinsa... Chief Suraj da Rakesh akwai wani gidan su dake garin nan suka je zasu zauna kafin su koma U.S, Madam Parveen kuwa ƙin binsu tayi wai ita tana nan tare da Amreesh ɗinta, bazata iya tafiya ta barta ba... ★★★★ Cikin dare Baiwar ALLAH ta fara wani irin mafarki tana jujjuya kai baki na motsi tana furta "Habeey! Habeey!! Habeey!!! kaga Mommy ta siya mun sarƙa gobe birthday ɗina, Habeey idan na girma muka yi Aure tare zamu na wanka ko? haka Mommy da Daddy tare suke yi, Habeey zamu yi party a church ina zaka je? Habeey church ɗin mu ya kama da wuta meyasa kuma masallacin ku bai yi gobara ba? nima zan rinƙa zuwa masallaci tinda baya gobara, Habeey zamu je Kaduna ni da Mommy nah ana bikin wata ƙawarta... Mommy! Mommy!! Mommy!!! idan muka koma Abuja zan sanar wa Habeey cewa ƙawarki a church akayi bikin ta, mu a masallaci za'ayi biki na da Habeey... Mommy! Mommy motar mu tana girgiza zamu faɗi wayyo, motar mu zata kife ki riƙe ni, Mommyyyy....." Cikin ihu Baiwar ALLAH ta farfaɗo tana ƙwalla ƙiran Mommy a ruɗe, gaba ɗaya ta wanke duk ilahirin jikinta da gumi, tana haki kamar wacce tayi gudun tsere... Madam Parveen tana gefenta a zaune tin farkon mafarkin ta har farkawar ta tana zaune idonta akan ta, a hankali ta furta "Daughter...." Juyowa Baiwar ALLAH tayi tana kallon Madam Parveen, lokaci guda ta fashe da kuka tana faɗin "Mommy..." ta fa ɗa jikinta, Madam Parveen rungumar ta tayi itama tana zubda hawaye tare da mamakin wai yau ita ce tare da Amreesh ɗinta.... Sai da ta gama rarrashin ta tukun Baiwar ALLAH ta share hawaye ta ce "zanyi sallah..." ta tashi ta nufi bathroom, ba juma wa ta fito da alwalar ta, hijab ta cire ta zura sannan ta shimfiɗa sallaya ta tsaida sallah... Madam Parveen kuwa tana zaune idonta akan Baiwar ALLAH, ga yanda take hawaye a cikin ranta tana faɗin "daman nasan zaki tashi da musulunci, yanzu ya zamu yi da ke, iyayen ki suna Christal ke kuma kina musulma da Yayanki Mohandas.... Baiwar ALLAH tayi sallar lafulolin ta sannan ta kalli Madam Parveen ta ce "Mommy ki sauƙo kizo yanda nake..." Madam Parveen ce ta sauƙa daga kan gado ta zauna a gefen sallayar da Baiwar ALLAH take, Baiwar ALLAH juyo wa tayi tana fuskantar Madam Parveen tare da riƙo hannayen ta biyu a cikin nata tana kallon ta, tana motsi da lips ɗinta ta ce "Mommy kinyi farin cikin gani nah?..." Madam Parveen ta ce "ban taɓa shiga cikin yanayin farin ciki kamar na wannan lokacin ba, ganin ki yasa duk wani damuwata ta wanke, zuciyata tayi fari tass...." Murmushi Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "Nima haka, ina sonki Mommy tin daga lokacin da na fara ganinki a asibiti ke da Madam Aliya zuciyata take bani wani abu akan ki, idan baki manta ba a lokacin likita ya sanar miki cewa muna kama, kuma jinin jikin mu ɗaya dole zan ji wani abu...." Ta ƙarasa maganar tana kuka haka itama Madam Parveen take kuka tana goge hawayen Baiwar ALLAH da hannunta. Madam Parveen ta ce "ki daina kuka Daughter, yanzu ba gamu ba, mun bayyana zuwa gare ki, addu'ar mu tayi tasiri, daman pastor ya sanar mana cewa kina nan da ranki..." Girgiza kai Baiwar ALLAH tayi tana kallon Madam Parveen sannan ta ce "Mommy idan nace ki bini zaki biyo ni?..." Madam Parveen ta ce "yanzu bazan ƙara yin nisa da ke ba, ƙafarki ƙafata zan bi ki muje ko ina...." Baiwar ALLAH ta ce "kinyi alƙawarin haka?..." Madam Parveen ta shafa gefen fuskar ta tana faɗin "promise my beautiful girl..." Baiwar ALLAH ta ce "to ina so ki biyo ni..." Cike da rashin fahimta Madam Parveen take binta da kallo ta ce "zuwa ina?..." Itama Baiwar ALLAH idonta a cikin nata ta ce "zuwa musulunci..." Ƙirjin Madam Parveen ne yayi wata muguwar bugawa tare da zaro idanu waje, cikin ƙiƙƙinar magana ta ce "musulunci? n n never..." Baiwar ALLAH tana hawaye ta ce "Please Mom 😭..." Madam Parveen ganin yanda take ta kuka ne yasa ta cewa "o o okay don't worry, amma Daddyn ki bazai yadda ba..." Baiwar ALLAH ta ce "ke ki fara idan yaga kin musulunta shima zai yi..." Madam Parveen ta ce "no zai rabu da ni ne..." Baiwar Allah ganin yanda Madam Parveen ta rikice lokaci guda yasa ta rungume ta tana bubbugan bayanta a hankali tare da faɗin "Ni bazan bar hakan ta faru ba, nayi miki alƙawari..." Madam Parveen ta ce "shikenam tinda kina so na musulunta zan musulunta nima amma ki bari sai gobe..." Baiwar ALLAH ta ce "yanzu nake so..." Idonta a cikin na ta, Madam Parveen ta ce "to waye zai musuluntar da ni yanzun?..." Baiwar ALLAH ta ce "Ni zan musuluntar da ke..." Madam Parveen murmushi tayi tare da faɗin "toh Daughter I agree..." Baiwar ALLAH ta ce "zan furta kalmar shahada kema ki maimaita sannan bayan mun kammala zaki yi wankan tsarki, a cikin daren nan zan koya miki abubuwan da ya kamata ki sani da farko, yanzu ƙarfe 1:30 ne zuwa sallar asuba zamu kammala...." Madam Parveen jinjina kai tayi da murmushi akan fuskar ta... ★★★★★ Ƴar Amana tana kwance ido a rufe ga yanda jini yake ɗigo wa a hankali. Asubar fari jin yanda ake ta ƙiraye-ƙirayen sallar asuba ne yasa Ummy ta fara juyi tare da furta kalmar shahada, a hankali take buɗe idanuwanta taga ɗakin haske tarwar da mamaki take bin ɗakin da kallo, tana faɗin "to waye ya shigo mun ɗaki, hasken ɗakina a kashe yake yanzu kuma na samu a kunne impossible..." Ƙoƙarin sauƙa daga kan gado take idonta ya sauƙa akan Ƴar Amana dake kwance gefen ta, a tsora ce Ummy ta ja da baya bata san lokacin da ta faɗo daga kan gado ba, ba shiri ta tashi da gudun gaske tayi hanyar fita tana ihu, a san sauƙowa daga saman beni ƙafarta ta zame ta kife akan benin haka take gangaro wa daga sama, dai-dai lokacin da Abbah ya sauƙo da hanzarinsa jin ihu da Hajiya Kilishi dake tafe ta bayansa, itama Aunty Yolash fitowa tayi da gudu tayi alwala ko sallah bata fara ba, dai-dai da shima Roshan ya shigo yana so yazo ya duba jinin da ya ɗaura wa Ƴar Amana domin yasan jinin ya ƙare, Ko wannen su da gudu ya isa wurin benin yanda Ummy ta faɗo, a ruɗe Ummy ta miƙe goshi a fashe ta rungumo Abbah tana ihu tare da nuna hanyar ɗakin ta da yatsa... Su Pinky ne suma suka sauƙo da gudu jin ihun da ake a tsorace suka sauƙo suna zazzaro ido... Aunty Yolash ce take faɗin "meya faru ne kiyi mana bayani mana?..." Daƙer Ummy ta dai-daita nutsuwar ta sannan ta ce "wata aljana ce a kwance kan gado na, wayyo Allah Abbah ka taimake ni...." Aunty Yolash ido ta haɗa da Roshan ta kwashe da dariya tana faɗin "shirmen banza wai yarinyar nan da ta gani shine take wannan shiɗewar, zaki je ki kashe kan ki..." Roshan ne ya kafaɗar Ummy tare da faɗin "look my love, baƙuwa muka yi ne shine aka kaita ɗakin ki ku kwana tare..." Abbah ya ce "ai dole ta tsorata, bata kwanta da mutum ba kuma ta tashi ta tarar da mutum mai zai hanata tsorata..." Aunty Yolash ta ce "saboda haka fa muka bar hasken ɗakin a kunne saboda kar ta tsorata..." Roshan da hanzarinsa ya haura domin shi kwata-kwata ya manta da ya ɗaura mata jini, kuma jinin ba lallai ne ya kai haka bai ƙare ba... Su Abbah ne suka bi bayansa, Roshan yana shiga ya tarar ledar jinin ya ƙare sai da ƙirjinsa ya buga da gudu ya ƙarasa wurin, yana zuwa ya samu an cire mata da jinin ya ƙare.... Aunty Yolash tana tsaye ta ce "ai yau kusan kwana nayi ina zirga-zirga zuwa ɗakin nan, dana ga jinin ya kusan ƙarewa sai kawai na zauna sai da ya ƙare tukun na zare mata, sai a lokacin naje na samu yin bacci..." Dogon numfashi Roshan ya ja yana faɗin "Allah na gode maka, wallahi na manta sai yanzu danayi alwala zan tafi masallaci na tuno da ita...." Ummy ta ce "Abbah wannan ɗin wace ce?..." Abbah ya ce "baƙuwa muka yi, kuma bata da lafiya..." Pinky fuska a haɗe ta ce "ikon Allah, daga wannan sai wancan mudai a haka zamu ƙare, gidan nan kawai a mayar shi gidan marayu...." Abbah ya kalli Pinky ya ce "fita ki bar ɗakin nan tin kafin na saɓa miki dan ubanki, wawuyar banza mai baƙin hali..." Pinky fita tayi tana tura baki itama Rikky bin bayanta tayi duk suka fice... Abbah ya kuma cewa "yanzu dai tinda bacci take kowa yaje yayi sallah, Roshan kaima kazo mu tafi masallacin tare kafin mu makara...." Duk suka bita sai Ummy wacce idonta akan Ƴar Amana sai yanzu hankalin ta ya kwanta, ta shige toilet tayo alwala... ★★★ Baiwar ALLAH da Mommyn ta a lokacin da suke jin ɗan hayaniya suna sallah ne, Duk yanda Baiwar ALLAH tayi haka itama Madam Parveen take yi, a nutse suka kammala sallar su tare da yin Addu'o'i.... Baiwar ALLAH ta canza wa mahaifiyar ta suna daga Parveen zuwa Zainab.... ★★★★★ Bayan kwana biyu Ƴar Amana ta fara samun sauƙi sosai, tinda aka kawo ta ɗakin Ummy bata samu fitowa ba, sai dai aje ɗakin a dubo ta, Ummy da Ƴar Amana jininsu ba ƙaramin haɗuwa yayi ba, hatta su Pinky da basa son mutane suma suna shiri da Ƴar Amana kullum a ɗakin Ummy suke wuni a wurin ta, ba ƙaramin nishaɗi suke sanya ta ba duk da bata magana sai dai tai ta jinsu kawai, idan sunyi abun dariya tayi murmushi amma hankalin ta har yanzu yana kan Razhdeen, damuwar ta shine taga Razhdeen, kuma bugu da ƙari abinda zai ƙara sa hankalin ta ya kwanta shine ganin Roshan da take kullum, kuma ba ƙaramin kulawa yake bata, hatta abinci shi da kansa yake bata saboda ta samu ta ci ta ƙoshi, idan lokacin cin abincin ta yayi duk abunda yake zai zo ya bata sannan ya bata magani ta sha domin ta fi yadda da shi. Itama Aunty A'isha daga lokacin da tayi ido huɗu da Ƴar Amana kullum sai tazo yanda take, domin yarinyar ba ƙaramin shiga ranta tayi ba a cewar ta, haka zata zo ta sakata a gaba tai ta kallonta kamar madubi, Sunan da Aunty A'isha take ƙiran Ƴar Amana da shi shine Ƴar ƙasar mu, domin taga tayi kama da ƴan ƙasar tasun, kuma Kowa yaga Ƴar Amana sai ya haɗa ta da Aunty A'isha, kowa cewa yake suna kama musamman wurin sumar gashin iri ɗaya sak dake duk murɗaɗɗen gashi gare su, hasken fata ne Aunty A'isha tafi Ƴar Amana amma idan ka zuba ido sosai ka lura suna mungun kama da juna... Duk manyan gidan sun fahimci hakan wato Abbah da Aunty Yolash da matan gidan har yaran gidan ma, sai dai ana fargaban furta hakan ne saboda kar Aunty A'isha ta tayar da hankalin ta akan ɗiyar ta wacce ta rasa, dole sai an bincika tukun, Shima Mai martaba ganin Ƴar Amana jikinsa ba ƙaramin sanyi yayi ba, indai zai haɗa ido da ita to sai zuciyar sa ta buga, ya rasa gane mai hakan yake nufi, Aunty A'isha tin safe take zuwa wurin Ƴar Amana bata barin yanda take sai dare, daren ma daƙer ake korata part ɗin su, kullum dai Ƴar Amana bata rabuwa da mutane a wurin ta sai dare idan zata yi bacci, su kwanta ita da Ummy a gado ɗaya... Baiwar ALLAH da Maamie ne kawai basu je sun ga baƙuwar da aka kawo ba, Ita Maamie abinda yasa bata je ba saboda bata son shiga cikin family su ne, domin ba ƙaunar su take ba, a tunanin ta sun fi son mu'amala da Aunty A'isha akan ita shiyasa itama take jan jiki da su, gwara tayi rayuwar ta ita kaɗai.... Ita kuma Baiwar ALLAH abinda yasa bata je saboda a room ɗin Ummy take kuma yanzu basa shiri da Ummy, Ummy bata zuwa yanda take haka itama ba wanda yake yiwa wani magana a cikin su shiyasa itama Baiwar take zaune a yanda take, sai Mahaifiyar ta da take tare da ita, Mahaifinta da ɗan uwanta sai dai su zo su duba su amma basa kwana a gidan, Mahaifiyar ce take zaune da ita su kwana gado ɗaya, hakan yasa Baiwar ALLAH take samun damar koya mata abubuwan da ya shafi addini sosai, a karatun su na Alkur'ani har sun ɗanyi nisa domin Madam Parveen tana da ƙwaƙwalwa sosai, koman yawan karatu lokaci guda take riƙe shi a ƙwaƙwalwarta haka itama Baiwar ALLAH... Domin ita Baiwar ALLAH tin tana gidan marayu ta haddace Alkur'ani mai girma sannan ta haddace litattafai da dama na musulunci... Har ila yau babu wanda yasan Madam Parveen ta musulunta.... Su Minal kuwa suma gidan su daban duk bayan kwana ɗaya ko biyu sukan zo ziyara gidan Abbah da yaron su, wani sa'in kuma iya yaron ake kawo wa yazo ya wuni kafin a kai shi wurin Maman sa.... *BAYAN WATA BIYU....* A yau ne kowa da kowa ya hallaru a babban falo, su Minal da mijin ta Mohandas suma sun zo, ga kuma Chief Suraj da Rakesh su ma suna zaune dake yau ne komawar su ƙasar U.S sun gama hutun su, Madam Parveen da Baiwar ALLAH su ma suna zaune a kujerar da su Chief Suraj suke a zaune dake doguwar kujera ne... Shima Mai martaba yana zaune da matan sa a gefe da gefen sa su ma a yau ne zasu koma ƙasar Jidder, Sai Roshan shima yana zaune da Ramlat a gefensa, har ta ɗan rame saboda kishi da tasa a ranta, mutane biyu ne a cikin ranta waɗanda take kishi akan su daga Baiwar ALLAH ce sai kuma Ƴar Amana, ita Ƴar Amana kulawar da Roshan yake bata ne yasa abun yake damun Ramlat, taga har abinci yake zuwa bata da magani alhalin ga matan gidan, sai abun yake cin ranta sosai, gwara ita Baiwar ALLAH yanzu Roshan ya ɗan ja mata baya, baya sauraron ta yanzu, sannan baya zuwa yanda take, Itama Baiwar ALLAH yanzu bata damuwa da hakan saboda kulawar da take samu a wurin mahaifiyar ta, ganin Mahaifiyar ta a kusa da ita duk ya wanke mata wani ƙunci da damuwa, kuma most especially yanzu bata da wani lokaci sai koya wa mahaifiyar ta karatu hakan yasa bata damuwa da rashin ganin Roshan.... Abbah shima yana zaune da matansu a kujerar da yake wato Hajiya Kilishi da Ammy, sai kuma ɗayan kujerar Aunty Yolash ce da Razhdeen suke zaune, yau kwana biyu da farfaɗowar Razhdeen wanda tsawon watanni huɗu yake kwance a sume, amma sai dai ya farfaɗo ne baya iya yin komai da kansa, baya iya yin magana balle ya iya aikata wani abu, hatta abinci bashi ake a baki, abinda ya iya sai dai kawai yabi kowa da ido amma kuma yana iya jin duk abinda ake fa ɗa, duk wanda yaga Razhdeen sai ya bashi tausayi gaba ɗaya ya rarrame yayi fari tass kamar ba jini a jikinsa, domin sai da akayi aiki sosai akan sa kafin ya farfaɗo, Sumar kansa kuwa har ya fara dawowa yanda yake, domin a lokacin da za'ayi masa aiki a ƙwaƙwalwarsa tas aka Aske, yanzu kuma a cikin wata biyu sumar ta ƙara tofowa sai dai bai kai na baya tsayi ba, amma yanzun ma yayi kusan zuwa kafaɗarsa, an kwantar da shi a jikin kujerar domin bazai iya normal zama yanda kowa yayi ba, sai Aunty Yolash dake gefen sa... Sauran yaran gidan kuma Ummy da Pinky da kuma Rukky da Ƴar tinny duk suna zazzaune a ƙasin carpet.... Abbah ne ya tambayi Ƴar Amana yana faɗin "ina Sarah take yau kam inason ganin ta a cikin mutane, zaman ɗakin ya isa haka domin muna so mu tattauna akan maganar ta da yadda za'ayi, ga kuma Razhdeen ya dawo gida amma babu yanda zai yi mana bayani akan ta ko ya gano asalin ta...." Mai martaba ya ce "hakane kam yanzu wata taje ta ƙira mana ita..." Uwar masu gida ta ce "idan akaje bazata fito ba, kusan kullum ina janta akan ta fito koda falo ne amma ta ƙi...." Aunty Yolash ce ta miƙe tana faɗin "bari naje na tafo da ita..." tana kaiwa nan ta wuce kai tsaye upstairs ta haura, Razhdeen idonsa ya tsayar akan Baiwar ALLAH tin zamansa ko ƙibtawa bai yi ba, ita kuwa duk ɗagowar da zata yi sai ta haɗa ido da shi, sai ta ƙara sunkuyar da kanta ƙasi tana wasa da ƴan yatsun ta gira a haɗe... Roshan kuwa duk yana lura da kallon da Razhdeen yake mata, sai dai kawai ya kalle shi sannan ya kalli Baiwar ALLAH sai kawai ya kawar da kai gefe, idan ya tuno da abinda suka aikata gani yake kamar yau ya kamasu a ɗaki domin abun ya gagara wankuwa a ransa, kullum abun yake haskowa a idonsa hakan yasa har zuwa yanzu yake ƙara jin haushin su.... Aunty Yolash a ɗaki ta tarar da Ƴar Amana tana ƙoƙarin saka belt a wandon jikinta, Murmushi Aunty Yolash tayi tare da nufan yanda take tana faɗin "wando ya kasa riƙe kunkumi ga ba'a iya ɗaura belt ba..." Daman Ƴar Amana indai zata saka wando mai belt to Madam Blessing ce take ɗaura mata shiyasa har yanzu bata iya ɗaura wa ba, Aunty Yolash ce ta tsuguna tare da sa hannu zata ɗaura mata, Ƴar Amana sake wandon tayi ita kuwa Aunty Yolash bata yi gaggawar riƙo wandon ba sai kawai wando ya sulale har ƙasi, da sauri Ƴar Amana tasa hannu ta rufe fuska saboda tsananin kunya, Aunty Yolash tana dariya ta ce "inna'ilaihi ya haka kuma, ta riƙo wando zata ja mata shi sama Allah yasa tana da pant a ciki, sai da ta zo sai tin cinyar ta da wandon idon Aunty Yolash suka sauƙa akan zanen dake kan cinyar ta, ƙara zaro ido waje tayi ganin zanen kamar na masarautar ƙasar Jidder, Aunty Yolash hannu tasa tana murtsika idanuwanta ko dai mafarki take ganin da gaske ne yasa ta saka hannu a kan zanen tana shafa gurin cike da mamaki. suna cikin wannan halin sai ga Aunty A'isha ta shugo ɗakin tana faɗin "ina Auntyn yara ku fa ake jira a falon kun juma...." Cike da mamaki Aunty A'isha ta ƙaraso yanda suke ganin Ƴar Amana tana rufe da fuska da hannayenta biyu ita kuma Aunty Yolash tana durƙushe tana riƙe da wandon Ƴar Amana bata gama jansa sama ba, Aunty A'isha ta ce "ha'a bata iya saka wandon bane?...." Aunty Yolash ce tayi saurin riƙo hannun Aunty A'isha ta durƙusar da ita ƙasi tana nuna mata zanen kan cinyar Ƴar Amana, A tsorace Aunty A'isha ta ja da baya tare da zazzaro ido waje tana faɗin "wannan ai tambarin masarautar mai martaba ne, ya akayi naga irin zanen akan cinyar yarinyar nan ?...." Aunty Yolash cike da mamaki take faɗin "kuma zai iya kasance wa Reemah ce...." A zabure Aunty A'isha ta ce "Reemah kuma? ai lokacin da aka haifi Reemah ba'ayi mata wannan zanen ba...." Aunty Yolash idonta akan zanen ta kuma cewa "zai iya kuma kasancewa Razhdeen ne yasa ayi mata, tinda ta ɗau tsawon lokaci a wurin sa..." Aunty A'isha hannu na kakkarwa ta kai kan haɓar Ƴar Amana ta ɗago da kanta suna kallon juna, itama Ƴar Amana kallon Aunty A'isha ta tsaya yi ganin yanda ta ƙura mata ido, lokaci guda Aunty A'isha taji wani irin yarr a jikin ta, haka zuciyar ta take bugun uku-uku... Aunty Yolash ce ta ɗaura mata belt ɗin wando tare da ɗagowa ta dafa kafaɗar Aunty A'isha tana faɗin "kar muyi gaggawar yanke hukunci sai mun tsawar ta bincike tukun, in ma ita ce za'a gano, idan ma ba ita bace duk dai gaskiya zata bayyana da yardar Allah...." Aunty A'isha jinjina kai tayi tana zubda hawaye ta juya zasu fita, Aunty Yolash riƙo hannun Ƴar Amana tayi suka fita tare.... Suna sauƙa falo Abbah ya ce "bacci ne ya ɗauke ku a ɗakin ne?..." duk zama suka yi ba tare da kowa ya furta komai ba, Aunty Yolash zama tayi a kujerar da take kusa da Razhdeen tana riƙe da hannun Ƴar Amana zata zaunar da ita, Ƴar Amana idonta ta sauƙar akan wanda yake zaune kusa da Aunty Yolash, a ruɗe ta zaro ido waje ganin Razhdeen, shima Razhdeen ɗin idonsa ya sauƙar kan Ƴar Amana wanda ko motsi baya iya yi... Ƴar Amana cike da farin ciki tana washe baki haɗi da kuka ba tare da ta dubi waɗanda suke falon ba tayi tsalle ta fa ɗa jikin Razhdeen... Cike da fargaba Aunty Yolash ta ce "wayyyyyooo ta kashe shii...." Razhdeen jin yanda ta fa ɗa jikinsa bai san lokacin da ya ce "Asshhhhh....." abunda ya iya furta wa kenam.. Ita kuwa Ƴar Amana rungumar sa tayi sosai tana kuka ba tare da ta dubi halin da yake ciki... Duk kowa na falon tsaya kallon su suke da murmushi akan fuskokin su ganin yanda suka shaƙu da juna sosai ... Baiwar ALLAH tin shugowar Ƴar Amana ta zazzaro ido waje tana binta da kallo, a ruɗe ta miƙe tsaye tana zazzaro manya-manyan idanuwanta baki a buɗe ta gagara furta komai... Idon kowa sai ya koma kanta, a tunanin kowa sun yi zaton ko dan saboda ta rungumi Razhdeen ne yasa, Roshan shima idonsa akan Baiwar ALLAH haka yake jin bugun zuciya kamar zai fasa ƙirjinsa, wani sabon kishi ne ya ziyarci cikin zuciyar sa... Ƴar Amana kifar da kanta tayi akan ƙirjin Razhdeen tana kuka bata ma lura da Baiwar ALLAH ba, A ruɗe cikin kakkarwar murya Baiwar ALLAH ta soma faɗin "Ƴ Ƴ Ƴar Amana...." wannan sunan ne ya daki dodon kunnen Ƴar Amana dake kwance akan Razhdeen, sunan da rabon da taji an ƙirata da shi tin tsawon shekara uku yanzu... Baiwar ALLAH ce ta ƙara nanata sunan "Ƴar Amana..." Ƴar Amana jin sunan da gaske ake ƙiranta ba gizo ba yasa ta juyo da sauri tana kallon yanda ake ƙiran sunan, Ganin Baiwar ALLAH a tsaye yasa itama ta miƙe da sauri tana zaro ido, baki a buɗe kamar wacce zata yi magana haka ta ƙura wa Baiwar ALLAH ido, Baiwar ALLAH cikin kuka ta ce "Ƴar Amana ta...." Itama Ƴar Amana shirin yin kuka take haɗe da dariya, haka ta rufo kan Baiwar ALLAH da gudu itama Baiwar ALLAH tafo wa tayi suka rungumi juna sosai kamar bazasu ɓanɓaru ba, duk ɗin su kuka suke domin ba ƙaramin kewar juna suka yi ba... Kowa a falon cike da mamaki suke binsu da kallo. Baiwar ALLAH ce ta ɗago kan Ƴar Amana tana kuka ta ce "Ƴar Amana daman zamu sake ganin juna? daman ashe da rabon zamu sake ganawa da juna, Allah nagode maka daka bayyano mun Ƴar Amana ta, ina kika shiga ne inata neman ki, nayi kewar ki sosai...." Ƴar Amana itama kuka take sai yanzu take ƙara jin takaicin rashin iya maganar ta domin tana da maganganu tarin-tarin a bakin ta, ganin bazata iya cewa komai ba yasa ta ƙara rungumar Baiwar ALLAH sosai, sai da suka gama koke-koken su da kukan su tukun hankalin su ya koma kan mutanen falon, Abbah ya ce "Daughter ya isa haka ku nemi wuri ku zauna..." Baiwar ALLAH tana riƙe da hannun Ƴar Amana suka zauna a tare wuri ɗaya... Abbah ya ce "daman kun san juna ne?..." Jinjina kai Baiwar ALLAH tayi... Abbah ya ce "aina ku ka san juna?...." Baiwar ALLAH anan ta kwashe labarin zaman su a gidan marayu tin suna yara har kawo Ƴar Amana da akayi tana jaririya, da kuma wahalar da Yallaɓai ya basu har aka sace Ƴar Amana, da jinyar da tayi Madam Aliya ta kaita asibiti har zuwa wannan lokaci bata ɓoye musu komai ba, sannan ta ƙara da cewa "sai yau Allah ya haɗa ni da Ƴar Amana...." Kowa ya jinjina labarin su, abun tausayi kowa sai da ya tausaya musu banda Mamie da ta toshe kunnen ta da earpiece ta ƙura volume waƙar da take ji, duk abubuwan dake faruwa bata san mai ake tattaunawa akai ba... Aunty A'isha gaba ɗaya hankalin ta ya kasa kwanciya, jikinta ne yake kakkarwa kamar zazzaɓi ne yake shirin rufan ta, tasa a ranta cewa Ƴar Amana ɗiyar ta ce, tin daga labarin ta da taji ta ɓata ne tana jaririya... Aunty Yolash ce ta lura da halin da Aunty A'isha ta shiga gaba ɗaya ta ƙanƙame jikinta sai rawar sanyi take tayi... Aunty Yolash itama taji hakan a ranta ta ce "am Daughter ina so nayi miki wata tambaya..." Baiwar ALLAH itama Aunty Yolash ɗin take kallo, Aunty Yolash ta ce "akwai wani zane akan cinyar Sarah shin kin san da shi ko kuma babu a lokacin da take jaririyan?..." Cikin rashin fahimta Baiwar ALLAH ta ce "wata Sarah?..." Aunty Yolash ta ce "au to Ƴar Amana...." Jinjina kai Baiwar ALLAH tayi tare da faɗin "tabbas akwai zanen masarauta akan cinyarta kuma tin tana jaririya da aka kawo ta dashi ne...." Aunty Yolash kallon Aunty A'isha tayi suka haɗa ido, nan da nan idon Aunty A'isha ya kaɗa yayi jawur... Aunty Yolash girgiza mata kai tayi akan ta dakata kar ta nuna alamun komai... Abbah ya ce "toh Alhamdulillah tinda Allah yasa yanzu kun ga junan ku, ke Allah ya bayyanar miki da iyayenki itama ki tayata da addu'a Allah ya bayyano mata da nata..." Abbah ya kuma cewa "ina so na kawo ƙarshen rashin fahimtar juna da ake a cikin gidan nan domin abun ya ishe ni haka, tsakanin Razhdeen da Roshan, to shi dai Razhdeen ba shine mai matsalar ba domin tsawon watanni ba'a cikin hayyacinsa yake ba..." Abbah ya kalli Roshan sannan ya ce "ga wannan memory inaso kaje ka saka a jikin plasman akwai abinda nake son gani..." Roshan ba mu su haka ya karɓi memory sannan yaje ya saka a jikin plasman tare da maida film ɗin da ake kalla zuwa USD... ya koma yaje ya zauna. Abunda aka fara kalla shine a lokacin da Pinky da Rukky suka je suka ajiye kwalin gift a bakin ƙofar falon part ɗin Roshan sannan sukayi knocking tareda guduwa.... Pinky da Rukky ganin haka yasa suka zazzaro ido waje cike da fargaba da tsoro haka zuciyoyinsu suke bugun uku-uku... Daga baya Baiwar ALLAH ta buɗe tare da ɗauka tayi ciki... Abbah ne ya danna stop tare da kallon su ran a ɓace ya ce "mai ku ka ajiye..." Baiwar ALLAH itama idonta akan plasman ganin ba Razhdeen ne ya ajiye ba yasa tayi kallon yanda yake a zaune... Pinky kame-kame ta fara yi ganin haka yasa Abbah ya darara musu tsawa, a ruɗe Rukky ta ce "wallahi Abbah zan gaya maka gaskiya, kyautar Abaya ce muka rubuta cewa Uncle Deen ne, sannan akwai letter a ciki..." duk ta zayyano abinda suka rubuta a cikin takardar... Jinjina kai Abbah yayi sannan ya danna remote suka cigaba da kallo, Iya wurin da aka yi abinda bai dace ba aka yanke, already sai da Abbah ya kalli video nan tass kafin ya yanke wurin da akayi ta'addanci tukun, Gani suka yi Baiwar ALLAH ta fito ta shiga mota security ya fita da ita... Nan ma Abbah stop ya danna sannan ya kalli Baiwar ALLAH ya ce "Daughter ina kike je a lokacin?..." Itama Baiwar ALLAH fara magana tayi tana faɗin "a lokacin da na karanta saƙo na fita ne akan naje na samu Razhdeen da maganar sharrin da ya mun, nayi tunanin shine ya ajiye mun saƙon...." Nan ma Abbah jinjina kai yayi sannan ya kunna suka cigaba da kalla, Showing wurin da Razhdeen yazo akayi ka yanda suka tsaya a falo suka yi rikici akan ta bayyana masa yanda Reemah take, a wurin har Razhdeen ya mare ta.. Sai a lokacin Roshan ya gane cewa anan Razhdeen yasan cewa Baiwar ALLAH Amreesh ce, domin a lokacin da Razhdeen yasan ita ce Amreesh fita yayi jiki ba ƙwari ya fice, daga nan Razhdeen bai ƙara zuwa ba sai ƙiran da Baiwar ALLAH tayi masa, duk akwai video anan, a cikin video bedroom ɗinta ne kawai babu CC Camera, amma bayan Baiwar ALLAH ta ja shi ciki acikin video ba da wata manufa suka shiga ciki ba domin tana kuka tana masa magiya akan ya bata sarƙar har suka shiga ciki, kuma alamun abu zata nuna masa, daga baya sai ga su Pinky da Rukky suka shigo hannunsu riƙe da wani kwalbar turare, ana kallonsu suka tsuguna ta ƙasi suna feffeshe turare ta cikin ƙasin ƙofa fuskar su ɗaure da facemark... daga nan suka gudu, bayan awa sai ga Roshan da Ummy sun shigo tare anan ake kama su... Abbah ya tsayar da video idonsa akan su Pinky ya ce "meye abinda ku ka fesa musu?..." Rukky ta ce "feeling fresh..." Abbah ya ce "ku je ki ɗauko mun na gani..." Rukky ce ta miƙe jiki ba ƙwari taje ta ɗauko ta miƙawa Abbah, Abbah karɓa yayi tare da karanta ƙarfin yanda turaren yake da ƙa'idojinsa, Kowa sai da ya karɓa ya duba, duk sun san amfanin wannan turaren bashida kyau wurin fitar da mutum a cikin hayyacinsa, mungun abu ne, yanzu haka kana feshe falo cikin ƙanƙanin lokaci zai fitar da kowa daga cikin hayyacinsa, kowa zai nemi ɗan uwansa ne ba tare da an sani ba.... Roshan wani irin yawu ya haɗiya cikin takaici yake bin yaran da kallo, Kowa sai da yaji haushin su, amma ta wani ɓangaren Roshan ya yi magana akai, cewa "Amma Abbah shiga ɗakin da suka yi ne ya bawa yaran damar aiwatar da abun, me zai sa su shiga bedroom ba muharraminta ba?..." Abbah ya ce "zan ɗau ƙwaƙƙwaran hukunci akan wannan al'amarin, zaku gane kuran ku, ina dai ku iblisai ne ko? zan yi maganin ku..." Rukky ce ta fara kuka tana faɗin "dan ALLAH Abbah kayi haƙuri wallahi Pinky ce take sawa ayi..." Bata ƙarasa maganar ba Abbah ya daka mata wani irin gigitaccen tsawa tare da faɗin "ki mun shuru, ku jira sakamakon ku..." Sannan Abbah ya kalli Baiwar ALLAH ya ce "Daughter kiyi haƙuri kinji, ni dai nasan bazaki taɓa aikata wannan da saninki ba, amma zan ɗau mataki akan su kar ki damu...." Baiwar ALLAH tana kuka ta ce "ba komai Abbah ni na yafe musu kawai abar su, komai ya wuce....." Abbah ya ce "bazan taɓa barin su ba domin sun aikata laifin da basu cancanci yafiya ba...." Ƴar Amana itama kukan take ganin abinda ya faru tsakanin Baiwar ALLAH da Razhdeen, taji ƙuna sosai a ranta da kuma bugun zuciya, jure wa kawai take gaba ɗaya idanuwanta sun kaɗa sunyi jawur..." Iyayen Baiwar ALLAH kuwa ganin abinda ya faru da Razhdeen ne yasa basu wani damu ba, daman can ita ɗin nashi ne, amma tinda yanzu bata tare da Roshan sun mayar da alƙawarin da suka ɗau na haɗa Baiwar ALLAH da Razhdeen...." Duk kowa babu wanda yaji daɗin abinda ya faru amma ƙaddara ta riga fata... Ƴar Amana ganin bazata iya jure wa ba yasa ta miƙe tare da nufan hanya zata koma ciki tabar falon, tazo wuce wa tayi tuntuɓe da ƙafar Maamie ta kife a ƙasin carpet... Maamie a fusace ta cire earpiece ɗin kunnen ta takai hannu ta ɗago Ƴar Amana ta zabga mata mari... Kowa na falon a ruɗe suke bin Maamie da kallo cikin ɓacin rai, Ƴar Amana ɗagowa tayi takai idonta kan Maamie wacce take ta zuba masifar ta, haɗa ido suka yi ana Maamie kamar an ɗauke mata wutar kanta ta tsaya cakk, idonta a cikin ƙwayar idanun Ƴar Amana, Maamie gani take wani hayaƙi yana fita daga cikin idanuwanta kuma ta kasa ɗauke kanta daga kan Ƴar Amana, itama Ƴar Amana idonta ne ya ƙafe wuri ɗaya a cikin na Maamie hayaƙi yana fita, idanuwanta sun zama jajawur hatta ƙwayar baƙin idanun ya ɓace sai zallar jaaaaa......... Typing ✍️ *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 31 to 35 Gaba ɗaya mutanen falon miƙe wa tsaye suka yi suna kallon ikon ALLAH, Banda Razhdeen dake zaune babu halin tashi, cike da mamaki suke kallon Maamie da Ƴar Amana ga yanda ko wannen su suke ƙafe guri guda, Ƴar Amana idanuwanta ne suka yi jawur bayan hayaƙin nan ya gama fita a lokacin Ƴar Amana ta yanki jiki ta faɗi sumammiya... Maamie a ruɗe ta dafe goshin ta tare da faɗin "wayyo kaina, kaina ciwo, zai fashe wayyo Allah Boka kar ka bar hakan ta faru, Boka! Boka!! Boka!!! ka taimake ni, wayyo ka taimake ni Bokaaa...." Nan ta tintsire da dariya tana tafa hannayen ta tare da faɗin "haba! haba Ghali ni da nace ka je ka bisine Reemah da ranta shine ka barta a raye? Boka fa ya sanar mun cewa duk lokacin da na haɗu da Reemah zan haukace, wayyo Allah Ghali ka cuce ni, Reemah dana rufe mata baki shikenam yau asiri na zai tonu, Reemah ta bayyana mun a gaba na...." Baiwar ALLAH tafo wa tayi da gudu ta tsuguna a yanda Ƴar Amana take a kwance bata san halin da take ciki ba, Jin yanda Maamie take ta ɓare-ɓaren maganganu yasa Abbah faɗin "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allahumma ajurni fi musibati wa akhlifli khairan minha...." Mai martaba kuwa idanuwan sa a waje yanda yake da zazzaro su sai bin Maamie yake da kallo jin irin aika-aikan da tayi wa ɗiyar sa Reemah, kuma sai tonawa kanta asiri take tayi... Duk abinda ya faru da Ƴar Amana tin haihuwar ta Maamie bata ɓaye ba, har sawa da tayi a cire wa Aunty A'isha mahaifa da tayi duk sai da ta faɗe su... Daman Boka ya sanar cewa duk lokacin da suka haɗa ido huɗu da Reemah toh hankalinta zai gushe duk wata gaskiyar da ta ɓoye sai ta faɗe su.... Kowa a falon sai da ya jinjina wa mugunta da makircin Maamie, Aunty A'isha tsabar yanda zuciyar ta yake bugawa da harbawa da ƙarfin gaske yasa gaba ɗaya ta fita hayyacinta, har ƙoƙarin shiɗewa take, numfashi yana shirin ɗagewa.. Aunty Yolash ce tazo yanda take zaune ta zauna kusa da ita tare da rungumar ta a jikin ta tana rarrashinta, Duk babu wanda yaji daɗin wannan al'amarin, duk zama sukayi suna sauraron abubuwan da Maamie take faɗi na makircin ta... Madam Parveen mahaifiyar Baiwar ALLAH da sauran ƴan uwan ta duk jin labarin suke kamar a Film domin basu taɓa ganin irin wannan al'amarin a zahiri ba... Yanzu ta tabbata Ƴar Amana ita ce Reemah, tana kwance akan cinyar Baiwar ALLAH tana shafa mata sumar kanta... Mai martaba jikinsa ne yake zaƙami gaba ɗaya ya rasa yanda zai sa kansa, ji yake kamar ya kashe Maamie a yanzun nan... Maamie bayan ta gama maganganun ta ba tare da ta san abinda take faɗi ba, tayi shiru tana kuka domin ba'a son ranta ta faɗi duk waɗannan maganganun ba, kamar wanda ake matsar bakin ta... Falon tsit akayi sai ƙaran kukan Aunty A'isha kake ji, daga baya suka ji an turo ƙafar falo, duk kallon bakin ƙofar suka yi, wacce suka gani ne yasa Mai martaba yayi saurin miƙe wa tsaye idanu duk sun kaɗa sunyi jawur, A ruɗe ya furta "Maimuna...." Itama Maamie tashi tayi tsaye tana nuna bakin ƙofa da yatsa murya na kakkarwa take faɗin "wayyo fatalwa! fatalwa!! fatalwa!!! innalillahi ta mutu fa, meyasa kika dawo? au kin zo ne ki tona mun asiri? to a hir ɗin ki..." Maimuna ƙarasa shugowa tayi cikin falon tana murmushi zuciyar ta fari sol, ranar da take jira yau gashi ta zo kuma tazo a dai-dai... zama tayi akan kujera tana kallon Mai martaba sannan ta ce "ka zauna mana king..." Mai martaba zama yayi itama Maamie zama tayi hawaye ya gagara tsayuwa, idonta akan Maimuna gaba ɗaya hankalinta ya kasa dawo dai-dai, jikinta har wani ɓari yake cike da tsoro da fargaba.. Maimuna kallon kowa tayi na cikin falon da wanda ta sani da waɗanda bata sani ba duk suna nan, sannan ta ce "kuyi haƙuri kunyi mamakin gani na ko?..." Abbah jinjina kai yayi tare da faɗin "dole zamu yi mamaki, tsawon shekaru kin ɓata babu labarin ki sai daga baya muka ji cewa guduwa kika yi sakamakon kama wani namiji daban akan gadon Auren ki, yanzu kuma wannan la'ananniyar matar tana ƙiranki da fatalwa, bamu sani ba ko mutuwa kika yi..." Murmushi Maimuna tayi sannan ta ce "Ghali ka shugo mana..." Sai ga wani ya shugo jiki ba ƙwari haka ya ƙaraso cikin falon ya zauna akan carpet, Mai martaba yayi mamakin ganin yaron gidansa a cikin wannan al'amarin, daman shine ɗan hannun daman Maamie, ita take saka shi yayi duk abunda tace... Maimuna ce ta fara kora bayani kamar haka, "nasan dai kun san ni ce masoyiyar Mai martaba tin farko, kuma ni ce yayi burin Aura, ita kuma Maamie ƙawata ce sosai, tare muka tashi tin yarinta, sai dai kuma ita Allah ya yo ta a gidan talakawa, kullum tana cikin damuwa da tashin hankali musamman lokacin da taji labarin Aurena, na ɗauka saboda zanyi Aure ne yasa ta kasa kwantar da hankalin ta, hakan yasa na nemi alfarma a wurin Mai martaba cewa inaso ya haɗa mu ya Aura ni da Maamie, a lokacin ya nuna mun rashin yardar sa, amma na dage akan saiya Aure ta saboda zata fi samun kulawa da nutsuwa, nayi tunanin Maamie mutumiyar kirki ce ashe mai fuska biyu ce, Bayan mai martaba ya Aure mu a lokacin na ɗauki Maamie tamkar ƴar uwata, na ɗauke ta da zuciya ɗaya, ashe Maamie ƙulle-ƙulle take akan ta fitar dani daga gidan Mai martaba, Duk wani sirri na sai na gaya wa Maamie, duk abunda ya faru dani sai na sanar mata, duk hirar da mukayi da mai martaba indai akan abinda ya shafi rayuwar mu ne gaba ɗaya saina sanar mata, A lokacin da na samu juna biyu kafin na sanar wa mai martaba sai da na fara sanar wa Maamie, ta nuna farin cikinta matuƙa a fuska amma a cikin zuciyar ta tamkar ana hura wuta ne, duk ban gano hakan ba, na sanar mata cewa inada ciki amma ina jiran Mai martaba ya dawo shima saina sanar masa, Maamie ta ce mun kada na sanar masa yanzu na bari nayi masa bazata, sai dai yaga cikin ya fito, na amsa mata da hakan, bance masa inada ciki ba, Maamie daga lokacin ta ɗaura ɗamarar yaƙinta akaina, wata rana na shiga bathroom yin wanka ashe Maamie ta ƙira wani mutumi gidan suna jiran na shiga wanka ta turo mutumin, mutumin ya shigo ɗakin da nake tare da cire rigar jikinsa ya hau saman gado na ya kwanta dai-dai lokacin da Mai martaba ya dawo cikin masarauta, kuma dake a ranar kwanan ɗaki nane anan ya tarar da mutumin yana kwance yana daddanna wayar sa, jin hayaniya yasa nayi saurin fitowa daga cikin toilet, abunda na tarar ne ya tayar mun da hankali, daga lokacin mai martaba yasa aka kama mutumin, ni kuma bai ƙara saurarona ba, ya ƙaurace mun, ya ɗauki tsanar duniya ya ɗora mun, duk ban kawo a raina cewa tarkon Maamie bane, ita kuma Maamie bata daina bani kulawa ba na makirci, kullum tana ɗakin da nake tana shan ciki na, a lokacin da nake baƙin cikin mijina ya ƙaurace mun ita kuma a lokacin kamar anyi ma ta bushara da gidan Aljanna ne, Bayan kwana biyu akwai ƙasar da Mai martaba ya tafi kuma sai yayi kwana biyu kafin ya dawo, cikin dare ina kwance na fara jin bugun ƙofar ɗakin da nake, ina buɗe wa naji an shaƙo wuyana tare da ɗaure baki na da wani ƙyalle akayi waje da ni, inaji ina gani ba halin yin ihu haka aka sakani a cikin mota aka fita dani, ba'a sauƙe ni a ko ina ba sai a cikin daji, haka na buɗe ido na ganni a cikin wannan halin, baki na kuma yana ɗaure da ƙyalle sai ido da nake bin wurin da kallo ga hasken mota da ya haska wurin sakamakon duhun dake wajen, Idanu nane suka fara sauƙa akan Maamie wacce ta tsaya mun a gaba, sai kuma wannan mutumin wato Ghali, nayi mamaki sosai domin ban taɓa tunanin Maamie zata iya aikata mun wannan ta'addanci ba sai ranar, tafi so ta zauna ita kaɗai a gidan Mai martaba duk da ni na sa aka aure ta, sannan babban baƙin cikinta shine cikin dake jikina har na tsawon wata huɗu, ina ji ina gani ga ƙaton ramin da aka tona kafin zuwa na yanda za'a bisine ni da raina, Ina ɗaɗɗaure da igiya hannu da ƙafa suka hankaɗani ciki tare da zuba mun ƙasa, Maamie tana tsaye Ghali ya gama rufe ni da ƙasa saida suka shafe ni da ƙasa kafin Maamie taje ta shiga mota ita da Ghali suka tafi, daga lokacin ban ƙara sanin a inda nake ba, ashe daga baya Ghali ya dawo ya buɗe ni ba tare da sanin Maamie ba, yasa aka fitar dani daga ƙasar Jidder gaba ɗaya, Bayan farfaɗowa ta Ghali na gani shi yake zuwa dubani a yanda ya killace ni, ya sanar mun halin da ake ciki sannan ya cigaba da bani kulawa, ita kuwa Maamie a tunanin ta an rufe shafi na, a ƙasar da na cigaba da zama shine ƙasar Iran, anan har cikina ya tsufa na haifi jaririn ɗana, amma kuma duk wasu bayanai na masarautar Jidder ina sani, nasan duk halin da ake ciki a masarauta, har yaro na ya girma a lokacin da naji labarin Mai martaba ya ƙara Aure ba ƙaramin tausayawa Amaryar sa nayi ba, dan ma ƴar sarkin ƙasar Niger ce su ma sunada ƙarfi amma duk da hakan bai hana Maamie ƙuntata mata ba, duk biye-biyen bokayenta na sani, tayi yunƙurin hana Indo ɗaukar ciki amma sai dai bokan bashida ikon aiwatar da aikinsa akan Indo saboda itama iyayenta basu barta haka ba, amma su ba ta hanyar bin boka ba, har Allah yasa Indo ta haihu a lokacin naji labarin an cire mata mahaifa kuma nasan makircin Maamie ne, a lokacin da tasa aje a bisine jaririya Ghali bai bi maganar ta ba haka ya wuce Nigeria da ita ya kaita gidan marayu, duk halin da Reemah ta shiga duk akan idon mu ne, da lokacin da Razhdeen ya tsince ta, sai dai kuma ni kafin zuwa wannan lokacin na rasa yarona, ba mutuwa yayi ba ɓata yayi ban sani ba shin sace shi akayi ko kuma mutuwa yayi Allahu a'alamu, Ni dai na barshi ne akan zai je ƙasar jidder can masarauta, akan zai bayyana cewa shi ɗan mai martaba ne sannan zai sanar cewa ina nan da raina, bayan ya tafi nake jin labarin anyi kidnaping ɗin su, nayi shige da fice amma har yanzu banji labarin sa ba, da haka har na haƙura da Yareema Ashmar mai shekara 28....." Maimuna fashewa tayi da matsanancin kuka bayan ta gama bada labarin abinda ya faru da ita.. Ghali dake zaune shine shaidar hakan domin shi yake kai mata wasu bayanai na cikin masarauta, fuska biyu yayi yana ɓangaren Maamie sannan yana ɓangaren Maimuna amma ita Maamie yana zaune ne da ita saboda duk abubuwan da zata aikata na sirri zai ɗauka yakai wa Maimuna.... Mai martaba yana zaune yayi tsumu da shi ga yanda hawaye yake ta zuba daga cikin ƙwayar idanuwansa, Aunty A'isha da gudu ta zo yanda Ƴar Amana take a kwance saman cinyar Baiwar ALLAH ta ɗago da ita tare da rungumar ta jikinta sosai tare da fashewa da matsanancin kuka tana girgiza ta tare da faɗin "Reemah ta ta dawo gare Ni, Allah na gode maka, wayyo Allah Reemah ta, Allah na gode maka daka bayyanar mun da Reemah...." Abbah rasa abun cewa yayi sai jinjina kai yake tayi domin wannan al'amarin babba ne, Duk mutanen falon babu wanda bai tausaya wa Maimuna da Reemah ba, ita wannan an rabata da mijinta ita kuma Reemah an rabata da iyayenta... Mai martaba yana kuka ya ce "Maimuna meyasa baki dawo gare ni ba?..." Maimuna itama kukan take ta ce "Yaro na yaso ya bayyanar da ni Allah bai so ba, ni kuma ina fargaban bayyana kaina saboda Maamie zata iya ɗana mun wani tarko kuma du, ina tsoron Allah ina tsoron Maamie, matar da zata iya kashe mutum ai babu sauran imani a tattare da ita...." Maamie wani irin tsalle ta daka tare da miƙewa tsaye tana jumping tare da faɗin "hEheeee Ahayyeeee nanayeeee Anayi muna jin daɗi ana bariii muna jin haushi, duk saina kashe ku wallahi tallahi, na rantse da Allah sai na kashe ku gaba ɗayan ku...." Pinky da Rukky a zabure suka tashi cikin tsoro suka nufi yanda Hajiya Kilishi take a zaune duk suka rurrungume ta, itama Hajiya Kilishi rungumar su tayi sosai jin yanda take ta rantsuwa zata kashe su, kowa tsoro ne ya bayyana akan fuskar sa banda mazan wajen, Uwar masu gida itama da gudu taje da rungumi Aunty Yolash sosai jikinta har wani kakkarwa yake, Madam Parveen itama a zabure tazo ta jawo Baiwar ALLAH a jiki ta rungumeta tana faɗin "dan Allah dan Annabi ku bata haƙuri kar ta kashe mu..." Ammy rufe idonta tayi tana jero Addu'o'i.. Roshan cikin fushi da takaici yake bin Maamie da kallo domin abubuwan da ta aikata ko wanda bashida addini iya kaci... Razhdeen yana zaune duk yana jin abubuwan da yake faruwa amma ba halin motsawa... Maamie tana cikin haukar ta Mai martaba ya zuciyo ya tashi a fusace ya zabga mata wani irin gigitaccen mari har sai da ta kife akan kujera, haka yasa hannu ya shaƙe mata wuya yana faɗin "kafin ki kashe su ni zan fara aika ki lahira, na tsane ki wallahi...." Abbah da Chief Suraj ne suka taso su na ƙoƙarin janye Mai martaba, Ramlat itama duk ta wanke fuskar ta da hawaye, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi kanta a sunkuye, duk haukar da Mamie take yi bata ɗago ba balle ta kalli yanda take, duk wannan zaluncin da Mamie ta aikata Ramlat bata san da labarin ba.... Abbah ne ya ƙira waya, ba jumawa sojojin sa suka shigo su uku ƙarfafa, aka sanar musu cewa a tafi da Mamie a kaita kotu, duk abunda kotu ta yanke mata shikenam duk da bata cikin hankalin ta yanzu..... Sannan Abbah ya ce wa ɗaya daga cikin sojoji cewa ya tafi da su Pinky can headquarters a je fa su ɗakin duhu tare da gana musu azabar da sai sun kusan mutuwa, Abbah ya lissafo irin hukuncin da za'a rinƙa gana musu, sannan a tsayar da su, su kwana a tsaye, da zaran sun zauna a jona musu shocking a jiki, kullum aita gana musu azaba ba ƙaƙƙautawa sannan abinci sau ɗaya za'a basu su ci sai kuma washe gari har sai sun gane kuran su.... Ammy ta ce "a'a wannan azabar ai tayi musu tsauri su na ƴaƴa mata..." Abbah ya katse ta da cewa "babu ruwan kowa, sai yanda naso ayi da su..." Hajiya Kilishi tana hawaye haka take kallon Abbah domin hukuncin yayi tsauri duk da sun cancanci hakan, Pinky da Rukky haka suke ƙanƙame jikin Hajiya Kilishi suna faɗin "wayyo Allah Mommy kar ki bari a tafi da mu, ki taimaka mana Mommy, wallahi kashe mu zasu yi wayyo Allah...." Daƙer Sojan ya fincike su daga riƙon da sukayi wa Hajiya Kilishi, ita kuwa kanta na kallon gefe tana jin yanda suke ta faman rirriƙe ta amma bata kula su ba sai zubda hawayen da take, da haka aka fita da su suna ihu, Maamie kuwa itama an daɗe da ficewa da ita, ita wannan direct zaman prison zata yi.... Bayan awa guda kowa ya gama jimamin abinda ya faru, suna cikin jajanta wa juna suka fara jin kuka ana faɗin "Mama! Mama!! Mamana!!! Mamana!!!!...." Duk juyowa sukayi suna kallon yanda Ƴar Amana take a kwance kan cinyar Mahaifiyar ta akan kujerar falon, Baiwar ALLAH zaro ido waje tayi baki a buɗe tana kallon Ƴar Amana ganin bakinta ya buɗe, babu abinda take furtawa illa Mamana.. Kowa na falon farin ciki ya shiga yi, Mai martaba kamar bazai bar duniya ba tsabar farin cikin bayyanar ɗiyarsa sannan bayan ita akwai namiji wato Yarima amma sai dai zasu binciko a yanda yake... Aunty A'isha shafa fuskar Ƴar Amana take da murmushi akan fuskar ta, Itama Maimuna murmushi take tana sharar hawayen farin ciki, yau ga Reemah da iyayenta... A hankali Ƴar Amana take ƙoƙarin buɗe idanuwan ta, har sai da ta gama buɗe su gaba ɗaya, babu fuskar da ta fara gani illa na mahaifiyar ta wato Aunty A'isha dake ɗauke da ita akan cinya... Daƙer take shirin tashi zaune har sai da Aunty A'isha ta tallafa mata tukun ta iya tashi, tana kallon kowa na falon ɗaya bayan ɗaya... maida kallon ta tayi kan Baiwar ALLAH taga yanda take ta mata murmushi itama mayar mata da martani tayi lokaci guda kuma ta tuno da video da ta gani a plasman ita da Razhdeen, da sauri ta kawar da kanta gefe, Aunty A'isha ce ta riƙo fuskar ta da hannu biyu suna fuskantar juna ta ce "Yarinya ta Reemah yau ga ki a gaban iyayen ki da kika rasa tin haihuwa, ni ce mahaifiyar ki na halal, ni ce wacce na haife ki a cikina Reemah..." Ƴar Amana kallon Aunty A'isha take itama idonta ya cicciko da ƙwallah, sai ga Mai martaba shima yazo ya zauna a gefen ta tare da riƙo hannunta yana faɗin "Shalele..." da murmushi akan fuskar sa... Jan hannun rigar sa yayi sama sai ga zanen tambarin masarauta akan dantsensa, Ƴar Amana idonta akan zanen ganin irin na kan cinyar ta sak yasa ta washe baki tana dariya bata san lokacin da ta furta "Babaaa...". ta rungume shi sosai tana kuka... Aunty A'isha itama rungumar ta tayi ta haɗe Mai martaba da Reemah duk ta rungume su tana kukan farin ciki... Kowa na falon bai san lokacin da ya tsinci kansa cikin farin ciki ba, itama yanzu Ƴar Amana tasan su waye iyayenta... Maimuna itama tsabar farin ciki haka ta tashi ta nufi wurin su ta durƙusa tare da sa hannu ta rungume su gaba ɗaya, daga Mai martaba har Aunty A'isha sai Reemah da suka sakata a tsakiya, shima Mai martaba hannu yasa ya ɗora akan gadon bayan Maimuna ya rungume ta haka itama Aunty A'isha tasa hannu itama ta rungumi Maimuna duk suka haɗe kayuwan su guri guda su huɗu... Baiwar ALLAH ganin yanzu burikansu ya cika yanzu bata san lokacin da ta fashe da kuka ba ta rungumi Mamanta itama, Madam Parveen wacce akafi sani da Zainab itama rungumar ta tayi sosai a jikin ta... Bayan wasu ƴan mintuna kowa ya dawo cikin nutsuwar sa, Abbah ne ya kalli Maimuna sannan ya ce "yanzu haka zamu iya samun photon Yarima a wurin ki?..." Maimuna da sauri take ɗaga kai sama tana faɗin "eh! eh akwai suna cikin wayata bari na duba..." haka ta fara daddanna wayar ta, cikin lokaci ƙanƙani ta taso tare da bawa Abbah wayar ta ce "gashi nan shine..." Abbah ƙarewa photon kallo yayi sannan ya ce "Insha Allahu zamu nemo shi..." Roshan ne ya taso ya karɓi wayar yana dubawa, yana ganin photon ya zaro ido waje tare da faɗin "wannan ai GUESS ne, yana daga cikin mutanen da Razhdeen ya kamo acan daji suna safaran Ƴar mata, yanzu haka suna can gadurum na sojoji, yaron kullum da baƙar hula akan fuskar sa, sanadin kamashi ne yasa muka ga fuskar sa shine daman Yarima?...." Maimuna haka zuciyar ta yake bugu da ƙarfin gaske jin suna safaran Ƴan mata, haka shima Mai martaba da sauri ya karɓi wayar yana dubawa gaba ɗaya ya zamo kalar tausayi..... Abbah ya ce "ina buƙatar ganin sa a yau ɗin nan..." Nan ya ɗauki wayar sa yayi dialing call bugu ɗaya aka ɗauka ya kara a kunne yana faɗin "hello akwai yaron da ake ƙiransa da Guess ina son ganinsa yanzu, a kawo mun shi..." daga nan Abbah ya katse ƙiran... Chief Suraj ne yayi gyaran murya tare da faɗin "Halaluyya! a yau na shiga wani tashin hankali dana ji labarin wasu daga cikin mu abun tausayi amma yanzu Masha Allah tinda an kawo ƙarshen komai, sannan nayi matuƙar farin ciki sosai ganin yanda iyaye suka haɗu da ƴar su na taya ku farin ciki sosai...." Mai martaba shima cewa yayi "Alhamdulillah kuma muna taya ku cikar family, mun gode wa Allah...". Gaba ɗaya kowa ya taya ƴan uwansa murna... Daga baya ne Chief ya sanar cewa zasu koma ƙasar U.S... Abbah ya ce "kar dai da Daughter nah zaku tafi?..." Chief ya ce "duk tare zamu tafi, babu abinda zamu ce sai dai Allah ya saka da alkhairi, kun riƙe mun yarinya tamkar ku kuka haife ta, thank you very much...." Abbah ya ce "ba komai ai duk ƴaƴa ne, kuma Insha Allahu zamu rinƙa zuwa muna duba ku kafin Razhdeen ya samu lafiya sosai...." Baiwar ALLAH cikin rashin fahimta take binsu da kallo a cikin ranta tana faɗin "meyasa za'a sako Razhdeen a cikin lamarina, shin idan ya samu lafiya me zai faru?..." Chief ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "Daughter zamu iya tafiya ko?..." Baiwar ALLAH girgiza kai tayi tare da faɗin "ni da Mommy bazamu tafi ba..." Chief cike da mamaki yake kallon ta ya ce "why?..." Ta ce "saboda mu ɗin musulmai ne, idan kuna son zama da mu to kuma ku musulunta, Daddy Kai da Yaya Rakesh kune ku ka saura baku musulunta ba...." Chief sai da yaji bugun zuciya da sauri ya kalli Madam Parveen cike da mamaki ya ce "wai ke ɗin kin musulunta ne?..." Madam Parveen tana hawaye ta ce "ey na musulunta na koma suna Zainab..." A ruɗe Chief ya miƙe tsaye tare da faɗin "whattttt?...." Abbah shima miƙe wa yayi tsaye ya nufo wurin da yake tare da dafa kafaɗarsa yana faɗin "relax Chief, inaso kabi komai a hankali...." Chief cikin ɓacin rai ya ce "wani irin robish ne wannan, kin musulunta ba tare da kin sanar mun ba? ita Amreesh daman nasan dole ta zauna cikin musulunci saboda wanda zata aura musulmi ne, tin tana ƙarama nayi alƙawarin ta a musulmi, Razhdeen zata Aura....." A ruɗe Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye itama tana zazzaro ido waje tare da faɗin "meeeeeeeee?...." Itama Ƴar Amana bata san lokacin da ta zabura ta miƙe tsaye ba, zuciyar ta na bugun uku-uku.... Lokaci guda kan Baiwar ALLAH ya sara ga wani irin tashin zuciya da yake shirin hargutsa mata tunani, yunƙirin amai ta soma yi, da sauri tasa hannu tana toshe bakin ta ganin bazata iya riƙe aman ba yasa ta ru ga da gudu ta shige room ɗinta, kai tsaye toilet ta shige... Madam Parveen ganin haka yasa ta bi bayanta da sauri itama ta shige cikin room ɗin, a toilet ta tarar da Baiwar ALLAH sai kwarara amai take tayi a cikin sink... sai da ta gama mai isar ta tukun ta wanke bakinta ta juya tana kallon Mommyn ta, jikinta har wani ɓari yake yana kakkarwa alamar zazzaɓi ne ya rufe ta, Madam Parveen hannu tasa tana taɓa jikinta ganin jikin ya ɗau zafi sosai yasa ta faɗin "Ya Allah! zazzaɓi ne a jikin ki fa, meyasa baki ce baki da lafiya ba?...." Riƙo hannun Baiwar ALLAH tayi suka yi waje, kai tsaye falo suka koma, Madam Parveen ce ta sanar cewa Daughter bata da lafiya... Abbah a ruɗe ya ce "ba lafiya kuma?..." ya kalli Roshan sannan ya ce "kaga kaje ka duba ta shin me yake damun ta..." Baiwar ALLAH kifar da kanta tayi akan cinyar ta tana tariyo maganar Daddyn ta na cewa Razhdeen zata Aura, ɗagowa tayi a gigice tana faɗin "ni wallahi bana son Razhdeen, bazan Aure shi ba...." Roshan ne yazo gaban ta tare da riƙo hannunta ya ɗagota suka nufi medicine room acan kayan gwaje-gwaje yake, Baiwar ALLAH tana kuka idonta akan Roshan da haka suka tafi... Chief cike da mamaki ya kalli Abbah sannan ya ce "shin Auren Roshan da Amreesh akwai ne ko babu?..." Abbah girgiza kai yayi tare da faɗin "a gaskiya babu, saki ne anyi shi yanzu tsawon wata huɗu kenam, ta gama iddar ta...." Acan kuma Roshan ne ya duba ta, gaba ɗaya jikinsa ba warki domin ya tabbatar da wani abu, nan da nan idonsa ne suka cicciko da ƙwallah ga yanda suka kaɗa suka yi jawur, Baiwar Allah ganin yanda ya chanza lokaci ƙanƙani yasa zuciyar ta bugawa ... Murya ciki-ciki ya ce "kwanta akan gado...." Kamar yanda yace haka tayi, ta hau ta mimmiƙe idonta akan sa, hannu yasa ya buɗe mata riga idonsa akan cikinta, anan yayi mata scanning ya gama tabbatar da komai, jinjina kai yayi sannan yasa hannu ya ɗago ta yaja ta suka fice, suna isa falo ya miƙa wa Abbah wata takarda... Abbah karɓa yayi tare da dubawa a ruɗe ya ce "whattt? pregnant? har na tsawon wata huɗu?..." Baiwar ALLAH a ruɗe ta ɗago tana kallon Abbah tare da zazzaro manya-manyan idanuwanta, Roshan kuwa kawar da kansa gefe yayi yana zubda hawaye... Ƴar Amana cikin rashin fahimta take bin su da kallo domin a tunanin ta cikin Roshan gare ta saboda taji ana batun rabuwar Aure a tsakanin su.. Abbah idonsa ya sauƙe kan Roshan yana faɗin "shin cikin ka....." kafin Abbah ya ƙarasa maganar A firgice cikin ɗaga murya Roshan ya ce "Not my own...." Kowa zaro ido waje yayi jin abinda Roshan ya faɗa, Aunty Yolash tana kallon Roshan ta ce "to idan ba naka ba kana nufin kace na Razhdeen ne don saboda abinda ya shiga tsakanin su? kai daka zauna da ita na tsawon shekara biyu baka karɓa ba sai wanda ya kasance da ita sau ɗaya?...." Cikin ɓacin rai Roshan ya watsa mata wani irin kallo wanda idanuwansa suka yi jawur ga hawaye kwance akan idon..... Sai da Aunty Yolash ta tsorata da irin kallon da Roshan yake mata, tinda take bata taɓa ganin ɓacin rai a fuskar Roshan irin na yau ba... Ƴar Amana jin cikin yanada alaƙa da Razhdeen yasa zuciyar ta bugawa da ƙarfin gaske, lokaci guda numfashi ya ɗage sai luuu ta faɗa kan Mamanta dake itace a kusa da ita...... Typing ✍️ *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 36 to 40 _______________★★★ Cike da takaici Roshan ya tashi yabar falon gaba ɗaya, Abbah gaba ɗaya ya rasa ya zai yi da wannan al'amarin gashi cikin dake jikin Baiwar ALLAH ba'a tabbatar cewa na Roshan ne ko na Razhdeen, Abbah juyo wa yayi yana kallon Baiwar ALLAH cikin kwantar da murya ya ce "Daughter gaya mun gaskiya wannan cikin na waye a cikin su, kina ji a gabanki Roshan yace ba nashi bane..." Baiwar ALLAH kuka ne ya kuɓuto mata itama da gudu ta bar falon ta shige ɗakin ta tana kuka, Ita kuwa Ƴar Amana tana kwance akan cinyar Mamanta wanda ba'a san dalilin sumar ta ba, Ummy ce ta ɗauko water bottle Mai sanyi ta kawo aka feffeshe mata fuska da ruwan, a zabure ta farfaɗo tana faɗin "dan Allah kar ku raba ni da shi ina sonsa sosai, ina sonsa sosai kar ku rabani da shi, bana so ya auri wata bayan Ni...." Aunty A'isha zaro ido tayi tana binta da kallo cike da mamaki, Shima Mai martaba abun mamaki ya bashi taya Reemah ta fara soyayya tin yanzu? ... hannun ta ya riƙo tare da faɗin "Shalele nah, ki kwantar da hankalinki kinji za'a baki wanda kike so..." Sai a lokacin ta dawo hayyacin ta, haka take bin kowa da kallo lokaci guda ta fashe da kuka itama, Aunty A'isha ce ta rungume ta a jikin ta tare da rarrashin ta... Abbah ne ya ce "shin ita ɗin wa take so ne?..." kowa karkaɗa kai yayi alamar basu sani ba, sai Maimuna da ta buɗe baki ta ce "waye in banda Razhdeen..." kowa tsumu yayi yana jinjina zancen, Aunty Yolash ce ta furta "cab ana wata ga wata, chakwakiya kenam, to yanzun mai ya kamata ayi?..." Mai martaba wanda idonsa akan Reemah ya ce "dan Allah ina so abar komai yanzu sai Razhdeen ya samu lafiya, duk wani maganar soyayya ko Aure a barshi ba yanzu ba, idan ya samu lafiya sosai in yaso sai ayi komai domin yanzu samun lafiyar sa shine abu mai muhimmanci a yanzu...." Abbah ya ce "shikenam yanzu abinda ya kamata ayi shine Daughter zata cigaba da zama da mu anan gidan har Allah yasa ta haihu..." Aunty Yolash ta ce "to amma ita Daughter bata son Razhdeen kuma ga cikinsa a jikin ta sannan kuma ga Reemah ita da take matuƙar son sa shin ya za'a ayi kenam...." Mai martaba ya ce "duk wannan maganar a bar shi sai Razhdeen ya samu sauƙi sannan itama idan ta haihu duk za'a warware matsalar..." Chief yana tsaye ya goya hannayensa biyu akan ƙirji kansa na kallon ƙasi, ƙwaƙwalwarsa ce take ta faman jujjuyawa ga Matarsa ta musulunta ba tare da sanin sa ba ga kuma alƙawarin da yaso cikawa na haɗa Ɗiyarsa da Razhdeen kuma yanzu yaji wani batu da ban akan cewa Ƴar uwar sa tana son sa again, abun da ya ɗauka shine bazasu taɓa faranta wa ƴarsa sannan su baƙanta wa nasu ba.... Abbah ne ya katsar da Chief daga dogon tunanin da ya zurfafa, yana faɗin "naga kayi shiru Allah yasa dai lafiya..." Girgiza kai Chief yayi sannan ya ce "kawai ku aura mata Razhdeen ɗin tinda tana son sa kuma ɗan uwanta ne, ita kuma Daughter zan tafi da ita..." Abbah ya ce "to alƙawarin fa...?" Chief a taƙaice ya ce "na janye, ina so a faranta wa wancan, kuma nasan Daughter ta nuna bata son Auran Razhdeen bana so a samu matsala ne..." Abbah ya ce "amma kuma cikin sa ne fa a jikin ta ..." Chief ya ce "zata haifa masa kayansa Insha Allah..." Aunty Yolash ta ce "to in kuma Roshan take so ba sai a maida musu Auren ba, bayan ta haihu..." Chief girgiza kai yayi yana murmushi ya ce "Bama Auran mata biyu sannan ƴaƴan mu bama Aura musu masu mata, haka ƙa'idar mu take..." Mai martaba ya ce "Insha Allahu dole za'a haɗa Auren Razhdeen da Amreesh saboda mai haɗawa ya rigada ya haɗa tinda akwai juna biyu a tsakani, ita Reemah zamu san yanda za'ayi da ita. ..." Abbah cike da damuwa ya ce "Insha Allahu Razhdeen zai miƙe ya koma kamar kowa za'a magance matsalar nan, zai kuma zaɓa idan Amreesh ne za'ayi Auren idan kuma Reemah ne nan ma zai zaɓa, idan kuma duk biyun ya zaɓa sai dai ya rasa su gaba ɗaya...." Chief kallon yanda Madam Parveen take a zaune ya yi sannan ya ce "tashi mu tafi..." Kallon sa tayi sannan ta ce "kasan zaman mu bazai yu ba, ina musulma kai kana Christal...." Cikin fushi Chief ya darara mata tsawa tare da faɗin "you are not a Muslum..." Itama miƙe wa tayi tsaye suna facing juna ta ce "i'm a muslum..." Chief ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba yana nuna ta da yatsa ya ce "okay don't worry, but you better stay away from me..." Yana gamawa ya juya kan Rakesh yana faɗin "tashi mu tafi..." Rakesh motsi-motsi ya fara yi kamar wanda baya son tashi idonsa akan Mommyn su... Chief ya ce "tashi mana ina maka magana..." Rakesh gira a haɗe ya ce "sorry Dad me too i want to be a musulum..." Chief zaro dara-daran idanuwansa yayi yana kallon sa ya ce "whattt?..." Rakesh ya ce "Sorry Dad, my brother Mohandas ya musulunta still My mother itama ta musulunta sannan ga my younger sister she's a muslum why bazan zama musulmi ba...." Chief cikin ɓacin rai ya daka masa tsawa tare da faɗin "shut up very stupid, okay kaima ka cigaba da zama a wurin su, bana son ganin kowa a cikin ku yaje yanda nake...." yana kaiwa nan yayi ficewar sa, Madam Parveen ce ta fashe da kuka tsabar takaici kuma gashi tana son mijinta, Aunty Yolash ganin yanda take ta kuka yasa ta taso ta je yanda take tare da rungumar ta suka zauna tana rarrashinta.. Mohandas da Rakesh suma gaba ɗayan su babu wanda yaji daɗin abinda ya faru amma sai dai dole daman zasu fuskanci kalubale... Abbah zama yayi yana kallonsu cike da tausayawa ya ce " kuyi haƙuri zai dawo gare ku Insha Allahu, zaku cigaba da zama anan gidan, kafin Allah yasa komai ya daidai ta...." Suna cikin wannan halin sai ga wani soja ya shigo da sallama a bakinsa yana riƙe da hannun wani saurayi fari tass suka shigo tare, Maimuna tana ganin Ashmar ta tashi da gudu ta nufo yanda yake tare da rungumar sa tana kuka tana faɗin "Yarima na ya dawo gareni, Allah na gode maka..." tana shafa fuskarsa cikin kuka take faɗin "Ashmar ina ka shiga ne haka? ka tafi ka barni cikin ƙunci da tashin hankali, meyasa ka jefa rayuwarka cikin hatsari?...." Shima kukan yake ya rungumi Mamansa sosai.... Ƙarasa shigowa ciki suka yi, Mai martaba ganin Ashmar bai san lokacin da ya fara washe baki ba cike da farin ciki shima ya tashi yaje ya rungume shi yana faɗin "yanzu shima yaro nane? Ikon Allah kenam Allah nagode maka, ashe zubar hawaye na bai zube a banza ba, addu'a ta bai faɗi ƙasi banza ba, zubar hawaye na alkhairi ne, ga Yarima da Reemah Allah ka bar mun su..." Kowa cike da farin ciki yake binsu da kallo, Maimuna da Yarima duk zama suka yi cikin rashin fahimta Ashmar yake bin kowa da kallo, idonsa ne ya sauƙa akan Ƴar Amana, a ruɗe ya buɗe ido yana kallon ta... Ita kuwa Ƴar Amana har zuwa wannan lokacin bata daina kuka ba tana kwance kan cinyar Mahaifiyar ta, kallon Ashmar tayi jin ana faɗin ɗan uwanta ne, ganin yanda yake ta kallon ta ne yasa abun ya ɗaure mata kai ga baƙin cikin abinda ya faru tsakanin Razhdeen da Baiwar ALLAH, Ita bata san shi ba dake lokacin koda yaushe fuskar sa a rufe take... Madam Parveen hankalin ta ne ya kasa kwanciya ganin a halin da Baiwar ALLAH ta bar wurin, itama tashi tayi tare da barin falon ta koma cikin ɗaki, anan ta tarar da Baiwar ALLAH kwance akan gado sai sharar kuka take ba ƙaƙƙautawa, baƙin cikin ta shine cikin dake jikin ta kuma na Razhdeen... Madam Parveen zama tayi a bakin gado ta riƙo hannun Baiwar ALLAH tare da ɗagota tana share mata hawaye, tana faɗin "Amreesh! kukan me kike yi?..." Cikin kuka Baiwar ALLAH take faɗin "haba Mommy dole nayi kuka, ji nake kamar na kashe kaina wallahi, ciki ne fa dani? cikin Razhdeen shin meye sunan cikin dake jikina? cikin shege kenam fa, da igiyar Aure a kaina na aikata alfasha kuma har da ciki, me zance wa Ubangiji na idan naje gabansa...." Madam Parveen girgiza kai tayi ta ce "kina gani fa ba'a son ranki kika aikata ba, bakida laifi kuma haka shima Razhdeen bashi da laifi akan wannan al'amarin..." Baiwar Allah tana kuka ta ce "taya zaki ce bashida laifi alhalin shi ya jefa ni cikin hargutsi..." Madam Parveen ta ce "idan kuwa yana da laifi to kema kinada laifi tinda ke kika ƙira shi gidan ki, meyasa zaki ƙira shi? Kuma kina ga ƴan uwansa ne suka jefa ku cikin matsala, kinsan ƙarfin turaren nan kuwa? ki daina ganin laifin kanki da kuma Razhdeen ki ɗauka cewa ƙaddarar ki ce tazo da haka..." Baiwar ALLAH ta ce "Mommy na fuskanci duk bakwa son ganin laifin Razhdeen, duk kunfi son Razhdeen..." Madam Parveen dafa kafaɗarta tayi tare da faɗin "duk muna sonku hakan yasa za'a haɗa ku Aure..." Baiwar Allah a zabure ta doke hannun Mommynta daga kan kafaɗarta tana girgiza kai tare da faɗin "har abada bazan taɓa auransa ba, sai dai idan mutuwa nayi aka ɗaura masa aure da gawata, wallahi tallahi idan har ku ka dage akan haɗani da Razhdeen saina kashe kaina, gwara kawai na mutu nabar muku duniya, domin yanda na tsani Razhdeen ko mutuwa ta ban tsane ta ba, kuma wallahi cikin nan zubar shi zanyi bazan haife shi ba...." Madam Parveen rarrashinta take tana bata haƙuri akan ta dakata da wannan shirmen nata amma Baiwar Allah sam taƙi fahimta sai surutan ta take tayi marasa kan gado, ganin ta kasa dawo hayyacinta ne yasa Madam Parveen zabga mata mari tare da faɗin "wani irin hauka ne wannan, shin kin manta a inda kike ne? bafa a gidan ubanki kike ba, a gidan ubansa kike amma kike faɗin cewa kin tsane shi bakya sonsa har kina iƙirarin zaki zubar da cikin anya kinada hankali kuwa? yanzu idan iyayensa suka ji wannan furucin nakin zasu ji daɗi ne? shikenam kije ki zubar tinda ke mahaukaciya ce...." Madam Parveen tana kaiwa nan ta fice a ɗakin, Baiwar ALLAH fashewa tayi da kuka tare da kifar da kanta a kan gado.... Abbah yana zaune idonsa akan Ashmar ya ce "taso kazo yanda nake magajin gobe...." da murmushi akan fuskar Abbah.. Ashmar kallon Mamansa yayi tayi masa alamar yaje da idonta, tashi yayi ya nufi yanda Abbah yake zaune yaje ya zauna kusa da shi, dafa kafaɗarsa Abbah ya yi yana tsokanan sa, daga baya yake cewa "meyasa ka tafi ka bar Mamanka?...." Ashmar ɗago wa yayi yana kallon Abbah kamar zai yi kuka domin abubuwan da suka faru da shi bazai misaltu ba.. Abbah ya sake tambayar sa cewa "shin zaka iya tuno duk abinda ya faru dakai bayan tafiyar ka? Mahaifiyar ka ta sanar mana cewa ka nufi ƙasar Jidder zaka je ka bayyar da kanka cewa kai ɗan sarki ne, shin meya faru baka je ba sannan kai baka koma gurin mahaifiyar ka ba...." Hawaye ne suka gangaro masa daga cikin ƙwayar idanuwansa yana girgiza kai tare da faɗin "bazan iya tunawa ba ...." Abbah ya ce "meyasa? zaka iya mana please nan duk ƴan uwanka ne family mahaifinka da shi kansa mahaifin nakan ne..." Ashmar ya ce "a shekara takwas da suka wuce akwai jirgin da aka rasa daga Iran zuwa ƙasar Jidder wanda aka ɗau tsawo kwanaki ana nema amma ba'a gani ba, nasan kun san da wannan labarin, to a cikin mutanen jirgin har da ni a ciki, jirgin ba ɓata tayi ba sace wa akayi, duk mutanen jirgin an yi kidnaping ɗin su, wasu manya-manyan ƴan fashi ne waɗanda suka amsa sunan su, a cikin mu an kashe wasu, wasu kuma sun maida su yaran su, aciki har da ni suka mayar mu yaran su, mata kuma sun kashe tsofi, ƴan mata kuma sun mayar su karuwen su, akwai alluran da suke mana wanda zai sa mu manta gida, mu daina tunanin gida sannan ya dasa mana rashin imani acikin zuciyoyin mu, waɗannan ƴan fashi akwai baƙaƙen fata sannan akwai turawa, sun bamu horo na musamman, duk wanda ya kasa jure horon nan sai dai asa bindiga a harbe masa kai domin a tunanin su babu abinda zai iya, an fita da mu ƙasashen waje mabanbanta domin aiwatar da fashi, duk wani fashin da za'ayi mu ake turawa, a cikin bama so har muka saba, a cikin mu akwai waɗanda suka zamo manya-manyan ƴan fashi wanda babu imani a tattare da su, wanda idan basu yi kisa ba basa jin daɗi daman ƴan fashin ƙasar waje ne , Amma ni yanda na gode wa Allah har yau Allah bai bani iko da damar aiwatar da kisan kai ba, da hannaye na ban taɓa yin harbi da hannuna ba, sannan ban taɓa kashe wani bawa ba, kuma ban taɓa buɗe baki nayi magana ba hakan yasa suka bani wani matsayi da ban suke ƙirana da Guess bana magana, na mayar da kaina kurma sannan bana haɗa ido da mutum, hakan yasa suka bani umarnin rufe fuskata saboda zan zamo musu mai leƙen asiri, A cikin mu an zaɓi babba sannan an bashi yara waɗanda zasu yi aiki a ƙarƙashinsa duk ƙasar da aka tura ka nan zaka je ka zauna a cikin daji, A ciki har da ni, Ni kuma sai aka turo ni nan Nigeria da yarana waɗanda zasuna mun aiki, aka ƙera mun gida a cikin daji anan ake aiwatar da aikin ta'addanci, har Allah yasa wani mutumi da ya ji labarin mu sai yazo yanda muke ya haɗa hannu da mu, ya zuba maƙudan kuɗaɗe sosai hakan yasa daga ƙungiyar mu aka bashi matsayi domin yana bada gudumowa sosai waran tura wa shuwagabannin mu ƴan mata, yakanyi safaran ƴan mata ya tura su sannan a bashi kuɗi ganin aikin da yake musu ni banayi yasa suka karɓi matsayin da suka bani suka bashi, sai ya zamana sai abinda ya cemun ni kuma saina saka na ƙasa dani suyi, haka rayuwar mu ta cigaba a cikin daji, har Allah yasa aka kawo mana wannan yarinyar ....". Ashmar ya ƙarasa maganar tare da nuna yanda Ƴar Amana take a kwance, ganin ya nuna ta ne yasa tayi saurin tashi tana tuno da abinda ya faru da ita a baya, a cikin ranta ta ce "kenam wannan shine mai rufe fuskar sa da baƙar hula?..." Duk mutanen falon kallon yanda Ƴar Amana take suka yi suna jinjina lamarin... Ashmar sai da ya gama basu labarin abinda ya faru da shi kab sannan ya ce "a rana ta ƙarshe da ake son kashe ta ni na tura wa Major Razhdeen saƙon yanda take saboda na bincika sunada kyakkyawar alaƙa a tsakanin su, daga lokacin da aka kamani Razhdeen bai bari an azabtar dani ba saboda ni na bayyanar masa a yanda yarinyar take, su kuma sauran mutanen mu ban san a ina suke ba, shin an kashe su ko suna raye sai Allah, a lokacin da Razhdeen ya sanar cewa a barni nayi tafiyata na roƙe shi akan ya ƙyale ni a wurin sojojin sa domin zan fi samun nutsuwa, nasan ina fita daga waransu za'a nemi rayuwata ce domin mutanen mu kashe ni zasu yi....." Maimuna ba abinda take sai kuka jin ƙibtili'in da yaron ta ya shiga, Kowa ba ƙaramin tausaya masa ya yi ba.. Mai martaba yana sharar hawaye ya ce "ni kuma tawa ƙaddarar kenam, duk a cikin ƴaƴana babu wanda yayi rayuwar jin daɗi, duk su biyun sun shiga bala'i da masifar rayuwa, Allah sarki...." Abbah ya ce "kar ka damu duk jarabawar rayuwa ne, Allah yasa mu ci jarabawar...." Duk suka amsa da Amiin.... Ramlat ce ta tashi jiki ba ƙwari zata wuce Abbah ya tsayar da ita tare da faɗin. "zo ki zauna mana..." Zama Ramlat tayi kai a sunkuye sai zubda hawaye take, Abbah ya ce "kar ki sa damuwa a ranki saboda a halin da kika ga Ƴar uwarki da kuma hukuncin da za'a yanke mata, duk ita ta ja wa kanta...." Ramlat tana kuka ta ce "Abbah banji takaicin hukuncin da aka yanke mata ba, babban takaicina shine da na haɗa jini da ita, ban so hakan ba, amma dan ALLAH kada laifin da ta aikata ya shafe ni, wallahi ban san duk ta aikata wannan ta'addanci ba..." Abbah ya ce "ai daman ko a wurin Ubangiji laifin wani baya shafan wani, mu dai abinda zamu gaya miki shine ki kwantar da hankalinki ki zauna a ɗakin mijinki, kada kiyi abinda zai sa kema a tsane ki, kinga dai halin da ƴar uwarki ta tsinci kanta abun babu daɗi, kada ki ɗauko halin ta ko kaɗan, domin a zamanin yanzu ka zama mutumin kirki ya ka ƙare da duniya balle ka zaɓi abun tsiya, ita duniya budurwar wawa ne, wanda bai zo cikinta bama ya yaƙare balle wanda yake cikinta, don haka kiyi ƙoƙarin aikata abin alkhairi dan ALLAH....." Ramlat tana kuka ta ce "Insha Allahu Abbah ba zaku samu matsala daga gareni ba, zan zamo mai muku biyayya da kuma mijina, Allah ya huci zuciyar ku...." Abbah ya ce "ba komai Allah ya miki albarka...." ta amsa da Amiin... Sannan ta miƙe taje ta zauna a gefen Ƴar Amana tare da kamo hannunta tana murmushi ta ce "Ƴar uwata ina taya ki murnar dawowa gida..." Ƴar Amana jinjina mata kai tayi ba tare da ta ce komai ba, Domin Ƴar Amana har yanzu akwai wannan miskilancin nan.... Anan Abbah ya sanar cewa za'a fita da Razhdeen ƙasar Ethiopia domin zai fi samun sauƙi anan sosai.... Daga nan bayan an wuni guda Minal da mijinta Mohandas da yaronsu Afif tafiya suka yi gidan da suke kafin lokacin komawar su ƙasar U.S saboda aikin da Mohandas yake acan... ★★★★ Bayan Sati biyu Daƙer Mai martaba yasa aka fito da su Pinky da Rukky daga ɗakin horo domin a niyar Abbah sai sunyi wata biyar suna kulle, a sati biyu gaba ɗaya sun fita hayyacin su domin azabar da ake gana musu ko namiji iya kar abinda za'a masa kenam, sunyi baƙi sun rame kamar masu cutar HIV, especially Rukky tafi jikkata sosai domin ko baccin kirki ba'a barin su suyi sai kwanan tsaye ga shocking da ake kwana ana jona musu, abinci kuwa kamar yanda Abbah ya sanar sau ɗaya ne a rana idan aka basu da rana sai washe gari da rana hakan ma ba isar su yake ba, abun breakfast da abincin dare duk babu lissafin wannan domin zama da yunwa ma horo ne, a cikin ɗakin horon nan sun suma yafi sau adadi, gaba ɗayan su sai da suka raina kansu, ba ƙaramin danasani suka yi ba, kullum kukan su shine abar su suje su nemi yafiyar Abbah amma anƙi barin su, shi kuma Abbah ba zuwa yanda suke yake yi ba sannan ya hana kowa yaje dubo su, A yanzun ma dalilin fitowar su shine akwai sojan da ya samu Mai martaba akan maganar su yana faɗin cewa "yaran nan fa zasu iya mutuwa a kowane lokaci domin azabar da ake musu yayi yawa ba zasu iya jura ba, ga sauraye sannan ga rashin abinci idan sunyi rashin lafiya babu magani, yanzu haka duk suna kwance rai a hannun Allah babu wacce take iya motsi da kanta..." Mai martaba hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba jin halin da yaran suke ciki, bai bi ta Abbah ba haka yasa aka ɗauko su a kafaɗa domin ba zasu iya tashi suyi tafiya ba, ko gida ba'a kai su ba haka aka miƙi hanyar hospital da su, daga baya gidan suke jin labarin halin da suke ciki, kowa ba ƙaramin tausaya musu akayi ba banda Abbah da yake ta masifa cewa "meyasa aka fitar da su?, ba rashin lafiya ba ko gawarsu aka tarar nafi son sai sunyi adadin kwanakin da na yanke musu..." Mai martaba sam bai ji daɗin kalaman Abbah ba shima cewa yayi "haba ai rashin imanin zai yi yawa ai idan har aka barsu acikin wannan halin, ƙarewa ko kisan kai suka aikata dai-dai hukuncin da yakamata ayi musu kenam, waɗanda suke gidan prison ma sun fisu gata wani irin abu ne haka? to nidai na fitar da su..." daga nan Abbah bai ƙara furta komai ba, har sai da su Pinky suka yi kwana biyu akan gadon asibiti, sai yanzu suka dawo hayyacin su, mahaifiyar su ita take jinyar su babu yanda ta iya dole zata saurari ƴaƴanta ko me suka aikata, Bayan su samu sauƙi sallamar su aka yi, sun samu lafiya amma sai dai har yanzu akwai wannan ramar da fitar hayyaci, domin babu wanda bai tausaya musu ba... Pinky da Rukky bayan sun koma gida sun je sun samu Abbah a falon sa suka durƙusa har ƙasi suka gaishe shi, Abbah sama-sama ya amsa musu rai a ɓace, neman yafiyar sa suka fara yi suna kuka, sai da suka yi kukan su mai isar wa suna bawa Abbah haƙuri kafin Abbah ya ɗago yana bin su da kallo, daga baya ya ce "a wannan rayuwar da muke ciki wasu da kuɗin su sun nemi su sayi mutunci wa kansu amma sun kasa, saboda shi mutunci kamar madara ne idan ya zube ba halin kwashe wa, da yawa mutane suna son su zama mutanen kirki amma tin tinin sunayen su ya rigada ya ɓaci a ko ina babu yanda zasu yi su zama mutanen kirki a cikin al'umma, a zamanin yanzu idan baka linbanci damar ka ba har ya wuce to kuka ne ka rinƙa yinsa har ƙarshen rayuwar ka, yanzu zan baku misali da matar Uncle ɗin ku kuna gani a gaban ku abinda ya faru da ita, ta mayar da kanta mahaukaciya, su waɗanda ta shuka musu sharri gasu nan suna nam cikin kwanciyar hankali ita kuwa tana can sai yanda rabbani yayi da ita, a cikin satin nan muka ji labarin haukar da take yi muraran yasa ta fita daga prison da gudu garin haka mota ya buge ta, gashi tayi sanadiyar rasa ƙafarta ɗaya kuma haukar yanan a kanta, yanzu wannan al'amarin wa gari ya waya? kuna yara ƙanana zaku ɓata future ɗin ku, yanzu duk namijin da yaji labarin abinda kuke aikata wa shin akwai wanda zai yi sha'awar auren ku ne? impossible wallahi, to ya kamata kuyi ƙoƙarin maida kanku mutanen kirki tin kafin lokaci ya ƙure muku, domin yanzu da sauran lokacin ku...." Pinky da Rukky kuka suke sosai kamar ransu zai fita haka suke ta zuba godiya wa Abbah tare da yin nadamar abinda suka aikata, kuma sunyi alƙawarin bazasu sake aikata wani kuskure ba.... Abbah ya ce "Ɗan Adam dole ya aikata kuskure amma ba wanda za'ayi Allah wadar ba, don haka ku tashi kuje ni na yafe muku, ina so kuma kuje ku nemi yafiyar kowa na gidan domin ba ƙaramin ɓata musu rai ku ka yi ba musamman ita Daughter da kuma Roshan, shi Razhdeen baya nan an fitar da shi ƙasar waje..." Suka amsa cikin girmamawa sannan suka yi wa Abbah sallama tare da fice wa... Ƴar Amana yanzu gaba ɗaya haushin Baiwar ALLAH yasa ta daina zama a yanda take, duk hanyar da zata haɗa su bata bari su haɗu, Baiwar ALLAH ta sha dakatar da ita akan ta tsaya suyi magana ta fahimtar juna amma Ƴar Amana taƙi sauraron ta, yanzu har ta kai idan Ƴar Amana tana zaune a falo Baiwar ALLAH ta shigo sai ta tashi tabar falon, a cikin ba'a fahimci komai ba har aka zo kowa ya fahimci halin da suke ciki... Baiwar ALLAH shawara ɗaya ta yanke cewa da daddare zata je wurin makwancin Ƴar Amana ta tilasta mata akan meyasa take jin haushin ta yanzu, dake a ɗaki ɗaya suke kwana Ƴar Amana da Ummy domin jinin su yafi haɗuwa, Baiwar ALLAH tura ƙofar ɗakin su tayi da sallama a bakin ta, tarar da su tayi su duk akan gado, ita Ummy tayi bacci, Ƴar Amana kuma sai buɗe litattafai take tana duba abubuwan da aka koyar da ita, jin sallama yasa ta ɗago tana bin Baiwar ALLAH da kallon daga bisani ta maida kanta kan littafin ta cigaba da dubawa, Baiwar ALLAH zama tayi a bakin gado idonta akan Ƴar Amana, gaba ɗaya Baiwar ALLAH cikin jikinta ya fara nuna ta domin ba ƙaramin fari tayi ba daman gata fara ce tass sai yanzu kuma har ta ɗan haɗa da yellow-yellow kamar ba jini a jikin ta amma kuma ba rashin jini bane domin tana samun kulawa sosai, domin abincin ta ma daban ake girka mata na samu juna biyu wanda zai ƙara mata lafiya da ƙarfin jiki tare da jaririn jikinta... motsi ta fara yi da lips ɗinta a hankali ta furta "Ƴar Amana..." Ƴar Amana kuwa ko kallon ta batayi ba balle ta saurare ta, Baiwar ALLAH ƙara ƙiran sunanta tayi anan ne Ƴar Amana ta ɗago da dirarrun idanuwanta waɗanda suka kaɗa sukayi ja lokaci guda domin idan ta ga Baiwar ALLAH gaba ɗaya zuciyar ta hargutsuwa yake... Baiwar ALLAH ta ce "dan Allah ina so ki sanar mun me nayi miki ne haka? ko dai baki yi murnar haɗuwa da ni bane? dan Allah ki sanar mun ko meye kike so zan yi ƙoƙarin ganin na faranta miki...." Ƴar Amana idonta ta sauƙar kan cikin Baiwar ALLAH tare da faɗin "bazaki taɓa dawo mun da farin ciki na ba har abada domin aikin gama ya rigada ya gama, lokaci ya wuce amma sai dai mallakar farin ciki na abu ne mai sauƙi a gareni, ke kuma in har ke zaki sanya ni farin ciki to kin yaudari kan ki ne domin bana jinki a raina...." Baiwar ALLAH tana kuka ta ce "to ki gaya mun mana me nayi miki?...." Ƴar Amana ta ce "meye ma bakiyi ba, kinga dan Allah tashi ki bar mana ɗaki bana buƙatar ganin ki..." Baiwar ALLAH ta ce "Ƴar Amana ni ce bakya son gani?..." A fusace Ƴar Amana ta watsar da litattafan da suke gaban ta a tsawa ce ta ce "ki tashi ki bar yanda nake please, kin lalata mun gobe na, mijin da nake sa ran zai zamo uban ƴaƴana kin zo kin dasa ɗan da bana sunnah ba a cikin rayuwar mu, ƴaƴan da zan haifa kin zo kin fara zuba musu gura gurbi a cikin su, taya bazan tsane ki ba? hakan ma kinada aure maimakon ki fara haifan tsabtataccen yaro amma sai kika fara zuba wa mahaifarki dattin zina wanda ta sanadiyar haka zaki haifo dattin jariri da sunan ɗa a gurin mijin da nake sa ran shi zai zamo madubin dubawa ta dana ƴaƴana....." Baiwar ALLAH jin kalaman da Ƴar Amana take jifanta da shi ne yasa ta fusata ta zabga mata mari tana kuka, miƙe wa tayi tana nuna ta da yatsa tare da faɗin "ki san irin maganganun da ya dace kina faɗa domin indai kika cigaba da jifan munanan kalamai akan abinda ke cikina zamu samu matsala sosai..." Ummy wacce ta daɗe ta farkawa jin hayaniya itama ta tashi zaune idonta akan Baiwar Allah ta ce "to ba gaskiya bane? shin ta hanyar Aure kika samu cikin? ai ba ƙarya akayi miki ba tinda tin da kike da Roshan bai taɓa kusantar ki ba balle ki ɗaura mar sharrin cikin, ke da bakin ki kike sanar mun haka to kinga kuwa sai dai ki toshe kunnuwan ki, kuma kada ki sake sa hannu ki mari ƴar uwata akan ta faɗi gaskiya...." Baiwar ALLAH tana kuka ta juya zata fi ce itama Ƴar Amana a cikin kuka ta furta "tirrrr...." A wannan ranar Baiwar ALLAH kwana tayi bata rintsa ba sai kuka sai yanzu ta ƙara jin ta tsani cikin dake jikin ta, bata ƙaunar cikin ko kaɗan, kamar yanda ta tsanin uban cikin haka ta tsani cikin shima.... Bayan kwana biyu anyi wani babban baƙo a gidan Abbah wanda koda yaushe yake busy yanzu ne ya samu lokacin kawo musu ziyara duk da wani ɗan lokaci yakan zo amma baya kwana, yanzu ne ya samu lokaci sosai har zai kwana, kowa ya hallaru a falo ana murnar zuwansa, wannan baƙon ba kowa bane illa Barrister ARASH yaron Ammy Amaryar Abbah wanda yake gudanar da aikinsa a ƙasar Saudiyya, Arash ba laifi asalin Balarabe ne dake mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa duk larabawa ne, kyau kamar shi ya halicci kansa, yau kwana biyu kenam da zuwansa ya samu wadataccen lokacin ganawa da mahaifiyar sa Ammy, kuma dama sati guda yayi niyar yi kafin ya koma... A yau ne kowa da kowa yake zazzaune a falo bayan Abbah ya sanar cewa yana buƙatar ganin kowa, har da su Minal da mijinta dake can gidan su suma an gayyato su, ga Rakesh wanda yake nam da Mahaifiyar sa bai koma ƙasar U.S ba, sannan ga Mai martaba da iyalansa biyu Aunty A'isha da Aunty Maimuna da yaransu Yarima Ashmar da Reemah, sannan Madam Parveen da Baiwar ALLAH suma suna nan a zaune, Hajiya Kilishi da Ammy suma suna zaune a kujera ɗaya da Aunty Yolash dake gefen kujerar su, ga kuma yaran gidan a zaune a ƙasin carpet duk sun sha makeup duk Aunty Yolash ce ta tsaya ta shirya musu makeup ta gyara su sosai kamar wasu Amare dake yau an sanar cewa duk yau za'a zaɓar musu mazajen Aure a cikin samarin gidan, domin a cikin samarin kowa ya nuna yana son ɗaya daga cikin ƴar matan gidan shine duk aka tara su akan kowa ya zaɓi gwanar sa, Pinky da Rukky da Ummy duk suna zaune kowa yana son ganin mijinsa a cikin su... Ga Roshan shi da Ramlat suma a zaune... Abbah ne ya fara magana tare da faɗin "Ma sha ALLAH kowa da kowa ya hallaru, ba komai ne ya tara mu anan ba sai don gudanar da wani alkhairi, lokaci yayi wanda yanzu ne dai-dai lokacin da kowacce zata tafi ɗakin mijinta, duk da ku acikin matan babu wacce tasan da wanda za'a haɗa ta amma su mazan tin ba yau ba sun zaɓi wacce zasu yi rayuwar Aure da ita yanzu ne kuma za'a bayyanar, haƙiƙa nayi farin cikin zuwan Arash domin zuwan sa yasa duk zan haɗa ƴan matan gidana na Aurar, duk da akwai guda ɗaya wacce ta rage wato Reemah ita ba yanzu zamu yi maganar Auren ta ba saboda wani dalili, yanzu dai a gurguje zamuyi abinda ya tara mu sannan a yau za'ayi baiko wato a yanke ranar Auren...." Abbah ya ƙarasa maganar yana sakin murmushi tare da bin yaran da kallo yana farin cikin kowacce zata kama ɗakin mijinta, kowa yayi matuƙar farin ciki sosai, Abbah ya cigaba da faɗin "a cikin samari uku akwai Arash da Yarima Ashmar sai kuma Rakesh wanda ya juma da musulunta shima, sai kuma a cikin ƴan matan muna da Balkisu da Ruƙayyat da Ummy wato uwar masu gida...." Abbah ya kalli Arash sannan ya ce "kai zamu fara daga kan ka ne domin kaine babba a cikin su, shin a cikin yara matan nan wacece ka zaɓa wacce zata zamo uwar ƴaƴanka?..." Arash murmushi ya yi sannan yakai idonsa kan Ammy, haɗa ido suka yi itama tasau masa murmushi tare da jinjina masa kai, sannan ya kai idonsa kan Pinky lips ɗinsa na motsi a hankali ya furta "Ni a cikin su ba kowa bace illa Balkisu, ita na zaɓa ta zamo matata ta sunnah..." Pinky sunkuyar da kanta tayi ƙasi sai zabga murmushi take tayi domin itama har cikin ranta tana sonsa sosai tin ba yau ba... Abbah ya ce "Ma sha ALLAH abu yayi kyau Allah ya tabbatar mana da alkhairi...." duk suka amsa da Amiin... Sannan Abbah ya maida idonsa kan Rakesh ya ce "to kai kuma fa mai sunan kakana wacece taka a cikin su?..." Abbah ya ƙarasa maganar yana masa dariya domin ba ƙaramin burge shi Rakesh yake yi ba domin yaron yana da hankali da son yin biyayya. Rakesh idonsa akan Ƴar Amana yana murmushi ya ce "ni wancan nake so..." ya nuna Ƴar Amana, a fusace Ƴar Amana takai dararan idanuwanta waɗanda take zazzare su cikin fushi ta ce "ko da wasa kar kayi tunanin nuna ni domin idan mafarki kake gwara kai ta marin kan ka, kada kowa ya sako ni a lissafi domin na rigada na kama gwani na...." ta ƙarasa maganar tana turo baki tare da wurga masa harara... Aunty A'isha da sauri ta bugi cinyarta tana mata magana a hankali cewa "ke bakida hankali ne? a gaban iyayen sa kike fa ko kunya baki ji ba?...." kowa girgiza kai yayi domin Ƴar Amana ba ƙaramar masifaffiya bace kuma dalilin da yasa take cikin fushi koda yaushe saboda cikin Razhdeen da yake jikin Baiwar ALLAH, gaba ɗaya cikin ya tsole mata ido.... Baiwar ALLAH jin yanda take gaya wa ɗan uwanta maganganu yasa ta ƙafe ta da ido tana mamakin abubuwan da Ƴar Amana taka yi... Mai martaba ne ya ce "meyasa haka ne Shalele? daga magana sai cibi ya zamo ƙari? ki rage wannan shiriritan na gaya miki, shi ɗin abokin ki ne?..." Ƴar Amana kawar da kai tayi gefe gira a haɗe kamar zata yi kuka. Abbah ya ce "ka ga Rakesh kayi haƙuri ka ji, acikin waɗannan biyun zaka zaɓa tsakanin Rukayya da Ummy..." Rakesh girgiza kai yayi tare da faɗin "ba komai Insha Allahu zan zaɓa a cikin su..." ya kalli Mommynsa haɗa ido sukayi sannan ta jinjina masa kai akan ya zaɓa sannan ya maida idonsa kan Babban yayansa wato Mohandas, nan ma Mohandas alama yayi masa da ya zaɓi wacce tayi masa, Rakesh gaba ɗaya ya rasa wacce zai zaɓa bayan Ƴar Amana domin daman ita ya saka a ran sa... Babu yanda ya iya haka ya ɗago da yatsar sa yana nuna Ruƙayyat lips ɗinsa na motsi ya ce "wancan..." Abbah hamdala yayi sannan ya ce "to an baka ita..." cikin zolaya yake masa wasa... Sannan Abbah ya ce "Ashmar sauran kai, muna so ka zaɓi ta ƙarshen idan kuma bata burge ka ba sai mu baka damar ka nemi wacce kake so..." Ashmar idonsa akan Ummy daman kafin azo wannan lokacin har sun fara soyayya, a cikin zuciyar sa addu'a yake kar kafin azo kansa a zaɓe ta sai kuma gashi daman rabonsa ce ita, Itama Ummy ɗagowa tayi suka haɗa ido tasau murmushi, duk akan idon kowa, anan Aunty Yolash ta ce "wannan ai basai an bashi zaɓi ba domin tintinin sun rigada sun fahimci junan su..." Mai martaba ya kalli Ummy sannan ya ce "Uwar masu gida shin kin amince zaki zamo surkuwa ta?..." Da sauri Ummy ta rufe fuskar ta da tafin hannunta biyu waɗanda suka ja zanen lalle, kowa farin ciki yayi sannan Abbah ya sanar cewa next week ɗaurin Auren su ba wani jinkiri... Aunty Yolash zaro ido waje tayi tana faɗin "wonderful! da sauri haka?..." Anan aka gama tattaunawar su aka tsayar da magana ɗaya, sannan gobe da sassafe Aunty Yolash da Hajiya Kilishi zasu fita ƙasar waje domin yowa siyayyan kayan ɗaki na mutum uku.... Bayan an gama watse wa Madam Parveen ce da yaranta a cikin ɗakin da suke Mohandas da Rakesh da Amreesh suna tattaunawa akan yanda za'a gudanar da bikin, kuma babban damuwar su shine mahaifinsu yayi fushi ya tafi, son samu yana nan za'a yi Auren nan, suna neman mafita yanda zasu je su samu mahaifin nasun, sun tsayar akan cewa gobe Mohandas da Rakesh zasu je ƙasar U.S wurin mahaifinsu... Bayan sun gama tattaunawa Mohandas riƙo hannun Baiwar ALLAH tare da faɗin "Babyn Daddy nasan kina cikin damuwa amma ki kwantar da hankalin ki komai zai zo ƙarshe kinji ko, ina yinki over my...." ya ƙarasa tare da sumbatar ta akan goshi, shima Rakesh shafa gefen fuskar ta yayi yana sakin murmushi, daga nan suka fice a tare, Baiwar ALLAH tana zaune da Mommynta sai murmushi take ta zabgawa domin ba ƙaramin farin ciki take tsintar kanta ba idan tana tare da Ƴan uwanta, domin ba ƙaramin kulawa suke bata ba... Washe Gari Mohandas da Rakesh sunyi ƙasar U.S sai kuma Aunty Yolash da Hajiya Kilishi suma sun fita ƙasar waje.. Madam Parveen da Baiwar ALLAH addu'ar su Allah yasa Mahaifinsu ya saurare su idan sun je, domin abin gori ne ace anyi bikin ɗansa babu shi a ciki... Typing ✍️ *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 41 to 45 Yau ake shagali ranar bikin manyan mata ƴaƴan masu kuɗi wankan madara kalar Camera 📸.... A gidan General manya manyan baƙi ne suke ta sauƙa a cikin satin nan har rana ya ta yau ranar Aure. nake ga duk ƴan uwa wanda bai zo ba shine Razhdeen amma kowa da kowa daga ɓangaren mahaifi da ɓangaren mahaifiya kowa yazo, hatta ƴan uwan Madam Parveen da ƴan uwan Chief duk christoci sun zo dake bikin har da nasu wato na Rakesh, sannan za'ayi hidimar bikin Minal da Mohandas da ba'ayi ba a wannan lokacin suma zasu yi nasu duk da yanzu har da yaronsu, kowa murna yake domin Auren mutane uku ba wasa bane, Amare uku da Angwaye uku. Madam Parveen ta ɗan shiga damuwa ganin kowa yazo amma banda mijinta wato Chief, tana zaune ita kaɗai a ɗaki tayi tagumi dake duk baƙin kowa yana harƙoƙin gaban sa babu mai zama wuri ɗaya, Baiwar ALLAH ce ta shigo da sallama a bakinta cike da mamaki take kallon Mommynta, taje ta zauna a kusa da ita tare da dafa kafaɗarta tana faɗin "Mom meyasa zaki kasance a haka alhalin yau ranar farin ciki ne, meya faru?..." Madam Parveen ta ɗago tana kallon Baiwar ALLAH sannan ta ce "Amreesh dole na shiga damuwa Mahaifinku har yanzu fushi yake da mu, bai zo ba, gashi duk ƴan uwansa da ƴan uwana duk sun zo dake su sun nuna cewa babu ruwansu da musuluntar da muka yi..." Sauƙe nannauyar numfashi Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "Mom tashi muje..." Madam Parveen ta ce "Ni bazan fita a cikin wannan yanayin ba..." Baiwar ALLAH ta ce "please Mom I want to show you something..." Ta ce "which something?..." ta ƙarasa maganar tana kallon Baiwar Allah. Baiwar Allah riƙo hannunta tayi tare da ɗagota suka fita waje, Falon nan a cike da mutane maƙir anata kai kawo, haka Baiwar ALLAH tana jan mahaifiyar ta suka fice daga falon gaba ɗaya, kai tsaye falon Meeting ɗin Abbah suka nufa wanda ba kowa ne yake zuwa nan ba sai baƙin Abbah, baƙin ma manya-manya, Madam Parveen ta kalle ta sannan ta ce "ke ina zaki kaini ne?..." Baiwar ALLAH tana murmushi ta ce "You should see...." Shiga cikin falon suka yi da sallama a bakin su, Madam Parveen ganin Mijinta Chief yasa ta washe baki cike da farin cikin ganinsa, Baiwar ALLAH ta ce "daman cewa akayi na ƙira ki, ganan Daddy yazo..." Madam Parveen jinjina kai tayi tsabar farin ciki ta ma rasa mai zata ce, Sai Abbah dake wurin ne ya ma ta iso da cewa "ki zo ki zauna mana, kema Daughter zauna..." duk zama sukayi, ga Mohandas da Rakesh su ma suna wurin, sai Chief da Abbah da kuma Madam Parveen da Baiwar Allah iya su kaɗai ne... Abbah ya ce "Alhamdulillah duk abinda yayi farko zai yi ƙarshe, idan akayi haƙuri da juna wata rana sai labari, yanzu dai Allah ya bada iko Chief Suraj shima ya musulunta ya dawo kan ƴaƴansa..." Madam Parveen hannu tasa ta toshe bakin ta duk biyu tana zaro ido cike da farin ciki da kuma mamakin yanda ya amince ya musulunta, Baiwar ALLAH itama murmushi take ta yi tsabar yanayin farin ciki da ta tsinci kanta..... Mohandas da Rakesh su ma ba ƙaramin farin ciki suka tsinci kan su ba, Chief yana zaune shima sai zuba murmushi yake domin yanda yaga iyalansa a cikin farin ciki sai abun ya bashi sha'awa... Chief ya ce "Insha Allahu idan aka ɗaura Auren yau gobe zamu koma ƙasar U.S, zan bar Daughter ana hannun General har Allah yasa ta haihu....". Baiwar ALLAH sai da taji wani irin bugun zuciya jin anyi maganar cikin ta, ita kwata-kwata bata so ayi maganar cikin domin ba ƙaramin takaici take ji ba, gaba ɗaya ta tsani cikin jikinta don babu yanda ta iya ne amma ta so ta raba cikin da jikinta, idan tana cikin farin ciki har mantawa take da Razhdeen amma idan akayi maganar cikinta sai ya faɗo mata a rai daga nan ne zata nemi farin ciki ta rasa, yanzun ma shuru tayi ranta a matuƙar ɓace, kamar zata yi kuka ta ce "ni dai zan bi su mu tafi..." Abbah ya ce "kiyi haƙuri Daughter zaki zauna da mu har sai kin haihu, bazaki koma ƙasar can da ciki a jikin ki ba, shin yanzu cikin ya shiga wata nawa?..." Shuru Baiwar ALLAH bata bada amsa ba, sai Madam Parveen da ta furta cewa "yanzu five months..." Abbah ya ce "to kinga idan kika kwantar da hankalin ki ma sauran wata nawa, Insha Allahu zan yi ƙoƙarin ganin na faranta miki sannan duk abinda kike so za'ayi miki, kinji ko?..." Baiwar ALLAH kanta na kallon ƙasi sai ji tayi Madam Parveen ta dafa kafaɗarta, ɗagowa tayi tana kallon ta, Madam Parveen ɗaga mata kai tayi alamar tayi haƙuri ta zauna... Sai da suka gama tattaunawar su tukun Abbah ya ce "toh masha Allah yanzu lokacin ɗaurin Aure ya yi ku tashi muje..." Duk tashi suka yi dake duk mazan a shirye suke waɗanda zasu fita ɗaurin Aure, Mohandas yana sanye da wata danƙararriyar shaddar sa yasha gariya ba ƙaramin kyau yayi ba, yana ɗauke da yaron sa shima yasha shadda irin na Babansa ga wata hula kalar shadda mai tsada suka fita domin a ƙofar gidan General za'a ɗaura Auren ga manya-manyan baƙi duk sun hallaru. Rakesh ba ƙaramin kyau yayi ba dake tinda yake bai taɓa sanya manyan kaya ba, shadda ne mai bala'in tsada wanda suka sha anko duk Angwayen, duk fararen shaddodi ne a jikinsu da hular sa ko wanne yasha kyau, Commender Rakesh da Yarima Ashmar da kuma Barrister Arash duk sun jeru suna takawa kamar masu tambayar ƙasa ana yayyafa musu ruwan kuɗaɗe... Bayan la'asar da yamma kowa yana shirin tafiya wurin dinner... Ɓangaren Amare masha Allah tufarkallah duk sun sha swezlace iri ɗaya masu bala'in tsada, da gyalellukan irin na kayan ba ƙaramin kyau suka sha ba, dake yaran duk babu laifi duk kalolin Camera ne da hasken su, musamman aka ƙira wacce ta ƙware wurin makeup ta zo ta tsara musu, Pinky da Rukky da Ummy tare da Babbar yayar su Minal duk ba ƙaramin kyau suka yi ba na bugawa a jarida.... Wacce ta ɗara kowa a ɗaukan wanka ta ci gasar kwalliya hatta Amaren ma sai da ta ɗara su kyau wato Ƴar Amana, daman ita can ƴar wash ce kuma tayi kalar wash, wani irin dogon riga na net ta sanya har jan ƙasi yake, fari tass mai duwatsu a jere ta ko ina, rigar daga sama ta matse zuwa kunkumin ta kuma ya baje sosai, hannun rigar dogo ne mai net tana sanye da takalmi jinin sarauta mai tsini fari mai duwatsu ta sama, takalmin tana yin ƙwaƙƙwaran tafiya da shi zata faɗi tsabar tudun sa, ga anyi mata wani irin gyaran gashi na musamman, ga yanda yake sheƙi tsabar mayukan da yake, ta gaban gashi zuwa baya an ɗame yayi tsantsi sai aka ɗaure da revon mai duwatsu, zirin gashin kuma sai aka bar shi a murɗi-murɗin sa har gadon bayan ta, sai aka ɗora mata kambun sarauta akan ta na zinare, ga sarƙoƙin da aka jera mata wurin kala uku hawa-hawa da ɗan kunne su ma a jere hudi huɗu duk da ɗan kunne ga warwaraye da zobina da sarƙar ƙafa yanda kasan itace Amaryar kuma ta fito asalin ƴar sarki, tana fitowa falo idon mutane duk suka sauƙa akan ta wasu har suna tambaya cewa shin ita ce amaryar?... Aunty Yolash mutanen fashion itama tana sanye da danƙareren shadda lace na bugawa a jarida, ba ƙaramin kyau tayi ba, Duk matan gidan su ma sun sha wankan gezner matan Abbah da Matan Mai martaba... Ga itama Madam Parveen ta sha wanka ta zura itama shaddar ta mai bala'in tsada da ɗaurin goggoro ga ta sha sarƙoƙi kalar shaddar akan wuyan ta daman ga wuya ba ƙashi ko ɗaya, bayan ta kammala shirin ta tsab zata fita ta kalli Baiwar ALLAH dake zaune a bakin gado sai kallon Mommynta take domin ba ƙaramin kyau tasha ba, Madam Parveen cike da mamaki take bin Baiwar ALLAH da kallo ta ce "ke bazaki shirya bane kina ganin kowa yana ƙoƙarin fita zuwa wurin dinner party..." Murmushi Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "Mom kawai ku je, ni bazan je ba domin idan naje ma zaman takura zanyi sannan ga cikina ya fito sosai ba yanda zan yi nayi gadara da shi...." Madam Parveen kamar zatayi kuka tsabar tausayin ɗiyarta, Ta ce "shikenam amma bana so kina zaman kaɗaici, gashi duk gidan za'a tafi babu wanda za'a bari..." Baiwar ALLAH ta ce "ni daman nafi son haka saboda bacci nake son yi sakamakon ciwon da kaina ke yi..." Madam Parveen matsowa kusa da ita tayi tasa hannu tana shafar gefen fuskar ta tare da faɗin "shikenam Daughter ki kula mun da kan ki..." Baiwar Allah murmushi tayi tare da jinjina kai, amma har cikin zuciyar ta taso itama taje, amma bazata iya shiga cikin jama'a a wannan yanayin ba saboda tana matuƙar jin kunyar haka, ga ciki ya fito sosai... Madam Parveen fita tayi itama. tana fita Baiwar ALLAH ta fara zubar da hawaye, ta juma tana zaune bata motsa ba tana tunanin yanda zaman ta zai cigaba da gudana a haka, Iya sleeping dressing ne a jikinta sai dogon hijab da ta zura har ƙasi mai hannu... Jin tashin motoci yasa ta miƙe a zabure taje jikin window ta tsaya tana kallon kowa da kowa, haka tana ganin yanda mutane suke ta shiga mota ana tafiya da su, motar Amare kam an daɗe da tafiya da su, Wata mata ce tayi magana tana ɗaga murya tare da faɗin "iyyeeee masoyan juna kyau haka, ahh lallai Roshan dole ku ƙi fito wa da wuri..." Baiwar ALLAH ce ta ɗan juyar da kai abinda ta gani ne ya tayar mata da hankali, ganin Roshan yasha farar gezner da gariya har ɗaukar ido yake, ba ƙaramin kyau yayi ba, most especially hular da ya sanya yanda kasan Balarabe ga takalmi sahun ciki fari da ɗan kwalliya ata sama... Gefensa kuma Ramlat ce itama ta ɗau fashion ba ƙaramin kyau tayi ba, tasha lace mai tsadar gaske sannan ta ɗora alkyabba a kai har ƙasi yanda kasan sarauniya, ta ɗaura siririn sarƙa akan goshinta da wuyanta da ƙafarta duk da warwaraye da zobina, Ramlat asalin kyakkyawar mata ce Black beauty amma yanzu ta ɗan yi haske alamun ciki gare ta, Haka suka jeru su biyu suna takawa a hankali cikin izzah, wasu har photo ake ɗaukar su da video tsabar ba ƙaramin burge kowa suka yi ba, Baiwar ALLAH idonta akan su ta window ga yanda hawaye yake zuba mata kamar da bakin ƙwarya, Ramlat ce ta ɗan ɗago tana kallace-kallace idonta ya sauƙa akan Baiwar ALLAH ta window dake window a buɗe take ga kuma yanda ta ɗage labule, ganin haka yasa Ramlat yin murmushi takai hannunta cikin na Roshan ta riƙe hannunsa duk akan idon Baiwar ALLAH, Shi kuma gaba ɗaya bai lura da hakan ba, Ramlat ce ta ƙara matsawa jikin Roshan suna riƙe da hannun juna idonta akan Baiwar ALLAH, cikin takaici Baiwar ALLAH ta juya zata koma ciki kenam taji an soma hura algaita tare da buga ganga maroƙa ne suka fara ƙirari da cewa "to jama'a gimbiya sarautar mata ta fito, ya ke ƴar sarki, jikar sarki, tattaɓa kunnin sarki, gabanki sarauta bayan ki sarauta Ƴar sarki, Allah ya rabaki da sharrin mahassada masu son ganin bayan ki...." Ramlat murmushi take tana wani ɗagun kai hannunta riƙe da na Roshan ganin ana mata ƙirari... Baiwar ALLAH ido ta zuba musu ganin yanda ake ta koɗa ta, Idon Baiwar ALLAH ne ya sauƙa akan Reemah wacce ta bayyano tana taku cikin izzah, ashe da ita ake ta wannan kururuwa tin daga nesa ake mata ƙirari kafin ta iso, a tunanin kowa a Ramlat ake wannan ƙirarin har wasu sun fara tsegumin cewa "aina ta ci gadon masarauta? sannan ta wani fanni take da alaƙa da masarauta?...." Sai daga baya suka ga ashe Reemah suka hango da kuma Matan Mai martaba dake bayan Reemah, Aunty A'isha da Aunty Maimuna... Sai yanzu maroƙan suka ambaci sunan Reemah, "Reematu gimbiyar mata, bayanki sarauta, gabanki sarauta, duk wanda ya nuna miki yatsa ƙarshen rayuwar sa kenan, Allah ya ja da kwananki Reematu, Ga kuma matan sarki Aishatu ƴar sarkin Niger, ƴar tushen sarauta Allah ya ja da kwananki, Amarya a wurin sarki sarauniyar mata, Ga kuma Uwar gida ran gida, in babu ke gida ya lalace, uwar gida a wurin sarki sarauniya Maimunatu ƴar sarkin Fiji Hindi Allah ya ja da kwananki....." Duk mutanen wurin sai kuma photo da video ya koma kansu duk sun haɗa kansu, matan sarki da ƴar sarki... Baiwar ALLAH ita kaɗai sai murmushi take ta yi domin ba ƙaramin burgeta suka yi ba, especially Ƴar Amana ta fito kamar ƴar sarkin America, tayi shigar ta wanda zai nuna ita ƴar sarauta ce, ba ƙaramin kyau tayi ba, Baiwar ALLAH ce ta maida idonta kan Ramlat, dai-dai lokacin da Ramlat itama ta ɗago suka haɗa ido, Baiwar ALLAH kanne mata ido ɗaya tayi tana sakin murmushi. Ramlat ɗan tsuka ta ja a cikin harshen ta tare da wurga mata harara... Aunty Maimuna ce ta buɗe jakarta ta ciro wasu maƙudan kuɗaɗe dami guda ta miƙa musu. Ƴar Amana gira a haɗe takaicinta ta rasa handbag ɗinta na kayan jikinta kuma akwai abubuwan ta a ciki, ta rasa a yanda ta ajiye jakar, tana cikin wannan nazarin idon ta ya sauƙa akan jakar ta dake hannun Ramlat wacce ta tafo mata da shi yanda ta manta a part ɗin ta... Gudu-gudu sauri-sauri Ƴar Amana ta yo kansu zata amshi jakar, su kuma suna tafiya a hankali suka nufi motar da aka tanadar musu, Ƴar Amana ce ta iso su tare da sa hannu ta karɓi jakar ba tare da ta furta komai ba, ta juya zata nufi motar da su ma zasu shiga sai kwatsam ƙafar ta gurmuɗe sakamakon tsinin da takalmin yayi ga ta juya da sauri, Ƙasa tayi zata faɗi har mutane sun zazzaro ido cike da fargaba, Itama Baiwar ALLAH ta tsorata sosai ta buɗi baki zata ambaci sunanta sai kawai taga Roshan yayi sama da ita tare da rungumar ta a jikinsa, itama Ƴar Amana cikin tsoro da fargaba ta zagaya hannunta ta bayan wuyansa ta rungume shi sosai tana sauƙe numfashi kamar wacce tayi gudu tsabar tsoro, sun ɗau tsawon mintuna a haka kafin Roshan ya ɗago da kanta suna kallon juna, murmushi ya sau mata tare da faɗin "zaki tafka mana babban asara idan ƙafar gimbiyar mu ta karye..." Itama bata san lokacin da tasau wani ƙayataccen murmushi ba har sai da fararen haƙwaranta suka fito, lokaci guda zuciyar sa ta buga wanda bai san dalilin bugawar sa ba, first sight ya ji wani irin shauƙi a ransa, kallon ta yake bai san Reemah tana da wannan kyau haka ba sai yau, gaba ɗaya ta firgita tunaninsa, Ƴar Amana ƙibta masa ido ɗaya tayi tare da sa hannu ta ja lips ɗinsa na ƙasi tana dariya, shima dariya yayi yaga kambun sarautar ta ya goce gefe guda yasa hannu ya gyara mata shi a yanda yake. Ramlat cike da mamaki fuskarta a hargutse take binsu da kallo gira a haɗe, ga yanda take ta zaro ido kamar zata yi kuka, ga yanda mutanen wurin suke musu photo da video, Wata tsohuwa ce ta ce "a'ahhh kodai za'ayi haɗin gida ne, ai kuwa wallahi kun dace da juna Masha Allah, kai ku cigaba da ɗaukar su a photo..." matar tana magana ne da biyu don saboda Ramlat taji haushi, domin duk ƴan uwa ba son ta suke ba, most especially jin labarin aika-aikan da Yayar ta Maamie ta aikata, kuma daman can ba son ta suke ba.... Ƴar Amana jin abinda Matar take faɗi yasa ta zaro ido cikin jin kunya ta juya zata gudu taji ƙafar ta ya riƙe domin gurmuɗewar da tayi taji ciwo duk da bata faɗi ba, da sauri ta ƙara cakumar Roshan jin ƙafar tayi tsami, ganin haka yasa Roshan kai hannunsa ƙasin ƙafarta ya yi mata ɗaukar luɗa, ita kuma tana riƙe da wuyansa duk hannu biyun, kai tsaye mota ya nufa da ita suka bar Ramlat a tsaye a wurin idonta duk ya cicciko da hawaye, Duk waɗanda suke wurin ne suka kama hanci tare da yin guɗa, lokaci guda aka fara hura algaita, Shigar da ita cikin mota ya yi wanda motar ita kaɗai za'a ɗauka a ciki, Bayan ya sakata ya juya zai tafi, ganin ita kaɗai zata zauna a cikin motar yasa tayi saurin riƙo hannun sa tana faɗin "Yayana ni kaɗai zan zauna?..." yana sakin murmushi ya ce "ai motar a gimbiya aka tanadar..." haɗe gira tayi sannan ta ce "ai gimbiya tana buƙatar ɗan tayin zama..." Ya ce "okay don't worry!..." Ya ɗago tare da kallon yanda Ramlat ta ƙafe a wurin ya ce "taho mana ki taya ta zama..." Matar nan tayi cab ta tari yawonsa da cewa "a'ahh kenam babu ƴar sirri a tsakanin Yaya da Ƙanwa? wata ƙila akwai abinda take son sanar maka wanda sirri ne..." Ƴar Amana leƙo matar tayi tana mata kallon mamaki yanda take ta faɗan maganar da ba shikenam ba..." Roshan ya ce "okay shikenam..." ya ƙarasa maganar tare da shige wa cikin motar da Ƴar Amana take... Matar ce ta kalli Ramlat sannan ta ce "ke kuma zaki iya tafiya wancan motar ki zauna..." Ramlat kamar zata haɗiyi ranta tsabar takaici ta ɗaga kanta sama tana kallon Baiwar ALLAH, Ita kuwa Baiwar ALLAH abun surprise 🫢 ya bata, da kuma dariya, haɗa ido tayi da Ramlat sannan ta ƙara kanne mata ido ɗaya tare da zaro harshen ta tana mata gwaliyo, Ramlat hararar ta take cike da ɓacin rai, Baiwar ALLAH wasa take da harshen ta idonta akan Ramlat ga yanda fararen haƙwaranta suka fito tana dariya, gaba ɗaya dimple ɗinta ne suka lotse, ta ɗago da hannunta biyu ta manna su akan lips ɗinta sannan ta hura mata iskar kiss ɗin da ta manna akan tafin hannun ta.... Ramlat da sauri ta kawar da kanta gefe tare da nufan motar da aka ce mata taje ta shiga rai a ɓace, tinin motar su Roshan ta tafi, Motar matan mai martaba kuwa tin tinin sun tafi duk wannan chakwakiyar da akayi basa nan sai baƙin da suke wajen, su ma daga baya motar kowa ta tafi, sai ya zamana babu kowa a gidan sai sojojin da suke bakin gate da kuma Baiwar ALLAH dake cikin ɗakin ta, Baiwar ALLAH zama tayi a bakin gado tana jinjina lamarin da ya faru a tsakanin Roshan da Ƴar Amana, sai take tunanin shin wasa tsakanin Yaya da Ƙanwa ne ko kuma akwai alaƙar soyayya a tsakanin su, sai kuma ta tuno da maganar da matar ta faɗa cewa sun dace da juna, ayi haɗin gida kawai... Lokaci guda Baiwar ALLAH tasau murmushi tare da faɗin "zan so hakan ta faru, ni na rigada na fidda rai akan Roshan domin bashi ba ko wani namiji bazai so ya ƙara haɗa alaƙa da ni ba sakamakon abinda ya faru da ni..." Haka take ta tunani-tunani har ta kwanta bacci yayi awun gaba da ita..... A wurin Party kowa da kowa ya hallara sai sauƙe manya-manyan baƙi ake daga mota, Lokacin da motar su Roshan ta isa sun ɗan juma basu fito ba har wasu motocin suka iso, Ramlat ce ta fito idonta akan motar da su Roshan suke, ganin shuru yasa tayi tunanin ko sun shiga ne, har tayi gaba taga an buɗe murfin motar, gani tayi Roshan ya fito yana dariya tare da sa hannu ya cicciɓe ta tare da yi mata ɗaukar luɗa ya shiga cikin dinner hall da ita domin ta sanar masa ne akan bazata iya tafiya ba, Ramlat cike da damuwa ta ɗan bubbuga sawayen ta kamar zata rausa ihu haka take bin su da kallo tare da furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, wannan wani irin ƙaddara ce haka..." Itama ciki tayi ganin yanda kowa yana ta shiga da pass a hannun kowa, itama nuna nata tayi ta shige ciki, Roshan kuwa yana shiga ciki kallo ya koma kansa ganin ɗaukar da yayi wa Ƴar Amana, kowa zuba musu ido yayi sai kuwa aka juyar da kan Camera kansu ana musu video, ai kuwa nan aka fara watsa musu ruwan kuɗi domin ba ƙaramin bada show suka yi, Aunty A'isha da Aunty Maimuna abun mamaki ya basu suna faɗin "to ina ita Ramlat?..." Sai ga Ramlat tana biye da su ta bayan su, har Roshan ya zaunar da ita shima ya zauna a kusa da ita, Ramlat tana ƙoƙarin neman wani wuri ta zauna taji ya ƙira sunan ta da cewa "Beb zo mana ki zauna anan..." Ɗan murmushi ta sau tare da nufan yanda yake zaune ta gefensa kuma Reemah ce, itama zama tayi a kujerar gefen sa, zuwa akayi aka jejjera musu lemuka kala-kala kamar yanda aka ajiye wa kowa... Acan sama kuwa kujerun Amare ne da Angwayen su duk suna zazzaune kowacce tana gefen mijinta, suma ga kalolin lemuka da aka jejjera musu, ba ƙaramin kyau suka sha ba, video na musamman ake musu, duk ƴan uwan Amare da Angwaye sai da kowa ya fito tare da gabatar da kansa da kuma yiwa Amare fatan alkhairi da zaman lafiya... Ta gefe guda kuwa an tanadar wa manya-manyan baƙi wurin zama na musamman, duk sun halarci wurin party irin su Ali nuhu, da Adam A zango, sani danja, yakubu muhammad, ibrahim mai shunku, hamisu breaker, Lilin baba, mai shadda, umar m sharif, Abdul m sharif, Adamu nagudu, Ali jita, Nura m inuwa, nazifi asnanic, naziru sarkin waƙa, da dai sauransu duk mawaƙan Hausa da masu drama kowa da kowa indai mutum ya shahara to yazo wurin party, ga su Rema da duk mawaƙan turanci suma sun hallara, matan kannywood duk babu wacce bata zo ba, ga kuma babbar baƙuwar da akayi a yanzu wanda yanzu shugowar ta kowa ya saka tafi da shewa wato ba kowa bace illa "Elisa..." wacce bata juma da sauƙa daga jirgi ba, itama ta halarci wurin, ga manya-manyan masu kuɗi da ƴaƴan masu kuɗi, duk wanda ba'a gayyace shi ba ba'a barinsa ya shiga domin kowa sai ya nuna pass ɗinsa kafin security su bari ya shiga, bikin ƴan gata kenam, anan kowa a cikin baƙi aka gabatar da shi, mawaƙa kuwa duk babu wanda bai rera nashi waƙar ba, kuma duk wanda zai yi waƙa sai ya zaɓo zankaɗeɗiyar budurwa kafin suyi rawa da waƙa da ita, A lokacin da akazo kan Hamisu breaker sai da ya fito tukun ya ƙyalla idonsa akan Reemah wacce take ta faman danna ƙatuwar wayanta ga tsinken lemo a bakinta yanda take ta zuƙa cikin salo, Sai da Breaker yaje har side ɗinta tukun ya fara rera waƙar Jaruma... Reemah ganin mutum a tsaye a kanta sai faman rera waƙa yake yasa tayi saurin ɗagowa tana masa kallon up and down gira a haɗe, alama yayi mata da hannu akan ta fito filin rawar, Reemah ɗan tsuka taja ta cigaba da pressing phone ɗinta, Roshan ganin ba daɗi ta bonsa shi a cikin jama'a yasa ya miƙe tare da riƙo hannun ta ya ɗago da ita tare da kanne mata ido ɗaya da wayo da dabara ya fitar da ita filin rawar, kowa ya ganta a wurin yasan ɗiyar sarki ce wato princess, Sai da Roshan ya fitar da ita tukun ya koma ya zauna, ita kuwa bin breaker take da kallo ita har cikin zuciyar ta wannan bai burgeta ba, sai wani haɗe rai take tana kallon kowa da kowa, tana tsaye ko motsawa bata yi ba, shi kuwa sai zagaye ta yake yana rera Baitukan sa, haka ake zuwa ana watsa musu kuɗaɗe... Ali nuhu a ransa cewa yake "anya wannan bazamu ɗauke ta a film ɗin kannywood ba kuwa, nasan zata yi action yanda ya kamata kuma sannan zata yi farin jini, ta ɗaukaka mana kamfani..." Duk mawaƙannan babu wanda bai so yayi waƙa da ita ba, haka shima M sharif da sauran su, gaba ɗaya Ƴar Amana tabi ta gaji da tsayuwa, duk wanda ya fito sai ta kushe shi a cikin ranta, An gama da masu waƙoƙin Hausa sai kuma na turanci, Rema ne ya fito shima yana son yin waƙa da Ƴar Amana, Ƴar Amana kallo ɗaya tayi mishi gaba ɗaya zuciyar ta ya soma hargutsa sai wani tashin zuciya da take yi especially kansa da ta gani duk wani ƙulli-ƙulli ba daɗin gani, ga kuma yana waƙar yana rirriƙe mata hannu tare da rungumar ta, cikin ɓacin rai Ƴar Amana takai hannu ta zabga masa mari tare da hankaɗa shi... Ƴar Amana da sauri ta bar wurin ta sauƙa daga manbarin ta koma wajen zaman ta kamar zata yi kuka domin a ranta cewa take "aikin banza kawai, waɗannan masu baƙaƙen fuskoki sun wani zo sun takura mun..." Roshan cike da mamaki yake binta da kallo ganin irin abinda ta aikata, kowa zaro ido yake yana jinjina lamarin. Rema gaba ɗaya kunya ce ta kamashi ganin yanda yarinyar ta zabga masa mari a cikin mutane yana cikin rera waƙar sa, yana riƙe da fuska ya cigaba da rera waƙar yana abu kamar irin action ne aka bata.... Yana kammalawa itama Elisa ta fito, tana fitowa kowa ya fara ihu ana watsa mata kuɗaɗe domin kowa yana son waƙoƙin ta, itama haka ta fara rera waƙa tana rawa, haka mutane suke fitowa ana tayata rawa da amshi.... Su Abbah da Mai martaba kuwa suma suna can tare da baƙin su, sunata tattaunawa... Da haka aka sha hidima kowa ya fara wawwatse wa, waɗanda suka zo daga ƙasar waje duk an kama musu hotel, da waɗanda suke wasu garuruwa, shi kuwa Rema bayan an tashi haƙuri aka fara bashi akan abinda ya faru.... kowa ya koma gida cikin ƙoshin lafiya, ana komawa gida Aunty A'isha da Aunty Yolash ne suka dira akan Reemah abinda tayi a wurin party ana mata faɗa da cewa bai kamata ta mare shi ba, Aunty Yolash ta ce "mai laifin kiyi tafiyar ki kije ki zauna amma saboda iskaci ki mare shi kowa yana ganin mutuncinsa ga fan's ɗinsa, yanzu haka kana hawa tiktok da social media maganar sa ce ta bazu kowa yana kai gurmi, waɗanda basu sani bama sun sani, ga video yanda kika mare shi duk an ɗoɗɗora, kin ja masa abun magana...." Aunty Maimuna ce ta ce "dan ALLAH ku barta haka kar kusa mana ita kuka, abinda ya faru ya rigada ya faru..." Aunty A'isha tana nuna ta da yatsa tare da faɗin "ke ba Allah ya shirya mun ke..." Reemah cikin ɓacin rai ta shige ɗakin da suke kwana taje ta cire kayan jikinta sannan ta sanya ƙananun kaya wando zuwa gwiwa da riga mai hannun best, ta baje sumar kanta duk ta warwargaje gyaran gashin da akayi mata sai boom take ta haɗawa, fitowa falo tayi zata fice, Aunty A'isha ta ce "ina zaki je?..." tsayawa tayi ba tare da ta waiwayo ba ta ce "part ɗin Yayana zan je..." Aunty A'isha ta ce "me zaki yo a wannan daren yanzu misalin ƙarfe 11 kowa ya sha gajiyar hanya..." lips ɗinta na motsi a hankali ta ce "zan je ya rarrashe ni ne..." Aunty Yolash ta ce "ai yanzu kam sun kwanta ai..." tsayawa tayi tana zubda ƙwallah, ta juya musu baya tana kallon bakin ƙofar falo, Aunty A'isha ta ce "ki dawo kije ki kwanta ko kije ɗakin da Amaren suke ki je kuyi hirar tare..." Reemah tana tsaye ko waiwayowa bata yi ba, Sai Aunty Maimuna ce ta sako baki tana faɗin "ku barta mana taje ta dawo yanzu, idan bata je ba yanzu haka da fushi zata kwanta sannan ta tashi da fushin..." Aunty A'isha ta ce "haba dan ALLAH Aunty Maimuna Sam bai dace taje musu a wannan lokacin ba, suna ma'aurata wannan lokacin lokacinsu ne..." Aunty Maimuna ta ce "yanzu fa aka dawo daga wurin party nasan basu yi bacci ba..." Ta kalli yanda Ƴar Amana take a tsaye ta ce "je ki ma za Shalele, ki ce ina gaishe su da gajiyar hidima...." Ƴar Amana ana bata wannan damar tayi ficewar ta da sauri saboda kar a tsayar da ita, zuwa tayi security ya kaita har part ɗin da mota... Baiwar ALLAH wacce take zaune itama a falon duk tana jin tattaunawar da suke yi, ganin Ƴar Amana ta fice ne yasa ta sau murmushi domin tasan dole Ramlat bazata ji daɗi ba..." Su Abbah kuwa suma suna can babban falo su uku suke tattaunawa akan sha'anin rayuwa ga yanda har aka ɗora video party a kannywood, ganin yanda Reemah ta zabga wa Rema mari yasa mai martaba faɗin "subhanallahi mai wannan yarinyar ta aikata haka? a cikin bainar jama'a ta mari mutum wani irin rashin tarbiyya ne wannan?..." Abbah ya ce "ba rashin tarbiyya bane, shine yaso ya nuna mata rashin tarbiyyar sa shine tayi masa hukuncin daidai da abinda ya aikata, don haka ban ga laifinta ba sai ma ƙara burgeni da tayi..." Shima Chief yana zaune da shi duk ake hirar... Mai martaba ya ce "hakane amma ni tsakani Roshan da Reemah anya babu wani abu?..." Abbah ya ce "sanin cikin su sai Allah..." A falon cikin gida kuwa matan gidan ne suke zazzaune suna shan hirar su, Matan mai martaba su biyu da kuma Matan Abbah suma su biyu sai Aunty Yolash da Madam Parveen (Zainab), Baiwar ALLAH ce ta tashi zata koma ɗaki domin hirar na iyayenta mata ne, Aunty Yolash ce tayi saurin dakatar da ita tana faɗin "Daughter ba dai ciki zaki koma ba ko?..." Baiwar Allah murmushi tasau tare da faɗin "bacci nake ji ne..." Aunty Yolash ta ce "a'ah kam yanda kika wuni kina shan bacci nasan yanzu ba bacci zakiyi ba, kuma wallahi da nasan bazaki je wurin hidimar nan ba da ni da kaina zan shiryaki na sakaki a gaba mu tafi, amma banda iskaci sai ki zauna ke kaɗai a gida kamar wata mayya, kina wani cire kanki a cikin ƴan uwa, yanzu kije can room ɗina su Minal suna can kije ki zauna kuyi hirar tare, bana son baƙin da suka zo su fahimci halin da kike ciki...." Baiwar ALLAH kai a sunkuye ta ce "tam shikenam Aunty..." haka ta nufi room ɗin Aunty Yolash anan Amaren duk suke suna shan shabta, Pinky da Rukky da kuma Ummy sai Minal da yaronta a kwance kan gado yanda yake ta shan bacci, duk sun sha gajiya ko wacce ta rage kayan jikinta, duk suna cikin farin cikin yau an ɗaura musu Aure da mazajen da suke so... Baiwar ALLAH ce ta fara knocking, Minal ta ce "Yes shigo mana..." Baiwar ALLAH ce ta tura ƙofa tare da yin sallama ta shige, duk juyowa suka yi tare da amsa sallamar suna farin cikin ganinta especially Minal da Rukky waɗanda suka auri yayun ta, Rukky tana sakin murmushi ta ce "zo ki zauna mana Aunty Daughter..." Baiwar ALLAH ta zauna a bakin gado itama tana murmushi, Pinky ta ce "yooo wai Ni kam naga itace ƙarama da Rakesh ai yanzu Rukky kin zama Antynta..." Rukky ta ce "ahhh kuma fa hakane amma ai taci sunanta Aunty Daughter..." Minal ta ce "dan ubanku ai Auntyn ku ce tinda ta auri Yayan ku..." Pinky ta ce "kuma fa hakaneee..." Minal ta ɗago tana kallon Baiwar ALLAH ta ce "yawwa ni Aunty Daughter me ya hanaki zuwa wurin party ne kam?..." Baiwar ALLAH ta ce "wallahi Aunty Minal kaina ne yake ciwo shiyasa banje ba..." Rukky ta ce "wai kina nufin kice iya ke kaɗai aka bari a gidan?.." Pinky ta ce "ni ban lura da ita ba wallahi saboda abubuwa sun sha mun kai, ni yanzu bazan iya tantance su waye suka je da kuma waɗanda basu je ba, har a cikin ƙawayen mu..." Baiwar ALLAH murmushi kawai ta saki kanta a ƙasi tana wasa da yatsun ta, can ta ɗago tana waiwaye tare da faɗin "wai ni ina Yaro nane..." Minal ta ce "ga shi can yanata shan baccin wahala..." Baiwar ALLAH ta ce "Ayyah yaron kirki ai da an bar mun shi..." Minal ta ce "gaskiya ne ai kuma da kin je wurin party ba shiri..." Duk suka kwashe da dariya.... Ummy dake zaune a tsakiyar gado sai danna wayarta take tin shugowar Baiwar ALLAH bata ɗago ba balle tasa musu baki a hirar su... Rukky cike da mamaki ta ce "ikon ALLAH! wai yanzu duk ɗin mu kowa zai kama ƙasar da zai je da Aure ko?..." Pinky ta ce "daga gobe ne fa, duk kowa zai watse gaskiya zamuyi missing ɗin juna, gwara ku Aunty Minal da Rukky a ƙasa ɗaya zaku zauna tinda duk mazajen ku a ƙasa ɗaya suke hakan ma gida ɗaya uwa ɗaya uba ɗaya, zaku na haɗuwa kusan kullum, ni da Ummy ne sai Allah, ni ƙasar Saudiyya Ummy kuma ƙasar Jidder...." Minal ta ce "ai gwara ita Ummy tana kusa da Uncle duk da ba'a gida ɗaya zasu zauna ba amma nasan zata na yawan zuwa masarauta ga kuma ƙawarta Reemah..." Pinky ta ce "Allah sarki Ni kaɗai ce zanje wuri a baƙunta babu na gida..." Rukky ta ce "kina tare da ƴan uwan Ammy ai..." Pinky ta ce "Ammy ai kishiyar uwa ce, ban shaƙu da ƴan uwanta sosai ba..." Minal ta ce "sai ki ɗauka tamkar uwar ki ce, kina musu biyayya kuma..." Pinky fari tayi da idonta tana faɗin "ai Ni gidana ni ɗaya ne..." Minal ta ce "kowa ma ai gidansa shi ɗaya ne, kina nufin baza kina zuwa musu ziyara bane?..." Pinky ta ce "zan rinƙa zuwa mana...." Ummy ce ta ɗan ja tsuka tare da sauƙa daga kan gado zata fice.. Minal ta ce "ina kuma zaki je..." Ummy tana harare -harare ta ce "ni bana iya zama inuwa ɗaya da mutum..." Duk sun san da wacce take, kuma itama Baiwar ALLAH tasan da ita take, Minal rai a ɓace ta ce "duk wanda yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake, wai ni Ummy yaushe kika zama hakane? wallahi kwata-kwata kin chanza, yanzu kin zama mahaukaciya..." Ummy ta ce "na daɗe da zama mahaukaciya ai tin yaushe..." ta juya zata fita, Minal tayi saurin cewa "ki dawo kizo ki zauna..." tsayawa Ummy tayi ita bata fita ba sannan bata juyo ciki ba, har Minal ta tashi ta fice taje ta ƙira Aunty Yolash suka shigo tare, Aunty Yolash cewa tayi "me yake faruwa ne?..." Nan Minal ta sanar mata cewa "Aunty wallahi Ummy bata da hankali, gava ya ƙi ƙarewa ita da Aunty Daughter, kuma duk laifin Ummy ce, bata mata magana, yanzu haka fita take son yi wai bata son zama inuwa ɗaya da Aunty Daughter, kenam ita ba'a isa a gaya mata taji ba?..." Aunty Yolash riƙo hannun Ummy tayi suka ƙarasa ciki ta zaunar da ita itama ta zauna tare da faɗin "Uwar masu gida meye matsalar ki ne?..." Ummy ta ce "idan na tuno da abinda ya faru ita da Uncle Deen ne sai inji raina yana ɓaci...." Aunty Yolash ta ce "dan ƙaniyarki ina ruwanki da batun nan, ko shi Roshan baya mata wannan ƙiyayyar, amma ke saboda shashanci sai kace ke ce mijin da akayi wa laifin, idan haushin ne sai ki sauƙe haushin ki akan ƴan uwanki tinda su sukayi silar faruwar haka, kuma ko shi Roshan bai isa ya bata laifi ita da Razhdeen ba sai dai yaƙi gaskiya, kuma dan ubanku daga ke har Roshan ɗin yanzu haka idan ku ka tsaya aka feshe ku da turaren nan bazaku san lokacin da zaku aikata wani abu ba, duk da yana ɗan uwanki jini ɗaya hankalin ku gaba ɗaya zai gushe, an gaya miki cewa ba laifin ta bane, an gaya miki da yaren Hausa sannan an sanar miki da yaren English uwa uba an nuna miki video yanda abun ya faru, to tinda haushin ta kike mai zai hana ki ɗauko wuƙa ki caka mata in yaso sai mu san ƙiyayyar da gaske kike nuna mata, kuma abun nakin har da son kai wallahi, baki ji haushin ƴan uwanki ba sai ita saboda bata da iyaye daga sama ta faɗo, to bari kiji ko wani ɗan adam a rayuwa baya taɓa tsallake ƙaddarar sa, tin kafin mutum yazo duniya ƙaddarar sa take a rubuce, Allah ne yasa zata samu cikin jikinta ta hanyar nan babu yanda ta iya saboda haka ƙaddarar ta yake, bata isa kuma ta tsallake ba, itama kanta ba'a son ranta take ajiye da cikin nan a jikinta ba, kuma duk damuwar da zaki shiga da shi Roshan ɗin bazaku taɓa kai rabinta a shiga damuwa ba, inda kin san irin damuwar da take ciki wallahi da ke bakida bakin magana, idan kuma baki yadda da ƙaddara ba to imanin ki bata cika ba, domin cikar imani shine ka yarda da ƙaddara mai kyau ko akasin haka, Ummy inaso ki sani fa gidan wani zaki je kuma tafiya mai nisa zakiyi, ba tare zaku zauna ba yanzu baki sani ba shin zaku ƙara haɗuwa ne ko kuma bazaku ƙara ganin juna ba, ita fa mutuwa bata sallama, babu kyau ki tafi gidan miji kina mai jin haushin wani a cikin ranki, Pinky da Rukky sun aikata laifi kuma sun nemi yafiyar wanda suka yi wa laifin daga Daughter har Roshan da Abbah duk sun nemi yafiyar su kuma an yafe musu, yanzu Razhdeen suke jira duk lokacin da ya dawo shima zasu nemi yafiyar sa akan abinda suka saka shi ya aikata a bisa dole, Don haka kema Ummy inaso a yanzun nan ki bawa Daughter haƙuri ku rabu lafiya da juna...." Baiwar ALLAH itama tana zaune hawaye sai gangaro mata yake, Itama Ummy zubda hawayen take tana wasa da yatsun ta, ga Pinky da Rukky su ma yanda suke kuka domin duk su suka jawo komai... Ummy jinjina kai tayi tare da faɗin "shikenam Aunty Insha Allahu komai ya wuce...." Aunty Yolash ta ce "masha Allah! yanzu kiyi mata magana..." Ummy tashi tayi ta koma gefen Baiwar ALLAH ta zauna tare da riƙo hannun ta tana faɗin "Aunty Daughter Dan ALLAH kiyi haƙuri a bisa mis-understanding ɗinki da nayi, gaba ɗaya idanuwa na sun rurrufe tare da kunnuwa na, na kasa tantance baƙi da kuma fari, duk da video da na kallah naga ba laifin ku bane amma shaiɗan bai daina cusa mun ƙiyayyarki a cikin zuciyata ba, na faɗa miki maganganu marasa daɗin ji kuma duk kin jure dan ALLAH ki yafe mun, kiyi haƙuri komai ya wuce, mu koma kamar yanda muke a baya, ni a wurina Roshan da Razhdeen duk ɗaya ne a wuri na, AM so sorry please...." Baiwar ALLAH tana kuka babu bakin magana sai hannu da tasa ta rungumi Ummy, itama Ummy hannu tasa ta rungume ta tana kuka, ɗagowa tayi suna kallon juna Baiwar ALLAH ta ce "ba komai, na yafe miki nima inaso ku yafe mun..." Ummy ta ce "ai ke babu abinda kika yi mana, kinada kyakkyawar zuciya..." Ummy takai idonta kan tumbin cikin Baiwar ALLAH sannan ta ɗora hannunta akai ga shi yanda ya girma sosai, Ummy rufe idonta tayi lips ɗinta na motsi hannu akan cikin alamun addu'a take yiwa cikin... Bayan sun gama sai ga Pinky da Rukky su ma sun matso kusa da Baiwar ALLAH suna faɗin "Aunty Daughter Dan ALLAH muna mai ƙara neman yafiyar ki akan mummunan abubuwan da muka miki..." Baiwar ALLAH share hawayen ta tayi tare da faɗin "haba dai ai mun daɗe da wuce wannan layin, yanzu banida damuwa da kowa a cikin ku sai Ƴar Amana..." Aunty Yolash ta ce "ita wannan ai ƴar juju ce, yanda kasan mai aljanu haka take, ta nuna tana son Razhdeen kuma yau ga yanayin da aka ganta ita da Roshan a wurin taro, amma kar ki damu zan san yanda zan yi na shawo kanta, dole ta haƙura itama, ƴar banzar yarinya ga ƙarantar shekaru sai iya shege..." Duk murmushi suka yi, Baiwar ALLAH ta kalli Pinky da Rukky ta ce "meye to kuke kukan, ku matso ku ji..." Duk rungumar su Baiwar ALLAH tayi, itama Ummy rungumar Baiwar ALLAH tayi duk suka haɗe kayuwan su... Aunty Yolash ganin haka yasa tasau murmushi tare da ficewa daga ɗakin domin yau babu alamar kowa zai kwanta yin bacci.... Ƴar Amana kuwa tinin ta isa part ɗin Roshan ta fara buga musu gate, sai da ta ɗan juma kafin taji motsin mutum anzo buɗe mata, Ramlat ce ta buɗe cike da mamaki take bin Reemah da kallo, sai kallonta take tayi daga sama har ƙasa ta ce "ke kuma fa a wannan daren?..." Reemah ta ce "inason ganin Yayana..." Ramlat ta ce "mai zai zauna yayi har zuwa wannan lokacin bai yi bacci ba..." Reemah ganin bazata iya juran yin magana ba yasa ta ratsa ta gefen Ramlat ta wuce ciki, cike da mamaki Ramlat ta bi bayanta da kallo daga baya itama ta shige ciki, Ganin bata ga Reemah a falo ba yasa ta faɗin "to tana ina kuma?..." zuciyar ta na harbawa ta nufi bedroom ɗinsu tana sanye da sleeping dress, tana shiga ta tarar da Reemah kwance a gefen Roshan wanda ya juma da yin bacci.. A fusace Ramlat ta ƙarasa shigowa ciki tare da faɗin "ke baki da hankali ne? akan gadon mu na Aure zaki zo kiyi seƙe-seƙe dake ke ba ƙaramar yarinya ba..." Reemah cikin lumshe ido wacce bacci yake ƙoƙarin ɗaukar ta ta ce "yau anam zan kwana..." Ramlat ta ce "amma ba'a cikin ɗakin nan ba ko?..." Reemah gira a haɗe ta ce "ke nifa kin takura ni, shin aina zan kwana wanda ya wuce nan, ai kuwa yau da Yaya Roshan nayi niyar kwana a ɗakin nan...." Ƙirjin Ramlat ne yake bugawa da ƙarfi-ƙarfi domin al'amarin Reemah ya fara bata tsoro... Roshan jin surutu yasa shi buɗe idonsa tare da faɗin "me yake faruwa ne?..." Ramlat tana tsaye ta ce "gata nan a kusa da kai, ban saniba ko yau an haɗa Aurenka da ita anyi ne..." Roshan kallon yanda take a kwance yayi ya ce "ƙanwata ya akayi ne?..." Reemah tashi zaune tayi tana tura baki ta ce "nazo ana korata shikenam, daman kwana nazo taya ku amma matarka shine take faɗa mun maganganu ko..." Shima tashi zaune yayi yana binta da kallo ya ce "yi haƙuri ƙanwata kwanta kiyi baccin ki..." tana turo baki ta koma ta kwanta, shi kuma tashi yayi ya riƙo hannu Ramlat suna shirin barin ɗakin, Reemah ta ɗago ta zauna tana faɗin "iyyeeee! tafiya zaku yi ku barni ni kaɗai kenam, ai wallahi duk yanda ku ka je sai na biku...." ta ƙarasa maganar tana shirin tashi, Roshan ya ce "kinga kwanta mun dawo to..." Ya kalli Ramlat ya ce "kuje ku kwanta tare ni zan kwanta akan doguwar kujerar nan..." Ramlat fuska a ɗaure sai fushi take tayi tana kumbura kamar zata fashe, ji take kamar ta rufa Reemah da duka, haka ta hau gadon ta kwanta tare da jan mayafi ta rufe kanta ga kuma Reemah a gefenta itama ta ja mayafi a kanta domin bacci take ji, Roshan kuwa kashe hasken ɗakin yayi zai bar musu ɗakin yaji Reemah tana cewa "Yayana ka ce akan doguwar kujera zaka kwanta yanzun ina zaka je?...." Roshan ya ce "zan koma other room ne naje can na kwanta nima akan gado..." Reemah tana cikin mayafi ta ce "to tunda akan gado kake son kwanciya kazo nan ka kwanta a tsakiyar mu...." Roshan zaro ido waje yayi yana kallon ta yanda ta rufu, Girgiza kai yayi sannan ya ce "shikenam zan kwanta akan doguwar kujerar..." ya rufe ɗakin ya zo yabi kan kujerar ɗakin ya kwanta, su suna kan gado shi kuma yana kan kujera da haka har bacci ya ɗauke su, sai iya Ramlat ce ta rage da idonta sai faman kuka take ta sha a cikin mayafin, ta daɗe bata yi bacci ba tana kuka itama daga baya baccin ya ɗauke ta, A haka har sallar asuba Reemah ta hanasu sakattt...... Typing ✍️ *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 46 to 50 Washe gari Duk a dinning suka zauna zasu yi breakfast su uku Roshan da Ramlat da kuma Reemah wacce tayi musu ƙarfa-ƙarfa, Roshan ne da Reemah kawai masu hira amma ita Ramlat takaici kamar ta hallaka, sai faman hararar Reemah take, Roshan ne ya ɗago yaga yanda take ta mata kallon banza, tsaya kallon ta yayi daga bisani ya ce "me hakan yake nufi?..." Juyowa tayi tana kallon sa fuska a ɗaure tana turo baki ta ce "cin fuskar ne yayi yawa, bazan iya jure wa ba..." Reemah ce ta juyo itama tana kallon ta cikin rashin fahimta, sannan takai idonta kan Roshan tana son sanin abinda take nufi... Roshan ne ya ce "idan kin yi haƙuri sauran kwana nawa ne ya rage, bana son yawan complain fa..." A fusace Ramlat ta miƙe tsaye tana faɗin "ai dole ka ce haka saboda ni ba komai bace a wurin ka, daman nasan ba Sona kake ba dole ce tasa ka Aure ni, to bazan iya ba, idan ana son na cigaba da zama a gidan nan to sai dai a ja mata kunne akan shiga tsakanin ma'auratar da take, ita mahaukaciya ce? ko jahilci hauka ne, ina ga bata je islamiyya ba shiyasa jahilci da rashin tarbiyya yayi mata yawa..." Bata ƙarasa ba taji Roshan ya darara mata tsawa tare da miƙe wa tsaye a fusace yana nuna mata yatsa tare da faɗin "ya isa haka! idan ita jahila ce kina nufin kice duk har da mu jahilai ne ko? hakane tinda tsatson mu ɗaya, ina so nayi miki warning akan wannan kishin nakin..." Cikin ɓacin rai Ramlat ta ce "dakata Yaya Roshan, me kake nufi ne? kana nufin kace bazanyi kishi akan ka ba? gaskiya ni ina kishi akan ka ne saboda tsananin son da nake maka, kai kuma sam bana gabanka balle kayi kishi da ni amma ita Baiwar ALLAH da kake masifar sonta ai kana kishi da ita tinda har kuka kayi cir da idanuwanka...." wani irin kallon takaici yake mata cikin fushi ya ce "idan kinga zaki iya zama dani a haka to sai kin cire wannan kishin nakin, idan kuma bazaki iya ba ga nan hanya...." ya ƙarasa maganar yana nuna mata hanyar waje dai-dai Lokacin da idonsa ya sauƙa akan Baiwar ALLAH wacce take tsaye a bakin ƙofar falon tana tsaye ta zuba musu ido... Daga nan Roshan bai ƙara furta komai ba idonsa akan Baiwar ALLAH. Ganin haka yasa Ramlat juyawa tana kallon bakin ƙofa fuska duk ya jaƙale da hawaye, ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa ganinta... Reemah wacce take zauna cikin izzah ko ɗagowa ta kalle su bata yi ba sai ma cigaba da yin breakfast ɗinta jin faɗan akanta ake, Baiwar ALLAH ƙarasa shigowa ciki tayi tazo ta tsaya a gaban su idonta akan Roshan tana son isar da saƙo Ramlat tayi saurin katse ta da cewa "ke meyasa kanku baya ja ne? anya ƙwaƙwalwar ku bana kifaye bane? especially ke marar zuciya mutum ya ce baya yinki amma sai ƙoƙarin cusa kanki kike, yanzu har takai kina shigo mun ɗaki ba excuse, idan kika tarar da mu a cikin wani yanayi fa?...." Baiwar ALLAH goya hannayenta tayi akan ƙirji tana kallon ta ta ce "yanayi kam ai na rigada na riske ku a ciki, sannan kun ci sa'a tinda a iya falo na tsaya bance zan taya ku kwana a ɗaki ɗaya ba...." Ramlat gaba ɗaya ta gama ƙuluwa ta ce " to ina so ki fita daga shirgin mijina domin baya hulɗa da ƙazamai masu aikata alfasha, sai ki je ki nemi uban cikin ki kuje can ku cigaba daga yanda ku ka tsaya..." Roshan idonsa ya sauƙar kan Ramlat jin abinda ta furta, kasa cewa komai yayi domin shi bai cika son hayaniya sosai ba, yanzu zai iya jawa kansa ciwon da zai dame shi.. Baiwar ALLAH tana shirin zubda hawaye tayi saurin kawar da fuska tana ƙoƙarin matse hawayen, murmushin yaƙe tayi tana kallon Ramlat ta ce "karfa ki manta har yanzu akwai igiyar Aure na da Roshan..." Ramlat kwashe wa tayi da dariya tare da faɗin "rabuwar Aure kuwa na nawa tinda a gaban kowa yayi sakin..." Baiwar ALLAH cije lips ɗinta na ƙasi tayi ta ce "kin taɓa jin anyi saki da ciki? Roshan ya sake ni amma ban saku ba har sai na haifi ɗan dake ciki na, kinga kuwa har yanzu a mazannin mijina yake..." Ramlat ta ce "ai dai zaki haihun koh? to ki haihu kiga in Auren zai zauna tinda na tabbata bazai taɓa maida ke ɗakinsa ba..." Ramlat ta ƙarasa maganar tana ɗaga mata gira ɗaya... Roshan ne ya katse su da cewa "ku dakata mun da wannan shirmen nakun..." Ramlat ta maida idonta kan Roshan tana faɗin "taya zan dakata? wallahi yau sai an faɗa mun matsayi na a cikin gidan nan, idan har ina matsayin matar ka ce ta sunnah to ina so daga yau ka ja wa waɗannan masu zuciyoyin kare kunne kada su sake zuwa yanda kake..." Roshan kallon ta yayi cike da mamakin ta ya ce "to Fatima Bintu mahaifiya ta kenam, naji zan bi zaɓin ki..." Ramlat tana turo baki ta ce "Ni dai ka zaɓa idan su ka zaɓa to inason sa ni yanzu idan kuma haukar su suke to inaso kayi mana iyaka da su, domin bazai yu ba, ita wannan yarinya saboda ta raina mun wayo da rashin mutunci har da kwana mun akan gado to bazan iya ba..." Roshan cikin ɓacin rai ya kalli Reemah sannan ya ce "Reemah..." Reemah ta maida idonta kansa gaba ɗaya Ramlat ta gama ƙular da ita, haka zuciyar ta yake ta hargutsuwa, itama kallon sa take, Ya ce "taso ki zo nan..." Reemah tashi tayi ba mu su taje gabansa tana hararar Ramlat, itama Ramlat ɗin wani irin harara take wurga mata, Roshan ya riƙo haɓarta suna kallon juna ya ce "Reemah kina so na? zaki Aure ni ?..." Ramlat a zabure ta ja da baya tana zaro ido waje cike da mamaki take bin su da kallo tinin idanuwanta har sun cicciko da ƙwallah, Baiwar Allah kuwa idonta akan Ramlat tana sakin murmushi ganin halin da ta shiga lokaci ƙanƙani, ita ko kaɗan bata damu ba domin tasan hakan zata faru.... Shi kuwa Roshan idonsa akan su idan ya kalli Ramlat sai ya juyar da idonsa kan Baiwar Allah domin a tunanin sa hakan shi zai kawo maslaha a tsakanin su, kuma tin yanzu Ramlat ta fara nuna kishinta akan Reemah shiyasa yayi haka domin ta yi kishin da gaske, sannan bugu da ƙari cin mutuncin ta da tayi a gabansa har tana ƙiranta da jahila.... Reemah kuwa idonta akan Roshan ta kasa furta komai, Ƙara maida idonsa yayi kanta still ya ce "kodai bakya sona?..." Reemah murmushi tayi sannan ta ce "ina sonka sosai Yayana..." ta ƙarasa maganar tana kallon Ramlat domin ta ƙara ƙuntata mata... shima murmushi ya sakar mata, cikin jin kunya ta rufe fuskar ta tare da juyawa da gudu ta nufi hanyar fita daga falon.. Roshan maida kallon sa yayi kan Ramlat sannan ya ce "ina so ki sa ni cewa ita ɗin ƴar uwata ce jinin jikina, ba ko wani irin furuci zan juri ji ana gaya mata ba, kina jifan ta da munanan kalamai saboda sakarci irin naki kuma a gabana, to zan Aure ta sai kuma naga mai zakiyi, sannan ke baki isa ki bani umarni ba, ki tsaya a iya matsayin ki idan kuma ba haka ba zamu fiskanci rashin jituwa a tsakanin mu..." Sannan ya juya da kallonsa kan Baiwar Allah ya cigaba da cewa "ke kuma last warning da zan yi miki na ƙarshe shine kada ki sake nuna cewa ni mijinki ne, ki tsaya a yanda kike yanzu rabuwa ne na kuma rabu da ke har abada, bana jin haushin ki yanzu akan komai domin na tsawaita bincike na gano cewa bakida laifi sannan ƙaddara ce ta kuma riga fata, a baya na so ki kamar raina zai fita haka nan kuma yanzu ma idan nace bana sonki nayi ƙarya, zama ne bazan iya cigaba da zama da ke ba saboda inada matuƙar kishi na gaske, sannan kuma tin kafin ki kai haka aka kyautar da ke saboda haka na haƙura na barwa twins ɗina..." Jin ƙarshen maganar sa yasa tayi saurin kallon yanda yake zuciyar ta na bugun uku-uku domin a rayuwarta ta tsani a yi mata maganar Razhdeen, kuka ne ya kuɓuto mata ta juya da sauri tana kuka, shi kuwa binta yayi da kallo zuciyar sa na harbawa domin har yanzu yana jinta a ransa.. Ramlat itama tana kuka ta koma cikin room ɗinta, Roshan goya hannayensa yayi akan ƙirji yana hura iskar bakin sa, daga bisani ya girgiza kai shima ya nufi hanyar waje zai nufi part ɗin su Abbah... Reemah lokacin da ta koma part ɗinsu bata tarar da kowa a falo ba kai tsaye room ɗinsu ta haura da gudu, tana shiga ta tarar da Ummy tana zaune akan kujerar mirror tana makeup, Reemah tsaya kallon ta tayi tare da faɗin "Amarya wai shin ba yau zaku tafi gidajen mijinku ba ne?..." Ta cikin mirror Ummy take kallon Reemah sannan ta ce "wato har an gaji da ganin mu kenam, abun har da kora..." Reemah ta ce "ey ai tambaya nayi, ba yau bane?..." Ummy ta ce "ai dake zamu tafi idan lokacin tafiyar yayi..." Reemah turo lips ɗinta tayi sannan ta ce "sai dai na iso ku daga baya..." Ummy ta ce "Oh ashe dai kin ce sai kin jira dawowar Uncle Deen koh?..." Kallon gefe tayi tana tunanin wani abu daga bisani ta nufi yanda Ummy take zaune tana fuskantar mirror taje ta dafa kafaɗar ta tana murmushi ta ce "kin san meye?..." Ummy tana kallonta ta cikin madubi ta ce "me ya faru?..." Reemah tana rungume da ita tana tsaye ta ce "Aunty Ummy Allah ya ga zuciya ta ina son Uncle Deen, amma sakamakon abinda ya faru a tsakanin sa da Aunty Baiwar Allah yasa gaba ɗaya bana jinsa a raina, amma yanzu na samu wanda zai maye mun gurbinsa a cikin zuciya ta..." Ummy cike da mamaki ta juyo da kujerar ta tana kallon ta tace "wa kika samu amma?..." Reemah tana kallon ta tace "Yayana Roshan..." Ummy zaro ido waje tayi tana kallon ta cike da mamaki ta ce "whatt?..." Reemah ta ce "yess shi da kansa ya ce yana sona, kuma naga ya iya kula da mace da kuma soyayya, ga yanada sauƙin kai sai kuma naji lokaci guda ya kwanta mun a rai, sannan kuma matar sa Ramlat sai na koya mata hankali kinji irin maganganun da ta gaya mun kuwa? har ni zata ce wa jahila marar tarbiyya da ilimi sannan wai ban je islamiyya ba, ai wallahi sai nayi maganinta...." Ummy sauƙe numfashi tayi tana jinjina zancen ta ce "yanzun kin koma kan Yaya Roshan kenam, toh amma meye dalilin da yasa ta zage ki haka kuma naga Ramlat yanzu tayi sanyi ba kamar baya ba lokacin da Auntyn ta Maamie take zuga ta ba..." Reemah ta ce "Hmmm! ƙyale ta kawai zan rama domin ni bana barin bashi..." Ummy ta ce "wai ma tsaya shin aina kika kwana?..." Reemah ta ce "naje taya su kwana ne..." Ummy zaro ido tayi tare da faɗin "su waye wai?..." Reemah ta ce "su Yaya Roshan mana, a ɗaki ɗaya na kwana da su hakan ma akan gado, ni da matar sa akan gado shi kuma Yaya Roshan yana kan kujerar ɗakin..." wani irin haɗiyar yawu Ummy tayi tare da faɗin "amma ban taɓa sanin cewa ke mahaukaciya ba ce sai yau, taya zaki je ɗakin ma'aurata ki ce zaki kwana ai kin takura musu kuma hakan ma bai dace ba sam..." Reemah ta ce "hakan shine dai-dai domin na fahimci akwai ƙwari a cikin ƙwaƙwalwar Ramlat, kaɗan daga cikin aiki na kenam..." Ummy ta ce "au kenam da biyu kika yi musu haka? ai dole ta zage ki domin kinyi mata abubuwan da ba ko wace mace bace zata yadda ayi mata ba, da farko a gabanta ya yi miki ɗaukar luɗa ya shiga da ke wurin taron al'umma fa sannan kuma kije ki kwana a ɗakin su na Aure?..." Reemah gaba ɗaya fuskar ta ba annuri haka take kallon Ummy rai a ɓace ganin yanda take mata magana cikin fushi, zuciyowa tayi ta juya zata fice daga ɗakin sai taci karo da Mamanta Aunty A'isha, Aunty A'isha tsaya wa tayi tana kallon ta cikin fushi daga bisani ta ce "ina ma kika ce kin kwana?..." Reemah tana turo baki ta ce "na je na taya su Yaya Roshan kwana..." kafin takai karshen maganar Aunty A'isha ta zabga mata mari har sai da ta faɗi ƙasin carpet, tana faɗin "kinje kin taya su kwana ke mahaukaciya ce? ai yau da safe daman Ramlat ta ƙira ni a waya tana kuka take sanar mun aika-aikan da kika yi musu, meyasa hakane? na tsani mummunan hali a rayuwata, ni ba haka nake ba, dan Allah ki zama mai kyakkyawar hali wanda a duk yanda kika zauna za'a yabe ki" tsuka taja tsabar takaici bata ƙarasa maganar ba ta fice.. Reemah tana zaune ƙasin carpet yanda ta faɗi tana dafe da fuskar ta ga yanda hawaye yake gangaro mata, Ummy ce ta tsuguna tana rarrashin ta... Sai da suka ɗau lokaci suna haka babu wanda ya motsa a cikin su daƙer Reemah haƙura tasa hannu tana sharar hawaye ta ce "yanzu laifi ne dan Yaya Roshan ya ce yana sona nima kuma ina son sa?...?" Girgiza kai Ummy tayi sannan ta ce "ba laifi bane matsalar shine zuwa da kika yi ki ka taya su kwana..." Reemah ta ce "shine kuma zata ƙira Mamana ta faɗa mata?..." Ummy ta ce "kiyi haƙuri ki mance da komai..." Reemah tana zubda ƙwallah ta ce "to wallahi saina Auri mijinta sai dai ta mutu, yanzu ma kuwa zan fara nuna masa asalin ƙauna..." Suna cikin wannan yanayin sai ga Aunty Yolash da Minal da Pinky da Rukky da kuma Ramlat wacce bata juma da zuwa ba duk suka shigo, da sallama a bakin su.. Aunty Yolash ce ta gansu a haka ta ce "ha'a lafiya dai kam ko? meya faru da Shalele take kuka kuma?..." Ummy ganin har da Ramlat aka shugo yasa ta cewa "babu komai wai an sanar mata cewa duk yau zamu tafi shine take kuka..." Aunty Yolash ta ce "naga da ita duk za'a tafi.." Ummy ta ce "sai fa ta jira Uncle Deen ya warke kafin..." Aunty Yolash ta ce "toh pah! amma naji labarin yanzu Roshan take so ai kodai duk biyu zata Aura?..." Reemah ɗago da dararan idanuwanta tayi waɗanda suka kaɗa sukayi jawur tana yiwa Ramlat wani irin kallo fuska ba annuri... Itama Ramlat ɗin ita take kallo tana wani yamutsa fuska domin duk halin da ake ciki ta sanar musu... Aunty Yolash ce ta kuma cewa "Reemah meyasa hakane? kina fushi da Baiwar Allah saboda Razhdeen, yanzu kuma kin koma samun matsala da Ramlat saboda Roshan Anya kuwa akwai ƙamshin gaskiya a cikin lamarin nan?..." Reemah ta ce "Razhdeen da Baiwar Allah amanata suka ci shiyasa..." Aunty Yolash ta ce "oh kafin lokacin kin san sunada alaƙa ne? ko shi Razhdeen kin san yana tare da ita ne? kuma hakanan Baiwar Allah bata san kina tare da Razhdeen ba, babu maganar cin amana anan ke dai tsantsar kishi ne yake damun ki, hmmm! Razhdeen da Baiwar Allah lallai kam to ku zauna in baku wani labari naga har yanzu baku gane komai ba..." Duk zama suka yi suna sauraron Aunty Yolash, Aunty Yolash ta fara da cewa "a shekarun baya akwai wasu maza su biyu aminan juna wanda kullum a tare suke, to ɗaya daga ciki yana da wani ɗansa babba mai shiga rai wanda ɗayan abokin yayi alƙawarin cewa idan ya haifi ɗiya mace zai aura masa ita, yayi alƙawarin tin kafin a haifi yarinyar, shi kuwa Yaron jin haka yasa tin daga lokacin ya fara saka abun a ransa, kullum bashi da zancen da ya wuce Allah yasa a haifo masa yarinyar da aka yi masa alƙawarinta, yasa yarinyar sosai a ransa, wasu daga cikin abokansa har cewa suke to idan aka haifo namiji fa? a lokacin ya samu matsala da su duk wanda yace namiji za'a haifa sai ya samu matsala da shi, daga lokacin da matar abokin mahaifinsa ta haihu kafin a sanar masa ta haifu sai da yaron ya ɗauro alwala ya tsaida sallah ya roƙi Allah yasa haihuwar da akayi mace aka haifa domin ba ƙaramin saka rai yayi akan yarinyar ba, a lokacin da aka sanar masa cewa mace aka haifa bai san lokacin da ya dungura goshinsa ƙasi yana sujjada ba, ya gode wa Allah bana wasa ba, kamar yanda abokin mahaifinsa yayi alƙawarin daga lokacin ya damƙa masa ita yana faɗin ya cika alƙawari, ba ƙaramin farin ciki ya shiga ba lokacin, Hmmm! daga lokacin yaron ya fara rainon yarinyar har ta fara girma, idan ya ɗauke ta tin safe baya maida ita wurin mahaifiyarta sai dare, har lokacin da yarinyar ta cika shekara biyu, itama yarinyar dake ta tashi tana ganinta a hannun yaron yasa itama ta saka shi a ranta, idan bata gànshi ba a ranar wuni da kwana zatayi tana kuka, tsabar girman alƙawarin da yake tsakanin su ne yasa suka shaƙu da juna bana wasa ba, a lokacin birthday ɗin yarinyar a ranar yaron ya sanya mata zoben alƙawari itama yarinyar aka bata akan ta sanya wa yaron kuma kar ku manta a lokacin tana ƴar shekara biyu fa, wata rana kwatsam sai aka ji labari marar daɗin ji na cewa yarinyar da mahaifiyarta sunyi hatsarin mota, daga lokacin aka nemi yarinyar aka rasa, yaron jin labarin ba ƙaramin shiga damuwa yayi har jiya sai da yayi, nema kuwa babu yanda bai shiga nemanta ba domin a lokacin bai yadda cewa yarinyar ta mutu ba, anan har akayi tsawon shekara da shekaru kowa ya fidda rai akan ta, yaron kuma daga lokacin bai ƙara saka ko wace mace a cikin zuciyar sa ba, bai taɓa neman wata mace da suna soyayya ba hatta kallon mace baya son yi, shi dai ya ɗora ransa akan yarinyar wai bazai taɓa yin aure ba har sai ta bayyana, kuma yanzu shekara 23 kenam...." Kowa tsayawa yayi yana kallon Aunty Yolash domin basu taɓa jin wannan labarin ba, koda sun ji ma bazasu fahimci labarin waye ba, Ummy ta ce "Aunty cigaba mana shin har zuwa yanzu bai haƙura da ita ba? sannan kuma bai yi Aure ba? naji kince tsawon shekara 23..." Pinky ta ce "Allah sarki naji tausayinsa wallahi..." Rukky ta ce "itama yarinyar ta saka shi a ranta lokaci guda suka rabu duk da bata mallaki hankalin kanta ba..." Ramlat idonta akan Aunty Yolash ta ce "Allah yasa dai cigaban labarin suna haɗuwa da juna..." Reemah itama idonta akan Aunty Yolash domin tana son jin ƙarshen labarin domin bata so taji cewa har zuwa yanzu basu haɗu da juna ba..." Minal ce ta ce "cigaba mana Aunty...." Aunty Yolash murmushi tayi sannan ta ce "lokaci guda yarinyar ta bayyana a gidan su yaron..." Duk gaba ɗayansu zaro ido suka yi cike da farin ciki suke faɗin "wayyo farin ciki zasu haɗu da juna Alhamdulillah..." Aunty Yolash ta cigaba da basu labari da cewa "yarinyar ta bayyana a gidansu yaron wanda abokin mahaifinta ne ya tsince ta ba tare da sanin ko ita wacece ba domin yarinyar ta zama budurwa ta gaske cikakkiya, haka mai gidan ya cigaba da riƙe ta a mazannin ɗiyarsa har yaron gidan ya nuna yana sonta, amma kuma sai dai kash yaron da aka masa alƙawarinta bai gane cewa yarinyar sa bace sannan yayi alƙawarin bazai taɓa sauraron wata yarinya da sunan soyayya ba inba yarinyar sa ba, shiyasa gaba ɗaya baya shiga harƙar yarinyar da aka kawo gidan su, sai ɗan uwansa da ya nuna yana sonta har akayi Auren su...." Ummy cikin ƙunci da tashin hankali ta ce "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, amma banso haka ba..." Minal ta ɗan ja tsuka ta ce "ni wallahi har naji labarin ya fara fita mun a rai..." Kowa dai baiyi farin cikin haka ba. Aunty Yolash ta cigaba da cewa "haka suke zaman Aure har nan da wasu ƴan shekaru yarinyar bata haihu ba, sai lokaci guda mijin da ta aura wata rana ya gano cewa itace yarinyar da akayi wa ɗan uwansa alƙawarinta ta hanyar wata shaidar da zai nuna cewa ita ce, daga lokacin bai ƙara samun sukuni ba saboda wannan al'amarin kuma yana ganin saboda itace yasa Ɗan uwansa bai yi Aure har yanzu ba, haka shima Yaron yana zaune ya gano cewa wacce ɗan uwansa yake Aure itace wacce yake jira, ya gano haka ta hanyar sarƙarta da kuma zoben alƙawarin da aka musu tin tana ƙarama itama kuma yarinyar tana ajiye da shi, daga lokacin shima bai ƙara samun sukuni ba, ita kuma yarinyar bata san da wannan al'amarin ba, ita damuwar ta sarƙar ta da zobenta dake hannun wancan ɗan uwan mijinta take so ya bata, domin ta hanyar nan take son neman iyayenta, ganin bazata iya jurewa ba yasa ta ƙira ɗan uwan mijin natan akan yazo ya taimaka ya bata sarƙar ta, shi kuwa jin ƙiran daga gareta ne yasa yazo shi, Mijinta kuwa baya nan lokacin haka ta fara roƙon sa akan ya bata sarƙarta da zobe, duk wasu alamun da zai nuna masa cewa itace yarinyar sa ya duba kuma ya tabbatar, ganin a tunaninta bai yadda cewa sarƙar ta bace yasa ta ja shi ɗakinta ta ɗauko Alkur'ani mai girma ta dafa tana masa rantsuwa akan cewa sarƙar ta ce, bata san cewa ya gane itace yarinyar sa ba, ita kuma bata san halin da ake ciki ba, suna cikin wannan halin har zai bata sarƙar kwatsam wasu daga cikin yaran gidan waɗanda basa son farin cikin ta suka feshe su da turare mai sanya munguwar sha'awa wanda a lokacin hankalin su ya gushe suka fita hayyacinsu har suka aikata alfasha dai-dai lokacin da mijinta ya dawo...." Ƙirjin Ummy ne ya buga jin irin abinda ya faru tsakanin Uncle Deen da Baiwar ALLAH, Pinky da Rukky kallon juna suka shiga yi... Aunty Yolash ta ce "a lokacin mijinta yazo ya kamasu daga lokacin ya saka ƙiyayyar su a cikin zuciyar sa sannan ya rabu da matar sa ita kuma matar ta ɗauki ƙiyayya ta ɗorawa ɗan uwan mijin natan, sai dai a lokacin anyi rashin Sa'a juna biyu ya shiga, shi kuma saboda wannan damuwar yasa ya tafi a hanyarsa yayi hatsarin mota, shi kuma mijin yarinyar shima yayi jinyar damuwar da ya shiga daga ƙarshe yayi auren sa, Amma ita yarinyar har zuwa yanzu bata san cewa wanda ta tsana shine wanda akayi mata alƙawari da shi tin yarinta ba sannan an kasa sanar mata domin a halin yanzu yanda ta tsane shi bazata taɓa yadda da shi ba, Shin kun san labarin waye wannan?..." Duk shiru sukayi sai Reemah da Ramlat da suka girgiza kai alamar a'a.. Murmushi Aunty Yolash tayi sannan ta ce "to labarin Razhdeen da Baiwar ALLAH ne..." Reemah zaro ido waje tayi tare da haɗiyan wani irin yawu zuciyar ta na bugun uku-uku, Ramlat itama sake baki tayi tana kallon Aunty Yolash cike da mamaki. Aunty Yolash kallon Reemah tayi sannan ta ce "kin ɗauki tsanar duniya kin ɗorawa mata alhalin ita ce take da Razhdeen, wannan labarin zai nuna miki cewa Razhdeen bazai taɓa sauraron ko wace mace ba indai ba Amreesh ɗinsa ba, don haka wannan ƙiyayyar ki janye shi, sannan kada na sake jin wata daga cikin ku ta ƙira cikin ta da shege ko ƙazamin ciki inba hakaba wallahi zan yi mungun samun matsala da mutum..." Ta kalli Ramlat ta ce "ke ma har zaki iya ce mata ƙazamin ciki? to ina so ki sani cewa Baiwar Allah ba mazinaciya ba ce, wallahi tallahi ko kamo ƙafar ta bakuyi ba a tsoron Allah da kuma yawan ibada, kawai dai ƙaddarar ta ce tazo da haka...." Reemah tana zubda hawaye tare da murmushi ta ce "Allah na gode maka da kasa cikin jikinta na wanda akayi mata alƙawari ne, Allah yayi hakane domin yasan hakan shine zai kawo ƙarshen lamarin, in ba dan ta hanyar nan ba taya Yaya Roshan zai yi gaggawar rabuwa da Aunty Baiwar Allah har Uncle Deen ya same ta duk da bata san shi ba, amma kuma lokacin da muke gidan marayu tana yawan mafarkin wani mai suna Habeey tin shekarun baya baazan taɓa manta sunan ba, kenam shine Habeey?...." Aunty Yolash murmushi ta sau tare da faɗin "tabbas shine Razhdeen shine Habeey ɗinta..." Ummy tana dariya ta ce "wallahi nima na taɓa jin tana wannan mafarkin a lokacin ma baccin rana take wai Habeey ina so na tambaye ta akan waye Habeey ɗin nan amma na kasa..." Aunty Yolash ta ce "Naji Mahaifiyar ta ma tace har yanzu kullum sai tayi mafarkin Habeey, duk maganganun da tayi su tana ƙarama sai ta maimaita su, shine Maman take cewa ko zata sanar mata gaskiyar lamarin ne, muka ce ta bari sai Razhdeen ya dawo tukun duk za'a bayyana mata komai..." Ramlat itama ta tausaya mata da shi kansa Razhdeen sannan tayi farin cikin jin wannan ƙayataccen labarin, kuma tana so ace an bayyanar wa Baiwar Allah wannan kyakkyawar Albishir, sai kuma taji zuciyar ta tayi sanyi yanzu ta cire Baiwar Allah a Bible ɗinta.... Pinky cikin farin ciki ta ce "wayyo farin ciki ashe dai abun alheri muka haɗa har akaita azabtar da mu...." Rukky ta ce "wonderful wayyo zan so muga ƙarshen labarin nan, yanda Aunty Daughter da Uncle Deen zasu ga junan su..." Reemah da hanzarin ta ta miƙe tana faɗin "Ni dai sai naje na gaya mata..." Aunty Yolash ce tayi saurin riƙo hannun ta tare da faɗin "ke wallahi bazata taɓa yadda ba, ai da dabara za'a sanar mata, kada kowa ya kuskura ya sanar mata..." Reemah ta ce "to shikenam bazan gaya ba amma ina son zuwa wurin ta..." Aunty Yolash ta ce "to je ki..." Reemah fita tayi da gudu cikin farin ciki... Ramlat itama tana cikin farin ciki lokaci guda ta haɗe rai domin a yanzu Reemah ce zata zamo abokiyar kishinta domin Roshan ya sanar mata cewa yana sonta... Haka suka cigaba da hirar su a ɗakin... Reemah kuwa haka tazo ta wuce matan gidan a falo da gudu su biyar matan mai martaba da matan Abbah sai Madam Parveen, kai tsaye ta wuce room ɗin Baiwar ALLAH, tana shiga ta tarar da ita kwance akan gado ta kifar da kanta akan gado ba komai take ba sai kuka, domin tin daga lokacin da Roshan ya sanar mata magana da kuma munanan kalaman da Ramlat ta gaya mata yasa take kuka har zuwa lokacin nan, Reemah ce tayo kanta tare da hawa saman gado itama ta kwanta tare da rungumar bayanta.. Baiwar ALLAH ɗagowa tayi ta sauƙe idonta akan Reemah, ganin ta yasa tayi saurin tashi zaune tana faɗin "Ƴar Amana yau ke ce a yanda nake?..." Ƴar Amana ganin hawaye akan fuskar ta yasa tasa hannu tana share mata hawaye itama kukan ne yake shirin kuɓuto mata da sauri tasa hannu ta rungume ta sosai, Baiwar ALLAH cike da mamaki da kuma farin ciki itama bata san lokacin da ta rungumeta ba.. sun ɗau tsawon lokaci a haka kafin daga bisani suka ɗago suna kallon juna, Ƴar Amana tana kuka ta ce "Aunty Baiwar Allah dan ALLAH kiyi haƙuri ki gafarce ni, na aikata miki kuskure saboda son zuciya ta, sannan nayi miki butulci na manta alkhairin da kika mun, tin ina jaririya ta ake baki raino na komai ke kike mun, kin sabar wa kanki wahala saboda Ni, idan bani da lafiya kwana kike bakiyi bacci ba duk ata dalili na, idan na gusa a kusa da ke hankalin ki baya kwanciya har sai kin jawo ni a kusa dake, amma yau ni ce duk na manta wannan saboda son zuciya ta, banyi adalci ba Aunty Baiwar Allah ina matuƙar ƙaunar ki ina sonki ...." ta ƙarasa maganar tare da fashe wa da matsanancin kuka, Baiwar ALLAH ce itama ta rungume ta tana kuka tare da faɗin "duk me ya kawo waɗannan maganganun, nifa nayi miji ne saboda Allah, banaso kina tayar da hankalin ki akan wannan, duk abinda zan yi a rayuwa ina yinshi ne da zuciya ɗaya kuma inayin komai don Allah da kuma ladan da zan samu a wurin sa, saboda ki kwantar da hankalin komai ya wuce, duk abinda ya wuce ya wuce kenam ko a wurin Allah, a rayuwa duk abinda nayi miki da wanda zan yi muku duk bai kai wanda iyayenki suka yi miki ba saboda su sukayi silar kawo ki duniya, ni kuma a duniyar muka haɗu, dan Allah kin san bana son ganin hawayen ki ba..." Reemah ɗagowa tayi tana kuka ta ce "na faɗa miki munanan kalamai na ɓatanci, sannan na kushe miki jaririn dake cikin cikin ki, alhalin ke ma mahaifiya ce a wuri na, shin kin yafe mun? ...." Baiwar ALLAH murmushi tayi sannan ta ce "ni babu abinda kika yi mun, saboda haka ki kwantar da hankalin ki na yafe miki duniya da lahira, ai dai nasan duk kishi ne, kishi kuma kumallon mata, nima ai inada kishi bakida yanda nake kishi akan Yaya Roshan ba..." Dariya Reemah tayi tana girgiza kai ta ce "Aunty Baiwar ALLAH kenam zuciyar ki ta kusan hutawa kema, kin kusan samun muradin ki na gaskiya..." Baiwar ALLAH cikin rashin fahimta take bin Ƴar Amana da kallo tana sakin murmushi... A wannan lokacin Baiwar ALLAH da Ƴar Amana wuni sukayi a ɗaki suna shan hirar su, wanda tsawon shekaru basu haɗu sun zauna kamar yau ba... Har zuwa yamma Baiwar Allah da Ƴar Amana suna tare, tare suka yi sallah sannan suka ci abinci, Baiwar Allah gaba ɗaya ji tayi kamar an yaye mata damuwar ta gaba ɗaya domin a wannan ranar Ƴar Amana ba ƙaramin ɗebe mata kewa tayi ba, suna cikin hirar su sai ga Ƴar tinny ta shigo da gudu tana faɗin "Aunty Daughter wai kuzo Amarya Aunty Pinky zata tafi ƙasar Saudiyya gidan mijinta ...." Ƴar Amana ta ce "a yau ne daman?..." Ƴar tinny ta ce "ai ita kaɗai ce zata tafi a yau har da mijinta Barrister Arash..." Baiwar Allah riƙo hannun Ƴar Amana tayi tana faɗin "tashi muje..." Pinky an shirya ta tsab cikin wedding gown har jan ƙasi yake, an yafa mata gyalen net mai irin rigar jikinta ba ƙaramin kyau tayi ba, Ga masu rakiyar Amarya suma sun sha fashion motoci ne a jere sun kai ashirin duk zasu nufi airport daga nan su shiga jirgi, kowa ya shirya har da su Ummy da Rukky suma dake tafiyar su ba yau bane, su ma har da su zasu je ƙasar Saudiyya ganin ɗakin ƴar uwarsu, ga Minal da Ramlat da Aunty Yolash da matan gidan kab har da baƙin da suka zo biki, Baiwar ALLAH da Ƴar Amana sakin baki sukayi suna kallon kowa da kowa domin su ba'a sanar musu cewa za'a tafi a yau ba shiyasa basu shirya ba, Especially Ƴar Amana da ta kasance daga ita sai wando zuwa gwiwa da T-shirt turo baki tayi ganin kowa yana ta shiga mota ga wankan da suka sha ba ƙarya, Ƴar Amana ganin Mahaifiyar itama tana shirin shiga mota yasa ta ruga da gudu taje wurinta ta riƙe ta tana faɗin "Mama! Mama tafiya zakiyi ki barni..." Aunty A'isha buɗe baki tayi tana kallon ta daga sama har ƙasa ta ce "me zan gani haka? me ya hanani shiryawa kina ganin kowa yana ta shiri..." Reemah ta ce "to ni ban sani ba, naga cewa akayi gobe ne za'a rakasu, tinda safe nake ɗakin Aunty Baiwar ALLAH kuma wallahi sai naje..." Ta ƙarasa maganar tana kukan shagwaɓa haɗi da bubbuga ƙafarta tana jumping, Aunty A'isha ta ce "cab ɗin ai kuwa baki isa ki bini a haka ba kamar wata ƴar inyamura..." "wallahi sai na biku, kuma naga kafin na shirya tafiya zaku yi ku barni, kuma! kuma ban taɓa zuwa ƙasar Saudiyya ba...." Aunty A'isha ta ce "to dole ne sai kinje? ki bari wata rana Abul ɗin ki zai kai ki..." Aunty Maimuna ce tazo gaban Reemah da doguwar rigar Abaya a hannunta yanda taje ta ɗauko mata, ta zura mata tare da yafa mata gyalen Abayar, dake ƙananun kaya ne a jikin ta sai kayan cikin bai nuna ta ba, Aunty Maimuna ta riƙo hannunta tare da faɗin "zo mu shiga cikin motar, ina za'a tafi a barki Shalele..." Ƴar Amana juyawa tayi tana kallon Baiwar Allah wacce take tsaye daga nesa tana mata dariya ganin irin shagwaɓar da take zubawa, Ƴar Amana ta ce "Aunty! Aunty!! ga can Aunty Baiwar Allah itama zata bimu fa..." Aunty Maimuna ta ce "to shiga ciki bari naje na mata magana..." Kai tsaye ta nufi wurin ta, tana zuwa ta same ta tare da faɗin "ya kike tsaye ne kizo mu tafi mana..." Baiwar ALLAH ta ce "gaskiya bazan iya zuwa ba saboda bana jin daɗin jikina sannan bana son hayaniya..." Aunty Maimuna ta ce "to shikenam komai ɗan lafiya ne, ya kamata kije ki kwanta ki huta ko?...." Baiwar ALLAH ta amsa mata tare da sakin murmushi... Ƴar Amana ganin Baiwar ALLAH taƙi zuwa yasa ta fito daga cikin mota tazo yanda take tana faɗin "Aunty Baiwar Allah dan Allah kizo mu tafi kowa fa na gidan tafiya zasu yi..." Baiwar ALLAH ta ce "kinga saboda cikina banason shiga cikin jama'a, nasan za'a iya mauje mun ciki sannan kuma idan hayaniya tayi mun yawa kaina ciwo yake, kawai ku tafi..." Ƴar Amana ta ce "to shikenam nima na fasa zuwa zan taya ki zama, kinga ba kowa a gidan fa..." Baiwar ALLAH ta ce "kinga kije kawai bacci nake son yi, akwai maganin da ake sha, inason zama ni kaɗai ne..." Ƴar Amana ta ce "shikenam Auntyna ki kula mun da kan ki..." ta rungume ta tare da sumbatar ta akan goshi ta tafi, murmushi Baiwar Allah tayi tana farin cikin kasancewar ta da Ƴar Amanar ta... tana tsaye har duk motocin suka tafi, motar Amarya da ƴan uwanta kuwa tin tinin suka tafi, yanzu babu mota ko ɗaya a gidan kowa ya tafi sai iya ita kaɗai, Madam Parveen da Aunty Yolash sunyi tunanin Baiwar Allah da Ƴar Amana a mota ɗaya zasu tafi domin basu yi tunanin bazata je ba, da bazasu barta ita kaɗai ba tinda ba yau zasu dawo ba sai gobe.... Baiwar ALLAH tana tsaye ita kaɗai ta shiga nazarin duniya, can taji cikinta ya yi wani irin murɗewa alamun jaririn ne yake juyawa, da sauri ta kama cikinta tare da sakin ƙara dai-dai lokacin da Roshan ya buɗe gate ɗin compound ya shugo, idonsa ne ya sauƙa akan ta tana shirin kaiwa ƙasi tana riƙe da ciki sai ihu take ta kurmawa... Da sauri ya nufi yanda take yayi saurin riƙo ta kafin taje ƙasi ya mannata a jikinsa yana faɗin "Sorry! Sorry!! Sorry!!! Okay..." hannunsa yakai kan tumbin cikinta yaji cikin ne yake motsi ya ce "Sorry! jaririn ne yake juyi alamun yana cikin ƙoshin lafiya, muje ciki ko ki huta..." Haka ya rirriƙe ta yana tafiya da ita a hankali, ganin tafiyar zai ɓata masa lokaci yasa ya ɗauke ta yayi mata ɗaukar luɗa ya nufi ciki da ita........ Typing ✍️ Asmeetah writer. *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 51 to 55 Kai tsaye ɗakin ta ya nufa da ita, yana shiga ya kwantar da ita akan katafaren gadonta a yayin da ita kuma take ta faman rirriƙe cikin tana hawaye, cikin tausayawa ya kalle ta sannan ya ce "wait am coming..." yana kaiwa nan yayi ficewar sa, ba jumawa sai gashi ya dawo hannunsa riƙe da abun gwaji, yazo ya yi mata gwaje-gwaje yanda ya kamata sannan ya bata wasu magungunan da zata rinƙa sha, a lokacin ya ɓare wasu ya bata ya zauna a gefen ta yana shafa sumar kanta tare da rarrashin ta yana faɗin "sorry yanzu ciwon zai daina, ki kwantar da hankalin ki..." Itama idonta akan sa tana zubda hawaye, tsananin tausayin Roshan ne ya kamata, duk da cikin ba nashi bane kuma ba ta hanyar da ya dace aka samu ba amma bai hanashi bada kulawar sa akan cikin ba, hannunta ta ɗora akan nashi wanda yake riƙe da kanta itama ta riƙe hannun sosai a hankali ta furta "Yaya Roshan..." Idonsa akan ta ya ce "kina buƙatar cin wani abu ne ?..." Girgiza masa kai tayi alamar "a'ah..." Cikin lallami ya ce "ina so ki ɗan taɓa ko kayan fruits ne, zaki ji dama-dama a jikin ki, kuma shima Baby zai samu isasshen lafiya sosai..." Kawar da kanta tayi gefe tana mai jin takaicin halin da ta tsinci kanta. shi kuwa tashi ya yi ya fice bayan wasu ƴan mintuna sai ga shi da parantin kayan fruits har da kular ferfesun kaji da aka ajiye ya ɗauko mata, ajiye parantin yayi akan gado sannan ya jawo table ɗin ɗakin gaban gadon ya ajiye kayan akai, kallon ta ya yi sannan ya ce "zaki iya tashi?..." idonta akansa yanda ta ƙafe shi da su bata ma ji abin da ya gaya mata ba, ganin haka ya kai hannun sa ya riƙo nata sannan ya tallafo bayanta da ɗayan hannun ya ɗagota, sannan ya sa pillow ta bayanta tare da jin gina ta a jikin gadon, cikin kulawa yake ɓare mata ayaba da lemo yake bata a baki, sannan ya yayyanka Apple da pineapple sai da ya gama feeding ɗin ta da kayan fruits sannan ya tsiyaya madara a cup daƙer ta yadda ta sha domin ji tayi ta ƙoshi, ferfesun kajin kam sam ta ƙi ci haka ya haƙura, ya kalle ta sannan ya ce "sauran magani ko dai allura kike so?..." Da sauri ta girgiza kai tare da faɗin "ko ɗaya bana so..." Murmushi ya yi tare da faɗin "wannan zance ne Ammata..." Sanin halin ta bata son shan magani yasa ya je gefen ta sosai tare da janyo ta jikinsa ya matse mata hannayen duk biyun a matsematsin cinyarsa already ya bare duk maganin da zata sha, buɗe bakin yayi tana kakkauce wa amma da haka ya jefa mata su sannan ya kora mata ruwa tare da matse mata hanci, ai ba shiri ta haɗiye su ganin numfashi ya ɗage, ganin tana shirin shiɗewa yasa ya rungume ta sosai a jikinsa yana faɗin "it's okay, shikenam yanzu ya wuce..." Itama rirriƙe shi tayi tana kife da kanta akan ƙirjinsa tana sauƙe numfashi, da haka har ta sauƙo amma bata motsa ba, Roshan ganin shiru sun ɗau mintuna a haka yasa ya ɗago ta yaga ashe har tayi bacci, a hankali ya kwantar da ita tare da ɗora kanta akan pillow sannan ya rufa mata mayafi zuwa saman ƙirjinta sai iya fuska a waje, ido a lumshe sai zararan gashin idon da su ma suka kwanto, shima kwanciya yayi a gefenta ta bakin gado ya zuba mata ido sai kallon kyakkyawar fuskar ta yake ba ƙaƙƙautawa, hannu yasa yana kwantar da girar fuskar ta waɗanda suka kusan haɗewa biyu tsabar yawansa ga a kwance yake gwanin burgewa, hancin ta kuwa a miƙe ziyat kamar ƴar asalin larabawa, hannunsa yakai kan lips ɗinta waɗanda suka ci maroon light ga bakin ɗan ƙarami, haka yake shafawa a hankali, tsananin ƙaunar ta ne a cikin zuciyar sa wanda bazai iya misaltuwa ba, ya kai hannunsa yana shafar lallausar sumar kanta, fuskar ta ya yi fari sol kamar jikin ƴar dedi, a hankali ya kai lips ɗinsa kan nata ya sunbace ta yana lumshe sexual eyes ɗinsa daga bisani ya tashi ya bar ɗakin gaba ɗaya domin baya iya juran zama kusa da Baiwar ALLAH saboda yanzu zata jefa shi cikin matsalar da ba iya magance ta zai yi a halin yanzu ba.... A wannan ranar Roshan yayi zirga-zirga ɗakin Baiwar ALLAH ya kai sau nawa kasancewa babu kowa a gidan balle a samu mai kula da ita, saboda ita ya kasa fita ko ina saboda zata buƙaci wani abu kuma baya so tayi zaman kaɗaici ita kaɗai a gida.. Da daddare misalin ƙarfe 11 Baiwar ALLAH tana zaune ita kaɗai akan sallaya yanda ta idar da sallar lafular ta kafin ta kwanta, tana riƙe da carbi lips na motsi a hankali tana tasbihi, tana cikin wannan halin sai taji an turo ƙofar ɗakin tare da yin sallama, murya ciki-ciki ta amsa ta waiwayo tana kallon sa, shima zama yayi a bakin gado idonsa akan ta can daga bisani ya ce "baki yi bacci ba ne?..." Murmushi tasau kanta a ƙasi ta ce "banyi ba amma yanzu nake shirin kwanciya..." Jinjina kai ya yi sannan ya ce "dare yayi kam, ki kwanta ki huta amma ina zaki iya kwana ke kaɗai anan?..." Ɗago wa tayi tana kallonsa ta ce "kai ɗin ina zaka je?..." In short answer ya bata da cewa "part ɗina..." Kawar da kai tayi ba tare da ta furta komai ba.. Miƙe wa tsaye ya yi tare da faɗin "ni zan tafi, ki kula da kan ki..." Ɗaga masa kai kawai tayi ba tare da ta komai ba sannan kan ta a ƙasi ta kasa ɗogo wa. Fita yayi daga ɗakin bayan ya yi mata sallama, a falo ya tsaya yana tunanin barin ta ita kaɗai, ko cikin dare wata matsala zata iya faruwa, girgiza kai yayi tare da faɗin "i can't leave..." zama yayi akan doguwar kujera ya kwanta tare da yin sakaya kan sa akan pillow kujerar yana kallon ceiling, Twins ɗinsa ne ya faɗo masa a rai lokaci guda ya sau murmushi, ɗaukar wayansa ya yi tare da danna wata number bugu ɗaya aka ɗauki ƙiran Roshan ne ya kara wayar a kunne tare da faɗin "Hello good day my man..." Other side "well Done my twin hw far..." Roshan ya ce "My man ya jikin nakan naji yanzu maganar ka is normal..." Razhdeen ya ce "jiki normal ina son dawowa but Dad ya hana i don't know why..." Murmushi Roshan ya sau tare da faɗin "No Abbah baya so ka dawo yanzu sai ka gama warkewa gaba ɗaya..." Razhdeen ya ce "na gama warkewa fa, just ya barni na dawo am tired, ya haɗani da wasu security ko fita outside basa barina na fita..." Roshan ya ce "ok let me ask you shin kana iya tafiya sosai ba tare da ɗingishi ba sannan ka gudu?..." Razhdeen ya ce "in har sai na gama warkewa har haka akwai lokaci a gaba na kenam, domin tsayuwar ma yaushe nake iya yin sa sosai balle normal tafiya har kuma da gudu..." Roshan ya ce "da sauran ka to, kai da Nigeria sai ka shirya da gaske..." Razhdeen Hmmm! kawai ya ce... Roshan ya kuma cewa "Meyasa baka tambaya ta Amreesh?..." Daga ɓangaren Razhdeen zuciyarsa ce tayi wani irin bugawa, haka zuciyar sa take harbawa da ƙarfi-ƙarfi Muryar sa ce ta fara kakkarwa a hankali yake furta "please Twins she's your wife bai kamata kana mun maganar ta ba, ni na sallamar maka ita..." Girgiza kai Roshan yayi sannan ya ce "My Man! ni fa na haƙura da ita because of you, nafi kowa sanin irin wahalar da ka sha akan Amreesh da halin da ka shiga da kuma jinyar da kayi duk akan rashin ta, kuma sannan ita ta hanaka kula ko wace mace balle kayi tunanin Auren ta, My man adalcin da zanyi maka a rayuwa shine na mallaka maka Amreesh, ina so na cika maka burin ka da kuma mafarkin ka, inaso yanzu ka ɗauki Amreesh tamkar taka ce sannan idan muka yi waya kana mun maganar ta, ni kuwa nayi maka alƙawari Insha Allahu duk wata shawarwari da taimaka wa zan yi ƙoƙarin baka da kuma yi maka, kuma itama zata so na tamkar yadda kake son ta..." Razhdeen daga ɓangaren sa idanunsa ne suka yi jawur tsabar kukan da yake, gaba ɗaya ya rasa mai zai furta wa twins ɗinsa Roshan, cikin cije lips ya ce "My Twins a rayuwa duk wani rashin adalci banyi maka shi ba, na cutar da zuciyar ka tare da ƙuntata maka, babu abu mai muni da tozarci kamar ace mutum ya kwanta gado ɗaya da matar wani, wannan al'amarin yana damu na a raina, ban san ya akayi na aikata haka ba sannan ban san da wani ido zan kalle ka ba, na ci amanarka sannan na zubar da mutunci da kimar family mu, idan na tuno da wannan al'amarin sai in ji gaba ɗaya na tsani kaina, na tsani gida gaba ɗaya, wani sa'in gwara na zaɓi zama ni kaɗai ba tare da family ba, shin idan na dawo aka mun wannan tambayar akan dalilin da ya haɗani da matar ka mai zance? ...." Roshan shima hawaye yake zubda wa idonsa a lumshe ya ce "kaga My Man ka kwantar da hankalin ka mutuncin family da kuma kimar su da darajar su na nam babu abinda ya sauya, sannan maganar wannan al'amari da ya faru mun riga da mun wuce layin nan, bana so muna dawo da magana baya, tinda na ce maka komai ya wuce shikenam ya wuce har abada, Please my man ka daina ɗauko mun wannan zancen, tinda ba laifin ku bane ko a wurin Allah baku da laifi, kuma ƙaddara ce babu wanda yake tsallake ta shi, saboda haka ka fuskanci gaba ka ɗauka komai ba faru ba, shima Abbah da ya san ba yin kan ku bane ai bai yi wata magana akai ba sannan kai ma bai nuna maka wata damuwa ba...." Jinjina kai Razhdeen ya yi tare da goge hawayen fuskar sa ya ce "okay, Insha Allahu zan sassauta wa kaina..." Roshan ya ce "good yanzu dai ka fara shirin yanda zaka mallaki mafarkin ka...." Razhdeen jin ya ambaci mafarki sai kuma Ƴar Amana ta faɗo masa a rai, wani irin yawu ya haɗiya cikin sassanyar murya ya ce "where is Sarah?..." Roshan ya ce "Sarah tana tana gaban iyayen ta cikin ƙoshin lafiya..." Razhdeen murmushi ya sau ganin yanzu Sarah ta gana da iyayen ta, hankalin sa a kwance ya yi hamdala... Roshan ne ya ce "my man bari na bar ka haka saboda ba wani lafiya gare ka ba, insha Allahu nima a cikin wannan satin zan zo duba ka..." Razhdeen ya ce "kai baka gajiya da tafiya ko?..." Roshan ya ce "ai in ban ganka ba hankali na kasa kwanciya yake, especially a halin da kake ciki dole zan rinƙa zuwa yanda kake..." Razhdeen murmushi ya sau tare da faɗin "wish you the best my twins..." Roshan ya amsa masa cikin kulawa da kewar juna a haka suka katsai wayar ba tare da sun so ba... (Ikon ALLAH twins kenam, wato duk wanda ya shiga tsakaninsu shi ya ji kunya...." Roshan yana gama wayar bacci ya ɗauke shi domin yanzu ya daina sa wata damuwa a ransa, ya cire komai a ran sa amma banda soyayyar Baiwar ALLAH, shima a sannu a hankali zai cire ko ba du ka ba.... Cikin dare Baiwar ALLAH ce akan sallaya tayi sallar daren ta kafin da asuba, wani irin yunwa ne ya kawo mata ziyara haka take jin cikinta yana kaɗawa domin yanzu ba ita kaɗai ba ce, tashi tayi ba shiri ta fice daga ɗakin tana sanye da hijab ɗinta har ƙasi, tana fita falo ta tarar da Roshan a kwance kan doguwar kujerar falo sai sharar baccin sa yake, nufan yanda yake tayi har sai da taje gaban sa tukun ta durƙusa ƙasi yanda zata kalle shi da kyau, yana facing ceiling ido a lumshe fuska ɗauke da murmushi haka take kallonsa itama bata san lokacin da ta sau murmushin ba, a hankali ta furta "Yaya Roshan am so sorry but I really loved you, anya zan iya rayuwa da wani ɗa namiji bayan kai? no no no bazan iya baa......" "Zaki iya...." zaro ido tayi waje tana kallon fuskar sa jin amsar da ya bata still idonsa a lumshe.... A ɗan ruɗe ta miƙe tsaye ba shiri ta bar wurin kai tsaye kitchen ta nufa, tana shiga ta tsaya a gaban sink tare da kunna ruwan fanfo ta tsaya idonta akan ruwan amma hankalin ta ya bar jikin ta, dogon tunani ta zurfafa, tana cikin wannan tunanin ganin ruwan da idonta yake kai ya tsaya yasa ta dawo hayyacinta ta waiwaya tana kallon wanda ya kashe ruwan, Roshan ne shima ya tsaya idonsa akan ta ya ce "mai kike son ci?...." Girgiza kai tayi ta ce "babu komai..." Ya ce "Nop! nasan yunwa ne ya fito da ke don haka ki gaya mun mai kike son ci ko sha na haɗa miki ki..." Cikin sassanyar murya ta ce "madara nake son sha..." Ya ce "ok koma ɗaki zan kawo miki..." ba mu su haka ta juya ta fice, shi kuwa bin bayanta yayi da kallo daga bisani ya maida idonsa kan flask zai haɗa mata... tana zaune a bakin gado ya shigo hannunsa ɗauke da cup mai milk a ciki, miƙa mata yayi sannan ya ce "akwai abinda kike buƙata bayan wannan?..." Girgiza kai tayi ba tare da ta furta komai ba, shima juya wa yayi tare da faɗin "Asuba ta gari..." A wannan lokacin babu wanda ya rintsa a cikin su har sallar asuba, haka kuma suka kai rana a lokacin kuma mutanen gidan sun fara dawowa, Baiwar ALLAH da Roshan a falo suke zaune ga table na abinci a gabanta yana bata abincin a baki ata gefe kuma magunguna ne da water bottle, Yana cikin bata sai ga Ummy da Pinky da Ramlat da Minal tana ɗauke da yaronta sun shigo a jere suna shan hirar su, ganin su yasa duk suka tsaya suna kallon ikon Allah, Baiwar ALLAH ce ta motsa zata tashi ganin su zata musu sannu da dawowa ya yi saurin riƙo hannun ta tare da faɗin "wallahi sai kin cinye abincin nan ko zaki tashi..." Babu yanda ta iya haka ta bi umarnin sa idan ya ɗebo abincin a spoon sai ta ɗan buɗe bakin ya bata, ƙarasa shugowa suka yi tare da faɗin "Yaya Roshan tsohuwar zuma ce ta motsa..." Ramlat bin su kawai take da kallo ta gagara cewa komai, neman wuri tayi ta zauna kamar yanda sauran ma suka zauna idonta akan su... Shi kuwa Roshan ko a jikinsa haka ya cigaba da feeding ɗin ta. Reemah ce itama ta shigo da zumuɗin ta tana son ganin Baiwar ALLAH domin tayi missed ɗin ta, tana shugowa baki ta buɗe zata yi sallama idonta ya sauƙa akan su Roshan, sallamar da bata ƙarisa ba kenam, cike da mamaki ta nufi yanda suke tana faɗin "Yaya Roshan ka ce daga jiya zuwa yau kun sha soyayyar ku har kun ƙoshi...." ta ƙarasa maganar tana maida idonta kan Ramlat wacce ko ƙibta idon bata yi ganin yanda ko lura da ita bai yi ba balle yasan tana wurin... Da haka har sauran matan gidan su ma duk suka shishshigo duk wacce ta shigo sai ta tofa albarkacin bakin ta especially Aunty Yolash da Ummy uwar masu gida su kam bakin su ya gagara rufuwa... Bayan ya tura mata abincin haka ya ɗauki maganin gaba ɗaya ya ɓare su ya juyo yana kallon ta ya ce "Haaaa! buɗe bakin..." Girgiza kai tayi tare da faɗin "Yaya Roshan na warke fa..." wani irin kallo ya mata ya ce "ko sai na danne ki irin na jiya...." Ummy wangale bakinta tayi tana faɗin "Ah! Ah!! Ah!!! Danne wa kuma..." Aunty Yolash ta ce "to pah ikon Allah mai kuma ya faru jiya rai ?...." Reemah zaro ido waje tayi tare da faɗin "an zo wurin..." Ramlat takaici kamar ya hallaka ta bata san lokacin da ta ja dogon tsuka ta tashi tabar falon ba, tana fita waje ta fashe da kuka zuwa tayi ta zauna akan wani ɗan dakalin flower sai sharar kuka take.... Can taji an dafa kafaɗarta da sauri ta ɗago tana kallon Roshan wanda fitowar sa kenam, zama yayi a gefen ta tare da faɗin "mai yasa kike kuka?..." Ramlat kallon sa tayi tare da cewa "Baiwar ALLAH da ka nuna baka sonta yanzu me yasa kake bata abinci a baki? sannan a gabana kake furta cewa zaka danne ta irin na jiya shin me haka yake nufi?...." Sauƙe numfashi Roshan ya yi sannan ya ce "ina son tambayar ki wani abu Please, shin kafin ki Aure ni wacece ta fara Aura na? sannan kafin na so ki wacece na fara so? kafin na zauna dake da wa na fara zaman Aure? ina so ki amsa mun tambaya ta..." Ramlat shiru tayi ba tare da ta furta komai ba, ganin tayi shiru yasa shi faɗin "ki bani amsa nace miki..." Tana sharar hawaye ta ce "Ita..." Ya ce "okay kin san dai in badan ta bani matsala ba da babu wanda zai sa na ƙara Aure, a burina da iya ita kaɗai na tsara rayuwata har ƙarshen rayuwata, domin ina yi mata son da babu macen da nayi mata irin sa hatta marigayiya Mariam, kin dai san labarin ta, to ina so ki fitar da idonki akan ta idan har kina son zaman lafiyar ki, abinda kike yayi yawa Ramlat, ba ta hanyar nan zaki mori mutum ba, bana son damuwa Please...." Yana kammalawa ya tashi yayi tafiyar sa... Ita kuwa sabunta kukan ta tayi ita kaɗai a wurin... A washe gari da safe an shirya tsab za'a raka Amaryar Rakesh wato Rukky can ƙasar U.S itama Minal yau zasu koma can itama da Madam Parveen duk zasu tafi gaba ɗaya, Ummy kuwa ita sai gobe zasu tafi da su Mai martaba, A wannan ranar kam har da Baiwar ALLAH za'ayi rakiyar saboda zata je ta ga gidan Mahaifinta amma idan aka tashi dawowa da ita za'a dawo... Ramlat kuwa ƙin binsu tayi saboda family su Baiwar ALLAH ne, haka ta zauna daga ita sai mijinta.. Bayan isar su ƙasar U.S daga lokacin wasu suka fara santin ƙasar domin ƙasar yayi a rayuwa har su ka je gidan Chief domin anan zasu fara sauƙa kafin akai Amarya gidan ta dake cikin country itama, Innalillahi ai kana shiga gidan Chief zaka fara zauce wa domin sai ka gagara tantance wa shin a duniya kake ko a lahira, lahirar ma a aljanna, domin wannan gidan shi ake ƙira da aljannar duniya domin kaf Nigeria babu mai irin gidan nan, gidan ba ƙaramin tsaruwa yayi ba, mutum sai ya ɓata a cikin gidan, Kowa tsaya kalle-kalle yake, sai da suka gama hutawar su kafin daga baya wasu zafafan motoci sun kai hamsin suka zo ɗaukar Amarya za'a kai ta can ɗakin ta, daga nan aka raka Minal itama ɗakin mijinta, washe gari da safe kuma yan Nigeria zasu koma, anan ne aka fara shan fama da Baiwar ALLAH wai ita bazata koma ba, kuma dalilin da yasa bata son komawa saboda Mommynta itama ta dawo kenam bazata koma ba, sai kuka take ta sha ita bazata tafi ba tare da Mommynta ba, daƙer daƙer sai da Daddynta ya rarrashe ta yana sanar mata cewa "da zarar ta haihu zai ɗauko ta..." sai da aka lallame ta tukun ta yadda suka koma Nigeria... Bayan komawar su da kwana ɗaya Mai martaba da iyalansa da Amaryar su Ummy su ma zasu tafi, sun yi niyar tafiya da Reemah amma sam Reemah ta ƙi wai ita zata zauna da Baiwar ALLAH, domin a halin da ta ga Baiwar ALLAH bazata iya tafiya ta barta ba saboda yanzu gidan Abbah ya watse kowa ya kama gabansa, ba sa'o'inta yanzu balle su na ɗebe mata kewa, Ramlat ce daman kuma ita ba shiri suke yi ba tana can part ɗinta, Sai Autar gidan wato Ƴar tinny ita kuma tayi ƙanƙantar da zata zauna da ita tayi hira, sai matan gidan su kuwa ba sa'o'inta bane ba ko wace irin hira zasu yi ba, sannan Hajiya Kilishi tana zuwa wurin aikin ta sai Ammy, hakan yasa Reemah cewa zata zauna da ita har ta haihu kafin ta koma ƙasar su U.S itama ta koma wurin iyayenta ƙasar Jidder.... Tin daga wannan lokacin duk wani kulawar da ya dace Reemah tana bawa Amreesh komai tare suke yi, yanzu kwana ma a ɗaki ɗaya suke kwana, suna kyautatawa junan su yanda ya kamata, Ramlat kuwa idan ba ita tazo part ɗin Abbah ba bata ganin kowa ita kaɗai zata wuni a part ɗinta har sai Roshan ya dawo daga wurin aiki zuwa yamma tin da safe, Baiwar ALLAH da Ƴar Amana yanzu basa zuwa part ɗin Roshan saboda Ramlat, ba kowa ne ya tsayar da zuwan ba sai Baiwar ALLAH, ita ta hana Ƴar Amana zuwa saboda sun fahimci Ramlat tana da kishi sosai ba son zuwan su take ba.... Shi kuwa Roshan kullum kafin ya fita aiki sai ya zo ya duba Baiwar ALLAH ya tambaye ta akan akwai abinda take buƙata ko ji a jikin ta, sannan Ƴar Amana idan ƴan rashin mutuncin ta suna kusa haka zata ce zata raka Roshan wurin aiki, shi kuwa babu yanda ya iya da ita tare zasu tafi, idan ranar weekend ne Roshan da Reemah zasu je bakin swimming pool su zauna su sha hirar su har da video, wannan video kuwa dole sai ta tura wa Ramlat ta Whatsapp, haka ko fita yawon shakatawa zasu yi sai Ramlat ta sani ta hanyar tura video, Ƴar Amana tana mata haka ne saboda ta ƙara ƙuntata mata domin ta lura tana da kishi na hauka ita bata son wata mace ta raɓi jikin mijinta ko alaƙa ta shiga tsakani.. Ramlat ganin abun ya isheta haka kuma da duk kan alamu kamar soyayya ce a tsakanin su yasa ta kai ƙarar Roshan da Reemah wurin Abbah... A falo Abbah ya tara su ga Roshan ga Ramlat ga Reemah da kuma Amreesh sai matan gidan, Abbah ya kalli Roshan sannan ya ce "Roshan an kawo mun ƙarar ka, akan kai da Reemah shin wata alaƙa ce a tsakanin ku?..." Baiwar ALLAH itama tana zaune da ƙaton cikinta wanda haihuwa yau ko gobe, tasan Ƴar Amana tabbas ta kamu da soyayyar Roshan, domin ta taɓa tambayar ta cewa tana son Roshan, ta nuna mata tana son sa sosai da kuma irin kulawar da yake bata.... Amma sai dai shi ba'a san meye a cikin zuciyar sa ba... Roshan kallon Abbah yayi sannan ya ce "Abbah alaƙa kuma? nake ga akwai alaƙa sosai a tsakanin mu...." Abbah ya ce "ba alaƙar ɗan uwantaka ba, alaƙar soyayya nake magana akai domin a cikin gidan nan babu wanda bai lura da irin ƙaƙƙarfar shaƙuwar da ke tsakanin ku ba wai ita kaɗai Ramlat ba..." Reemah itama tana zaune sai sakin murmushi take domin har cikin ranta tana jin Yaya Roshan a ranta, a cikin tana yin wasa don Ramlat taji haushi har takai yanzu da gasken gaske son sa ta shige cikin zuciyar ta, daman wannan ranar take jira wanda kowa zai san akwai soyayya a tsakanin su.... Roshan girgiza kai yayi sannan ya ce "gaskiya Abbah babu wata soyayya a tsakani na da Reemah...." Da sauri Reemah ta ɗago tana kallon sa a tsorace kamar zata yi kuka.. Itama Baiwar Allah ɗagowa tayi ta kalle shi cike da mamaki domin a tunanin ta shima son ta yake... Abbah ya ce "to shishshige wa juna da ku ke fa? ku fita yawo tare koda yaushe kuna tare..." Roshan ya ce "nifah Abbah Reemah na ɗauke ta a mazannin ƙanwata ce jinin jikina, nake ga duk wani kulawar da zan bata da kuma kasancewa wuri ɗaya ba hakan ne zai nuna kana son mutum ba, ina bata kulawa ne a matsayinta Na ƴar uwata, amma ni ko sau ɗaya ban taɓa ji a raina cewa zan Auri Reemah ba gaskiya...." Ramlat ta ce "amma ka taɓa cewa kana sonta ai kuma wai zaka Aure ta..." Kallon ta yayi sannan ya ce "bana so ki rinƙa jefani cikin matsala, a wannan lokacin wasa nake mata kuma itama tasan wasa ne, kuma da dalilin da yasa na furta hakan saboda ke ce kin sako ni a gaba da wannan kishin nakin..." Abbah ya kalli Ramlat ya ce "to kinji abinda ya ce...." Ramlat ta ce "eh Abbah daman ina so ne ayi komai a gaban kowa, tinda shaƙuwar bata soyayya bace shikenam, daman ina son ji ne, idan har soyayya ce anan sai a tsayar da magana ɗaya tinda ita Reemah a matsayin ƴar uwa na ɗauke ta uwa ɗaya uba ɗaya, idan abun farin ciki ne ya same ta zan taya ta idan kuma abun jaje ne sai mu taru mu jajantawa juna...." Ta ƙarasa maganar idonta akan Reemah wacce take sunkuye da kanta ƙasi, domin Ramlat har cikin zuciyar ta ba haka bane, saboda wulaƙancin da Reemah take mata akan mijinta yayi yawa most especially video da take turo mata, gashi yanzu anyi mai kankat a gaban kowa.... Wannan al'amarin Baiwar Allah sam bata so shi ba domin bata san halin da Reemah zata shiga ba ganin yanda Roshan ya bonsata a gaban Ramlat.... Reemah ce ta ɗago da rinannun eyes ɗinta waɗanda sukayi ja lokaci guda ta sauƙe su akan Ramlat jin abinda take faɗi.. Itama Ramlat idonta akan Reemah wani irin murmushi ta sau mata.. Roshan ne ya ce "ni na ɗauka wani magana mai muhimmanci ne ashe duk akan wannan ne, Abbah ina so zan ɗan fita...." Abbah ya ce "to duk ku tashi ku tafi..." Reemah da Baiwar ALLAH tashi suka yi suma zasu koma room ɗinsu, Roshan ne ya kalli Reemah tare da faɗin "Ƴar ƙanwata ko zaki yi rakiya ne?..." Reemah tsabar takaici bata san lokacin da ta wurga masa wani irin kallon harara ba tana shirin yin kuka, da sauri ta wuce room ɗin su.... Roshan cike da mamaki yake binta da kallo daga bisani shima ya fice, Ramlat itama tashi tayi tana faɗin "bari naje na same su mu ɗan yi hira..." Itama ta wuce ɗakin su Baiwar ALLAH da Reemah..... Typing ✍️ Asmeetah writer *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 56 to 60 Ramlat shigar ta cikin ɗaki ta tarar da Baiwar ALLAH tana rungume da Reemah sai sharar kuka take, domin bata taɓa zaton zata fiskanci wannan wulaƙanci ba, suna cikin wannan halin sai ga Ramlat ta shigo tare da faɗin "da kin daina asarar hawayen ki domin ba lallai ne abinda yake ranki ya zama shima hakane ba, daman kece kike shishshige masa domin shi ko kaɗan bakya gabansa, kina ji da bakin sa yake cewa bai taɓa ji a ransa cewa zai Aure ki ba to kinga kuwa iska tana wahalar da mai kayan kara, shawarar da zan baki shine ki daina son maso wani domin kece a wahalai...." Baiwar ALLAH juyo wa tayi tana kallon ta cikin ɓacin rai ta ce "ya kamata ki dakatar da wannan shirmen nakin, har ke ɗin wacece da zaki na kallon kanki wata..." Ramlat ta ce "ni wata ce mana tinda na zama mallakin Doctor Roshan wanda babu ko wace mace a gabansa face ni..." Baiwar ALLAH ta ce "aikin banza kawai bayan ke ya so wasu wanda har yanzu soyayyar ki bai kai rabin nasu a cikin zuciyar sa ba, ke haɗi ne na dole wanda babu yanda ya iya..." Ramlat cikin ɓacin rai take kallon Baiwar ALLAH ta ce "mai kike nufi?..." Baiwar Allah ta ce "ina nufin Auren huce takaici yayi dake, kuma Auren ni na so a lokacin tinda sai da ya ce ya haƙura, har ke kinada bakin magana, wallahi ban san bakida kunya ba sai yau, har zaki dubi idon Ƴar Amana ki rinƙa gaya mata maganganu alhalin iyayenta ne suka suturtaki har suka Aurar dake...." Ramlat a tsawace ta ce "dakata Malama! gori zakiyi mun ne? to sai ki bar masu gidan su yi amma ba ke wanda kike a sakaye ba babu dangin iya bare na Baaba..." Baiwar ALLAH ta ce "ai dai inada asali ko? kuma kaf family na babu abun rainawa sai dai ayi ɗaukin shigan sa..." Ramlat ta ce "familyn da za'aji ɗaukin shigar sa shine familyn da zai kai ka Aljanna direct, ina nufin masu ƙarfin imani da kuma riƙon addini...." Ƴar Amana ɗago kanta tayi daga kan kafaɗar Baiwar ALLAH tana bin Ramlat da kallo, a lokacin take tuno da kalan maganganun da ake gaya wa Baiwar ALLAH a gidan marayu... Baiwar Allah miƙe wa tayi tsaye ta nufi yanda Ramlat take tsaye, tana zuwa ta goya hannayenta akan ƙirji idonta akan ta tasau murmushi sannan ta ce "gwara su saboda tin a baya kafin su musulunta sunada kyawawan ɗabi'u da kuma kyakkyawan zuciya da kuma hali, ko kaɗan basu da abun kushe wa sai dai ace su ɗin Christal ne, kuma yanzu Alhamdulillah ko a yanzu suka koma ga Ubangijinsu Aljanna direct insha Allahu, basu ajiye abun gori ba kuma kyakkyawan niyansu da ayyukansu yana kan binsu har yanzu har ƙarshen rayuwar su, Amma ke fa? abun gori da magana yana ƙarƙashin ki tinda yanzu haka cikin Umanki wanda ku ka sha nono ɗaya tana can gidan prison hauka tuƙuru take ga kuma jarabta daga Ubangiji tana fama da yankekken ƙafa ɗaya duk tsutsotsi sun cinye naman ƙafar, bin bokayen ta da zalunci da girman kai duk baiyi mata amfani ba sai abun gori da ta bar miki, itace shirka bijirewa Ubangiji sannan ita ce sawa ayi kisan kai tirr in banda tsautsayi da ƙaddara ba mai zai sa a haɗa jini daku......." Baiwar ALLAH bata ƙarasa maganar ba taji an ɗauke ta da wani irin gigitaccen mari, ɗagowa tayi tana kallon Ramlat hannu akan fuska tana binta da kallo... ai kafin Baiwar Allah ta furta wani abu taji Ƴar Amana itama ta ɗauke Ramlat da mari, kafin Ramlat ta ɗago haka Ƴar Amana ta ƙara zabga mata a ɗayan ɓangaren, A ruɗe Ramlat ta ce "ni kika mara Reemah? to wallahi bazan ƙyale ki ba..." haka Ramlat ta rarumi glass bottle akan table ta doka akan goshin Reemah... Ƴar Amana ƙara tasau tare da dafe goshin kafin kace mai jini har ya wanke mata fuska, Ramlat ganin haka yasa ta zaro ido waje baki a sake gaba ɗaya ta gama tsorita tsabar ɓacin rai bata san ta doka mata ƙwalba akai ba. Baiwar ALLAH gaba ɗaya hankalinta ya gama tashi haka zuciyarta take harbawa da ƙarfi-ƙarfi, tsabar a kiɗime take ko motsi ta kasa yi sai ƙafar ta da yake ta kakkarwa idonta akan Reemah wacce jini ya gama wanke mata fuska.. Ramlat ce tayo kan Reemah tare da furta "wayyo Allah nashiga uku Reemah dan ALLAH kiyi haƙuri, wallahi ban san lokacin da na aikata miki haka ba...." tana kuka hannunta na kakkarwa ta riƙe hannun Reemah cikin damuwa.. Tsabar raɗaɗi da juyawar ƙwaƙwalwa Ƴar Amana bata san lokacin da tayi kukan kura ta hankaɗa Ramlat baya da iya ƙarfin ta, Ramlat faɗawa tayi kan table sannan ta faɗa ƙasi tana riƙe da cikin ta domin ba ƙaramin buguwa tayi a cikin ba... Itama Ƴar Amana ganin kanta yana ta juyawa tana ganin abubuwa suna komawa bibbiyu bata san lokacin da ta kai ƙasi ba, Baiwar ALLAH ganin haka yasa ta nufi yanda take da gudu itama tayi tuntuɓe da ƙafar Ramlat wacce take kwance sai faman shure-shure take, Baiwar ALLAH sai da ta ɗagu sama kafin ta doku a ƙasi itama, dokuwar da tayi sai akan ƙaton tumbin cikin ta, a ruɗe tasau wani irin gigitaccen ihu na fitar hayyaci lokaci guda ta sume a wurin... Wannan ihun Baiwar Allah sai da ta ratsa kunnen kowa na gidan, Roshan dake cikin motarsa a wurin parking gama wayarsa kenam da Razhdeen yana shirin tayar da mota yaji wannan ihun, ai ba shiri ya fito a cikin motar ya nufi cikin gidan, shima Abbah da saurin sa ya baro falon sa ya koma ciki, duk matan gidan Hajiya Kilishi da Ammy su ma ko wacce sauƙowa tayi daga part ɗinta duk suka nufi ɗakin su dake daga nan muryar ta fito, Abbah da Roshan su ma a tare suka wuce ɗakin. Ƴan aikin gidan kuwa dattijan mata su biyu sukam a falo suka tsaya sai faman lelleƙawa suke, ɗaya ta fito daga kitchen ɗaya kuma dama a falon take tana goge-gogen kujeru da dinning... Su Abbah suna shiga suka tarar da abun mamaki duk tsayawa sukayi suna binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya kuma duk babu mai motsi a cikin su, Reemah tana kwance itama ta suma ga jini yanda yake ta gangaro mata akan goshi har da ƙananun ƙwalba akan goshin yanda suka sossoke ta dake ƙwalbar akan ta ya fashe.... Ramlat itama tana kwance ba motsi ga yanda jini yake bin ƙafarta duk ta wanke sket ɗinta da jini... Sai Baiwar ALLAH ita kam tafi kowa jikkata domin yanda ta kife da cikinta bata ƙara motsawa ba... Abbah bakin sa ne yake ta motsi yana furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un! Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, me zan gani haka..." Ammy girgiza kai take tare da faɗin "wannan da duk kan alamu faɗa sukayi domin gashi har da fashewar ƙwalba kuma a Reemah aka ƙwaɗawa tinda ga duk goshinta yankuwan ƙwalbar ne..." Hajiya Kilishi ta kalli Ramlat ta ce "Blinding kuma Ramlat? kuma tana da ciki fa?..." Roshan tsabar yanda jikinsa yake ɓari bai tsaya furta komai ba haka ya nufi Baiwar ALLAH da hanzarinsa yaje ya ɗago ta domin ita ta ta matsalar babba ce ga kuma a yanda take, especially abun da ke cikinta zai iya raunana sosai, ɗaukar luɗa yayi mata ya fice da ita a gaggauce kai tsaye wurin parking motoci ya nufa, Ramlat itama Hajiya Kilishi da Ammy ne suka ɗago ta tare da fitowa da ita suka nufi da ita wurin motoci, kafin su kai Ramlat kuwa tin tinin Roshan ya ja mota ya tafi da Baiwar ALLAH hospital, Ana saka Ramlat sai Ammy ta shiga Security yaja suka tafi... Sai ga Reemah itama an fito da ita Ƴan aiki su biyu ne suma suka ɗauko ta, itama shigar ta cikin motar akayi Hajiya Kilishi ta shiga Security nan ya tafi da su, daga baya shima Abbah ya shiga mota Sojansa ya ja shi suka nufi hospital, sai ƴan aiki aka bari a gidan da kuma sojojin dake bakin gate.... A wannan ranar wuni suka yi a hospital har dare, Reemah dai ta riga su farfaɗowa duk an ɗaure mata kai da bandeji bayan an ciccire mata ƙananun ƙwalbar da ya shige ta, amma ba ƙaramin ciwo kanta ke mata ba domin anyi mata bugu na gaske ne, duk da ta farfaɗo amma bata gama dawowa hayyacinta ba, bata iya furta komai sai kuka... Itama Ramlat da misalin ƙarfe 10 na dare ta farfaɗo bayan anyi mata wankin ciki domin buguwar da tayi ya janyo mata yin ɓari domin har cikin ya fara juyewa zuwa mutum almost 4 to 5 months, Ramlat jin babu labarin cikin ta yasa ta shiga damuwa sosai haka take kuka ba ƙaƙautawa.. Hajiya Kilishi da Ammy ne suke tare da ita a ɗakin sai faman rarrashin ta suke suna bata haƙuri, Roshan ne ya shigo shima idonsa akan ta cikin ɓacin rai ya tsaya a bakin gadon yana faɗin "duk me ya janyo haka? abun nakun har ya kai haka? a cikin kuna maganganun ku ta fatar baki yanzu har ta kai sai kun taɓa jikin juna? ku karnuka ne?..." Ammy ce ta kalli Roshan ta ce "kaga Roshan ka sassauta haka ka dubi halin da take ciki..." hura iskar bakinsa yayi yana jinjina kai ya ce "shikenam ai, kin yi losses kin rasa abunda ke cikin ki kin huta tinda bakida haƙuri da juriya, itama Ammata gata can har yanzu bata farfaɗo ba tana nan rai a hannun Allah, tana cikin watan haihuwar ta wannan al'amarin ya afku yanzu dole Operation za'a mata yanzu, fatana Allah yasa jaririn yana cikin ƙoshin lafiya...." Yana kaiwa nan ya fice, Ramlat sabunta kukan ta tayi tana faɗin "wayyo Allah na shikenam na rasa cikina, innalillahi wa inna'ilaihi raju'un wayyo ciki naaa...." Baiwar ALLAH tana can duk wani gwaje-gwaje da ya kamata ayi mata anyi yanzu sauran operation.. Abbah kuwa shine a wurin Reemah sai lallamin ta yake akan taci abinci amma taƙi, ga kayan fruits a ɗore kan table ko kaɗan ta ƙi sai hawaye, Roshan ne ya shigo ya zauna a gefen kujerar da Abbah yake yana faɗin "har yanzu ta kasa cin komai?..." Abbah kamar zai yi hawaye ya ce "ina tsoron kar ƙwaƙwalwar ta ya taɓu fa..." Girgiza kai Roshan yayi sannan ya ce "bai shafi ƙwaƙwalwa ba domin duk wani gwajin kai anyi mata, har photon ƙwaƙwalwar aka ɗau tare da tsawaita bincike amma matsalar a iya wajen kai ya tsaya, amma dole zata fiskanci matsanancin ciwon kai da hajijiya haka..." Abbah ya ce "to amma taƙi yin magana da cin abinci gaba ɗaya..." Roshan idonsa akan Reemah ya ce "Shalele Ƙanwata zaki sha milk?..." ya kai hannun sa kan flask na ruwan tea ya haɗa mata shayi mai kauri ya zauna a kusa da ita a bakin gado, ya ɗebi madarar a spoon zai kai saitin bakinta cikin kulawa, wani irin kallo ta watsa masa tare da sa hannu ta buge kofin cikin ɓacin rai, kofin madarar ce ta kife a ƙasin tiles. ɗago wa yayi yana kallon ta ya ce "why?..." Harararsa tayi tare da faɗin "babu ruwanka da ni...." Abbah murmushi yayi jin tayi magana, domin ya tsorita sosai ganin tinda ta farfaɗo bata yi magana ba har wannan lokacin sai yanzu, Roshan kallon ta yake cike da mamaki ya ce "me kuma nayi? ai kune ku ka yi babban laifi tinda ku ka so kashe kan ku..." Reemah ƙoƙarin tashi take zata sauƙa daga kan gadon, Abbah ya ce "ina zaki je Shalele?..." Ta ce "ina Aunty Baiwar ALLAH ban ganta ba tin ɗazu...." Abbah ya ce "itama tana kwance ba lafiya..." A ruɗe ta ce "Meya sameta Abbah?..." Abbah kallon Roshan yayi cike da mamaki, ya ce "ba faɗa ku ka yi a ɗaki ku uku ba? ai gaba ɗayanku sai da aka kawo ku asibiti..." Roshan yana kallon ta ya ce "me ya faru daku har ku ka ji rauni a kayuwanku haka?..." Reemah ƙoƙarin tunowa take tana faɗin "ni gaskiya ban san su ɗin meya same su ba amma dai nasan cewa Aunty Baiwar Allah da Aunty Ramlat suna kan faɗa ne sai Aunty Ramlat ta mari Aunty Baiwar ALLAH, ni kuma bazan iya barin a mareta a gabana ba hakan yasa nima na rama mata marin har sau biyu, shine Aunty Ramlat ta ɗauki ƙwalba ta ƙwaɗa mun akai na...." daga nan Reemah ta fashe da kuka... Roshan zuciyarsa ba ƙaramin sosuwa tayi ba idonsa akan Reemah ya ce "Ramlat ce tayi miki wannan aikin? okay shikenam...." Rai a ɓace ya tashi zai fita Abbah ya dakatar da shi da cewa "ina zaka je?..." Roshan ya ce "zanje na same ta ne, na gaji da ita, ta fara takura mun..." Abbah ya ce "bakada hankali ne, ka je ka ce mata mai? baka ga halin da take ciki bane? da wanne zata ji ga abinda yake cikin ta ta rasa shi kuma du kaje ka sake hawa kanta meyasa haka?...." Roshan ya ce "Abbah baka ga halin da ta jefa su bane? kuma nasan duk laifin ta ne me zai kaita room ɗinsu alhalin ba shiri suke ba..." Abbah ya ce "ita bata shiga halin bane? to ban yadda kaje ka sameta da wannan batun ba..." Roshan ya ce "shikenam..." yana kai wa nan yayi ficewar sa... A wannan Daren akayi wa Baiwar ALLAH Operation an ciro mata zureriyar yarinyar ta kyakkyawar balarabiya cikin ƙoshin lafiya, jaririyar sai kuka take ta sha ga sumar gashi ya rufe mata fuska tsabar yawansa... Ita kuwa Baiwar ALLAH tana kwance bata san a yanda take ba, shin a duniya take ko a lahira duk bata sani ba domin ko alamar farfaɗowa babu.... Washe gari da safe an fitar da Baiwar Allah daga operation room an maida ta wani room ita da jaririyar ta amma sai dai har wannan lokacin bata farfaɗo ba, Hajiya Kilishi ce take tare da ita, ga jaririya a kwance a cikin gadon jarirai an gyara ta an sanya mata kayan sanyi farare na jarirai masu kyau da tsada an rufa mata mayafin kayan, Roshan ne ya shugo da sallama a bakinsa, Hajiya Kilishi ɗagowa tayi ta amsa, samun wuri yayi a bakin gadon da Baiwar ALLAH take ya zauna idonsa akan ta yana faɗin "har yanzu bata farfaɗo ba?..." Hajiya Kilishi ta ce "wallahi ni ko motsi ban ga tayi ba..." Jan dogon numfashi yayi tare da faɗin "Insha Allahu zata tashi bada jumawa ba saboda akwai alluran da aka mata..." Hajiya Kilishi ta ce "Allah ya tashi kafaɗunta..." taje ta ɗauko jaririya tana ƙudundune a cikin mayafi ta kawo wa Roshan tana faɗin "to ga ƴarku nan cikin ƙashin lafiya..." Roshan hannu yasa ya karɓe ta da murmushi akan fuskar sa, ya ɗan buɗe mata fuska sai yamutsa ɗan ƙaramin bakin ta take kamar wacce take shan nono, fatar bakin jajawur, haka Roshan yake bin fuskar yarinyar da kallo, ganin sumar gashin dake kan yarinyar har zuwa kan goshin ta yasa ya kalli Baiwar ALLAH yaga itama irin sumar gareta ga gashin gira itama yarinyar hakane da zararan gashin ido, amma kamannin sak irin na Razhdeen ta ɗauko da hancin kamar an tsaga kara, ga yarinyar fara sol har ta fi uwarta da ubanta fari.. Roshan shi kaɗai sai sakin murmushi yake, A hankali ya furta "so beautiful..." Hajiya Kilishi ta ce "ai kwana tayi tana kuka sai da aka kawo madara tasha kafin tayi bacci..." Jinjina kai yayi sannan ya ɗago ta tare da kai bakinsa saitin kunnen ta yayi mata ƙiran sallah tare da jero mata Addu'o'i a kunnen duk biyun.. Hajiya Kilishi ta ce "amma har yanzu ba'a sanar wa Razhdeen yanada jini a ajiye ba ko?..." Girgiza kai Roshan yayi sannan ya ce "bai san ta ɗauki cikinsa ba, har sai ya dawo tukun ya gani da idonsa..." Suna cikin hirar su sai ga Abbah da Reemah sun shigo, da sauri Reemah ta nufi kan Baiwar ALLAH ta zauna a kusa da ita dab da Roshan tana shafa fuskar ta tare da faɗin "Allah sarki Aunty nah ashe haka kika shiga wannan halin ban sani ba, Allah ya baki lafiya..." ta ɗago tana faɗin "ina jaririyar tamun?..." hannu tasa ta karɓe ta a hannun Roshan tana dariya, ganin yarinyar yasa ta calla ƙara tana dariya ta ce "wayyo kyakkyawar halitta, anya wannan mutum ce? kyan ta yayi yawa wallahi tafi mamanta da babanta kyau wallahi, ga fara ce sosai har ta fi ƴan india kyau, kamar balarabiya amma kuma kamar tafi su kyau su ma, ni na rasa gane kyan su wa ta ɗauko yarinyar nan, ga gashi tin yanzu ya rufa mata kafaɗu, amma sumar gashin Maman ta da babanta duk sunada sumar gashi don haka su ta ɗauko, amma kuma ina ganin kamannin Yaya Razhdeen a fuskar ta fa...." Haka Reemah take ta maganganu marasa kan gado, su kuwa su Abbah sai dariya suke ta mata, Hajiya Kilishi ta ce "ke wai ni zaucewa kika yi ne?.." Reemah ta ce "ai dole na zauce Mommy Babba Yarinyar ta shiga mun rai sosai..." A wannan ranar duk a asibiti suka sake wuni, Abbah ne kawai ya tafi, dake an sallami Reemah yanzu su biyu suke zaune da Baiwar Allah da ita da Hajiya Kilishi, Ammy kuma tana ɗakin da Ramlat take itama babu halin tashi sai an zauna da ita, A haka har suka yi kwana uku a hospital a wannan ranar ne mutanen ƙasar Jidder suka zo, Aunty A'isha da Aunty Maimuna da kuma Ummu uwar masu gida yau anzo Nigeria sai murna take, duk sun zo asibiti duk wanda ya ɗauki jaririya sai ya yi hamdala, itama Ummy ba ƙaramin zaucewa tayi akan yarinyar ba, duk ta tafi da imanin duk wanda yazo ganin ta, Baiwar ALLAH tana zaune jikinta ya fara warwarewa, tin da ta tashi bata ɗauki jaririyar nan ba idan aka bata kawar da kanta take gefe taƙi karɓa, sai dai taga yarinyar a hannun mutane amma bazata ɗauke ta ba, especially idan ta tuno ta hanyar da aka sameta sai taji ta tsani kanta da jaririyar gaba ɗaya, Nono kuwa ko sau ɗaya bata ba ta ba sai madara mai kyau da tsada ake bata.. Washe gari da safe Reemah da Ummy sune suke tare da Baiwar ALLAH yau sun ci alwashin dole sai Baiwar Allah ta ɗauki jaririyar nan sannan ta bata Nono, Babu yanda basu yi ba amma Baiwar Allah fur ta ƙi, daƙer da dabara da lallami suka sa Baiwar Allah ta karɓi yarinyar sannan Reemah ita da kanta ta buɗe rigar Baiwar Allah takai bakin yarinyar sai tin ƙirjinta, da haka har yarinyar ta kama, babu yanda Baiwar ALLAH ta iya haka ta bar yarinyar ta sha nono har sai da ta ƙoshi tukun... Ummy ce ta kalli Reemah sannan ta ce "ni bakije kin duba jikin Aunty Ramlat ba koh?..." Reemah ta ce "ina ruwana da ita bazan je ba, naji wai har yau kuka take saboda cikin ta ya zube ko...." Ummy ta ce "ai dole tayi kuka ɗora rai akan cikin, kuma ya wuce zube wa sai dai ɓari domin cikin ya fara zama mutum fa kuma naji tana cewa ke kika yi silar ɓarar mata da cikin..." Reemah ta ce "ai dole nasan sai ta ɗora mun sharrin nan, kinga fa ciwon goshi na ita ta kwaɗa mun ƙwalba fa har sai da bottle ɗin ya fashe da yanzu ƙwaƙwalwata ta juye...." Ummy ta ce "ai kuwa ran Mamanki ba ƙaramin ɓaci yayi ba har sai da tayi kuka, wai ma duk mai ya jawo hakane ?..." Reemah ta ce "au ita bata sanar akan meye akayi faɗan ba?..." Ummy ta ce "wallahi kuwa ita matsalar ta ta faɗa..." Reemah ta kalli Baiwar ALLAH wacce take zaune tana jinsu ga yanda ta kwantar da ƴarta a gefen ta, Reemah ta ce "ki ji Aunty Baiwar Allah..." Baiwar ALLAH jinjina kai tayi ba tare da ta furta komai ba.. Ummy ta ce "akan Yaya Roshan ko?..." Reemah ta ce "zancen maganar kenam, ita ta jawo ruwa sama, ruwa kuwa ya mata shegen duka, ba gashi ta jawo abinda zai dame ta yanzu ba tinda ta sanadin haka ta rasa cikin da take burin haifan sa..." Suna cikin hirar su sai ga Roshan ya shigo tare da faɗin "shikenam in an haɗu an ringa tsegumi kenam ko?..." Murmushi Ummy tayi ta ce "Yaya Roshan kenam ka ji abinda muke cewa?.." Roshan ya ce "ina zan tsaya sauraron shirmen ku nan da baya ƙare wa..." Reemah kawar da kanta tayi tana kallon gefe fuska a haɗe, Roshan ya ce "ƙanwata ya dai kwana biyun nan nake ganin ki a haka?..." Juyowa tayi ta harare shi sannan ta ce "Ni ba ƙanwar ka ba ce, ban san ka ba baka sanni ba.." Roshan ya ce "Ni ban isa nace ban sanki ba Ƙanwata, amma me yayi zafi haka, idan nayi laifi a gafarce ni..." Reemah ta ce "Yaya Roshan ba ka ce baka sona ba, to tinda baka sona sai ka daina kulani, duk wanda baya sonka ai maƙiyin ka kenam..." Roshan ya ce "subhanallahi maƙiyi kuma? ni na isa nace bana sonki Shalele?..." Reemah ta ce "a gaban kowa ka sanar wa Abbah cewa baka Sona, kai da iya matarka zaka zauna har ta samu bakin yi mana rashin kunya ...." Murmushi Roshan yayi sannan ya ce "wannan ai akan Aure yake tambayata, kinga kuwa ba soyayyar Aure muke ba..." A zabure Reemah ta miƙe tsaye cikin kuka take faɗin "to ni Soyayyar Aure nake maka Yaya Roshan, ina sonka ina son Auren ka..." Daga bakin ƙofa suka ji ance "to kuwa bazaki taɓa Auren sa ba dan ubanki wawuyar yarinya marar sanin kara..." Duk waiwaya wa sukayi suna kallon Aunty A'isha wacce ta shigo tana riƙe da hannun Ramlat suka ƙarasa shugowa sai Aunty Maimuna da Hajiya Kilishi da Ammy duk suka shigo, Aunty A'isha zaunar da Ramlat tayi akan kujerar ɗakin sannan ta juyo kan Reemah tana faɗin "baki da hankali Reemah? ashe zaki iya yin sanadiyyar zubar da cikin mutum? kashe Ramlat zakiyi ne? to bari kiji kamar yanda kike a mazannin ƴanta wanda na haifa haka itama Ramlat a matsayin ƴar ciki na na ɗauke ta, ƴar uwa take a wurin ki tinda tin tana yarinya ƙarama take tare da Mahaifinki, shi ya raine ta, kafin ya saba da ke da ita ya fara sabawa tsawon shekara da shekaru, kin zubar mata da ciki meye ribar ki? daman ni wallahi ban so zaman ki anan ba saboda nasan bazaki bar su suyi zaman lafiya ba saboda tin kafin mu tafi kike nuna alamun haka...." Reemah tana kuka ta ce "Mama wallahi....." bata ƙarasa ba taji Mamanta ta ɗauke ta da mari tare da kai mata duka.. Roshan ne ya jawo Reemah jikinsa yana faɗin "dan ALLAH banda duka, kuma itama taji rauni sosai kar aga laifin ta ita kaɗai, kuma babu yanda za'ayi da hankalinta ta ɓarar mata da ciki..." Ramlat itama tana kuka ta ce "wallahi ita ta ture ni na faɗi cikina ya zube..." Sai a lokacin Baiwar ALLAH tayi magana idonta akan Ramlat ta ce "kafin ta ture ki mai kika aikata mata?..." Ramlat shiru tayi kanta a ƙasi sai zubda ƙwallah take.. Baiwar ALLAH ta ce "ya kamata a rinƙa yi wa juna adalci...." kaf abubuwan da suka faru duk Baiwar ALLAH ta zayyanar bata ɓoye komai ba da sanadiyyar raunanar kowa ... Roshan wani irin kallon takaici ya wurga wa Ramlat yana faɗin "daga mari sai ɗaukan ƙwalba ki doka mata akai saboda rashin tunani, hakan nan idan wuƙa kika raruma zaki caka mata..." Ya kalli sauran mutanen ya kuma cewa "to meye laifin Reemah anan? har ana cewa ita ta ɓarar da ciki tayaya? to idan hakane itama Ramlat ita ta jawo akayi wa Ammata Operation har ta jikkata sai da tayi kwana biyu kafin ta farfaɗo, idan a lokacin jaririyar cikin ta ta raunana fa? saboda haka bana so aga laifin kowa in ba na Ramlat ba, saboda ita ta kai kanta sannan bada arziƙi taje musu ba, har tana goranta wa Ammata cewa iyayenta Christal? wani irin hauka ne...." Ramlat miƙe wa tayi tana kuka ta ce "Yaya Roshan daman ba Sona kake ba, baka taɓa goyan bayana ba sannan cikin jikina dana rasa baka nuna damuwar ka akai ba, ni kaɗai na damu da cikina amma kai sam babu ruwanka saboda ba Sona kake ba...." Roshan cikin ɓacin rai ya ce "eh bana sonki kije, indai da haka zan zauna da ke ba zan taɓa sonki ba, idan kina so na damu dake to kema ki damu da waɗannan mutane biyun, Reemah da Ammata domin su ɗin masoyana ne, kuma wallahi tallahi indai aka ƙara sa hannu a jikin Reemah da suna duka ko mari ta sanadiyar ki to kisa a ranki cewa daga ranar na rabu da ke har abada...." Ramlat ba abinda take sai kuka, duk babu wanda ya ƙara furta komai a cikin su sai Reemah da tayi hanyar fita, Aunty Maimuna ce ta kalle ta ta ce "ina zaki je Shalele?..." Reemah tana kuka ta ce "zan tafi ne..." ta ce "ina kuma?..." Reemah ta ce "zan koma inda na fito, zuwana cikin ahalin nan ya sanya wasu cikin ɓacin rai, kullum a cikin fushi ake da ni, idan ina nam babu kwanciyar hankali gwara kawai na tafi...." Aunty Maimuna ta ce "Shalele mai kike faɗi hakane?..." Baiwar ALLAH buɗe baki tayi tana kallon ta kamar zata yi kuka.. Aunty A'isha idanuwanta ne suka cicciko ta ce "Reemah ki dawo nace..." Reemah girgiza kai tayi ta ce "Bakya sona ya za'ayi na zauna da ke, kin nuna mun kin fi son Ramlat akaina, na haƙura da iyayena gwara naje na zauna ni kaɗai nafi jin daɗi..." tana kaiwa nan ta fice, Aunty A'isha a ruɗe ta ƙwalla ƙiran sunanta, Tare da bin bayanta da gudu, suma bin bayan ta suka yi har Roshan da Ramlat kowa fita yayi... Baiwar ALLAH tana zaune ita kaɗai da jaririyar ta a jefe, a hankali ta ɗauki jaririyar tana kallon ta sosai ga hawaye yanda yake ta zuba mata a fili ta ce "Baby na ina matuƙar ƙaunar ki har cikin zuciyata, laifin Abbanki ne ya shafe ki, duk da nasan ban kyauta miki ba, nayi miki babban laifi, ta hanyar da ya dace na kawo ki duniya bata nan kika zo ba, nasan zaki ji haushi na, dan Allah ki yafe wa Mamanki, kar kiyi fushi da Mamanki kinji ko, ina so kiyi rayuwa cikin ƴanci, inasonki...." ta sumbaci yarinyar akan goshi sannan ta sauƙar da ƙafar ta ƙasi ta miƙe daƙer taje ta kwantar da yarinyar akan gadonta na yara, sannan ta ɗauki wani littafi akan table da biro tayi dogon rubutu ta nannaɗe ta ajiye a cikin gadon jaririyar ta gefen ta, sai da ta shafa kan yarinyar kafin ta yafa gyalen ta ta fice daga ɗakin..... Reemah kuwa tana kan gudu kwatsam ta ci karo da su Abbah da Mai martaba wanda isowarsa kenam, Abbah ya ce "ha'a Shalele ina zaki je haka kike ta gudu..." Mai martaba murmushi yayi tare da faɗin "My rigimata zo mana..." yasa hannu ya rungume ta cikin nuna farin ciki domin ba ƙaramin ƙaunar Reemah yake ba, yana matuƙar ji da ita har cikin zuciyarsa.. Sai ga sauran su ma sun fito da saurin su, Aunty Maimuna ce ta ce "yawwa Allah mun gode maka daka kawo mana agaji..." Abbah ne yake tambayar su cewa "me yake faruwa ne?.. " Aunty Maimuna ce ta kora musu bayanin abinda ya faru, Abbah ya ce "meyasa haka kuma? ya zaku sa yarinya a gaba ku ce ita ta zubar da ciki meye haka? faɗa suka yi a junan su kuma kowa ya raunana, ita Daughter ba Operation dole akayi mata ba? Ƙaddara ne da tsautsayi ya kuma afku sai a bar maganar haka..." Mai martaba sam bai ji daɗin abinda Aunty A'isha tayi wa Reemah ba domin tasan dole yarinyar zata ga kamar ba'a sonta.. ɗagota yayi tare da faɗin "Shalelen Abul kiyi haƙuri kinji, idan kika tafi mutuwa zanyi, kina so Abul ɗinki ya mutu?..." Da sauri Reemah ta girgiza kai, ɗagowa tayi tana kallon Mahaifinta sai anan Mai martaba yaga shatin hannun Aunty A'isha yanda ta mare ta bayan ɗaurin bandejin dake ɗaure akan goshin ta, shafa wurin yayi rai a matuƙar ɓace ya ɗago yana kallon Aunty A'isha ya ce "wani irin mari ne haka?..." kallon Mai martaba tayi kamar zatayi kuka tazo yanda yake tasa hannu ta juyo da fuskar Reemah taga zanen shatin hannu, kallon ta tayi cikin tausayawa ta ce "My Reem kiyi haƙuri ki yafewa Mamanki, rai nane ya ɓaci sosai shiyasa, ba wai bana sonki bane bana so Ramlat tayi zaman kaɗaici ne kinga yanzu bayan mu bata da kowa, idan ban nuna na damu da ita ba zata ga kamar mun jefar da ita ne saboda mun same ki, don haka kiyi haƙuri kimun uzuri ..." Reemah fashewa tayi da kuka haka Aunty A'isha tasa hannu ta rungume ta a jikin ta tana rarrashin ta, tare da faɗin "Insha Allahu bazan ƙara dukan ki ba, tare zamu koma dake bazan bar ki ba kar wani abu ya sake ɓullo wa...." Ramlat kuwa tin kafin ta fito marar ta ya riƙe a wurin ta faɗi tana kame da cikin ta, Roshan ne ya waiwaya jin kamar ƙaran kuka, ganin Ramlat a durƙushe yasa ya juya baya ya koma gareta, ɗagota yayi ya zaunar da ita akan kujerar wurin shima ya zauna a gefenta yana faɗin "meya faru ne?..." tana kuka ta ce "ciki na ciwo..." Ya ce "kin san da hakan kika fito? ai da sai ki zauna a ciki tinda kinsan kinada matsala..." Kallon sa tayi tana kuka gaba ɗaya ta zamo kalar tausayi, Roshan a hankali ya ce "Ramlat ki daina kukan nan mana..." Ta ce "kai ne baka Sona Yaya Roshan..." Roshan ya ce "kiyi haƙuri rai nane yake a ɓace banaso kina haɗa ƴa da uwa, gashi a kan ki mahaifiyar ta tazo tana dukan ta alhalin itama tanada ciwo a jikinta ta sanadiyar faɗan ku, nace ki daina shiga damuwar su, kina kawar da kan ki akan su, duk abinda Reemah zata yi just leave her she's a younger girl, yarinta yana damunta shiyasa nake binta a hankali, please ki kwantar da hankalin ki, gashi yanzu kin mun losse Baby...." Ramlat tana kuka ta kwantar da kanta akan ƙirjinsa, shima rungumarta ya yi yana rarrashinta... Suna cikin wannan halin sai ga su Abbah sun shigo, Mai martaba yana riƙe da hannun Reemah ga Aunty A'isha da Aunty Maimuna da kuma Hajiya Kilishi da Ammy da kuma Ummy duk ana suka tarar da Roshan da Ramlat, Abbah ne ya ce "lafiya kuwa kuke zaune anan?..." Roshan ya ce "wallahi jikin ne bai gama warwarewa ba..." Reemah wani irin harara take wurga musu, zuciyarta wani tafarfasa yake yana harbawa... Abbah ya ce "to ka kaita ɗakin da aka kwantar da ita gwara ta kwanta ta huta...." Roshan ya ce "tam shikenam..." Mai martaba ne ya dubi Ramlat sannan ya ce "Ramlatu ya jikin nakin?..." Sai yanzu Ramlat ta lura da Mai martaba cikin fara'a ta gaishe shi, Amsawa yayi tare da jajanta mata rashin da tayi. Roshan yana riƙe da ita ya wuce da ita room ɗin ta, suma wuce wa suka yi ɗakin mai haihuwa, tin kafin su shige suke jin kukan jaririya, shiga suka yi da sallama a bakin su gani suka yi babu Baiwar ALLAH sai yarinyar dake cikin gadonta mai basket, Abbah ne ya ce "ha'a ina kuma tayi tabar yarinya sai kuka take?..." Ummy ce ta ɗauki yarinyar, Hajiya Kilishi ta ce "ko dai tana cikin toilet ne, mu jira ta fito...." Kujera aka bawa Mai martaba da Abbah suka zauna, sauran kujerun kuma Aunty A'isha da Aunty Maimuna da Ammy ne suka zaune sai Hajiya Kilishi, Reemah da Ummy kuma a bakin gado suka zauna, Suna zaune har minti talatin shuru babu labarin Baiwar ALLAH, Mai martaba ya ce "lafiya kuwa har yanzu shuru?..." Roshan da Yarima ne suka shigo a tare, ganin yanda akayi shiru ne yasa Roshan cewa "lafiya kuwa?..." Hajiya Kilishi ce ta ƙara cewa "to kun san wankan jego sai a hankali....." Abbah ne ya katse ta da cewa "ke dallah haba ko wankan mutuwa ne iyaka ci, ki tashi ki shige kije ki dubo mana ita..." Hajiya Kilishi tashi tayi taje ta buɗe toilet ta shige ciki, ba jumawa ta fito tana zazzaro ido, Abbah ya ce "yadai?..." Hajiya Kilishi "wallahi bata nan..." A zabure Abbah ya miƙe yana faɗin "bata nan kuma?..." Mai martaba ya ce "to ina kuma taje ta bar jaririya?..." Roshan wani dimm yaji cike da mamaki ya ce "whattt?..." Kallon jaririyar yayi dake hannun Ummy, Zaro wayar sa yayi zai ƙira number ta, bugu ɗaya yaji wayar tana ringing a cikin gadon jaririya, nufan wurin yayi yasa hannu a ciki ya ɗauki wayar yana jujjuya wa, idonsa ne ya sauƙa akan wata takarda, cike da mamaki yasa hannu ya ɗauki letter, ganin takarda yasa zuciyar kowa bugawa,.. Aunty Yolash ce ta shigo da sallama a bakinta cikin farin ciki ta shigo tana faɗin "a gafarce mu sai yau muka zo ganin ƴar jikallen mu..." Aunty Yolash ganin kowa fuska ba annuri yasa ta tsaya ta ce "lafiya kuwa? ..." Ummy ce ta ce "Aunty yanzu muka shigo muka tarar da Aunty Daughter bata nan, ga jaririya sai kuka take..." Aunty Yolash ta ce "subhanallahi to ina taje?..." Abbah idonsa akan Roshan ya ce "meye a cikin takardar nan?..." Aunty Yolash ce tasa hannu ta karɓi takardar ta buɗe da sauri, a fili ta fara karantawa kamar haka: "Assalamu alaikum! Abbah na dan Allah kuyi haƙuri daman na ƙudurta a raina cewa duk lokacin da na haihu zamana a gidan ku ya ƙare sakamakon abinda ya faru a tsakani na da Razhdeen, idan yarinyata ta taso ban san da wani ido zata rinƙa kallo na ba, nasan itama zatana mun kallon mazinaciya kamar yanda kowa yake mun kallon haka, kuma nasan bazan iya juran ganin ana goranta mun yarinya kamar yanda ake goranta mun ba, ga shi na haifa muku dan Allah kuyi haƙuri ku riƙe mun ƴata kamar yanda ku ka riƙe ni da amana, Nagode sosai da irin kulawar da ku ka ban, Yaya Roshan ina matuƙar ƙaunar ka amma a yanzu dole zan cire sonka a cikin zuciyata domin kai ɗin ba nawa bane, kuma nima ba naka ba ne domin ban cancanci ka zauna dani a matsayin matarka ba, amma ina so ka ɗauki ɗiyata tamkar ɗiyarka, sannan magana ta ƙarshe inason sanar maka cewa ƴar uwata Reemah tana matuƙar ƙaunar ka dan Allah kayi mata halacci, ita ɗin yarinya ce ƙarama bana so ta kamu da ciwon soyayya, kamar yanda kayi niyar zama da mata biyu wato Ni da Ramlat inaso yanzu Reemah ta maye gurbi na dan ALLAH Yaya Roshan, Sannan idan Razhdeen ya dawo ku sanar masa cewa ga ɗiyarsa nan na haifa masa, sannan na yafe masa amma banaso na ƙara yin ido huɗu da shi, idan kuwa hakan ta faru to bazan yafe masa ba domin zai fame mun ciwon dake cikin zuciyata, Kada kowa ya neme Ni domin babu wanda zai same ni, hatta iyayena su ma ba zasu san a yanda nake ba, Alfarma ta ƙarshe da za'a mun shine idan yarinyata ta girma ku sanar mata cewa Mamanta ta mutu, Kowa da kowa ya gafarce Ni, Bissalam!...." Cikin tashin hankali Abbah ya doku akan kujera yana firfito da ido waje, tare da faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, me zan ce wa iyayenta? gashi yau suna kan hanyar su ta zuwa...." Mai martaba ba abinda yake faɗi illa "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un...." A ruɗe Reemah ta miƙe tsaye tana zubda ƙwallah, Aunty Yolash cikin tashin hankali ta ce "nashiga uku na shigo cikin farin ciki ashe zan tarar da labari marar daɗin ji..." Kowa babu wanda bai ji daɗin wannan lamarin ba.. A ruɗe Roshan ya yi waje da hanzarin sa..... Typing ✍️ Asmeetah writer *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 61 to 65 Fitar Roshan motarsa ya shiga ba shiri ya ja motar da gudu wanda shima kansa bai san ina ya nufa ba, baza idanuwa kawai yake ko zai ga Baiwar Allah amma duk layin da ya bi baya dace, ya yi tambayar amma babu wanda ya ce ya ganta har photonta yake nuna wa amma babu labari, Roshan har ana ƙiran sallar mangariba amma bai koma ba, ta ko ina bi yake lungu da sa ƙo amma Baiwar Allah shiru babu labarin ta, bai tashi komawa hospital ba sai ƙarfe 10 na dare... Abbah gaba ɗaya ba ƙaramin shiga damuwa yayi ba, kowa na waran babu wanda bai jijjiga ba, ga jaririya a hannun Ammy tana bata madara, dake bata wani saba da shan nono ba kullum madara mai kyau ake bata, domin tin da aka haife ta sau ɗaya tasha nonon mahaifiyar ta.. A wannan daren Abbah ya sanar cewa su wuce gida, Gaba ɗayan su gida suka koma har Ramlat, a wannan ranar kowa kwanan baƙin ciki ya yi... ★★★★★ Ita kuwa Baiwar ALLAH gidan marayun da suka zauna ta koma, taje a mazannin ta kai musu ziyara ne, cikin sa'a ta samu mutuminyar ta wato Aunty Habiba, akwai da ta sani sosai waɗanda ta barsu har yanzu suna nan da kuma sabbin fuskoki waɗanda suka je daga baya, waɗanda suka san Baiwar ALLAH sunyi matuƙar farin ciki sosai da ganinta, Akwai wata ƙawarta a ɗakinta ta sauƙa, sun yi mata tarya ta musamman, sannan Baiwar Allah tayi musu dubun alkhairi domin tana da maƙudan kuɗaɗen da bata san yawan su ba a cikin account ɗinta, saboda kuɗin da take da su account ɗinta sunyi biyar kuma ko wanne da lodin kuɗi a ciki, iyayen ta kullum a cikin turo mata kuɗi suke, mahaifinta kullum yana kan turo mata, sannan mahaifiyar ta itama tana kan turo mata ga Yayunta su ma koda yaushe idonsu akanta yake, shima Abbah sai dai taga ya tura mata kuɗi duk da bata rasa komai a gidan ba, ita kuma ba komai take siya ba, ko kaɗan bata iya kashe kuɗi ba, da ta tashi zuwa gidan marayu sai da taje super market tayo siyayyan kayayyaki da takalma kala-kala komai-komai sannan ta loda su a cikin motar haya kai tsaye sai gidan marayu, sannan da ta je ta raba musu kuɗaɗe masu yawan gaske, Suna zaune a ɗaki duk waɗanda suka santa suna ɗakin duk zagaye ta, Baiwar Allah ƙaresu da kallo tayi daga bisani ta ce "ya na ganku bakuda yawa ne duk ina sauran ƙawayen namun? sai sabbin fuskoki nake gani..." wata daga ciki ta ce "wallahi duk basa nan muma Allah ne yasa zaki tarar da mu, wasu sun haɗu da iyayensu, wasu kuma masu kuɗi ne suka ɗauke su a mazannin ƴan aiki, wasu kuma sun yi Aure, yanzu gamu nan bamu fi mu goma ba..." Baiwar Allah ta ce "Allah sarki rayuwa kenam, kamar baza'a kawo wannan lokacin ba, kuma Allah ya fidda ku, zan so ku haɗu da iyayen ku..." Wata daga ciki ta ce "yo mu kam ina zamu ga iyayen mu bayan an tabbatar cewa sun rasu, dangin su kuma duk babu masu ƙarfi suka ce kawai na cigaba da zama anan har Allah yasa mijin Aure ya fito mun, kinsan fa wasu mazan har nan ake zuwa neman matan Aure saboda sun fi son su ciyar da marayu..." Baiwar Allah ta ce "Allah sarki..." ta kalli Aunty Habiba sannan ta ce "Aunty Habiba meyasa bakiyi Aure ba keɗin? kuma sannan duk ina sauran shuwagabannin matan gidan waɗanda na sani?...." Dogon numfashi Aunty Habiba ta ja tana murmushi ta ce "Baiwar ALLAH kenam, kinga sauran ni kaɗai na rage ko? wallahi dalilin da ya hanani tafiya shine saboda waɗannan yaran da na saba da su tin shekara da shekaru bazan iya tafiya na barsu ba, iya su goma yanzu suka rage da zaran ko wacce ta samu mafita Nima zan kama gabana..." Baiwar Allah har da hawayen ta tace "Aunty Habiba Allah ya saka miki da gidan Aljanna, su suma Allah ya kawo musu ɗauki ta hanya mafi alkhairi..." cikin haɗin baki suka ce "ya labarin Ƴar Amana ne?..." Murmushi Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "Ƴar Amana tana nan cikin ƙashin lafiya itama ta haɗu da iyayenta, ita ɗin Ƴar sarkin ƙasar Jidder ce kuma sannan bakinta ya buɗu yanzu tana magana sosai..." Gaba ɗaya basu san lokacin da suka saki ihun farin ciki ba, murna kamar bazasu mutu ba, Aunty Habiba hamdala ta soma yi tana godewa Allah, duk babu wanda bai kasance cikin farin ciki ba.. Wata daga ciki ta ce "Amma Baiwar ALLAH meye asalin sunan Ƴar Amana?..." Baiwar Allah ta ce "Reemah..." Duk ɗinsu fatan alkhairi suka yi musu da taya su murna... Aunty Habiba ta ce "to ke ɗin baki sanar mana labarin yanda ta kasance miki ba, Allah yasa kema kin haɗu da iyayen nakin..." Murmushi Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "na haɗu da iyayena amma sai dai su ɗin ba'a nan Nigeria suke ba, suna can ƙasar Australia, Mahaifina shine shugaban sojoji na ƙasar, inada Yayuna guda biyu suma duk sojoji ne, asalin sunana Amreesher..." Duk haɗa baki suka yi suka ce "wonderful, labarin ki kamar a Film, film ɗin ma kamar irin indian film, gaskiya kinyi babban dace a rayuwa Baiwar ALLAH, Addu'ar ki bata faɗi a banza ba, ke ƴar gata ce sosai kuma sannan ke ba abun rainawa bane..." Aunty Habiba ta ce "na taya ki murna sosai Baiwar ALLAH, kinyi babban Sa'a a rayuwa, da ke da Ƴar Amana ashe ku ɗin ba ƙananun yara bane shiyasa jinin ku ya haɗu sosai, ita ƴar sarkin ƙasar Jidder ke kuma ƴar shugaban sojojin ƙasar U.S, Allahu Akbar..." wata ce a ciki ta ce "Amma Baiwar ALLAH shin abinda ake faɗi lokacin cewar iyayenki Christal ne shin gaskiya ne?..." Baiwar Allah kallon ta tayi tare da jinjina kai ta ce "gaskiya ne amma sai dai yanzu sun musulunta..." Duk cewa suka yi Alhamdulillah cikin nuna farin cikinsu, Suka ɗauko hirar Yallaɓai anan Baiwar ALLAH take jin labarin abinda ya faru da shi kuma har ya mutu, Sun jajanta sosai sannan idan suka tuno da labarin abubuwan suka wakana a baya gaba ɗaya sai su tintsire da dariya, musamman labarin Ƴar Amana da Yallaɓai, sannan suka yi jimamin mutuwar Madam Aliya, A wannan lokacin ne suke sanar da Baiwar ALLAH cewa yanzu komai Alhamdulillah, sun samu ƴanci sosai, suna samun wadataccen abinci da komai na rayuwa amma har yanzu akwai dokan hana fita... A wannan ranar sun juma suna shan hira, anan Baiwar ALLAH ta kwana.... ★★★★★★ Washe Gari da hantsi sai ga sauƙar mutanen U.S, motoci ne sun kai 15 na sojoji waɗanda suka je ɗaukar su a airport, Abbah da mai martaba da matan su da Ummy da Reemah da Ramlat sai Roshan duk suna zaune a falo, basu ankara ba suka ji shugowar su Chief cikin farin ciki, da Madam Parveen da kuma Minal da Rukky da mazajen su, ganin kowa a cikin tagumi yasa jikin su yin sanyi, cikin yaƙe Abbah ya tarye su, Chief da ya gaza yin haƙuri ya ce "me yake faruwa ne naga kamar ba lafiya ba?..." Murmushi takaici Abbah yayi sannan ya ce "babu lafiya kam..." Madam Parveen ƙirjin ta ne yayi wani irin bugawa, tana ganin jaririya amma hankalin ta yana kan Baiwar ALLAH ganin bata tarar da ita ba, bata san lokacin da hawaye yake gangaro mata ba, ta ce "ta mutu ko?..." Abbah girgiza kai yayi sannan ya ce "ba mutuwa tayi ba, ta tafi bamu san ina tayi ba sai letter da ta bari..." Abbah ya kalli Aunty Yolash ya ce "ki basu..." Aunty Yolash ce ta tashi taje ta bawa Chief, Chief ya ce "indai rubutun Hausa ne ki karanta mana..." Jinjina kai Aunty Yolash tayi jiki ba ƙwari ta karanta musu abinda yake cikin takardar... Hura iskar bakinsa Chief yayi yana faɗin "why Daughter, why! why my Daughter..." Madam Parveen ta ce "ta tafi tabar Baby?..." suna cikin jajanta wa sai ga wasu sojoji su uku sun shigo tsayawa suka yi suka sanar wa Abbah cewa "Sir mun duba ko ina babu labarin ta..." Abbah ya ce "ku tafi ku ban wuri..." Chief ya ce "kar ku damu za'a same ta Insha Allahu, ku jinkirta nemanta yanzu domin bazaku same ta ba, na tabbata ta samu wani wuri ta zauna kaga kuwa samun ta zai yi wuya..." Ammy ce ta taso ta kawo wa Madam Parveen jaririyar tana faɗin "ganan jikar ki" Madam Parveen karɓan ta tayi tana murmushi haɗi da hawayen baƙin cikin tafiyar Amreesh... ★★★★★ Baiwar Allah kwana ɗaya tayi a gidan marayu ta shirya tafiya, suna kuka haka suka rabu ba'a son ransu ba amma Baiwar ALLAH tayi musu alƙawarin wata rana zasu sake ganawa da tare da ƴar Amana, daga nan ta tafi.... Su Madam Parveen kuwa basu tashi komawa ƙasar U.S ba sai da Jaririya tayi sati guda da zuwanta duniya, akayi suna ba tare da anyi hidima ba sakamakon rashin uwar yarinya, Roshan ne ya raɗa wa jaririyar suna ta ci sunan Mahaifiyarsu wato Fateemah (Afaf)... Ƴar Amana kullum yarinyar tana hannun ta, domin yanda take ji da yarinyar nan ko uwar da ta haife ta bata kaita ba, bata barin kowa ya ɗauke ta hatta madara yanzu ita take bata, Shima Roshan gaba ɗaya ya ɗora ransa akan Afaf domin idan bata hannun Reemah to tana hannun Roshan to idan tana hannun ɗaya daga cikin su to ya kuwa suna tare ne domin indai Afaf tana hannun Roshan Reemah bata barin wurin sa, haka nan idan Afaf tana hannun Reemah to Roshan sai ya yi zarya wurin Reemah ya kai sau nawa, hakan yasa yanzu alaƙar ta dawo tsakanin Roshan da Reemah ta silar Afaf, bugu da ƙari kuma Roshan ya bata haƙuri akan abinda yayi mata sannan jin abinda Baiwar ALLAH ta rubuta a letter ta yasa ya fara saka abun a ransa domin a rayuwa babu abinda Baiwar ALLAH zata nema a wurinsa ta rasa indai bai fi ƙarfinsa ba, amma har yanzu bai nuna hakan ba, sannan kowa ya bar zancen a gefe saboda halin da Ramlat zata shiga idan taji zancen, domin ɓoye mata ake kuma daman ba shiri suke yi ba.. Roshan sunan da yake ƙiran Afaf shine *BIJU MAMA* ma'ana Manana... hakan yasa kowa yanzu yake ƙiranta da haka, duk wata gata da nuna ƙauna ana mata domin yarinyar da shiga rai take... A lokacin da Madam Parveen zasu tafi taso a bata Afaf amma Abbah ya ce "abar masa ita zasu raine ta..." Babu yanda Madam Parveen bata yi ba akan abata ita domin hankalin ta ya kwanta tinda babu Amreesh, har Abbah ya amince akan ta tafi da ita tinda ta nuna damuwar ta akai amma fur Reemah ta ƙi bayar da Yarinyar, har da kukan ta wai ita baza'a rabata da Afaf ba, Babu yanda ba'ayi ba amma Reemah ya ƙi, Madam Parveen har da hawayen ta... Kuma shima Roshan baya so a tafi da ita, kowa ma baya so domin suna matuƙar ji da yarinyar, daƙer aka karɓe Afaf daga hannun Reemah aka damƙawa Madam Parveen... Babu wanda yasan Reemah tanada Aljanu na al'ajabi sai yau, Bayan an karɓi Afaf, Reemah tsayawa tayi kai a sunkuye... Madam Parveen da iyalanta sallama sukayi da kowa cikin kewar juna zasu tafi har sun nufi bakin ƙofa suka ji wani irin ƙarar murya mai toshe kunne kamar daga sama an darara tsawa, duk babu wanda bai firgita ba, Madam Parveen ƙanƙame Afaf tayi sosai jikinta na kakkarwa kowa ya maida idonsa kan Reemah, Ganinta yasa kowa jikinsa ya fara kakkarwa, kowa ya ƙanƙame na kusa da shi banda Abbah da Mai martaba da suke ta faman jero Addu'o'i, Roshan zaro ido waje ya yi yana kallon Reemah cike da mamaki, Chief shima bakinsa ne yake ta motsi alamun addu'a yake domin abun da abin firgitarwa da al'ajabi... Ƴar Amana ce ta ɗago da dara-daran idanuwanta waɗanda suka kaɗa suka yi jawur, fuskar da gangan jikin duk ya canza launin yellow kamar ba jikin bil-adama ba, sumar kanta da yake kwance har gadon baya yanzu duk sun mimmiƙe tsaye kamar wanda aka tsayar da su, wani irin haske ne ya zagaye ta, a tsawace ta fara magana tana faɗin "Duk abin da ku ke a tafin hannun mu kuke, muna yin abu bakwa mana uzuri to ku sani cewa ƙyale ku muke, kuna yin abinda ranku yake so muna zuba muku ido alfarma muke muku saboda ku ɗin iyaye ne kuma a'hali, kuyi duk abinda ku ke so babu ruwan mu amma kada a shiga gonar mu, abinda muke so namu ne don haka a bar mana kayan mu....." Mai martaba cikin damuwa ya ce "ku ɗin su waye? sannan wa ya turo ku? daga ina kuke? sannan ku nawa ne?..." Dariya Reemah tayi sannan ta ce "mu ɗin jinin jikinta ne, muna tare da ita ne tin daga lokacin da aka haife ta, ita ɗin Amanar mu ce, muna son abunda take so, bama cutar wa don haka kada a cutar da mu, babu wanda ya turo mu kuma..." Mai martaba ya ce "yanzu mai kuke buƙata?..." Ta ce "Abinda take so shi muke so don haka a bata Jaririya, muna tare da jinin Razhdeen don haka muna son ganin Jaririya a kusa da mu...." Mai martaba ya ce "meye haɗin ku da Razhdeen kuma?..." Ta ce "jini biyu muka ɗaukaka a doron duniyan nan, Razhdeen da kuma Reemah hakan yasa muka haɗa jinin, amma mun haramta yin Aure a tsakanin su, yanzu kuma tinda ga jinin Razhdeen na biyu mun ɗauke ta, mun damƙata a hannun Reemah, raba ta da jaririyar zai haifo babbar matsala..." Mai martaba ya ce "idan kuma Uwar jaririyar ta buƙaci ƴarta fa?..." Ta ce "tayi haƙuri wannan ta zamo tamu kuma mun damƙa amanar ta a hannun Reemah, da zata haifo yara 100 a gaba to babu ruwan mu da su amma kuma zamu ɗaukaka yaran in har jinin Razhdeen ne, wannan ta farkon tamu ceeee, in kuma zaku karɓe amanar da muka damƙa wa Reemah to kuwa zamu ɗauke jaririyar mu tafi da ita can duniyar mu...." Abbah ne yayi saurin cewa "a'ah! a'ah!! dan ALLAH kar ku tafi da yarinyar gwara ta zauna a hannun Reemah tinda Reemah tana tare da mu zamu kula da su gaba ɗaya..." Reemah tana tsaye a cikin wannan yanayin sai yanzu kowa ya lura da ƙafarta ba'a tsaye da ƙasi take ba, an ɗan ɗagata sama, an rabata da ƙasi kaɗa, Ta ce "Kada mu ji! Kana mu gani!!!...." Tana kaiwa nan hasken nan ya ɓace aka sauƙar da Reemah ƙasi sai yaraf ta faɗi ƙasin carpet sumammiya, sumar gashin ta ne ya dawo yanda yake ya kwanta sannan launin Fatar ta ta koma yanda yake... Mai martaba ne ya nufi yanda take da sauri ya ɗago ta saman cinyar sa yana hawaye yana shafar fuskar ta.. Abbah zama yayi ya dafe kansa da hannu biyu yana jinjina lamarin, Madam Parveen hannu na rawa tazo gaban Mai martaba da yake ɗauke da Reemah ta miƙa masa jaririyar hannu na kakkarwa, lips ɗinta ma haka yake kakkarwa ta ce "ga ga ga Baby..." Gaba ɗaya ta gama tsorita, Mai martaba ne ya karɓe ta, da sauri Madam Parveen ta ja da baya taje ta riƙo hannun Chief tana faɗin "ku zo mu tafi dan ALLAH, bana so ina nan ta tashi ta same ni..." Mai martaba ɗagowa yayi yana kallon ta ya ce "kar ki damu babu abinda zai faru..." Ai Madam Parveen da ta tada hankalin ta sai da suka fice daga gidan tukun hankalin ta ya fara kwanciya, Duk airport suka nufa Madam Parveen da Chief a mota ɗaya, sai Mohandas da Minal a mota ɗaya, Rakesh da Rukky a mota ɗaya duk suka tafi don ko ƴan rakiya basu nema ba... Abbah ne ya taso yazo gaban Reemah shima ya ɗora hannun sa akan goshin ta, girgiza kai yayi sannan ya kalli Roshan ya ce "Roshan zo ka kaita room ɗinta jikinta ya ɗau zafi..." bayan sun tottofa mata Addu'o'i... Mai martaba ne ya ƙira Ummy yana faɗin "Uwar masu gida zo ki karɓi yarinyar nan..." Ummy jin haka yasa ta zille ta bar falo babu wanda ya sani sai gani akayi bata nan.... Roshan wuce wa yayi da Reemah cikin ɗaki, idonsa akan ta domin bai taɓa tunanin tana cikin wannan matsalar ba.. Abbah ya ce "to ke Auntyn yara zo ki karɓe ta tinda uwar masu gida bata nan..." Aunty Yolash sai da taji wani rass, kallon jaririyar tayi tare da haɗiyar yawu tana murmushin yaƙe ta ce "ai matsala tayi baƙin jini a wurin bil'adama, kar kana zaune kaji an yaƙe maka wuya..." tana kaiwa nan bata jira an furta komai ba tayi saurin barin falon itama... Hajiya Kilishi ganin ta haɗa ido da Abbah yasa ta faɗin "laaa! nabar girki akan wuta, nasan yanzu ya ƙone wayyo..." itama da gudu tabar falon ta nufi kitchen, tayi hakane saboda tasan ita za'ace ta ɗauki yarinyar... Ammy murmushi tayi ta je tasa hannu ta karɓi Afaf daga hannun Mai martaba.. Mai martaba ne ya ce "to ku ƙira mun Uwar masu gida tazo mu ma zamu koma tinda an gama komai..." Aunty Maimuna ta ce "to ita Reemah fa?..." Mai martaba ya ce "indai zamu tafi da Reemah to dole tare da jaririyar zamu tafi..." Abbah ya yi murmushi sannan ya ce "Ku bar mun Reemah kawai zata cigaba da zama anan..." Mai martaba ya jinjina kai anan suka yi sallama suma suka tafi, Ummy duk son da take wa Afaf da ta zo tafiya bata bari ta kalle ta ba ma haka su ma suka tafi..." Ramlat ai tin lokacin da Roshan ya shiga da Reemah ciki babu wanda yasan lokacin da ta fice daga falon, cikin tsoro da fargaba ta nufi part ɗin ta, tana zuwa ta shige bedroom tasa key, wani irin nannauyar numfashi take fitar wa tana hasasho yanayin da ta ga Reemah, haka jikinta yake ɓari tana kakkarwa... ★★★★★ Chief da iyalan sa suna koma wa ƙasar U.S kowa ya ɗauki matar sa ya tafi da ita gidansa, Chief da Madam Parveen ne kawai suka sauƙa a wantalelen gidan su, sojoji ne guda uku suka nufi yanda motar su take, bayan sun yi musu Barka da dawowa anan suka sanar cewa sunyi baƙuwa amma basu barta ta shigo ba...". Madam Parveen ta ce. "aina take?..." Suka ce "tana ɗakin visitors room yau kwana biyar da zuwan ta..." Chief ne ya bada umarnin a kawo ta, kafin nan suka wuce ciki, Madam Parveen tana shiga falon su ta jefar da handbag ɗinta akan sopa ta zauna tare da ɗora hannayenta biyu akanta sai zubda ƙwallah take cikin damuwa da tashin hankali... Chief ne ya zauna kusa da ita ya ɗora hannunsa akan kafaɗa tare da rungumar ta yana rarrashinta cikin kulawa. suna cikin wannan halin suka ji ana knocking, bada umarnin shugowa akayi wani soja ne ya shigo tare da faɗin "Sir gata nan..." duk da yaren turanci suke magana domin in har suka zo gida basa Hausa kwata-kwata. Madam Parveen saboda tsananin damuwa ko ɗagowa bata yi sai Chief ne ya ɗago, idonsa ne ya sauƙa akan Baiwar ALLAH wacce ta shigo tana sanye da manyan kaya ta ɗage niƙab ɗinta sama, A zabure Chief ya miƙe tsaye tare da faɗin "Daughter...." Madam Parveen jin haka yasa itama ta zabura ta tashi tsaye tana kallon bakin ƙofa, buɗe baki tayi a ruɗe ta ce "Amreesh?.." Da gudu ta nufi bakin ƙofa tana zuwa ta rungume ta sosai, itama Baiwar ALLAH rungumar mahaifiyar ta tayi tana kuka.. Sai da suka gama koke-koken su tukun suka ƙaraso ciki, Madam Parveen ce ta zaunar da ita tana hawaye ta ce "Amreesh ina kika shiga ne, kin bar mana Baby Aljanu sun mallake ta..." Baiwar Allah tana kuka tasa hannu tana goge hawayen Mommynta murya na kakkarwa ta ce "Mom kuyi haƙuri, ba'a son raina bane, hankali na bazai taɓa kwanciya ba idan ina tare da Babyna, gwara na nisanta kaina da ita ko zan samu sassauci, kullum ina cikin damuwa da tashin hankali, Mom na bar musu ita..." Madam Parveen rungumar ta tayi tana faɗin "it's okay my Daughter, stop crying okay, zaki cigaba da zama a wurin iyayen ki kema, ki bar musu yarinyar Insha Allahu zata kasance cikin ƙoshin lafiya..." Chief shima murmushi yayi tare da faɗin "Daughter taya kika zo nan ƙasar ke kaɗai?..." Baiwar Allah tashi tayi taje ta zauna a kusa da Daddynta ta rungume shi tana dariya ta ce "Dad inda kuɗina ina ne bazan je ba, idan na sauƙa a ƙasar nan gidan ka ba ɓoyayye bane domin kai ɗin ba ƙaramin mutum bane..." Murmushi ya yi ya ce "Ma sha ALLAH, yanzu dai bari na ƙira can Nigeria na sanar musu cewa My Daughter tana tare da mu..." Baiwar Allah kamar zata yi kuka ta ce "Dad kada ka sanar musu domin ni bazan koma ba kuma bana so a kawo mun Baby..." Chief ya ce "zan sanar musu saboda hankalin su zaifi kwanciya..." Chief sanar musu yayi, Abbah ba ƙaramin farin ciki yayi ba, sai da ya nemi haɗa su da Baiwar ALLAH, Daƙer Baiwar ALLAH ta karɓa cikin jin kunya ta ce "ina wuni Abbah..." Cikin nuna farin ciki ya ce "Daughter kin tsoratar damu sosai, fatan kina lafiya..." Ta amsa masa, Abbah ya ce "kar ki damu zamu kula miki da yarinyar ki..." Baiwar Allah miƙawa Chief tayi wayar ta juya kan Mommynta tare da kifar da kanta akan ƙirjinta tana kuka... Da haka wannan rububin ya wuce yanzu Baiwar Allah itama ta koma gida... ★★★ Reemah kuwa ta samu Jaririya a bononza kullum ita take rainonta, sai kuma Roshan da yake karɓar ta, Ramlat kuwa duk inda Afaf take bata zama a wurin, idan Roshan ya tafi da ita part ɗinsa to kuwa Ramlat zata baro part ɗin... ★ One Year ★ Wasu zura-zuran motocin sojoji ne kusan guda hamsin suka baro airport kai tsaye gidan General suka nufa, A ƙofar gidan General kuma wasu sojoji ne da baƙin fuskoki duk suke tsatstsaye aciki har da Roshan da Abbah da wasu mutane daban, ƙofar gidan da ciki duk a cike suna jiran taryar babban baƙo wato Razhdeen wanda sai wannan lokacin Allah ya bashi damar dawowa tsawon shekara...... Typing ✍️ Asmeetah writer *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 66 to 70 Wasu zura-zuran motocin ne suka yi parking a wajen gidan General, sojoji ne suka firfito daga bisani wani soja ya buɗe murfin wani zureren mota dake tsakiyar motoci, wanda yake ciki ne ya zuro da ƙafarsa wanda yake sanye da ƙaton takalmi irin na sojoji, sai da ya ɗan juma tukun ya fito gaba ɗaya yasa sanye da baƙin glass akan dara-daran idanuwansa, ga yayi wani irin fari na hutu wanda rana baya taɓa shi, sumar kansa ya koma yanda yake kamar ba'a taɓa aske shi ba har ya wuce kafaɗarsa, ga sajen nan ya kwanto luf akan kyakkyawan fuskar sa wanda yake ta shining, lips ɗinsa yanda kasan ya shafa lip glow sai sheƙi yake tayi ga ya ci red sosai, ba ƙaramin kyau Razhdeen ya yi ba, yana sanye da wandon sojoji na ƙasar U.S da baƙar riga mai high neck da dogon hannu sai kuma sweater da ya ɗora akai. Yana tsaye a jikin motar da ya fito yana bin kowa da kallo, idonsa ne ya sauƙa akan Roshan wanda ya nufo shi da murmushi akan fuskar sa, yana zuwa suka rungumi juna sosai cike da kewar juna, Roshan ɗago wa yayi da fararen haƙwaransa ya ce "My Man your welcome..." Razhdeen shima cike da murnar ganin twins ɗinsa ya ce "thanks my twins..." Suna cikin ganawa da juna sai ga Abbah ya zo wurin yana faɗin "Deen saboda ka haɗu da twins shine ka manta da Dad?..." Murmushi ya yi sannan ya rungumi Abbah tare da faɗin "i missed you my Dad..." Abbah shima rungumar sa yayi yana bubbugan bayansa ya ce "me too my Son, ku ƙarasa shiga gidan..." Razhdeen da Roshan a tare suka shiga mota aka shigar da su cikin gidan.... A babban falo Hajiya Kilishi da Ammy ne zaune a kujera sun sha fashion shigar gizner doguwar riga iri ɗaya, ga Ramlat itama ta sha danƙareren less mai ɗinkin bu ba ga cikin ya girma haihuwa yau ko gobe, tasha ɗaurin ɗankwali da yafin gyalen ta fari akan kafaɗa tana zaune da su Hajiya Kilishi, Ta ko ina an gyara tsab-tsab an canza kayan furnitures na ɗakuna saboda dawowar Razhdeen, ga girke-girke na musamman da akayi duk aka jejjera akan dinning, dake Abokan Razhdeen sojoji su ma sun zo, da waɗanda suka yo rakiyarsa, gidan ya cika da manyan baƙi sojoji... Roshan da Razhdeen ne suka shigo falo da sallama a bakin su, duk waɗanda suke falon miƙe wa tsaye sukayi cike da farin cikin ganin Razhdeen, kowa masa sannu da dawowa yake da taya shi murnar samun lafiya, zama suka yi duk wanda ya gaishe shi cikin fara'a yake amsawa, gaba ɗaya Razhdeen ya sauya kamar ba Uncle Deen ba, yau shine yake murmushi abun ya bawa kowa mamaki ganin Razhdeen sai zabga murmushi yake ga ya ƙara kyau kamar asalin Balarabe, kowa bai san lokacin da ya tsinci kansa cikin farin ciki ba ganin yanda shima yake cikin farin ciki.... Bayan kowa ya hallaru duk a dinning suka zauna sai da kowa ya ci ya sha tukun aka sake haɗa sabon hira, Razhdeen a wannan ranar wuni ya yi yana wurwurga ƙwayar idanuwansa ta ko ina, yana son ganin Amreesh amma bai ganta ba shi kuwa ya kasa tambayar ta, duk halin da yake ciki kuwa Roshan duk ya fiskanta, shi dai murmushi kawai yake sa ki sai daga baya Roshan ya tashi, ɗakin Reemah ya nufa idon Ramlat akan sa domin ta tsani taga Roshan ya shiga room ɗin Reemah duk da saboda Afaf yake zuwa, yana shiga ya tarar da Reemah a tsakiyar gadonta ita da Afaf suna wasa, shima zama ya yi a bakin gado idonsa akan Afaf ya ce "Biju Mama wasa ne?..." Ɗagowa tayi tana kallon sa da sumar gaban gashin ta duk ya rufe masa goshi har zuwa girar ta, ta baya kuma ya sauƙa mata har gadon bayan ta, ta ce "Daddy..." Shafa sumar kanta Roshan yayi tare da faɗin "zo mu tafi ko..." Da sauri Afaf ta miƙa hannun ta Roshan ya ɗauke ta, ya kalli Reemah ya ce "bazaki zo ki gaishe da Uncle Deen ɗin ki ba?...". Yamutsa fuska tayi ta ce "bana buƙatar sa..." Girgiza kai Roshan yayi sannan ya fita da Afaf a hannunsa... Roshan bayan ya sauƙa falo ya tarar da Razhdeen baya nan sai iya Abbah da matansa da kuma Ramlat, Roshan zama yayi Afaf akan cinyar sa ya ce "ina baƙin suke?.." Abbah ya ce "ya fita raka abokansa zasu koma..." Suna zazzaune a falo sai ga Razhdeen ya shigo, idonsa ne ya sauƙa akan yarinyar hannun Roshan ƙirjinsa ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske har sai da ya dafe gefen ƙirjinsa ta saitin zuciyarsa, Abbah ganin haka ya sa shi cewa "lafiya kuwa Razhdeen?..." Roshan kuma idonsa akan Afaf wacce itama dafe ƙirjinta tayi yanda Razhdeen ya yi, lokaci guda ta fashe da kuka, cike da mamaki yake kallon ta sai kuma ya ɗago ya kalli Razhdeen still hannunsa akan ƙirjin, Shima Razhdeen idonsa ya sauƙar kan ta ganin yanda yayi itama tayi yasa shi shiga mamaki, haka kowa ya fahimci haka.. Abbah ne ya ce "Razhdeen zo ka zauna mana..." Razhdeen idonsa akan Afaf haka yaje ya zauna, cike da mamaki ya ce "Dad wannan yarinyar fa? daman twins ka samu Daughter baka sanar mun ba?..." Girgiza kai Abbah yayi sannan ya ce "Razhdeen kun samu Daughter gashi yanzu tana da shekara 1 daman kai muke jira ka dawo sai a mata birthday...." Razhdeen kallon Roshan ya yi tare da faɗin "congratulation my twins..." Roshan cije lips ɗinsa na ƙasi yayi sannan ya ce "is your Daughter..." Razhdeen murmushi yayi sannan ya ce "Yes your Daughter is my Daughter and than my Daughter is your Daughter too..." Roshan ya ce "Yes i believe it but this girl is your real daughter from Amreesh...." Razhdeen zuciyarsa ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske yana zaro ido waje ya ce "what?..." ya maida idonsa kan Abbah yana karkaɗa kai alamar bai yadda ba.. Abbah ya ce "da gaske Razhdeen abinda Roshan ya faɗa gaskiya ne, ƴarka ce ta cikin ka, abinda ya faru a tsakanin ka da Amreesher Allah ya baku rabon wannan yarinya..." Razhdeen a ruɗe ya zura zara-zaran yatsunsa a cikin sumar kansa yana cakuɗawa tare da faɗin "oh my God, innalillahi wa inna'ilaihi raju'un...." Itama Afaf hannunta biyu ta tusa a cikin sumar kanta tana hargutsawa kamar yadda Razhdeen yake, Ɗagowar da Razhdeen zai yi idonsa ya sauƙa akan ta ganin yanda take hargutsa sumar kanta kamar yanda yake yi, Shima Roshan ita yake kallo hatta su Abbah, Roshan girgiza kai yayi yana murmushi ya ce "Abbah a koda yaushe ina sanar muku duk ɗabi'un yarinyar nan irin na Razhdeen ne amma baku taɓa yadda ba, wasu abubuwan da yake yi itama takan yi su sa'in-sa'in, wani abu idan tana yi nasan shima a lokacin yana irin sa ne, yanzu gashi kun gani da idon ku, she do something like him..." Sai yanzu Abbah ya gaskaka tare da faɗin "ikon ALLAH kenam, ga kamanni sak kamar an tsaga kara, komai da komai iri ɗaya..." Kowa ya gama tofa albarkacin bakin sa, daga baya Roshan ya kalli Afaf sannan ya ce "Biju Mama waye wancan?..." ya nuna Razhdeen.. Kallon Razhdeen tayi sannan ta yi dariya da hakwaranta da basu gama fitowa ba, ta ce "Abiiii...." Razhdeen bai san lokacin da ya sau ƙayataccen murmushi ba idonsa akan ta.. Roshan ya ce "to je ki wurin Abi koh..." ya sauƙe ta tana takawa a hankali irin tafiyar bai gama nuna ba, tana sanye da doguwar riga na kanti ta ƙasi ta baje sosai da ƴar takalmin thorns ɗinta, ta ƙarasa wurin Razhdeen da gudu-gudu yayi saurin ɗaga ta ya rungume ta sosai a jikinsa bai san lokacin da ya fara zubda hawaye ba, haka ya ɗago ta tare da sumbatar ta akan goshi yana shafa sumar kanta.. Reemah kuwa tana tsaye a bakin matakalar beni ta kasa ƙarasowa falon idonta akan Razhdeen, ganin yanda ya damu da yarinyar ga yanda ya rungumeta sai sunbatar sumar kanta yake yana hawaye itama bata san lokacin da hawaye yake zubo mata ba, tsananin tausayinsa ne ya kama ta sai sakin murmushi take tana goge hawaye. Razhdeen ne ya sauƙe idonsa akan Reemah, miƙe wa yayi tsaye yana ɗauke da Afaf ya ce "Sarah zo..." Reemah tafo wa tayi wurinsa, tana zuwa ta rungume shi, shima rungumarta yayi da ɗayan hannu yana faɗin "my fine girl an girma, to meye na kukan..." Reemah tana kuka ta ce "My super man..." ta ƙira sunan tana dariya... Shima dariyar yake ba ƙaramin kewar juna suka yi ba, sai da suka gama koke-koken su tukun kowa ya samu wurin zama, Razhdeen yana zaune Afaf akan cinyarsa sai kuma Reemah a gefen sa tana riƙe da hannunsa kamar wanda zai gudu.... Abbah fuska ɗauke da murmushi ya ce "Deen tunda Allah ya dawo mana da kai lafiya yanzu abinda zai faru shine dole zaka bi mana bayan Amreesh, domin yarinyar nan bazata taso ba tare da mahaifiyar ta ba indai tana raye, Amreesher mallakin ka ce an riga da an baka ita tin kafin a haife ta don haka zaka amshi matar ka, ba tare da ɓata lokaci ba za'a ɗaura muku Aure..." Razhdeen jin zuciyar sa yake kamar ana sukar sa domin ba ƙaramin son Amreesh yake ba, kamar zai yi kuka ya ce "Abbah Amreesh bazata taɓa aminta da ni ba, gani take laifi nane abinda ya faru but ina ƙaunar ta sosai..." ya ƙarasa maganar yana kai idonsa kan Roshan, wanda shima Roshan idonsa akan Razhdeen yake, haka kawai yake jin tausayin Razhdeen domin ya sha wahala akan Amreesh, inda ace an gado Amreesh tin wuri da bazai yi garajen Auren ta ba, Roshan cikin tausayawa ɗan uwansa ya ce "My man kar ka damu idan ka tashi tafiya zan raka ka zuwa wurin Amreesh, zata yadda da kai sannan zaku zauna da ƴarku cikin aminci da ƙaunar juna...." Wani irin kallo Reemah ta watsa wa Roshan jin za'a raba ta da Afaf, A gigice Reemah tasa hannu ta karɓi Afaf daga hannun Razhdeen.. Razhdeen ji yayi an fizgi Yarinyar daga hannun sa da sauri ya waiwaya yana kallon Reemah, Reemah rungumar Afaf tayi sosai tare da miƙe wa ta nufi room ɗinta da gudu.. Roshan kallon Abbah yayi sannan ya ce "Abbah! ya za'a yi da wannan al'amarin? ina tunanin matsalar da za'a samu idan uwa ta buƙaci ƴarta..." Abbah jinjina kai yayi ba tare da ya furta komai ba.. Razhdeen cike da mamaki ya ce "me yake faruwa ne?..." Roshan ne ya sanar masa halin da ake ciki, Razhdeen lumshe ido yayi tare da luma yatsun sa a cikin sumar kansa sai da ya ɗan juma kafin ya buɗe idon yana sauƙe numfashi ya ce "indai yarinyar ce babu matsala za'a iya bar mata, babban matsalar shine haɗa alaƙa da jinn, bana son su shafi yarinyar, itama Sarah inaso a rabata da su..." Ammy tana zaune sai yanzu tayi magana ta ce "to kai banda abinda Razhdeen ai yarinyar ce tasa suka bar jikin ka..." Razhdeen ya ce "eh ina so su bar jikin ko wacce a cikin su, bana buƙata..." Abbah ya ce "tayaya kenam?..." Roshan ya ce "Addu'a shine makamin mumini don haka zamu tsayar da addu'a sosai, zamu gayyato manyan malamai..." Ammy ta ce "ba masu cutar wa bane, sai ma kariyar da suka basu don haka ban goyi bayan a tada su ba saboda ba'a san irin matsalar da za'a fuskanta ba, tinda ba ƙaramin ƙarfin iko gare su ba, matsalar shine kada su raba ƴa da uwa da kuma uba...." Abbah ya ce "to ke taya kika san da haka?..." Ammy ta ce "ta hanyar yin magana da su, saboda haka Ku bar su kawai, mutanen kirki ne kuma zasu cigaba da basu kariya babu wani abun citarwar da zai same su, sai dai abu ɗaya ne za'a nemi alfarmar su shine su damƙa yarinyar a hannun mahaifiyar ta..." Roshan idonsa akan Ammy ya ce "babu wata alfarmar da za'a nema daga wurin su, indai ba zasu cutar ba to a bar su kawai, ita uwar yarinyar ai bata son ƴar, inda tana sonta da bazata kama hanya tabar jaririyar yarinya tana kuka ba, bata ji tausayin ta ba har ila yau shekara guda da watanni bata tako ƙafa tazo ganin ƴarta ba ko a photo bata taɓa neman ganin ta ba, to akan da wani dalili zaku damu kada a raba uwa da ƴa? in aljanun basu raba ba ai ita uwar da kanta ta raba alaƙar ta da ƴarta, saboda haka Reemah tana son yarinyar kuma an bar mata ita babu wanda zai raba ta da ita saboda tin tana Jaririya take riƙe da ita...." Razhdeen idanuwansa ne suka yi ja jin abinda Amreesh ta aikata wa ɗiyarsa, tana hukuntata saboda shi, dafe goshin sa yayi yana tunanin ta yanda zai fara tinkarar Amreesh, gashi ƴar da ta haifa ma ta hukuntata saboda shi balle shi da kansa... Abbah ya ce "shikenam zamu zuba ido idan uwar yarinya ta buƙaci ƴarta duk za'a san yanda za'ayi saboda baza'a hanata ƴarta ba ...." Sai da suka gama tattaunawa daga bisani kowa ya watse a falon, already Razhdeen da Roshan sun shirya akan gobe zasu nufi ƙasar U.S, Roshan ɗaukar matar sa ya yi suka nufi part ɗinsu da ƙaton cikin ta.. Shi kuwa Razhdeen room ɗin Reemah ya nufa, yana shiga ya tarar da su akan gado duk sunyi bacci, Reemah rungume da Afaf da haka bacci ya ɗauke su, zama yayi a bakin gado yana ƙare su da kallo, idonsa akan Reemah sai sakin murmushi yake ganin yanda take matuƙar ƙaunar ƴarsa, ya ƙara maida idonsa kan Afaf tare da kai hannunsa yana shafa sumar kanta lokaci guda ya zufafa tunani yanda akayi aka same ta, abunda ya shiga tsakaninsa da Amreesh yake tunowa, da irin matsalolin da suka fuskanta tin farkon haɗuwar su, wani abu idan ya tuno sai yayi murmushi especially farkon haɗuwar su ganin farko da ta suma, da kuma rufe ta da yayi a ɗakinsa har tsawon sati guda, sai kuma ya tuno da itama ta so shi kamar ta mutu, har ta bayyanar da hakan tin tana kwance a asibiti a ranar Auren ta sai kuma ya ji ƙunci a ransa da Allah yasa ba shi ne ya Aure ta ba, A yanda yake jin soyayyar Amreesh a ransa gani yake bazai iya haƙura da ita ba, abinda ya shiga tsakanin su ma sai ya ƙara jin ƙaunar ta a ransa, haka yake ta tunanin Amreesh hannunsa a dafe akan sumar kan Afaf, bayan ya dawo daga dogon tunanin yakai lips ɗinsa kan goshinsa ya sumbata, sannan ya shafa kan Reemah itama yabar ɗakin... Yana sauƙa falo kai tsaye ainihin part ɗinsa ya nufa dake cikin babban falo, haurawa yayi bayan ya haura sai da ya tsaya yana kallon layin part ɗin Roshan yana murmushi ya girgiza kai sannan ya wuce part ɗinsa wanda ya sha gyara sosai, duk furnitures ɗin ɗakinsa an canza, ba ƙaramin kyau yayi ba, tsaya wa yayi yana ƙare falonsa da kallo wanda ya juma bai shige shi ba sannan ya wuce bedroom ɗinsa, yana shiga ya rage kayan jikinsa ya shige bathroom ya watsa ruwa a jikinsa tare da yin brush sannan ya fito ya sanya ƙananun kayansa already yayi sallar sa abunda ya rage masa shine bacci, hakan kuwa akayi ya miƙe akan katafaren gadonsa, sai da ya juma yana tunanin Baiwar ALLAH kamar yanda ya saba kullum kafin nan bacci ya yi gaba da shi.... ★★★★★★ Misalin ƙarfe 8 na dare Ramlat ta idar da sallar isha'i har da lafula tana zaune akan sallaya haka kawai sai zubda hawaye take, Roshan ne ya shigo ya dawo daga masallaci ya cire jallabiyan sa duk bai lura da halin da take ciki ba, kallon yanda take yayi tare da faɗin "mai kike buƙatar ci?..." Kanta a sunkuye tana hawaye ta ce "babu..." Kallon ta ya yi jin kalar amsar da ta bashi, nufan yanda take yayi yaje ya zauna a bakin gado kusa da ita yana fuskantar ta, hannu yasa ya ɗago da haɓar ta suna facing juna, ganin hawaye kwance akan fuska yasa shi cewa "meya faru?..." Ta ce "Babu komai..." Ya ce "bana son ƙarya fa, haka kawai zakiyi kuka?..." Ta ce "Yaya Roshan haka kawai nake jin yin kukan..." ta riƙo hannayensa tare da karya wuya ta ce "Yaya Roshan nasan na ɓata maka rai, kayi fushi sosai akaina saboda kishi na, ina neman alfarmar ka dan ALLAH ka yafe mun, wallahi bazan ƙara ɓata maka rai ba, bazan ƙara nuna kishina ba, Baiwar ALLAH ta bar maka saƙo akan cewa ka Auri Reemah, nasan saboda ni ne yasa baka amince ba har yanzu, amma nasan Reemah tana sonka sosai, nima yanzu na amince ka Aure ta, zan riƙe ta hannu bibbiyu, zanyi ƙoƙarin faranta maka rai, dan ALLAH kaima ka amince ka auri Reemah, mahaifinta ya mun halacci a rayuwa zanso zama da ita, kishi ne ya rufe min ido yasa na kasa gane wannan amma yanzu na bawa zuciyata ruwan sanyi, dan ALLAH Yaya Roshan...." Roshan cike da mamaki yake binta da kallo ya ce "duk mai ya kawo waɗannan maganganun?..." Ramlat tana kuka ta ce "Yaya Roshan ka yafe mun?..." Jinjina kai Roshan yayi sannan ya ce "na yafe miki..." Ta kuma cewa "kayi mun alƙawarin zaka auri Reemah?..." Shiru yayi bai bata amsa ba sai ido da ya zuba mata... Ta ce "Please Yaya Roshan..." tayi magana tana fashewa da kuka.. Roshan ya ce "it's okay nayi miki alƙawari...". Sakin murmushi tayi tare da tashi daga kan sallaya ta rungume shi sosai a jikin ta tana faɗin "ina sonka sosai Yaya Roshan...." Shima rungumarta yayi yana rarrashinta da haka tayi shiru ya ɗauke ta suka fita, kai falo suka nufa wurin dinning zasu yi lunch ɗin dare.... ★★★★★ Acan ƙasar U.S Baiwar Allah yanzu ta zama ainihin Amreesh ɗinta, domin idan ka ganta bazaka iya gane ta ba saboda farin da ta ƙara tayi kyau sosai, ga jikinta ya murmure ta zama dirarriyar mace wanda hips ɗinta ma abun kallo ne, ƙugunta ba ƙaramin cikowa yayi ba, uwa uba breast ɗinta kamar bata taɓa haihuwa, ta samu hutu sosai duk abinda take so shi ake mata, kulawa da gata duk tana samun su, hankalin ta a kwance yake tana tare da mahaifiyar ta da mahaifinta cikin ƙoshin lafiya, bata wani saka damuwar kowa a ranta, ta cire kowa a ranta, har mantawa take da tayi zaman Aure balle ta tuno da wani Razhdeen ko Roshan, mutum ɗaya zuwa biyu ne kawai a ranta yanzu wanda koda yaushe tana kan tuna su, na farko ƴarta wacce ta haifa kullum tana ranta ko sau ɗaya bata taɓa cire ta a ranta ba, itace wacce idan tana tunanin ta take hawaye sai kuma Ƴar Amana itama ba sosai ba... Saboda ta tsani jin labarin Razhdeen yasa kwata-kwata ba'a mata maganar sa, Amma akwai dabara ɗaya da ake mata wanda ta sa abun a ranta ba tare da tasan ko waye ba, Kullum Madam Parveen takan bata labarin mutumin da akayi alƙawarin ta a shi da irin kulawar da yake bata amma ba'a sanar mata cewa Razhdeen bane, tasa mutumin a ranta sosai wanda take muradin son ganinsa amma anƙi nuna mata shi. Akwai wani ƴar Babynta ƙato wanda aka siya mata tana yarinya, a jikin bebin akwai memory a ciki wanda duk recording maganganun da take yiwa Razhdeen ne tana yarinya, tana magana ana mata recording, har maganar Aure da komai da komai idan tanayi akanyi mata recording, to shine aka saka a jikin bebin kana kunnawa recording zai fara aiki, sai kayi tunanin Bebin ne take magana, A yanzu wannan Bebin koda yaushe Amreesh tana riƙe da shi, kullum saita kunna maganganun da take yiwa Habeey ɗinta tana ƙarama idan taji ita kaɗai sai tayi ta dariya, domin abin na yarinta ne, kuma yana ɗebe mata kewa sosai most especially idan Madam Parveen ta tafi wurin aiki da Daddynta ita kaɗai a gida sai ta kunna Muryar ta tayi ta sauraro da maganganun Habeey ɗinta, Ji tayi haka kawai take son jin Muryar Habeey, da irin rarrashin ta da yake idan tana shagwaɓar kuka, kulawa na musamman yana bata sosai, hakan yasa ta saka shi a ranta kuma take son ganinsa, tayi tayi Mommynta ta sanar mata aina Habeey ɗinta yake amma Madam Parveen taƙi sanar mata, Amreesh tayi akan a nuna mata ko photonsa ne amma anƙi nuna mata, tayi akan a haɗa ta tayi waya da shi amma anƙi bata number sa, hakan haka yasa tayi kuka sosai amma sai dai a rarrashe ta tayi shuru... Yanzu iya Habeey ne kawai take jin ƙaunar sa a zuciyar ta duk da ta ce bazata ƙara yin soyayya ba amma saboda Habeey yasa ta janye ƙudirinta, Kuma itama tayi alƙawarin indai yana sonta har yanzu to itama zata aure shi, Chief ya sanar mata cewa saboda ita yasa har yanzu bai yi Aure ba yana jiran dawowar ta, hakan yasa Amreesh ta ƙara saka shi a ranta, ta bisu akan a sanar wa Habeey cewa ta dawo amma anƙi bin maganar ta, kullum addu'ar ta shine Allah ya kawo mata Habeey.... ★★★★★ A yau ne su Razhdeen suka sauƙa a airport dake ƙasar U.S shi da Roshan.. A yau ne kuma aka sanar wa Amreesh cewa yau Habeey yana kan hanyar sa ta zuwa gare ta, dake su Chief da Madam Parveen duk sun san da zuwan su, Amreesh tsabar farin ciki haka ta fara tsalle tana hawa kujera tana durƙowa ƙasin carpet kamar wata yarinya ƙarama, haka ta kunna waƙa ta ƙura volume take rawa kamar ba jini a jikin ta, daga bisani taje ta ɗauro alwala sai da tayi sallollin lafulolin ta na godewa Ubangiji kafin ta tashi musamman aka ƙira wacce zatayi mata makeup na musamman, ga wedding gown fari sol kamar yau ne ɗaurin Auren ta, kwalliya na musamman aka tsara mata ba ƙaramin kyau tayi ba, yanda kasan shugaban ƙasar england ne zai zo, babu wanda zai ganta bai yabe ta ba, Dake yau su Minal sun zo gidan Chief jin labarin su Uncle Deen suna hanya ita da Rukky da mazajen su Mohandas da Rakesh kowa ya hallaru a falon gidan, Razhdeen da Roshan ne suka zo gidan da ƴar rakiyar su sojoji wanda Chief ya tura akan aje a ɗauko su a airport.. Suna shiga falo kowa farin cikin ganinsu yake, Musamman Minal da Rukky ganin ƴan uwansu sun zo, Chief tsabar farin ciki haka duk ya rurrungume su, Razhdeen dai gaba ɗaya hankalinsa ba'a jikinsa yake ba, shi damuwar sa yayi ido huɗu da Amreesh ɗinsa sai faman leƙe-leƙe yake, duk babu wanda bai fahimci haka ba sai tsokanansa ake ana dariya... Ita kuwa Amreesh tana room ɗinta a zaune a gaban mirror tana kallon kanta sai zabga murmushi take, an gama shiryata tsab kamar wata amarya, Minal da Rukky ne suka shigo da sallama a bakinsu tare da tsokanan ta suna faɗin "Amaryar Habeey bakya laifi, to yanzu dai Habeey yana buƙatar ganin Amaryar sa..." Amreesh ta ɗago cikin shagwaɓa ta ce "Ni wallahi sai yanzu nake jin kunyar ganinsa..." Minal ta ce "oh ya koma kenam? to Rukky muje mu ce bazata fito ba..." Da sauri Amreesh ta riƙo hannunsu tana faɗin "dan ALLAH ku taimaki zuciya ta muje naga Habeey ɗina..." Duk dariya suka yi suna faɗin "wow matar Habeey..." da haka suka fita da ita suna tsokanan ta tana tsakiyar su, Suna fita falo Amreesh tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasi tana kunyar ɗagowa, da haka har aka je tsakiyar falo da ita, Razhdeen yana ganinta yayi saurin miƙe wa tsaye idonsa akan ta, baki a buɗe ya gagara rufe wa gani yayi ta chanza masa ba ƙaramin kyau tayi ba, ji yake zuciyar sa tana harba masa tsantsan ƙaunar ta, haka yake murmurza hannunsa domin ji yake kamar ya rungume ta ba dan a cikin mutane suke ba, tinda yake bai taɓa jin ƙololuwar ƙaunar wata mace kamar Amreesh ba... Shima Roshan tinda ya ɗora ƙwayar idanuwansa akan fuskar Amreesh bai ɗage ba, gani yayi kamar wacce akayi mata wanka da ruwan kyau, domin ta fito a asalin Diyana, Roshan ganin kar ya kwabsa yasa shi saurin sunkuyar da kansa ƙasi... Har zuwa yanzu Amreesh tana sunkuye da kanta ta kasa ɗagowa wai ita kunyar haɗa ido da Habeey take, musamman idan ta tuno da maganganun da tayi ta masa tana ƙarasa abun sai yake bata kunya.... *ZARA TA ZARE WA RAZHDEEN ƘWAƘWALWA GA ROSHAN SHIMA YANA SHIRIN ZAREWA 🤣🤣🤣🤣🤣* Typing ✍️ Asmeetah writer *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 71 to 75 Madam Parveen ce tayo kan Baiwar ALLAH ta dafa kafaɗar ta tare da faɗin "Amreesh Daughter ki ɗago ki kalli Habeey ɗinki yau kam..." Amreesh tana sunkuye da kanta ƙasi taji Madam Parveen ta sa hannu ta ɗago da haɓar ta, a hankali Amreesh ta ɗago da kanta tin daga kan ƙafar Razhdeen take bi da kallo har zuwa kan fuskar sa, ganin idon ta kamar gizo yake mata yasa tasa hannu tana murtsika idanuwanta, ƙara buɗe idon tayi sosai girman idonta ta ƙara buɗe wa tana zazzaro su a firgice take kallon Razhdeen, girgiza kai take murya a harɗe take faɗin "ni ni ni Habeey nake son gani, meyasa za'a kawo mun wannan, meyasa zaku mun haka, ni bana son ganin sa, ku yi mun waje da shi dan ALLAH...." Baiwar Allah fashe wa tayi da kuka tana faɗan maganganu, Razhdeen matsowa kusa da ita ya yi yana faɗin "Please Reesh listing to me..." Kafin ya rufe baki ta zuciyo da iya ƙarfinta ta hankaɗa shi baya a tsawa ce ta ce "ka bar kusa da ni, bana son ganin ka..." Chief ya ce "Daughter ki dakatar da wannan shirmen ki saurare mu..." Amreesh tana kan girgiza kai idonta ya sauƙa akan Roshan dake zaune idonsa akan ta, Amreesh goge hawayen ta tayi tana sauƙe numfashi ta ce "wato kun zo ku ɗaura mun damuwa ko? kun zo ku ƙarasa kashe ni ko? me yasa ku ke son shiga mun rayuwa ne? yanzu hankali na a kwance yake babu ku a cikin lissafi na shin me ya kawo ku? Yaya Roshan ka ɗauki ɗan uwanka Ku bar ni haka Please...." Roshan miƙe wa yayi yazo dab da ita ya tsaya yana ƙare ta da kallo hannayensa a goye akan ƙirjinsa ya ce "Ammata shin kin manta jaririyar da kika bari ne? baki sani ba ko tana raye ko ta mutu..." Amreesh da sauri ta katse shi da cewa "Please na bar muku ita duniya da lahira, bana buƙatar jinin da ya shafi wannan azzalumin mutumi..." ta ƙarasa maganar tare da kai idonta kan Razhdeen... Ta cigaba da cewa "Ni Habeey nake son gani yanzu..." Roshan ya ce "wannan shine Habeey da kike magana akai...." Ta katse shi da cewa "ƙarya ne wannan ba shi bane Habeey nah..." Razhdeen kamar zai yi kuka haka ya riƙo hannunta duk biyun yana faɗin "Please Reesh, Reesh..." A firgice ta fizge hannunta tare da zabga masa mari har sau biyu a duk ɓangaren fuskar sa.. Kowa na waran sai da ya firgita ya tsaya kallon ta, Razhdeen dafe fuskar sa yayi da hannayen sa biyu idonsa akan ta ko ƙibtawa baya yi... Chief cikin ɓacin rai ya ce "Daughter are you crazy?..." Mohandas cike da mamaki yake kallon Amreesh domin tinda Razhdeen yake wata mace bata taɓa sa hannu ta mare shi ba, abun ya yi masa ciwo a ransa haka ya tashi gadan-gadan ya yo kan ta zai kai mata mari Razhdeen yayi saurin riƙo shi yana girgiza masa kai, cikin ɓacin rai Mohandas ya ce "wannan wani irin shirme ne? saboda rashin hankali har ki sa hannu ki mari wanda ya girme ki? to ko ki yadda ko kar ki yadda wannan shine Habeey domin baza ayi miki ƙarya don hankalin ki ya kwanta ba, kuma wallahi ki ka ƙara faɗan wani mummunan kalma akan sa sai na tattaka ki a wurin nan..." Madam Parveen gaba ɗaya ta rasa me zata ce a wannan lamarin, itama hawaye take domin tana son ganin farin cikin Amreesh amma ita ta kasa fahimta... Roshan kawar da kansa gefe yayi domin Amreesh ba ƙaramin ɓata masa rai tayi ba, ganin yanda tasa hannu ta mari twins ɗinsa.... Amreesh fashewa tayi da kuka cike da takaici da rashin son ganin Razhdeen yasa ta juya zata koma room ɗinta, da sauri Razhdeen ya ƙara sa hannu ya riƙo hannun ta tare da durƙusa wa ƙasi yana riƙe da hannunta ya ce "Reesh ke da bakin ki fa kika ce bazaki iya rabuwa da ni ba, kin manta kika ce idan kin girma muka yi Aure tare zamu na wanka, kin manta zoben alƙawarin da kika saka mun a yatsa na nima na saka miki...." Haka yake ta lissafo mata maganganun da tayi ta faɗa lokacin da take yarinya, kuma duk tana sauraron su a recording babu abinda ya ɓata a cikin maganganun da ta faɗa, bugu da ƙari a cikin ranta take nanata sunan da yake ƙiranta da shi wato Reesh wanda babu mai ƙiranta da sunan sai Habeey. A hankali take furta "Reesh! Reesh!! Reesh kuma? naji a cikin recording Habeey yana yawan ƙira na da Reesh...." Juya wa tayi tana kallonsa ga yanda idanuwanta suka yi jawur tsabar kuka, shima idonsa akan ta hawaye sai gangaro masa yake, yana durƙushe da gwiwowinsa ya ce "Reesh forgive me please, nasan nayi miki kuskure, ban kyauta miki ba amma ina so ki yafe mun, ki kawo ƙarshen ƙoyayyar da kike mun ko dan saboda ƴar mu, bana so ta taso ta tarar da mu a cikin wannan rayuwar ƙiyayya, ina matuƙar ƙaunar ki Reesh, amma ina so ki sawa ranki cewa banida laifi akan abinda ya faru, bansan na aikata hakan ba kuma ke ma kinsan cewa ba'a cikin hayyacin mu muka aikata ba, kinsan waɗanda sukayi dalilin hakan kuma an hukunta su meyasa bazaki iya yafe mun ba alhalin kinsan ba laifi na bane, tsautsayi ne da ƙaddara da kuma rabon samun Ƴar mu ..." Amreesh haɗiyar yawu tayi ta wani ɓangaren ta yadda akan cewa shine Habeey amma ta wani ɓangaren kuma ta kasa yadda da shi... Madam Parveen wani dabara ne ya faɗo mata da sauri ta bar falo kai tsaye part ɗinta ta nufa, bayan wasu seconni sai ga ta ta fito da wani littafin photuna a hannunta, kamar yadda ta bar su haka ta dawo ta same su a haka tana tsaye shi kuma Razhdeen yana durƙushe yana riƙe da hannunta, Madam Parveen zuwa tayi gaban su ta sunkuya tare da riƙo Razhdeen ta ɗago shi tsaye tana faɗin "it's okay Razh everything will be come easy..." Ta juya kan Amreesh ta ɗago hannunta tare da damƙa mata littafin tana faɗin "ki nutsu ki kalli waɗannan photuna nasan dai kin san photonki kina yarinya domin shine a manne a bangon falon nan..." Amreesh jiki ba ƙwari haka ta soma buɗe littafin tana sharar hawaye, a farko taga photon ta ita kaɗai, tana buɗe wa taga photonta da family ta next page kuma taga photonta da Habeey ya ɗauke ta akan kafaɗarsa, a ruɗe ta zaro ido waje tana bin photon da kallo ganin wani saurayi fari tass da sumar kansa har zuwa kafaɗa tin a lokacin ma, da sauri ta ɗago tana kallon Razhdeen, domin shi ɗin ne a photon babu abunda ya chanza sai girman jiki da tsayi... Ƙara buɗe photuna take kuma yawancin photon ta ne da Razhdeen, nan suna swimming pool nan kuma sun je super market nan kuma a wurin birthday, da kuma photon yanda ya sanya mata zobe da itama ta saka masa, haka take kuka tana ganin photunan sannan ta kai idonta kan Razhdeen, Kowa na wurin tsaya kallon ta yake sai yanzu fuskar kowa ya fara sake wa domin yanzu Amreesh ta fara gaskata wa lamarin, Chief da murmushi akan fuskar sa ya yo kan Amreesh ya dafa kafaɗarta yana faɗin "Daughter kina son ƙara gaskata wa again?..." Amreesh ɗagowa tayi tana kallon Chief hawaye kuwa ya ƙi tsayuwa ga yanda idonta yayi jawur, Chief miƙawa Rakesh carset ya yi ya ce "kaje ka sa carset ɗin nan ka kunna plasman..." Rakesh karɓa yayi yaje ya kunna, Chief kuwa rungumar Amreesh ya yi yana rarrashin ta domin ba ƙaramin kuka take ba, A hankali ya zaunar da ita akan kujera yayi facing ɗin ta da plasman yanda zata kalli video da kyau... Video lokacin birthday party ɗinta ne musamman aka tanadar musu da kujera ɗaya ita da Habeey, a lokacin aka sanar wa kowa alƙawarin da ke tsakanin ta da Razhdeen, itama a lokacin ta sanar cewa itama tana son Habeey ɗinta... Bayan an gama kallon video Amreesh ta gama yadda cewa Razhdeen shine Habeey ɗinta amma ta kasa cewa komai, kamar ba jini a jikinta haka take zaune ta kwantar da kanta a ƙirjin Daddynta, Chief ya ce "Daughter yanzun kin amince da Habeey ɗin ki?..." Kowa shuru yayi ana son jin abinda zata ce ganin yanda ta damu da Habeey.. Amreesh ido a lumshe ta ce "su tafi kawai, bana buƙatar su yanzu..." Roshan cije lips ɗinsa na ƙasi yayi tsabar takaici haka ya dafa kafaɗar Razhdeen yana faɗin "my man please tashi mu koma Nigeria..." Razhdeen idonsa akan Amreesh ya ce "Reesh Please help me, bazan iya rayuwa ba tare da ke ba, ina matuƙar ƙaunar ki..." Amreesh ta ce "Daddy ka ce su tafi dan ALLAH, ko kuma na tafi na bar muku gidan gaba ɗaya..." Roshan cikin ɓacin rai yake faɗin "My man tashi mu tafi, ka roƙi Allah ya fitar maka da sonta a cikin zuciyar ka, Allah zai baka wacce ta fita, bata sonka banga amfanin tilasta mata ba ...." Razhdeen babu yanda ya iya haka ya miƙe tsaye idonsa akan ta sai da ya ɗau mintuna kafin ya ce "shikenam zan tafi Reesh! amma ki sani cewa ina nan akan baka ta na cewa bazan taɓa yin Aure without you..." Kowa na wurin bai ji daɗin abinda ya faru ba, gani suke tinda yanzu tasan shine Habeey zata iya haƙura amma sai suka ga akasin haka... Amreesh idonta a lumshe ta ce "Go away from me...." Roshan riƙo hannun Razhdeen ya yi suka nufi bakin ƙofa zasu tafi, Chief ya dakatar da su da cewa "baza ku koma Nigeria a yau ba, Mohandas zai kai ku wurin masauƙi a other house ɗina..." Shima Mohandas miƙe wa yayi cikin jin haushin ƙanwarsa zasu fita a tare, Har zasu fita suka ga Razhdeen ya tsaya cakk suma Roshan da Mohandas tsayawa suka yi tare da juyawa su ga meke faruwa sai gani suka yi Amreesh ta rungume shi ta baya, Razhdeen kasa juyawa yayi ganin yanda aka rungume shi amma ya tabbatar da cewa Amreesh ce, kuka take a hankali take furta "Habeey i hate you too much..." ta ƙara wa kukan ta volume sosai, riƙo hannunta yayi tare da zagayo da ita ta gabansa suna kallon juna daga bisani ya rungume ta sosai shima ya ce "I hate you my Reesh..." Bugan ƙirjinsa tayi tana dariya domin lokacin da take ƙarama idan tace masa I love you shi kuma cikin wasa sai ya ce mata I hate you da haka ta koya itama take ce masa i hate you.... Cikin farin ciki Minal da Rukky suka fara tafa hannayen su tare da faɗin "wow congratulation so nice wannan salon soyayyar ya yi kabce da yawa...." Madam Parveen itama bata san lokacin da ta fara dariya ba, Duk haka kowa ya kasance cikin farin ciki lokaci guda, Shima Roshan bai san lokacin da ya tsinci kansa cikin farin ciki a yayin da yake baƙin ciki rashin mutuncin da tayi wa twins ɗinsa ba... Haka suka juya cikin falo cikin farin ciki, Razhdeen da Amreesh a kujera ɗaya suka zauna suna riƙe da hannun juna..... A wannan ranar ne first sight of love da Razhdeen da Amreesh suka kasance, wanda ya kasance iya su biyu ne a falo kowa ya tashi ya bar musu wuri bayan an gama tattaunawa akan batun, Ba ƙaramin shauƙi da kewar juna suka tsinci kansu a ciki ba, lokaci guda soyayyar Razhdeen ta dawo wa Amreesh ɗanye shakaf fiye da yanda ta so shi a baya, wannan so shi zai kai su har ƙarshen rayuwar su.. ★★★★★★ Washe gari da safe Razhdeen da Amreesh suna zaune akan kujeru a wurin shakatawa dake bakin swimming pool na gidan Chief, ga wani lema a saman kujeru yanda rana bazai taɓa su ba, suna shan hirar su kamar babu wata ƙiyayyar da ta shiga tsakanin su, Amreesh tana zaune sai ga wani zazzafan hawaye yana gangaro mata, a ruɗe Razhdeen ya taso ya zauna a kujerar dake gefen ta ya riƙo hannunta cikin kulawa yake faɗin "wannan hawayen tamkar mashi yake a cikin zuciyata, ganinsa tamkar ana caka mun a tsakiyar zuciya ta ne..." yana kaiwa nan ya riƙo fuskar ta da hannayensa biyu sannan ya kai bakinsa saitin fuskar ta tare da zaro harshen sa ya fara lashe hawayen fuskar ta, tas sai da ya lashe hawayen da ya gangaro mata, Ita kuwa abun dariya ya bata hannu tasa ta bugi ƙirjinsa tare da ture shi tana faɗin "kai Habeey meye haka kumaaa..." Murmushi yayi sex eyes ɗinsa akan kyakkyawar fuskar ta ya ce "da zaki cigaba da zubar da hawaye haka ni kuma zan cigaba da shanye su domin bazan taɓa barin hawayen ki ya zuba ƙasi ko da ya ƙwayar zarra, domin hawayen ki na da matuƙar mahimmanci a rayuwa ta, asarar sa kuma dai dai yake da rasa rayuwa ta..." Murmushi tayi itama ta ce "Ni kuma bana buƙatar ganin ƙarshen rayuwarka sai dai kai kaga ƙarshen rayuwa ta, ina matuƙar ƙaunar ka Habeey, bana so mu rabu da juna, ina so mutuwa in ta zo ta ɗauke mu tare, ina so soyayyar mu tayi ƙaurin suna ta kuma bayyana kamar Mahadi, ina so soyayyar mu ta cigaba da gudana a cikin jijiyoyin jikin mu sannan al'umma suyi alfahari da mu tare da zuriyar mu ga baki ɗaya...." Razhdeen jinjina kai yayi sannan ya ce "bazan iya misalta miki yanda girman soyayyar ki take a cikin zuciya ta ba amma zan nuna miki yanda soyayyar mu zata cigaba da gudana a cikin jijiyoyin mu..." Amreesh sauƙe numfashi tayi tare da faɗin "okay show me how..." Razhdeen ajiye wata glass cup yayi a gaban sa tare da tsiyaya ruwan bottle a cikin cup ɗin, ya ciro wata sabuwar reza a cikin poket ɗinsa ya ɓare ledar jiki sannan ya ɗago hannun Amreesh tare da buɗe tafin hannunta fari tass mai ɗauke ido, Idonsa akan fuskar ta ita kuwa idonta akan hannunta yanda ya riƙo babbar yatsar ta ya ɗora reza akai, zaro ido waje tayi murya na kakkarwa ta ce "H H H Habeey mai zaka yi kuma, yanka ni fa zaka yi...." Idonsa akan fuskar ta ya ce "kina tunanin zan iya cutar da ke ne?..." Da sauri ta girgiza masa kai, ya ce "to rufe idonki idan kina jin tsoro..." kamar yanda ya ce haka tayi, lips ɗinsa na motsi a hankali ya furta "Bismillah..." ya ɗan dirza rezar akan yatsar ta, a ɗan ruɗe tasau ƙara tare da buɗe idonta taga yanda jinin ta yake zuba a cikin glass cup da ya ajiye, nan da nan ruwan cikin ya canza launin ja, idonta takai kan fuskar sa tana kallon ikon Allah baki ya gagara rufuwa, Bayan jini ya ɗan zuba a cikin cup haka ya sa bandej ya manne wurin yankuwan, ɗagowa yayi shima yana kallon ta shima miƙa mata reza yayi yana ɗaga mata kai alamar ta karɓa, itama karɓa tayi cike da mamaki da rashin sanin dalilin yin haka, Ya ce "kamar yanda na miki kema ki mun, ki zuba jini na a cikin wannan cup ɗin da yake ɗauke da jinin ki..." Miƙa mata hannun sa yayi tare da saita yatsarsa akan cup ya damƙi hannunta mai riƙe da reza ya ɗora rezar akan yatsar yana faɗin "ki yanke ni mana..." Haka hannun Amreesh yake kakkarwa tana girgiza kai ta ce "ni ni ni bazan iya baaa..." Murmushi ya yi tare da faɗin "ke fa matar soja ce ina so ki zama jaruma, idan kina sona da gaske ki yanke ni, amma idan bakya sona shikenam daga yanzu nasan matsayina..." Amreesh tana shirin yin kuka Razhdeen yayi saurin dakatar da ita yana faɗin "kada na ga hawaye akan fuskar ki domin idan ba haka ba zan iya mutuwa yanzu saboda na sanar miki cewa hawayen ki mashi ne lokaci guda zai iya cakar zuciyata, idan kuwa ya caki zuciyata to mutuwa zanyi....". Dasauri Amreesh ta goge guntun hawaye da yake shirin zubo mata, ta ce "Habeey dan ALLAH ka dakatar da wannan abun ba zan iya yankan hannunka ba..." Razhdeen ya katsar ta da cewa "sai dai idan bakya so nane, nasan inda kina sona da bazaki tsaya yin jayayya da ni ba..." Amreesh rufe idonta tayi a hankali ta dirza rezar sai ga jini jajawur yana zuba a cikin glass cup sai ya haɗe da nata ruwan ya ƙara yin jaa sosai. Razhdeen ganin idonta a rufe yasa ya kai lips ɗinsa kan ɗan ƙaramin bakin ta yayi mata wani irin hot kiss, da sauri ta buɗe ido tana bin sa da kallo bata san lokacin da tasau murmushi ba, Ɗaukar cup yayi yana juyawa da spoon jinin ciki ya gama haɗe wa kamar lemon juice, idonsa akan ta yakai cup ɗin bakinsa yana sha kamar juice itama kallonsa take cike da mamaki haka suke kallon juna, sai da yasha yayi rabi tukun ya miƙa mata yana ɗaga mata kai alamar itama ta sha.. Karɓa tayi ba musu ta ɗora bakin cup akan lips ɗinta itama ta fara sha har sai da ta shanye gaba ɗaya, tana gama shanye wa kuka ya yanko mata tinin ta fashe da kuka tare da rungumar Razhdeen sosai a jikin ta, shi kuwa haka yake bubbugan bayanta yana rarrashi... Sun kai mintuna a haka, Roshan ne yazo ya tarar da su a haka shima ya juma yana tsaye idonsa a kansu sai sakin murmushi yake domin yanzu babu soyayyar Amreesh a cikin zuciyar sa da taimakon Ubangiji domin tin daga lokacin da Baiwar ALLAH ta bayyana a mazannin Amreesh daga lokacin ya fara roƙon Allah ya cire masa sonta a cikin zuciyar sa, yanzu dai a hankali komai ya dai daita, bazai ce baya sonta ba amma irin soyayyar Aure ko sha'awa babu ita yanzu, sai da ya juma shima a haka yana maganar zuci daga bisani yayi gyaran murya, duk ɗagowa sukayi tare da juyawa suna kallon Roshan, Da murmushi akan fuskar sa ya ce "sannun ku masoya..." Amreesh kawar da kanta gefe tayi cikin kunya, shi kuwa Razhdeen tsaya kallon Roshan yayi daga bisani ya ce "ba dai tafiya ba ko?..." Roshan ya ce "dole zan tafi mana yanzu ake sanar mun cewa Ramlat ta haifi ɗa namiji..." Razhdeen ya ce "congratulation dole tare zamu tafi domin bazan bar ka ka tafi kai ɗaya ba...". Itama Amreesh cewa tayi "gaskiya duk tare zamu tafi, su Ramlat an zama Mama, ma sha ALLAH dole zamu je ganin jariri..." Roshan idonsa akan Amreesh ya ce "meyasa bakya tambayar Biju Mama ne?..." Amreesh ta ce "ko ban tambaye ta ba ai tana cikin raina..." Roshan ya ce "let us go idan kun gama shan love..." dariya suka yi duk suka bar wurin, Kowa shiryawa yayi tsab za'a tafi Nigeria, Minal da Rukky murna suke zasu je su ga iyayen su... Roshan gaba ɗaya zumuɗin sa shine yaje ya ga handsome boy ɗinsa duk da an turo masa photon yaron a waya, har da Madam Parveen itama ta shirya zasu tafi.... °°°°°°°°°°°°°°° Nigeria Kowa ya taru a babban falon gidan General, Mai martaba shima ya samu zuwa shi da iyalansa Aunty A'isha da Aunty Maimuna da kuma Ummy uwar masu gida da mijinta Yarima, Ga kuma Abbah da iyalansa shima Hajiya Kilishi da Ammy da kuma Aunty Yolash wacce take riƙe da jariri a hannunta, ga Pinky itama tazo da mijinta Arash, Reemah da Afaf kuma suna cikin ɗaki dake Reemah ba mai son zama a cikin mutane bane shiyasa take fakewa a wuri guda ita da abar ƙaunar ta Afaf, Sai yanzu isowar su Roshan suma samun wuri sukayi shi da Razhdeen suna zauna, Madam Parveen itama zama tayi kamar yanda taga kowa a zaune falon yayi tsit ko motsi bakwa ji, Minal da Rukky suma a kujera ɗaya suka zauna, ita kuma Amreesh kujerar da Ummy take nan taje ta zauna, Aunty Yolash ce ta miƙe tsaye taje gaban Roshan wanda yake zaune yana bin kowa da kallo fuskar kowa ba annuri, haka yasa hannu ya karɓi yaron dai-dai lokacin da hawaye ya ɗigo a hannun Roshan, da sauri ya ɗaga kansa yana kallon Aunty Yolash wacce hawaye ya gama wanke mata fuska, Wani irin bugu zuciyarsa tayi wanda bai san lokacin da jikinsa ya ɗau kakkarwa ba, Ummy itama hawaye take wanda Amreesh gaba ɗaya ta kasa gane wa, Sai a lokacin Abbah ya ce "Yolash zo ki zauna..." haka taje ta zauna jiki ba ƙwari, Razhdeen cikin rashin fahimta ya ce "wai me yake faruwa ne?...." Roshan yana riƙe da jariri idonsa akan fuskar sa yana sakin murmushi ga hawaye shima yanda yake zubo mishi ya ce "Boy kaga suna ɓoye mun cewa Mamanka ta rasu ko, kaima kan ka kasan Mamanka ta rasu bazaka kasa ɓoye mun ba tinda ga nan bakinka yana motsi, Mamanka ta tafi ta bar mun kai why?...." Razhdeen a ruɗe ya daga kafaɗarsa yana faɗin "twins wai me kake faɗi haka ne?..." Cikin ɗaga murya Roshan ya ce "My Man ka dubi duk fuskokin su hakan yana nuna alamar isar da wani mummunan saƙo ne, shin idan ba saƙon mutuwa suke son isarwa ba to saƙon meye? shin ina Ramlat? ban ganta a cikin ku ba hakan na nufin tabar duniyan nan, Ramlat ta tafi tabar jaririn yaro, nasan in ba mutuwa ba babu yanda za'ayi Ramlat tabar mun jaririn yaro dole sai aikin mai yankan ƙauna wato mutuwa...." Duk matan falon fashewa suka yi da kuka, Minal da Rukky ne suke tambayan Abbah cewa "Abbah da gaske ne wai Aunty Ramlat ta rasu?..." Amreesh ƙafewa tayi gaba ɗaya ta kasa yin kukan ma jin yanda zuciyar ta yake bugawa jin mummunan labari, Razhdeen shima idonsa ya kai kan Abbah yana son jin ƙarin bayani, Abbah jinjina kai yayi tare da faɗin "tabbas wanda ya fi mu sonta ya ɗauke kayan sa..." A firgice Madam Parveen wacce itama take son ji daga bakin su ta dafe ƙirji tare da faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un...." A ruɗe Baiwar ALLAH ta ƙanƙame hannun Ummy wacce take kusa da ita tana jinjina labari, haka kanta yake juyawa domin labarin mutuwar Ramlat ba ƙaramin girgiza kowa yayi ba.... Roshan jaririn hannunsa ya manna a ƙirjinsa tare da fashewa da kuka, haka Razhdeen yake bubbugan bayansa yana rarrashinsa... Mai martaba ya ce "kuyi haƙuri haka rayuwar take wata rana kayi farin ciki wata ran kuma kayi kuka, hakan ma mun godewa Ubangiji da Allah yasa muka sake samun ƙaruwar ahali, kuka ba maganin mutuwa bane hakanan zamu cigaba da yi mata addu'a domin tafi buƙatar sa a halin yanzu...." Madam Parveen ce taje ta karɓi jaririn hannun Roshan domin yanzu ba'a cikin hayyacinsa yake ba, ba abinda yake sai kuka... Suna cikin wannan halin sai ga wasu mutane sun shigo da sallama a bakinsu, ƴan uwan Ramlat ne suka zo ta ɓangaren mahaifinta da kuma mahaifiyar ta domin daman su ake jira, an gama gyarata tana can cikin ɗaki a kwance cikin makara... Roshan a zabure ya miƙe tsaye yana faɗin "ina take?...." Mai martaba ne ya nuna masa ɗakin da take kafin a fita da ita gurin jana'iza domin an sanar wa mutane har an taru, Roshan da gudu ya wuce ɗakin a yayin da Razhdeen ya bi bayansa, itama Baiwar ALLAH bin bayan su tayi, a ɗaki suka tarar da gawar Ramlat a cikin makara an gama rufa mata likkafani, Roshan durƙusawa yayi a gabanta yana kuka tare da faɗin "Ramlat ashe daman yafiyar da kike cewa nayi miki tafiya daman xakiyi ki barni? hawayen da kike zubar wa a gabana ashe daman kukan ƙarshe kike mun? Ramlat inasonki, na yafe miki duniya da lahira, Allah Ubangiji ya haskaka miki kabarin ki yasa kina ɗaya daga cikin salihan bayi ƴan aljanna....." Daga nan ya fashe da kuka, Razhdeen ne shima ya durƙusa a gabansa tare da dafa shi ya rungume shi a jikinsa yana rarrashin sa, Itama Baiwar ALLAH durƙusawa tayi tana kuka ta ce "Ramlat yau Amreesh ce a gabanki wacce muke yawan faɗa tsawon shekara guda bamu ga juna ba, nasan na ɓata miki rai dan ALLAH ki yafe mun, kin tafi kin bar mu amma nasan kina ji na, ki yafe mun ɓata miki rai da naita yi ashe ma haka duniyar take ba waran matabbata bane, ni na yafe miki kema nasan kin yafe mun ko? yawwa Ramlat ɗina nagode sosai..." Itama fashe wa tayi da kuka ji take kamar ba da gaske bane mutuwar Ramlat.... Suna cikin wannan halin har aka shigo ɗaukar gawa.... Duk mazan fita sukayi zasu yi sallar jana'iza daƙer Razhdeen yaja Roshan suka fita, Matan kuwa duk a falo suka taru ana jimamin mutuwar Ramlat, Amreesh tana zaune a ƙasin carpet ta kifar da kanta akan gwiwowinta sai sharar kuka take, tana cikin wannan halin taji ana bubbuga mata kai, a hankali ta ɗago da rinannun idanuwanta tana kallon yarinyar da take tsaye a gabanta tana faɗin "Mamma! Mamma!!...." Amreesh cikin kuka ta rarumo ta tare da rungumar ta a jikin ta sosai tana kuka domin tasan ɗiyar ta ce... Haka take sumbatar da akan goshi tana shashshafa sumar kanta ji take kamar ta mayar da Afaf cikin cikinta domin ba ƙaramin ƙaunar ta take ba, da kuma kewar ta haka take kuka tana faɗin "Yarinya ta ki gafarce ni dan ALLAH, nasan nayi miki kuskure Please ki yafe wa Mamanki, na tafi na bar ki cikin jin haushi na, ban barki kin sha nono ba, ina ji kina kuka amma haka na tsallake ki yanzu kuma maimakon ki guje ni sai kuma kika yo kaina Allah sarki abar ƙaunataa, ga shi wasu suna haifan ɗansu suka rasu ko tsaya shayar da su basu yi ba, ni kuma da Allah ya bani dama da áron rai sai na tsallake nabar Jaririya ta wayyo Allah....." Baiwar Allah ƙara rungumar Afaf tayi tana kuka... Duk mutanen wurin babu wanda bai tausaya mata ba.... Itama Reemah (Ƴar Amana) tana zaune fuska da idanu duk sunyi jawur tsabar kukan da ta sha... A wannan ranar Ramlat ta riga mu gidan gaskiya anje a bisine ta a cikin ɗakin ta mafi daraja... Ana zaman makoki har akayi kwana uku yau, daga can prison sun yo waya akan ko za'a kawo Maamie amma Mai martaba ya dakatar saboda a halin yanzu hauka take tuƙuru bata hayyacinta kowa ya ji abinda ta aikata sai yayi Allah wadar da ita, hatta ƴan uwanta sun ƙi karɓan ta suka ce ta cigaba da zama a gidan prison har ƙarshen rayuwar ta... Kowa ya watse yanzu iya family ne suka rage, Roshan kuwa kullum Razhdeen ne a wurinsa domin har yau bai dawo taitayinsa ba, sai lissafe-lissafe yake yana faɗin "wani irin ƙaddara ce take bibiya ta? farkon masoyiya ta wacce na bata zuciyata gaba ɗaya hatsari tayi ta mutu ta barni har an tsayar da maganar Auren mu, masoyiyata ta biyu Allah yasa ba rabona bace itama bata mutu ba amma tsautsayi ya gibta a tsakanin mu sannan na samo wata itama Allah bai bar mun ita ba ta tafi ta barni, ta bi bayan wancan, wannan al'amarin daga jini nane babu wacce zan ƙara zaman Aure da ita gwara kawai nayi zaman kaɗaici ni kaɗai ....." Haka yake ta wannan surutan har Allah yasa masa sukuni da tawakkali a cikin ransa, yau kwana bakwai da rasuwar Ramlat, akan kai wa Roshan jaririnsa sa'in-sa'in, Amreesh kuwa kullum Afaf tana jikinta bata bari tayi nisa da ita domin yanzu wani irin ƙaunar ta ne ya shiga cikin zuciyar ta fiye da yanda take ƙaunar Razhdeen, itama Afaf har ta saba da Amreesh duk da wani sa'in ana shan gwagwarmaya da Reemah akan Afaf, Ita Reemah bata so Afaf tayi nisa da ita itama Amreesh kullum tana riƙe da ita, haka Reemah zata shiga ɗaki taita kuka duk da ita Amreesh bata san meye a tsakanin Reemah da Afaf ba, Itama Afaf idan ta kasance a wurin Amreesh bata son barin jikinta.... Da haka ake kan ɓoye wa Amreesh cewa Afaf yarinyar Reemah ce yanzu, ba'a son barin Amreesh ta san halin da Reemah take shiga akan Afaf idan bata jikinta..... Typing ✍️ Asmeetah writer *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 76 to 80 Baiwar Allah tana tsakiyar gado ita da ƴarta Afaf suna wasa tare sai ga Madam Parveen ta shigo, itama zama tayi a bakin gado tana sakin murmushi ganin yanda suke ta ƙyalƙyala dariya suna wasa, Baiwar Allah juyowa tayi tana kallon Madam Parveen da murmushi akan fuskar ta ta ce "Mommy kin shigo ne?..." Madam Parveen ta ce "eh daman akwai maganar da nake so nayi dake..." Baiwar Allah ta ce "to ina jinki Mommy..." Madam Parveen ta ce "Amreesh naga kin shaƙu da yarinyar nan sosai duk da ke kika haife ta amma dole zan gaya miki abinda ake ɓoyewa a cikin gidan nan, akan ƴarki Afaf da kuma Reemah..." Baiwar Allah cike da mamaki take binta da kallo ta ce "me yake faruwa ne Mommy, me ya faru da Ƴar Amana ta da kuma Afaf?..." Madam Parveen sai da ta sauƙe nannauyar numfashi kafin ta sanar mata duk halin da ake ciki da kuma abinda ya faru lokacin da suka zo ɗaukar Afaf..." Baiwar Allah lokaci guda hawaye har ya wanke mata fuska ta ce "daman nasan baza'a rasa aljanu a jikin Ƴar Amana ba, aljanun ta kuma sai suka haɗa ta da yarinya ta, Allah sarki Ƴar Amana indai Afaf ce farin cikin ta to ni na bar mata ita duniya da lahira, domin duk wanda ya nuna yana son jininka to babban masoyinka ne..." Madam Parveen jinjina kai tayi sannan ta ce "shikenam kin sadaukar da ƴarki?.." Baiwar Allah ta ce "na sadaukar da ita indai ba cutar mun da ita za'ayi ba, nasan zata fi samun kulawa sosai a wurin Ƴar Amana fiye da yanda zan bata, kuma Ƴar Amana tin Afaf tana jaririya take riƙe da ita kamar yanda na riƙe ta lokacin da take jaririya why ni bazan bata nawa ba, don haka zanje na sanyata cikin farin ciki..." Ta ƙarasa maganar tana kallon yanda Afaf take ta wasan ta ta ce "Biju Mama zo ma za na kai ki wurin Auntyn ki..." tasa hannu ta ɗauke ta suka fice a ɗakin, Madam Parveen binta kawai tayi da ido tare da girgiza kai tana jinjina lamarin nan... Baiwar Allah tana fita falo kai tsaye ɗakin Ƴar Amana ta nufa, tana shiga ta tarar da ita zaune akan gado ta rungumi pillow sai kuka take ga kuma Ummy a gefenta sai rarrashin ta take... Baiwar Allah tsayawa tayi tana ɗauke da Afaf idonta akan Reemah tasan duk akan Afaf ta shiga damuwar nan, cike da tausayawa Baiwar ALLAH ta ƙira sunan ta tare da faɗin "Ƴar Amana..." Reemah ɗagowa tayi tana haɗa ido da Baiwar ALLAH tare da Afaf tayi saurin tashi daga kan gadon ta nufi yanda suke tsaye tana ƙoƙarin karɓan Afaf duk da Yarinyar tayi wayo 2 years amma ɗaukar ta ake kamar jaririya, Baiwar Allah tana murmushi ta miƙa mata ita tana faɗin "ga nan ƴarki na kawo miki ita..." Ƴar Amana dariya ta soma yi tana faɗin "Nagode sosai wallahi ina matuƙar ƙaunar ta, dan Allah Aunty Baiwar ALLAH ki bar mun ita, wallahi zan kula miki da ita sosai...." Baiwar Allah dafa kafaɗarta tayi tana murmushi ta ce "kar ki damu Ƴar Amana ta, na bar miki Afaf..." A ruɗe Ƴar Amana ta ce "wai da gaske Aunty Baiwar ALLAH? wayyo farin ciki nagode sosai, shikenam Biju Mama ta zamo tawa har abada..." Haka Ƴar Amana take sumbatar Afaf akan goshi tsabar farin ciki.. Ummy itama tana zaune bata san lokacin da ta tsinci kanta cikin farin ciki ba, lokaci guda kuma ta maida idonta kan Baiwar ALLAH sai taji tausayinta domin tasan tana buƙatar ɗiyarta a kusa da ita amma ta sadaukar da ita.... Baiwar Allah juyawa tayi ta fice daga ɗakin ganin hawaye yana shirin zubo mata domin itama tasa Afaf a ranta sosai, tana fita falo hannunta akan fuska yanda take ƙoƙarin share hawaye zata wuce taji an riƙo hannunta, da sauri ta sauƙe hannun tare da ɗaga kanta tana kallon wanda ya riƙe ta, Razhdeen ne ya riƙo ta yana ƙareta da kallo murya ciki-ciki ya ce "why are you crying?..." Girgiza kai tayi tare da faɗin "ba komai..." Ya ce "Please i need to know who make you cry, idan har kina son ganin farin ciki na ki sanar mun abinda yake ranki...." Baiwar Allah gani tayi bazata iya riƙe kukan da ya kuɓuto mata ba yasa ta rungumi Razhdeen tare da kifar da kanta akan faffaɗan ƙirjinsa ta fashe da kuka. Sauƙe numfashi yayi yasa hannu ya ɗauke ta kai tsaye part ɗinsa ya nufa da ita, a hankali ya haura upstairs sannan ya miƙe hanyar room ɗinsa, yana shiga falo ya wuce da ita bedroom ɗinsa bai sauƙe ta a ko ina ba sai akan katafaren gadonsa, a tsakiyar gado ya zaunar da ita shima ya hau ya zauna yana fuskantar ta, yasa hannu ya tallafo fuskar ta ya ce "Reesh! Me ya same ki?..." murya ciki-ciki ta ce "ban san halin da Ƴar Amana da Biju Mama suke ciki ba sai yau, na sadaukar da ƴata, na bar mata ita har abada domin ta nuna mun ta fini sonta sosai, kuma tayi ɗawainiya da Biju Mama tin tana jaririya..." Razhdeen sauƙe numfashi yayi yana riƙe da fuskar ta ya ce "to meya sakaki kuka? shin sadaukarwar da kikayi ne yasa kike kuka ko kuma me ye?..." Baiwar Allah ta ce "Ni bazan ɓoye maka ba nima ina son Biju Mama, bana so na ƙara yin nisa da ita, ina so yarinyata ta shaƙu da ni sosai, amma bayar ta da nayi a Ƴar Amana duk ban faɗi ƙasi ba tinda duk ɗaya muke amma babban damuwa ta shine aljanun da suka raɓe su, ina tsoron aljanu sosai..." Razhdeen jawo ta yayi jikinsa yana rarrashin ta ya ce "kar ki damu zamu sake haifan wasu ai, kuma sannan aljanun ba masu cutar wa bane ki kwantar da hankalin ki Biju Mama ai tana tare da mu tinda a wurin Sarah take, naji Abbah da Uncle suna maganar cewa zasu haɗa Roshan da Sarah...." Baiwar Allah ɗagowa tayi lokaci guda ta saki ranta cikin fara'a take faɗin "Ma sha ALLAH! inason haɗin nan sosai, kuma sun dace da juna, kasan Ƴar Amana tana son Yaya Roshan, shi kuma abinda yasa bai ɗora ransa akan ta ba saboda marigayiya Ramlat ce amma nasan shima yana sonta...." Razhdeen hannu yasa ya ɗan ja kuncin ta yana murmushi ya ce "taya kika san Roshan yana son Sarah?..." Baiwar Allah kwantar da kanta tayi akan ƙirjinsa tana faɗin "na fa zauna da Yaya Roshan, na gama sanin duk wani take-takensa abinda yake ɓoyewa da kuma sirrin cikin zuciyar sa, na gama yin bincike na na gano cewa yana son Ƴar Amana sosai, tin kafin na tafi na gama sanin haka kuma itama tana son sa, amma kuma jaririnsa wa zai riƙe masa ?..." Razhdeen ya ce "baza a rasa ba..." Baiwar Allah kasancewar ta da Razhdeen ya ƙara je fa ta cikin shauƙi, haka kawai sai sakin murmushi take, ta ƙira sunansa a hankali "Habeey..." Ya amsa mata cikin kulawa. Ta ce "yaushe ne Auren mu?..." Murmushi yayi shima ya ce "ƙarshen watan nan ranar da Ramlat zata cika wata uku a ranar twins ɗina shima za'a Aura masa Sarah..." Baiwar Allah ta ce "kenam kai da shi za'ayi bikin rana ɗaya ?..." Ya ce "of course my wife, kinga ana bikin mu zamu koma U.S domin zan koma wurin aiki na shima Roshan zai koma Egyph shi da matar sa da yaransa Biju Mama da kuma Boy..." Baiwar Allah ta ce "kenam duk yara biyun zasu tafi?..." Ya ce "to waya sani ne sai lokacin yayi komai zai bayyana..." Baiwar Allah sai da ta ɗan yi shiru na wani lokaci sannan ta ce "ni sai a bar mun yaron zan riƙe shi...". Razhdeen ya ce "ke da zaki fara aikin soja..." A zabure Baiwar ALLAH ta ɗago tana kallonsa gira a haɗe ta ce "wani soja? impossible wallahi haka naji Daddy na yake faɗa Ni kuma bazan iya ba..." Ya ce "zaki iya mana ke fa jaruma ce..." Kamar zata yi kuka ta ce "Ni kawai bana so, ku daina mun zancen nan..." Dariya ya yi yana bubbugan bayanta irin na rarrashin nan, da haka suka wuni a ɗakin..." Roshan yana part ɗinsa a zaune kan kujerar falo misalin ƙarfe 8 na dare ya haɗe kansa da gwiwa yana tunanin abubuwa da dama, Bai ankara ba yaji an dafa kafaɗarsa ta baya dasauri ya ɗago yana kallon wacce ta ɗora masa hannu, Cikin sassanyar murya ta ƙira sunan sa "Yaya Roshan...." Haɗiyar yawu yayi idonsa akan ta ya ce "Shalele ya akayi ne?..." Ƴar Amana cikin damuwa ta ce "meyasa bazaka dawo yanda kake a baya ba, bana son ganinka cikin damuwa, wanda ya mutu ya tafi kenam ba halin dawowa dan Allah Yaya Roshan...." Sauƙe numfashi ya yi tare da faɗin "ki kwantar da hankalin ki bawai ina jimamin mutuwar bane har yanzu komai na barwa Allah, haka Allah yaso da ni kuma ina fatan hakan shine mafi alkhairi a rayuwa ta gaba ɗaya..." Ƴar Amana jinjina kai tayi sannan ta ce "ma sha ALLAH! to yanzun tunanin me kake?..." Girgiza kai yayi sannan ya ce "kawai dai haka ne idan na kasance ni kaɗai...". Cikin nuna damuwa ta ce "shin kana son kasancewa da ni? bana so ka rinƙa zama a haka..." Ya ce "Shalele daman ai a tare muke..." Girgiza kai tayi tare da faɗin "ba irin wannan tarayyar ba, ina nufin tarayyar zaman Aure..." Murmushi ya yi sannan ya ce "Reemah kenam, kamar yanda nace bazan ƙara yin Aure ba har ƙarshen rayuwata to na faɗa ne da zuciya ɗaya, har cikin raina bana buƙatar zama da wata mace a mazannin matar Aure ...." Ƴar Amana hawaye ne ya fara gangaro mata ta ce "Yaya Roshan ina tunanin lokacin da ka ƙini saboda ganin idon Ramlat ne ashe duk ba haka bane tinda ga shi yanzu bata duniyar gaba ɗaya amma still ka furta baka sona, meye a jikina wanda ban cancanci a soni ba, Yaya Roshan mena maka ne? shin da me duk matan da kaso suka fini? basu fini komai ba but meye matsalar?..." Roshan ya ce "Reemah kina ji ba, tashi ki tafi bana son maganar Aure yanzu..." Ƴar Amana tana kuka ta rirriƙo hannayen sa tana faɗin "Yaya Roshan dan Allah, wallahi ina sonka sosai, dan Allah ka cika wa zuciyata burin ta, shin meyasa bata dacen samun abinda take so, taso Yaya Razhdeen bata dace ba, sannan kuma yanzu tana shirin fashewa saboda tsananin ƙaunarka amma kana shirin hanata abinda take so..." Roshan cikin ɓacin rai ya ce "Reemah tashi ki tafi..." Ƴar Amana buɗan baki tayi zata yi magana ya yi saurin miƙewa tsaye ya bar falon gaba ɗaya, ficewa ya yi ya nufi motar sa ya shiga already security ya buɗe masa get ya fice a ɗari... Ƴar Amana fashe wa tayi da kuka, ta juma sosai a zaune bata motsa ba tana kan yin kukan ta taji kamar ana ƙiran sunan ta, "Reemah! Reemah!! Reemah!!!..." Ƴar Amana ɗagowa tayi tana kallon sama, cike da mamaki take waige-waige cikin kuka ta ce "meyasa ake ƙiran sunana, waye ne?..." wani haske taga ya bayyano a cikin hasken taji an fara kaɗa jita mai daɗin sauraro.. Ƴar Amana tsaya kallon wannan hasken take ga jitar da ake kaɗawa cikin lokaci ƙanƙani taga wata mata ta bayyano a cikin hasken tana riƙe da jita tana kaɗawa fuska ɗauke da murmushi... itama Ƴar Amana murmushin take ganin yanda matar take kaɗa jitar bata san lokacin da duk wata damuwa ya yaye mata ba, duk da bata san matar ba amma ganinta yasa hankalin ta kwanciya.. Matar zama tayi a yanda Ƴar Amana take zaune dai-dai lokacin da ta dakatar da kaɗa jitar, ta ce "Reemah kin san bama son ganin ki cikin damuwa, saboda ki faɗa mana me kike buƙata idan aiwatar wa ne zamu aiwatar miki idan kuma shawari ne nan ma zamu baki..." Reemah karkatar da kai tayi cikin nuna damuwa ta ce "a yanzu damuwa ta shine yanda zan yi Yaya Roshan ya karɓi soyayya ta, ina sonsa sosai..." Murmushi matar tayi sannan ta ce "Reemah kina son sanin wani abu? inda son samu ne bazamu barki kiyi Aure ba saboda wasu dalilai, kin buƙaci yin Aure kuma zamu bar ki kiyi amma baza mu bar ki kiyi abu ɗaya ba..." Ƴar Amana cikin tsoro da fargaba ta ce "meyasa to, dan Allah ku bar ni nayi Aure nima na kasance da mijina..." Matar ta ce "zamu bar ki kiyi amma da sharaɗi..." Ƴar Amana ta ce "meye sharaɗin?..." "Baza ki taɓa haihuwa ba..." A cewar matar idonta akan Reemah... Ƴar Amana ta ce "na yadda da hakan amma nima ina so ku taya ki shawo kan Yaya Roshan domin ina matuƙar ƙaunar shi..." Matar tayi murmushi ta ce "kar ki damu indai wannan ne amma sai mun ɓullo ta wani siga, sai kin ɓace wa ganin kowa..." Ƴar Amana ta ce "bangane mai kike nufi ba, taya kenam?..." Matar ta ce "zamu ɗauke ki zuwa duniyar mu, amma ba wai kin tafi na har abada ba, zamu dawo da ke da zaran Roshan ya kamu da soyayyar ki cikin ƙanƙanin lokaci, zaki na ganin kowa naki amma su ba halin su ganki, zasu nemeki ki rasa mu kuma bayyano wa Roshan da siffar ki ta cikin mafarki har ma a zahiri, zakina masa gizo har sai ya kamu da soyayyar ki sosai duk da mun san yana ji da ke..." Ƴar Amana cike da mamaki take bin matar da kallo a fili ta furta "Aljana za'a mayar ni?..." Matar ta ce "ko ba'a mayar ki aljana ba zaki fito kamar siffar aljanun domin babu wanda zai gan ki, idan kin yadda da haka to nan ne zaki magance matsalar ki..." Ƴar Amana ta ce "ban ƙi wannan ba amma damuwa ta shine bana so nayi nesa da Afaf..." Matar ta ce "baza kiyi nisa da ita ba, zaki na ganin ta a duk lokacin da kika so, amma ita bazata ganki ba..." Suna cikin tattaunawarsu suka fara jin motsin shugowar mutum domin yanzu dare yayi, lokacin kwanciyar Roshan yayi, shugowar sa kenam ya tarar falon wayam babu kowa, girgiza kai yayi domin a tunanin sa zai tarar da Reemah ne..." Ita kuwa Ƴar Amana miƙewa tsaye tayi tana faɗin "Yaya Roshan! Yaya Roshan Dan ALLAH inaso kayi tunani a kaina wallahi bazan wahalar da kai ba..." Matar kuwa tana zaune sai sakin murmushi take, Haka Roshan ya wuce bedroom ɗinsa bai ma san Reemah tana yi ba, Ƴar Amana da sauri ta juyo tana kallon matar, Matar ta ce "har mun aiwatar da aikin mu, yanzu wasan zai fara, duk waɗannan maganganun nakin Roshan bai san kina yi ba, ko ganin ki bazai iya yi ba balle ya ji mai kike faɗa, Ga wannan jitar yanzu shi kaɗai zai rinƙa jin kaɗa jitar ki, ki rinƙa fito masa a mafarki...." Ƴar Amana cike da mamaki ta ce "tayaya kenam?..." Murmushi matar tayi sannan ta ce "na barki lafiya..." daga nan ta ɓace ɓat... Ita kuwa Ƴar Amana room ɗin Roshan ta nufa da gudu tana zuwa ta samu har ya kulle ƙofar ɗakin, tsayawa tayi tana kallon ƙofar cikin jin takaici tana tunanin ko ta ƙonƙosa masa ne, hannu takai zata kifar da kanta a jikin ƙofa kwatsam tayi ciki zata faɗi sai da tasau wani ƙara, ta ɗago tana kallon ƙofar da ta ratso ba tare da an buɗe ba, kallon Roshan tayi wanda yake kan sallaya ya idar da sallar lafula zai kwanta, cike da mamaki ta koma waje ta hanyar ratsa jikin ƙofar sannan ta ƙara shugowa tana dudduba jikinta, tunani tayi da cewa "kenam zan iya ratsa jikin gini ma?..." kamar da wasa a hankali tazo wuce wa jikin bango taga ta ratsa sai ta bayyana ta waje still ta ƙara shugowa tana haka har ta yadda da cewa yanzu ta koma aljana, a bakin gado ta zauna idonta akan Roshan wanda ya sanya sleeping dress ya kwanta bayan yayi addu'a, Ita kuwa magana take masa amma sam baya jin ta bai ma san tana ɗakin ba, Bayan bacci ya ɗan fara ɗaukar sa can yaji wayar sa tana ringing, cikin gaga'ar bacci ya rarumo wayar tare da karawa a kulle, Ƴar Amana kuwa har wannan lokacin tana zaune a bakin gadon sa, Roshan jin muryar Abbah yasa ya buɗe ido tare da tashi zaune a zabure jin an faɗi mata magana kamar a mafarki, A ɗan ruɗe Roshan ya ce "Dad you said what?..." Daga ɓangaren Abbah kuwa cewa yayi "ka fito yanzu mun nemi Reemah mun rasa, kuma duk yanda ya kamata a duba a cikin gidan nan an dudduba bata nan..." Ƴar Amana duk taji abinda Abbah ya ce girgiza kai kawai tayi tare da sakin murmushi, bata ankara ba taji Roshan yana faɗin "whatttt? Shalele bata gida? ina zata fita taje kuma alhalin security suna nan..." ɗaga kansa yayi yana duba agogon bango yaga misalin ƙarfe 11 na dare, a rikice yake furta innalillahi wa inna'ilaihi raju'un ba shiri ya tashi a ruɗe ya fice daga ɗakin kai tsaye falo ya nufa zai fita waje, ita Reemah haka take binsa a baya, shiga mota yayi itama ta shige a gurguje yabar part ɗinsa... A falo kowa ya fita ana tsattsaye ana jimamin rashin ganin Reemah, mai martaba ne kawai baya nan ya koma ƙasar jidder shi da Aunty Maimuna, sai Aunty A'isha da Ummy aka bari su sai bayan bikin Uncle Deen, Aunty A'isha ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, itama Baiwar ALLAH ta fito ita da mahaifiyarta cikin damuwa, duk sauran mutanen gidan fitowa sukayi Minal da Rukky da kuma Pinky wanda sai bayan biki kowacce zata koma ɗakin mijinta, Hajiya Kilishi da Ammy suma zama ya ƙaurace musu, Abbah kuwa sai kai kawo yake a falon yaƙi tsayuwa wuri ɗaya, shima Razhdeen ya fito wanda Abbah ne ya tashe shi shima, suna cikin wannan halin sai ga Roshan ya shigo a ruɗe yana faɗin "ina taje Abbah?..." Abbah ya ce "duk na tara sojojin gidan nan sun sanar mun cewa babu wacce tayi hanyar get, kuma an duba CCT camera gidan gaba ɗaya sai muka ga part ɗinka ta nufa kuma ba'a ga dawowar ta ba, Roshan wai kana nufin kace Reemah bata tare da kai?..." Cike da mamaki Roshan ya ce "daman Shalele bata bar part ɗina ba? but nasan taje amma na barta a zaune a falo daga baya dana koma na tarar bata nan, a tunani na ta dawo...." Abbah ya ce "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un me ake nufi kenam?..." Roshan buga goshinsa yayi da hannu cikin damuwa, ya ce "ya kamata mu duba ko ina na gidan nasan tana cikin gidan nan, tinda sojoji sun sanar cewa babu wanda ya fita..." Abbah ya ce "gidan nan ko part ɗin ka? bata fito daga part ɗinka ba don haka duk can zamu je mu dubo ta...." Pinky ta ce "kar muje ta shiga ruwan swimming pool ta kasa fitowa ta mutu a ciki..." A zabure Abbah ya juyo tare da danƙwalon Pinky yana faɗin "Allah ya tsine wa bakin ki nan da baya faɗan alkhairi...." Pinky ƙame bakinta tayi tare da sunkuyar da kanta... Abbah ya ce "me kuke jira ne kuzo mu tafi..." Duk suka nufi hanyar waje shima Razhdeen yana jan ƙafa wanda bacci yaci idonsa haka ya bi bayan su... Ƴar Amana kuwa tana tsaye ba abinda take sai dariya tana faɗin "ashe dai kuna sona, hahaha na hana kowa bacci woo ni shalele, kaima Yaya Roshan dole ka damu da ni tinda ka nuna bazaka Aure ni ba to kuwa yau ba bacci wollah..." ta gama yin didimar ta a falo daga bisani ta wuce room ɗinta da gudu tana faɗin "wayyo Afaf ɗina inason ganinki..." tana shiga room ɗin ta tarar da Biju Mama sai shan baccin ta take ga fida a bakin ta yanda ta riƙe sosai idan ta ɗan motsa sai ta fara zuƙan fitar ta wanda yake cike da madara a ciki.... Ƴar Amana haurawa saman gado tayi cikin farin cikin ganin Afaf, tasa hannu tana shafa sumar kanta tana faɗin "Biju Mama kinyi musu wayo ke kina shan baccin ki, su kuma suna can yawon nema na, Biju Mama ina sonki sosai kuma inason Yaya Roshan idan ba haka nayi ba Yaya Roshan bazai daina nuna cewa baya sona ba...." Bayan su Abbah sun je part ɗin Roshan kai tsaye ɗakin CCT camera na part ɗin suka shiga, suna duba yanda Reemah ta shiga, abun mamaki sun ga shugowar ta part ɗin har ta shiga falon gidan, sun ji duk tattaunawar da suka yi da Roshan har Roshan ya fice ya barta a falon tana kuka daga nan sai CCT camera ta nuno duhu, ba'a ganin komai sai duhu kuma ba magana, sai da lokacin da Roshan ya shigo kafin Camera ta dawo normal, sai kuma aka ga babu Reemah sai Roshan da ya nufi bedroom ɗinsa, abun ya bawa kowa mamaki...... Typing ✍️ Asmeetah writer *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 81 to 85 A wannan ranar haka duk mutanen gidan suka zauna babu wacce ta rintsa, sai Afaf da Ƴar tinny, Most especially Roshan da ko wurin zama bai samu ya zauna ba, yana kai kawo zirga-zirga ya fita ya shigo da haka ya wayi gari domin yanda kasan an wanke masa jin bacci haka ya tsinci kansa, washe gari kowa ya wuni cikin jimamin ɓatar Ƴar Amana... Abbah ya hana a sanar wa Mai martaba halin da ake ciki domin zai tashi hankalinsa ba ƙarami ba, da haka har akayi sati guda, duk wani binciken da ya kamata ayi anyi amma ko labarin ta babu.. Ita kuwa Ƴar Amana tana gidan sai dai tabi kowa da kallo, itama ta tashi hankalin ta ganin kowa na gidan cikin tashin hankali, hatta abinci wasu da ƙer suke iya ci, wasu kuma basa iya cin abinci Roshan yana daga cikin waɗanda basa sauraron abincin sai Abbah da mahaifiyar Reemah, Baiwar ALLAH itama bata iya sa abinci a bakinta sai da taimakon Razhdeen domin abu kamar wasa ya zama gaske har tsawon sati guda babu Ƴar Amana babu labarin ta, kowa yana cikin zullimin abinda ya faru domin ba ƙaramin mamaki ya bawa mutanen gidan ba ganin lokaci guda Ƴar Amana ta ɓace kuma ba'a ga lokacin tafiyar ta ba... Roshan kullum a cikin tunani yake ganin daga falonsa babu yanda Reemah taje kuma abun mamaki sai da aka zo daidai tafiyar ta Camera ta lalace, yana part ɗinsa zaune kan kujerar falo yayi tagumi ga idanuwansa yanda suka yi jajawur tsawon lokutan nan ko bacci baya iya yi gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, ita kuwa Ƴar Amana tana zaune gefensa ta zuba masa ido gaba ɗaya taji tausayinsa ya kamata, a fili take furta "Yaya Roshan meyasa kake da zurfin ciki? nasan kuma a nine kake wannan zurfin ciki! kana sona amma ka kasa bayyanar wa meyasa? ni ina sonka meyasa bazaka fito muyi Aure ba, gashi yanzu ka shiga damuwa saboda ni, ni kuma lokacin bayyanata bai yi ba har sai ka amince da Aure na..." Duk waɗannan maganganun da take faɗi Roshan bai ji ba, har ɗora hannunta tayi kan kafaɗarsa amma bai ji ba, murmushi tayi sannan ta ce "bari nayi maka abinda zai nuna ina tare da kai..." Fuskarta ta kawo sai tin nasa fuskar ta fara hura masa iskar bakinta, Roshan jin yanda iska take shigar sa yasa ya lumshe ido ya fara motsi da lips ɗinsa a hankali yake furta "Shalele nah a tunaninki bana sonki ne yasa kika tafi kika bar mu? har cikin zuciyata nake ƙaunar ki tin ba yau ba, na fara dakon soyayyar ki ne tin lokacin da kika bayyana a matsayin Ƴa ga Uncle na wato mai martaba, domin ke na fara zaɓa a matsayin masoyiya ta tin kina cikin mahaifiyar ki, daga lokacin da aka haifo ki naci alwashin zan sanar akan cewa nayi babban kamu na matar Aure na, a washe gari kuma sai labari yasha banban na cewa an sace ki, tin daga lokacin na fara zurfin cikin soyayyar ki ban sanar wa kowa ba, kuma har yanzu na kasa sanar da hakan alhalin kece zaɓi na, kin riga kowa shiga cikin zuciyata Reemah, ke babbar Allurar cikin ruwa ne wanda na daɗe da kamawa, ina sonki with all my heart Reemah, idan ina tare da ke wani irin farin ciki ne yake wanzuwar mun, taya zan bayyanar da hakan Reemah? Shalele idan gangan jikin ki baya tare da ni nasan ruhin ki yana tare da ni, domin zuciyata ta ki ce haka kema zuciyar ki an halitto ta ne saboda Roshan, dan ALLAH Shalele ki dawo gare ni, ina cikin tashin hankali Shalele...." Duk waɗannan maganganun idonsa a lumshe suke, Ƴar Amana kuwa tintinin hawaye duk ya wanke mata fuska, kuka take sosai jin abinda Roshan ke faɗi, itama haka ta fara mayar masa da martani da cewa "Yayana meyasa kake azabtar da zuciyar ka akan abinda bai kai ayi masa zurfin ciki ba, ina sonka kaima ka fito fili ka nuna hakan Yaya Roshan, haƙiƙannin gaskiya soyayyata ta gaskiya ce tinda tin kafin na bayyano zuwa duniya ka ke nuna mun ƙauna, dan ALLAH Yaya Roshan ka daina wahalar mana da zuciyoyi Please, zuciyata tana cutuwa da rashin samun soyayyar ka haka taka zuciyar tana cutuwa da rashin furta a wanda kake ƙauna kalmar soyayya, Yaya Roshan......" Gani tayi ya juyo yanda take zaune gefensa sun haɗa ido, sai da ƙirjinta ya buga ganin yanda suka haɗa ido suna kallon juna, Ji tayi ya furta "shin ina zan samo ki Shalele, ina kika shiga dan ALLAH ki bayyana mun kan ki ina buƙatar ki a kusa da ni, ko letter ki aiko mun nasan a yanda kike Please..." Ƴar Amana sauƙe numfashi tayi ganin ashe ganinsa ne yazo dai-dai da yanda take.... Roshan yana cikin wannan halin sai ga Razhdeen ya shigo da sallama a bakinsa, samun wuri yayi a gefen Roshan yakai mazaunen sa zai zauna Ƴar Amana tayi saurin matsawa gefe domin a yanda take zaune shima yake shirin zama, Ƴar Amana idonta akan Razhdeen ta ce "tab haba Uncle Deen ka zauna mun akai ai sai dai lahira direct..." Razhdeen ɗora hannunsa yayi akan lap ɗin Roshan yana ambatar sunansa cikin taya shi jimami ya ce "My twins meyasa bazaka kwantar da hankalin ka ba ne? Reemah zata dawo nasan bazata taɓa ɓata ba, yarinyar da tin tana jaririya take ɓacewa mutane dan yanzu ba'a ganta ba ai babu wanda zai yi tunanin bazata dawo ba, just ka kwantar da hankalin ka bana son ciwon ka nan ya motsa please...." Roshan yana zubda hawaye ya ce "haba my man! why bazan damu ba, yarinyar nan part ɗin nan tazo daga nan ba'a ga fitar ta ba, an duba cikin ruwa bata nan duk wani lungu da saƙo an dudduba amma bata nan, kuma tana cikin gidan nan domin sojoji sun tabbatar da bata fita ba, na rasa gane mai hakan yake nufi..." Razhdeen ya ce "indai a cikin gidan nan take to za'a ganta, kodai ɓuya tayi ne?..." Roshan ya ce "ɓuya kuma? ba ci ba sha tsawon sati guda?..." Razhdeen hura iskar bakin sa yayi tare da faɗin "ohh my God, Sarah where are you..." Ƴar Amana tana zaune ita kuwa tana jin duk tattaunawar da suke, turo baki tayi tana kallon Razhdeen ta ce "Ni banga alamar nuna damuwa a fuskar ka ba Uncle Deen, saboda ka samu wacce kake muradi zaɓin ranka ko? to shikenam sai ka bar wanda ya rasa masoyiyarsa ya yi kewar ta sosai, ya nuna damuwa matuƙa saboda anan ne zan gane cewa yana matuƙar ƙaunata..." Razhdeen ganin yanda Roshan ya koma kamar ba shi ba yasa shi faɗin "twins meyasa ka damu haka akan ta?..." Roshan juyo wa yayi yana kallon Razhdeen daga bisani ya ce "bcox I love her, I really loved her and I want her to be my wife forever..." Razhdeen cije lips ɗinsa na ƙasi yayi sannan ya ce "okay amma meyasa ka kasa sanar wa Abbah cewa kana sonta da ya tambaye ka, sai ka nuna cewa bazaka ƙara yin Aure ba..." Roshan ya ce "ita ce abokiyar rayuwata ta ƙarshe, ita ce farkon masoyiyata sannan ita ce last, akwai abinda yake damuna a raina shiyasa na kasa sanar da hakan, shiyasa duk wanda ya tambaye ni nake bashi amsar cewa bazan ƙara yin Aure ba..." Jinjina kai Razhdeen yayi sannan ya ce "it's okay komai zai zo cikin sauƙi Insha Allahu, sannan itama zata bayyana bada jumawa ba, nima fatana shine Allah ya yaye maka duk wata ƙuncin zuciya, ka kwantar da hankalin ka Please my twins..." Roshan jinjina kai yayi idonsa akan Razhdeen ya ce "shikenam my man Insha Allahu zan kwantar da hankali na..." Razhdeen ya ce "proud of you my twins, sannan Abbah ya bada umarnin cewa ka koma part ɗinsa da zama, baya son zamanka anan kai kaɗai sannan acan zaka fi samun ko wace kulawa da kuma ɗebe kewa..." Roshan jinjina kai yayi sannan ya ce "tinda umarni ne zan koma yanzu ma..." Razhdeen ya ce "muje na taya ka ɗaukar kayan ka wanda zakayi amfani da su..." Murmushi Roshan yayi sannan suka tashi a tare kai tsaye bedroom suka nufa, haka suka ɗauko Akwatuna suka fito, Ƴar Amana kuwa tana biye da su sai dai kawai ta bisu da kallo..... Bayan kwana biyu Roshan yana kwance akan katafaren gadonsa dake yanzu ya dawo ainihin ɗakinsa dake part ɗin Abbah, yana shan baccin safen sa dake yau ranar weekend ne, a cikin bacci ya fara jin sautin jita, ɗan buɗe idonsa yayi yana jiyo sautin miƙewa yayi zaune yana bin bakin ƙofa da kallo daga bisani ya sauƙar da ƙafafunsa ƙasin carpet ya miƙe tsaye ya nufi hanyar waje, hannu yasa ya buɗe ƙofar ɗakin wani irin sanyi ne ya fara hura shi da ƙarfin gaske, haka ya fice a ɗakin yana fita yaga ya bayyana a cikin wani hayaƙi kamar wanda yake cikin gajimare, babu kowa babu komai sai gajimare ga yanda ake hura iska kamar zai ɗaga shi sama, wani irin haɗiyar yawu Roshan yayi cike da tsoro da fargaba yake bin wurin da kallo yanda kasan barza'u, yana juya bayansa yaga ɗakinsa ya ɓace babu komai sai hayaƙi, kallon ƙasa yayi yaga akan gajimare yake tsaye, a wannan lokacin hankalin sa ba ƙaramin tashi yayi ba, haka jikinsa yake ɓari ga sanyi ga tsoro, lokaci guda yaji an dakatar da kaɗa jitar sai wurin yayi tsit, ta bayansa ya ji an furta "Yaya Roshan..." Da sauri ya waiwaya ganin Ƴar Amana riƙe da jita yasa shi ja da baya yana zazzaro ido, Ta kuma cewa "Yaya Roshan ga Shalelen ka shin baza kayi farin ciki ba ne?..." Roshan binta yake da idanuwansa waɗanda suka shashshanye kamar mai jin bacci haka lips ɗinsa yake kakkarwa a hankali ya furta "Shalele..." Ƴar Amana tana sanye da farar doguwar riga har ƙasi babu takalmi tana riƙe da jitar ta, wanda itama akan gajimaren take. Roshan ne ya matso dab da ita ga hawaye yanda yake gangaro masa haka yayi saurin rungumota jikinsa yana kuka yana faɗin "Shalele meyasa zaki tafi ki barni cikin ƙunci? so kike zuciyata ta buga? so kike kema na rasa ki? idan har na rasa ki na tabbata rayuwata bata da wani amfani mutuwa nima zanyi...." Sai da ya gama rungumar ta bayan ya gama sambatu yana hawaye ya ɗago da kansa ya riƙo gefe da gefen fuskarta da hannayensa biyu ya ɗora goshinsa akan nata kamar zasu haɗe baki ya ce "Shalele meyasa zaki tafi ki bar masoyin mijinki? kinsan irin damuwar da nake ciki kuwa? Shalele nayi miki alƙawarin zan Aure ki, zamu yi Aure Shalele..." Itama Ƴar Amana kuka take ta ce "Yaya Roshan ni ɗin taka ce, sannan kaima nawa ne, ina matuƙar ƙaunar ka, sannan ina so mu kasance a tare har ƙarshen rayuwar mu..." Roshan ya ce "to kin san da hakan meyasa zaki tafi ki bar Ni?..." Ƴar Amana ta ce "Yaya Roshan ka kasa sanar cewa kana Sona zaka Aure ni, bazan iya kasance ni ɗaya ba tare da kai ba Yayana, kayi zurfin ciki ka kasa sanar wa, bazan iya ganin wannan takaicin ba hakan yasa na ƙaurace wa kowa..." Roshan ya ce "Shalele yanzu ne dai-dai lokacin da kowa zai fahimci yanda nake ƙaunar ki, yanzu ne dai-dai lokacin da zan mallake ki a mazannin matata ta Aure, yanzu ne zan yi Auren da zan kasance cikin farin ciki na har abada, Shalele you are my life..." Itama Ƴar Amana kuka take sosai goshinsu a haɗe ta ce "You are my life Yayanaaa..." Wani irin haske ne ya fara bayyana a jikin Ƴar Amana, lokacin ganin juna ya ƙare daman an bata lokaci ne wanda zata kasance da Roshan, A ruɗe ta ɗago da kanta tana kallon Roshan gaba ɗaya idanuwansu sun yi jawur tsabar kuka, a rikice take faɗin "Yayana lokacin tafiya ta yayi, Yaya Roshan zan tafi..." Roshan riƙe ta yayi sosai yana faɗin "Babu yanda zaki je Shalele, bazan ƙara yin nesa da ke ba, bazan barki ki tafi ba..." Ƴar Amana sama ta fara yi haske yana shirin rufe ta gaba ɗaya tana kuka tana faɗin "Yaya Roshan! Yaya Roshan zan dawo gare ka..." Haka shima Roshan ya riƙe hannunta yana jawo ta a yayin da haske yake ɗauke ta sama har ta zama haske gaba ɗaya lokaci guda ta ɓace... Wani irin ihu Roshan yayi tare da ambatar sunan ta "Reeeeemmaaaahhh...." Dai-dai lokacin da ya farka daga bacci a ruɗe ya tashi zaune yana fitar da numfashi da ƙarfi-ƙarfi, gaba ɗaya ya haɗa gumi haka zuciyar sa take bugawa fatt! fattt! fattt!!!. A hankali ya ke furta "Shalele! Shalele meyasa kike tafiya ki barni, yanzun ma kin tafi ko? my Shalele I want you inside me...." Daƙer ya dawo hayyacinsa haka yasa hannu ya dafe goshin sa domin kansa ba ƙaramin ciwo yake ba, Ga fuskar sa yanda aka tsara masa kwalliya kamar irin matan ƙauyen nan fuskar nan tayi fari tsabar yawan pawder dake farar powder ce sannan aka ɗauki red jan baki aka guggurza masa akan lip sai bakin yayi jawur, aka ɗauki baƙin kwalli aka zana masa gira, aka goga masa aishado mai colour red a saman idanuwansa, gaba ɗaya an cakurkuɗa masa fuska da makeUp Dai-dai lokacin aka fara knocking, murya ciki-ciki ya amsa da "Yes..." turo ƙofar aka yi sai ga Ummy (uwar masu gida) ta shigo da tumbin cikin ta wanda ya girma, ƙarasa shiga tayi ta tsaya tare da faɗin "good morning Masoyi..." Roshan tashi yayi ya zauna fuska ɗauke da murmushi ya amsa mata da cewa "morning to you Maman baby..." Ummy sake baki tayi tana kallon Roshan wanda yanzu tayi ido huɗu da shi, ai bata san lokacin da ta tintsire da dariya ba, dariya take kamar zata shiɗe har da kama ciki idonta akan Roshan... Roshan cike da mamaki ya tsaya kallon ta gaba ɗaya ya rasa akan me take wannan uban dariyan, ganin dariyar ya ƙi ƙarewa ne yasa shi faɗin "wait! wai akan me kike dariya? sannan me yake tafe da ke?.." Ummy daƙer ta dakatar da dariyar ta ta ce "Yaya Roshan, Yaya Roshan...." nan ma ta ƙara tintsire wa da dariya, daƙer ta samu damar cewa "Yaya Roshan wai kaje ayi breakfast yanzu..." ta ƙara tintsire wa da dariya, Shi dai girgiza kai yayi ya tashi ya bi ta gefenta ya ce "mahaukaciya..." ya fice a ɗakin, ita kuwa sai da ta ƙare yin dariyar ta mai isar wa kafin ta fice itama tana mamakin ganin kwalliya a fuskar Roshan, sai yanzu kuma abun yake ɗaure mata kai, da wannan tunanin ta sauƙa falo... Roshan kuwa yana sauƙa falo ya tarar da Razhdeen yana ɗauke da Biju Mama akan cinyarsa sai kuma Baiwar ALLAH a gefensa suna shan soyayya kamar yanda suka saba kullum domin yanzu basa ɗau tsawon mintuna basu haɗu ba, bacci ne yake raba su, baccin ma sai kowa yayi bacci kafin su ma su kama makoncinsu amma ba'a son ransu ba domin in da son samu ne a ce makoncinsu ɗaya. Roshan tsaya kallon su yayi ta bayan kujerar da suke ya jinjina kai tare da faɗin "sannun ku masoya ku koda yaushe bakwa ɗan rabewa ne?..." Duk juyowa suka yi da murmushi akan fuskokin su haɗa ido da Roshan yasa ƙirjin Baiwar ALLAH bugawa domin ba ƙaramin tsorita tayi ba tayi zaton Aljan ne ya fito musu ganin wani irin kwalliya na ƴan ƙauye a fuskarsa, jan bakin duk ya zazzaɓo ƙasin lips ga yasha jan aishado da girar sa har da su barbaɗa kumatu 🤣. Baiwar Allah ruƙo hannun Razhdeen tayi ta ƙanƙame ido a zazzare tana kallon Roshan, wanda shima Razhdeen idonsa akan Roshan ya ce "my twins meye haka kuma?..." Baiwar Allah da ta fahimci Roshan ne bata san lokacin da dariya ya ƙwato mata ba, haka take dariya kamar ranta zai fita tana nuna Roshan da yatsa tare da faɗin "wai daman Yaya Roshan?..." A wannan lokacin Roshan ba ƙaramin ƙuluwa yayi ba rai a haɗe yake bin Baiwar ALLAH da kallo ganin dariyar da take masa ga ya baro Ummy itama, Razhdeen kasa cewa komai yayi sai ido da yake bin Roshan da shi.. Ƴar tinny ce itama ta tsaya a gaban Roshan ta zuba masa ido ta ce "Yaya Roshan ka koma mace ne?..." Wani irin kallo ya watsa mata, Ƴar tinny kuwa dariya ta tintsire da shi tare da barin wurin da gudu... Sai ga Minal itama ta fito tana riƙe da hannun yaronta ganin Roshan yasa ta ƙamewa a wurin, buɗe baki tayi ta ce "woooowww yau ɗin comedy za'ayi mana a gidan ne, kaii wayyo nayi niyyar fita unguwa yau amma na fasa saboda kar ayi banda ni...." Itama ta kwashe da dariya, sai ga Pinky da Rukky su ma sun fito yin breakfast, suna ganin halin da Roshan ya kasance suma ba magana sai dariya, gaba ɗaya falon ya kaure da dariyar su, Baiwar Allah da Ummy da kuma Minal da Pinky da Rukky har da Ƴar tinny wacce ta dawo daga yin gulma taje ta sanar wa Mommynta cewa Yaya Roshan ya zama Dodo duk dariya suke masa ba ƙaƙƙautawa, sai Razhdeen shima wanda yake zaune yana ƙunshe da dariyar sa wanda bai bari ya fito fili ba, Ammy wacce ta fito daga kitchen tana jera kayan breakfast a dinning table jin dariya yayi yawa a falo yasa itama ta fito tana faɗin "wai me yake faruwa ne?.." haɗa ido tayi da Roshan cike da mamaki ta ce "wannan ɗin waye?..." Roshan abun mamaki ya bashi jin itama Ammy abinda ta furta.. Hajiya Kilishi sauƙowa tayi daga upstairs tana son ganin meke faruwa ne domin Ƴar tinny ta sanar mata cewa Roshan ya zama Dodo, tana sauƙowa ganin Roshan yasa ta zaro ido cikin rashin sanin abun cewa yasa ta faɗin "AAAA'UZUBILLAHI MINASHAIƊANIN RAJIIIINN, INNA ASHANA MINAL BALBALINA...." Da iya ƙarfinta ta furta hakan cikin tsoro, Jin abinda Hajiya Kilishi ta furta ne yasa itama aka fara kwashe mata da dariya, hatta Ammy sai da ta ɗan dara. Roshan ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba domin ya dudduba jikinsa bai ga abun dariya ba, amma haka ake ta masa dariya, cikin fushi da ɗaga murya ya darara tsawa tare da faɗin "Ya Isa haka! wani irin rainin hankali da wayo ne wannan, kun sakani a gaba kuna mun dariya shin na haukace ne? Ni mahaukaci ne ko kun ganni ina tsine-tsine a bola ne?..." Ummy uwar masu gida ce ta buɗi baki zata yi magana yayi saurin katse ta da cewa "bana son abinda zaki ce duk ba ke kika fara mun kallon mahaukaci ba, meye zaki ce mun?..." Pinky ƙare shi da kallo tayi taga yana masifar ma abun dariya bata san lokacin da ta ƙara tintsire wa da dariya, cikin zafin rai Roshan ya ɗauki pillow ya wurga mata, Baiwar Allah girgiza kai tayi cike da mamakin taya kwalliya ta bayyana a fuskar Roshan alhalin bai san da kwalliyar ba, tunani tayi gwara ta sanar masa gaskiyar lamarin tinda ta fahimci bai san da shi ba, buɗe baki tayi ta ce "Yaya R...." ɗaga mata hannu yayi ya ce "ke ma ki dakata mun haka? meyasa tinda na fito baki yi magana ba sai da kika gama mun kallon mahaukaci kafin zaki samu bakin yin magana..." MINAL ta ce "kaga Yaya Roshan dan Allah kayi haƙuri....." tana kaiwa nan itama ta ƙara tintsire wa da dariya... Roshan har ya buɗe baki zai yi magana suka yi motsin Abbah wanda ya shigo falo yanzu, yana faɗin "lafiya kuwa nake jin hayaniya?..." Kowa ya yi tsumu da bakinsa sai Roshan wanda ya fuskanci Abbah tare da faɗin "Abbah yaran gidan nan sun haukace, suna buƙatar zuwa sakatiri..." Abbah dai ya kasa sauƙar da idonsa akan Roshan sai baki da ya sake yana jinjina kai ya ce "Ahhh gaskiya a cikin kai da su za'a tantance mahaukacin da za'a kai shi sakatiri..." Roshan ya ce "Abbah saboda iskanci sun gama rainani ni suke ɗauka mahaukaci tunda na fito suke mun dariya, meye a jikina?..." Abbah ya ce "ai dole suyi maka dariya irin wannan shirmen da ka aikata, kai ɗan daudu ne?..." Roshan cike da mamaki yake bin Abbah da kallo a ƙasin harshen sa ya furta "bayan an ƙira ni da mahaukaci sannan kuma du ɗan daudu? daudu kuma?..." Ammy ce ta riƙo hannun Roshan tana faɗin "kazo kuyi breakfast Roshan..." Zame hannunsa yayi yana girgiza tare da faɗin "sai an sanar mun meye abun daudancin da nayi, shin an ganni ina ɗaure da zani ne ko ɗan kwali ko kuma kwalliya ku ka gani a fuskata..." Abbah ya ce "au baka ma san da abun a fuskar ta ba?..." Roshan fara shafa fuskar sa ya yi, sai ga Baiwar ALLAH wacce ta koma ɗaki ta ɗauko madubi tana zuwa ta saita masa, Roshan kallon cikin madubin yayi a ruɗe ya zaro ido waje yana furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allahumma ajurni fi musibati wa akhlifli khairan minha, taya hakan zata faru kuma?..." Ummy ce ta ƙara kwashe wa da dariya har da tafa hannu, cikin nuna fushi Roshan ya juya yana kallon ta tare da faɗin "nasan ba mai mun wannan aiki sai ke, meyasa kika mun haka?..." Ummy ta ce "ni kuma? taya zan maka haka Yaya Roshan..." Tsawa ya darara mata wanda tin da yake bai taɓa ɗaga murya wa Ummy ba sai yau, "Ƙarya kike kin shiga kin same ni ina bacci shine zaki mun wannan shirmen, shugowar ki na biyu kika fara mun dariya bayan na farka, kin kyau kin ɓata mun fuska hankalin ki ya kwanta, bazan ƙara shiga shirgin ki ba balle ki sake mun wannan haukar..." Yana kaiwa nan ya haura upstairs saman ɗakin sa, Ummy lokaci guda idanuwanta suka kaɗa sukayi ja, hawaye ne suka fara gangaro mata. Baiwar Allah ta dafa kafaɗar ta ta ce "dilla kar kiyi kuka, kin san Yaya Roshan bashida hayaniya yau ne ransa yayi matuƙar ɓaci shiyasa amma zaki ga zuwa anjuma zai kula ki..." Ummy tana kuka ta ce "saboda ni ya raina shine zai je nina masa kwalliya har yana mun tsawa? babu abinda na tsana illa mutum ya mun tsawa amma ba komai ..." Hajiya Kilishi ta ce "to ke meyasa zaki masa kwalliyar?..." Ummy cikin ɓacin rai ta ce "wai wa ya ce muku nina masa? tinda nake a cikin gidan nan na taɓa masa makamancin irin haka? shima hasashe kawai yayi ya ce ni ce, Amma sai Allah ya saka mun?..." Abbah ya ce "ya isa haka kuje ku zauna akan dinning kowa ya yi breakfast..." Ummy a zuciye ta nufi upstairs yanda zai kaita room ɗinsu tana faɗin "Ni dai bazan ci ba..." Abbah ya ce "Uwar masu gida ki zo ku zauna ku ci abinci...." Ta juyo tana faɗin "Abbah bazan iya cin komai a halin yanzu ba, zuciya ta tafasa take..." tana kaiwa nan ta haura upstairs, Su kuwa duk hallaruwa sukayi akan dinning sai da Abbah yayi musu faɗa akan dariyar da suka yi wa Roshan... Roshan yana zuwa room ɗinsa kai tsaye bathroom ya shige, ya tsaya a wurin sink yana kallon kansa a cikin madubi ga yanda yake ta huci, ruwa ya kunna ya haɗa da sabulu ya fara wanke fuskar sa, Ƴar Amana ce itama ta tsaya a gefensa tana murmushi ta ce "Allah sarki masoyi maimakon kayi farin ciki sai kuma ka shigo a cikin ƙunci? kar ka damu da abinda akayi maka ni ina tare da kai, kuma zan cigaba da sanya ka cikin Dawwamammiyar farin ciki mai ɗorewa har abada...." Zuwa tayi ta tsaya ta bayansa sannan ya zura hannayenta ta gaba ta rungume shi sosai a jikin ta tare da kwantar da kanta akan bayansa.. Roshan wani irin yarrr yaji a jikinsa, tsinkar jikinsa ne yake tashi lokaci guda ya tsinci kansa a cikin wani hali ga yanda sanyi yake ratsa shi, Lumshe idonsa yayi a hankali yake furta "me yake faruwa da ni ne?..." Ita kuwa hannunta ta sa a cikin rigar sa tana shafa jikinsa a hankali lips ɗinta na motsi haka take furta "Yaya Roshan ina matuƙar ƙaunar ka, inasonka sosai da sosai har cikin zuciyata nake jin ka, bazan iya misalta yanda nake tsananin ƙaunar ka ba...." Gaba ɗaya jikinsa mutuwa yayi babu wani sukuni, haka yake ɗebo ruwa yana watsawa akan fuskar sa har sai da ta koma normal, Lumshe ido yayi yana sauƙe numfashi daga bisani ya buɗe su a hankali idonsa ne ya sauƙa akan mirror wanda ya hango mace a tsaye ta bayansa kuma kamar fuskar Reemah ya gani, tana tsaye sai zuba masa murmushi take ta goga hannayenta akan ƙirji, bayan ta gama rungumar sa shine ta bayyana masa kanta a cikin madubi, Zaro ido waje Roshan yayi a ruɗe ya waiga baya da sauri ya ga wurin wayam ba kowa, maida idonsa yayi cikin madubin nan ma ta ɓace wa ganinsa, haka yake sakin numfashi ya ɗora hannunsa akan goshi yana faɗin "Oh my God! Reemah where are you, ki daina fito mun a mafarki ko gizo i just want to see you actual not your spirit please I beg you....." Gaba ɗaya ya fita hayyacinsa lokaci guda, haka ya fara jan ƙafa a hankali ya fice daga toilet, yana fita ɗagowar da zai yi yayi ido huɗu da Ƴar Amana zaune akan kujerar mirror tana facing ɗinsa, haka take ta sakin murmushi idonta akan sa, shima sake baki yayi yana kallon ta, a hankali ya sau murmushi tare da faɗin "kin dawo gare ni Shalele? nagode! nagode!! nagode!!!..." ya nufi wurin ta da gudu yana faɗin "Nagode..." yana zuwa yasa hannu zai rungume ta sai yaji ya rungumi iska, tinin ta ɓace masa, ganin ta ɓace yasa shi lumshe idonsa da ƙarfi cikin takaici, bai san lokacin da ya fara cakurkuɗa sumar kansa ya fara ihu, duk abubuwan da suke kan mirror haka yasa hannu ya faɗo da su, shima kansa mirror haka yasa hannu ya doko shi madubin ya dagargaje ihu yake bana wasa ba, Ammy wacce lokacin ta iso bakin ƙofar sa da trey ɗin kayan abinci a hannun ta cike da tsoro ta tsaya tana jin yanda Roshan yake ta ihu, tana cikin wannan hali na tsoro sai ga su Abbah da Razhdeen da sauran ƴan gidan jin ihun Roshan ya karaɗe gidan, Abbah yana zuwa ya tura ƙofar ta buɗe a hanzarce suka shiga ciki, suka tarar da shi a durƙushe ya kifar da kansa ƙasin carpet, hannayensa a cikin sumar kansa, Abbah yana zuwa shima ya durƙusa tare da sa hannu ya jawo shi jikinsa yana faɗin "Look Roshan me yake faruwa da kai ne haka? ka sanar mun idan abun na magani ne sai mu nema maka..." Ɗagowa yayi da jajayen idanuwan sa yana kuka ya ce "Abbah! Abbah magani na ɗaya ne shine Reemah ta dawo gare ni, ina buƙatar ta a kusa da ni, meyasa zata rinƙa fito mun a spirit, ina son ganinta a zahiri, tana cikin ɗakin nan ku gaya mata ta fito, Abbah ka gaya mata mana..." Abbah rungumar sa yayi sosai yana rarrashin sa, Roshan sake ganin Ƴar Amana yayi a zaune a bakin gado itama sai kukan take tana son dawowa yanda take a zahiri amma sai dai ba halin yin haka domin akwai lokacin da aka yanka mata.. Roshan a ruɗe ya fara nuna Ƴar Amana da yatsa yana faɗin "Abbah gata can ku ce mata da dawo, bana son ta ƙara tafiya ta barni, kuka take Abbah ku ce ta daina tana taɓa mun zuciya ta, dan Allah Abbah...." Abbah kuwa girgiza kai yake yana faɗin "Roshan ya haukace da gaske, Roshan ɗina ya haukace, ƙwaƙwalwarsa ta taɓu ya zan yi..." Razhdeen shima durƙusawa yayi a gabansa yana ambaton sunan sa "twins kayi haƙuri zata dawo, kana ta cewa gana nan kuma mu bama ganin komai, gizo kawai take maka..." Roshan ne yayi saurin katse shi da cewa "Ya zaka ce gizo take mun alhalin gana nan ina ganinta ido da ido, itama kukan take..." Ammy durƙusawa tayi tana tofa masa Addu'o'i... Hajiya Kilishi itama tana nan har da hawayenta tsabar tausayinsa da ya kamata tana riƙe da yaron Roshan wanda yayi wayo yanzu mai sunan Mai martaba wato Abubakar Sadeeq inkiya kuwa (Ra'ees).... Baiwar Allah itama kuka take domin halin da Roshan yake ciki dole zai sa kowa hawaye tana ɗauke da Afaf ɗinta... Minal da Pinky da Rukky suma kukan suke, Ata bakin ƙofa kuwa Ummy ce itama tazo jin ihun Roshan, itama kukan take a cikin ranta take faɗin "meyake damunka Yaya Roshan, haƙiƙa yanzu baka cikin hayyacinka dole sai ana maka uzuri, saboda haka nayi maka uzuri Yaya Roshan...." Roshan a zabure ya bar jikin Abbah ya nufi yanda Ƴar Amana take ya riƙo ƙafar ta yana faɗin "Abbah ya kamo ta wallahi baza ki sake ɓace mun ba, na riƙe ta sosai ku nemo mun igiya na ɗaure ƙafarta, ku riƙe mun ita kar ta tafi..." Ƴar Amana itama kuka take sosai tasa hannu ta tallafo fuskar sa tana furta "Yaya Roshan ka kwantar da hankalin ka zan dawo wallahi..." A tsawace Roshan ya ce "bazan kwantar da hankali na, kina ta cewa zaki dawo kuma kin ƙi dawowa why Shalele nah..." Kowa yayi shiru muryar Roshan kawai ake ji, sai surutai yake yana magana da Ƴar Amana, ita kuma ba mai jin abinda take faɗi, Abbah da Razhdeen ƙoƙarin riƙo shi suke yana zame wa sai janye zanin gado yake yake faɗin "bazan taɓa sake ki ba, babu yanda zaki ƙara tafiya..." Ammy kuwa Addu'o'i take ta jerowa masu ƙarfin gaske tana tottofa wa Roshan, Da sauri Rukky ta kawo wa Ammy cup da ruwa a ciki haka Ammy ta fara tofa addu'a a cikin ruwan kofi ta juma tana yi kafin ta fara feshe Roshan da ruwan har da wurin da yake riƙe da shi har yake faɗin ya riƙe Ƴar Amana, Ƴar Amana jin yanda ake watsa mata ruwan Addu'a a jiki yasa ta yin ihu ta toshe kunne duk biyun da hannu lokaci guda ta ɓace ɓatt domin a jikin ta akwai tarin abokanta Aljanu... Roshan wani irin ihu ya ƙara kurmawa ganin Ƴar Amana ta ɓace masa ya ce "Wayyo Allah Shalele ta ƙara tafiya, Abbah ya zanyi ta gudu, duk laifin ku ne tin ɗazu nake cewa ku nemo mun igiya na ɗaure ta amma kun ƙi, bakwa son Rayuwata ta dawo gare ni meyasa?..." Haka ya kwanta akan ƙirjin Abbah yana kuka, shima Abbah rungumar sa yayi sosai yana bubbugan bayansa cikin lallami, Razhdeen riƙo hannun Roshan yayi yana murza tafin hannunsa duk biyun ido a rufe shima yana jero nasa Addu'o'i, Da haka har Roshan ya samu yin bacci lokaci ƙanƙani.... A wannan ranar Roshan wuni yayi yana bacci akan gadonsa, sai kuma Razhdeen a gefensa a zaune domin shi aka bari a wurin sa, Idanuwansa ya fara buɗe wa a hankali yana furta "la'ilaha ilallah, Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wa sallama..." Razhdeen idonsa ya sauƙe akan sa ganin ya farka, Roshan idonsa ya fara juyawa yana kallon ceiling, daga bisani ya ɗora hannunsa akan goshi, Razhdeen ya ce "twins ka tashi ne?..." Roshan idonsa ya sauƙe kan Razhdeen wanda sai da yayi magana kafin ya gan shi, ɗaga masa kai yayi tare da shirin tashi zaune, sai da Razhdeen ya tallafa masa gaba ɗaya jikinsa ba ƙarfi duk ya mutu... Razhdeen dafa kafaɗarsa yayi yana faɗin "your welcome my twins..." Cikin kasalalliyar murya Roshan ya ce "my man ina son yin wanka da kuma sallah..." Razhdeen ya ce "ok bari na haɗa maka ruwan zafi ko..." Roshan ɗaga masa kai yayi yana murmushi a yayinda shi kuma Razhdeen ya shige bathroom, bayan wasu ƴan mintuna ya fito ya sanar masa akan yaje ya watsa ruwan, Roshan tashi yayi a hankali cikin kasala da mutuwar jiki ya shige bathroom sai da yayi brush kafin ya kunna shower, yana cikin wanka yaji kamar an rungume shi, yaji hakan a jikinsa dakatar da yin wankan yayi ya kashe shower ya tsaya cakk, girgiza kai yayi ya ƙara kunna shower a kansa idonsa ne ya sauƙa akan inuwar mutum ta jikin bango, tsayuwar inuwar kamar siffar mace ganin haka yasa ya juya baya da sauri yana son ganin ko mutum ne a tsaye ta bayan sa, still gani yayi babu kowa sannan ya sake ganin jikin bangon babu inuwar ta ɓace, cike da mamaki ya cigaba da yin wankan sa, yana cikin yin wankan ya ga an kashe hasken toilet, ɗaga kansa yayi yana kallon glob, nan aka sake kunnawa, still aka ƙara kashe wa, lips ɗinsa ne ya fara motsi yana kakkarwa ya furta "My Man..." Razhdeen jin Roshan ya ƙira shi ya ce "meya faru ne Twins..." Roshan murya na rawa ya ce "meyasa glob ɗin ɗakunan suke mutuwa?..." Razhdeen ya ce "mutuwa kuma? gaskiya normal suke..." Roshan cike da mamaki yake bin bathroom ɗin da kallo ganin glob su kawo su ɗauke su ƙara kunnuwa su mutu again, haka aka rinƙa yi, Roshan cikin ɗaga murya ya ce "wai waye ne? me yasa ƙoyayen nepa suke mutuwa su kawo ne nima i scared, wa yake son tsoratar da ni..." Razhdeen jin Roshan ya fara birkicewa yasa shi nufan cikin bathroom, yana shiga aka tsayar da kashe glob, suka dawo normal... Razhdeen ya ce "me yake faruwa ne Twins, naga glob normal suke..." Roshan cikin tsoro yake bin ko ina da kallo, Razhdeen ne ya jawo towel ya miƙa masa yana faɗin "karɓi ka ɗaura muje waje..." Roshan karɓa yayi ya ɗaura towel aka kunkuminsa suka yi waje, Kafin ya shafa cream da turaruka har Razhdeen ya ciro masa ƙananun kaya Three quarter da T-shirt ya gama shiryawa tsab, already an kawo musu kayan abinci, haka suka zauna suka ci a tare daga bisani Razhdeen ya sanar cewa su fita can babban falon su na gidan, Hakan kuwa akayi a tare suka zo fito cikin sassanyar murya aka furta "Yaya Roshan..." daga cikin ɗakin, Jin ƙiran sunan yasa Roshan juyawa da sauri yana kallon cikin room ɗin, Razhdeen ya ce "lafiya kuwa muje mana..." juyawa suka yi kuma du yaji an sake ƙiran sunan sa "Yaya Roshan..." ƙara juyawa yayi a ruɗe domin ƙiran sunan na gaske ake masa, Razhdeen ya ce "meye haka twins?..." Roshan ya ce "baka ji ana ƙiran sunana ba?.." Razhdeen girgiza kai yayi ya ce "i didn't hear any sound, let us go..." Roshan ya ce "naji kamar muryar Reemah..." Razhdeen ko sauraronsa bai tsaya yi ba ya ja hannunsa suka fice, a falo suka tarar da kowa da kowa na gidan, Abbah yana zaune suna tattaunawa da wani babban malami da yasa aka ƙira masa akan batun Roshan, Abbah yana ganin Roshan ya miƙe tsaye tare da nufan yanda yake yana faɗin "Roshan ka tashi ne?..." Zaunar da shi Abbah yayi yana nuna wa malamin Roshan ya ce "Malam ga shi nan..." Malamin ya kalli Roshan sannan ya ce "Roshan ko zaka iya gaya mun mai da mai kake ji a jikinka? sannan wasu abubuwa kake gani wanda mutane basa iya ganin abun?..." Roshan tintsirewa yayi da dariya yana faɗin "duk meye na wannan tambayar? ce muku akayi ni mahaukaci ne?..." Malam ya ce "akwai mutanen ɓoyen da suke takura maka shin hakane? idan ka sanar mun zan ɗoraka akan magani ne na ayoyin Alkur'ani wanda idan kana yinsu Insha Allahu zaka dawo cikin ƙoshin lafiya...." Girgiza kai Roshan yayi sannan ya ce "kuna son dai rabani da Reemah, ina farautar ta dawo gare ni ku kuma kuna mun maganar Aljanu, meye haɗina da su? ina cikin ƙoshin lafiya bana buƙatar wani magani..." Ƴar Amana tana gefe guda tana jin duk tattaunawar da suke, sai zubda hawaye take tana faɗin "dan ALLAH a maido ni cikin ahali na, ina son kasancewa da su da kuma Yaya Roshan ɗina, bana so na rinƙa ganinsa a cikin wannan hali na tsoro da fargaba, ku barni na bayyana a cikin ahali na dan ALLAH...." nan ta fara sheshsheƙar kuka... Wannan sautin kukan sai a kunne Roshan, a ruɗe ya ɗago yana bin kowa da kallo yaga babu wanda yake kuka, can yaji an furta sunan sa "Yaya Roshannnn...." A zabure ya miƙe tsaye tare da faɗin "Reemahh..." duk kowa na ɗakin tsaya kallon sa akayi, har zai bar wurin yana ƙiran sunan Reemah yaji Razhdeen ya riƙo hannunsa, Roshan ƙoƙarin zame hannunsa yake yana faɗin "ka sake ni kukan Reemah nake ji, dan Allah ka sake ni kuka take fa..." Malamin jinjina kai yayi sannan ya ce "akwai aljanar da take fito masa a siffar Reemah, ko kuma Reemah tana tare da Aljanu kuma suna shirin mayar ta aljana itama nan bada jumawa ba..." Abbah ƙirjinsa ba ƙaramin bugawa yayi ba jin abinda Malam yake faɗi, a ruɗe ya ce "kana nufin kace Reemah tana tare da Aljanu? kuma sun kusan mayar ta aljana? dan ALLAH malam ya za'ayi a ceto yarinyar nan? ...." Malam ya ce "babu halin ta baro wurin su domin sun riga da sun karɓe ta da wayon zasu dawo da ita alhalin ƙarya suke, suna son mayar da Reemah ɗiyar su Aljana, amma da ikon ALLAH da ƙarfin addu'a zamu dawo da ita, yanzu haka tana tare da mu, ta zaɓi Roshan ne akan shi zai iya ganinta sannan yaji duk maganar da zata rinƙa furta wa amma shima babu yanda zai yi ya dawo da ita asalin mutum ɗinta...." Abbah cikin karayar murya ya fara faɗin "dan ALLAH Shalele nasan kina jin mu, ki bawa mutanen ɓoyen haƙuri su dawo da ke cikin familyn ki, munyi kewar ki Reemah, idan zaki iya bayyana ki bayyano mana..." Malam girgiza kai yayi sannan ya ce "bazata iya ba..." Ƴar Amana kuwa duk tana jin tattaunawar da suke idan tayi magana ma ba jin ta zasu yi ba, sai dai idan zata yiwa ROshan magana shi zai iya jinta amma sai dai idan da shi zatayi... Malamin haka ɗauki gorar ruwan magani ba Addu'o'i ya miƙe tsaye yana feffeshe ɗakin da ruwan tare da faɗin "idan har tana nan za'a sani muddin ruwan nan ya taɓa jikinta, za'a iya yin magana da ita..." Ƴar Amana da sauri ta miƙe tsaye daga zaune tana ƙoƙarin barin falon bata ankara ba taji sauƙar ruwan nan akan ta, faɗuwa ƙasi tayi tana ihu tare da burburwa domin ji take kamar ana watsa mata ruwan asir a jiki tsabar zafi da ƙuna, a wannan lokacin Roshan ma baya jinta bare ganinta, daƙer shima ya zauna bayan ya daina jin sautin kukan ta, haka take ja daƙer tana matsawa dab da Roshan domin bazata iya tashi ba, tana zuwa dab da Roshan ta ɗora hannunta akan ƙafar sa tana faɗin "ka taimake ni, ka taimake ni! ka taimake ni..." Roshan wani irin shocking yaji ya bi jikinsa a zabure ya ƙanƙame Razhdeen wanda shine a kusa da shi sai Abbah dake ɗayan ɓangaren sa duk sun saka shi a tsakiya saboda kar ya tafi, Ruwan nan haka yake sauƙa akan ta fatar jikinta har yayi jawur, inda asalin aljana ce shigewa jikin wani zata yi a cikinsu tayi magana amma Ƴar Amana bazata iya shiga jikin kowa ba sai dai aita gana mata azaba da wannan ruwan, ganin tana shirin shiɗewa shi kuma Roshan jikinsa ne yake ƙakkarwa kamar wanda aka jona masa shocking sai da Abbah da Razhdeen suna rirriƙe shi, a tunanin kowa aljana ce ta shige jikinsa, duk wannan abunda yake hannun Ƴar Amana ce akan ƙafarsa azabar da take ji shima haka yake jin hakan, Ƴar Amana tinin ta sume a wurin tana kwance sai ga wani haske kamar walƙiya an ɗauke ta sai kuma aka turo wata aljanar da zata maye gurbin Ƴar Amana a wannan halin domin an ɗana tarkon da aljana bazata iya kuɓuta ba, Aljanar tana bayyana ta shige jikin Roshan amma sai dai aljanar da aka turo kurmiya ce bazata iya yin magana ba sai dai aita gana mata azaba domin turo mai baki zai sa taji azaba ta faɗi wata gaskiyar da ake ɓoyewa, Roshan jin an shige shi yasa shi sakin dogon numfashi haka ƙirjinsa yake sama da ƙasa, ɗauke Ƴar Amana yasa ya daina jin shocking, yanzu kuwa baya cikin hayyacinsa gaba ɗaya........ *ASSALAMU ALAIKUM* *BARKAN KU MASOYA DAN ALLAH INA MAI ƘARA BAKU HAƘURI AKAN JINKIRIN UPDATE, AKWAI AIKIN DA NAKE ZUWA TIN SAFE BANA DAWOWA SAI YAMMA KUSAN MANGARIBA, IDAN NA DAWO KUMA BA LOKACI NAN MA A GAJIYE GA BACCI SHIYASA BANA SAMUN YIN TYPING, KUYI HAƘURI YAU DAI BA AIKI PAGE BIYU ZANYI MUKU NAGODE.....* Typing ✍️ Asmeetah writer *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 86 to 90 Ba irin maganin da ba'ayi ba akan Aljanar tayi magana amma sam ko gyaran murya bata yi ba, Roshan gaba ɗaya ya bi ya ƙaƙƙafe ko motsi baya iya yi, anan Malamin ya fahimci Aljanar kurmiya ce, a lokacin sai ya fara ƙoƙarin cire ta daga jikinsa, cikin ƙanƙanin lokaci aljanar ta gudu domin ba ƙaramin azaba take sha ba, tana fita Roshan ya dawo hayyacinsa daga nan sai ya wuce da yin bacci, Abbah ya ce "ina Reemah take kuma?..." Malamin yayi murmushi tare da girgiza kai ya ce "ai ba zasu barta a yanda za'a ganota ba, sun ɗauke ta.. Abbah dafe goshin sa yayi yana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, wannan wani irin masifa ce da ƙalubale, Allah ka kawo mana ƙarshen wannan al'amarin..." Malam ya ce "Insha Allahu zata bayyana amma sai mun dage da roƙon Allah, babu abinda yafi ƙarfin Allah, shi kuma Roshan a halin yanzu yana buƙatar hutawa zan baku maganinnuwan da zai rinƙa amfani da su da kuma turare Insha Allahu zasu yi nesa da shi..." Abbah ya ce "ga shi Roshan baya son magani da ya shafi na hayaƙi ko jiƙo ko rubutu ban san ya zamu kaya ba..." Malam ya ce "indai kuna son samun lafiyar sa haka zaku daure ku saka shi dole yayi amfani da su..." Abbah ya ce "shikenam ba damuwa Allah yasa a dace..." Malam ya amsa masa da Amin sannan ya ba shi maganin daga bisani ya yi tafiyar sa... Roshan kuwa gyara masa kwanciya akayi aka miƙar da shi akan doguwar kujera tare da lulluɓe shi da mayafi, anan aka bar shi a falo yake ta shan baccin sa, Duk mutanen gidan daga manyan har yaran gidan babu mai farin ciki kowa fuskarsa ɗauke da damuwa, Ammy ce ta ɗauko kasko ta haɗa hayaƙin da malam ya basu taje tana karawa a jikin Roshan, haka ta bi ko ina lungu da saƙo tana bi da hayaƙi har ɗakin Roshan ta shiga ko wani ɗaki babu yanda bata shiga ba... A cikin kwana biyun nan Roshan bai ƙara jin motsin Ƴar Amana ba, ya koma normal yanda yake, magani kuwa Abbah daƙer yake saka shi a gaba ya sha da hayaƙi da turare, ganin yanzu Roshan baya wasu abubuwa kamar mahaukaci yasa hankalin kowa kwanciya, ana tunanin yanzu ya samu sauƙi, daman Ƴar Amana ce take rikita shi yanzu kuwa bata nan, dalilin da yasa bata zuwa masa shine itama tana can tana jinya, maganin da aka wawwatsa mata ne yasa ta fita hayyacinta, tinda ta suma bata ƙara farfaɗowa ba tana hannun aljanun ta, yanzu tsawon satin guda, Kullum Roshan a cikin tsammanin ganinta yake domin ya damu sosai da rashin ganin spirit ɗinta... Bayan sati biyu Roshan ne ya tashi da safe yayi wanka ya shirya tsab cikin blue jeans da white T-shirt mai dogon hannu, ya sanya cover shoe ɗinsa mai white colour ya feffeshe jikinsa da turaruka kala-kala, ya gyara sumar kansa sai sheƙi yake sannan ya ɗauki agogonsa mai bala'in tsada ya ɗaura a hannunsa ya buɗe gidan glass ya ciro white glass ya sanya akan dara-daran idanuwansa ba ƙaramin kyau yayi ba, Ta bayan sa kuwa Ƴar Amana ce take tsaye ta zuba masa ido ga sumar kanta a baje har gadon baya, sai dai a wannan lokacin bata fito masa a yanda zai ganta ba, ta miƙe itama daga jinyar da ta sha, tana tashi babu wanda ta fara sawa a rai sai Roshan hakan yasa ta bayyana domin taga kyakkyawar siffar shi... Murmushi tayi sannan ta ce "Yaya Roshan kayi kyau sosai, bana son ƴan mata su gane mun kai dole zan zana maka alamar da zai nuna cewa kai mijin wata ce..." Yana tsaye a gaban mirror ta zo dab da shi ta bayansa da baƙin maker a hannunta ta rubuta masa (MIJIN ALJANA) ga rigar asalin fari ne sai rubutun ya fito sosai wanda ko daga nesa za'a iya karantawa, Dai-dai lokacin da ya kammala shirin sa ya ɗauki jakar sa na zuwa wurin aiki hospital ya fice daga cikin ɗakin, itama bin bayansa tayi suka fita a tare, Yana sauƙa falo ya tarar da kowa da kowa sun hallaru akan dinning daman shi kaɗai ake jira, da murmushi ya isa wurin yana faɗin "good morning to you all..." duk suka amsa masa, Abbah ne baya nan yana can falonsa da baƙi, Madam Parveen da Aunty A'isha kuwa su sun daɗe da komawa sai da Abbah ya roƙi Aunty A'isha akan kada ta sanar wa mai martaba halin da ake ciki na ɓatan Reemah, Roshan zama yayi shima suka fara breakfast, bayan ya ɗan taɓa abincin ya tashi yana goge bakinsa domin sauri yake zai fita, sallama yayi musu ya juya zai tafi, Ummy ce ta fara ganin rubutun bayan sa ta ce "innalillahi Yaya Roshan haka kuma..." Duk sauran juyawa suka yi suna kallon sa, lokacin shi kuma ya waiwayo yana faɗin "kinga sauri nake sai na dawo..." ya ƙara juyawa anan ne Kowa yaga rubutan, duk zaro ido suka yi suna kallon sa, Razhdeen ya ce "Twins....." Roshan ɗaga musu hannu yayi ba tare da ya juyo ba ya ce "duk maganar da zaku yi ku ajiye sai na dawo..." daga nan ya buɗe ƙofar falo yayi ficewar sa. Baiwar Allah ta ce "ai da an sanar masa kafin ya fita..." Razhdeen ya ce "me za'a sanar masa bayan shi ya rubuta kayansa..." Minal ta ce "kuma sai ya rubuta mijin Aljana?..." Hajiya Kilishi ta ce "to ba masoyiyar sa yana ganinta a mazannin aljana ba shiyasa ya rubuta hakan..." Rukky ta ce "ai kuwa zai sha dariya kam a wurin mutane..." Pinky ta ce "ko kuma su yi ta guduwa masa ba..." Haka duk suka gama tsegumin su, daga baya shima Razhdeen ya tashi ba tare da ya sake furta komai ba.. Roshan yana fita harabar gidan zai buɗe motar sa sai ga su Abbah sun fito shi da wasu baƙinsa su biyu manyan mutane, Ɗaya daga cikin baƙin ne ya karanta rubutun bayan rigar Roshan ya ce "Roshan kuwa yana da hankali?..." Abbah ne ya kalli wurin da yake yana tambayar "me ya faru ne?..." Mutumin ya ce "baka ga abun da yasa aka rubuta masa a bayan rigar sa ba ne?..." Sai yanzu Abbah ya karanta cike da mamaki yake binsa da kallo ba bakin magana har Roshan ya shige motarsa ya fice a ɗari daman already an buɗe masa gate... Bayan isar sa hospital yana sauƙa a harabar hospital wasu Nurse su biyu suka gaishe shi ɗaya daga ciki kuma tsananin masifar son sa take, zai wuce ta sha gabansa ita kuma ɗayar ta ɗan koma gefe anan taga rubutun bayan sa, zaro ido tayi tare da toshe bakinta da hannayen ta biyu, Ita kuma wacce ta sha gabansa Salma tsayawa tayi tana facing ɗinsa, Ya ce "lafiya kuwa?..." Ta ce "haba Roshan meyasa kake son wahalar mun da zuciya, tin yaushe nake bin ka da soyayyata amma baka sauraro na, wannan ai wulaƙanci ne..." Roshan sauƙe numfashi ya yi sannan ya ce "bana son wulaƙanta mutum hakan yasa bana sauraronki amma tinda ban ma kulaki ba kince ina wulaƙanta ki yanzu abinda nake so da ke ki fita sabgata, bana son raini..." Ta ce "wallahi Roshan ko yankan jikina kake da wuƙa bazan daina bibiyanka ba, ina sonka kuma banga wanda ya isa ya rabani da kai..." Ƴar Amana sarkin kishi tana gefe guda ta kama kunkumi idonta akan Salma dake duk yanda Roshan zai je tana biye da shi, Roshan ya ce "ban hanya na wuce..." Ta ce "wallahi ba inda zan matsa naje har sai ka karɓi soyayya ta..." Roshan hannu yasa zai ture ta gefe Dai-dai lokacin da Ƴar Amana tasa hannu itama ta hankaɗata, lokaci guda Salma tayi gefe ta doku a ƙasin floor nan take ta gurɗe a hannu dake akan hannu ta faɗi, Roshan cike da mamaki yake bin ta da kallo domin shi ba wani ture ta da har zata faɗi ya yi ba, ɗago hannunsa ya yi yana dudduba wa, Ƙawar ta da take gefe ta tafo da gudu zata yo kanta taga Roshan ya miƙa mata hannu zai ɗagota, Salma miƙa masa hannunta marar ciwo tayi tana murmushi domin ita damuwar ta ba ciwon ba, haka ya ɗago ta yana faɗin "sorry! fatan baki ji ciwo ba..." Ƴar Amana wani irin kallo ta watsa mata cike da takaici da baƙin ciki domin ta tsani wata budurwa ta raɓi jikin Roshan, Salma miƙa masa hannun da taji ciwo tayi ta ce "naji ciwo a hannu na..." Roshan riƙe hannun ya yi ya ce "Ok muje na duba miki...." har sun juya zasu nufi cikin hospital Ƙawar Salma ta taɓa ta baya, juyawa tayi tana kallon ta da murmushi akan fuskar ta anan ƙawar take nuna mata rubutun bayan sa, bayan ta karanta itama zaro ido tayi baki a sake ta tsaya cak, shima tsayawa ya yi ya ce "muje mana..." Girgiza masa kai tayi ta ce "a'a ka je kawai zan zo daga baya..." ta ƙare maganar murya na kakkarwa... Ya ce "Ok shikenam.." yayi gaba abinsa... Salma rungumar ƙawar ta tayi tana sauƙe numfashi ta ce "mijin Aljana kuma? akwai alamar tambaya akan Roshan daman Wayyo Allah..." Ƴar Amana murmushi tayi sannan ta buɗe wa Salma kunne yanda zata ji duk abinda zata ce, anan ta fara magana tana faɗin "wannan tsoritar da kika yi kaɗan kenam..." Salma jin an furta haka yasa ta ɗago tana kalle-kalle domin jin maganar take kamar daga sama, Ƴar Amana ta cigaba da cewa "zan yi miki gargaɗi na ƙarshe akan Roshan domin shi ɗin rayuwata ne, duk wacce ta raɓi jikinsa da niyyar soyayya to ta fara ƙirga kwanakin barin ta duniya nan da kwana ɗaya ko a cikin na biyu, Roshan rayuwata ne na ƙara maimaita miki, duk wacce kika ji tana son yin soyayya da shi to ki bata shawara idan ta ƙi to wallahi zata bar duniyar nan, Roshan nawa ne, Roshan nawa ne ni kaɗai..." Haka Salma ta toshe kunnen ta domin jin muryar take kamar zai fasa mata kunne domin muryar tana fita ne da bibbiyu, ba abinda take faɗi illa "wallahi indai Roshan ne na rabu da shi duniya da lahira, bazan sake shiga sabgar sa ba amun afuwa dan Allah kar ku kashe ni..." Ƙawar ta kuwa rirriƙe ta take tana tambayar ta "wai me yake faruwa ne? kodai Aljanar Roshan ce ta bayyana miki?..." Salma ɗagowa tayi tana kallon ƙawar ta cikin kuka ta ce "wallahi ita ce, na shiga uku yau Aljana ta fito mun da muryar ta..." Ɗayar ta ce "ai kaɗan kika gani indai baki rabu da shi ba nan gaba zata fito miki a zahirance ne..." Cikin tashin hankali Salma ta ce "mai zai sa bazan rabu da shi ba? ai na rabu da shi an gama, kinga tashi mu bar wurin nan..." A ruɗe Salma ta miƙe tsaye wanda jin muryar aljana yasa ta durƙusawa haka suka bar wurin da gudun gaske... Roshan yana shiga duk wanda ya karanta rubutun bayansa sai ya gudu, wasu kuma suyi ta dariya har da masu furtawa a fili suna faɗin "Mijin Aljana! Mijin Aljana..." Roshan gaba ɗaya ya gama tsarguwa duk da ba wanda ya tuntuɓe shi da maganar, da ma'aikatan da waɗanda suka je duba majinyata kowa haka ake nuna shi da yatsa ana maganarsa, duk ba wanda bai ga rubutun ba, sai wani abokinsa ne ya miƙa masa hannu alamar gaisuwa yana faɗin "Congratulation Mijin Aljana yaushe aka yi Auren ne ba gayya?..." Sai yanzu Roshan ya gama tabbatar da cewa duk gurmin da ake yi da shi ake, cikin rashin fahimta haka yake bin mutumin da kallo har ya tafi, haka yake bin mutane da kallo ɗaya bayan ɗaya yanda suke ta masa dariya wasu kuma suna faɗin "Mijin Aljana..." Roshan ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba ganin an maida shi mahaukaci, a fusace ya nufi office ɗinsa ya shige, yana zuwa ya zauna akan kujerar sa ya kifar da kansa akan table ɗin gabansa wanda yake ɗauke da takardu da computer, tsabar takaici bai san lokacin da hawaye yake zubo masa ba, shi takaicin sa yana matsayin shugaba a cikin hospital ɗin nan amma mutanen da basu kai ba har da su ake masa izgilanci da yaransa ma'aikata, ya daɗe yana tunanin meyasa suke ƙiransa da mijin Aljana, Jin yayi an knocking ɗagowa ya yi yana goge hawayen sa da handkerchief daga bisani ya bada umarnin a shigo, wata mata ce ta shigo zata faɗi matsalar da ke damunta, ganin Roshan yasa ta juya da gudu tana faɗin "Wayyo Allah mijin Aljana ne daman a cikin office ɗin? wallahi na yafe..." Roshan abun sai ya ƙara ɗaure masa kai, yana cikin tunani sai yaji an turo ƙofa da sallama, ɗagowa ya yi yana kallon wanda ya shigo yana tunanin shima da nashi izgilanci yazo masa, wani babban Abokinsa ne mataimakin sa a wurin aiki, zuwa ya yi ya zauna yana kallon Roshan wanda shima Roshan tagumi ya yi yana binsa da kallo.. Doctor Aliyu ne ya fara yin magana ya ce "Good morning Doctor Roshan..." Roshan ɗaga masa kai kawai ya yi ba tare da ya furta komai ba domin shi kaɗai yasan abinda yake ji a ransa. Doctor Aliyu ya ce "Doctor Roshan kasan abun zai dame ka meyasa ka rubuta hakan? meye dalilin rubuta mijin Aljana a bayan rigar ka kuma? kasan dole mutane sai sunyi magana wasu kuma su tsorita..." Roshan cike da mamaki yake bin Doctor Aliyu da kallo cikin rashin fahimta, murya ciki-ciki ya ce "ban fahimci abinda kake nufi ba..." Doctor Aliyu ya ce "Oh kana nufin kace baka san da rubutun bayan rigar ka ba?..." Roshan cike da mamaki ya fara ɓalle bottle ɗin gaban rigar sa ya cire rigar dake akwai wani T-shirt mai gajeren hannu ta ciki, yana juya bayan rigar ya ga an rubuta Mijin Aljana, a ruɗe ya furta "what! who do this for me?..." Doctor Aliyu ya ce "indai baka san da shi ba to wani ne ya rubuta maka..." Roshan ya ce "amma lokacin da zan saka rigar babu rubutun nan, sannan lokacin da zan yi breakfast duk ƙannena a zaune suke har iyayen kuma nine first ɗin barin wurin, still motar da na shiga ni kaɗai nayi driving ban tsaya a ko ina ba sai anan hospital..." Doctor Aliyu ya ce "akwai matsala to, amma ka tuntuɓa shin tin daga gida hakan ya faru ko kuma sai da kazo nan..." Roshan ɗaukar wayansa ya yi ya danna ƙiran wayan Razhdeen, bugu uku ya ɗauka domin Razhdeen baya saurin ɗaukan ƙira ko wayar tana hannunsa sai ƙiran ya kusan yanke wa tukun yake ɗagawa, already Roshan yasan hakan shine halinsa shiyasa bai damu ba saboda yasan zai ɗauka, bayan Razhdeen ya ɗauki ƙira abinda ya fara furtawa shine "ya akayi ne mijin Aljana..." Roshan ya ce "kana nufin kace tin a gida rubutun yake bayan rigana?..." Razhdeen ya ce "ina kai ka rubuta hakan da hannunka meyasa zaka tambaya alhalin kasan kowa zai kalla..." Roshan kamar zai yi kuka ya ce "My Man wallahi ban san da wannan rubutun ba, bani da rubuta ba kuma lokacin da na ɗauko rigar babu rubutun nan..." Razhdeen yana kwance sai da ya tashi zaune yana faɗin "what? kana nufin kace ba kai ka rubuta ba? Oh my God akwai matsala Please twins come back to home now, we've to do something..." Roshan amsa masa ya yi da "okay..." Idonsa gaba ɗaya ya kaɗa ya yi ja tsabar damuwar da ya shiga lokaci guda... miƙe wa ya yi idonsa akan Doctor Aliyu ya ce "i need to go home..." Yana kaiwa nan yayi ficewar sa da rigar a hannu, Doctor Aliyu girgiza kai ya yi ba tare da ya ce komai ba domin shima abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba... Kafin Roshan ya koma gida har Razhdeen ya sanar wa Abbah halin da ake ciki, shima Abbah hankalin sa ba ƙaramin tashi yayi ba, cikin ƙanƙanin lokaci Roshan ya isa gida, a falo ya tarar da su Abbah, Abbah yana ganinsa ya miƙe tsaye tare da yowa kansa yana faɗin "Roshan da gaske ne abin da nake ji?.." Roshan ya ce "Abbah seriously ban san da wannan rubutun ba kuma ba mutum bane ya rubuta ba..." Razhdeen karɓan rigar hannunsa yayi yana duba rubutun rigar, yana gani ƙirjinsa ya buga da ƙarfin gaske domin sai yanzu ya lura irin rubutun Ƴar Amana ce, domin rubutun ta tana yi ne haɗi da design kafin ta tsara, a ruɗe ya ce "Dad wannan ai rubutu Sarah ce..." Abbah ya ce "rubutun Shalele kuma?..." Roshan shima maimaitawa ya yi "Shalele?..." Ummy dake wurin itama ta ce "tabbas wannan rubutun Reemah ce..." Itama Baiwar ALLAH ƙarewa rubutun da kallo tayi sannan ta ce "wannan rubutun Ƴar Amana ce..." Abbah ya ce "Razhdeen meye mafita? ya zamu yi mu samo Shalele? ta wani hanya zamu bi ta dawo gare mu, hakan na nufin ta koma aljana kenam? yanzu idan Mahaifinta yasan da wannan maganar wani irin hali zai shiga? muna buƙatar ta..." Ammy ta ce "gaskiya idan a haka zamu zauna bazata taɓa dawowa ba sai mun miƙe tsaye, duk da muna kan yin Addu'o'i amma kamata yayi a tara malamai a tsaya akan al'amarin..." Roshan cikin rashin fahimta ya ce "kenam kuna nufin kuce Shalele ta koma aljana? kenam da gaske ne ni mijin Aljana ne indai haka ne, to kuwa sunan nan bazai taɓa goguwa ba ko ina zan iya shiga da sunan mijin Aljana indai bata bayyana ba..." Roshan yana kaiwa nan ya haura upstairs, yana shiga room ɗinsa ya wurgar da rigar sa saman gado, juyawar da zai yi yaga anyi rubutu a jikin madubi da jini an rubuta "SAVE ME YAYA ROSHAN..." Ƴar Amana ce ta rubuta haka a yayin da take tsaye sai zubda ƙwallah take domin tana gab da rasa Roshan indai ta zama Aljanan asali kuma sauran kwana ɗaya hakan ya faru domin manyan Aljanu sun haɗa Meeting akan ta, in har ta zama Aljana bazata taɓa dawowa mutum ba balle ta kasance a cikin ƴan uwanta... Roshan gaban mirror ya je ya tsaya murya na kakkarwa ya furta "Shalele! Dan ALLAH ki bayyana mun kan ki Shalele, ina buƙatar ki a kusa da ni..." Ƴar Amana gaban mirror taje itama tayi facing ɗin mirror sai ga ta ta bayyana a jikin madubi, a ruɗe Roshan ya ja da baya ganin Ƴar Amana ta bayyana, muryarsa haka yake kakkarwa ya ce "Shalele..." Ƴar Amana tana kuka ta ce "Yaya Roshan na kusa na rasa ka, an yaudare ni Yaya Roshan, sunce zasu dawo dani da zaran ka bayyana soyayya ta sai kuma suka canza magana, daman so suke su ɗauke ni sai ga shi dama tazo musu, ban san ya zanyi na kuɓuce musu ba, dan Allah ka taimake ni Yaya Roshan, gobe da yamma suke son mayar ni Aljana domin rana ce ta musamman a wurin su, inason kafin lokacin ka cece ni ina cikin tashin hankali..." Roshan yana kuka ya ce "Shalele ta wani hanya zan bi na ceceki?..." Ta ce "akwai mafita guda ɗaya kana yin wannan shikenam sauran ƙwatoni..." Roshan ya ce "meye mafita?..." Ƴar Amana ta ce "yau da misalin ƙarfe 2 na dare zaka ga wani haske ya bayyano maka, cikin wannan hasken zaka shiga daga nan za'a kai ka yanda nake, Amma muddin baka yi bacci ba, idan hasken ya bayyana ya same ka kana bacci to ɓace wa zai yi daga nan babu wata hanyar da zaka same ni..." tana kaiwa nan tayi ɓacewar ta, A gigice Roshan ya fara ƙiran sunanta "Shalele! Shalele!! Reemah!!! Reemahhh!!!!...." Haka yake ambatar sunan ta Dai-dai lokacin da Abbah da Razhdeen suka shigo, da hanzarin su suka ƙarisa wurin da Roshan yake.. Abbah da Razhdeen ne suka riƙe shi suna faɗin "meya faru Roshan..." Roshan cikin tashin hankali yake faɗin "Abbah zasu mayar ta Aljana shikenam zan rasa abar ƙaunataa..." Abbah ya ce "insha Allahu bazaka rasata ba, zata dawo da yardar Allah..." Daƙer suka samu su ka rarrashe shi... ★★★ Misalin ƙarfe 12 na dare Roshan yana nan da idonsa sai zarya yake a cikin room ɗinsa, ko zama bai samu damar yi ba duk da yasan ba baccin zai yi ba domin yanzu kusan kwana yake baya bacci sai da safe yake baccin safe, jira yake yaga zuwan hasken da Ƴar Amana ta sanar masa zai zo, domin a halin yanzu a shirye yake da ya rasa rayuwar sa saboda ita, haka ya cigaba da zirga-zirga a cikin ɗakin idan ya gaji sai ya zauna a bakin gado, da haka har lokaci ya yi, yana duba agogo ya ga ƙarfe 2 dai-dai miƙewa tsaye ya yi yana son ganin bayyanar hasken domin yana muradin ganin Reemah... Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga hasken nan ya bayyana kamar walƙiya, haske ne na kashe ido sai da Roshan ya rufe idonsa da hannayensa, haka yake tafiya a hankali idonsa a rufe yana yowa wurin hasken tare da ambatan sunan Allah, ba abinda yake sai jero Addu'o'i da haka ya shige cikin hasken, nan take hasken ya ɓace da shi... Wani wuri ne shi ba kogo ba sannan shi ba ɗaki ba, wurin a gewaye babu ko hanyar fita bare window, ga haske ta ko ina shi kaɗai ya bayyana babu motsin kowa, Roshan ganinsa a wurin da hasken ya ajiye shi ne yasa shi faɗin "Reemah! Reemah!! gani nazo yanda kike ki bayyana mun kan ki, kina inaaa...." Roshan yana magana haka wurin yake ɗaukan maganar sai muryar sa take fitowa bibbiyu, sautin muryarsa ne yake fita da ƙarfi haɗi da rarrabe wa, Haka ya cigaba da magana yana ƙiran sunan Reemah amma babu wanda ya bayyana a wurin, sai da ya ɗau tsawon lokuta yana zarya a filin wurin kafin ya ji an ambaci sunan sa ta bayan sa "Yaya Roshan..." Dasauri ya waiga ganin Ƴar Amana yasa shi sakin murmushi yana faɗin "Allah na gode maka daka bayyanar mun da farin ciki na..." Da hanzarin sa ya nufi yanda take kafin ya isa yaji an ƙara ƙiran sunan sa ta bayan sa "Yaya Roshan.." dakatawa ya yi da tafiyar ya ƙara juya ya kuma ganin Ƴar Amana cike da mamaki yake bin su da kallo su biyu siffar su iri ɗaya hatta kayan jikinsu komai da komai, kamanni kamar an tsaga kara, haka ya shiga cikin zulumi idan ya kalli wannan sai ya juya ya kalli wancan gaba ɗaya sun kasa masa tunani, juyawa yayi zai koma kan wacce ta zo daga baya still ya ji an ƙara ƙiran sunan sa "Yaya Roshan..." kuma du ta ukun ta bayyana kuma duk kamannin su ɗaya, Roshan tsayawa yayi yana binsu da kallo kuma du ta huɗu ta sake bayyana tare da ambatar sunansa "Yaya Roshan..." Haka ta biyar ma ta bayyana sai da Ƴar Amana ta kasu kashi goma ko wacce tana ƙiran sa da Yaya Roshan... Gasu nan kashi-kashi ko wacce tana tsaye a wurin ta babu abinda ya banbanta a jikinsu komai nasu iri ɗaya hatta sumar gashin bazaka iya tantance wannan Ƴar Amana ce ba, Roshan gaba ɗaya hankalinsa yayi matuƙar tashi ganin wannan al'amarin, Ji yayi sautin ƙatuwar murya ta bayyana ana faɗin "Roshan a cikin ƴan matan nan masu kamanni ɗaya ka zaɓi Reemah ka, idan ka zaɓi wacce ba asalin ita bace to duk zasu ɓace ne kuma ka rasa ta har abada, idan kuma ka zaɓe ta to duk sauran zasu ɓace su bar maka ita amma bazaka tafi da ita ba a halin yanzu ba amma zamu kwatanta maka a yanda zaka same ta a matsayin mutum, kuma zamu zare hannun mu akanta wannan alƙawarin mu ne..." Daga nan aka daina magana... Su kuwa Ƴan matan duk suka fara kuka suna faɗin "Yaya Roshan ni ce Reemah ka taimake ni, wallahi ni ce Shalelen ka..." Haka muryoyi suke fita daga bakinsu, kuma duk muryoyin iri ɗaya, lokaci guda duk suka yi shuru daga nan ko wacce ta fara maganar ta da ban, ta farkon ce ta fara tana kuka ta ce "Yaya Roshan ka taimake ni ina cikin tashin hankali ni ce Reemah..." Ɗayar ma ta fara kuka ta ce "Yaya Roshan kar ka yarda da su ni ce Shalelen ka..." Ɗaya ma ta ce "Yaya Roshan Dan ALLAH ka taimake ni wallahi ni ce Shalelen ka..." Ɗayar ma ta ce "Yaya Roshan ashe akwai lokacin da bazaka iya tantance jikinka ba? Shalelen ka ce fa take magana..." Ɗayar ma ta ce "Yaya Roshan kar ka yarda da su duk yaudarar ka zasu yi ni ce asalin Reemah kuma Shalelen ka..." Duk haka suka kasance cikin launa magana, ko wacce tana magana ne yanda zai yadda akan Reemah ce... Roshan hannu ya ɗora akansa yana faɗin "Oh my God! Shalele meyasa zaki mun haka, dan Allah ki mun wani alamar da zai nuna mun cewa kece Shalele nah..." Duk hawaye suka fara yi ko wacce ta fara faɗin "Yaya Roshan nace maka ni ce Shalelen ka amma kaƙi yadda wata alama zan nuna maka, ka yadda da ni dan Allah..." Roshan gaba ɗaya hankalinsa ne yake shirin barin jikinsa, suna shirin rikirkita masa ƙwakkwalwa, domin babu wata alama da zai nuna cewa wannan ce Reemah, ba shi da wata mafita haka ya durƙusa da gwiwowinsa ya yi sujjada anan ya kaiwa Allah kukan sa da neman taimakon Allah, "Ya Ubangijina na kawo kuka na gare ka domin kai kaɗai zaka iya magance mun damuwa ta, Ya Allah ka taimake ni, ka kawo mun agaji, ka ceci baiwar ka tana cikin wani hali...." Sai da ya gama Addu'o'in sa da neman taimakon Allah kafin ya ɗago a hankali ga yanda idanuwansa suka yi jawur, Haka yake bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya cikin ikon ALLAH idanuwansa suka sauƙa akan ta tsakiya wacce alamu ya nuna cewa Reemah ce ta hanyar ganin inuwar ta, wanda sauran kuma inuwarsu bai bayyana ba sai ita kaɗai, zaro ido ya yi waje cike da farin ciki da gudun gaske ya miƙe ya nufi yanda take, a kiɗime ya rungume ta tare da ɗagata sama yana juyawa da da ita tsabar farin ciki... Su kuwa sauran duk tsaya kallonsu suka yi lokaci guda duk suka ɓace, sai ya rage daga Roshan sai Ƴar Amana, har zuwa yanzu suna rungume da juna cikin farin ciki daga bisani suka rabe a ruɗe Roshan ya kama fuskar ta yana faɗin "Shalele nah kin bayyana, Allah nagode maka daka bayyanar mun da matata, Allah nagode maka, Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!..." Ƴar Amana kuka take haɗe da dariya ta ce "Yaya Roshan taya ga gano ni? ina so na nuna maka alamar da zaka gane ni amma sai dai duk abinda nayi suma yinsa suke, nagode sosai, ka ceceni daga hannunsu Yaya Roshan..." Roshan ya ce "yanzu abinda zai faru shine ki nema mana hanyar fita daga nan, ina so na koma da ke gida..." Murya suka ji daga sama an furta "Bazaka tafi da ita ba, yau ƙarfe 6 na safe zamu turo maka wani ɗan maƙullo wato wani ƙaramin aljanin mu shi zai nuna maka hanyar da zaka bi kaje wurin da zaka samu Reemah, bil adama basa shiga wurin da daddare sai da safe, don haka ka shirya zuwa wurin da safe ƙarfe 6, don haka yanzu zamu mayar ka yanda ka fito..." Roshan ya ce "bazan tafi na bar Reemah ba, ko ku bani ita mu tafi tare ko kuma nima ku barni anan tare da ita..." Ji yayi ance "kar kayi mana gardama..." Ƴar Amana cikin tsoro da fargaba ta ce "Yaya Roshan kaje kawai gobe zaka same ni a yanda zasu kai ka, insha Allahu zaka kasance dani har abada, kaje kawai..." wani haske ne ya bayyana, Roshan girgiza kai yake yana faɗin "ba yanda zan je na barki Shalele..." Ƴar Amana ganin Roshan yana shirin fusata Aljanin yasa ta hankaɗa shi da ƙarfi bai ankara ba ya faɗa cikin hasken da ya kawo shi nan danan hasken ya ɓace da shi, Roshan bai sauƙa a ko ina ba sai a saman katafaren gadonsa, cikin tashin hankali yake ambatar sunan Reemah yana kuka, ganin ya kasa samun sukuni ne yasa shi shige wa toilet ya ɗauro alwala ya fito ya tsaida sallah, har akayi sallar asuba yana kan sallaya, a cikin ɗakinsa yayi sallar asuba saboda gudun kar ɗan muƙullo ya bayyana ba tare da yana nan ba..." Ƙarfe 6 na safe na yi dai-dai lokacin ɗan Aljanin ya bayyano, ɗan ƙarami da shi wanda gaba ɗayansa bai wuce tsayin jariri haihuwar yau ba sai ƙaton kai ga jikinsa yanda yake fitar da farfatsin haske, a zabure Roshan ya miƙe tsaye yana sanye da jallabiyar sa ganin ɗan Aljanin ya bi ta ƙofa ya fice yasa Roshan ɗaukan key ɗin motarsa shima ya fice da hanzarin sa, A falo ya tarar da Baiwar ALLAH ko tsaya mata magana bai yi ba haka ya wuce, cike da mamaki ta bi bayansa da kallo itama ta bi bayansa ta fice, Roshan yana fita ya tarar da su Abbah shi da Razhdeen dawowar su daga masallaci kenam, Abbah ganin Roshan ya ce "ina kuma zuwa Roshan? ban ganka a masallaci ba..." Roshan idonsa akan Aljanin wanda shi kaɗai yake iya kallonsa ya ce "Abbah zan fita..." Abbah ya ce "ina kuma zaka je..." Roshan ya ce "wani wuri bana buƙatar rakiyar kowa..." daga nan ya shige motarsa daman gate a buɗe take, Baiwar Allah itama fitowa tayi tana faɗin "Allah yasa dai lafiya..." Abbah ya ce "dole zamu bi bayansa, sojoji biyu su rakamu muje..." Kamar yanda ya ce hakan kuwa akayi, Razhdeen ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "ki koma ciki zamu bi bayansa yanzu..." Sojoji biyu a gaban mota ɗaya shine mai driving sai kuma Abbah da Razhdeen a bayan mota, kafin motar ta tashi Baiwar ALLAH ta lallaɓa ta buɗe bayan booth ta shige ta rufe, lokaci guda motar ta tashi a ɗari suka fice... Roshan yana driving idonsa akan ɗan Aljani wanda yake bin iska yana furawa shine a gaba da motar Roshan sai ɗikar gudu yake shima Roshan gudu yake da motarsa, Suma su Abbah haka motar su take gudu har sai da suka hango motar Roshan, duk yanda yabi haka suma suke bi, Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske kafin Roshan ya shige cikin daji da motar sa yanda Aljanin yabi kenam... Daga Abbah har shi Razhdeen cike suke da mamaki kowa yana saƙe-saƙe a cikin ransa, Abbah ya ce "Anya kuwa ba aljanu ne suke son ɗauke shi ba shima?..." Razhdeen ya ce "ina zai je?..." Baiwar Allah wacce take cikin booth gaba ɗaya ta gama gajiya... Gani suka yi Roshan ya yi parking da motar sa ya fito da hanzarinsa ya shige cikin wani kogo, yana shiga suma su Abbah suka fiffito suka shige kogon, Baiwar ALLAH itama fitowa tayi tana bin bayan su a hankali itama ta shiga cikin kogon, tafiya suke bana wasa ba a cikin kogon domin ɗan uban zurfi gare shi, sai da akayi tafiya mai nisa kafin aka fita daga cikin kogon, ana tafiya kaɗan kuma du aka sake iske wani kogon, yanda Aljani yake bi haka Roshan yake bin bayansa, ta ɗan nesa da shi kuma su Abbah ne su huɗu, sojoji biyu da Razhdeen da bayansu kuma Baiwar ALLAH ce wacce ta gama jikkata domin ba ƙaramin gajiya tayi ba, tafiya kawai take... suma ƙara shigewa wani kogon suka yi daƙer Roshan ya wuce wurin tsabar baƙaƙen tsuntsaye sun dubu da haka ya ratsa ta cikinsu ya wuce, su Abbah suma cikin fargaba suka wuce tsuntsayen, Baiwar Allah tana zuwa wurin ganin sun wuce ta cikin su yasa itama ta kutsa ciki saida tazo tsakiyar su taga duk sun mamaye ta kuma suma hakane sai dai a ture su, ita kuwa tsoronsu ne ya hanata ture su haka ta fara rausa ihu tana faɗin "Wayyo Allah na nashiga uku kuzo ku taimake ni, na mutu na lalace..." Su Razhdeen waɗanda basu gama yin nisa ba suka fara jin ihu, shi kuwa Roshan ya yi nisa bai ji ihun ba, A kiɗime Razhdeen ya ce "wannan kamar muryar Reesh..." har zai juya wani sojan ya riƙe hannunsa yana faɗin "Oga nan wurin fa akwai tarin aljanu wata zata iya fito mana..." Razhdeen zamar da hannunsa ya yi yana faɗin "dallah sake ni wani irin aljanu kuma, har ya juya zai koma sai ga Baiwar ALLAH ta fito daga cikin kogon da gudun gaske tana ihu haɗi da cewa "dan Allah ku jira ni Wayyo Abbah..." Tana isowa ta rungumi Razhdeen tana sauƙe numfashi ga yanda duk tsuntsayen suka yakushe ta, Razhdeen ya ce "meyasa kika biyo mu bayan nace ki zauna..." Abbah girgiza kai kawai yayi ya ce "ku zo mu tafi kar ya mana nisa..." Haka Razhdeen ya riƙe hannunta suka fara tafiya, sai da suka yi tafiya mai nisa kuma du suka tarar da wani ƙaton rami wanda cikinta ruwa ne yake ta ambaliya, gani suka yi Roshan har ya tsallaka da taimakon Aljani, sai dai akwai ɗan ƙaramin kada wanda girmansa bazai wuce girman katako ba, Abbah ya jinjina kai ya ce "yanzu taya zamu fara wuce wannan wurin?..." Razhdeen ya ce "zamu iya amma sai dai abi a hankali ta gefe da gefe..." wani soja ne ya fara ɗora ƙafarsa akan icen jikinsa na rawa a hankali yake jan ƙafar sa, Abbah kuwa ba abinda yake faɗi illa "kayi a hankali, a hankali, a hankali..." da haka sojan ya wuce, shima ɗayan sojan kamar yanda wancan yayi haka ya wuce shima a tsorace, Abbah shima haka ya taka matakalan a hankali yana jan ƙafa domin tsabar ƙarantar icen baka isa ka ɗaga ƙafarka ba, nan zaka ji hajijiya inba sa'a ba ka faɗa cikin ruwan, daƙer shima Abbah ya samu ya wuce.. Razhdeen kallon Baiwar ALLAH ya yi ya ce "sauran ke..." Baiwar Allah tin kafin ta ɗora ƙafar ta jikinta ya fara ɓari yana kakkarwa kamar wacce ta faɗa cikin ruwan ƙanƙara, haka take faɗin "to, to, to, to mu je, a hankali, wayyooo..." Razhdeen ɗorata yayi akan icen kafin ya sake ta, tana hawa da ta leƙa ƙasin ruwan nan ta fara jin hajijiya, tangal-tangal ta fara yi har ƙafar ta ya rabe da icen tayi cikin ramin zata faɗa cikin ikon Allah Razhdeen ya yi saurin riƙo hannunta, gangar jikinta duk yana cikin ramin iya hannunta kawai ya iya riƙe wa haka zuciyar sa yake bugawa da ƙarfin gaske, Shima Abbah hankalin sa ba ƙaramin tashi yayi ba haka yake faɗin "Razhdeen ka riƙe ta sosai, kar fa ka sake ta, ka riƙe ta sosai..." Ita kuwa ba abinda take ihu tana faɗin "Wayyo Allah na dan kar ka sake ni, wallahi bana so na mutu yanzu, hannuna zai yanke Habeey..." kanta ta sunkuyar ƙasi tana kallon ruwan da yake ta ambaliya gani tayi wani ƙaton shark ya yi tsalle yayo sama bakinsa a wangale, wani irin ihu ta ƙara kurmawa tana faɗin "wallahi akwai shark 🦈 wallahi akwai shark 🦈 wallahi akwai shark 🦈 shikenam yau kam na hallaka..." Haka shark waran su biyar suke yin tsalle su koma cikin ruwan, Razhdeen kuwa haka ya ruƙe ta sosai ya barta so yake ta gama tsorata sai ya ciro ta, Abbah kuwa cewa yake "Razhdeen kanada hankali kuwa, ka ciro ta mana ya ka barta a haka..." Razhdeen sai da ya gama yinsa tukun ya ɗagota da hannu ɗaya, yana ciro ta sai da ya zabga mata wani kyakkyawan mari tare da faɗin "Banga amfanin biyo mu ba, gashi yanzu kin zamo mana ƙarfen ƙafa..." Baiwar Allah fashewa tayi da kuka, bata ankara ba taji ya ɗaga ta sama tare da saɓata a baya, sai da ya goye ta kafin ya ɗora ƙafarsa akan icen ya fara tafiya a hankali yana jan ƙafa, Baiwar ALLAH wani irin ƙanƙamo tayi masa haka jikinta yake rawa da haka ya samu ya wuce da ita, Bai sauƙe ta ba haka suka cigaba da tafiya, Roshan kuwa yayi musu nisa domin basa iya hango shi amma sai dai tafiyar hanya ɗaya ne babu wata hanyar da ta kauce, nan ma sai da suka ƙara yin tafiya mai nisan gaske kafin suka isko wani ƙaton rami kuma du amma bai kai wanda suka baro ba, Abbah ya ce "wani tashin hankali kuma du..." Wannan ramin zurfi gare shi baka iya hango tsayinsa sannan wannan babu wani icen da aka saka alamun sai kayi tsalle kafin ka tsallaka.. Razhdeen sauƙe Baiwar ALLAH yayi daga bayansa ya kwatanta musu yanda zasu yi su tsallaka, soja ɗaya ne yayi baya sosai kafin ya tafo da gudun gaske ya yi tsalle ya tsallaka, haka ɗayan sojan ma yayi, Razhdeen ya kalli Abbah sannan ya ce "Dad zaka iya kuwa?..." Abbah ya ce "wai ina zan samu ƙarfin jikin da zan iya tsalle har na tsallaka wannan ramin?..." Razhdeen kallon Baiwar ALLAH yayi sannan ya zamar mata da gyalen jikinta dake yanada tsayi ya rabe shi gida biyu ya ɗaure sannan ya cire rigar jikinsa ya yage gida biyu ya haɗa duk ya ɗaɗɗaure duk da hakan igiyar bai isa faɗin ramin ba, ya rasa yanda zaiyi babu wata mafita haka ya cire rigar Baiwar ALLAH ya barta daga ita sai dogon wandonta da shumi (best ) dake kayan irin na larabawa ne rigar dogo ne har ƙasi sai ƙaton wando a baje, Baiwar Allah ba ƙaramin kunya ta shiga ba ganin yanda Razhdeen ya cire mata riga a gaban Abbah, Haka Razhdeen yasa hannu ya yage rigar kashi biyu ya haɗa ya ɗaure, sai a lokacin tsayin igiyar ya kai. Abbah ya ce "wai duk mai zaka yi da wannan igiyar?..." Razhdeen ɗaukan dutsi yayi ya ɗaure da igiyar sannan ya ce wa sojojinsa "ga nan igiya zan wurgo muku ku riƙe sosai..." Haka ya wurga musu suka riƙe shima ya riƙe igiyar daga ɓangaren sa ya kalli Abbah sannan ya ce "Dad ka zauna a bakin ramin saika riƙe igiyar ka wuce da haka..." Abbah buɗe baki yayi yana kallon Razhdeen ya ce "amma ban taɓa sanin baka sona ba sai yau Razhdeen, taya zan riƙe igiyar nan gangan jikina a cikin rami igiya ba ƙarfi ba wanda zai iya tsinkewa..." Razhdeen ya ce "oh my God! Dad I know what am doing, zaka wuce da yardar Allah..." Abbah ya ce "shikenam to, idan na faɗa na mutu na yafe maka..." Haka Abbah ya zauna a bakin ramin ya riƙe igiyar yayi ciki, su kuwa suna riƙe da igiyar sosai, Daga ɓangaren Sojojin su biyu suke riƙe da igiyar, sai kuma Razhdeen wanda ya tattaro ƙarfinsa ya riƙe shima, haka Abbah yake bin igiyar yake tafe a hankali, haka yake cilla hannayensa yake kama igiyar har sai da yazo tsakiya igiyar ta fara shirin tsinkewa, A ruɗe Razhdeen ya ce "Abbah too fast, kana sauri Please igiyar ta kusan yankewa..." Muryar Abbah ne ya fara rawa yana faɗin "ai daman na gaya maka, so kake dai kawai na mutu, ban san me na tare maka a duniya ba..." Nan da nan Abbah ya ƙara sauri yana isa ya riƙe bakin rami dai-dai lokacin da igiyar ta yanke, da sauri Sojoji suka riƙo hannunsa, su biyu suka jawo shi sama anan Abbah ya samu ya kuɓuce... Razhdeen sauƙe nannauyar numfashi yayi yana hamdala, Baiwar Allah tana hawaye ta ce "to ni ɗin ya zakayi da ni? wallahi bazan iya yin irin yanda Abbah yayi ba ina kallo igiyar ta yanke, kuma bazan iya yin tsalle ba..." Razhdeen riƙo ta ya yi cikin ɗaga murya yake sanar wa sojojinsa cewa "Guys get ready..." Duk suka kasance cikin shiri domin sun fahimci mai yake nufi, riƙe hannunta ya yi duk biyun ya ɗaga ta sama nan ya fara hajijiya da ita, ba abinda take sai ihu, sai da ya yi nisa a hajijiyan da yake da ita tukun yayi wurgi da ita, bata faɗa a hannun kowa ba sai a hannun sojojin da sukayi shirin karɓar ta, ita kuwa nan da nan har ta sume a wurin, daga baya shima Razhdeen ya tsallako, ɗaukanta yayi ya sake goyata a baya suka yi gaba, sai da suka ɗan yi tafiya kaɗan kafin ta samu farfaɗo wa, ganinta a bayan Razhdeen yasa ta yin hamdala domin a tunanin ta ta sheƙa ne... Shiga cikin wani kogo suka ƙara yi anan suka tarar da wani rami wanda dole sai ka shiga ciki, nan ne hanyar wuce wa, wurin tsantsi gareshi kamar lilo, idan zaka shiga sai ka zauna tsantsin wurin ya zamar da kai cikin ramin, Abbah ya ce "wai wannan wani irin tashin hankali muke fuskanta ne? ina Roshan yake son zuwa ne kodai shima ya zama Aljani ne kam, kar muje mu kai kan mu wurin da zamu hallaka..." Razhdeen ya ce "Dad kawai mu je..." Sojan farko ne ya fara zama sai yayi sululu ya wuce cikin ramin, haka sojan na biyun yayi, sai Abbah bayan ya shiga sai da Razhdeen ya ɗaure bakin Baiwar ALLAH da mayafin ta da ya tafo da shi, haka ya ɗaure mata baki gamm gudun kar tayi ihu sannan ya zaunar da ita ya tura ta ciki, haka take zazzaro ido waje tana son yin ihu amma ta kasa har sai da ta je ƙarshe, shima ya biyo bayanta, duk faɗawa suka yi cikin wani dusan ƙanƙara da hanzari suke miƙe duk suka nemi wuri suka ɓuya a cikin lawani, Abbah da sojoji biyu suna ɓangare guda cikin lawali, Razhdeen da Baiwar ALLAH suma su biyu a gefe guda, ta gaba kaɗan kuma Roshan ne yake tsaye a bakin ruwa wanda baka iya hango ƙarshen sa, duk bai san ana biye da shi a baya ba amma Aljanin da yake bashi hanya yasan da zuwan su sai dai bai tanka musu ba saboda shi ɗan aike ne, rakiya ne aikinsa saboda haka ne yasa bai dakatar da su ba.. Abbah a cikin ransa ya ce "mai wannan yaron yake anan kuma?..." Kowa da saƙe-saƙen da yake a ransa, duk basa son Roshan yasan da zuwan su har sai sun ga me zai aiwatar... Roshan cikin ɗaga murya ya ce "gani nazo gare ku, ku kawo mun Reemah ina nan jiran ku, Reemah ki fito ga Yayan ki Roshan yazo gare ki..." Duk su Abbah suna jin abinda yake faɗi suna laɓe, Baiwar ALLAH itama idonta akan Roshan bayan ta since ɗaurin bakinta, duk idonsu akan sa cikin ƙanƙanin lokaci suka ga Ƴar Amana ta bayyana a bakin ruwa tana zaune, Roshan da gudu ya isa wurin ta yana ƙiran sunanta, yana zuwa ya rungume ta sosai, itama rungumar sa tayi tana kuka.. Baiwar Allah cikin tsoro da fargaba ta buɗe baki zata kurma ihu Razhdeen ya yi saurin toshe mata baki da hannunsa, Abbah shima abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, Ƴar Amana miƙewa tayi tsaye cikin nuna farin ciki take faɗin "Yaya Roshan na dawo, na dawo Yaya Roshan bazan sake barinka ba, yanzu na zama cikakkiyar mutum kamar kowa..." Cikin farin ciki Roshan bai ma san me zai ce ba haka ya ƙara rungumar ta yana shashshafa mata sumar kanta... Baiwar Allah tana tsugune ta fara jin motsi ta wurin ƙafar ta, idonta ta sauƙar akan wani ƙaton maciji a nannaɗe, a ruɗe ta miƙe bata san lokacin da tayi tsalle ta fita da gudu tana sakin ihu mai ƙarar gaske, a firgice tayi kan su Roshan da ihu.. Ba shiri Roshan da Ƴar Amana suka rabe da juna duk suka kallo wurin da ake ihun, ganin Baiwar Allah ta nufe su yasa Roshan ƙarasa wa wurinta yana faɗin "Ammata meya kawo ki wurin nan?..." Ita kuwa ba abinda take faɗi sai "Maciji! Maciji!! Maciji ne wallahi!!! Yaya Roshan Maciji na gani wani ƙato acan wurin..." Roshan riƙe ta yayi yana faɗin "kinga ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai miki, amma taya kika zo nan?..." Jikinta na kakkarwa ta ce "ni da Abbah da Habeey da sojoji biyu muka zo..." Cike da mamaki Roshan ya ce "suna ina su ɗin?..." ta nuna wurin da suke da yatsa ta ce "suna can cikin lawali sun ɓuya..." Roshan ya ce "okay it's okay..." Ƴar Amana nufan wurin Baiwar ALLAH tayi tana faɗin "Aunty Baiwar ALLAH nah..." suna kuka suka rungumi juna... Razhdeen ganin Baiwar ALLAH ta riga da ta tona musu asiri yasa shi miƙewa ya kalli wurin da su Abbah suke ya ce "Dad muje wurinsu kawai..." duk tashi suka yi suka nufi wurin su.. Roshan yana ganinsu yasau murmushi haɗe da girgiza kai, Abbah yana zuwa ya tsaya a gaban Roshan ya ce "kai kace kazo ɗaukan Amaryar ka ne shine ba gayya?..." Razhdeen shima murmushi ya yi ba tare da ya furta komai ba, Ƴar Amana rungumar Abbah tayi tana faɗin "Abbah nahh..." Abbah cikin farin ciki ya ce "Shalele nah nayi kewar ki sosai..." haka suka gama koke-koken su daga bisani suka ga wani hayaƙi kamar guguwa ya fito musu, haka guguwar nan ta haɗa kayuwansu ta fara hajijiya da su gaba ɗayan su, daga Abbah har Razhdeen da Roshan da Baiwar ALLAH da Ƴar Amana da kuma sojoji su biyu duk a cikin guguwar, da ƙarfin gaske guguwar nan ta ɗaga su sama tana hajijiya da su, Baiwar Allah ita kaɗai ce mai ihu a cikin su, domin ita Ƴar Amana dake tasan da abun bata wani tayar da hankalin ta ba, su kuma mazan dake jarumai ne babu wanda yayi ihu amma sun yi mungun tsorita, lokacin guda guguwar ta ɓace da su ɓattt... A babban falo duk matan gidan sun hallaru ko wacce tana riƙe da Alkur'ani a hannunta duk suna sanye da hijab, Ammy da Hajiya Kilishi suna kujera ɗaya suna karatu, minal kuma a one seater itama da Kur'ani a hannunta, Ummy da Pinky da Rukky su ma suna zaune a Three seater suna karatu, Ƴar tinny itama tana zaune a gefe guda har da ita ake karatun, kowa ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba na rashin ganin su Abbah wuni guda gashi har ana shirin ƙiran sallar mangariba... Afaf da Ra'ees kuma suna can bedroom suna shan baccin su... Tafiya ba sallama babu wanda yasan da tafiyar su, Baiwar ALLAH suna tunanin ko tana tare da su Abbah, ga Roshan da Razhdeen suma basa nan... Suna cikin karatun su bayan sun yi Addu'o'i kwatsam suka ga mutane daga sama an ciccillo su, duk dokuwa suka yi a tsakiyar falo, Ai kuwa haka kowa ya ajiye littafinsa duk suka bar falon da gudu suna ihun neman agaji, sunyi tunanin Aljanu ne, iya Ammy kawai suka bari a zaune ta rufe ido sai jero Addu'o'i take, Hajiya Kilishi kam ba'a san lokacin tashin ta ba nan itama ta fece ɗaƙin da duk yaran gidan suka shige, A ɗaki ɗaya duk suka hallaru suna sauƙe numfashi, Hajiya Kilishi da yaranta gaba ɗaya haka zuciyar su take ta bugawa da ƙarfi-ƙarfi tsabar tsoro... Ammy buɗan idon da zata yi ta tarar da su Abbah, Razhdeen ne ya fara miƙe wa yayo kan Abbah ya tallafa masa ya tashi tare da zaunar da shi akan kujera, shima Roshan tashi yayi ya ɗago da Baiwar ALLAH da Ƴar Amana sai kuma sojojin da suka miƙe suma, Ammy cike da mamaki take bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya tana zazzaro ido waje.... Typing ✍️ Asmeetah writer *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 91 to 95 A falo suka cigaba da zama kowa jiki a ma ce babu ƙwari domin ba ƙaramin gajiya sukayi ba, Á yau Abbah ya ƙira Malaminsa yazo yayi Addu'o'i, ya yi magani sosai wa Reemah sannan ya ba da magani akan kowa ya shafa akan goshi, Baiwar Allah itama karɓa tayi ta shashshafa sannan ta shafawa Ƴarta Biju Mama ta ko ina, Ummy uwar masu gida itama shafawa tayi akan goshi sannan ta buɗe ƙaton cikinta ta shafa, Ammy ta ce "ha'a Ummy har da tumbin ma?..." Ummy ta ce "Ammy bar ni kawai ai dole na shafa wa Babyn cikina shima ya samu kariya..." duk sukayi dariya. Itama Minal shafawa tayi ita da yaranta biyu duk maza, babban ɗanta da wanda take goyo yanzu... Pinky itama shafawa tayi akan goshi da tumbin cikin ta wanda ya girma sosai, tana nemawa ɗan cikinta kariya... Sai Rukky itama ta shafa sannan ta buɗe shafaffen cikinta tana shafawa, Pinky ta ce "ke kuma me zaki shafawa cikin nakin da babu komai a ciki..." Rukky ta ce "wa ya gaya miki to naje an gwada ni nima inada cikin wata biyu, kinga dole na shafa kar amun gadara..." Minal ta ce "to ikon ALLAH meye abun gadara wanda in kinje labour sai kin mance kan ki..." Duk dariya suka yi cikin raha. Hajiya Kilishi ma ta Shafa sannan ta shafa wa Autar ta Ƴar tinny, sai Ammy itama ta shafawa Ra'ees yaron Roshan... Abbah ma ya shafa sannan yasa Roshan shima ya shafa, Razhdeen ne ya nuna gardama akan shi bazai shafa wannan abun ba, daƙer daƙer Abbah ya tilasta masa ya shafa ba'a son ransa ba, Malamin ya sanar musu cewa "wannan maganin yanada matuƙar tasiri a jikin ɗan Adam, ƙamshin maganin Aljanu basa son sa balle su raɓi jikin mutum, sannan maganin ratsa jiki yake wanda zai zauna ne har ƙarshen rayuwa, ya tabbatar musu cewa da yardar Allah wani Aljan bazai ƙara raɓen jikin wani daga cikin yaron gidan nan ba... Anan Abbah ya masa godiya sannan aka sanar cewa gobe za'ayi sauƙar Alkur'ani mai girma a gidan gaba ɗaya na tsawon kwana uku... Ɗaya bayan ɗaya haka kowa ya watse zuwa ɗakinsu domin suna buƙatar hutawa... Bayan kwana biyu duk Abbah ya hallara su a falo, sai da yayi musu nasiha mai ratsa jiki sannan ya ƙarfafa musu gwiwa akan rayuwar Auren da zasu yi, a wannan ranar ne aka yanke bikin Razhdeen da Baiwar ALLAH, Roshan da Reemah zuwa nan da sati biyu, Soyayyar Roshan da Reemah sai dai su bawa maƙiya mamaki domin in ka gansu sai kayi Alfahari da su, domin soyayya suke zubawa na bugawa a jarida, kullum suna manne basa rabuwa, sometimes Reemah takan bi Roshan zuwa hospital saboda ta taya shi aiki, yanzu soyayyar Roshan ya maye mata gurbin komai a cikin zuciyar ta, domin sai ta wuni bata ga Biju Mama ba tana can tare da mijinta Roshan... Su ma ta ɓangaren su Razhdeen sai abinda ya ƙaru a soyayyar su, rayuwa suke kamar ma'aurata ga ƴarsu a tare da su, dake yanzu Biju Mama ta dawo hannun uwarta ganin Reemah yanzu ta makance akan soyayya, Baby Ra'ees kuma yana hannun Ammy ita take rainonsa... ★★★★★ Bayan sati Ummy ce ta tashi da naƙuda, cikin ikon Allah ta haifi ɗiya mace bayan kwana biyu itama Pinky ta haifo ɗiya mace, a cikin kwanakin nan gidan Abbah cike suke da farin cikin samun ƙaruwa har mutum biyu ga shirye-shiryen biki yana ta matsowa, sauran Rukky ce kawai ta saura wacce ƙaramin ciki gare ta bai wuce 3months ba... A yau ranar Wednesday Aunty Yolash tana zaune a falo ita kaiɗai tana bawa Ra'ees madara, jin sallama yasa ta ɗago tare da amsawa, Abbah ta fara gani ya shigo sai Mai martaba, bayan su kuma sai wani babban mutumi dake biye da su kana ganin sa kasan hutu ya zauna masa, asalin mai kuɗi ne domin baya zaman Nigeria, yana gudanar da kasuwancin a can ƙasar London... Aunty Yolash ganin mutumin yasa ta miƙe tsaye tana zaro ido cikin tsoro da fargaba, a ruɗe murya na rawa ta furta "Mansur...." Shima tsayawa yayi yana kallon ta ya ce "Khadijah..." Abbah ne yayi masa iso da cewa "ka shigo ka zauna mana..." Haka ya shigo cikin tausayawa kansa da kuma Aunty Yolash, duk zama suka yi su huɗu a falon, Abbah da Mai martaba da kuma mutumin da ake ƙira da Mansur sai Aunty Yolash, Abbah ya ce "to Alhamdulillah yau dai zan kawo ƙarshen wannan al'amarin da ya kasa wuce wa..." ya kalli Aunty Yolash sannan ya ce "Saboda shi kika ƙi yin Aure yanzu kinada shekara kusan arba'in a duniya, kuma shima Mansur saboda ke yaƙi yin Aure tsawon shekaru yana gudanar da kasuwancin sa a ƙasar waje, to yanzu lokaci yayi da za'a kawo karshen wannan al'amarin..." Aunty Yolash tana hawaye ta ce "aka ce Mansur ya yi hatsarin a jirgi ya mutu ashe duk ƙarya ne kawai so ake a rabani da shi..." Mansur ya ce "Khadijah wannan shine solution da nake da shi, iyayena basa son Aure na da ke, hakan yasa suka nema mun wata a cikin dangi, a lokacin na ƙi karɓar yarinyar a matsayin matata na dage akan sai ke, iyayena suka ce idan har ke zan Aura sai dai na mutu banyi Aure ba, duk wata hanyar da zan bi akan na mallake ki babu mafita, na yanke shawara akan nazo na same ki mu gudu muje muyi Aure kika ƙi amincewa, sannan suma iyayenki suka ce bazasu bani Auren ki ba tunda iyayena basa so, daga lokacin na shiryawa kaina mutuwa a idon kowa yanda zan yi nisa da kowa, akwai wani jirgi da yayi hatsari nasa aka sa sunana a cikin waɗanda suke cikin jirgin, ni kuma na wuce ƙasar wajen da babu wanda ya sanni, anan nake gudanar da kasuwanci na, sannan nayi alƙawari a kaina cewa bazan taɓa yin Aure ba indai ba ke ba, tsawon shekaru babu wanda yasan a yanda nake kowa ya ɗauka cewa na mutu amma duk da hakan ban daina bibiyan yanda kike ba, duk wani motsin ki akan idona yake, ganin kema har yanzu kina nan kin ƙi yin Aure saboda ni yasa na bayyana kaina a yanzu domin bazan so ki ƙare rayuwarki a haka ba, zan so kema Allah ya ɗauki rayuwarki a gidan mijinki, inasonki Khadijah har zuwa yanzu har kuma ƙarshen rayuwata...." Aunty Yolash tana kuka ta ce "kana nufin ka dawo gareni?..." Mansur ya ce "na dawo gareki Khadijah..." Aunty Yolash ta ce "naga ƙiyayya ta a idon iyayenka shin taya yanzun ma zasu amince maka?..." Mansur ya ce "na dawo na samu iyayena cikin ƙoshin lafiya na kuma nemi gafarar su akan ƙaurace musu da nayi sannan sun goya mun baya akan nazo na nemeki bayan sun ji labarin har yanzu bakiyi Aure ba..." Aunty Yolash ba ƙaramin farin ciki ta shiga jin wannan kyakkyawan labari, hawayen farin ciki kawai take zubdawa... Anan Abbah ya yanke cewa a rana ɗaya za'a haɗa bikin su Razhdeen da na Aunty Yolash.... Bayan kowa yaji labarin Auren Aunty Yolash ba ƙaramin mamaki kowa ya sha ba domin har an fidda zaton zata yi Aure, ba ƙaramin farin ciki kowa ya tsinci kansa ba, Auran mutane uku duk a lokaci ɗaya sannan ga hidimar suna na haihuwan mutum biyu... Ana washe garin ranar ɗaurin Aure gida ya cika fam da al'umma dake Abbah mai jama'a ne da zuriya har da ƴan ƙasar waje, duk wanda yaji har da Auren Aunty Yolash ko mutum bashi da niyyar zuwa sai yaje domin tayi farin jinin mutane, ƙawaye da mutanen ta na bauchi, kowa yana ta shabta, Amare duk suna killace Amreesh da Reemah ita kuma Aunty Yolash tana wani ɓangare daban ita da ƙawayenta domin ita ɗin babba ce bata son shiga hidimar yara... A washe garin ranar juma'a a masallaci aka ɗaura Auren su gaba ɗaya, Roshan and Reemah Razhdeen and Amreesh Mansur and Khadijah (Aunty Yolash).... A cikin wannan al'umma Reemah ta fito tana zazzagaya ko ina cikin mutane kowa ta gani sai ta tambaye shi Roshan, domin rabon da ta gànshi tin jiya, abokane sun riƙe su shi da Razhdeen especially Razhdeen wanda yanzu ne bikinsa na farko, abokansa sai tsiya suke masa na cewa yana saurayi ya Auri bazawara suna tsokanansa da mijin bazawara... Minal ce ta riƙo hannun Reemah a wajen cikin mutane tana faɗin "ke ina zaki je kuma? wa ya gaya miki Amarya tana yawo ne?..." Reemah ta zamar da hannunta tana faɗin "ni neman Yaya Roshan nake ban gànshi ba..." Minal ta ce "ina zaki gan shi ana tsaka da hidima, me zaki masa ai gwara ki ƙira shi a waya ko ki jira idan aka kai ki ɗakin ki sai ku haɗu..." Reemah kamar zata yi kuka ta ce "Ni gaskiya bazan iya jira ba, kuma na ƙira wayansa bata tafiya nayi kewar ganinsa sosai, so nake na gànshi Ni kam..." Minal ta ce "ikon Allah, to ai baza ki ga Yaya Roshan a halin yanzu ba..." Ƴar tinny ce tazo wuce wa da ƙawayenta ƴan uwanta waɗanda suka zo daga ƙasar waje, Reemah tayi saurin tsayar da ita tana faɗin "yawwa Ƴar tinny baki ga Yaya Roshan ba?..." Ƴar tinny ta ce "yana can waje shi da Abokansa har da Uncle Deen..." Reemah ta ce "ƴar albarka Nagode..." Da gudu ta nufi hanyar waje tana jan dogon rigar ta wanda ya sha aikin wuta dake gizner ne, kuma sai ta saje da ƴan matan baƙin da suka zo biki babu wanda ya lura da ita, Minal girgiza kai tayi tare da faɗin "Allah ya shirye ki Reemah..." Reemah a free ta samu ta wuwwuce gate ɗin gidan dake babu masu dakatarwa yau ranar kowa da kowa ne, tana fita waje ta tarar ƙofar gidan a cike tam da mutane duk maza, abokan Angwaye ne da waɗanda suka zo daga ƙasar waje da kuma waɗanda suke garurruwa gasu nan kaca-kaca, ƴan mata kuwa ba'a magana wasu suna tare da samari su, wasu a wurin bikin suka haɗu har suka fara soyayya, Reemah ido kawai ta bisu da shi, wasu ne suka lura da ita dake Amarya a duk inda take saita fita daban, nan suka fara nuna ta suna faɗin "laa wancan ba ɗaya daga cikin Amare bane?..." Wata daga cikin dangi ta ce "Reemah ce fa Amarya meta fito yi kuma?..." Acan gefe guda kuma Razhdeen da Roshan da wasu abokansu su biyar suna tsaye a jikin wata ƙatuwar mota baƙa ƙirin mai bala'in tsada alamun shigar ta zasu yi suna son zuwa wani wuri... Reemah baza idanu take tana son ganin yanda zata ga Roshan, ji tayi an dafa kafaɗarta tana juyawa taga wata ƴar uwarsu ce Fa'iziyyah, Fa'iziyyah ta ce "Reemah kina da hankali kuwa kika fito waje?..." Reemah cikin haɗe gira ta ce "ban gànshi ba, ina zan same shi?..." "Wa kike nema?..." a cewar Fa'iziyya. Reemah ta ce "Mijina nake nema ban gan shi ba..." Dariya yarinyar tayi domin ba ƙaramin dariya ta bata ba jin abinda ta ce, nuna shi tayi da yatsa tana faɗin "wancan ba shi bane? naga suna shirin shiga mota..." Dasauri Reemah ta kalli wurin da ta nuna, cikin farin ciki tana washe baki ta ce "yawwa shine wallahi..." nan ta tafi da gudu tana ƙiran sunan sa "Yaya Roshan! Yaya Roshan!! Yaya Roshan!!!..." Duk waiwayowa akayi ana kallon ta jin yanda ake ƙiran sunan Roshan, Shima Roshan juyawa ya yi yana kallon ta, wani daga cikin abokan sa ya ce "wancan kamar Amaryar ka..." Wani daga cikin su ne ya ce "buro uba shiyasa bazan taɓa Auran yarinya ba wallahi, domin yarinta zata rinƙa nuna mun har na bugeta..." Razhdeen murmushi ya yi tare da kawar da kansa gefe... Tana isowa ta rungume shi tana faɗin "wallahi har naji daɗi a raina ganinka da na yi..." Idon kowa akan su, Roshan ya ɗago ta tare da faɗin "akwai abinda ya faru ne Shalele?..." tana turo baki ta ce "naga tin jiya ban ganka ba, kuma idan nayi kwana biyu ban ganka ba bazan iya cin abinci ba da bacci..." Roshan ya ce "to ai ba ke kaɗai bace Amarya su da basu ga mijinsu ba ai basu damu ba..." Reemah ta ce "to kuma ai ba za'a haɗa soyayya ta da nasu ba, ni nafi su shiga shauƙin soyayya..." Roshan ya ce "okay to yanzun kin ganni ko, ma za koma gida..." Kamar zata yi kuka ta ce "to to ina zaka je naga zaku shiga mota?..." Roshan kallon mutanen wurin yayi yaga duk idanunsu akan sa suke ya ce "kinga Shalele baki ga ina tare da abokaina bane? tare zan fita da su..." Ta ce "Yaya Roshan zan bi ku..." yayi saurin katse ta da cewa "ina? a'a bazai yu ba, ya kamata ki san cewa Amarya tana da kunya, yanzu a idon mutane zan ɗauke ki a mota mu fita? ki koma gida..." Reemah ta ce "Ni wallahi sai na bika duk yanda zaku je, haka kawai sai kana yin nisa da ni..." Wani daga cikin Abokinsa ne ya dafa kafaɗarsa ya ce "kaga mijin yarinya wata ƙil tafiyar nan bada kai zamu yi ta ba, kaje ka zauna da Amaryar ka domin bazamu ɗauke ta mu tafi da ita ta hana mu rawan gaban hantsi ba, ƴan sirrikan da muke so mu ɗan tattauna akai bazai yu muyi ta a gabanta ba..." Wani soja a cikin su Abokin sa daga ƙasar italia ne ya buɗi baki ya ce "wallahi bazai zauna ba tare zamu tafi kuma babu yanda zamu tafi da ita, shirmen banza kawai su duk Amaren mutuwa suka yi ne da basu ga mazajen su ba, get out my friend..." Reemah ɗagowa tayi tana hararar sa tare da turo baki ta ce "eh a bar mun kaya na ko kuma mu tafi tare ehen...." Sojan ya ce "Ke get out for here before I finish you..." Roshan dafa kafaɗar ta yayi tare da faɗin "Shalele ki kwantar da hankalin ki kinji, ina dawowa zan zo mu yi hira kiyi haƙuri ki koma gida, kinga idan mun tafi tare wannan sojan zai takura mun ke kin ga yanada zafi sosai..." Reemah baki a ɗane ta ce "to shikenam..." Roshan ya ƙira wasu ƴan mata biyu daga cikin ƴan uwansa ya sanar musu akan su raka Reemah cikin gida... Reemah da wasu ƴan mata sun sakata a tsakiya har sun fara tafiya Reemah ta tsaya sannan ta juyo, su kuma su Roshan suna shirin shiga mota suka ji Reemah ta ce "Kai Sojan nan...." Duk juyowa suka yi su ma hatta Razhdeen, Sojan yana kallon yanda take cikin fushi ta ɗago ta hannayenta biyu ta danƙwale shi cikin tsoro kuwa ta juya da gudu ta nufi gida, anan tabar ƴan matan da aka haɗa ta da su... Sojan buɗe baki yayi cike da mamaki ya ce "whatt! Ni yarinyar nan zata dankwala ?..." Roshan ya riƙo hannunsa yana bashi haƙuri, sauran Abokan kuwa dariya duk suka fara yi domin Reemah ba ƙaramin dariya ta basu ba, cike da mamaki kuma wai a haka Amarya ce wacce aka ɗaura Auren ta yau, da haka suka shige mota cikin lokaci ƙanƙani suka bar wurin.... Reemah tana surutai da masifa da haka ta shige falo wanda yake cike da mutane, Aunty A'isha tana ganinta tayo kanta tare da jan hannunta suka shige wani ɗaki wanda anan Baiwar ALLAH take an gama shiryata cikin wedding gown fari tass har jan ƙasi yake, an gyara mata gashi ta gaban goshin nan gashi ne a kwance luf-luf yanda akayi wani irin design, ta sha makeUp bana wasa ba, Wasu ne ƴan mata biyu suke tsara mata kwalliya, Aunty A'isha tana shigo da Reemah ta zaunar da ita akan kujerar mirror tana faɗin "ina kika shiga ne haka ake neman ki za'a gyara ku, wa ya gaya miki Amarya tana yawo ne..." Reemah ta ce "Mama dan naje wurin Yaya Roshan shine wani soja zai mun rashin kunya ni kuwa na tanƙware shi na gudo abuna..." Aunty A'isha ta ce "ai da sai ki tsaya tinda rashin kunya zai yi miki, ban da hauka me zai kai ki wurin Roshan kuma..." Reemah buɗan baki tayi zata yi magana Aunty A'isha tayi saurin katse ta da cewa "yi mun shuru ki tsaya a gyara mun ke, kin san akwai walimar da za'ayi a can hall..." Reemah ta ce "Mama ba party za'ayi ba?..." Aunty A'isha ta ce "Aunty Yolash ta ce bata buƙatar yin party tinda bikin har da ita a ciki, walima duk za'a haɗu ayi..." Reemah tana turo baki ta ce "naso ayi party wallahi yanda za'a ƙira mana mawaƙa mu ma kamar yanda akayi a bikin su Aunty Ummy da Pinky da Rukky, amma a bikina kamar bikin mutuwa...." Aunty A'isha ta ce "to wa ya sani ne ko ke zaki mutu..." ta ƙarasa maganar tana mata dariya... Reemah ta ce "nikam bazan mutu yanzu ba, yaushe ma nayi Auren..." Ta cikin madubi Reemah ta hango Amreesh a zaune a bakin gado an gama tsarata kamar sarauniyar ƙasar india, a ruɗe ta ce "kai kai kaiiii Aunty Baiwar ALLAH so kike yau ki rikirkita Uncle Deen? innalillahi daman haka kike da wannan kyau? wallahi ba ƙaramin kyau kika sha ba..." Baiwar Allah tana zaune sai zuba murmushi take tana jinta... Aunty A'isha ce ta ce "haba ki tsaya a miki kwalliyar nan duk kin ishi mutane da surutu..." Reemah ta kuma cewa "ai kuwa dole ayi dinner party wannan kwalliya haka..." Aunty A'isha ta ce "yaushe aka gama magance matsalolin Aljanu shine zaki wani cewa dole ayi party, sai mu gani ai..." Wata budurwa ce ta shigo tare da ce musu "kowa fa ya shishshirya Amare ake jira, kar lokaci ya ƙure..." Aunty A'isha ta ce "ai wannan rigimammiyar ce duk ta ɓata mana lokaci wallahi..." Aunty A'isha tana tsaye aka gama gyara Reemah itama aka sanya mata wedding gown irin na Amreesh, duk kwalliyar ko wacce ya yi mata kyau sosai, sai dai dake Baiwar ALLAH tafi Ƴar Amana hasken fata sosai duk da itama fara ce ƴar Amana.... Kowa ya shirya tsab har masu jego suma anyi bikin suna an raɗa wa kowa sunan jariri, Ummy ta sanya wa uwar mijinta mai suna wato Maimuna, sai kuma Pinky ita kuma a uwar mijinta tayi wa mai suna sannan matar mahaifinta wato Ammy, Ummu Salamah... Motar Amare ne suka fara tashi wanda ya kasance Amreesh da Reemah ne a ciki sai wani mota daban wanda aka ɗauki Aunty Yolash a ciki tana sanye da wata danƙareriyar gizner yasha aikin wuta da ƙaton gyalenta kalar gizner ba ƙaramin kyau tayi ba itama, anan kowa da kowa suka watse aka bar gida empty babu kowa sai security da sojoji... ★★★★★★ Cikin wani ƙaton hall wanda tarin dubban al'umma ne suke zazzaune kowa da robar lemo da farror a gaban sa da kuma naman ƙatuwar dabba da aka yanka kowa da nashi a ƙaton faranti wanda naman yasha gashi, wurin ba'a shiga sai da card da sunan mutum a rubuce da photonsa, in kazo wuce wa sai sojojin wurin sun duba card idan sun tabbatar kaine sai ka wuce, A ta saman hall wani dogon kujera ne wanda ya sha kwalliya sai sheƙin haske kujerar take, ga wani table mai bada haske kala-kala a jiki wanda lemuka ne akai, a kujerar Amreesh ce da mijinta Razhdeen sai kuma a gefe guda Roshan da Amaryarsa Reemah suke zazzaune, Aunty Yolash kuma ƙin fitowa tayi tana cikin mutane a zaune, a cewar ta bazata haɗa kanta da yara ba, ita yanzu ta girma Aure kawai aka ɗaura mata amma inda ita kaɗai ce walimar ma bazata yi ba.... Kowa da kowa ya hallaru ga abokan Angwaye da ƴan uwa, har Madam Blessing itama tazo ana jiran mai za'a fara gudanar wa, wani dogon kujera aka ajiye a gaban hall da table da wata ƙatuwar jita, Razhdeen ne ya yi surprise a Reemah yanda ta iya kaɗa jita har tayi makaranta akai yayi alƙawarin idan lokacin Auren ta yazo sai kowa ya ji sautin kaɗa jitar ta, Razhdeen ne ya tashi daga yanda yake zaune yazo gaban hall tare da ɗaukan lasfika ya fara sanar wa kowa cewa "wannan jitar ba'a kowa na tanadar ba illa Ƴar uwata jinin jikina wato Amaryar twins ɗina Reemah, wannan kyauta ta ce a gareta domin tanada wata baiwa wanda ba kowa ne yasan da haka ba, sannan na tanadar da wannan jitar ne saboda ita, ina neman Alfarmar ta da ta fito ta kaɗa wa masoya zazzaƙar jitar ta mai saka mutum cikin shauƙi, wannan shine surprise ɗina a gare ta...." Lokaci guda wuri ya kaure da tafin hannayen mutanen wurin, Razhdeen ne ya juya zuwa wurin da Reemah take a zaune, da murmushi akan fuskarsa ya miƙa mata hannu, ɗagowa tayi tana kallon sa itama murmushin take ta ɗora hannunta akan nashi ta miƙe tsaye, yana riƙe da hannunta suka nufi wurin jita tana taku a hankali dake takalmin ta mai tsini ne sosai, har sai da ya kaita wurin jitar tukun ya sake mata hannu... Dasauri Reemah ta juya tana kallon sa ta ce "Uncle Deen..." ya katseta da cewa "Please my Sarah, inaso kowa yayi alfahari da gimbiya ƙanwata..." Jinjina kai tayi cikin ƙwarin gwiwa ta zauna akan kujerar ga jita a gabanta, Roshan shima cike da farin ciki da ɗaukin son jin kaɗa jitar ya zuba mata ido... Itama Baiwar ALLAH da murmushi akan fuskar ta take kallon wurin da Reemah take domin itama shaida ne akan baiwar kaɗa jitar da Reemah take da shi... Reemah zama tayi tana tunanin shin idan ta fara kaɗa jitar taya zata fara rera waƙar? ita jitar kawai ta iya kaɗawa amma bata iya waƙar ba, bazata iya bin sautin kiɗan ba, babu yanda ta iya haka ta fara kaɗa jitar, tin daga farkon sautin mutane suka fara ihu ana tafa hannaye, anan Reemah ta samu ƙwarin gwiwa nan ma ta dage sosai ta fara kaɗa jitar a nutse mai jan hankali, haka take kaɗawa kowa yayi shiru domin sautin irin mai ratsa zuciya ne, Akwai sauti kala-kala wanda Ƴar Amana ta iya su amma wannan sautin na daban ne, ta zaɓe shi ne saboda ta tuna lokacin da suke rayuwa a gidan marayu, idan wahala tayi wahala takan kaɗa wannan sautin ne saboda ta fi samun nutsuwa, Baiwar Allah jin kalar sautin da take kaɗawa ne yasa itama ta tuno da wahalar da suka sha a gidan marayu, lokaci guda ta fara zubda hawaye, wanda itama Ƴar Amana zubar da hawaye take idanuwanta a lumshe, duk wanda yaji wannan sautin sai ya zubda ƙwallah saboda lokaci guda sautin yake kashe zuciya, Ƴar Amana kaɗa jitar take a hankali dai-dai lokacin da wata sautin murya ta fara fitowa tana bin sautin kiɗan, a hankali Ƴar Amana ta fara buɗe idanuwanta domin tasan muryar Baiwar ALLAH ce, saboda ita kaɗai ce ta iya bin sautin kiɗan nan take rera waƙar, murmushi tayi domin hakan yasa ta zaɓi wannan sautin saboda tasan indai Baiwar ALLAH taji sai ta rera waƙar ta, domin ita ta ƙirƙiri waƙar kamar yanda Ƴar Amana ta ƙirƙiri sautin, Haka ƴar Amana ta cigaba da kaɗa jitar itama Baiwar ALLAH miƙe wa tayi tsaye tana rera waƙa... Wasu ma'aikata ne suka kawo wani abu mai tsayi na fitar da murya, zuwa tayi ta tsaya a wurin bakinta a saitin abun idonta akan Ƴar Amana, lokaci guda suka sau wa junan su murmushi nan suka fara, wannan tana kaɗa jita mai daɗin sauraro wannan kuma tana rera waƙa da zazzaƙar Muryar ta, Razhdeen cike da mamaki ya sake baki yana bin Baiwar ALLAH da kallo, dasauri ya dafe kansa yana tariyo kalar muryar nan haɗe da sautin da yake sauraro a cikin mafarkinsa a kwanakin baya, already ya gano Ƴar Amana ita ce mai sautin amma har zuwa yau bai samo mai muryar ba sai yanzu da Allah ya nuna masa, a hankali ya furta "Reesh! daman ke ce? ke ce daman? muryar ki ce how comes ban san da hakan ba sai yanzu?...." Haka yake ta maganar zuci cike da mamaki, bai damu akan Ƴar Amana ba shi damuwar sa da kuma abinda ya firgita shi shine Baiwar ALLAH, tayi masa tsantsar bazata bayan ya bata labarin duk halin da ya kasance a baya hatta sautin Muryar da yake ji amma bata taɓa sanar masa cewa ita ce kuma tasan ita ɗin ce, tinda a labarin har da ƴar Amana... Roshan jikinsa ne yayi mungun sanyi shima jin waƙar da sautin duk kashe jiki gare su, na tausayawa ne kuma kamar labarin wahalar da suka sha ne a cikin waƙar, sauran kaɗan ya zubda ƙwallah... Kaf matan wurin babu wacce batayi hawaye ba, hatta mazan wasu sunyi hawaye wasu kuma jurewa kawai suke, Suma Baiwar ALLAH da Ƴar Amana duk kuka suke domin kaf labarin su ne a cikin waƙar... Aunty Yolash da Aunty A'isha da Aunty Maimuna da Ammy da Hajiya Kilishi da Madam Parveen da Minal da Pinky da Rukky da Ummy da sauran duk kuka suke... Sun daɗe suna waƙar kafin suka dakata ko wacce tayi nisa a kuka duk sun ɓata fuskar su da hawaye, Baiwar ALLAH tana tsaye idonta a lumshe sai kuka take, ji tayi an dafa kafaɗarta ta baya, a hankali ta juya ta buɗe idonta a nutse haka take bin ƙirjinsa da kallo har ta ɗage kanta sama ta haɗa ido da Razhdeen wanda shima ita yake ta kallo fuska ɗauke da damuwa a hankali ya furta "ke ce?..." Ɗaga masa kai tayi alamar eh lokaci guda ta fashe da kuka, tasa hannu ta rungume shi shima rungumarta yayi sosai a jikinsa... Ƴar Amana itama kifar da kanta tayi akan jitar kuka take sosai kamar ranta zai fita, Roshan ne ya taso yazo yanda take cikin tausayawa yasa hannu ya ɗago ta tare da rungumar ta sosai a jikinsa, itama zagayo da hannayenta tayi ta bayansa ta rungume shi sosai tana kuka... Daƙer kowa ya dawo cikin hayyacinsa suma Amaren aka rarrashe su duk kowacce ta koma wurin zamanta ita da mijinta, Daga bisani Aunty Yolash ta fito tana sharar hawaye, itama ta gudanar da wa'azinta na gaske mai ratsa zuciya, Aunty Yolash wa'azi tayi sosai kuma daman Malama ce tanada haddar Alkur'ani akanta da fassara ga littafai na hadisai da A'halari kaf litattafan musulunci kusan ko wanne tayi karatu akansa, nan ma sai da kowa ya zubda ƙwallah domin wa'azin ya shafi imani ne da kuma mutuwa... Wasu ƴan mata da yawa sunyi tunanin party za'ayi sai suka ga akasin haka, wata kam kuka ta fara yi tana faɗin "nayi tunanin zamu zo mu kwashi rawa ne ashe kawo mu wurinda zamuyi ta kuka akayi, har tsoro da fargaba ya kamani wallahi, yanzu zan fara yin Sallah akai-akai tinda ita mutuwa bata yin sallama..." Sai da Aunty Yolash ta kammala wa'azin ta itama har da sharar hawaye tukun ta dakata haka, kafin ta sauƙa daga mambari sai da mai ɗaukan photo ya ɗaɗɗauke su a photo ita da Amare da Angwaye, ƴan uwa duk zuwa suka yi akayi photuna sosai ko wacce sai da akayi photo da ita, mijin Aunty Yolash shima fitowa yayi akayi photon da shi, daga bisani Aunty Yolash tayi musu sallama akan zata koma gida sakamakon ciwon da kanta ke yi tsabar hayaniya, anan ta bar su, mijinta ne ya ɗauke ta a mota ya komar da ita gida, Sojoji ne suka buɗe musu gate suka shige har can cikin harabar gidan, kafin su fito daga cikin motar sai da suka ɗan sha hirar su, Aunty Yolash ce ta sanar masa cewa "Mijina zan je na sha magani sai nayi sallah naga ana shirin ƙiran mangarib kafin mutanen gidan su dawo..." Mansur ya ce "amma kisa a ranki cewa yau zamu kasance a tare gida ɗaya, za'a kai ki ɗakin mijinki kema..." Murmushi tayi sannan ta ce "yau za'a kaini ɗakina, Allah Ubangiji yasa na tarar da alkhairi..." Ya ce "insha Allahu alkhairi zaki tarar har ƙarshen rayuwar mu..." Ta ce "to sai da safe..." Yayi saurin katse ta da cewa "sai da safe kuma? naga a yau ne ko wacce za'a kaita ɗakin mijinta..." Cikin zolaya Aunty Yolash ta ce "Au hakane fa ashe, amma kafin nan nasan duk zamu hallara a babban falon Abbah saboda gudanar da nasiha..." Mansur ya ce "hakane shikenam sai zuwa anjuma..." Ana suka yi sallama cikin so da ƙaunar juna, Aunty Yolash tana shiga falo ta tarar wayam ba kowa haka ta nufi ɗakin da ba'a fiye shigar sa ba domin bata son hayaniya kuma yanzu mutanen gidan zasu dawo, Bayan ta shiga bedroom ta ajiye gyalenta da jakar hannunta ta shige toilet ta ɗauro alwala sannan ta zo ta zura hijab har ƙasi ta tsaida sallah, tayi raka'a uku na sallar mangarib sannan tayi raka'a biyu na lafula tana son godewa Ubangijin ta da ya nuna mata ranar Auren ta da mijin da take matuƙar ƙauna, A sujjadar ƙarshe ta fara jero Addu'o'i tana godewa Ubangiji..... Sai yanzu kowa ya fara dawowa gida jiki ba ƙwari, Amare suna dawowa aka nufi wani ɗaki dasu saboda su huta ko wacce ta dawo hayyacinta, kowa yayi farin cikin gudanar da walimar da akayi saboda ko ba komai mutane da yawa sun ƙaru, sun ilmuntu, wasu da dama masu aikata miyagun ayyuka sun shiryu, masu wasa da Sallah sun tsorita jin wa'azin da aka gudanar, imani ya shige su sosai.... Aunty Yolash tana kan sallaya ta roƙi kowa akan bata son ganin mutum a ɗaki saboda tana buƙatar hutawa, har akayi sallar isha'i ta tashi ta tsaida sallah.. ★★★★★ Bayan sallar isha'i su Abbah suma sun dawo da mai martaba da kuma Chief duk suka hallaru a babban falon Abbah wanda ba kowa ne yake shiga ba, Abbah yasa a ƙira masa duk mutanen gidan banda baƙin da suka zo, Razhdeen da Roshan da Yarima Ashmar da Arash da Mohandas da Rakesh da kuma mijin Aunty Yolash Mansur, a ɓangaren mata ma duk an ƙira su, Ammy da Hajiya Kilishi da Madam Parveen da Minal da ƙanenta, sai Amreesh da Reemah wanda aka ƙara shirya su cikin wani danƙareren swizlace iri ɗaya domin daga falon Abbah za'a wuce da su ɗakin mazajen su, duk kowa ya hallara banda Aunty Yolash, Abbah ne ya kalli Rukky ita da ba yaro a hannunta ya ce "je ki ƙira mun Auntyn ku...". Rukky tashi tayi ta fice, kai tsaye ɗakin da Aunty Yolash take ta nufa ga baƙi a falo yanda suke ta shan kallon su wasu kuma suna cin abinci, Rukky knocking ta fara yi tana ƙiran sunan Aunty Yolash, jin shuru yasa ta buɗe ɗakin ganin ta akan sallaya tayi sujjada yasa ta juya tare da rufe ƙofa, ta koma falon Abbah ta sanar cewa "Sallah take..." Nan suka sake wani sabon zama wurin awa guda Aunty Yolash bata zo ba, Abbah ya kalli Ammy ya ce "kije ki ƙira mun ita kice ita muke jira..." Ammy ta tashi ta fice, Itama ɗakin Aunty Yolash ta shiga still ta tarar da ita akan sallaya tayi sujjada, Ammy ta ce "wani irin sallah kike ne Auntyn yara..." Ammy ta zauna a bakin gado tana jiran ta ɗago nan ma sai da tayi mintuna kafin Ammy tasa hannu ta taɓa ta tana faɗin "Auntyn yara lafiyar ki kuwa..." gani tayi Aunty Yolash tayi gefe ta faɗi ƙasi, a ruɗe Ammy ta furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Auntyn yara meya same ki ne?..." Ammy ɗagota tayi tana tattaɓata ganin bata motsi yasa ta ajiye ta akan sallaya ta miƙe da gudu ta fice a ɗakin, Da gudu Ammy ta wuce mutanen falon ta fice kai tsaye falon Abbah ta nufa wanda har sun gaji da jira, a ruɗe Ammy ta shiga tana haki, a tsorace Abbah ya miƙe tsaye yana tambayar lafiya kuwa?..." Nan Ammy ta sanar musu a halin da ta ga Aunty Yolash, a firgice Abbah ya fice shima da gudu haka mai martaba da mijinta da sauran gaba ɗaya duk ɗakin da Aunty Yolash take suka shige, akan sallaya suka tarar da ita, nan Abbah ya ɗagota ya ɗorata akan gado yana faɗin "A ƙira Doctor, ku ƙira mun Doctor..." Ammy girgiza kai tayi domin tasan babu wani sauran numfashi a jikin Aunty Yolash amma bazata iya sanar da hakan ba, Roshan ne ya riƙo hannunta yana dubawa ya taɓa sai tin wuyanta ganin babu alamun numfashi kuma duk wasu alamun mutuwa ya gani a tattare da Aunty Yolash, A ruɗe Roshan ya miƙe tare da ja da baya yana furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..." Dafe saitin zuciyarsa yayi jin bugawar da yayi, a ruɗe Abbah ya ce "meya faru da ita?..." Roshan cikin zubda ƙwallah murya na kakkarwa ya ce "a ƙira Doctor ya duba ta...". Razhdeen shima haka zuciyarsa take bugawa domin halin da ya ga Roshan yasan akwai matsala, Abbah ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba shi da Mai martaba, Mansur yana manne a jikin gini haka jikinsa yake kakkarwa, matan kuwa duk har sun fara hawaye... Abbah a kiɗime ya ƙira Doctor akan yazo ya duba jikin Aunty Yolash, Cikin lokaci ƙanƙani sai ga Doctor ya shigo, Roshan da sauri yabar ɗakin yana sharar hawaye itama Ammy fita tayi domin bata son ganin halin da zasu kasance, Doctor yana duba Aunty Yolash ya fara girgiza kai cikin nuna damuwa ya ce "Allah Ubangiji ya gafarta mata, ta riga mu gidan gaskiya..." daga nan Doctor ya yi tafiyar sa... Abbah baya yayi zai faɗi sakamakon hajijiyan da yake ɗaukansa, dasauri Razhdeen ya riƙo shi tare da zaunar da shi a bakin gado, Mai martaba bai san lokacin da ya zauna akan sallayar dake shimfiɗe ba gaba ɗaya ya ɗauke wuta, Hajiya Kilishi jan yaranta tayi gaba ɗaya suka bar ɗakin ganin ko wacce tana shirin zunduma ihu, Ummy kam da jaririya a hannunta haka tasau yarinyar da sauri Hajiya Kilishi ta tare ta, ta riƙo hannunta suka yi waje, suna fita falo duk suka fara rausa ihu, kuka suke bana wasa ba, Reemah tana ɗaki ta manne da jikin bango idonta akan Aunty Yolash sai faman ƙaƙƙafewa take, Aunty A'isha ce ta rungume ta sosai a jikin ta, ta kifar mata da kanta akan ƙirjinta ta fice da ita, Baiwar Allah kuwa lokaci guda ta yanki jiki ta faɗi sumammiya, sai da Yayanta Mohandas ya ɗauke ta shima ya fice da ita kai tsaye room ɗinta ya wuce da ita yaje ya kwantar da ita, Mansur mijin Aunty Yolash kam a ruɗe yayi kanta yana faɗin "bazaki tafi ki barni ba Khadijah, ina tare da ke duk yanda kika je, ƙafata ƙafar ki wallahi bazan bari ki tafi ki barni ba, meyasa zaki mun haka Khadijah, sai da rayuwa tazo mana mai daɗi shine zaki tafi? meyasa bazaki bari mu inganta rayuwar mu ba, meyasa bazaki bari mu gudanar da zamantakewar Auren mu ba, why Khadijah! why Khadijah!! why Khadijah!!!...." Lokaci guda shima ya fara amar da jini hannunsa akan ƙirjinsa wurin zuciya, ya kifar da kansa akan ƙirjin Aunty Yolash yana tari shima lokaci guda ya tsaya cakk, kowa yana cikin jimamin rashin Aunty Yolash basu ankara da Mansur ba, sai da Chief mahaifin Baiwar Allah ya ɗora hannu akan kafaɗar Mansur zai ɗagoshi yaga shima jikinsa ya sake, dasauri Chief ya dudduba shi a ruɗe ya ce "shima fa mijin baya motsi..." Dasauri Razhdeen ya fice ya je ya ƙira Roshan, jiki ba ƙwari Roshan ya shigo da abun duba numfashi yana zuwa ya gwada Mansur, girgiza kai ya yi ya ce "Shima ya tafi..." A ruɗe Abbah ya miƙe tsaye ya ce "ya tafi ina?..." Roshan ya ce "ya tafi can..." Cikin ƙiƙƙina Abbah ya ce "kana nufin ka ce ya bita sun tafi?..." Cikin kuka Roshan ya ce "eh Abbah..." Abbah ba abinda yake faɗi illah "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..." Mai martaba kam babu bakin magana, domin a halin yanzu ba'a cikin hayyacinsa yake ba... Lokaci guda labari ya baza ko ina na cewa Aunty Yolash ta rasu ita da mijinta, Kowa ya yi jimamin rashin Aunty Yolash, ga mijinta shima ya rasu sanadiyar rashin ta. Ƙawayenta waɗanda suka zo bikinta kusan kowa bata yadda akan cewa ta mutu ba, Cike da mamaki kowa yake jijina lamarin mutuwa lokaci guda ba jinya ba komai ƙarar kwana. A wannan daren aka sanar wa ƴan uwan Mansur su ma.. Bayan kowa ya dawo hayyacinsa anan aka sanar cewa za'a bar gawar su sai zuwa gobe ayi jana'izar su, Abbah ne kawai ya ƙi amincewa ya ce "kamar yanda Allah ya ɗauki rayuwar su a yau Jumma'at to dole a daren juma'an nan za'a kai su ɗakunan su na gaskiya..." Kamar yanda Abbah ya ce haka kuwa akayi, a wannan daren akayi musu wanka aka sallace su, tare da kai su kabarin su, ga kabarin mata ga na miji, sun kwana a ɗakin su na gaskiya... A washe gari labari har a jarida aka bubbuga, a television da ko ina, wasu sunyi tunanin ko hatsarin mota suka yi sai suka ji labari yasha bambam, Ƴan uwa da abokan arziƙi duk babu wanda bai shiga tashin hankali ba, sanadiyar haka yasa hawan jinin Abbah tashi, Ana bikin murnar Aure da kuma haihuwa sai kuma mutuwa ta shiga tsakani..... Typing ✍️ Asmeetah writer *MY ENEMY* *TAKUN ƘARSHE* *BOOK 3* 96 to 100 *END OF BOOK 3* Mutuwar Aunty Yolash ba yanda bai zaga ba, ma sha ALLAH tayi Al'umma sosai, waɗanda basu zo Auren ba jin mutuwar ta yasa suka zo ta'aziyya, gidan Abbah mutane ne tam masu zaman makoki ciki da waje, motoci kuwa tsabar mutane ba'a iya shigo da mota cikin unguwar, haka gidan su miji nan ma mutane ne na fitar hankali dake babban mutum ne, Roshan kam a ɗan kwanakin nan anyi masa mutuwa mai zafi, ga na matarsa Ramlat ga kuma yanzu na Auntynsu mai shigar rai itama kwana ya ƙare, duk babu mai wargi a duk mutanen gidan, Ummy itama ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, gani take kamar zata ga Aunty Yolash a cikin mutanen gidan, yau kuka gobe kuka ta kasa kwantar da hankalin ta, Haka Reemah tinda tayi ido huɗu da gawar Aunty Yolash daga nan bata ƙara dawo hayyacinta ba, haka kawai sai tana firgita gawar ce kawai take mata gizo, ga yawan mafarkin ta, gaba ɗaya ta kasa shiga taitayinta, Baiwar Allah wacce ta farfaɗo har yanzu bata gama tabbatar da cewa Aunty Yolash ta mutu ba, bakin ta ba abinda yake furtawa illah "bata mutu ba ƙarya ne, babu alamun mutuwa a jikin ta kuma bata nuna hakan ba..." Reemah da Baiwar ALLAH tsabar suna cikin jimamin mutuwa yau har akayi kwana bakwai basu yi ido huɗu da mazajensu ba, suma haka Razhdeen da Roshan basu nemi ganin su ba har yau, domin mutuwar ba ƙaramin jijjiga kowa yayi ba, Sai da akayi kwana bakwai kafin mutane suka fara raguwa, ƴan ƙasar waje suka fara tattafiya, haka ƴan wasu garuruwa, a kwana a tashi har aka wayi gari zaman makoki ya ƙare babu mutane a gidan Abbah sai ƴan gidan, shikenam Auntyn yara ta tafi abu kamar a mafarki ya zamto gaskiya, Bayan wata biyu. A yau Abbah ya buƙaci akai Amare gidan mijinsu, har ilah yau babu wargi a jikin Abbah da Mai martaba especially Abbah, ba Amare ba hatta masu wankan jego Abbah ya sanar cewa kowa ta koma ɗakin mijinta, Dake ba wani isheshshen lafiya Abbah yake da shi ba ko rakiyar Amare ba'ayi ba, ko wacce daga gidan Abbah sai ɗakin mijinta, A yau Mai martaba ne ya fara tattaran iyalansa zasu koma ƙasar Jiddah, Aunty Maimuna da Aunty A'isha da Ummy tare da jaririyar ta sai mijinta Yarima Ashmar, duk tafiya sukayi bayan Mai martaba ya gama yiwa Reemah da mijinta nasiha da fatan alkhairi mai ɗorewa har ƙarshen rayuwar Aurensu da fatan samun zuriya masu albarka.... Washe gari itama Pinky da ƴar jaririyar ta ta tafi tare da mijinta Arash wanda tin Aure har rasuwar Aunty Yolash yake nam bai koma ba sai yanzu zai tafi da Matar sa.... A washe gari Chief Suraj Mahendra Marka shima ya hallara kan iyalansa gaba ɗaya zasu tafi wanda duk ƙasa ɗaya zasu zauna, yana tare da matarsa Madam Parveen, Mohandas da matar sa Minal da yara biyu, sai Rakesh da matar sa Rukky, shima Razhdeen ya shirya tsab da Amaryar sa Amreesh wanda zasu cigaba da zama a ƙasar U.S sakamakon komawar Razhdeen wurin aikin sojan sa wanda ya ɗauki lokuta da dama bai je ba, itama Afaf wato Biju Mama ƙin zama tayi a wurin kowa wai ita zata bi Mamanta, haka kuwa aka ɗauke ta ba'a son ran Reemah ba domin a tunaninta za'a bar mata Biju Mama, Baiwar ALLAH bata karɓi Biju Mama ba sai da Reemah ta ce ta haƙura da ita kafin Baiwar Allah ta ɗauke ta dake Biju Mama tana da matuƙar wayo tin yanzu ta gane mahaifiyar ta, suma duk airport suka nufa sai ƙasar Australia 🌏.... Yanzu wanda ya rage shine Roshan da Amaryarsa Reemah wanda shima sun shirya tsab zasu koma ƙasar Egyph wanda anan babban hospital ɗin Roshan yake, ya zuba ma'aikata a asibiti sai haɓaka yake yana ƙaurin suna duk da baya can da zama, amma ana kula masa da harƙoƙinsa, yanzu ya kammala aikin da yake gudanarwa anan ƙasar Nigeria, zai koma ainihin yanda yake da aikinsa wanda zai tafi ne tare da matar sa da kuma yaron sa Ra'ees... A lokacin da zasu tafi Ammy ta buƙaci a bar Ra'ees ya ɗan ƙara wayo kafin a kai shi saboda su samu damar cin Amarcinsu, Roshan har ya yadda da hakan amma ita Reemah sai ta nuna cewa bata yadda ba, tana son zama da yaro, a cewar ta tana son Ra'ees ya tashi yana kallon ta a mazannin mahaifiyarsa... Babu yanda aka iya haka aka bar mata shi, Ammy ce tayi musu rakiya har ƙasar Egyph wanda sune kawai suka samu ƴar rakiya, ita kuma Hajiya Kilishi ta zauna tana kula da Abbah, Ammy sai da tayi kwana biyu tare da su kafin ta dawo Nigeria, gida yanzu babu kowa sai gidan yayi shiru ba daɗi, iya Ƴar tinny ce kawai yarinyar gida sai mata biyu Hajiya Kilishi da Ammy sai masu aiki... A wannan lokacin ne Abbah yayi ritaya a wurin aikin soja, saboda yanzu gani yake duniyar babu daɗi, jikinsa ba ƙwari yanzu kuma duk mutuwar Aunty Yolash ne ya saka shi cikin wannan halin, hakan yasa ya ajiye aikinsa.... A can ƙasar U.S sai da Baiwar ALLAH tayi kwana biyu a gidan su kafin aka kaita gidan mijinta dake ko wacce gidanta daban, Razhdeen shi da kansa ya ɗauki Amreesh da ɗiyarsa Afaf ya kai su gidansa wanda ya tanadar musu, dake a wurin su ba'a rakiyar Amarya, miji da kansa yake ɗaukar Amaryarsa daga baya kuma aje a duba gidan ta, wani zureren mota ne black colour wanda a ciki wani jibgegen soja ne bature yake driving, ta baya kuma Razhdeen ne sai Amreesh dake gefensa, Afaf kuma akan cinyarsa, suka miƙe hanyar new York road yanda gidan Razhdeen yake, tafiya suke babu wanda yayi magana a cikin su sai Afaf wacce take wasa da ƴar tsanar ta, Razhdeen juyowa ya yi yana kallon ta a yayinda ita kuma kanta yake kallon ƙasi tana wasa da yatsun hannunta, a hankali ya ɗago da hannunsa ya ɗora akan nata hannun ya riƙo mata su, ɗagowa tayi tana kallon sa jiki ba ƙwari, fuska a sake ya ce "meya faru ne?..." Girgiza kai tayi ta ce "babu komai..." Ya ce "Please bana son ganin ki a cikin wannan yanayin, nifa mijinki ne duk abinda yake damun ki ki sanar mun, nayi miki alƙawari duk abinda ke damunki zan magance miki shi..." cikin damuwa ta ce "ba komai ne yake damuna ba, haka kawai Aunty Yolash take mun gizo, na damu sosai da rashin ta..." Sauƙe numfashi Razhdeen ya yi sannan ya ce "she already passed away almost 2 months now, yakamata ace rashin ta yabi jikin ki yanzu, ki daina damun kan ki saboda a rayuwar nan duk mai rai mamaci ne, shin kin manta mutuwar Ramlat matar twins? ita fa barin jariri tayi gashi yanzu sai dai labari, everything has passed, shi mutuwa ba yaro ba babba idan lokaci yayi sai tafiya sannan baya sallama, Please bana son ki rinƙa shiga damuwa..." Jinjina kai tayi sannan ta ce "shikenam Insha Allahu zan daina damun kaina akai, tinda dole ne mutuwar nan kuma tana kan mu da iyayen mu gaba ɗaya, waɗanda suka riga mu gidan gaskiya zan cigaba da musu addu'a..." Ya ce "ina so kimun alƙawari ɗaya..." Ta ce "ina jinka mijina, ko wani irin alƙawari zan yi maka indai bai saɓawa Ubangiji ba..." Jinjina kai ya yi sannan ya ce "bana so ki ƙara saka wani abu a ranki, duk abinda yake damunki a ranki ki sanar mu domin yanzu nine abokin shawarin ki, idan naga wani unreachable a tattare dake zamu samu matsala ne..." Murmushi tayi tare da kwanta mishi akan ƙirji hannunta a cikin sumar kansa tana bin tsayin gashin tana ja tare da yin wasa da shi ta ce "nayi maka Alƙawarin babu wani matsalar da zaka same ni da shi, nayi alƙawarin zan cigaba da faranta maka rai har ƙarshen rayuwa ta mijina Daddyn Afaf..." Shima murmushi ya yi tare da sumbatar ta akan tsakiyar kanta dake kanta akan ƙirjinsa yake, haka ya haɗe su ya rungume su daga uwar har ƴar tasun da haka suka isa gidan, Baiwar Allah gani tayi motar ta karya kwana ta nufi yanda aka buɗe wani ƙaton gate mai design kalar ruwan zuwa, a zabure ta tashi tana kallace-kallace ganin girman gidan da suka shiga, a ruɗe ta kalli Razhdeen ta ce "Habey wani irin gidane ka kawo mu?..." Murmushi kawai yayi ba tare da ya furta komai ba, Baiwar Allah wasu ɗirka-ɗirkan manya-manyan sojoji ta fara gani a jere suna tsaye samƙam da manya-manyan bindigu a hannayen su sunyi guda ashirin, goma fararen fata wato baturaye goma kuma baƙaƙen fata, motar ce tayi parking a wurin ma'ajiyin motoci wanda yawan motocin wurin sun kai arba'in ko wacce ta kalar design ɗinta, fitowa suka yi haka idanuwanta suke jujjuyawa tana bin ko ina da kallo, haɗiyar yawu kawai take domin marubuciyar ma ƙwakkwalwar ta bazai iya zayyano mata yanda tsarin gidan yake ba, tsayin gidan ba'a magana domin upstairs ne hawa-hawa a gidan, Baiwar Allah tana cikin kallace-kallace kwatsam taji kukan karnuka ata gaban su dasauri hankalinta ya dawo jikinta a tsorace ta rungumi Razhdeen tana furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..." ganin karnukan turawa ne masu buzuzun gashi yasa ta dawo hayyacinta domin a can gidan mahaifinta Chief akwai irin su, amma tsarin gidan ne har ya ci uban gidan Chief tsaruwa da girma da kuma tsayi, a hankali ta juyo tana kallon Razhdeen murya ciki-ciki ta furta "Habeey kana nufin duk girman gidan nan a ciki zamu zauna? ni kaɗai? wai?..." Murmushi ya yi yana ɗauke da Afaf akan kafaɗarsa ya ce "ɗaya daga cikin gidaje na..." Zaro ido tayi tana faɗin "kana nufin kace kanada wasu gidaje anan ƙasar bayan wannan?..." Jinjina mata kai yayi sannan ya ce "iya gidaje kawai kika lissafo, banda wasu kadarori daban-daban, kedai zaki san komai a hankali domin idan na tsaya lissafa miki zaki kusan zaucewa, muje daga ciki..." Ya ƙarasa maganar yana nuna mata hanya dai-dai lokacin da wasu mata turawa masu blue eyes su 6 suka iso wurin da suke a tsaye, duk durƙufar da kai ƙasin gwiwa sukayi suna kwasar gaisuwa, ɗaya daga ciki tasa hannu ta karɓi Afaf a hannun Razhdeen, Baiwar Allah binsu tayi da kallo cike da mamaki ta ce "waɗannan matan fa daga ina?..." Duk suna sanye da farar doguwar riga zuwa gwiwa iri ɗaya , uniform ne na aikatau kalar na ƴan ƙasar kenam, Razhdeen ya ce "waɗannan sune ƴan aikin ki waɗanda zasu na miki hidima, gyare-gyare da su wanki, girki ko meye idan kina so zasu yi miki, domin gidan nan bazaki iya gudanar da aikin gida ba, sannan zasu taya ki zaman gida idan bana nan, aikin da nake babu lokaci tin safe idan na fita bana dawowa sai yamma, kina buƙatar waɗanda zasu na ɗebe miki kewa, sannan zasu na miki rainon Afaf...." Jinjina kai Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "amma a gidan suke da zama ko kuma zuwa zasu na yi kullum?..." Razhdeen ya ce "a gidan suke sai dai idan suka ɗan daɗe zasu na kaiwa ziyara a iyayensu, ɗakunan wajen nan shine wurin kwanan su..." Sai ta waiwaya tana ganin ɗakunan kafin a shiga falon gidan, ta wajen ma sai ka haura upstairs mai hawa ta uku kafin ka iske ɗakunan su... Hura iskar bakinta tayi daga bisani ta ce "shikenam Allah yasa na iya zama da su..." Razhdeen ya ce "bangane ba? su ɗin sunada aibu ne? sunada daɗin zama da mutane sosai..." Baiwar Allah ta ce "to ai naga ba ƙabilan mu ɗaya ba, naga wasu chinoni ne a ciki wasu kuma turawa, amma basu iya Hausa ba ko?..." Dariya Razhdeen ya yi sannan ya ce "Anan kuma wa ya san miki Hausa? ko can gidan Chief kinga suna hausa ne? to yanzu ma da suke sauraron mu kallon baibai suke mana domin jin yaren suke kamar yaren jinn..." Kafin Baiwar ALLAH ta buɗe baki tayi magana har yasa hannu ya yi mata ɗaukan luɗa suka nufi ciki tare da ce mata "idan baki iya turanci ba just tell me I'll find away for you..." Bugan ƙirjinsa tayi ta ce "lallai ma Habeey baka san da turanci aka haifeni ba..." Sauran ma'aikatan gidan suma ko wacce hanyar ta tayi suka koma kan aikinsu, wacce take ɗauke da Afaf kuma bin bayan su Razhdeen tayi, suna shiga Baiwar ALLAH ta fara kallace-kallace a falo tareda faɗin "wow 😲..." sai a lokacin ya sauƙe ta, ji tayi zata lotse cikin ƙasi tayi saurin rungume shi tana ihu, riƙe ta yayi sosai yana faɗin "Please cold down, ki lura da kyau tudun carpet ne..." Baiwar Allah sauƙe numfashi take cikin tsoro da fargaba ta ce "ayyo carpet ne daman, wayyo Allah na ɗauka burmawa ƙasi zanyi ai..." Riƙo hannunta yayi ganin yanda take ta bin falon da kallo, buɗe wata ƙofa suka yi nan ma wani falon ne yana ɗauke da wasu arnakun kujeru masu lion designer, anan ne suka haura upstairs, sai da suka haura upstairs hawa bakwai kuma a ko wani upstairs guda ɗaya akwai ɗakuna a ƙalla sunyi biyu, a upstairs na bakwai suka tsaya, wani wantalelen ɗaki suka shiga wanda yake ɗauke da wata shegen gado mai designer ɗawisu, sai kujeru ata gefe da gefen gadon sai wata glass table a ta tsakiyar ɗakin, ga wata ƙatuwar plasman tana gaban gadon a manne a jikin bango, da wasu flawowi a gefe da gefen plasman, ta ɗan gefe guda kuma frig ne ɗan ƙwaƙwas gwanin sha'awa shi ba ƙato ba sannan ba ƙarami ba, sai wani ɗan matakalan beni ata gefe wanda bai wuce taku biyar ba wani curtain ne mai yanka-yanka kamar taliya kana ratsa wa sai wani ɗan dinning table wanda na iya mutum biyu ne, Baiwar Allah baki ya kasa rufuwa tsabar tsaruwan ɗakin, ji tayi an riƙo hannunta Razhdeen yana janta suka buɗe wani ƙofa again a cikin bed room ɗin wani babban ɗaki ne kuma a cikin bedroom amma na kayayyakin sakawa ne, Wasu arnakun kayayyaki ne a shirye yanda aka lallanƙaya su, layi guda duk Abayoyi ne kala-kala, layi na biyu kuma ƙananun kaya ne na kanti wanduna da rigunan su da kuma skirt kala-kala da su mini skirts da T-shirt, ga kuma ɓangaren Lace-lace da su swizlace, da layin gizner kala-kala, ga ɓangaren Atamfofi ba'a magana, kayayyaki ne a jejjere kuma duk na mata kamar shagon kayayyakin mata, yana riƙe da hannunta suka wuce can ciki wuri ne wanda a jikin bango drowowi ne daga sama har ƙasa duk wanda ta buɗe jerin takalma ne, drower thorns daban, plate-plate ma daban haka masu tudu ma daban, ga drower sarƙoƙi da ɗankunnaye da warwaraye, sai drower mayukan shafe-shafe kala-kala, duk wani kayan makeup akwai drower sa, zuwa gaba kaɗan wardrobe ne a jikin bango ƙato ga tsayi da faɗi a ciki kuwa wasu Akwatuna ne manya-manya a jere kala-kala sai wanda ka zaɓa, ga ɓangaren jakakkuna manya da ƙananu, ɗakin nan dai gaba ɗaya kayayyakin Amreesh ne, Bayan ya gama nunnuna mata ne suka fita, Bayan sun koma asalin bedroom ne ya kuma nuna mata bathroom tana fitowa daga wanka kawai zata shige ɗakin kayan sakawar ta... Kallonsa tayi ta ce "amma kuma banga naka kayayyakin ba..." Murmushi ya yi sannan ya ce "wannan ai room ɗinki ne, me zai kawo kayana nam..." Cikin farin ciki ta ce "duk waɗannan kayayyakin wai duk nawa ne? shiyasa ka hanani ɗauko kayana ko ɗaya a gida, na jikina ma sabon sakawa ne shiyasa ka barni na tafo da shi...." Razhdeen ya ce "sabon Aure kika yi kina buƙatar sabon komai a rayuwar ki, don haka ki bar maganar wasu kayan ki a gida, ga waɗannan idan sunyi kaɗan zan sa a ƙaro miki wasu sabbin kayan, ko idan babu kalar kayan da kike so now kiyi magana a kawo miki su...." Toshe bakinta tayi da hannayenta biyu tana zaro ido ta ce "kaiiii Habeey ina zan kai kayayyaki haka, a cikin waɗannan ma inaga har na mutum bazan saka wasu ba tsabar yawan su, tsabar yawan su a cikin ina ƙirgawa har na daina, kuma a ƙirgen nawan nakai ɗari da tamanin da wani abu hakan ma da yawa ban ƙirga ba, gaskiya zan ƙira mommy a waya na sanar mata cewa Akwatunana na gida a kyautar da su...." Dariya Razhdeen ya yi tare da faɗin "sai dai a aika wa yaran ƴan Nigeria su zasu fi buƙatar kayan, amma nan kam babu wanda zai saurari kayayyakin ki..." Baiwar Allah rungumar sa tayi tana masa godiya... Ya ce "bana buƙatar hakan, muje na nuna miki part ɗina..." suna fita a tare kai tsaye room ɗinsa suka shiga wanda ba rata a tsakanin su duk a upstairs na bakwai suke, Baiwar Allah tana shiga room ɗin Razhdeen taji kamar ba'a duniya take ba, Idan nace zan tsaya tsara muku yanda ɗakin yake zamu ɓata lokaci ne sosai amma ya ninka room ɗin Amreesh tsaruwa da haɗuwa da girma sosai, shima har da ɗakin kayayyakin sa kamar yanda na Amreesh yake... Suna fita suka sauƙa down upstairs wanda anan room ɗin Afaf yake na biyun ƙarshen beni kenam, shiga suka yi ɗakin Afaf ɗan ƙwaƙwas gwanin burgewa da gadon ta itama har da plasman da frig ɗinta ɗan ƙarami, ta ɓangare guda kuma computer ne a ajiye akan table wanda yake cike da Game's da videos na karatu, ga kuma abubuwan wasan yara a ɗakin har da su mota wanda zata iya shiga ita kanta da keke da dokuna, ga bathroom ɗinta itama da ɗakin kayayyakin ta a jere a cikin wardrobe su takalma da kayan kwalliyar ta a baje akan mirror, daga nan suka fice a ɗakin Baiwar Allah ba abinda take sai jinjina kai ganin ƴar yarinya ƙarama ma ba'a barta a baya ba, kayayyakinta kamar na hauka... Suna fita daga ɗakin Afaf ya nuna mata wani ɗaki yana faɗin "muje can..." Baiwar Allah kawai binsa take domin idan bata yi a hankali ba zata iya ɓata a cikin gidan nan, suna shiga wani ɗaki suka tarar da wasu irin kayayyaki na yara maza da mata wanda bazasu ƙirgu ba, Baiwar Allah buɗe baki tayi cike da mamaki ta ce "waɗannan kayayyakin yara fa?..." Murmushi ya yi sannan ya ce "kayayyakin yaran da zasu zo nan gaba, kuma nasan suna nan tafe da yardar Allah...." Baiwar Allah dariya tayi tare da bugan ƙirjinsa ta cigaba da bin ko ina da kallo har da gadon wasan su da abubuwan wasan yara, kayan kanti da takalma da kayayyakin sanyi sweaters ba'a magana, waɗannan kayan ko ƴaƴa ɗari za'a haifa a gaba iyakaci kenam, Haka Razhdeen ya nunnuna mata ko ina na gidan daga bisani suka koma public falor zasu yi lunch, akan dinning wasu irin kayayyakin abinci ne aka tanadar musu, dake dinning ɗin babbane dogo kayan abinci sun fi kala goma a ciki har da su ferfesun kaji dana kifi da eggs soups and meat da vegetable soups haɗi da tuwon shinkafa da na semo, sai shinkafa da jar miya da nama baje-baje a ciki 😋😋, sai ɓangaren kayan fruits komai da komai akwai ba sai na lissafo su ba domin wasu abubuwan ban san sunayen su ba.... Bayan sun kammala lunch Razhdeen ne ya ƙira ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ta zo, sanar mata ya yi akan ta ɗauki Afaf ta kaita room ɗinta tayi mata wanka sannan ta shiryata cikin sleeping dress sai ta sakata yin bacci... Ƴar aikin ce ta amsa masa tare da ɗaukan Afaf ta nufi da ita upstairs yanda room ɗinta yake, bayan ta je ta kammala mata abubuwa har sai da Afaf tayi bacci tukun ta fito, dai-dai lokacin da su ma suka tashi suna ɗan taku a hankali suna hira cikin so da ƙauna suka haura upstairs, wasu ma'aikata su biyu suka zo suna kwashe abubuwan da aka bari a dinning nan danan suka gyara wurin fess, sauran kayan abincin kuma ƙarshen ta zubar wa za'ayi ko a bawa karnuka domin ya gama amfani, wani kular kam ma ba'a buɗe shi ba balle aga wani irin girki ne a ciki... Baiwar Allah kafin ta ƙarasa haura upstairs sai da ta shiga room ɗin Afaf ita da Razhdeen suka tarar da ita tana shan baccin ta, Baiwar ALLAH haurawa tayi ta tottofa mata Addu'o'i kafin ta kashe hasken ɗakin ta kunna green lamp ɗakin ya ɗan bada hasken colour, daga nan suka fice a ɗakin. Razhdeen room ɗinsa ya nufa shima. itama Baiwar Allah ta shiga room ɗinta, tana shiga ta zauna a bakin gado tare da yin tagumi tana tunanin kenam shikenam sai da safe ko zamu ƙara haɗuwa, a cikin ranta take faɗin "wannan wani irin Aure ne..." bayan wasu mintuna taga Razhdeen ya shigo shima ya rufe ɗakin, miƙewa tayi tsaye tare da haɗe gira ta ce "miyasa ka dawo ka koma room ɗinka mana..." Murmushi ya yi sannan ya ce "bakya son muyi sallah mu godewa Ubangiji da ya nuna mana wannan ranar?..." Kama goshi tayi ta ce "Oh na manta mijina..." Jinjina kai ya yi ya ce "okay je ki yo alwala..." Ba musu ta shiga bathroom tayo alwala ta fito, ta samu har ya shimfiɗa musu sallaya, already shi ya yi alwalarsa a can room ɗinsa, tsayar da Sallah suka yi suka yi raka'a biyu na godewa Allah da ya nuna musu rana kamar ta yau mai tarin albarka.. Bayan sun kammala ne Baiwar ALLAH ta miƙe tare da cire hijab ɗinta tana faɗin "tam Habeey tashi ka koma room ɗinka..." Shima tashi ya yi idonsa akan ta yana nufan yanda take, ja da baya take tana faɗin "lafiyar ka kuwa Habey? shin magani ka sha ne naga sai lumshe ido kake ta yi..." Iskota yayi a yanda ta kai ƙarshen bango yasa hannu ya Cafko kunkuminta tare da manno ta jikinsa yana goga hancinsa a jikin nata, numfashin su ne yake hargutsuwa a hankali ya kai hannunsa kan sumar kanta ya since rivon ɗinta sai ga gashi ya tarwatso har gadon bayan ta, Sannan yasa hannu ya zuge mata zip ɗin rigar net ɗinta ta baya dake doguwar riga ne, Baiwar Allah ido a lumshe ta ce "Habey mai kake yi haka ne..." Ba tare da ya furta komai ba haka ya danna kansa cikin wuyanta yana kissing and socking gaba ɗaya babu abinda baya yi, nan danan ta fara fita hayyacinta, a slow ya zamar mata da rigar jikinta ƙasi sannan ya ɓalle mata breziyyar ta, a hankali ya yi mata tsiyaya cikin ƙwarewa haka ya fitar da ita daga cikin hayyacinta, magana kawai take ba tare da tasan mai take faɗi ba, "Habeey ka daina, ka daina mana Habeey, Habeey nahh...." Cikin lokaci ƙanƙani ya toshe mata bakin magana da nashi haka yake tsotsan bakinta kamar wanda ya samu lollipop, itama rungumar sa tayi ta fara mayar masa da martani, a hankali yake tafiya da ita baya har suka zo bakin gado, a tare suka faɗa saman gadon suna romance kamar zasu cinye junansu, kamar daman a matse suke, sun juma suna horar da kansu da romance kafin shima ya yi nasarar cire sauran kayan sa, ɗagowa ya yi kamar wani ɗan maye ya kashe musu hasken ɗakin ya kuma kunna blue lamp daga nan suka shige cikin mayafi, Ni kuwa Asmeetah da gudu nabar ɗakin domin bakyau ganin ma'aurata a yayinda suke aiwatar da sunnah, naje na taya Afaf kwana😒😒.... Washe da asuba daƙer Razhdeen ya ɓanɓare Amreesh a jikinsa yanda ta ƙanƙame shi bata son raba jikinta da nashi, a haka ya ɗauke ta ya shigar da ita cikin bathroom ya taya ta yin wanka sannan ta ɗauro alwala, tazo tayi sallar asuba, Shima wankan yayi ya zura jallabiyar sa ya fice a ɗakin, kai tsaye room ɗinsa ya nufa ya je ya shirya sannan ya fice zuwa masallaci dake akwai masallaci a kusa da gidan sa... Misalin ƙarfe 9 na safe Ɗaya daga cikin ma'aikatan ne ta hauro zuwa ɗakin Afaf zata duba taga ko ta tashi ta gyara ta.... Itama Amreesh ta calla wankan ta cikin wanin danƙareren lace mai bala'in tsada, ta ci kwalliya tana tsaye a jikin window tana kallon mutane turawa yanda suke ta wuce wa ta titi, dake ɗakinta a can saman upstairs yake tana iya hango wanda yake waje, ga tsare-tsaren gidaje masu kyau, wasu mutane lawanci da karnukan su suke yawo da kayan sanyin su dake ana sanyi sosai a ƙasar, wani wuri har feshin ƙanƙara ake musu, haka kawai sai zabga murmushi take, weather ba ƙaramin daɗi yake mata ba, tana cikin wannan halin taji an rungumota ta baya, juyawar da zata yi taji an sumbaci ƙasin lips ɗinta, da murmushi akan fuskarta ta juya tare da riƙo kwalar rigar sa tana faɗin "Habeey har ka tsoratar da ni...." rungumar ta yayi tare da faɗin "Reesh fatan kin tashi cikin ƙoshin lafiya..." murmushi tayi sannan ta ce "Kamar yanda kake Habeey..." Dafe saitin tumbin ta yayi sannan ya ce "naji cikin ki ya lotse nasan yunwa kike ji, muje muyi breakfast 🥞🍳...." maƙalo da hannunta tayi ta wuyansa tana rungume da shi da haka suka fita..... ★★★★★ Ta ɓangaren Roshan Shima gidan da yake ko a mafarki sai kayi da gaske kafin ka iya tsara haɗuwar gidan, gidan babbane amma bai kai gidan Razhdeen ba, shima Roshan yanada gidaje a ƙasar da yake wato ƙasar Egyph, ya zaɓi gida ɗan ƙwaƙwas ne saboda baya son hayaniya, kuma yafi son ya rayu daga shi sai Shalelen sa da kuma ɗan su Ra'ees, Mata ɗaya ne take gidan a matsayin ƴar aiki da kuma rainon Ra'ees idan Reemah tana tare da Roshan, idan kuma baya kusa to kuwa Ra'ees yana hannunta, yau ma kamar kullum Reemah ta shirya Ra'ees tas ta fito dashi falo anan ta tarar da Roshan zaune ya ɗora kansa akan pillow kujerar da yake yana kallon sama ido a lumshe, Reemah wuce shi tayi ta fice waje tana ƙwalla ƙiran sunan "Mama shosho! Mama shosho!! Mama shosho!!!..." Matar ce ta fito tana faɗin "gani nam Babey Mah..." Reemah ta ce "ina kika shiga ne inata ƙiran ki..." Matar da ake ƙira da Mama shosho ta ce "Babey Mah wanki nake shiyasa..." Reemah ta ce "ok ga nan yaro na ki kula mun da shi..." Mama shosho ta karɓe shi tana masa wasa, dake ita zuwa take ba'a zaune take a gidan ba, tin safe idan tazo bata barin gidan sai yamma kusan dare, dake matar ba yarinya ce sosai ba, kuma itama baturiya ce duk maganar da take da Reemah ta harshen turanci suke, Reemah koma wa ciki tayi a yanda ta bar Roshan anan tazo ta tarar da shi, zama tayi a kusa da shi tare da ɗora hannunta akan cinyar sa ta ce "Yaya Roshan what is going wrong?..." Ɗagowa yayi yana binta da kallo daga bisani ya ce "You're my problem Shalele..." Zaro ido tayi tare da dafe ƙirjinta ta ce "Ni kuma Yayana? me kuma nayi bayan nayi alƙawarin bazan ƙuntata maka ba, sannan Abul nah ya ce duk lokacin da kayi fushi da ni ina cikin fushin Ubangiji, dan Allah Yaya Roshan ka taimake ni kar Allah ya yi fushi da ni...." Murmushi ya yi sannan ya ce "idan bakya so nayi fushi da ke meyasa har yanzu bazaki amince da ni ba?..." Reemah kamar zata yi kuka ta ce "Yaya Roshan tinda na Aure ka ai na gama maka komai, mun faranta wa junan mu..." Girgiza kai yayi tare da faɗin "baki gama mun komai ba Shalele, kuma bakya sona da gaske..." Fashewa tayi da kuka tana faɗin "wallahi ina sonka da gaske Yaya Roshan..." Ya ce "okay yanzu satin mu nawa da dawowa nan ƙasar?..." Cikin kuka ta ce "sati biyu..." Cikin kwantar da murya ya ce "to why baza ki bari na kwanta da ke ba Shalele? muyi irin yanda ma'aurata suke, muna kwana gado ɗaya mu rungumi junan mu, muyi wanka tare..." Turo baki tayi tare da faɗin "cab amma wallahi Yaya Roshan baka da kunya, har wanka tare? kuma ni damuwa ta dakai idan mun kwanta gado ɗaya sai ka rinƙa shashshafa ni, kana abu kamar irin ƴan iska..." Dafe goshinsa ya yi yana furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un..." ya ɗago yana faɗin "look Shalele haka ma'aurata suke, ki kwantar da hankalin ki ..." ya kai hannu ya riƙo hannunta yana shirin jawo ta jikinsa, dasauri Reemah ta miƙe tsaye tana faɗin "wallahi bazan yadda ba, ni ka ƙyale ni ai lokacin da Abul da Abbah suke mana nasiha basu ce ayi wannan al'amarin ba, sunce muyi zaman lafiya ba tashin hankali..." Roshan kamar zai yi kuka ya ce "Reemah akwai tashin hankali indai baki amince mun ba, dole a wannan lokacin sai kin amince mun..." Shirin guduwa take ya riƙo ta sosai tare da mannata a jikinsa sai shashshafa ta yake yana kissing ɗinta a ko ina, ita kuwa ƙoƙarin ƙwacewa take tana son guduwa, tana ja da baya yana binta tare da aika saƙonninsa har suka riske jikin bango, ganin ya tura hannunsa cikin rigar ta yasa ta buɗe baki zata yi ihu yayi saurin haɗe musu baki, tsotsa kawai yake yana matsa mata manya-manyan breast ɗinta masu laushin gaske, lokaci guda ta fara fita hayyacinta, ido a lumshe jiki duk ya mutu haka take fitar da numfashi sama-sama domin ba ƙaramin shiga baƙon yanayi tayi ba, wani irin abu take ji yana bin jikinta wanda tinda aka haifeta bata taɓa ji ba sai yau, Shi kuwa Roshan sai faman aikin romance yake haka yake socking jikinta ta ko ina, shima gaba ɗaya ya fita hayyacinsa jin yanda yake ta matsa breast kamar wanda aka saka yeast tsabar girma da laushi, ƙirjin ta a cike yake fam dake tanada ƙirar jikin girma kamar kajin Agric, Har sunyi nisa sosai ƙarar waya ya katse musu hanzari, gaba ɗayan su ne suka dawo hayyacinsu jin yanda wayar Roshan yake ta ringing, Reemah daƙer ta zamar da jikinta tayi saurin nufan room ɗinta da gudun gaske tana shiga tasa key, jikin mirror taje ta tsaya tana sauƙe numfashi domin jikinta ba ƙaramin mutuwa yayi ba, sam babu wani ƙwarin jiki, kallon kanta tayi a cikin madubi gira a haɗe ta ce "amma Yaya Roshan ɗan iska ne wallahi, aina ya koyo wannan abun haka, kodan ya taɓa yin Aure dole ya ƙware sosai, amma kuma abun da daɗi wallahi...." Sakin murmushi tayi tana magana da kanta a cikin madubi ta kuma cewa "ba maganar wasa ba abun da daɗi sosai, tab ashe haka abun yake da daɗi? kodai na ƙara zuwa ya mun ne?..." sai kawai ta kwashe da dariya... Cikin dare misalin ƙarfe 12 na dare Roshan yana kan sallaya ya idar da sallah dai-dai lokacin da ya fara jin knocking, cike da mamaki yake bin bakin ƙofar da kallo yana tunanin waye ya zo masa, tashi ya yi yaje bakin ƙofar ya tsaya murya ciki-ciki ya ce "waye anan?..." Muryar Reemah ya ji ta ce "Ni ce Yaya Roshan..." Jin ita ne yasa ya buɗe mata ƙofar, shigowa tayi tana sanye da sleeping dress riga da wando tayi ciki ta tsaya, rufe ƙofar ya yi sannan ya zo gabanta yana faɗin "lafiya kuwa Shalele?..." Cikin kuka-kukan shagwaɓa ta ce "babu lafiya Yaya Roshan, na gagara yin bacci..." Ya ce "subhanallahi meya faru?..." Ta ce "naga duk kai ne, kai ka jawo mun rashin yin baccin..." Ya ce "me kuma nayi Shalele?..." Turo baki tayi tare da faɗin "ɗazu daka rungume ni kana shan bakina kuma kasa hannunka a cikin breziyya ta kana tattaɓa mun nonuwa na abun ya mun daɗi sosai shine na kasa yin bacci..." Roshan juyar da kansa yayi tare da tintsirewa da dariya, a cikin yana ɓoye dariyar har ya fito fili yasa hannu ya rungumeta yana faɗin "Shalele wai yaushe zaki girma ne? saboda ke Auta ce shiyasa kike nuna hali irin na ƴan last born..." Haɗe gira tayi ta ce "saboda na faɗi gaskiya shine zaka faɗa mun magana Yaya Roshan..." Ya ce "yi haƙuri Shalele yanzu gaya mun me kike so ayi?..." Anan tayi murmushi sannan ta ce "so nake ka ƙara yi mu irin abinda kayi da rana..." Ya ce "shikenam amma da sharaɗi..." Ta ce "gaya mun duk abinda ka ce zan yi Yaya Roshan..." Ya ce "idan har zamu kwana tare a ɗakin nan to zan yi miki, idan kuma bazaki kwana da ni ba kawai ki koma ɗakin ki Nima bazan miki abinda ranki yake so ba..." Dasauri ta ce "na amince Yaya Roshan zamu kwana tare..." tana murna zasu kwana zai rinƙa mata romance .. Jinjina kai ya yi sannan ya cire jallabiyar sa ya zauna daga shi sai short pant na maza, itama cire mata kayan jikinta ya yi yana faɗin "idan kika cire kayan gaba ɗaya zaki fi jin daɗin abun..." Yana lallaminta har ya gama cire mata duk kayan jikinta har pant da breziyya bai bar mata ba, haka ya kwantar da ita a tsakiyar gadon ya miƙar da ita tare da da buɗe murfin gorar zuma ya fara mata wanka da ruwan zuma, yabi duk ilahirin jikinta da wannan zumar har su matse-matsin ta da saman farjinta, ita kuwa lumshe idanuwanta tayi ta kasa buɗe su tsabar kunya, ganin yanda ya mata tsirara, yana kammalawa a hankali ya fara kai kansa wurin wuyanta ya zaro harshe ya fara socking cikin ƙwarewa yana lashe zumar jikinta, yunƙurawa take tana shure-shure jin yanda yake mata wani irin socking cikin salo, kan breast ɗinta haka yake lashe zumar kai sannan ya kafa bakin sa akan nipple ɗinta yana tsotsa cikin ƙwarewa, Reemah a cikin tana fitar da numfashi daƙer har ta komo tana nishi sosai yanzu abun takai ga yin ihu, dai-dai lokacin da ya sauƙar da harshen sa cikin farjinta, Babu abinda take faɗi illa "Yayana zaka kashe ni, wayyo numfashi na zai ɗage kar ka daina mun, ka cigaba Yaya Roshan, wallahi ina sonka sosai bazan iya rabuwa da kai ba, dan Allah kar ka Auri kowa ka zauna dani iya ni kaɗai Yaya Roshan, wayyo Yaya Roshan ina ƙaunarka sosai, ka yafe mun Yaya Roshan da tin farko ban amince maka ba, ashe cutar da kaina nake Yaya Roshan, meyasa tin farko baka sanar mun haka abun yake da matuƙar daɗin gaske ba, wayyo Aure daɗi, daɗi Aure...." Roshan kuwa shima gaba ɗaya ya fita hayyacinsa haka yake nishi-nishi bayan ya gama tsotsarta ta ko ina bai san lokacin da ya ja musu mayafi ba, ko kashe hasken bai samu damar yi ba, ita kuwa Reemah tin tinin bata cikin hayyacinta.. Bayan seconni da rufa mayafi wani irin sautin murya ne mai ƙarar gaske ya daki dodon kunnen marubuciya Asmeetah 🤣🤣🤣 "Wayyo Allah na nashiga uku wayyo Mamanaaaaa, Yaya Roshan! Yaya Roshan!! Yaya Roshan!!! Ka kashe ni na lalace, ka cuce ni macuci azzalumi ka ɗaga ni, ka ɗagani Yaya Roshan, ka ɗaga ni haka Yaya Roshan zan mutu, wallahi sai na gayawa Abbah da Abul nah kaci amanarsu, sun baka Amanata ka ci amana, wallahi bazan yafe ba Yaya Roshannn..." Reemah har tayi ihu ta shiga uku amma Roshan bai dawo hayyacinsa yanda zai tausaya mata ba, sai faman aiki kawai yake, Tsabar azaba haka ta sume akan gadon ta daina motsi gaba ɗaya, sai da ya gama yinsa tukun ya sauƙa a kanta yana sauƙe numfashi ido a lumshe, sai da ya ɗau mintuna waran talatin kafin ya dawo hayyacinsa, haka yake jin jikinsa yana masa ciwo a hankali ya juya yanda Reemah take a sume, ganin ta ido a lumshe ya ɗauka bacci take ga fuska yanda ya cakurkuɗe da hawaye, yasa hannu yana shafa sumar gashin ta cikin so da ƙauna, a hankali ya tashi zaune yana sauƙe numfashi haka ya tashi tsirara ya shige bathroom, tsayawa yayi a jikin mirror yana kallon kansa, gani yayi duk jikinsa yakushi ne da tabon cizo, girgiza kai ya yi sannan ya watsa ruwa a jikinsa ya fito ɗaure da towel, sai da ya shirya jikinsa tas cikin ƙananun kaya na bacci tukun ya haura kan gado yana son ɗaukar ta yaje ya mata wanka, ya ye mata mayafin ya yi yaga duk ta ɓata bedsheet da jini, sauƙe nannauyar numfashi ya yi tare da ɗagota domin yasan dole hakan saita faru, yau ne first night ɗinta kuma hakan yana yawan faruwa akan duk wata mai ƙaramar shekaru, haka ya ɗauke ta ya wuce da ita cikin bathroom, sai da ya haɗa ruwan zafi a cikin baho tukun ya zaunar da ita duk da tana sume, jin ta a cikin ruwan zafi yasa tayi firgit ta farfaɗo tana faɗin "Yaya Roshan! Yaya Roshan!! dan ALLAH ka taimake ni zan mutu, ka ɗaga ni..." Roshan cikin tausayawa yake kallon ta shima bai ji daɗin abinda ya faru ba, yanzu in ba dace akayi ba ya zamo mata dodo kenam, haka ya gyara ta sannan yazo ya gyara gadon ya shimfiɗa wani sabon bedsheet sannan ya kwantar da ita bayan ya sanya mata kayan bacci da tazo da su, ya kwantar da ita daga nan bacci ya yi awun gaba da ita... Roshan bai samu yin bacci ba har sallar asuba, alwala yayi sannan ya fice zuwa masallaci, bai tashi dawowa ba sai misalin ƙarfe takwas na safe yanda ya shiga ya tarar da Reemah zaune a kujerar falo cikin kayan bacci tana ɗauke da Ra'ees sai jijjigansa take bayan ta gama bashi madarar sa, Zama ya yi ata gefenta yana faɗin "good morning my wife kin tashi ne?..." Reemah banza tayi da shi ko kallonsa bata yi ba, ya kuma cewa "Shalele kin yi sallah ne?..." Nan ma ko kulashi bata yi ba, ya fahimci tana cikin fushi ya ce "Please Shalele kiyi haƙuri akan abinda ya faru, haka ko wace mace take fuskanta a lokacin daren farkon ta, yanzu zaki ga idan mun sake na biyu bazaki ji ciwo kamar na farkon ba..." Wani irin harara ta wurga masa tare da faɗin "lallai sai yau na tabbatar bakada kunya Yaya Roshan, har tinani kake zamu ƙara? to bada ni ba sai kaje ka Auro wata daban ku zo kuyita abun ku...." Tana kaiwa nan ta miƙe tana ƙiran sunan "Mama shosho ..." fitowa tayi daga kitchen ta ce "Babey Mah ina haɗa kayan breakfast ne..." Reemah ta ce "okay je ki cigaba daman riƙon Ra'ees ne inason yin wanka..." Roshan ya miƙe yana faɗin "kawo shi kije ki yi..." Dasauri ta kawar da shi gefe tana faɗin "kar ka taɓa mun shi, na tsane ka..." tana kaiwa nan ta wuce roon ɗinta tana ɗauke da Ra'ees.... A kwana a tashi gaba ɗaya Roshan ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin Reemah abun natan da gaske ne, ba irin haƙuri da magiyan da bai bata ba amma taƙi haƙura, daƙer daƙer ya ci nasarar shawo kanta wanda sai da suka yi tsawon wata biyu tana bijire masa, yanzu ta amince masa daman hora shi tayi akan abinda yayi mata, itama ba irin haƙuri da magiyan da bata bashi ba a lokacin da yake kanta amma ko sauraron ta baya yi har sai da ya kammala ya yinsa tukun.... Rukky matar Rakesh wacce cikin ta yake wata shiga yanzu, yau ta tashi da naƙuda tayi ɓarin cikin Baby boy ɗinta, Ni Asmeetah ina jajanta miki ƴar uwa Rukky, Allah ya mayar miki da mai albarka... *THREE YEARS* A ranar da akayi birthday ɗin Afaf wacce ta cika shekara biyar a duniya a ranar mahaifiyarta wato Amreesh ta haifo mana zura-zuran ƴaƴa triplets mata biyu da namiji ɗaya, duk wacce taji labarin Baiwar ALLAH ta haifi ƴan uku sai tayi tsalle tsabar farin ciki da murna, ƴan uwa da abokan arziki babu wanda bai ji labarin samun ƙaruwar da Razhdeen ya yi ba, A washe garin haihuwar Reemah da Roshan suka zo U.S duba jarirai daga ƙasar Egyph tare da Ra'ees shima ya girma yanada shekara uku a duniya, su Ummy daga ƙasar Jiddeh da iyalan mai martaba duk sun zo suma sai matan Abbah, Pinky itama ta zo daga ƙasar Saudiyya, su minal da Rukky kuma a ƙasar daman suke, duk gaba ɗaya ƴan uwa sun cika maƙil tin kafin ranar suna, Abbah kuma ya nemi Alfarma akan Baiwar ALLAH ta koma Nigeria ayi bikin suna acan... Bayan kwana biyu waɗanda suka zo daga wasu ƙasashe duk sun koma kafin ranar suna wanda za'a gudanar a Nigeria.... Reemah ce take zaune a falo tana wasa da Ra'ees sai ga Roshan ya shigo shima zama ya yi idonsa akan Reemah wacce bata san ya shigo ba hankalinta duk yana kan Ra'ees, kallon tausayawa yake mata fuska ɗauke da damuwa ya ambaci sunanta cikin sassanyar murya, ɗagowa tayi tana kallonsa cikin dariya ta ce "Yaya Roshan yaushe ka shigo ban sani ba?..." cikin gajerar amsa ya ce "yanzu..." Ta ce "lafiya kuwa naga gaba ɗaya yanayinka ya canza..." Jinjina kai ya yi sannan ya ce "Reemah rashin haihuwar ki yana damuna, idan naga yanda ƴan uwa suke hayayyafa suna samun ƙaruwa sai na sha'awanta miki haihuwar kema, ban san meye solution ba anyi miki ko wani irin gwaje-gwaje amma abun mamaki babu mahaifa a jikin ki, ba cire wa akayi ba taya za'a rasa mahaifa kuma?..." Sauƙe numfashi Reemah tayi sannan ta ce "Yaya Roshan na gaya muku cewa tin kafin a Aurar da ni da matsalar aljanu suka shigo mun su suka cire mun, daman sun sanar mun cewa idan nayi Aure ba batun haihuwa, sun cire mun mahaifa yanda bazan haihu ba amma tinda suka bar ni a matsayin mutum ɗina sai mu gode wa Allah kuma yanzu sun cire hannunsa akaina nan ma abun godewa Ubangiji ne, ni bana damun kaina da rashin haihuwar nan saboda Ra'ees ɗina kaɗai ya isheni, kuma ina mai farin ciki da ya tashi yake gani na a matsayin mahaifiyar sa har yake ƙirana da Mommy, Yaya Roshan sai dai kai idan kana buƙatar samun ƴaƴa ban toshe maka hanya ba kuma bazan dakatar da kai ba kaje kayi Aure dan Allah, na baka goyon baya kaje kayi, idan na hanaka ma na cutar da kai ne...." Roshan a tsawace ya ce "ya isa haka dallah..." cikin ɓacin rai ya tashi ya nufi part ɗinsa domin ba ƙaramin ɓata masa rai tayi ba da ta masa maganar Aure... Reemah ganin yanda ya tashi rai a ɓace yasa ta ce wa Ra'ees "jira ni ina zuwa ..." itama ta bi bayansa, a cikin room ɗinsa ta iske shi yana zaune a bakin gado, itama zama tayi tare da ɗora hannunta akan cinyarsa tana faɗin "Yaya Roshan kullum burina shine na faranta maka, bana son ganin ɓacin ranka ko da wasa, Yaya Roshan a cikin maganganu na meya ɓata maka rai? ka sanar mun ni kuma sai na kiyaye faɗin haka..." Juyowa ya yi yana kallon ta ya ce "Shalele banaso idan muna maganar da ya shafi haihuwa kina kawo mun zancen Aure, kina nufin ki ce dan bakya haihuwa ne zai sa na ƙara Aure? a misali ace bani da Ra'ees wallahi bazan ƙara yin wani Aure don na haihu saboda bakya haihuwa ba, zan cigaba da zama da ke a haka har ƙarshen rayuwar mu, bana ƙaunar wata ta shigo mana cikin rayuwa Shalele, don haka ki sa wa bakinki linzami...." Reemah gaba ɗaya ta rasa abun cewa a wannan al'amarin rungumar Roshan kawai tayi tana kuka, shima ƙara mannata yayi a jikinsa yana rarrashin ta.... Bayan wasu ƴan kwanaki ana washe garin suna kowa ya hallaru a gidan General dake Nigeria Abuja City, Baiwar Allah da ƴan ukun ta tare da Afaf duk sun dawo Nigeria har da su Minal da Rukky wacce itama bata samu haihuwa ba har yanzu, idan ta samu ciki sai ya zube ko tayi ɓari, wasu likitoci sun sanar cewa mahaifar ta ne yayi ƙarami bazai iya ɗaukan jariri ba, yanzun ma ciki gare ta taƙi haƙura duk da ta dage da neman magani haka mahaifiyar ta Hajiya Kilishi tana nema mata magani sosai... Pinky itama tazo da ƴan uwan mijinta dake tsatso ɗaya ne, ƙasar Jiddah su ma kowa yazo, su Ummy uwar masu gida da ƴaƴanta biyu itama, Roshan da matar sa Reemah da ɗansu suma sun zo, kowa yaga Reemah sai ya yi maganar ƙibar ta, ta zama ƙatuwa babbar mace duk wani farin ciki da jin daɗi da hutu tana samu sosai, matsalar ta ɗaya shine rashin haihuwa... Ranar suna kowa ya cika a gidan, triplets sunyi mutane sosai Alhamdulillah, Ɗaya ta ci sunan Aunty Yolash wato Khadijah (NIHLA) ɗayar kuma sunan mahaifiyar Baiwar ALLAH wato Zainab (NIHAL) Namiji kuma ya ci sunan Roshan, junior Roshan (NU'AYN) Roshan ba ƙaramin farin ciki ya yi ba, ya haɗa kayan mai suna na hauka, domin duk wanda yaga kayan sai ya yi magana, har da gadon jariri... Abbah kuma ya haɗa wa mai sunan Aunty Yolash kayan mai suna, tin daga ƙasar Ethiopia aka haɗa kayan, shima har da gadon jaririya.. Madam Parveen itama ta haɗa kayan mai sunan ta, itama har da gado.. Anyi bikin suna cikin ƙoshin lafiya, anan ne Baiwar ALLAH tasa aka tara mata mutane a babban falo tana son isar da saƙo akan wani lamari, bayan kowa ya hallaru har da su Abbah da mai martaba da Razhdeen da Roshan da kowa da kowa, Baiwar ALLAH cikin nuna farin ciki tayi wa kowa godiya akan hidimar da suka mata sannan ta sanar wa kowa cewa "a cikin ɗaya daga cikin jariran mata biyunta zata bayar wa Reemah ɗaya duniya da lahira sannan ta sanar cewa tana neman alfarma a wurin kowa na cewa koda yarinyar ta girma kada a sanar mata cewa ba Reemah ce mahaifiyar ta ba, domin ta mallaka mata ita har abada... Kowa ba ƙaramin farin ciki ya shiga ba, sai fatan alkhairi ake musu da sanya albarka, Reemah kamar ta haukace tsabar farin ciki ga tana masifar son yara, bakinta ya ƙi rufuwa ta kasa furta komai, Shima Roshan ya yi matuƙa farin ciki da jin wannan sanarwa kamar wanda aka masa bushara da gidan Aljanna, ga yaran sun shiga ran kowa, Baiwar Allah ganin yanda Reemah take ta dariya tsabar farin ciki ta kasa furta komai, ta tashi tana riƙe da yara mata biyu daƙer take tafiya dake operation aka mata ta nufi yanda Reemah take a zaune, ta zauna a kusa da ita fuska ɗauke da murmushi ta ce "Ƴar Amana ta tinda Afaf ta miki butulci ga wata zan baki ita, kiyi nesa da ita kar ma ta rinƙa ganin fuskata, ki nuna mata cewa kece mahaifiyar ta, don haka a cikin su biyun nan ki zaɓi ɗaya, Aunty Yolash ko kuma Mommy na wato NIHAL ko NIHLA ki zaɓi ɗaya, Reemah har da hawayen farin cikinta ta ce "haba Aunty Baiwar Allah nah, ki mun babban kyauta hakan ma sai na zaɓa?..." Baiwar Allah ta ce "eh mana wacce hankalin ki yafi kwanciya da ita zaki ɗauka..." Reemah ta ce "a'ah duk sun shiga raina sosai, hankalina a kwance yake da su amma tinda kin bani zaɓi, na zaɓi Aunty Yolash wato NIHLA...." Tasa hannu ta karɓe ta tana sakin murmushi tare da faɗin "ban san da wani baki zan fara miki godiya ba Aunty Baiwar ALLAH, babu abinda zan biya ki da shi sai dai nace Allah ya saka da alkhairi..." Baiwar Allah ta dafa kafaɗar ta tare da faɗin "kar ki damu Shalele daman nayi niyyar yin haka, na ɗau alƙawari a kaina cewa idan Allah ya ƙara azurtani da ƴa ko ɗa zan mallaka miki shi ko ita..." Kowa hamdala ya yi tare da nuna farin ciki, Abbah idonsa akan Baiwar ALLAH ya ce "amma sai kin shayar da ita ko kuma tin yanzu kin bayar da ita?..." Baiwar Allah ta ce "shayar da ita ya ƙare daga yau Abbah, zasu cigaba da shayar da ita..." Jinjina kai Abbah yayi tare da taya su murna... Bayan wasu watanni Baiwar ALLAH ta gama hutun ta a Nigeria, tana riƙe da Nu'ayn da Nihal sun shirya zasu koma U.S. Reemah kuwa sun juma da komawa ƙasar da suke da jaririya Nihla da kuma Ra'ees... Itama Rukky Allah ya sauƙe ta lafiya ta hanyar yi mata operation bayan aikin da akayi akan ta na gaske kafin cikin ya zauna, an cire mata ɗiya mace tayi wa mahaifiyar ta mai suna wato Hajiya Kilishi.... 🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ *ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALI* *ALLAH NA GODE MAKA DAKA BANI IKON KAWO ƘARSHEN LITTAFINA MAI SUNA MY ENEMY WATO MAƘIYI NAH* *NAGODE SOSAI MASOYANA DA BANI HAƊIN KAI DA ƘWARIN GWIWA KAMMALA LITTAFIN, DOMIN DA TAIMAKON KU NA KAMMALA BOOK ƊIN MY ENEMY TA HANYAR DAMU NA DA CEWA UPDATE! UPDATE!! UPDATE!!!* *NAGODE MUKU SOSAI, YAU DAI ALLAH YA KAWO ƘARSHEN LITTAFIN....* *SHARHI, COMMENTS, SHARHI, COMMENTS, DUK DA KUNA MUN SOSAI AMMA INA SO NA YAU YAFI NA KULLUM👌👌👌*