Bismillahir'rahmanir Rahim. From the writer of KUNCIN ZUCI...And now MURADIN ZUCI📖 Bintu Musa ✍️ Wannan Littafin qirqirarren labari ne, banyi dan wani ko wata ba, in yazo dai dai da rayuwar ku, kumin afuwa a bisa kuskure ne. Ban kuma yi dan cin zarafin wani ko wata ba, in sabanin hakan ya gifta, shima ayi min afuwa bisa kuskure ne. A Blurb for you... KADDARA....Itace sanadin da yasa ta tsinci kanta acikinsu. Daga lokacin da ta fara mallakar hankalinta ta fahimci banbancin ta da ahalin da ta daukesu jininta. "Amma menene laifinta dan kaddararta tazo a hakan?" "Shin me tayi da yasa take fuskantar kalubale daga garesu?" Wannan sune tunanin FADWA a kullum. Amma kuma duk hakan tana daukansu da sauqi wani lokacin in aka hada da zafin da takeji na yadda kaddara ta hado ta cikin ahali daya da SHI. Ta aminta da cewar har abada batada babban maqiyi kamarsa. Tana jin har abada zuciyarta bazata taba sauqowa akan abunda ya mata ba. Saidai abunda bata sani ba shine kaddarar rayuwar ta tana manne da tashi. Ya zatayi Idan ya zamo shine qarshen bangon majinginar ta a lokacin da ta rasa madafa? Labarin Muradin zuci zai tabo wani bangare ne na sabanin fahimta da ake samu a rayuwa. Kuma zamuga shin har tsawon wane lokaci zuciya take iya danne son wanda take matuqar so? Shin soyayyar da aka rayu da ita acikin zuciya takan iya boyuwa? Har zuwa yaushe? Assalamualaikum Everyone, Bintu ta dawo muku da sabuwar tafiya da take muradin ayi tare daku. Littafin Muradin zuci zaizo muku a paid book ne wannan karon. Akan 500 kadai. ku tuntubeni ta wannan line din 08134692758 Sannan zaku samu sameshi akan manhajar AREWAPEN. Ga wa'inda mukayi tafiyar KUNCIN ZUCI babu su kuma you're welcome on board in this journey, masu neman Littafin Kuncin zuci kuma zaku iya samunsa a Arewapen ko Wattpad for FREE. ko kuma ku tuntubeni ta numbern dana rubuta a sama dan samun complete document. Nagode. Love, Bintu Musa. https://www.arewapen.com/book?id=6a284ace1fd5770fa0dc53fa Ina miqa godiyata sosai ga qunguyar mu ta Wow (women of words) Association. Da kuma godiya ta musamman ga: Ramlat (Mai Dambu) Sayyid (Legends pen) Nusaiba Rimi (Nusy Bee) Thank you so much for been there for me when i need you, Allah ya bar zumunci. Fatima Dahiru Hajara Usaini Ina matuqar godiya agareku for your support, My sisters from another mother, Allah ya saka da alkhairi da dukkan qwarin gwiwan da kuke bani a koda yaushe. MURADIN ZUCI📖📚 Bintu Musa ✍️ Chapter 01 Free page Houston, United States. 25th October. Daren Talata, 9:00 pm. Hankali a tashe matashiyar balarabiyar take tuqin motarta qirar Honda prelude, wadda ta kasance daya daga cikin motocin da suke tashe a wannan lokacin. Tafiya take ba tareda itama ta san inda ta nufa ba, idanunta na kan titi tunda ta fara tuqin taqi juyawa ta kalli seat din dake gefenta. Hannunta da suke riqe da steering wheel din ta kalla ganin yanda suke rawa sai ta sake damqe sitayarin tana mai qara gudun motan a yayin da zuciyarta ke kadawa da wani irin yanayi da yasa idonta kawo kwalla. Tafi awa daya tana yawo acikin garin kuma har sannan bata tsaida inda ta nufa ba sai zagaye take acikin wata makekiyar unguwa ta rasa a wane taqamaiman gida zata tsaya, gashi har sannan jikinta sai rawa yake, can kawai ta samu kanta da tsaida motan a gefen hanya ta kifa kanta akan sitiyarin da hannunta duka biyu ke riqe dashi har sannan. Hawaye masu zafi taji suna zuwa mata idanunta ba tareda ta sharesu ba ta dago kanta tana bin gurin da ta faka motan nata da kallo, ganinta tayi gaban wani babban gida mai cike da alatun rayuwa ga haske a ko'ina tar, samun kanta tayi da qurawa compound din gidan ido ganinsa dauke da gajeran gate irin wanda yawancin 'yan qasar suke amafani dashi a gidajensu, nan kuma idonta yakai kan shukokin compound din da take hangowa daga inda take zaune cikin motan. Sai kuma ta kai hannu ta fara share hawayen da ya sauqa a fuskanta, ahankali ta juya ta kalli seat din dake gafenta ganin har sannan babu wani motsi da basket din dake ajiye a gurin yayi, sai ta kai hannunta ahankali ta yaye farin towel din dake lullube akai tana kallon kyakkyawar jinjirar dake baccinta hankali kwance sai tashin qamshin turaren babies take mai dadi, kuka ne yazo wa matashiyar da sauri ta kai hannunta ta rufe bakinta gudin kar ta tada Babyn. Aqalla ta kai minti biyar tana kallonta sannan cike da jarumta ta maida towel din ta rufe yarinyar, da haka ta jawo baqin gyalen kanta ta rufe fuskanta sannan ta juya ta duban street din unguwar, kasancewar kebababbiyar unguwa ce ta masu hannu shuni sosai sai ya zamtoh babu kowa a daidai street din da take, ganin haka yasa ta bude motan ta fice tareda zagayawa daya bangaren domin daukan jinjirar. Ahankali ta dauko basket din ta juya tana waige waige ganin ko ana kallonta sannan ta fara tafiya a sannu ta tura qaramin gate din and to her luck kuma ba'a datse yake ba, da sauri ta nufi gefen shukokin ta duqa ta ajiye basket din hawayenta na diga kan towel din amma haka ta miqe ta fice da gudu gudu tana sake waigawa ko da wani ya ganta har ta qarasa ga motarta ta shige da wuri ta tayar. Sai da ta kai qarshen layin sannan ta faka motan ta juya tana kallon gidan ta madubi sai kuma kuka mai qarfi ya kwace mata, wani irin zafi takeji a zuciyarta kamar wuta a wannan lokacin tana kukan ahankali take ambaton sunan jinjirar. Can kuma ta kasa daurewa tayi saurin bude motan da nufin ta koma ta dauko yarinyar dan ji take duk wani jarumtar da ta fito dashi kuma ya watse, bazata iya ba...bazata iya ba. Fitan ta ke da wuya ta hango fitowan wani magidancin mutum daga gidan tareda wasu yara guda biyu suna tafe a jere dashi zasu fita daga compound din gidan, da sauri ta sake komawa cikin motan ta tayar tareda figanta ta bar arean da gudunta. Tasani..Lokaci ya qure mata..Ya qure mata har abada kuma.. A yayin da magidancin ya fito daga gidansa tareda yaransa maza da suka kasance 'yan biyu kuma 'yan kimanin shekaru sha biyu, hankalinsa naga fita kwata kwata bai lura da abunda aka ajiye masa a compound din gidansa ba sai daya daga cikin yaran ne ya riqe masa gefen riga domin jawo hankalinsa yace "Papa look..A basket" sai ya juya shida dayan yaron nasa suka kalli gurin da IMRAN ke nunawa da yatsansa ya sake cewa "Papa menene?" a sannu shi Papan ya fara nufan gurin cikin kaffa kaffa yaran na biye dashi a baya, kafin ya qarasa kawai dayan yaron nasa dake bayansa ya tafi kansa tsaye ya tsugunna zai bude, da sauri Papa yace "Kash. IMAM meyasa bak.." kafin ma ya qarasa maganan Imam ya bude towel din suka kalli cikin basket din a tare, Imran dake boye a bayan mahaifin nasu shima ya leqo kansa, dago kai Imam yayi yace "Papa it's a Baby" daskarewa Baban nasu yayi yana kallon kyakkyawar Babyn dake bacci hankali kwance ga kuma kayan sanyi na yara mata mai kalan ruwan hoda a jikinta dauke da zanen flowers wanda hakan ke nuni da kasancewar babyn 'ya mace, hannu Imam ya kai zai dauketa sai Papa ya janye hannun nasa still yana kallon jinjirar da kana ganinta kasan farinta ba na 'ya'yan mu hausawa bane, Imran ya duqa kusa da dan'uwansa shima yana kallon yarinyar sai ya dago kai yana murmushi yace "Papa let's keep it" shidai Papa har sannan baice komai ba gashi alamun tashin hankali ya bayyana qarara a fuskarsa sai kuma ya miqe ya fara bin arean wajen gidan nasu da kallo ko da zai hango wanda ya musu wannan ajiyar a daren nan, can kuma ya juyo yace "Ku tashi mu koma ciki akwai sanyi" sai Imran yace "Papa anan zamu bar Babyn?" Imam dai yanata kallonta har sannan bai sake cewa komai ba, sai Papa yace "No, we're taking her with us" da haka ya sunkuya ya dauki jinjirar tareda furta duk addu'an da tazo bakinsa, sai twins suka miqe suma Imam ya dauki empty basket din suka fara tafiya a gaba while mahaifin nasu yana biye dasu a baya riqe da babyn a qirjinsa suka koma cikin gidan nasu. A lokacin da suka shiga babban falon gidan nasu suka samu Momma zaune a inda suka barta ga jakadiyarta mai suna Habiba na matsa mata kafafunta da suka kumbura dalilin tsohon cikin dake jikinta, dago kai tayi tace "Ha'a, har kun dawo?. Da mota kuka fita ne?" sai Imran ya qaraso gurin ta da saurinsa yace "Momma we found a Baby" sai ta dan hade gira ta juya tana bin mijin nata da kallo ganin yana riqe da nannadadden towel a qirjinsa, qarasowa Papa yayi tareda zama a gefenta atake kuma Habiba ta miqe kanta a duqe cikin ladabi ta matsa gefe, sai ya duqo ya bude wa Matar tasa towel din tana ganin yarinyar kamar idanunta zasu fado, sai ta dago kai tana kallonsa tace "Menene wannan din?" yana kallonta shima yace "Jinjirace Fatima, anan cikin compound dinmu aka ajiyeta" sai ta dafa cikinta ta fara qoqarin miqewa yana kallonta, da sauri Habiba ta matso zata taimaka mata amma ta daga mata hannu da nufin ta barta sannan ta qarasa miqewan da kyar duk suna kallonta ta kalli Imam dake riqe da basket din har sannan, fuska a hade tace "Bani abun nan" sai ya matso ahankali ya bata ta karba tana kallon mijin nata tace "Kawo ta mu fitar da ita daga gidan nan tun kafin ta jawo mana masifa muna zaman zaman mu" da mamaki Papa yake kallonta yace "Meye haka kike cewa ne Fatima, clearly dai kina gani jinjirace alamun bata sha iskan duniya sosai ba, meye nata kuma?" Momma tayi qanqan da ido tace "Shiyasa zamu mayar da ita inda muka ganta sannan mu kira police da social services, we are not keeping a stranger's Baby in this house wallahi" da mamaki Papa yace "Haba Fatima, ki nutsu da Allah. Ta yaya zamu maida baiwar Allahn nan out there in this cold weather kawai dan kina tsoron abunda hukuma zasuyi, kin manta akwai CCTV a street din ne? Anan zasu gani su kuma shaida ajiye mana ita akayi ai" a fusace tace "Ni ba hukuma nake gudu ba, qananun maganan da hakan zai jawo mana acan gida nake gudu, ya muna zaune qalau zaka jawo mana masifa har cikin gida" sai ya dan girgiza kai ya miqe tareda miqa mata yarinyar yace "Dan Allah ki riqeta, ki kula da ita kafin insan ta inda zan bullowa al'amarin, the mother might come back, bakisan yanda nake burin hakan a raina ba, it's too cruel for the baby, social services will just be passing her from one home to another in the name of adoption, she's innocent" tsayawa Momma tayi tana kallon yarinyar yayin da duk wani annurin fuskanta ya gushe, idonsa a kanta ya sake miqo hannunsa "Riqeta mana Fatima" sai lokacin Imam ya matso tareda dan miqa hannu zai karbeta ai da sauri Momma ta tureshi har sai da ya fadi, rai a bace take kallonsa tace "Uban 'yan karfin zuciya, inna gaura ma mari ba" kafin Papa ya dagosa ya riga ya miqe yana kallon mahaifiyar tasa dake harararsa, sai Papan ya juyo gareta yace "Wai me yake damunki ne Fatima, Lafiyan ki kuwa?" tace "Ba lafiya nake ba, ta yaya muna zaune lafiya zaka shigomin gida da jinjira sabon haihuwa har kana fadin in riqeta, wallahi ka koma da ita duk inda ka daukota tun wuri" da haka ta juya tana riqe da cikinta da yayi nauyi sosai ta wuce dakinta dake nan downstairs wanda tun zuwansu gidan take zama acikinsa dalilin bata iya hawa stairs taje asalin dakinta dake can sama, sai duk suka bita da kallo yayin da Habiba tabi bayanta da hanzari gudun kar ta mata masifan da ta saba. Wannan littafin Paid ne akan Naira dari biyar (500), masu buqatan kasancewa cikin wannan tafiyan zasu iya biya ta wannan layin. 8134692758 Opay Fatima Musa Maina Shaidar biyar ta wannan layin. 08134692758 MURADIN ZUCI📖 Bintu Musa ✍️ Chapter 02 Free page. Papa daskarewa yayi anan tsaye a falon ya gagara zama yana bin matar tasa da kallo, ya sani wannan din ba sabon abu bane sanin masifa da fitinar matar tasa da yake fama dashi tun fil azal wanda kowa ya shaida a kaf danginsa cewa Fatiman fitinanniya ce kuma in bataso zaman lafiya ba toh ba wanda zai zauna lafiya a can gidansu dake Nigeria. Sai ya koma ya zauna kan kujerar a hankali ya duqar da kansa yana kallon Babyn wadda kamar hadin baki itama ta bude idanunta a hankali, dan stiff yayi yana kallon kwayar idanunta da suka kasance grey color, duk da kasancewar ta jinjira hakan bai hana manyan idanunta fitowa fili ba a lokacin da take kallonsa. Duk yanda yake jin nauyin tashin hankalin dake tunkarosa hakan bai hanasa samun kansa da yi mata murmushi ba, sai ya kwantar da murya ahankali yace mata "Assalamualaiki" nan twins suka matso suna kallonta, Imran yace "Papa please let's keep it" sai ya dago kai yace "She's a girl Imran". Imam kuwa sai kallonta yake baice komai ba shima, sai Papa ya sake duqawa ya kalleta yanajin tausayinta na shiga kowane sashi na zuciyarsa, tayaya wannan innocent being din zata zamo masifa bayan in za'a bata zabi itama bazata so abunda ya faru da ita ba ko kadan, har sannan bata dauke idanunta daga kan Papan ba sai can kuma ta fara motsi tana dan bata fuska alamun zatayi kuka nan ya hau jijjigata yana kallon kayan sanyin dake jikinta, mamakinsa daya a wannan lokacin shine ta yanda kayan jikin jinjirar yake fes da kyau ga wani tashin qamshi da takeyi, sai ya dan dago ta yana sake duba kayan dan ko daga texture din mutum zai fahimci ba daga cikin wahala ta fito ba. Idonsa ne yakai kan wani rubutu ajikin farin towel din nata sai ya kai hannu ya yaye kadan yana ganin sunan da akayi engraving kamar saqa ajiki da harafin larabci "FADWA" ya maimaita sunan a fili, sai lokacin Imam yace "Papa sunanta ne?" ya gyada kai "Sunanta Fadwa" Imran yayi murmushi ya duqa kansa gareta yace "Hi Fadwa" sai Papa ya shafa kansa bai bar murmushin qarfin halin ba, yace "Yes.. Her name is Fadwa" ya qarasa fadi yana danne duk wani tashin hankalin da ke kokarin taso masa a zuciya. Rai a bace Momma ta shiga dakinta Habiba na biye a bayanta, cikin kwantar da hankali tace "Ranki shi dade kiyi hakuri kar hakan ya ja miki matsala ga lafiyarki" ta juyo a fusace tace "Sai an fitar da yarinyar nan daga gidan nan, ke yanzu yarinyar nan bata miki kama da aljana ba?" Habiba ta dan duqar da kanta tace "Ki gafarceni ranki shi dade, amma yarinyar ba lallai ta kasance aljana ba sai dai asalinta ne zai iya zama da tangarda" Momma tayi saurin cewa "Dama batun shegiya kam shegiya ce, kuma wallahi ba zan raini 'yar cikin shege tareda 'ya'yana ba" kafin Habiba tayi magana suka jiyo tashin kukan yarinyar Momman 'yar kimanin shekara biyar dake kwance akan gadon tana bacci, sai Momman ta juya gareta da sauri tace "Jidda na kin tashi" yarinyar ta gyada kai tana murza idanunta sai uwar ta miqa mata hannu da nufin ta iso gareta. Tana shafa bayan Jiddan ta juya zata fadi magana a Habiban aka turo kofan dakin Imran ya shigo a daddare, qin qarasowa yayi cikin dakin yayi sai ya tsaya anan bakin kofar yace "Mama Habiba kije Papa na kiranki" da sauri tace da Momma "Ranki shi dade bari naje" gyada kai kawai Momma tayi batace komai ba tana kallon Imran din dake tsaye a bakin kofan yaqi shigowa, dan hararansa tayi sannan tace "Meye na tsayawa a bakin kofan toh?" sai yayi murmushi ya juya while Habiba na biye dashi suke fice tana kallonsu, sai can kuma tayi tsuka ta cigaba da shafa bayan Jidda dake shirin komawa wani baccin. Fitan Habiba falon ta samu Papa na tsaye yana jijjiga Fadwa dake kuka a hannunsa, cikin ladabi ta duqar da kanta tace "Ranka shi dade akwai abunda kake buqata ayi ne?" sai ya juyo yace "Kuka take bansan me takeso ba ko zaki gwada lallabata" nan ta miqa hannu ya bata ita ta cigaba da lallabatan, amma har zuwa karfe goma na dare Fadwa bata bar kukan ba duk da ruwan dumin da Habiba ta bata tasha, har zuwa sannan kuma Momma bata sake fitowa daga dakinta ba duk da kukan jinjirar da take jiyowa ya karade gidan. Hankalin Papa in yayi dubu ya tashi a wannan lokacin ya rasa me ke masa dadi. Sai bayan Habiba ta danyi dabarunta ta gano ciwon ciki ne ke damunta sannan ta fada masa, aikuwa nan da nan ya dauki car key twins na biye dashi zasu fice siyo mata maganin sai Habiba ta sake tuna masa yarinyar na buqatan madara da kayan sakawa har dasu pampers ya gyada kai tareda ficewan. A daren Papa suka fita zuwa super market don nemo madaran nata, yana tafe a motan yana tunani har sai da Imam dake seat din gefensa ya ankarar da shi isowarsu gurin ganin zasu wuce sannan ya dakata, daga nan kuma suka biya boutique na saida kayan yara amma kuma sai suka samu a kulle, haka ya hakura ya biya dasu pharmacy ya siyo maganin ciwon ciki na daidai jinjiri sabon haihuwa sannan suka koma gida. Bayan Habiba ta bata maganin cikin sa'a suka samu ta fara bacci sannan Papa ya sake dubasu kasancewan suna cikin daya daga cikin dakunan dake nan downstairs, ganin Fadwan tayi bacci yasa shi ficewa sannan ya nufi dakin matarsa, anutse ya bude kofan sai ya sameta a zaune a bakin gado sanye cikin kayan bacci tana dan dafa cikin ta dake dan mata ciwo kadan, da sauri ya qarasa yana mata sannu amma bata ko dago kanta ba sai ya zauna kusa da ita ya sake cewa "Sannu, ko in taimaka miki ki kwanta?" nan ma ta girgiza kai bata ce komai, shiru sukayi sai can yayi qasa da murya yace "Fatima, yarinyar nan itama batada zabi akan abunda ya faru da ita" sai sannan ta dago kai tana kallonsa tace "Ni bance laifinta bane daman, kawai bazan riqe yarinyar da bansan asalinta bane, ya kawai daga ganin yarinya a yashe zaka dauko ka qaqabamin nima inaji da kaina" sai yayi murmushi tareda kamo hannunta yace "Haba mana Binta na, ai ba lallai sai ke zaki raine ta ba, ga hadimanki dayawa da duk abunda kikace shi zasuyi, Ina laifi in kin taimaki yarinyar da batada gata ayanzu sai na Allah da namu, ki tuna fa muma ba dabarar mu bane ya bar mana namu 'ya'yan cikin gata kuma a gaban mu" sai ta kwace hannunta tana hade fuska tace "Ni ka daina dangantamin yarana da irin wannan maganganun, kuma ai ba mu kadai bane mutanen da zamu iya riqeta, akwai orphanages dayawa ai" Papa na kallonta yace "Then..Menene makomar yarinyar kenan? what if.." kafin ya qarasa ta fara qoqarin gyara kwanciya tace "Ni kawai banaso, nace banaso ana dole ne? naji yau ta kwana a gidan amma zuwa gobe bazan lamunci zamanta a gidan nan ba" da haka ta kwanta ta juya masa baya yana kallonta, can ya sauqe numfashi ya miqe ya fice. Dakin twins ya tafi a upstairs dan tabbatar da ko sunyi bacci sai ya samu Imran nata munsharin bacci abunsa while Imam na zane a takarda anan zaune kan upper bunk dinsa dake saman na Imran din, murmushi Papa yayi yace "Imam bazaka bar zanen nan haka ba kayi bacci?" sai ya dago kansa, ahankali yace "Saura kadan" yace "No son, it's late..ka kwanta haka nan sai gobe ka qarasa" da haka ya qaraso bakin gadon ya fara tattare masa takardun, sai ya dago takarda guda daya yana gani a zuciyarsa yana mamakin baiwar yaron a kullum in yaga abubuwan da yake zanawa kala kala. Sai da ya tabbatar ya kwanta sannan ya nufi switch din dakin zai kashe wutan yaji Imam din yace "Papa, cikin ya daina mata ciwon?" sai ya juyo yace "You mean Fadwa?" ya gyada kai ahankali, sai Papa yayi murmushi yace "Eh ya daina har tayi bacci, now sleep....saida safe" da haka ya kashe wutan sannan ya fice tareda rufo musu kofan.. Tunda ya koma dakin kwanansu Momma bata juyo ta kallesa ba duk da idonta biyu har sannan, har ya gama shirin baccinsa yazo ya zauna a gefen gadon bata motsa ba kuma idanunta a bude tana kallon wall din dakin ta bashi baya, sai ya juyo yana kallonta yace "Kinyi bacci?" shiru tayi bata amsa ba, qasa qasa ya sake cewa "Ya cikin naki?" nan ma tayi shiru, ganin halin nata ne ya motsa yasashi kwanciya shima ya juya bayansa yana jin zafin hali irin na matar aurensa. Bintu ✍️ Paid Book (500) 8134692758 Fatima Musa Maina Opay Shaidar biya: 08134692758 MURADIN ZUCI📖 Bintu Musa ✍️ Chapter 03 Free page.. Washegari tun da lokacin sallahn asuba yayi Papa ya kwankwasa dakin su Habiban dan jin lafiyan yanda suka kwana. Bayan ta bude sai ta sunkuya ta fara gaisheshi cikin ladabi sannan ta fito daga dakin domin bashi guri, da ya amsa mata sai ya shiga cikin dakin direct ya nufi gadon inda Babyn ke kwance tareda Jidda, bacci ya samu tanayi kamar ba ita ta tada musu hankali jiya da kuka ba, sai ya maida towel din ya rufe tareda gyarawa Jidda duvet dinda take lullube itama sannan ya juya ya fice daga dakin. A falon ya tadda Habiban tana jiran fitowansa sai yace "Ya cikin nata?" kai a duqe tace "Da sauki, bata sake wani kukan ba ranka shi dade" ya gyada kai sannan ya nufi upstairs gurin 'yan samarin yaran nasu. Tare da twins din yayi sallah anan falon suna biye dashi ya jagoranci sallahn dalilin rashin yawaitan masallatai a kasar a wannan shekarun. Har Habiba ta gama hada breakfast Momma bata fito ba, da Papan ya leqata ya mata magana ma bata kulasa ba sai ya dawo dinning area din suka cigaba da cin abincin da yaransa wanda suma a daddare suka gaisa da mahaifiyar tasu a wannan safiyar. Habiba dai ita take tsaka mai wuya, fushin Momma uwargijiyar tata take tsoro matuqa gashi tasan ko giyar wake tasha bazata tsallake maganar Papa ba. To wa ya isa ya tsallake magana ko umarnin Yarima mai jiran gado bayan sarki Abdulfatah, sahun giwa ne ya taka na raqumi shiyasa babu yanda ta iya ta amshi kulawan jinjirar ta hada da aikinta na kula da uwargijiyar ta da tazo yi takanas a qasar. Da Papa ya shirya fita gurin aiki ne Habiban ta sake tuna masa batun tufafin Babyn sannan ya sake shiga dakin dan dubota, nan ma ya samu ta koma wani baccin bayan Habiba ta bata madaran tasha kadan. Duqawa yayi idonsa akanta zuciyarsa na qara karyewa, sai ya kai hannu ya kama qananun fingers dinta duk bata motsa ba, wani irin nauyi yaji zuciyarsa nayi akanta, what a cruel world! This beautiful innocent child didn't deserve this, wane mara imanin ne zai yasar da wannan yarinya?.. Da wannan maganganun zucin ya miqe cikin sanyin jiki sai twins suka shigo dakin Imran na gaba suka qaraso bakin gadon suna kallonta. Sai Imran ya hau gadon ya kai hannu yana taba fuskanta yace "Papa bacci take har yanzu?" ya gyada kai yanajin nauyin yin maganan kar suga gazawarsa, sai ya juya yana kallon Imam ganin ya tsaya dan nesa da gadon idonsa quri akan babyn baice komai ba, dan murmushi Papan yayi sannan yace "Daga nan zaka gaisa da ita kuma Imam?" sai ya girgiza kai ya qaraso bakin gadon amma bai hau ba, cikin nutsuwarsa da ta zame masa jiki dukda yarintarsa yace "Papa ya cikin nata?" sai Papan ya amsa da "Ta samu sauqin, gashi har baccin ta takeyi ma" ya gyada kai bai sake cewa komai ba sai Imran dinne yake wasa da hannunta suna magana da Papan, sai da suka dauki lokaci a dakin sannan suka fice while Papan yayi kiran Habiba dake wajen Momma, bayan ta fito a hanzarce yace mata "Kayan sakawa ne kadai ya saura acikin abubuwan da take da buqatan ko?" tace "Eh ranka shi dade, da dai mayukan yara irin wanda kuka siyo kwanaki da Gimbiya" ya gyada kai sannan ya dauki qaramar jakansa dake dauke da takardun da zai buqata a wajen aikin nasa sannan ya sake leqawa dakin matar tasa suyi sallama. Tana hakimce a bakin gadon hannunta riqe da plate Habiban ta kawo mata nata breakfast din, ganinsa yasa jidda baro gurin mahaifiyarta ta qaraso garesa tana maqalqale kafansa, sai yayi murmushi tareda shafa kanta yace "Where is my little pumpkin?" tana dariya tace "Mee Papa" da haka suka qarasa gurin Momman da idanunta ke kan plate din bata dago ba har sannan, saida ya zauna a kusa da ita ya umarci jidda da taje gurin yayunta sannan ya sake maida hankali gareta yace "How are you feeling?" a nutse tace "Na dauka samun 'yar tsintuwar yasa ka mantawa dani da kuma jininka dake jikina" madadin ya nuna haushin kalaman nata sai ya danne tareda dan yin murmushi yace "Jiya kadai dan ban bi abunda kikeso ba yaci ki zamo me fahimta ta Fatima, i thought ko bance ki kula da ita ba ke me jin tausayin tane, cikin sanyin nan akayi dumping dinta batareda tausayi ba, menene nata aciki, sannan menene laifi na dan na nemi kulawa da ita, ke kanki kin sani babu yanda za'ayi in fitar da yarinyar nan waje a jiya, in kaita Ina? Haba Fatima, Ina imaninki ya tafi?" sai lokacin ta dago kai tana kallonsa, nan hawaye suka fara taruwa mata a Idanu sannan tace "Wato dan na nemi kare mutuncin ka shine rashin imani, yarinyar da kana gani kasan 'yar qazanta ce, wane irin maganganu kake son jawo mana da mutuncin ka, daraja da kuma kimarka?" nan kuma ransa ya fara baci yace "Kina gurin ne da aka sameta ta hanyar qazantar, wai me yake damunki ne Fatima, da kike maganar kima da daraja kina tsammanin mahaifan nawa zasuyi alfahari da cewar na yardar da yarinyar ba tareda na bata shelter bane?" Tayi shiru bata basa amsa ba sai ya sake cewa "Zan zamo jagora bisa mulkin iyayena da kakanni da zan karbi ragama kuma ace tun yanzu bazan iya kwatanta jinqai ba me na zamo kenan? will you be proud of that man?" nan ma tayi shiru batace komai ba, sauqe numfashi yayi sai ya nutsar da muryarsa wannan karon cikin lallashi ya kuma fadin "Ki tayani mu samu ladanta koda na qanqanin lokaci ne Fatima, tunda baki amince da mu riqetan ba zan samo mafita tunda wannan ba qaramin case bane a qasar nan. But before that, please ki ban hadin kai mu kula da baiwar Allahn nan, gidaje dayawa acikin estate dinnan amma sai Allah ya kawota garemu, bamu san me ya boye a cikin lamarin nan ba" ta gyada kai nan ma bata amsa ba sannan ta cigaba da cin abincinta, ganin tayi shiru yasa shi yi mata sallama tareda miqewa ya nufi kofa ta bisa da kallo sannan ta dan tabe baki tana qara hade fuska. Papa bai dawo gidan ba sai karfe sha daya na safen ya shigo gidan hannunsa niqi niqi da kaya. A dan gigice ya shigo falon sanadin jiyo kukan Fadwa da yayi tun kafin ya bude kofan, sai ya samu su Imam da Imran din tsaye a dan nesa da dakin da Fadwan ke kwance tana ta tsala ihu sun kasa shiga ciki. Da sauri ya ajiye kayan akan table sannan ya nufi dakin ya shiga nan ya sameta har fuskar nan tata tayi jaa abunka da farin fata, cikin hanzari ya dauketa dalilin wani irin tausayi da ta basa ya dorata a kafadansa ya hau jijjaga ta, baiwar Allah sai ta tsaida kukan ta fara ajiyan zuciya jin ta ajikin mutum, sai ya juyo yana kallon twins da suke kallonsa a bakin kofan, idon Imran tsuru tsuru dayake yafi dan'uwansa Imam din tsoro a tarin lokuta, da sauri yayi magana ganin yanda baban nasu ke kallonsu "Momma tace kar mu shiga" ya sake cewa "Imam ya shiga ta dakeshi" sai Papan ya kalli Imam din da ya sunkuyar da kai baice komai ba, da haka ya fito ya wucesu yana kiran Habiban, da saurinta ta fito daga dakin Momman tana sunkuyar da kai jikinta na dan rawa na sanin me tayi, amma kuma ba laifinta bane tunda itama uwar dakin nata ce ta umarceta da tayi mata wasu ayyukan tabar yarinyar, ganin yanda take a tsoracen sai Papa ya fahimci wani abu, ya fara kokarin danne bacin ran nasa yace "Ya kika barta tana kuka, bayan na bar miki kulawanta" da sauri tace "Ka gafarceni yallabai, hakan bazai sake faruwa ba" sai ya gyada kai tareda sauqo da Fadwan daga kafansa yana kallon yanda ta fara kokarin komawa bacci, ya miqota ga Habiban yace "Ki mata wanka, ga kayanta can na kawo, ki tabbatar ta qoshi sosai kafin ta koma baccin, banason abunda ya faru yau ya sake maimaituwa" jiki na bari Habiba ta amsa da "Kayi hakuri yallabai ka gafarceni, bazai sake faruwa ba" sannan ta miqe tareda karban Fadwan ta nufi dakin kwanan su da ita, da dan hanzari Imam ya dauki kayan da Papan ya siyo wa Fadwan yabi bayan Habiban Imran na biye dashi da wasu a hannu suka shige dakin dukansu. Sauke numfashi Papa yayi yanajin bacin ran abunda matar tasa ta aikata bayan ko awanni uku masu kyau ba'ayi ba ya gama neman alfarman tallafinta gurin kula da marainiyar Allah, sai ya girgiza kai kawai ya nufi dakin nata aransa yana tunanin yanda halinta ke sake banbanta a kullum sabanin yanda ya santa baya. Sai 12 ya shirya tafiya wajen aikinsa bayan ya tabbatar da Fadwan ta samu kulawan da take buqata sannan yayi sallama da iyalinsa ya fice, bayan ya gamo ayyukansa wajen 4 o'clock bai koma gida ba ya nufi gidan Abokinsa me suna Ladan dake living anan Houston din shima da familynsa, dan zuwa sannan duk tunanin da zeyi yayi akan lamarin nan and it's all leading him to one option, shine dole ya bada jinjira nan ga child services, dole yayi reporting ga police, duk yanda yake son yarinyar da kuma son samun ladanta dole haka zai hakura saboda jalala irinta matar da Allah ya hadasa da ita. Paid Book 500 8134692758 Fatima Musa Maina Opay Shaidar biya: 08134692858 From the writer of KUNCIN ZUCI...And now MURADIN ZUCI📖 Bintu Musa ✍️ Chapter 04 Free page Papa bai dade ba ya isa gidan Abokin nasa mai suna Ladan, wanda ya kasance citizen din qasar dalilin iyayensa da suka kasance Nigerian immigrants and living in the united states for a long time, a yayinda kuma abota ta hadosa da Papa tun samartakarsu a sanadiyar degree dinsu da suka yi tare a makaranta daya. Iso Ladan ya masa zuwa dan qaramin garden dinsa dake backyard na gidan suka zauna bisa kujeru na shan iska sannan matarsa mai suna Zulaiha ta kawo musu abun sha ta kuma gaisa da Papan. Sun dau lokaci suna hiran rayuwa da kuma businesses dinsu a inda Ladan din yace dashi "Kargi is high time ka fara tunanin expanding cooperation dinnan naku zuwa Atlanta, there's alot of business potentials there, inda ni nakeda irin privilege dinka na rayuwa da wuya in zauna a guri daya haka sai dai wani ikon Allah. Duniyar matsawa take da gudu yanzu. There will come a time that zuwa America zai zamo abu mafi sauqi ga mutane unlike yanda ake wahalar samun zuwa yanzu" sai Papa ya ajiye cup din hannunsa ya kallesa "Abunda nake ta tunani yanzu haka kenan, in sha Allah zanyi maganan da mai martaba sai muyi shawara, dan kaga yanzu hankalina yafi karkata ga haihuwan mai dakina tukunna, da kuma passport din Babyn, amma zamuyi hakan da yardar Allah" Ladan ya gyada kai cikin gamsuwa sannan yace "Hakane, Allah ya sauketa lafiya" ya amsa da Amin suka danyi shiru while nursing their drinks, can Papa yace "Ladan, nazo neman shawararka akan wani al'amari daya tunkaromu nida iyalina, nayi tunanin iya tunani amma kaina ya kulle akan ta yadda zan bullowa lamarin" nan Ladan ya dan gyara zama yana kallonsa, sai ya hau bashi labarin abubuwan da suka farun daga daren da aka ajiye musu babyn har zuwa wannan ranan, kafin ya gama maganan Ladan yace "Abdulaziz meyesa zaka saka kanka acikin irin wannan matsalan?" sai Papan ya dan hade gira yace "Bakaji me nace bane? Ce maka nayi fa har cikin compound aka ajiye mana ita, ya kakeso inyi? left her in this cold freezing weather?" Ladan ya sauqe numfashi yayi shiru na wasu sakkani tukunna, can yace "Ai lamarin qasar nan dinne, bakayi bama kamar jira suke balle issue irin haka ya faru? But you should've call the police Kargi, nan da Nigeria akwai banbancin mai matuqar yawa" Papa yace "Nasani, shiyasa nazo ka bani shawara ai, raina nason riqe yarinyar nan Ladan, wani irin protectiveness nake ji akanta banason ta fada wani mugun hannun wallahi, Inason riqeta in bata duk wani kulawan rayuwa ta yanda bazata rasa duk wani gatan da ake tunanin yara kamarta suke rashi ba" Ladan yace "Me matarka tace akan haka? ta amince da ku riqetan ne?" ya girgiza kai yace "A'a, as a matter of fact a ganinta na farko da yarinyar ta qi komai dangane da ita, can you believe har hana hadimarta kula da yarinyar tayi, haka na dawo gidan nasamu tanata kuka abun tausayi" sai Ladan yace "Toh kaga matsala ta farko kenan Kargi, dan wannan matsalace babba, the best idea shine ka bada yarinyar nan ga child services, tunda Fatima bataso babu ta yanda zaka taba jin dadin kula da yarinyar nan, Happy wife Happy home" Papa ya girgiza kai "Na dade bama fuskantar same angle nida Fatima, it's always the opposite Ladan, she never understands where I'm heading, yara irin wannan ba qaramin lada ake samu da riqonsu ba. Allah ya gani Ina tausayinta" sai Ladan yayi shiru yana kallonsa baice komai ba, ganin haka sai Papa yace "Amma tunda kaima hakan kace shikenan zan bada itan, addu'ana daya kar Allah yasa ta fada mugun hannun ko kuma ta taso cikin Christianity, Qasar nan ba ruwansu da wannan in suka tashi bada yaro, Allah ya dubeta duk inda take" a sanyaye Ladan ya amsa da Amin sannan suka koma wani batun daban. Da wannan tunanin ya koma gida, amma abun mamaki yana dosar gidan nasa ya samu motoci biyu a fake a daidai bakin gate. A kallo na farko ya gane daya data kasance ta police daya kuma bazai shaida ta waye ba, duk yanda yakai ga taurin zuciya sai da yaji hantarsa ta kada, tunaninsa a wannan lokacin kodai neighbors dinsu sunsan me yake faruwa toh?. Da haka yayi parking a gefensu yana fitowa sai daya daga cikin polisawan ya qaraso garesa suka gaisa ya qara da "Sir, we need to have a few words with you" shima yace "Let's go inside then" da haka ya musu jagora zuwa cikin gidan suka shiga tare yana gaba. A falo ya tadda Momma zaune kusada wata middle age woman wacce ke riqe da folders a hannunta tana nazarin bayanin da Momman ke mata, ta gefe dasu kuma Habiba ce tsaye riqe da Fadwan a hannunta ga twins tsaye a gefenta suma, sai bayan su Papan sun zazzauna matar ta kallesa ta fara magana cikin harshen turanci kamar haka "Matarka ta kira office dinmu akan yarinyar da aka ajiye muku jiya, shine muka zo saboda akwai buqatar zamu riqe yarinyar a hannun mu Mr. Kargi" sai police daya ya karbi maganan shima "Amma kafin nan munada buqatar muje station kayi cike cike, mun duba cameras na street dinku mun tabbatar ajiyeta akayi amma dole sai mun tafi dakai dan buqatar bayani daga bakinka" jiki a sanyaye Papa ya juya yana kallon Momma da taqi kallon idonsa, duk yanda yakai ga danne bacin ransa saida hakan ya bayyana akan fuskarsa, sai matar can din ta sake cewa "Ka fahimcemu Mr Kargi, bamu zo da tashin hankali ba aikin mu muka zo yi, yara irin wa'innan daman aikinmu ne na tabbatar da sun samu kulawan da suke buqata" nan Papa ya gyada kai ahankali, a turance yace "I understand...Miss??" tayi saurin cewa "Eva..It's Eva Hollaway, from Texas Department of Family and Protective services" ya gyada kai "Okay, Miss Eva..I understand" da haka suka mimmiqe sai ta juya tayi godiya a Momma da ta kirasun, a nutse ta amsa da "Thank you Miss Eva" Papa na kallonta, Har suka fice kuma taqi kallonshi sai sunkuyar da kai take tana wani ciccin magani. Papa bai dauki wani dogon lokaci a station din ba ya gama cike ciken da ake buqata daga garesa, amma da aka nanu masa clip na record din matar da ta ajiye jinjirar sai da ya qame a zaune dan mamakin ganin motar da ta fito daga cikinta, kansa ne ya kulle ganin babu wani alamun talauci a tattare da matar duk da yanda ta rufe fuskarta, hasali ma irin motar da yake hawa tazo da ita sannan daga yanayin kayan da ya gani jikin yarinyar tun farkon ganinsa da ita ya shaida cewan duk inda ta fito babu talauci a ahalin. Anan suka sanar dashi plate numbern motan matar was not registered kwata kwata duk iya tracing din da sukayi, ya gyada kai cikin fahimta yana jin wani tausayin jinjirar na sake shigansa a wannan lokacin amma haka ya danne komai har ya gama abun suke buqata daga garesa a station din. Kasancewan maghrib ta masa a nan din sai bai je social service office din ba, sukayi agreement da miss Eva dake tare dasu a station akan zai dawo washegarin ranan. Fitowa sukayi a tare da ita tana riqe da Fadwan sannan ta nufi motan ta ta sakata suka tafi da ita yana kallonsu wanda hakan ba qaramin karya zuciyar sa ya sake yi ba. Ga tsananin bacin ran abunda matarsa ta masa wanda har sannan yana jin dacin rashin ganin mutuncinsa da batayi ba tayi abu gaban kanta batare da shawararsa ba, haka ya hadiye komai ya nemi taxin da zata kaisa gida. Da ya isa gidan yana bude falon Momma ta dago kai tana kallonsa sai ya dauke kansa ya nufi dakinsu dan yayi sallah, saida ya zo wucewa ta gabanta ta fara kokarin miqewa da kyar dan Habiba da twins basa falon, tana kallonsa tace "Baban Jidda i had to do what is safe for us, this is the only way and you're not making any effort to do so" sai ya juyo a nutse yace "Kinji nace wani abu ne?" tayi shiru tana kallonsa batace komai ba, ya juya tareda nufan dakin yana danne duk wani abunda ke taso masa a zuciya. Har suka zo kwanciya Papa baice mata qala game da abunda tayin ba, itama ganin haka sai taqi kulasa aganinta duk inda aka samu kwana biyu komai zai wuce, zasu dawo yanda suke a baya dan sanin da tayiwa mijin nata mai hakuri ne da kuma rashin riqe abu arai...Saidai abunda bata sani ba shine wannan karon tayi kuskure, ta kuma tura shi har zuwa maqurar da ya dau damarar nuna mata matsayinta na macen dake qarqashinsa. The following day beyi qasa a gwiwa ba ya tafi office dinsu Eva da safe. Da isarsa ya fara neman izinin yaga Fadwan amma suka qi barinsa acewarsu hakan "It's not allowed" sai aka kaisa office din shugaban sashen a inda shima shugaban yayi kiran na qasa dashi a qaramin meeting room wanda a nan Papa ya sake musu bayanin duk abunda ya farun, bayan sun gama paperwork sai ya nemi magana da over roll shugaban nasu a office dinsa. Sanin co-operation companyn su Papan ba boyayye bane a Houston yasa shugaban bashi girman sa har da kawo masa ruwa amma bai sha ba, ya gyara zama tareda dan matsar da glass cup din gefe yace "What are the necessary requirements that I'll need to fulfill before adopting this child legally?". Sai shugaban me suna Carl yace masa abune me sauqi tunda duk wani qualities din da ake nema na wanda zeyi adopting yaro shi Papan ya cikesu, kawai za'a bi legal paperwork ne for court approval amma kuma akwai abu guda daya, sai da consent din both married couple din which means sai lallai da amincewar ita Momman sannan za'a basu yarinyar, Jan aiki. A farkon satin da ya fara going through process din ko bin ta kan Momman beyi ba ganin yanda ta manta da batun ma ta cigaba da rayuwar ta cikin kwanciyar hankali a gidan, duk yanda hankalin twins yake kan Fadwan more especially Imam haka ya danne in sun tambayesa inda take sai yace musu "Tananan lafiya". Habiba ma taji zafin uwargijiyar tata amma babu yanda ta iya balle tayi magana, haka ta cigaba da abunda ya kawota gidan tana ganin yanda Momman ta kama sabgoginta kamar ba uwa ba. Papa na iya kokarinsa na danne komai dukda tana ganin coldness dinsa lokaci lokaci dan abune da ya quduri niyya a ransa na sai ya bata mamaki akan abunda tayin. Zata sha mamakinsa matuqa. A wani dare ya yanke shawaran kiran mahaifin sa dan sanar dashi duk da yasan ko bai fada masa ba abunda yake shirin yi din daidai ne. A lokacin da ya gama isar da bayanin nasa ta waya, sai Dattijon ya nutsar da muryarsa gurin cewa "Abu ne mai kyau hakan, kuma Allah zai muku jagora matuqar niyyarku akan yarinyar tsaftatacciya ce" yace "In sha Allah. Nagode, Allah ya qara girma" sai mahaifin nasa ya sake cewa "Mai dakin taka ce zata riqeta?" Ya amsa da "Muna shawara akan wannan din tukunna" sai yace "Yayi, Allah yayi albarka" ya amsa da Amin yanajin nauyin abun da yake shirin yi din na sauqa daga zuciyar sa. Sati biyun da suka biyo baya ya cigaba da cukucukun adoption din tareda Eva kuma zuwa sannan suna barinsa yaga Fadwan in yaje office din nasu, atarin lokuta in aka kawo masa ita sai yaji kamar ya tafi gida da ita a lokacin, wani irin iko na ubangiji sai ya saka masa so da tausayin yarinyar matuqa aransa, da ita yake kwana arai most days saboda tunanin yanda batada kowa da kuma gata a wannan lokacin sai inda aka miqata. Da akazo batun lallai ana buqatan consent din Momma sai yayi confiding da Eva akan halin da yake ciki da me dakin nasa, itama taji ba dadi sosai amma cikin qarfafa gwiwa tace "Mr Kargi, Ina ganin soyayyar yarinyar nan a idanunka da kuma actions dinka, wanda hakan ya nuna min cewa Fadwa is safe with you, zata samu dukkannin gatan da muke fatan duk yaron da muka bada shi ya samu, abun da zakayi yanzu shine ka nemo qwararren lawyer da zai shige maka gaba akan hakan, Ina tabbatar maka da in process din ya tafi daidai ba sai matarka tayi signing komai ba zaka tafi gida da 'yarka" ta qarasa tana murmushin bashi qwarin gwiwa, godiya ya mata sosai yana jin dadin shawaran nata sannan ya bar office din. Da wannan Papa yayi wining case din a kotu a ranan Thursday, 15th of November. A yayinda qwararren lawyernsa da ya shige masa gaba ya jajirce sosai dan ba qaramin kudi ya zubar akan case din ba duk dan saboda suyi winning case din...And right there agaban su Ladan da sauran jama'an dake zaune cikin kotun Alkalin ya qaddamar da cewar Fadwa ta zama 'yarsa halak malak. Paid Book 500 8134692758 Fatima Musa Maina Opay Shaidar biya: 08134692758 MURADIN ZUCI 📖 Bintu Musa ✍️ Chapter 05 Free page Bayan kwana biyu da gama zamansu na kotu sai department of child services din suka yi masa duk wasu cike cike na takardu da yake buqata akan Fadwan wanda bayan nan har asibiti sai da suka kaita tare dashi akayi mata duk wasu gwaje gwajen da ya kamata kuma Alhamdulillah sai results dinta suka fito "Disease free", ba qaramin dadi Papa ya ji ba more especially da ya ga genotype dinta was excellent. Da fari su Eva sun nemi zabinsa na canja mata sunanta in yanada buqatan hakan amma bai amince ba. Sai da akazo cike mata surname ya nemi su cire Kargi daga cikin sunanta su saka mata "Fadwa A. Abdulfatah" akan wasu dalilai nasa da bai bayyana musu ba, har Ladan dake zaune a gefensa sai da ya kallesa a wannan lokacin amma baice komai ba. A kwana na uku. Yana riqe da ita suka fito daga social service office din Eva na biye dasu, sai da suka qarasa ga motarsa sannan ya juyo ya fara godiya a Eva, tana murmushi tace "This child is lucky to have you, Mr Kargi" yayi murmushi "Thank you once again Miss Eva" da haka ya bude motan sai Ladan ya nemi yi masa rakiya sanin me zai tarar a gidan nasa, girgiza kai yayi yace masa "Ba damuwa, zan kiraka" ya qarasa maganan yana saka Fadwa acikin baby stroller da yayi attaching da car seat dinsa wanda takanas ya siyo guda biyu, daya nata dayan kuma na upcoming babyn da za'a haifa masa. Bai dauki lokaci ba ya isa gidan sannan ya zagaya ya sake daukanta a hankali yana murmushi ganin yanda ko motsin tashi batayi daga baccinta. A compound din ya tadda su Imran na wasa da bingirar ruwa, Imran din na gudu Imam na biye dashi yana jiqashi suna dariya, ganin Papa da Baby hannu yasa suka nufesa da saurinsu, Imran yace "Papa, ka dawo mana da Fadwa?" ya gyada kai yana murmushi "She's back, as your sister" Imam yayi murmushi yafara kokarin karbanta sai Papan ya basa ita ya dora ta a kafadansa har da dan jijjagata kadan duk Papan na kallonsa, da haka kuma sannan suka shiga cikin gidan. Basu samu Momman a falon ba sai Habiba da take ta goge goge, tana ganinsa ta tsugunna suka gaisa sannan yace "Karbi yarinyar nan a mata wanka, akwai madaranta ko sai an siyo?" da sauri ta kalli hannun Imam ta kasa amsawa saida Papa ya sake maimaita maganan sannan ta amsa da "Eh ranka shi dade, akwai" da haka ta karbi Fadwan jiki a sanyaye tana hasko rikicin da za'a kwasa da uwardakinta. Maganarta Dutse....Momma na zaune a bakin mirror'n ta Papa ya shigo dakin, ta juyo ta kallesa sau daya ta dauke kai dalilin har sannan suna 'yar sama sama da juna, amma ga mamakinta sai taga ya zauna a bakin gadonta yayi patting gefensa yace "Zo ki zauna zamuyi magana" asannu ta tashi sannan ta qaraso kusada shi din ta zauna. Saida suka dauki wasu mintuna sannan cikin nutsuwa ya fara jefa mata tambaya "Fatima, Inason ki fadamin ko da akwai abunda na rageki dashi a iya zamanmu?" sai ta kallesa tana hade fuska tace "Meya kawo wannan maganan kuma?" yace "Inason ki bani amsata" ta girgiza kai tana kawar da fuskanta, ya sake cewa "Akwai ta inda na sabo a zamanmu? ko ta furuci..ko kuma ta yanda nake mu'amalantarki da yasa kike yawan daukana ba'a komai ba" nan kuma ta dan ware ido tace "Ni yaushe na dauke ka ba ba'a komai ba?" "In akan maganan 'yar tsintuwar can ce yasa kake fadan hakan ai nayi abunda ya dace ne" cike da bacin rai yace "Kina nufin kin fini sanin abunda ya dace kenan Fatima?, ace Ina mijinki amma kullum maganata ce zata zamo abun tsallakewarki, abun takawarki yanda kika ga dama, a kullum ke sai kinyi qoqarin defying dina a duk abunda zance kenan" a zafafe itama tace "Ya Ina matarka zakace sai kayi forcing dina akan abunda banaso. Tun kawowar yarinyar nan gidan nan nace maka ka fitar da ita kaqi to ya kake so in maka in ban kira an fitar min da ita daga gidana ba" Papa baisan lokacin da ya miqe ba yana munata da yatsa yace "Baki isa ba Fatima, baki isa ki juyani yanda kika ga dama ba in kyaleki. Bamu gaji haka a gidanmu ba kuma baza'a fara daga kaina ba kina jina?" "Yarinya kuma gatacan na kawota gidan nan a matsayin 'yata halak malak sai inga abunda zakiyi. Ta zama 'yata da tayi taking sunana a bayan sunanta na matsayin ubanta sai in gani ko ni da ke waye yafi wani sanin abunda ya dace" da haka ya juya tareda ficewa a zafafe ya barta nan zaune bakin gadon a daskare. Yana kaiwa tsakiyar falon yaji ta jawo hannun rigar sa da qarfi tana huci, ya juyo yana kallonta shima ransa na quna, cikin qwayar idanunsa take kallo tace "Wallahi bazan riqeta ba Abdulaziz, saidai ka zaba koni ko ita, kuma ayau ba gobe ba nakeson komawa gida na fasa haihuwa a qasar nan, ka maidani gida... ko zan haihu a jirgi yau bazan kwana a gidan nan yarinyar nan tana cikinsa ba" ta qarasa maganar qirjinta na hawa da sauqa. Shi mamakin qarfin halin ta ma yake matuqa, ace tana mace amma zuciyarta kamar ta mutanen fari wannan wace irin mace ce ita. A hankali ya zare hannunsa daga riqon da ta masa yace "Ba inda zakije daga gidan nan har sai kin haihu" sai kawai gani yayi ta nufi dakin da Fadwan ke kwance da hanzarinta kamar ba tsohon ciki ne a jikinta ba, ta tura kofar da qarfi tareda shigewa yabi bayanta da saurinsa, Imam ta samu a kusada Fadwan yana rainon ta kafin Habiban ta gama hado madaranta acan kitchen A zafafe ta qarasa bakin gadon Papan yana qoqarin riqota amma kafin ta duqa ga Fadwan Imam yayi saurin yi mata rumfa akanta da nufin kareta, cikin bacin rai ta hau dukan bayansa Papa na riqeta tana fadin "Wallahi sai an fitar da ita daga gidan nan" bai tsaya sauraronta ba ya matsar da Imam din tareda daukan Fadwan zai fice daga dakin, sai kawai Momman ta fashe da kuka me qarfi tana fadin "Ni ka maidani gidanmu ni da abunda ke cikina tunda ka samu wadda ta fimu a wajenka" bai kulata ba ya fice daga dakin Imam yayi saurin bin bayansa suka nufi upstairs. Dakin boys din ya kaita ya ajiye ta a upper bunk din Imam dan Imran yayi bacci akan nasa, sannan ya juya ga Imam din yace "Ka kula da ita karta fado" ya gyada kai tareda hawa gadon, da haka Papan ya sake ficewa amma kuma sauqansa downstairs din sai bai samu matar tasa a dakin daya barta ba, ya juya zuwa dakinta tareda murda handle din amma yaji a kulle kuma yana jiyo kukanta acikin dakin. Habiba ce ta fito daga kitchen din jiki a sanyaye dan ta jiyo komai sai ya kalleta yace "Kije dakinsu Imam tana can, in kin bata sai ku dawo dakin naku" ahankali ta amsa da Toh sannan ta wuce saman ba kuzari. Har dare Momma taki bude dakinta ga Jidda ma ta tashi daga bacci tana kuka duk Papan na jiyosu amma ba yanda beyi da ita ta bude kofan ba taqi. Habiba ma tayi iya kwankwasawanta amma Momma tayi biris dasu, ganin har karfe takwas na dare bata bude ba yasa Papa dauko landline phone dinsu na gidan dan kiran mutum daya da yasan zata iya tankwara masa ita, duk da yasan tsakiyar dare ne acan gida Nigeria amma haka ya danna kira ga layin da yasan zai samu yayar matar tasa mai suna Aina'u. A bugu na biyu mijinta ya amsa kiran cikin muryarsa dake cike da bacci sai Papan ya bashi hakurin tashinsa da yayi, yace "Ba damuwa Yarima ai kafi haka, mai dakin ta samu sauqa kenan" anutse Papa yace "Har yanzu da sauran lokaci, na kiraka bisa wani uzurin ne daban" sai yace "Ina jinka Yarima" nan Papa ya fara masa bayani a nutse duk da yanda kira yake matuqar tsada a wannan lokacin bai dameshi ba, burinsa daya a wannan lokacin shine yanda zai seta barakar da ta fara kunnowa a gidansa. Sun dauki lokaci me tsaho suna magana wanda iya adadin kudin da suka bata a wannan kiran in aka baiwa wani faqirin zai iya fitar dashi daga talauci na har abada, amma Papa baibi ta kan wannan batun ba har saida ya tabbatar ya isar da duk maganganun da suke bakinsa ga Alhaji Saminu mijin Anty Aina'u, a inda daga qarshe shima ya miqa wayan ga Aina'un ta cigaba da magana dashi Papan. Jim kadan da gama wayan nasu aka sake kira sai be dauka ba ya tafi daidai kofar dakin Momma yace "Fatima ki bude kofan nan ga Maman Kasim akan waya zakiyi magana da ita" shiru tayi daga farko bata kulasa ba har saida telephone din ta sake yin wani qaran alamun kira sannan ta murda key din kofan tareda miqo hannunta ya dora mata a tafin hannunta sannan ta maida kofan ta rufe. Momma bata dauki kiran ba sai da ta sake zama a bakin gado, aikuwa tana dauka ta fara cin karo da maganan Anti Aina'u a zafafe "Meye hakan kuma kikeyi kamar wata qaramar yarinya Binta?" tana shirin yin wani hawayen tace "Amma kinsan dai bai kyautamin bako?" Aina'u tace "To dan bai kyauta miki ba shine zaki bi lamarin ta kulle kanki a daki, da kikaje kan yarinyar dukanta zakiyi ko me?" "Kefa bakida hankali wani lokacin wallahi, ai ta nanata miki magana amma yana bi ta bayan kunnenki, banda ma Yarima yana matuqar sonki ai da baku kawo iyar haka ba da wannan banzan halin naki, toh wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki in ba so kike in kira Mama ba a goben nan, ke har Mai Martaba zan kira yasan abunda kikeyi tunda ke baki isa a miki magana kiji ba, ki na abu kamar bakya tuna inda kika fito, meyasa ke kullum sai anyi ta miki bita akan sha'anin zaman duniya ne wai?" nan kuma Momma ta fashe da kukan cin rai, jin wai har iyayenta za'a kira akan abunda aka mata dole tun fari, jin ta kasa magana yasa Aina'un cewa "Ki nutsu ki san me kike yi Binta, dan mijinki ya nemi taimakon marainiyar Allah ba hakan yana nufin ya shiga hakkinki bane, a yanda kika tara hadimai suna miki duk wani bauta ai kula da yarinyar nan bazai zamo abun damuwanki ba. Mijinki babban mutum ne dole ko bai riqe na waje ba zai riqe wasu na cikin gida ma, kuma nasha fada miki ba haka ake zaman duniya ba, da salo ake tafiyar da abubuwa irin haka. Koda bakya sonta ai bazaki nuna masa ba" ta dan dakata da maganan tareda sauqe numfashi sannan ta cigaba "Kin taso gidan mulki gaba da baya amma har yau bakida wayon yin dabarun iya zaman duniya" sai sannan Momman ta share hawayenta tace "Toh Adda me kikeson inyi ?" tace "Ki ajiye komai ki riqe mijinki, wannan yarinyar bata kai ta saka muku matsala a tsakaninku ba sai dai in ke kikaso, kuma wani batun kinason dawowa gida bai taso ba. You will born that child in good condition and come back home safe kina jina?" ahankali tace "Naji" da haka Aina'un tace "Sai gobe da azahar zan kira kafin nan garinku ya waye, banason inji wani batu sabanin wanda muka zanta dake yanzu kinji" ta gyada kai tareda fadin "Toh, saida safe" tace "Amin, kici abinci kuma ki bude kofan yanzu" nan ma ta amsa da Toh sannan sukayi sallama. Paid book 500 8134692758 Fatima Musa Maina Opay Shaidar biya: 8134692758 MURADIN ZUCI 📖 Bintu Musa Chapter 06 Free page Ta bude kofan amma sanin hali irin nata yasa ko shi Papan baya shiga sabgarta in ba dole ba duk da kuwa suna kwana kuma su tashi a daki daya. Every morning in sun tashi zai tambayi yanayin jikinta koda bazata amsa ba wani lokacin, sannan kuma yana lura da duk motsinta dalilin haihuwanta na nan tafe ko yau ko gobe. Wani zubin ma in yaga tana takawa da kyar shida kansa zai riqe ta ya tallafa mata wajen zuwa toilet da sauransu amma har sannan bata kulasa sosai. Ga yaranta ma hakan take saboda sun san halin mahaifiyar tasu a duk lokacin da take cikin irin wannan halin sai suke kaffa kaffa da ita. Banda Jidda da take zama a gurinta su twins zuwa suke gaisheta sannan su koma dakinsu, barin ma Imam da daman maganar bakinsa aiki ta zame masa. A tarin lokuta suma kansu iyayen suna mamakin hali irin na yaron nasu da ya kasance mai nutsuwar da ta kere sa'anninsa, wani irin haiba da nutsuwa Allah ya saka masa mai ban mamaki. Abun qarin burgewa game da lamarinsa shine yanda he's always attentive akan komai. Duk abunda yakeyi indai za'a yi masa magana nan zai maida dukkan hankalinsa yana sauraro kamar wani babba, dadin qarawa ta yanda ya dauki lamarin Fadwa da girma shi ya qara baiwa Papa mamaki game dashi, yayin da gadon sa ya zamo gurin baccin Fadwa a tarin lokuta, ko da Habiba ta tafi yin hidimar Momma shi yakan zamo mai kulawa da Fadwan har ta gama abunda take wanda bazaka taba ganin Imran yana yin hakan ba saboda yanda ya daukaki bacci da muhimmanci a rayuwar sa fiye da komai. A wannan lokutan da Fadwa take yawan yin bacci akan gadon Imam din haka zai tisata a gaba yana zanata a white sheets dinsa kuma ba wanda yake nunawa ko da wasa sai Imran kadai da ya sani kuma bai maida hankali akai ba dalilin sabon da yayi da ire iren zanen da Imam din keyi, dan harshi ma yana zanashi. in kuma Fadwa ta tashi Imam dinne zai kaita gurin Habiba ta bata duk kulawan da take buqata amma kuma yanayin hakan duk bada sanin mahaifiyar tashi ba. Dan wani irin zaman daki Momma ta koma yi kamar wadda ake kora daga gidanta, bata dai yin wannan mugun fushin amma kuma duk wani fara'anta da ake gani a gidan ta dauke daga fuskarta, kuma duk da hakan Papa bai fasa siyo mata duk abunda yasan tanason din ba, bai fasa kulawa da lamuranta ba, bai fasa zama da yaransa suyi hira ba, bai fasa cin abinci tare da iyalinsa ba, bai kuma fasa kula da Fadwa ba dan itama ya dauketa kamar 'yar cikinsa da kulawanta solely yake qarqashinsa yanzu. Duk wani abunda yasan Baby na buqata yana siyo mata shi harda maji gaba sannan bai fasa rainonta ba, akasarin lokuta Idan ya dawo daga gurin aiki zai dauketa a hannunsa su zauna anan falon suyita hira shida yaran nasa suna kallon wild life a TV, dan Papa mutum ne mai son kallon abunda ya shafi rayuwar dabbobin jeji sosai. Hakan da sukeyi shima sai ya zamto abunda yake qara tunzura Momma ganin 'ya'yan nata mazan ma basu damu da zuwa gurinta suyi hira ba wanda kuma itace sanadin hakan, mace ce da Idan tana cikin yanayi na bacin rai ko nukra sai ya shafi har 'ya'yan cikinta, abu kadan ta kai bugu, abu kadan tayi hantara ko zagi wanda duk yana daga cikin abunda yasa 'ya'yan nata suke janye jikinsu daga gareta in tana cikin wannan halin...They know better than to go near her. Bata sake zuwa inda Fadwa take ba tun incident dinda ya farun, ta danne komai aranta tana rayuwarta batareda ta waiwayi inda jinjirar take ba ko sau daya. Bata kuma damu tasan halin da mijin nata suke ciki akan kula da yarinyar ba wanda hakan ke qara ba Papa mamaki akan miskilancinta, amma sai ya danne komai arai shima ya cigaba da sauqe nauyin yarinyar da ya rataya a wuyansa batareda yabi ta kan matar tasa ba. Bayan sati biyu a wani yammaci Papa ya dawo gidan daga gurin aiki, a gajiye ya shigo falon sai ya samu Momman da yaran nasu duka a falo suna zaune ranan, Habiba na zaune a qasan Momma dake zaune akan kujera tana yanke mata farcen kafafunta, bayan Jidda ta taro shi da murnan ta sai suka qarasa ciki ya zauna a kujeran dake facing din matar tasa, twin suka masa sannu Habiba ma tana qoqarin miqewa tace "Barka da dawowa ranka shi dade" ya amsa da Yauwa sannan ya kalli Momman yace "How are you feeling?" cikin qanqanuwar murya ta amsa "Lafiya" sai ya sake kallon su Imran dake zaune a gefenta yana cin popcorn while Imam na riqe da nashi a hannu, yace dasu "Yau baku dauko qanwar taku ba ne?" dan tun da ya shigo ya lura da dukansu ne zaune a falon banda Fadwa, Imam baice komai ba amma dai Papan ya lura ba cin popcorn din yake ba yana zaune agurin ne kawai, kallon Habiba yayi data kawo masa drinks da bottle water yace "Yau tayi baccin yamma ne?" tace "Yanzu zan qara dubota ranka shi dade" Imran yayi saurin cewa "Batayi bacci ba Papa" sai kuma ya kalli Maman tasu da har sannan bata dago kanta daga gyaran farcen hannunta da takeyi ba, kallonta Papan ya tsaya yi yana ayyanawa aransa yau ma ta hana a kula da yarinyar kenan, sai ya dan girgiza kai tareda miqewa ya nufi dakin da Fadwan take Imam ya bisa da kallo. Bai dade ba ya fito falon hannunsa riqe da Fadwan sannan Habiba na biye dashi a baya cike da sanyin jiki, sai da ya iso gurin Momman ya juya yana kallon yaran nasa yace "Go upstairs" suka miqe Imam ya kama hannun Jidda suka nufi saman, saida ya jira suka shiga dakinsu sannan ya sake kallon Matar tasa da taqi kallonsa, a nutse ya budi baki yace "Fatima, kinsan Allah zai iya miki hisabi da wannan yarinyar?" ta dago kai tana hade fuska tace "Wane irin hisabi? Menene hadina da ita? Ko ka taba ganina a kusa da ita balle wani abun ya hadoni da ita?" bai bar kallonta ba yace "Why are you so cruel ne nikam? She's just a baby, a few weeks baby. Me ta sani a duniyar nan da har zaki rinqa mata irin wannan hukuncin?" rai abace Momma tace "Wai me na mata dan Allah?" Yace "Kin fini sanin me kikayi Fatima, yanzu ki duba fa kiganta, kashi ne a jikinta tun na safe yana wari, sannan ko madaranta baki bari an bata ba, bata samu na mahaifiyarta ba sannan wannan din ma sai an mata katanga dashi?" ya qasara maganar zuciyarsa na karyewa yana qara riqe Fadwan a jikinsa wadda har sannan idonta biyu kuma batayi kuka ba, sai Momman ta fara kokarin miqewa tace "Yaushe na hana a bata madaran?" ta kalli Habiba dake bayansa "Ni na hanaki bata madaranta?" Habiba ta girgiza kai da sauri tana qara sunkuyar da kanta, sai Papan ya sauqe numfashi yace "Fatima, duk wani fushinki da zakiyi ya qare a iya kaina, in kina qaunar Allah da manzonsa ki daina uzzzurawa yarinyar nan, babu ita acikin lamarin nan dan bata zabi hakan ba itama, in laifi ne naji. Ni na miki laifi amma ki cire ta aciki" sai lokacin Momma tayi wani qaramin murmushi tace "Au kasan kamin laifi kenan?" cikin gajiyawa yace "Face me, but don't drag this innocent child into this please" tace "Ka maida ita inda ka daukota, na fada kuma zan qara fada bazan riqeta ba Abdulaziz. Tun ba'a je ko Ina ba ni da yarana ka fara nuna mana banbanci akanta. Tun ba'a je ko Ina ba ka fara fifita ta akanmu" Papa baisan lokacin da ya zauna a kujeran gurin ba yana kallonta, ta cigaba da kallonsa tana fadin "Bazan lamunci ganin bare tana zama abun fifiko a zuciyarka fiye da jininka ba" ba shi kadai ba har Habiba ta girgiza da furucin bakin Momma, amma kafin ya amsa mata ta juya da saurinta ta nufi dakinta tare da bude kofan da karfi sannan ta shiga ta banko kofar duk suna kallonta shida Habiba dake tsaye a gefe har sannan. Sauqe nauyayyen numfashi yayi sannan ya miqa Fadwan ga Habiba yace "Ki mata wankan, amma ki fara bata madaran nata tukunna" ta qaraso ta karbi yarinyar itama zuciyarta na karyewa ganin yanda Fadwan ta fara koyan hakuri ala dole, sai taji ya sake cewa "Please ki rinqa iya kokarinki na ganin kin bata duk abunda take buqata, kuma ki rinqa fahimtar da uwar dakin taki akan gaskiya ko da a fakaice ne, yarinyar nan itada maraya banbancinsu kadan ne. Kema zaki iya fuskantar naki hukuncin a gurin Allah in har kika tauye mata hakkin kulawanta da na rataya miki" a sanyaye tace "Ka gafarceni ranka shi dade, da yardar Allah zan gyara" ya gyada kai kawai tareda daukan ruwan dake kan table din ya fara sha, da haka kuma ya miqe ya nufi dakinsa da ke upstairs dan yanda mai dakin tasa ta banko kofarta yasan ta datse harda makulli kuma. Amma ga mamakinsa da dare bayan ya gama putting yaran nasu to bed ya dawo dakin nata sai yaji a bude ta cire makullin, kan gado ya hangota ta kwanta as usual ta juya masa baya tana kallon ginin dakin, sai da ya kwanta tareda jan duvet ya juya bayansa shima sannan yaji muryanta qasa qasa tace "Ladan ne ya baka shawaran daukanta?" ya juyo amma bai amsa ba, sai ta miqe zaune itama ta juyo tana kallonsa ta sake cewa "Ladan ne ya saka ka daukota ko?" yace "Meyesa Ladan zai sani yin abu kamar wanda yayi owning dina?" tace "In bashi ba nasan ba ta yanda za'ayi nace maka banason abu kuma kaje ga abun nan, bamu taba haka da kai ba Baban jidda, meyasa zamu fara yanzu?" nan ya miqe zaune shima yace "Tun farkon ganina da yarinyar nan naji tausayinta kuma naji Inason kulawa da ita, da kika nuna bakyaso sai na fara tunanin in bada itan tunda baki aminta da mu riqetan ba, amma sai kikayi defying maganata Fatima. Kika nunamin kinada ikon kiyi abu a karin kanki bada izinina ba" tana share hawaye tace "Wallahi zuciyata bata aminta da yarinyar bane, yara irinsu akasari zakaga ba ta hanya me kyau aka samesu ba, d'an bature ba abun riqewa bane" sai yayi saurin cewa "D'a na kowa ne sannan Fadwa ba baturiya bace, abayyane yake tana da hadin jini da balaraben mutum, ko yau kika fara ganin jinjirin bature ne? And again D'a na kowa ne Fatima, muma bamusan..." tayi saurin katseshi da "Banason kana dangantamin yarana da irin maganganun nan" sai yace "Babu wanda yasan gobe Fatima, kar kiga muna cikin arziqi da daular mulki gaba da baya...Babu wanda yasan gobe" a dan fusace tace "Toh ni kodai 'yarka ce ne yarinyar nan?" ya ware Idanu da kyau yana kallonta yace "What??" ta sake cewa "Ka bani amsa in yarka ce Abdulaziz" sai kawai ya tsaya kallonta kamar wadda kai na biyu ya tsiro mata a wuya, bata bar kallonsa ba tace "Abdulaziz" a nutse ya amsa da " Fatima, are you insane?....kaf zuri'armu kin taba ganin me irin idon yarinyar nan?" tace "Probably ta biyo na uwarta wadda kayi tarayya da ita mana" nan kuma hakurinsa yakai geji, rai a bace ya daga murya yana cewa "Da mutuncina?. Da kimata?. Na fito daga tsatson mutunci irinna gidanmu sannan ki zargeni da bin wasu matan a waje har a haifamin dan gaba da fatiha...Fatima you're insane!" kawai ya miqe daga gadon dan zamansa a dakin zai iya sawa ya fada mata abunda ze iya regretting, ganin haka ta sake hasala itama tace "Toh in ba 'yarka ba ace ka dage lallai sai ka kula da ita, baka damu da mutuncin naka ba balle kimarka" yana tsayen yace "Kinsan me?...kiyi tunanin komai ma, ki yarda da duk abunda zuciyarki zata kitsa miki akanta, ga ki ga yarinyar ki kasheta. Ni kuma zan nuna miki nine ubanta a yanzu dan sai nayi shari'a dake wallahi, Fadwa mazaunin 'yar cikina take yanzu kamar yanda hakkin kulawan Jidda ya rataya a wuyana haka itama" da haka ya juya da sassarfa ya fice daga dakin tana kallonsa with shock. Paid book 500 8134692758 Fatima Musa Maina Opay Shaidar biya: 08134692758 From the writer of KUNCIN ZUCI...And now MURADIN ZUCI 📖 Bintu Musa Chapter 07 Free page A wannan daren babu wanda bacci ya yiwa dadi shida itan, and for the first time tunda suka zo qasar kimanin wata na biyu kenan a wannan daren suka raba makwancinsu, wanda hakan ba komai ya qara jawowa ba illa tsanar Fadwa da duk abunda ya shafeta a zuciyar Momma. Tayi kuka kuma tayi tsinuwa mara adadi ga wanda ma ya ajiye musu yarinyar a gidansu in the first place, dan a nata tunaninta gani take babu abunda riqon yarinyar zai jawo musu banda rushewar duk wani farin cikinsu a rayuwa. Da aka wayi gari twins sukazo gaishe ta tun daga bakin kofa Imam ya sha jinin jikinsa ganin yanayin mahaifiyar tasu, sai ya qarasa gareta a sanyaye tana zaune a bakin gado ta sunkuyar da kanta. Ahankali ya zauna kusa da ita sannan Imran ya zauna ta dayan barinta shima duk sukayi shiru, sai ta dago kanta tana kallonsu tace "Meye kun wani sani a tsakiya?" ahankali Imran yace "Kiyi hakuri" ta kalleshi sannan tace "Me kuka min? ba kun samu qanwa har kuna qin zuwa gurina ba, kuna gani banida lafiya amma rainon ta ya fi muku zuwa gurina ko?" nan ma Imran yace "A'a Momma" sai kawai sukaji Imam yace "Momma please let her stay with us" batasan lokacin da tureshi da dan qarfinta ba har saida ya kusa faduwa, a zazafe tace "Ficemin daga dakinnan kafin in saba maka, wanda baisan kishin nasa ba" sai kuma ya sake dawowa gefenta ya zauna bai fitan ba, kamo hannunta yayi ahankali yace "I'm sorry Momma" ta kwace hanun nata "Ka rufemin baki" yayi murmushi tareda sake kamo hannun nata, sai kuma tace "Kunyi breakfast?" ya gyada kai sannan Imran yace "Momma yaushe zamu koma gida? an koma hutun fa kuma Papa baice komai ba" sai ta shafa kansa da dayan hannunta tace "Soon. We'll go back soon". Papa ne ya leqo dakin ganin yanda suka sa uwar tasu a tsakiya yasa shi yin murmushi, yace "Sirri kuke yi ne?" suka murmusa amma banda Momma data kauda kanta bata kallesa ba, sai ya qaraso ya zauna shima a gefen Imam yana kallonta yace "Ya jikin naki?" ta juyo kadan ta amsa da "Lafiya" Imran yace "Papa yaushe zamu koma gida?" yace "Ka gaji da qasar nan kaima ko?" ya gyada kai sai Papan yace "Zamu koma in Momma ta haihu in sha Allah" nan kuma Imran din ya sake cewa "Allah yasa namiji za'a haifa mana" sai Papa yayi murmushi yana kallonsa kawai, anutse shima Imam yace "Amin" nan kuma Momma tace "Meyasa kuke son namiji?" kafin su amsa Papa yace "Ai haka debate din yake daman, namiji na son a haifa musu namiji, mace na son a haifa musu mace" Imran yace "Munason namiji tunda munada Fadwa yanzu ai" kawai iyayen suka tsaya kallonsa, ganin haka sai ya miqe adan hanzarce zai fice daga dakin sai Imam ya miqe shima, Papa bai bar kallonsu ba yace "Ina zakuje kuma?" Imran ya amsa da "Banyi breakfast ba" da haka ya nufi kofa Imam na biye dashi suka fice, sai sannan Papa ya juyo yana kallonta da kyau, ganin yanda ta dinke fuska yasashi nausar da murya yace "Fatima, abun da ya faru jiya.." bai qarasa ba tace "Banason jin komai daga gareka indai ba akan bayar da yarinyar nan bane Baban jidda, sabanin da muke samu akanta ya nunamin zaman ta a gurinmu ba wani alkhairin da hakan zai haifar" sai ya miqe anutse yace "Bazan bayar da ita ba, you should learn to live with that...abunda na fada miki jiyan shi zan sake fadi, Fadwa 'yata ce yanzu and nothing changes that" da haka ya juya zai fice kawai ta duqar da kanta tareda dafa goshinta tana jin wani zafi na taso mata tun daga qasan zuciyar ta. Atake kuma cikinta yayi wani irin juyawa da qarfi, ta buga wani uban qara tana salatin da yasa Papan juyowa daga bakin kofan da sauri ya sake nufota yana tambayan lafiyanta a rikice, durqushewa tayi bata bar yin salatin ba tana dafa cikin, dakyar ta iya fadin "I think my water broke" ya zare ido tareda juyawa ya kwala kiran Habiba da qarfinsa, aikuwa da gudunta ta qaraso dakin su Imam na biye da ita dalilin jiyo qarar da mahaifiyar tasu tayi, da sauri Habiban ta rufe kofa sanin zasu iya shigowa sannan ta qarasa da saurinta tafara riqe Momman dake fitar da numfashi, ga wani gumi da ya fara jiqata tun ba'a je ko Ina ba, atake Papa ya hau tambayanta in zata iya tashi, ta gyada kai dakyar alaman Eh sannan suka hau dagata shida Habiban dan ficewa da ita zuwa mota, dan a bayyane yake haihuwar ce tazo gadan gadan. A wannan yanayin suka isa asibitin a inda tun kafin su qarasa da ita ciki nurses suka taho da gadon daukanta akayi ciki da ita Papan da Habiba na biye dasu, sai da aka shiga da ita labor room sannan Papa yace da Habiban ta koma gida dan kula da sauran yaran tunda an barsu su kadai. Ranan wuni Momma tayi tana labor, ta azabtu iya azabtuwa kafin ta haifo 'yarta kyakkyawa me kama da ita. Bayan an shiryata aka miqo wa Papa ita ya rungumeta a jikinsa kamar ya maida ita ciki dan murna. Sai bayan Momma ta huta sosai zuwa 9 na dare sannan ya kira can gida Nigeria, sunyi murna iya murna barin ma Anti Aina'u data fara tunanin zuwa, amma sanin itama tana dauke da nata cikin yasa Papa yace mata A'a ba sai ta zo ba, a inda ya tabbatar mata da kuma sauran 'yan'uwansa akan sunanan dawowa cikin sati uku dan zuwa America a wannan lokacin ba abu bane me sauqi. A washegarin ranan Papa ya koma gida ya taho da yaran nasa har da Habiban zuwa asibitin, ganin Momma da Baby ba qaramin farin ciki ya sanya 'ya'yan nasu ba, suka dauki jinjirar fuskokinsu cike da yalwan murmushi kamar basu suka ce sunason namiji ba. Hankalin Papa na kan Fadwa har Habiba ta sauqe ta daga goyen da take a bayanta, nan ya dauketa sannan ya hau tambayan ko ta bata madaranta, ta amsa da Eh a ladabce duk Momma na kallonsu. Bayan shudewan wasu mintuna masu tsayi Ladan yayi sallama a dakin shida matarsa Zulaiha wadda yara ke kiranta da Mami, 'yar asalin Nigeria ce a inda ta kasance 'yar'uwa ga Ladan din ta fannin iyayensu har auren hadi ya shiga tsakninsu. Da fara'a suka qaraso sai Ladan ya dubi Momman yana mata sannu da jikin nata, sai Mami ta karbi jinjirar daga hannun Habiban sannan ta zauna a gefen gadon itama tana mata sannu sannan suka gaisa. Ladan kuma sai ya miqa hannu gurin Papa dake zaune a resting chair ya karbi Fadwa yana fadin "Kaga yarinya tayi wayo kamar ba ita ba" Papa na murmushi yace "Gaskiya, kullum qara wayo take" zama Ladan din yayi a gefensa sannan ya dan dunguri hancinta yana mata murmushi, kallonsa take qur da ido kamar ba jinjira ba sai kace mai haddace kamanninsa, bai bar murmushin ba yake kallonta sannan yace "An miki qanwa kema" Mami na kallonsu tace "Uhm, gaskiya ne" ta qarasa maganan tana juya kanta gurin Momma dake kallonsu Ladan din kawai. Sai da suka gama gaisawa bayan Ladan ya bada Fadwan ya karbi jinjirar shima yayi nasa addu'an sannan duk suka fice tare dasu Imam din kuma har sannan Fadwa na riqe a hannun Papa ya fitan, sai lokacin Mami tace da Momman "Ban taba ganin inda Iyaye suka fifita son dan wani akan nasu ba, kina ma da hakuri Maman Jidda" sai Habiba ta nufi toilet yin wani uzurin dan tasan kwanan zancen kuma, Momma ta dan gyara zamanta jin an sosa mata inda yake mata qaiqayi, tace "Hmm, kema kin ga abunda nake gani kullum ko" tace "Ai iya abunda na gani kadai ya isheni shaida Maman Jidda" ahankali Momma tace "Ashe dai bani kadai bace nake ganin rashin daidai a lamarin nan, Kinsan har hadani yayi da Anti Aina'u akan lamarin yarinyar nan, dan nace bazan riqeta ba" Mami tace "Haka Baban Kareem ya fadamin. A Ina aka taba yin hakan?. Tunda baki aminta da riqonta ba ai ba'a dole, bare ma D'an wani ai ba abun riqo bane sam, kar ma azo ga dan farin mutum da basu gaji da'a ba ko kadan" ran Momma na suya tace "Ina yin magana sai yace min tausayinta yake ji, akan ta babu irin maganan da baya ganin daman fada min, Idona fa ya kalla yace min ta zama 'yarsa da zatayi amfani da sunansa na matsayin ubanta sai inyi abunda zanyi, ki fadamin dan Allah ko dutse ne a qirjina bazan ji dacin hakan ba? A yanda Baban Jidda ya juya hali akan yarinyar nan shi yafi komai baqanta min rai, ba haka nasan mijina a baya ba Maman kareem, Yarima mutum ne da Idan nace banason abu to komin son da yake wa abunnan sai ya hakura dashi koda Uwah zata nuna baqin cikinta akai, ban taba tunanin akwai ranar da zatazo wai ni zai kalli Idona yace min 'Yayi abunda banaso din sai inyi abunda zanyi in na isa' Ni faaaa!" ta qarasa maganan hawayen na zuba mata tana sharesu, sai Mami ta kamo hannunta daya tace "Kiyi hakuri Maman Jidda, a gaskiya nuna miki cewan baki kai din ba shine mistake na farko da yayi, yarinya kuma dan kince bakyason riqeta babu mai miki dole ai" sai da ta gama share hawayen sannan tace "Maman Kareem ki bani shawaran yanda zanyi, wallahi Allah ne shaida banason yarinyar nan har raina kuma bazan taba sonta ba, da nayi tunanin harda hadin bakin mijinki aka daukota amma yanda Yarima ya juye gaba daya na tabbatar da ba sa hannun shi" sai Mami ta sauqe numfashi sannan ta girgiza kai "Ko daya wallahi Maman jidda, hasalima Baban Kareem ba yadda beyi dashi akan ya hakura da daukanta ba amma ya dage akan qudirinsa. Mijinki mutum ne mai addini sosai da sanyin hali ga kuma tausayi , kuma kiyi duba da irin gidan da ya fito, shiyasa hakan yayi tasiri sosai akan yarinyar. Amma kuma shi dan wani ba'a nuna masa so irin haka, duk inda akaje aka dawo nakan nan dai shine mai tausayinka" Jinjirar ce ta katsesu da kukanta sai Mamin ta miqa mata ita ta karba, sai da Momman ta dage riganta ta saka mata abincinta a baki ta karba sannan ta dago kai tace "Kinsan sau uku kawai ya dauki yarinyar nan, amma hankalinsa na kan waccan din ana kawota ya dauketa kina gani da ita ma ya fice riqe a hannu" sai Mamin ta dan tabe baki tace "Abunnan fa ke zakiyi tufka a lamarin tun wuri, ko sama da qasa za'a hada karki karbi yarinyar ko da kun koma can gida, zaki gani shida kansa zai bayar da ita riqo a wani gurin, ai saida kwanciyar hankalin matar gida ake samun nutsuwar tafiyar da kowanne lamura" Habiba da fitowanta daga toilet kenan sai ta dan tabe baki tana girgiza kai ganin yanda Mamin ke qara kunna wani wutar a zuciyar uwar dakin nata, amma babu halin ta kwabesu. Da irin wa'ennan maganganun Mami ta rinqa qara ingiza zuciyar Momma akan lamarin, ta rinqa dorata a hanyar da kwata kwata babu mabulla acikinta sai tarin kurakurai, kasancewan daman Momman tana neman abokin kuka yasa taji dadin yanda Mami ta kalli lamarin a fuskar da take kallo itama, har saida likita tazo duba Momman sannan zancen nasu ya tsaidu wanda hakan ba qaramin dadi yayiwa Habiba ba, dan abune dake bayyane akwai rashin tausayi a lamarin nasu barin ma Momman saboda tun ranar farko da tace a maida yarinyar waje cikin sanyin ta bata tsoro matuqa. Sannan bata tashi yarda da rashin imanin uwar dakin nata ba sai da ta fara hanata kula da yarinyar qarfi da yaji, wanda ita batasan dame zata fasalta zuciyar Momman ba saboda duk wanda zeyiwa jinjiri dan kimanin satikai horon yunwa toh lallai rashin imanin yakai maqura. Cikin kwanaki biyu da suka biyo baya aka sallamesu suka koma gida Habiba ta cigaba da kula da Momma sosai, sai ta tsiri goyon Fadwan akai akai ta yanda ko kitchen taje yin aiki zata kunceta ta bata madaranta, ko kuma inta shiga gyaran bandakin Momman nan ma ta sauqota ta wanke mata sayin da tayi, kuma taga nutsuwar hakan a idon Papan sosai dan burinsa shine yarinyar ta samu kulawan da ya dace daman. A kwanaki uku da suka sake biyo baya kuma yayi waya da Mai martaba a inda ya sanar dashi sunan da yake son a sakawa jinjirar, sanin cewa mahaifin nasa zai sa ayi yanka a 'yar tasa yasa yayi shiru bai kashe wayan ba bayan sun gama magana, jin haka sai dattijon nasa yace "Kana da wani abun fadi ne?" a ladabce yace "Ina neman alfarman a hada musu yankan ranka shi dade" dan shiru Mai martaba yayi da fari kafin yace "Ba damuwa". Da wannan Mahaifin nasa yasa akayi yankan raguna da shanukai akayi sadaka, a inda Yarinyar taci suna Khadijah, Fadwa kuma aka bar mata sunanta. Cikin sati uku da 'yan kwanakin da suka biyo baya wanda ya kama new year suka hau fara shirin komawa gida. Paid book 500 8134692758 Fatima Musa Maina Opay Shaidar biya: 8134692758 MURADIN ZUCI 📖 Bintu Musa Chapter 08 Free page Tun ana sauran kwana biyar su koma Nigeria Papa yasa Habiba hada kayan Fadwa tsaf acikin jibga jibgan akwatunan da ya siyo mata guda biyu. Dan kayan da ya siya mata zuwa wannan lokacin bazasu dauku cikin madauki daya ba saboda tarin yawansu, wuni biyu Habiba tayi tana hade kayan guri daya sannan ta hau killace na uwar dakin nata dana Baby Khadijah, su Imam kuwa sun riga da sun hada komai daman tun kafin zuwan wannan lokacin. Da Papa yaga yanda Mamma ta hada komai nata kamar wanda bazata dawo qasar ba saida yayi mata magana "Fatima bazaki bar wasu ba? I want us to return during fall (Autumn season), saboda akwai sauran ayyukan da ban gama kammalawa ba anan" batareda ta juyo ba tace "Ni dai na gama zaman qasar nan babu abunda zai dawo dani zuwa nan da September kuma, babu alkhairi ko na misqala zarratan acikinta, zaman cikinta bai qareni da komai ba sai guzirin baqin ciki" ta qarasa magana tana sake tula wasu sauran kayan cikin qaton box dinta, yana kallonta yace "Wane irin maganane wannan kuma, kinaji fa maganan aikina nake miki wanda dole zan buqaci iyalina a kusa dani saboda dogon zaman da zan dawo yi" sai sannan ta kallesa tace "Wallahi bazan sake takowa cikin qasar nan kwana kusa ba. Nasani gaba kuma ko 'yan biyu za'a ajiye mana a kofar gida" tsayawa kallon juna sukayi sai can ya girgiza kai sannan ya nufi crib din da Baby Khadija ke kwance aciki ya fara kokarin daukanta. Tana tsayen take kallonsa amma ganin bai kulata ba yasa tayi kwafa ta cigaba da jera kayanta tana ayyana yanda zata bullowa alamarin in sun koma. Ana gobe zasu tafi su Ladan sukazo yi musu sallama tareda 'ya'yansu biyu wadda babbar suke kiranta da Kamila sai ma biyinta da shima ake kiransa Kareem wanda shekarunsa sukazo daidai danasu Imam. A wannan lokacin ma saida Mamin ta san yanda tayi ta dora Momman akan wasu maganganun da suka kebe a dakinta. Ladan kuwa da ya karbi Fadwan sai tausayinta shima ya kamasa na ganin za'a tafi da ita inda ko a mafarki batada wani hadi da mutanen dake rayuwa a qasar, can ya miqata ga Papan yace "Allah ya baku ladan riqonta ya kuma albarkaci rayuwarta da na 'yan'uwanta gaba daya" Papa ya amsa da Amin yana kallonta, dan a badini shima in aka tona zuciyarsa tausayin yarinyar yake ji a kullum, saboda har sannan bai cire rai da dawowar mahaifiyar ta ba, a kullum yana fatan suji sallamanta akan ta dawo karban yarta amma ya sani wannan mafarki ne da bai san ranar farkawansa ba. Ranan da zasu tafi tunda sassafe Ladan din yazo sannan Papa ya kira musu Uber guda biyu, daya Ladan ya shiga dasu Imam harda Habiba dake goye da Fadwan, dayan kuma shi ya shiga tare da mai dakin tasa yana riqe da Khadijah suka tafi Airport. Isarsu basu dau wani lokaci ba yayi sallama na aminci da aminin nasa sannan jirginsu ya tashi. Wuni guda sukayi cur kafin suyi layover a Heathrow Airport -London na wasu qalilan din awanni sannan suka sake bin wani flight din da zai kaisu Lagos. Nan ma sai da suka kwana biyu a Lagos suna hutawa a Babban family house din su Papan sannan suka sake bin wani flight din zuwa Kanon Dabo, inda anan ne kuma zasu kai ga Masarautar Kumi dake garin Kano, babbar daula da karfin iko da dukiya yasa tayi qaurin suna a kaf fadin Nigeria a wannan lokacin. Sunan Masarautar Kumi babu lungu da sakon da bai zagaya ba tun a 18-hundreds har zuwa wannan qarnin da ake ciki, wanda sarki Abdulfatah yake jagorancin ta a wannan shekarun tareda 'ya'yansa maza guda hudu wanda uku suka fito daga dakin uwar gidansa mai suna Amina (wadda ake kira da Uwah) sannan guda daya kuma ya fito daga dakin Amaryarsa mai suna Aisha (wadda Allah yayiwa rasuwa shekaru biyu kenan) . Sarki Abdulfatah dattijon mutum ne da ya kasance mai sanyi da dattako ta kowanne fanni, a inda wannan kyawawan dabi'un nasa suka sauqa har zuwa kan 'ya'yansa guda hudu da Allah ya basa, Abdulaziz (wato Papa) shi ya kasance na fari kuma Yarima mai jiran gado a wannan lokacin, sai na biyunsu Abdulrazaq da na ukunsu Abdulmalik sannan Abdulrahman da suke uba daya dashi kuma qaraminsu. Sanin hali da kuma irin tarbiyar da mahaifinsu ya tasosu dashi yasa Papa baiji shakku ko kadan akan daukan Fadwa ba. Hasalima yasani wannan shine hukunci mafi daidai da mahaifinsa zaiso ya yanke a wannan lokacin, shiyasa baya dana sani ko kadan akan daukanta kuma cike yake da yaqinin iyayensa zasu karbeta kamar yanda ya karbeta shima. Auren Papa da Momma hadi ne na Allah a sanadin iyayensu a inda masarautu biyu suka hade ta fannin aure. Momma ta fito daga daular Kubaya da ke garin Bauchi, 'yar sarkin dake reigning a wannan lokacin shima, su uku mata suka fito a dakinsu, babbarsu Aina'u sai Binta da Khadija wadda suke kira Madina sai kuma babban yayansu daya kabiru . Kasancewarsu 'ya'yan mace ta biyu a gidan sai hakan yasa mahaifiyarsu ta zamo mace mai babban buri a rayuwa, dan daga Binta har Aina'u da ta kasance yayarta saida kowaccensu ta shiga gidan gani na fada, a inda Aina'u take auren hamshaqin mai kudi a Abuja wanda kuma ake juya qasar dashi a siyasance, sai ita Binta (wato Momma) dake auren dan sarkin Kumi mai jiran gado. Daula da tarin dukiya ta sarki Abdulfatah da 'ya'yansa yasa mahaifiyarta ta san yanda tayi ta tusawa mahaifin nasu aqidar auren har ta isa kunnen sarki Abdulfatah, wanda shima yayi farinciki da kuma amanna da kasantuwar hakan har auren ya qullu tsakanin 'ya'yan nasu. A farkon tarayyar aurensu Binta ta kasance mace mai duqar dakai ga mijinta kuma tayi kokari sosai wajen boye halayenta na badini amma akace hali zanen dutse, da tafiya ta fara nisa nan kuma Abdulaziz ya fara gane wace irin mace iyayen nasa suka aura masa ta fuskar halayya. Haihuwarta na farko mai martaba ya sa aka musu cuku cukun visa suka tafi United States ta haihu acikin garin Houston, inda ta haifo 'ya'yanta biyu maza masu haiba, na farin daya fito a mintuna ashirin na farko aka saka masa suna Imam sai na biyunsa Imran. Ya'yan da suka fito cikin gata ta kowanne fanni na rayuwarsu, ta inda Imran ya dauko kamannin Papa gaba da baya harda duhun fatarsa sai kuma Imam ya dauko mahaifiyarsu ta fannin hasken fatarsa. Papa bai taba jin yana alfahari da Momma irin na wannan lokacin ba, dan wannan kyauta da Allah ya basa ta silar ta ba qaramin farin ciki hakan ya saka masa ba, ya kuma dauki damarar zama da jure kowanne hali da mai dakin tasa zata bijiro dasu ko agaba ne. Dan Adam da samun waje..sai ya kasance Momma batayi duba da hakuri da sanyi irin na mijinta ba gurin wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu, sai tayi amfani da kyawawan mu'amalarsa a gareta gurin baje kolin duk wani fitinarta akansa, amma a dukkan mafari dole ya kasance da qarshensa, dan karo na farko tayi gamo da wani bangaren halayya daga mijin nata akan jinjira Fadwa, kuma a karo na farko ya fara taka mata burki akan halin da ta sabarwa kanta dasu. Amma kunaga wannan soyayyar da yake nunawa Fadwan a gurin matarsa ba wata wutar yake sake cinnawa a zuciyarta ba? Shin hakan zai fidda da mai ido kuwa?... Ba miqaqqiyar tafiya bace a wannan labarin. Sai mun hau tudu da kwari dangane da labarin Fadwa acikin wannan babban gida na sarauta a inda zamu gani shin da gasken zata kasance daya daga cikinsu, ko kuma zata rayu ne a qarqashin kaddarar da ta barota da qasar haihuwarta? ------- Ranan da jirginsu ya sauqa garin Kano da yammaci suka samu motoci har guda biyu suna jirar isowarsu dan kaisu gida kuma duk a qarqashin umarnin Mai martaba dan mutum ne da yake daukaka lamarin 'ya'yansa ta fuska me kyau wanda kowa ya shaida hakan, kar ma azo batun 'yan biyun jikokinsa da yake matuqar so. Duk wanda yake kwana ya kuma tashi acikin Masarautar nan yasan soyayyar dake tsakanin Mai martaba da jikokinsa biyun nan wanda hakan har ya taba mahaifiyar su, shiyasa duk fitinar Binta a gidan kusan tarin lokuta mai martaba yana kauda kansa ne dalilin wannan 'ya'yan nata guda biyu, duk yanda Uwah take kwana da abun a ranta haka take hakurin zama da matar dan nata mai shafaffen ido. Sai yamma lis motarsu ta isa shimfideden gate din da zai shigar da mutum cikin tanqamemen gidan, a inda gidan Papa yake nesa da sashen mahaifan nasa, dan tafiya ce mai dan nisa da aqalla zata dauki mutum 15 minutes in yana tafe bisa kafa ba abun hawa ba. Gefe da babban building din su Papan kuma wani building ne da bai kai nasun ba amma ya tsaru shima iya tsaruwa sannan bana kowa bane face 'ya'yansu guda biyun nan, gini ne tsararre da Mai martaba yasa aka yisa musamman dansu ya kuma zuba hadimai masu kulawa da sashen, sai ya zamto Twins suna da nasu kebabben gidan wanda ko basu wuni acikinsa ba suna zuwa kwana acikinsa. A yammacin nan sun san sun dawo gida dan tun kafin aje ko'ina jama'a suka fara cincirindon zuwa sashensu, sanin za'a shigo dinne yasa tun wuri Papa ya ware daki daya dake cikin falo na farko na sashen Momman yasa Habiba kintsa kayan Fadwan anan, dayake suna da hadimai masu tarin yawa sai ya zamto ko Ina tsaf yake a gyare. Momma kuwa gaba tayi zuwa falonta na biyu kafin a dangana da makeken dakinta, sai ya kasance duk wa'inda suka shigo can falon nata suke isa dan Papa ficewa yayi zuwa nasa sashen daganan kuma ya wuce gurin Uwah. A babban falonta ya sameta zaune da wasu qannenta da suke cousin suna magana, shigansa ya samu guri ya bisa kujera ya gaisa da mahaifiyar tasa, ta amsa da "Ma sha Allah, ya gajiyan hanya" yace "Alhamdulillah" sai ya juya ya gaishe da iyayen nasa dake zaune ta dayan sashen falon, daya da suke kira Baba Ladi tace "Sannunku da dawawo, kunsha zaman turai ba laifi" yayi murmushi kawai, sai ta sake cewa "Naji labarin har da wata 'yar ka dauko riqo daga can" yace "Eh Babah, Allah yayi ikonsa" kafin ta sake cewa komai Uwah ta katseta da fadin "Wato anan dai zakuyi gaisuwan barkan, ai kwa qarasa kuga 'ya'yan nasa" sukayi murmushi sai Baba Ladin tace "Zamuje Dada" ta kalli Papan tace "Allah ya taya riqo, ya bada ladan niyya, gaskiya kayi qoqari sosai" dayar ma tace "Sosai gaskiya, Allah yayi jagora" ya amsa da "Amin Amin". Sai da ya jira suka gama sauran maganganunsu da Uwah suka tafi sannan ya gyara zama sukayi sabuwar gaisuwa, nan da nan Hadimarta mai suna Laraba ta cika masa gabansa da kayan ciye ciye, yakai hannu ya dauki yankan kankana guda daya Uwahn tana kallonsa tace "Ya iyalin naka?" ya amsa da "Alhamdulillah, suna kintsawa ne" ta gyada kai sannan tace "Sai anjima zaka qarasa gurin Dattijon?" Yace "Eh yanada baqi yanzu" tace "Toh ba damuwa, anjima sai mu hadu acan din". A daren kowa ya hallara a Babban Falon Mai martaba dake sashensa, wanda anan ne yake gudanar da duk wani taron da ya qunshi iyalinsa da 'yan'uwa. Momma na riqe da Khadija ta shigo Habiba na biye da ita a baya riqe da Fadwa a nannade cikin towel. Imam da Imran daman suna gefen Mai martaba an cika musu gabansu da kayan marmari shi kuma yana kishingide da hannunsa daya kan tum tum pillow irin na gidajen sarauta. Sanye Dattijon yake cikin alkyabba amma madadin rawani akansa sai ya zamto hulace da ta zanu da adon irin na alkyabban. Papa dake sanye cikin nashi kayan sarautar shima yana zaune tare da Abdulrazaq sannan Abdulrahman dan Abdulmalik baya qasar shima a lokacin yana matakin karatunsa na Phd a Manchester (England). Samun waje Momma tayi a gefen matar Abdulrazaq din mai suna Maimuna ta zauna. Cike da nutsuwa Mai martaba ya fara gudanar da taron da addu'a, sannan aka gaggaisa, Momma kanta a qasa ta gaishe da surukan nata sannan Mai martaba ya dan miqe zaune, ganin haka sai Abdulrahman ya miqe tsaye tareda nufan Momman ya karbi Khadijah sannan ya kaita ga mahaifin nasu, karbanta yayi yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi yace "Ma sha Allah, Sannu Khadija" Uwah tayi murmushi tana kallon jikar tata itama, sai da ya mata addu'o'i sannan ya miqata ga Uwah itama ta sanya wa yarinyar albarka sannan ta miqata ga Uncles dinta suma, sai kuma yace "Ina baquwar tamu?" duk mutan falon sai da sukayi murmushi harda Papan, Uwah tace "Ai da ita ake tafe daman" nan da nan Habiba ta miqe tareda kai Fadwan gurin Uwah, ta karbeta tana kallonta sosai, kasancewan ko'ina da hasken wuta a falon sai ya zamto idonta tar yake a bude tana kallon kowa, nan da nan idon kowa ya koma kanta suna kallonta, Uwah na murmushi tace "Ma sha Allah, kaga yarinya kamar ita tayi kanta" Abdulrahman dake kallonta shima yace "Ma sha Allah" sai Momma ta dago kai tana kallonsu, da aka miqa Fadwan gurin Mai martaba ya karbeta sai yace "Tubarakallah wannan Idanu kamar daman da shirinta na aurena tazo" sai duk mutan falon suka dara banda Momma, Maimuna da kuma Habiba. Uwah tace "Ai kuwa bazan iya kishi da wannan ba, inaa" sai Momma ta juya tana kallon yarta dake riqe a hannun Abdulrahman din amma idonsa na kan Fadwa, ji tayi kamar ta miqe ta karbeta ta bar falon amma tasan ko giyar wake tasha bazata fara kwatanta yin hakan ba ko da wasa, sai ta gyara zama tana duqar dakai cikin qunar rai, wato dagasken dai 'yan'uwansa zasu goyi bayansa akan daukan yarinyar, lallai bataga ta zama ba, lallai ne tasan ta yanda zata bullowa al'amarin tun kafin dare ya mata. Ta bangaren Papa kuwa fuskarsa cike take da fara'a a wannan lokacin, dadin ganin yanda ahalinsa suka karbi Fadwan ya sanya masa farin ciki matuqa arai. Da Mai martaba ya mata addu'a har dashi aka amsa a falon shima yana kallon diyar tasa da har sannan idonta ke bude. Sai da aka miqata ga su Abdulrazaq sannan Mai martaba ya fara nusar dasu gaba dayansu game da ita, ya musu nuni da yadda da kaddara da kuma taimako a rayuwa, cikin girmamawa mutan falon suke amsa nasihar tasa, a tausase ya sake cewa "Wannan yarinya ita irin tata kaddarar kenan a rayuwa. Mafi kyawun riqon da za'a mata shine a alaqanceta ta fuska me kyau. Fada mata abunda ya faru da ita ba daidai bane, Inason dukkaninku ku zamo masu rufe wannan al'amari. Ban yadda wani ya tona mata wannan sirri in ba dolen hakan ce ta faru ba" duk suka amsa har Momma da Papa. Paid book 500 8134692758 Fatima Musa Maina Opay Shaidar biya : 08134692758 MURADIN ZUCI📖 Bintu Musa Chapter 09 Free Page Bayan kwana biyar da dawowar su Papan ya fara shirye shiryen gagarumar walima na sunan 'ya'yan nasa. Zuwa sannan labari ya karade ko Ina acikin Masarautar da wajenta akan batun ya dauko 'yar riqo daga America, duk da har zuwa wannan lokacin ahalin gidan basu yarda an bude zancen na cewar tsintar yarinyar akayi ba, sai mutane suka dauki zancen akan Papa ya taho da yar riqo ne, amma sanin daga gurin waye dinne kuma kowa ya kasa fahimta, duk qwaqwai din 'yan gulma a dangi haka suka fara hakura, dan ko Momma haka taja bakinta tayi shiru akan Fadwa dan abunda take binnewa a zucyarta kadai ya isheta. Ana gobe hidiman ne 'yan'uwanta Aina'u da Madina suka iso daga Abuja suma. Kasancewan isowar dare sukayi nan da nan Papa ya aika driver aka daukosu, bai shigo sashen ba har saida suka huta suna cin abinci, cikin mutuntawa suka gaisa sannan ya juya tareda nufan kofa ya fita sai Momman ta dan bi bayansa da kallo fuskarta a dinke, ganin haka yasa Aina'u ta ajiye spoon din hannunta tace "Banason wannan abun da kikeyi Binta, a bayyane yake abun naki ya fara wuce gona da iri" sai Momman ta sauqe riganta data daga tana shayar da Khadijan, sai da ta ajiye ta a gefenta nan kan kujera sannan tace "Ni me nayi kuma Adda?" Madina ta kalli Aina'un itama ta dan tabe baki bata bar cin abincinta ba, sai Aina'un tace "Kin fini sanin abunda kikeyi ai, ke abu baya wucewa a gurinki ne wai?" caraf Madina tace "Fisabilillah sai kar ta nuna bacin ranta bayan an mata ba daidai ba" nan Momma ta kalli Madinan tace "Ai ita Adda a kullum ko me za'a min a gidan nan bata taba ganin laifinsu sai nawa, bayan kuma a ko da yaushe ni ake duka sannan a hanani kuka. Meye nawa dan nayi kishin soyayyar mijina da ta 'ya'yana?" Aina'u na kallonta tace "Wannan son zuciya ne kawai Binta, ba wani kishin soyayya, kina magana kamar wadda mijinta ya qauracewa gaba daya a rayuwa" tace "A yanda muka dauko wannan hanyar ni dashi daf muke da shiga wannan fannin, Adda wai ni zai nunawa 'yar tsintuwa ta fini da 'ya'yana a idonsa" rai a bace Madina tace "Toh wai ni meya hanaki rabasa da yarinyar tun a can ne?" Aina'u ta banka mata harara sannan tace "Banason irin haka Madina, kema watarana in kina abu kamar kanki a kunce" Momma tace "Ai gaskiya take fada nima da nawa sakacin kuma zan dauki mataki nan bada jimawa ba dan bana hada soyayyar mijina da kowa bayan 'ya'yana a gidannan wallahi, ko Uwah haka tayi hakuri ta barni, dan haka baza'a fifita d'an wani data kasance bare akan 'ya'yana kuma akan Idona sannan nayi shiru ba" Ainau tace "Yanzun har yaushe ma ya dauko yarinyar da zaki rinqa yin irin wannan maganganun? Grow up mana, it's high time ki rinqa tantance abunda ya dace da wanda be dace ba" tana kallon Yayartata ta wani hade fuska "Menene abunda bai dacen ba? Dan nace banason yarinyar?" Aina'u ta amsa da "Eh mana! Toh in kikace bakyason ta kina son kiga shima ya qi yarinyar ne, ya kike so yayi da yarinyar toh in ke baki jata a jikinki ba" Madina tace "it's obvious ai Adda, sai ya bada ita a wani wajen daban tunda matarsa bata so. Simple" Aina'u dake jin ranta na baci da qannen nata tace "Banason Ina magana kina saka min baki Madina, wannan raini ne kina jina? In bazaki tayani mu dorata akan hanya me kyau ba sai ki rufemin baki" sai Madinan ta juya kanta tana hade rai, can kuma ta ajiye spoon din hannunta ta miqe sai Momman tace mata "Me kikeyi har yanzu baki koma gidan ba?, aure da saura wata biyu" saida ta zauna akan kujeran dake kusa sannan tace "Sai nan da sati hudu zan koma, mitan Mama dayawa wallahi, komai sai tayi fada akai" Aina'u tace "Sai kace bamusan halinki ba" sai Madinan ta kalleta tace "Adda ki fito fili kice in bar miki gidanki kawai" tace "Meyasa zance ki bar gurina Madina, kema kinsan duk fadan da nake miki suna bayan soyayyar da nake miki ne" Momma tayi murmushi tace "Madina duniya, da sai ince to kizo nan muyi zaman mu kawai" Aina'u tayi saurin cewa "Ai saidai bayan Idona zaku zauna guri daya a irin wannan lokacin, sai ta zauna ta tayaki uzzirawa mijin naki kenan" sai duk suka fashe dariya Madina har da kyakyatawa, nan kuma twins suka shigo tareda Kasim da shima yake sa'ansu, Imran na ganin Madina ya fara murmushi sai ta daga masa hannu da nufin suyi shake tace "My boyyy" yana dariya ya miqa hannunsa sai Kasim kuma ya zauna a gefenta. Idon Aina'u na kan Imam tunda ya shigo har ya zauna a kujerar dake dan gefe dasu yayi kwanciyarsa dan daman sun gaisa tun zuwansu, sai tayi murmushi tace "Imamu ana nan da hali dai" Momma ta juya tana kallonsa itama, tace "Sai ki rasa me yake dannewa a cikinsa da bazai fitar ba, ayi mutum sai dan banzan zurfin ciki" sai ya juyo yana kallonsu bai ce komai ba, Aina'u ta sake yi masa wani murmushin tace "Kaci abinci?" ahankali ya amsa da "Eh" ta sake cewa "Me yake damunka?" sai gani sukayi ya dan yi murmushi tareda girgiza kansa, Madina na kallonsa tace "Allah ya baki daya Adda Binta" nan ya miqe tareda nufan gurinta yace "Kai Anti" ta dan turesa tana dariya tace "Ni ka matsa min daga nan jare, kana ganina ai ka dauke kai" bai fasa kwanciyan a gefen nata ba sai ta kyalesa ta cigaba da hiranta tareda su Imran da Kasim. Can suna zaune daya daga cikin hadimar Momman ta shigo Mai suna Laure dalilin kiran da uwar dakin nasu ta mata, sai da Momma ta gama lissafo mata abubuwan da zata mata sannan ta kalli Yan uwan nata tace "A kawo muku ita ne?" Aina'u tace "Jinjirar?" ta gyada kai sai Madina tayi saurin cewa "Mezamu mata in mun gantan Adda?" Kafin Momman ta amsa sai Aina'un ta dubi Laure tace "Ki kawo ta kinji" da haka Lauren ta amsa a ladabce sannan ta juya ta fice. Bata dade ba ta dawo falon dan sanar musu an kaita gurin Uwah, Momma ta tabe baki batace komai ba ganin yaransu na zaune dasu agurin. Suna cikin hiran Aina'u ta miqe a sannu zata shiga dakin Momman, dan itama cikine a jikinta na wata shida, Sai Maimuna ta shigo falon hannunta riqe da yarinyar ta mai suna Sajida dake da shekara daya da wasu watanni, komawa tayi ta zauna da fara'arta dan sun san juna kuma suna zumunci da juna a Abuja. Maimuna ta qaraso ta zauna sai Twins suka mimmiqe har Kasim din suka fice. Saida suka gama gaisawa sannan Maimuna tace "Anti Binta sai hakuri fa, naji maganganu na tashi akan lamarin yarinyar nan" Momma tace "Uhm, kuma babu yanda aka iya dani ba, masu maganan sai su karbi riqonta ai ba laifi" Aina'u ta dan dafa kafar Momman amma sai tayi biris zata cigaba da maganan, nan da nan Aina'u tace "Ai dama sha'ani irin haka sai an hada da hakuri" Madina ta gyara zama tana tabe baki a fakaice, dan itafa tun kafin ta ga yarinyar ma taji ta fita ranta sanadiyar matsalan da yayarta ke samu akanta. Maimuna bata bar sashen ba sai da Momma ta fada mata kusan duk abubuwan da suka faru tun a Houston, Aina'u dai miqewa tayi daga qarshe ta shige dakin Momman dan tayi uzurinta, dan in ta cigaba da zama tasan tsaf zasu hau sama su fado itada qannen nata, kuma agaban faccala. Ansha hidima sosai dan 'yan uwan Momma sosai suka zo gurin taron daga Bauchi. Ganin yanda kowa in yazo yake tambayar jinjirar da aka taho da ita yasa Uwah ta aika hadimarta zuwa sashen su Momman aka taho mata da Fadwan dan ta matsar da ita daga idon mutane, dan har zuwa sannan idanuwanta a bude suke tana lura da yanda al'amuran yarinyar zai tafi a gidan d'an nata, saboda zuciyarta taqi aminta da cewar matarsa ta karbi yarinyar kamar yanda ya fada musu. Wunin ranar sai ya zamto ita ta kula da yarinyar da taimakon babbar hadimarta Laraba. Har aka gama hidiman aka watse Momma bata nemi sanin inda aka kai Fadwan ba haka zalika ko da yan uwanta sun tambayeta inda Yarinyar take bata dogon zance akai. Sai washegarin ranan su Aina'u suka fara shirin tafiya, sai da suka gama kintsawa tace da Madina "Muje muyi sallama da Uwah yanzu" da haka suka fito Babban falon sashen sai suka hadu da Papa da shima shigowarsa kenan tareda Abdulrahman a biye dashi, gaisawa sukayi dan rabonsu dashi tun daren da suka iso sai dai Momma taje sashensa sannan ta koma wajensu, sai gamuwar tasu tayi wuya. Da fara'arsa yace "Mun gode da hidima fa Maman Kasim" ya kalli Madina "Mungode Khadija" fuska a sake Aina'u tace "Ba komai mune da godiya, Allah ya raya zuri'a" yace "Amin, an kawo muku yar'uwartata kun ganta kuwa?" cike da waskewa tace "Eh mun ganta, Allah ya taya riqo ya bada lada", sai Papa ya amsa da "Amin summa Amin, ba dai ayau zaku koma ba" nan ma tace "Yau ne, zuwa anjima in Allah ya kaimu" sai yace "Okay Kamal zai kaiku" ya juya ga Abdulrahman dake bayansa yace "See to it please, yazo da wuri kar su jirashi" ya amsa da In sha Allah sannan su Aina'un sukayi godiya, Papan ya sake cewa "Agaishe da Honorable da Allah, mungode sosai" ta amsa sannan suka fice shikuma ya nufi nasa sashen. A falon Uwah suka sameta tareda wasu matan dattawa guda biyu, bayan sun gaisa aka kawo musu kayan ciye ciye sannan tace da Laraba ta dauko musu Fadwan. Da ta fito da yarinyar sai ya zamto Madina ce ta kusa da ita amma sai ta kafse taqi karbanta wanda yasa Aina'un miqa nata hannun da sauri ta karbi Fadwan dake nannade a towel tana bacci, da fara'a tace "Ma sha Allah, Uwah kinga yarinya tas da ita" fuska a sake Uwah tace "Sai Ma sha Allah" tace "Allah ya taya riqo yasa ta zamo cikon addinin muslinci" Matan ne suka riga Uwah amsawa sannan itama tace Amin tana lura da Madina da tace "Allah ya raya". Bayan kwana biyu Uwah ta kira Papa zuwa sashenta da dare, ita kadai ya samu zaune riqe da Fadwan a hannunta tana jiran isowarsa, sai da suka gaisa sannan ta fara magana cikin nutsuwa "Ban kasance mai kai idanuna acikin gidanka ba sai wannan karon da yazama dole, da farko banyi niyyan saka hannuna a lamuran da suke tafiya da iyalinka ba amma gudun sai ta baci azo ana dana sani yasa zan yi magana" sai Papa yayi shiru yana sauraronta har ta sake gyara zama ta yi masa tambayan dake ranta tun dawowarsu qasar "Shin da amincewar matarka ka dauko marainiyar Allah'n nan kamar yanda ka fada mana?" da fari shiru Papa yayi sai kuma ya d'an sauqe numfashi sannan yace "Har yanzu muna fahimtan juna akai tukunna" sai itama tayi shiru tana kallonsa. Tasan za'ayi haka dan tun ranar zuwansu taga hakan shimfide a fuskar matarsa amma sai ta kawar da komai. Jin shirun nata yasa Papa yace "Babu matsala in Allah ya yarda, nasan zata kula da ita" sai ta dan hade fuska tace "Shine har aka gama waliman aka kwana biyu bata nemi yarinyar ba?, Yau kwana uku kenan jinjirar nan tana hannuna, ai ko ba komai sai ta biyo bayan 'yarta indai har ta karbeta a matsayin hakan" nan kuma Papa yayi shiru yanajin bacin rai na taso masa, ta sake cewa "Amma ba damuwa, yarinya dai in har riqonta zai zamo da mishkila sai ku bani ita in riqe ai" sai lokacin ya dago yana kallon mahaifiyar tasa, a nutse yace "Da yardar Allah za'a gyara hakan" sai tayi murmushi sanin cewa a kaikace yake fada mata bazai iya bata yarinyar ba, ganin haka sai shima ya sake cewa "Inason ta taso cikin 'yan'uwanta ne su shaqu, a ganina ta hakan ne zasu samu hadin kai da junansu batareda sun wareta ba" kadan ya rage Uwah bata tabe bakinta ba saboda a yanda tasan matar d'an nata zuwa yanzu ma ta ware yarinyar daga cikin 'ya'yanta, sai kawai ta danne komai tace "Allah ya rayasu gaba daya" ya amsa da Amin. A daren ranan tasa aka maida Fadwan sashen nasu gurin Habiba ta cigaba da kula da ita. Bayan sati biyu Papa ya shirya tafiya Abuja, a inda babban companynsu yake aiki. Tafiyarsa America yasa Abdulrazaq daya kasance daya daga cikin executive directors yake running a gurbinsa while Abdulrahman kuma yake running branch dinsu na Kano. Sai yanzu da dawowar shi Papan tasa zai cigaba daga inda ya bari dan shine President a Empire din nasu sannan Mai martaba kuma chairman gaba daya. A ranar da zai tafi sai da ya sake maganan kulawan Fadwan da Momma, suna zaune tana tsiyaya masa tea dinda hadimarsu ta kawo masa while shi kuma yana duba wasu takardun da zai tafi dasu gurin aikin. Sai da ta gama zuba masa sannan ya ajiye takardun ya karbi Khadijah dake riqe a hannunta daya, sai tace "Da ka fara da tea din tukunna" bai amsa ba ya cigaba da wasa da Khadijan, sai can ya dago yana kallonta yace "Fatima, fadamin ya zakiji in ace yau ba kya raye kuma aka rasa mai kula mana da Khadijah" sai ta hade girar ta cikin rashin fahimta, ya sake cewa "Ina miki kwatancen hakan ne da yanda har yau kika kasa karban Fadwa a qarqashin kulawarki" sai ta dinke fuska tace "Koda 'yan'uwanka basu kula dasu ba nasan nawa 'yan'uwan bazasu taba barin 'ya'yana a wulqance ba" ya sake danne komai sannan yace "Kika sani ko ita tafi namu 'ya'yan gata amma Allah ya rabota da kowa nata" sai ta dan juya kanta rai a bace ba tace komai ba, anutse ya sake cewa "All I'm saying is that, sai ka taimaki wani sannan Allah zai dubi naka a rayuwa Fatima, Think about it. Banason yarinyar nan ta taso ta fahimci tun tana da qarancin kwanaki a duniya kika gujeta da duk abunda ya shafeta, bamuda tabbacin me Allah ya ajiye mata a gaba, me zata zamo agaba, ko kuma wani irin kaddarar ce a harde tsakaninki da ita. Akwai mutanen da ko baka son kusancinsu a gareka sai Allah ya barsu a kusa dakai na har abada babu rabuwa, wanda babu yanda zakayi in baka so su ba. Ki fara taming zuciyarki tun yanzu a kanta in ba so kike Allah ya gwada ikonsa a tsakanin ki da yarinyar nan ba" da haka ya dauki shayinsa ya fara kurba amma har sannan bata juyo da kanta ba tana kallon Tv dake aiki a falon. Paid book 500 Fatima Musa Maina Opay Shaidar biya : 08134692758 MURADIN ZUCI📖 Bintu Musa Chapter 10 Free page A wannan tafiyar da Papa yayi sai ta zamo daidai da tafiyar su Mai martaba da Uwah zuwa saudiya yin Umrah. Sai da yayi wata guda kafin nan ya fara shirin komawa gida. Bayan ya sallama sauran ayyukansa ga qaninsa Abdulrazaq da yake zama da iyalinsa anan Abujan sannan ya tafi. Amma daren ranar da ya dawo sai da zuciyarsa ta tsinke da aka miqo masa Fadwa a hannunsa yana kallonta. Cikin sati hudu-sati hudu kawai yarinyar ta fita daga hayyacinta kamar ba jinjira ba, tayi wani irin bala'in rama har wasu quraje ne suka fito mata kamar na qyanda gashi babu alamun kula a jikin yarinyar kwata kwata. Danne ransa yayi ya riqe yarinyar baice komai ba, bayan an kawo masa Khadijah ne kuma yaga son kai irinna matarsa qarara a fasalin yaran nasa wanda a bayyane yake basai an fada ba. Duk wasu alamomin lafiyayyen jinjiri mai samun kulawa sun bayyana akan Khadijah amma akasarin hakan akan Fadwa, baiwar Allah sai idanun nata suka sake fitowa rauu dasu kamar wadda take zaresu da saninta. Dogon kallon da Papa ya yi mata ne abubuwa dayawa suka darsu a zuciyarsa a wannan lokacin, Amma sai ya danne komai a ransa. Cikin kwanakin da suka biyo baya ya tsananta saka ido akan lamarin yarinyar, anan ya lura da yanda matar tasa ta maida schedule din kula da Fadwan abun walagigi, bata tashi barin Habiban ta kula da Fadwan sai dare, kuma duk yawan hadimanta bata saki Habiban ba sai ya zamto aduk wunin ranar jefi jefi Habiban zata yanke wasu ayyukan nata taje ga dakin Fadwan ta bata madaranta. Gashi a wannan lokacin su Imam sun koma makaranta suma basa zama sosai, balle yanzu da ba a sashe daya suke zama dasu akai akai ba. Abunda yafi qona ran Papan ma shine yanda duk da dawowarsa Mai dakin tasa bata chanja yanayin kulawan yarinyar ba kodan ganin idonsa, It's so extreme that sai da ya fara tunanin anya akwai zuciya a qirjin Fatimansa da yake gani a yanzu kuwa. A wannan tsukun su Mai martaba suka dawo daga Umrah. A ranar da suka iso da Momman taje gaishe da Uwah bayan ta baro sashen Mai martaba sai ta sameta riqe da Fadwan tasa an kawo mata ita, ganin yanayin kallon da Uwahn ke jifanta dashi itama sai da ta dan sha jinin jikinta amma da yake zuciyarta ta riga ta bushe akan alamarin sai ta maze tana gaisheta, nan take babu boye boye rai a bace Uwah tace "Fatima! Allah ya qara gyara miki zuciyarki dan ki samu rabauta da lahirarki, in ba haka ba rayuwarki da kallo, kuma halinki bai zamo abun koyi ga 'ya'yan da suka fito daga tsatsonki ba" nan take kuwa Momma ta fara kuka saboda yanda maganar ta dake ta kuma ta mata daci arai, ita me tayi toh?. Uwah ta girgiza kai sanin hawayen kada take gani a fuskarta dan ta sani ba gyarawan zatayi ba. A zuciye Momma ta baro sashen Uwah ranan cikin qunan rai ta tafi direct zuwa falon mijinta ta samesa zaune da yaransa har Jidda na kwance a jikinsa, ganin haka sai yace da su Imam dake zaunen su dan bashi guri, sai da suka fice sannan ya kalleta amma baice komai ba har saida ta gaji da shirun sannan tace "Ka fadamin shin fina da yarinyar nan tayi a wajenku har yakai a fara zagina a bayyane saboda ita?" anutse ya girgiza kansa batareda ya nuna alamun bacin rai ko akasinsa a fuskarsa ba sannan yace "Ko daya Fatima, Fadwa kaman Khadijah take a gurina dan haka babu ta yanda zata fiki a gurina har abada, kin fi min ita. Sai dai abubuwan da kike mata yasa zan rabakin da ita kamar yanda kikeso din" kallonsa ta tsaya yi, sai ya kamo hannunta yace "Zan rabaki da itan, kulawanta bazai sake zama abun damuwarki ba har abada in sha Allah, sai dai zan AURO wadda nakeson ta kulamin da ita tunda itama 'yatace Fatima, hakkin kulawanta ya rataya a wuyana kamar na sauran 'ya'yana, banason mu shiga hakkinta muyi laifi a gurin ubangiji" a sannu ta zare hannunta daga nasa cikin wani irin sanyin jiki, wani irin daskarewa jikinta yayi kamar batada jini, ganin haka sai ya sake nutsar da murya ya sake cewa "This is for the best Fatima, banason yarinyar nan ta zamo priority a sabanin dake shiga tsakaninmu, Ina sonki matuqa. Kisani wadda zata shigo bazata taba finki a zuciyata ba har abada" cikin diri tace "Just shut up Abdulaziz" ta miqe jikinta na wani irin rawa tace "Niiii !!..Ni zakayiwa kishiya akan 'yar tsintuwaaa! Ka rasa akan me ma zakamin kishiya sai akan 'yar da ka tsinto a yashe cikin sanyin Texas" kallonta yake quri baice komai ba, ta buga wani uban tafi tace "Qaryar me qarya ma, wallahi qarya kake Abdulaziz" sai lokacin yace "I've made my mind Fatima, kuma hakan shine zai zamo maslaha a tsakaninmu" muryarta na rawa tace "Wallahi karyane, maslahan banza da wofi! In maslahan kake nema ka dauketa ka bada ita a 'yan'uwanka su riqeta mana, ka kaita gidan Abdulrazaq mana, sai kace zakamin kishiya akanta" tayi wani qwafa mai qarfi tace "Gaskiya ne, lallai Abdulaziz" kawai ta juya a zafafe ta fice daga falon yana bin ta da kallo. A daren ranar ya fadawa Uwah decision dinda yayi making. Kawai sai ta tsaya kallonsa taqi cewa komai, ganin haka sai ya dan nusar da murya "Ina ganin hakan ne kawai zai kawo mana maslaha, Inason Fadwa ta taso cikin gatan da duk sauran yaran namu zasu samu, kuma Fatima is not making any effort regarding that" sai sannan Uwah ta gyada kai cikin gamsuwa dan kowa ya kwana da sanin haka a gidan, sai kuma tayi murmushi tace "Ita wannan da kake son aurowa Yar Ina ce haka?" Yace "Bamu dade da fara magana ba.Y'ar gidan Muhammad Shettima ce" sai tace "Sarki Muhammad Shettima na Borno?" Papa ya gyada kai a hankali yana kallon mahaifiyar tasa. Sauqe numfashi tayi sannan tace "Hakan duk ba laifi bane, kuma dan ka qaro aure shima ba laifi bane. Allah ya tabbatar da abunda yafi alkhairi, in har hakan kana ganin shi zai dinke barakar gidanka, na baka goyon baya dari bisa dari. Allah yayi jagora" ya amsa tareda miqewa zai fice ta bisa da kallo abubuwa dayawa na mata yawo arai. Abunda ta dade tana jirane Allah ya nuna mata, dan ba shakka wannan matar tasa abokiyar zama ce kawai zata dusasar da kaifinta, tayi wa Abdulaziz kaifi dayawa. Kuma wannan decision da yayi making ba qaramin sanyi ya mata a rai ba, hakan na nuni da cewar d'an nata ya fara tsayawa tsayin daka a sama da matar tasa. Hakan jarumta ce a gurinta. Saida suka idar da sallahn isha, Papa ya tabbatar Mai martaba ya samu zama a sashen sa kamar ko wane dare sannan ya samesa da maganar. A nutse Dattijon ya sauraresa yana kuma fahimtarsa. Sai da Papa ya gama maganarsa sannan Mai martaba ya nusar da murya "Banqi taka ba, amma banason ka gina yaqin da bazai taba qarewa a tsakanin yarka da mai dakinka ba. Zaifi dacewa ka qaro aurenka a domin kana da niyyan hakan amma karka kafa wannan yarinyar da hujja alhalin bata san komai ba. Zaka rufe ta da wani shinge ne mai hatsari da batasan ta Ina mafarinsa yake ba in ta mallaki hankalin kanta a gaba. Hakan kuma bazai taba haifar muku da d'a mai ido ba acikin ahalinka" Papa ya gyada kai cike da alhinin furucin mahaifin nasa. Yasani shima hakan ba qaramin tsana zai jawowa Fadwan ba, amma babu yanda ya iya ne, bazai iya zuba ido ana cutar da yarinyar batareda ya dauki mataki ba. Ya daukota dan ya bata duk wani kulawan data rasa sannan ya samu lada, amma abubuwan da suke faruwa a yanzu, bashi da tabbacin in ya bari aka tafi a hakan zai cimma burin daya daga cikin abunda ya lissafo. Cikin nutsuwa ya qara yin bayani ga mahaifin nasa. Sannan yasan a yanda Uwah ta karbi lamarin, ita zata sake tausasa masa Dattijon akan alamarin, dan bai manta ba alaqace mai kyau tsakanin mahaifin Binta da shi Mai martaban, kallon 'ya yake mata a koda yaushe. Amma sai Allah ya juya alamarin, dan bai bar sashen ba sai da suka fara maganan tsarinsa akan auren, nan ya fada masa bai son a dau lokaci. Yaji sauqin nauyin zuciyarsa ganin yanda mahaifansa suka karbi alamarin, daya koma sashensa bai samu Momma anan ba kamar yanda ta sabar masa duk dare, kuma yasan za'ayi haka dan ya shiryawa duk wata fitinarta a wannan karon. Sai ya qara fita yaje sashen Twins dan wunin ranar tun safe ranbonsa dasu. A bakin part din nasu ya tsaya tareda gaisawa da dogarai biyun dake kula da gurin kamar ba basarake haka ya amsa gaisuwarsu, suka rinqa zubo masa kirari har ya shige. A Babban falon ya samesu bayan Laure ta zuba musu abinci da ta dafa musu ire ire daban sai wanda suka zaba. Imam na kwance a kujera yana zane a white sheet while Imran yana kallon Tv. Shigarsa Imran ya juyo yace "Papa barka da dare" yana murmushi ya qarasa tareda zama a kujera, Imam ya miqe zaune suka gaishesa ya amsa, again sai ya qara kai hannu ya dauki sheet dinda Imam din ke zane a cikinsa yana kallo a tsanake, yaso ya gane building din amma sai kansa ya kulle, sai ya kalli Imam din yace "What's this?" Imam ya dan matso suna kallo a tare sai ya kai yatsa yana nuna gurbin da bai gama sketching ba, yace "This has to go from here to the top" ya sake nuna wani gurbin "And from there, it goes straight to the outer layers of..." bai qarasa ba Papan ya sake kallonsa yace "Ina nufin building din Imam, Ina zan san outer or inner layers" ya qarasa maganan yana murmushi, sai Imam yayi murmushin shima sannan yace "It's JPMorgan Chase Tower" Papa ya dan hade girarsa in confusion da fari, sai can yace "Houston??" Imam ya gyada kai tareda kai hannunsa ya juya zaman sheet din a hannun Papa dan a kaikaice ya riqe ta shiyasa bai gane ba, aikuwa nan Papa yadan ware ido bayan ya fahimci zanen, sai ya sake juyawa ya kalli Imam din da mamaki, yace "Taya kas..." "How do you know it?" sai lokacin Imran yace "Papa you took us there, remember?" ya gyada kai yana sake kallon zanen. Har gobe baya jin zai daina mamakin abubuwan da Imam ke zanawa, it's just raw talent da Allah ya bawa yaron tun baije ko Ina a rayuwa ba. Sai ya sake cewa "But who taught you this?" Imam ya girgiza kai sannan yace "I just did it" shiru Papan yayi baice komai ba yana kallon d'an nasa. Anan part din yaci abinci tare dasu sannan ya tafi. Har yazo kwanciya baiji shigowar Momma ba sai kawai ya tafi sashen nata. Yana shiga hadimanta suka fice duk suka bashi guri ya qarasa har bakin dakinta tareda tura kofar, amma sai ya jita a datse. Ahankali ya kwankwasa shima shiru bata amsa ba. Haka ya hakura ya nufi dakin da Fadwa take, nan ma Habiba ta fice ta bashi guri ya qarasa ciki, tana kwance acikin crib dinta amma batayi bacci ba dan ga feedernta nan akan wani stool Habiban ta ajiye alamun bata dade da bata madaran ba. A hankali ya sunkuya ya daukota sannan ya zauna a resting sofa dake dakin yana dan mata wasa da yatsansa a kumatunta tana kallonsa. Quri yayi yana kallonta cikin tausayawa, yarinyar abun tausayi ce, so vulnerable a hannunsa. Hamma tayi sai yakai hannu ya kare bakin nata da haka kuma idanunta suka fara lumshewa alamun bacci, sai ya danyi murmushi na sanin yawan baccinta. Madadin kuka sai yarinyar ta zamo me yawan bacci akai akai, maida ita yayi cikin crib dinta sannan ya lullubeta, saida ya mata addu'o'i sannan ya fice. Bai koma dakin Momman ba ya wuce bangarensa. Paid Book 500 8134692758 Fatima Musa Maina Opay Shaidar biya 08134692758 MURADIN ZUCI 📖 Bintu Musa Chapter 11 Free page Har garin Allah ya waye Momma bata rintsa ba, wani irin zafi da nauyi ta rinqa ji a zuciyarta kamar ana diga mata wuta. Babu abunda ke mata dadi a wannan lokacin, kuka kuwa ta yisa har ta gaji, ta kuma tsinewa jinjirar da duk ahalinta da suka ja mata wannan fitinar a gidan aurenta. Ita babu abunda yafi ci mata ranta irin wai akan yar tsintuwa za'a mata kishiya, akan yarinyar da ba'a san asalinta bama balle susan wacece ita. Indai haka ne toh tana jin har duniya ta nade babu ranar da zatazo Fadwa da abunda ya shafeta, bazata taba manta baqin cikin data qunsa ta dalilinta ba. Tun gari bai gama wayewa ba ta danna kira a Aina'u, a bugu na uku ta dauki kiran sai ta fashe da kuka me cin rai, hankalin Aina'un a tashe tace "Subhanallahi, Binta meya faru?" Momma bata bar kukan ba tace "Adda in nace banason yarinyar nan ko a gaba kar kowa ya kamani da laifi. Wallahi na tsani komai game da ita, ji nake kamar in kasheta in huta" da sauri Aina'u tace "Innalillahi, meya haka wai. Kanki daya kuwa, ki nutsu ki fadamin meya faru?" Cikin gunjin kuka tace "Wai akanta Abdulaziz yake ikirarin qaromin abokiyar zama, kishiya fa Adda, kuma wai akan yar tsintuwa" ta qarasa maganan wani kukan na zuwa mata da karfi. Shiru Aina'u tayi dan wannan batu ya daketa sosai itama, amma cikin dakewa tace "Binta kowa da irin kaddararsa a rayuwa, taki tazo a hakane sai ki zamo me karba ki godewa Allah, bawai kuma Ina bin bayan Abdulaziz bane, haqiqa dan kyautawa bai kyauta ba. Hakan da yayi kuma sake tabarbare lamuran yayi, duk da kema kinada naki kamashon kusan kashi saba'in acikin alamarin nan, na fada miki ki danne komai ki riqe yarinyar nan, ta hakan ne zaku samu maslaha tunda kin fahimci yanason yarinyar sosai, da ta hakan ne zaki qara janyo mijinki a jiki amma kikayi biris da maganata Binta, kika nuna ke kin isa kiyi yanda kike so babu mai tanqwaraki, Kinga irin kofar da kika bude yanzu ko, kinga irin matsalan da nake guje miki ko? Yanzu wa gari ya waya?" Momma ta share hawayenta cikin qunan zuci tace "Nida Yarana mun zamo abun banza agurinsa kenan? Kinason kicemin yar tsintuwar ta fimu a gurinsa kenan?" Aina'u tace "Ko daya, ni nasan bata fiku a gurinsa ba, amma laifinki anan shine. Tunda kikaga a karo na farko Abdulaziz bai bi ra'ayinki akan yarinyar nan ba sai ki sauqo ki karbeta, da shine zaman lafiyan naku, amma kika nuna naki taurin kan. Ta Ina kikaji ance Maza suna son macen da kullum tanason nuna ra'ayin ta ne abun fifiko akan nasu, Namiji ba'a masa haka duk sanyinsa Binta, amma baki fahimceni ba, sai da nace miki kota salon kissa ki karbi yarinyar da yanzu wata maganar mukeyi" Momma tayi shiru tana dafa kanta, ji take komai na duniyar ya fita kanta a wannan lokacin, wani kukan ne yana qara zuwa mata, sai kawai ta sakeshi a hankali wannan karon, shiru Aina'u tayi tana sauraron ta, dan itama bawai bataji zafin lamarin bane, amma tasani Binta tana aure a gidan sarauta ne kuma ko ba yanzu ba, there are high chances sai Mijinta ya qaro mata abokan zama, amma cewar ta dalilin Fadwan ne kwata kwata yasa itama taji ta fara qin yarinyar a zuciya. Tunda yarinyar ta shigo picture din abubuwa suke ta lalacewa a gidan auren qanwar tata. Hakuri ta hau bawa Momman, ta qara da fadin "Kiyi hakuri, kuma a yanzu ma lokaci bai qure ba. Ki samesa kuyi magana ta fahimta, mijinki yanada sanyin hali ta wani wajen. Nasan ko yau kika karbi yarinyar zai ajiye wannan batun agefe. Try that Binta, in sha Allah komai zai wuce" sai sannan Momma tace "Bazai taba wucewa ba, wannan baqin cikin da nake ji ayanzu bazai taba wucewa ba wallahi" Aina'u ta sake cewa "I said try that Binta, I'll be traveling later. It's a morning flight, 10 o'clock" Momma tace "Yau ne tafiyar?" tace "Eh in sha Allah, we decided Bristol was okay" tace "Allah ya sauqeki lafiya Adda, sai nan da two months din kenan?" Aina'u ta dan ja numfashi "I wish I'll be there for you, amma in sha Allah zan rinqa kira, ni dai dan Allah ki sauqo da kanki kibi lamarin nan ta hankali. Sannan ki kama bakinki, ba kowacce magana zaki rinqa fadi ba yanzu, nasan halinki in kina cikin bacin rai, akan gab'a mijinki yake yanzu komai zai iya faruwa. Ki sauqo ku fahimci juna, sannan banda wannan banzan dabi'ar taki na rufe daki. Kun dawo cikin jama'a ne yanzu. Ki bashi girman sa sosai. Mutumin nan is in line for the next ruler of that Emirate Binta, yanda kike mu'amalantarsa kwata kwata bai dace ba. A Gidan mulki respect yana zuwa fiye da komai, kin taso cikinsa amma sai in kasa gane ta inda halinki ya banbanta" shiru Momma tayi tareda dago kai ta kalli kofar ta data rufe tun jiyan, sai Aina'un ta cigaba da magana "I'll call you in muka isa" tace "Toh Adda Allah ya kaiku lafiya" ta amsa da Amin sukayi sallama. Saida Momma ta ajiye wayan kuma taji abubuwan na dawo mata da daddaya, maganganun da Papan ya fada mata suna amsa kuwwa a kanta da daddaya, ta duqar da kanta tareda dafawa da hannunta duka biyu. Tananan zaune aka kwankwasa kofan nata, shiru tayi da farko sai taji Laure tace "Ranki shi dade kiyi hakuri ki bude" sai kuma kukan Khadija ya karade dakin, da dan hanzari Momma ta yaye duvet dinta ta sauqa daga gadon ta nufi crib din da Khadijan ke kwance, a hankali ta dauke ta sannan ta nufi kofan ta bude. Da Jidda ta fara cin karo an shiryata cikin blouse dinta na yara me kyau a jikinta tana tsaye a bakin kofa ta fara kuka itama. sai ta miqa mata spare hannunta alamun ta iso gareta, da sauri yarinyar ta taho gurinta, sai ta nufi makeken gadonta hannuwanta riqe dasu. Zaman ta bakin gadon sai da ta fara feeding Khadijan sannan ta riqo Jiddan a jikinta tanajin sonsu na shiga lungu da saqon zuciyarta. Sun fi minti biyar a haka sannan Laure tayi sallama. Momman ta dago kai tareda bata izinin shigowa, nan ta shigo ta gaisheta cikin girmamawa, ta gyada mata kai tana maida hankalinta kan Khadija, fita Laure tayi bata dade ba ta kawo mata breakfast dinta in different dishes har kala uku, ta jera mata su a kan ottoman din dake tsakiyan babban dakin sannan ta sake fita. Batafi 30 minutes da fita ba su Imam suka shigo dakin suma, kasancewar weekend suna gida ranar. Ganinsu yasa Momma ta musu murmushi tace "My boys, kun tashi kuma?" dan ta quduri niyyan bazata sake fushi da 'ya'yanta ba akan wani dalilin bacin ran da mahaifinsu zai saka mata. Ganin fara'arta yasa su Imran suka iso wajenta da murmushi suna gaisheta, tana kallonsu ta amsa sai ta kai hannu ta shafa kan kowannensu aranta tana karanto musu addu'a. Ita sai yanzu take ganin kuskurenta na dora fushinta ga 'ya'yanta, to me sukayi su?. Hira suka fara mata Imran harda kwanciya da miqewa a gadonta duk tana kallonsu. Tana gama feeding Khadijan sai Imam ya miqo hannu zai karbeta, a nutse ta dago ta daga jikinta tace "Oya! go to your big brother" tana murmushi ta miqa masa ita ya riqeta yana kallonta, bayan shudewan sakanni kuma ahankali tace "Imam" sai ya dago kai yana kallonta, sannan ta kalli Imran ta kira sunansa shima, sai duk suka bata hankalinsu suna saurarenta, tace "These are your sisters, kunji? Bakuda wasu qannen sai su biyun nan, Inason ko me zakuyi ku jasu a jiki kunji" Imran ne ya fara amsawa da "Toh" while Imam yayi shiru yana kallon uwar tasu, sai ta cigaba da maganan "Duk inda za'a je a dawo bakuda kamar qannenku biyun nan, ku hada kanku kunji" Kafin su amsa Papa yayi sallama a bakin kofan, Jidda ta tafi da gudunta tana kiran sunansa. A nutse ya shigo dakin yana kallonsu da murmushi a fuskarsa, saida ya zauna a dayan bangaren gadon sannan Momman ta gaishesa, ya amsa yana kallonta sai kuma ya miqa hannunsa gurin Imam ya basa Khadija. Sai da Papa ya jira yaran suka fita ya miqe tareda dawowa kusa da Momma har sannan hannunsa riqe da Khadijahn, a nutse yace "Meyasa kike son rufemin kofa ne Fatima?, banason sabuwar dabi'ar nan taki" bata kallesa ba tace "Ai na bude, yanzu ma ai ba a kulle ka samota ba" sai ya kawar da zancen da fadin "Inason zuwa Abuja gobe, and maybe it'll take me one week or so" rass Momma taji zuciyarta ta tsinke tuna yanzu yanada wata a waje da har maganar aure ta fara shiga tsakaninsu, sai ta dago ta kallesa tace "Ka bani yarinyar a qarqashin kulawata zan riqeta" dan stiff yayi yana kallonta, ta sake cewa "Naji zan riqeta a gurina, sai mu bar zancen auren naka" nan ma bai amsa ba ya dauke kansa, ganin haka tace "Dama akanta zaka qaro min abokiyar zaman kuma yanzu na yarda zan riqetan. Shikenan ai ko?" sai sannan ya dan dubeta yace "A'a... Kiyi hakuri jiyan ma nayi kuskure wajen yin maganar cikin bacin rai, amma tun asali inada niyyan qarin auren ko ba dan zuwan Fadwa ba. I'm sorry i made you think it's because of her" ya juyo gaba daya, ahankali ya nusar da murya "I'm sorry Fatima" cikin bacin rai Momman tace "Wallahi saboda ita ne, ai babu abunda zaka fadamin in yarda dakai yanzu Abdulaziz" sai ya juya ya kwantar da Khadija da tayi bacci akan gadon sannan yace "In Allah ya kaimu gobe zan tafi, akwai abunda kukeda buqata?" muryarta na rawa tace "Gurinta zakaje ko, baka dade da dawowa ba amma har zaka koma, in ba gurin ta ba Ina zakaje?" cikin gajiyawa yace "Gurin aiki na zanje Fatima, I'm the leader in this family co-operation, and basically! They need me there everytime to analyze most of the work. Sannan ita wadda kike fadin zanje gurinta ba'a Abuja take ba, A Maiduguri take. Ina Abuja Ina Maiduguri?. Sannan wannan magana taje gaban iyayena, sun kuma bani ammana akan hakan. Yanzu maganarki kike so in bi kenan ko me?" Kawai sai ta fashe da matsanancin kuka, nan ya hau lallabinta amma bata fasa ba, daga qarshe tace "Dan Allah ka fita, banason ganinka. Kaje can ka qaro mata dubu ma Abdulaziz, ka auri duk matan duniyar nan sai ka gutsittsira Yar tsintuwar taka ka raba musu kowa ta riqe nata sashen". Da bacin rai Papa ya bar dakin a wannan karon ma. Paid book 500 8134692758 Fatima Musa Maina Opay Shaidar biya 08134692758 From the writer of KUNCIN ZUCI...And now MURADIN ZUCI 📖 Bintu Musa Chapter 12 Last Free Page Bayan tafiyar Papa da kwana biyu, Maimuna ta kira Momma. "Anti Binta kiyi hakuri, alamarin dai beyi dadi ba. Yarinyar kamar wanda aka jefemu da ita, daga wannan sai wannan" Momma tace "Ni dai haka kuma za'a ganni a barni, ana zaton mutuwa zanyi dan ya fara neman wani auren kome?" Maimuna tace "Kai Anti Binta, ni ai kinsan duk abunda ya shafeki kamar ni ya shafa. Muma ba dadin wannan lamari mukeji ba. Kuma naji zafin wannan maganar auren nima. Amma kuma kema kinyi sanyi sosai akai Anti" tace "Kamar ya nayi sanyi akai" Maimuna ta danyi qasa da murya "Yar sarkin Borno fa yake nema yanzu haka, shekaran jiya ma Baban Sajida ya fadamin suna shirin zuwa da manya neman auren, Mai martaba yayi reaching out to Masarautar, kuma ga dukkan alamu ana daf da shirin basa auren" Wani irin buguwa zuciyar Momma tayi, 'Yar sarkin borno' bama common mace za'a kawo mata cikin gidan ba, Yar wata Masarautar me qarfi. Gumi ne ya yanko mata batasan lokacin da ta miqe daga zaunen da take akan kujera ba, tace "Yaushe za suje?" Maimuna tace "kamar dai yace cikin satin da zamu shigan nan dan basaso adau lokaci. Anti ki fitar da yarinyar nan daga gidanki, zamanta ba alkhairi bane kwata kwata. Tun ba'a je ko Ina ba kinga abunda ta fara jawowa, wallahi ni kwata kwata ma banason yarinyar nima" jikin Momma na rawa tace "Bari zan kiraki Maman Sajida" da haka ta kashe wayan. Kira ta dannawa Madina har ya katse bata dauka ba, ta sake bugawa a na biyun ta dauka tareda sallama, Momma bata ma tsaya amsa sallaman ba tace "Madina kishiya za'a min dai saboda yar tsintuwarcan" ta qarasa maganan muryarta na rawa, Sai Madina tace "Hasbunallahu, Adda kishiya akanta kuma. Toh saboda me?" tace "Saboda zai kawo mai kula masa da yarsa da kyau. Madina wai ni yau Abdulaziz yake nunawa duniya wata tsintacciya ta fini a gurinsa, wai ni ya tozarta saboda yarinyar da shima kansa baisan asalinta ba. Shikenan yanzu kam sai maqiyana su zuba ruwa a qasa su sha son ransu dan dadi" Madina tace "Wallahi tallahi bazata sabu ba, Yar Ina ce?" cikin rawar murya Momma tace "Yar Shettiman Borno" sai da Madina tayi shiru na wasu daqiqu tukunna, can tace "Me Adda Aina'u tace? Kin fada mata?" Tace "Na fada mata tace in karbi kaddarata, inyi hakuri" a zafafe Madina tace "Shi hakurin mun bi kansa mun taka da kafarmu. Wallahi baza kiyi hakuri ba Adda, bazata sabu ba, bamuga ta zama ba. Yar sarkin Borno fa!" "Kuma fa ki tuna wannan karon choice dinsa ce, shi ya ganta yake son aurenta, in baki manta ba zan tuna miki Adda. Auren hadi aka muku da juna" Kukan da Momma take riqewan ne ya kubuce mata, tana yinsa tace "Amma Abdulaziz yana Sona" Madina tace "Nasan hakan Adda, amma dole ki tashi tsaye wannan karon, dan yana sonki ai ba zama zakiyi ki tankwashe kafarki ba, ni mijina na biyun nan da zan aura Kinsan fafutukar da nayi akansa ne?" Momma ta danyi shiru tana digesting maganar na dan wasu sakanni sannan tace "Madina bazan je gurin malami ba, Wallahi akan tatsitsiyar yarinyar nan bazan je gurin malami b..." Madina ta katseta  "Ai ita wannan zan baki shawaran yanda zakiyi da ita, ita ai qaramar alhaki ce. Akan wadda za'a kawo miki zaki dau mataki. Mutanen Maiduguri yawancin su basa zama hakanan Adda, wasunsu guma guman 'yan bin malamai ne, ba ga qawayena nan muna ta fafutukar tare ba. In baki sani ba wanda yamin aiki akan mijin nan nawa har can Maidugurin na bisa ya gama min komai, Wallahi ba'a zama hakanan Adda. Itama da shirinta zata shigo miki kinaji kina gani kin zama 'yar kallo a wajen Babban jidda" cikin firgici Momma tace "Na shiga uku na ni Fatima!! Madina nidai ko jifana akayi da yarinyar nan ne? Kamar wadda tazo ganin bayana. Daga wannan sai wannan duk a dalilin 'yar tsintuwaaa" Madina tace "Toh kin ma san yadda zakiyi a samu maslaha....kawai ki hallaka yarinyar sai muga ta inda za'a bullo da auren, ai me renon ta za'a auro miki ko? To ki kashe ta kowa ma ya huta Adda" Dif Momma tayi shiru tukunna, maganar na samun waje a kwakwalwarta, Madina ta sake cewa "Kiyi tunani ki gani Adda, wallahi in ba haka ba kin rinqa qunsan bakin ciki ta dalilinta, ai wasu haka Allah yayisu, da ibtila'i suke yawo a jikinsu, wannan mafari ma kenan tun tana wata biyu a duniya, Ina ga ta girma?" sai sannan Momma tayi magana cikin wani irin sanyin jiki "Kina ga hakan ne mafita Madina?" da sauri ta amsa da "Tabbas. Adda ki dau mataki yanzu kafin gaba kizo kina danasani" "Zaman yarinyar nan a gidanku ba alheri acikinsa. Uwarta ma ta jefar da ita ko ta mutu ko tayi rai balle ke. Masifa ce mai zaman kanta inkin ga hakan" har sannan Momma jikinta bai dawo daidai ba, sai kawai tace "Bari zanyi shawara, zan kiraki zuwa gobe" tace "Toh Adda. In kuma bazaki iya ba ai kinada amintacciyar hadimarki. In bakyayi da Habiba yanzu ai akwai Laure, wannan idonta a bude suke zata iyayin komai dan kudi" Momma ta sake cewa "Zan dai kirakin" da haka sukayi sallama ta kashe wayan cikin sanyin jiki. Tunani ta fada wanda batasan lokacin da Lauren ta shigo falonta na biyun tana sanar da ita tayi baqi a falon farko ba, firgit ta dago kai tana kallon Lauren, sai ta sake cewa "Kinyi baqi ranki shi dade suna Babban Falo" ta gyada kai kawai batace komai ba. Da wannan maganar Momma ta kwana arai tana tishi akan tishi. Ita dai tasan batason yarinyar ko na misqala zarratan, amma kuma anya kisan beyi tsauri ba kuwa. What if Abdulaziz ya gane, what if asirinta ya tonu kowa ya gane ita ta kashe yarinyar? tasan Abdulaziz bazai taba yafe mata ba. Toh amma inta bar yarinyar tun yanzu ga abunda ta jawo mata, then what if nan da wasu shekaru in ta girma, wani irin masifa zata rinqa janyo mata? What if Abdulaziz ya fifitata akan su Jidda da Khadija, kai har dasu Imam ma. Inaaaa abunda bazata taba zuba ido ta gani ba kenan, 'ya'yanta sune gaba akan komai a gidan nan, 'yan asali, tsatson mulki gaba da baya. Da wannan shedan ya kanainaye zuciyar Momma a wannan daren. Takai ta kawo ma babu abunda take hasaso wa sai jana'izar Fadwa da za'a yi nan da kwanaki qalilan. Washegari haka ta tashi da wannan tunanin. Da wata Hadimarta mai suna Yalli ta zo yi mata hidima sai tace "Kice da Laure Ina buqatar ganinta" ta amsa da "Toh ranki shi dade" da haka ta miqe daga tsugunnen da take sannan ta fice. Bata dade da fita ba Laure ta shigo falon, bayan ta gaisheta cikin girmamawa sai Momman ta miqe ta nufi dakinta tareda fadin "Biyoni". A kan resting sofan dakinta ta zauna sannan ta umurci Lauren da ta rufe kofa, da hanzarinta tayi abunda aka sata sannan ta zauna a qasan carpet tana sunkuyar da kai. Saida Momma ta nausa sannan cikin nutsuwa tace "Magana nakeson muyi, amma Inason ya kasance daga ni sai ke, kuma har duniya ta nade banason jin na ukun mu a cikin wannan maganar" cikin hanzari Laure tace "Allah ya qara miki girma, wane ni...har in mutu baza kiji ba, wannan alqawarine" Momma ta gyada kai cikin amincewa, dan ba tun yau suke tare da Laure ba, ta mata sani tun da kuma tana ji ajikinta bazata bata matsala ba, sai taji Lauren tace "Amma kafin nan ranki shi dade Inason ki amincemin in leqo ko Ina, dan tabbatar da babu na ukun a boye" tace "Na amince" nan Laure ta miqe tareda leqa manyan windunan dake dakin ta tabbatar babu alamu kowa a gurin sannan ta jasu ta rufe gaba daya, da haka ta dawo ta zauna tana maida dukkan hankalinta kan uwar dakin nasu. Saida ta Jira Momma tace mata akan Fadwa ne batun sannan tace "Ranki shi dade. Nidai tun dawowar ku na qissima abubuwa dayawa game da yarinyar nan. Shegu irin su ba sa kawo alkhairi a duk gidan da suka shiga daman" Momma ta gyada kai cikin gamsuwa tace "Inason mu hada kai wajen kai qarshen yarinyar kowa ya huta, ko nawa kikeso zan biyaki in har aikin ya tafi daidai" cikin  gamsuwa Laure tace "Ko baki biyani ba zan iya miki wannan aikin, kuma hakan shine daidai ranki shi dade. Ai qaramar alhakice, ba wahala zeyi ba. Ta hakan ne hankalin mai girma Yarima zai dawo jikinsa. Yara irinsu ba abun riqo bane. Hakan da zamuyi taimako ne" Mamma ta sake gyada kai tace "Kije sai na nemeki, kuma kinji dai abunda na fada miki ko? Kar na uku ya shigo cikin maganar nan dan ke zan sako a gaba" da sauri tace "Nayi rantsuwa kuma nayi alkawari ranki shi dade, babu mai ji har tashin qiyama" da wannan ta fice daga dakin tabar Momma a zaune tana qissima abubuwa a rai. Washegari Momma taje sashen Uwah dan gaisheta kamar yadda ta saba. Laure na riqe da Khadijah tana biye da ita a baya suka yi sallama a babban falon. Basu samu kowa anan ba sai suka zauna zaman jiran fitowarta. Hadimarta laraba ce ta isa ciki dan sanar da ita isowarsu, Jim kadan Uwah ta fito daga dayan falon nata tare da wasu mata guda biyu wanda daga gani mutum zai shaida 'yan'uwanta ne. A ladabce Momma ta gaisheta tana sunkuyar da kai, ta amsa a tsanake kamar ko da yaushe. Saida Momma ta gaisa da sauran matan sannan daya daga cikin su tace da Laure ta miqo musu Khadija su ganta. Suna riqe da itan sai Uwah ta miqa hannu zata karbeta su Momma suka jiyo kukan jinjira daga can falon da Uwah suka fito din, da hanzari Uwah tace da Laure "Maza jeki daukomin Fadwa ta tashi" da haka ta fasa karban Khadijan duk Momma na kallonta. Kawo Fadwa dakin sai Momma ta rinqa binta da kallo, nan da nan Laraba ta kawo ruwanta da madaranta Uwah ta karba da kanta ta hau bata ruwan a nutse. Daya daga cikin matan ne ta kalli Fadwan tace "Ina abun qi ga d'a irin wannan, yarinya ma mai hakuri. Inajin tun zuwanmu bata budi baki ba sai yanzu" dayar tace "Ko daya, ai irin wa'innan in dai ka riqesu tsakani da Allah kaine da riba, kuma aljanna na nan tana jiranka" daya ta sake cewa "Wallahi kuwa, Allah dai ya kawo mata uwarta ta gari itama" Uwah dai zuwa sannan ta koma bawa Fadwan madara kuma batace uffan ba hankalinta na kanta. Momma takai qololuwar cika da  maganganunsu da tasan jifanta suke a kaikaice, amma har ta baro sashen itama batace uffan ba. Haka ta kade zaninta ta musu sallama sannan ta fice Laure na biye da ita riqe da Khadijan. Saida suka isa sashenta sannan tace da Laure "Zan nemeki gobe da dare" ta amsa da "Toh ranki shi dade".. Tsabar bacin rai ma koda Papa ya kirata a wannan daren bata dauka ba, ta cika tayi maqil da zancen kishiyar da matan nan suka jefeta dashi. Washegari da safe ta aika a mata kiran Habiba. Da Fadwan goye a bayanta ta shigo har cikin dakin Momma da tace ta shigo. Sai da Momma ta dauki minti biyar batace komai ba tana feeding Khadija sannan ta dago kai "Bandakin nan zaki shiga ki qara wankemin towels dinnan, sannan ki wankemin shi" ta amsa da Toh tana kokarin miqewa tareda Fadwa a bayanta sai Momma tace "Da itan zaki shiga kenan?" nan da nan ta sauqo da Fadwan, ganin yanda ta riqetan tana kokarin kwantar da ita akan carpet yasa Momma cewa "D'orata kan kujera". Saida ta jira shigan Habiban bandakin sannan ta kwantar da Khadija a tsanake ta miqe tareda nufan gun Fadwan. Sunkuyawa tayi a hankali tana kallonta sosai, tana bin kowanne features na fuskar yarinyar da kallo a tsanake tanajin zuciyar ta na qara bushewa akanta. Har a wannan lokacin batajin nadaman decision dinta akan yarinyar. Ita kuwa Fadwa sai kallonta take da manyan idanunta, hasken dakin na qara fito da color na kwayar idanunta da suka kasance Grey. Baiwar Allah sai wasa take da hannunta a baki tana damalmala yawu kamar yanda jirajirai sukeyi. Momma takai tsahon minti uku a duqen tana kallonta, sai taji ance "Momma". Da wani mugun firgici ta miqe daga duqen abunka da mara gaskiya, idonta wuri wuri ta kalli Imam dake tsaye a bakin kofar yana kallonta shima, a dan zafafe tace "Meye haka? Ba sallama zaka shigo har nan, Meya faru?" a nutse yace "Imran bai shigo nan ba?" tace "Imran din abokin yawo na ne da zaka min tambayar nan, ba tare kuke ko yaushe ba?" sai yayi shiru yana kallonta, can kuma ya maida idanunsa kan Fadwa dake kwance, har sannan idonta na kan Momma tana wasanta da hannunta, sai kuma ya sake kallon mahaifiyar tasa. Ganin yanda yake binsu da kallo yasa Momma cewa "Meye kake kallona?" "Kaje sashen Uwah ka dubosa" a hankali ya juya daga bakin kofar ya tafi. Da sauri ta koma bakin gadonta ta zauna dan har sannan razanar da tayi yasa bugun zuciyarta bai dawo daidai ba. Habiba ce ta fito daga bandakin tace "Ranki shi dade na kammala komai, akwai wani abun da kikeda buqatar ayi?" fuska a hade Momma tace "Dauketa ku tafi" da haka Habiba ta dauki Fadwan suka fita tana binsu da kallo. Da yammaci ta sake kiran Madina. Sun dauki lokaci mai tsayi tana sake qarfafa mata gwiwa akan alamarin, ta kuma ce zata kirata da daddare kar ma tace zata canja shawara, sai tace "Madina a yanda nakejin zuciyata a yanzu ba sai kin qara bani wani qwarin gwiwa ba, I'm a goner now. na gaba yayi gaba sai dai Abdulaziz ya samo gawarta in yanada halin isowa da wuri kenan" Madina tace "Ai na sanki ne Adda, wani zubin kema komawa kike kamar Adda Aina'u. May be ma a binne ta kafin ya dawo, Kinga ya huta ta baqin ciki" "Zan kiraki dai anjiman duk da haka" Momma ta amsa tareda kashe wayan. Dare nayi kafin ta kira Laure sai gata tazo da kanta. Daki suka shige Momma tayi qasa da murya "Menene shawararki akai? Ta wacce hanya zaki yi batareda an dau lokaci ba?" ahankali Laure tace "A cikin dakin zan gama komai ranki shi dade, ki bar komai a hannuna" ta gyada kai sannan tace "Kiramin Habiban".  Da Habiba tazo sai Momman ta gyara zamanta a bakin gadon kamar ba wani abu, tace "Kin gama kula da yarinyar zan saki aiki ne" a ladabce tace "Nagama ranki shi dade, tana bacci ma" tace "Toh kije babban kitchen, ki dafomin tuwo acan. Miyan kubewa zakimin, na nan din banji dadinsa ba yau" Habiba tace "Toh, yanzu zanje inyi" da haka ta miqe ta fice. Jim kadan Laure ta shigo sai Momma ta miqe tayi qasa da murya "Ta tafin?" tace "Eh ta tafi can sashen, tabar yarinyar a daki" sai Momma tace "Toh ki fadamin ya zakiyi tukun" tace "Jinjira ce fa, da pillow ma bazai dauki lokaci ba" Momma ta gyada kai gumi na hade mata a goshi tace "Toh Ina jiranki" da haka Laure ta fice, sai kuma Momma ta kasa zama ta fara pacing a dakin tana zuwa da dawowa ta harde hannuwanta a qirjin tareda cizan yatsa daya cikin tsumayen abunda zai faru. Batayi pace hudu ba Laure ta dawo dakin ad'an gigice tace "Bata dakin" cak Momma ta tsaya zuciyarta na bugawa tace "Kamar ya..Kamar ya bata dakin?" Laure ta dan qara yin qasa da murya hankali a tashe tace "Wallahi bata dakin kuma banga Habiba ta fita da ita ba"  da hanzari Momma ta fita daga dakin suka nufi can dakin Fadwan, amma sai suka samu babu kowa acikinsa, a firgice tace "Nemomin Habiban?" "Dubomin ita yanzunnan" da haka suka fice tare Laure tayi waje. Da farko tsayuwan jira Momma tayi a falon sai kuma ta nufi dakinta ta samu Madina na kiranta, tana dauka tace "Madina na shiga uku, kar wani ya san abunda muka qulla, an dauke yarinyar" itama adan firgice tace "Kuma kin tabbatar ba Habiba bace ta dauketa" tace "Laure ta tabbatar min ta fita babu yarinyar, ita Habiban da kanta tace min tayi bacci ma" a zafafe Madina tace "Qarya take, ku nemota tun kafin ta muku tonan silili. Inada tabbacin tasan komai" ai a rikice Momma ta jefar da wayar a gado zata fita suka ci karo da Laure da ta shigo tana haki, tace "Wallahi batacan din ma, har sashen  Uwah sai da naje, mun shiga uku. Tasani wallahi, ta gudu da yarinyar" Momma ta dora hannuwanta duka biyu akai tace "Na shiga Uku ni Fatima"  ....... ---------------------------- Eighteen Years Later...... -------------------- End of free pages. Bintu Musa. Littafin Muradin zuci paid book ne akan 500 kadai, sannan zaku iya samun more chapters a Arewapen App. Karku bari muyi tafiyar nan babu ku, there's so much to unravel, dan labarin daban yake wannan karon. Ku biya kudin ku ta wannan account din. 8134692758 Fatima Musa Maina Opay Shaidar biya 08134692758 Sneak Peak on Chapter 13 https://www.arewapen.com/chapter?id=6a363dedca0887b357abd7c5 Eighteen Years Later. Kano, Nigeria. Thursday, 4:pm Kwance take akan makeken gadon hannunta riqe da wayarta tana dannawa, tayi ruf da ciki akan pillow ta bada hankalinta gaba daya akan abunda takeyi acikin wayan. Laraba ce ta shigo dakin tareda qarasowa bakin gadon ta dan yi tapping kafafunta data miqar, tace "Fadwa" sai ta ajiye wayar ta juyo a hankali tana kallonta "Kije Uwah na kiranki" da haka ta juya tabar dakin. Miqewa zaune tayi tana gyara zaman doguwar rigar atamfar dake jikinta, sannan ta janyo dankwalinta daya ware a gefenta, madadin ta daura saita fara tattare dogon gashinta daya sauqa har gadon bayanta sannan ta miqe tsaye tana neman ribbon din nata akan gadon, amma sai tayi ta lalube bata ganshi ba. A hakan ta fita falon da dankwalin a daure akanta wanda ko rabin gashin nata bai rufe ba. Uwah na zaune akan babban dardumanta tana jan tasbaha ta juyo tana kallonta, sai tace "A kammala gashin nan guri daya Fadwa" cikin muryarta mai sanyi da dadin sauraro tace "Narasa ribbon din ne, Inata nema bangani ba" Uwah tace "Je ki bude closet dina akwai wanda kika bari satincan yananan" Khadijah dake kwance a kujera ta dago kanta daga kallon wayan hannunta tana bin Fadwan da kallo batace komai ba har ta juya ta koma dakin. Bata dade ba ta dawo falon kanta a nannade har da gyalenta hannunta riqe da wayoyinta guda biyu, sai Uwah ta juya ga Khadija tace "Ki tashi ki shirya nasan drivern ku yana hanya yanzu" sai itama ta miqe zaune fuskar nan a dinke ba alamun fara'a. Basu jima a zaune ba daya daga cikin hadiman Uwah ta shigo falon da sallama tana sanar dasu zuwan mai daukan nasu. Ba yabo ba fallasa Khadija tace da Uwah "Mun tafi" sannan ta riga Fadwa fita daga falon. Sai itama Fadwan ta miqe amma ta dan tsaya tace "Inason in kwana anan" Uwah na kallonta tayi murmushi "Kinsan dai Mai martaba na dawowa zai nemeku" tace "Ai bai dawo daga wajen taron ba" Uwah tace "Kije dai yanzu, in yaso sai ki dawo a weekend ki kwana din" sai ta sake cewa "Toh yaushe zaki dawo?" Uwah ta dan tsaya kallonta har sannan fuskarta a sake, tace "Sai na dan qara hutawa tukun, amma bazan dade ba" sai Fadwa ta gyada kai a hankali tanajin ba dadi a ranta, ita ta rasa yaushe Uwah zata fahimci cewar masarautar ba dadi yake mata ba in bata nan, babu ranar da in zata koma batajin zuciyarta na mata qunci. Gurin Mai Martaba kadai takejin sanyi arai indai taje gaishesa, she feel more at home with him each day. Da haka ta fice daga falon cikin sanyin jiki ta nufi parking lot din gidan. Sai ta samu Khadija tsaye a jikin motan ta harde hannu a qirji tana wurga mata wani mugun kallo, tun kafin ma ta qarasa Khadija tace "Ki bari in kika siyi motar ki sai kiyi ikon naki akai, amma ba yanzu da ake miki alfarma ba" ko ci kanki Fadwa batace mata ba ta zagaya ta bude back seat din ta shige, Khadija tayi tsaki itama ta bude back seat din bangarenta ta shiga. Har suka isa ba wadda ta juyo ta kalli 'yar'uwarta balle magana ta hadasu, kowacce tana zaune at far end na motan tana kallon window....... Ku biya 500 mu tafi tare. Bintu ✍️ 📖